💋💋 ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Paid book ne Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 Dedicated to my daughter Narnah khadija( Muhibbaty) allah ya albarkaci rayuwarki my daughter much love for you fisabillilah ♥️ 😘 ♥️♥️♥️♥️♥️♥️ _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 1️⃣ Gida ne mai kyau gwaurgwadan gidan talaka bawan allah mai rufin asiri, d'aki biyu ne a gidan sai dai ba'a jere suke ba d'aya na dubin wannan 'bangaren d'aya na dubin wannan, Wani mutum ne ya shigo ahankali yake tafiya kamar mai tsoron kar a kamasa, ahankali har ya isa bak'in k'ofar d'aya d'akin, sai da ya juya bayan sa yaga ba kowa yayi sauri ya shige ciki Zaune take saman sallaya tana lazumi, ganin sa yasa ta saki murmushi tare da saurin Mik'ewa tsaye tana fad'in " Sannun da zuwa" Hannu ya d'aga mata alamun tayi k'asa_k'asa da muryar ta, kana yace " Ina inna ne? " Tana d'akin ta "Ungo kar'bi wannan bara na d'auko takalmi na kar ta gane na dawo" To" ta fad'a tare da sa hannu ta kar'bi ledar hannun sa, Cikin sand'a ya sake komawa bak'in k'ofar yasa hannu ya d'auki takalmi sa juyawar da zai yi ya koma yaji muryar inna ta doki kunnuwa sa tana fad'in "Allah ya toni asirin ka fito fito naganka" Sumi sumi ya juyo tare da zube takalmin k'asa ya fito, inna ta k'arso wajen "Wato dan kar insan ka dawo ne shine ka shigo gida kamar 'barawo to allah ya nunamin kai " Inna ba haka ba ne nayi sallama banga kowa ba shiyasa nayo d'aki" Ohh so kake dai kace k'arya nake maka ko toma dai idan ba haka bane su talakmin da ka dawo d'auka ina zaka kai su? " Shuru yayi tare da sosa kai kana yace" Inna daman naga alamun akwai hadari ne shiyasa nadawo na d'auke takalmin kar ruwa ya jikasu su lalace " Inna ta saki baki tare da d'aga kanta sama"Kai nasuru kaji tsoron allah ina hadari yake wanga waje ga rana nan tarmasisi kace min wai dan kar ayi ruwa takalmin ka su jik'e to naji ina ledodin da ka shigo da su? " Suna d'aki ya fad'a yana k'abar fuska "To d'auko su Mik'omin nan nagani " Bai ce komai ba kuma bai motsa ba ganin haka yasa inna cewa" Au bazaka shiga ka d'auko ba ne to ni bara nashiga na d'auko ai ba kunyar shiga d'akin nake ba" ta fad'a tare da bangaje shi ta shiga d'akin ya biyo bayanta Tana shiga bata tsaya ko ina ba sai gaban matar da ta hango ledodin a hannun ta, tana zuwa ta Mik'a hannu tare da fad'in " Mik'o min" Mik'a mata tayi tasa hannu ta amsa, ta bud'e ledar kayan miya ne aciki ta ajiye ta bud'e d'ayar d'aurin nama ne gassashe guda biyu a ciki babba da k'arami, bud'e k'ara min d'aurin tayi ta jefa tsoka d'aya a baki tana fad'in "Wai sau nawa ina fad'a maka ba'a sabama mata da cin dad'i ne idan ka siyo ka rik'a mik'o min na kamma bata wannan ai yayi mata yawa " ta fad'a tana k'ara jefa d'aya a baki "To inna allah ya bani idan ban siya mata ba wazai siyo mata ai kuma kinga ba koda yaushe bane nake siyowa ba sai idan na samu kud'i ne nake siyo muku " Uhmm haka ne kuma to ku kar'bi wannan" ta fad'a tana Mik'a masa k'ara min d'aurin data bud'e take ci " Inna wannan ai naki ne bakiga wancan yafi yawa ba wancan mubiyu ne wannan kuma ke kad'ai ce" Nagani Nasuru nace nagani amman wannan zan baku wai kai bakasan gata ne nake muku ba bana son ku saba da cin irin wad'an nan abubuwa kamata yayi nida nake tsohuwa na rik'a cinsu baku ba kar'bi ka gani naje naci nawa " ta d'aura masa a hannu ta fice Juyowa yayi ya Kalli matar sa yace " Fatima kiyi hak'uri kinji in Sha Allah komai zai wuce karki damu "Murmushi ta saki tare da fad'in"Lahhh wallahi babu komai ai gaskiya inna ta fad'a ita ya dace ace ta rik'a cin wad'an nan ba mu ba "Uhmmmmm " Nasir ya fad'a Dan yasan ta fad'i hakan ne kawai dan kar ya damu "Kar'bi ki ci ni daman ba ci zanyi ba" Miyasa to? " Naji cikina na d'an murda min idan naci sa ciwon zai iya zama babba 'Subhanallah sannu ka sha magani kuwa?" Eh nasha gama sauran a aljihu" Okay sannu to ko zaka k'ara sha ne sai ka d'an kwanta ka huta " Wa ni rufamin asiri na kwanta yanzu kar kisa inna ta shigo d'akin nan ta kasa ta tsare"Hhhhhhhh " Dariya tayi tare da fad'in" kai Abban humaira"Ai kema kinsani sarai basai na fad'a ba " To yanzu dai bara na d'ebo ma ruwa ka k'ara Shan maganin"To shikenan " Ta cire hijabin ta wuce dan d'ebo masa ruwan, da kallo yabi bayanta har ta fita ya lumshe idanunsa, allah ya gani yana buk'atar kusantar matar sa shine ma dalilin da yasa ya dawo gida amman yasa ba daman yin haka tsaki yaja a k'asan ransa Har ta d'ebo ruwan ta kamo hanya sai ga inna ta fito da d'akin ta, ta tsare ta tare da fad'in " Ina zaki je da ruwa kuma cikin d'aki ko wani abu kika ci nashan ruwa? " Aah kai masa ne zanyi yasha magani "Au wai daman bai koma ba to meya tsaya yi haryanzu bai koma ba" Cikin sa ke ciwo " To maza kai masa ruwan yasha ya koma kasuwa"To " ta fad'a tare da wuce wa tayi d'aki Tana zuwa ta Mik'a masa ruwan ya 'ballo maganin yasha ta kar'bi kofin ta ajiye tare da fad'in"Sannu yanzu ya kake ji? "Da sauk'i sosai "ya fad'a tare da janyota ta fad'o jikin sa, bakin sa yakai satin kunne ta yad'an ciza kad'an tayi y'ar k'ara cikin shagwa'ba tana yarfa hannu tace "Da zafi fa"Dagaske? " Kai ta gyad'a masa"Uhmmm i need you maman humaira ta " Zaro ido tayi waje tare da fad'in"Yanzu?" Kai ya gyad'a mata tare da mairairaice face " Tabb kai ma fa kansan inna baza ta bari ba ka bari har anjima idan ka dawo kaji"Wayyoooo ki tausayamin mana nafa dad'e banyi ba " To ai ba laifi na bane inna ce bata bari da mun shigo d'aki tace mu fito waje " Uhmmmmm, ya fad'a yana shinshinan wuyan ta Inna ce ta k'aullah masa kira" Nasuru! !Nasuru! Kai wannan nasuru" dak'yar ya iya furta kalmar "Naam inna"Uban me kuke a cikin d'akin har yanzu da baka fito ka wuce ba "Gani nan fitowa"Aah karma ka fito ku dangoma a ciki " Fatima ta tashi daga saman k'afafunsa, ya Mik'e, ta mik'o masa hular sa ya saka, hannu yakai zai janyota tayi saurin jan baya "Muje dan allah kar mu k'ara wani laifin" ba tare da yace komai ba ya kama hanya ya fito ta biyo bayansa Yayi ma inna sai ya dawo tace "Allah dawo lafiya,har ya kusa fita ta dakatar dashi tare da fad'in"Yawwa idan zaka dawo kad'an biyomin da abu mai d'an dad'i dad'i wanda zan sama bakin salatin nan nawa "To" ya fad'a tare da fita "Wannan! wannan ! Anyi bita zaizai awajen nan kai gaka dad'ah duk inda mata ta jaka kana can ohhh inda ranka kasha kallo"Inna ta fad'a tare da juyowa ta kalli wajen da fatima take tsaye "Ke tsohuwar munafuka tsanyuwar uban mekike yi anan baza ki wuce d'aki ba, juyawa tayi ta shige d'aki "Shegiya kamar wata mutuniyar kirki idan ka ganta simi simi da ita................ 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 Had'aden saurayi ne zaune gaban ammin sa fari ne soll kamar balarabe ga kwantacen sajen sa wanda ya k'ara masa kyau ya had'u tako ina, Marairaice face yayi kamar zaiyi kuka ya kalli ammi tare da fad'in" Ammi please" "Ansar auren nan fa ko kanaso ko baka so dole sai anyi shi danma ka sani abbanku sun riga da sun yanke hukunci "Yanzu ammi ba abinda zaki iya yi akan maganar auren nan " Babu dan bani da ikon da zan sa ayi kuma bani da ikon da zan hana ayi " Innalillahi haba dad yazakumin haka wallahi akwai wacce zuciyata ke so kuma mun riga da munyi alk'awarin aure a tsakanin mu " iKon Allah to sai a warware alk'awarin shikenan" Ammi dan allah ki taimakemi kimin wata alfarma dan allah ammi na"Tame kenan? " Yawwa ammi dan allah a had'a da wacce nake so a d'aura muna auren nasan idan ke kika jema dad da maganar zai amince amman wallahi ni idan naje ko tsayawa saurarena ma bazai yi ba dan allah ammi ki taimakamin wallahi muna son junan mu sosai"Ammi ta kallesa tare da nazarin kalamansa Sannan tace "To shikenan zan gwauda amman kasani idan bai amuntaba"zai ma amince in Sha Allah "Allah ya yarda yasa kuma hakan shi yafi zama alkhairi"Amin ammi na ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️ Kyakkyawar budurwa ce fara ce sosai, gata da manyan ido eyelashes d'in ta zagar_zagar ga dogon hancinta bakin ta dan dai_dai la'b'banta pink dasu girar ta cikakka fuskarta ma haka, ga fuskar sumul_sumul gwaunin burgewa Tana sanye da abaya mai shegen kyau tayi rolling kanta da mayafin abaya, hannun ta sanye da wani tsadadden agogo mai masifar kyau, tayi tsaye bak'in k'ofar wani d'aki ta k'wank'wasa k'ofar "Shigo" Bakin ta d'auke da sallama ta shiga "Wowwwwww my princess irin wannan kyaun haka ma sha allah tubarakallah " Murmushi Kawai tayi tare da k'arasawa wajen matar ta zauna kusa da ita, tare da gaidata cikin girmamawa, ta amsa " Daddy baya nan ne " ta fad'a" Eh suna wajen meeting "Okay allah ya taimaka"Amin kin San dalilin da yasa nace kizo zamuyi magana "Aah mom"To zarinat ina son ki natsu ki bani aron kunnuwanki anan wannan maganar mai muhummanci ce" To mom" Zarinat "Naam"Kin san dai bazamu za'ba miki abunda zai cutar dake ba ko?" Eh " ta fad'a tare da d'aga kai " To daddyn ku ya yanke hukunci zai aura miki d'an uwanki Ansar"da wani irin mahaukacin sauri ta d'ago tare da kallan mom tana tunanin ansar! Ansar! To wane ansar kenan? Mom kamar tasan tunanin da take yi yasa tace "Ansar d'an kawunku" Wani irin harbawa zuciyar ta tayi da k'arfi nan da nan saiga hawaye sun zobo mata............................................... 💋 💋ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 2️⃣ Kuka ta fashe dashi mai sauti, mom ta janyota jikinta tare da bubbuga bayanta alamar lallashi, "Ya isa haka mana princess" mom ta fad'a tare da d'agota takai hannunta gefen gado ta janyo tissue tasa tana goge mata hawayen fuskarta " Princess kiyi hak'uri ki d'auki wannan hukunci da mahaifin ki ya zartar akan ki ina san ki kasance mai hak'uri da juriya mai tawakkali a wajen allah idan kika kasan ce a hakan sai kiga al'amurra sun zo miki da sauk'i duk da nasan kina yi ni kaina ina son naga kinyi aure kinje d'akin mijin ki, kinsan wani abu kuwa princess? " Mom ta fad'a tana kallan fuskarta, Kai ta girgiza mata tana sauke ajiyar zuciya "Kinsan irin wannan auren shi ne ake kira da auren gata saboda bako wace mace bace take samun irin wannan auren ba sai yan gata kamar princess d'ita " Mom ta fad'a tare da shafo face d'in zarinat, murmushi tad'an yi, tare da fad'awa jikin mom ta kwantar da kanta gefen kafad'arta, mom ta rungumota tana bubbuga bayanta tace " Zarinat"Naam" ta fad'a cikin muryar kuka " Nasan ba'a kyauta miki ba bakya son wannan auren amman ki d'aure kiyima iyayenki biyayya in Sha Allah zakici ribar wannan biyayyar " Hawaye ne masu zafi suka zubo mata"Princess kin san banasan ganin xubar hawayenki d'aga min hankali suke yi please ki daina wannan kukan ko kinasan na shiga cikin damuwa?" Da sauri ta girgiza kai "Yawwa to kidaina idan ba haka ba zan iya shiga cikin damuwa, abu d'aya nake so dake princess ina san ki kasan ce surukar kirki mata ta gari " Mom taya zan iya hakan bancin ban shiryama wannan al'amarin ba"Shiiiiiiiiiiiiiiiiiiiii babyna bana son kina fad'in haka nasan zaki iya in Sha Allah zaki iya " da haka mom tayi ta bata kalamai masu sanyi ( Wacece zarinat) Su biyu ne a wajen iyayen su sannan manyan mutane ne attajirai masu ji da nera, daga ita sai yayan ta, lokacin da aka haifi yayanta bilal, an d'auki tsawon shekaru kafin mom ta sake samun wani ciki, iyayen su naji dasu sosai suna basu gata da kulawa yarda ya dace kuma sun basu tarbiyar da ta tadace, zarinat Yarinya ce da tunda ta taso bata ta'ba yin k'awa ba ko saurayi ita kad'ai take rayuwar ta itama abun na damunta sai dai ba yarda zatayi tunda allah bai kawo mata ba , sai da aka kaita boarding school sannan ta samu k'awaye, tunda suka kammala school shikenan duk suka rabu Saboda babu wacce suke gari d'aya amman suna chatting, har group d'in makaranta suka bud'e, haryanzu duk da tana university amman bata da k'awa, Tana da timetable tasan lokacin da suke da lecture dan haka tun kafin lokacin zataje ta zauna har ayi a gaba ta wuce, Wannan kenan 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 Bayan dad ya dawo, ammi taje masa da zancen ansar, yace "ina sam hakan bazai ta'ba yuwuwa ba" Ta sanar ma ansar yarda sukayi, ya shiga cikin damuwa da tashin hankali, can wani tunani yazo masa, dan haka ya shirya ya nufi gidan su zarinat, ya samu daddy ya fad'a masa duk abunda ake ciki nak'in amincer da dad yak'i yi akan auren sa da waccen, daddy ya ce yaje Kawai in Sha Allah daga ya Fito daga gida zaije ya samesa akan maganar kuma zai amince, Ansar ya tashi da farin ciki dan yasan, shi kad'ai ne wanda idan yacema dad ga abunda za'a yi bazai musaba saboda tsananin k'aunar da yake yima d'an uwansa shiyasa baya iya yin musu dashi ( Ansar da zarinat d'iyan wah da k'ane ne Mahaifin ansar shine babba Mahaifin zarinat shi ke bimasa, suma su uku ne ga iyayen su, Alhaji abubakar, dad kenan Mahaifin ansar, Alhaji sani, daddy Mahaifin zarinat, sai hajiya rabi, k'anwar su) Ansar su biyar ne a wajen iyayen su maza hud'u mace d'aya, wacce ita ce ta zamo y'ar autar su, kuma ita ke bima ansar Daddy na fita kamar yarda yayima ansar alk'awari kuwa sai da ya fara zuwa wajen dad, da yaje ma dad da maganar duk da baya iya masa musu akan magana amman wannan sai da yayi dak'yar daddy ya shawo kansa ya amince ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️ Abincin fa baka ciba" Fatima ta fad'a " Hmmmmmm ni yanzu bata wannan nake ba zo ki d'an ji " Uhm uhm harfa na zuba kar yayi sanyi"lallai naki wasa ne yarinya" ya Mik'e tare da zuwa ya rufe d'akin ya dawo ya cire kayan jikin sa ya rage daga shi sai gajeren wando, yasa hannu ya d'ago ta, tana sanye da hijab dogo har k'asa hannu yasa ya cire hijabin daga ita sai wata y'ar riga lahelahe marar nauyi ita kad'ai ce a jikin, ya janyota jikin sa tare da had'e bakin su waje d'aya, ya tallabe ta suka fad'a gado, suka shiga farantawa junan su........................................... 💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 3️⃣ Bubbuga d'akin inna keyi da k'arfi " Nashiga uku na nasuru cikin wannan uban zafin zaku shige d'aki ku rufe wai zaka zo ka bud'e k'ofar nan ko kuwa, kajimin d'an banza tasakaka d'aki tana baka kana shanyewa kana tsotsewa zaku bud'e k'ofar ne ko sai na fita na samo majiya k'arfi sunzo sun 'balle k'ofar " Nasir da sauri ya Mik'e daga saman fatima ya lalubi jallabiyar sa ya zura, itama ta janyo rigarta ta mayar, Koda ya bud'e k'ofar har ta juya, ai kuwa da sauri ta juyo tana kallansa"Cikin wannan uban zafin me kukeyi a d'aki salon wata cuta ta kamaku azo ana 'barnatar da kud'i wajen neman magani " Yi hak'uri inna bamu jiki bane bacci muke yi"Iyyeeeee lallai yaro mayar dani k'aramar yarinya tunda bansan aikin da nake yi ba ta saka ka d'aki ta rufe ta bud'e maka kana lasa " Wata irin kunya ce ta kama nasir kamar ya nitse duk da bayau ta saba da fad'in abun da duk yazo bakin ta ba, harta fatima da take bakin k'ofa la'be kunya kamata tayi "Ina ita tsohuwar munafukar take? " Fatima jin ta fad'i hakan yasa tayi saurin fitowa kanta a k'asa " To a wuce ga keso can na shimfid'a aje a zauna kuma kusha iskan duniya ace duk wannan iskan mai dad'i da ke kad'awa ku sunk'e cikin d'aki kamar wasu sabbin aure to a wuce" Fatima gaba nasir biye da ita a baya suka nufi keson " Wannan! Wannan! anya ba'a baka ka shanye ba wannan bita zaizai haka mtswwww" inna ta fad'a tana nuna nasir Dukan su zama sukayi saman shimfid'ar, sunyi shuru bamai cewa uffan gwauda ma inna tana d'an magana duk da mafi yawancin maganar tata fad'a ne Suna zaune hadari ya taso nan da nan ruwa suka sauko, duk sukayi d'aki har inna ta biyo su d'akin, dukan su da mamaki d'auke a fuskarsu suke kallan ta, inna ko ta nemi waje ta zauna Nasir ya d'auko lema yace "Inna gashi ki kunna sai kiyi d'aki kar ruwa su jik'aki kinga dare nayi kuma ruwan nan kamar zasu d'an jima kafin su d'auke" Mai suwa ka aje dan anan zan kwana yanzu fisabillilah wannan ruwan da akeyi masu k'arfi so kake naje d'aki ni kad'ai gina ta fad'o min ko?" Ta fad'a tana kallan fuskarsa "Yi hak'uri ba nufina ba kenan allah ya huci zuciyar ki "Amin" Fatima ranta yayi mugun 'baci, kar tayi magana kuma ace bata da kunya Nasir ya juyo ya kalleta, tayi saurin d'auke kanta tare da hayewa gado tayi kwanciyarta tare da jan bargo ta lullu'be jikinta 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 Ansar kwance saman makeken gadon sa hannunsa dafe da waya a kunnen sa "Please stop crying baby" idan banyi kuka ba beb mezanyi yanzu ace harda wata za'a d'aura maka aure bayan ni"Nafa gaya miki komai nima ba'a san raina za'a yi auren nan ba zuciya ta ke kad'ai ce wacce take so da burin kasancewa a tare da ita " Uhmm har kasa naji wani sanyi acikin rai na love you so much my dear" Love you too baby ni ba wannan ba wai yaushe zaki dawo gashi antura anje anyi magana auren nan fa ba jansa za'a yi ba idan ma anjasa da