[1/23, 10:30 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS* *ASSO...💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN💞* *SLIMZY✍🏼* *Wattpad@slimzy33* *1* Daga zaunen dayake saman wheel chair ya d'ago ido yana kallon ta yana saukar mata da murmushi me sanyaya zuciya, Tabare masa fuskar nan tayi wane zatae kuka "Amma ni Yaa zain banace wai idan kanajin wannan abin ba ka dinga adu'a dan Allah" kanshi dayake a karkace ya k'ara juyarwa yawun bakin nashi suka k'ara gangarowa zuwa saman kirjin sa, da sauri ta sanya tissure ta share masa su ta wurga a kwando, lokaci d'aya k'wallan datake k'ok'ari tarewa ya silalo mata da sauri ta sanya bayan hannunta ta d'auke shi tana me kawar da kanta karya gani, wani azababben bak'in ciki ne ya taso mata ya tokare mata k'irjin ta zuwa wuya, da k'yar ta had'iyi wani yawu me d'acin gaske sannan ta furta "Sannu yaa Zain, yanzu inane yake maka ciwo?" Kasa magana yae sabida abinda yakejin yana taso masa yana danne masa mak'oshinsa da k'yar yake numfashi ma, hannunsa yakai yana shirin mak'ure wuyansa da sauri ta rik'eshi ta soma karanto masa adu'o'in tsari tun yana k'ok'arin qwacewa harya hakura ya lafe tayi ta masa adu'a kusan 15mns ko ita gumi takeyi, seda taga ya lafe alamun yashiga duniyar bacci sannan ta sakeshi tasoma kuka wiwi tamkar wata zararriya, tausayi sosai yaa Zain yake bata d'an sarki guda d'aya, lamarinsa kullum sekace me ciwon iska, tayi wa Sarauniya maganar amasa na gargajiya amma ta kafe akan haka Allah ya haliccesa, wane ciwon ne bashida magani?" Jansa tayi zuwa cikin b'angaren sa har tsakiyar d'akinsa sannan ta kira fadawan sa suka kwantar mata dashi, kallon bafade d'aya tae tace dashi "Nasan halin baccin sa baze wuce 1 houf ba bari zanje na dawo, idan ya farka kafin 1 hour ka aika akirani" tana gama fad'ar haka ta juya ya bita da harara, an baiwa yarinyar nan dama da yawa, harsu take commanding irin haka?..... ******** Hararar sa ta keyi sosai, yanayin kallon dake idanta kurin ya isa ya sanya kasha jinin jininka, sadda kanshi yae a k'asa cikeda rotso, besan kose yaushe ze dena tsoron ta ba, besan kose yaushe zata dena shiga rayuwar sa ba, meya mata ne wai? Aduk fad'in masarautar nan bashida abinda ya tsana da gani sama da ita, gata sekace aljana duk inda yae idonta na kasan "Idan abinda nake fahimta daidai ne kana nufin bazaka sab'awa waccem jakar ba kenan?, so kake ka nunamun kai kanada taurin kai da kafiya ko? Dacen dawa kake amfani bada 'yar taka ba! Se yanzu danka gama rainan hankali zaka ce wai baka san yan da zaka datse alak'ar tasu ba" D'agowa yae ranshi ba dad'i, xuciyarsa tamkar zata fasa k'irjinsa tayo waje yace "Kece kike amfani da ita bani ba, tun faruwar al'amarin nan roqon meye ban miki ba akan ki sake kuruwar yaron nan? Ya kamata kisani nifa ba yaronki bane ba, banida kuma almakashin datse wannan alak'ar kece kike dashi, keda kima dasa alak'ar tasu tun suna jinjiraye" Cikin baqin ciki tabishi da kallo "Amma ba haka mukai dakai ba, wannan aikin tare muka faroshi kuma da sanya hanmun 'yarka da ita akayi komai ko kanaso ko bakaso, idan ma so kake lallai seka had'a aure a tsakaninsu ka sani zan fasa k'wai kowama ya huta" Yanzukam idan shi yayi ja jajir "Bazan miki uzuri ba kika sako Ummaty acikin maganar nan, kece kika turata kece zaki warware komai, yanzu yara sunyi shak'uwar dabazasu iya rabuwa ba shine zaki tayarmun da hankali" A yamutse ta kallesa "Da gasken kake mafarkin had'asu aure kake kenan, kasan Allah wlhy tsaf zan b'atar da Ummatyn inga k'arshen iskancinka" Mik'ewa yae daga zaman dayake ya bugi babbar rigarsa "Ga fili gamai doki, wacce bata tsoron Allah kawai" yae ficewar sa,Koda ya fito hanyar fita yayi gidan gabaki daya saboda tsananin bacin ran da ya tsinci kansa.... ********* Tunda ta shigo gidan take kuka tamkar wadda aka aikowa da sakon mutuwa ko hijabin jikinta ta kasa cirewa neman waje kawai tayi gefen mahaifiyarta ta zauna Tana sharar hawaye.... Kallon ummaty takeyi cike da kulawa da tsananin tausayin Yar Tata,dakyar ta sauke gwauron numfashi takai hannunta kafadarta ta dafata ta Soma magana cike da kulawa, "ummaty lokaci yayi da Zaki daina zubar da hawayenki Domin rashin lafiyar zainul abideen,zuwa yanzun ya kamata ki fahimci cewar wanan lafiyar tashi daga Allah ce Allah ne kadai zai iya yi Masa maganin rashin lafiyar Nan tasa ba wani Dan Adam ba sai addua da zakiyi mishi na samun sauki daga ubangiji Amma kuka Babu abinda zai Miki sai Karin bakin ciki da damuwa da zai saki kinji ummaty?"ta karasa maganar cike da kulawa, Idanuwanta sunyi jajir saboda kuka fuskarta jike da hawaye ta juyo ta dubi mahaifiyarta cikin shasshekar kuka "innah ki duba kiga halin da zainul abideen yake ciki Amma Mai martaba yakasa yin wani Abu dangane da rashin lafiyar ta dansa daya tilo namiji a cewarsa Wai rashin lafiyar ya zainul na asibiti ne bana gargajiya ba kullum saidai a daukesa a kaisa asibiti ayi gwaje gwaje a tilo magunguna a dawo batare da ansan takamai man abinda yake damunsa ba,yanzun Haka innah nabaro sa a kwance Yana bacci saboda ciwon nasa ya motsa dakyar nasamu bacci ya daukesa"ta karashe maganar cike da takaici ta Sanya hannunta ta share hawayen dake fuskarta, Tsananin tausayi yasanya innah kasa magana kusan minti biyar idanuwanta na Kan Yar Tata Tana sauraren sautin kukanta dake fita,...ta lula duniyar tunani sallamar da sukaji CE dukkansu ya sa suka juya suna kallon hanyar shigowa, Fuskarsa Babu walwala ya karasa shigowa cikin gidan inda suke zaune a tabarmar kaba a tsakar gidansu,yanayin fuskarsa kadai zaka kalla da kwayar idanuwansa kasan Yana cikin tsananin damuwa ,dukkansu hankalinsu na kanshi ganin yanayin nasa ba yadda ya Saba shigowa cikin gida ba, Innah ce ta dubesa cike da kulawa tace "barka da shigowa sarkin dawaki" "Barka"shine abinda yace mata a takaice, "Ya Naga yanayin naka Sam ba a yadda ka fita ba ko wani Abu ya faru ne?" "Babukomi kawaidai ranar garin ce yau sai a hankali kawomin ruwa insha"ya kauda maganar Yana Mai duban inda ummaty ke zaune wadda fuskarta Tai jajir saboda kuka.... "Ummaty lafiya na ganki haka?meyasameki fuskarki kamar kinyi kuka?" Hawayen da take kokerin boyewa ne suka sulalo Mata a fuskarta tasa hannu ta goge hade da Jan hancinta,cikin sanyin murya irin nata ta Soma magana "baba wallahi dama rashin lafiyar ya zainul ce yau ma ta Kara tashi Dan yau bakaga abinda yayi ba wallahi gwanin tausayi baba" Saida gabansa ya fadi Jin sunan zainul data ambata a bakinta Amma sai ya dake Yana Mai Kara fuskantarta"shine dik kikabi kika tada hankalinki kenan ummaty?ki kwantar da hankalinki zai samu sauki matukar Yana Shan maganinsa Wanda kike basa insha allahu zai samu lafiya kamar kowa kinji?" Gyada kanta tayi ciikin sanyin jiki ta bude baki da kyar ta amsa da "Allah yasa" "Ameeen"innah ta amsa da shi Tana Mai mikawa mahaifin nata ruwa.... ********* Tunda garin Allah ya waye yake kwance a Kan gadonsa Wanda saidai a kwantar saidai a tayar bakinsa Yana Nan yadda yake kamar kullum a karkace miyau na zuba a gefen rigarsa ya zurawa kofar dakin idanu... Turo kofar da akayi ne yasa fadawan dake dakin saurin Shiga taitayinsu hade da zubewa kasa lokaci daya suna kwasar gaisuwa... "Barka da zuwa ranki ya dade sarauniya rumana uwar gida a wajen sarki Mai martaba" Hannu kawai ta daga musu cike da Isa da izzah Wanda indai sarauta ce kallo daya zakai ma wadda aka Kira da sarauniya ka tabbatar da ta amsa sunanta.... Gefen gadonsa ta tsaya Tana karewa zainul abideen kallo Wanda bemasan tanayi ba idan har idanuwanta ba gizo sukeyi ba to tabbas ko motsa idonsa yau bayayi da alamar ciwon nasa Yana kusa, Cike da tausayawa ta sunkuyo daida fuskarsa Tana Mai dubansa cike da kulawa a Fili take fadin "Allah sarki zainul Allah ya baka lafiya kamar kowa kaji?Allah ya yaye maka wanan ciwon naka ya tashi kafadarka"Tana maganar ne Tana shafa gefen fuskarsa Wanda da alamu bemasan tanayi ba, Takai minti goma Sha biyar cikin dakin da kanta ta dagosa ta jinginasa da jikin gado takai hannunta gefen gadon ta dauko wani farin towel me kyau ta Shiga share Masa miyaun dake zulalowa daga bakinsa hannunta daya na kansa Tana shafa kansa cike da kulawa, Baiwarta dake tsaye ta dubeta "zubamun breakfast dinsa Dan da alama beci wani Abu ba" Da sauri ta juya table din da aka jera kulolin abinci Wanda dama Nan ne ake aje Masa abincinsa dik lokacin da aka tashi bashi saidai a Diba,ta dibo abincin ta zo har kasa ta tsugunna ta Mika Mata... Bude kofar dakin akayi da sauri gimbiya rumana ta juya suka hada Ido da Mai martaba sarki gefensa wata matace matashiya ke biye da shi sai fadawa da bayi dake take musu baya, Murmushi Mai martaba yayi lokacin da yake karasowa gaban gadon na zainul abideen,"Gimbiya rumana uwar zainul abideen yau da kanki Zaki bashi abincin?lallai kinaji da wanan yaro naki" Murmushi ta sauke "barka da tashi ranka ya dade" "Barkanki,ya jikin Dan naki?"...Nan da Nan fuskarta ta canja idanuwanta suka kawo ruwa ta sunkuyar da Kai batare da tace komiba, Ganin Haka yasa Mai martaba girgiza kansa tausayinta da soyayyarta na ratsa sassan jikinsa yadda ta shaku da zainul abideen take kulawa dashi komi nasa itace ko kyamarsa batayi mahaifiyarsa batayi Masa hakan,kodan hakan nada nasaba da yadda ta shaku dashi tun daga haihuwarsa?kasancewarsa shine da namiji a fadin masarautar? ********* Tunda ya doso harabar sashinta gabansa ke tsananin faduwa saboda fargabar yadda zasu kwashe shida ita... Da sallamarsa ya Shiga babban parlorn nata Wanda ya kasance Nan ne wajen sirrin su Babu kowa bakajin sautin komi sai karar fanka dake gudu a parlorn, Gefen kilisa ya nema ya tankwashe kafa zuciyarsa na harbawa sauri da sauri Tana tsaye ta harde hannuwanta ta baya, Dakyar ya lalubo natsuwarsa cike da fargaba yace "sakonki ya ishemun na son ganina Ina fatan dai lafiya kika aika kirana" Murmushi ta sauke a fuskarta "sai yanzun sakon ya ishe maka kenan?Koko yanzun ka gadamar zuwa Kiran nawa?hmmm sarkin dawaki ka Shiga hankalinka Domin wasa Dani da kake Shirinyi tamkar kana wasa da rayuwarka ne" "Ina sauraronki"shine abinda yace Mata a takaice, Sosai ta tsaye sanan ta nuna wani farin gorar swan water dake gefe tace "lokaci yayi da zaabada magani Kuma kasan aikinka shiyasa na kiraka Domin ka aiwatar da umarnina,rashin aiwatar da umarnina Yana barazana da rayuwarka data Yar daka Haifa kanta,idan ban aiwatar maka da komiba to hukuncinka zai sauka akan yarka wadda kake tsanin kauna...ka dauka ka Bata takai Domin waadin Shan maganin nasa yau ne,idan besha yau ba komi zai iya lalacewa,sanan Ina Mai sanar maka idan har baka Bata ba ta bashi zan sani kuma zaka fuskanci hukuncina"....Tana karasa maganar Bata jira cewarsa ba ta juya cike da takama fuskarta dauke da murmushin mugunta.... A sandare yake a zaune ya kasa kwakkwaran motsi a wajen ya rasa dalilin dayasa wanan matar ta rasa Wanda zatayi amfani dashi wajen cutar da yaron Nan sai shi?sanan abun takaici tasa yarsa fadawa soyayya da nakasasshe Wanda Babu tabbacin aurensa da ita?me take nufi dashi ne?babban tashin hankalinsa be wuce yadda yanzun ta canja Masa sanin cewar shakuwar yarsa da yaron Yana nuna cewar akwai wata alaka ta zuciya a tsakaninsu,tabbas ta sakashi a tsaka me wuya besan yadda zaiyi da fitinanniyar matar Nan hatsabibiyaba, Juyawa yayi ya dubi gorar dake ajiye a gefe wadda itace zai dauka ya Kai...gabansa ya fadi wani irin gumi ne kawai ke tsattsafowa a fuskarsa..ajiyar zuciya ya sauke ya Mike jiki a sanyaye ya dauki gorar yana Mai dagata sama yana bin ta da kallo bashi da wani zabin daya wuce aiwatar da umarminta haka ya juya ya fice..... *SLIMZY 😍* [1/23, 10:31 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS ASSO...💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN💞* *SLIMZY✍🏼* *Wattpad@slimzy33* *2* ******** Shirinta tayi tsaf kamar yadda ta Saba yau ma tayi latti sauri sauri take shiryawa,sanye take da doguwar Rigar jallabiya baka budaddiya da gyalenta Baki ta yane kanta fuskar Nan fayau babu abinda ta shafa tayo hanyar tsakar gida daga dakinta, A tsakar gida taci karo da mahaifinta Nan da Nan ta zube a gabansa ta Soma gaishesa,"barka da tashi baba fatan antashi lafiya?" Cike da kulawa ya dubeta "ummaty an fito zaa tafi?" "Ehh baba" Gorar hannunsa ya kalla ya Mika Mata "ga wanan ummaty lokacin Shan maganin zainul abideen yayi kinsan dai yadda kike bashi sanan wannan abun da kikeyi taimako ne Allah zai baki Lada Allah Kuma zai bashi lafiya" Ta Kara sunkuyar da kanta ta Mika hannu cike da ladabi ta amshi gorar ruwan "wallahi baba narasa Gane Kan wanan rashin lafiyar na ya zainul jiya ma fa bakaga yadda jikin ya rikice ba wallahi,gashi Mai martaba yaki amincewa da akaisa ai Masa magani" Ajiyar zuciya ya sauke Yana Kara duban Yar tasa sanan ya nisa yace "kada ki damu ummaty zai warke insha allahu shiyasa Nima nabaki goyon baya wajen taimakonsa wajen bashi magani a boye batare da sanin kowa ba har Allah yasa yasamu lafiya kinji?tashi kije Rana tanayi" Ta Mike jiki babu kwari dakyar take taka kafarta ta Shiga dakin mahaifiyarta Tana zaune Kan dadduma Tana sauraren radiyo ,direct wajen drawer ta nufa ta bude ta Ciro babbar Jakarta ta zura gorar ciki Sanan taiwa mahaifiyarta sallama ta fice.... ******* Shasshekar kukanta ce yasata saurin juyowa bangaren da take zaune ta jingina da kilisa gefenta wayarta ce ajiye,da kyau mahaifiyarta ta kalleta Tana karantar yanayin nata Wanda ya nuna tsantsar damuwa a fuskarta, "Yanzun safiyya bazaki daina kuka Akan rashin lafiyar zainul ba kiyi Masa addua?Babu abinda yake bukata sama da adduarmu kiyi Masa addua a matsayinki na kanwarsa jininsa inaga zaifi bukatar hakan sama da kukan da kikeyi" Juyowa tayi fuskarta jike da hawaye cikin tsananin tashin hankali ta Soma magana "Ammy lokuta da dama idan abubuwa suka taru sukai maka yawa babu abinda zakayi kasamu sassauci a zuciyarka inba ka zubar da hawayen ba,Babu abinda narasa a rayuwata ban rasa ci ba ban rasa Sha ba ban rasa komi ba Amma akwai gib'i a cikin rayuwarmu bakuma wani bane face ya zainul Ammy ki duba kiga halin da yake ciki shine kada'i namiji kaf zuri'ar mahaifinmu Amma shine Allah yayiwa wanan mummunar jarabar shine mummunar kaddara ta fadawa Wanda mahaifinmu ke matukar so yake alfahari da samunsa a d'a namiji magajin sarki Amma ya tashi cikin tsananin rashin lafiyarda har yanzun aka rasa maganinta, Dole inyi kuka ammy,sanan babban abinda ke damuna be wuce yadda yake cikin wanan halin Amma Kun kasa yin wani Abu Akan ciwon nasa Ammy daga ke kuwa har Mai martaba kullum saidai kice ciwon ya zainul na asibiti ne ni Kam a ganina bana asibiti bane wanan ciwon nasa ya kamata a binciki masana addini da masu maganin gargajiya ko zaa Dace"ko kafin ta Gama maganar hawaye ya Gama wanke fuskarta tasa hannunta ta share Tana Mai duban mahaifiyar Tata wadda kalaman na Yar Tata suka fama Mata wani ciwo dake cikin zuciyarta, "Fiyya dik wani mutum Wanda zai kaunaci zainul abideen ya nuna Masa soyayya bayana ne mahaifiyarsa nikadai nasan ciwon da nakeji ganin nakassar da zainul abideen ya tashi cikinta, Amma bani da yadda zanyi sama da inyi yadda ya Dace,ciwonsa na asibiti ne fiyya bana gargajiya bane Babu abinda maganin gargajiya zai Masa face ya Kara rikitar da jikinsa gobe insha allahu munada ganin likita idan munje zanyi Masa bayanin komi dangane da jikin nasa ,Dan Haka ki kwantar da hankalinki insha allahu Dan uwanki zai samu lafiya yanzun Haka zan tura tabawa taje ta sanar wa da masu kula dashi zuwana dubashi" Girgiza Kai kawai fiyya tayi batare da tace komiba ta sauke sassanyar ajiyar zuciya.... ********* "Ku gyara gimbiya bilkisu zata shigo duba jikin yarima" Da sauri fadawan dake cikin dakin suka shiga taitayinsu Jin wadda akace zata shigo duba jikin zainul abideen Nan da Nan kowa ya zube a kasa ta shigo dakin da takunta na kasaita da girma Wanda kowa yasan gimbiya bilkisu da sarauta kaf masarautar.... "Barka da zuwa gimbiya bilkisu uwar yarima magajin sarki"shine abinda fadawan suka hada baki sukace a tare,...hannu kawai ta daga musu batare da tace musu komiba ta karasa har gaban gadon, Ummaty na tsugunne kanta a kasa dakyar ta iya motsa bakinta ta hada harrufa tace "barka da zuwa ranki ya dade" Juyowa tayi gefen ummaty tayi murmushi Wanda shine amsa gaisuwarta,....kallo daya Tai Masa jikinta yayi tsananin sanyi tausayi da soyayyar Dan nata na ratsa sassan jikinta da jijiyoyin dake cikin jikinta,gefen gadon ta zauna sanan ta juyo ta dubi inda fadawan ke kame ko kwakkwaran motsi basayi Tai magana a takaice "kubamu waje"tun kafin ta karasa maganar suka Shiga fita daya bayan daya, Ummaty ma juyawa tayi jiki a sanyaye ta koma can kofar dakin ta tsugunna kanta a kasa kirjinta sai bugawa yakeyi,Wanda ita kanta batasan dalilin dayasa dik lokacin da gimbiya bilkisu zasu hadu saita tsunci kanta cikin tsananin faduwar gaba hakan nada nasaba da mulki da Kuma kwarjini da Allah ya bawa matar... Miyau ne kawai yake gudu a bakinsa sai harshensa da rabinsa yake waje Wanda shike zulalo da miyaun hannunsa daya a lankwashe yake shi kadai sai kada kansa yakeyi Yana murza kafafuwansa, Kara rungume Dan nata tayi batasan lokacinda hawayen bakin ciki ke gudu daga idanuwanta ba saboda takaici,dubi dik yadda rashin lafiya tasa yake kullum tamkar karamin yaro,janyosa tayi Rabin jikinsa a jikinta ta rungume Dan nata Tana sharar hawaye, "Allah ya baka lafiya kamar kowa zainul Allah ya nunamin ranan da zan ganka ka koma mutum sak kamar kowa" Dago kansa yayi Yana kallonta miyau na gudu a bakinsa dakyar ya iya motsa harshensa dake karye ya furta kalmar "ame..en"shafa kansa tayi tana cigaba da zubda hawaye yayinda ya kwantar da kansa a jikin mahaifiyar tasa Fiyya dake gefensu tsaye sai shasshekar kuka kawai takeyi Tana duban halin da Dan uwan nata yake ciki,sun dauki kinti ashirin kafin ta share hawayenta ta gyara Masa kwanciyarsa ta dubi fiyya tace" muje" Haka suka juya suka fice jiki Babu kwari a bakin kofa sukai karo da ummaty Tai saurin durkusawa "ummaty kiyiwa fadawan yarima magana su canja Masa kayan jikinsa dik ya Gama jika rigar da miyau" "To ranki ya dade" Tana Shiga ta dubesa ta sauke Masa lallausan murmushi hade da sauke ajiyar zuciya,ta janyo jakar datazo dashi ta Ciro gorar ruwan maganin ta ajiye a gefe ta gyara zamanta da kyau ta dago kansa taga ita yake kallo murmushi Tai Masa ta furta a Fili "Allah ya baka lafiya ya zainul kaji inaso ka warke cikin kankanin lokaci kaji?" Gyada Mata Kai yayi Yana Dan murmushi ta gefe,dago kansa tayi a hankali ta daga gorar ta Shiga bashi wanan ruwa,yasha sosai dikda rabi sun zube a jikinsa Amma Saida ya shanye tas ta gyara Masa kwanciyarsa sanan ta maida gorar cikin Jakarta tadawo gefensa ta zauna.... Dan littafin data Saba zuwa dashi ta Ciro cikin Jakarta ta bude yana ganin Haka ya Soma murmushi itama murmushin tayi Masa tace"ya zainul karatunmu zamuyi kaji" Ya gyada Mata Kai.... ********* "Sarkin dawaki"Mai martaba ya Kira sunansa, Kara durkusawa yayi sosai cike da girmamawa "Allah ya taimaki adalin sarki ya Kara maka girma da daukaka da nisan kwana da lafiya da arziki ranka shi Dade" Jinjina Kai Mai martaba yayi hade da murmushi na nuna Jin dadin kirarin da sarkin dawaki yayi Masa, Gyaran murya kadan Mai martaba yayi ya nisa "jamaan gari da Yan uwa da dik wani a Hali na wanan na wanan masarautar suna cikin alhini na rashin lafiyar zainul abideen" Kara durkusawa yayi sosai zuciyarsa na harbawa "Hakane ranka ya dade" "Shawarwari sunata zuwamin daga wurare daban daban da wadanda sukeda kusanci Dani game da rashin lafiyar zainul abideen cewar Mai zai Hana mu Mika lamarin Nasa ga malaman addini da masu maganin gargajiya cewar ciwon nasa bana asibiti bane ko zaa Dace" Gabansa ne ya yanke ya fadi a karo na biyu Nan da Nan hankalinsa idam yayi dubu to ya tashi dik wata natsuwa dayake ciki ya nemeta ya rasa Jin abinda Mai martaba yace bakaramin dimaucewa yayiba Amma be nuna Masa hakan ba sai kawai ya Kara durkusawa sosai "ranka ya dade dik wani Wanda zaice ayiwa zainul abideen maganin gargajiya zaicene kawai a fadarsa Domin su kansu masu maganin yanzun baa yadda dasu musamman yanzun da macuta sukai yawa,so dayawa masu magani sukan hada surkullensu su mikawa mutum a matsayin magani karshenta idan yayi amfani dashi jikin mutum ya Kara rikicewa wasu har mutuwa ma sukeyi sanadiyyar masu magani ranka ya dade,ni a ganina a cigaba dayi Masa na asibitin kawai shine maslaha Domin yanzun Ana cewa zaakaisa gun magani to fa idan labarin hakan ya kaiwa wasu tsaf zaa cutar maka da danka kwaya daya tilo magajin ka Kuma ni a tawa shawarar idan ma rashin ci gaba ne a canja mishi wani asibitin a gwada basirarsu a gani ranka ya dade" Numfashi ya sauke Mai martaba saboda bayanin da sarkin dawaki yayi Masa ya gamsu dashi matuka Dan kaf masarautar hatta su waziri be yarda dasuba kamar yadda ya yarda ya amince da sarkin dawaki dalilin hakan ne Yasa ake kiransa amintaccen sarki.... Da shawarar sarkin dawaki Mai martaba ya aminta na take ya watsar da sauran shawarwarin da sauran mutane ke bashi..... ******** Tallabo fuskarsa tayi tana Kare Masa kallo yadda kullum kamanninsu suke Nan sai Kara canjawa da yakeyi dikda rashin lafiyarsa da canjawar halittar bakinsa be hana kyawun fuskarsa bayyana ba, Idanuwanta ne suka cika da hawaye "zainul nakosa ka warke hankalina ya kwanta insamu sassauci a zuciyata na ciwon d'ana, zainul Ina fatan batare da na mutu ba kasamu lafiya kaji?kaima ka canja ka koma ainihin mutum kamar kowa..."hawaye suka Shiga gangarowa a idanuwanta,...kansa ya Shiga girgiza Mata alamar ta daina kuka,dakyar ya motsa labbansa ya furta "ki...shi ru"murmushi gimbiya rumana tayi ta juyo ta dubi ummaty dake tsaye a gefe Tana dubansu cike da tausayawa lallai soyayyar da gimbiya rumana take nunawa zainul abideen soyayyace ta gaskiya Dan kullum batada wajen zuwa sama da wurinsa tana duba lafiyarsa minti minti ta shigo ta duba jikin nasa, "Allah ya saka Miki da alheri ummaty yadda kike kulawa da zainul Allah ubangiji ya saka Miki da gidan aljannah yadda kika dauki dawainiyar zainul abideen muna matukar Jin Dadi da alfahari dake" Kwalla ce ta cika idanuwan ummaty ta sunkuyar da kanta "babukomi ranki ya Dade koba komi zainul abideen yayana ne Dole in kula dashi" Murmushi gimbiya rumana tana karewa yarinyar kallo cike da so da kauna,yarinyace karama Amma komi nata irin na manya ne ga natsuwa ga hankali dikda kananan shekarunta tasan yadda ya kamata tasan kyautatawa da tausayi, Kuriiii yayi da idanuwansa akanta ko kiftawa bagayi ga miyau dake sauka daga bakinsa Yana diga a jikin rigarta Bata damu da hakan ba sai kuka takeyi Tana Kara tausayinsa Nan da Nan jikinsa ya Shiga jijjiga kafafuwansa suna lankwashewa ko Ina jikinsa rawa yakeyi hankalinta ba karamin tashi yayi ba ganin yadda jikin nasa yakeyi, ta rikesa sosai dikda nauyin da taji yayi Mata be hanata rikesa da karfinta ba Tana ambatar sunansa a bakinta, Ta dubi ummaty wadda dik ta rikice itama Tai saurin zuwa ta Kama matashi suka rikesa sosai,kuka kawai gimbiya rumana keyi Tana ambatar sunansa, Tana Kara rikesa, ********* "Ni Kam narasa dalilin dayasa kika Shiga rayuwata kikai Kane Kane Babu Wanda kike takurawa saini,menayi miki haka ne kika gayyatoni kika tsundumani cikin halaka?" Murmushin Nan nata ta sauke a fuskarta takai hannunta Kan glass cup na ruwa ta dauka ta kurba ta ajiye kofin sanan ta Soma magana, "Bana bukatar jin wadanan tambayoyin daga gareka,ka Adana kalamanka kila zasuyi maka amfani Nan gaba,...inaso ka saurareni sosai da kunnen basira inaso kasani idan har kace xaka bijirewa umarnina to tabbas kashinka ya bushe,...bawani Abu bane yasa na kiraka nakiraka ne in Kara jadadda maka maganar da mukayi jiya Akan yarka ummaty inaso ka datse alakarta da zainul idan ba hakaba zanyi maka alkawarin nadama" A fusace ya juyo Yana kallonta idanuwansa sunyi jajir ransa a bace "nagaji da wadanan dokokin da kike gindayamun akan me? menayi miki?me yarinyata tai Miki?yadda kika jefaki cikin halaka itama kika dauko hanyar jefata cikin halaka kina tunanin Allah zai barki ne?koko kina tunanin Babu lahira ne?dik abubuwan da kikesani nake aikatawa nake kullawa be isheki ba kenan?saikin hada da Yar Dana haifa?to nagaji wallahi banki asirinmu ya tonu ba Koda hakan na nufin karshen numfashi na a duniya" Dariya sosai takeyi Tana dubansa yadda yake kumfar baki ta nunasa da yatsa "dubesa saikace wani mutumin airziki Kai a tunaninka idan kwai ya fashe har Dani zata shafa?hmmm bakasan koni wacece ba har yanzun wallahi,shawara daya ce zan baka shine ka kwantar da hankalinka ka saki jikinka yadda muka dauko tafiyar Nan tare mu cigaba tare kabi umarnina sabawa umarnina tamkar barazana da rayuwarka ne Dana iyalinka...." Zufa ce kawai take tsattsafowa ko Ina a jikinsa ta Yaya zai Soma tunkarar ummaty da wanan maganar?shin Yaya zata dauka?me hakan ke nufi?..... *SLIMZY😍* [1/23, 10:31 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS ASSO...💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN💞* *SLIMZY✍🏼* *Wattpad@slimzy33* *3* Nisawa yayi ya sauke ajiyar zuciya ya dubeta a karaye, "kina ganin raba ummaty da zainul shi zaisa kisamu cikar burinki na ganin cewa zainul abideen bashida sauran amfani a masarautar Nan da doron kasa?idan har kikace sai na raba ummaty da zainul abideen zanyi hakan Domin cika umarninki Amma kisani boyayyen kudirinki da nufinki bazai cika yadda kikeso ba Domin ita yarinyar itace jigon tafiyar Nan da mukeyi,rabata da zainul abideen zai kawo cikas a wanan tafiyar da muka dauko muna gab da samun nasara" Kallonsa tayi na dan wani lokaci Sanan da kauda idonta kamar bazatace wani abuba sai ya tsinkayi muryarta "ta Yaya kake ganin tafiyar bazata yuwuba sarkin dawaki?" "Idan muka Raba yaran Nan babu hanyar da zamuyi amfani da ita wajen bashi magungunan da muke bashi,ko kin manta cewa ummaty ce take bashi magani idan ankarbo?ko kece Zaki bashi idan anrabasu?kisani idan na rabasu to wallahi baki isa ni kisani kice nine zan cigaba da wanan aikin na hatsari ba don itanma dabara nayi Mata yasa kikaga komi Yana tafiya daidai yadda mukeso" Juyowa tayi wanan karon Tana fuskantarsa fuskarta Babu annuri tamkar Bata taba dariya ba a duniya cikin kakkausar murya wanan karon ta Soma magana,"naji na amince da dik bayaninka na fahimceka Amma kasani wallahi tallahi bazan taba amincewa soyayya ta kullu tsakanin yaran Nan ba,idan har hakan ta kasance to har Yar taka zan batar da ita a doron kasa" Wani irin faduwar gaba ya tsinci kansa Nan da Nan jikinsa yayi sanyi Jin abinda tace"Babu soyayya a tsakanin me lafiya da nakasasshe,sanan babu soyayya ko aure tsakanin me hankali da Wanda bashida hankali Wanda bashida sauran amfani a wanan duniyar,bazan taba lamunta diyar Dana Haifa a cikina me cikakken koshin lafiya ta auri wanan nakasasshen kotayi soyayya dashi ba,Dana fahimci hakan nidakaina zanyi amfani da almakashi in datse alakarsu Dan Haka ki kwantar da hankalinki ummaty batakai shekarun da zata kulla soyayya yanzun ba dududu kwaya nawa take?inaji yanzun ne zatayi shekara goma Sha bakwai shi kansa zainul din Ina ashirin da biyu yake?Babu Hadi" Ajiyar zuciya ta sauke Ta tsugunna ta dauke hand bag dinta dake gefenta ta zuge zip din Jakarta ta ciri wrappers din kudi Yan dubu dubu guda biyu dubu dari biyu kenan ta Mika Masa "ga sadakin ka Nan buri na be wuce in bude Ido Inga gawar zainul abideen ba dikda boka ya sanarmun da cewa mutuwarsa tanada wahala,to tunda bazai mutuba ya dawwama a kwance har karshen rayuwarsa"....Tana Gama magana ta juya Tai hanyar fita abinta, Kudin da ta Mika Masa yake bi da kallo zuciyarsa cike da fargaba ********** "Ya zainul kagafa yamma tayi Kuma munyi karatu gobe Insha Allahu zan Kara maka a inda na tsaya yanzun zanyi Shirin tafiya gida sai idan Allah ya kaimu gobe ko?" Canja fuskarsa yayi Nan da Nan ganin tanata Shirin tafiya gida ta barshi kusan dik lokacin da ummaty zata tafi gida to Nan da Nan fuskarsa takan nuna damuwa a kwayar idonsa,Tana Shirin daukar Jakarta ta waigo ta dubi inda yake kwance miyau na gudu a bakinsa suka hada Ido taga kamar hawaye a makale a Ramin idanuwansa,...tausayinsa ne ya lullubeta taji jikinta yayi sanyi ta janyo kujerar gaban gadonsa ta zauna dafdashi Tana Kara kallonsa cikin tausayawa, "ya zainul kardai kacemin abinda nake gani a kwayar idonka hawaye ne na tafiya da zanyi inbarka?Koda na tafi akwai masu kula dakai ya zainul Kuma gobe zanzo kaji?"ta karashe maganar idanuwanta cike da kwalla saboda tausayinsa,...ga mamakinta sai ya Shiga girgiza kansa alamar be yarda ba, Numfashi ta sauke tasan zaayi haka musamman yau da suka wuni ita dashi batare da ciwonsa ya motsaba tasan inhar zata tafi sai sunyi drama gashi kuwa,ganin ya kafeta da Ido yasa ta boye kwallar dake makale a idanuwanta,"kaga kayi hakuri ya zainul bazai yuwu in kwana a wajenka ba kaji?Amma Ina Mai tabbatar maka da insha allahu da kaina zan tasheka a bacci gobe saidai ka tashi ka ganni nayi maka alkawari kaji ya zainul?umm?ka yarda? Gyada Mata Kai yayi Yana murmushi,itama murmushin ta maida Masa ta Mike ta dauki Jakarta tabi hanyar kofa ya bita da kallo harta bace sanan ya rufe idanuwansa shikadai a daki Dan fadawan dake kula dashi wani lokaci sukan fice su barshi dagashi sai ummaty ******* "Meya hanaki bacci har wanan lokacin rumana?"Mai martaba ya jefo Mata wanan tambayar Yana karasa shigowa cikin dakin Yana sanye da Yar shara irinta sarakai ya nemi gefen gadonta ya zauna, ",Ki duba kigani yanzun kusan karfe goma Sha biyu da rabi na dare har yanzun Baki bacci ba ko akwai wani Abu ne?".. Fuskarta Babu walwala ta dago idanuwanta ta dubesa a raunane sanan ta maida kanta kasa ta dukar "Haka kawai na rasa samun sukuni cikin Daren Nan,tunanin yaron Nan zainul ya hanani sukuni inaso ingansa Inga halin da yake ciki yanzun"....murmushi yayi irin na manya ya rungumota jikinsa Yana shafa kanta a hankali "haba rumana zuwa yanzun ya kamata kisaba da rashin lafiyarsa tunda ya dauki shekaru Yana wanan ciwon kusan tun bayan haihuwarsa,nikam Banga sabon abuba a wajen ciwon Dan naki" Kwantar da kanta ta karayi a kirjinsa Tana sauke numfashi "muje ki ga Dan naki kinaso?"...da sauri ta daga Masa Kai alamar ehh ,girgiza kansa yayi yana murmushi rumana Bata girma dikda ta girma ta haifi yara Amma kullum jinta take kamar karamar yarinya,Haka ya tasata a gaba suka nufi sashin yarima zainul, Rike suke su biyu da zainul dukkansu bacci ne a idanuwansu Amma Babu damar yi saboda yadda zainul abideen ya Bata jikinsa gabaki daya da amai da yayi Wanda sukansu basusan dalilin Aman NASA ba,su kansu sun gaji dashi,suna Shiga dakin fadawan suka zube a kasa suna kwasar gaisuwa, Ganin halin da zainul ke ciki yasata saurin karasawa ta rukosa jikinta ta Shiga share Masa jiki da kanta da Dan karamin towel din dake wajen ,Mai martaba Yana tsaye Yana kallon yadda take rungume da zainul abideen ko kazantar jikinsa bataji batadamuba ta tsaftace Masa jiki kawai takeyi ita,Saida ta kammala gyara Masa jikinsa ta juyo ta dubi inda Mai martaba ke tsaye hannunsa rungume a kirjinsa ta dubesa a raunane ya sakar Mata murmushi kawai ta sadda kanta kasa hawayen da take boyewa suna sauka a kuncinta, Kallonta sosai zainul abideen yakeyi Yana girgiza kansa alamar tayi shiru ta Kara rungumesa sosai tanajin soyayyarsa na ratsa sassan jikinta..... ******** Yau ta kasance jumaa yaune mahaifiyar me martaba da ahalin gidan sarki suke zuwa fadar sarki kawo gaisuwa Dan Haka dik ranan jumaa zakaga cikin gidan tamkar Ana wani shaani, Zazzaune suke a babban parlorn gidan kowa ya hallara anata ciye ciye, Yatsina fuska tayi kadan "nikam banajin zan Shiga duba zainul yau ko zakuje ni boyewa zanyi Dan banjin zan iya Kai kaina ganin wanan kazantar dake cikin wanan dakin"ta karasa maganar hade da yatsina fuska, "Kai warisat kada ki manta ya zainul fa Dan uwanki ne be kamata ki kyamace sa ba kiduba halin da yake ciki" Dan tsaki tayi tana dubanta cike da tsiwa"banson iyayi zahira Zaki fara Koh?kinji nace dama ba Dan uwana bane?kawaidai banida raayin zuwa dubasa ne"ta kauda kanta gefe, Tabe bakinta zahira tayi "kedai kikasani mu zamuje mu dubashi idanke bazakije ba Kuma ya zainul a tsaftace yake masu kula dashi suna iya bakin kokarinsu sanan ummaty ma Tana tare dashi ai Yar sarkin dawaki" "Kwadayi ne kawai yasa take makale a gidan sarauta da son asani" Wani dogon tsaki fiyya tayi daga gefe dik hirar da cousins din nata sukeyi a kunnenta tsananin takaicin kalaman warisah ne yasa ta tabar parlorn Dan ji take tamkar ta shaketa, ********* Karatun alkurani takeyi da muryarta Mai dadin saurare ya kafeta da idanuwa da alamar yanajin dadin yadda take karatun,....shigowarsu tawagarsu yasata zumbur ta Mike tsaye jikinta na rawa ta zube a kasa Tana kwasar gaisuwa wajen dattijuwar matar da aka shigo da ita wadda ta kasance kakar zainul abideen ta wajen uba.....wani irin kallon kyama da wulakanci warisat da zahira suke bin ummaty dashi Wanda yasata kasa tsayuwa a wajen tayi hanyar fita..... *SLIMZY😍* [1/23, 10:32 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS ASSO....💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN💞* *SLIMZY✍🏼* *Wattpad@slimzy33* *4* Gefe ta nema ta raku'be zuciyarta Babu Dadi,kwata kwata batajin dadin yadda warisat takeyi Mata dik lokacin da zasu hadu sai ta bi ta da wanan kallon na wulakanci da kyama Amma hakanan take jurewa, Hajiya ce ke kallon zainul abideen Wanda shima idon Nasa akanta yake kallo daya zakayi mishi tausayinsa ya kamaka duba da yanayin nasa Amma hakan be hanashi murmushi ba dikda murmushin ba fita sosai yakeyi,ba itama murmushin ta maida Masa takai hannu ta shafa sumar kansa "ikon Allah sai kallo sannnu zainul Allah ya kawo karshen wanan rashin lafiyar taka ya baka lafiya magajin baba" Jinjina Mata Kai yayi "ameeen hajiya... Kaka"yadda yayi maganar bakinsa na furzar da miyau sai ya baka tausayi,...jin dadin maganar tasa yasa kakarsa sakin kayataccen murmushi Tana shafa sumar kansa, Daya bayan daya suke karasawa kusa dashi suna duba jikin nasa yayyinsa manya Mata guda uku sai kannin mahaifinsa Mata da iyalansu Suma suna dubashi cike da tausayawa, Hajiya ce ta dubi warisat da zahira dake gefe suna yatsina fuska tamkar sunji wari ta daure fuskarta "ku kunfi karfin kuzo ku duba jikin yayan naku ne kuna raku'be gefe daya?" Tura Baki zahira tayi sanin halin kakar su Bata daukar raini yasa ita takaraso gaban gadon Tana magana Tana yatsina fuska ta gaisheshi Banda warisat da ko kallon gefen da suke batayiba ta maida kanta gefe, A fusace mahaifiyarta ta dubeta "me kike nufi ne warisat?ke kinfi karfin ace kiyi Abu kiyi ko?hajiya Bata isa tace kiyi Abu kiyi ba kenan to karyarki yarinya kafin in bude idanuwana kinzo kin cika umarninta kafin in tattakaki" Murmushin takaici gimbiya rumana tayi tana karewa warisat kallo Sanan ta dubi mahaifiyarta tace"hajiya kubra kibita a hankali yarinya ce"... Dakyar warisat ta Tako gaban gadon Tana Harare Harare ta tsaya ta wani bishi da mugun kallo ta kauda kai Tai Masa ya jiki sama sama ta juya Tana wani irin taku,kallo zainul ya bita dashi ya rufe idanuwansa gammn.... Sun dauki lokaci a sashin na zainul sanan suka fito a waje sukai Karo da ummaty tsugunne, "Allah sarki yarinyar kirki Allah yayi Miki albarka yasa ki Gama da duniya lafiya yadda kike kokari da zainul kinji?"cewar hajiya kakar zainul, Murmushi ummaty tayi ta sadda kanta kasa, . Tabe baki warisat tayi "kwadayi ne kawai irin na yaran talakawa shiyasa ta manne"...kowa yaji abinda tace Amma suka basar sukai gaba ummaty tabi bayansu da kallo,ta Dade tsugunne sanan ta Mike jiki a sanyaye tayi hanyar Shiga wajen zainul ********* "Banji dadin abinda kikayi ba warisa,wanan abun da kikayi kika nuna kyamar dan uwanki a cikin mutane kin Saida mutuncinki ne a idon kowa kina tunanin iyayensa zasuji dadin abinda kikayi?koko Mai martaba idan yaji labari zaiji dadin abinda kikayi warisah?" Turo baki tayi batare da tace komiba yadda uwar ke zazzaga Mata masifa tamkar zata daketa, "Haba momy nifa ba kyamarsa nakeyi ba" "Ubanki kikeyi ba kyamarsa ba?Ina ganin take taken ki kema bakifi karfin Allah ya maidake haka yadda kika ganshiba, wanan yaron da kike gani yafiki gata a wajen kowa a dangi Dan dai Allah yayoshi Haka ne Dan Haka kibi a hankali shashasha kawai" Tana gama fadin haka ta wuce tabarta Nan zaune Tana ture turen Baki, Wata baiwace hannunta dauke da tray tazo wucewa ta karamin parlorn ta Dan durkusa ta gaida warisa wadda ke zaune kafarta daya Kan daya harta wuce ta Kira sunanta a wulakance "ke sadiya zo Nan"da sauri ta zube a gabanta "Ina zakije da wanan tray din?" "Ummaty ce tace a dafowa yarima zainul hanta ruwa ruwa ko zai iyaci shine na dafo mashi" "Jeki"...shine amsar data Bata a takaice ta Mike jiki na rawa, Lallai yarinyar Nan wato har mukaminta yakai tasa bayi Abu suyi?ita wacece?waye ubanta inba sarkin dawaki ba?samun gurin nata har yayi yawa ace tanabawa maaikatan gidan sarki izinin suyi Abu suyi wadda ita kanta Bata wuce a aiketa tajeba tunda ubanta shi kansa be wuce a aikeshi ba "mtseww"tayi Tsaki a Fili ta janyo Jakarta ta rataya ta dauki gyalenta Tai waje..... ********* "Umma..ty Ina matukar jin dadin karatun Nan da kikemun sosai waya koya Miki?"yayi maganar a hankali dikda maganar ba fita takeyi sosai ba Amma ta fahimci abinda yake nufi hakan ne yasata sakin lallausan murmushi Wanda wushiryar bakinta ta bayyana, "A makaranta aka koyamun Yaya zainul shine nikuma nake koya maka saboda inaso ka iya karatu da rubutu" Dan murmushi yayi kadan miyau ya zubo daga bakinsa tasa Dan towel din da take goge Masa ta share Masa,"ta Yaya zanyi karatu da rubutu bayan ga halin da na tsinci kaina ciki?" Ta bude baki zatayi magana aka turo kofar aka shigo hade da sallama, Ganin wadda ta shigo yasata sauri zubewa a kasa, gimbiya bilkisu ce mahaifiyar zainul abideen sanye da tsadadden leshi ja da Baki ta yane jikinta da lafaya hannunta sanye da kambu na ruwan gold dazobba na zinari zagaye da yatsunta fuskar Nan Tata ma dauke da kyau da kwarjini irin na sarauta kamar kullum haka ta karaso gaban tankamemen gadon da zainul abideen ke kwance ita kadai ta shigo Babu Yan rakiya masu take Mata baya.... "Barka da yamma ranki ya dade"shine gaisuwar da ummaty Tai Mata, Dafa kanta tayi tana shafawa batare da tace komiba ta juya ga d'an nata da tunda ta shigo hankalinsa ya koma ga mahaifiyarsa,yau shigowarta hudu kenan wajensa dikda suna Zama sashi daya Tana iya juyo motsinsa Amma hakan be hanata zagayowa lokaci lokaci, "Yarima na ya jikin naka?da sauki Koh?mekedamunka yanzun?"lokaci daya ta watso Masa wadanan tambayoyin, Girgiza kansa yayi "Babu abinda ke damuna ammiey"ya Bata amsa a hankali harshensa na hardewa, Yadda yake maganar kadai Saida yasa kwalla ta ciko a idon gimbiya bilkisu Amma gudun kada ya fahimci wani Abu yasata dannewa tai murmushi ta juyo ga littafin da ke gefe takai hannunta ta dauka Tana dubawa,murmushi kawai takeyi Tana dubba littafin ta Dan juyo kadan ta dubi ummaty dake tsugunne a gefe "ummaty karatu kike koyawa yayan naki ne?" "Ehh ranki ya ammiey" "Masha Allahu hakan nada kyau"bata sake cewa komiba ta Dade zaune tare dasu kafin kanwar zainul afnan ta shigo da gudunta ta fada jikin mahaifiyarsu Tana zuba Mata surutu suka fice tare.... ******** Tunda ummaty tazo gida yau takejin jikinta wani iri a Haka Tai sallar magriba tazo ta zauna gefen mahaifiyarta, Ganin yanayin da ummaty ke ciki yasa Inna ta fahimci akwai wani Abu "ummaty lafiyanki kuwa?tunda kika dawo yau naganki sukuku kamar wani Abu ya faru" Girgiza Kai tayi sanan ta sauke ajiyar zuciya ta dubi innah tace "innah Haka kawai banajin dadin Raina tunda nabaro ya zainul yana Dan shakuwa kadan yadda yakeyi idan ciwonsa zai tashi shiyasa dik nakejin tamkar wani Abu zai faru dashi " Shafa kanta tayi "ki kwantar da hankalinki Babu abinda zai sameshi insha allahu bakomi bane zuciya take ayyana Mana Kuma ya faru kinji?" Gyada kanta kawai ummaty tayi badan hankalinta ya kwanta ba,haka cikin dare idanuwanta a bushe ta kasa runtsawa sai fargaba takeyi.... ******** Jijjiga kawai jikinsa yakeyi yana wata irin shakuwa dakyar take sauka kirjinsa harshensa ya kara fitowa waje sai wani irin gurnani yakeyi tamkar zai mutu, "Yi sauri yusha'u ka dibomin ruwa mubashi dubi yadda yakeyi tamkar ransa zai fita"a rikice ba faden yayi magana yana rike da shi, "Kai wanan yaro Yana fama da lalura wallahi ni bansan ya zamuyi dashi ba wallahi idan ya fara wanan abun ummaty ce kadai take iyawa dashi ita kadai tasan abinda takeyi mishi"Haka ta juya ya fice a dakin ya nufi parlor sai gashi da gorar ruwan suwan water ya shigo ,dik yadda sukai subashi ruwa yaki amsa saboda yadda jikinsa keyi harshensa ya cika bakinsa dik sun firgice gashi dare ne, Haka suka yanke shawarar zuwa su kwankwasa dakin bayi su tashi daya daga ciki ta sanarwa gimbiya bilkisu abinda ke faruwa....Koda aka sanar Mata a rikice ta fito sanye da hijabi jikinta ganin zainul kwance warwas tamkar gawa ya Kara rudata Tana fadin "daukesa muje asibiti Bari intaso Mai martaba"..... *SLIMZY😍* [1/23, 10:33 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS ASSO....💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN💞* *SLIMZY✍🏼* *Wattpad@slimzy33* *5* Kusan a tare suka shigo da Mai martaba da gimbiya bilkisu dukkansu a rude suke ganin yadda yake jijjiga ga idanuwansa da suka canja kala baka ganin bakin sai farin,cikin kuka gimbiya ta dubi Mai martaba Wanda ke tsaye tamkar an dasashi Yana kallon zainul gwanin tausayi, "Ranka ya dade kayi shiru kayi umarni da mudaukesa mukaisa asibiti Mana ka duba kaga yadda yaron Nan yakeyi banaso in rasa d'ana shikadai gareni"cikin kuka take maganar, Janyota jikinsa yayi ganin Haka yasa fadawan sukai saurin barin dakin yana bubbuga bayanta "haba bilkisu ya kamata kisawa zuciyarki hakuri da dangana Akan ciwon zainul tunda ba yanzun ya fara ba ba sabon Abu bane a wajenki Dan haka kiyi Masa addua kidaina wanan kukan Bari in dauko maganinsa Wanda doctor dinshi yabamu Akan dik lokacin da ciwon ya tashi abashi zai samu bacci"fuskarta jike da hawaye ta dago ta dubesa sai ta zare jikinta daga NASA ya juya ya fice ta tsaya gaban gadon zainul Tana kallonsa tausayinsa na Kara Shiga jikinta....Tana Nan tsaye Mai martaba ya shigo hannunsa rike da magani da cokali,da kansa ya sa maganin a cokali ya dama ya zo gaban gadon ya janyosa jikinsa da kyau saboda yadda yayi nauyi ya samu ya zuba masa a bakinsa dikda ba duka ya Shiga bakinba, Yana Nan rungume dashi mahaifiyarsa na tsaye tana kallonsa kusan minti goma Sha biyar idanuwansa suka rufe alamar bacci ya daukesa.... ********* "Ummaty bazaki tsaya kici abinci ba?ki karya haka xaki fita da sassafen Nan?" "Innah bazan iya cin komiba sai naje Naga halin da Yaya zainul yake ciki saboda inaji a jikina akwai abinda ya sameshi".....shiru innah tayi tana bin ta da kallo Sanan ta sauke ajiyar zuciya "to shikenan Allah ya tsare" "Ameen innah"ta juya ta fita sauri sauri sanye da dogon hijabinta,....girgiza Kai innah tayi ikon Allah kenan Allah me hada jinin bayinsa batare da ya shawarcesu ba inbadan haduwar jini ba Ina ummaty Ina zainul abideen Dan sarki?... ******** Zaune take a gefen gadonsa ta zabga tagumi idanuwanta kirr akansa dik motsinsa akan idonta yakeyi yadda yake sauke numfashi a wahale kadai abin tausayi ne,....Tana Nan zaune taga Yana motsawa alamar kamar zai tashi,gudun kada ya Kara tashi da ciwon yasata saurin mikewa Tana tofa Masa ayatul kursiyyu da amanar rasulu kusan minti biyar sanan taga a hankali Yana bude idanuwansa tamkar Wanda gari ya wayewa ,idanuwansa sunyi jajir kamar ba idanuwansa masu fari Tass kamar Madara ba,...cike da tausayawa murya na rawa tace "sannu ya zainul"...kallo ya bita dashi batare da yace komiba jimm kadan taga Yana alamar son yayi magana ta Mike tsaye da sauri ta sa kunnenta daidai bakinsa Taji Yana ambatar ruwa... Da sauri ta juya side din gadonsa ta dauko gorar ruwansa ta zuba a glass cup har ta juya zatayi wajensa ta tsaya tsaye ta juya baya ta Shiga tofa Masa addua cikin ruwan sanan ta juya ta bashi a hankali yake amsa dikda yadda rabi ke zubewa, "Umm.maty inaso intashi"shine abinda yace Mata bakinsa na hardewa,sanin bazata iya dagasa yadda ya Dace ba yasa ta fice da sauri zuwa parlor... "Ya zainul ne yakeda bukatar tashi,shine nace ko zaku taimaka kuzo kusashi a wheelchair dinsa" Wani mugun kallo dukkansu suke bin ummaty dashi Wanda yasata Tasha jinin jikinta,"ke kinma samu dama dayawa wallahi ki dubeki fa?kece zakizo kice muyi abu muyi?ko bamusan aikinmu bane malama?kinfimu sonshi ne?"ta girgiza Kai da sauri, "To shisshigin na meye ne kin like kece ke jinya uwar iyayi shegen iyayi kamar wata uwar Mata ke ga me jinya kin kwaso kafa kice muzo muyi Abu kece ma ke bamu umarni to Baki isaba Yar talakawace ubanki ba kowa bane a gidan Nan sai sarkin Doki,ai da kin dorasa a wheelchair din tasa tunda kece ke jinyar,Ashe dai munada amfani"Tass suka karewa ummaty tanadi itadai Tana Nan tsaye kamar an dasata takasa cewa komi Tana sauraren irin cin fuskar da fadawa ma keyi Mata suda bakowa ba a gidan,..juyawa tayi kawai batare da tace musu komiba suka bi bayanta... ********* "Ammiey na Shiga dakin ya zainul nasameshi kwance idonsa a bude,Amma ummaty Tana zaune Tana hawaye ammiey kukan me takeyi?" Shafa kanta tayi "afee ba kuka takeyi ba kila wani Abu ne ya shigar Mata Ido Amma me zaisa ummaty kuka?...Kinga ya kamata asama Miki lesson teacher saboda jarabawar Shiga senior section da zakiyi Koh?diyata ummul kairi ta girma"...take ta kauda maganar gudun kada afee ta cigaba da watso Mata tambaya, "Jeki wajen anty fiyya ko Aysha kice nace Ina kiran daya daga cikinsu kinji?"...jiki Babu kwari Afee ta Mike Tana takawa a hankali ta fice a dakin ganin Haka yasa gimbiya mikewa ta nufi sashen zainul abideen taga meke faruwa... ********* Ransa ba karamin baci yayiba da kalaman da wanan Yar rainin hankalin matar take jifansa dashi,lallai ma ta Gama Raina Masa wayau,kallonta yakeyi wanan karon Ido cikin Ido "gaskiya kin kaini makura a wanan tafiyar abinda kike Shirin aikatawa fa bazan iyashiba bazanyi ba wallahi saidai ki nemi wani yayi Miki shi Dan wanan aikin yanada matukar wahalar gaske" Murmushi tayi "meye aikin wahala a ciki?ai ka Gama komi sarkin dawaki wanan karashene ya rage kawai kayi shikenan kaga na cika burina sai sakamakonka Mai tsoka" Takaici ne ya Kara lullubesa yadda take magana a gadarance Tana nuna shi kwadayayye ne shiyasa ya biye Mata suke wannan mummunan aikin kenan "wani sakamakon zan jira?Banda Wanda idan asirina ya tonu sarki zaisa a tsireni?karshenta kiyi amfani da makircin Mata ke ki kubuta ni in kwana ciki,Dan Haka bazan tabayin abinda kikesoba yanzun dai" "Idan bakayi abinda nakeso ba to wallahi zanyi amfani da ummaty burina ya cika....kafi kowa sanin yadda nake akan abinda nakeso na kudira a Raina bani da sauran sukuni sai Naga na sameshi Dan Haka zanyi amfani da yarka wajen cikar burina,ko Kuma inyi sanadiyyar tarwatsa mata dik wani farin ciki na rayuwa...ni zanyi sanadiyyar da hanyar gidan Mai martaba ma idan ance tabi bazatabi ba,Dan Haka na baka Nan da zuwa gobe kaje kayi shawara....." Gumi ne kawai ke karyo Masa ta ko Ina,ta wani fannin Kuma zuciyarsa keyi masa lugude tamkar zata fasa kirjinsa ta fito....babban tashin hankalinsa be wuce yarsa da takeso ta sa a bala'i ba shin menene Shirin wannan shedaniyar matar Akan yarsa?... innalillahi wa Inna ilaihi rajiun...bakinsa ke ambato jikinsa na tsananin rawa..... *SLIMZY 😍* [1/23, 10:35 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS ASSO...💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY✍🏼* *Wattpad@slimzy33* *Assalamu Alaikum.... Fan's a duk inda kuke ina muku fatan alheri. Wannan book na zainul Abiddeen na kud'ine, wanda yake sha'awar siya ze iya tura kud'insa ta wannan number akan naira dari biyu kacal.* *2073065733 Sha'awa Ibrahim UBA bank* Tura shaidar biyan kudinka ga wanan number 08161306299 6019111117 keystone Amina jibril Shaidar biyanka ga wanan number 08166177830 Kokuma ya tura katin waya na mtn na 200 ta wannan number 08039424298 kokuma 07084161619 Kud'in littafin d'ari biyuce kacal game buqatar ci gaban zainul Abiddeen seya tuntub'emu. *6* Idan har na bari matar Nan taci galaba Akaina nayi babbar asara,idan har ban amsa mata bukatar ta ba to tabbas abinda tace zatayi nasan zatayishi dan ba cikakken imani gareta ba zata iyayin komi Dan ganin ta tarwatsamum sauran farin cikina, Nisawa yayi ya sauke ajiyar zuciya ya Dan dubeta,..."ka shiryawa bukatata ko har yanzun kana ko kwanto akan hakan?"ta jefa Masa tambaya tare da kafesa da idanuwanta Babu annuri a fuskarta, Kad'a kansa ya shigayi Yana murmushin takaici "Dole in amsa dik wata bukata taki tunda tun farko kin rigada kin jefani cikin masidar da fitarta yanada matukar wuya a gareni,zan aikata dik abinda kikeso Amma kisani badan zuciyata naso ba sai Dan kin tursasani da yin haka,Fadi bukatarki Ina sauraronki" Kayataccen murmushi ta sauke hade da yin kasa da murya cikin lallashi ta soma magana,"sarkin dawaki abubuwan da nakeso ya zamana zainul abideen ya kasance cikinsu har yanzun burina bai Gama cika ba sarkin dawaki,naso ace zainul abideen bayaji,baya gani sanan baya iya magana ganobin jikinsa da yake motsa su lokaci lokaci ya zamana Suma basa motsawa ya zamto ga Rai Amma Babu amfani bana bukatar ganin farin ciki wajen iyayen zainul ko kadan nafiso ganin dansu a wanan halin su dawwama cikin bakin ciki na harabada" Tunda ta soma magana yake bin ta da kallo da tsananin mamaki da rashin imani irin nata,tunawa da yadda zainul abideen yake Amma dikda hakan beyi mataba tafiso ta gansa a nakastat da tafi haka,dakyatya hadiye wani mugun miyau ya kalleta idanuwansa jajir yaga itama shi take kallo,karantar yanayinta yasashi fasa fadin abinda yayi niyya sai kawai ya furzar da iska mai zafin gaske yace "Fadi bukatarki daidai nake da inyi yadda kika umarceni Dan a halin yanzun banida maraba da Zama bawanki" Can kasa ta sassauta muryarta Babu Wanda ke iyajin abinda take fada sai shi da ya ke sauraronta har ta Kai Aya a zancenta,a firgice ya dago Yana dubanta da tsananin mamaki da tsoro sai kawai ta gyada Masa Kai Tana fadin "zaa kawo aikin Kuma ummaty nakeso ta aiwatar da komi yadda ya dace yadda na fada maka mistake daya zaai wajen aiwatarwa komi zai lalace Zanyi asarar makudan kudin Dana kashe wajen yin wanan abun Dan haka ka kiyaye sanan ayi yadda nakeso rashin biyan bukatata tamkar rasa farin cikinka ne sarkin dawaki"...a gadarance ta karasa maganar,zufa ce take karyo Masa ta ko Ina Babu abinda yake ambata a ransa sai innalillahi wa Inna ilaihi rajiun....hakan yanaji Yana gani tai ficewarta ta barshi Nan zaune kamar mutum mutumi hotiho... ******** Zaune take a parlor hannunta rike da remote kanta Babu Dan kwali gashin kanta ya Sha gyara tayi matukar kyau,hankalinta gabaki daya Yana kan tv lokacin da taji sallama a parlorn da kyar ta maida dubanta ga bakin kofa sukai Ido biyu da zahira sai Kuma ta dauke Kai kamar bazatayi magana ba, "Nifa tsiyata dake mugun Jin Kai tamkar wata sarauniya haka kikejin kamki warisat,yanzun idan ba iskamci ba ki juyo ki kallemu nida Yaya musaddik ki wani juyar da kanki gefe kamar Kinga Kashi"ta karasa maganar suna shigowa cikin parlorn, "Daga zuwanki zaki fara complain sarkin rashin hakuri?sai kace wata bakuwa da zan tashi Ina rawan jiki kinzo" "Yaayah musaddik fa da muke tare dashi ko baki ganshi bane?idan ni banci arzikin maraba ba?"