*ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 1 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Littafin ZAN BI ZAB'IN UMMANA hakkin mallakata ne ban yarda a juya min shi ta kowace sigaba ba tareda izinina ba.* WhatsApp 09169472057 A Garin Katsina, Gida ne ginin jar kasa, irin gidajen hayar nan wanda suke dauke da dakuna da yawa amma bandaki da kitchen guda daya, mata ne zaune a tsakar gidan a karkashin iccen mangoro suna hirar duniya. A daya daga cikin dakunan, wata mata ce zaune akan tabarma yayinda wata kyakykyawar budurwa take durkushe a gabanta, matar ta dubeta fuskarta a murtuke tace, "Hafsat baki isa ki watsa min kasa a idanu ba, nice na haifeki don haka dolenki kibi abun da nike so koda kina so koda baki so, tun wuri ki rabu da Umar, ki saurareni da kyau, ke ba Matar Talaka bace ba, ban yi wahalar nakudarki domin na aurar dake wa talaka ba, nayi kuskuren aure talaka don haka bazan bari ki maimaita wannan kuskuren ba." Yarinyar wacce ta kira Hafsat ta d'ago da damuwa akan fuskarta tace, "Talauci da arziki duk na Allah ne. Kin ce bazan auri talaka ba, Umma idan kuma na auri mai kudi ya talauce, ko kuma talakan da na bari yayi kudi, mutum bazan tab'a tsallakewa kaddararsa ba...." Umma ta katseta da sauri kamar zata kai mata duka, "Ji min yarinya, ina magana kina maida min saboda kin rainani, magana ta karshe idan Umar yazo ki korashi ko kuma in shayar dake giyar mamaki domin k'aramin aikina ne in fita in koreshi da kaina. Tunda kin nuna baki jin maganata, gwara ki kwana da sanin cewa ba zan aurar dake wa talaka ba, sai mai kudi, mai gida da mota." Hafsat ta d'ago da damuwa akan fuskarta tace, "Umma mun dade da Umar idan na rabu dashi nayi butulci." Umma ta fusata ta daka mata tsawa har saida ta razana, "Haka nan auren mai kudi ba haramun bane ba, ki tashi ki bani waje, na dai fad'a maki, ko ki koreshi da kanki ko kuma in fita in korashi da kaina saidai ace ban kyauta ba tunda ba wani ya haife min ke ba, idan kuma yafi maki ni sai in gani. Tunda babu wanda ya tayani nakudarki sai in fita in korashi." A daidai lokacin wata matashiyar budurwa ta d'aga lalube ta shiga dakin, "Salaam alaikum." A tare suka amsa sallamar da tayi. Hafsat ta goge hawayen dake akan fuskarta tace, "Jalila amma kikace saida rana." Jalila tana mai karantar yanayinsu yayinda ta zauna a gefen tabarma, tace, "Na sauya shawara ne. Umma Ina kwana?" Umma tace, "Lafiya lau." Jalila tace, "Umma na sauya shawara sammako zamuyi." Umma tace, "Babu komai, Allah ya bada sa'a, Allah ya sakawa kasuwancin albarka." Jalila ta amsa da, "Amin." Tana mamakin abun da ya had'a Hafsat da Umma. Umma ta katse mata tunani, "Jalila ki rink'a fad'awa k'awarki gaskiya, gani take saurayi yafi ni a wajenta." Hafsat ta rumtse idanu jin furucin da Umma tayi ji take kamar ta fasa ihu, Umma ce take mata wannan shaidar domin kawai tana son ta tursasata rabuwa da Umar domin ta auri mai kudi, kudin da a duniya aka samesu a nan za'a tafi a barsu, tana mata hannunka mai sanda akan mutunci yafi kudi amma da alama Umma tayi nisa bata jin kira. Umma ta suri buta ta fice, "Sai kun dawo." Bayan fitar Umma, Jalila ta dubeta tace, "Angel baki kyautawa abun da kikeyi..." Hafsat ta katseta. Jalila tace, "Gaskiyar da baki so sai mun fad'a maki." Hafsat tana sanye ne da atamfa dinkin riga da zani ta bud'e jikkar ghana most go da take saka kayanta a ciki ta zaro dogon hijab har kasa ta zura ta duba fuskarta a madubi tace, "Muje." Fitowa sukayi, suka gaida matan dake zaune a tsakar gidan, santa ce wadda take dauke da gidajen mutane masu karamin karfi, gidajen dake akan santar mafi akasari kananu ne wasu ginin kasa ko shafe babu, babu kwalta a santar amma mota zata iya shigowa saidai akwai wurin da idan ta kai saidai ta tsaya, shiru santar take kasancewar yara sun tafi makarantar boko. Wata dalleliyar mota ta tsaya a gabansu, wanda yake ciki ya kurawa Hafsat idanu yana murmurshi yace, "Barka da warhaka en mata." A ransa yana yaba kyawunta mai daukar hankali, fara, mai matsakaicin tsawo. Ta murtuke fuska tace, "Babu ko'ina." Yayi dariya yace, "Nasan wajen muje in saukeku." Zuciya ta kawota wuya, a fusace tace, "Tsallake titi zamuyi, kaje ga wasu can suna neman abun hawa sai ka rage masu hanya." Yace, "Muje sai in tsallakar daku." Murmurshi da yake da nacin da ya nuna ji take kamar tayi ihu, taja hannun Jalila suka bar wajen ganin yana binsu ta tsaida kekenapep suka shige. A kasuwa bayan Jalila ta gama siyayya, suka jingina da wata expensive mota kirar Mercedes Benz suna jiran Kekenapep kasancewar dukkanin wadda zata shigo ko ta fita a cike take. Jalila tace, "Hafsat mi kikayi wa Umma?" A lokaci guda yanayin fuskarta ya sauya, tace, "Umma ta buk'aci in rabu da Omar in kawo mata mai kudi that ba zata aurar dani wa talaka ba, tace sai mai gida da mota zata aura min." Jalila tace, "Ya zakiyi yanzu?" Hafsat tace, "Tunda ina son farin cikinta zan rabu dashi. Ita kadai nike da a rayuwa, idan na rasata rayuwata zata tarwatse ne, kamar hakane idan nayi kuskuren zaben tumun dare akan miji aure zan hadu da kalubale, saidai ta fiye min shi a rayuwa don haka zan bi zab'inta koda zuciyata bata so." Ta lumfasa sannan tace, "Zan rabu da Umar in samu mai kudi kamar yadda take so, Umma ta zame min gata a rayuwa, ban da ita da bansan ya rayuwata zatayi ba. Umma ta hadu da kalubale masu yawa a rayuwarta a sanadina, iyayenta basu so aurenta da mahaifina ba saboda halayensa amma soyayya ta makantar da ita ta bujure masu, wannan ya saka sukayi fushi da ita. Tun da ta aureshi take haduwa da bakin ciki da kunci, bayan haihuwata ya gudu ya barta da ni, danginta suka koreta, rayuwa tayi mata juyin waina, haka ta rink'a yawon haya, tayi wankau, tayi sirfau, tayi aikatau a gidaje domin ta inganta rayuwata, dukkanin wani burinta a kaina yake, tasha wahala ta hadu da kalubalen rayuwa domin ganin na cigaba da karatun gaba da secondary. Ta ya zan bujire mata saboda saurayi wanda da girmana ya ganni." ****** Hisham ya bude idanunsa da sauri jin sautin muryarta ta wajen motarsa, kamar mai rad'a yace, "Bilkisu." Ya zafe zuciyarshi yayinda abubuwa da yawa suke dawo mashi a kai akan muryar wacce take magana. Da sauri ya b'alle murfin motar ya zagaya inda suke ya zuba mata idanu saidai idanunta kawai yake gani kasancewar ta rufe fuskarta da niqab. Hafsat tayi baya da sauri ganinsa tsaye a kanta, ta ware idanu ganin ya durfafo inda take, "Bilkisu." Ta tsaya cak jin sunan da ya kirata dashi, tayi zaton wata ce a bayanta yake wa magana amma ga mamakinta yana zuwa kusa da ita, ya saka hannu tareda warware niqab dake a fuskarta yana mai furta, "Bilkisu. Ina kika tafi?" Ya ware idanu ganin ba wacce yake tunani bace ba, yayinda maganar da ya fara ta makale mashi a makoshi. Ji tayi ranta ya b'aci ta fizge niqab dinta dake hannunsa tare da wanka mashi mari, a fusace take tana nunashi tace, "Idan kana cin kasa ka kiyaye ta suri." Hisham ya dafe kuncinsa yana kallonta ba tareda yace komai ba, ta kai mashi duka a kafa saidai ko gizau baiyi ba, tayi mashi mugun kallo sannan taja hannun Jalila suka dauki hanyar fita daga kasuwar tana mita akan abun da yayi mata. Jalila tace, "Angel kina da karfin hali har kika mareshi, mutumin da bugu daya zaiyi maki ki rasa inda kanki." Hafsat tayi murmurshi mai ciwo sannan tace, "Dukkanin abun da nayi mashi shine ya janyo kansa." Jalila tayi dariya sannan tace, "Lokacin da kika mareshi saida bakin glass dake a fuskarsa ya fadi kasa." Hafsat ta tab'e baki, "Raina a b'ace yake ko kallon fuskarsa ban yi ba." Suna fita bakin titi suka samu Kekenapep, Hafsat tana kwafa tana mita akan abubuwan da suka faru. "Daga ganin mace sai ya k'ura min idanu yana magana yana kallona kamar wanda bai tab'a ganin mace ba, shi kuma wancen har da zare min Niqab yana kirana da sunan da ba sunana ba." Jalila da neman fad'a tace, "Ayyerh yaga bamu iya tsallake titi bane shiyasa yake so ya tsallakar damu amma kikayi mamu bakin ciki." Hafsat tayi kwafa tace, "Ina zaune zaki dawo neman wacce zata rakaki kasuwa." Jalila ta marairaice fuska tace, "Haba k'awata kiyi hakuri, zanyi maki wainar fulawa. Kema ya kamata ki fara sana'a, zama hakanan babu hanyar shigowar kudi babu dadi musamman wa diya mace wacce bata da dan uwa ko uba namiji a kusa da ita wanda zai tallafawa rayuwarta." "Koda ina so, Umma ba zata bari ba, tace karatu take son inyi, bata son in raba hankalina waje biyu." A daidai lokacin ne kekenapep ta saukesu a kofar gidansu Jalila, Jalila ta toya masu wainar fulawa suka ci sannan ta fara yanka. Hafsat ta janyo wayarta ta kira Umar, bata tsaya doguwar gaisuwa ba tace, "Umar idan ka samu lokaci a yau ka zo Ina son ganinka." Daga daya bangaren yace, "Kinyi kewata ne." Ta bi takan maganar da yayi ba tace, "Ina son magana da kai a yau." Ta tsinke kiran ba tareda ta jira amsar da zai bayar ba. Umar yana, "Hello. Hello. Hello." Yaji shiru yana dubawa yaga ta tsinke kiran, da mamaki yake kallon wayar saidai bai kawo komai a ransa ba, ya saka a ransa watakila network ne. Jalila ta ajiye yankan da takeyi tace, "Angel mi kike k'ok'arin aikatawa?" Fuskarta dauke da damuwa tace, "Na kirashi yazo in fad'a mashi soyayya a tsakaninmu na k'are, ya rabu dani ya nemi wata. Ita kuma Umma inyi maka albishir da na yarda zan auri mai kudi kamar yadda take so amma akan sharadi guda daya, that zata barni in samu na gari wanda ba ya da damuwa." Jalila tace, "Har Umar ya bani tausayi. Yana matuk'ar sonki ba kadan ba." Hafsat ta share hawayen da suka zubo akan fuskarta tace, "Babu yadda zanyi, bani da wata mafita da ta wuce wannan, dolena in rabu dashi saboda Ummana ta fiye min shi a rayuwa. Na wuce kada Umma tayi fad'a. Yaushe ne muke da lectures?" Ta tambaya. Jalila tace, "Jibi. Lecture safe ne, eight to ten." Hafsat tace, "Alright, muje kiyi min rakiya." Jalila ta saka hijab suka fito, wata mata ce zaune akan tabarma tana kulla citta da sauran kayan miya a gabanta, Hafsat tace, "Mama na tafi." Matar wacce ta kira da Mama tace, "Ki gaida Ummanki." Hafsat tace, "Zata ji." Jalila tace, "Mama zan rakata gida." Mama tace, "Torh." Saida Jalila ta rakata har kofar gida sannan ta juya ta koma gida, Hafsat ta shiga ciki ta wuce dakinsu inda ta tarar Umma bata nan har ta wuce gidan da take aikatau. Da marece, tana zaune tana kuncewa Umma kitso, Umma tace, "Hafsat wacce shawara kika yanke akan maganar da nayi maki d'azu da safe, zaki koreshi da kanki ko kuma in shirya korarshi da kaina, zuwa da kai yafi aike, gwara in fita da kaina in koreshi, karkiyi mashi k'aramar kora ya dawo washegari." Hafsat ta rumtse idanu ta bud'e fuskarta dauke da damuwa tace, "Umma zan rabu da Umar in auri mai kudi kamar yadda kike so amma ina so kiyi min alfarma guda daya. Umma zan bi zab'in da kikayi min koda kuwa zuciyata bata so amma Umma a rayuwata ban san auren da zanje in fito ina sone inyi aure a inda zan zauna, Ina sone in auri miji na gari wanda y'ay'ana zasuyi alfahari da zab'in da nayi, ina sone ki barni in samu na gari wanda ba ya da damuwa, wanda yasan darajata." Umma ta saki gud'a fuskarta dauke da fara'a tace, "Yauwa er albarka. Yana zuwa ki korashi, ki rink'a kallon kanki a madubi daga kallonki babu tambaya mutum zai tabbatar da Matar Manya ce, ba kiyi irin talauci ba, ke matar masu kudi ce, ta sakawa a gaban mota." Hafsat ta rumtse idanu yayinda hawaye suka zubo akan fuskarta. Kafin ta k'ara magana yaro yayi sallama, "Angel ki zo in ji Umar." Umma ta yatsine fuska sannan tace, "Ka je ka ce mashi tana zuwa. Hafsat ki je na k'arasa kwantar kitson da kaina, ki je ki korashi ya k'ara gaba, saidai abi wani sarkin, kin fi karfinsa, kwalelen kare da hantar kura, kowa ce kworya da abokiyar gurbinta, ya je ya nemi daidai shi." Mik'ewa tayi jikinta a sanyaye ta zura hijab ta fita kofar gida, inda ta sameshi jingine da bango ta tsaya gefenshi tace, "Ina kwana?" Da murmushi akan fuskarsa yace, "Lafiya lau. Angel mi ya b'ata maki rai?" Tace, "Ka manta kawai." Furucinta ya matuk'ar bashi mamaki, ya dubeta yace, "Ta ya za'a yi in manta bayan naga wacce nike matuk'ar so a cikin damuwa." Kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace, "Abun da ya had'amu shine zai rabamu a yau shiyasa nace maka ka manta. Umar ina san ka manta da ni, ka manta da mun tab'a da mun tab'a soyayya ka je ka nemi wata, ba zan iya aurenka ba." Ya zaro idanu yace, "What? Saboda mi?" Saida ta juyar da kai sannan tace, "Saboda baka da kudi, saboda kai talaka ne, Ummana tace sai mai kudi zan aura, sharadin shine gida da mota. Kai kuma baka dasu." Da sauri yace, "Hafsat!." Tace, "Please ka rabu dani ka je ka nemi wata." Ji yayi ranshi ya b'aci yace, "Ke har ni zaki wulakanta bayan na bijirewa dangina da nayi nace sai ke. Mi kike takama dashi? Kyau ne kawai kike dashi amma baki da asali, zan taimaka maki ne kawai, bambamcinki da shegu shine saida aka d'aura aure sannan aka haifeki kuma ansan a inda dangin mahaifinki suke, ke da kike diyar mace, tun da aka haifeki mahaifinki ya tsallake ya gudu, ko kina tunanin bamu da labari ne, torh ubanki mahaifi d'an caca, mashayi." Ta zaro idanu yayinda hawaye suka zubo akan fuskarta tace, "Umar ni kakeyi wa gori?" Kanshi tsaye yace, "Ko nayi k'arya ne? Ay gaskiya na fad'a, ita ummarki saboda kwadayi don tana aikatau a gidan masu kudi taga yadda suke jin dadi shine take mafarkin zaki iya auren mai kudi, ki koma ki fad'a mata ko talakawa basu auren mace marar asali ballanatana masu kudi, ki fad'a mata ta sauya shawara domin wannan hanyar ba mai bullewa bace ba, nima taimaka maki zanyi in rufa maki asiri." Ta fashe da kuka ta juya ta shige cikin gidan da gudunta tana gumjin kuka. Umar ya dafe kai yana nadamar maganganun da yayi mata. Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 2 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 Hafsat ta tsallake matan dake a tsakar gidan ta shige daki ta fad'a akan gado tana mai fashewa da kuka, Umma ta shigo tana kallonta da mamaki tace, "Hafsat mi ya faru dake ne kika shigo kina kuka kamar wacce aka ce mata na mutu?" Hafsat tana mai cigaba da kuka tace, "Umma kinyi gaskiya da kika ce Umar BAI DACE DANI BA." Umma tace, "Ki sanar dani abun da ya faru, yanzu sai in shukawa mutum rashin mutunci domin ban hadaki da kowa ba." Tana mai sheshshekar kuka ta sanar da Umma abun da ya faru ta dora da cewa, "Umar yayi min gori akan mahaifina sannan ya kirani da diyar mace, yace min marar asali." Saida Umma ta lailayo ashar ta watsa sannan tace, "Lallai kuwa Ummaru ya janyo fad'an da ya fi karfin dukkanin danginsu, mik'o min mayafina inje har gida inci mutuncin iyayensa tunda bashi da kirki, sai yasan ya tab'oki, ni za'a yi wa rashin mutunci." Tasan halin Umma da fad'a idan taje gidansu Umar ba za'ayi da dadi ba, magana ce wacce bata fatan ta fita domin babu abun da zata janyo sai gulma da tsugunne-tsugunne a tsakanin mutanen unguwar wanda basu raina gulma. Ta mik'e zaune tareda had'e hannayenta waje guda alamar roko, tana mai cigaba da kuka tace, "Umma na rokeki da girman Allah ki rabu dashi, koda babu komai anyi walkiya na ganshi." Umma tayi mata wani kallo ta janyo mayafi ta yafa zata fita, da sauri tace, "Umma idan kikaje zan janye alk'awarin da nayi maki na auren mai kudi." Umma ta tsaya cak, ta dawo ta zauna tana maida lumfashi ranta a matuk'ar b'ace, "Shikenan na fasa amma duk ranar da ya k'ara maimaita abun da yayi sai yayi nadama, sai naje har gidansu anyi ta, har ya isa ya aibatani, yana kiranki diyar mace wannan diyar macen ta fi en uwanshi mata gata tunda bata tara samari tana rokonsu kudi, waye ba ya da labarin gidansu da rayuwar karya da danginsa mata suka sakawa kansu, yarinya anyi tuwo gidansu tace ba zata ci ba ta kira saurayi ya siya mata Indomie da nama, ya k'ara maki gori sai anyi tone-tone a tsakaninmu." Hafsat ta koma ta kwanta tayi lamo yayinda hawaye suke zarya akan fuskarta, cikin ranta tana ayyana, "Tabbas baiyi karya ba, ubana mahaifi mashayi ne, dan caca, wanda ya gudu ya barmu a gararin rayuwa, har zuwa wannan ranar bamu san halin da yake ciki ba, yana raye ko ya mutu bamu sani ba." ******* Katon parlor ne wanda yake zaune da setin expensive kujeru a kalla guda biyar, wata farar mata ce zaune akan kujera mai daukar mutum ukku yayinda wata kyakykyawar budurwa take zaune a gefenta tana kallo a TV. Hisham yayi sallama tareda kutsa kai cikin falon yana tafiya a sanyaye kamar wanda bashi da lakka, ya zauna kusa da matar tareda bata side hug, fuskarsa babu walwala yace, "Barka da warhaka, Momcy." Momcy tana mai shafa sumar kanshi cike da kulawa tace, "Barkanmu, ya office?" "Alhamdulillah." Fatima ta gaisheshi ya amsa da kulawa. Ya mike da nufin ya wuce bedroom dinsa Momcy ta tsayar dashi, "Abinci yana akan dinning table." Yana mai cigaba da tafiya yace, "Na koshi, zan ci anjima." Fatima tace, "Yaa Hisham. Coffee ko kunu?" Ba tareda ya tsaya ba yace, "Kunu." Momcy ta girgiza kai fuskarta dauke da damuwa tace, "Aisha ta cuceni a rayuwa, Hisham mutum mai fara'a da barkwanci amma ta maida min dashi miskilin karfi da yaji. Ta kassara min yaro. Ta kassara mashi rayuwa." Fatima ta share hawaye da suka zubo mata tace, "Allah shine zaiyi mamu sakayya akan abun da Aisha tayi mamu, ta rabamu da farin cikinmu, zanyi farin ciki idan yaya Hisham ya koma kamar yadda yake kafin faruwar wannan abun, koda kana cikin damuwa barkwancinsa kawai zai saka kayi dariya." Momcy tace, "Allah ya bayyana Bilkisu." Fatima tace, "Amin." Ta mik'e ta wuce kitchen domin dama mashi kunun. ******* Hisham yana shiga bedroom dinsa ya fad'a akan gado, ya janyo frame dake cikin bedside drawer, ya k'urawa fuskarta idanu yana tuna muryar wannan yarinyar (Hafsat). Fatima ce tayi knocking, "Salaam alaika." Da sauri ya b'oye frame dake hannunsa sannan yace, "Wa alaikissalaam." Ya bata izinin shiga. Ta kutsa kai tana dauke da flask da cup, ya mik'e ya zauna akan kujera, ya kirkiro murmurshi wanda iyakarsa akan fuska ne yace, "Little sis kina ji dani fa." "Dole inji da kai saboda kaine farin cikinmu a gidan nan. A koda yaushe ka rink'a tunawa da kaine farin cikinmu." Ta zauna tareda zuba mashi kunun, "In saka maka suger?" Ta tambaya. Ya girgiza kai, "A'a. Kin sanni bana sonshi da suger, na fi son dandanonsa a yadda yake." Har ta mike sai kuma ta koma ta zauna tace, "In tsaya inyi maka hira." Yace, "A'a, ina son kasancewa ni kadai." Ta ware idanu, "What! Amma mun dade da maganar nan kayi min alk'awari akan zaka rage sakawa kanka damuwa." Ya dafe kai, "Fatima ba haka nike nufi ba, ina nufin ki bani waje zanyi wanka in huta, kinga na gaji." "Ka tabbata ba tunani zaka zauna kayi ba." Ya gyad'a mata kai yana kirkiro murmurshi, tace, "Shikenan. Na tafi. Ka kula da kanka." Tana fita ya ajiye kofin ya janyo wayarsa ya shiga gallery hotonsa ne tareda wata kyakykyawar yarinyar wankan tarwada. A hankali yace, "Bilkisu kina ina ne? A wani hali kike ciki? Tunda kika b'ata nike a cikin damuwa. A yau na hadu da wata mai irin muryarki sak, the more take magana the more nike tunawa dake, ina son k'ara haduwa da ita saboda KAMANNI da muryarku ta ke yi." Ya dauki kofin yana sirfing kunun a hankali, wayarsah tayi ringing, ganin bakuwar number yayi jim kamar ba zai amsa ba sai kuma yayi picking yana fatan labari ne akan inda Matarsa Bilkisu take. Daga daya bangaren Aisha tace, "Ranka shi d'ad'e." Da sauri ya cire wayar daga kunnansa tareda tsinke kiran, wani kira ya k'ara shigowa, yayi rejection kiran tareda kashe wayar baki daya, ji yayi komai ya fitar mashi a kai ya mik'e ya shiga bathroom ya sakarwa kanshi shower yayi tsaye yayinda ruwa suke sauka akan jikinsa, yana tuna abubuwan da aka aikata mashi wadanda sune sanadin rushewar farin cikinsa, ya jima a hakan sannan ya d'aura towel ya fito ya fad'a akan gado ya zubawa ceiling idanu yana tuna baya. The following day, a hankali yake saukowa daga stairs yana sanye da suit brown cikin shirinsa na zuwa aiki, yayi matuk'ar kyau, sumar kanshi irin ta buzaye tana a kwance, yana tafe yana baza kamshi mai sanyi, kai tsaye ya wuce dinning table, yaja kujera ya zauna yana mai gaishe da Momcy. Ta amsa da kulawa. Fatima da ta ajiye flask tace, "Ina kwana yaya Hisham?" Yace, "Lafiya lau. Kin tashi lafiya?" "Lafiya lau. D'iyar direba babu lafiya a asibiti suka kwana, please ka sauke ni a school." "Babu damuwa, uhmm musha hira abunmu." "Haka, muyi gulmar Momcy." Momcy tace, "Ji min yara nema kuke ku mayar da ni kakarku. Zan hadu daku ne." A tare sukayi dariya. Fatima tayi serving dinsu sukayi breakfast, saida ya ajiye Fatima a makaranta sannan ya wuce company, yayi parking motarsa a parking lot dinsa wanda yake underground, ya fito yana dauke da briefcase, Najeeb ya amshi briefcase din saying, "Good morning sir." Hisham yace, "Morning. Bana son hayaniya zanbi private elevator dina." Najeeb yace, "An gama ranka ya dade." Hisham yana gaba Najeeb yana biye dashi heading to the elevator, Najeeb ya danna bottom din, ya bud'e suka shiga, ya danna floor na ashirin da daya 21 wanda shine floor na karshe a inda ofishin CEO yake, suka fito suka bi wani corridor, Hisham ya danna hannunsa akan wata na'ura, ya dauki finger print dinsa sannan kofar ta bud'e suka bayyana a wani katon office, gini ne na glass. Najeeb yace, "Sir Hisham, Coffee ko Tea?" Hisham yace, "Ka koma ofishinka, idan ina buk'ata zanyi wa secretary magana." Najeeb yace, "Okay sir." Ya juya ya nufi kofa, Hisham ya kira sunansa, "Najeeb." Najeeb ya juyo saying, "Sir." Hisham yace, "Na gode sosai Najeeb da tsayawa da kake akan al'amurana. Ina matuk'ar godiya, Allah ya saka da alheri." Najeeb yace, "Allah ya bayyana Bilkisu." Ya juya heading out yana mai tausayinsa. Hisham yace, "Amin." Tunda yaji muryarta ya kasa sukuni, the more yake tuna Bilkisu the more muryarta (Hafsat) take mashi amsa kuwwa a kunne a lokacin da take baiwa k'awarta labari. Wani kamshi mai ne ya doki hancinsa ya rumtse idanu yayinda b'acin rai ya bayyana k'arara akan fuskarsa, ba tareda ya kalli wacce ta shigo ba ya danna landline yace, "Secretary, how dare you let her walk into my office. Waye ya bata izinin shigowa ofishina." Daga daya bangaren yace, "I'm sorry sir, she didn't listen to me, ina mata magana tayi banza dani, ta bangajeni ta shigo." Cike da b'acin rai yace, "Huh haka aka yi? Baka da yadda zakayi da ita shiyasa ka barta ta shigo? Alright then." Secretary yace, "Sorry sir." Da kakkausar murya yace, "Damn it, daga yau idan ka kuma bari ta shigo ofishina ka rasa aikinka. Idan ta bangajeka ta shigo, aikinka ta bangaje, ka rasashi." Ya d'ago ranshi a b'ace ya daka mata tsawa, "Aisha!." She is chubby, brown skin mai matsakaicin tsawo, tana sanye da atamfa dinkin half gown, ta kashe dauri samfurin ture kiga tsiya, fuskarta dauke da simple makeup, tasha Jan lipstick, kafafunta rufe da takalma kirar half cover, da mayafi akan kafad'arta, tana kallonsa tana wani shegen murmushi, tayi tako tareda d'aura hannu akan desk dake gabansa ta rik'e kugu da daya hannun tace, "Tabbas Aysher shine sunana saidai tsawarka ba zata saka in koma inda na fito ba har sai na aiwatar da abun da ya kawoni tukunna." Ya daka mata tsawa a karo na biyu, "Ki fitar min daga office, tun kafin in hadaki da security." Saidai tsawarsa bata razanata ba, sai murmushin gefen baki da tayi tace, "Kwantar da hankalinka, koda baka ce ba ai dole zan fita tunda ba ofishin ubana bane ba, na zo ne in k'ara tuna maka abun da ka riga ka sani, jiya na kira ka tsinke min kira, ina baka shawara gwara ka hakura ka mayar da ni, idan har Bilkisu ce kake jira ba zata sake dawowa ba, ta tafi kenan, tana garari akan titi tana hauka. Ni ce kadai wacce zakayi rayuwa da ita a matsayin matarka a zauna lafiya, babu macen da ta isa inyi zaman kishiya da ita a gidanka. Tun wuri kayi wa kanka fad'a ka mayar da aurenmu. Hisham da wata mace ta rab'eka gwara kowa ya rasa. Ba Bilkisu ba, kowace mace da zata rab'eka sai na b'atar da ita, sai na zame mata guguwar bala'i. Kaje ka dawo ina nan ina jiranka." Hisham ya kira sunanta a tsawace, "Aishaaa!." Duk da ta razana da tsawa da yayi mata a wannan karon saidai bata nuna ba, ta kanne ido guda daya sannan tace, "Kana wahalar da kanka ne domin tsawarka ba zata tab'a razanar da ni ba, domin ban fito ba saida na shirya. Ya yarona Abdallah?" Yayi banza da ita kamar baiji abun da tace ba, tayi dariya mai sauti, "Koda yake na tabbata yana a cikin koshin lafiya a tare da danginka, ka fad'a mashi ya k'ara idan ka gama zagaya duniya ka tabbatar da dukkanin wacce ka nuna interest a kanta fad'awa take taskon rayuwa, daga karshe dole zaka dawo gareni, ni duwawu ce zama dani dole, kishiya a gidana babu. Na barka lafiya." Ta juya tana tako daidaya yayinda baki daya jikinta yake girgiza, juyowa tayi fuskarta dauke da wani shu'umin murmushi tace, "Da fatan ka rik'e gargadin da nayi maki, idan kana ganin barazana ne ka kwatanta ka gani idan har zaka rab'i wata mace ni kuma zan kassara rayuwarta. Idan baka gaji ba, nima ba zan gaji, a shirye nike a koda yaushe domin kassara rayuwar dukkanin wacce ta rab'eka ko kuma ka rab'eta." Hisham yace, "Mugun abu jakada ne idan ka aikeshi komai daren dadewa sai ya dawo zuwa gareka domin ya sanar da kai cewa yaje." Aisha ta girgiza kai tace, "I totally disagree with this proverb, whatever. Saidai idan mutum bai iya takonsa ba, kamar yadda Bilkisu take a uwa duniya tana hauka, wannan shine kwatankwacin abun da dukkanin wata mace daka rab'a zata fuskanta, shawara ka taimaka karka tilasta min tarwatsa rayuwar wata, ka taimaka masu ka dawo zuwa gareni sai a zauna lafiya. Ka rage sakawa kanka damuwar wacce ba zata tab'a dawowa ba. Ayyerh Bilkisu, tana zamanta lafiya a akurkin gidansu ka janyo mata fitina." Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 3 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 Hisham ya daka mata tsawa yayinda idanunsa suka kada sukayi ja ya nuna mata kofa, "Ki fitar min daga office." Ta razana har saida tayi baya, duk da haka bata karaya ba tace, "Idan naki fita ba, miye kake ji zaka iya aikatawa. Nace or else what? Do your worst I don't care." A fusace ya mike ganin haka ta juya ta fita, ya fad'a akan kujera tare da dafe saitin zuciyarsa yana maida lumfashi, ya jima a haka kafin ya bud'e idanunsa wadanda suke sauya launi a sanadin b'acin rai, ya danna landline yace, "A fito min da mota yanzu." Ya jingina da kujera ya lumshe idanu yana sauke lumfashi ransa a matuk'ar b'ace. ***** Hafsat da Umma ne zaune a saman tabarma akan baranda yayinda sauran matan gidan suke zaune a bakin bishiyar mangoro dake a tsakar gidan, Hafsat tana jerawa Umma celatap zata saka mata lalle, lokaci zuwa lokaci wayarta tana tsuwwa, tun tana tsinke kiran har ta kashe wayar baki daya. Umma tace, "Hafsat ki amsa kiran." "Umar ne." Tace a takaice. Umma ta murtuke fuska, "Saboda mi yake damunki bayan anyi walkiya kin ganshi ganin idonki..." da sauri ta katseta sanin matan gidan sun kasa kunne suji abun yadawa a gulma. "Na kashe wayar ne baki daya." Umma ta ware idanu tace, "Akan miye zaki kashe wayarki." Ta fizgo wayar ta kunna kafin ta mik'a mata tace, "Amsa ki sakashi a wannan abun wanda koda mutum ya kiraka ba zai samu ba." Ta gane blacklist take nufi, tace, tace, "Umma Blacklist." Umma tace, "Eh shi, makashi a can, ke dashi saidai hange daga nesa, nan gani nan bari sadakin bazawara ai koda na budurwa ne yafi karfin wasu." Wani kiran ne ya shigo ta tsinke tareda saka numbobinsa a blacklist. "Kin saka." Umma ta tambaya. Hafsat ta gyad'a kai tace, "Na saka." "Yauwa er albarka, idan ya kuma kiranki da wata numbar kina jin muryarshi itama ki sakata a can." Ta gyad'a kai. Umma tace, "Haka nike son ji." Ta lumfasa sannan tace, "Angel iya zama da mutane yayi a rayuwa, bikin da za'ayi a gidan da nike aiki amaren da kansu muke cewa dani za'aje kaisu, daya za'a kaita Abuja daga nan su wuce Italy inda mijin yake zaune, daya kuma Kano." "Amma Umma ina zakije a ciki?" Hafsat ta tambaya. Umma tace, "Abuja kai yayar, idan zamu dawo zamu biya ta gidan k'anwar a Kano. Ki tattara kayanki goben ki wuce gidansu Jalila har in dawo, bani san zamanki a gidan nan ke daya, mugu ba ya da kama, ga gulmar matan gidan nan ke kuma ba iya fitina kikayi ba, idan kin gama min kunshin kema ki cike kumbarki, ina so ki auri mai kudi amma kina yawo da hannuwa da kafa kamar na kato, kina gyara kanki kina abu irin na mata, sai kiga cikin sauki kinyi wuff da wani attajirin mai kudi." Murmurshi ne ya sub'uce mata tace, "Umma zan yi." "Allah yayi maki albarka." "Amin." Washegari Umma ta wuce wajen biki yayinda Hafsat ta tattara kayanta ta koma gidansu Jalila, ta yada zango a dakin Jalila. Washegari da marece suna zaune a tsakar gida, Jalila tana chat na cinikin wasu Hijabi da ta dinka, ta d'ago tace, "Umar fa?" Hafsat tace, "Umar mi?" Jalila was like, "Ikon Allah kina amsa min tambaya da tambaya." Hafsat tace, "Ki fito ki fadi abun da yake ranki." "Ya sameni ne da maganarki." Hafsat ta rumtse idanu ta bud'e fuskarta dauke da b'acin rai tace, "Ban fad'a maki abun da yayi min bane saboda ina cikin b'acin rai makura, idan na sanar dake raina ne zai k'ara b'aci idan na tuna, bayan da na sanar dashi yadda mu ka yi da Umma na fad'a mashi ya rabu da ni, shine yayi min gori ya kirani da er mace sannan ya aibata mahaifina." Ta kwashe abun da ya faru a tsakaninsu ta sanar da ita, ta dora cewa, "Shiyasa na godewa Allah da ban bijirewa Umma a kanshi ba." Jalila ta jingina kai, "Umar bai kyauta ba, ya bani mamaki, ban tab'a tunanin zaiyi haka ba amma duk da haka Angel kiyi hakuri ki ganshi saboda..." ta katseta, "A wanne dalili zan ganshi?" Jalila ta dafata, "Please kiyi min alfarma nayi mashi alkawari, yanzu haka yana akan hanya, da nasan abun da ya faru bazan yi mashi alkawari ba." Hafsat tayi shiru cike da takaici, Jalila tace, "Kiyi hakuri ban san abun da ya faru bane ba, babu dadi yazo baki fita ba amma duk da haka bazan maki dole ba idan kina ganin akwai damuwa idan yazo sai in fita in bashi hakuri." Ta daureta da jijiyoyinta, Jalila tana da matsayi mai girma, tayi mata halarci, sau da yawa tayi abubuwan da bata so saboda ita. Ta lumfasa sannan tace, "Idan yazo zan fita." Jalila tace, "Na gode." Hafsat ta rufe idanu yayinda ta lula a duniyar tunani. Bayan Rabin Hour Umar ya kira Jalila akan yana a kofar gida, fahimtar shine ya kira tun kafin tayi mata magana ta mike ta fita, bata fatan k'ara haduwa dashi a rayuwarta, yayi mata gori, ya aibata Umma, ya aibata mahaifinta, wanda bai mutunta iyayenta ba mijin aurenta bane ba koda kuwa shine autan maza, koda kuwa shine wanda yafi kowa arziki, bata tab'a sanin mahaifinta ba, ya watsar dasu, bai waiwayesu amma a zuciyarta tana mashi uzuri domin Uba uba ne. Jalila ta zura dogon hijab akan kayan da suke a jikinta, ta biyo bayanta, tace, "Umar ga Angel nan, na barku lafiya." Umar yace, "Na gode." Ta juya ta koma cikin gida. Umar ya dubi Hafsat wacce ta murtuke fuska, yace, "Angel ina mai baki hakuri akan abun da ya faru a waccen ranar, nayi nadama matuk'a akan abun da nayi maki, ban yi da nufi ba, raina ne ya b'aci shine nayi sub'utar baki." Ta rasa bakin magana, tun da suke tare dashi bata tab'a tabbatar da bai iya magana ba sai a wannan ranar, ya dubeta yace sub'utar baki, lallai Umma tayi gaskiya akan cewa da tayi Umar bai dace da ita ba. Da ace ta bujure mata ta aureshi tana mashi laifi kadan zai fara mata gorin iyaye yana zaginta. Tayi murmushi mai ciwo sannan tace, "Ba sai ka bani hakuri domin naji matuk'ar dadin wannan sub'utar bakin da kayi saboda ya saka anyi walkiya naga ainihin waye kai, na gode Allah da ban bijirewa Ummana a kanka ba, na gode Allah da ya kubutar dani daga aurenka domin na tabbata da ace na aureka, gorin da zaka rink'a min kenan bayan aurenmu." Kamar zaiyi kuka yace, "Angel..." ta katseshi, "Eh Angel sunana ne, mi aka yi? Mi kake son kace? Ka fad'a ta cikinka domin ina da abun yi." Ya marairaice fuska yace, "Hafsat ina so ne ince maki kiyi hakuri hakan ba zai sake faruwa ba, nayi nadama sosai akan maganar da nayi maki." Ta d'aga mashi hannu tana mai girgiza kai, "Umar nadamar da kayi ba shi da amfani domin bakin alkalami ya riga ya bushe, umar ka b'ata rawarka da tsalle, kaje ka nemi wata, bazan tab'a aurenka, bazan tab'a auren wanda bai san dajarar iyayena." Ji yayi ranshi ya b'aci, yana bata hakuri tana abu kamar diyar gold, bayan yasan komai a kanta, bayan taimaka mata zaiyi ya aureta, kyawunta ne kawai take dashi amma bata da asali. Ya rumtse idanu ya bud'e yayinda suka sauya kala zuwa launin ja, ya daka mata tsawa, "Ke! Mi kika dauki kanki ne? Ina baki hakuri kina b'audewa, naga dai abun da na fad'a gaskiya ne, ba k'arya nayi ba." Ji tayi hawaye sun zubo mata bata tab'a tunanin rana zata zo da umar zaiyi mata gori, bata tab'a tunanin wannan abun daga gareshi, a tunaninta idan aka yi mata gori shine mutum na farko da zai bi mata hakkinta yaji dadi amma sai ya bige da yi mata da kanshi. Tana mai zubar da hawaye tace, "Shiyasa hausa suka ce rashin sani ya fi dare duhu, ina mai baka hakuri akan bata maka lokaci da nayi kayi soyayya da marar asali irina tunda yanzu idanunka sun bude ka gane gaskiya." Yace, "Na san komai kuma na zab'eki saboda ina matuk'ar sonki." Ta rasa bakin magana, yana tukfa yana warwarewa, mamaki yake bata, tace, "Umar kaje ka nemi daidai kai, domin nafi karfinka." A fusace ya taso mata, "K'arya kike, tunfa har nike sonki dole sai na sameki, daga ke har kwadayayyar mahaifiyarki baku isa kuyi min wasa da zuciya ba, ina ce kudi ne matsalarku, torh zan shiga duniya inyi kudi ta kowace hanya sannan in dawo in aureki, ke tawa ce." Hafsat tayi mashi mugun kallo, akan idanunta yake kiran Ummarta da kwadayya, ji take kamar tayi ball dashi, tace, "Angel da kake gani nafi karfinka, koda kudinka ba rabonka bace, bazan tab'a aurenka ba Ban san *BURIN ABBANA* ba amma _BURIN UMMANA_ shine in auri mai kudi, ni kuma burina shine in auri miji na gari don haka zan had'a burikanmu a waje guda in auri mai kudi sannan kuma miji na gari, domin a tsakanin masu kudi da talakawa ana samun na gari da mugaye." Umar ya daka mata tsawa, "Hafsat dolenki ki aureni saboda ina sonki." Tayi murmushi na takaici sannan tace, "Umar nayi nadamar b'ata lokacina da nayi a wajen soyayya da kai, ina so ka saka a ranka cewa baka tab'a soyayya da ni ba, ka manta da ni, ka saka a ranka cewa ka tab'a soyayya ne da wacce take shigen KAMANNI da ni. Zan jure komai amma ban da wulakanta mahaifana..." ya katseta, "Wulakanci ko kuma gaskiya. Angel Idan ke kince baki sona, ita ummar taki idan naje nayi kudin ina dawowa na watsa mata su a fuska, kwadayin kudinta ya tashi, zata bani aurenki koda kina so koda baki so, burinta shine kudi, torh zanyi kudi. Ki cire wa ranki cewa zaki iya rabuwa dani domin nine kadai hope dinki, ka fad'awa kanki gaskiya koda talaka bazai auri mace marar asali ba ballanatana kuma mai kudi, ke da kyau ne kawai kike taqama, saidai kinyi rashin sa'a domin akwai mata masu kyawu da yawa a gari wadanda suke da asali da nasaba." Ta fashe da kuka tana mai jin tsanarsa a ranta, "Umar na tsaneka, nayi nadamar soyayya da nayi da kai." Ta juya da gudu ta shige ciki ta tsaya a soro ta fashe da kuka, saida tayi mai isarta sannan ta goge fuskarta ta shiga ciki ta wuce dakin Jalila, ta kwanta tayi lamo tana hawaye. Jalila ta biyo bayanta tana mai tambayarta abun da ya faru. Tana mai cigaba da kukan tace, "Ina kuka ne saboda bakaken maganganun da yayi shiyasa ban so fita ba." Jalila ta ware idanu tace, "Kina nufin bakaken maganganu ya fad'a maki. Ashe ba ya da mutunci, dama saka na fitar dake ne domin ya b'ata maki rai, lallai kuwa zai san ya raina min hankali, ni zai mayar mutuniyar banza." Sanin halin Jalila da daukar zafi, idan ta fita ba zaiyi kyau ba, tace, "Ki barshi kawai, rayuwa ce, wata rana sai labari." Jalila tayi mata wani mugun harara tace, "Dalla kiyi min shiru, ke dama idan mutum ya biye maki sai ayi mashi dukan tsiya sannan ya bada hakuri, yau sai Umar yasan ya b'ata maki rai." Ta kira numbarsa yana picking tayi mashi tas, ta inda take shiga bata nan take fita, dukkanina aibun gidansu da ta sani sai ta amayar, yayi rashin sa'a Jalila basu da abun fad'a, saida tayi mashi wankin babban bargo sannan ta tsinke kiran tana sauke lumfashi ranta a matuk'ar b'ace. Bayan Kwana Hudu, Hafsat ce take waya da Jalila, tace, "Besty, kizo ki amshi tsarabarki Umma ta bud'e jaka." Daga daya bangaren Jalila tace, "Ayyerh k'awata, kunyarki nikeji akan abun da na janyo Umar yayi maki shiyasa kikaji ni shiru." Hafsat tayi dariya tace, "Kai babu komai tunda kin rama min kuma dolensa yayi shiru tunda kowa ya tabbata gidanku basu da aibu." Jalila tace, "Kiyi hakuri ban san zai b'ata maki rai bane shiyasa." Hafsat ta girgiza kai kamar tana gabanta sannan tace, "Na fad'a maki babu komai beside kin rama min abun da yayi min, a tunaninsa ni ce kadai nike da abun da za'a fad'a amma kin tuna mashi shima cewa shima iyayensa suna da abun fad'a kowa ya sani, kara kawai muke masu muna yi kamar bamu sani ba." Jalila tayi dariya sannan tace, "Naso ace ke fitinanna ce." Hafsat ta sauya hirar lura da kallon da Umma take mata, kallo ne da yake nuni da cewa ta fahimci wani abu akan wayar da take, tana jira ta gama ta fad'a mata ba'asi akan abun da ya faru. Tace, "Ki zo ki amshi tsarabarki." Jalila tace, "Alright, Angel, zan shigo yanzu kuwa Allah yasa har da alkaki." Hafsat tace, "Har dashi kuwa." Tana tsinke kiran Umma ta tutsiyeta da kallon tuhuma tace, "Mi ya faru?" Tayi shiru, Umma ta daka mata tsawa, "Zaki fad'a min ko kuma sai na kira Jalila na tambayeta tunda ita tana ganina da mutunci zata fad'a min." Hafsat ta girgiza kai, "Umma ba haka bane, abun b'acin rai ne shiyasa." A ranta tana tunanin k'arya da zatayi Umma domin ta tabbata idan ta fad'a mata gaskiya sai rai b'aci domin babu abun da zai hanata zuwa gidansu Umar. Umma tace, "Ina sauraronki, mi fad'a min abun da ya faru, yadda ya b'ata maki shima sai ranshi ya b'aci." Ta lailayo ashar ta saki, zama da mutanen haya na gidan ya saka Umma ta koyi fitina, zagi da rashin hakuri. Hafsat tayi dariya tace, "Bayan kin tafi biki yaje gidansu Jalila da nufin yayi min cin mutunci da gori, kin san Jalila babu hakuri ta fita tayi mashi wankin babban bargo, tayi mashi gori akan abun fad'i na gidansu, har kuka yayi domin kowa yasan gidansu Jalila basu da abun fad'a, basu da aibu." Tayi mata k'arya. Umma ta share hawayen da suka zubo mata tace, "Shiyasa yake da mu nemawa yaranmu iyaye na gari, kaicona na bujurewa iyayena na aureshi duk da halayensa amma soyayya ta rufe min idanu, saidai tun ba'aje ko'ina ba nike ganin ba daidai ba, ya gujeni, gashi yau har mutane suna maki gori akan zab'i marar kyau da nayi. Ki yafe min." Hafsat ta share mata hawaye, "Ummana ta kaina ki daina kuka, ki barni inyi tunanin yadda zani samo maki suruki irin wanda kike so." Umma tace, "Yauwa er albarka." A tare sukayi dariya. Jalila ta bude labule saying, "Mu shigo ko mu koma." Umma tace, "Shigo er albarka, yanzu Hafsat take bani labarin yadda kukayi da Umar." Jalila ta zauna akan tabarma tace, "Ba ya wayo ko kadan, shi a ganinsa babu wanda yasan abun fad'a da suke dashi, yana tunanin bamu da labari akan dalilin da ya saka suke dawo cikin gari, kakan kakansa ya addabi kauyensu da haurawa gidajen mutane yawon kwartanci, suka koresu shine suka dawo cikin gari da zama. Shiyasa yake da kyau mutum ya tauna magana kafin ya fad'a, idan mutum ya biyewa b'acin rai sai yayi maganar da zai dawo yana nadama, koda ka baiwa wanda ka fad'awa hakuri ya hakura wannan bazai saka ya kwanta da ciwon maganar ba." ********* Gidansu Hisham, Ranar Asabar, Momcy ce zaune a parlor tana kallon News, Fatima tana daga gefe idanunta akan laptop dake gabanta yayinda Abdallah yake wasa da ball, Hisham ya fito daga study room yana sanye da dogon trouser da farar vest, Abdallah ya ruga inda yake, ya daukeshi yana mashi wasa suna dariya, kammanin yaron daya sak da Hisham, babu abun da ya baro na kamanninsa, har dariyarsu iri daya ne, ya saukeshi, yace, "Okay, kaje ka cigaba da wasanka." Abdallah ya ruga ya dauki ball yayinda Hisham ya zauna kusa Momcy ya d'aura kanshi akan shoulder dinta yace, "Momcy." Tace, "Na'am Fad'a min abun da yake damunka." Saida yayi jim kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace, "Kwanaki na hadu da wata yarinya muryarta daya sak da Bilkisu." Jin abun da yace ta cire idanunta daga kallon da take ta fuskanceshi, "Hisham don muryarta daya da Bilkisu, wannan bazai mayar da ita Bilkisu ba." Yace, "Momcy ba haka nike nufi ba." Ta maida hankalinta a kansa fahimtar akwai abun da yake son sanar da ita, tace, "Ina sauraronka." Saida ya lumfasa sannan yace, "Muryarta iri daya ce sak da muryar Bilkisu, the more take magana the more nike tunawa da Bilkisu, banbancin muryarsu daya ne shine ita tana da saurin magana..." jin yayi shiru, tace, "Ina jinka." Domin tana da tabbaci ba'a nan maganar ta tsaya ba, kamar ba zaiyi magana sai kuma yace, "Ina son in aureta." Momcy ta dubeshi da mamaki sai kuma ta saki murmushi tace, "Hisham yau kaine kake min maganar aure. Alhamdulillah. Wacece ita?" Yace, "Sunanta Hafsat amma ana kiranta Angel, tana rayuwa tareda mahaifiyarta, mahaifiyarta ta bujurewa iyayenta ne ta auri mahaifinta, ashe bashi da kirki, bayan ta haifi Hafsat din ya gudu, danginta sunyi fushi da ita sukaki karbarta har sai ta maida diyar zuwa ga dangin mahaifinta ita kuma ta kiya saboda a cikin dangin mahaifin yarinyar babu na kirki, dukkanin inda ta bada diyarta rayuwarta zata tarwatse, a haka suka rayu a gidan haya, mahaifiyar tana aikatau." Momcy tace, "Amma kana jin furucin da Aisha tayi, kada a k'ara maimaita abun da ya faru da Bilkisu." Hisham ya girgiza kai, "Barazana ne kawai takeyi." Momcy ta jinjina kai tace, "Amma kana tunanin idan sukayi bincike sukaga wannan matsalar zasu dauki diyarsu su baka?" Ya girgiza kai yace, "Babu bincike da zasuyi." Da mamaki take kallonsa jin abun da yace. "Ba zasuyi bincike ba saboda mahaifiyar yarinyar burinta kawai shine diyarta ta auri mai kudi." Jin haka tace, "Ya halayyar yarinyar yake kada azo a maimaita na Aisha." Yace, "Bata damuwa na fahimci hakane ta yadda ta sadaukar da farin cikinta domin ta cika burin mahaifiyarta." Fatima ce ta dawo kusa dasu tareda zama akan hannun kujera tace, "Yaa Hisham yaushe zaka kaini in ganta?" Ya girgiza kai, "Ban yi mata magana ba, uhmm, saidai na saka ana bibiyarta, bayan auren zaki ganta." Fatima ta ware idanu jin abun da yace, tace, "Yaa Hisham kayi sauri ka gabatar da kanka a wajenta tun kafin ai maka wuff da ita. Muga hotonta?" Ya fiddo wayarsa ya lalubo hotonta guda daya da yake dashi a wayar, ya mik'a mata yace, "Ita ce farar." Ta ware idanu tana yab'a kyawunta, "Wow, ta had'u, tana da kyau kamar jinin Arab. Amma ina ka samu hotonta?" Ta tambaya. Yace, "A social media k'awarta ta d'aura." Fatima ta matsa wajen Momcy tana nuna mata hoton, "Momcy kin ganta, itace farar." Momcy ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi tace, "Masha Allah." Hisham ya janyo dayar wayarshi yayi kira yayi jim sannan yace, "Tana ina?" Daga daya bangaren aka ce, "Sir tana shopping mall." Saida yayi jim sannan yace, "Tare da wa? Okay, na gane." Mikewa yayi yace, "Momcy zan shirya in fita." Fatima tana dariya tace, "Yaya yana kishi, yana gudun samari suyi mashi wuff da ita." Ya amshi wayarsa ya dungure mata kai, yace, "Gulma. Uhmm, yaushe zaki kawo min saurayinki." Ta rufe fuskarta ta mik'e ta gudu tana cewa, "Babu ruwana." Hisham da Momcy suka bita da kallo suna dariya. Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 4 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 Shopping mall, A jere suke tafiya a cikin shopping mall din, Hafsat tace, "Ina zamana lafiya kika tadoni, gashi ina ganin abu ina so babu damar in dauka tunda ban zo da shiri ba." Jalila tayi fuskar dariya tace, "Ki dauki dukkanin abun da kike kike so zan siya maki." Hafsat ta kai mata duka, ta goce saying, "Na sanki da kaunar chocolate. Ki zabi kowane iri kike so zan siya maki." Hafsat ta kumtse dariya tana kallon tulun chocolate dake wajen tace, "Amma kin tuna kince kowane iri..." Jalila ta katseta, "Amma idan bai fi karfina ba." Hafsat tace, "Kince duk wanda nike so, kuma kin dawo kince idan har baifi karfinki ba, wacce maganar zan dauka a ciki." Jalila tace, "Maganar hankali." A tare sukayi dariya, suna zagayawa Jalila tana daukar perfumes, cream, lipstick, brusher yayinda Hafsat take busy tana duba chocolate. Jalila tace, "Ki gama dubawa ki zabi wanda zaki dauka mu wuce." Ta kalleta ta watsar, "Tunda na jiraki kika gama, dolenki ki jirani in gama, ina zamana a dakin Ummana ina hutawa kika tadoni." Jalila tace, "Ki zo ki daina zaman banza ko data ne ki fara siyarwa." Hafsat ta zaro idanu tace, "Da kuwa dake da kika bani shawara, dani da na dauka duk sai Umma taci kaniyarmu." A tare sukayi dariya, suka wuce inda ake biyan kudi aka lissafa masu, Jalila ta mik'a card dinta aka zare ta amsa aka zuba masu kayan a leathers suka fito suna tafiya a hankali. Jalila tana bata labarin dalilin fitowar, "Ciniki nike sosai a cikin kwanakin nan shiyasa nace gwara in fito inyi wa kaina shopping inci mai kyau, kin san abaya guda biyar na siya amma ukku kawai na nunawa Mama, suma ban fad'a mata aihinin kudinsu ba." Hafsat ta fashe da dariya tace, "Sai ranar da tace kije ki siya mata irinsu ne, a ranar ne zaki gane k'arya babu kyau. Ya kikayi da sauran?" Jalila tace, "Na b'oye na saka a kasan akwati." Wani kyakyatawan saurayi ne yasha gabansu yana murmushi, sukayi turus suna kallonshi cike da mamaki, idanunsa akan Hafsat yace, "Kamar na sanki." Ta gane sarai bai santa ba, kawai neman hanyar da zaiyi magana da ita yake yi, tace, "Laa kamar baka sanni ba." Ya dubi Jalila yace, "K'anwata kinji ta fa?." Jalila tace, "Na rasa bakin magana." Yace, "Ko kuma kina san ki tarewa k'awarki ne. Sunana Al'ameen." Hafsat tace, "Besty muje." Yace, "Idan babu damuwa muje sai in saukeku a motata." Ya k'arasa maganar yana nuna masu dalleliyar kirar Mercedes Benz ash colour dake a parker, Hafsat tace, "Mun ce maka muna shigar mota dukkanin wanda yayi mamu tayi ne. Bamu shiga motar samari." Al'ameen yayi murmurshi yana mai yaba kyawunta, yace, "Shikenan." Ya mik'a mata katinsa, "Ga katina ki kira mu k'arasa hirar, tunda na daura idanu a kanki kyawunki ya tafi dani." Hafsat ta raba ta gefensa ta wuce ba tareda ta amshi katin ba, ta k'arasa bakin titi ta tsaida kekenapep, Jalila ta shiga, Hafsat tace, "Kofar kaura." Jalila tayi dariya tace, "Kuna dirama." Hafsat ta tab'e baki sannan tace, "Yana da naci." Jalila tace, "Ya bani katin na saka a cikin biscuits dinki." Hafsat ta kalleta da sauri tace, "Mi yasa kika amsa?" Jalila tace, "Naga abun nema ne ya samu, dama mai kudi ake jira kuma yana dasu tunda kinga motarsa." Hafsat tace, "Hakanan kin saka na saka mayafi ina yawo a takure." Matar dake a ciki tace, "Miye na cewa sai mai kudi?" A fusace jalila tace, "Ke kuma miye ya saka bakinki a maganarmu. Ki dubeta sosai, kyawunta ya kai shiyasa tace sai mai kudi, ke idan kin isa kice sai mai kudin kiga idan baki shekare a gidanku ba, koda yake daga gani babu tambaya wahala kike sha shiyasa kikeyi wa wasu bakin cikin su huta." Ganin da matar tayi idan ta tanka ba zatayi masu kyau ba ya saka tayi shiru har saida tazo inda zata sauka sannan ta dubi Jafsar tace, "Na lura ke kina da kunya, ina mai baki shawara ki zab'i miji na gari akan mai dukiya." Ta juyawa Jalila, "Ke kuma kiyi hakuri shawara mai kyau na bayar ba neman fad'a ba." Har suka koma gida maganar mata tana damun Hafsat a zuciya, suka yada zango a dakin Umma, Umma tace, "Har kun dawo kenan." Jalila ta zauna tana mai cewa, "Dama mun ce ba zamu jima ba." Umma tace, "Fatan kunyi min wuff da masu kudi." A tare Hafsat da Jalila suka kalli juna, Hafsat ta girgiza kai tana mata gargadi da idanu, Umma ta lura tayi mata dakuwa, "Ungo nan." Ta juyawa jalila, tace, "Rabu da ita ki fad'a min." Jalila tace, "Angel tayi babban kamu har da motarsa kamar zatayi lumfashi." Umma tace, "Masha Allah, wannan labari da d'ad'in ji yake." Hafsat tace, "Umma!." Umm ta murtuke fuska tace, "Ke dalla rabu da ni. Jalila bani labari." Jalila tace, "Ya bata katinsa taki amsa amma na saka mata shi a ledar biscuits dinta." Umma ta saki gud'a tace, "Tafiya tayi kyau." Jalila da neman magana tace, "Kuma Umma kin ganshi kyakykyawa mai gemu." Hafsat ta janyo pillow ta wurga mata, ta goce tana dariya, Umma tace, "Ki gama b'ata fuskar zaki dauko katin ne ki kirashi." Hafsat ta mik'e ta fice tana turo baki, Jalila ta biyo bayanta tace, "Haba k'awata." Gidansu Jalila suka wuce, Hafsat tace, "Kin bani haushi." Jalila tace, "Kece wallahi, yana da kudi kuma daga gani ba ya da damuwa, idan na barki kina iya bari ya kufce maki bayan kuma kin fad'a min abun da Umma tace akan maganar nan, shiyasa na fad'a mata." Hafsat tace, "Duk da haka, ba nufina bazan kirashi ba. Ina sone inyi tunani a kai." Jalila tace, "Uhmm. Angel, torh yaushe zaki kirashi?" Tayi mata banza, saida ta dameta sannan tace, "Ban sani ba, ay kin janyo min, ina gaya maki daga yau na boni da fad'an Umma na safe daban na rana daban na dare daban har sai na kirashi sannan zan samu salama." Jalila tace, "Sai ki kirashi a zauna lafiya." ***** Bayan Sati Daya Umma ta shigo dakin tana fad'a ta inda take shiga bata nan take fita ba, tace, "Ace sati guda ina maki magana akan ki kirashi amma kinyi kunnen uwar shegu dani, torh maza ki dauki waya ki kirashi ko kuma inci maki mutunci a gidan nan." Kamar zatayi kuka tace, "Umma zan kirashi." Umma tayi mata mugun kallo sannan tace, "Abun da kike fad'a min kenan a kullum kuma ba kiran kikayi ba, hakanan kina nema kiyi min salalar tsiya, idan yaje ya samu wata fa sai muyi ya." Ba kiran ne bata son tayi ba, haushinta daya card ya bata a maimakon ya amshi numbarta ya kira da kansa, tace, "Umma yanzu in kirashi kamar wacce bata da aji kuma..." Umma ta katseta, "Hafsat na lura dake kin amsa min zaki auri mai kudi ne kawai amma a zuciyarki ba haka bane." Tace, "Umma ba haka bane." Umma ta dungure mata ta kasa ta tsare, tace, "Koma miye ki dauki waya ki kirashi ko kuma inyi mugun sab'a maki, bani son iya shege." Ta turo baki tace, "Babu kudi a wayar." Umma ta daro kudi daga gefen zafinta ta mik'a mata tace, "Ina ce kati ne babu, amshi naira dubu daya kije ki saka katin, ki kashe sauran canzi ki sayi abun da yayi maki." Ganin bata amsa ta murtuke fuska, "Zaki amsa ko kuma na sab'a maki, nayi kasa-kasa dake a wajen." Ba domin ranta yaso ta amshi kudin ta zura Hijabi ta fita, kai tsaye ta wuce gidansu Jalila, ta samu wani dattijo zaune a kofar gida, ta rusuna ta gaishe dashi, "Baba Ina kwana?" Ya amsa da kulawa, ya dora da cewa, "Kina lafiya?" Tace, "Lafiya lau." Yace, "Allah yayi albarka." Tace, "Amin." Tana ganin girmansa saboda ba ya rabo da saka mata albarka, ba ya rabo da bata shawarwari wadanda idan ta dauka tana jin dadinsu sosai, ya dauketa kamar yadda ya dauki diyarsa Jalila. Ta shiga ciki, Mama tana a kitchen, tace, "Barka da aiki Mama. Ina kwana?" Mama tace, "Lafiya lau. Ya ummarki?" Hafsat tace, "Tana nan lafiya lau. Jalila fa?" Ta tambaya. Mama tace, "Tana daki tana yankan Hijabai da zata tura sokoto." Hafsat ta wuce dakin inda ta sameta akan keken dinki, saida ta harareta sannan ta zauna akan tabarma, Jalila tace, "Ya da harara? Duk yau bamu hadu ballantana ince laifi nayi maki." Ta kalleta ta watsar sannan tace, "Hakanan kawai kin saka Umma ta hanani zaman lafiya, tunda safe ta tusani gaba tace ko in kirashi ko taci min mutunci, nace babu wayar ta bari idan na saka zan kira, kamar ta gane dubarata ta bani dubu daya tace in saka katin in kirashi shine na gudo nan." Jalila ta dakata da abun da takeyi tace, "Ki kirashi, wannan shine kadai mafitarki." Saida tayi jim, kamar zatayi kuka ta zaro katin tana danna numbarsa tana mita, "Saboda ya rainani shine zai bani kati, idan numbana yake so ya tambaya mana." Tana cikin ringing daya ya tsinke kiran, ji tayi kamar ta fasa ihu ta kalli wayar ta tab'e baki tace, "Shi ya sani." "Ya aka yi?" Jalila ta tambaya. A kufule tace, "Tana ringing ya tsinke kiran." Tana rufe baki kira ya shigo wayar tana dubawa taga numbarshi, tace, "Shine." Jalila tace, "Kiyi picking." Hafsat ta tab'e baki tace, "Ban yi." Saida kiran ya kusa tsinkewa sannan ta amsa tayi shiru. Daga daya bangaren yace, "Salaam alaikum." Saida tayi jim sannan tace, "Wa alaikassalaam." Yace, "Waye?" Ji tayi kamar ta fasa ihu tace, "Waye ko wacece ba." Dariya yayi har tana jiyo sautinsa yace, "Wasa nike. Na gane, wacce muka hadu a shopping mall ce satin da ya wuce." Kamar wacce aka yi wa dole tace, "Eh." Yace, "Tun da muka rabu nike sauraren kiranki amma naji shiru." Tayi shiru, Al'ameen yace, "Alright, ina wani abu amma zan kiraki idan na gama cutiee." Ta tab'e baki jin sunan da ya kirata dashi, ta janye wayar daga kunnanta. Jalila ta kalleta tana neman karin bayani, tace, "Wai yana abu zai kira anjima." Jalila da neman magana tace, "Wow. Ta tabbata kinyi wuff da zuciyarshi." Saida ta tab'e baki sannan tace, "Ke kika sani, bari ki gani in koma gida tun kafin Umma ta fusata dani ta biyo bayana." Jalila tace, "Alright sai na shigo." Hafsat tace, "Baki min rakiya ba." Jalila tace, "A'a. Hijabs din nan gobe nace zan turasu ga shi lokaci ya k'ure ban so inyi k'aramar magana." Hafsat tace, "Alright na wuce." Saida tayi sallama wa Mama sannan ta fita zuwa gida, a daki ta tarar da Umma zaune, tana ganinta ta murtuke fuska, tace, "Daga tafiya siyan kati shine kikayi zamanki kika barni a nan ina jiran gawon shanu, kika barni Ina zaman jiranki kamar wacce bata da mafadi, ko nace maki ne bani da aiki, nayi maki kalar zaman kashe zani ne." Ta jefo mata tambaya, kadan ya rage ta kai mata duka, tayi baya da sauri tace, "Umma na je gidansu Jalila ne na kirashi a can." Umma ta kalleta na wani lokaci sannan tace, "Angel k'arya ba halinki bane ba karki fara, zanyi mugun sab'a maki ne." Tace, "Da gaske nike." Umma tace, "Idan ma k'arya kike zaki hadu dani ne, kuma ba zaiyi maki kyau ba." Wayar ce tayi ringing saida ta duba sannan tace, "Shine." Umma tace, "Ki d'aga kadda ta tsinke." Sanin idan ta tsaya jan aji Umma zata iya kai mata duka, tayi picking tareda kanga wayar a kunne. Al'ameen da yake kishingide akan wani katon gado yace, "Hello." Tace, "Salaam alaika." Ya gane nufin ta yace, "Sorrry. Wa alaikissalaam. Ya kike?" Tace, "Lafiya lau." "Tun daga ranar da naga baki kira ba nike zuwa wajen ko zamu sake haduwa amma shiru." Tace, "Bamu sake zuwa bane." "Yaushe zaku k'ara zuwa?" Ya tambaya. Tace, "Babu tabbas." Kamar mai rad'a yace, "Cutiee." Tace, "Sunana Hafsat." Yace, "Okay, Hafsat tun da na hadu dake kika mallake min zuciya. Ina sonki." Ya lumfasa sannan yace, "Hafsat ke kyakykyawa ce dukkanin wanda yayi tozali dake zai tabbatar da hakan, Hafsat ina sonki." Tayi dariya tace, "Torh na gode." "Yaushe zanzo gidanku in ganki tunda muka rabu nike missing dinki?" Ya tambaya. Ganin Umma tana sauraron amsar da take bashi, kuma idan ta bashi amsa kai tsaye zata gane tambayar da yayi, sai tace, "Okay, torh na gode, zanyi abu sai anjima." Daga daya bangaren yace, "Alright." Umma ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi sannan tace, "Ko ke fa, kwara ki saki jiki ku fahimci juna, na fad'a maki bazan baiwa talaka aurenki ba, sai mai kudi zaki aura, sharadin shine gida da mota, shiyasa na saka kika kori Ummaru." Dukkanin maganar da Umma takeyi akan kunnen Al'ameen ne kasancewar kiran bai tsinke ba, yana jin shiru yayi sauri ya tsinke kiran yana wani shu'umin murmushi, yace, "Dawa tayi nama. Kunzo hannu, tunda har kike da idanun cin naira ni kuma zanyi amfani dasu in b'ata rayuwar diyarki, tun da dora idanuna akan zubin halittarta naji ina son kasancewa tare da ita, ta mallaki komai, zan watsa maki naira na more rayuwa da diyarki, babu aure a tsarina saidai jin dadi kawai. Yarinya tazo hannu, dole sai na tsallakeki." Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 5 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 Tun daga wannan lokacin yana yawan kiranta sannan yana saka mata kudi a layinta sosai, idan ta kirashi ba ya dauka saidai idan ta tsinke ya biyo kiran, ta rasa dalilin da ya saka har zuwa wannan lokacin bata jin wani abu a dangane dashi, tana iyakar k'ok'arinta domin cusashi a ranta amma abun yaci tura. **** Somewhere in Europe Wani handsome saurayi ne tsaye a saman dogon bene yana kallon garin, ya zaro waya tareda kiran numbar Nigeria, daga daya bangaren aka ce, "Ashraim." Yace, "Habib. Miye labari akan Hafsat?" Ya fad'a mashi halin da ake ciki ya dora da cewa, "Shiyasa nace maka ka bayyyana kanka a gareta tun kafin ka tafi." Ashraim yayi murmurshi karfin hali yace, "Nan da shekara daya zan dawo, IDAN HAR RABONA NE aje a dawo zan sameta." Habib yayi karfin hali yace, "Idan ka dawo zai fiye maka idan ka ajiye miskilanci ka bayyana soyayyarka a gareta." Ashraim yayi murmurshi sannan yace, "Hafsat zuciyata ce, koda ban fad'a mata ba, idan ta kalli kwayar idanuwana zata fahimci yadda nike matuk'ar sonta." Habib yayi dariya yace, "Miskili kawai." Ashraim ya tsinke kiran yana kallon hotonta dake akan majigin wayarsa. **** A daren wata rana Hafsat tana kwance akan tabarma har ta fara barci, Al'ameen yayi mata video call, da mamaki take kallon majigin wayar sai kuma ta mik'e zaune ta janyo hijab ta zura kafin ta amsa kiran, ta zaro idanu ganin daga shi sai guntun boxer daidai cinya, har tana hango tudun joystick dinsa, da sauri ta tsinke kiran, ya k'ara kira amma wannan karon voice call ne, taki picking, ta kashe wayar baki daya tana mamakin wannan al'amari. Washegari tun da safe ta soma shiri kasancewar tana da lectures na safe, tana gama sallar subh ta shiga wanka ta shirya tayi kalaci, Umma ta zaro dari biyar ta bata tace, "Gashi kiyi amfani dasu, Allah ya bada sa'a." Ta amsa da, "Amin." Ta saka kudin a jikarta ta fice, ta biya gidansu Jalila kafin suka suka wuce school, a makaranta ta wuni sai karfe biyar sannan ta koma gida ta samu Umma bata dawo daga gidan da take aikatau ba. Tun wannan kiran bata k'ara amsa kiransa ba, kiransa ne ya shigo wayarta saida tayi jim kamar ba zata amsa ba sai kuma ta amsa, "Yanzu kuma... Amma ba ka ce min zaka zo... No, ba haka bane, ban jima da dawowa daga makaranta bane amma babu damuwa... Sai kazo.." Ta rage kayan dake jikinta tayi daurin kirji ta d'aura hijab akai sannan ta fita tsakar gida ta janyo ruwa a rijiya ta cika bucket ta shiga bayi ta jima tana cuda jikinta sannan ta fito ta shirya, powder da kwalli kawai ta saka a fuskarta, ta shirya cikin leshe dinkin riga half bubu, straight skirt, ta kashe dauri samfurin ture kiga tsiye, ta fesa jikinta da turaruka masu saukin kamshi, har ta dauki hijab sai kuma ta ajiye ta yafa mayafi akan kafad'a ta saka flat shoes, ta fita tana tafiya a hankali. Mota ce fara sabuwa dal Jeep, ya bud'e bangaren direba kadan yayinda ya zuro kafafunsa, yana sanye da kananan kaya, ta k'arasa tareda jingina da motar tayi mashi sallama. Ya amsa da murmurshi akan fuskarsa, ya kurawa kirjinta idanu yana wani shegen murmurshi saidai bata lura ba kasancewar inda take kallo daban. Ganin bata da niyyar shiga motar yace, "Ki shigo." Ta girgiza kai, "Na fad'a maka bana shiga motar samari." Ya ware idanu yace, "Saboda baki yarda da ni ba." Ta girgiza kai tace, "A'a ba haka nike nufi ba." Yace, "Then ki shigo." Still girgiza kanta tayi tace, "A'a nan yayi, bana shiga motar samari." Al'ameen ya d'age mata gira daya yace, "Kin tab'a saurayi mai mota ne?" A bazata tambayarsa tazo mata, ta kalleshi fuskarta dauke da mamaki sai kuma tace, "Eh, ga shi nan a kusa dani." Al'ameen yace, "Ohhh." Ganin ba zata shiga motar ba ya fito ya tsaya a gefenta ta matse mata har tana iya jin saukar lumfashinsa, da sauri ta matsa, yace, "Miye?" Tace, "Babu komai." Ya k'ara matse mata, ta matsa, yace, "Naga kin matsa ne." Tace, "Kana matse min ne sosai." Ya d'aura hannuwansa akan motar yana mai kura mata idanu yace, "Miye don na matsa kusa dake kina abu kamar er kauye, ke babbar yarinya ce, karki cuci kanki kiji dadin rayuwarki, ki more rayuwarki." Taso ta gane inda maganarsa ta dosa saidai bata son tayi mashi mummunar fahimta, tace, "Pardon me amma ban gane ba." Ganin bai samu fuska yace, "Ohhh. Ina zuwa." A ranshi yana ayyyana idan kin san wata baki san wata ba, ya bud'e gidan baya ya fiddo leather, ya mik'a mata yace, "D'azu kin ce baki shiga motata, idan kika ki amshi kyauta da na baki hakan ba zaiyi min dadi ba. Waya ce Samsung da iPhone sai kuma tablet, akwai kudi a ciki da kuma sakon Umma." Jin yawa da tsadar abubuwan da ya lissafa tace, "Amma..." Da sauri ya katseta, "Amma idan baki amsa ba, raina zai b'aci, zanga kamar kina min kora da hali tunda dama kinki shiga motata bayan ni aurenki zanyi." Bata da wani zab'i da ya wuce ta amsa, tace, "Na gode, kuma kayi hakuri ban ki shiga motarka da wata manufa ba." Ya kanne mata ido daya ya karkace kai yana k'are mata kallo yace, "Kin ce baki dade da dawowa daga makaranta ba." Bata nutsu da kallon da yake mata ba, tace, "Eh dawowata kenan ka kira, wanka kawai nayi na shirya na fito." Yace, "Na manta da na tafo maki da abinci, shinkafa da kaza. Muje restaurant sai kici abinci." Ta girgiza kai, "A'a, naci gurasa a school." Ya dan kalleta yace, "Gurasa kuma babu eatery ne." Kanta tsaye tace, "Akwai, ban dauka da zafi bane, na tsaya a matsayina ne." Duk da haka bai hakura yace, "Ina nufin muje in siya maki ko fried rice ne da kaza, da duk abun da kike so." Tayi murmurshi tace, "Na koshi, akwai tuwo a gida idan na shiga zan ci. Kasan tuwon da ya kwana yafi wanda aka girka a ranar dadi." Kiran tuwo da tafi ya saka yaji amai ya tafo mashi. Zatayi magana sai kuma tayi shiru ganin kekenapep ta sauke Umma a kofar gidan, shima inda take kallo ya kalla yana yatsine fuska saidai bai yarda ta lura. Tace, "Umma ta dawo na wuce ciki kada tayi fad'a." Yace, "Alright, idan kin shiga kiyi mata magana zan shigo in gaidata." A ransa yana ayyana idan kin san wata baki san wata ba. Tayi jim sai kuma tace, "Alright ina zuwa." Ta wuce ciki tana tafiya yana bin bayanta da kallo yana hadiye yawo. "Har ya wuce ne?" Umma ta tambaya. Ta girgiza kai, "A'a, yace ne zai shigo ya gaidaki." Umma ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi tace, "Kije ki shigo dashi. Amma wannan ledar fa?" Hafsat tace, "Da ita yazo, akwai sakonki a ciki." Umma tace, "Kuma kika amsa." Tace, "Ya matsa ne shiyasa amma zanyi maki bayani idan ya tafi." Tana gaba yana biye da ita suka shigo, yana kallon dakunan dake a jere yana yatsine fuska, idan yaga zata juyo sai ya wayance. Suka shiga dakin, Al'ameen ya zauna akan tabarma yana k'arewa dakin kallo ya gaishe da Umma ta amsa da fara'a, "Ya wajen tsohin?" Yace, "Lafiya lau suke." Yana ji kamar yana zaune a saman allura. Tace, "Munga abun alheri mun gode, Allah yayi albarka." Yayi murmushi yace, "Babu komai." Sai kuma ya zaro en dubu daya sabbi dal dami biyu ya ajiye akan tabarmar yace, "Gashi. Zan wuce." Umma ta ware idanu tana kallon kudin tace, "A'a bazan amsa ba, ka dauki kudinka, na gode." Al'ameen yayi wani shegen murmushi yana tuna maganar da yaji tayi a waya, yace, "A'a." Ya mike ya fita. Umma tace, "Hafsat ki maida mashi kudin nan bazan amsa ba." Ta dauki kudin tabi bayanshi har ya shiga mota ta dafa murfin motar tace, "Ga kudin Umma tace ba zata amsa ba." Yayi murmushi yace, "A tunaninki akwai wanda ba ya san kudi." Tace, "Ban gane ba." Ya d'aga mata hannu yana murmurshi yace, "Karki damu, na wuce sai munyi waya." Ya rufe murfin motar ya jata ya wuce ya barta a tsaye tana k'ok'arin had'a ma'ana wa maganar da yayi mata. Tyi jim tana juya maganar da yayi mata sai kuma ta d'aga kafad'a ta juya ta koma ciki. Umma tace, "Ya kika dawo da kudin?" Ta zauna a gefen gado tareda zare mayafi dake a jikinta tace, "Bai amsa ba." "Ki ajiyesu a wajenki, idan ya dawo ki mayar masa." Hafsat ta zazzage leather da ya bata, waya ce babba kirar Samsung tareda iPhone, da turare, a gefe atamfa ne da leshe, Umma tace, "Ki tattarasu ki ajiye, ba zamuyi amfani dasu ba." Hafsat ta maida kayan a cikin leather ta saka kudin a ciki, ta turasu a karkashin gado, ta fita waje jin ana kiran sallar Magrib, bayan ta gama sallar Isha'i ta dauko handout tana dubawa, kiransa ya shigo wayarta sai a lokacin ta tunda da ya kamata ta kirashi, ta dafe kai, "Gosh. Ya kamata ace na kirashi." Ta amsa kiran ta kanga wayar a kunne. Daga daya bangaren Al'ameen yana sakin lumfashi tareda sakin gurganin iskanci yace, "Hafsat ki taimaka min ciwon mara zai kasheni." Ta tsorata, idanunta a waje, "Kaje asibiti." Innocent her bata fahimci manufarsa ba, yace, "Please ki taimaka min in rage zafi." Da mamaki tace, "Pardon me, ban gane ba." Al'ameen yana kukan iskanci kamar wanda yake tarayya yace, "Ki turo min hotunanki in rage zafi, gobe zan shigo in daukeki muje muji dadi, zan aureki, zan baki kudade masu yawan gaske, zan siya maki mota irin wacce nike hawa, zan baki gida babba." Hafsat ta ware idanu tace, "Subhanallahi!." Daga daya bangaren taji yace, "Angel kina abu kamar wacce bata waye ba." A fusata tace, "Idan har wannan itace wayewa, torh ina rokon Allah da ya kasheni a wacce bata wayewa domin bana buk'atarta a rayuwata." Yace, "Please ki bani hadin kai zan sakar maki naira kiji dadin rayuwarki, zan siya maku gida babba da motoci na alfarma, kuma zan aureki." Ji tayi hawaye sun zubo mata, tayi shiru tana sauraren kalamansa na yaudara, yana so yayi lalata da ita har yake ikirarin zai aureta daga muryarsa ta fahimci ba akan ya fara ba, maganganunsa karya ne yana fad'a ne domin ya samu abun da yake so, tana da tabbaci akan ba aure bane ya kawoshi ba musamman idan tayi la'akari da maganganu da ya yab'a mata wanda sai a yanzu take fahimci izgili ne da wulakanci. Jin shiru yace, "Kina jina?" Tace, "Sai kazo." Ya saki murmushi nasara, "Ki fara tura min hoton." Hafsat ta rumtse idanu tana iyakar kokarinta domin daidaita fushinta, "Sai kazo." Ta fad'a a takaice ta tsinke kiran, tayi wurgi da takarda (aww nima na koyi hausar can) tayi wurgi da handout din ta kwanta akan tabarma tayi lamo tana share hawaye wasu sabbi suna zubowa. Umma tace, "Ki tashi kici abinci." Hafsat ta mik'e zaune hakanan take tura abincin ba domin yayi mata dadi ba, ta wanke hannuwanta tayi alwalla ta kwanta saida ta raba dare sannan ta samu dakyar bacci yayi awon gaba da ita. ********** Al'ameen ya daka tsalle, "Yeah. Gobe akwai jin dadi." Yana sakin wani shegen murmurshi na nasara, yace, "Hafsat kin fad'a tarkona." Washegari Hafsat ta tashi da ciwon kai a sanadin kukan da tayi da daddare, wunin ranar bata fita ba. Da misalin karfe sha biyu na rana tana kwance akan gado tayi lamo tana hawaye, kiranshi ya shigo wayarta batayi picking ba har ya tsinke ta saka numbarshi blacklist, ta mik'e ta zura hijab ta janyo leather da ya bata jiya, kudin da komai suna a ciki, ta hangoshi yana jingine da mota, tunda ta fito yake kallonta yana murmushi har ta k'arasa inda yake, yace, "Hafsat. Muje." Tayi murmurshi takaici tace, "Muje ina?" Yace, "Hotel muji dadi." Tayi dariyar takaici tace, "Are you kidding me? Nayi maka kama da wacce take zuwa hotel ne." Yace, "Sai muyi a mota." Da alama dukkanin maganarta yana da amsa, tace, "A hotel, a mota, ko a gidanka, a ko'ina ba zaka sameni ba domin ba haka nike ba." Ta nuna kanta tace, "Ni ba er iska bace ba, er mutunci ce, daga gidan mutunci da tarbiyya." Tayi mashi mugun kallo sannan tace, "Ka kira kana min maganar banza, well ni ba haka nike ba." Ta dungure mashi leather dake hannunta, "Here abubuwan da ka kawo jiya har da kudadenka, daga yau kada na k'ara ganinka a kofar gidanmu." Yayi dariya yace, "Gidanku ko kuma gidan haya." Tayi murmurshin takaici tace, "Afuwan, zan gyara, Aminu daga yau kada na k'ara ganinka a kofar wannan gidan da nike haya." Yace, "Idan kuma na kama daki haya fa." Tayi dariya tace, "Mata masu zaman kansu da maza basu samun haya a ciki." Ya tafa hannuwa, "Ita kuma Umma a wani take naga bata da aure ko tana dashi ne." Ji tayi hawaye sun zubo mata, tana mai zubar da hawaye ta nuna mashi kofa, "Aminu ka dauki motarka ka koma inda ka fito ko kuma in tara maka jama'a, suyi maka dukan tsiya." Ya rike kugu, "I dear you to give it a try, ruwa ba sa'an kwando ba. Idan kudin ne sukayi maki kadan ki fad'i farashinki na biya muje na biya buk'atata na maidoki." Ta fashe da kuka, "Aminu kaji tsoron Allah." Yace, "Angel kina b'ata min lokaci." Tana mai zubar da hawaye tace, "Well ba haka nike ba, kudinka basu isa su sayi mutuncina ba." Ya gyara tsayuwa yana mai karewa kallo, yana mata kallon kaskanci tace, "Ita kuma tsohuwa fa, naga burinta shine ki auri mai kudi." Tayi mamakin jin wannan furucin, tana tantamar a inda yaji magana, ta juya domin shiga gida taji yace, "Zabi biyu ne ki tsaya muyi cinikin ko kuma inyi cinikin da tsohuwa tunda mayyar kudi ce." Ya fahimci bazai sameta haushin rashin samun abun da yake so ya saka ya tsaya yana datsa mata maganganu. Ta daka mashi tsawa, "Karka kuskura ka kara fad'in magana marar dadi akan ummata domin ban hadata da komai ba..." ya katseta, "Sai kikayi rashin sa'a bata had'a kudi da komai ba. Kwara ki daina b'oye-b'oye ki shiga mota muje inyi in gama, biyanki zanyi." Ba zata iya jurar maganganun da yake yab'a mata ba, ta juya ta shige gidan da gudu, ta dauki buta ta shiga bandaki, ta takure a bango tana kuka marar sauti, mutanen gidan idan tayi kuka mai sauti ta shiga gulma ana janyo mata bala'i daban-daban. A rayuwa rahama ne idan kana da dakinka wanda zaka shiga kayi kuka ka wanke fuska ka fito, tana so tayi kuka a cikin salama amma bata da iko domin koda mintina ukku ba tayi ba salme ta fara mita, "Wanene ya shiga bandaki yayi shiru kamar mai naquda, koda sauya fata mutum zaiyi yaci ace yama don haka koma waye ya fito ya wani waje in sauke abun dake damuna a ciki domin kudin haya basufi kudin haya ba." Hafsat ta wanke fuska ta fito tun maganar bata tada bala'i a gidan ba, domin akwai mata da yawa da suke jin haushin juna wata akan mijinki yafi nata samu, wata akan kin fita sutura, wasu kuma en neman fitina ne, ta tabbata kadan suke jira su zauna a kai a fara zubar da habaici, bata shirya zama sanadin fitina ba. Ta koma daki ta zauna akan kujera tayi shiru kawai tana maida lumfashi, ranta a b'ace yake. Umma wacce bata ga fitarta ba tace, "Miye?" A takaice tace, "Babu komai, ina nazarin karatu ne." Washegari ta dawo daga makaranta ta tarar da matan gidan cirko-cirko Umma tana tijara akan su fito mata barawo da ya shigar mata daki yayi mata sata. Ji tayi kamar kasa ta tsage ta nutse a ciki, tace, "Umma miye aka sata?" Umma tana maida lumfashi tace, "Leather da muka ajiye a karkashin gado." Tace, "Umma kin manta kin ce in mayar mashi dasu, jiya na mayar mashi." Sabuwar fitina ce ta tashi jin inda leather ta tafi, su salme suna bala'i akan sata da Umma ta laka masu. Umma tayi mursisi da idanu tana nade tabarmar kunya da hauka, "Halinku na sani na sata shiyasa na fad'a, cokali wannan idan mutum yayi wanke-wanke ya manta kafin ya fito an samu wata marar tsoron Allah tayi ciki dashi. Mutum yayi k'arya ya kirani da barauniya saidai ace min fitinanna kuma fitinata sai an janyoni nikeyi, aikin banza aikin wofi." Ji Hafsat tayi ba zata iya zama ba ta juya ta koma gidansu Jalila, Jalila tayi mamakin ganinta la'akari da basu dade da rabuwa ba amma bata tambaya ganin yanayinta. Ta zubo mashi abincin sanin yunwa da suka debo throughout fitarsu gurasa kawai suka ci a student center. A gidansu fitina aka yi sosai, Salme tace sai takai Umma k'ara anbi mata hakkinta, Umma tace, "Da kuwa anyi tone-tone akan sace-sace da kikayi min wanda ina sane na kyaleki ne kawai domin idan kafi karfin abu kawar da idanu kakeyi." Salame ta shige daki fuu a cewarta zata dauko mayafi daga nan babu wanda ya k'ara jin motsinta. Saida dare ta koma gida, Umma ta dubeta da tuhuma tace, "Hafsat mi ya faru? Ban ce maki ki mayar da sauran." Hafsat ta sauya maganar ta hanyar cewa, "Umma ina abincina idan tuwo ne ba zan ci ba." Umma ta dauko warmer ta ajiye a gabanta tace, "Gashi nazo dashi daga gidan aikina." Zata janyo Umma ta rike hannunta ta murtuke fuska tace, "Tambayarki nike, mi ya faru kika mayar mashi dasu?" Ta rumtse idanu sannan tace, "Mun rabu, alakata da Al'ameen bazata yiyu ba shiyasa na mayar mashi da kayansa tareda kudin." Ta mike ta fita domin tayi alwallar barci, ta fito tsakar gida tana ganin matan gidan zaune suna gulma ta kawar da kai tana mamakinsu, sun ki sana'a sun zauna majalissar gulma. Tayi alwalla ta koma daki ta ajiye buta a bayan kofa, ta kwanta, Umma tace, "Abincin fa." Tace, "Naci abinci a gidansu Jalila." Umma tace, "Amma da kanki kika tambaya." Tace, "Ina k'ok'arin sauya hirar ne." Daga nan bata sake magana ba, tayi lamo kamar tana barci. Umma tayi kwafa, cikin ranta tace, "Wannan yarinya kin cika taurin kai, Hafsat kenan, idan kin san wata baki san wata ba." Washegari da safe ta shirya ta wuce school, sai karfe goma sha biyu na rana sannan ta dawo gida, tayi turus tayi tareda sakin jikkar dake hannunta a sanadin halin da taga Umma a ciki. Umma ce a cikin halin ciwo, tana kwance akan tabarma tana maida lumfarfashi yayinda k'awarta Nana take zaune a gefenta tana mata firfita da mafeci, da gudu ta k'arasa inda suke ta durkushe ta kamata tana kuka tace, "Umma mi ya sameki? Mi ya faru?" Umma tana maida lumfashi dakyar tace, "Hafsat karkiyi kuka, In sha Allahu zan tashi, ba zan mutu ba, ki kwantar da hankalinki." Hafsat tana mai fashewa da kuka tace, "Aunty Nana mi yake damunta?" Nana tace, "Likita dai yace ta sakawa kanta damuwa ne har ciwon zuciya yana barazanar kamata." Ta ware idanu tana mai cigaba da hawaye tace, "Umma miye damuwarki? Please ki fad'a min. Mi yake saka maki damuwa har kika shiga wannan halin na ciwo? Ki fad'a min abun da zan yi maki?" Umma ta kama hannunta tana maida lumfashi tace, "Hafsat damuwa da ya wuce burina na ganin aurenki, bana fatan na mutu na barki ba tareda aure ba, zan mutu ne a salama idan nasan da kina da miji wanda zai kula dake, bana son mutuwata ya zama sanadi na tagayyara rayuwarki, dangin mahaifinta babu na kirki, dangina ba zasu amsheki ba, kaicona da na janyo maki wannan rayuwa mai cike da kalubale." Hafsat tana sheshshekar kuka tace, "Umma In sha Allah, zakiga aurena." Umma da muryarta dake fita dakyar tace, "Allah yasa." Hafsat tace, "Ameen." Wuni tayi tana nanike da Umma, da marece Jalila tazo ganinta tareda Mamarta, Hafsat ta damu sosai akan rashin lafiyar Umma, ta rasa abun da yake mata dadi. Da daddare ta kasa bacci ganin yadda Umma take jin jiki, tace, "Umma ko komawa asibitin zamuyi?" Umma ta girgiza kai tace, "A'a sun bani magani kuma nasha." Hafsat tayi tagumi tana tunanin yadda zatayi da rayuwa a lokacin da aka ce Umma bata a doron kasa, ita kadai gareta, ita kadai ta sani, bata san danginta ba, dangin mahaifinta kuma dasu da babu duk daya ne, bata rumtsa ba har asuba, yadda taga rana haka taga dare, sai bayan da tayi sallar asuba sannan ta samu bacci yayi awon gaba da ita. Karfe tara na safe ta farka, da sauri ta kalli inda Umma take domin gani take kamar zata rasata, Umma da muryarta wacce bata fita sosai tace, "Hafsat." Hafsat ta janyo hannunta ta rike tana mai zubar da hawaye tace, "Umma. Kina buk'atar wani abu?" Umma ta girgiza kai, Hafsat tace, "Umma ya jiki?" Umma ta d'aga kai tace, "Da sauki." Tace, "Allah ya k'ara sauki." Yace, "Amin." Kira ne ya shigo wayar Hafsat ta kalli sunan wanda ya kira sannan ta amsa, tayi jim sannan tace, "Kuma yau? Dole ne ko yau. Okay, na gane." Ta zare wayar daga kunnanta, Umma ta dubeta, Hafsat tace, "Daga makaranta ne ana son ganina yau kuma gashi baki da lafiya, ban san in fita in barki a wannan halin." Umma tayi murmushin karfin hali tace, "Ki shirya ki tafi, Nana zata zo ta zauna a tare dani." Hafsat tayi jim, Umma tace, "Ki tashi ki tashi, karatun nan da kike burina ne." Ba don ranta yaso ba ta gyad'a kai, "Okay. Umma Allah ya k'ara sauki amma please idan kinji ciwon ya k'aru ki kirani in dawo muje asibiti." Umma ta gyad'a kai. Hafsat ba don ranta yaso ba tayi shiri, ta tsakuri abinci kadan, ji take kwata-kwata babu dandano a bakinta a sanadin damuwar da take a ciki akan rashin lafiyar Umma, tana tafiya tana waigowa har ta fita, wuni tayi a school, tana a makarantar ne amma hankalinta yana gida ta damu akan halin da Umma take ciki, kallo daya za'a mata a fahimci tana cikin damuwa, tun kalaci da tayi bata k'ara cin wani abu ba har karfe biyar da ta baro makaranta, lokacin da ta koma gida ta tarar da tashin hankali, jikin Umma ya k'ara tsanani, kwana tayi tana kuka saboda halin da Umma take ciki na tsananin ciwo. Washegari wuni tayi tare da Umma tana kula da ita. Tace, "Umma ki tashi muje asibiti." Umma tace, "Zamuje tareda Nana." Hafsat tace, "Amma mi yasa ba zakije dani ba?" Umma ta dubeta tace, "Saboda zakije makaranta." Hafsat ta girgiza kai, "A'a, ba sai naje ba, lafiyarki ta fiye min komai." Umma ta girgiza kai tace, "Gobe ki shirya kije makaranta, zamuje asibitin tareda Nana." Washegari, saida ta tabbata tayi wa Umma komai sannan ta wuce school yanayinta cike da damuwa ganin har lokacin Umma tana jin jiki sosai, two hours lecture tayi attending ta dauki drop aka kawota har kofar gida, ta mik'a mashi kudinsa sannan ta fito ta shige, tana tunkarar kofar dakinsu ta jiyo muryar Umma tana waya tana dariya tana shewa tana cewa, "Na kad'ata ta tafi makaranta. Ta cika taurin kai shiyasa nayi mata haka, ta amsa min ne kawai akan zata auri mai kudin amma idan nayi mata saku-saku sai inji wani zancen, kinga da nayi wannan ciwon na karya, duk taurin kanta ba zata bijirewa maganata ba, kina nan zakiga ta gabatar da wani. Tana zuwa zan marairace mata akan ta nemo kada na mutu ban ga aurenta ba." Hafsat ta ja da baya tana mai girgiza kai yayinda hawaye suke zubowa daga idanunta, ta d'aga labulen dake dakin ta kutsa kai. Umma ta zaro idanu tana kallonta, Hafsat tana hawaye tace, "Umma mi yasa kikayi min haka? Jina nike kamar wacce aka koda yake bamu amfanin fad'a. Umma did you have to get this far. Nace maki zan bi zab'inki koda zuciyata bata so. Nace maki zan auri mai kudi kamar yadda kike so. Umma na sani dukkanin abubuwan da kikeyi kina yi ne saboda kina son rayuwata ta inganta, saboda baki son in shiga kwatankwacin halin da kika tsinci kanki a ciki. Amma tambayar a nan itace shin na shirya auren mai kudi? Shin na shirya rayuwa a dangin masu kudi? Shin zasu karbeni hannu biyu ko kuma zan ci karo da kalubale na gori irin wanda Umar yayi min, shi zancen duniya ba ya b'uya." Ta lumfasa tana sheshshekar kuka tace, "Umma an gaya min magana ance min kina da son abun duniya, ance maki mai idon cin naira amma na jure saboda nasan ba haka kike ba. Umma mi yasa zakiyi haka? Koda yake babu komai, ba sai kinyi haka ba, yadda kike so hakanan za'ayi. Umma mun gama wannan maganar a nan, kada a sake tadota, shikenan, magana ta k'are. Ba sai kin nemeni ba ina gidansu Jalila." Ta hade hannayenta waje guda alamar roko sannan tace, "Umma na rokeki da girman Allah idan na dawo kiyi kamar wannan abun bai faru ba." Juyawa tayi ta fita tsakar gida, saida ta wanke fuskarta sannan ta fita waje tana tafiya dogon hijabinta yana sharar kasa. Kai tsaye ta wuce gidansu Jalila, ta kwanta, Jalila ta dubeta tace, "Angel kwana biyu naji baki maganar Al'ameen ba." Kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace, "Mun rabu. Ban Dace Dashi Ba koda yake shine bai dace dani ba. Kin tuna kwanaki na fad'a maki ina ji kamar ana bibiyata." Jalila ta gyad'a kai tace, "Hakane." Hafsat ta mike daga kwanciyar da take ta gyara zama sannan tace, "Tabbas akwai wanda yake bibiyata kuma yau zan kawo karshen komai. Ki jirani ina zuwa." Ta zura takalma ta fita daga dakin ta dauki hanyar kofar gida. Tana fitowa ta hango motar, tafiya ta fara tana lura da ita, ganin zai gane nufinta tayi kamar hankalinta ba ya akan motar, tayi wuff ta tare gabanta tana kwankwasa gilasin motar. Bashir yayi kasa da gilashin yana kallonta idanu a waje, saida ta kare mashi kallo sannan tace, "Ka fita daga motar ko kuma in tara maka jama'a." Bashir ya b'alle murfin motar ya fito, ta kalleshi daga sama har kasa, tace, "Mi yasa kake bibiyata? Wa ya saka kake bibiyata?" Bashir yace, "Ni kuma?" Wayar dake hannunsa ce tayi tsuwwa yayinda sunan _BOSS_ da manyan haruffa ya bayyana akan majiginta, kallonta yayi ya ware idanu ganin itama sunan take kallo, ta girgiza kai tace, "Da alama sakaka aka yi kana bibiyata." Ta fizge wayar ta amsa kiran, kafin yayi magana ta riga shi, "Na kama wanda ka saka yake bibiyar rayuwata? Waye kai? Mi yasa ka sakashi yake bibiyar rayuwata? Idan kana da damuwa dani ne ka tunkareni? Wannan Motar dashi wanda yake tukata bazasu bar inda suke ba har sai kazo da kanka ko kuma in tara mashi jama'a." Ta tsinke kiran. SHIN MI ZAI FARU? SHIN WACECE BILKISU? MI YA FARU HAR TA B'ACE? SHIN A WANI HALI TAKE CIKI? SHIN HAFSAT ZATA AURI HISHAM? SHIN MI ZAI FARU DA ITA IDAN TA AURESHI? SHIN AISHA ZATA AIKATA ABUN DA TA FAD'A KUWA? SHIN MI ZAI FARU IDAN BILKISU TA BAYYANA? SHIN INA OMAR YAKE? SHIN WAYE ASHRAIM? Muje zuwa Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 6 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 Hisham ya saki murmurshi yana kallon majigin wayar, ya ajiyeta yana mai cigaba da duba file dake a gabansa. ****** Hafsat ta duba agogo dake a hannunta, a fusace tace, "Tunda shi bazai zo, ka kaini inda yake domin a yau za'a yita ta k'are sai ya fad'a min dalilinsa na sakawa ana bibiyata." Bashir ya share zufa yana zare idanu, ta murtuke fuska tareda b'alle murfin mota ta zauna a gidan baya, Bashir ba ya da wani da ya wuce ya koma mazauninsa ya tada motar ya dauki hanyar kamfani inda yake kyautata zaton zai sameshi, babban kamfani ne, wanda ya dauke da dogon gini iya ganinta, ginin glass, ta jingina da motar ranta a b'ace tace, "Wanda ya saka kake bibiyata kaje ka fito dashi, ayita ta k'are." Ya share zufa da ta karyo mashi yace, "Na'am." Ta kalleshi ta watsar, ganin zai b'ata mata lokaci, tace, "Waye ya saka kake bibiyata?" Muryarsa tana rawa yace, "Mai wannan kamfani." Hafsat tayi jim sannan tace, "Kana nufin CEO na kamfanin." Ya gyad'a kai. Ji tayi ranta ya k'ara b'aci ta shige ciki fuu, tayi tsaye tana k'arewa katon kamfanin kallo wanda yake kamar a kasar waje. Najeeb ne ya hangota, ya k'arasa inda take yace, "Ma'am." Ta murtuke fuska tace, "A wanne floor ofishin CEO yake?" "Hawa na ashirin da daya." Ya bata amsa yana mamakin ganinta a wajen. Ta raba ta gefensa ta wuce fuu zuwa elevator, sau biyu ta danna da alama akwai wadanda suke a ciki, gani tayi zai b'ata mata lokaci ta juya ta bude wani kofa tabi ta emergency stairs (ni kuma nace sauri kuma, ina sauri wa wanda yabar elevator yabi emergency stairs har hawan bene na ashrin da daya, tab 😂😂😂), ranta a b'ace yake shiyasa ko gajiyar hawan benen bata ji ba, tana haurawa tana kallon numbobin dake a saman kofar kowanne floor da take wucewa domin tabbatar da bata wuce hawan benen da yake ba. Najeeb ya zaro wayarsa ya kira numbar Hisham, daga daya bangaren Hisham yace, "Buddy. Ya ake ciki?" Najeeb yayi dariya sannan yace, "Hafsat tazo, she is in this building, tana akan hanyar ofishinka. Ya haka?" Hisham yayi jim sannan yace, "Ta kama Bashir yana bibiyarta." Najeeb ya kyalkyale da dariya yace, "Kace yau akwai daru kenan domin ranta a matuk'ar b'ace, sai nike ga kamar ka taka samun barawo ne." Hisham yace "Ina nan ina jiranta." ***** Ta jima tana haura matakalar benen kafin ta k'arasa hawa na ashirin da daya wanda shine hawa na karshe. A fusace ta bamka kofar ta kutsa kai cikin ofishin, ranta a matuk'ar b'ace yake, tun daga bakin kofa take zazzaga mashi bala'i, idanunta a tsatsaiye, dama neman wanda zata sauke fushinta a kansa take. "Waye kai? Miye haka? Mi yasa ka saka ake bibiyar rayuwata? Ina tambayaraka. Ka amsa min tun kafin na fara tara maka mutane." Hisham yayi relaxing akan kujera yana kallonta, yadda take magana a lokacin shine kwatankwacin yadda Bilkisu take masifa idan aka kaita bango, Bilkisu mutum ce mai hakuri saidai idan aka kaita bango bata da hakuri. Ji tayi ranta ya k'ara b'aci ganin yana kallonta yana murmurshi, ta doki teburin dake a gabanshi, "Ina maka magana ka mayar dani mahaukaciya." Hisham yayi murmurshi yana shafa gemunsa yace, "Angel. Miye?" Ji tayi ranta ya k'ara b'aci, tambayarta yake miye bayan yasan abun da yake magana a kai, ji take kamar tayi ball dashi, a tsiwace tace, "Nace waye kai? Mi kake takama dashi da har ka saka ake bibiyar rayuwata?" Bai san lokacin da ya k'ara murmusawa ba, the more take magana the more take tuna mashi da matarshi Bilkisu. Ta daka mashi tsawa tace, "Heyyy! Da kurma nike magana ko kuma raina min hankali da kayi ne ya saka ina kumfar baki kana min dariya." Tambayar da take jira mashi ya amsa a takaice, "Sunana Hisham. Na saka ana bibiyar rayuwarki ne saboda ina da burin aurenki." Duk da haka bata ji ta huce daga haushinsa ta watsa hannuwa a iska idanunta a waje, da tsiwa tace, "Idan aurena kake so, gidanmu zakaje ka gabatar da kanka, daga rana irin ta yau idan na k'ara ganin wani yana bibiyata jama'a zan tara mashi, idan kunne yaji jiki ya tsiri." Ta juya ta kama hanyar fita, ji tayi yace, "Hafsat. Shin baki son sanin dalilin da ya saka nike son aurenki?" Ba tareda ta juya ba tace, "Ban damu in sani ba." Ya ware idanu da mamaki akan fuskarsa domin baiyi tsammanin samun wannan amsar daga gareta ba, yace, "Ki tsaya in rage maki hanya." Ta juyo a fusace tace, "Nasan hanya tunda ba kai kawoni ba." Ta juya ta fice, kamar d'azu emergency stairs tabi. Hisham ya danna landline yayi jim sannan yace, "Ka fito mota zan fita yanzu." Ya mike tareda zura kot ya b'alle cufflinks, ya fita yana tafiya a nutse zuwa private elevator dinsa, sarai ya gani ta emergency stairs tabi wannan ya saka ya rigata kaiwa kasa. Ta fita daga harabar kamfanin ta rik'e kugu, sai a lokacin taji kafafunta sun fara ciwo, ji tayi ba zata iya k'ara koda tako guda daya ba, ta durkushe tana maida lumfashi. Hisham ya fito daga katuwar Jeep dake a gabanta, ya zagaya ya bude bangaren mai zaman hakanan ya dubeta yace, "Muje, inyi dropping dinki a gida daga nan sai in gaida Umma." Ta dan kalleshi tace, "Ban so." Ya dan dubeta yace, "Kin tabbata?" Saida tayi mashi mugun kallo sannan ta shiga motar ya rufe tareda zagayawa bangaren direba, ya danna horn aka bud'e mashi get, yana tuki a nutse yayinda ta juyar da kanta tana kallon waje abubuwa da yawa suna dawo a kai, ji tayi hawaye sun zubo mata. Da sauri ta saka hannuwa ta goge hawayen da suka zubo mata, har yayi parking a kofar gidansu babu wanda yayi magana a tsakaninshi da ita, ta b'alle murfin motar ta fita, ta tarar da Umma zaune akan tabarma tayi jigum, tana ganinta ta mike tana jera mata tambaya. "Hafsat ina kika shiga, tun d'azu nike jajenki?" Hafsat tayi iyakar k'ok'arinta domin b'oye b'acin ran da take a ciki, tayi kamar kamar abun da ya faru d'azu bai tab'a wanzuwa ba, tace, "Umma ban tab'a fad'a maki bane, na jima da lura da ana bibiyata da motoci mabanbanta, a yau na rutsa matukin motar har saida ya kaini wajen wanda ya saka yake bibiyata, yace yana sona da aure ne shiyasa ya saka ake bibiyata, yana a kofar gida zai shigo ya gaidaki." Umma ta dubeta da mamaki saidai ba tace komai ba, Hafsat tace, "Bara inyi mashi magana ya shigo ya gaidaki." Tana gaba yana biye da ita suka shiga gidan, yana mai karewa gidan kallo, ya zauna akan tabarma da aka shimfida a gefen bango, ya gaishe da Umma. Ya dora da cewa, "Umma na gama gyara gidan da zaku koma wanda yake a G.R.A, nan da kwana biyu sai ku tare." Umma ta dubeshi da mamaki sannan tace, "Mu tare kuma?" Ya gyad'a kai yace, "Umma da ni da Hafsat duk daya ne a wajenki." Ya zaro kudi da bai san adadinsu ba yace, "A saka mamu albarka." Umma tace, "Allah yayi albarka amma kudin sunyi yawa...." Kafin ta k'arasa magana har ya fita, tace, "Hafsat ki mayar masa da kudin nan." Hafsat tace, "Koda na mayar mashi ba amsa zaiyi ba, kuma surukinki mai kudi ne, wannan ba wani abu bane a wajenshi." Ta fita ta bar Umma a zaune kamar wacce aka dasa tana mai nadamar abubuwan da tayi mata. Hisham yana jingine da mota, tunda ta fito yake kallonta har ta tsaya a gefensa, tana da matuk'ar kyawu saidai muryarta shine abun dake k'ara sakawa yaji yana son kasancewa tare da ita. "Zuwa ranar alhamis zaku tare a sabon gidan da na siya wa Umma." Da mamaki tace, "Har gida ka siya mata?" Ya sakar mata murmushi yace, "Ki shirya tunda gobe ajin safe kawai gareku idan kuka gama zanzo in daukeki in kaiki kiyi siyayya. Kiyi wa Jalila magana ta rakamu." Da mamaki kwance akan fuskarta tace, "Ban yi maka maganar Jalila ba, amma ka ambaci sunanta kamar ka santa, sannan waye ya fad'a maka gobe lecture safe ne kawai nike dashi." Saida ya murmusa sannan yace, "Mai son dan tsuntsu ne yake binsa da jifa, shin a cikin abubuwan da na fad'a akwai k'arya?" Tace, "Kana nufin kasan komai a game da ni?" Ya gyad'a kai, "Na san komai akan wacce nike son aura." Tace, "Kuma a hakan kake da burin aurena. Ka tabbatar da ka san komai kuwa?" Hisham ya gyara tsayuwa yace, "Angel, babu abun da ban sani ba a game dake. Sai goben idan mun hadu, zan tafo maki da wayarki da system." Ta nuna mashi wayarta wacce take a hannunta, tace, "Wayata tana a hannuna." Hisham ya girgiza kai yace, "Ina nufin wayar da na siya maki." Ya juya ya shiga mota yayi mata key tare da ficewa daga santar saida taga fitar motar sannan ta juya ta koma ciki, ta tarar matan gidansu akan tabarma sun hade kai suna kuskus wanda tana da tabbaci akan Umar suke magana kasancewar unguwar baki daya gulmar da ake yi kenan, kowa yana tofa albarkacin bakinsa. Basu ganin abun da yayi mata sai ita suke cewa ta yaudareshi bayan rufa mata asiri zaiyi. Ta zauna a gefen katifa tace, "Umma yau dai na kawo maki surukinki." Umma tace, "Hafsat amma?" Hafsat ta had'e hannayenta a waje guda fuskarta tana zubar da hawaye tace, "Umma na rokeki da girman Allah karki tayar min da wancen maganar, kiyi kamar bai tab'a faruwa ba. Ni Hafsat. Zanbi zab'inki koda zuciyata bata so. Kuma a yau na kawo maki suruki irin wanda kike so, mai kudi, ba kiga kamfanin da yake dashi ba. Yace gobe zamuje shopping tareda Jalila, na fita zanje gidansu in sanar da ita." Ta goge hawayen dake akan fuskarta sannan ta fita, ta zura takalma ta fice daga gidan zuwa gidansu Jalila, dukkanin kallon da mutane suke mata akan hanya ta sane da abun da yake nufi amma bata da lokacinsu, ta barsu suji da damuwarsu. Mama tana a tsakar gida tana wanke-wanke, Hafsat ta gaishe da ita, "Mama. Ina wuni?" Mama tace, "Lafiya lau. Ki shiga tana ciki." Hafsat ta kutsa kai a dakin. Jalila ta dubeta, "Hafsat kin san kuwa abun da yake faruwa a unguwar nan." Hafsat ta girgiza kai tana mai zama a gefen tabarma tace, "A'a saidai nasan da yawansu suna gulmata akan rabuwata da Umar." Jalila ta ajiye scissors dake a hannunta tace, "Kasan asalin abun da ya faru ba kenan, Umar ya tattara kayanshi ya tafi har yanzu babu wanda yasan inda yake, a cewarsa ya tafi ya nemo kudi a dukkanin infa suke haram ko halal, ta kowace hanya, domin ya aureki." Hafsat ta tab'e baki tace, "Wannan kuma damuwarsa ce, yayi min gori, ya aibata Ummana, sannan kuma ni bazan auri mai dukiyar haram ba, shi kuma yace ta kowace hanya zai nemi dukiya, duk girman dukiyar da zaiyi da abun da zai zama a fagen dukiya bazai tab'a samuna ba. Jalila ba wannan ne ya kawoni ba, nayi sabon kamu, sunanshi Hisham, har yaje gida ya gaida Umma." Jalila kallonta take fuskarta dauke da mamaki tace, "Hisham?" Ta jingina kai, "Shine wanda ya saka ake bibiyata, har gida ya siyawa Umma, yace gobe idan mun gama lectures zaki rakamu shopping...." Jalila ta katseta, "Angel tsaya. Kina nufin kin yarda zaki aureshi, daga haduwa babu bincike, babu fahimtar juna. Kina hauka ne." Hafsat tace, "Yana da kudi kuma Umma tace sai mai kudi kuma aurena zaiyi, shikenan magana ta k'are." Jalila ta zaro idanu jin furucin da Hafsat tayi, tace, "Hafsat ina rabaki da aikin gaggawa, ina guje maki aikin gaggawa." Hafsat ta mike tana mai cewa, "Kinga bani a yanayin da zan tsaya ina juya magana this and that." Jalila ta kamata ta zaunar da ita ta fuskanceta sannan tace, "Hafsat akwai abun da yake damunki wanda shine ya sakaki yanke wannan hukuncin, amma san ki tsaya kiyi wa kanki fad'a domin abun da kike k'ok'arin kiyi babban kuskure ne, kina k'ok'arin tafka babban kuskure a rayuwarki. Angel karki tarwatsa rayuwarki da kanki, ban ce ki bijurewa zab'in umma ba amma kibi zab'inta da taka tsantsan domin gujewa dana sani na abun da zai biyo baya. Ki je kiyi bincike kisan waye shi, mi yasa yake son aurenki." Hafsat ta fizge hannunta ta mike tsaye tace, "Kinga, eh akwai abun da yake damuna wanda ya saka na yanke wannan hukunci, ban sanar dake ba kuma bazan sanar dake ba. Siyayya ne idan zaki rakamu ki fad'a min, idan ba zaki rakamu ba babu dole sai muje mu biyu. Kowa yana da sirrinsa shi kuma ciki ba anyi shi ne domin zuba abinci kawai ne ba." Jalila tace, "Allah ya kaimu goben, zan rakaku siyayya." Hafsat ta had'e hannayenta waje guda alamar roko sannan tace, "Please na rokeki da girman Allah wannan ya kasance karo da karshe da zamuyi wannan magana, ke k'awata ce tun a yarinta bana fatan mu samu damuwa." Ta juya ta fita. Jalila ta bita da kallo cike da mamaki, a ranta tana mamakin miye ya faru da ita, ba halinta bane ba. Shin miye ya saka ta yanke wannan hukuncin wanda zai iya zama sanadin tarwatsewar rayuwarta. ***** Tana komawa gida tace, "Ummana mi zan dafa maki?" Umma tayi jim, Hafsat tace, "Koda yake sai na girka taliya da wake abun da kikafi so." Ta zage ta girka abincin dare, tana iyakar k'ok'arinta domin b'oye b'acin ranta, tana yi kamar babu abun da ya faru amma a cikin zuciya abun yana mata ciwo, daurewa kawai take saidai ta fakaici idanu ta goge hawayen da suka kasa daina fita daga idanunta tana yi kamar hayaki ne yake sakata hawayen. ********* Washegari tunda asuba ta mike ta had'a masu kalaci, tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta material ta zura dogon hijab ta fita tareda biyawa gidansu Jalila suka wuce makaranta. Jalila bata yi mata maganar jiya ba itama bata tada maganar ba. Misalin karfe goma daidai suka fito daga lecture threater, da mamaki kwance akan fuskarta take kallonshi, yana jingine da mota yana aika mata da sakon murmurshi, kamar mai rad'a tace, "Hisham." Jalila ta juya ta kalli inda take kallo, Hisham ya bude bangaren mai zaman hakanan da murmurshi akan fuskarsa, ta mayar mashi da martanin murmurshi ta shiga. Jalila ta bude gidan baya ta shiga, yana mai murza key yace, "Jalila." Jalila tace, "Har ta fad'a maka sunana." Hisham ya danna motar akan kwalta yana cewa, "Ba ita ta fad'a min sunanki, nine na sanar da ita na sani. Sannu dear kunyi lectures an gaji, zamu fara zuwa restaurant." Hafsat ta gyad'a kai kawai, Jalila tace, "Restaurant kuma?" Hisham yace, "Ehh, kun kwaso gajiya na lecture." Jalila tayi mamakin da Hafsat ta ba yarda babu gardama akan zuwa restaurant. Hafsat tayi zuru tana karanta wasikar jaki akan abubuwan da suka faru. Muryarta kawai yake son ya ji saidai taki magana har abun ya fara damunsa, yace, "Angel, fushi ake dani ne har yanzu bakiyi min magana ba, bani labari." "Ba ni a yanayin bada labari." Ta fad'a a takaice. Ya ware idanu yace, "Shine kike sauke komai a kaina, hakanan jiya na tabbatar da sawon barawo na taka domin fushin da kika nuna yafi karfin na abun da nayi kawai." "Wani labari kake son na baka?" Tace domin kawar da maganar. "Kowanne iri, muryarki kawai nike da burin saurare." Ta gyara zama tana bashi labarin LITTAFIN AYSHER ANGEL da ta karanta wanda yayi mata dadi sosai ya tashi kanta sunan littafin MUTUWA A MAKOSHI na siyeshi akan naira dari shidda 600 daga baya da yayi mata dadi ta cika dari hudu 400 ta koma Vvip, murmurshi yake har yayi parking a wani katon wajen cin abincin zamani, fitowa yayi tareda bud'e bangaren da take, ta fito suka jera zuwa ciki yayinda Jalila ta mara masu baya, direct VIP suka wuce, su ukku ne kadai a wajen, waiter ya kawo masu menu, Hafsat tabi menu da kallo, tana mamakin shin yana nufin a gabanshi ne zata ci abinci, wasa yake. Hisham da kanshi yayi ticking abun da za'a kawo masu. Babu jimawa aka jera masu komai akan table, fried rice ce, pepper chicken da suya, ta kalleshi, ji tayi yace, "Ki ci ta yadda za ki ji dadin bani labari, kiji dadin da zakiyi siyayya sosai." Dukkanin maganar da yayi kanshi yana akan wayarsa da yake dannawa lura da tana jin kunyar taci abincin a gabansa, a nutse suka ci abinci, bayan sun gama ya biya bill, ya bude mata bangaren mai zaman hakanan ta shiga sannan ya zagaya bangaren direba, ya murzawa motar makulli yace, "Angel a haka zamuje shopping mall. Gaskiya da sake, kin kusa zama matar Hisham, ya kamata ki fara ado da shiga irin na matar Hisham. Shopping mall da zamuje mallakina ne." Da mamaki tace, "Na'am..." Tana k'ok'arin fahimtar abun da yake nufi, ta kalli kayan da suke a jikinta bataga aibu akan kayan dake jikinta ba. Yace, "Kiyi min murmurshi kawai." Murmurshi tayi wanda iyakarsa akan labb'anta ne kawai, the more ta tuna da abun da Umma tayi mata the more take jinta a cikin matuk'ar damuwa da b'acin rai. A daidai wani katon waje yayi parking ya zaro wayarsa yayi jim sannan yace, "Naja'atu gani nan a bakin titi... Alright..." ya dubeta yace, "Zata zo ta tafi daku, zatayi maki manicure, pedicure, ta baki kayan da zaki saka." Tayi jim sai kuma ta gyad'a kai tace, "To shikenan." Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 7 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 Naja'atu ta k'araso wajen motar da murmurshi akan fuskarta tace, "Yaa Hisham." Ya mayar mata da martanin murmurshi yace, "Naja'atu, ga matata ko ince wacce zan aura Hafsat, Angel." Naja'atu tayi mata murmurshi tace, "Sannu Angel." Hafsat ta mayar mata da murmurshin tace, "Yauwa." Ya dubeta yace, "Kije da ita idan kuka gama zan dawo in daukesu." Naja'atu tace, "Okay, Angel muje." Naja'atu, Hafsat da Jalila suka wuce ciki yayinda Hisham yaja mota ya wuce office, bayan hour biyu Naja'atu ta kirashi ya koma, tun da suka fito yake kallon Hafsat yana mamakin matuk'ar kyawu da take dashi, mai kyau ne matuk'a, kyakykyawa ta karshe, farar mace sol har yellow fatarta take saboda haske, tana sanye da leshe dinkin rigar half boubou da straight skirt, da sarkar hanci akan hancinta, ta murza dauri da yayi suiting shigarta, tana rike da poss, mayafi akan kafad'a, tana tafiya da rashin sabo da mayafi da bata saba sakawa ba. Idanuwansa a kanta ya saki murmurshi yace, "Naja'atu aikin yayi kyau." Naja'atu ta murmusa tace, "Naga alert na gode, Allah ya k'ara budi." Ta bude daya bangaren Hafsat ta shiga yayinda Jalila ta zauna a baya. Kai tsaye ya wuce dasu katon shopping mall wanda yake mallakinsa ne, tun a waje take mamakin girman wajen, lokacin da suka shiga ta zuba idanu tana mamaki a ranta, yayinda ysoro ya kamata, Anya bata dauko ruwan dafa kanta ba? Anya bata kai kanta inda ya fi karfinta ba? Hausa suka ce idan akwai kwadayi akwai wulakanci, bata da kwadayi saidai ta gujewa kanta wulakanci da zai iya biyo baya akan zab'in da tayi. Dukkanin inda suka gitta employee ne suke kwasar gaisuwa saidai ya d'aga masu hannu kawai. Ya juyawa Jalila yace, "Kawarmu ki zagaya ki dauki dukkanin abun da kike so, zan taya Angel." Ta gane nufinsa ta gyad'a kai kawai, har zata zauna sai kuma tayi wani tunanin ta juya ta wuce bangaren turaruka. Hafsat da Hisham suka jera, ta nuna mashi pointing trolley, yace, "Babu buk'ata dukkanin abun da kike so ki nunashi kawai." Tana yawan kamashi yana kallonta saidai tayi murmurshi, ta sani ita mai kyau ce kuma tayi matuk'ar kyau a yau, suna zagaya tana pointing dukkanin abun da yayi mata wanda ya had'a da sutura, takalma, jewelry, jikuna, mayuka, mayafai, dogayen riguna, turaruka da sauransu. A wajen turaruka suka hadu da Jalila, suka wuce inda ake biyan kudi ya mik'a card dinsa aka zare kudin suka fito aka biyosu da manya-manyan ledoji da suke dauke da tambarin shopping mall din, saida ya fara sauke Jalila sannan ya wuce da ita gida, ya saka yara suka shigar mata da ledojin, da mamaki akan fuskarta take kallon ledojin, ido ba mudu bane duk da nuni kawai takeyi amma tana da tabbaci akan kayan sunfi karfin shopping da tayi. Ta dubeshi tace, "Babban mutum amma siyayya da nayi bai kai wadannan kayan ba, kaya kamar wacce zata bude shago." Saida ya murmusa sannan yace, "Girmanki ne, beside tun jiya na fara maki shopping ke kuma kika k'arasa a yau. Ki gaida Ummi. Zan shigo gobe inyi saukeki school." Ta girgiza kai, "A'a zan bi school bus ba sai ka wahalar da kanka." Ta fad'i hakane domin gujewa kanta cin bashi da bata da kudin da zata biya. Bata san abun da zai faru a gaba ba, ya tsura mata idanu, kwarjini yayi mata tayi kasa da kanta yace, "Matar Hisham a motar Hisham zataje school." Kafin tayi magana Rahama makotansu tazo wucewa har ta gittasu gulma ta dawo da ita, tana kallonsa tace, "Angel." Hafsat ta dubeta tace, "Rahama." Rahama tace, "Kece da Umar." Rahama tasan ba Umar bane itama Hafsat tasan Rahama tasan ba Umar bane, gulma ce da neman fad'a domin ta kora mata saurayi. Tayi wani shegen murmurshi sannan tace, "Umar ay talaka ne ni kuma daga ganina babu tambaya matar masu kudi ce. Rahama ki duba da kyau, wannnan mai kudin da zan aura ne, koda ganina baki buk'atar ki tambaya domin kallo daya zakiyi min ki gane cewa ban yi kama da matar talaka ba." Rahama tace, "Eh hakane." Hafsat ta murtuke fuska tace, "Tunda kinyi gulmar da ta kawoki sai kiyi gaba, Allah ya raka taki gona, kina fama da kanki amma baki daina gulma da neman fitina ba." Rahama zatayi jaraba ta lura da bodyguard dinsa dake a gefe, ta juya da sauri ta wuce har tana tuntub'e. Hisham yace, "Mi yasa kikayi mata haka?" Tace, "Tana magana ne akan tsohon saurayina wanda d'an unguwar nan ne, mutumin da suka tashi a tare zata ce ta manta kamanninsa, gulma ce ta ciyota shine tazo tana min maganarshi tana nuna tayi zaton kaine. Hisham na yarda da aurenka ne saboda kana da kudi domin burin ummana shine in auri mai kudi domin bata son in maimaita kuskuren da tayi a rayuwa." Hisham yace, "Amma Hafsat bakya ganin ya kamata kin san dalilin da ya saka nike son aurenki." Ta girgiza kai tace, "Bani da buk'atar sani, na wuce, sai munyi waya." Yana tsaye har saida yaga shigarta gidan sannan ya shiga mota. Washegari har ta manta da ya fad'a mata zaizo ya kaita school, tayi turus ganin motarshi a gefen gidansu, fuskarta dauke da mamaki take kallonshi, bata yi tunanin zaizo ba, kasancewar tace mashi sha biyu take da lectures saida asuba da ta duba sannan taga ashe takwas ne, ta dauka laraba ashe alhamis ne. Hisham ya bude bangaren direba ya fito yana jefarta da murmurshi, suit gray color ne a jikinsa, sumar kanshi tana a kwance tayi lub, yana baza kamshi mai sanyi, ya zuba mata idanu a kullum idan ya d'aura idanunsa a kanta sai yaga ta k'ara mashi kyau, yana matuk'ar mamaki akan kyawu da take dashi. Tana sanye da abaya ta yane kanta da mayafi, fuskarta dauke da simple makeup, handbag dake a hannunta da kuma flat shoes dake a kafarta brown ne, ta zuba gold wuya da hannu, har ta k'arasa inda yake ta tsaya gefenshi bai ya lura ba, tayi tapping hannunta a kusa da fuskarsa yayi firgigit, dariya ya bata, tana k'are fuskarta tana dariya. Ta bude bangaren mai zaman hakanan ta shiga, yana tuki a nutse yace, "Miye labari. Ki bani labari." The more yake tare da ita, the more yake son yaji muryarta domin tana tuna mashi da Bilkisu, mai gadon zinarinsa. Tace, "Babu wani labari. Na dauka ba zaka zo ba, nayi mamakin ganinka, ashe takwas ne, nace maka sha biyu." Yace, "Serious students, tsakiyar semester amma kina manta timetable, na dauka farkon semester ake manta timetable, tsakiya da karshe an riketa a saman kai." Tayi rolling idanu tace, "Yaushe mukayi da kai nace ni serious students ce." Sai kuma tayi shiru, yana son cigaba da sauraren muryarta, ko rabin tafiyar ba suyi ba, da gangan yake tafiya speed kadan, bashi da topic da zai kawo da zai saka ta cigaba da magana. Yace, "Zan koya maki mota." Ba tareda ta d'ago ba tace, "Na hutar da kai, Yaa Aliyu ya koya min." Hisham ya ware idanu da mamaki kwance akan fuskarsa yace, "Waye Yaa Aliyu?" Yana son yasan waye Aliyu a lokaci guda yana farin ciki da ya samu hirar da zaiji muryarta. Ta maida dubanta a kanshi sannan tace, "Gidan da Ummana take aiki, babban yaron matar gidan ta biyu, muna mutunci sosai kamar wasa yace zai koya min mota, kuma ya koya min." Yace, "Ya hutar dake na fara tunanin kaiki makarantar koyon mota, ashe har kin kware daga nan har legas." Dariya ya bata ta girgiza kai, "A'a daga nan har batagarawa dai." Yana son hirar tayi tsayi amma sai yaga tayi shiru. Tana duba note da ta dauki hoto a wayarta, ji tayi yace, "Idan na dawo daukarki zan shigo maki da wayarki da system." Ba tareda ta d'ago ba tace, "Na gode. Allah ya k'ara budi." Yace, "Amin." Shiru ya ratsa wajen, ji tayi yace, "Miye sunan littafin da kika ce min kin siya jiya?" Hafsat ta mayar da wayarta a handbag, bata son yaga kamar bata kyautawa, idan ta shiga makaranta ta duba kafin su fara lectures, tace, "Sunanshi Matar Aliyu labarin soyayyar Fatimazahra da Aliyunta, ka san kuwa kuwa tun marubuciyar tana amfani da pen name Hafsat Hisham nike bibiyar rubutunta har zuwa yanzu da take amfani da ainihin sunanta Aysher Angel." Yace, "Ina kallon films da series, ina karanta English Novel amma ban tab'a karanta na hausa ba." Tace, "Ka karanta kaga yadda za'a tashi kanka kakai karfe biyun dare a zaune kana karatu saboda suspense. Amma ko na yaki tunda naga maza sunfi karanta littafin yaki." Ya girgiza kai, shiru ne ya ratsa a tsakani, ya girgiza kai yace, "Not again." Jin kamar yayi magana tace, "Kace?" Yace, "Kina min rowar littafin ne, ki karanta min inji yadda yake, watakila ya dauki hankalina idan mukayi aure ki rink'a karanta min." Ta bude jikkarta tare da zaro waya tace, "Mu fara da shafukan kyauta tukunna." Da muryarta mai sanyi da dadi ta fara karanta mashi littafin wanda yaja hankalinsa sosai, yayi dariya har da kwolla na diramar Fatima da Aliyu. Ya gyad'a kai yana mai jin dadin muryarta wacce take tuna mashi da Bilkisu matarshi. Yana parking a faculty dinsu, ya fito ya bude bangaren da take ta fito, ya bude gidan baya ya zaro leather ya mik'a mata yace, "Breakfast dinki." Ta dubeshi da mamaki tace, "Saidai nayi breakfast." Yace, "Na sani umma ba zata barki ki fito da yunwa ba, da kaina na shiga madafa na girka maki, kiyi karatu, ban da wasa. Guruwa." Tayi rolling idanu tace, "Gurguru." A tare sukayi dariya, ta juya ta kama hanyar venue da zasuyi lectures, ta zauna kusa da Jalila, wanda yayi daidai da shigowar lecturer din. Karfe goma daidai suka gama ajin, suna da lokaci har hour biyu kafin su k'ara shiga wata lecture, suka bi k'awayensu hostel, Jalila ta bude abincin yayinda kamshi ya bade dakin, suka zagaye suna ci. Farida tace, "Yayi dadi." Jalila tace, "Ina ya siya maki shi?" Hafsat ta ware hannuwa tace, "Ban sani ba saidai na tambayar maki shi inda ya sayi kayan hadin abincin domin da kanshi ya girka." Sunyi matuk'ar mamakin jin da kansa ya girka. Jalila tace, "Yayi maki girki." Farida tace, "Saurayi mai kulawa kamar wannan, ki rikeshi da kyau." Saura mintina talatin su shiga lectures suka dawo faculty, karfe biyu tana fitowa daga inda suke sallah a faculty din taci karo dashi jingine da mota yana jefarta da murmurshi, wata motar ce daban yazo da ita. Farar shadda ce a jikinsa ya daura zabuni a samanta, ya murza hula tangaram, yana kallonta yana murmurshi. Ta lumshe idanu ta bude, da mamaki akan fuskarta tace, "Har ka dawo, nayi tunanin ba zaka zo ba, har zan hau bus sai kuma na tsaya nayi sallah." Yana jefarta da murmurshi yace, "Matar Hisham zaki zama, na siya maki mota, da ita zaki rink'a zuwa unguwa da makaranta da dukkanin inda zakije." Tace, "Ka rufa min asiri gidanmu kofa ce, bani da wajen ajiye mota." Yace, "Akwai a gidan da na siya maku. Ya kikaga wannan motar." Ya k'arasa maganar yana nuna mata mota da yazo da ita, bata fahimci dalilin tambayar ba, tace, "Tayi kyau." Yace, "To shikenan tunda tayi maki kyau zan sauya maki da irinta." Ta zaro idanu tace, "Wannan tafi karfina, waccen ma ban ce zan amsa ba, nayi godiya ne kawai, wannan motar tayi min tsada, mota kowace iri ce, tafi karfina." Ya gyara tsayuwa yana mai tsareta da idanu yace, "Bata fi karfinki ba, Matar Hisham ake magana." Tayi kasa da kanta, yace, "Jalila fa?" Tace, "Jalila suna tana da lectures karfe biyu zuwa hudu, tana carrying 200 level course." Yace, "Okay, muje." Ya bude mata daya bangaren ta shiga sannan ya zagaya bangaren direba, shiru ne ya ratsa motar, yana tuki yana satar kallonta, gani yayi ta janyo littafi zata fara dubawa, da sauri yace, "Ki cigaba da karanta min littafin, yayi min dadi." Ta rufe littafi tareda janyo wayarta tace, "Ban san in takura maka shiyasa nayi shiru, idan yayi maka dadi zakayi magana." Tana karanta mashi yana gyada kai har yayi parking gefen gidansu, zata fita ya danna lock. Ta dubeshi da sauri, yace, "Baki gama karanta min littafin ba, yayi min dadi kuma." Hafsat ta ware idanu tace, "Tab, bazai k'are a yau ba, wata ranar sai in k'arasa maka." Ya girgiza kai, "A'a. Nidai ki cigaba da karanta min." Yana mata shagwab'a tana daukarshi video tana dariya, the more yake mata shagwab'a the more yake mata kyau. Ganin bazai barta ta fita ba ta turo baki tace, "Yunwa." Ya zura hannu a backseat ya zaro warmer tareda bottle water da zobo ya ajiye mata, "Kici, idan kika gama sai ki cigaba da karanta min, babu inda zanje sai an cigaba da labarin tunda yayi min dadi." Ta kalleshi ta kalli warmer da ya ajiye mata, yana nufin a gabanshi zata saki baki tana cin abinci. Kamar ya fahimci abun da take tunani yayi kasa da kujerar da yake a kai, yayi relaxing tareda lumshe idanu, yace, "Da kaina na girka maki, kici hankalinki kwance masoyiya." Yana maganar ne ba tareda ya bude idanunsa ba, fankasu ne da miya da taji naman rago, girkin d'azu yayi mata dadi sosai, tana budewa kamshi mai dadi ya doki hancinta ta lumshe idanu, ta ci sosai, ta kora da ruwa tareda zobo wanda shima ba dai dadi ba. Idanunsa a lumshe tana karanta mashi yana gyad'a kai, mintina talatin har awa daya da rabi, tunda motar tayi parking yake lura da ita har zuwa wannan lokacin, ganin babu wanda ya fito daga motar kuma tinted gareta, ya karasa tareda taping glass dake a bangaren seat. Hisham yayi kasa da gilashin a daidai lokacin da suke dariya wa diramar Fatima da Aliyunta, makocinsu ne, ya kalli Hisham sannan kalli Hafsat dake a bangaren mai zaman hakanan, ya girgiza kai ya juya ya koma inda yake zaune ba tareda yace dasu komai ba. Hisham ya ware idanu yayinda Hafsat ta tab'e baki tareda mayar da wayarta a handbag, ta b'alle murfin motar ta fito wanda yayi daidai da fitowar Hisham shima. A daidai lokacin ne wata bakar Jeep tayi parking a kusa dasu, ta zaro idanu ganin Omar ya fito daga motar yana sanye wata dakakkiyar shadda golden color. Kanshi tsaye ya durfafi inda take ranshi a matuk'ar b'ace yace, "Tunda naje nayi kudin sai ki rabu dashi ki dawo gareni." Hisham ya murtuke fuska yace, "Hey!.." Hafsat ta juyawa Hisham tace, "Ranka shi dade na rokeka da girman Allah dukkanin abun da zai faru karka ce komai ka barni dashi." Ta juya wajen Umar tace, "Na fad'a maka, ka rasani koda kudinka ba rabonka bace, sannan idan ka manta zan k'ara maimaita ni Hafsat bazan auri wanda yace zaiyi kudi ta kowace hanya ba saboda ina tsoron haram, ina gudun haram." Umar yana huci yace, "Shi wanda kike tare dashi kina da tabbacin dukiyarshi ta halal ce. Hafsat k'arya kike! Ke tawa ce, ni kadai!." Hafsat ta daka mashi tsawa tace, "Karya kake!." A fusace yace, "Ki bar ganin ina sonki, nima taimaka maki zanyi, kowa ya sani baki da asali, ke diyar macece, ubanki mahaifi dan chacha, mashayi." Ta fashe da dariya sannan tace, "K'arya kake ina da asali, da uba aka haifeni don haka kayi karya ka kirani da marar asali. Ka iya bakinka wa aibata mahaifina." Yayi dariya yace, "Ki musa idan k'arya nike, da bamu san asalin barbabela ba sai tace daga masar take. Ubanki mahaifi dan caca ne mashayi, ki gode Allah da ya gudu kafin ya sakaki a caca, yadda kike da kyau zakiyi daraja." Ji tayi hawaye sun zubo mata ta gogesu tace, "Careful! Ka iya bakinka." Umar yace, "Hafsat dolenki ki aureni, kudi ne ina dasu a yanzu, itama mota ina da ita, kayan da ya siya maki da gold nima zan siya maki. Idan har ina lumfashi baki isa ki auri wani ba, yadda na rayu da sonki, haka dole in rayu dake." Umar yana bata mamaki koda yake rashin ilimi ne yake damunsa, babu Arabia babu boko, tace, "K'arya kake wannan dake a bayana shine muradina. Da in aureka gwara in mutu." A fusace yace, "Haka kikace, torh bari in saka a illatashi sai inga ta yadda zaki rayu dashi. Shege ku fito kuyi mashi dukan tsiya, kuyi mashi jina-jina, iya illar da kukayi mashi iya kudaden da zani baku." Hafsat ta zaro idanu ganin kartai guda hudu en shaye-shaye sun durfafo inda suke. Hisham yace, "Angel. Ki matsa, babu abun da zasu iya min. Daidai nike dasu." Kallon dan hutu take mashi marar karfi, ta d'aura hannu a kai tace, "Na boni. Baka ganin makamai dake a hannunsu ne." Saida ya murmusa sannan yace, "Makami a hannun wanda bai san yadda zaiyi amfani dashi ba, aikin banza ne." Ta had'e hannayenta waje guda alamar roko sannan tace, "Na rokeka da girman Allah ka tsaya a inda kake a bayana, duk haukanshi bazai bari su tab'ani ba, shima ba zaiyi gigi ba." Tayi tsaye a tsakaninsu tace, "Idan ka isa nima ka saka su dokeni." Umar yace, "Idan dukan kike so da kaina zan dokeki idan har shine yaren da zai saka ki aureni." Ya juyawa en shaye-shayen yace, "Shege ku sauyawa motar KAMANNI." Kamar jira suke su dura akan mota suna fasa gilashintq, Hafsat ta janyo Hisham suka koma gefe, ta fashe da kuka ganin yadda suke fasa motar sun sauya mata KAMANNI, ta koma kamar ba ita ba. Mutane sunyi taro suna kallo amma an rasa wanda zai hana, suna tsoron suyi magana Umar ya had'a dasu tunda ba ya jin kunyar uban kowa. Tana mai fashewa da kuka tace, "Umar na tsanenka, nayi nadamar soyayya da nayi da kai. Umar ka fita daga rayuwata, soyayya ce nace bana yi, ana dole ne. Ni Angel nace bazan aureka sai kaje ka nemi wata." Umar ya nunata da hannuwa da gargadi yace, "Keh, diyar mace, mara asali, diyar mashayi kuma dan chacha, dolenki ki aureni ko kina so ko baki so. Idan ban sameki ba, saidai kowa ya rasa. Sai na sameki ta kowace hanya." Shiru yayi jin k'arar motar Jami'an tsaro wanda Hisham ya kira, shege da sauran yaranshi suka fara neman hanyar gudu amma tuni sunyi masu k'awanya. Bodyguard din Hisham suka zagayeshi suna mazurai. Jami'an tsaro sun kama Umar, shege tareda yaransa suka tusa kewarsu a motar da suka zo dashi. Daya daga cikin yaja motar da Umar yazo da ita. Hafsat ta durkushe tareda fashewa da kuka tana kallon asarar da sukayi mashi, sun fasa mashi mota. Hisham yace, "Please mana Matar Hisham, mota ce, ina dasu da yawa." Tana mai cigaba da kuka tace, "Amma asara bata da dadi, musamman b'arnar da akayi wa mutum da gangan. Kaje, zan wuce gida." Hisham ya ware idanu yace, "Wani gida? Zamanku a wannan unguwar ya k'are, bakiji furucin da yayi ba, ku dauko abubuwanku masu muhimmanci mu wuce, ba komai zaku daukq ba, na zuba maku komai a can." Har zatayi magana sai kuma ta gyad'a kai, bata fatan ta k'ara ganin tashin hankali da ta gani a yau, ta juya ta nufi hanyar shiga gidan, mutane suka bita da idanu kasancewar har yanzu akwai taron mutane basu watse ba, bodyguard dinsa guda biyu suka rakata har kofar gida, ta samu Umma bata dawo ba, dama tayi mamakin rashin fitowar Umma. Tsakar gidan wayam, sai bayan shigarta sannan matan gidan suka fara shigowa daya bayan daya, daga wacce take rataye da kallabi, sai wacce ta daura hijab kamar mayafi duk a saurin fita ganin abun dake faruwa domin a samu na gulma. Umma ta shigo tana mita, "Yaushe kuma kamun en daba ya zama abun tsayawa kallo?" Duk da tasan k'aramin aikin mutanen unguwar ne musamman wanda suka mayar da gulma halinsu. Kallon da mutanen gidan suke mata ya saka ta gane akwai wata maganar bayan wannan, ta maida dubanta akan Hafsat tana neman karin bayani. "Umar ne yazo a katuwar Jeep ya saka en daba suka fasa motar Hisham." Saida Umma tayi ashar sannan tace, "Aikuwa ya tarowa kanshi abun ya fi karfin baki daya danginsu, muje har gidansu sai ubanshi ya biya b'arnar da ya saka aka yi." Hafsat ta kamata tace, "Umma, Hisham ya kira Jami'an tsaro sun tafi dasu." Umma tace, "Ki fad'a mashi babu yafiya har sai sun girbi abun da suka shuka." Hafsat ta jata suka shiga daki suka zauna ta kwashe dukkanin abun da ya faru ta sanar da ita, ta dora da cewa, "Umar yayi wasu maganganu na barazana a gareni, Hisham yace a yau zamu koma wancen gidan, ya zuba komai, mu dauki abubuwa masu muhimmanci." Umma zatayi magana, Hafsat ta katseta, "Please Umma, zamanmu a wannan gidan ya k'are, na tsorata da al'amarin Umar, wannan fitinar ta fi karfina, gwara mu koma wancen gidan ya fi kwanciyar hankali, ba zan iya kwana a wannan dakin ba wanda za'ayi kofar bugu daya ta b'alle." Jalila ce ta shigo gidan da sauri, "Angel. Mi yake faruwa? Karima ta shigo gida tana ce mamu ana fad'a saboda ke, tace har da en daba da Jami'an tsaro." Hafsat tace, "Babu wanda yayi fad'a saboda ni, Umar ne ya saka en daba suka fasa motar Hisham har yana barazanar zai saka su dokeshi." Ta kwashe dukkanin abun da ya faru ta sanar da ita, Jalila ta gamsu ta shawarar da Hisham ya yanke, tace, "Umma, abun da Hisham ya yanke shine abun da ya dace, babu tsaro a wannan gidan ki duba kofar dakin nan bugu daya za'ayi mata ta b'alle. Bari na kira Mama na sanar da ita sai in tayaku hada kayan." Jalila ta kira Mama ta sanar da ita abun da ya faru tareda dorawa da fad'a mata zata rakasu har sabon gidan, ta tayasu suka hada abubuwan da suke bukata wanda suturarsu ne kawai sai takardun makarantar Hafsat, suka fito tare saka kwado a kofa. Umma tace, "Jalila idan zaki tafo zan baki makullin ki duba mamu, idan akwai abun da muka manta sai ki tafo mamu dasu, sauran kuma ki bayar." Shamsiyya wacce dakinta yake a kusa da dakinsu tace, "Fita zakuyi ne." Umma tace, "A'a ba fita zamu ba, tashi zamuyi zuwa sabon gidanmu." Dukkanin matan dake a tsakar gida saida yanayin fuskarsu ya sauya zuwa na mamaki, wasu kuma na bakin ciki ne da hassada, sun tsani Umma saboda tana bakin k'ok'arin ganin Hafsat ba tayi rayuwar wahala da y'ay'ansu sukeyi ba, har suke ganin girman kai ne, isar baka isa ba, gulma iri daban-daban. Salme tace, "Tashi kuma babu sanarwa." Jumala ta sab'a diyarta a baya tace, "Muje inga inda zaku koma, zuwa gobe sai muje muga sabon waje. Na tayaku murna, Allah ya saka da alheri." Sun sani sarai gulma ce zata kaita, saidai basu ce da ita komai ba, ta bisu zaram-zaram, zani daban, riga daban, takalma ware da ware, bata lura ba saboda sauri taje taga gulma domin ta zama mutum ta farko da ta maida yadda aka yi. Fitarsu ke da wuya, d'aya daga cikin bodyguard dinsa ya bude masu daya daga cikin Jeep da suka zo da ita, dayar motarshi da shege suka fasa har an wuce da ita. Mama ta shiga tareda Jalila, Hisham yana ta kallonta tayi banza dashi, zata shiga, Jumala tayi wuff ta shige. Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 8 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 *This Page Goes To Mama Gee, Fahaus chambo, Diamond Bhatool, Mjungudo, Oum Hafsat, Maman Kamal, Mmn Useey, Mummy Khairat, Garba Fatima, Fauziyya Ibrahim Kam, Oum Aftnoor, Aeesharh, Nudar Rabiu, Hauwau Abdullahi and Muhammad Phatymerh Othman, ku yi yadda kuke so dashi.* Hafsat ta dafe kai ta juya inda Hisham yake, ya nuna mata motar da zai shiga, ya bude mata baya ta shiga, bodyguard ya bude mashi daya bangaren ya shiga. Gida ne madaidaici, wanda yake dauke da get da yake hade da tsakar gida, a gefe kitchen ne da toilet, store yana hade da kitchen, parlour guda daya ne da dakuna ukku, daya na Umma, daya na Hafsat, daya kuma na guest. Babu abun da babu. Jumala ta saki baki tana kallon ikon Allah, gida har gida, gini mai kyau, yasha fenti, with complete tale. Hisham yayi masu sallama ya wuce ana kiranshi gida, ta rakashi har mota, ya mik'a mata makullen gidan yace, "Akwai kayan abinci a store. Akwai solar, idan sun dauke wuta ku kunna, akwai ruwa a tanki, idan da wuta zai cigaba da hawa. Ba sai kunyi girki ba zan aiko a kawo maku." Tayi rolling idanu da murmurshi akan fuskarta tace, "Mun gode ranka ya d'ad'e." Yace, "Yauwa ranki ya dade." Tayi kasa da kai tana murmurshi, ya juya ya shiga mota suka wuce, ta juya ta koma ciki. Tana shiga parlour tace, "Jalila na kira Mama na sanar da ita a nan zaki kwana." Da mamaki Jalila ta tambaya, "Yaushe kika kirata?" Ta zauna a saman kujera mai daukar mutum daya kafin tace, "Yanzu kafin in shigo." Jumala tana zaune akan daya daga cikin kujerun tana k'arewa gidan kallo tana daukar detail na gulmar da zatayi. ***** Hisham ya fad'a akan kujera tareda lumshe idanu yace, "Wash!." Momcy ta dubeshi da kulawa sannan tace, "Tun d'azu nike kiranka baka d'agawa sai daga baya ka amsa." Ya kwashe dukkanin abun da ya faru ya sanar da ita. Momcy ta jinjina kai tace, "Allah ya tsare." Fatima tace, "Naso ace ta barka ka banbance masu tsakanin aya da tsakuwa, basu san abun da suke tunkara bane." Momcy ta girgiza kai tace, "A'a gwara da bai biye masu yayi fad'a dasu ba, fitina a kwance take Allah ya la'anci mai tayar da ita." Fatima ta turo baki tace, "Amma Momcy sune suka tsokaneshi har sukayi b'arna." Momcy ta kusa kai mata duka, "Tashi ki bani waje. Miye motar da sukayi b'arna a kanta, motar da muke da kudin siyen dubunsu." Fatima tayi baya da sauri kamar zatayi kuka. Hisham yace, "Didi ki kawo min kunu." Ta mike ta wuce kitchen ta b'ata lokaci ta had'a mashi kunu ta zuba a jug ta d'aura glass cup a kai. Ta tsiyaya mashi ta bashi tareda zama a kusa dashi tana turo baki wa tsawa da Momcy tayi mata. Hisham yace, "Sun koma wancen gidan, zan siya mata mota ta rink'a zuwa school." "Ta iya mota ne?" Momcy ta tambaya. Ya gyad'a kai yace, "Ta iya, yau da zamuje gidan na bata tayi driving dinmu saida muka kusa zuwa sannan na amsa. Bari na kira Najib ya saka a aika masu da abinci." **** Har aka kira Magrib Jumala bata wuce ba, tana nan aka kawo masu abinci, taci har da guzuri a leather tace, "Ummar Hafsat ban fito da kudin komawa ba." Jalila ta tab'e baki tace, "Kin san baki da kudin komawa kuma kika biyomu." Hafsat tace, "Tunda ta saba da tafiya a kafa sai ta saka harama, tafiya a kasa ba bakonta bane. Ki tashi tun dare baiyi maki ba." Umma ta tsawar masu, "Jalila. Angel. Bana son in k'ara jin bakinku a nan, tana sauri ta tayamu murna ne. Ke Hafsat bata kudin da zata koma." Hafsat ta bude jikkarta ta zaro duba daya ta mika mata. Jumala ta amsa tana zuba godiya. Jalila tace, "Tafiyar da bazai wuce naira dari ukku ba, shine har da bata dubu daya." Hafsat tace, "Kin san idan mutum yafi karfin abu. Taje dashi." Umma ta daka masu tsawa, "Angel! Ku tashi ku wuce daki." Jalila ta mike, Hafsat ta mara mata baya, Umma tace, "Jumala, mun gode, Allah ya bar zumunci." Jumala tana washe hakora tace, "Amin. Gobe zamu zo tareda en unguwa suga waje." Umma tace, "Sai kunzo, Allah ya kawoku lafiya." Umma tayi mata rakiya har tsakar gida daga nan ta juya ta koma ciki sanin zaiyi wahala ta hau kekenapep bata son ta tursasata hawa. Jumala tana fita, ta kalli dubu daya da aka bata, ta daura abinci da tayi guzuri a saman kai, ta taka a kafa har gida tana tafiya tana tsara yadda zata zuba gulma, fad'a ba'a tambayeka ba. ****** Babu abun da bai saka masu ba, har da sutura suka ci abinci sukayi hira, Umma ta wuce dakinta. Jalila ta kwanta akan gado yayinda Hafsat ta kwanta akan doguwar kujera tana waya da Hisham saida suka raba dare yana janta da hira, ya koma mata kamar k'aramin yaro, yana zuba mata shagwab'a yana mata dubara yana k'ara tsayin hirar domin ya sakata tayi magana yaji muryarta. The more suke waya the more take k'ara sonshi. Bayan an dauke wuta, ta kunna masu solar, Ac, iska ta ko'ina, bacci sukayi mai dadi har saida suka kusa makara sallar asuba. Hafsat tana gama sallar asuba ta koma bacci kasancewar basu da lectures, kuma bacci ne sosai a idanunta. Jalila ta kunna tv a parlor tana kallon series da tayi missing jiya. Umma ta shiga kitchen ta dama koko, ta soya kosai, ta zuba ta zubawa Jalila ta ajiye na Hafsat a warmer, kokon kuma ta zuba a flask. Knocking sukaji, Umma ta saka Hijab, Jalila ta bi bayanta, daya daga cikin bodyguard din Hisham ne. Ya rusuna ya gaishe da ita, "Mama. Ina kwana?" Umma tace, "Lafiya lau." Ya mik'a mata basket dake hannunsa yace, "Inji ranka shi dade." Jalila ta amsa, Umma tace, "Mun gode. Ka tsaya in baka sako ka kai mashi." Ta juya ta koma ciki. Ya gyad'a kai yana mai gyara tsayuwa. Jalila tabi bayanta, Umma ta dauki abincin da ta ajiyewa Hafsat, ta mik'awa Jalila tace, "Ki kai mashi, ya kai mashi." Jalila ta fita ta mik'a mashi. Ruwan shayi ne, bread, dankali da kwai, jalof rice wacce taji nama. Duk da Jalila taci kosai da kokon da Umma tayi amma saida ta k'ara. ******* Hisham ya kalli koko da kosan ya girgiza kai yace, "Ba zan ci, idan ina da buk'ata zan kira Momcy ta girka min." Najeeb ya dubeshi da mamaki yace, "Amma kai ta aikomawa." A takaice yace, "Ba zanci abun da suka girka ba, ban san yadda tsaftarsu take ba." Najeeb yace, "Kai ka sani, ni ina ci, ina laifin wanda ya yaba da kai har ya aiko maka abinci, kai da aika masu suka amsa sun san tsaftarshi." A takaice yace, "Ni nasan tsaftata." Najeeb yace, "Suma sun san tsaftarsu." Najeeb yana cin kosai yana korawa da koko yana gyad'a kai yana jin dadi a tsakiyar kansa, Umma ba baya ba akan girki. "Uhmm. Yummy. Hisham dadi ya wuceka." Hisham yayi banza dashi ya kira numbar Momcy, "Momcy a girka min koko da kosai, zan aiko a amsar min." Bayan ya tsinke kiran ya maida akalar kiran zuwa numbar Hafsat. Daya daga bangaren Hafsat tace, "Na gode da abinci. Allah ya k'ara budi." Ya amsa da, "Amin." Ya dora da cewa, "Nima kiyi min godiya a wajen Umma." Hafsat tayi dariya tace, "Umma dai, nawa ne fa, har ta ajiye min, ta bada aka kawo maka. Nayi magana tace ay ina barci ta shiga madafa ta dafa don nima in shiga in dafa da hannuna." Ya lumshe idanu yayinda muryarta take mashi matuk'ar dadi a kunnuwa, yace, "Umma tafi ji da ni, kuma yayi dadi sosai." Ya k'arasa maganar yana kallon Najeeb dake cin kosai yana lumshe idanu, yana tsokanarta tana biye mashi, hayaniya ya fara jiyowa yace, "Waye?" Hafsat wacce ta d'aga labule dake a parlour tace, "Makotanmu ne suka zo." Hisham yace, "Alright, na barki lafiya." Najeeb yace, "Kamar da gaske har da cewa da dadi bayan baka ci ba." Hisham yace, "Ka isheni da santi, nima nawa yana akan hanya." ****** Hafsat ta zare wayar daga kunnanta tana kallon makotansu da suke shigowa, wasu bayan wasu, tawaga guda. Jalila kallonsu take ido waje baki bude. Umma tana ta masu sannu da zuwa da fara'arta mutum rahama ne. Murjah tace, "Angel ki bada kudi a baiwa masu kekenapep, guda hudu muka ciko." Hafsat tace, "Kun san baku da kudin kuma kukazo." Jalila ta amsa da cewa, "Sai kace zuwan ya zama dole." Da kakkausar murya Umma tace, "Hafsat ki basu. In k'ara jin bakin mutum a wajen in sab'a mashi, miye laifin wanda yazo inda kake tayaka murna, bakonka annabinka." Hafsat ta juya ta koma ciki, jim kadan ta fito ta mika masu dubu ukku. Ta samu har Umma ta shimfida masu tabarma a tsakar gida. Saida suka gama yawo suka zagaye gidan baki daya sannan suka zauna. Nafisa tace, "Angel. Nifa ko kalaci ban yi ba na biyosu kada su tafo su barni kuma bani da kudin zuwa." Jalila tace, "Da kin sani kin bari kinyi kalaci sannan ki tafo, yadda muka biya kudin zuwanku a tare, sai a biya a rabe." Umma tace, "Angel ki dauko mata abincin da Hisham ya aiko." Hafsat ta ware idanu tace, "Wanda zanci ne kawai kuma nima yunwar nikeji." Umma ta murtuke fuska tace, "Nace ki tashi kije ki dauko mata, ita da yake yunwa takeji da gaske tayi magana ke kuma tun d'azu kina ganinsa kika zauna bakici ba." Ba don ranta yaso ba ta dauko mata, Nafisa tayi wuff ta amsa ganin zasu saka mata wawa ta koma gefe ta rantse babu wanda zaici tunda ita daya aka kawomawa. Murjah tace, "Nima yunwar nikeji amma sai kice ke daya zakici, kin fi wani ne." Nafisa tace, "Oho." Ganin zasuyi masu fad'a Jalila tace, "Murjah kiyi amfani da cikon kudin da suka rage ki siyo abinci kici, magana ta k'are." Jumala tayi karaf tace, "Yunwar nan kowa jinta yake, nima ban yi kalaci ba." Umma tace, "Gashi kuma bamu sauran abinci amma bari in tashi in girka maku." Tana rufe bakinta aka soma shigowa da manya_manyan kuloli wadanda suke da dauke da jalof na shinkafa da taliya da nama. Yaran da suka shigo dasu suka ce, "Gashi inji ranka shi dade." Umma ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi tace, "Mun gode. Allah yayi albarka." Suka amsa da, "Amin." Duk yawan abincin saida su Jumala suka cinyeshi, ci sukayi na tsiya har da guzuri. Ta kira Hisham ta fashe da kuka hankalinsa a tashe yake tambayarta abun da yake mata, tana sheshshekar kuka tace, "Umma ce ta dauki breakfast da ka aiko tayi kyauta kuma yunwa nikeji, Umma ta daina sona, wayyo cikina yunwa." Ya ware idanu yace, "Kuma ban jima da aiko abinci ba na bakin da kukayi, da na sani da na aiko maki dashi." Jin kamar yana cin abinci ne, tace, "Miye kake ci?" Yace, "Koko da kosai Momcy ta aiko min." Da sauri tace, "Ka gutsara ne a yanzu?" Yace, "Ehh." Yana kallon sauran kosan da yake a hannunsa, kanta tsaye tace, "Ka mayar dashi ka rufe ka aiko min." Dariya yayi yace, "Amma wasa kike." Kyit ta tsinke kiran. Ya kira har ta tsinke bata amsa ba, saida ya ajiye mata miss call ukku bata amsa ba kuma tana kallon kiran, Umma ta aiko mata da abincin da ya kawo taki ci, a dole ita tayi zuciya. Umma tayi kwafa, "Yunwa ce ba k'anwar uwa bace, idan zakiji shawarata ki tashi kici yunwa da kike ganinta bata da hankali." Ta kwashe abincinta ta wuce dashi bayan da ta balbaleta da fad'a, "Kuma ko yunwa zata kayar dake ba zakici wannan abincin ba saidai kije ki girka da kanki, da ni kike magana." ******* Hisham ya dubi Najeeb yace, "Miye mafita?" Najeeb yace, "Mafita kenan ka aika mata dashi idan kana son zaman lafiya." Kamar zaiyi kuka yake kallon koko da kosan. Yana ji yana gani yana son yaci domin yayi mashi dadi amma dole ya bada aka wuce mata dashi. Ya ajiye mata sakon text message. "Za'a kawo maki yanzu." Tana ganin sakonsa ta mike ta wuce tsakar gida ta janyo farar kujerar rubber ta zauna kusa da get tun kafin Umma ta amshi abincin ta kyautar dashi. Ana knocking ta bude ta amsa, ta wuce parlour dashi, Umma ta girgiza kai kawai. Kosan da kokon yayi mata dadi sosai, tana ci tana gyad'a kai, gutsiren da ta saka ya mayar dashi ta fara. Saida taci ta koshi sannan ta kira, tace, "Na gode da abinci." Cike yake da ita ya saka Momcy tayi mashi girki tayi kwace karfi da yaji that yana ji yana gani ya aiko domin a zauna lafiya. Yace, "Ina zuwa." Ya kira Momcy ya hadasu a kiran gamayya. Yace, "Momcy tana jinki kiyi mata godiya da kanki." Ta zaro idanu ta dauka da wasa yake har saida taji muryar Momcy, a kunya ce ta gaidata tayi mata godiya. Bayan ya cire Momcy daga kiran tace, "Mi yasa zakayi min haka?" Yace, "Ramawa nayi, kikayi min karfi da abinci, kuma dolena na aiko domin a zauna lafiya." Tayi dariya tace, "Umma ta aiko maka sannan Momcy ta aiko maka kuma in barka dashi saboda yunwa bata dameni ba." Yace, "Na rama mun zama daidai." Sun jima suna waya hakan yayi mashi dadi sosai. Ta biye mashi ne saboda Umma cike da take da ita, idan ta fita ko kallon arziki ba zatayi mata ba. Jalila tana wajen Umma tana tayata hidima da mutanen. Misalin karfe biyu na rana ya k'ara aiko masu da abinci, shima saida suka cinye har da guzuri. Abincin da ya aikowa su Umma daban yake. Jalila ta zubawa Hafsat, Umma ta murtuke fuska, "Tazo da kanta ta zuba ko kuma ta wuni da yunwa, kuma ta saka ya aiko abinci daban a gabanta inyi kyauta dashi inga k'arar taurin kai." Jalila ta tura mata text message yadda sukayi da Umma. Babu arziki ta fito ta zuba da kanta, Umma tace, "Kika ce taurin kai gareki." Hafsat tayi dariya tace, "Ayyerh Umma kiyi hakuri na tuba." Ta zauna a parlour tana ci, cokali daya tayi ta lumshe idanu tace, "Wannan girkin Hisham ne." Jalila tayi mamaki tace, "Ya kika gane?" Hafsat tayi murmurshi sannan tace, "Saboda Hisham ne, ni kuma MATAR HISHAM." Umma tace, "Torh mara kunya a gabana." Hafsat ta mike ta wuce daki da abincin tana dariya. Jalila ta biyo bayanta, Hafsat ta kalleta ta watsar tace, "Sai yanzu kika san hanyar dakina." Jalila ta harareta tace, "K'aramin aikina ne in koma inda na fito. Ke a haukanki sai in biyoki d'azu fushin da Umma takeyi yake ya shafeni, babu ruwana." Saida marece sannan su Jumala suka tafi bayan da Hafsat ta basu kudin mota amma suna fita kofar gida suka rabe kudin, kadan daga cikinsu ne suka hau kekenapep, sauran suka nanike kudinsu a kugunsu suka taketa a kafa, tawaga guda. Tun a daren suka fara yada gulma a unguwa, suna cewa kwadayi ya kai Umma ta siyar da diyarta, kafin washegari kowa yaji a unguwar, suna ta en tsugunne-tsugunne suna zagin Hafsat da Umma suna cewa kwadayi ne da son abun duniya sunga mai kudi sun manne mashi saboda yana basu. **** Da Magrib Hisham ya aiko direba ya kai Jalila gida. Washegari aka saki Omar, duk da gargadi da aka yi mashi da rubutu da yayi amma taurin kai da zuciya ya kwasheshi kai tsaye ya wuce gidansu Hafsat, matan gidan suna zaune a tsakar gida suna gulmar Hafsat da Ummarta wanda ya zama maganar gulmarsu saidai idan basu zauna ba. Ya fado masu ko sallama, suka mike da sauri suna kallonshi, yayi turus ganin dakinsu wayam babu komai a ciki, ya juyo tareda daka masu tsawa yace, "Suna ina?" Farida muryata tana rawa tace, "Sun tashi." A tsawa ce yace, "Ina suka koma?" Saida suka mashi kwatance sannan ya fita, Jumala ta tab'e baki tace, "Gwara yaje yaci uwarsu, maganin kwadayayyu, shine daidai dasu. Rokona Allah ya saka su dawo su cigaba da zama a nan." Murjah tace, "Allah yasa ya k'arya Hafsar muga yadda wancen zai aureka. Rayuwar k'arya kawai. Suna kai kansu inda basu kai ba." ******* Hafsat tana zaune a tsakar gida ta baza takardu a saman carpet tana karatu, Umma ta fito ta dauki buta ta wuce bandaki, motsi taji ta d'ago wanda yayi daidai da shigowar Umar, gadan-gadan ya nufo inda take kamar mayuwacin zaki, da gudu ta shige parlour ta maido kofa ta saka sakata, ta kware murya tace, "Umma ki kulle kofa, Umar yana a tsakar gida." Umma ta mike tareda saka sakata ta sama bayan ta kasa da ta saka tun bayan shigarta, hankalinta a tashe tace, "Angel kina ina? Mun boni." Hafsat ta kware murya tace, "Umma ina a parlour na kulle, bazai iya shigowa ba." Dukan kofar falon yake kamar zai b'allata yana cewa, "Angel tun muna shaida juna ki bude kofar nan, idan kika bari na b'allata abun ba zaiyi mamu da kyau ba, yau za'ayita ta k'are, da in rasaki gwara kowa ya rasa." Ta dafe kirji tana mai godewa Allah da suka baro wancen domin idan can ne bugu daya zaiyi wa kofar ya cimmata. Ya daka mata tsawa, "Zaki bude kofar ne ko kuma sai na b'allata na had'a maki da hukunci." Ta zaro idanu yayinda baki daya jikinta rawa yake, Umma dake a bandaki itama a tsorace take. Hannun Hafsat yana rawa ta zaro wayarta ta kira Hisham, ta fashe da kuka yayinda muryarta ta kasa fita saboda tsoro. Ya murmusa yace, "Umma bata son zaman lafiya damu, miye kikayi mata yau kuma na tabbata kece baki da gaskiya." Tana mai k'ara sautinta kukanta tace, "A tsorace nike, Umar yana tsakar gida yana dokan kofa zai b'alleta." Ta k'arasa maganar da muryarta da take rawa saboda tsoro. Ta kwashe abun da ya faru dashi ta sanar dashi muryarta tana rawa. Zaro idanu yayi yace, "Ki shiga daki ki kulle." Tana mai cigaba da kuka tace, "Umma tana bandaki amma itama ta kulle." Hisham yace, "Gani nan zuwa." Ya dauki makullin motarsa ya kama hanyar gida, Najeeb yabi bayanshi yana tambayarshi abun da ya faru. "Najeeb saida nace kubar yaran nan ya girbi abun da ya shuka amma kuka hanani, gashi nan yana baro ofishin en sanda ya wuce gidansu." Jami'an tsaro suka zagaye gidan yayinda wasu suka shigo suka damkeshi, ihu yake yana hargowa, Hisham ya shiga ciki yayi knocking akan kofa yace, "Angel. Ki bude nine." Hafsat ta bude da sauri tareda rungumeshi muryarta tana rawa tace, "Hisham a tsorace nike. Tsoronsa nikeyi." Hisham yayi mutuwar tsaye jin shock a jikinsa, ya zagaye hannuwansa a bayanta yana bubbuga bayanta, ankara da katobarar da tayi ta sakeshi da sauri ta tureshi, ta kwankwasa kofar bandaki tace, "Umma ki fito, sun zo sun kamashi." Umma ta bude kofa, suka rungume juna yayinda Hafsat ta fashe da kuka tace, "Umma na tsorata, yazo ne ya cutar dani, mun boni mun lalace." Umar ya kufce ya nufo inda suke gadan-gadan, Hafsat ta fasa ihu ganin ya nufo kanta kamar mayuwacin zaki. Kamar walkiya Hisham ya shiga tsakaninsu tareda kai mashi duka, a take Umar ya zube a kasa warwas, suka kwasheshi sukayi waje. Hafsat ta durkushe tareda fashewa da kuka tace, "Umar miye haka? Soyayya ce, ba'a dole. Tun da ba tare aka haifemu ba, sai ka rabu dani." Hisham yace, "Umma ku fito in wuce daku daya gidana wanda yake a titin gidanmu, zamanku ku kadai bazai yiyu ba, a wancen gidan akwai mai guard da security." Umma ta mikar da Hafsat suka tattara abubuwan da suka zo dasu suka fito, Hafsat ta bude bangaren mai zaman hakanan ta shiga yayinda Umma take a gidan baya, Hisham ne yake jan motar, bodyguard dinsa suna biye dasu. A bakin wani katon gida yayi horn aka wangame mashi get ya danna motar ciki, da mamaki suke kallon gidan, katon gida ne gari guda wanda yake dauke babban harabar gida, wajen ajiye motaci, wajen wasan yara, garden, swimming pool, boys quarters yana daga gefe, gida ne mai girma sosai. Mai guard ya rusuna yana kwasar gaisuwa, Hisham ya d'aga mashi hannu kawai, yayi gaba suka bi bayanshi, katon parlour ne wanda yake dauke da kusan setin kujeru guda biyar a wajaje daban-daban, akwai study room, kitchen, toilet, dinning area, dakuna ne birjik a kasan bene da saman bene. Hafsat tayi turus, Umma tace, "Hisham wannan gidan yayi mamu girma." Ya girgiza kai yace, "Umma a nan ne kawai zan barku hankalina ya kwanta, akwai tsaro sosai, zamanku ku kadai bazai yiyu ba, akwai mai guard da security. Ku zauna." Ya k'arasa maganar yana masu nuni wa kujera. Gida kamar a kasar waje. Suka zauna, bai jima ba ya wuce. Bayan ya sanar da Momcy abun da ya faru tace, "Hakan yafi. Allah ya k'ara tsarewa." Hisham yace, "Na aika a kai mata motar da na siya mata." ***** Hafsat ce tsaye a harabar gidan tana kallon motar dake a gabanta cike da mamaki, irin wacce suka dawo daga school ce sak saidai kalarta ce ta banbanta, ta amshi makullin motar ta shiga, da murmushi kwance akan fuskarta ta danna mashi kira yana d'agawa tace, "Na gode sosai motar tayi kyau. Allah ya k'ara budi." Daga daya bangaren yace, "Tunda tayi maki kyau kiyi min hira." Ta zauna a balcony tana mashi hira yana dariya. A ranar ya saka aka cika masu store da abinci, ba na wancen gidan bane ba, wasu ne daban, Jalila ta taimakawa Hafsat suka saka fruit, ruwan gora da drink a fridge. Suka saka kaji a freezer. Saida Magrib sannan Jalila ta wuce gida, washegari da safe suna a parlour aka yi kwankwasa, Hafsat ta yane kanta da mayafi sannan ta fita, daya daga cikin yaransa ne tareda wasu mata guda ukku, ya rusuna ya gaidata sai taji kunya ta kamata kasancewar ya girmeta, yace, "Ranka shi d'ad'e, yace in kawosu, en aiki ne." Tayi jim tana kallonsu sai kuma tace, "Okay, su shigo." Ta zaro kudi kimanin dubu talatin ta bashi tace, "Gashi ka saka fuel." Ya amsa yana godiya. Kadan da kadan Hisham yake koyar da ita yadda masu kudi suke rayuwa, da kanshi ya bata kudade saboda irin haka. Ta juya ta koma ciki yayinda sukabi bayanta, Umma da mamaki take kallonsu, ta jefa mata tambaya, "Su waye?" Tace, "En aiki ne inji ranka shi dade." Umma ta ware idanu tace, "Kika ce?" Tace, "Masu aiki ne inji yaya Hisham." Suna a tsaye, Hafsat ta tuna yadda tayi da aka gabatar mata dasu, tayi mamaki ne a lokacin amma idan aka had'a da yadda sukayi yanzu, matan zasu daukeshi a matsayin mutane masu wulakanci da izza ne. Ta ajiye wayarta tace, "Ku zauna. Miye sunanku." Suka zame a kasan carpet, daya tace, "Sunana Iman." Ta tsakiyar tace, "Ni kuma sunana Hajara." Ta daya gefen tace, "Sunana Mardiyya." Hafsat ta jinjina kai sannan tace, "Iman. Hajara. Mardiyya. Kun san miye aikinku, ba sai na tsaya maimaita maku, a boys quarters zaku zauna, idan kuka zo kuka gama ayyukanku zaku koma wajen zamanku, ban san hayaniya, idan kuka kiyaye zamu zauna lafiya, ban san yawan shige da fice, babu girki a cikin ayyukanku har sai idan an umarceku ne, ku girka abincin da zaku ci a boys quarters ku baiwa mai guard da sauran masu kula da gidan nan, ban san inji wani yayi kukan yunwa kowa a zuba mashi daidai cikinsa. Ban san ganinku kusa da kitchen, da girkinmu, da gyaran kitchen zamuyi abunmu saidai idan muna buk'ata su tayamu zamu kiraku. A cikin ayyukanku ban da gyaran dakunanmu, da kaina zan rink'a gyara dakina da na Ummana, ku gyara sauran da kuma parlour. Bana san k'azanta, kowace tasan a inda tafi kwarewa sai kuje kuyi shawara da kanku, kowace ta dauki abun da zatayi. Ban san hayaniya, ban san gulma, da shiga harkar da babu ruwan mutum, zaman hira da maza masu aiki. Zaku iya tafiya." Ta ajiye masu kudi, daya daga cikinsu ta dauka sukayi godiya suka fita. Suna fita, Mardiyya tace, "Da farko har jikina yayi sanyi ganin kamar tana da izza da wulakanci." Iman tace, "Koma miye hakuri zakiyi neman kudi kika zo, kowa kika gani yana hali mai kyau da marar kyau saidai wani ya rinjayi wani. Idan kikayi zama da masu ne zaki samu alheri a wajensu." A falo, Umma ta dubeta tace, "Hafsat. Miye haka?" Hafsat tace, "Umma nayi mamaki ne, mune da masu aiki, saura kadan dariya ta kufce min shiyasa na fuske nayi haka. Umma gidan nan mune muke zaune a ciki, dole mu lura saboda gudun samun b'araka daga wajensu." Umma ta gyad'a kai tace, "Amma kamar abun yayi yawa." Hafsat tace, "Umma kin fini sanin hakan, idan aka barsu sakaka kowa cewa zaiyi yayi abun da ranshi yake so." Umma tace, "Hakane." Ta tuna kalubale da ta hadu dashi a gidajen da tayi aiki kafin ta samu gidan da take aiki a yanzu. Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 9 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 *This Page Goes To Fahau's Chambo, Hajara B B, and Bhatool Diamond. MATAR ALIYU ina gaishe daku. Nace maku; Wait for it, well here is it, drama iya drama 😅 🤣 😂* Har Hafsat ta mike sai kuma ta koma ta zauna tace, "Umma gidan aikinki fa." Umma tace, "D'azu nike tunanin haka, daga daukar hutu sun jini shiru, ya kamata inje inyi masu bayani." Hafsat ta gyad'a kai tace, "Gobe sai muje tare a motata." Umma tace, "Makarantar fa?" Hafsat tana mike tana tunkarar matakalar bene tace, "Test kadai zamuyi kuma yace sai wancen satin. Bani da komai gobe." Ta zauna a balcony dake a bedroom dinta, ta kira numbar Jalila, tace, "Yau sai ga ranka shi d'ad'e ya turo mamu en aiki, sai mamaki nike wai mune da en aiki, dariya ta kusa kufce min na fuske, na tuna yadda ake yi a novel." Jalila tayi dariya tace, "Hajiya Hafsat Haruna. Hisham's Angel. Bani labari?" "Da farko na tambayi sunayensu, na sanar dasu girki da gyaran dakunanmu zanyi da kaina, ban san ganinsu kusa da bedroom dinmu ko kitchen. Suyi girki suci suba maza masu aiki. Nace ban san k'azanta, hayaniya, gulma, shiga harkar da babu ruwanka, magana da maza masu aiki, suna gama ayyukansu ban san ganinsu a bangarenmu. Kowace ta zab'i aikin da zatayi." Jalila ta fashe da dariya har tuntsurawa tace, "Hajiya Hafsat. Mata a gidan Hisham." Hafsat tace, "Idan aka barsu sakaka, kowace cewa zatayi tayi abun da ranta yake so, wasu lokuttan kana zafi ne domin a zauna lafiya." Daga daya bangaren Jalila tace, "Yaushe zaki shigo?" Hafsat tayi jim sannan tace, "Gobe zamuje gidansu Yaa Aliyu tareda Umma tayi masu bayani. Saidai jibi zan biyo in daukeki mu wuce school." Jalila tace, "Gobe zan shiga school, course da nike carrying, muna da test." Hafsat tace, "Allah ya taimakeki da aka fasa wancen." Jalila tace, "Ke dai bari. Allah ne ya dubi al'amarina, kadan nayi karatunshi, na maida hankali akan wannan, sai kuma Allah ya taimakeni aka fasa." Hafsat ta saka dariya tace, "Wannan semesterr idan muka gama jarabawa, idan nayi bacci, hutu, sai na mayar da jikina." Sun jima akan waya, Hisham ya kira ta tsinke kiran ta amsa kiransa, kamar kowane lokaci tana picking yace, "Angel. Ya aka yi? Ki bani labari." ******** Washegari bisa umarnin Hafsat, bayan sallar asuba masu aiki suka shigo suka gyara gidan ban da kitchen, dakin Umma da dakin Hafsat. Karfe goma na safe Hafsat ta tashi daga baccin da ta koma bayan sallar Magrib, ta janyo wayarta dake akan bedside drawer ta duba sannan ta mike zaune ta duro kafafunta kasa ta wuce bathroom, ta jima tana hade jikinta a kwamin wanka sannan ta sakarwa kanta shower, ta d'aura towel ta fito ta bude closet wanda yake shake da kaya kala daban-daban wadanda koda zatayi shekaru tana sakawa ba zasu k'are ba, ta saka doguwar riga marar nauyi, ta yane kanta da mayafi ta gyara dakinta, ta wanke bandaki sannan ta dauki wayarta ta fita parlour. Umma tana kallon wa'azi, tayi hugging dinta daga baya, tace, "Ummana. Ina kwana?" Umma ta shafa kanta tace, "Lafiya lau. Kin tashi lafiya?" Hafsat tace, "Lafiya lau. Umma bara inje in gyara maki bedroom." Umma ta rike haba tace, "Sai in zauna zaman jiranki, tun da asuba na gyara dakina, abincin safe yana akan teburin cin abinci." Hafsat ta dafe kai tace, "Ina son in samu lada amma barcin safe ya janyo min. Sun zo sun gyara gidan ne?" Ta tambaya. Umma tace, "Tun da asuba, suka gama suka wuce." Hafsat tace, "Ya fi, ban san ina yawan cin karo da mutane." Umma ta girgiza kai tana mamakin wannan halin na Hafsat na rashin son mutane, "Angel na rasa inda kika samo wannan halin na rashin son mutane, duk duniya k'awarki daya, Jalila sai kuwa k'awayenki na boko, suma idan kina dasu kenan." Hafsat tayi murmurshi tace, "Jalila, aminiyata ta kaina, saboda tana son ta cigaba da karatu kuma mahaifinta ba ya da halin daukar nauyinta shiyasa ta fara kasuwanci, take fad'i tashi domin ta samu ilimi." Umma tace, "Allah yayi maku albarka." Hafsat ta amsa da, "Amin." Ta wuce dinning table, bread ne, kosai da kunu, taci ta koshi sannan ta koma parlour dake a saman bene ta kunna kallo. Ta koma dakinta ta shirya cikin lifaya fara mai tsada, ta zuba gold masu tsada, a wuya da hannu, piecer, ta zura takalma half cover ta feshe jikinta da turaruka, duk da simple makeup ce akan fuskarta amma tayi matuk'ar kyau. Ta dauki hotuna a balcony, ta samu Umma zaune a parlour dake kasan bene, suka fita harabar gidan, ta gangara da motarta inda Umma take, ta shiga, ta danna horn mai guard ya wangame mata get, ta danna motar waje, tana janta a nutse. A wani katon gida tayi parking, Umma ta fito tace, "Bari in fara zuwa bangaren Hajiya Kaka." Hafsat tace, "Ina bangarensu Yaa Aliyu." Aliyu yana zaune a parlour yana karanta jarida, kyakykyawa gaske, kyakykyawan namiji mai cikar kamala, kakkarfa, son kowa kin wanda ya rasa, ta zauna a hannun kujerar dake a zaune, tace, "Yaa Aliyu." Aliyu ya d'ago tareda zuba mata idanu ba ya koda kyaftawa, har saida ta k'ara kiransa yayi firgigit yace, "Lovely." Ta murmusa sannan tace, "Amma kana nufin tun da na shigo baka lura dani ba saida nayi maka magana." Aliyu ya ajiye newspaper dake hannunsa tareda maida hankalinsa a kanta yace, "Na bari ne ki gama kare min kallo abunki. Har haka kike son Angel." Ta saka hannu ta rufe fuskarta tace, "Babu ruwana." Yace, "A ranar aurenmu akwai ruwanki." Wasu en mata guda hudu suka sauko daga saman bene suna kallonta da mamaki, daya daga cikinsu tace, "Angel." Hafsat tayi masu murmurshi, ta lura da kallon da suke amma tayi kamar bata gane ba, tace, "Na'ima. Rumana. Oumsalmerh. Hajjo. Kuna lafiya." Kallonta suke da mamaki, idanunsu akan gold dake a wuyanta wanda yake da dogon igiya mai fad'i, ta lura dasu saidai ta nuna kamar bata sani tana wa Aliyu hira, wanda ya mayar da hankalinsa baki daya a kanta. Halima ta shigo da mamaki tace, "Naga sabuwar mota a compound. Munyi baki ne?" Rumana tace, "A'a." Halima tace, "Yaa Aliyu, ka sayi sabuwar mota ne." Aliyu ya girgiza kai. Halima tace, "Kuzo kuga motar, sabuwa, ta linka motar Yaa Aliyu kudi sau ukku." Hagsat ta gane akan motarta suke magana amma ta zab'i da tayi shiru abunta, "Yaa Aliyu. Da fatan zata zo aurena?" A lokaci yanayin fuskarsa ya sauya, ya tsareta da idanu yace, "Kin tab'a ganin inda ango ya rasa aurensa." Ta fashe da dariya tace, "Waye angon? Waye amarya?" Ya murmusa yace, "Hafsat ce amarya. Aliyu angonta." Hajiya Zainab ce ta sauko falon tana kallonsu yayinda ta murtuk'e fuska, kallon kaskanci da tayi wa Hafsat, saida Hafsat taji ta muzanta. Aliyu ya dauki jarida da ya ajiye, Hafsat ta koma ta zauna akan kujera tace, "Ummi. Ina wuni?" A takaice Ummi tace, "Lafiya." Umma ce ta shigo ta gaidata ta amsa a takaice, yaran gidan suka zagaye Umma suna fad'a mata yadda zasuyi kewarta. Aliyu yace, "Maman tuwo zamuyi kewarki." Suna kiranta da maman tuwo ne saboda ita ce take kula da tuwon Alhaji Muhammad Abbansu. Hafsat ta wuce sauran sassan gidan, Aliyu ya mike, Ummi ta murtuk'e fuska tana kallonsa ya koma ya zauna, jim kadan ya fakaici idanunta ya fita. Hafsat ta fito daga bangaren Hajiya Kaka wanda shine na shiga karshe, ta jingina da motarta tana jiran fitowar Umma daga bangarensu Aliyu, bata son komawa lura da Hajiya Zainab ba ta sonta. A fusace Aliyu ya fito daga bangaren ya durfafo inda take kamar mayuwacin zaki, ta tsorata matuk'a, ta takure a jikin mota tana jiran ya wanka mata mari duk da bata san abun da ya b'ata mashi rai amma daga yanayinsa ba k'arami bane ba, ya daka mata tsawa saida tayi baya da sauri. A fusace yace, "Aka ce aure zakiyi?" Ta gyad'a kai muryarta tana rawa tace, "Eh." Tana tantamar idan shine abun da ya b'ata mashi rai, hargowa da yake ne ya janyo hankalin mutanen gidan suka fito sukayi cirko-cirko suna kallonsu. Ya daka mata tsawa yace, "Ni kuma sai kiyi ya dani? Ina kike son in saka sonki da na dauki shekara da shekaru ina ginawa a cikin zuciyata." Da mamaki take kallonsa da tsoro a bayyane a fuskarta, tace, "Ban gane abun da kake nufi ba." Ya daka mata tsawa a karon da bata san adadinsa ba yace, "Kina nufin baki son ina sonki ba." Ta gyad'a kai alamar eh hakane, ya fashe da dariyar takaici yace, "Kina nufin dukkanin alamomin da nike nuna maki baki gane ba. Waye kike son ki rainawa wayo? Huh. Kiranki waya da nikeyi mu jima muna hira, sakonni da nike tura maki ina tambayar halin da kike ciki, kasancewa a tare dake, ziyara da nike kai maki makaranta akai-akai, duk kina nufin baki dauki haske ba, duk kina nufin baki gane sonki nike ba, torh hafsat kaunarki nike, wacce irin kwakwalwa gareki ko kuma kina sone sai na fasa kirjina na dauko zuciyata na baki sannan zaki fahimta, a tunani na koda kallon da nike maki mai hankali zai gane so da kauna dake tattare da kallon." Ta fashe da kuka tace, "Yaya Aliyu kai yayana ne, ina daukarka ne a..." ya daka mata tsawa, "Kiyi min shiru a nan tun kafin na falla maki mari a wajen. Tun da kwakwalwarki da zuciyarki basu gane ba, yanzu zanyi maki da yaren da zaki fahimta." Ya lumfasa sannan ya saka hannu ya d'ago da fuskarta ya tsura mata idanu da kallonsa mai rikita zuciyarta yace, "Hafsat ina sonki, ina kaunarki, a shirye nike da yin rayuwa ta har abada dake, kije kiyi tunanin idan zaki iya rayuwa da wannan bawan Allahn wanda ya shafe shekara da shekaru yana dakon soyayyarki a zuciya." Ya zaro handkerchief ya goge mata hawayen dake fuskarta ta lumshe idanu yayinda kamshinsa ya ziyarci hancinsa. Saida ya kalli tsakiyar idanunta yace, "Hafsat ina matuk'ar sonki." Sannan ya juya ya wuce bangarensu. Dukkanin abun da yake faru Alhaji Muhammad yana tsaye a balcony yana gani. Mutanen sukayi cirko-cirko aka rasa mai bakin magana. Hafsat ta durkushe tareda fashewa da kuka tana tuna abubuwa masu yawa a tare dashi wadanda da ta kalleshi ta fahimcesu sosai a wancen lokacin zata gane yana sonta, kaiconta yana sonta amma wautarta tana mashi kallon yayanta. Tana tuka motar tana kuka har suka iso gida, ganin Hisham a compound ta tsaya ta wanke fuskarta sannan ta nufi inda yake fuskarta a murtuke, da mamaki yace, "Waye ya b'atawa gimbiyata rai inji dalili." Kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace, "Hisham daga yau karka k'ara dawowa sai na nemeka da kaina." Ya ware idanu yana kallonta yayi mamakin kiran sunanshi da tayi kai tsaye da kuma furucinta. Yace, "Hafsat." A fusace tace, "Idan har ba kaine ka siyi goron sunana ba torh ka dakata da kiran sunana haka. Na rantse da Allah idan ka matsa min a yau zan kawo karshen soyayyarmu dama goguwa tayi gaba tubalin soyayyar marar foundation." Ta juya ta shige ciki. Jiki a sanyaye ya shiga mota ya wuce, yana kiranta bata d'agawa ya shiga damuwa matuk'a, yana son ya tambayi Umma saidai ba ya da numbarta, gashi Hafsat tayi mashi gargadi da gaskiyarta take maganar, ba ya fatan abun da zai rabashi mai tuna mashi da mai gadon zinarinsa. ****** Kwana Hafsat tayi tana kuka tana d'aura laifin komai a kanta akan rashin gane Aliyu yana sonta, tunda safe ta shirya ta fita Umma tasan wajen Aliyu zataje amma tana hanata. Aliyu yana daya daga cikin mutanen da Umma take ganin mutuncinsu matuk'a domin yana ganin girmanta, yana girmamata, a shirye take ta bashi Hafsat koda shine ya fi kowa talauci, ta shirya ta bashi Hafsat koda itace zata ciyar dasu. Namiji wanda kowace uwa da ta san ciwon kanta zata so diyarta ta samu. A compound ta tsaya ta kira numbarshi har ta tsinke bai d'aga ba, ta d'aura kanta akan starry tayi shiru. Wayarta tayi tsuwwa shine yake kira ta d'aga. Daga daya bangaren yace, "Amincin Allah ya tabbata akan furen zuciyata mai haskaka zuciyata." Ba ya da ra'ayi akan irin wannan soyayyar amma ya shirya sauyawa saboda ita, saboda sonta, tayi murmushi tace, "Tare da kai." Yayi dariya yace, "Ya aka yi baby na? Kinyi kewata ne inzo ki ganni." Saida ta murmusa sannan tace, "Ka fito ina layin gidanku." Ya ware idanu yace, "Har haka kike sona." Ta gyad'a kamar yana a gabanta tace, "Har haka nike sonka Aliyu, sai jiya na fahimci matuk'ar son da nike maka." Ya saki k'aramin ihun nasara yace, "Gani fitowa." Babu jimawa ya fito tun daga get yake sakar mata murmushi har ya shiga motar yace, "MATAR ALIYU, zinariyar zuciyata." Ta rufe fuskarta da tafukan hannuwa tana mai sakin murmushi. Ya ware idanu yace, "Haka zamuyi soyayyar da kunya." Tayi shiru, yace, "MATAR ALIYU daga nan sai ina zamuje?" (ZAN BI ZAB'IN UMMANA COMMENT SECTION Kuyi mashi gargadi ya daina kiranta da sunana, sunan MATAR ALIYU na marubuciya Aysher Angel ne). Ta turo baki tace, "Makaranta kuma ban ci komai ba." Ya shagala da kallonta, yace, "Kina nufin kallona da kikayi bai kosar dake ba, akwai inda naga ance kaunarka ta saka naji na koshi, bana iya cin komai sai na kalleka." Dariya ya bata, ta fashe da dariya tace, "Anya kuwa? Ina gaya maka yunwa bata da hankali." Ya ware idanu yace, "Tunda hakane ina zamuje matata tayi kalaci." Ta ware hannuwa, "Ban sani ba." Yace, "Ni na sani." Ya amshi tukin motar ya jata zuwa babban gidan cin abinci wanda ziyartarsa sai mai kudi da ya amsa sunansa mai kudi. A tare suka ci yana mata hira tana dariya, sai take mamaki kamar bashi ba, tare sukaje makaranta ya tsaya gama lectures suka juyo. Tun daga bakin get suke jiyo hargowa da ake yi cikin gidan. Ji tayi hawaye sun ciko idanunta ba zata manta wannan muryar ba, Hajiya Zainab ce. A sanyaye suka fito daga mota. Hajiya Zainab tareda wata mata ne tsaye suna wa Umma tujara saidai abun mamaki koda uffan Umma bata ce. Wannnan ya k'ara tabbatarwa da Hafsat girman da Aliyu yake dashi a wajen Umma domin ta tabbatar da wani ne da ba wannan zancen ake yi. A fusace Hajiya Zainab ta nufi inda suke ta d'aga hannu ta wanke Aliyu da mari, tayi wa Hafsat kallon kaskanci tace, "Tun wuri ki fita daga harkar yarona, tun dare baiyi maki ba." Ta juya wa Aliyu ta daka mashi tsawa, "Muje shashasha wanda bai san inda yake mashi ciwo ba, ina ganinka da izza ashe fanko ne, ka rasa wacce zaka furta kana so sai diyar er aiki, dangin tsiya da talauci marassa asali." Hafsat ta durkushe ta fashe da kuka saida tayi mai isarta sannan ta mike wuce ciki. A bangaren Aliyu suna komawa gida Alhaji Muhammad ya gyare Hajiya Zainab akan ta sanar dashi inda taje domin ya kira inda tace zatace a tabbatar mashi da bataje ba. Tayi shiru, ya dakawa Aliyu tsawa yace, "Ina kuka hadu?" Aliyu yayi kasa da