tsawo bazai wuce 1 month ba amman kina ejib zaman ki kamar ba amarya ba "Hhhhhh kai dear next week in Sha Allah zan dawo da yanzu ma jibi zan dawo amman saboda auren nan dayazo girshi yasa mom tace nazauna a can akwai shirye_shiryen da za'a min gobe ma mom zata zo nan" " Okay wane irin shirye_shirye ? " Abun sirri ne" To shikenan tunda baza'a fad'a min ba " Meya hanaka zuwa office yau? " Wallahi na d'an d'auki hutu ne na kwana biyu " Hutu tun yanzu tun kafin mu fara cin amarcin mu"Ai lokacin hutu na mussaman zan d'auka "Ai kam dan kasan ba d'aga k'afa zamu gurji amarcin mu yarda ya dace " Haka dai suka ci gaba da hirarsu har aka fara kiran sallah, sukayi sallama ya wuce masallaci ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️ "Princess! Princess! Princess "Naam mom" zarinat ta fad'a tana saukowa upstairs, sanye take da atamfa mai kyau d'inkin riga da siket, d'inkin ya kama jikin ta shafe d'in ta ya fito, mace ce ita mai diri, Tana sanye da fashion hijab irin mai shape d'in nan tayima hijabin kyau sosai, fuskarta ba makeup sai man baki da ta shafa, ta gyara girar ta kamar wacce aka zana, tana rataye da fashion bag hannun ta rik'e da papers sai mukullin motar ta Yarinyar kamar ita tayi kanta, ta had'u sosai Tun da ta 'bullo mom ke kallan ta tana k'ara yaba kyawon y'ar tata, ganin tayi kuma tad'an rame mata Murmushi d'aure akan face d'inta ta k'araso wajen mom " You look so beautiful my princess "Oooh Thank you mom "Ta fad'a tana karyar da wuya"Welcome, princess meyake damun ki ne kodai daga ido na ne naga kin rame ko wani tunanin kika sakama ranki har ya ramar dake"Ni ba komai" ta fad'a tana turo baki cikin shagwa'ba" Mom tayi murmushi tare da fad'in" To shikenan tun da kince ba komai, har kin fiton kenan? " Eh " Okay allah ya bada sa'a, kiyi saurin dawowa yau su yayanki zasu zo "Lahh mom shi ne ba'a gayamin ba sai yanzu"To nima sai da suka taso ne suka sanar da ni nasa a gyara musu d'akin su "Okay sai na dawo mom"Allah ya tsare ya bada sa'a da rabo yasa a samu abunda akaje nema " Amin mom" banda tuk'in ganganci saman titi " In Sha Allah mom bazan yi ba" Good girl " Fitowa tayi ta nufi compound d'in ajiye motoci, ta nufi wata had'ad'd'iyar mota black, motar tayi kyau sosai, ta bud'e bag d'in ta ta ciro key, ta latsa wani madanni daga jikin mukullin nan da nan motar ta bud'e ta shiga ta zube kayanta saman d'aya mazaunin dake gaba ta tada motar, tun kafin ta iso bakin gate d'in an jima da bud'e mata, ta tsaya suka gaisa da mai gadin ta wuce................................................. Comment and share fisabillilah 💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 4️⃣ Fitar ta keda wuya sai ga motar su ta danno kai, hl sukayi mai gadi ya bud'e musu gate, cikin wata dalleliyar mota suke, parking sukayi, Kusan duk a tare suka bud'e murfin motar suka fito, su uku ne, mutumen da ka gansa kaga kamannin zarinat a tare da shi sosai, kallo d'aya zakayi masa kasan hutu ya zaunu a jikin sa, matar fara ce ita ma sosai ba laifi tana da kyauwonta, tana sanye cikin wani material onion colour, mai shegen kyau ga cikin ta jikinta da ya fara girma, sai yarinyar da bazata wuce 7 to 8 years ba, kammannin su d'aya da baban ta Mai gadin ne ya k'ara so wajen su da sauri, cikin girmamawa yana gaidasu, suka amsa, yah bilal ya basa key d'in motar dan ya shigo musu da kayan su, suka wuce Suna shiga babban falon gidan, yarinyar ta ruga aguje ta hau upstairs tana kiran " Granny! Aunty! Granny! Aunty"mom da take k'ok'arin saukowa ta tarbe tana fad'in "Kai lale lale lale marhaban manyan bak'i ne haka suka iso " Yarinyar ta washe bakin ta yan hak'oran ta k'ananu suka bayyana, dimple d'in ta ya lutsa "Ina grandfather?" Yayi tafiya "Mom ta fad'a suna saukowa k'asa " To ina auntynaa ban gantaba " Yanzun nan taje school" Shine tayi tafiyar ta bancin kuma tasan zan zo "To afrah nidai dan allah yi hak'uri ki adana rigimar ki idan tadawo sai kuyi tayi"Mom ta fad'a suna k'ara sowa wajen su yaya bilal "Sannun ku! Sannun ku! Kun sha hanya fa sannu"Yawwa mom fatan mun same ku lafiya "yaya bilal ya fad'a"Wallahi alhamdulillah " Aunty maryam ta d'urk'usa k'asa tare da gaida surukar tata cikin girmamawa, mom ta d'ago ta tare da fad'in "Wai dan allah maryam sau nawa zan fad'a miki banason irin wannan gaisuwar idan zaki gaidani ba dole sai kin duk'a ba bare kuma ga ciki a jikin ki ai sai ki wahalar da kan ki, Aunty maryam tayi murmushi tare da fad'in"Yi hak'uri mom in Sha Allah ba za'a sake ba "Hmmmmm allah sa dan wannan kalmar nasha jin ta a bakin ki amman hakan baisa kin daina ba" Ita dai aunty Maryam murmushi kawai tayi tana k'ara jin k'aunar surukar tata a ranta dan mom mace ce mai dad'in zama bata da matsala irin wacce ake fad'a ta suruka, "Yanzu dai duk ba wannan ba kuje ku samu kuyi wanka ku huta dan nasan kun d'ebo gaji " Wallahi fa mom " yawwa idan kuka huta sai ku fito kuci abinci " "Mom wai ina amaryar ne? " Aunty maryam ta tambaya" Wallahi kamar kinsan abun da yake rai na tun d'azu nake son tambaya " Yaya bilal ya fad'a "Y'ar albarka tana wajen neman ilimi "Allah sarki allah yasa aci amfanin sa"aunty maryam ta fad'a "Ai kowa d'an albarka ne"yaya bilal ya fad'a yana tafiya "Kaji nace akwai wanda ba d'an albarka ba ne?" Dariya kawai yayi yayi gaba, aunty maryam ta Mik'e afrah tayi saurin cewa "Nidai wajen granny zan zauna"Ai bance ki bini ba malama "aunty maryam ta fad'a tabi bayan mijin ta, mom tace" Muje kici abinci kafin auntyn ki ta dawo"To " ta fad'a tare da kama hannun mom suka nufi dining area, Abinci ta zuba mata kad'an dan tasan bata cin abinci sosai, kamar ko ta sani dan ko rabin wanda ta zuba mata bata ci ba, suka dawo falo suka zauna Su yaya bilal suka fito, sunyi wanka sun sauya kaya,suka nufi dining suka ci abinci, suma suka dawo falo suka zube gabaki d'aya hankalin su nakan tv suna kallan wani program da ake gudanar wa harta afrah duk da ba ganewa take yi ba amman hankalin ta nakan tv "Yeeeeeee babyna" jin muryar zarinat gabaki d'aya suka juyo suna kallan k'ofar Da gudu afrah ta nufeta tana dariya, d'aukar ta tayi tana jujjuyawa suna dariya, sannan ta ajeta suna maida numfashi, ta rik'o hannun ta suka k'ara sa Cikin falon "Amarsu an dawo" aunty Maryam ta fad'a, zarinat ta turo baki gaba tare da zuwa gefen mom suka zauna "Amarya wai miye sirrin ne naga sai wani shining kike mai d'aukar ido kin k'ara k'iba "Kema dai kya fad'a"yaya bilal ya fad'a "Mom wai me kike bama autar nan taki ne haka ahhh lallai ba k'arya da anganki anga amarya" Mom kin gansu ko " zarinat ta fad'a cikin shagwa'ba"Barin dasu kawai princess, mom ta fad'a tare da juyowa ta kalli gefen su yaya bilal dasuke ta dariya " To ya isheku haka yarinya da dawowar ta makaranta ko hutawa batayi ba zaku demeta da wani zance " mom ta fad'a tare da mayarda dubanta kan zarinat tace"Princess kyalesu kawai je kiyi wanka ki fito kici abinci "To mom" ta fad'a tare da Mik'e wa afrah tace "Aunty nima zanyi wanka" To zo muje kayan da zaki saka idan anyi wanka "aunty maryam tayi saurin cewa "Kayan ta na d'akin ki "Okay let's go" ta kama hannun ta suka wuce 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 Mik'o min cefanen nagani yau tsoka nawa ce, inna ta fad'a Fatima ta Mik'a mata ledar, ta bud'e"kai yau naman nada kyau da gani na shanuwa ne " ta fad'a tana lissafa ko yanka nawa ne "Kar'bi jeki d'ora yanka goma sha biyu ne tsoka, k'ashi guda hud'u "To inna" ta kar'bi naman taje ta fara girki Bayanta gaba ta tsame naman cikin miya ta kawo ma inna, ta amshi robar ta sake lissafawa, taga sune cif tace "To mik'o min hannun ki" Fatima ta bud'e tafin hannun ta biyu ta aza mata tsoka d'aya da k'ashi uku yace wannan naki ne "To" ta sake aza mata tsoka biyu da k'ashi gudan da ya rage tace "Wannan na nasuru ne shida ya wahala wajen nemowa gwaunda ya d'an ci da yawa ya guyguya Kashi to tashi tafi wannan kuma nawa ne" ta fad'a tare da d'aukar tsoka d'aya ta jefa baki tace " Uhmmm uhmmm uhmmm dajin naman nan miya tayi dad'i sosai bara na tashi na zobo nawa naci" Fatima ta Mik'e tayi kitchen ta d'auko d'an k'aramin filet ta zuba naman ciki takai d'aki...................................................... Comment and share fisabillilah 💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 5️⃣ Sai da ta fara fito musu da kayan da zasu saka sannan suka fad'a toilet, Ta fara yima afrah ta fito da ita ta kunna mata game a waya ta bata ta koma toilet, itama tayi ta fito d'aure da towel Shiryawa sukayi cikin wasu k'ananun kaya riga da wando pink color, ta d'aura after dress saman kayan, ta kama ma afrah kanta da ribbon 🎀 pink and white, ta gyara mata face d'in ta, itama ta kama kanta da ribbon 🎀 white, gashin kanta bak'i k'irin sai k'yalli yake yi ga tsawo sosai ga man da ta shafa masa ya kwanta gaunin burgewa, ta yafa k'ara min mayafin after dress d'in akai, ta feshe musu jikin su da turaruka masu k'amshin dad'i, sunyi matuk'ar kyau sosai kallo d'aya zaka musu kaji sun burgeka Pictures ta musu, sannan suka fito " Aunty"Naam "Uhm muje mu siyo chocolate" To kina da kud'i ko? " Zarinat ta fad'a tare da kallan fuskar afrah murmushi d'auke akan fuskar "Banada " To dame za'a siyo chocolate d'in? " To ai ke kina da kud'i " Ni"zarinat ta fad'a tare da bud'e ido " Eh " Hhhhhhh nikam banada kud'i " Uhm uhm uhmm" Bara mu ci abinci sai muje shikenan "Yeeeeeee"Afrah ta fad'a cikin jin dad'i " suka k'ara sa cikin falo Aunty maryam tace " iyyeee Wowwwwww ma sha allah yaran mom irin wannan kyaun tubarakallah ma sha Allah kunyi kyau sosai " Thank you Oum twins"Wallahi a kanki dan allah zubar da wannan yawun "Hhhhhhhhhhh wannan cikin ai daganin wannan girman da yake yi kema kinsan ba d'aya ne a ciki ba" zarinat ta fad'a tare da zama kusa da mom dake waya, afrah ta zauna saman k'afafun zarinat "Ni bama zan biye miki ba" Hhhhhhhhh " Mom ta gama wayar tare da mayarda dubanta kan zarinat ta sakar mata murmushi" Princess kunyi kyau sosai iyyeee "Mom ta fad'a tare da shafo kan afrah, dake game a wayar auntyn ta "Mom please idan muka ci abinci zamu d'an fita "Zuwa ina? " Supermaker " Okay amman kar a dad'e"To nagode "Aha"Mom abincin fa yunwa nakeji"Muje na zuba miki "To "Afrah kema zaki ci? " Kai ta gyad'a mata tare da fad'in " Tare da aunty zan ci"To y'ar aunty muje " Suka nufi dining area Aunty maryam tace"Wallahi mom gaskiya kina sangarta yarinyar nan sosai ace harta da abincin ke zaki zuba mata " To idan ban mata ba wazai mata" mom ta fad'a, zarinat ta juyo tare da yima aunty maryam gaulo Dariya kawai aunty Maryam tayi, 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 Ansar dan allah zo ka kai auta supermarket driver baya nan na aike sa kai sak'o wani waje ita kuma kasan bata iya driving ba" To ammie ta shirya ne" Eh " Okay ta sameni a moto" ya fad'a tare da wucewa "Auta!Auta! "Naam ammie " wata budurwa ce ta amsa tare da nufo ammie tana da tsayi kamar ansar sai da bata kai hasken saba bata da irin hasken nan sosai tana sanye cikin wata atamfa doguwar riga, rigar mai rafa ce ta yafa mayafi fari hannun ta rik'e da jaka Ta k'ara so wajen ammie " Ammie gani"Yace ki same sa waje "To ammie sai mun dawo"Adawo lafiya " ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️ Sai da suka ci suka k'oshi, sannan suka tashi, zarinat ta koma d'aki ta d'auko ma afrah hula ta d'auko key d'in mota, ta saka mata hular, ita kuma ta k'ara gyara mayafin rigar taje ta amso ATM d'in mom suka fito, afrah ta rik'e hannun ta tana d'an tsalle_tsalle suka nufi motar ta ta bud'e afrah ta shiga gaba itama ta zaga ta shiga, ta tayar suka wuce Tafiya suke kowa yayi shuru sai karatun k'ur'ani da yake tashi cikin zazzak'ar murya zarinat na biya, afrah ta kalle ta tare da fad'in "Aunty"Naam " ta fad'a amman hankalin ta nakan titi"Nima ina son na iya mota "Haba? "Eh idan zanje school na rik'a zuwa da kaina basai baba drive ya kaini ba "karki damu allah ya nuna kin isa fara driving da kaina zan koya miki"Yeeeeeeeee " ta fad'a tana murna tace"Aunty da yawa fa zamu siyo "Miye? " Chocolate "Ohh sosai ma" muci abun mu daga ni sai ke ko? " Afrah ta fad'a" Kwaurai kuwa bazamu samma kowa ba "Da biscuit da sweet " Komai sai mun siyo " zarinat ta fad'a tana k'ok'arin parking a gaban wata katafaren babbar supermarket, suka fito suka nufi ciki Komai akwai cikin supermarket d'in in dai 'bangaren mak'ulashe ne, chocolate 🍫 sosai suka kausa da biscuit 🍪 "Aunty zarinat" d'ago kanta tayi jin an kira sunan ta, minal ta gani tsaye yaya ansar a bayanta, data gansa sai da gabanta ya Fad'i, ta sakar ma minal murmushi Minal ta iso wajen su tare da rungumar zarinat tace "Aunty zarinat allah gobe ma nake son naje wajen ki"Uhmmmm ai koda yaushe hakan kike fad'a sai kin ganni zaki ce aunty zarinat daman gobe nake san zuwa wajen ki "ta k'arshe maganar tare da kwaikauyon maganar ta Dariya sosai minal tayi tare da fad'in"Kai aunty zarinat "Ai gaskiya na fad'a" In Sha Allah gobe zan zo" Allah yasa" Wai afrah ce?" Eh ita ce" Ma sha Allah ta girma yaushe suka zo? " D'azu, afrah bakiga aunty ba ne ki gaidata" Ina kwana "afrah ta fad'a "Ina zuwa"zarinat ta fad'a tare da nufar wajen da yah ansar yake tsaye yana dannar waya, dannar wayar ne kawai yake yi amman hankalin sa nakan su k'asa_k'asa yake kallan su tare da k'arema zarinat kallo tunda sama har k'asa har ta iso wajen sa " Ina wuni yaya " ta fad'a tare da yi k'asa da kanta, d'ago kansa yayi tare da fad'in " Lafiya ykk" Alhamdulillah "Good" dukan su sukayi shuru zuwa can yace " Akwai abinda zakuyi ne wanda zaki buk'aci kud'i" Kai ta girgiza masa alamar aah" okay, bani wayan ki" Mik'a masa tayi ya kar'ba yashiga phone numbers 📱 ya saka number sa ya kira ta shiga ya tsinke tare da Mik'a mata yace " Ga number ta nan idan an kawo I V zan kira ki sai ki fito ki kar'ba "To" aha kun gama siyayyar ne? " Eh " okay " ya fad'a tare da takawa ya nufi wajen su minal itama ta biyo bayansa "Aunty kinga harda irin wanda daddy ya ta'ba siyo min kuma akwai dad'i" Nima kin d'auka min?" Eh dayawa" Yawwa good girl to ya isa haka muje " To " Itama minal tace ta gama suka nufi wajen biyan ku, aka lissafa kud'in yah ansar ya Mik'a ATM d'in sa yace a cire kud'in duka har nasu zarinat godiya tayi masa, Sannan suka fito kowa ya hau motar sa suka wuce "Mommy mun dawo" To sannun ku da zuwa injin nima an siyo min nawa? " Aunty maryam ta fad'a "Aah dani da aunty kawai muka siyo " To ni ina nawa"Bamu siyo miki ba "Aikuwa bazan yarda ba" "Princess kun dawo"Eh mom "To ai nazata baku siyaba banga an cire kud'in ba" Eh yah ansar ya biya kud'in" ayyah tare kuka je? " Acan muka samesu" ta fad'a Aunty maryam tayi gyaran murya tare da fad'in " Adai fad'i gaskiya" zarinat najinta tayi kamar bata ji ba Washe gari, bayan sallah azahar ya kawo mata IV Zarinat gyara mom ke mata sosai tare da aunty maryam, ciki da waje gyara take sha Yau sauran kwana biyu d'aurin aure, gidan ya cika sosai tare da yan uwa da abokan arziki na nesa dana kusa, amarya an mata k'unshi maroon yayi bala'in kyau kitso dai akayi akayi da ita tace bata so, daman bata san kitso, da aunty maryam ta dameta da maganar ma har kuka tasa, ganin hk yasa ta kyale ta taje aka k'ara gyara mata gashin ta, yayi kyau ga k'yallin da ya k'ara yi har wani daddad'an k'amshin yake yi mai ratsa sassan jiki, ita kanta amaryar k'amshin da take yi na mussaman ne dan duk yarda ta biyo ta wuce a wajen koda baka gantaba zaka ji k'amshin turaren ta wanda kasan da kaji irin shi kasan na amare ne ko amaren sai wance da wance kwance take bayan sallah isha'i afrah a gefen ta tayi bacci, tayi shuru tama rasa tunanin da zatayi, hawaye taji suna gangaro mata ta gefen kunnuwa, hannu tasa tana gogewa tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya, kukan take sosai tana fad'in " wannan wane irin aure ne ace har sauran kwana biyu aure amman yah ansar bai ta'ba kirana ba da sunan wai zamuyi hira ko magana, ta fad'a tare da fashewa da sabon kuka ita kad'ai tasan yarda take ji a cikin zuciyar ta, hannu tasa ta share hawayen tare da fad'in "Shukran yaa rabbi shukran allah ka bamu ikon cinye duk wasu jarabobin da za'a muna allah ka k'ara muna juri da hak'uri ka sa mu kasan ce cikin masu kyautatawa mahaifanmu da musu biyayya allah kaine gatana gareka na wallafa dukan al'amarina allah ka zamo gatan na kasa wannan auren akwai alkhairi a cikin sa ya ubangiji Allah idan babu alkhairi a cikin sa allah kasa koda ranar d'aurin auren ce ace an fasa yah rabbil alamien yah hayyu ya gayyum ya zaljalalu wal'ikran " daga haka tayi shuru tana sauke ajiyar zuciya ta juya ta rungume afrah da haka bacci yayi awon gaba da ita..........................,................. Comment and share fisabillilah ♥️ 💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Wannan page d'in sadaukarwa ne ga mabiyan wannan