...wani kallo takebim musaddik dashi ya kashe mata Ido sai kawai ta kauda kanta tamkar Bata san Yana yi ba,"barka da zuwa yaayah"shine abinda tace kawai ta Mike ta bar parlorn Tana tafiyar Nan Tata mai daukar hankalin Maza, Shafa kansa yayi ya dubi zahira ransa Babu Dadi "nifa bana son wulakamcin yarinyar Nan shiyasa tun farko kikaga naki Nuna mata Ina sonta Dan dik son da nakeyi mata bazam dauki wulakanci ba" "Ka kwantar da hankalinka ya musaddik zaka samu warisat a hannunka Nina fada maka da zarar ta shigo hannunka shikenan sai yadda kayi just be patient ok?" Gyada Mata Kai kawai yayi batare da yace komiba yadda ransa ya baci,...shigiwar hajiya kubra mahaifiyar warisat yasasu sauri natsuwa suka tsugunna a tare suna gaisheta cike da ladabi, "Zahira da musaddik ne a gidan namu?sannunku da zuwa" "Yauwa momy ya gida?" "Lafiya lau ya maman naku?" "Lafiya lau take" Warisat ce ta shigo dakin da alama ruwa ta watsa Tana sanye dadoguwar Riga mai launin ja ta amshi fatarta,wani mayen kallo yake bin warisat dashi ganin ko kallonsa batayiba yasa ya Mike ya fice a parlorn, Gefenta zahira ta koma ta zauna "dadina dake sarauta kamar wata matar sarki,Koda yake bamu saniba ko Yar gida zaayi keda Yaya zainul"...ta karashe maganar Tana rufe baki cike da tsokana, Wani mugun kallo warisat tabi zahira dashi cike da takaici ta dubeta "Amma kin cuceni zahira da badan ke bace kika fada da wani ne da Nika dai nasan irin hukuncin da zan dauka akanshi,kin Gama Dani zahira" Dariya kasa kasa zahira keyi "akan me zakice hakan?bayan kin manta shine magajin sarki?" "Wanan nakasasshen?kike hadani dashi?Amma zahira kin cuceni kingama Dani wallahi,ai ko Maza sun Kare a duniya bazan auri wanan halittar ba bazan taba sonshiba gara in karar da rayuwata a gida wallahi Dan ni banajin zainul zai warke" Murmushi wanan karon zahira tayi "Amma kinsan yanada kyau?kin taba lura da hakan?" "Kece kikaga kyaunsa kika tsaya kallon wanan halittar ni bazan iya kallonsa na second talatin ba Dan sai inyi amai saboda ka kazantar dake fitowa daga bakinsa na tsana....ke rabu Dani da wanan maganar ma mubarta"...take suka kauda maganar zahira ke shaida Mata date din da zasuyi resuming Nan da kwanaki goma zasu koma makaranta zasu shiga 200 level, Nan zahira ta wuni tare da warisat har wajen yamma sanan ya musaddik sukazo da abokinsa yazeed Don daukar zahira,mahaifiyar warisat ce tacewa zahira ta fadawa ummanta su shirya suje gidan mai Martaba su karasa hutunsu tunda haka sukeyi...... ******* "Kai ya zainul Nasha fada maka ka rinka yawaita addua da zarar kajika a wanan yanayin,Kai da kanka kasan adduoi kala kala Wanda basai na fada maka ba Amma Sam bakayi narasa dalili, kullum Ina fada maka muhimmancin addua, Amma Sam bakayi"ta karashe maganar kamar zatayi kuka, Kallon yanayinta yakeyi take tausayinta ya kamashi ,saboda yadda take dawainiya dashi Babu ranar da zatazo ta wuce batazo wajensa ba sanan Babu abinda yafi tada Mata da hankali irin ganinsa a halin rashin lafiya "ummaty Nima bansan dalilin da yasa nake tsintar kaina da kasa yin addua ba a dik lokacin da na fada cikin wanan halin dik yadda Zanso in motsa harshena inyi adduar nakan kasa yinta,wani lokacin Kuma nakan manta da yin wata addua saboda yadda nakejin kaina a wata duniyar ta daban,tamkar ana dagani sama ana yawo Dani a sararin samamiya wani lokacin Kuma nakan rasa hankalina na kankanin lokaci sai Kuma Inga na dawo" Tunda ya soma maganar take kallonsa cike da tausayawa wata kwalla ce ta makale Mata a idanuwanta Wanda ta kasa matsota,..."ya zainul Dan Allah inaso ka yawaita karanta hasbunallahu wa niimal wakeel kaji,nasan kasani Ina Kara tunatar dakai ne". "Ummaty Ina kokarin yin addua kinsani bakina Koda yaushe cikin ambaton isrigfari da salatin annabi nake Amma da zarar naji yanayin jikina na canjawa sai in tsinci kaina da kasa yin adduar"ya karasa mgnr cike da damuwa Shiru tayi cike da tsananin damuwa zuciyata ta tsunduma cikin tunani kala kala,wanan wani irin mugun ciwo ne dake mantar da bawa daga fadin ambaton Allah yayi rashin lafiya?tabbas wanan ciwon na zainul abideen yana dauke da sirhiri ne na manyan aljanu,Dan inba aljanu ba Babu yadda zaayi ya kasa motsa bakinsa yayi addua yayin rashin lafiya,idan haka ne kuwa Dole su dage da addua,Dan itace zata kawo karshen wanan jarabawar...tayi nisa cikin tunani ta tsunkayi kuryarsa Yana fadin "Ummaty bani da isassun kalmomin da Zanyi amfani dashi wajen gode Miki akan dawainiyar da kikemun "hawaye suka sauko daga idanuwansa, Farin kyalle tasa ta share Masa hade da goge Masa miyaun gefen bakinsa "ya Isa ya zainul tsakanina da Kai Babu godiya kaji?ko ka manta Kai yayana ne?"gyada Mata Kai yayi Yana murmushin karfin Hali, Aysha da fiyya kannensa ne suka shigo a tare suka zauna gefen gadon suna Jan ummaty da Hira sama sama take amsa musu Dan ita bamai yawan son magana bace... ********* Mutum uku ke zaune a fadar sarki da sarkin dawaki wazirin sarki da sarkin aska,...dukkansu gurfane suke a gabansa suna tayasa jimamin jikin na zainul abideen, "A ganina ranka ya Dade lokaci yayi da zaa duba ciwon yaron Nan a fahimci cewa ciwonsa ba na asibiti bane na gida ne,ni Nan inada Wanda zai iya yi Masa magani Kuma ya warke tamkar be Taba wanan ciwon ba ranka ya Dade,"cewar waziri Yana Kara gurfanawa a gaban mai Martaba Yana cike da alhini, "Waziri ni kaina ciwon zainul abideen yana daya daga cikin abubuwan da suka tsayamum a rayuwata banida yadda Zanyi ne da kaddarar Allah wadda take rubuce akanmu Amma nima inada wanan tunanin... "Inada hasashe akan ciwon Nan na zainul abideen ba haka kawai bane akwai wani Abu kasa ranka ya Dade da zaa kaishi wajen Mai magani da in akwai sa hannun wani a ciki ma komi zai bayyana"cewar sarkin aska Jimm kadan Mai Martaba yayi Yana nazarin zamcen nasu "bana zargin kowa da sawa Dan Dana Haifa hannu Dan haka inhar maganin zaayi Masa to da zuciya tsarkakakkiya zaayi Masa shi"... Hankalin sarkin dawaki ba karamin tashi yayi ba Nan da Nan cikinsa ya shiga kugi Amma sanin cewar magana daya zaiyi ya rushe maganar sauran yasa shi gyara Zama "ranka ya Dade me zai Hana a canjawa zainul abideen asibiti idan haka ne?ni a ganina a Gama na asibitin tukunna sanan a fuskanci na gargajiyan wadanan masu maganin mafi yawancinsu macuta ne" "Nima hakan nake gani sarkin dawaki zuciyata Bata aminta da zuwa wajen masu maganin gargajiya ba sanin sunsan zainul din asalinsa da inda ya fito" Waziri yace "ranka ya Dade yadda kakeso haka zaayi akai zainul asibiti muga abinda Allah zaiyi" Sarkin aska dake gefe mamakin halin Mai Martaba ya Kara cikasa... ********* "Zuciyata badan taso ba zahira hakan zanje gidan mai Martaba wallahi kawai Dan momy ta matsa sai munje ne" "Ki shirya da wuri gobe ya musaddik zai kaimu zamuzo mu daukeki kinji?" Badan taso ba ta amsa da to sukai sallama ta jefar da wayarta gefen gado Tana Jan tsaki ******** Shafa kansa gimbiya bilkisu takeyi yau "zainul jiki na samun sauki alhamdulillahi koh?" Daga Mata Kai yayi "ehh ammiey kwana biyu banji abun Nan da nakeji ba" "Masha allahu Ina ga magungunan Nan da aka canja maka sun amsheka kenan zainul zanyiwa mahaifinka magana akan magungunan sun amsheka" "Toh ammiey".... Ummaty dake gefe Tana faman hada Jakarta Dan tafiya gida ammiey ta dubeta "ummaty yau kinyi yamma a gidan Nan gashi ke kadai zaki tafi me zai Hana ki zauna tare dasu safiyya zan aikawa mamanki cewar zaki kwana a Nan" Shiru ummaty tayi Tana wasa da yatsunta kanta a kasa batare da tace komi ba,... Yanayin da zainul abideen ya Nuna Jin hakan ya tabbatarwa da gimbiya bilkisu yaji dadin cewar ummaty zata zauna a Nan din sai kawai tai murmushi ganin danta cikin farin ciki.... ********* Kaiwa da komowa sarkin dawaki yakeyi a cikin dakinsa Yana tunanin yadda zaa aiwatar da maganin da aka kawo batare da ansamu matsala ba gashi ummaty Bata dawo ba Tana can gidan tayaya zai ganta har ya yi Mata dabarar da ya sabayi? Shiru yayi na Dan wani lokacin take wata dabara ta Fado Masa ya sauke ajiyar zuciya..... *SLIMZY😍* [1/23, 10:36 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS ASSO...💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY✍🏼* *Wattpad@slimzy33* *Assalamu Alaikum.... Fan's a duk inda kuke ina muku fatan alheri. Wannan book na zainul Abiddeen na kud'ine, wanda yake sha'awar siya ze iya tura kud'insa ta wannan number akan naira dari biyu kacal.* *2073065733 Sha'awa Ibrahim UBA bank* Tura shaidar biyan kudinka ga wanan number 08161306299 6019111117 keystone Amina jibril Shaidar biyanka ga wanan number 08166177830 Kokuma ya tura katin waya na mtn na 200 ta wannan number 08039424298 kokuma 07084161619 Kud'in littafin d'ari biyuce kacal game buqatar ci gaban zainul Abiddeen seya tuntub'emu. *7* Kwance take idanuwanta a lumshe tamkar wadda take bacci Amma ba baccin takeyi ba ,minti minti takan juya kwanciyarta saboda gajiya da takeyi kwanciya gefe daya ga bacci yaki daukanta ko kadan,hakan Nan ta bude lumsassun idanuwanta kurriii a kan fankar dakin dake juyawa a hankali,meke damunta yau ne?bacci yayi kaura a idanuwanta?...ko wani Hali ya zainul abideen ke ciki oho?dikda yau ne Rana ta farko da ta kwana a cikin gidan nasu Amma tanada bukatar sanin halin da yake ciki yanzun,dago kanta tayi ta dubi agogo karfe daya da minti goma Sha biyar na dare sai kawai ta maida kanta pillow ta tsunduma cikin kogin tunani,dik tunaninta be wuce akan yadda zainul abideen zai samu lafiya bane?ta auna ta juya dik yadda tai tunanin sai taga babu mafita, mafita guda daya ce shine iyayensa su amince su nema Masa maganin gargajiya ko zai samu lafiya Amma abun ya faskara,kwata kwata basuda raayi akan hakan babu ma maganar zuwa gun Mai magani sai maganar likita,kullum narkar da naira akeyi Amma kullum jiya iyau,hakan besa sunyi tunani akam lamarin su kamo bakin zaren ba,to ita ta Yaya zata tunkari wanan ciwon na zainul gashi tana bashi magani a boye Amma kullum jiya iyau,....sauke numfashi tayi ta gyara kwanciyarta Dole ta nemi mafita akansa Dan tabbas tana tsananin tausayin sa tanaso Shima ya samu lafiya kamar kowa...tayi nisa a cikin kogin tunani ta dau tsawon lokaci Mai yawa tana tunani har bacci barawo ya saceta batare da ta tsaida shawara a zuciyarta ba.... ******* Washe gari ta shirya tsaf ta maida kayan jikinta da hijjabinta tana zaune a parlor dik ta takura ta kosa ta Shiga inda zainul yake taga ya ya kwana,...dago Kai gimbiya bilkisu tayi ta dubi ummaty "ah ah ummaty ya kika maida kayan jiya?bayan nace fiyya tabaki kayanta kala daya kisanya tunda jikinku daya ko Baki Bata bane fiyya?ta juyo da dubanta inda fiyya ke zaune tana kaeyawa da karamar kanwarsu afee, "Na ajiye Mata a kan gado ammiey Kuma na fada mata ga kaya Nan,kawai dai kinsan ummaty Bata sakin jiki da mutane batada sabo" "Tashi ki canja kayan jikinki ummaty"..babu musu ummaty ta Mike ta nufi dakin da suka kwana jiya dam ta canja kayan jikinta,...jimm kadan baafi minti goma ba ta fito sanye da kayan Amma ta maida hijabin jikinta,kallonta kawai ammiey tayi ta girgiza kanta tana murmushi yarinyar dabiunta masu kyau ne tun tana kankanuwarta ba karamin burgeta takeyi ba... ********* "Wadanan sune files din zainul abideen na asibitin Nan gabaki daya Kuma dukka sun kunshi dik wani treatment da akeyi Masa Kama daga ranan daya fara zuwa har yanzun da muke magana ranka ya Dade,Kuma dik wani treatment Yana ciki na magungunansa da testes da akeyi Masa da gwaje gwaje komi da komi ranka ya Dade babu inda bamu gwada ba a jikin yarima,dik wata gaba ta sadarwa mun bimciketa Amma sakamakon guda da'ya ne komi lafiya Lau yake sawa"numfashi Mai martaba ya sauke hade da gyaran murya, "Yanzun likita babu abinda zaa iya yi mishi bayan haka?bincike nakeso sosai ayi mishi likita ko zamu gano ciwon dake damun d'ana shine kadai da namiji da Allah ya bani ya Sanya mun soyayyarsa a cikin zuciyarta nakeji zan iya salwantar da duka dukiyar Dana mallaka inhar zainul abideen zai warke ya hau gadon sarauta" "Ranka ya Dade nadade da tunani akam ciwon da'n Nan naka tamkar jifansa akayi,ko shafar aljaju,Inba hakan ba babu yadda zaayi dik wanan gwaje gwajen da mukayi mu kasa gano abinda yake damunsa sakamakon kwaya d'aya ne shine lafiyarsa kalau ranka ya Dade a duba lamarin Nan" "Ban taba zargin wani ko wata zayiwa dan Dana Haifa wani abuba bana zargin kowa zuciyata tsarkake take da kowa Dan haka zamu cigaba da nema Masa lafiya a asibiti har Allah yasa mudace likita"sosai kalaman Mai martaba suka sanyayarwa likita da jiki babu abinda ya Kara burgesa da dattijon kamar yadda yake da dattako da tawakkali danyarda da kaddara sosai ya Kara ganin girmansa da kimarsa a idanuwansa... "Insha allahu Zanyi iya bakin kokari na ganin ansamu cigaba wajen samun lafiyar magajin sarki,Allah ya Kara maka lafiya da kaunar talakawa ranka ya Dade,da haka sarakuna suke a fadin duniyar Nan da talakawa da alummarsu basuyi kukaba Allah yabawa magajin sarki lafiya" Kyataccen murmushi Mai martaba yayi da alama yaji dadim adduar da doctor yayi yace "ameen"ya Sanya hannnunsa cikin aljihunsa ya Ciro check din kudi ya mikawa likita kamar yadda ya Saba yi mishi kyauta yau ma hakan ne,likita ya Shiga zubo adduoi tare da fatan alheri ya biyo bayansa Nan fadawa suka zagaye sarki da Yan rakiyarsa,suka Shiga bi daki daki na asibitin da Mai martaba suna duba marasa lafiya sarki nayi musu alheri. ******** Washe gari sauri sauri ummaty ta shirya ta fito mahaifinta ya tsaidata "ummaty tun shekaran jiya aka kawo maganin magajin sarki to ganin Baki kwana a gida ba shiyasa na ajiye Miki zuwa yau" "Baba ka manta dik bayan wata shida ake kawo maganin?Wanda na bashi karshe ko wata daya baayiba gashi an kawo wani Kuma kace lakanin maganin dik bayan wata shida ne ko uku"take zuciyarsa tai darrr baiji mamaki da Jin hakan daga gareta ba sanin wacece Yar tasa wajen kaifin basira da kula sai ya dake "ummaty ganin halin da yaron Nan yake ciki ne yasa nai tunanin a canja mishi lokacin bada maganin zuwa sati biyu biyu ko sati daya yadda zamu rinka ganin cigabam maganin anasamun waraka ko babu?tausayin yaron nakeji da iyayensa wallahi"wani irin farim ciki ne ya lullube ummaty hannunta har rawa yakeyi wajen karbar gorar ruwan maganin ta rike da kyau a hannunta ta dubi mahaifinta cike da farim ciki "Kai baba nagode Allah yasaka da alheri yasa kafi haka Allah yasa wanan maganin ya Zama silar warkewar ya zainul" "Ameen"yace ya bita da kallo yadda take farin ciki tana sauri sauri ta tafi har takai zaurem gidan ta dawo "kaceda innah idan tadawo islamiyya nayi girkin Rana kafin in tafi"to kawai yace Mata ta fice tana zumudi ,tausayin ummaty ne ya lullube sarkin dawaki yadda take cike da zumudi Allah sarki baiwar Allah da tasan menene da dikda shi ya haifeta saita tsanesa,shi Kansa jikinsa yayi sanyi haka ya shige daki... ******* Tafe take a nutse dik tayi zufa saboda saurin da takeyi ta karasa gidan dik tagaji Dan a kasa ta tako Saida sukazo daff da ita a mota suna tafe sunajin kida zahira ta dubi warisat "kinsan wacece waccen take tafe tana hardewa da zani?ga uban hijabin?"batare da ta kalleta ba ta amsa da "wacece?" "Ummaty ce Yar aikin ya zainul Yar wahala sai sauri takeyi taje saboda tsabar Neman suna da Neman gindin Zama wajen masu kudi' Kallon ya musaddik warisat tayi kasantuwar itake gaban motar tace "takamun ita da mota"ta kauda kanta tamkar ba ita tai maganar ba,lashe leben sa yayi Wanda hakan shine al'adarsa Koda yaushe "dik yadda kikace hakan zaayi ta wajena,Amma wanan bazai yuwu bane saboda yarinyar tanada kyau"ya karashe maganar Yana me kallon yanayin warisat din, Tabe bakinta tayi batare da ya fahimci inda ta dosa ba tamkar bazatayi magana ba sai tace "ka nemeta Mana"tai maganar daidai yayi parking a kofar gidan,"da inada raayin auren yaran talakawa to tabbas Dana nemeta,da zuciyata na kaunarta babu abinda zai Hana ban nemeta ba Koda da holewa ne,saidai zuciyata babu Wanda takeso take muradi take marari kamarki warisah Amma narasa gane kanki,Ina azabtuwa da sonki ki tausayamun"batare da tace komiba ta bude murfin motar daidai Nan ummaty ta Iso har zata wuce warisat ta kirata "zoki shigarmun da wanan jakar sashen ammiey"shine abinda tace ta juya tai gaba abinta,turussss ummaty tai Tana bin warisat da kallo yadda take take taka kasa tamkar tana kirgawa lallai wanan ta Gama Raina mata wayau,wato ita zata aika da jaka ta shigar Mata dashi saboda ta wulakantata ta Nuna Mata ita bakomi bace face Yar talakawa?Koda yake ubanta ma be wuce Dan aikensu ba, Har ta Kai kofar Shiga ta juyo ta kalli ummaty dake takowa a hankali hannunta na rike da jakar warisat da ya musaddik suna biye da ita "karki bari in rigaki Shiga gidan"....tabdijan me wanan take nufi?to idan ta rigata Shiga me zatayi matq?Koda yake jikar sarauta ce zata iya wulakantata cikin mutane ba damuwarta bane, Sashen gimbiya rumana zahira da warisat da musaddik suka Shiga Dan su gaisheta kafin su karaso sashen gimbiya bilkisu. Cike da masifa fiyya ke magana tana kallon ummaty rike da jaka "ke Yar aikin gidansu ce da zata dau jaka ta Baki?Koko ta ganki da uniform din bayi ne da zata Baki dakon jaka tun daga kofar shigowa ta kudu?wanan wani irin wulakanci ne da kaskamci?"sadda kanta ummaty tayi batare da tace komiba ta ajiye tana Shirin barin wajen fiyya ta tsaidata "daga yau Kar wata shegiya ta sake Baki dakon jaka ko wani aiki kiyi tunda ke ba kuyanga bace ba Kuma baiwa bace"tana cikin fadin haka warisah ta shigo ko kallonsu batayiba fiyya ce ta bita da mugun kallo kamar ta shaketa ta huta,...Sumi Sumi ummaty ta juya Rai babu Dadi ta nufi sashen zainul abideen. ******* "Ya na ganki yau wani iri ummaty?"yace Yana karewa yanayin nata kallo,sai kawai ta kirkiro dariyar karfin Hali tana fadin "dama zolayarka nakeyi inji mezakace babu komi yaayah"kallo kawai ya bita dashi badon ya yarda da maganarta ba, Gorar ruwan maganin ta Ciro "kaga ya zainul ruwan adduarka ya dawo dik sati biyu ko sati daya zaa rinka baka yadda zaka warke da wuri ka Mike koh?"..ya gyada Mata Kai Yana murmushi,ta bude gorar takai bakinsa ba musu ya hau Sha Nan da Nan ya shanye gorar tasss ta janye daga bakinsa ta rude gorar ta jefa a Jakarta ta maida hankali Kansa tana murmushi,"zamuyi karatun mu koh?"ta tambayeshi tana murmushi ya daga Mata Kai ta Ciro Dan karamin littafin ta suka soma karatu,sunkai awa biyu tare sunayi sanan ta Mike da niyyar yin alwala Tai sallah ta Shiga toilets din dakin, Koda ta Gama alwalar ta fito abinda ta ta gani ne yayi matukar furgitata a guje ta fito tayi Kansa ganin yadda yakeyi har Kansa ya karkace Yana Shirin fadowa daga gadon ta taresa,jikinta sai kyarma yakeyi tsananin tsoro ya kamata,dik yadda taso da ta taresa abun ya faskara dukkansu sai suka Fadi kasa,Jin karar faduwa yasa fadawan shigowa a guje dakin sukai Kansa, "Shegen iyayi irin naki kina ganin zai Fadi Mai makon ki kiramu shine kikazo ki dagasa gashinan ya Fado Miki a jiki kun Fadi duka dama kinji ciwo"haka ta Mike tana hawaye,Tana bin sa da kallo shi kam sai kakari yakeyi tamkar Wanda zai sheka lahira, Nan da Nan daki ya cika hankalin mutanen gida a tashe babu Wanda takai gimbiya bilkisu tashin hankali itada gimbiya rumana dik yadda sukaso su dake Suma Saida suka zubda hawaye,har hajiya Kaka Saida labari yaje mata taxo hankali a tashe, Ita kuwa ummaty sai kuka takeyi dik ta Gama rudewa Dan hankalinta ba karamin tashi yayiba take zuciyarta ta Shiga ayyana Mata ko maganin data basa ne,wata zuciyar tace dama ya kwana biyu ciwon be motsaba ba maganinki bane da wanan ta kauda tunanin ta cigaba da sharar kwalla tana addua tana tofa Masa a fakaice,dik wanan budurin tashin hankalin da akeyi zahira da warisah suna patlorn ammiey suna kallo suna cin apple ko a jikinsu,warisat da kakarin zainul ya isheta earpiece tasa a kunnenta tana yatsinar fuska kamar zatayi kuka. ******** Kowa ya watse a dakin sai su kadai yasamu barci ta kafesa da Ido ko kiftawa batayi tunanin mafita kawai takeyi tana hawaye..Anya ba abinda take ayyanawa a zuciyarta shine mafita ba? *SLIMZY😍* [1/23, 10:36 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS ASSO...💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY✍🏼* *Wattpad@slimzy33* *Assalamu Alaikum.... Fan's a duk inda kuke ina muku fatan alheri. Wannan book na zainul Abiddeen na kud'ine, wanda yake sha'awar siya ze iya tura kud'insa ta wannan number akan naira dari biyu kacal.* *2073065733 Sha'awa Ibrahim UBA bank* Tura shaidar biyan kudinka ga wanan number 08161306299 6019111117 keystone Amina jibril Shaidar biyanka ga wanan number 08166177830 Kokuma ya tura katin waya na mtn na 200 ta wannan number 08039424298 kokuma 07084161619 Kud'in littafin d'ari biyuce kacal game buqatar ci gaban zainul Abiddeen seya tuntub'emu. *8* Wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tare da gamsuwa da shawarar da zuciyarta ke Bata dikda Bata bada karfi akan hakan ba Amma tabbas akwai haske ga wanan shawarar, Kallon gefensa tayi sai sharar baccinsa yakeyi Yana sauke numfashi a hankali dik ya fada a fuskarsa cikin Yan awanni ya canja gabaki daya,fuskar Nan ta Kara fari tasss hancinsa ya fito zir tamkar balarabe gashin girarsa kwance lufff,lumshe idanuwanta tayi ta bude "Allah ya baka lafiya ya zainul ya kawo karshen wahalar Nan... ******** Washe gari yau jiki da jini ummaty ta tashi da ciwon Kai tun dare take fama dashi irin ciwon kan Nan na gefe daya har safiya ko kanta Bata iya dagawa,shiru shiru innah bataga fitowar ummaty tunda suka hadu da asuba a wajen alwala tayi tashiga daki Bata ganta ba har karfe Tara da wani Abu na safiya,mikewa tayi daga zaunen da take a kofar daki inda suka Saba Zama suyi Karin safe ta nufi kofar dakin ummaty,labulen dakin ta da'ga da sallamarta ta Shiga kasantuwar ko Ina a rufe sai dakin yayi duhu Amma tana iya hangenta lullube akan katifarta,a hankali ta karasa ta xauna gefen katifar ta Kira sunanta,"ummaty lafiya dai ko?tun safe Banga fitowarki ba balle ki karya kitafi gidan Mai martaba" "Kai na ke ciwo gefe daya innah tun Daren jiya haka na kwana yanzun ma na tashi dashi ko iya daga kaina banayi" "Assha subhanalillahi,shine kikai shiru kika kasa fadamin ummaty?kika kwanta a daki?a haka Zaki samu lafiya?ai Dole sai da magani ko?yanzun tashi Kisha kunu ga kosai can malam ya siyo kafin ya fita,ni Bari inje chemist din bawa insiyo Miki magani ko?"dakyar ta yunkura ta xauna ta bude idanuwanta da sukai jajir daka kalleta kasan batada lafiya tace "toh innah" "Yau a hakura da zuwa gidan Mai martaba tunda Kinga bakida lafiya ko?komi sai da lafiya akeyi"gyada Mata Kai kawai tayi batare da tace komiba ta Mike ta je jikin drawer ta dau brush dinta Tai hanyar fita...itama innah mikewa tayi ta zura hijjabinta ta fice, ******* Mai martaba na saman kujerarsa a zaune gefe da gefensa matansa ne sunsha ado da kwalliya da tsadaddun laces irin na alfarma ko wacce sanye take da Dan kunne da abun wuya na zinari da kambu na zinari a hannayensu sunyi matukar kyau Dan dukkansu ba baya bane wajen iyau musamman gimbiya bilkisu da ta kasance amarya Kuma Mai kananan shekaru sanan ga kyau irin na usulin hausa Fulani idanuwan Nan farare tassss da jerarrun hakora farare,itama gimbiya rumana ba bayaba wajen kyau,katton plate ne da fruits cike a ciki danginsu apple,ayaba,kankana,da abarba dik an yayyankasu .gyaran murya Mai martaba yayi, "Na taraku ne a Nan wajen Dan in tattauna daku dangane da ciwon yaron Nan zainul abideen,abun kullum gaba yakeyi,sanan mutane sunata maganganu akan cewar tunda har yakai wanan shekarun ciwonsa ba na asibiti bane na gargajiya ne shine nakeso inji shawarar iyayensa "murmushi kadan gimbiya bilkisu tayi ta dubi rumana tace "kece uwarsa ai ke yakamata kice wani Abu ni banida abin cewa dangane da ciwon Nan na zainul" Ajiyar zuciya gimbiya rumana tayi "ya kamata muyi hakuri da kaddarar data fadowa magajin sarki mu fawwalawa Allah lamarin ba zancen mutane ko shawarar mutane zamubi ba,yawanci mutane da kuke gani macuta ne,abinda yasa suke wadanan maganganun be wuci Dan sunji ubansa sarki bane akeso ayi amfani da wanan damar a cucemu,bama kudin da zamu kashe bane damuwa face tsoron garin nema Masa magani a janyo Masa wani cutar,ni gaskiya ban amince a Mika d'ana wajen wani me magani ba,idan hakan akeji me zai Hana a canja mishi wani asibitin Mai martaba?idan wadanan sun kasa aikinsu"ta karashe maganar cike da damuwa idanuwanta na kawo ruwa,....tausayi sosai tabawa Mai martaba yadda ta dauki son duniya ta dorawa zainul abideen tamkar ita ta haifeshi,"shikenan uwar maganin sarki dik yadda kikeso hakan zaayi insha allahu zansa a bimcikamun asibitin da yafi wanan din sai mu kaishi mu gwada muga abinda Allah zaiyi koh?"jinjina Kai gimbiya bilkisu tayi batare da tace komiba Banda murmushi da tayi Dan ita dama akwai sarauta.. Mai martaba ne yayi musu umarni akan su tashi su Shiga ganin jikin nasa a tare babu musu ko wacce ta kike Yana gaba suna biye dashi a baya sauran fadawar kofar fada sukabi bayansu da bayi dake zagaye da sashin na sarki... Rukosa tayi jikinta tana shafa Kansa cike da so da kauna,gimbiya rumana kenan..."ya jikin naka yarona?kana samun sauki umm?"ta kafesa da Ido tana karantar yanayin nasa,...murmushi ya kirkiro Mata "da sauki ummah yau Banga ummaty ba"yayi maganar tamkar zaiyi kuka, Waige waige gimbiya rumana keyi "la wallahi ban lura ba da muka shigo zainul banganta ba to me ya hanata zuwa yau din?" Gimbiya bilkisu ta karbe zancen "keda danki bakuda adalci ranki ya dade,wanan yarinyar fa ba aikin kudi takeyi ba ballantana ace Dan me batazo ba?Kuma ma dai jiki da jini,kunsan yau da gobe sai Allah kila wani abun ne"murmushi gimbiya rumana tayi batare da tace komiba,shi kam Mai martaba tsaye yake akansu Yana binsu da kallo Yana Kara Jin son iyalinsa har cikin ransa yadda ko wacce ta rungumi yaran Yar uwarta kamar ita ta haifesu musamman gimbiya rumana da komi na yaran a hannunta yake,...shasshekar kukan zainul ce ta fargar Dasu gabaki daya har suna hada Baki wajen tambayarsa "zainul abideen lafiya?me kakeso" "Ummaty banganta ba yau batazo ba ace tazo"shine abinda yace Yana cigaba da hawaye tamkar karamin yaro...dukkansu dake dakin sukai tsit suna binsa da kallon mamaki,lallai shakuwarsu har ta Kai haka?Koda yake yau da gobe batabar komiba,...shafar Kansa gimbiya tayi "kayi shiru yanzun Nan zan aika dik inda ummaty take a nemomin ita tazo yarona nason ganinta Amma sai kayi shiru kaji?kayi shiru"ya daga Mata Kai kawai tasa kyallen towel ta share Mai hawaye,ta dubi gimbiya bilkisu "yanzun zan aika Kiran ummaty gidansu"murmushi kawai gimbiya bilkisu tayi batare da tace komi ba sun Dade a dakin zainul abideen Yana rigima sanan suka fito suka barshi da masu kula dashi... ******** "Nikam warisah Wai yau Banga wanan Yar iyayin tazo ba ko dai an koreta ne?"cewar zahira cike da son Karin bayani, "Ita tasani dama kwadayi ke tafe da ita ba wani abuba kila dai akwai abinda ya hanata zuwa,ni wanan yarinyar haka kawai jinina be haddu da itaba taita sumsum da Kai Wai ita ustaziyya kullum cikin hijabi kamar muna fuka,gata da kyau Amma kullum a lullube sai kace nakasasshiya,ni dama taimakonsa tayi ta auresa suje can su karata ta cigaba da jinyar tasa har ya mutu"ta karashe maganar hade da tsaki tana maida dubanta ga tv . Sallamar ummaty ce ta katse Masu zancensu dukkansu kamar hadin Baki suka juyo suna kallonta a tare sai Kuma suka kwashe da dariya suna Kare Mata kamar sunga wata halitta ta daban,...iya kuluwa ummaty ta kulu da abinda sukai Mata saidai tasan ko giyar wake Tasha Bata Isa tace komiba akan abinda sukayi Mata tunda ita din ba Yar kowa bace,sai kawai ta ratsa su ta babban patlorn ta nufi kofar da ta raba sashin zainul abideen Dana mahaifiyarsa Tai shigewarta,. Kuriiii yayi da idanuwansa akan kofa tamkar me jiran wani Abu,kamar daga sama yaji sallamarta da sauri ya daga idanuwansa ya sauke akanta,take ya sauke nannauyar ajiyar zuciya a fili,sai Kuma ya Bata ransa ya rufe idanuwansa ruff Karasowa tayi cikin dakin ta nemi kujerar data Saba Zama ta xauna tana Kare Masa kallo fuskarta dauke da guntun murmushi,fahimta da tayi Wai yayi fushi ne Nan,"ya zainul"ta Kira sunansa cikin wata irin murya Mai sanyi,shiru be amsaba ta Tai Yar dariya "bude idonka Mana ya zainul kaji?"Tai maganar cike da shagwaba tana tura Baki gaba,...sai kawai ya bude idanuwansa ya sauke akanta kamar bazaice komiba sai ya bude Baki a hankali yace "ummaty Ina kika Shiga yau?bakizo ba tunda muke dake Baki taba fashin zuwa ba sai yau,dik na damu ko kin fara gajiya Dani ne"yai maganar a sanyaye, "Haba ya zainul banyi tsammanin wanan kalmar ta gajiya daga bakinka ba,Dan kawai yau daya baka ganniba sai kace Wai nagaji dakai?ban tabajin mummunar kalma kamar wanan ba gaskiya Raina ya baci Kuma nayi fushi"ta juya baya tana Kara turo bakinta gaba, "Kiyi hakuri nayi laifi kinji,nayi kuskure bazan sake fadin wanan kalmar ba tunda bakyaso...kawaidai na damu ne dayawa shiyasa Amma na daina"ya kafeta da Ido, "To shikenan ya wuce nadaina fushin"ta karasa maganar tana dariya,shigowar gimbiya rumana ne ya katse musu zancensu da murmushi dauke a fuskarta "d'iyata ummaty Ina kika Shiga yau bakizo ba sai yanzun?kinsa yarona rigima Wai be ganki ba harda Yan hawayensa?gaskiya karki Kuma,yanzun tabawa kecemun taga wucewarki Ina Shirin aikawa gidan naku ne inji ko lafiya dama"sunkuyar da kanta ummaty tayi "lafiya Lau ummah kawai yau natashi da ciwon Kai ne shine Nasha magani na kwanta da na tashi naji sauki shine nace Bari inzo" "Toh Allah ya Kara sauki,Bari inje dama nazo inji motsinsa ne tunda Baki zoba Bari intafi tunda mutuniyar tazo ko zainul"murmushi kawai yayi ya daga Mata Kai,ta fice ta rufo kofar, Jakar da tazo da ita ta bude ta Ciro sabon MP3 Mai shegen kyau tana murmushi "ya zainul kagani na biya kasuwa na siyo maka wanan Dan ka rinka sauraren karatun alkurani kaga har haddarka ma sai ka rinka tulawa ko?"sosai zainul abideen yaji Dadi daga ganin yadda yake faraa a fuskarsa,itama faraar takeyi ta Shiga har hadata "kagani har kurani nasa aka tura complete a ciki idan na saita maka sai insa maka a kunne idan ma sura ta Kare zai Shiga ta gaba ko?kaga idan kana sauraren karatun kur'ani zaka samu sassauci ko?Kuma kurani Kansa waraka ne Kuma haske ne ga ko wace irin cuta Gama al'ummar musulmi Baki daya" "Nagode ummaty Allah ya biyaki da gidan aljannah" "Ameen"tace ta Shiga gwargwada karatun... ******** "Sarkin dawaki nafada maka bana bukatar shakuwa a tsakanin zainul abideen da ummaty Amma abinda nake gani tamkar sun shaku har shakuwar ta wuce inda muke zato"Tai maganar Rai a bace, "Shakuwar zainul da ummaty dole ne fa,tunda kullum suna tare Kinga Dole su shaku idan basa tare babu yadda zaayi hakarki ta cimma ruwa,idan Kuma Kinga kinfison a rabasu shikenan wanan ba matsala bace a wajena,Dan Nima Dole ce tasa ummaty take kusantar sa Dan baso nakeyi ba"ajiyar zuciya ta sauke "akwai abinda nake Jin tsoro nake gudu ne dangane da zamanta da shakuwarsa da shi" "Me kike tsoro kike gudu ya wuce kice Mai martaba yace a hadasu aure?to harabada bazan Bari ummaty ta auri zainul abideen ba Koda warkewa yayi kuwa ballantana yadda yake a nakashe ah ah wallahi"gwauron numfashi ta sauke hade da lallausan murmushi,sai yanzun zuciyarta Tai Mata sanyi da Jin abinda sarkin dawaki yace,ballantana Bata fatan zainul abideen ya warke harabada. *SLIMZY😍* [1/23, 10:37 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS ASSO...💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY✍🏼* *Wattpad@slimzy33* *Assalamu Alaikum.... Fan's a duk inda kuke ina muku fatan alheri. Wannan book na zainul Abiddeen na kud'ine, wanda yake sha'awar siya ze iya tura kud'insa ta wannan number akan naira dari biyu kacal.* *2073065733 Sha'awa Ibrahim UBA bank* Tura shaidar biyan kudinka ga wanan number 08161306299 6019111117 keystone Amina jibril Shaidar biyanka ga wanan number 08166177830 Kokuma ya tura katin waya na mtn na 200 ta wannan number 08039424298 kokuma 07084161619 Kud'in littafin d'ari biyuce kacal game buqatar ci gaban zainul Abiddeen seya tuntub'emu. *9* ******** Kwance suke su biyu kan makeken gadon dakin zahira da warisah gefe fiyya ce zaune kan kujerar hannunta rike da wayarta tana latse latse hankalinta na kan wayar,...shiru dakin babu me yiwa Dan uwansa magana kusan dama fiyya da warisah ba shiri sukeyi sosai ba ko wacce ji da kanta takeyi da sarauta musamman warisah da idan bakasaniba sai ka dauka cewa itace Yar sarki, Dan tsaki warisah taja tai jifa da story book din dake hannunta ganin wayarta na haske,."lafiya dai kikejan tsaki haka?" "Wanan Dan anacen ne yayanki zai dameni da Kira,yakira yakira ban daukaba Yana Kara kirana nifa ban fiyeson damuwa ba zahira kinsani ki fada mishi"mtsww taja dogon tsaki,"nikam warisah Wai me kike takama dashi ne haka?kikewa ya musaddik wulakanci?ba kyau kika fishi ba fa ballantana kice Zaki wulakantasa ba Kuma asali kika fishiba Dan asalinku daya yadda kike takama da mulki haka Shima hakan ,kawai dai soyayya gamon jini ce yasa ya nacce Miki ai ga Yan Mata Nan a family da yawa da be nemesu ba?ni ya fiyya ma naso ya nema"ta karashe maganar cike da haushin warisah, "Kanki akeji,da kinsani kice ya nemi fiyyar Mana ya daina nacemun haka,ni dik ya takurani wallahi so yakeyi yazo Amma Wai beson zuwa Nan Dan kada Mai martaba ya fahimci akwai soyayya tsakaninmu ace ai Mana aure da wuri Wai ya kosa in dawo gidanmu,besan Nima a takure nake da Nan din ba kamar nazo prison wallahi,gashi bacci ya gagari mutum saboda numfashin wancen mutumin na daki ya isheni" A hassale fiyya ta dago kanta wadda tunda suka soma hirarsu Bata bi ta kansu ba sai yanzun da warisah Tai wanan furucin "karki kuskura idan kina rashin kunyarki kice Zaki sako ya zainul ciki Dan shi ba saanki bane Kuma karki fara kice Zaki aibantashi Dan zan wulakantaki" "Ni kike cewa Zaki wulakanta saboda yayanki nakasasshe?"a hassale safiyya ta Mike ta sharara Mata Mari Karo na farko tana nunata da yatsa "ki Shiga taitayinki warisah dik take takenki Ina kallonki ne Ina kyaleki tunda kikazo gidan Nan Amma kada kice Zaki Shiga gonar Dan uwana nafada Miki tunda bakida mutunci ko wanine kikaji Yana zaginsa ke ba me tare Masa bace?Amma har ki iya bude Baki ki aibantasa to kulll ya tsaya daganan ai Shima ba yin Kansa bane,Kuma insha allahu sai kinyi danasanin abinda kika fada sai kinzo da Kanki kina Neman ya kalli inda kike ma balle ya kulaki da izinin Allah" "Saidai in a mafarki ne zanzo in nemi kulawar tasa ko kuwa warkewar tasa Kuma wallahi sai kinsan kin mare ni" "Idan kece ke bada lafiyar saiki hanasa lafiyar Mara mutunci kawai,kizo har gidansu kina ci Masa fuska ko da yake gado kikai indai rashin tarbiyya ce da rashin mutunci"zuwa yanzun warisah ranta ya Gama baci wato ita fiyya ta kalla ta kirata da dangin marasa mutunci?su waye Mara mutuncin kenan?uwarta data kasance jinin Mai martaba kanwarsa uwa daya uba daya ko kuwa mahaifinta da ya kasance attajirin gaske Shima Kuma jinin sarauta?,Bata Gama tunani ba afnan ta shigo dakin tana binsu da kallo daya bayan daya sanan ta dubi safiyya tace "anty fiyya kizo Wai su ya Zahra sunzo Kuma ammiey taji Kuna hayaniya"tana Gama fadin haka ta juya Tai waje abinta cike da natsuwa, Fiyya ficewa tayi Tana bin warisat da harara , Zama tayi gefen gadon cike da masifa take fadin "wallahi saina Rama abinda taimun sai NASA ya haris ya ramamun wanan wulakacin da taimun ai Ina sane da cewar soyayya sukeyi zatasha mamakin yadda zai wulakantata,kafin nata yayan ya warke ya wulakantani kamar yadda tace nawa zai fara yi Mata,sai na tar watsa Mata farin cikinta,tunda haka tace zamuyi mu zuba,Kuma yau din Nan zanbar gidan Nan in koma gidan ubana gidan marasa mutunci Kuma saina fadawa momy"ajiyar zuciya zahira Tai "da zakiji tawa da Baki Fadi maganar Nan ba Dan wata wutar Zaki Kara hasawa kinsan halin momynki dai nidai ba ruwana kada ace mune" "Farar Kura matsoraciya ai bazaki iyaba,Toni zan iya me suka fimu dashi?mulki ko sarauta?(Fatima Zahra)ko dokiya?dik abinda suke takama dashi munadashi kawai dai Dan iyayenmu Mata ne ba maxa bane shiyasa Kuma Mai martaba shine kadai yaron hajiya Kaka shiyasa" Shiru zahira Tai batasake cewa komi ba,Amma har ga Allah tasan abinda warisah tayi Bata kyautaba,Kuma wanan wulakacin da rashin mutuncin babu inda zai kaita sai danasani Mara amfani. ********* "Ah lallai zainul jiki yayi kyau gaskiya kwana biyu kasamu lafiya,Dan ammiey da mukai waya tace tun daga ranan da ciwonka ya tashi yau kwana hudu kenan ciwon be Kara tashi ba Kuma gashi har kana iya dadewa zaune a wheel chair alhamdulillahi"murmushi yayiwa babbar yayar tasu Zahra "gaskiya alhamdulillahi ku Kara sani a addua Allah ya karamin lafiya".. "Ameen kanina,kagani ga kula cen na shigo da ita favourite Dinka nayo maka da kaina nazo maka dashi" "Dambun couscous anty?"daga Masa Kai tayi Tana dariya "ehh zainul shine kaji Dadi koh?" Shima daga Mata Kai yayi Yana murmushi batare da yace komiba, "Ummaty ki zuba Masa Dan Allah ki tabbatar yaci sosai kinji kema ki zuba kici karkice Zaki fulatancin Nan naki Dan kin Zama Yar gida"sunkuyar da Kai ummaty tayi Tana murmushi kasa kasa, "Fiyya muje sashen ammiey annnur ya gaisheta"tare suka fita da fiyya tana rungume da yaron babbar yayarsu Zahra, Bayan fitarsu ummaty ta dubi zainul "ya zainul kwana biyun Nan jikin naka yayi kyau gaskiya alhmdllh"murmushi kawai yayi Mata yanajin kaunarta cikin jinin jikinsa,...a wanan zamanin samun kamar ummaty ba dik Mata ba... ******** "Ummah ai kam kwana biyu jikin zainul yasamu sauki yau bakiga yadda yayi kyau dashi ba kamar bashi ba wallahi,bakiji yadda naji dadin ganinsa ba Allah ya tasar Mana kafadarsa " "Ameen" gimbiya rumana tace,Tana bin diyar Tata da kallo tamkar zata hadiyeta, "Ummah Amma dai ya kamata a canjawa zainul wajen magani ko?ko wani asibitin ne akaishi kila magungunan wancen asibitin ne Basu karbesa ba suke Kara da jikinsa rikicewa tunda ammiey tacemun kwana biyun Nan baa bashi maganin asibitin ba"shiru gimbiya rumana tayi batare da tace komi ba kusan minti biyar "ummah magana nakeyi"a hankali ta maida kanta ga Yar Tata "wallahi tausayin yaron Nan nakeji zahrau ace shekara da shekaru yaro be huta ba yau ciwo gobe lafiya?wanan wace irin jarabawa ce?astagfirullahi Kar nayi sabo Allah ya bashi lafiya " "Ameen ummah" ********* Kamar yadda sarki dawaki ya fadawa ummaty bada magani ya dawo dik kwana bakwai yau hakan ta kasance "ummaty ga maganin Dan uwan naki" Cike da zumudi ta dubi mahaifinta "yauwa baba dama yau zan tuna maka maganar maganin nasa gara a rinka bashi akai akai ko Allah zaisa mu dace"tausayin gaske ta bashi firucinta sai ya dauke Kansa,. "Insha allahu zaa dace ummaty kiyi ta kokarin Yi Masa" "Insha allahu baba" ********* Kamar ko da yaushe a kwanakin Nan biyu da yake samu ya xauna Akan wheel chair yau ma zaune yake Yana sanye da bakaken kaya kaftani masu tsadar gaske anyi musu aiki irin na sarauta yayi kyau sosai yadda yake zaune zaka dauka idan kace ya tashi zai tashi,kunnensa makale da karatun alkurani cikin sabuwar mp3 din da ummaty ta kawo Masa Yana saurare Yana lumshe idanuwa ta shigo, besan ta shigo ba ta Dade tsaye tana jifansa da murmushi sanan ta karaso cikin dakin Shima ya bi ta da nasa murmushi "Barkanki da zuwa ummaty maanociyar murmushi"yace Yana kallon gefenta tamkar me tsokanarta, "Umm ya zainul kenan irin kirari din Nan kakemun sai kace wata sarauniya ko matar sarki?ka manta ni din ba kowa bace?" "Ke din wani Abu ce Mana ummaty tunda ko ba komi babu Wanda yasan tsakaninki da mahaliccinki,idan ya kasance kinada kyakkyawar maamala wajen ibadah da bautar Allah Kinga kinada babban matsayin da shi basarake bashi dashi,saidai shi matsayinsa a duniya ne kadai ke kuwa harda lahira"murmushi tayi batare da tace komiba tana jinjina kanta cike da gamsuwa da maganar tasa,Batare da wani Bata lokaci ba ta Ciro gorar ruwan maganinsa ta bashi ya shanye Tass hade da Yar gyatsarsa ,kallonta yayi Ido cikin Ido "yau karatun da kikemun na boko Zaki cigaba da yimun ya kamata a karamin sabon darasi " "Angama ranka ya Dade" "To ki ciremun wanan karatun na kunnena Kinga zai rinka daukarmun hankali idan muna karatun ko?idan mungama sai ki maidamun kunnuwana". "Toh"tace tare da mikewa tana kokarin cire Masa karatun ta ajiye mp din akan gado ,ta janyo kujerar da take zaune daf dashi suna soma karatun, Sun dauki lokaci sunayi tana koya Masa Yana dauka,ta sunkuyar da kanta tana karanto mishi yayi shiru Yana saurare,har ta Gama batace komiba "ya zainul a Kara ko a tsaya a Nan?" Nan ma shiru taji ta sake maimata tambayar shiru be amsaba,da sauri ta dago kanta Dan a tunaninta bacci ya daukehi,sai kawai taga Kansa ya karkace gefe Yana wani irin Abu dik gumi ya jikasa sharkaf tamkar ana kwara Masa ruwa "innalillahi wa Inna ilaihi rajiu ya zainul lafiya?menene?" Nan ma shiru babu amsa ba karamin tsorata tayi ba ta firgice sosai ta Shiga jijjigasa sai kawai taga Yana kokarin fadowa daga wheel chair din,...daga murya tayi Tana Kiran fasawansa,shiru Saida Tai Kira sau biyu sanan mutum uku suka shigo dakin ,ganin yanayinsa yasasu saurin rukosa sukai kan gadonsa dashi,sai sassarfa jikinsa keyi tamkar mejin sanyi ga hannuwansa dake lankwashewa kamar ana juyasu, Hawaye kawai ke gudu a idanuwanta tana tsaye akansa ta kasayin komi,ga zuciyarta dake tsananin harbawa sauri da sauri tamkar zata fasa kirjinta ta fito,Nan ta Shiga tofa Masa adduoi Amma inaaa abun Kara gaba yakeyi sai kuka takeyi ganin yadda jikinsa yakeyi a wahale,idanuwanta ta Kai kan mp3 dinsa Tai saurin dauka ta kunna ta makala Masa a kunne da kyar,ta rukosa da kyau tana faman zubda hawaye....sun dauki minti arbain a haka sanan jikinsa ya fara daidaita yabar wanan abun da tamkar ana lankwasashi,...numfashinsa ke sauka a hankali ga wata zufa dake zuba a fuskarsa, "Alhamdulillahi"shine abinda ta furta ganin ya samu bacci sanan ta xauna gefen gadon ta tsura Masa Ido... ******** Karfe shida da wani abu ana Shirin Kiran sallahr magriba ta fito dik jikinta babu kwari tana so taje gida Amma zuciyarta cike da tunanin yadda zata barshi takeyi,hakanan ta fito fuskarta babu walwala da nufin tafiya gida,...sashen gimbiya rumana ta nufa Dan ta gaisheta dik yau bataga ta leko wajen zainul ba batasaniba ko lafiya tunda A Rana takan shigo wajensa sau uku ko sau hudu Dan taga jikin nasa, A parlor ta taddata baiwarta na gefenta tana matsa Mata kafa tanayi Mata kirari,idanuwanta a lumshe,sallamar ummaty yasa ta bude idanuwanta a hankali ta saukesu akanta,take ta sakar Mata lallausan murmushi, "Ummaty kece?" "Nice ummah"ta xauna gefen ta nesa kadan "barka da yammaci ranki ya Dade" "Barkanki dai ummaty ya dawainiya?Kai Allah dai ya biyaki da alheri kinji?" "Ameen Ummah"Tai jimm kadan a zaune,tana yunkurin mikewa ta tsinkayi muryarta "yau kinyi yamma sosai ummaty,Hala Dan rikicin ya hanaki tafiya ne' Fuska babu walwala ummaty tace "ehh ummah,Kuma madai yau ciwonsa ya motsa sosai,mundade tare kafin nasamu bacci ya daukesa abun babu Dadi ummah...Kansa kawai Naga ya karye gefe daya" "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiu,yanzun ya jikin nasa?" "Toh da sauki ummah,nasa mishi mp3 a kunne na kunna Masa karatun alkurani shine nasamu bacci ya daukesa" "Mekikace ummaty?ubanwa ya Baki izinin sa Masa wani Abu a cikin kunnensa?tunda kike kintaba ganin ansa Masa Abu a kunnensa na karatu ko wani Abu?waya Baki izini?wani irin karambani ne wanan?wata masifar kike Shirin janyo Mana kenan tunda kike sa Masa Abu a kunne"a firgice ummaty ta girgiza kanta cikin tsananin tsoro tana Shirin yin kuka, "Inba masifa ba meye hakan?so kike yasamu matsala a kunne kenan Kinga sai ya Zama kurma maganar ma ya daina nakastar ta tabbata kenan mu ki kaimu ki baro" "Ah ah ranki ya Dade Dan Allah kiyi hakuri bansanibane,da gani nayi tamkar ciwon nasa bana asibiti kadai bane shine nace in rinka sa Masa ko zaa dace" "Kinfi Mai martaba sanin abinda ya dace ne?ko mu kikafi sani muda muke iyayensa?karki kuskura kice Zaki Kara wanan gangancin idan ba hakan ba zan hadaki da Mai martaba"a firgice ummaty ke girgiza Kai tana hawaye tunda take da gimbiya Bata taba canja Mata irin na yau ba Tai Mata masifa,....ita kuwa gimbiya rumana Nan da Nan Tai sanyi da murya ganin yadda yarinyar ta firgice tana hawaye, "Kiyi shiru ummaty kinji?banji dadin yadda kikayi bane kinsan yanayin jikin nasa sai ki janyo Masa wani abun Kuma shiyasa nai fada Kuma Mai martaba bazaiji dadiba idan yaji labari kinji?da kinsani kitambaya tukunna kafin kiyi haka?daga yau kome zakiyi Masa kizo kitambayeni nice uwarsa kinji?"ummaty ta gyada Mata Kai tana share hawaye, "Tashi kije gida zan tuntubi Mai martaba akan hakan,ai babbar shawara kika kawo ummaty,kawai dai mahaifinsa bayaso ayi Masa komi na gargajiya shiyasa sai na asibiti Nima nafara ko kwanto akan ciwon nasa kibari inyi magana dashi tukunna" "Toh ummah" "Tashi kije kinji ana Kiran magriba ki gaida innar Taki kinji?" "Toh" ********* Kaiwa da komowa kawai takeyi cikin dakinta wajen karfe daya na dare abubuwa sun taru sun cunkushe Mata zuciya,mafita kawai take nema ga wanan al'amarin daya bullo...shin tayaya zata bullowa lamarin yarinyar?...Zama Tai gefen gadonta ta kafe gefe daya da Ido ta fada duniyar tunani....kusan minti ashirin ta sauke ajiyar zuciya hade da murmushi ..."tabbas hakan shine mafita cikin sauki ma"....ta furta a fili tana Dan murmushin nasara. **KADA KU MANTA LITTAFIN NAN NA KUDI NE GA MAI BUKATA GA DETAILS* *NAN A SAMA KUMA DAGA PAGE NA GABA NAGAMA BADA FREE* *PAGES ....INA MARABA DA MASOYA A DIK INDA KUKE* *SLIMZY😍* [1/23, 10:39 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS ASSO...💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY✍🏼* *Wattpad@slimzy33* *Assalamu Alaikum.... Fan's a duk inda kuke ina muku fatan alheri. Wannan book na zainul Abiddeen na kud'ine, wanda yake sha'awar siya ze iya tura kud'insa ta wannan number akan naira dari biyu kacal.* *2073065733 Sha'awa Ibrahim UBA bank* Tura shaidar biyan kudinka ga wanan number 08161306299 6019111117 keystone Amina jibril Shaidar biyanka ga wanan number 08166177830 Kokuma ya tura katin waya na mtn na 200 ta wannan number 08039424298 kokuma 07084161619 Kud'in littafin d'ari biyuce kacal game buqatar ci gaban zainul Abiddeen seya tuntub'emu. *10* ******** "Ya zainul Wai menayi maka ne yau tunda Nazo kake shareni bakason kulanu?ta tunzuro Baki gaba idanuwanta cike da Yar kwalla tana kallonsa,...Shima idanuwansa akanta suke ko kiftawa bayayi yafi minti biyar a haka sanan ya kauda Kansa gefe batare da yace komiba, Hawayen dake makale cikin idanuwanta ne suka sulalo a fuskarta zuciyarta na harbawa sauri da sauri tsoro falll zuciyarta,batasan laifin da tayi Masa ba tunda tazo yau yaki sakar Mata fuska suyi hira yadda suka saba,Kuma a iya saninta lafiya kalau suka rabu jiya hasalima bacci yakeyi batasan tafiyarsa ba,shin kodai Mai martaba yayi fada akan abinda tasa mishi a kunne ne na karatun kur'ani?har Shima bayaso yasa yake Sha Mata kamshi yau,dikda cewar tasan halinsa Sarai be cika son magana ba miskili ne ajin farko sanan dikda ciwon da yakeyi baya hanasa sarautarsa ta motsa ya rinka magana sama sama kamar bayasonyi,...idan har laifin da tayi jiya ne to tabbas zata daina kunna Masa Kuma insha allahu zata dauke mp3 din ma ta wuce gida da ita. Murya na rawa ta Kara dubansa "ya zainul kafadamun menayi maka yau kaki kulani wallahi hankalina ya matukar tashi ya zainul kaji?na Bata maka Raine?idan na Mata maka Rai kayi hakuri bazan sake ba"Tai maganar tana shasshekar kuka,kamar daga sama ta tsinkayi muryarsa a dishe "Ummaty babu abinda na tsana a rayuwata sama da injuya gefen dama da haguna bangankiba,banji motsinki ba sanan Banga ko inuwarki a kusa Dani ba,tun bayan tashina jiya da yamma bangankiba zuciyata bataimun Dadi ba,naso ace Naga tafiyarki munyi sallama dake shine zaisamun salama da kwanciyar hankali"share hawayenta tayi ta sauke sassanyar ajiyar zuciya, "Kayi hakuri ya zainul kasan yanayin tafiyar tawa,da yamma tayi nake haramar tafiya gida kafin magriba ta riskeni Akan hanya,da Naga kana bacci shine kawai banyi yunkurin tashinka ba na kimtsa natafi kawai kayi hakuri daga yanzun ko dare zankai inhar kana bacci bazan tafi inbarkaba batare da munyi sallama ba" "Yanzun wanan hawayen na menene kikeyi?umm? Turo Baki tayi "ba Kai bane tunda Nazo kaki kulani sai dauremun fuska kakeyi?Kuma fa da har naji tsoro nafara tunanin kila kadaina kula ni ne" "Komi girman laifin da zakiyi ummaty baxaki tabayin laifin da ni zainul abideen zan kasa bude Baki inyi Miki magana ba,bazan jure ba bazan iyaba,bana tunanin akwai wanan ranar a rayuwata Koda kuwa kinyimun babban zunubin da ya dace ingujeki infita hanyarki,Amma bazan iyaba....shin tayaya ma zaayi nakasasshe kamar ni ingujeki ummaty?dik fadin duniyar Nan bayan iyayena yanzun Kam banida tamkarki ummaty...babban tashin hankali bai wuce idan na tuna watarana Zaki aure kibarni ba a cikin wanan halin ,nakan tsinci kaina cikin tsananin takaici da bakin ciki,duniyata takanyi mun duhu komi bana iya gani bana iyaji,dikda nasan wanan ranan tana zuwa,Amma burina be wuce inhar ban warkeba zuwa lokacin to Allah yasa in mutu in huta..." "Shhhhh ya zainul banason Jin wanan kalmar daga bakinka karkasake fadamun irinta idan ba hakan ba Zanyi fushi Kuma Zanyi kuka"Tai maganar tana shagwabe fuska, Murmushi yayi "banason hawayenki ya diga ko kadan ta dakililina Dan ban cancanci hawayen kyakkyawar budurwar yarinya kamarki ya zuba akan nakasasshe kamata ba,Niba kowa bane yanzun a wanan duniyar,dani da babu dik daya ne tunda babu wani Abu na amfani da nake amfanawa alummah sai ma wahala da nake Basu"sosai tausayinsa ya kamata ta matso daff dashi tasa bakinta daidai fuskarsa ta hura Masa iska ya lumshe idanuwansa ya budesu lokaci daya Yana kallonta, "Ko bakada amfani a wajen jamaa,to kasani ni kanada amfani a wajena ya zainul Dan inada yakinin tabbas zaka warke zaka Kuma taka doron kasa insha allahu"...murmushi yayi Wanda iya fuskarsa ya tsaya,wani irin zafi zuciyarsa takeyi Masa dik lokacin da ya kalli Kansa ya ga bashida wani Abu da yakeyi Wanda ya wuce zaman daki,kwanciyar kan gado sai cin abinci,Kashi da fitsari dik taimaka Masa akeyi wajen yinsu,me yakai wanan bakin ciki a wanan rayuwarsa?abubuwa biyu da ko wani Dan Adam idan zai yisu sai ya kadaice shi sai an taimaka Masa,tunda ya taso ya girma ya tsinci Kansa kwance a gadon jinya har zuwa wanan lokacin shekara da shekaru saanninsa dik suna karatu wasu ma sun Gama Amma shi gashi kwance a gadon jinya....hmmmm baa mamaki da ikon Allah Dan shi ikon Allah sai kallo,babu abinda zaice a rayuwarsa saidai kawai alhamdulillahi...ya lumshe idanuwansa ya Dade kafin ya budesu sunyi jajir ya saukesu akanta yaga itama shi take kallo fuskarta tamkar me Shirin yin kuka, "Ya zainul lafiya?kayi shiru sai tunani kakeyi fa,dubi yadda idanuwanka suka canja kala lokaci kankani haba ya zainul" "Ummaty tunanin rayuwata kawai nakeyi yadda nakeyinta,sanan babban damuwata yanzun be wuce yadda kika kashe karatunki tun bayan Gama secondary dinki last year Baki koma makaranta ba kina Nan zaune tare Dani babu dare babu Rana Anya ban Shiga hakkinki ba kuwa" Girgiza Masa Kai tayi "baka Shiga ba ya zainul kadaina wanan tunanin ka kwantar da hankalinka kawai har Allah ubangiji ya amshi adduarmu ya baka lafiya kaji". "Ameeen ummaty Allah ubangiji ya Nuna min wanan ranar ya bani ikon saka Miki da abinda kikaimun in kula dake tamkar fiyya da afnan da Aysha kannena na cikina kinji?"farrrrr Tai da idanuwanta ba karamin kyau Tai Masa ba,baisan lokacin da ya tsinci Kansa cikin sakin murmushi ba, Zahira ce tai kasa da murya yadda babu Wanda zai jiyota,"Anya kuwa ummaty da ya zainul ba soyayya suke ba warisah" "Natayasu murna idan ma soyayyar sukeyi Dan sun dace sosai tunda akwance yake ita Kuma kwadayi na bibiyat shegiya" "Ni Kam ya zainul na balain yimun kyau warisah"....wani kallo warisah Tai Mata sanan ta saki wani malalacin murmushi, "To ko kina cikine?idan kinaciki kawai akai magana wajen Mai martaba a hadaku aure Kinga jinyar ta dawo hannunki kenan,idan Kuma dukamku kukesonsa Mai martaba zai aura muku shi Dan nasan tabbas Neman nayi akeyi dashi" "Amma kinsan wani Abu kuwa?wallahi ya zainul da lafiyarsa kalau har dambe Mata zasuyi akansa,saboda koba komi shidin kyakkyawa ne uwa uba ga mulki ga dukiya ga Kuma sarauta da yakedaita Kinga ba karamin farin jini zaiyiba" "A wajenki kike ganin hakan,ko Kuma kina cikin wadanda zasuyi damben akansa koh?"tabe Baki tayi Tana ci gaba da tazar gashin kanta dake kwance agadon bayanta, "Rabani da zancensa ki kakomin wani zancen Dan baya gabana ko kadan zahira,Dan ni Ina mantawa Allah yayi ruwan tsiransa a cikin gidan Nan wallahi,ni Banda ammiey ta hanani tafiya da tun jiyan nasan inda dare yamun,Dan haka ki rabu Dani da zancensa" Murmushi kawai zahira tayi ta ta lumshe idanuwanta ta budesu tana ayyana abubuwa da dama cikin zuciyarta... ******* Mai martaba ne tallabe da zainul a jikinsa Yana karewa Dan nasa kallo cike da so da kauna,dik wata gaba ta jikinsa ta sadarwa wadda take bugawa hade da numfashinsa to tana bugawa ne tare da soyayyar da'nsa kwaya d'aya dilo jinin jikinsa Wanda ya dauki so da kauna na dik duniya ya Dora Masa,ya dauki buri masu yawan gaske Akan wanan da'n nasa daya tilo sai kaddarori da jarabawa tazo mishi a hakan,Amma hakan besa yaji son dam nasa ya ragu cikin zuciyarsaba,sai ma karuwa da yakeyi fiye da baya ga tausayi irin na iyaye na da da mahaifi da yakeyiwa Dan nasa,kallon da yakeyi Masa ko kiftawa bayayi yayi yawa,...gefe da gefenshi Zahra ce babbar yarda sai me bi Mata halima sai gefensu gimbiya rumana ce cikin Shiga ta alfarma Tasha alkyabba irin na matan sarakai na wanan lokacin, Halima ce ta dubi mahaifin nasu tace"Abbu wanan kallon yayi yawa da kakeyiwa zainul sai kasa dik yaron yaji wani iri ya fara daukar Kansa wani abun na daban ranka ya Dade"Tai maganar cike da tausayawa,...Zahra ma karbe zancen tayi "idan anayi Masa hakan ana karayar Masa da zuciya ne Abbu sai yaga tamkar shidin bazai warke ba kamar kowa" Murmushi irin na manya Mai martaba yayi ya dubi gimbiya rumana dake tsaye tana famar sheki tana zuba kamshi "kinji abinda yaranki suke cewa Akan kaminsu ko?basaso Ina karya mishi gwiwa Wai" "To ai Kaine ranka ya Dade gaskiya baayin haka,yaro ai karfafa Masa gwiwa akeyi yadda ka kafesa da Ido ai saikasa yarona yayi kuka ka rungumesa tamkar jariri umm?bayan yarona ya girma?inasaka ran idan ya warke yayi aure insamu jikoki?kaga ranka ya Dade Bari ma in koma kusa da abuna ga abincinsa Nan inbashi yaci ya koshi ya kwanta ko zainul?"ta karasa maganar tana kallon kwayar idon zainul din ,sai kawai yayi dariya dukkansu Suma dariyar sukai ,halima ce ta duka da kanta ta Shiga zuba abinci a plate ta mikawa ummahnsu ta zuba ruwa a glass cup Shima ta Mika mata.gimbiya rumana da kanta take bashi abincin har ya koshi ,dik abinda sukeyi da dramar da yakeyi idan yanacin abinci dik mahaifinsa na tsaye akansu Yana kallo Yana famar zuba murmushi soyayyar iyalinsa na Kara Shiga zuciyarsa... A tare suka fito dakin,a kofar daki ummaty ke tsugunne yayinda gimbiya rumana ta kalleta fuskarta dauke da murmushi,ummaty ta gaidata ta amsa cike da kulawa har sunyi gaba ta sa baiwarta ta dawo ta sanarwa da ummaty akan idan zata wuce gida ta biyo sashinta zata bada sako takaiwa innarta. ******* Yammaci nayi ummaty ta Shiga haramar tafiya gida musamman da ya kasance yau garin akwai hadari hadari kada ruwa ya rutsata,dik inda hankalinsa yake a tashe yake babu abinda ya tsana sama da yamma nayi ummaty ta fara hada kayanta na tafiya gida,gashi yau garin akwai hadari ba yamma bace tayi Amma gida take haramar tafiya Dan kada ruwa ya tareta, "Ya zainul kaga akwai hadari kaji?kayi hakuri zuwa gobe insha allahu da wuri zan shigo zan xauna har dare babana zaizo ya tafi Dani kaji?"Jin hakan yasashi Dan sakin fuska sukai sallama ta fice. ******** Durkushe take a gaban gimbiya rumana zuciyarta sai lugude takeyi Mata tamkar zata tsaga kirjinta ta fito,ta rasa dalilin dayasa ta tsinci kanta cikin wanan yanayin na tsananin tsoron matar,kodan jiya ta zare Mata Ido ne yasa hakan oho Allah yasadai ba laifi ta sakeyi ba Dan harga Allah yanzun ummaty ta tsorata, "Akan maganar jiya da mukai dakene Akan ciwon yarona zainul abideen"gaban ummaty ya yanke ya Fadi, "Kamar yadda na fada Miki zan tuntubi mahaifinsa Akan ciwon nasa da mukai magana kikace bana asibiti bane na gargajiya ne shine nai Masa magana" Ummaty ji tayi tamkar ta saki fitsari saboda tsananin tsoro, "Be amince da hakan ba ummaty Amma ni tausayin yaron nakeyi har cikin Raina ummaty"idanuwan gimbiya suka kawo ruwa tamkar zataiyi hawaye,...ummaty ta natsu tana saurarenta, "Dan haka na yanke shawarar nemawa zainul abideen magani Kota halin Yaya ne inhar zai warke banida farin cikin daya wuce hakan,na kwana da tunanin abun a zuciyata,sanan na auna hankalinki da natsuwarki nasan bazaki tabayiwa zainul wani Abu na cutarwa ba,...shiyasa na yanke shawarar nema Masa lafiya cikin sirri tare dake tunda mahaifinsa be yarda da wani maganiba sai na asibiti,Kuma Kinga rukon yaron Nan a hannunna yake tun Yana yaro ummaty,nasan uwarsa tanasonyi Masa magani Amma tanayimun Kara irin na hausa fulani shiyasa tasa Ido" Ummaty takara natsuwa sosai tausayin gimbiya ya Shiga jikinta,"Dan haka nakeso ki taimakeni musamawa yaron Nan lafiya kinji?Dan kinfini kusa dashi ummaty ,zan karbo magani wajen kakana in Baki ki rinka bashi nasan zaisha idan kece ummaty,idan kikai min haka kingamamun komi a rayuwata matukar yarona zai samu lafiya"ta share hawayen dake zuba a idanuwanta, Sosai tausayin gimbiya ya kamata sanan wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyar ummaty na zainul zai samu lafiya ya warke kamar kowa mafarkinta zai Zama gaskiya kenan? *SLIMZY😍* [1/23, 10:40 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS* *ASSO...