🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZANBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ECRITE: _PAR_ *QUEEN ZEEFAT* Yar Mutan Niger Wattpad@nazhabibou 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _BISMILAHIR RAHAMANIR Page 1 Dandanzon matasa ne maza da mata ke fitowa daga cikin wata babba kofa wada a samata aka rubuta *LYCEE TECHNIQUE DAN KASAWA DE MARADI* hakan ya nuna cewa makarantar boko ce gashi kuma kowane matashi da jakar makarantar sa a baya wasu kuma a hannu kowa sai kama gaban shi yake sanadi tashi da akayi daga makarantar, wata yarinya ce ke tafowa tana nufo kofar makarantar hannun rike da wata farar takarda da jikar makarantar a dayan hannu sanye take cikin dongon hijabin ta har kasa da nikaf a fuskar wada ko eyes inta ba'a gani don fuska rufe take gaba daya ga safa da take sanye da ita ta hannu da ta kafa duka ilahirin jikinta rufe yake babu abinda ake gani, tana tafiyar ta mai kama da hawainiya cikin kwonciyar hakali da nutsuwa kamar mejin tausayin kasa a haka har ta kawo baki kofar makarantar tayi wajan wani shago dake gefan makarantar mai shagon dake zaune daga daya bangaren shagon yana ganin ta ya taso yace malama mikike bukata banji mitace ba sai gani nayi ta mika masa takarda hanuta ya karba yayi cikin shagon da takadar a hannu sa ba'a fi minti biyu ba sai gashi ya fito daga shagon ya mika mata takarda biyu a maimakon guda da tabasa karba tayi ta bude jakar makarantar ta fido kudi ta mika masa ta juya takoma cikin makarantar da takardun a hannu ta daidai wani office ta tsaya ta kwonkwasa sai ga wani datijo ya fito wanda baza ya fuce 50 years tadan rusuna ta mika masa daya takardar ta juya da dayar wajan parking space dake cikin makarantar ta nufa tsayawa tayi daidai wata hadadiyar benz kirar mercendy ta bude jakar ta makaranta ta fito da makulin mota budewa tayi tashiga ta tayar da motar tare da barin cikin makarantar a lokacin da daliban dake cikin makarantar basu huce mutun shida sabida kowa ya kama gabansa. Driving tayi natsawon minti 20 kamin take kawowa wata kayataciyar anguwa daga ganin anguwa ba me yawon mutane bace sabida yanayin ta ya nuna hakan ga wani hadadan kuma babban filin ball daya ya karama anguwar kyau macha allah Wajan wasu mayan tsararu kuma kayatacin gidaje guda biyu dake irin daya naga ta nufa komin su gidajan irin dayane sedai guda yafi guda girma shima ba sosai ba wanda ya fi girma a cikin gidajen ta nufa tana dana hon mai gadi ya wangale mata tagamemiyar porte (get) in gidan ta tura hancin motar ta a ciki, tsaruwa haduwa kayatuwa kai yayine gidan karsha ne wajan haduwa babu abinda ba na rayuwa a gidan parking space kadai ma na gidan abin kalon to baran tanama farfajiyar gidan Parking in motar tayi a parking space dake cike da motoci sun kai kala 10 ta fito daga cikin motar ta kule tareda fitowa daga parking space in tayi hanyar shiga gidan, gidan dauke yake da sashe guda uku daya a gefen hagon gudan a kefan dama se dayan natsakiya kuma shine bangare mafi girma da ke cikin gidan hanyar babban bangaren tanufa tare da murda wata daleliyar kofar da zata sadaka da falon gidan shiga tayi hade da salama a bakin ta wada in ba kusa kake da itaba ba zaka taba jin abinda ta fada wooow nace tare da furta allah sarkin dadi inji barawon takanda lokacin dana tsintsi kaina a wani katarfaran falon da ya tsaru iya tsaruwa komi na falon brown and milk color ne, falon dauke yake da bedroom guda biyar da cuisine (kitchen) guda se set uku na kayatatun kujeru sabida girman falon da dan madaidaicin table central (center table)milk color shi ba babba ba shiba karami ba wanda ya kawata tsakiyar kujerun se TV stone dake jikin bangon falon akasa tare da wata tangamemiyar TV dake manne a bango babu ce kadai ha babu a ciki ga wani kayatacen kamshi dake tashi a falon mara misali sabida shagalta danayi wajan kalon tsaruwar falon har na manta da rahoto nake dauko maku falon ne ya tsaru irin tsaruwar da ban taba gani irinta ba sai a TV Babu kowa a falon hakan yasa ta nufi kofar daya daga cikin bedroom din dake falon ta mudar kofar tashiga da kafar dama hade da yar siririyar salama a bakinta wani ni'imtacan kamshi mara misiltuwa ya daki hancina nace macha allah, babu wani tarkace a ciki amma ya hadu daga bed da wardrobe sai dressing miror da kujera babba guda dake gefe sai douche interne (bathroom) da abin ajiyar jaka kusa da armoir (wardrobe ) da abin rataye kaya da ke manne da bangon dakin sai agogo itama manne a can saman bango babu abinda babu a cikin na more rayuwa kana ganin yanayi dakin zaka gane na yan mata ne daki dai macha allah Tana karasa shiga dakin taje dan gaba da kofar dakin tacire takalmin dake kafarta ta juya tayi bakin gadon dake cikin dakin ta zauna ta cire nikaf da hijabin da ke jikin tare da cire safar hannu ta da ta kafa ta mike tare da nufar wardrobe ta bude ta ciro serviette (tawel) juyowa tayi da niyar nufar hayar toillet take nan takardata da biro dake hannu na suka subice min la'illaha illa anta subhanaka inni kuntum bina zalim ku kuke ganimu bamu muke ganin kuba na furta tare dajan baya da karfi sanadiyar tozalin da nayi da kyakyawar fuskarta juyawa tayi tare da shigewarta toillet da sauri nayi wajan peper da biro na dan na dan labarta ma masu karatu haduwar yarinyar da kyau dinta bai musultuwa banta ganin kyau irin nataba ko acikin larabawa da turawa Yarinya yace da bazata fuce 18 years ba dogowa amma ba can ba tsayin ta daidai da ita siririya ce amma ba sosai ba ita ba fara ba kuma ba za'a sanyata a layin bakake ba yarinyar café au lait ce (shacolate in milk color) irin black americain din nan ce idan kanganta a kusa da wani black americain din ita zaka iya cewa tanada haske amma ba sosai ba da kaire mutun zai tantance kalar fatar ta ma saidai a kimanta gashi girar ta ya kwanta luf luf sai sheki yake da daradaran idanun ta farare tas dasu se bakin da ke cikin idanu ita nata brown ne mai kamar baki da zarazaran gashi idanuta tsaf dasu sai dogon hancin ta har baka da dan karamin bakinta da ya karama fusakar kyau da sheki allah ya mata kyau na gasken gaske baza taba iya musulta kyau irin nata sedai a kiman tashi shima sabida du yanda zaku misilta ta tafi da hakanan Turo kofar toillet din tayi ta fito daure da tawel da ya sauko mata har ga gwiwa sanan da daya kuma a saman kanta ga ma zauna da allah ya azirtata dasu kamar ba na karamar yarinyar yar shekara 18 ba wajan dressing mirror tanufa ta ja dan taburan ta zauna mika hannu tayi saman dressing mirror din ta dauko wasu hadadun turare guda uku irin na shafawa ajiki ta shafe jikinta gaba daya dake da damshin ruwa kafin ruwan su tsane a jikin ta janye tawel din dake saman kanta saiga gashi ta ya bayana wanda yake dogon baki kirin dashi daga zaune da take gashi yakai har kusa da ma zaunanta da kadan bai ida tabo suba ta dauki abin busar da gashi tana busar dashi da ya bushe ta dauki man kai mai kyau ta shafa masa tare da daukar mashaci ta shace gashin take gashi ya gara kyau da sheki ta dauki shoushou (ribon) zatasa saka ta kasa sabida yawa da tsayin gashi baza iya daure shiba tayi tayi ta kasa a haka ta hakura ta barshi zube a bayan ta tashi tayi ta nufi wardrobe ta fido wata hadadiyar doguwa riga mara nauhi baka mai ratsin ja tasaka tare da dauko hijab da darduma ta rufe wardrobe komawa tayi wajan dressing mirror din ta feshe jikinta da dadadan turare na fesawa mai kamshin gaske tsakiya dakin ta dawo tashinfida darduma tasaka hijab tare da tayar da salllah. Tana idar da sallah tayi adu'o inta ta mike ta linke dardumar da hijab sanan ta mayar dasu inda suke komin ta cikin tsari nutsawa da kwonciyar hankali take yinshi ta dauko dan kwalin rigar dake saman gado ta aza a saman kanta daya rufe duka ilahirin kanta sai dan jelar gashi daya fito a bayan ta da ya kusa tabo mazaunan ta komawa tayi wajan dressing mirror din ta dauko ribon din ta fita daga cikin bazata Commenté Et partager Comments And share 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZANBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ECRITE: _PAR_ *QUEEN ZEEFAT* Yar Mutan Niger Wattpad@nazhabibou 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _ BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM Page 2 tana fita daga dakin ta nufi stairs dake dauke da bedroom uku dakin dake gefen dama ta murda ta shiga da salama, wata mata ce da ba zata fuce 45 ans (years) ba fara tass da ita kamar ka kwontala jini ya fito matar tayi masifar haduwa kana kalon fuskar ta zaka hango muguwar kamar da suke sosai da yarinyar sedai sosai tafi yarinyar haske amma yarinyar ta fita kyau nesa ba kusa amma kana ganin ta zakasan cewa mahaifiyar tace sabida kamar da suke dakin mahaifiyar tata shima yayi matukar haduwa masha Allah Murmushi ne dauke ga fuskar mahaifiyar tata ta lokacin da ta dago tana mai amsa mata salama oyoyo AFREEN dina diyar albarka karaso ki zauna wada aka kira da AFREEN ta karaso ta zauna kusa da mahaifiyar ta da murmushi a fuskar tace Maman sannu da gida yawa AFREEN ya akayi yau kuka jima baku taso daga makaranta tunda zu nike falon kasa inajiran zuwan ki har nagaji da zama na taso na tafowa ta daki dan nayi sallah danaga lokaci yayi, AFREEN tace wly Maman wani exercise ne mukayi na mass mai wahalar gaske duk ya caza mana kwakwalwa sai fah 12:30 muka fito daga aji kuma sai na karbi peper excercise din ga malamin mu nayi copin ta a wani shago da ke jikin ecole (school)din tamu sabida inaso nasake yinta a gida sanan na mayar masa da tasa tarkardar sanan natafo gida da copie din danayi, kamin na nufo gida 12:50 tayi shiyasa gashi har lokacin komawar mu da yamma ya kusa tayi maganar cikin wata irin murya me nuna nutsasiyace yarinyar ce, mahaifiyar tata tace gaskiya kam yanzu karatu se kun kara bada hima sabida kuna shekarar ku ta karshe kinga ga exam din ku na karshan shekara sai kun shirya masa tun yanzu fa ba se lokaci ya kure maka kinga kuma in mutun na son samin cikar burin shi dole sai ya wahala kamin ya ke cin ma nasara dan haka AFREEN a dage da karatu nasan bakida wasa amma akara saman wanda akeyi Allah dai ya taimaka kuma yamaki albarka tace ameen Maman bari naje na kwanta koda na minti 30 kamin lokaci ya karasa yi ta na fadar haka tare da mikewa tsaye maman tace to jeki amma kitabatar da kinyi Sallah kamin ki kwonta tace maman ai har nayi sallah da wanka kamin na shigo nan to madala kinci abinci ma kuwa a'a maman ban jin yunwa AFREEN ta fada a takaice, maman tace ko alama, yama zaki cemin bakin jin yunwa alhalin daga makaranta kike nasa da har kikaje kika dawo baki ci komi ba muje nazu ba miki abinci kici ina aka taba yin karatu ba cin abinci sai mutun ma yakasa gane abinda ake koya masa maman ta fada tana mikewa daga zaman da take ta nufi kofa kamin takai ga fita dakin AFREEN tace to Maman ga ribon ku daure min gashi na ni nakasa amsa ribon din Maman tayi ta daure mata gashi tareda juyawa ta bar daki ba musu AFREEN tabi bayan ta suna sabka down stairs din suka nufi dinning table taja kujera ta zauna maman zata zuba mata abincin tayi maza ta karba tace Maman bari dan Allah zan zuba ma maman ta barmata ta zuba tare da komawa cikin falon ta zauna daya daga cikin kujerun dake falon tana ganin maman tabar dinning ta fara cin abinci, ba dayawa taci ta tashi ta nufi cikin falon tace maman na koshi fah maman tace kedai AFREEN bakya son cin abinci ko??? to tashi ki tafi ki kwanta ki futa amma da dadare sai kinci da yawa to maman insha Allah Tashi tayi ta nufi dakin ta tana shiga tayi kan gado ta kwanta tare dayin bismillah hade da karanta adu'o in da ake karan tawa idan za'ayi bacci, bata jima da kwanciya ba barci yayi awon gaba da ita. Maman na zaune a falo tana kalon TV aka bude kofar wani daki wada ke daya daga cikin bedroom din dake falon wata farar mata doguwa mai matsakaicin jiki tafito daga dakin ta karaso cikin falon ta zauna tace Maman fauzia barka da warhaka barka dai umman Zeinab har kin fito tace eh a takaice daganan ba wanda yasake cewa komi falon yayi shiru baka jin motsin Komi tv sunfi minti 10 a wajan kamin ake kara bude wata kofar nan ma dai wata matar ce ta fito ita ba doguwa ba kuma ba gajeriya amma wanan baka ce kuma macha Allah tana na dan jikin amma ba irin mai yawan nan ba, murmushi dauke a fuskar ta karaso falon ta nemi guri ta zauna tare da furta sanun ku da futawa a tare suka juyo suka amsa wada aka kira da Maman fauzia tace Tanti yara yau najiki shuru tun dazu baki fito ba injin dai lafiya tanti yara tace wly Maman fauzia kaina ne naji ya na min ciwo shiyasa amma koda nayi sallah nasha magani wanzu kam da sauki cikin nuna kulawa Maman fauzia tace Allah Sarki da bacci ma kikayi da shikenan da kin tashi sai kiji kin warware tanti yara tace a'a bama sai na kwanta ba yayi sauki ina yata sabida itama nafito Maman fauzia tace Allah kara sauki tana ciki dakin ta tana bacci kin san yau sai kusan 1:00 tazo gida tace wani exercise aka basu mai zafi shiyasa suka jima a makaranta Allah sarki diyata ta kwaso gajiya kenan gashi kuma lokacin komawa na yama yayi Tanti yara tafada hade da daga kanta a saman bangon falon tare da kalon agogon dake manne da bango tace kinga ma har 2:20 tayi bari naje na tasheta kada ta makara Tanti yara tafada tare da mikewa tana mai nufar dakin AFREEN murmushi kawai Maman su fauzia tayi tareda maida hankalin ta ga TV umman Zeinab dake wajan batasa masu baki a maganar suba tabi bayan Tanti yara da harara tace wajan neman a sanka har a manta dakai Allah rabamu da shishigi da cusa kai taja wani dogon tsaki hade da mikewa ta nufi dakin abinta binta da kalo Maman fauzia tayi har ta shige dakin ta banko kofar Maman fauzia ta girgiza kanta tace Allah ya shirya sabida ita yanzu abin umman Zeinab ya daina bata mamaki Tanti yara nashiga dakin AFREEN bata sameta a ciki ba amma taji kara ruwa a toillet alamun tana ciki hakan yasa ta nemi gefan gado ta zauna tana jiran fitowarta bayan kamar minti 5 da zaman ta aka turo kofar bayin AFREEN dake ciki ta fito daure da da tawel da alma wanka tayi, bata lura da tanti yara dake cikin dakin ba kawai ta nufi wajan dressing mirror ta zauna tana mai tsane jikinta kamar daga sama taji murya Tanti nacewa AFREEN diyata har kin fito da sauri ta juyo ta sauke mayan idanun akan Tanti ta saki wani kayatacan murmushi tare da tasowa ta nufo wajan tanti da sauri tare da rungume ta tace tanti na yanzu nake cewa idan na shirya sai naje wajanki kamin na fuce makaranta sai gashima Allah ya kawomin ke Tanti tayi dariya tare raba jikin da na AFREEN tace kai AFREEN kedai kinki girma dubi fa yanzu da a tsaye nake da kin kayar dani wai yaushe zaki girma ki daina shirme cike da shagaba AFREEN tace wlh tanti nidai bason na wani girma nayi zamana a haka ya fimin tanti ta dafe kanta tace kinji shirmen ko bafa kiyi kiba nake cewa ba a'a nufi na yaushe zakiyi hankali tanti ina fa da hankali kinga fa shekara ta har 18 fah AFREEN ta fada tana mai turo dan karamin bakinta cike da shagwaba to shikenan naji jeki ki shirya ki karasa shiryawa kada kiyin lati AFREEN tace to tashi tayi daga gaban Tantin ta koma ta zauna gaban dressing mirror tafara shafa mai da turare cikin nutsuwa take komi ha ta gama shirya wa cikin wata hadiya doguwa riga ta Atanfa da ta karbi jikin tayi matukar yi mata kyau saka safarta ta hannu da ta kafa tayi tare da dauko dogon hijabin ta tasaka har ya najan kasa taje ta sake bude wardrobe ta ciro nikaf ta ruke a hannu ta juyo wajan tanti da tunda tafara shiryawa take kalonta tace tanti na kamala ajiyar zuciya tanti ta sauke tace waike AFREEN yaushe zaki daina irin wanan shigar haka an ce mutun ko fuskar sa ba ya bari a gani to koni dai ni dake da aure a kaina bana irin wanan shigar taki to wai tayaya wani zai ganki yaji yana sonki har ayi wata maganar aure a cikin wanan shigar du wanda ya ganki zaiyi zaton matar wani baban malami ce ke AFREEN ta waro idanu ta tareda turo dan garamin bakin ta tace tanti ni ina ruwana da wani kuma nida ke harakar karatu na nidai nafison nayi shigana a haka kofa cikin class bana cire nikaf dina tanti kinga fa shekarana biyu yanzu ina cikin ta uku a school din mu amma bu wanda ya taba ganin fuska na kwanaki da aka kawo mamu wani sabon malami yace dole sai na bude fuska na ko na fitar masa daga aji ni kuma nafita bayan fitana wai yake tambayar yan ajimu wai miyasa bana bude fuskana sukace ce masa suma basu sani ba suma tunda suke basu taba gani fuska na ba ko ance na bude bana budewa sai kawai yace aje acemin na dawo nazo na zauna haka na dawo ajin na zauna ba tareda na fida nikaf din ba amma ana ganin eye dina. AFREEN tace tanti bari naje kada nayi lati tare da saka takamin a kafarta Tanti tace yi maza ki fuce naga har 2:50 tayi amma yau AFREEN ki ban mamaki yada kika yi magana da yawa haka AFREEN tasaki murmushi tare da bari cikin dakin tanti na biye da ita a baya tace tanti wai ina anti khairat tunda nazo ban ganta ba Maman ki ta aiketa gidan yayar ku amma yanzu ta dawo nasan dai sai kin dawo zaku hadu tanti ta fada AFREEN tace to Tanti dan Allah ki fada ma maman cewa nafuce sabida nayi lati kamin na je saman stairs nayi mata salama lokaci zai kure ta fada tana me murda kofar falon tafita Tanti na mata Allah kiyaye hanya ta amsa da ameen tare da ficewa daga falon gaba daya Wajen parking space ta nufa tac ciro makulin motar tareda nufar motar da tashigo da ita dazu ta bude ta tashiga ta tada motar tare da barin cikin parking space din ta nufi kofa mai gadi na ganin haka ya wankale mata kofar ta fita a guje sabida latin da tayi tafiyar minti 10 yakai ta makarantar parking space taje ta paka motar ta fito ta kule ta yin hanyar ajin nasu da aka riga aka shiga tsaya wa tayi bakin kofar ajin ta taba hannu daga ciki aka amsa da oui rentre(yes enter) tashiga da salama tare da gaida malamin ta nemi waje ta zauna malamin binta yayi da kalo har ta zauna kamin yaci gaba da explaind din lesson daya ke. Karfe shida daidai suka fito daga ajin nasu ita da wata farar yarinya da bazata wuce shekarun AFREEN ba tsayisu yaso ya zo daya sai dai AFREEN ta fita da kadan itama kyaukyauwace yarinyar ba lafi sanye take da riga da sket na Atanfa sunyi matukar yi mata kyau sanye take da dan karamin hijab da baikama ta gwiwa ba, yarinyar tace AFREEN wai yaushe zanga fuskar ki dubi fah tun lokacin da muke dake, har gidan ku nasha zuwa baki taba bari naga fuskar ki ba basan ko sabida miyasa kike boyemin fuskar ki ne wai idan ma kin boyema kuwa ai ni bai kamata ki boyemin ba duba fa kiga yanda yanzu ko a hanya nagaki bazan sheda kiba inba tafiyar ki nagani ba AFREEN tace hasina kenan wlh ba abinda yasa ni ke boye wanan fuskar ta waba saida dalili babu wani dalili AFREEN idan dai kin dauke ni a matsayi kawa to ki nuna min fuskar ki yanzu ba se anjima ba gaskiya yanzu ai zanji kunya idan aka tambaye kamanin kawata nace ban saniba ai za'amin dariya ace du kawancan dake tsaka nin muma basanki ba AFREEN tace kiyi hakuri dan Allah kawata wlh watarana zan nuna maki fuska ta amma yanzu rishin ganin fuskata a gareki shine mafi alkairi a'a ni wlh bazan taba yarda ba gaskiya wata muguwar kama ce gareki daza kice wai rishin ganin fuskar ki shine mafi alkairi ka mardai wata aljanah AFREEN tace wlh hakan da fada maki gaskiya ne hasina a'a kedai ki nunamin don wly idan baki nuna min yau ba kuma yanzu wlh bana shiga motar kiba kuma kawancan mu daga yau ya kare haba hasina meyasa zakice haka nan hasina tace kindai ji abinda nace ai ko to kinga ma tafiya ta da sauri AFREEN ta riko hannuta tace yi hakuri kawata muji mota sai na bude fuskar ki gani haka hasina ta bita suka nufi idan motar take tabude motar ta shiga hasina ta bude wajen me zaman banza ta shiga ta rufo kofar AFREEN nagani tashiga tayi saurin wiwa motar key tare da barin cikin makarantar hasina na mata masifa amma ko kulata ba tayi ba, bata tsaya ko'inaba sai kofar gidan su hasina, hasina na ganin ta tsaya takai hannun jikin kofar zata bude ta fita taji ta a kule fuska a matukar daure ta juyo daniyar masifan ce AFREEN lokaci guda tasaki wata irin kara hade da furta wa innahu suleymanu wa innahu bismilahir rahamin rahim, inna lillahi wa inna illaihi raji'un la'illaha illah anta subhanaka inni kuntum mina zalumin a tatare ta jero wa yanan adu'o in gaba daya a lokaci guda sanadiyar arba da tayi da kyaukyauwa fuskar AFREEN. Ganin yanda ta firgice tana kokarin bude motar ta fita yasa AFREEN sauri bude mata motar da sauri ta fice daga motar ta shige gidan su kamar wada tayi wani mugun gamo da abin tsoro mafi tsoratawa a fadin duniya. Commenté Et Partager Comment And Share 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZANBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ECRITE: _PAR_ *QUEEN ZEEFAT* Yar Mutan Niger Wattpad@nazhabibou 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM Page 3 AFREEN ta aza kanta saman steering din motar ta ce ga abinda nake gudu ya faru yanzu bansan yaza ta doki abin ba da ban bude mata fuskan ba kuma tace ban doketa a matsiyin kawata ba dana bude mata fuskar kuma nasan yanzu ma gudu na zatayi wai wane irin kyau ne dani wanda mutane basu iya jure ganisa kodai wata kama gareni mai ban tsoro wada ni ban ganin ta sai na tare dani tare ta jero ma kanta wa'inan tambayoyin da taga batada mai amsa mata su yasa ta mayarda nikaf inta ta tayar da motar ta nufi gida,tana zuwa gida bayan mai gadi ya bude mata get ta shiga tayin parking motar a parking space tafito ta nufi cikin gidan ta na shiga falo da salama ta tarar da mahaifiyar ta dake zaune tana kalo gaida ta tayi sanan ta karasa kusa da ita ta zauna a saman carpet mahaifiyar ta ta amsa tace AFREEN yanzu dinma kin jima a makarantar injin dai lafiya Lafiya lau Maman AFREEN ta fada a takaice tana mai cire nikaf din fuskar ta maido da kalon ta tayi wajan mahaifiyar tata cike da damuwa kamin takai ga magana Maman tace lafiya ki AFREEN naga kama akwai abinda ke damunki dubi fuska na Maman wai ni kyau gareni ko muni wace irin munmuna kama ce dani da duk wanda ya kaleni ya ke firgita alhali ni banga abin firgita a cikin tsarin halita na taba ko kama nike da mutanan boye ban saniba kodai da gangan mutane kemin hakane tunda ni ban ga abin tsoro a tatare dani ba AFREEN ta tambayi mahaifiyar ta ta da hawaye kwance cikin idon ta da alamun damuwa a tatare da ita Maman tace ko alama ba ko daya daga cikin abinda kika zayana a tare dake AFREEN maza mayar da hawayen ki kada kiyar da su zubo dole ne mutune su ringa firgita da irin kyau da Allah ya maki ba wani ba ma ko ni dake mahaifiyar ki mamakin wanan baiwar kyau da Allah ya maki nake AFREEN. Yan magana nace wada yayi fari ya gama kyau amma ni tuni na karyata wanan magana tunda Allah ya azurta ni dake tunda kinga kedai ba za'a saki a layin farare ba haka ma ana bakake babu ke a ciki sedai asaka ki a tsakatsakiya amma kinga duda haka Allah ya miki kyau irin wanda baza'a iya musilta shi ba dan haka godiya ya kamata kiyi wa ubangiji da yabaki baiwa kala kala ba wai butulce mashi ba. Kuma ina me gargadin ki da kada kiyi anfani da kyau da Allah ya maki wajan saba masa ki zamana me kyautatama sa komi rantsi duda banda shaku a kanki amma yanzu zamani ya canza kawaye ma na iya sauya ma mutun tarbiyar da iyayensa suka mashi dan haka ki kula AFREEN kisan irin kawayen da zakiyi mu'amala dasu ba kowa ake kawance da shiba. Dan haka ki fida damuwa a ranki sabida kyau ki ba me tsoratarwa bane kawai dai dole ne ya firgita mutane bama karma a bazata mutun ya ganki, tunda wasu za su ringa tunanin cewa kedin munmuna ce shiyasa baki yarda aga fuskar ki wasu kuma suce kyau ne dake shiyasa amma baza su taba tunanin kyau naki ya kai haka ba wasu zasu ce ra'ayi ne da ganin dama ko suce da gangan ne yasa kike saka nikaf ba mai taba zaton dalili ki nayi haka kinga Maman ni yanzu harma na saba ban iya fita babu nikaf sabida dana fita mutane sai su dinga min kalon kurila wasu ma har guduwa suke wasu kuma mamaki nake basu kamar dai babu wanda ya fini kyau a duniya Maman kinsan a kawai masu kyau sosai wanda suka fini nesa ba kusa ba amma kuma nawa kyau se yadinga firgita mutane ga laraba wa da indiyawa nasan da cikin su a kwai wanda suka fini kyau nesa ba kusa ba amma su ba'ayi mamakin nasu ba sai nawa, hum AFREEN kenan bazaki ganeba ne kefa naki kyaun na daban ne indiyawa ko larabawa suma nasu kyau daban yake bama yanayin ki guda dasu kinga su a cikin suma za'a iya samun wanda kyau su zai iya firgita mutane fiye da naki to kinga ke yanayi kyau naki ne yake firgita mutane da basu mamaki badan wai ba za'a iya sami me kyau fiye danaki ba ne a'a ke hada baiwa da Allah ya baki me sa du wanda ya ganki yake ganin annuri da kyau suna karuwa a fuskar ki fiye da yada ke kike gani Dan haka ki kula kiji tsoron Allah ki guji sabama ubangijin ki dan bai cancanci haka daga garemu ba Allah abin bauta ne dan haka mu bauta masa fiye da yanda ya umurce mu idan har za muyi ma kan mu adalci ma halicin ya cancanci mu kadaitashi ko dan rayuwa da ya bamu sadakar yi aiko ubangiji mu ya gama mana komi Allah dai ya kara mana imani da tsoron sa a ciki zukatan mu ya bamu lafiya da kwonciyar hankali mai daurewa ya tsare mu kuma ya kare mu daga duk wani iftala'i da sharin duk wani mai shari Allah yamana kyaukyauwan karshe yasa mugama da duniya lafiya. AFREEN ta amsa da ameen Maman zata sake magana Maman ta katseta da cewa kada kikara ce wa komi AFREEN. Tashi kije daki kiyi wanka ki futa kinga magariba ta gabato ba musu ta mike tace Maman wai ina anti khairat tace tana dakinta to Maman bari naje na shirya sai naje wajan ta Tana juyawa idanun suka sauka cikin na tanti da take tsaye tun dazu tana sauraran su amma su ba su san tana wajan ba take ta sakar mata da murmushi tace tanti barka da wara haka tanti ta amsa tana mai mayar mata da murmushi tace tanti zanje inyi wanka ne zan fito idan nayi sallah tace to sai kin fito AFREEN ta nufi dakinta ita ko tanti ta karasa cikin falon. ****** Hasina a guje ta shiga falo gidan su tana wage wage da sauri mahaifiyar ta dake cikin falon ta mike tace subhanalahi ke lafiya kika shigo min falo a guje hasina data durkushe kasa saman carpet tana sauke ajiyar zuciya ta dago ta kali mahaifiyar ta tace ummi gamo nayi koko miye ni ban saniba gamo kuma hasina a ina . wlh ummi nidai nasan mun fito daga aji tare da AFREEN wanan kawarta wa danake baki labarin nace mata yau ita zata kaini gida tunda direba daya kaini makaranta yake ce min da ya sauke ni zaiyi tafiya idan mun tashi na shiga napep to sai na matsama AFREEN kan cewa doli sai ta nuna min fuskar ta a yau inba haka ba zamu daina kawancan to sai tayar da zata nuna min tace muje mota muna shiga sai taja motar bamu tsaya ko'ina ba sai kofar gidan nan na juyo gunta daniyar balbaleta da masifa kawai mizan gani, Hanisa ta dan nisa kanan taci gaba ummi kinsan mi nagani ummi ta girgiza mata kai hasina tace wata daleliyar yarinya mai masifar kyau nagani du yanda zan kwatanta kyauta ba zaki gane ba ummi wlh ba AFREEN nagani ba aljana ce sabida babu mai irin wanan kyaun nan acikin mutane to wani ummi ina ma tayi da AFREEN din da muka tafo tare nashiga uku ummi kawata naci kin hadari abinda yakara firgita ni ummi tunda muka biyo hanya nakema AFREEN masifa ta min shiru hakan na nufin cewa dama tun bisa hanya bada AFREEN nike magana ba oh Allah ka tsare AFREEN ka kareta daga sharin wanan aljana wlh ummi kyau din ta ya yuce musali hasina ta fada a firgice tana mai sake waigen kofar falon wai kar ace aljanar ta biyota Komawa ummi tayi ta zauna tace haba hasina ya zaki ma kawarki haka yanzu ya kike su taji tunda kike ban labarin ta kina cewa ko a aji bata fida nikaf nasan da akwai abin take boyewa kuma tanada dalilin yin hakan ta yiyuwa sabida kyau inta yasa bata bude fuskar gudun faruwar abinda kika mata yanzu kewace irin birkitata ce da bazaki iya aje hankali ki tantance ba ka kikace ta nuna maki fuskar ta amma kuma sai ki saka mata da haka haba hasina baki kyauta kawai baki taba tunanin kyaun ta yake haka bane kuma gani fuskar ta ya zo maki a bazata shiyasa amma ba wata aljana dakika gani kawarki din daice AFREEN Wata irin nauyayar ajiyar zuciya hasina ta sauke tare da kura ma mahaifiyar ta ido na wajan sakan 5 kamin ta nisa tace hakane fah zancan ki ummi sabida kamin ta yarda zata nuna min fuskar ta seda tace min nuna min din ba alkairi bane ba amma na matsama ta nayi wawanci sosai miyasa nayi mata haka oh ni hasina Allah shirya min halina ya fitar min da tsoro. Amma fah ummi ba laifina bane wlh kyau AFREEN ne ya wuce tunanin mai tunani kuma hakan yazo min a bazata ummi tace hakane yanzu tashi kishiga ciki ki futa sai ki kirata ki bata hakuri Haka hasina ta tashi ta shiga dakin ta da tunani iri iri a zuciyar ta ****** AFREEN nashiga daki ta cire kayan jikin ta ta fada toillet wanka tayi tare da dauro alwala ta fito tayi wajen dressing mirror ta gama abinda take sanan ta nufi wardrobe ta sake ciro wata doguwa rigar tasaka tare da hijab ta nufi gun da take ajiye darmuma ta dauko ta shinfida tare hawa ta kabarta sallah. Tana idar da sallah da adu'o inta ta nufi ma'ajiyar kur'anai da litatafan adini ta dauko kur'ani Ta koma saman darduma ta fara karantawa tana nan zaune a haka har aka kira sallar isha ta tashi ta mayar da kur'anin ta dawo saman darduma ta tayar da sallah tana idawa ta nike darduma da hijab ta maidasu ma'ajiyar su ta koma inda gadon ta yake ta doki dan kwalin rigar da ta ajiye a saman gadon tare da ribon ta daura dankwalin rigar da ribon a hannu ta ta nufi kofa tana bude kofar dakin suka ci karo da wata farar yarinya a bakin kofar kyaukyauwa ce itama bazata fuce 21 years suna da kamar jini a tsakanin su sai dai ita fara ceda sauri AFREEN ta saki kofar tana murmushi wanda har saida fossette (dimple) dinta suka bayana tayi tsale ta rugumeta tace wayo anti khairat nayi kawarki duk yau tunda safe da na ganki bansake ganin ki ba tunda zu nake tambayar Maman ke khairat tace to kuma shine in kinyi kewata shine bakije waje naba ai gashi nida nadamu dake nazo na ganki, AFREEN tace dagaske Anti khairat yanzu ma da kika ganin na bude kofar nan zan fita wajan kine zanje bakiga yanda na kagu naje na ganki ba dan Allah Anti khairat shigo mana tace a'a dama ai yurina kikayi niyar tafiya ko AFREEN ta daka kai alarma eh sai Anti khairat tace to muje daki na AFREEN tace to Anti karbi ribon din nan ki daure min sai mu fuce. Karba ribon din Anti khairat tayi tace to juya AFREEN ta juya tare da since dan kwalin dake kanta khairat tace ni ban san ranar da zaki iya daura ribon a kanki ba tace wlh anti nima ban san ranar ba baki ga gashi nane yayi yawa ba gashi kuma da tsayi sosai ni ha tsoro ma yake ban Anti khairat tace to idan ya baki tsoro ki daina karba mana murmushi kawai AFREEN tayi batace komi sabida tagane mitake nufi tana gama daure mata gashi ta kama hannuta suka bar kofar dakin ta ce mu fara zuwa mu gaida papa kamin nan cike da zumudi AFREEN tace papa ya shigo ne khairat ta amsa da eh. Aimé Commenté Et Partager Like Comments And Share. 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZANBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ECRITE: _PAR_ *QUEEN ZEEFAT* Yar Mutan Niger Wattpad@nazhabibou 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_ Page: 4 AFREEN da khairat suka haura saman escalier (stairs) hannu khairat rike da na AFREEN direct kofar dakin mahaifin nasu suka nufa. khairat ta saki hannu AFREEN ta tura kofar tare dayin salama daga cikin dakin aka amsa masu salama tare da basu izinin shiga, kara turo kofar khairat tayi tareda sakai suka shiga a tare. Wani datijo ne daba zai fuce 55 ans (years) ba, zaune saman daya daga cikin hadadun kujerun dake falon, launin fatar sa daya da na AFREEN sedai babu kama a tsakani su sai ta jini sabida AFREEN da mahaifiyar su take kama sedai ta dauko launi fatar mahaifin su, amma duda kamar da take da mahaifiyar ta tafi Maman kyau nase ba kusa amma kuma kana kalon ta zaka san mahaifiyar ta su ta debo, khairat kuwa tak tak da mahaifin su take kama sedai ta dauko farin mahaifiyar su. Da sauri AFREEN ta karasa kusa da mahaifin nasu tare da zaunawa saman moquette (carpet) tace "papa na ina yuni, mahaifin nasu dake kalon ta tun shigowar su ya saki murmushi tare da aza hannu sa akanta yace "lafiya lau AFREEN din papa ya karatu. tace "alhamdulilah" yace "to madala Allah ya taimaka kuma Allah bada sa'a a maida hankali da karatu kinji ko, tace "insha Allah ya kasuwa papa yace "an gode Allah. Daganan khairat ta karaso itama kusa da mahaifin nasu ta zauna tare da gaida mahaifin nasu amsawa yayi tare da cewa "khairat ya makaranta kema wanan ce shekaraki ta karshe a universsité (university) sai an bada himma, kuma naga tunda kikazo shiru bakice zaki koma ba ya haka . khairat tace "eh wlh papa ai kasan mu yada karatun mu yake on peut faire plus d'un mois sans nous programmer un cours (we can do more than a month without scheduling a course), shiyasa nikuma da naji nayi kewar gida nadawo, amma idan satin nan ya kare cikin sati me zuwa zan koma insha Allah papa yace "to madala Allah ya nuna mana tare suka amsa da ameen "ku taso mu sauka kasa muci abinci "to papa suna zaune har seda mahaifin nasu ya mike ya fara tafiya sanan suka rufa masa baya. Suna sauka en bas de l'escalier (down stairs) suka isko kusan kowa na gidan yana salle à manger (dinning) suka dai akejira, shiga suka salle à manger (dinnig ) din da salama aka amsa masu da sauri AFREEN ta shiga gaban mahaifin nasu kamin ya ida karasawa taja masa kujera da yasaba zama a table à manger (dinning table) ya karaso ya zauna tare da cewa "Allah maki albarka ta amsa da ameen ta ja tata kujerar dake kusa da papa ta zauna umma ta tashi zatayin servir (servin) din su sabida yau ranar girkin tane, AFREEN tamike tace "umma yi zaman ki bari nayi servir (servin) din. da karfi umma ta karb'e koshiyar (spoon) tace "ke bani ni ban iya munafurcin ki ba, karamar yarinya dake se kinibibin asara, yaushe nace inason ki taimaka min, munafukar banza da wofi, to ko uwarki bata isaba bare ke, ni matsa kiban gu, ta dan turata tayi baya zata fad'i papa yayi saurin riko ta, umma ta koma cewa "wai sai tayin ta abunda za'a cema ta yar kike to kowama dan kirkin ne. Papa ya jawo AFREEN dake ya zaunar da ita hawaye cike da idonta yace "AFREEN maza yi zaman ki tunda bata son ki kama mata. wani yaro da bazaya fuce 12 ans (years) ba yace "Maman dubi yanda umma kema anti AFREEN fada hada tureta da kadan ta fad'i alhalin batayi mata komai ba, Maman kice ta bar mata fada kada tayi kuka maman ta juyo garshi ta na mai murmushi tace "laifi tayi shiyasa amma bakaga ta daina ba yace "to Maman mi tayi tace "yanzu dai yi shiru ci abinci ka ya maida hankali sa yayi ga abincin sa ya fara ci. Umma ta gala masa harara dai bai masan tanayi ba. Papa ya kali AFREEN "yace maida hankali kici abinci ki kinji AFREEN tadago takali mahaifin nasu daidai lokacin da hawayen da take kokarin boyewa suka zubo. Subhanallah "AFREEN kuka??? Maza share hawayen ki, tashi dauko abinci mu koma cikin falon in baza ki iya ci nan ba papa ya fada yana mai mikewa. Da sauri AFREEN ta mike tare da daukar assiete (plet) biyu nata dana papa, suka bar dinning d'in tare da koma wa cikin falon, papa ya zauna saman kujera, ita kuma saman tapis (carpet). Papa yace" AFREEN miye kuma abin kuka daga maki magana tace papa baka ji munafuka tace min fah "to in tace miki hakanan sai mi bakin san bahaka nan bane ba, ta daga kai alamar "eh" to ki daina zubda hawayen ki sabida Salamatou,in ba haka ba to ta dinga maki abinda taga bakiso kenan, kina abudai kamar baki san halinta ba. haka dai papa yata bata baki har suka gama cin abincin,ta dauke assiete din takai cuisine (kitchen). Ta dawo ta dauko masu ruwa da jus (juice) da verre (cup) dukawa tayi kusan papa ta zuba masa jus (juice) sannan ta zuba ma kanta ruwa tasha, suna gamawa ta tatare komi ta mayar dashi ma'ajiyar sa. sannan ta dawo wajan papa ta dan duka "tace papa zanje nayi karatu yace to 'yar albarka ayi karatu lafiya. Daganan AFREEN ta nufi dakin ta. Papa na zaune falo 'yan ci abinci a salle à manger (dinning) suka shiga falon da alama sun karasa cin abincin. Maman bata tsaya cikin falon ba ta nufi escalier (stairs) dan zuwa dakin ta, umma ta karaso ta zauna kan kujerar da papa ke zauna, tare dacewa "yo shalelan taka tafiya tayi ta barka, dagowa yayi ya kaleta ba tare da ya ce mata wani abuba ya maida kalon sa a tv, ta koma cewa " hada wani kicihin biyu yarinya falo wai ita yar so, "du ba kai ke daure mata gindi ba tana abinda take so nan ma baice mata komi ba hankalin shi ma bai wajan ta, take umma ranta ya bace tace "kar dai mukaga lega wlh, adai juri zuwa rafi watarana tulun zai fashe. "Wato baban fauzia nice na ke maka magana kana shareni sabida 'yar zinariya ko, wato kenan ga mahaukaciya wada batada hankali tana magana ana shareta to alhamdulilah watarana za'aga ranar magana ta. Tanti yara dake tsaye tana sauraren abinda umma ke gayi tace "haba Salamatou miye abin cika mutane da surutu kamar an jonaki kinyi magana d'aya kinyi biyu an shareki, to miyasa bazaki hakura da zancan ba kinata nanata abu d'aya, du kinbi kin takurawa yarinya da bata maki komi ba kawai don kiyaya, Tanti taja wani dogon tsaki... Bata ida rufe bakinta ba, umma ta tashi cikin tsawa tace" yimin shiru 'yar biya yar cusa kai inda ba'a san darajar ta yar' neman gurin zama gun miji da kishiya kina wani shishige ma ya'yan' ta don munafurci wai ke mai son su, dan mahaifin su ya dinga kalon ki da dajara dan kinibibi, to wlh anyi walkiya mun ganku sedai ayi ma wasu ba muba munafuka ai wlh na ganoki kar nake kalonku gaba d'aya ah to, kuma wlh ki fita haraka ta ki daina samin ido tunda ni ba 'yar biya bace ehe. Ta tab'a hannu tare da komawa ta zauna, tanti harta bude baki zatayi magana, papa ya dago ya watsama ta wani irin kalo mai nuna cewa yi tafiyar ki, ki barta batada hankali, yasa Tanti juyawa ta nufi dakin ta itama, tajin umma nacewa "kika ki tsaya ki fad'i abinda ke ranki in ba tsoro ba, yanzu kiga b'acin raina, Tanti dai tashige daki batace mata kala ba bare tajuyo ta kaleta. Falon ya rage daga umma da papa sai wasu yara 'yan maza guda biyu dake zaune suna kalon umma dake ta masifa kamar an aiko ta, don tuni ya'yan umma su nufi dakin su tunda sukaji tafara banbami fada. Dan babban daga cikin daba zaya fuce 16 ans (years) ba ya mayar da kalon sa gun mahaifin nasu yace "papa mu zamu koma ban'garen mu don muje muyi revision, cikin kulawa papa ya dawo da kalon sa garesu yace " to maza ku tashi ku tafi kuyi karatu, ka dinga nunawa k'aninka ida bai gane kaji ko fahad. Wanda aka kira da fahad "yace insha Allah to ku tashi ku je Allah maku albarka suka amsa da ameen sanan suka fita daga falon gaba d'aya. AFREEN na komawa daki ta nufi gun da take ajiyar kayan karatun ta na école (school) ta ciro papier (peper) da tashigo da ita d'azu taje tanemi guri ta zauna ta fara traité din exercice (exercise) din cikin nutsuwa. Khairat na fitowa daga salle à manger (dinning) dama ita bata tsaya cikin falon ba direct dakin AFREEN ta nufa, tana shiga ta sameta tana exercice ta zauna kan kujerar da ke dakin, "tace ma soeur (yar uwata) miyasa kike damuwa da abinda umma tamiki kamar bakisan halinta ba AFREEN ta dago ta kaleta tare da sakar mata murmushi da yasa fossette (dimple) dinta fitowa, tace "bakomi gande soeur (big sis) juste (just) munafuka da tacemin ne ya d'an sosa min rai, amma yanzu ni harma na manta da abin, wanan exercice din ke gaba na. khairat tace "kin tabata tace "wlh kuwa soeurette (sister) "to shikenan bari na barki ki karasa karatun, idan kin gama kizo daki na muyi fira sai ma ki kwana a can "to anti na sai na shigo AFREEN ta fada. Khairat ta tashi ta nufi kofa ta fita daga dakin ta nufi nata. 30 munite AFREEN ta dauka tana traité din exercice (exercise) din kamin ta kamala, wayarta dake saman gado kamar jira take ta ida karatun ta dauki tsuwa tana neman agaji karasa wa tayi ta dau wayar mon amie intime (aminiya ta) taga yana yawo kan écran ( screen) din wayar murmushi ta saki tare da dauka kiran ta kai kune har ga Allah taji dadin ganin kiran hasina. Daga cikin wayar akayi salama ta amsa, hasina cike da jin kunyar kawar tata tace " kawata bakiyi bacci ba ina ta tunanin kiranki yanzu, ina gudun kinyi bacci kar na tayar dake. "A'a banyi bacci ba ya kike, hasina ta dan nisa tace "lafiya lau, dan Allah kawata ki yi hakuri ki yafemin abinda da miki dazu wly ba da niya nayiba kanin fuskarki yayi min bazata, wlh bata kamantaki ba da irin wanan mugun kyau da nagani a gareki bane shiyasa, wlh kyau ki ya firgitani sabida wlh kyau ki bai musultuwa kawata, Allah dai ya tsareki ya kare ki daga sharin mutun da aljan da karfe bature ashe ba banza kike rufe fuskaki ba, dan Allah kiyafe min. AFREEN dake sauraren ta sauke wata agajeriyar ajiyar zuciya tace " Ameen bai komi kawata kuma ni baki min komi ba inda ma kinyi na yafe maki "alhamdulilah na gode kawata Allah barmu tare, bari na barki ki kwanta sabida gobe akwai école (school) hasina ta fada, AFREEN "tace to kawata Allah tashe mu lafiya, ameen hasina ta fada tare da katse wayar. AFREEN na ajiye wayar ta nufi armoir (wardrobe) ta dauko kayan bacci ta ta fita daga dakin. Bangaren hasina kuwa tana katse kiran ta daka tsale tace "ashe batayi fushi dani ba Allah na gode ma da kaban kawar kirki irin AFREEN.......... Ina kaunar ku masoya ...........💞 Commenté Et Partager Comment And Share 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZANBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ECRIT: PAR QUEEN ZEEFAT Yar Mutan Niger 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ Bismilahir rahamanir rahim Page 5 Tana fita ta nufi d'akin Khairat da ke kusan nata da sallama ta shiga amsa mata sallama Khairat tayi dake bakin gado tana manipuler d'in wayar ta mike wa Khairat tayi taje ta kamo hannu AFREEN ta zaunar da ita bakin gado, tace "yawa 'yar k'anwata, ina aza baza ki zo ba?" AFREEN tace "mi zai hana anti? kawai natsaya yin waya ne." "waya kuma AFREEN, a cikin daren nan, to ko dai nayi k'ane ne banda labari ? "Lah anti wane irin k'ane kuma," "to ni sani nayi AFREEN, nufi na ko kinyi saurayi ke da toujour (kulin) kina cikin nikaf, bansan ko taya wani zai gan ki ba har yace yana son ki a cikin nikaf ba, an yi mutun kulin cikin nikaf kamar dai wanda yayi wani mugun laifi Police na neman shi, Allah dai shirye ki AFREEN." "Hum anti kenan saurayi fah kika ce? wanan ai sai ku 'yan mata, ina ni ina saurayi yanzu duka ta nawa ni ke." AFREEN ta fad'i maganar tana dariya tare da kalon 'yar uwar ta, itama Khairat dariya tayi tace "ke d'in ce ba 'yan mata ba? Tubarkallah god'aigo'd'ai da ke da 18 ans din shi ne zaki ce a ta nawa kike, baki isa aure bane ko miye nufin ki? ni dai naga har 'yan 15 ans an masu aure baran tana ke macha Allah da babu abinda kika rasa na manyan 'yan mata masu ji da kansu," "haba anti a 18 ans (years) a ka min aure ai rishin tausayi ne gaskiya ni ban wani isa aure ba yanzu, tu vois je n'ai même pas fini mon étude, kin ga kenan ban girma ba" AFREEN ta fad'a tare da yin murmushi. Khairat tace "ah kenan sai muntun ya k'arasa karatu ne ya girma kuma ya isa aure? to tun yuri garama ki farka daga baccin da kike ah to, kingan ninan idan ahmad yace zai kawo kudin aure na a gobe, to wly yarda zanyi ah to mi kake yi da karatu ga sunnah manzon Allah saw, idan naje gidan nasa sai na karasa karatun a can, ke ni daga na k'arasa wanan shekaran shikenan bawani karatu da zanci gaba da shi, kedai rik'a min adu'a na karbi licence d'ita shekara nan shikenan nida école (school) munyi ban hannu sai d'akin miji insha Allah" ta fad'a tana dariya. "To ameen grande Soeur Allah ya taimaka kuma ya kawo miji na gari musha biki ranar akwai casu in Allah ya yada." "Hum kinji kamar da gaske, ga ki nan wa ta irin ustaziya dake wane casu za kiyi gayi ne kawai kike" ita dai AFREEN murmushi kawai tayi bata ce komi ba. "Yawa 'yar uwa na ma tuna kisan wai dazu na dawo daga gidan anti fauziya na had'u da wani a hanya wai shi abdul majid bari na nuna maki photon (pic) shi, yanzu ya turo min a whatsapp wai so na ya ke da aure kuma yace min ba garin nan yake ba dan tahoua ne shi, kedai ban matsaya na saurare shi da kyau ba Kawai nace mishi ni gaskiya ban nan gayin fira a titi sai yace na shigo motar sa ya ragemin hanyan nace nagode, babu yanda baiyi ba kan na shiga motar sa wai ya karaso da ni gida nakiya dad'a daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki, ban san sa ba, ban taba gani sa ba shikenan sai na d'ane motar sa ya kawo ni gida kinji kamar wace bata da daraja da kamun kai, ko bama haka nan ba, in fah yana kawo ni daidai papa nazo wa ya gan ni to sai yaya, Lale yau da papa ya kakarya ni wlh." Khairat ta fad'a tare da shiga ma'adanar photo na wayar ta. AFREEN tace "Lalai kam gara dai daba ki shiga ba ko ba dan ka papa ya gan ki ba ai se ka nema ma kan ka daraja." Ta fido photon ta nuna wa AFREEN tace "kin ganshi fah sis?," "lah anti shima kyakyawa amma fah ya ahmed ya fi shi kyau, to anti ya batun ya ahmed naga kuma kinyi wani Abdoul majid, ko kun b'ata da shine?" AFREEN ta tambaye ta a tak'aice. Khairat tace "ah haba ahmed fah shi ne k'ark'ashi zuciya ta shine na ke so da kauna, wanda nake mafarkin ya zaman miji na insha Allah taya ma zamu b'ata, sedai wani inkon Allah kuma kawai dai na yada na bashi numéro (number) na ne sabida baka san yata Allah zata kasan ce da kai ba, tunda bakada masaniyar ko waye mijin ka ba sai wanda Allah ya zab'a maka." ''hakane kam rabin raina Allah kawo da mafi alkairi," Khairat ta amsa da "ameen petite Soeur, tashi kije kiyi wanka kiyi change kizo ki kwanta kinga akwai école gobe in Allah ya kaimu, idan kika dawo makaranta gobe mun karasa firar insha Allah." Tashi AFREEN tayi ta nufi douche (toillet) wanka tayi tare da yi brossage din baki ta dauro alwala ta fito, direct wajan coiffeuse (dressing mirror) ta nufa tayi abinda yaza ma mata al'ada kamin ta kwanta, sannan ta wuce gun armoir ta ciro kayan baccin ta, sabida a d'akin ko wane cikin su akwai kayan d'an uwan shi a cikin nashi kayan sabida gudun irin haka, kamin ta dawo saman gadon ta kwanta tuni Khairat tayi bacci haura wa tayi itama kan gadon ta fara karanto adu'o in bacci tana idawa tayi bismillah ta kwanta kusa da Khairat, bata wani d'auki lokaci ba bacci ya k'washe ta. K'arfe biyu daidai na dare AFREEN ta farka da adu'ar tashi daga bacci a bakin ta, sauko wa tayi daga kan gadon ta nufi toillette, shiga tayi ta wanke baki, ta dauro alwala, ta fito ta canza kaya ta d'auko hijab da darduma ,saka hijab d'in tayi tare da shinfid'a darduma ta koma bakin gadon kusa da Khairat, ta dan ja hannun ta tace"anti tashi ko yau ba zakiyi sallan ba ne." Khairat ta buda idon da suka mata nauhi tace" s'il te plait AFREEN laisse moi dormir wly j'ai sommeil ("please AFREEN let me sleep wlh I'm sleepy)" "dan Allah Anti tashi mana" mtsss taja dan k'armin tsaki sannan tace AFREEN dan Allah ki barni wlh yau bacci nake ji sosai je kiyi taki kawai" daga haka AFREEN ta nufi kan darduma ta tada salllah, sai da ta kai karfe ukun dare ta na nafila kamin take sallame wa gabada ta mike ta ninke darduma da hijab ta mayar da su ma'adanar su, ta dawo saman gadon ta kwanta, ba itace ta farka sai wajan karfe 5:15, tashi tayi ta nufi toillette ta d'auro alwala ta fito ta nufi gadon ta tayar da Khairat, tare da gabatar da raka'atanul fijir sannan tayi sallah asuba, kur'ani' ta d'auko ta fara karanta wa, sai 6:30 kamin ta koma toillette minti 10 ta fito d'aure da serviette (tawel) cikin k'ank'anin lokaci ta shirya tsaf da ita cikin riga da jupe (sket) na atanfa da suka mata matuk'ar kyau macha Allah, ta ciro hijab tasaka da nikaf ga hannu, da jakar makarantar ta tace ma khairat, dake zaune har lokacin kan darduma. "anti na tafi, sai na dawo" Khairat ta dago ta kale ta tace to a dawo lafiya Allah ya tsare" ta amsa da "ameen" tare da fice wa daga d'akin. Tana fita ta nufi escalier direct d'akin mahaifin su ta nufa, tashi ga da sallama, yana zaune a falo kan darduma da kur'ani a gaban sa da alama karatu ya gama zauna wa tayi kusa da shi tace "papa ina kwana antashi lafiya" papa ya amsa da "lafiya lau AFREEN, har kin shirya, yau dreba zai kaiki ko kuwa da kanki za kiyi conduire (driving)?" tace "a'a dreba zai kaini yau bana jin conduire d'in" papa yace "ok to kinyi kari kuwa" " a'a amma yanzu zanyi kamin na wuce makaranta" papa yace "to shikenan ki samu fah ki kayar kamin ki wuce, karb'i kudin makarantar ki" papa ya fido da 1000f ya mika mata yace to a dawo lafiya" AFREEN tace "ameen papa na gode. Daga nan ta nufi dakin mahaifiyar su ta gaida ta a gurguje ta fito sanadin gani da tayi ta kusa makara. kasa ta sauka tayi dakin umma ta gaida ta, umma ta watsa mata harara tace "in ban kwana ba kin gani kinibabiya Kawai nace ban son wanan gaisuwar dole ne sai kin gaida ni koni uwar kice" AFREEN batace komi ba ta juya zata fita wata yarinya da ba zata fuce 14 ans (years) "tace dan Allah anti AFREEN nazo ki wuce dani makaranta tunda ke da yuri kike zuwa idan natsaya jiran su marie zasu sa nayi retard (lati) dubi fah har yanzu ko shirya wa ba suyi ba bare ma ayi batun karyawa", da murmushi AFREEN ta juyo tace to ke kin karya ne" girgiza kai tayi tace "a'a yanzu zan karya anti" AFREEN tace "to shikenan d'auko jakar ki sai ki fito mu karya tare sai mu wuce" yarinyar tace "to anti gani nan zuwa." AFREEN na fita yarinyar ta juya ta dubi mahaifiyar ta tace "umma gaskiya abinda kike yiwa anti AFREEN ba ki kyautawa, du gidan nan akwai me biyo ki har d'aki ya gaida ki inba ita ba, ko kin taba gani anti Khairat ta shigo dakin nan ta gaida ki, sedai idan kun hadu a falo, yanzu ma da ta gane halin ki ta daina gayar dake gaba d'aya, sabida irin wanan abin da kikewa anti AFREEN, amma ita anti AFREEN nasan da komi zaki mata ta ba zata daina gaida ki ba." Wani irin mugun kalo umma ta watsa ma yarinyar tace "kinsan wlh Zeinab ki fita ido na, na rufe ke wace irin banza yarinya ce da ba ta san ciyon kanta ba ke dai ba ki kaunar ki ga an taba wacan munafukar yarinyar, to wlh ki kiyaye ni Zeinab, ko nuna maku da ake a gidan nan a fi son ta daku ko ciyo abin bai maki, to wly ki shiga taitayin ki, ki dawo hankalin ki ma in kina dawo wa." Simi simi yarinyar da aka kira da Zeinab ta fice d'akin ba tare da ce ma umma komai ba. AFREEN na fita daga d'akin umma ta shiga na Tanti ta gaida ta Tanti ta amsa tace "AFREEN har zaki makaranta." "Eh" AFREEN ta fad'a a tak'aice tanti tace k'arbi zumu ki sha" tanti ta d'auko zumuwar ta mik'a mata, karb'a tayi tasha cuillère (spoon) guda ta mayar mata da sauran ta fita, take gun cin abinci ta nufa idan ta tardo Zeinab gama karyawa ta na jiranta, thé (tea) kawai ta had'a ma kanta tasha suka fice daga falon, direct inda dreba yayi tsaye da mota yana jiran su suka nufa, gaida dreba suka yi sannan Zeinab ta bude masu gidan baya suka shiga dreba ya tayar da motar ya doshi k'ofar fita daga gidan mai gadi nagani haka ya tashi ya wangale masu tamgamemiyar k'ofar gidan ya fice da motar. Shiru kake ji cikin motar ba me cewa komi, can dai Zeinab ta katse shirun tace " anti dan Allah ki yi hakuri da abinda umma ke ma ki wly watarana zata gane ta dena maki hakan" AFREEN ta juyo tayi d'an murmushi me sauti wada seda kyawawan fararen hakoran ta suka bayana tace "kar ki damu k'anwata ni ban taba rike umma a zuciya ba, sabida nasan watarana sai labari bai komi kinji, itama umma uwa take a gare ni ,dan haka ni ba d'auki abinda take min a wani abu ba, ki ma daina min wanan zancan, in kina ban hakuri sai na ga kama kin nuna min umma ku ka dai ta haifa ban da mu," "anti wlh ba haka nake nufi ba" Zeinab ta fad'a da sauri, daidai nan a ka kawo k'ofar makarantar su Zeinab dreba ya ja ya tsaya, Zeinab ta bude k'ofar motar ta fita. AFREEN tace "to petite Soeur (lil sis) a maida hankali da karatu a daina tsayawa wassa" Zeinab tace insha Allah anti, karfe 1:30 muke tashi ki tunawa dreba yada dawo d'auka na," tace "to insha Allah ayi karatu lafiya Allah ya taimaka Zeinab ta amsa da "ameen, bye bye my lovely anti ina sonki sosai Allah tsare ki" daga nan ta gudu cikin makarantar, dariya AFREEN tayi tare da girgiza kai tace "Zeinab sai shirme." ********** Wasu manya manyan kuma had'ad'un motoci ne guda uku biyu bak'ake d'ayar dake tsaka fara ce tass mai masifar kyau, suka kunno kai cikin wani hatsabibin hamshakin kuma tangajejan gida, had'uwa gidan ba sai na fad'a kowa ya canka......... Muje zuwa💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 Commenté Et Partager Comments And Share 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZANBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ECRIT: PAR QUEEN ZEEFAT Yar Mutan Niger Wattpad@nazhabibou BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM Page 6 Chigar motocin keda wuya suka parcking a farfajiyar gidan bud'e k'ofofin babak'un motocin guda biyu akayi, wasu sojawa ne maji ya k'arfi guda bakwai suka fito daga cikin babak'un motocin sanye suke da kayan garde da gendarme hannayen su rik'e da manya mayan bundigogi fuskar su sanye da verre noir (glass baki), fuskar a matuk'ar murtuke kana kallensu zaka hango da babu alamun wasa ko tausayi a tare dasu to bare muntunci, in ka kallesu dole zaka razana. Da gudu suka nufi farar motar da ke tsakiyar bak'ak'en motocin, suka zagaye ta gaba daya tare da haka bindigogin su, suna jiran fitowar na cikin motar, bud'e k'ofar gaba ta farar motar akayi wani farin dogon guy kyakyawa ya fito da tenu garde sanye a jikin sa, rufe murfin motar yayi ya tako da sauri ya zo ya bud'e k'ofar baya ta motar. wajan minti biyar wanda ke banyan motar ya zuro wata k'ayattaciyar k'afa me d'auke da wasu tsadadun takalmi masu matuk'ar kyau ba tare da b'ata lokaci ba ya ida ziro d'ayar k'afar, daga bisani ya fito ma gaba daya daga cikin motar. Wani had'ad'en kyakyawa saurayi ne mai jini ajika da ba zai wuce 30 ans ba, gashi da matuk'ar d'aukar hankali da ka ganshi dole ya birge ka, dogo ne mai doguwar fuska mai d'auke da d'an siririn sage iya bakin kunnuwa, café au lait ne shocolat colour, da d'an siririn hancin shi, sai dara daran idanun sa masu mugun haske da k'ayattacan bak'in a cikin su mai d'aukar ido da birgewa, da matsakaicin jiki dayasa tsayisa yayi daidai dashi macha Allah fatar jikin sa kad'ai zaka duba ka gane d'an futu ne babu alamar wahala a tatare da shi kuma daga ganin shi zaiyi miskilanci, a take zaka hango kwonciyar hankali, nutsuwa da kamala a tatare da shi. Yana fitowa take nan garde corps (body guard) d'in sa suka k'ank'ame yuri guda tare da sara masa, ko kallon inda suke baiyi ba bare ya nuna alamun yasan abinda suke, fara tafiya yayi suka rufa masa baya garde d'in da ya bude masa mota shine baya da shi kamar zasu jera sauran kuma a bayan su. Takawa yake sannu sannu cikin k'asaita da izza da nuna isa kamar d'an sarki sukuwa garde corps (body guard) d'in su na biye da shi karma jela. A haka har suka kawo wani babban filin gida mai girman gaske ga kyau mara misali mai d'auke da b'angare guda fud'u duk manya, hanya wani katafaren b'angaren suka nufa, gab da zasu kai bakin k'ofar da zata sadaka da falon b'angaren, garde d'in dake kusa da shi ya juyo ga garde corps d'in ya masu nuni da hannu alama suyi tafiyar su, juyawa sukayi suka bar gun shi kuma yayi saurin shiga gaban sa kamin yake karasa wa ga k'ofar shi ya rigasa kaiwa ya bud'e maya k'ofar, sa kai yayi cikin falon tare da sallama shima ya bi bayan sa tare da rufe k'ofar. Wata had'ad'iya mata ce zaune cikin k'ayatacan falon cikin d'aya daga cikin had'ad'un kujerun dake falon. Itama dai ba fara bace kuma baza'a kirata da baka ba kyakyawa ce sosai masha Allah. D'agowa tayi tare da mayar da kalon ta garesu tace "Oyoyo filston (d'ana) sannun da dawowa" ta fad'a lokacin da ya karaso kusa da ita ya zauna a k'asa tare da aza kansa saman cinyar ta, ta cire masa fular dake kansa tana shafa lalausan gashin kansa, tace "Shalele mike damun ka, ko gajiyar aiki ne?" d'aga mata kai yayi alamar eh, lokacin da garde d'in da suke tare ya karaso shima ya zauna a k'asa kusa da matar yace"Mama ina yuni ya wunin gida" shima aza hannun tayi saman kanshi da murmushi a fuskar tace "Lafiya lau abba na ya gajiyar aikin ku? gaskiya kuna fama." Yace "Wlh aiki da godiya mama kuma bama gajiya tunda mun riga da mun saba, sedai irin wada ba'a rasa" sake sakin murmushi tayi tace "To Allah ya taimaka kuma ya taya ku rik'on wanan kujera da aiki da gaskiya, Allah kare ku daga sharin mutun ko aljan da sharin karfe Allah tsare ku da tsare warsa." Yace "Ameen mama mun gode Allah ja da kwana ya kara lafiya" Ta amsa da "Ameen Allah maku albarka." Shi kuma miskilin yana nan har yanzu baice komai ba sai kawai ya amsa da ameen a zuciyar sa. Can ya nisa cikin wata irin tausashiya kuma nutsatsiyar murya irin kamar an ma sa dolin nan, yace "Mama dan Allah kiyiwa Ali magana ban son abinda yake man," Tace "Mi kuma yake ma filston nasan kafa da rigima kamar d'an k'aramin yaro." Da kayr ya iya bude bakin sa kamar wanda akama dole yace "Mama wai fah Ali sai ya ta yi min abinda ba na so, na fad'a masa cewa ya daina sara min, ko kuma idan ya gani ya tsaya k'ame yana wani k'auda kai gefe ba ma yason mu hada ido, ko kuma idan zan fito a mota sai ya bude min," sai da ya sauke ajiyar zuciya alama ya gaji da maganar da yake, sannan ya nisa yace " ko ki ji yana kirana da wani chef, ji fah miye wani chef da ko dad'i ji babu kamar bai san suna na ba, wlh Mama ki masa magana gaskiya in bai bari ba zamu b'ata a da ai ba haka yake min ba, sai yanzu ko fah magana bai so yana min bare ma gun aiki," mtsss ya dan ja tsaki kamin yaci gaba. "Mama inada wanda zamuyi fira ko shawara ne, bayan shi amma kuma sai yayi ta yi min haka gaskiya ba jin dad'i abin nan, ban ma san miyasa akasa shi a matsayin garde corps d'in na ba" ya fad'a tare da koma wa ya kwanta saman cinyar mahaifiyar tasa yana me hararan Ali da ke gefe, murmushi Ali yayi tare da sosa kai. Mama ta kalesu ta girgiza kai tana murmushi sannan tace "Umm AFREED sarkin rigima to ba aikin sa yake ba ai aikin sa ne haka shiyasa, kuma shin d'an uwan ka ne shiyasa aka aza sa a matsayin garde corps d'in ka sabida in yana kusan ka ba wani wanda zai cutar da kai sedai kawai wani ikon Allah" d'an turo baki yayi kamar karamin yaro har zaiyi magana kuma yayi shiru. Sannan mama ta mayar da kallon ta gun Ali tace "Kai kuwa abba na ka daina yin haka ku koma yanda kuka taso tun yarinta, kada matsayin da yake dashi ya sa ka d'in ga gani ko ya fika, to ba haka bane babu abinda ya fika, manzon tsira (SAW) yace ba wanda ya fi wani a wajan ubangiji sai wanda ya fi ji tsoran sa, dan haka ka daina kawai tunda bai so kaga kai d'an uwansa ne kuma aminin sa ba wani bare ba." wani k'ayattacan murmushi Ali ya saki yace "To shikenan Mama na daina amma banda bude mota ina nufin zan dinga bude masa mota indan zai shiga ko zai fita, idan bai yada ba to ba zan daina duk abinda na saba ba" Ali ya fad'a yana dariya tare da kallon gefan da AFREED yake, wani irin kallo AFREED ya watsa wa Ali me nufin zan mu had'u, yace a shagwabe "Mama kinji shi ko!!! Mama tayi dariya tace "Umm ni dai ba ruwa na kun fi kusa, ku wuce kuje ku rage kayan jikin ku sai kuzo na zuba maku abincin, mikewa sukayi a tare suke ce d'accord. Fita sukayi daga falon suka nufi nasu b'angaren direct d'akin AFREED suka shiga d'akin ne wanda ya amsa sunan sa d'aki, kana ganin shi kasan na ya'yan manya ne 'yan futu kuma sangartaci, suna shiga AFREED ya juwo ya kali Ali. Yace "Wane gulma ne ya kawo ka d'aki na?" Murmushi Ali yayi yace "Eh an shigo d'in, ko fitar dani zakayi" wani mugun kallo AFREED ya watsa masa yace "Ai kasan zan iya tunda d'akin na wane, sai lokacin da naso muntun zai shigo, haka lokacin da naso za'a fitar min a d'akin, wata muguwar dariya Ali ya saki yace "Eh d'aki naka ne amma ku zanga wanda ya isa ya fitar dani, a nan zanyi wanka kuma ana zan kwana." K'wafa AFREED yayi tare da shigewa doushe sabida ya gaji da maganar da yake, yana fitowa d'aure da tawel a k'ugun sa daya a kafad'a ya rufo kofar doushe (toillet) d'in tare da sa makuli ya kule ya ciro makulin ya nufi gaban coiffeuse (dressing mirror). Ali na ganin ya zauna ya tashi ya nufi doushe d'in ya murda k'ofar ya jita a kule murmushi d'auke da fuskar sa ya juyo ya kali idan AFREED ke zaune ya nufi ya tako a hankali ya nufi gun sa yace "Haba mutumi na miye abin wani rufe k'ofar toillette d'in ka san fa shiga zanyi," ko kallon inda Ali yake baiyi ba bare ya amsa masa, kara fad'ada' murmushi sa yayi yace "Wai dan na ce bazaka iya fitar dani a d'akin ka ba shine ka rufe doushe d'in, to wlh da wasa nike ka isa ma har kayi yawa yi hakuri ban makulin kaga fah an kusa kira magaribah ka ban nayi na gama na fito ko na shirya kamin ayi kiran sallah, nan ma dai shiru bai ce masa komai ba "Dan Allah fah nace AFREED, sai lokacin ya juyo ya kalesa yace "daba sai ka k'wataba nagani d'an raini hankali, in badan gulma, ba ga d'akin ka can ba amma ba zaka ba dan kawai ka takura man zanyi maganin ka, shi dai Ali yana tsaye bai ce komai ba sai murmushi yake d'auko makulin yayi ya mika masa karb'a Ali yayi tare da juyawa ya bar gun ya nufi doushe d'in yasaka makulin ya bude sannan ya juyo yace "Ba dole yaro ya ban makuli ba ya na gudun kada nayi k'asa k'asa dashi, da sauri ya shige doushe d'in tare da kulo k'ofar. Wani k'ayattacan murmushi me k'ara masa kyau da kwantar da zuciya AFREED ya saki tare da girgiza kai cikin zuciyar sa yace zaka fito ka same ni. Shirya wa yayi cikin bakin wondo 3 quart (3 quater) da riga fara mai k'ananun hannu wa ya kali kansa a madubi, nida kaina nasan ina da kyau ne AFREED ya fad'a cikin zuciyar sa yana murmushi d'aukar wayar sa dake saman gado yayi sannan ya kwanta a gadon yana dane dane a wayar. Yayi daidai da fitowar Ali daga toillette yazo ya shirya shima kamar yanda AFREED yayi sedai shi na sa kayan jaune (yelow) da fari ne, sannan yazo ya zauna kusa da AFREED, yace "Wai mutumi na yaushe ne zaka tafi marad'i, naji kana cewa zaka d'auki ko da hutun kwana biyu ne ka je ganin tanti Aicha sabida tana tayi ma k'orafin baka zuwa gun ta." Maido kalon sa yayi gun Ali "Yace nima ban saniba wanan aikin ne zai bar muntun zumucin, ai hutun sati zan d'auka idan nasamu dama kawai da naje sai na d'an huta." Ali yace "Gaskiya kam idan kayi mata sati zata daina yawan k'orafin da take, sabida ko jiya sai da ta kira mama ta fad'a mata" sauke ajiyar zuciya yayi yace "Itama dai tanti ta cika k'orafi, ni kamar wata mace za'a dage da sai na wani je idan ma a garin nan take da da sauki" seda ya dan yi shiru na kusan minti 2, kamin yace "Da yake sada zumucin zan je nayi kuma dan ta damu dani ya sa ta ke son gani na, bai komi zanje insha Allah ina fatan Allah ya bani iko" Ali ya d'an tabe baki kanan yace "Da daidai zai fi." Suna cikin tataunawa a kayi kiran sallah magaribah tashi sukayi don yin alwala AFREED ya shige doushe d'in sa, shima Ali fita yayi tare nufar nasa d'akin da bashi wani banbanci dana AFREED ya fad'a toillette dan d'auro alwala." AFREED na fitowa ya nufi armoir (wardrobe) d'in sa ya ciro jalabiya (doguwa farar riga ) kusan a tare suka fito suka nufi masalacin da ke lik'e da gidan nasu. ********* Marad'i... Har cikin makarantar su AFREEN direba ya shiga da motar daidai inda ake tsaya wa ya ja ya tsaya AFREEN ta bude murfi matar tafita direba ya juya ya bar makarantar AFREEN ta juya da nufin barin gun da direba ya ajiye ta, taji an kira sunnan ta juyawa tayi , hango hasina na nufo ta murmushi ta saki daga cikin nikaf sai wanda ya lura zai gane hakan. Tsaye tayi tana jiran k'araso war hasina, tana k'arasowa gun AFREEN tace "Abikiya ta ustaziya ko ina nata rufe rufe da shi, dake da shigar ki duk ku na birgeni da nima zan iya da na dinga yin irin shigar ki k'awata, in jin dai kin huce daga fushin da kike dani?" kamo hannun ta AFREEN tayi tace "K'awata kin fiya surutu gaskiya, mi kika min da zanyi fushi dake in dan abin jiya ne yasa kike cewa hakanan kima daina sabida ni ban d'auke shi abin fushi ba ki barmin wanan zance da na riga na manta." Hasina tace "Allah ko k'awata?" Kai AFREEN ta d'aga alamar eh, rugumeta hasina tayi tace shiyasa nike son ki k'awata baki fushi baki da rik'o tu est trés simple plus que je le pense, que le bon dieu nous laisse ensemble ma chérie," AFREEN ta amsa "Da ameen ma puce tare cewa ke cika ni mana ki wuce muje classe (class) kada profe de comptabilité ya shiga kinfa san halin sa da ko k'afar sa ya aza bakin classe ba me shiga shikenan sai ka jira fitowar sa" sakin ta hasina tayi ta kamo hannun ta tace "To muje." Suna shiga ajin kowa ya dawo da kalon sa wajen su 'yan ajin nasu nata ga 'yan biyu nan sun shigo "To indai k'awatawancan ku ya kai yau hasina kisa ta bude fuskar ta mu gani" wata daga cikin 'yan ajin tace "Mi zaku gani ga munmunar fuskar AFREEN sabida munin ta fah ne yasa bata barin a ga fuskar ta sai ta nuna wai ita ustaziya, kar dai muga lega ah to ni na dad'e da gano munafurcin ta." Kwashe wa da dariya 'yan ajin sukayi, a hasale hasina na ta warce hannun ta daga na AFREEN zata nufi gun wada tayi maganar da sauri AFREEN ta riko hannun ta tace "Haba k'awata na aza karatu kika zo a makarantar nan ba fad'a da cece kuce ba, rabu da ita mu ba muda wanan lokacin abinda ya kawo mu za muyi mu koma gida kinga shiru ma ai magana ce." Koma wa tayi ta zauna ranta a matukar b'ace tama kasa magana sai huci take AFREEN tace "Haba wai hasina miye abin fushi a ciki kin maganar nan da zaki bar ranki ya bace ai sai taji dad'in cewa taci galabar b'ata miki rai, dan Allah saki raki man nida tayi ma abin ma raina bai b'aci ba se ke sai a sannan hasina ta saki ran ta tare da cewa "Ai ni sai a min abu na hakura idan a ka maki kuma na kasa hakura da bari na ki kayi naje na koya mata hankali wlh ba k'armin haushi ta ban ba." AFREEN tace "Yi hakuri dai k'awata idan muka biye mata mun taru mun zama d'aya kenan" kwafah hasina tayi tare da hararen wace tayi maganar. Wada tunda taga hasina tayi kukan kura da nufin ta shak'o ta ta sha jinin jikinta. Daga haka malamin su ya shigo suka fara karatu.............. 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZANBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ECRITE: _PAR_ *QUEEN ZEEFAT* Yar Mutan Niger Wattpad@nazhabibou 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_ Page 7 K'arfe sha biyu daidai suka fito daga aji dama duk ranar da suke comptabilité ko fitowa récreation (break) basayi sai sunyi awa biyar a cikin classe, dan haka a gajiye suka fito, hasina tace "Wash Allah k'awata wly duk na gaji, ga yanda comptabilité ke caza k'wak'walwa ga kuma gajiyar zaman awa biyar ai dole mutun ya gaji wlh," AFREEN tace "Hakane k'awata akwai gajiya kam amma daga mun k'arasa shekara nan wahala ta k'are insha Allah," Hasina ta girgiza kai tace "Allah sa muna cikin masu sa'a Allah kawo k'arshan wahalar mu" AFREEN ta amsa da "Ameen" daidai lokacin da suka kawo bakin k'ofar makarantar sun tardo direban har yazo d'aukar AFREEN. Hasina tace "K'awata ke har anzo d'aukar ki ma, kije kawai da yamma mun ha'du amma k'awata ki daina saka nik'af mana dan Allah." Saida ta juyo ta kalleta tace "Je peux pas kallo na ake sosai wasu ma su ma kamar zasu cinye ni wlh sabida kallon k'urila da suke man, nikam banga abin kallo a tatare dani ba, kyau naga akwai wanda suka fini to miye na wani damuna da ido wlh hakan na takura man sosai ba, ina fad'a maki a nik'af ma ban tsira ba bare na bude fuska na hakan ya fi min kedai, na riga da nasa ba idan nace maki zan iya fita a haka to wlh nayi k'arya kunya ma nake ji." Hasina tace "Shikenan amma taya kike gani zakiyi saurayi a cikin nik'af." Hararen ta AFREEN tayi tace "Ni ba su ne a gabana kada ki k'aramin wannan zancen su a dole sai sunga fuskar mutun ne zasu ce suna son su kenan fuskar ce suke so ba mutun ba mtsss ku ne samari su ka dama amma ban dani ba wallahi. Wai haka sis Khairat tace man, bari naje direba na jira na." D'ariya Hasina tayi tace "Gaskiya k'awata bakida dama to yi hakuri." murgud'a mata baki tayi sannan tayi gaba abinta tace "k'awata seda yamma in Allah ya kaimu. Murmushi Hasina tayi, kamin AFREEN ta k'arasa tasu motar direban su Hasina yazo a tare suka bar bak'in makarantar. Direba nayin parcking AFREEN ta fito tare da cewa "Baba direba ka juya ka d'auko Zeinab yanzu sun fito itama," direba yace "Yanzu kam d'iyar albarka" daga nan AFREEN ta nufi cikin gidan, tana shiga falon ta tarar da Maman da Tanti a falon da sauri Tanti ta mike ta tarbo ta tare da cewa "oyoyo d'iyata ya gajiyar makaranta" murmushi ta saki tace "Wlh Tanti akwai gajiya kin san fa yau awa 5 biyar mukeyi a cikin aji muna d'aukar darasi ba hutu." Tanti tace "Kai yau alhamis ba da gobe juma'a kuna shan zama sai hakuri daga bana da yarda Allah kun k'are muje ki yi wanka da sallah sai ki samu ki huta, tace to bari na gyada maman tare da kallon inda mahaifiyar ta take wada tun shigowar AFREEN da ta juyo ta kallesu ta mayar da kanta a tv, tace "Maman ya yuni gida" juyo tayi tace "Lafiya lau AFREEN kun taso ko? Jeki ki fito kizo kici abinci" amsawa AFREEN tayi da "Toh" tayi gaba Tanti na biye da ita suka shiga dakin, AFREEN tace "Wash Tanti duk nagaji" ta fada tana mai cire nik'af da hijab sannan ta rage kayan jikinta ta shige douche (toilet). Bin bayan ta da kallo Tanti tayi har ta shige douche tare da sakin wani kalan murmushi mai nufin abubuwa da yawa wanda ita kadai ta san min hakan yake nufi tashi tayi daga bakin gadon da take ta nufi armoir tare da ciro ma AFREEN wata bleu (blue) d'in doguwar riga mara dogon hannu tare da hijab sannan tazo ta shinfid'a mata darduma ta aza kayan a gado sannan ta juya ta fita. Minti biyu bayan fitar ta dawo d'oke da abinci ta ajiye kan moquette ta koma bakin gado ta zauna tana jiran fitowar ta. Ba b'ata lokaci AFREEN ta fito ta nufi gaban madubi ta zauna ta fara shafe shafan ta na turare tana gamawa ta tsane gashin ta da abin busar da gashi, sannan ta taso tazo baki' gadon ida Tanti ta ajiye mata kayan da ta d'auka ta saka tace "tanti nagode" Tanti tayi murmushi ta ce "Miye kuma abin godiya dan nayi wa 'yata abu." Murmushi itama tayi wanda ya sa fossette d'in ta fitowa tasaka doguwa riga tana me mika ma tantin chouchou ta saka mata k'arba tayi ta saka mata tace "Yi maza kiyi sallah ga abinci nan na kawo maki bama sai kinje table a manger (dinning) ba." Saka hijab kinta tayi ta nufi darmuma da tanti ta riga da shinfid'a mata. Tana idar da sallah ta tashi ta linke dardumar ta maryar da ita ma ajiyar ta, dawo wa tayi gun da tanti ta ajiye mata abinci ta zauna ta bud'e tayi bismilah ta fara ci, tanti dake zaune bakin gado ta dawo da kallon ta gun AFREEN tace " Yaushe ne saukar ku." AFREEN dake cin abinci ba tare da ta d'ago ba tace "Nan da wata guda da sati biyu insha Allah." Tanti tace "to Allah ya kaimu gaskiya d'iyata kina da k'ok'ari sosai kinga fah an yi miki saukar alkur'ani mai girma tun da dad'e wa yanzu gashi za'a yi maki ta tahafiz (saukar harda) da litatafn adini to Allah taimaka a ci gaba da bada hima, yima za ki cinye abinci ki bani assiéte d'in na mayar sai ki kwanta ki futa kamin lokacin école d'in yamma yayi." "Ai nama goshi" AFREEN ta fada tana mai mikewa ta koma cewa "Tanti gaskiya kina ji dani irin wanan hidimar da kike man ai ko mahaifiyata sai haka sedai nace Allah ya biyaki da gidan Aljannah ina alfahari dake a matsayi matar mahaifina ku abukiyar zama gun mamana sabida Tanti ke ba kishiya ba ce sedai abukiyar zama ke uwace ta gari wada samun irinta a fad'in duniyar sai an tona, yanzu ba kowa bane zai iya kula da d'an da banasa ba, mun gode sosai da kulawarki da soyayar ki a garemu." Ajiyar zuciya Tanti ta saki tare da sakin murmushi tace "Haba AFREEN idan kika cemin haka ai sai naga kamar baki d'auke ni a matsayi uwa ba, gaskiya bana so ki daina." "To tanti ai yaba kyauta tukwici dole ce ta sa nace haka amma na bari bazan sake ba kiyi hakuri." mikewa tanti tayi tare da d'aukar assiète tace to "Shikenan ya wuce tashi kije ki kwanta ki huta kan ajima sai na shigo na tayar dake kinji ko." Tace "To tanti wai ina anti Khairat najita shiru ko batanan ne." "A'a barci take shiyasa", daga nan ta juya ta bar dakin. Murmushi AFREEN tayi ta d'ane gado ba da jimawa ba barci ya kwashe ta. ********** Niamey....... AFREED da Ali na dawo wa daga masallaci suka nufi b'angaren Mama suna shiga suka tarar da ita ta gun salle à manger (dinning) da hannu ta masu nuni da su k'araso gun ta suka k'arasa kowa ya ja ma kansa kujera ya zauna tayi servir d'in su. Sun fara cin abincin kenan Ali ya dago ya kali mama yace "Mama ina su fariya tunda munka dawo aiki ban gansu ba" dariya mama tayi AFREED kuwa yayi murmushi yace "Gaskiya mama yau girkin ki yayi dad'i" irin wannan santi haka". Ali Sosa kan sa yayi tare da cewa "Kashe yanzu nan wai santi ne nayi gaskiya mama girki yayi dad'i sosai, amma su na ina wly seda na fara cin abincin ma na tuna Allah bar mana ke mamamu" tace "Amin abba na, suna gidan tanti ku d'azu karim yazo ya tafi da su daga tasuwar daga école kaya kawai suka canza ya tafi dasu, amma yanzu nasan suna bisa hanya tunda bacan za su kwana ba." "To Allah dawo dasu lafiya Ali ya fad'a AFREED da mama suka amsa da "Ameen." Ba su kai ga rufe baki ba a kayi sallama aka shigo falon, wasu 'yan mata ne da ba zasu wuce 18 ans ba suka shigo kyawawa kamanin su guda wankan tarwada masu matsakaicin jiki tsayin su daidai da su bai masu yawa ba da kagan su kasan yan biyu ne, da gudu suka nufi salle à manger guda ta rungume Ali guda kuwa AFREED. "Oyoyo su yaya tun mun taso makaranta bamu ganku ba" murmushi AFREED yayi yace farissa ni narasa ranar da zaku girma wallahi? a tare suka sakesu tare da zuwa suka zauna suka saki murmushi a tare fariya tace "Mama wai yaya na tambaya yaushe zamu girma? 