littafin much love for you fisabillilah ♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️😘 Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 6️⃣ To aka ce Rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya, wannan haka yake Yau juma'a yau dubban jama'a suka shaida d'aurin auren MUHAMMAD ANSAR ABUBAKAR DA ZARINAT SANI DA HUSNA AL'AMIN akan sadaki naira dubu d'ari d'ari lakadan ba ajalan ba Zarinat zaune a d'aki daga ita sai wata y'ar makarantar su da ta sanar ma auren saudat, tayi kyau sosai tasha makeup ta mutumci tana sanye cikin wata shadda light blue, an kashe ma shaddar d'inki na alfarma, wuyan ta sanye da sark'a gold, hannun ta sanye da wani tsadadden agogo mai masifar kyau da zobe d'aya hannun kuma sanye da awarwaro masu kyau, sai k'amshi ke tashi a jikin ta hannun ta rik'e da dank'areriyar wayarta tana dannawa D'ago kanta tayi tare da kallan gaban saudat da aka cika shi da kayan abinci da lemuka a hankali ta bud'e baki tare da fad'in " Saudat baki ci komai ba fa" Murmushi saudat tayi tare da fad'in " Allah kuwa naci sosai duba kiga" ta fad'a tare da nuna mata gefen da taci " Uhmmmm haka ne kika ci dayawa" Eh mana abincin nan yawa ne fa dashi sosai " Hmmmm naji"kinji baki yarda ba kenan? " Ban fad'a ba" To ai hakan kike nufi " To saudat nagani kinci sosai shikenan" Dariya saudat tasa Sannan tace " Yawwa yanzu naji amsa K'wank'wasa k'ofar ake yi zarinat tace" Waye? " Auntyn ki ce" tana k'ok'arin tashi saudat tace yi zaman ki bara naje na bud'e "Okay thank you" bud'e k'ofar tayi aunty maryam ta shigo hannun ta rik'e da gorar tsumi Takalli saudat tare da fad'in "Saudat ko? " Eh" Ashe ban manta sunan ba ta fad'a tana murmushi"Aikuwa " Mik'a ma zarinat gorar tayi tare da fad'in"Shanyewa zakiyi yanzu gaba d'aya " baki ta turo tare da fad'in"Haba dan allah aunty ni wallahi na gaji dashan wad'an nan abubuwan " Auu haba to malama indai wad'an nan ne yanzu ma kika fara sha" To wai miye amfanin su ne?" Zaki san amfanin su nan gaba kad'an nidai shanye ku tashi muje ga camera man nan yazo " wai yanzu fita zamuyi wallahi banasan hayaniyar nan shiyasa ma muka dawo nan" Pictures kawai za'a yi sai ku dawo" Shanyewa tayi kamar zatayi amai, suka fito suka nufi babban falo wajen da za'a yi hoton 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Kid'a kawai ke tashi a gidan tun kafin ka k'araso bakin k'ofar ka kejin sautin kid'a na tashi, cikin falon mata ne da yawa wasu na zaune wasu na tikar rawa, d'aya daga cikin matan dake zaune ne wata tace " Wai ina husna ne? " Tana d'aki tana baccin gajiya kinsan jiya muka dawo to kuma yau da safe muka siyo abubuwan da babu " Okay gaskiya kam dole ta kwanta ta huta gashi zuwa anjima za'a kaita d'akin ta" Ai shine dalilin da yasa na barta tayi baccin ta yanzu " Wannan gaskiya ne" 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀'Bangaren ango, da ka kallesa zakasan yana cikin tsantsar farin ciki, Sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda fara, an kashe masa kwaud'o na alfarma ga babba riga, ga hular kansa wacce ta k'ara fito dashi hannun sa manne da dank'areren agogon sa sai zoben azurfa gashin gemun nan nasa ya sha gyara sosai gashi bak'ik'irin har kyalli yakeyi idan ka gansa zaka iya rantsuwa kace balarabe ne sai baza k'amshi yake yi, su aunty yasira da maman salma da maman ummu, matan yayun sa sai tsokanar sa suke da ango kasha k'amshi, Anci ansha anyi murna taro yayi albarka K'arfe goma dai_dai akaje d'aukar amare kasan cewar motocin nada yawa yasa aka raba biyu sauran suka je d'aukar zarinat wasu kuma d'aukar husna Zarinat kuka take sosai tace bazataje ko ina ba anyi lallami anyi lallashi amman tak'i sai da aka kira daddy yazo shi da kansa ya kaita har mota sannan aka tafi Mom itama tayi kuka na rabuwa da y'ar lelenta princess Bakin wani Dank'areren gida suka tsaya tare da hn, mai gadi ya Bud'e Dank'areren gida ne babba ko bakin gate d'in gidan kawai abun kallo ne, gidan ko ta ina haske ne kamar dare baiyi ba ko ina glub ne wani wajen kuma solar lights ga fulawowi masu kyau gefe_gefe Cikin gidan suka wuce babban falo ne yaji kayan alfarma yarda falon ya tsaru hmmmmmm ban san ma ta yarda zan fara misilta muku shiba Cikin falon akwai kitchen a ciki da toilet, sai 'bangaren su zarinat ko wacce da nata, upstairs can ne d'akin yah ansar yake, 'bangaren zarinat suka wuce nan ma babban falo ne d'akin anzuba kayan alfarma masu kyau da inganci, bedroom d'akin biyu ne suka wuce da ita cikin d'aya wowwwwww ma sha allah tubarakallah ba k'arya d'akin ya tsaru matuk'a sai k'amshi yake yi, Zarinat har yanzu kuka take yi, aunty Maryam ta zauna kusa da ita tare da bata kalamai masu sanyi cikin nasiha, An kawo zarinat ba'a jima ba aka kawo husna, yarda d'akin zarinat yake haka nata yake, ita ma ba k'arya an kashe mata naira d'akin yayi kyau Su aunty Maryam sun fito zasu wuce, dama al'adar su ce idan aka kawo amarya basa jira sai ango yazo suke wuce wa, sun fito suma wad'an da suka kawo husna sun fito suka tsaya aka gaisa cikin mutumci suka fito su duka, kowa ya nufi motar da ya shigo aka mayar dasu Bayan sun mayar dasu suka dawo tare da ango aka shiga cikin falo suka zauna aka yi musu addu'a kowa ya watse, yah ansar ya dawo da rakiyar su yayi zaune a falo yad'an yi kusan 10 mint sannan ya Mik'e ya d'auki ledadodin hannun sa ya ajiye d'aya saman table d'in wajen ya nufi 'Bangaren zarinat da d'ayar................................................. *Nace ba wai kuna da labarin shahararriyar matar nan mai kawo mk maganin mata masu kyau da inganci mai siyar da kayan gyaran aure Hmmmmmmmm wannan matar shahararriyar ce wajen kawo kaya masu kyau da inganci* *In dai matsalar ki rashin gamsu ne ko rashin ni'ima bushewar gaba saurin kawowa rashin sha'awa bud'ewar gaba warin gaba k'aik'ayi rashin gamsar da mai house da dai sauran su* *To hajiyata share hawayen ki kukan ki yazo k'arshe domin malam habiba ta shirya tsaf dan ganin ta share ma duk wasu masu fama da irin wannan matsalolin hawayen su* *shahararriyar ce wajen kawo kaya masu kyau da inganci kayanta ba gaibu da yarda allahu duk wacce ta siya sai ta dawo saboda kyaun su da inganci bata kawo kayan banza* *Ga kad'an daga cikin abubuwan da take siyar wa* *Set d'in mace ta gari* *Set d'in buje jagab* *Set d'in 'bata gaban kishiya* *Set d'in mai jego* *Set d'in guguwar dad'i* *Set d'in kullum cikin ruwa* *Set d'in sabon budurci* *Set d'in mak'ura* *Set d'in ambaliya* *Tsumin zumar dad'i* *Tsumin kankana* *Tsumin bata gaban kishiya* *Tsumin ta baje* *Kacha_kacha* *Bita zai_zai* *Wayyo dad'i* *Sa kishiya tagumi* *Hana kishiya bacci* *Gumbar madara* *Gumbar kwaukwa da dabino* *Gumbar zallar haki* *Matar minister* *Sama ruwa k'asa ruwa* *Private package* *E T C* *Ga mai buk'ata akwai sauran wad'an da ban lissafo ba zaku iya tuntub'ar ta wannan number kamar haka👇👇👇👇👇* *08109623693* *Hajiyata akwai set d'in da sai kin yi rantsuwa bakyada kishi take baki saboda wannan set d'in ba'a bama mai kishiya saboda k'arfin aikin sa* *Sanyen nagari maida kud'i gida🤩💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃* Comment and share fisabillilah ♥️ 💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 7️⃣ Kai tsaye ya nufi bedroom, bakin sa d'auke da sallama ya shiga tana zaune a gefen gado ta manna bayan ta da fuskar gado, ya taka ahankali har zuwa gaban ta "Kina lafiya? " Ya tambaya kai ta gyad'a masa kana yace "Okay, tare da ajiye ledar hannun sa a gefen gadon yace "Ki samu kici wani abun sai ki kwanta ki huta"nan ma kai ta gyad'a masa Yayi mata sai da safe ya fice, har ya fita bata ce komai ba da kai take basa amsa Yana fita ta k'ara gyara zaman ta jin ta gaji da zaman yasa ta kwanta, bata jima da kwanciya ba bacci yayi awon gaba da ita ba tare da ta sani ba D'akin husna ya nufa, tana zaune a tsakiyar gado, ganin sa yasa tayi saurin janyo mayafinta ta rufe face d'in ta, murmushi ya saki tare da nufar ta ya hayo gadon ya matsa cikin ta sosai tare dasa hannu ya yaye mayafin " Amarya bakya laifi, murmushi tayi tare da kwantar da kanta gefen kafad'arsa "Babu abunda zamu ce ga allahu subhanahu wata'alah fa ce muyi masa godiya da ya nuna muna wannan ranar da muka dad'e muna son gani yau gashi ya nuna muna muna zaune a gado d'aya matsayin mata da miji "Haka ne kam dear"Yawwa to yanzu kinga sai mu tashi muje muyi alwala muyi sallah mununa godiyar mu a garesa " Sauka sukayi saman gadon suka nufi toilet tare da d'auro alwala, ya shimfid'a musu sallaya yajasu sallah raka'a biyu suka sallame ya musu addu'a, tashi yayi ya nufi kitchen ya d'auko filet da cups ya dawo ya d'auko ledar da ya shigo da ita ya ciro kaza d'aya ya d'aura saman filet ya aza a gabasu ya d'iba ya nufi bakin ta dashi ba musu ta bud'e bakin ta, ta kar'ba dan yunwa take ji Yah ansar kad'an yaci duk ita ta cinye, ya tsiyaya musu yogurt ya Mik'a mata shima ya d'auki nashi ya sha, sai da suka ci suka k'oshi ya tattara kayan ya kai kitchen sauran kazar ya saka a fridge ya dawo Har yanzu tana nan zaune inda ya barta yace "Je kiyi wanka nima na tafi nayi"Okay " ta fad'a tare da Mik'e wa sai da yaga ta shiga toilet sannan ya fita ya nufi d'akin sa dake sama Wanka tayi ta sanya wata rigar bacci red wacce da ita da babu duk d'aya dan rigar bata 'boye komai ba, kitson da aka yi mata na attach style d'in zuru tahi dabai ta saki ya zubo, ta d'auki turare duk ta feshe jikin ta dashi, k'amshin turaren sa da taji ne yasa ta d'ago kanta dan bata san lokacin da ya shigo ba, k'ofar d'akin irin wannan ce wacce idan aka bud'e bazaka sani ba dan bata da k'ara, shima yayi wanka yana sanye cikin wasu kayan bacci milk color sai k'amshi yake zubawa, yah ansar k'are mata kallo ya tsaya yi tun daga saman ta har k'asa ba laifi kayan sun mata kyau mussaman da ta saki kitson nan ya zobo, kaulbar turaren dake hannun ta ta ajiye saman mirror tare da takawa cikin sigar jan hankali ta isa wajen sa, hannuwan sa ta kama tare da d'aura su saman k'ugunta ta zageye, ta d'aura hannuwan ta gefen wuyan sa tayi ma wuyan nasa zobe da hannuwan, ido d'aya ta kanne masa tare da fad'in "Dearrrrrrr kayi kyau sosai kayan nan sun ma kyau"K'ara tallabo k'ugunnata yayi tare da fad'in "Really"Yeah " yawo ya shigayi da hannun nasa a bayan ta tana wani lumshe ido hannu yakai ya kashe light d'in d'akin ya tallabeta suka nufi gado, ya d'aurata saman gadon shima ya hau yakai hannu gefen gadon ya laluba ya kunna dim light, tashi tayi zaune ta fara cire masa botiran rigarsa ya taya ta, ta cire rigar itama ta cire tata takoma daga ita sai pant, bakin su ya had'e waje d'aya suka shiga tsotsar bakin juna, hannun sa yakai tare da cafkar breast d'in ta tayi wani irin nishi romantic d'in junan su suke sosai Tashi d'aya ya samu hanyarsa, yayi mamaki matuk'a kuma bai sha wata wahala wajen shiga ba, 'Bangaren husna kuwa itama bata sha wata wahala ba sai dai tad'an ji zafi lokacin da zai shigeta, itama tayi mamakin jin bata ji zafin da ake fad'a akwai ba, tasan d'ah namiji bai ta'ba sex da ita ba iya kajin ta da maza romantic ne bata ta'ba yarda wani yayi sex da ita ba Firgit ta tashi daga baccin da ya d'auke ta tare da tashi zaune tana murza idanunta, agogon dake manne a d'akin ta duba taga k'arfe uku har ta gota, ta sauko saman gadon ta bud'e ledar da yah ansar ya ajiye mata, taga kaji ne guda biyu a ciki sai yogurt shima biyu d'auka tayi ta fito tayi kitchen ta bud'e fridge ta saka ruwan da tagani a ciki ta d'auka har sun fara k'ank'ara ta koma bedroom ta ajiye ruwan gefen gado ta shiga toilet tayi tsarki tare da d'auro alwala tazo ta shimfid'a sallaya tayi nafila raka'a hud'u tayi addu'oin ta ta Mik'e ta nufi akwautunan ta na lefe ta bud'e ta sleeping dress ta ciro wasu riga da wando masu had'e da hula yellow ta aza saman gado ta koma toilet tayi wanka ta fito d'aure da towel, cikin k'ank'anin lokaci ta shirya ta haye gado taja bargo sai bacci Yah ansar kwance fuskar sa na kallan sama, kan husna saman k'irjin sa ta wani k'ank'amesa, fuskarta ya shafa ta d'ago tana kallan sa yace "Muje muyi wanka" fuska ta yatsina tare da fad'in "Wallahi zafi nake ji a gabana" Ayyah sorry sannu muje idan kika shiga ruwan zafi ko zai rage " To amman sai dai ka d'auke ni dan inaga harda tafiya bazan iya ba" bata ko ida rufe bakin ta ba tayi ya tallabeta suka nufi toilet, ruwa ya had'a mata masu d'an zafi ya sata a ciki, sai narke masa takeyi shi kuma abun har yad'an fara bashi haushi yadai danne dan shi baiga wata wahalar da ya bata ba dahar take masa haka, ya cigaba da fad'a mata "Sannu" sukayi wanka sannan yace suyi na tsarki yah ansar tsinkewa yayi da lamarinta dan tsaye tayi ita harga allah bata san yarda ake wankan tsarki ba, ganin dagaske take yasa yace tayi duk abinda taga yayi, da haka dai itama tayi, bayan sunyi yace ta sakeyin wani dan ya tabbatar da idan ta iya yanzu, sake yi tayi ba laifi ta iya yanzu suka d'auro towel suka fito Suka saka kayan su, agogo ya duba yaga hud'u tayi dan haka ya fasa kwanciya yaje ya d'auro alwala yazo ya kabarta sallahr lafila, husna kam gado ta haye nan da nan bacci yayi awon gaba da ita 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 "Abban humaira wallahi yau jin nake kamar kayi zamanka mu kasance a tare basai kaje kasuwa ba" Hhhhhhh maman humaira kenan idan banje kasuwar nan ba akwai matsala"To shikenan ubangiji allah ya dawo min dakai lafiya allah ya kawo kasuwa mai yawa mai albarka "Amin amin, har yayi gaba yad'an dawo tare da fad'in"kinga har na manta kema kuma baki tuna min ba ko kin fasa zuwa kitson ne?" Aah na sha'afane nima"To ai kinga gwauda da na tuna "Ya fad'a tare dasa hannu aljihu ya ciro kud'i Yace"Nawa ne?" Duk abunda allah ya hore"Dubu da d'ari biyar ya kawo hannu zai Mik'a mata har zata kar'ba gani kawai sukayi inna tazo kamar wacce aka koro da gudu tasa hannu ta kar'be kud'in har na ga hannun sa tace " Wai kai wane irin sakare ni bakasan kud'i al'aura ce ba ba'a nunasu gaban mutane bare kuma matar ka yanzu wad'an nan kud'ad'en har dubu da d'ari biyar duka na kitso ne kawai ehhh lallai dole ne tunda kana tsoron kazo jan ruwa ta hana ma idan ba haka ba taya zaka bata har dubu da d'ari biyar wai na kitso"Haba inna wallahi ba haka bane kinga unguwar da zata je nisa ne da ita a k'allah cikin ma an maka sauk'i a kaika d'ari uku to kinga zuwa da dawowa d'ari shida cikin naira dubu sauran d'ari hud'u kinsan mata ba'a rabasu da y'ar ciye ciyen kaulama sauran d'ari hud'u sai tayi amfani dasu d'ari biyar kuma ta bama mai kitson" Ahhh lallai to sannu alhaji ke"inna ta fad'a tare da Mik'a ma fatima d'ari biyar tace kar'bi "Wannan ta isa ki bama mai kitson d'ari uku ki samu abun hawa ki talla'basa ya kaiki d'ari biyu ga dawowa kuma ki dawo k'asa wallahi tafiyar k'asa ma tafi dad'i ki wana jinin jikin ki ki k'ara samun lafiya " sauran naira dubu inna ta soke ta gefen zanen ta, ta lissafa kud'in da ta kar'be na nasir taga dubu takwas da d'ari biyar ne ta cire dubu biyu da d'ari biyar ta Mik'a masa sauran tace"Kar'bi maza boye ba'a wasa da kud'i kud'i al'aura ne " kar'ba yayi yasa aljihu har ga allah abun da Mahaifiyar sa ke masa yafara isar sa sai dai ba yarda zai yi, fuskar fatima ya kallan tare da yi mata magana da idanu d'aki ta shigewar ta yace sai na dawo"To allah ya bada sa'a adan sayo muna abun motsa baki Fatima jin ya fita yasa ta fito tayi hanyar d'akin inna tare da kiran ta ta fito "Lafiya?" D'ari biyar d'in ta Mik'a mata tare da fad'in "Gashi ki k'ara kiyi abunda zakiyi" tana fad'in haka ta juya tayi d'aki, inna tabi bayan ta da kallo tare da ta'be baki ta shige d'aki............................................. *Hohohooooooooooo akace wasu kayan sai amale hajiya kina da labarin maman afnan kuwa?