*💡 💞 *ZAINUL ABIDEEN💞* *SLIMZY✍🏼* *Wattpad@slimzy33* *Assalamualaikum zuwa ga masoyana Ina muku fatan alheri,wanan book din na zainul abideen na* *kudi ne Wanda ke bukata dari biyu ne kacal ka nemi* *wanan numbers* 08166177830 *ko* 07084161619 *daga* *wanan page din nagama bada free page zakuji shiru inawa kowa fatan alheri.....SLIMZY* ✍🏼 11 Murmushi kawai takeyi tana ayyanawa a zuciyarta zainul ya samu lafiya,wani irin farin ciki zata tsinci kanta a wanan ranan?lumshe idanuwanta Tai ta budesu sukai Ido hudu da gimbiya rumana wadda ta kafeta da idanuwa ko kiftawa batayi,samm ta manta a inda take ma saboda tsananin farin ciki ,sadda kanta Tai kasa bakinta yaki rufuwa "ranki ya Dade tabbas ke uwace ta gari nadade Ina Neman ganin ranan da zaayiwa zainul abideen magani ya warke Amma babu halin hakan saboda kasancewar ni ba kowa bace a cikin gidan Nan shiyasa ban taba tunkarar wani da maganar ba, alhamdulillahi tunda ke mamansa kinyi wanan tunanin Allah ubangiji yabamu nasara a wanan tafiyar gaskiya nayi matukar farin ciki da Jin wanan labari"ta karashe maganar cike da ladabi, Murmushin nasara gimbiya rumana tayi hade da sauki sassanyar ajiyar zuciya wani farin ciki Yana ratsa zuciyarta tun daga kanta zuwa yantsun kafarta "Masha allahu shikenan ummaty Zanyi magana da Wanda zai rinka bashi maganin idan yaso sai ki rinka zuwa kina amsa a nan wajena kina bashi cikin sirri batare da kowa ya sani ba inada burin da fatan saidai Mai martaba yaga zainul ya tako da kafafuwansa har fadarsa" "Allah ubangiji ya sa ranki ya Dadi,Allah ya Baki Lada"Tai maganar cike da farin ciki,....ledar dake gefe gimbiya rumana ta janyo ta Ciro turamen atamfofi guda biyu ta mikawa ummaty "amshi wanan ummaty ki kaiwa mamanki daya ki dinka daya kema kisa kinji?" "Allah ya saka da alheri gimbiya ,Allah ya Kara girma da arziki ya Kara Miki lafiya da nisan kwana sanan Allah yasa kifi haka ya cika Miki burinki na alheri"...sosai gimbiya ke faraa ta kasa boye farin cikinta,...a zahirin gaskiya Bata taba tsintar kanta cikin farin ciki irin na yau ba,ita kadai tasan me take tunani kasan zuciyarta. "Tashi kije kada ruwa ya tsareki kinji ki gaida innar Taki"to ummaty tace ta Mike rungume da kayan da gimbiya ta Bata ta fice gimbiya ta bita da wani irin kallo tana kada kafa fuskarta dauke da murmushin mugunta,cije lebenta tayi "hmmmm lallai nasamu cikar burina,yanzun ne nakeda damar da zan dama,yanzun ne nasamu yadda nakeso nake muradi farin cikina be wuce in bude idanuwana Inga yaron Nan rayuwarsa ta lalace ta kazanta fiye da wadda yake ciki,banida burin daya wuce a nunamin gawarsa a kwance ya mutu,shine babban buri na a rayuwa....Zanyi amfani da damata tun kafin ta kubucemin nasani inhar nayi amfani da wanan yarinyar to tabbas babu ranar da asirina zai tonu a hakan zamuyita tafiya babu Wanda zai fahimci wani Abu tattare Dani,gwauron numfashi ta sauke hade da janyo wayarta Tai dialing wata number,ta Dade tana waya sanan ta tsunke wayar cike da tsananin farin ciki.... ********* Bayan sallar isha'i ummaty ce zaune hannunta rike da littafin adduoi na hisnul Muslim tana Dan dubawa,minti minti takan sauke ajiyar zuciya hade da lallausan murmushi,...innarta dake zaune gefe tana cin tuwo miyar taushe tana cin abincin ne Amma hankalinta gabaki daya Yana wajen Yar tata,ko meyasa yau tunda ta dawo take farin ciki oho?hakan bazai rasa nasaba da kyautar da gimbiya tayi Mata ba,ta Kai lomar tuwo bakinta a Karo na farko ta Kara dago fuskarta har yanzun wanan murmushin na Nan manne a kyakkyawar fuskarta wanan yasa innah yin gyaran murya,da sauri ummaty ta dago fuska ta kalli innar sai Kuma ta maida kanta kan littafin da take dubawa lokaci lokaci, "Ummaty Wai nikam lafiya yau naganki cikin tsananin farin ciki haka?kekadai zaune tun dazun Ina lura da yadda kike murmushi tamkar wadda akaiwa goron albishi"...cikin tsananin farin ciki ummaty tace "innah kedai Bari wallahi gimbiya rumana Yar aljannah ce insha allahu,Wai kinsan me?"...sai Tai saurin dakatawa da maganar,tunawa da kalmar gimbiya da tayi,"ummaty banaso kowa yasan da maganar Nan dagani sai ke so nakeyi kawai Mai martaba yaga zainul ya taka da kafafunsa har fadarsa .....sai kawai ummaty Tai shiru, "Kinyi shiru ummaty me gimbiyar tayi hakan" "Yadda take kyautatawa jamaat gidan da al'ummar wanan gari gabaki daya,bakiga yadda take raba kyaututtuka ba dik Dan Allah ya bawa ya zainul lafiya,Kai Allah ya saka Mata da alheri,gaskiya tana matukar kaunar yaron Nan nata zainul abideen" "Ameen ameen ummaty dik shine yasa kike tsananin farin ciki haka?gabaki daya murnarki yau Taki boyuwa ummaty,Baki da burin daya wuce ace zainul yasamu lafiya"hannuwanta tasa ta rude fuskarta rufff tana dariya cike da kunya,itama innar dariyar tayi ta cigaba da cin abincinta. ******* Yau tunda safe yake kiraye kiraye daga cikin dakinsa kasantuwar fasawansa sun danyi nisa sai Kira yakeyi babu Wanda ya amsashi,..breakfast dinsu sukeyi hankali kwance kamar basajin Kiran da yakeyi daga cikin sashinsa, "Mtswww gaskiya wanan ya takura Mana,dubi yadda yake Kira sai kace wani makaho tun dazun kake Kira babu Wanda ya amsa ai kasan babu me zuwa wajen naka"ta Kai kofin tea bakinta,...Kara Kira yayi a Karo na uku, zahira ta ajiye kofin tea dinta "idan bamuje wajensa ba bazamu samu sukuniba da wanan Kiran nasa,Dan hakan Bari inje Inga menene yake kiran"...tabe Baki Tai kawai batare da tace komiba. Kofar dakin ta tura hade da yin sallama a gaggauce,Yana zaune saman wheel chair dinsa Yana gab da fadowa zahira ta Shiga "lafiya kaketa faman kwalawa mutane Kira haka Kuma kasan masu hidimar taka babu kowa?"...a hankali ya sauke idanuwansa akanta tana rike da kwankwaso tamkar me shirinfada "gyaramun zamana nakeso ayi,ko kafar Nan tawa data lankwashe idan ba hakan ba zan Fadi"...tsaki tayi cike da takaici taje tana kokarin gyara Masa kamar yadda yace,...Jin zahira shiru yasa warisah biyo bayanta taga meke faruwa,...daidai Nan ta shigo dakin tana raba idanuwa,turus tayi a tsaye ganin yadda zahira ke kici kicin gyara Masa zama dik tayi zufa,dakyar tasamu ta gyara shi ya zauna dakyau, "Ke Kam da ba aikinki ba meya kaiki yin wanan aiki?ai be kamace ki ba zahira Aida saiki Kira wadanda keda alhakin kulawa dashi ko Kuma ya Kira wahalalliyar tasa ta karaso ta Dora daga inda ta tsaya" ******* Gurfane take a gaban gimbiya rumana tana kwararo Mata bayanin yadda zatai amfani da maganin na zainul abideen dik yadda zata bashi ta sanar Mata komi,sanan ta Dora da, "Maganar kunna karatun alkurani kidaina saboda nayi magana da malamin me bada wanan magani akan cewar zainul Yana dauke da bakaken aljanu a tare dashi,wanan maganin daya bada shine zakiyi mishi amfani dashi musamu waraka da haske,idan kina kunna Masa karatun alkurani fushi sukeyi Suyita bashi wahala kala kala shiyasa kikaga Koda yaushe cikin tashi ciwonsa yakeyi,sanan Abu na biyu ya sanarmun da cewar Koda munsamu ciwonsa na tashi idan muka bada maganin muyi hakuri na Dan lokacine zamuga ya daina Kuma aljanum zasuyi nisa dashi insha allahu,Ina fatan kin fahimta"...ajiyar zuciya ta sauke ta gyada Kai cike da natsuwa.."tashi kije Allah yayi albarka ki tabbatarda kinyi yadda akace" "Insha allahu...ta Mike jiki babu kwari ****** Zahira Tai murmushi,"Taimakonsa kawai nayi a matsayinsa na Dan uwana,Kuma iya abinda Naga zan iya din kenan Dan wallahi inda taimakon ya wuce hakan bazanyi ba"...turo kofar ummaty tayi bakinta dauke da sallama Yana zaune Yana bin kowaccensu da Ido cike da takaici na abinda kannen nasa sukeyi Masa,...kallo ta Shiga binsu dashi daya bayan daya. "Malama kallon me kikeyi man haka irin na rainin wayau?ko kina tunanin zamu cutar dashi ne?to Taimakonsa mukai dan da yanzun kimzo ki taddashi a kasa warwas "cewar zahira tana watsawa ummaty harara "Ke kika tsaya kula lamarinta har kikasan tana kallonki,tunda kinyi taimakon da kikai niyya Kuma Dan Allah kikayi to Allah ya Baki Lada,nikam tunda babu niyya dama ko tabasa bazanyi ba Dan tsoro nakeji ko da wata najasar a jikin nasa ya shafamun mtsww"Tai gaba abinta zahira ta take Mata baya... Tsananin bakin cikin da takaici yasa zainul abideen zubarda hawaye besan yanayi ba,gudu kawai hawaye keyi a fuskarsa zuciyarsa Tai Masa bakin Kirin saboda bacin Rai,....kallon yadda yake hawaye ummaty tayi kadai tasan bacin Rai ne yaja Masa hakan,tausayinsa ya lullubeta ta rasa yadda zatayi sai kawai ta janyo kujerar ta ta zauna daf dashi tana kallonsa cike da tausayawa "ya zainul menene Naga hawaye suna sauka a kwayar idon jarumin namiji kamarka?meyasaka kuka"a shagwabe Tai maganar itama tamkar zata fashe da kuka. "Nima bansan daliliba ummaty...Abu daya nasani shine ban taba bakin cikin kasancewata cikin wanan halin ba kamar na yau,Shima bawai nayiwa Allah butulci bane,saidan abinda kannena jinina sukaimun da kansu ummaty" Hannu tasa ta Shiga share Masa hawaye Tana girgiza Kai,sosai ya Bata tausayi "kayi shiru insha allahu ciwonka yazo karshe ya zainul zakasamu lafiya kamar kowa kaima har ka taimakawa wani Dan Adam din kaji?"...cikin tsananin bakin ciki yake kada Kansa kawai wani irin tsanar yaran ce ta darsu cikin kahon zuciyarsa... ******** Tayi zurfi cikin tsananin tunani tana jingine da jikin kilisa irinta sarakai ,ummaty kema bazan taba barinki rayuwarki ta tafi a hakan ba saina bibiyi rayuwarki na tabbatar da cikar burina sanan zansamu kwanciyar hankali dik wani taku ko numfashin da Zaki sauke tamkar akan idanuwana zakiyi shi Dan bazan taba Bari wanan Karon asamu matsala ba....ta lumshe idanuwanta ta budesu sunyi jajir tasa hannu ta dauki apple ta gutsira tana taunawa a hankali...tabbas tayi amfani da wayau da hikima da shekaru akan yarinyar tayi amfani da kalaman da babu yadda zaayi yarinyar ta tsallake umarninta...yanzun komi na ragamar zainul Yana hannunta sai yadda tayi...wani murmushi ta saki Wanda iyakarsa fuskarta tana ayyana abubuwa da dama a zuciyarta... *KADA KU MANTA WANAN LITTAFIN NA KUDI NE KUMA YAU SHINE LAST DA* *ZANYI POSTIN FREE PAGE, GA MAI BUKATA* *GA NUMBERS NAN ASAMA YA NEMI KARIN BAYANI NAIRA* *DARI BIYU CE KACAL INA MAI TABBATAR MUKU* *BAZAKUYI* *DANASANIN SIYA* *BA,* 2073065733 *Shaawa ibrahim* *UBA bank* *Tura shaidar biyanka ta* *wanan number* 08161306299 601911117 *keystone* **bank Amina jibril* * *Shaidar biyanka ga wanan* *number** 08166177830 *Ga masu tura Katin waya MTN ake bukata zuwaga wanan number 08039424298 shaidar tura Kati ga wanan* *number 07084161619....* *SLIMZY😍* [1/23, 10:40 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS* *ASSO...*💡 💞 *ZAINUL ABIDEEN💞* *SLIMZY✍🏼* *Wattpad@slimzy33* *Assalamualaikum zuwa ga masoyana Ina muku fatan alheri,wanan book din na zainul abideen na* *kudi ne Wanda ke bukata dari biyu ne kacal ka nemi* *wanan numbers* 08166177830 *ko* 07084161619 *....SLIMZY* ✍🏼 *12* "Ya zainul inaso kabani hadin Kai sosai wajen Shan maganin Nan domin inada yakinin zakasamu lafiya cikin kankanin lokaci"ta kafesa da Ido Babu alamar Wasa a fuskarta yadda Tai maganar kadai zaka fahimci maganin nada tsananin muhimmanci,...kallo kawai yake bin ta dashi yadda Tai maganar Yana Kuma bin gorar maganin da kallo zuciyarsa na ayyana Masa Anya zaisamu lafiya kuwa?wanan magani ummaty ta dauki lokaci tana bashi irinsa tunda yasan maganin gorar kanta da ake basa maganin da ita itace dai baa canjawa shin yaushene zaisamu wanan lafiyar da ake Kira Masa zai samu zai samu?...Sarai ta fahimci tunani yakeyi sai ta hura Masa Isa a idanuwansa "lafiya dai Naga kana kallon gorar maganin kodai bakaso ka Sha ne ka gaji?" Girgiza Mata Kai kawai yayi Yana sauke ajiyar zuciya "gani nayi ummaty mundauki tsawon lokaci kina wahala akaina batare Dana warke ba,sanan Baki taba gajiyawa ba kullum cikin yimun hidima kikeyi,shine nake tunanin Niko da wani irin Abu zan saka Miki dashi wanan dawainiya da kikeyi tawa Koda yaushe babu dare Babu Rana?" Wani kyataccen murmushi tayi Wanda ita kanta batasan tayishi ba,ba karamin kyau tayi Masa ba Wanda yasa Masa Jin wani Abu ya tsarga Masa daga kwakwalwarsa zuwa zuciyarsa take abinda ke aika sakwanni na jikinsa ya Shiga aikawa dik wata hanya da jinin jikinsa ke yawo ya gawraya gabaki daya...zuciyarsa ta Shiga bugawa sauri da sauri Wanda besan dalilinsa na hakan ba...ya shagala da kallonta ya manta a wace duniyar ya tsinci Kansa sai muryarta ya tsinkayo tana fadin "haba ya zainul,bantaba tunanin Nan gaba idan ka warke zanji inaso ka sakamun da wani Abu ba dangane da taimakon da nayi maka nayishi ne kawai Dan Allah "yadda take motsa bakinta ba karamin burgesa tayi ba siraran lips dinta bakake wadanda suka Dace da doguwar fuskarta Mai dauke da manyan idanuwa shanyayyu masu Kama da me jin bacci...shagwabe fuska ta karayi "yaayah Wai lafiya nake ganin wasu canje canje a tattare dakai meyafaru ne" Murmushin karfin Hali yayi yanajin wani Abu na taso Masa tun bayan daya shanye maganin data kawo Masa "me kika gani ummaty?"ya tsareta da idanuwansa..."nifa sai Inga Kanata kallo na kamar zaka hadiye ni"ta turo Baki. "Da inada damar hadiyeki Dana hadiyeki ummaty a yadda nakejin bakon lamari tattare Dani a Yan kwanakin Nan banida wani aikinyi Banda tunaninki ummaty da zarar kika tafi kika barni,wasu lokutan har gizo fuskarki takeyi sai Inga kamar kina kusa Dani"ya karasa maganar hade da cije lebensa Yana lumshe idanuwansa... Kallonsa sosai tayi "yaayah kodai wani Abu Yana damunka ne?"Tai maganar dauke da damuwa a fuskarta tamkar me Shirin yin kuka "Babukomi ummaty mekika gani?" Ta shagwabe fuska "nidai nidai Naga kamar bakada lafiya kuma kaki fadamin yaayah haba?"...dariyar karfin Hali ya karayi batare da yace komiba yanajin wani Abu nayi Masa yawo a sassan jikinsa tamkar Wanda shocking ke shigarsa musamman kafafuwansa da sukai Masa nauyi lokaci daya kamar an Dora Masa bulo sosai yakejin abun na karuwa cikin jikinsa Amma ya dake ya kasa cewa komi da zuciyarsa dake harbawa sauri da sauri tamkar zata fasa kirjinsa ta fito,take ya soma jujjuyawa yana ganin dakin nayi Masa yawo....tana Nan zaune jikinta na karkarwa tana lura da yanayin nasa da yafi na Koda yaushe,batai aune ba ya saki wata irin gigitacciyar Kara wadda Saida ta razana ta toshe kunnuwanta lokaci daya ta runtse idanuwanta tanajin karar har cikin kwakwalwar kanta ga wani irin faduwar gaba,lokaci daya network din kanta ya dauke gabaki daya,ta dauki kimanin seconds talatin a hakan sanan ta fara bude idanuwanta Wanda yayi daidai da shigowar jamaar cikin gidan a rude manya da Yara ciki ko harda Mai martaba Wanda a lokacin Yana cikin sashen gimbiya bilkisu,.. "Subhanalillahi zainul abideen meke faruwa Kuma?innalillahi wa Inna ilaihi rajiu wanan wace iriyar Kara ce wadda ta gigita kowa dake cikin gidan tamkar Mai shigar aljanu?ta karasa maganar tana fashewa da kuka a rude gimbiya bilkisu ke magana yau karar da takeyi takasa nuna damuwarta ta kasa boyewa Tai Kansa tana girgiza sa,idanuwansa sun shige bakin sai fararen sai wani irin Abu yakeyi hade da gurnani kasa kasa kimfaffaki na fitowa ta cikin bakinsa tamkar Mai aljanu...sosai Mai martaba ya rude ganin Dan lelensa a halin da bai taba ganinsa cikba shi Kansa baisan lokacin da yace "asamu malam ya'u ya tofa Masa addua yanzun yanzun" "Wani malam ya'u ranka ya Dade bayan baya cikin gidan Nan Yana kauye anyi Masa rasuwa?ai a gaggauta Kiran likitansa yazo kawai shi kadai yasan me yakeyi Masa idan hakan ta faru"sosai gimbiya rumana kw zubda hawaye Tana Kara tallabo zainul jikinta sosai wani irin rawa jikinta yakeyi tana Kara rungumesa tamkar zata maidasa cikinta saboda tsananin so...hawaye fiyya ta share ta dubi gimbiya rumana "ummah inaga Bari in ruga asibitin da kaina in dakko likitan Nan tunda Kinga tsayawa ma lalubar nimbersa Bata lokaci be Kinga kowa a rude yake" "Yi sauri fiyya karki tsaya jiran driver ki driving da Kanki Dan allah".... Bata rufe bakiba likita yayi sallama cikin dakin ganin halin da zainul ke ciki yasa shi saurin ajiye jakarsa a gefe ya bude ya Ciro allura da syringe da sauri ya zuko allurar batare da Bata lokaci ba yayiwa zainul abideen ita Nan da Nan ya Shiga jijjiga suna rirrikesa sosai bakajin sautin komi cikin dakin Nan sai koke koke yau har zahira Saida ta zubdawa zainul hawaye saboda tsananin tausayin halin da yake ciki,ikon Allah cikin minti arbain da tashin ciwon da shigowar likitan bacci Mai nauyin gaske ya daukesa jikinsa ya jike sharkaf da gumi.. Tana Nan rungume dashi kowa ya watse cikin dakin daga ita saishi sai ummaty wadda saboda tsabar kuka idanuwanta sunyi jajir dik sun tasa sai faman ajiyar zuciya takeyi tana tsugunne kanta a kasa zuciyarta cike da tsananin tsoro da fargaba....wani irin kallo gimbiya rumana ta bita dashi Mai dauke da maana kala kala sanan ta dauke kanta gefe daya Jim kadan ta kwantar da zainul abideen ta Mike tsaye ta gyara zaman lafayarta sanan ta kwashi wayoyinta ta dubi ummaty "ummaty idan zakije gida kibiyo sashina" Bata jira cewarta ba Tai gaba baiwarta ta take Mata baya ... ********** "Ranki ya Dade Zanyi iya bakin kokarina wajen sawa yarinyar idanuwa gaba da baya kamar yadda kikace ranki ya Dade" "Hansa'u banaso asamu matsala akan wanan aikin Dana saki bawani Aiki bane face kisawa shige da ficenta Ido sosai ki gano mun dik wani Abu da takeyi itada wanan yaron saboda Ina kallon akwai boyayyar soyayya a tsakaninsu Kuma ni zainul bazai auri Yar sarkiin dawaki ba da Raina" "Insha allahu ranki ya Dade Zanyi dik abinda kikasani harda Wanda Baki saniba ranki ya Dade Zanyi kokari wajen samo Miki labarai kala kala daga wanan sashen"....jinjina Kai gimbiya tayi cike da gamsuwa sanan tace "Zaki iya tafiya daga yanzun aikinki ya fara har illa Masha allahu" "Angama ranki ya Dade,Allah yaja zamaninki yaja da ranki da lafiya da arziki Mai amfani"...murmushi ta sauke tana jinjina kanta... ******** Gimbiya bilkisu na zaune a bakin gadon zainul ya bude idanuwansa a hankali Yana bin ko Ina da kallo tamkar Wanda ya tsinci Kansa a cikin wata sabuwar duniya...kalle kalle ya shigayi a cikin dakin na Dan wani lokaci sanan ya juyo da idanuwansa kan mahaifiyarsa da sukai jajir ...dakyar ya bude bakinsa ya motsa harshensa da yayi Masa nauyi sosai yace "Ammiey..jiki..na ciwo"Yana maganar harshensa na sarkewa tamkar me koyon magana dukkansu Basu fahimci me yake fada ba Saida ya sake maimaitawa sanan mahaifiyarsa ta ruko hannuwansa idanuwanta na kawo ruwa "zainul Dole jikinka yayi ciwo saboda bakada lafiya kagani yau ciwonka ya tashi sosai har yafi Koda yaushe d'an ammiey"hawaye ya gangaro a fuskarta wani irin bakin ciki da tausayin d'anta ke dankare cikin zuciyarta ,yadda takejin son zainul zata iya sadaukar da komi Dan farin cikin da'nta Anya kuwa tayiwa d'anta adalci?ya kamata ta saki jiki wajen kulawa da d'an nata da soyayyar da dik wata uwa take bawa d'anta, tana kawaici da Kara be bawai Dan Bata sonsa ba Amma lokaci yayi da zata rinka shigowa wajen Dan nata akai akai tare da ziyarar ba zata Dan ganin lafiyar tasa. Dakyar ta sauke numfashi ta dubesa ta share hawayenta ta Shiga shafa Masa sumar Kansa ta Dade tare dashi sanan Tai sallama ta fice dakin.... "Ya zainul ya jikin?"a sanyaye Tai maganar tana kallonsa..Shima kallon nata kawai yayi zuciyarsa ta harba ya lumshe idanuwansa ya budesu sanan yayi Mata murmushi batare da yace komiba kallo daya zakayi Masa ka fahimci Yana matukar Jin jiki sosai... ******* Bayan sati biyu cikin sati biyun Nan abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa harda yawan tashin ciwon zainul abideen abun kullum Kara gaba yakeyi ummaty dik ta kade ta rame ta Kara fari saboda damuwar da take ciki ta dage da bashi maganin da gimbiya rumana ke Bata sanan ta Dade da daina sa Masa karatun alkurani.... Shakuwa da soyayya Mai tsanani ta kullu a tsakanin zainul abideen da ummaty tun be fahimci abinda ke cikin zuciyarsa game da itaba har ya fara ayyanawa zuciyarsa yadda zai rayu batare da itaba Dan ya Gama fidda Rai da samun lafiya tunda shi Kansa yanzun zuciyarsa ta fara Raya Masa ciwon Nan nasa ba na asibiti bane ko na ruwan addua na gargajiya ne saboda yadda dik lokacin da ciwonsa zai tashi yakeji tamkar wasu abubuwa ke Shiga cikin jikinsa suna juya Masa duniyarsa.... ********* Tunda ta fara bashi magani ta daina kunna Masa karatun alkurani kamar yadda aka umarceta akan ta daina saboda a cewar gimbiya aljanu ke basa wahala idan ansa Masa karatun alkurani,yau ce Rana ta farko tun vayan fara basa magani taga jikin nasa babu Dadi ciwon nasa naso ya tasar Masa ta Ciro MP3 din daga Jakarta ta rike a hannunta tana kallonsa... "Ya zainul Naga kamar kanajin wani Abu a jikinka,tamkar bakajin Dadi ciwonka zai tashi ko?" Gyada Mata Kai yayi zufa na karyo Masa "hakan nakeji a jikina ummaty yanzun haka Babu abinda nakeyi kamar faduwar gaba Dan nasan irin wahalar da nakesha idan ciwon Nan ya tasar mun ga kafafuwana da suka sirance kamar ba nawa ba ummaty halittata gabaki daya ta canja kamar ba jinsin Dan Adam ba"...tausayinsa ne ya lullube ilahirin jikinta batai aune ba taji saukar hawaye daga idanuwanta ,tasa hannu ta share sanan wata zuciyar ta umarceta da ta kunna Masa alkurani tagani ko zai kori aljanun yanzun Koda zasu dawo daga baya dai ta koresu dikda gimbiya tayi Mata gargadi da hakan gabanta na tsananin faduwar makomar abinda zai faru kawai ta Saida Rai ta kunna karatun alkuranin ta makala Masa a kunne kirjinta na dukam uku uku... Minti minti takan kallesa taga yanayin nasa sai taga idanuwansa a lumshe zufa na karyowa ta ko Ina a jikinsa,muguwar zaune tayi Tana Kiran makomarta.. shiru shiru kusan minti goma Sha biyar Babu wani abun da ya faru sai ma gani da tayi tamkar yasamu sauki Akan shudewar mintuna dazun ta sauke ajiyar zuciya ta cire Masa daga kunnensa ta dubesa fuskarta dauke da damuwa "ya kakeji yanzun ya zainul?" "Alhamdulillahi ummaty banajin komi,jikina ya dainamun abinda yakemun dazun saidai rashin karfi kawai da bani dashi Kuma inaji tamkar Zanyi bacci"...murmushi ya subuce Mata a fuska "alhamdulillahi"tace a fili Koda aljanun zasu dawo zata cigaba da bashi magungunan ta gani sanan ta rinka gwadawa da karatun alkuranin Koda a boye ne....irin kallon da yakeyi Mata idanuwansa na rufewa yasa ta rufe fuskarta da tafin hannuwanta "ya zainul kayi bacci sai kallona kakeyi" "Baki so Ina kallonki ne ummaty?idan kallon naki yanasamun farin ciki fa?" "Toh shikenan ka cigaba"...sai kawai ya lumshe idanuwansa Yana ayyanowa Kansa abubuwa da dama...Babu abinda ke tada Masa da hankali irin idam ya tuna yadda zai rayu Nan gaba idan ummaty tayi aure tasamu miji,ya rabu da farin cikina harabada Dan gabaki daya ya Gama yanke hukuncin bashida sauran farin ciki a rayuwarsa sai ummaty,yasani ya saka Kansa a cikin tsaka Mai wuya Dan ta Gama kamuwa da soyayyar yarinyar wadda yanada tabbacin harabada bazai sameta a matsayin Mata ba a matsayinsa na nakasasshe Wanda ke kwance saidai a kwantar saidai a tayar...wasu hawayene masu zafi sukebin gefen fuskarsa Yana kwance kan gadon idanuwansa a rufe tamkar Mai bacci.... ******** Bayan ta idar da sallar magriba tana zaune ta janyo Jakarta tana Shirin Ciro littafin adduointa gorar ruwan magani ta Fado daidai Nan