🎍🎍🎍🎍      🎍🎍🎍           🎍🎍                🎍 🎍 *ZAUNJUN MAJNUN* 🎍 (Miji mahaukaci) *BOOK 2* 1️⃣to5️⃣ 🎍 🎍🎍 🎍🎍🎍 🎍🎍🎍🎍 WRITTEN BY 🎍 *AMINA UMAR FARUQ* 🎍 OR 🎍 *MEENAL*🎍 Marubuciyacer *DA SANNU* *ZUCIYATA CE* *AFSANA* *KYAUTAR ALLAH CE* *HASKE BAYAN DUHU* *ZAUNJUN MAJNUN part 1* *TAWAKKALI* *TASEERI* and now *ZAUNJUN MAJNUN part 2* _SADAUKAWAR GA_ Iyayena abin alfarina ina godiya bisaga tarbiyyar dakukai mu, dan haka ina rokon Allah yasaka maku  da alkairi yakareku daga sharrin mutum da aljani, ubangiji yasa kugama da duniya lfy ameen ya rabbi. Wannan littafin na kudi ne akan farashi me sauki, 200 naira only zaku iya turo kudin tawannan account no 0047769671 Amina Abdullahi A., sannan kuturo shaidar ku ta hanyar yin screen short ta wannan no 08161850024, Idan kuma katine sai ku tuntubi wannan lambar 09022880912, sai naji ku. ✍🏼 _Bismillahirramanirraheem!_   """"""Cikin bugawar zuciya tace tarbiyyar damukai maki kenan?..tafadi tareda sha'kemata wuya, cikin mugun bacin rai tasake cewa nace" irin tarbiyyar damukai maki kenan eye?... tambayarki nake, tana me sake  sha'ke mata wuya sosai tamkar zaka fitar mata darai. "Aikam tuni kyakkawan idonun *Beenazar* din sun fito waje saboda sha'kar da *Ammu* tayi  mata wanda bana wasa bane, cikin mugun bacin rai had'eda daka tsawa tace zaki fad'amun kosai na illataki eye?.... "Kai *Beenazar* din take girgizawa yayinda tuni hawaye sun wanke mata fuska, magana takeso tayi amma takasa domin ko kad'an *Ammun* bata batadamar yiba asalima cikin mugun bacin rai take sake sha'karta, dafad'in wlh ko kifad'amun wanda yai maki wannan cikin naji kinki ko na kasheki, domin garaki mutu dadai na cigaba daganinki d'auke da wannan abin kunyar dakike jawo muna, konace kika jawo mun tunda ubanki yana kallo amma yakyaleki dayake shid'in na mijine be damu abin kunyar dakika jawo manaba kai!. Innalillahi'wa'inna'ilaihirraju'un ni Fatima wai cikin shegen ke jikinki *Beenazar* tabd'ijam wato kenan duk tsawon shekarun damuka dauka muna baki tarbiyyar, shine rana d'aya kika tsaya "wani yarud'eki da banzayan kalamashi" kika watsar saboda ked'in shashashace wacce batasan ciwon kanta ba ko?... dan haka kifad'amu! fad'amun!! nace" ki fad'amun "wanene wanda yaimiki wannan cikin shege eye?.....takarashe fadi tareda sake shaketa sosai tana me jijjigata da karifin, idan kuma har bazaki fad'amun wanda yai maki cikin shegen nanba ko to wlh yanzu zan kasheki nahuta domin bazan iya daukar wannan bakin cikin ba. "Daidai lokacin da *Abbu* yashigo kasan cewar tin lokacin da *Ammun* takira *Beenazar* din suka shiga daki sai yaji hankalinsa be kwanta ba, dasauri yakarasa gurinsu yana fadin Subhallahi fatimata kisan kai zakiyi?...,tareda kokarin kwace *Beenazar* din daga hannun *Ammu* yana sake fadin haba Fatima kasheta zakiyi bakiga halinda take ciki bane eye?... yakarashe fadi tareda kwace *Beenazar* wacce tuni numfashinta yakusan barin jikinta...zaunar da'ita yai agefen gado aikam ta tafi luuuu! zata fad'i, dasauri yarikota yarungeme agefensa sai kuma tafara tari sosai cike da tausayinta yake fadin, sannu *Beenazar* tareda daukan ruwa dake gefen gado acup yabata tasha sai sauke ajiyar zuciya wahala takeyi, "Yayinda *Ammun* takoma gefe tana sauke numfashi cike da tsanani bacin rai taname banka masu hharara shida *Beenazar* din. Cike da bacin rai yace haba fatima wannan wani irin d'anyan aikine ki keshirin aikatawa eye?..., saboda Allah fa idan kikai masu illah itada abinda yake cikinta fa sai kice Allah yakawo kome eye?...cikin mugun bacin rai tace abinda dai kaceso kace mun kenan, wato shi wannan shegen cikin najikinta Allah ne yakawo ba sakacin kaba ko?... kallonta yai fuska had'e yace fatima me kike nufi ne?... cikin bacin rai had'eda fad'a tace *Abban* *Beenazar* kenan aikasan abinda nake nufi, cikin shegen dake jikinta nake magana akai wanda konayi rantsuwa bazanyi kaffara ba sakacinka ne yasa tayishi. Kai ya girgiza tareda cewa humm! Allah sarkin rashin sani yafi dare duhu, haba Fatima taya kike tunanin zanyi sake har haka tafaru da *Beenazar* eye?...kuma ke kanki kinsa airin tarbiyyar damukaimata babu yanda za'ai hakan tafaru saida idan kaddaran ubangiji wanda babu wani mahalukin dazaya ta'ba kauce mata. Cikin takaici tace eh ai haka zakace amma tabbas idan bakai sakaci ba to ya'akai tasamu cikin shege eye?....duk irin tarbiyyar dana bata saboda Allah fa, yace a ah Fatima kidaina kiran cikin jinkin *Beenazar* shege domin ba shege bane, cike da takaici tace to idan ba shege bane to mene eye?.. Tabbas bashege bane kamar yanda kike tunani yanada uba kamar kowa ne d'a dayake da uba. Cike da mamaki ta kalleshe tareda cewa *Abban* *Beenazar* me kake nufi, abinda nafada nashinake nufi cikin jikinta yanada uba da sauri cike da d'an tsoro tace *Abban* *Beenazar* kenan aure kayi mata ban saniba?....,yace kwarai fatima saidai kisani hakan Allah yakaddara tace kamar yayafa?.. "Ahankali yamike yanufeta tareda kamota yazaunar agefen gadon sannan shima ya zauna, ruwan yadauka yabata tasha saidai me fuska daure ta kawauda kai gefe alamar bazata shaba, cikin kwantar da hankali yace yi hakuti fatimata ai bakitaba yimun gaddamaba dan haka nasan bazaki fara yauba ko?... kai ta gyad'a idonta yana me cikowa da kwalla, yace yauwa mar'atussaliha karkiyi kuka har kizubar mun da tsadaddan hawayeki, nasan zuciyarki tayi zafi abisa rashin sabi dan haka kisha zuciyarki zatayi sanyi kinji?...kokarin karba takeyi yai sauri hanata tahanyar kafamata cup din abaki kad'an tasha takauda kai. Yayinda *Beenazar* take kallonsu tana sauke numfashi ahankali, zuciyarta cike da kaunar iyayenta sosai zaman takewarsu take mugun birgeta. Saida *Abbu* yatabbatar da *Ammu* ta nutsu sosai sannan sannu ahankali yafada'a mata komai tundaga ranan da *Blue* yabiyo su *Beenazar* gida, dazaman dasukai dashi saboda ganin halinda yake ciki natabuwar kwakwalwa, har ranan da akaganshi sukazo nan gidan inda *Dad* yabukaci yaba d'ansa auran *Beenazar* din saboda tsananin shakuwar dasukai, inda shikuma yamemi jin tabakinta ta amince har akai auran wanda shine dalilin dayasa aka gyara mashi kafansa, sukuma aka biya masu kudin makaranta har kawo ranan da *Beenazar* din tadawo gida da kuka, wai sunce cikin jikinta bana d'ansa bane da zuwan dasukai shida *Bassam* saboda suji daga bakinsu, dayanda suka 'kekyashe kasa sukace sam bacikin d'ansu bane dayanda sukai dukkai saida yafada mata komai. sannan yakarashe fad'a mata irin halin kuncin dasuka shiga saboda rashin dawowarta, har zuwan da *Beenazar* din tayi abuja dan ganin lafiya bata dawo ba dakuma rashin sanin halinda take ciki duk saida yafada mata. Cike da bacin rai tace lallaima mutumin nan shikenan tunda d'anshi bayada hankali sai bazaya iyayin tarayya aure da mace ba?...*Abbu* yace humm!, Nima abinda nace kenan ai wannan ba hujja bane dan bayada lafiyarka kwakwalwa hakan bayana nufin shikenan, bashida lafiyar jiki bane dazaya hanashi tarayya aure da mace ba dan haka na kyalesu domin nasan inasha'allah gaskiya zatayi halinta, cikin fushi tace shikenan sai ka kyalesu?...to fatimata idan ban kyalesu ba yazanyi masu?, cike da jinhaushi tace eh tunda "sun gwada maka finkarfi dole ka kyalesu" ko dayake kaima harda kai tunda kaje kai masu sakwasakwa, dole suyi maka haka amma da saika kaisu" kara idan sunfi karfinka ai basufi karfin hukuma ba, tunda abin nasu rashi mutunci ne da butulci dan haka ni zankaisu kara gurin "yaya idan yaso suyi bayani agaban alkali, tayanda cikin yazama bana d'ansu ba domin mudai munyima yarmu tarbiyyar me kyauta ta yanda bazata taba kwaso mana abin kunya har abada. "Cikin murmushi yace haka ne fatimata gaskiya kika fad'a, saidai idan mukayi karansu munkoma irinsu" kenan wato butulu, fuska had'e tace eh mana bashikenan ba sai muzama d'aya. A ah fatimata bazamuyi hakan na yanda nace haka za'ayi wato mu kyalesu inasha'allah gaskiya zatayi halinta kuma da izinin Allah sai sun neme mu dakansu, aranan zakiga abinda zanyi masu nayi miki alkhawarin, badan ranta yasoba tace shikenan amma zan fad'ama yaya duk abinda yafaru yace ba damuwa. ********* "Sannan itama cikin sanyin jiki tafad'a mashin duk abinda yafaru tundaga ranan da taje abujan gidan kawu Mado, da abinda yaimata wato akasheta wanda dayake batada hakkinsa sai Allah be basu iko ba, tafarfado shine alkali yabigeta har tayai losing memory ta har kawowa kwatar mata hakkita da Abban yayi wato Alkali wanda take kiransa da yaya, sosai *Abbu* yaji dad'in hakan tace yakumace yau zamu tafi dukka saboda haka saikaje kayi masa godiya cike da farincikin yace yanzu kuwa fatimata kai alhamdulillahi sannan yafita. Wani irin kallo *Ammu* tayima *Beenazar* tareda matsawa gurinta wanda yada *Beenazar* jin mugun bugawar zuciyata y to Kallon *Ammun* cikeda tsoro, yayinda cikin wani irin yanayi *Ammun* tace...... Muje zuwa *LUFHAT CE or MEENAL* _Allah kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu mu_ 🎍🎍🎍🎍      🎍🎍🎍           🎍🎍                🎍 🎍 *ZAUNJUN MAJNUN* 🎍 (Miji mahaukaci) *BOOK 2* page 6️⃣to🔟 🎍 🎍🎍 🎍🎍🎍 🎍🎍🎍🎍 WRITTEN BY 🎍 *AMINA UMAR FARUQ* 🎍 OR 🎍 *MEENAL*🎍 Marubuciyacer *DA SANNU* *ZUCIYATA CE* *AFSANA* *KYAUTAR ALLAH CE* *HASKE BAYAN DUHU* *ZAUNJUN MAJNUN part 1* *TAWAKKALI* *TASEERI* and now *ZAUNJUN MAJNUN part 2* _SADAUKAWAR GA_ Iyayena abin alfarina ina godiya bisaga tarbiyyar dakukai mu, dan haka ina rokon Allah yasaka maku  da alkairi yakareku daga sharrin mutum da aljani, ubangiji yasa kugama da duniya lfy ameen ya rabbi. Wannan littafin na kudi ne akan farashi me sauki, 200 naira only zaku iya turo kudin tawannan account no 0047769671 Amina Abdullahi A., sannan kuturo shaidar ku ta hanyar yin screen short ta wannan no 08161850024, Idan kuma katine sai ku tuntubi wannan lambar 09022880912, sai najiku. ✍🏼 _Bismillahirramanirraheem!_ """"""''''Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ba tareda datace komai ba saidai tad'an rungumo *Beenazar din akafad'arta, cikin kwantar da murya cike da tausayi had'eda lallashi tace kiyi hakuri da abinda nai maki, hankali nane yai mugun tashi dana ganki dauke da wannan cikin, wanda kowace uwace taga 'yarta dauke da ciki, alhalin ba aure tayiba kinsa dole ne hankali ta yai mugun tashi taji ba dad'in ace yarta na dauke da cikin shege ko?....,kai *Beenazar* ta gyad'a alamar "eh idonta yana cikowa da hawaye, tace to kingani dan haka kiyafe mun kinji?....     Rungume  *Ammu* tayi tareda sakin kuka me ta'ba zuciya tana me fad'in  *Ammun* abinda kikaimun shine dai-dai, wanda na tabbata kowace uwa tazo ta'iske 'yarta haka irin hukunci da zatayi mata kenan dan haka dan Allah kidaina bani hakuri, tunda bakiyi mun komai ba.         "Cikin murmushi tace nayi maki mana *Beenazar* irin wannan sha'ka danayi maki idan da tsautsayi na illataki fa koma kika mutu gaba daya fa?....,tace  *Ammu* ko na mutu na cancanci hakan kuma kisani babu abinda zaya faru dan kin kasheni, kinyi hakan ne saboda kina kaunata. "Kai ta girgiza cike da kaunar 'yartata tace hakane saidai hakan zata farune kasan cewar ina acikin tsananin fushi, wanda bayan na aikata hakan zan kasance cikin nadama matuka tareda yin kuka me tsanani wanda har karshe rayuwata. Da sauri tace *Ammau* saboda me?...kanta tashafa tareda cewa saboda ban dauki faruwar, hakan amatsayin kaddaraba wacce bata wuce kan kowaba tunda babu wani d'an Adam da be san da'ita ba aduniya, cikin sanyin jiki tace haka ne *Ammu* saidai kisani Ita *ZINA* bashice duk wanda yaci sai yabiya komai daren dad'ewa, ta hanyar idan kayi da matar wani ko 'yar "wani sai anyi danaka",  ko idan kayi dajikar wani sai anyi da jikarka *Ammu* Ita *ZINA dakike gani  saboda tsabar masifarta da bala'inta idan har bakada d'an ko  jika sai anyi da bangon gidanka.      "Nikuma na tabbatar da cewa iyayena basuci bashinta ba balle subiya damu iyayansu, dan hakan kisa aranki hakan bazaya ta'bafaruwa akaina ba ko akan kannai na da izinin Allah, sai dai ko kaddara wacce bawa baya tabba kauce mata, wanda ko dayaushe muke fatan Allah yahadamu da kyakkawa kaddara  ba mummuna irin wannan ba tace tabbasa haka ne to ameen yah Allah.    "Sannan cike da kulawa ta taba wuyanta tareda fadin sannu naji jikinki yai zafi yanzu ina yake maki ciwo?...,cikin sanyi murya tace *Ammu* lafiyata kalau saidai yanzu inajin kaina yana yinmun ciwo kad'an, tace sannu tsoro dafargafan abinda yafaru yanzu ne amma inasha'allah zayadaina, kinada maganin da ki keshane?... "eh *Ammu* akwaisu ina suke?...nan tanuna mata inda tad'auko tabata tashi, bayan tasha tasake cemata sannu  inafata dai kina zuwa asibiti  ganin likita ko?...eh *Ammu* yauwa ina nufin kina awo domin dai naga cikin kamar yakai wata bakwai ko?....eh *Ammu* alissafin dana keyi yanzu ina cikin wata na bakwai din. tace yauwa ko danaji domin naga irin cikina zakiyi idan yakai wata bakwai duk sai yashige cikin cinyoyina, sai idan yashiga watan haihuwa wato wata tara sai yafito, kai *Beenazar* ta gyad'a a alamar gamsuwa domin tafashimci hakan ne akan cikin *Banu*. "Sai kuma cikin fargaba tace saidai nakwana biyu banje asibintin ba, da sauri tace saboda me?.. cikin d'an shagwaba tace *Ammu* ni banason maganin nan dasuke bawa mutun warisa babu dadi. Dariya *Ammun* tayi tareda fadin aikam dai kuma dole kije ki karbosu tunda suna taimakama me juna biyu sosai, cikin d'an turo baki tace "eh dama *Abbu* yace" *Bass* zaya rakani muje nayi masu bayanin rashin barcin da banayi idan dare yayi. Tace "eh hakan nima sai dayawan lokuta idan inada ciki bana barci da dare sai gari yawaye, dan haka yanada kyau kuje kiga likita sai kiyi masa bayani saidai nakula ke" rashin barcin naki" yanada nasaba da tunani, wanda natabbatar kina tunani ne akan abinda yafaru ko?..., saidai kisani Ita me ciki ba'asonta da yawan tunani saboda hakan yana iya haifar matada matsala tareda abinda yake cikinta.    "Dan haka inaso ki kwantar da hakalinki ki daina duk wani tunani, kifita batun "mutanan nan tunda sun din butulune masu rama khairi da sharri, ai *Abbunku* suka samu inda ina nan aisu basu" isaba wlh dasai nayi masu wanki babban bargo, nakuma kaisu kara kotu dagama sun samu antaimaka masu an auri *MAJNUNIN* "d'ansu, shine zasuyima mutane rashin mutunci amma bari da "yaya zan had'asu zasu gane kurensu wlh. "Kuka *Beenazar* din tafashe dashi tareda cewa dan Allah *Ammu* kiyi hakuri tabbas basu kyautaba, sun kuma cancanci  hukunci daga uwar da aka zalunci 'yarta ta hanyar yimata kazafin *ZINA*, domin dai kazafi sukai mun saboda ni tunda nake ban ta'ba tarayya da wani d'a namiji ba idan ba *yah Bilal* ba, dan haka duk hukucin da zakiyi masu kiyi masu amma dan Allah karki hukunta "*yah Bilal*, saboda shi bayada laifin komai asalima bashida lafiya dan haka kinga baruwanshi". Kingama ranan dazan taho yanata kuka yana fadin karna tafi gwanin tausayi Allah *Ammu* koke kikaga halinda *yah Bilal* yake ciki na rashin lafiya wlh sai kin tausaya mashi.          "Ni yanzu ma tunanina bansan halin dayake" ciki ba gashi sai nayi ta mafarkinsa yana cikin wani hali kuma kinsan me *Ammu*?..., "Kura mata ido *Ammun* tayi zuciyarata cike da mamakin yanda tazama me magana haka, wanda ta tabbatar duk haduwarta da wannan *MAJNUNIN* ne ta iya, sosai take kallonta inda tagano tsantsan kaunar mijinta acikin kwayar idonta. "Kai ta girgiza mata alamar a ah bata saniba sai tasanar da'ita yanzu, tana me cigaba da kuka tareda share hawaye sannan tace *Ammu* lokacin danake chan gidansu, kullum cikin dare sai kanshi yayi ciwo sosai sai yaita kuka yana "cewa narike masa kan, Allah *Ammu* abin tausayi sai idan narike kan nayimasa" addu'a sannan yake samun yin barci, takarashe fadi tareda kwantar da kanta akan kafad'ar *Ammun* tame cigaba da kukan, zuciyata cike da tausayin mijinta had'eda kaunarsa. "Jikin *Ammun* yai sanyi inda taji cewa duk wani abu da ta'kudirta aranta zatayi akan ahalinsu *Blue* din, duk sai taji tazama wani iri kamar bazata iyaba saboda ganin halin da 'yarta take ciki, saidai kumafa yazama dole tayi wani abin. Ta hanyar tauna tsakuwa dan aya taji tsoro, domin su gane cewa halinta sunada kima da daraja sosai. Dan haka cikin sigar lallashi tafara shafa kanta cikin sanyi murya tace to kiyi shuru kidaina kukan haka nan, ki kwantar da hankaliki inasha'allah zayaji sauki kedai kiyi masa addu'a kinji?... cikin shashshekar kuka tace to *Ammu* ai inayi, yauwa to ki kara sosai akan wanda kikeyi kinji inasha'allah zayaji sauki, tace to *Ammuna* nagode inasonki over. Shiyasa da bamusan inda kikeba muketa kuka, Allah dai yabar manake da *Abbu* domin kune farinciki mu.     "Murmushi *Ammu* tayi tace nima inasonki *Beenazar* dita dake da "yan'uwanki kune farincikin mu, tun ranan danadawo hayyacina nake tunaninku, saidai kirike wannan kalmar shine Allah baya BARIN WANI dan WANI, kinsan hakan tunda kin karanta ko?.... cikin sanyin jiki ta gyad'a kai alamar "eh tace yauwa dan haka ki kwanta kiyi barci, tace *Ammu* saboda farincikin ganki naji barci yafita daga idona. Cikin murmushi jin dad'in tace to shikenan tunda bakijin barci bari nakira maki, *Basmatina* kuyi fira dama tuni na kulla maku kawance saboda ina kaunar yarinyar kamar yanda take kaunata, tanada natsuwa sosai kamarki haka take kulada lamurana tun ina cikin gushewar tunani, har lokacin da tunanina yadawo gareni. dan haka inaji da'ita" sosai kamar yanda nakeji daku 'ya'yana nakuma bata labarinku musamman ke dakike tsaranta, saboda haka ki kulamun da ita sosai kinji?... ta karashe fadi tareda kama kunnanta cike da zolaya ciki dariya tace inasha'allah *Ammuna*, yanda kikace hakan za'ayi nitunima naji ina kaunarta tunda take kaunar *Ammun* mu. tashi tayi tareda gyad'a kai tace yauwa haka nakeso yar albarka to bari naje gurin yaya, domin nasan yanda za'ayi da maganar gidan nan.      "Da sauri tace *Ammu* me za'ayi da gidan?....tace sayarwa ko kuma asaka 'yan haya, cikin zaro ido tace sayarwa kuma *Ammu* ko asaka 'yan haya kikace fa?.. "eh to mu zauna a ina?..., zamu tafi abuja dukanmu zamu koma chan dazama adaya daga cikin gidajen da'aka bani cikin gadona , ahankali tace Allah sarki *Ammu* ashe kawu Muda yabaki gadonki?...cikin murmushi tace eh yabani yi hakuri banfad'a maki yanda akai har yabani ba ko?...eh *Ammu* nan tafad'a mata komai, tace Allah sarki Allah yasakama *Abba* da alkhairi shida ahalinsa tace ameen, sannan tafita tana cewa bari naturo maki *Basman*  tace to tareda kwantawa, tafad'a kogin tunanin halin da *Blue* yake cike da kaunar shi had'eda tsananin tausayisa, dayagama bin Jini da bargonta tun ranan da tafara ganinsa.   "Sallamar *Ammu* da *Basma* ne yakatsema *Beenazar* tunaninta, inda *Ammu* ta tsaya daga bakin kofa tace to ga *Basma* nan kema ga *Beenazar* nan asha fira lafiys, Kallon juna sukai itada *Basman* sukai murmushi sannan *Ammu* tafita tabarsu. ********* Koda *Ammu* takoma falon ta'iske tuni *Abbu* yaima alkali godiya sosai wato *Abba* akan abinda sukaima *Ammu*, yace aiba komai yiwa kaine. sannan *Ammu* ta zauna tafad'a masa komai akan abinda halinsu *Blue* din sukai, aikam sosai *Abban* yaifad'a saidai yace dasu *Ammu* karsu damu inasha'allah dakansu zasu nemeta, tunda dai cikin d'ansu me suka ce to.     Daga nan kuma sai suka fara fira wacce rabinta duk akan abinda yafaru da *Ammu* ne, wacce tuni ta tashi tashiga kichin don yinmasu girkin rana cikin sa'a kuma taga akwai komai, dan haka tace bari tayi jalof din shinkafa da wake. Bayan takunna gas saita tadora ruwa atukunya sannan tad'ebo kayan miya ta'ajiye gefe, tana kiciniyar debo wake tawanke sai ga *Basma* tashigo. kallonta tayi cikin murmushi tace a ah *Basmatina* ya'akai ne badai har kungama fira da yar'uwar takiba?... cikin dariya tace a ah ummata yaufa muka hadu, dan haka bamu faranba balle har mugama, dariya tayi tace au! hakane kumafa to yanaga kin fito?...tace eyya ummata kinsa sis ba Ita KAD'AI bace, so muna cikin firan sai barci yakwasheta shiyasa nafito nabarta tahuta,  sai na natayaki aiki ko ummata?,. ta karashe tareda rungumeta tabaya. Cike da kaunar yarinyar ta shafa kanta tana murmushi tace Allah sarki *Basmatina* aidakin huta, cike da shagwaba tace a ah nidai zan tayaki tace yanzu kiyi jajjage nan tace to tareda karba tafara. ***** Su *Abbu* kuwa shida *Abba* fira suke sosai kamar dama sun chan sun sannan juna, sai da aka kira sallamar azahar sannan suka tashi zuwa yin sallamar inda *Abbu* Abba dasu *Bassam* da *Bunayya* suka tafi masallacin. yayinda umma dasu *Banafsha* suka nufi daki danyin sallah, suma su *Ammu* cikin lokaci kankani suka gama had'a komai, bayan sun gaman ne suka fito dan gabatar danasu sallah, inda suka iske su *Umman* suna sallah suma sukaiyo alwala sukabi sahu.      "Bayan sun idar *Ammu* taje taduba girkinta wanda tuni yatsotse, nan tazuzzubama kowa *Abbu* da *Abba* *Bunayya* *Bassam* da *Bash* sai *Bana* da *Banu*, sannan *Beenazar* da *Basma* bayan *Basma* takaima kowa nashi. sannan tadauki nasu kasan cewar tuni *Beenazar* ta tashi hartayi sallah dan haka suka zauna sukaci abinci gwanin sha'awa. Bayan duk sun gama cin abincin  sannan duk aka had'u aka cigaba da fira, tsawon wani lokaci sannan *Abbu* yace akira Abban Abdul da maman Abdul *Abbu* dan suka fad'a masu komai, nagame da tashin dazasuyi sukoma abuja dazama sosai sukaji ba dad'i, nan aka ba Abban *Abdul din kalihun gidan yasa yan haya yace bakomai inasha'allah zayasa. daga nan suka fara shirin kayansu wanda koda karfe hudu zatayi tuni sun gama kintsa komai, har ansaka kayansu adaya daga cikin motar da'akayo shata guda biyu, bayan sun idar da sallar la asar sannan suka fito dan tafiya. inda *Ammu* umma dasu *Beenazar* da *Basma* dasu *Bana* suka shiga dayar mota, sukuma su *Abbu* da su *Abba* da *Bassam* da sauran yan mazan suka shiga motan dasu *Abban* suka zodashi, wanda *Bunayya* ne yakejan inda suka tashi zuwa abuja cike da kewar su maman Abdul wanda dakuka akarabu. Koda suka isa abuja dare yayi tuni har ayi isha'i dan haka kai tsaye gidansu *Abban* suka sauka idan gari yawaye, sai sukoma nasu wanda agyare yake sannan gida biyune atsakaninsu danasu *Basma*, hakon ko akayi washegari suka koma cike da farincikin wannan kenan. ****** "Aban garen aunty *Bebe* kuwa zuciyarta cike takeda farincikin da jin dad'in marar musaltuwa, tun ranan data maida *Blue* gurinta dasunan tana jinyarsa, kimanin wata biyu kenan wanda hakan bakaramin damar sake cuta mashi takeyiba, cikin ruwan sanyi idan kaganshi sai kayi masa kuka saboda tsabar tausayinta. Shikam *Dad* yanachan Zaria yanata aikinsa hankalinsa kwance, tin bayan dayakai masu ziyara sau uku besake zuwaba koshi tin lokacin dabata dad'e da daukan *Blue* yakoma gurinta ba, dan haka besan abinda ke faruwa da tilon d'ansa ba, tunda atunaninsa yana hannu nakwarai kuma kullum sukai waya idan ya tambayi *Blue* din sai tace yanaji sauki, idan kuma yabukaci ganinsa sai tace yasha magani yana barci, kuma wai likitan dayake dubashi yace" kar atadashi saboda cikin barcin yake samun sauki, to kasan cewar sa likita yakuma san da hakan sai yakwantar da hankalinsa sosai, tareda tabbacin cewa yaronsa" zaya samu lafiya yakoma yanda yake sosai tunda tace likitan yatabbatar mata da hakan. dan hakan ne *Dad* yaciga da aikinsa hankalinsa kwance. *Bayan wata biyu* ****** Ranan wata juma'a tunda gari yawaye *Dad* yakejin san ganin tilon d'ansa, dan haka bayan ansako daga masallaci juma'a suna cikin tafiya amota shida *Papa* da *Bulama* kasan cewar dama tare suke zuwa sallar ko alokacin da *Blue* yakeda lafiya, dan haka ko yanzu da bayanan tare suke zuwa. Cikin sanyi jiki yace *Barr* idan bakada shari'a mutafi abuja mana yau tunda na tashi nakeson ganin my Boy, yace a ah banida shara'a so mutafi kawai, da sauri *Bulama* yace yauwa *Dad* muje nima inason ganinsa nayi miss nashi over kaima haka ko *Papa*?.., cikin murmushi *papa* yace gaskiya we really miss him alot I know "shima yayi kewar mu sosai, cike da farin ciki *Dad* yace sosai makuwa so direba kaimu kaduna mu hau jirgi yace ok Sir dan haka suka kama hanya, *Bulama* yace *Dad* ka kira aunt *Bebe* kafad'a mata gamu nan zuwa. cikin dariya yace no son surprise zamuyi masu cikin dariya yad'aga babbar yatsa tareda cewar yes! my *Dad*, tafiyar awa daya takaisu kaduna cikin kankanin lokaci suka gama komai jirginsu yad'aga zuwa abuja. ******* Suna isa abuja *Dad* yakira direban gidansa na nan abujan yazo yadaukesu kai tsaye yace yakaisu gidan aunty *Bebe* dan haka yadauki hanya, tafiyar minti shabiyar yakaisu unguwar hon yayi me gadi yabude yashiga bayan sun fito suka nufi ciki *Dad* nagaba *Papa* na bayansa  yayinda *Bulama* yake biye dasu. Wani irin tuntu'be *Dad* yai da abu sauran kad'an yakifa sai yai saurin rike hannun kofa tareda yaye labulen cikin zafin nama, dan yaga me haka *Bebe* ta ajiye akan hanya yake shirin fad'arda mutane, ido yazaro saka makon ganin *Blue* kwance akan tayis kamar matacce, sanye da riga t-shirt baka da wando three quater fari, cikin zafin nama ya tsallakasa tareda zubewa agansa yad'agosa yana kallon fuskasa gaba daya yarame yayi duhu kamar bashiba, gawani uban kasunba dayataru akan kyakkawar fuskarsa me cike da haiba da kwarjini bakinsa yayi fari fat, wanda kallo daya zakai masa kagane bayada lafiya ga cikinsa yasake d'ahewa alamar yanajin yinwa cike da tsoron ganinsa haka *Dad* yace..... Muje zuwa *MEENAL or LUFHAT* _Allah kasa sukace da imani ameen ya hayyu ya kayyu_ 🎍🎍🎍🎍      🎍🎍🎍           🎍🎍                🎍 🎍 *ZAUNJUN MAJNUN* 🎍 (Miji mahaukaci) *BOOK 2* 1️⃣1️⃣to1️⃣5️⃣ 🎍 🎍🎍 🎍🎍🎍 🎍🎍🎍🎍 WRITTEN BY 🎍 *AMINA UMAR FARUQ* 🎍 OR 🎍 *MEENAL*🎍 Marubuciyacer *DA SANNU* *ZUCIYATA CE* *AFSANA* *KYAUTAR ALLAH CE* *HASKE BAYAN DUHU* *ZAUNJUN MAJNUN part 1* *TAWAKKALI* *TASEERI* and now *ZAUNJUN MAJNUN part 2* _SADAUKAWAR GA_ Iyayena abin alfarina ina godiya bisaga tarbiyyar dakukai mu, dan haka ina rokon Allah yasaka maku  da alkairi yakareku daga sharrin mutum da aljani, ubangiji yasa kugama da duniya lfy ameen ya rabbi. Wannan littafin na kudi ne akan farashi me sauki, 200 naira only zaku iya turo kudin tawannan account no 0047769671 Amina Abdullahi A., sai kuturo shaidar kuta hanyar yin screenshot kuturo da wannan layin 09022880912 dan kuma katine sai ku tuntubi wannan lambar 08161850024, sai naji ku. ✍🏼 _Bismillahirramanirraheem!_ """"""""""What! my Boy kaine ka zama haka Oh! god najima jikinka yai zafi alamar zazzabi yakamaka, yakarasa fadi tareda rungumeshi yana sake fadin wai! ina mutanan gidan ne "eye?..ke! *Bebe* inakuka shigane ku kabarmun yaro shid'aya agida eye"?.... Shuru ba amsa dai-dai lokacin da su *Bulama* suka karasa shigowa *Papa* yace Dr ina ganinfa kamar babu kowa agidan.       "Cikin sauri *Bulama*  yace "eh da alama basunan yaname tsugunnawa agaban *Blue* din, wanda yaketa lumshe" kyakkawan fararan idonshi dasuka sakeyin fari kalkal alamar bayada lafiya sosai ga numfashisa sai fisga yake, da sauri *Bulaman* yata'ba wuyan *Blue* din cikin rawar murya yace *Dad* my guy fa bayada lafiya ga jikinsa nan yai zafi sosai.      yace "eh son taimaka mun mud'agashi mukaishi asibiti *Papa* yace yanada kyau hakan gaskiya, saidai kuma amatsayinka na kwararran likita be kamata ace sai mun kaishi asibiti ba, tunda da alama zazzabine so zaka iya bashi taimakon dayadace ko?... *Dad* yace hakane kumafa Barr duk na rikice ne ganinsa haka ko banza dama kasanni duk wani abinda zaya taba *Boy* komai kankantarsa baso nakeyi ba, ciki murmushi *Papa* yace haka ne. *Dad* yace saidai ni abindama yake bani mamaki to wai ina duk "suka tafine suka barshi shikad'ai alhalin sunsan cewa koba zazzabi bayada cikakkiyar lafiya. "Ke! *Bebe* wai "kuna ina ne" eye?...dai-dai lokacin dasuka dago *Blue* din yana kokarin zubewa, alamar babu wani karfin kirki atareda shi sai kuma jikinsa yafara jijjiga tamkar wanda kwamboshan keson kamawa.    "Da sauri *Papa* yakai hannunsa suka rikoshi dukkansu yana cewa Dr bafa kowa gidan nan, so mu daukeshi kawai mutafi dashi gidanka sai kadubashi tunda dai nasan kanada first aid box acan ko?..yace "eh, suka fito dashi da sauri me gani yanufosu ganin yanda suka fito da *Blue* din ranga-ranga, yana cewa Subhallahi! meyasami Alh *Bilal* din?...   *Dad* yace malam barau muma kwance muka ganshi afalo alamar bayada lafiya, Allah sarki beko dad'e daya shiga ciki ba damuna nan munata fira. tsaki *Dad* yai mtww! tareda cewa to wai shin malam barau ina masu gidan ne?.. cikin girmamawa yace Alh da Haj duk  basanan, dama su Nana basu kwana gidan ba chan gidan aminiyar Haj suka kwana amma dai ita shalelen hajiya tana nan bata dad'e da dawo daga makarata ba, _yana nufin Jiddo_. *Dad* yace ikon Allah to aibamuga Ita *matar tawaba da sauri yace to ko "takwanta ne?....ok badamuwa idan *Bebe* ta dawo kace tasameni gida inason ganinta, to Alh Allah yabashi lafiya to ameen. Har zasu tafi sai malam barau yai saurin  yasake cewa Alh dama inason naganka, yace to malam barau yi saurin kafada menene kaga boy bayada lafiya inason naje nadubashi, cike da girmamawa yace Alh dama nace" ne ko za'a gwada yima Alh *Bilal* maganin addini tunda anatayin na asibiti Allah besa andace ba, kila wannan din Allah yasa adace. "Shuru *Dad* yai chan yace to shikenan zan duba nagani, yace to Alh Allah yasa adace ameen sannan yashiga mota kasan cewar tuni su *Bulama* sun shiga shi suke jira kai tsaye gidan *Dad* suka nufa.. ******* Cikin sauri me had'eda tsantsan kwarewa akan aiki *Dad* yake bawa *Blue* din, taimakon gaggawa kasan cewar kafin duk su karaso kwamboshan yakamashi sosai, saidai kuma cikin kankanin lokaci *Dad* yaimasa abinda yasauka. Sannan  yadaura masa drip domin yaga yana bukatar hakan tareda zuba wasu allurai masu saurin saukar da zazzabi, aiko sai gashi barci yadaukesa yaname sauke numfashi ahankali cikin natsuwa bakamar daba, da numfashi yake kai kawo tareda jijjiga cikin jin tsantsan zafin zazzabin. Sannan suka koma gefe suka zauna tareda zuba mashi ido cike da tausayin halinda yake ciki musamman *Dad*, cikin kwantar da murya *Papa* yace Dr da sauri *Dad* yakallesa tareda cewa na'am Barr yadai?.. Saida *Papa* yagyara zama sannan yafara magana dafadi dan girma Allah Dr wannan karon ka fahimceni akan maganar dazanyi, cikin sanyi jiki yace inajinka Barr. "Yace akan rashin lafiyar "Son ne wlh Dr banajin dad'in ganin Son haka ciwon nan nasa yana damuna shine nakeson muyi magana akanshi, kai *Dad* yagyad'a alamar yana sauraransa,yace tunda anyi na asibitin ba adaceba me zayasa baza mu gwada na islamin ba eye?..., to Barr mugwada din mugani nidai burina boy yaji sauki yakoma yin harko kinsa kamarda, Yace inasha'allah zaya koma dan haka idan yafarka zazzabin yasauka, dan Allah mutafi dashi zaria idan mukaje zankira wani malamin addi yadubashi, mutum ne dayake iya gane duk wata laluran datake damuwar d'an Adam data ciki da ta waje, kuma da izinin Allah ana dacewa sosai kaji?...      "Cikin sanyin murya yace shikenan badamuwa idan yafarka sai mutafi dashi, domin nikaina laluran nan tashi yana matukar damuna wlh cike da jin dad'in*Papa* yace yauwa nagode. Nan kukun gidan yazo yace masu ga abinci chan yashirya masu akan dinning table, nan suka mike dukkansu sukaje sukaci bayan sun gama cin abincin ne, sannan suka fita danyin sallar la'asar kasan cewar ankira sallar la'asar din.   "Koda suka dawo sun iske aunty *Bebe* zaune agefensa tana rike da hannunsa cike da kulawa had'eda tausayawa, shigarsu yasa ta saurin mikewa tanufesu cike da kissa tace *Dad* sannunku dazuwa ya hanya, *Papa* da *Bulama* ne suka amsa alhamdulillahi, amma *Dad* batareda ya kalleta ba fuska had'e yace lafiya. hakan yasa cikin sanyin jiki tace ai inshigowa malma barau me gadi yace" mun kunzo, har kun tafida my lil boy wai zazzabi yanada munshi. Fuska had'e *Dad* yace ai ba wai bane tunda "gashinan kwace kinganshi nan saida nadaura mashi" drip harda kwamboshan yaso kamashi, tace Oh! ikon  Allah kumafa lafiya lau nabarshi afalo yana kallon katun fa, rai bace yace shikenan kuma tunda kin barshi lafiya lau sai akace ki ringa "barshi shikad'ai", alhalin kinsan yana fama da lalura ko?...gaskiya banji dad'in hakan dakikai ba ko kad'an.   "Cikin sanyin tace eyya *Dad* gurin malam barau nabarshi kasan cewar nasan yau friday *Jiddo* zata dawo dawuri daga school, saita tsaya dashi to Ita kuma tadawo cikinta yana ciwo shine datasha magani takwanta barci yakwasheta, dan haka nema bataji zuwan kuba. Amma dan Allah *Dad* kayi hakuri hakan bazata sake faruwa ba, kasan cewar yarigada ya yarda da'ita sosai dan haka yace shikenan bakomai yawuce, to yajikin matar tawa?...taji sauki to Allah yakara sauki ameen. ******** Sai misalin karfe hudu da rabi, sannan *Blue* yafarka tuni zazzabi yasakeshi, sai zufa yake nasamun lafiya yana ganinsu *Dad* kewaye dashi, yasaki wani irin karan murna kamar ba marar lafiyaba.        "Sai kuma yasaki kuka cike da shagwaba cikin turanci da maganar sa ta sangartattun yara, yace *Dad* my friend *Papa* shine kuka tafi kuma barni kuma inatayin kewarku sosai, pls *Dad* karku sake tafiya ku barni u my friend and *Papa* kaji?.. yakarasa fadi tareda rungume *Dad* yana cigaba da kukan shagwa'ba irin na sangartattun yara.    "Ajiyar zuciya *Dad* yasauke tareda sake rungumeshi sosai ajikinsa yana shafan bayansa, yana fadin it's ok my Boy I promise bazan musake ba, ko Barr murmushi *Papa* yayi yana shafa kansa yana gyad'a kai alamar "eh, yayinda *Bulama* yarike hannunsa shima yana murmushi cike da kulawa hadeda tsantsan kaunarsa. Sukace we I promise bazamu sake barinka ba, dako kai yayi yakallesa cikin turanci kasan cewar duk rabin maganarsa da turanci yakeyi, dan haka yace promise?...yaname saka yatsarsa dana *Bulama* yace yess we promise, ok to zantafi tareda ku ko?...kallon juna sukai sukai dariya sukace yesss! shima yai dariya. sai kuma ya yamutsa fuska tareda rike cikin shagwa'ba yace *Dad* inajin yinwa, da sauri *Dad* yakwalama kuku kira sai gashi da gudu yace jeka had'oma son abinci yanzu ka kawo masa yanajin yinwa, oya do quickly yisauri ok "Sir. *******      Suna cikin haka sai-ga aunty *Bebe* tashigo kasan cewar tace zataje tadawo, ganin *Blue* din zaune suna fira yasata karasawa da sauri tana cewa Oh! my lil boy katashi, da sauri yakalleta cike da d'an tsoron ganinta dai-dai lokacin da tariko hannunsa fuska dauke da wani irin murmushi me kama dana dole, tace sorry my lil boy kaji sauki?...       Allah sarki bawan Allah murmushi yake yayi tareda gyad'a kai alamar "eh, but amma kuma kallonta yake cike da tsoro tace yauwa sai mutafi gida ko?...da mugun sauri yama'kale kafad'a tareda fisge hannunsa yana turo baki, yace no I want to go with them yakarashe fadi tareda nunasu *Dad* yana turo baki.      Cikin dariyar yake tace lah! lil Boy yanzu bazaka zomu koma gidana ba, da sauri yace no still yana sake makale kafad'a tace to shikenan badamuwa kutafi nima aizanzo zarian, *Dad* yaushe zaku tafi?...yace yau dinnan tunda mun riga munyi bukin jirgi, so dayaci abinci yai wanka zamu tafi kai ta gyad'a tareda cewa ok, to sai nazo gobe sai nakawo mashi kayasa,     "yace  badamuwa kibawa masu aikin gidanki tunda akwai wasu acan nanma akwaisu, kawai kice suyi mashi addu'a Allah yabashi lafiya, cike da takici tace to, nan tabarsu ta tafi zuciyarta cike da bakin ciki.      "domin dai ba haka tasaba tasone koda *Dad* zayazo tariga tagama nakasa *Blue* da azabarta, tahanyar tsafi da takeyi masa tareda horon yinwa datake barinsa dashi wanda shine yasa duk yafita hayyacinsa, sai gashi *Dad* yakatse mata shirinta  saidai ta kudirta aranta itafa sai taga bayan *Blue* din, domin yanda ta tsani mutuwarta haka tatsani *Blue* shida "uwarsa.     "Bayan *Blue* yaci abinci sai *Dad* yasashi yaje yai wanka koda yafito yaciro masa wani dakkaken shadda sky blue, cikin kayasan dayake nan aikam sai gashi yafito sak mutum tamkar cikakken me hankali, wato dai sak *Bilal* dinsa, sai dariya yake yana kallon kayan kamar dai yanda yaro yake idan akasa masa sabon kaya, sai nunama *Bulama* da *Papa* yake tareda fadin su kalli sabon kayansa, cikin murmushi suke gyada masa kai nan dai driver kaisu airport suka hau jirgi. Bayan sun isa sai *Dad* yakira driver yazo yakwashesu saida aka sauke su *Papa* agidansu, sannan aka wuce dasu gida inda suka rabu akan gobe *Papa* zayazo da malamin dayace *Dad* yace ok Allah yakaimu  *Blue* yana tad'ama *Bulama* hannu. ****** "Washegari kamar yanda *Papa* yace hakane, misalin karfe shad'aya nasafe suka isa gidansu *Blue* tareda malam da *Bulama* bayan angaisa, sai duk aka zauna yayinda *Blue* yake rikeda hannun *Bulama* sai jin dad'in ganinsa yake kamar bajiya suka rabuba, inda *Papa* yace da malam ga yaron nawa nan dabayada lafiya kagansako malam wlh ada nagartaccan mutun ne, me tsananin kamala da natsuwa had'eda tsananin kwarjini.     "Amma yanzu duk babu wannan ahalayyar ta kamala, sai halayyarsa tazama tamkar tayaro dan shekara biyu ko biyar  dan haka don *Allah malam ataimaka aduba munashi, kai malam ya gyad'a inda kallo daya yaima *Blue* yace ai har yanzu shidin nagartaccan mutun ne sannan akwai natsuwa had'eda kwarjini wanda ajininsa suke, saidai  sihiri da akaimasa sannan aka had'asa da aljanu yara sai duk suka dakushesu, *Papa* yace kajiko?...yana me Kallon *Dad* wanda cike da tsananin mamaki yazaro ido cike da tsoro yace..... Muje zuwa *MEENAL or LUFHAT* _Allah kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyumu_ 🎍🎍🎍🎍      🎍🎍🎍           🎍🎍                🎍 🎍 *ZAUNJUN MAJNUN* 🎍 (Miji mahaukaci) *BOOK 2* 1️⃣6️⃣to2️⃣0️⃣ 🎍 🎍🎍 🎍🎍🎍 🎍🎍🎍🎍 WRITTEN BY 🎍 *AMINA UMAR FARUQ* 🎍 OR 🎍 *MEENAL*🎍 Marubuciyacer *DA SANNU* *ZUCIYATA CE* *AFSANA* *KYAUTAR ALLAH CE* *HASKE BAYAN DUHU* *ZAUNJUN MAJNUN part 1* *TAWAKKALI* *TASEERI* and now *ZAUNJUN MAJNUN part 2* _SADAUKAWAR GA_ Iyayena abin alfarina ina godiya bisaga tarbiyyar dakukai mu, dan haka ina rokon Allah yasaka maku  da alkairi yakareku daga sharrin mutum da aljani, ubangiji yasa kugama da duniya lfy ameen ya rabbi. Wannan littafin na kudi ne akan farashi me sauki, 200 naira only zaku iya turo kudin tawannan account no 0047769671 Amina Abdullahi A. gt bank ne, Sai kitura shaidar ku ta wannan lambar 08161850024, sai naji ku. ✍🏼 _Bismillahirramanirraheem!_   "Sihiri akai masa sannan kuma aka tura masa aljanu yarafa kace malam?...yace tabbas, cikin mugun tsoro *Dad* yace ikon Allah malam sammu kenan "eh to wanene "ke da wannan mugun aiki?...ga tilon d'ana"?.., wanda a iyasanina bayada abokin fad'a ko Barr?..., yace tabbas "Son bayada abokin fad'a ko Boy acikin "abokanku" yanada wanda basa jituwa ina nufin wanda sukeyin yauwan fad'a. Da sauri *Bulama* yace no *Papa* shidama wani lokaci magana take zama mishi aiki, so wlh bashida wani abokin fad'a.       "Cikin wani irin yanayi na tsanan tsoro had'eda mugun mamaki *Dad* yace, a ah to nikam wanene yacutarmun da yaro haka?....murmushi malam yayi yace Allah shine masanin abinda ke bayyane da boye, dan haka "shine yasan.  "Wanda yaimasa hakan kuma ko wanene" tabbas baya kaunarasa, tunda har ya'iya yimasa wannan mugun sihirin wanda saida aka kwauce hanya sosai, kuma ko wanene beki yaji an wayi gari ya mutu ba wato yadaina ganinsa adoron kasa. *Papa* yace tabbas ko wanene lallai bayada imani kuma babu digon kaunarsa azuciyar mutumin nan, da sauri *Dad* yace innalillahi'wa'inna'ilaihirraju'un! tabbas hakane, saidai kuma wanene bazan taba yafe masaba  har abada, kuma inasha'allah sai yaga abinsa dan haka dan Allah malam kayi wani abu akan wannan lamarin, domin banajin dad'in ganin yarona haka. ******* Yace karka damu da izinin Allah yau din nan yaronka zayasamu lafiya yanzu abani ruwa me kyau acikin cup, da sauri *Bulama* yamike dan zuwa d'ebo ruwa inda *Blue* yabishi tare sukaje suka d'ebo ruwan yamikawa malam yakarba, bayan yai addu'a sosai acikin ruwan  sannan yabukaci da *Blue* yazo gabanshi yazauna, amma sai yakiya saida *Dad* yace yaje sannan yaje yazauna yana kallon malam din tareda turo baki.      "Addu'a malam farayi yatofa masa inda *Blue* din yaringa kauda kai yana sake turo baki, tareda fad'in *Dad* kaganshi ko yana zubamun miyau afuska ko?...,yace sorry boy yanayi maka addu'a kaji sauki kaga aibaka da lafiya ko?...kai ya gyad'a still yanasake turo baki to katsaya malam yaimaka addu'a ka samu lafi kaji still kai yasake d'awa. Saida malam yayi addu'a sosai sannan yafara watsamashi ruwan addu'ar afuska, zuwa jiki da sauri yarufe ido tareda kwatse wani irin kara me tsanani, wanda yai mugun gigitasu sai kuma yafara wani irin zabura tamkar ana jona masa shocked, yayinda malam yacigaba da addu'ar tareda watsamashi kuma ruwan addu'ar afuska da jikin.       shikuma yanata cigaba da zabura da had'eda kara me tsanani, chan kuma sai yafara sakin wani irin gurnani kamar zaki sannan yafara magana da wata irin murya, wanda kanaji kasan banashi bane cikin tsawa yace da malam yadaina konashi haka nan mana, ko dayake sai duk yasake mashi fata da wannan abin dayakeyi. Shima cikin tsawa malam din yace bazaya daina ba har sai fad'a mashi me wannan bawan Allah yaimasa yashiga  jikinsa, tsawon lokaci yana cutar dashi eye?... cikin macifa yace shibeyi masa komai ba. "Malam yace to kafita daga jikinsa cike gadara da iko yace shifa bazaya fitaba", domin kuwa turosa akayi kuma ance karda yasake yafita tunda saidai aka biyashi da abunda yafiso, wanda ya tabbatar shiba zaya'iya biyansa dashi ba yace dame aka biyasa?....dakarfin aljanin ya amsa dacewa da *JININ BIL'ADAMU*.    "Cike da tashin hankali da mugun tsoro su *Dad* suka kalli juna tareda furta Subhallahi, yayinda malam yace wa'iyazubillahi! jinin bil'adamu fa kace?...cike da fad'a yace "eh dan haka bazan fitaba,   to shikenan shikuma yanzu yafara konasa da *AYAR ALLAH* domin baza taba biyansa dako jinin kaza ba balle dabba to balle kuma uwa uba jinin d'an Adam me daraja dakima. "Dan haka yacigaba da yimasa addu'a tarefa tofamasa ruwan addu'ar, aiko *Blue* yacigaba da ihu da kara wanda kanaji kasan banashi bane, chan dai dayaji azaba tayi yawa yace da malam yatsaya zaya fita saidai wlh zaya koma jikin wanda ya aikosa ne, zayai masa illame muni daga shi har iyalinsa tunda yasa aka salemasa fata, malam yace shidai babu ruwansa yafita dai daga jikin wannan bawan Allah wanda baimasa komaiba. "Yace yaji zaya fita saidai su sani akwai sihirin me tsanani ajikinsa", wanda idan basu dauki mataki akansa ba to akwai matsala babba, malam yace yagani kuma inasha'allah hardashi duk yau zayabar jikin nasa da izinin Allah, dan haka ta ina zaya fita?.. yatambayi aljanin inda yace ta hanci to bismillah muna jiranka. "Wani irin atishawa *Blue* yashigayi ba sassautawa chan kuma sai yai shuru, dan haka malam yabashi ruwan addu'ar yasha da taimakon *Bulama* wanda yake rikeda *Blue*, yana gama shan ruwan addu'ar saiya fara wani irin kakari amai chan kuma sai yafara wani irin mugun bakin amai, Saida yai aman sosai sannan sai kuma yafadi agurin tamkar matacce.  "Malam yace Alhamdulillahi! cike da tashin hankali sukai kan *Blue* din musamman *Dad*, da yadago *Blue* ya rungume batareda yadamu da aman dake jikinsa ba, asalima fadi yake my Boy! sai kuma ya kalli malam yace" malam naji kace Alhamdulillahi!, kuma gashi yafad'i bayako matsi.     Cikin murmushi yace karka damu insha'allah komai yazama tarihi daga ciwon dayai da izinin Allah yaji sauki, yanzu kukaishi daki ku kwantar dashi zayai barci saidai koda kunga be tashi dawuri ba karkudamu zayai barci sosai ne wanda yake daukeda sauki acikinsa. "   "Ajiyar zuciya *Dad* yasauke tareda kwalama kuku kira yazo ya gyara gurin yace ok sir, sannan yace da *Bulama* Son taimaka mukaishi ciki mu kwantar ok *Dad*, suka dauke shi suka kaishi saida suka cire masa wannan kayan najikinta kasan cewar duk sun facida aman da yai, inda suka barshi dagashi sai farar singilet da farin box suka kara masa gudun a c kasan cewar sai wani irin mugun gumin yakeyi, sannan suka fito inda suka iske malam yana yima *Papa* bayani cewa akwai wasu magun-guna dazaya bashi wanda zayai amfani dasu, insha'allah zasu taimaka mashi dayaki da duk wani sihirin daza asakeyi masa domin dai wannan  dayake jikinsa yanzu yazama tarihi da yardan Allah, sannan yanada kyau kuma suce yayi kokarin yaringa rikoda addu'a sosai, wanda insha'allah hakan yazai nisantashi da duk wani shaidanin aljani da mutum. Nan *Papa* yafada'a *Dad* abinda malam yace" sosai ya gamsu da bayanin, tareda fadin insha'allah zaya sashi ya aiki da duk abinda malam din yace, sannan sukai mashi godiya sosai sannan *Bulama* yadaukesa yamai dashi gidan inda yakarbo magun-gunan, bayan duk yafada mashi yanda *Blue* din zayai amfani dasu sannan yadawo. Idan ya iske su *Dad* suna nan  zaune suna fira cike da alhinin akan wanda yaima *Blue* wannan aiki, bayan yaba *Dad* tareda fad'a mashi yanda malam din yace yai amfani dasu sannan suka mike zasu tafi gida, inda *Dad* yaketa yimasu godiya *Papa* yace badamuwa zasu dawo zuwa karfe uku tunda yanzu biyu takusa, wanda sunada tabbacin kila lokacin *Blue* din yafarka yace to shikenan, ya gode Allah yabar kauna da zuminci me dorewa *Papa* ya amsa da ameen ameen suka tafi. inda bar *Dad* zaune yafada'a tunanin wanda yaima *tilon D'ansa wannan aiki, wanda iya tunaninsa yakasa tunowa wane yai masa har aka kira sallar azahar, sannan yamike yafita zuwa masallaci bayan yashiga ya gyarama *Blue* kwanciya cike da matsananci kaunar 'Dansa. *******   "Aban garen su *Beenazar* kuwa", cikin wata biyun dasuka koma abuja da zama abubuwa da dama sun faru na cigaba agaresu, da farko dai ranan dasuka koma da kwana biyu lokacin sun natsu sai *Ammu* tadauko kudin gadonta taba *Abbu* tace", yacire yabiyama su *Beenazar* kudin makaranta sauran kuma yaja jari sosai yai farin ciki da hakan. Idan ko hakan akayi bayan ankarboma su *Bassam* tresfar sai akasa su sabuwar makaratar kudi me kyau tareda biyan kudad'en, suka fara zuwa cike da farincikin. inda itama *Beenazar* kasan cewar takardunta suna hannu kuma sunyi kyau sosai, dan haka akasamo mata addimition anan university of abujan inda *Bunayya* yakeyi, wanda tareda *Basmati* aka samo masu kasan cewar tunda nan Bestinta *Beenazar* zatayi nan, sai tace to itama tafasa zuwa alhikimat university din nan zatayi.      "Hakan bakaramin jin dadi *Beenazar* tajiba, wanda daman har tafara tunanin yanda zata ringa zuwa school Ita kadai, dan sai *Bunayya* yana daukar suna tafiya tare wani lokaci su dawo tare tunda kowa da kwas dinsa dayake karantawa, yayinda kuma wani lokacin  ya rigasu dawowa idan yahuta sai yakoma yadaukosu ba tareda nuna gajiyawa ba.       "Yayinda shikuma *Abbu* suka yanke shawarar yafara zuwa abba yana siyo yadin hijabai, aiko hakan akayi bayan sun samu hayan wani babban shago acikin kasuwar abuja, sai yafara siyo yadin hijabai yana siyarwa inda ko cikin sa'a abin yakarbu Allah yasa masu albarka, domin kuwa sosai akeyin cinikin tareda samun alkhari me yawa kafin kace me tuni arziki yafara zama, tuni *Abbu* yasiya mashin na hawa wanda *Abbu* ce tace yasiya ko yasamu saukin zuwa kasuwa, sosai yake samata albarka yaname jin kaunar matarsa aransa.      "Yayinda *Bassam* da *Bash* suke bin *Abbun* zuwa kasuwa gurin siyarda hijabai, amman sai ranan asabar da lahadi idan lokacin zuwa Islamic yayi sai sudawo sutafi, hakan dai suke rayuwaru gwanin sha'awa cike da jin dadi da kwanciyar hankali, haka su *Beenazar* suna tazuwa school inda kuma suke maida hankalinsu sosai akan karatunsu.    "Yayinda inda basu ganeba *Bunayya* yana nuna masu suna kuma ganewa sosai, haka dai rayuwar tamika inda zumunci yasake kulluwa tsakanin umman *Basma* da *Ammu* sosai, kasan cewar sun kulla kasuwanci nasaida zannuwan gado wanda sukeyo order daga Dubai, kuma sosai abin yakarbesu kasan cewar Umma tanada kawaye "matan manya" dan haka sosai suke samun ciniki me cike da alkhairi wannan kenan. ******* *Zaria* "Aban garen su *Dad* kuwa sosai *Blue* yake barci wanda yai mugun basu" tsoro, musamman *Dad* dayake lekashi lokaci bayan lokaci dan ganin ko yafarka saidai kuma har alokacin be farkaba sai barci yake, hakan yasa yace da *Papa* *Barr* kaga har yanzu boy be farkaba kana ganin babu wata matsala?... ni naga kamar barcin yayi yawa. murmushi *Papa* yai yace insha'allah babu matsalar komai, kar kamanta malam yace"   zaya da'de yana barci kuma karmu damu dan munga haka duk cikin samun lafiya ne ko ?...yace "eh fa haka ne kawai nad'an damune darashin tashin nasa.       *Blue* kam barci yayi sosai me cike da wasu irin mafarkaiya wayanda bazaya iyacewa adadinsu yawansu ba, sannan kuma bazaya iyatunasu duka ba saidai kwai wani guda daya da yatsaya mashi arai, wanda dashi yatashi dashi aransa.      "Misalin karfe bakwai saura minti goma shabiyar alokacin ma har anfara kiraye kiraye  sallar magrib", sannan *Blue* yafarka tareda tashi yana mi'ka bakinsa dauke da salati ahankali yazuro dogayan fararan kafafunsa kasa, wayanda suke dauke da lallauwan kwantaccan gashi.      Sannan yabude hannunsa yai addu'ar tashin daga barci wanda atunaninsa safiyane, bayan yashafa sannan yamike ahankali cike da jin wani irin kasala me tsanani wanda yasa yaji jikinsa yai wani irin nauyi, agogon dake manne abangon d'akin yakalla inda yanuna mashi karfe shidda da minti hamasin na yamma, Ido yamurza da sauri tareda sake budewa, cikin turanci cike da mamaki ganin lokaci yaja yafurta _what!_6:50pm, ya akai nayi barci awannan lokacin eye?...sai kuma yaja guntun tsaki mtww! tareda tabe baki yace I think zazzabine yakeson kamani, naji jiki yai nauyi sosai maybe shiyasama nayi barci nan da "mom take cewa barcin la'asar barcin la'ana", saboda rashin kyansa, shiyasa natsanesa but amma kuma gashi nayi still tsakin yasake ja mtww! sannan cikin siririyar muryarsa yace astagafurilla.   Sai kuma ahankali ya lumshe kyakkawan idonshi dasukai masa nauyi saboda barcin dayasha, wanda hakan yasa komai yadawo masa tun daga ranan dasuka dawo daga kasar waje shida *Bulama*, wanda idan be mantaba suna saukowa daga kan jirgi yaji kansa yai wani irin bala'i sarawa, wanda tunga sannan bazaya iyacewa kuma ga abinda yafaruba, sai yanzu dayatashi daga wannan nauyayyan barcin me dauke da wasu irin mafarkaiya barkatai.      "Sai kuma yabude ido da sauri zuciyarsa tana wani irin mugun bugawa, kallon wani d'an karamin kalandar kwali dake kan drowar jikin gadon yai wanda yake dauke da rana kwanan wata hadeda shekara, kuri yaima kalandar da ido na yan mintuna wanda yanuna cewar yana karantawa ne, inda yaga yanuna muna yau asabar biyar ga watan shidda shekara ta dubu biyu da ashirin da d'aya, Da haka yadauki kwalin da sauri jikinsa yana rawa yasake kalla tareda dubawa still dai abinda yagani yakaranta shine yasake gani yakaranta.     "Hakan yasa yai saurin mikewa hannunsa rikeda kwalin zaya fita har yafara kiran *Dad*, sai kuma yatsaya cak! agaban mirron dakin tareda zuyawa ahankali cike da bugawar zuciya yakalli kansa amadubin, inda yaga wani irin uban kasumba dayataru akan fuskarsa wacce tayi wani irin fau, alamar dai_ she is not feeling fine_ gaduhu dayaga yayi sosai kamar dai bashiba haka yaga kansa amadubin.    Dan haka yawaro ido cikin turanci yafurta me anya ni ne *Bilal* hada'ddan _guy_ da guys suke kira da *Blue* kuwa????....nooooo! is not me!...., *Dad* yafita da sauri yana kwalama *Dad* kira cikin tashin hankali har yana buga tuntu'be da kafet, yafita falon dai-dai lokacin da su *Dad* zasu fita zuwa masallaci yin sallar magrib.     Da sauri suka tsaya tareda juyowa suna kallonsa fuskarsu cike da annuri, yayinda tuni *Blue* yakarasa gurinsu jikinsa yana rawa sosai had'eda bakinsa yaname, kallonsu tareda nunama *Dad* kwalin dake hannusa, yana sanyin magana amma bakinsa yakasa furta komai saboda wani irin nauyi dayaji yai masa. "Cike da tsananin farincikin *Dad* yace" Masha'Allah *Barr* my Boy yafarka lafiya cike da murna *Papa* yace alhamdulillahi!, Allah mun gode maka Allah yakara lafiya alfarman annabin rahma (SAW) sukace ameen, sai kuma duk suka had'a baki sukace masa sannun yajikin?... murmushi *Blue* yai da kyar kafin yafisgo am ok" da sauri yafada'a, sai kuma yakalli *Dad* wanda shima kallonsa yake fuska dauke da tsananin farincikin ganin ga dukkan alamu yaronsa yadawo hayyacinsa, dan hakan yace my Boy ya'akai ne?... cikin rawar murya yace *Dad* pls tell me today is what?... cike da mamaki yace boy ban gane ba today is what ba, son kenan yaukam ai yaune ko *Barr* ?...yana me kallon *Papa* kai ya gyada alamar eh yana murmushi. Shikam *Blue* ido ya lumshe sai kuma yabud'e cikin d'an kosawa dasan abashi amsar abinda ya tambaya, sai kuma ahankali yace *Dad* ina nufin yau din wace ranace muke sannan wani wata muke kuma wace shekara muce ciki, domin ina ganin wannan kalandar tayi expired dan hakan ban yarda da abinda yafada'a ba.   Murmushi *Dad* yai me kayatarwa tareda karban kalandar yakalla, sannan ya kalli *Blue* wanda ke kallonsa yaname san yatabbatar masa dacewa yesss! kalandar nan tayi expired, kafad'arsa yadafa cikin dariyar jin dadi yace my boy kalandar nan batayi expire ba tana tafiya dai-dai tabbas yau asabar 5-6-2021, ya'akai ne boy?...shuru yai na yan wasu dakika sai kuma ya yaro ido cike da mugun bugawar zuciya had'eda tsananin tsoro bakinsa yana rawa yace...... Muje zuwa *MEENAL or LUFHAT CE* _ALLAH kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu_ 🎍🎍🎍🎍      🎍🎍🎍           🎍🎍                🎍 🎍 *ZAUNJUN MAJNUN* 🎍 (Miji mahaukaci) *BOOK 2* Page 2️⃣1️⃣to2️⃣5️⃣ 🎍 🎍🎍 🎍🎍🎍 🎍🎍🎍🎍 WRITTEN BY 🎍 *AMINA UMAR FARUQ* 🎍 OR 🎍 *MEENAL*🎍 Marubuciyacer *DA SANNU* *ZUCIYATA CE* *AFSANA* *KYAUTAR ALLAH CE* *HASKE BAYAN DUHU* *ZAUNJUN MAJNUN part 1* *TAWAKKALI* *TASEERI* and now *ZAUNJUN MAJNUN part 2* _SADAUKAWAR GA_ Iyayena abin alfarina ina godiya bisaga tarbiyyar dakukai mu, dan haka ina rokon Allah yasaka maku  da alkairi yakareku daga sharrin mutum da aljani, ubangiji yasa kugama da duniya lfy ameen ya rabbi. Wannan littafin na kudi ne akan farashi me sauki, 200 naira only zaku iya turo kudin tawannan account no 0047769671 Amina Abdullahi A., sai kuturo shaidar ku ta hanyar yin screenshot sannan kuturo ta wannan lambar 08161850024, sai naji ku. ✍🏼 _Bismillahirramanirraheem!_ "''''''''*D.....a....d.....* kenan da gaske kalandar nan batayi expire ba?...yace tabbas Boy batayi expire ba, "shin my son me yafaru ne"?...naga duk katayar da hankalika gashi bakada lafiya so kanutsu kaji ko?....yakarashe fad'a tareda dafa kafad'arsa,cike da kulawa yayinda shikuma ya gyad'a kai. "Sai kuma wani irin gumi yashiga feso mashi agoshi" cike da tashin hankali, yace *Dad* yanzu haka naji ajikina cewa banda lafiya sabodama banajin karfi ajikina, saidai pls *Dad* tell me me yasame ni haka it mean wani irin rashin lafiya nayi haka.        "Wanda alissafin danayi yau kimani shekara daya da rabi kenan, harda wasu watanni ko?...tunda ai mun dawo ne biyar ga wantan shidda shekara ta dubu biyu da ashirin ko my _guy_ ?.., yakarashe fadinda kallon *Bulama*, wanda shima kallonsa yake  kafin yace" tabbas hakane my _ guy_.         "Yauwa *Dad* to wani irin rashin lafiya nayi haka tsawon shekara daya da rabi harda wasu watanni, nadai san aranan da muka dawo ina saukowa daga jirgi naji kaina yai wani irin masifaffen sarawa, wanda ban ta'ba jin irinsa ba tunda nake arayuwata.  "To saidai kuma dagan ban sake sanin me yafaru daniba, sai yanzu dana farka nagannin wani irin atsamutse *Dad* sai naga kamar banine fine Boy din nan d'an gatanka ba, yakarasa fad'i cike da shagwa'ba harda d'an turo baki sannan yadora da cigaba dafad'in so pls *Dad* kafad'a mun meye yasa meni wai haka ne eye?.         "Cikin murmushi jin dad'in me tabbatar dacewa yaronsa yasamu lafiya kwarai da gaske, *Dad* dafa kafad'arsa yayi tareda cewa my Boy wannan maganar me tsawoce, yanzu abinda nakeso dakai shine kaje kai wanka kadauro alwala sai ka'iskemu masallaci. tunda kaga ankira sallar magrib idan muka dawo sai nafad'a maka komai ko?, cikin sanyi jiki yace to *Dad* sannan suka tafi masallacin "Shikuma yanufi daki jiki ba kwari zuciyarsa cike da tunanin wani irin ciwo yayi haka, tsawon wannan lokacin batareda yasani ba. ****** "Koda *Bilal* yashiga daki tsaye yayi agaban mirron yana kallon kansa sosai yake mamakin yanda yakoma haka, ahankali yashafi kasumbar fuskarsa sannan yafurta Oh! god what happen to me ne wai eye?...see me fa like mad, yana me sake kallon jikinsa tareda nunawa yana kuma turo baki cike da shagwa'bar dayasaba yima *Dad* still yana sake shafa 'kasumbarsa.     "Sai kuma take wata zuciyace, tace" dashi shi wai ba *Dad* yace" kayi wanka kaje kai sallah ba tukun na idan kuka dawo sai yafa'da maka komai ba eye?.., da sauri yace yesss! tareda nufar toilet din cikin kankanin lokaci yahada makanshin ruwan wanka dayaji turaruka kasan cewar shi ma'aboci san kamshi, sannan yashiga yai wanka yafito bayan yadauro alwala da sauri yagoge jikinsa da towul, ba tareda yashafa maiba saidai bayan yagoge jikinsa da towul sai yafesa body spray perfume me tsananin kamshi, sannan yasa farar jallabiya tareda daukan farin casbi, yasa wani silifas fari me kyau sannan yafita da sauri domin yaji ana fadin adaidaita sahu. ******        "Bayan sun idar da sallar sannan suka fito saidai *Bilal* bai fitoba yana chan yanata zuba addu'a hakan yasa suka tsaya jiran fitowarshi, inda *Bulama* yake cewa *Dad* da *papa* kungani ko nafad'a maku "my _guy_ yana addu'a sosai, koda muke U S idan mukayi sallar magrib sai munyi isha'i. sannan muke fitowa daga masallaci kuma sai my _guy_ yadade yana addu'a sannan mufito, kawai dai Allah yatsara cewa sai hakan tafaru dashine, murmushi *Dad* yai cike da jin dad'in jin haka, yayinda *Papa* yace tabbas hakane kasan duk abinda Allah yatsarama bawa, cewa ai sai abu kaza yasameshi arayuwarsa tofa babu makawa sai yasameshin, dan haka sai dai muce Allah yatsare gaba. "Sannan kuma ku cigaba da addu'ar nan aduk inda kuke sai kuga Allah yana tsareku daga dukkan abin cutarwa, saboda haka Allah yatsaremu baki d'aya duk suka amsa da ameen. "Sannan *Dad* yace yauwa dan Allah ina rokonku idan zan fad'ama "Boy abinda yafaru dashi bazan fad'i cewa nayi masa aure yana cikin wannan halinba, da sauri  *Papa* yace  *Dr* saboda me?... yace *Barr* saboda nasan Boy bazayaji dad'in hakan ba, nikaina nayi dana sanin aura mashi "yarinyar nan wacce inda nasan cewa batada tarbiyya da bazan aura mashi "itaba, ai Son yaga yanda muka kwashe dasu saboda rashin d'a'a har mahaifinta yana sa'insa dani, alhalin yasan "yarsa tanada ciki amma yabawa d'ana auranta dan haka banason "yasan da zance dan Allah kunji?.     "Cikin sanyi jiki *Bulama* yace insha'allah bazaya taba saniba, *Dad* saidai nikam inagani kamar cikin jikin sis *Beenazar* na my _guy_ saboda fa tare suke kwana *Dad* kaga komai yana iya faruwa, kai ya girgiza tareda cewa a ah son hakan bazata faruwa tunda bashida lafiya, dan haka besan ta yanda za'ai yaima mace cikiba sam banashi bane tunda kana ganin saida *Bebe* ta aunata, dan haka mubar zancan nanma  atsakani mu kawai. "Ahankali *Bulaman* yace to *Dad* insha'allah bazamu fad'a mashiba saidai idan kaine kabukaci muyi hakan, shikam *Papa* baice komai ba sai gyad'a kai dayai domin yarasa abinda zayace cikin wannan magana, saidai aransa yanaji kamar "mutanan nan sunfi  *Dad* da *Bebe* gaskiya.    "Domin kuwa ayanda *Bulama* yafad'a mashi tabbas "sunada gaskiya tunda kwakwalwarsace batada lafiya, ba gangar jikinsa ba daza'ace bazaya iyayin tarayyar sure da mace ba to amma tunda sunce haka bakomai, insha'allah gaskiyar zatayi halinta ne komai daran dad'ewa. Sannan yace karka damu *Dr* insha'allah bazamu fad'a "mashiba, yakarasa fadi yana kallon *Dad dashima yake kallonsa cikin murmushi yace nagode Allah yabar zumunci yace ameen ai bakomai. "Dai-dai lokacin da *Blue* din yafito hannunsa rikeda casbi yana ja cikin nutsuwa, kallonsa sukai duk suka saki murmushi shima ganinsu tsaye yasashi sakin murmushi, domin yasan tabbas shi suka tsaya jira cikin sanyi jiki yakarasa gurinsu yana me fadin "eyya *Dad* shine baku tafiba ku katsaya jirana ko?...,yakarasa fadi tareda mika masu hannun sukai musabiha. *Bulama* da *Papa*, yayinda yamikama *Dad* hannu cikin murmushi yasaka hannunsa cikin na *Bilal* din tareda jawosa jikinsa yace munyi laifine damuka tsaya jiranka ko *Boy*?....cike da shagwa'ba yace no *Dad* banufina kenan bafa, to me kake nufi my darling boy umuh?...yana me rungumeshi sosai akafad'a yanajin so da kaunar tilon 'dansa har cikin jinin da jijiyoyinsa, inda suka fara tafiya ahankali cike da nutsuwa, yayinda su *Papa* suke biye dasu aransu suname jinjina kaunar dake tsakanin uba da d'ansa fiyeda yanda sukema junansu". "Yace *Dad* nufina dasai kutafi idan na'idar sai na iskeku ko?...,yace "eh hakane to aikaga yanzu munsamu ladan jiranka da musabihar damukai, sannan kuma gashi zamu tafi tare muna fira gwanin sha'awa ko *Barr*?...cikin murmushi yace kwarai kuwa dai-dai lokacin dasuka shiga falon bayan sun zazzauna sannan cikin 'kaguwa *Bilal* yace *Dad* pls tell me yace ok my *Boy*. *******           "Saida *Dad* ya gyara zama sannan cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, yafara yafad'a mashi duk abinda yafaru tun daga ranan dasuka dawo daga kasar waje, sukuma sukaje airport daukarsu har kawowa yau din nan saida yafad'a mashi inda cikin hikima ko kad'an maganar *Beenazar* be fito aciki ba.    Saidai duk irin wahalar dasukai dashi tun daga kan *Dad* aunty *Bebe* da *Bulama* *Papa*da kasashen da aka kaishi dan yasamu lafiya harda mom dinsa, duk saida *Dad* yafada mashi komai inda *Bilal* din yaketa kuka cike da tausayin kashi danasu", na irin wahalar da suka sha akansa.    "Rungume *Dad* yai yana fadin *Dad* hauka nayi kenan?...cikin tausayinsa yace tabbas son hakane, saidai malam yatabbatar mana cewa yimaka akai ta hanyar tura maka aljani yasaka nata d'abi'ar yara, cikin sheshsheka yace *Dad* "wanene kuma me nayi masa"?... Son Allah masani kuma insha'allah sai yaga abinsa, da yardan Allah kayi hakuri kaji my darling *boy* kai ya gyad'a yauwa to kayi shuru kadaina kukan hakanan kaji?...yakarashe fad'i dashare masa hawaye, yace to my *Dad* nagode sosai Allah yabarmun kai cikin murmushi yace ameen son. "Sannan yamike ahankali ya'isa gurin *Papa* tsugunnawa yai agabansa, sai kuma yakwantar dakansa akafafun *Papan* cike da shagwa'ba yace *Papaaaa!* cike da kulawa yasa hannunsa akan lallausan suman kanshi yafara shafawa tareda fad'in my Lovely son ya'akai ne?...yace thanks so muchhh!, yace son for what?... cike da shagwa'ba yace no *Papaaaa!* for everything dakai mun so i love u so very muchhh!, cikin murmushi yace no son don't thank me is my work to do everything for u, sannan nima inasonka sosai kaji yarona?...kai ya gyad'a yauwa sannan inason kasake yin riko da addu'o'e sosai kaji?...to *papa*, yauwa hakan zaya kareka daga dukkan abin cutarwa, to *papa* nagode sosai insha'allah zan cigaba dayi sosai. "Yauwa son haka nakeso sannan magun-gunanka suna nan da "malam yabayar kayi amfani dasu, dan Allah karkayi wasa gurin amfani dasu kaji ko?... insha'allah *papa* bazanyi wasaba zanyi duk yanda akace nayi amfani dasu da izin Allah, yauwa to Allah yasa ameen. "Sannan yamike yanufi gurin *Bulama* yaname yimasa kallo, me cike da kauna irinta aminan dasuka aminta da juna kwarai dagaske, cikin murmushi *Bilal* din yamikama *Bulaman* hannun inda shima yamiko masa hannun fuska dauke da annuri, jansa *Bilal* din yayi hakan yasa *Bulama* mikewa da sauri yana dariya suka rungume juna cike da kaunar junansu, *Bilal* yana me shafa bayan *Bulama* yana fadin thanks so muchhh!, da abubuwan dakai mun my _guy_ u are the best friend in the world, I love u very very muchhh! Allah yabarmu tare cikin aminci dajuna, cikin murmushi *Bulama* yace ameen my best friend in the world. ******** "Sannan suka zauna dagan nan kuma sai suka fara fira, inda duk rabin firan akan rashin lafiyar *Bilal* din ne har aka kira sallar isha'i, sannan suka tashi sukaje sukai sallah bayan sun dawone sukaci abincin dare da kuku ya girka masu, sannan *Bilal* yace da *Bulama* pls my _guy_ tashi muje karakani babin saloon nayi gyaran fuska, yace ok. "Daga gurin babin saloon din sai suka d'an zagaya gari inda sosai *Bilal* yaga abubuwa dayawa sun chanja, agarin zaria yayinda *Bulama* yake tayima firan abubuwan dasuka faru dashi, na irin shirmen da yaitayi na yarinta wani yai murmushi wani kuma yagyad'a kai yadinda can kasan zuciyarsa cike yake da tunanin "wanene yaimasa haka?...,saidai yakasa samun amsa kamar yanda *Dad* yakasa samun amsa. "Sun d'an dad'e suna yawo sannan suka kama hanyar gida misalin karfe 11:00pm koshi saida *papa* yakira *Bulama* awaya yace" yazosu tafi gida dare yanayi sannan suka dawo, bayan yasauke *Bilal* sannan suka tafi gida. "Inda suka bar *Bilal* din yana cewa *Dad* yabashi wayoyinsa yakira sweet aunty *Bebensa* yaimata surprised, ciki murmushi yamika masa wayarsa yana fad'in son gadai wayata ka kirata" dashi, amma wayoyinka suna chan abuja ajiye ni nama manta da jiya damukaje na dauko maka    saidai idan kaje kadauko abinka but amma dai gaskiya yanzu kam sun zama Old monden, andaina yayinsu so yakamata kasamu sababbin yayi gasunan anata zubosu.    "Cikin turo baki yace *Dad* dama ni kasan waya bawani dad'ewa sukeyi ahannanu naba nachanja, so dan haka bazanyi amfani dasuba kyauta zanyi dasu sim card dina kawai zan cire nasiya sababbin. "Kai *Dad* yagyad'a yaname kallonsa cike da so da kauna yayinda yakejin wani irin matsananci farincikin, ganin yaronsa yadawo cikakken mutu.     "Shikam *Bilal* zama yayi me makon yakira aunty *Beben* kamar yanda yace" *Dad*, sai beyi hakan ba sai yafara kiran lambar *Mom* dinsa, murmushi *Dad* yai tareda cewa son kenan to ai tuni nafad'a mom dinka, yace ok *Dad* inason naji muryar tane yace ok aji lafiya sannan yamike yashiga ciki. "Daidai lokacin da wayar *Mom* tashiga wacce ke zaune tazuba uban tagumi, wanda kusa kullum tana cikin tunanin halin da 'danta yake ciki sai taga kiran waya da lambar *Dad*, sai da gabanta yafadi cike da tashin ahankali ta dauka ciki zullumi  tareda tayin sallama saboda tsabar zullumi kartaji labari ba wanda takeson jiba, tace *Dr* ina fatan yaron naka yafarka cikin koshin lafiya kamar yanda kace" malam din yafad'a. "Cikin shagwa'ba yace yesss! am ok assalamu'alaikum my lovel *Mom* the one and only, shuru tayi domin dai rabon dataji wannan nagartacciyar murya yau kimanin shekara daya kenan darabi harda wasu watanni, kuma acikin wannan tsawon lokacin babu ranan dazata fito tawuce batayi tunanin jin wannan murya me cike da natsuwa da kamalaba. cike da shagwa'ba yasakeyin sallama tareda cewa *Mom* answer me now, u know I really miss u sweet voice ba?..., saida ta lumshe idon idan wasu hawayan farincikin suka zubo sharrr! akan kyakkawan fuskarta, sannan tace yesss! nasani u know nima nayi kewar wannan muryar taka me cike da natsuwa had'eda shagwa'bawa *Mom* da *Dad* da kuma aunty *Bebensa* ko?...,     "Cikin murmushi yace yesss! my sweet *Mom* nakira nafad'a maki naji sauki, tace masha'allah *Dad* ka yafad'amin saidai namatsu na tabbatar da hakan sai kuma gashi naji alhamdulillahi yarona yadawo kamar yanda yake da, to bani labari yanda aikai sauki yazo cikin kankanin lokaci ko dayake duk *Dad* ka yafad'a mun yanda akai saidai hakan aikin ubangijinmu ne, Wanda shine yake sanya cuta ajikin d'an adam alokacin dayaso yakuma cireta alokacin da yagadama batareda yai shawara dakowa ba. " Kuma shine maji rokon bayinsa ayaukuma nasake gasganta hakan tunda gashi ya amsa addu'ata, konace addu'armu nida *Dad* ka da duk wani masoyinka akan yabaka sauki sai gashi yakarba alokacin damuka fitarda tsammani hakan, ko dayake ni akoda yaushe inajin araina dajikina cewa yarona zaya dawo kamar kowa, sai kuma gashi yau Allah yatabbatar mun da hakan alhamdulillahi! alhamdulillahi!! alhamdulillahi!!! Allah nagode maka Allah ka karama annabinmu daraja (SAW), inda suka karasa salatin tareda shi. Sai kuma kawai yafashe mata dakuka wanda kanajinsa kasan nashagwaba ne, me cike da kaunar mahaifiyarsa da sauri tace a ah! wai shin yarona besan cewa yanzu yagirma bane?..,cikin turo baki yace *Mom* idan ina gabanki da *Dad* ni yarone, cikin dariya tace hakane to amma me makon naji kana farincikin kasamu sauki sai kuma naji kana kuka eye?...., cikin kuka yace hakane *Mom* nayi farinciki da samun lafiyata nakuma godema Allah da ya azurtani da hakan, zan kuma cigaba da gode masa har karshen rayuwata, saidai ina kukane saboda dalilin rashin lafiyar tawa. "Tace yarona kenan tabbas Allah abin godiya ne akowane hali d'an adam yatsinci kansa, dan haka kayi shuru kafada mun meye dalilin rashin lafiyar taka da haryasa kake kuka alokacin da yakamata kayi farin ciki eye?...shuru yayi cikin sanyin murya yace haka ne *Mom* amma bakijin dalilin rashin lafiyar tawa bane?...tace a ah son dalilin kenan shine Allah yasa maka cuta yanzu kuma yayaye maka, da sauri yace eh *Mom* amma ai ance yimun akai tace kul! nasake jin hakan yafito daga bakinka, kasa aranta Allah shine mesama bawa cuta kuma shike yayema bawa kaji ko?... ahankali yace to *Mom* yauwa tareda sake tambayarsa to yajikin?..., yace alhamdulillahi to masha'allah Allah yakara lafiya nan sukai magana tsakanin d'a da uwa sannan sukai sallama, akan bayan kwana biyu yana nam zuwa abuja yaganta sannan yakira lambar aunty  *Bebe* zuciyarsa cike da farincikin. *Abuja* ******** "Aban garen aunty *Bebe* kuwa tin bayan dasu *Dad* suka dauko *Bilal* suka taho dashi, hankalinta yakasa kwanciya musamman dataji cewa aiza ayimasa magani Islamic, hakalinta yake atashe domin tana da tabbacin idan har zunje gurin malamai na kwarai, to tabbas zasu iya karya duk wani asirin datayi masa kuma tabbas zaya warke ne. "Dan haka suna tafiya data koma gida tashiga toilet tadauki tukunyar tsafinta dan tasake birkice  kwakwalwar *Bilal*, cikin tsananin confidence nacewa zatayi nasaran akanshi  tafara sirkulle magana kamar yanda tasaba, saidai wani abin mamaki shine rawa hannunta yakamayi inda tukunyar takeson fad'uwa, kamar yanda kwanakin baya takeyi mata  aduk lokacin data d'auko zatayi tsafinta.     "Hakan yasa cikin matsananci tsoro da faduwar gaba me tsanani, ta ajiye tukunyar jikinta yana wani irin bala'in rawa kallon tukunyar take cike da mugun tsoro hade' da matsananci mamaki, tana tunowa damaganar boka dungu nacewa duk ranan da tabari tukunyar nan tafashe tofa aranan dukkan asirinta zaya tonu. Hakan yasa tayi sauri ajiyawa tareda maida ita ma'ajiyarta, tafito daga toilet din jikinta sai rawa yakeyi da sauri tashirya doguwar rigar atamfa baka, tasa gyale fari tareda rataya jaka tadauki key mota tafito falon inda ta'iske duka yaranta suna kallo, da sauri Jiddo ta kalleta cike da mamaki tace mom yanzu fa kika dawo sannan kuma zaki tafi to ina kuma zaki?..., cikin tsawa tace Jiddo dani dake waya ajiye wani ne wai?....cikin d'an turo baki tace mom kece kika ajiyeni, to shine duk sanda zan fita saiki tsareni da tambaya eye?...ni sa'ar kice?...cikin sanyi tace a ah mom, to bansan haka nan kinji ko?...to mom Allah yabaki hakuri saidai wlh mom kirage yawo *Dad* yafara jin haushin yawan fitar da kikeyi. Tsaki taja mtww! tareda fadin ke!ni banasan surutun banza kinji ko?...cikin turo baki tace to mom ina zakije?...fuska hade tace unguwa zani amma bazan da'de ba, idan Dad ku yadawo kice yanzu zan dawo, kai kawai ta gyad'a Ita kuma tafita da sauri.     "Tana kokarin tada mota sai *Dad* yakira wayarta da sauri tad'aga bayan sun gaisa take tambayarsa yajikin lil *Boy*, cike da farincikin yafa'a mata abinda yafaru wato ankira malam yaima *Boy* addu'a yai barci, yace" idan yafarka insha'allah zaya tashi dasauki tamkar be taba ciwa ba, sannan yafada mata cewa malam yace" yimasa akai, sosai tanuna farincikinta najin zaya samu sauki da kuma alhinin wanda yaimashi. "Sannan sukai sallama inda hankalinta yai mugun tashi dajin wannan mummunan labarin, aikam take ta tayarda mota jikinta yana bala'in rawa, kai tsaye gidan kawarta taje me suna Haj kulu ta labarta mata abinda yafaru aikam zama be ganmu ba, dan haka suka bazama gurin neman bokaye. saidai duk inda sukaje basu iske bokan ba haka dai suketa fafutukan neman hatsabibin bokan dazaya mata aiki akan kada Allah, yaba duk wani malamin dasu *Dad* zasu kira yai nasaran warkar da *Bilal* din. "Ahaka dai har kusayi nasaran samun wani shahararran hatsabinbin boka, wanda yake aiki tamkar yankan wuka saidai koda sukaje sun iske mutane sunyi mashi yawa, hakan yasa yasallami mutane akan cewa suyi hakuri bazaya samu ganinsu yauba saidai yai masu alkawari suzo gobe, aciki harda su aunty *Bebe* badan tasoba suka tafi. Tana kokarin shiga gida taji wayarta yana kara koda ta dauko taduba sai taga lambar *Dad* hakan yasataji mugun faduwar gaba saurin dauka, tana fadin good evening *Dad* saidai jin natsatsiyar muryan me cike da kamala had'eda tsananin kwarjini, wanda rabon dataji ta andauki lokaci sai yau hakan yasata sake jin muguwar faduwar gaba. har wayar tana kokarin faduwa daga hannunta, da sauri tasake rikewa da kyau.     "Cikin rawar jiki bakinta yana rawa cikin dariyar yake tace hey my lil *Boy* yakake?.. ina fatan kasamu lafiya kamar yanda *Dad* yace wai wani Malami yace?...daga chan yace yess my sweet aunty lafiya lau nake, naji sauki, kuma *Dad* yafada mun duk abinda yafaru dani, thanks nagode sosai da kulawarki tareda irin kaunarki agareni nima ina kaunarki Allah yakarasa mama dankon zumunci. cikin dariyar yake tace hey my boy kaifa d'an uwana ne dan haka kardamu duk abinda nayi maka kaina nayima, yanzu ina fata babu inda yakeyi maka ciwo daiko?...yace a ah sis kawai dai banajin karfin jikina ne, tace karka damu ahankali zaka dawo normal kaji ko?...to my sweet aunty nagode, yauwa zanzo gobe naganka ok to sai kinzo sannan yakashe wayar zuciyarsa cike da kaunar yar uwansa. "Yayinda Ita kuma taja wani mugun tsaki mtww! yayinda zuciyarta cike da tsanarsa" cike da bakin ciki tace banza, harda wani cewa ina kaunarki  Allah yabar zumunci wawan banza nikuma bana kaunarka, shiyasama natsaneka  kuma sai naga bayanka sannan tashiga cikin gida tana sake jin tsanarsa aranta. *Bayan sati biyu* *******   "Aban garen su *Beenazar* kuwa komai yana tafiya dai-dai gwani sha'awa suke rayuwarsu, tasakeyin girma sosa kasan cewar tuni cikinta yashiga watan haihuwa dan hakane ma yafito sosai, wanda alissafin mada sukeyi har yafara wuce lokacin haihuwar hakan yasa ko dayaushe cikin shiran haihuwar suke.     "Yau Laraba tin da *Beenazar* ta tashi takejin maranta yanai mata ciwo, amma haka ta daure suka tafi school kasan cewa tanada lecture safe, saidai kachar suka gama lecture tafito takira *Bunayya*  kasan cewar shima yanada lecture, inda ko tayi sa'an yana fitowa tasa meshi daga jin muryarta yasan ba lafiya da sauri ya'isa gurinta tuni har tafara gumi, yace lafiya ciki rawar murya tace yah *Bunayya* marata ke ciwo kamar zata fashe da sauri yace Subhallahi! to ko dai haihuwarce?..., tace yah* *Bunayya* ban saniba ok to tashi muje gida, nan yabud'e mata mota tashiga shima yashiga yaja suka tafi.   "Gudu yake sosai saboda tuni har tafara fita hayyacita sai murkususu takeyi, tana salati tareda kiran sunan *Ammi* da *Abbu* dashi kansa *Bunayya* tana cewa zata mutu, hakan yasa hankalin *Bunayya* tashi sosai tunk kuma yagane cewa haihuwa zatayi, domin yaji su umma nafadi takusa haihuwa dan haka cikin sauri yace sis *Beenazar* haihuwa fa zakiyi dan haka bari muwuce asibiti kinji ko?.., kai tagyad'a cikin tsananin wahala aikam *Bunayya* yana rufe baki  faya tafashe, dan hakan cikin sauri juya kan motarsa zuwa asibiti. Cikin sauri akazo aka tarbesu inada kaitsaye dakin haihuwa aka nufa da'ita, tareda bukatar kayan haihuwa yace to daga school yasuke, amma yanzu za'akawo sannan yakira waya gida yafad'a hakan yasa cikin lokaci kankaci sai ga Umma  direba yakawota, tareda tarkacen haihuwar kasan cewa *Bunayya* yafad'a nan yafad'a mata cewa sun shiga da'ita dakin haihuwa tace to tareda komawa gefe tana addu'ar Allah yadaukesa lafiya. ***** Duk wani kokarin da likitoci sukai dan ganin *Beenazar* tahaihu dakanta abin yaci turo, har yamma gaba d'aya ta galabaita, hakan yasa sukace dole sai anyi mata c s dan haka tuni Umman takira *Ammu* da *Abbu* harda *Abba*, nan *Abbu* yasa hannun inda cikin kankanin lokaci akashiga da'ita aiki batareda bata lokaciba, aka ciro mata kyakkawan katon d'anta me kama da ubansa" sak *Bilal* tamkar yayi kaki ko kad'an be dauko *Beenazar* ba.   koda Umma shi taba *Abba* yaimasa addu'a sannan yaba *Abbu* yana ganin tsananin kamar dayai da ubansa yace alhamdulillahi, sannan yaimasa Addu'a yaba *Ammu* itama tayi masa addu'a sannan tamikama *Bunayya* shama addu'ar yaimasa cike da so, yaba*Basma* kasan cewar tuni itama tazo  aikam cike murna ta rungumeshi sai zuba mashi miliyoyin kiss take cike da kaunar yaron dataji yadarsu mata arai, sosai tarike shi da kyar tabasu *Bassam* suka dauke shi aikonsai fad'i suke lah! wlh yana kamada yah *Bilal*. "Kwanan *Beenazar* hudu a asibiti aka sallameta inda kai tsaye gidan Umma *Ammu* tace akaita kasan cewar itake kulada ita acan asibitin, dan hakan ta ko yanzu ta cigaba da kulada ita har tayi arba'in sannan takoma gurin *Ammu*.  Ranan suna yaro yace sunan *Abbu* wato Usman, dan haka bayan suna sai Umma ta cigaba da kulawa da *Beenazar* da d'anta kamar yanda *Ammu* ta bukata, inda suke kiran yaron da *Baffa boy* wanda kafin suyi arba'in tuni sunyi wani irin kyau da 'kiba gwanin sha'awa, musamman *Baffa boy* da babu abinda yadamesa illa idan yai kuka abashi abincinsa, sabani *Beenazar* data d'an fad'a kad'an saboda tunanin halinda uban d'anta yake ciki, wanda akullum so da kaunarsa yake sake shiga ranta had'eda tausayinsa. Hakan yasa tun bayan rabuwarsu bakinta be taba daina yimasa addu'ar samun lafiya ba, yayinda cikin zuciyarta takejin so da kaunar *Baffa boy* fiyeda da tunanin me karatu wanda akullum  kamanninsa dana mahaifinta suke sake fitowa wannan kenan. *Bayan wata biyar* ****** Muje zuwa *LUFHAT CE or MEENAL* _Allaha kasa mucika da imani ameen ya rabbi?_ 🎍🎍🎍🎍      🎍🎍🎍           🎍🎍                🎍 🎍 *ZAUNJUN MAJNUN* 🎍 (Miji mahaukaci) *BOOK 2* Page 2️⃣6️⃣to3️⃣0️⃣ 🎍 🎍🎍 🎍🎍🎍 🎍🎍🎍🎍 WRITTEN BY 🎍 *AMINA UMAR FARUQ* 🎍 OR 🎍 *MEENAL*🎍 Marubuciyacer *DA SANNU* *ZUCIYATA CE* *AFSANA* *KYAUTAR ALLAH CE* *HASKE BAYAN DUHU* *ZAUNJUN MAJNUN part 1* *TAWAKKALI* *TASEERI* and now *ZAUNJUN MAJNUN part 2* _SADAUKAWAR GA_ Iyayena abin alfarina ina godiya bisaga tarbiyyar dakukai mu, dan haka ina rokon Allah yasaka maku  da alkairi yakareku daga sharrin mutum da aljani, ubangiji yasa kugama da duniya lfy ameen ya rabbi. Wannan littafin na kudi ne akan farashi me sauki, 200 naira only zaku iya turo kudin tawannan account no 0047769671 Amina Abdullahi A., sai kuturo shaidar ku ta hanyar yin screenshot sannan kuturo ta wannan lambar 08161850024, sai naji ku. ✍🏼 _Bismillahirramanirraheem!_      *Abuja* ""''''''"""""BAYAN wata biyar din dasuka wuce wanda acikinsu abubuwa dayawa sun faru masu dadi da marasa dadi, kamar aban garen aunty *Bebe* kuwa marasa dadine sukayi mata dumu-dumu, domin kuwa tsawon watanni nan dasuka shud'e duk abinda tasa agaba batayi nasara akanshi, duk wani boka da malamin tsubbun da yakwana yatashi agarin abuja inda taji labarainsa" to saida sukaje gurinsa da kawarta inda take fadin bukatarta, na asake nakasa mata bawan Allah *"Bilal* saidai kuma har yanzu takasa samun nasara akansa". "Saboda karfin addu'o'e dake fitowa ta'ban garori dadama, daga gurin masoya da malamai dan hakan har yanzu takasa samun nasaran, gashi kuma duk wayanda sukaje gurin bokayan da malamai tsubbun anyi masu aikin sun kumayi nasara amma banda "Ita, dan hakane yasa duk tazama wani iri, wanda idan ka kalleta dakyau zakaga kamar atsorace takeda mutane.       "Sannan ga wasu irin mugayan mafarkai datakeyi masu matukar tsoratarwa, haka zalika har yanzu idan tadauki tukunyar tsafinta dan tayi tsafin saidai bayayi domin kuwa abin yacitura saboda har yanzu tukunyar rawa take sosai, wanda idan har tamatsa dole sai tayi tsafin kamar yanda takeyi ada chan, to ko tabbas tukunyar zata tarwatse ne. "Gashi kusan kullum saiyi mafarkaiyan nan wanda aciki akesake tabbatar mata, da idan har tayi gangancin BARIN tukunyar nan tafashe to tasani komai nata yazo karshe, danka tadaina daukar tukunyar bawai dasunan tahakura tadai tsafinba, saidai dankwai tabarta tukunyar tahuta har zuwa tsawon wanin lokacin domin tunaninta yabata cewa ai tukunyar tagajine.          "Ga wani abu dayafara bata tsoro koma yake bata wato shine, yanzu idan yaranta sunyi badai-dai ba tayimasu fad'a ga mamakinta sai suma suna mayar matada fad'an had'eda rashin kunya, musamman ma Jiddo yanzu sosai takeyi mata rashin kunya tun tana mamakin abin har yakoma bata tsoro sosai. "Dan hakan duk tazama sukuku, saidai acikin zuciyarta mugun nufin nan nata yana nan akan sai taga bayan dan uwata, bawan Allah *Bilal* wanda yakemata sahihiyar kauna ta uwa daya uba daya domin shi betaba daukarta yar uba agareshi ba, yayinda  itakuma take masa matsananciyar kiyayya irinta wasu 'yan uban dasuka tsani abokan haihuwar su" ba gaira babu dalili wannan kenan. "To Allah yasawake, yakuma hadamu da yan uwan da suke kaunarmu tsakani da Allah ameen. *Zaria* ******* "Yayinda aban garen *Bilal* shima hakan abin yake wato abubuwa dayawa sun faru ta'ban garanshi sosai, masu dadi da masara dad'in saidai kuma shikam agurinsa masu da'din sunfi yawa, wanda sune suka baibayesa. "Domin kuwa tuni yasamu lafiya fiyeda tunanin me karatu, kasan cewa kokad'an  baiyi wasa gurin amfani da magungunan da aka bashiba tareda yin addu'o'en da yasani, na neman tsari daga sharrin mutum da na aljan, dakuma wasu addu'o'en wanda malam yabashi yaitayi sosai hakan yasa yaji sauki matuka, yai garau abinsa.       "Inda yadawo kyakkawa _guy_ abinsa kamar yanda yakeda harma yaso yafida yin kyau, saboda harda wani kiba yakara inda farinsa yasake fitowa sosai gashin kannan nasa sai sheki yake yanasake cukurkud'ewa, saboda tsabar gyara dayake mashi hakanan sajen nan nasa yasake kwantawa luf-luf, afuskar me cike da kwarjini da annurin ibada, hakan yasa sai wani shanin takeyi gwanin sha'awa idanka kallesa sau d'aya saika sake kallonsa saboda sha'awa.    "Tuni yacigaba dayin harkokinsa na business dinda sukeyi shida *Bulama* wanda sosai suke samun riba, har suna shirin sake bude wani kamfani saboda bakaramin ma'kudan kud'ade suke samuba, dan haka suka zama wasu irin youngers alhaji kasan cewar kota'ina kudin shigo masu yake tunda tuni *Dad* da *Papa* sun bud'ema ko wani tabkeken pharmacy, agarin abuja.      "Wanda suke ajere da juna guda ana admitin din mutane idan basu da lafiya, guda kuma anzuba magunguna masu kyau da'ake odarsu daga kasar wanje, duk da basu *Bilal* din ne ke zama ba wasu aminttatun mutanansu suka zuba, hakan bai hana ana tururuwar zuwa kai mutane ba tareda siyan magunguna saboda sauki dasukeyi, sosai suke tausama talakawa saidai duk bayan sati daya ko biyu suna zuwa, suga yanda komai ke tafiya kuma alhamdulillahi komai yana tafiya dai-dai.          "Yayinda hakan bakaramin sake bakanta ran aunty *Bebe* yaiba shikam *Bilal* bai masan tanayiba, tunda azahiri bata nuna masa komai ba sannan itakanta babu abinda *Dad* yarageta dashi, balle tace" ai *Dad* komai shi yakeyi mawa Ita baya yimata gashi sosai yake kulada yaranta ta hanyar yimasu hidima, wanda ko Dama chan haka yakeyi masu to amma dai duk da haka zuciyarta tana nan cikeda tsanarsa, dakuma bakin ciki da kyashin abinda *Dad* yake masa.      "Yayinda shikuma yake cigaba da har kokinsa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, bashida wata damuwa sai guda daya zuwa biyu wanda shine yakasance abu marar dad'i dayake faruwa agaresa tsawon watanni dasuka wuce, wato idan yana mafarkinsa da queen of the dream dinshi atayar dashi, sannan yaushe ne queen of the dream dinsa zata bayyana agaresa"?.. "Kamar yanda kullum take fad'a mashi cewa zata bayyana masa, kasam cewar tin bayanda yasamu lafiya kullum yakwanta barci sai yayi mafarkin kyakkawar black beauty girl, wacce sannu ahankali so da kaunarta yasamu gurin zama acikin zuciyarsa da jini da jijiyar jikinsa.        "Wanda dalilin dayasa mata suna queen of the dream kenan, wacce ayanzu duk wanda yake kusada shi babu wanda baisan da zamanta azuciyarsa ba, daga *Dad* aunty *Bebe* da *papa* da *Bulama* harda *Mom* dake chan kano tasan da zaman sarauniyar mafarkinsa,  "Da farko *Dad* tsoro yaji atunaninsa ko aljanun ne suka dawo zasu aureshi,   tunda ance ai aljanu suna auran mutum dan haka yafadawa malam inda yai istahara akai yagani basu bane "mutumce kuma ita ce" abokiyar rayuwarsa, dan haka hankalinsa yakwanta.     "Yayinda itaka aunty *Bebe* taso ace ai aljanun nan ne data tura  masa suka dawo, itakam *Mom* dinsa dataji hakan azahiri tanuna masa hankalinta ya kwanta, saidai kuma abadili chan 'kasan zuciyarata bata yarda da maganar malam din ba, sai tanagani kamar duk shati fadine irin na malamai ne, dan haka akoda yaushe idan sukai waya ko idan sukaje gaida Ita sai tayi masu maganar suyi aure shida *Bulama*,  haka man mana karsu tsaya jiran abinda basuda tabbas akansa lokacifa tafiya yake yakamata ace yanzu sunada mata harma da yara, saidai suyi murmushi dukansu inda *Bulama* yakance insha'allah zamuyi, yayinda shikuma *Blue* sai yace *Mom* karki damu *Mom* very soon my dream queen zata bayyana muyi aure, alokacin my guy yasamu mata sai muyi gaba d'aya idan kuma bai samuba sai nayi nabarsa, yana me kallon *Bulama* cike da zolaya, sai itakuma tayi dariya tace Allah dai yahad'aku damata nagari wayanda zasu kuladaku da kyau sai suce ameen. ******** *Bayan kwana biyu* _Abuja_ "Hakan su *Bilal* suka cigaba da gudanar da rayuwarsu gwanin sha'awa shida *Bulama* "kansu ahade yake, ko su" *Dad* sai sunyi da gaske suke gane masu, bazaka tabajin fad'ansu ba sai aguri d'aya wato Idan *Bilal* yana barcin me dad'i dayake cike da mafarkin queen dinsa, idan *Bulama* yatadashi to yanzu zakaji ruwan masifa agurin *Bilal* din. "Inda zakaji yana fadin _my guy_ bafanason walakaci saunawa zan fad'a maka idan kaga ina barcina kadaina tayar dani eye?..., amma saboda tsabar iskanci irin naka sai katayar dani ko?...yayinda shikuma zayaita dariya yana fadin "eh din natayar mijin sarauniyar aljana kawai.      "To sarkin mafarkin aljanar mafarki sai aje ayi wankan tsarki domin dai yanzu nasan duk ka baci, dan natabbatar yanda kake fama da 'd'an guntuwar jarabarka, bazaka rasa d'an ta'ba wannan aljanar taka tamafarkin kaba ko?...inda yake kasara fadi tareda d'age masa gira d'aya cike da zolaya.       "Yayinda shikuma idan yaji yace" haka sai yai tsaki mtww! cike da d'an haushi ya kyalesa, idan afalo yake kwance sai yatashi yashiga cikin bedroom ya cigaba da barcinsa, idan kuma yashiga wani lokacin baya komawa barcin saidai yai wankan domin kuwa, da gaske acikin mafarkin harda tarayyar auren yakeyi da "Ita. "Kamar yanzuma misalin karfe goma shad'aya da kwata na safer asabar, *Blue* yana kwance afalo yana barcisa cikin nutsuwa me daukeda mafarkinsa da yasaba sai ga *Bulama* yashigo sanye dawani shadda gold color me d'an haske anyi mata dinki zamani, kafarsa sanye da farin half cover shoe hannunsa rikeda wayoyinsa kansa ba hula sai tarin kashi irin wanda samarin yanzu suke bari, saidai nashikam ba irin murd'ad'd'an nan bane nashi agyara yake sai walkiya take kamshi sai tashi yake aajikinsa me dad'i, sosai shigar tayi masa kyau. Fuska cike da mamaki yake kallon *Blue* din wanda yake sharan barci hankalinsa kwance, duka yamaka masa akafa aikam ad'an forgive yafarka tareda kallon wanda yadukesa, inda yaga *Bulama* tsaye akansa cikin shirinsa tsaf sai taunan  chumgam yake  tareda sakar masa murmushi, fuska yahade tareda tashi yazauna cike da masifa yace uhum! ainasan saikai my _guy_ me yasa kakeyi mun hala  ne wai eye?.., cikin kayataccan murmushi yace nayi din malam dall katashi kasan zamu fita amma kawani kwantawa, kanata barci nan me dauke da wannan mafarkin nakada baya karewa so katashi kai wanka kashirya mufita, tsaki yaja mtww! tareda cewa bazan tashi din ba kajiko?..baka kuma isaba malam tashi yayi yashige toilet yana turo baki cike da takaici tashinsa dayai daga barci. ******** "Aban garan su *Beenazar* kuwa suma cikin wayan nan watanni dasuka wuce arziki yasake ahabbaka sosai, inda har *Abbu* yasiyi mota sai yabarma *Bassam* mashin din suna hawa yakuma yasiyama *Ammu* mota, wacce suma sosai harkan siyar da bedshit din yakar besu.   "Sosai *Abbu* yake kulada ahalinsa, haka zalika duk wani abinda su *Beenazar* din keso yana siya masu babu wani abinda yaragesu dashi, dan haka hankalinsu akwance yake sosai domin babu abinda yake damunsu, idan kagansu bataka taba cewa sun ta'ba shiga kuncin talauci arayuwars ba dan hakanan suma suke cigaba da rayuwarsu gwanin sha'awa wannan kenan . ***** Pls sis *Beena* kiyi sauri kifito yah *Bunayya* fa yafita tin d'azu mu yake jira kinji?...., to sis *Basma* gani nafito muje sanye suke cikin boyal les ja me fulawoyi fari da baki, dinkin doguwar rigane dayai matukar karban jikinsu musamman *Beenazar* wacce sosai sharp dinta yafito,   sai suka yafa fararan mayafi tareda saka jaka da takalmi duk farara sunyi kyau sosai gwanin sha'awa, nan suka jera suka fita.  Inda suka iske *Bunayya* cikin mota shida *Baffa boy* sai wasa yakeyi mashi shikuma sai kyalkyata dariya yake, wanda shima aka shiryasa cikin yan kayansa riga t-shirt baka da wando ja abu ga fari sai yai kyau gwanin sha'awa kamar d'an turawa, yayinda shima *Bunayya* cikin shirinsa yake tsaf inda yasa riga t-shirt ja da wandon jeans baki, shima yayi kyau sosai gaba *Beenazar* ta zauna yayinda *Basma* tashiga baya idan *Baffa* yana ganinta yasa rigima wai zayaje gurinta, kasan cewar tuni yashaku da'ita da sauri *Bunayya* yamika natashi yana cewa to yimaza kaje yaron mom *Basmatin* umma, kar kayi mana kuka.    "Cike da kauna takar'besa tana dariya tareda fadin Allah sarki yarona zonaji kaji wane yata'ba mun kai nai masa duka, aikam yafara bulbula dariya itama tanayi masa dai-dai lokacin da *Beenazar* tace eye lallai kenan yah *Bunayya* za'a daka?..., cikin murmushi *Bunayya* yatada mota yana fadin ai zata iya indai akan *Baffa boy* ne, tace ah! lallai kam da alama yah *Bunayya* sabon shopping mall din me suna *LUFHAT CE* zaka kaimu yace ok ai suna kawo nagartattun kaya masu kyau. *******     "Cikin nutsuwa su *Beenazar* ke siyayyarsu itada *Basma* datake rungumeshi da *Baffa boy*, wanda tun shigowarsu yaketa kiriniya hakan yasa tadauke shi tarike, shikam *Bunayya* tunda yasiya abinda yakeso yafita bayan yabasu kudi yace masu su iskesa amota, tunda su idan sukazo siyayya sai suyita nuku-nuku suna shiririta shikuma abinda yatsana kenan. dan haka yafita yabarsu *********     "Achan gefe kuma wani kyakkawan saurayi ne, sanye yakeda wata tsadaddan dakakkiyar shadda gold color da akaimasa dinkin zamani wanda yakarbi jikinsa, kamshin turare sai tashi yake ajikinsa tabbas shidin kyakkawane ajin farko, tsaye yake agaban gurin turaruka wanda kallo daya zakai masu kagane masu asalin kyaune da tsada. "Ahankali yake daukan turaran yana dubawa waya yake amsawa cike da nutsuwa da kuma ladabi, wanda zaya nuna maka cewa wanda yake wayar dashi yanada matukar muhimmaci agaresa. "Ahankali yajuyo fuskarsa dauke da kayataccan murmushi bakowa bane face *Bilal*, hannunsa dauke da wani turare yamikama *Bulama* dake gefensa yakarba yasaka cikin basket din dasuke zuba siyayyar dasukeyi, cikin dariya had'eda sauri sauri yakarasa maganar dayake awayar dafadi *Mom*, nace maki very soon ok to yanzu muna shopping ne idan mun koma gida zankiraki yakatse wayar kitttt.           "Sannan ya kalli *Bulama* yana murmushi shima murmushi ne akan fuskarsa yace *Mom* ce ko?..kai ya gyad'a masa alamar "eh sannan yace duk tadamu muyi aure, yace aitanada gaskiya hakana *Mama* take damuna wai ko sai mun tsufane tukunna zamuyi auran. Nace" mata a ah insha'allah zamuyi dazaran lokaci yayi, kai kuma dan Allah kafita maganar "wannan tacikin mafarkin munemi "yammatana gasuna birjik mu aura kaji?.., harara yabanka masa tareda cewa to bazan nema din ba "kai kaje kanema mana, ok to shikenan kada Allah yasa kanema din kuma bari kagani kwanan nan zanfara neman matar aure eheee!, domin nagaji da soyayyar nan tashan minti.       "Cikin dariya *Blue* yace nikam ina ruwana dama kaine kaga zaka iya wannan soyayyar tawani shan minti cha, haka kawai sai kayita rungumar kowace kazamar "yarinya tareda had'a bakinka danata kilama wata ko brush batayi", har kaje ka kwashi warin baki cike d'an jin haushi yace "eh din ina ruwanka.   "Cikin dariyar zolaya yace aidama baruwana din domin nikam idan kaga nasha bakin "wata to na my queen ne" kagane?.., so sai mutafi ko domi dai nagama nawa shopping din kaifa kagama naka ne ko zaka siyama yammatanka na shan sweet ne?...,yakarasa fadi tareda d'aga masa gira d'aya cike da zolaya. "Yace malam aikasan nagama sarai sukuma ko na siya masu ai ba laifi bane, dan haka mutafi idan kuma zaka tsaya yimun iskancine to sai katsaya ni nayi nan, yawuce yanufi gurin biyan kudi yayinda *Blue* yabi bayansa yana masa dariyar zolaya, bayan sun biya sannan me k suka fito suna isa gurin mota *Mom* tana sake kiran *Blue* murmushi yayi tareda amsawa yashiga motar yazauna, yana cewa *Mom* nace maki idan muka koma gida zan kiraki dai-dai shima *Bulama* yashiga ya zauna tareda ja suka bar harabar shopping mall din.     "Fitar su *Blue* keda wuya su *Beenazar* suka isa gurin biyan kudin, kasan cewar shopping mall din babban gaskene yasa harsu *Bulama* suka gama siyayyar suka fita, batareda su *Beenazar* din sun gansu ba hakanan suma su *Bulaman* basu gansu *Beenazar* din ba. *Baffa* ne yafara rikici wai sai mamansa tadaukesa, hakan yasa takar'besa tana fad'i kai! Babana Mom*Basma* ce kuma yanzu kake guduwa daga gurinta eye?.., cikin dariya tace ah! kyalesu aida mun shiga mota zayace gurina zayazo, nan *Basma* tabiya kudin suka dauki kayan suka fita. "Suna kokarin fita sai ga *Dad* zaya shiga cikin rashin sani yad'an buge *Beenazar* har saida wayarta yafad'i, da d'an sauri yace sorry tareda dukawa dan d'auko wayar wanda kusan tare suka duka, inda cikin sauri tarigashi daukan wayar tana dubawa inda taga batayi komai ba, yace kiyi hakuri inafata dai batayi komai bako?...da sauri tace lah! bakomai ai batayi komai ba dai-dai  lokacin  da tad'ago fuskarta dauke da murmushi.   "Wazata gani idan ba *Dad* ba ido tazaro cike da tsoro yayinda gabanta yai wani irin bugawa, kallonshi takeyi yayinda cikin rawar baki tafara kokarin kiran sunansa *D...a..d*, shima kallonta yakeyi cike da alamar mamakin ganinta anan tareda tambaya me yakawota garin abujane,?...to ko dai ba ita bace?...sai kuma yai saurin kauda wannan tunanin inda yamaida kallonsa ga *Baffa boy* bagansa ne yai wani irin mugun bugawa saboda ganin tsananin kamar dayake da *Blue*.     "Ahankali yafara matsawa zuwa gurinta still yana kallon *Baffa boy* dayake rige a hannunta sai wasanshi yake da sarkar wuyanta, aikam tana ganin yana nufosu tayi sauri juyawa tareda cewa sis *Basma* muje tana me sake rungume *Baffa boy* sosai akafad'arta kamar za'a kwacemata shi, yayinda *Basman* tabita abaya cikin sauri tana d'an waigen *Dad* wanda yabisu da kallo! tareda yatsayawa cak! tamkar andasa shi sosai yake kallonsu" inda sukuma cikin sauri suka isa gurin motarsu suka shiga, *Bunayya* yaja wanda dama yagaji dajiransu. Sai kuma yai sauri yabisu *Beenazar* din saidai yana isa motarsu nawucewa saidai cikin sauri yadauke lambar mota, batareda yakoma yashiga shopping mall din ba, yanufi gurin motarsa jikinsa yana rawa yashiga, tareda cema direbansa yajasa suka tafi zuciyarsa cikeda tsananin fargaba, had'eda tarin tambayoyi???. ****** *Bulama* yanayin fakin mota aharabar gidansu *Blue* still *Mom* tana sake kiransa, cikin dariya yace kai! *Mom* wai yau yayaye?...bari yai saida ta tsinke sannan yakira tareda fitarda karan maganar, tana dauka yace haba my lovely *Mom* nace" maki very soon kedai kawai kiyi addu'a kinji?...    "tace naji addu'a kam kullum cikin yimaku nakeyi, dama zance makane idan har baza kayi auran ba to kadawo da "matarka koda ban santa ba amman naji ance yarinyar kirkice kaji ko?....tsitttttt! yayi tamkar wanda ruwa yacinye, yayinda zuciyarsa tashiga wani irin bugawa tsawon wasu yan mintuna baice komai ba, hakan yasa daga chan taketa fad'in hello! hello!! hello!!! kana jina kuwa?... cikin wata irin rikitacciyar murya yace *Mom* najiki saidai but ban fahimci inda maganarki tadosaba, dama nidin nata'ba aure ne da har narabu da "matar?...tace eh! *Mom* yaushe?...a ina sannan "wacece kuma tana ina yanzu?... tace to nasan amsar tambayarka biyu, nafarko dai azaria akai kuma lokacin da bakada. "Saidai wacece "ita ban saniba sannan yanzu tana ina" shima ban saniba *Dad* kane zaya baka wanyan nan amsoshin, nidai fatana kafita maganar bad'ili wato wannan matar tamafarki kamaida hankali akan zahiri wato matarka ta ainihi, tana kainan takashe wayar kitttt. "Kallon *Bulama* yai wanda suna had'a ido yakauda kai kamar baiji maganar dasukai ba, cikin in'iniya yace umh! kagama ko so muje ko?,...wani irin kallo *Blue* yaimasa domin yasan sarai yaji kuma alamarsa tanuna cewa yasan da maganar hakan yasa yace my _guy_, dama *"Dad* yaimun aure amma shine baka ta'ba fad'amun ba?..., da sauri  yace aure kuma?....kai dinne" akayima aure to yaban saniba eye?... fuska had'e yace kaga malam kafasan komai so banason basarwa kafad'a mun, ciki  sauri yace a ah! nikam bansan komai ba kabari *Dad* yazo ka tambayesa" kamar yanda *Mom* tace", tsaki mtww! *Blue* yai zuciyarsa tana halbawa yad'aga waya yakira *Dad* wanda motarsa take kokarin karyo kwanar shiga unguwar su, da sauri yad'aga tareda cewa son ya'akai ne?...*Dad* kana ina?...son gani nan nakusa shiga gida kaifa kana ina ne?...*Dad* ina gida ina kuma san nayi magana dakai me mahimmanci, ok to gani nan shigowa ok yakashe wayar. "Da sauri yanufi ciki inda *Bulama* yabisa jiki asanyaye, bayan ya mikama wani saurayi key mota yace masa yabude boot kaya na nan yashigo masu dashi, safa da marwa ya'iske shi yanayi zama yai yana kallonsa, domin shidai bazayaji komai abakinsa ba indai akan wannan maganar ne, tunda dai yadauki alkhawari bazaya fad'aba. "Ahaka *Dad* ya'iskesu" sannun sukai masa ya amsa bayan yazauna, sai shima *Blue* zama yai yana kallon *Dad* wanda shima kallon *Blue* din, yace son naga kamar  ranka abace me yafaru?.... cikin had'e fuska yace *Dad* aidole kaga raina abace, shin *Dad* da gaske kayimun aure lokacin da banida lafiya?.. kallonsa yayi cikeda tsoro yace son waya fad'a maka?....cikin bugawar zuciya yace *Dad* kenan da gaske ne?...cikin wani irin yanayi yace...... Muje zuwa *MEENAL ro LUFHAT CE* _ALLAH kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu mu_ 🎍🎍🎍🎍      🎍🎍🎍           🎍🎍                🎍 🎍 *ZAUNJUN MAJNUN* 🎍 (Miji mahaukaci) *BOOK 2* 3️⃣1️⃣to3️⃣5️⃣ 🎍             🎍🎍 🎍🎍🎍 🎍🎍🎍🎍 WRITTEN BY 🎍 *AMINA UMAR FARUQ* 🎍 OR 🎍 *MEENAL*🎍 Marubuciyacer *DA SANNU* *ZUCIYATA CE* *AFSANA* *KYAUTAR ALLAH CE* *HASKE BAYAN DUHU* *ZAUNJUN MAJNUN part 1* *TAWAKKALI* *TASEERI* and now *ZAUNJUN MAJNUN part 2* _SADAUKAWAR GA_ Iyayena abin alfarina ina godiya bisaga tarbiyyar dakukai mu, dan haka ina rokon Allah yasaka maku  da alkairi yakareku daga sharrin mutum da aljani, ubangiji yasa kugama da duniya lfy ameen ya rabbi. Wannan littafin na kudi ne akan farashi me sauki, 200 naira only zaku iya turo kudin tawannan account no 0047769671 Amina Abdullahi A., Idan kuma katine sai ku tuntubi wannan lambar 08161850024, sai naji ku. ✍🏼 _Bismillahirramanirraheem!_    """"""""Boy ina kaji wannan maganar da nace abinneta but amman wanene yatonota eye?..,da sauri yace *Dad* kamar wanene yatonota kuma?...boy tambaya cikin tambaya, to *Dad* ni ban fahimceka bane dama kai anufinka wannan maganarce zata binnu?...."eh son hakan naso shiyasa nece wanene yafad'a makan eye?...yace *Dad* kenan kasan malam bahaushe yace"  idan har andafa boye ba za'a tabaci boye ba ko?.., kwarai haka yake. "To *Mom* ce tafad'a mun kuma kasan bazatayi mun karyaba, *Dad* yace hakane nima kuma kasan bazanyi maka karya ba ko?...cikin tsananta faduwar da gabansa yake cigaba dayi bakinsa yana rawa yace "ehhhh! *Dad* nasani. "Yauwa to tabbas zance haka yake nayi maka aure lokacin da bakada lafiya, da sauri yace *Dad* kenan da gaske ne?...yana mesake tsura masa ido yanason yasake tabbatar masa, cikin sanyi jiki yace kwarai da gaske shiyasa kaji nace wanene yafad'a maka wannan maganar banso kajita ba tabbas naso abinneta tazamo tarihi arayuwa, to amma kuma yana iya tunda *"Mom* dinka tafad'a maka".              "Sannan kuma nasan ko da bata "fad'a makaba, banajin maganar zata zama tarihi kamar yanda naso, domin kuwa abinda nagani yau yatayar mun da hankali matuka, yakuma sani cikin tsananin d'imuwa da rud'ani had'eda tarin tambayoyi. ******* "Shikam *Blue* tunda *Dad* yatabbatar masa da gaske yai masa aure, sai jinsa yatsa cak! na wucin gaji yayinda zuciyarsace kad'a take cigaba da halbawa sai kuma wani iri gumi dayashiga tsatsomasa tagoshinsa, sai kuma sannun ahankali yalumshe kyakkawan idonsa wayanda suka fara chanja kala saboda wani irin bacin rai dayaji yana ziyartar zuciyarsa, domin tsakaninsa da wanda yahaliccesa Allah ko kad'an baiji dad'i jin hakan ba.           "Ahankali yabud'e idon tareda zubasu akan *Dad*, wanda shima kallonsa yake yana jiran yaji abinda zayace akan abinda yaimasa batareda sanin shiba, wanda kallo daya yai masa yagane cewa baiji dadin hakan ba. "Aikam cikin wani irin yanayi narashin jin dad'in, yace *Dad* meyasa kayimun aure ina cikin wannan halin eye?...,            *Dad* meyasa alokacin bakayi tunani idan naji sauki bazanji dad'i ba kamar yanzu eye?..,humm wlh *Dad* banji dadin auran ba gaskiya bazan boye maka ba yakarasa fadi tareda sake lumshe ido sosai yakejin bacin rai.           "Ahankali *Dad* yakai hannunsa akan kafad'ar *Blue* yafara shafawa cikin sigar lallashi, yace son kayi hakuri kakuma gafarceni tabbas sam ban kyauta makaba saboda banyi tunanin, cewa idan kaji sauki kadawo hayyacinka bazakaji dad'i abinda nayi maka ba, ni dai kawai alokacin dana aikata hakan fatana nasamar maka da farinciki, dan hakan na yanke shawaran yimaka auran.  "Wanda kai kanka kasani indai akan farincikin kane zan iyayin komai dan nasamar maka dashi, sannan kuma nayaba da tarbiyyar "yarinyar hakan yasa nayi mata kallon yarinya me kamun kai, saidai kuma abinda yabiyo bayan auranku ne yasa nayi da nasanin aura maka "ita.             "Dan haka kayi hakuri amman bari kaji nafad'a maka dalilin dayasa nayi maka aure, alhalin kana cikin rashin lafiya nan yafara fad'a masa duk abinda yafaru, tin daga lokaci da yafita daga gida har su *Beenazar* suka had'u dashi dazaman dayai agidansu" na wasu kwanaki, da shakuwar dasukai da*Beenazar* dince shine dalilin dayasa yaje yanema mashi auranta, har kan cikin da "tasamu wanda shine dalilin rabuwar tasu" wannan atunaninsu ba cikinsa bane duk saidai yafad'a mashi yanda akai. "Ahankali *Blue* yabude idon tareda sauke ajiyar zuciya cikin sanyin jiki Dana murya, sannan yakalli *Dad*, yace naji kuma yarda dacewa hakan Allah ya kaddara mun, saidai kasani wannan ba hujja bane wato da zukuce" wai dan bana cikin hankalina sai bazan iya tarayya ta aure da'ita ba, tunda acikin labarin daka fad'amun ai kunce komai tareda Ita mukeyi kenan harda barci ad'aki d'aya da'ita muke kwana ko?...., da sauri *Dad* yace kwarai kuwa son, aiko nan dachan baka bari tamatsa sai dole, cikin bacin rai yace to *Dad* kaga komai yana iya faruwa.             "Yace tabbas domin dai abinda nagani yau yasa duk abinda yafaru achan baya yatabbata gaskiya ne, fuska had'e yace *Dad* kamar yafa?...cikin dayake jikin *"Beenazar* tabbas cikin kane, ido yasake rintsewa yanasake jin babu dad'i aransa har yana fad'in wai shine akaima aure batareda yasaniba har yaima matar ciki ikon Allah. Cikin sanyi murya yace *Dad*  kenan to ai tin wancan lokacin baka tabbatar ba, sai yanzu ne zaka tabbatar?..."eh boy to saboda me?....saboda yau naga *Beenazar* tareda "d'anka, da sauri yace no! *Dad* bafa d'ana ba d'anta" dai ko kamanta kace cikin sake jikinta" banawa bane eye?...cikin rawar jiki yace no! my son wlh wannan yaron d'anka ne domin kallo d'aya nayima shi na tabbatar shid'in jininkane saboda tsanani  kamar dakukai da yaron tayi mugun yawa tamkar kaine lokacin dakake yaro. Cikin tsanani zumud'i *Bulama* yace *Dad* ina kaga sis *Beenazar*?...wani kallo *Blue* yaimasa me cike da takaici, kafin duk *Dad* yabashi amsa *Blue* yayi sauri bashi cikin masifa yace malam bai saniba din d'an rainin hankali kawai, dana tambayeka ai cewa kayi "kai bakasan komai akan maganar ba amma yanzu dan rainin hankali kana wani tambayar ina akaganta" ko?..., Shima cikin masifa yace eh! din malam aibakai na tambaya ba *Dad* nake tambaya kanji ko?.. tsaki mtww! *Blue* yai tareda dauke kai daga barin kallonsu, domin wani irin haushinsu yakeji. *"Dad* kam murmushi yai domin yasan wannan fad'an duk haushi yakeji saboda anyi masae auran bai sani bane, sai kuma yad'afa kafad'ar *Blue* din tareda cewa my *Boy* karkaga laifin son nine nan, me laifin tunda ni nace kar wanda yafad'a maka komai, akan maganar auran kaji ko?...ba tareda yakalli *Dad* ba fuska murtine yace naji  *Dad* amma aidana tambayesa. nuna mun yai baisan komai fa, to kayi kakuri kaji yarona?. kai ya gyad'a. "Dai-dai lokacin da *Bulama* yasake cewa *Dad* yanzu sis *Beenazar* ta haihu?... fuska dauke da annuri yace kwarai kuwa son tahaihu, "yaronku" yana nan kyakkawan gaske tamkar d'an uwanka yayi kaki tsabar kaman dasukai, gashi d'an lukuti kamar d'an turawa yakarasa fadi fuska dauke da murmushi yana kuma Kallon *Blue* wanda yaketa cika yana batsewa. "Cike tsanani farin ciki fuska dauke da murmushi *Bulama* yace kai! masha'allah, Allah yaraya *Dad* wai ina kaganta" ne sannan kuma meyasa kabari ta tafi bakutaho tareba munga beautiful boy dinmu eye *Dad*?..."Harara *Blue* yabanka masa tareda cewa ehe! laillai  saboda gata" mara zuciya, tayi maku halacacci ta hanyar auran mahaukaci d'anku" sai kuma kukai mata, butulci ta hanyar koranta sannan dan tagansa yanzu sai tabiyosa saboda san kanku yayi yawa ko?....hararansa shima *Bulaman* cike da zolaya yace kaga malam bafa dakai mukeyin maganarmu ba, amma sai faman saka mana baki ka keyi. "Cike da hassala yace nasa din kayi maganin hakan kaji ko?...yace kaga malam nidai kayimun shuru karnazo nabuge bakinka agurin nan, banza yai masa.              "Hakan neyasa *Bulama* cewa uhum! da kasake magana agurin nan dakasani, *Dad* kyaleshi fad'amun ina kaganta"?.. murmushi *Dad* yai me kayatarwa sannan yace son naganta ne a *LUFHAT* shopping mall, cike da mamaki yace *Dad* to aimuma daga chan muke amma bamu gantaba kuwa, ikon Allah kenan aiko nikam achan naganta nan yafara tambayarsa sunyi magana me tace" masa meyace mata?...      yace son batace mun komai ba asalima tsoro nagani yabayyana akan fuskarta, sannan kuma ta gudu. "Ido *Bulama* yazaro cikeda mamaki yace *Dad* tsoro kuma sannan ta gudu?..."eh kaidai, a ah *Dad* ko dai bata ganeka bane eye?...hum! son kenan wlh taganeni, abunda har  tana sake rungume d'anta tamkar nace zan kwace mata "shi yakarasa fadi, daidai lokacin da *Papa* yashigo bakinsa dauke da sallama. "Suka amsa tareda yimashi sannun, ya amsa yana nufar gefen *Blue* ya zauna yana cewa son ya'akai ne cikin sanyi murya yace lafiya lau *Papa* sannun da dawowa yauwa son, yayinda *Dad* ya kallesa tareda cewa *Barr* harka dawo?..."eh *Dr* ya'akai ne naga kamar ran son dina abace, me kukai masa kaida "d'anka ne eye?...    murmushi yai yace *Barr* laifin namune duka harda kai, saidai nawa yafi yawa dan haka kanema mun afuwa gurinsa.          "Kallon *Blue* yai yace a ah wai haka ne son?...fuska tur'bune yace "eh *papa* ai hakan da akayi ba aimun adalciba gaskiya, yace to son kafin naji abinda akai maka kayi hakuri, sannan ina nema mana afuwa kaji?....yace ok *papa* nayi, yauwa son Allah yaimaka albarka ameen my *papa*.      "Sannan *papa* yasake cewa Dr me mukayima son dina ne?...cikin dariya yafad'a mashi komai, masha'allah Allah sarki *Beenazar* ta haihu?...eh wlh Barr d'anta" yana nan tamkar d'anka yayi kake, cikin murmushi yace madallah Allah yaraya akan sunna to ameen inji cewar *Dad*. "Cikin bacin rai *Blue* yace to yanzu *papa* anyimun adalci kenan?.., ace aimun aure banida lafiya naji sauki amma ba'a fad'amun ba har gashi matar tahaihu, duk ban saniba saboda Allah fa?....kafad'arsa *papa* yad'an bubbuga cikin sigar lallashi.     "Sannan yace am very! very!! very!!! sorry my son tabbas munyi maka laifi babba, saidai kasani duk dan muga farincikin kane mukai hakan kaji?...cikin sanyi murya yace to shikenan *papa* komai yawuce. "Yauwa son nagode amma kasani lokacin dana dawo naji hukuncin da Dr ya yanke nakoran *"Beenazar* din, dacewa wai cikin jikinta banaka bane" ko kad'an banji dad'i ba wanda naso nanuna masa hakan ba dai-dai bane, to amma sai bai bani damar hakan ba shiyasa kawai nabi dashi ayanda yakeson. "Yace *papa* aina fad'a mashi na basu kyautaba, *Dad* yace lallai nayi kuskure ina kuma sake neman afuwarka, itama *Beenazar* din zan nemi gafararta insha'allah sannan inason kamaida matarka albarkacin yaronku ko Barr?... "Yace tabbas hakan yanada kyu shine dai-dai, shidai *Blue* baice komai ba domin sosai yakejin haushin wannan al'anadin. "Yayinda *papa* ya cigaba da cewa to yanzu dr yazamuyi mugano inda *"Beenazar* din take anan cikin garin eye?...yace to shine kuma abin tunani, gashi kuma batako tsaya kunyi magana ba balle tafad'a maka inda suke ko?...yace "eh wlh saidai naga lambar motarsu", yauwa to yalambar take?.... nan yakaranto masu, aikam nan take *papan* yace ah! to ai wannan lambar motar gidan alkali sasu ne, cike da farincikin*Dad* yace masha'allah shikenan sai muje da sauri *Blue* yace *Dad* wai me zakuje yine kuma?...yace a ah boy muyo maka bikon "matarka mana ko Barr?...yace tabbas, haba *papa* bayan kunsa keta.            "Cikin dariya yace son aiwannan sakin bai sakuba tunda wani baya sakarma wani mata, dan haka insha'allah zamuje mudawo maka da "matarka kayi hakuri ka zauna da "Ita kodan albarkacin yaron ku" kaji?....ko kad'an azuciyarsa baiji son wannan matarba wacce ko saninta baiyi ba.        "Amma yasan bazaya taba jayayya da mahaifiyarsa da mahaifinsa da kuma aminin mahaifinsa ba, domin sud'in mutanene masu matukar muhimmaci agaresa, dan haka cikin sanyin murya yace to *papa* duk yanda kukai shine dai-dai.       "To shikenan yanzu mu zamu fara zuwa sannan kuma sai kuje ko Dr?..eh Barr hakan za'ayi, ko son yakarasa fadi tareda kallon *Bulama* yace "eh *Dad* hakan za'ayi, yauwa to Allah yai maku albarka suka amsa da ameen dai-dai lokacin da *Blue* yamike yakalli *Bulama* wanda  yake kallonsa yanai masa murmushi kasa-kasa, yace to malam aisai katashi muje ko?.... dariya yasaki tareda tashi yana fadin ok my _guy_ muje, suka fita inda suka bar su *Dad* suna tattaunawa akan yanda zasu tunkari gidan alkali sasu. ******** "Aban garan su *Beenazar*  kuwa da gudu *Bunayya* yacilla hanci motar kan titi, cikin rawar murya tace pls yah *Bunayya* kayi sauri mubar nan kaji?...cike da mamaki ya kalleta batareda yace komai ba, yacigaba da tukinsa yake cikin kwarewa saidai kuma had'eda sauri wanda yake nuna cewa shima yanada uzurin zuwa wani wurin ne. "Yayinda *Beenazar* din sai sake kwakume *Baffa boy* takeyi ajikinta tamkar *Dad* yabiyota yakwaceshi, kirjinta kuwa sai aikin bugawa yake cike da tsoro sai leke takeyi tagefen wondon datake zaune, hakan yasa *Bunayyan* cewa sis *Been* _kasan cewar haka yake kiranta wani lokaci_ wai ya'akai ne?..naji kince nayi sauri mubar shopping mall din, yanzu kuma naga sai faman leka wondo kikeyi shin meke faruwa ne?...       "Da sauri *Basma* tace yah *Bunayya*, wlh wani mutumine daga kawai sunyi karo shikenan kuma sai naga yabiyo mu, cike da mamaki yace kamar yafa "ya biyoku to yai maku meye"?...wlh yah ni bansani ba, but amman sai naga kamar sis *Beena* tasanshi. Da sauri yakalli *Beenazar* din tareda cewa sis *Been* wai kinsan shi?..., kai ta gyad'a alamar "eh ok wanene?..me makon tabashi amsa sai kawai tafashe da kuka.          "Hakan yasa yace Subhallahi sis *Beena* halan "wanene shi"?.., meyasa dan na tambayi wanene shi kike kuka eye?...cikin kuka tace yah *Bunayya* inajin tsoron karda yakwace mun yarona ne, cikin mamaki yace yakwaceshi saboda me to?... cikin kukan tace yah *Bunayya* "shine *Dad* mahaifin yah *Bilal*, fuska had'e yace ok no wander to akan wani dalilin zasu kwaceshi" bayan sunce ba cikinsu bane eye?..., tace "eh duk dasunce hakan to amma yanzu zasuce" nasune tunda sunga yaimugun kamada yah *Bilal* din, dan haka zasu iya kwaceshi ni kuma gaskiya bazan iya rabuwa da yarona ba takarashe fadi tareda kara sautin kukanta.              "Cike da tausayinta *Bunayya* yai fakin gefen hanya yakashe motar, sannan cikin sanyi murya yace kiyi shuru kidaina kukan, insha'allah bazasu ta'ba rabaki da d'anki ba kinji ko?...kai ta gyad'a alamar to sai da yatabbatar tayi shuru, sannan yatada motar suka nufi gida alokacin tuni bawan Allah *Baffa boy* yayi barci. ***** Ahaka su *Beenazar* suka isa gida sukuku jiki bakwari dukansu, bayan *Bunayya* yasaukesu akofar gida yabud'e masu boot *Basma* ta kwashe kayansu sannan yatafi, inda sukuma kai tsaye suka nufi 'ban garen su *Beenazar* din suka shiga, da sallama *Ammu* ta amsa wacce kallo d'aya tayimasu tagane babu lafiya, tuni *Basma* tanufi ciki dan ajiye kayan dake hannunta. "Cikin d'an faduwar gaba *Ammu* tace lafiya naganku haka?...takarashe fadi tana kurama *Beenazar* ido, tareda mika hannu takarbi *Baffa boy*, tana sake cewa me yasame shi?...murya asanyaye tace bakomai barci yakeyi ok. "To ke kuma me yasameki kikai kuka har idonki yai kozai-kozai eye?...me makon tabata amsa sai tafashe dakukan wanda dama yana kusa, kallonta tayi tareda cewa hum! kedai kuka baya ta'bayi maki wuyar yi, to ya faruwar ne?...dai-dai lokacin da *Basma* tafito dan haka ita ce tafad'a mata abinda yafaru, duk dacewa taji faduwar gaba hakan bai hanata cewa shine kike wannan kukan?.... cikin shagwa'ba had'eda d'an turo baki tace *Ammu* idan suka kwaceshi" kuma fa?....,to sai me idan sun kwaceshi sai shikenan bazaki iya rayuwa ba komai eye?...dai-dai lokacin da*Abbu* yashigo, sannu sukai masa ya amsa tareda cewa a ah lafiya gaku tsayyaye chirko-chirko kamar kajin dasukai fad'a suka gaji, yakarasa fadi tareda sakin dariya itama *Basma* dariyar tayi, Amma banda *Ammu* da *Beenazar* dake aikin sharan hawaye, kallonta yai yace a ah! wanene kuma yata'bamun uwata eye?...yana me ruko hannunta suka nufi falo zomuje naji halan fatimata ce ko?..., a ah *Abbu* ba ita bace to wanene? fad'amun..... Bayan sun zauna sai tafad'a masa duk abinda yafaru, murmushi yai me kayatarwa tareda dafa kanta yace anzo gurin, sannan kuma ranan takusa zuwa wanda dama nadad'e ina jiran tazo dan haka karkudamu mamana, insha'allah babu wanda zaya rabaki da d'anki kinji ko?... kai ta gyad'a alamar to yace yauwa ki kwantar da hankalin, to *Abbu* yauwa to tashi kuge ga yar uwarki can tana jiranki idan *Abbanku* yadawo kizo kifad'amu zamu wata muhimmiyar magana dashi kinji ko?...tace to*Abbu* tareda tashi tafita, inda ta iske *Basma* suka nufi gidansu. ******* Kodasu *Blue* suka fito kai tsaye gardin suka nufa, inda suka zauna akan wasu fararan kujeru 'karkashin bishiyar mangwaro, cike da farincikin *Bulama* yace kai my _guy_ wlh naji dad'in jin cewa sis *Beenazar* tahaihu Allah sarki baiwar Allah, nikam har namatsu su" *papa* suje su dawo muma muje, da sauri  *Blue* yace ka daije kai kad'ai domin ni man daka ganni babu inda zanje saboda wannan matar wlh, cike da mamaki *Bulama* yace me kake nufine wai?...wani irin kallo yai masa tareda cewa ina nufin ni bazanje ko'ina ba, dasuna wani abu wai shi biko saidai kai kaje.         "Cikin sanyi murya yace saboda me?.. saboda wlh ko kad'an banji inason taba balle har naji, san zama da'ita muyi rayuwar aure da sauri yace kai! my _guy_ to da dakai da'ita fa?...Harara ya watsa mashi yace dakace, kuma ada dinma banida hankali yanzu kuma da hankalina.     "Sannan tuni zuciyata tayi nisa da so da kaunar my dream queen, wacce naji ajina kwanan nan zata bayyana agareni muyi aure, wato kenan duk abinda kafad'a agaban *Dad* da *papa* kad'ai fad'ane but amma baikai zuciyarka ba kenan?.... "Eh kusan hakane saboda bazanyi masu musu akan abinda sukace nayiba, but amma sam bana ra'ayinta zandai zauna da'ita ne saboda su" cike da mamaki *Bulama* yake kallonsa, sannan yace kuma har cikin zuciyarka iyakar gaskiyarka kake fad'a?... yace kwarai kuwa. "Kai ya gyad'a alamar gamsuwa da abinda yafad'a wanda yatabbatar iyakar gaskiyarsa kece tunda yasan shi ciki da bai, saidai kuma ko kad'an baiyi tsammani hakan daga garesaba. hakan yasa, yace kenan dakace munyi "mata butulci ashe kai wanda zakai mata yafi namu ko?...cike da rashin fahimceta, yace kamar yafa?....cikin bacin rai yace kamar ban ta'ba sanin cewa kai  butulu babe sai yau, cike da mugun mamaki yakallesa yace!..... Muje zuwa *MEENAL or LUFHAT* _Allah kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu mu_ 🎍🎍🎍🎍      🎍🎍🎍           🎍🎍                🎍 🎍 *ZAUNJUN MAJNUN* 🎍 (Miji mahaukaci) *BOOK 2* 3️⃣6️⃣to4️⃣0️⃣ 🎍 🎍🎍 🎍🎍🎍 🎍🎍🎍🎍 WRITTEN BY 🎍 *AMINA UMAR FARUQ* 🎍 OR 🎍 *MEENAL*🎍 Marubuciyacer *DA SANNU* *ZUCIYATA CE* *AFSANA* *KYAUTAR ALLAH CE* *HASKE BAYAN DUHU* *ZAUNJUN MAJNUN part 1* *TAWAKKALI* *TASEERI* and now *ZAUNJUN MAJNUN part 2* _SADAUKAWAR GA_ Iyayena abin alfarina ina godiya bisaga tarbiyyar dakukai mu, dan haka ina rokon Allah yasaka maku  da alkairi yakareku daga sharrin mutum da aljani, ubangiji yasa kugama da duniya lfy ameen ya rabbi. Wannan littafin na kudi ne akan farashi me sauki, 200 naira only zaku iya turo kudin tawannan account no 0047769671 Amina Abdullahi A., Idan kuma katine sai ku tuntubi wannan lambar 08161850024, sai naji ku. ✍🏼 _Bismillahirramanirraheem!_     """"Guy ni ne butulu"?....cikin mugun bacin rai yamike tareda nunashi da yatse, yace "eh kai! din ne butulu babbama kuwa irin wanda ban ta'ba ganiba arayuwata, shima cikin bacin rai yamike yace malam wai meye hakane kaketa faman kirana da wani mugun suna wai butulu?...ankiraka dashi d'in domin ka cancanci akiraka dashi kaji ko?..., cike da takaici yace tukun nama tsaya wani irin butulci nai maka da har zaka ringa kirani butulu, saboda tsabar mugunta har da wani cewa babban butulu ko?...yace "eh kai babbn butulune nafad'a, kuma ni bani kaima butulci ba *"Beenazar* kaima butulci. "Yarinyar data sadaukar darayuwarta ta aureka" alhalin kana cikin halin hauka ba tareda damuwa da haka dinba shine zakai mata butulci, yace to ni ina ruwana da sadaukar da rayuwarta datayi eye?..."eh dama shi d'an adam butulu ne arayuwasa kai masa halacci shiko yaimaka butulci.    "Cikin jin haushi yaja tsaki mtww! tareda cewa to waini me nawa aciki, tunda bani taimawa halacci ba ku tayimawa dazaka wani dameni dacewa tayimun halacci nai mata butulci eye?... "Harara yasake banka masa tareda cewa "eh lallai kace haka mana saboda tsabar walakaci irin naka, sannan tunma baka gantaba  har kana wani cewa baka ra'ayinta" dayake kaidin babban butulune ko?... cikin mugun jin haushi yanda yaketa kiransa butulu yace kaga malam kadaina kirana da butulu kaji ko?...shima cikin jin haushin yace bazan dainaba din, tunda butulci kayi. Ok" to ka cigaba dakirana butulun nadai ce bana ra'ayinta kuma bazanje bikon ba kaji ko?...to kada Allah yasa kaje din mana sai me to idan bakaje ba eye?...fuska murtik yace sai kayi yanda zakai dani, yace uhum! ni babu yanda zanyi dakai saidai kai kayi yanda zakai dani tunda bafashi sai zanje eheee!, cikin hassala yace to ina ruwana kai tazuwa mana idan ka'iya kafinruwa saurin zuwa kaji ko?..., kuma wlh idan kafad'awa *Dad* banjeba sai mun samu mummunan matsala dakai eheee!.           "Cikin bacin rai yace Oho! dai wannan kuma yarage naka, saidai naje nayo maka bikonta" insha'allah kuma dole sai zauna da'ita eheee!. ya karashe fadi yana kokarin tafiya, yayinda shima cikin bacin rai yace zama "da'ita nabanza tunda bana ra'ayinta" kada Allah yasa kayi ra'ayinta din kuma insha'allah sai Allah yajarabeka da masifar kaunarta", cikin masifar bacin rai yace mugu ba ameen na domin zuciyata my queen dream KAD'AI takeso, yace oho dai insha'allah sai Allah yakarbi addu'ata ni kuma nace ba ameen ba eheee.         "Haka dai suka rabu baran baran kowa rai bace, inda *Blue* yabi bayansa da kallo yajin wani irin mugun bacin rai ganin yanda suka rabu da *Bulaman*, wanda wannan shine karo nafarko a tsawon zamansu dasuka samu matsala irin hakan da juna, hakan ne yasa *Blue* sakejin haushi da tsanar *Beenazar* wacce yatabbatar duk ita ce silar faruwan haka, tsaki yaja mtww! cike da mugun bacin bacin rai  sannan yanufi cikin gida yana fad'in I hate this girl before I see her. ********* "Aban garan su *Dad* kuma aranan basuyi sanyi aguiwa ba, sukaje gidan alkali sasu inda kuma cikin sa'a suka iske baida d'eda dawowa, daga kotuba kasan cewar yau ya yanke hukunci akan wata shari'a da akadad'e ana gabatarwa.      "Wanda  fitar *Abbu* kenan sukazo kasan cewar yashiga yafad'a mashi abinda *Beenazar* tafad'a yafaru tsakaninta da *Dad*, da yanda tanuna jin tsoron karsu" rabata da d'anta" yace mashi kar yadamu insha'allah baza su rabata da "d'anta ba. "Bayan *Abban* yabukaci sanin suwaye aka fad'a mashi, ba tareda bata lokaci ba yasa akashiga dasu babban falonsa dayake ganawa dabaki inda ya'iskesu cike da girmamawa suka gaisa, kasan cewar yasan *Papa* dan haka bayan sun gama gaisawa yake tambayarsa yada cewa Barr *Bulama* aikin?... alhamdulillahi ranka yadad'e, masha'allah kwana biyu ban ganka akotun mu ba I hope dai lafiya?...cikin murmushi ya amsa da cewa ranka yadad'e, lafiya lau wlh kwana biyun ne banyi aikin bane na tafiya ne.    "Masha'allah to Allah yataimaka ameen, to ina fatadai ba ankawo mun cin hanci bane, akan wata shari'a da'akeson agudanar ba ko?....cikin dariya *papa* yace a ah yallabai ai nasanka" kai baka kar'ban cin hanci, sannan nikaina idan har baka mantaba bana tsayawa marar gaskiya. Murmushi*Abba* yai tareda cewa haka ne to meke tafe daku?..nan *papa* yafara fad'a mashi abinda ke tafe dasu, aikam kafin duk *papan* yagama fad'ar abinda yakawosu" *Abban* yafara fad'a da *Dad*  tareda cewa ainasan da maganar,  dama inajiran zuwanku shin dr abinda kai sam baka kyauta ba, ai bahujja bane dan d'anka bayada hankali sai bazaya iya tarayya aure da mace ba, nan dai sukai tabashi hakuri musamman *Dad* wanda shine me laifin.         "Sannan *Abban* yad'aga waya yakira *Abbu* yace" yanason ganinsa, chan saiga shiya shigo da sallama suka amsa yana ganinsu" *Dad* yad'auke kai tareda zaunawa kusad'a *Abba*, ba tareda yakallesu ba yagaidasu" fuska had'e inda  suka amsa, ya kalli *Abba* yace yaya gani kace kanason ganina ?._ kasan cewar yanda yaji *Ammu* nakiransa yaya haka shima yake kiransa_ ."Yace "eh dama su Barr ne, nan yafad'a mashi duk yanda sukai harda hakurin dasuka bashi gasunan kuma yakarajin komai abakinsu, aikam nan shima yafara fad'a ta inda yake shiga batanan yake fitaba, inda har yana cewa aikunce bacikin ku bane to yanzu kuma meya kawoku?....ko dayake nagane wato tunda kunga "yaron yayi kama danku shine kukazo danku rabata" da d'anta ko?..., saboda sabar sonkai irin naku to yaya kasani bazan ta'ba yarda su raba "mamana dayaronta" ba, wanda dama sunce natane Ita kad'ai bada d'ansu ba. "Nan dai yaketa fad'a yayinda suketa bashi hakuri inda *Abba* yasa baki dacewa lallai basu kyautaba to amma tunda hakan tariga tafaru yayi hakuri, cikin sauke ajiyar zuciya yace shikenan yaya nahakura komai yawuce. ******* "Bayan komai yalafa sannan suka fad'i abinda yakarkare kawosu", *Abba* yace masha'allah hakan yayi kyau sosai Allah yasanya alkhairi, Alh Usman kaji abinda suke bukata ko?...eh yaya naji kuma nayi farinciki sosai dajin cewa *Bilal* yasamu lafiya, dan haka badamu insha'allah mamana zata koma d'akinta wanda nakesa ran cewa zatasamu farinciki me d'orewa na har abada, tunda dai nasan tana kaunar mijinta shima kuma nasan yana kaunarata cike da farin ciki *Dad* yace tabbas haka ne suna kaunar junasu sosai. "Yace dan haka sai akula mun da'ita" domin itad'in tamkar tsokar jikinace, koma nace maka itad'in tsokar jikinace ko kad'an banason bacin rainta, ko wancan lokacin sosai naji zafin abinda akai mata" musamman idan natuna da irin sadaukar da rayuwarta datayi dan farincikina data "yan'uwanta, sannan aka kuntata mata duk sai naji ba dad'i to amma kuma sai na dan gana hakan da kaddaranta ne saboda haka Allah yabasu zaman lafiya da kwanciyar hankali acikin auran nasu.    "Cikin sanyin jiki suka amsa da ameen, sannan *Abba* yace to masha'allah yanzu yaushe kukeson takoma ko Alh Usman?... yace "eh yaya hakane sai kufadi ranan dazata koma, cikin murna *papa* yace a ah kufad'a dai...a ah mun yarje maku kufad'a yace to idan babu damuwa nan da kwana biyu, *Abba* yace jibi kenan ciki dariya yace "eh yallabai domin mu bamuki bama ace mutafi da'ita yauba,  a ah jibi yayi kusa kasan mata da kintse-kintse dan haka abari ta kintsa idan yaso rana Ita yau sai takoma ko Alh Usman?...eh yaya hakan yayi dai-dai, sukace to shikenan Allah yakaimu akamar gobene agurin Allah. "Sannan  *Dad* yace idan babu damuwa inaso naga daughter *Balkisun* domin na nemi yafira abinda nayi mata, *Abbu* yace badamuwa bari nakirata yana me mikewa *Abba* yace kafad'awa Fatima abinda ke faruwa amatsayinta na uwa ko?..."eh gaskiya, yau kace kuma tazo inason ganinta to sannan yafita. ******** Koda *Abbu* yafad'ama *Ammu* yanda duk sukai dasu *Dad*, batace komai ba saidai aranta bataso su *Abbun*sukai saurin yafe  masuba, taso sai tanuna masu cewa yarta tanada gata sannan ba mutumiyar banza bace kamar yanda suka dauketa, amma yazatai tunda mijinta da yaya sun rigasun yanke hukunci.      "Saidai duk da haka sai ta fad'a masu magana kallon *Abbu* tayi wanda shima kallonta yake, yanason yaji tabakinta tace bakomai muje naji kiran yayan, yace yauwa ninasan fatimata macece me matukar jin maganar mutane tareda girmamasu shiyasa kullum kaunarki take sake shiga cikin raina Allah yabarni dake har abada.     "Cikin jin kunya "tace ainima haka kullum kaunarka tana sake shiga raina musamman saboda irin kyautatawar dakakeyi mana nida yarana", shiyasa kullum nake rokon Allah yabarmu tare har abada cikin jin dad'i yajanyota jikinsa, tareda fad'in da gaske fatimata kema kinayin iri addu'ar dana keyi mana kenan?... kai ta gyad'a cike dajin kunya cikin murmushi yace ameen fatimata Allah yai maki albarka cikin jin dad'i tace ameen, yauwa to ina *Beenazar* din take?..tace ai tana chan part  dinsu yayan yace ok to muje. ******** Koda Nan *Abba* yafad'a mata hukuncin dasuka yanke, na komawar *Beenazar* din d'akinta batareda sunji tabakinta ba, cewa tayi to yaya sunci arzikinka sosai dan haka duk yanda kujayi dai-dai ne, saidai yaya su sani cewa kamar yanda suke takama d'ansu yanada gata to hakan itama *Beenazar* tanada gata, sannan mun bata tarbiyya me kyau tayanda ko kad'an bazata ta'ba aikata abinda ba dai-dai ba, dan haka karsu sake jifanta da kazafin zina domin wlh bazanmu sake dauka ba ehee! da sauri *Dad* yace Subhallahi zina kuma da yaushe mukayi mata kazafi zina?... wani kallon tayi masa tareda cewa cikin dakace bana d'anka bane dashi tazo gidanku me kuke nufi da hakan eye?...,ajiyar zuciya yasauke tareda cewa kiyi hakuri, nine nace hakan kuma wlh ban fadi da nufin abinda kike nufiba amma insha'allah hakan bazaya sake faruwa ba, wancanma sharrin shaidan ne da rashin kwankwaran bincike.     "Har zata sakeyin magana *Abba* yace Fatima ya'isa hakan ayi hakuri komai yawuce, ciki sanyin jiki tace shikenan yaya yawuce Allah yabasu zaman lafiya, yauwa to ameen inda aka amsa duka dakin sannan tamike tafita inda sukaci karo da *Beenazar* zata shiga, tana dauke da *Baffa boy* wanda tashinsa d'aga barci kenan, tace mata idan kinfito kizo inason ganinki tace to *Ammu*.      "Sannan tashiga bakinta dauke da sallama suka amsa, kusada *Abbu* ta zauna cikin girmamawa had'eda jin kunya ta gaidasu suka amsa fuska dauke da farinciki *papa* masha'allah abokin namune nan?...,kai ta gyad'a tareda mikashi yakarbesa yana cewa kai masha'allah! yasunansa?... Barr ne ko Dr eye?...yayinda *Dad* yaketa kallonsa yana murmushi cike da sha'awa.... cikin dariya *Abbu* yace a ah takwarana ne tunda Barr da Dr sunce basuyin abotar dan haka sai nikuma nace inayi, cikin dariya *papa* yace kumafa gaskiya ne to yanzu kam muna cikin manyan-manyan abokai ko Dr?... murmushi yasaki me kayatarwa tareda cewa kwarai kuwa, yauwa to gashi ku gaisa nan yakarbi *Baffa boy* wanda yaketa bulbula dariya abisa, gwanin sha'awa.      Sai kallonsa yakeyi sosai yake ganinsa tamkar lokacin da *Bilal* yake yaro, aika take yaji kaunar yaron tashiga cikin zuciyarsa sosai ya rungumeshi akirjinsa, sannan yakalli *Beenazar* cikin kwantar da murya yace "yata *Balkisu* kiyi hakuri da dukka abinya yafaru abaya kinji?...kai ta gyad'a, sosai yaita bata baki kafin ta tashi zata fita danufin tabarsu da *Baffa boy* saidai me. Kuka yasaki tareda mika hannu wai ta d'aukesa, dariya suka saka gaba daya inda *Dad* yace a ah babana 'kiwane haka to karbeshi kutafi, bayan fitar *Beenazar* ba da dad'ewa ba su *Dad,* sukai sallama dasu *Abbu* suka tafi bayan sun sanar dasu cewa su *Bilal* na nan zuwa. *******   "Adaren ranan *Bulama* yaje gidansu *Beenazar* batareda yatsaya jiran suje tareda *Blue* ba, tunda yace bayajeba to ko yatabbatar bazayaje dinba dan haka sai tafiyarsa abunsa, inda ko akayi masa tarba me kyau domin kuwa har cikin gida yashiga yagaidasu *Ammu* da Umma inda yasanar masu cewa d'azu tafiya takama *Blue* zuwa U.K sukace eyya to Allah yadawo dashi lafiya yace ameen. sannan aka kaishi d'akin saukar baki, inda *Beenazar* ta iskeshi cike da girmamawa tagaida shi, ya amsa tareda daukar *Baffa boy* yanai masa wasa cike da kaunar yaron dayaji yad'arsu aransa cikin kankanin lokaci, yayinda shikuma yaketa kyalkyala dariya.      "Tsawon mintuna yanayi masa wasa chan kuma sai yafara daukarsu hoto da wayarsa, duk tana kallonsu yayinda zuciyarta take cike da tambayar ina yah *Bilal* dinta me yasa bai zoba?....to ko jikinsa ne har yanzu, da sauri sai kuma takauda tunanin hakan daga ranta to hanyar fadin a ah kam bajikin bane tunda ance" yaji sauki, har yaci gaba da harkokinsa kamar yanda yakeyi chan da ila dai wani abin ne yahanashi zuwa, murmushi tasaki cike da gamsuwa da abinda zuciyarta tafad'a mata. Dai-dai lokacin da *Bulama* yace sis *Beenazar* yabayan rabuwa?...cikin murmushi tace sai alkhairi ya *Buhari* ya aiki yasu mama?...yace alhamdulillahi tana lafiya tace" nagaida ke, ina amsawa yakuma gurin mom?...itama tana nan lafiya lau da auny *Bebe* dasu Jiddo ko dayake aisu suna nan abuja ko?..."eh duk suna nan kalau, sai kuma tayi shuru tareda sun kuyar dakai kasa tana wasa da yatsun hannunta cike da jin nauyinsa kana cewar ko dama chan tanajin nauyinsa.    "Cikin murmushi yace sis dafatan anyi mana afuwa akan abinda yafaru?...,cikin murmushi tace lah! yah *Buhari* wlh komai yawuce, yauwa to muna godiya me yawa saidai ya'akai ne kin tambayi "kowa amma baki tambayi yah *Bilal* friend dinki ba, meyasa ko kina fushi dashi ne saboda bai zoba eye?... cikin dariya tace a ah yah *Buhari* bana fushi "dashi tunda abaiyi mun komai ba, sannan kuma kilan akwai abinda yahanashi zuwa ne dan haka nayi masa uzuci shima cikin dariya yace haka ne to ai banji kince ina "yake bane", cikin d'an jin kunya tace umh umh! dama inason na tambayeka sai kuma.... yace sai kuma baki tambaya ba ko?...nan yafad'a mata kamar yanda yafad'ama su" *Ammu* wato dai wani uzurin ne yahanashi zuwan.      Cikin sanyi murya tace Allah yadawo dashi lafiya yace ameen, sun d'an ta'ba fira sannan yawuce inda abin mamaki yabar *Baffa boy* yana kuka wai zaya bishi. ******** *Bulama* kam tin kafin ya'isa gida yad'ora hotuna dayai da *Baffa boy* a status, aikam *Blue* ne first din wanda yafara kallon cike da mamakin yanda yaron yai mugun kama dashi, Infact masai kace shine lokacin yana yaro tsintar kansa yayi dasakin murmushi tareda furta yes! this is the *Blue* Junior, ahankali yaketa kallon hoton tareda yin zumin dinsa yana sake kallo sosai, take yaji wani irin mugun kaunar yaron yashiga cikin ransa yai kane-kane fiyeda tunanin me karatu. d'aga chan *Bulama* yarubuto masa cewa malam meye nakallon mun status eye?..bai bashi amsaba sai yadauka daga whatsapp din bayan yacire hotuna. *Bayan sati daya* ******** Sosai *Ammu* ta gyara 'yarta ciki da waje indako tayi wani irin kyau me ban sha'awa, sai walkiya take kamar kwalba yayinda jikinta yake santsi kamar tarwad'a. Yaune *Beenazar* zata koma d'akinta kamar yanda aka fad'a, inda tuni angama gyara mata d'akin kasan cewar anan abujan zata zauna saboda karatunta, duk dacewa akwai komai amma hakan bai hana anzo mata danata kayan d'akin ba, wanda *Abbu* baiyi mataba awancan lokacin saboda rashin hali dan haka yanzu yasa akayo mata odansu daga Dubai, had'eda kayan kitchen masu kyau da tsada. "Inda su Umma dawasu kawayenta sukaje suka gyara mata d'akinta tsaf, misalin karfe takwas darabi nadare *Bulama* dawasu abokansu sukaje daukota, kasan cewar har zuwa wannan lokacin *Blue* baije ba inda kuma yatabbatarma da *Bulaman* cewa bafa zayaje dinba, dan haka cike da bacin rai ya kyalesa saidai kawai yanata cewasu *Beena* aiyuka ne sukai masa yawa. "Kamar yanzuma dasukaje umma tace ina angon newai?...cikin murmushi yace umma adai sakeyima angon nan hakuri wlh yau dinnan tafiyar gaggawa ta kamashi zuwa Dubai, amma insha'allah jibi zayadawo tace to shikenan Allah yadawo dashi lafiya yace ameen, nan suka daukesu *Beenazar* *Basma* *Bana* *Banu* hardasu *Bassam* da *Bash* duk *Abbu* yace suje su rakata, tareda wasu kawayensu Umma kusan dai takwas suka rakata d'akinta. "Sosai su Umma da kawayanta sukai mata nasiha me shiga jiki, aikam tanata kuka sannan suka  tafi inda su *Banu* suma sunata kukan rabuwa da yar'uwarsu me kaunarsu, inda sukarta itada *Basma tana lallashita. Anan waje kuwa *Blue* ne shida *Bulama* suketa kwasan fad'a, akan yace yatashi suje yarakashi gurin *Beenazar* din, amma ya'ke'kesa kasa yace bazaya je ko'ina ba wlh yace kada Allah yasa yaje din, dan haka rai bace yanufi part din.  "Bakinsa dauke da sallama yashiga *Basma* ta amasa wacce *Bulama* yana ganinta yajin dukkan bacin ransa yagushe, kasan cewar tin ranan dayaje gidansu yaganta yaji takwanta masa arai, dan haka batareda bata lokaci ba tuni yagabatar dakamshi gurinta inda akai sa'a itama yakwanta mata arai dan haka tuni suka fara soyayyar su. Fuska dauke da annuri tace sannun dazuwa, cikin murmushi yace yauwa my dear ke kad'ai aka bari?...tace "eh Allah sarki ina my Boy, tace gashi chan yai barci nan dai yasake yima *Beenazar* nasiha akan tayi hakuri, sannan yace da *Basma* my dear tashi muje nakaiki gida, tace to tareda yima *Beenazar* din sallama tana me cewa sai tadawo gobe tace to tareda rakasu, bayan tadawo sannan tadauki ledar da *Bulaman* yashigo dashi taduba inda taga kaza da fresh milk me sanyi kitchen tashiga tadauko flet tazuba taci tasha milk, takoshi sannan taje tayi wanka tai brush tazo tasa kayan barci har zata kwanta kenan, sai taji karan sako yashigo cikin wayarta dake kan tabur d'auka tayi tabude tareda fara karantawa, atsaye kamar haka..... _SLM barka da zuwa matar *MAJNUN* fatan kindawo gidan *majnunin naki* lafiya?...saidai kuma kashhhh! kinyi rashin sa'a yanzu babushi *majnun* din naki agidan, domin kuwa yazama tarihi so kisani yanzu wannan  gidan na *Bilal Lawai Usman*, ne shi da "sarauniyar mafarkinsa dan haka kisa aranki bagidan zamanki bane aro akabaki, nadan wani lokaci domin kuwa me gidan tana nan tafe, wacce Ita ce abar kaunarsa dazaran "tabayyana zaki barmata gidanta ne" dan haka ki rubuta ki ajiye wannan sakone, daga mutumin dabaya ra'ayinki balle yaso zama dake wato shine *Bilal Lawan Usman* (Blue*)_. Tana gama karantawa tazube kasa ragwajab cike da tashin hankalin, yayinda zuciyata yashiga wani irin bugawa cikin tsananin tsoro tafurta innalillahi'wa'inna'ilaihirraju'un ni *Balkisu* meyake shirin faruwa dani?....,yah ilahi mutumin da zuciyata tamato akan kaunarsa ashema baisan inayiba wato ma shi watacan yakeso baniba, wayyo Allah na sai kuma tafashe da kuka me cike da tausayin kanta sosai take kuka taname rokon Allah karyasa tazamo meyin san maso wani, sai da taci kukanta sannan tamike ahankali alokacin karfe shabiyu harda rabi, toilet tashiga ta wanke fuska tafito dai-dai lokacin da *Blue* yashigo atunaninsa tayi barci dan haka ahankali yanufi d'akinsa domin ko kad'an bayaso yaganta. "Jin motsisane yasa tayi sauri taleka ta window, saboda itakam so take taganshi domin tayi kyawarsa tsawon lokaci, aikam tayi sa'ar ganshi cikin kyakkawar shiga takamala ahankali yake takowa, sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda sky blue da akaima dinkin zamani wacce tayi matukar yimasa kyau ajikinsa, sosai *Beenazar* take kallonsa cike da sha'awa, inda taga yakarayi mata girma tareda wani irin kyau naban mamaki, sannan gawani irin kwarjini dataga yakarayi mata fiyeda lokacin da yake cikin halin hauka. Wani irin so da kaunarsa ne taji suna sake bin Jini da bargonta, ahankali ta lumshe ido dai-dai lokacin dayawuce gurin window, taname shakar daddad'an kamshin turaransa datayi bala'in kewarsa tsawan wani lokaci, sai kuma wasu sababbin hawaye suka zubo mata saka makon jidatayi wata zuciyarta tace da'ita ke! *Beenazar* raba kanki da wahala domin yanzu yah *Bilal* yafi karfinki, dan haka ki zauna dashirin barmasa gidansa shida sarauniyar zuciyarsa kamar yanda yace" maki. hakan yasa taja kafa ahankali tanufi bed takwanta tareda jan *Baffa boy* ta rungumeshi kam ajikinta tamkar wani zaya kwace mata shi, yayinda takejin kaunar yaron da ubansa acikin rai fiyeda tunanin me karatu, ahaka dai sarkin barayin duk duniya yadauketa wato barci. ******* "Aban garan auny *Bebe* kam komai yasake kwa'be mata musamman yau, da *Dad* yakirata yafad'a mata komai game da *Beenazar* din kasan cewar sam yamanta bai gaya mataba, sai yaudin inda yake fad'a mata aima *Beenazar* din tana nan tadawo, inda azahiri tanuna farincikita akan hakan, har tana cewa Allah sarki ashe cikin *Bil boy* ne?.., yace "eh wlh kedai yaron ku yana nan kamar kaninki yai kaki, cike da farinciki tace Allah sarki yayinda achan kasan zuciyarta kuma wani irin bakin ciki taji yakamata, nan dai suka ta'ba fira har yana fada mata cewa sun shirya da mom din *Boy* harma ansake daura aure jiya dan haka itama zata dawo jibi idan Allah ya yarda, tace kai masha'allah *Dad* ka kyauta dama inata ce maka kamaida ita tunda dai auran ku bai kare ba, cikin murmushi yace aikana shima *Boy* yaketa damuna to agashi nan yauna maida itan, bayan sun d'an yi magana sannan sukayi sallama akan cewa sai tazo goben ganin *Beenazar* yace to sai tazo. Bayan sun gama wayar ciki tsananin bakin ciki da hassada da kyashi, tace kan uba yanzu saida "yarinyar nan tadawo cikin rayiwar wannan d'an iskan yaro, watoma tahaifi cikin nan danaso yazama shege sannan kuma d'a namiji, shikenan tawa kare duk dukiyar *dad* zata sake zama tashi da uwarsa kenan ko?...tuda gashi uwar tashi zata dawo?.... tabdijam ina bazata sa'buba wlh wai bundiga aruwa, yaudin nan sainaga bayan shegen yaron na shida "uwarsa da wannan matar tasa da idan