* *Shahararriyar likitar nan wato maman afnan da tayi fice wajen ganin ta gyara zaman takewar ma'aurata* *Hmmmmmm to idan ma bakyada labarin ta to yanzu kin sani likitar mata ce da tayi fice wajen ganin ta inganta zaman takewar ma'aurata yarda zaku zauna lafiya keda mai gidan ki da izinin allahu mai gidanki zai ji dad'in zama dake har yaji baya sha'awar ko wace mace face ke* *Ga neman ka'rin bayani zai iya tuntub'arta ta wannan number kamar haka 👇👇👇👇👇👇* *09039506644 or 09133559099* *Maman afnan likitar mata ta k'aure wajen kawo muku kaya masu kyau da inganci kad'an daga cikin kayakkinta sune* *Tana gyaran amare ciki da waje* *Had'in uwar gida* *Had'in mai jego* *Turaruka jiki dana kaya masu saukar da nishad'i* *Maganin matsi, hajiyata ki matse gam_gam* *Maganin sanyi* *Maganin mallaka* *Maganin farin jini* *Maganin k'iba* *Maganin hips, ki samu na juyawa mai house asamu na zama falo* *Maganin breast, su ciko sosai su tsaya k'am* *Maganin lalata sihiri* *Takalmi* *Ribon na gashi* *Hulah & safuna* *Mayafai, na yan k'aulisa* *Kayan kitchen, da* *Nesa tazo kusa kudai Kawai ku kasance tare da maman afnan in Sha Allah zakuji dad'in huld'a da ita🥳🤩* *Sanyen nagari maida kud'i gida🤩💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃* Comment and share fisabillilah ♥️ 💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 8️⃣ Kiran sallah da ake ne ya tadata daga bacci ta tashi zaune bakin ta d'auke da addu'a, sallahr da taji ana k'ok'arin tayarwa ne yasa tayi saurin saukowa saman gado ta nufi toilet ta d'auro alwala ta shimfid'a sallaya ta bud'e wardrobe ta d'auko hijabin ta ta saka har k'asa 'Bangaren su yah ansar kuwa, yana saman sallaya har aka fara kiran sallah ya tashi yaje yayo wata alwala ya fito zai wuce masallaci ya tada husna dan tayi sallah yana fita ta koma baccin ta, koda ya dawo ya tambeta tayi sallah tace,eh Shima kwanciyar yayi suka ci gaba da bacci Misalin k'arfe sha d'aya na rana bugun Kiran da ake masa ne a waya ya farkar da su, Tashi yayi ya sauka saman gadon ya nufi inda wayar take, yana isa kiran na tsinkewa saiga wani ya sake shigowa, sunan minal yaga na yawo akan screen d'in wayar, D'auka yayi Daga d'aya 'bangaren akace "Yaya gani bakin k'ofa tun d'azu nazo ina ta kiran wayarka ba'a d'aga ba "Okay ina zuwa"ya fad'a tare da kashe kiran Ya kama hanya zai fita " Dear ina zakaje?" Minal ce tazo tana waje "Okay" Bud'e mata yayi ta shigo hannun ta d'auke da basket, gaidasa tayi tare da tambayar su zarinat suna lafiya, ta Mik'a masa sukayi sallama ta wuce, kulolin abincin guda hud'u ne dan haka ya cire guda biyu ya nufi d'akin zarinat dasu ya kai mata, da alama ma bata tashi ba dan haka kai tsaye ya nufi bedroom d'in ta, hangota yayi kwance tana bacci screen d'in wayarta dake kusa da ita yaga yakawo haske, tsaye yayi yana k'are ma surar jikin ta kallo tun daga sama har k'asa, kayan baccin dake jikin ta sun masa kyau sosai, gasu irin wad'an nan ne na roba wad'an da ke mannewa a jikin mutum, juyawa tayi cikin baccin ta basa baya, saurin d'auke idanunsa yayi a kanta ganin yarda mazaunanta suka fito sosai cikin wandon, gefen gadon ya nufa ya ajiye kulolin, hannu yasa ya janyo wayar ta data haye wajen juyi, har yanzu screen d'in da haske dubawa yayi yaga karatun k'ur'ani ne take yi, bacci ya d'auke ta, Danna power yayi ya kashe wayar ya aza mata ita saman drawer sake kallan ta yayi tare da sakin murmushi wanda shi kansa baisan yayi ba ya wuce Yana fita tana bud'e ido, k'amshin turaren sa da taji ne yasa ta tashi zaune tare da dube_dube idanun ta suka sauka akan kulolin da ya ajiye, wanda ya tabbatar mata daya shigo d'akin ne Saukowa tayi saman gadon ta bud'e kulolin, d'aya dankalin turawa ne da kwai d'aya kuma dafaffiyar kaza ce, rufewa tayi ta gyara gado d'akin baiyi datti ba amman sai da ta d'auko mashari tad'an sharesa sama_sama ta kunna turare sannan ta fad'a toilet Nasu abincin ya d'auka ya nufi d'akin husna, tana nan zaune saman gado saima wayarta data janyo tana charting, ganin sa yasa tayi saurin kashe wayar tare da fad'in " Abinci ne aka kawo muna?" Eh ki tashi kije kiyi wanka sai mu ci "okay,ta fad'a tare da sauk'owa tayi toilet shima fita yayi ya nufi d'akin sa Zarinat, wanka tayi ta had'e cikin wata atamfa d'inkin doguwar riga, tayi d'aurin ture, ta gyara face d'in ta, sai lipgloss d'in da ta shafa ta saka awarwaro masu kyau sai k'amshi take zubawa tayi kyau sosai, ta d'auko kulolin abincin ta yo falo ta nufi dinning table ta ajiye taje ta d'auko filet ta zuba iya wanda tasan zai isheta ta d'auko ruwa tayi zaune ta fara cin abincin ta Wanka yayi ya shirya cikin wani yadi mai fari mai kyau kallo d'aya zakayi ma yadin kasan na manya ne, an masa d'inki mai kyau na zamani, k'amshin turaren sa keta tashi, ya nufi d'akin husna, tsaye take gaban mirror tana gyara d'aurin da tayi, tana sanye cikin kamfala d'inkin bubu ta zubo kitson nan na attach a baya tayi kyau abinta Murmushi ta sakar masa shima ya mayar mata, takawa tayi har inda yake ta mak'ale hannun ta a kafad'arsa " Dear" uhm "Banyi kyau bane"Kinyi mana sosai "ya fad'a tare da k'ara matsota jikin sa"Naji baka yaba ba "Uhm saurin magana ne kawai kika yi"dagaske?" Yeah" ya fad'a tare da d'aga mata gira " To abani goron wannan wankan"Okay, ya fad'a tare da had'e bakin su waje d'aya ya shiga tsotsa, sunyi wajen 5 mint suna tsotsar bakin juna sannan ya saki bakin ta tare da fad'in " Muci abinci sai na baki babban goru" Murmushi tayi tare da shafo gemun sa D'aukar abincin sukayi suka dawo falo............................................... Comment and share fisabillilah ♥️ 💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 9️⃣ Abinci suka ci suna gamawa suka koma bedroom suka fad'a duniyar ma'aurata, yin ranar duk a d'akin husna yayi shi kiran sallah kawai ke fitar dashi yaje yayi sallah, ita kuma daya fita ta d'auro sallaya ta shimfid'a ta saka hijab ta d'auko waya tayi zaune tana charting da yan samarinta ba tare da tayi sallahr ba, koda zai dawo masallaci ya tarda ta zaune saman sallayar duk a tunanin sa tayi sallar ne ta zauna tana lazumi Ammi ta aiko musu abincin rana dana dare Yau sati d'aya da auren su, amman tun ranar da ya shiga 'bangaren zarinat ya kai mata abinci ya sameta tana bacci har yanzu bai sake shiga 'bangaren nata ba kuma bai sake ganin ta ba, saboda minal ke kawo musu abinci sai ya d'auki nasu ya Mik'a mata na zarinat ta kai mata Soyayyar su suke sha sosai shida husna suna gurzar amarcin su yarda ya dace Husna tuni tasa Mahaifiyarta ta nemo mata yan aiki wand'an da zasu rik'a yi mata girki da gyaran d'aki Sai dai basu fara girki ba saboda ammi ke aiko musu abinci gyaran d'aki kawai suke yi Yau minal bata samu zuwa ba aka bama driver ya kawo musu, bayan driver ya kawo ya wuce yah ansar ya kira ammi tare da fad'a mata, ta bar girkin haka nan sun gode sosai, ammi tace to shikenan daman na sati d'aya taso ta musu amman tunda yace tabarsa hakan shikenan D'aukar nasu yayi yakai 'bangaren husna tana kwance tana bacci, ya fito ya d'auki na zarinat yayi 'bangaren ta, murd'a hannun k'ofar yayi ya jisa a bud'e ya tura tare da yin sallama ya shiga, Yana tura kansa wani irin ni'iman taccen k'amshin turaren garwashi ne ya ziyar ci hancinsa sai da ya lumshe ido ga sanyin AC daya ratsa sa, kwance take saman had'ad'd'un kujerun ta na alfarma mai mazaunar mutum hud'u, idanunta na ga TV da ta kunna tana kallo amman kallo d'aya zakayi mata kasan hankalin ta baiga kallon ta fad'a duniyar tunani ne, tana sanye cikin wani material yellow d'inkin riga da siket irin d'inkin nan na dai_dai jikin ka wanda za'a fito maka da shape d'in jikin ka sai yan kunnen sarkarta ta gold da tasaka, bata son sark'a shiyasa bata cika sakata ba sai dai idan ta belo mata wani lokacin ta saka, hannunta kuma sanye da wani awarwaro mai kyau sai kyalli yake yi, tayi kyau sosai K'afafuwan ta yake kallo k'unshin da akayi mata wanda ya fara gogewa sai ya bada wata kala mai kyau, Dogon numfashi taja tare da rufe idon ta ta sake bud'ewa k'amshin turaren sa taji duk ya mamaye hancinta ta d'ago kanta tana dubin hanya had'a ido sukayi ta tashi zaune, d'ankwallin kanta ya Fad'i gashin ta ya bayyana, "Ya salam" yah ansar ya fad'a lokacin da ta Mik'e zaune ganin yarda breast d'in ta suka cika tam kamar zasu fasa rigar su fito duk sun bullo ta saman rigar D'ankwallinta ta d'auka tare da aza d'ankwallin a kai yarda ta d'ora sa saima yafi mata kyau bisa ga d'aurin da tayi K'arasowa yayi wajen ta tare da ajiye kular hannun sa ya zauna saman kujerar da take zaune, sauka k'asa tayi tare da duk'awa cikin girmamawa tace "Yaya ina wuni" Lafiya k'alau, ya fad'a murmushi d'auke akan fuskarsa yace "Fatan kina lafiya?" Alhamdulillah " Ma sha Allah, taso ki zauna" ta fad'a yana nuna mata inda ta tashi Ba musu ta tashi ta zauna, dukan su shuru sukayi saima shi da ya mayarda hankalinsa kan TV ita kuma kanta a k'asa tana wasa da awarwaro dake hannun ta " Tunanin me kike yi?" Taji ya jefo mata tambaya, d'agowa tayi ta kallesa taga fuskarsa nakan TV sake duk'ar da kanta Kawai tayi taci gaba da wasa da awarwaron Juyowa yayi ya kalle ta tare da kallan hannun ta da take wasa dashi " Tunanin me kike yi?" Ya sake tambayar ta Ahankali ta furta "Ba komai" ba tare da ta d'ago kanta ba "Bakomai zan shigo tayi ta sallama amman bakiji ba" yayi maganar tare da k'ara gyara zaman sa yana kallan ta, shuru ta masa batace komai ba ganin bata ce komai ba kuma karya takura ta yasa yace "Ga abinci nan anjima baza'a kawo na dare ba ku zaku rik'a girka kayan ku daga yau"To mungode sosai Allah yasaka da alkhairi " Amin sai ki duba idan akwai abinda kike da buk'ata wanda bakyada ki rubuta idan an fito sallah zan bayar a siyo"To"tashi yayi zai wuce tayi saurin cewa "Uhmm yaya"Naam "ya fad'a tare da juyowa ya kalleta d'an shuru tayi ya koma ya zauna tare da fad'in"mene ne ina sauraranki Fad'i me kike so?" Yaya daman ina son na koma makaranta ne"Shuru ya d'an yi can yace "Okay amman ba wannan satin ba sai wani sati "Allah ya kaimu"Amin shikenan?" Kai ta gyad'a masa ya tashi ya wuce.................................................. Comment and share fisabilillah ♥️ 💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 1️⃣0️⃣ D'akin husna ya shiga ya tarar da ita kwance tana video call, ganin sa yasa tayi saurin kashe wa tare da kashe wayar gabaki d'aya ta ajiye a gefe tare da sakin murmushi,wanda da ga kanta kasan batada gaskiya Ya lura da hakan amman sai kawai ya basar yace tayi list d'in abubuwan da take da buk'ata na kayan girki wanda bata da Wayarta ta kunna tare da kiran lami d'aya daga cikin masu yi mata aiki tace "Ta shiga store ta duba duk abinda babu ta rubuto ta kawo mata" 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Fatima yau koda ta tashi bata jin dad'i sai dai bata nunama nasir ba kar ta hanasa zuwa kasuwa inna tazo tayi ta masifa shiyasa Kawai tak'i sanar masa, aikuwa ciwo kamar jira yake ya fita ya k'aru zazza'bi ya rufe ta Har shabiyu ta wuce inna taga bata fito ta d'ora musu girki ba ga cefane nan an kawo tun d'azu har ta kama hanya zataje d'akin na su, sai taji sallamar aunty larai yayar fatima, tayi saurin komawa bakin k'ofar ta, Tun da aunty larai ta shigo inna ke mata wani kallan uku saura kwata, aunty larai ta lura da ita tsaff da irin kallan da take mata, dan da aunty larai da inna tasu bata jitu ba inna nuna isa da iko da masifa da sakin magana duk yarda tazo mata ba ruwanta, ita kuma aunty larai rashin hak'uri "Aikin banza a ka ce ga banza anwa kuti bulala" aunty larai ta fad'a tare da wucewa dan tasan idan tace zata tsaya to bazasuyi mai kyau ba gashi kuma ita ta isko ta dan haka koda ita ce da gaskiya za'a ce batada gaskiya don ita ta sameta har gida "To yarda aka zo haka za'a koma ba'a girka ba bare a yi zaune a bud'e rumbun ciki ayi ta ci ba" Inna ta fad'a sosai yarda aunty larai zata ji, aunty larai har ta fara cire takalmi taji abinda inna ta fad'a ta mayar da takalmin tare da juyowa ta dawo ta tsaya gaban inna tace "tsohuwa Kallan ni da kyau ki gani, aunty larai ta fad'a tare da juyawa" Kinga alamun yunwa a tare da ni? Ko namiki kama da maicin irin wannan abincin naku "K'aryar banza har ni za'a nunama arziki "Wallahi dole a nuna miki kinsan ko gaba da gabanta in banda k'addara mai zai kawo fatima a gidan nan bare har aji wai anan take aure mtsssssww kai allah dai wadaran naka ya lalace "K'addarar nan da kika kira ita ta kawo ta sannan da naci ta nace masa sai da ya aure ta " Hehehehe sauya magana dai naci wallahi ba wanda baisan yarda d'anki ya nace mata ba tana da wanda zata aura yazo ya lik'e sai da akayi da shi " yanzu dai koma mine ne ke ya dama" Mtsssww, aunty larai taja tsaki tare da juyawa "Me kike fad'a idan ba tsoro ba ki dawo ki fad'a? " Kanki akeji mahaukacin ya fad'a rijiya " D'akin ta shiga ta ga Fatima kwance ta kudumdume cikin bargo"Iyyeeeee lallai yarinya baccin kima kike yi "ta fad'a tare da sa hannu ta yaye bargon, idan ta biyu ba bacci take ba sanyin da take jine yasa ta lullu'be aunty larai takai hannu ta ta'ba ta tare da fad'in"Bakyada lafiya ne?" Kai ta gyad'a mata" Subhanallah sannu ina nasir? Yasan bakyada lafiya?" Nan ma kai ta gyad'a mata" wayarta aunty larai ta d'auka ta lalubo number nasir bugu d'aya ya d'auka ta sanar masa gata tazo ta sami Fatima ba lafiya zasuje asibity, yace to shikenan in Sha Allah shima gashi nan tafe ta kashe wayar Hijab d'in ta ta d'auko mata ta saka mata ta taimaka mata suka fito, inna na d'aki suka fice da motar ta tazo dan haka basu tsaya neman wani taxi ba suka wuce asibityn dake kusa dasu suka je aka amshe ta suka yi gwaje_gwajen da zasuyi suka ga maleria ce da ita suka rubuta maganin da za'a siya, nasir ya iso aunty larai tace ya tsaya wajen ta taje ta siyo magani, an saka mata ruwa ko zataji k'arfin jikin ta Aunty larai taje ta siyo maganin ta dawo, ruwa na k'arewa aka sallame su, aunty larai tace nasir ya koma Kawai kasuwa dan yanzu jikin nata yayi sauk'i sosai, godiya yayima aunty larai sannan ya wuce suma suka wuce saman hanya ta tsaya ta siya mata hanta gashashshiya, da kayan marmari Suna shigowa gidan inna na fitowa daga d'aki, da kallo ta bisu tare da tunanin yaushe suka fito to, Hannun aunty larai inna ta kallah ganin uwar zundur cike da kayan marmari, sai da ta had'iyi yawu, had'a ido sukayi da aunty larai suka sakarma juna harara aunty larai tace "Nan gani nan bari" Fatima ta gaida inna amman ko kallo bata isheta ba bare ta amsa suka wuce d'aki Suna zaune saiga wata yarinya inna ta aiko yarinyar mak'otansu tace "Wai hajiya tace ki fito ki d'ora girki"aunty larai tace "Je kice ni hajjatani larai ita idan haji sau d'aya taje to ni hajjatani larai nace baza tayi ba kinji "yarinyar tace" Eh " Tazo ta sanarma inna abunda tace, inna ta koma d'aki dan bata iyawa dan ma yau sunyi da sauk'i ita da aunty larai Aunty larai bata wuceba sai da taga jikin Fatima ya dawo normal sannan ta wuce, tana fita inna ta shigo d'akin tayita zazagama fatima masifa tare da fad'in ta tashi ta d'ora musu girki, ta bud'e ledar kayan marmarin ta d'ibi wanda take so ta fito allah dai bai kai idanunta ga ledar hanta ba da itama sai taci Fatima ba yarda ta iya haka ta fito ta d'ora girkin... 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 "Wai baki gama girkin bane? " Yah ansar ya tambayi husna" Wallahi bansani ba ko sun gama " Ban gane baki sani ba ko sun gama wai badai kina nufin harda ni abincin yan aikin nan zanci ba "Eh mana"Hmmmmm kema kinsan bazai yuwuba dan Wallahi bazan ci abincin da yan aikin nan zasu girka ba "To yanzu me kake so? " Ki tashi ki girka min nawa " Ai kasan ban iya girki ba" Baki iya girki ba?" Ya fad'a cikin jin mamaki da furucin ta" Eh" kallanta yake yama rasa mezai ce Tace " To idan bazaka ci ba kaje gida wajen ammi ka ci " Miye amfanin auren nawa da nayi indai har zanje gida cin abinci" Ta'be baki tayi ta koma ta kwanta Fita yayi daga d'akin ransa a 'bace ya nufi d'akin sa, Zarya ya rik'a yi cikin d'akin shidai bazai iya cin abincin yan aikin ba kuma baya iya cin abincin siyarwa sannan bazai iya zuwa gida cin abinci ba dan abun akwai kunya gashi yunwa yake ji to yanzu mezanyi? Ya fad'a a fili, toilet ya shiga yayi wanka ya fito d'aure da towel a k'ugunsa yaje gaban mirror kamar mace ya shafa wannan ya shafa wancan ya gama ya saka boxer ya zura jallabiyar sa ya haye gado yayi kwanciyarta sa, cikin sa yaci yana k'uwa dan haka ya tashi zaune tare da zura takalmin sa ya sauko saman gado, ya nufi kitchen d'in 'bangaren sa, Tsaye yayi yana tunanin mezai dafa shida ba girki ya iya ba Lipton kawai yasan ya iya dafawa, k'arasawa ciki yayi ya dafa tea ya fito dashi............................................... Comment and share fisabilillah ♥️ 💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 1️⃣1️⃣ Zama yayi saman kujerar d'akin, ya shanye tea d'in gabaki d'aya ya ajiye cup saman table d'in wajen, cikin sa ya shafa wanda yakejin yanzu kam alhamdulillah ya k'oshi ya jima zaune a wajen sannan ya Mik'e ya nufi gado ya hau ya kwanta agogon hannun sa ya cire ya aje a gefen sa, ya lumshe idanunsa da haka bacci yayi gaba dashi Husna ganin har goma ta gota bai shigoba yasa taji dad'i dan a takure take tana san tayi wayarta sosai, kuma tunda yakai wannan time d'in bai shigoba tasan ba'a nan zai kwana ba, ta tashi ta saka wata arniyar rigar bacci wacce bata 'boye mata komai ba, tana gama saka rigar aka kira ta a waya, number bata nan ce ba number k'asar waje ce, d'auka tayi cikin hanzari ta kara a kunne banji abinda aka ce daga d'aya 'bangaren ba amman naji tace " Sorry gani nan" ta kashe kiran tare da hayewa gado ta kunna data sai gashi an kira ta video call da number nan cikin sauri ta d'aga tana wani yauk'i irin na yan barikin nan Fira suka d'an ta'ba da mutumen zuwa can yace "Wai yaushe zaki dawo ne?" In Sha Allah nan bada jimawa ba zan