'Yar dariya tayi tare dace "Sai ranar dana kaiku d'akin mijin ku." da sauri farisa tace "To yaya kaji mama ta fad'a maka. Yiyai kamar baiji ba yace "Mita ce" fariya tayi saurin magana tace "Mama tace sai ta mana aure," hararen wasa yayi mata yace "Ko kunya baki ji" dariya tayi ta sunne kai, Ali yace "Fariya aure takeso mama tunda har a gaban mu take maganar aure." Da sauri tare da zaro ido fariya tace "Wallahi mama ba haka nake nufi ba kawai na maimaita abinda kika fad'a ne , shine nayi laifi." Girgiza kai mama tayi sannan tace "Sai mi idan aure suke so tunda ku manyan banza har yanzu kun kasa fitar da mata kuyi aure, ai dole su na ma su aure ko hakan zai sa ku manyan ku san ciwon kanku, ku na kallo zan wanke su na kaisu d'akin su, amma kuma mahaifinku na dawo wa zan sa ya zab'a maku wada ya ga dama ya aura maku." Da sauri AFREED da Ali suka waro ido suna kallon ta a tatare sukace "A zab'a mana kamar ya? Sai kace wasu mata, auren dole kenan fah wanan ai sai mace, mu da ba mata ba." "Haka kuka ce to kuyi fatan Allah dawo da mahaifinku lafiya ku ga ikon Allah, zanga abinda zakuyi idan muka yanke hukunci a kanku." "Dan Allah Mama ki daina fad'ar haka gaskiya duk a nawa muke da za'aga kamar mun jima ba muyi aure ba, Mama ki kwantar da hankalin ki kina nan har gida zamu kawo maki su ki gansu insha Allah." "Ba wani ni za kuma wayo baku isa ba." AFREED da ke kallon su baice komi ba yace "Ali gaka tashi mu tafiyar mu inaga Mama ta gaji damu tunda so take mu bar mata gidan ta shiyasa takeso muyi aure duk a nawa muke ba wani girma mukayi ba amma Mama ta dage sai munyi aure." "Umm!!! Dube su ko kunya basa ji wai suce ma kansu a nawa suke mahaifin naku ai na nan tafe cikin satin nan zanga in kun girma ko baku girma ba ko su fariya ba sucewa basu girma ba barku k'artin banza k'artin wofi." Mikewa AFREED yayi tare da barin gun ya koma cikin salon Ali ma ya biyo bayan shi suka zauna kan kujerun. Farisa tace "Gaskiya mama kada a yiwa su yaya auren dole a barsu su zab'a ko mu ai ba a mana auren dole ba bare su kinga Mama ki barsu kina zaman ki zasu kawo maki surukai." "Humm ke kinga alamu aure a gaban su kin tab'a jin sun yi maganar aure ko da sau daya ne shekaru ja suke kuma mutun bai cika mutun sai ya ajiye iyali, lokacin kowa zai dinga kallon ka da daraja, kinga k'ara Ali da AFREED shi zai iya samo matar aure to AFREED fah ko kallon mace bai yi bare har tayi mashi yaji ya na son ta har yayi maganar aure, bai da wanan niyar ko kadan a zuciyar shi." Fariya tace "Hakane Mama kuma kinga hada lokaci bayi ba idan lokaci yayi su zasu fitar da kansu ba sai kun masu maganar ba kidai d'an k'ara masu lokaci kinji Mama." To shikenan zan k'ara masu lokaci muga yanda Allah zaiyi.... Tashi sukayi suka bar gun cin abincin tare da kiran mai aiki dan tazo ta gyara wurin cin abincin. Suma shigo wa sukayi cikin falon tare da zauna saman moquette (carpet) mahaifiyar ta su kuwa ta zauna kan d'aya daga cikin kujerun dake solon (falon) d'in. Sun jima suna fira kamin su AFREED suka mike su masu saida safe tare da barin falon su ka nufi nasu b'angaren. Suna shiga kowa ya nufi d'akin shi don yi shirin bacci........... ************** Tuchen Labarin: Alhaji Asmane Sanga haifafan kasar Mali ne kuma rik'ak'en dan kasuwa ne, yana da da shaguna uku na sayar da shadodi wanda sukayi fice a k'asar ta Mali sabida bubu kalar shadar da babu a cikin shagu nan sabida idan kaje wani gun baka samu shada ba shi nashi shagon idan kazo zaka samu shiyasa yayi fice kowa yasan da shagu nan sa a k'asar, yana da mata guda mai suna Hajia zakiya wada ita yar kasar Niger ce a jahar Zinder su had'u ne a ta dalin zuwan da ya tab'ayi Niamey bud'e wani katafaren shagon shadodi a garin, ita kuma ta zo yin soutenance kinta ta karshen karatu, to tunda ya ganta ya kwalafa rai a kanta saida Allah yayi har ya aure ta dama iyayen ta ba wasu masu k'arfi ba ne to ko da suka ga mai kud'in danda nan suka amince a ka d'aura aure a kaita Mali, shekarasu guda da aure Allah ya bata haihu ta samu d'iya mace aka samata fati, Fati na da shekara uku aka haifi Mariama, sannan Adamu, da shekara biyar a ka haifi sadissu, to tunda ga kan sadissu haihuwa ta tsaya, yara sun tashi cikin gata da tarbiya ta kowane fanni da karatu islamiya da na boko babu wanda suka bari a baya. Sadissu na da shekara 12 a duniya Allah yayi wa alhaji Asmane Sanga rasuwa saka makon wata irin rishin lafiya metsanani da ta same shi ta tsawon sati biyu, wani dare juma'a yace ga garin ku mutuwar da ta girgiza matar shi da ya'yan shi amma banda dangin sa, sabida ana yi sadar uku suka zo ma da matar margayi maganar ce wai tatara ta koma garin su ta bar masu yaran su zasu kula dasu da dukiyar tunda suma iyayen su ne ta nuna masu kan bata yarda da abinda suke so ba sudai bata gadon ya'yanta su tatara su bar masu garin, suka nuna mata da ba haka nan ba, to da ta gane dukiyar yaran ce suke son ciyewa, sai tace masu su bar mata yaranta ta tafida su in yaso sai su rike dukiyar can su dinga juya masu, aiko suna jin haka a take suka amince dama su dukiyar ce suke so wani daga cikin su yace to hakama yayi,Tare da miko mata 20000 wai suyi kudin Mota, girgiza kai tayi alamar bazata k'arba haka wanda ya miko mata da kudin ya mayar abinsa cikin aljihu da tak'i amsa tare da cewa "Yaushe zaku tafi." Tace "Gobe insha Allah", suka amsa da "Allah ya kaimu," tare da juya wa suka bar gidan. Tun daren ranar Hajia zakiya ta fara had'a kayan ta da na yaranta tare da taimakon babba yarinyar ta Fati, suna cikin gyaran kayan fati tace "Umma lafiya kike ta hada kayan mu" saida umma ta nisa kamin tace "dagin mahaifinku ke son na bar musu kasar sabida dukiyar da d'an uwansu ya bari su ce na barku a hannu ni kuwa nace ban yada ba sabida Allah kadai yasan kalar rayuwar k'uncin da za kuyi a hannun su sabida dama tun mahaifinku na da rai ba kaunar mu suke ba ni daku gaba daya, sabida ni ina 'ya Niger sukuwa 'yan Mali kuma suka so ya auri 'yar uwarsa yaki kuma shima ba kaunar sa suke ba kawai dan yana da arziki ne tunda shi kadai ne shima ga maihaifiyar sa duk sauran 'yan uba ne, amma bai tab'a nuna masu banci ba ko na bar ku nan wahala zaku sha shiyasa zan tafi daku." "Umma muma bamu yarda ma ki bar mu gunsu k'arfar ki k'afar mu to dukiyar Abba mu fah su zaki bar mawa." "To dama sabida mi suke so na barku don su rike dukiyar sa ne, ni kuma nace su rik'e d'in su bar min ku don ku fiye man komi a duniyar nan shi ne dalilin amince war su." To mama ke da ba aikin da kike baki kasuwar komi to dami zaki rike mu yakamata ko wasu 'yan kud'i su baki ko wata kasuwa kiyi." "Hum yaro yaro ne karki damu Fati Allah na tare damu , kuma bancin haka akwai wata millions 10 da tarkardun wani gida na mahaifin ku dake cikin garin Niamey da ya tab'a bani kamin ya kwanta rishin lafiya yace na ajiye masa kuma kada na fad'awa kowa, to kinga idan Allah yayi masu albarka shikenan a cikin su zan samu na k'arasa biya muku kudin makaranta mu d'anyi abinda ba'a rasa ba shi kuwa gidan muje cikin mu zauna, da yarda Allah ba zamu tagayaraba Allah dai ya ru fa mana asiri duniya da lahira." Da "ameen" fati amsa wada ta fahimci inda uwar ta dosa. Da ganan suka ci gaba da gyaran kayan, su na idarwa ta tataro yaranta ta fad'a masu da gobe zasuyi tafiya zuwa kasar Niger kuma ba zasu dawo kasarnan ba har abada amma bata sani ba kosu watarana suji suna son gani dangin mahaifin su to fah baza ta hanasu zuwa sada zumunci ba, ta had'a da cewa nasan kuma kowa nan ku nason yi min tambaya? Ban baku wanan damar ba sabida yanzu banida kyakyawa amsar baku ha bani da wata isha shiyar nutsuwa don haka kowa ya bar tambayar shi har watarana, daga haka kowa yayi gum da baki sa ba damar yin tanbaya. Washe gari da safe wajan karfe 9 sun gama karyawa.............. , Muje zuwa....... Godiya ta musan man a gareku masoya na💞 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZANBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ECRITE: _PAR_ *QUEEN ZEEFAT* Yar Mutan Niger Wattpad@nazhabibou 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_ Page 8 Washe gari da safe wajan k'arfe tara sun gama karyawa kenan se ga dagin mahaifin su biyu sun shigo, ko salama babu tare da cewa "Yo zakiya har yanzu baku tafi ba?" juyowa tayi da sauri sabida kamar daga sama taji maganar tunda bata ji shigowar su ba, da ido ta bisu tare da watsa masu wani mugun kallo tace "wai ku mi mu ka tare muku? duka yau kwana biyar da rasuwar bawan Allah nan amma duk kun bi kun takura man, nina ce zan tafi kuma ni nayi niyar tafiya, idan naga dama sai na yi zamana kuma ba yanda za'ayi dani tunda gidan nan na miji na ne da ya'ya na, sai in nayi ra'ayi ne zan tafi ba wai tilasta min zakuyi ba idan naga dama ba ida zani, ku dai kawai ku gode ma Allah inason koma wa k'asata ta haihuwa, da ba dan hakanan ba wly da ba abinda zai sani barin nan d'in wallahi se dai kuyi duk yanda zaku yi Ah to, tunda nawa d'iyan sun girma suma sun isa kula da kansu kuma da dukiyar mahaifin, amma duk da haka na zab'i na tafi da ya'yana sabida a zauna lafiya to kuma sai ku dawo kuna takura man? mun bar muku dukiyar a hannun ku kuma ai kun san hak'i ci zalin marayu ba sai na fad'a maku ba in kun gyara kun sani inbaku gyara ba ma kun sani, sudai sun bar komi nasu hannun ku duk yanda kukeso kuyi daidai ne wallahi kuma kuyi niya ku fita ku bar min gida sabida komi na maku ku kuka ja, idan mun tashi tafiya zan bayar da makulin gidan akai muku sabida ba abinda zanyi da shi ehe." K'wafa tayi tare da mayar da kallon ta ga abinda take ran ta a matuk'ar b'ace. Tsaye sukayi sina kallon ta baki bud'e suna tunanin yaushe matar Asmane ta samu baki maida magana, juyawa suka yi suka bar gidan tare da mamaki da tunani iri iri duk jikin su yayi sanyi. Su na fita k'ofa guda ya kalli guda yace "Anya wanan matar ba so take ta zame mana matsala ba kuwa?" nisa wa wanda aka yiwa tambaya yayi yace "Wallahi ni kuwa tausayi ta bani vraiment elle à besoin d'un peu du temps pour qu'elle puisse se soullager de ce qu'elle resent a cause de la mort de sont mari,sa fait que 5 jours que son mari est decèder, c'est pas bon ce qu'on est entrand de faire, comme maintenant elle a besoin de notre soutient parce qu'elle n'a personne ici que nous et ses enfants (really she needs a little time so that she can relieve herself of what she feels its fact that 5 days that her husband died, it's not good what we are going to do, like now she needs our support because she has no one here but us and her children). Wani shek'ek'e d'ayan ya kalle sa yace " Ban gane mikake nufi ba, kanaso ka nuna min cewa ka saduda sabida tayi wani w'azin ta can da barazana to Wallahi ahir d'inka mudai bazamu fasa abunda mukayi niya ba Suley sedai kai ka hakura." Wanda aka kira da Suley yace "To nidai Wallahi na fida hannu na daga cikin wanan rishin gaskiyar na ku na son ku handame dukiyar marayun Allah da basu ji basu gani ba ba ruwana ba hannu na ciki, idan Allah ya tashi k'watar masu hakin su, wallahi naga dai tun uban yaran nan na da rai yake mana abin arziki duk da nuna masa banbanci da muke, muna nuna masa shi d'in uba kad'ai muka had'a da shi, amma shi bai tab'a banbanta mu da kanshi ba, ko ya d'oki wani bare da muhimmanci fiye da mu sabida abinda muke masa amma bai tab'a nunawa ba dan haka ni ba ruwana ku kuje kuyi Allah bada sa'a." Juyawa yayi tare da komawa gidan ya sami yaran sun gewaye uwasu na kuka gaba d'aya hada uwa tasu, duk'awa yayi kusa da su yace "Dan Allah Hajia kiyi hakuri ki yafe man ni wallahi babu ruwana acikin abinda suke niyar yi, ki tatara 'ya'yan ki ku bar musu garin nan idan har zaki iya, indan kin ga zaki tsaya karb'a gadon yaranki toh ni me taimakon ku ne wajan ganin an k'watar maku hakin ku daga garesu, ko dan d'an uwana Asmane kun cancanci abubuwa da dama daga gareni sabida mu bai tab'a mana wani abu ba mara kyau kulun shi Alkairi ya ke fata a gare mu ba sharri ba duk da nuna masa k'iyaya da muke shi bai tab'a k'in mu ba Allah nagani dan haka duk abinda kuka yanke ina tare daku duk rantsi duk wuya, shi kuma da ya rigamu gidan gaskiya Allah ya jikan sa ya masa rahama ya sa ya huta." da ameen suka amsa. Sannan Hajia zakiya ta share hawayen ta tare da cewa "Nagode alhaji Suley kai ne kad'ai mai hali na gari dama tunda na ganka a cikin su nasan ba da son ran ka hakan ke faruwa ba ni da 'ya'ya na mun yafe maka Allah bar zumuncin kuma ni na riga da na wanke hukuncin barin k'asar nan ta Mali tunda ba mahaifata bace dama sabida shi mijin nawa nike zaune a cikin ta amma tunda wanda yafi mu son sa ya karb'i abinsa ba zan zauna ba, haka yaran nan da abina zan tafi sabida in suna gabana hakalina zai fi kwanta kuma idan Allah ya yada za su diga kawo maku ziyara sabida basuda wanda yafi ku, su kuma da sukeso son cinye masu dukiya suje sunci kad'an watarana sai labari, aka rasama mutum bare daud'a duniya bai komi wallahi su suka sani." daga nan tayi shiru tare da goge hawayen da suka zubo mata sukuwa yaran suna tana kuka. Sauke ajiyar zuciya Suley yayi yace "Amma naso kiyi zaman ki ko dan makarantar yaranki duk da yanzu a cikin hutun karshan shekara ne." saida ta dan nisa kamin tace "Bai komi idan munje zan canza masu makaranta in Allah ya yada tunda karatun Mali da na Niger kusan d'aya ne ba wani banbanci." "To shikenan amma ita Fati ki barta ta zauna gu na sabida ita tana shekarar ta karshe a université (university) bai kamata a fitar da ita ba idan ta k'arasa shekarar sai ta koma wajan naki, nima ko zan samu ladar rikon maraya kuma na samu damar sauke hak'in da d'an uwana ya tafi ya barmin ko da kuwa a kan tane kad'e zanyi murna haka, ga kuma soyayar da ke tsakanin su da isma'il d'an waje na, da sabida wata ma nufa tawa da zuga naso hana auren su amma yanzu ina goyan bayan had'in nan d'ari bisa d'ari yanzu ne nasan zafi da mahimmancin d'an uwana da baya nan ina ma zai dawo gare mu dan zan nuna masa matsananciyar k'aunar da nake masa kawai ina dane wane sabida a lokacin gurb'atacan halina ya dane mai kyau d'in mugun abu kad'ai ke cikin zuciya ta...... Bai k'arasa maganar ba sabida kuka da ya ci k'arfin sa. Suma yaran sake fashewa da kuka sukayi mai ban tausayi, Shima alhaji Suley kukan yake sosai kamar wani k'armin yaro mahaifiyar su ma kukan take mai tsanani sabida mutuwar yanzu take dawo masu sabuwa kamar yanzu ne yarasu, sun zama kalar tausayi gaba d'aya ba mai ba wani hakuri. Sun k'washi kamar minti sha biyar a haka kamin alhaji Suley ke tsagaita nasa kukan yace "Gaskiya munyi babban rashi Allah dai ya jikan sa da rahama, kuyi hakuri yanzu ne kuke da bukata ta a matsayin mahaifi kuma nine nan zan shige maku gaba insha Allah s'il vous plait pardon moi (please forgive me)." Hajia Zakiya ta tsagaita nata kukan tare da cewa "Alhaji ni ba zan hanaka Fati ba sabida kaima kana da iko a kansu a matsayin ka na wan mahaifin su, amma da'ita zan tafi idan Allah ya sa hutun nasu ya kare sai ta dawo insha Allah nayi maka wanan alk'awarin idai da rai da lafiya, kuma gobe tunda asuba zamu barin garin nan insha Allah sai in sun dawo ganin ku kuma, ita kuma idan sun daidai ta kansu itada isma'il to sai nafi kowa murnar had'in nan kuma komi na hannun ka na baka wuk'a da nama kawai kayi abinda ya dace a yanzu basu da wani gata sai Allah se kai uba garesu dan haka banida damuwa da hakan kuma mu baka mana komi ba idan ma kayi mun yafe." "Yanzu tun goben zaku tafiba zaki bari ku kara kwana biyu ba?" tace "A'a tafiyar dai zamu yi insha Allah zafi mana zaman nan d'in, kallon yaran yayi tare da mikewa yace to Allah kaimu goben, bin kan yaran yayi da d'aye d'aye ya na shafawa a sanu ya futar "Allah maku albarka ya jikan mahaifin ku kuma ya baku hakuri da juriya rashin sa tare daku." Da ameen suka amsa sannan ya kali Hajia yace "To ni zan tafi anje ma zan dawo muyi ban kwana insha Allah." Tace "Ba damuwa saika dawo." Daga nan ya fita ya bar gidan yana mai tausayin su har cikin rashin, umma ta ci gaban da lalashin 'ya'yata har suka hakura kowa ya tashi ya shiga harakokin gaban shi banda sadissu dake zaune har lokacin ya na tunani, daga bisani ya mike ya nufi k'ofa tare da barin gidan ga baki d'aya. K'arfe hud'u daidai na dare bus d'in su ta bar cikin k'asar Mali don zuwa Niamey a kasar Niger Allah da ikon tun suna gani duhun asuba har gari ya fara wayewa sannu a hankali ha rana tafito haka har yamma tayi duk inda lokacin sallah yayi haka direban motar zaya tsayar da mota kowa ya fito yayi sallah, har Allah da ikon sa ya kawo su cikin k'asar Niger a garin Niamey suna shiga k'arfe biyar da minti goma yayi, suna saukowa daga cikin bus (car) d'in Hajia zakiya tayi wani k'ayatacan murmushi tare da cewa "Alhamdulilah yau na dawo k'asata da zama Allah nagode ma." A take suka tatare kayansu da aka fido daga cikin motar tare da nufi gun da masu taxi ke tsaye suka musu magana taxi biyu suka d'auka sabida yawan kayan su duk da sun bar wasu a can. Wata k'ayataciyar anguwa suka nufa tare da yiwa masu taxin k'watance gidan da zasu sauka bakin wani had'ad'en gidan masu taxi suka ja suka tsaye fitowa suka mahaifiyar tasu ta sake sakin murmushi ta sake furta alhamdulilah ala kuli halin, bud'e jakar ta tayi ta fito da key d'in gidan ta bude sannan ta dawo ta biya masu taxin kud'in su, kamin suka dinga jidar kayan su suna shiga gidan da su masha Allah gidan ba k'aramin kyau gare sa ba suna shiga suka gyara abin gyarawa sannan kowa ya nufi d'akin sa don yin wanka, da suka gama shirin suka dawo falo suna neman abinci sabida yinwar da suka k'waso a hanya. Da suka buga suka buga basu sami komi a cuisine (kitchen) ba sai a ka tura Adamu nema masu abinci kamin ya dawo akayi kiran sallah magarib haka kowa ya nufi nasa dak'in don gabatar da sallah. Sai banyan sallah isha'i Adamu ya shigo gidan d'auke da abinda ya siyoo masu." Umma ta dube shi tace "Yanzu Adamu sai yanzu ka dawo duk da kasan muna jin yinwa sosai" saida ya d'an nisa yace "Wallahi umma saida na wahala kamin nasamu abin siyowa." Suna gama cin abincin kowa ya nufi dakin shi don yin bacin gajiya. Haka safiya na wayewa Fati da Mariama suka tafi kasuwa siyar kayan abinci da abinda ba'a rasaba sunna dawo suka nufi magasin (store) suka shirya komi sannan a ka fara hada hada had'a abincin rana haka suka ci gaba da rayuwa cikin farin ciki da annashuwa, yayiinda Hajia ta bud'e kanfanin siyar da shada da lace da atanta ida ta aikawa alhaji Suley kud'i ya na siyo mata shadodi daga mali yana aiko mata lace da atanfa kuwa haka take zuwa da kanta Nigeria ta saro tazo ta siyar masha Allah sanu a hankali kanfanin nata na ciganba cikin yardar ubangiji. Konci tashi ba wuya a wajan ubangiji yau ya kama saura kwana hud'u a koma école (school) da marecan ranar alhaji Suley ya kira umma yake tambayata ya butun da wowar Fati makaranta Mali? tace "ka kwantar da hankalin alhaji insha Allahu alk'awarin da nayi maka yana nan ban tada shi ba nan da kwana biyu zata zo in Allah yayada" daga cikin wayar aka amsa "Da Allah ya kaimu." Da dadare Hajia Zakiya ta tada ma Fati maganar kan cewa jibi zata tafi Mali insha Allah sabida da d'azu alhaji Suley ya kira kan maganar, mayar da kanta k'asa tayi tace "Umma gaskiya ni ban zan koma ba." "Ko sabida mi kika fad'i haka?" ba tare da ta d'ago ba tace "Kawai ku kuna nan ni ina can ban iya zama ida baki nan gaskiya umma kawai kice wa baba ya yi hakuri." Sak'e umma tayi tana kalon ta kamin tace "Ki k'wantar da hankalin kin Fati kije kawai ki k'arasa karatun ki can d'in Allah na tare dake kuma baban ku Suley da matar sa za su kula dake kamar yanda zanyi, ga isma'il saurayin ki zai fi kowa kula dake sedai ki rike mutuncin ki, idan baki son zama Mali wa yasaki fara soyaya da d'an uwanki wanda kinsan tôt ou tard tu va retourné laba de que tu sois sa femme (sooner or later you will return to the fact that you are his wife) kiyi hakuri ki tafi tunda mahaifinku na son zuwanki." D'ago da kanta tayi ta kalli mahaifiyar tasu tace "To umma Allah ya kaimu da "Amin" ta amsa sannan ta bar gun......... Ranar da Fati zata tafi ta had'a mata shatara ta arziki don ta kaiwa 'yan k'asar Mali, har gidan bus (car) suka rakata tana ta kuka su ne basu dawo gida ba har saida suka ga tafiyar motar su tana kuka tana d'aga masu hannu har suka ba'ce mata itama umma saida ta saki 'yan k'walla. ************** BAYAN SHEKARA HUDU Abubuwa da yawa sun faru wanda cikin shekaru hud'un nan hada auren Fati da Isma'il wanda suke zaune a k'asar Mali cikin so da k'auna tare da kwonciyar hankali da nutsuwa da yaron su guda Abdallah hada tsohon ciki a jikin itama Mariama tayi aure a Zinder inda take d'auke da tsohon ciki, shi kuwa Adamu ya kamala karatun shi yana kulla da kanfanin mahaifiyar su da matar sa guda wada umma ce ta had'a auren su tare da d'iyar 'yar uwar ta dake garin Maradi, yana zaune yuri guda mahaifiyar sa da matar sa, shi kuwa sadissu yana université (university) ta garin Agadez yana shekara karshe ta doctorat. Arzikin mahaifiyar su hab'aka yake masha Allah komi na rayuwa sunada shi sai abinda ba'a rasa saba sabida Hajia Zakiya tayi arziki sosai ba wanda bai santa ba a cikin garin Niamey, yanzu ba abinda zasu ce sai suce alhamdulilah Allah ya gama masu komi a rayuwa. Watarana sadissu ya fito daga cikin makaranta zai d'an zaga gari a lokacin yana da 28 ans masha Allah kyakyawan saurayi dashi mai jini ajika kamanin sa na Malienne sun fito sak kamar mahaifi sa dogo dashi abin birgeewa da ko wace mace 'yan mata bouzaye na ta haukan shi amma shi ko ta kansu bai bi duk da kusan yanda bouzaye keda kyau da har idan ka kalleso bakason ka d'auke ido, amma shi ko akansa, a yanda ya tsara ma kansa baida ma lokacin soyaya a yanzu sai ya kamala karatu, kwatsame yana fito daga université ya d'an yi nisa da makarantar tasu ya kai bakin titi har zai tsalaka hanya yaji kuka kamar na mace a kusa dashi. Juyawa yayi da k'arfi gefan da yake jin kukan, wata matashiyar budurwa ya gani duk'e ta had'a kai da gwiwa tana kuka kamar ranta zai fita............ Na Queen Zeefat Kuyi comments masoyan zanba cikin aminci hakan zai sa nayi wani page💓💖❤️ 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZANBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ECRITE: _PAR_ *QUEEN ZEEFAT* Yar Mutan Niger Wattpad@nazhabibou _BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_ Page 9 Juyawa yayi da k'arfi gefan da yake jiyo kukan, wata matashiyar budurwa ya gani duk'e ta had'e kai da gwiwa tana kuka kamar ran ta zai fita, d'auke kan shi yayi daga kallon ta da niyar ya bar gun, kawai sai ya tsintsi kansa da kasa barin wurin sake juyowa yayi ya kalle ta take ya ji wani matsanacin tausayin ta ya shige sa. D'aga k'afafun sa yayi ya k'arasa kusa da ita ya tsuguna yace "Asalama aleikum baiwar Allah lafiya mi yasa meki kike zaune bakin hanya kina kuka." Firgigite tayi ta d'ago da sauri lokaci d'aya ta mike tsaye yarinyar buzuwa ce mai massifar kyau duk da hawaye da suka cika fuskar ta da idanun ta duk sunyi ja haka duk illahirin fuskar yayi ja abinka ka farin mutum, hakan bazai hana ka hango tsananin kyau da Allah ya mata ba sabida ko a cikin buzaye samun mai kyau irin nata sai an tona kuma sai ansha wuya gun neman koda za'asamu mai kyau irin nata sabida kyakyawa ce ta gasken gaske. Zuba mashi manyan idanun ta tayi cikin na shi. Take yaji wani abu ya tsirga mashi cikin zuciya da sauri ya k'auda idon sa yana kallon wani gefe yace "Baiwar Allah magana nake maki ko kurma ce ke ban sani ba." Har yanzu idon ta na kanshi amma ta kasa magana, kusan minti biyu da yaji shiru ya juwo dan yaga ko ta tafi ne, sai yaga tana tsaye, har lokacin shi take kallon hawaye na k'ara bulbulowa ga fuskar, kuma tak'i magana, ganin haka yasa ya k'auda idonsa sabida bai jurar kallon cikin k'wayar idanun ta don da sun had'a ido wani abu yake ji yana masa zirrrrrrrrr tun daga saman kanshi har cikin tafin k'afar sa. Da yaga bata da niyar yin magana sai ya juya da niyar barin gun da sauri ta rik'o hannu shi ta k'ara fashewa da wani matsanancin kuka mai tab'a zuciya. Juyowa yayi da k'arfi yana fuskantar ta yace "Dan Allah baiwar Allah ki daina kukan nan wallahi har cikin rai nake jin wanan kukan naki." Har yanzu dai kallon sa take hannuta rike da na shi kuma tak'i cewa komai, amma ta bar kukan sai hawaye dake anbaliya a fuskar ta kamar ruwan teku. K'ara kallon fuskar yayi da tagama yin ja yace "Ki daina kukan nan kada kisama kanki ciwon kai, kuma ni ki sakeni na tafiya ta tunda baza kiyi magana sabida na lura ke ba kurma bace kina jin duk abinda nake fad'a." ya fad'i haka tare da fizge hannu sa daga nata. K'ara sauri riko hannu tayi cikin wata siririyar muyar ta bud'e baki da kyar cikin kuka tace "Dan Allah ka taimaka min aike na akayi da 2000f shine yanzu ina shirin tsaleke titi wasu maza biyu suka zo suka sabce suka gudu gashi yanzu idan naje gida nace an sabce min wallahi dukan mutuwa za'a man ka taimaka min dan kashe ni zatayi, tun d'azu nake nan ba wanda ya min magana bar inyi tunanin za'a taimaka min se kai duk wanda na tsayar nace dan Allah ya taimaka min sai ya fara min wata maganar banza ni kam ba halina bane." Tunda ta fara maganar ya k'urawa d'an k'aramin bakin ta ido yana kallon yanda take magana sannu sannu cikin nutsuwa da kuma yanda bakin ke motsawa. Jin shiru baice komai ba yasa ta d'ago da kanta ta ga ita yake kallo ko k'yabtawa baiyi da sauri ta saki hannu nasa tana ja da baya d'aga mata hannu yayi alamar ta tsaya sabida bakinsa ya masa nauhi, ja tayi ta tsaya d'an nesa dashi jikin ta na rawa sabida gani take shima d'aya yake da sauran mutanen da tayi ta tsayar wa, wanda a farin ganin shi da tayi bata mishi wannan kallon ba amma yanzu da taga ya tsura mata ido yana kallon ta kawai sai take ganin shima d'aya yake da sauran. Cikin sark'ewar murya yace "Baiwar Allah dakata ba cutar dake zanyi ba tambayar ki kawai zanyi." "To.... i...na jin...ka," ta fad'a cikin in ina hawaye na koma zubowa a fukar ta. Shiru yayi na kusan sakan 5 sannan yace "Miyasa za'a yi miki fad'a idan kince sabce kud'in akayi? Su a gidan basu san.........." Bai k'arasa maganar ba sakamakon katse sa datayi. Tace "Oh mon dieu (oh my god) idan fad'a ne kawai za'a min da sauki da bazan zauna anan ina asarar hawaye na ba kuma ina neman taimakon jama'a ba, kawai idan zaka taimaka min toh inko ba zaka taimaka min ba? na kama gabana tare da k'ara matso k'walla a idanun ta. Wata irin ajiyar zuciya ya sauke tare da saka hannun sa cikin aljihun wanda sa ya ciro da kud'in sannan ya k'arasa kusa da ita yace karb'i kije ki siyo abinda aka aike ki siyowa sai ki koma gida, amma dan Allah ki daina tsayawa a hanya kina kuka kina min asarar tsadadin hawayen ki wanan ba girman ki bane kin ga ke ba wata karamar yarinya ba kuma ki daina fitowa ba hijab gaskiya kina barin kowa na kallon surarar jikin ki bazan lamun ta da hakan ban kuma shine yasa duk wanda kika tsayar yake gayami ki magana banza. Sororo tayi tana kalonshi kamar taga wata sabuwar halita, sake waro ido tayi lokacin da idonta ya sauka kan kud'in dake hanun sa tace "Dan Allah ka rufa man asiri ni fa 2000 nace maka an sabce min ba wai 5000 ba taya zaka d'auki har 5000 ka bani ya zanyi da ita, kuma dakake cewa kan na daina maka asarar hawaye na na za'a kaima cewa kayi hawaye na to taya zan maka asarar su? da kace kada na sake fita ba hijab sabida ba zaka yarda ba to ni shine ban gane ba bawan Allah? Amma zan daina. Wani irin had'ad'en murmushi ya saki yace "Nima bansan na fad'i hakan ba, amma tunda kince zaki daina ai shikenan kuma yanzu bazaki gane da cewa wanan kukan da kike nine kikewa asarar hawayen ki ba sai nan gaba insha Allah zaki gane, karb'i kud'in ni na wuce. Saida ta nisa kamin tace "Dan Allah ka rufaman asiri ya zanyi da'ita sedai ka tafi mu tafi na sami canji sai na baka cikon." D'aga k'afafun sa yayi ya fara tafiya tare da cewa "To mu tafi." Jerawa sukayi suna tafiya kamar saurayi da budurwa masha Allah couple in su yayi suyi matuk'ar kyau duk idan suka gifta sai an kallesu shi kuwa da ya ga haka sai yai tunanin kowa itace ya ke kallo, tsayawa yayi cak ya daina tafiyar, juyowa tayi tana kollon sa da alama tambaya a bakinta amma kamin tace wani abun shi ya rigata. Fido da rigar sanyin sa yayi tare da cewa "Karb'i wanan kisa naga kamar kina jin sanyi kuma mutane sai kallon ki suke" dayake lokacin sanyi ne. Ba musu ta karb'i rigar ta saka ta soma tafiya bin bayan ta yayi da kalo tareda sauke wata kyakyawa ajiyar zuciya sannan ya fara tafiya. Sun k'washi kusa da rabin awa a hanya suna neman canjin 5000 basu samu ba ja yayi ya tsaya yace kinga ni gaskiya nagaji dayawa kawai kije ni bar miki 5000 d'in juwo tayi ta kalleshi idonta ya shiga sosai cikin nasa wani irin fa'duwar kaba taji tayi sauri k'auda idonta ta tunanin miyasa gaban ta fad'uwa yanzu tayi alhalin tun dazu da take kallon cikin idonshi bata ji hakan ba sai yanzu. Katse mata tunanin yayi yace "Lafiya kika yi shiru." Ba tare da ta d'ago ba tace "To katsaya a nan dan Allah naje na kai kud'in adashan dama sune aka aike ni kaiwa tsausayi ya samesu idan matar ta bani cikon sai na kawo ma wallahi idan naje da cikon kud'in nan gida matsala za'a samu tunda kaga ga gidan da zan shiga can ba jimawa zanyi ba ina kai mata zan fito." ta fad'i haka tana nuna masa wani gidan. Kollon gidan yayi sannan ya dubeta yace to jeki ina nan ina jiranki." D'ago kanta tayi da niyar masa magana ta kasa sakamakon haduwa da idanun su su kayi sanadin jin wata irin bugawa da zuciyar ta tayi kawai sai tayi saurin juyawa ta fasa maganar ta nufi hanyar gidan. A k'ala zata kai kusan minti goma da shiga gidan sannan ta fito, kanta na duk'e ta na kallon k'asa ta nufo idan yake tsaye yana jiranta. Sallama tayi masa ya amsa sannan tace cikin sanyi jiki "Dan Allah kayi hakuri na b'ata ma lokaci daga taimako na, wallahi matar ta tsayar dani itama bata da canjin kuma har yaro ta aika ya nemo bai samu ba, shine tace na bar mata kud'in idan ta samu canji zata kaimin har gida, to shine na fito na tambaye idan har ka yarda sai ka gayamin ida zan sameka in ta maido da cikon sai na kai ma." Murmushi yayi sannan yace wai miye kike ta wani sunne kai baki son kallo na tunda d'azu duk kin wani canza duk naga jikin ki yayi sanyi, kuma ni na ce maki na barmi ki sauran kud'in kawai ki rike idan ta dawo da cikon." Waro idon tayi waje tana kallon wani gefe tace "So nawa zan gayama ka cewa da akwai matsala idan a gida a ka gani da kud'in nan dan Allah ka rufan asiri ka gayamin inda zan ganka? Don na mayar maka da kud'in ka, yanzu ma sedai nace ma mai a dashan idan ta sami canji kada ta kai min gida zan zo na karb'a wallahi." Sak'e yayi yana kallon ta ita kuna ko da wasa bazata k'ara yarda ta sake had'a idon da shi ba. Wani tunani yayi sannan ya saki murmushi yace "To gashi nikuwa bason na saka ki a matsala amma kinsan mi za'ayi? Gigiza masa kai tayi alamar a'a, sannan ya ci gaba "Yanzu muje ki nuna man gidan ku idan kin karb'o canjin sai naje da kaina har gidan ku na karb'a." Ba tare da ta d'ago ba tace "Taya zaka gane cewa na karb'o." "Bata yada zayi na gane kin karb'o gaskiya, amma ba gobe sai na dawo nazo na karb'a ba, sabida nasan bazaki fuce gobe da yamma ba baki karb'o kudin ba nikuwa sai nazo da dadare na karb'a." Ba tare da tayi wani tunani ba tace "To muje na nuna maka." Tafiya suke ba me cewa dan uwasa wani abu kowa da tunanin da yake suna shiga wata wahalaliyar anguwa wada kana ganin ta kasan ta irin wanan talakawa nan talak ne. Ja tayi tatsaya dan nesa da wani gida batare da ta kalle shi ba tace "Kaga wacan gidan to shine gidan mu idan kazo nan zaka shiga ka tambaye dani sai na fito na baka kud'in ka." Sak'e wayi ya kollon gidan da ta nuna masa ya kuma juyo ya sake kallon ta yakai a kala sau biyar yana hakan, "Ko kad'an yarinya nan batayi kama da wada ke rayuwa cikin gidan nan ba duk da kayan jikin ta ka'dai ya isa ka gane cewa d'iyar talakawa ce amma bai tab'a tunanin har ya kai haka ba, ya fad'i haka a zuciyar sa sakamakon ganin ginin gidan da yayi na jar kasa duk yabi ya rarake sabida idan a kusan gidan kake ma zaka iya hagon mutanan gidan sabida k'ank'antar katangar take ya kara jin tausayin ta ya mamaye shi burin zuciyar sa ya k'ara k'arfi, a cikin zuciyar sa ya ce "Allah ka cika min burina." Katse maya tunanin tayi tare da mika masa rigar sanyin sa tace "Ungo rigar ka nagode ni zan wuce gida. Juyowa yayi ya kalle ta itama shi take kallo da sauri ta k'auda idonta, murmushi yayi sannan yace "Ki rike na bar maki." Saida ta sauke numfashi sannan tace "So nawa zan gayama ka cewa idan nashiga gida da wani abu wanda ba a sanni da shi ba zan shiga matsala amma ka k'i yarda." haka ta fad'a tare da sake mika masa rigar. Yana karb'a riga kamin yace wani abu ta bar gun ta nufi hanyar gidan su, bin bayanta yayi da kallo har ta shige cikin gidan, a sanan ne ya tuno da ko sunnan ta bai tambaya ba, murmushi yayi sannan yace "Bai komi idan na dawo zan san sunan." daga nan ya bar gun ya kama gaban shi. Ita kuwa tana shiga gidan wata 'yar dattijuwa ta yo kanta da masifa tace "Oh ni duniya ina zaki damu yarinyar nan tun yaushe na aike ki, amma dan gantali sai yanzu kika dawo kina can kina yawon iskancin ki da kika saba to yau uban mi ya tsayar dake kuma? Yo tambaya mima zan maki nida na riga da nasan hali? maza ki wuce daga gaban tun kamin na b'ab'alaki wallahi, nidai wallahi an barmin fitina miyasa uwarku da zata mutu baku mutu tare kika je can ki bita ni kawai sai a barmin jaraba ni da ban haihu ba amma wata ta haifa tabar min bala'i." Jikin yarinya na rawa ta gusa da ga gun matar tana sauke ajiyar zuciya ko kukan ma kasawa tayi sabida sabo da tariga tayi da halinta taje ta d'auki tsintsiya ta fara share tsakar gida. Da marece wajan karfe biyar sai ga matar da taje kaiwa kud'in adashe ta shigo gidan da sallama, matar gidan na zaune saman tabarma tana sauraran radio ita kuma yarinya na cikin wata rub'ab'a cuisine (kitchen) ta na dafa masu abincin dare, wanda tunda taji sallamar matar gabanta ya yanke ya fad'i da k'arfi har saida ta saka hannu ta dafe gaban ta. Mai adashan ta shigo ta zauna kussa da matar gidan tana washe baki, "Ah yar uwa kece tafe da marecan nan bari na koyo maki ruwa." matar gidan ta fad'a tare da k'ok'arin mikewa. "A'a yi zamanki banida k'ishirwa." Komawa tayi ta zauna tana me cewa "To kodai wacan 'yar iskar bata kai maki kud'in ba ne." A'a ki kwantar da hankalin ba shine ya kawo ni ba wata magana ce na zo muyi." "Ah to shikenan ina jinki." matar ta fad'a tana mai sake gyara zama. Mai adashan ta saka hannu a cikin jakar ta tafido da kud'i ta mika ta sannan tace "Ga cikon kud'in da dazu yarinyar ta kai min 5000 to banda canji sai nace tayi tafiyar idan nayi canza sa nazo nakawo maki, amma sai cemin tayi a'a kadana kawo maki na bari taje ta k'arba , to ni kuwa sai nayi tunanin ko so take ta kashe maki kud'in shiyasa na taso da kaina na kawo maki sauran canjin ki." Aiko ran matar a matuk'ar b'ace tace "Ni wallahi ban aikata da 5000 ba da 2000 na aiketa nace taje ta kai maki, amma bari na kirata na ji gidan ubanwa ta samu kud'in nan sabida nima da kyar na sami 2000 d'in na bata ta kai maki cikin d'aga murya tace ke uban miye ma sunan ki zonan yau sai naji ubanda ya baki kud'in nan. Yarinyar da tunda mai adashan ta shigo gidan hankalin ta ke tashe, tana ji kiran da aka mata tasan ba lafiya ba take cikin ta ya murd'a ya bada sauti k'ululu, mikewa tayi da sauri har tana tuntub'e ta fito daga cikin cuisine (kitchen) ta k'arasa inda suke ta tsugun bakin ta na rawa tace "Gani Ufadi." Bata tantance ba ta ji saukar mari biyu a tatare da sauri ta dafe kunci ta tana hawaye. Ufadi tace "Ubanwa ya baki 5000 da kika kai ma mai adashe banyan 2000 na baki? Tsinanniya tambad'ad'iya mai yawon gantali wane mazinacin ne da yaje ya gama shanye ki ya d'auki 5000 ya baki, oh ni yau naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba dama ni nasan jimawar da kikeyi baki dawo gida ba idan an aikeki yawon iskanci ne kike zuwa shegiya mai biyan maza wallahi halinki sai ya k'are kanki, bari ubanki yazo sai na fad'a masa shi dake d'aure maki gindi idan ance mashi kinyi abu yace bahaka bane to yau zai zo yaga abinda nake fad'a masa ya tabata da kina bin maza gashi kud'ad'en da suke baki tun kina b'oyewa har sun fara fito wa sannan kuma abiya ni tawa 2000 d'in wly, karuwa kawai tsinanniya, k'ara uban naki yazo ya san abin yi tun kan ki d'auko mashi abin kunya. Da sauri ta d'ago tana kuka tace " Wallahi Ufadi ba haka bane." Ta kwashe duk abin da ya faru ta gayama ta na mai k'ara fashewa da wani matsanancin kuka, ban abinda ya mata ciwo kuma ya sata kuka shine cewa wanda ya taimaka da ta kira mazinaci shine babban abinda ya ke kara sata kuka, idan itane ta riga da ta saba da wa'inan mugayan kalaman nan daga Ufadi har sun daina d'aga mata hankalin, amma gashi ta ja ma bawan Allah da baiji bai gani ba daga taimakon ta, bata k'arasa zancan zucin da take ba taji Ufadi nace wa. "Kinji mak'aryaciya toh ko uban ki bai isa ya min k'arya ba na yarda ba bare ke banza wofi kawai, ni maza tashi daga gaba na tun kamin na buge ki daga ganin wanan banzan halin naki na uwarku kuka d'auko tunda gashi shima tambad'ad'en dan uwan naki yana can yawan neman mata har Canada wai da sunan karatu itama karama an kaita wai Arlit gun k'anwar uwar ku Allah kad'ai yasan abinda ake can ana koya mata dagin tambad'ad'u sai ni aka bar make dan jaraba, miyasa kema ba'a kaiki wani gun ba. irin asarar da kuka d'auko halin uwarku. Tashi tayi daga gun Ufadi ta koma cuisine (kitchen) tana hawaye cikin zuciyar tace najawa uwata zagi baiwar Allah dake can cikin k'abari bata masan abinda ake ba, niko wace irin d'iya mai jama uwarta zagi, kara fashewa tayi da wani kukan mai tsanani abin tausayi. Mahaifinta na dawo Ufadi ta nufe shi da maganar ta kara hada abinda bata ji ba kuma ba tagani ba ta k'ulla makircin ta. Rai b'ace mahaifin nata yace " Jeki ki kikara min ita" fita tayi tana murmushi ta shiga d'akinta tace ubanki na kiranki ko jiran abinda zata cewa batayi ba ta fice daga d'akin. Tashi tayi hankalin kwonce ta nufi d'akin mahaifin nata sabida tasan tana gaya masa yanda abin yake zai yarda, da sallama ta shiga sannan ta sami guri ta zauna kusa da mahaifin nata tace "Abbu sannun da gida." Kallon ta yayi sannan yace "Yawa Arahamat, Ufadi tazo man da wani zance da bangane inda ta dosa ba shine nace ta kirawo man ke naji gaskiyar maganar a bakin ki." Saida ta sauke ajiyar zuciya sannan ta shiga labarta ma mahaifin nata abinda ya faru sannan tace "Wallahi abbu ni ban ma sansa ba a hanya na had'u dashi kuma na nemi ya taimaka min, gudun kar na dawo nace wa Ufadi an sabce kudin ta dokeni amma shine daga baya da ta sami labari tace zina nayi aka bani su kuma ma yace zai dawo ya k'arbi saura kud'in idan ba gaskiya na fad'a ba idan yazo a tambaye sa." Lokacin da ta fad'i zina mahaifin nata ya runtse idon sa har saida ta yi shiru kan nan ya bud'e yace "Shikenan tashi kije idan yazo karb'a kud'in nasa ki ce yazo ina neman sa. To tace sannan tashi ta bar d'akin a bakin k'ofa ta tarar da Ufadi rai b'ace sanadin jin duk abinda suka tatauna ita da mahaifin ta alhalin ba haka taso ba... Gaisuwa mai tarin yawa ga duk wani mai kauna ta da kaunar litafin nan ina ma kowa fatan alkairi.........💖💖💖💖💖💖 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZANBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ECRITE: _PAR_ *QUEEN ZEEFAT* Yar Mutan Niger Wattpad@nazhabibou 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_ Page: 11 & 12 Sanadin gigitaciyar k'arar da Arahamat ta saki yasa 'yan cikin d'akin suka fitu da gudu har suna bangazar juna kowane na k'ok'arin k'arasa ida take a yashe babu alamun numfashi a tatare da ita, suna k'arasowa tashin hankalin da suke ciki ya k'ara nin kuwa, a tare suka durkusa gaban ta suna kiran sunan ta su girgiza ta, sabida tsanani tashin hankalin ko lura da namijin da ke rik'e da ita yana girgiza ta basuyi ba, wanda shine bak'on da yayi sanadiyar firgicin ta har ya kaita ga suma. "S'il te plait ma soeur reveille toi dan Allah il ne faut pas partir me laissé(Please my sister wake up dan Allah you must not leave left me)" Bak'on ya fad'a yana mai k'ara girgiza ta. Duk da maganar da yayi hankalin su bai kai garesa sunata Arahamat, tanti Fatima ce tayi hausar tafiya ta d'ebo ruwa, tana zuwa ta zuba mata ruwan, wata atishawa tayi da k'arfi tare da sauke ajiyar zuciya mai k'arfin gaske, sannu a hankali tafara bud'e idonta har ta sauke su kan tanti Fatima da kiran sunanta tana mai jero mata sannu. Tare da cewa "Lafiya Arahamat miya firgita dake haka har kika suma mu mun fito ba muga komi ba." Da sauri ta mike zaune tana mai zubar da hawaye, tace "Tanti wallahi yaya Ibrahim nagani ya shigo ta k'ofar gidan nan dan Allah kada kuce man ba shine ba Kar kuce man mafarki ne nake." Da sauri Tanti Fatima ta juya ta na kallon k'ofar shigowa gidan, shima da sauri ya matso kusa da Arahamat dake zubar da hawaye har yanzu yace "Nine k'anwata ba mafarki kike ba zahiri ne." A tatare suka juyo daidai saitin da suka ji muryar shi ta fito suka tsura masa ido suna kallon shi baki sake, kowa ya kasa magana, da sauri Arahamat ta fad'a jikin sa tana kuka sosai tare da cewa "Ashe yaya zan kara ganin? kulum sai nayi kukan rashika a tare da mu ba kad'an mukayi kewarka ba, ashe dai yaya kana raye ka manta da mu? Mu kuwa babu ranar da ba zamuyi hirarka da Abbu ba, amma kai kana can kana jin dad'i ka manta da mu se mune muka damu dakai kasan cikin tashin hankalin da muka shiga kuwa sabida rashinka a tare da mu......." kasa k'arasa maganar tayi dalilin kuka da ya ci karfinta. Sukuwa su Tanti Fatima kasa magana sukayi suna ta kallon shi cike da mamaki shine kuwa ko wanine me kama dashi, tare da tambayar kansu lokacin da ya shigo gidan da ta inda ya fito? D'ago ta yayi daga jikin sa yana cewa "Dan Allah kuyi hakuri soeur (sister) wallahi ninan nafi ku damuwa sabida ku nan kuna ganin juna nikuwa ni kadai ne a can ba wanda nasani, kumin uziri mana tunda ba kusan abinda ya hanani zuwa gareku ba." Sai a sannan Tanti Fatima ta sami damar magana tace "Oh Allah Ibrahim ashe kana raye? munan har mun sadak'ass muyin tunanin ka koma ga mahalicinka ashe Allah yayi zamu had'u gaskiya naji dad'in dawowar ka duk da ba kyauta ba shekaru aru aru aru ka tafin ka bar dangin ka da iyayen ka, to muna son muji abinda ya hanaka dawowa sai yanzu kuma daidai wanan lokaci." Sai da ya sauke naunau yar ajiyar zuciya ya gyara zaman kamin yace "Tonku zauna sai na fad'a maku." suna zaunawa san ya fara da cewa "Tunda zan tafi dama banso tafiyar nake ba Abbu ya dage sai naje, dalilin shin nason nunamin mahinman cin karatun da zanje nayi zai min anfani tunda baiga anfanin zamana nan ba sabida ko na zauna babu abinda zanyi sai zaman banza yace naje nayi karatu shine mafi alkairi a gareni, ta haka na tatara na tafi ba dan raina yaso ba. To muna zuwa saida muka sha wuya kamin muke samin gurin zama karatu ya kankama watan biyu da zuwa guzirin danaje dashi ya k'are sai wani abokina da muke zama d'akin guda muke maneji da nashi guzirin shima muna da wata shida nashi ya k'are, amma dayake baban shi mai rufin asirine sai ya kirasa aka k'ara turo masa da kud'i, nikuma tunda na bar garin nan Abbu baida waya nima kuma banda ita kuma ban tafi da number kowa ba ko da kuwa cikin abokai nane tunda nima ba wayar ce dani, bansan ya zanyi na neme ku ba, haka muka tayin maneji da kud'in da ake aiko ma abokina har mukayi shekara guda aka bamu hutun wata biyu muka nuna muna son muzo ganin gida manyan da muke tare dasu acan, se a sannan suke fad'a mana cewa ai inda gomnati ta kawoka karatu kasashan waje to sai ka kamala shekarun da zakayi na karatu sannan zasu iya maido sa gida, inko har mutun nason zuwa ganin gida sedai iyayen sa su biya masa kud'in da zaizo ganin gida sannan su biya masa na komawa idan an koma makaranta. Daga jin haka kawai sai na sadak'ass nasan nida dawowa gida kuma sai wani lokaci in tak'aice maku ranar dai har hawayen bak'in ciki saida suka zubo man, sabida nasan ko ina da hanyar da zan nemi Abbu ba kud'in turo min ke garesa ba ko wanda zanci abinci ne bare har na jirgi, haka ina kallon abokina da muke d'aki d'aya ya shirya kayan sa dan zuwa gida har yake cemin ni ba zani gida ba nace masa a'a anan zan zauna haka ya shirya yayi tafiyar sa ya barni, wanda 'yan kud'in da ya barmin ko sati bayi da tafiya ba suka k'are, ya zamana kulum da yinwa nake kwana nake tashi har zuwa kwana biyar a lokacin na kamu da rishin lafiya da yasa aka d'aukeni aka kaini asibiti cikin mayan da muke tare dasu, a asibiti ne suke sheda masu cewa yinwa ce ta min yawa daga nan suka min aiki muka dawo gida wanda ya kaini asibitin ya sayo man abinci mai yawa ranar dai yini nayi ina cin abinci." Sannan ya d'an nisa yace "Ke Arahamat ba sallah ce zakiyi ba Nagan ki kina alwala?" Kai ta girgiza masa alamar eh sannan ya koma cewa "To tashi kije kiyi sallah kowa maje yayi sallah idan kuka gama sai na k'arasa baku labarin." Arahamat ta mike ta kakab'e jikin ta sannan ta kalle shi tace "Yaya amma dai ba wayo kamin ba ko? kada naje na shiga d'aki yin sallah ka koma tafiyar ka barmu." Murmushi yayi yace "Ko can ba barin ku nayi ba nesa dai ne nayi daku kuma insha Allah nazo gida kenan ba zan sake komawa ba ina nan a tare daku duk rintsi duk wahala." Murmushi tayi itama sannan ta juya ta d'oki buta ta koma sake alawa tana jin ta yau cikin wani irin farin cikin mara musultuwa a haka har ta gama alwala ta tashi ta nufi d'aki. Yana gani ta shiga d'aki ya tashi shima ya nufi wani d'aki wanda yake malakinsa tun yana gidan ya bud'e ya shiga d'akin wanda kulum Arahamat sai tashiga ta share ta gyara masa shi sabida duk ranar da taji kewar yayanta ya mata yawa d'akin nasa ma take kwana da yaga ko ina tsatsab ya saki d'an murmushi, yasan ba wanda zai wanan aikin sai Arahamat, cikin farin ciki ya shiga ya rage kayan da ke jikin sa sannan ya fito ya d'ebi ruwa ga bokiti ya shiga wanka. Arahamat na gama sallah ta fito ta nufi d'akin yayan nata cikin farin ciki da anashuwa ta tardo bashi nan sai kawa tashiga k'ara gyara d'akin sabida taji lokacin da yake d'iba ruwan tasan yana doushe (toilet). A haka ya shigo ya sameta yace tare da murmushi kwance a fuskar sa"Arahamat sarkin aiki kedai baki gajiya da aikin d'akin nan baida komi amma kuma dan kiba kanki wahala sai kin k'ara gyara shi dama tunda na tardo d'akin tsaftsaf nasan kece me gyaran Allah dai ya maki albarka ya baku miji na gari keda 'yar uwarki dan nasan itama yanzu ta girma. Amma ya naga banganta ba alhalin ga Tanti Fatima nagani?" Cike jindad'i tace "Ameen yayamu abin k'aunar mu godiya muke baka jin wani irin farin ciki danake ciki ba yau duk sai nake jin duk duniya ba wanda ya fini farin cikin nayi farin ciki sosai da ganin ka yaya har narasa ya zan nuna farin ciki na, Jannah(sunan k'anwar Arahamat) itama tanan zuwa jibi makaranta ne ya hanata biyo Tanti wallahi yaya kazo lokacin dana ke mugun buk'atar ka bar na barka ka shirya kamin na kawo maka abinda zakaci sai nazo muyi fira sai ka k'arasa bani labarin ka da Canada." Tana gama fad'ar haka tashi tare dayi tsale ta gudu abinta, murmushi yayi da yasa har fararen hak'oren sa suka bayana sannan ya nufi gun da kayan sa suke ya ciro kala guda yasaka sannan ya d'oki tapis ya shinfid'a ya tada sallah. Arahamat na dawowa tashigo masa da kulolin abinci har guda uku da kallo ya bita sannan ya fara bud'e kulolin yana ganin abinda ke ciki guda d'atacan da kalin turawa ne da yaji kayan had'i su kwai su tomatir su mayonaise su albasa su maggi sosai dai ya had'u guda kuwa perpesun kaji ne a ciki sannan guda kuwa farar shinkafa da taji decoration k'ara kallon ta yayi sannan yace "A ina na kika sami abincin keda baki fuce minti 15 ba da fita a d'akin nan ko nace ina kika sami kud'in haka." A shagwabe tace "tace yaya wanan dankalin turawan dama tanti ta zo dashi da yawa da zata zo tun d'azu Ufadi ta dafaya dan muci da rana kuma sai ta fasa tace sai dare shine na d'ebo na kwalla maka shi yanzu, wanan perpesun kuwa shima tanti ta bada kud'in aka sayo kajin sabida Ufadi tace mata daginta dake tchirozerine nanan zuwa sabida ka su zo su tardo gidan ba abinci idan su kwaso yinwa shiyasa tanti ta bayar a ka siyo Ufadi ta dafa masu, shine tace na d'iba maka na kawo ma." "To nagode sosai amma miya faru naga bak'i sosai a gidan nan naga ha dagin Abbu ma sunzo." Murmushi tayi tana sun ne kanta k'asa tace nima yaya bansani ba ka tambayi Tanti Fatima sai ta gayama ka nidai banda labarin komi nima ganin su kawai nayi." "Anya gaskiya kike fad'a min kuwa Arahamat ban fa sanki da k'arya ba amma dai bari zan tambayi Tantin." Jawo kulolin abinci tayi ta fara zuba masa ta tura masa gabansa fara ci yayi sannan yace "Ke bazaki ciba." Tace "A'a yaya ni fah a k'oshe nake kaci abinka." Murmushi yayi sannan yaci gaba da cin abinci sa suna fira, tace "Wallahi yaya idan na kalle ka sai naga kamar mafarki nake amma da nayi maka magane ka mayar min sai na yarda da zahiri ne ba bacci nake ba yau dai ina cikin farin ciki mara misali alhamdulilah Allah nagode ma da ka dawomin da yayana, wa ya isa ya min haka ko ya saka ni cikin wanan farin in ba kai ba ya ubangiji alhamdulilah alhamdulilah wallahi yaya sai nakeji kamar da ummu (mahaifiyar su Arahamat da ta rasu) ne nake fira a yanzu ina maka kallon ummu na yaya shiyasa farin cikina ke k'ara k'aruwa Allah ya duba maraicina shiyasa ya dawo min dakai adaidai wanan lokacin da nake da bukatar uwa a tatare dani Alhamdulilah bazan gaji da gode masa ba." 'Yar siririyar dariya ya saki sannan yace "Wallahi petite soeur nafi ku farin ciki au moins ku kuna gani Abbu da tanti Fatima ga Ufadi to nifa ba wanda nake gani sai jar fata amma gashi yau gani a tare daku ai kinga farin ciki na yafi naku bance ba yau zan iya yin kwana sabida farin ciki Allah shine ya cancanta a gode mawa dan haka Alhamdulilah." "Hakane yaya bari na barka ka huta kamin ka k'arasa mana labarin ka." Mikewa tayi tare da barin d'akin ta na jinta cikin matsanancin farin ciki. Tana fita ya k'ara maida hankalin sa ga cin abincin yana gamawa ya fito daga d'akin ya wanke hannun sa tare da kuskure bakin sa ya nufi d'akin da aka ta nadarwa Tanti Fatima da sallama ya shiga inda ya tardo su ita da Ufadi da Arahamat ana kuskus da kallo suka bishi har ya nemi guri ya zauna sannan ya d'ago ya kalle su yace "Ufadi kuskus d'in miye ake banda ni? nima asaka ni a ciki man tunda yanzu Allah yayi dawowa ta." Murmushi Ufadi tayi kamar ba itace mai galazawa Arahamat ba tace "Ai kam wanan magana sirine tsakanin mu kabari idan ka k'arasa bamu labarin ka sai d'an sanar da kai kad'an daga cikin wanan sirin karka damu ai dole a sakaka a ciki, amma kamin nan kaje ka kwanta ka huta ka kwaso gajiya." "Ufadi ai banjin bacci ne wallahi sabida farin ciki nakasa yin bacci har kwantawa nayi da naga bacci ba d'okata zai yiba na taso na fito." Tanti Fatima tace "Hakane yanzu ci gaba da gayama na yanda akayi har kazo gida muji kuma ma har ka gane hanya ka kawo kanka." Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan ya fara da cewa "Wanda ya kaini asibiti shi yaje ya samin sauran manyan akan yi shawara cewa su saka gwamnatin Niger ya dinga ma yan makarantar daake turowa k'asashen waje biya sabida in iyayen wasu na da hali wani na shi iyayen basuda. Haka dai sukayi ta taunawa har suka tsaida magana guda akan zasu tintib'in gwamnati, To Allah da ikon sa sai da suka tintimb'i shuwagabani Niger da maganar sai suka amince da shawarar haka aka dinga bamu 50000 duk wata kuma nasami wata restaurant ina masu aiki shara da guga suna biyana a haka nake samin kud'in nike wasu yan buk'atu na sabida a restaurant din da nake aiki nan suke ban abinci wajan kashi uku a yini, kuma ina tara wasu kud'i da nake b'oyewa a cikin kayana sabida na d'aukar wa raina cewa dana tara kud'in jirgi baro garin zanyi, a haka har muka koma karatu abokina shima ya dawo, kwanci tashi ba wuya a wajan har na cika she kara uku a garin kuma a lokacin ne na tara kud'in jirgi da zan dawo, daran wata alhamis nake gayawa abokina da yanzu nasami kud'in jirgi gidan zan koma, sai yake cemin idan kaje gidan zaka dawo ne nace masa a'a ina tafi na tafi kenan, wace Ibrahim kada kayiwa karatun ka haka kuma shekara guda ya mana saura mu k'arasa sannan idan kajewa Abbu gida a haka ba kai ba diploma ba degree ba wata takada da zai nuna masa cewa ka k'arasa karatun gaskiya ba zaiji dad'i ba kuma fushi zaiyi dakai, sabida dan ga sami sheda me kyau ne da karatu mai zurfi yasa ya tilasta maka zuwa gari nan kuma dan katsaya da k'afafun ka ne ba sai ka je nema wajan wani ba kuma dan ka talafawa k'ananka mata da shi kanshi Abbu d'in tunda ba k'arfi da shi ba, ga shekarun da kayi ba kaje ganin su kuma sai ka koma masu ba wani labari mai kyau sannan kuma shekaru ukun da kayi sun tafi a banza kenan? "To da ya fad'i haka sai naga yayi gaskiya kuma naga shima tun farkon zuwan mu da yaje hutu bai k'ara zuwa ba sedai yayi waya dasu, sedai baban tashi hankali na shine wani sa'in idan na kwanta bacci sai nayi mafarkin Arahamat tana kuka ta na rik'o hannu na amma kuma idan zan mata tambayar duniyar nan baza ta fad'a min abinda ke sa ta kuka ba sedai ma idan taga zan takura ta da sai ta fad'a sai ta tafi ta barni hakan ba k'aramin tayar min da hankali yake ba, sedai kawai nayi ta yi mata adu'a sabida, kuma sai nake tunanin duk lokacin da take cikin damuwa ne ko aka mata wani abun ya kesa ina marfakin ta tunda ba kulum nake yi ba. In tak'aice maku dai a shekara da na kamala karatu na a shekara ne ina shirye shiryen zowa gida wata babba ma 'aikata ta d'aukeni aiki sanadin nasami sakamako mai kyau fiye da nakowa nine ma nayi na farin gashi fannin da na karanta shi sukeda buk'ata amma nak'i mutanan sunyi sunyi har linka min albashi sukayi amma nak'i saida abokina ya lalab'a ni tareda k'armin kwarin gwiwar cewa zai jirani har nayi shekara guda ina aikin sai mu dawo gida tare kuma yace idan nasamin kud'in shekara guda zaifi min sabida da kud'in shekara guda yace zan iya bud'e wani kasuwaci da zan tallafi dangina da shi ya fad'a min hakane sabida gani yayi duk sanda aka nemi nayi wani abu nak'i to da ya kawomin zancan dangina shikenan ko minene zanyi." Sai da ya d'an nisa kamin yaci gaba "A haka dai na yarda ba dan naso ba. Bayan shekara guda da wata biyu da kama aikina, nayi niyar zowa gida sabida nayiwa kaina alk'awali yanzu babu abinda zai hanani zuwa gida sai wani ikon Allah ban fad'a wa abokina k'udirina ba har saida ya gani ina had'a kaya ya ke tambaya ta lafiya nace ni tafiya ta zanyi wace." Yace "Shine baka gayamin ba, ba munyi alk'awalin tare zamu koma ba?" Nace "Gani nayi duk ina fad'a maka tafiya ta hanawa kake yi shiyasa ni kuma wanan nayi alk'awalin ba wanda ya isa ya tsayar dani daga abinda nayi niya gaskiya nayi kewar dangina nesa ba kusa ba." Murmushi yayi sannan yace "Karka damu abokina nima wanan karan ina bayan ka sedai wani hanzari ba gudu ba shin kasanidan ma'aikatar da kake aiki suka san tafiya zakayi kuma bazaka dawo ba zasu iya bin duk hanyar da suke so su hanaka komawa ba, in jindai ka shirya abinda zaka ce masu ko? A take gabana ya fad'i sai na shiga tunanin mafita ai kuwa nasamu. Sai nace masa inada mafita yanzu zanje na sami shi babban na fad'a masa na take na gayawa abokina nawa mafitar dana samu sai kuma yayi na'am da ita haka, a tare da shi mukaje muka fad'a ma mai kanfanin cewa zanje ganin gida ne mahaifina ya kira yana son gani nan sabida yau shekara biyar tun da nazo garin ban koma ba Allah da ikonsa ina fad'a masa ya yarda hada tambaya ranar da zanyi tafiyar nace masa gobe haka ya bani mak'udan kud'ad'e tare da yimin fatan sauka lafiya sannan kuma yace ga jirgi sa nan a kaimu har garin mu naji tausayin sa sabida idan yasan k'udirina ba zai yarda da tafiyar tawa. Haka dai muka shiga gari muka yo sayaya sosai ina ta tunanin shin Arahamat ta kai yaya yanzu nasan dai tana da tsayi kuma nasan da yanzu ta k'ara kuma shekarunta ishirin yanzu, haka nayi ta jidar masu kaya ita Jannah masu tsayi, nakima Tanti Fatima inata k'iyastawa na Ufadi ma haka Abbu ma haka nadai siyo nidai bansan zasuyi ba ko ba zasuyi ba Allah wa'alam kuma sai in kun saka, safiya na waye wa muka baro Canada mukasa sauka garin Niamey a take naji wani matsanacin farin ciki ya lulub'eni yau ganin cikin Niger tunda nabarta yau kimanin shekara 5 da 'yan watani bantab'a lek'ota ba sai yau na juya na rugume abokina ina farin ciki sabida gani nake har nazo gida cikin yarda Allah." "Kwanan mu guda Niamey na shigo bus kin Agadez abokina kuwa dayake d'an Marad'i ne yabi bus kin marad'i sai gashi yau dai Allah yayi nazo gida da fatan duk zaku yafe man ba da son raina haka ya faru ba, batun kuma nayi yanda akayi na kawo kaina gida mai sauk'i ne dama ban manta da sunan anguwa mu ba haka kamanin gidan muma bai b'ace min ba duk da naga ya k'ara zubewa amma haka bai hanani k'in ganesa ba taxi kawai nashigo nayi masa kwatance ya kawoni har k'ofar gidan nan." Yana gama fad'a labarin ya sauke wata irin ajiyar zuciya sannan. Ya na jiran jin abinda zasuce. Suma ajiyar zuciyar suka sauke kamin Tanti Fatima tace "Allah maka albarka kuma Allah yafe mana gabad'aya tunda ma dai lafiya kake ai shikenan, gashi kazo daidai lokacin da ake da buk'atarka sabida nan da kwana hud'u za'a d'aura wa Arahamat aure insha Allah." A take yaji wani farin ciki ya k'ara lulub'e shi yace Alhamdulilah naji dad'in samin wanan labari nayi farin ciki sosai k'anwata Allah sa alkairi, oh Allah nagode maka da ka dawo dani a daidai wanan lokacin kinga Allah da ikonsa inada rabon shafa fatihar auren k'anwata mafi soyyiwa a gareni Allah maki albarka Arahamat Allah sanya alkairi a cikin auren ya baki zaman lafiya da farin cikin mai d'aurewa da zuri'a d'ayaba, zako aminki aure irin na 'ya'ya gata sabida yanzu haka maganar danake maku ina da mak'udan kud'in da ni kaina basan yawan su ba dan haka Tanti Fatima gobe ku shirya tare da ita ku bi jirgi ku tafi Dubai siyaya ta zabo abinda takeso." Aiko take Arahamat ta fashe da kuka tace "Yaya nagode allah saka da alkairi banida kamar ka yayana bayan mahaifina kaine uwata." Shima saida kwalla suka zubo masa yace "Baikomi k'anwata yi shiru ki daina kuka nima ban da kamarku idan ban maku ba wa zan ma ko da kuwa ace banda wanan kud'in zan shiga in fita in samo wanda za'a fita kunya to baranta nama inada anfanin mi zasu man idan ban muku." Tanti Fatima ta nisa sannan tace "yanzu dai wuri ya k'ure da zuwa Dubai kawai abinda kenan shine a hau jirgi a tafi Niamey sayaya ko Marad'i dan can akwai komi sai d'an abinda ba'a rasaba sai ta zab'o abinda takeso." Haka dai suka tsayar da maganar zuwa Niamey Gobe in Allah ya so ya yarda. Haka dai suka ci gaba da firar yaushe gamo har Abbu ya dawo, lokacin da Abbu yayi tozali da Ibrahim sedai gabansa ya fad'in dan a tunanin sa fatalwa ce dan bai tab'a tunanin yana da rai ba ga shekarun da ya d'auka bai dawo ba. Nan dai daya ta bata ba fatalwa bace yayi mugun mamaki sannan kuma bai yi fushi da shi ba don ya nason ya hujarshi haka kuwa akayi ya kwashe komi da ya fad'awa su Arahamat ya gayawa Abbu a take yayi samasa albarka tare dacewa "Gaskiya shawara da abokinka ya baka tayi sabida da ka dawo mani gidan ba sakamako mai kyau da ba zanji dad'in ba tunda banida wani buri kamar naga kunyi karatu mai zurfi ku duka. Haka ma ya isa mugode wa Allah tunda lafiyar ka lau ba abinda ya sameka Allah maka albarka. Sannan a kaci gaba da fira ana wasa da dariya har dare yayi sosai kowa yaje ya kwanta da niyar tafiya Niamey sayayya gobe in Allah ya so ya yarda. Shima sadisu angon Arahamat ba k'aramin dad'i yaji ba lokacin da labarin zuwan yayan amarya sa ya zo kunan saba sabida kusan kulum idan yazo zance sai ta masa fira yayan ta itadai yayan ta har zowa yayi ganin sa kuma suka dad'e suna fira karmar sun san dad'e dasani juna. Ga goben suka shirya suka tafi Niamey sayayya hada Ufadi sayayya sukayi sosai sannan ana gobe d'aurin aure suka dawo aka ci gaba da shirin biki. Darzn ranar da suka dawo k'anwa Arahamat takira su tana kuka wai an samasu examen (exam) bazata sami zuwa ba dama tunda rana suke neman number basu samu ba. Badan Arahamat taji dad'i ba amma a haka ta hakura tunda tasan harakar karatu sai a hankali. Yau ya kama ranar d'aurin aure, k'arfe tara na safiyar asabar a ka d'aura auren Arahamat musa da Sadisu Asmane Sanga akan sadaki 50000 d'aurin aure kam ya tara mutane sosai sabida mahaifin Arahamat malami ne da kowa ya sanhi a cikin garin na Agadez ga mutunci da datako gashi kuma daga b'angaren ango ma dangin shi da dama sun halarci taron duk da nisan dake dakwai tsakani Niamey da Agadez, Alhamdulilah kuma aure ya d'auru. Arahamat najin an d'aura kuwa tayi ta kuka wanda kyar yaya Ibrahim ya shawo kanta tayi shiru. Kwana d'aya da d'aura auren suka bi jirgi sai Niamey sabida a can za'a kai amarya banyan nasiha da tasha wajan abu da yayanta da Tanti Fatima kuma da Ufadi sannan tanemi iyayen gafara Mahaifin Arahamat hada kuka yayi yana samata Albarka, haka dai aka tafi da ita tana kuka Yayan ta da mahaifin ta na tayata. Haka dai su Tanti Fatima da Ufadi suka tafi raka Arahamat Niamey gidan mijin ta.......... Sai muyi fatan Allah kaisu lafiya........... Na QUEEN ZEEFAT yar mutan Niger Muje zuwa..............💃💃💃💃💃 Alhamdulilah 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZANBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ECRITE: _PAR_ *QUEEN ZEEFAT* Yar Mutan Niger Wattpad@nazhabibou 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_ Page 10 Yau kwana shida kenan da haduwar Arahamat da Sadisu, amma har yanzu bai sake dawowa ba duk tabi ta damu, haka yanzu ma tana cuisine (kitchen) tana aiki tunanin sa take, cikin zuciyar tace "To wai miyasa na damu da rishin zuwan sa ne? Duk Nabi nadamu" wani b'angare na zuciyar yace sabida sauran kud'in sa dake wajan ki ne, da sauri ta furta "Hakane allah sa dai yazo ya karb'i kud'in sa kar ya barni dasu in shiga uku gashi kuma ni ban san idan zan gansa ba bare na kaima sa." Da dadare banya sallar isha'i wani yaro ya shigo gidan su Arahamat yace "wai ana kiran wata yarinya buzuwa doguwa waje." Ufadi dake zaune tsakar gida da tace "Wake kiranta." Yaron yace "wani a waje." Ufadi tace "Je kace tana zuwa". Yaron ya juya ya fita Arahamat dake cikin daki tunda taji yaron da ya shigo yace ana neman wata buzuwa doguwa gaban ta ya yanke ya fad'i ta san da itace ake nema "To amma waye? itadai tasan ba mai zuwa wajan zance kuma ita ba wanda ta tab'a nunawa gidan su to yanzu waye ke nemanta? Bata k'arasa tunanin da take ba tajiyo muryar Ufadi na cewa "Ke Arahamat taso ki fito ana neman ki a k'ofar gida yau dai kin sami meso da kulun kina cikin gida har kin kai girma na gida idan aka shigo ba mai gane tsakanin ni dake wacece uwar wace d'iyar, mutana ta guga kafad'a kizo kin tile a gida ba mai sonki, yarinya sai bak'in jini mtssss." Fitowa tayi daga d'akin tace "Ufadi Abbu fah?" "Mtsss yana cikin d'akin shi munafuka zakije kiyo masa gulma ko?" Ita dai ba tace mata komai ba ta nufi d'akin mahaifin ta samun shi tayi yana zaune da alkur'ani a gaban sa da alama karatu ya gama ta d'an rusna tace "Abbu ana nema na a waje." Ba tare da ya dago ya kale ta ba yace "Waye?" "Nima ban sani ba Abbu." "To jeki amma kada ki dad'e kuma ki kula da mutuncinki." Ta amsa da "To" sannan ta tashi tafita bata tsaya bin ta kan Ufadi dake ta yada mata magana da jefa mata harara ba directe (direct) waje ta wuce. Dayake da duhu a wajan sai haskin farin wata yasa tayita dubawa bata ga kowa ba, tana shirin juyawa ta koma taji ance "Sannun ki malama." Da sauri ta waigo gun da taji sautin maganar ya fito, bata dai gane kowaye ba kawai sai ta k'ara matsawa kusan shi, aiko ta ganeshi tace "Lah kaine?" "Eh nine ashe kin gane ni?" "Haba ba dole na ganeka ba tunda sauran kud'in ka na guna, ai se in ka karb'e su kawai zan manta a lokacin nasan ba ha'kin kowa a kaina." Waro ido yayi waje yace "Lah ashe ma zaki manta dani daga zarar na karbi kud'i na ko? Ko irin wanan d'an zumuncin ba za muyi ba dan mu ringa kaisawa." Tace "A'a bahaka nake nufi ba idan dai mun had'u a hanya ai zamu gaisa." "A'a gashinan kin fad'a da bakin ki cewa da zarar na karbi kud'in na zaki manta da ni." "Oh Allah ba haka nake nufinufi ba ai d'an halak bai manta alkairi kaga kenan idan na manta ka ai na manta da aikairin da kamin, kuma nazama butulu kenan fah!! Kaga ko gaisawa ma bamuyi ba, ina yuni ka yuni lafiya?" "Lafiya lau alhamdulilah da fatan kina lafiya, ya kwana biyu." "Lafiya lau nake, kwana biyu sai alkairi bari nashi na karb'o ma kud'in ka Abbu ya ce kana dad'e." "Abbu na ciki ne? "Eh yana ciki." "Shine kuma baza ki man tayin naje na gaidashi ba ko dai rowar baban zaki min?" "Ko d'aya wallahi manta wa nayi shima Abbu d'in yace idan ka dawo karb'a cikon ka nace ya neman ka manta wa nayi." "Woow!!! Har kin ba Abbu labarina ashe kema kina ciki?" "Ina ciki kamar ya?" "Share kawai, ko baki ciki to ni nagani kuma na k'aisa yi sauri kije ki sanarwa da Abbu zuwana." Arahamat da ta kasa gane inda kalaman sa suka dosa kawai sai tasa kai ta nufi cikin gida ta nazuwa ta sanarwa Abbu cewa wanda ya taimaka mata da kud'in ne lokacin da a ka sabce nata ne ya zo. Abbu yace taje ta shigo dashi. Komawa tayi ta gaya ma sa sok'on Abbu kannan suka dawo tare, da sallama ya shigo gidan, aka amsa masa lokacin Abbu na tsakar gida tare da uwar gida Ufadi sunna d'an tab'a fira k'asa k'asa duk yawan maganar Ufadi k'orafi yafi yawa. Haka dai ya shigo ya samesu kansa duke durk'usawa yayi ya gaida amsawa sukayi cikin sakin fuska, Abbu yace "Bismillah yaro ga guri zauna" tare da nuna masa tabarmar da yasa Arahamat ta shinfid'a tashi yayi daga tsugun nin da yayi koma kan tabarmar ya zauna kansa na kollon k'asa ita kuwa Arahamat tana kawo tabarmar ta shigewar ta d'aki. Gyaran murya Abbu yayi sannan yace "Yaro mi sunnan ka?" Ba tare da ya d'ago ba yace "Sadisu?" "Masha Allah Sadisu kana lafiya?" "Lafiya lau." "To madalah Arahamat ta zo da kud'in ranar nan tace kaine kabata wane dalili ne yasa kaba ta alhalin baka santa ba kuma tana yiwu ma baka tab'a ganin taba?" "Eh wallahi nine naba ta sanadin ganin ta da nayi tana kuka sosai a hanya a lokacin gaskiya tausayi ta bani shiyasa natsaya na tambaye ta miya faru tace kud'in ta aka sabce kuma idan ta dawo gida tace sun b'ata f'ada za'a mata shiyasa sai na taimaka na bata kud'in to har neman canjin tayi da bata samu ba ta bar kud'in idan aka aike ta, kuma saida nayi nayi da itama ta rike sauran canji ta ki shiyasa nace ta nuna min gidan idan ta karb'o saura kud'in sai nazo na karb'a, amma baba a zahirin gaskiya yanzu ba karb'a kud'in nazo b........... Bai k'arasa zancan ba Ufadi ta katse shi da cewa "Ji min munafinkin yaro to mika zoyi in ba karb'a kud'in ka ba, ko ka zo ne ka k'arasa lalata ta a cikin gidan uban ta kai malalaci wai wane taimakon kayi? ka b'ata yarinya yanzu wake taimako dan Allah ai sai dai bani in baka, ka lalata yarinya ka bata kud'i muku ma kace mana wai gani kayi tana kuka dan k'arya, ni dama tunda na ganka nasan ba d'an kirki bane diboka kayi kama da malal............ Bata k'arasa fad'in abinda zata fad'a ba a tsawa ce Abbu yace " Yiman shiru Ufadi wa yasaka ki acikin maganar nan ko kinji an kira sunan ki ne a cikin zancan nan ne." "Ah to malam ga gaskiya sai naki fad'a dan dai ba'ajin tsoron Allah." "Wallahi idan baki min shiru a nan ba ranki sai yayi mumunan b'aci manzon tsira SAW yana cewa fal yak'ul khairan aw liyasmut, to idan kisan ba alkairi zaki fad'a ba ki tashi ki bar min nan tunda dama ba gayato ki nayi ba, ko kunya ta bakiji a gabana kina ai batamin yarinya to nagaji dajin irin wad'an nan munanan kalaman naki kan y'ata kinan zargin ta akan abinda ke da kanki kin san ba gaskiya bane, ban san mi tayi maki ba kike mata haka." Abbu ya k'arasa maganar ransa a matuk'ar b'ace sumi sumi Ufadi tata shi tana cewa "Ga gaskiya sai a hanani fad'ar ta" tashige d'akinta da sauri sabida tasan da Abbu ya zafi ba wasa. Tana shiga d'akin kuma sai tace "Miyasa ma nake aibata yarinya can gaban yaron nan idan fa auren ta yakeson yi shikenan na b'ata auren, gaskiya da sake idan auren ta yazo nema kam zan san yanda zanyi na gyara maganar inaaaaaa mijin auren da nadad'e inason ta samu don taje ta bar min gidan in huta da jaraba kuma da rikon d'an da ba nawa ba, ai da sake koda ba neman auren ta ya zoba zan shiga in fita sai ya aureta tunda dai har ya kawo kansa gidan nan tun yaushe nake fatan Allah ya kawo man mafita na jefar da d'an mangoro in huta da k'uda ko kad'an banison ganin yarinyar nan a cikin gidan nan wallahi dole ma tayi aure ta bar min gida duk da cewa gidan ubanta ne amma yazama dole ta bar shi." Ufadi ce ke ta wanan maganganu ita d'aya a d'aki." B'angaren Abbu kuma Ufadi na tashi ya juyo kan Sadisu yace "To yaro bismillah ina jikan da mikazo dashi baya ga karb'ar sauran cikon kud'in ka." Sai da ya d'an nisa tare da girgiza kai idonsa na kallon k'asa sannan yace "A gaskiya baba tun ranar da naga Arahamat ta kwanta min inason ta so kuma na aure ba na yaudara ba kuma ni ba malalaci ba ne baba idan kanaso ma kasa a yima bincike a kaina." "To Alhamdulilah nayi farin cikin jin haka daga bakin ka dan daga nin kai yaron kirki ne, amma wanni hanzari ba gudu ba ni da na tambayi Arahamat ce man tayi babu komi a tsakani ku gashi kai kazomin da wani zance ya haka?" "Et baba gaskiya ban fad'a mata cewa inason ta ba shiyasa kuma abinda yasa nayi haka dan kar tayi tunani sabida na taimaka mata ne yasa nace inason ta ko kuma ta fassara zancan da wata manufa, shiyasa na zabi har sai nazo maka da zancan tunkun na dalilin da yasa na mata wayo kan cewa ta nuna min gida su idan sai nazo na karb'i sauran canjin, a zahirin gaskiya ba karb'ar kud'in nazo ba ganika na kuma na fad'a maka manufata a kanta tunda nidai tun ranar dana bata kud'in nan manta dasu sabida ni gabad'aya na bata ba wai don ta mayar min da canji bane, dan Allah baba ina neman alfarma da a taimaka a bani auren Arahamat." Sadisu ya fad'a ba tare da ya d'ago da kansa ba. Wani farin ciki ne ya mamaye Abbu sabida Allah kad'ai yasan yanda yake fatan Allah ya kawowa Arahamat miji na gari tayi aure ko dan ta futa da uk'uba Ufadi gashi da gani alamu wanan yaron mutuman kirki ne, sai dai Abbu bai nuna tsanani farin cikin da yake cikin sabida ma ka Sadisu yayi tunani ko an gaji da zaman ta a gidan ne alhali ba haka bane. Abbu ya fad'ad'a murmushin yace "Gaskiya nayi farin ciki sosai da jin haka, amma miye sunan ka kai d'an waye kuma ina ne gidan ku a gari nan miye kuma sana'ar ka? kasan Yanada kyau nasan asalinka da halinka da abubuwan da baza'a rasaba na rayuwa tunda zancan aure fah babban abune ko ba gaskiya ba?" "D'an murmushi yayi har kansa na duk'e yace "Hakane baba, da farko dai ni sunana Sadisu Asmane Sanga mahaifina cikaken d'an asalin garin Mali ne can ne garin su na iyaye da kakani dagin sa duka suna can, nima can aka haifeni ni da dangina baki d'aya mahaifiyata cikaka 'yar Niger ce haifafa garin zinder, yanzu ma a cikin garin Niamey muke da zama sakamakon rasuwar mahaifina muka tataro muka baro Mali kuma muka dawo Niger inada yaye mata biyu da namiji guda nine k'arami a cikin kuma nine banyi aure ba, kuma karatu ne ya kawo ni cikin garin amma nan da wata biyu zan k'arasa na koma garin mu, sanan kamin na baro gida ina d'an tab'a kasuwanci idan na koma gida kuma da k'asuwancin zanci gaba." "Masha Allah Sadisu naji tak'aitacan labarin ka, da alamu bakayi kama da mutuman banza ba dan haka indai ni ke bada auren Arahamat to nabaka ita duniya da lahira kuma abisa amana kaga dai ita marainiya ce kada ka cutar da ita sabida amana na baka ita idan kaci amana ta Allah zai saka mata ko dan maraicin ta, kuma itama buzuwace gaba da baya kamar yanda ka lura mahaifiyar ta rasu wajan haihuwa k'anwata, kuma su uku ne ga mahaifiyar su har nima sune k'adai gare ni duk fad'i duniyar nan banida kamar su sedai shi baban wan nasu tunda gomnati ya turasa karatu a Canada har inda yau ke kwana ban gara sashi a idona ba yau kimanin shekara hud'u kenan, yana raye ko ya koma ka mahalicin shi Allah kad'e yasani ita kuma k'anwartata tana Arlit gun yar uwar mahaifiyar su, sedai wani hanzari ba gudu ba, kaje kasami ita Arahamat d'in kanemi soyayar idan ta amince da haka taji tana sonka alhamdulilah idan kuma bata amince sedai kayi hakuri sabida bazan mata doli ba duk abinda takeso to nima shi nakeso." Wani sihirtacen murmushi Sadisu ya saki sannan yace "Alhamdulilah baba nagode da karamci da kauna da aka nuna min nayi farin ciki mara misiltuwa baba Allah kara lafiya da nisan kwana kuma insha Allah za'a ga wan su da ikon Allah ya na a raye bai mutu ba da yarda ubangiji, in Allah yaso ya yarda idan har Arahamat ta amince da aure na baza ka taba nadamar bani ita da kayi ba da ikon Allah." Seda ya kara sunne kai san yace "Baba idan son samu ne ina neman alfarma har in ta amince nan da wata biyu a d'aura mana aure kamin na koma sai mu koma tare da ita sabida yanzu ina fita daga nan zan kira mahaifiya ta na sanar mata insha Allah." Abbu yace "To Sadisu wata biyu baiyi kusa?" Seda ya d'an sosa kai sannan yace "A'a baba." Murmushi Abbu ya saki ciki zuciyar shi yace "Yaran zamani" a zahiri kuma sai yace "To karka damu kai dai kaje ka nemi soyayar ta in ta amince shikenan sabida ni najima ina shirya ma auren yarinyar nan da k'anwata." Sun d'an jima suna tataunawa kamin daga bisani yayi wa Abbu sallama ya fita. Yana fita Abbu ya k'wala mata kira a firgice ta farka sabida har bacci ya fara d'ibarta kawai sab'o hijab tayi ta fito taje gun Abbu ta durk'usa yace "Tashi je kiyi masa sallama tafiya zaiyi." Da sauri ta d'ago ta kalli mahaifin nata tace "wa?" don ita har ga Allah ta manta da wani yazo gidan. Abbu yace "Wa kuma? Sadisu mutuman daya taimaka miki ranar nan yana can waje yana jira." "Oh wallahi Abbu har na manta da yazo gidan nan ni harma na fara bacci, kenan sad.... Bata k'arasa fad'in sunan ba sanadi nuhi fad'i da taji ya mata a baki sanan tace "Kenan Hakane sunan shi bari naje muyi sallama" haka ta fad'a tare da fita daga gidan. Abbu yayi murmushi tare tashi ya shiga d'aki. Tana fita ta tardo shi baki k'ofar gidan yana jiranta tace "Har zaka tafi?" "Hum wai har zaka tafi?" yayin yanda tayi sannan yace "Bayan nakusa kwana a gidan ku sabida ke." "Kwana a gidan mu kuma ka rufa man asiri nidai." "To baki son na kwana a gidan kune? ni ina cewa yanzu mun zama 'yan uwa zan bar kwana a cikin makaranta na dawo da kayana gidan ku a sama min gun bacci? amma shine zakimin rowa." Waro ido tayi da sauri tare da cewa " Yo zaka iya?" "Yo mi zai hana?" "To shikenan zan gayawa Abbu sannan." Dariya yayi sannan yace "Kewa wasa nake maki." Murmushi tayi tare da sun ne kai gyara tsayiwa yayi sannan ya kira sunan ta "Arahamat." Amsawa tayi da "Na'am." Yace "Ki nutsu ki bani hankalin ki nan zamuyi wata magana." A sanyaye tace "To ina jinka." Seda ya k'ara gyara tsayiwa sannan yace "Zaki aure ni?" Kamar saukar aradu taji maganar da sauri ta d'ago ta dubeshi tare da yin sauri maida kanta k'asa wai itace yau wani ke furtama wanan kalmar da ba wanda ya tab'a mata ita shin mafarki take ko a farke take? da alama ba bacci take ba da gaske ne." "Yanaji kinyi shiru ko baki ji mi nace ba ko baki fahimci mi nake nufi ba? In hakane bari na miki yanda zaki gane, Arahamat inason ki ina kaunarki fiye da yanda kike tunani sonki ya ratsa ko ina na jikina, shin zaki aureni?" Da sauri tasaka hannu ta rufe mashi baki a lokaci guda kuma ruga da gudu cikin gida sabida jin kalaman sa take kamar ana mata ihu cikin kunne. Amma ba karamin farin ciki tayi dajinsu ba. Yau sati biyu kenan da Sadisu ya baya nawa Arahamat abinda ke cin zuciyarsa kuma ta amince shakuwa da soyaya mai k'arfi ta shiga tsakanisu Sadisu kuwa har ya shedawa mahaifiyar sa kuwa tayi na'am da zancan yawaci ma idan yaje zance yana kiran Hajia Zakiya ya bata su gaisa da Arahamat wada tun tanaji kunya har yakai ta saki jiki suna fira sosai dan hajia Zakiya tace ita ba surukar ta bace kamar 'ya haka ta ke gunta, kuma hajiya zakiya ta shedawa yaronta ta cewa nan da sati biyu za'a zo kawo komi da komi na aure harda lefe, shima kuma har ya shedawa iyayen Arahamat. B'angaren Ufadi kuwa ta rage tsangwamar da take yiwa Arahamat sanadin aure da zatayi taje ta bar mata gida. Yau ta kama lahadi kuma yau ne ranar da za'a kai lefe shalele kuma auta a gun hajiya zakiya tunji jiya alhaji suley da wasu abukan sa biyu sukazo da komi da komi da za'a bukata. Haka yau ma suka d'auki niki niki kayan lefan sukai gidan su Arahamat ida a ka kashe kud'ad'e sosai sabida auren buzuwa fah sai mutum ya shiyar dole sai kasaka g'wala g'walai kuma ka siye rak'uma anyi bajin ta masha kuma ankashi kud'i akasa aure nan da wata guda. Kawanci tashi ba yuya a wajan ubangiji yau ya kama saura sati biyu auren Arahamat da Sadisu, yau ne kuma tanti Fatima k'anwar mahaifiyar su tazo gidan gani tayasa Arahamat cikin farin ciki da anashuwa amma da taga ba da k'anwar a ka zoba sai murna ta koma ciki tace "Tanti où est ma petie soeur (where is my lil Sister)." D'an murmushi Tanti tayi tace " kwantar da hankalin sai saura kwana uku zata zo sabida école (school) sai a sannan ne ta saki ranta nanfa tanti Fatima tashiga gyaran amarya. Yau ya kama saura sati d'aya d'aurin aure Arahamat na zaune tsakar gida tana alwala taji anyi sallama da sauri kuma a firgice ta mik'e don jin murya da ko ta mutu bata zata iya mantawa da ita ba tsurawa k'ofar shigo wa gidan tayi tana adu'a Allah sa abinda take tunani ya zama gaskiya aiko wanda yayi sallama na shigo wa ta saki wata irin razananiya k'ara mai sauti sai wani tippppppp kake ji ta fad'i k'asa somamiya.......... To masu karatu mai ya tsoratar da Arahamat da yasa ta fasa ihu, sallamar wa taji ta firgice, wane abu ta gani har yasa ta suma? Ku biyoni a next page don samin amsar wa'inan tambayoyin???? Amma sai kuyi comments kuma next page sosai zata k'ayatar daku. In bakuyi comments ba ba zanyi next page d'in ba. Ina jiran comments d'inku💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZANBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ECRITE: 📝📝📝 _PAR_ *QUEEN ZEEFAT* Yar Mutan Niger Wattpad@nazhabibou 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ Hh https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_ ~Masoyan wannan novel nasan kuna hakuri sosai akan d'aukar lokaci da nake banyi typing ba, to ina mai baku k'ara baku hakuri wallahi karatu ne yaman yawa, nima ba da son raina hakan ke faruwa love you more my FANS....