naganta . "Da sauri tamike tadauki tukunyar tsafinta tanufi toilet, saida takunna fanfo kamar yanda tasaba sannan tafito tukunyar tafara gudanar da tsafinta, nan tukunyar tafara rawa kafin duk tayi wani yin kuri tuni tukunyar tafad'o tadaga hannunta ta tarwatse. "Wani irin kara tasaki cike da tsoro takoma gefe, tana zana zaro ido cikin mugun tsoro take kallon tukunyar jikinta sai kerma yake, inda tana gani wani din kulallan bakin hayaki yafito acikin tukunyar yafita tawundo kai tsaye hayakin nan, yanufi falo, su Jiddo suna kallon t.v aikam hayakin nan yashige jikinta take tasaki wani irin mugun kara tareda zubewa kasa sume... Gani hakan yasa suka saka ihu tareda kiran momi wanda jin ihun nasu dakiran sunanta ne, yasata fitowa daga toilet din dasauri abinda tagani ne yai mugun d'aga mata hankali, cikin rawar jiki tanufi gurinsu tareda d'agota tana fad'in nashiga uku meyasa meta?...,cikin kuka sukace basu saniba sunadai cikin kallo sukaga tasaki kara tareda zubewa asume. "Da sauri tace subata ruwa, koda suka bata tazuba mata afuska sai gashi tafarka tana yamutsa fuska chan kuma sai tamike tayi zaune tana wasu harare harare, sai kuma tamike tana tsaki tashiga daki batareda tace dasu komai ba cike da mamaki suka bita da kallonta, itakam aunty *Bebe* wani iri tsorone yakama ahankali tamike tashige daki zuciyata yana mugun bugawa. ******* Washa gari ko kafin *Beenazar* ta tashi tuni *Blue* yarigata kasan cewar ranan lahadi ne, babu zuwa aiki dan haka yana idar da sallar asuba yatafi motsa jiki, shiyasa koda tafarka bata ganshi sallarta tayi tareda d'an ta'ba karatun al'qur'ani, sannan tamike  dai-dai lokacin da*Baffa boy* yatashi dan haka tad'aukeshi taje tayi masa wanka itama tayi, sannan tashirya ciki riga da zani na atamfar english shima tashiryasa cikin kananan kaya riga da wando, sannan ta goyashi tashiga kitchen tadora karin kumallo, inda cikin kankanin lokaci tagama inda taje tad'ora akan dinning table. sannan tad'auki *Baffa boy* tareda daukan kolar abincin *Dad* tanufi part dinsu dan takai masa alokacin karfe goma shad'aya nasafe. "Bakinta dauke da sallama tashiga falon inda ta iske *Dad* zaune yana Kallon t-v, fuska dauke da annuri ya amsa mata sallamar tareda fad'in *Balkisu* ne?...tace "eh *Dad* sannun dahutawa yauwa *Balkisu*, tana me nufar dinning table tadora kulan. Sannan tanufi gurin *Dad* tana cewa ina kwana *Dad*?...lafiya lau *Balkisu* fatan kun tashi lafiya keda babana?....eh *Dad* alhamdulillahi, ga breakfast chan nakawo maka yace madallah sannun da kokari. To yabakunta?...ko dayake nan din gidanki ne so dan haka ba bakuwa bace ke, ko?... yakarasa fadi yana dariya, cikin murmushi ta gyad'a tareda mikashi *Baffa boy* cike da farinciki ya karbeshi yana fad'in Babana zo mugaisa. "Nan yafara masa wasa shikuma yana dariya, can sai yakalleta yace ina "mijinki ne wai ni tunda muka gaisa dashi amasallaci, kuma ban sake ganinsa ba har yanzu, ko har yanzu yana chan yana barci ne tunda yau lahadi, kallonsa tayi inda taji gabanta yafadi domin batasan amsar da zata bashi ba, har zatayi magana sai kuma yace "Ok natuna duk ranan yau yana zuwa gurin motsa jiki, sai yadawo ne sannan yakoma barci amma nasan yana nan yanzuwa yanzu, tunda shad'aya tayi. kai ta gyad'a alamar eh tana me sauke ajiyar zuciya. "Sannan tamike tana cewa *Dad* kaje ka karya kumallo, yace to *Balkisu* muje kizuba mun tace to *Dad* tana cikin zuba mashi ne, kamshi turaran *Blue* farayin sallama kafin duk yashigo, bakinsa dauke da sallama yashiga dukkansu suka amsa saidai *Dad* abayyane ya amsa, sa'banin itada ta amsa acikin rai tanajin faduwar gaba. "Sanye yakeda riga t-shirt brown color me hoton zuciya agaban rigar wacce akai da white color, sai yasa wandon jeans dark blue kafarsa sanye cikin takalmi boot fari brown ta gefe-gefe, kai gaskiya shirin yaimasa kyau sosai kashin kansa sai kwalkiya yake, hannusa dake daure da kyakkawan agogo dashi yake rikeda wayoyinsa kamshin daddad'an turaransa kuwa gaba daya yacika falon. Cikin nutsuwar da kamala yaja kujera yazauna yana fad'in *Dad* barka da hutawa, batareda yakalli inda *Beenazar* take tsaye ba yazuba wayoyinsa akan table din, dai-dai lokacin da *Dad* ya amsa da yauwa barka kadai *Boy* katashi "eh *Dad* amma yakamata yanzu kadaina kirana *Boy*, cikin murmushi yace gaskiya ne kuma fa tunda yanzu kai baban *Boy* ne gashinan yanata famanyi mun kiriniya.      Cikin murmushi yace "eh mana shidin big boy ne like he father ko?..yana kallon *Baffa boy* din tareda mi'ka mashi hannu, yace good morning my sweet darling boy how are u?... cikin dariya *Baffa boy* yakai hannunsa cikin na *Blue* yana bugawa tatata, dai-dai lokacin *Blue* yace *Dad* nifa yinwa nakeji, yinwa kuma son?.... yes *Dad* ban karyaba, ok to aiga breakfast nan da ma....dai-dai lokacin da *Beenazar* tace da *Blue* yah *Bilal* ina kwana.....da sauri yad'ago yakalle aikam yamike zumbur cikin bugawar zuciya, yake kallonta tareda nunata da yatsaya cikin rawar murya yace Ita ce! ita ce!! wlh *Dad* Ita ce!!!!, cike da mamaki *Dad* yamike yana kallonshi, sai kuma yamaida kallonsa ga *Beenazar* wacce itama kallon *Blue* takeyi ciki bugawar zuciya had'eda mugun tsoro, yayinda shima kuma sai kallonta yakeyi yana cigaba da fadin Ita ce!  *Dad* tabbas wannan ce, yace a ah! Son wai me kake nufine da Ita ce eye?... murmushi yai me kayatarwa tareda sake cewa wlh *Dad* Ita ce aidama nafad'a maku zata bayyana. Shuru *Dad* yai aransa kuma yake fadin badai Son bai taba ganin *Balkisu* ba sai yau?...,take zuciyarsa tace tabbas lallai kuwa biri yai kama da mutum tunda ga alama nan kagani, kenan son *Buhari* ne keta zuwa gidan batareda shiba?...take yaba kanshi amsa da "eh mana tunda gashi nan yanuna bai santaba, tunda gashi nan sai fadin yake Ita ce! ita!! ce to Ita ce!!! wa?... wato yaron nan duk irin hakurin dana bashi baiyi ba kenan ko?...take yaji ransa yabaci, hakan yasa yakallesa dai-dai lokacin da yake matsawa gurinta fuska dauke da matsananci annuri, yana fadin ninasan zaki bayyana kamar yanda kikai mun alkawari gashi kuma yau kin tabbatar mun da hakana ko?....itakam *Beenazar* batagane inda zancanshi yadosa ba, dan haka cike da tsoro yajuya tafita da gudu daga falon. "Da sauri yace no my queen don't go yana me kokarin bin bayanta, inda *Dad* yai saurin tsayarda shi ta hanyar cewa son tsaya mana, cikin rawar murya dana jikin yace *Dad* karta "tafi fa kuma na fad'a maka Ita ce, fuska had'e yace "eh son nasani Ita ce" *Balkisu* matar d'an abokina" dayake kano "mijinta ne yakawota ta gaidani kasan cewar ban samu zuwa auran suba, cikin tsoro had'e da bugawar zuciya yace *Dad* me kace?....cikin sake had'e fuska yace..... Muje zuwa ~_Insha'allah wannan ne second to the last page_~ *MEENAL or LUFHAT CE* _Allah yakasa mu ciki da imani ameen ya hayyu ya kayyu mu_ 🎍🎍🎍🎍      🎍🎍🎍           🎍🎍                🎍 🎍 *ZAUNJUN MAJNUN* 🎍 (Miji mahaukaci) *BOOK 2* 4️⃣1️⃣to4️⃣5️⃣ 🔚 🎍 🎍🎍 🎍🎍🎍 🎍🎍🎍🎍 WRITTEN BY 🎍 *AMINA UMAR FARUQ* 🎍   _Kwantagora_ OR 🎍 *MEENAL*🎍          _KNT_ Marubuciyacer *DA SANNU* *ZUCIYATA CE* *AFSANA* *KYAUTAR ALLAH CE* *HASKE BAYAN DUHU* *ZAUNJUN MAJNUN part 1* *TAWAKKALI* *TASEERI* and now *ZAUNJUN MAJNUN part 2* _SADAUKAWAR GA_ Iyayena abin alfarina ina godiya bisaga tarbiyyar dakukai mu, dan haka ina rokon Allah yasaka maku  da alkairi yakareku daga sharrin mutum da aljani, ubangiji yasa kugama da duniya lfy ameen ya rabbi. Wannan littafin na kudi ne akan farashi me sauki, 300 naira only zaku iya turo kudin tawannan account no 0047769671 Amina Abdullahi A., Idan kuma katine sai ku tuntubi wannan lambar 08161850024, sai naji ku. ✍🏼 _Bismillahirramanirraheem!_ """"""""Son kenan abinda kunnuwanka sukaji shine fad'a, cike da mugun tsoro had'eda tsantsan bugawar zuciya, yake Kallon *Dad* kafin da karfi yafur a ah! *Dad* wannan "Ita ce nake fad'a maka ta cikin mafarkina, wacce kullum sai nayi mafarkinta *Dad* wlh ko barcin yau saida nayi mafarkinta, tazo mun cikin kyakkawan shiga kamar yanda take zuwamun ako dayaushe, *Dad* saboda yawan mafarkinta" dana keyi yasa tuni ta rikid'a takoma sarauniyar zuciyarta. *Dad* i swear to god ina kaunarta" fiyeda tunaninka kuma "itama tana kaunata sosai, kullum sai tafad'a mun  mafarkinna, kuma sai ta tabbatar mun cewa zata bayyana agareni yanzu kuma ta bayyana agarenin sai acewa wai "matar wanice", a ah *Dad* hakan bazata ta'ba yiwuwa ba domin wannan din "matatace insha'allah, yakarashe fad'i tareda kwasan wayoyinsa dayazube akan table jikinsa yana wani irin rawa yafita da sauri. *Dad* yana kiransa amma bai juyoba, asalima cewa yace *Dad* zan bitane karta 'bace mun so let me come back.     "Da sauri *Dad* yadauki wayarsa yakira *Bulama* bugu d'aya yadauka, cikin sauri yace my son inason kafad'amun gaskiya shin baku  ta'ba zuwa gidansu *Balkisu* tareda son bane ko?...,take yace yes *Dad*domin nayi-nayi dashi akan muje ya'ki zuwa asalima ce mun yai "shi baya ra'ayinta, infact baya kaunarta" shi wannan tacikin mafarkin nasa yakeso, cike da mamaki yace son idan na fahimceka kenan bai "ta'ba ganinta" bako?..., *Dad* to yaza'a yaganta tunda baije inda "takeba ko jiya nayi-nayi dashi akan muje narakashi amma yace" baza yajeba, shiyasa na kyalesa kuma ajiyan bashi yashiga gidaba sai da yabari dare yayi sosai alokaci tuni nasan tagaji da jirasa tayi barci, kuma natabbatar ban garensa zaya shiga batareda yashiga nata garanta ba, tunda yafad'amun harda ganinta baya ra'ayint sannan yauma nasan tin kafin tafarka daga barci yafita, dan haka tabbatar be gantaba balle yasan yanda take.        "Ciki da gamsuwa *Dad* yace son naga alamar hakan, domin yanzun wani abu yafaru da yabani mamaki, nan take yafa'da mashi duk yanda akai cike shima da mamakin yace *Dad* haba?...wlh kuwa son, kaga kenan ,"Ita ce tamafarkinsa cikin wani irin matsananci farin ciki yace tabbas kuwa *Dad* Ita ce, Allah sarki *Beenazar* batada hakkinsa" ne sannan kuma tsakaninta" da Allah take kaunarsa shiyasa, Allah sata cikin mafarkinsa tsawon lokacin tareda jarabtarshi da kaunarta me tsanani, domin wlh *Dad* ni shaidane akan irin kaunar dayake yimata yace kwarai kuwa son nima na shaida, kuma naji dad'in hakan domin yarinyar nan tayi mana halacci sosai mune dai mukai mata butulci amma komai yawuce.   Haka ne to *Dad* yanzu meye abinyi?...yace abinyi shine wani abu zamu shrya yanzu kana ina?...,yace *Dad* gani nan acikin gida ina part dinsa" nakawo *Basma*, saidai kuma bamu iske kowa ba daga sis *Beenazar* din har my _guy_ har zamu fito  amma kuma sai ga *Beenazar* din tashigo da gudu kamar atsorace take, gata chanma suna magaba da *Basman* lafiya dai ko?...      Cikin murmushi yace lafiya lau saidai mutumin nakane yafirgita" da maganarsa wanda tarasa inda yadosa, shima murmushi yai yace auhaka ne?...yace "eh to *Dad* me  zamu shirya ne?....yace yauwa shirin da zamuyi shine, da farko dai naji dad'in zuwan *Basman* ai naji ance sun shaku da babana ko?....sosai makuwa *Dad*, yauwa to zo ga baban nawa nan sun barmun shi zoka karbeshi kakai shi gurin Ita *Basman*, sai kafad'ama su komai kaga sai  kace tayi art like Ita ce *Beenazar* din, Ita kuma *Beenazar* din tayi art like matar "d'an abokina danace, kadai gane abinda nake nufin ko?...     yace yes *Dad* nagane yauwa inason muyi haka na tsawon kwana biyu, wanda hakan shine hukunci da zanyima "son tunda baiji maganata ba, kuma ayanda naga kaunarta" acikin kwayar idonsa na tabbatar kafin kwana biyun nan yagalabaita, gud *Dad* shirinka yayi kyau yanzu ka kira *Abba* kace" kanaso *Basma* zata taya *Beenazar* kwana kafin mijinta yadawo, tayanda shirin namu zayai tafi dai-dai yanda muka tsara ko?... tabbas hakan zakayi, yauwa yanzu to kazo ka karbi yaronku gashi nan yanata famanyi mun 'kiriniya, cikin dariya yace to *Dad* gani nan zuwa yakashe wayar. Sannan yanufi karamin falon dan yafad'a masu, kasan cewar shiyafito babban falon ne dan ya amsa wayar *Dad*, inda ya'iske *Beenazar* din tana kuka yayinda *Basma* keta faman lallashinta kasan cewar ta fad'amata duk abinda  yafaru tundaga kan test din da *Blue* yaimata har yanzu, da taganshi yaganta yanacewa wai Ita ce" to Ita bata gane meyake nufi da ita ce ba. Inda tacigaba da maganarta dacewa sis *Basma* yau danaga "yah *Bilal* naji kaunarsa tasake ninku acikin raina fiyeda koda yaushe, fatana shima yakaunace ni kamar yanda yakaunace ni achan baya koda yake wance baya cikin hayyacinsa, yanzu kuma yana cikin hayyacinsa  hakan yasa naji ajikina kamar hakan bazaya samuba, saboda asakonsa dayaturo mun jiya yatabbatar mun "watace acikin zuciyarsa baniba. Sis *Basma* inason yah *Bilal* bana fatan narasashi domin shine mahadin rayuwata, wanda rasahinsa tamkar rasa numfashina ne.....da sauri *Bulama*  yace daina fadin hakan sis *Beenazar*, kallonsa tayi da idanunta dake zubarda hawaye cikin sanyi murya tace "yah *Buhari* to idan bance haka ba me zance?....cikin murmushi yace sai kice alhamdulillahi domin kuwa bakowa bace wacce ke cikin ransa face "ke! *Balkisu Beenazar*, cike da mamaki tace yah *Buhari* kamar yafa ban gane nice acikin ransaba?..... Nan take yafa'da mata duk abinda ke faruwa, tin daga ranan da yawarke yake mafarkinta har zuwa yau da yaganta shine dalilin dayasa yace Ita ce wato Ita ce tacikin mafarkinnasa, cike da matsananci farin ciki tamike takalli alkibila tayi sujudu-shukuriyya nagodiya ga ubangijinmu, dayasa batada rabon wahalar son maso wani sannan tamike fuska dauke da annuri tace yah *Buhari* da gaske?...cikin dariya yace sis *Beena* aikinsan bazayin maki karyaba, kinga shiyasama *Dad* yace ga abinda zamuyi nan yafad'a masu cikin murmushi *Basma* tace eye lallai sis kinsamu shiga wato, harda *Dad* za ahad'a baki abawa yah *Bilal* din wahala?... "eh mana dear aimaganisa kenan my _guy_  yacika taurin kai, tace to aishikena yauwa bari naje nakarbo *Baffa boy* *Basma* tace ok har yajuya sai *Beenazar* tayi saurin cewa *yah Buhari*, amma dai baza'a dad'eba anayi masa" hakan bako?...,cikin murmushi  *Basma* tace to me imani soso miji sai ankai wata anayi hakan ko my dear?....cikin zolaya yace kwarai kuwa my dear wata biyarma zamuyi, cikin zaro ido tace no pls *yah Buhari* I can do that u know I miss him so very much, dan haka ayimasa afuwa, cikin dariya yace to za ayi tareda kokarin fita dai-dai lokacin da wayarsa take kara. *********** *Blue* kam koda yafita baiga  *Beenazar* ba saidai yatabbata tana part dinsu", kuma shi bazaya shiga part dinnan ba tunda yasan wannan "yarinyar tana nan ciki shikuma ko kad'an bayaso yaganta", dan haka yai tsaye jikinsa yana rawa inda yafara tunanin abinda zayai.        Chan yafurta my _guy_ dan haka cikin rawar jiki dana hannu yafara laluban lambar *Bulama*,  saidai yana kira yaji busy kasan cewar alokacin yanata waya da *Dad* tsawon lokacin yana kira still busy, hakan yasa yaketa faman doka tsaki chan dai yai sa'a yasamu tashiga yadauka.     "Ajiyar zuciya yasauke tareda fad'i shin wai dawa kaketa wayane haka tin d'azu busy busy eye?..., Cikin masifar jin haushinsa yace ban saniba malam ina ruwanka da wanda nake waya eye?...,cikin sanyi murya yace a ah! my _guy_ fad'ane kuma, ko dai har yanzu fushi kakeyi dani?...cikin sauri yace "eh _guy_ indai bazaka kula "yarinyar nan *Beenazar* ba kodan halaccin datai maka arayuwa", to dani dakai mun dinga fad'a kenan kuma bazan daina fushi dakai ba, har saika yarda da'ita amatsayin matark..... "Da sauri ya katseshi dacewa stop _guy_ kaga ni ba wannan maganar nakiraka muyiba, cike da mamaki yace au! Allah ko?....kai tsaye yace "eh yace ok to inajinka maganar me kakirani muyi eye?...yakarashe fad'i cike da jin haushinsa aransa yana fadin kenan har yanzu yananan akan bakansa nakin *Beenazar* din ko?...bari aizaya gane kuransa. Yayinda *Blue* yakatse mashin zance zucinsa ta hanyar fadin yanzu kana ina ne?...., fuska hade yace kaidai kafadi abinda zaka fad'a inajinka, fuska dauke da tsanani annuri yace kai my _guy_ yau my dream queen tabayyana fuska had'e yace au! haba?...cike da zumud'i yace Allah kuwa, hum! to naji yanzu "tana ina kuma me kakeso nayi maka  agame da'ita" eye?....yauwa my _guy_ shiyasa nake kaunarka, humm! inajinka.      "Yauwa tana nan gidan kuma tana part dina, saidai gaskiya bazan iya shiga cikin ba saboda banason ganin wannan yarinyar....ok to yayi kyau to aigani apart dinka nazo ban ganka ba, ah! haba dai "eh ok to fito ganinan yace ok. "Da sauri yasake cewa yauwa kafin nan bakaga wata black beauty tashiga ba?...,yace uhmm! naganta mana "matar d'an abokin *Dad* ce tun jiya da yamma sukazo lokacin kafita, tazo gaida *Dad* ne, najima yace sati daya zatayi saboda mijin nata yayi tafiya, da sauri yace what! wai da gaske ne ashe abinda *Dad* yafad'a?....yace Oh! baka yarda ba kena?....pls nidai kafito gani nan ina jiraka muyi magana ok yakashe wayar yana sakin murmushin zolaya.. Tsaye ya iske *Blue* sai safa da marwa yakeyi, cikin d'an tashin hankali yana ganinsa yanufe shi yana cewa pls my _guy_wai Ita dince matar d'an abokina*Dad*?...eh mana, cike da bugawar zuciya yatura hannun cikin lallausan suman kanshi yace gaskiya akwai matsala?...cikin dan mamaki yace matsala kamar yafa?...,yace saboda "ita ce my dream queen din danake fad'a maku" da sauri, *Bulama* yace me?...tare da d'an zaro ido alamar tsoro. Yace wlh kuwa kuma gaskiya saidai ayi wacce za'a domin nidai wlh ina kaunarta" fiyeda tunaninka, dan haka dole "yasaketa na aura saboda wlh bazan iya hakuri da Ita ba....."Baki da hanci yasaki yana kallonsa kafin yafurta, shin _guy_ kasan me kake fad'a kuwa?...fuska had'e yace nasani mana, yace ok to Allah dai yataimake mu ba rashin lafiyarka bane yadawo. Cike da masifa yace malam kamar yafa meka kenufi eye?... fuska had'e yace ina nufin indai baka sake dawo majnuniba, domin sai mahaukacine kawai zayayi abinda kake kokarinyi yanzu wato yace" asaki mata ya aura ina kata'ba ganin anyi haka eye?...cikin 'kufuluwa yace malam niba mahaukaci bane da hankalina kuma wlh tunda ina sonta" dolene "yasaketa na aura kagane ko?...yace tabd'ijam eh lallai nagane sosai makuwa saidai yaro kasani kana ruwa tsubul kuma kusada, so kaga tafiyata nan domin naga kamar bakada aikin yi nikam dai inada abinyi yawuceshi yanufi part din *Dad* yana dariya kasa-kasa,   Cike da mamaki *Blue* wai asaki mata ya aura humm! wannan ma bayada hankali ko awani garin akeyin haka oho, Allah sarki sis *Beena* Allah ba azzalumin bawa bane saidai wanda yazalunci kansa, yau dai ga yah *Bilal* dinki Allah yakama makishi yana kokarin zama *MAJNUN* akan so da kaunarki koma nace yazama, yakarasa  fad'i da kyalkyalacewa da dariya dai-dai lokacin da yashiga falon *Dad* inda ya'iske yanata yima *Baffa boy* wasa suna dariya. ******* "Nan yafad'a mashi yanda sukai da *Blue* din aiko nan sukai tayi mashi dariya, sai gashi yashiga fuska had'e inda sukuma suka gintse dariyar tasu, *Bulama* yakarbi *Baffa boy* yada fadin *Dad* kawoshi nakaishi gurin mom dinsa, yafita yanai masa wasa ta hanyar challasa sama yana cha'bewa shikuma yanata dariya. Yayinda *Blue* yabisu da kallo gwanin sha'awa sosai yakejin so da kaunar yaron acikin ransa, amma yarasa meyasa zuciyarsa takasa aminta da mamansa tsaki yaja mtww, tareda zama yame kallon *Dad* wanda shima kallosa yake inda yahango tsantsan rigima kwance akan fuskarsa, murmushi yai yace son yadai?...ciki shagwa'ba me cike da tsabar rigima yace *Dad* I tell you "Ita ce kuma I really love her, kai ya girgiza tareda cewa son naji to yanzu me kakeso ayi tunda matar aure ce eye?. da sauri yamike ya'isa gurinshi tareda zubewa kasa yadafa guiwoyinsa yace yauwa *Dad*, ka kirasa kace yasaketa" sai ni na aureta ido *Dad* yazaro yace haba son ina kaga ana hakan eye?....fuska yahad'e, kafin yace to nidai afara akaina dan wlh nibazan iya hakura da'ita sonta ba, da dai *Dad* yaga alamar rigama yake nema sai kawai yace kaga son barci nakeji so bari nage na kwanta, yamike yanufi d'aki yabarshi nan zaune inda yabisa da kallo yayinda yakejin zuciyarsa tana wani irin bugawa me cike da tsoro da fargaba. *Bayan kwana biyu* ******* "Wasa wasa shirinsu *Dad* yana tafiya dai-dai yanda suka tsara, domin kuwa acikin kwana hudun nan duk yanda *Blue* din yaso ganin *Bilkisu* abin yacitura, hakan ne yasa harda wata yar rama yayi saboda damuwar rashin ganin nata gashi so da kaunarta had'eda wata irin zazzafar sha'awarta, sai sake ninkuwa yake azuciya da gangar jikinsa yayinda bayada aiki sai natasa *Dad* agaba dafad'in, dan Allah yasa d'an abokin nan nasa yasaki *Beena* shikuma ya aureta". Saidai yai murmushi yace son kenan nibazan ta'ba iyacewa da d'an abokina yasaki matarsa ka auraba, alhalin suna ganin mutumcina ai ba'ayin haka domin yin hakan haram ne acikin addini, kuma kasan da hakan son amma meyasa kake kokarin take sani eye?...saidai kawai yaturo baki cike da yace *Dad* nidai kawai inasonta. Maganar zuwa  gurin aiki kuwa tuni ya maida shi gefe domin kuwa yadaina zuwa, saboda gaba daya yamaida hankalinsa gurin ganin ya mallaki *Beenazar* dan haka sai *Bulama* ne kawai yake zuwa. *"Dad* da *Mom* sunyi magana har sun gaji, kasan cewar tuni tadawo kuma tasan dashirin ta ko dayaushe yana zaune babban falon part dinsu ko zaya ganta amma ina, ko gilmawanta baya gani saidai *Basma* wacce tadage sai art take amatsayin *Beenazar*, tana tashige masa tareda kiransa yah *Bilal* kamar yanda *Beenazar* take kiransa tana kuma kokarinyi masa duk wani abu da mata takeyi ma miji, yayinda shikuma yaketa shareta had'eda daure mata fuska, agefe d'aya kuma sunata shana soyayyar su itada  *Bulama* wanda tuni har manya sun shiga ansaka ranan aure bayan sun gama jarabawa kasan cewar sun kusa fara jarabawar.   "Haka dai komai ya cigaba da tafiya yanda suka tsara har yau kwana hudu sosai, *Blue* yafad'a inda duk wanda yaganshi sai ya tausaya mashi kamar *Mom* sosai take tausaya masa dan haka tuni tafara rokon *Dad*, asassauta mashi hakanan wanda shikansa zuwa wannan lokacin tuni yafara tausayama tilon 'dan nashi, saidai kuma yana ganin har yanzu bai horuba tukun domin soyake  *Beenazar* tasake daraja da kuma kima a idonsa tayanda bazaya iya rabuwa da'ita ba, hakanan itama *Beenazar* din harda kuka takeyima *Basma* tareda cewa idan dai saboda Ita ake bashi wannan wahalar to ta hakura tayafe mashi, yayinda itakuma sai tayi dariya tace to ai *Dad* baice" masu sudaina ba, dan haka suka cigaba da gudanar da aikinsu. ******** "Aban garen aunty *Bebe* kuwa cikeda tsoro tabi Jiddo da kallo har tashige daki, yan mintuna kad'an sai gata tafito sanye da riga body hug da wandon crazy wanda yasa dukkan surar jikinta fitowa, musamman kirjinta tayafa gyale d'an karami akai tana rataye dajaka, yayinda kafarta sanye dawani high hil kallo d'aya zakaimata kagane babu tarbiyya atareda ita sai taunan cingam takeyi 'karas-'aras. Kallonsu tayi sama dakasa batareda tace komai ba tasakai zata fita, da sauri aunty *Beben* da zuciyata yake aikin bugawa tace ke! Jiddo ina zakida wannan shirin haka eye?....,juyowa tayi dakarfi tareda buga mata wata uwar harara cikin tsawa tace ban saniba kuma baki isa ki hanani fitaba, sannan tasakai tafita inda tabar yan'uwanta sake da baki cike da mamakin wannan sauyi na yar'uwarsu, itakam aunty *Bebe* mutuwar zaune tayi inda ta cika da mugun firgicir. To tun daga wannan ranan sai komai yasake ta'bar'bare mata wanda saidai muce Allah yasawake, domin kuwa tun ranan da tukunyar tsafinta yafashe siddabarun dake ciki yakoma kan Jiddo, shikenan tun daga wannan ranan sai jiddon tazama wata irin tantiriyar fitsararriya ta hanyar bin maza tamkar wata karya, wayanda duk rabi samarin datake yima walakaci ne shine yanzu sunga tazama wata iri, shine suke kwansan suna rama abinda tayi masu ta hanyar yin lalata da ita, school kuwa tuni tadaina zuwa sai aikin yawon iskancin tareda shaye-shaye, yayinda kuma auny *Beben* bata iyai mata magana, asalima wani irin tsoronta takeji saboda tsawar datake buga mata dazaran tayi mata magana. ********* *Bayan kwana biyu* Ranan wata alhamis aunty *Bebe* ce zaune tabuga uban tagumi, duk talalace tafita hayyacita kasan cewar yau kimanin kwana uku kenan Jiddo  bata kwana agida duk inda take tunanin zata ganta bata gantanba, bata kuma san inda zata gantaba hakan yasake d'aga mata hankali kasan cewar duk wannan abun dake faruwa *Dad* jiddon bayana gari kimanin watansa uku kenan, yau yakirata yake saida mata yanan dawowa next week dan haka ciki masifar fad'an dayakeyi mata kwana biyun nan, wanda batasan abinda tayi masaba. Yace da'ita tace da "Jiddo tadawo yanason ganinta yayi kewarta, tunda shi baisan abinda yasamu wayarta ba, idan yakirata baya samunta kasan cewar tace masa tana chan takoma gidan kawarta dazama, cikin masifar fad'a yace to fad'a mata tadawo gidan ubanta idan bahaka ba ransu zaya baci itada Jiddon, sannan yakashe wayar. Hakan ne yasa suna gama wayar hankalinta atashe tanufi gidan kawarta, tafad'a mata duk halinda take cikin wanda daman tasan dasu saidai kari nan tabata labarin, cewa wani hatsabinbin boka yabayyana akasar Niger, batareda yin wani dogon tunani ba tace sutafi kasan cewar koce dama suna zuwa har can niger din neman asiri, dan haka  suka kwashe jiki suka tafi inda wani yaron kawarnata yajasu kasan cewar itama tuni tashanye mijinta, sai abinda tace kamar yanda itama aunty *Beben* ta yanshe nata mijin wanda yanzu yafara karyewa tunda harda tsawa yake mata. Kwana dayini sukai ahanya sannan suka isa sunyi sa'a sun iske bokan, wanda sukaima bayanin abinda yake tafedasu, cewar "yarta tabata tanason bokan ya taimaka yaimata abinda yarta zata dawo gida koda zasu koma su isketa agindan, sannan yakashe mata *Bilal* domin ta tsani ganinsa aduniya kilama shiyaima yarta asiri ta lalace. Aikam take yabuga kasa yace masu aljanu aka tura mata dan su lalata mata rayuwa, dan haka karsu damu koda zasu koma gida zasu isketa, sannan yabata maganin yace tazubawa *Blue* acikin abinci idan har yaci shikenan za'a nemeshi sama ko kasa arasashi adoron kasa, kuma yatafi kenan har abada bazaya dawo ba sosai sukai murna tabiyashi ma'kudan kudi sannan suka dawo, sunso sudawo aranan amma hakan bata samuba suka bari sai gobe.  ******* "Misalin karfe biyar na yammar ranan wata jumma'a da *Blue* bazaya ta'ba mantawa da'ita atarihin rayuwarsa ba, wacce kuma tayi yai dai_dai da kwana biyar kenan da suke gudanar da shirinsu, *Basmace* tafito cikin doguwar rigar shadda royal blue wacce tasha aikin duwatsu, anko sukai Ita da *Beenazar* har *Baffa boy* shima irin shaddan ne akasa mashi, sai suka yafa fararan gyale dasaka takalma farare shima *Baffa* takalmi farin suka saka mashi tareda hulla fara sai yaikamar dan larabawa, sunyi kyau sosai gwanin sha'awa kallo daya zakai masu kagane fita zasuyi. Har sun mike sai sukaji motsi ta babban falo hakan yasa *Basma* tanufi falon inda taga *Blue* yana kokarin fita, sanye yakeda wata dakkaken shadda brown color, wacce tayi masifar yimasa kyau ta hanyar fito masa farar fatarsa wacce take shaki da kwantaccan gashi luffff!, sai kamshi turare yakeyi tashi ajikinsa kashin babu hula sai cukurkud'an gashin kansa dayaketa walkiya. Cike da zolaya tanufi gurinsa da sauri fuska dauke da annuri, cak! yatsaya fuska murtik! cikin turanci tace hi my dear husband happy friday, woww! u are looking so good kayi masifar kyau gaskiya, to nifa yaka ganni nayi kyau?...taname juyawa, 'Dauke kansa yayi tareda kokarin bita gefenta zaya wuce da sauri tasha gabansa tareda d'an had'e fuska, tace wai nikam dai yah *Bilal* me nayi maka katsaneni ne eye?....cikin masifa hadeda tsawa yace malam saboda bana ra'ayinki ne wacce tazo gurinki Ita nake ra'ayin hope kingane ko?...,cike da nuna alamar mamaki tace yah *Bilal*  ni danake matarka baka ra'ayina sai ra'ayin matar aure Subhallahi! wannan wacce irin maganace haka?....cikin tsawa yace ban saniba kuma ko matar wanene ina sonta kuma sai nasameta, dan haka bani guri nawuce fashewa tayi da kukan karya tareda wucewa dagudu taje tafad'a ma *Beenazar* aikam suka shige daki suka ringa dariya kasa-kasa. Can say suka fito inda *Basma* takarbi *Baffa boy* ta rungume dai-dai lokacin da, wayarta tayi kara koda taduba suna my dear ne yabayyana cikin murmushi tadauka, tace amincin Allah yatabbata ga mijina insha'allah ok gamunan zuwa suka fita suna yar fira part dinsu" *Dad* suka nufa. ******** Bakinsu da sallama suka shiga falon wanda yake dauke da mutane, *Dad* da *Mom* *papa* maman *Bulama* da kuma *Blue* wanda shigarsa kenan suma suka shiga, da sauri *Blue* yatashi tsaye yana me Kallon *Beenazar* wacce tayi masa masifar kyau, cikin rawar jiki dana murya yace haba my queen meyasa kike guduna kinsan irin azabar danasha kuwa saboda rashin ganinki, yana kokarin isa gareta da saurin *Dad* yace son tsaya mana hakan yasa yatsaya cak! yayinda ita kuma kanta duke tanufi gurin *Mom* ta zauna tana dariya kasa-kasa zuciyata cike da kaunarshi tana me jin wani irin  farin cikin.         Yayinda duka falon ake kallonsu ana murmushi dai-dai lokacin da itama *Basma* ta zauna kusada *Beenazar* din, bayan tamikama mama *Baffa boy* shikam *Blue* da sauri yazube gaban *Dad* tareda kama hannunsa yarike, jikinsa yana rawa zuciyarsa kuma sai akin bugawa take, yace *Dad* gatanan tazo ita ce my queen kataimaka mun kace" kartasake guduna wlh ina kaunar banason narasata, *Dad* rasata dai-dai yake darasa numfashina kaji?... Kai yagyad'a tareda sakin murmushi sannan yace naji son yanzu ka nutsu ka saurari abinda zan fad'a maka kaji ko?..., kai ya gyad'a alamar to ya zauna ahankali tareda kurama *Beenazar* ido yanajin tamkar yaje yarungumeta yafad'a mata irin tsantsan kaunar dayake mata. Gyaran murya *Dad* yayi tareda Kallon *Bulama* yace son yimana addu'a, nan yayi bayan yagama sannan *Dad* yace *Beenazar* tazo inda tazo kusada shi ta zauna cike dajin kunya, hakan ne yasake ba *Blue* damar cigaba da kallonta yana sakin murmushi me kayatarwa. Cikin kwanciyar hankali *Dad* sannan yanuna *Beenazar* tareda fara bayani kamar haka son wannan din Ita ce *Balkisu* wacce ake kira *Beenazar*, da sauri yakalli *Dad* domin idan har baya mantaba sunan matar da'akace tashice, cikin murmushi yace "eh ita ce kuma matarka wacce na aura mata kana cikin halin rashin lafiya, Ita ce kuma naje nasake yimaka bikonta inda kace mun ka hakura zaka zauna da'ita to amma sai kakiyin haka, sai kuma akayi sa'a Ita dince dai wacce Allah yake nuna maka amafarki tareda jarabtarka da tsanani kaunarta, fahimtar hakan danayi yasa muka. Nan yafad'a mashi duk yanda suka tsara har zuwa yau, dan haka ga queen dinka nan wacce kuma takasance matarka kema dota ga mijinki nan, inafata zaku rike juna amana cikin sanyi murya me nuna alamar tausayin kanta tace *Dad* inada magana, to dota inajinki...fuska had'e tace *Dad* yace baya ra'ayina so nima bana ra'ayinshi kaga zama dani dashi bazaya yiwuba, dan haka yasallami. Wani uban zamura yai ya'isa gurinta tareda kama hannunta yarike, jikinsa da bakinsa suna yarawa yace kiyi hakuri kiyimun rai wlh bazan iya rabuwa dakeba ki gafarceni bisaga abinda nai maki, wanda nayishi abisa kuskure wato danace bana ra'ayinki bansan kece ba, aida ban fadi hakaba. Cikin had'e fuska tace sannan kuma to aikace baka kaunata so zaman mezanyi da wanda baya kaunata eye?,.. haba my queen taya zance bana kaunarki alhalin kece rayuwata wlh ina kaunarki da dukkan zuciyata fatana kimanta duk abinda yafaru, sannan ki kaunaceni kamar yanda kike fad'amun amafarkina dan Allah kinji?. Kai ta kawar d'aga barin kallonsa da  sauri yajuyo da fuskarta yana kallonta yace kin amince muyi zamanmu babu rabuwa har abada?...kai ta gyad'a alamar cike da kaunarshi aranta, yarungumeta batareda damuwa da mutanan dake falon ba, cike da tsanani farinciki yace nagode nagode sosai my *Queen* Allah yabarmu tare. Gwanin sha'awa kallon d'aya zakai masu kaga sunyi matukar dacewa dajuna sosai suka burge dukkan wanda yake cikin falon, hakan yasa *Bulama* tafa masu su *Dad* suka tafa masu suna dariya, yayinda shikuma sai aikin kiss fuskarta yakeyi cike da matsananciyar kaunarta har yana kokarin kiss din bakinta, batareda yasan zayai hakan ba da sauri takauda kanta tana murmushi cike da kunya, dai-dai lokacin da*Bulama* yace hey are a mad, halan kamanta inda kakene ko?...Harara yabanka ma *Bulaman* tareda cewa "eh ni mahaukaci ne but amma akan kaunar my queen ko?...yana me sake rungumeta, dariya akai gaba daya falon. Sannan *Papa* yace to alhamdulillahi! tunda komai yadai-dai fatanmu kurike junanku da gaskiya da amana, nan dai akaita yimasu nasiha me shiga jiki daga nan kuma aka fara fira inda acikin firar ake sanarda *Blue* zancen auran *Bulama* da *Basma*, sosai yai farincikin jin haka domin yai matukar yabawa da natsuwar *Basman* ahaka dai har aka kira sallar magrib su *Dad* suka tashi suka nufi masallaci inda sukuma su *Beenazar* zasuyi tasu anan. ****** "Bayan dasukai isha'i sannan suka dawo, sukaci dinning wanda su *Beenazar* suka had'a *Blue* sai nan nan yakeda *Beenazar* har suka gama, *Dad* yace dasu *Blue* dauki *Basma* su kaita gida haka ko akai bayan su *Mom* da mama sun cikata da abin arziki, sannan suka kaita wanda kuma wannan ne karan farko da *Blue* yaga *Ammu* da sauran yan'uwanta su *Bassam*, aikam sosai sukaji dad'in ganin yah *Blue* dinsu dasukai matukar kewa inda shima yaji dad'in ganinsu, tareda jin kaunarsu aransa *Banuja* sarkin tambaya aikam tana tafaman tambayarsa inayaje tadaina ganisa, murmushi yai tareda cemata yayi tafiya ne  haka dai suka rabu cike da kaunar juna. Adaran nan *Blue* ya angwance da amaryarsa *Beenazar* wacce yajita tamkar budurwa, shikam idanma badan dayasan tahaihuba dasai yace har yanzu itad'in budurwace gar aleda, cike da tsantsan kaunarta ya rungume matarsa suka sha barcinsu me dad'i wanda suka da'de basuyi ba, yayinda suka wurgar da *Baffa boy* chan gefe lol. Washegari asabar ba aiki, dan aka sai misalin karfe goma shad'aya da rabi nasafe, suka tashi sukai breakfast bayan sunje sun gaida su *Mom* inda suka bar *Baffa boy* achan, sun dawo sai suka yada zango akaramin falonsu, inda *Beenazar* tayi kwance akan cinyar *Blue* tanata zuba masa shagwa'bawa yana biye mata, sanye yake cikin dakakkiyar shadda gold color Ita mahaka saidai nata yellow dinki daguwar riga, sunyi kyau sosai kana kallonsu kaga amarya da ango masu matukar kaunar juna.         Cike da nishad'i yace my queen fad'amun dani da yah Bilal majnuni wakika fiso?...,cike da zolaya ta kallesa tareda shafa kyakkawan sajansa sannan ta yamutsa fuska tace gaskiya nafison *MAJNUNINA*, ido yazaro yace really?..yesss! baki yaturo cike da shagwa'bawa inda take taga yadawo sak! majnunisa, dariya tayi tareda rungumeshi yace why? kikafi son shi?... tace saboda yafisona bayason ko kad'an yaga 'bacin raina lokacin muna tare inajin wani irin nishad'i marar musaltuwa, yace ok i promise daga yau sai nafishi" sonki bazan ta'ba barin na'bata maki raiba saidai abisa kuskure insha'allah, sannan zan riga saki nishad'i fiyeda yanda yasaki, yaname rungumeta sosai ajikinsa cike dajin dad'i tace nima nayi alkawarin faranta maka da dukkan karfina insha'allah.     Haka nan suka wuni sunata zuba soyayyarsu gwanin sha'awa, babu inda *Blue* yaje sai sallah kawai yake zuwa yadawo, misalin karfe biyar na yamma lokcin tuni sunyi wani wankan sun sake wasu kaya, suna zaune ababban fall suna fira still yanzuma kwance take akan cinyarsa tanayi masa firan irin abubuwan dayai tayimata lokacin yana cikin hauka, idan wani yai dariya wani kuma ya girgiza kai cikeda tausayin kanshi.    "Suna cikin haka sai wayarsa tayi kara kamar bazaya dauka ba, saida *Beenazar* tace anafa kiran wayarsa sannan fuska yad'an yamutsa tareda cewa nifa banason muna soyayyarmu atakura mana, miko mun nakashe da sauri tace a ah! kasani kowani muhimmin abune yataso ok to bani nagaji, bakuwar lamba yagani dauka yayi tareda sallama chan yace "eh nine sai kuma yayi shuru yana saurare abinda ake fad'a.   Sai kuma yamike zumbur cikin tashin hankalin yace ok ok gani nan zuwa yanzu yakashe wayar, da saurin tace lafiya....cikin tashin hankalin yace aunty *Bebe* ce wai tayi hatsari tana asibiti kwance, Subhallahi!..ahanyar dawowa?..eh ina ganin bari naje pls ki kulamun dakanki kinji?...yana me shafar gefen fuskarta kai ta gyad'a tareda cewa nima ka kulamun da kanka adawo lafiya, ok Allah yasa my queen yadauki key mota yaimata kiss agoshi yafita da sauri.        Aharabar gidan yaga *Dad* yafito shima cike da tashin hankalin ya isa gurisa yana cewa, *Dad* yanzu aka kirani wai aunty *Bebe* tayi hatsari "eh nima haka, to yaushe "ta dawo daga inda aka turasu agurin ankin nata?...yace wlh bansani ba tunda ko d'azu nakira lambarta bayashiga, to ko ahanyar dawowan tayi hatsarin?...to kila yanzu dai mutafi asibitin mugani. "Aban garen aunty *Bebe* tsabar  farinciki yasatace saidai suka baro garin niger acikin daran nan, dan haka suka taho saidai suna gafda shigowa abuja ne sukai mummuna hatsari saka makon matsananci barcin daya kama direban, inda take shida kawarta suka mutu yayinda itakuma tayi mugun raunin ta hanyar karairayewa, adukkan wata gaba dake jikinta hakan yasa gaba daya halittarta yachanja, inda aka kwashesu zuwa asibitin shine aka kira *Blue* da *Dad* wanda sun d'auka ne acikin wayarta. Koda su *Dad* suka isa da kyar suka ganeta wanda ita ce dakanta ta tabbatar masu ai Ita ce, banda haka inda wani yafad'a masu to da bazasu taba yarda ba duk da hala saida *Blue* yace no *Dad* wannan ba aunty *Bebena* bace, Cike da tsanani nadama wacce za'a iyacewa marar amfani tace nice Bil boy, da sauri yamatsa gurinta yakura mata ido yana kallonta sosai halittarta yachanja tamkar wata dodanniya, yayinda miyau sai zuba yake takarka taccan bakinta gawani wari-wari datakeyi sannan wasu irin tsutsotsi sai zubowa suke takasanta.    Cikin bala'in tashin  hankalin *Blue" yace wayyo na aunty *Bebe* wannan wani irin hatsari ne haka?...magana tafarayi dai-dain da *Bulama* da *papa* suka shigo, inda take cewa Bil boy alhakin kane yakamani akan abubuwan danayi taimaka kai da *Dad* harda *Mom*, dakuma mijina uban 'ya'yana Cike da mamaki *Dad* yace *Bebe* me kika aikata mana?...nan tafad'a masu dukkan abinda ta aikata babu abinda taboye har tarayyar datake da bokaye tana matar aure...da kuma wannan tafiyar dasukai wanda duk dantaga bayan *Blue* din ne.    Wani irin tsalle *Blue* yai tareda komawa gefe yana kallonta, sai kuma yadafa kasan da dukkan hannusa yasaki kara me cike da tsanani bakin ciki da bacin rai wanda yasa idonsa sukai wani irin jajir, jijiyoyinka shi sukai rud'uru'u sannan yawatsa mata wani irin Harara me cike da tsanani tsanarta akaro nafarko dayaji hakan iya tsawon rayuwar dayai zuwa yanzu, sannan cikin bacin rai yace nima natsaneki ko lahira  bana fatan Allah yahad'ani dake kuma ban yafe makiba muguwa maciya amana, azzaluma macuciya fasik....sai yafashe da kuka tareda juyawa yafita da sauri inda *papa* yace da *Bulama* yabishi da sauri, karce zayai tuki dakanshi. *Dad* kam tsaye yake 'kikam tamkar gunki yakasa cewa komai, sosai yake ganin abun kamar almara wai *Bebe* ta akata dukkan wannan mugayan aikin ga d'an uwanta, yayinda itakam sai kuka take me cike da nadama *papa* ne, yace da'ita keko meyasa kika aikata hakan ga mutanan dasukai matukar abinta dake eye?...cikin kuka tace *papa* san zuciya, yace bacinta tabbas baki kyautama kankiba gashi nan takaiki tabaro. *Dad* yakalla yana kokarin magana *Dad* yarigashi dafad'in Barr in badan ni da hannuna nakarbi haihuwar yarinyar nan ba, to danace anchanja mun Ita ne to amma ko yanzu ina zargin Ita din bajinina bace da sauri yace haba *Dr* karka sheganta yarka mana dakanka, da sauri yace wannan din ai shegiyarce duk d'an halak bazaya ta'ba aikata wannan mugun halinba, dan Allah *Dr* kadaina fadin irin wanyan nan maganganun, cikin baci rai yace *Barr* nafad'a kuma kinji dai nace bai yafe makiba ko?...to nima ban yafe makiba dan haka gobe kiyama zakiyi bayani, abinda kika aikata sannan yasakai yafita zuciyarsa na 'kuna. Fitar *Dad* tayi dai-dai da wani irin shakkuwa da tafarayi, da sauri *papa* yamatsa kusada ita yanai mata sannu kai ta gyad'a kafin tace dan Allah yanema mata gafara agurin *Blue* da *Dad*, yace karta damu insha'allah chan kuma sai yafara kakari da sauri yafara karanto  mata kalmar shahada, sai duk yanda yaso takarba abin yafaskara har rai yai halinsa, ba tareda bata lokaciba aka bashi gawarta yanufo gida. Inda ya'iske *Blue* saboda tsabar bacin rai har wani dishi-shi yake gani amma wai ahakan yake kokarin tayarda mota saidai yakasa, hakan yasa *Dad* yakarbi key yamikama *Bulama* dan yajasu tunda shima ayanda yakejinsa bazaya iyatukin ba, suna isa gida *Blue* yabud'e mota yafito kai tsaye part dinsu *Mom* yanufa, domin ita kawai yakeson gani aikam tana falo itada *Beenazar* yashiga yafad'a akan jikinta tareda sakin wani irin mahaukaci kuka, yana fadin *Mom* mena tsare mata haka arayuwa datayi mun mugun tsana eye?... *Mom* kam cikin tashin hankalin tace wacce?...bai iya bata amsaba, sai *Bulama* ne da suka shiga shida *Dad* yafad'a mata dukka abinda yafaru, yayinda *Dad* yakoma gefe yana sauke ajiyar zuciya, itakam *Mom* batayi mamakin jin hakan ba tunda abayyane tasha nuna mata tsanani kiyayya dan hakuri kawai tabasu, yayinda tace da *Beenazar* tashi ki kama mijinki kije ki lallashesa nima zan lallashi nawa, cike da kunya takamashi suka fita zuciyarta cike da mamakin aunty *Beben*. Isar say *Dad* bada wani dad'ewa ba *papa* ya'iso da gawarta, sosai *papa* yayima  *Dad* da *Blue* nasiha hakan yasa suka yafe mata, dan lokaci kankani cikin lokaci kankanin *Mom* da mama sukai mata wanka batareda nuna kyamar gawarba, wacce kokad'an batada kyaun kallo suka shirayata akayi mata sallah aka kaita gidanta na gaskiya. Bayan sadakar bakwai *Blue* yasa akanemo Jiddo inda aka ganta d'akin wani saurayi duk ta lalace gwanin tausayin, asibitinsu aka kaita inda aka duba lafiyarta tareda yimata wankin ciki, sannan aka dauko malamin dayai masa addu'a lokacin da bayada lafiya, itama yaimata cikin sa'a itama tawarke tayi kuka sosai daji abinda yasame ta tareda mutuwar Mom dinsu.     Kasan cewar *Dad* dinsu Jiddo marayane ba uwa ba uba sai dangin ubanshin, sukuma yasan bazasu rike masa suba saboda irin walakaci da aunty *Beben* tayi masu, dan haka yanemi alfarman da yabarsu nan hannun *Mom* har yayi aure sai yakarbesu tace bakomai ai yaro nakowa ne, dan haka tarikesu inda tafara basu tarbiyya me tsabta wanda mahaifiyarsu bata basuba.       Aikam sai gashi wani irin nutsuwa yashigesu tamkar basuba, haka komai yacigaba da tafiya gwanin sha'awa agaresu tuni rayuwarsu ta sauya, hakan su *Beenazar* sosai suke gudanar da rayuwarsu me cike da zallar kaunan junansu da  kwanciyar hankali, tuni aka yaye *Baffa boy* wanda dakanshi yadaina shan nonon wannan kenan. *Bayan shekara uku* Raran wata lahadi da misalin karfe goma shad'aya nasafe *Beenazar* ce naga tafito daga d'aki tu'kui-tu'kui da tsohon ciki, sanye take da doguwar rigar atamfar english blue da ratsin fari, tayafa farin mayafi tareda takalmi fari flat wanda yaso yad'an matseta kad'an saboda d'an kumburin da kafafunta sukai, sosai tazama babbar mace wance kallo d'aya zakai mata kagane tuni wayewa yazauna jikinta.      "Ahankali take takawa tana yamutsa fuska tareda rike kwan-kwaso, bayan *Blue* sanye yake da riga marron color da wando na jeans black kashi sanye da facing cap baka, wacce batayi nasaran rufe lallausan suman kanshi ba. Rungume yake da  kyakkawan Baby me kamada *Beenazar* sak! harda chocolate color fatar *Beenazar* duk baby tad'auko, wacce akasama sunan *Mom* wato hauwa'u sai suna kiranta *Basoo* yayinda *Blue yake kirata da *Sona*, kasan cewar yana matukar jida Ita tako'ina gata sweet mom gata darling heart dinsa, so bai had'ata dakowa ba duk bata wuce shekara d'aya da rabi ba sanye takeda wata jar rigar kanti me kyau, da d'an karamin hijab dinta wanda ake kira half sunna wanda yafito da kyakkawan goshinta da gefe-gefen fuskarta dake kwance da yankananan suma, yatsunta biyu sanye cikin baki sai tsotso takeyi abinta hankalinta kwance sai sake lafewa take akan kafad'ar *Daddy* ta datake masifar jidashi.     Yayinda yake rikeda hannun *Baffa boy* wanda yaketa aikin zuba surutu tahanyar antayo masa da tambaya *Daddy* yauma zamuje gidan momina ne?...yana nufi *Basma* kasan cewar tahaihu jiya akai suna yanzu yaranta biyu dame sunan *Papa* da me suna umma. Cike da yace eh boy zamuje gidan mominka amma sai anjima kaji?...yace to dai-dai lokacin da *Beenazar* take kokarin zama amma takasa saka makon rikewa da bayanta yayi hakan yasa tace wayyo *MAJNUNINA* bayana zaya karye, _kasan cewar haka yace taringa kiransa saidai batayin hakan sai lokaci-lokaci_ Da sauri yace sorry queen nace kitsaya na dubaki amma kin kiya, cikin shagwa'ba tareda turo baki tace banaso tunda jiya nima saida nace kayi karkayi kakiya saida kayi.   Dariya yai cikin sigar lallashi yace to yihakuri bazan sakeba harsai bayan kin haihu kinji tawan?...cikin turo baki tace to, yauwa to yanzu tashi muje nakaiki Dr Luba tadubaki tunda naga ai edd dinki kamar yaune ko?...kai ta gyad'a dai-dai lokacin da mararta tayi wani irin hautsinawa, aiko da sauri tafurta ya salam wayyo marata sannu bari nakai su *Sona* nazo mutafi, kai ta gyad'a. Suna isa asibintin aka tarbesu da sauri kasan cewar sosai nakuda yataso, inda ko cikin sa'a batareda tayi dogon nakuda ba tahaifo kyakkawan katon d'anta me kama da ubansa, kalar fatane kawai yad'auko irin nata bayan tahuta aka sallamesu kasan cewar batajin ciwon komai, ranan suna yaro yaci suna *Dad* wato Lawai sai suna kiransa da *Barrak* haka rayuwarsu tamika gwanin sha'awa sosai *Blue* yake so da kaunar *Beenazar* tamkar yamaida ciki. Tammatttt _Ina mika godiya me tarin yawa ga d'inbin masoyana aduk inda kuke afadin duniya alkhairi Allah yakai maku_. Alhamdulillahi anan nakawo karshe wannan littafin nawa me suna *ZAUJUN MAJNUN* na biyu, ina rokon inda nai daidai Allah yabani ladani nida masu karantawa inda nai kuskure Allaha kayafe mana, ameen sai mun had'u sabon alittafina idan Allah ya yarda me suna *KYANDIR* (wato me kyan banza) kai daga jin sunan littafin kasan akwai magana aciki, da haka insha'allah sai yafi wannan fad'akarwa, da nishad'arwa tareda soyayya me tsayawa arai, yana kuma dauke da tsantsan yaudara cin amana da hassada da kyashi, masu tambayar *Taseeri* document ya kammala dan haka kune meni a lambar wayana 08161850024 sai najiku nagode. *MEENAL or LUFHAT CE* _ALLAH kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu mu_