zo " Gaskiya kam ya kamata nayi kewarki sosai ina mijin ki ne?" Yana d'akin sa " ta fad'a tare da ta'be baki " Beb tun da na d'and'ani zumar ki naji ba macen da nakeson na kasance koda yaushe a tare da ita kamar ke " Murmushi ta saki tare da fad'in"Wacce irin zuma kenan? " Dariya yayi irin ta shak'iyan nan kana yace" Zan baki wani labarin da bakisan dashi ba " Wane irin labari ne? Ina jinka" Kin tuna kafin ku wuce kusan kwanan ki biyar a waje na iya kar mu romanc kin hanani na kusan ce ki, da naji labarin aure zakiyi naji bazan iya hak'ura wani d'ah namiji ya fara sex da ke ba kafin ni shine na nemo k'waya mai k'arfi na zuba miki a lemo kika sha na biya buk'ata ta kwanan ki biyu kina bacci kin tuna lokacin da kika farka kika ce min jikin ki duka ciwo yake miki?" Shuru tayi tana nazarin kalamansa tare da zancen zuci" Kenan na dad'e da rabuwa da budurci na ba ansar bane ya kar'bi budurcin ba to ya akayi hakan ban gano ba? Hmmmmmm lallai odo sai na nuna masa kuskurensa na kusan ta ta ba tare da sahalewataba duk da hakan dai nagode allah da yasa ansar bai gane komai ba "Hi beb " Numfasawa tayi tare da kallan wayan ta banka masa harara ta cikin wayan ta kashe kiran, tana kashewa ya sake kira ta kashe da taga zai dameta sai ta kashe wayar gabaki d'aya Yau kwana hud'u kenan yah ansar kullum cikin shan tea yake da safe da rana da dare saboda bazai iya cin abincin masu aiki ba, ita kuma husna ba iya girki tayi ba gashi yana jin kunyar yaje gida yace ma ammi ta samai abinci dole ya hak'ura ya rik'a shan tea Misalin k'arfe goma na safe ya shiga 'bangaren ko wacce yace suzo babban falo zasuyi magana, ya dawo falon ya zauna jiran su, husna ta fara fitowa tana tafiya tana juyi sanye da wasu k'ananun kaya riga da wando, yah ansar kallo d'aya yayi mata ya d'auke kai shi baisan miyasa take son saka k'ananun kaya ba gashi ko kyau basa mata idan ta saka su ta koma Kamar wata balbela K'ara sowa tayi tare da zama kusa da shi cinyar su na gugar ta juna, Kwantacen sajen sa wanda yasha gyara ta shafo tare da fad'in "Dear naga kamar ka rame kodai idanuwa na ne" Hmmmmmm ba dole na rame ba kina barina da yunwa nine koda yaushe sai dai nasha tea da auren ka " Sorry kar ka damu akan ka Kawai zan koyi girki zansa a turomin video's na girki kala_kala sai abincin da kake so zan girka " ya bud'e baki zaiyi magana k'amshin turaren zarinat ya bugi hancin su gabaki d'aya d'agowa sukayi tare da kallan hanyar d'akin ta Sanye take da wani material red mai masifar kyau an masa d'inkin da ya k'ara fito dashi sosai, kuma ya mata kyau kunsan dai yarda abu red yakema farar mace kyau hmmmmm ta saka sark'a ta da awarwaro na alfarma, yau kam har powder ta shafa ta mata kyau sosai ita dai ce bata san shafawa, sai lipgloss d'in da ta sha ta gyara girar ta, kamar abunda aka zana, sai k'ara min mayafinta da ta yafa white, takalmintama white shoes, hannun ta dafe da waya a kunne da alama waya takeyi, yarda takeyi ne zai tabbatar maka da mom takewa saboda yarda take zuba shagwa'ba Husna cikin ta ne ya murd'a ganin zarinat dan bata ta'ba tsammanin takai kyawon haka ba tasan nesa ba kusa ba tafita da komai Sallama sukayi da mom ta k'ara so wajen tare da duk'asawa ta gaida yah ansar, wanda ya kafeta da ido tun d'azu, amsawa yayi cikin fara'a ta tashi ta zauna Gyaran murya yayi tare da fad'in "Abinda yasa na tara ku anan bakomai bane face na samar muku driver na nan yazo wanda zai rik'a kai ku duk inda zaku je sai kuma abu na biyu wanda jan kunne ne a gareku ban yarda ba ban lamunce ba d'aya daga cikin ku tahau taxi ba idan ma ta kama dole sai kun hau to tare da k'auk'auran dalili wanda zaisa khau kunji ni dakyau? " Ya fad'a tare da kallan su zarinat ya gyad'a masa kai husna kuwa bata ma san me yake fad'a ba tanacan ta fad'a duniyar tunanin yarda zata k'ara mallake yah ansar ya zamana ba macen da yake so da K'auna kamar ta Yah ansar ya kira sunanta da k'arfi ta zabura, zarinat ta d'ago ta kalleta suna had'a ido husna ta harari zarinat itama ta mayar mata Yah ansar yace" Kin ji mena fad'a banyarda da hawan taxi ba " Murmushi ta saki tana k'ara shigewa jikinsa tare da fad'in "Dear ai kaima kasan bana hawan taxi " Good zaku iya tashi " yana fad'in haka zarinat tayi saurin Mik'e wa dan bazata iya jurar kallan wannan iskancin da taga husna nayi ba Yah ansar baiso ta tashi ba jin yayi kamar ya bita yayi ta kallanta shi kansa baisan dalilin da yasa yake son kallanta ba Suma tashi sukayi suka nufi d'akin husna Zarinat na shiga ta fara aikin abinci ta gashi yau zatayi bak'i yan department d'in su sunce zasu zo, tun da safe ta surfe wake dan alale ce zatayi K'arfe goma sha biyu, yah ansar zaune yana aiki a system d'in sa dan yau baije aiki ba gaba d'aya bayajin dad'in jikinsa, wayarsa ce ta fara rura alamun kina na shugowa d'auka yayi yaga sunan faruk abokinsa ne ya kara a kunne, daga 'bangaren faruk yace " Gamu bakin door " au haba dan allah " Nidai zoka bud'e muna kasan madam yanzu ba jurar tsayuwar nan takeyi ba" Yana fad'in haka ya kashe kiran, ya juyo ya kalli matar sa tare da fad'in"Sorry gashinan tafe............................................... Comment and share fisabilillah ♥️ 💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 1️⃣2️⃣ Aje aikin da yakeyi yayi yaje ya bud'e musu k'ofa, murmushi d'auke a fuskarsa ya bama faruk hannu suka gaisa tare da k'ara sowa cikin falon suka gaisa da zarah Yah ansar yace " Ko sanarwa babu sai dai kawai na ganku girshi "Ai daman nace idan zamu zo bazan sanar maka ba sai dai ka ganmu ahhahhh ango! ango! ango kasha k'amshi " Hhhhhhh kai bana san iskanci muje ciki ku fara ganin husna sai muje wajen zarinat"Okay let's go " faruk ya fad'a tare da kama hannun matarsa suka nufi 'bangaren husna yah ansar gaba suna biye dashi a baya Waje ya basu suka zauna ya wuce uwar d'aki dan kiran husna, Tana nan kwance tana abunda ta saba ( chart kenan) sanar mata yayi ta fito sunyi bak'i, tace " To bak'i kuma daga ina? Su waye? " Idan kika zo zaki gansu " yana fad'in haka ya fice Yatsina fuska tayi tare da jan tsaki tace"Mutum na tsaka da jin dad'insa azo a katse masa" ta fad'a tare da Mik'e wa ta nufi hanyar falo Tana zuwa bako sallama ta samu waje ta zauna tare da d'aura k'afa d'aya saman d'aya tana dannar waya, zarah ta saki baki tana kallanta Yah ansar yayi gyaran murya tare da fad'in "Husna miye haka kinyi bak'i amman zaki shigo ki zauna ko sallama baza ki musu ba" D'agowa tayi tare da fad'in " Ohhhhhhhhhhh I'm very sorry i forget wallahi kasan abubuwan ba d'aya ba ina wani abu ne a phone shiyasa hankali na ma baya nan sorry fa, ta fad'a tare da kallan su faruk zarah ta cika sosai dan taga wulak'ancin na husna yayi yawa wato ma bata ko lura dasu ba bayan kuma akan su aka kirata ta fito Yah ansar yace "Abokina ne faruk wanda nake baki labari sai kuma matar sa zarah" " Ayyah Sannun ku" Yawwa sannu fatan kuna lafiya ya amarci?" Faruk ya fad'a" fine " ta fad'a tare da ci gaba da latsar wayarta Zarah ta sakarma faruk harara na kula ta da yayi Yah ansar shima baiji dad'in yarda ta musu ba Zarah tace" Muje muga d'ayar sai mu wuce dan inaga ba dad'ewa zamuyi ba "Okay ku tashi muje" duk suka Mik'e "Amarya mu mun wuce" faruk ya fad'a ba tare da ta d'ago kanta ba tace " Okay sai anjuma" Mu jima da yawa" zarah ta fad'a tare da yi gaba ta barsu a baya, suma biyota sukayi 'Bangaren zarinat suka nufa Bakin su d'auke da sallama suka shiga, wani irin daddad'an k'amshi ne ya ziyar ci hancinsu, suka shiga raba ido musamman zarah da take d'auke da jaririn ciki, ba kowa a falon sai TV dake kunne tana aiki, zarah ta rik'a kallan falon ba k'arya kayan sunyi masifar kyau sun mata kyau ga yarda kuma aka tsara komai zaa kyau Yah ansar ya nuna musu waje su zauna, ya nufi bedroom d'in ta dan kiran ta har ya kusa kai sai gata ta fito ta sauya kayan d'azu tana sanye da abaya black tasha kyau sosai, mayafin abayar ta d'aura sa saman kafad'arta ta kama gashin kanta da white ribbon 🎀 hannunta rik'e da wayarta, tana tunanin yarda zatayi da alaler da ta dafa tunda su saudat sunce ba zasu samu daman zuwa yau ba sai wani lokaci Yah ansar ta gani tsaye a gabanta, baki ta bud'e zatayi magana yayi saurin cewa "Kinyi bak'i muje ki gansu abokina ne tare da matar sa"To,ta fad'a tare da d'ora mayafinta a kai suka k'ara so cikin falon sallama tayi duk suka amsa ta zauna tare da fad'in " Sannun ku da zuwa ya hanya" Alhamdulillah,duk suka fad'a, zarah ta sake fuskarta dan da ganin zarinat tasu zata so d'aya ba irin husna ba ce tare da yaba kyawon zarinat a zuciyarta Mik'e wa tayi ta nufi kitchen taje ta d'auko lemon juice ya d'au sanyi sosai da cup's uku ta d'ora saman filet takawo, ta ajiye tare da zuzzubawa ta Mik'a ma kowa zata Mik'a ma yah ansar sai da tad'an duk'a cikin bangirma ya amsa, yana jin dad'in yarda ta kar'be su Zarah tasha lemon tare da fad'in "Waiii kin sanyayamin zuciya ta daga 'bacin rai da ta shiga" Yah ansar da faruk duk sun gane mai take nufi Zarinat tayi murmushi "Ni nama manta ban gabatar miki dasu ba" yah ansar ya fad'a yana kai cup bakin sa " Wannan abokina ne faruk duk cikin abokai na dashi muka fi shak'uwa wannan kuma matarsa ce Zarah in Sha Allah muna sa ran nan da wata shidda zata haifo muna d'an mu" Lahhhlahhhlahh kace har an kawo ma rahoto " zarah ta fad'a cikin wasa" Tun yaushe kedai allah ya sauke ki lafiya "Hmmmm amin ai kaima kamar gobe ne za'a cemin matarka zarinat nada ciki, zarinat ta kalli zarah tare da sunkuyar da kanta k'asa yah ansar ya kalleta tare da sakin k'ayataccen murmushi " Waya sani ma ko ta harbu" faruk ya fad'a" Wallahi fa abu a duhu waya sani"zarah ta fad'a Zarinat ta Mik'e tare da fad'in"ina zuwa" ta nufi kitchen, yah ansar yace" kun gani ko kun korar min mata kunya gareta sosai " Uhmmm kunya ko duk nan muka fito takalmin mu suka tsinke" cewar zarah duk suka sa dariya Kulolin abinci ta kwauso daga kitchen takai dining ta aje ta koma kitchen ta d'auko filet guda uku, ta bud'e kular da alalen ke ciki ta banye leda uku uku ta zuba a filet, kasan cewar manyan d'auri tayi shiyasa ta zuba ma ko wane filet uku_uku amman banda d'ayan bata zuba na d'aya filet d'in ba tasa spoon ta yayyanka tsakiyar a lalen, ma sha Allah mai kwai ce a ciki tayi, ta zuba sauce d'in da tayi mai kayan ciki a ciki abun sai wanda ya gani gwaunin burgewa sai k'amshi ke tashi Ta d'auko ta nufi falo, ta ajiye d'aya gaban zarah d'aya kuma gaban faruk ta koma kitchen ta d'auko musu ruwa masu sanyi, ta koma dining dan had'ama yah ansar nashi zarah k'amshin alalen ya bugi hancin ta yawunta harsun kawo ta d'auki filet d'in ta tare da fad'in "Kaii allah dai ya biyaki matar nan kamar kinsan abunda nake so" ta fad'a tare da kai loma d'aya sai da ta lumshe ido tun da take bata ta'ba cin alalen da tayi mata dad'i sosai ba kamar wannan "Ma sha Allah wallahi alalen nan tayi dad'i sosai" Uhmmmm" faruk ya fad'a dan ko magana ya kasa, yah ansar dariya sa yake yi ganin yarda suke yaba girkin Dawowa tayi falon hannunta d'auke da filet wanda ta Had'oma yah ansar d'auri hud'u ta saka masa, aje filet d'in tayi taja table d'in dake wajen takai gabansa ta d'auko filet d'in ta aza tare da turawa gabansa taje ta d'auko masa ruwa, koda ta dawo harya fara ci shima girkin ba k'ara min dad'i ya masa ba duk da bai ta'ba cin alale ba amman yaji dad'in ta sosai, Kowa ya cinye tasa tasss, bare yah ansar da ya kwana biyu baici abinci irin haka ba kullum tea ne Zarah tace "Gaskiya sai nazo kin koyamin yarda ake irin wannan alale mai dad'i haka"Murmushi Kawai tayi To ciki ya d'auka aka fara fira zarinat tun tana kaucewa har itama tasa bakin ta cikin firar, Kiran sallah ne ya tada su maza sukayi masallaci sukuma sukayi alwala suna gama sallah suka ci gaba da fira, Su faruk basu shigo gidan ba har sai da akayi sallahr la'asar Basu wani jima da dawowa ba suka tashi zasu wuce, zarinat ta bama zarah abu cikin leda ta kar'ba tare da yi mata godiya suka fito itama ta rako su sun fito babban falo sai ga husna ta fito daga 'bangaren ta kallan mamaki take musu dan ita duk a tunanin ta sun wuce tun d'azu k'ara sowa tayi tare da fad'in "Ashe kuna nan baku wuce ba" Eh wallahi muna inda akasan darajjarmu " Zarah ta fad'a "Okay " husna ta ce dan bata gane abunda take nufi ba, zarinat ta musu sallama suka wuce ta koma 'bangaren ta.................................................... *Karfa a manta paid book ne ba tsada 200 only haryanzu muna cikin free page's ne mun kusa gama free page's * Comment and share fisabilillah ♥️ 💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 1️⃣3️⃣ "Mik'o min nan ki gani" inna ta fad'a tare da zafce ledar hannun fatima "Haba inna kin dai san naman nan idan na dafa ba ci zanyi ba sai na kawo miki ki d'ebe muna namu" Baci zakiyi ba oho wannan kuma ke ya dama amman nama sai na lissafa naga ko tsoka nawa ce a ciki " Fatima ta girgiza kai tayi tsaye tana jiran ta gama lissafawa ta bata " Yawwa kingani gwaunda da na lissafa gashi nan an samu ka'rin tsoka biyu da ban lissafa ba nasan wufff zakiyi dasu " Fatima hannu Kawai tasa ta kar'bi naman tayi kitchen, har ta wanke naman zata zuba a tukunya sai wata zuciya ta bata mezai hana ta ragema naman girma in yaso sai ta kaima inna adadin tsokokin da ta lissafa Haka kuwa akayi ta d'auko wuk'a ta fara rage musu girma, daman tsoka goma sha biyar ce da k'ashi uku, Tsoka goma ta ragema girma sauran biyar d'in ta barsu suka kama tsoka ashirin da k'ashi uku "Hhhhhhhhhh inna in kinsan wata ai bakisan wata ba"ta fad'a tare da sakin murmushi ta k'ara wanke naman ta zuba a tukunya tare da yanka albasa da kayan k'amshi Tana kitchen tana aikin ta, taji sallamar nasir ta fito kusan a tare suka fito ita da inna " Sannu da zuwa" Fatima ta fad'a "Yawwa" " Har ka dawo?inna ta fad'a" Nazo ne na kawo mata abun nan na koma " Nagani me aka siyo muna banga ledar na matsk'iba" ta sa hannu ta kar'bi ledar kayan kwalliya ne a ciki su powder, jan baki, lipgloss, jagira, barbad'a kumatu, k'yalk'alin balaga, duk sune a ciki inna ta washe baki tare da fad'in "Aah kayan kwalliya ne aka siyo muna " Nasir yayi dariya najin furucin inna yace "Haba inna in banda abunki ina ke ina kuma wasu kayan kwalliya wannan fa fatima na siyoma ai ke kin wuce lokacin wad'an nan kayan " " Bangane ba "inna ta fad'a tare da kallan nasir"Nice na fad'a maka na wuce yin kwalliya ko kuwa? Ohhh so kake ka mayar dani tsohuwar k'arfi da yaji ko to baka isa ba yarda kasan matar ka zata shafa tayi kyau nima haka zan shafa dan ba'a fini kyau ba kuma nima ina san da an kalli fuskata aga tayi haske kai wallahi da ganin powder nan zata min kyau " ta fad'a tare da ciro k'yalk'alin balaga tana murmushi " Nasan yarda take k'yalk'alin nan nima haka zan rik'a yi amman na lura kanasan ka mayar dani baya haba wannan ai muma lokacin mune zamanin mu ne" powder da lipgloss ta ciro ta Mik'a ma fatima tare da fad'in "Ungo kar'bi naki wannan kuma nawa ne nima ina da hak'k'i akan kayan d'ana" To inna nagode " Fatima ta fad'a Nasir yayi tsaye yana kallan inna ganin ita fa bilhak'i take yama rasa mezai ce kar kuma ya sake magana ta rufe sa da fad'a yama gode allah da yasa matar sa bata raina Mahaifiyar sa ba dan wannan abun da take wallahi yasan da fatima bata da hak'uri da an dad'e da samun matsala "Maman humaira ni zan koma"To allah ya bada sa'a "Amin ya allah, ya wuce itama taje takai nata kayan d'aki ta fito inna na nan tsaye hanyarzu tana duba kayan" Waii ai da ganin wannan kasan kud'ad'e ne ya kashe a wajen nan haka kawai ni kuma sai na bari ya kwaushe ya Mik'a mata ai nima ina so koda banda mijin da zanyi ma nayi abuta naga shawa allah sarki malam allah ya gafarta maka da yanzu kai ne zakaga wannan kwalliyar" ta fad'a tare da share y'ar kaullahr da ta zubo mata Ita dai fatima na jinta ta kama hanya tayi kitchen, har zata shige inna ta kira sunanta ta tsaya tare da juyawa, inna tace" Ki tabbatar kin muna irin miyar jiya d'in nan mai d'an banzan dad'i kai miyar nan ta jiya tayi dad'i sau uku ina cin abinci cikin dare" Yau fa miyar kuka ce bata alayyahu ba"Auu shin kuka ce ko to kidai yi mai dad'i " Fatima ta juya ta shige kitchen Bayan ta gama girkin ta tsame naman ta cire tsoka goma ta ajiye ta rufe ta d'auki sauran ta kaima inna, inna na dubawa tace" Uhm uhmm uhmmm ya akayi naga naman nan duk ya tsuke "Dahuwar da yayi ne sosai shi yasa ya koma haka" inna ta d'auki tsoka d'aya ta kai baki " Kai gaskiya kam na yau yafi dahuwa da dad'i to daga yanzu ki rik'a barinsa yana dahuwa sosai kamar haka"To " Yau tunda kinyi abun k'aurai bari a baki tsoka biyu kema kisama bakin salati" Ta Mik'a mata tsoka biyu da k'ashi biyu, sannan ta sake Mik'a mata tsoka uku da k'ashi guda tace "Wannan nasa ne tashi kije" ta Mik'e ta nufi kitchen tana dariya k'asa_k'asa.... 