kai yace, "Gidansu Hafsat." Alhaji Muhammad ya dubeta ranshi a b'ace yace, "Na hanaki shine kika je, torh gobe zanje da kaina neman mashi aurenta, ki kwantata wani abun kiga yadda zamu kwashe dake a gidan nan, aikin banza aikin wofi." ***** Washegari da safe ta samu kiran Aliyu, daga yanayin maganarsa ta fahimci damuwa da yake ciki, saida ya lumfasa sannan yace, "Hafsat ina son na rokeki wata alfarma." Tayi jim sannan tace, "Wacce alfarma?" Kamar ba zaiyi magana yace, "A yau Abbana zasu zo neman min aurenki a wajen mahaifin Jalila, ina son idan sun nemi ganinki kice mashi kina da wanda kukayi alkawarin aureshi." Ta fashe da kuka tana mai girgiza kai tace, "Amma ina sonka Aliyu." Yace, "Na sani. Abun ya fi karfina. Please kiyi min wannan alfarmar, ina maki fatan alheri a rayuwarki." Kyit ya tsinke kiran ta fashe da kuka, kuka take da dukkanin karfinta, kuka take kamar wacce aka aikowa da sakon mutuwa tana son Aliyu tana kaunarshi. Wuni tayi tana kuka ta kasa cin komai, kallo daya mutum zaiyi mata ya gane taci kuka ba kadan ba, wajen karfe hudu Malam Jafaru mahaifin Jalila ya kirata akan yana son ganinta. Ta zura dogon hijab ta jata motarta zuwa gidan. A can ta tarar dasu Alhaji Muhammad. Malam Jafaru ya nemi ganinta, a gabansu ya tambayeta, "Hafsat sun zo nemarwa Aliyu aurenki, miye ra'ayinka?" Ta fara kokowa da lumfashin tana tuna alfarmar da Aliyu ya nema da kuma kaunarsa da takeyi. A hankali tace, "Nayi alk'awarin aure da wani, sai daga baya ya fad'a min yana sona, bayan da nayi wa wani alk'awarin aure. Kuyi hakuri." Alhaji Muhammad yace, "Babu komai diyata. Kije abunki, Allah yayi maki albarka." Ta share hawayen da suka zubo mata tace, "Amin." Ta mike ta fita. Tana tuki tana ganin hanya biyu-biyu ikon Allah ne kawai ya kaita gida lafiya. Tayi parking ta wuce ciki tana tafiya tana raba hanya, tana shige parlour ta zube a kasa. Umma tayi kanta tana bubbugata saidai bata motsa ba, hankalinta a tashe ta janyo wayarta ta kira Hisham. Yana kusa da gidan hankali a tashe ya iso ya dauketa ya saka a mota suka wuce asibiti. Likitoci suka dukufa a kanta domin ceto rayuwarta, likita ya tabbatar mashi da damuwa ce tayi mata yawa, su guji b'ata mata rai. Ciwo tayi sosai, taji jiki kamar ba zata rayu ba, saukinta suna hutun tsakiyar semester ne, wannan yasa ciwon bai shafi lafiyarta ba, watanta biyu a asibiti sannan aka sallamota kuma Alhamdulillah tana samun lafiya saidai damuwa wacce har a lokacin take manne a zuciyarta. Ranar talata sun fita unguwa da Umma, akan hanyarsu ta komawa Umma tace, "Muje gidansu Jalila, ina son inyi magana da Malam Jafaru akan turowa da Hisham yake so yayi." Hafsat tayi saurin share hawayen da suka zubo mata ta sauya akalar motar zuwa unguwarsu a baya, tana parking suka fito, en unguwa suna ta kallonsu, Hafsat ta girgiza kai kawai kamar bata san suna yi ba. Daga bayanta taji ance, "Sai shegen fi'ili sai kace bamu san asalinta ba, ubanta dan chacha, mashayi, uwarta er aikatau, uban ya gudu ya barsu, uwarta korarra ce daga danginsu, wacce danginta suka yafe." Wata tace, "Ke kada ta ji ki." Wacce tayi maganar tace, "Taji mana, ai ba karya nayi ba, ina sone ta tanka in casata saidai duk abun da zai faru ya faru." Hafsat a cikin ranta tace, "Ba zanyi fad'a dake ba mai karfin maza. Ban had'a kashi dake, hakanan kawai ki goga min talauci." Ta juya ta d'aga masu tana murmurshi, ta kular dasu ba kadan ba. Umma tana a tsakar gida tana magana da Baba, Hafsat ta wuce dakin jalila wacce bata dade da dawowa daga makaranta ba. Saida marece sannan suka koma gida, da mamaki take kallon motoci guda hudu dake a wajen ajiye motoci, Benz guda biyu, Jeep and range rover new model. Yana zaune a bayan motarsa dake a gefe, ya gaida Umma, ta amsa da kulawa tana tambayarshi mutanen gida, ta wuce ciki. Hafsat ta k'arasa tareda tsayawa a gefenshi, tace, "Da fatan ban shanyaka ba, ranka shi dade?" Ya girgiza kai yace, "Ko kadan." Ta murmusa tace, "Ba ka ce min zaka zo ba, kuma muka wuce gidansu Jalila." Yace, "Na dauka kun dawo. Motocinki na kawo maki. Benz, Jeep, da rangers rover new model. Daya benz ta Umma ne, direba ya rink'a kaita unguwa idan baki nan, da sauran aiken gida." Ta girgiza kai, ya fahimci abun da take nufi, ya murtuke fuska yace, "Zamu b'ata." Tace, "Tuba nike ranka ya dade." Yace, "Yauwa Matar Hisham." Maganarsa ta tuna mata da Aliyu, ta saka hannu ta goge hawayen da suka zubo mata tana mai kawar da tunanin daga zuciyarta. Ta amshi makullin motocin tana shiga tana murmushi, tace, "Na gode ranka shi d'ad'e. Allah ya karo arziki." Ya gyara tsayuwa yace, "Idan kinji dadi, kiyi min kalaman soyayya in nada a wayata ina saurare ina jin dadi." Ya kunna recording, Hafsat ta janyon gefen mayafi dake a kanta tace, "Ina matuk'ar sonka ranka shi dade. Allah ya k'ara arziki da lafiya. Allah ya jikan Abbu." Ta mik'a mashi wayarta tana shiga motocin yana daukar hotuna, kiran sallar Magrib suka jiyo yayi mata salaam ya shiga motarsa ya wuce. Ta juya ta koma ciki, a gajiye take, tana gama sallar Isha'i, tayi wanka ta kwanta bacci ne yayi awon gaba da ita bayan da ta maida wayarta silent, Hisham yana kira bata sani ba. ***** Washegari tana da lecture karfe takwas na safe wannan ya saka tana gama sallar asuba ta fara shiri ganin shirinta yana daukar lokaci, ta samu breakfast akan table, ta murmusa tana mai jin kaunar Ummarta da tausayinta na sadaukarwa da dawainiya da tayi bata a rayuwa, bata da abun da zata biyata dashi da ya wuce biyayya a gareta, kamar mai rad'a tace, "ZAN BI ZAB'IN UMMANA KODA ZUCIYATA BATA SO. Ummana ta kaina." Taci ta koshi, ta leka ta gaishe da Umma. Lokacin da ta koma bedroom ta tarar da miss call dinsa guda biyu, Ta shirya cikin leshe dinkin boubou ta murza dauri, ta zuba gold wuya da hannu, ta maida dubanta akan inda takalman suka ajiye tana shawarar saka masu tudu ko kuma flat, karshe ta saka half cover, ta yafa mayafi akan kafad'a, tayi matuk'ar kyawu, ta k'arasa inda handbag suke ta dauki guda daya ta saka jotter tareda wayoyinta, school I'd card, ATM card da sauransu, saida ta shiga tayi wa Umma sallama. A compound ta samu masu aiki suna shara, a tare suka rusuna suka gaishe da ita, ya amsa da fara'a. "Da fatan babu wata damuwa?" A tare suka ce, "Babu." Ta gyad'a kai, "Okay, idan wani abun ya taso kuyi magana, in sha Allah babu abun da zai gagara." Sukayi godiya, ta wuce parking space, ta bud'e motarta Jeep ta shiga, tana akan hanya kira ya shigo wayarta ta gangara akan titi kafin ta amsa, Jalila ce, tace, "Kina ina? Okay na fito, ki fito bakin titi." Ta tsaye ta sameta, ta gangara gefenta ta parker motar, tayi kasa da glass tace, "Ki shigo, mi kike jira, ko sai kin saka mun makara." Jalila ta ware idanu fuskarta dauke da mamakin ganin Hafsat ce, ta zagaya bangaren mai zaman hakanan. Da mamaki tace, "Yaushe kikayi sabuwar mota k'awata?" Idanunta akan titi tace, "Jiya ya kawo min motoci guda hudu, wannan sai Range rover new model da kuma benz, sai benz ta Umma da kuma aiken gida. Jiya na tura maki ta what'sapp." Jalila ta bude data dinta tana mai cewa, "Rabon da in bude data dina tun jiya da marece. Wow amma kin gode, kinga har an saka order ban gani ba, har da receipt." Saida tayi replying sannan suka dasa hirar motocin tana yabasu, tayi parking suka wuce venue da suke da lectures, karfe goma suka fito suka shiga wata lectures, saida suka biya cafeteria suka ci abinci sannan suka kama hanyar gida a motar Hafsat. Jalila tace, "Zamu tsaya kasuwa in amshi wasu shaddoji da aka aiko min daga Kano." Hafsat tana mai cigaba da tuki yayinda idanunta suke akak titi tace, "Okay." Jalila tace, "Jiya da rana ya turo kudin, wai kuma da dare yake sonsu, nace zanyi mashi refund ban san order ta sauri, hakanan a tada maka hankali, shiyasa ban amsa komi yawan abun da zan samu. Shine yace ya hakura zuwa yau da rana." Hafsat tayi murmurshi tace, "Jalila er kasuwa." Jalila tace, "Hisham's Angel. Hajiya Hafsat Haruna. Mata a gidan Hisham." Hafsat ta bugi starry tana dariya tace, "Nayi maki kyautar gida da mota." A tare sukayi dariya, ta tsaya kasuwa, Jalila ta kira ya kwatanta mata inda yake, suka fito sukaje inda yake, ya dauki numbar dake a saman wrapping da aka yi wa shaddojin, ta nuna mashi wayarta dake ringing, ta bashi kudi ta amsa suka juyo. Hafsat tana mai tada motar tace, "Gida zan wuce dake kiga motoci." Jalila tace, "Mama zatayi fad'a." Hafsat tace, "Da kaina zan mayar dake gida, ban da ban san barin Umma ita kadai, da a can zanyi kwanciyata." Saida ta tsaya ta nuna mata motocin sannan suka shiga ciki, tayi wanka suka ci abinci suka zauna a balcony suna hira, Jalila ta kira mai shaddojin, tayi mashi kwatance, bayan ya iso ya kirata, tace, "Angel. Muje." Bakar abaya ce a jikin Hafsat ta warware mayafi dake a saman kanta ta yaneshi, black arebain gown ce a jikinta, tayi rolling veil dake a saman kanta, ta zura takalma dake kusa da ita, ta janyo wayarta suka fita, motarsa tana parker a gefen titi, suka gaisa ya amshi shaddojin suka juyo suka dawo, mai baiwa flower ne yana cutting wasu branches, yayinda yarinya er kimanin shekaru goma take zaune daga gefe tana wasa, ya rusuna tareda gaidasu. Hafsat ta amsa tana kallon yarinyar, ya fara kame-kame kasancewar yaji ance bata son hayaniya, "Wacece?" Ta tambaya. Muryarsa tana rawa yace, "Diyata ce." Tace, "Kirata." Isah ya kwalawa yarinyar kira, "Rufaida." Rufaida ta rugo tace, "Gani Baba." Hafsat tayi murmurshi tace, "Miye sunanki, daughter?" Rufaida tace, "Rufaida." "Kina cin abinci?" Ta tambayeta. Ta gyad'a kai, Isah yayi saurin cewa, "Taci abincin masu aiki da aka bani." Tace, "Yauwa." Ta lumfasa sannan tace, "Bata zuwa makaranta ne?" Isah yace, "Ehhh. " Hafsat tace, "Gobe zan had'aka da wani, ku je a yi mata registration, a biya kudin karatunta tun daga primary har zuwa secondary." Isah ya fashe da kuka na jin dadi yana godiya, "Na gode sosai Hajiya. Allah ya k'ara budi." Tace, "Amin." Ta kama hannunta tace, "Rufaida muje kibi abinci." A parlour suka barta tana cin abinci yayinda Umma take kallon wa'azi suka wuce balcony, Rufaida ta gama cin abinci, tana wasa bacci yayi awon gaba da ita. Da Isah ya tashi tafiya, Iman ta shigo ta dauketa, Hafsat ta bashi atamfofi guda biyar ya kaiwa mamarta, ta bada kudi a yi wa Rufaida siyayya. Hafsat ta shirya cikin leshe dinkin half gown da zani, ta zuba gold wuya da hannu, ta kashe dauri, ta rike kugu ta juya ta k'ara juyawa. Jalila tace, "Besty kinyi kyau ba k'arya." Ta zura takalma half cover, tareda feshe jikinta da perfumes masu saukin kamshi, ta suri mayafi ta daura akan kafad'a dauki wayarta suka fita, Jalila tayi wa Umma sallama sannan suka sauko kasa suka fita, a motarta Jeep suka fita, tayi parking a kofar gidansu Jalila suka fito suka shiga ciki, tana lura da kallon da mutane suke mata suna kus-kus suna gulma, tayi kamar ba taga suna yi ba. Hisham ya kira, Aliyu ta tuna yayinda hawaye suka cicciko akan idanunta. Har ta tsinke bata d'aga ba har saida ya k'ara kira. Ganin bata da niyyar d'agawa Jalila ta dan juyo tace, "Bakiji wayar tana tsuwwa." Ta goge hawayen da suka zubo mata ta amsa kiran kamar mai rad'a tace, "Ranka shi d'ad'e." Daga daya bangaren yace, "Kina ina?" Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 10 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 Tace, "Ina gidansu Jalila amma yanzu zan dauki hanya." Daga daya bangaren yace, "Okay, ki biyomu ta wajen gidanmu mu gaisa." A cikin ranta ta maimaita kalmar mu gaisa, tayi zaton zaice ne in ganki domin nayi kewarki akwai abubuwa da yawa da yake mata da suke matuk'ar bata mamaki, red flag mai kyau amma ta kawar da kai domin ta cika burin umma, saboda ta rasa Aliyu, bata wani zab'in da ya wuce Hisham atleast yana nuna ya dawo da ita yana bata kulawa, yana damuwa da damuwarta. Yace, "Ehhh, Mu gaisa." Sai a lokacin ta farga da zancen zuci da tayi ya fito fili. Tace, "Alright, yanzu zan fito." Ta gangara da motarta gefen titi, tayi parking kusa da get din yayi daidai da fitowar Hisham, ta bud'e murfin motar tareda zuro kafafunta ba tareda ta fito ba, ya dafa motar yana sakar mata murmushi yace, "Angel." Yana sanye da kananan kaya da suka matuk'ar mashi kyau. Aliyu ya fado mata a rai. Da sauri ta kawar da tunaninsa ta sakarwa Hisham murmurshi tace, "Ranka shi dade." Yace, "Kina lafiya?" Ta gyad'a kai tace, "Lafiya lau, ban yi kyau bane." Ta fad'a jin bai yaba mata ba. Ya lumshe idanu ya bude yace, "Kinyi kyau, lovely." Tayi murmurshi tace, "Kayi kyau." "Kiyi min voice kice ina sonka masoyi." Taji yace. Da sauri ta dubeshi tana mamakin abun da ya furta, ita da take a gabansa miye amfanin voice note. Har saida ya maimaita abun da yace sannan tace, "Gani a gabanka babu buk'ata inyi maka voice saidai in kalli cikin kwayar idanunka in fad'a maka abun da yake a cikin zuciyata na sonka." Ya girgiza kai yace, "A'a kiyi min voice note." Abun ya fara sakata a cikin kokonto mi yasa dole sai voice note bayan tana a gabanshi. Ta zaro wayarta ta shiga chat ta danna wajen voice note tayi jim sannan tace, "Ranka shi dade ina sonka." Hishim ya girgiza kai yace, "Ba haka zakice ba. Cewa zakiyi ina sonka masoyi." Da mamaki tace, "Miye banbanci ina ce ranka shi dade da nace yafi masoyi da kake son in fad'a. Yace, "Ki furta min inji." Ta kalleshi tace, "Ina sonka masoyi." Ta furta hakan ne Idanunta suna a kanshi. Hisham ya lumshe idanu ya bude yayinda a lokaci guda yaga fuskarta ta rikide ta koma fuskar Bilkisu. "Torh, Kiyi min voice." Taji yace. Tayi jim tana mamakin dalilinsa na san tayi mashi voice note, kamar ba zatayi ba sai kuma ta danna wajen voice note tace, "Ina sonka masoyi." Ganin lokaci yaja tayi mashi sallama, ya rufe mata motar ta kama hanyar gida yayinda ya juya ya ciki. Saida ya raba dare yana sauraron voice note da tayi mashi a lokaci guda yana tuna yadda Bilkisu take furta wadannan kalmomi a gareshi. Maganar aure ta kankama, magabatan Hisham sun samu Baban Jalila sunyi magana sun bada kudin neman aure har an saka rana, watanni biyu masu zuwa. Maganar ta bugeta sosai musamman da har a lokacin Aliyu yake manne a cikin zuciyarta, ta hana kanta kwanciyar hankali yana zaune a office saidai ganinta yayi, ta fashe mashi da kuka, "Na rokeka Aliyu ka fad'a masu ban san aurenshi, ka fad'a masu kaine a cikin zuciyata." Kafin ya yunkura har ta zube a kasa warwas, hankalinsa a tashe ya sureta ya fice yaja motarsa zuwa asibiti, aka karbeta tareda bata taimakon gaggawa, yana tsaye yana kaiwa da komowa hankalinsa a matuk'ar tashe, idan ciwon zuciya ya kamata shine sanadi, ya daura laifin komai a kansa. Ta farfado tana barci likita ya k'ara tabbatar mashi da damuwa ce take damunta idan suka sake komai zai iya faruwa, damuwa da take a ciki ba kadan bane. Ya rike hannunta yana murzawa a hankali ya kira sunanta, "Hafsat." Ta d'ago da hannunta ta kalleshi da muryarta da bata fita sosai tace, "Aliyu ina sonka." Ya gyad'a kai yace, "Na sani, ina matuk'ar sonki, saidai ba zamu iya kasancewa a tare ba, domin Hajiyata ta rantse idan na aureki sai ta tsine min, Alhaji yayi rantsuwa akan idan tayi yunkurin hanawa zai iya rabuwa da ita. Please Hafsat mu hakura da junanmu. Muyi wa junanmu fatan alheri, ba zan yafewa kaina ba idan na zama dalilin mutuwar auren iyayena hakanan idan kika samu damuwa a dalilina bazan tab'a yafewa kaina ba. Soyayya da zaki nuna min a yanzu shine ki hakura dani, ki auri wanda yake sonki." Ta fashe da kuka, "Hisham yana sona, kai kuma kana matuk'ar sona idan aka bani zab'i kaine wanda zan zab'a domin kaine burina." Ya girgiza kai, "Hafsat ki manta da ni." Ta girgiza kai, "Aliyu bazan iya ba." Sarkewa tayi lumfashinta ya fara sauka sama-sama, da sauri ya kira likita ya dukufa a kanta, kamar ba zata rayu ba, hankalinsa ya tashi ya kira Umma ya sanar da ita asibiti da suke, babu jimawa direba ya kawota hankalinta a tashe ganin halin da Hafsat take a ciki saidai tayi kuka. Ciwo tayi sosai kamar ba zata rayu ba, ta rame ta fita hayyacinta wanda ya tilasta masu k'ara kwanankin auren. ****** Momcy, Fatima, Hafsat da Jalila suka lula Dubai hado lefe daga nan suka wuce London suka k'arasa had'awa duk da mafi yawan lokuttan sunyi yawon bude idanu ne domin ragewa Hafsat damuwa da take a ciki, daga nan suka wuce Umrah, a nan suka hadu da Hisham, daga nan suka juyo gida Nigeria, biki ya matso, dukkanin bangaren sun dukufa shirye-shiryen biki. ***** Hisham ne yayi parking motarsa, Hafsat ta fito tana nufar inda motarsa take tana tafiya a nutse, ta b'alle murfin motar tace, "Barka da zuwa ranka shi d'ad'e. Umma tace lallai-lallai in tusaka gaba mu shiga tare." Kallo daya yayi mata ya gane damuwa da take a ciki saidai bai tambaya. Ya fito yayi gaba tabi bayanshi, ya gaida Umma tare da zama akan kujera mai daukar mutum daya, Umma ta amsa da kulawa tana tambayarshi mutanen gida. Ta dora da cewa, "Tunda baka shigowa gaidani shine nace ta shigo da kai." Ya sosa keya yace, "Zan rink'a shigowa." Umma tace, "Madallah. Angel ki zuba mashi abinci." Ya ware idanu jin abun da tace. A rayuwarsa girkin Momcy da na Bilkisu kawai yake iya ci, sai wanda ya girka da kanshi ko kuma Fatima ta girka mashi, dadin dadawa har lokacin bai san yadda tsaftar girkinsu take ba, idan ya tuna wancen gidan da suka taso sai yaji kamar zaiyi amai, idan yaci abincin zai iya amaye dukkanin abun ya saka a cikinsa tun daga safiyar yau. Dubara ce ta fad'o mashi, yace, "Angel kece kika girka?" Hafsat ta girgiza kai tace, "A'a. Umma ce ta girka." Ya girgiza kai kamar baiji dadi ba yace, "Angel baki kyautawa kina a gidan kike barin Umma tana shiga kitchen. Zo muje in koya maki neman albarka tunda baki iya ba." Ya juya wa Umma yace, "Umma zan shiga kitchen in girka maki tuwo miyar kubewa." Umma tace, "A'a. Ba za'ayi haka ba." Ya girgiza kai yace, "Neman albarka zanyi, da ni da Hafsat duk daya ne a wajenki." Tace, "Allah yayi albarka." Yace, "Amin." Ya mike ya nufi hanyar kitchen yana mai sauke ajiyar zuciya, Hafsat ta dauki wayarta tabi bayanshi, tana mashi bidiyo, ya saka afro yana girki cike da nutsuwa, the more take kallon yake girkin the more yake mata kyau, girki yana mashi kyau musamman yadda yake motsawa da karsashinsa na maza majiya karfi. Mamaki take sosai ganin kwarewarsa, yana tureta tana komawa tana mashi bidiyo, "Wow. Girki yana maka kyau." Ya tuka tuwo ya gama miya, ya zuba mata a plate ya mik'a mata, ya zuba a daya plate ya zauna a kusa da ita. Hafsat tace, "Muci tare." Da sauri ya dubeta sai kuma yace, "A'a. Kowa yaci abincinsa." Tana ci tana lumshe idanu yana mata dariya, suka gama ta tayashi suka wanke abubuwan da aka bata, ya dauko warmer da ya saka na Umma, ya ajiye mata a dinning table. Umma tace, "Ka zauna kaci." Hafsat tace, "Munci wanda ya girka a kitchen." Umma ta jingina kai tace, "Allah yayi albarka." Suka amsa da, "Amin." Yayi Umma sallama, ya fita tabi bayanshi. Suka zauna a balcony tana kallon bidiyo da tayi mashi tana mashi hira tana murmushi, zuciya tana son mai kyautata mata, a kullum cikin faranta mata yake, sannu a hankali take jin sonsa yana shiga zuciyarta saidai tana tabbaci akan ba zata tab'a mashi son da takeyi wa Aliyu ba, kauna ce zallah, ya jima sannan ya wuce. ******** Biki ya matso, hidima ake to kowane bangare, a gidan da ya zauna da Bilkisu za'a kaita, bangaren da Aysha ta zauna, an gyara sashen, ya sauya mata komai. Lefe akwatu guda ashirin da hudu aka kawo, yawa, tsad'a da kyawun akwatunan da yawan kayan da suke a ciki saida yaba Umma tsoro, satin biki yazo, Hafsat tasha gyaran jiki ciki da waje wanda aminiyar Umma ce take mata, tayi kyau fatarta tayi subul-subul, dukkanin inda ta gitta kamshi ne yake tashi. Sunyi dinner, sunyi Lunch, sunyi Bridal shower and football, amarya da ango sunyi kyau, kyau ne ya hadu da kyau, Masha Allah, sai ka rasa da ango da amaryar wanene yafi kyau, naira tayi kuka, bikin ne kawai yake trending saboda yadda aka saki zallar naira. Kwallo ne kawai en unguwarsu Hafsat sukaje duk da shima tasan gulma ce ta kawosu amma ta tarbesu da fara'arta, aniyar kowa ta bishi. ********** RANAR DAURIN AURE. Ashraim yace, "What? Kana nufin a yau za'a daura mata aure." Daga daya bangaren Habib yace, "Labarin da nike samu yanzu kenan, sun sauya gida ne, shima wancen suka k'ara tashi shiyasa na rasa labarinta." Ashraim ya kashe wayar tareda durkushewa ya dafe saitin zuciyarsa, yana matuk'ar sonta, ba ya da burin ya rasata. (Aliyu yana kaunarta, Ashraim yana sonta, Hisham yana son muryarta irin ta matarshi Bilkisu. Muje zuwa.) INA LABARIN AYSHA? Duk abun da yake faruwa bata da labari sai a satin auren take samun labari kasancewar tana London, ta bar aikin bibiyar al'amuran Hisham a hannun K'aninta Jameel. Tunda ta saka kafa ta tafi, Jameel yayi zamanshi a gida yana cin kudaden da ta bar mashi, idan ta kira ta tambaya yace mata babu komai, sai a satin bikin take samun labari, babu shiri ta sayi tickets ta hawo jirgi zuwa Abuja, daga Abuja ta k'ara hawa wani jirgin zuwa Kano, direba ya sameta a Kano ya daukota zuwa Katsina. Tun daga compound take huci tana bala'i. A fusace ta wuce dakinsa, yana ganinta yayi kasa da kai, saida tasa hannu ta wanka mashi mari sannan ta fasa ihu tace, "Jameel ka cuceni. Ka kassara min rayuwa. Ina can ina tunanin komai daidai ashe yana a nan yana shirin angwancewa da wata daban." Jameel yace, "Kiyi hakuri." Tayi mashi wani mugun kallo tace, "Hakuri dolena inyi tunda cuta ce ka cuceni. Ina kudadena? Nace ina kudadena? Tunda baka yi aikin kudin ba sai ka maido min abuna." Jameel yayi kasa da kai yace, "Babu su. Na kashe dukkanin kudin." Ta daka mashi tsawa tace, "Ka iya ka zauna kabi takan kudadena amma baka iya kayi min aikin da na sakaka ba. Yaushe ne daurin auren?" Ta tambayeshi tana mai zare idanu. Yace, "Yau. Karfe biyu da rabi." Aysha ta maida idanunta akan agogo dake manne a bango wanda ya nuna karfe ukku da mintina goma daidai, ta fasa ihu tace, "Jameel, ka cuceni! Ita kuma wanda ta aureshi sai na saka ta tantance cewa ta auri wanda yafi karfinta, shi kuma idan yana ganin barazana nike, zan nuna mashi aiki da cikawa, da ni yake magana." Ta fice fuu tana kiran numbar k'awarta wacce take rakata yawon wajen bokaye. ****** BAYAN DAURIN AURE Hisham yana gaisawa da mutane fuskarsa dauke da zallar farin ciki, yana sanye da farar shadda dinkin babbar riga, har ya manta Aysha a rayuwarsa, wayarsa ce tayi tsuwwa, ya zaro ya duba itace ta tura mashi text message, saida gabansa ya yanke ya fad'i amma ya dake. Aliyu ne ya mik'a mashi hannu suka gaisa yana mai tayashi murna. ****** Tunda ya kirata ya fad'a mata an d'aura gabanta yake faduwa wanda ta rasa dalilin haka, daya daga course mate dinsu ya kira ta amsa tayi jim sannan tace, "Bari in turo maku su Jalila." Ta tsinke kiran tana maida dubanta akan course dinta da suka zo, "Jalila. Nasreem. Nu'ayma. Nafeesa. Meerah. Jidderh. Ku shigo da su Yusuf suna a bakin get, ku wuce dasu daya bangaren kafin nan nayi wanka." Suka fita suka shigo dasu zuwa wancen bangaren inda a nan ta shirya tarbarsu, abinci ne a manyan kuloli wanda ta tanada saboda mutanenta, zuba da kanka, shinkafa jalof, da nama, da tsire, lemu a gefe, suka ci suka koshi. Ta shirya cikin daya daga cikin dogayen riguna na fitar biki, mai kwalliya da suka dauko ta baje basira ta cancara mata kwalliya da tayi mata kyawu tayi matuk'ar kyau, ta zuba gold, ta fita tareda Jalila wacce ta dawo ganin shiru-shiru ba ta je ba kuma sauri suke kasancewar suna hutu ne, wasu daga wasu garuruwan suka zo. Ta kofar baya suka bi zuwa daya bangaren tayi masu sannu da zuwa, suka tab'a hira, suka tayata murna, tayi masu godiya, suka dauki hotuna sannan suka wuce bayan da ta saka aka yi masu takeaway na snacks da kaza tare da drink. Hisham yazo, babu kunya ya rungumeta aka daukesu hoto, k'awayenta suna masu bidiyo, shine yayi amma itace aka bari da kunya, hotuna sukayi sosai. Durkushe take tana kuka yayinda Mama take mata nasiha, ta gama k'awayen Umma sukayi mata suna nusar da ita dubarun zaman duniya, yadda zata kula da mijinta, tasha kuka sosai, tana kuka aka banbareta daga jikin Umma aka fita da ita, aka sakata mota. Gidansu Hisham aka fara wucewa da ita, aka damka amanarta a hannun Momcy daga nan aka kaita gidanta, ta takure a gefen gado tana kuka. Jalila suna mata dariya. Washegari walima, wacce za'ayi a gidansu Hisham, ta shirya cikin leshe brown wanda yayi matuk'ar mata kyau, makeup artist ta cancara mata kwalliya, ta kashe dauri, mayafinta akan kafad'a, ta zuba gold wuya da hannu, jikka da takalma da take sanye dasu masu matuk'ar tsad'a, kada aje kan gold da take sanye dashi, uwa uba leshen dake a jikinta. Hisham ya shigo aka masu hotuna da bidiyo, ya sakata jikinsa yana juyawa da ita yana rawa, ya dauketa cak yana takawa ana masu bidiyo, ji tayi kunya ta kamata amma shi ko a jikinsa, ta b'oye fuskarta a kirjinsa tana ji kamar kasa ta tsage ta shige. Anyi walima lafiya an tashi lafiya, k'awayenta sun wuce gidajensu kasancewar Hisham ne zai wuce da amaryarsa, bayan ta gama sallar Isha'i tana rakube a dakin Momcy ita kadai, Fatima ta shigo ta sanar da ita zuwan Hisham daukarta. "Aunty Hafsat, yaya Hisham yazo." Mikewa tayi tabi bayanta, kallo daya tayi mashi tayi kasa da kanta tareda zama kusa dashi, Momcy tayi masu nasiha sosai tareda saka masu albarka. Fatima ta rakasu har bakin mota sannan ta juya ta koma ciki. Yana tuki tayi shiru tana wasa da zoben dake a hannunta. Yace, "Matar Hisham, babu hira ne." Ta turo baki tace, "Ban yi." Ware idanu yayi yace, "Mi yayi zafi haka?" Tace, "Oho." Sai kuma ta fashe da kuka tace, "Ni ka mayar dani wajen Ummana na fasa auren." Abu biyu ne suka tarar mata, idan ta tuna har ta girma, har tayi aure a yau amma mahaifinta bai tab'a waiwayarsu ba, da kuma damuwa ta rabata da Umma da aka yi. Yace, "Kin fasa auren?" Ta gyad'a kai tana sheshshekar kuka tace, "Ehhh, na fasa." Yace, "Ni kuma ban fasa ba. Miye mafita kenan?" A daidai lokacin ne a gidan aka bude get ya shiga da motar, ta zuba idanu tana kallon katon gidan, wanda a rashin saninta ba zata tab'a rayuwar jin dadi a cikinsa ba. Yana gaba tana biye dashi, ya bude wani bedroom ya shiga, ta zauna a gefen gado, ya jasu sallah raka'a biyu ya dafa kanta yana motsi da bakinsa, ya janyo leather dake a gefensu ya dauki kaza guda daya tare da bottle water, ya bar mata daya, ta dauka zai ciyar da ita da kansa ne amma ga mamakinta sai taga ya koma gefe, tana ci tana hawaye, bata ci na kirki ba ta ajiye. Ya dawo kusa da ita ya matse mata har tana iya jiyo lumfashinsa, tayi baya da sauri, ji tayi yace, "Ki je ki yi wanka ki saka kayan bacci. Ina zuwa?" Ta dauki doguwar rigar barci ta wuce bandaki. Lokacin da ta fito ta tarar dashi kwance akan gado yana sanye da guntun boxer kawai, ta kawar da kanta yayinda kunya ya kamata, ta rab'a ta zauna a daya bangaren, da mamaki take kallonshi jin yace, "Ki bani labari." Maganarsa bata bada magana ta k'ara kallonshi domin share tantamar watakila wasa yake mata da barkwanci saidai da gaskiyarsa yayi maganar, yace, "Babu abun da zanyi maki, ki bani labari, kince marubuciyarki Aysher Angel ta fara sabon littafi ki karanta min." Da mamaki tace, "Littafin hausa kuma?" Damuwarsa shine ya ci gaba da sauraren muryarta. Tayi tunani iri-iri amma bata tab'a sakawa a ranta wannan abun zai faru ba, tace, "Na gama karanta maka wancen, sabon kuma ban siya ba." Yace, "Kiyi payment yanzu sai ki turo mata receipt idan ta gani zata tura maki." Tayi kamar yadda ya fad'a sannan ta ajiye wayar tace, "Bata online kuma bacci nikeji." Tana mai sakin hamma, yayi jim sannan yace, "Okay, saida safe." Ta gyad'a kai tareda kwanciya ta takure a waje daya, bacci yayi dadi ta gangaro inda yake tareda shigewa jikinsa, yayi still yana kallonta, tana da matuk'ar kyau saidai KAMANNI da muryarta take da muryar Bilkisu shine abun da yake janshi zuwa gareta. Ta shige sosai har ya soma jinsa a wani yanayi da ya kasa jurewa, ya haye a kanta yana murzata cike da salo, ta dauka a cikin barci ne har saida taji abun yayi yawa, ta bude idanunta tareda ja da baya saidai ta makara, azabar zafi ya ratsata a yayinda yake shigarta, ta fasa ihu tana mai tureshi saidai bai san tana yi ba, yana murzawa yana sambatu, tasha wuya, tasha kuka, tana kuka tana dukan kirjinsa amma ko gizau baiyi ba, saida ya samu nutsuwa sannan ya gangara gefe yana mai sauke lumfashi yayinda take kuka, koda yatsanta bata iya d'agawa, baki daya jikinta rawa yake, ji tayi yayi sama da ita, tana tureshi amma ko gizau baiyi ba, ya sakata a ruwan zafi, ta k'are kirjinta tana turo baki ganin yadda ya tsura masu idanu, tana tureshi tana dukan kirjinsa tana kuka amma yayi mata banza, ya gasata, yayi mata wanka, ya nadota a towel ya fito tareda kwantar da ita, ya turata jikinsa ya rungumeta, ta fara mutsu-mutsu yayi mata rad'a, yace, "Kina son muyi na biyu ne." Ya fad'a yana mai tura hannunta a cikin wandonsa yana murza joystick dinsa yana lumshe idanu yana gurnani. Ta fizge hannunta tace, "Na bari." Tayi lamo a kirjinsa babu jimawa bacci yayi awon gaba da ita, ya tsura mata idanu yana mamakin matuk'ar kyawunta, dirinta da halittarta, bata da makusa ta kowane bangare amma har zuwa wannan lokacin ba ya jin sonta a cikin zuciyarsa, muryarta ce take janshi zuwa gareta. A hankali ta bud'e idanu wayam taji babu shi babu alamarsa, motsi taji a bandaki tayi saurin rufe idanunta, ya fito jikinsa yana digar ruwa, ya zura farar jallabiya, gani tayi ya nufo inda take, da sauri ta k'arasa rufe idanuwan, ya zauna a gefen gadon ya kama hannunta yana murzawa a hankali yace, "Angel." Ta zare hannunta ba tareda ta bude idanunta ba, ya gane nufinta kunyarsa takeji, mikewa yayi ya nufi yana mai cewa, "Ki tashi, kiyi sallar asuba." Ta mike tana tafiya dakyar tana yatsine fuska saboda zafi da takeji a kasanta, ta dannawa kofa makulli kafin ta shiga bandaki ta k'ara gasa jikinta, ta dauro alwalla, ta tada sallah, ji tayi cikinta ya fara kukan yunwa, ta rarumo sauran kazar jiya ta cinye, taja bargo tana b'ata fuska a sanadin ciwon da kasanta yake mata, tana ji yana kwankwasa tayi kamar tana barci, kunyar had'a idanu take dashi, tana kuma jin haushinsa bayan dukkanin rokon da tayi mashi jiya amma yayi banza da ita. Hisham ya juya ya wuce kitchen ya had'a kunu ya zauna a parlor yana sha yana kallon labarai, misalin karfe bakwai da rabi Momcy ta aiko masu da breakfast, ya ajiye a dinning table ya zubawa kansa, ya ci sannan ya koma saman bene ya dauki spare key ya bud'e kofar ya hangota a kudundune akan gado tana bacci, ya juya tareda rufe mata kofa. Karfe goma na safe, ta sauko kasa, kallo daya tayi mashi tayi kasa da kai ta gaishe dashi. "Ina kwana?" Idanunsa a kanta yace, "Kin tashi lafiya." Ta turo baki tace, "Lafiya lau." Tana jin kunyarsa kuma tana jin haushin banza da yayi mata a daren jiya duk da rokonshi da ta rink'a yi. Ta zauna akan dinning table, ta turo baki da shagwab'a tace, "Ka zuba min." Hisham ya ajiye newspaper dake a hannunsa, yaja kujera dake a kusa da ita ya zauna, ya bude warmer ya zuba mata abincin ya tura mata a gabanta, ta maido mashi gabanshi, turo baki tace, "Da kanka zakayi bani." Cikin ranta tace, "Yadda ka wahalar dani, nima sai na wahalar da kai." Ya dauki cokali ya ciko da abincin ya nufi bakinta dashi, ta ture cokalin tace, "Ban son cokalin da hannunka nike so ka bani." Yayi banza da ita tareda tura mata abincin a baki, cokali na biyu ta goce tare da datsa mashi cizo a hannu tana gunguni, ya b'ata fuska yace, "Ouch." Tayi rau-rau da idanu tace, "Yunwa." Na ukku ta amsa, na hudu ta goce ta k'ara mashi cizo, na biyar ta rink'a gocewa tana wahalar dashi, idan ya ajiye ta turo baki tace, "Yunwa." Saida ta gama wahalar dashi a wajen cin abincin, ta mashi cizo sunfi biyar, bayan ta koshi ya bata ruwa tasha ta koshi, ta ture hannunsa tana turo baki, ji tayi yayi sama da ita ya dauketa, ya ajiyeta a saman kujera yayi pillow da kafafunta ya mik'a mata newspaper da yake karantawa yace, "Tun da kin cije hannuwan da nike rikewa dasu sai ki karanta min da kanki." Ta cune fuska tace, "Bacci." Yace, "Ko muje a yi abun da mukayi jiya a saman gado." Ta zaro idanu gane abun da yake nufi. Ta amshi jaridar tana mai turo baki, kasa-kasa tace, "Shi mutum kullum sai yayi ta sakaka magana amma idan kayi kwalliya bai iya cewa kayi kyau ba." Hisham yayi murmurshi, ya lumshe idanu tana karanta mashi, tana turo baki, da gangan take tsallake ya saka ta dawo baya, tana gunguni zata dawo ta had'a da inda ta tsallake. Bilkisu bata da shagwab'a amma muryar Hafsat tana mashi dadi idan tana shagwab'a. Bacci yayi awon gaba dashi, ta mike ta wuce kitchen ta had'a masu abincin rana ta jera akan dinning table, bayan ya dawo daga masjid, ta tarbeshi da fara'arta, tace, "Yaa Hisham, abincin rana ya sauka." Ya nuna mata kwandon dake hannunsa yace, "Momcy ta aiko mamu." Tace, "Kaci wanda na girka, da daddare sai muci na Momcy, zan saka maka wargi saboda santi." Ta jashi dinning table ta zuba mashi fried rice da romon kai data girka, ya kalli abincin, a rayuwa girkin mutum biyu yake ci, Umma da Bilkisu sai kuma k'anwarsa Fatima ko kuma idan ya girka da kanshi. Yace, "Hafsat abincin Momcy zanci, bamuyi dake ki shiga kitchen, idan kina son girki kiyi min magana in girka mamu." Ta soma bubbuga kafafu tana fad'in "A'a." Tana shagwab'a akan yaci wanda ta girka. Ya ture abincin da ta girka ya zuba wanda Umma ta aiko, da mamaki take kallonsa, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa itama ta zuba taci ta ajiye wanda ta girka da nufin su ci da dare, saidai ga mamakinta da daddare da kansa ya shiga kitchen ya girka masu tana mashi maganar wanda ta girka yayi banza da ita ya kyale, karshe saidai mai guard ta mik'awa girkin da tayi, abun ya bata mamaki da kuma haushi. Daga wannan ranar bai k'ara mata komai ba, suna zaman lafiya, ya hanata shiga kitchen da kanshi yake masu girki, idan ta girka yaki ci saidai taci abunta ita daya, idan tace suci a plate daya yayi mata banza, kullum cikin daukar wanka take amma ba ya yabawa saidai yawan saka tayi mashi hira da karanta mashi jarida, abun yana damunta saidai ta rasa yadda zata b'ullo mashi, koda tayi mashi korafi ba ya gyarawa. Jalila tazo tareda k'awayensu, Fatima itama tazo tayi masu wuni. BAYAN SATI DAYA. Hafsat sakarwa kanta shower tayi brush ta fito ta zura guntuwar rigar barci ta kwanta tana mai janyo laptop dake a gefe, tana kallon series, tunda daga episode na daya takeyi wa kanta karyar bari in k'ara guda daya sai in kwanta, har ta raba dare tana kallon bata ajiye ba saidai ta sauya kwanciya tare da sauya mazauni wa laptop da take kallo a ciki, kadaici ya dameta ba ya kulata tana kunyar samunsa da kanta, lokaci daya taga wutar dakin ta dauke yayinda wani jan haske ya bayyana, wata murya mai amo ta fara ihu tana kiran sunanta ana fashewa da mahaukaciyar dariya. Hafsat ihu take tana guje-guje amma a banza, babu mai jinta, tayi iyakar k'ok'arinta domin ta bude kofa amma abun yaci tura, da gudu ta haye gado ta kwanta tareda jan bargo ta rumtse idanu ji tayi ana lilo da dagon yayinda ta fara sautin fashewar glass, tana bude idanu taga dakin ya wuya sama ta koma kasa, an fasa kayanta. Ta toshe kunne tareda fashewa da kuka, har karfe ukku ana abu daya, dakyar ta samu bacci yayi awon gaba da ita. Hisham ya shigo dakin yana tayar da ita, da sauri ta bude idanunta zata fasa k'ara taga komai daidai, ta mike zaune tana k'arewa dakin kallo ganin komai yana zaune a mazauninsa, yana kallonta da mamaki yace, "Kina neman wani abu ne?" Tace, "Wayata." Yace, "Ki tashi kiyi sallah." Ya juya ya fita, ta maida kallonta akan system dake a gefenta, a inda ta tsaya a nan yake, an saka pause kuma ta tabbata ita dai bata saka pause, saidai kuma rashin sauyawar dakin ya saka ta soma tantama, kanta ya kulle, shin mafarki ne tayi ko kuma ya faru da gaske, saidai tambayar shine; Shin waye ya danna pause? Da mamaki tareda tsoro a ranta ta shiga bandaki tayi alwalla ta fito ta tada sallah, bayan ta gama ta kasa komawa bacci tana tsoron ta k'ara mafarkin da tayi jiya, a cewarta mafarki ne, babu wanda ta baiwa labari amma abun ya tsaya mata a rai, wuni tayi tana tunanin abun. Daddare a tsorace ta kwanta, saidai ga mamakinta ta nemi bacci a idanunta ta rasa, gani tayi dakin ya fara juyawa ta mike da sauri tare da kama gefen gado, dakin ya fara girgiza yana juyawa, idan ya juya baki daya kayan su koma a daya bangaren, kamar yadda ake juya waina a cikin tanda hakanan dakin yake juyawa, tana ihu tana kururuwa amma babu mai cetonta, baki daya kayan dake a dakin sun fashe sun tarwatse ruwa suna kwaranyowa daga bandaki. Kuskuren da Umma tayi a rayuwa shine rashin saka baiwa Hafsat ilimin addini sosai, tunda ta gama sekondire ta ajiye karatun islamiyya saidai boko. Har aka fara kiran sallar asuba ana abu daya, gilashin mirror ne ya nufo fuskarta gadan-gadan, ta rumtse idanunta kamar daukewar ruwa taji shiru sai kuma takon tafiyar mutum, tana bude idanunta taci karo da Hisham, yace, "Har kin tashi kenan." Ta gyad'a kai, ya kalli hannunta da sauri yace, "A ina kika ji ciwo?" Da mamaki take kallon ciwon dake a hannunta, sai kuma ta maida dubanta wa dakin wanda yake kamar yadda yake, babu abun da ya sauya. Babu jimawa ya dawo da first aid kit, ya gyara mata ciwon yana tambayar yadda ta sameshi, ta rasa amsar da zata bashi, ta ware hannuwa alamar bata sani wanda yayi daidai da kai dubanta da tayi akan mirror wanda taga ya tsage, ta k'arasa inda yake da sauri, da gaske ya tsage, Hisham dake bayanta, yace, "Ya aka yi ya fashe? Ko dashi kikaji ciwon?" Ta girgiza kai tareda ware hannuwa, da mamaki ya kalleta sai kuma ya fita ya wuce Masjid, ta shiga bandaki tayi alwalla ta fito tayi sallah, bacci da ba ta koma ba kenan, duk bacci ne cike da idanunta amma tana tsoron komawa har barawon bacci yayi awon gaba da ita, bayan ta tashi ta shiga bandaki tayi wanka ta fito da nufin tayi kwalliya a gaban mirror maimakon taga fuskarta sai taga fatalwa a mazauninta, ta fasa ihu tare da komawa gefe, ta k'ara lek'awa amma still fatalwa ta gani, tayi tunanin watakila ta fara gane-gane ne, ta shirya ta fita tareda kama hannunsa, tace, "Kazo kaga idan nayi kyau." Tayi hakane domin tabbatar da fatalwa ta gani da gaske ko kuma gane-gane ne takeyi. Tayi tsaye a gaban mirror duk da fatalwa take gani amma ta dake tana son jin abun da zaice, tace, "Ya kalleni ta cikin wannan madubin ka fad'a min idan nayi kyau." Ga mamakinta ji tayi yace, "Kinyi kyau MATAR HISHAM. Muje ki karantawa mijinki jarida." Ya tabbata ita kadai take gane-ganenta, a ranar ta saka zani ta rufe dukkanin madubi dake dakinta, ganin wannan fatalwar tada mata hankali yake, tun daga ranar bata sake duba kanta a madubi ba saidai tayi wanka ta shafa cream ta goge fuskarta. Hisham bai lura ba, da yake ba damuwa da yayi da kwalliyarta ba, abubuwa suka taru sukayi mata yawa, ta rasa wanda zata sanar mawa, babu wanda zai yarda da ita, abun ya fi kama da mafarki amma sai yake mata shige da zahiri; Shin miye yake faruwa da ita? Tambayar da take fatan tana da amsarta. Dare yana farawa jikinta ya soma rawa, ta takure a jikin gado tana rawar jiki, dakin ya fara girgiza, da gudunta ta nufi kofar da ta bari a bude, saidai kafin ta k'arasa kofar ta rufe kanta da kanta, yayinda wasu kananun halittu suka bayyana suka yanyameta suna cizonta, tana ihu tana kururuwa amma a banza, sukaji mata ciwo, jini ne yake ta zuba daga jikinta. A hankali ta bud'e idanunta ta tsinci kanta kwance akan gado, ta mike da sauri tana bin jikinta da kallo, babu koda kwarzane a fatarta, sawun cizo daya ta gani a gefen hannunta, ta ware idanu. Hisham ya bude kofar ya shigo sai kuma ya tsaya daga bakin kofa yace, "Har kin farka kenan." Ta gyad'a kai ba tareda tayi magana ba, ya juya da nufin ya wuce yana mai cewa, "Ki tashi kiyi sallah." Ganin zai fita tayi sauri tace, "Ranka shi dade." Hisham ya juyo tareda zuba mata idanu, tace, "Tsakar dare ina bacci na rink'a jin ihu da kururuwa." Ya girgiza kai yace, "Ban ji komai ba." Tace, "Ina jin banji daidai bane." Ta duro daga saman gado ta wuce bandaki tayi alwalla ta fito ta tada sallah ta gama tayi kuri da idanu, duk da idan ta koma bata gane-ganen amma tsoron komawa take, tana zaune tana karantar wasikar jaki har bacci b'arawo yayi awon gaba da ita. Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 11 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 A wannan daren Hafsat taga tashin hankali, sama aka rink'a yi da ita ana shillo, ana juyar da ita sama zuwa kasa ana dariya, ana fara kiran sallar asuba aka wular da ita kasa, tana bude idanunta ta ganta kwance akan gado, har zuwa wannan lokaci ta kasa ganewa, shin mafarki take ko kuma gane-gane? Ta rasa wanda zata tunkara da maganar tana gudun a yi mata kallon mahaukaciya. Hisham ya shigo yaji k'arar ruwa a bandaki ya juya ya wuce Masjid, a ranar da ciwon kai ta wuni na rashin barci, ta wuni tayi kanta yana juya mata, ji take kamar zai fashe saboda ciwo tana son tayi barci amma ya kasa, ji take komai ya fice mata a kai, ta rasa abun da yake mata dadi, tana jin barci tana son abun da zaije ya dawo, wuni tayi sukuku, har ya tambayeta, ko karatun jarida ba tayi mashi ba, tayi shiru ita kadai tana tunani, ba zata iya ba koda k'aryata za'ayi sai ta fad'a. Da daddare ta dauki katuwar rodi ta rike a hannunta tana jiran abun da zai faru, ji tayi an danneta yayinda iska ya fizge rodin daga hannunta, aka rink'a bugar mata fuska da kai dashi, dukanta rodin yake tana ihu yayi mata jina-jina yayinda dukkanin wani abu mai tsini dake a dakin yake farmakarta suna bullewa a jikinta, tana ihu yayinda wata murya mai amo take cewa, "Kinyi gangancin auren wanda ya fi karfinki, kinyi gangancin auren mijin wata, Hisham ya fi karfinki, tun wuri ki san inda dare yayi maki tun bamu haukata ki ba, mune muke maki komai, tsayawar wahalarki yana a hannunki." Ba karamar wuya tasha ba. A hankali ta bud'e idanunta, ta ganta kwance a bandaki, ta mike da sauri tana dube-dube inda zataga rodin amma babu shi babu alamarsa, tunawa da tayi abun bedroom ya faru, ta fito da sauri domin ganewa idanunta, saidai komai yaja a inda yake, ta hargitsa dakin ta bincike komai amma babu rodi babu alamarsa. Hisham yayi tsaye yana kallonta da mamaki, ganin ta hargitsa dakin, yana mata magana, ta tureshi ta wuce inda ta dauko rodin bata ganshi ba, ta zagaye gidan tana nema amma babu shi babu alamarsa. Ta durkushe yayinda maganganun da aka yi mata suke dawo mata a kai, Hisham ya tab'ata, "Angel, miye kike nema?" Ya tambaya. Abun da yake damunta yafi karfin tambayarsa, ya gama zama a gidan, ta tureshi tareda fasa k'ara, ta shige motarta ta mata ta fice zuwa gidan Umma, ko parking din kirki ba tayi ba, ta b'alle motar ta fito ta wuce ciki da gudunta, ta wuce su Iman a parlour suna gyarashi ta haura saman bene. ***** Hankalin Hisham ya tashi sosai, da gudu ya koma ciki ya dauko makullin mota yabi bayanta saidai bai san hanyar da tabi ba, ya bugi starry yana mai fasa ihu, yana tsoron kada abun da ya faru da Bilkisu ne ya faru da ita. ***** Da mamaki Umma take kallonta ganin daga ita sai daurin kirji, gashin kanta kamar na mahaukaciya sabon kamu. "Angel, lafiyarki?" Umma ta tambaya tana kallonta daga sama har kasa. Hafsat ta fashe da kuka tace, "A motata nazo, Umma na gama auren Hisham, aljana ce ta aureshi, kullum sai tazo min da dare tana wahalar dani, tana tsoratani, abubuwan firgici da razani, rabona da inyi barcin kirki har na manta." Ta kwasge dukkanin abun da yake faruwa ta sanar da Umma. Umma tace, "Muga cizon da kuma ciwon." Ta ware idanu ganin babu cizon babu ciwon, Umma ta kanga mata madubi tace, "Mi kika gani?" Hafsat ta ware idanu fuskarta dauke da mamaki ganin fuskarta a maimakon fatalwa da take gani, saida Umma ta maimaita mata tambayar sannan tace, "Umma, fuskata na gani." Umma taja tsoki tace, "Hakanan saboda mafarki kinzo kin tada min hankali. Angel kece kallo da daddare, baki alwalla idan zaki kwanta, baki damu da addu'ar kwanciya bacci ba, wasu lokuttan kina kallo bacci zaiyi awon gaba dake, ai dole kike mafarkai, ke da kanki kika siyawa kanki." Ta lumfasa sannan tace, "Hafsat yaushe rabonki da karatun Alk'ur'ani?" Hafsat ta ware hannuwa domin ba zata iya tunawa ba, Umma tayi salati tana tafa hannuwa tace, "Kina nufin karatun Alk'ur'ani saidai na karatun sallah kikeyi, sannan kice zakiga daidai. Hafsat ki rike karatun Alk'ur'ani da azkhar, babu wani mugun mutum ko aljan da zai samu nasara a kanki, addu'a takobin mumini ce, Alk'ur'ani waraka ne." Hafsat ta gyad'a kai tace, "In sha Allah." Umma ta jingina kai tace, "Kiyi kalaci, kiyi wanka, ki sauya kaya ki wuce gidan mijinki." Hisham ne ya fado kamar wanda aka jefo, ya sauke ajiyar zuciya ganinta, Umma tace, "Sai ki tashi kibi mijinki, motar direba zai kai maki. Daga mafarki sai ki biyo kafa ki tafo saboda sakarci." Hisham yana tukin motar ya dubeta yace, "Miye ya faru?" Tayi shiru kamar bata ji ba har saida ya maimaita tace, "Mafarki ne kuma laifina ne ina sakaci da addu'a zan gyara." Daga nan bata sake magana ba har suka iso gida. Saida gabanshi ya yanke ya fad'i, hango motar dake a harabar gidan, ya gangara da motarsa suka fito. Aysha ta b'alle murfin motarta ta fito tana tafiya tana murmusawa, murmushi na mugunta, Hafsat ta kalleta da mamaki, Hisham yace, "Aisha." Aisha tace, "Ehhh Aisha shine sunana wanda aka daura mamu aure... Sannu Amarya Hafsat ko ince Angel. Hisham's Angel. Da fatan kina lafiya koda yake daga ganin yadda kike daga ke sai daurin gaba da wannan kan kamar mahaukaciya nasan aikina yayi aiki." Hafsat ta ware idanu tana maimaita abun da tace, "Aikinki yayi aiki." Aysha ta fashe da dariya tace, "Ohh yanzu na gane dalilin da ya saka ya rude a kanki, muryarki ce ta saka ya aureki." Hafsat ta zaro idanu tana had'a abubuwan da suka faru tunda haduwarsu har zuwa wannan rana, tabbas biri yayi kama da mutum, sakata tayi mashi hira, ta karanta mashi littattafan hausa, ta karanta mashi jarida, a koda yaushe burinsa yaji muryarta. Aisha ta kwashe da dariya tace, "Bari in gama dashi kafin in dawo a kanki." Hisham ya daka mata tsawa, "Aisha!." Ba ta razana ba saidai rike kugu da tayi tana wani shegen murmurshi tace, "Hisham tsawarka ta daina tsoratar da ni don haka ka daina wahalar da kanka. Nayi maka gargadi amma ba kaji ba kaje kayi aure, kai a tunaninka barazana nike, babban kuskuren da kayi shine tsallake magana kuma ita ce zata girbeshi, zakaga aiki da cikawa, ni ce matarka ta farko, uwar gida ran gida, daga ni ka rufe, dukkanin wacce tace zata rab'eka ta janyowa kanta bala'i, kamar yadda na mahaukata amaryar da kayi min Bilkisu ta gudu har yanzu ba'a san inda take ba, kamar hakan ne zan haukata wannan idan ba tayi wa kanta karatun ta nutsu ba, ta gudu da kanta, tun kafin ta gudu a halin hauka." "Miye kike cewa akan muryata? Wacece Bilkisu?" Hafsat ta jefa mata tambaya. Aysha tayi murmurshin samun nasara, tayi aiki taga kamar bai ci ba shiyasa tazo ta ganewa idanunta sannan ta haddasa rikici a tsakaninsu ta hanyar fallasa abun da ya faru da Bilkisu domin ta tabbata dukkanin mai hankali ba zata aureshi ba idan taji abun da ya faru da ita. "Ki tambayeshi, yana da amsoshinki, ke a tunaninki kin samu daula a banza, kinga mai kudi, kin makale mashi babu bincike, kwadayin kudinki ya saka kin auri wanda ya fi karfinki, tun wuri ki san inda dare yayi maki tun kafin in fusata in haukataki kika bi duniya ba, kamar yadda Bilkisu take a can, sun nemeta har sun gaji. Kina ganin kin samu miji," ta nuni zuwa Hisham ta dora da cewa, "Torh mijina ne ni kadai, bake ba, ko wacece tace zata rab'eshi sai na illata rayuwarta, zai zame maku guguwar bala'i mai tarwatsa farin ciki. Abun da ya faru dake kwanaki biyar da suka wuce, gargadi ne, idan kikayi burus zaki hauka ce. Idan kina ganin k'arya nike, ki zauna ki gani." Hafsat tayi murmurshi mai ciwo tana mai cewa, "Kin zo kina min barazana da asiri, a baya asirinki ya wahalar da ni ne saboda sakaci da nayi da addu'a amma a yanzu daidai nike dake, muje zuwa, ni fake shege ka fasa dan halak sai yanka." Ta juya ta shige ciki barci ne sosai a idanunta ji take kamar zata fad'i, ta rakasa dakinta tayi alwalla tayi sallar asuba, ta kunna karatun Alk'ur'ani tana mai binsa da kira'arta mai dadi yayinda nutsuwa ta sauka a dakin, taji nutsuwa har cikin zuciyarta, babu jimawa bacci yayi awon gaba da ita, bacci mai cike da nutsuwa, ta samu barci sosai, lokacin da ta tashi ta nemi ciwon kan ta rasa, tana mai jinta a cikin nutsuwa, ta karanta addu'ar tashi daga barci kafin ta duro daga saman gadon ta wuce bandaki tayi wanka ta zura doguwar marar nauyi ta fito ta sameshi a parlour kallo daya tayi mashi ta wuce dinning table ta sameshi wayam, ta kalli inda yake tace, "Yunwa nikeji ko kuma har da horon yunwa ka shirya min bayan rufeni da kayi ka aureni duk da kasan abun da zai faru dani." Mikewa yayi ya wuce kitchen ya dauki lokaci kafin ya fito ya zuba mata abincin ya koma parlour ta dauki cokali tayi bismillah kafin ta faraci, tana cin abinci tana sauraron karatun Alk'ur'ani mai girma, rabonta da taci abinci a cikin kwanciyar hankali har ta manta, taci tayi nak ta wanke hannuwanta ta sameshi a parlour, kallo daya yayi mata ya maida dubansa akan TV yayinda gabanta yake faduwa akan abun da zaije ya dawo game da abun da Aysha tazo ta fad'a mashi. Duk da yayi nufin fad'a mata tun farko saidai koda a waccen lokacin yayi nufin b'oye mata abun da ya faru da Bilkisu domin ya tabbatar da ba zata yarda da aurensa ba idan taji, abun da ya shirya fad'a mata shine yana sonta ne saboda muryarta saidai bata bashi wannan damar ba. Tayi tsaye a kanta, zuciya ta kawo mata wuya ta fizgi remote ta kashe kallon baki daya, ya juyo yana mai tsareta da idanu yace, "Baki ga kallo nike ba." Ta rike kugu tace, "Na gani." Yace, "Kunna min." Kanta tsaye tace, "Fitina nike son muyi don haka bazan kunna ba." Ya mike ya nufo inda take da nufin ya rarrasheta, tayi baya da sauro tana mai fashewa da kuka tace, "Hisham karka tab'ani. Hisham ka amsa tambayoyina." Ta lumfasa sannan tana mai sheshshekar kuka tace, "Hisham miye akan muryata da ya saka ka aureni? Wacece wannan matar da tazo? Wacece Bilkisu? Miye ya faru da Bilkisu? Da gaske ne ta hauka ce." Ganin yayi mata shiru ta fasa k'ara tace, "Hisham a wani bala'in ka sakani." Ya rungumeta yana bubbuga bayanta yace, "Ki nutsu. Ki nutsu." Ta kai mashi duka a ciki, babu shiri ya saketa ya dafe wajen, a fusace tace, "Kace min in nutsu. Da hankalina zan nutsu bayan abun da naji. Tana maganar ta haukatar da wata tana can ba'a san inda take ba, kuma nima abun da ya faru da ita yana jirana, shine kake cemin in kwantar da hankalina." Ya nufota, ta dakatar dashi tana mai k'ara jefa mashi tambayoyinta na d'azu. "Waye kai? Mi ya saka aureni? Wacece waccen matar wadda ka kira da Aysha? Mi nayi mata da zafi da har ta saka aljannu suke wasan kura da ni tsayin kwanaki biyar? Shin wacece Bilkisu? Mi ya faru da ita? Tana ina a yanzu?" Hisham yace, "Zan fad'a maki amma sai na dawo daga Paris." Hafsat ta fashe da dariyar rainin wayo tana mai tab'a hannuwa tace, "Ba ka isa ba ka bar gidan nan ba har sai ka amsa min tambayoyin da nayi maka." Ya wuceta ya shige ciki, ta bishi har dakinsa, gani tayi yana zuba kaya a akwati, ya gama ya fito harabar gidan ya saka a bayan motarsa, ta zuba mashi tana al'ajabi, bai kyauta mata ba, shima kansa yasan bai kyauta mata ba amma ta tambaya ya kawo mata uzuri akan sai ya dawo daga Paris, a yayinda hankalinta ne yake tangal-tangal a wannan maganar, mi yake nufi da ita? Bilkisu ta hauka ce, ya aureta duk da sanin hakan. Shin ba ya ji a ransa cewa bai kyauta ba idan wani abu ya sameta? Shin ba ya ji a ransa cewa bai kyauta ba? Ganin da gaske tafiyar zaiyi kuma bazai amsa mata ba, tace, "Dukkanin inda zakaje ina zaune zaka dawo ka sanar da ni komai, sannan kasan yadda zakayi dani domi ba zaka tafi ka barni a wannan gidan ba hakanan ta saka aljannu su sauya min KAMANNI." Ya raba ta gefenta ya shige motata, mamaki yake da yadda a yau da tasan gaskiya yake nuna halin ko in kula a kanta. Ta yarda da cewa bai tab'a sonta ba, muryarta ce yake bibiya, ji tayi hawaye sun zubo mata tana d'aura laifin komai a kanta, saida Jalila tayi mata gargadi akan yanke hukunci cikin fushi, saida Jalila tayi mata gargadi akan aikin gaggawa amma tayi