😍😍😍😍~ Page : 13 & 14 Lafiya lau suka sauka cikin garin Niamey direct gidan hajiya Zakiya aka nufa dasu suna zuwa ta k'arb'esu hannu bibiyu da fara'a a fuskar ta ta masu tarba ta mutunci a falon ta suka sauka aka kai masu kayan su a cikin d'aki da zasu zauna, amma kayan Arahamat a d'akin hajiya Zakiya aka kai mata su cikin k'ank'anan lokaci aka cika gaban su da kayan ciye ciye da lashe lashe, tanti Fatima da Ufadi sunci sun sha amma banda Arahamat dake rakub'e yuri guda ta k'asa koda d'aga kanta har saida Hajiya Zakiya ta fito daga d'aki kamin tajata suka nufi d'akin ta sannan lalab'ata ta ci abincin tana gamawa tasa tayi wanka da sallah sannan hajiya Zakiya tasaka ta d'ane gado ta kwanta bata dad'e da kwanta wa ba bacci ya kwashe ta. Sukuwa su Tanti Fatima na d'akin da aka tana domin su suma sunyi wanka tare dayin sallah suka kwanta don hutawa. Arahamat ba itace tashi ba sai da ana kiran sallah magariba sannan hajiya Zakiya ta shigo d'akin ta tayar da ita. Koma yin wanka tayi sannan ta d'auro alwala magariba tazo tayi sallah, tana gama hajiya Zakiya ta shigo mata da abinci ta d'an ci kad'an sannan aka shirya don kaita gidan ta dake cikin gidan hajiya Zakiya. Ana gama shirya ta su Tanti suka nufi d'akin hajiya Zakiya suka tardo ta zaune bakin gado tasha ado tayi kyau sosai kamar balarabiya suma zaunawa suka, suka soma mata nasiha mai ratsa jiki tanata kuka, haka hajiya Zakiya ta shigo ta iskosu tace "Dan Allah ku barta haka zaku saka kwalliyar da aka mata ta goge daga ganin d'iyata ba mai kwaramniya bace nasan zata zauna lafiya da mijinta insha Allah, gashi tun kamin kuzo nan nasan kunyi mata nasihar kuma ta d'auka, gaskiya ku barta haka kuma insha Allah Arahamat ba zata maraici a gidan nan ba da yarda Allah, ni d'iyace kuka kawo min ba suruka ba don haka ku kwantar da hankalin ku, kuma ke Arahamat ki d'auke ni a matsayin mahaifiyar ki inason duk abinda Sadisu ya maki na k'untatawa ki fad'a min kiga hukuncin da zan yanke a kansa wallahi ko da kuwa kece mai laifin idan har ya nemi takura ki zo ki sameni ki sanar dani zaki sha mamaki insha taron dangi zamu masa" Hajiya Zakiya ta fad'i haka tana dariya. Tanti tayi saurin cewa a'a zaluntar yaron albarkar nan zakuyi kenan to wallahi baku isaba zan kirasa na fad'a masa daga Arahamat tayi masa laifi ya hukunta ta sannan ya kirani ya sanar dani don wallahi mota zan tako daga Arlit har Niamey nazo nayi maganin ta sabida bani goyon rashin kunya da zata masa, sannan kuma ace shine mai laifi ko alama ki dai ji abinda na fad'a kuma kinfi kowa sanin zan iya aikata wa da haka kada ma ku taru kumasa taron dangi nima shigar masa zanyi ehe ga kuma Ufadi nasan itama tana bayana ah to." "Ah wallahi ina bayan ki ai tare zamu biyu mota muzo hukunta ta ai tafi kowa sanin halina sedai ta ba wani labari ehe" haka Ufadi ta fad'a tana dariya. Hajiya Zakiya ta yi dariya sosai, sannan tace "Kam ashe dai da kunga irin namu taron dangi sabida ko banza muda kenan mun fiku yawa, kuma kamin kuzo mu mun riga da mun gama namu hukuncin, sannan zanga wanda ya isa ya shigo gidan mu yace zai hukunta min yarinya wallahi da zaku sha mamakina." Haka dai suka yita raha suna dariya har Arahamat ta daina kuka ta koma murmushi, daga dai bisani suka jata suka nufi da ita b'angaren dake nesa sosai dana hajiya Zakiya suka ce ta shiga da bismillah sannan da k'afar dama haka kuwa tayi, tubarukallah yayanta ba k'aramin kud'in ya kashe ba wajan zuba mata kayan d'akin ba, ba wani jimawa sukayi ba suka koma b'angaren hajiya Zakiya suka barta ita d'aya, tana nan zaune idan suka barta har Sadisu ya shigo d'akin da sallama cike da farin ciki ya nufe ta tare da cewa "Alhamdulilah yau Allah ya nuna min ranar nan da bazan tab'a mancewa ba haka dai ya sata ta shiga douche tayi wanka tare da d'auro alwala suka zo sukayi sallah ta neman albarka aure sannan ya bud'e ya d'auko plet ya zuba masu kazar da ya shigo masu da ita ta amarci kad'an Arahamat taci shima dan ya takura ne da suka gama ya tatara kyan dasuka b'ata ya mayar cuisine (kitchen) yana fita ta koma douche (toilet) ta k'ara wanko baki tafito Sannan sukayi shirin bacci suka kwanta aranar dai sai Sadisu ya mayar da ita cikakiyar mace yana ta sa mata albarka ita kuwa sai kuka take. Kwonci tashi babu wuya a wajan ubangiji gashi yanzu shekara guda kenan da wata shida da auren Arahamat da Sadisu har Allah ya basu k'aruwa ta d'an namiji wanda yaci sunan mahaifin Sadisu wato Asmane suna kiransa da Kalifa yaron ya taso cikin gata da soyayya tare da kulawar iyayensa da ma ta dangi gabad'aya. Kalifa nada shekara uku da haihuwa ya kamu da rashin lafiya mai tsananin wada tayi sanadiyar tafiya da rayuwar sa, rasuwar Kalifa tayi matuk'ar girgiza wannan famille (family) ba kad'an ba, ba ma kamar Arahamat da seda aka had'a da adu'a kamin take dawowa hayacin ta. Haka suka ci gaba da rayuwarsu cikin farin ciki da kaunar juna Sadisu na kasuwancin sa tsakanin Marad'i da Niamey sannan yana fita kasashan waje siyar kanyan sai dawarsa har lokacin da kasuwancin sa gabad'aya ya koma Marad'i, haka shima ya tatara iyalensa tare da mahaifiyar sa suka koma Marad'i da zama baki d'aya suka bar Adamu da iyalensa Niamey lokacin Adamu matansa biyu da 'ya'ya hud'u. Kasuwancin Sadisu sai bunkasa yake yanzu yayi arziki sosai ba kad'an ba yayi fice babu wanda baisansa ba cikin garin Marad'i da kewayen ta kowa yasan alhaji Sadisu mai sayar da kayan gini a cikin farashi mai sauki harda sauran jahuhi na karsar Niger zuwa ake sayan kayan gini a shagugu kansa dake cikin Marad'i da Niamey yanzu kam ya zama millioniya Sadisu nada wani aboki wanda suka tashi tare tun lokacin da suka baro Mali suka dawo Niamey me suna sumana tare sukayi collège wato(secandiri school) har sukaje universsité tare inda Sadisu yayi karatu afanin kasuwancin shikuwa sumana ya karanta ingenier suna da shekara biyu a makarantar Agadez baban sumana ya mayar da sumana karatu a France inda can ya k'arasa nashi karatun shima kuma yayi aure yama riga Sadisu da wata biyar sannan akayi na Sadisu har yanzu amintarsu nanan sai ma k'ara k'aruwa take yanzu haka shike kula da da kampanonin Sadisu dake Niamey sannan shike sanar da Sadisu abubuwan da yaka mata ya siya don azuba a kampani sabida shi aikin gini yake, sumana ingenier ne shi. Banyan rasuwar d'an Arahamat da shekara biyu Allah ya koma ba wata haihuwar ta d'iya mace wada aka saka ma Fauziya shekara Fauziya biyu da watani aka haifi khairat, khairat nada shekara hud'u aka haifi AFREEN wada saida ta sha wuya wajan haihuwar ta alhalin sauran a sauk'ak'e haihuwar ta zo mata, kamin a yaye AFREEN Sadisu ya zuba masu haji suka tafi shida Arahamat da hajiya Zakiya da Fauziya wada a lokacin shekara takwas da haihuwa. Bayan wasu shekara hud'u Arahamat ta sami wani cikin ta haihi d'an namiji inda ya ci sunan Fahad, Fahad nada shekara d'aya Sadisu ya auri Salamatou (umma) wada irin fulanin nanne masu sayar da hura a hanya kuma ta nan suka gamu da Sadisu sedai fitinaniya masifafiya ce tashin hankali ba irin wanda bata iya ba, ga kishi da rashin ilimi batada tunani ko kad'an sabida muguwa jahilace batada ilimi ko misk'ala zaratan itadai tashin hakali kad'ai ta iya bata buk'atar ganin mutun cikin farin ciki batayi sanadiya b'ata masa rai ba tun Arahamat bata gano halinta ba hata gane ta ta daina biyemata dama ita ba mai son tashin hanli bace. Salamatou nada 'ya'ya biyu Zeinab da Safina, Allah ya koma bata Arahamat ciki wanda hata fida rai da samunshi sabida Fahad shekara sa shida da haihuwa sannan aka sami k'anan sa imran, itama Salamatou ta koma haihuwa ta sami Amira. Sannan Sadisu ya k'ara aure, ya auri Sakina(Tanti) itama ya san tane ta dalilin zaman majalisa da suke a k'ofar gidan su Sakina wasu nacewa asiri ne suka mashi sabida tarasa mujin aure ta lak'e masa gashi har yayata da k'anwarta suna gida basu yi aure ba kuma saida takai shekara 37 sannan ta samin auren Sadisu sannan ta taushe kunan ta da maganar yan anguwa tayi aurenta ita kuwa mahaifin ta marok'ine (ma'ana irin masu gid'a ganga da kirarin nan ne idan za'ayi aure ko suna). Saida Sakina tayi shekara bakwai a gidan Sadisu sannan ta sami haihuwa, inda ta haifi Hamida to itama tun daga shi haihuwar ta tsaya... Arahamat na d'a biyar: Fauziya tayi aure kuma da d'an ta guda me suna humaid sai khairat da AFREEN sannan Fahad sai auta imran, ita kuma Salamatou da 'ya'ya uku: Zeinab, safina da Amira ita kuwa sakina da d'iya guda wato Hamida wada a halin yanzu shekara shida ke gareta. AFREEN Allah yayita da rashin son kwaramniya ga rashin magana don idan ba niya tayi ba tana iya yini batayi magana ba banyan ta gaida iyayenta da safe to bazaka karaji maganar taba sai in taso ga ilimi da Allah ya mata na école (school) da na islamiya sabida da shekara 12 aka mata sauka alkur'ani, nan da 'yan watani kuma za'a mata ta harda izo sitin, a école kulum ta farko take zowa AFREEN ga kyau kamar ita tayi kanta ga tsari uwa uba nitsuwa da kamala, hausa sun ce d'an adama tara yake bai cika goma ba dana ce ita AFREEN komi ma ta had'a da zance ita goman ce daidai. Kuma Abin birgewa a gidan su AFREEN shine duk yaran gidan suna da ilimi amma basu kai ga AFREEN ba ita duk ta fisu sedai karamin k'aninta imran ita ya d'ebo wajan ilimi gashi ma har yana son ya fita sabida shima tun yana shekara goma aka masa sauka alkur'ani mai girma kuma ilimin dage garesu duk gadon sa sukayi wajan mahaifin wato Sadisu dan ba k'aramin ilimi ne da shi ba don gaskiya Allah ya bashi sai kuma su AFREEN wanda gadon ilimin sai yazo masu ta hanya biyu wajan mahaifin da mahaifiyar su don itama Arahamat ba bayaba yajan ilimi duk suma na mahaifin suka gado. Ibrahim yayan Arahamat yayi aure hada d'iyansa uku kuma ya koma Canada zama sanadin zuwan mai gidan sa daga Canada har Agadez nema sa alfarma ya zo yaci gaba da masa aiki har ta dalilin zuwan mai gidan nasa Niger shi mai gidan nasa ya musulunta ganin haka yasa mahaifin su Arahamat ya yarda ya koma garin na Canada ya ci gaba da aikin sa kuma ya tafi tare da iyalensa, amma duk k'arshen shekara yana zuwa ganin gida shida familyn sa gabad'aya. Jannah kuwa k'anwar Arahamat itama tayi aure idan ta auri wani hamshakin mai kud'i suna can suna rayuwar su a London Haka dai rayuwa tayita ci gaba da kasan cewa har kawo yanzu............ Cigaban labarin............ Sai mun had'u a next page💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 Taku har kulum mai kaunarku❤️ "QUEEN ZEEFAT"📝📝 ✍ ina yinku irin sosai d'in nan🥰🥰🥰🥰🥰 Alhamdulilah.... Sai mun had'u a next page nan bada jimawa ba insha Allah💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZANBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ECRITE: 📝📝📝 _PAR_ *QUEEN ZEEFAT* Yar Mutan Niger Wattpad@nazhabibou 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_ Page: 15 & 16 Cigaban Labarin..... AFREEN ce zaune saman kan darduma a d'akin ta da alama sallah ta k'arasa alkur'ani na a gaban ta, ta na karan tawa cikin sanyayar muryata mai zak'i da dad'in sauraro, bud'e k'ofar d'akin nata akayi Khairat ce ta shigo tare da isa bakin gado ta zauna tana sauraran dad'ad'a kira'a dake fitowa daga bakin k'anwartata. Saida AFREEN takai karshan surar ta alkaf da take karan tawa sannan ta d'ago ta kali Khairat dake kallon yanda take karatun ta cikin nutsuwa da kamala tace "Anti Khairat ina kwana kin tashi lafiya???" "Lafiya lau AFREEN da fatan kema kin tashi lafiya, gaskiya yada kike karatu yana matuk'ar birgeni dubi yanda karatun ki ke fita da kyau duk wani harfi kina basa hakinsa sabida nutsuwar da kikasa a cikin kuma da mahinmancin da kika basa ga k'ira'ar mai d'adin sauraro Allah dai miki albarka Allah d'aukakaki Allah sa kifi haka kuma sa kiyi anfani dashi ameen ya Allah baki miji na gari wanda zai kula dake da k'arfafaki a kan adiniki fiye da yanda kike 'yar k'anwata ina alfahari dake," Khairat ta fad'a tana me sanki murmushi. AFREEN ma murmushin ta mayar mata sannan tace "Ameen, Lafiya lau na tashi anti amma ai duk karatuna ban kaiki ba anti kinfini fitar da hakin ko wane harfi inda ko aka zo kan k'ira'a ban ma kamoki ba, amma a hakama ba karamin godiya nikema Allah da ya lafiyar da nake samun damar karatun nan." "Kai kai AFREEN daina fad'ar haka ina ni, ina ke wallahi ke ta dabance 'yar uwa ina duk wanda ya sami wanan baiwar taki ya gama morewa a rayuwa haba ma soeur daina maida kanki baya kina had'a kanki da ni, regarde fah yanzu saukar tahafiz d'in alkur'ani za ayi maki da litatafai nan da 'yan watani, toh ni fah sauk'ar kallo kad'ai akamin amma duk da haka nagodewa Allah sabida nafi wasu sosai, ai ke AFREEN taki ta daban ce ba kowa ke samun irin takiba." Har AFREEN tabud'e baki zatayi magana, sai Khairat ta rigata dacewa "Kinajiko AFREEN zuwa nayi muyi wata shawara, tun jiya da dadare naso muyi maganar nan tunda inasa ran zakizo d'akina kina ki kwana sai najiki shiru har nayi bacci." "Eh wallahi karatu nayi har kwana ya kwashe ni a ida nayi karatun sai dana farka sallar dadare naga ashe saman darduma na kwana." "Ok to shawara nakeso kibani kinji k'anwata sabida wataran kin fini tunani da hagin nesa." "To Anti ina jinki Allah bani ikon baki ta k'aurai." "Ameen, AFREEN kinsan sati uku da suka wuce na tab'a ce maki nayi wani saurayi Abdul Majid ko?" Khairat ta tambayi AFREEN tare da kallon ta, kad'a kai AFREEN tayi alamar eh. Sannan Khairat ta ci gaba da cewa "To kinsan ban bari yazo gidan nan ba bare har yazo ya gaida papa sedai muyi waya da shi kuma kulum matsamin yake akan yanaso yazo ya ga gidamu sannan ya gaida papa da Maman, amma naki amince wa sabida ni idan yazo gidan nan basan ya zancewa papa ba alhalin yasan da zaman Ahmed to idan nace yazo ya gaida su papa, papa cemin zaiyi ko na b'ata da Ahmed ne yasa na kawo masa wani gashi kuma kowa yasan cewa Ahmed yazo yanemi aure na a wajan papa idan na kawo wani kuma za'ayi tunanin mun b'ata ne, gashi kuma shi Abdul Majid ya matsamin so yake yazo ya gaida su papa sannan idan papa ya yarde masa nan da sati biyu iyayensa zasu kawo kud'in aure, to ke Soeur ya kike ganin wanan lamarin zai kasance?" Saida AFREEN tayi gyaran muryan sannan tace "To Soeurette (yar uwata) yanzu wanan lamari gyaran shi yana wajan Allah kuma ya wajan ki kuma wanan matsalar kece kike da ikon magani ta ba kowa ba sabida ragamar lamarin nan tana hannu ki kuma ba wata matsala babba ce, mai saukin warwarewa ce amma idan kin so hankan ko ba gaskiya ba." Khairat tace "Ban gane mikike nufi ba iman da wara wara ko zan gane dalilin da yasa kika fad'i haka." "To sis abin dubawa anan shine shi dai Ahmed saurayin kine dan kukai kusan shekara uku kuna tare kowa yasan ku tare shi kuwa Abdul Majid duka ko wata bakuyi da had'uwa ba dubara ta rage taki ki fida wanda kikeso cikin su sannan kada ki manta da abinda papa zaice idan har kika k'ara kawo masa wani alhalin sun ajiye magana da iyayen Ahmed akan idan kika k'arasa makaranta zasu kawo kud'in auren da sa rana baki d'aya kinsan mi papa zaice? Girgiza kai Khairat tayi alamar a'a, "To cewa zaiyi baki isa kisa ka shi ma magana banza ba ko kuwa shi zaki kunyata ko ki maida shi k'aramin mutum sabida wanan lamari da kika d'auko har k'ananan mutanece, amma in tambayeki man shi baki son Ahmed kin ne har kike k'okarin kawo wa su papa wani?" A'a inason shi mana amma kuma nafara son Abdul majid shima." To ça veux dire que kina iya barin Ahmed ki koma ga abdul Majid tun da har kika fara tunanin kawo shi gun papa, to walahi anti idan baki cikin hankalin ki to tun wuri ki dawo hayacin ki anti Khairat sabida idan kika bar yaya Ahmed bazaki tab'a samun kamar shi ba sai wani ikon Allah bare idan cin amanar sa kika yi Allah zai kama ki walahi Anti yaya Ahmed mutun ne na gari ga addini da sanin yakamata dubi yanda yake girmama iyayenki kamar nasa walahi samin irin shi sai an tona bare yanzu da duniya ta lalace, banson kije kiyi abinda kuma daga baya zai ki koma dana sani dan haka kaki ma fara walahi," AFREEN ta fad'a tare da kallon 'yar uwartata. Kai sister walahi duk kin sarar min da gwiwa walahi amma duk da nace haka ba yana nufin zan daina kula Ahmed ba ne sabida inason sa har yau amma idan na bawa Abdul Majid damar yazo yaga su papa ba wani abu bane idan cikin su biyu wanda yariga kawo kud'in sa gidan mu sai ayi dashi, amma tunda kince haka gaskiya zan rabu da Abdul Majid dama ba wani son sa nake ba zan fad'a masa gida an riga da an min miji shikenan sai murabu lafiya sabida gaskiya nasan idan na auri wani wanda ba Ahmed zan iyasa shi cikin wani hali amma Ahmed shi ne ya dace dani ni da kaina na sani kuma ina nema zab'in Allah, bari na barki ki tashi kiyi shirin école (school) lokaci na tafiya ni ma dai ranar lundi (monday) zan koma ga karatuna yi maza ki shirya ki fito muyi kari," Khairat ce tayi wanan maganar tare da mikewa ta fita daga d'akin. Tana fita AFREEN ta tashi ta kintsa d'akin sannan ta shiga wanka a gagauce ta fito sabida ta lura da ta kusa yin retard (lati), tana fitowa ta shirya cikin wata had'ad'iya dokuwa riga bak'a batada kwaliyar komai amma ta had'u bare da tasaka ajikin ta sai ta k'ara fito da kyayon rigar masha Allah, sab'o zunbulelan hijab d'in tayi tasaka tare da rike nik'af a hannun ta ta saka takalmi mai dan tsini sannan ta fito tayi yanda ta saba saida ta nufi d'akin kowa ta gaida shi a d'akin tanti ne ta d'an jima sabida kulum idan ta shiga gaida ta to za bata wata zumuwa tasha sannan ta kad'a mata wani magani cikin madara ta bata, duk wanan abin da Tanti ke bawa AFREEN idan ta shiga d'akin ta AFREEN bata tab'a gayawa uwarta ko wani kuma bata tab'a tambaryar Tanti ko maganin miye take bata ba sai ita Tanti idan taji bata tambaye ta saitace "Wai AFREEN miyasa bazaki tambaye ko maganin miye nike baki ba, sedai da na baki sai ki karb'e ki shanye idan ma na cutarwane ke dai kin sha kenan nan ya cutar dake d'in babu ruwanki?" Sai AFREEN tace "Kai tanti ai nasan bazaki cutar dani ba miyasa kuma zan tambayeki? kamar dai ban yarda dake ba." Itama Tantin sai tace "A'a AFREEN yana dai kyau kisani sabida gudun zarki." Zarki kuma Tanti? Kamar dai bansan ki ba haba dan Allah ni walahi nayarda da ke d'ari bisa d'ari nasan bazaki cutar dani ba ni ko maman ban gayama bare har naji zargin a zuciya ta." "A'a aini dad'ewa na fad'a mata AFREEN sabida banson abinda zaije ya dawo ayi dibin cutar dake zanyi walahi nikuwa maganin bakine da na tsari nike baki sabida lura da nayi mutane na yawon samiki ido da nuna maki bakin ciki k'irik'iri ko bakin umma kad'ai ya isheki ga yanda take nuna maki k'iyayya k'irikiri ba'asan abinda mutun zai iyayi ba duniya ba gaskiya, Allah dai maki maganinta." AFREEN tace walahi ni tanti umma ko ganin ta banyi sabida nasan duk abinda take wata rana zata daina walahi ko kad'an ban rik'eta ba koda na minti d'aya ne bare har ya zama nasaka ta a zuciya ta kulum ina fatan Allah sa tagane, ko da kuwa ace ta tsaneni nasan da wata rana zata so ni kuma nasan da k'inane kawai take bata nufana da wani shari sai dai fatan Allah sa tagane." To ko yanzu da AFREEN ta shiga d'akin tantin haka ce ta faru suna ta irin wanan firar har lokacin da tanti ta jefoma AFREEN tambayar cewa "Wai AFREEN kulum kina min firarki ta makaranta ko kuma ta k'awayenki ko kuwa ta wani abu dai haka amma baki tab'a yimin firar saurayin ki ba ko miyasa ko baki son na sanshi ne na'aza mukai lokacin da ba zaki iya boyemin wani abuba ko dan nabaki shawara?" "Lah tanti walahi har kinsa ma naji kunya dama tanti har zakiyi tunanin akwai abinda nake boye maki wanda nake zaunawa muyi fira dake muyi shawara ko da Maman ba mayi haka, tanti nifa karatu nake yanzu samari basa gabana walahi babu wanda nake kulawa karatuna kawai nakeyi." "A'a AFREEN wajan karatu daban kuma yin saurayi daban to zaunawa zakiyi har sai kin gama karatu sannan ayi batun aure a'a to ko alama gaskiya ki daina saka wanan nik'af d'in sabida kowa da ya ganki sai yayi dubin matar aure ce gashi Allah yayi maki kyau amma kina boyeshi to gaskiya da sake ni surikina nakeson gani ah to." Da gudu AFREEN ta baro d'akin tana dariya tare da cewa "Walahi tanti kinsa na daina shigo d'akin nan naki." Wani irin murmushi tanti tayi tace "Hum zaki dawo ga hanya yarinya muje zuwa dai." AFREEN nafita daga d'akin tayi hanyar barin falon gaba d'aya sabida tayi lati bama zata iya tsaya wa yin kari ba ta nufin motar ta ta shiga ta kuna tare da barin gidan ta nufin makaranta. K'arfe shad'aya na rana AFREEN ta dawo daga makaranta, tana shiga falon gidan ba kowa a cikin direct d'akin ta nufa tare da rage kayan jikin ta shige toilet tayo wanka juma'a sannan ta fito k'ara shiryawa tayi cikin wata dogowar riga vert (green) mai ratsi jaune (yellow) ta saka hijab green da takalmi green sannan ta d'auki nik'af ta bar d'akin tare da shiga d'akin Khairat da sallama Khairat ta amsa mata sallamar sannan AFREEN tace "Anti kin shirya ne mu tafi masallaci kinga fah har 12:30 tayi sabida ke d'aya zan iya tsaya ma dan ko su zeinab idan basu shirya ba sedai su wuce tare da papa sai mu dawo tare gaskiya bana son k'arfe 1:00 tayi ban tafi masallaci ba." Al'ada gidan su AFREEN ce duk ranar juma'a 'yan gidan gabad'aya kan babba kan yaro mace da namiji har mai gadi kowa da kowa dai a gidan harta iyayen su mata tafiya masallaci suke dan yin sallar juma'a, a baban masallaci cin juma'a na sahaba dake cikin garin Marad'i.a AFREEN ke d'auka yaran a mota su tafi Khairat ma ta tafi a motar ta idan kuwa taga dama sai bi AFREEN su shiga tata motar tare da yara su tafi masallaci, shikuwa papa ya kwashi matan sa su tafi tare, Fahad kuwa ya d'auki motar sa su tafi shida Imran sabida makaranta ma tare suke zuwa. To yau ma haka ce ta faru AFREEN suka tara gabad'aya aka rufa gidan suka nufi masallaci don yin sallah juma'a kuma duka cikin su AFREEN ce kad'ai keda nik'af. Sai mu had'u da next page💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 Taku harkulin mai kaunar ku❤️🥰💓 "QUEEN ZEEFAT📝📝✍🏻 Inayinku irin sosai d'in nan masoyan 🌸ZANBA CIKIN AMINCI🌸 alkairin Allah ya kaimaku duk inda kuke💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZANBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ÉCRIT: _PAR_ *QUEEN ZEEFAT* Yar Mutan Niger Wattpad@nazhabibou 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM Page: 17 & 18 Tangamemiyar ma'aikata ce mai matuk'ar kyau, ma'aikatar karshe ce wajan tsaruwa a saman k'ofar ma'aikatar da mayan harufa an rubuta *MINISTÈRE* (wato ma'aikatar ministoci, inda ko wane minister keda babba kuma had'ad'en office) sojoji ne sosai gewaye da ma'aikatar daga cikinta har wajan ta tsaro ke akwai sosai, wasu had'ad'un motoci ne guda biyar suka kuno kai a cikin ma'aikatar suna gama parking sojojin da ke cikin motocin guda hud'u suka fito da sauri tare da nufar cikon motar ta biyar, duk suka tsaya a tsaye kyam kamar an dasa su tare da haka bidigogin su irin ma su jiran tab'in nan su sakar maka alburushi, gaban motar aka bud'e Ali ne ya fito ya nufi k'ofar baya ta motar ya bud'e, kusan minti biyu da bud'e k'ofar sanan na cikin motar ya ziro kyakyawa k'afar sa mai sanye da wasu had'ad'un takalmi masu mugun kyau Kana ganin su kasan bana na k'ananun kud'i bane. Ida fito da k'afar guda yayi kamin ya k'arasa fitowa gabad'aya, sai a sannan na gane da AFREED ne ya had'e colin wata dakakiyar shada bleu (blue) da tayi matuk'ar d'aukar jikinsa dan ba k'aramin kyau kayan suka masa ba. Jerawa sukayi shida Ali suna tafiya sannu sannu cikin kwonciyar hankali da nutsuwa kamar basa son taka k'asa su kuwa garde-corps (bodyguard) d'insa na take masu baya abin kwanin sha'awa masha Allah, kana ganin AFREED da Ali zaka iya tunanin 'yan biyu ne sabida suna matuk'ar kama da juna, sedai AFREED ya fishi tsayi shikuwa Ali ya fi AFREED haske. Suna shiga cikin katafariyar ma'aikatar k'ananun ma'aikata na kwasar gaisuwa amma hannu kawai AFREED ya samu damar d'aga masu 'yar karama tafiya suka Ali yayi Saurin k'arasawa bakin k'ofar Wani bureau (office) wanda sama k'ofar bureau (office) d'in an rubuta *MINISTRE DE DÉFENSE ET DE SÉCURITÉ* (wato ministan sojoji da na tsaro). Masha Allah baban office ne k'ayatace wanda ya amsa sunan sa office don table ma da kujerun dake cikin bureau (office) d'in kad'ai abin kalo ne. AFREED da garde-corps d'in sa na ida k'arasawa bakin k'ofar office d'in bai tsaya komai ba ya shige ciki sukuwa suka tsaya a bakin k'ofar kamar an dasasu, directe (direct) wajan luntsumemiyar kujerar sa da ke gaban table d'in bureau sa ya nufa ya zauna da bismillah ya fita da hular dake saman kansa tare da fad'in oh mon dieu (oh my god) ya duk'e tare da aza hannayan sa da kan sa a saman table d'in dake gaban sa. Ali dake bakin k'ofar tare da garde-corps ya kalesu yace "biyun da suka saba tsayawa a bakin k'ofar su tsaya ku kuwa sauran kuje kuyi wanda kuka saba har a nemeku da sauri suka sara masa tare da cewa d'accord monsieur (ok sir) biyu suka tsaya sauran sukayi gaba shi kuwa ya fad'a cikin bureau (office) d'in AFREED tare da rufo porte (door) d'in yaje ya zauna cikin d'aya daga kujerun dake fuskantar AFREED. Kalon AFREED ya tsaya yanayi na tsawon minti biyu kamar wanda keson gano wani abu kamin ya d'an nisa yace "Wai fréro (broh) mike damunka ne tun fah jiya da dadare bayan mun dawo daga gun dady naga kamar baka cikin walwala na tambaye ka Kuma kamin shiru dan Allah yanzu dai ka fad'a min kwakwata nima ka saka hankali na ya k'i kwanciya duk na damu walahi bana son ganin ka a haka."Ali ya fad'a da damuwa k'arara a fuskar sa. A hankali AFREED ya d'ago ya kalli Ali tareda sakin boyayar ajiyar zuciya sannan yace "Fréro ( broh) mi kake ganin zai dameni da ya wuce abinda dady ya mana magana akan shi jiya." Wani k'ayatacan murmushi yayi sannan yace "Dama nasan babu abinda zaiyi mugun daga maka hankali kamar wanan maganar da dady yayi amma miye abin d'aga hankali kan abu me sauk'in irin haka." Wani uban harara AFREED ya narkawa Ali kamin yace "Mike me sauk'i a cikin abinda da dady ya fad'a ko ka d'auka da wasa yake ne, ko dai dan kai a shirye kake ne sabida kasan duk fad'a a kaina aka sauke kai banda kai shiyasa kake wani cewa sauk'i ne da shi." "Hum AFREED kenan banga miye abin tada jijiwoyin wuya abinda wanan abin sauk'i ne dashi kamar yanda na fad'a maka kasan ko miye sauk'i shi?" Girgiza kai AFREED yayi alamar a'a. D'an nisawa Ali yayi tare da gyara zama sannan yace "AFREED abinda ya kamata kayi ana shine kayi gagawar fitar da matar aure tun kafin dady yayi maka auren da bakaso, wato ya zab'a ma matar da kanshi ga mata nan iri iri sunna kawo kansu gareka amma baka kulasu ka darje kawai ka zab'i d'aya a cikin masu kawo maka hari, dubi fah wanan farin jinin da Allah ya maka yanda mata da kansu suke kawo maka talar kansu amma kana sharesu, gashi babu inda Allah ya rage ka AFREED kayi niya kamin lokacin da dady ya iba mana ya k'are." "To wai kai Ali da kake tacewa nayi niya nayi niya tayaya kana ganin ni ko secrétariat ta (My secretary) ban ida tantance ta ba itada kulum tana shigowa office d'in nan fiye da so goma a rana to ko ita akace yanzu na gwadeta to wallahi a saramin babban aiki to tayaya zan kalli wata harnaji inason ta gashi kuma na fison na fida mata da kaina tun kan dady ya zab'a min gashi kuma ni bansan daga zan fara neman matar da zan aura ba, Kuma kai Ali dakake cewa mata masu cewa suna sona tun kamin ni na furta mata masu kalamar so ai har abada ta kayar da darajar ta gareni haba yo ina ajin na mata duka ta zubar to ni mizanyi da mace marar aji da kamun kai kuma wanibi irin matan da suke Nuna ma namiji suna sonsa tun kamin shiyace yanason su to fa'aksarin su ba son gaskiya suke masa ba kawai dai dan wani abu ne da Allah ya yi maka to ka ga irin matanan ba irin matan da yadace ya zauna dasu bane indai yana son samin mata ta gari dan haka babu wace zan zab'a a cikin su." AFREED ya fad'a Ali yace "Hakane to taya wai zaka sami matar kaida ba kulla su kake ba kasan idan har lokacin da dady ya ibar mana ya k'are bamu fitar da matan aure ba wallahi zamuga b'acin ransa sabida zai iya aikata abinda yace zai aikata a kanmu sabida dai kasan shekara guda ba kwana guda bace bai kamata ace shekara guda da ya d'ibar mana har ta k'are baka fitar da matar aure ba don gaskiya dady ba zaiji dady ba ni wallahi kai nafi tausayi ma sabida baka iya kallon mace bare har kace kana sonta nidai kaga inada wada nakeso ko yanzu dady yace na gabatar da ita to zan gabatar masa da ita kai fah da ko secrétariat ta baka sani ba da kai kawo daga office inka zuwa nata har yanzu baka tantance ta ba to Inama zaka samu damar sanin wata." "Nima fah shine nike tunani Ali amma Allah zai shige man gaba insha Allah zan samu wada tayi daidai dani kamin dady ya fitar min da mata ina neman zab'in Allah, ina fatan Allah bani mata ta gari ni wallahi inba dan dady ya matsa ba ni babu aure a gabana yanzu duk nawa nake da za'a matsa sai nayi aure." "Kam wallahi AFREED baka jin kunya kai ne zakace a nawa kake shekara 30 da kakeda itace a nawa kake wanda gashinan har ma kazama tuzuru Ali ya fad'a tare da tuntsirewa sa dariya." Dariyar shima AFREED yayi sannan yace wallahi Ali kayi mugun rainani ma yanzu shekara 30 kince zaka wani cewa na zama tuzuru to wallahi ka kiyaye ni idan na zama tuzuru to wallahi kaima tuzuru ne tunda dai ba girme maka nayi ba." Koma dai minene to kaji dashi wajan wata biyar ka bani da haihu ko da kuwa second guda ne ai dai ka girme min don haka yanzu dai nasan kana da ayuka da yawa a gaban ka ka d'auka ka fara ni kaga tafiya ta zanje na dawo." Murmushi AFREED yayi sannan yace sai ka dawo to ai kasan yau da wuri zamu tashi." D'aga masa kai Ali yayi sannan ya juya ya fice daga office d'in." Sai mun had'u a next page💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 Alhamdulilah... 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ÉCRIT PAR *QUEEN ZEEFAT* Ƴar Mutan Niger _Wanan page taki ce my kawa my Aminiya ta_ *Rida* *Chou* _que le bon dieu te protège kawar arziki ina yinki irin sosai ɗin nan_ 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan -niger-111773560677003/ _BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_ *Page* : 19 & 20 Ƙarfe 12:00am Ali ya shigo office ɗin AFREED tare da ƙaraso kusa da table ɗin AFREED yace "Ranka ya daɗe kataso mu wuce gida lokacin tashi daga aiki yayi, kuma naga kamar da aiki a gaban ka baka kamala ba, kaga kuma ni yinwa nakeji inason naje gida naci abincin don nasan yanzu momy tagama mana spécial, amma dai zan zauna har ka ƙarasa sai mu wuce." AFREED dai bai tanka masa ba, kujera Ali yaja ya zauna, yana zaunawa AFREED ya fara tatara takadun dake gabansa yana kammala hada su guri guda ya tashi daga saman kujeran dayake Ali na ganin haka shima ya mike ya nufi ƙofa ya buɗe masa don yasan tashin da yayi fita zaiyi duk da bai fad'a masa haka ba, AFREED na kawowa bakin ƙofar Ali ya ida buɗe ƙofar AFREED ya fice sannan Ali ya bi banyan sa tare da rufo ƙofar garde-corps ɗin dake bakin ƙofar suna jiran fitowarsa suka ƙame guri guda suna sara masa batare da ya kalle suba yayi gaba abinsa sukuwa suka mara masa baya. Ali daya tsaya rufe ƙofa suka barshi abaya, yana ƙarasa kule ƙofar tare dayin saurin tardo yace "Haba AFREED sai ku tafi ku barni don kawai kasa sai nayi gudu idan inason cimmar maku kuma fa kaji nace yinwa nakeji gashinan yiwar ta ƙaru sabida ɗan gudun da nayi." AFREED dai bai tanka masa ba hasali ma ko kallon sa beyi sai ma damun sa da surutu yayi don ji yake kamar ya makesa ma ya futa ko zai yi shiru da bakin sa. Ali da yaji shirun yayi yawa ya gane da surutun da yake masa ya damesa kawai sai yayi shiru bai sake cewa komi ba har sukakai ida suka parking motocin su duka garde-corps ɗinn saida suka nufi motar da AFREED zai shiga suka kewaye ta sannan Ali ya buɗe masa ma zauni sa ya shiga kamin kowa ya nufi motar da zai shige, daga bisani aka tayar da motocin sai gida. Suna isa gida direct ɓangaren mahaifiyar su suka nufa kamar yanda suka duk in sun dawo daga gun aiki sai sun biya gun mahaifiyar su sun gaida ta kamin su wuce ɓangaren su, suna kawowa bakin ƙofar ɓangaren mahaifiyar tasu Ali ya juya yayiwa garde-corps ɗin signe da suka ma gaban su a take suka juya suka bar gun, kamin Ali ya juyo AFREED har ya buɗe ƙofar kawai sai suka shige lokaci guda tare da yin sallama. Hajiya Falmata na zaune saman ɗaya daga cikin haɗaɗun kujerun dake falon ta hakimce tana kallon télé (TV), tanajin sallama su farin ciki ya luluɓe ta juyowa tayi ta sakar masu murmushi tareda amsa sallamar sannan tace "Oyoyo da ɗiyan albarka na ku ƙaraso kuzo ku zauna," tana nuna masu kusa da ita, ƙarasawa sukayi sedai basu zauna saman kujerar da take a zaune ba sai suka zauna ƙasa kowanan su ya za'a kansa saman ciyar ta ita kuwa ta shiga shafa masu kai a tatare sukace "Momy ya gida?" Ta amsa da "Alhamdulilah ya aikin ku ya gajiya?" A tare suka kuma cewa "Da godiya." Mom tace "To madala Allah ya taimaka, Allah tsareku ya kareku daga duk wani sharin mai sharin da kuma sharin ƙarfe." Suka amsa da "Ameen momy." Ali sai ya zarce da cewa "Wallahi ni fah momy yinwa nakeji dama da safe wanan fitinanan ɗan uwan nawa bai bari nayi Kari mai kwari ba ya fitineni da na tashi muje wajan aiki duk gashinan yanzu yinwa duka tabi ta dameni anyi mutum sai fitina," ya watsawa AFREED tare da murguɗa baki kamar wata mace. Dariya sosai momy tayi sannan tace "Kaga kuwa harna gama dafa maku abinci kuma abinda kafiso na girka maku." "Yawa momy dan haka nake ƙara sonki Allah dai ya biya ki da gidan aljanna." Da ita da AFREED suka amsa da "Ameen." Momy tace "Bari naje na kira ƙanan ku sun ce bazasu ci abinci ba har sai kun dawo ku ci tare." "Ah momy bari naje nawo masu magana su fito muci to." A'a Abbana yi zaman ka, ka huta zanje na kira su kuyi hutawar duk kun gaji kaga daga aiki kuke nikuwa ina gida zamana ina hutawa ba abinda nayi sai girki nan shima dan AFREED ne bai girkin masu aiki shi yasa na girka maku da kai dan nasan kai babu ruwa da wannan iwayin nasa Allah maku albarka," faɗar mom tana ƙoƙarin hawa escalier don kiran su Fariya. AFREED dai najin su bai tankasu ba gani momy tayi saman yasa shi tashi ya nufi hanyar barin falon da niyar sa ta komawa ɓangaren su, Ali na ganin ya mike yace "Ina kuma zaka??? nagani zamuci abincin." Cigaba da tafiyar sa yayi baiko tsaya ba bare yayi tunani zai amsa masa. Ali yace "To wallahi baka isa mu jiraka ba idan kanaso ma kada kaci abincin ko kuma kaci kai kaɗai ah to." AFREED ya juwo yace "Kaga Ali fita haraka ta ni nace ku tsaya jirana kokuwa dole ne sai naci abincin tare daku ko an gayama ka sai tare daku zan iya cin abinci?" "Anji ɗin kuma anki a fita harakar taka kayi abinda zakayi ko an gaya maka ana tsoron kane wallahi ina tausayawa matar da dady zai haɗaka da ita don narantse ba ƙaramin aiki ne gabanta ba, haba anyi mutum sai baƙin miskilancin tsiya,"Ali ya faɗa tareda sakin murmushin mugun ta dan yasan da ya gama ɓatawa AFREED rai. AFREED najin haka ya juya ya bar falon don ya tabatar cewa Ali so yake ya ɓata masa da rai. AFREED na fita momy da su farissa suka sauko ta wanga nan ta wanga nan bataga AFREED ba tace "Abbana ina ɗan uwan naka kuma yayi alhalin yasan za'a ci abinci?" "Wallahi momy yayi tafiyar sa ɓangaren mu babu wanda banyi dashi ba ya tsaya amma ya ƙi." Ɗan ƙarmin murmushi momy tayi sannan tace "AFREED yau halin akeji tunda gaka yayi tafiyar sa ba zai cin abincin anan ba ƴan miskilancin su na busa kai yau." "Barshi dai mom bari na kai Masa abincin acan sai ya ci." "A'a abbana yi zaman ka har kaci abinci barshi daga baya a kai masa." "Hum ai su AFREED manya ne mom, ba maiyin irin tasa ace mutum ko yana jin yinwa babu abinda ya damesa kamar cikin wani zai sakawa abincin to ai dan kansa mu dai Kam ba fasa cin zamuyi don AFREED ɗan gayu ne yinwar ma bai cinka jinta ba ai duk miskilanci na ba zan ƙi cin abinci ba gaskiya sabida bana iya jurar yinwa," Ali ya faɗa yana Mai miƙewa daga zaman dayake. Dariya momy da su Farissa suka yi sannan Fariya tace "Kai yaya irin wanan surutu haka bama kajin yinwar da ka faɗa." "Kai kai ƙanwata sosai nake jin yinwar nan kisan hausawa sunce baki abun magana, to shiyasa ba najin daɗi idan banyi ba cikin ko wane hali kuwa." Koma yin dariya sukayi daidai lokacin da suka ƙaraso bakin table à manger (dinning table) kowa yaja kujerar da yasaba zama ya zauna banda Farissa dake servir ɗin su tana gamawa itama ta ja tata kujerar ta zauna, shiru kakeji gun cin abincn babu mai cewa komai sedai ƙarar cuillère (spoon) kawai kakeji har suka kammala, Ali ya fara tashi ya nufi cikin falon ya zauna kan ɗaya daga cikin kujerun dake falon, momy ma falon ta dawo ita kuwa Farissa ta zubawa AFREED abincin ta tafi kai masa, Fariya kuwa ta tare kayan da suka ɓata ta mayar cuisine (kitchen). Ali yakai kusan minti 30 suna fira da momy da ƴan biyu wato Fariya da Farisa, sai daga bisani ya miƙe yace "Momy zanje na duba frèro naga ko yaci abincin kuma na sauya kayan jikina duk sun takura man." Momy tace "To jeka abinka sai ka fito idan kuma AFREED baici abincin ba ka yi min waya zanzo na same shi don bazan lamunci rishin cin abincin nan nasa ba gaskiya." "A'a bama sai kinzo ba ai, zai ci insha Allah tana yiyuwa ma har ya kammala cin abincin." "Hum AFREED ɗin ne zaka ce ya kammala kana dai son ƙulle masa gidine amma idan har bai ci ba ka ɓoyemin to wallahi idan na gano haka duka zakuga ɓaci raina ehe kadai ji abinda na faɗa maka, ban cin wannan naga kamar wani abu na damusa ko zan iya sanin miye? Dan nasan baƙin ɗaya ba ƙi faɗa maka zai yi ba. "Babu abinda ke damun AFREED momy kawai dai yanayin sa ne ya nuna hakan, idan kuma akwai bai wuce akan magana da dady ne yayi mana juya dadare ba amma in bashi ba to ba wani abun." Hum AFREED kenan yo ai in a kan maganar da dadyn kune ya maku yasa damuwa a ran to garama ya daina dan babu guda babu ja da baya, amma ai ba sai na faɗa maku ba kun fiini sanin halin abban naku, kun sani sarai abinda ya faɗa sai ya aikata kawai abinda ya kama ce ku shine ku fitar da matan aure tun kafin lokacin da ya ɗibar maku ya ƙare gashi kuma ya baku isashen lokacin sabida shekara guda ai ba kwana guda bace hakan daya maku daidai kuma ya nason ya ga kun ɗoki maganarsa da muhimmanci ko kuwa, sabida haka kuyi ƙoƙari yurin ganin kun faranta masa ba, bawai ku ɓata masa ba wai dan baya don ku ne yace muku haka ba hasali ma sayayyar taku ce da yake maku yake ƙaunar ya kun zama cikakkun mutane sabida ku ƙara daraja a idon kuma ku raya sunnah manzon tsira Sallallahu alaihi Wasallam." "Insha Allahu mom zamuyi abinda kukeso dan samun albarka kuma ran ku bazai taɓa ɓaci ba a kan wanan maganar zamu baku mamaki." "To dako kun kyauta dan ni a cikin wanan maganar bani bayan ku gaskiya saboda nima inason ganin ƴan jikokina amma kunzo kuyi zama kunƙi yin aure ko so kuke sai mun mutu kuyi auren in hakanan kuma kukeso to ai shikenan." "A'a insha Allahu haka bazata faru ba abinda kukeso zamuyi momy kun kwantar da hankalin." Murmushi momy tayi mai matuƙar nuna farin cikin ta tare dacewa "To ai shikenan tashi kaje Allah maku albarka." Da amin ya amsa sannan ya tashi ya fice daga falon ya nufi ɓangaren su, yana shiga direct ɗakin AFREED ya wuce, tardo sa yayi kwace idonsa a lumshe kamar mai bacci, juyawa yayi ya kalli abincin da aka kawo masa wanda ko kallon sa baiyi ba bare ma ace ya ci sa, da sannu sannu ya nufi bakin gadon ya zauna sannan yace "Ɗan uwana AFREED tashi kaci abincin mana ya za'a kawo maka abincin tun ɗazu kaƙi ci tashi dan Allah." Shiru kakeji AFREED bai ko motsa ba bare ya nuna ya jisa har ayi maganar zai amsa masa, Ali ya koma cewa "AFREED ka tashi man kada abincin yayi sanhi kuma ka kasa ci," nan ma shiru AFREED bai motsa ba, "Haba ɗan uwana mi yayi zafi haka?" Har yanzu AFREED bai motsa ba bare ayi tunanin zai tashi daga kwanciyar dayake. Shiru Ali yayi na tsawon minti biyu yana kallon AFREED sannan ya kuma cewa "Nifa nasan ba bacci kake ba, amma tunda kaƙi tashi bari na kira momy na faɗa mata baka ci komai ba dama tana can cikin damuwa sabida ka taso ka ta howarka baka tsaya kaci abincin ba shine ta aikoni nazo nagani idan baka ci ba naje na faɗa mata." AFREED najin haka yayi sauri ya tashi zaune tare da ƙoƙarin saukowa daka saman gadon Ali yayi saurin riƙo sa yace "Ina kuma zakaje?" Wani mugun kallo AFREED yayiwa Ali sannan yace "Kai dan Allah cikani ina fah zanje da ya wuce gun momy naga halin data ke ciki." Mtsss Ali yaja wani ɗan ƙaramin tsaki sannan yace "Dan Allah dakata malam ka damu da halin da zata shiga ne ka kama hanya kayi tafiyar ka kamin taje ɗakin su Fariya ta dawo sannan kuma kaje gunta da alamu damuwa a fuskar idan baka don sata cikin damuwa miyasa ka aikata haka, abu guda ne zaka yi idan kana son kaga damuwar ta ta gushe shine ka karɓi abincin nan ka ciye shi sannan kasamu kayi sallah idan ka gama sai kaje gunta cikin sakin fuska a take za kaga farin cikin ta mara musultuwa amma ba ka wani tashi da sauri haka ba wai kai ga meson gani halin da take ciki, idan kaje haka ba sedai ka ƙara mata damuwar ba ɗan raini hankali kawai." Saƙe AFREED yayi na wajan second 3 yana kallon Ali daga bisani dai ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi ba tare da yace wani abu ba ya karɓi abincin daga hannun Ali ya fara ci har sai da yaci fiye da rabin assiette (plet) sannan ya ajiye, yana ƙoƙarin tashi daga bisa gadon Ali ya riƙo sa yace "Yo ina kuma zaka kaida baka ƙarasa cin abincin ba?" Da sauri AFREED ya fizge hannun sa yana cewa wallahi Ali ka fita haraka kazo ka sakani cin abincin nan naci ba dan maso sannan kuma so kake sai na cinye wannan uban abincin to wane irin ciki ne dani da zan iya cinye sa? kuma wallahi baka isaba don na tabata ko kai dake cin abincin sosai ba iya cinye wannan abincin zaka yi ba amma ni kake son kaga na cinye shi a cikin wane cikin kake son gani na saka shi? to wallahi duk fitinar ka yau sai ka barni," mtsss yaja tsaki tare da shigewa douche da sauri ya banko ƙofar toilette ɗin da ƙarfi. Murmushi Ali ya saki tare da cewa "Ɗan uwana, abokina, kuma uban gidan AFREED Allah tsare min kai ya baka mata ta gari wada zata iya jure wannan halin naka sannan kuma ta zama sillar gyara maka wannan bahagon halin naka amin tunda dai kaci abincin ai shikenan dama da gaganne nace sai ka cinye shi." Daga na shi ma ya tashi ya fita daga ɗakin AFREED ya nufi nasa ɗakin. Shikuwa AFREED dake cikin douche yana jin fitar Ali ya fito a cikin zuciyarsa yana cewa anyi mutum sai shegin surutu da fitina da son takurawa jama'a, mtsss yaja ɗan ƙaramin tsaki tare da shimfiɗa darduma ya tada sallah. *WANENE AFREED* AFREED Sumana Gissa shine cikakken sunan AFREED wato ɗan ga Alhaji Sumana Gissa wanda yake cikakken bazabarme ne ɗan asalin garin Dosso kuma ingénieur (injiniya) ne aiki ne ya maido sa Niamey da zama, sai mahaifiyar AFREED Hajiya Falmata Ita kuwa cikakkiyar babarbara ce gaba da baya ƴar asalin garin Diffa, su biyu iyayen su suka haifa ita ƙanwarta Kaltum sun haɗu da Alhaji Sumana ne wajan walimar taron buɗe wata ma'aikata gina-gine a garin diffa ita kuwa tatafi wucewa ta gaban ma'aikatar ta dawo Ga aikin da aka mata yana ganinta ya ruɗe sabida Allah yayi mata kyau ga wani uban kamshi dake tashi a jikin ta, kun san barebari game da kamshi babu kamar su sedai kuma ba fara ce sosai ba haka dai har ya samu ya tsayar da ita ta yi masa kwatancan gidan su ida yaje ya sami mahaifin ta da maganar, da mahaifin nata yayi bincike a kansa ya samu kyakyawa shaida a tatare da shi, ya bashi auren Falmata cikin ƙanƙanan lokacin akayi komi da komi haka a ɗaura auren Falmata da Alhaji Sumana Gissa cikin aminci, suka tare a babban gidansu dake cikin garin Niamey wata uku da auren Falmata akayi na ƙanwarta Kaltum wani bafilatani mai rufi asiri a garin Tillaberi amma ba ɗan asalin garin bane neman kuɗi ya kawo sa Niger shi ɗin ɗan asalin garin Senegal ne. Bayan shekara guda da auren Falmata da Alhaji Sumana Allah ya basu ƙaruwar ɗan namiji murna wajan wannan famille (family) ba'a magana kowa ka gani cikin farin ciki yake yaro mulmulmul dashi kyakkyawan gaske sai farin jini kowa ya gansa sai yaji kamar a basa shi kuma duk wanda ya ɗauka ba yason ya ajiye har saida jikinsa yayi ciwo kamin suna, ranar suna yaro yaci sunan AFREED, bikin sunan ya ƙawatu dan anci ansha sai dai son barka. AFREED na da wata shida da haihuwa Kaltum ƙanwar Hajiya Falmata Ita ma ta haihi ɗan ta fari kal mai mugun kama da AFREED tunda yazo duniya mahaifinsa yayi masa huɗuba da Ali wato sunan mahaifinsa su Hajiya Falmata sedai tunda Kaltum ta haihu jini yaƙi tsayawa, likitoci suyi iya bakin ƙoƙarin su wajan ganin sun shawo kan matsalar amma abin ya ci tura, kwana biyu da haihuwar tace ga garinku aikuwa tashi hankali gun Hajiya Falmata ba'a magana taci kuka taci kuka har ta godewa Allah har yakai kukan baya fitowa saida ayita jin tana sauke ajiyar zuciya, sosai takasa hakura da rasuwar ƙanwarta ta kullum cikin kuka take ganin haka yasa Alhaji Sumana ya roƙi mahaifin Ali da ya taimaka ya bawa matarsa yaron sai taci gaba da shayar dashi tunda ita cikin jegon take, kuma ganin ɗan ƴar uwatata zaisa ya dinga ɗebe bata kewa haka kuwa akayi Mahaifin Ali yace ya bata shi halak malak tasa ma kanta cewa itace ta haifesa sannan ya ƙara da cewa shi yanzu ƙasar su zai komawa dama sabida Kaltum yake zaune a Niger amma yanzu komawa zai yi tunda ya gama abinda yake a Niger abinda ya samu Allah sa masa albarka, kuma yace su taimaka idan Ali ya girma su bashi labarin shin duk dacewa zai dinga zuwa ganisa lokacin zuwa lokaci amma daya ke bai san halin rayuwa ba ko yanada rai zai girma kokuwa Allah dai masani. Ai kuwa kuka sai ya koma dariya gun Hajiya Falmata don ba ƙaramin farin ciki tayi ba daji an bata Ali har abada, ba ma ta iya musulta farin cikin da take cikin don ji take kamar ƴar uwata in ce gaba-ɗaya take raino, haka dai Hajiya Falmata ta haɗa ɗiyanta biyu gaba ɗaya ta na shayar dasu cikin tsantsan so da gata dan ba ƙaramin ji dasu take ba shima Alhaji Sumana ba'a barsa a baya ba sabida idai yana gari to a kowa ne lokacin suna tare dashi babu wani banbanci da iyayen AFREED ke nunawa ga Ali duk ɗaya suka ɗokesu, har ma sufi yiwa Ali Abu basu ma AFREED ba, Ali dai kam baida maraicin uwa da uba don Hajiya Falmata da Alhaji Sumana ba ƙaramin sonsa suke ba. Shikuwa mahaifin Ali ya riga da da ya koma ƙasar su ya bar amanar Ali a hannun iyayen AFREED. AFREED da Ali na da shekara uku uku aka saka su école coranique (islamiyya) da jardin d'enfants (nursery school) Mai tsadan gaske Masha Allah duk da yarinta su haka bai hana su rike abinda ake koyar dasu ba kuma idan sun zo gida Hajiya Falmata ta ƙara koyawar dasu su, AFREED sun tashi cikin gata sosai amma hakan bai hana iyayensu basu tarbiyya ba Hajiya Falmata da Alhaji Sumana suna iya ƙoƙarin su wajan ganin sun basu cikakkiyar tarbiyya, AFREED ya tashi miskili mara son magana bai ƙaunar zama inda ake hayaniya da yawan surutu sedai halinsa yasha banban da na Ali wanda shi kuwa ma'abucin surutu ne da barkwanci duk da wannan halin na surutu na Ali da AFREED bai so amma ba ƙaramin ƙaunar junansu suke ba ko kaɗan basa son ganin junansu cikin damuwa a tare suke komai nasu, ko Hajiya Falmata da Alhaji Sumana basu san tsakanin su ba. Kwanci tashi babu wuya a wajan Ubangiji su AFREED har sunyi shekara bakwai bakwai sosai sukayi wayo masha Allah idan ka gansu zakayi tunanin sufi shekarun dake garesu sabida tsananin wayo da Allah ya masu. Ita kuwa Hajiya Falmata tunda ta haifi AFREED Ko ɓatan wata bata taɓa yi ba bare ayi batun samun cikin shiru shiru kakeji har saida su AFREED su kayi shekara goma sannan Allah ya ƙara bata haihuwa wanda har sun fida rai da samun ta idan ta haifi ƴan biyu duka mata ranar suna yara aka raɗa masu sunan Fariya da Farisa murna gun AFREED da Ali ba'a magana kullum suna tare dasu an samu ƙanai duk in sun taso daga makaranta suna tare da su bacci kaɗai ke rabasu da ƙannansu. Su AFREED na ƙarasa primaire (primary) Alhaji Sumana ya mayar da su France a can sukayi secandary school da University sannan suka dawo Niger dan su riga da sun kammala karatun su nacan, watan su biyu a gida AFREED yace zai koma yaci gaba da karatunsa a USA shikuwa Ali yace makarantar horon sojoji zai wuce. Haka kuwa akayi don iyayensu sun yi na'am da ƙudirinsu cikin ƙanƙanan lokaci aka shirya yawa kowa tafiyar sa ba dan sun so ba haka suka rabu da juna cikin kewa. Lokacin da Ali ya kammala makarantar sa ta horon sojojin shikuwa AFREED yana sauran shekara ɗaya ya ƙarasa karatun sa, sabida degree da diploma da kega Ali yana samun aiki ya fito babba mai babban matsayi wanda aikinsa shine tsaron lafiyar shugaban ƙasa ko ministoci, AFREED kuwa yana kammala karatun sa ya dawo gida satin shi guda da dawowa daga USA aka ɗoke shi aiki cikin ministère kuma babban office yake occupé, amma cikin ƙanƙanan lokaci ya sami ƙarin girma idan aka ɗoke sa matsayin *MINISTRE DE DÉFENSE ET DE SÉCURITÉ* sabida gaskiyar sa da riƙon amana kuma ta dalilin sake zaben shugaban ƙasa da akayi wanda shine da zai zaɓi ministoci ya zaɓa hada AFREED, a lokacin nan ne AFREED ya nemi Ali ya dawo gunsa da a matsayin mai tsaron lafiyar sa kuma na kusa dashi domin shawara kan abinda ya shige masa duhu haka kuwa akayi ba wani bata lokaci aka dawo da Ali gun ɗan uwansa sukaci gaba da aiki guri guda cikin farin ciki da anashwa. *CIGABAN LABARIN* Yau ya kama week-end ne, misalin ƙarfe 11:20 AFREED ne kwance saman makeken gadon sa me kyau da laushi yana ta kwasar bacci cikin natsuwa kana ganin yanda yake baccin kasan ya najin daɗin sa, kirrrrrrrrrrr wayar sa ta fara tsuwa tana neman agaji amma har kiran ya tsike AFREED ko motsa wa baiyi ba sabida yayi nisa cikin bacci sa mai daɗin mai tatare da mafarkai irin masu daɗin nan da kwantar da zuciya ana cikin haka wayar ta sake ɗaukar tsuwa a karo na biyu sannan ya farka tare da sakin tsaki cikin bacci ba tare da ya buɗe idanunsa ba yasa hannu ya lalabo wayar ya ɗauki kiran ya kara a kune ba tareda duba sunan me kiran nan sa ba ya kara a kunne. Daga can cikin wayar aka yi sallama firgigit AFREED ya buɗe ido tare da tashi zaune da sauri ya ƙara gyara zama yana murtsike ido sannan ya amsa sallama tare da cewa.............................. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar Mutun Niger_ Wattap:@nazhabibou 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_ PAGE: 21 & 22 Daga can cikin wayar akayi sallama firgigit AFREED ya buɗe ido ya tashi zaune da sauri jin Muryar da tayi sallama ya ƙara gyara zama tare murtsike ido, cikin natsuwa ya amsa sallamar tare dacewa "Tanti ina kwana antashi lafiya?" Daga cikin wayar wada aka kira da tantin tace "Riƙe gaisuwar AFREED banida bukata wallahi gaisuwar daba za'a kirani Amin ita ba sai in nakira, can kaje ka gaida uwarka ita da kake so tunda ni ba kaunata kake ba, wai AFREED yanzu ace kafi ƙarfin ka kirani kaji yanda nake sedai ni a matsayi na na ƙanwar uwar mahaifin ka dan Allah ya azamin ƙaunar na kira na ji idan kana lafiya amma ba wani abu, shi mahaifin naka da ya san mahimmanci na ai kullum sai ya kira kuma duk idan ya dawo daga ƙasashen waje sai ya biyo tanan ya ganni, amma dayake kai bakasan kima taba ai ko kirana bakayi bare nayi tunanin zaka zo idan nake wallahi AFREED kaji tsoron Allah rishin son zumuncinka yayi yawa, zan kira uwar taka naji idan ita ke hana ka zuwa idan nake." Wata gajerar ajiyar zuciya AFREED ya sauke sabida ba kanɗan ba maganar da tantin tayi masa me tsayi taso saka masa ciwon kai sabida rishin son hayaniyar sa, lumshe idon sa yayi sannan ya koma buɗe su kamin yace "Dan Allah Tanti kiyi hakuri wallahi yanda kike tunani ba haka bane sosai nakeso nazo na ganki kodan na samu nayi profiter na huta zaman Niamey din nan ya dan minyawa inason inje ida zan samu na shan iska yanda nake ba tare da wani ya takuraman ba, saida ya koma sauke wata ajiyar zuciya mai karfi kamin yaci gaba da cewa wallahi Tanti duk aiki ne ke rikeni badan ba naso zuwa b......." Bai ƙarasa faɗar abinda yakeson faɗa ba ta katse shi da cewa "Yimin shiru AFREED dama ai nasan haka zakace kai kullum aiki aiki kamar injin, to ko injin na hutawa bare kai ɗan adam, ace aiki ya hanaka zuwa ida nake to ai ba zai hanaka kirana ba ko, ko har kiran aikin bai bari?" Shiru yayi har kusan minti 2 sabida ba karamin gajiya yayi ba da wannan ƴar maganar da yayi ba ya buɗe baki zai koma yin magana, ta katse sa ta hanyar cewa "To kaga kai matsalar ka fah, ya za'a ce mutum da bakinsa amma magana na masa wahala yi yanzu zaka iya ce man bakin ka yayi ciwo daga yi wannan ƴar maganar da ko ta second 30 batayi ba, kai ba zuwan naka ba rashin maganar kane matsalar ba'a iya zauna wa dakai ayi hira haba AFREED dan Allah ka canza hali man, rishin son maganar ka yayi yawa, anyi mutum dai kamar gumki ba umm ba ummmmm ya kamata ka canza, naso naga yanda matar ka zata zauna dakai da rishin maganar nan taka ban sani ba ko ita ma irin ka zaka ɗauko, yawa m....." Bata ƙarasa faɗar abinda tayi niyar faɗa ba yayi sauri katse ta da cewa "Insha Allahu Tanti ranar talata zan ɗauki hutu Alhamis zan shigo maraɗi da yarda Allah idan nazo kuwa sai na ƙarshe hutu na gun ki ko na dawo." Ya hana Tanti ƙarasa maganar tane sabida yasan ta kaiwa ƙarshen zancen ta zatayi masa maganar aure ne shikuwa babu abinda ya tsana yanzu kamar amasa maganar aure dalilin kuwa shine baisan mi zaice mata ba sabida ba matar auren garesa ba kuma bai ma san ya za'ayi ya sameta ba yana tsoron kada lokacin da dady ya ɗibar masa yaje ya ƙare bai fito da matar da zai aura ba, shi kuwa dady yayi masa auren dole da baisan da wa zai haɗa saba. Shiyasa baison zancen kwata kwata. Cikin wani irin farin ciki Tanti tace "Dagaske kake ɗan albarka? kai amma naji daɗi cewa zakayi in shiryar zuwa babban ɗana mafi soyiwa a gareni nasan idan kazo nan zakayi wata biyu ko uku ko?" Wani gajeren murmushi ya saki sannan yace kai Tanti idan nayi wata biyu ko uku aikin nawa fah? Idai ba so nake a cireni daga aikin ba, sati biyu ne kawai za'a ban? Murna ta koma ciki a faɗa ce tanti tace sati biyu ai wallahi baka isaba duk wanda ma zai maka signe hutu sati biyu kace masa nace bai isa ba duk ubanda ma ya ɗaure maku gidi idan kazo garin nan sai kayi wata wallahi kama shirya nida nakeso ka dawo Maraɗi da aiki, haba AFREED dan ni baka ɗauke ni uwa ba shine za kazo ka yi sati biyu ka koma, yaushe rabon ka da garin nan yanzu kusan shekara goma kuma sunan ace kanada uwa a garin nan kiran ma a gaidani ban samu ba shine kuma yanzu kace zaka zo amma wai sati biyu kawai zakayi ko dan kaga inason zuwan ka guna ne? To har indai sati biyu ne zakazo kamin kayi zaman ka kawai," aiko sai ta fashe da kuka sannan taci gaba "Kana son yaro amma shi yana nuna maka ƙiyayya ƙikiri." Da sauri AFREED ya ce "Dan Allah Tanti kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki wallahi zanyi wata gurinki insha Allahu ina zowa sai nayi wata ko na dawo in badan aiki ba ai da ma gurin ki zan koma da zama baki ɗaya, haba Tanti Ni na'isa nace ban kaunar uwata adai min hakuri ai na kusan zuwa duk laifin da nayi zan karkare insha Allahu ma tanti chérie je t'aime beaucoup mon adorable mère (I love you so much uwata mai kauna) Aiko sai ga Tanti da washe baki tana dariya sosai a sauti dariya zaka gane taji daɗi shikenan kuka ya koma ciki daman bana gaskiya bane kukan "Toh toh toh dan albarka na ba damuwa inajiran ka sosai naso ace yau ne zakazo amma ba komi yau da ranar Alhamis duk ɗaya ne wajen Ubangiji Allah kaman kai lafiya ɗan kirki kazo man tare da wannan ɗan uwan naka mai surutun tsiya shima najima ban ganshi duk da shi ya fika zumunci yana kirana mu gaisa, kuma zan samu abokin hira tunda kaidai ba magana kake ba kaji ko ka gaishe man mahaifiyarka da ƴan biyu da dady naku ko da yake shi baya gari amma yace man yau zai shigo." Murmushi AFREED yayi sannan yace "Insha Allahu Tanti zasuji a gaida min kowa da kowa a huta lafiya." "Ameen ameen ɗan kirki sai anjima." sannan ta kashe wayar Murmushi AFREED ya koma yi tare dayin mika yana karanto addu'ar tashi daga bacci wada bayi ba a lokacin da ya farka da kiran ne silar tashin nashi sannan yace "Kai Tanti yanzu zata birkice tayi ta faɗa kuma a take zata sauko Allah dai kara lafiya da shekaru masu albarka Tanti na, oh ni yanzu ya zamemin dole nayi wata guda a maraɗi idai banaso ɓaci ranta, bai komi zan gyara komai gun aiki, Ni zai fi min ma naje nasha iska ba kamar nan ba da kullum akwai masu tsaronka kamar kayi wani babban laifi." mtssss yaja wani ɗan ƙaramin tsaki kamin yake sauka daga saman gadon ya nufi douche (toillet). Yana fitowa daga wakan ɗaure da tawel a ƙugunsa ɗaya a hannun sa yana goge ruwa da ke saman kansa kuma yana ida tsane jikinsa yana kamawa ya nufi gun mirror ya je yayi shafe shafen da ya saba yana gamawa ya nufi drawer ya fito da kayan da zai saka yana saka kayan kuma yakoma nufar mirror ya ƙara ɗaukar turare ya kara feshe jikinsa da shi sosai yayi wanka da turaren kamar ba kuɗi akasa aka siya ba daga kamshi turaren zaka gane tsadadine, ya kammala shiryawa ya fita ya rufe ɓangaren su ya nufi na mahaifiyar sa Yana shiga ya tardosu zazaune su duka harda Ali suna hira cikin farin ciki da anashuwa, suna ji ƙarar buɗe ƙofa gaba ɗaya suka dawo da kallon su gun daya ke, mahaifiyar sa tasaki wani irin ƙayatacan murmushi me ciki farin dan gani ɗan nata cikin walwala, nuni tayi masa da ya ƙara so ida take sannu ahankali yake takowa cikin natsuwa da tafiyarsa ta ƙasaita da kair ma yake ɗaga ƙafarsa kamar mai gudun jiwa ƙasa ciwo, yana ƙarasowa wajan mahaifiyar sa ya zauna gab da ita a saman capet yana mai tanƙwashe kafafun sa tare da aza kansa saman cinyarta sannan yace "Momy ina kwana antashi lafiya?" Murmushi ta koma yi sannan tace "Lafiya lau ɗan kirki harka tashi da fatan lafiya lau ka tashi?" "Lafiya lau Momy." AFREED ya faɗa ataƙaice Zai koma yin magana ƙanan sa suka rigasa da cewa "Yaya ina kwana ka tashi lafiya?" Murmushi ya saki tare da kallon ida suke yace "lafiya lau ƴan tagwayen Momy kuma kuna lafiya?" "Lafiyar mu lau yaya." Farissa ta faɗa tana murmushi Bata ƙarasa rufe bakinta ba Ali cike da shegantaka shima yace "Yaya AFREED ina kwana?" Wani murmushin ni zakama iskanci AFREED yayi tare da cewa "Lafiya ta lau ɗan ƙaramin ƙanina." Dariya sukayi su duka banda AFREED da yayi murmushi shi kuwa Ali ya game fuska Wata muguwar harara Ali ya sakarwa AFREED tare dacewa "Kaga AFREED fita haraka ta waye karamin kaninin naka kasan da ko shekara baka ban ba duka wata biyar ne zuwa shida ka ban shine zaka ce min wai wani ƙanin ka wai ma harda ceman ƙarami, gadai ƙananun ƙannin ka," Ya faɗa ya nuna su Fariya. Wani murmushin AFREED yayi tare da cewa "Koma dai miye ni ke babba koda kuwa second 1 na baka aidai na girmemaka." Ali zai koma magana Momy tayi saurin cewa "Kai AFREED kanason ɓatawa ɗana raiko tashi huce muje na zuba maka abinci kayi déjeuner (breakfast) ni ka daina tsokanar min abbana." Ba musu ya mike yanayi wa Ali gwalo tare dacewa "Ai Momy wannan abban nakine bayajin magana." Shikuwa Ali ya cika bam ya juwo yayiwa AFREED kallon zan rama. Tare da Momy ya ƙarasa gun cin abincin sannan ya ja kujera ya zauna ita kuwa Mom ta fara servir ɗin sa shayi ta fara haɗa masa ta miko masa cikin ladabi ya ƙarɓa ya fara sha yana lumshe shanyayun idanunsa mai nuna yana jin daɗi shahin da yake sha, Momy ta turo mai da assiette da ta gama zuba masa soyayar doya da kwai da taji wata hadaddiyar soup wani haɗaɗen kamshi ne ke tashi sai ɗayan assiette (plet) da ɗauke da ferfesun kayan cikin, bin plet ɗin yayi da kallo, sannan ya ɗaugo da kansa ya dubi mahaifiyar ta sa da alamar tausayi a fuskar sa kuma a shagwaɓe yace "Haba Momy ya zanyi da girkin nan tsakanin da Allah mom wane irin ciki ne gareni da zan iya cin wannan abincin Kallon sa tayi da kyau sannan ta ja kujera ta zauna sai tace naji baka iya cinye sa ɗin nima ai bance ka cinye duka ba, kaci daidai cikinka ka bar sauran. Shiru dai yayi amma yasan da koda kuwa bai cinye duka ba sai yaci rabin kowane plet gashi Mom ɗin tayi zaune tana nufin a gaban ta zai ci abincin kenan baida incin cin kaɗan ya tashi yasan da gangan ta zuba masa wannan uban abincin karmar mutum 5 zaici amma a ganinsa fah. Yana cikin wannan tunanin Momy ta katse sa da cewa "Mi kake jira baka fara cin abincin ba?" Da sauri yace "Zanci Mom." "To ina jira fara cin." Bai wani ci sosai ba yace "Momy na ƙoshi." Ya faɗi maganar kamar wani ƙaramin yaro. "Hum ai baka isa ba AFREED maza maida hankali kaci abincin sai in nace ka daina zaka daina daya ke bai mata musu a duk abinda tace kawai sai ya mayar da spoon ɗin ya naci sannu sannu irin an takuraka in nan, sosai ya ci abincin har saida taga yana shirin amai sannan tace to shikenan ya isa ta miko masa da jus ya girgiza mata kai yana nuna ruwa ajiye jus din tayi ta miƙa masa ruwan ya sha sannan suka mike suka koma falo a tare Momy cikin zuciyar ta tana cewa ai haka zan dinga maka tunda naga bakason cin abincin. Suna shiga falon Momy ta zauna gun kujera da tashi shima ida Mom ɗin ta zauna yaje ya zauna tare da aza kansa saman cinyarta ya kwanta tare da lumshe idon sa ita kuwa Momy tana shafa kansa." Cike da tsokana Ali yace "Jishi ko kunya baiji goɗai-goɗai da shi ya zo ya ɗane kan ciyar Momy ya kwanta abinda ko su Fariya baza suyi ba an daiji kunya." Murmushi AFREED yayi ba tare da ya buɗe ido so ba yace "in fitsari banza ne kaza tayi mugani." Ali yace "Allah ya sawaƙe aini nasan na girma ba kamar kai nake ba." Shiru baice masa komai sabida yasan jan sa ne yakeson yi don shima yana zuwa ya kwanta a saman cinyar Mom ɗin. Ƙannan su dai da Momy sai dariya suka suke masu. AFREED ya ɗan buɗe idonsa yana kallon Momy cikin sanyayar muryarsa yace "Momy idan Allah yaso ya yarda kuma muna cikin masu rai ranar Alhamis zamuje Maraɗi nida Ali gun Tanti Marie kuma idan muje zamu samu wata guda can insha Allahu." Kamin Momy tayi maga Farissa tayi tsale ta dawo kusa da Momy tace "Lah Momy muma zamubi su yaya dan Allah." Momy bata kula taba tace cewa AFREED "Allah ya kaimu ai kam naji daɗi da zaku tafi saboda kullum idan nakira ta na gaisheta sai tamin ƙorafin baka zuwa gunta kaga kama gara kaje kasauke wannan nauyin dake saman kanka." Shikuwa Ali cewa yayi "babu ida zanje an taɓa tsara tafiya da mutum ba'a sanar dashi ba? To ba zani ba." Wani mugun kallo AFREED ya watsa masa sannan yace "Yo kada kaje ɗin ai tafi nono fari koma an faɗa maka dole se dakai zan iya tafiya?" Dariya Ali yayi yace Eh an daiji ba za abika ba." Shiru ya mashi baice komai ba sabida idan ya tanka masa yanzu zai cikasa da surutu. Farissa ta shagwaɓe fuska ta koma cewa "Mom ce maki fah nayi muna zuwa dan Allah za muje maraɗi muma tunda mun dade ba muje." Shiru mom bata cemata komai ba. Shirun da Momy tayi ne yasa Fariya itama dawowa kusa ga mom ɗin tace "Dan Allah Mom ki bari aje damu." Waini da kuke ta tambaya ta aje daku nice zanyi tafiyar ne? Yayan kune za suyi tafiya ku tambaye su man idan zasuje daku ai shikenan." Da sauri suka nufi wajan Ali sukace "Dan Allah yaya zakuje damu kagafa mun daɗe muma ba muje ba muna son ganin Tanti da su Khadijah," sukayi kalar tausayi. Sunƙin nufar AFREED ne sabida sun san idan yace ba zai je dasu ba to hakane dan baya magana biyu. Murmushi yayi tare dacewa to makaranta fah idan munje daku sai ku bar zuwa makarantar." Da sauri har suna haɗa baki suka ce "Yaya ai hutu zamu shiga ranar mercredi." To shikenan zamuje daku insha Allah wani ihu daɗi suka saki tare da tashi dasauri suka ɗane kujerar da Ali yake zaune suka rungume sa su duka suna murnar. Dariya shima yayi tare da cewa "To kuma sai kuje ku bar Mom ita ɗaya?" A tare sukace "Yaya yau fah dady zaizo." Kamin Ali yace wani abu Momy tace "Indai nice suyita tafiya........ Suna nan suna fira su jehi jehi AFREED kesa baki sa har ya kai ya daina magana saboda har ya kaji da duk baiyi wata magana mai tsayi ba. Kiran sallah azahar ta sasu miƙewa suka nufi ɓangaren su dan ɗauro alwala su wuce masallaci, su Momy kuwa da ƴan biyun ta sukayi sama da suma su gabatar da sallar 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattap@nazichou* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_ Page : 23 & 24 Yau yakama weekend babu school, al'ada gidansu AFREEN ne duk week-end yaran gidan ke aikace akacan gidan sukuwa masu aikin gidan weekend ranar hutun suce, haka kuma suke da al'adar karatun Alkur'ani mai girma duk asuba ta Allah, haka kowa ke yin karatun nan daga papa har hamida dake autar gidan amma kowa acikin ɗakin sa yake nasa ƙananun yaran kuwa ɗakin papa tare dashi suke yi har sai rana ta fito kamin kowa ya tashi yayi aikin dake gabansa suna kammalawa sai su karya su tafi islamiyya, idan kuwa ranar school ne to ƙarfe 6:30 suke rufe Alkur'ani kowa ya shirya tare da karyawa su wuce school. To yau ma haka ta kasance AFREEN ce ke naɗe darduma da ta ƙarasa karatunta a sama ta mayar gun dayake tare da cire hijab ɗin jikinta shima ta mayar ida yake, barin ɗakin tayi baki ɗaya ta nufi kitchen dan haɗa masu petit déjeuner (breakfast). Bata wani ɗauki lokaci ba ta kammala girkin ta tattara kayan da ta ɓata ta wanke su baki ɗaya sannan ta dauko flask din shahi ta juye ruwan zafi da tayi, ta harhaɗa komai dai zai bada haɗaɗen shahi sannan ta aza akan babban plet tare da ɗaukar kula guda ta fito dasu domin taje ta shirya dinning ɗin. Tana fitowa ta hangi Zeinab na gyaran falon tana ƴan goge goge dadai sauransu, cikin murmushin ta ta ƙaraso kusa da Zeinab ɗin tace "Sister kema harki fito?" A tsorace Zeinab tayi saurin juyowa tana dana ƙirjinta idonta a warwaje tace "Lah anti kece? wallahi harkin ban tsoro ina shirin gudu wa bansan kina nan ba ashe kece ke girki a kitchen ko motsinki ba'a ji wallahi ni inasama breakfast déjà yana kan dinning saboda wani mugun kamshi dake tashi wallahi kinji wai kamshin zanice a kusa na yake ashe yana cuisine yanzu ne aka fito dashi kai amma anti ki iya girki irin wannan kamshi haka kullum girkin anti da kalar kamshin sa babu rana dazakaji wannan na kalar kamshin wannan ga ɗadin ɗanɗano, ɗaɗin girkin anti ni ban ma taɓa jin irin sa ko girki Maman dake da mugun ɗaɗin mai taɓa ƙwaƙwalwa wallahi naki ya fishi, gabaɗaya gidan maman ta koya mana girki amma babu wanda ya kamo ki ya iya wa hata anti Khairat ma da a tare aka koyamaku amma naki yafi ɗaɗin certe itama nata yaji garɗi amma bai kai naki ba, ai gidan nan iya girki mai mugun daɗi daga ke sai maman da anti Fauziya, kam anti kinji watanan wada ta iya girki kamar ka cire kanka ka bata idan kana cin girkin ta dan garɗi girkinta wato anti Fauziya amma duk da haka bata kaiki ba naki na daban ne wallahi anti ni inaso na iya girki sosai anti amma duk in nayi ba zai yi ɗaɗi naki ba dama zaki cire hannuwan ki kiban?" Murmushinta mai ƙara mata kyau ta saki tace "Kai Zeinab uwa tsoro da surutu wannan zuba haka kamar an jonaki, idan an ji tsoro addu'a ake ba waro ido ba kinji ko, kuma girki ai kema kin iya kuma yana ɗaɗi sosai sannan idan kina so ai sai na cire hannuwan nawa na baki?" "Kai anti wasa fah nake maki wallahi ya zance ki ciro hannuwan ki ban to ke fah, wallahi anti ke komai naki mai kyau ne idan kina magana ko murmushi kuncin ki har lotsawa yake bama saikinyi dariya ba ga tafiyar ki da tafi komai mugun birgeni idan kina tafiya kamar bakison taka ƙasa ne ko kina mugun jin tausayi ƙasa yanda kikasan hawainiya na tafiya haka taki tafiyar take ko kaɗan ba'ajin ƙarar tafiyar ki idan kina yi mutum zai iya cewa idan kina tafiya ƴangace kike alhalin ba haka bane wallahi kalar taki tafiyar ce haka nidama zaki koyamin anti inaso wallahi anti idan aka kalle ki dole mutum ya koma kallon ki ko yanason ko bayaso koda kuwa mace ƴar uwakice, dan ma baki fita kullum sai da niƙaf, nida nikeda wannan kyau naki da babu wata niƙaf da zansa sedai na diga firgita mutane da baiwar kyau da Allah ya min hum," Zeinab ce ke wannan surutun tana murmushi. "Oh ni Zeinab yaushe ne wai bakinki ya buɗe haka kina tazuba kamar an biyaki to Allah ya shiryaman ke ni bari naje na ajiye kayan nan na tsaya ina sauran shirmanki har hannuna yayi sanhi," AFREEN ta faɗa tana me yin gaba abinta. Da sauri Zeinab tasha gaban tareda tara hannu zata ƙarɓi kayan dake ga hannu AFREEN tace "Anti kawo na tayaki kaiwa dinning ɗin." "A'a Zeinab jeki ki ƙarasa aikin ki zanji da wannan kinjiko na hutar dake." "Anti ai har na ƙarasa kawo kawai na tayaki shirya mana table ɗin." "To jeki ida ƙarasa fito dana na cikin kitchen ɗin." Da gudu Zeinab ta juya ta nufi hanyar kicin tanacewa "Wallahi anti duk abinda na faɗa akanki gaskiya ce ba shirme ba." Murmushi AFREEN tayi tare da girgiza kanta tana cewa "Allah shirye ki Zeinab, a tare suka shiyar dinning ɗin tsaf. Zeinab tace "Anti wallahi duk in kinyi girki sai naji idan inaci kamar karna daina." Wani murmushin AFREEN ta koma yi sannan tace "Dan Allah Zeinab surutun nan naki ya isa haka kada kikai gasamin ciwon kai jeki kiyi wanka sai ki fito ki karya kinji ƴar albarkar ƙanwata." Kollon AFREEN ɗin tayi sai tace "To shikenan anti na mai tsada."A guje ta kwasa da nufi ta bar gun da sauri AFREEN ta tsayar da'ita tace "Zeinab ban hanaki gudu ba wai ke ba zaki iya tafiyar hankali ba dole sai kin haɗa da gudu?" "Lah anti na manta yi hakuri daga yau na daina insha Allahu," sannan tabi hanyar ɗakin nasu ta shige. Ita ma AFREEN ɗakin nata ta nufa. Tana shiga ɗakin ta ta wuce toillet dan yin wanka, bata tare da ta ɓata lokaci sosai ba ta fito da tawel ɗaure a ƙirjinta bakinshi iya cinyoyinta ɗaya tawel ɗin ɗaure akanta kusan wani drawer ta ƙarasa ta buɗe ta fito da abin busar gashi sannan ta rufe drower taje gun soket ta saka abin busar da gashin sannan ta fara busar da shi tana kammalawa ta mayar da shi ma'ajiyar sa tareda komawa gun mirror ta zauna ta fara shafe shafen mai da turaruruka humra masu mugun kamshi mai gigita tunanin masoyan da haɗaɗen kamshi mai kwantar da zuciyar duk wani ma'a buci son kamshi ta ƙarasa shafe shafen ta nufi wardrobe ta fitar da wasu haɗaɗu English wears riga da wando riga puple wando baƙi a take ta haɗe cikin ƙananun kayan ta wanda suka kamata sosai suka fito da gaba ɗaya surar jikinta ba ƙaramin kyau tayi ba idan ka ganta kamar ka saɓe ta ka gudu, komawa tayi gun mirror ta dauki turaren feshe kala uku ta shiga fesawa jikinta idan ta fesa wannan ta ajiye ta fesa wannan zakace wani babban bahon turare ne aka malayar a jikinta da kuma ɗakin nata sabida wani haɗaɗen kamshi ne ke tashi a jikinta da kuma ɗakin gabaɗaya ita dama ba ba'a buciyar yin kwalliya ba kuma ba dan wai bata iya bane kawai bata yine tana kammala kominta ta koma kan gadon ta kwanta tare da janyo wayar ta kuna data tana chatting da kawayenta. Wani group ɗin familyn sune ta shiga tareda yin sallama tare da tura emoji na sannun ku ai kuwa kamar jiranta suke suka mata ca ah AFREEN kece yau da magana a group ɗin kullum ke karatu karatu ba damar ki hayo ayi fira wasu kuwa suna ah sis munyi miss ɗinki ya karatu duk tayi ta basu amsa daidai da saƙon kowa, tana cikin chatting ɗin Zeinab ta shigo ɗakin tare da sallama sannan ta ƙara so inda take tace "Anti inji papa ki fito mu ƙarya ke ɗaya ake jira." AFREEN ta tashi zaune sannan tace "Jeki kice ganinan zuwa." "A'a anti zanjira ki mufita tare wallahi anti AFREEN kinji wani kamshi mai sanyin ɗaɗi dake tashi a ɗakin nan da jikinki lale anti kina jin ɗaɗinki kuma idan nace komai naki na daban sai kiyimin gardama amma ko bani ba nasan watarana wani zai faɗa maki ko kuwa har antaɓa faɗa maki hankan wa ya sani." "To sarkin ƴan iya magana nidai bari na ɗauko hijab ɗinna mu wuce," ciro hijab ɗin ta tayi daga wardrobe tasaka har yana jan kasa sannan ta kama hannu ta suka fice a ɗakin, kowa ya halarta a gun cin abincin sune kawai ake jira suna zuwa suka zauna AFREEN ta gaida iyayenta sannan ta zubawa kanta abinci baki wanda zata iya ci kamin papa yayi bismillah ya fara ci sannan kowa dake wajen suka fara ci al'adar gidan suce duk idan zasu ci abinci sai papa ya fara kaiwa bakinsa kannan iyayen su mata sai yaran daga babba zuwa ƙarami shiru bakajin ƙarar komai sai ta spoon can maman da ke hankalce da AFREEN tace "AFREEN abincin nan fah sai kin cinye shi naga kamar bakai sonci, kuma miye abin saka hijab dan zakizo nan, anyi mutum kullum cikin hijab dai wai baki gajiyane?" Murmushi tayi sannan tace "Kai maman ai zan cinye shi insha Allah ba wani dayawa bane, kuma ƙananun kayane a jiki na shiyasa na saka hijab gudun kada wani ya shigo." Kamin maman tayi magana dan ƙaramin ƙanansu wato Imran yace "kai anti kedai kinason saka hijab ne." Dayake kusanta yake sai ta ɗan shafa kanshi tace "Autan maman ai na sabane da kaima mace ne ai da zan koyama ka ne ya ƙaratu injin dai nata ƙoƙari?" "Karatu alhamdulilah, Allah ya sawaƙe ko dani macece bazan yarda nayi ta saka hijab kullum kamar wani kala." Duk wa'inda ke gun su kwashe da dariya banda umma da duk haushi suke bata, sai Fahad da yayi murmushi dan bai cika yin magana ba kokuwa kace ka ganshi yana dariya sai ajima sabida shi magana ma wahala take mashi bare yayi dariya idan yana ga yuri zaya iya ƙinyi magana duk abinda kuwa za'a ce har abada gun ba zai ce komai ba wani lokaci ba har mantawa ake da yana gun kusan halinsu guda da AFREEN saidai itata ma fishi yin magana. Papa yace "Imran bakada dama" "Wallahi papa da gaske nake inada ni mace ne bazan iya irin na anti AFREEN ba gaskiya." "To kuma sai Allah ya fito dakai a namiji." papa ya faɗa yana murmushi. Aiko da sauri Imran yace "Inda naji daɗi kenan." Nan ma dariyar sukayi sun tsagaita dariyar ne Tanti tace "Gaskiya AFREEN ki rage saka niƙaf da mayan hijaban nan naki idan bahaka ba taya zaki wani zai gangi yace yana sonki har kiyi aure nida nakeson ace tare dake da Khairat za'a aurar a lokaci guda kinga maman Fauziya zata dinga mana kurin cewa zata aurar da ɗiyar ta amma kinga idan auren Khairat da naki yazo lokaci guda babu batun mana kuri." "Ah to faɗa mata sabida kunfi kusa." maman ta faɗa Ita kuwa AFREEN duƙe kanta tayi tare da cewa "Kai Tanti aure nikuma tun yanzu." Tanti tace "Ban gane miki nufi da tun yanzu ba kina nufin baki isa aure bane ko miye? to ko Zeinab yanzu aurar da ita ake bare ke masha Allah da kika girme mata sosai sabida kin bata kusan shekara 6." AFREEN dai kanta a ƙasa bata ƙara cewa komai ba." Sai papa yace "Haba Sakina jimin kinason hana min ɗiyata ƙarasa cin abinci duk kinsa taji kunya, ai irin su AFREEN har gida Allah ke kawo masu nagartacan miji nagari wanda zai kula da ita ko bayan ba ran mu insha Allahu zakusha mamakin kalar mijin da zaizo mata har gida ba tareda ita kanta ta shiryawa hakan ba." Tanti tace "Hum to muna zuba ido mu gani tunda ka ƙule mata gidin amma nidai kam dole a rage saka niƙaf ɗin nan sabida so nake na aurar da ɗiyata da yuri ah to." "Karki damu ai zata sumu ne koda kuwa cikin niƙaf ne shi aure Allah ke haɗa shi kuda ke ƙanin sabida saka niƙaf ɗin da take yi samarin za suyi tunanin matar aure ba haka bane budurwa nawa ke saka niƙaf amma kuma ta sami mijin aure ai Allah ya banbanta mai aure da mara aure ko da kuwa cikin niƙaf ɗin ne za'a iya ganewa." Papa ya faɗa tare da kallon gun da AFREEN take da har yanzu bata ɗago da kanta ba. "Allah sarki to Allah nuna min wannan ranar da AFREEN zata zo tace anti ga sirikinki nan yazo gaidaki kai ranar kowa sai yaga kwasar shoki aka kara kwashewa da dariya har yanzu dai banda Umma da suka gama ɓata mata rai ƙiris take jira ta fashe, AFREEN ma sai da ta ɗan murmusa Haka dai suka yi ta raha da farin ciki har aka kammala cin abincin, AFREEN ta ɗago ta dubi mahaifin na tace "Papa anjima inason zanje gidan anti Fauziya na kwana biyu ba mu haɗu ba sai ta waya, idan mun taso daga islamiyya sai na biya tacan daga sai nayo gida." Kamin papa yayi magana Zeinab tayi "saurin cewa "Dan Allah anti ina zuwa nima na jima bangan taba." da khair ta samu tayi maganar dan tunɗazu take son tayi magana tanason tsoma bakin ta cikin cikin firar da suke amma umma ke hararen tana mata nunin da inta kuskura tayi magana sai tayi maganin idan suka gane ɗaki." Aikuwa itama umman da sauri tace "Jacan dan Allah da bakinsa san ciwon kanki ba ni anya kuwa Zeinab ba hurhuran ki akayi min a asibiti ba irin wanga abu na kutsa kanka inda ba'asan darajar kaba to dan ubanki babu ida zakije shegiya mai kama da maƙiyan ta kwakwata na rasa yanda akayi baki yo halina ba ko da yake yawan zama tare da masu mugun hali ai dole ki koy........ Bata ƙarasa faɗar abinda tayi niyar faɗa ba papa ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu sannan yace "Wallahi salamatou ki fita daga idona na rufe yanzu gabana kike zagin yarinya nan ta uwa ta uba ko kunya bakiji kuma ko kara babu, in ba abinki ba aikece mai mugun halin babu mai fatan ya yi hali irin naki kuma kaki koma sheganta min yarinya dan ni ubanta gani a kusa, abu na biyu shine sai taje gidan yar uwata dan baki isa ki rabamin kan ɗiyaba." Dama tunda papa ya fara magana Fahad da Imran suka bar gun haka Safina da Amira da hamida ma su bar gun yayi saura daga maman sai tanti da umma da kuma AFREEN da Zeinab, maman har ta miƙe zata bari yurin papa yace ta dawo ta zauna." Sannan ya juwo gun su AFREEN yace "Ku tashi kuje daga lokacin zuwa islamiyya yayi kuyi tafiyarku daga can sai ku wuce gidan Fauziyar hada su Safina kuje ku duka kukai mata ziyara." AFREEN ta kalli papa da murmushin ɗauke afuskarta ta ce "To shikenan papa mun gode." Yace "Akwai saƙo dana bayawa mamanku nace ta bada aikaiwa Fauziya tunda zaku tafi to ku tafi mata dashi." Insha Allahu papa AFREEN ta faɗa tare da barin gun itama Zeinab tabi bayan kowa ya koma nasa daƙin umma sakin tsaki tayi tare da barin gun bin ta papa yayi da kallo har ta ɓacewa ganinsa ransa du a ɓace ya juwo da niyar yin magana maman tayi saurin cewa "Dan Alhaji na kada kabari abinda umma Zeinab tayi ya ɓata maka rai idai halinta ne ai ka riga ka saba kuma ina mai tabbatar maka da watarana zata daina dan Allah kayi hakuri ko kaɗan bani kaunar ganin bacin ranka mijina." Aiko a take papa ya washe baki yana cewa "Allah kuwa sarauniya ta?" ɗan shiyasa nakeson zama a kusa dake kullum kina faranta raina baki bari wani ya bata min shi dan haka kullum nike ƙara godewa Allah da ya banike a matsayin mata aurena." Haka dai datijawan nan sukayi ta faɗawa junansu kalaman soyayya kamar dai wasu ƙananun yara, Tanti dage zaune wajan da suka gama ɓata mata rai ta sulale ta barsu nan ba tarare da sun saniba dan kuwa su sun ma manta da tana yurin zauna a riga da an tuno da soyayya yarinta. AFREEN na shiga cikin ɗaƙi komawa tayi kan gadon ta kwanta sannan ta kuma janyo wayar da ta bar datar a kune ne tun da zata fita kumawa tayi cikin group ɗin da ta bari suna hira taga yau duk maganar da suke akan tane nafa itama ta biye masu suna ta fira cikin nishaɗi da farin ciki kamin daga can taga saƙo wata sabuwar number ya shigo mata fita tayi daga group ta koma wajan bakuwar number kamin ta buɗe saƙon sai tayi ta tunanin to wacece ta turo mata da saƙo ta danganta saƙon da na mace ne sabida tasan babu namijin da yasan number ta inba cousins ɗin taɓa kuma sun ɗin ma ba kowa keda ita ba saƙo ukune aka turoma ta ta baƙuwar number. Buɗe saƙon tayi a take gabanta ya yanke ya faɗi da sauri ta tashi zaune cike da firgici tana ƙara karanta abinda ke cikin saƙon tana ganin kamar ba gaskiya bane abinda ta karanta, cikin ƙanƙanan lokaci jikinta yafara rawa dandanan yanayin ta ya canza ƙarara ake hango tashi hankali a tare da ita bata masan lokacin da wayar ta kubece ta faɗi ƙasa ba saida taji ƙarar faɗuwar ta Batabi ta kan wayar ba ta faɗa duniyar tunani. Ga saƙon kamar haka.................................. Ku biyoni don jin wane irin saƙone ya firgita AFREEN har haka 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutun_ _Niger_ Wattpad@nazichou 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003 _BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_ Page : 25 & 26 Buɗe saƙon tayi a take gabanta ya yanke ya faɗi da sauri ta tashi zaune cike da firgici tana ƙara karanta abinda ke cikin saƙon tana ganin kamar ba gaskiya bane abinda ta karanta, cikin ƙanƙanan lokaci jikinta yafara rawa dandanan yanayin ta ya canza ƙarara ake hango tashi hankali a tare da ita bata masan lokacin da wayar ta kubece ta faɗi ƙasa ba saida taji ƙarar faɗuwar ta Batabi ta kan wayar ba ta faɗa duniyar tunani. Ga saƙon kamar haka: *ASALAM ALEIKUM MALAMA AFREEN DA FATAN KIN WUNI CIKIN KOSHIN LAFIYA, NI SUNANA KAMAL A GASKIYA TUN DA NA GANKI NAJI KIN KWANTA MIN DUK DA BAN TAƁA GANIN FUSKAR KI BA AMMA NAJI INA ƘAUNAR KUMA NASAN KE BA MATA AURE BACE SABIDA SAIDA NA BIBIYEKI HAR NAGANO DA HAKAN KO NUMBER WAYARKI SAIDA NA WAHALA SOSAI WALLAHI HAR NA FIDA RAI DA SAMU SANNAN ALLAH YA TAIMAKE NI NASAMU AFREEN WALLAHI BADA WASA NAZO BA NI AUREN KI ZANYI DUK DA BASANIN KAMAN NIKI NAYI BA ZAN ZAUNA DAKE DA KO WACE IRIN KAMA KO DA KUWA DAGA BAYA NA NA GANKI WALLAH KE MAI KYAUCE KO AKASIN HAKA WANNAN BA MATSALA TA BACE, KAWAI ADDINI DA NA LURA KINADA SHI YAJA HANKALI NA GA REKI AFREEN INA SONKI INA ƘAUNARKI DAN ALLAH INA JIRAN JIN HUKUNCIN DA KIKA YANKE DAN ALLAH BANDA SHARIYA MASOYIYATA INA JIRAN JI RA'AYIN KI A KAINA KUMA IDAN AN BAN DAMA NAZO HAR GIDA NA GABATAR DA *KAINA* * AFREEN da ta faɗa cikin duniyar tunani a can cikin ƙasan zuciyar take waye wannan a ina ya samu number na ya'akayi yayi bincike a kaina yasan banda aure kuma yasan sunana duk boye kaina da nake saida aka samu wanda zai nemo asalina. Ƙarar da wayar tane tayi ya dawo da ita duniyar tunani data lula da sauri da duƙa ta ɗauko wayar da ta faɗi ƙasa kamin ta ɗago tana duba screen ɗin ganin me kiran nata yasata sakin wani sanyenyen murmushi a take ta ɗauki kiran ta kara a kunne tare dayin sallama da murmushi ɗauke a fuskar ta, daga ci wayar aka amsa sallamar tare dacewa "Hum sister ashe kina a raye amma kika manta dani har haka?" Wani murmushin AFREEN ta ƙara saki sannan tace "Haba rabin raina kin san hakan ba halina bane wallahi karatu ne ya ɓatar dani ga na école ga na islamiyya inba dan haka ba ai kinsan ba zan iya mantawa dake ba dan Allah ki hakuri my Fanna kina raina ban manta dake ba." Daga cikin wayar wada aka kira da Fanna tace "To shikenan my rabin rai ƙorafi ya ƙarɓu nasan da ba zaki manta dani ba to ya kwana da yawa kuma yaushe ne sabkar ku ta tahafiz?" "Kwana da yawa sai alkairi cœurly (heartly) nan da sati ukune saukar insha Allah oubien tu va venir pour participer (ko zowa zakiyi dan ki halarci saukar)?" "Oui cœurly je veux venir s'il plaît à dieu comme on sera en congé d'ici une semaine je veux vraiment participer pour la deuxième fois à ta sauka comme ta première sauka j'étais à Maradi et aussi même celle là je participerai insha je viendrai de Diffa jusqu'à Maradi juste pour entendre ta voix entrant de lire le coran pour la deuxième fois devant beaucoup de personnes woow Macha Allah que le bon dieu nous montre ameen,("Yes heartly I want to come please God as we will be on leave within a week I really want to participate for the second time in your sauka as in your first sauka I was in Maradi and also even this one I will participate insha Allah i will come from Diffa to Maradi just to hear your voice coming in to read the quran for the second time in front of many people woow Masha Allah may the good god show us ameen)." "Woow je serai très heureuse si tu viendras cœurly (Woow I'll be very happy if you come heartly) tu va venir quand? (yaushe zakizo)?" "Kai cœurly irin wannan gaggawa haka, ai ni nace zan zo? to ki zuba ido bazata zan miki." Fanna ta faɗa AFREEN tace "Haba cœurly kada kimin surprise (bazata) mana ki sanar dani koda lokacin zaki shigo bus ne please." Dariya Fanna tayi tare da cewa "To zan duba naga ni idan zan iya sanar dake ina papa da maman da tanti da umman Zeinab duk ko lafiya ko?" "Lafiya lau suke alhamdulilah, ya su anma da baba suke ina ƴar ƙanwata Aicha da Sagir? wallahi nayi kewarsu sosai kamar dai na bar maraɗi nazo na ganku nakeji amma dai idan zakizo tare da Aicha zakizo ko?" Fanna tace "A'a ni daya zanzo sai ki bari idan zan dawo sai ki biyoni kizo ki gansu in har kewar ta gaskiya ce." "To shikenan zan nuna miki kuwa nayi kewarsu." "Dan Allah ki gaida min su anma sosai da sosai idan kuwa Aicha na kusa ki bata wayar mu gaisa." "Bata kusa ta tafi islamiyya Fanna ta faɗa a taƙaice." AFREEN tace "Idan tazo ki gaida min ita." "Zataji insha Allah cœurly wallahi sai nakeji kamar ace har yanzu a gari guda muke nima ki gaida min ƴan gidan baki ɗaya sai anjima dama nayi kewarki ne sosai nace bari na kiraki." "Wallahi cœurly sosai nima nayi kewarki amma insha Allah sai kun dawo Maraɗi ko kuwa mu haɗe a University guda zamu dai kasan da juna yuri ɗaya insha Allahu." Fanna tace "To Allah ya yarda wai ina Hasina? kwana biyu itama bamu gaisa ba ki gaida min ita." "Zataji insha Allahu," AFREEN ta faɗa ataƙaice. Sannan Fanna tace "Sai musake waya naji anma na kirana." Ba tare da ta jira abinda AFREEN zata cewaba ta katse kiran ta tafi idan mahaifiyarta ke neman ta. **** **** **** *WACECE FANNA* Fanna Musa ƙawar AFREEN ce tun suna yara a tare sukayi primary da secandary mahaifinta da mahaifiyarta barebari ne na garin Diffa aiki ne ya dawo dashi Maraɗi kuma hakama yanzu aikin ya ƙara mayar da shi mahaifar sa wato garin Diffa, sanadin ƙawace da muguwar shakuwar da ke tsakanin AFREEN da Fanna yasa iyayen kula amintaka wato maman mahaifiyar AFREEN aminiyar Anma ce mahaifiyar Fanna sabida maman batada wata abukiyar shawara kamar anma haka papa suna mutunci sosai da baban Fanna, yanzu haka Fanna da iyayen su koma Garin Diffa da zama sabida aiki da ya dauke su ya mayar da su can kuma dama nan ne garin su na haihuwa. **** **** **** AFREEN na gama wayar idon ta suka ƙara sauka kan saƙon da kamal ya aiko mata a lokacin ya ƙara turo da wasu saƙunan ku san guda huɗu bata bi ta kan saƙon ba kawai ta'ajiye wayar ta nufi wordrobe don canza kayan jikin ta zuwa na islamiyya, akayi sallama tareda buɗe ƙofar aka shigo amsa sallamar tayi tana kollon bakin kofar, Firdaoussi ce cousin ɗin ta shigo da sauri AFREEN ta saki hijab din datake ƙoƙarin sakawa da gudu ta nufita ta rungume ta sakin murmushi tare da cewa "Sannun ki da zuwa cousin wallahi tu m'a beaucoup manqué (I miss you a lot) naji daɗin ganin ki tana faɗi haka tare da rabata da jikin ta itama Firdaoussi tana murmushi tace "Gashi ai ni da nafi kewarki nazo naganki cousin yanzu dai kam kin rage ziyara." AFREEN tace "Firdaoussi ko ranar naje gidan ku ba kainan ke ɗin ce da wayon tsiya." "Ah habadai AFREEN da kikaje baki sameni ba ai sai kikirani duk abindab nake sai na barshi na zo kuma kinga mama bata sanar dani kinje ba nasan ko ta manta." "Eh nasan mantawa tayi amma naje wallahi ko sati ma ba'ayi ba, yanzu dai zo ki zauna na barki a tsaye naje na kayi maki abinda zaki ci." tare da jawo ta ta zaunar da ita saman babbar kujerar dake cikin ɗakin. Firdaoussi tace "Kai cousin wallahi a ƙoshe nake sai da nayo breakfast daga gida kamin na fito yanzu kinga fah yanzu ƙarfe tara da rabi ne kawai ban daɗe da yin kariba, yanzu idan da dambu nama ki kayomin da ruwa masu sanhi sannan ki kara gudun AC dakin nan zafi sosai naje kodan nabiyo ranane." To shikenan ƴar uwa kiyi kamar kina cikin ɗakin ganinan zuwa," AFREEN ta faɗa tare da ɗaukar remote ɗin kuna AC ta ƙara mata gudun ta sannan ta fice a ɗakin. Bata jima ba ta dawo da plet dauke a hannu ta ɗayan hannu kuwa da jus (juice) mai sanhi sosai da kofi ta'ajiye a gabanta tace "Sarkin son dambun nama to bismillah taso kici kinyi sa'a akwai shi jiya maman tayi shi." AFREEN ce ke maganar Ɗagowa daga ɗan kishingilan da tayi tana murmushi shi tace "Kai AFREEN nice ma sarki cishi kenan ai duk son dambun namana ke kinfini ai nima dake na koya, ya nagangi da kayan islamiyya ko tafiya zakiyi ne?" Firdaoussi ta faɗa AFREEN tace "Eh wallahi shirin islamiyya ne nayi baga hijab ɗin can ba da na ganki na jefar dashi a wajan can dan murna, amma tunda kinzo bari naje na sauke su Zeinab a islamiyya sai na dawo muyi hira nasan dai ba banza ba aka zomin ziyara ba da safan nan." Murmushi Firdaoussi tayi tace "Sai kin dawo bari nima nagama cin abincin na sai naje na gaida su maman sabida da nashigo falon babu kowa, kuma nasan zan samu gani papa tunda nasan yau yana gida na kwana biyu banzo na gaida sa ba yau zanje na ɗan zanta da ubana." AFREEN tace " To shikenan bari naje na dawo to kamin nan kin gama komai, nufar idan ta jefar da hijab ɗin ta tayi ta saka sannan ta fita a ɗakin da niƙaf a hannu ta. Tana dawo ta tardo Firdaoussi tana kallo a wayarta da sallama tashigo ɗakin kamin take fida hijab ɗin ta linke ta mayar dashi ida yake tare da fida kayan islamiyyar suma ta nike sannan ta saka wata haɗaɗiyar dagowar riga mara nauhi sabida Allah yayiwa AFREEN son saka riga doguwa don yawancin kayan jikinta dogayan riguna sunfi yawa, dawowa tayi kusa da Firdaoussi ta zauna Sannan tace "To sis toshi muyi hira." Miƙewa Firdaoussi tayi zaune sannan tace "Malama AFREEN que babu komai a wayarki sai wa'azi." AFREEN tace "To miki keson nasaka a ciki banda wa'azin ƴar uwa." Murmushi sukayi su duka kamin suka ci gaba da fira. Firdaoussi tace "Yawa AFREEN yanzu ina ɗaukar wanki naga anturo miki da wani sako baki bayar da amsa ba se kawai na'ari bakin ki naci maki dusa na mayar maki da sakon." AFREEN najin haka ta gane ko wane saƙo take nufi da sauri tace "inna lilahi wa inna ilaihi raji'un miyasa kika mayar ban fah San ko waye ba kawai naga ya turo man da message ne." Eh nagani ai tunda naga inda yake gabatar maki da kansa AFREEN ke ce kike hani da yiwa ɗan adam wulaƙanci, amma kece yau ke shirin yin wulaƙanci ga ɗan uwanki Musulmi, bawani mugun abu ba yake neman gunki sonki ne kawai yace yanayi miyasa bazaki saurare shiba kiji da miyazo Allah kaɗai yasan yanda yasha wahala kamin ya samu numbaki duba ga wanda babu me number ki ko a family mu masu numbaki basu wuce muntun biyar amma yayi yanda yayi ya nemo numbaki sannan ya nemi labari a kanki ki basa dama mana kiji dami yake tafe." Firdaoussi ta faɗa tana mai kallon AFREEN. AFREEN tace "Haba Firdaoussi kisan fah karatu nake babu soyayya a cikin tsari na yanzu sabida bazan iya haɗa karatu da soyayya ba kuma kina gani shima fah bai saniba bai taɓa ganin fuskata ba to ganinki duk ranar da ya gani ni akwai matsala kuma duka shekaru na 18 amma harzan fara cazawa kaina ƙwaƙwalwa a wani batun soyayya ina gudar wa kaina abinda bazan iya ba ne shiyasa amma banda wannan Ni banada niyar wulaƙanta shi sabida kin san hakan ba halina bane." Firdaoussi tace "Yo ai rashin mayar masa da amsa shi zai iya fassara hakan da wulaƙanci kuma miye a cikin soyayya da ba zaki iya haɗa ta da karatu ba sannan ita soyayyar kika yiwa ƙanƙanta AFREEN shekara 18 din ne ba masu yawa ba ko so kike sai bayan ki sami degree da diploma sannan zaki nemi mijin aure a lokacin da yuri ya rigada ya ƙuremaki? to tunyuri ki fida wannan a ƙidarta daga cikin kanki kawai ki saurare shi koda kina cikin karatun ne kina iya yin soyayya harma kiyi aure can gidan mijin sai ki ƙarasa karatun hakan shine daidai ba wai ki tsaya jiran sai kin gama karatu ba sannan kuma ai ba munmunar kama gareki ba tunda muma muka iya jure kallon ki kowa ma zai iya idan har yasa ba AFREEN wannan fitinanan kyau da Allah yayi maki idan an gani ai za'ayi tunani ke kika tsara kanki kuma Allah kaɗai yasan gidan wadan zai wannan kyau naki ya adana wallahi dole mutum ya ganki zaice kamar aljanna dan masifar kyauki, haka dai Firdaoussi tayi ta nunawa AFREEN mahimmanci kula KAMAL da jin abinda yazo dashi har AFREEN ɗin ta yarda zata saurare shi ɗin. Suna zaune suna fira Firdaoussi na nunawa AFREEN yanda taka mata ta mayar wa KAMAL da saƙo, aka buɗe ƙofar ɗakin aka shigo da sallama, Hasina ce ƙawar AFREEN wada suke school guda tashigo haka itama AFREEN taje ta tarbota ta rungume ta tare da cewa "Welcome besty tana murmushi tareda farin cikin ganinta sannan suka saki juna tare da nufar bakin gadon kusa da Firdaoussi suka zauna Hasina da Firdaoussi suka gaisa sosai sabida su san juna tun ba yauba ta dalilin AFREEN sannan sukaci gaba da fitar su cikin aminci da kaunar juna, bayan sallarsa azahar kuma bayan suci abincin rana Hasina tace ku tashi muje ku rakani KALLA TRANSA MALL suyo shopping, AFREEN tace "To muje daga can sai mu wuce gidan anti Fauziya." Tare suka miƙe suka ƙara fesawa jikinsu turare sannan Hasina da Firdaoussi suka ƙara ƙara murza hoda ga fuskar su banda AFREEN da ita dama ba ma'abuciyar kwalliya bace uwa uba ita niƙaf ma take sakawa, fita sukayi a ɗakin AFREEN taje tayiwa maman sallama ta fito a falo ta tardo Zeinab tace "Zeinab jiki ki sako hijab ɗin ki mu tafi gidan anti Fauziya." Da sauri Zeinab da mike ta faɗa dakin su dan doko hijab ɗin ta itakuwa AFREEN ta ɗaura niƙaf ɗinta sannan suka fito gun ajiye motoci suka sa AFREEN ta jawo motar sannan suka shiga dai dai nan Zeinab ta ƙaraso itama ta shiga me gadi ya buɗe masu get suka fice daga gidan. **** **** **** Yau Alhamis ranar da AFREED yayi wa Tanti alkawarin zuwa Maraɗi hak kuwa aka tun jiya suke Ali ya gyara kayan sa da na AFREED aka suma ƴan biyun Momy sun shirya misalin ƙarfe 9 na safe sukayiwa garin Niamey ban kwana suka ɗau hanyar Maraɗi tare da addu'ar Allah ya kiyaye hanya daga iyayen, a moto ta sukayo tafiyar sabida AFREEN yace bazai yi balaguro cikin ki jirgin ba don a kowane lokaci indan zai yi balaguro to a jirgi ne to wannan karon wace a mota yake sabida yanason yaga hanya sosai sannan ya hana duk wani escort ɗin sa biyo sabida baya don ta kura soyake yayi rayuwar kamar shi ba wani mai matsayi bane idan yaje Maraɗi, Ali ne kejan motar AFREED na zaune wajan mai zaman banza su kuwa ƴan biyun Momy suna baya ana ta ɓana rai sabida AFREED ya hana su bin jirgi yasa zasu wahala a mota, sosai Ali ke gudu da motar ita kuwa Tanti dandanan ta kiransu don jin idan suke, yau Tanti tana cikin farin ciki AFREED zaizo tun safe take ta gyare gyaren ta Da yake lafiyayar motace sabuwa fil da ita ƙarfe 3:40 suka shigo garin Maraɗi wata sanyayar ajiyar zuciya AFREED ya sauke ya na jin kansa cikin wani matsanancin farin ciki alhamdulilah ya furta a zuciyarsa yace nayi nesa da takura da yanzu ana nan duk an zagaye da sunan tsaro ya sake cewa alhamdulilah. Anguwar zaria Ali ya nufa bakin wata tangajejiyar get Mai kyau da ɗaukar ido Ali ya ja ya tsaya sannan ya dana hon da gudu mai gadi ya leko ta ƙaramar ƙofa dan ganin masu dana hon ɗin idansa bai sauka a kowa ba sai ga AFREED ai kuwa yana ganin sa ya ganesa tare da yin saurin rufe ƙaramar ƙofar ya wangale masu babba ƙofar a take Ali ya dana hancin motarsa a cikin gidan gudu mai gadi yayi ya bi bayansu tareda yafito mai ba flower ruwa ya mai nuni da ya biyo bayan sa a guje shima yabi bayan mai gadin, inda ake ajiye motoci Ali ya nufa yayi parking ɗin motar tasu kamin suke fitowa baki ɗaya duk a gajiye gudu gudu sauri sauri Tanti takeyi dalilin jin zuwan shalelen ɗan nata tana kawowa ida suke tayi saurin rungume AFREED tane cewa "Alhamdulilah yau gani ga ɗana AFREED Allah yayi zan ƙara ganin ka cikin garin Maraɗi na godewa Allah da ya kawo min ku lafiya" ta faɗa tana rabashi da jikin ta sannan ta juya ta kamo hannu Ali tace "Ɗana sannu ka da ƙoƙari AFREED ya baka wahala ya hana ku biyo jirgi ahalin shi ba tuƙa motar zaiyi ba kawai dan ya gajiyar min daku." Murmushi Ali yayi, sannan ta mayar da duban ta gun su Farisa tace ku ƙaraso mana ƴan biyun Momy ƙaraso wa sukayi da murmushi kwance a fuskar su riƙe hannayensu tayi sannan tace "To ku huce muje ciki kusamu kuyi wanka ku huta ku ci abinci." Hannu ta riƙe da su Fariya tayi gaba su AFREED na bin bayan ta tana jinta cikin da farin ciki haka suka ƙarasa cikin wani haɗaɗen falo mai girma man gaske duka suka zube a kujerun dake falon a matukar gajiye AFREED ya ɗago yace "Tanti ina yuni mun sameku lafiya?" "Lafiya lau alhamdulilah yasu Falmata dafatan kun barosu lafiya." Nan dai suka shiga gaisawa kamin AFREED ya miƙe yace da tanti shi zai yayi wanka sannan ya kwanta dan ba ƙaramar gajiya yayi ba sabida rabon da yayi balaguro a mota yanzu kusan shekara goma sha biyu kenan baisan zaiyi irin wannan gajiyar ba da jirgin zasu biyo, ɓangaren da aka gyara kawai da sabida shi da Ali ya nufa sabida yasan shine dan tun yana yaro yake, idan yazo nan ne suke sauka, kuma kullum gyara ɓangaren ake kamar akwai mutane a cikin kokuwa ace mamalakin yurin kullum yana zuwa wannan zuwa ma da zaiyi hada pinti aka canzawa ɓangaren aka fitar da kayan dake ciki aka zuba sabi masha Allah andai ƙawata ɓangaren sosai abin gwanin sha'awa. Shima Ali Bin bayansa yayi, binsu Tanti tayi da kallo da murmushi ɗauke a fuskar ta kamin take mayar da kallon ta gun su Farisa tace "To ku ƴan biyu ku taso muje ku ci abinci tun da su wa'ican sun tafi su yi bacci su huta." Fariya tace "Tanti muma bamu tare da yunwa sai gajiya idan muka yi wanka muka huta sai mu ci." Tanti tace "To shikenan ku taso muje sai kuyi wanka ku huta kuma bin bayan ta sukayi, kiran ma su aiki tayi tace masu su shigo masu da kayan su cikin ɗakin sabida mai gadi da mai ban ruwa bakinsu falo suka shigo dasu. AFREED sunayi Wanka suka yi sallar la'asar sai bacci kowane daga cikin su ya kwata kwanan gajiya, sune basu tashi ba sai da ana kiran sallarsa magariba, sukuwa su Fariya har saida Tanti ta tayar da su sannan suka tashi. Wanka AFREED yayi tare da ɗauro alwala sannan ya fito a gagwace ya shafa mai da turare tareda zura doguwar jalabiya ya fito da sauri dan yaji ana ƙoƙarin tayar da sallah a masallaci dake kallon gidan yana fitowa ya gamu da Ali se kawai suka jera suka tafi tare sune basu dawo gidaba sai bayan sallar isha suna shigowa mai gadi yayi saurin tasowa yana cewa "Sannu da zuwa Alhaji ƙaramin da fatan an iso lafiya?" Murmushi AFREED yayi yace "Lafiya lau baba mai gadi mun sameku lafiya?" "Lafiya lau to sannu ku da zuwa?" Da yawa Ali ya amsa sunan suka bargun duk masu aikin gidan sun san AFREED da Ali da zarar ance maka AFREED yazo to sun bar zama ba kuɗi ko da kuwa bai da su sai yaje ya karbo gun Tanti ko gun mijinta ya shiga raba musu tun yana yaro haka yake bare yanzu da yayi shekaru ba zoba gashi duka sun matsayin sa a yanzu suna sane da sai sun sha kuɗi sosai kamin ya tafi. Suna shiga falon Tanti suka tardo tare da yaranta ƴan mata wato Khadijah da suke shekara guda da su Fariya sannan Amal mai bi mata sai kuma Ummi mai sunan kaka su AFREED ta wajan uba da gudu yaran suka tashi suka nufi su tare da rugume suna oyoyo yaya AFREED oyoyo yaya Ali banda Khadija da takasa ƙarasawa tayi tsaye a kusa da su ta sunkuyar da kai tana murmushin, don sosai take jin kunyarsu bama kamar Ali da take matukar so amma shi bai masan tanayi ba. Da murmushi kwance a fuskar AFREED yace "To ku cikamu kada ku kayar damu sakin su sukayi suna dariya, cike shagwaɓa Ummi tace "Yaya ni sai ka ɗauke ni." Murmushi AFREED yayi sannan yace "Kai mai sunan kaka har yanzu wannan shagwaɓar tana nan." Jan hannu ta yayi ya zauna kan kujera ya ɗoketa ya aza kan ciyoyin sa yana mata dariya itama dariyar tayi, Amal kuwa ta kamo hannu Ali tace "Yaya zo muje ka zauna bari yaya AFREED da wacan rigima miyar." Binta yayi suka zauna a ɗayar kujerar ya na mamakin yanda AFREED ya saki jiki ba kamar da idan sun zoba yau shine hada rugume Ummi yana surutu haka." AFREED ne ya lura da Khadija dake tsaye tanata murmushi kanta a duge yace "Khadija ke kam yaushe ne zaki daina jin kunyar mutane ne wai?" zo nan naji miyasa kike da kunya haka ne kamar ɗiyar Fulani?" Ƙarasawa tayi kusa dashi ta zauna a kasan kapet daidai ƙafafun sa, sannan tace "Yaya ina yuni ya hanya da fatan kunzo lafiya?" "Lafiya lau mukazo Khadija mun sameku lafiya?" Saida taƙara sune kanta sannan tace "Lafiya lau yaya ya kuka baro su Momy?" "Lafiyar su lau kidaina jin kunyata kinji ƙanwata ki saki jikinki muyi fira." Murmushi kawai tayi ta ƙara duke kanta seda ta daci kallon Ali kamin tace "Yaya ina yuni anzo lafiya?" Wani haɗaɗen murmushi ya sakar mata wanda shi kanshi baisan yayi mata shi ba ita kuwa anan take wata soyayyar ta ƙara shigar ta ai da sauri ta kauda idonta daga gareshi. Ali ya amsa da "Lafiya lau Khadija ai ni yau ina fushi dake ne sabida kwata kwata yau baki ganina sai AFREED?" Kara sunkuyar da kan nata tayi tana jin soyayyar sa na ƙara shigar ta sabida duk wani harafi da zai faɗa a maganarsa tsikar jikinta tashi take, tace "A'a yaya ba haka bane?" Ali yace "Yane idan bahaka bane ba gashi gunsa kikaje kika zauna ba, to idan dai ba haka bane ki taso ki dawo kusana muyi hira." Kasa tashi tayi daga inda take sabida ita kaɗai tasan halin da zata shiga idan har ta koma kusa dashi anan ɗin ma da take zaune ya ta ƙara bare ta koma kusa dashi." Murmushi AFREED yayi yace Khadija tashi ki koma kusan sa shi nikam Ummi ta isheni abukiyar hira shi kuwa ai tunda surutu ya masa yawa ai ko mutum goma zai iya haɗawa yayi caca baki dasu." Tayi niyar tashi sai ga su Fariya sun fito daga ɗaki, suna ƙarasowa nan cikin falon su shayo kwalliya masha Allah sai zuba kamshi suke. Suna ƙarasowa suka nemi guri suka zauna tare da cewa "Tanti ina yaya Umar ne yazo ya kai yawo." Tanti dake ta sauraran ɗiyan nata tun ɗazu tana murmushi tace "Yanan saman hanya tessaoua yaje tunda safe wajan wani aiki yanzu kunga ya shigo to wai da kukayi shirin fita abinci fah?" Ali yace "Gaskiya dan ni yinwa nakeji kusan ni bana jimirin yunwa ko." Tanti tace "Shikenan ku tashi muje kuci man ko kuwa a kawo abincin nan?" Ali yace "Tanti akayo nan kawai sai ci a saman kapet." Haka kuwa akayi suka nemi guri Fariya Farisa da Khadija sukaje su ɗauko kulolin daga kan dinning su ka kawo su nan cikin falon Khadija duƙa tayi servir ɗin su ta zubawa kowa sannan suka gewaya gaba ɗaya suka faracin abincin cikin farin ciki........... 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 ZAMBA CIKIN AMINCI 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *_Wattpad@nazichou*_ 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003 *_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_* *Page* : 27 & 28 Suna cikin cin abincin Umar babban ɗan Tanti ya shigo falon da sallama ɗauke da bakinshi, gaba ɗaya suka ɗago tare suna masu amsa sallamar da murmushi ɗauke da fuskokinsu, da gudu ummi tashi daga kan ƙafafuwan AFREED taje ta rungume ɗan uwan nata, dariya yayi tare da ɗaukar ta sannan ya ƙarasa inda suke. Mahaifiyarsa ya gaida ta masa da murmushi ɗauke a fuskar tana masa ya hanya, juyawa ya gun su AFREED yana dariya yace "Wata sabon gani broh yau kaine da kanka zaune cikin garin Maraɗi a cikin falon mama, yaude kam mama zata kwana farin ciki sabida kullum bakinta ya dauke da sunanka Ita dai AFREED, broh da ace lokacin damina ne yau da Allah sai yayi ruwa bansa wace addu'a bace mama tayi har Allah ya kaɗo mata kai yau garin nan." Dariya sosai Ali yayi sannan yace "Kai AFREED kowa yasan baka son fita daga garin Niamey kowa nason ganin ka amma kaje ka zauna gu ɗaya." Murmushi AFREED yayi yace "Umar irin wannan shari haka kamar dai ban taɓa zuwa Maraɗi nan ba to ni na dawo nan da zama bakiɗaya ma ta man shari sai ta ƙare, kai kuwa Ali ɗan sa ido duk abinku baku isa ku haɗa Ni da tanti ta ba." Umar yace "Ba wani shari an san halinka ne ni yanda ma akayi ka zauna anata hira da kai haka ko ka iya ɗumine yanzu? dan nasan magana wahala take maka AFREED." Ali yace "Ashe kaima ka gano haka tunɗa zu yake ban mamakin maganar nan da yake da har yanzu banji yace ya gaji ba." Murmushi AFREED yayi baice komai ba sannan cema Umar "Yanzu dai zauna kaci abincin nasan ka kwaso yunwa idan ka gama sai ka ƙarasa min iskancin ai naga kaima ba zuwa garin namu kake ba." Umar yace "Aidai nafika tunda ni ko wata uku bayin ba da naje garin naku ba." AFREED yace "To anji zauna dai ka cika cikin ka tukun na." Zama Umar yayi sannan ya kalli su Farisa yace "ƴan biyun Momy ashe daku akazo da fatan kunzo lafiya wannan gumkin ɗan uwan nawa injin dai bai ta kura ku ba a hanya." Murmushi su kayi tare sannan sukace "Yaya ina yuni lafiya lau muka zo kuma babu abinda yaya yayi muna a tare suke maganar babu mai wuce ɗan uwan sa kamar ɗaya tasan abinda ɗayar zata ce. Umar yace "Allah ya mashi sa'a da ace ya taɓa min ku ai dan yanzu na rama maku." Murmushi AFREED yayi baice komai ba sabida ya fah gaji da maganar nan dan ba ƙaramin ƙoƙari yayi ba yau na magana mai tsayi da yayi har haka." Umar ya dubi Ali yace "Gaskiya Ali kana fama ban masan ya kake zama da wannan ɗan uwan naka ba?" Ali yace "To ya zanyi haka nan dai nike ɗan hakuri da shi kamin ya ɓata min rai na bigeshi ai matar sace ke da aiki nan gaba." Gaba ɗaya suka kwashe da dariya har da tanti, AFREED ya kalli su Farisa ya game fuska kamar bai taɓa dariya ba yace "Kun wani zauna kuna yiwa mutan dariya dan samun yuri to maza ku bar nan tun kan raina ya ɓace nayi maganin ku." sumi sumi suka tashi su duka harda ummi suka bar gun dama su daɗe da gama cin abincin har sun gyara gun da suka gama. Tanti da farin ciki ya cika mata zuciya ta kalli AFREED tace "Ji AFREED ka korar min yara ba sai ka bari ayi ta duramar nan da suba suma su rage dare tunda basu sami zuwa yawon ba." AFREED yace "Tanti kawai sai su zauna suna jin hirar mutane kawai su rai namu." Tanti tace Hum AFREED uwayan son girma." Hira sukaci gaba dayi har dare ya soma yi sannan sukayi wa Tanti sallama suka koma ɓangaren su, suna shiga Umar yayi nasa ɗakin tare da ce masu ya shiga yayi wanka dan cewa yayi tunda su AFREED sunzo to yadawo ɓangaren su da zama ya baro nasa sai kuma idan sun koma tunda ɓangaren da su AFREED suka sauka yana ɗauke da ɗakuna huɗu ne. Umar na shiga ɗaƙin shi Ali ya dubi AFREED yace "Broh yana ga yau kanta hira sosai ka saki jiki ana kwasa hira dakai don gaskiya kaban mamaki ko dai ka fara koyon yawan magana ne bansani ba?" Kallon shi AFREED yayi sannan yace "Wallahi broh daurewa kawai nake sabida tanti tana farin cikin zuwana bai kamata nayi gum da baki naba dan gudun kar farin cikin nata ya koma ciki sabida rashin magana ta duk da itama tasan ban wani cika yawan magana nayi ba, amma bancin haka wallahi nan duk nagaji da maganar da nayi yau." Ali yace "To haka da kayi yayi daidai yanzu sai kaje ka kwanta dan bakin naka ya huta tunda ma kaga dare yayi." AFREED yace "Hakane bari naje na ɗan watsa ruwa sai na kwanta." Daga nan kowa ya nufi ɗakin sa domin samun bacci da hutu mai kyau,sedai muce asuba ta gari su AFREED. **** **** **** AFREEN suna fita daga gida direct wajan shopping suka nufa suna ida shopping sukayi gida anty Fauziya, sosai tayi farin cikin ganin su haka su ka wuni gidan, a nan ne Firdaoussi ke yi Hasina maganar KAMAL, Hasina najin zancen tayi farin ciki sosai, ta ƙara bawa AFREEN kwarin gwiwar kula shi haka dai suka tasa ta a gaba suna nuna mata mahimmanci fara soyayya sukace dan Allah ta bashi dama. Sai bayan magariba suka bar gidan anty Fauziya sabida saida suka mata girki, don sunce tunda sun zo ta huta gata da tsohon ciki na wata shida kuma mai mata aiki ta tafi garin su sabida rasuwa da kakar tayi shine taje gaisuwa, da zasu tafi anti Fauziya ta haɗa kowace daga cikinsu da leda ɗoke da kayan kwalliya da turaruka masu ɗadin kamshi, ita kuwa AFREEN turaruka kaɗai ta saka mata sabida tasan ita ba ma'abuciyar kwalliya bace. Suna fita daga gidan anty Fauziya suka nufi anguwar su Hasina suka ajiye ta a ƙofar gidansu sannan suka nufi gida a bakin ƙofar gidan su Firdaoussi AFREEN taja ta tsaya sannan itama Firdaoussi ta sauka tana masu saida safe, idan masu karatu basu manta ba ai nace muku gida biyu ne a haɗe waje guda wato gidan Alhaji Sadisu mahaifin su AFREEN da na yayan shi Alhaji Adamu wanda shi Alhaji Sadisu ne ya gina wa ɗan uwan nasa dan haka suke makwabtan juna katanga ce kawai ta rabasu to Firdaoussi ɗiyar Alhaji Adamu ce kuma itace suke ƴan wari guda da AFREEN. AFREEN na shiga cikin gidansu tayi parking ɗin motar ta wajan da suke ajiye motoci sannan suka fito ita da Zeinab suka nufi ɓangaren Hajiya Zakiya wato kaka su wada ta haifi mahaifin su, suna shiga suka tardo ta saman darduma da alama sallah ta ƙare, zama sukayi saman kujerun dake cikin folon sannan suka ce Mamy (Kaka) ina wuni ya yunin gida?" Da murmushi take kallon su sannan tace "Lafiya ƴan albarka jikoki na sai yanzu kuka dawo daga gidan Fauziyar? ɗazu Sadisu ya shigo nan nake tambayar sa AFREEN dan naga duk yau baki shigo nan ba, sai yace ai kuna gidan Fauziya." Murmushi AFREEN tayi tace "Eh Mamy wallahi sai yanzu muka dawo mun kama mata aiki ne kinsan tayi nauhi sosai cikin jikin tane ɗan wata shida amma saika kace yau ko gobe zata haihu da tsananin girman sa." Hajiya Zakiya tace "Allah ya raba lafiya, ai ita Fauziya girman ciki ne da ita." Da ameen suka amsa sannan AFREEN tace "Mamy ga tsarabarki inji anty Fauziya tace a kawo maki wannan kuwa da mukaje shopping na siyo maki dan ki motsa bakin ki." Karɓa Hajiya Zakiya tayi tanata sa masu albarka da masu fatan samun miji na gari, sannan suka mata sallama suka koma nasu ɓangaren, basu sami kowa a falon ba dan haka kowace ta nufi nata ɗaƙin dan a gajiye suke, direct AFREEN tana shiga ɗakin ta toillet ta faɗa ta yi wanka tare da ɗauro alwala dan gabatar da sallar isha'i, tana idar da Sallah tayi shirin bacci cikin wasu haɗaɗun kayan bacci farare riga da wando masu mugun kyau, sannan ta saka dogon hijab har ƙasa ta fita daga ɗakin, ta nufi ɗakin mahaifiyarta da sallama tashiga, bata sameta a ɗakin ba, a sannan ne ta tuno da yau girkin maman ne kenan ta ɗakin mahaifin su, bata tsaya komai ba ta fita a ɗakin ta nufi ɗakin tanti zaune ta tardota ta na kaɗa wani magani da tasaka ma kindurmu tana motsawa, da spoon sai ga AFREEN ta shigo da sallama saida tanti ta ɗan firgita kamin ta basar tana mai amsa sallamar tare dacewa "Yawa AFREEN dama yanzu nake cewa bari naje na kai maki maganin nan ɗakin ki kuma naga kun dawo lafiya, tunda ma kinzo da kanki yi maza zauna kisha," ba musu AFREEN ta zauna ta karɓi kofin da maganin ke ciki tayi bismillah sannan ta kafa kai ta shinye ruwa tanti ta koma zuba mata a kofin ta karkaɗe ta mika mata karɓa tayi ta kuma shinyewa kamin take mayar ma tanti da kofin tare da miƙewa tana shirin barin ɗakin. Da sauri tanti tace dakata AFREEN kada ki tafi baki ƙarasa shan maganin ba," dawowa AFREEN tayi ta zauna sannan tace "To tanti yi sauri ki ban bacci nakeji." Da sauri tanti ta ƙara ƙaɗa mata wani maganin ta mika mata, koma ƙara kafa kai tayi ta shinye, sannan kuma tanti ta miƙa mata wani magani ƙule a leda tace "Ƙarɓi wannan idan kin shiga ɗaki ki zuba shi cikin abinda kike turaren huta ki turare jikinki baki ɗaya sannan ki kwanta." Ba musu ko tambayar na miye, nan ma AFREEN ta koma ƙarbar maganin ta nayi wa tanti saida safe, tanti ta amsa da Allah tashe mu lafiya tana ƙara jadada mata cewa kada tayi bacci ba tayi turaren maganin nan ba dan taga bacci sosai a idanunta. Da to AFREEN ta amsa sannan ta nufi ɗakin ta, da shigar ta ɗakin ta dauki abinyi turaren huta ta saka a soket, sannan ta zuba magani ta turara ma jikinta shi kamar yanda tanti tace mata, tana gama turare jikinta da maganin kanta yar fara juyawa, da sauri ta fida wayar abin yin turaren a soket ta nufin gadon ta a dadafe da kyar ta iya yin addu'a barci sannan ta kwanta tanajin yanda kanta ke juya mata kuma tsikar jikinta na tashi a hankali a hankali barci ya fara figarta har ta samu bacci ya kwashe ta bakiɗaya. Ƙarfe biyar daidai na asuba AFREEN ta farka lafiya lau da addu'a tashi daga bacci a bakin ta lalubo wayar ta tayi tana duba lokacin, da sauri ta duro daga kan gadon da furta "Inna lilahi yani irin bacci ne ya kwashe ni yau haka har ban farka sallah dare ba," tana faɗar haka a lokacin har takai bakin kofar toillet buɗewa tayi ta shiga, bata jima ba tafito bayan ta ɗauro alwala tazo ta shinfiɗa darduma ta tayar da raka'a tanul fijir, tana ƙarasawa ta koma mayar da sallah asuba, da ta ida baki ɗaya ta shiga karanta suratul kahaf sabida yau safiyar juma'a ce, 6:30 ta kammala karatun ta shi tayi toillet dan yin wanka, minti 15 ta ɗauka kamin take fitowa daga wanka sannan tayi komai da ya zame mata al'ada idan ta fito daga wanka, wardrobe ta nufa ta fitar da wani haɗaɗen lace bakin da design puple riga da siket ta saka dumkin ya kamata sosai shi bai mata yawa ba kuma shi bai matseta ba sosai kayan suka zauna mata ajiki dan ba ƙaramin kyau suka mata ba gashi dama jikin AFREEN irin jikin nan ne wanda komai kasa kyau yake maka, haka ta fito kamar wata ba indiya shar da ita tayi kyau masha Allah duk da kwali ne kawai ta saka a idonta amma tayi matuƙar yaɗuwa kamar ka saceta ka gudu, a gagwace ta ciro dogon hijab ɗin ta puple da niƙaf ɗinta itama puple Wada akayi wa ado da duwatsu farfaru masu shegin ƙaili, ƙara feshe jikinta da turare tayi ta saka takalmin puple masu ɗan tsini sannan ta saɓo jakar makarantar ta tafi daga ɗakin, AFREEN tayi wannan shigar ne sabida su a makarantar su ba'a saka uniform kowa da kayen da yakeso yake zuwa makarantar. Ta tafi da niyar hawa escalier (strais) dan zu gaida papa da maman suda ke sama, sai ta tsinkayi muryar Zeinab nace "Anty AFREEN gamu nan." Juyowa tayi ta gansu su duka ƴan gidan zaune kan dinning har da papa kowa dai na wajen, ita kaɗai har babu a wajen cin abincin, juyawa tayi ta nufi dinning ɗin tana zuwa ta sakar masu murmushi tare da gaida iyayen na ta sannan ta ja kujera ta zauna ta zuba ma kanta abin breakfast ɗin sannan ta fara ci da sauri sauri, papa ya kalleta yace "Kici a hankali mana AFREEN kada ki sarƙe." Tsayar da cin breakfast ɗin tayi tare da mayar da kallon gun papa tace "Papa sauri nake yau nayi lati 7:30 muke shiga gashi 7 har da minti 12 kuma idan nace bazan karya ba, ba barina zakuyi na tafi ba." Papa yace "To maida hankali kici dan gaskiya bazaki school baki ci komai ba." ci gaba tayi da cin abincin." Tanti da tunda AFREEN ta zauna take bin ta da kallo tanisa tace "Masha Allah ɗiyata kinyi ƙyau gaskiya ke ba ƙaramar kyakkyawa bace." Ɗagowa AFREEN tayi da murmushi tana kallon tantin tace "Nagode my tanti adoré." "Karki damu gaskiya ce na faɗa, amma a zuciyarta sai tace "Narasa wane irin masifafen kyau ne kega yarinya nan kamar aljanna to Allah dai ya tsare." Umma kuwa dogon tsaki taja tsusssssss sannan tace "Cusa kai Allah raba mu da neman yurin zama, wajan biɗar a sanka har a mance dakai." Babu dai wanda ya tanka mata dan sun rigada sun san hali, AFREEN kuwa miƙewa tayi tana cewa "Maman na ƙoshi zan yuce kada nayi lati." Maman da papa da tanti da sauran ƙannanta banda umma suka mata fatan a dawo lafiya, amsawa tayi da ameen sannan tace "Zeinab yau ki bi direba sauri nake idan muka taso daga makaranta zan biyo na ɗauko ki keda su amira kinjiko?" Da fara'arta tace "To anty Allah kiyaye hanya." Da ameen ta amsa sannan ta juya zata tafi tanti tace "AFREEN baki sha zumar ki ba yau." Ba tare da ta juyo ba tace "Kashe na manta kawai sai ta nufi ɗakin tanti ta sha zumar ta fito ta ƙara masu sai ta dawo." Har ta kai bakin ƙofar falon papa ya ɗaga murya yace "Ki tafi a sannu bana son tuƙin gaganci." Ba tare da ta juwo ba tace insha Allahu papana sannan ta fita. Ƙarfe sha biyu na rana su AFREEN suka fito daga aji, jerawa sukayi itama da Hasina suna tafiya suna fira har suka kawo inda AFREEN tayi parking ɗin motar ta, ta buɗe zata shiga Hasina tace "Besty yau zakizo masallaci?" Murmushi mai sauti AFREEN tayi tace "Mi zai hana besty saide in banda lafiya ko wani cikin ƴan gidan mu abinda ban ma kan mu fatan hakan duk da dai ita lafiya bata samuwa kullum." Hasina tace "To shikenan besty sai mun haɗu a masallaci, bari na shiga ki ajiye bakin babba ƙofar makarantar dan nasan yanzu direba na bakin ƙofa yana jirana," shiga sukayi su duka sannan AFREEN ta tayar da motar suka bar cikin makarantar, saida AFREEN ta kaita har kusan motar da direba yazo ɗaukar ta sannan taja tatsaya Hasina ta fita tana ƙara jadada mata sai sun haɗu masallaci, sannan taja motar ta nufi makarantar su Zeinab. 12:40 suka isa gida AFREEN na parking motar duk suka fita, shiga falon sukayi da sallama babu kowa a ciki, dan haka duk sai suka kama gaban su, AFREEN na shiga ɗakin ta ta cire kayan jikinta ta saka wata doguwar riga mara nauhi tazo ta dan kwanta saman bed ɗin tareda sauke ajiyar zuciya ta gajiya. Ƙarfe ɗaya na rana na bugawa AFREEN ta tashi da kwanciyar da tayi ta faɗa toillet don yin wanka zuwa sallar juma'a. Ta fito cikin shigarta ta zuwa masallaci sai tashin kamshi take, duguwa riga ce baƙa sanye a jikinta da aka yiwa kwalliya da Stone ruwan gold rigar tayi masifar kyau, da hijab ɗin ta kalar golden, takalmin ƙafar ta ma golden ne amma wannan karon plat ne ta saka maras tsini, haka ma niƙaf inta golden ce ita ma, sabida yawan saka niƙaf da AFREEN take yasa kusan kowane color na hijab ɗin tanada kalar niƙaf ɗin ita kanta batasan iya adadin yawan hijab da niƙaf da takeda ba, uwa uba kayan sakawar ta bata iya musilta yawansu, dan sun lumka yawan hijaban da takeda, duk da ana fitar da zakar kayan a kowane lokaci amma kuwa kullum cikin dumka sabi ake ko aje shopping don siyo dogayan riguna da ƙananun kayan dan zaman gida, gashi kuma idan papa ya fita ƙasashen waje ya siyo masu kaya irin na can dan sosai take da riga da wando irin na Pakistan da kuma riga da buje na kanti irin na ƙasashen waje. Ta tardo su Zeinab ita kawai suke jira dan papa da matan sa har sun rigada sun tafi, haka Fahad da Imran, daga su sai masu gadi da suke jiran su fita su kule gidan dan zuwa masallaci Mamy kawai da mai aikinta ake bari cikin gidan. A gagwace suka fito suka shiga mota ta tayar da motar suka bar gidan, gudu take sosai sabida ganin da tayi lokacin tayar da sallah ya kusa gashi kuma har Zaria ne masallaci yake dan daga anguwar su zuwa anguwar da masallaci yake ya akwai nisa sosai Tana zuwa bata matsaya lura da inda zata yi parking ba kawai ta nufi idan maza ke parking ta ajiye tata motar sannan suka nufi cikin masallacin basu daɗe da shiga ba aka tayar da sallah. Ana idar da sallar malamai suka shiga yin ɗaurin aure da ya gabata ana gamawa mutane sukayi ta watsewa sannu sannu, a ƙa'idar AFREEN ne idan aka ida sallah sai mutane sun rage sosai kamin take jawo ƴan ƙananan ta su fito tare da ƙawarta Hasina dan tafiya gida. Hakama yau ta kasance saida mutane suka rage yayi sauran ƴan tsiraru sannan suka fito, har taje zata nufar parking ɗin da mata ke ajiye motocin su, Zeinab tayi saurin cewa "Ai anty ba ana kika ajiye motar ba wajen parking ɗin maza kika ajiye ta." Da sauri AFREEN ta juyo tana kallon ta tareda waro idon ta alamun firgici tace "Ya akayi har haka ta faru oh ni AFREEN ina hankali nane yaje har nakai mota can na ajiye ban saniba? kuma ke Zeinab kina gani amma kikaƙi sanar dani." Zeinab ta ce "Wallahi anty dan naga kina sauri ne kuma an kusa tayar da sallah shiyasa amma naso faɗa maki." "To wanzu dai ba wannan ba ta yaya zan ɗauko mota a parking ɗin ƴan maza tsakanin da Allah ya zani inshiga yurin nan, gashi yanzu nasan da su Fahad sun riga da sun tafi gida, da ba sai nasa ya fito man da ita ba." Dariya sosai Hasina tayi sannan tace "Besty miye abin wani ɗaga hankalin ki haka? kamar wada idan taje ɗaukar motar mazan cinye ta zasuyi, ki kwantar da hankalin ki muje na rakaki ki fitar da motar ki da kanki baki ga mutane duk sun watse ba tana iya yiyuwa ma motar takice kaɗai cikin gurin nasan yanzu haka ma kowa ya fitar da tasa sabida kinsan maza da uzuriruka." Sai a sannan ne AFREEN ta ɗan ji sanhi a zuciyarta sai tace masu "To ku tafi mu tafi." Suna tafiya suna fira har sun kusa ƙarasawa yurin parking ɗin kamar ance AFREEN ta ɗaga kanta aikuwa sai ta tsinkaye shi tsaye jigine da motar sa kansa duƙe ya na danna wayar sa da alama wani yake jira, a take gaban AFREEN ya wanke ya faɗi, kawai sai taja ta tsaya, da kallo su Hasina suka bita sannan Hasina tace "Malama lafiya kikayi mana tsaye kokin fasa ɗauko motar ne?" Da hannu AFREEN ta nuna mata AFREED da ke tsaye jigine da motar sa yana dan ne dan ne a wayar sa sannan ta marairaice tare dacewa "Kinga da namiji a wajan abinda nayi gudu kenan fah." Duka suka juyawa suka dubi gun da AFREEN ke nunawa. Ɗan ƙaramin tsaki tsussss Hasina taja tare dacewa "Dan Allah malama ki wuce muje idan zakije bakiga ko lura damu baiyi ba harakokin gabansa ya ke sannan kuma daga motarsa sai takice cikin wajen, kuma ba wani abu zai mana ba kawai muje muma muyi kamar ba mu ganshi ba ki ɗauko motar mu fito c'est tout." Ba dan taso ba haka ta bisu har suka ƙarasa gun, yaji shigowar su wajen parking ɗin amma ko ɗagowa baiyi ba ya kalle su bare yasan ko su wanene haka kawai dai yaji gaban sa ya faɗi, bai kawo komai a ransa ba sai ma cewa da yayi *la'ilaha illah anta subhanakah inni kuntun mina zalumin* , ya karanta addu'ar nan ne sadin jin dayayi gabansa ya faɗi sannan yaci gaba da abin da yake. Bai an kara ba yaji maganar Hasina nacewa ma AFREEN "Besty dan Allah yau idan kika ajiye ni gida ki shiga ku gaisa da ummi dan ranar nan tana tambaya ta ke kuma ma ki daɗe ba ki shiga gidan mu ba sedai ki ajiye nia bakin get kiyi tafiyar ki." AFREED na cikin tunanin mi ya kayo mace wajan parking ɗin maza ko dai tare da mijinta ne take, bai ƙarasa tunanin da yake ba yaji zazaƙa muyar AFREEN mai sanyi da taushi da ɗaɗin sauraro ta dakin dodan kunnansa shi a lokacin da tace cikin sanyayar ta "Wallahi kinga ban faɗa wa maman da papa ba cewa zanjima ko zan biya yani gun Kinga faɗa déjà yau mun ɓata lokaci ba mu koma gida ba, yanzu haka hankalin su nacan ya tashi zasu ce ko lafiya har yanzu bamu dawo ba, gashi fa ke har anguwar ali dan sofo mai uban nisa nan zan kaiki kinga ko kamin mukai ki mu dawo mun karancin wani lokaci." Tunda ta fara maganar AFREED ya juwo yana kallon ta sosai ya shagalta da kallon ta kamar yana ganin fuskar ta, kuma kamar mai son gano wani abu a tatare da ita, sabida saida ya bisu duka da kallon kamin yake yarda da cewa wada dai ke cikin niƙaf ɗin dai itace ke maganar, sabida yaga baki kowace a rufe sannan yana hango yanda bakinta ke motsi daga cikin niƙaf ɗin sosai a lokacin yaji wani abu ya cakar masa zuciya ba tareda ya shirya jin hakan ba, riƙe daidai satin da yaji abin yayi yana mai lumshe idonsa, kwata kwata baiji ɗaɗin shurun da yaji tayi ba a lokacin da ta kai ƙarshen zancen ta............ 😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ Wattpad@nazichou 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ *_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_* *Page* : 29 & 30 Tunda ta fara maganar AFREED ya juwo yana kallon ta sosai ya shagalta da kallon ta kamar yana ganin fuskar ta, kuma kamar mai son gano wani abu a tatare da ita, sabida saida ya bisu duka da kallon kamin yake yarda da cewa wada dai ke cikin niƙaf ɗin dai itace ke maganar, sabida yaga baki kowace a rufe sannan yana hango yanda bakinta ke motsi daga cikin niƙaf ɗin sosai a lokacin yaji wani abu ya cakar masa zuciya ba tareda ya shirya jin hakan ba, riƙe daidai satin da yaji abin yayi yana mai lumshe idonsa, kwata kwata baiji ɗaɗin shurun da yaji tayi ba a lokacin da ta kai ƙarshen zancen ta............ "Bawani nan Besty idan kika kira Maman kika faɗa mata cewa zaki kaini gida daga can zaki shiga ku gaisa da ummi ba abinda zata ce dan haka, ki kira maman yanzu nan ki faɗa mata idan kuwa gidan mune ba zaki ba to shikenan har kaini ɗin bana so ki bari zan je na tari adaidaita sahu ya kaini gida ko ma na kira direba kawai," Hasina ta faɗa tana ƙoƙarin bari gun ranta a ɓace. Da sauri AFREEN ta kamo hannuta da niyyar tsayar da ita gani ranta ya ɓace sannan tace "Dan Allah Besty kiyi hakuri ba gidanku bane banason zuwa wallahi, amma tunda kin matsa bari na kira maman ɗin sai na faɗa mata, ko kuwa mu yaje na sauke su Zeinab a gida sai na gayawa maman cewa zanje gidan ku na dawo daga nan sai mu wuce." Wani murmushin farin ciki Hasina ta saki sannan tace "Ko kega ƙawata dan shiyasa nake son ki, kinga maman bazata hanaki zuwa gidan mu, gashi kuma tare zamu tafi, kai ummi sai tayi farin cikin gani ki yau ku tafi mu tafi." Murmushi AFREEN tayi sannan ta buɗe motar duk suka shiga sannan ta tayar suna ƙoƙarin barin gun Ali ya ƙaraso har lokacin nan AFREED bai daina kallon ta ba har ta shige mota, Ali na ƙarosowa yace "Broh na tsayar dakai ko? yi hakuri nasan bakason jira." Firgigit AFREED yayi tare da saurin juyowa yana kallon Ali Ɗan hararen sa AFREED yayi sannan yace "Dan Allah muje kawai ka wani je kayi zaman ka, ka wani shanya mutane a nan." Murmushi Ali yayi kamin yake buɗe motar ya shiga mazaunin direba shi kuwa AFREED ya buɗe wajen mai zaman banza zai shiga sai ya juya idan AFREEN suka ajiye mota da zunmar son ya ƙara ganin ta ko da kuwa ba zai samu ganin fuskar ta ba, ko zaiji idan zata ƙara buɗe baki tace wani abu, amma sai yaga wayam aiko sai ya shiga wage wage ko ƙurar motar bai gani ba bale kuma su na cikin motar, cikin zuciyarsa yace to ina sukayi ko sunyi tafiyar su ne ni ban maji lokacin da ta tayar da motar ba har suka tafi, to wacece ita??? Bai kai ga samun amsar tambaya da yake wa zuciyar sa ba ya tsinci muyar Ali nacewa "Wai AFREED mikake jirane da ba zaka shigo mutafi ba, kodai ka fasa tafiya gidan ne?" Sai a lokacin AFREED ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula, tare da ƙarasa shiga motar cikin nutsuwa da kwanciyar hankali sannan ya rufo murfin motar, lumshe idonsa yayi tare da kwantawa jikin kujerar ya shiga tunani yana jin yanda wani abu ke shigar sz ya na ratsa jinin jikinsa, da ƙarfi gabansa ya daɗi a lokacin da ya ke ma kansa tambayar kadai matar aure ce na zauna ina kallon ta Inna lilahi wa'inna illaihi raji'un ya akayi haka ta faru mima ya kaini kallon ta? Ni komi kyau mace ba isheni kallo ba amma na buge da kallon mai niƙaf ma da yanzu haka ko kyau bata shi, da sauri ya furta astagfirllah a tunanin sa a zuciyarsa ya furta kalmar ta istigfari ashe a fili ne sai Ali ya juwo ya kalle sa yaga idonsa a lumshe suke kamin yake maida duban sa ga tit sannan yace "AFREED magana kake?" shiru baice masa komai ba amma yaji abinda ya faɗa. AFREED ya koma cewa a zuciyarsa "Wacece ita, tanada aure ko kuwa, miyasa ta ajiye motar a parking ɗin maza? a take yaba kansa amsa da cewa amma naji tana cewa Maman zatayi mata faɗa idan taci lokacin da yawa bata koma gida ba, hakan ya nuna ba tada aure kenan, to idan hakane miyasa take saka niƙaf, bata son aga fuskarta ne kokuwa wani kuma salon muna furcin ne irin na mata? amma naga a garin nan mata na son saka niƙaf , to miye manufar su tayin hakan, nikam na tsani naga mace na saka niƙaf sai naga duk munafurci ne da son kallon maza daga cikin niƙaf ɗin, can wani ɓangare na zuciyarsa yace " Wai ina ruwanka da ita daga gamuwa da yarinya ka wani zauna sai tunanin ta kake itada ko saninta bakayi ba, kuma ko fuskarta baka gani ba miye matsalar ka da ita ne da ka wani damu da ita? atake yaji haushin kansa na kallon mi ya tsaya yana yi mata shida bai taɓa ganin mace ba ya zauna yana kallon ta ba ko da wada fuskarta ke buɗe bare wannan, to dafa kamashi tayi yana kallon ta fah, da kawai rainasa zatayi wani kuma abinda ya zuba, shida mata ke kawo kansu gareshi yana ƙin kula su amma shine yau ya bige da kollon wata, watar ma dake cikin niƙaf, ɗan karamin tsaki yaja tare da furta "Ta ma ban haushi." Atunanin sa a zuciyarsa ne ya fali haka amma ashe maganar ta fito fili. Saida yaji Ali na cewa "Lafiyar ka kuwa frèro sai magana kake kai ɗaya tare da jan tsaki wa ya taɓa minke ne dama tun da nafito daga masallaci naga kana kallon wata mota, ko na cikin motar ne ya ɓata maka rai yanzu nasaka a ne moshi tun na ɗauki number motar sanadin ganin da nayi kana kallon motar sosai da na cikin motar nayi gudun ace ko wani abu yama, tunda nasan zaka iyaƙi faɗa man a nan take har sai mun tafi gida." Da sauri AFREED ya ɗago daga kwancin da yayi saman kujera tare da buɗe lumsashin idonsa ya ƙurawa Ali su a lokacin da yaji yace ya riƙe number motar dan jin ko dagaske ne ya riƙe number motar, amma yanayin wani tunanin kawai sai ya koma ya kwanta tareda lumshe idonsa kamar mai shirin yin bacci, Ali kamar yasan abinda ke cikin zuciyarsa yace "Eh na ɗoki numba motar idan da wata matsala ne ka faɗa min a ɗoki mataki tun yuri guda kar ya mana nisa, ka kama fuska kasaka abinda ake rufe baki da hanci karmar wani mai gudun kamuwa da cutar Corona virus, wai kai a dole ba kaso a gane kaine MINISTRE DE DÉFENSE ET DE SÉCURITÉ ɗin da ake yawan nunowa a TV, ba dole mutane su maka abinda sukaga dama cikin rashin sanin matsayin ka ai kaine zaka jawa kanka AFREED da ka bayana kanka babu mai yarda yayi koda hada ido da kai bare harma yayi maka batanci, to faɗa man miya faru? Dan nasan daga ina zan fara neman mai motar." Hankali kwance cikin gajiya da sauran surutun da Ali yake masa dake mai saka masa ciwon kai AFREED ya buɗe bakinsa yace "Babu komai." Ali ya sake da baki yana kallon AFREED da ya Koma lumshe idonsa sannan yace "Ai dama nasan bazaka ce komai ba to idan tayi wari munji ɗan rainin wayo kawai." Shi dai AFREED baice da shi komai ba sai ɗan murmushi da ya saki mai tafiyar da zuciya a duk wanda ta kallesa. Ali na shirin sake yin wata maganar, AFREED kamar wani me ganin sa shida idanuwon ke lumshe yace "Dan Allah Ali kada ka ƙara cewa komai surutun nan naka nason sakamin ciwon kai haba anyi mutum sai wayan magana." Hararen sa Ali yayi sannan yace"Eh anje anyi wayan maganar ai surutu ma rahama ne kuma nafi ka kaida kake nan dunkum kamar gumki." AFREED dai bai ce masa komai ba har suka ƙarasa gida shima Ali bai ƙara magana ba, suna zuwa bakin get ɗin gidan Ali ya dana hon mai gadi ya wangale masu babba ƙofar suka shige ciki, ba tare da bata lokaci ba Ali yayi parking ɗin motar suka fita tare da nufar ɓangaren tanti, suna shiga suka tardo kowa na kan dinning suka kaɗai ake jira a fara cin abincin, ba tare da sun tsaya komai suma suka nufi dinning tare da yiwa tanti sannu da gida sannan suka zauna, Khadija ta tashi tayi servir ɗinsu, shiru gun yayi ba kajin motsin komai sai na spoon, can tanti ta ɗaugo tace "AFREED mi ya tsayar daku naga yau kun jima har hankali na ya fara tashi wallahi." Murmushi yayi tare dacewa "Wallahi wannan banzan ne ya tsayar da mu ya je ya buɗi guri yayi zaman sa a cikin masallaci ban ma san miye yayi aciki ba." "Eh anje anyi ko zakayi wani abune, mi ya hana da kaga najima kaƙi tuƙa motar kayi tafiyar ka?" Ali ya faɗa yana yiwa AFREED murmushin mugun ta. AFREED yace "Au haka ka faɗa to ba laifi ai zaka gani." Su Farisa da su Khadija nason yin dariya amma babu dama sabida gudun kada AFREED ya watsa su, sai Umar da tanti ne suka ɗan dara sannan Umar yace "AFREED da Ali kamar kusu da mage kuke kwata kwata ba ku iya zama gu guda ba kuyi barkwanci ba, shirman nan da kukeyi ko su Fariya basa yin sa." AFREED dai shiru yayi baice komai ba sai ma miƙewa da yayi tare dayin gaba abinsa batare da ya gama cin abincin ba, saboda tunda ya ji muyar AFREEN daga masallaci yake jin kansa ba normal ba, duk jikinsa yayi masa sanhi ya ma rasa mike masa daɗi, gashi yama rigada ya manta da yaji zazaƙa muyar wata a masallaci, bai taɓa kawo cewaba rashin ƙarfin jikinsa da bayaji ba yana da nasaba da jin muyar AFREEN dayayi baisan muyar ta ɗoke masa hankali da da nutsuwar ba sai dayaje kwanci bacci da dadare, yanda kasan yanzu ne take maganar haka ya dingajin kalaman da ta ɗinka faɗa wa ƙawarta na dawowa cikin dodon kunnansa zazaƙa muyar nanta ta ke mugun bugun kunne sa kwata kwata ya rasa ya zaiyi, gabaɗaya yakasa bacci ya rasa miye dalilin da yasa ya kasa mantawa da muryar, shida baisan ta ba fuskar ta ma aɓoye take, yanzu idan cewa za'ayi ya nuna ta acikin jama'a ba zai iya ba indai ba da kalar shigar da ya ganta ba zai sake ganinta to a lokacin nan ne zai shedata, sosai tunanin ta ya adabi rayuwarsa, har yana ce Allah sa ba matar aure, idan kuwa matar aure ce ya zanyi a take wani sashe na zuciyarsa yace masa idan ma matar auren ce ko akasin haka miye haɗinka da ita da ka zauna kana tunanin ta AFREED, ita ba wata yar uwar ka ba amma duk kabi ka damu da ita haka, a fili kuma sai yace miyasa na damu da ita ne zauna ina tunanin ta ko dai taimako takeda buƙata ne? amma ai banganta cikin yanayin masu neman taimako ba hasali da mota tazo ko ba tata bace ba ai zai iya yiwuwa ta gidansu ce." AFREED da yaga tunanin AFREEN na neman zaman masa matsala kawai sai ya tashi daga kwanciyar dayake yana jan ɗan ƙaramin tsaki, tare da miƙewa baki ɗaya ya nufi toillet ya ɗauro alwala sannan ya fito ya shimfiɗa darduma ya shiga yin ƙiyarmar lailih, saida akayi kiran sallar farko ta ƙarfe huɗu dare kamin bacci ya fara fizgar shi, ba tare da ɓata lokaci ya sallame daga sallar da yake ya nufi lafiyayen bed ɗin sa ya kwanta a take wani bacci mai dadi da mafarkai kala kala ya yi awon gaba dashi. ***** ***** ***** AFREEN nazuwa gida tayi parking motar a ƙofar gidansu sannan suka fito su duka a motar suka shiga cikin gidan suna shiga falon suka tarda maman zaune tana zaman jiran su, Maman na ganin su ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "Miya tsayar da ku harhaka baku dawo ba? kunsa hankalin mu duk ya tashi yanzu nan papan ku ya shiga ɗaki dan sauya kaya yaje neman ku a masallaci sabida anyi ta kiran wayan ki yana ƙara ba a ɗagawa, sai daga baya da na shiga ɗakin na tarar da wayar a saman bed ɗin kika barta." AFREEN ta saki murmushi tace "Maman ku kwantar da hankalin ku mana babu idan mukaje duk lokacin da muka ɗauka bamu dawo ba muna masallaci." Maman tace "To ai chikenan tunda gashi Allah ya dawo daku lafiya bari naje na faɗa ma papan naku." Tana ƙoƙarin tashi saiga mahaifin nasu ya sauko da key mota a hannu sa maman na ganinsa ta koma idan ta shi ta zauna, magana ya fara a lokacin da yazo ya zauna yace "AFREEN ɗin papa ina kuka tsaya hakane yau?" Kallon mahaifin nata tayi cike da kaunar sa tace "Papa babu inda muka tsaya muna masallaci mota na ne na ajiye a inda maza ke ajiye tasu motar ba tare da nasani ba ina sauri munyi lati zuwa kuma ana shirin tayar da sallah, saida muka fito ne Zeinab ke sanar dani a can na ajiye shine muka bari saida mutane suka tafi sannan mukaje na fitar da motar." Murmushi papa yayi sannan yace "Dama nasan babu inda zakije ba tare da kin sanar damu ba Allah maku albarka yanzu ku shiga daga cikin ku fido hijaban ku sai kuzo kuci abinci." Da to suka amsa su duka harda Hasina sannan suka wuce ɗakin AFREEN, su Zeinab kuwa suka nufi ɗakin mahaifiyarsu, suna shiga Hasina tace "Besty wai ya maganar KAMAL ne baice dake zaizo ba?" "Kai besty wallahi Ni har na manta dashi ma wallahi amma yace man yau zaizo ya ga papa ni kuma ma na kasa faɗa ma papa maganar zuwan nasa wallahi ko maman bazan iya faɗa mata ba, kuma bai kamata yazo ba, ba tare da na sanar dasu ba kinga hakan bai kamata," AFREEN ce ta faɗa ta ƙoƙarin cire hijab ɗin jikinta." Ajiyar zuciya Hasina ta sauke tace "Wallahi har naji dadi besty, dan gayawa papa wannan mai sauƙi ne, kawai tanti zaki faɗa mawa sai ta faɗa masu baki ɗaya sabida nasan da itace kaɗai zaki iya faɗa ma." AFREEN tace "Hakane duk na ruɗe narasa ya zanyi shiyasa ma na manta da na faɗa wa tantin." Hasina tace "To ai yanzu na tuna maki." Wata nauyaya ajiyar zuciya AFREEN ta sauke tace "To muje muci abinci, muna ƙarasa wa sai naje na faɗa wa tantin, sannan muje na faɗa wa maman da papa zanje gidan ku tunda yau bazamu makarantar yamma ba." Fita sukayi a ɗakin sannan suka nufi dinning inda su Zeinab ke zaune suna jiran fitowar su ba tare da ɓata lokaci ba aka zubawa kowa abincin sannan suka fara ci, suna ƙarasa cin abincin AFREEN da Hasina suka nufi ɗakin tanti, suka tardo ta tana ninke kayan ta sallama sukayi tare da nufar gefen bed ɗin suka zauna AFREEN tace "Tanti sannu da gida kikawo na ƙarasa nike maki kayan." Murmushi tanti tayi sannan tace "Yawa AFREEN, kibar shi ai nama ƙarasa AFREEN, tanti ta faɗa tare da dawo kusa da su ta zauna tana cewa "AFREEN faɗamin mike faruwa naga alamun da magana a bakinki." Murmushi AFREEN tayi tareda sade kanta ƙasa sannan tace "Tanti dama.....dama." sa kumai tayi shiru ta kasa gayin abinda tayi niyar faɗa." Gaban tanti ne ya wanke ya faɗi har saida alamun tsoro ya bayyana a fuskarta tana addu'ar Allah yasa ba abinda take tunani bane, kamin take basarwa tace "Gayamin mana ma fille tsakani na dake babu wannan kunyar." Saida AFREEN ta ƙara duke kanta ƙasa sannan tace " Tanti dama..... Wanine yace zaizo ya gaida ku, dam dam gaban tanti ya faɗi da ƙarfi a lokacin AFREEN har ta riga da ta fice daga ɗakin dan kunya sai ta jin abin gashi banba rakwai wai itace saurayi zaizo gunta." Hasina ta dawo da tanti daga duniyar tunanin da lula a lokacin da take cewa " Tanti shine takeson ki faɗa wa papa dan ita ta kasa yanzu ma da kyar na taso ta gaba da ta faɗa maki." Murmushi yaƙe tanti tayi sannan tace "Aiko AFREEN akwai kunya nima wai dan muna yawan fira ne da ita har ta iya faɗamin insha Allah zan faɗa masu shi da maman ta Allah kawo sa lafiya wane lokaci zaizo?" "Bayan sallar isha'i." Hasina ta faɗa a taƙaice. To shikenan babu damuwa sosai nayi farin ciki da jin haka na kusa shan bikin ɗiyata Allah nuna min lokacin nan da alkairi." Murmushi Hasina tayi sannan ta tashi ta fita tabi bayan ƙawarta. Tanti na zaune a inda suka barta kusun minti 10 tana zaune tana saƙa da warwara sannan ta tashi ta nufi ɗakin maman, tana shiga suka gaisa sannan ta faɗa abinda suka tattauna tsakanin ta da su AFREEN cikin da farin ciki take faɗa maman abinda AFREEN ta faɗa mata. Murmushi Maman tayi sannan tace "Hum AFREEN sarkin kunya to kije ki faɗa wa mahaifin nasu kamin ya fita dan yasan dazancen." "A'a maman Fauziya mi zai hana ke ki faɗa masa." Tanti ta faɗa tana kai duban wajan maman. Maman tace "A'a ki daije da kanki waka abakin mai ita tafi daɗi sabida ke a ka baiwa saƙon kuma kunfi kusa keda d'iyar taki." Dariya tayi tace ƙwarai kuwa bari na tashi dama wannan saƙon farin ciki nidai ce ya kamata na faɗesa." Sannan ta miƙe ta bar ɗakin ta nufi ɗakin papa, ta tardo shi zaune cikin falon sa yana karatun jarida kujera da ke fuskantar sa ta zauna ta fara koro masa da bayani. Cikin ƙanƙanan lokaci farin ciki ya bayyana a fuskar papa yace "Masha Allah AFREEN ta fara hankali da har iya kula wani har ta bashi damar zuwa gidan nan wannan wane mai sa'a ne haka? To Allah kayosa lafiya." Da ameen tanti ta amsa sannan ta tashi ta koma ɗakin ta, ita kuwa AFREEN har sun tsufa gidan su Hasina maman Hasina taji daɗi ganinta har tarasa ma ina zata saka ta dan farin ciki, bayan sallar la'asar AFREEN tayi masu sallama ta tafi gida bayan Hasina ta nuna mata yanda zata karɓi KAMAL idan yazo sabida ita sabon shiga ce a wannan fannin." Bayan sallar isha'i AFREEN tayi wanka ta shirya cikin wani haɗaɗen ɗumki na atanfa da aka mata doguwar riga sosai rigar ta kamata ta mata mugun kyau ba kwalliya tayi ba sai kwali da tasha wanda ya ƙara fito da hasken idonta wanda suka bada wani irin kala mai kyau maron ɗin cikin su sai wawalniya yake ko kai kewa ka kalleta dolene ka ƙara kallon ta. Amma gabanta sai faɗuwa yake tana tunanin ya KAMAL zaiyi idan yaga fuskarta kadai yaje shima ya tsorata da ita shikenan ya daina sonta bayan kwana biyu nan dayake kiranta suna gaisawa yasa ta fara sakin jiki dashi, kada yaje ya mata kallon aljana kamar yadda kowa kemata idan suka ga fuskar dan wasu ma har guduwa suke. Tana zaune tana saƙa da warwara taji wayar ta ɗau ringin aikuwa sai gabanta ya yanke ya faɗi har saida ta riƙe daidai gun da taji ya buga din, addu'a tayi sannan ta ɗauki wayar takara a kunne tare da yin sallama, daga cikin wayar aka amsa sallamar tare da cewa "Sarauniya ta gani a ƙofar gida." Da To ta amsa sannan ya katse kiran, tashi tayi ta fita ta tardo Zeinab da Safina zaune a falon suna kallo kusa da Zeinab taje ta zauna tace "Zeinab tashi kije nayi baƙo a waje ki shigo da shi." "To anti." Zeinab ta faɗa sannan ta miƙe ta fice. Maida duban ta tayi ga Safina tace "Sister tashi kije ki faɗa wa su papa gashi nan ya ƙaraso." Itama miƙewa tayi ta nufi ɗakin papa sannan AFREEN ta koma ɗakinta ta zauna...... Zeinab na fita ta tardosa zaune cikin motar yana dana waya ƙarasa wa tayi gun motar tayi sallama sannan tace "Ina yuni yaya ance ka wucike daga ciki." Kallon ta yayi sannan ya saki murmushi yace "Lafiya lau ƙanwata, to shikenan bari na fito." "A'a yaya da ka shigo da motar a ciki mana" A'a ƙanwata Bama sai na shigo da ita ba tunda ba jimawa zanyi ba." "To ba damuwa yaya." Zeinab ta faɗa tare da juyawa zata koma ciki. KAMAL yace "Ah ƙanwata ki bari mu shiga tare man, ya faɗa tare da ƙoƙarin fitowa daga motar, tsayawa tayi sannan ya fito daga motar, masha Allah KAMAL fari ne dogo mai ɗan kakabran jiki kyakkyawan gaske ajin farko. Ƙaraso yayi inda take cikin ƙayataciyar tafiyar sa sannan yace " Mutafi." Jerawa sukayi suka shiga gidan suna kawowa ƙofar da zata sada su da falon ya ja ya tsaya Zeinab ta juyo ta kalle sa tace "Yaya Lafiya naga ka tsaya." Murmushi yayi sannan yace "Lafiya lau mu shiga ." Buɗe ƙofar Zeinab tayi tashi ga da sallama shima haka ya shiga kansa aka kasa yana kallon ƙasa da sallama ɗauke a bakin sa, papa ne zaune a falon ya ɗago ya kalleshi tare da amsa masa sallama sannan yace "Ƙaraso mana yaro." Ƙarasawa yayi tare da zubewa kasa saman kafet tare da gaida papa kansa a ƙasa ya ƙasa ɗagowa ya kalli sirikin nasa, sannan papa yace "Tashi ka zauna mana ya ka zauna a ƙasane nan fah gidanku." Murmushi KAMAL ya saki da har yau kansa a ƙasa sannan yace "A'a papa nan ma ya isa." Murmushi papa yayi a cikin zuciyarsa ya na faɗin wannan daga ganinsa yaron kirki ne, amma a fili sai yace "To shikenan." Ba tare da ɓata lokaci ba aka cika masa gabansa da ƙayan ciye ciye da lashe lashe sannan papa yace masa "To bismillah." Girgiza kansa yayi alamun a'a, papa yace "To kodai bakasan yanzu nan yazama gidanku ba kaima ka cire kunya mana ni kamar mahaifi nake a wajan ka, saki jikin ka yaro." Murmushi KAMAL yayi sannan ya ɗauki kofi ya tsiya juice ya sha sannan ya ajiye." Sannan papa ya kallesa ya fara masa tambayoyi kamar haka............ Ina sonku irin sosai ɗin masoyan wannan littafi........ Bon Mardi 💖💖💖💖 Happy Tuesday💞💞💞 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *_Teemah_* ina jinjina maki game da ƙoƙarin comments sosai nake jin daɗin idan naka comment ɗin ki sannu ki da ƙoƙari Allah saka maki da alkairi. *_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *Page*: 31 & 32 A nutse papa ya dubi KAMAL yace "To yaro mi sunan ka sannan inane gidan ku kuma mike tafe dake a game da yarinyar nan AFREEN?" papa na kaiwa nan yayi shiru. KAMAL ya gyara zaman sa da kyau sannan ya ƙara sada kansa kasa yace "Papa ni sunana KAMAL mahaifina Alhaji Aminu mai gyaran TV, gidan mu kuwa yanan cikin anguwar buzu ɗan zambaɗi wajen shagon Sagir mai ƙarfuna, ni kuwa ina aiki a baba ma'aikatar ƙera leda dake cikin garin Maraɗi ta wajan hanyar anguwar ƴan belbelu, sannan inada shagon biyu cikin grand marché ( babba kasuwa) kuma inada shago biyu a ƙaramar kasuwa wanda nikeda yara masu tsare min su, kuma duk ina sami lokacin ina zuwa Dubai wajen sayo kaya kamar lace, antafa shada da dai sauransu, kuma abinda ya kayo ni gun AFREEN shine aure🙈 papa wallahi ban zo da wassa ba da aure nazo, kuma nutsuwar ta kamalarta da addini ta ya ja hakalina gareta ba dan wai na taɓa ganin fuskarta ba ɗan ko yanzu dana ke maka maganar ban taɓa ganin kamanin ta ba a whatsapp sai nayi nayi ta turoman da photon ta amma taƙi, duk da haka banji haushin ta sedai ma da tayi hakan birgeni tayi, kuma ni ko ya take to naji nagani inason ta a haka. Papa yace "To masha Allah KAMAL duk na gamsu da bayan nan ka, kuma na yaba da hankalin ka sannan duk garin nan babu wanda baisan mahaifin ka mutuman kirki bane dan haka nidai na baka AFREEN, sai kaje ka sameta dan ku daidai ta kanku." Wani farin ciki ne😊 ya sauko wa KAMAL, baisan lokacin da ya furta "Nagode papa Allah saka alkairi." Murmushi papa yayi sannan yace dashi "Bai komi bari naje nasa a turo maka ita sai ku gaisa." papa ya faɗa tare da miƙewa ya bar gun ya nufi ɗakin Umma yana shiga ya tardo su Zeinab zaune bakin bed ita kuwa umma tana toillet dubensa ya kai ga Zeinab yace "Tashi kije ki mayar da KAMAL ɓangaren saukar baƙi sannan sai ki sanarwa da AFREEN cewa taje su gaisa." Haka kuwa akayi tana zuwa tardo shi zaune ida papa ya barshi bai motsa ba ta ƙara so ta sanar da shi saƙon papa sannan ya miƙe ya bi bayan ta, tana raka shi ɓangaren baƙi ta fito taje ta gayawa AFREEN sannan ta dawo ta ɗoki abin motsa baƙi ta kai masa sannan ta fito. AFREEN na fitowa ta nufi ɓangaren baƙi amma ta kasa shiga tsaye take bakin ɓangaren sai zare ido take kamar mara gaskiya ita ganin abin take gashi nan, wai itace saurayi yazo wajan to ita idan tashiga ma ya zata ce mashi abinda ba sabon ba, gashi ita sabon shiga ce a wannan fannin to ya zatayi? Tana ciki yi wannan tunanin taji ƙarar tafiya ai bata san lokacin da ta buɗe ƙofar ba ta shige da sallama a bakin ta, yana zaune yana dana wayar sa, da sauri ya ɗago sanadin jin zazaƙa muryar ta na yawo cikin kunnuwa sa, sakin wani haɗaɗen murmushi yayi sannan ya taso ya ƙaraso ida take tsaye yace "Oustaziya na bismillah ki zauna mana ba musu ta ɗaga ƙafar ta ta nufi gun manyan kujerun dake falon ta zauna, ba tare da ta ɗago fuskarta ba dake duƙe. Shima yadawo ya zauna kan kujerar dake fuskantar ta yana murmushi😊 ba tare da ta ɗago ba tace "Ina yuni" take yanke yaji wani farin ciki ya luluɓe shi. Yace "Lafiya lau Oustaziya na da fatan na sameki lafiya." "Lafiya lau," ta faɗa a taƙaice ba tare da ta ɗago ba. Murmushi ya koma yi sannan yace "Yau ma ba za'a bani damar ganin wannan kyakkyawar fuskar ba, ko nayi lafine da akeson hukunta ni ta wannan fannin." Girgiza kai tayi sannan tace "ba haka bane" Wani murmushin ya ƙara saki cike da farin ciki dan ba ƙaramin jin daɗin muryar ta yake ba sannan yace "To a taimaka min dan Allah a ceci rayuwa ta tunda dai yau gani na kawo kaina, a nuna min wannan kyakkyawa fuskar ba dan halina ba na ƙagu naga fuskar nan dan Allah."