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Yah ansar daga rakiyar su faruk bai dawo ba da can ya fita sai da akayi sallahr magrib sannan ya dawo d'akin hunsa ya je ya tarar da ita kwance masu aikin ta na mata tausa tana charting gefen ta kuma shinkafa zube cikin filet wanda yah ansar ya kasa tantance ko wane irin abinci ne, dan shinkafar ta ca'be Ya tsina fuska yayi a zuci yace" Allah ya kyauta nima da wannan abincin ne zan rik'a ci" Ganin sa yasa masu aikin suka dakata da abunda sukeyi D'ago kanta tayi tare da fad'in "Dear"Uhmm, tana k'ok'arin tashi yace tayi zaman ta zaije yayi wanka, ta koma ta kwanta ya fice, suka ci gaba da aikin su D'akin sa yaje yayi wanka, har ya shiga kitchen zai dafa tea sai kuma wata zuciya tace "Mezai hana yaje ya tambayi zarinat ko akwai sauran abun nan da suka ci d'azu, kai haka ma za'a yi Ya fad'a tare da fitowa daga kitchen ya bud'e d'aki ya fito kai tsaye ya nufi 'bangaren ta, murd'a hannun k'ofar yayi tare da shiga, yana shiga tana fitowa daga kitchen tana sanye da hijab d'in ta blue black dogo har k'asa mai hannu, hannun ta rik'e da gorar ruwa faro da cup Yah ansar kallanta yake kamar yau ya fara ganin ta tayi kyau sosai cikin hijab d'in hijab na mata kyau sosai Zama yayi cikin kujerun falon, ta k'ara so tare da yi masa sannu da zuwa, dining ya fara lek'e yaga baiga komai akai ba zarinat na lura da shi, ganin bai ce komai ba yasa tace " Yah wani abun kake so? Kai ya d'an sosa tare da fad'in" Nace ko akwai sauran abun nan da muka ci d'azu yama sunan nasa?" Zarinat tayi dariya ganin yarda yayi maganar Tace " Alele" Eh shi " Wallahi babu" okay " Ganin kamar yunwa yake ji kuma gashi bata dafa komai ba sauran alaler zarah ta bama taje da ita bata raga ko kad'an ba saboda batayi tunanin zai nema ba Zarinat tace *Sai dai ko na dafa maka wani abu" Eh to dan allah dafa min bara naje masallaci na dawo " To" ya Mik'e saboda kiran sallah da aka fara ya fice Ita ma ta nufi bedroom d'in ta, sai da tayi sallah sannan ta fito ta nufi kitchen, ta tsaya tunanin abunda zata dafa masa mai sauk'i spaghetti 🍝 ta yanke shawarar dafawa, ta fara aiki Da yaje sallah bai dawo ba sai wajen k'arfe tara da rabi koda ya dawo ta dafa masa spaghetti mai d'ankaran dad'i ga kifin da ta zuba a ciki, duk da ta zuba kifi idan kaci zaka iya rantsuwa kace ba kifi a ciki sai dai idan ka gansa saboda ta cire masa k'arni, ai kuwa yah ansar yana ci sai shi mata albarka yake yi a zuci daidai wacce zai ci ta dafa gaba d'aya ta zube masa a filet sai da ya cika Yah ansar gaba d'aya ya tashi da filet d'in ya kaunkaud'i lemo mai sanyi da ta kawo matsa ai sai gaytsa ciki ya cika, Ta kaushe kayan takai kitchen ta dawo, yana part d'in ta har goma da rabi tayi suna kallo sannan ya tashi tare da mata sai da safe ya wuce yayi part d'in husna................................................ Comment and share fisabilillah ♥️ 💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 1️⃣4️⃣ Yau monday, tun da tayi sallahr asuba bata koma bacci ba, tayi karatun k'ur'ani mai girma, ta had'a breakfast, doya da kwai ne sai ta d'an soyata da yawa yarda zata isheta har dare saboda tasan koda zata dawo school ta gaji bata ji zata iya yin girki ba, ta gyara d'akin ta kunna turare sai k'amshi ke tashi lungu da sak'o na ko ina, wanka ta shiga, ta fito d'aure da towel ta tsaya gaban mirror, ta bushe gashin ta daya jik'e wajen wanka ta fara mulke jikinta da mayuka masu k'amshi da gyaran fata, bayan ta gama ta kawo humrar ta itama ta mulke jikinta da ita, ta gyara fuskarta ta shafa lipgloss Already daman ta fitar da kayan da zata saka, riga da siket sun zauna tsaff a jikinta tayi d'aurin d'ankwalli mai kyau ta saka yan kunne da agogo ta d'auko fashion hijab d'in ta da fashion bag ta rik'e a hannu taje gaban mirror ta k'ara feshe jikin ta da turare sannan ta fito falo Tea ta had'a mai kauri sai k'amshi yakeyi, ta dawo falo saboda bata san cin abinci a dining, tuna tayi bata d'auko filet ba ta tashi taje kitchen ta d'auko, shigarta kitchen yayi dai_dai da shigowar yah ansar, yana sanye cikin dakakkiyar shadda fara yayi kyau sosai sajensa ya kwanta gemunsa har k'yalli yakeso akan tsananin gyaran da yake sha, hannun sa rik'e da jakar aikin sa shima ya shirya zai fita Ganin kula a tsakiyar falon yasa yayi hamdallah ga allah dan yana da yak'inin cewa breakfast ne a ciki Fitowa tayi ta gansa tsaye, shi kuma tunda ta fito yake ya kafeta da ido har ta iso, ta aje filet d'in hannunta tare da durk'usawa ta masa ina kwana amsawa yayi tare da k'ara sowa cikin falon ya nemi guri ya zauna ita ma ta zauna, dukan su sukayi shuru shikam idanunsa akanta Maganar zuci ta shigayi ita dai gaskiya bazata iya cin abinci a gabansa ba idan ma taci to a ta kure zata ci gashi shima ya shirya da alama aiki zai je amman taga baya ma da alamun tashi to ko baiyi breakfast bane? kai ina bama zai yuwuba nasan matarsa zata masa amman dai bara na taya masa ko zai ci, tana gama fad'in haka a zuci ta tashi ta nufi kulolin ta bud'e ta zuba soyayyar doya da kwai, wacce ta zuba a filet ta fi yawa akan wacce ke cikin kula, ta bud'e d'aya kular egg sauce ta zuba a gefe ta d'aura filet d'in saman table d'in wajen taja takai gabansa ta d'auki tea da ta had'oma kanta shima ta aza masa, ga mamakinta sai taga kamar yayi murmushi ta koma ta zauna, ganin tayi ya k'ara jan table d'in gabansa ya cire hular kansa ya aje gefe ya kai hannu ya d'auki cup d'in tea yakai baki, yaji dad'in sa sosai dan sai da yasha kamar kusan rabi sannan ya aje ya fara cin doyar, spoon d'in da ta saka masa ma aje shi yayi yasa hannu yana ci Zarinat tashi tayi taje ta sake had'o wani tea tana sha, kallan ta yayi yaga bata sakama kanta ba yace "Ke baza ki ci bane? zonan ki zauna muci tare" ya fad'a tare da nuna mata gefen sa " Yaya wannan ya isheni" wani kallo yayi mata tare da fad'in "Tea ne zai k'osar dake" Yaya damanfa banajin yunwa kuma idan nace zan ci yanzu to zan makara school "Ga gaskiyar magana nan ta fito saboda kada ki makara yasa baza ki ci ba ko to ba inda zakije sai kinci ko zaki makara" Marairaice fuska tayi tare da fad'in " Allah banajin yunwa" Breakfast ne ko bakyajin yunwa sai kin ci, hak'uri tayi ta basa tare da magiya sannan yace "alright jira ni nagama sai na sauke ki" Aje shan tea ma tayi tasaka hijab d'in ta ta rataya jakarta ta samo masa wajen da zai wanke hannun sa idan ya gama tayi zaune tana jiran sa, ajima ajima ta kalli agogon hannun ta ganin lokaci na tafiya, yana lura da duk abunda takeyi Sai da ya cinye gaba d'aya sannan ta taso ta zuba masa ruwa ya wanke hannun sa ta Mik'a masa tissue ya k'ara goge hannun sa ta kaushe kayan takai kitchen ta fito tana sauri dan ta k'osa suje ta kusa makara, suka fito yana gaba tana bayansa har suka isa wajen mota suka shiga ya tada Har kusa da inda zasuyi lecture ya kaita dan yaga 8 har ta wuce, yana tsayawa ta fito da d'an sauri ta nufi hol d'in da zasuyi lecture Tana zuwa kawai ta tura kai ta shige tare da yin sallama cikin zazzak'ar muryar ta hol d'in anyi shu tsiff_tsiff_tsiff kamar ba mutane a ciki, saboda malamin yanada tsauri sabon zuwa ne baya wasa sannan idan har ya riga ya shigo ba wanda zai sake shigowa kuma ba mai fita, koda 8;1 ka shigo tofa sai ka fita, surutu haramun ne indai yana ciki idan kuma kayi ya kamaka zai baka kyautar C/O shiyasa bamai wasa Dr abbas da ido ya bita har ta samu waje ta zauna kusa da wata sabuwar zuwa, Dr abbas tsintar kansa yayi da kasa korarta yadai bita da ido, ci gaba yayi da lecture, yan class sunyi mamaki sosai ganin bai koreta ba bayan kuma kafin tazo akwai wad'an da suka zo ya kore su amman ita ya kyaleta, har hakan yaja aka fara yan surutai sai da ya daka musu tsawa sannan Yana lecture yana kallan ta har ya gama ya fita, bayan ya fita wacce ta zauna kusa da ita tace " Sister sannu"Yawwa "Sunana faridah Kefe ? " Zarinat "Nice name" Thank you " welcome kusan sati na d'aya da zuwa but ban ta'ba ganin ki ba" Nayi tafiya ne " zarinat ta fad'a " Okay sannu da hanya "Yawwa" Kar kiga na dameki fa idan kina so sai na yi miki bayanin lectures d'in da akayi bakya nan " Kai dako na gode wallahi" Kai ba komai zamu iya farawa yanzu kenan " Eh" To amman gaskiya ba lallai ne namiki bayanin su duka yau ba " To shikenan ko rabi mukayi yau gobe sai mu ida" Okay " faridah ta bud'e jakarta ta ciro littafin ta da take jotting a ciki, nan ta fara yi mata bayani kuma ba laifi zarinat ta gane sosai Faridah irin black beauti nan ne sannan allah ya bata ilimi ga son jama'a Exchanging numbers sukayi, zarinat taje suka gaisa dasu saudat ta dawo suka fita ita da faridah dan suje su siyo ruwa, suna tafiya faridah na fad'a ma zarinat k'a'idojin Dr abbas zarinat tace "Ahh lallai kice d'azu sa'a naci" Wallahi kuwa " suna tafiya suna fira suka siyo ruwa suka dawo a hanyar su suka had'u da Dr abbas tun daga nesa ya kafe zarinat da ido har suka iso kusa dashi saboda nan ne hanyar da zasu bi take, gaidasa sukayi ya amsa hankalinsa nakan zarinat har suka wuce bai dena kallon ta ba sai da suka shige class sannan ya nisa tare da sakin murmushi yabi hanyar sa, suna shiga malamin da zai shugo musu ya zo Suka fara karatu Shabiyu daidai ya fita, wanda zai shigo 12 ya fita 2 yace bazai samu daman zuwa ba su had'u wani sati, suna fitowa taga driver, tun d'azu yazo saboda baisan time d'in da zasu tashi ba, sallama sukayi ita da faridah ta wuce............................................ Comment and share fisabilillah ♥️ 💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Wannan shafin sadaukarwa ne a gareku masoyan wannan littafin masu bibiyarsa 🙏much love for you fisabillilah ♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️😘😊💕💕💕💕 alkhairin allah da rahamarsa ya kai muku aduk inda kuke allah ya lullu'be ku da bargon rahamarsa 🤲🫶🫶🫶🫶🥀🥀🥀🥀🥀🥀✨ love's you all masoya masu k'amshin tufa 🍎🍎🍎🍎🍎 Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 1️⃣5️⃣ Inna ce ta fito daga d'aki fatima na zaune tana aiki, kamar ance ta d'ago kanta sai ga fuskar inna, ta shafa barbad'a kumatu (k'yalk'alin balaga) ta shafa shi kamar powder ya mannu a fuskar sai k'yalli takeyi wata irin dariya ce tazo ma fatima sai dai ba damar yi dole ta k'umshe abarta amman duk da haka sai da ta rik'a yi k'asa_k'asa Nasir na shigowa yaganta baisan lokacin da dariya ta kubce masa ba yayi ta yin dariyar sa har inna ta k'ulu dan bata san abinda yakema dariya ba ta zabga masa ashar tayi sannan ya daina yace " Inna hala dai baki kalli madubi bane ? kinga yarda fuskarki ta koma kuwa? hhhhhh "Ahhahhhh ga ja'irin yaro me fuskar tawa tayi ne da kazo ka sakani gaba kana dariya " Fatima" Naam " Je ki samomin madubi"To" ta fad'a tare da Mik'e wa tayi d'akinta ta d'auko wani k'ara min mirror ta kawo masa, Mik'a ma inna yayi tare da fad'in ta duba ta gani "Innalillahi wannan wace irin y'ar banzar hoda ce haka wallahi sun suceka sun siyarma da wacce ta lalace " Hhhhhhh inna sai da na fad'a miki wannan ba irin naku bane ba haka ake shafa shi ba"To kunsan yarda ake shafawa amman kuka kyaleni bakuyimin bayani ba bama ba laifin ka bane duk laifin waccen bak'ar munafuka ce, ta fad'a tare da nuna fatima" tunda taga bata samu masu kyau irin nawa ba shine tak'i sanar min yarda ake shafa wa dan kar nayi kyawo to ta allah ba taki ba "Haba inna miye kuma laifin ta a ciki" Eh ai dole ka goyi bayan ta tunda kana tsoron ta "Allah ya huci zuciyar ki kiyi hak'uri yanzu idan na fita zan siyo miki mai kyau"Kuma wallahi mai tsada zaka siyo dan nama lura kamar nata sunfi kud'i " Girgiza kai kawai yayi, fatima na duk'e tana aikin ta bata ce komai ba Nasir ya wuce ya shige d'aki ita ma ta aje aikin da take tabi bayansa inna ta bisu da harara tare da fad'in" Jarababbu kawai " ta d'auki buta tana wanke fuskarta 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Zarinat yanzu idan zata dafa abinci to na mutum biyu take dafawa ita da yah ansar saboda a wajen ta yake cin abinci safe da rana da dare duk anan yake ci sai dai har yanzu bai ta'ba kwana 'bangaren nata ba idan ya shiga dai zai jima a can suyi hira sometimes har 12 yake kai sai idan yaga tana son yin bacci zai tafi, Zarinat da faridah sun shak'u sosai k'awance su suke cikin aminci da yarda 'Bangaren husna kuwa tuni suka shirya ita da odu suka ci gaba da gudanar da haramtacciyar soyayyar su Dr abbas ya fad'a cikin matsanancin son zarinat, ko wacce safiya gani yake son ta na k'ara ninkuwa a zuciyarsa, idan aka tashi school ya koma gida har allah allah yake safiya ta waye yazo makaranta ya ganta hankalin sa ya kwanta, idan har ya shigo musu lecture har ya fita idanunsa a kanta wanda har hakan yasa bata ma san ya shigo musu, duk da bata san abunda ke zuciyar sa ba, saboda kawai yaji zazzak'ar muryar ta yakesa wani lokacin ya jefa mata tambaya cikin ikon allah kuwa duk tambayarda yayi mata sai ta bayar da amsa Yau ma fitowar su daga lecture kenan sun gama zasuje gida sai ga Dr abbas ya tsayar dasu tare da fad'in " Har kun gama lectures d'in ne? "Eh, faridah ta fad'a " Okay zarinat ko?" Ya fad'a tare da nuna ta, kai ta gyad'a masa yace " Good akwai group assignment da nakeson bayar wa ina san ki zamo leader sai ki bani number ki idan na fitar na sanar miki " Okay sir amman ni banada waya sai dai ko ka kar'bi number faridah" Haba big girl kamar ki ace bata da waya " Murmushi tayi tare da fad'in" Sir banada " is okay bama saina kar'bi tataba idan na fitar zan sanar miki"okay sir, ta fad'a tare da kama hannun faridah suka wuce Faridah tace"Masoyiya wallahi gwauda da baki basa number ba dan ni Dr abbas d'in nan take takensa ya fara yawa " Abar K'auna bari kawai ai shiyasa nace banada waya" To daki ka ce masa ga tawa daya ce abasa fa "Hhhhhhh ai nasan bazai kar'ba ba ne" gwaunda hakan" suna tafiya suna maganar Dr abbas kuwa yana nan tsaye inda suka barshi kamar an dasa icce, ba wani group assignment da zai bayar kawai dai yayi haka ne ko zai samu number ta ne, ya dad'e a wajen tsaye har su zarinat suka bar makaranta yana wajen Tana dawowa school ta d'ora girki yau tuwo take da sha'awan ci, cikin k'ank'anin lokaci ta kammala girkin tuwon shinkafa da miyar alayyahu taji egusi sosai dan idan ba am fad'a maka miyar alayyahu bace bazaka gane ba, gashi tayi kauri sosai tayi kyau sosai a ido sai k'amshi ke tashi, tana gamawa ta fad'a toilet tayi wanka tare da d'auro alwala Sai da ta fara yin sallah sannan ta shirya cikin wasu k'ananun kaya riga da wando na roba black colour, kayan sun mata kyau sosai kuma sun kama jikinta ta saka hula white colour, sai ni'iman taccen k'amshin ke tashi a jikinta ta fito falo Yah ansar na dannar waya k'amshin turaren ta da yaji yasa ya d'ago kansa tare da zube idanunsa a kanta " Tsarki ya k'ara tabbatar ga ubangijin sammai da k'asassai ma halaccin wannan kyakkyawar halittar kai subhanallah " ya ansar ya fad'a a zuci lokacin da take isowa wajen sai da ta gaidasa sannan ta zauna Kallan da yake mata taga yayi yawa ta turo baki gaba cikin shagwa'ba tare da fad'in " Uhmm uhmm yaya ni sai kayita kallo na kamar yabaka sanni ba" ta fad'a tana wasa da k'umbar hannun ta, murmushi yayi mai sauti tare da fad'in " In banda abunki reena idan ban kalleki ba wazan kallah? Kefa matata ce ko haramunne miji ya kalli matarsa? " Uhmmm nidai ban ce ba" ta fad'a tare da Mik'ewa ta nufi dinning, bayanta yabi da kallo ganin duk yarda ta taka sai jikinta ya raya mussaman mazaunanta da k'irjin ta da suke cike taf Kawar da kansa yayi daga kallanta dan bazai iya jurar kallan ta ba har wani abu yake ji a jikinsa.................................................. Comment and share fisabilillah ♥️ 💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 1️⃣6️⃣ Abinci ta kawo masa yaci yaji dad'in tuwon sosai yarda bakuyi tsammani ba har santi ya rik'a zuwa ba, zarinat kuwa sai aikin dariya take, bayan ya gama ta kawo masa waje ya wanke hannun sa, dan shi yafi san cin abinci da hannu bai cika cin abinci da spoon ba Ta kaushe kayan takai kitchen ta dawo wayarta da ta aje tun d'azu a falo ta d'auka missed call tagani dayawa, tana k'ok'arin duba wanda ya kirata sai ga kiran mom ya shigo ta d'aga tare da kai wayar kunnenta " Assalamu alaikum" princess lafiya ina kika shiga ne nayita nemanki a waya baki d'aga ba" daga 'bangaren mom ta fad'a " Ohh I'm very sorry mom nabar wayar ne a falo " Okay fatan dai kina lafiya" Lafiya k'alau mom " Ma sha allah auntyn ki tace itama tayi kiran ki bagi d'aga ba " Mom ban gani bane" Okay to albishirin ki " Goro kuma fari k'alk'alk'al, ta fad'a tare da yin fari da idanunta, yah ansar ya tasa ta gaba yana kallo kamar ya samu tv Mom sai da tayi dariya sannan tace" To auntyn ki ta sauka lafiya an samu d'ah namiji " Yeeeeeeeeeee, ta fad'a da k'arfi tare dayin tsalle, mom sai da ta janye wayar a kunnenta saboda k'arar da tayi Suna had'a ido da yah