burus da ita ta aureshi ba tareda bincike gashi tun ba'a je ko'ina ba ta fara nadama. Ta tsaya gaban motar tace, "Babu inda zaka tafi ka barni." Ya leko yace, "Mi kike jira, ki shiga?" Ta bude bangaren mai zaman hakanan ta zauna, yaja motar, tana kallonshi tana ji haushinsa yana kamata akan rufeta da yayi ya aureta bayan yasan abun da zai iya faruwa, tana zaman zamanta ya sakata a cikin bala'i. Gani tayi ya nufi hanyar gidansu, ta gane nufinta tayi saurin girgiza kai tace, "A'a. Ka kaini wajen Ummana." Yayi banza da ita ya kyale, saida yayi breakfast sannan ya wuce ya barta a wajen Momcy, tun daga wannan ranar bata k'ara razana ba ta dage da addu'a da karatun Alk'ur'ani, barci take hankalinta kwance ta daina gane-gane. Ranar ta kunna kallo barci ya kwasheta mugun mafarki da tayi ya sakata tashi a firgice, ta fara razana tana ihu, tana zabura, tun daga ranar ta koma kwana dakin Momcy, tana zuba idanu tana kirga kwanakin dawowarsa, sati daya ya wuce har aka shiga sati na biyu bai dawo ba, yana yawan kiranta saidai bata amsawa ta tabbata da muryarta ce take sakashi kiranta. ****** Tunda ta tashi take jin tashin zuciya, tayi wanka ta sauko kasa domin taci abinci, tana sauke idanunta akan shinkafa da miya aka yi, amai ya tafo mata, da gudu ta fad'a bandaki dake parlor ta durkushe tana kwarara amai. Fatima da Momcy suka biyo bayanta suna mata sannu, ta gama ta wanke bakinta, suka taimaka mata ta mike saboda jiri da takeji, ta zube akan kujera tana maida lumfashi. Momcy tace, "Mi ya sakaki amai haka?" Hafsat ta ware hannuwa alamar bata sani ba sai kuma tace, "Tana bude abincin naji kamshinsa amai ya tafo min." Momcy ta zuba mata idanu tana nazarinta. "Mi zan dafa maki?" Fatima ta tambaya. Tayi jim tana tunani sannan tace, "Taliya mai daudawa da ruwanta, ita kadai zan iya ci yanzu." Fatima ta wuce kitchen domin girka mata taliya da daddawa kamar yadda ta buk'ata. Momcy ta kama hannunta tana dubawa sai kuma ta tale idanunta kamar mai son ganin wani abu, gani tayi murmurshi tace, "Ki gama muje asibiti." Hafsat ta girgiza kai tace, "Momcy babu inda yake min ciwo, Amai ne kawai, shima abincin ne ya janyo min." Momcy bata bi ta kan maganarta ba, tace, "Ki gama muje." Fatima ta gama girka mata taliya ta juye a plate ta fito dashi, matsakaicin plate ne ta cikashi har yayi soro amma abun mamaki Hafsat ta tadashi, da mamaki suke kallonta, tace, "Fatima akwai saura?" Fatima ta gyad'a kai tace, "Ehhh akwai saura." Ta amshi plate ta koma ta juye mata sauran, saida ta cinye fiye da rabinsa sannan ta ture plate din, tana maida lumfashi, ta kora da ruwa. Momcy tace, "Fatima dauko mata dogon hijab muje." Hafsat tace, "Zan dauko da kaina." Momcy ta girgiza kai tace, A'a zata dauko maki." Har mota Fatima ta rakasu tace, "Momcy, anya ba ciki take dashi ba?" Momcy tace, "Nima abun da nike zargi kenan." Fatima ta daka tsallen murna tace, "Yanzu zan kira yaya in fesa mashi." Momcy tace, "A'a ki bari mu tabbatar." Fatima taso ta bisu Momcy ta hana, sakamakon awo da aka yi mata yana fitowa sukaga ciki ne dan sati hudu, Momcy tayi handalah tana mai godewa Allah. Hafsat ta ware idanu, ta rasa a yanayin da take a ciki, cikin ranta tace, "Sau daya ne fa. Har ciki ya shiga." Tunda suka tafo Fatima take kira, Momcy ta d'aga kiran tace, "Ciki ne." Fatima tayi tsallen murna tana mai tsinke kiran ta kira numbar Hisham, yana d'agawa tace, "Aunty Hafsat tana da ciki, d'azu tayi amai, sukaje asibiti." Daga daya bangaren yace, "Ciki. Alhamdulillah. Allah shine abun godiya. Dole na baki babbar kyauta saboda wannan albishir da kikayi min." A lokacin yana dubai, a take ya sayi ticket ya kamo hanyar Nigeria. Tunda suka dawo take ganin gata da kulawa, mugun cin abinci da ya sameta ne yake matuk'ar bata mamaki. Washegari tana zaune a balcony ta daga sama ta hango shigowar mota, Hisham ne ya fito, ta tab'e baki ta mik'e ta koma daki tayi kwanta abunta, idan ta tuna abun da ya faru da kuma rufeta da yayi ya aureta ya sakata da bala'i sannan ya nuna mata halin ko in kula sai taji ranta ya b'aci, haushinsa ya kamata. Mintina biyar a tsakani ya shigo ya zauna gefen gado tare da daura hannunsa akan cikin, ta buge mashu hannu ta mike zaune ta murtuke fuska tace, "Tun da ka gama gudun ka dawo sai ka sanar dani abun da ya faru." Haushi ya kamata tana da tabbaci akan maganar cikin ce ta dawo dashi tace, "Sai ka amsa min tambayoyin da nayi maka a waccen ranar tunda cikinka ya saka ka dawo." Ya kama hannunta yana murzawa a hankali yace, "Zan amsa maki idan mukaje gidanmu. Allah ya saukeki lafiya." Ta ware idanu tace, "Yaushe mukayi da kai zan koma waccen gida? Kaga Malam ka amsa min tambayoyina tukunna in yanke hukunci akan komawa gidanka ko kuma komawa wajen Ummana, ina da tabbaci akan baka da wata hujja da zaka bani ta saka in tsaya babu mai hankalin da zata zauna da kai bayan abun da taji, bayan yaudara da kayi ka rufe gaskiya." Yace, "Ki sameni a mota," Ya juya ya fita. Cikin ranta tace, "Dani kake magana kana barin gidan nan zan wuce wajen Umma." Fatima ta leko ta sanar da ita yana jiranta a mota, bata son su fahimci abun da yake faruwa wannan ne ya saka ta zura hijab ta fita. Fatima tace, "Har na gama maki jalof din shinkafa da daddawa in zubo maki ki wuce dashi." Hafsat ta girgiza kai tana mai zare hijab ta zauna akan kujera tace, "Ki zuba min in ci a nan." Cikin ranta tace, "In ci in ji dadin tada mashi hankali, inji dadin zazzaga mashi jaraba." Hisham ya gaji da jira ya shigo, ya ware idanu yana kallon tulun abincin da aka ajiye mata, yayi mamakin ganin ta cinyeshi har ta nemi kari, aka karo mata ta cinye. Momcy kamar tasan abun dake ranshi tace, "Kowace mai ciki da yadda yake zo mata, ita ci yake sakata, jalof da daddawa kawai take ci, zaka iya saka mata nama amma karka saka kifi amai yake sakata." Ya gyad'a kai. Har compound suka rakasu, Abdullahi ya rungume Babansa yace, "Abba. Ina zaka tafi da Aunty Hafsat? Ka barta ta zauna a nan." Ta shafa kanshi tace, "Zan dawo wata rana." Ya b'ata fuska kamar zaiyi kuka. Fatima ta kamashi, suna tsaye suna masu d'aga masu hannu har motar ta fita daga gidan, lokacin da suka isa gida ana kiran sallar zuhr yayi, yayi alwalla ya wuce Masjid, sai bayan sallar Asr sannan ya dawo ya shigo da kaya niki-niki ya wuce kitchen ta tab'e baki tace, "Gwara in ci in koshi, in dadin tutsiyeshi ya fad'a min gaskiya. Babu dole idan naji zan iya zama in zauna idan naji bazan iya ba in k'ara gaba." Ta d'aga murya tace, "Ka dafa min taliya da wake." Hisham ya zage ya girka mata jelof na taliya da wake mai daddawa sannan yayi mata farfesun kaza shima mai daddawa, da gangan tace saidai ya bata da hannunsa, yana bata ta cije mashi hannu, da gayya ta cinye abincin baki daya har farfesun ko kadan bata rage mashi, ya tattara kayan ya wuce da su kitchen, ya dama kunu yasha sannan ya fito ya zauna a kusa da ita yace, "Angel. Ina jinki." Hafsat ta tab'e baki tace, "Ina jinka dai. Muryata da ka aureni saboda ita ba zakaji. Inyi magana saidai idan ta zama dole." Yace, "Mi kike son sani?" Tace, "Waye kai? Mi yasa ka aureni? Miye akan muryata da ya saka ka aureni? Wacece wannan matar wacce ka kira da Aysha? Wacece Bilkisu? Mi ya samu Bilkisu? Shin tana a ina? Shin da gaske ta haukace?" Hisham ya lumfasa sannan yace, "Zan fara da sanar dake waye ni, zaki samo amsoshin tambayoyin a nan." Ta gyad'a kai tace, "Duk da bashi na tambaya amma ina sauraronka ka gama zagaye-zagayen da jan lokaci dolenka daga karshe ka sanar dani gaskiya akan tambayoyin da nayi maka." ******** "Sunana Hisham Mahmoud, mahaifina Alhaji Mahmoud mutum ne mai tarin dukiya, Allah yayi mashi rasuwa shekarun baya da suka wuce, a lokacin Fatima tana jinjira, ya barni da tarin dukiya, na tashi mutum mai son mutane da kuma barkwanci, idan ka zauna kusa dani dole kayi dariya, nayi degree na farko da na biyu a kasar waje, a can ne na hadu da Aysha, wacce ta zo gidan nan, ta nuna tana sona, tun bana kulata har na fara kulata, zuciya tana son mai kyautata mata, itama er Nigeria ce, iyayenta suna zaune a can amma danginsu a nan suke, a garin nan, soyayya ta shiga a tsakaninmu, Aysha macece ta kasance mace mai son jiki komai saidai en aiki suyi mata, yaran gidansu basu ji kuma na gani amma sai nike gani zata sauya a dalilina, a lokacin da na kammala degree na biyu a lokacin ne ta had'a degree na farko, a shekarar ne aka saka mamu ranar aure, wata biyar a tsakani aka d'aura aure, tun farkon aurenmu muka fara samun damuwa, ba ta girki saidai na restaurant ni kuma bana iya cin abincin saye, da aurena amma saidai in je gidanmu in ci abinci, duk da Momcy bata min magana amma ranta yana matuk'ar b'aci akan abun har bana son zuwa saboda ban san ganin b'acin ranta. A wannan lokacin ne Bilkisu ta shigo rayuwata, a ranar na kai ziyara wa abokina, muna hira a ofishinsa aka kawo mashi awara da yayi order a wajen wata food vendor a online, tunda ya bude awarar kamshinta ya dokeni na lumshe idanu ina ji yawuna yana tsinkewa. Kabir yace, "Ka ci." Na girgiza kai, Kabir yace, "Kaci, tana da tsafta." Kamar ba zan ci ba sai kuma na dauki cokali mai yatsu na soki guda daya sau ukku ina gwada sakawa a bakina ina fasawa, karshe na yanke shawarar inci, na jinjina kai ina jinjinawa dadin da tayi, Kabir yace, "Abun da nike fad'a maka kenan." Na janye takeaway daga gabansa tace, "Kayi order din wata, nima a kawo min takeaway biyu." Kabir ya ware idanu yace, "Kuma sai ka amshe min wannan." Nace, "Kayi order." A gabana Kabir ya kirata ya k'ara order na takeaway ukku, ya aika aka amso mashi, da abincin na wuce gida na ajiye a dakina, na ci da marece sannan na ci da dare, koda Momcy ta kirani nayi mata k'arya cewa Aysha tayi min girki ne shiyasa banje ba, duk da bata yarda ba saidai bata ja maganar ba. Washegari bayan nasha coffee na wuce office, na soma jin yunwa na kira Kabir. "Kabir wannan yarinyar miye abubuwan da take siyarwa?" Saida yayi dariya sannan yace, "Yayi maka dariya ne har haka." Nace, "Ina jinka?" Yace, "Okay zan tura maka numbarta da business flyer dinta." Nace, "Alright." Tare da tsinke kiran, koda na kira bata d'aga ba, na duba na ganta online na mata magana ta amsa, nayi order na Meatpie, Cincin, Awara and Dambun nama. Sunanta Bilkisu, gidansu yana a kofar keke, da kaina na je na kira na sanar da ita ina kofar gidan. Ta aiko k'aninta ya kawo min, na amsa na wuce, tun daga ranar na dauke zuwa gidan Momcy cin abinci, ina zuwa amma ba kullum ba, ban tab'a ganin Bilkisu a idanu ba, koda nuna min ita aka yi ban cewa gata, hotonta ne a dp dinta saidai abaya ne a jikinta ta rufe fuskarta da niqab. Maganar business takeyi kawai idan ka sako wata hirar tayi shiru, na shaku da ita har a zuciyata, kullum abincinta shine abincina, bata abinci amma ina biyanta tayi min. Kabir yace, "Mi kake jira? Ka aureta kawai, ina guje maka ka tsaya ganin kallon ruwa kwado yayi mata kafa, idan wani ya aureta, kai ne za ka yi nadama." Damuwar shine koda nayi mata wata hirar bata amsa nasha tura mata hotunana saidai ta biyoni da sticker shikenan. Kabir yace, "Kai kasan yadda zaka bullo mata." Nace, "Ba a nan gizo yake saka ba, ina gaya maka tun da nike zuwa gidansu bata tab'a fitowa da kanta ba saidai ta aiko k'annanta." Nayi jim yayinda dubara ta fad'o min, a tare dashi muka fito. Kai tsaye gidansu muka nufa a motata, dama na saka order, kamar kullum ina kira ta aiko k'aninta, na bashi dubu goma nace, "Tsaya." Na gutsiri cincin guda daya na b'ata fuska nace, "Kace mata gani ban tafi ba, nace ya aka yi bai yi dadi." Yaron bai jima da shiga ba ta fito tana sanye da dogon hijab har kasa, muryarta kawai na sani, a ranar ne na fara ganin fuskarta, doguwa ce, wankan tarwad'a, mai matsakaicin tsawo, tana da kyau daidai ita, idan aka kwatantata dake ba za'a kirata mai kyawu ba. Ta tsaya gefenmu, tace, "Kuma duk wadanda suka siya babu wanda yayi korafi amma ina ganin wani abun ne ya fad'a mashi." Kabir yace, "Ki rabu dashi, yayi dadi. Wajenki muka zo baki fito ba shiyasa. Ke ya kike haka, abokina yana sonki amma kina ja mashi aji, idan yazo baki fitowa, ace mutum yana tsoron d'an uwansa mutum." Bilkisu ta girgiza kai tace, "Ba haka bane." Kabir yace, "Torh, abokina yana matuk'ar sonki, ba ya da burin da ya wuce ya aureki, ya za'ayi?" Ta juyar da kanta gefe tace, "Allah ya zab'a mamu abun da yafi zama alheri." Ta amshi wayata ta saka min daya numbarta sannan ta juya ta koma ciki. Ban boye mata komai ba, na sanar da ita matsala da nike dashi a gida, tun daga wannan ranar bata k'ara amsar kudina saidai na fad'a mata abun da nike so ta girka min na aika a amso, abinci ukku a rana itace take girka min na aika a amsar min, soyayya mai karfi ta shiga a tsakaninsu. Bilkisu daga makarantar sekondire karatunta ya tsaya, tun da ta fahimci cewa Babanta ba ya halin da zai dauki nauyin karatunta ta hakura da karatun, abun da zasu ci a gidan wahala yake masu, wata ranar da yunwa suke wuni saida dare suci gari ko kanzo, bayan dogon tunani tayi wa kanta fad'a shine ta fara awara tana talla a dandalin sadarwa na yanar gizo, tana amfani da ribar ne tana taimakawa mahaifinta, a gefe guda tana siyan kayan kitchen tana ajiyewa, tayi classes da yawa na koyon girki, tana tuntub'ar na gaba da ita a harkar abinci, tana koyo daga garesu, cikin k'ank'anin lokaci ta fad'ad'a kasuwancinta ta fara dambun Nama, meatpie, cincin, donot, alkubus, waina da sauransu, har abincin biki tana amsa tayi a biyata, ta koyi dubulan, tana wa amare ana biyanta, k'anwarta Naja'atu tana gama sekondiri ta samu Miji, kayan Kitchen da Bilkisu take siya tana ajiyewa sune aka kai mata, tayi ciko wa carpenter da take barin kudin kayanta a wajenshi yayi kayan dakin Naja'atu, har abincin da aka yi wajen bikin Bilkisu ce ta bada rabin kudin, mahaifanta suka rink'a saka mata albarka. Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 12 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 A ranar da Aysha ta samu labari kwana tayi tana bala'i ta inda take shiga bata nan take fita ba, "Ni zaka tonawa asiri, ni zaka ce zaka yi wa kishiya, baka isa ba, baka isa ba, itama tayi kadan ta shigo gidan nan a matsayin matarka. Idan abinci ne zanyi maka. Idan akan abinci ne torh abun ya tsaya a siyen abincin mana, miye na auren mai siyarwa da abinci. Ka rasa wacce zakayi min kishiya da ita sai er talla..." na katseta, "Food vendor dai." Tace, "Oho kuma baka isa kayi min kishiya ba. Miye kake son ci in girka maka?" Dariya ta bani, na murmusa nace, "Daga baya kenan." Tana mita ta shiga kitchen ta had'a abinci ta jera akan dinning table, cokali daya nayi na maidoshi saboda yaji na da na ji, gishiri yayi yawa, mai yayi yawa, na b'ata fuska nace, "Wannan jagwalgwalon ne abinci, abu babu dadi. Idan baki iya ba kije wanda suka iya su koya maki." Tayi kasa da murya tace, "Ka bani numbarta inje ta koya min." Ta zaro waya tana jiran ya bata numbata ta kira tayi mata zagin k'are dangi, tayi mata gargadi akan mijinta. Yayi mata kallon amma kin rainawa kanki wayo yace, "Kije wani wajen ki koya." A fusace tace, "Haka nike girka abincina kuma dole ka ci a yadda na girki ko kuma a dauko er aiki." Ya fashe da dariya yace, "Nine kike tunanin zan ci abincin mai aiki, ki daina rainawa kanki yawo da kanki." Tace, "Ka bani numbar yarinyar muyi ciniki da ita tazo tana girka mamu ina biyanta, ai diyar talakawa ce." Yayi dariya sosai har da kyakyatawa tace,."Bilkisu ce zata zo maki a er aiki, idan kanki ya samu damuwa kije likita ya dubaki." Ya tsallaketa ya haye bene zuwa dakinsa, yana ji tana bala'i yayi mata banza, tun daga ranar fitinar rana daban, ta dare daban. "Baka isa kayi min kishiya ba, saidai a mutu, kai da k'ara aure saidai kaga wasu suna yi. Ban da butulci bayan duk kaunar da na nuna maka amma shine zakayi min kishiya. Ka rasa abun da zakayi min sakayya dashi sai kishiya." Ya d'aga kai ya kalleta yace, "A kaunar ne kika kasa min girki." Kanta tsaye tace, "Na ga kana zuwa gidanku ka ci, ni kuma ina siyowa daga restaurant." "Da aurena sai in rink'a zarya gidanmu cin abinci, ina tadawa mahaifiyata hankali." "Shine ni kuma yanzu zaka tada min hankalin." "Kece kika janyowa kanki." "Tun kafin ka aureni ka san ban san girki, ban iya ba." "Nima kuma tun kafin muyi aure kin san ban cin abinci siye?" Tayi dariya tana tab'a hannuwa tace, "Miye banbancin? Huh. Ina wahala da cikinka amma koda tausayina baka yi zaka min kishiya." Yace, "Ni ba kishiya zanyi maki ba...." ta katseshi a fusace tace, "Idan ba kishiya bace, wacece? Huh." Yace, "Abokiyar zama, idan kika rike girmanki zatayi maki biyayya, Bilkisu bata da damuwa." Tayi ihu tana tab'a hannuwa tace, "Daga kai har ita Bilkin kunyi kadan ku tona min asiri. Koni ko ku? Wanda ya fasa ya raina kanshi." Magabata sun shiga magana har an saka rana, biki saura sati biyu Aysha ta haifi Abdullahi, saboda bala'i taki komawa gida wanka, a satin bikin muka koma gidan da Umma take a zaune, a sashen da kuke a can ne Aysha ta zauna, yayinda aka kai Bilkisu a daya sashen. Tunda aka kawo Bilkisu, Aysha ta hanamu zaman lafiya, fitinar rana daban, ta dare daban, a kullum Bilkisu k'ara shiga raina take tana sona tana kyautata min, tana girmama mahaifiyata, tana daukar Fatima kamar k'anwarta, tana baiwa Aysha girmanta duk da rashin mutunci da takeyi mata dare da rana. Tare da Bilkisu muke shiga kitchen tana koya min girki, saida taga na kware, duk girkin da nike maki ita ce ta koya min. Bilkisu ta samu ciki wanda yake wahalar da ita, a lokacin ne kuma ta fara gane-gane tana mafarkai kamar yadda kikeyi, ta rame ta fita hayyacinta, cikin yana da wata biyar aka nemeta aka rasa, munyi mata neman duniya muka rasa. Ranar na shiga sashen Aysha na samu tana hira da k'awarta suna tattaunawa akan yadda suka haukata Bilkisu tabi duniya. Saidai ganina tayi a dakin, ta zaro idanu fahimtar naji komai. Ji nike kamar in rufeta da duka, na dauki biro da takarda na rubuta mata saki biyu, na mik'a mata ina zubar da hawaye nace, "Aysha kin cuceni, kije na sakeki saki biyu, kin cuceni, kin cuci Bilkisu. Allah yana gani kuma shine zaiyi mamu sakaya." A lokacin ta yaye Abdullahi yana wajen Momcy, tun daga wannan lokacin nike neman Bilkisu amma babu ita babu alamarta, Bilkisu ta kula da ni, ta kaunaceni, ta girmama ni, ta kwantar min da hankali, ta bani shawarwari a rayuwa wadanda naga amfaninsu. Shine ranar naji muryarki kina magana, na dauka Bilkisu ce har na bude maki Niqab kika mareni, muryarki tana KAMANNI da muryar Bilkisu, a dukkanin lokacin da kikayi magana kina tuna min da ita shiyasa nike yawan janki hira, nike sakawa kina karanta min jarida. ****** Hafsat ta fara girgiza kai tana hawaye tana mai cewa, "Hisham ka cuceni, ka tarwatsa min rayuwa, ka sakani a cikin bala'in da bai shafeni ba, kasan abun da yake damunka amma ka aureni, ka yaudareni ka saka na yarda da cewa kana sona, ashe baka tab'a sona ba, ashe muryata ce ta janyoka." Hisham ya kama hannunta ta fizge tana mai ja da baya, yace, "Amma Hafsat saida nayi k'ok'arin in sanar dake amma kika ki saureni kika ce baki da buk'atar sani." Hafsat ta fasa ihu tace, "Kasan girman duk da nace haka sai ka sanar dani, kai da kanka ka tabbatar da cewa da nasan wannan bala'in ne tun kafin ka fad'a min zan gudu da kafafuna, babu mamaki ka kasa auruwa, wacece zata aurarwa kanta tikitin hauka. Kana sane da bala'in dake zagaye da kai amma ka yaudareni ka aureni. Ashe duk akan muryata ne, ka yaudareni ashe muryarta kake bi, shiyasa kake sakani karanta maka jarida da littattafan hausa, shiyasa baka tab'a yaba kwalliyata ba saboda ba kaunata kake ba, muryata ce kake da buk'ata. Don haka bazan iya ba, ka sauwake min, ka sakeni in koma gidanmu. Na gama aurenka. Na fasa auren." Ya girgiza kai yana kama hannunta, ta fizge ta fasa ihu tace, "Baka isa ba, dole ka rabu dani." Hisham yayi baya da sauri tareda toshe kunnuwansa saboda karfin ihu da tayi, tana kuka tana fad'in, "Hisham. Ka sakeni. Sai ka sakeni." Hisham yayi mata tsawa yace, "Angel ki dawo hayyacinki." Ta ware idanu tace, "Ina a hayyacina shiyasa nace ka rabu dani, wacce take a cikin hayyacinta ce zata nemi hanyar rabuwa da kai domin ta kub'uta da hankalinta. Ko ka sakeni, ko baka sakeni ba, na fasa auren gidanmu zanje." Ta juya ta haye saman bene ta zuba kaya a akwati ta janyoshi ta fito tareda saukowa parlour, yasha gabanta yace, "Angel babu abun da zakije." Ta rab'a ta gefensa tace, "Bani zama da kai in hauka ce." Yace, "Ba zan sakeki ba." Tace, "Idan ta samu labarin bani gidan zata shafa min lafiya, kai kuma idan ka gaji da jiran gawon shanu sai ka sakeni. Miye na turjewa akan ba zaka sakeni ba, bayan da ni da kai mun san cewa ba sona kake ba, muryata ta janyo ka, ko muhimmanci muryar a gareka yafi hankalina." Ya daka mata tsawa yace, "Cikina kike dashi, ba zaki bar gidan nan ba har sai kin haifar min cikina, tunda ba dashi kika zo ba, bayan nan idan kika ce min in sakeki zan sakeki, amma yadda kikazo ke daya haka zaki koma ke daya, ba zaki wuce min da gudan jini ba." Ta fashe da kuka tace, "Dukkanin tada jijiyoyin wuya da kakati ashe akan cikin da nike dashi ne, torh ba zan zauna ba." Ya daka mata tsawa a karo na biyu yace, "Idan kin isa ki fita ki gani." Ta durkushe tareda fashewa da kuka, ya tsallaketa ya wuce sama, tayi kuka har ta godewa Allah, tayi kira numbar Umma ta fashe da kuka ta kasa magana, tana ta kuka ta tayarwa Umma da hankali. Hankali a tashe Umma take tambayarta dalilin kukanta. Tana sheshshekar kuka tace, "Umma na boni. Hisham ya cuceni. Ashe bai tab'a sona ba, dukkanin abun da yake ashe akan muryata ne, saboda ina da irin muryar matarshi ta biyu, wacce matarshi ta farko ta haukata ta shiga uwa duniya tana hauka, babu wanda yasan inda take. Dukkanin abubuwan da na fad'a maki a ranar da na zo da gaske sun faru, ba mafarki bane, matarshi ta farko ta saka aljannu suke wasan kura da ni, har gida tazo tayi min gargadi idan ban rabu dashi ba nima zata haukani in gudu a rasa inda nike." Umma ta dafe kirji idanunta a waje na jin abun da yake shirin faruwa da gudan jininta, tace, "Na boni. Hafsat ki tattara kayanki ki dawo gida dolenshi ya sakeki, dolenshi ya rabu dake." Hafsat tana mai cigaba da kuka tace, "Umma yace ban isa in bar gidan ba, ciki gareni, yace sai na haifa mashi cikinsa sannan in bar gidan." Umma ta ware idanu tace, "Yana nufin ki zauna kema ta haukataki kamar yadda ta haukata waccen, tunda ance mashi ban kaunarki, ki tafo karki zauna ko kuma inzo da kaina in wuce dake." Hafsat tana mai cigaba da kuka tace, "Umma yace kada in sake in fita, gwara mu bishi a hankali, idan muka ce za mu bi ta tsiya mune a kasa. Na riga na saka kaina a tsaka mai wuya, fitata a cikin sauki ba mai yiyuwa bane ba." Umma ta fashe da kuka, yau ne rana ta farko Hafsat taji Umma tana kuka, tace, "Umma ki daina kuka." Daga daya bangaren Umma tana mai cigaba da kukan tace, "Hafsat kiyi hakuri ki yafe min, son kudina ya janyo na sakaki a cikin hatsari, kudi sun rufe min idanu babu bincike na aura mashi ke. Hafsat nice na cuceki tun farko." Hafsat ta ajiye wayar tareda fashewa da kuka, tun daga ranar bai k'ara ganin fara'arta ba, cikin saka mata yunwa yake, ci kamar tsohuwar gara, zata tusashi gaba ya girka mata abinci, ta saka dole ya ciyar da ita tana ci tana bashi wahala tana cizon hannunsa, yadda cikin yake wahalar da ita itama haka take wahalar dashi, ta hanashi zaman lafiya. Ta dage da karatun Alk'ur'ani da azkhar, bata sakaci dasu, hankalinta ya kwanta da daina mafarkai da gane-gane. Cikin haka ne haushinsa ya rinjayeta har tayi sakaci da addu'a, asirin yayi tasiri a kanta, abu kamar wasa ta fara mafarakai masu ban tsoro, ita kadai sai ta rink'a zabura, tana rufe idanunta zata soma ganinsu, babu dama ta kwanta bacci, dare yana kawo jiki zata fara razana tana firgita, fatalwowi suna farmakarta. Kira ta gani da bakuwar number, tana amsawa Aysha tace, "Shine kika saki jiki har kikayi ciki, kin janyo wa kanki, ko ya sakeki idan baki zubda wannan cikin ba bazan rabu dake." Hafsat ta ajiye wayar tareda fashewa da kuka, ta kira Umma ta sanar da ita komai, Umma tayi jim sannan tace, "Hafsat kece baki damu da addu'a ba, ki rink'a karatun Alk'ur'ani da azkhar, ki rage kallo musamman da dare, ki rink'a alwalla idan zaki kwanta bacci." Hafsat ta gyad'a kai tace, "InshaAllah." Tana rike da maganar amma dare yana kawo jiki ta manta ta kwanta ba tayi ba, ta farka tare da fasa ihu, Hisham ya shigo da saurinsa ya kamata yana tambayarta abun da ya faru, baki daya jikinta rawa yake ta kasa magana, tun daga wannan lokacin ne ta koma kwana a dakinsa, zata wuni tana tunawa da alwallar kwanciya bacci amma dare yana yi mantuwa zata zo masu baki daya, su kwanta basu yi ba, mafarkai take masu ban tsoro, fatalwowi suna kawo mata farmaki, ta rame, ta fita daga hayyacinta, ta koma zautacciyar karfi da yaji, Hisham saidai ya daina fita kullum yana zaune da ita a gida. Ranar ya shiga bandaki yana fitowa ya nemeta ya rasa, tashin hankali k'aramar magana ta zama babba, anyi neman duniya babu Hafsat babu dalilinta, Umma babu abun da take sai kuka tana nadamar abubuwan da tayi na tilasta mata auren mai kudi, ga dukiyar amma babu kwanciyar hankali, kwadayinta ya saka ta jefa gudan jininta a bala'i da tashin hankali. Hisham yana kaiwa da komowa yana cikin tashin hankali, Momcy ta tada sallah tana mai sanar da Allah halin da suke ciki, Fatima tana daga gefe tana kuka, Jalila tunda taji labari take kuka har zuwa wannan lokaci, wasa-wasa har washegari babu Hafsat babu labarinta. Suna zaune jigum-jigum, kira ya shigo wayar Jalila, tana dubawa taga 'Jameel Borno' tana ganin hakan ta gane cikin wadanda suka tab'a mata ciniki ne online, kamar ba zata d'aga ba sai tayi picking tareda komawa gefe, daga daya bangaren yace, "Jalila. An wuni lafiya?" Jalila tace, "Lafiya lau." Ji tayi yace, "Ina k'awarki wacce nike ganin kina yawan d'aura status da hotunanku tare, Angel." Da sauri tace, "Ehhh. Ina jinka." Yace, "Yanzu naga wata mai KAMANNI da ita saidai kamar bata a cikin hayyacinta." Jalila ta fashe da kuka tace, "Itace, tun jiya ta b'ata muka nemeta muka rasa, na rokeka da girman Allah ka saka a kamata a kulle a daki kafin muzo, kada ta gudu mu rasata, wahala take sha sosai, ciki ne da ita. Mahaifiyarta damu suna cikin tashin hankali." Daga daya bangaren Jameel yace, "Karki damu za'a kaita gidan mai unguwa, sai ku kamo hanya." Da gudu ta koma inda suke ta sanar dasu kiran da ta samu. "Cikin wanda suke ciniki dake Borno yaga Hafsat, shine ya kirani, ya ganeta saboda ina yawan daura hotunanmu a tare." Da mamaki Umma tace, "Borno!." Hisham yace, "Borno kuma!." Momcy tace, "Ta ya taje Borno!." Suna mamaki la'akari da nisan dake a tsakanin Katsina da Borno." Ta nuna masu hotonta da ya tura mata wanda suka dauka a lokacin. Hisham ya amshi wayar tabbas kayan da take sanye dasu ne. Umma tace, "Alhamdulillahi." A private Jet dinsa suka wuce Borno, Hisham, Umma, Momcy, Jalila da Fatima, aka saukesu a gidan mai unguwa, a lokacin an bata rubutu tasha har ta fara bacci, suka ci suka sha, Hisham yayi godiya sosai wa Jameel tareda mashi sha tara ta arziki, da marece suka juyo suka dawo Katsina, tunda suka shigo gidan take k'ok'arin gudu. Umma ta fashe da kuka tana nadamar tursasata da tayi ta nemo mai kudi duk da Umar ba mijin aure bane amma da ta dage mata da addu'a suna zaune Allah zai kawo dalilin rabuwarsu, ya kawo mata miji na gari. "Hafsat na cuceki, son kudina ya janyo maki." Hisham tausayinsu ya kamashi, yayi nadamar aurenta da yayi, ya jefata a cikin damuwa. "Hafsat nayi nadamar kawoki da nayi a cikin rayuwata, na jefaki a cikin tashin hankali, dukkanin abubuwan dake faruwa dake nine sanadi." Suka kulleta a daki ta fasa glass dake a kofar balcony tana k'ok'arin haurawa, har ta jiwa kanta ciwo, a ranar ya kira aka mayar da window na dakin na rodi, suka kulleta. A koda yaushe yana tare da ita, da kanshi yake mata girki yana bata, dole Umma ta dawo gidan da zama, suna kula da ita a tare, a kowace rana abun k'ara ta'azzara yake. Umma ta fashe da kuka tana mai cewa, "Hafsat zan nema maki magani, ke daya gareni bazan bari a illata min ke ba." Dukkanin inda Umma taji labarin mai magani sai taje, lungu da sako, garuruwa har ta tsallaka Niger da sauran kasashen kusa, cikin yana k'ara girma, abun yana k'ara ta'azzara, ta zama mahaukaciya tuburan, cikin wahalar da ita yake sosai, mintina kadan zata ce yunwa, idan ba'a bata ba ta fara kuka, tana ci aka dade zata k'ara cewa yunwa, an sauya mata KAMANNI tayi kib'a kamar ba ita ba. Umma ta rame, kullum itace akan hanyar nemar mata magani, Alhamdulillah ana samun cigaba, cikin yana da wata tara, sun dage mata da saukar Alk'ur'ani da addu'a, ciyar da mutane da sadaka. Umma ta dage da tsayuwar dare, karatun Alk'ur'ani mai girma. Karfe sha biyu na dare ta fara ihu tana kururuwa, Hisham yana tsaye baki daya hankalinsa a tashe yake, da taimakon Umma ta santalo yaronta Namiji mai KAMANNI da ita sak kamar an tsaga k'ara an karya, Umma ta janyo rubutu ta bata, tana sha ta fara atishawa, bacci yayi awon gaba da ita, tana farkawa ta fara bin dakin da kallo fuskarta dauke da mamaki, tace, "Umma a ina nike? Mi ya faru dani?" Umma ta fashe da kuka ta rungumeta, tana kuka tana fad'in, "Alhamdulillah. Allah shine abun godiya." Hafsat tana kallonta da mamaki tace, "Umma mi ya sakaki kuka?" Umma tana mai cigaba da kuka tace, "Hafsat haihuwa kikayi." Hafsat tace, "Haihuwa kuma? Yaushe cikin ya girma har na haifeshi ban sani ba?" Umma tace, "Haukata min dake tayi, har guduwa kikayi kikaje Borno, a halin hauka da wahala kika raini cikin kika haihu. Na nemar maki magani a wajeje daban-daban, sai a wannan lokaci Allah yasa muka dace. Hafsat ki yafe min, nice na janyo maki." Umma ta kwashe dukkanin abun da ya faru ta sanar da ita. Hafsat ta goge hawayen da zubo mata na tausayin kanta, tace, "Ina yaron da na haifa?" Umma tace, "Yana a wajen Hisham." Hisham ya shigo yana dauke da yaron, Umma ta mike ta fita, Hisham ya zauna a gefen gadon tareda mik'a mata shi, ta amsa tana kallon yaron wanda babu abun da ya baro a KAMMANI da ita, yayi shiru yana kallonta, tayi kamar bata san ya wanzu a wajen ba, ya gaji da zama ya mike ya fita. Suna zaune a parlour, Fatima ta sauko kamar wacce aka jefo tace, "Aysha ta hauka ce. Ta gudu. Har yanzu babu wanda yasan inda take." Momcy tace, "Alhaki kyuwkuyo." Umma tace, "Allah ba azzalumin bawansa bane. Mugun abu jakada, idan yaje zai dawo ya sanar da kai zuwansa." Hafsat dake fitowa daga kitchen akan kunnanta saidai bata ce komai ba, ta sauke ajiyar zuciya jin babu sauran barazana, ta wuce sama. Baby yaci suna Muhammad, Hisham ya kashe naira, raguna biyar ya yanka mata tareda shanu guda biyu, bayan kaji da zabbi da aka yanka, ya kashe naira babu k'arya, a ranar suna ne Hafsat taga Iyayen Bilkisu saida suka bata tausayi, har zuwa wannan lokaci magana bata hadata da Hisham ba, idan yazo karbar yaro zata bashi, idan ya maido mata ta amsa. Momcy tana lura dasu saidai bata ce dasu komai ba, Hafsat bata tada maganar ba har tayi arba'in, Hisham ya tarasu baki daya, Umma, Momcy, Hafsat da Babansu Jalila. Hisham ya lumfasa sannan yace, "Umma. Baba. Ina mai baku hakuri akan abun da ya faru. Dukkanin abun da ya faru da Hafsat nine na janyo mata. Angel, kiyi hakuri ki yafe min." Ya lumfasa sannan yace, "Akan aurena da Hafsat, zanyi farin ciki idan tace zata zauna dani, amma idan taga ba zata iya ba, zan sawwake mata amma zata bar Muhammad a hannun Momcy." Hafsat ta dubeshi da sauri jin maganarsa ta karshe, duk wahalar da tasha da cikin amma yana k'ok'arin rabata dashi, tace, "Hisham mi yasa kake da sonka kanka ne? Nayi wahala da cikinsa amma kana min barazana dashi domin abun da fad'a ya fi kama da barazana wato idan ina son zama tareda yarona saidai in zauna da kai, wannan ba adalci bane ba." Hisham yace, "Kiyi hakuri ina son gudan jinina..." ta katseshi tace, "Sai aka ce ni bani son kasancewa dashi, miye ka daukeni muguwar uwa ko kuma sakarar uwa." Yace, "Ba haka nike nufi." Ta daka mashi tsawa tace, "Torh miye kake nufi? Kayi min bayani. Huh." Baba yace, "Hafsat. Hukunci yana a hannunki, dukkanin hukunci da kike yanke muna tare dake." Umma tace, "Hafsat dukkanin hukunci da kike yanke ina tare dake, na janye waccen maganar, ko waye kika kawo indai har nayi bincike na samu ba ya da damuwa zan aura maki." Hafsat tayi shiru ba tareda tace komai ba. Idanun kowa suna a kanta suna jiran jin hukuncin da zata yanke. SHIN WANI HUKUNCI NE ZATA YANKE? ZATA HAKURA DA RUFETA DA YAYI KO KUMA ZATA NEMI SAKI? SHIN IDAN TA NEMI SAKI ZAI IYA RABUWA DA ITA? SHIN ZAI BARTA TA TAFI DA YARON KO KUMA ZAI AMSHI YARONSA KAMAR YADDA YA FAD'A? SHIN INA LABARIN BILKISU? MUJE ZUWA Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 13 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 Momcy ta kawo karshen shirun da ya wanzu a falon, ta hade hannuwa a waje guda alamar roko sannan tace, "Hafsat na rokeki da girman Allah kiyi hakuri karki tsinke auren nan, ki tsaya ki kula da yaronki, Ina mai baku hakuri a madadinshi da ni kaina." Hafsat tayi jim sannan tace, "To shikenan." Suka zuba mata idanu suna neman karin bayani, Hisham ya kasa hakuri yace, "Hafsat ina buk'atar karin bayani. Bamu fahimceki ba." Hafsat ta mike tare da mashi wani mugun kallo tace, "Idan na yanke shawarar rabuwa da kai, mika hannu zanyi ka bani takardata tunda ba tsoronka ni ke ji ba. Baba, Umma, Momcy, Allah ya kiyaye hanya. Momcy don Allah ku ara min Abdullahi yayi min hutu a nan." Momcy tace, "Fatima zata kawoshi." Hafsat tayi godiya ta mike ta wuce saman. Momcy tana komawa gida, ta turo Fatima ta kawo Abdullahi. Hafsat ta shiga kitchen ta had'a masu abincin rana, ta soya waina, ta girka miya, ta jera komai a dinning table, ta zubawa Abdullahi sannan ta zubawa kanta, suna ci ya sauko yaja kujera ya zauna yana kallonta yace, "Angel ina nawa?" Ba tareda ta kalleshi ba tace, "Ka tab'a cin abun da na girka ne, da kanka kake girkawa, gaka ga kitchen." Ta k'arasa magana tana nuna mashi kofar kitchen, Hisham ya bude warmer yace, "Duk da ba dani kika girka ba, akwai saura sai inci." Abdullahi ya washe baki yace, "Abba muci tare." Hisham yace, "Kaci naka, nima zan zubawa kaina." Yana ci yana lumshe idanu saboda dadi, dadi ya wuce shi, yana nadamar girkinta da bai ci ba, suka gama ta tattara kayan da suka b'ata ta wuce dasu kitchen ta wanke, zama suke babu yabo babu fallasa, bata mashi magana, bata fara'a idan yana kusa, ya bata hakuri har ya gaji amma a banza, bata bashi abincinta, saidai ya zuba da kanshi yaci, kib'ar da tayi har tsoro take bata, tayi muni, har bata son kallon kanta a madubi, ta fara ragewa, da gangan take barin kanta da yunwa sannan tana motsa jiki, ta dawo kamar yadda take kafin aurensu, kullum cikin kwalliya take, yayi ta binta da kallo, tana lura dashi. Ranar ya fito ya sameta ta cakare ta kure kyawu, kayan sun matseta komai ya bayyana, ya kasa hakuri yayi sama da ita ya ya wuce master room ya rufa a kanta yana murzata tun tana tureshi har tayi lamo ta bada kai. Daga ranar suka daidaita kansu, soyayya suke babu kama hannun yaro, a kullum suna manne da juna, Abdullahi ya dawo da zama a wajen Hafsat, ta had'ashi da Muhammad ta rike, bata nuna banbanci a tsakaninsu. ******* A tare suka fito a jere, yana mata magana tana murmushi ta mik'a mashi briefcase ya amsa tare da sumbatar kumatunta, tana tsaye tana d'aga mashi hannu saida taga wucewar motarshi sannan ta juya ta koma ciki. Karfe hudu da rabi ya danno motarsa a cikin gidan, ta fito da murnarta domin ta tarbarshi, tayi turus hango wata mata kamar mahaukaciya ta shigo gidan, tana goye da yaro, tayi baya da sauri, Hisham ya tarota tareda juyawa domin ganin abun da ya tsoratar da ita, ya zaro idanu yana fad'in, "Bilkisu." Ya saketa saidai jinta tayi a kasa, ta buge kugu, Bilkisu ta sulale a kasa, ya dagota yana kiran sunanta. "Bilkisu. Nanerh. Ki farka mai gadon zinare." Hafsat ta mike tsaye yayinda gabanta ya yanke ya fad'i. Hisham ya dauki Bilkisu ya saka a gidan baya sannan ya dauki yaron ya kwantar a bangaren mai zaman hakanan, kai tsaye ya wuce asibiti. Hafsat ta kira Momcy ta sanar da ita bayyanar Bilkisu sannan ta shirya yaran tabi bayanshi asibiti, suna a can dangin Bilkisu suka zo suna ta kuka. Da Daddare Umma tazo, Bilkisu tana jin jiki, Hisham ne yake jinyarta, a kullum yana manne da ita, a kullum Hafsat ce take girki ta kai masu, na safe, na rana, da na dare, kullum tana akan hanyar asibitin, ranar suna zaune, wasu mata biyu suka shigo, Ummin Bilkisu tace, "Sadiya ce, makociyarmu, wannan kuma kishiyarta ce." Da sauri Bilkisu tace, "Kishiya." Yayinda jikinta ya fara rawa, ta soma girgiza, jikinta ya rikice, dakyar likitoci suka samu nasarar ceto ranta, likita ya gargadesu akan maganar kishiya a gabanta, tana da trauma na kishiyar idan suka cigaba zasu iya rasata. A lokacin da Hafsat taji labari saida gabanta ya yanke ya fad'i, haka take wuni jikinta sukuku, ta rasa dalili. ***** Hafsat tana zaune a gefen gado tana rike da Muhammad, Hisham ya shigo ya zauna a kusa da ita yace, "Gobe za'a sallameta." Tace, "Allah ya kaimu." Saida ya lumfasa sannan yace, "Hafsat ina mai baki hakuri akan abun da zan sanar dake, Hafsat dole in rabu dake, matata tana da trauma na Kishiya, kalmar kishiya kawai idan taji tana yi kamar zata mutu ballantana kuma ace tana da ita. Dukkanin abun da ya faru da Bilkisu nine na janyo mata, nine sanadi." Hafsat ta tsareshi da idanu tace, "Ni kuma dukkanin abun da ya faru dani kwadayi ne ya janyo min, ni ce na janyo wa kaina." Da sauri yace, "Ba haka nike nufi ba." Ta katseshi, "Torh mi kake nufi Hisham?" Yayi shiru, da karfi tace, "Tambayarka nike." Muhammad ya fara kuka ta mike tana rarrashinsa. Ba tareda ya had'a idanu da ita ba yace, "Hafsat kiyi hakuri, na sakeki saki daya. Dukkanin abubuwan da na baki har da gidan da Umma take ciki, na bar maki. Ina maki fatan alheri a rayuwa." Ta durkushe a kasa tareda fashewa da kuka, ta rasa abun da yake mata dadi, tayi hakurin zama dashi despite abun da yayi mata amma a yau shine yayi mata butulci ta hanyar sakinta. Tana sheshshekar kuka tace, "Hisham ka cuce ni. Ka tarwatsa min rayuwa. Kudinka ba na so, gidanka bana so, bana son komai da ya fito daga gareka. Yadda na shigo gidanka ni kadai, hakanan zan fita ni kadai, kayan da suke a jikina zan ajiye maka a wancen gidan." Ta juya ya kamota tareda amsar Muhammad dake hannunta, da mamaki take kallonshi, ta fasa ihu tace, "Baka isa ba, baka isa ka rabani dashi ba." Hisham yace, "Angel kiyi hakuri amma bazan raba kan y'ay'ana ba." Hannu daya ya saka ya fitar da ita waje, ta share hawayen dake a fuskarta tana mai kiran sunansa, "Hisham." Ya juyo tace, "Ka sani Allah ba ya zalunci, na yarda na zauna da kai bayan yaudarata da kayi amma sai ka zab'i kayi min butulci, dukkanin abubuwan da kakeyi min na tabbatar domin kana ganin bani da gata ne. Ina mai tuna maka Allah ba ya zalunci, alhakina bazai barka ba, akwai ranar kin dillanci wacce itace ranar da ka gurfana a gabana saidai bakin alkalami ya riga ya bushe, ka tab'a rawarka da tsalle, koda maza na duniya sun k'are, koda kaine autan maza bazan tab'a komawa gidanka ba, a dukkanin lokacin da alhakina ya juyo kanka ka tuna da wannan maganar, ka tuna da cewa nace koda kaine kadai namiji da ya rage a duniya bazan koma gidanka ba, ka tuna da cewa da nayi koda kaine autan maza bazan koma gidanka domin ina da zuciya, domin nasan mutuncin kaina." Ya juyo ya kalleta sai kuma ya maida kofa ya rufe, tayi ihu da hargowa amma a banza, ATM dinta wanda take dashi tun kafin aurenta, kudadenta da take ajiyewa a lokacin da kuma wadanda ta samu na haihuwar da tayi ne kawai a ciki, shi kadai ta dauka ta dauki wayarta ta fita, ta hau mota ta wuce gidan Umma, Umma tana zaune a parlour, Hafsat ta shiga ta durkushe tareda fashewa da kuka tace, "Umma, Hisham yayi mamu butulci. Umma, Hisham ya yaudaremu, duk da na zab'i na zauna dashi a wancen lokacin amma a yau ya zab'i da ya sakeni sannan ya amshi Muhammad." Umma ta dafe kirji idanunta a waje tace, "Mi ya faru?" Hafsat tana sheshshekar kuka tace, "Saboda matarshi tana tsoron kishiya, sunan kawai yana sakawa ta kusa mutuwa." Umma ta fusata ranta ya b'aci tace, "Ki tashi muje gidansu, bai isa ba." Hafsat ta girgiza kai tace, "Umma ki rabu dashi, yana ganin bani da gata ne shiyasa yayi min haka." A fusace Umma tace, "Waye yace mashi baki da gata? Ki mik'o min waya in kira Aliyu muga da uwar da yake takama da har zakisha wahalar nakuda sannan ya amshe yaron bayan mune aka cuta, muka hakura amma shine ya zab'i yayi mamu sakayya da butulci." Hafsat tace, "Umma ki rabu dashi, akwai lokaci, a duk lokacin da na waiwayi yarona ba zaiji da dadi ba, dukkanin fitinar da za'ayi sai ya bani shi tunda ba tare dashi nayi nakuda ba." Umma tace, "Ki zauna kici abinci." Hafsat ta ware idanu tace, "Abinci? Ai dukkanin wani abu na Hisham bana so, dukkanin abun da ya mallaka min na mayar mashi da abunsa, zan tashi in nema, zan jajirce na nemi gumina, in gina kaina, sai na nuna mashi na fi karfin wulakanci." Ta kira numbar Jalila, "Jalila. Hisham ya sakeni, ya amshe Muhammad. Ki zo gida yanzu, ki tafo min da kaya guda daya sannan itama Umma ki tafo mata da kaya guda daya, har hijab da takalma." Sai kuma ta tsinke kiran. Mintina ashirin a tsakani sukaji k'arar mota, Hafsat ta fita da sauri, ba motar Hisham bace, aka yi parking, Jalila ta fito daga bangaren mai zaman hakanan yayinda Aliyu ya fito daga mazaunin direba, Hafsat ta juya ta koma ciki ba tareda da tace dashi komai ba. Aliyu ya gaida Umma sannan yace, "Jalila ta fad'a min abun da ya faru, bai kamata a barshi haka ba." Ranshi yayi matuk'ar b'aci. Hafsat tace, "Yaa Aliyu ku barshi da yaron, dukkanin ranar da na tashi amsarshi sai yayi nadamar sanina da yayi. Na rokeku da girman Allah kada wanda ya sake min wannan maganar. Umma ki tashi ki sauya kaya muje." Hafsat ta sauko tana sanye da kayan da Jalila ta kawo mata, babu jimawa Umma ta sauko, Hafsat ta tara masu aikin gidan tayi masu bankwana, suna ta jimami. Umma ta zauna a baya, Jalila ta zauna a daya bangaren, Hafsat ta bud'e bangaren mai zaman hakanan ta shiga, tace, "Yaa Aliyu ka biya dani in sayi waya, sannan ina ne zan samu gidan haya." Da mamaki Aliyu yace, "Gidan haya kuma? Angel idan har ina raye kin fi karfin zama a gidan haya." Tayi murmurshi mai ciwo sannan tace, "Saidai kuma wannan Hafsat ta daina dogara da wani, zan nema a wajen Allah, zan jajirce in gina kaina da kaina." Da kakkausar murya yace, "A gidana zaku zauna, magana ta k'are." Zatayi magana yayi mata kallon cikin idanu babu shiri ta juyar da kanta yayinda bugun zuciyarta ya k'aru, yayi dariya yace, "Kin fasa maganar ne?" Tayi mashi banza. A bakin wani plaza yayi parking, Hafsat da Aliyu suka fito suka shiga ciki, k'aramar waya ta dauka keypad, tareda waya Samsung, aka yi mata bill dubu dari biyu, Aliyu ya mik'a katinsa. Da kakkausar murya tace, "Ni na sayi waya, da kaina zan biyaka kudinka, idan ka zare a katinsa saidai in ajiye maka abunka inje wani wajen in siya." Aliyu yayi shegen murmurshi yace, "Tare muke, nine zan sayi wayar, ka had'a mata da iPhone zan biya." A fusace ta juya ta koma mota, ya mik'a mata leather ya tada mota, alert ya gani ta saka mashi kudinsa ya ware idanu yana kallonta, tace, "Saidai kuyi hakuri dani." Ya wuce dasu gidanshi dake a sabuwar kasuwa, da kanshi ya fito ya bude get ya shiga da motar, gidan ba zai fi wanda suka fara komawa a lokacin da suka tashi ba, dakuna gida biyu room and parlor, sai kuma fallen daya guda biyu, kitchen, store, bandaki tareda k'aramin tsakar gida wanda zai dauki motoci biyu, sai parlour dake a tsakanin dakunan. Yace, "Ku zauna a nan kafin in gyara gidana dake a dutsen safe sai koma a can." Ji yayi tace, "Jalila ku tayani mu duba gidan idan yayi." Jalila ta dubeta da mamaki, Hafsat tace, "Eh ku tayani dubawa tunda kudin haya zan biya." Aliyu ya murtuke fuska yace, "Hafsat lokacin da nace maki ina sonka da gaske ina sonki, na saka kinyi k'arya ne saboda bani da wata mafitar bana fatan auren mahaifiyata ya mutu a dalilin nawa auren, na sa ni ina da kasona na laifi akan abun da Hisham amma ina ganin ban cancanci wannan hukuncin ba, ki duba na mayar maki da kudin da kika saka min." Muryarta a sanyaye tace, "Inyi maka sadaka dasu?" Ya juyo yace, "Idan kikayi sadaka Allah zai baki lada, kudinki ne ba kudina ba." Ya ajiye mata makullin motarsa ya fice ya amshi motar da direba ya kawo mashi. Jalila ta raka Hafsat kasuwa ta siya masu tsohuwar katifa guda biyu, sutura, kayan abinci da sauransu, da marece sosai suka koma gida. Ta shiga daki ta kulle sannan ta kira numbar Aliyu yana d'agawa ta fashe da kuka, hankalinsa a tashe yake tambayarta abun da yake faruwa, tana mai sheshshekar kuka tace, "Ina neman alfarma guda biyu a wajenka kamar yadda ka nema a waccen ranar nayi maka ina son a yau ka mayar wa kura aniyarta nima kayi min alfarma." Ya lumfasa sannan yace, "Ina sauraronki." Tace, "Na farko ina son kayi min alk'awari akan ba zaka tab'a tursasani komawa gidan Hisham, ka rokar min Umma da Jalila suyi min wannan alfarmar nasan dalilin da ya saka nayi wannan maganar. Na biyu ina son kayi min hanya in sayi gida a wani wajen gidan da ba ya da alaka da kai, kayi min hanya in sayi mota, ka taimaka min da dukkanin karfinka amma ban da kudinka, soyayyar da zaka nuna min a yau shine ka kyaleni in fuskanci kalubalen rayuwa a yadda suka zo min, inyi surviving a karan kaina." Yayi shiru na wani lokaci kamar zatayi kuka tace, "Aliyu." Ya ware idanu yace, "Yaushe ne kika fara kirana da sunana kai tsaye." Ta share hawayen da suka zubo mata tace, "Tun daga lokacin da na fad'a soyayya da sunan." Yayi mata hanya ta sayi gida a dutsen safe, babba ne sosai, ta dubeshi tace, "Wannan gidan yafi karfina." Ya murtuke fuska yace, "Irinsa ne nike da hanya idan kuma kin san dilallin gidaje muyi mashi magana ya nema maki gida a cikin kwatoci muga idan zaki iya kwana biyu a ciki." Ido ba mudu bane amma yasan daidai, kudin da aka fad'a mata tasan gidan yafi karfin haka, ba tayi kasa a gwuwa ba ta biya domin bata son yaga kamar tana hukuntashi akan abun da ya faru ne. Ta raba dare tana tunanin kasuwancin da ya kamata tayi, Washegari suna zaune a falo, tace, "Jalila wani kasuwancin kike ganin ya kamata in fara?" Jalila tayi jim sannan tace, "Siyar da abinci online tunda kin kware a girki." Hafsat ta ware idanu tace, "Abinci dai? Sana'ar wacce aurena ya mutu a kanta, kawo wata ban da wannan, girki ci min rai yake." Jalila tayi jim sannan tace, "Tunda kina da numbobin mata, matan masu kudi, ina ganin ki fara kasuwancin siyar da shadoji, atamfofi, leshe, mayafai, material, abaya, jilbab, jikkuna da takalma, kina d'aurawa a status, wanda yake so yayi payment a turo, sai in hadaki da wanda nike siya a wajenshi. Sai ki k'ara da kayan shiga da wankan na maza su kuma ki rink'a d'aurawa a Facebook da Instagram." Ji tayi hawaye sun zubo mata ta rungumeta tace, "Jalila na gode, ke k'awa ce ta gari, bazan tab'a mantawa da halarci da kikayi min a rayuwa ba." Jalila tace, "Angel ya kamata ki koma makaranta, ki ida session daya da kikayi difering." Hafsat tace, "In shaa Allah. Jalila rashin daukar shawarar da kika bani tun farko shine ya janyo min wadannan abubuwan." Ta share hawayen da suka zubo mata tace, "A lokacin da na ji maganarki, da ban yanke hukunci a cikin gaggawa ba, da duk haka ba ta faru ba." A gidan Jalila ta wuni saida marece sannan Hafsat ta rakata ta hau kekenapep ta wuce gida, ita kuma ta juya ta koma gida. Kwana biyar a tsakani Jalila ta wuce Sokoto inda a can ne aka turata bautar kasa. ****** Hafsat ta dage kasuwanci, kuma Alhamdulillah tana samun ciniki, duk da wasu lokuttan abun yana tsayawa, idan mutum yayi order ta siya a turo mata daga Kano ya amsa, idan kuma a wani garin yake daga Kano take tura mashi zuwa garin da yake, tana fasa dila a gida ga wadanda suke zaune a garin Katsina. Numbobinta na what'sApp suna mata ciniki sosai, tana samun shawarwari a wajen Aliyu, kuma tana hakuri da mutane, idan ta samu order na Ready made na maza, ta sayi yard ta bada shago a dinka sannan ta aikawa mutum garin da yake, zabuni, manyan riguna aiki mai aska duk tana yi. ****** Ta tashi da tashin zuciya da kasala, Umma ta matsa mata taje asibiti, awo ya nuna tana dauke da ciki, ta kule a daki tana kuka, Umma tayi tambayar duniya amma bata sanar da ita ba, tana kuka ta kira numbar Jalila tace, "Jalila na boni. Ciki ne dani." Jalila tace, "Baki boni, ciki ne da ubansa, kuma da aure kika sameshi. Kije ki samu Hisham ki sanar dashi, idan kin dawo ki kira ki sanar dani yadda kukayi. Idan kuma baki kira ba, karki nemani." Ta tsinke kiran, ta lura idan sukayi wa Hafsat saku-saku a banza ciwon zuciya zai kamata. Hafsat ta jima tana nazari kafin ta mike ta zura dogon hijab ta fita, ta tsaida kekenapep tare da sanar dashi inda zai kaita, yana ajiyeta ta bashi kudinsa, ta kwankwasa kofar dake gefen get, Mai guard ya bude yana ganinta yayi murmurshi tareda matsa mata, yace, "Barka da zuwa, Hajiya. Ki shigo." Hafsat ta girgiza kai tace, "A'a baba adamu. Ina wuni?" Ya amsa da, "Lafiya lau Hajiya." "Yana nan kuwa?" Ta tambaya. Ya gyad'a kai yace, "Eh yana nan, ki shiga." Ta girgiza kai tace, "A'a, ba sai na shiga ba, kayi min magana dashi." Ta zauna akan bench. A tare suka dawo, tun daga nesa yake kallonta har ya k'araso inda take, saida ya rufe kofar sannan yace, "Angel, miye haka? Na fad'a maki abun da zai faru da matata idan ta ganki, ko taji zancen kishiya." Ji tayi hawaye sun zubo mata ya fara korarta tun kafin yaji abun da ya kawota, ta share hawayen tace, "Amma dai, ka tsaya ka ji abun da nike tafe dashi sannan." Hisham ya had'e hannayensa waje guda alamar roko sannan yace, "Please, ki tafi, kada ta fito ta ganki." Tace, "Mu hadu a ofishinka." Ya kama hannunta yana janta har bakin get yace, "Please ki fita daga rayuwata." Tace, "Abun da nike tafe dashi fa?" Ya dafe kai yace, "Angel mi yasa kike haka? Bana son rasa matata, idan ta ganki aka fad'a mata zata iya mutuwa. A yau zan tattara matata, yarana, mahaifiyata da k'anwata mu koma London. Idan matsalar kudi ce, ki turo min account number." Ji tayi haushi ya kamata, zuciya ta kawo mata wuya, ta daka mata tsawa tace, "Hisham baka da kudin da za ka bani, baka da abun da za ka bani, kudi indai har daga gareka ne bana buk'atarsu. Kasan waye Aliyu kuma kasan tarin dukiya da yake dashi, kasan shine wanda nike so, na aureka ne saboda na rasashi. Abun da na kawoni kuma zan koma da abuna, akwai ranar kin dillanci ranar da zaka gane kuskurenka akan rashin adalci da kayi min." Hisham ya fitar da ita waje ya maida kofa ya rufe tana ji yana wa mai guard gargadi akan kada ya k'ara barinta ta shigo gidan, ya kira yana sanar da a siya mashi tikitin zuwa London. Ji tayi hawaye sun zubo mata ta saka hannuwa ta gogesu, ta juya saida tayi tafiya mai nisa sannan ta samu Kekenapep ta hau ya sauketa ofishin Aliyu. Ta zauna ta fashe mashi kuka, yana rarrashinta amma kamar k'ara tunzurata yake, ta kwashe dukkanin abun da ya faru ta sanar dashi. Ya fusata ranshi ya b'aci, "Ki tashi muje, a yau sai na nuna mashi cewa kina da gata." Tana sheshshekar kuka tace, "Please idan har kana sona ka rabu dashi." Ya daka mata tsawa yace, "Kiyi min shiru a nan, ki tashi muje." Ta fashe da kuka tace, "Shikenan idan na mutu kun hutu." Ya koma ya zauna yace, "Angel ina sonki shiyasa na fusata da abun da yayi maki." Tace, "Na sani amma kayi hakuri ka rabu dashi akwai ranar kin dillanci a ranar ne nike son ka nuna mashi b'acin ranka, a ranar ne nike son ka nuna mashi ina da gata." Har gida ya sauketa da kansa yayi wa Umma bayani akan abun da ya faru, ran Umma ya b'aci sosai ta kira Malam Jafaru mahaifin Jalila ta sanar dashi, suka yanke akan washegari zaije har gida ya sameshi da maganar. Tana kuka ta kira Jalila ta sanar da ita yadda sukayi, tana tuna abun da yayi mata tana k'ara jin ciwo a zuciyarta, tayi zaman aure dashi tayi mashi halarci na zama dashi duk da gaskiya da taji akan yaudararta da yayi amma ya rasa abun zai saka mata dashi sai butulci. Tana mai cigaba da kuka na tausayin kanta da kanta tace, "Jalila na je ko tsayawa ya saurareni bai yi ba, yana treating dina kamar wata annoba har da cewa zai daukesu har da Momcy da Fatima zuwa London a yau saboda kawai taje gidan, bai tsaya ya saurareni ya kama hannuna ya fitar dani waje ya kulle kofa, ina ji yana kiran waya akan a siya masu tikitin zuwa London, ina ji yana wa mai gadi gargadi akan idan ya k'ara barina na shiga gidan a bakin aikinsa." Jalila ta jinjina kai tana mamakin butulci irin na Hisham shiyasa yake da kyau bincike kafin aure, Umma tace sai mai kudi, Hafsat ta fusata da abun da tayi mata ta yanke hukunci a cikin fushi, yanzu waye gari ya waya, su. Daga daya bangaren tace, "Ki share hawayen ki daina kuka akan abun da muke da maganinsa, yanzu zan kira Baba in sanar dashi sai asan yadda za'ayi." Hafsat ta ajiye wayar, tana mai fashewa da kuka, bayan mintina talatin Umma ta shigo ta sameta kwance akan gado tayi lamo, ta zauna a gefen gadon tace, "Hafsat kiyi hakuri ki yafe min, dukkanin abun da ya faru da ke ni ce na janyo maki. Kwadayin kudina ne ya jefaki a damuwa da kike a ciki." Ta mike zaune tana mai girgiza kai tace, "Please Umma, babu abun da kika yi min. Na sa ni cewa ba kwadayi bane ya saka kika ce sai mai kudi, na sa ni kin ce sai mai kudi saboda kina son rayuwata ta inganta saboda kina son in huta a rayuwa. Abun da ya faru laifina ne, na auri Hisham ne saboda na yanke hukunci a cikin fushi. Umma kinyi min sadaukarwa mai yawa a rayuwata, kin soni fiye da komai, kin sadaukar da farin cikinki a saboda ni, saboda baki son rayuwata ta tarwatse. Komai da ni ke yi ina yi ne domin in faranta maki. Umma idan har ina raye ba zakiyi hawaye ba." Umma tace, "Allah yayi albarka." Hafsat ta amsa da, "Amin." Washegari da marece Malam Jafaru ya nemi ganin Umma da Hafsat, a motarta sukaje gidan wanda Hafsat ta siya masu a lokacin da tana auren Hisham. Fuskarsa babu walwala yace, "Hafsat naje har gidanshi da gidansu amma an sanar dani cewa sunyi tafiya kasashen waje." Umma tace, "Yanzu ya kike ganin za'ayi?" Hafsat tace, "Umma. Baba. Ku rabu dashi. Allah yana sane dani kuma shine zai kawo min mafita." Sun jima suna tattaunawa akan al'amarin saida marece sannan suka koma gida, ta cigaba da karatunta tareda kasuwancinta, tana mai rainon cikinta, Aliyu ya taimaka mata sosai a wajen kula da cikin musamman a lokacin da cikin yayi nauyi, he help her throughout the pregnancy, yana bata kulawa sosai, har a zuciyarta tana matuk'ar sonshi, bata da burin da ya wuce aurenshi domin ya nuna son da bata tunanin zata samu wanda zai sota har haka, tana mashi son da ba zata tab'a wa waninsa ba. Da tsohon ciki tayi jarabawar karshe, ranar graduation saidai ta kanga graduation jacket dinsu tayi a saman jikinta, sukayi hotunan graduation. Sati biyu a tsakani, da misalin karfe goma na dare nakuda ta kamata, hankali a tashe Umma ta kira Aliyu, mintina biyar a tsakani yazo a motarsa, Umma ta tayar da ita, ya wuce dasu asibiti, aka wuce da ita dakin haihuwa. Hankalinsa a tashe yana kaiwa yana komowa, dukkanin wanda ya gansa a wannan lokacin sai ya dauka matarsa ce. Karfe hudu na asuba ta santalo d'anta namiji mai KAMANNI da Hisham sak kamar an tsaga k'ara an karya. Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 14 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 Aliyu ya amshi jaririn yana kallonshi yana murmurshi, jin yaron yake tamkar gudan jininsa, Hafsat ta d'aga kanta dakyar tace, "Yaa Aliyu kayi mashi huduba da dukkanin sunan da kake so." Ya dan kalleta yace, "Kin tabbata." Ta gyad'a kai tana mai sakar mashi murmurshi, yayi mashi huduba da suna Aliyu, da murmushi akan fuskarsa yace, "Allah ya raya takwarana Aliyu." Tayi matuk'ar farin ciki da wannan sunan, tana son Aliyu, tana son sunansa da komai a kansa, ya nuna mata so, yayi mata halarci. Ta share hawayen da suka zubo mata a sanadin tunawa da tayi da wulakanci da kaskanci da Hisham yayi mata. Ta ce, "Babana." Ya dan dubeta, tace, "Ka zame min tamkar uba, ka zame min gata, ka zame min bango majingina, Ina sonka Aliyu." Yayi mata murmushi yace, "Koda wannan Aliyun yayi maki laifi," yayi nuna wa kansa ya dora da cewa, "Ga wani Aliyu a tare dake. Koda anyi nasarar rabaki da wannan Aliyun a karo na biyu, ga wani Aliyu a tare dake. Ki kula da Aliyu." Ya zuba mashi idanu ban da kinta da mahaifiyarsa takeyi miye zai rabata dashi, yana matuk'ar sonta, yana tausayinta, ya damu da damuwarta. Tana zubar da hawaye ta ce, "Ban tab'a kin Aliyu ba. Burina shine in auri Aliyu." Yace, "Allah ya ba Aliyu ke." Ta amsa da, "Amin." Tana jin matuk'ar farin ciki akan addu'ar da yayi. Yadda yake kallonta ya sakata juyar da kai bata jure wannan kallon ba, ji tayi yace, "Aliyu ya gode da kauna." Tace, "Allah ya raya Babana." Aliyu yace, "Amin." A ranar Jalila ta dauki hutu ta kamo hanyar Katsina daga Sokoto, a asibiti ta tarar da su, nurses da likitocin da suka karbi haihuwar Aliyu sukeyi wa kallon Mahaifin yaron saboda yadda yake zirga-zirga a kansu, washegari aka sallamesu suka wuce gida. Siyayya sosai Aliyu yayi masu saidai ganinsa sukayi da kaya niki-niki, tun cikin yana k'arami ta sayi dukkanin abun da zasu buk'ata, har rago ta siya, da geron kunu, suger, da kayan abinci. Ranar suna sai ga Aliyu da raguna har guda biyu, aka hada da wanda ta siya aka yanka raguna ukku, kwangilar abinci ya bada saidai suka ga ana shigowa da manya-manyan kulolin abinci, anyi shagali sosai, (a nan na hango Member na ZAN BI ZAB'IN UMMANA COMMENT SECTION, Mama Gee, Fahaus chambo, Diamond Bhatool, Mjungudo, Oum Hafsat, Maman Kamal, Mmn Useey, Garba Fatima, Fauziyya Ibrahim Kam, Oum Aftnoor, Aeesharh, Nudar Rabiu, Hauwau Abdullahi da sauran members suna ta kaiwa da komowa na hidimar baki, nidai babu ruwana tunda ba'a gayyaceni ba, atorh 😅 🤣 😂) anci, ansha, baby da maman baby suna samun kulawa sosai. Cike da kulawa Hafsat take rainon Aliyu, sabon shafin soyayya suka bude ita da Aliyu, a koda yaushe sonshi k'ara linkuwa yake a cikin zuciyarta, Hajiya Zainab (mahaifiyarsa) har gida ta tarar Angel tayi mata tatas akan tayi gaggawar rabuwa da Aliyu domin diyar er uwarta zata aura mashi. "Saboda rashin zuciya na rabaki da yarona kin manne mashi, tun wuri kiyi gaggawar rabuwa dashi domin ba sa'an aurenki bane." Hafsat tana zubar da hawaye tace, "Amma Ummi ina sonshi yana sona, miye illata da har baki son ya aureni." Ummi tayi mata kallon kaskanci tace, "Saboda ke talaka ce marar galihu, wacce bata da asali mai kyau. Na fi karfin in had'a jini da talaka kamar ki tun wuri ki nemi sa'an aurenki domin diyar er uwata Aliyu zai aura idan baki da labari a yau na sanar dake." Ummi ta fita tareda Aliyu wannan ya saka babu wanda yasan abun da ya faru. A ranar kwana tayi tana kuka, suka rasa gane kanta, wata biyu a tsakani aka d'aura auren Aliyu da cousin dinsa. Hafsat ta maida hankali akan kasuwancinta da yake cigaba da bunk'asa har ta bude shago ta zuba yara suna kula mata dashi, ta sayi gidan dake a kusa dasu, ta k'ara fad'ad'a gidansu, ta sayi wani gidan a kusa dasu saboda Abbanta, a shekarar da tayi gyaran gidan a shekarar ne ta bud'e plaza da ta gina, ta zuba kayan sakawa, kayan Kitchen, kayan dinki, shagunan dinkin, wajen siyar da kayan dinki, shagon siyar da wayoyi da sauransu. Arzikinta yana k'ara linkuwa, tana ji da Umma, tana ji da Little Aliyu, dukkanin neman da ta ke yi ta na yi ne sabo dasu, bata so su nemi komai su rasa, ta zame masu gata a rayuwa, ta zame masu bango majingina. Shekaru sun ja, har matar Aliyu tayi haihuwa biyu, zuwa wannan lokacin ta fara hakura da Aliyu amma har a lokacin babu abun da ya sauya na kaunar da takeyi mashi, har zuwa wannan lokacin sonshi yana manne a cikin zuciyarta, maza suna fitowa neman aurenta saidai yawanci samari ne, ita kuma tafi son ta auri magidanci, Jalila tayi aure wani yaron mai kudi, a sokoto suka hadu saidai shima d'an katsina ne, Little Aliyu ya girma, shekarunsa biyar har ta sakashi a makarantar boko, tana nuna mashi gata sosai, ta dauki kaunar da takeyi wa Aliyu ta mayar a kanshi, dukkanin laifin da zaiyi mata bata dukanshi saidai ta tusashi gaba tana mashi fad'a tana dariya. Umma ta kan ce, "Hafsat zaki sangarta yaronki ne da kanki." Sai Hafsat tayi murmurshi tace, "Umma bazan dukan Babana ba, mai sunanshi shine gatana a rayuwa. Mutumin da har yau nike matuk'ar so da kauna." Tunda Little Aliyu ya tashi, Aliyu ya sani, yana kiranshi da Abba, kuma a daukarshi shine mahaifinshi, Aliyu yana nuna mashi kulawa matuk'a amma hakan bai saka ya sangartashi ba, tsoronshi yake sosai, kallo kawai ya isa ya saka ya shiga taitayinsa, wasu lokuttan idan yayi mata laifi saidai ta kira Aliyu tana dariya tana fad'a mashi, idan yace, "Angel ki daina sangartashi." Sai tayi murmurshi tace, "Aliyu ne bazan iya d'aura hannuna a kansa da nufin duka ba saboda mai sunanshi shine gatana a rayuwa." Tunda ta haifeshi bata tab'a koda dungurinshi ba, ranar ta gama soya miya yace ta zuba mashi shinkafa, tace ya bari ta gama, ya fakaici idonta tana shiga daki ya shiga kitchen ya zuba shinkafa ya zuba miya, ya ci ya koshi ya b'arar da miyar. Tana dariya take kallon miyar, Umma tayi tagumi tana kallon Ikon Allah, Jalila ce ta shigo tayi turus tana tambaya, "Umma mi ya faru take dariya?" Umma da ta rasa bakin magana tana kallon ikon Allah, tace, "Aliyu ne ya b'arar mata da miya, b'arnar da gangan amma shine ta tusashi a gaba tana dariya." Ta kwashe dukkanin abun da ya faru ta fad'a mata. Kallo daya Jalila tayi mashi ya gudu bayan Hafsat, ta zaroshi daga bayanta ta zaneshi, saida ta saka yaba Hafsat hakuri yace bazai k'ara ba sannan ta rabu dashi, suna shiga daki, tace, "Ke dai Angel banza ce, yaro yayi maki b'arna amma kin tusashi a gaba kina dariya, salon yaji dadin k'arawa gobe." Hafsat tace, "To ya zanyi dashi? Ni dai ba zan d'aura hannu akan Babana ba saidai inyi mashi fad'a." Jalila ta harareta tace, "Kada ki rainawa kanki wayo, kina magana kina dariya shine fad'a, idan mutum yana fad'a murtuke fuska yake amma ke sai ki tusa yaro a gaba kina dariya sannan kice fad'a kike mashi. A yaushe kika tab'a ganin anyi haka? Kinga komawa zanyi inda na fito, ban iya zaman kallon wannan kayan haushin." Hafsat ta marairaice fuska tace, "Yi hakuri, k'awata ta kaina." Jalila ta koma ta zauna tana cewa, "Angel, Mata a gidan Alhaji suleiman." Hafsat tace, "Kin san satinsa biyu a Paris.".Jalila tace, "Alhaji Suleiman shidai yana sonki." Hafsat tayi murmurshi kawai, ta sani Alhaji Suleiman yana sonta sai dai ita Aliyu take so, kamar Jalila ta san abun da take tunani tace, "Hafsat babu ba zan ce maki ki hakura da Aliyu ba, saboda Aliyu miji da zamuyi maki murna idan kika aureshi, yayi maki sadaukarwa a rayuwa, amma ya kamata ki zauna kiyi tunani na kanki, ki nemawa kanki mafita, idan Aliyun ne ki tashi kiyi yaki a kanshi tunda mahaifinsa yana sonki." Kafin tayi magana suka jiyo hayaniya daga compound, a tare suka fito, wani magidanci ne tareda mata guda biyu da yara wadanda yawansu zai kai goma sha biyu, Hafsat tayi turus tana kallonsu. Umma tace, "Haruna." Wannan ta tabbatar mata da abun da take tunani, a yau taga mahaifinta, muryarta tana rawa tace, "Abbana." Ya fashe da kuka yace, "Hafsat ki yafe min, na cuceku, na zalunceku a rayuwa, Hajara ta soni da zuciya daya amma na gudu na barku, dukkanin abun da ya faru daku nine na janyo maku." Hafsat ta girgiza kai tana mai zubar da hawaye tace, "Abba kada kace haka." Tayi masu gajora zuwa ciki ta tarar da kofar parlour a kulle, ta kira Umma, daga daya bangaren Umma tace, "Ku tsaya a balcony ku gama maganar da zakuyi ki saitasu gidan da kika siya, kika sake haruna ya tako kafarshi cikin falona zakiga b'acin rai ganin idanunki." Tace, "Ayyerh Umma, ki zama mai yafiwa." Umma ta fusata ta inda take shiga bata nan take fita, bata tab'a mata fadan da tayi mata a ranar ba, da sauri Hafsat tace, "Umma kiyi hakuri, za'ayi kamar yadda kika ce." Umma tace, "Da ya fiye maku, akwai abinci a kitchen domin ni ban gaji rowa irin tashi ba, kiyi magana masu aiki su kai masu, kada su biyo dashi ta falona su bi ta kofar baya." Ta zare wayar daga kunnanta suka zauna a balcony, Abba ya gabatar mata da yaran tareda matan da yake tare dasu, "Hafsat, wadannan matana ne, wadannan kuma k'annanki ne." Hafsat ta gyad'a kai tace, "Okay, Jalila muje in budewa Abbana gidan da na siya mashi, su huta, akwai abinci da Umma tace a basu sai mu wuce masu dashi." Ta koma ciki domin dauko hijab tunda Aliyu ya nuna mata basa son yawo da take da k'aramin mayafi take k'ok'arin gyarawa. Tunawa dashi kawai ya saka ta saki murmushi tana mai jin tsimin sonsa dake a zuciyarta yana k'ara tsiro fure, ita dai tana son Aliyu, addu'arta a kullum shine Allah ya bata Aliyu, idan kuma babu alheri Allah ya mantar da ita Aliyu ya hadata da rabonta saidai a kullum k'ara sonshi take. "Ina kika barsu?" Umma ta tambaya. Hafsat ta tsaya ta k'arasa falon tace, "Zan saka hijab ne in wuce dasu gidan da na siya mashi." Umma ta tab'e baki tace, "Shi kuma abincin da na ce ki basu fa? Ko kuma nema kike ki mayar da marowaciya kamar yadda ubanki yake, idan mugunta ce kanki kiyi wa, gwara ace ubanki marowaci, uwarki mai hannun kyauta, akan ace dukkaninsu marowata ce." Taji zafin maganar da Umma tayi saidai ba ta ga laifinta ba tunda har Umma ta iya wannan maganar a gabanta wannan yana nuni da cewa abubuwan da yayi mata ba kadan bane. Saidai uba uba ne duk yadda yake ba zaka zo a aibatashi a gabanka shiyasa a kullum yake da kyau mu zab'awa y'ay'anmu uwaye na gari domin guje masu gori, ku duba abun da ya faru da Umma, danginta su koreta saboda taki yarda ta mayar da Hafsat wajen dangin Haruna. Shin mi yasa taki maidata? Saboda babu mutanen arziki a danginsa na kusa wadanda ta sani. Da ace miji na gari ta aura daga dangin kirki ba zataji tsoron barin diyarta a hannunsu ba domin tana da tabbaci akan zata samu tarbiyya, er uwa kada ki bari so ya saka ki auri mutumin banza, auri rayuwa ce da ake zaman mutuwa ce zata raba don haka ki lura. Hafsat tace, "Ayyerh Umma ba haka nike nufi ba." Umma ta taso mata tace, "Torh miye kike nufi? Kina nufin nima marowaciya ce kamar shi." Hafsat ta lura Umma a wuya take, ta zauna sannan tace, "Naga sun gaji ne shiyasa na ce mu kaisu gidan sai mu wuce masu abincin." Umma ta gyad'a kai kawai tace, "Torh naji." Hafsat ta mike ta wuce sama ta zura hijab. Abba yana a motarta yayinda sauran suka cika Jeep guda biyu suka kama hanyar gidan wanda babu nisa a tsakani, bango daya ne dasu. Abba yayi tsaye yana bin gidan da kallo yana kuka yana nadamar abun da yayi a rayuwa, yana nuna tuna wulakanci da aka yi masu a gidan haya wanda ya tilasta masu kwana a titi. Suka ci abincin da aka tafo masu dashi, Hafsat tana matuk'ar ji da Abbanta, a ranar ta saka aka cika masu store da kayan abinci, ta zuba mashi furniture's a bangarensa, ta zuba wa matanshi da kuma k'annanta suma, ta saka k'annanta a makarantar kudi dake a kusa dasu, ta bud'e katon provision wa Abbanta yana amfani dashi yana hidimar kansa tana son ya ginu da kansa ne domin babu wanda yasan gawar farko, bata fatan mahaifinta ya wulakanta, fatanta shine koda bayan ranta ya fi karfin hidimar gidansa. Ta zauna da Abba suka sha hira ya bata labarin abun da ya faru tun bayan tafiyarshi har zuwa matan da ya rink'a aura yana saki har zuwa korarshi da aka yi daga gidan haya, yawon da suka yi a titi, suka rink'a kwana a makarantar firamare. "Hafsat na dade nadamar abun da na aikata saidai kunya ta hanani zuwa gareku amma kina a raina. A kullum kina a raina." Hafsat ta kwashe dukkanin abun da ya faru da ita ta sanar dashi musamman b'igiren auren Hisham da tayi da kuma wulakanci da ya biyo baya, ta b'oye mashi abun da ya faru a tsakaninta da mahaifiyar Aliyu. Abba ya fusata yace, "Har yanzu baku san inda yake ba?" Hafsat tace, "Tun daga ranar ban k'ara nemanshi ba, na shafe shafinsa daga rayuwata." Abba yace, "Aliyu fa? Mutane zasuyi mashi kallon marar uba, kuma a kwana a tashi wata rana shi da kansa zai so sanin waye ubansa, a kwana a tashi rana zata zo da zai fahimci ba Aliyu bane mahaifinsa, a lokacin sai kice dashi mi." Hafsat tace, "Ni ce Mamarshi, Ni ce Babanshi." "Mi yasa kika saka ake kiranshi da Aliyu Aliyu?" Abba ya tambaya. Tace, "Saboda babu abun da Hisham ya sani na daga wahala dashi. Aliyu shine ya tsaya mamu, ya taimakeni a lokacin, shine ya zama gatana." Abba yayi jim sannan yace, "Ki shirya gobe zan kaiki wajen dangina, daga nan zamu wuce wajen dangin mahaifiyarki in basu hakuri nine sanadin lalacewar zumunci da tsakanin Hajara da danginta." Washegari ya kaita wajen danginsa, sunyi matuk'ar farin ciki da ganinsa, suna ta haba-haba da ita, dangi masu dadi, daga nan suka wuce wajen dangin mahaifiyarta a babban gidansu na gandu inda kakanninta suke zaune, Abba da kanshi ya basu hakuri akan abun da ya faru, suma sunyi nadamar abun da sukeyi, suna ta neman Umma saidai basu san inda take ba, sunyi matuk'ar farin ciki da ganinta, a can Hafsat ta kwana. Washegari ta koma ta dauko Umma suka koma tare. Tun daga wannan ranar gidanta ba ya rabo da mutane, danginta suna akan hanya, musamman cousin dinta na bangaren Abba, tana yi tana tsawatarwa saboda wasu daga cikinsu basa ji ko kadan, sun so mayar da gidanta dandalin tara samarinsu ta tsawatar sai a lokacin ta k'ara fahimtar da dalilin da ya saka Umma taki maidata wajensu a lokacin da danginta suka ki karbarta. Umma da Hafsat suna zaune, Hafsat tace, "Umma. Ina son muyi magana saidai ban san yadda zaki dauki maganata ba." Umma tace, "Akan miye?" Saida Hafsat tayi jim sannan tace, "Akan Abba ne." Umma ta murtuke fuska sannan tace, "Akul, karki kuskura kiyi min maganarshi, mahaifinki ne don haka ba zan hanaki mu'amala dashi ba amma ni bani da wata dangantaka da shi. Karki kuskure koda wasa kice zakiyi min maganarsa ko kuma ki dangantani da shi. Nayi nadamar auren Haruna da nayi, shiyasa ake son ka zab'awa y'ay'anka uba na gari. Kina ganin halayen da y'ay'an en uwansa suke a gidan nan, koda ba'a fada ba nasan ban yi maki adalci ba. Har gobe har jibi danginki ne kuma ni na janyo maki idan aka goranta maki a kansu." ***** Hafsat tana wa Aliyu shirin makaranta yana rigima har ya makara, sukayi wa Umma sallama, ta bud'e mashi daya bangaren ya shiga sannan ta zagaya bangaren direba, sanye take dakekken leshe dan ubansu anyi mata doguwar riga bubu, ta zura takalma half cover, ta kashe dauri samfurin ture kiga tsiya, ta d'aura mayafi akan kafad'a tana zuba kamshi. Sunyi nisa motar ta tsaya, ta daki starry tace, "No." Tana duba lokaci. Ta jingina da motar tana tunanin yadda za ta yi, Little Aliyu ya fara kuka za'ayi mashi bulala idan ya makara. Tun daga nesa Ashraim ya hangota har ya gotata ya dawo da baya, yayi kasa da gilashin motarsa yace, "Angel." Ta zaro idanu tana kallonsa da namaki jin ya kira sunanta saidai ba ta ce komai ba, yayi mamakin ganinta rabonshi da ita tun lokacin da aka sanar dashi tayi aure. "Motar ta tsaya ne?" Ya tambaya. Ta gyad'a kai tace, "Eh, kuma Babana ya makara." Ji tayi yace, "Mu je in sauke ki." Tayi jim sai kuma ta nuna mashi motarta, yace, "Za'a kawo maki ita har gida." Tayi jim tana shawarar ta shiga ko kuma ta tsaya, ganin bata da wani zab'i da ya wuce ta bishi la'akari da lokaci ya kure, ta bude mazaunin baya ta saka Little Aliyu sannan ta zauna a bangaren mai zaman hakanan, ta fad'a mashi sunan makarantar. Ashraim yace, "Abokina miye sunanka?" Little Aliyu yace, "Aliyu Aliyu... Are you my father? Shin kaine babana?" Ashraim yayi mamakin tambayar da yaron yayi mashi, ya ware idanu yana kallonta tunda tayi aure ya dakatar da bibiyar rayuwarta da yake. Little Aliyu ya dora da cewa, "Wata mata tace Abba ba shine babana ba. Ammi waye Babana? Dama akwai wadanda basu da Baba." Hafsat ta daka mashi tsawa tace, "Kayi min shiru a nan tun baka sha mari ba." Little Aliyu yayi shiru tunda take dashi ranar ne ta fara d'aga murya a kanshi har tana barazanar zata dokeshi. Yayi parking a harabar makarantar ta fito tareda b'alle murfin baya, Little Aliyu ya fito yana mata rigima ta kaishi har class kada Aunty ta dokeshi. Ta rakashi har class, tayi mamaki dawowa da ta tarar da motar, ta lek'a tace, "Ba sai na wahalar da kai ba, zan tari kekenapep. Na gode." Ya girgiza kai yace, "Mu je har na kira mai gyara min mota, yana akan hanya." Tayi jim sannan ta b'alle murfin motar ta shiga, ya koma dasu inda motarta ta tsaya, suka tarar da mai gyara, ta bashi makullin motar ya bashi, tana zaune a mota har ya gama gyaran, Ashraim ya maido mata makullin motarta. "Nawa ne kudin?" Ta tambaya. Ashraim yace, "Na biya." Tayi mashi godiya tana k'ok'arin fita daga motar sai kuma ta dakata tace, "D'azu ka kirani da Angel, sunan da ba kowa ya ke kira na da shi ba. Shin mun san juna ne?" Ashraim ya sakar mata murmushi sannan yace, "Sunana Ashraim Hamid. Na soki tun kafin ki yi aure sai dai ban furta maki ba sannan ban tunkareki ba, a lokacin da na shirya bayyana kaina a gareki a ranar ne aka daura maki aure, tun daga ranar ban k'ara bibiyarki ba sai yau na ganki. Yaronki Aliyu, babanshi ya rasu ne?" Magana ce wacce bata son yi don haka tace, "A'a, karka damu." Ya zaro card dinsa ya mik'a mata yace, "Please ki kirani." Ta amsa tareda fita daga motar ta b'alle murfin motarta ta shiga tayi mata key ta wuce, saida yaga tafiyarta sannan yaja motarsa ya wuce. Wunin ranar ta b'ata shi ne tana tuna maganar da Little Aliyu yayi mata; Shin wacece ta sanar dashi haka? Tun yaushe? Garin ya? Ba ta da wanda zai ba ta amsa. ******* Kai tsaye Ashraim ya wuce kamfaninsa, ya hau elevator zuwa ofishinsa dake a hawa na karshe ofishin CEO, ya zauna tareda kiran numbar Habib yana sanar dashi ganin Hafsat da yayi. "Buddy yau naga Angel?" Daga daya bangaren Habib yace, "Angel kuma?" Ashraim yace, "Eh, Hafsat, Angel. Dazu na ganta motarta ta b'aci akan hanya, har da yaro take dashi, amma akwai abun da na ji wanda ban gane ina. Ina son kayi min bincikie, ina son sanin abun da ya faru da ita a tsayin wadannan shekaru." Habib yace, "An gama ranka ya dade." Ashraim yayi dariya yace, "Yauwa ranka ya dade." A tare sukayi dariya. Yace, "Wait... Waye wanda ta aura a lokacin?" Habib yace, "Hisham Mahmoud." Ashraim yace, "Hisham Mahmoud, kamar ya dawo Nigeria bayan shekaru shidda da yayi a kasar. Komai kenan ka kirani." (Ku zo ku tayani dubawa; Ga Aliyu, Ga Ashraim, Ga kuma Hisham wanda ya dawo Nigeria, shin miye zai faru a lokacin da Hisham yayi tozali da Little Aliyu?). Tun da ta dawo ta ajiye jikkarta ba ta k'ara tunawa ba, tana da jikkuna da yawa shiyasa yake daukarta lokaci kafin ta maimaita, wata rana tana duba abu a jikkar ta ci karo da katin, tayi jim tana son tunawa, ta ware idanu tare da dafe kai, ta copy numbar tare da kira. Tana sallama ya gane muryarta, kamar mai rad'a yace, "Angel." Kunya ce ta kamata tace, "Na ajiye jikkar kuma yana a ciki, ban tuna ba sai yau ina neman abu a ciki naci karo dashi." Daga daya bangaren yace, "Na ji dadi da kika kira. Ya Aliyu? Ya Umma da Abba?" "Lafiya lau." Ji tayi yace, "Ranar na je school dinsu." Tayi mamaki domin Little bai sanar da ita, tace, "Bai fad'a min ba." Yace, "Inzo?" Tayi jim tana juya maganar da yayi, ta yarda da wani abu kowane namiji da salonsa, tace, "Sai ka zo." Washegari da marece ya kirata akan yana akan hanya, ta mike ta shiga wanka ta jima tana durje jikinta da sabulai masu kamshi sannan ta sakarwa kanta shower, ta fito ta cancara makeup tare da shiryawa cikin expensive atamfa dinkin riga da zani, ta kashe dauri samfurin ture kiga tsiya, simple kwalliya ce akan fuskarta, ta zuba gold wuya da hannu, da piecer a hancinta, ta feshe jikinta da turaruka masu saukin kamshi, ta zura takalma half cover ta fita bayan da ta amsa kiransa ya sanar da ita yana a compound, ta saukeshi a parlour da take sauke bakinta, aka ajiye mashi snacks da drinks. Ta kasa jure kallon da yake mata har saida tayi da kanta, tace, "Barka da zuwa. Na gode da taimakon da kayi min a wannan ranar." Ya gyad'a kai yace, "Da fatan kin san abun da yake tafe da ni." Cikon ranta tace, "Ikon Allah." Amma a zahiri sai tayi rolling idanu tace, "Ina jinka." Ya ce, "Gorgeous. Kinyi matuk'ar kyau." Abun da ya tashi kanta a kansa shine yadda yake karin hularsa a kaikace samfurin da zata iya kira da ture kaga tsiya. Ya tsura mata idanu the more yake kallonta the more take k'ara mashi kyau, sai yake ganin ta fi da kyau a yanzu, saida ya lumfasa sannan yace, "Hafsat a shekarun baya nayi zurfin ciki wanda ya saka na rasaki, kuskure ne da nayi nadamar aikatashi, ba zan maimaita wannan kuskuren ba a yanzu. Hafsat ina matuk'ar sonki a shekarun baya da kuma yanzu. Ina da mata daya da yaro daya." Ya lumfasa sannan yace, "Da fatan ban yi maki tsufa ba?" Tayi murmurshi ba tareda tace komai ba, yace, "Samarinki nawa?" Ta ware idanu, ya gyad'a kai yace, "Mace mai kyau kamarki ba za'a rabata da samari ba, tun da wuri in san aikin da yake a gabana, kada in zauna bacci wani yayi min kafa, a yi min wuff da ke." Dariya ya bata tana k'are fuskarta tana dariya. Ya jima sannan ya wuce bayan da ta rakashi har mota, katuwar leather shake da chocolate ya baiwa little Aliyu, tayi mashi godiya, zuciya tana da son mai kyautata mata, Hafsat tana matuk'ar son Little Aliyu, Ashraim yana nuna kulawa a gareshi, ya daukeshi tamkar D'an da ya haifa, wannan ya saka take ganin girmansa sosai, tana ji har a ranta zata aureshi saboda tana sonshi, ta yanke shawarar ta hakura da Aliyu tunda mahaifiyarshi bata sonta, ta saka a ranta cewa tana son Aliyu tana matuk'ar sonshi kuma tana addu'a na yarda da cewa IDAN HAR RABONTA NE zata sameshi. Ashraim yana yawan kiranta susha hira, yana zuwa a weekend. ****** Hamida diyar k'anin mahaifin Hafsat, za ta je bikin gidansu k'awarta ta tafi da Little Aliyu, bayan sun dawo sun fito daga kekenapep zaya bada kudi. Tunda ya hawo titin idanunsa suka sauka akan yaron, gani yake kamar gizo ne yake gani, har ya gotasu yayi reverse ya dawo da baya tareda gangarawa da motar a gefen titi, ya fito ya k'arasa inda suke yace, "Hi boy." Little Aliyu ya juya ya tsura mashi idanu, Hisham ya ware idanu ganin matuk'ar KAMANNI da yaron yake yi dashi kamar kobo da kobo, Little Aliyu ya kama hannunsa yace, "Kasan Ammi na?" Hisham yace, "Wacece Amminka?" Little Aliyu yace, "Ammi mana. Idan baka santa ba, you are stranger ban yi maka magana." Hisham yayi murmurshi yace, "Na santa. I'm not stranger." Ya juya baya don haka ba ta hango fuskarsa, ta janyo Little Aliyu tana mai cewa, "Malam. Ya haka?" Ta ware idanu ganin matuk'ar KAMANNI da su ke yi. ******* Hafsat tana zaune a parlour tana waya da Ashraim, Hamida ta fad'o falon a rikice tana fad'in, "Little Aliyu." Hafsat ta mike da sauri tana mai dafe kirji idanunta a waje tace, "Na boni. Mi ya samu Babana?" Hamida ta ce, "Yaga wani mai KAMANNI dashi ya makale mashi ina mashi magana yaki biyoni." Hafsat ta ware idanu tace, "What! Hisham! Ya sake ya tafi min da Little Aliyu sai yaga tashin hankali da bai tab'a gani ba. Ko wa ya tsaya mashi a garin nan bai isa ba. Saidai a mutu." Ta warware mayafi dake a saman kanta ta yaneshi ta zura takalma ta fita zuwa compound, "Muje." ta fita ta kofar dake a kofar get. Tana a gaba Hamida tana biye da ita, Hisham yana tsaye ya daurashi a saman bayan mota, tun da suka tafo ya tsura mata idanu yana jin wani yanayi yayinda zamansu yake dawo mashi a kai, the more take tunkaro inda yake the more take k'ara mashi kyau, sai yake jin wani yanayi a zuciyarsa. Ba tayi wata-wata ba ta sauke Little Aliyu daga saman motar tare da watsa mashi mugun kallo tace, "Ban hanaka magana wa strangers ba. Tun da har baka jin magana, sai na fad'awa Aunty Jalila tayi min maganinka." Little jin zata fad'a wa Jalila ya fara kuka yana bada hakuri, "Kiyi hakuri kada ki fad'a mata. Shine yace min ya sanki that he's not stranger." Kanta tsaye tace, "K'arya yake. Makaryaci ne." Little Aliyu ya kama baki yana kallonta idanu a waje kamar wacce tayi babban zagi. Hisham ya ware idanu yace, "Nine nike k'arya." Ta murtuke fuska tace, "K'arya ka ke yi mana, ka sanni ne, a ina ka sanni?" Hisham yace, "Shin d'ana ne? Is he my son?" Tayi dariyar rainin wayo tace, "Yaushe mukayi haka da kai, daga ganin yaro sai kace d'anka ne, ka bani ajiya ne, daga yau idan na k'ara ganinka a kusa dani ko yarona sai na shuka maka ranshi mutunci. Daidai nike da kai. Aikin banza aikin wofi." Ta fizgi Little Aliyu suka wuce, Hisham ya d'aga murya yace, "Mi za ki ce akan KAMANNI da ni ke yi da shi." Hafsat ta juya tareda buga tsaki tace, "KAMANNI manya. Hisham! Hisham! Hisham! Ka fita daga hanya ta tun kafin nayi maka atishawar tsaki domin yanzu ba shekarun baya bane." Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 15 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 Umma ta tareta da tambaya kasance taji maganganu da takeyi kafin su fita. Hafsat tace, "Hisham ne, kuma nayi mashi gargadi, don a wannan karon idan yace zai shiga gonata saidai a mutu." Little Aliyu yace, "Ammi, is he my father? Muna KAMANNI." Ta fusata ta daka mashi tsawa, "Daga yau idan ka k'ara ganin wani kace mashi babanka sai nayi maka dukan tsiya, sai in zaneka ai ba wancen Aliyun bane, sunanshi kawai kake dashi. Ni da kake gani," tayi nuni wa kanta ta dora da cewa, "Ni ce uwarka, ni ce ubanka. Babu wani kato da ya isa ya kawo min wargi tunda ba tare muka sha wahalarka ba. Idan kuma mutum ya fusatani har wancen sai in bi in amso abuna tunda ba wani ya tayani nakudarsa ba. Tun da nike ban tab'a shan wahala irin ta cikin Muhammad ba amma babu tausayi babu imani aka rabani dashi." Ishaq daya daga cikin k'annanta ya kawo mata wayarta da take ringing. Ashraim ne sai a lokacin ta tuna tana wasa dashi aka kawo mata maganar Little Aliyu yana tare da Hisham. Ta ce, "Ranka ya d'ad'e." Daga bangaren Ashraim yace, "Da fatan babu abun da ya samu Little Aliyu." Ta girgiza kai kamar yana a gabanta tace, "Hisham ne, kuma nayi mashi gargadi, wannan karon sai dai a mutu tunda ba tare da shi nayi nakuda da wahalar yaron ba." Ashraim yace, "Yace zai amshi yaron ne?" Hafsat tace, "A'a, tambaya yayi idan D'anshi ne, sai ka ce wanda ya ba ni ajiya." Lura da ranta a matuk'ar b'ace yake, yayi mata sallama akan zai kira anjima. ****** A karo na biyu Hisham yace, "Momcy." Momcy tace, "Idan ba zaka fad'a min abun da yake tafe da kai ba, ka tashi ka bani waje, ina da abun yi." Yana tabbaci idan ta ji labarin abun da yayi ba za ta yi mashi da sauki ba shiyasa yake shakku akan fad'a mata saidai gwara taji a bakinsa akan taji maganar a wani wajen. Saida yayi kasa da kanshi sannan yace, "Momcy abun da na fad'a maki a shekarun baya akan rabuwata da Hafsat k'arya na yi maki. Ba Hafsat ba ce ta nemi saki, sannan ba ita ba ce ta bar min Muhammad. Ni ne na saketa sannan na amshe shi daga wajen ta, bayan wasu en kwanaki ta dawo ban saurareta ba, a ranar ne kuma muka wuce London. A yau na ganta tare da wani yaro mai KAMANNI dani kamar kobo da kobo." Momcy ta ware idanu tana kallonshi tana salati, tace, "Hisham ni za ka mayar mutuniyar banza, kayi min k'arya, ka mayar dani sakara, ka mayar da ni mai son zuciya, da wanne idanu zan kalli iyayen Hafsat. Yarinyar da ka yaudara ta aureka ba tareda sanin abun da yake faruwa a rayuwarka ba, ka rufeta amma daga baya da ta samu zab'i tayi min alfarma ta zauna da kai amma da yake kai butulu ne shine ya ka rabu da ita saboda matarka ta dawo. Na rasa da wasu kalmomi zanyi tur da Allah wadai da abun da ka aikata." Hisham yace, "Momcy yaron da yake KAMANNI da ni, ina ganin D'ana ne idan ba haka ba taya zai yi KAMANNI dani sak." Momcy ta daka mashi tsawa tana nuna mashi tace, "Ka fitar min daga gida, tun da ka aikata abun da ranka ya ke so, nima na zare hannuwa daga lamarin nan, babu ruwana. Kuma ka saurari hukuncin da zai biyo baya domin ba zai yi maka dadi ba." ******** Najeeb yace, "What amma a lokacin ba haka kace min ba, kaine kake da laifi, amma sai ka dauki laifin baki daya ka daura akan Hafsat. Hisham, ka cuci Hafsat, shiyasa bayan faruwar abun da na je gidansu tana ganin ni ne ta koma ta kulle kofa, ko saurarena ba ta yi ba." Hisham ya dafe kai yace, "Miye mafita yanzu?" Najeeb ya ware hannuwa yace, "Ban sani ba. Kai yanzu tunanin amsar waccen kake shima. Na jinjina maka. Da ni ne ita har wanda yake hannunka sai na amshi abuna." Ya mike ya fita ba tareda ya k'ara bi ta kan Hisham dake mashi magana ba. Hisham ya rasa yadda zai yi, tun da yaga yaron a kullum yana manne a ranshi jinsa yake sosai a ransa, tun da yayi tozali da Hafsat tunaninta ya tsaya mashi a rai, da ya rufe idanu fuskarta yake gani, ya rasa gane miye yake faruwa dashi. ******** Abun yana damunsa sosai, tunaninta da tunanin yaron ya tsaya mashi a rai, ranar ya ka sa hakuri, tun da safe yake tantamar ya je ko kada ya je, yana akan hanyar komawa gida, ya juyar da motar ya nufi gidansu Hafsat, tun daga nesa ya hango mota a parker, Little Aliyu yana a saman motar yayinda Aliyu yake a tsaye yana mashi wasa, Hisham yayi parking motarsa ya fito zuwa inda suke, ya mik'a hannu wa Aliyu. Little Aliyu yace, "Abba kada ka gaisa dashi. Ba mu sanshi ba kumq makaryaci ne, ranar yayi min k'arya ya saka Ammi tayi min ihu." Aliyu ya ware idanu yace, "Little kada ka k'ara fad'in haka." Ji Hisham yayi muzanta, nauyi ya kamashi. Little Aliyu yace, "Da gaske nike, ranar yayi min k'arya ya ce ya san Ammi, Ammi ta ce ba ta sanshi ba, kuma k'arya haramun." Hisham yace, "Angel fa?" Aliyu yace, "Tana ciki, ka shiga." Yana nuna mashi kofar parlour. Hisham ya girgiza kai yace, "A'a. Zan jira ta fito." Ya zauna a bayan motarsa yayi parking a harabar gidan. Ya juya ya koma motarsa, yana ganin kiran Bilkisu ya ki d'agawa, karshe ya kashe wayar baki daya yayinda yake jin kuna a cikin ranshi, mintina biyu a tsakani ta fito tana sanye da atamfa mai golden, dinkin doguwar riga wacce ta dace da ita, ta kashe dauri tayi mashi dauri ya zauna daram, mayafinta, jikkarta da flat shoes dake a kafarta brown, saida zuciyarsa ta buga yana yaba kyawunta, tun da ta fito yake kallonta har ta k'arasa inda motar take ta sauke Little Aliyu daga kan motar ya wuce parlour yayinda Aliyu yake mata magana ta juyar da kai tana dariya. Ji Hisham yayi kishi ya kamashi, ya b'alle murfin motar ya fito, kallo daya tayi mashi ta juyar da kai tana mai tab'e baki, yace, "Angel. Ina da magana dake." Hafsat ta murtuke fuska tace, "Sai kuma aka ce maka da kowane kato nike magana, torh ba haka nike ba." Aliyu yace, "Angel ki je ki ji abun da ya ke tafe da shi." Ta murtuke fuska ba tareda ta bashi amsa ba har saida ya maimaita tace, "Shin ka manta da alkawari da kayi min." Ya hade hannuwa a waje yace, "Tuba nike ranki ya dade." Aliyu ya juya mashi yace, "Malam ka koma inda ka fito ba za ta ganka ba." Hisham yace, "Waye zai da zaka fad'a min haka." Hafsat ta tari lumfashinsa tace, "Har tambaya kake, torh a matsayinsa na wanda zan aura yake fad'a maka hakan don haka tun wuri ka ja motarka ka fitar min daga gida tun kafin na saka a daukeka kamar kayan wanki a watsar a bola." Jikinsa a sanyaye ya juya ya nufi motarsa, yana gani tana shagwab'a Aliyu yana mata magana, ta juyo tareda nufo inda ya ke, ta tsaya a gefenshi tace, "Miye?" Hisham yace, "Abun da kikayi min kin kyauta kenan, kin saka D'ana yana kirana makaryaci a gaban bare." Hafsat ta murtuke fuska tace, "Waye bare? Waye na gida? Kaine bare, Aliyu shine na gida, ka gode Allah da na manta da had'a da fad'a mashi butulcinka ba, butulu kawai. Shi wanda kake kira bare albarkacinsa ka ci na zo inda kake. D'azu kamar ki kira Little Aliyu da D'anka. Yaushe aka yi da kai cewa D'anka ne." Hisham yace, "Dukkanin wanda ya ganni ya ganshi yasan D'ana ne." Hafsat ta fashe da dariyar rainin wayo tana tab'a hannuwa tace, "Kai yanzu ba ka ji kunyar kiranshi da jininka ba, kana ina a lokacin da na dauki cikinsa na tsayin watanni tara? Kana ina a lokacin da nayi nakudarsa? Kana ina a lokacin da nike hakilon neman abun da zan ciyar da kaina a lokacin da nike da cikinsa? A lokacin da naje sanar da kai wanzuwarsa korata kayi ka kulle kofa ka dauki danginka kuka wuce London..." ya katseta yace, "Amma ai baki fad'a min ciki kike dashi ba." "Ka tsaya ka saurareni ne, ko kuma ka bani damar da zan sanar da kai abun da nike tafe dashi." "Kiyi hakuri. I'm sorry." Hafsat tayi mashi kallon rainin wayo sannan tace, "Shi sorry da kace zai gyara b'arnar da kayi min ne, ka ga Malam tun muna shaida juna ka fitar min daga gida, gidana ba wajen zuwan kowane kato bane." Yana kallonta da mamaki yace, "Kato? Gidan ki?" Kanta tsaye tace, "Gidana, idan kuma akwai kobonka a ciki sai kayi magana, ba na tunanin ka na da gadona." Hisham yayi goya hannuwa a kirji yace, "Amma yarana suna da gadonki?" "Kai yanzu baka jin kunyar kiran Little da jininka? Kaga Hisham ka fitar min daga gida ina mai taya kaine bakin da na zauna ina magana da kai." Ya ware idanu yace, "D'ana ne, gudan jini ne." Ta gane maganar da tayi yayi mashi zafi shiyasa ya kauce mata ya bata wannan amsar. Ta rike kugu tace, "Eh yana dauke da kwayar halittarka amma babu abun da ka sani akan wahalar da nayi dashi. Don haka ni ce uwarshi, ni ce ubanshi." Yace, "Ki kirashi in ganshi." Ta nuna mashi kofar parlour tace, "Ka shiga yana wajen Umma." Ya girgiza kai, "A'a." Hafsat tace, "Ohhh... Ashe kana da kunya? Nayi zaton zaka shiga ne. Tun da ka gama b'ata min lokacin sai ka san inda dare yayi maka tunda ba gidanka vane inda ka gware da cin mutunci da gadara a ciki." Yana mata magana tayi banza dashi ta wuce wajen Aliyu, ta turo baki tace, "Ka turani ya b'ata min rai, har yana da karfin halin da zai kira Little Aliyu da jininsa." Aliyu ya hade hannayensa waje guda yace, "Tuba nike MATAR ALIYU." Kiranta da yayi MATAR ALIYU ya sakata dariyar farin ciki sai kuma ta make kafad'a tace, "A'a, sai ka goya ni sannan zan hakura." Ya kanne mata ido daya yace, "Idan goyo ne kada ki damu, zan goyaki idan mukayi aure, ranar da kika zama matata zan kasance a matuk'ar farin ciki, kin sani ina matuk'ar kaunarki. Amarya a gidan Aliyu. Amarya bakya laifi." Ta juyar da kanta tana dariya. Ashraim yayi parking kusa dasu, yayi still yana kallonsu saida gabanta ya yanke ya fad'i tana kallon motar, Aliyu ya kalli motar yace, "Waye?" Muryarta tana rawa tace, "Ashraim ne." Aliyu yace, "Alright, sai munyi waya, ki kula min da kanki." Ya shige mota har mata blowing kiss. Saida ya wuce sannan ta juya zuwa motar Ashraim, ya fito yana kallonta yace, "Angel. Kina kasheni da kyawunki." Tayi dariya tana k'are fuskarta, ji tayi yace, "Waye?" Ta ware idanu tace, "Na'am. Kace?" Duk da kuwa taji abun da yace. Ashraim yace, "Wanda ya tafi. Waye?" Tace, "Ohhh. Aliyu ne. Babana." Ashraim ya gyada kai yace, "Wanda Little ya ci sunanshi." Tace, "Eh." Ya duba agogo dake a hannunsa yace, "Little Aliyu fa. In ba shi sakon shi." Ta lura kamar yanayinsa ya sauya sai taji kuma bata kyauta mashi yana sonta amma tana b'ata mashi lokaci akan Aliyu mutumin da bata da tabbacin samunsa wannan shi ake kira sakin na hannu kamun na dawa. Ta make kafada tace, "Ba zan kirashi ba nima sai ka bani sakona tunda wariyar launin fata kake nuna min." Ashraim ya ware idanu yace, "Zaki sha chocolate?" Ta gyad'a kai tana mashi shagwab'a tace, "Eh ina so." A tare sukayi dariya, ganin yana duba agogo tace, "Bari na turo maka shi. Sai anjima. Ka kula min da kanka." Ashraim yace, "Kema ki kula min da kanki." Ta shiga ciki tare da turo mashi Little Aliyu da ta samu a tsakar parlour yana buga ball, ya ruga da gudu jin Ashraim ne, babu jimawa ya dawo da katuwar leather yana nuna mata, tace, "Ina fatan kayi mashi godiya." Little Aliyu yace, "Eh. Na ce mashi na gode." Hafsat ta shafa kanshi tace, "Yauwa yaron kirki kaje ka nunawa Umma." Little Aliyu ya dauki leather din ya wuce dakin Umma. Ranar litinin bayan ta dauko Little Aliyu daga makaranta, yana gama cin abinci ya fara mata hira, "Wannan mutumin da muke KAMANNI ya je makarantarmu, ya ce shine Babana, ya saka aka maida sunana Aliyu Hisham. Ya siya min chocolate, ya ce zaizo hutun karshen mako ya fita da ni." A karo na farko a rayuwa, ta daka mashi tsawa tace, "Ka b'ace min daga gani, tun kafin inyi maka dukan tsiya. Duk wahalar da na sha da kai, yanzu daka girma ya dawo shine zaka koma mashi, butulu." Little ya fashe da kuka, tace, "Zaka tashi ko kuma sai na mareka, don kana da sunan Babana ai bashi bane. Kuma ya zo ka bishi inyi maka dukan tsiya a gidan nan." Little Aliyu ya mike da gudu yana kuka, ta bishi da mugun kallo tana bala'i tace, "Da uban miye yake takama da garin nan." **** Little Aliyu yana kuka yace, "Ammi ta min tsawa, ta ce min butulu, za ta mareni." Umma tayi matuk'ar mamaki la'akari da bata tab'a dukansa ba koda laifi yayi mata tana dariya take mashi fad'a wanda tasha mata gyara akan hakan. Tace, "Duka kuma, ba k'aramin abu kayi mata ba." Little Aliyu ya turo baki ya wuce dakinsa ganin Umma bata goya mashi baya ba, Umma tace, "Ina zaune zaka dawo ka sameni ne." Little Aliyu ya dauki wayarsa ya kira Aliyu, shiru-shiru suka nemeshi suka rasa kuma ba ya gidan Abba. Hafsat ta fara bala'i, "Idan Hisham ne ya zo ya daukeshi zai ga danyen kai, sai naga wanda ya tsaya mashi a garin nan, da shi da wanda ya tsaya mashi daidai nike da su." Aliyu ne ya kira numbarta tana d'agawa yace, "Shine kikayi wa mai sunana tsawa, kika ce mashi butulu zaki dokeshi." Ta sauke ajiyar zuciya tace, "Kuna tare?" Daga daya bangaren Aliyu yace, "Muna tare." Ta koma ta zauna tana cewa, "Na dauka Hisham ne har fara tuna rashin mutuncin da zan yi mashi." Aliyu yayi dariya yace, "Ba Hisham bane. Aliyu ne, shi wani rashin mutuncin za'ayi mashi." Kamar yana gabanta ta mak'e kafad'a tace,."Oh, Oh." Aliyu yace, "Aliyu ne, wani iri za'ayi mashi." Cike da shagwab'a tace, "Shi soyayya za'ayi mashi." Ya murmusa yace, "Na gode." Kira ne ya shigo, ta duba taga Ashraim ne, da sauri tace, "Ashraim yana kira." Aliyu yace, "Okay, ki kula da kanki." Tace, "Ka kula min da kanka." Tayi tsinke kiran tare da amsa kiran Ashraim tace, "Ranka ya dade." Daga daya bangaren Ashraim yace, "Angel. Da wa kike waya?" Tace, "Babana. Aliyu." Ashraim yayi shiru, sai a lokacin ta ankara da katob'arar da tayi, da sauri tace, "Little ne yayi min laifi nayi mashi tsawa, shine ya kirashi, muka nemeshi muka rasa, ashe Aliyu ya kira, torh shine ya kira yana sanar dani suna tare." Ashraim yace, "Okay. Yaushe zanzo?" Tace, "Kazo yanzu, yanzu nike son ganinka." Yace, "Yanzu kuma?" Tace, "Eh kayi tsuntsuwa kazo." Saida yayi murmurshi sannan yace, "Tsuntsuwa kuma, ni da bani da fuka-fukai. Ayi min afuwa, gobe in zo da kafafuna." Ta mak'e kafad'a kamar yana a gabanta sannan tace, "Shine zaka wahalar min da kanka. Indai a kafa ne kada ka zo." Ashraim ya murmusa sannan yace, "Inzo a motata?" Hafsat tace, "Ehhh." Yace, "Wacce? Ki zab'a min." Saida tayi rolling idanu sannan tace, "Idan na tuna zan fad'a maka." Yace, "Ina son ganinki. Inyi maki video call?" Saida ta kalli kanta sannan tace, "Babu damuwa." Ya tsinke kiran tareda mata video call, yana zaune a ofishinsa tana mashi shagwab'a yana biye mata, Little Aliyu ne ya shigo yana kama hannunta yace, "Ki zo in ji Abba ya rama min tsawar da kikayi min." Tayi dariya tace, "Ina zuwa Babana yana kira." Ashraim yace, "Okay. Ki bani Little." Ta mik'awa Little Aliyu wayar sannan ta wuce harabar gidan wajen Aliyu, yana ganinta ya juya baya yace, "Mun b'ata." Tace, "Tuba nike, kaina a kasa." Aliyu ya juyo yace, "Torh a daina wa Little tsawa." Tayi dariya tace, "Na daina." Aliyu ya tsura mata idanu, ta k'are fuskarta tana dariya, yace, "Kin ji dadi abunki. Da kyawunki kike koda ba ki yi kwalliya ba. Ba kwalliya bace ta ke yi maki kyau, kece ki ke yi kwalliya kyau." Yana mata video tana k'are fuskarta yana dariya har Ashraim ya gaji ya tsinke kiran bayan da Little ya bungire bacci, saida ta koma sannan ta tuna tana kira ba ya picking ta tura mashi sako yace _Busy_ duk sai taji bata kyauta ba. ********* RANAR ASABAR Ta koma bacci bayan sallar subh, wajen karfe tara na safe, Umma ta tayar da ita, tace,."Kina da bako a waje." Hafsat tace, "Bako kuma, waye?" Umma tace, "Ba su fad'a ba, ya dai ce a mota yake." Tayi jim sannan ta duro daga saman gado ta wuce bandaki tayi wanka ta jima sannan ta fito ta cancara kwalliya ta shirya cikin atamfa dinkin riga da skirt ta feshe jikinta da turaruka masu saukin kamshi, ta suri mayafi ta fita, tayi turus ganin Hisham a tsaye, tun da ta fito yake kallonta ba ya koda kyaftawa, ta murtuke fuska tace, "Aniyar kowa ta bi shi. Mutum ya daina kallona." Yayi murmushi yace, "Gorgeous. Dukkanin wannan kwalliyar ni aka yi mawa." Ji take kamar tayi kwallo dashi. Ta harareshi tace, "Ko a mafarki." Hisham ya kanne ido daya yace, "Har da kallon so." Zuciya ta kawo mata wuya ta murtuke fuska, "Da na san kaine doguwar Hijab da niqab zan saka, hakanan kato ya rink'a kallewa Aliyu mata." Ya ware idanu yace, "Nine kato." Ta taso mashi tana bala'i, "Ka godewa Allah da ban ce katon banza ba." Yace, "Ki kira min yarona nayi mashi alkawari zan kaishi Park." Hafsat ta nuna mashi kofar parlour tace, "Gaka ga gidan, ka shiga ka fito dashi." Yace, "A'a. Ki kira min shi." Tace, "A'a. Ka shiga da kanka. Umma ce a ciki, naga ba bakuwarka bace, idan kace ta baka zata baka." Yayi shiru, ta gane mai yake nufi da shirun da yayi, tace, "Ohh. Ashe kasan kunya. Sai ni da ka raina kake min haka." Ta juya ta hango Little mak'ale a kofar parlour tayi mugun kallo tace, "Zaka koma ciki ko sai naci ubanka. Ubanka nace." Da gudu Little Aliyu ya koma ciki yayinda Hisham ya ware idanu yace, "A gabana kike zagina." Ta juyo tace, "Ko zaka rama ne." Ya girgiza kai, "A'a, na gane duk a cikin so ne." Tayi mashi kallon tsana sannan tace, "Hisham ko a mafarki ka ga na ce ina sonka ban yafe ba." Ya murmusa yace, "Ina sonki Angel. Tun da baki barshi ba zan koma, tun da na ganki naji sanyi a raina." Tayi tsaki ta juya ta shige ciki, yabi bayanta da kallo yana murmurshi. Bilkisu ce ta kirashi ya d'aga yace, "Hello. Eh. Ina wajen Najeeb." A ranar ta saka security su hanashi shigowa gidan, ta hanashi ganin Little saidai ya tarar dashi a makaranta, shima tayi gargadi idan ya bishi sai tayi mashi shegen duka, abubuwa sunyi mashi yawa sai a lokacin ya k'ara tantance yana sonta, idan ya ganta tare da wani zuciyarsa ta rink'a kuna, ya kora mata samari ya fi a kirga. Ranar wani ya aika kiranta tana fitowa ta tarar Hisham yana korashi, "Nine wanda zai aureta har an saka rana." Ta ware idanu tana kallonshi, yace, "Ki tsaya inyi maki bayani." Ta girgiza kai, "Babu bayanin da zakayi koda kayi bayani bazan saurareka ba. Ashe kaine kake kora min samari. Ka janyo wa kanka, da abun da ka ke yi yanzu, da wanda kayi min shekarun baya, sai na shuka maka rashin mutunci." Ta juya ta koma ciki, kwana daya, biyu, sati daya, sati biyu, ya ga ba ta yi komai, sai da ta bari ya manta sannan ta durar mashi, yana zaune a parlour tareda boys dinsa, Abdullahi wanda ya girma sosai, Muhammad wanda yake da shekaru tara sai Sulaiman (wanda bilkisu ta haifa) sai dai ganinta yayi, ya ware idanu yayinda gabanshi ya yanke ya fad'i, yana wiki-wiki da idanu yana kallon Bilkisu wacce take zaune a daya bangaren. Hafsat ta bi yaran da kallo, Abdullahi wanda kallon sani ya ke mata, Muhammad wanda yake KAMANNI sak da ita, da Suleiman wanda Bilkisu ne sak. Bilkisu ta dubeta da mamaki tace, "Saidai ban wayeki ba?" Hafsat tana kallon Hisham tace, "Ayyerh, ai ba za ki wayeni ba, na zo makotanku ne kuma ba su nan, kishirwa nikeji ki taimaka min da ruwa." Bilkisu ta mike ta wuce kitchen, Hisham ya mike da sauri yace, "Angel. Miye haka?" Hafsat ta murtuke tace, "Ko kayi min shiru ko kuma in fayyace mata komai, dukkanin abun da zai faru ya faru, babu ruwana, ai kaine ka fara." Zaiyi magana ya hango Bilkisu tana fitowa, yayi shiru ya koma ya zauna. Bilkisu ta mik'a mata bottle water, Hafsat tace, "Sannu. Na gode." Bilkisu tace, "Yauwa." Tana fita compound, Abdullahi ya biyota, "Aunty Hafsat." Ta tsaya tare da juyowa yayinda hawaye suka ciko idanunta saida taga Muhammad a yau da taga Muhammad ta k'ara jin tsanar Hisham akan rabata da yayi da gudan jininta, tasha wahalar cikinta, ta haihuwa a wahalar ce amma ya rabata dashi babu tausayi babu tausayawa. Ta share hawayen da suka zubo mata tace, "Abdullahi. Kana lafiya?" Yace, "Lafiya lau." Tace, "Allah yayi albarka." Abdullahi yace, "Amin. Bari na tafo maki da Muhammad." Sai Hafsat ta samu kanta da tsayawa babu jimawa suka dawo tare, Muhammad yayi tsuru yana kallonta, Abdullahi yace, "Ka gaidata mamarmu ce." Muhammad yace, "Ina wuni?." Idanunta suka ciko da hawaye tana mai kallon gudan jininta, tace, "Lafiya lau. Ya kake?" Muhammad yace, "Lafiya lau." Ta juyar da kai tare da goge hawayen da suka zubo akan fuskarta Tace, "Allah yayi albarka." Yace, "Amin." Ta dubi Abdullahi tace, "Abdullahi, na gode. Na gode sosai. Ka kula min dashi." Abdullahi ya gyad'a kai. Ji tayi hawaye zasu zubo mata, ta shige mota da sauri, ta kama hanyar gida, tun da ta koma gida take tunanin Muhammad, da irin wahalar da tasha da cikinsa, har ta kasa hakuri, "Saidai duk abun da zai faru ya faru amma sai na amso yarona tunda ba wani bane yayi min nakudarsha. Da uban mi yake takama da har zai korar min da samari." (Ni kuwa na ce Hisham ya janyo wa kanshi 🤣🤣🤣). Da dare suna zaune a dinning table suna cin abincin dare, Hafsat tace, "Umma cikin satin nan zan je Abuja gidan Hajiya Babba, tare da Little da Muhammad." Umma ta dubeta na wasu dakiku tana mamakin sunan Muhammad da ta fad'a yaron da ba'a hannunta yake ba. "Muhammad kuma?" Hafsat ta gyad'a kai ba tare da ta ce komai ba, har Umma za ta yi magana sai kuma tayi shiru. Washegari, da misalin karfe sha daya na safe ta shirya cikin leshe dinkin bubu, ta kashe dauri, ta yafa mayafi akan kafad'a, ta fita a motarta kirar Range Rover da ta siya shekarar da ta wuce, kai tsaye ta wuce gidansu Hisham, tayi sa'a ta samu yaje gaida Momcy, ya mike da sauri yana kallonta yace, "Hafsat. Mi ya kawoki?" Ta murtuke fuska tace, "Muhammad na zo amsa tunda ba kai bane kayi min nakudarshi ba." Ya kalli matakalar bene yace, "Kina hauka ne." Tace, "Idan kana tantama ka hanani yarona a lokacin ne zakaga hauka ganin idanunka." Ta zauna ta daura kafa daya akan daya, ya nufo inda take ta daka mashi tsawa, "Kada ka fara ko kuma a yau in nuna maka ainihin kalata idan raina ya b'aci. Try me, I will do my worst. Saidai a mutu, rashin mutunci ne kowa ya iya." Sautin takon Momcy ta tilasta mashi komawa mazauninsa, Hafsat ta gyara zamanta tare da cire kafa da ta d'aura akan daya. Momcy ganin Hafsat, ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi tace, "Bakuwa mukayi. Hafsat." Hafsat ta rusuna tace, "Momcy, Ina kwana? Mun sameku lafiya?" Momcy ta zauna akan kujera mai daukar mutum ukku tana mai amsawa da, "Lafiya lau." Ta maida dubanta akan Hisham da ke mazurai tace, "Zaka tashi ka bamu waje ko kuma mu tashi mubar maka falon." Ba don ransa yaso ba ya mike ya fita balcony. Momcy ta ce, "Angel na rasa da wani idanu zan kalleki, kunyarki ta ke ji akan abubuwan da Hisham yayi maki na butulci. Ina mai baki hakuri akan abubuwan da suka faru. Ban san gaskiyar abun da ya faru ba sai watanni baya da suka wuce. Ce min yayi zaman yaki dadi a tsakaninku shine kika nemi saki kika bar mashi yaro, sai da ya ga Little Aliyu sannan ya ke fad'a min gaskiya, raina ya b'aci sosai na ce na fidda hannuna tun da har ya mayar da ni mutumiyar banza. Ki gaida Ummarki, ki bata hakuri a madadina, kuma zanzo har gida." Hafsat tace, "Za ta ji. Momcy nazo ne domin in amshi Muhammad ina so zan je da su Abuja." Momcy tace, "Babu damuwa." Ta d'aga waya ta kira numbar Hisham. Hisham ya dawo, kallo daya Hafsat tayi mashi ta dauke kai, Momcy tace, "Hisham ka kira a kawo Muhammad za ta je wani gari da shi." Hisham ya zaro idanu jin abun da tace, yace, "Muhammad kuma? Ina zasuje?" Momcy ta murtuke fuskarta tace, "Ka tutsiyeni in fad'a maka, zaka kira a kawoshi su wuce ko kuwa sai na sab'a maka KAMANNI." Hisham yace, "Amma Momcy na cancanci in san inda za ta je min da D'a." Momcy ta fusata tace, "Ohh ita kuma bata cancanta ba shiyasa ka rabata dashi tun yana zanen goyo. Zaka kira ko kuma ban isa ba. Sai in dauko wayata in kira da kaina. Ka ce a kawo da kayanshi idan sun dawo an kai mashi sauran." Ya zaro idanu kamar zaiyi kuka yace, "Momcy ban gane ba." Momcy tace, "Daga yau Muhammad ya koma hannun mahaifiyarsa daga yau har abada. Idan kuma kana da ja inji, idan iyakata zaka nuna min." Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 16 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 Duk Ac dake a falon amma zufa ce take karyo mashi, ya juyawa Hafsat yace, "Please ki ce mata unguwar kawai kike son zuwa dashi idan kika dawo zaki maido dashi." Ta kalleshi ta watsar tace, "Ka kwaceshi a hannuna babu tausayi babu tausayawa, a yau Momcy tayi hukunci wanda shine adalci sannan kake son in bada mata kasa a idanu. Kallon uwa nuke mata har gobe don haka na amsa da godiya. Momcy na gode Allah ya k'ara girma." Momcy ta murtuke fuska tana mai tsareshi da idanu, kamar zaiyi kuka ya kira, mintina talatin a tsakani direba ya shigo dashi, yana jaye da luggage, Muhammad yana biye da shi, Muhammad yayi hugging Momcy yace, "Nayi kewarki kaka." Momcy tayi murmurshi tace, "Nima nayi kewarki," ta nuna mashi Hafsat sannan tace, "Wannan ita ce mahaifiyarki ka je ka gaidata." Ya gane ita ce wacce taje gidansu watan da ya wuce har Abdullahi ya sanar dashi itace Mamarshi. Ya isa inda take yace, "Ina wuni?" Tayi murmurshi mai tafowa da hawaye tana kallon gudan jininta tace, "Kana lafiya?" Muhammad yace, "Lafiya lau." Momcy tace, "Itace mamarka, za ku je unguwa tare, ban da rashin ji, ka rink'a jin maganarta. Tasha wahala sosai lokacin da take dauke da cikinka har hauka tayi." Muhammad ya gyad'a kai, kwatankwacin abun da Abdullahi ya sanar dashi kenan duk da karancin shekarunsa amma ya tsinci wasu abubuwan a ciki. Hafsat ta rasa da kalmomin da zatayi amfani dasu tayi mata godiya akan karamci da tayi mata, tace, "Na gode sosai Momcy. Allah ya k'ara girma." Momcy tace, "Amin. Ki fad'awa Ummarki ina nan zuwa." "Fatima fa?" Tambaya ganin tunda tazo bata ga gilmawarta ba. Momcy tace, "Fatima tayi aure a London, a zamanmu a can ta samu miji bature." Hafsat tace, "Okay a bani numbarta." Muhammad yayi hugging Hisham yace, "Mun tafi Abbu." Hisham yace, "Allah ya tsare hanya." Hafsat ta kama hannunsa suka fita. Sai a lokacin Hisham ya samu zarafin tada maganar yace, "Momcy. Amma Bilkisu fa?" Momcy ta murtuke fuskarta tace, "Ita ta yi mata rainon ciki ko kuma ita ce tayi mata nakudarsa. Tambayarka nike, ita tayi mata rainon cikin ko nakuda. Kuma koda wasa naji wani labarin sai na sab'a maka." Washegari Hafsat ta wuce dasu Kano inda sukayi boarding flight zuwa Abuja, Hisham ya dameta da kira ta saka numbarsa a blacklist, saida su ka yi watanni biyu sannan suka baro Abuja ta biya ta sokoto ta barsu a wajen Jalila sannan ta dawo Katsina ita kadai. Washegarin da ta dawo sai ga Hisham kamar wanda aka jefo, ganin da gaske ba tareda yaran tazo ba, yace, "Hafsat ina kika kai min yarana?" Ta murtuke fuska tace, "Ka kawo sauran kayan Muhammad ne. Momcy ta yanke hukunci akan yaro ya dawo a hannuna don haka babu abun da zaka fad'a da zai saka na daukeshi na baka." Yace, "Ina kika kai min yara?" Tace, "Ban sani ba ka je ka tafo da wanda ya tsaya maka ya amsar maka. Tun da har ka ce ba zan zauna lafiya ba, kaima ka yi kadan ka zauna lafiya. Dani kake magana." Yana mata magana tayi mashi banza ta koma ciki, yana ji yana gani ya juya ya koma gida, yana matuk'ar jin kunyar Umma bazai iya had'a idanu da ita ba. Umma take sanar da ita zuwan Momcy da hakuri da ta bata akan bai sanar da ita gaskiya ba, Hafsat tace, "Momcy uwa ce ta gari." Umma tace, "Kwarai kuwa, matar bata da damuwa, yaro ne ka haifeshi baka haifi halinsa ba." Sati daya, sati biyu da dawowarta amma har zuwa wannan lokacin bata niyyar dawo da yaran ko ta sanar dashi inda suke, idan yayi mata tace, "Ka aiko mai karfin gidanka ya zo ya tambayar maka." Yace, "Idan kin isa kice gidanmu." Tayi murmurshi mai ciwo tace, "Gidanku gidan Momcy kenan ita kuma uwa take a wajena. Allah ya saka mata da gidan aljanna domin uwa ce ta gari mai adalci ko kuma hakan zai b'ata nata rai." ***** Hisham ya tusa Momcy a gaba yace, "Momcy please ki kira Hafsat ta fad'a min inda ta kai min yarana, ta fad'a min inda suke, na cancanci insan inda suke." Da gatse Momcy tace, "Gaskiya ne, ka cancanci kasan inda suke." Abun da bai sani ba shine Hafsat ta sanar da ita inda suke har waya takeyi dasu. Hisham yace, "Kin gani." Momcy tace, "Hakane bari a kirata ta fad'i inda ta kaisu." Ta janyo wayarta ta kira numbar Hafsat, bayan ta amsa gaisuwar da Hafsat tayi mata tace, "Jiya nayi waya dasu Muhammad sun fad'a min sai hutunsu ya k'are sannan zasu dawo." Hisham ya ware idanu fuskarsa dauke da mamaki jin abun da Momcy ta fad'a a waya. Daga daya bangaren Hafsat tace, "Hakane." Momcy tace, "Hafsat waye ya dauki cikin Muhammad tsawon watanni takwas?" Hafsat bata gane dalilin tambayar amma sai tace, "Ni." Wanda shine amsar tambayar da tayi mata. Momcy ta jefo tambaya ta biyu, "Hafsat waye yasha wahalar cikin har na tsayin watanni takwas?" Hafsat mamaki ya kamata amma sai tace, "Ni." "Shin akwai wanda ya tayaki nakudarsa?" Momcy ta jefa mata tambaya ta ukku. Hafsat tace, "Babu." Momcy tace, "Don haka kamar yadda na fad'a maki hukunci da na yanke yana nan idan sun dawo ki rikeshi a wajenki, tsakaninshi da Hisham saidai ziyara shima idan kin amince, ko kallon banza yayi maki ki kirani yaga yadda zamu kwashe dashi." Hafsat tace, "Na gode sosai Momcy. Allah ya k'ara girma." Momcy ta amsa da, "Amin. Allah yayi albarka." Hafsat tace, "Amin." "Ki gaida Ummarki da Abbanki." "Za su ji." Momcy ta tsinke kiran, Hisham yace, "Amma Momcy." ta daka mashi tsawa sannan tace, "Idan ka isa ka tada maganar kaga yadda zamu kwashe da kai. Kadan nayi maka idan aka duba girman zalunci da butulci da aikata mata don haka ka gode Allah. Consider yourself lucky da ban ce ta hanaka ganin yaran ba. Ka tashi ka bani wuri." Zaiyi magana tayi mashi tsawa, ya mike ya fita. Bilkisu har ta gaji da tambaya. Hisham yana ji yana gani tsakaninshi da yaran saidai ziyara ko kuma hutun karshen mako ya fita dasu. Momcy ta tusa Hisham a gaba yaje yaba Umma hakuri akan abun da ya faru, ta saka aka rakashi ya gaida Abba, daga wannan ranar ya soma shiga har cikin gidan. Mostly zaka sameshi a gidan ya kasa ya tsare, yana fakar idanu yana korarwa Hafsat samari, tace ya fitar mata daga gida, yace bai fita tunda Umma tana ciki, suyi ta fad'a. A ranar da ta kira ta sanar da Momcy korar mata samari da yake a ranar ne yaga b'acin ranta, ta inda take shiga bata nan take fita ba, ta tusa keyarsa har gidansu Hafsat, ta nemi ganin Hafsat. Momcy tace, "Hafsat shin baki da hankali ne da har kika sakar mashi fuska yake korar maki samari, a yau ya ce min yana sonki. Shin kin shirya komawa gidansa ne? Ina son inji ne domin in yabawa shashancinki." Hafsat ta girgiza kai tace, "Bayan abun da yayi min koda shine autan maza na yafeshi koda kuwa zan mutu babu aure. Aliyu shine wanda nike so shine wanda zan aura." Momcy ta juya wa Hisham tace, "Na gode Allah da tayi wa kanta karatun ta nutsu a kanka domin koda idan nice na haifeta tace zata koma gidanka sai na kaita gidan mahaukata an duba kwakwalwarta sannan. Na sani saboda ni suka bari kake shigowa amma ka rasa da abun da zaka biyani dashi sai korar mata manema don haka a yau na hana daga yau idan yazo wajen yaransa ya tsaya a compound, su kasa a saka maku idanu a kansa domin bamu san wata tsiyar zai kulla a gaba." Ta mike ta fita. ***** Tun daga ranar Bilkisu ta kasa gane kansa a kullum cikin tunani yake, tunanin Hafsat ne manne a cikin zuciyarsa, sai a yanzu ya gane matuk'ar son da yake mata, idan ya ganta tare da wani ji yake kamar zuciyarsa za ta fashe, idan ya ganta tana murmushi wa wani ji yake kamar zuciyarsa zata tarwatse, ya ganta a kusa dashi shine farin cikinsa koda kuwa bak'ar magana ce za ta fad'a mashi. Hankalin Bilkisu ya tashi ganin da sannu da sannu ciwo yake cinsa, yana da damuwa amma tayi tambayar duniya bai fad'a mata ba, ranar da ta tutsiyeshi a gaba akan ya fad'a mata gaskiya, ganin ba zata fitar mashi daga daki ba ya janyota waje ya danna makulli, tana knocking tana mashi magana yayi mata banza da ita. Ganinshi a cikin damuwa yana tada mata hankali, tana matuk'ar sonshi, bata da burin ganinsa a cikin damuwa, ranar yaje ya tarar da Hafsat tare da Aliyu, ya dawo gida ranshi a b'ace, Bilkisu ta tareshi da fara'arta tana sanar dashi abincinsa yana akan dinning table. Tsawa yayi mata, a fusace yace,."Na ce maki ban ci, ana dole ne. Ki je ki zuba a shara." Bilkisu tayi mutuwar tsaye tana bin bayanshi da kallo, mijinta da yake matuk'ar kaunarta, mijinta da yake bata kulawa shine ya koma haka, bata gane mashi kamar an sauya mata shi. Washegari taje har gida ta sanar da Momcy abun da yake faruwa. Momcy ta fayyace mata komai akan abun da ya faru tun daga haduwar Hisham da Hafsat har rana irin ta yau. Bilkisu tayi still tana wiki-wiki da idanu yayinda baki daya jikinta yake rawa, ta janyo maganinta tasha, ta mike tace, "Na wuce Momcy." Momcy tace, "Ki gaida gida. Ki cigaba da hakuri." Bilkisu bata nuna mashi tasan gaskiya ba, ta daina shige mashi idan ba ya a cikin yanayi mai kyau, itace kullum a cikin damuwa, idan ta tuna abun baki daya jikinta rawa yake, tsoro ya kamata, ta rasa yadda zatayi ta ceci mijinta daga halin da yake ciki. ********* Hafsat tana zaune a parlour ana mata lalle, ta jiyo muryar Bilkisu a tsakar gida tana gaida Umma, tayi still tana tantamar anya kuwa ta jiyo daidai ko kuma kunnanta ne yake mata gizo idan ba haka ba miye zai kawo Bilkisun Hisham har gidan. Umma tayi still tana kallon Bilkisu sai kuma tace, "Lafiya lau. Ki zauna." Bilkisu ta zauna a gefen tabarma yayinda Muhammad tun da ya ganta ya manne mata, Bilkisu tace, "Matar Hisham ce, Bilkisu." Umma ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi tace, "Sai yanzu na gane. Kuna lafiya?" Bilkisu tace, "Lafiya lau. Little, zo." Ganin yaron baije ba, Umma tace, "Aliyu, kazo ka gaidata." Little Aliyu yace, "She is stranger, Right? Ammi tayi min fad'a." Umma tayi mashi dakuwa tace, "Karka k'ara min wannan yaren, ni ina nike jinsa." Bilkisu tayi murmurshi, Little yace, "Ina wuni?" Bilkisu tace, "Kana lafiya?" Yayinda ta tsura mashi idanu ganin matuk'ar KAMANNI da yake yi da Hisham kamar kobo da kobo. Umma tace, "Hisham mutumina, d'azu yana nan muka sha hira, bai jima da tafiya ba." Bilkisu tace, "Hakane. Angel fa?" Ta tambaya. Umma tayi mata alama wa kofar shiga parlour tace, "Tana parlor ki shiga." Bilkisu ta mikawa Muhammad da Little Aliyu chocolate da tazo masu dashi. Hafsat wacce ta zubawa kofar parlour idanu, ta waresu tana kallonta, Bilkisu ta tsura mata idanu yayinda gabanta ya yanke ya fad'i ganin matuk'ar kyau da Angel take dashi, tserayyar dake a tsakaninsu banbancin a bayyane yake, the difference is clear. Mariya da ke yi wa Angel kunshi tace, "Ki shigo mana." Bilkisu ta zauna akan kujera tace, "Na gode." Mariya ta fita. Hafsat tace, "Barka da zuwa. A kawo maki ruwa?" Bilkisu tace, "A'a. Daga gida nike." Hafsat tace, "Okay. Ayyerh." Bilkisu ta lumfasa sannan tace, "Sunana Bilkisu... Matar Hisham..." Hafsat ta jinjina kai tace, "Eh na sani." Bilkisu ta damke daya hannunta da yake rawa sannan tace, "Nazo wajen ki ne akan Mijina." Hafsat ta ware idanu tace, "Ki saka ranki a idanu domin mijinki ba ya a gabana koda daura min shi aka yi a kafa zan kwance in gudu da kafafuna." Bilkisu tace, "Hafsat. Hisham yana sonki, yana matuk'ar sonki. Momcy ta sanar da ni dukkanin abubuwan da suke faruwa. Dukkanin abubuwan da suka faru a sanadina ne, ina mai baki hakuri akan hakan. Hisham yana cikin damuwa, yana matuk'ar sonki, ki taimakeni ki yarda ki aureshi." Hafsat tayi murmurshi mai ciwo sannan tace, "Ciwon y'a mace na y'a mace ne, amma abun da kike nunawa a yanzu son zuciya ne, da bakinki kika ce ya fad'a maki abun da ya faru amma har kika samu karfin gwuwa na zuwa inda nike da wannan magana. In tambayeki mana, idan kece yayi wa abun da yayi min zaki koma gidansa, ya samu damarsa yayi wasa da ita, a lokacin an bani zab'i kuma na zab'i zama dashi saboda ina son in kyautata amma shi da ya samu zab'i watsar dani yayi, yayi min butulci. Godiya wa Aliyu wanda ya tsaya a lokacin da ban san halin da zai shiga ba." Bilkisu ta hade hannayenta waje guda alamar roko sannan tace, "Please. Hisham yana a cikin wani hali, idan baki aureshi ba zai iya shiga matsananciyar damuwa." Hafsat ta d'aga mata hannu tace, "Kinga maganar gaskiya muyi ta da gaskiya, mijinki ne bazan aura ba, akwai wanda zan aura Aliyu Muhammad, na tabbata kin sanshi." Bilkisu ta cigaba da rokonta, "Amma Hisham yana matuk'ar sonki." Hafsat tayi murmurshi mai ciwo sannan tace, "Aliyu yana matuk'ar sona, kada ki zama mai bakin ciki mana, na fad'a maki ina da wanda zan aura Aliyu Muhammad, kin sanshi, ya fi mijinki kyau, ya fi mijinki nutsuwa, ya fi mijinki kudi, ya fi mijinki sona, don haka ba zanyi wa kaina salalar tsiya ba. Kema saidai ki so kanki amma kin san Aliyu ya fi mijinki komai, bugu da kari shine wamda ya kula dani a lokacin da mijinki ya watsar dani. Bayan dukkanin abun da ya faru ko kece a mazaunina aka ce ki zab'a ba zaki zab'i Hisham ba," ji tayi hawaye sun zubo mata tana tuna abubuwan da yayi mata a shekarun baya, ta saka hannu ta share hawayen tace, "Bilkisu mijinki Hisham butulu ne, marar tausayi, don haka please ban da bakin ciki, kiji da mijinki nu kuma in auri wanda ya fi sona, namiji mai nutsuwa. Mijinki Hisham tsoro yake bani domin ba ya da tabbas. Kiyi hakuri amma bazan iya auren mijinki ba, na barki lafiya. Shawarar da zan baki itace kije ki kula da mijinki ki fad'a mashi gaskiya akan ya manta dani" Ta mike ta wuce saman bene. ******* Ashraim yayi parking motarsa, Hafsat ta bude backseat Little Aliyu da Muhammad suka shiga sannan ta zauna gefen direba, ya ja motar zuwa katuwar shopping mall, da kanshi ya bude bangaren da take ta fito, suka wuce ciki tana rike da hannun Little Aliyu, yana rike da hannun Muhammad. Ashraim yana jan trolley yayinda Hafsat da yaran suke daukar dukkanin abun da yayi masu suna sakawa, suna sanye da shadda iri daya dinkin babbar riga. Ashraim ya biya aka saka masu kaya a booth suka kama hanyar gida, wayarta ce tayi ringing tana dubawa taga Aliyu, ta manta tana tare da Ashraim tace, "Hello, love." Gabanta ne ya yanke ya fad'i tunawa da Ashraim dake a gefenta yana tuka motar, ta wayance tace, "Jalila, k'awata. Ya ake ciki? Ok zan kiraki, anjima. Ina tare da ranka shi d'ad'e." ******* Aliyu ya zubawa wayar idanu da damuwa kwance akan fuskarsa, yana sonta, yana matuk'ar sonta, amma Ummi tayi mashi katanga da aurenta, ya dafe zuciyarsa dake mashi matsanancin ciwo. Batuul ta sameshi a wannan halin kamar ba zatayi magana sai kuma ta zauna, tace, "Miye?" Yayi shiru. Bata takura ba ta mike tana tafiya tana magana, "Ka bar dawo min gida da damuwar wata idan har kana sonta kayi yaki a kanta, bana tsoron kishiya ko gudunta, damuwa ce bana so." Ya bita bayanta da kallo har ta fita, ya kira numbar Hafsat ta sameta a kashe, bai ga laifinta don ta kula wasu, lokaci yayi da ya kamata ya daina yaudarar kansa, lokaci yayi da ya kamata ya barta tayi aure. ***** Tana a balcony maid ta sameta, ta dubeta da mamaki tace, "Miye?" Safiyya tace, "Wata mata ce take sallama dake." Da mamaki tace, "Take sallama dani ko kuma take jirana a parlour." Safiyya ta girgiza kai tace, "A'a tana a bakin titi a motarta taki shigowa." Tayi matuk'ar mamaki saidai bata san dalilin wacce ta aiko na kin shigowar ba wannan ya saka ta warware mayafi dake a saman kanta ta yaneshi ta fita. Tayi turus ganin Bilkisu ce wacce take sallama, tace, "Ki shigo." Bilkisu ta fito daga mota tana mai girgiza kai tace, "A'a ba sai na shiga ba, na dawo ne akan maganar ranar nan, Hisham yana cikin damuwa, sonki ya hanamu farin cikin kullum yana cikin damuwa da fushi, abu kadan zai fara fad'a ba ya ji ba ya gani, please ki yarda ki aureshi bana son in rasashi." Hafsat tayi dariya tace, "Nana kina da abun dariya, yanzu da bakinki kike fad'a min matsalolin da kike samu dashi amma shine har kike rokona in aureshi. Malama kije kiji da mijinki wannan MATAR ALIYU ce. Idan har kina sona kiyi min addu'a akan Allah ya bani Aliyu." Bilkisu tace, "Idan kuma Hisham ne alherinki." Hafsat tayi murmurshi tace, "Zan amsa da godiya domin shine ma fi sani akan abun da yafi zama alheri a rayuwa don haka kije gida ki nutsu kiyi tunani akan hanyar zaki bullowa matsalar da kike fuskanta a gidanki. MATAR ALIYU nike ba Hisham ba. Na barki lafiya." Washegari tana kwance akan gado tana waya da Ashraim, Little Aliyu ya shigo yana video call da Aliyu, ya mik'a mata wayar yace, "Abba ne." Ta manta da akan waya take da Ashraim. Ta amshi wayar ta saki baki suna hirar soyayya. Aliyu ya d'aga mata hannu yace, "Barka da wannan lokacin gimbiyata." Ta gane barkwanci yake ji tayi dariya tace, "Barka da warhaka yariman zuciyata. MATAR ALIYU tana gaishe da Aliyu." Yaja lumfashi yana mai tsura mata idanu yace, "Nayi kewarki." Tace, "Nima nayi kewarka." Dukkanin wannan hirar da takeyi Ashraim da har lokacin bai tsinke kiran ba yana ji. Daga daya bangaren Aliyu yace, "Yaushe ne MATAR ALIYU za ta yi min kwalliya in zo in ganni." Tayi mashi fari da idanu tace, "Dukkanin lokacin da Aliyu yake so MATAR ALIYU za ta yi mashi kwalliya ya zo ya gani." Sun jima akan wayar dukkanin hirar da sukayi akan kunnan Ashraim, jin suna sallama yayi sauri ya tsinke kiran.Hafsat ta manta da waya take ta cigaba da harkokinta. washegari da marece tana kallo a parlour taji k'arar shigowar mota tayi mamaki domin babu wanda sukayi zai shigo, jim Maid ta shigo ta sanar da ita zuwan Ashraim. Tace, "Okay, ki ce mashi ina zuwa." Ta warware mayafi da tayi kallabi dashi ta yafa a kanta ta fita, yana jingine da motarsa ta tsaya a gefensa tace, "Sannu da zuwa ranka ya d'ad'e ka shammaceni sai dai kuma na ji dadin ganinka." Babu yabo babu fallasa yace, "Ina Little Aliyu da Muhammad?" Ta ce, "Suna makaranta." Ji tayi yace, "Miye a tsakaninki da Aliyu?" Saida gabanta ya yanke ya fad'i amma ta dake, tambaya ce wacce bata tab'a zatonta daga gareshi ba. Tace, "Aliyu babana, ya tsaya min a lokacin da Hisham ya gujeni. Yayi min gata a rayuwa. Na daukeshi kamar uba mahaifi." Ashraim ya dubeta da mamaki sai kuma yace, "Kina nufin wannan shine kadai abun da yake a tsakaninku." Hafsat ta samu kanta gyad'a kai duk da tasan k'arya ne, Ashraim ya girgiza kai yace, "Hafsat na so a ce kin fad'a min gaskiya. Angel, a rayuwata na tsani k'arya da wasa da hankali." Ya kunna recording na wayar da nada na video call dinta da Aliyu. "Hafsat na soki a shekarun baya kuma har yanzu ina sonki saidai na lura ba tani kikeyi ba, a kullum idan nayi maki maganar aure sai ki ce in dakata. Hafsat zuciyarki tana wajen Aliyu don haka na hakura dake, ina maki fatan alheri a rayuwa." Tana kiran sunanshi yayi banza da ita, ya shige motarsa ya wuce, tunda ranar bai k'ara kiranta ba idan ta kirashi bata samu, tayi kuka har ta gode Allah, wannan shine abun da Jalila take guje mata, she brought it upon herself, ta janyo wa kanta da kanta, ta kori wanda yake shirye da aurenta, akan wanda mahaifiyarsa tace ko bayan ranta ya aureta bata yafe ba. Tayi matuk'ar nadama abun da ta aikata wanda hausawa suke kira da 'Sakin na hannu kamun na dawa' ***** Kwana biyu Aliyu ya lura da ta daina mashi maganar Ashraim yana son ya tambayeta amma yana tsoron kada abun da yake zargi ya zama gaskiya, dukkanin samarin Hafsat shine sanadin rabuwarta dasu, shine sanadin da ya saka har yanzu ba tayi aure ba. Aliyu ya tsareta da idanu yace, "Ina Ashraim?" A karo na biyu tayi k'ok'arin kawar da hirar saidai kallon da yayi mata ne ya saka ta bashi amsa, "Na rabu dashi." Tace a takaice. Aliyu ya murtuke fuska yace, "Mi yasa kika rabu dashi?" Kanta tsaye tace, "Saboda Aliyu nike so kuma ya fahimci hakan, ya gaji da yawo da hankali da nike mashi. Bugu da kari yayi min tambaya akan abun da yake a tsakaninmu sai na zab'i da inyi mashi k'arya. Saidai kash abun da ban sani ba shine yana hujoji akan soyayya dake a tsakaninmu." Tausayinta ya kamashi yace, "Hafsat mi yasa kikayi haka? Ummana bata sonki, na sani idan nayi magana wa Alhajinmu zai bari in aureki saidai Hafsat kin sha wahala a rayuwa, kin hadu da kalubale masu yawa, ina guje maki da kiyayyar uwar miji ba." Hafsat ta fashe da kuka tace, "Amma Aliyu ina sonka." Aliyu ya ware idanu sannan yace, "Yau kuma a Aliyu nike." Ta share hawayen dake fuskarta tace, "Tun da kana so ka rabu dani ne na daina cewa Yaa Aliyu, Aliyu zan ce." Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 17 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *ZARAH GRAPHICS DESIGN AND GALLERY* *WE CREATED ALL KIND OF GRAPHICS SUCH AS: FLYER, LOGO, BANNER, INVITATION AND MORE* *WE SELLS SHADDA, ATAMFA, SHOES AND BAGS, MATERIALS, VEILS, UNDERWEAR, HIJABS AND KITCHEN UTENSILS* *CALL 09160588758 CHAT 09017040402* *Kina Buk'atar Flyer, Logo, Banner, Invitation Card Da Sauran Ayyuka Da Suka Shafi Graphics Design, Kina Son Aiki Mai Kyawu Akan Farashi Mai Rahusa, ZARAH GRAPHICS DESIGN AND GALLERY Shine Amsarki.. A ZARAH GRAPHICS DESIGN AND GALLERY Zaki Samu Tsala-tsala Da Galla-gallan Shaddoji, Atamfofi, Takalma, Jikkuna, Material, Under wears, Veils, Hijabs Da Kayan Kitchen, Kayansu Suna Da Sauki Da Rahusa, Ku Kira 09160588758 Ko Kuma Kuyi Magana Ta WhatsApp 09017040402 Domin Gwangwaje Kanku Da Kayansu Masu Sauki Da Rahusa.* Jin shiru ta zare wayar daga kunnanta tana mai kai kallonta akan majigin wayar, tsinke kiran yayi, ta fashe da kuka tana mai tausayawa kanta akan abun da ta aikata ta yi sanadin tafiyar Ashraim akan Aliyu, wanda ba ta da tabbacin samun sa, ta yi sakin na hannu kamun na dawa, ta yi sanadin tafiyar wanda ya ke sonta a dalilin wanda ba ta da tabbacin samu. Tun daga ranar ba su k'ara waya ba, idan ta kira numbarsa ba ta samu, ta shiga damuwa sosai, ta rame, ba ta iya cin abincin kirki sai dai ta tsakura kadan ta bar ragowa. Har Umma ta lura ta tusata a gaba tana tambayarta abun da ya ke faruwa, ta share hawayen da su ke zubo mata ta ce, "Ashraim ya tambayi abun da ya ke tsakanina da Aliyu na yi mashi k'arya, a tunanina bai fahimci komai ba, ashe har hujja a yana da ita, ya ce ya tsani k'arya, ya ce ya hakura da ni. A ranar da mu ka yi waya da Aliyu na sanar da shi, tun daga ranar bai k'ara samun numbarsa ba." Ta dakata da magana tana mai fashewa da kuka sannan ta ce, "Umma na yi babban kuskure na kori wanda ya ke shirye da aurena akan wanda mahaifiyarsa ba ta kaunata." Umma ta jinjina kai, ta yi shiru na wani lokaci kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce, "Allah ya zab'a mako abun da ya fi zama alheri a gare ki duniya da lahira." Hafsat ta amsa da, "Amin." Hawaye suna zubowa daga idanunta, da sauri ta goge hawayen a dalilin shigowa da yaran su ka yi, mikewa ta yi ta haye bene ta shiga dakinta, durkushewa ta yi a kasa ta fashe da kuka idanunta akan hoton Aliyu da ke manne akan bangon dakin. Kira ya shigo wayarta kamar ba za ta duba ba sai kuma ta mika hannu ta janyo wayar ta duba, Aliyu ne, ta amsa ta yi shiru tana mai sheshshekar kuka. Daga daya bangaren muryarsa kamar wanda ya tashi daga barci ya ce, "Koda kin kira numbata ba ki samu ba karki damu kanki, zan yi tafiya da zarar na dawo zan aureki. Hafsat ni Aliyu zan aureki, wannan alkawari ne da na yi maki." Ya tsinke kiran ba tare da ya ba ta damar da za ta yi magana ba. Tun daga ranar ta fara kirgar kwanaki, kwanaki suka koma watanni har aka yi wata shidda, ta kasa hakuri ta kira numbar k'anwarsa Mufida. "Tun da yaya Aliyu ya ce min zaiyi tafiya watanni shidda kenan ban k'ara samun numbarsa ba." Mufida ta fashe da kuka, hankalin Hafsat ya tashi tana tambayarta abun da ya faru. Tana kuka ta ce, "Ya dawo daga tafiya Italy watanni biyu da suka wuce, a ranar da ya dawo yazo gida akan hanyarsa ta zuwa gidansa ya yi hatsari ya shiga doguwar suma, yana a coma na tsayin watanni hudu." Hannunta ya fara rawa, wayar ta sub'uce daga hannunta kanta ya yi mata doom. Ta zube a kasa daga nan ba ta sake sanin inda kanta ya ke ba sai dai farkawa ta yi ta tsinci kanta kwance akan gadon asibiti da karin ruwa akan hannunta. K'arar ruwa da ta ji a bandaki dake a ward din ya tabbatar mata da Umma tana a ciki. Ta yi hanzarin zare karin ruwan daga hannunta ta duro daga saman gadon ta fita. Sai dai fitowa Umma ta yi ta ga wayam. Hafsat ta taka a kafa har bakin titi ta tsayar da kekenapep ya sauketa a asibitin. "Ina kudina?" Ya tambaya ganin tana neman tafiya. Ta girgiza kai ta ce, "Babu kudi a wajena." Ya fito zai yi mata tijara, matar dake a ciki ta dakatar dashi, "Ba ka ga halin da take a ciki ba." Ya juya a fusace ya ce, "Za ki biya mata ne? Na ga ba ta sanar da ni ba ta da kudi ba har saida na sauketa, muguwa kawai." Hafsat ta yi murmushi mai ciwo, tashin hankali ne ya saka ta manta da babu kudi a hannunta. Matar ta ce, "Da ina da kudi da na biya mata." Hafsat ta yi murmushi ta ce, "Er uwa na gode..." Da sauri ya katseta, "Idan kunnenki baiji daidai ba torh cewa ta yi ba ta da kudi da ta biya maki." Hafsat ta jinjina kai ta ce, "Na ji abun da ta ce da kyau, ina ce akan kudinka ne torh zan biya." Ta juyawa matar ta ce, "Please er uwa ki ara min wayarki." Matar ta fiddo wayar daga jikka ta mik'a mata, ta amsa ta dauko application tayi logging ta mik'awa matar ta ce, "Ki saka account numbarki?" Da mamaki matar take kallonta sai kuma ta amsa ta saka, a take Hafsat ta tura mata dubu dari biyar 500k. Matar ta ware idanu ta ce, "Dubu dari biyar ne." Hafsat ta murmusa ta ce, "Ki gode Allah da ya ciyar da ke, kyakyatawan halinki na tausayi da son taimako ne ya janyo maki." Ta juyawa mai kekenapep wanda jikinsa yayi sanyi, "Nawa ne kudinka?" Ta tambaya. Ya ce, "Dari biyar." Ta juyawa matar ta ce, "Ki bashi dari biyar daidai kudinsa." Ya washe baki ya ce, "Hajjaju." Jin ta tura dubu dari biyar wa matar amma shi ta ce a ba shi naira dari biyar, ta gane nufinsa ta girgiza kai ta ce, "Duk da ka gani ina a cikin damuwa amma sai ka zab'i ka ci min mutunci har kana kirana da muguwa. Damuwa da tashin hankali ne ya sakani mantawa na hau kekenka babu kudi a jikina, ka zama mai taimakon wanda ya ke da buk'atar taimako, maganar kudi daidai kudinka zata baka." Tana gama fad'ar haka ta juya ta shiga cikin asibitin. Ya dubi matar yace, "Gaskiya sai kin bani wani abu, dubu dari biyar ake magana." Da fad'a yake maganar har da zaro idanu tana ganin haka ta fito ta ce, "Daga inda ka daukoni zuwa nan nawa ne?" Ya ce, "Naira dari." Inda zai kaita dari shidda ne wadanda sune kadai kudin da ta ke da su, ta zaro ta mik'a mashi, ya yi tsaye yana neman ya yi mata tijara, ta murtuke fuska ta ce, "Ka kwata na karfi ne, kana tab'ani zan tara maka jama'a kaci duka, rashin mutunci ka shirya kayi mata saida kaga tana da kudi ka fara washe baki, ta taimakeni ne saboda na tausaya mata, naira dari biyar shine kudinka na wajenta shine abun da ta ce in baka don haka ko kobo bazan k'ara maka a kai ba." A fusace ya ja kekensa yana mai kiranta da, "Muguwa, er wahala." Ta tsallaka titi ta ciri kudi a POS ta hau wani dan sahun yana sauketa ta bashi dubu biyar yace, "Hajiya sunyi yawa." Tace, "Kada ka damu, ka godewa Allah." Ta shiga gida. ***** Mufida da sauran k'annansa ta hango, "Ina yake?" Ta tambaya, suka nuna mata ward ya ke, suka bi ta da kallo cike da tausayi ganin babu takalma a kafarta. Ta hangoshi kwance da na'urori a jone dashi. Ji tayi kafafunta sun kasa daukarta ta durkushe a kasa tare da fashewa da kuka, ta rarrafa har wajen gadon, ta tsura mashi idanu tana kuka tana girgiza kai, Aliyu shine a kwance kamar gawa, Aliyunta. Ta mike ta isa inda Ummi take, ta ce, "Ummi ya mai jiki?" Duk da ta ji ta amma ba ta amsa ba, ta matsa kusa da ita, Ummi ta kawar da kai. Hafsat ta girgiza kai hawaye suna fita daga idanunta ta ce, "Ummi miye nayi maki da zafi har haka da kika tsaneni? Ummi miye na aikata a gareki da zafi har haka da baki sona da Aliyu bayan kuma muna kaunar junanmu? Aliyu yana sona ina sonshi, miye laifinmu a nan? Miye laifina don na kasance diyar talakawa?" Still Ummi bata tanka mata ba. Hafsat ta juya ta kalli inda Aliyu yake kwance tana mai zubar da hawaye ta ce, "Allah ya sani ina son Aliyu, ina matuk'ar son Aliyu." Ta juya ta fita tana mai zubar da hawayen tausayin kanta da kuma tausayin Aliyu. Ta tsayar da kekenapep ya kaita gida ta amshi kudi a wajen mai guard ta ba shi, shiru gidan yake kasancewar yaran suna gidansu Jalila. Ta kira Umma, hankali a tashe take tambayarta a inda take. "Umma na je asibiti ne ganin Aliyu." Umma ta ce, "Shine ba za ki sanar dani ba kin tadawa kowa hankali, ba wannan ba, shin keda baki da lafiya miye na zuwa ganin wani." Hafsat tace, "Aliyu ne...." Umma ta katseta tace, "Kina tabbacin zaiji dadi idan yaji labarin ki fizge karin ruwa kin tashi daga gadon asibiti ba tareda likita ya sakeki ba kinje ganinsa." Hafsat ta dafe kanta dake sara tace, "Umma sai kin dawo." Umma tace, "Kina nufin ba zaki dawo asibitin ba." Hafsat ta fashe da kuka tace, "Umma zan sha magani." Umma tayi jim sai kuma tace, "To shikenan zan biya in tafo da yaran." Hafsat tayi lamo akan gado tana mai zubar hawaye. Aliyu ya fi Hisham kudi saidai kuma Ashraim ya fi Aliyu kudi amma tun da take da dangin Ashraim ba su tab'a mata kallon banza ko goranta mata kasancewarta talaka ba, saidai janta a jiki da sukeyi bata manta zuwa bikin diyar yayarsa da taje taga karamci har yau tana jinjinawa karamcinsu. Kasancewarsu masu kudi na gasken gaske bai saka sunyi wulakanci sai dai halin dattako da taimako da suke dashi domin dukkanin wanda ya sansu yasan hidimarsu na taimakon mabukata, hidima wa masallatai da sauransu. ***** Mufida ta shiga ward din ta samu Ummi tayi tagumi, ta ce, "Ummi ta fito tana hawaye?" Ummi ta dubeta da damuwa kwance akan fuskarta ta ce, "Mufida ka sa had'a idanu na yi da ita saboda kunya, ina jin kunyar abubuwan da nayi mata a rayuwa. Ku zauna a wajen yayanku zanje gida in gyara abun da na b'ata da kaina." Ta mike ta fita, kai tsaye ta koma gida ta samu Alhaji Muhammad a falonsa. Da mamaki yake kallonta yace, "Wa kika bari a wajensa?" Ummi tace, "Mufida." Yayinda take tsoron abun da zaije ya dawo idan ta sanar dashi abun da ta aikata saidai fad'ar gaskiyar shine kawai mafita a gareta. "Alhaji nice na hana Aliyu auren Hafsat, a ranar ya dawo har daki ya sameni ya rokeni akan in barshi ya aureta amma na hana, ya fita a cikin damuwa wanda bana raba daya biyu shine sanadin hatsarin da yayi." Ji tayi yace, "Ki fice min daga gida har sai na nemeki." Ta zaro idanu tace, "Na'am." Ya daka mata yace, "Za ki tashi ki fice min daga gida ne ko kuma sai na kira security na saka sun watsar dake a waje." Zatayi magana ya dakatar da ita, "Za ki fita ne ko kuma sai na nuna maki cewa kowa ya iya wulakanci kuma koda wasa naji labarin kinje ko kusa warc da Aliyu yake hukuncin da zan yanke ba zaiyi maki dadi ba." Jikinta a sanyaye ta mike ta fita. Ta wuce gidan yayanta tana ji tana gani bata damar zuwa duba Aliyu saidai ta kira k'annansa taji halin da yake a ciki, ta shiga damuwa ta rame, abincin kirki ba ta iya ci, tayi matuk'ar nadama akan abubuwan da ta aikata. ******* Hafsat tana kwance akan gado tayi lamo tana son zuwa duba Aliyu amma Umma ta hanata, tayi magiya har ta gaji, k'arar shigowar motoci taji, ta fito balcony domin gani waye. Ganin mahaifiyar Aliyu ya saka gabanta faduwa ta dafe kirji tace, "Na boni, mi tazo tayi min kuma." Ta koma bedroom tayi tagumi, babu jimawa Umma ta leko tace, "Ki fito kina da baki a parlour." Ta juya ta koma. Jiki a sanyaye Hafsat tabi bayanta ta samu Umma tana a falon, ta zauna akan kujera tayi shiru tana jiran gargadi da take tunanin shine Ummi tazo tayi mata. Ga mamakinta ji tayi Ummi tace, "Hafsat ki yafe min akan abubuwan da nayi maki, na nuna maki tsani, na nuna tsama wa talaka, na manta cewa arziki da talauci duka na Alheri, nayi nadama akan abubuwan da nayi saidai kash lokaci ya kure min, yarona ma fi soyuwa a gareni yana kwance akan gadon asibiti a doguwar suma a dalilina akan abun na hanashi wanda ba haram bane. Hafsat satina biyu bana gidansu Aliyu, ina gidan yayana, mahaifinsu ya hanani zuwa ganinshi, ina zaune ina jiran tsammani akan aurena da zai iya mutuwa a kowane lokaci. Ranar da kika zo na kasa had'a idanu dake ne saboda kunyar abubuwan da na aikata maki." Ta juya wa Umma, tace, "Maman tuwo please ki tayani bata hakuri ta yafe min, kema ki yafe min, Aliyu yana matuk'ar kaunar Hafsat nice nayi mashi katanga wa aurenta kaicona, ban kyauta mashi a rayuwa ba." Hafsat tace, "Ummi ban tab'a rikeki a raina ba domin ina maki kallon uwa ne. Allah ya yafe mamu baki daya, gobe zanje in duboshi." Ummi tace, "Na gode." Ta juyawa Umma tace, "Ummar Hafsat ki yafe min abubuwan da nayi maku." Umma tace, "Babu komai, Allah ya yafe mamu baki daya." Hafsat ta raba dare tana tunani akan maganganun da Ummi ta fad'a mata, idan ta bari auren Ummi ya mutu, dukkanin sadaukarwa da Aliyu yayi ya ta fi a banza. Washegari gari ta shirya taje duba Aliyu tare da Umma da yaran, sun samu mufida ta amshi numbar Abbi a wajenta, suna dawowa gida ta kira, bai ganeta ba har saida tayi mashi kwatance. "Abbi a lokacin da nace maku nayi alkawarin aure da wani, na fad'i haka ne saboda Aliyu ya nemi alfarma a wajena, Aliyu yana yawan fad'a min cewa idan aurenku ya mutu a kansa bazai tab'a yafewa kansa ba, na rokeka da girman Allah ka bari Ummi ta dawo. Ina son Aliyu kuma nayi maka alkawari zan zauna dashi a kowane a hali, a shirye nike in aureshi koda a yau ne a yanzu. Amma na rokeka da girman Allah kayi min alfarma ka bari Ummi ta koma dakinta." Yayi jim sannan yace, "Babu damuwa, Allah yayi maki albarka." Ta amsa da, "Amin. Na gode, Allah ya k'ara girma." Washegari Ummi ta koma dakinta, ta rasa da bakin da zatayi wa Hafsat godiya. Saidai tunda ta koma gidan bata samu fuska a wajensa ba, ranar tayi karfin halin samunsa da maganar, kallo daya yayi mata yayi shiru har saida ta k'ara magana, yace, "Lokacin da yaronki yana fa lafiya goranta mata kikayi kika hanashi aurenta, sai yanzu da kikaga ba shi da maraba da gawa ne kike k'ok'arin cutarta ta hanyar lika mata aurensa, ki tashi ki bani waje." "Nayi magana ne saboda ranar da Hafsat ta sameni a asibiti da bakinta ta fad'a min cewa tana matuk'ar sonsa hat a wannan lokacin, yana daya daga cikin abun da ya saka jikina ya k'ara sanyi duba na gujeta dashi a lokacin da yake da lafiya amma wannan bai saka ta gujeshi a yanzu ba." Tana fad'in haka ta mike ta fita, tayi babban kuskure, ta sani daidaituwar al'amurra a tsakanin ta da Alhaji Muhammad zai dauki lokaci, burinta shine ta cika burin Hafsat da Aliyu, ta shaida aurensu. ********* Washegari Hafsat taje duba Aliyu ta samu kiran Malam Jafaru mahaifin Jalila, akan taje gida yana nemanta a lokaci, ba ta yi kasa a gwuwa ba taja motarta ta kama hanya, motoci ta samu a harabar gidan wanda ya matuk'ar bata mamaki tayi parking motarta ta shiga ciki. Ta samu Mama a sama ta gaishe da ita, ta amsa da kulawa tace, "Sannu kin sha hanya, kije yana falon baki idan kun gama ki dawo kici abinci mawa nayi da miya." Hafsat ta ware idanu tace, "Kai, har guzuri zanyi, Mama you are life saver." Tayi kasa da kanta tana sauraronsu, Alhaji Muhammad ya lumfasa sannan yace, "Hafsat a ranar kin rokeki akan inyi maki alfarma in maidata kuma na mayar da ita. Nima a yau nazo ina rokonki da girman Allah kiyi min alfarma ki fad'a min gaskiya akan tambayar da zanyi maki, kada kiji kunyata ko nauyina ki cuci kanki. Hafsat shin akwai wanda kuka daidaita dashi a yanzu na maganar aure?" Ta girgiza kai tace, "Babu..." "Ashraim fa?" Ya tambaya tayi mamakin jin tambayar saida tayi jim sannan ta ce, "Ya rabu dani saboda ya fahimci ba shi nike so, wanda nike so daban." "Waye kike so?" Ya tambaya. Kamar ba zatayi magana sai kuma tace, "Aliyu." Yace, "Amma Aliyu ba shi da lafiya, mutumin da yake kwance kamar gawa, ba'a da tabbacin abun da zai tashi dashi ko kuma lokacin da zai tashi. Shin ba ki gujewa kanki zaman takaba? Shin ba ki gujewa kanki zama jiran wanda baki san ranar farkawarsa ba? Da yarintarki ko ba Ashraim zaki samu miji wanda yake sonki inda hankalinki basu kwanta." Tace, "Saidai kash Aliyu ne a zuciyata, ita zuciya tana da son mai kyautata mata, koda Aliyu zai shekara hamsin a haka, a shirye nike da aurensa, Aliyu nike so, shi nike so, ina da tabbaci akan idan nice a wannan halin bazai gujeni ba." Ta mike ta fita. Ta samu Mama a babban falo, babu jimawa Baba ya shigo ya zauna yana mai sanar da ita yadda sukayi. "Ya nemi a d'aura auren a sati mai zuwa? Mi kike gani?" Ta gyad'a kai tace, "Allah ya bamu zaman lafiya." Suka amsa da, "Amin." "Abbanki fa kina ganin mu yanke hukunci ba tare da tuntubarsa ba?" Baba ya tambaya. Hafsat tayi murmurshi tace, "Mama kiji baba wai tambaya yake. Mama a yanzu a garin nan Abbana ba ya da wani amini da ya wuce Baba." Mama tace, "Hakane kuma. Malam dukkanin hukuncin da ka yanke ka sani bazai ce komai ba." Baba yace, "To shikenan." Ya koma falon baki wajensu Alhaji Muhammad. Mama ta zubowa Hafsat masa da miya ta gyara zama akan carpet ta ci ta koshi ta kora da zubo. Ta gama suka sha hira da Mama. Hafsat ta kira Jalila tana mata tsiya, "Yarinya kinyi missing kin gani a gaban Mama ina ganin gata masa da miya in gaya maki naci har babu waje." Jalila tace, "Shine sai kin kira kinyi min gori." Hafsat tayi dariya tace, "Har kin bani tausayi koda yake bari na dauki hoto in tura maki." Daga daya bangaren Jalila tace, "Sai inja Allah ya isa." Hafsat tayi dariya tace, "Saboda kinga na samu gata, ke kuma sai kin shiga kitchen kinyi, yarinya ina gaya maki girkin Mama duniya ne har guzuri zanyi, in shige da abuna daki inyi kurmusu." Jalila tace, "Sai kikayi rashin sa'a ina da numbarsu, yanzu zan kira in fad'awa yarana kina zuwa su dauke abincin su cinye na basu, koda ban ci ba idan yarana suka ci kamar na ci, bugu da kari sun ayi halin rowa a gidansu." Hafsat ta zaro idanu tace, "Kai! Kyauta da abun wani." Tace, "Mama kinji ta wai labari zata kaiwa yaranta idan naje tayi masu kyautarsa." Mama tayi dariyarsu ta manya tace, "Idan Masa ce bata had'a fad'a kowa da kowa zai samu." Hafsat tace, "Jalila kinji kowa da kowa zai samu, ban dake." Tana dariyar shakiyanci. Sun jima suna waya ta sanar da ita abun da ya faru. Jalila ta tayata murna sosai tare da masu fatan alheri domin ita shaida ce akan matuk'ar son da Hafsat ta ke yi wa Aliyu, ita shaida ce akan matuk'ar son da Aliyu ya ke yi wa Hafsat. Saida marece Hafsat ta wuce gida da cooler niki-niki, abincin dare da basuyi ba a gidan kenan, masar Mama ta wadatar. Sati guda a tsakani Al'ummar musulmai, en uwa da abokan arziki suka shaida daurin auren Aliyu Muhammad tare da Hafsat Haruna (Angel), daurin aure da ya samu halartar mutane masu yawa, manyan masu kudi, mutane da yawa sunyi mamaki da al'ajabi duba da angon yana a doguwar suma wanda babu tabbacin ranar tashinsa, suna jinjina amaryar tayi matuk'ar k'ok'ari, ta nuna sadaukarwa. Hafsat ta tare a asibiti jinyarsa, Batuul tana wuni saidai dare yana yi take wucewa gida. Hafsat ce a gaba a kula dashi, itace take mashi komai, ba ta tab'a korafi, Aliyu yayi mata abun da ba zata tab'a mashi butulci ba, tayi mashi kaunar da bata tab'a wa wani ba. (INA LABARIN HISHAM?) ********* Tun bayan auren Hafsat da Aliyu. Bilkisu ta kasa gane kan Hisham abubuwan sun k'aru, abu kadan zai fara fad'a yana tumfar baki, kullum shine cikin damuwa da tunani, idan tayi magana ya balbaleta da fad'a, yaronta Suleiman bai isa ya rab'eshi zai fara fad'a yana zare idanu yaron ya dameshi. Ta gama abinci ta jera akan dinning table ta caba ado ta zauna a parlour tana jiran dawowarsa, ko kallon inda take baiyi ballantana amsa gaisuwarta da sannu da zuwa da ta tarbeshi dashi. Ya raba ta gefenta ya wuce upstairs, ba ta yi kasa a gwuwa ba tabi bayanshi, yana zaune a gefen gado tayi still tare da kiran sunansa, "Hisham." Ya d'ago da idanunsa da suka sauya launi yace, "Miye? Kin zo ne ki k'ara min akan damuwa da nike da ita, huh, ki fice min daga daki." Tace, "Amma ba ka ci abinci ba." Ya daka mata tsawa saida ta razana tayi baya da sauri, ya mike yana durfafo inda take kamar mayuwacin zaki yace, "Sai kuma aka ce dole sai abincinki ne zan ci, huh, na ce ki b'ace min daga gani." Tace, "Hisham kai mijina ne, ni kuma matarka, idan ban tambayeka damuwarka ba waye zai tambaya, nice muke zaune a gidan nan tare, Hisham tsoro kake bani a yanzu." Da hannu daya yaja ya wurgar a kofar daki, "Idan zaman da ni baki iyawa sai ki tattara ki wuce gidanku babu dole." Yaja kofa ya rufe har da murza makulli. Jiki a sanyaye ta koma parlour, saidai bayar da abincin tayi, ta rasa abun da yake mata dadi, tayi tagumi a parlour har dare bai fito ba. Ta wuce sama ta kwankwasa, ta k'ara kwankwasa, "Abbansu." Da tsawa yace, "Miye kuma?" Tace, "Tun d'azu baka fito ba." Saida ya k'ara mata wata tsawar sannan yace, "Sai kuma aka ce dolene sai na fito zaki wuce daga nan ko kuma sai na fito na watsar dake a compound na kulle kofa tukunna." Za ta yi magana sai kuma ta fasa ta juya ta koma dakinta yunwa takeji sosai amma ta kasa saka komai a bakinta saboda damuwar halin da Hisham yake a ciki. Tsakiyar dare matsananciyar yunwa ta tayar da ita dolenta ta shiga kitchen ta girka abincin taci har zata wuce dakinsa sai kuma ta dawo ta kanga kunne akan kofar, sheshshekar kuka taji, tace, "Abbansu kuka kake ne?" Ya bamko kofar ya kama hannunta ya wurgar da ita compound ya maida kofa yayi locking gashi kuma kofar baya ta kitchen a kulle take. Tayi tsaye tana zullumin yaro da ta bari a bedroom, tana knocking amma shiru har ta gaji ta sulale a kasa tana mai fashewa da kuka, haka ta kwana a zaune a harabar gidan, hankalinta ya rabu gida biyu a tsakanin tunanin halin da Suleiman yake a ciki, ya farka? Miye zaiyi idan bai ganta ba? Cikon ikon Allah ya farka ya sauko falo tana jin motsi ta ce, "Waye a nan?" Suleiman yace, "Nine Momma." Da sauri tace, "Bude min kofa." Yace, "Waye ya rufe maki kofa Momma." "Na fito ta rufe." Tayi mashi k'arya. Ya bude mata kofa ta shiga tana tambayarta ta shareshi ta kama hannunsa suka wuce sama ta rufe dakinta zuwa yanzu al'amarin Hisham ya fara bata tsoro. Bayan ta gama sallar asuba ta shiga kitchen ta had'a masu breakfast, ta soya masu kosai, ta dama kunu, ta soya dankali da doya da ruwan shayi tareda indomie saboda Suleiman, sanin da tayi koda tayi wa Hisham magana ba zai ci ya saka ta zuba a kwando ta saka mashi a mota. Ta zauna tayi kalaci tareda Suleiman, bata jin cin abincin amma ta daure taci gudun kada yaron ya fahimci halin da take a ciki, ta shiryashi cikin uniform ta dauko lunch box direba ya wuce dashi makaranta. Tana zaune a parlour lokacin da Hisham ya sauko parlour zai fita, ba tayi yunkurin mashi magana saidai cewa da tayi, "A dawo lafiya." Wanda bata samu zarafin amsa ba ya fice abunsa, ta bi shi da kallo fuskarta dauke da damuwa. Bayan fitarsa ta fito harabar gidan taci karo da kwandon da saka mashi abincin a watse a kasa wanda ya tabbatar mata bata arziki aka fitar dashi ba, abincin da ta dauko lokaci ta shirya masa shine ya watsar a kasa, ji tayi hawaye sun zubo mata. Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 18 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 Bilkisu tana zubar da hawaye ta tattara wajen ta wanke tana ji tana gani ta zubar da abincin a shara, abincin da ta shafe lokaci tana girkawa, ba tayi kasa a gwuwa ta girka taliya da shinkafa da miya wacce taji naman kaza ta zuba a kwando ta aika direba ya kai mashi office saidai tana zaune a inda ta bada sakon ya maido mata dashi cewa, "Ranka ya dade yace a maido maki dashi." Ta juyar da kai ta goge hawayen da suka zubo sannan ta kakaro murmurshi tace, "To shikenan babu damuwa." Damuwa ya saka ta kasa cin abincin, kamar Suleiman ya fahimci halin da take ciki, ya dawo makaranta ta zuba mashi yaki ci, "Ka ci." Tace tana mai tura mashi abincin. Ya girgiza kai yace, "Mommah kici." Dole ta zuba suka ci a tare. Da dare tayi girka ta ajiye a dinning table, taci tareda Suleiman ya rage na Hisham ne. Tun fitarsa da safe bai dawo ba sai karfe goma na dare, ta d'ago tace, "Barka da dawowa." Saidai koda kallon inda take baiyi ba, ya wuce, ta mik'a ta zuba abincin a tray tabi bayansa, k'arar ruwa taji ta fita, jim kadan ya sauko ya dubeta yace, "Ki zo." Tabi bayansa tana mamakin kiran, ya murtuke fuska yana nuna mata tray da ta ajiye mashi yace, "Dauki abunki ki b'ace min daga gani." Tace, "Amma..." bata rufe baki ba yayi kwallo da tray din abincin ya tarwatse a wajen, "Ki tabbata ki gyara wajen, aikin banza aikin wofi, na ce ban ci." Ya fita yana fad'a. Suleiman ya leko, tayi mamakin ganin yaron tayi saurin goge hawayenta tace, "Suleiman har ka tashi." Ya gyad'a kai yace, "Mommah wa ya sakaki kuka?" Da sauri ta girgiza kai tace, "A'a abu ne ya shigar min cikin idanu." "Mi aka yi wa Abbu yake ta fad'a?" Ya k'ara jefo mata wata tambayar, tace, "Wasu ne suka b'ata mashi rai, muje kayi barci." Ta maidashi dakinta ta sakashi barci sannan ta dawo ta gyara wajen tayi mopping ta zuba turaren wuta tana ji tana gani ta gama wahalar girki ya k'are a kwandon shara. Washegari still ta saka breakfast dinsa a kwando ta ajiye mashi a mota, yana saukowa tace, "A dawo lafiya, kalacinka yana a cikin mota." Ya tsaya cak ba tareda ya kalli inda take ba yace, "Zaki je ki cire min daga mota ko kuma sai na b'arar dashi sannan." Tace, "Amma..." bai tsaya saurarenta ba ya fita saidai jin k'arar fitar motarsa tayi tana fita ta samu ya fita a wata motar ne daban, ta dauki abincin ta baiwa mai guard ta koma ciki. Wajen karfe sha biyu na rana ta tura mashi sakon text message 'Idan Suleiman ya dawo zanje gidanmu daga in biya ta gidan Momcy na gaidata.' Amsar da ya maido mata ba ta yi mata dadi ba, 'Na hanaki zuwa ko kuma na rike kafafunki ne, idan bangon duniya zakije ke kika sani, ki dawo ko ki zauna a can ke ya shafa.' Ji tayi kuka ya kwace mata ta k'ara tura mashi wani sakon, 'Nagode, in aiko maka da abinci ne.' Ya maido mata amsa, 'Eh idan baki gaji da wahalar banza ba.' Ta tura mashi, 'Don nayi maka girki bazai zama wahalar banza ba domin mijina nayi wa.' Ya maido mata amsa, 'Amma zai samu gurbin zama a shafin almubazzaranci tun da kin san bazan ci ba kika girka, wai mi yasa kika cika naci ne, idan nine ke tattara kayana zanyi in wuce gidanmu, haba ki kyaleni inji da kunci da damuwa da nike a ciki.' 'Dukkanin abun da ya faru, ya faru ne sabo da ni, ka aikata mata hakan ne sabo da ni don haka ba zanyi butulcin barinka a damuwar kai daya ba.' 