sarkin dawaki ya shigo cikin dakin nata,bai lura da abinda takeyi ba hankalinsa na kan radiyon innarta daya shigo dauka ita Kam tsare gorar maganin tayi da idanuwa tamkar Mai nazarin wani Abu...hannunta tasa gefen kunnenta ta sama alamar tanason tunoda wani Abu dangane da wanan gorar magani....tamkar ta taba ganinta a wajen babanta?Basu da banbanci da wadda ta taba gani ta bude gorar ta sunsuna ta har kamshin maganin irin wancen nne?to ya haka Anya Kai gaskiya ba iri daya bane...ta kafe akan kallon gorar akan lallai tanason gano wani Abu a hakan mahaifinta ya juyo ya Kira sunanta "ummaty"shiru Bata amsa ba ya sake kiranta Bata amsaba hankalinta ya tafi yayi saurin juyowa Dan ganin me takeyi haka Bata amsa kiransa ba kawai sai yaga idonta kirrr akan gorar magani.... . *SLIMZY😍* [1/23, 10:41 AM] 😍SLIMZY😍: *13* Wani irin faduwar gaba ya tsinci Kansa ciki lokacin da yayi tozali da gorar ruwan maganin da ummaty ta kafe da Ido lokaci daya yayi saurin dago Kansa daidai Nan idanuwansa da nata suka hadu ganin fuskarta da alamun magana ya sanyasa mummunan faduwar gaba da saurin kauda idonsa kirjinsa na tsananta faduwa..."baba barka da dawowa" "Barkanki dai ummaty,karatun aketatayi ne?injidai kinci abinci?Kuma ba tuwo innarki tayiba"dik a rude yayi maganar Dan ya kauda zatonsa na wurgo Masa tambaya da yake ganin kamar tanada niyyar yi dikda besan irin tambayar ba sanan baisan daga inda tasamu gorar ruwan maganin ba a iya saninsa tunda ya Bata maganin na karshe har yau gimbiya Bata Kara nemansa Dan ya Bata magani tabawa zainul abideen ba...zuciyarsa ta Dade tana zarginta da abubuwa da dama sai yau ya tabbatar da zargin da yakeyi akan gimbiya rumana,wato taje ta bayan gida ta hada Kai da yarinyar Tai Mata wayau tana bashi maganin nakasa Bata sani ba?Kai gimbiya rumana shedaniyar gaske ce tabbas ta saka yarsa a tsaka me wuya dakyar ya iya gyara zamansa akan daddumar ya zurfafa cikin tunani ummaty nata zuba Masa Hira be ma San me take cewa ba sai tsinkayar muryarta yayi da karfi tana fadin "baba meke damunka ne Wai?inata maka magana kayi shiru"Tai maganar kamar zatayi kuka "Yi hakuri Yar baba kada kiyi kuka dik banji me kike cewa ba hankalina ya na kan wanan labaran na radiyo da nake saurare me kikeso ne Yar baba"ta tunzuro Baki gaba cike da shagwaba ya Shiga lallashinta Yana dauke Mata hankali da labari har ta soma Jin barci.... ******** Kwance yake kan gadonsa yayi shiru Yana tunani ya rasa yadda akayi hankalinsa gabaki daya ya koma kan yarinyar da bashi da tabbacin samunta,shin Yaya zaayi yayi aure Yana cikin wanan halin da bashida wani amfani ga ya mace,dik nacinsa dik soyayyarsa da ummaty bazai taba aurenta ba Dan ba Abu bane me yuwuwa yanajin matukar ciwon kasancewarsa cikin wanan nakasar a rayuwa Amma ya gode Allah wani ma ya fishi Jin jiki...runtse idanuwansa yayi ya bude su itace take Masa yawo a kwayar idanuwanta murmushinta,shagwabarta da kukanta komi nata burgesa yakeyi ya Gama yadda da cewa son yarinyar yakeyi dikda besan meneneso ba tun bayan tashinsa har zuwa yanzun yake kwance a nakashe.....babban abinda yake Masa yawo a Rai be wuce yadda yarinyar ke wahala dashi ba harta magani ita ke Nemo Masa Wanda iyayensa suka kasa nema Masa magani a cewarsu ciwonsa na asibiti ne bakin ciki ne ya lullubesa ya Shiga kada kansa,...daidai Nan aka turo kofar dakin hade da sallama Koda cikin duhu yake wanan kamshin na mahaifiyarsa ne Wanda ya banbanta Dana kowa a cikin wanan masarautar "Zainul bakayi bacciba" Tai maganar tana neman wajen Zama a gefen gadon ta zauna ta kamo hannnunsa.. Murmushi ya sauke Wanda iya Kansa fuskarsa yace "ammiey banyi bacci ba banajin bacci tunani kawai nakeyi"...shiru tayi Tana Kare Masa kallo "zainul tunani Kuma?tunanin me kakeyi da har zai hanaka bacci kana kallon yadda kake"Tai maganar cike da damuwa tare da maida hankalinta sosai ga Dan nata tana murza hannnunsa tana jiran Karin bayani,...dakyar ya iya motsa labbansa ya soma magana a hankali "ammiey tunanin ummaty nakeyi"shi Kansa besan lokacin da wanan maganar ta fito bakinsa ba Wanda take yayi shiru kamar an dauke wuta,da sauri ta dubesa cike da mamaki da al'ajabi "ummaty Kuma zainul kake tunaninta?Akan me kake tunanin nata"Ta jeho Masa tambaya a Karo na biyu,Mai makon ya Bata amsa sai kawai ya lumshe idanuwansa fuskarsa dauke da murmushi yayi shiru..."kayi shiru zainul"...Nan ma bai tanka Mata ba shirun dai yayi idanuwansa Kuma a bude suke ba bacci yakeyi ba,mamakine da al'ajabi suka lullube gimbiya bilkisu tabbas tasan watan watarana sai hakan tafaru idan hakan ne kuwa to Dan nata ya fada tsaka Mai wuya Dan Babu yadda zaayi ummaty ta auresa Yana cikin wanan halin ko ba ma hakan ba Mai martaba bazai taba yarda ya aura Masa yarda ba jinin sarauta ba....biri yayi Kama da mutum,wato shiyasa yake tada hankalinsa idan har batazo ba,ko Kuma idan tazo ta tafi yayita kunci Babu walwala saidai yayi shiru?Koda Yan uwansa ne sukazo Masa Hira baya kula su?...lallai zainul ya daukowa Kansa abinda bazai taba yuwuwa ba Dan soyayyarsa da ummaty ba zata taba yuwuwa ba gara ma ya cireta a ransa ya duba halin da yake ciki...tunani sosai ta fada hade da tausayin Dan nata tana Nan zaune batasan bacci yayi gaba dashi ba sai da ta juyo da niyyar Masa magana taga idanuwansa a rufe yana sauke numfashi a hankali...hannu tasa ta shafa Kansa zuwa fuskarsa ta Dade tana kallonsa sanan ta tofesa da adduoi ta lullubesa ta rufesa ta fice dakin.. ******** "Ummaty Naga kamar ana samun ci gaba Akan magungunan Nan da muke amsowa koh?"Tai maganar tana murmushi Gaban ummaty ya tsananta faduwa lokaci daya ta tuna da irin wahalar da yakesha da zarar ta bashi maganin Nan sanan ta lura dik lokacin da zaisha maganin ciwonsa yafi tashi Mai tsanani shin me hakan ke nufi?Koda yake ance idan mutum yasamu maganin waraka sai ciwo gabaki daya ya tashi sanan lokaci daya Kuma sai Allah ya kawo warakarsa saita sauki numfashi murya na rawa tace"ehh to anasamun sauki ranki ya Dade Amma idan yasha maganin ciwonsa yafi tashi sosai" "Dagani har ke sai munyi hakuri zamu samu nasara Akan abinda Mukasa gaba domin Mai maganin ya sanarmun da irin aljanun dake tare dashi wuyar magani ne Dasu da zarar anyi magani sai sufara tashi suna wahal da mutum Amma idan aka daure aka cigaba da maganin da kansu zasu gudu,Dan haka ki kwantar da hankalinki Allah dai ya bamu nasara ga wanan"ta dauko gorar ruwan maganin kamar ko yaushe yau kamar ma rubutu ne da tsaki tsaki ciki ta Dade tana karewa gorar kallo zuciyarta na bugawa lokaci lokaci tanason tuno inda tasan gorar ruwan maganin Nan Wanda Basu da banbanci Amma hakan ya faskara hakanan ta amshi gorar Tai sallama da ita ta fice Murmushin nasara gimbiya tayi tace a fili "ta yaro kyau take Bata karko,da sannu zan cimma bukatata Akan ko wani shege a cikin wanan masarautar"....ta janyo wayarta tana Mai dialing wata number tana murmushi... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 07084161619* ********* Koda ta je da maganin wasiwasin bashi maganin take tayi ga faduwar gaba data tsinci kanta ciki da ta dubi gorar sai hotonta yayita yawo a idanuwanta ta rasa a inda tasanta....dakyar Tai shahada ta tsiyayo maganin a cikin Kofi Dan kadan ba kamar yadda take bashi ya shanye dukaba ta fara bashi ta gani ko aljanun nasa zasu tashi?tausayi yake Bata sosai bataso tabashi su tashi su wahal dashi ta Mika Masa Babu musu ya karba ya shanye....shi Kansa fargabar Shan maganin yakeyi Dan dai kawai Kar yayi Mata musu ne bayason bacin ranta bayaso tace Tana kokarin Taimakonsa Yana gwasaleta shiyasa...ya runtse idanuwansa wasu abubuwa nayi Masa yawo akai tamkar tsutsa ganin yadda yakeyi yasa ta furgita da sauri ta Shiga tambayarsa ko lafiya?saidai ya kada Mata Kai kawai kusan minti talatin a hakan ganin Yana kokarin fita hayyacinsa yasata saurn Ciro MP3 ta kunna tasa Masa suratul baqara a cikin kunnuwansa dikda hakan gabanta bai daina tsananin faduwa ba ta kafesa da idanuwa ko kiftawa batayi a hakan taga bacci ya daukesa....sassanyar ajiyar zuciya ta sauke ta dauko gorar maganin tana kallonta tamkar me Shirin gano wani Abu...kome zuciyarta ta Raya Mata oho sai kawai ta Mike tsaye tana jinjina Kai a hankali idanuwanta suna Shirin kawo ruwa.... ******** "Gimbiya meye hadinki da ni ne da Yar Dana Haifa kikeda niyyar sai kin halakamu hankalinki zai kwanta?" Wata uwar tsawa ta daka Masa "Kai sarkin dawaki me kake nufi da kalamanka?ka iya harshenka idan ba hakan ba zansa a datse maka shi Dan na lura kwanakin Nan kanada son ka rinka jefamun maganganu marasa Dadi ka manta da wadda take gabanka?ko ka manta da wacece gimbiya rumana matar sarki abdulazeez?ko ka mance da iko da mulki da izzah irin tawa?wadda cikin minti goma zuwa ashirin idan nayi niyya Zanyi abinda sarki zaisa a ratayeka?Dan hakan ka iya kalamanka idan kana gabana matar sarki nake"ta maida kanta gefe tana huci tamkar wata zakanya....ganin yadda take mazurai tana hura hanci yasa hankalin sarkin dawaki tashi lokaci kankani ya nemi dik wata natsuwa tasa ya rasa ya rasa dalilin dayasa wanan matar take amfani da mulki da kissa da tuggu irin na Mata Akan kowa a masarautar Nan babban tashin hankalinsa da damuwarsa be wuce yadda sarki da gimbiya bilkisu da dik wasu a Hali na gidan sarki da mutanen gari suka dauki soyayyar duniya suka Dora Mata ba rashin sanin ko ita din wacece...da sunsan yadda take a wajensu da tuni sun Nemi tsari daga sharrinta,dafinta yafi dafin maciji gimbiya rumana hawainiya ce me rikida dik yadda ta gadama zata rikidar maka Kuma cikin seconds da Basu wuce talatin ba dik bukatar datazo maka da ita Dole ka amince da ita saboda sanin ilimin magana da sarrafata da wayau tsantsa da Allah ya Bata... "Sarkin dawaki"ta Kira sunansa a kausashe Wanda Saida hantar cikinsa ta kada Bata jira amsawarsa ba ta cigaba da magana... "Ka bini a hankali idan ba hakan ba daga Kai har yarka Kuna cikin balai Dan gab kuke da ku tsinci kanku a cikin Rami ana muku tambayoyi,Dan da zarar asiri ya tonu to Babu makawa sarki zaisa a kasheku daga Kai har yarka Kuma dik yadda kaso da ka tonamun asiri inada hanyoyi da dama da zambi in Kare kaina batare da nasamu wata matsala ba Dan hakan Ina Mai Baku shawara a wanan tafiyar Babu bijirewa sanan Babu kin bin umarnin gimbiya rumana hakan tamkar Wasa da rayuwarku ne..... WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU CE KACAL TA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619 **HASKE WRITER ASSOCIATION* 💡 * *ZAINUL ABIDEEN* *SLIMZY😍* [1/23, 10:42 AM] 😍SLIMZY😍: 14 Ajiyar zuciya yayi Yana Kare Mata kallo yadda take kumfar Baki saboda masifa...karara ya hango rashin Imani a fuskarta tunda ta furta hakan to zata aikata,Dan haka bazaiso asiri ya tonu ba Dan Babu wadda yakejin tausayi kamar yarsa ummaty wadda take tsananin Shan wahala akan zainul a tunaninta dik abinda takeyi tana yinsa ne Akan samun lafiyarsa .."Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"ya fada a fili ya furzar da wata iska Mai zafi daga bakinsa... "Ranki ya Dade yanzun me kikeso ayi"yadda yayi maganar a sanyaye sarkin dawaki sai ya baka tausayi gabaki daya a rikice yake,ita kanta yadda yayi maganar yaso Bata tausayi Amma rashin digon Imani a cikin zuciyarta yasata Kara tamke fuskarta ta dubeshi Babu walwala "dabara ta rage ga Mai Shiga rijiya ai,inma yayi tsalle ya fada,ko Kuma ya taka a hankali ya Shiga,gargadi na gareka na karshe shine kada ka kuskura kace zakayimun Wasa da hankali hakan babban gangancine ga rayuwar zuriarka gabaki daya sanan kada ka kuskure ka sanarwa da yarinyar Nan kasan tsakanina da ita kamar yadda batasan tsakaninka Dani ba na fada maka"... Zufar dake karyo Masa yasa hannnunsa ya share Yana Shirin Yi Mata magana ta Nuna Masa kofa"ga hanya ka fita nagaji da Jin muryarka a Nan saina nemeka wani lokaci"...jiki a sanyaye ya fita dik jikinsa Babu kwari tamkar Wanda akaiwa duka haka yakejin Kansa,dakyar yaja kafarsa ya bar gidan gabaki daya... ******** Hasa'uh ce makale a jikin sashen gimbiya rumana tana kaiwa da komowa jiran shigowar ummaty kawai takeyi kamar yarda uwargijiyarta tabata umarni Akan ta tabbata taga shigowarta Dan tabata sakon da aka kawo shi Akan lallai ta bashi yasha zataga abun mamaki,tana Nan tsaye ummaty ta shigo sauri sauri tana Shirin wucewa kamar daga sama taga hansa'u a gabanta da sauri taja da baya saboda yadda ta tsorata,wani kallo hansa'u tayi Mata sai Kuma ta tabe Baki "meye na ja da baya sai kace Kinga abun tsoro?ko gudun bayi kikeyi?nagadai banbancina dake a gidan Nan shine uniform Amma ai aikin bautar kikeyi Zaki ganni ki wani ja da baya kamar Kinga dodan jiya"daga ganin yadda take magana Taji haushin yadda ummaty taja da baya,ita kuwa ummaty dariya tabata Dan harga Allah Bata ganta ba Dan haka murmushin Nan nata Tai Mata hade da cewa "Allah ya huci zuciyarki hansa'u wallahi tsoro naji Dan bansan da zuwan naki ba kiyi hakuri"ta kureta da Ido Sake tabe Baki hansa'u tayi "komadai menene kyaji da iyayinki ni gimbiya rumanah ke kiranki tana wancen sashenn"ta Nuna Mata kebabben sashi inda Nan gimbiya ke Zama dik lokacinda zata Bata magani tabawa zainul,Jim abinda hansa'u tace yasa ta tsinci kanta cikin tsananin faduwar gaba,gabaki daya yanzun ita batason muamala da gimbiya rumana Dan akwai abubuwa da dama da takeji a jikinta dangane da wanan matar....inhar maganar bawa zainul magani ne gaskiya ita zuwa yanzun ta hakura da samun lafiyarsa gara ya zauna a hakan da yadda yakeshan wahala dik lokacin da zaisha wanan maganin gashi uwa uba ta rasa dalilin dayasa maganin da gimbiya rumanah ke karbowa ya zainul yayi iri daya da Wanda mahaifinta ke karbowa shekara da shekaru Yana Bata Akan nema Masa magani ita kanta ya daure akan wanan lamarin,da wanan zancen zucin nata ta Isa sashen da gimbiya ke jiranta da sallamarta a bakinta ta Shiga ta nemi kasan carpet inda tasaba Zama idan ta shigo ta zauna "ranki ya Dade gani ance kina kirana inji hansa'u"Tai maganar tana dukar dakai "Dawo kusa Dani Mana d'iyata ummaty,banaso kina banbanta Kanki da diyan Dana Haifa inajinki tamkar su fiyya afnan halima Aysha da zahrau yarana matso kusa"Tai maganar fuskarta a sake,Dan hakan a d'arare ummaty taja jiki ta matsa kusa da ita kasan kujerar datake zaune ta sunkuyar da kanta gabanta na tsananin faduwa Dafa kanta gimbiya tayi Tana murmushi "kokefa ummaty,nasa ankiraki ne saboda wani rubutu da malam ya Aiko dashi zaabawa zainul Akan aljanum Nan nasa masu tashi su gajiyarmun da yaro yace kada a wuce yau baa bashi ba idan har aka bashi zaaga abun mamaki"Bata fuska ummaty tayi batare da tace komiba tunawa da tayi da irin wuyar da zainul Kesha idan aka bashi maganin Nan "Ummaty ko bakison yayan naki ya warke ne umm?Naga kinyi shiru" Da sauri ummaty ta kada kanta tana kakalo murmushin Dole "ah ah ranki ya Dade sai nafi kowa farin ciki idan hakan ta kasance" "Yauwa ko kefa,Dan hakan ki Mike tsaye wajen jajircewa Dan uwan naki yasha maganin Nan kinji" "Toh"shine abinda tace Amma badan yakai zuciyarta ba ta karbi maganin sukai sallama tasaka a jaka Tana tafe tana zancen zuci,yanzun tana zuwa ta bashi wanan maganin jikinsa zai rikice Yar hirar da sukeyi yanayi Mata murmushi tanajin Dadi a ranta asa dik yakiyi yayita ciwo,Anya zata yarda ta Kara bashi wanan maganin akai akai kuwa?dikda na neman lafiya ne?zuciyarta ta fara yi Mata waswasi Akan maganar maganin Nan,ya kamata ace aljanu yanzun sunyi nisa dashi tunda ya kwana biyu Yana Shan maganin Amma da yasha sai aljanun sunzo,sanan Kuma basason karatun alkurani?tabbas aljanu basason karatun alkurani Amma idan akasa musu korarsu yakeyi,ta tuna malaminsu ya taba sanar Dasu a islamiyya da su yawaita karanta alkurani ko saurarensa hakan na nesantamu daga aljanu,shedanu,da shedanun mutane....ajiyar zuciya ta sauke..idan hakane kuwa zata cigaba da sa Masa karatun alkuranin Koda a boye ne Kuma zata tsaya da bashi maganin taga yadda jikinsa zaiyi...da wanan tunanin ta karasa cikin gidan ta Shiga sashen ammiey da sallamarta.... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI...08166177830 KO 07084161619* ********* Shiri sosai fiyya sukeyi itada afnan da Aysha kannen zainul abideen zasuje wajen bikin diyar sarkin kudu Wanda ya kasance babban amini ga mahaifinsu Aysha ta dubi fiyya tana dariya kasa kasa "ya fiyyah wanan kyau haka karfa kije kiyiwa uncle nurah kishiya,Dan kina haduwa da wani Dan sarkin a wajen ya kyalla Ido ya ganki babu makawa abbah zaice zai aura Miki shi"cike da zolaya Tai maganar tana gimtse bakinta,wani kallo da fiyya Tai Mata yasata ta Sha jinin jikinta Dan tasani Sarai fiyya batason raini shiyasa Bata cika Wasa da su ba,ganin hakan yasa afnan maida maganar datayi niyyar yi a cikin bakinta itama tana dariya kasa kasa A can fada suka tarar da zuwan ya musaddik da zahira wadanda zaayi tafiyar tare dasu wanan Karon Banda warisah ,sai wani rawan Kai zahira takeyi Tasha ado ta Sanya wani tsadadden lece ja me flowers golden ba karamin kyau tayi ba cikin Dinkin Riga da sket da yayi matukar karbar fatar jikinta ta yafa gyale red da Jakarta golden takalmi golden shi Kansa musaddik yayi matukar kyau gida ya cika sosai da tawagar Yan rakiyarsu da motoci da bayi da fadawa da aka hadasu dashi tamkar da shi Kansa sarkin zaayi tafiya Yana tsaye yasha rawani sai jinjina Kai yakeyi duka yaran suke zuwa daya bayan daya sunayi Masa sallama fuskarsa dauke da faraa da kulawa yake amsa musu ganin musaddik Saida yaji wani Abu cikin ransa ji yakeyi inama ace da zainul abideen zaayi tafiyar Nan ba Mata ba shida ya kasance magajinsa Kuma babban da'nsa na miji Wanda inda lafiyarsa kalau da dik wani Abu shine zai rinka wakiltar Mai martaba Amma ga yadda Allah yayi dashi....ganin canjawar fuskar Mai martaba yasa gimbiya rumana fahimtar wani Abu a cikin ranta tasani Sarai da zainul abideen lafiyarsa kalau ba karamin banbanci zai Nuna ba Dan tundaga haihuwarsa kowa ya fahimci sarki na mugun sonsa sanan ya zamana shine kadai da namiji Wanda ya Haifa Dan hakan bazata taba Barinsa ya Zama Yana cikin lafiya ba saidai in mutuwa tayi Dan tsatson bilkisu bazai taba gadar sarauta tana raye ba,hakan zai Kare rayuwarsa a kwance sarauta shi da ita sai a lahira... ********* Zaune take gabansa Yana zaune a wheel chair dinsa yau dik Wanda ya gansa yasan akwai alamar sauki a tattare da shi kasantuwar kwana biyu ciwon nasa be tashiba Dan har wata Yar kiba yayi sosai ga Kumari jikinsa yayi sanan wuyansa dake karyewa wani lokaci be tsayawa yanzun Yana tsayawa ga maganarsa dake fitowa sosai yanzun Babu laifi "Ya zainul kaganka kuwa yadda kayi "ta kashe Masa Ido daya cikin sigar zolaya "Menayi kanwar ya zainul"ya kwaikwayi maganarta Yana murmushi...sai kawai ta turo Baki cike da shagwaba "shine kake kwaikwayon maganata?" "Yi hakuri nadaina tunda bakyaso kinji kanwata"yayi maganar cikin sigar lallashi "oya yanzun gayamun menayi" "Kayi kyau kayi kiba sosai gashi kwana biyu ciwonka alhamdulillahi baya tashi"...jinjina Mata Kai kawai yayi batare da yace komiba... Hakan suka wuni tare suna hirarsu cike da nishadi Wanda akasari inhar zata tafi gida dakyar take tafiya,ita kanta yanzun ko a gida cikin tunaninsa takeyi batada wani aiki Wanda ya wuce zancensa Koda da innarta ne wani lokaci sai ta ji inama ta zauna tare dashi su dawwama a hakan,yau ma hakan ta kasance Dan ta manta da zancen wani magani da gimbiya rumana ta Bata,Dan yanzun ta fara Jin ciwo idan ta gansa Yana wahala ta dalilin maganin shiyasa ita kanta ta yanke shawarar tsayawa da basa maganin ta dalilin wani tunani da shiri nata nadaban....akwai abinda takeso ta gasgata game da hakan,tanaso ta fahimci hanyar da gimbiya rumana ta bulla Amma zuciyarta nayi Mata kokwanto Akan yuwuwar hakan....inhar haka ne abinda takeji zuciyarta na fada Mata to tabbas zasu fara Wasa ita da ita saidai idan ta tuna wani Abu zuciyarta na tsananin bugawa,takan tsinci kanta cikin mummunan tashin hankali tsoro da furgici ke lullube Mata zuciya.... ******* "Idan har ya kasance abinda kika fadamun gaskiya ne hansa'u to tabbas daga ita har ubanta sun Gama yawo a cikin garin Nan"... "Ranki ya Dade bana taba Baki labarin karya sai na tabbatar dashi abinda na fada Miki gaskiya ne ranki ya Dade".... Mikewa gimbiya rumana tayi ta Shiga kaiwa da komowa a cikin patlorn tana jinjina Kai cike da tashin hankali..... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 07084161619* *HASKE WRITERS* *ASSO💡* *ZAINUL ABIDEEN💞* *SLIMZY😍* [1/23, 10:43 AM] 😍SLIMZY😍: 15 ******* "Meyasa kikeso kiyi mun Wasa da dukiya da lafiyar yarona ummaty?"gimbiya rumana ta jefa Mata wanan tambayar Wanda take kirjin ummaty yayi wani irin bugu Wanda Bata taba Jin irinsa ba...ta tsorata matuka da tambayar Amma sai tayi shiru batace komiba kirjinta na cigaba da bugawa... Cikin sigar lallashi gimbiya rumana ta matso daf da ummaty tana fadin "haba ummaty meyasa zakiyi haka umm?yanzun maganin da nake kashe kudi Ina amsowa yaron Nan ya warke Ashe bakya bashi?"da sauri ummaty ta dago Kai cike da fargaba da mamaki?ta Yaya tasan Bata bashi magani ba kwana biyu?yadda take kallon gimbiya yasa ta gyada Mata Kai tana furzar da iska a bakinta "ehh ummaty Baki bashi ba Mana,nakosa insamu gagarumar kyautar girma daga Mai martaba dik ranan da zainul ya warke na bayyana Masa cewar nice silar warkewarsa da ke to na tabbatar da ke Kanki Zaki samu kyauta da girmamawa na ban mamaki saboda Babu abinda Mai martaba yafi bukata a yanzun haka sama da lafiyar zainul abideen,ba wani Abu yake kwadayi ba kamar da'nsa ya gaji sarautarsa,Kinga Babu yadda zaayi a dauki sarauta a bashi a cikin wanan halin,ki tausayawa Mana ummaty"...dik maganar da gimbiya ke Yi ummaty nada ko kwanto akan maganar,sosai ta Shiga rudani fiye da Wanda take ciki a kwanakin Nan Amma akwai abinda zatayi ta warware kokwanton da zuciyarta keyi Mata,sai kawai ta sauke ajiyar zuciya ta dubi gimbiya..."ranki ya Dade ni kaina Ina tayaku alhinin wanan kaddarar da kuke tattare da ita ta ciwon danku daya tilo,insha allahu Zanyi bakin kokarina wajen ganin min cimma nasarar sama mishi lafiya" Murmushi gimbiya rumana tayi "alhamdulillahi nagode ummaty nagode sosai da wanan goyon baya Allah Kuma ya bamu saa" "Ameeen"ummaty tace cikin tsananin rudani take Wanda kana kallon yadda take hada gumi kasan akwai wani Abu can kasan zuciyarta,"karbi wanan na Shan yau ne da shafawa kibashi ki shafa Masa" "Toh"tace ta karba cikin ladabi sanan ta Mike ta fita....tana tafe hansa'u na biye da ita a bayanta,take zuciyar ummaty ke sanar da ita akwai wani Abu a kasa Amma ko menene zatayi amfani da shawarar da zuciyarta ta Bata idan hakan ne zata fahimci ko menene Kuma karshen rashin lafiyar tasa tazo a hakan ta karasa sashin zainul abideen... ********* Bacci sosai ta sameshi yanayi da alamar tun bayan da akayi Masa wanka ya koma baccin Dan hakan batayi yunkurin tashinsa ba saita ajiye Jakarta kasa gorar maganin Mai Kama da rubutu na ciki, Yusha'u dake gefe sai leken jakar ummaty yakeyi cike da gulma ya taba dayan bafaden dake gefensa ya Nuna Masa a tare suka kalla sanan yusha'u yayi Masa alama da menene wanan din a Jakarta ,dayan ya girgiza Kansa alamar be saniba shidai yusha'u girgiza Kansa kawai yayi Amma zuciyarsa cike take da son sanin menene a ciki Amma sai ya share kawai...sun Dade zaune ganin ta dauko littafin adduointa tana karantawa sai kawai suka Mike dukkansu har zasu fita yusha'u ya dubi ummaty "idan akwai abinda yake bukata Wanda bazaki iyaba ki nememu a kofar gabas ta wajen sashin gidan waziri"...gyada masa Kai kawai tayi alamar to,yadan dubeta ya dubi jakar ya fice.... Ajiye littafin adduointa tayi gefen drawer saboda yadda zuciyarta ke azalzalarta akan abubuwa da dama,shin menene yasa gimbiya ta damu da zainul yasha magani ya samu lafiya?dik soyayyarce ko menene?sanan ta tabbatar Mata da tanason yasha magani batare da kowa yasan Yana Sha ba batare da kowa yasan suna bashi ba har Allah ya bashi lafiya,to ya akai tasan cewar Bata bashi maganin ba kwana biyu?meyasa ta damu har tasa akesa Mata Ido Akan tabashi ko Bata bashi ba?wani tasa ya da Ido ko kuwa zainul abideen din ta tambaya ya fada Mata?,kaiiii bazata tambayeshi bama tunda besaniba.....wadanan tambayoyin da batada amsarsu sune ke damunta cikin kwakwalwarta jiya zuwa yau da gimbiya ta tareta Akan hakan,ya dace tayi bincike sosai Akan hakan,to wa zata tambaya?.....take idanuwan ummaty sukai jajir saboda damuwa da tashin hankali,tagumi tayi ta zuba Masa Ido yadda yake bacci cikin kwanciyar hankali,kwana biyu da besha maganinba har yayi wata Yar kiba yasamu lafiya tamkar ba me ciwo ba....yanzun mafita shine kawai ki gwada bashi maganin Nan kigani idan ciwonsa zai tashi ko bazai tashi ba?idan zaisamu lafiya ko bazai samuba...bashi maganin shine zaisama Miki amsa guda daya cikin tambayoyin dake kunshe cikin zuciyarki...tambayar maganin na lafiya ne koba ba lafiya bane?"