ansar ya girgiza kai, gefen fuskarta ta shafa, wai ita taji kunya ta koma ta zauna Fira suka d'an ta'ba da mom, zarinat sai shagwa'ba take zuba mata, zasuyi sallama yah ansar ya amshi wayar suka gaisa da mom tare da mata barka ya Mik'a ma zarinat waya, mom tace " Princess wai daman yana kusa kike wannan abun" Uhmmmm, ta fad'a tare da turo baki " Allah ya shiryamin ke" Amin mom let me call aunty " Okay, sukayi sallama Ta kira aunty maryam tayi mata barka, yah ansar shima yayi mata barka, ta bama yaya bilal suka gaisa Kwana biyu da haihuwar zarinat ta fara yi masa maganar tafiya, to kawai ya cewa, sunah sauran kwana uku ta masa magana har yafi a k'irga ce mata kawai yake yaji, har tayi fushi ta daina yi masa maganar harda zaman da suke suyi fira ta daina da ta kawo masa abinci zata shige bedroom sai ya fita take fitowa, wanda hakan na damunsa dan ya saba da su zauna suna fira ko suyi kallo tare, shi bawai hana mata zuwa yayi ba aah yafi son sai ranar sunah sai suje tare marece nayi su dawo saboda baya son taje ta kwana idan taje ta kwana wazai masa girki? a ina zai ci? Idan ya dawo gida dawa zai zauna suyi fira, husna koda yaushe cikin latsar waya take idan ma aka mata magana, ga amsar da zata bayar amman sai kaji ta fad'i wani abun daban hankalin ta nakan waya shida samun kulawar ta sai dare idan sunzo kwanciya Wannan ne dalilin da yasa bai barta taje ba har yanzu, Kamar kullum ta kawo masa abinci tare da jan table d'in dake gefensa ta d'aura akai tare da lemo ta juya zata wuce, dasauri ya rik'o hannunta ta tsaya cak ba tare da ta juyo ba "Yaushe ne sunan?" yah ansar ya tambaya, mai makon ta basa amsa sai kawai tasaka masa kuka, janyota yayi tare da zaunar da ita saman k'afafunsa yana bubbuga bayanta alamar rarrashi, ya kafe d'an k'aramin pink lips 👄 d'in ta da ido runtse ido sa yayi tare da furzar da iska, yasan dalilin kukan nata don bazai wuce tambayar da yayi mata bane ya 'bata mata rai Zuwa can yace " Shiiiiiiiiiiiiiiii ya isa mana me aka miki? tambayar ki fa nayi ko nace wani abun ne? Girgiza masa kai tayi, k'ara gyara mata zama yayi saman k'afafunsa tare dasa hannu ya zagaye k'ugunta "Rinah" ya kirata ta d'ago ta kallesa " Yaushe ne sunan? " Jibi " ta fad'a cikin muryarda da kaji kasan kuka take " Ki shirya idan allah ya kaimu gobe sai na kai ki" wani farin ciki taji tace" dagaske?" Kai ya d'ago mata Wata kyakkyawar rumguma takai masa tana fad'in " Nagode sosai yaya nagode " Murmushi kawai yayi tare da k'ara rumgumeta sun jima a haka sannan ya saketa ta fara k'ok'arin tashi daga jikinsa, rik'e ta yayi tare da fad'in " Ina zakije?" Zanje ne na zauna " yanzu a tsaye kike ne?" K'asa kawai tayi da kanta ba tare da ta basa amsa ba, hannu yasa ya d'ago ha'barta batai aune ba kawai taji lips d'in sa akan nata yana tsotsa, zarinat ko k'auk'auran motsi ta kasa, sai da ya tsotsesu yarda ransa ke so sannan ya cire, taso tashi amman ya hanata dan ya rik'e ta ne sosai " Muci abinci" ya fad'a " yaya banajin yunwa..................................................... Comment and share fisabilillah ♥️ 💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 1️⃣7️⃣ " Kin tabbata?" Kai ta d'aga masa alamar eh, yace" alright to ni bani yunwa nakeji" To " ta fad'a a sanyaye, ta d'auko filet d'in abincin ta d'ora saman k'afafunta ta d'auki spoon, yayi saurin fad'in "No! No! No! da hannun ki zaki bani" ba yarda ta iya dole tayi hakan, fried rice ce taji kayan ciki sosai ga k'amshin dad'in da takeyi ko daga kallo ka kalleta ba tare da kaci ba zaka gane tayi dad'i 'Debowa tayi ta d'ago hannunta amman ta kasa kai bakin sa ganin haka yasa ya rik'e hannun ta tare da turawa cikin bakin sa ta zuba masa, yana taunawa yana wani irin juyi dakai idanunsa a rufe irin na alamun idan dad'i yakai maka dariya ce ta kubce ma zarinat ba shiri ganin abunda yake yi" Wai kin ci abincin nan kuwa? Kin ji dad'in da yayi? " Hhhhhhh naci " anya kuwa? Ya fad'a tare da sa hannun sa cikin filet d'in ya d'ebo loma tare da kai bakin ta yace" Ci wannan kiji " ta bud'e baki ya saka mata " Kin ji? gaskiya nikam nayi sa a matata ta iya girki sosai allah ya miki albarka " cikin jin dad'i da yaba mata da yayi tace"Amin yayanah " Tana basa yana ta yabon girki har ya cinye tasss ta basa lemo da ruwa yasha ta tashi taje takai kayan kitchen ta wanke hannunta ta dawo falon ta zauna tare da d'aukar remote ta canza musu channel " An daina fushin?" yah ansar ya fad'a, murmushi kawai tayi Yau tara da rabi nayi yayi mata sai da safe ya wuce saboda baccin da yakeji kuma yana son kafin ya kwana yad'an yi wani aiki cikin system d'in sa Yana fita itama ta wuce bedroom ta had'a kayan da zataje dasu, tana gamawa ta fad'a toilet tayi wanka ta shige cikin kayan bacci tayi kwanciyarta ganin baccin yak'i zuwa mata yasa ta janyo wayarta ta kunna data ta shiga wajen chatting Yah ansar kuwa yana fitowa 'bangaren zarinat d'akin sa ya wuce yayi wanka, ya d'auko system d'in sa yayi d'akin husna, yau dai kam anci sa a bata dannar waya tana kwance sanye da wasu arnayen sleeping dress, kallo d'aya yayi mata ya d'auke idanunsa akanta aiki yake son yi idan ya ce zai biye mata bazai yi aikin nan ba, ya zauna saman kujera tare da jan table ya aza system d'in sa Husna ta saki wani shu'umin murmushi tare da saukowa saman gado ta nufosa tana tafiya mai jan hankali, tana zuwa kawai ta fad'a jikinsa tare da fad'in " Dear tun d'azu fa nake jiran ka" ya bud'e baki da niyar yi mata magana kawai ta had'e bakin su waje d'aya, wasu abubu take masa wanda ya k'asa jurewa kawai ya d'auke ta suka nufi bed, sai da ya samar ma kansa natsu sannan, bacci ya kaushe su ba tare da yayi aikin ba Da asuba da yaje masallaci bai dawo ba sai da gari yayi haske, ya wuce d'akin husna zama yayi tare da kunna system d'in sa ya fara aikin da zaiyi, aikin nada yawa sai kusan sha d'aya ya gama, yana gamawa kuma ya haye gado ya kwanta bayan husna da take baccinta tun d'azu shima baccin yayi gaba dashi 'Bangaren zarinat kuwa tana gama sallar asuba ta d'ora musu breakfast d'in da zasu ci daman already jiya ta had'a kayan ta, tana gamawa ta gyara d'akin ta turare sa ta fad'a toilet ta tsala wanka ta shirya cikin wani boil lace yellow riga da siket sun mata kyau sosai d'inkin ya amshi jikinta ya sark'a da abun hannu, ta kashe d'auri mai kyau hannunta manne da tsadadden agogonta sai zobuna biyu dake sanye a yatsunta ta yafa mayafi ta feshe jikin ta da turaruka tayi kyau sosai ta fito falo tayi breakfast ta zauna jiran yah ansar, tun tana dubin agogo har ta daina, kasa hak'ura tayi sai da ta Fito waje ta duba taga motarsa na nan, Wanda ya tabbatar mata bai fita ba yana cikin gidan, wani 'bangaren na zuciyar take fad'a mata " yana can tare da matarsa ya manta dake, ciki ta koma tana jin wani abu ya tokare mata zuciya Cikin bacci kamar wanda aka tuna ma ya tashi da k'arfi tare da salati ya dubi agogo" innalillahi wa inna'ilaihi'raji'un wane irin bacci nayi ne haka " ya fad'a yana saukowa saman gado ya tada husna ya kaushi kayansa yayi d'akin sa a gaggauce yayi wanka ya shirya ya fito ya nufi d'akin zarinat Kwance ya sameta idanunta a rufe amman ba bacci take yi ba, kallanta yake tun daga k'afafuwan ta har sama tayi masa kyau sosai K'amshin turaren sa da ya addabi hancinta yasa ta bud'e ido ta zubesu a kansa tashi tayi daga kwance da take yazo ya zauna kusa da ita tare da fad'in " Sorry kinganni sai yanzu bacci ne ya d'auke ni" Uhmm, kawai ta fad'a tare da Mik'e wa ta kawo masa breakfast d'in sa sannan ta masa ina kwana ta koma ta zauna nesa dashi Yana cin abincin yana lura da yarda take wani cic_cin magani har ya gama ta d'auke kayan taje kitchen sai da ta wanke kayan da yayi amfani dasu sannan ta fito, yace suje ta d'auko akwauti, ya amsa tare da fad'in " wad'an nan kayan da kika deba fa? Kin san fa da anyi sunah zaki dawo" ita dai bata ce komai ba har suka fita taja 'bangaren ta ta rufe Ya aje akwautin da niyar zuwa 'bangaren husna ya sanar mata sun tafi sai gata ta fito tana sanye cikin wata atamfa doguwar riga ta mata kyau ta k'ara so wajen su " Dear ina zuwa haka? " Tafiya zamuyi zan kaita ne na dawo " Okay har kasa na fara jin kad'ai ci amman da naji ka ce dawowa zakayi naji sanyi a raina kasan bazan iya bacci ba tare dakai a gefena ba " ta fad'a tare da sak'ala hannayenta a wuyansa Zarinat taja akwautin ta tayi gaba, juyowa tayi daniyar ta kar'bi mukullin mota ta saka kayanta kafin yazo, taga bakinsu a had'e, da sauri ta juya ta fizgi akwautin ta fita Yakai kusan 10 mint kafin ya fito, zarinat na tsaye bakin mota haushi duk ya cika ta ga wani abun da takejin yana taso mata a zuciya, a haka ya fito ya sameta ta cika Mazaunin baya ya bud'e ya saka akwautin suka shiga yaja motar Tafiya suke yana mata magana daga eh sai aah kawai take cewa, sun kusa fita gari ya tsaya wata kanti, ya shiga ya siyo kayan baby's kala goma, ya shiga wata supermarket dake wajen ya siyo ice cream guda hud'u ya dawo ya tada motar suka ci gaba da tafiya Ice cream d'in ya Mik'a mata, ta girgiza kai yace " Miyasa? " Haka nan " what is wrong with you?" Nothing " ya zaki ce ba komai bayan kuma ga damuwa nan a face d'in ki kuma ba haka na saba ganin ki ba? " Ba komai, ta sake fad'a tasa hannu ta d'an kwantar da sit d'in ta juyar da fuskarta gefen glass tana kallan ti_ti Dukan su sukayi shuru bamai cewa komai, sun yi tafiya mai nisa ya juyo tare da kallanta ya kira sunan ta ba tare da ta juyo ba ta amsa yace " Shikenan yanzu nida sake cin abinci sai kin dawo sai dai nayita shan lepton " juyowa tayi tare da fad'in" Yaya kamar ya? Ba matar ka na nan ba? " Hannun ta ya rik'o cikin nashi ya furzar da iska tare da fad'in" tana nan bata iya girki ba masu aiki ke dafa mata nikuma bazan iya cin abincin yan aiki ba " Ayyah, ta fad'a cikin jin tausayin sa tace" To yaya kaje wajen ammi kaci mana " girgiza mata kai yayi alamar aah " To zan fad'a ma mom a rik'a kai ma " juyowa yayi ya kalleta tare da sakin murmushi ya k'ara damk'e hannun ta dake cikin nashi yace" Miye amfanin auren nawa idan har zan koma gida na rik'a cin abinci " Yaya to yanzu sai ka zauna da yunwa" waya gaya miki zan rik'a shan tea" Tea ai ba abinci ba ne" Zan daure har ki dawo gobe ne sunah ko? " Eh" okay allah ya kaimu " Amin ta fad'a tare da d'aukar robar ice cream d'aya ta bud'e tasa k'aramin spoon d'in da aka had'a wa dashi ta fara sha Kallan ta yayi yace" Nima a bani nasha " To, ta fad'a tare da k'ok'arin bud'e masa d'aya yace" No wanda kike sha zaki bani ai kinga driving nakeyi bazan iya bama kaina ba " d'iba tayi tare da kai bakin sa ya bud'e ta zuba masa, idan tasha ta basa haka suka rik'a yi har suka shanye roba biyu Sunyi yi tafiya k'arfe uku suka isa gidan, mai gadi ya Bud'e musu gate suka shigo, d'aya daga cikin ma ai katan gidan yazo ya kar'bi kayan su ya shiga dasu ciki Afrah na ganin su da gudu tazo ta rungume zarinat tana murnar ganinta, su aunty Maryam na nan zaune a falo ana mata k'unshi harda yaya bilal na wajen zaune suma sunyi farin cikin ganin su sosai Nan suka zauna aka gaggaisa a ka shiga fira kiran sallah la'asar ne ya tada su maza sukayi masallaci sukuma sukayi d'aki Bayan sun dawo masallaci zarinat ta kawo ma yah ansar abinci wanda k'anwar aunty maryam ta girka, bai wani ci da yawa ba ya aje tare da Mik'e wa yayi musu sallama ya fito zarinat ta rakasa har mota ya shiga itama yace ta shigo ta kar'bi sak'o ta shiga Kud'i ya Mik'a mata masu yawa yace ta bama aunty maryam, ya d'auko ledar kayan baby's d'in da ya siyo ya mika mata tare da fad'in "Wannan a bama baby" To sun gode sosai " ya sake bata kud'i yace wannan nata ne koda zata siya wani abu, godiya tayi masa sosai, ya matso face d'in sa dai_dai tata yana k'ok'arin d'aura lips d'in sa akan nata, tunowa tayi da yarda ta gansu d'azu shida husna tayi saurin janye fuskarta tana turo baki, Kallanta yake" Why?" Kalmar da ta fito masa kenan "Why rinat?" uhm uhm to ai matarka ta maka kafin ka fito " ta fad'a cikin shagwa'ba, yah ansar da mamaki yake kallanta, ita kanta sai da ta furta maganar ne sannan taji nauyin ta, hannu tasa ta bud'e murfin motar ta fito tayi masa allah ya kai lafiya ta wuce, sai da ta shige sannan ya tada motar ya fice Kayan ta bama aunty maryam da kud'i, tayi gadiya sosai, aunty maryam ta zaunar da zarinat aka sa mata lalle Ranar suna yaro yaci sunan aminu, sunan Mahaifin aunty maryam wanda aka masa lak'ani da abba..................................................... Comment and share fisabilillah ♥️ 💋💋 ZARINAT ( زرينة )💋 💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 1️⃣8️⃣ Kwana biyu da sunah amman bata koma ba duk da yah ansar ya kira ta yace zai zo d'aukar ta tace, yayi zamansa basai yazo ba yaya bilal zai wuce da ita dan shima garin zai je, amman har yanzu shuru ka keji Yau yah ansar koda ya dawo daga wajen aiki a gajiye gashi yunwar da yake ji allah ya gani ya gaji da shan tea ya kwanta dan haka yana dawowa ya tasa husna a gaba akan dole sai ta girka masa wani abu yaci, tashi tayi ta shiga kitchen shi kuma ya wuce d'akin sa yayi wanka Tsaye tayi cikin kitchen tana kallan komai gadai kayan abinci nan kala_kala amman bata san yarda ake dafawa ba wata dabara ce ta fad'o mata dan haka ta d'auko wayarta ta kunna data ta shiga wajen Downloading tayi searching na video ake had'a delicious food Wani video taci karo dashi na fried rice 🍚 shi ta d'auka tayi downloading, ta d'ora tukunya ta zuba ruwa, ruwan na fara zafi ta zuba shinkafa a ciki, ga video taga ansa boiling in ten minutes, ta k'ara wuta sosai cikin 5mint ta saukar da shinkafar ta juye a gwau_gwau( mazubi) ta mayarda tukunyar kan wuta ta zuba mai yayi zafi ta zuba markad'ad'd'un kayan miyan ta Cikin k'ank'anin lokaci ta kammala ta zubo masa takai cikin falo ta aje tayi zaune tana huci, Tun da ya shigo d'akin yake jin k'aurin girki ya iso ya zauna " ka dawo? " Eh ya na ganki haka ne?" Dan bakaga wahalar da nayi bane wajen girkin nan duk na gaji" Yawwa sannu ko kefa da haka kike min girki ai ba wanda zaiji kanmu " Nidai gashi nan ka d'auka wallahi na gaji bazan iya kawo ma ba " Ba matsala" ya fad'a tare da Mik'e wa ya d'auko abincin yana bud'e wa k'aurin girkin ya bugi hancin sa " Baby wuta kika saka da yawa ne naji sai k'auri yakeyi" Eh wai saboda nayi saurin gamawa " okay, ya fad'a tare da Mik'e wa ya nufi kitchen yaje ya d'auko filet da spoon yazo ya zuba ya zauna Sai da ya cika spoon ya tura baki, cikin mugun sauri ya fito dashi, husna dake kallansa tace "Dear lafiya?" Sai da ya d'an d'auki lokaci kafin ya samu daman magana dan ji yayi bakinsa ma ya d'auke " Wannan wane irin girki ne haka,ya fad'a a fusace" Me yayi?" D'auka kici kiji" d'auka tayi itama tana saka wa ta fito dashi ta tayi kitchen da sauri ta wanke bakin ta ta fito Abincin gashi bai dahuba ga gishiri da magi da yayi yawa kamar me Kallanta yayi yaja tsaki tare da fad'in " Aikin banza" ya fice daga d'akin " To mena zuba da yawa haka wanda yasa abincin ya kasa ciyuwa? Husna ta tambayi kanta, masu aiki ta kira suka d'auke abincin 'Bangaren su zarinat, suna zaune a d'aki ita da aunty maryam tana k'ara koya mata wasu dabaru na yarda zata kula da mijinta da yarda zata saye zuciyar sa da kyawawan dabi'u Wayar tace ta fara rura alamun kira na shigowa, dubawa tayi taga yah ansar ne ta d'aga, aunty maryam ta fita ta bata waje Sallama tayi masa ya amsa " Ki tabbatar da gobe kin dawo" kalmar da taji ya fad'a kenan " Yaya dan allah ka barni har zuwa jibi idan yaya bilal zai zo sai mu wuce tare" Umurni nake baki ba neman shawara ba" yaya please please please 🥺" kinji me nace ai" yana fad'in haka ya kashe wayan Zarinat shuru tayi ta rasa abun yi, harda wayar ta kasa janyewa saman kunne allah ya gani bataso komawa gobe ba, tana zaune a haka har aunty maryam ta dawo ta sameta, aunty maryam ta tambeta lafiya take zaune haka kamar wacce aka aikoma da sak'on mutuwa, sanar mata tayi aunty maryam ta bata hak'uri, tana k'ara lurar da ita wasu abubuwa Washe gari, yaya bilal ya bayar da mota a kaita Koda suka iso bataga motarsa ba alamun baya gidan, Cikin main falo ta shigo bakin ta d'auke da sallama ta shiga husna na zaune a falo tana kallon tv, kallo d'aya tayi mata ta d'auke kai taja kayanta tayi 'bangaren ta, husna tabi bayan ta da harara tare da fad'in " Gayyar tsiya an dawo kenan" Sarai zarinat tajiyo ta sai dai bata tamka mata ba ta yi tafiyarta Tana shiga ko hutawa bata tsaya yi ba ta aje kayan ta ta fara gyaran d'aki duk da ba wata k'ura ko datti da yayi ta share tayi mopping ta saka turare d'akin ya d'au k'amshi ga sanyin AC ga k'amshin turare suka had'e sanyayen k'amshi na ratsawa, tana gamawa ta d'ora girki, tuwon semo da miyar egusi ne Bata wani jima ba ta gama, ta fad'a toilet tayi wanka tare da d'auro alwala sai da ta gabatar da sallah sannan ta shirya