🙏🏻🙏🏻 Ji abinda ya faɗa yasa AFREEN ba dan taso ba sabida tana gudun kar ya ga fuskar shima ya ji tsoron ta har ma ya gudu daga gidan nasu, fara ɗago fuskarta tayi a sannu sannu kamin take ida ɗago fuskartata ta sauke manyan idonta cikin nasa ba tare da tasan idon nasu zasu sarƙe cikin na juna ba. Saida yaja baya a ɗan firgice 😿😳kamin yake Furta "Tsakiyar ya tabbata ga Ubangiji da ya halicci wannan halitta, AFREEN dama haka kike da kyau badan ina cikin gidan ku da a lokacin da naga wannan fuskar taki da nace gamo nayi, ce ba banza kike rufe fuskar kiba AFREEN gaskiya ni me sa'a ne da nayi irin wannan zaɓin, yanzu nan na ga ribar rufe fuskarki da kike da ace baki saka niƙaf da yanzu wani ya kwashe min ke tun kan in ganki, amma yanzu ke tawace ni kaɗai dole ne na ƙara maki kwarin gwiwar saka niƙaf dan adana min wannan kyakkyawa fuskar har na kilace a gida na wanda ko abokai na ba zan barsu su gangi ba my AFREEN inason ki sosai dama ni tun farko shigar ki ta alfarma da hankali da nutsuwa da addini suka ja hankalina a kanki abinda yasa, sai gashi nazo naga ashe babban kamu nayi Allah na gode maka," a take ya sauka daga saman kujera da yake ya kai goshisa ƙasa yanayi wa Allah sujida tare da gode masa. AFREEN murmushi☺️ tayi tare da saurin kai hannu ta ta rufe fuskarta, kamin shi kuwa ya ke ɗagowa ya koma saman kujera ya zauna yana binta da wani mayatacan kallo. Daga nan dai ya samu suka ɗan gaisa dan kwata kwata ta kasa sakin jiki suyi fira sabida tsananin kunyar sa🙈 da take ji, kamin daga bisani ya mata sallama ya tafi ba dan ya so ba kawai dan ya lura dare ya farayi, amma in ba haka ba babu abinda zai sa ya bar gun, kofa bazata masa magana ba matsala indai har zata barshi yayi ta kollon ta, haka na saukar masa da wata nutsuwa da farin ciki. Tunda ga wannan ranar soyayya mai ƙarfi ta kulu tsakanin KAMAL da AFREEN, duk ranar da tace masa ba zatayi karatu ba to ranar wajen ta yake zuwa su sha fira sosai har baison ya barta kamar dai ace ya ɗoketa ya kai gidan sa yake ji. Sannan duk ina yazo gidan kullum sai ya shiga ya gaida iyayen ta da kuma kakata Hajiya Zakiya. Kuma gashi duk lokacin da yazo ya kawo mata wani abu to idan taƙi amsa sai ya kira Zeinab ya bata yace ta ba AFREEN idan sun shiga cikin gida. haka har sai ta fara nunawa Tanti kamin ta kaiwa mahaifiyarta haka kuma tanti bata daina bata maganin da take bata ba. Kwanci tashi babu yuwa a wajan Ubangiji yau ya kama saura kwana takwas saukar su AFREEN, dan haka sunata ta shirye shirye a islamiyyar su yanzu aji aka bawa AFREEN nayiwa yan saukar gyaran karatu, kasancewar ita ta daɗe da yin saukar Alkur'ani mai girma, yanzu kuwa za'a mata saukar tahafiz ne da litattafan addini da ta karance ce kuma ta hadace, idan kaji AFREEN na karatun Alkur'ani mai girma tana bawa ko wane harafi haƙinsa ba kuskure ko ɗaya a ciki zaka iya cewa duk duniya tafi kowa iya karanta shi da bashi mahimmanci. ****** ****** ****** ****** AFREED ne kwance ya lumshe idonsa kamar mai barci, amma ba haka bane, ya faɗa duniyar tunanin, tunanin da yarasa sa dalilin da yasa yakeyin sa, kwata kwata hankali sa ya kasa kwanciya a kan abinda ke addabar zuciyarsa, a take ya azawa kansa tambayar miyasa nakasa manta wa da muryar tane wane dalilin ne yasa nakejin wani abu na tsiramin a zuciyata a duk lokacin da na tuna muyar ta, miyasa duk sanda nake zaune ko nake kwace sai tunanin ta ya addabi rayuwa ta, miyasa kullum nakeji muryar ta cikin dodon kunnuwa na kuma hakan na sakamin faduwar gaba da sakani, cikin damuwa, miyasa tsikar jikina ke yawan tashi akan ta minayi mata, kodai itaɗin ba mutum shiyasa ta addabi tunanin na ɗan gaskiya zaƙin muyar ya huce misali pourquoi je pense a elle ( why nake wayan tunanin ta), d'abord qui est-elle ( who is she)????? Wannan tambayoyin ne AFREED ke ta aza ma kansa kuma yara sa mai bashi amsa su, tashi yayi zaune ba tare da ya buɗe idon shi ba yanajin yada kansa ke sara masa, buɗe ƙofar ɗakin a kayi aka shigo har yanzu idonsa a lumshe suke, duk da yaji buɗewar kofar hakan bai sa ya buɗe su ba, Ali ne yashigo sannan yayi sallama, can ciki AFREED ya amsa wanda in ba kusan sa kake ba to ba zakiji ya amsan ba, kuma ya amsan sabida sanin mahimmancin sallama, da badan haka to babu wanda zai sashi buɗe bakin. Ƙarasowa Ali yayi shi ma ya zauna bakin bed sannan ya kalli AFREED cike da damuwa yace "Frèro wai mike damunka ne? Ina lura dakai kwana biyu baka cikin walwala tanti duk ta damu. Sai a lokacin ya buɗe shanyayun idanunsa da sukayi ja sosai kamar an watsa masa barkono sanadin ciwon da kansa yake da kuma damuwa ta taru tayi masa yawa, ya sauke su akan Ali sannan yace "Babu komi broh kawai kaina ne ke yawan yimin ciwon kwanakin nan." Da sauri Ali ya kai hannu sa saman goshi AFREED, ai da sauri ya janye sanadin jin wani irin zafi sosai sannan ya maida kallon sa akan AFREED a gigice yace😳 "Tashi muje asibiti AFREED ya kake zama da irin wannan ciwon kan haka, in wani abu kuma ya sameka fah kasan ba zan taɓa yafewa kaina tashi muje bari na sanarwa tanti halin da ake ciki," daga nan Ali ya miƙe da niyyar zuwa ya sanarwa tanti ( ƙanwar mahaifin AFREED). Da sauri AFREED ya koma hannun sannan dakyar ya ɗaga bakinsa yace "Ali ba wani babu bane mai tsanani ka kwantar da hankalin ka, yanzu da nasha magani na kwanta na huta yanzu nan zakaga na wartsake, idan kaje ka faɗa wa tanti ai zata tayar da hankali tane sosai." Sai Ali ya kura masa ido na ɗan lokacin kamin yace " ka tabbata?" Murmushin ƙarfin hali AFREED ya sakar masa sannan yace "Insha Allahu." Wajen ida AFREED ke ajiye magunguna Ali ya nufa ya ɗoko masa kalla biyu sannan ya nufi firjin ɗin dake ɗakin ya ɗoko masa ruwa, kamin yake nufarshi da magungunan da ruwa, ya dawo ya zauna daga inda ya tashi ya ɓalla masa maganin da ruwa ya basa ba musu ya ƙarba yasha, sannan ya lumshe idonsa ya kwanta yace "Ali yau wace rana ce?" Ali yajuyo ya kallesa ganin idonsa a lumshe sai yace mashi "Laraba." Saida ya ɗoki minti biyu sannan yace "Kenan saura kwana guda juma'a to Allah ya kaimu." Da mamaki Ali ya juyo ya kallesa yace "Eh amma lafiya kake son zuwan ranar juma'a?" "Ba komi." AFREED ya faɗa a taƙaice. Miƙewa Ali yayi sannan yace "To shikenan yanzu dai kasamu kayi bacci ka huta ko ciwon kan nan naka zai rabu dakai." A zuciyarsa yace "Da zan ganta ko naji muryar ta da yanzu nan na wartsake tunda itace ta sakamin ciwon kan, amma a fili sai yace " To" kamar wani ƙaramin yaro ga yanda yayi maganar. Fita Ali yayi daga ɗakin sanadin ganin da yayi kamar bacci ya fara ɗaukar sa, tare da rufo masa ƙofar. ****** ******* ******* JUMA'A BABBA RANA Ya tunda AFREED ya farka yake jinshi cikin wani irin farin ciki mara musultuwa sai fara'a yake haka kawai badan yasan dalili ba har ƴan gidan sai da suka fahimci haka daga gare shi, suna zaune suna karyawa yawa sai murmushi yake shi ɗaya, tanti ta lura da hakan tun shigowar sa falon ta gane cewa yau ɗan nata na cikin farin ciki ko dan gani da tayi masa yau ana magana yana saka bakin ba kamar kullum ba itama murmushi tayi ta kallesa tace "Yau ɗana lafiya na ganka cikin farin ciki haka sai wani sakin murmushi kake, ai ya kamata araba farin cikin nan damu dan muma mu tayaka murnar kodai sirika a samar min ne?" Kamin AFREED yace wani abun Farisa tayi saurin cewa "Ko dai yaya kayi waya da Momy ne shiyasa kake ta farin ciki nidai kam kamar tanti yau na lura kana cikin jin daɗin." Maida kallon sa yayi wajen Farisa ya sakar mata murmushi sannan ya dawo da kallon sa ga tanti yace "Lah Tanti wallahi ba haka bane kawai dai nima yau na tashi na tsintsi kaina cikin farin ciki da bansan dalilin sa." Murmushi tanti tayi sannan tace "To Allah dawamar da kai cikin sa." Da ameen suka amsa su duka, sannan suka miƙe daga cin abincin suka koma falon, basu jima suna fira ba AFREED da Ali da Umar suka miƙe tareda cewa Tanti Aicha ( ƙanwar mahaifin AFREED dama sunanta Aicha to yanzu namai da su AFREED su ringa kiranta da tanti Aicha dan a banbantata da tanti kishiyar Maman AFREEN dan masu karatu su fahimta) su AFREED su kacewa tanti Aicha sun koma ɓangaren su kamin lokacin tafiya Sallah juma'a yayi haka." Da to ta amsa masu sannan sukayi gaba abinsu, suna shiga ɓangaren su kowa ya nufi nashi ɗakin, AFREED zaune saman gadon da ƙur'ani a hannu sa yana karanta suratul kahaf kuma yanayi yana duba montre ( agogo) sabida ya matsu lokacin zuwa masallaci yayi ko zai ganta ba dan komai sedan yaji muryar ta. ****** ******* ****** Kamar kullum haka mutanen gidan su AFREEN suka tattara su tafi masallaci yau kam a tare suka tafi dan AFREEN bata bari suka barsu ba, mota papa da matansa sa ita ke gaba AFREEN na binsu a baya sannan motar su Fahad shida ƙanansa Imran sun jera tsaf kwanin ban sha'awa, Suna ƙarasawa masallaci su Fahad suka nufi wajan parking ɗin maza shi kuwa papa saida ya ajiye matan sa bakin masallaci mata sannan ya juya itakuwa AFREEN direct parking ɗin mata ta nufa ta paka tata motar sannan suka fito ita da ƙannanta suka jera suka nufi hayar shiga masallacin, sun ɗan jima da zuwa sannan aka tayar da sallah dan har nafila sai da sukayi, huɗuba ma suna can aka fara har aka ida tare da su. Ana sallamcewa daga Sallah aka fara ɗauri aure da aka gama kowa ya fito banda su AFREEN wanda haka ya zama al'adar tane sai mutane sun rage suke fitowa, kuma gashi tanata dube dube ganin ko zataga ƙawarta dan duk yau basu haɗu ba kuma yau ba makaranta sukayi ba suna hutu, kuma gashi cikin masallaci duk mutane sun watse bata ganta ba sai take tunanin ko batazo, sai kuma tace amma tace man zata zo kodai tana ƙasa yau ba a sama tayi sallah ba bari naje na dubata, daganan ta juya ta kalli su Zeinab dake jiran ta tace "ku taso mu tafi." Ba musu suka tashi. AFREED na bakin ƙofar masallaci yana ta wange wangen ina zai ganta ko yauma a parking ɗin maza ta ajiye motar ta?" Ya tambayi kansa tareda nufar hanyar wajan ko da zai ganta acan to dama idan mutun zaije parking ɗin maza sai ya bi ta hanyar masallaci mata kamin yake kai wajen parking ɗin na maza, hakane ta kasance yanzu AFREED na shirin wucewa ta ƙofar masallaci mata dan zuwa parking ɗin maza dan tun tuni Ali ya kecan yana jiransa, ita kuwa AFREEN ta fito kenan dan zuwa neman Hasina ƙawarta, dama ta rika da tace ma su Zeinab suje mota su jirata. AFREED ya taho kansa duƙe yana dana waya itama ta taho ta kusa kawowa gun shi kawai sai taji ance "Bestyyyyyyy." ba tare da ta tsaya da tafiyar da take ba ta juyo da ƙarfi dan jin muryar Hasina shima ya taho ba tareda yasan da itaba kawai ji sai tayi ta bangaji mutum ai kuwa a take ta juyo da sauri a lokacin da wayar da ke ga hannu sa ta faɗi ƙasa, da sauri AFREEN ta tsuguna dan ɗauko wayar shima ya tsuguna a tare suka kai hannu zasu taɓa wayar aikuwa sai hannuwan su suka gamu da na juna a take sukaji wani yar yar tun daga cikin kwalwarsu har tafin ƙafafun su da sauri AFREED ya janye hannunsa dake saman na AFREEN sabida shi shok ɗin yafi jansa, a tare suka ɗago cikin sauri hankan yayi sanadiyar kwarewar niƙaf ɗin AFREEN ba tare da ta sani ba ko ta lura da hankan ba, cikin firgici da mamakin kyau irin nata AFREED ya waro idanso kuri 😳 yana kallon ta ba tare da yasan yayi hakan ba, gabansa na mugun faɗuwa, a zuciyarsa ya aiyana cewa anya wannan mutum, idan mutum ce kuma wane irin masifafen kyau ne da ita haka? A take ya ba kansa amsar cewa kai ba mutum bace dan gaskiya a cikin duniyar nan babu muntun mai irin wannan bala'iyayen kyau nata. Ya dawo daga duniyar tunanin daya lula ne a lokacin da ya tsinci zazakar muyar ta na furta " Dan Allah kayi hakuri ba da gangan nayi ba." Tana faɗar haka tan miƙa masa wayar da ke ga hannuta." Ƙoƙarin control ɗin kansa yayi ya ƙarɓi wayar da ta gama gogewa cikin zuciyarsa yake faɗin wallahi itace wace nake nema itace ke da muryar nan mai sanhi da daɗi sauraro dole ne tayi kyau koda na jin muryar ta, ai kasan ta haɗu, a take wata zuciyar tace masa idan fah ba mutum bace?" Sauri kauda zancen yayi sannan a fili kuma sai yace "A'a karki damu ba wani abu." Murmushinta mai kwantar da zuciya da saka mutum natsuwa ta sakar masa kuma har yanzu bata san cewa niƙaf ɗin ta janye daga fuskarta ba sannan tace "Nagode." Da sauri AFREED yayi saurin dafe daidai zuciyar sa da ke harba masa da sauri da sauri tareda lumshe idonsa sannan ya buɗe sanadin sakar mashi ƙayatacan murmushi shinta mai kashe matum jiki da tayi, tareda kallon lips ɗinta ƙananu suna matsi a hankali idan tana magana ga gefan kumatunta duka biyu na lotsawa koda kuwa magana take ba sai tayi murmushi ba, cikin zuciyarsa ya furta zata kashe ni, hankalinsa na ƙoƙarin barin jikinsa yayi saurin ɗaga mata kansa ya bar gun ba tareda yaso hakan ba, dan gudun kada ya bada kansa. Itama juyawa tayi ta bar gun ta nufi inda aminiyarta ke tsaye tana kallon su, tana ƙarasawa Hasina tace "Kai besty yau kinyi babban kamu kinga yanda mutum can ke kallon ki duk ya wani rikice a kanki kuwa gashi niƙaf ɗinki kuma ta ɗage sosai, kowama ke yakema kallon ƙurila juya kika yanda mutane ke kallon ki kamar sunga sabuwar halitta." Sai a sannan ta lura da niƙaf ɗin bata ga fuskar ta ai da sauri ta gyara zaman niƙaf ta daidaita ta sannan ta saketa ta rufe mata fuska rufe sannan ta juya taga wanda mutane suka taru suna kallon ta da sauri ta ja hannu Hasina suka nufi wajan motar ta ida su Zeinab ke tsaye suna jiran ta, sai a lokacin ta samu damar sauke ajiyar zuciya tace "Besty kinga abinda yasa nan nake ɓoye fuskata duba kiga wanda mutane suka taru suna kallon na wallahi duk sai najini a takure." "Rabu dasu haba kallon kaɗai ke nasu, ina maki maganar mutuman nan da kika yadawa waya kinyi min shiru." Hasina ta faɗa tana kallon AFREEN Murmushi AFREEN tayi tace to "Besty ya kikeso nace maki ni babu wani kallo da naga yanayi min kawai daga haɗuwa, shirme ne kawai irin naki, idan kuma wani kallon ya min to bai huce shima na mamaki ne kamar yanda sauran mutanen sukayi ba." Hasina tace "Hum sedai in kece baki gani ba nikuwa nagani wallahi bama kamar rikicewar danaga yayi, ni kam nahango wani abu a cikin idansa wanda ke baki ajiye hankali ba bare ki gani, kuma ni wallahi naga kamar ma MINISTRE DES DÉFENSES ET DE SÉCURITÉ ne wallahi baki ga shima da babette a fuskar sa, amma firgici ganinki da yayi bai san ma ya cire shi ba." "Kai besty mi zai kawo minister (minista) nan gurin ba tare da masu tsaron sa ba shi ɗaya haba kema dai kinsan hakan ba zai yiyu ba, da shine da a lokacin da na bangaje shi har nayi sanadiyar faɗuwar wayar sa to da yanzu matakan tsaron sa sun lalasani koda ace anesa da shi suke to yanzu zakiga sun rugo sunyi magani na, barema basa yin nisa da shi kullum suna liƙe da shi kamar shiwinggum, kuma da a ce anan yayi Sallah da kin dinga ji kukan motacin jami'an tsaron da suke kare lafiyar sa tun kamin a shiga masallacin, kuma gashi bama a maraɗi yake ba, yanzu haka ma bai taɓa zuwa garin nan ba, kinga ko a TV ba muji ance zai zo ba, dan haka ki bar ma faɗa kada ajiki. Hasina tace "Kuma hakane fah to amma wannan yayi mugun kama dashi, ta yiyuwa ko wani ɗan uwan sa ne kuma fah kawata kusan sunan ku irin ɗaya ne ministan da tsaro, Shi AFREED ke AFREEN ni ina ma zaizo ya aure minke." AFREEN ta taɓe baki tare da cewa kindaiji da shi ni mi zanyi da wani minister, KAMAL ɗin na ya ishe ni, shi kaɗai nakeso da kauna, kuma insha Allah shine mai gida na, yanzu dai ba wannan ba ku shiga mu tafi gida." Gaba ɗaya suka shiga sannan ta tayar da motar sai gida.................. ( nima sai nabi tawa hanyar nace bari na barsu hakanan har bayan kwana biyu kuma sai mu waiwayesu) Fatan alkairi ZAMBA CIKIN AMINCI FANS🥰🥰🥰 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ *_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_* *Page* : 33 & 34 Ali na ganin AFREED ya ƙaraso gun motar yace "Dan Allah AFREED miye haka ka wani zo ka shanyani anan kamar wani kayan wanki tun ɗazu ina nan inata jiranka, tunkuna ma ina kaje kayi zamanka har ka jima haka nidai nasan tare muka fito daga masallaci muna cikin tafiya na waiga ban ganka ba." Kollon sa AFREED yayi ya sakar masa murmushi kawai sannan ya buɗe motar ya shige, mamaki ne ya cika Ali kamin shima ya buɗe mazaunin direba ya shiga tare da tayar da motar yaja suka tafi. A hanya sai sakin murmushi yake shi kadai, Ali ya juyo ya kallesa da mamaki yace "Wai AFREED lafiya kake kuwa naga sai sakin murmushi kake kai ɗaya ko wani abun ne ya samu." Lumshe idonsa yayi tare da sakin ajiyar zuciya sannan ya buɗe su kan Ali yayi fuska kamar ba shine yanzu ya gama sakin murmushi ba sannan yace "Kai Ali sa idonka ya min yawa, toh sai da wani abu zan dinga murmushi ko baka taɓa gani na ina murmushi bane, har kake son damuna da tambayoyi???" Juwowa Ali yayi ya kallesa kamin ya maida hankali sa ga tuƙi sannan yace "Hum in tayi wari munji." Shiru AFREED yayi ba tare da ya tanka masa ba, sai lumshe idonsa da ya komayi kamar mai bacci tare da kwantar da kujerar sai ya ɗan gincira har suka kai kida yana a haka kamar mai bacci alhalin bahaka ba ne, kawai ya faɗa duniyar tunanin ta ne. Suna shiga gidan Ali na gama parking ya buɗe motar ya fice, direct ɓangaren su ya nufa ba tareda yayi ɓangaren tanti Aicha ba, Ali na ganin haka a ransa yace "To mike damunshi ne har haka? sai kuma yace bari naje tanti taga dawowar mu sai naje na tambaye shi ko mike damunsa." Yana shiga falon babu kowa, sai Khadijah ita kuwa tana jin ƙarar buɗe ƙofar ta ɗago dan ganin ko waye ya shigo aiko sai idanuwansu suka sarƙe cikin juna, murmushi Ali ya sakar mata yanajin wanda soyayyarta ke ƙara shigar sa, a zuciyarsa yace "Yakamata na fito na faɗa mata abinda ke raina kada wajan kallon ruwa kwalo ya mani ƙafa, idan haka ta faru kuwa bansan ya zanyi ba, sabida ba ƙaramin so nake mata ba." Ƙarasawa yayi gun datake zaune shima zama yayi kan kujerar dake kallon tata, ita kuwa tun shigowar sa da suka haɗa ido tayi saurin duƙe kanta ƙasa bata sake ɗagowa ba har yazo ya zauna sannan tace cikin siririyar muryar ta "Yaya ina wuni, barka da juma'a." Ta faɗa ba tare da ta ɗago ba. Kallon ta yake yana murmushi batare da ya amsa ba, jin shiru yasa ta ɗago dan taka ko bai jita bane, aiko sai take idanunta suka sauka cikin nashi, dam dam gabanta ya faɗi, da sauri ta ɗauke idanunta daga nashi tare da duƙe kanta, a zuciyarta tana cewa "ko dai yaya Ali ya naji abinda nakeji game da shine idan ko haka ne da naji daɗi." Bata ƙarasa tunanin ta ta tsintsi muryar nacewa "Khadijah zaki iya aure wani garin ki bar maraɗi?" Kamar daga sama taji tambayar tashi da sauri ta ɗago ta kalleshi suna haɗa ido ta sune kanta ba tareda tace komai ba amma cikin zuciyarta ta sai tace "Mizai hana yaya idai kaine mijin zan iya barin maraɗi na zauna duk ida kake, wani ɓangaren na zuciyarta yace kenan zakiyi iya tafiya ki bar mamanki da dadyn ki?" Atake kuma jikinta yayi sanhi. Ali ya ɗan nunfasa yace "Khadijah tambayar yaki nake, ko bakiji minace ba?" Cikin bugun zuciya ta buɗe bakinta ta ce "Ta ni yaya banda zaɓin kaina sai na Allah, idan Allah ya tsaro rayuwa ta akan zan bar garin nan ta dalilin aure to j'ai pas la choix, Ubangiji shi ne yasan daidai, kuma shine kan daidai ni ina farin ciki da duk inda Allah ya ajiye ni." Wata ɓoyaya ajiyar zuciya Ali ya sauke sannan yace "Alhamdulilah hakane kuma ƙanwata kinada gaskiya to bani labarin samarin dan ni tunda mukazo nan ban taɓa ganin kinyi fira ba ko miyasa, ai yakamata ace yanzu aure za'ayi maki dan kam yanzu kin girma." "Lah yaya saurayi kuma ni yaya banida wani saurayi dady bai barin mu kula samari kuma ni banda wannan ma duk a nawa nike da zan fara wani kula samari," Khadijah ta faɗa cikin shagwaɓar da ba tasan tayi ba. Shagwaɓar da tayi ba ƙaramin tafiyar masa da imani tayi ba, a zuciyarsa wani farin ciki ne ya luɓeɓe sa jin cewa babu wanda yayi masa rigagin shiga zuciyarta, dan haka yanzu yanzu ba sai anjima ba zaiyi mata bayanin abinda kecin ransa, gyaran murya yayi ya ƙara gyara zaman sa tare da maida hankalinsa sosai akanta yace "Ƙanwata kinason na zaki aure ni." Duk da abinda Khadijah keson jine ya fito daga bakinsa, sabida son da take masa amma haka bai hana gabanta faɗuwa ba, cikin sauri ta ɗago da niyar satar kallon sa aiko se idanunsu suka sarƙe cikin juna, da gudu ta tashi ta nufi sama tana murmushi direct dakin su ta nufa. Shikuwa Ali baiyi ƙoƙarin tsayar da itaba sabida yasan dole zai bata lokaci tayi tunani, amma sosai ya cika da farin ciki sabida ganin hakan ma da tayi ya nuna masa ta amince da tayinsa, a fili ya furta "Alhamdulilah yaudai na faɗa mata Allah na gode da kabani ƙaurin gwiwar bai yana abinda ke raina." Murmushi ya saki tareda tashi ya bar gun shima ya nufi ɓangaren su. Khadija na shiga ɗaki ta tardo Fariya da Farisa zaune saman gado suna fira suna dariya kana ganin su zaka gane cewa firar da suke suna jin daɗin ta, da gudu tayi wajen su ta faɗa tsakansu tare da rungume su tana dariya, kamin ta ɗan sassauta rungumar da ta masu tana kallon ɗaya bayan ɗaya, suma ita suke kallon cike da mamakin miyasa ta farin ciki haka, dan daga ganin yanayin aikasan tana cikin farin ciki mara misali, ganin mamaki ta suke kuma sun kasa cewa komai, kawai sai tajuyo ta sakesu baki ɗaya ta zaune tsakiyar su sannan tace "Sisters albishirin ku," Khadijah ta faɗa tana murmushi. Haɗa baki sukayi da sauri wajen cewa "Goro" cike da zaƙuwar jin wane albishirin ne tazo masu dashi. Sai ta ce "Fari ko ja?" A tare suke cewa "Fari tass sœurette dan Allah yi sauri ki faɗa mana har mun ƙagu muji ko miye." Tsalle tayi ta sauka daga saman gadon ta juyo ta na fuskantar su har yanzu dai murmushi ɗoke a fuskarta tace "Yaya Ali ya tambaye ina son shi zan auresh...... bata ƙarasa faɗar abinda tayi niyar faɗa ba sukayi tsalle suka sauka daga gadon tare da yowa kanta suka rungume ta su duka biyu har suna dariya da murnar jin wannan labarin har saida suka kai ƙasa da tsanani farin ciki da rungumar da suka ma juna, na saman kafet ɗin dake ɗakin suka faɗa tare dayin zama dirshan suna maida numfashin murna. Fariya ce tayi ƙarfin halin buɗe bakinta dan sun kasa ma yi magana dan tsanin farin ciki tace "Wayo Allah sœurette Khadijah zata koma Niamey da zama zatayi aure garin mu tana yiyuwa ma a kusan gida zaku zauna ko a gidan mu ɗin dama ba tun yau nakeso kikoma gidan mu ba amma na kasa samun hayar da zaki koma ɗin, yanzu dai gashi yaya zai mayar mana dake weeeeeee tayi ihu mara sauti sosai tare da daka tsalle farin ciki sannan ta koma ta zauna da murmushi kwance a fuskar ta tace "Alhamdulilah." Ita kuwa Farisa sai ta kamo hannuta na dama da duk hannayenta tace "Anty Khadijah to ke mi kikace ma yaya da yace maki hakanan injin dai kin amince?" Murmushi tasaki tace "Ah har na koma antyn kenan, ashe duk zakuyi farin cikin hakan, kenan kuma kuna so na auri yaya Ali, kun san mi nima sosai na faɗa soyayyarsa a zuciyata amma ai kunsan da haka dan ba tun yau nake faɗa cewa ina son ba amma na kasa faɗa masa sai gashi shi da kansa ya furtamin hakan, amma ni bance masa komai ba yana min tambayar na ji kunya na gudo ɗakin ban tsaya ba." Fariya tace "Ina ai dole ne ki koma anty tun yanzu, kuma hakan da kikayi shine daidai dama ba daga mutum ya faɗi yana sonka ba kake ce masa ka amince ba, hakan da kikayi ya nuna masa da amincewar taki yanzu kawai ya kamata tanti A'isha taji wannan dadaɗan labarin, dan a faɗa ma dady sai a saka ranar auren nan da yuri kokuwa Farisa?" Fariya ta tambayi Farisa tare da kallon ɓangaren da take zaune Farisa tayi saurin ɗaga kanta alamar eh ta na murmushi. "Ah kijimin Sisters ɗin nan kawai daga magana kuma sai shirya aure ai kun bari har mu ƙarasa daidaitawa kamin akai maganar ga manya mana, wannan sauri haka kamar dai kune angon." Murmushi sukayi sannan Farisa tace "Ah to mi za'a jira? Batun daidaitawa kuma ai kun riga da gun daidaita tunda kun daɗe da soyayyar juna a cikin zuciyar ku dan nasan yaya Ali ba tun yau bashi ma yake sonki baide faɗa ba ne dan haka mu alkairin abin kawai muke nema." Fariya tace "Lale dai kama Allah sanya alkairi kawai zamuce yanzu ku tashi muje mu ci abinci sai mu dawo mu zauna mu fara tsara yanda bikin nan zai ƙayatar da yardar Allah." Da ameen suka amsa sannan suka miƙe suka fita a ɗakin. *****. ******. ******. ****** Ali na shiga ɓangaren su ɗakin AFREED ya nufa, tardo shi yayi kwance ya lumshe lumsashin idanunsa kamar mai bacci da murmushi kwance a fuskar sa, ba tareda yaji shigowar Ali ba sabida faɗa wa da yayi duniyar tunanin, saida Ali yace "frèro waini yau wane irin farin ciki ne kake ciki haka da kakasa sanarmin ne har yaushe ka fara ɓoyemin abinda ke damun ka?" Ahankali AFREED ya fara buɗe idonsa kamar me tsoron idan ya buɗe su zaiga wani abin tsoro ko abin ƙi, ya sauke su kan Ali cikin kwanciyar hankali ya miƙe zaune yace "Ali kenan babu abinda nake ɓoye maka kawai dai nima yau tunda na farka na tsintsi kaina cikin wannan farin cikin da bansan dalilin yin sa ba kada ka damu kaji ɗan uwana idan da wani abu ai zan faɗama kaima kasani." Ali yace "To shikenan nikam nazo maka da wani albishir mai daɗi." "Dagaske ɗan uwa to faɗa man naji." AFREED ya faɗa cikin zaƙuwa. Ali ya gyara zaman sa sannan yace "Yaudai nasamu na faɗa wa Khadijah cewa inason ta zata aure ni." Waro ido AFREED yayi yace "Lah wai Ali da gaske kake kenan, yau ka samu ƙarfin halin faɗa to ya tace maka ita?" "Batace dani komai ina faɗamata ta rufe fuskarta tana murmushi se kawai tayi saman da gudu, hakan na nuna min ta amince, tunda ba zata fito ta faɗa min hakan kai tsaye ba, kasan halin mata da alkunya." AFREED yace "Hakane ɗan uwa ina taya ka murna sosai naji daɗin zancen dama ba tun yau nake cewa ka faɗama ta tun kafin wani ya riga ka amma tunda ta amince yanzu dai ya kamata kafin mubar garinan tanti Aicha tasan da zancen tunda kigin kwana biyar mu bar garin, kabari ni zan faɗa mata, ita kuwa sai ta sanarma dady." "Eh haka za'ayi ɗan uwa." Ali bai ida rufe bakinsa ba akayi sallama tareda turo ƙofar ɗakin AFREED Umar ya shigo, amsa masa sallamar sukayi kafin ya ke ƙarasowa gun da suke shima ya ne mi guri ya zauna sannan yace "Yaya AFREED wajanku nazo ku duka Allah ya taimake ni kuna tare, nazo ne muyi wata magana mai mahimmanci Allah yasa dai zaku goyi bayana kuma kusamin hannu ku masu albarka." Murmushin shi mai birgewa yasaki sannan yace "To muna jin ka Umar ai tunda naji kace min yaya yau nasan da abinda zaka faɗa yanada mahimmanci, to faɗi muna sauraran ka idai maganar Allah da Annabi ce mizai hana mu saka maka hannu." Ali yace "Sosai kam mu masu baka goyon baya ne akan komai idan dai bai saɓa wa Allah ba." Murmushi Umar ya saki tareda sosai kansa sannan ya duke kansa yace "Yaya AFREED yaya Ali dan Allah ku taimaka ku bani auren ƙanwata kuma masoyiyata abar ƙauna ta Fariya ku taimaka ku min rai ba dan niba sai dan Allah, kuga dai kam ina da halin kwarai kuma zan riketa amana wallahi ba za'a samu matsala ba insha Allahu." Sai yayi shiru daganan yana jiran jin abinda zasu faɗa. Kwashewa sukayi da dariya sosai suke yin dariyar, dan AFREED dariyar da yayi yau bai ma taba yin taba sabida abin ya mugun bashi dariya, saida sukayi mai isarsu sannan AFREED ya maida hankali sa sosai garesa tare da dafa masa kafaɗa yana murmushi yace "Dama ai nasan da walaki goro a miya, inba haka ba babu abinda zaisa ka zauna kana min magiya harda wani kirana da yaya yau da wani ladabi kamar da gaske, to wai ku yau wahayin soyayya aka maku ne da kowa yabi ya zare da zancen yana son waga yana son waga, dan yanzu Ali ya gama faɗa min cewa wai shima yanason Khadijah harma ya faɗa mata, injin dai kaima ka sami Fariya ka sanar da ita har kun daidaita?" Da Dariya shima Umar ya kwashe sannan ya ɗan tsagaita yace "Ashe bani kaɗai ne na kamu ba to nagode wa Allah da yanzu kun haɗe man kai kuyi ta surfaman iskanci dan haka yanzu ai sedai a yiwa juna kuma na ma fasa ladabin daidai nake daku duk wanda ya taka ni zan rama." Murmushi AFREED yasaki yace "Kaida Ali dai kudai ma juna dama ni ba ajinkun bane kusan da duk na girme maku, sannan kuma ni nace maku ga Wada nakeso nazo na zauna ina magiyar ku taimaka ku bani wacan inaso dan haka kuyi biyayya kokuwa na hana ƙannina wallahi naje waje na sama musa mazaje na gari na aura masu sabida kam yanzu nine mahaifin su kuma yayan su sai wanda nakeso zan bamawa kuma kam ko iyayenmu ba zasu can za zabina ba akan ƙannina." Ya ƙarasa faɗa yana murmushi. Saukowa suka da sauri ƙasa tareda kama ƙafafunsa "Yaya AFREED gamu ƙasa dan Allah a taimake mu a bamu aurensu mun tuba ai ba zamu ƙaraba." Murmushi AFREED yayi sannan yace "To shikenan ashe dai anaso da bakuyi biyayya ba sai na nuna ƙarfin ikona akan ƙannina na bama wasu amma tunda kunyi ladabi na baku halak makalak sedai wani abu da baku sani idan kuka kuskura kuka ɓata masu rai nima kam zakuga ɓaci raina." Da sauri sukace "Hakama bazata faruba baba AFREED, dan wannan ya wuce yaya sai baba suka faɗa tare da kwashewa da dariya sannan suka koma gurinsu suka zauna." Umar yace "To nifa yaya ban samu na sanar da ita wallahi dan na ƙasa sanar mata, gani nake kamar ba zata amince ba ko zaka taimaka ka faɗa mata?" AFREED ya murmusa sannan "Ashe ban sani ba kai matsoraci ne haka za'ayi abin naje baka ƙanwar tawa idan akayi sallama ka shige ƙarƙashin gado kace taje ta buɗe mutanen banza su hallaka min ita, to nafasa baka." Da sauri Umar ya riƙo hannu AFREED yace "Haba yayanmu ayi hakuri karmin haka, zanje na sameta na faɗa mata yau ɗin nan ba sai gobe ba a taimaka min idan basamu Fariya ba zaucewa zanyi." AFREED yace "Dadai yafiye maka kaje kasame ta ku daidaita daganan sai musan abinyi." Daga haka suka miƙe suduka suka nufi ɓangaren tanti. ******* ****** ****** ****** Yau saura kwana uku saukar su AFREEN kuma ya kama saura kwana biyar su AFREED za su koma garin su wato Niamey tunda hutun ya ƙare, kenan idan ayi sabkar da kwana biyu su zasu tafi. Kuma sabkar da za'ayi harda Khadijah d'iyar tanti Aicha itama tana cikin wa'inda za'ayiwa saukar kallo kuma da Zeinab ƙanwar AFREEN. AFREEN na zaune ɗakin tanti suna tsara abinda za'ayi a saukar Alkur'ani nasu mai girma, wayar tace ta hau ringin, tana dubawa taga KAMAL ne ke kiranta a take ta ɗaga sabida ita ganita miye abin ɓoyewa tanti wani abu daya dagan cewa ba dan haka, ta ɗoki wayar a gabanta, daga cikin wayar aka yi sallama ta amsa tare da cewa "Ina yuni?" Batare da ya amsa ba yace "An yuni lafiya?" "Lafiya lau, ya gari, ya aiki?" KAMAL yace "Alhamdulilah, ya mutan gidan duk suna lafiya ko?" Tace "Lafiya lau" a taƙaice KAMAL yace "My FREENKA ( AFREEN KAMAL) dama na kirane naji abinda kukeda buƙata na saukar ku kinji ina jinki faɗa min." A sanyaye tace "Non on a besoin de rien (a'a bamuson komai)." Sai yace "Ah ban gane bakuson komai ba, kodai abinda zai fitowa daga gareni ne bakuda buƙata?" A shagwaɓe ta ƙara lankwasar da murya tace "A'a wallahi ba haka bane mon roi (My king) kawai dai komai papa yace zai siya mana." KAMAL yace "Haba my FREENKA to ni miye anfani na idan har na bar papa ya siya maku abinda za kuyi anfani da a saukar ku ki faɗawa su papa cewa na ɗoki nauhin komai na saukar nan dan Allah a barni nayi." "A'a Please mon roi da ka barshi wallahi ai babu wani abu." To bakinga irinta ba kece dama bakiso nayi shikenan babu matsala." Yana ƙoƙarin kashe wayar tace "Tsaya kada ka tsike kiran dan Allah naya yarda zan faɗa masa shikenan ko." Murmushi KAMAL ya saki mai sauti sannan yace "To koke fah yanzu kiyi liste ɗin abubuwan da kuke buƙata."anjima zanzo nakarɓa sai na siyo komai da komai." AFREEN tace "Ok to babu damuwa insha Allahu zanyi." Yace "To D'accord sai nazo ko?" Tace "Eh Allah ya kawo min kai lafiya." Yace "Ameen, ki kulamin da kanki." Tace "Insha Allahu kaima ka kulamin da kanka." Yace "Karki damu za'ayi yanda kikeso gimbiya ta." Murmushi tayi tace "To sai anjima." Ba tare da ta tsaya jin abinda zai faɗa ba ta katse kiran." Tareda juyowa ta kalli tanti ta lokacin guda ta sada kanta ƙasa, dan ita tama manta cewa tanti na ɗakin ta biye masa sunata fira haɗa wani ya kulla mata da kanshi, kai amma naji kunya gaban tanti na zauna inata soyayya." Tsira mata idon tanti tayi kamar mai son gano wani abu a tatare da ita, sai ɗan musƙuta tace "Aya ɗiyata ki daina jin kunyata ninan kamar abikiya ta na ɗauke ki dan haka ki daina kunyata kinji ko." Murmushi tayi sannan tace "Wai tanti cewa yayi kada papa ya siya komai shi zai yi mana komai da akeyi." Kura mata ido tanti tayi na ɗan lokacin sannan tace "To ai bai wani abu kawai abarshi yayi tunda hakan yakeso yanzu kije ki faɗa wa papa naku kamin je ya siyo abubuwan saukar ta ku dan nasan ba zasu wuce yau ba." Tashi AFREEN tayi ta fita ta nufi sama dan zuwa ta gayawa papa. Tana fita tanti tayi ƙwafa tare da cewa............... Kuyi hakuri da wannan ba yawa😊😊😊🥰🥰🥰 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *Page* : 35 & 36 Tana fita tanti tayi ƙwafa tare da cewa "Zanyi maganin ku ke da KAMAL ɗin, indai ina raye ai ƙarya ne kiyi farin ciki yarinya, cikin gidan ace anfi sonki kan kowa to ha indai ba Hamida ce akeson kamar yanda ake sonki ba, to insha Allahu farin cikin da na uwarki ya ƙare zanyi maganin keda maifiyar taki badai ku ƴan gaban goshin Alhaji ba, hum ai sai ya dawo daga rakiya ku har indai da raina sai na saka maku ɓakin cikin da zaku ƙasa fita daga cikin sa har ƙarshen rayuwar ku." Ko da AFREEN ta faɗa ma papa sai da yayi faɗa kamin ya amince, sannan taje ta ɗauki takarda da biro ta rubuta masa abinda suke da buƙata, da yamma KAMAL yazo saida suka hira har ana shirye shiryen kiran sallah magariba sannan ya karɓi takardar ya tafi. Washegari wajan ƙarfe sha biyu na rana KAMAL yazo ya kawo abubuwan da ta rubuta masa a takarda gudan dayawa zakace shago guda ne ya saye duka sabida mota guda aka ciko da kayan, plower buhu biyar, wasu su biscuits, chocolats 🍫 sweet, juice, pop corner sosai aka ciko motar da su sai kace za'a buɗa wani babban shago, sannan ga rago biyu suma yace na girkin gobe, sai wata rantsatsiyar shada da wani haɗaɗen lace da ya sayar o AFREEN da Zeinab. Sosai abin ya ba wa AFREEN tsoro ganin wa'inna uban kayan da ya jibgo tsaye tayi tana kallon sa ta ma kasa ce masa koda ina yuni ne saboda tayi mugun mamakin ganin kayan. murmushi KAMAL ya saki sannan yace "Miye abin mamaki a ciki, ni akanki zan iyayin komai koda kuwa ace Aljihu na zai zama babu komai a cikin, sabida ke da ɗiyan da zaki haifa min masu kama dake ne nake neman kuɗin nan kin ga kam dan na ɗan na kashe maki su ba wani abu bane, ni da nakeson kiyi yanda kika ga dama da Aljihu na kamin ɗiyan mu su zo su tayaki wasa da shi sabida nakune ba nawa ba ni dan ku na nema." Murmushi AFREEN tayi tareda rufe idon wai taji kunyar maganar ta haifa masa yara da a ɗan shagwaɓe tace "Wallahi kayan nan sunyi yawa sosai, idan papa ya gani sai yayi faɗa, dama da kyar ya amince ya bari ka yi sayar hakan ma saida yayi faɗa amma babu komai bari kashiga daga ciki ai papa ma yana nan sai kayi mashi bayani." Zaro idonsa KAMAL yayi yace "Haba dai ni ne zan shiga da wannan kayan niki niki haka, ke dama bake zaki siyo ba aka maki faɗa ina gani ai nasan ni har mari sai nasha, kuma suna iya cewa sai an mayar dasu sunyi yawa, yanzu dai yanda za'ayi ki bari a ƙarasa shiga da kayan sai ki tura Zeinab ta faɗa masu, amma nidai kam tsoro nakeji." Dariya AFREEN tayi mai ƙara mata kyau tace "Wato kaida ke namiji ma kana tsoro ina gani mace kuma yarinya, kaga kai zai iya ƙinyi ma faɗa amma ni kam sai anyi min." KAMAL yace "To ai shiyasa nace ki saka Zeinab ta faɗa masu shi da su maman yanda kema ba za'a maki ba dan nikam bazan iya ido biyu da papa ba cikin wannan halin." Suna ciki maganar papa ya fito tsagar gidan tareda ƙaraso idan suke daga ita harshi ba wanda ya ga fitowar sa saida suka ji yayi masu sallama, da sauri suka ɗago a tare suka ƙaleshi sannan suka maida kansu ƙasa KAMAL yayi sauri duƙawa har ƙasa ya gaida papa, ita kuwa AFREEN tayi tafiyarta ta barsu nan, cike da kulawa papa ya amsa gaisuwar sa, sannan yace "Tashi ɗan kirki tashi haba." KAMAL yace "A'a papa ba sai na tashi hakan ma yayi." Papa yace "A'a tashi kaji ɗan albarka idai baso kake ni ma nayi durƙu shin ba." Da sauri KAMAL ya miƙe tareda sunne kasan." Papa ya ƙara gyara tsayuwar sa sannan ya ɗan musƙuta yace "To ko kaifa KAMAL, ci gaba yayi da cewa gaskiya KAMAL kayan can da ka jibgo sunyi yawa bai kamata haka ba banason maida alkairi komai ƙanƙantar sa da nasa anraba kayan can gidan biyu ka mayar da sauran kuma haka idan an mayar wanda kayi sayayyar wajan sa ya ga amshi ba daidai tun ya samu cinaki sosai, amma bai komai sedai kada a ƙara irin haka ka jiko, Allah maka albarka. Juyawa papa yayi ya koma ciki, KAMAL na ganin papa ya shige shima ya tashi ya nufi motarsa sa ya bar gidan. ******. ******. ****** AFREED kwance ya na ta juyi sabida bacci yaƙi ɗaukar sa babu abinda yake sai tunanin ta daga ya rumtse idonsa ita yake gani ta masa murmushi ta mai kyau da kwantar da zuciya, tashi yayi zaune tareda dage kansa a fili yace "Wai ni miyake damuna ne akan yarinyar nan? Tun ranar da na fara ganinta ta rikitamin da lissafi ta mamaye min tunani na baki ɗaya, kwata kwata bana tunanin kowa sai nata, duk motsina da hankali na da komai nawa sun koma mata, miyasa take son sakani cikin damuwa? ni da ba ma sanin ta nayi ba amma ta nason wargaza min tunani da lamurana baki ɗaya, yanzu hakan ma babu abinda nakeso kamar naganta a kusa dani, na samu kollon wannan kyakkyawar fuskarta ta da murmushinta mai birgewa da ɗan ƙaramin bakinta wanda idan tana magana kamar kada tayi shiru." A take yaji wani abu ya cakar masa zuciya da ɗan ƙarfi ga kuma faɗuwa da gabansa yayi da sauri ya dafe gefan zuciyarsa yana mai karanta lahaula wala ƙuwata illabillah, sannu a hankali ya ke sauke ajiyar zuciya yace "Miyasa ki keson takura min ne, mikike so ne daga gareni? ki taimaka ki faɗa min ko zan samu sukuni, shin ina zan ganta ko hankalina zai kwanta, miyasa na kasa daina tunanin ta ko dan ina cikin garin su ne? amma ai mu kusan barin garin mu komawa Niamey zan manta da ita ne, mais il faut que (yaka mata) kamin mu tafi na samu na ganta hankan ne zaisa hankalina kwanciya." Komawa yayi ya kwanta tare da lumshe ido da niyyar yin bacci, amma hakan ya gagara, dan ya na rufe idonsa hoton fuskar ta ya shiga yi masa waibuwa, tashi yayi gaba ɗaya ya fara safa da marwa cikin ɗakin yarasa ya zaiyi tunanin AFREEN ya adabi zuciyarsa, a sannu ya furta "Ina zan ganta ne? dama a masallaci na saba ganinta to gashi yau asabar gobe Lahadi mukuwa zamu ɗaga daga garin ranar talata, to kodai maida tafiyar tamu nake har sai ranar wata asabar ɗin mai zuwa in Allah ya yarda ko?" Shi kaɗai ke tambayar kansa sai kuma yace "Kai nayi kewar Momy da dady gaskiya bance zan iya ƙara wasu kwanaki a nan ba gaskiya, amma dai naso naganta ko dan na tambaya ta miyasa take damun tunanina ne ko namata wani abune bansani ba?" Yana cikin wannan halin na rashin samun bacci a kowane dare tun haduwar sa da AFREEN ya daina samun isasshen bacci kullum bacci ɓarawo ne ke yin gaba da shi, ko da hakan ta kasance yanzu, kawai sai ya mayar da tunanin de côté (apart) ya nufi toillet ya ɗauro alwala sannan ya fito yazo ya fara jero nafilfili cikin addu'ar sa kuwa fatan Allah sa ya ganta ko a hanya ne kamin ya tafi. Ɓangaren tanti A'isha tunda AFREED yaje mata da maganar Ali da Umar tayi farin ciki sosai har da ƴar rawa ta taka, haɗa cema AFREED sai ta bashi tukuici wannan albishir mai daɗi haka, sannan ta ɗaura da tambaya AFREED kan shi wa yake so, idan yanada ita ya gabatar da ita dan a saka biki lokaci guda, amma kawai sai yayi murmushi ya kama hanya ya fita daga falon, baki tanti ta saki tana kallon sa har sai da ya b'ace ma ganinta kamin ta ke maida hankali kan wayar ta data ɗauki ruru sakin murmushi tayi gani mai kiranta ahankali ta furta "Ɗan halak kaƙi anbato." tare da ɗaukar wayar ta ƙara a kune tace "Assalamu alaikum yaya ina yuni." Daga cikin wayar wanda takira da yaya ya amsa sallamar tare da cewa "Lafiya A'ishah ya gida ya yara." Tanti A'ishah tace " komai lafiya lau yaya da ma yanzu nan nake cewa zan kiraka kuma sai gashi ka kira." Anhan "To ina jinki A'ishah nasan dai da magana a bakinki tunda yanayin da naji muryar ya tabbatar da kina cikin farin." Murmushi tanti A'isha ta komayi sannan tace "Hakane Abban AFREED wallahi wani abun farin ciki ne ya samu, yaran nan suka zo mana da magana mai daɗi Ali ne yace yana son Khadijah da aure, shi kuwa Umar Fariya yakeso, amma abinda ya rage min hanzarin shine yarona AFREED shi kam na tambaye sa ida da wada yake so ya faɗa man sannan ya gabatar da ita dan a haɗe bikin nasu baki ɗaya amma mi sai baice dani komai, sai ma tashi da yayi yana murmushi ya barni anan zaune. Sai da dadyn su AFREED ya nisa ya saki wani ƙayatacan murmushi kamar tantin na gaban shi yace Alhamdulilah "Amma naji ɗadin wannan zance A'ishah gaskiya kinci baban tukuici ba tun yau nakeson ganin yaran nan sunyi aure ba amma suka ƙiya gashi yanzu Allah ya karɓi addu'ar mu Allah na godema, shikuwa wannan sangartacan ɗan naki ki barni dashi nasan maganin sa, dama na basu délai kan su fitar da matan aure nan da shekara guda, nayi niyyar idan basu fitar ba zan fitar masu da kaina, amma tunda su sauran sun fitar ba damuwa shi kam zan barshi har lokacin da na ibar masu ya cika idan bai fitar ni zan nema masa." Tanti A'ishah tace "A'a yaya ba haka za'ayi ba ai shi namiji ne bai kamata a masa auren dole ba a dai barshi ya zaɓan, kuma idan Allah ya yarda kamin lakacin da aka bashi yayi zai fitar da wace yakeso, gaskiya bama son auren dole." Hum A'ishah kenan kedai kada ku bari lokaci ya kure maku, amma auren dole har nayi makushi na gama, su ɗiyan naki da suka ceci kansu kan hukunci na, su aure nasu nan da wata shida a lokacin yaran sun gama yi exam kuma a lokacin result ta su ta fito idan tayi kyau se a gama baki ɗaya ayi walimar bikin aurensu da na makarantar su." Tanti tace "Insha Allahu ma zamu fitar da namu zaɓin muma, kuma Allah kaimu nasu lokacin suma nida nakeso kamin nasu Ali shima AFREED ya fitar da tashi musha biki baki ɗaya." Dady yace "Kanku dai akeji nikam nagama yanke hukunci." Daga nan suka ƙara gaisawa ya mata zancen sabkar Alkur'ani da za'ayi yiwa Khadijah a gobe lahadi sannan ya mata sallama tareda da katse kiran. Da murna sa yake sanar da Momy AFREED wannan albishir da tanti tayi masa, itama cike da farin ciki take ta kwararo masu addu'a da Allah sa alkairi sosai taji daɗi har tana hango ta taci shiri tana cin bikin auren ƴayanta, kamar yanda ita take zuwa bikin ƴaƴan abukanta itama an kusan zuwa na nata ƴaƴan." Shima Umar ya samu ya faɗa wa Fariya abinda ke ransa kuma ta amince da tayinsa dan haka soyayya ce me ƙarfi ta shiga tsakani Ali da Khadijah wada tu tanaji kunya har ta saki jikin ta suna shan soyayyar su, haka ma ɓangaren Umar da Fariya abin ba'a magana. Washegari ya kama safiyar ranar Lahadi kuma yau ne saukar su AFREEN da za'ayi ƙarfe hudu na yamma, tunda safe gidansu su AFREEN ya cika da ƴan'uwa da abokan arziki, ana ta hidimar walimar saukar, AFREEN ce zaune cikin falon gidan nasu da waya a hannuta tana ta mayar da saƙon da ƙawayen ta ke ta turo mata wa'inda zasu samu damar zuwa da wa'inda ke faɗa mata uzurun su, sosai take chatting da kawayen da kuma annurrin zuciyarta wato KAMAL, wayar tace ta ɗauki rururi alamar kira ya shigo, wani irin farin cikin ne ya mamaye zuciyarta hada ɗan wani tsalle tayi daga zaune tace "Ma très très chère Momy jannah adoré" (my anti adorable) sannan tayi picking call din tana murmushi tare da yin sallama, kamin daga cikin wayar a amsa sallamar tace "Wayo mom na mai sona nayi kewarki sosai rabon da muyi waya tun shekaran jiya fah." Daga cikin wayar akayi dariya mai ɗan sauti sannan wada ta kira Momy jannah cikin wata dadaɗa murya mai kamala tace "Haba my beautiful daughter irin wanan murna haka kamar dai nace gani a hanya zanzo Niger ke dai kam naga baki ƙiba kowane lokaci muna liƙe da waya nidake muna hira, to ya shirya shiryen saukar ne ana tayi ko? naso ace ina nan za'ayi wannan saukar sabida ta farin ma da aka maki ba na Niger amma ai dolene inda kin tashi aure nazo Insha Allah." ( In masu karatu basu manta Momy jannah itace ƙanwa Arahamat mahaifiyar AFREEN da kuma Ibrahim yayan su) AFREEN tace "Haba Momy har sai zanyi aure ne zakizo, nida sai na ƙarasa karatu kamin nayi aure, ai Momy daga bakizo ba kwanakin nan muna samun hutu ni sai nazo Dubai ɗin dan nikam na matsu na ganki shekara 7 rabon dana sakaki a idona Momy tun inada shekara sha ɗaya rabon dana ganki a zahiri sedai ta waya ko indna munyi apple video ni kawai so nake naganki gani gaki Momy tu m'a beaucoup manqué (nayi kewarki sosai)." Murmushi Momy jannah ta saki kamar AFREEN ɗin na gabanta sannan tace "Ai da zakizo ɗiyata danaji daɗi, sosai nakeson zuwan ki garin nan amma makaranta ta hanaki, kawai kuna shiga hutu ki kirani ki faɗa man ni zan kira mahaifin naki na tambaye sa zuwanki nan insha Allah." To shikenan Momy ina yaya Aban, da ya Fujai da Inayah?" "Duk sun fita wallahi daughter, Inayah kawai kenan bari na bata ku gaisa," bata jira cewar AFREEN ba ta shiga kwalawa Inayah kira yarinyar da bazata wuce 9years bata fito daga ɗakinta, tana zuwa uwar tace "Inayah karɓi ku gaisa keda anty AFREEN." Inayah najin ance anty AFREEN ta karɓe wayar da sauri tana jin daɗi, sannan suka shiga yin hira itada AFREEN, sosai yarinyar keson AFREEN, sun ɗauki kusan minti 10 suna hira kamin suke yin sallama. AFREEN na gama wayar da Momy jannah da Inayah, tana sauke wayar daga kunnanta kawai sai taji an rufe mata ido ai kuwa da sauri ta ɗan zabura sabida bataji shigowar kowa falon ba, cike da tsoro ta riƙe hannu wada ta rufe mata idon a tsorace tace waye saida ta maimaita sau uku kamin a sakar mata ido juyowa tayi da karfi da niyyar ganin wanda ya rufe mata ido, ai batasan lokacin da saki wani ihu can cikin maƙoshi ba tare da waro ido sanadin ganin Fanna ƙawarta dake Diffa a kusa da ita abin kamar almara ba tare da ɓata lokaci ba ta ƙarasa gun Fanna tare da rungumeta tana farin ciki sun kai minti biyu a haka sannan ta saketa tace "Cœurly da gaske kece yaushe kikazo, wallahi har na fida ran zuwanki naga jiya ta wuce baki zoba kuma na kiraki sedai ace wayar a kashe take, nace nasan baki samu dama ba, sai gashi kinzo amma dai ba daga Diffa kike ba ko? naga yanzu safiya ce uniform ɗin da za'a a saukar na nan kema nasa an dumka maki dama nace ko bakizo tu sai na turo makisu ta bus." Fanna ta ƙara faɗaɗa murmushi dake fuskanta tace "Nidai ce cœurly tun jiya nazo dadare ina gidan cousine ki ta shamsiya dama nace suprise zanyi maki kuma gashi." Ƙara rugumeta AFREEN tayi ta na murmushi sosai taji daɗin zuwan nata, suna a haka aka turo ƙofar falon aka shigo ba kuwa bace illa bancin Hasina dan haka itama idanunta suna sauka kan Fanna ta rugo ta rugumeta tace "Sis Fanna yaushe kika zo wayo Allah yaushe rabon da na ganki nayi kewar sosai." Murmushin tayi tace "Nima nayi kewarku sosai kawai nayi niyyar yi maku bazata ne wallahi sosai naji daɗin ganin ku tare dani." Daga nan sukayi ɗakin AFREEN, inda AFREEN kin ke ɗauke da jakar kayan Fanna har suka shige ɗakin saman gado suka baje sunata hira sun kai kusan minti talatin suna fira sai ga Firdaoussi cousin din AFREEN itama ta shigo, aiki nan suka gamu suna hira cike da farin ciki, sai wajan ƙarfe biyu da rabi na rana suka tashi da ɗaiɗaya suna shiga toillet suna yin wanka don shirin zuwa jan saukar." Haka ɓangaren su tanti A'ishah ma anata shirye shiryen zuwa wajan saukar da za'ayi yiwa Khadijah kowa na ƙoƙarin shiri banda AFREED sabida so yake suna fita, shikuwa ya shiyar yaje masallaci inda ya saba haɗuwa da AFREEN ko Allah zaisa ya ganta cikin anguwar koda zata wuce ne, don wallahi shi idan yau bai ganta ba ana iya samun matsala, amma mi Ali ya nuna masa bai isa yaƙi zuwa saukar masoyiyarsa ba, dan haka babu wanda ya iya ya tashi ya shiga wanka dan ya shirya shima ya bisu badan yaso ba, amma ya ɗau alwashin, suna dawowa Sai yaje masallacin nan dan yau bata yiwuwa ma ya iya kwana ba batare da ya saka ta a idon sa ba, koda kuwa bazai samu damar gani fuskarta ba. Duk sun na bakin motocin su AFREED kaɗai suke jira aikuwa sai gashi ya fito cikin wata irin dakakiyar shada Green kamar pomme (apple)🍏dumkin rigar iya kar ta bakin gwiwa da wando shima ya kamasa daidai musali da hula wanda iya ajiyar hular ma akan AFREED na daban ne, takalmin sa kalar shada ne agogon sa ma haka komai da komai dai yayi macin Masha Allah kayan sunyi matuk'ar masa kyau sosai suka ƙara fito da class dinsa ga wani uban kamshi da yake zubawa sai kace da ruwan turare yayi wanka, kannansa ma se da suka shagala da kallon sa kama tun daga Ali har zuwa ummi ya ƙaramar cikinsu, har tanti A'ishah ma ba'a barta a baya ba wajan kallon shalelen ɗan nata, Farisa ta saki murmushi a cikin zuciyarta tace "Dole ne yayana tun ba yau ne nagano cewa ka iya dressing cikin jinin ka yake ba Allah Ubangijin ya kare mana kai abin alfahari mu." Daidai nan AFREED yaƙaraso gun, Ali ƙamewa yayi ya sara masa sai kace suna bakin aiki, sannan yace "Woow mutume na irin wannan dressing haka kamar zakaje zaɓen wanda yafi iya dressing ko kuma na kyawawa wai kaga yanda kayi matuƙar kyau kamar kaine ake yiwa saukar ko kuma kaine saurayin mai saukar." Hararen Ali yayi ba tare da yace masa komai na ya nufi wata haɗaɗiya Prado green wada ta ɗan ciza color ɗin ya buɗe yacema tanti ta shiga su tafi sabida shi zaiyi driving da kansa dan yau yana sha'awar tuƙi, kuma haka kawai yake jinsa cikin farin cikin, batayi musu ta buɗe baya ta shiga kamin take ƙarasa rufa ƙofar Farisa ta ɗan matso da sauri ta buɗe gidan mai zaman banza ta shige, sabida tace sedai AFREED ya mata abinda zai mata amma kam ba zata shiga motar su Ali. Shima shigayayi bai ce mata komai ba ita Amal tashi gidan baya kusa da tanti A'isha ya tayar da motar , su Ali na ganin haka shima ya buɗe motar su ya zauna wajen zaman direba shima Umar ya buɗe wajan mai zaman banza ya shige, Fariya da Khadijah kuwa suka shige sannan Ali ya tada motar shikuwa AFREED har an wangale masa ƙofa ya fita Ali na binsa a baya, ƙwayen Tanti A'isha kuwa har sun riga da sunje makarantar kawai jiran tanti ne suke da kuma ita kahdijah da za'a yiwa saukar............ Muje zuwa.....😜😜😜😜😜 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* Barka barka *Mom Lalla* (sis sajida) ina tayaki murna ƙarasa littafinki mai takai ( *MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR)* gaskiya ki zuba ilimi da basira a wannan littafi yayi ma'ana sosai fiye da tunanin mai tunani Allah ya biyaki da gidan aljanna, gaskiya kin nishaɗan tar damu mun ƙaru da abubuwa sosai a ciki Allah ya yafe maki kurakuran dake keci, Allah ƙara basira da ƙarfin ido sai mun haɗu a sabon littafin ki wanda muke fatan samu kafin azumi💃💃💃💃💃💃 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ *_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_* *Page* : 37 & 38 AFREED da Zeinab sun saka wata rantsatsiyar shada golden color wada KAMAL ya kawo masu an masu ɗumkin doguwar riga ba'ayi kwalliyar komai ba a rigunan amma yankan rigar kaɗai abin kallo ne, masha Allah ɗumkin ya karɓe su sosai ba ma kamar AFREEN sosai doguwar rigar ta zauna ajikinta ɗas, suka saka farin hijabi dogo har ƙasa sannan AFREEN ta ƙara da wata golden ɗin niƙaf mai mugun kyau, sai fara safa da ke sanye da ƙafarsa da takalmin musu ɗan tsini golden, sosai ta fito kamar wata cikakkiyar balarabiya irin larabawan na Sudan Firdaoussi da Fanna da Hasina sukaci ankon da aka fido ta saukar ta wani haɗaɗen materiel fari da maron ɗin hijab, suma kuwa nasu hijab ɗin har ƙasa, bayan sun gama shirin nasu tsaf suka fito falon suka tarar da iyayen nasu suma su gama shiryawa suna jiran saukowar papa dan su wuce wajan saukar, haɗa kakar su AFREEN Hajiya Zakiya za'a je wajen saukar. Iyayen nasu nata murmushi jin daɗin ganinsu cikin kamala kamin wani yace wani abu Hajiya Zakiya tayi saurin cewa "Ah masha Allah ƴan jikokina kunyi kyau Allah maku albarka" ƙara kai dubanta tayi gun AFREEN kamin tace "Ke kam AFREEN har yau bazaki iya haƙura da wannan abin rufe ido ba? Anyi mutum shi kullum fuskar sa a kulle kamar munafiki, ke dan Allah cire mana wannan abin da sai maras gaskiya ke saka shi, ke kuwa da gaskiyarki haba dan Allah." Hajiya Zakiya ta faɗa tana hararen AFREEN dan ta bata haushi sabida yawan saka niƙaf da takeyi. Murmushi AFREEN tayi sannan tace "Kaka kinga kin fara ko, to ni wallahi bana fitar da ita ba kawai se ki sakamin ido." "Kijimin ja'irar yarinya Arahamat ina guje maki zafi kina cewa na saka maki ido, to kada fida man ai dan kanki, ga dangin ki nan kowa da fuskarsa buɗe saike kin wani kayo wannan tashin hankali kin saka." AFREEN ta ɗan turo bakin daga cikin niƙaf tace "Eh anji ɗin kuma ni ban saka tashin hankali ba ehe." Arahamat mahaifiyar AFREEN tace "Barta dai mama ai ita ce zataji zafin ba wani ba." Hajiya Zakiya tace "Ah to Arahamat ke ganar min hanya ni kam sai nafasa zuwa wajan saukar nan tunda naga wada akewa saukar ta gama zama fitsarariya." Da sauri AFREEN taje ta zauna kusa da Hajiya Zakiya tare da riƙo hannu ta tace "Haba kakata mi yayi zafi haka ai idan baki jeba saukar nan ba, ai ba zatayi armashi ba, kuma cewa kin fasa zuwa nima kam zan cire kayan nan nayi zama gaskiya." Murmushi Hajiya Zakiya tayi tace "Ina ai bazan fasa zuwa da wasa nake jikokin nawa har biyu su na sauke Alkur'ani mai girma sai naki zuwa nasaka masu albarka haba ai ba zai yiwu ba, kuje muje kawai." ta faɗa tare da miƙewa daga inda ta ke zaune, duka ƴan falon suka kwashe da dariya, daidai na papa ya fito shima cikin shirin sa. Batare da ɓata lokaci ba suka fice daga falon suna isa harabar gidan suka tarar da Fahad da Imran da yan aikin gidan maza da mata hata mai gadi da matarsa da yaransu uku sun shirya suna jiran su domin halartar wajen saukar, banda mutanen da sukazo taya aikin wato yan uwa da abunkan arziki na nesa da na kusa wanda tun ɗazu direbobin gidan suke jida suna kaisu islamiyya. Papa ne ya isa kusan motarsa ya fitar da ita daga wajan parking sannan AFREEN shikuwa Fahad ya riga da ya fitar da tasa motar, papa ya buɗe ma Hajiya Zakiya gidan baya yace tashiga, amma ƙiri ƙiri tace kam bazata shiga ya saka matan shi su tafi dan ita kam motar Fahad zata shiga, haka kuwa akayi ta shige motar Fahad gidan bayan shikuwa Imran ya zauna wajen mai zaman banza shi kuwa Fahad mazaunin direba, motar papa kuwa Arahamat ke wajen mai zaman banza, umma da tanti gidan baya, papa mazaunin direba, motar AFREEN, Fanna ke mazaunin direba sabida sunce kam yau ba zasu barin AFREEN yin tuƙi ba, AFREEN zaune wajen mai zaman banza, sai Hasina da Zeinab da Firdaoussi gidan baya. Sauran motocin guda uku kuwa ƴan aikin gidan ne da direbobin gidan da mai gadi da matarsa da ƴaƴan sa a ciki, motar su AFREEN ta fara fita sabida gani da sukayi lokaci nason ƙurewa sannan ta papa baya ta Fahad sannan na ma'aikatan gidan wanda da suka fito saida suka tsaya mai gadi ya fita ya kulo gidan kamin suka kama hanya wada a lokacin motacin mutanen gidan sun kusa ƙarasawa makarantar islamiyyar. Suna ƙarasawa islamiyya, AFREEN da Zeinab su kayi saurin fita daga motar suka nufin gun ƴan saukar suka nemi gu suka zauna sabida lokacin fara saukar ya kusa, so anan ne wani malami yazo kusa da AFREEN yace mata ai ba nan ne gun zaman ta ba ga inda aka tanada can domin ita sabida ita ɗaya ce za'a yiwa saukar hada da ta littatafan addini tunda suka shiga filin saukar ake bin su AFREEN da kallo sosai shigarsu ta ɗauki ido mutane wasu kam mamaki suke a ina yarinyar ke samu niƙaf ta ko wane kalan kayanta abin na matuƙar ɗaure masu kai sosai yake basu mamaki, bare niƙaf ɗin da ta saka kala golden ga adon Stone dake mugun kyalli. Lokacin da suka shigo AFREED kanshi duƙe yake yana ɗane danen waya ya dai ji Ali dake kusan shi yace masha Allah, kuma hakan baisa ya ɗago ba, dan ganin abinda Ali ke faɗawa masha Allah. Ba musu AFREEN ta bi bayan malamin nan har suka ƙarasa gun wata haɗaɗiya kujera sannan yace mata nanga ne gun zamanta, cikin ladabi ta juyo ta kalli malamin tace "Malam da na zauna tareda su can ɗin zan fi sakewa, kaga tunda muka shigo mutane ke bina da kallo ina ga na zauna ana ni ɗaya zan takura, amma idan can ne, sai na zauna a bayan su kaga na kare kaina daga kallo mutane." Murmushi malamin yayi yace "AFREEN wannan daraja Allah yayi maki godema sa kawai, dolene ki zauna anan sabida yurin da ke ya dace najima banga yarinya mai kwazo da basira irinki ba, wannan baiwar da Allah yayi maki itace yau har ta saka aka wareki daka cikin duban jama'a aka kawo ki nan yarinya 57 da na miji biyu ake yiwa saukar nan amma babu wani da ya kamo koda farcan ki ne bare kafarki, kuma zancen mutane na kallo ki ba wani abu bane, tunda basu ma fara kollon ki ba, sai idan kin fara karatu tunda ai baki manta cewa kece zaki fara karatu duk a cinkin yawan mutanen ga, ke zaki buɗe hilin saukar muyarki mutane zasu faraji da kuma daga ƙarshen muyar dai nan taki ce zata rufe filin saukar nan da addu'a dan haka ki kwantar da hankalin ki fiskanci abinda ke ganki ba yau bane kika fara haka." AFREEN tace "To shikenan malam." Murmushi malamin yayi kamin ya bar gun nata. Taro har taro yuri ya cika sosai da sosai idan kaga yanda ɗan adam ya taru a wajen zakayi tunanin cewa duniyar ce baki ɗaya ta haɗu a wajen alhalin ko kaso 1 bai kai ba a cikin ɗari ba. Babban malamin wato mai islamiyyar ne yaje ya hayo kan manbari ya yi gyaran murya tare da yin sallama sannan yace mutanen su dawo da hankalinsu wajen ɗaya za'a fara sannan yayi wa mutane godiya halartar taron nan da sukayi, sannan ya ƙara da cewa "Ba tare da ɓata lokaci ba zamu kira malama kuma ɗalibar mu, mai hazaƙa kamilala yarinya mai nutsuwa da tarbiyya mai hankali da girmama kowa da kowa koda kuwa ta girmeka zata baka girman ka wada tasan ya kamata mai jin tsoron Allah, kowa na ƙoƙari sosai a makarantar nan kowa nada hazaƙa sabida mukam mun yarda da ɗaliban mu, sedai babu wanda ya kamo ƙafar wannan ƴar albarkar yarinya, zato zo ne ta buɗe mana fili da addu'a sannan tayi karatun. AFREED najin yanda malamin ke taɗa wannan yarinyar amma bai ɗago daga duƙin da yake ba yana dana wayar sa, har saida Ali yace masa "Wai AFREED miye haka kaida kazo gun sauka kuma shine ka wani buge da dana waya, dan Allah ka ajiye wayar nan ka kalli abinda ya kawo ka nan." Ba tare da AFREED ya ɗago ba yace "Ali kaga kada ka takura man, da ma banyi niyyar zuwa ba kuka ta kuraman, idan kuwa angaji da gani nane a gun nan sai nayi tafiya ta dama inada abinyi." Ali yayi murmushi yace "Hum ai babu inda zaka kana nan tare da mu har sai an kammala saukar ehe." Ko kollon sa AFREED baiyi ba bare yayi tunanin ya amsa masa, Ali ya mayar da hankali sa wajen saukar AFREED kuwa ya ci gaba da aikin da yake a wayar sa. Can cikin lasipika babban malamin yace " Ba wata bace wannan ɗiyar albarka sai *AFREEN SADISU ASMANE SANGA* , ta fito tazo ta buɗe mana taro da addu'a." AFREEN ta taso daga inda take zaune ta nufo malamin a nan take idanun jama'a suka dawo kanta, Ali yaro ido dalilin jin suna mai kama dana AFREED taɓo yayi yace "Broh kaji wata mai kalan sunan ka ashe za'a sami mai irin sunanka kuma mace kai amma nata yafi naka daɗi masha Allah." Keda kecen AFREED in ya tanka to kin tanka bai ma ɗago ba bare Ali yayi tunanin samun amsa kuma badan baiji shi ba, da Ali yaga haka ya san ba tanka masa ba zaiyi, sai ya mayar da hankali sa gun da yafi masa mahimmanci. AFREEN na ƙarasowa gun manbarin malamin ya sauka ya mata nuni da ta hayo kan mimbarin, ba musu ta ɗale kan tayi sallama kamin ta ke gabatar da kanta, lokacin da tace "Ni sunana *AFREEN SADISU ASMANE SANGA* ina ma kowa barka da zuwa." Lokacin da AFREED ya ji muryar AFREEN na gabatar da kanta da sauri ya ɗago harda ƴar zabura yayi jin muryar da ba zai taɓa mantawa da ita ba a tarihin rayuwar sa, sosai yayi mamakin ganinta yurin nan, dan sosai ya gane ta duk da tana cikin niƙaf, lokacin ɗaya yaji wani sanhi ya ziyarci zuciyarsa, murmushi yayi can ƙansa zuciyarsa yace "Ashe anan ne zan ganta, daban zoba dana yiwa kaina." Bai an kara ba yaji zazaƙa muryar ta ta fara addu'a buɗe taro, sosai ya nutsu yana sauraran yanda zazaƙa muryar ta ke fitar da sautin lafiyayar ƙira'a mai daɗi sauraro, duk mantawa yayi da wajan mutane suke kawai shi gani yake shi ɗaya ne a gun kuma shine kaɗai ke sauraran dan haka ya shagala sosai da kallon ta ko kyafta idon sa baiyi, har ta fara karatun Alkur'ani tana kuka sosai ba har muryar ta na shaƙewa, wani mungun tausayin ta ne ya ɗari a zuciyarsa ba tare da ya an ƙara ba yaji wasu ruwa masu ɗumi sun sauko masa a fuska, bai kai ga shafe hawayen da suka zubo masa ba yaji muryar Ali nacewa " woow broh ban taɓa jin wani na karatun Alkur'ani ya birgeni naji kamar kar ya daina irin yarinyar nan sosai ƙira'ar tayi daɗi zakace wata balarabiya." Sai a sannan ya tuna da gun sauka ne suke da sauri ya share nasa hawayen dan kada Ali ya gani, sabida yasan idan ya gani iskanci zai masa, sai kuma ya fara yan wange wange yana kallon mutane gurin duk sai yaji duk baiji daɗin ba ganin idon mutane akanta kowa ita yake kallo sai yake jin inama ace yana da ikon da zai je yace ta dakata da karatun nan ta tafi gida, haka dai ya dingajin ba daɗi a zuciyarsa duk da cewa bawai ganin fuskarta ake ba amma hakan ma ji yake inama ace kowa zai daina sauran muryar nan a barshi shi ɗaya ya saurara haka kawai yaji zuciyarsa na masa zafi. Yanata zancen zuci har AFREEN ta kammala karatun ta koma gurin zaman ta, kowa na ta santin karatun sai ji kake ana macha Allah, papa baki ya ƙi rufuwa sai jin daɗin yake sosai nan daga bayan shi ya ji yasu mutane nace "Allah yayiwa iyayen wannan yarinyar albarka da suka sakata a islamiyya da kuma ita karan kanta yarinyar" sosai papa yake jin wani farin ciki na shigar sa, sai ya juya yace Amin nagode, sukuwa harda tambayar ko shine mahaifinta sabida kamar da suka gani sunayi sai papa ya amsa masu da eh daga haka suka fara masa fira harda masu karɓar number sa sukace dan ayi zumunci, sannan da ɗaya ɗaya ɗaliban da ake yiwa saukar suka fara tashi suna yin karatu har duk suka kammala karatun, sannan aka shiga raba kyaututtuka wa ƴan saukar. Har yanzu dai AFREEN ce farin bawa kyauta, ga lasipika babban malamin yace "Alhaji Issa ɗan canjin shine zai bawa AFREEN kyauta (Alhaji Issa ɗan canji shine mijin tanti A'ishah wato tantin AFREED). Alhaji Issa ya miƙe yana gyara malumalu dinsa ya ƙarasa ida AFREEN take tsaye kusa da kyaututtukan, ya ɗoki kyautar da aka tanada dan ita yana murmushi ya miƙa mata sannan ya saka hannu sa cikin Aljihu ya fitar da jika Talatin (50000) yamiƙa mata, risinawa tayi ta ƙarɓa tare dayi masa godiya, kafin Alhaji ya koma inda yake zauna, wani shima ya fito ya bawa AFREEN rafar ƴan 1000 da baisan iya adadin suba ya bata sannan yace "Allah maki albarka yarinya kiriƙe halinki kada ki canza shi." Ta amsa da ameen tana godiya, haka mutane sukayi ta tashi suna bata kayauta har saida taji bazata iya rikesu a hannu ba dama wasu ta riga da ta ajiye a ƙasa, anty Khairat ce ta taso ta ƙara so inda AFREEN take tsaye da kyaututtuka kamar zasu rufe ta, tana ƙarasowa tace "Sannu ƴar ƙanwata." Da mamaki ta juyo tana kallon Khairat amma ta kasa mata maga, kollon yaushe tazo garin ne take mata "Khairat na ganin haka ta lumshe idonta sannan ta buɗe su tace "Maida hankalinki wajan ƙarbar kyaututtukan ki daga baya nayi maki bayani." ba musu ta juya ta ci gaba. Sannu a hankali AFREED ya tashi daga gun dayake zaune ya nufi idan zai sada dashi da AFREEN da takunkumi a fuskar sa gudun kada mutane su sheda ko shi waye, Ali ya zuba masa ido yana kallon sa da tambayar ina kuma zaije, yana ƙarasawa gun AFREEN da Khairat da babban malamin da su suke tayaya karbar kyaututtukan ya je gab da ita ya tsaya ya fido da key ɗin mota da sheck na miliyan ɗaya CFA ya miƙa mata sannan ya gusa sosai gab da ita yayi magana cikin wata muryar mai kama da ta raɗa yada babu wanda zai jiyoshi yace "Yakamata ki bar gun nan gaskiya sabida idon kowane gardi akanki yake duk da niƙaf ce a fuskar ki hakan bai kamata ba kowa na kalleki, sannan kishiyar hajin bana hadake duk da nasan kin taɓa zuwa dan na tsinkayi haura Makkah a bakin ki kwanaki nan da muka haɗu, ina tayaki murna malama AFREEN Allah ya riƙa Allah sa aci anfanin abin, sannan Allah bada ikon anfani da abinda aka sani, ga kuma kujera huɗu daban sai ki zaɓi wanda zaki bawa dan kuje hajin a tare." yana gama faɗar haka yajuya ya bar gun. Dam da dam haka AFREEN taji gaban ta ya faɗi lokacin da AFREED ke mata magana, ɗago da idonta tayi ta bishi da kallon har sai ya kai gun zamanshi ya zauna, ya mayar da duban sa kanta, suna haɗa ido ya kashe mata ijiyarsa guda da sauri ta ɗauke kanta daga gareshi tare da sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya. Babban malamin makarantar tayiwa bayinin kyautar da AFREED yayi mata dan haka ya dauki lasipika ya fara dacewa, "Jama'a mungode Allah saka da alkairi yarinyar nan AFREEN ta gode da kyaututtukan da duk aka bata dan ta cancanci hakan, yarinya ce da samun irinta wannan zamanin sai an tona, masha Allah ta samu kyaututtuka masu dama, wani bawan Allah ya bata kyautar kujera maka biyar da mota da sheck na miliyan ɗaya sannan wani ya bata babur biyu da 100000 da sauran su an gode an gode Allah saka da alkairi KAMAL ma ya bata mota da 300000 da sauran wasu abubuwa, duk wanda ba a faɗi tasu kyautar ba suma angode kyaututtukan ne da yawa tsayawa faɗa kyautar da duk mutane suka mata bata lokaci ne. Sosai AFREEN ta gane AFREED duk da yasa abin rufe hanci da baki, ƙara ɗagowa tayi ta kallesa, ai kuwa suka haɗa ido sabida shima ita yake kallo dan ya kasa daina kallon ta da sauri AFREEN ta kauda kanta shikuwa ya saki murmushi. Yana gama faɗa aka shiga kiran sauran ƴan saukar ana basu nasu kyaututtuka da 100000, dan sosai alhazzan Maraɗi sukayi wasa da salla wajan bawa ɗaliban kyauta cikin kuwa da mahaifin AFREEN da maman ta Arahamat, ana kammalawa AFREEN ta ƙara rufe taro da addu'a wannan karan da kyar muryar ta ke fita sabida kuka da tasha haka yanzun ma wasu hawayen ne ke ƙara bin kuncin ta, idon AFREED na kanta dan haka duk sai take jita a takure, ta kammala addu'ar, suka fara ɗaukar photo ita da ƙawayen ta na makarantar ida suka matsa mata cewa yau dai kam sai ta fida niƙaf a masu photo babu yanda ta iya sai da ta cire niƙaf ɗin aikuwa kallo ya kuma gareta mutane na ta mamakin kyau irin nata, sosai wasu ke zuwa a masu photo tare kawai dan ta birgesu wasu kuwa dan su aza a status a total kuri, wasu kuwa dan gulma, aka fara mata tare da ƴan gidan su da su Fanna da Hasina suna ta arerewa abinsu suna farin cikin, haka wajan su AFREED suma ana ta masu photo tareda Khadijah da ƙawayen tanti A'ishah shi kuwa AFREED hankalin sa bai ma wajen su yana ida AFREEN ke tsaye tare da ƙawayenta suna photo dan ƴan gidansu sunyi tafiyar su. Sosai ya shagala da kallon ta yana cikin kallon nata ya tsinkayi KAMAL wajenta yaje yace ƙawayen nata dan Allah su bashi aronta dan za'ayi masu photo ita kuwa AFREEN bata iya yi masa magana ba kuma ba ta ɗago ba ta kallesa ba, da su Hasina sukaga ha sai suka bar masu gun, ɗan duƙawa yayi yace "Yau ko ga gayar dani ba za'ayi ba kuma kinwani buɗe man fuskar ki sai kallon ki ake to kizo muje daga can ayi mana photo ko biyu ne kinji." Ba musu ta bishi ida mai daukar hoto ke tsaye yana jiransu har suka ƙarasa wajen mai daukar hoton ba tace dashi komai ba, suna zuwa mai hoton ya fara masu, ana cikin yi mai hoton ya ɗauka yace madame ki kallesa sai kiyi ɗan murmushi sai a ɗauka hankan zaiyi kyau sosai, aikuwa haka ta faru, ta saki wani tsadaden murmushi tana kallon KAMAL daidai lokacin da hakan ta faru akan idon AFREED aikuwa zuciyar AFREED tashiga wani irin motsawa tana wani yin sama tana dawowa sosai zuciyarsa kemasa zafi dalilin gani KAMAL da AFREEN da yayi an masu hoto hada murmushin ta mai tsada take sakar masa, a cikin zuciyarsa yake cewa "Wanene wancen da har ya samu wannan damar, miye haɗinsa da ita, kadai saurayin tane? Dam dam dam gabansa ne yayi wata muguwar faduwa har sai da ya riƙe zuciyarsa sai yaji ba KAMAL ba har AFREEN ɗin haushin ta yakeji kamar mi, sai kuma ya koma yace "To koma waye ɗin tane mike ruwana a ciki." Taku har kullum mai kaunar ku💖 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ *_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_* *Page* : 39 & 40 Daga haka ya ɗoke idonsa akansu sabida sosai ransa ya ɓace yarasa dalilin hakan gani yake idan yaci gaba da kallon su zai iya aikata abinda ba shineba kuma hakan ba girman sa bane jin yanda zuciyarsa ke suya ya saka shi barin gun ya nufi motar sa ya shiga ya tayar tare da barin gun. Saida Ali ya waiwaya yaga babu AFREED babu dalilin sa kawai sai girgiza kai yayi dan ya san da tafiyar sa ne yayi, da zasu koma gida kuwa tanti A'ishah motar mijinta ta shiga da Farisa da kuma da Amal da kuma aouta tanti, tunda wanda ya kawo su yayi tafiyar sa. Haka taro ya watse lafiya kowa ya kama gaban sa, su AFREEN na zuwa gida duk suka nufi ɗaki kowace ta watsa ruwa tayi sallah mangariba sannan aka fito cin abincin, suna tsaka da cin abinci papa yace "To AFREEN kujerar Makka da kika samu har guda biyar ya zakiyi dasu?" Saida ta ɗan nisa Sannan tace "To papa da cewa nayi na bawa babban malamin islamiyyar mu guda sannan kaida maman guda guda sai kuma ɗaya zan bawa anma (wato mahaifiyar Fanna kawar AFREEN dake Diffa) ɗayar kuwa kaka na bawa (wato Hajiya Zakiya) sannan cikin kuɗin dana samu zan biyawa kaka malam (mahaifin Arahamat) shima kujerar Makkah. Murmushi papa yayi yace "Masha Allah yarinyar kirki Allah maki albarka hakan da kikayi yayi dadai, amma keda aka bamawa miyasa baki fitar wa kanki ba AFREEN wannan kyautar kice yaci ace kema zaki ɗauki ɗaya duk ba zuwanki na farin bane ke kije a matsayin kujerar dakika bamawa Hajiya in kuwa kiyi niyya ne kin bata to kema kuwa zaki koma haji na biyu bana Insha Allah, zan biyawa kowa a gidan sai muje tare baki ɗaya banda ni da mahaifiyar ki kuma da Hajiya, kinga an samu ragowa kujera uku kenan tunda mu uku kiyimana kyautar kujerar haji yanzu baki ɗaya zamu tafi kowa ya sake sauke farali hada Ufadi (wato matar mahaifin Arahamat maman AFREEN idan masu karatu basu manta ba) sannan itama Fanna hada ita da kuma mahaifin ta kenan kinga su ukun duka, da kuma Hasina itama duk da ta taɓa zuwa yanzun ma zaku koma tare kamar yandata kasan ce farkon tafiyar ku Insha Allahu da Firdaoussi ɗiyar yaya Adamu tunda duk tare kuke abukan junana ne ya kamata ku koma tare." Fanna ƙawar AFREEN najin haka ta tashi daga kan kujerar da take zaune tana cin abinci da hawaye farin ciki a fuskarta ta durƙusa gaban papa tana kuka tana godiya tace "Allah sarki ashe zanga wannan rana dan haka aka ce kada mutum ya fida da rai daga rahamar Ubangijin, ban taɓa tunanin wata rana zanje haji ba sai gashi sanadiyyar ƙawance Allah ya haɗani da mutane kirki masu su jin tsoron da ƙaunar mazon sa, papa mun gode mun gode mun gode Allah saka da alkairi, Allah ƙara lumka arziki mai albarka, Allah ya shirya maku ƴaƴan ku zuri'a ku baki ɗaya, Allah rufa maku asiri duniya da lahira, Allah saka maku da mafificin alkairi, ya biyaku da gidan aljanna, Allah hanaku jin kunyar duniya da ta lahira, Allah sa ku fi haka, ya ya kauda fitina da tashin hankali a tsakanin ku, ya Allah na roƙeka duk mai neman wannan zuri'a da shari ko wani mugun abu Allah ka da ka bashi iko ko kayi gaggawar mayar masa da kayanshi na gode papa iyayena ma sun gode godiyar ma ta gode," Sannan ta juya gun AFREEN ta ƙara fashewa da kuka tace "Ƙawata ƙawance na dake alkairi ne Allah kaɗai yasan miye dalilin yaɗuwar mu har muka ƙulla zumunta sabida ni na ɗaɗe da daina kallon ki a matsayin ƙawa sai ƴar uwa ta jini wada muka fito ciki ɗaya duk duniyar nan in aka fida maki iyayena to ban da kamar ki ƙawata sosai nake ƙaunar ki ko rayuwa ta zan iya baki wallahi samun mutane irin ku sai an tona na gode da kyaut........ Da sauri AFREEN ta rufe mata baki tare da tayar da ita tsaye tace ."Haba cœurly miye haka dan Allah, anya kuwa kin ɗoke a yanda kika faɗa? idan hakane miye abun wi mana wannan godiyar ni na ɗauke ki ne kamar yanda na ɗauki anty Fauziya ko anty Khairat, mun riga mun zama cikin ɗaya ki daina haka." Papa ma cewa yayi "Gaskiya dai kam Fanna ni zaman mahaifin ki nake ba wani abu bane idan hakan ya kasance, je ki koma gun zaman ki ki ƙarara cin abincin ki kinjiko ƴata Allah maku albarka." Duka wanda ke nan gun cin abincin saida ya ce ameen har anty Fauziya da tazo gun saukar tana jiran mijinta yazo ya ɗoketa, amma banda umma da tanti suda tunda papa yace zai biyawa Fanna da mahaifin ta Makkah da kuma kujerar da AFREEN ta bawa mahaifiyar Fanna ɗin suke ta hararen Fannar da jin haushin ta. Suna kammala cin abincin suka koma falo sabida gajiyar da suke yau masu aikin gidan ne suka tatare dinning ɗin suka gyara wurin duk da ba wani ɓata sa sukayi ba, basu jima da zama a falon ba mijin anty Fauziya yazo tare da yaranta biyu sukayi ta wasa da dariya kamin suke masu sallama su bar gidan. Papa ya kalli anty Khairat yace "Khairat yaushe kika zo ne? dan mu kam sai da muka ganki a wajan saukar nan." Murmushi tayi tare da sade kanta ƙasa sannan tace "Tunjiya misalin ƙarfe 8 na dare nazo papa, amma sai na sauka gidan anty Fauziya sabida inason yi maku bazata sabida AFREEN dalilin kuwa shine ta matsa min da tambayar zanzo saukar su nace mata a'a shiyasa nace sai kawai kun ganin kamar daga sama ta kalli AFREEN ta dariya." Itama AFREEN dariyar tayi sannan ta mata kallon zan rama." Papa yayi murmushi yace "To masha Allah Allah maku albarka ya karatun naki. Anty Khairat tace "Ai na kammala dady yanzu kusan sati biyu kenan sakamako ne kawai nake jira ya fito sai na koma na karɓa, abinda yasa ban dawo gida da yuri ba Tanti Maryam ta tsayar dani yanzu ma sabida saukar AFREEN ta bari nazo (Idan masu karatu basu manta ba Maryam ƴaƴa mahaifin su AFREEN ce wato Alhaji Sadisu wada ke aure a garin Niamey, dakuma Fatima mai aure Mali) Ba wani jimawa sukayi a falon ba suka bar iyayen su anan suku suka yada zango a ɗakin AFREEN, suna shiga suka zazauna bakin gado suna sakin murmushi, wata irin ajiyar zuciya Fanna ta sake sannan ta ɗoki wayar ta tana cewa "Bari na sanarwa su anma wannan abin alkairi dana farin ciki nasan idan sukaji wannan labari yau sedai kwana ɓarawo ya kwashe su." Murmushi sukayi AFREEN tace "Ki bari har da safe mana." Fanna tace "Cœurly ba zan iya ba nidai ki bari na faɗa ina bahaka ba ba zan iya bacci ba. AFREEN tace "To ai shikenan ki kira su ɗin." Kamin takai gayin kiran Khairat ta riƙe mata hannu tace "Dakata ƙanwata na faɗa maku wani abin farin cikin sai ku ji daɗin gaba ɗaya," hannun AFREEN ta kamo da hannunta na dama shi kuwa na Fanna na cikin hannuta na hagun sannan ta koma cewa "ina farin cikin gayamaku cewa Ahmad yace na faɗawa papa jibi zai turo iyayen sa gidan ma'ana zasuzo neman aurena." Khairat ta faɗa da ƙayatacan murmushi kwance a fuskar ta. Da sauri AFREEN da Fanna suka ƙwace hannunsu daga nata suka rugumeta suna ihu farin ciki, kuma ihu ba wani mai sauti ba mai cike da hankali da nutsuwa. "Alhamdulilah" suka faɗa a tatare sannan suka saketa baki yaƙi rufuwa su AFREEN sai kwasa dariyar farin ciki take ta ma kasa yin magana sai kallon Khairat ɗin take." Fanna ce tayi ƙarfin halin cewa "Barka barka anty Khairat gaskiya na tayaki murna sosai farin cikin da nake ciki yau baya musultuwa gaskiya Allah ya tabbata mana da alkairi, ashe mun kusa shan biki ehe, kai Allah kaimu wannan rana akwai didima ashe, fatan alheri anty mu," sai suka ƙara rugumeta suna ta farin ciki. Sai da sukayi mai isarsu sannan suka saketa, sai a lokacin AFREEN ta samu damar magana tace "Anty miyasa baki faɗawa papa dazun ba da muna falo ana hira?" "Kunya nakeji AFREEN kedai zaki faɗa masa, nikam bana iyaba." "Hakane kuwa ko ni idan nawane zanji kunya faɗa da kaina bari naje na faɗa masa yanzu tunda dare bayi sosai kuma a kira anty Fauziya itama a sanar da ita." AFREEN ta faɗa tana ƙoƙarin tashi ta fita. Da sauri Khairat ta riƙo hannunta tace "Ke kuwa sister ki bari hada safe man irin wannan zazari haka." Fanna tace "A'a antyn mu taje ta faɗa tun yanzu a bari ya huce shike kawo rabon wani gara ayita ta ƙare." AFREEN tace "Ah ki barta ni kam yau din nan zan faɗa wa papa duka yanzu ƙarfe tara tana yiyuwa ma papa suna nan a falo." Ƙwace hannunta tayi tayi gaba abinta. Tana shiga falon tayi sa'a papa na zaune shida umma suna hira tare da kallo, sallama tayi aka amsa mata sannan ta nemi guri kusa da papa a saman kafet ta zauna tare da duƙe kanta bata ce komai ba. Papa ya zuba mata ido na kusan sakan talatin sannan yace "AFREEN ɗin papa yi magana mana nasan abu mai mahimmanci ya kawoki nan gashi kuma na hango farin ciki luluɓe a fuskar ki." Ɗagowa tayi ta kalli papa tare da sakin murmushi sannan tace "Dama papa Ahamed ne ya cewa anty Khairat ta faɗa maku jibi iyayensa zasuzo neman aurenta shine tace tana jin kunyar faɗa nikuwa sai nace ta bari zan sanar da kai." Ta ƙarasa faɗar maganar da murmushi kwance a fuskarta. Aiko papa ya washe baki yana ta fara'a cewa yake "Alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah Allah abin godiya kai masha Allah, to madala Allah ya kaimu jibin da rai da lafiya naji daɗi wannan labarin." Kamin AFREEN tayi magana umma tace "Ah da ita baza tayi faɗa ba saike ƴar rashin kunya ko kika zo kika faɗa to ya maki kyau." Keda ke can AFREEN bata ma ɗago ta kalle ta ba bare tayi tunanin zata tanka mata sabida tariga da ta saba da halin umma indai itace wajenta batayin daidai. Papa ya kalli AFREEN yace "Tashi yi ta fitar ki kin jiko ƴar albarka, ba musu ta mike ta koma ɗakin ta, shi kuwa papa ya ɗauki waya ya kira ya'yan sa Adamu ya sanar dashi cike da farin ciki ya taya papa murna sannan suka ɗan taɓa hira kamin sukeyin sallama, haka ya kira maman yace ta sauko kasa yana son ganin ta, itama tanti ya kirata yace ta fito zasuyi magana, batare da jimawa ba duk suka halar a falon nan yake sanar masu abinda AFREEN ta faɗa masa cike da farin ciki suka taya juna murna, amma ko abinda ba'aso umma bata faɗa ba itama tanti da kaga yanda take barka kasan bata kai ciki ba, daga bisani kowa ya watse ya nufi nasa ɗakin. Itama AFREEN tana shiga ta sanar dasu abinda papa ya faɗa sannan Fanna ta kira iyayenta ta sheda musu cewa sun sami kujerar Makkah farin ciki gun su ba'a magana ranar kam yuni sukayi hira yanda hajin nasu zata kasance sannan tace da safe zata kira mahaifiyar AFREEN da mahaifin nata suyi masu godiya shima baban Fanna yace zai kira papa yayi masu godiya daganan aka basu AFREEN suka mata godiya tare yiwa Khairat fatan Allah sa alkairi. Fanna na gama wayar, AFREEN tace a kira anty Fauziya a sanar da ita, Khairat tace "Ai tariga kowaji." Daga nan suka ci gaba da fira sai wajen ƙarfe 11 na dare kanan sukayi shirin bacci, yau Khairat a ɗakin AFREEN zata kwana AFREEN da Fanna ke kan bed ita kuwa tana saman wata ƙatuwar matala tayi ɗai ɗaya, AFREEN tayi addu'a ta kwanta tare da rumtse idonta ina sai bacci yace baya da yuri ga idanunta, dalilin kuwa shine daga ta rufe idonta sai taji cikin kunnuwanta maganar AFREED na dawo mata a lokacin da yake ce mata "Yakamata ki bar gun nan gaskiya sabida idon kowane gardi akanki yake duk da niƙaf ce a fuskar ki hakan bai kamata ba kowa na kalleki." Maganar nan ta kasa barin dodon kunnanta, kuma ta kasa bacci dan tana rufe idonta take jin maganar na dawo mata cikin kunnanta sai juyi take ta rasa mike damunta, har ƙarfe 1 dare tana kwance ta kasa bacci kawai sai ta tashi ta shige toillet ta ɗauro alwala, ta fito ta saka rigar ta doguwa ta sallah da babban hijab ɗinta ta kabarta sallah duk da lokacin tashinta sallar dare baiyi ba, amma haka ta dake tanata jero nafilfili dalilin bacci da ya ƙwaracewa idonta har saida aka yi kiran sallar farin sannan kwana ɓarayo ya ɗoke a nan saman dardumar. ****** ****** ****** Da kyar da taimakon Allah AFREED ya kai gida dan sosai zuciyarsa kemasa zafi kuma ya rasa dalilin haka, ya isa gida yayi parking ɗin motarsa ya fito ya nufi ɓangaren su direct ɗakin sa ya nufa ba tare da ya tsaya komai ya rage kayan jikin sa ya faɗa toillet ya sakar ma kansa shower 🚿 na ruwa masu sanhi dan so yake zuciyarsa tage zafin da take masa amma ina hakan bai samu ba har sai da ya gaji da dukan da ruwan kemasa ya fito dai lokacin ana kiran sallah magariba da sauri ya shirya cikin doguwa rigar sa ta zuwa masallaci yafito dan tafiya masallaci daidai lokacin su Ali da kowa da kowa suka shigo gidan, tsayawa ya masu nuni hannu cewa masallaci zai tafi ana shirin tada sallah, ba tare da ya tsaya jin amsar su ba ya nufi masallacin dake kofar gidan. Ali da Umar da mijin tanti A'ishah da sauri suka nufi cikin gida dan ɗauro alwala ba tare da sun jima ba suka fito sai masallaci dan har an tayar da sallah. Haka tanti da ƴan matan ta suma suka shiga suka fara sai gabatar da sallah suna kammala suka baje kan bed suna sauke numfashi gajiya, Fariya ta fara tashi ta nufi toillet tayi wanka sannan Khadijah tana fitowa Farisa ta shiga, haka Amal da ummi suna nasu ɗakin suna hutawa, suna gana shiryawa suka gabatar da sallah isha'i sannan gaba ɗayan su suka dawo falo dukan su a saman kafet suka zube sannan suka shiga hira suna cikin hira ne Farisa ta kalli Khadijah tace "Sister yau naga wata halitta dama akwai mutane masu mugun kyau kamar aljanu wannan yarinyar kyau ɗinta yayi mungun bani tsoro dan ko a India samun mai kyau irin nata sai an tona duk da tana zubi da indiyawa sabida idan ta shiga a cikin su ba za'a gane cewa ita ɗin ƴar Niger ce kuma ƴar maraɗi, amma dai mamanta ba'indiyace shi kuwa mahaifin ta balarabe ne ko? dan gaskiya sai in wannan yaren ne guda biyu suka haɗu har za'a samu damar samun mai kyau irin ta, lokacin da idona ya sauka kanta wallahi har saida na zabura kaɗan ya rage na zuba da gudu sai naga mutane nata zuwa wajen ta suna hoto sannan na yarda da muntun ce ba aljana ba, kuma danaga tayi karatu, ke ita har muryar ta daban take da ta kowa wallahi kinji yanda take sakin karatu cikin sanyayar ku zazaƙa muryar ta sosai yarinyar ta birgeni dubi fah ko ƙwayar idonta chocolat color ne. Murmushi Khadijah tayi tace "AFREEN kenan kikenufi ai nima sau ɗaya na taɓa ganin fuskarta sai yau na biyu sabida kyau dake gare take rufe fuskarta ita da kanta tsoron kyau ɗin ta take har ƴan gidansu suna mamaki shi, kuma batun babanta balarabe ne ko mahaifiyar ta ba'indiyace ban sani ba wannan, abinda na sani shine mahaifin ta haifaffen garin Mali ne amma bansan mahaifiyar ta ko wace irin ce ba shima dalilin ƙanwarta Zeinab na sani tunda da ita muke gaisawa duk da ita AFREEN ɗin muke sa'a guda da ita, kuma wallahi babu ruwanta, gata da son mutane ga mutunci ga kamala uwa uba tsoro da addini da masu zama da ita sunce idan kana tare da ita to wallahi ba zaka taɓeba, sosai nakeson ƙawance da ita to ba sosai muke haɗuwa ba shiyasa, ai AFREEN tayi a rayuwa yarinyar tanada hankali sosai ga nutsuwa kuma ita kowa nata ne." Amal tace "Wallahi anty Khadijah nima dana ganta saida naji tsoro gaskiya tanada masifafen kyau mara misali." Farisa tace "Da garin nan nake da sai nayi ƙawance da ita wallahi." Fariya tace "ina ma ya AFREED zai ganta yace yana sonta daga nan idan ta yarda sai ya aureta ta haifa mana yara masu kama da ita gaskiya da munji daɗin samun ta cikin zuri'armu kodan kyawawan halayen ta wallahi, dan na lura AFREEN ɗin nan matar manya ce iri su ya AFREED ɗin dasu ta dace Allah ba yayan mu ita ameen." Khadijah har ta buɗe baki zatayi magana , kamar ance ta juya sai taga ga AFREED tsaye kusa da su, Ali da Umar da mahaifin sa suna ƙarasowa cikin falon, ganin Khadijah tayi shiru yasa su ɗaga kawanan su dan ganin miye yasa ta yin shiru suna haɗa ido da shi ya watsa masu wani uban harara, da sauri duk suka sada kansu suna muzurai kamar munafukai daga nan kowa ya shiga taitayin sa. Basu wani ɓata lokaci ba a falon ba tanti A'ishah ta fito itama, sannan masu aikin gidan suka kawo masu abincin nan saman kafet gaba ɗaya suka gewaya suka ci abinci. Suna kammalawa kowa ya nufi ɗakin shi, yau basu tsaya fira ba sabida gajiya da suke da. AFREED na shiga ɗakin ya koma shiga toillet ya watsa ruwa sannan ya fito yayi shirin bacci cikin sanhin jiki duk yau jinsa yake wani irin, wayoyinsa da ke saman kujera dake cikin ɗakin ya ɗoko sannan ya nufi bed ɗin sa tare da kashe hutar ɗakin sannan ya ƙara ƙarfin AC dan mugun zafi yake ji kamar yanda zuciyarsa har yanzu bata daina yi masa zafi ba yana cikin yin addu'a shiga bacci wayarsa da itace duk wani ɗan uwansa ko iyayensa ke samun sa, itace ta ɗauki rururi, kollon wayar yayi ganin wanda ke kiransa bai sa ya daina addu'ar ba saida ya kammala sannan ya ɗauki wayar da niyyar maida kira sai ga wani kiran ya shigo, ɗoka yayi ya ƙara a kunan tare dayin sallama, ana amsa sallamar yace "Dady ina wuni, anyuni lafiya, ya gida, ya Momy, da fatan duk kuna lafiya?" Dady yace "Lafiya lau AFREED da fanta kuma kuna lafiya?" "Lafiya lau dady." Dady yace "To madala yaushe ne zaku dawo." AFREED yace "Jibi insha Allahu." "To Allah kaimu, amma inason kafin ku dawo kuyi ƙoƙari kuje gidan aminina Alhaji Sadisu ku gaido shi na faɗa masa kana cikin garin nan kuma har kuna shirin dawowa shine yayi ta faɗa miyasa da zaku zo ba a faɗa masa ba aida kun sauka gidan sa, indai taiƙaice maka dai ya nuna min baiji daɗin rashin sanin zuwan kaba shine yace na bashi adress ɗin gidan A'ishah shi yazo ya ganka kamin ku tafi sabida rabonsa dakai tun kana jinjiri da yazo sunanka , sai kuma inya haɗu da hoton ka a TV, shine nace masa ya bari kai zaka zo har gida ka sameshi." Sedai AFREED ya ɗan nisa sannan yace "Inshallah dady gobe zamuje kwai ka turoman da adress ɗin gidan sai muje nida Ali da Umar insha Allahu." Murmushi mai sauti dady ya saki wanda har saida AFREED ya juwo shi sannan yace "yawa ɗan albarka yanzu zan turoma da adress idan Allah ya kaimu goben sai kuje, sai da safe Allah maku albarka. Da ameen AFREED ya amsa sannan yace Allah kaimu safiya lafiya." Daga nan dady ya kashe kiran komin minti 1 ba'a yi ba sai ga soƙon adress ɗin gidan Alhaji Sadisu ya turo masa ta whatsapp, yana duba bawa sai ya kashe data ya kwanta ai yana rumtse idonsa.............. Sai kunji ni a page ta gaba😜😜😜😜 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ *_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_* *Page* : 41 & 42 Daga nan dady ya kashe kiran komin minti 1 ba'a yi ba sai ga soƙon adress ɗin gidan Alhaji Sadisu ya turo masa ta whatsapp, yana dubawa sai ya kashe data ya kwanta ai yana rumtse idonsa ya fara hango photon AFREEN lokacin da ta ke kallon KAMAL tana sakar mai wani ƙayatacen murmushi ana masu hoto, da sauri AFREED ya buɗe idonsa yana sauke ajiyar zuciya batare da ya tashi daga kwanciyar da yayi ba, ya ɗauki kusan minti 5 a haka kamin yake kara rufe idon nasa amma ina hoton AFREEN tana yiwa KAMAL murmushi ya ƙi barin ƙwaƙwalwar da idon AFREED, bacci yake son yayi amma hakan taƙi samuwa, ya ɗauki dogon lokaci a haka kamin yayi shawarar shiga toillet ya ɗauro alwala dan gabatar da sallah nafila saboda samun saukin raɗaɗin da zuciyarsa ke masa. Shima a nan saman darduma bacci ɓarawo ya kwashe shi, washegari wajen misali ƙarfe 12am AFREED da Ali suka kuno hancin motar cikin anguwar su AFREEN ba tareda sun sha wahala ba suka samu wani yaro ya nuna masu gidan Alhaji Sadisu wato maihaifin AFREEN suna kawowa bakin ƙofar gidan Ali yaja ya tsaya tareda dana hon da sauri mai gadi ya fito tareda ƙarasowa kusan motar yana tambayar su wayesu sabida bai sheda su ba kuma yaga bakuwar fuska, haka motar ma bai taba ganita cikin gidan ba. Murmushi Ali ya sakar ma baba mai gadi danji yana tambayar sa wajenwa sukazo kuma wasu ke nema sannan Ali yace "Baba ina yuni an yuni lafiya? Ai wajen mai gidan mukazo ko yana ciki." Baba mai gadi najin haka ya saki murmushi yace "lafiya lau yaro, aya wajen Alhaji kukazo kenan ai kuwa yana ciki kun taki Sa'a dan ina gani yau ko fitama baiyi ba amma yasan da zuwan naku ko shiyasa bai fitaba, ku bari na buɗe maku ƙofar sai ku shigo daga ciki." Shidai Ali baice masa komai ba, sai murmushi da ya sakar masa, juyawa baba mai gadi yayi yaje buɗe masu kofar, ba tare da ɓata lokaci ba Ali ya dana hancin motar su cikin gidan, daidaita motar yayi yayi parking ɗin ta sannan suka fito har yanzu shi AFREED babu abinda ya faɗa zaki iya cewa ma baya gun, Ali ya kalle shi yace "Ɗan uwa to yanzu waye za mu aika yaje ya sanar da zuwan mu?" Hararar sa AFREED yayi sannan yamashi nuni da ido cewa ya tambayi mai gadi, murmushi Ali yayi yana girgiza kai cikin zuciyarsa yace "Ah yau abubuwan ke bisa kai ko maganar ma ba za'a min ba." Bai ƙarasa tunanin da yake ba yaji baba mai gadi nacewa "Ku ƙarasa daga ciki mana." Da sauri Ali ya juyo gareshi yace "Yawa dama baba munaso a sanar dashi mun ƙaraso, yasan da zuwan mu amma bamu faɗa masa cewa yanzu zamu zoba ace masa ɗiyan abokinsa ne Sumana." Baba mai gadi yace "Ah nagane to bari na sanar da su." Baba mai gadi na kaiwa bakin ƙofar falon ya kwankwaso ba tareda ɓata lokaci ba AFREEN tazo ta buɗe ƙofar, tana ganin baba mai gadi ne tayi murmushi tace "Baba Barka da warhaka ku shigo daga ciki mana." Shima baba mai gadi murmushi yayi yace "A'a ɗiyar albarka ba sai na shigaba dama Alhaji yayi baƙi shine sukace nazo na sanar da zuwan su dan haka ki koma ki faɗa ma Alhaji cewa yayi baƙi kuma sun ce ace ɗiyan abokinsa ne Sumana, abinda alhajin yace sai ki dawo ki faɗa man ina nan ina jiranki." Jin abinda mai gadi ya faɗa yasa gaban AFREEN faɗuwa ba tareda da tasan dalilin hakan ba, haka kawai taji tanason gani ko su waye, koma yin murmushi tayi sannan tace "To shikenan bari na sanar da shi." Ba tareda AFREEN ta jira jin abinda baba mai gadi zai koma cewa ba ta juya ta koma falon, Papa na zaune saman babba kujerar dake cikin falon AFREEN ta ƙaraso kusa dashi ta zauna tace "Papa inji baba mai gadi yace a sanar dakai cewa kayi baƙi kuma sunce su ɗiyan abokinka ne Sumana." Papa najin abinda AFREEN ta faɗa yayi saurin ɗagowa daga kishingiɗan da yake tareda gyara zaman sa sosai a kujera sannan yace "Yima maza je kice a shigo dasu ya za'a barsu a tsaye waje kuma cikin rana," maida kallon sa yayi ga Zeinab yace "Zeinab tashi ki shigo da su, ke kuwa AFREEN kuje keda Fanna ku haɗa masu abu mai sanhi da abinci mai rai da lafiya." Ba tareda ɓata lokaci ba duk suka nufi gun abinda papa yasaka su AFREEN da Fanna suka nufi kitchen ita kuwa Zeinab ta nufi hanyar fita daga falon inda suke tsaye ta ƙarasa tare da gaishe su cike da sakin fuska suka amsa mata sannan tace "Papa yace ku shigo daga ciki" tana faɗar haka ta juya ta fara tafiya. Ba musu suka bi bayan ta daidai ƙofar falon suka ja suka tsaya a lokacin Zeinab har ta buɗe ƙofar tare da zura ƙafarta ta dama, amma jin sun tsaya yasata juyowa ta sakar masu murmushi sannan tace "Yaya ku shigo mana papa nanan falo yana jiran ƙarasowar ku." Murmushi suma suka sakar mata AFREED harda lumshe ido saboda sosai yaji dadin kiransu da yaya da tayi a cikin zuciyarsa yake faɗin "Daga gani gidan nan akwai tarbiyya." Ali ne ya fara ɗaga ƙafarsa yayi cikin falon sannan AFREED ya bi bayan sa tareda sallama a bakunan su, dam da dam AFREED yaji gabansa ya faɗi lokacin da ya tsintsi kansa a daidai shigowa falon ba tare da kawo wani abu a ransa ya yi addu'a ya ida shiga daga cikin, da fara'a papa ya taso har idan suke ya shiga tsakaninsu ya kama hannuwan su ya ida ƙarasawa dasu a cikin falon ya zaunar dasu saman kujerar daya tashi kamar wasu ƙananun yara sudai kam binsa suke a duk inda yayi dasu, sannan ya nufi kujerar dake fuskantar su ya zauna da murmushi ɗoke da fuskar sa, har papa ya buɗe baki zaiyi magana sai ya tsintsi muryar su suna gaishe shi, amsawa yayi cikin fara'a. Sannan papa yace "Masha Allah AFREED Ali kun girma fah dan sosai na daɗe rabona da ku tun kuna yara yan shekara sha ɗaya sai kuma in an nunoku a TV, amma duk ganin da nake maku sai naga yanzu a gaba naga kunfi girma, ya kuke ya gida ya aiki dadyn naku yace man kuyi wata ɗaya a garin nan amma fah ko ya faɗa man kunanan." AFREED yayi murmushi tareda ɗago da kai kalli papa a take ya ji mutuman ya kwanta masa yace "Lafiya lau alhamdulilah papa da fatan mun sameku lafiya, eh wallahi muyi wata a garin gobe ma zamu koma insha Allah. Papa yace "To har zaku koma kenan nida naso ace a nan kuka sauka amma babu komai akwai wata rana." AFREEN da Fanna ne sun fito daga kitchen rike da abinci da juice da ruwa a hannu suna tunkaro falon gaban AFREEN nata faɗuwa kuma ta rasa dalili, dan tunda taji muyar wanda ya shigo falon ta shiga cikin wannan halin sai tambayar kanta take ina tasan wannan muyar, haka take wajen AFREED ma sai faduwa gaban sa kuma yarasa dalili dan fira da suke da papa bawani jinsa yake dan hankalin ba ya wajen shi, suna gab da ƙarasowa falon wayar AFREEN tashiga ruri tana neman agaji, duba wayan tayi taga sunan data sakawa KAMAL ne ya fito sai ta saki wani irin murmushi, sannan ta juyo ta kalli Fanna tace "Sister dan Allah ki ƙarasa da kayan abinci cikin falon zanje na ɗaga waya KAMAL na kirana." Fanna tace "To shikenan cœurly ajiye a nan idan na kai wannan sai na ƙarasa da wannan ɗin." Murmushi AFREEN ta sarka mata sannan ta ce nagode cœurly," tayi gaba abinta ba tareda ta tsaya jin abinda Fanna zata faɗa ba." Fanna na ƙarasawa falon tayi sallama tareda gaishesu batare da ta kalle su ba, kallo ɗaya duk suka mata sannan suka amsa gaisuwar tare da ɗoke kansu daga gareta lokaci guda sannan ta duƙa ta ajiye plet ɗin dake ga hannu ta, har ta miƙe tsaye papa yace mata "Ina AFREEN ɗin take ne na ganki ke ɗaya." AFREED najin haka gaban ya ƙarayin wani irin lugude ya faɗi har saida ya riƙe wajen zuciyarsa, yana cewa AFREEN kuma to su anan garin basu da sunan sakawa yaransu sai wannan sunan kodai AFREEN ɗin da nasani ce? Kai ba ita bace watace daban amma ni sai naga kamar wada nasani din sunyi kama da wannan abokin dadyn bare idonsu kusan irin dayane kwayar idonta brown ne shima kuma papa nashi brown ne kodai abinda nake zargi ne idan hakane ai abin yazo man da sauƙi, anya kuwa nidai ina tantama. Yana cikin wannan tunanin yaji muyar Fanna na cewa "An kirata a waya ne shiyasa nace ta tafi zan ƙaraso da abincin." Murmushi papa yayi yace "Toh madala Allah maku albarka je ki ida kawo sauran." Da to Fanna ta amsa sannan ta juya ta ida kawo sauran plet ɗin daganan papa yace "Taje ta kira masa matan nasa dan su gaisa da su AFREED." Haka Fanna ta juya take kiran su maman AFREEN ba tare da ɓata lokaci ba duk suka haɗu a falon duk sun gaisa maman AFREEN ce ƙarshan fitowa tana saukowa daga escalier (stairs) cikin shiga ta kamala ta wata dakakiya shada irin uwar gida ta ɗoki yurin ta ɗin nan tana ƙarasowa falon ta zauna kusa da papa tana sakin murmushi tare da kallon inda su AFREED suke a zaune sannan tace "Sannu ku da zuwa yarori na ya kuke ya hanya?" Ba tare da sun ɗago ba saboda duk kanun su a duƙe suke, Ali ne yayi magana kamar haka "Lafiya lau mama Alhamdulilah mun sameku lafiya?" Shikuwa AFREED sai murmushi yake ya kasa cewa komai sabida lokaci guda yaji ya jin kunyar matar da wani girman da yake gani a a nan take, duk da ko fuskarta bai gani ba." Can suka tsintsi muryar maman nacewa "AFREED da Ali Macha Allah kun girma kamar dai ba ku bane mukaje bikin ku nida papan su Fauziya lokacin ina amarya bayan wata shida kuma na koma ni ɗaya wajen bikin Ali lokacin papan su baya gari Allah sarki Ali Allah ya jikan mahaifiyar ka Allah mata rahama kuma yasa aljana ce makomar ta ameen, ina mahaifiyar taku Hajiya Falmata da fatan tana lafiya?" Da sauri AFREED da Ali suka ɗago suna kallon maman jin yanda ta kama sunan su kuma take ɗan bada ɗan ƙaramin labarin rayuwar su, dam da dam AFREED yaji gabansa yayi wani wawan faɗuwa lokacin da yayi tozali da fuskar maman wada yake kallon kamanin AFREEN shinfiɗe a fuskar ta ƙara waro idonsa yayi sannan ya lumshe su tare da maida kansa ƙasa. Yana cike da mamaki suka amsa mata cewa "Tana lafiya." Kuma kamar an tsayar dasu sai suka yi shiru shikuwa AFREED na tunanin zuci na cewa "Shin itace mahaifiyar ta ko kuwa kama ce dai suke, ko dai gizo ne yarinya nan keyi min da duk wanda na kalla a gidan nan yake min kama da ita? Ya Allah ka samamin mafita ka ƙara haɗani da yarinyar nan kamin na bar garin nan." Can dai ya daina tunanin da yake ya dawo da hankalin sa wajen su suka ci gaba da fira su tanti sai washe baki ake anji cewa AFREED shine ministan tsaro a ran ta tana cewa inama ace Hamida ta isa aure da na baya ita ya aura ko ta halin ƙaƙa ne." Sune basu bar gidan ba har sai ana shirye-shiryen sallah azahar suka masu sallama sun tashi zasu tafiya maman tace "Ku tsaya na baku saƙo ku kaiwa mahaifiyar ku." Ba tare da maman ta tsaya jin abinda za su ce ba tayi saman escalier (stairs) bata jima ba ta sauko ɗoke da wata leda ta basu tace "Ku kaima ta kuce nace ina gaisheta tunda yanzu ta yarda ni bata zumuncin dani." Murmushi sukayi sannan Ali ya ƙarɓa suka bare falon, papa ya rakosu har bakin motarsu yana tajin daɗin zuwan su kuma sai yaji ma kamar kada su tafi, haka suka shiga mota suka tada suka bar gidan papa na ɗaga masu hannu tare da masu fatan Allah ya tsare har sai ya daina gani su sannan ya koma ciki. Su AFREEN kuwa ana can anata waya da KAMAL. *Agurguje* Yau wata uku kenan da su AFREED suka bar Maraɗi kuma a cikin wannan watan uku abubuwa dayawa sun faru kamar fasa auren KAMAL da AFREEN dalilin mahaifiyar KAMAL da tashiga ta fita ta wargaza abin sabida so da take KAMAL ya auri wata ɗiyar ƙawarta wada ɗiyace a wajen gouverneur (governor) kin Zinder, dalilin haka ba karamin shiga tashin hankali AFREEN da KAMAL sukayi ba amma ya zasuyi haka suka haƙura, bayan KAMAL ma tayi wasu samarin har guda uku, amma duk suna rabuwa komin suka ɗaɗe da mutun to da an fara maganar aure sai abin ya lalace. Wajen AFREED kuwa tunda suka koma gida ya ƙasa sukuni soyayyar AFREEN da bai taɓa zata ba tayi masa mugun kamu wanda har sai ya sashi ya kwanta rashin lafiya, kullum cikin tunani ta yake har yana ji a ransa idan bai sami AFREEN to zai iya rasa ransa amma kuma yaƙi faɗawa kowa cikin kuwa harda Ali dan har lokacin da ya kwanta asibiti likita ya sheda masu cewa tunani ne da damuwa suka masa yawa idan bai daina ba kuwa zai iya kamuwa da rashin lafiya dan sosai yake rashin lafiya yanzu hakama ba koda yaushe ya zuwa office ba sabida rashin ƙarfin jiki. AFREEN saboda yawan samun matsala da fasa aurenta da akeyi yasa ta daina kula samari ta maida hankalin ta ga karatun ta. A yau ne ya kama saura sati uku auren Anty Khairat yayi daidai da saura wata biyu da sati ɗaya auren Ali da Umar tare da ƴan matan su Khadijah da Fariya. Duk da abin nan dake damun AFREEN na yawan fasa auren ta da akeyi ba tare da sanin dalilin da yasa hakan ke faruwa da ita ba, hakan yasa idan ta keɓe ita kaɗai a ɗakin, ta kanci kuka sosai har sai ta godewa Allah sannan take fitowa ta ci gaba da harkokin ta na cikin gida, kuma hakan bai hanata shiga cikin daginta ba aka shiga shirye shiryen auren ƴar uwar ta. AFREEN tayiwa kanta alkawarin ce wa daga RAHIM ba zata sake yin wani saurayi ba zata zauna hakanan ba sai tayi auren ba tunda haka Allah ya tsara mata rayuwa akan duk mutuman dake da niyyar aurenta sai ya fasa,tashi tayi daga kwanciyar da take ta koma gaban mirror tana kallon kanta daga sama har ƙasa ta juya ta ƙara juyawa sannan ta koma duba kanta cikin mirror tace "Babu inda Allah ya rageni, saboda ina da kyau irin mugun kyau ɗin nan da yake yawan tsorata mutane da basu mamaki ina da diri iya diri haka ƙirjina a cikin yake masha Allah no banga abin makusa ba a jikina ba da maza ke yawan fasa aurena banga inda na raguba duk da ƴan magana sunce mutun tara yake bai cika goma, duk ni dai banga aibu na ba kodai inada wani hali mara kyau ne ban sani? ya Allah kayaye min duk wata damuwa ta Allah ka shiga lamarina ka duba halin da nake ciki ka fitar dani kada ka ƙara bawa kowane namiji damar wulakanta." Kawai sai ta fashe da kuka ta koma saman bed ɗinta, ta shiga rera kuka mai cin zuciya idan kaga halin da take ciki dole ka tausaya mata, tana cikin kukan ne wayar ta ta kama ruri har kiran ya katse bata ma san an kirata ba sabida tana cikin tashin hankali. Haka kullum take fama da zuciyarta duk ranar da ta kasa hakuri da abinda ke damun ta to zata fashe da kuka ita ɗaya a ɗaki tayi tayi har sai ta ƙoshi dan gaban kanta tayi shiru, yau ma haka ce ta kasance ta shiga ɗaki yin Sallah azahar kawai sai abin ya faɗo mata a rai sai tashiga tambayar kanta shin wai miye aibunta da kullum sai za'a aurenta a fasa ko dai ita haka Allah ya yi mata tata ƙaddarar tanayiyuwa ma ba zata taɓa aure ba a rayuwar ta, haka dai tayi ta zancen zuci ita ɗaya a ɗaki wani abin ta masa kuka wani tayi murmushi. Daga nan saman darduma bacci yayi awon gaba da ita, a cikin bacci da take ne tayi mafarkin wani mutum na mik'o mata hannu tare da cewa *"AFREEN ki taho mutafi duk faɗin duniyar nan bakida miji da ya wuce ni dan haka ki daina ba ma kanki wahala, sabida ko gobe idan kikayi wani sabon saurayi sai kun rabu sabida ba mijin ki bane ni daine mijin ki kuma ina nan zuwa in tafi dake, dan haka ki tausaya min ki daina zubar da hawayen ki saboda wasu, dan wallahi kukanki na ci min zuciya, ko kinason nayi kuka ne?"* Batasan lokacin da ta shiga girgiza kai ba cikin bacci tana ƙoƙarin share hawayen, kallon ta yayi yace "Koke fah to yimin murmushi ko zanji sanhi cikin zuciyata dan Allah banason ganin ki cikin damuwa ni ma duk sai naji bana cikin natsuwa." Aiko sai ga AFREEN na sakin murmushi cikin bacci, shima murmushi ya saki tare da matsowa kusa da ita yana cewa "Ko ke fah yanzu dana ganki cikin farin ciki nima sai dana naji wani irin farin cikin ya ziyarci zuciyata dan Allah kada kiƙara min asarar hawayen nan naki masu tsada kinji ma femme ?" Ɗaga kai tayi alamar to sannan yayi murmushi tareda cewa "Je t'aime beaucoup beaucoup (ina sosai da sosai)." Harta buɗe baki itama ta fara da cewa "Moi...... Sai taji an fara tashin ta daga bacci Khairat ce ke tashin ta tana cewa "AFREEN tashi man bacci ya isa haka kije kiyi sallah har ƙarfe biyar tayi." Firgigit ta tashi tana salati tareda cewa "Subhanallahi!!! soeurette ya akayi nayi bacci mai tsayi haka har lokacin sallah la'asar ya wuce ni inna lilahi." Ba tare da ta jira mi Khairat zata faɗa ba ta tashi ta shige toillet bata wani jima ba ta fito ɗaure da alwala ta koma saman darduma ta tayar da sallah ba tare da tabi ta kan Khairat ba da ke saman bed ɗin ta tana saka mata murmushi. Tana ƙarasa sallar ta juyowa ta kalli Khairat tace "Kai yau antyn nayi bacci sosai daga fah nayi sallah azahar sai na ɗan gincira shikenan nan fah sai bacci ya kwashe ni, wallahi duk banji daɗi ba da lokacin sallah ya wuce ni wannan wane irin bacci ne nayi haka?" Dariya Khairat tayi sannan tace "Hum bacci kam mai daɗi kikayi tunda na tardoki kina ta murmushi da magana ƙasa ƙasa cikin baccin naki nasan wani mafarki ne kikeyi mai daɗi shiyasa ko, to bani labarin nasha." Saƙe AFREEN tayi tana kallon Khairat na Kusan minti biyu sannan ta buɗe baki har zatayi gardama cewa batayi ba kawai sai mafarkin da tayi ya faɗo mata a rai da sauri ta waro ido waje tace "Anty Khairat da gaske nayi magana cikin bacci duk ana jin abinda nace?" Da sauri Khairat tace "Dakata little sister kwantar da hankalin ki gayaman mike faruwa shin kinji tsoro ne a mafarkin naki ko kinga wani abin mamakine? amma da alamu mafarki ya maki daɗi tunda tsintar kinayi kina murmushi cikin bacci naki kowa ya ganki yasan mafarki ya maki daɗi." Khairat ta faɗa tana murmushi. Shiru AFREEN tayi tana tunanin mafarkin da tayi tana mamakin ina tasan wannan fuskar Ita dai ta sanshi amma ta kasa tuna ida tasan shi ɗin. Juyowa tayi ta kalli Khairat tace "Ni nakasa ma tuna mafarkin anty." Ta faɗi haka ne saboda idan tace ma Khairat ta tuna mafarkin to fah zata dameta ne da sai ta faɗa mata ko wane irin mafarki ne amma ita kuwa gaskiya ba zata iyawa faɗa wa anty Khairat wannan mafarkin ba ta mata dariya. Khairat najin haka tasan bata son faɗa mata ne kawai sai tayi murmushi tace "To shikenan ƴar ƙanwata kada ki damu tashi kike kiyi wanka sai ki fito kirakani gidan su Maryam na kai mata katin gayata aure da goro kinji." AFREEN tace "Kai anty yamma tayi fah mu bari har gobe mana in Allah ya yarda." Sai Khairat tace "A'a gobe inda zamuje da yawa suke, ki shirya kawai mutafi yanzu, kamin magariba mun dawo." "To shikenan anty bari na shirya." Ba tareda da jiran jin abinda Khairat zata ce ta faɗa toillet. Tana shiga ta tsaya tunanin mafarkin ta cikin tunanin ne ta hango fuskarsa yana mata murmushi, da sauri tace "Nagane shi wallahi shine na taɓa haɗuwa da shi masallaci cin sahaba kuma da gun saukar Alƙur'ani da nayi, to miya ke nufi da shine mijina, wai miye ke shirin faruwa dani ne miyasa yake bibiya ta?" *BONNE FÊTE* *HAPPY SALLAH* *BARKA KU DA SALLAH* *MASOYANA* *MASHA ALLAH.......* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *Page*: 43 & 44 Tana shiga ta tsaya tunanin mafarkin ta cikin tunanin ne ta hango fuskarsa yana mata murmushi, da sauri tace "Nagane shi wallahi shine na taɓa haɗuwa da shi masallaci cin sahaba kuma da gun saukar Alƙur'ani da nayi, to miya ke nufi da shine mijina, wai miye ke shirin faruwa dani ne miyasa yake bibiya ta?" Ta ɗauki lokaci tana zancen zuci kamin daga bisani tayi watsi da zancen ta fara wanka, ba tare da ɓata lokaci ba ta ƙarasa ta fito, a gaggauce ta shirya cikin wata haɗaɗiya doguwar rigar atanfa sannan ta murza mai ba tare da ta saka ko lips ba ta zaro hijab ɗin ta da niƙaf ta fito falon gidan a nan ta saka hijab ɗin sannan ta ɗaura niƙaf ta fice daga falon sabida ba kowa a falon kuma anty Khairat na waje bakin mota tana jiranta. Tana ƙarasowa inda Khairat ke tsaye ta sauke wani ɗan gajeren lumfashi sannan tace "Anty na tsayar dake ko? To dan Allah kiyi hakuri, kisan halin shirina." "Karki damu ƴar ƙanwata karɓi key ɗin motar ke zakiyi conduire (driving) ɗin mu dan ni gajiya gareni." Ba musu AFREEN ta ƙarɓi clé (Key) ɗin ta kewaya ta shiga mazaunin direba ita kuwa Khairat ta shiga ta zauna wajen mai zaman banza, sannan AFREEN ta tayar da motar suka bar gidan. Daga gidan su Maryam abikiyar Khairat suka wuce gidan anty Fauziya, suka sha hira, sai bayan sallah isha'i suka dawo gidan. *************************** Ɓangaren AFREED kuwa har yanzu abu yaƙi yin baya sai cigaba yake, kwance yake idonsa a lumshe kamar mai bacci amma ba bacci yake ba da hannunsa na dama dafe daidai saitin zuciyarsa yana jin yanda take masa raɗaɗin ciwon son AFREEN, sosai yake mamakin kansa cewa wai shine yau yake son wata daba tama san yana son taba, shida bai taɓa soyayya ba amma gashi ya faɗa tarkon wata Wada ko a kashe shi yanzu bai san ina zai gan taba sosai yayi nadamar zuwan sa maraɗi dan gani yake ida baje ba da bama zai haɗu da itaba bare har yayi ta rashin lafiya sabida ita. Yana cikin wannan tunanin ne ciwon nashi ya tashi, ya fara kakari amai ke nan Ali ya faɗa ɗakin da sauri ya ƙarasa gunshi ya kamusa a lokacin har ya faɗo daga saman gado, daidai lokacin da Ali ya riƙosa kawai sai ya fara aman jini saman jikin Ali, ai kuwa hakalin Ali yayi mummunan tashi da ganin ɗan uwansa cikin wannan halin bai taɓa tunanin abin nasa ya kai haka ba, tsananin ruɗewa da Ali yayi sai jijiga shi yake ya ma rasa ta ina zai fara basa taimakon gaggawa, cike da tashin hankali yake cewa "S'il te plaît AFREED relax (please afreed relax)." Da ya ga haka sai ya ƙara fita hayacin sa yasa kawai sai ya fita daga ɗakin a guje ya kira direba gidan ganin Ali cikin tashin hankali yasa shima Ilya direba tada hankalin sa yana cewa "Mai gida lafiya kuwa." Ina Ali baida ko bakin maga sai nuna masa ɓangaren su wake ai Ilya na ganin Ali ya kwasa aguje shima ya bi bayan sa a guje suka faɗa ɗakin AFREED a lokacin ciwo har ya ci ƙarfin sa dan har ya suma, Ali na taɓasa ya ga alamun babu numfashi a jikin sa ai baisan lokacin da ya kwala wata uwar ƙara bayana kuka sosai kamar mace da AFREED riƙe a jikinsa yana "Faɗin dan Allah ɗan uwa ka tashi kada ka mutu ka barni inna lilahi." Yana cikin wannan tashin hankali yaji Ilya direba nace masa "Mai gida kama shi mu kai shi asibiti tana yiwuwa suma yayi." Sai a wannan lokacin ne Ali ya tuno cewa shima da yaje kiran Ilya direba dan ya kama ma AFREED ɗin ne suje asibiti ai da sauri ya ciciɓi AFREED shida Ilya direba suka fito da shi da sauri suka saka sa a mota Ilya direba na ƙoƙarin shiga motar Ali ya dakatar dashi ta hanyar cewa "Kaje ka sanar da Momy cewa mun tafi asibiti." Batare da ya tsaya jiran jin abinda Ilya direba zai faɗa ba ya fizgi mota a tsiyace ya ɗo hanyar asibiti cikin ƙenƙanan lokaci ya ƙarasa ba ma gun da ake yin parking ba yayi parking ya fito a guje ba tare da ya ma tsaya rufe murfin motar ba, ba'ayi minti biyu ba sai gashi ya dawo tare da nurses maza da gadon aza marasa lafiya a guje suke tafe da sauri suka za'a AFREED saman gadon suka tura sai cikin asibitin emergency room akayi dashi cikin gaggawa likitoci suka rufa kanshi, Ali nada bakin ƙofar ɗakin ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai kawo yake, hawaye sai zubowa suke saman kumcin shi yana ta addu'a a cikin zuciyarsa. Ba ayi minti 5 da shiga da AFREED Momy da ƴan biyu suka shigo cikin asibitin a guje suna ta waige waige sai can suka tsinkawo Ali na kai da kawo bakin ƙofar wani ɗaki da gudu suka ƙarasa hankali a tashe momy ke riƙe da Ali tana tambayar sa miyasa mi AFREED mike faruwa sukuwa ƴan biyu kuka kawai suke suna kallon sa suna jiran jin abinda zai cewa momy, amma ina shima ya kasa magana sai kukan yake ya shige jikin momy yana kuka suma ƴan biyu na ganin haka gaba ɗaya suka faɗa jikinta suna kuka tana tayasu an rasa mai bama wani haƙura ko magana sun kasa, sai Ali da ke cewa "Momy dan Allah ki faɗawa AFREED kada ya mutu ya barni banida wani ɗan uwa da ya wuce shi bani da abokin hira banida abokin dariya, shine abokin na na wasa na faɗa na rigima kuma shine ɗan uwana na komai ma Mom ko ke bakinsa tsakanin mu ba, to in ya mutu da wa zanyi daga ni har shi ba wasu abokai garemu ba , mu dai ne abokan juna mu yanzu ya zanyi?" Momy ma sai hawaye take zubar wa tarasa mi zata cewa Ali duk sun kama sun riƙe ta suna kuka, ɗago su tayi gabaki ɗaya ta shiga share masu hawaye sannan ta fizgo magana da kair cikin dangana tace "Kuzo mu nemi guri mu zauna mu daina zubar da hawaye a banza muyi masa addu'a samun lafiya yanzu ita AFREED ke buƙata gun mu ba kuka ba." Zaunawa sukayi saman kujeru dake gab da ɗakin da AFREED ke ciki kowa nata addu'a amma har yanzu hawaye basu daina zuba ba daga idanuwan Fariya da Farisa ba shi kuwa Ali idanu sun mashi ja kamar gauta, momy ta juyar da fuskar ta cen tana ta share hawaye saboda bata son su ga ita ma ba ta daina kukan ba dan kar ta ƙara ɗaga masu hankali amma duk inda hankalin ta yake a tashe yake saboda gudan jinin ta abu ma fi soyuwa a gare ta na kwance kan gadon asibiti ba lafiya, rashin lafiya da basu ma san halin da yake ciki ba, a cikin zuciyarta tace "Ya Allah ka tashi kafaɗun wannan yaro nawa Allah ka yaye masa damuwar da ke tattare da shi ka bashi damar cinye wannan jarabawar." Tsam Ali yayi ya miƙe kamar an tsilike shi ya dawo bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da AFREED ya konkwasa yace "Kai wai mi kuke yiwa ɗan uwa na ne da ba zaku fito da shiba wallahi zan karya ƙofar nan idan baku fito man dashi ba, idan kuwa kuka yarda kuka kashe min ɗan uwa wallahi sai nayi kashe ku kuma." Su Fariya na ganin yanda Ali ya zare yana gayi abubuwa irin na masu taɓin hankali suka sake ƙare fashewa da wani sabon kuka, suna ganin kamar idan likitocin sun fito zasu ce masu AFREED ya mutu ne. Momy na ganin haka tayi saurin tashi ta kamo hannu Ali ta zaunar dashi sannan tace "Haba ɗana ɗan albarka miyasa zaka dinga irin haka zaka ƙara tayar mana hankali ne idan muna ganin ka cikin wannan halin idan kaida ke namiji baka sa juriya ba mu mata ya kakeson muyi, dan Allah kayi hakuri kayiwa ɗan uwan na ka addu'a Allah ya tashi kafaɗu sa, narasa wace irin soyayya ce ke tsakaninun haka, na tabbata ko kaine a cikin wannan halin AFREED zai iya shiga tashin hankali fiye da haka ma inada tabbacin cewa yan da shima yake ƙaunar ko su Fariya bai ƙauna hakanan, sosai wannan haɗin ƙan naku da soyayyar dake tsakanin ku ke matuƙar birgeni ni kuma take faranta min rai har yasa nale jin daɗi mara musultuwa dan nasan ko bayan raina Ali ba zaka taɓa kukan rashi uwa ko dangi ba, wannan haɗuwar kawunan naku kesa ni manta cewa akwai wata wada ta tsuguna ta haifeka bani ba, dan wallahi mantawa nake da cewa kai ɗin ɗan yar uwata ne, ni a kullum kallon ka nake a matsayin wanda na duka na haifa kamar AFREED da ƴan biyu, ina fatan Allah ya ƙara haɗa min kanku ɗiyan albarka na ta na faɗa tana share hawaye. Juyowa Ali yayi ya rungume Momy yana share hawayen sa shima yace "Dan Allah momy kiyi hakuri na daina kukan wallahi hankali na a mugun tashe yake gani nake kamar za su fito su ceman ya mutu wallahi da bazan taɓa yafewa kaina ba momy, kuma ni a rayuwar nan ba nida wata uwa sai ke ni ban sa ɗaɗin tawa mahaifiyar ba dan ko kamanin tama bansani ba sai a hoto ta kawoni duniya sai ta tafi ta barni bakina da ita addu'a dan samun rahamar Ubangiji da soyayyar dake tsakanin ɗa da uwa in bashi ba bu wani abun, in badan mahaifina dake raye ba ni nasa da bazan taɓa sani cewa dake da dady ba kune kuka haifeni ba dan kun riƙe ni matsayin ku na iyaye fiye da wasu iyayen ma, da akwai wani matsayi da ya fi matsayin iyaye a wajen ɗa ga iyayen sa to da na baku matsayi wannan matsayin dan kune komai na rayuwa ta sai kuma mahaifin na, ina mama(mahaifiyar Ali) addu'a cewa Allah ya sadata da Mala'ikun rahama kuma ya sadamu a aljanar Firdaoussi." Ali ya faɗa ya ƙarasa share hawayen sa kuma har yanzu yana rugume jikin Momy, itama a boye tana share hawayen ta dan bai kamata ita dake babba ba tayi tayi abu kamar wata karamar yarinya dan tasan suna gane tana cikin ta shin hankali zata iya tayar masu dana su, dama gashi a tashan yake dan ta nuna masu dauriya ne suma suke ɗan rage damuwa. Kamin momy tace wa Ali wani abu wayar ta ta ɗauki rururi da sauri ta duba tana ganin dady ne ta tuna da ta shiga tashi hankali nan ta ma manta bata faɗa masa halin da ake ciki ba, da sauri ta saki Ali ta shiga ƴar couloir (korkorda) da ke bayan ɗakin da AFREED yake ta ɗaga wayar sallama yayi tayi shiru ya kara ta biyu babu amsa sai yace "Mama ƴan biyu kina jina kuwa, kodai yau sai angama min jan ajin irin naku na mata kamin za'a amsa min, oh kodai dan ɗazu da safe kin kirani ne ban ɗaga ba? wallahi ina wajen meeting wayar kuma tana cikin bureau na (office)." Shiru batace komai ba dan ita tana ƙoƙarin mayar da kukan da ke shirin zuwar mata idan ta yarda ta buɗe baki da niyyar yin magana." Kusan minti uku yana jiran yaji tace wani abu amma shiru sai yayi tunanin ko ta kashe wayar ne, saiya sauke wayar a kunanan shi ya duba amma yaga ba kashe kiran bane tayi, sai yaci ka da mamaki yayi saurin mayar da wayar a kunanan sa tare da cewa maman ƴan biyu (da yake haka yake kiranta da shi) laifin nawa har yakai a ƙiyi min magana wallahi ina meeting ne shiyasa ban ɗaga kiran ki ba, Ni bansan nayi wani laifi ba in ba wanan ba, dan haka kiyi hakuri idan wani laifin ne nayi da ban sani ba shima ayi hakuri Allah ya huci zuciyar uwar gida na kuma uwa ƴaƴana masu albarka, ko dayake nasan anjima zaki huce bari na kashe zan ƙara kiranki anjima (ya faɗi hakan cikin zolaya kuma yasan da yace zai kashe to zatayi masa magana, ah ni tsofaffi da soyayya). Momy najin alamun dady zai kashe wayar cikin sauri da wani irin kuka da ya kubce mata tace "Dady AFREED." Ta faɗa ba tare dama sunan ya fito da kyau ba sabida kukan daya ci ƙarfin ta, kuma ta ƙasa ƙarasa abinda tayi niyyar faɗa." Ai dady najin kukan matar shi farin cikin shi abin alfahari sa kuma mafi soyuwa a cikin zuciyarsa ai sai hankalinsa ya tashi iya tashi baisan lokacin da ya faɗi sunanta ta zane ba yace "Falmata lafiya mike faruwa ya naji muyar cikin tashi hankali haka rabon da naji ko na gani kiyi kuka tun rasuwar yar uwarki kuma ƙanwar ki mahaifiyar Ali ko kuma tashin hankali irin wannan dan Allah faɗa min mike faru yawe ya rasu ko ya tayar min da hankalin ki ko waye babu lafiya? wallahi tun safe da natashi naji hankali na ya ƙi kwanciya naso na kiraki kuma mutane suka azazaleni sai na fito mun shiga meeting, haka ba dan hankali na ya kwanta ba na bisu muka shiga meeting sannan kuma ina fito na tarda appelle manque (miss call) ɗin ki kawai sai gabana ya faɗi dan Allah daure faɗa min abinda ke faru kisan hankali na ya ƙara tashi." Cikin kuka da ta ɗan rage tace "Dady AFREED dama AFREED ne......." Kuma sai kuka ya kwace mata ta kasa ƙarasa abinda tayi niyyar faɗa. Ai kuwa hankalin dady in yafi dubu to ya tashi jin abin ma saman kan ɗan sa ne gudan jininsa abin kaunar sa, da sauri cikin ɗaga muyar cike da tashin hankali yace "Maman ƴan biyu daure ki faɗa miyasa mi yaro na da kuka boyemin, mike faruwa dashi ne idan kuka yar wani abun ya sameshi dani daku ba zamu shirya ba, kada ki yarda ki faɗa man cewa bashi da rai?" Hankali momy ya ƙara mugun tashi ganin har mahaifin nasa da take gani zai yi dangana amma ya rikice har haka wai wane irin so ne suke yiwa AFREED haka dan ma Allah yasa basa nunawa sosai da babu san ko AFREED zai iya zama mai wani juyayan hali ba duk da ko yanzu ɗin halin sai a hankali uwa uba miskilanci, kawar da wannan tunanin tayi, lokacin da taji dady AFREED ya daka mata tsawa yana cewa "Ba zaki faɗa min abinda ya sami yarona ba." Da sauri momy itama cikin dusashewar muyar tace "Dady AFREED wallahi nima ban sani ba ina ganin ciwon sa ne ya tashi nima ina cikin falo nida su Farisa, Ilya direba ya shigo yace man ga Ali cen ya tafi da AFREED asibiti kuma AFREED ɗin baya cikin hankalin sa yana tunanin a some yake lokacin da ya tafi da shima, ba tare da na tsaya ya ƙarasa maganar saba, na shige ɗaki na saɓo hijab ya kawo mu asibitin muna zuwa kuwa har an shiga dashi urgence (emergency) mun tardo Ali a bakin ƙofar ɗakin dayake cikin, nayi masa tambayar duniyar nan ya faɗa abinda ya sami AFREED ya kasa faɗa min sai kuka yake da kair na samu na rarashe sukayi shiru kuma mun kusan awa huɗu anan har yanzu babu likitan da ya fito daga ɗakin ma bare su faɗa mana hali da yake ciki kwata kwata hankali na yaƙin kwanciya na kasa daurewa zuciyata ta ƙarye gani nake zan rasa shine abu shiru haka dan Allah dady AFREED kayi wani abu." Sai a sannan dady ya sauke wata ajiyar zuciya, ba dan hankali sa ya kwanta ba a'a dan dai shin ke namiji kuma shine babban indan bai kwantar masu da hankali ba ko ya nuna dangana ba to su ya zasuyi, ɗan nisawa dady yayi cikin sanyayar muryar mai kwantar da hankali yace "Ke kina kuka yaranki nayi wa zai bawa wani haƙura a cikin ku gashi kuma ke ce babba idan baki nuna dangana da kawaici ba su ya kike so suyi kuje asibiti kuyita koke koke kamar wasu maras hankali kece babba fah ke zaki basu haƙura ba wai ki biye masu ba ayita kukaba, je ki ƙara kwantar masu da hankali sannan ki rarashesu da ikon Allah, Allah zai tashi ƙafaɗu sa in Allah ya yarda zai sami lafiya, sannan batun inyi wani abun bai taso ba nida bani gari, ke koma a gari nake ba zanja da ikon Allah ba, ba zan iya bashi lafiya ba saidai wanda ya aza mashi shi zai yaye masa wahala nima kuma ina a hanya nan da ƙarfe biyu jirgin mu zai sauka insha Allahu faɗa man wani asibiti kuke dan ina sauka nan zan wucike." "Clinique HADAMALAH" momy ta faɗa a taƙaice. Ok ta Dr Inusa kenan ai abokinna ne gayamin number ɗakin da yake zan kira yanzu Dr Inusa na faɗa masa yaje ya duba shi da kanshi kamin na karaso." Momy tace "Bon ɗakin dayake ciki numéro (number)45 amma idan sun fito dashi za a kaishi ɗaki personnel inda zai huta ba za'a haɗasa da kowa ba yanzu zanje nasa Ali yaje ya biya kuɗin babban ɗaki mai komai da komai a cikin." "Eh hakanan ya kamata yi sauri ki koma gurin su kin barsu su ɗaya yanzu haka suna cen su na kukan." Momy tace "To shikenan sai kazo Allah ya kawo ka lafiya." Da ameen dady ya amsa tare da kashe wayar, dady na kashe kiran momy ta koma wajen su Ali tace "Ya je ya biya kuɗin ɗakin da za'a saka AFREED idan an fito da shi. ba musu Ali ya miƙe ya nufi inda ake biyan kuɗin." Shiku dady ya na gama waya da momy ya kiran Dr Inusa ya sanar da shi Dr Inusa najin cewa ɗan abokinsa ne kuma a matse yake, yasa shi saurin miƙewa ya kashe kiran dady ba tare da ya bari ya idasa jin abinda dady zai ce ba ya tashi ya nufi ɗakin da AFREED ke ciki su momy na nan zaune saida sukaga muntun ya buɗe ɗaki ya shige suka ƙara baza ido. Dr Inusa bai fi minti talatin da shiga ba sai gashi ya fito, ida su momy ke zaune ya nufa yace "Madame kune ku ka kawo AFREED Sumana ko naga kama" Da sauri momy da su Farisa su ka miƙe momy tace "Eh mune." Dan murmushi ya saki yace "Kun kwantar da hankalin ku biyoni office." Momy tace "To." Tana ƙoƙarin kiran Ali a waya dan ta faɗa masa cewa ya tardosu office ɗin Dr Inusa. 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ *_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_* *Page* : 45 & 46 *Wanene DR Inusa* Dr Inusa wani shahararren likitane da yayi suna a faɗin duniyar nan kuma da yasan aikin sa, yayi karatu sosai a fannin ciwu wuka da yawa dake damun ɗan Adam, yayi karatu akan ciwon dake damun fatar jikin ɗan adam yana da ilimi akan ciwon ƙwaƙwalwa da ciwon ido ciwon haure da irin wanda ya shafi mata da na kwada dana sihe da na zuciya dama sauran ciwuka da ban zana ba, dan haka yayi fice ko ina a san shi, da Alhaji Sumana dadyn AFREED da kuma Alhaji Sadisu mahaifin AFREEN da shi Dr Inusa duk abokan juna ne tun suna yara, shi ya fi su yin karatu mai zurfi dan yana kasashan waje yana karatu duk su dadyn AFREED da papan AFREEN sukayi aure dan haka baisan matan su ba, itama Arahamat mahaifiyar AFREEN wato matar Alhaji Sadisu, yasan tane dalilin auren ƴar uwar ta daya ke. Sosai yayi yawon duniya, dan kasanshan duniya ɗaya ɗaya ne baje ba, ba tare da ya ƙarasa karatun sa ba yayi aure ya auri Jannah (wato ƙanwar Arahamat mahaifiyar AFREEN) haɗuwar sa da Jannah kuma ta dalilin abokinsa ne Ibrahim (wato ƴayan su Arahamat da Jannah) da suka game wajen karatu a New York (in masu karatu basu manta ba Ibrahim na wani aboki ɗan masu arziki da suka haɗe wajen karatu a kasashen waje), yanzu suna zaune a Dubai yanzu haka, ba gari guda suka zauna ba sabida yawan tafiye tafiye da mijin nata keyi yau in suna wannan ƙasa gobe suna wacen Niger kaɗai idan zai taho sai ya barosu saboda karatun yaransu da suka saba da irin na ƙasar waje, ya shahara sosai a aikin sa kuma ya ƙware iya ƙwarewa fiye da tunanin mai karatu, ya san aikin sa sosai dan har a ƙarsa wajen neman sa suke zuwa idan wani abu ya ƙaƙare masu to da ikon Allah shi zai warware sa sabida ya nemi ilimi sosai yanzu haka cikin neman sa yake, idan yazo Niger yana wata uku bai koma gun iyalinsa ba saboda ya malaki asibiti guda huɗu biyu a babban birnin Niamey ɗaya a Maradi ɗaya a Zinder, yana wata ɗaya a cikin asibitin sa da suke cikin garin Niamey yaje Maraɗi ya wata ɗaya ya koma Zinder yayi wata ɗaya, to shi duk mara lahiyar da yayiwa aikin da ikon Allah sai yaji sauƙi sedai idan ciwon ajali ne mara lafiyar yake ko kuma ciwon da bai shafi asibiti ba. Kamar wata baiwa ce Allah ya bashi dan taimakon al'umma duk ta dalilin wannan aikin nasa ya zama wani shahararren mai arziki, kuma baisa tsada a cikin harakar yiwa mutum magani cikin asibitin sa ba, dan haka kowa najin ya zo gari ko lafiyar ka lau zaki ga mutane na tafiya ya duba su. Suna shiga cikin office ɗin na Dr Inusa yace su zauna, momy dai sai binsa da kallo take ta matsu ya faɗa mata halin da ɗan ta yake ciki suna cikin, suna zauna wa suka fara gaisawa sannan yace "Madame nasan baki sani ba amma nasan kin koda a bakin mijin ki ne kunji sunana, mu abokan juna ne tun muna yara dalilin da yasa baku sanni ba ni bana wayan zama a nan kuma idan nazo ayyuka sun min yawa ban samu dama na leƙaku bare har mu gaisa shima mai gidan naki sai in yana gari yake zuwa mugaisa har nan asibiti ko ya isko ni ɗayar, shima Alhaji Sadisu haka yake oisko ni asibiti idan naje Maraɗi ai nasan kisan shi, amma shi nasan matar sabida ita ɗin yayar mai ɗakina ce." "Kema kuma nasan ƴaƴan ki maza da ɗaya daga cikin ƴan biyun nan sabida Alhaji Sumana ya taɓa kawo ɗayar nan tana ciwon ciki an yi katari lokacin ina gari ni nama duba ta, ba tare da na cikaku da surutu ba bari na faɗa maku abinda ke damun ministan namu wato AFREED." Bai ƙarasa rufe bakinsa ba Ali ya turo ƙofar da sallama ya shigo, cike da sakin fuska ya amsa masa sannan Ali ya ƙarasa gab dashi ya duka yace "Dady ina kwana ya aiki." Dr ya saki murmushi tare da shafa kan Ali sannan yace "Lafiya lau alhamdulilah ashe ɗan uwan naka ne ba lafiya." "Eh wallahi dady" "To miyasa a lokacin da kuka kawo shi baka zo ka faɗa man ba tunda ai kunsan ina gari dan shekaran jiya ma ranar asabar a nan kuka yuni ko?" Ali yace "Wallahi dady duk na rikice na marasa mizan yi shiyasa na kasa tuna ma da kana nan." Dr Inusa yace "To shikenan tashi ka zauna insha Allahu ɗan uwan ka zai samu lafiya duk ku kwantar da hankalin ku." Ali ya nemi guri ya zauna yana jiran ji ƙarin bayani. Dr yayi yasu rubuce rubuce a saman wata pepper sannan ya ɗago yace "Ba komai bane ke da mun AFREED sai tunani damuwa wanda haka yayi niyyar saka mashi ciwon zuciya sedai an riga da an shawo kan matsalar insha Allahu ciwon ba zai ƙara tashi ba sai wani abu daga Ubangiji dan sosai aka shawo kan matsalar, sai kuma taimakon da kuma zakuyi mashi shine a daina barin shi yana zama shi ƙaɗai hanka na bada gudunmawa wajen saka shi tunani ko da bai zai yi maku magana ba ku dinga zama kusan da shi kuna hira ta wasa da dariya tun yana shiru har sai yakai ya saka maku baki a zancen ku, kuma wajen aiki ya daina zuwa har na tsayi sati biyu saboda ya ƙara warware wa, a daina barinsa cikin damuwa kuma a guji abinda zai ɓata masa rai har na tsawon watanni shida kuma kada a yarda ayi wani abu da zai tayar masa da hankali sosai har na tsawon watannin nan da na an bata sannan yanzu idan har ya ji sauki kada ku matsa masa dole sai ya faɗa maku abinda ke damun sa dan baiyi niyyar faɗa ba kuka sa shi dole, zai iya shiga damuwa kuma a kuma ƴar gidan jiya ciwo ya dawo sabo idan yayi niyya shi zai faɗa maku da kanshi cikin lalama, idan aka yi haka insha Allahu komai zai dawo normal da ikon Allah. Sai a lokacin momy ta sami damar magana tace "Mungode sosai wallahi ba ƙaramin daɗi naji ba dajin cewa zai samu lafiya kuma an shawo kan matsalar, godiya muke Allah ƙara ilimi." Ameen Dr Inusa ya faɗa sannan ya ƙara da cewa "Zaku iya shiga ku ganshi nasa an tanadi special chambre sabida shi ni nace ka wanda ya ƙarɓi kuɗin komai a wajenku har na ɗaki da Ali yaje biya, sabida nima ai ɗana ne, idan na masa aiki ai kamar nayiwa yaro na ne fata na dai Allah bashi lafiya." A tare suka amsa da ameen sun Fariya dai sun zama ƴan kallo sai bin kowa na office ɗin suke da kallo sun ƙasa magana da sosai ɗan dattijon nan abokin dady ya birgesu sabida yanda suka lura ya ƙare da aikin kuma daga gani baida matsala wayis ne ba ruwan sa da ɗaukar kai duk da arzikin da Allah ya masa bai ɗauki kansa wani abu ba, sai ma sauƙin kai da yake dashi sosai, su da suke ganin a na nuna sa a télé (TV) basuyi tunanin za su ganshi mai sauƙin kai haka ba. Farisa tace kin zuciyarta"Ashe shine ya duba ni da na yi ciwon ciki ni ban ma lura ba lokacin ina halin rashin lafiya, da ace masu kuɗi da ilimi zasu ɗauka cewa ɗaya suke da kowa da duniya ta gyaru." Farisa na zancen zuci bata masan har su tashi suna niyyar fita ba sai da momy tace mata "To ke mi kike jira?" sannan ta dawo hankali ta bi bayan su. Shikuwa ya cigaba da duba takardunsa. Suna shiga ɗakin da AFREED ke kwance a ciki wani kamshi mai ɗadi ya bigi hancin su ga ɗaki tsaf tsaf kamar ba a cikin asibiti ba sedai ace masha Allah a guje Fariya da Farisa suka ƙarasa idan AFREED ke kwance yana baccin wahala da abin sérum (ƙarin ruwa) a hannu sa kwana yake cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, duk suka riƙe masa hannu suka fara kiran "Yaya yaya tashi daga bacci kayi mana magana dan Allah ko faɗa ne kayi mana kaji yaya." Ali ne ya ƙaraso ya katsa masu tsawa tare da cewa "Baku da hankali ne baku ga ya samu bacci ba amma kukeson ta yarda da shi baku san ma yanda akayi ya samu bacci ba amma kukeson sai kun tashe shi maza ku matsa daga nan." Da sauri suka ja da baya dan sun san Ali bai taɓa masu irin haka ba yanzu ma sun san da dalili duk sai suka nemi kujera suka zauna momy ta kalle su ta girgiza kai tana murmushi a ranta tace "Yau fah ba zaku gane kan Ali har in ba gani yayi ɗan uwan na nasa ya buɗe ido sun koma gida lafiya mai ba." Sannan ta ƙarasa ta zauna kusa da AFREED tana kallon fuskar da bakin sa kamar zai yi magana Suna a haka Dr Inusa ya shigo da magungunan da yada ce AFREED ya dinga sha har sai sun ƙare Ali ya miƙawa sannan yace "Nan da awa biyu zai faraka insha Allahu sannan zai ji sauƙi sosai dan haka kada kuyi magana sosai har sai ya tashi dan gaban kansa, su kuwa wa'inan magungunan idan ya tashi abashi wani abu mai ɗan nauhi ya ci sai ya sha." "Ok dady mun gode za ayi yanda kace." Murmushi Dr Inusa yayi ya ce "Ku daina gode man ai nima ɗana ne." Ya juya zai fita daga ɗakin har ya kai bakin ƙofa ya buɗe sukayi kiciɓis da dady zai shigo wanda dirowarsa kenan garin, gama hannu sukayi suna dariya tare da gaisawa sannan suka koma daga ciki a tare." Su Fariya a na ganin dady sai aka shiga farin ciki da gudu suka taso suka rungume shi shima ya riƙe su sosai suna mashi sannu da zuwa Ali ma ya taso ya ƙara so inda suke a tsaye momy kaɗai ke zaune tana kallon su tana sakin murmushi." Cikin zolaya dady yace "Oh ni ƴan biyun Momy su zasu kayar dani ban san ranar da zasu girma ba su daina rigima da shagwaɓa, tunda sun girma sun ƙi yarda da hakan gashi yanzu suna shirin karya ni daga dawowa na." Sakin sa sukayi suna dariya tare dan toro baki gaba suna ɗan bubuga ƙafafun su a ƙasa cikin shagwaɓa suka ce a tare "Gaskiya mu kam papa bamu girma ba har yanzu yan pici pici muke." Gaba ɗaya ɗakin suka kwashe da dariya Dr Inusa yace "Kai lale ƴan biyu akwai rigima irin wannan shagwaɓa haka, da sauri suka koma mazaunin su suka zauna suna rufe fuska da murmushi kwance a fuskar su wai su sunji kunya. Dariya duka ɗakin suka komayi sannan doctor ya koma cewa "Haka nake da su kai kasan cewa ma ƴan matan ne ke shagwaɓaɓi ni har ƴan mazan haka suke da girmansu gwaɗe gwaɗe basu jin kunya haka suke zama suyi ta zuba min shagwaɓa." Dariya sukayi sannan dady ce "Yaran ne namu na yanzu duk sangartaci ne gata ya masu yawa, har wannan mara lafiyar wata ran haka yake Ali ne kaɗai ya nuna ya girma amma shima ba kullum ba idan ka tarda su suna yiwa mahaifiyar nan tasu shagwaɓa zaka ce wasu ƙananun yara baiwar Allah ai tana fama dasu ta iya ɗaukar rigimar kowa a cikin ni har tausayin ta nake idan suka mamaye ta suna mata rigima ba babba ba yaro kuma kamar haɗin kai lokaci guda suke aza tabara su ka dai gansu." 'To Allah dai ya raya ma musu cikin koyi da addinin musuluncin nikam duk sun fi takura man kan mahaifiyar tasu inda ina gari ta kullum suna liƙe da ni suna min taɓara ba kamar yanda mahaifiyar zasu mata ba su mata shagwaɓa kamar yanda suke ko fa bani ƙasar zakaga sun kirani suna ta zuba min shirme, ita mahaifiyar tasu kaga AFREEN ɗiyar ƴar uwar ta wato matar Alhaji Sadisu, idan kaga tana zuba mata shagwaɓa tana biye mata kamar wata ƴar jinjira sosai suka shaku da ita kamar zata mayar da ita ciki har dariya suke ban idan suna appelle video ita da ita suna shirmen su kwani ban dariya." Lokacin da doctor ya faɗi sunan AFREEN sedai AFREED dake kwana yaji wani irin faɗuwar gaba dan har cikin baccin sa yaji an faɗi sunanta har sai da ya ɗan motsa ƙafar sa da hannu sa na dama amma ba wanda ya lura. Dady yace "Hakane dama wata soyayyar Allah ke haɗa ta, ni kamayi batun Alhaji Sadisu ka tuno man da auren ɗiyar sa nan da sati ɗaya ban san ko ka sani ba?" Dr Inusa yace eh na sani ya faɗaman shi yasa ma har yanzu banje Maraɗi ba so nake nayi tafiya guda da ta zuwa ɗaurin aure da sabida aiki, kuma madame ta kirani ta ce tana son zuwa hidimar bikin nace ta bari har ƴar lelan ta AFREEN za tayi aure sai su taho su duka a lokacin Inayah tayi nisa da karatu shi Aban ya riga da ya ƙarasa har ya fara aiki Fujai ne dai bai fara aiki ba tukuna sauran wata bakwai ya ƙarasa karatu sa ka kenan sai su zo tare baki ɗaya." "To madala Allah masu albarka idan bikin ya tashi sai kamin magana mu tafi tare har da maman ƴan biyu za muje tare insha Allahu da ƴan biyun ma idan zasu je, ya jikin yaron naka." Dady ya ta tambayi doctor." Dr Inusa yace "Ah jikin sa da sauƙi sosai nan da awa ɗaya zai farka insha Allahu tunda yanzu ya samu baccin kusan awa ɗaya." "To madala Allah tashi kafaɗun sa." Inji dady Nan doctor ya masu sallama ya fita dan ya barsu su gana da iyalansa, dady yace masa ya iskoshi office ɗin sa suyi fira yaushe gamo. Doctor na fita dady ya isa kusan gadon AFREED ya ke kwance ya ɗan kamo hannu sa ya yayi masa kiss sannan ya shiga jero masa addu'oi, da ya gama ya nufi wajen matar sa ta kallesa da murmushi tayi masa sannu da zuwa sannan tace "Dady AFREED kaje direba ya mayar da kai gida kayi wanka sai ka kwanta ka huta tunda mu gamu a wajen AFREED ɗin kuma doctor yace da sauƙi sosai." Dady yace "To shikenan madame in haka kike so ai shikenan." Bai ƙarasa rufe bakinsa ba Ali ya ce momy da kema tare da dady kuka tafi gida da su Fariya sai ni na zauna da shi kamin ya farka sai su Fariya su yi masa girki su taho da shi ko." Ba karamin daɗi dady yaji ba da yaji furucin Ali dan sosai ya keda buƙatar matar sa a kusa da shi tunda dai jinkin AFREED ɗin da sauƙi gara su tafi gida shi ta kula da shi, dan haka sai yayi saurin cewa "Eh to haka za ayi ku tashi mu tafi." Ba musu suka miƙe suka fita tare da cema Ali sai sun dawo, shima Ali ya faɗi hakane saboda ya san dady yanzu ya dawo da gajiya ya na bukatar kulawar momy." Suna fita ya koma kusa da AFREED ya zauna yayi tagumi yana kallon sa yan jiran farkawarsa, Bayan awa ɗaya KU BIYO NI DAN MI ZAI FARU TA KU HAR KULLUM MAI KAUNAR KU 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ *_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_* *Page* : 45 & 46 Suna fita ya koma kusa da AFREED ya zauna yayi tagumi yana kallon sa yana jiran farkawarsa. Bayan awa ɗaya shiru AFREED bai farka ba kuma bai motsa koda hannun sa ba bare ayi tunanin zai farka, haka wata awa gudar tazo ta wuce shiru, Ali na zaune wajen awa biyu yana jiran farkawar sa amma babu ko alamun zai farka, bayan awa biyu da minti ishirin hankali Ali in ya yi dubu to ya tashi ganin har yanzu AFREED bai farka ba, shida ake ce ma sa nan da awa ɗaya zai farka amma har yanzu shiru, hakan yasa shi miƙewa da sauri ya tashi ya fita bai tsaya ko ina ba sai office ɗin Dr Inusa, amma sai yayi rinshin sa'a baya nan da sauri ya fito yana ƙoƙarin kiransa sai ga wata infirmière (nurse) ta fito daga wani ɗaki, kawai sai Ali ya tare ta yana tambayar ta dan Allah bata ga inda Dr Inusa ya shiga ba?" Nurse din tace "Ai yana block opération (ɗakin tiyata)." Ali da zufah ta Kariki ke masa yace "Tun yaushe yashi ga" "Ya kai awa biyu da shiga dan ina saran nan ba da jimawa ba zai iya fitowa." "Kamar nan da minti nawa kike ganin zai fito?" To wallahi ban sani ba, inaga dai ba zai wuce minti talatin ba zuwa arba'in zai fito." "Kai har minti talatin gaskiya yayi yawa ɗan uwana nacen cikin wani hali, dan doctor yace sai nan da awa ɗaya zai farka amma har ya haura awa ɗaya da minti talatin da biyar shiruko motsi baiyi ba, dan Allah muje ki du bashi ki gani idan kuwa akwai wani doctor dai zai duba shi kamin Dr Inusa ya fito to muje ki masa magana." Infirmière ɗin mai kirki, gani hali da Ali ya shiga dalilin ɗan uwan sa tace " Eh akwai muje na kaika office ɗin sa sai kama sa bayani." Suna kaiwa bakin ƙofar doctor kin sai nuser ɗin tace masa ka shiga da ga ciki ka sanar mashi, ni gaba zan ƙara akwai masu jirana." Godiya yayi mata sannan ya kama hannun ƙofar office ɗin Dr da ta kawo shi, kawai kamar ance ya juya sai ya tsikayi Dr Inusa na tafowa ai da sauri ya saki ƙofar ya nufe sa ya faɗa masa cewa AFREED ya ƙi farfaɗowa." Bata tare da ya ƙarasa jin bayani Ali ya shige ɗakin da AFREED ke kwance a ciki dama sun kawo bakin kofar ɗakin. Suna shiga ɗakin suka tardo AFREED zaune da ƴan biyu a kusa dashi suna jero masa sannu da sauri Ali ya ƙarasa kusa dashi yace "Kai ɗan uwa yaushe ka farka ina can hakalina ya tashi da naga baka farka, yanzu ina kema ciwo?" Ali ya faɗa yana ta taɓa shi, da ido kawai AFREED ya bishi bai ce masa komai. Dr ya ƙaraso inda suke yana mai sannu da murmushi a fuskar sa sannan yace "Minista ya ƙarfin jikin?" AFREED ya ɗaga idonsa ya duba shi sannan yace "Da sauƙi." Doctor yace "To madala yanzu ina kema maka ciwo sannan kuma mi kake ji?" AFREED yayi shiru bai ce komai ba saida Dr ya ƙara mai maitata masa tambayar sannan a matuƙar gajiye da magana yace "Alhamdulilah babu inda ke mani ciwo dady." "To masha Allah tashi kaje cikin douche ka wanko bakinka sai kazo ka ci abinci da ɗan thé (tea) sai kasha magungunan ka." Ba musu AFREED ya miƙe ya nufi douche (toillet) yana kaiwa baƙin kofa yayi tagata zai faɗi da gudu Ali ya yi wajen sa ya riko sa yace "Yi sannu man AFREED kada ka faɗi in ba zaka iya ba sai kace na rakoka ba da fa yanzu ka faɗi kuma sai ka ƙara tayar mana da hankali dan Allah kabi a hankali." AFREED dai baice masa komai ba ya buɗe ƙofar douche ɗin ya shige, bai jima ba ya fito ya na tafiya ya na dafa bango sabida jiri yake gani Ali yaje ya riƙo shi suka dawo bakin gado ya zauna. Fariya ta haɗa masa tea mai kauri da zafi kamshi sai tashi yake, ta miƙo masa ba musu ya ƙarɓa sabida yunwa ya keji sosai. Cikin ƙaƙanan lokacin ya kammala sannan ta zubasa tuwon shinkafa da biyar kuɓewa ɗanya ta ji kifi da man shanu, nan ma bai musa ba ya ƙarba ya sabida abincinsa ne wanda ya fi so, bai ci wani da yawa ba ya ajiye, Ali na ganin haka yace "Dan Allah AFREED ka ƙara mana regarde tu n'as pas beaucoup mangé (bakaci sosai ba)." Da kyar AFREED ya buɗe bakin kamar mai raɗa yace "Na ƙoshi." Sanin cewa AFREED idan ya riga ya furta ya ƙoshi to komai za'a yi masa ba zai ƙara cin komai ba dan haka Ali ya miƙo masa ruwa ya ƙaraba ya sha sannan ya ɓalo maganin ya mika masa da wasu ruwan marasa sanhi haka ya ƙarba ya sha duk abinda ke faruwa akan idon Dr Inusa, yana ganin AFREED ya kammala duk abinda aka saka shi ya sakin murmushi ya ce "Masha Allah yarona Allah ya ƙara baka lafiya." Sannan ya ƙara tambayar abinda ya keji yace masa baijin komai sannan ya fita ya bar ɗakin. A lokacin AFREED ya kamo hannu Ali yace "Ali ka sa dady ya rubuta mana takardar sallama na ji sauki babu abinda ke min ciwo yanzun, nagaji da zaman asibitin. Ɗan hararen sa Ali yayi yace "Naƙi na saka ya bamu sallamar bancin kaje kana wani banzan tunani ka kana shirin hallaka mana kanka." "To nace ban iya zaman ka saka a sallame mu ko na tashi nayi tafiya ta ba tareda....." Bai kai ga ƙarasa sa abinda yayi niyyar faɗa ba aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, Momy da dady su ka shigo da murmushi ɗoke da fuskar su ganin AFREED zaune har yana magana sallama sukayi tare da da ƙaraso wa gun da gadon da AFREED ke kwance da sauri momy ta riƙo sa ta masa sannu tace "Ɗan albarka na ka farka, Allah na gode maka da ka tashi ka faɗun wannan yaro, yanzu mike maka ciwo?" Murmushin ƙarfin hali AFREED yayi sannan yace "Momy ina yuni da fatan kin yuni lafiya, dady sannu da zuwa anzo lafiya, dady yaushe kazo." Farin ciki ne ya mamaye zukatansu baki ɗaya sannan momy tace "Lafiya lau ɗan momy ya jikin naka?" Kamin AFREED ya bata amsa dady ya kamo hannu sa ya shiga shafa kansa da hannu sa na dama yace "Yau nazo yarona momyn ka tayar mana da hankali ba dole nazo ba shiri ba, ga yanda nazo na tarar da kai na'aza ma rasa ka zamuyi amma kaga Allah da ikon sa ya tashi ƙafaɗun ka cikin ƙanƙanan lokacin naga alamun har gida zaka iya tafiya ma ko ba haka na tara kana faɗa wa Ali ba." Murmushi AFREED yayi tare da duƙe kansa ƙasa, nuni yayiwa Ali da yazo ya taimaka masa yayi Sallah haka Ali yazo ya kamasa suka nufi toillet ya shiga ya ɗauro alwala sannan ya fito Ali ya kamasa ya kawo sa har gun darduma da Momy ta shinfiɗa masa ya fara gabatar da sallah azahar da ya kammala bai bar saman darduma ba ana suke ta fira shida dady, momy, Ali, da kuma Fariya da Farisa suna nan a zaune akayi kiran sallah la'asar dady da Ali har da AFREED mara lafiya suka nufi masallacin da ke cikin asibitin saboda yace zai iya takawa da kan sa har masallacin dan kuwa yanzu ya daina ganin jirin da ke diɓarsa tun farkawarsa haka kuwa suka tafi masallacin a tare, idan kaga AFREED sai kace wani cikakkin mai lafiya dan lafiya lau yake takawa ba wani tangaɗin marasa lafiya, Momy kuwa da ƴan biyu suka gabatar da tasu sallah a ɗakin da suke jinyar AFREED. Ba'a ɗauki wani lokaci ba su dady suka shigo cikin ɗakin wannan karon su huɗu ne suka shigo har da Dr Inusa, AFREED ya nemi gurin ya zauna bakin gado da ya tashi, duk suka ƙara so bakin gadon suna kallon sa, Dr Inusa ya kalli momy yace "Madame naga yaron naki ya warware ko dai gida yake da buƙatar zuwa tunda yayi saurin korar rashin lafiyar." Kamin momy tace wani abun AFREED yayi saurin cewa "Eh dady wlh naji sauƙi zan iya ta fiya gida ko da kaina ne." Duk ƴan cikin ɗakin suka kwashe da dariya suna masa dariya shima ɗan murmushi yayi ya sune kansa. Dr Inusa yace "To madala yaro na amma duk da haka sai gobe insha Allahu zan baka sallama, dan na ƙara ganin yanayin jikin ka, zuwa goben yanzu ka yi shiru ka rage magana amma kada kayi bacci, kai Alhaji biyoni office akwai abinda zamu tattauna." Murmushi dadyn AFREED yayi sannan yace "To muje." Suna fita AFREED yace "Gaskiya ni momy ban ce zan iya bacci a nan ba a barni naje gida goben da safe idan Allah ya kaimu sai na dawo a dubani." Wata ya ƙaramar harara momy ta sakar masa tace "Wato ni daka raina zaka faɗa wa wannan banzar maganar shi Dr Inusa da dadyn naku da suna nan mi ya hanaka faɗa masu haka to babu inda zaka a nan ɗin zaka kwana, in badan ma Allah yaga tausayin mu ya ga halin da muka shiga ya taimake mu ya baka lafiya, da a lokacin da muka kawo kane, ka ga halin da kake ciki ko iya magana kanayi shasha kawai maza imani shiru ai kaji abinda doctor yace." Badan yaso ba AFREED ya kame bakinsa ya yi shiru gudun kada ya ƙara magana ya ɓata ma mahaifiyar sa da rai, dan haka babu yanda ya iya ya jingi na da abin gado ya shiga tunani. Bangaren dady da Dr Inusa kuwa suna shiga bureau ɗin doctor suka nemi gurin zama suka zauna a wata haɗaɗɗiyar ƙatuwar kujera dake cikin office ɗin, sannan suka sake gaisawa, tare da ɗan taɓa fira sannan Dr Inusa yace "Yawa abokina dama abinda yasa nace ka biyo ni wata shawara nakeso muyi akan AFREED." Sai kuma ya ɗan yi shiru. Ganin yayi shiru yasa dady cewa "To ina jinka doctor saida Dr Inusa ya gyara zaman tare da yin gyaran murya yace "Alhaji ya kamata a yiwa AFREED aure hakan ne zaisa ya rage duk wani tunani da yake yawan damun sa har yake ƙoƙarin saka masa ciwon zuciya, kuma idan ka bincika bai wuce dalilin mace ne ya shiga wannan halin da yake ciki ya kamata asamu ma fita, ku tuntuɓe shi idan har yanada wace yake so ya fitar da ita sai ayi gaggawar zuwa neman aurenta gidansu saboda AFREED ya kai mizanin aure yanzu, yana da buƙatar wace zata ringa taimaka masa da shawarwari da kuma lamura na yau da kullum." Sai da dady ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Hakane doctor nima abinda nake tunani kenan wallahi kamar ka shiga zuciyata wallahi, amma maganar cewa saboda mace ne ya shiga wannan halin gaskiya ina tamtama, abinda kuwa yasa nace haka shine AFREED bai kulla mace, kada a kai ta nesa ma kasan ko cousins ɗin sa mata bai cika kulawa ba bare har ya kulla wata a waje." "Duk da haka abokina yanzu ba zaka taɓa gano bakin zaren ba sai ka bincika zakasan ko daga ina matsalar take, idan kuma kasan da babu wace ya ke so to kawai ka nema masa mai hankali da nutsuwa ko cikin cousins ɗin sa ne sai ka aura masa ko da bai sonta zai sota daga baya." "To shikenan babu damuwa insha Allahu zan je na duba mashi wada zata dace dashi sai kawai a haɗa su." Doctor yace "A'a ba hakanan ba za'a yi sai ka fara tuntuɓar sa kaji babu wace yake so kannan sai ka yanke hukunci." Ok Insha Allahu haka za'ayi yanzu sai da safe za a sallame shi ko." "Eh sai da safe insha Allah." Bayan haka suka ciga ba da fira tafiya bikin auren Khairat ɗiyar Alhaji Sadisu yayar AFREEN, daga bisani kuma suka bar office suka nufi dakin da aka kwantar da AFREED. *Washegari* Da safe wajen ƙarfe 10 na safe AFREED ne kwance kan gadon asibiti yasha wasu ƙananun kaya masu masifar kyau wanda su Fariya su kawo masa tun jiya da yayi wanka yau ya saka bayan ya fitar da na bacci da ya kwana dasu, idan ka ganshi zakace bashi ne mara lafiyar ba, shi ne ya yiwa mai jinya rakiya sai wani game fuska yake shi a dole ya gaji da zama asibiti, Ali na lura da hakan shima ya game ta sa fuskar dan ba ƙaramin zafi AFREED ya ke ji ba, shi a ganin sa sabida min zai ki faɗa masa damuwa sa da har ta kai sa ga rashin lafiya, Ali gani yake da ya faɗa masa abinda ke damun sa da damuwar bata kai ga saka masa ciwon zuciya da sun haɗa kai sun shawo kan matsalar ko kuwa su nemi mafita kamin haka ta faru, amma shine ya ki faɗa masa, dama akwai abinda AFREED zai iya ɓoye masa kenan? Ali na cikin wannan tunanin dady da doctor suka buɗe ƙofar ɗakin tare da sallama a bakin suka shigo, da ma momy da ƴan biyu suna daga gefe suna fira Ali ne ke kusa da gadon AFREED ɗin ya na dane dane a waya sa shikam fushi ma yake da AFREED ɗin dan ganin ya samu lafiya kuma ya ƙi sanar dashi damuwar sa, su dady na shigo wa doctor ya dubi gun da su momy suke a zaune ya buɗe baki da niyyar zai magana ƴan biyu suka katse sa ta hanyar gaida sa cike da kulawa ya amsa sanan yayi wa momy sannu da gida tare da tambayar mai jiki. Sannan ya juya wajen AFREED. Yana ƙarasawa bakin gadon shi da dady AFREED ya tashi zaune ya gaida shi cike da sakin fuska suka amsa sannan doctor ya kama hannun sa na dama yace "My son ya ƙarfin jiki." Ɗan murmushin yaƙe AFREED ya saki sannan yace "Jiki da sauƙi dady ai na ma warke yanzu babu abinda nake ji." Murmushi doctor ya saki sannan yace "Ah yarona irin wannan zuba haka dan ka nuna min kaji sauki saboda ka matsu ka tafi gida to sai gobe, takarda sallama da nazo maka da ita ma bari na koma da abita." Murmushi AFREED yayi tare da sun ne kansa yana susa kai wai irin yaji kunyar nan dan shi kam babu abinda yake so yanzu kamar ya ganshi gida. *_Kumin afuwa masoyansa ZAMBA CIKIN AMINCI kwana biyu banada dama ko yanzu ma kokarin ne nayi wa jan gani na faran ta maku.....* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ *_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_* *Page* : 47 & 48 Doctor ya koma cewa "To na sallame ka tunda dai baka ce komai, amma kuma sai ka rage saka kanka a damuwa kaji my son komai yayi tsanani yana tare da sauki idan kayi hakuri komai zai zo ya wuce, idan kuwa ƙaga abin yafi karfin tunanin ka to ka nemin ɗan uwan ka kuyi shawara idan baku samu mafi ta ba ku nufi iyayen ku da maganar sai kuga komai ya zo da sauƙi, sabida ƴan magana sun ce duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutse ba zai hango ba, duk abinda ya shige maku duhu ku fara kai maganar ga manya sai kuga Allah da ikon sa ya sa an shawo kan matsalar." "Insha Allahu dady hakan bazata sake faruwa ba." Inji AFREED "In ta ƙara faruwa kuma fah ya kakeso na maka?" "Ba ma zata faru ba dady." AFREED na faɗin haka duka ɗakin suka kwashe da dariya jin yanda yayi maganar kamar karamin yaro, banda Ali daya game fuska shi a dole fushi yake da AFREED. Ba tare da ɓata lokaci ba suka yiwa doctor sallama tare da gangama kayansu suka saka a mota Ali ya nufi motar da yazo asibitin da ita inda AFREED ya riga da har shiga Ali kawai yake jira, Ali na shiga ya zauna mazaunin direba ba tare da ya ko kalli AFREED ba shima AFREED bai kulla sa ba sabida lura da yayi yana ta cin magani, Ali ya tayar da motar ya bar hararbar asibitin haka dady shima ya tayar da tasa motar wada momy da ƴan biyu ta ke ciki suka kama hanya, har suka ƙara so gida babu wanda yayi wa wani magana tsakanin AFREED da Ali kawai dai sunyi tafiyar kurame ne, Ali nayin parking ya fice daga motar ya nufi hanyar ɓangaren su da kallo AFREED ya bisa yana tunanin shin mi yake damu Ali yake wani share shi a zuciyarsa yace "Ko dai fushi yake dani ne to mi na masa ko dai wani ya taɓo sa shida bai fiya yin fushi ba ko miye aka masa nasan babba ne, idan kuwa ni yake ma fushi na san da an jimawa zai daina ba saboda bai iya fushi dani." AFREED na cikin mota yana wannan tunanin baisan lokacin da su momy suka shigo gidan ba sai da yaji dady yana ce masa "Mi kake yi a cikin motar?" Da sauri AFREED yayi firgigit ya juyo tare da cewa "Babu komai." Sannan ya buɗe motar ya fito shima ya nufi ɓangaren su, su momy suka tsaya suna kallon sa har ya shige sannan suma sukayi nasu ɓangaren, Ali dake tsaye ta window dakin sa yana kallon AFREED yana hamdala da godewa Allah da ya bawa ɗan uwansa lafiya ganin AFREED ya nufo ɓangaren nasu yasa shi komawa ya zauna bakin gadon sa ya na tunani. AFREED na shiga ɓangaren na su shima ya nufi nasa ɗakin ya tare da rage kayan jikin sa ya nufi toillet ya saka ma kanshi ruwa ta tare da ya jima ba ya fito ya shirya cikin kayan bacci ya ɗane gado ya shiga yin bacci har sai da aka kira sallar azahar sannan ya farka ya nufi toillet ya sake yin wani wanka tare da ɗauro alwala ya fito ya shirya cikin fara doguwar rigar sallah ya fito daga ɗakin da niyyar tafiya masallaci a bakin ƙofar fita daga falon nasu ya haɗu da Ali na ƙoƙarin buɗe ƙofar ya fita shima ya ƙara so ko kallon inda yake Ali baiyi ba bare yasa ran zaiyi masa magana, Ali ya buɗe kofar ya fice, mamaki sosai ya kama AFREED wai shine ya ke share wa haka to mi ya masa?" Yana cikin wannan tunanin yaji an tayar da sallah da sauri ya rufe kofar ya nufi masallacin, kusa da Ali yayi sallah saboda yana son idan sun dawo tare ya tambaye sa ko lafiya yake ta share shi haka, ana gama sallah kamin AFREED yake gama addu'oi déjà Ali ya ƙarasa tasa ya tashi ya fice daga masallacin yayi tafiyar. Da mamaki AFREED ya ƙarasa nasa addu'oi shima ya nufi cikin gidan ɓangaren momy ya shiga a nan ya tarda Ali yana ta wasa da dariya shida su Fariya, yana ganin sa ya gimtse fuska har abin yaso bawa AFREED dariya sedai bai dara ba kawai sai ya nemi guri ya zauna ya na jiran saukowar momy. Momy na saukowa ta nufe su da dariya tana masu sannu da shigowa su kuwa suka gaida ta ta amsa tare da nufar dinning, ita da Farisa suka ɗauko abinci daga saman dinning suka yo dashi falo, saman kafet suka ajiye suka jera komai nan kowa ya sauko ƙasa suka zauna suna jiran dady, shima ba tare da ɓata lokaci ba ya sauko sannan momy tayi servir ɗin kowa daga nan sukayi Bismillah suka fara cin abincin bakajin ƙarar komai sai na cokali suna gamawa AFREED ya mike yace "Momy zanje na kwanta na ɗan huta." Murmushin manya momy ta sakar masa sannan tace "To a huta lafiya ɗan momy." Daga nan ya nufi mahaifin da ya sunbace shi sai mahaifin na sa ya sha masa kai yace Allah maka albarka da Amin ya amsa sannan ya fice." Da AFREED ya fita momy da dady da Ali da su Fariya suka shiga fira har firar auren su akayi, AFREED tun yana jiran shigowar Ali har bacci ya kwashe shi Ali bai shigoba, kuma shima Ali ya na sane ya ƙi shigowa saboda yasan yana can yana jiran sa. Ali shine bai fito daga ɓangaren momy ba har saida aka yi kiran sallah la'asar kan suka fito shida dady dan zuwa masallaci a hanya suka haɗu da AFREED shima zai tafi masallaci sai suka jera suka tafi tare bayan AFREED ya gaida dady haka ana gama sallah suka jero tare, su nufo gida suna kawowa daidai ida zasu nufi ɓangaren su suka yiwa dady sallama, suka nufi nasu ɓangaren babu wanda yayiwa wani magana har suka shiga falon su, AFREED yaka Ali baida niyyar tsayawa suyi magana dan ganin da yayi ya nufi hanyar ɗakin sa yasa shi dakatar dashi ta hanyar cewa "Ɗan uwa inason magana da kai." cak Ali ya ja ya tsaya ba tare da ya juyo ba kusan minti biyar babu wanda yace wani abu daga cikin su Ali na ganin haka ya ɗaga ƙafarsa har zai fara tafiya, AFREED kuwa har ya kawo inda yake a tsaye kamo kafaɗar sa ya yi yace "Kazo ka zauna muyi magana." "Ba zan zauna ba ka faɗi duk abinda kakeso ka faɗa ni inada abun yi." "Dan Allah ka zauna maganar ba zata yiwu daga tsaye ba." "To shikenan tunda kace dan Allah sedai ka yi sauri ka faɗi ko miye ni akawi abinda ke gabana." Murmushi kawai AFREED yayi ya karasa suka zauna ɗaya daga cikin manyan kujerun dake falon, sai da ya nisa yace "Lafiya Ali naga kana ta share ni mi nayi maka haka mai muni da har bakason ganina, ko kuwa rashin lafiyar da nake kake so na koma, in baka gama jinya ta bane sai naji." Da sauri Ali ya ɗaga kai ya kalle sa bai ce masa komai, AFREED ya ɗaura da cewa "Sai wani guduna kake ko dan ban da lafiya ne ko kuwa wani abu doctor yace inada wanda idan ka ci gaba da yi min magana ko kulani kai ma zaka kamu da shine ban sani ba." Da wani irin sauri Ali ya ɗago ya kalli AFREED kallo irin na har akwai abinda zai same ka na guje ka ne, kamar AFREED ya san abinda Ali ke tunani yace "Ah to dole na faɗi haka rabon da kamin magana ko kamin sannu da jiki tun muna asibiti da na farka tunda ka taimaka min na shiga bayi na fito baka ƙara koda yiman magana Ali ba dole na faɗi haka ba." Wanda Ali yaga damuwa ƙarara a fuskar AFREED waga alamun ya marairaice da gudun kada damuwar da ya shiga yanzun ta ƙara je fasa cikin wani ciwon ya sa shi saurin buɗe baki ya fara magana kamar haka "Haba AFREED a tunanin ka akwai wani da zai sameka na kujeka ko da kuwa abin ya fi ƙarfin tunanin duniya baki ɗaya duk faɗin duniyar ban da mahaifi na da Momy da dady ganin ka ina da wani da ya fika a rayuwa ta ne kenan baka san son dana kema maka ba da har zaka kalle ni ka faɗa min wannan zancen da mai hankali ba zai ɗauka anya kuwa kama ɗauke ni wanda na ɗauka kuwa ni kallon wanda muka fito cikin ɗaya nake maka wanda banida kamar sa a rayuwar nan, amma ina ga kai wanjan ka ba haka ba ne." "Ni ba dan komai nan ke fushi da kai ba sai dan ka zauna har wata damuwa ta dameka har ka saka kanka a mugun tunanin da ya ke neman rayuwar ka wai ka kasa faɗa min idan ni ne ba zan taɓa boye ma komai ba, duk da nasan halin na rashin son magana da miskilanci da kuma zurfin ciki bai kamata ace ni ka kasa gayamin damuwar ka ba ko kana ganin bazaka iya faɗa ma su momy ba sai ka faɗa min idan muka kasa shawo kan abun sai mu san hanyar da za mubi mu faɗawa su momy, su sai su sa ma mana ma fita idan ta wajen su ba'a samu mafita ba, sai su taya mu gayawa Ubangiji lamarin da, samun abin yi daga, haka har asamu ma fita kasan ance addu'ar iyaye bata faɗuwa ƙasa banza." Sai da AFREED ya sauke ajiyar zuciya sannan ya fara da cewa "Wallahi ɗan uwana ba haka bane ni irin son da nake maka ya ma linka wanda kake yi min sau dubu na kasa samun ta hanyar da zan sanar da kaine wannan babban lamarin da ke shirin samu na ko ma nace ya sameni, kai da kanka kunyar faɗa maka nake ban san ta ina zan fara ba domin samun damar yiwa tufkar hanci abin ne yanada wahalar fasarawa wallahi, amma yanzu banida wata mafita da ya wuce na sanar da kai ko da zaka taimaka min da wani abun ko da kuwa addu'a ce dan a gaskiya ina cikin matsala da tashin hankali sedai fatan Allah ya yaye mani wannan wahala." AFREED ya ɗan nisa tare da niyyar sake yin wata maganar Ali yayi saurin dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu sannan yace "Karka damu ɗan uwana Allah zai shige mana gaba a cikin wannan lamari insha Allahu duk da ban san ko miye matsalar ba, amma tun ka fin ka faɗa man na ji ajikina akwai nasara akan hakan zaka samu nasara Insha Allahu komai zai warware da izinin Allah, amma yanzu kada ka faɗa man ko miye damuwar ka, ka bari na shiga wanka na fito sai ka faɗa man a nutse saboda na lura ka gaji, dan wannan ƴar maganar da kayi kamin na fito ka ɗan huta sai na zo har ɗakin ka sanar dani sai a nemo mafita da iznin Allah." Murmushi AFREED yace "Wallahi kamar ka sani kuwa na gaji da maganar gudin kuma kar kace bana son faɗa maka yasa na so ƙarasa zancen." Daga nan suka rabu kowa yayi ɗakin sa. Su AFREEN sai shirya shiryen bikin Khairat suke inda ya rage saura kwana goma ɗaurin aure amarya tayi wani freish da ita, tayi kyau sosai haskin anty Khairat ya fito ana ta gyara amarya saboda anty Fauziya ta dauko wata mata yar Diffa tana ta bawa amarya kullawa sannan ita maman tana nata ƙoƙarin wajen gani an gyara amarya sosai da sosai tana bata irin haɗa haɗen su irin na buzaye komai yima mata ake masha Allah idan ba sani Khairat kayi sosai ba, zaka iya ƙin ganeta idan ka ganta yanzun, wajen satin ta uku bata fitowa koda falon gidan su ne bare har takai farfajiyar gidan haka ko ganin ta ba'a bari sai dolin ta, ita da Ahmad kuwa sai ta waya don kam an hana sa ganin amaryar sa duk ya bi ya damu haka itama idan yace zai yi mata video call bata yarda kullum sedai yaji murya ta. AFREEN ce tayi sallama ta shigo ɗakin taje kusa da yayar ta ta zauna tace "Wai anty Khairat kinga yanda kika koma kuwa, kina duba madubi anty kinga duk kin sauya kamar bake ba." Ita dai Khairat murmushi kawai take sakarwa AFREEN, tashi AFREEN tayi taja hannun kai Khairat tace "Zo ki gani anty." Ba musu Khairat ta bi ta hannu ta na cikin na AFREEN dai dai mirror ta tsaya da ita tace "To dubi kanki a madubi anty ki ga wanda kika sauya anya kuwa ya Ahmad zai ganeki idan yan ganki kuwa kai anty wallahi yanzu har kin fini kyau." Wani fari Khairat tayi da idanu sannan tace "Kai ƙanwar anty Khairat wannan taɗin ni ɗaya anya bai min yawa ba? kuma da kike cewa yanzu har nafi ki kyau, ta ya za ayi haka ta faru ina ni ina ke wajen kyau ai ko farcen ki ban kamo ba sister, duk kuwa kyau ɗin da zan yi bazan taɓa kamo ki ba yanzu kawai annurin amarci nekinsan ita amarya komin munin ta dole ne sai tayi wannan annurin, shi yasa kika ga haka amma ke kyawon ki na daban ne soeurette idan har ke ma naki auren ya tashi a ka fara maki irin wannan gyaran idan har kika duba madubi to zaki fara bawa kanki tsoron ma sabida wani kyau ne zakiyi irin wanda babu shi a cikin mutane wallahi wata irin haɗuwa zaki yi Allah dai ya nuna mana wannan lokaci musha didima." Murmushin yaƙe kawai AFREEN tayi sannan tace "Duk da haka anty a halin yanzu dai kin fini wallahi." "Hum na ji dai ƙanwata kina son sa kai na fashewa inji babu wata kamar ni." "Wallahi ba hakane sister ba wai ina koɗa ki bane abinda na gani ne na faɗa." To shikenan na yarda ƙanwata yanzu kuma waye ƙanin nawa faɗa man dan mun daɗe bamu yi fira dake ba kika faɗa da wanda kuma kike tare yanzu, dan gaskiya so nake ki samo muntun na gari mai amana wanda ba zai gudu ba tunda sauran duk mutanan banza ne." "Kai anty ni nasan ko da kuwa sauran ba na kirki bane KAMAL mutuman arziki ne kawai dai abin daga mahaifiyarsa ne kuma Allah yayi ni ba matar sa bace, saboda nasan shi bai da niyyar cutana, anty kinsan yanda yake so na kuwa?" "Haka ne nima na yaba da halayyar KAMAL gaskiya, shi ba zai iya yau darar ki ba, ko dan an ce ɗan Adam tara yake bai cika goma, amma ina da yaƙini sosai akan KAMAL ba zai cutar dake ba, kawai haka Allah ya tsara maku kuma sai ku rungumi kaddara ku gode masa ku roƙe sa ya haɗa kowa da rabon da na alkairi." "Ameen AFREEN tace a taƙaice." Wajen minti biyu babu wanda ya ce komai AFREEN na ɗan gyara ma Khairat kashin kanta da ya fito daga cikin adikon ta, ita kuwa Khairat ta faɗa duniyar tunani can dai ta ɗan nisa tace "Ni gaskiya soeurette lamarin ki na bani tsoro anya ba akwai lauje cikin naɗi ba kan wannan al'amari naki, il faut qu'on passe une bonne enquête sur ça vraiment ta situation m'étonne sincèrement." Shiru AFREEN tayi na wajen second biyar sannan tace "Anty moi j'ai pas compris ce que tu veux me dire, quelle enquête on va faire sur ma situation, d'abord de quelle situation tu parles?" Khairat tace "Hai sister ne fait pas semblant de me montrer que tu ne savais pas de quoi je parle." "Wallahi anty je n'ai sais pas de quelle situation tu veux parlé." "To d'accord na yarda baki gane ba ina nufin lamarin aurenki ya na so ayi bincike gaskiya ya za a ce kullum maganar aure sai ta kankama ana shirya shan biki kuma sai abu yazo ya lalace gaskiya ya kamata a duba lamarin nan, gaskiya ban yarda haka nan kawai maganar auren ki ke lalacewa ba, ina tunanin da akwai wani abu a ƙasa." "Kai anty ki daina ki tunanin komai kawai daga Allah ne, kuma kalla tawa ƙaddarar kenan, kama ki saka komai a ranki harki Kai ga saka wani a zargi, babu wani abu da za a yi bincike a kansa kawai su wa inda muke haɗuwa muna rabuwa to fah ba alkairi tsakanin mu wannan shine kawai." *INA MA KOWA FATAN ALKAIRI💃💃💃💃* *Taku har kullun mai kaunar ku* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ *_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_* *Page* : 49 & 50 "Ke dan Allah jan cen mallama ki ajiye wa'azin ki a nan har ki fita a nan sai ki yima masu buƙata, tunda ko kina so ka ba ki so sai na faɗi haka, kuma a na hango maki abinda da ke kika kasa gani da idonki, amma wata rana zaki gane abinda na faɗa gaskiya ne, sannan kuma zan samu maman muyi wannan maganar tunda ke baki da hankali har yanzu ƙuruciya na damunki." Shiru AFREEN tayi saboda ta kasa abinda zata ce wa Khairat ɗin, sai kawai ta saki gashin Khairat tace "Soeurette bari naje gun tanti dan marabina da ita tunda safe." Khairat tace "To mara sani ciwon kai tantin mi kuma da zaki ce zaki tafi gun ta dan kawai tun safe baki koma gani ta ba ko ita uwarki ce da baki da tunani a na nuna maki Annabi ki rufe ido, to ni bari kiji na faɗa maki maganar gaskiya tantin nan da kike shi shi gema ni wallahi yanzu ban yarda da ita ba dan ina zargin ta sosai yanzu a kan wasu abubuwa dake faruwa a gidan nan." AFREEN tace "Kai anty Khairat tantin na aza kema kinsan halin ta kin na sane da yanda take son mu da son ci gaban mu kamar yanda maman ke yi mamu kuma kema kin yarda da ita dan shiyasa kike alfahari da kyawon halinta." Da sauri Khairat tace ga da ba, amma yanzu bari kiji na faɗa maki yarinya yanzu ni har nafi yarda da umma kanta ita dake masifaffiya, a san masifa da bala'i kawai ta ajiye amma bata *ZAMBA CIKIN AMINCI* gaskiyar ta lakadan take faɗa komin ɗacin ta amma ita wacen Sakinar muguwar boye ce." Shiru AFREEN tayi tana yiwa Khairat kallon yaushe ta fara iya yiwa mutum sharri yaushe wannan halin zargin jama'a ya sameta ko dai duk auren ne ya sata ta zare haka. Kamar Khairat ta san mi take tunani tace "Ban zare ba lafiya ta lau yarinyar, sanar dake gaskiya tace nayi, ki yarda dani tanti babu abinda ta aje sai *ZAMBA CIKIN AMINCI* dan wallahi ba ƙaramar munafuka ba ce gaya maki nake, ba son mu take ba kawai tana nunawa ne, indan baki yarda dani ba ki gwada tambayar wataran miye an fanin zumuwar da take baki kullum, ke kuma da bakida hankali kin bi kin sakankance wai ga wada akeso ko dai ake ƙi ba, da turaran da take baki kinayi tana cutar dake amma kin kasa gane hankan." Da sauri AFREEN ta ɗago ta kalli Khairat tana mamakin yanda akayi Khairat duk tasan haka itada ko maman bata taɓa faɗa ba amma Khairat. Wani ɗan ƙaramin murmushi Khairat tayi sannan tace "Kina mamaki ina nasani ko alors que toi tu n'a rien dit à personne (ke kuma gashi baki faɗawa kowa ba) to bari na faɗa maki hali na idan kin manta ki sani duk abinda na saka ma ido to sai na nemo cikin da wajen shi ina ga ki manta ko wacece Khairat shiyasa kike mamakin abu nan da ya fito daga baki na, to ki ma daina mamaki komai zan iya bincikowa inda har na damu dashi ko kin manta abinda na karanta ne, amma ki samu ki ɗanyi bincike kema zaki gano abinda na gano, waini bana ce tayin wani abu ba, amma nasan da akwai *ZAMBA CIKIN AMINCI* a lamarin ta kuma nasan watarana zaki ce na faɗa maki." Shiru dai har yanzu AFREEN ta kasa cewa komai dan abun yayi mugun ɗaure mata kai sai can ta ɗan nisa tace "Anty bari naje na ɗan watsa ruwa sai na fito muje jardin (garden) muyi fira ko da yake ashe ke baki fita zan dai dawo." Tace "To ƴar ƙanwata sai kin dawo." Ba tare da tace mata komai ba ta fice daga ɗakin direct ɗakin maman tayi tana shiga ta tardo tana saka kayan da aka goge ma ta a wardrobe tayi sallama ta ƙarasa shiga ɗakin tace maman sannu da hutawa." Maman wada tun shigowar AFREEN da tayi sallama ta ɗago tana kallon ta tace "Yawa AFREEN daga ina kike ɗazun na tura Zeinab kiranki tace man baki nan." "Eh wallahi maman ina ɗakin anty Khairat." "Ah ok to shikenan mi Khairat kin keyi yanzun." "Babu abinda take na bari ta a zaune amma ta yiyu yanzu ta shiga wanka tunda naga gommage ɗin dake ga jikinta ya bushe, maman bari na tayaki mayar da kayan." AFREEN ta faɗa tare da tashi daga saman gadon ta nufi mahaifiyar ta." Aa barshi AFREEN jeki ki huta kinji ko." "Maman ba fa abinda nayi bare ace inda na gajiya naje na huta." Eh duk da haka ki zauna ki huta ke da kullum ba kison kina hutawa sedai aiki ai rai nason hutu, yanzu kam na hutar dake ɗanewar ki kan gado ki kwanta ki ɗan huta koda kaɗan ne, kin ga ma na kusa ƙarasawa kingin abu huɗu na ƙarasa gyaran." AFREEN tace "To shikenan maman bari naje nayi wanka sai na zauna na huta." AFREEN ta faɗa ta na ƙoƙarin miƙewa ta bar ɗakin mahaifiyar ta. Maman tace "Aa ba sai kin koma ɗakinki ba shiga toillet ɗin na kiyi wankan ki tunda kina da kaya a nan sai ka canza idan kin gama shirya wa sai ki kwanta ki huta." "To maman." AFREEN ta faɗa tare da tashi ta nufi toillet ɗin." Ba wani jimawa tayi a toillet ɗin ba ta fito ta yi shirin ta cikin wata doguwar riga mara nauhi tare da ɗanewa saman bed ɗin mahaifiyar ta ta yi kwancin ta ba tare da ɓata lokaci ba bacci yayi awon gaba da ita. Ali na gama wanka ya shirya tsaf ya fito daga ɗakin ya nufi na AFREED ya shiga tare da sallama, ya na zaune bakin bed ɗin ya faɗa duniyar tunani dan bai ma san shigowar Ali ba har saida ya dafa shi, da sauri ya ɗago yace "Broh har ka fito?" Ba tare da Ali yace masa komai ba ya nemi guri kusa dashi ya zauna sannan yace "Broh ka fah san doctor ya hana ka yawan tunanin amma kaƙi daina hankan zai iya ƙara saka maka wani ciwon dan Allah ka daina ya ƙa faɗa man abinda ke yawan ɗaga maka hankali har haka sai mu nemi mafita tare da taimakon Ubangiji sai kaga komai ya daidai ta." Wata naunauyar ajiyar zuciya AFREED ya sauke tare da juyowa yana kallon Ali sannan yace "Wallahi broh ina cikin matsala ban ma san daga ina zan fara faɗa maka abinda ke damuna ba." Ali yace "Fara daga inda ya dace ɗan uwa." AFREED ya ƙara sauke wata ajiyar zuciyar sannan yace "Broh ina wata yarinya wada sunanta yake kaman ce ceniya da nawa ana ce mata AFREEN idan ba zaka manta ba ita ce ta buɗe taro a lokacin saukar su Khadijah, wata ƴar doguwa ba zakace mata fara ba kuma ba zaka ce mata baƙa ba teint café au lait dai (chocolat color ) Kai tana da ma haske dan gaskiya ga wani ba za'a cema chocolat color, ba zaka iya cewa ma ba fara bace don gaskiya teint (fatar ta) ɗin ta tana da fari se dai ba can ba, ban san ko ka gane wada nake nufi ba, don ita ce damuwa ta." Ali ya ƙurawa AFREED ido yana kallon sa yace "To ina jin ka na gane yarinyar wata mai zazzaƙa muryar kamar sucre yarinyar ta birgeni sosai ai seda nayi enregistrer (saved) ɗin muryar ta lokacin da tana karatun Alkur'ani, amma kai miye haɗin ka da ita da har ta zame maka matsala?" AFREED yace "Babba matsala ma kuwa saboda ba a nan muka fara haɗuwa da ita ba don mu san juna tun kamin zuwa gun saukar nan, nan dai AFREED ya kwashe tun farkon haɗuwar da AFREEN ya faɗa masa har abinda ya keji game da ita da duk abinda ke saka shi cikin halin rashin lafiya duk a kanta babu dai abinda ya ɓoyewa Ali komai ya sanar da shi. Ali da AFREED ya gama zayana masa komai da komai ya tsaya yana nazarin ɗan uwan nasa na kusan minti biyu, kuma daga bisani ko mi ya tuna sai ya kwashe da dariya yana tayi sosai har saida ya yayi mai isar sa." A lokacin har ya ƙula da AFREED ya ɓata ran shi sannan ya miƙe ya bar gun ya koma wajen window yana kallon farfajiyar gidan, Ali na ganin haka ya tashi ya nufi gun AFREED yana gumtse dariya sa yace "Broh dan Allah yi hakuri zo zauna muyi magana." A ɗan fusace AFREED yace "Naƙi na zauna ɗin ya zan faɗa maka matsala ta, amma ka zauna kana min dariya yau ga mai abun dariya naga da wasa ma ka ɗauki lamarin." Ali yace "Wallahi ba haka bane ɗan uwa ke ɗin ne ka ban dariya, amma kayi hakuri zo muje muyi shawara samun yanda zamu bulowa wannan lamari a sauƙaƙe, komai zai daidaita da ka faɗa man da yuri da duk haka bata faru ba, amma insha Allahu yanzu komai ya zo ƙarshe." AFREED naji abinda Ali ya faɗa ya bisa suka koma bakin gadon suka zauna, Ali ya ɗan saki wani ƙayatacen murmushi sannan yace "An zo wajen wai yaushe ɗan uwana ya faɗa soyayya banida labari har ta kai ga yi masa mummunan kamu haka, har take neman sa ɗan uwana ya rasa ranshi, wallahi yaya AFREED ban taɓa tunanin zaka so wata ƴa mace ba, har soyayyar ta tayi maka wannan kamun wa na kama, gaskiya a jinjina wa wannan yarinya da tayi nasarar sace min zuciyar ɗan uwa na abinda ban taɓa tunani ba, mutuman da ko kallon mace baiyi bare har a saran zai mata magana, yanda ƴan matan Niamey ke rububun ka amma basuyi nasarar samuka sai ƴar maraɗi, kai gaskiya matan maraɗi sun ciri tuta ya kamata a jinjina masu." AFREED yace "Kaga nifa ba dan kayimam iskanci bane na faɗa maka idan kana bani shawara da zata anfane ni to ka faɗa man ni banson iskanci, ko faɗawa soyayya haramun ne ko kuwa ni kaɗaine hakan ta fara faruwa da ni ne." Ali na ganin ransa ya ɓace yace "Haba yi hakuri broh ba wai dan wani abu bane na faɗi haka ba kawai kaban mamaki ne par surprise na ji zancen (a bazata) dole na ce haka, amma ina da wata mafita idan ta maka to matsalar nan ta kau." AFREED ya wani haɗe fuskar kamar ba yason jin mafitar a dakile yana wani shan magani yace "Ina jinka." Murmushi Ali yayi yace "To saki fuskar man kana wani yimin yanga kamar baka son jin abinda zance." Shidai AFREED bai ce masa komai basai fido wayar sa da yayi ya shiga dan nawa kamar bai sauranran shi." Ali ya ƙara yi wani murmushi dan yasan halin mutum nashi ba tanka masa ba zai yi sannan yace "Mafitar da na samu itace zan shiga in fita in sama maka number ta daga nan sauran ya rage naka sai kasan abin yi." Ɗan ɗagowa AFREED yayi daga kallon wayar sa ya dubi Ali da yaga Ali shi yake kallon sai yayi saurin maida idon sa ga wayarsa dan kar Ali yaga damar sa, amma a zuciyarsa sai da ya furta "Alhamdulilah." Ali ya yi murmushi yace "Hum ba ma ko zaka godeman ba to na fasa nemo da number tata sai kayi ai." Ali na faɗar haka ya tashi ya fice daga ɗakin." AFREED ya bi bayan sa da kallo har sai da ya fita, yana ganin Ali ya rufo masa ƙofar yace "Allah nagode ma nan ba da jimawa ba zan fara waya da farin ciki na, broh ai nasan ka faɗa ne zaka nemo man number ta alhamdulilah." Shi kuwa Ali ya na fita ya nufi ɗakin sa ya zauna ya na tunani ta ina zai fara neman number AFREEN, can cikin tunanin ya tuna ashe makarantar su ɗaya da Khadijah, kawai ba tare da ɓata lokaci ba ya fido wayar sa da ga aljihu ya nemo number Khadijah yayi lancé appelle (ya turo kira) tare da karawa a kunne, sai da kiran ya kusan tsinkewa a ka ɗaga wayar tare da sallama. Ali ya amsa sallama sannan yace "Hubby yau ko dai laifi nayi ban sani ba naga ba'a ma son daukan kiran nawa." Murmushi mai sauti Khadijah tayi sannan tace "Wallahi Hubby ba haka bane bana kusa da wayar ne na shiga wanka ina fitowa na tarda wayar tana ruri da ba ma zan ɗaga ba, kawai idona ya sauka akan sunan da nasaka maka ne ke yawo saman screen ɗin sai nayi saurin ɗaga dan kada ta katse." Ali yace "Ah kane ya faru to shikenan na maki uzuri ya kike ya gida ya su tanti da tonton injin dai kowa lafiya?" "Lafiya lau wallahi, ya su momy da yaya AFREED dan yan biyu kuma?" Yace "Kowa lafiya, ya karatu?" Tace "Alhamdulilah." Ali ya ɗan nisa sannan yace "To madala Allah ya taimaka, kina jina Khadijah wani ɗan aiki ne zan sakaki dan Allah in babu damuwa?" "Lah Hubby dan zaka sakani aiki har sai kace dan Allah mi zaka sakani na ƙasa yi in dai ba saɓon Allah ba ne, ai ko babu komai a tsakanin mu kai ɗin yaya na ne kana da ikon sakani ko wane irin aiki ne kuma nayi ko inaso ko ba naso." "Hakane hubby amma duk da haka ya kamata na fara tambayar ko kina da dama ko ai sa c'est normal?" "Hakane kuma to ina jinka miye aikin da zan yi ɗin?" Saida Ali ya ƙara gyara zaman wayar a kunanan sa sannan yace "Number wata ƴar islamiyyar ku nake so ki samo min a na cema ta AFREEN wata ƴar fara doguwa farin nata dai ba sosai ba wada ta fara karatun a ranar saukar ku." Fuskar Khadijah da ke ɗauke da murmushi ta koma kamar bata taɓa dariya ba cike da game fuska tace "banga ne taba kuma miye zakayi da number ta, sannan karasa wanda zaka saka wannan aikin sai dan baka ɗauke ni da mahimmanci ba." Murmushi Ali yayi yana jin daɗi wai saboda shi ne Khadijah ke ta wannan shan maganin alhamdulilah shima an fara kishin sa, daga bisani sai yace "Kwantar da hankali hubby ki yarda dani babu abinda zanyi da number ta ina da ke kuma mi zai kaini kula wata kawai inada buƙatar number ne daga baya zan sanar maki dalilin neman number nata kawai ki taimaka ki nema man idan kikayi hankan kamar kin ceto rayuwa ne." "To shikenan hubby na gane ta ai dama da gangan nace ban gane ta ba zan nemo number ta insha Allahu sabida ƙanwata ƙawata tace." "Masha Allah kinga abin ya zo da sauƙi, to sai naji ki gaida su tanti." "Za su ji insha Allah." Daga nan Ali ya kashe kiran sannan Khadijah ta ajiye wayar ta na murmushi ta nufi wardrobe dan fitar da kayan da zata saka." Bayan kwana biyun da Ali ya yi kiran Khadijah don ta nema masa number AFREEN, sai gata ran cikon kwana na uku ta kira shi ringing biyu ya ɗaga tare da sallama yace "Hubby barka ki da warhaka da kin yuni lafiya?" Tace "Lafiya lau ina yuni?" Yace "alhamdulilah ya gida?" "Gida lafiyar sa lau." "To madala ina aikin da na saka ki komai ya daidaita ko kuwa?" Tace "Komai normal hubby aiki na ƙarasa kiran dana maka kenan na baka résultat ɗin aikin." Ali ya waro ido kamar tana ganin shi sannan yace "Da sauri haka hubby injin dai baki ce wani ke buƙatar number ba." Tace "Haba hubby kamar banda hankali, kamar kuma ba mace ba, kawai sai na fito fili na tunawa kai na asiri, to da nayi haka ai da yanzu ban samo lamba ba dan ita da kanta Zeinab ƙanwar ta ɗin bata san na ɗauko number a wayar ta ba." Ali yace "To ya akayi ki ɗauke ta ba tare da ta saniba." Murmushi Khadijah tayi sannan tace "Ƙarɓa wayar ta nayi nace ƙawata bari naka sunan da kika saka min a matsayin na ƙawar ki wace baki da kamar ta a islamiyyar nan, sai Zeinab ɗin tace to shikenan bari na baki ƙawata a tunanin ki mi zan saka, kawai sai ta miƙon man wayar na shiga nayi ta duba numbobin mutane banga inda ta saka sunan AFREEN ba, amma sanin yanda ta ke ƙaunar AFREEN ɗin yasa wani suna da nagani ta saka ma deuxième mère (my second Mom) ya ɗaukar man da hankali sosai sai natsa akan sa na tambayeta nace wacce kuma wada kike ji sosai ki ka saka ma wannan sunan, tana murmushi tace man anty AFREEN ce daga nan nayi hamdala sannan nace a lallai yanzu nayar kuna jin juna sosai, tace sosai kuwa ban san ya zan kwatanta yanda nake son ta ba wallahi ni banda kamar ta duk cikin yaye na, ba tare da ta lura ba na hardace number a kaina, sai nayi mata sai anjima nayi tafiya ta harda tambayar naga sunan da ta sakamin ɗin nace mata eh, ina gusawa daga gun ta na saka number a phone ɗin na na saving ɗin ya dan kar na manta." Ali ya saki murmushi yace "Woow very nice shiyasa nake alfahari dake hubby gaskiya kinyi taimako, ban zan tamɓa mantawa da wannan ba yanzu ki turoman number ta whatsapp yanzu yanzu ina jiranki nagode sosai hubby." Ba tare da ya jiran jin abinda zata ce ba ya katse kiran. Ba musu Khadijah ta tura masa number daidai ya kuna data saƙon number ya shigo, buɗe saƙon yayi tare yi mata reply kamar haka "Nagode sosai Allah saka da alkairi kinyi ƙoƙarin sosai." sai ya tura sannan ya sake tura mata sticker da aka rubuta i love you sai kawai ya kashe data ya nufi toillet danyin wanka saida ya ɗauki kusan min ashirin kamin yake fito ya shirya cikin wasu haɗaɗun ƙananun kaya masu mugun kyau kuma su ka zauna a jikin sa tsaf kamar dan shi a kayi kayan, sannan ya feshe jikin da daɗaɗan turaruka masu mugun kamshi a take ya fara zuba uban kamshi kamar yayi wanka da tekun turare sannan ya fito daga nashi ɗakin yana ta sakin wani haɗaɗen murmushi kamar wanda akayiwa albishirin shiga aljanna, don yau jin sa yake a cikin wani irin farin cikin mara musultuwa, saboda gani yake ya samo maganin ciwon ɗan uwansa zai warke har abada. Ɗakin AFREED Ali ya nufa kai tsaye ya buɗe ƙofa ya shiga tare da yin wata ƴar siririyar sallama AFREED dake zaune saman wata haɗaɗiyar kujera dake ɗakin kansa a duƙe da ya dafe a hannuwan sa ya rasa abinda ke masa ɗadi saboda tunanin AFREEN ya amsa masa sallamar ba tare da ya ɗago ba. Kusan minti biyu Ali ya yi a tsaye ya nazarin ɗan uwan na sa da bisani sai ya ƙarasa kusa AFREED ɗin ya zauna tare da dafa shi, sai a lokacin ya ɗago kansa ya sauke idonsa da suka yi ja kamar gauta cikin na Ali, da sauri Ali ya janye hannunsa da ke saman kafaɗar AFREED tare da ɗan gusawa kaɗan daga kusa dashi a ɗan tsora ce yace "Broh lafiyar ka mi ya sami idon ka kuma komi yake damun ka yanzun, ku ma dan Allah faɗa man kada kasa hankali na tashi." Ɗan riƙo hannun sa AFREED ya yi sannan ya koma kallon sa yace "Wallahi broh ina cikin matsala nakasa jure rashin yarinya nan, yanda nake ji a cikin zuciyata da yanda son ta ke bin duk sasan jikina yana ratsa jinin jiki na da ilahirin jikina baki ɗaya ya hanani sukuni, gani nake inda banje Maraɗi na nemo ta ba na faɗa mata abinda ke raina zan iya rasa rai na wallahi." kawai sai ga hawaye na gudu a saman fuskar AFREED. Da mugun mamaki Ali ke kallon AFREED da wani irin tausayin sa da ya ɗarsu a zuciyarsa wai yau AFREED ne ke zubar da kwala sabida wata ɗiya mace, macen wacce bata masan yanayi ba, shida yasan da ko kallon mace baiyi bare har yace yana son ta har soyayyar ta ta kaishi ga haka Allah kenan mai yanda yaso bai taɓa tunanin haka ga AFREED ba. Bai ƙarasa mamakin saba yaji AFREED na cewa "Ka taimaka min ɗan uwa dan gaskiya nakasa jurewa har ma na yanke shawara zuwa Maraɗi gobe Insha Allahu dan nemo farin cikin rai na." Da sauri Ali yace "Ai ba se takai ga haka ba ka kwantar da hankalin ka insha Allahu AFREEN taka ce, kai ko yanzu kake so masa zaka iya jin muryar ta dan kuwa har na riga da na nemo maka number ta, saboda ni ma ba jure ganin ka a cikin wannan halin wallahi yanzu komai zai daidaita Insha Allahu." Wani irin farin cikin ne ya mamaye zuciyar AFREED da har bai san lokacin da ya kama Ali ya rungume ba, ya sakin murmushi tare da hawayen farin ciki yace "ba nida kamar ka ɗan uwa ba zani taɓa samun farin ciki mai ɗaurewa ba in babu kai, ni ban masan wane irin godiya zan maka ba, mi ka keso nayi maka da zai sanya ka farin ciki ka gama min komai a rayuwa Allah ya biyaka da mafificin alkairi ya sada ka da aljannar fidaoussi. Ali yace "Ni sakeni dan Allah miye na wani yi min godiya ne, ka nagani ina iya farin ciki ne idan kai baka tare da shi, ni kawai ka ɗauki number ta na baka ka samu ka kirata tun kan lokaci ya ƙure maka, ka san ƴan mata ba su zama babu saurayi to idan ka bari wani ya riga ka shiga zuciyata, to fa sunan ka sorry, abinda zaka min naji daɗi kuwa shine kayi gaggawar saka ma yarinyar nan soyayyar ka mai tsananin kamar yanda itama ta yi ƙoƙarin wajen saka tata a zuciyarka, koda kuwa ta nada wanda take so inason kayi ƙoƙarin mayar da soyayyar ta sa a kanka har kazo ka ci nasarar aurenta, idan kayi to ni ka gama yi man komai wallah." "To shikenan Ali naji saka man number a nan," AFREED ya faɗa ya na mai miƙa masa waya sa cike da farin ciki. Karɓa Ali yayi ya saka number sannan ya tashi ya fice ya na mai cewa nan da kwana biyu inji dadaɗan labari." Ali na fita AFREED ya saki wani haɗaɗen murmushi tare da mai da gaba gabas ya yiwa Ubangiji sujada ta nuna godiyar sa a garesa, sannan ya miƙe ya nufi toillet yana farin ciki kamar ba shine ya gama hawaye yanzu ba." Yana fitowa daga wanka ya tsantsara shiri wanda rabon da da yin sa har ya manta kai kace gun AFREEN ɗin zai je zance ya gama feshe jikin da daɗaɗan turaruka ya fito daga ɓangaren na su gaba ɗaya ya nufi garden inda iskan sanyin maraice ke bugawa, yana ida shiga garden ɗin ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun dake gun, tareda fido wayar sa don kiran AFREEN har ya tura kiran kuma da sauri kamin kiran ya shiga sai ya katse kiran, yana tunanin to idan ya kirata mi zai ce mata shi da ba soyayya ya ɓayi ba, hasali ko mace bai taɓa yiwa magana inba secretary ɗin sa in ka fida iyayen sa mata da kuma ƙananan sa, ya na cikin kuma wannan tunanin, saikuma gabansa ya faɗi dalilin tuna cewa ya taɓa ganin AFREED da saurayin ta wajen saukar da su kayi kada a ce ma tayi aure ko da yake da Ali ya samo man labari inda tayi sai kuma yace "Zanyi ko ƙoƙarin saka soyayyata a zuciyarta koda kuwa ta nada wani ai ita allura ce cikin ruwa mai rabo kan samu, kuma in Allah ya yarda malaki na ce shiyasa ma par coïncidence sunayan mu suke shigin na junan mu. Can AFREED yayi tunanin bari ya fara mata magana ta whatsapp idan tana yi, ai ko take yanke ya shiga whatsapp ɗin sa ya shiga neman sunan da ya sakan mata mai taken ma femme insha Allah (my wife) yana dubawa kam yaga sunanta ya fito a whatsapp kawai ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗaga mata hannu tare da rubuta mata salut (hello) sai ya tura cikin sa'a kuma sai a ka yi katarin tana en ligne (online). *Kashi nayi kokarin wajen ganin na faranta maku har nayi page uku ki da jina kuma sai bayan sallah in da rai da lafiya insha Allahu* 😘😘😘 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ *_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_* *Page* : 51 & 52 Can AFREED yayi tunanin bari ya fara mata magana ta whatsapp idan tana yi, ai ko take yanke ya shiga whatsapp ɗin sa ya shiga neman sunan da ya sakan mata mai taken ma femme insha Allah (my wife) yana dubawa kam yaga sunanta ya fito a whatsapp kawai ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗaga mata hannu tare da rubuta mata salut (hello) sai ya tura cikin sa'a kuma sai a ka yi katarin tana en ligne (online). AFREEN na cikin chatting da kawayenta a cikin wani group ɗin su da suke tura abubuwan ƙaruwa na Musulunci sai kawai taga alamun saƙo ya shigo da wata bakuwar number da bata sani ba, sai ta fita daga group ɗin ta ƙurawa number ido na kusan minti 3, sai ta sauke ajiyar zuciya tare de cewa can cikin ƙansan zuciyarta "Waye keda wannan number kadai KAMAL ne Idan kuwa shine mi zai ce man kai ba ma shi bane don ba number sa bace, to waye?" AFREEN ta tambayi kanta. Da har zata huce kuma sai ta buɗe saƙon ta karanta yafi sau uku sannan tayi ta tunanin tashare ko wanene ko kuwa ta mayar danjin ko waye, kawai sai ta yanke shawarar mayar masa da sakon sai ta rubuta masa cewa "salut Xava?" AFREED nagani ta maido sefa yaji wani farin ciki ya sabko masa a zuciya, bata tare da ɓata lokaci ba ya mayar mata da amsa ta gaisuwa nan dai suka gaisa sannan AFREEN tace "A qui j'ai l'honneur (dawa nake magana)." Ba tare da wani noke noke ba AFREED ya sanar mata ko shi wanene da kuma inda yasanta sai dai bai faɗa mata matsayin sa ba da kuma aikin da yake. Nan AFREEN ta sheda shi sannan tayi mamakin inda ya samu number ta, amma bata tambaye shi ba, nan suka ƙara gaisawa, nan dai ya nemi alfarma ta bashi izinin kiranta anjima akwai maganar da yake so zai gayamata, da har taso taki amincewa kawai sai taji ta na so jin abinda zai faɗa ɗin se kawai tace "Allah ya kaimu" Sannan sukayi sallama AFREEN ta daɗe a zaune ta na tunanin ina ya samu number ta kuma miye abinda yake son faɗa mata, kamin ta tashi ta nufi douche (bathroom) sabida kiraye kirayan sallah magarib da taji an fara ta na shiga ta dauro alwala ta fito ta shimfida darduma ta tayar da sallah. AFREED na jin AFREEN ta amince da ya kirata hada ɗan tsalle yayi sannan ya nufi ɗakin shi shima ya dauro alwala ya fito a hanya ya haɗu da Ali suka jera suka tafi masallacin a tare. Wajen ƙarfe goma na dare AFREEN na kwance a saman makeken gadon ta idonta a lumshe kamar mai bacci amma ba bacci take ba saboda bacci ya gagara daukar ta kawai tana kwance tana jiran kiran da AFREED zai mata bata san miyasa ba amma taji tana mugun son ji abinda zai faɗa mata, saboda tana tunowa da kiran nashi kawai sai taji gaban ta ya faɗi shiyasa ta matsu ya kira amma gashi kuma har yanzu bai kira ba, bata ƙarasa tunanin ta ba ƙarar wayar ta ya katse mata tunani da sauri ta tashi zaune ta ɗauki wayar ta riƙe a hannun tare da kurawa number dake yawo akan screen ɗin, wayar har ta katse bata dauka ba, bata ankara ba taji wayar ta sake ɗaukar ruri tana gab da tsinke ta daga kiran tare da kara wayar a kunne, kamin takai ga yin sallama har na cikin wayar ya riga ta da cewa "Amincin Allah ya tabbata a gareki." Cikin Wata irin sanyayar muryar da batasan tanada ita ba ta buɗe baki cike da faɗuwar gaba da batasan dalilin shi ba tace "Kaima amincin Allah ya tabbata a gare ka," sannan tace "Ina Yuni." Daga cikin wayar AFREED ya amsa da "Godiya nake cutie da fatan kin yuni cikin ƙoshin lafiya da farin ciki?" "Alhamdulilah." AFREEN ta faɗa a takaice AFREED yace "To masha Allah kamar yanda na sanar dake na kiraki ne don muyi wata magana da ta shafe ni kuma ta shafe ki, nasan zaki iya cewa hadake maganar ta shafa saboda ba wani sanin juna muka yi ba hasali maganar da ta taɓa shiga tsakani na dake bata huce biyu ko uku amma kuma Hakan ba abin mamaki dan haka ina buƙatar hankalin ki akan maganar nan." AFREEN ta sauke wata yar gajeriyar ajiyar zuciya sannan tace "Ba damuwa ina sauraren ka." Murmushi AFREED ya saki kamar AFREEN na gabansa sannan yace "Ba wani abu bane nakeso sanar dake illa soyayyar ki da ta mani shigar bazata ba tare da na shirya hakan ba ta mamaye ko wane illahirin jijiyoyin da ke cikin jikin na ta ratsa ɓargo da hanta tabi ta kanainaye min zuciya ta na kasa sukuni AFREEN bansan ya zan misulta maki irin ƙaunar da nake maki ba, sonki ya mamaye duk wani jini dake cikin jiki na, dan Allah AFREEN ki taimaka ki karɓi soyayya ta dan Allah wallahi tunda na fara ganin ki na kasa sukuni zuciya ta kasa hutawa kullum ina cikin tunanin ki." AFREED na kai wannan ya sauke wata irin nauyayyar ajiyar zuciya har sai da AFREEN tajiwo hakan a cikin zuciyarsa ya ke cewa, Allah na godema da ka bani courage ɗin bayyana soyayya ta ka wannan baiwa taka saura amincewar ta Allah ka samin hannun ta amince dani." AFREEN wada tunda AFREED ya fara magana gaban ta ya yawaita faɗuwa da sauri da sauri dan idan a gaban ta maka ke zaka iya jiyo sautin bugawar zuciyar ta, hakan yasa ta kasa koda ƙwaƙwaren motsi haka ta kasa cewa komai don sai juya maganar take a ƙwaƙwalwar ta gashi bakinta yayi mata nauyi ta kasa furta koda kalma ɗaya ce kuma idan ma tace zata buɗe baki tayi magana mi zata ce mashi." Jin shiru yayi yawa AFREED ya koma cewa "Dan Allah AFREEN ki daure kiyimin magana ko zuciya ta zata samu sallama please ki taimaka min." Nan shiru AFREEN bata ce komai don tsakanin ta da Allah bakin ta ya mata nauyi ta kasa buɗe shi tayi magana ji take ma bakin ba a jinkin ta yake ba, dan haka ta koma yin shiru saboda idan har ta mayi jarumta buɗe baki tayi magana to tasan da kuka ne zai kubce mata, kawai sai ta koma yin shiru. Ganin haka yasa AFREED ƙara duba wayar don ganin ko ta katse kiran ne amma mi sai yaga ba ta katse kiran ba da damuwa a fuskar sa ya mayar da wayar a kunnen sa sannan yace "Allo AFREEN kinaji na ki tausaya min kimin magana in har baso kike rayuwa ta ta kare daga yau ba dan Allah kiyi min magana koda ba zata sakani farin ciki ba, dan bansan ko kinada wanda kike so ba idan haka ta kasance ba zan sa dole sai kin so ni ba, amma ki taimaka yanzun kice wani abu s'il te plaît AFREEN." Ya buɗe baki zai kara cewa wani abun kawai sai yaji ta fashe masa da kuka ai kuwa hankali AFREED in yafi dubu to ya tashi a firgice yace "Inna lilahi wa inna alaihi raji'un AFREEN ki yafe man ban kiraki dan in takura maki ba har nakai ga sakaki kuka nayi ne dan sanar dake sirrin zuciya ta ɗan Allah kiyi hakuri in har abinda na faɗa ya ɓata maki rai, ki taimaki zuciya ta kiyi shuri sai na katse kiran idan har na kashe tare da sanin na barki cikin wannan halin, bazan taɓa iya samun sukuni ba dan ki tausaya man bazan kara takuraki ba idan har bakison magana dani." Da sanu a hankali ta fara rage kukan har ta ta daina baki ɗaya yanajin tayi shiru ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi sannan yace "To AFREEN Nagode sai da safe yi hakuri da takuraki da nayi hakan ba zai sake faruwa ba , ki kula da kanki." Sai ya katse kiran ba tare da ya jira jin abinda zata ce ba sabida ya ga alamun ba zata ce komi ɗin ba cike da damuwa ya faɗa kan gadon sa ya kwanta tare da lumshe idonsa yanajin yanda zuciyarsa ke harbawa da sauri da sauri, tare da addu'ar neman sassauci wajen Ubangiji game da abinda yake ji a game da ita, ya kai minti biyar a haka kamin ya buɗe ido sa da suka masa jajir don damuwa da radin da zuciyar sa ke masa. Ƙara lumshe idon sa yayi da niyyar yin bacci amma ina bacci ya ƙasa zuwa haka dai ha kusan ƙarfe ɗayan dare AFREED ya kasa rumtsawa kawai sai ya tashi ya nufi toillet ya dauro alwala ya fito, shimfiɗa darduma yayi ya fara jero nafilfili ya na kai wa Allah kukan sa cikin ikon Allah ya samu sasauci sosai daga abinda ya ke ji a zuciya sa, shine bai samu bacci sai wajen ƙarfe 4:00 sannan bacci ɓarawo yayi awon gaba dashi, kuma cikin ƙananan lokacin kiran sallah asuba ya farakar dashi cike da magagi bacci dake cinsa ya tashi ya shiga bayi ya watso ruwa a gaggauce saboda yaji ana shirin tayar da sallah ya na fitowa ya zura jalabiyar sa fara ya nufi masallaci, a ƙa'idar AFREED idan an idar da sallah asuba bai baro masallaci sai rana ta fito, amma ana gama sallah tare da yin adu'oin sa na bayan sallama daga sallah kawai ya taso yayi tafiyar sa cikin gida ba tare da yayiwa ko da dady ina kwana ba, hasali ma bai ma lura dasu ba har Ali dake kusa dashi, bacci kawai yake son yaje yayi, da mamaki Ali ya bishi da kallo, a zuciyar sa yace "To shi wancan lafiya kuwa ko dai duk soyayyar ce?" Murmushi kawai Ali yayi tare da girgiza kai yace "Sabon shiga dole ne ya kasa controlling ɗin kasa." Sannan ya juya ya ci gaba da addu'ar sa. AFREED na shiga ɗakin sa ya faɗa saman gadon sa ya shiga rankon bacci shi ne bai farka ba sai wajen 11 na rana yana tashi yayi miƙa tare da salati sannan ya faɗa toillet ya yi wanka ya fito ya shirya cikin shirin sa na tafiya office yayi kyau sosai saboda irin masu jikin nan ne wanda komi ka saka ya yi ma kyau, fitowa yayi a gaggauce saboda yayi latin zuwa aiki gashi har sha biyu na rana ya kusa tunda yau juma'a sauka guda sukeyi sai sun kai har ƙarfe ɗaya da rabi na rana a office, da sauri ya shiga ɓangaren maman shi ya gaida ta sannan ya cema "Ali ya tashi su wuce office." Ali da yake a shirye shi kaɗai kawai yake jira ya miƙe ya nufi ƙofa shi ma ya biyo bayansa, Momy ha sun kai ƙofar falon Momy tace "Ba zaka ƙarya ba zaka fita." Yace Momy zanyi idan na dawo." "A'a wuce ko thé (🍵) ne kasha babu kyau fita ba'a ci komai ba." Ba musu ya nufi dinning inda Momy har ta riga sa kaiwa ta haɗa masa thé (🍵) ta miƙa masa ya ƙarɓa ya sha sannan ya fice daga falon wanda Ali har ya kai gun motar shi kaɗe yake jira yana fitowa garde corps (Bodyguard) dinsa suka miƙe tare da nufar motocin su don kowane group da motar sa su wajen goma sha biyar, a cikin kowace mota da mutun biyar a cikin ta sai mota da AFREED ke shiga shida Ali da direban sa a ƙala suna fita da mota huɗu ko biyar wataran har bakwai, da sauri suka shiga gaida sa, su sunyi tunanin yau Bama za'a je wajen aiki ba tunda sun ga rana tayi. Cikin ƙananan lokaci suka isa ma'aikatar tasu ana gama parking yayi saurin buɗe ma kansa ƙofar motar ya nufi ciki da sauri suma Bodyguard din suna ganin haka suka mara masa baya da sauri wanda shi Ali har ya riga da ya cin masa, haka kuma ya shige gabansa da sauri ya buɗe masa office ba tare da ya tsaya watawata ba ya faɗa office ɗin da sallama a bakin sa, direct kujerar zaman sa ya nufa ya zauna nan take, shi ma Ali ya nemi kun zaman sa ya zauna ya tsura masa ido bai ce masa komai ba dan yasan duk wannan saurin da yake dan yayi lati ne kuma gashi an kusa tashi, AFREED ya shiga duba file ɗin dake gabansa cikin kwanciyar hankali ya fara aikin da ya tarar masa saboda jimawa da ya yi bai je office ɗin ba, ciki minti 40 ya kammala komai da komai a sannan yakai hannun sa kan téléphone☎️ ɗin dake saman table ɗin ya dana kira, 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* *_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_* *Page :* 53 & 54 "Tana fara rigin aka ɗaga a takaice yace "Amina ki zo office ɗin nan yanzu." Bai jira jin abinda zata faɗa ba ya katse kiran tare da ƙara duba file ɗin dake riƙe da hannu sa. Ko minti biyu ba ayi ba da katse kiran sai gashi ta kwonkwosa Ali ya bata izinin shigowa sannan ta buɗe ƙofar ta shigo da sallama, duk kansu suka amsa sallamar amma sai dai shi AFREED in ba kusan sa kake ba ba zakaji ya amsa ba, sannan ta gaida shi ya amsa sabida da ya shigo yana sauri bata samu damar gaida shi (wato Amina secrétariat ɗin AFREED ce) Cike da ladabi ta ɗan gusa kusa dashi tare da yi kasa da kanta kaɗan tace "Yalaɓai gani." Ba tare da ya kalle ta ba ya mika mata file ɗin dake ga hannun sa ta karɓa sannan yace "kije bureau ɗin ministre (minister ) Aliyu ki kai masa kice injini, idan hali gobe nakeso ya dawo man dashi." "D'accord chef." Sannan ta juya ta fita a office ɗin, sai a wannan lokacin ya ɗago ya dubi Ali ya sakar masa murmushi sannan yace "Ɗan uwa mu koma gida na riga na kammala abinda ya kawo ni." Murmushi shi ma Ali ya mayar kamin yace "To muje ai naga yi baka da dama shiyasa ban takaka ba har ka ida." AFREED ya yi murmushi yace "Wallahi kuwa amma yanzu tunda na ida ai shikenan." Daga haka suka miƙe suka nufi kofa suka fice daga office ɗin basu tsaya ko'ina ba sai gida. Ɓangaren AFREEN kuwa ta kasa gane kanta saboda tunda safiyar Allah ta waye take ta riƙon wayar ta ko zata ji AFREED ya kira amma shiru, haka rashin kiran nasa ya dame ta har zata zauna ta na tunanin yaye inta shi da ta damu dan bai kira ba daga fara kiran ta jiya, sosai hakan ya bata mamaki, amma kuma sai ta basar AFREEN har ta fida rai da AFREED zai kirata sai ga kiran nashi ya shigo wajen ƙarfe 4 na yamma bayan sallah la'asar waya na ta rigin tana kallo bata ɗaga ba kamar dai ba kiran take jira ba, sai ga kira na biyu shima yana gab da katse wa ta ɗaga tare da yin sallama AFREED najin ta ɗaga saida ya sauke wata irin ajiyar zuciya mai sauti har sai da taji dan shi ya ma fida rai da zata ɗaga. Amsa mata sallama yayi, kamin ya koma cewa wani abu tace "Ina yuni?" Wani farin ciki ne AFREED yaji ya luluɓe don kawai sai yaji yau ya kira cikin sa'a sabida kamar yaji maganar ta cikin sakin fuska, saida ya saki murmushi kamin yace "Lafiya klau" da fatan kin yuni lafiya kuma kina cikin koshin lafiya?" Ƙasa ƙasa ta amsa da "Lafiya lau" Yace "Ya gida ya su maman da kowa da kowa" Ta amsa da "Alhamdulilah" Nan dai suka ɗauki kusan minti biyar bawanda ya ƙara cewa komai amma zuciya AFREED sai bugawa take da ƙarfi fat fat fat yana tsoron ƙara mata maganar soyayyar sa ta ƙara fashe mashi da kuka can yayi ta maza yace "AFREEN dan Allah kiyi tunanin kan maganar da nayi maki jiya wallahi ina matuƙar sonki idan har kika ƙini zan shiga wani hali ki taimaka dan Allah." Kusan kamar second talatin bata ce komai bai sai kuma tace "Inshallah zanyi shawara a kai." "Zuwa yaushe zan samu amsar?" "Nan da sati haka, ko yayi kaɗan?" "Ki taimaka AFREEN wallahi sati ya yi min yawa ina laifin kice anjima." "Ina anjima ya yuri gaskiya, ai ko tunani ban fara a kai ba." To dan Allah ki tausaya wa rayuwa ta AFREEN kice gobe." Saida ta ɗauki kusan minti ɗaya batayi magana ba kuma sai tace "To shikenan amma goben sai da dadare in ka yarda." "To shikenan ba damuwa Allah ya kaimu goben lafiya." Ya samu saken biyu bai ce komai sai kuma yace "Dan Allah zan iya kiran yau da dadare mu ɗan yi fira?" Saida tayi ɗan jim kaɗan tace to ba laifi amma ba da dare ba sosai." "To shikenan an gama ranki ya daɗe yanda kika ce haka za'ayi sai na kiraki ɗin." Saida tayi ɗan gajeren murmushi sannan tace "To ba damuwa." "Ki gaida ƴan gidan." "Za su ji insha Allahu." Sannan ya katse kiran cike da farin ciki yaje ya samu Ali ya sanar masa yanda sukayi da ita nan take shima ya taya shi farin ciki." Kamar yanda yayi mata alƙawari dare bayi ba sosai ya kira ta bayan anyi sallah isha suka dan taɓa hira ta kusan minti arba'in sannan yayi mata saida safe, haka ga goben ma yayi mata kira uku kamin na dare, dare nayi ya kirata kamar yanda ya saba bayan anyi sallah isha, nan suka gaisa ya tambaye ta alƙawarin da tayi masa na bashi amsa yau, bata wani bata lokaci ba ta ce masa ta amince, farin ciki kamar ya kashe AFREED a ranar jiyake bai taɓa shiga farin ciki irin na wannan ranar ba nan suka shiga fira soyayya mai ratsa zuciyar masoya, da yake AFREED ba gwani bane wajen gayin kalaman soyayya tunda bai ta yi ba amma duk da haka ya ƙoƙarta sun sha soyayyar su harda dare yayi sosai sannan suka yiwa junansu sallama badan sun so ba, sai dan lokacin sallah dare da AFREEN keyi yayi, tunda ga wannan ranar soyayya mai tsanani ta shiga tsakani AFREEN da AFREED dan ko basu awa ɗaya basu ji muryar juna ba. Kwanci tashi babu wuya a wajen Ubangiji yau yakama saura kwana guda auren Khairat kuma yau ne dadyn AFREED da docter Inusa zasu zo Maraɗi dan su halarci ɗaurin auren diyar aminin su wato Alhaji sadisu da ake yi gobe misalin ƙarfe takwas na safe. Sun baro garin Niamey ƙarfe tara daidai amma da yake mota personnel ce ƙarfe huɗu nayi su na cikin garin maraɗi, a wani gida injiniya Sumana dake cikin anguwar Zaria, gidan ko ina a share a gyare kamar dai da mutane a ciki, ba su wani ɓata lokaci ba sukayi wanka suka huta, sai ga kiran Alhaji Sadisu ya shigo wayar injiniya Sumana yana tambayar su har yanzu basu ƙarso ba, yace masa su ji ma da ƙaraso wa dan sunyi har wanka sun huta, nan ya tambaye sa inda suke ya sanar da shi sannan Alhaji Sadisu ya ce gashinan zuwa ya ɗauko su zuwa gidan sa tare, da an riga da anyi abincin tarbar su bansu, ba tare da sunyi musu ba suka amince, kusan minti ashirin da gama wayar sai gashi yazo basu wani bata lokaci ba suka kule gidan tare da da shiga motar Alhaji Sadisu suka ɗauki hanyar gidan sa wani minti ashirin ɗin suka ɓata kamin suke isa gida, direct ɓangaren Alhajin suka nufa, suna shiga suka sauka saman mayan kujerun da ke falon daga nan suka ƙara gaisawa, sai ga uwan gidan suna shigowa da ɗaiɗaya suna gaisawa, nan fa aka fara servir ɗin su aka cika falon papa da kayan ciye ciye da lashe lashe kamar sunzo restaurant daga ƙarshe AFREEN ta shigo da sallama da juice 🥤 ɗin gwaba da yaji kayan haɗin sosai sai kamshi yake a hannun ta daga ji kasan zai yi ɗaɗin ɗanɗano, ciki shigar ta ta ƙaton hijabi har ƙasa tana shiga ta duka har ƙasa ta gaishe su da ladabi kan ta a duƙe." Kallo injiniya Sumana ya bita dashi sannan ya amsa gaisuwar ta, sannan AFREEN ta mike ta fice, tana fita injiniya ya kalli Alhaji Sadisu yace "Alhaji wannan ma yarinyar Arahamat ce ko saboda ga kama nan masha Allah kyakkyawa da ita har ta fi maman ta, se kuma ta ɗauko kalar fatar ka ba tayi hasken mahaifiyar ta din ba, ni ina tunanin daga Khairat Arahamat bata da wata yarinyar sai in maza ashe akwai wannan." Murmushi papa yayi kamin yace wani abun docter Inusa yace "AFREEN ba ɗiyar jannah kenan ai yanzu da muka yi waya da ita take ce min dan Allah idan zan dawo na zo mata da yara ta wato AFREEN." Wani murmushin papa ya koma yi sannan yace "Ai jininsu ya haɗu da jannah sosai fiye da yanda kake tsammani." Injiniya Sumana yace "Hakane yanzu nan zata iya yin wata shawara da jannah bata yi ta da mahaifiyar ta, amma nikam da za'a ban ita na bawa yaron nan AFREED, da ya kasa fitar da wace ya keso gashi nan kannin sa har saura wata biyu auren su so yake sai ya gama zama tuzuru nasan ko zaiyi auren, yaro sai taurin kan tsiya babu wanda banyi ya fitar da wace ya ke so ba ya ki ko dan a saka masu rana ɗaya da yan uwansa amma yaki." Dady ya fada dan ɓacin rai kaɗan a fuskar sa Murmushi Alhaji Sadisu yayi sannan yace "Ai kam da nayi farin ciki idan hakan ta faru zumunci mu zai ƙara ƙarfi sosai, ko maman su nasan da sai tayi farin ciki sosai da hakan kuma Allah sa alkairi ne zamu haɗa." Docter Inusa ma murmushin ya yi kamin yace gaskiya hakan kuwa abu ne me kyau, kuma insha Allahu alkairi ne gashi ma sunan yaran nawa kusan irin ɗaya ne AFREEN da AFREED kamar wasu yan tagwaye kuma dukan su akwai hankali da nutsuwa sosai a tatare da su daga gani zaman su zai yi armashi insha Allahu, sedai wani hanzari ba gudu ba ya kamata Ku sanar dasu ko sun amince ba auren dole zaku masu ba, dan ba kusan ko wani daga cikin yana da wanda yake so gaskiya a basu zaɓi." Da sauri injiniya Sumana yace "Ko alama bazan sanar da AFREED komai ba sedai ya ga amarya komai nine zanyi dama na faɗa masa idan har ya yarda ya kaini bango zan nema masa matar da kaina, gashi kuma yanzu na samu yarinya mai hankali da tarbiyya ɗiyar aminina ai babu abinda zai hanani yi masa auren nan, sedai in ita yarinyar ce bata so ko kuma tana da wanda take so nan babu wanda ya isa ya mata dole wallahi ni ne nan zan tsaya mata har sai an aura mata wanda take so." Nan ranshi a ɗan ɓace ya ida maganar." Alhaji Sadisu yace kwantar da hankalin injiniya insha Allahu haɗin zai yiwu kuma zai zama alkairi da yardar Ubangiji, duk da banjin cewa AFREEN na da wani sauri bayan wancen, da har bata faɗa min ba amma zan tuntuɓe ta, kuma zan faɗa maka shawara da na yanke daga nan idan ta amince sai muyi abinda ya dace dan nasan zata min biyayya insha Allahu. Farin ciki gun injiniya Sumana ba'a magana kamar ance masa yarinyar ta amince ko kuwa gashi har an kaita gidan sa a matsayin matar AFREED, shima docter Inusa ya nata farin ciki kamar wata ɗiyar sa. Daga nan suka sauka saman kafet suka fara cin abinci, sosai suka ci suka koshi, suka yi hamadah tare da ci gaba da fira su, sai wajajen ƙarfe goma na dare suka yiwa papa sallama suka kuma ma sauƙin su duk da babu yanda papa bayi ba su kwana a gidan suka tare da cewa haba Alhaji kai baka ga yanda baƙi suka cika gidan ba mu koma masaukin mu zai fi gobe in Allah ya yarda zamuyo samakon ɗaurin aure, haka suka ɗauki motar aminin na su suka tafi da ita, Washegari tun ƙarfe biyar kowa na gidan sai shirin ɗaurin aure suke, kamin karfe takwas tayi har kowa ya shirya ga gidan ya cika makil da yan ɗaurin aure, waje ko hanyar yucewa babu sai ka ɗan karkata kamin kasa mu shi ga gidan iyayen gidan mata gaba ɗaya sunci shiri cikin wasu narkakun shadadodi na ganin na faɗa kana gani kasan a kashi kuɗi a wajen nan, haka yaran gidan su ma da kalar tasu shadar mai mugun tsada. 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutun_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *Page* : 55 & 56 Sai kam ta AFREEN da tafi ta kowa haɗuwa dan ko ta iyayen nasu sai tayi saboda son da Alhaji Sadisu ke yiwa AFREEN ya saka komai na ta daban yake a gidan ta fito ta yi shar da ita, kamar wata matar shugaban kasa, kowa sai yaba kyaun ta da mamakin irin wannan kyau na ta mara misali, sai mutane ke mamakin kyau irin na AFREEN Ita dai tafi mahaifiyar ta kyau nesa ba kusa ba amma kana kallon ta ka san ita ta haife ta sabida suna ɗan kama sedai maman ta ta fita haske sosai, kalar fatar mahaifinta ta ɗauko mai ɗan duhu da sheƙi da haske wanda ba za'a iya saka ta a layin farare ba, sai ƙwayar idon ta dake kalar chocolat color amma cikin su fari tas ne mai walk'iya da ɗaukar ido har da ɗan ƙaramin baki da surcecen hanci har baka masha Allah. Ƙarfe takwas daidai duban jama'a suka shaida ɗaurin auren Khairat Alhaji Sadisu da angon ta Ahmed sufiyane bisa sadaki 100000F CFA, kamin kace mi labari har yaje ga kunnan Khairat wace ana gayama ta, tayi hamdalah ga Ubangiji a cikin zuciyar ta, taron ɗaurin aure ya watse lafiya ida aka maida taron yinin biki, Alhaji yana cen kofar gida cikin inuwa wata babba bishiya tare da abokansa kusan su goma suna ta fira su cikin farin ciki. Biki ya yi biki ida aka shirya amarya cikin wani haɗaɗan lace marron ta haɗu har ta gaji da haɗuwa, nan fa aka fitar da ita babban falon gidan ana ta photo, nan su AFREEN an shirya cikin wani haɗaɗan matériel blue 🔵 sai sheƙi yake mutane na ta photo da ita kamar ita ke amarya. Ƙarfe takwas daidai na dare aka tafi kai amarya gidan mijinta ta sai wajen tara da arba'in yan kan amarya suka dawo, masha Allah taro ya watse lafiya sai fatan zaman lafiya tsakanin ango da amarya. A gajiye su AFREEN ƴan kai amarya suka dawo gida, direct ɗakin ta nufa ta faɗa toillet ta yi wanka tare da ɗauro alwala ta zo ta gabatar da shafa'i da wutiri sannan taje gan mirror ta ɗauko wayar ta kashe tun farkawar ta da asuba bayan tayiwa AFREED Barka da safiya ta kashe ta ɗan ta samu tayi bikin ƴar uwar ta hankali kwance da nutsuwa. Wata ranar asabar da dadare ya kama sati uku kenan da ɗaura auren Khairat bayan ƴan gidan su gama cin abincin a dinning baki ɗaya suka koma falo, suna ta fira hada mai gidan wato mahaifin su AFREEN a nata wasa da dariya, sai papa ya miƙe ya masu saida safe ya nufi saman shi da yake maman su AFREEN ke aiki bayan kamar minti goma sai ita ta mike ta bi bayan shi, sannan AFREEN itama ta nufi nata ɗakin., Haka da ƙaɗan kaɗan kowa ya watse ya nufi ɗakin shi a ka bar falon tsit tunda kowa ya kama gaban sa. Maman na shiga falon papa ta sameshi a saman kujera a zaune yana nazarin wani abin ya yi tagumi, da sallamar ta shiga ya ɗago ya dube ta sannan ya amsa sallamar tare da sauke ajiyar zuciya, kusan shi ta zauna tare da riƙo hannun sa ta saka cikin nata hannun tace "Mijina na lura da akwai abinda ke damun ka kasa faɗa min dan na lura da maganar da kake son faɗa nice kake son gayama amma kaki samun courage ɗin sanar dani, kasani babu abinda muke boyewa juna koma miye kada kaji shaƙar sanar dani komiye saboda a ƙarƙashin ka nake kuma kana da iko dani gara ka faɗa dan tun yuri musan abunyi idan kuwa umarni zaka bani duk wannan ka cenci haka, saboda tun bayan auren Khairat na lura da akwai magana a bakin ka Alhaji na ka daure ka sanar dani ko nima hankali na zai kwanta." Saida papa ya sauke wata ƴar gajeriyar ajiyar zuciya sannan yace "Allah kuwa kamar kin shiga zuciya ta ɗan ina shaƙar sanar dake abinda ke raina gaskiya, amma ba komai yanzu tunda kince haka bari na faɗa maki," sai da ya gayar zaman sa sannan yace "Ba wani abu bane nakeson sanar dake ila ina son faɗa maki cewa nayi wa AFREEN miji wato ɗan gidan injiniya Sumana in ba zaki manta yaron sun taɓa zuwa gidan shida ɗan uwan sa wanda lokacin haihuwar sa kema kin halarci sunansa in bazaki manta to shine nakeson sanar dake narasa ta kowace hanya zanbi dan Kada kice na yanke hukuncin aurar da ɗiyar mu, ban sharwace ki ba dan maganar da nake maki har mun saka rana auren sani da yaya na Adamu da Dr Inusa se kuma shi mahaifin yaron Alhaji Sumana mun tsayar da wata biyu, ida yau yayi saura wata ɗaya da sati ɗaya, dan kuwa tun zuwan su bikin Khairat mu ka saka wannan ranar idan ki ka yi lissafi zaki ga hakane." Maman seda ta ɗauki kusan minti biyar bata ce komai ta tsurawa papa ido tana nazartar sa sannan ta sauke ajiyar zuciya tace "Allah ya sa haka shi ne ma fi alkairi, tsoro na ɗaya shi ne in ba mijina ne ya fara nemawa ƴarsa auren ɗan su ba dan gudu ka su dinga mata kallon matar cushe, kuma kada ace ganin ana ta saka ranar aure ta ana fasawa ya saka shin yin haka ko a ganin shi ba zata samu wani wanda zai aure ta ba amma in dai babu ko ɗaya a cikin to ni ina farin ciki da hakan, kuma Kanada incin zaɓawa AFREEN miji sabida ɗiyar ka ce kai keda hakki da ita ba wani ba." Murmushi Alhaji Sadisu ya yi ya ƙara riko hannun ta dake cikin nashi kamin yace " Allah maki albarka Allah ya biyaki da gidan aljanna sosai har yau har gobe bani da kamar ki a cikin mata na Allah ya biya ki da mafificin alkairi, sannan batun na cusa masu ita ko tunani zata rasa mijin aure ko ɗaya babu hasali ma shi ya fara kawo man magana kan yana son a yi haɗin zumunci, dalilin ganin AFREEN da yayi lokacin da tazo kawo mana ruwa ga ranar da suka zo ya nuna min yana son yaron da ita. Da wasu hujoji da ya sanar min ya saka na amince." Itama murmushin ta mayar masa sannan tace "To shikenan Alhaji na Allah ya sa alkairi ku ka haɗa sedai ku sanar masu dan Kada ku shiga hakkin yaran ku dan ita dai nasan ba zata ƙi yi ma biyayya ba." Papa ya amsa da ameen tare da cewa insha Allahu zuwa gobe zan sanar mata dama abinda yasa ki kaga banyi saurin faɗa mata ba na bari ne har muyi shawara dake ne, sannan na ɗan sama ta ido naga ko akwai wanda take so ko zata iya faɗa ko dai a ga wasu alamu haka to banga ko ɗaya ba inda bata boye bane." Maman tace "To Allah tabbata da alkairi bari naje ɗaki na na dawo." Tanti dake laɓe bakin ƙofar falon Alhaji alamu ta gama jin komai da suka tattauna tayi gudu ta ɓoye cikin wata ƴar coulouwar (corridor) dake bayan wajen dan itama tunda ta lura da akwai magana a bakin mijin nasu take ta son taji ko miye kuma ya ki faɗa masu idan suna su duka zaune waje guda tun a lokacin ta san cewa da Arahamat yake son faɗa wa ita ɗaya dan ta lura hada soyayyar da yake matane ta shafi waccan bakar yarinyar AFREEN mai kama da ita. Maman na shiga ɗakin ta tanti ta fito daga laɓan da take da sauri ta sauka daga saman benan tayi shige ɗakin ta da sauri hankali ta a mugun tashe ta buɗe baki ita ɗaya cikin ɗaki ta fara magana kamar haka "Wane yaron za'a haɗa da AFREEN garde corps (Bodyguard) ɗin ministre (ministan) ko ministre ɗin gaba ɗaya shi ne zai aure ta, kai gaskiya baza ta saɓu ba wallahi da sake ace duk abinda nake ya tashi a banza kam, to ai ko garde corps ɗin ne bazan bari ayi auren nan ba bare a ce minister ne da kan shi da wallahi sai in da ƙarfi na ya ƙare bari na kira anty hawa na gaya mata." Nan take ta dauki wayar ta nemo number ƴar uwar ta ta tura kira ta kara a kunne ringing ɗaya biyu aka ɗaga, hankali a matukar tashe ko gaisawa bata bari sunyi ba tayar ta na ɗaga tace "Aunty kinji kuma abinda suka ƙara jayo wa ko, wai aure za su ma wannan shegiyar yarinyar da duk burin mutan gidan ya na kanta, duk faɗi tashin da nake dan na hana ta aure har karshen rayuwar ta bai hana suka ƙara hango wanda zasu haɗata da shi kuma abin haushin ma kin san kowa?" Yayar Wada suke kira da anty hawa da tayi shiru tana sauraran ta tace "A'a sai kin faɗa ai zan sani ko?" Tanti tace "Wai ɗan gidan aminin Alhaji wannan injiniyan da nake baki labari cewa yaron sa ne keyin ministre de dépenses et de sécurité har nace da hamida ta isa aure da zanbi duk hanyar da zanbi in ga ya aure ta, amma ku inaso ko da ta biyu yayi da ita bayan nan da wasu yan shekaru, amma ina yanzu naji suna wannan banzan zancen bara digi naji yace uban yaron ne yake son a haɗa auren ba shi ba, amma bansan wane yaron daga ciki yake nufi ba tunda akwai yaron da ƙanwar matar sa ta muta ta bari tun yana jinjiri suka amshe shi suna kula da har ya girma a hannun su kusan yan sa'a guda ne shi ministan, shi ne ma garde corps (Bodyguard) ɗin ministre ɗin to shine nake tunanin wa ne daga ciki wanda za'a haɗa ta da shi, don gaskiya babu wada zan yarda daga cikin su yarinyar nan ta aure indai ina raye ko babu na zai kare sai na cika buri na na ganin yarinyar nan ta wulakanta, in bata auri nakasashe mugun matsayin ta tagayara ta zama abin tausayi wanda sai an taimaka mata ba, gaskiya hankali na ba zai ta taɓa kwanciya ba, ba dai sunce ita ta gaban goshi ba yaran mu duk kamar photo suke a gidan abinda AFREEN tace tana so shi ne ake yi a gidan nan ko da kuwa cikin mu ne iyayen muka ce bama so, anty ya kike ganin za'ayi?" Sauke wata irin ajiyar zuciya Aunty hawa tayi sannan tace "Lale zama bai sameki ba ke a ganin zasu haɗa ta aure da wannan yaron da matsayin sa bodyguard ai sedai ministan shida zata huta girki ma sai anyi mata komai yi mata za'ayi ko da ruwa takeso a bata za'a ta, wa ya gayama ki za su kai ta inda za ta sha wahala, dan haka idan kina bada himma wajen ganin kin maida komai akan ɗiyar ki to idan kuwa ba haka ba kina nan kina kallon ruwa kwalo ya maki ƙafa, dan wallahi ki na kallo yarinyar nan zata nasara kanki ke kuwa ki faɗi warwas dan haka gobe tun safe ki zo mu koma gun mutumin nan wallahi tun kan yurin ya ƙare maki, kawai ƙaramar yarinya ta zame maku annoba ga gida, ita ce duk gidan nan a ka fi so ita ta fi kowa ilimin addini da boko ita ga shegin kyau kamar aljana ke wallahi idan bakiyi da gaske ba wannan kyau fuska da kyau ƙira da na hali da na komai duk ita ɗaya, wallahi wata rana ba minister ba shugaban kasar gaba ɗaya za'a ace ta aura ko sarki ke zaki kiji ma ance an zo neman auren ta daga wata ƙasar waje idan bakiyi da gaske ba, ke kuwa dake da ƴar tillon ɗiyar ki kun shiga uku, kinga likita babu kalar da bamu gani ba an ce babu ke babu ƙara haihuwa, haihuwar Hamida ma da yaya kika sameta saidai muka kashi kuɗi sosai kamin ki samu cikin, mu so ki haifo mana namiji ki ka samo mace a haka ma mungode, sannan kuka zama kamar wasu tsitacin mage a gidan." 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* *_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_* *Page* : 57 & 58 "Arahamat da yaran ta kawai ke abinda suke so sabida ta amshe gida yaran ta biyar har maza biyu ke da ɗaya ita kuwa wacen mafaɗaciyar da uku ita kuwa duk mata, kin ga kuwa idan yau Alhaji ya faɗi ya mutu har ƙorarki ana iya yi daga gidan nan dan haka nake so ki samu ki mallaki wasu ƙadarori na Alhaji kamin mai tonan asiri tazo dan kuwa ya na komawa ga mahaliccin sa, wallahi kin banu sabida abinda za'a baki na gadon yarinyar ki da na wankan da zaki masa bai taka ƙara ya karye ba dan a lokacin ne zakiyi dana sani wallahi kin tashi a tutar babu dan ma wai kinada ɗiya da shi da ace baki da kowa wallahi da kin fi banuwa." "Wallahi haka ne Aunty ai duk sai naga bayan su sai na koma babu wanda ke faɗa aji in bani ba dan ba zanyi tallata ba sai Laraba dan wallahi bani tashi a taulauce kuma na mutu a haka gaskiya il faut que nayi arziki dan zan dinga zuwa Dubaï duk sati nima matan manyan su dama dani ba wai na zauna ina kallon kawai na wasu suna fantamawa ba yanda suke so ba ni banda ni wallahi da sake." Anty hawa tace "Ah ai dai na faɗa maki tun ba yau nake sanar dake wannan abin kin ƙi ki fahimta kiyi abinda ya dace." Tanti tace "karki damu anti yanzu dai mu fara maganin wannan matsalar kamin akai da wacen ɗin." Da sauri Aunty hawa ta tari numfashi ta ce "Ke daka ta ai a bari ya huce shi ke kawo rabon wani duka za'ayi gobe idan Allah ya kaimu ba waje guda ba zamu je, sannan ki kira wannan ƙawar taki ita ma ta raka mu wajen wannan babban bokan na ta, sannan muje wajen wanda ya ke maki aiki nima na san guda uku duka zamu je ayi aiki mai yawa kowa ya yi kalan nashi se ki ga ya yi saurin ci dan wanga karon ko ƙur'ani take zazzage wa a kanta tana kwana da shi dole muyi galaba a kan ta ke dai kawai gobe ki fito da kuɗin isasshi." "To shikenan anty Allah ya tada mu lafiya." Ta amsa da ameen sannan suka ajiye waya Tanti na ajiye wayar ta fara kai kawo cikin ɗakin ta ce yanzu najin sun ce zasu tuntuɓi AFREEN kan maganar idan ta yarda ni zan hure ma ta kunne ince ka ta yadda duk da naga kamar yanzu bata sanki jiki dani, amma zan gwada ko dai ta fara gane shirin da nake a kanta kai ba haka bane indai ba wannan munafuka Khairat kin ce ta fara hure ma ta kunnuwa dan naga ita ba wani yarda tayi dani ba, ko da yake itama zanyi maganin ta zan hana ta zaman lafiya da mijin nata, har sai ya watso ta gida insha Allahu kowa na shirya yanda zanga bayan shi ita fauziya ta daina farin cikin cewa tayi aure har yanzu mijinta bai yi mata kishiya ba zan yi abinda zai ƙara aure kuma irin kishiyar da zata maida ta kamar ƴar aiki za'a mata duka dai zan san yanda za'ayi, ba dai da ni suke ja ba za su sha mamaki duka sai na sa sun gane kurin su, sai na kuntata masu rayuwa kamar yanda yanzu suke cikin farin ciki mu kuma an mayar damu bare ga gida ba matsala zasu gani." Da safe wajen ƙarfe tara bayan sun gama petite déjeuner (breakfast) 🍳🍜🥗🍱 papa yana dakin sa bai fita ba tanti ta shiga da sallama papa ya amsa mata sannan ta nemi guri ta zauna tace "Papan yara da ma inaso naje gidan Aunty hawa na duba ta kwana biyu bata ji daɗin jikin ta ba shine na ce bari na sanar maka." Papa da idonsa ke ga télé (TV) ya juwo ya kale ta yace "Asha asha Allah ya bata lafiya kije kawai Allah koro sauƙi, amma ai kinsan bana son za'a fita a ƙi sanar da ni har sai ranar fitar ta zo ko." Tace "Eh wallahi nasan wannan jiya da dadare ne take sanar dani wallahi shi ne yasa ban sanar da kai da wuri ba." "To shikenan idan kinje kice ina gaishe ta da jiki." Tace "Insha Allahu zan sanar mata" "To shikenan ba damuwa tashi ki shirya kije dan ki samu ki dawo da yuri." Tanti har ta miƙe zata fita sai papa yace "Karɓi wannan ki sayi ɗan abinda dubiya ki biya mata da shi." Da sauri tanti ta karɓe 10000 da papa ke miƙo mata kamar yace zai fasa bata idan bata ƙarɓa ba da sauri. Bata tsaya komai ba ta ga ɗaki, ta nufi nata ɗakin tana shiga ta faɗa toillet tayi wanka ta tayi shirya cikin dogon hijab inta tayi kamar wata ta kwarai ta fice daga gidan. Maman na zaune ɗakin papa suna hira yace taje ta kira masa AFREEN itama ta dawo dan ayi komai a gaban ta. Maman ta shi ta fita ta nufi ɗakin AFREEN tana shiga ta tardo ta makale da waya ta na hira da masoyin nata sallama tayi sannan ta idasa shiga ɗakin, AFREEN da ta kashe wayar tunda ta ji sallamar mahaifiyar ta ta ɗago ta kalle tace "Maman barka da warhaka." "Yawa AFREEN na shigo kina waya ko har kin gama." "Eh maman dama da fanna muke magana." "Ok to ta shi mahaifin ki na neman ki." Dam dam gaban ta ya faɗi bata san dalili ba, idan kiran Mahaifin ta ne ai ta saba dashi tun ba yau ba to miyasa yau taji faɗuwar gaba daga ance yana neman ta. Ta ɗago tace wa maman gata nan tafe sai kawai taga maman har ta fice daga ɗakin jiki a sanyaye ta sauko daga saman bed 🛏️ ɗin ta ɗauki hijab ɗin ta nufi gun mahaifin ta, tana kaiwa bakin ƙofa ta yi sallama aka amsa ma ta sannan ta murɗa ta shiga kai tsaye duk jikin ta a mace ta nemi gu ta zauna kusa da ƙafafun mahaifiyar ta sannan ta ɗago tace "Papa gani maman tace kana nema na." "Eh hakane AFREEN ni nace ta kira minke akwai maganar da za muyi dake inaso ki nutsu kiji abinda zan faɗa kin gane ko dan maganar tana da mahimmanci sosai." Nan ma AFREEN taji gaban ta ya sake faɗuwa sannan ta ce "To papa ina sauraren ka." Yace "Yawa kinga mahaifiyar ki nan jiya mukayi maganar da 'ita shi ne naga ya dace ke ma a sanar dake, dan haka ba wani abu bane nakeson faɗa maki illa inason faɗa maki cewa na maki miji." Dam dam gaban ta ya yanke yayi wata irin muguwar faɗuwa ta ɗago da sauri tayi sauke idon cikin na Mahaifin ta suka yi ido huɗu da shi sannan da sauri kuma ta sunne kanta ta na kallon kasa tare da rumtse idonta da ƙarfi ta furta inna lilahi wa inna ilaihi raji'un cikin zuciyar ta. Papa ba tare da ya lura da hali da AFREEN ta shiga ba ya cigaba da cewa "Yaron ne me hankali da nutsuwa da sanin ya kamata in taƙaice maki dai yaron kirki ne iyayen sa suka nemi na ba shi auren ki ganin dacewar haka yasa na amince masu ba tare da na nemi shawarar ki ba saboda sannan halin yaron da kuma la'akari da nayi da gidan da ya fito gidan tarbiyya, gidan mutunci ne gidan mayan mutane ne ina nufin iyayen sa datawan kware ne haka kuma nasan da za'a riƙe ki da daraja da muntunci saboda mahaifinsa amini na ne tare muke tun muna yara tare mukayi komai har aure da kuma karatu kinga mahaifiyar ki nan itama ta sanshi farin sani dan mahaifiyar yaron ma kawarta ce, amma wani hanzari ba gudu ba, AFREEN ba doli ba ne za'a yi maki zaɓi ne kuma shawara ce idan har kin ga zaki iya auren ɗan amini na idan kuma ba zaki iya ba, babu mai takura ki ko kina da wanda kike so duk babu wata damuwa ni farin cikin ki kawai nakeso ba na wani, idan kin ce baki amince ba, zan iya kiran injiniya in ba sa hakuri kuma na san zai fahimce ni dan haka kina da zaɓi AFREEN ɗin papa gayaman yanda kike so ayi, zanyi farin ciki da duk amsar da zaki ban, kuma gaskiya nakeson ki faɗa man abinda ke cikin ranki kada ki kuskure ki man ƙaya saboda baki saba yin haka da sauri zan gano inda kika dosa." Cike da tashin hankali AFREEN ta ɗago ta kalli mahaifin nata taga ita yake kallo babu yabo ba fallasa cikin kwanciyar hankali ba ta ga alamun zai yi mata dole ba, kuma haka ta ga alamun ba zai ji haushi duk abinda zai fito daga bakin ta ba, da sauri ta mayar da kanta kasa ta na kallon kafet wani irin bugawa ne zuciyar keyi kamar zata fito waje kuka keson kubce ma ta amma tayi ƙoƙarin mayar dashi saboda idan ta bari kukan ya fito mata zai nunawa papa cewa batayi na'am da zaɓin sa duk da a cikin zuciyar ta hakan ne batason wanda papa ke shirin haɗa ta dashi sabida tana AFREED ɗin shi take so take kauna a cikin zuciyar ta ga halin yanzu duk da basu yi ko wata da haɗuwa ba har yanzu, gashi kuma papa na shirin faraƙa tsakanin su ita ya zatayi dan bai kamata tayi rejeté zaɓin mahaifin ta ba bai komai kawai zata aminci kodan papa ya gama mata komai a rayuwa ko a cikin gidan ya kan take farin ciki kowa da ita tayi farin ciki bai kamata ta yi masa butulci ba gaskiya... Bata ƙarasa zancen zucin da take ba papa na cewa "Ke nake saurare AFREEN kaki kuskura ki yi ma kanki gashé ɗin farin ciki da ganin kin faranta man dan kuwa ina maraba da duk amsa da zaki bani saboda kinsan ce ta farko a cikin gidan mai min biyayya yanda ya kamata idan aka cire mahaifiyar ki dan gaba ɗaya halayyar kika gado, dan haka ina sauran ki faɗa man duk abinda ke ranki." Wani murmushin ƙarfin hali AFREEN ta antayo ma Mahaifin nata sannan tace "Haba papa sai kasa naji kamar nafi ƙarfin kamin zaɓin abinda kaga yafi dacewa dani, sai kasa nayi tunanin na kasa ma biyayya yanda ya kamata papa, miyasa dan kayi min miji kuma sai kanemi shawara na kamar ni ce na haifi kaina dama ai a musulunci iyaye su suke zaɓa yaran su miji na farko to miyasa ni dan an zaɓa min kuma za'a nemi shawara na ai kawai umarni zaka ban papa kuma na bi umarnin wallah, ni kawai fata Allah ya sa haka shi ne mafi alkairi dan na san papa ba zaku taɓa yimin zaɓin wanda ba na gari ba na san da har da son da kake min yasa kayi min wannan gatan, ba abinda zan maka sai godiya da kuma godewa Allah da ya bani mahaifi irin ka duk wanda ya samu iyaye irin ku ai sai hamdalah ga rabbil izzati. AFREEN ta ja tayi shiru dan jin zuciyar ta nason karyewa yanzu nan zata iya fashewa da kuka abinda kuma bata son papa ya gane ta na cikin damuwa kan wannan zaɓin nasa, dan da zata iya ƙurma ihu a lokacin da papa ke sanar da ita da tayi sai dai bazata iya ba dan farin cikin mahaifin ta ya fiye ma ta komai. Cike da farin ciki papa ke kallon AFREEN da ta duƙe kai tana kallon ƙasa sannan yace "Allah maki albarka Allah maki albarka Allah maki albarka AFREEN har yau har kullum ina alfahari da ku duka yaran da Allah ya bani ba ma kamar ke ban taɓa aza magana kika tsallake ta ba Allah maki albarka Allah baki ɗiyan dake ma za su maki fiye da yanda ki ke ma mu Allah ya saka maki da aljanna firdaoussi." Ameen AFREEN da mahaifiyar ta suka amsa sannan papa ya koma cewa kin amince da zaɓi na, amma ke baki faɗa man ko ki nada wanda ki ke so ba?" Da sauri AFREEN tace ba bu kowa papa ai da na sanar da kai." 