'Ko da na bukaci hakan da kaina' Ta maida mashi da amsar, 'Eh..' ya rubuta mata, 'Ni kuma ina son kasancewa ni daya ne, bana buk'atarki a rayuwata a yanzu.' Ta rubata mata mashi, 'Kayi hakuri.' Saidai babu amsa tana kira taji numbarsa a kashe. Bayan direba ya dauko Suleiman daga makaranta tayi wanka suka fita ta tattara kayansa ta ajiyeshi a gidansu. Da mamaki Nene take tambayarta abun da yake damunta ganin tayi rama. Ta girgiza kai tace, "Babu komai." Daga nan ba ta sake tambayarta hakanan bata tambayeta dalilin kawo yaron ba lura da tayi da bata son magana a kai, tayi mata uzurin dukkanin ranar da ta shirya fad'a mata zata fad'a mata. Ba ta jima ba ta wuce gidan Momcy, tana zubar da hawaye take sanar da ita abun da yake faruwa. Momcy ta jinjina kai tace, "Ranar na kirashi nayi mashi fad'a tunda ranar bai k'ara zuwa ba, shi da yake D'a ya nuna yayi fushi ya dauke kafa daga gidana kinga kuwa ni bazan dauki kafa inje inda take ba, don haka sai dai in ce maki kiyi hakuri ki k'ara hakuri, wata rana sai labari, shi kuma ina mashi fatan Allah ya dawo dashi akan hanya. Ya ka sa tsaya ya dauki kaddara shiyasa yake samun damuwa, Hafsat ta auri wanda take so, zafin ransa da damuwarsa bazai sauya komai ba amma shi ya gagara tsayawa ya fuskanci wannan gaskiyar, Bilkisu babu abun da zan ce maki saidai ince kiyi hakuri sannan ki k'ara hakuri, idan kin je ki ce mashi ina nemanshi idan yazo zanyi mashi fad'a, idan kuma ya zab'i ya ki zuwa then babu abun da zan iya yi a kai." Bilkisu tayi mata godiya ta wuce gida, tayi girki ta jera akan dinning table, tana zaune a parlour ya shigo, ta d'aga kai tace, "Sannu da dawowa, abinci yana akan dinning table." Yayi mata banza, tace, "Momcy tana nemanka." Ya tsaya cak ya juyo kamar zaiyi magana sai kuma ya juya ya haye sama. Tun daga ranar ba ta k'ara matse mashi ba sai dai dare da safiya tana mashi gaishe dashi tareda sanar da shi abinci yana akan dinning table amma koda kallon arziki bata samu a wajensa amma bata karaya ba, tayi matuk'ar mamaki la'akari da Suleiman ba ya gidan kuma ba ta sanar da shi inda yake ba kuma bai tambaya ba. Tun tana hakuri tana kawar da kai har ya kai ta wuya ya fusatata, yana shigowa falon ta tari gabansa ya zuba mata idanu, idanunta a tsaitsaye tace, "Ko zaka tureni ne." Bai ce mata komai ba, tace, "Na gaji da wulakanci da kakeyi min a gidan nan." Ta fashe da kuka, "Wannan abun da mi yayi kama, ina binka kana wulankatani, wulakanci na yau daban na gobe daban. Ka dauki tsana da tsangwama na duniya ka dora min akan abun da ba ni ba ce na ce ka yi, laifina daya shine ka aikata abun a saboda ni ne, amma ay ban ce maka kayi ba kuma kana zab'i amma sai ka zab'i abun da aikata mata, kayi saboda gudun cutuwata kuma na gode amma wannan ba zai baka lasisin wulakantar da ni ba." Kuka ya ci karfinta wanda ya tilasta mata yin shiru. Ya kama hannunta har compound, yace, "Kije gidanku." Tana mai zubar da hawaye tace, "Hisham..." ya katseta, "Za ki tafi hakanan ko kuma sai na hadaki da takardar saki." Zuciya ta kawo mata wuya tana ji kamar ta fad'a mashi ya saketan sai mi. Ta girgiza kai tana mai kawar da tunaninta daga hudumar da shaidan ya ke yi mata, ta mik'a hannu tace, "Bani makullin mota." Ya mik'a mata makullin mota da ya dawo dashi, ta shiga ta kama hanyar gidansu. Tana kuka ta sanar da Nene abun da yake faruwa, "Tun kafin tayi aure yake min abubuwan nan, hakuri kawai nikeyi, tace ba za ta aureshi saboda abun da yayi mata, tayi aure ta auri wanda take so amma hakan bai saka ya hakura ba, ya daina min magana, ba ya cin abincina, idan nayi mashi magana ya hau ni da fad'a, abu kadan zai fara ihu wannan shine dalilin da ya saka na dawo da Suleiman gidan nan." Nene tace, "Mi yake nufi dake yanzu?" Bilkisu ta share hawayen da suka zubo mata tace, "Ya ce inzo gida shikenan." Nene tace, "Yana nufin ki zo kiyi ta zama kenan." Yanayin fuskarta ya nuna tsantsar b'acin ranta. Bilkisu tayi shiru kawai domin bata da abun cewa. Bayan sallar Isha'i Baffa ya shigo bayan sun gama cin abincin dare Nene ta sanar dashi abun da ya faru, ranshi ya b'aci matuk'a, yace, "Gobe idan Allah ya kaimu zan samu wakilinsa inji abun da yake nufi da turoki gida." Bilkisu ta girgiza kai tace, "Baffa ku rabu dashi, zafin kai, fushi da damuwa da ya d'aura ransa ne suke damunsa idan aka sameshi zai iya tsinke igiyar auren, a rabu da shi. Baffa ka san Hisham, ka san halin sa, mu rabu da shi lokaci yana zuwa da zai gane abun da yayi bai kyauta ba, addu'a da zamuyi mashi shine Allah ya ganar dashi gaskiya." ****** Sai bayan aurenta sannan ya fahimci matuk'ar son da yake mata, ya rasa nutsuwarsa, ya rasa kwanciyar hankali, ya rasa farin cikinsa, komai haushi yake bashi, tun da ya kori Bilkisu gidansu ya daina fita, kullum yana zaune a gida, ya rame ya fara kasumba da sumar kai ya koma kamar samun kamun hauka. Momcy tana sane ta rabu dashi tana fushi akan abun da yayi mata, daga tayi mashi fad'a ya dauke kafa daga gidanta, ta kyaleshi yaje taga inda zafin kansa da damuwar zasu kaisa, abun yayi yawa har yana neman tab'a lafiyar kwakwalwarsa, abokansa suka sameta suka bata hakuri. A ranar ta shirya direba ya kaita gidan Hisham, halin da ta ganshi a ciki saida ta zubar da hawaye, tace, "Ka tashi kaje kayi wanka ka dawo kaci abinci muyi magana." Babu musu ya mike ya wuce ya jima a bathroom sannan ya fito ya shirya cikin riga da wando na kananan kaya ya fito ta zuba mashi abincin da tazo mashi dashi, ya girgiza kai yana b'ata fuska yace, "Bakina babu dadi." Ta murtuke fuska wanda ya tilasta mashi daukar cokali tana tsakurar abincin ta ka sa ta tsare har saida taga yana neman yayi amai saboda koshi. Ta mike tace, "Mu je." Ya dubeta da mamaki yace, "Na'am." Ta murtuke fuska tace, "Za ka wuce mu je ne ko kuma sai na mareka a wajen." Ya yi gaba ba tareda ya k'ara magana ba, direba ya jasu zuwa gidan Momcy, ta kira direba ya dubashi ya yi mashi allurar barci, a take barci ya yi awon gaba da shi, ta zuba mashi idanu tana mai jin tausayinsa. Bayan ya farka ta tusashi a gaba tana mashi fad'a, "Hisham mamaki kake bani, saboda nayi maka fad'a, na fad'a maka gaskiya akan ka rabu da ita tun da kuskure ne ka yi ka rasata ta auri wanda take so sai kayi hakuri ka rungumi kaddara, yanzu fushin, zafin kai da damuwar da ka sakawa kanka ina ta kaika. Ina fushi da kai, ciwon zuciya yana neman kamaka, matarka tana gidansu. Shin in tambayeka mana, waye gari ya wa ya a nan? Kai." Ta lumfasa sannan tace, "Ka rufeta ka aureta ta shiga tashin hankali da damuwa har hauka tayi da tsohon ciki amma a lokacin ta samu zab'i na roketa alfarma kuma tayi min ta zauna da kai, amma kai a lokacin da zaka samu zab'i sai ka zab'i kayi mata butulci, ka saketa, yaron da tasha matuk'ar wahala ka amshe, tazo ta sanar da kai tana ciki ka koreta, kayi min k'arya ka tattaramu muka bar kasar. Shin in tambayeka, Idan kanwarka Fatima aka yi mawa zakaji dadi? Shin idan kaine Hafsat zaka yarda ka koma gidan wanda ya aikata maka haka? Bugu da kari na tusaka mukaje muka bada hakuri amma mi ka aikata daga baya, korar manema aurenta, Shin abun da kayi ya kyautu kenan? Tambayata a gareka ita ce Shin ka tab'a rokon yafiyarta akan abun da kayi mata?" Ya girgiza kai yace, "A'a." Momcy tace, "Hisham alhakin Hafsat ne yake wahalar da kai a rayuwa, ka cutar da ita, ka zalunceta zalunci mai girma, ya rage maka ka sauke zafin kai, girman kai, da damuwa da ka d'aurawa kanka muje ka nemi yafiyarta, idan kuma ka zab'i zama da alhakin zaluncin da kayi mata a kanka to shikenan sai in ce ka je ka yi abun da ranka ya so." Hisham yayi kasa da kai yace, "Zan nemi yafiyarta." Momcy tayi murmurshi tace, "Yauwa, Hisham kayi wa kanka fad'a ka fuskanci rayuwa a yadda tazo maka, ba komai muke samu ba, kowa da rabonsa, ka samu damarka kayi wasa da ita ka kufce maka don haka hakura da ita shine mafitarka a yanzu, ka dage sallar dare da karatun Alk'ur'ani mai girma komai zaizo maka da sauki. Har mamakinka nike Hisham mutum mai tausayi, taimako, wanda sallar Jam'i bata wuceshi shine ya dawo haka, Hisham kayi wa kanka fad'a." Tayi mashi fad'a sosai tareda nasiha, a wajen ya roki gafarta akan abubuwan da yayi. "Momcy ki yafe min." Ta shafi kansa tace, "Babu komai, na yafe, Allah yayi maka albarka." Ya amsa da, "Amin." "Yaushe za mu je wajen Hafsat?" Ya tambaya. Tayi jim sannan tace, "Sai ka k'ara samun sauki tukunna." Ya dage da karatun Alk'ur'ani, ya saka ransa hakuri, ya dauki dangana akan Hafsat, a cikin sati biyu ya murmure. Hisham ne yake tuka motar a yayinda Momcy take zaune a mazaunin baya, ya dauki hanyar asibitin da aka kwantar da Aliyu, yace, "Na yi tunanin abroad zasu fitar da shi." Momcy ta ce, "Mahaifinsa ne ya hana, yace mu barshi a nan, koda zai mutu ne gwara ya mutu a cikin dangi a kasarsa ta haihu yafi ayi zirga-zirga dashi, kwararrun likitoci ne daga kasashe daban-daban suke kulawa dashi." Ita kadai suka samu, ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi ta gaidashi, ta rungume Momcy tana mai cewa, "Sannu da zuwa uwata ta kaina." Momcy tace, "Yauwa diyata." Hafsat tace, "Yaya Hisham barka da zuwa, ka zauna." Suka zauna, suka k'ara gaisawa. "Ya mai jiki?" "Jiki da sauki." "Allah ya k'ara sauki." "Amin." Momcy ta dafata, "Diyata ki k'ara hakuri, ki cigaba da hakuri, jinya saida hakuri, jinya akwai lada musamman ke da kike jinya na mijinki, Allah ya bashi lafiya." Hafsat tace, "Amin, na gode." Tana ganin girman Momcy sosai, Momcy mutumin ce mai dattako, kowa nata ce. Hisham yayi jim sannan yace, "Hafsat na rasa da kalmomin da zanyi amfani domin baki hakuri akan abubuwan da na aikata maki tun daga haduwarmu har zuwa yau, Angel na zalunceki na cutar dake wanda bana raba daya biyu shine yake bibiyata, shine ya hanani nutsuwa. Ina maki fatan alheri akan aurenki da Aliyu, Allah ya baku zaman lafiya." Ya lumfasa sannan yace, "Ina mai hakuri akan dukkanin abubuwan da nayi maka na butulci da zalunci, please na rokeki da girman Allah ki yafe min." Hawaye ta gani a idanunsa wanda ya matuk'ar bata mamaki, bata tab'a tunanin rana zata zo da zaizo har inda take ya nemi yafiya, bata tab'a zaton rana zata zo da zai nemi yafiyarta ba tareda an tilasta mashi ba amma a yanzu abun da take gani a idanunsa tsantsar nadama ce. Tace, "Na yafe komai da komai, nima ka yafe min." Yace, "Babu abun da kukayi kuma koda kinyi na yafe." Tace, "Allah ya yafe mamu baki daya." Suka amsa da, "Amin." Sun jima kafin sukayi mata sallama suka tafi. Da daddare ya samu Momcy da maganar Bilkisu, tayi murmushi tace, "Mi kake son inyi a kai?" Ya sosa kai yace, "Ki rakani mu bada hakuri." Momcy ta girgiza kai sannan tace, "Mi nayi da zan bada hakuri? Kai da kayi mashi ba daidai ba, kaine zakaje ka bada hakuri." Ya marairaice yace, "Please mana Momcy, ko har yanzu kina fushi da ni." Ta girgiza kai tace, "Ko daya bana fushi da kai, ko wajen Hafsat ina da dalili da ya saka na rakaka, saboda in duba mai jiki, sannan bugu da kari ni ce sanadi da ya saka ta zab'i zama da kai a wancen lokacin. Kayi wa Bilkisu laifi ba karami ba, abun da ka aikata bai kyautu ba don haka ka shirye kaje ka bada hakuri, idan sun hakura shikenan idan kuma basu hakura sai ka rungumi kaddara ka girbi abun da ka shuka na fushi da zafin kai." Ya girgiza kai yace, "Bilkisu tana sona." Momcy tace, "Hisham, kana tuna abubuwan da kayi wa Bilkisu kuwa?" Yana komawa daki ya kira numbar Bilkisu tana shirin kwanciya kiran ya shigo wayarta ta dubi wayar da mamaki ganin sunansa, saida ta tsinke ya k'ara kira ta kusa tsinkewa sannan ta amsa. "Salaam alaiki." "Wa alaikassalaam." "Ki dawo gida." Bilkisu tayi murmurshin takaici tace, "Su kuma wadanda ka baiwa ajiyata wata da watanni sai ince masu mi, Hisham kana bani mamaki matuk'a gaya, bayan abun da kayi amma har kana da karfin halin da zaka kira kace min in dawo gidanka, miye kake tunani that ni er dadi miji zan wanko kafa in dawo saboda bani da mafad'a, to na san ciwon kaina don haka kamar yadda kace in tafi ko kuma ka had'a min da takardata, idan ka tashi ka tafo da ita zan amsa a wannan karon." Ta tsinke kiran, ya k'ara kira ta datse kiran tareda kashe wayar baki daya. Takaici ya kamata ji take kamar ta fasa ihu bayan abun da ya aikata amma har ya iya kiranta yana ce mata 'Ta koma gida' ko nauyi da kunyar fad'a bai ji ba. Washegari ya k'ara samun Momcy da maganar, "Please Momcy kiyi hakuri muje in basu hakuri, kunyar abun da na aikata nikeji." Momcy ta murmusa tace, "Tun jiya na gama magana babu inda zanje yadda kace mata taje ba tareda saka hannuna ko shawarata ba hakanan zaka dauki kafa a yau ko gobe kaje ka basu hakuri." Ya marairaice yana rokonta ta hakura suje tare, "Hisham babu inda zanje." Karshe da ya dameta ta koreshi, ta hana kowa yayi mashi rakiya. Sannan ta k'ara bashi deadline akan a ranar ko washegari yaje ko kuma tayi mugun sab'a mashi. Bai je ranar ba washegari ta tusashi a gaba ya shirya ta korashi, kanshi kasa yake zaune a falon ya kasa had'a idanu dasu. Baffa yace, "Ina saurarenka." Hisham yace, "Nayi nadamar abubuwan da na aikata, ina mai baku hakuri, hakan ba zai sake faruwa ba." Baffa yace, "Ba wannan ba, ina so ne inji laifi da tayi ka korota gida." Hisham ya rasa bakin magana, Baffa yace, "Ina sauraronka." Saida Hisham yayi kasa da kai sannan yace, "Abun da ya faru ba laifinta bane laifina kuma ina mai bada hakuri." Kwana biyu Hisham ya zarga gidan Baffa yaki sauraronsa, hakanan bai barshi yaga Bilkisu ba saidai Suleiman aka maido dashi gidan Momcy. Har ya cire tsammani a ranar ya samu kiran Baffa, daga daya bangaren Baffa yace, "Ka zo tare da wanda ya amsar maka auren Bilkisu." Saidai gabansa ya yanke ya fad'i yace, "Baffa a yi hakuri." Daga daya bangaren Baffa yace, "Ka zo tare da wanda ya amsa maka aurenta." Ya tsinke kiran. Ya samu Momcy da maganar, ta jinjina kai tace, "Babu damuwa zan yi mashi magana." Kallonshi kawai take amma tasan komai akan abun da yake faruwa, ita ce ta saka sukayi mashi hakan domin ya shiga taitayinsa akan abubuwan da yayi ta yadda a nan gaba bazai yi gigin maimaitawa ba. Abun da ya faru yasha banban da abun da yayi tunani, yayi fargaba akan zasu saka ya saketa ne saidai ba hakan ne ya faru, nasiha ne tareda fad'a aka yi masu ya dauki matarsa ya wuce da ita gida, kunya ta hanashi mata magana, yana so ya bata hakuri amma kunya ta hanashi magana, idan ya tuna abubuwan da yayi mata sai yaji kunyarta ta kamashi. Bilkisu tana lura dashi tayi kamar bata gane ba, ta fito daga wanka ta sameshi zaune a gefen gado, zaiyi magana ta d'aga mashi hannu, tace, "Hakuri ne na hakura, shikenan, bana son doguwar magana." Ya gane tana son rama abubuwan da yayi mata ne yace, "Mi zaki girka mamu?" Ta ware idanu tace, "Kana nufin mi zaki girka kici ne ka tambaya kayi jimla domin a iya sanina ka daina cin abun da girka kuma naga ba'a dole." Ya murmusa yace, "Amma nace kiyi hakuri." Ta murtuke fuska tace, "A yaushe?" Yace, "A lokacin da zanyi magana kika ce hakuri ne kin hakura." Ta k'arasa gaban closet tana duba kaya tace, "Sai kuma aka ce don nace haka kayo shiru kada ka bada hakurin." Yace, "Ikon Allah amma kin ce kin hakura." Haushi ya bata ta juyo tace, "To na janye hakuri." Sati biyu ya daukesu yana binta tana ja mashi aji, idan ya yi magana ta ce a wajenshi ta koya, dakyar ya samu ta hakura suka dinke soyayya suke zubawa babu kama hannun yaro. (Ni kuwa na ce soyayya sai idan Aliyu ya farka tukunna 😅 🤣 😂 saidai suje a basu course). Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 19 *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 Hafsat tana zaune a ward din tana goge mashi jiki, ta dauki Alk'ur'ani mai girma tana rerawa a cikin kira'arta mai sanyi, Batuul ta shigo dauke da kwandon abinci, bayan Hafsat ta kai aya ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi ta ce, "Sannu da zuwa Aunty." Batuul ta ce, "Yauwa, kiyi hakuri fa na barki ke daya, na biya ta gida ne na kai yaran." Daga nan ba ta sake magana ba taja kujera ta zauna. Ta dubeta ganin ba ta da niyyar zuba abincin kamar ba za ta yi magana sai kuma ta ce, "Ki zuba abincin ki ci mana." Hafsat ta gyad'a kai ta ce, "Zan zuba." Batuul ta d'ago daga danna waya da ta ke yi ta zubawa Aliyu idanu sai kuma ta maida dubanta akan Hafsat kafin ta ce, "Hafsat ba ni kishi da ke, idan ta ni ce zamu zauna lafiya babu fad'a babu hayaniya, duk da a lokacin da na ajiye abincin ban ce maki komai ba amma kin san naki ne sai ki dauka ki zuba. Ke kishiyata ce wannan suna ne wanda bazan sauya ba, ba'a sauya wa tuwo suna, ina da kishin miji na sai dai wannan ba zai saka inyi kishin hauka da ke ba, kishin da na yarda da shi shine wacce ta iya allonta ta wanke, kishi na kyautatawa miji. Hadin kai na kishiyoyi kamar k'awaye wannan ba zan iya ba, sannan ba zan iya kishin hauka da makirci da asiri ba, idan kina min kallon muguwa ne ki bari, ba ni da damuwa idan har ba'a tab'oni ba." Hafsat ta ce, "Allah ya bamu zaman lafiya." Batuul ta amsa da, "Amin." Mikewa Hafsat tayi ta janyo kwandon ta zuba abincin wanda ya kasance shinkafa da taliya da miya wacce ta ji naman kaza (ka da ku ga na cika cewa shinkafa da taliya with stew, kawai a kwanakin nan ita nike sha'awa kuma na kasa girkawa 🤣 😂 har mamakin kaina nike da kaina 🤣 😂) ta koma ta zauna ta dubi Batuul ta ce, "Bismilllah mu ci." Batuul ta d'ago tana kallonta da mamaki kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ga rashin kyautuwar hakan, ta girgiza kai ta ce, "Ikon Allah kamar ba yanzu na gama wannan maganar ba, na fad'a maki baki da damuwa da ni amma maganar cewa kishiyoyi suna abu kamar k'awaye ko en uwan jini wannan ba zan iya ba domin na san k'arya nike koda nace zan iya, and ban iya fuska biyu ko pretending ba, Allah ya sani babu mugunta ko cutarwa a zuciyata, ba ni damuwa da aurenki da yayi, kowa da halinta za ta zauna, ina sonshi shima kuma nasan yana sona, na sani dole akwai wacce ya fi so a tsakaninmu wannan kuma abu ne wanda ba zan iya sauyawa ba sai dai zan iya k'ara sona a zuciyarshi. Kishiyoyi suna cin abinci a kwano daya I suppose abu ne mai kyau sai dai ba zan iya ba gaskiya bugu da kari sai da na ci sannan na fito, idan ina son in ci na san inda abincin ya ke." Hafsat ta gyad'a kai tana mai tsakurar abincin ya yi dadi ba kadan ba, Batuul makura ce a fagen girki koda a wancen lokacin ta sani tunda yana yawan fad'a mata matarshi karshe a fagen girki, akwai aiki sosai a gabanta domin banbancin da ke tsakanin girkinta da girkin Batuul banbancin a bayyane ya ke, dama tana kankaro mutunci ne da girkin Umma. Memaah k'annansa ne suka shigo, "Aunty Fatima har kin dawo kenan." Batuul ta gyad'a kai ta ce, "Ban jima da dawowa ba." Rumana ta ce, "Sannu Aunty Hafsat kina k'ok'ari tunda ki ka zo asibitin nan ba ki fita, ya kamata ki je gida ki huta." Hafsat ta girgiza kai sanin ba za ta iya ba, "Rumana ba na iya motsawa daga kusa da shi gani nike komai zai iya faruwa, ina tsoron rasashi." Batuul ta dubeta sai dai ba ta ce komai ba har sai da suka fita. Ta ce, "Hafsat ban san abun da yake a zuciyarki ba amma abun da ki ke yi sai yana saka mutane suna min kallon ba na kyautawa, koda ba kiyi da nufi ba, sai suna ganin kamar ban damu da shi ba ne, kije gida ki huta gobe ki dawo sai mu fara raba ayyukan a tsakaninmu." Hafsat ta zaro idanu ta ce, "Na'am." Batuul ta ce, "Ina nufin mu raba kwanakin, idan na tsaya kwana biyu ina wuni dashi ki je ki yi girki ki dawo, nima in yi girki na kwana biyu." Hafsat ta ce, "Amma bazan iya motsawa daga kusa dashi ba..." Batuul ta katseta ta ce, "Kuma idan hakan ya cigaba da faruwa mutane za su yi ta kananun magana a kai don haka yadda na ce haka za'ayi." Hafsat ta rasa abun da ya ke mata dadi bata matsawa daga kusa dashi but maganar Batuul tana akan hanya, ta gyad'a kai ta ce, "Babu damuwa, ina mai hakuri idan hakan ya b'ata maki rai ban yi da nufi ba." Batuul ta gyad'a kai kawai. Hafsat ta mike ta fita ba domin ranta yaso ba sai bayan ta fita ta nuna babu mota a wajenta ta kira Umma ta turo direba ya daukota ta jira a receptionist har ya zo suka wuce, ba ta jima da tafiya Hajiya Zainab ta zo da mamaki take tambayar Batuul inda Hafsat take. "Na turata gida ta huta, ba bu dadi a barta da aiki ita daya, ya kamata nima na rink'a tsayawa." Ummi tayi murmurshinsu na manya kafin ta ce, "Idan ban da abunki kema kina wahala, ga kula da yara, ga girki, a hakan wuni kike a wajensa, ni babu abun da zan ce maku sai dai Allah ya saka maku da alheri." Batuul ta amsa da, "Amin." ***** Umma ta yi mamakin dawowar Hafsat duba da tasha ta yi mata magana akan ta dawo gida ta huta amma amsar daya ne that ba za ta isa nisa da shi ba. Hafsat ta gane ma'anar kallon ta zauna akan kujera tana mai cewa, "Aunty Fatima ce ta nemi da in dawo in huta idan ya so sai mu rink'a raba kwana, daya ta zauna da shi, dayar tayi masu girki." Umma ta gyad'a kai ta ce, "Hakan ya yi, ki tashi ki ci abincin ki kwanta ki samu kiyi barci kallo daya mutum zaiyi wa idanunki ya fahimci ba ki samun barcin kirki." "Yaran fa?" Ta tambaya. Umma ta ce, "Suna gidanku." Ta gane gidan Abba take nufi. Kadan ta tsakuri abincin ta wuce dakinta tayi wanka ta kure Ac ta kwanta bacci ne ya yi awon gaba da ita, abunka da wacce ta ke da bashin bacci sosai. Da dare ta kasa barci tunaninsa ya addabi zuciyarta bugu da kari barci da ta yi da rana, dakyar ta samu ta yi barci wajajen karfe biyu na dare. Washegari tun da safe ta dauki breakfast da Umma ta yi masu, ta wuce da yaran daga nan ta saukesu a makaranta, Batuul kawai ta tarar ta gaishe da ita, "Ina kwana Aunty Fatima?" Batuul ta ce, "Lafiya lau." Muhammad ya ce, "Ina kwana?" Tace, "Lafiya lau babana." "Ya mai jiki?" "Da sauki." "Allah ya k'ara sauki." "Amin." Aliyu ya ce, "Ina kwana?" Ta ce, "Lafiya lau mai gidana." Ta fi sanin Little Aliyu kasancewar Aliyu yana zuwa dashi gidan a wasu lokuttan. Hafsat ta ajiye breakfast da suka zo dashi, "Ga breakfast Aunty." Batuul ta ce, "Okay, na gode, sannu da k'ok'ari." Ba su dade ba suka wuce, Batuul ta kalli breakfast din ta janyo wayarta ta kira gidansu ta yi jim sannan tace, "A tafo min da breakfast da alkubus." Ummi ta zo tare da Na'ima, bayan sun gaisa da tambayar mai jiki. "Hafsat fa?" Umma ta tambaya. Batuul ta ce, "Ba ta jima da zuwa ba, ta kawo breakfast." Ummi ta gyad'a kai kawai ta ce, "Ki ci." Batuul ta girgiza kai ta ce, "A'a na kira za'a tafo min da alkubus na tashi da kwadayinsa ne." Ummi ta ce, "Okay." ******** Bayan ta sauke yaran ta kaisu class ta juyo ta hadu da Bilkisu kasancewar shima Suleiman a makarantar ya ke, suka gaisa, "Ya wajensu Abdallah mutunen London?" Bilkisu ta ce, "Suna nan lafiya lau. Ya wajen mai jiki?" "Da sauki." "Allah ya k'ara sauki." "Amin." Su ka yi sallama kowace ta wuce wajen motarta, Hafsat ta manta ta dauki hanyar asibiti har sai da ta yi parking motarta a wajen ajiye motoci sannan ta ankara. Ta yi reverse ta ja motar ta wuce gida, haka ta wuni sukuku ta rasa abun da yake mata dadi, ta saba da kasancewa a tare da shi tana kulawa da shi. Bayan sallar Asr ta kai mata abinci, da dare su ka je tare da Umma. Batuul ta mike tare da baiwa Umma kujerar da ta ke a zaune, "Ina wuni?" "Lafiya lau. Ya mai jiki?" "Da sauki." "Allah ya k'ara sauki." "Amin." "Sannu da k'ok'ari kinji, Allah ya saka maku da alheri." "Amin." Kwana biyu Batuul ta yi tana kwana a wajensa Hafsat ta amsa itama ta yi kwana biyu, Hafsat tana shiga damuwa sosai a dukkanin lokacin da kwananta ya k'are, idan son ranta ta kasance a koda yaushe a tare da shi tana mashi hidima, ya yi mata halarci a rayuwa, dukkanin abun da ta yi mashi ba ta fad'i ba, ba ta tab'a ji ta gaji da jinyarsa ba sai dai karsashi da ta ke samu a dukkanin lokacin da ta ke kula da shi. ******* Tana zaune tayi tagumi ya fara motsi da hannuwansa ba, ba ta lura ba har saida ya ware idanunsa a kanta ya kama hannunta yana murzawa a hankali ya ce, "Miye yake damun MATAR ALIYU?" Da sauri ta maida dubanta a kansa tana ware idanu jin muryarsa, ya yi mata murmushi ya ce, "MATAR ALIYU mi yake damunki? Ki kwantar da hankalinki zan cigaba da rokonta har sai ta yarda da aurenmu." Ta yi murmushi tana maida hannunta akan hannunsa ta ce, "Aure kuma? Da ma ana aure biyu ne? Wannan da take a gabanka MATAR ALIYU ce, MATARSHI TA BIYU." Ya ware idanu ya ce, "Ban gane ba." Ta ce, "Lokacin da baka farka ba aka d'aura auren." Da sauri yace, "Na ji wasu abubuwan sai dai yana min ne kamar a mafarki. Umma fa? Ta yarda?" Ta yi murmurshi ta ce, "Mamata kenan ta kaina, yadda take kulawa da ni ina jin sai ka yi da gaske domin tuni na kwace fadarka a wajenta." Ya fad'ad'a fuskarsa da murmurshi ya ce, "Alhamdulillah." The more yake murza hannunta the more hannun yake k'ara mashi taushi (Torh hajiya ki ce ki kula da jikinki kafin ki fara complain ba ya ba ki kulawa ki fara tambayar kan ki; Shin kina kula da tsaftar jikin ki? Shin kina kula da gyaran jiki? Haba sister ki kwana ukku ba ki yi wanka ba, bakin ki yana wari, hammata tana wari, turare kuwa daga biki sai suna a hakan ki ke tunanin za ki samu kulawa yadda ta dace. Kamar yadda na ce ki kula da tsaftar jikinki da ta gidan ki, kalolin girki daban-daban, kin ce ke kullum shinkafa da tuwo zaki rink'a girka mashi ay dole wata rana ya je wani wajen ya siya, kowa yana son canji, mun san akwai rashi amma wata koda shinkafa da wake ta girka sai kin ji ta yi daban, abun duk karatu da lissafi, kina iya asusu domin ki tara ki ware rana daya ki yi mashi girki mai kyau. Wata idan ta yi wa mijinta wata maganar sai kin ji kamar ki yi ihu; imagine ya yi mata matsa tsawa and she will be like kaga kada ka k'ara min tsawa or yoh miye nayi maka da zaka min tsawa, haba sister koda ya kawar da kai ke kanki kin san baki kyauta ba, let say yayi maki tsawa, ay kin san mijinki, na fad'i hakane saboda abun da za ki yi wa wani namijin ya yi dariya yana tsokanarki kina shagwab'a idan ki ka yi kuskuren yi wa wani namijin watalila sai kin samu tagomashin mari, mu je maganar da nike magana a kan ta, ya yi maki tsawa ay kin san mijinki kin san halinsa idan mutum mai son shagwab'a ne ki marairaice you can be like please mana ka bar min tsawa yana tsoratani, idan kuma mutum ne mai son girma ki ce, kayi hakuri daga nan ki yi shiru koda kuwa ke ce ki ke da gaskiya daga baya ki sameshi da lalama ki zayyana mashi komai, amma ranshi yana a b'ace ranki yana b'ace sannan ki ce dole sai kin nusar da shi ke ce mai gaskiya, anya kuwa abun zai yi kyau, idan yayi sama ke ki sauko. Ohhh ni MATAR ALIYU daga magana daya na buge da dogon sharhi). Hafsat ta yunkura ta ce, "Ka tsaya in kira doctor." Ya rike hannunta gam ya ce, "A'a ki kyaleshi hannunki ne yana min dadin tab'awa ashe haka hannunki yake da taushi ALIYU ya yi dacen mata." Ta yi rolling idanu ta ce, "Itama MATAR ALIYU ta yi dacen miji." Ya murmusa ya ce, "Bani labari." Kafin ta yi magana Batuul ta shigo tayi turus ganinsa a farke, ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi tana k'arasowa inda suke, ya mik'a hannu ya rike hannunta ya janyota kusa da shi yana murmushi ya ce, "Ranki ya d'ad'e." Echoe da ya ji har tsakiyar kansa ne ya tilasta mashi sakin hannunta ya dafe kansa yana sakin ihu tare da ture dukkanin abun da ya tari gabansa. Batuul ta tsorata ta yi baya da sauri ta nufi hanyar kofa, Hafsat ta matsa kusa dashi tana k'ok'arin rikesa ya tureta ta fad'i a kasa warwas, likitoci suka shigo suka dukufa a kansa. Ya farka ya warware sai dai gabobin jikinsa da suke mashi wahalar motsawa sai kuma ciwo da ya ke da shi a kansa, dalilin abubuwan da yake SUBDURAL HEMATOMA ne yake damunsa na jini da ya taru a kwakwalwarsa a sanadin ciwukan da ya ji, shine yake saka pressure a kwakwalwarsa yana janyo mashi abubuwan da suke faruwa dashi na abubuwan da yake, Abbi ya yi duba da akwai hatsari akan aiki da za'a yi mashi yana ganin Aliyun zai iya kamuwa da ciwon mantuwa ya manta da komai na rayuwarsa amma tunda jinin ba ya da yawa, jikinsa zai iya janye jinin ya samu lafiya ba tareda aikin ba. Abbi ya girgiza kai ya ce, "Babu buk'ata aikin, Allah ya bashi lafiya." Suka amsa da, "Amin." Washegari Umma tazo ta dubashi, ba ta dade da wucewa ba Abba ya zo tare da matanshi su biyu Aunty Halima da Aunty Jamila. "Ya mai jiki?" "Da sauki." "Allah ya k'ara sauki." "Amin." Abba ya ce, "Sannu ka ji. Allah ya k'ara sauki." Aliyu ya ce, "Amin Abba, na gode." "Allah ya sa albarka." "Amin." "Sannu kin ji Hafsat, Allah ya yi albarka." "Amin." Sun jima kafin suka wuce, kamar jira yake ya kama hannunta yana murzawa a hankali, ba ya gajiya da rike hannunta, ta murmusa ta ce, "Hannuna yana maka dadin rikewa." Ya sakar mata murmushi ya ce, "Eh saboda taushi da yake da shi, yana min dadin murzawa a cigaba da kula min dashi kin ji MATAR ALIYU." Batuul ta turo kofa ta shigo, Hafsat tana kiciniyar kwace hannunta ya ki saki ta kalleshi ta kalli Batuul, gani tayi shi ko a jikinsa, ya mik'a hannuwa ya rike hannunta ya sumbata ya ce, "Ranki ya d'ad'e." Ta murmusa ta ce, "Ina wuni?" Bai amsa ba saidai gaisuwar da ya mayar mata, "Ina wuni?" Ta zauna a daya bangaren tana mai amsawa da, "Lafiya lau." Yace, "Daga zuwanki har yawuna ya tsinke, kin iya kin huta ta wajena, na karya maki hula." Har da yi mata alamar karya hular, ta yi dariya ta ce, "Na gode." Ya girgiza kai ya ce, "Nine da godiya ranki ya dade." Ya juya wa Hafsat ya ce, "Yane MATAR ALIYU." Ta yi murmushi kawai. Ta k'ara ji Aliyu ya shiga ranta saboda ba ya da b'oye-b'oye. A bayyane yake yana matuk'ar son Hafsat sai dai kuma yana girmama Batuul matuk'a yana ganin girmanta, idan kana son ganin b'acin ransa ka nuna rashin kunya gareta, duk da kallo daya za ka yi masu ka fahimci ya girmeta nesa ba kusa ba amma yana bata wannan girman tamkar ita ce babba saboda ta zauna dashi duk da ta san akwai wacce yake so, duk da ta san cewa ba ita ba ce ba a zuciyarsa. Batuul ta zuba mashi abinci tana bashi yana lumshe idanu yana santi, tana mashi dariya, lokaci zuwa lokaci yana saka Hafsat a cikin hirar, babu zato babu tsammani abun yazo ya dafe kansa yana mai fasa k'ara ya ture plate din dake hannun Batuul abincin ya tarwatse a kasa, ya tureta har saida kanta ya bugi bango saidai ba ta ji ciwo, ta yi baya da sauri ta gudu kofa tana waiwayensa yayinda tsoro ya bayyana k'arara akan fuskarta, tana da matuk'ar musamman a yadda yake abu kamar wanda ba ya a cikin hankalinsa. Hafsat ta rikeshi tana k'ok'arin rungumeshi, "Ka nutsu, Aliyu ka nutsu." Da hannu daya yayi wurgi da ita ta bugu da bango tana mai sakin k'arar wahala tana shafa kanga taga jini. Batuul ta zaro idanu ganin abun da ya yi wa Hafsat, ficewa ta yi da saurinta ta kira likita ta tsaya daga kofa tana lek'e, tana da tsoro sosai musamman na mahaukata shiyasa ta tsorata sosai da abun da Aliyu yake yi, ji take kamar zuciyarta zata buga saboda tsoro. Har mamakin Hafsat ta ke yi ganin still tsaye a wajen duk da abun da ya aikata ba da jimawa ba, ta ga k'ok'arinta, abu ne wanda ba za ta iya ba tsoro zai iya ajalinta. Tun daga ranar bata k'ara dawowa asibitin saidai ta aiko mashi da abinci, tun yana tambaya har ya gaji, har Ummi ta lura ta tambaya, "Ni kuwa shan banban nike da Fatima ne?" Ta tambaya, Aliyu da Hafsat su ka yi shiru aka rasa wanda zai bata amsa. Ta dubi Hafsat sannan ta ce, "Daughter mi ya faru?" Hafsat ta yi jim kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ga rashin kyautuwar hakan, ta lumfasa ta ce, "Ina ganin ba ta da lafiya ne?" "Yaushe rabonta da zuwa?" Ummi ta tambaya. Hafsat ta ce, "Tun ranar abun ya faru." Ummi ta yi jim tana jinjina kai sannan ta ce, "Watakila ba ta da lafiyar ne amma abun akwai mamaki domin muna waya da ita, ina ganin saidai idan wani abun aka yi mata." Da sauri Hafsat ta girgiza kai ta ce, "Babu abun da nayi mata." Ummi ta girgiza kai ta ce, "Kada ki damu daughter na san halinki, na san halin Aliyu, zan yi shaidarku akan ba za ku yi mata abu da gayya ba saidai a rashin sani ko kuma kuskure." Kafin ta rufe baki Hajiya Fadila mahaifiyar Batuul (Mommy) ta shigo, bayan ta gaidashi da jiki, ta amsa gaisuwar da Hafsat ta yi mata, da mamaki ta ce, "Ina Batuul ne kullum na zo bana samunta idan nayi magana ta ce mun sha banban ne." Ummi ta ce, "Abun da nike tambayarsu kenan suke sanar dani rabonta da zuwa tun ranar da abun ya faru, na ce watalila wani laifin su ka yi mata, tuhumar da nike masu kenan." Mommy ta girgiza kai ta ce, "Kai A'a duk yadda aka yi itace ba ta da gaskiya domin kullum idan na yi mata maganar sai ta ce mun sha banban ashe zuwa ne ba ta yi, mu je gidan in ci mata mutunci." Ummi ta ce, "A'a mu bi abun a hankali." Mommy ta murtuke fuska ta ce, "Hajiya Zaynerb za ki tashi mu je ne in ci mata mutunci ko kuma ban isa ba." Ummi ta yi dariya ta ce, "Zan je domin in kare diyata." Mommy ta ce, "Allah ya k'ara sauki, ka yi hakuri ban san haukan da ta yi ba kenan." Suka fita tare da Ummi. Daga Aliyu har Hafsat babu wanda yake da gamsasshiyar amsa akan dalilin Batuul na kin zuwa da kuma k'aryar da tayi wa Mominta. ***** A fusace Mommy ta shigo falon tunda bakin kofa take fad'a ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. Batuul ta mike da sauri tana wuri-wuri da idanu ta raina gaskiyarta yayinda baki daya jikinta yake rawa, ta sanin Mommy farin sani, duk a kanta ta san cewa tana da dalilinta na rashin zuwan da kuma k'arya da ta yi amma tana tabbaci akan Mommy ba zata karbi uzurinta ba, ta yi sa'a idan a fad'a ta tsaya bai kai ga mari ba. "Mijinki yana kwance a asibiti amma ke kina zaune a gida kin mika kafafu saidai ki girka ki aika masu da shi wato kin fi karfin kije dubashi, wato kin fi karfin ki kai abincin da kanki, ba muzurai za ki yi min ko wuri-wuri da idanu na rashin gaskiya, bude baki za ki yi ki sanar da ni uwar mi ki ke yi a gidan da har ba za ki je ki yi jinyar mijinki." Batuul ta dubi inda Ummi take ta yi shiru, ba zata iya fad'in dalilinta a gaban Ummi ba, ta marairace fuska ta ce, "Mommy ina da dalilina, zan fad'a maki." Mommy ta zauna akan kujera ta yi kwafa ta ce, "Ina sauraronki isassa." Batuul ta yi kasa da kai ba ta son tayi maganar a gaban Ummi amma Mommy ta ka sa fahimtarta, ta ce, "Mommy zan fad'a maki. Mu je asibitin." Ta fad'a domin ta kawar da maganar. Mommy ta yi mata tsawa, a fusace ta ce, "Babu inda za ki je sai kin sanar da ni dalilinki na kin jinyar mijinki saidai kike aike abinci, babu inda za ki je sai kin sanar da ni dalilin ki na min k'arya kika ce kina zuwa shan banban mu ke yi bayan kuma zuwan ne ba ki yi." Sai a lokacin Ummi ta saka baki ta ce, "Adda Fadila kiyi mata a hankali, na tabbata tana da dalilinta." A fusace Mommy ta ce, "Dalilin nike jira ta fad'a min tun kafin hakurina ya k'are inyi ta dukan tsiya." Ummi ta ce, "A'a ban da duka." Mommy ta yi kwafa ta ce, "Ta bari in k'ara magana a wajen ta gani idan ban yi mata dukan tsiya ba, idan tana tunanin zaki iya hanani torh ina mai tabbatar mata da cewa kema na isa dake tunda nice babba bugu da kari kina ganin girmana." Batuul ta yi tsuru-tsuru da idanu ta rasa abun da yake mata dadi, Mommy ta sakata a tsaka mai wuya akan maganar da bata son tayi a gaban Ummi duk da tana da dalilinta amma akwai kunya. Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰 *ZAN BI ZAB'IN UMMANA* _(Koda Zuciyata Bata So)_ *NA* *AYSHER ANGEL* Page 20 *KARSHE.* *Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.* *Daga Marubuciyar:* 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) 9. Y'an Mata 500 10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 13. Ba ni da laifi 300 14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free 15. Rumana's Diary WhatsApp 09169472057 Batuul ta yi kasa da kanta ta ce, "Ummi, Mommy, duk da abun da zan fad'a abu ne da kuka riga da kuka sani amma ina mai baku hakuri tun kafin na furtashi. Mun ina k'arama har zuwa girmana ina da tsoro, tsawa kanta tsoratani ta ke yi, ranar da abun ya fara faruwa na tsorata matuk'ar tsoro, na daure na karfafa ta cigaba da zama duk da tsoro da yake addabata, tsoro yake bani, ji nike kamar zuciyata za ta buga. A ranar da abun ya k'ara faruwa a ranar ne na tabbatar da ba zan iya ba, idan na tsaya zuciyata zata iya bugawa shiyasa na dawo gida na zauna." Mommy ta fasa kuka tana mai taba hannuwa ta ce, "Fatima butulcin da za ki yi mamu kenan, Aliyuna yana da wacce yake so amma er uwata ta dage akan cewa sai ya aureka saboda gida bai koshi ba'a kai dawa ba, Aliyu miji ne na gari da kowace uwa za ta yi wa erta fatan samunsa, Aliyu yana ganin girmanki yana girmamaki duk da kuwa shine babba, amma butulcin da za ki yi mashi kenan, Fatima kin cika butulu." Batuul ta fashe da kuka ta ce, "Please Mommy ki bar zubar min da hawaye, tsoro nike shiyasa ina gudun kada zuciyata ta buga." Mommy ta kalleta da takaici ta ce, "Ba ke kikeyi wa kuka ba, kukan takaici nike da na dana sani na amincewa da nayi Aliyu ya auri butulu kamarki." Sai a lokacin Ummi ta saka baki, ta ce, "Adda Fadila amma maganar Fatima abun dubawa tunda har shi Aliyu yasan tana da tsoro." Mommy ta taso mata ta ce, "Idan ba zaki tayani jajen had'a Aliyu da wannan butulun da mu ka yi ba torh kiyi min shiru kawai ki barni inji da takaicin da yake damuna, na yi magana kun ce tsoro, ita wacce take zaune dashi ce maku tayi bata tsoron ne, ina ce a ranar har ciwo ya ji mata a kai, ko jiya da abun ya tashi saida yaji mata ciwo a hannu amma hakan bai saka ta gujeshi, yarinyar da muka kyamata saboda talaka ce, yarinyar da muka hana ya aura, yarinyar da muka fito kiri-kiri muka nuna masu sonta dashi, bugu da kari ba jininsa bace amma hakan bai saka ta gujeshi ba, yana kwance akan gadon asibiti a halin doguwar suma ta aureshi, ta zauna ta kula dashi, har yanzu da ya samu wannan matsalar bai gujeta. Sai ita da take jininsa ita ce zata bada mamu kasa a idanu, ta kunyatamu a idanun duniya, ta muzantamu, ta yi mamu butulci," ta nuna Batuul kafin ta ce, "Ba zan tabbatar da kina da tsoro ba sai kin kashe auren sannan tunda ke dai butulu ce." Mikewa ta yi tace, "Zaynerb ta shi mu wuce kafin zuciya ta debeni in yi mugun furuci akan butulun." Ganin ta dauki zafi sosai ya saka Ummi bata mu sa ba ta mike suka fito, Batuul ta biyosu tana baiwa Mommy hakuri amma koda kallon inda take ba ta yi ba ta saka Nauwara da Sultan a mota suka wuce. *** Bayan Ummi ta koma gida tayi tagumi tana tuna abubuwan da ta yi wa Hafsat, ta nuna mata kiyayya ta yi mata gorin talauci, ta yi mata gorin asali, ta wulakantata, ta hana Aliyu ya aureta amma wannan bai hana Hafsat aurensa a lokacin da yake kwance a doguwar suma ba saboda bata rama sharri da sharri, gashi a yanzu lalura ta sameshi that ita er uwarshi da Ummi ta tilasta mashi aura ba zata iya kula dashi ba that tsoro yake bata saboda hali da ta tsinci kanta na tsoro tun a kananun shekaru. Hafsat wacce suka nunawa tsana ita ce take kula da shi, ba ta ga laifin Batuul ba domin tana da uzuri, nadama ta ke yi na abubuwan da tayi wa Hafsat, da ace hannun agogo yana komawa baya da ta tariyo baya ta goge dukkanin abubuwan da tayi wa Hafsat ta bari Aliyu ya aureta tun daga asalin farko. Godiyarta wa Allah da ya ganar da ita gaskiya ta roki Hafsat ta auri Aliyu tun kafin lokaci ya kure mata, da a ce a wannan lokacin babu aurensa da Hafsat da damuwa ta yi mashi yawa, da ba ta san inda za ta saka kanta ba, ta share hawayen da suka zubo mata tana mai nadama abubuwan da ta aikatawa Hafsat a wadancen shekarun. **** Batuul ta durkushe a wajen tare da fashewa da kuka, ta sani ta wata fuskar ba ta kyauta amma mi zai saka ba zasuyi mata uzuri ba, tana dalilinta wanda dukkanin wanda ta tashi a gabansa yasan yarintarta da girmanta ya kamata yayi mata uzuri, ta mike ta share hawayenta ta koma ciki ta yi wanka ta shirya ta dauko abinci ta shiga motarta ta kama hanyar zuwa asibiti. Yana zaune Hafsat tana mashi hira suna dariya ta shiga tayi turus tana raba idanu, ya sakar mata murmushi yana mik'a mata hannuwa ya ce, "Zo inji waye ya b'atawa ranki ya dade rai in nemi ba'asi." Ta d'aure ta karasa duk da jikinta da yake rawa tana tuna abun da ya faru a ranakun tsoro ya kamata, ya kama hannunta ya sumbata yana mai sakar mata murmushi ya ce, "Ina wuni ranki ya dade?" Duk da sanin da ta yi mashi mutum ne mai fahimta amma bata yarda sun had'a idanu ta ce, "Lafiya lau." Ta gaisheshi sai dai kamar kullum bai amsa ba saidai cewa da ya yi, "Ba za ki yi min ya jiki, na gode da abincinki mai d'an karen dadi." "Ya jiki?" "Da sauki." "Allah ya k'ara sauki." "Amin, ranki ya dade." Ya juyawa wa Hafsat ya ce, "Ba zaki gaida ranki ya d'ad'e ba." Ta yi murmushi kafin ta ce, "Bana son na katse maku hira ne shiyasa, Aunty Fatima Ina wuni?" Batuul ta ce, "Lafiya lau Angel, sannu sa k'ok'ari na barki da fama ke daya." Ta juyawa Aliyu ta ce, "Ka yi hakuri na tsorata ne shiyasa na dauke kafa amma yanzu na dawo zama daram." Ta girgiza kai ya ce, "Babu komai ranki ya dade, dukkanin wanda ya sanki yasan yarintarki da tashinki ya kamata a ce ya yi maki uzuri." Ta ce, "Na gode," a rayuwa tana son Aliyu saboda halayensa masu kyau, yana da hali na fahimta, ba ya mumuna zato, bugu da kari ya iya zama da mata biyu, irinsu za su iya zama da mace hudu and idan har sun yi dace babu wanda zaiji kansu saidai idan an samu mai mugun hali ne a ciki ta rink'a tada zaune tsaye amma Ida har za'ayi mashi adalci yana iyakar k'ok'arinsa wajen kwatanta adalci a tsakaninsu. Ta koma gefe kadan dasu ta ja kujera ta zauna, Aliyu ya kama hannun Hafsat yace, "Kin ganta tsoro ne da ita kamar farar kura tun muna yara take da tsoro, idan abun ya k'ara faruwa na bar maki amanarta ki yi iyakar k'ok'arinki domin kareta." Ta gyad'a kai tana mai sakar mashi murmushi. Ji Batuul ta yi hawaye sun zubo mata, da sauri ta gogesu tun kafin ya gani ya tada hankalinsa akan sanin dalilin zubar hawayenta. Cikin ikon Allah abun bai k'ara samunsa tana nan ba, idan abun ya tashi Hafsat tana shan wahala ba kadan ba, akwai ranar da yanka mata hannu saida aka yi mata dinki amma wanna bai saka ta nisanceshi duk da rokonta da Abbi da Ummi (Iyayensa) sukayi akan ta hakura ta koma gida amma still ta zauna. Lokacin da ya farka ya dubeta tana barci daga zaune ta yi pillow da gadon, idanunsa suka sauka akan hannunta wanda ya tabbatar da cewa aikinsa ne, tausayinta ya kamashi ya bubbuga gadon, ta bude idanuwa ta mike zaune tana lumshe idanu tana budewa ta ce, "Aliyu." Aliyu ya b'ata fuska ya ce, "Ba ki jin kunyar kiran sunana kai tsaye." Ta marairaice murya ta ce, "Sunanka yana matuk'ar min dadi ne shiyasa amma ay ba na fad'a a gaban mutane." Ya gyad'a kai ya ce, "To shikenan." Ya kama hannunta yana kallon aika-aikar da ya yi mata, da damuwa ya ce, "Ki yi hakuri." Ta girgiza kai ta ce, "Babu komai." Ya ce, "Ki koma gida, raina ba ya dadi akan abubuwan da nike maki." Ta ce, "Lokacin da ina cikin matsala ka tsaya min ka zame min gata don haka nima zan tsaya a kusa da kai in kula da kai da iyakar iyawata." Ya ce, "Idan kuma na baki umarni fa." Ta shafa gemunsa tana wasa dashi tana jan dogon hancinsa ta ce, "Oh-Oh." Ya kama hannun ya tura a cikin wandonsa yana yawo dashi akan joystick dinsa ta zaro idanu jin girman abun da kaurinsa a hakan ma yana cigaba da mikewa ne, ta kalleshi ta zaro idanu, ya d'aga mata gira ya ce, "Ina matuk'ar sonki Hafsat, a yau zan tabbatar maki da matsayinki a zuciyata." Kafin ta samu zarafin magana ya hade bakunansu yana yawo da harshensa yana mata salon sumbata mai tsayawa a rai a lokaci guda yana yawo da hannunta a cikin wandonsa yana bata karatu akan yadda za ta yi mashi. Yana yawo da daya hannunsa a saman kirjinta da suke tsaye kamar zasu tsone mashi idanu, ya tura fuskarsa a tsakiyarsu yana yawo da tongue dinsa a tsakaninsu kamar k'aramin yaron da ya samu alewa. Dadi ya ratsata tana nishin dadi ta turo mashi su yayi yadda ya so, ya mikar da ita ya saka hannuwa yayi kasa da skirt dake a jikinta ya tura hannunsa a kasanta yana yawo dasu yana turasu ciki, babu abun da take sai nishin dadi, ya yi kasa da wandonsa, saida yayi addu'a sannan ya fara mai gaba daya yana murzata a hankali cike da nutsuwa yana sumbatu tare da saka mata albarka yana fad'a mata yadda yake sonta, yana kallon cikin idanuwanta tana kallon cikin idanuwansa komai ya wakana, yadda yake murzata, yadda yake turata, yana aikata komai cike nutsuwa da so, yayi matuk'ar bata mamaki bata san akwai irin wadannan maganganun a bakinsa ba, ya iya soyayya mai tsarawa a rai, ya matseta da bango ya hanata motsawa domin yaji dadin nuna mata soyayya mai tsayawa a rai. A ranar taji ta daban, ta jita a matuk'ar farin ciki, Aliyu ya nuna mata soyayya da bata tab'a tsammanin za ta samu ba, nagartaccen namiji da ya kure a fagen sarrafata, yana murza kirjinta a lokaci daya yana sarrafata da nutsuwarsa. Bayan komai ya lafa ya rungumeta a jikinsa yana mai saka mata albarka, ta sakashi a farin ciki marar misaltuwa, yayi sama da ita zuwa bandaki inda aka k'ara buga wani wasan kafin sukayi wanka suka fito ya haye saman gado yana mai nuna mata kusa dashi. Ta girgiza kai sai a lokacin kunyarsa ta kamata tana tuna yadda komai da wazana da irin da kallon da yake mata a lokacin wanda yake tattare da so da kauna, ta make kafad'a tana nuna mashi daya gadon inda take kwana, ya shammaceta ya janyota jikinsa ya kwanta tayi lamo a faffadan kirjinsa tana shakar kamshinsa mai sanyaya mata zuciya tana jinta a cikin matuk'ar farin ciki. Washegari dukkanin lokacin da suka had'a idanuwa zata tuna yadda komai ya faru, so da kauna da ya nuna mata da irin kallon so da yake mata a lokacin komai yake wazana, saidai kawai taji ta saki murmushi, ya tashi kanta a daren jiya, ya bata karatun so mai wahalar mantawa. Cikin ikon Allah abun yana raguwa, yana samun sauki har yakan jima sosai abun bai faru ba, anyi discharging dinsa suka koma gida ya tare a bangaren Hafsat wacce Abbi ya zubawa kaya naji da fad'a taso a ce ya ta siya da kanta saidai tana ganin girmansa ba zata iya mashi musu ba, ta tare a bangaren Hafsat ne saboda halin da yake a ciki duba da yanayin Batuul idan ya zauna a bangaren abun za'a iya kasancewa cutarwa a gareta. Har gida Batuul da Aliyu sukaje suka baiwa Mommy hakuri akan fushi da takeyi da Batuul, "Aliyu tunda har kazo da kanka babu damuwa na yafe, Allah ya saka maku albarka, Allah ya albarkaci aurenku, ya baku zaman lafiya. Ina diyata Hafsat?" Aliyu ya ce, "Tana gida." Mommy ta b'ata rai ta ce, "Shine baku tafo min da ita ba, baku kyauta ba." Aliyu yayi kasa da kai ya ce, "Za ta zo." Mommy ta ce, "Ina jira, ka gaida min da ita." Yace, "Za ta ji." Daga nan suka wuce gidan Ummi itama hakurin suka bata saidai ita bata dauki abun da zafi ba, ta fahimci Batuul sannan kuma tayi mata uzuri duba da yanayinta, nasiha tayi sosai. Koda suka koma gida bai manta da sakon Mommy, ya rungume Hafsat ta baya yana mai sakar kamshinta mai dadi, hannuwansa akan kirjinta yace, "Mommy tana gaishe dake, ta ce tana nan tana jira." Ta lumshe idanu tana mai amsar sakon da yake aika mata ta ce, "Ina amsawa, In sha Allah idan na fita zan je in gaishe da ita." Yace, "Da kuwa kin kyauta, Allah yayi maki albarka." Ta amsa da, "Amin." Ganin yana kunce wando ta ware idanu ta ce, "A parlour muke." Ya kashe mata ido daya ya ce, "Har a dinning table ana yi idan baki da karatun ki nutsu ki dauka sannu a hankali zan koyar dake komai." Yayi sama da ita ya sauketa akan kujera ya ware kafafunta ya rufa a kanta yana sarrafata cike da kwarewa da so, yana mata kalaman da suke sakata jin kunyarsa har mamakinsa takeyi, tana mashi kallon shiru-shiru ashe oga ne ta wannan fagen. Yana tashin kanta da salon soyayyarsa, yana kure mata karatu da salon soyayyarsa, tun tana jin kunya ta nokewa har ta saki jiki tana kallon cikin idanunsa tana more kallon son da yake mata a dukkanin lokacin da yake tarayya da ita. Bakinsa akan kirjinta wadanda ba ya gajiya da wasa dasu, idan har yana a kusa da gida ba ya gajiya da murzasu. Bayan komai ya lafa ya rungumeta yana mai sauke ajiyar zuciya ya mik'a hannu ya dauko makullin ya mik'a mata, "Gashi na siya maki." Ta rungumeshi tana mai nuna farin cikinta, ya sumbaci kumatunta ya ce, "Uhm mu je sama kiyi min godiya da kyau." Yayi sama da ita ya wuce sama yana dauke da ita. Tana kure ado a gidan, shiga take ta kece raini, idan har za ta yi kwalliya sau dubu to kuwa Aliyu yana kalmomin yaba kyawun da tayi guda dubun, ya matuk'ar sakata farin ciki kasancewarta mace wacce take son idan tayi ado a dubeta a yabata, yabon ya fiye kyautar da yake mata a wasu lokuttan, tana matuk'ar jin dadin yaba adonta da yake, ta zage damtse tana kure wanka a gidan, kullum shine yawo da guntun boxer ba ya tab'a gajiya da ita. A mafi yawan lokutta yana kure wanka ya murza hula dara ya sauko parlour ya hakimce ya ce ta zo ta biyashi wankan da yayi, he will like, 'Nifa koda an yaba sai an biyani kuma bani son biyan kudi, biyan soyayya nike so, a tashi kaina da salon soyayya ta yadda zanji cewa an burgeni inji cewa an faranta min' Aliyu yana cigaba da samun sauki, abun yana dadewa bai faru ba, yana iya watanni biyu abun bai faruwa sai dai still akwai sauran jini a cikin kansa. Daga bangaren Batuul ake kawo mashi girki safe, rana da dare, yana matuk'ar son girkin Batuul, Batuul kwararra ce akan fannin girki na gargaji da zamani, tasan hannunta saidai idan bata shiga kitchen ba, tana shiga babu jimawa kamshi mai dadi zai ziyarci falonta. Duk da Batuul ce take kawo masu girki amma idan Hafsat ta girka mashi yana ci kuma ya yaba domin itama ba daga baya saidai kawai banbancin dake a tsakaninta da Batuul a bayyane yake, Batuul karshe ce. Ranar suka hadu a bangaren Hafsat har dashi suka shiga kitchen suka had'a kalolin girki dadan-daban suka jera akan dinning table, Batuul ta wuce bangarenta domin tayi wanka ta shirya, Hafsat ta wuce sama, Aliyu ya rigata gama shirya ya sauko kasa yana sanye ne da dakakkiyar shadda dinkin zamani ya murza hula dara da matuk'ar mashi kyau, Batuul ta shigo tana sanye da leshe dinkin bubu ta kashe dauri, ya ware hannuwa ta fad'a jikinsa ya rungumeta tana mai shakar kamshinta ya ce, "Ranki ya dade an sha kyau." Yayi mutuwar tsaye yana kallon Hafsat da take saukowa cike da tako na salon burgewa tana tako baki daya jikinta yana girgiza, leshe ne a jikinta dinkin straight gown wacce matseta dukkanin wani lungu, sako da tudu na jikinta ya bayyana, ta wrapping kallabi a kanta tayi dauri irin salon saka dararsa wanda yake matuk'ar burgeta. Idanunsa akan Hafsat dake saukowa daga saman benen yace, "Ranki ya d'ad'e. MATAR ALIYU ta tashi kaina da wannan wankan, MATAR ALIYU makurar kyau ce." Hafsat ta sakar mashi murmushi ya kama hannunta yana shakar kamshinta ya lumshe idanu ya bude ya ce, "MATAR ALIYU kinyi matuk'ar kyau, kin tashi kaina da samfurin daurin kallabinki." Ta gyara mashi dara dake a kansa ta ce, "Ka yi kyau abunka, yadda kake daura darar nan yana tashi kaina." Ya juyawa Batuul ya ce, "Mu je ranki ya d'ad'e in kwashi garar girkinki." Suka k'arasa dinning table. Hafsat ta fara zubawa mashi sannan ta zubawa Batuul kafin ta zubawa kanta. Aliyu yayi lomar farko ya lumshe idanu ya ce, "Ranki ya d'ad'e wannan girki ya tashi kaina, dadi akan dadi, kin iya kin huta ta wajena, ta karya maki hula." Har karya mata hular saida yayi, tayi dariya ta ce, "Na gode, aci dadi lafiya." Hafsat tayi mashi bidiyo tayi mashi tana dariya, Batuul tana tayata. "Santi yake." Batuul ta ce, "Kawo waigi mu saka mashi." Girkin yayi dadi babu karya sai dai koda mintina biyar ba su yi da fara cin abincin ba abun ya motsa, ya toshe kunnuwa yana mai fasa k'ara, Batuul ta rabe a bango jikinta yana rawar sanyi, tsoro k'arara akan fuskarta, baki daya jikinta rawa. Hafsat tayi baya tana mai jin tausayinsa tana son matsa kusa dashi saidai idan ta tuna gargadi da yayi mata sai ta fasa, ya jiya kansa ciwo da wuka dake akan teburin, ya watsar da komai a kasa. Yayi luu ya zube a kasa ta tallafosa hankalinta a tashe ta warware kallabinta ta nannade mashi wajen da ita. Jiki a sanyaye Batuul ta koma parlour ta zube akan kujera tana mai sauke lumfashi yayinda tsoro k'arara ya bayyana akan fuskarta, baki daya jikinta rawa yake, ta dauki waya ta kira likita babu jima suka zo suka gyara mashi hannun tareda k'ara dubashi. Cikin ikon Allah ya samu sauki, ya tarasu a bangarensu yayi masu nasiha tareda raba kwana kowace kwana biyu-biyu, saida suka fara rabon kwana sannan ta tabbatar da ta yi sabo da shi, saida ta yi kuka a ranar ta rasa abun da yake mata dadi. Ranar da girkinta ya zagayo ta shiga kitchen ta zage ta girka mashi kalolin girki da ta koya a wajen Umma, tayi mashi amfani da recipe na Umma, ta gama ta jera akan dinning table, ta sha gayu ta kure karshen adaka ta kashe dauri samfurin da ta san yana matuk'ar so ta hakimce a parlour tana jiransa. Shigowa yayi a gajiye ya ware hannuwa yana mai yaba kyawu da ta yi, "MATAR ALIYU kin kure kyau fa." Ta taka ta shige jikinsa ya rungumeta yana mai sauke ajiyar zuciya, yace, "Kamshinki yana min dadi." Ta ce, "Na gode, mu je kayi wanka mu sauko ka ci abinci na zage nayi maka girki da kaina." Ya ware idanu ya ce, "MATAR ALIYU ta kyauta, na gode, muje in gama MATAR ALIYU sannan in sauko." Ta make kafad'a tana dure kafafu a kasa kamar karamar yarinya ta ce, "Oh-Oh ni ba za'a b'ata min kwalliya ba, na tab'a lokaci ina yi domin ka yabani." Ya ce, "Kuma na yaba." Ta make kafad'a tace, "Oh-Oh." Saida ya sumbaceta sannan ya ce, "Shikenan muje ki fadi adadin yabon da kike son inyi maki, nayi maki kafin na yab'a kwalliya akan gado, kika sani ko in balle gadon." Ta ware idanu ta ce, "A ina?" Ya nuna mata kugunsa yana juya kugunsa yana nuna mata yadda ake yi, ta juyar da kai, yayi sama da ita zuwa saman bene. ******* Jalila duniya sabuwa ita da mijinta yawo sukeyi kasashen duniya, dukkanin inda zaije kafarta kafarshi, amma sun zama a London, a can ta haihu ta santalo D'anta namiji kyakykyawa kamar mahaifinsa, Hafsat da Aliyu sun je har London ganin babynsu. Murna a wajen Jalila ba'a magana jin Umma da Mama suna akan hanya, sukayi shagalin suna abunsu. Hafsat tayi baby, jinsa take kamar gudan jininta, yaron Jalila yaronta ne, yaranta yaran Jalila ne, ba zata tab'a manta halarcin Jalila a gareta ba, ta rikid'a daga k'awa ta koma er uwa. Muhammad da Little Aliyu suna London karatu tare da Abdallah, har gidan Auntynsu Hisham ta kawosu, bayan sun suna suka tsaya suka zaga gari kafin suka juyo Nigeria, duk da a wajen k'anwar mahaifiyar Hisham yaran suke karatu amma idan zamansu yana a hannun Hafsat, idan suka dawo hutu a gidanta suke sauka, Aliyu ba ya nuna banbanci a tsakaninsu da yaransa. Hafsat ta zama er gatan Mommy da Ummi. Ummi tana ji da ita sosai, idan sukaje da Aliyu yadda Ummi take mata sai ayi tunanin ita ce diyar gidan ba Aliyu ba. Aliyu dama can na wajen Umma ne, Hafsat har mamaki Hafsat saidai hakan yana da nasaba da aiki da Umma tayi a gidansu da kuma girmamata da yake yi shiyasa take ji dashi. Umma ta zama hajiya ta ajiye fad'a da ta koya a gidan haye ta zage ibada da taimako mabukata da marassa lafiya. Batuul ta santalo diyarta mace yarinya taci suna Hafsat amma suna kiranta da Sawwama. Murna a wajen Hafsat da Aliyu ba'a magana, anyi shagalin suna anci ansha, yayi kyautar kudade wadanda shi kanshi bai san adadinsu ba. Watanni biyar a tsakani Hafsat ta santalo D'anta namiji mai kamanni da Aliyu sak kamar kobo da kobo, murna a wajen Aliyu da Hafsat ba'a magana, yaro yaci suna Aliyu amma suna kiransa da Haidar. Shekara daya da watanni biyar ta k'ara santalo tagwaye maza wadanda suka ci suna Muhammad da Taheer, sunyi wa Abbi da Abbu (that's mahaifin Batuul) takwarori amma suna wa yaran alkunya da Imam da Shureim. Haihuwa ta ke yi akai-akai, har en ukku tayi, ta k'ara twins maza, ta yi twins mace da namiji kafin haihuwar ta tsaya mata. Hafsat da Batuul suna zaune lafiya, Aliyu yana cikin kwanciyar hankali a kullum arzikinsa bumkasa yake yana jika matansa da yaransa da naira, babu abun da suka nema suka rasa, jin dadi na duniya yana basu saidai wannan bai saka yayi sakaci da tarbiyyarsu ba, yana matuk'ar k'ok'ari akan iliminsu na addini da na boko. Halinsa na taimako yana nan, kyauta da taimako yake da dukiyarsa kamar bai san zafin nemanta ba, arzikinsa a kullum k'ara habbaka yake. ALHAMDULILLAH, Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da Ya bani ikon kammala wannan littafi mai suna ZAN BI ZAB'IN UMMANA (Koda Zuciyata Bata So), Ina mika sakon godiya zuwa ga Members na ZAN BI ZAB'IN UMMANA COMMENT SECTION, sharhinku ya bada gudummuwa sosai a wajen bani karsashi na rubuta wannan labari, godiya ta Musamman zuwa ga; Writer Diamond Bhatool, Writer Maryam Annour, Writer Zouley Sabitou (Émilia), Faha'us Chambo, Zahra Graphic (Mamee), Princess Fulani, Mummy Khairat, Hajara BB, Aeesharh, Oum Hafsat, Jamila Shuaibu, Oum Gee, Asmau (Oum Ameer), Mmn Useey, Garba Fatima, Asmau Ih Usman, Hauwau Abdullahi da sauran wanda ban rubuta sunansu, MATAR ALIYU tana godiya. Ina da tabbaci akan kun shaida akan labarin nan is worth reading, thank you so much, Angel is grateful, Allah yabar zumunci, Allah ya bar kauna, Jazakallahulkhair. Kirkirarren labari ne idan ya yi daidai da rayuwarku arashi ne, ku yi amfani da darussan da ke a ciki, ku watsar da kurakuran da su ke a ciki, wanda wannan littafi ya farantawa rai burina kenan wanda kuma ya b'atawa rai ya yi hakuri. Sai kuma mun hadu a books da zan yi a nan gaba; *MATAR ALIYU.* (The Upside Of Down) REPOSTING, and then *SUNE SUKA JANYO MIN.* free book REPOSTING OR *ZANE A KAN RUWA.* (Mai Wahalar Gane Kamanni) Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu) marubuciyar 1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600 2. Mutuwa A Maƙoshi 600 3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500 4. Ban Dace Da Shi Ba 600 5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600 6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600 7. The Choice I Made 600 8. Y'an Mata 500 9. Ya fi Ƙarfin Kai na 600 10. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600 11. Chasing My heart, A Tsakanin So 600 12. Ba ni da laifi 300 13. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) free book 14. Rumana's Diary 15. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni) WhatsApp 09169472057 Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu) 💖 💖