cikin wani yadi marar nauyi daguwar riga, rigar tana da d'an Fad'i da k'asa wajen gefen k'afafuwa an masa tsaga kayan basu kama jiki sai dai yadin yana lik'ewa a jiki mutum haka ake siyar da kayan tare da mayafin su, ta gyara face d'in ta ta shafa jambaki pink, yayi mata kyau sosai ta feshe jikin ta da turaruka masu dad'i ta yafa mayafin kayan yarda ta yafa sa ta fito da gashin ta ya k'ara mata kyau sai k'amshi ke tashi a jikin ta Falo ta fito ta zauna, ta kira faridah ta sanar mata ta dawo suka d'an ta'ba fira 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 "D'an banza fito–fito tana baka kana shanyewa shiyasa kake k'ara lek'ewa ohh ni y'ar nan daman ance inda ranka kasha kallo yaron nan bansan lokacin ka koma haka ba tunda kayi aure idanunka suka bud'e nabar ganema kan ka wai zaka fito ne ko sai na shigo d'akin, inna ta fad'a had'e da rik'e k'ugu " Kadai san d'akin ba bak'ona ba ne wajen shiga dan ba kunyar shiga d'akin nake ba " ta fad'a tare da k'ok'arin cire takalmin ta tashiga sai nasir ya riga ta fitowa" Waya ce ka fito ne ai da kayi zamanka ka gani zan shigo ne ko kuwa? " Haba inna dan allah kiyi hak'uri wallahi magani nake bata bata jin dad'i sosai" iyyeeeee magani kake bata sannu wato ga MATAR SO ko tunda hannu ta sara da zaka zauna bata magani kaji min wani sabon salon iskanci " Inna bata jin k'arfin jikin ta taya zata iya bama kanta" To mu lokacin mu ba ai wannan iskancin ba magani ba wanda zai baka zai zaka d'auka kasha abun ka " Inna wannan ai zamanin ku ne aure fa saboda ibada da kuma taimakon juna yasa ake yi" Ahhahh malam nasuru bara na kawo maka shimfid'a ka zauna sai ka fad'a min dakyau yarda zan gane d'an jabbura kai ni zaka fad'a ma aure saboda ibada da taimakon juna tun kafin a haife ka nasan da wannan karatun " Allah ya huci zuciyar ki inna ban Fad'i maganar da niyar 'bata miki rai ba dan allah ki gafarce ni................................................................. Comment and share fisabilillah ♥️ 💋💋 ZARINAT ( زرينة )💋 💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 1️⃣9️⃣ In Sha Allah remains one page mu kammala free page's, so mai son ci gaba da karatun wannan littafin sai yayi payment a saka sa a paid group two hundred 200 ne kacal👌sannan da d'in da d'ahwa ba iya littafin kawai zan rik'a muku posting ba in Sha Allah zan koyar daku abubuwa guda 9 *1 Yarda ake madarar gari cikin sauk'i yarda zaki samu Sana'ar da zaki kama ki rabu da zaman banza* *2 Yarda ake sabulum gyaran jiki da fuska* * 3 Yarda ake yoghurt* *4 Yarda ake papaya soap*🧼 *5 Yarda ake had'in lalle yayi marron mai kyau* *6 Yarda ake sabulum cucumber* *7 Yarda ake tsami gaye* *8 Yarda ake orange soap* *9 Yarda ake tuwon madara* Duka wad'an nan abubuwan videos ne ta yarda zaku gani da idanu yarda zaku fahimta da kyau kuga yarda ake yi Haba y'ar uwa wace banzar ce kuma kike jira ki karanta littafi kuma ki koyi abubuwa har guda tara Wacce ta shirya biyan kud'i gashi * Banka name u b a* *Acc no: 2277089777* * Zainab mustapha dodo* Sai a turo da shaidar biya ta wannan number *09046495943* *Sai na jiku yan amana* "Wato kai nasuru na fuskanci kafi d'aukar matarka da muhimmanci akan ni uwar ka dana duk'a na haife ka wata tara da kwana tara da awa tara da sakon tara na d'auka kafin na haifeka amman yanzu ka shigo duniya idon ka sun bud'e tarrr dake kallo na har kake fifita matarka a kai na ko wato kai ga d'an balah ja'u ko " Haba inna dan allah ki daina fad'an irin wad'an nan maganganun kema kin san ba yarda za ayi na fifita ta akan ki sai dai kowa da nasa matsayin a waje na " " Kai nasuru ni allah d'aya kawai zaka cemin na yarda dan an rik'a da an shanye min d'ah, wuce muje ga shimfid'a can ka zauna d'akin dai ne bazaka koma ba " Nasir bai ce komai ba ya wuce ya zauna saman tabarmar ita ma ta zauna "Inna nace wai kinga kin kwana biyu baki lek'o su kuluwa ba mai zai hana ki lek'o su kiga yarda suke " Aah ka fito fili ka fad'a min ka gaji da ganina ne kora ta kake yi na tukura muku kai da matar ka na baku waje ku sha iska ba sai ka yi wata kwana_kwana ba " Haba inna ni na isa wallahi bada wata manufa na Fad'i haka ba naga wai kin kwana biyu baki je ba gashi ita ma bata zo ba shiyasa nace kije ki dibo lafiyar ta" Shuru inna tayi tare da nazarin maganar sa can tace " Eh to kuma kayi gaskiya ina ganin jibi zan shirya naje na dibo ta" To allah ya kai mu inna "Amin 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Yah ansar tun da ya shigo cikin babban falon gidan yake jin k'amshin turaren ta, wani irin farin ciki ne ya lullu'be sa har wani nishad'i yake ji, bai shiga 'bangaren nata ba har sai da yaje yayi wanka ya shirya cikin k'ananun kaya wad'an da suka kar'bi jikin sa, yaje d'akin husna ya ganta yayi d'akin zarinat Sallama yayi ya shiga, da kyakkyawar fuskarta ya fara cin karo tana kwance fuskarta ta facing door tana charting, Tsaye yayi ya zuba mata ido kamar wanda ya fara ganinta yau, k'amshin turaren jikinsa ya kaima hancinta sai kuma jikinta ya bata da ana kallanta, d'ago kanta tayi ta gansa tsaye ya had'e hannayensa biyu a k'irji, tashi tayi daga kwancen da take Ya k'araso cikin falo ya zauna, cikin girmamawa ta gaidasa ya amsa cikin sakin fuska tare da tambayar ta ya hanya da su yaya bilal, lafiya k'alau alhamdulillah tace masa " Yaya na kawoma abinci?" Wai har kinyi girki da dawowan ki? Murmushi tayi tare da fad'in " Eh" Sannu " Uhmm na kawo? " Rinat har sai kin tambaya tun daga ranar da kika yi tafiya ba abincin da ya sake shiga ciki na sai tea 🍵 amman naga ke hakan bai dame ki ba " Marairaice fuska tayi cikin jin tausayin sa tace" Yaya meyasa zaka ce haka " Saboda da yanzu kina can zaman ki" shuru tayi kawai ta Mik'e ta nufi dinning table ta d'auko kula da wani filet mai d'an zurfi wanda ta had'a cos low a ciki, ta koma ta d'auko filet da spoon tazo ta zuba masa ta kawo coslow d'in nan ta zuba a gefe, yaji kwai da bama, ta kawo masa lemo mai sanyi ta zuba a cup sannan ta zauna Tun da ya fara ci ko magana bayayi dad'in abincin ya Kai masa har cikin mid brain 🧠yaji dad'in sa sosai fa Kwanan ta d'aya da dawowa ta koma school, faridah taji dad'in ganin ta sosai saboda kwanakin nan da tayi bata nan duk bata jin dad'in zuwa makaranta sun saba da tafiya su biyu suyi karatu idan kuma basu da lecture su d'an yi fira amman da bata nan ta koma ita kad'ai, zarinat taje mata da kayan biki faridah tayi gadiya sannan ta sanar mata da yawan tambayar ta da Dr abbas ke yi Yah ansar zaune a d'akin sa, haka kawai yayi sha'awan shiga TikTok d'in sa ya duba kunna data yayi ya shiga, video's d'in wak'ok'i kawai yake gani yana wuce wa tsaki yaja ganin ba wani abun amfanin da ya gani wani video ya wuce, shuru yayi tare da fad'in " Kamar face d'in zarinat ya gani kai ina bama ita ba ce, ya fad'a a zuci Baya ya koma ya tsurama video ido zuciyar sa na tafasa, ganin video zarinat ita da afrah sun saka kaya iri d'aya sunyi kyau sosai, da alama photo ne sai ta d'ora wak'a akai, ransa ne ya 'baci sosai ganin face d'in ta a TikTok ga video nan tayi kyau sosai murmushi kwance a fuskarta, Shiga yayi ya duba yaga shi kad'ai ne abun da ta ta'ba yin posting, yaga ta samu likes sosai da followers, ga comment d'in da aka rik'a mata na sunyi kyau sosai zuciyarsa ce ta buga lokacin da yaci karo da comment d'in wani mutum, idanunsa suka rufe har wani dishi_dishi yake gani ya Mik'e ya fito kai tsaye ya nufi d'akin ta Bata falo ya wuce bedroom nan ma bai ganta ba har zai fita yaji motsin ruwa a bayi tsaye yayi a d'akin hannunwansa a baya yana zarya cikin d'akin, Bud'e k'ofa tayi ta fito tana d'aure da towel d'an guntu rabin cinyoyinta duka a fili ta nufi gaban mirror ta tsaya hannunta rik'e da wani towel tana tsane ruwan jikinta "Mene ne wannan?" Taji muryar yah ansar ta doki kunnenta, da sauri ta d'ago kanta ta gansa ta cikin mirror, takowa yayi har gabanta ya sake nuna mata video tare da maimaita tambayar sa, ganin ba wasa a idon sa yasa taba ce komai ba bare kuma bata da abunda zata fad'a dan tasan bata da gaskiya akan 'bacin rai idanunsa har ja sukayi, Fad'a ya shiga yi mata sosai inda yake shiga ba nan yake fita ta, gashi ta tsani ayi mata fad'a hakan yasa ta fashe masa da kuka tana basa hak'uri, wayarta ya kar'be ya fita Sai da taci kukan ta sannan ta koma toilet ta wanke fuskarta ta fito ta shirya, agogon dake manne a d'akin ta duba taga da sauran lokaci ta fito falo taci abinci ta d'auko bag school d'in ta, ta fito yah ansar na zaune a falo system d'in sa na gabansa da alama aiki yake yi yau kuma baya da alamun zuwa office Tun da ta fito k'amshin turaren ta ya kai masa sai dai bai d'ago ba bare ya kalleta har ta k'ara so wajen sa ta durk'usa ta gaidasa, amsa mata yayi cikin sakin fuska har yanzu kuma idanunsa nakan system d'in sa Tana durk'ushe a gabansa " Yaya makaranta zan je" A dawo lafiya " Allah ya yasa uhm uhmm yaya wayata" sai lokacin ya d'ago kansa tare da kallanta " Ba yanzu ba" To" ta fad'a cikin sanyin jiki ta Mik'e har ta fara tafiya ya dakatar da ita cikin Jin dad'i ta juyo d'an ta zata wayar zai bata, tun daga kan k'afafunta dake sanye cikin wasu cover shoes na mata masu shegen kyau da tsada yake kallanta har sama, sanye take da wani siket na roba black rigar ita ma ta roba ce pitch colour, sai afterdress d'in da ta d'ora akai black ta yafa mayafin ta siket d'in bai wani kamata ba sai dai rigar ta kamata dan har ana iya ganin shatin inda bre d'in ta ta tsaya da yarda breast d'in ta suka fito sosai ta saman bre d'in, face d'in ta ya kalla yaga bata shafa komai ba sai lipgloss d'in da ta shafa wanda yasa idan ga gani zakayi zaton jambaki ne pink a bakinta " Zo" ya fad'a, taje hannu yasa ya janyota tare da zaunar da ita a gefen sa batayi aune ba kawai taji lips d'in sa akan nata ya shiga tsotse la'b'banta, sai da ya tabbatar da ya tsotse lipgloss d'in sannan ya d'auke bakinsa kan nata " Je ki cire wad'an nan kayan ki sa wasu sannan kuma daga yau kar na sake ganin kinyi irin wannan shigar da sunan zaki je school ke ba school kad'ai ba ko ina ne ma kada ki sake fita da irin wannan shigar kinji abinda nace?" Kai ta kyad'a masa alamar eh ta Mik'e jiki a sanyaye ta nufi d'akin ta, ta jima a zaune sai da ta kalli agogo taga time ya tafi sannan ta Mik'e da sauri ta canza tufafi ta zura dogon hijabn ta ta fice........................................................ Comment and share fisabilillah ♥️ 💋💋 ZARINAT ( زرينة )💋 💋 Mallakar Zainab dodo✍️ Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 _____________________________ _______________ ________ TASKIRA WRITER'S FORUM 💫T. W. F💫 Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝 _____________________________ _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 2️⃣0️⃣ Last free page's Ku hanzarta yin payment dan morar wannan gara'basar ki karanta littafi kuma ki koyi yarda zaki samu Sana'ar da zaki rik'e akan d'ari biyu kacal y'ar uwa 👌🥺haba d'ari biyur ce zata gagareki har kiyi losing wannan gara'basar, ki samu Sana'ar da zaki rik'e ki dogar da kanki ki huta da yawon dan allah rantamin d'ari uku jibi zan baki 😀 ga abubuwan da zan koyar bayan karatun littafin da zakiyi 👇👇👇👇 *1 Yarda ake madarar gari cikin sauk'i yarda zaki samu Sana'ar da zaki kama ki rabu da zaman banza* *2 Yarda ake sabulum gyaran jiki da fuska* * 3 Yarda ake yoghurt* *4 Yarda ake papaya soap*🧼 *5 Yarda ake had'in lalle yayi marron mai kyau* *6 Yarda ake sabulum cucumber* *7 Yarda ake tsami gaye* *8 Yarda ake orange soap* *9 Yarda ake tuwon madara* Duka wad'an nan abubuwan videos ne ta yarda zaku gani da idanu yarda zaku fahimta da kyau kuga yarda ake yi Haba y'ar uwa wace banzar ce kuma kike jira ki karanta littafi kuma ki koyi abubuwa har guda tara Wacce ta shirya biyan kud'i gashi * Banka name u b a* *Acc no: 2277089777* * Acc name: Zainab mustapha dodo* Sai a turo da shaidar biya ta wannan number *09046495943* *Sai na jiku yan amana* *Yanzu ne zan gane masoyana masu K'auna ta🤩😍🥰* *Allah ya bada iko ya hore abun biya* " Inna ana nan zaune?" Nasir ya fad'a tare da aje filet d'in dake hannunsa yace " ga abun kumallon ki nan au na manta ban d'auko jug d'in ba" ya Mik'e ya je ya d'auko jug ya kawo Inna ta bud'e filet d'in baki ta sake tare da fad'in " Nasuru mene ne wannan?" Inna doya da kwai ce sai kuma k'osai ai wallahi fatima tayi k'ok'arin yin wad'an nan abun ko lafiya bata da fatima na k'ok'ari " Kai dan allah dakata yanzu dan allah sai a kawo min ita haka tsirara duk k'amshin da naji yana tashi a gidan nan ace wannan abun ne kawai ina wannan abun da nagani mai kamar carbi?" Inna wallahi iya kan abunda aka soya kenan ai k'amshin kwai ne kikeji kuma gashi nan an had'e da doya" " Nasuru! Nasuru! Nasuru kaji tsoron allah wallahi tun da baka san a fad'in laifin matarka ai dole kasan yarda zaka kare ta tashi kaje " To inna ayi hak'uri" Tun kafin ka shigo duniya muke yin shi " shi dai baice komai ba ya wuce D'auka guda tayi takai baki" Uhmuhmm amman ko tayi dad'i yan banza " jug d'in koko ta bud'e ta kur'ba, ta k'ara bud'e k'afafu ta fara ci Nasir da fatima suka fito waje suka shimfid'a tabarma bakin k'ofar d'akin su suna breakfast, Fatima ta Mik'e taje d'aki ta d'auko wata kulla, Nasir yace" Wannan kular fa? Ta waye ?" Aunty larai ce ta bayar a kawo min " ta fad'a tare da bud'e kular arish ne da kwai ( dankalin turawa) rabi ta zuba a filet tace " Nasan wannan ya ishe mu anjima sai muci wannan" ta rufe kular ta mayar ta dawo suka fara ci Suna tsaka da ci inna ta fito idanun ta akan filet d'in da sauri ta isa wajen tare da rafka salati tace " Me zan gani haka? Nasuru! Nasuru kuji tsoron allah ni ku bani koko da k'osai ku kuci kwai da wannan abun" Aah inna wallahi ba daga ni bane nima yarda kika gansu haka na gansu daga gidan su ne aka aiko mata " Gidan su?" Eh" shuru tayi, ita dai fatima cin abinta kawai ta ke yi, inna tasa hannu ta talla'be filet d'in tare da fad'in " Ko daga gidan su aka kawo koma daga ina aka kawo wannan ku ya shafa ba abunda yamin zafi nima ga nawa wannan rabona ne ehhheeeee da kake kawowa ai duk tare ake ci sai yanzu za'a nuna min wariya to ni bansan wariyar ba mutanen banza wallahi yaran nan ku rik'a kyautatama iyaye to " ta fad'a tare da juyawa tayi d'akin ta Nasir yayi tagumi yana kallan fatima, tayi murmushi tare da fad'in " Karka damu bara na d'auko muna wancan sai mu ci" 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Yau faridah bata je school ba, bata jin dad'i, zarinat kad'ai taje duk sai taji ba dad'i, malamin da zai shigo musu ya kira yace bazai samu daman shigowa ba dan haka kowa ya watse Zarinat na tsaye waje bakin gate d'in makaranta tana tunanin yarda zatayi, gashi ta fad'a ma driver time d'in da zai zo ya d'auke ta ashe bazasu kai lokacin ba kuma wayanta na hannun yah ansar har yanzu bai bata ba bare ta kira sa ta sanar dashi, hn d'in da aka mata ne ya dawo da ita daga tunanin da take yi Motar Dr abbas ce, glass d'in motar ya saukar murmushi d'auke fuskarsa yace " Drivern bai zo bane? Kai ta gyad'a masa yace" Okay let me drop you " Aah nagode zan hau taxi " Kar kice haka mana please kizo muje akwai maganar da nake son muyi dake mai muhummanci" Sir nagode " ta fad'a tare da tare wata taxi 🚕 ta shiga, Dr abbas yabi bayansu dan yau son yake ayita ta k'are ya gaji da DAKON SOYAYYAR da yakeyi gwaunda ya bayyana mata abunda ke zuciyar sa, tafiya suke yana binsu ba tare da zarinat tasan yana binsu a baya ba har suka iso Fitowa tayi cikin taxi taga motar Dr abbas,ya bud'e murfin mota yana k'ok'arin fitowa, saurin bud'e jakarta tayi ta ciro kud'i ta Mik'a masa ta kama hanya, Dr abbas da gudu yasha gabanta tare da fad'in "Haba zarinat kamar baki ganni ba kike k'ok'arin shigewa"Sir dan allah kayi hak'uri "Nayi hak'uri akan me"Saboda bai dace na tsaya ina magana dakai ba "Saboda me?" Saboda ni matar aure ce" ta fad'a tare da bi gefensa zata wuce d'aga kanta da tayi sai ga fuskar yah ansar, gabanta yayi mugun fad'uwa yana tsaye bakin k'aramar k'ofar gate hannayen sa nad'e a k'irjin sa, dawowar sa da masallaci kenan zai shiga cikin gida yaga taxi ta tsaya tun lokacin yake tsaye Juyawa tayi taga Dr abbas na tsaye har yanzu, rasa abunda zata yi tayi, Dr abbas ganin yarda ta sauya yasa ya juya tare da kallan wajen da take kallo, yah ansar ya gani tsaye yana kallan su ba tare da yace komai ba ya k'wank'wasa k'ofar mai gadi ya Bud'e masa ya shige, Sun kai mints biyar a haka kowa da abunda yake sak'awa a ransa, sai da taja doguwar ajiyar zuciya sannan ta kama hanya ta k'wank'wasa mai gadi ya Bud'e ta wuce........................................................... Alhamdulillah anan na kawo k'arshen free page's wad'an da sukayi payment sai mun had'u dan jin yarda zata kasan ce tsakanin yah ansar da zarinat 🤸💃💃💃💃💃💃💃💃 Comment and share fisabilillah ♥️