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ *_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_* *Page* : 59 & 60 "To shikenan Allah maki albarka ki rubuto man a takarda duk abinda kike so ki kawo man koma miye idan dai bai fi ƙarfi na ba zan maki shi kuma in ba na saɓan Allah bane, sannan zan turo maki da wasu kalolin motoci guda biyu sabin fitowa har yanzu basu kawo nan ba ko a ƙasashen waje ba ko wane ya san su ba sai ki zaɓi guda na siya ma kamin bikin ki sai a kawo maki insha allah da akwai wasu shaguna da na buɗe da sunan ki a garin Niamey na ki ne duka haka kayan dake cikin, dama faɗa maki ne bayan, amma idan kika duba account ɗinkin zaki ga kusan kullum kuɗin cikin ƙaruwa suke, har ma kin taɓa min magana akan haka na ce maki ni ne nake ajiya a cikin account ɗin to ba haka bane na ki ne kawai kuma duk ribar da ake samu ce ga shagunan Allah maki albarka." "Nagode papa Allah saka da alkairi amma gani nake kamar sunyi yawa papa duba da ba ni ɗaya ba ce." "Karki damu da wannan ke ta ki kyautar ta musamman ce, amma suma duk na shirya wa kowa ta shi sedai suma ma ba yanzu zan basu ba sai duk nan gaba sedai a gaskiya tasu ba kai taki ba." "To mun gode papa Allah ƙara arziki mai albarka Allah ƙara lafiya da nisan kwana Allah kare ka da ga sharin duk wani abun shari ameen." Da Ameen papa da maman suka amsa sannan papa ya ƙara cewa "Allah maki albarka ta shi kije ku fara shirin bikin ki tun yau saboda wata ɗaya da kwana shida ya yi saura." Gaban AFREEN ya ƙara faɗuwa kuma ta ƙara shiga damuwa sai taji kamar ta aza hannun a kai ta yi ta kuka amma ba dama, kuma sai ba ta nuna ma papa da maman hakan ba se miƙe da tayi cikin mutuwar jiki ta bar ɗakin. AFREEN na shiga ɗakin ta faɗa kan gado ta shiga rusa wani irin kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar duk wani mai saurare gwani ban tausayi, saida tayi mai isar ta sannan tayi shiru duk idanun ta sun kunbura sunyi tulutu gashi kuma abun ga mai mayan ido ta ta shi ta shige bayi ta ɗauro alwala ta fito ta gabatar da sallah azahar da ta dalilin kiran sallah yasa ta daina kukan, a sujidar ta ƙarshe ce ta shiga rera wani sabon kukan mai ci rai tana faɗawa Allah "Ya Ubangiji ya Sarkin sarakuna ya mai samai da ƙasai ya hayyu ya ƙayyum, ta shiga dai yiwa Allah kirari sannan tace ya Allah idan har zaɓin mahaifin na alkairi ne a gare ni Allah kasa na yarda da shi hakan kuma naso wanda zai haɗa ni dashi na amince idan kuwa AFREED shine alkairi a gareni Allah ka wargaza shirin mahaifina ka barni da masoyi na wanda nakeso idan shima ba alkairi ba ne Allah haɗi da alkairi sannan kasa nayarda da shi kuma na so shi." AFREEN dai tai ta jero addu'a ta na kuka mai tsananin sai da har taji kanta zai fara ciwo kan ta daina kukan ta bawa kanta hakuri, sannan ta ɗauki Alkur'ani mai girma ta shiga karantawa a nan ne ta ji salama taji hankali ya ɗan kwata yunin ranar ta kasa saka kofa ruwa ne a cikin ta bare abinci, sau biyu mahaifiyar ta na shigowa ta kira ta ci abinci sai ta tardo ta kwance ta lahe kamar mai bacci, alhali ba bacci take ba kawai daga taji takun tafiyar za ta shigo ɗakin tane sai ta yi maza ta yi kwace ta lahe kamar mai bacci, haka AFREEN ta yuni ranar ko kiran AFREED ta kasa ɗauka don gani take mi zata faɗa masa ya zai ɗauki zancen ta ya zatayi itama da son da take masa yanzu nan rabata da shi za'ayi, idan ta tuna haka sai ta shiga furta inna lilahi wa inna ilaihi raji'un, tare da rokon Allah ya kawo ma ta sasauci raɗaɗin dake cikin zuciyarta dan ba ƙaramin so take yi wa AFREED, saboda bata san ya akayi take son sa ya yi mata mugun kamu har take ganin bata iya rabuwa da shi duk ratsi, haka ma bata iya watsa ma Mahaifinta ƙasa a ido kawai ta bar ma Allah zaɓi. Da wajen ƙarfe huɗu da rabi AFREEN na zaune saman darduma wanda tunda ta gama sallah la'asar ba ta ta shiba saboda tana karanto azkar ɗin yamma mahaifiyar ta shigo ɗakin da sallama ɗauke da bakin ta, ba tare da AFREEN ta ɗago ba ta amsa sallamar, maman ta nemi guri bakin gado ta zauna sannan AFREEN ta ɗago tace "Maman barka da gida." Saida maman ta kwashi kusan minti ɗaya ta na karantar halin da AFREEN ke ciki sannan tace "Yawa AFREEN lafiyan ki naga duk idon ki ya kumbura, ko kuka ki ka yi?" Da murmushi AFREEN ta dubi mahaifiyar ta, Sannan tace maman kuka kuma da aka yi man mi zanyi kuka, kawai kaina yake man ciwo tun dazun nan nayi bacci na tashi amma bai daina ba sai na sha magani kuma na sake kumawa bacci saboda ina tunanin ko bacci da na jima bayi bane a daren jiya yasa hakan amma ashe ba haka bane, tunda ga shi yanzun ma ciwon ya ke min." Har ga Allah maman ta yarda da hakan shiyasa cikin tausayawa tace "Haba AFREEN ya zaki zauna da ciwon kai har tsayin wannan lokaci ba zaki faɗa ba, gashi kuma kika yi ta bacci baki ci komai ba duk safiyar yau ko yinwa ai zata saka maki ciwon kai mana, tashi muje kici abinci sai mu tafi asibiti a dubaki ai ba a zama da ciwo haka yanzu haka zafi ne ya maki yawa. "A'a maman da safe nayi breakfast fah lunch ɗin ma banji yinwa ne shiyasa bayi ba." "To yanzu tashi huce muje ko ba kaijin yunwa zaki ci abinci mu wuce asibiti ehe saboda baki isa mahaifin ki ya dawo ya ta do baki da lafiya ya hauni da masifa ba gaskiya." Ba musu AFREEN ta tashi ta lumke darduma ta mayar da ita inda take ta dawo kusa da mahaifiyar ta tace "Maman ai papa ba zai san haka ba idan bake ki faɗa masa ba kinga ba sai muje asibitin ba daga naci abincin sai na koma shan maganin shikenan zanji sauƙi da ikon Allah." Wata yar harara maman ta sakar mata sannan tace "Ke ni wuce muje." Maman tayi gaba AFREEN tabi bayan ta, suna zuwa falo maman ta nuna ma ɗaya daga cikin mayan kujerun dake falon tace "Zauna a nan zanje na sama maki abinda zaki ci." "Ba musu AFREEN ta zauna inda ta nuna mata, sannan maman ta juya ta nufi kitchen, ba wani dauki lokaci ba ta fito da plet da kuma juice 🥤 ɗin mangue (mango🥭) ta ajiye a gaban AFREEN da keta raraba ido don samun mafita da zata hana su je asibiti. Maman tace "Zauna saman kafet ki maida hankali kici bari na kawo maki ruwa, maman da ta nufi fridge sai ta ɗoko hada lait (milk🥛) da bidon ɗin ruwa ta nufo AFREEN da su sannan ta ajiye mata, ta zauna a saman kafet ɗin kusa da AFREEN tace "Mi kike jira da baki fara cin abinci ba maza ki fara kina ga bataman da lokaci," maman ta faɗa tana mai buɗe plet ɗin na sama. Soyayyar doyace da taji kwai sai yar vinaigrette a gefe, daga gani kasan taji daɗi. Har AFREEN ta fara ci ta ɗago tace maman ai dai kinsan ba duka zan ciye wannan abin mai yawa haka." Wannan abin ne ke da yawa kawai dai baki son cin abinci narasa komai yasa haka duk gidan nan kece a baya wajen kincin abinci, to yi maza kici baki wanda zaki iya ci sai muje asibitin. AFREEN tana ƙarasawa ta ɗoki lait ɗin tasha da ruwa ta bar juice🥤 ɗin, sannan ta kalli maman tace "Na ƙoshi." Maman tace "To bari naje na ɗauki hijab ɗina da key na mota na mu wuce asibiti." Kamin ta tashi AFREEN ta riƙon hannun ta tace "maman dan Allah ki dai na maganar asibitin nan wallahi na daina jin ciwon kan ya rage dama inaga yunwa ce tasa ya ki daina min ciwo amma ina ci yanzu ya rage kuma nasan zuwa anjima zai daina min ciwo gaba ɗaya." Ɗan hararan ta maman tayi tace "To sarki kin tsoron alura da magani na yarda kada muje asibitin amma da sharaɗin yanzu zaki kuma shan magani." Da sauri AFREEN ta ɗaga kai tare da cewa "Eh." Dan ita da ayima ta alura karama ta sha maganin duk da shima ba ƙaunar shan sa take ba." Murmushi maman tayi da jin ta amince dan Kada a aje asibitin sanin irin tsoron alura da AFREEN keyi. Ba ƙaramin tashi hankalin AFREED yayi ba ganin ya kasa samun AFREEN, babu kiran da bai mata ba shiru, haka maganar da yayi mata a whatsapp tafi a irga amma sai yaga tunda safe wajen ƙarfe bakwai da ta sauka ba sake kuma online ba haka yayi mata text message shima babu amsa daga ƙarshe ma idan ya kirata sai ace wayar ta kashe take saboda tunda AFREEN ta samu labarin miji da papa ya mata ta kasa ɗaga wayar sa dan bata masan mi zata faɗa masa ba daga ƙarshe ma ta kashe wayar da niyar zata canza number saboda inda ya daina samun ta a waya dole zai hakura, kuma tana gudun kada ta barshi yayi ta sonta alhalin ba auren sa ba zata yi gara dai ta fara nesa da shi gudu kada ta masa brisé coeur. A ranar kwana ma gagara sa yayi sai da ya yi sallar asuba kamin ya samu bacci ɓarawo ya sace shi. Tanti na fita daga gida ba ta tsaya ko ina sai gidan anti hawa ku ta shiga tarda yayar ta ta ta shirya kawai bai su tsaya komai ba suka ka ma hanyar gidan kawar tanti don tun jita sun sanar mata cewa yau akwai tafiya gidan boka, dan haka suna fita cikin motar da tanti ta zo da ita direct gidan Hajiya lubabatou suka wuce sun tarda ta shirya su kaɗai take jira basu wata wata ba suka ma hanya yini ranar a gidan bokaye dayan tsubo suka ƙare shi amma amsar guda suke samu cewa "Wannan auren na AFREEN sai anyi saboda rantsatsen aure daga Ubangijin dama ko cen da tayi ta ɓata ma ta auren saboda su wa'in cen din ba bu mijinta a cikin su ko da bata zama silar ɓata auren to zai lalace kamin tayi hakan amma dan wannan fa dai anyi sai idan anyi a hana su zaman lafiya da miji har ya sake don gaskiya idan AFREEN ta zaman ta yaron nan to ta gama dace da miji kuma zata ɗaukaka sosai da sosai. Hankali a tashe suke barin gidan ko wane malami, gidan na ƙarshe da suka fito tanti ta aza hannun ga kai ta fashe da kuka tace "Na shiga uku ita wannan yarinyar da wace irin sa'a tazo duniya ne wai da gaba ɗaya ta ki tamnuwa ta ki haɗu to bata isa ba ni sai nayi maganin ta." Anty hawa ta kamo hannuwan ta sauke su ƙasa, Hajiya lubabatou dafa ƙafaɗar ta tayi tace "Kawata kin kwantar da hankali ki ita ɗin banza miye ita, duka wajen malami biyar ne fa muka je ni ban kaiku wajen nawa bokan ba mai aiki kamar yankan yuƙa, shi kam idan muka je gun sa ta ƙare dan haka yanzu mu koma gida na shi da ke kusa muyi sallah azahar da la'asar tunda muka fito muke tangarara a titi ko sallah ba muyi ba gara muje mu sake nauhin ta daga nan sai muka hanyar daƙoro (Wani ƙauye ne dake cikin jahar maraɗi) idan zan haɗa ku da wani shahararren boka ƙasurgumin matsafi na tabbata nan ba makawa buƙatar ki zata biya." Ba musu suka bi shawarar ta tare da nufar gidan Hajiya lubabatou suna ida sallah suka suka ɗauki hanyar daƙoro tanti ke dreving, awa biyu sukayi a hanya suna shiga a ana kiraye kirayan sallah magarib, gidan waya ƴar uwar Hajiya lubabatou suka tsaya sukayi sallah Hajiya lubabatou na sanar da ƴar uwar ta cewa wajen mutumen suka zo bari su ƙara sa, sannan suka ɗauki hanya da zata sada su da wani daji wadan shine ida bokan yake, suyi tafiya ta kusan minti arba'in kamin sukai gun bokan da cikin wata matsiyaciyar buka idan ka ganta ba zaka ce akwai mutun a ciki ba sannan ga layin mata da suka tardo gashi kuma har ƙarfe 8:30 na dare yayi dan tanti ta nayi ta duba montre gudun ka papa ya kai ga kiranta idan yaga dare yayi ba ta zoba 9:00 nayi hankalin ta in yayi dubu ya tashi ga shi har yanzu layi bai kawo kansu ba, ta dubi anty hawa tace nashi ga uku Aunty wallahi idan Alhaji ya gane bana cikin gidan nan har zuwa warhaka da nasan yanzu su na shirin fara dinner to wallahi Allah kaɗai zai rabani da shi don wallahi ba ya son muna fita har dare yayi ba mu dawo gida ba." "To kinga dai ko aikin ga ba mu samu ba hasali ma layi ko kawowa gare mu baiyi ba sedai in hakura zakiyi mu juya sai ki faɗa masa rashin lafiyar nawa ne ya yi tsanani shiyasa baki samu kin dawo da yuri ba." "Haba anty har mun kai waraha ka kuma zan ce zan hakura da aikin a dai nemi wata shawarar ba wannan ba ai da kinga na koma to wallahi mun gana da bokan nan." Hajiya lubabatou tace "hakane gaskiya bai kamata ba ace kin hakura da abin nan tunda ga mu a wajen in dai ba ke zaki tafi ba ki bar mu nida Aunty sai mu gaya maki yanda ake ciki idan mun koma, ko kuwa ki kira shi alhajin ki faɗa masa jikin Aunty yayi tsananin shiyasa baki samun dawo wa tunda ke ce zaki zauna da ita a asibiti." "Eh ke ma kin ce wani abu amma wani hanzari ba gudu ba kada na ce muna asibiti ya ce zai da safe ya zo yaganta ko kuwa yanzu." "Sai kisan abinda zaki faɗa masa idan yace hakan, amma idai ba hakan ba zaki ce sedai ki tafi ki barni Ni da lubabatou sai mu yi masa bokan bayani dan ba nida matsala miji na bai nan ni yarana tun muna saman hanya na kira su nace sau muyi dare kamin na dawo." Hajiya lubabatou tace "nima nawa mijin ya yi balaguro yaran kuwa suna kidan kakan nin su dan haka hankali na a kwance ke dai da matsala." Tanti tace ai dakin ga na bar gun nan na samu ganin mutumin nan na fi son a komai gaba na bari na koma daga cen na kira shi." Tanti ta tashi ta ɗan yi gaba takira papa ta sheda masa cewa ita ce zata zauna gun anty hawa jikin ya yi tsanani ga su ma a asibiti nan papa yace mata ba damuwa shi bai ma gari yana madarunfa (shi wani kayane dake cikin garin maraɗi), wani abu ya taso masa na gaggawa Arahamat kaɗai ya kira ya sanar ma kan ta sanar da su sai zuwa jibi zai dawo sannan yai mata fatan Allah ya ba anty hawa lafiya. Wani farin ciki ya luluɓe ta jin bai ma garin amma kuma ta ji haushi da yace wai Arahamat kaɗai ya sanar mawa kenan su bai da lokacin sanar da su. Ta katse kiran ta ja wani uban tsaki, sai ko taji an mayar mata da tsakin cikin wata irin gawurtaciyar muyar aiko da sauri ta shiga wage wage cikin tsoro ta yi saurin barin gun tana waigawa har ta dawo inda ta barsu Aunty hawa, ta dawo tana basu labarin ashe papa bai ma garin da ta sani da bata ma kira sa ba, sannan kuma take sanar da su cewa wai Arahamat ƴar gaban goshin sa kaɗai ya sanar da ita ta fiyarsa wai ita kuma ta sanar masu ai dole ma ta tashi tsaye a kan su." Ƙarfe 10:30 suka samu shiga wajen bokan da ko kyau gani bai da idan ka cika kallon sa ha amai zaka iya yi ma, amma su dayake zuciyarsu ta ƙeƙashe ba ma su ganin haka ba tare da ɓata lokaci ba tanti tashiga zayana masa abinda ke tafe da ita. Da wata irin mahaukaciyar dariya yayi sannan cikin ƙananan lokaci ya kumtse kamar bashi yayi ba sannan yace "aikin ki ba mai yiyuwa bane saboda yarinya tana yawan neman tsari daga sharin mutum da aljani da kuma shaiɗan saboda kullum cikin addu'a take da saloli nafila da neman kariya wajen Ubangiji sannan ga yawan karanta littafi Mai girma da yin azkar na safe da marece dan haka ko asirin da kika tayi mata na ana saka ranar auren ta a na fasawa ba ita yake ci ba samarin nata ne yakeci, to shi wannan bai masan da batun auren bare ya ace za'ayi asirin a kai, idan anyi sihirin a kai to ba zai ci ba saboda wannan auren fa babu fashi sai anyi shi saboda rantsatsen aure ga Ubangiji kuma akwai alkairi sosai a ciki sa dan haka wahalar da kanki kawai zakiyi duk wajen wanda zakije ba zai iya hana faruwar auren nan ba sabida haka abu guda zan iya maki shine zan baki wani magani kije ki samu ɗanyan kwai ki fashe shi ki ga ma da ɗanyan nama na shanu ki samu anta rago ki yaka a ciki sai ki zuba maganin, ki soya shi sannan ki samu masu ɗuka laya su ɗumka maki da wannan wainar kwan da ki ka soya sai ki saka a pilon da yarinyar ke aza kanta, daga an daura auren za'a barta gida tayi ta zama iyayen ma zasu mance da sun aurar da ita haka iyayen mijin ma ba zasu tayar da maganar ba sedai akwai haɗari idan ha kika yarda wani ya ƙanki lokacin da kike soya wainar ko kuma ki ka saka antar da bata rago ba to abin ne zai juye a kanki ranar da'ake daura auren ke zaki bar gidan ba tare da kin yiwa mahaifin yarinyar wani abu ba zai maki kora kare a bainar jama'a idan kuwa kika tsaya basa hakuri to ina mai tabbatar maki da kanki zaki dinga faɗar abinda kika shuka kamin ki bar gidan, sannan ga kuma wani maganin ki zuba ma yarinyar ga abinci idan taci to mijin nata ba zai taɓa kwontawa da ita ba sunan yin mu'amalar aure ba sedai ta zame masa kamar hoto a cikin gidan amma idan kika bari zata ci abinci mai magani da tayi Bismillah to ina mai sheda maki cewa maganin ba zai ci ba koda taci kuma mijin na kwontawa da ita to ina mai tabbatar maki cewa ke kuwa haukacewa zakiyi hauka kuma na har abada." Tanti ta jinjina kai tace "Boka ai wannan abin da ka zana mai sauki ne a guna ka ban maganin kawai ka sake min bayani dan zan iya cikin sauƙi ma ba wani tan garɗa." Da kyau boka ya ƙara kallon ta sannan ya ce "Zaki iya ba'a a son a samu matsala fah." Tace "Eh zata iya." Anty hawa da Hajiya lubabatou sai taɓa suke kada ta amsa wannan maganin ya yi tsauri da yawa amma ina, tanti idon ta sun rufe bataji kuma bata gani kawai ta ƙarɓa." Bayan ta ƙarɓa kamin su fito daga bukar bokan anty hawa tace ma bokan "Bacin wannan babu wata mafita." Yace "Babu, mafita ɗaya ce sai in kashe yarinyar za'a yi ko yaron." Da sauri tanti tace "A'a ai bana son ta mu na fison na ganta cikin mayuyacin hali ta koma kamar ba ita, a bar wannan kawai zan iya." Yace "To shikenan sannan suka fita." Suna fitowa har ƙarfe 12:00 na dare yayi dan haka basu tsaya tattauna maganar ba suka kama hanya sai wajajen ƙarfe 3:00 suka isa cikin garin maraɗi gidan Hajiya lubabatou suka fara biyawa ta sauka sannan suka wuce gidan Aunty hawa a nan tanti ta kwana dan tasan idan taje gidan yanzu har sun daɗe da rufewa dan haka kawai tace sai da safe. Kamin sun kwanta Aunty hawa nata yi mata jimamin anya zata iya kuwa tace zata iya kada ta damu dan haka Aunty hawa tayi shiru da bakin ta, safiya nayi wajen ƙarfe 10 ta nufi gidan ta fara aikin ta da ya dameta. Yau sati guda kenan da AFREED ya kasa samun wayar AFREEN duk ya fita hayacin sa haka ya sanar da Ali halin da ake ciki, Ali ya kwantar masa da hankali wajen faɗa masa cewa zai ƙara bin hanyar da ya bi ya sama mashi number ta a wacen lokacin yanzu ma haka zata kasance, amma kashe wannan karan da mummunan na labari ya dawo wa AFREED cewa AFREEN ta daina aiki da waya baki ɗaya ranar kamar yayi hauka dan jiyake idan har bai ji muryar ta ba yau to zai iya rasa ransa dan haka ya ce ma Ali zai shirya yaje Maraɗi yau ɗin nan, don kuwa har ya fara jin zazzaɓi yace zai bi jirgin da zai tashi ƙarfe shaɗaya na safe dan haka ya shiga haɗa kayan dan muna ƙarfe tara ne na safe Ali na natseye yana kallon sa cike da tausayi da mamaki abinda ke damun ɗan uwan na sa dan bai taɓa tsammanin haka daga gare shi ba, idan har aka ce masa AFREED zai faɗa soyayya da wata zai iya yin gardama bare har yayi irin wannan azabtacen son. Haka ɓangaren AFREEN ta kasa jure rashin duk da ba wani tsawon lokaci suka ɗoka a tare ba amma tana mamakin yan da akayi ta kamu da son sa har haka, dan tayi tunanin zata jure rashin jin muryar sa amma ina abun ya ci tura, saboda har ga Allah ita ɗin ma na walaha dan kullum cikin kuka take, haka duk in zatayi bacci sai ta cire sim card ɗin sannan ta kuna wayar ta shiga whatsapp ɗin tunda ba goge shi tayi ba ta dinga kuna voice ɗin sa ta saurara har sai bacci ya kwashe ta, saboda idan bata yi haka ba to fah bata iya bacci, abinda AFREED bai yi tunanin yi ba. Yau dai itama AFREEN ta kasa jure rashin jin AFREED a waya dan haka kawai zuciyar ta ta yita ingiza ta da saka sim card ɗin ta ta kirashi ko zata samun ragin zogin da zuciyar ta ke mata haka kuwa akayi AFREEN take ta ɗoko sim card ɗin ta in da ta ajiye ta saka ta kuna wayar ba tare da ta tsaya komai ba kawai shiga contact ɗin ta, ta nemo number sa ta tura kira daidai ƙarfe 10:12 na safe AFREED ya fito da ga wanga kenan don yin shirin bin jirgin da zai kaisa maraɗi a ƙarfe 11:00 kawai sai yaji wayar sa na ringing babu abinda ya zoma masa a rai sai AFREEN dan kullum yinin yake yana jiran kiranta ko message ɗinta kusan a ko wane lokaci cikin duba wayar sa, dan haka da sassarfa ya nufi bed 🛏️ ɗin sa ya ɗoki wayar sa da mamaki yake kallon number dake yawo a saman screen ɗin wayar shi, ba tare da ya tsaya ƙarasa mamakin da yake ba yayi saurin ɗaga kiran gudun kada kafin ya gama mamakin kiran ya tsinke kuma shi ya maida kiran yaji shi a kashe, yana ɗagawa ya ƙara a kune kamin yake furta wata kalma AFREEN tace "Assalamu alaikum." Da sauri AFREED ya amsa sallamar duk yana ji kamar a mafarki da sauri ya "Dan Allah AFREEN kada ki kashe wayar bari na katse kiran na maido maki kira." Cikin sanyayar muryar ta tace "To" Da sauri ya katse kiran da sauri ya mayar gudun kata kashe wayar yana jin ta ɗaga ya sauke wata irin ajiyar zuciya mai nauyi gaske wanda ita kanta AFREEN saida ta lumshe ido tare da sakin ajiyar zuciyar a ɓoye. *Alhamdulilah wannan gamin dai nayi ƙoƙari* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *Page* : 61&62 Da sauri ya katse kiran da sauri ya mayar gudun kata kashe wayar yana jin ta ɗaga ya sauke wata irin ajiyar zuciya mai nauyi gaske wanda ita kanta AFREEN saida ta lumshe ido tare da sakin ajiyar zuciyar a ɓoye. Ba tare da ya tsaya ko gaisawa sunyi ba ya fara da faɗin "Wife ina kika shiga haka kinyi mugun tayar min da hankali duk na shiga wani saboda rashin ki yanzu kasa jurewa nayi na da rashin muyar ki kuma shiru babu labarin ki, kinga ni nan yanzu nake shirin zuwa Maraɗi har lokacin tashin jirgin da zan biyo ya kusa, inshallah ya zamuga juna nagaji da baye boye gara ayita ta ƙare zanzo na gaida papa sannan na faɗa, idan na dawo sai na turo su dady su zo kawo kudin auren ki ma chérie dan hakan zafi min komai farin ciki in buɗe ido in ganki a kusa dani." Ƙarshen tashin hankali AFREEN ta shige shi ɗan a mugun zabure ta sauko daga saman gadon ta kamar AFREED na ganin ta wani mugun fido ido abinka ga mai ido sai ko suka firfito waje sosai,kamar tana ganin AFREED, a mugun tsorace tace "A'a dan Allah ka faɗa tafiyar ka barta har daga baya ba yanzu ba, kuma papa bai nan yayi balaguro dan haka ba ma sai kazo daga yazo zan faɗa maka sai kazo." AFREED ya ɗan shiga shok jin daga yace zai zo ya gaida iyayen su duk tabi ta rikice, kawai sai yace "AFREEN lafiya kika rikice haka daga na faɗa zanzo na gaida iyayen ki, ko bakison gani na ne ko dai akwai abinda abinda kike boye min ne?" Saidai AFREEN ta daidaita nutsuwar gudun kar ya gane cewa ta ɓoye masa wani sannan ta koma ta zauna bakin gadon tace "Haba kamar dai bana sonka da zance bana son ganin ai kin har akwai wanda keson ganin ka bayana yake to amma ka bari har papa ya dawo sai kayi zuwa guda sai kuzo ma tare da su dady ayi komai da komai ai zaifi ko to ni da kaina na matsu na gammu a inuwa guda muna fira cikin nishaɗi yanzu dai kayi annulé ɗin zuwanka har wani lokaci zaifi." Da khair dai AFREEN ta iya convaincre ɗin AFREED ya fasa zuwa Maraɗi, da ganan suka ci gaba da fira su ta soyayya har AFREEN ta manta da cewa wani za'a aura mata ba AFREED. Yana saura sati biyu auren AFREEN tanti ta gama haɗa abinda abinda bokan su ya bata har layar ta kai an ɗumka mata sedai abinda bata sani ba da take sayan anta rago ta saniya ce aka bata ba tare da sani shima wanda ya sayar mata don rago yakai mayanka aka yanka masa sedai da zai zubo masa naman aka manta aka zuba masa kayan cikin saniya dan haka shima bai sani, a cikin tsakiyar dare ta je ɗakin AFREEN ta saka mayar a filonta dan ranar AFREEN ba a ɗakin ta ta kwana ba, ɗakin mahaifiyar ta tayi ɓaci da rabon dai sai tantin ta samu damar saka mata layar. Sannan da sassafe ta tashi ta yiwa yan gidan break fast abinda batayi koda ranar aikin ta ne sedai ƴan aiki suyi, amma yau dayake akwai wata manufa da take da se tayi kuma ta samu ta zuba maganin duka ga abincin gidan dan gani take aikin ai akan AFREEN aka yi shi ɗan haka ita kaɗai zai ci sannan tace ma ƴan aiki kada su ce ita tayi. Dan haka koda kowa ya fito cin abincin AFREEN bata fito maman ta tashi zata kirata saita ce a bari taje ta kai mata abincin kada a ta kura mata a cewar ta wai tana jimamin barin gida. Babu dai wanda yace mata ufan sai ma dai umma mahaifiyar zeinab da ta rakata da harara. Tana zuwa ta tarda AFREEN zaune a saman sallaya tana jan tazbi sallama tayi bayan wai har ta shiga ɗakin, kallon ta AFREEN tayi ɗan ita rabon da su haɗu har ta manta saboda yanzu ta rage shiga harakar ta tuna ta nuna ta bijire ma Mahaifin kan zaɓin da ya mata, ai take yanke kuma gaban AFREEN ya faɗi tunowa da tayi cewa za'a aurar da ita ga wani wanda ba AFREED ba, a take mood ɗin ya sauya har ida take zaune tantin ta ƙara da ta ajiye mata abincin tace gashi nan nace bari na kayo maki har ɗaka dan na lura tunda ki kaga sati biyu ne yayi saura ɗaurin auren kike cikin alhinin rabuwa da iyaye ko iya fita falo bakiyi bare nayi tunanin zaki je ki gaisa da mu. Gaban AFREEN ne ya yanke ya faɗi jin saura sati biyu auren ta, saboda ita yanda ta ɗauki zancen kamar ba da gaske ba haka yasa ta manta da wani lokaci auren ya kusa sosai hankalin ta yayi matuƙar tashi sedai bata nunawa tantin, wani sankaran murmushi da ta sakar mata tace "Nagode tanti." Tanti tace "Ba komai yi maza kici dan naji mahaifiyar ki na cewa yanzu Wada zata maki gyaran zata zo har an gyara ɗakin da zaki komai domin hakan." Nan ma dai gaban AFREEN kara faɗuwa yayi amma sai ta daure tace "Toh." Sannan tantin ta tashi ta bar ɗakin dan ta mance boka yace mata kada ta bari AFREEN tayi Bismillah ga abincin da ta saka maganin, dan haka ta fice tana jin daɗin burin ta ya kusan cika. Tana fita AFREEN ta buɗe abincin ta fara ci tare da Bismillah bata ci wani sosai ba dan jin yanda hankalin ta ya kasa kwanciya saboda ganin yanda auren da ta manta da shi yake ta matsowa, ta shiga damuwa iya damuwa hankalin ta ya ƙara mugun tashi, dan haka ta kasa zama a kan darduma ta koma saman bed ɗin ta ta shiga rera kuka mai cin rai har saida taji alamun mahaifiyar zata shigo ɗakin nata sannan ta tashi da saurin ta faɗa douche (toillet) ta ci gaba rera kukan ta har kanta ya fara ciwo kamin take fara wanka da sauri sauri dan taji mahaifiyar ta na kiranta. Yana saura sati ɗaya auren AFREEN, duk amarya ta bi ta kare ta rame duk ta lalace sai kyau ɗin nan nata kamar ƙara mata shi ake yi don gyara jiki da ake mata da kuma haɗa mata kayan mata da ake, AFREEN saboda halin da take ciki duk ta koma abin tausayi, kullum kuka abincin ba ta wani cika ci ba, in yau lafiya gobe ba lafiya tun ya sauran sati biyu auren tabi ta firgice idan an tambaye ta mike damun sai tace ji take bata iya rabuwa da iyayen ta duk abin ya bi ya dameta haka mahaifiyar ta zata zauna tana bata baki tare da kwontar mata da hankali. Zata nuna kamar ta kwontar da hankalin nata sannan mama ke barin gun, hasina kawarta kaɗai ta san halin da take ciki, kuma kasa har yanzu sanar ma AFREED cewa ita ga aure za'a mata, amma a yau ta yanke shawarar sanar dan haka ta sanar wa da hasina da ta dawo gidan da kwana tun da auren kawar ta ta ya yi sauren kwana goma da ita ake komai da komai na shirye shiryen biki kuma ta taya ƙawar ta jimami da ƙara mata kwarin gwiwar yiwa iyayen ta biyayya. Dan ta nemeta akan ta taimaka ta sanar wa AFREED aurenta dan kar yaji ga wani yace ta ci amanar sa, amma dakyar ta samu shawo kan hasina ta yarda zata faɗa masa, dan haka dan haka yau safiyar ranar asabar ya kama saura sati ɗaya auren nata suka yanke shawarar kiransa su sanar masa. Suna zaune daga ita sai Hasina cikin ɗaki bayan taci kuka ta ƙoshi, ta mika hannu ta ɗoko wayar ta dake bisa gadon ta dana kira a number AFREED da ta saving ɗin ta da sunan Destiny, tana ta ringing har ta katse bai daga ba dama haka ne idan zata kirashi ba zai daka ba sai ta kashe ya maida mata kira yanzu ma hakane ta kasance, tana katse kiran nashi ya shigo saida ta kusa tsikawa kanan ta ɗaga ta mikawa Hasina wayar gaban Hasina da na AFREEN na faɗuwa Hasina kara wayar a kunan tare da sallama cike da sanhin jiki, daga cen AFREED ya saki murmushi ya amsa sallamar yace "ƙawar mu kece a wayar da fatan kina lafiya ya gida." Hasina tace "Lafiya lau alhamdulilah ya gida ya aiki." A takaice AFREED yace "Lafiya klau ina kawar taki ne dama inason muyi magana dake." Tace "Bata kusa noma kam maganar nake so muyi shiyasa ma na kiraka da number ta." "Ok to ina jinki idan ki sanar da ni noma sai sanar dake nawa abin da zan faɗa maki." Hasina tace "A'a fara sanar dani taka maganar sai na dan ni tawa maganar tsayi ne da ita." Ayi haka naga fa kike ka fara neman sanar dani hakan na nufin maganar nada muhimmanci kada na katse ki kuma." "Ah bai komai ai ni na baka damar hakan." Yace "To shikenan dama ba wani abu bane faɗa maki illa tambaya ce nakeson yi maki akan kawaki, dan Allah nasan ke baki rasa sanin abinda ke damun, dan ta sauya min sosai ka saurin kuka daga nayi mata wata magana haka cikin fira sai kiga ta fashe min da kuka kuma ta daina sakin jiki dani badai kamar yanda muke a da ba dan ni gaskiya abin na damuna kuma idan nace mata zan zo Maraɗi dan nazo gidan sai kiji ta hana ko kuwa idan nace zan Turi Iyaye na nan sai ta ce a'a dan Allah mi hakan yake nufi kodai ta daina sona ne ban sani ba, idan kuwa hakan ta faru ai ban koma yin numfashi dan rayuwa ta ta zo ƙarshe." AFREEN dake sauren duk wani abinda yake faɗa saboda wayar a handsfree take, ta waro ido waje kawai sai ta fashe da kuka mara sauti dan kar yaji tana kusa, sannan tayiwa Hasina nuni data katse kiran. Katse kiran Hasina tayi sannan tace "Besty ki bari na sanar dashi gara ayita ta ƙare idan har kika bari yaji ga bakin wani to ba fah zai taɓa fahimtar abinda zamu fahimtar da shi ba wallahi." "To bakiji furicin da yayi bane ina gudun yaje ya rasa ransa ta dalili na dan Ali ɗan uwansa ya sha sanar dake halin da yayi ta shiga ta dalilin son da yake mani wallahi nidai.... Bata ƙarasa faɗin abinda tayi niyar faɗa ba kiran shi ya koma shigowa wayar ta aiko sai da ta ɗan zabura, Hasina tace "Kin ga besty ya maido kiran ki daure ki bari a faɗa masa dan a fitar dashi daga duhu wallahi gara ya sani yanzu da har sai an daura maki aure yaji labarin lokacin zai fi shiga halin da kike gudu ya shiga kuma Ni nasan mi zan sanar masa." A haka AFREEN ta amince da a ɗaga kiran sedai kamin Hasina ta ɗaga kiran ya katse, ba tareda ɓata lokaci ba ya maido wani kiran." Hasina tace "Yawa aboki kaji na katse kiran ko mama ce kirani shiyasa." Yace "To shikenan ina jinki." Saida da Hasina ta sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya sannan tace "Yawa aboki dama nima sabida wannan changement ɗin ne yasa na kora dan a samu mafita , saida ta ɗan nisa sannan taci gaba dacewa "Ai dai kasan irin son da AFREEN ke maka, kuma koni shaida ce AFREEN ko sauro batason ace ta dalilin ya shiga wani hali bare mutum sanan kuma kai da take so take kauna, ya kamata kayi tawakali ga Allah akan samun AFREEN ko rashin ta a gare ka idan kana hakan na nuna rashin juriya ka akan jarabawar da yake maka sai yaga kamar ka kasa gode masa ne, dan babu wanda AFREEN takeso kuma take kauna sai kai ɗin nan dai AFREED dan haka batada wani buri da ya huce taga kun malaki juna , sedai hakan da wahala dan kuwa wata matsala ta riga da ta Kunno Kai a tsakanin ku bani da tabbacin idan burin ku kai da ita zai cika a gaski...... Hankali a matukar tashe AFREED ya dakatar ta Hasina ta hanyar cema mata "Dakata Hasina ki daina man dogon bayani i man maga yanda zan fahimta dan Allah ki daina kwane kwane dan tunda kika fara magana gabana ke faɗuwa, narasa dalili amma sai nakeji a zuciya ta bana son jin abinda kison fahimtar da ni amma duk da haka ina sauran dan Allah imani da wara wara dan Allah." "To ka kwantar da hankali sai na faɗa maka ta yanda zaka fahimce ni da kyau." Ba zan iya ba Hasina dan Allah ke dai kawai ki sanar dani zan fahimta a haka ma. Hasina taci gaba da cewa "Matsala ce ta taso wani abokin papa ya zo ya nema ma ɗan sa auren AFREEN tun wata biyu da suka huce yau ya kama saura sati ɗaya ɗaurin auren kuma ta kasa bijirewa umarnin iyayen dan sun gama mata komai a duniya, amma kasani AFREEN kullum cikin kuka take da rashin lafiya ta dalilin son da take maka kuma ganin canjin da kayi na wasu yan kwanaki a game da ita to ta wannan dalili ka ko abinci bata ci haka iyayen ta har yanzu basu san da batason auren ba gayama nake ko waya ma basu taɓayi da wanda ake kokarin haɗa ta da shi, shi bai san ta ba ita bata sanshi ba kenan kada kayi condamné kin ta akan hakan ko kuwa kai ka saka kan a wani hali saboda ita kawai kasa ma kanka cewa tuncen da Allah ya rubuta ba zaku taɓa zama a inuwa guda ba dan wallahi AFREEN tana son kamar ta mut yanzu abinda nake faɗa batada wata isasa lafiya, AFREED kayi hakuri dan idan ka tayar da hankali itama ba zata taɓa samun sukuni a rayuwa ta kawai ku ɗoki hakan a matsayin ƙadarar ku." Kaskas sukaji ƙarar faɗuwar wayar AFREED sannan shima yabi wayar, shi ƙarar faɗuwar AFREED ya saka AFREEN sakin wani irin matsanancin kuka mai ban tausayi ta rugungume Hasina tana faɗin dan Allah besty ki taimaka min kada ace ya mutu inna lilahi wa inna ilaihi raji'un wallahi idan wani abu ya samesa bazan taɓa yafewa kaina ba na shiga wallahi shi nake bari naje na faɗawa papa banison zaɓin ya taimaka ya bani wanda nakeso kada na rasa shi na shiga ukuna,' daga nan itama AFREEN ɗin numfashi ta ya farayin sama ta kokowar dawo dashi amma ina sai gata ta idan faɗawa a jikin Hasina jikin ya saki alamun ta suma, Ai dake taya ƙawar tata kuka tana ganin yanda AFREEN ta some ta saki wata irin ƙara itama tana jijigata tana faɗin besty dan Allah ki tashi besty kada ki mutu ki barni Inna lilahi wa inna ilaihi raji'un besty dan Allah ki tashi kada kiman haka taimaka ki tashi sai mu sanar da su papa cewa kina da wanda kike so, Hasina da taga kuka da kururuwa basu gyara ta kawai sai ta sauka a gadon a tsiyace ta ta aza da gudu tana kiran maman maman AFREEN, da gudu duka ƴan gidan suka yo falo hankali a tashe suna tambaya lafiya miya sami AFREEN ɗin amma tsabar ta buɗe kasa cewa kumai tayi sai jan hannun maman take ta na nuna mata ɗakin AFREEN, bakita AFREEN da maman kawai yake faɗa, Ai a kuke mahaifiyar AFREEN ta kwasa ta nufi ɗakin da hannu ta riƙe da na Hasina sai zeinaf da ta mara masu baya a guje ita sai tanti da umma da ha gware sukayi wajen shiga ɗakin sai kuma kannan zeinab da Hamida da kuma mutanen da suka farazu wa bikin, duka dai suka kwasa a guje suka nufi ɗakin AFREEN, maman na shiga ɗakin direct ida AFREEN ke kwance ta nufa tana ta jijigata ta na kiran sunan ta amma ina AFREEN ko jinta batayi haka zeinab da Hasina sai kuka suke suna kiran sunan ta zeinab cewa take Aunty AFREEN dan Allah ki tashi kada ki min haka bani da kamar ki a rayuwar nan idan aka cire iyaye to wa zai dinga mani faɗa da nasiha dan Allah ki taimake ni ki tashi , maman ta tura Hasina daukaruwa a fridge tana kawowa aka zuba ma AFREEN amma ko motsi nan fa suka ƙara rikicewa dan tsananin firgici mantawa ma sukayi da batun asibiti zeinab ce wannan tunani ta bare da tace ma kowa komai ba ta yi wani irin tsalle ta dira a gadon ta fita ɗakin a guje dai dai tana shirin fita a filin dan zuwa kiran Fahad ya zo akai AFREEN asibiti sukayi kicibis da papa ya na kokarin shigowa falon wanda har sai da ta ban gajesa ba tare da ta masan tayi ba da sauri papa ya riko hannun ta yana tambayar "Lafiya mi take ma gudu mai ya faru da ita dawa." Jin muryar papa yasa ta juyo a gigice tace "Papa Aunty AFREEN bata motsi papa taki tash......" Ai papa baisan lokacin da ya saki hannun zeinab ba ya nufin ɗakin AFREEN cikin sauri sauri gudu gudu." Ita kuwa tana ganin ya saketa taba fasa abinda tayi niyya ta koma kwasa a guje ta nufi ɓangaren su Fahad, tun a bakin kofar shiga falon ta ke kwalla masa kira ya Fahad ya Fahad ya Fahad, ya ciki ɗakin sa ya duba litattafan shi na makaranta dan jibi suna da jarabawa yaji irin wannan kiran da zeinab ke masa yasan ba lafiya dan basa irin haka da ita tun ba wasa yake dasu ba, ba ma haka ya cika yiwa kannan nasa baga ba dan shima akwai shegai miskilanci, a daidai ƙofar shiga ɗakin nasa sukayi haɗu a birkice tace "Ya Fahad muje a kai Aunty AFREEN asibiti dan Allah ta kamo hannunsa ta na jan sa a rikice." Riƙe hannun ta yayi yace ke kwantar da hankalin ki faɗa miya sami AFREEN ɗin, tace "Ni bansani suna ɗaki ita da Aunty Hasina sai ga anty Hasina ta fito a guje ta na ce mana Aunty AFREEN muna zuwa muka tarda ko motsi batayi an zuba mata ruwa taki tashi tana faɗa masa tana kuka." Ai ko shima a guje ya kwaso dai bakin ƙofar shiga bangaren su suka gamu da imaran, shima bai tsaya wata wata ba ganin yanda suka wasa a guje shima ya bi bayan su har sai da ya wuce dan shi kan kame da gudu ya shahara da kyar za kuyi yar tsere ka wuce shi gaskiya samun mai wuce shi a gudu to sai an bincike kuma sai an wahala haka kawai Allah ya yi shi. Kamin su kai ga ɓangaren iyayen nasu suka haɗu da papa ya ɗauko AFREEN a hannun zasu je asibiti, Fahad karɓar makulin motar yayi daga hannun papan nasu ya yi sauri ƙara sawa wajen motar ya buɗe aka saka AFREEN baya da ka kwance kamar matata, maman tashiga Ida aka saka AFREEN ta aza kanta saman ciyowin ta, shima papa ya shiga ya aza ƙafafun AFREEN saman jikinsa Hasina ta buɗe wajen mai zaman banza ta zauna Fahad ya shiga mazaunin direba, ya rufe motar ya tada ya ya fice a gidan suka dauki hanyar asibiti, Imaran shima ya ɗoki mota ɗaya ya shiga tanti da umma da kannan zeinab a baya shi yana mazaunin direba zeinab kuma ta gaba kusa da shi. Ita kuma Hamida da yayan alhaji Sadisu da suka zo mata su biyu sukuwa direba ya ɗokesu sai asibiti ya zamana gidan sai ƴan tsurarun mutane da kuma masu aiki da mai gadi. 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *Page* : 63 & 64 AFREED na sakin wayar sa kasa donjin abinda Hasina ta faɗa masa duk ta fashe amma bata mutu ba kuma bai katse kiran ba, sannan kuma shi ba suma bane yayi tafiya ne yayi ya zauna a kasa dabas shine AFREEN ta kamar ya faɗi kasa tayi tunanin wani abu ne ya sameshi shiku wa ya zama dabas ya kama kansa da hannu bibbiyu da yake jin yana sara masa kamar zai tsage jin kukan AFREEN da abinda take yasa hankali da kara tashi amma kuma yaji bakin sa ya yi masa nauyi saboda ya kasa masa masu magana, wanda ita ma Hasina ganin AFREEN na kuka ma manta bata kashe kiran ba, jin ihu Hasina lokacin da AFREEN ta suma yasa shi fita hayacin da sauri ya nufi inda wayar tasa ta faɗi ya ɗauka ya kara a kunne ya na kiran Hasina lafiya miya faru jin tana cewa kada ki mutu ki barni ki tashi dan Allah ya saka shi ƙara rikicewa a gigice ya tashi yana kiran sunan ta kamar tana jin sa dan ko Hasina dake idon ta biyu bata ji sa ba duk da wayar a handsfree take tsananin rigicewa itama ko jinsa ba tayi, AFREED ya kasa yanda zai yi sai yawo yake cikin ɗakinsa shi ɗaya hankali a tashe, duk abinda ake yanaji daga fitar Hasina daga ɗakin har shigowar su maman da shigowar papa da fitar su a ɗakin don kaita asibiti duk yaji, sai a sannan ne ya katse kiran ya yi zaune a saman gadon sa ya yi tagumi dan ya rasa abinda ke masa daɗi ji yake kamar ya tashi ya tafi Maraɗi ya keji amma ina tuna ita ɗin ta wani ce ba tashi ba sai ya jikin ya masa sanyi lakwas. Cikin kankanin lokaci ya kira number Hasina yafi a ƙirga amma tana ta sonner ba'a ɗaga ba, abinda bai sani ita da kanta bata san ida tata wayar take ba har ta AFREEN dan kuwa duk nan ta sake su da ta rikice. Shima ya kasa taɓaka komai kansa sai wani mugun ciwo yake masa kar ya fida shi ya aje, ga farfaru idanunsa su yi wani irin mugun kamar gawauta dole kaji tsoro idan ka kalli cikin idonsa a halin yanzu. Su na zuwa asibiti urgence (emergency room) akayi da ita cikin gaggawa, Hasina da maman da zeinab sun kasa zama sai kai da kawowa suke, papa da Fahad da Imran kusan ɗakin da aka saka a tsaye sauran suna zaune duk sunyi tagumi, duk sun rasa abinda ke masu daɗi, banda tanti da a fuskar ta ne kaɗai ta nuna kallar tausayi, amma a zuciyarta cewa take Allah sa tayi paralysé (ciwon shanyewa ɓaren jiki). Wajen awa uku likitoci su kayi akan AFREEN sannan wani docter ya fito suna ganin su duka suka nufi shi suna tambayar sa ya ake ciki, murmushi docter yayi sannan yace "Ku kwantar da hankalin ku yarinyar ku tana lafiya kawai tarin damuwa ne ya mata yawa sai jinin ta da ya ɗan hau kaɗan amma da ikon Allah mun samu mun daidaita shi yanzu babu wata matsala komai normal, dama abinda yasa muka jima a kanta numfashi ta ne yayi mugun bamu wahala kamin musamu ya daidaita saboda yayi nisa sosai ga barin jikinta to amma da yake Allah ya nufa ta da sauran kwana a doron duniya kunga asamu an shawo kan matsalar, yanzu haka lafiyarta lau sai dai rashin ƙarfin jiki, kuma zai daina ne a sani sanu sai dai munyi mata allura bacci, ta samu bacci karku damu amma ba zaku samu ganin ta yanzu ba sai ta farka dan tana da buƙatar bacci, abinda kuma zai hana a baku sallama a yau shine munason muka yanayin jikinta zuwa gobe da safe sai na baku sallama inshallah." Doctor na faɗar haka yayi gaba abinsa. Duk wanda ke wajen saida ya ɗaga hannun sama ya faɗar alhamdulilah tare da murmushi kwance a fuskar sa amma banda tanti, sai a lokacin maman da zeinab da Hasina suka ɗan kwantar da hankalin su har suka nemi gun zama suka zauna tare da yi mata addu'a, a nan maman ke tambaya Hasina mai ya faru har ta shiga wannan halin. Sai a lokacin ta tuna cewa ashe dole a tambaye ta miya faru ita kuma bata shirya abin faɗa dan haka sai tayi kamar bataji ba abinda maman tace ba, har sai da maman ta sake ta tambayar, ta ɗago tana in ina sannan ta daure ta gyara maganar tare da cewa "Maman babu abinda ya faru daga fa muna cikin fira tana faɗaman cewa ita fah bata son barin gidan su bare garin baki ɗaya, gashi nan har Niamey za'a kaita alhali duk dangin ta suna maraɗi shi kenan sai ta fara rera kuka na shiga rashin ta ai fah da kukan yaci karfin ta sai kawai gani nayi ta sulale a kan jiki ta zube saman bed sumamiya." "Maman da bata fahimci ƙarya Hasina ta sheƙa mata tace "To ba dole tayi hakuri ba, ni da aka kayoni gidan mahaifinta tun daga Agadez har Niamey da kuma daga Niamey ɗin muka yo nan mi yasame ni ko wa nasani a cikin garin banda mahaifin ta, sai ita taki yarda da hukuncin Ubangiji? Ita dai Hasina bata ce komai ba, sai zeinab da tace "Maman ita ma fah zata jure kawai kun san hakan sai ta faru kuma idan ta samu watani ai ni cen gun ta zan koma dan ni idan bata gida bana iya zama gaskiya." Harara maman ta sakar ma zeinab sannan tace "Kun dai ji da shi keda ita ai kusan halin ku guda." Murmushi kawai zeinab tayi. Ba'a wani ɗauki lokaci ba ta farka suka runtuma duka cikin ɗakin suna mata sannu duk sai taji ba da taga yanayin iyayen duk hankali su a tashe saboda ita da sauri ta kamo hannun mahaifin tace "Papa kuyi hakuri na tayar maku da hankali wallah je pas l'attention de le faire kawai Allah ya kawo. Murmushi papa ya sakar mata sannan yace "Karki damu farin ciki family sadisu, dama hakan zata iya faruwa yanzu abu mahimmanci shine Allah ya baki lafiya." Murmushi tayi tare da faɗin "Ameen papa." Kowa hankali shi ya kwanta gani da sauki sosai, ƴan uwa da abokan arziki sai shigowa suke suna duba har da Adamu ƴaƴan papa da matan sa da ɗiyan ida Maryam cousin ɗin ɗiyar Abba Adamu Wada suke kusan sa'a ɗaya ita ta zo duba ta har ta ce ita wajen AFREEN zata zauna, idan ita Hajiya Zakiya kaka su da ta biyo Adamu ta zo tana ta masifa ta cikin gida amma a kasa sanar da ita jikata ba lafiya da so akayi sai ta mutu kamin a sanar dani ko babu dai wanda ya tamka mata." Wasu motoci ne guda uku masu masifar naga sun kun kai a cikin asibitin suka nufi gun parking sukayi daidaita suka tsaya da sauri naga direban motar da tafi kowace mota haɗuwa naga ya fito yaje ya buɗe kofar baya, wata kyakkyawa ƙafa naga an fara zurowa sannan a ƙara fido da ɗayar kamin mai ƙafafun ta fito baki ɗaya, baki da hanci da na saki tare da waro idanu ina mai furta tubarukallahu ahasanul kalikin ne Masha Allah saboda ganin wata haɗaɗiya kyakkyawa nagartaciya mata da tafito daga cikin motar nan kai cewa ma matar nan na da kyau zai iya zama zagi ne wallahi faɗi tana da kyau da tsarin halitta zan iya ƙarasa littafin nan ban gama bayani kyau da tsarin halitta irin nata ba, mata wata irin class lady ba'a ma iya maga. Inna ganin matar duk da bansan ko ita wacece ba naga wata irin muguwar kama da suka da AFREEN da kuma da kyau da komai ita ce AFREEN ta dabo abin ba'a cewa komai, tana ida fitowa wata kyakkyawar yarinya da bata wuce shekara goma ita ta fito wada kana kallon zaka sak mahaifiyar AFREEN, sannan cikin ɗayar motar wasu haɗaɗu samari maza suma suka fito ɗan bai zai wuce shekara 28 years ba ɗan kuwa zaiyi 25years ga su masu ga su farare tass kamar ka kwontala jini ya fito amma duk hasken basu kai matar nan ba wada nake tsammanin mahaifiyar su ce, gani nayi suna nufar shiga cikin asibitin noma nabisu a baya aikuwa zaton ya zama gaskiya dan kuwa ɗakin da aka kwontar da AFREEN nan suka shiga. Suna shiga da sallama AFREEN da ke kwance babu lafiya da ƙarin ruwa a hannun ta tanajin sallama matar ta juyo da ƙarfi daidai matar na ƙarasa shigowa ai kuwa AFREEN mantawa tayi da wani ciwo da wata jinya da take ta ta cire abin karin ruwan babu wanda ya lura saboda suma idon na kan matar nan da ta shigo ai da gudu AFREEN ta diro daga saman gadon marasa lafiya ta nufi matar dake ƙoƙarin karasowa gunta, AFREEN na kai gun matar ta yi wani tsalle ta rukunkumeta kamar ba mara lafiya tana faɗar oyoyo momy jannah oyoyo momy na ita, sai wannan lokacin na gane cewa ashe ƙanwar Arahamat ce jannah dake Dubaï ta aure matar docter Inusa abokin papa AFREEN. Ashe nan AFREEN tayi gadan kyau idan ka ganta ka ga AFREEN zakace itace ta haifeta ba Arahamat ba dan gaskiyar kamar su ta ɓace in badan ita ba mace mai shekaru da zaka iya cewa yan biyu ne ita da AFREEN, murmushi take ta saki kamin ta ɗago AFREEN da rugumar da tayi mata tace "Ma fille (my daughter) irin wannan gudu haka kodai lafiyar ki lau." AFREEN ta shagobe fuska ta ce "Momy na dai ji sauki ne." Momy Jannah ta rabata da jikin ta jawo hannun ta nufi gadon da ita ta zaunar da ita ta tace "Kinga zauna ki ƙara hutawa keda ke jinya kikayi irin wannan tashi haka ba sai kikara jima kanki ciwo ba Ni da nakeson na kuma dake kida yanzun mu tafi cen musha hira kokuwa." "Hakane Momy ai kafata kafarki bazan ƙara koda awa ɗaya a asibitin nan ba." Murmushi Momy Jannah ta yi sannan tace "Inshallah kuwa yanzu za'a baki sallama sai muje gida na ƙarasa maki traitement." Daga nan Momy ta ɗago ido ta kalli mahaifiyar AFREEN tace "Aunty ina yuni mun same ku lafiya." Tana murmushi tana magana Maman ta kaɓe baki tace "Ah sai yanzu kika ganni da kika shigo ai ɗiyar kaɗai ki yiwa magana alhalin ba ita ɗaya ba ce cikin ɗakin." Murmushi Momy Jannah ta ƙara saki tace "Ai ita ke jinya ni kuwa ita nazo dubawa saboda muna sauka a cen gidan naku aka ceman kuna nan asibiti ɗiyata ha ba lafiya shiyasa nawo azama dan na duba lafiyar ina dalilin kun samani IIyarinya rashin lafiya bako tausayi a matsayin ta na amarya ai ya kamata a dinga lalaɓa ta har ai kai gidan ta lafiya, amma tunda nazo yanzu ai shikenan zan ga wanda zai dinga takurata." Maman tace "To ai da dokar ta kike ku tafi cen garin ida kika fito ba sai har auren a fasa ba." "Haba Aunty ai fasa auren nan sai bayan raina wallahi yarinya ta sai ta shiga gidan ministre komin bakin cikin mutun wallahi." Maman najin haka ta san magana ce ta fara yadawa shiyasa bata ƙara ce mata komai ba." Momy Jannah na ganin yayar tata bata ce komai sai ta juya ta fara kallon mutanen dake cikin ɗakin ɗaya bayan ɗaya tana sauke idon ta akan tanti, sai tanti taji gaban ya faɗi da sauri ta sauke kanta ƙasa, ita kuwa Momy Jannah tana ganin ta sauke kai ƙasa ta kwalla mata harara a ranta tace munafuka, dan Allah ya bata wata baiwa idan har ta haɗa ido da mutum idan bai da gaskiya to ta na gane hakan a cikin idon idai kai mugun ne ko munafiki to fah sai ta gano ka ɗan kwata kwata baka iya jure kallon ta cikin ido. Momy Jannah ta maida kallon gun Hajiya Zakiya ta gaida suka gaisa sosai cikin sakin fuska dan Hajiya Zakiya tasan ta tun tana yarinya, sannan ta juya wajen Maryam da Fatima yayan alhaji Sadisu ta gaishe , sannan ta mayar da kallon ta gun AFREEN bata tare da ta gaida umma da tanti ba dan ita Momy Jannah ma ƙaramar mafaɗaciya ba halin da AFREEN ba ɗoko nata ba. Hasina da zeinab suka gaishe ta cikin sakin fuska ta amsa har tana tambaya ya makaranta ta. Dama ita yarinyar Momy Jannah tunda suka shigo ta nufi maman AFREEN tayi zaman ta a saman ƙafafun ta sukuwa yan mazan suka shiga gaida mutan wajen. Nan dai basu wani jima ba Momy Jannah taje gun doctor ta karɓar AFREEN takarda sallama sannan saboda asitin mijinta ce kuma ta nuna masa katin ta na aiki saboda ita likita ce tace masa zata ida kula da ita a gida. Shi kuwa papa tunda yaya sa Adamu yazo ya bishi suka fita tare dan haka bai masan da zuwan Jannah ba. Daga nan suka tattara suka yi gida suna zuwa suka tarda matar yayan su Ibrahim tazo (Wato yayan su Arahamat mahaifiyar AFREEN) da ku ƙanwar mahaifiyar su wada ta riki Momy Jannah sai kuma Ufadi matar mahaifinsu da ta riga ta sadako ma duniya tunda ta aurar da Arahamat da tayi ta yimata sha tara ta arziki duk da mahaifinsu ya rasu hakan baisa suka yadata ba. Gida dai ya cika da ƴan uwa da abokan arziki su Khairat da fauziya kusan kullum suna gida ana ta shirye shiryen biki zuwa dare wajen karfe takwas Fanna kawa AFREEN ita ma ta diro garin yau farin ciki gun AFREEN bai musultuwa, ga Hasina kawarta ga cousin ɗin ta Maryam ita da ta dawo gidan da zama har a gama biki ga Fanna kawarta da ke diffa tare da iyayen duk sun zo ga uwa uba Momy Jannah hakan yasa AFREEN ta saki ranta sosai kamar bata da wata damu daren ranar kwana sukayi hira hada Momy Jannah ta shige cikin su kamar wata yarinya, da sukayi sallah asuba sannan suka kwanta, Washegari misalin ƙarfe 11:00 na safe AFREED ya kira AFREEN a lokacin ta na tsakan kawayenta suna hira tare da son sun mantar da ita damuwar da take ciki, tana ganin mai kiranta saida gabanta ya yanke ya faɗi, ta kalli Hasina, alama Hasina tayi tama da ta ɗaga, tana ɗagawa tare da sallama saida ya lumshe idon sa da yaji Muryar ta, sannan yace kema amincin Allah ya tabbata a gareki AFREEN da fatan kin tashi cikin koshin lafiya ya karfin jikin ki?" "Alhamdulilah" ta furta tare da lumshe ido kamar yana gaban ta. Yace "To madala AFREEN naji bayanin da Hasina tayi man jiya na gamsu kuma kada ki ƙara tayar min da hankalin ki kinji Allah baiyi ba zamu kasance a inuwa guda ba Allah bai saka nine mijinki ba dan haka mu ɗoki dangana ki daure ki yiwa iyayen ki biyayya Allah sa haka shine mafi alkairi amma har yanzu ina ji a jiki na ked'in tawace." Da kuka AFREEN ta fashe masa ta kasa cewa komai, hada rumtse idonsa yayi don ji yanda kukan ta ke shigar masa zuciya,saida ya ɗan nisa sannan yace "Idan kina kuka kika kasa kwantar da hankalin ki zanyi kasa daurewa nima, kuma kisan idan hakan ta faru komai zai iya faruwa dani ko?" Da sauri AFREEN ta tsaida kukan ta sannan tace "Toh shikenan Allah ya baka wada ta fini amma nidai kai nakeso babu wani bance zan iya zama da wani wanda ba kai ba." "Hakane AFREEN ni banji ina iya zama da wata bayanke ba Ni nasan sedai na mutu banyi aure ba." AFREEN tace "Dan Allah kada kaminhaka." AFREED da zuciyar sa ke neman karewa yayi saurin katse kiran gudun kada taji shima kukan yake. Gidan su AFREED anata shirye shiryen biki wanda AFREED kullum yana cikin ɗaki yana jiyar zuciyar sa dake masa ciwo, kuma shi ma bai taɓa kawowa a kansa cewa hada shirin bikin sa ake yi ba kawai ya ɗauka shirin auren Ali da Fariya da Farisa ake yi ba dan kuwa itama Farisa ta samu nata saurayin wanda accounter ne dake aiki a wani babban banki dake Maraɗi wani aiki ne ya kawo sa Niamey suka haɗu ita kuma har su asaka ranar nasu auren tare da na su Fariya. Kwanci tashi babu wuya a wajen Ubangiji yau ya kama saura kwana biyu ɗaurin aure AFREEN, da kuma na su Ali da Fariya, turare kala kala irin iri masu wani irin nagartacen kamshi ake ta yiwa AFREEN gyara da su saboda maman ta haɗa kallan na ta mama mahaifiyar Fanna da ita kanta Fanna da sun haɗo nasu saboda nasun ba kallar na kowa bane wai kusan dai yanda barebari suka iya haɗa turaruka masu mugun kamashi da kwantar da zuciya sun kawo mata shi kalla yafi a ƙirga, sannan ga na Momy Jannah irin na larabawa kai AFREEN sai tayi Hai huwa goma turarukan da aka haɗa mata basu kare dan mugun yawan dake gare su. Momy Jannah da Maryam yayar alhaji Sadisu da maman Hasina sun tafi Niamey tun ga jiya dan yiwa AFREEN gyara ɗaki, wani irin tangajejen gidane kuma haɗaɗe da mahaifin AFREED ya gina ma Ali da AFREED irin ɗaya kuma liƙe da juna gidajen sun haɗu iya haɗuwa Masha Allah, mahaifin AFREEN ba ƙaramin kuli ya kashe mata gaskiya komai na gidan kalan pink ne daidai yanda painting gidan yake ɗaki biyar ne da kitchen da dinning da kuma ɗakin matsa jiki da falon biyu na saman si keda ɗaki biyar na kasan ɗaki uku da kitchen da dinning da gun motsa jiki shima. Ranar da yake saura kwana uku ne aka lefen AFREEN Akwati 28 duk makil da kawa masu mugun tsada ko ba'a faɗa ba kana kallon kayan zaka gane valeur din su Masha Allah, wanda duka kayan mahaifinsa ne ya bama mahaifiyarsa kuɗin taje kasashe daban-daban ta haɗa su ba tare da shi yana san mi suke shiryawa ba dan kuwa har yanzu basu faɗa masa. A na gobe ɗaurin aure akayi walima idan aka shirya amarya cikin wani haɗaɗan matériel red 🍒 mai mugun idan tayi wani sihirtacen kyau sai wani irin kamshi ke tashi a jikin ta wanda ko ke mace sai ya birgeki bare namiji ai shi sedai ya rikice an sha hotuna Su alhaji Sumana da docter Inusa da mahaifin Ali da danginsa AFREED da abokansa da Ali sun zo don abukai guda gare su kuma sun zo a kan ɗaurin auren Ali dan dukan su babu wanda yasan za'a yi auren AFREED har Ali, ida uwayen amaren da angayen suka amince da a ɗaura auren yaran duka a ƙofar gidan Alhaji Sadisu hake ce kuwa ta kasance. Washegari da misalin ƙarfe takwas na sake aka daura auren *ALI DA KHADIJAH DA KUMA UMAR DA FARIYA SAI FARISA DA ISMA'IL DAGA KARSHE A KA DAURA AUREN AFREEN DA AFREED* akan sadaki 100000 ko wane aure auren da ya tara duban mutane dan gayin yawan suma bana baki ce, kowa yayi mamaki cewa hada AFREED aka daura wa aure bare ma abokan sa dan shi yana cen yana waya bai maji an daura aure da shi ba wani abokin sa da mamaki ya gama cikashi ya je idan a ya tsabtace yana amsa waya ya warce wayar yace "Dakata malan da wata wayar ka ta munafurci ashe hada kai za'a daura wa aure shine ka ki sanar damu sai hidimar na Ali kawai mukeyi shiyasa ana shirin ɗaura naka auren kashi ga yin wata wayar karya to Allah ya toni asirin ka. *Kuyi hakuri da kurakurai* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *ZAMBA CIKIN AMINCI* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Écrit Par *QUEEN ZEEFAT* _Ƴar_ _Mutan_ _Niger_ *Wattpad@nazichou* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ *_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_* _*Fin*_ *Page*: 65 & 66 AFREED da bai gane inda ya dosa ba yace "Aure ni?" sai ya bushe da dariya "Auren Ali da kannaina dai." "To rai na min da hankali AFREED idan baka so ne mu sani sai mi." Abokin na sa yayi fushi. Zai juya AFREED ya rike shi yace "Wai mikake nufi ne mu zai sa na ɓoye maku aure na ne wallahi banda ni." Haba AFREED yanzu naji an daura maka aure da kunnuwa na naji sunan ka da suna wata mai irin naka sunan sannan kuma kacemin ba haka bane to mai dani ƙaramin yaro... Kamin AFREED ya yi magana sauren a bokan su kayi ƙaraso sunana ta masa masifa, shi dai kansa ya kulle ya rasa gane inda suka dosa AFREED da idonsa suka fara cenza kalla ya ɗago ya kalli Ali da alamar tambaya, shi Ali ɗaga masa kai kawai yayi dan shima yana cikin shok kwata kwata iyayen nasu basu sanar dasu hada AFREED a daurin auren ba, shima sai yanzu nan yaji abakin dady bayan har an daura auren yake tambaya sa abinda yaji gaskiya yace masa hakane ba ƙarya ko ɗaya a ciki. Dan kiɗimewa AFREED kasa magana yayi ya nufi motar da ya zo da ita ya shiga ya yi tafiyar ba tare da ya tankawa ko ɗaya daga cikin abokan nasa ba, Ali yake fahimtar dasu cewa shima baiwa labari kamin sun hakura da masifar da suke masa. Yana parking baki ƙofar gidan Aunty A'isha ya sauka ya wuce ɓangaren da suka sauka ya ɗauki kayan sa sai filin jirgi, za'a tayar da jirgin ya tura Ali test cewa shi ya koma gida ya zo filin jirgin ya ɗauki motar makulin na ga wani ma'aikacin jirgin zaman abokin sa yake babu inda aka diresa ya Niamey ya zuwa kuma bai nufin gidan su ba dan yanada bukatar hutu da tunanin makomar wanan auren dolin da aka yi masa. AFREEN tunda aka daura aure take kuka har da suma sau biyu da an tambaye ta sai tace ita batason ta bar gida da khair Momy Jannah ta samu ta lalaɓa ta ta fara yi mata nasiha da kuma ƙara mata karatu kan zaman aure ta yi ta koya mata yanda ake zama da miji ta kowane fanni komai AFREEN an nuna mata tayi komai na kula da miji tunda Momy Jannah ta dawo daga Niamey dan tace ita zata raka ɗiyar ta ha ɗakin miji bazata tsaya cen ba har sai an kai mata amarya ita zata zo ta ta fi da ita, take ta aikin rarashin AFREEN tare da yi ma nasiha. Bayan anyi sallah azahar wajen karfe uku gidan su AFREEN ya cika makil da mutane tanti ta sakankance cewa maganin ta yaci tunda hayanzu papa bai shigo ya koreta ba sai fara'a take, ai bata ƙarasa tunanin ba papa a gaban rai a matuƙar bace yana mata wani irin kallon da sauri ta tashi ta rike hannunsa da nufi ta ja shi suyi ɗaki amma ina sai ya warce hannun sa da ƙarfi tare da cewa cikin ɗaga muyar cikin bainar jama'a da gidan "Sakina (Tanti) tashi ki tattara kayan ki ki bar man gida macuciya azzaluma an namimiya na sake ki saki ɗaya tattara ki bar man gida ban son na kara ganin ki na tsane ki na kara maki wani sakin kije na sake saki biyu." Tanti da hankalin ta ya tashi ta rikice da sauri ta rufe masa baki dan kar ya ida cika mata na uku da niyyar ta bashi hakuri da sauri anty hawa ta riƙe tana faɗin "Sakashi Sakina kada basa hakuri wallahi kin manta abinda aka faɗa maki, ki tashi muje in ya wuce sai ki dawo kamin ya kai ga cika maki uku baki ɗaya." Ai Tanti da hankalin ya gama tashi ko sauran yar uwar tata bata yi ba kawai ta shiga bama papa hakuri ya yafe mata kamin take gama basa hakuri kenan ya idasa furta mata saki na uku duk da hakuri da mutane ke bashi dan ba wanda yasan abinda ya masa dan kuwa ko shi ba zai iya faɗa maka ga abinda ta masa. Yana ida yima saki na uku ai kuwa sai buga hannun da hannu tace shikenan ai dama dole ka sakeni tunda na maka asiri na kada kara haihuwa tunda nima tawa ta tsaya kuma duk auren AFREEN da ke sakawa rana ana fasawa nicenan keyin asiri na yauma nayi asiri kansa amma bai ciba gashi ni ya kama Arahamat ma ninayi asiri ta daina haihuwa tun kamin na maka da na ita umma zeinab tanayi sai na yima ka ɗan kowa ma ya rasa kai gaskiya na ji dadin wannan sakin amma kar damu zan komo gidan kuma bacin na nayi asiri kalla kaza nayi na kaza," haka dai tayi ta tunawa kanta asiri har sai da takai aya, mutanen da suka taru wajen suka cikin da mamaki abinda idan har ba da bakin ta gayi ba kuma gaban su to wallahi yanda take masu kirki zasu iya cewa karya ce saboda shiru shirun ta ashe lumbu lumbu ce macijin kaikai. Masu mata ya shirya suna mata masu zagin ta na mata kowa da abinda yake faɗa, papa da shok ta kama shi da mamaki ya ja ta hannun har waje ya fida ta Hajiya Zakiya nace masa mita masa tun ita batasan mike faruwa saboda yanzu tajiyo hayaniyar ta fito , papa kuwa bai ma bi ko takan mahaifiyar tasa ba sedai ya ga ya fida ta daga gidan mutane nace masa kada aje ta haukace ne har take tonawa kanta asiri ka ya sake taje tayi wani gun, Tajuyo ta kalli mutanen dake ke faɗar hakanan tace"Lafiya ta babu wata haukacewa da daniya kuma zan baku mamaki ta fara gayi sunan wanda ta sani a cikin su sannan ta kalli papa tace "toh kaje ka ɗako man hijabi ai kasan ba zan bi hanya haka ba." Tace bani ɗaukowa kuma bazaki kara takamin gida ba nan aka bashi hakuri yasa aka miƙo mata hijab tayi gaba abinta ko kunya babu. Dan ita Aunty hawa tana fara tonawa kanta asiri ta fice daga gidan. Biki sai ya komai na yada magana da kuma jimami da yi mata Allah ya isa Hamida ɗiyar ta kuwa ta shige ɗaki uwar tanata kuka. Taro dai ya tashi lafiya inda sai washegari za'a tafi da AFREEN gidan mijinta, ida da dadare Hajiya Zakiya ta tara albarka Alhaji Sadisu da matan da yaran tace sai an faɗa mata abinda ya sa ya yima tanti korar karya a bainar jama'a, saida ya nisa sannan "Wallahi Hajiya Ni bata min komai ba kawai ina waje sai na rin gajin na tsaneta bansan dalilin nayi ta kokarin kwantar da hankali na amma abin ya citura kamar ana hura man hutar kiyayar ta cikin zuciya hardai na kasa jurewa sai nazo na mata wulakanci sannan naji sallama kuma daga haka sai ta fara tu nawa kanta asiri abinda ta ringa yi nasan hakan yanada nasaba da abinda ta jayowa kanta. Washegari misalin ƙarfe 11 iyaye sun gama yiwa AFREEN nasiha aka shirya don kaita gidan ta da kukan ta da komai dan tana tirjewa ita bazata ba da khair mahaifinta ya lalaɓa dan ganin lokaci na kurewa saboda jirgin ƙarfe sha biyu zasu ya kaisu Niamey ita da uwan raki yar ta da zasu tafi Mandela hada hawaye duk juriyar ta ba wanda tayi kuka cikin diyanta don an masa aure za'a kaisa gidan miji sai ga AFREEN ko dan ita ba'a gari guda zasu zauna ba oho. Anty fauziya, Aunty Khairat, umma zeinab, Momy Jannah, Hasina, Fanna, zeinab Maryam, da anna mata baba Adamu sune ƴan rakiyar amarya gidan ta kuma su duka a jirgi guda zasu da amarya. Ba'a dauki wani lokaci ba suka sauka cikin garin Niamey gidan tanti Mariam yaya alhaji Sadisu suka sauka dan sai gobe za'a kai amarya gidan mijinta saboda shima Ali sai gobe za'a kai masa tasa dan ita ma har sun sauka gidan dady wajen Momy su AFREED Tunda mahaifin AFREED ya dawo Niamey yake neman sa bai gansa ba kuma da an kira wayoyin sa a kashe Ali kaɗai yasan inda yake kuma yace kada ya faɗa yana son ya huta ne Washegari da misalin ƙarfe 9:00 AFREED ya shigo gidan bai zarce ko ina ba sai ɓangaren Momy yana shiga ya tardo ta ita su Fariya da Khadijah Farisa kaɗai aka kai gidan mijinta Fariya kuwa sai sai idan anty aicha zata koma sai su tafi tare da sauran dangin mahaifiyar ta, suna ganin ya shigo fuskar shi ba annuri suka tashi su kayi sama suka barshi tare da Momy yan kai kusa da ita ya zauna saman kafet ya gaida ta ta amsa cikin sakin fuska sannan tace "Ango ka wani je ka ɓuya har amaryar ka sun sauka kai baka ma sani ba." Ɗaya kai yayi ya kalle ta sannan yace "Momy kenan da sanin ki aka min auren doli ko ki sanar dani ace sai bayan ɗaura man aure zan sani." Mahaifinsa dake sauka daga saman étage yace "Mahaifiyar ka batada laifin komai koma miye nine ke da laifin tun ninace kada a sanar da kai in ma laifi aka maka to ni nayi shi tunda gani kake an maka laifi. Har ya sauko ya kawo inda suke zaune ya zauna kusa da Momy, AFREED ya ɗago ya gaida shi ya amsa ba yabo ba fallasa. Kusan kamar minti biyu babu wanda yace wani abu, sai dady yayi gyaran murya ya ce "AFREED Ni ba yi ma aure dan bani sonka ko kuwa auren doli ko saboda wata manufa ko dan na bata maka rai ba a'a asalima gata na maka amma ba zaka gane haka ba sai nan gaba, dan kanka zaka gane ko wace irin mata na aura maka kuma babu yanda banyi da kai ba kan ka fitar da wata amma fir kaki dan haka na maka zaɓi idan kuma ka nagani laifi aka maka toh rubuta takardar sakin yarinyar mutane ka bani tunda kai ban isa da kai ba, ita da iyayen ta suka isa da ita ai gashi bata sanka ba ta taɓa ganin kaba amma ta baro iyayen ta da garin su da gidan su dan yiwa iyayen ta biyayya, kai kuma naga za'a samu akasin haka." Da sauri AFREED ya ɗago yace "Haba dady wallahi ba haka bane ko huta kace na faɗa zan faɗa ka sani ban taɓa bijire ma umarnin ka ba kawai dai nace yaka mata in sani kamin a ɗaura auren dady amma banci haka bance komai ba, Allah dai ya bamu zaman lafiya Allah sa ita ɗin alkairi ce. Murmushi Momy da dady su kayi sannan a tare suka ce Allah maka albarka. Dady yace "Tunda hakane inaso kaje ka gaida iyayen ta zan tura maka address ɗin gidan da suka sauka kamin dare ka tara abokanan ka aje dauko amarya, ai kasan gidan nan da na baku cen za'a kaita déjà iyayen ta sun gama saka komai a ciki an gama gyara gidan ." Sannan yace inchallah dady kamin yake tashi ya bar masu gidan baki ɗaya a ransa yake cewa ai inda wallahi tayi mata yawa ita da kanta zata nemi na sawake mata ba dai ta yarda aka aura mata ni ba zata gani (nikuma nace kkai zaka gani ba🤣🤣🤣🤣🤣🤣 ) Ali ya nema ya rakesa suka je gaida su Momy Jannah inda Momy Jannah ta tsare shi da masifa tace "Kaga badan ba'a son yarinyar nan aka aura maka ita ba asali ba duk gidansu ita aka fiji dan haka wallahi ba minister kake ba ko shugaban ƙasa kake ka kuskura kayiwa yarinyar na wani abu mara dadi wallahi da kaina zan zo na sameka na rama mata ba wasu nake kuma wallahi ɗan jinjirin aiki bane." AFREED ya ɗago ya kalle ta dam dam gaban sa ya faɗi ganin muguwar kama da matar take da AFREEN ɗin, a take zuciyar sa ta fara raya masa cewa kodai AFREEN ce matar da aka aura masa ɗin, amma ina inda itace ai da ba haka ba kawai ta fara maya kizo ne da duk abinda ya gani sai yaga kamar ita. Hardai Momy Jannah ta gama masifar ta suka tashi sukayi tafiyar su Ali dai na ta masa dariya a hanya yana cewa ashe dangin fitina aka aura maka. Dadare aka shirya AFREEN cikin wata irin narkaka shada pink kalar kayan da aka saka mata a ɗakin ta da kuma painting ɗin dake ga gidan, shada ta sha aiki blue 🔵 Masha Allah da AFREEN da shada duk sun haɗu iya haɗuwa ta saka takalmi blue 🔵 gyale blue 💙 sarka blue Kai komai blue 💙 aka mata kayin kyau wanda AFREEN tayi ɓata lokaci ne dan ko ba kwalliya ita mai wani irin ni'imtacen kyau bare yanzu da aka haɗa da kwalliya bare ita da bayi take yi ba to ya kuke ganin zata zama a daren, kowa sai santin kyau da tayi ake Masha Allah. Angaye basu jima ba suka zo ɗauka amarya, da ke ta zuba wani uban kamshi mara misali na turarukan ta da aka haɗa mata iri iri na barebari na buzaye na larabawa na Ethiopia gasu nan dai ba'a cewa komai sai fatan zaman lafiya da ango. Ana ɗaukar amarya gidan surukan ta aka fara kaita inda suka samu tarba ta karamci kamin ake nufa da ita gidan wooow Masha Allah gidan AFREEN ya haɗu iya haɗuwa komai na gidan pink sai ratsin blue da ke akwai kaɗan kaɗan shoglass da ke akwai ta tura ta kai bakwai huɗu saman uku ƙasa. Ƴan kan amarya basu wani jima ba suka yi tafiyar su bayan Momy Jannah da su Aunty fauziya sun ƙara mata huɗubar Zama Da miji yanda zata kama abunta hannu bibbiyu tana kuka na fita hankali har suma sai da suka koka dan ta basu tausayi matuƙa amma babu yanda suka iya dole su tafi su barta dan suma duk haka suka ji Fanna da Hasina kaɗai suka zauna cewa har abokan ango su zo sai su tafi dasu. Bayan wani lokaci ango da abokansa suka shigo suna ta raha ango na zaune kusa da amarya bai nunawa kowa cewa baya sonta ba amma a ɓoye kamar ya shaƙeta ta mutu yakeji, su Hasina zasu fita ta riƙe tana ta kuka tana cewa dan Allah kada su barta har yanzu yakan rufe ba'a buɗe ta ba. AFREED ya dawo daga rakiyar abokansa bai zarce ko ina ba sai ɗankin da AFREEN ke ciki har yanzu da mayafi liƙe da fuska ta da ƙarfi ya ja mayafi ya yi jifa dashi gefe yajuwo da karfi yace "Kai sai.... Ai ba ƙarasa faɗar abinda yayi niyyar faɗa ba idon suka sauka a kan kyakkyawar fuskar AFREEN da ta sha kuka take cikin yinshi ma zaro ido yayi ya rasa bakin magana da shi niyyar sa ya mata wulakanci amma mi sai ya Wada bai taɓa tsammanin gani ba da sauri ya koma kusa da ita ya zauna jikinsa har rawa yake, ya kamo hannun ta, ita tunda suka yi ido huɗu kukan ta ya tsaya cak tana wani mugun mamaki. AFREED cikin i......ina..... Yace "ke..... ce ..... ko gizo kike min AFREEN ya muza idonsa ya ƙara murzawa ya buɗe su ga fuskar ta ya gudun kada ace mafarki ne yake. Ita ma AFREEN cikin rawa jiki tace "Ya akayi haka." Cike da farin ciki AFREED ya mata yara irin runguma mai kyau duk ya rikice ya rasa ma mi zai faɗa, ai sai hawaye suka shiga ganga to masa daga cikin ido yakai kusan minti goma yana rugume da ita kamin ya saketa ya ɗaga hannu sama yana gode ma Allah da hawaye tafi a fuskar sa, hamdalah sukayi su duka ta rada yiwa iyayen su godiya da suka yi masu wannan haɗin sunata kwarara ma iyayensu addu'a. Da farin ciki ya ishe su sai suka tashi suka nufi toillet suka ɗauro alwala suka yi nafila raka'a biyu ta suna godewa Ubangiji sannan ya fita ɗauka kazar da Ali ne ya siya guda biyu ya bashi ɗaya ba dan ya so ba ya amsa ashe zata mashi rana, ya shiga kitchen ya ɗauko plet da cofi ya kawo masu har ida take a zaune ta kasa kara ɗaya ido ta kalle saboda kunya, da khair ma yasa mu ta ci kazar kaɗan dan ya ɗan lalaɓa ko son wani abu ya taɓa baiyi kamar wata jinjira. Har dai suka gama ya umurce ta da ta je tayi wanka shima zaije yayi ya dawo. Yana dawowa har tayi wanka ta shirya cikin kayan baccin ta haye gado ta rufe da da bargo Dan a garin a dan sanhi ga kuma sanhi ac, shima ya zuwa bai tsaya komai ba ya sama ɗakin key ya kashe huta ya dawo kusan ya kwanta tare da sakata cikin jikinsa ya na shafa gashin kanta tanjin shi ta lahe dan duk a tsorace take, da shafa ya koma sha fa mata kunne daga nan ya kuma ga bakin har dai ya kasa jurewa ya shiga aika mata wani zafafen kiss daga nan kuma salo ya canza, a ranar dai AFREEN ta wahala iya wahala Allah ne ya kare bata suma ba dan sai AFREED ya maida ta cikakar mace sannan ya raga mata badan ya kaushi ba shima kiran sallah asuba ne ya fargar da shi cewa ya illata ɗiyar mutane Sannan kuma ya koma lalashi. Da safe Momy ta ai ko masu da abun kari duka gidan biyu wato gidan Ali da AFREED. Su Hasina suka zo mata bankwana anan take shaida masu cewa ashe masoyin ta papa ya aura mata. Sati biyu da auren suka shirya sukaje gidan su AFREED gaida iyayen sa nan Momy ta sakata ɗaki ta haɗo mata kayan mata da turaruka irin nasu na barebari. Bayan shekara takwas wata class lady ce na tsikaya cikin wani katafaren gida wanda dukan shi glass ne ina ƙara kura ido na hango AFREEN ce tayi ƴar ƙiba ta ƙara kyau fatar jikin sai sheƙi yake dan hutu wannan form ɗin tata ta kara fitowa, da wasu kyawawan yara guda uku namiji biyu mace ɗaya wanda tun haihuwa ta fari ta haifesu shi bata ƙara haihuwa ba sai yanzu da take ɗauke da tsohon ciki Hasina tayi aure Ita a nan cikin garin Niamey da yaranta biyu Fanna kuma tana Dubai babban ɗan Momy Jannah ya aure da yarta guda sai zeinab ita ɗan Momy Jannah na biyu ya aure ta suna Turkiya, Fariya da Farisa duk sun haihuwa Farisa ta samu ƴan biyu duk mata ita kuwa Fariya ta samu namiji Khadijah matar Ali ita ma yaranta biyu mace da namiji zeinab ana ɗauke da tsohon ciki. Maryam tayi aure da yaranta uku tun da tana saurin haihuwa Umma zeinab ta rage masifa da ma ita sharin shaiɗan ne amma ku gidan malamin tsibo bata sani ba bare gidan boka ta nemi alhaji Sadisu da Arahamat gafara yanzu suna zaman lafiya. Ita kuma tanti daren da AFREED ya sadu da AFREEN ta haukace ta bi duniya babu wanda yasan ida take ta girbi abinda ta shuka AFREED da AFREEN kullum sai ƙara son juna suka cikin aminci *ALHAMDULILAH* *ALHAMDULILAH* *ALHAMDULILAH* Anan na kawo karshen wannan littafi Mai taken *ZAMBA CIKIN AMINCI* kuskure da nayi Allah ya yafe mani sai mun haɗu a sabon littafi na dai zai zo na ba da jimawa ba. *Bisallam* *Sai mun haɗu a sabon littafi na ina ma kowa fatan alkairi*