...zuciyarta ke karanta Mata wanan shawarar Wanda take ta amince da hakan ta sa gefen hijjabinta ta share fuskarta dake gumi kamar ana watsa Mata ruwa....Bata lura da tashinsa ba tayi nisa cikin tsananin tunani sai bayan ta share fuskarta ta dago idanuwanta da niyyar kallonsa suka hada Ido sai kawai ta sakar mishi lallausan murmushi "barka da tashi ranka ya Dade magajin sarki"tace tana murmushi,shi kuwa gabaki daya ita yake kallo Yana karantar fuskarta tun bayan tashinsa minti goma Sha biyar da suka wuce batasan idonsa biyu ba....kasa ce Mata komi yayi sai kallonta kawai da yakeyi kirrr kifta idonsa bayayi,ganin hakan yasata tunzuro bakinta gaba "ya zainul kayimun magana Mana inji Dadi,kasan tun yaushe nazo kana barci Kuma ka tashi baka kulani ba"Tai maganar cike da shagwaba,kamar daga sama taji Yana fadin "Nima kinsan tun yaushe na tashi daga baccin Ina kallon kyakkyawar fuskarki kina tunani kin hada zufa?...da alamar ummaty tana cikin tsananin damuwa...menene damuwarki ummaty na"yayi maganar idonsa akanta,sai kawai ta shagwabe fuska tamkar zatayi kuka "nifa ba tunani nakeyi ba kallonka nakeyi kana bacci da alama kanajin dadin baccin,sanan banida wata damuwar data wuce inganka ka Mike kana tafiya da kafafuwanka kamar kowa,sanan gabobin jikinka da Basu aiki kana motsa su cike da karfi da koshin lafiya dik shine ya dameni"idanuwanta suka ciko da hawaye....harga Allah ya yarda da batun nata Dan yasan batayi Masa karya Dan haka sai ya tausasa muryarsa cikin sigar lallashi "meyasa Zaki damu bayan yayan naki yafara samun lafiya?bakiga yadda nai kiba na canja ba?sanan inayin magana na Dan tsawon lokaci batare da hardewar harshe ba?ga canji Nan da mukasamu sakamakon samun lafiya da nayi?"ya tsura Mata Ido...share kwallar data zubo Mata tayi saboda tausayinsa daya lullubeta....take shawarar da zuciyarta ta Bata dazun ta Fado Mata,Dan haka batare da Bata lokaci ba ta dauki Jakarta ta Ciro gorar maganin ta rike a hannunsa ta dubesa,yanayin yadda yayi da fuskarsa kadai ta fahimci Yana cikin tashin hankali Dan ta lura Koda take basa maganin ba son Sha yakeyi ba gabaki daya ma nature dinsa ne beson Shan magani ko kodan Kona asibiti aka bashi haka yakeyi sai kawai ta Dan hada Rai "ga maganinka yau na amso maka kwana biyu baka Sha ba ya kamata kasha"Tai maganar cikin faduwar gaba, Shi Kansa faduwar gaban takeyi Amma bashida zabin da ya wuce Shan maganin kodan yasamu lafiya da farin cikin ummaty sai kawai ya daga Kansa ta tallabosa ta kafa Masa a Baki ya shanye take....hade da yamutsa fuska Yana lumshe Ido "halan maganin bashida Dadi koh?"Ta jefa Masa tambaya saboda ganin yadda taga yanayi da fuskarsa,girgiza Kai kawai yayi "ai ummaty ko menene idan akace magani ne to tabbas bashida Dadi badai kashashi Dan kaji dadiba sai dai kashashi Dan biyan biyan bukatarka.." *WANAN LITTAFIN* *NA* *KUDI NE GA ME BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 07084161619* ******** cikin awanni da Basu wuce biyu zuwa uku ba gabaki daya halittar zainul abideen ta canja sakamakon wanan magani da yasha har wani kumfa ke fita daga bakinsa tamkar yasha guba....dik wani mahaluki dake cikin gidan Saida hankalinsa ya tashi na ciki Dana waje jamaar gidan kowa ya hallara a babbar fadar sarki inda aka shimfideshi masu kuka nayi masu furgici nayi kowa hankalinsa a tashe yake musamman gimbiya bilkisu wadda ta kasa boye furgicin ta sai sharar hawaye takeyi cike da faduwar gaba.. Rungume take dashi tana shafa sumar Kansa gimbiya rumana yayinda anty Zahra yayarsa ke matsa Masa kafafuwa "ummah ya dace ayi wani Abu wanan Karon akan wanan rashin lafiyar ta zainul gaskiya"gabaki daya fada kowa ya Shiga maganganu cike da gamsuwa akan maganar ta Zahra shidai Mai martaba tsananin bakin ciki ya hanasa magana hajiya Kaka ta dubi gimbiya rumana "ke rumana me kikaga ya dace ayi akan hakan ni yaron Nan gabaki daya abun nasa tsoro yake bani tamkar Mai ciwon aljanu ko tabin hankali,wani lokaci ki ganshi cikin lafiya harda Yar kiba yayi Kai ni wanan abun ya fara bani tsoro" Kuka ta fashe dashi Mai ban tausayi "kafin ayi wani Abu yanzun mujira zuwan likitan nasa tunda Naga kamar yasamu bacci sanan likitan nasa na hanya yanzun haka idan ya duddubabshi yayi Masa allurar da yakeyi Masa Yana samun sauki kafin musan abunyi ko" Ajiyar zuciya hajiya Kaka tayi cike da alhini "haka ne mujira zuwan nasa"....baafi minti goma ba sai ga likita,abinda yasaba sai shi yayi Masa wato allurar baccinsa Nan take ko yayi bacci dama ya soma baccin,masu kula dashi suka gyara Masa jiki aka daukesa akai dakinsa dashi aka kwantar dashi kowa da fargaba zuciyarsa.... ******** Hajiya kubra mahaifiyar warisah itace zaune tare da gimbiya bilkisu kallo daya zakayi musu kasan suna cikin tsananin damuwa duba da yanayin fuskokinsu..."nikam hajiya bilkisu mezai hana yaron Nan a canja Masa asibiti ko Kuma a nema Masa maganin gargajiya?Dan wanan abun ya isheni gaskiya haba kullum jiya iyau yaro Kara girma yakeyi da shekaru ansa Masa Ido cikin lalura?idan kasar waje zaa kaisa akaisa idan Kuma masu magani zaa nema a nema gaskiya nagaji idan bazakiyi wani abuba ni zan tari Mai martaba Akan maganar" Share hawaye gimbiya bilkisu tayi "ki tareshi da maganar ko ki samu hajiya Kaka Akan hakan Amma ni nagaji da kafiyarsa Dan dik abinda Zanyi ko ince saidai yace ciwon zainul bana gargajiya bane na asibiti ne" "To idan na asibiti. Ne a kaisa wasu Mana ga asibitocinan a kasashen duniya sai Wanda akaje dikda cewar anyi yawon na asibitin har angaji a gwada wasu Mana ai akwai kwararru. Likitoci zagaye da duniya" "Toh zaayi Masa din".... ******* Tsura Masa idanuwa tayi Tana Kara nazarin abinda yake faruwa ta Gama fahimtar inda komi ya dosa a cikin wanan masarautar....Dan hakan abinda takeso tasani tasanshi,...ta gyara zamanta da kyau "insha allahu komi yazo karshe zainul....zuciyata ta aminta da zargin da nakeyi a kwanakin Nan gaskiya ne...Dan hakan insha allahu zaka warke zaka taka da kafafuwanka cikin kankanin lokaci..."ita kadai take sambatu tana zaune a gabansa tana gadinsa dik ta kwarkwance gabaki daya ta rasa meke Mata Dadi...insha allahu tasamu mafita akan komi batare da gimbiya tasani ba.....saidai tana cikin tsananin tashin hankali can kasan zucuyarta damuwace dankare wadda batasan meye mafitarta ba....... WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 07084161619 *ZAINUL ABIDEEN*💞 *HASKE WRITERS* 💡 *ASSO* *SLIMZY😍* [1/23, 10:43 AM] 😍SLIMZY😍: 16 *HAPPY BIRTHDAY..my exceptional sister,she's one in millions,my wonderful sister she's* *smart and strong,I just can't resist her😍,I am so glad u are with me,I really luv u as u plainly can see😉so have a great BIRTHDAY SOFFY* *GALADANCI...I luv u FURATY...🤭* ********* Bayan kwana biyu, Zaune yake Akan wheelchair dinsa jikinsa ya fara kyau sosai Dan tun ranar da gimbiya ta bada magani Bata Kuma badawa ba saboda yadda burinta ya cika ganin yadda ya koma lokaci kankani Dan haka ba karamin farin ciki tayi da hakanba ******** yau ma kamar kullum ummaty shiri takeyi dan zuwa gidan Mai martaba kasantuwar tayi Rana saboda makara da tayi...tsaf ta shirya cikin jallabiya budaddiya baka Mai stones jajaye fuskarta Babu wani make up Dan ita dama bameson kwalliya bace sai kawai ta yane kanta da gyalen jallabiyar ba karamin kyau tayi ba a gaggauce ta Shiga dakin innarta inda ta tarar Dasu da kanwar babanta da tazo daga garinsu,har kasa ta tsugunna ta gaishesu tare suka amsa cikin sakin fuska....tana Dan tsugunne jimm kadan ta dago Kai ta dubi mahaifiyarta"innah inaso zan tafi gidan Mai martaba yau nayi Rana saboda na makara" Innah ta bude Baki zatayi magana kanwar babanta ta karbe maganar cike da masifa "Ina Kuma zakije da sassafen Nan har kina cewa kin makara?ummaty wanan wani iri yawo ne kikeyi?tun kwana biyu da nazo kike fita da sassafe bakya dawowa sai yamman maraice a cewarki kina gidan Mai martaba ko,kodai aikatau kikasamu a can din ne?"tana dubanta cike da son Karin bayani, Tura Baki ummaty tayi cike da Jin haushin abinda gwaggonta tace sai kawai ta daure tace"gwaggo hauwa ba aikatau nakeyi ba ya zainul nake zuwa jinya da debe Masa kewa"Tai maganar a sanyaye "Jinya?au ummaty har yanzun kina zuwa jinyar wanan yaron da baasan ranan warkewar tasa ba ko?kinki cigaba da makaranta kin maida lokacinki da komi naki ga wanan nadaddem yaron da ke kwance kamar gawa ko?to ki Shiga hankalinki kisan abinda ya kamaceki ba ki zauna kina bautar banza ba,Dan bautar banza kikeyi kinki cigaba da karatu ke Kuma ba kawo miji kikaiba kina wahala Akan Wanda yafi karfinki,na tabbatar da ko warkewa yayi wanan yaron yayi Miki nisa bazai aurekiba wlhy kidai Gama wahalar,lokacin da zai warke ke ki rasa ma nema,Kinga kinyi biyu Babu kenan...Dan Allah dubi dik yadda kika Kare kika kanjale saboda jinya kankanuwar yarinya dake,kodayake harda kwadayi Dan Inba kwadayi ba Banga abinda kike tsinta ba a wanan shirgin"tunda ta soma zazzaga masifa daga ummaty har innarta Babu Wanda yace komi har tayi shiru sanan ne innah tace a sanyaye "hauwa nikam a ganina taimako ne yarinyar takeyi ai ko?" "Dik fadin gidan sarauta Wanda ke cike da jamaa kala kala babu Wanda zai taimakesa sai ita?bashida maaikata ne ko fadawa dazasu kula dashi da har sai ita ta je ta Kula dashi?wallahi Ina jiye muku masifa irinta gidan sarauta Ina jiye muku abinda zaije ya dawo garin kwadayin abin duniya Tam" "Insha allahu babu abinda zai faru hauwa,ki rinka kyautatawa Dan uwanki zato na alheri...wanan yarinya bamu Isa mu rabasu ba tunda tun suna kanana suke tare har ciwon Nan ya samesa,sun matukar shakuwa da juna, shiyasa Nima nabarta take zuwa din" "Toh ta daibi a hankali ku taka a sannu nidai shine shawarar da zambada," Gwaggo ta dubi ummaty dake tsugunne kanta a kasa Tana Wasa da yatsanta ta tabe Baki tace "tashi kije Allah ya tsare adaibi a hankali"....a sanyaye ummaty ta dubi innar tata suka hada Ido ta gyada Mata Kai alamar taje saita Mike ta fice zuciyarta babu Dadi... ********** Zaune take kan babban gadonta a kuryar dakinta kofarta ma a rufe ko Ina a rufe yake sai karar fanka da AC kawai ke tashi ga sassanyan dadin turare da aka turare dakin dashi ko Ina ya dauka kamshi ne kawai ke tashi wayarta makale a kunnenta da alama waya takeyi Mai matukar muhimmanci tunda har ta killace kanta haka Babu kowa ga yadda take wayar kasa kasa.... "Kikace wanan maganin da aka Aiko dashi Mai muhimmanci ne daga gobir aka Aiko dashi?...Kai hajiya rakiya kinyimun kokari a wanan tafiyar na Kuma ki Dadi na yaba Allah ubangiji yabarmu tare ya Kara hada kanmu... Babban burina be wuce insamu yadda nakeso a masarautar Nan ba,hajiya bakin cikina be wuce yadda aka tabbatarmun da na Gama haihuwaba,da dik yadda Zanyi inshiga infita insamu da namiji da nasamu Amma banida yadda na iya Dan haka Wanda ake takama dashi Shima a nakashe yake Matan su zauna da lafiyar"Tai maganar fuskarta cike da takaici,shiru tayi Tana sauraren dayan bangaren sanan ta kyalkyale da wata muguwar dariya da alama maganar da aka fada Mata Tai Mata Dadi sanan tace, "Kai hajiya nagode ki gaida oga sai kinjini insha allahu Zanyi yadda kikace zan sanarwa da yarinyar insha allahu komi yazo karshe da izinin Allah "...sun Dade suna magana sanan ta kashe wayar fuskarta dauke da murmushi.... ********* Saida ta gamawa ummaty bayani tsaf ummaty ta bita da wani irin kallo sanan ta cije lebenta cikin kunar zuciya ta Mike ta fice....Koda ta fita ba sashen cikin gida ta nufa ba hanyar kofar yamma ta nufa Bata zame ko Inaba sai wajen famfo ta juya gabas da yamma kudu da arewa ta tabbatar da babu Mai ganinta sanan ta Ciro wata roba empty daga cikin Jakarta ta juye maganin Tai musaya dikda robobin iri daya ne Amma akwai shedar da tayi Wanda zata gane haka ta canja maganin Nan ta Kara wawwaigawa taga Babu Mai kallonta sanan Tai hanyar cikin gidan,Koda ta juya tana hangen hansa'u ta fito sashin rumana da alamar ita ta turo ta duba taga ko zata bashi maganin Dan haka fuskarta cike da walwala ta nufi sashen gimbiya bilkisu inda ta taddasu duka zazzaune a parlor har su fiyya matafiya sundawo Dasu zahira inda suka yada zango a Nan sukwana biyu,ta tsugunna har kasa ta gaida ammiey ta amsa Mata cikin sakin fuska tare da tambayarta ya innarta ta amsa da lafiya Lau tayi hanyar shigewa dukkansu sukabita da kallo da jakar dake hannunta.... Jingine yake a jikin gadonsa idanuwansa a lumshe daidai Nan tayi sallama cikin zazzakar muryarta Mai dadin saurare...ta tsaya tsaye a kofar tana kallonsa tana murmushi,a hankali ya bude idanuwansa wadanda suka kasance farare Tass ya saukesu akan fuskarta,murmushi kawai takeyi Shima ya maida Mata da martanin murmushi zuciyarsa na bugawa sauri da sauri wani Abu keyi Masa yawo cikin jinin jikinsa tamkar mashi Wanda be tsaya ko Inaba sai a kirjinsa.....ita kanta wani yanayi takejin kanta Mara misaltuwa Wanda Bata tanajin irinsa ba wani irin farin ciki ke ratsa ilahirin jikinta Wanda yasata takowa a hankali tana tafiyarta Mai daukan hankali har tazo gabansa besaniba idanuwansa na kanta ta janyo kujera ta zauna ta dire Jakarta a gefe..."yadai ranka ya Dade wanan kallonfa?"Tai maganar cikin sigar daukar hankali..besan lokacinda ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ba a fili hade da lumshe idanuwansa ya budesu Wanda ya zame Masa dabiarsa ce hakan... "Kyakkyawa nagani shine nake kallo"...waige waige ta shigayi kamar me duban wani Abu tace"Ina take".... "Gata Nan a gabana tana tambayata?bayan tasan da ita nake...hmmm kanwata kinyi kyau sosai"yayi murmushi,da sauri tasa hannu ta rufe fuskarta tana dariya kasa kasa Shima dariyar yayi... Zahira ce ta turo kofa tana duban zainul sanan ta dubi ummaty takai Mata wata muguwar harara ummaty kuwa ta daga Mata gira daya alamar lafiya...ta kafeta da manyan idanuwanta,sai kawai zahira ta tabe Baki ta fice fuuuuuu kamar kububuwa ta bugo musu kofa shidai zainul abideen bece komiba sai kauda Kansa da yayi kawai... Bayan ta Ciro gorar maganin da ta canja ta juye Masa maganin a Kofi sanan ta Dan tofa addua a ciki ta Mika Masa,ganin hakan ba musu ya karba Dan yadda yaga gorar tamkar ruwa bayan yasha ya dubeta "wanan ruwa ne?"tambayar da ya jefeta dashi kenan sai kawai ta gyada Masa Kai "ehh ruwan zam zam ne zan rinkayi maka addua ciki kana Sha" Murmushi ya Yi Mata Yana kallonta batare da yace komiba....sun dauki lokaci suna Hira sanan bacci Mai nauyi ya daukesa tana zaune gefensa tana kallonsa zuciyarta nayi Mata Dadi wani farin ciki Yana ratsa ko Ina a jikinta hansa'u ta turo kofa... "Gimbiya nada bukatar ganinki"...gabanta ne ya Fadi Nan da Nan jikinta ya soma rawa ta ko Ina hankalinta a tashe ta Mike da sauri tana fadin "meya faru Kuma"a ranta addua takeyi Allah dai yasa ba matakan tsaro tasa sukaga lokacin da ta canja ruwan maganin ba a zuciyarta Babu abinda take ambata sai innalillahi wa Inna ilaihi rajiun dik ta firgice hansa'u na lura da yadda ta firgice sai. Kawai ta tabe Baki "meye na furgicewa sai kace kin aikata wani mummunan aiki?dik kin bi kin hargitse daga cewa gimbiya na kiranki?cikin seconds da Basu wuce ashirinba kin fita hayyacinki?ummmm kedai kika sani muje ko meye kyaji"...dakyar ummaty ta hadiye miyau ta bi bayan hansa'u gabanta na tsananin faduwa.. *WANAN LITTAFIN NA KUDI' NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 07084161619 DAN KARIN BAYANI* ******** "Hauwa wanan shawarar da kika bada me kyau ce Akan ummaty nikaina yanzun bason zuwanta gidan sarki nakeyiba Amma gudun in hanata ya janyo mun magana yasa na kyaleta Amma yanzun tunda kika kawo wanan shawarar shikenan Kinga Babu me cewa hanata akayi" "Gaskiya bazamu zubawa zabgegiyar budurwar Ido a hakaba sarkin dawaki yadda kaji na fadan Nan shine mafita itama tasamu inda zata tsugunna yafi kawai"... Dik hirar da sukeyi innah dake tsakar gida tana tsunce wake tana saurarensu hakika hankalinta ya matukar tashi da Jin sarkin dawaki ya amince da shawarar kanwar tasa tashi daya batare da ita ya nemi shawararta ba a matsayinta na mahaifiyarta Amma Babu komi tasan abunyi bazai Sabu ba wankan kuturu da sabulu... ********* Kafafuwan ummaty tamkar ansa Mata shocking hk ta Shiga da sallama can kasan makoshi saboda yadda ta tsorata ta nemi gefen carpet ta tsugunna da kyar ta hada harrufan bakinta tace "gani ranki ya Dade" "Ummaty"ta Kira sunanta cikin wata irin siga da gabanta ya Kara faduwa kamar zata saki fitsari... "Naam ranki ya Dade" "Ba wani Abu yasa nakiraki ba shine in jadadda Miki muhimmancin bawa zainul abideen magungunan Dana karbo saboda ummaty nakosa yaron Nan yasamu lafiya,gashi bashi maganin akeyi kamar baa bashi kullum jikin jiya iyau ummaty"wasu hawaye suka zubowa gimbiya rumana tasa gefen lafayarta ta share.."shiyasa nakiraki inkara rokonki in jadadda Miki kibashi maganin Nan nasa Akan lokaci musamman na yau Wanda na Baki Dan ba karamin kudi na bada ba Mai maganin ya hadashi saboda bakaken aljanun dake bibiyarsa kinji"ta Kare maganar cikin sigar lallashi... Gyada Mata Kai ummaty tayi "insha allahu ranki ya Dade Allah dai ya bashi lafiya Kuma yanzun haka na bashi wanan maganin na yau ma"...murmushi ne ya kubucewa gimbiya rumana saboda farin ciki Wanda sukai Ido hudu da ummaty daidai lokacin itama ta sakar Mata nata murmushin Wanda ita kadai tasan dalilinta.... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS 08166177830 KO 07084161619 DAN* *KARIN BAYANI* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *HASKE WRITERS* *ASSO💡* *SLIMZY😍* [1/23, 10:43 AM] 😍SLIMZY😍: 17 Ajiyar zuciya gimbiya rumana tayi,tadan samu sassauci Akan azalzalarta da zuciyarta keyi gabaki daya batada natsuwa a cikin kwanakin Nan haka kawai take tsintar kanta cikin wani yanayi na rashin yarda....zuciyarta nayi Mata waswasi kala kala Dan haka sai kawai ta dubi ummaty ta gefe kadan "Zaki iya tafiya ummaty sai kinjini" "To ranki ya Dade,Allah ya Kara Miki lafiya da nisan kwana Allah ya bawa zainul lafiya ya takaita Masa wanan wahalar ya kawo karshen ta albarkacin annabi da alkurani"ta karasa adduar tana Mai dagowa ta saci kallon gimbiya rumana ,sai kawai taga yanayin fuskarta ya canja ta yatsina fuska tace a ciki "ameeen" Murmushi ummaty ta sauke,ta gano wani Abu a Nan ma sai kawai ta Mike batare da tace komiba tai hanyar fita,wani mugun kallo Mai tattare da tsantsar tsana da wulakanci gimbiya rumana tabi ummaty dashi wadda ita batamasan tanayi ba hankalinta yayi gaba abinta... ********* Zazzaune suke a fadar Mai martaba kasantuwar yau jumaa kowa na gidan na ciki Dana waje suna zuwa gaisuwar jumaa da sada zumunci a gidan Mai martaba kwansu da kwarkwatarsu hatta da hajiya Kaka mahaifiyar Mai martaba baa barinta a baya itama tana zuwa. Abinci aketa zuzzubawa kowa a plate ana Mika Masa burabusco da miyar alayyaho Wanda yaji kayan Hadi tayi kyau Tai Kore sharr dik inda ka hautsuna cikin abincin nama ne haka ake zubawa kowa gefe daya Kuma gasasshen naman rago ne Wanda aka badeshi da yaji da mangyada a babban matankadi irin Wanda ake amfani dashi a gidan masu sarauta da gidajen gargajiya bakajin sautin komi a parlor sai karar cokula da plates shiru Babu Mai magana.... Hajiya kubrah ce ta dubi warisah wadda Kecin abinci tana famar yatsine yatsine tace "ke warisah jeki sashen zainul abideen kice a fito dashi cin abinci Shima yaci a cikin Yan uwansa"...dibbbb warisah tayi ta kasa tauna abincin dake bakinta saboda takaici ita ta tsani zuwa sashen wanan kazamin haka ta Mike badan ranta yasoba tana faman zumbure zumbure ta fice hajiya Kaka ta wurga Mata harara tace a fili "ja'irar yarinya Mara mutunci"...kowa yaji abinda tace Sarai sunsan da warisah take Dan dama ba shiri suke sosaiba Dan hajiya Kaka batason raini itako warisah uban kowa ta rainasa ga kyamar talakawa da takedashi... Girgiza Kai kawai hajiya kubrah tayi Ta cigaba da cin abincinta batare da tace komiba.... Firarsu sukeyi sosai suna dariya shida ummaty lokacinda warisah ta turo kofar ko sallama Babu,ta shigo daidai fuskarsa dauke da tsadadden murmushin Nan nasa me fitowa da ainihin kyawunsa Wanda Allah ya basa sukai Ido hudu da warisah wadda gabanta ya Fadi lokaci daya ,ta kauda kanta gefe shiko daure fuskarsa yayi tamkar be taba dariya ba,...shiru ne ya ratsa na Dan wani lokaci sanan warisah ta dubi ummaty a wulakance tace "ke malama Baki iya tambayar abinda ya kawoni ne?kinyi shiru kina kallona kamar wata mayya" Murmushi ummaty ta sauke "ya zaayi insan meya kawoki bayan ko sallama wadda adinin musulunci ya tanada bakiyi manaba Kinga Dan ban kulakiba bawani abubane koh?" Tabe Baki warisah tayi "well dama bawani abubane ya zainul zaakai fadar sarki inda Yan uwansa ke sada zumunci Shima yasada zumunci Koda da bakinsa ne,sanan baa bukatar bare a wajen" "Ke warisah wanan wani irin magana kikeyi kamar wata jahila?dik maganganun Nan da kikeyi da wa kike?"...da sauri warisah ta juyo a Karo na biyu sukai Ido hudu da zainul Wanda ya tamke fuskarsa ya kafeta da idanuwa,take yayi Mata wani irin kwarjini Wanda wani be taba Yi Mata Shiba har ta kasa jurewa ta kauda idonta daga cikin nasa gabanta na tsananin faduwa,Amma hakan be hanata turo Baki gaba ba batare da tace komiba ta tsaya... "Ya zainul Bari in kaika koh?" Girgiza Mata Kai yayi "gyaramun zamana dai kawai a wheel chair din zan iya turawa ai hannuna sunfara aiki inajin dadin jikina".. gaban ummaty ne ya Fadi data tuna wani Abu sai kawai ta fitittike "haba ya zainul ya zakace zaka tura kanka da kanka?ni Banga wani warkewa da kayiba sodai kawai kakeyi ka Fadi Bari kagani muje inkaika sai indawo"...badan yaso ba haka ya amince da bukatar ummaty ta gyara Masa zama ta tsaya a bayansa warisah kuwa gaba tayi cike da takaicin ummaty kamar ta shaketa takeji shegiyar yarinya Yar shisshigi mtswww Tai tsaki Tai gaba da sauri.... Da faraar hajiya Kaka ta tarbi jikan nata "lale marhabin da Mai gidana jiki yayi kyau"yadda Tai maganar kowa sai ya juya ga zainul abideen Wanda ke zaune kan wheel chair bayansa ummaty ce da ke gungure dashi,idanuwan zahira suka sauka Akan fuskarsa Mai annuri da kwarjini Wanda dik Wanda ya kallesa baya iya Kara hada Ido dashi saboda kwarjinin haibarsa uwa uba kyau da Allah ya bashi ,wani abune taji ya tsarga Mata tun daga kafafuwanta har zuwa kwakwalwar kanta Wanda ita kanta ta rasa gane menene kawaidai ta tsinci kanta da son Kara kallonsa a Karo na biyu,hakan Nan zuciyarta na harbawa ta Kara dago idanuwanta ta saukesu akansa ta tsura Masa idanuwa hannunta rike da spoon tana jujjuyawa shiko samm hankalinsa baya wajen Yana wajen iyayensa da sukai Masa caaaa kowa na kokarin Nuna Masa kulawa da kauna da soyayya... Warisah ce ta zunguri zahira wadda ta lula wata duniyar "malama meye hakan saikace Kinga wani abun kallo?" Ajiyar zuciya zahira ta sauke "abun kallo ne Mana"tace hade da murmushi "Ina abun kallo ga wanan nakasassan"tace kasa kasa hade da sauke tsaki "Tab wlhy yau ya zainul yayi mugun kyau musamman marrooon din kayan Nan dake jikinsa sun masifar karbar jikin nasa ga Yar kiba da yayi,Kuma kingani yafara samun sauki wlhy kamar ba Shiba,babu miyaum Nan Babu hardewar harshe a maganarsa,yadda yake maganar ma tamkar basarake... gaskiya ya zainul ya hadu yanzun Abu daya ya rage Masa shine kafarsa Amma tabbas shidin namiji ne hadadde" Waigawa zahira tayi ta dubesa da sauri ta kauda kanta hade da tabe bakinta batare da tace wani abuba.... ********* *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS* *DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* tun bayan barowarta fada take cikin tsananin tashin hankali tunda idanuwanta sukai tozali da zainul abideen gimbiya rumana ta Shiga rudani Wanda Bata taba Shiga ba a rayuwata.. zaune take cikin taron yaranta zagaye da ita da yaransu Amma hankalinta gabaki daya baya jikinta Ya Zahra babbar yarta ce tace"Wai ummah yau lafiya kuwa dik na ganki haka?meke faruwa ne?"ta jefa Mata tambaya tana jijjiga d'anta yanaso yayi bacci... Girgiza Kai kawai tayi fuskarta na dauke da damuwa Amma saita kakalo murmushi "babu komi zahrau kawaidai yau banajin dadin jikin Nan nawa ne tun jiya daddare ma" "Ummah Aida kin Kira likita ya dubaki ko" Gyadawa Yar tata Kai tayi alamar to batare da tace komiba ta maida kanta gefe....Nan yaran suka sauya akalar hirarsu suka koma hirar dangi gabaki daya harda yadda kowa ke Nuna farin cikinsa na ganin jikin zainul yafara kyau... ******** Gimbiya bilkisu ce zaune kusa da Dan nata a patlornta an jingina sa Yana kallon tv hannunta na Kansa tana shafashi cike da kaunar Dan nata,haka kawai yau takejin kanta cikin tsananin farin ciki Wanda ita kanta tasan yanada nasaba da yadda jikin yaron nata yayi kyau su kansu kannen nasa farin ciki ya kasa boyuwa a fuskokinsu sai surutu afnan take zubawa zainul abideen saidai ya dago Kai kawai yayi murmushi Dan shi bame son surutu bane.... Dik wanan budurin da akeyi ummaty na bayan sashen zainul hankalinta a tashe,tun da suka hada Ido da gimbiya rumana a fadar sarki zuciyarta keyi Mata lugude Dan Babu tantama ta fahimci wani Abu dangane da samun lafiyar zainul abideen... Gaban ummaty sai faduwa yakeyi tunanin mafita kawai takeyi ta rasa inda zata tsoma ranta taji Dadi babban tashin hankalinta be wuce tasani tunda gimbiya rumana ta lura to tabbas zata Aiko da magani ita Kuma tayi alkawarin harabada daina basa wanan maganin Mai cutarwa Wanda take kawowa a matsayin nema Masa lafiya Nan kuwa cutar dashi takeyi,tasani cewa akwai babban aiki a gabanta Dan tonuwar asirin Nan ba karamin tashin hankali bane a garesu Baki daya...bama a garesu ba a gareta...ya zaayi ta fahimtar da zainul abideen?Babu hanyar fahimtar da shi,sanan Bata Isa ta Nuna Masa ya rinka pretending Akan ciwonba Dole sai ya tambayeta dalilin nata na hakan...wace amsa zata bashi?"ta rafka uban tagumi idanuwanta sunyi jajir tamkar ta fashe da kuka... ******* "Ya musaddik baka lura da ya zainul ya fara samun lafiya ba" "Sai akai Yaya"yace fuskarsa a daure Yana daddana waya,...zahira ta turo Baki "kawaidai naji dadin hakan ne" "Ina kallonki kina satar kallonsa ai a fadar sarki ko meye dalilin hakan oho" Dariya ta fashe dashi "wallahi ya musaddik bani kadai bace harda warisah ma ta kalleshi kawai dai ita haushinsa takeji bansan daliliba,Amma hakan be hanata kallonsa ba"....wani Abu ne ya tasowa musaddik ya tokare Masa kirji ya dubi zahira ransa a bace "ke yimun shiru da wanan zancen ya isheni dik kinbi Kim cikani da shegen surutu" Mahaifiyarsu dake gefe me aiki na yanke Mata kumba ta dubi musaddik Tai murmushi sai sanan ta ce "to Kai meye abun haushi daga baka labari?zaka fara hantarar mun yarinya?ya isheka musaddik,Kinga zahira zonan kibani labari kinji me akayi ya akayi da shi zainul din"Tai maganar fuskarta a sake...cike da shagwaba zahira ta Mike tana murmushi tana waigen musaddik dake watsa Mata harara kamar ya shaketa kishin warisah dik ya cika shi... Zama tayi dafff da mahaifiyar tata suka cigaba da hirarsu,kasa kasa zahira ke magana kawai sai ta soma dariya tana rufe fuskarta...itama mahaifiyartata dariya tayi ta girgiza Kai... ******* "Warisah ya Dace ki cirewa Kanki tsanar Dan uwanki haka Nan wanan wani irin bamzam Hali ne kikedashi?mukami kikafishi ko uban me kika fishi?Ina lura da dik abubuwan da kikeyi a gidan sarki ki Shiga hankalinki nafada Miki" Zuburo Baki warisah tayi ta Mike fuuyhhh tabar patlorn tabar mahaifiyarta na zazzaga masifa Akan abinda takeyi....dik zuciyar hajiya kubrah Babu Dadi Babu yadda ta iya da warisah dik yadda taso ta lankwasata Bata lamkwasuwa Babu abinda take jiye Mata sai gaba....mtswww Tai tsaki tabar patlorn tabita daki..... ********* Tunda ta shigo gida ta dubi fuskar mahaifinta gabanta ya Fadi,ta juyo ta dubi mahaifiyarta wadda ke zaune kan tabarma fuskarta dauke da tsananin damuwa tasan akwai matsala a kasa....kirjinta ke bugawa sauri da sauri hakan be hanata durkusawa gabansu ba bakinta na rawa tace"barkanku da gida"mahaifiyarta ce ta amsa cike da kulawa sabanin mahaifinta da ya amsa Babu yabo Babu fallasa gwaggo hauwa ko kauda kanta gefe tayi ta janyo karamin radiyo dake gefenta ta Kara a kunnenta tana sauraren zaben almuru... Ta Dade tsugunne sanan ta Mike da niyyar zuwa Tai alwalar magriba kamar yadda takeyi idan ta dawo...da wata iriyar murya mahaifinta ya kirata "ummaty"...gabanta ne ya yanke ya Fadi ta tsaya cakkk na Yan dakiku sanan ta juyo a tsorace tace "naam"Baki na rawa....a hankali ta karasa gabansa ta tsugunna kirjinta na dokawa sauri da sauri..... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN* *BAYANI 08166177830 KO 07084161619* *HASKE WRITERS* *ASSO💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY😍* [1/23, 10:44 AM] 😍SLIMZY😍: 18 "Ummaty umarni nakeson Baki akan zuwanki gidan Mai martaba inaso in datse alakarki da gidan saboda inason hadaki aure da modibbo Dan kanwata" Wani irin faduwar gaba ne ya ta tsinci kanta wanda hakan Saida ya haufar Mata Zama daga durkuson da takeyi badan ta shiryaba,jikinta ne kawai yake rawa tamkar an watsa Mata ruwan kankara kallon fuskar mahaifinta tayi idanuwanta a waje,yadda taga fuskar tasa Bata taba ganin hakan ba ya Kara rikita Mata tunani sanin halin mahaifin nata da waye shi yasa wasu zafafan hawaye Wanda Bata shirya saukarsu ba suka fara zuba Akan kumatunta dakyar ta bude Baki tace "baabah menene dalilin hakan?" "A matsayinki na Yar Dana Haifa Baki Isa in yanke hukuncin ki tambayeni daliliba Dan nikeda iko dake bakece keda iko Dani ba kinaji ko" Kanwar babansa ce ta gyada kanta tana watsawa ummaty harara wadda ke zaune dabas a kasa tamkar an tureta a kasa,hawaye ke gudu a idanuwanta tamkar an bude famfo wasu gumi ke karyo Mata ta ko Ina, mahaifiyarta na gefe tana jinjina Kai cike da damuwa hankalinta ba karamin tashi yayi ba Dan tasan halin ummaty Sarai wajen saka Abu a cikin ranta.."Zaki iya tashi kitafi na sanar dake hakan ne da wuri kafin lokaci yayi Dan a yadda na tsara inaso kibi hauwah kutafi can anka ki zauna wajen yayana"...da sauri ta dago kanta bakinta Yana rawa zatayi magana gwaggo hauwa ta tarbi numfashinta "ke Mara kunyar inace ana magana kinason tsoma Baki?yaran zamani?mahaifinki na magana kina neman gaddama dashi?to Bari kiji Baki isaba mun rigada mun yanke hukunci Bari kiji Kuma Baki Isa mu fasa abinda mukai niyya ba saboda wani banza can Wanda kike wahala akansa yaro musaki yaki warkewa sai aikin banza kikeyi iyayensa basusan kinayi ba" Shasshekar kuka kawai ummaty takeyi zuwa yanzun kuka yaci karfinta harda majina jikinta rawa kawai yakeyi tanaji tana gani mahaifinta ya Mike ya fice fuuuhhhh yabar gidan a fusace hankalinsa a tashe yake shi Kansa badan yaso ba ya amince da shawarar kanwar tata saboda sanin masifar dake kwance a kasa tsakaninsu da gimbiya,ita kuwa hauwa kulu sautin radiyonta ta Kara saboda kukan da ummaty ta cika Mata kunne dashi Dan haka ma daukar radiyon tayi ta Kara kunnenta ta janyo plate din shinkafa da wake da ke gabanta Wanda yaji kayan salad irin na talakawa ta hau kaiwa bakinta.... Kuka kawai takeyi Babu kakkautawa haka mahaifiyarta ta tako tazo har inda take ta dafa kafadarta ta dagota da niyyar kaita daki Dan canja kayaj jikin nata,sai kawai ta rungume innar tata tana famar ruzgar kuka itama rungumeta sosai tayi Tana shafa bayanta cike da tausayi.... Cikin dare kasa zaune yayi ya kasa tsaye sarkin dawaki ya tsinci Kansa cikin tsananin tashin hankali Wanda be taba tunanin samun Kansa ciki ba babban abinda ya Kara furgitasa be wuce yadda gimbiya rumana ta Aiko kiransa da gaggawa ba zuwa safiya,sosai ya rasa inda zaisa kajsa,karfe biyu na dare ya zare sakatar kofar dakin kwanansu shida innah wadda itama take lafe Akan gado ba baccin takeyi ba tana kallonsa ya fice dagashi sai Yar sharar dake jikinsa Mai shara shara....ta dago kanta daga kan pillow ta girgiza kanta cike da alhini ta zauna daram kan gadon ta rafka uban tagumi tana tunanin meke Shirin faruwa Dasu?shin ta rasa gane kan mijinta a Yan watannin Nan tarasa wace irin damuwa yake ciki haka Wanda gabaki daya ya rasa dik wata walwala tasa?..... Tsaye yake a jikin windown ummaty Yana iya hango tsakiyar cikin dakinta saboda hasken farin wata ,idan ba gizo take Masa ba to tabbas itace tsaye ta hada kanta da bango tana ruzgar kuka Mai ban tausayi....shi Kansa zuciyarsa ta karye besan lokacinda wata kwalla ta cika Masa kwarmin idanuwansa ba,Kansa ya kulle mafita kawai yake nema Akan wanan masifar dake tunkaro su Dan tabbas yasa an buga Masa kasa a gidan sarkin baka tsohon bokansa ya sanar Masa da asiri ya kusa tonuwa suna gab da Shiga bala'i...ya zaiyi da kunyar Mai martaba daya kasance ya daukesa amintaccensa?ya zaiji da kunyar mutanen gari wadanda Babu Wanda besan zumunci da kaunar da Mai martaba adalin sarki yake Masa ba.... innalillahi wa Inna ilaihi rajiun shine abinda yake ambata bakinsa na rawa hawaye na kokarin saukowa daga idanuwansa Wanda tunda ya girma dik balain da zai Shiga be taba tsintar Kansa cikin zubda hawaye ba saboda jarumta irin tasa,...kasa cigaba da kallon ummaty yayi saboda tsananin tausayin Yar tasa,besan wata mafita ba bayanta,gani yakeyi hakan shine mafita Amma ta Yaya zai sa almakashi ya datse alakar ummaty da gidan Mai martaba?Wanda yasani zasu zargi wani Abu?idan Kuma ya barta ta cigaba da fadawa halaka tayaya zai fiddata?.... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI* *WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830* *KO 07084161619* Jiki Babu kwari ya juya yabar wajen batare da ta sani ba,Yana Shiga dakinsa ya tadda innah zaune ta rafka tagumi,tana Jin alamar shigowarsa ta zabura ta bisa da kallo cike da tuhuma sai kawai ya zauna gefen gadon ya tsurawa waje daya Ido.....kallon yanayin nasa tayi sosai sanan dakyar ta hadiye miyau murya kasa kasa tace "malam lafiya kuwa?" Janyota jikinsa yayi Yana shafa bayanta a hankali hade da furzar da iska Mai zafin gaske "lafiya Lau " "Ah ah malam gaskiya ba lafiya ba,akwai dai wani abun kafadamun Dan Allah"Tai maganar cike da tsananin damuwa.. Murmushi ya kakalo "lafiya kalau nace Miki ki kwantar da hankalinki,idan akwai zan sanar Miki ai,ko?ko kuma idan lokacin sanarwar Taki tayi zakiji ballantana ma babu kinji mu kwanta"ya rungumota jikinsa suka haye gado Yana shafa kanta can kasan zucuyarsa cunkushe take da damuwa musamman idan ya tuno da ko sunan gimbiya rumana sai ya tsinci Kansa cikin tsananin faduwar gaba.... ******** Washe gari da duku duku ya nufi gidan Mai martaba cike da faduwar gaba har yayi Yar Rama shi Kansa,da yanada zabi da bezo Kiran gimbiya ba Amma sanin Halin wacece gimbiya rumana yasashi Dole yaje amsa Kiran nata dikda ba alheri bane...tana zaune kan makadediyar dadduma sanye da babban hijabi Ash colour da alama sallahr asuba ta idar tana zaune kan dadduma gari ya fara wayewa,kallo daya yayi Mata ya kauda idanuwansa ganin yadda take kada kafa da alama sarautar da mulki da izzah da rashin mutuncin suna kusa besan lokacin da ya ambaci hasbunallahu wa niimal wakeel ba...a fili...dik a tunaninsa a zuciyarsa yayi,wani mugun kallo ta watsa Masa lokaci daya ta sauke murmushi Wanda iyakarsa fuskarta....tsaye yayi ya kasa Zama saboda yadda yake a rude sai kawai tasa hannu Tai Masa alama da ya zauna....a d'arare ya zauna ya kalmashe kafa sanan ya kawo gaisuwa 'barka da asuba ranki ya Dade gimbiya rumana uwargidan Mai martaba sarki adali na wanan kasa tamu"...jinjina Masa Kai tayi cike da izzah...ta Dade sanan ta shafa adduar ta juyo garesa, "Kayi mamakin Kiran da nayi maka na gaggawa ko?"ya jinjina Kai cike da faduwar gaba, "To ba abun mamaki bane domin Shirin da kayi kaida yarka kuci amanata ya rushe na fahimci komi"...cike da rashin fahimta ya dubeta ta cigaba da magana "Kun hada Baki da ummaty ta fara karya unarnina ko?ka sanar Mata da wani irin magani take bawa zainul abideen ko?ka fahimtar da ita tafiyar tamu har ta soma mun taurin Kai da karya umarnina ko?to karyarka Tasha karya ko ince karyarku wallahi Dan na rantse da sarkin da ke busa numfashi matukar ummaty tace zataimun taurin Kai wajen cutar da zainul abideen to tabbas zan halakata kaji na rantse Kai kasan koni wacece kasan halina kasan abubuwa da dama da nayi cikin masarautar Nan kashe mutum a wajena ba wani Abu bane,zainul abideen shine kawai ya gagareni wajen kashewa nasamu hanya mafi sauki wajen kwantar dashi shine kukeso kuyi Wasa da umarnina ko?to na tausaya muku Dan wallahi na hango bala'i dake tunkaro ku daga Kai har danginku kaf kaji na rantse".... Wani irin faduwar gaba sarkin dawaki kawai yakeyi yadda zucuyarsa keyi da zaiyi kwakkwaran hadiyn miyau to tabbas sai ya hadiyi zuciya yabar duniya, Ina ma zaiyi hakan ya huta da kunyar Mai martaba da balain dake tunkarosa?Amma ummaty fa?yarsa daya tilo wani irin Hali zata Shiga?..zufa ce kawai ke keto Masa ta ko Ina..... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* _Dan Allah kuyi hakuri Dani jikin ne har yanzun Amma insha allahu zakujini akai Kai yanzun nafara samun sauki_ 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *HASKE WRITERS* *ASSO💡* *SLIMZY😍* [1/23, 10:44 AM] 😍SLIMZY😍: 19 Ajiyar zuciya ya sauke tare da Dora Mata rinannun idanuwansa Wanda suka canja kala lokaci daya,kallon da ta wurga Masa ne ya sashi saurin dauke idanuwansa daga nata kirjinsa da zuciyarsa na tsananta bugawa,bashida wani zabi Wanda ya wuce bin umarninta a wanan lokacin Dan yasan hakan shine zaman lafiyarsa da ta iyalinsa indai gimbiya rumana ce "ranki ya Dade yanzun me kike bukata ayi Miki ?"yayi maganar jiki a sanyaye tamkar ya fashe da kuka "Bukatata itace kawai Kar a sabawa umarnina kada a karyamin doka da sharrudana shine kawai zaman lafiya idan ba hakaba koma menene ya biyo baya Kai ka jawa kanka kaji na fada maka kuwa".. "Yadda kikeso hakan zaayi shugabata,Amma inaso ki dubamin lamarin d'iyata Kar kisata cikin bala'i da halaka Ina matukar kaunarta ummaty yarinya ce batasan komiba"yayi maganar muryarsa na rawa tamkar zaiyi kuka gwanin tausayi,....kallonsa Tai kawai tayi dariya batare da tace komi ba ta Nuna Masa hanyar kofa maana ya fice Mata kenan... Durkusawa yayi gwiwa biyu a gabanta Yana rokonta hade da magiya Amma fafur gimbiya rumana ko kallonsa batayi ba ta cigaba da abinda takeyi ganin zai Bata wa Kansa lokaci yasashi mikewa ya fice jiki Babu kwari ga garin ya soma wayewa ... ********** Wanke wanke takeyi Amma Sam hankalinta baa wajen yake ba tana wankewa ne zuciyarta da gangan jikinta da ruhinta suna can wani waje na daban tunaninta gabaki daya ya tsaya cakkk a Daren jiya Akan maganganun da mahaifinta ya fada Mata na son aurar da ita,bawai batason aure bane Amma burinta be Gama cika ba a rayuwa,burinta na son ganin zainul abideen na takawa da kafafuwansa kamar kowa,burinta be wuce ganin zainul abideen cikin koshin lafiya kamar yadda ko wani mutum saurayi me ji da Kansa da sarauta yakeyi ba,burinta na karshe Wanda shine babban tashin hankalinta a yanzun shine alkawarin da ta dauka na daina bawa zainul abideen wani magani na cutarwa ta daukarwa kanta alkawarin dik runtsi bazata bashi abinda zai cutar dashi ba harabada....Koda gimbiya ta Bata bazata taba bashi ba kome zatayi Mata gara tayi Mata da shi ya cutu....wasu zafafan hawayene suka sulalo Mata a fuskarta tasa hannu ta share ta cigaba da wanke wanken nata har ta gama sanan ta Mike tayi share share na cikin gida ta sa ruwan wanka ta shige dakinta... ******** Kaiwa da komowa kawai gimbiya rumana takeyi ta rasa hukuncin da zata dauka Akan wanan Abu gabaki daya tunaninta ya kulle dik yadda taso tasamu mafita hakan baya yuwuwa,dakyar ta yankewa kanta shawarar bawa ummaty magani a Karo na karshe Wanda ta Dade da ajiyarsa a cikin dakinta maganine Wanda ta ajiyeshi Dan wata manufa tata daban ba yanzun ba Amma ganin bala'i dake shirin faruwa gara ta bada a bashi yasha kowa ma ya huta sanan bataki asiri ya tonu ba a wanan Karon... Wayar salula ta hannunta ta janyo ta daddana wasu numbobi cikin mintuna Basu wuce biyu ba tana Kira baa daukaba takara dialing number sanan aka dauka "yusha'u inason ganinku a bangarena yanzun haka".. Yusha'u da a lokacin Yana gyarawa zainul kayan jikinsa ya dubi Dan uwansa yace "ana Kiran mu fa "....Shima zaro idanuwa dayan yayi batare da yace komiba dik hantar cikinsu ta Gama kadawa... ******** Shiru shiru yau ummaty batazo ba dik hankalin zainul abideen a tashe yake tun jiya yake Jin wani irin faduwar gaba Wanda besan dalilinsa ba,dikda yasan tun bayan tashinsa da mallakar hankalinsa idan har wani Abu zai sameshi to tabbas yanajin abun a cikin jikinsa...saidai yayita ambatar Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun shine mafitarsa kawai.... Gimbiya bilkisu ce ta turo kofar kamshin turarenta ya kauraye dakin gabaki daya taci ado kamar Koda yaushe hannunta rike da Dan karamin Kofi da farin ruwa cikinsa haka ta karaso cikin dakin,murmushi kawai takeyi tana jinjina kanta cike da Jin dadin ganin yadda zainul yayi kyau yasamu lafiya,matsalarsa daya itace rashin kafarsa da karfi da bashi da shi ta nemi gefen gadon ta zauna... "Yadai magajin babansa akwai wani Abu ne"...jinjina Mata Kai yayi fuskarsa Babu walwala "Ban yardaba,na hango damuwa karara a fuskarka,Dan haka kada ka boye mun komi ka fadamin gaskiya ni din mahaifiyarka ce bakada wadda ta fini zainul Ina sauraronka" "Ammiey maganar ummaty ne dama,Naga batazo ba har yanzun sanan Kuma madai banajin dadin Raina Ina tsintar kaina cikin faduwar gaba Wanda bansan dalilinsa ba".....yayi maganar dauke da damuwa Yana kallon mahaifiyarsa tamkar zaiyi kuka... Cikin sigar lallashi ta soma magana "haba magajin babansa umm?shine dik kasa kanka cikin damuwa haka?rashin ganin ummatyn ne?"...ya gyada Mata kai,kallonsa takeyi sosai tana nazarin Dan nata,Babu abinda take hange a kwayar idanuwansa sai tsantsar soyayya da kewar ummaty ta Dade da fahimtar akwai soyayya da shakuwa a tsakanin yaran tun suna kanana ballantana yanzun da sukai girma suka mallaki hankalinsu sunyi sabon da bazasu taba iya rabuwa da juna ba daidai da minti daya....Dan haka kawai sai ta hau lallashinsa tana jansa da Hira haka har bacci ya soma figarsa,Nan ta samu ta janyo cup din da ta shigo dashi ta tofa adduoi ciki sanan ta shasshafa Masa a jikin nasa kamar yadda ta sabayi Masa batare da ya sani ba,ganin bacci Mai nauyi ya figesa yasata mikewa ta bar dakin ta rufo Masa kofa.... Cikin baccinsa Mai Dadi yake mafarki da ummaty tana kuka sosai tana miko Masa hannuwa ana janta ta baya wasu mutane dik yadda ya so da ya Mika Mata hannun ya kasa Shima kukan yakeyi sosai cikin mafarkin nasa sanan wani jarumta yazo Masa ya yunkura da karfin gaske da addua a bakinsa ya Mika Mata hannu zai fizgota wani bakin duhu ya garwaye ko Ina baya ganinta sai sautin kukanta da yakeji yanayin nesa dashi tun Yana iya jiyota har ya daina Shima kukan yakeyi....a hankali haske ya soma bayyana Masa a wurin da yake,Yana bude idanuwansa yaga batanan sai takalmanta ya kwalla karar gaske Wanda yayi furgigit ya farka daga baccin da yakeyi..... Kalle kalle kawai yakeyi cikin dakin ya jike da zufa sharkaf ta ko Ina,dakyar ya samu ya ambaci kalmar la haula Wala kuwatti illah billahil aliyul Azeem,.... Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun....ya runtse idanuwansa Jin yadda Kansa ke Sara Masa tamkar zai rabe biyu...ta dayan bangaren Kuma zucuyarsa kawai keyi Masa lugude.... ******** Gurfane su yusha'u ke gaban gimbiya rumana tana koro musu bayanin yadda takeso su kula sosai da zainul abideen batason wani Abu ya taba Mata shi sanan ta jadadda musu wani umarni da ta Basu Wanda Tai musu alkawarin Mai tsoka tare da samun mukami babba a wanan masarautar matukar hakan ta kasance....sosai suke farin ciki ko wanne bakinsa yaki rufuwa...gimbiya rumana kuwa murmushi kawai take zubawa a fuskarta,tana tsintar kanta cikin tsananin nishadi....macece ita Mai masifar wayau da bariki shi take amfani dashi wurin juyar da hankalin kowa a masarautar cikin ruwan sanyi batare da asirinta ya tonu ba.... Sallamarsu tayi tare da jaddada musu umarninta dukkansu suka amince suna Mai Kara Jin tausayin zainul abideen.... ********* Rike yake da gefen kirjinsa na hagu saboda yadda zucuyarsa keyi masa azabar zugi da radadi juyi kawai yakeyi Akan gado dik minti biyar sai ya kalli agogon bango na dakin ko zaiga shigowarta Amma shiru har anyi azahar Babu ummaty Babu dalilinta...ya kasa hakuri ya kasa jurewa daidai da minti biyar baya iya daurewa rashinta saboda tsananin kaunarta da yakeji...... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS* *DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* ********* Da sauri sauri ta shigo gidan gabanta na tsananin faduwa har tana hardewa garin sauri Babu abinda take da bukata sama da ganin zainul abideen akwai maganar da takeso suyi dashi,Koda ta bullo ta kofar kudu sashen gimbiya rumana a idonta ta shigo Dan tana kallon ta ta window Nan da Nan ta tashi baiwarta dake bare Mata lemo tace ta tsaida Mata ummaty maana Tai Mata kiranta,...Babu musu da sauri ta fita ta sanarwa da ummaty Kiran na gimbiya rumana Wanda ya haifar mata da furgici da tsananin tsoro,turus tayi Dan bataso hakan ba Babu yadda ta iya haka ta juya ta nufi wajen Kiran nata cike da karfin gwiwa..... Har kasa tsugunna ta gaidata kamar yadda ta Saba,itama ta amsa Mata cike da kulawa tamkar babu komi a zuciyarta sanan ta juya ta sallami baiwarta dake wajen ta fice, "Ummaty magani ne gashi na zainul abideen na karbo zaa bashi....basai na tsaya rokonki ki bashi ko karki bashi ba,saidai inaso in sanar dake cewar matukar Baki bashiba zan sani Kuma Zaki fuskanci hukuncina domin dik takunki a gidan Nan da dik wani Abu da kikeyi kada kice baa ganinki ana ganinki yarda ce da kaunarki da Amana da muka damka Miki yasa kikaga Babu Wanda ya maida hankali Akan lamarinki,Amma ke Kanki kinsan Dan sarki kamar zainul abideen Dole akwai masu tsaronsa Koda da Ido ne Dan hakan ki tashi kije kiyi abinda nasaki idan ba haka ba Zaki ga abinda zai biyo baya wallahi.....fada Dani tamkar fada da aljanu ne Babu Dadi"Tai maganar cikin kwanciyar hankali fuskarta dauke da murmushi... Zuwa yanzun xucuyar ummaty ta Gama konewa ji takeyi tamkar ta mutu Dan bakin ciki kalaman gimbiya akwai wata magana a kasa matukar Bata bi umarninta ba to tabbas tana hangen zata jefata cikin bala'i,Dan hakan ta yankewa zuciyarta bin umarnin gimbiya yau na karshe Dan tanaji a jikinta idan tabar gidan tabari kenan harabada sanan zataso bayan tabashi maganin ta tattauna dashi Koda bazai fahimceta ba....ajiyar zuciya ta sauke cikin rauni tace "insha allahu ranki ya Dade zan bashi maganin Zanyi yadda kikeso,Allah ya bashi lafiya" "Ameeen ummaty"tace hade da sakin lallausan murmushi....hakan ummaty ta Mike jiki Babu kwari gimbiya rumana tabita da wani irin kallo tana murmushi... ******** Tana turo kofar ya bude idanuwansa ya saukesu akan fuskarta wadda Tai bakin Kirin tayi zuru zuru tamkar wadda Tai shekaru tana ciwo.....itama kallonsa takeyi kallo Mai cike da tsantsar soyayya da kauna Mai dauke da tausayi da kulawa kallo ne takeyi Masa dauke da sakwanni kala kala daga zuciyarta zuwa kwayar idanuwanta.... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* *HASKE WRITERS* *ASSO💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY😍* [1/23, 10:45 AM] 😍SLIMZY😍: 20 A hankali take takowa daga bakin kofar zuwa cikin dakin tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki,dik batada karsashi haka ta janyo kujerar data Saba Zama ta zauna hade da dafe kanta Wanda ke tsananin Sara Mata,a hankali ta furta "wash Allah na"tana cije lebenta...gabaki daya hankalinsa na kanta ya kafeta da Ido Yana nazarin yanayin nata,shiru shiru batace komi ba tana rike da kanta tana jujjuyawa yasa shi hadiyar miyau a hankali sanan ya Kira sunanta da wata irin siga "ummaty"...shiru Bata amsa Masa ba kusan seconds talatin sanan ta dago manyan idanuwanta da sukai jajir ta dubesa,lokaci daya ta kauda kanta gefe Jin wani kuka na Shirin taso Mata... "Ummaty menene yake faruwa ne haka dik na ganki a hargitse kamar wani mummunan al'amarin ya sameki?meke damunki"yace muryarsa na hardewa Girgiza Kai tayi hade da dago kanta tana kokarin boye kwallar data taru cikin idanuwanta "Babu komi ya zainul kawai dai tun jiya da naje gida nake fama da ciwon Kai ko baccin kirki banyi ba shiyasa kaga ma banzo da wuri ba" "Ban yarda da wanan maganar ba ummaty,karkimun karya ki fadamun gaskiya,tunda muke dake Baki taba boyemun damuwarki ba Baki taba yimun karya ba kina fitowa ki fadamin gaskiya komi muninta Dan haka ki fada mun matsalarki"....a raunane yayi maganar Yana Kare Mata kallo,kawai sai hawaye ya Shiga gudu a idanuwanta babu control ... Dik yadda ya so da ya lallasheta Amma fafur Taki kuka kawai takeyi dik ta fita hayyacinta,ga ajiyar zuciya da take saukewa minti minti,hankalinsa idan yayi dubu ya tashi shi Kansa zuciyarsa karyewa tayi besan lokacinda ya soma zubar da hawaye ba,ji yakeyi tamkar ya Mike da kafafuwansa ya rungumeta a jikinsa ya lallasheta,kukan da takeyi ba karamin ci Masa Rai yakeyi ba zucuyarsa na zafi tamkar an hura wuta....Jin saukar numfashinsa ya sanyata dago fuskarta data jike da hawaye da zufa da majinu taga Shima kukan yakeyi Nan da Nan tasa gefen hijjabinta ta Shiga goge fuskarta tana kada Kai "ya Isa ya zainul bana son hawayen kaji?kaga fa bakada lafiya kake kuka Kuma bana son hawayen Nan naka" Shagwabe fuska yayi hade da makale kafadarsa cikin sigar shagwaba ya soma magana "ba ke bace kema kike kuka?nace menene meyafaru ki fadamun kin ki fadamun shiyasa Nima nake zubar da nawa hawayen,Dan ummaty bazata zubar da hawaye batare da na zubar ba Nima"...murmushi ne ya subuce Mata yadda yayi maganar tamkar karamin yaro,sai kawai ta kada Kai ya zainul rigima ga shagwaba tamkar jinjiri matarsa ta Shiga uku...shine abinda tace a zuciyarta sanan ta dubesa.... "To ya Isa nayi shiru nadaina kukan kaima ka daina,sanan zan fada maka abinda yasa nake kuka sai zantafi anjima kaji?" Gyada Mata Kai kawai yayi idanuwansa akanta.... ********* "Saida na fada Miki kada yarinyar Nan ta fita Amma kika barta ta fita ta tafi gidan da na gaya Miki nayi Mata iyaka da wanan gidan Amma bakiji ba koh?to dik abinda ya biyo baya kece sila tunda nace kartaje" Kallonsa shekeke innah takeyi cike da mamakin mijin nata "malam bansan lokacin da ummaty ta tafi gidan Nan ba,sanan tun shekarun baya da ummaty ke zuwa gidan baka taba tunanin wani Abu zai biyo bayaba sai yau?me hakan yake nufi?malam bangane maka ba kwanakin Nan gabaki daya Dan haka inaso ka sanar Dani abinda yake faruwa kasani a cikin duhu" A fusace ya soma magana "Baki Isa kisani inyi ko kada inyi ba kingane ko?ke harkin Isa ki tsareni sai na fada Miki abinda nake nufi?kece kike aurena ko Nike aurenki?sanan ke kika haifamun ummaty?ko kece ubanta?iyakadai kice kece uwarta koh?ni Kuma nine ubanta Dan hakan nikeda iko da ita bake ba saboda haka idan kika kuskura kika ce zakija da hukuncina zakisha mamakina nafada Miki"....kallo kawai innah ke bin sarkin dawaki dashi gabaki daya ya haukace Yana surfa masifa kamar tababbe..... Ganin yadda yake huci yasa Bata sake cewa komiba ta cigaba da tankaden gari da takeyi....sai kanwarsa ce ta fito daga daki xani a hannu tana fadin "kayi hakuri bakada yadda zakayi Allah ya hadaka da yarinya kwadayayya Inba kwadayi ba an hanaki zuwa waje kin nace kamar tsohuwar mayya,ko da yake dik abinda ummaty tayi uwarta ce tasata Banga laifinta ba" Sarkin dawaki na zaune gefe rike da linzamin doki yace "Aiko zamci ubanta Zanyi maganinta".... "Da dai yafi".... ********* Shafff ta mance da zancen wani magani da gimbiya rumana ta Bata hirar su kawai suke Sha dikda zuciyarta Babu Dadi tayi kokarin danne hakan Dan haka Koda ta tuna da zancen maganin gimbiya rumana wanan Karon bataji wata faduwar gaba ba Dan ta rigada ta shiryawa komi yadda zuciyarta ta Bata shawara,....dik wani tsoro ya Kau daga zuciyarta da dik wani kuka da tayi cikin awa daya tasamu mafita.....Dan haka Babu tsoro ta Ciro gorar maganin fari karrree ta dubi gorar sosai Tai murmushi sanan ta dubi zainul Wanda ke kwance Yana bin ta da kallo dik wani motsi nata...."ya zainul ga maganinka kwana biyu ban baka kasha ba koh?nasan kila ka manta da zancen maganin ma ko?" Gyada Mata Kai yayi yana. Murmushin Nan nasa Mai tsada yace "to ai sauki ya fara samuwa shiyasa kika mance da zancen bani magani koh?" Gorar takai bakinsa Babu musu yasa Baki ya soma Sha sosai tamkar me Shan ruwa .......Saida ya shanye sanan ta dire gorar kasa Tana bin sa da kallo.....dik faduwar gaban da take ciki Bata yarda ta Nuna Masa ba sai kawai tayi haramar tafiya gida saboda yamma da tayi gashi ga yanayin yadda tazo gidan yau Dan haka sauri sauri ta shirya Tai Masa sallama tabar gidan dikda yadda taga yanayi da jikin nasa tausayinsa ya lullubeta haka ta bar gidan tare da tararrabin abinda zai biyo baya.... ********** Tsaye yake a tsakar gidan minti minti yakan dubi agogon hannunsa yayi tsaki,har yanzun Bata shigo gidan ba... Wanan Karon Yana dago Kai yayi daidai da shigowarta cikin gidan a sanyaye tayi sallama gabanta na tsananta faduwa..... "Daga Ina kike ummaty?a wanan lokacin?"ya daka mata tsawa Yana kallon agogon hannunsa.... Wani mugun miyau ta hadiye sanan ta tattaro dik wata jarumta tata tace "baba kayi hakuri naje wajen zainul abideen ne naje duba jikinsa naje in kula dashi kamar yadda kasani Kuma kake bani goyon baya Akan hakan" "Dan ubanki ni kike fadawa hakan?....da Ina Baki goyon baya yanzun na daina bada goyon bayan sai me?shine kike taka mun doka kike tsallake umarnina?kinsan dalilina nayin hakan ne?" "Baba bansan dalilin ka na hakan ba Amma yau ya Dace in rokeka wata alfarma wadda cikin kwanaki biyu naso rokonka ita,sanan akwai tambayar days Dace inyi maka ita Amma nakasa haka....." Kallo kawai yake bin ummaty dashi zuciyarsa na harbawa sauri da sauri lokaci daya ya tsinci Kansa cikin tsananin faduwar gaba.....muryarta ce ta farfado dashi daga suman wucin gadi da yayi...."baba wani Abu ke damuna ba wani Abu bane face inaso intambayeka ko ya zainul yayi maka laifi ne kadaina karbo mishi magani kamar yadda kake karbo mishi a baya?".. Tai tambayar hade da kafesa da idanuwa tanaso taga yanayin na mahaifin nata tanaso ta tabbatar da zargin da ya ke makale cikin zuciyarta Wanda takeyi cikin watanni uku da suka wuce..... "Ummaty ni kike so ki tsare?Koko akwai wani tunani a cikin zuciyarki Wanda kika barwa zuciyarki kikeso yau ki tabbatar dashi?yasa kikazo ki tu kareni ki turkeni Akan kamin ubanki?zainul abideen ubanki ne?meye hadinki dashi?Naga Nina gadamar bashi maganin Kuma na daina sai me?" Murmushin gefen fuska ummaty tayii ganin yadda babanta ya rikice gabaki daya ya haukace sai zufa ke karyo Masa a fuskarsa "kayi hakuri mahaifina, banyi maka wanan tambayar da wata manufa ba sai Dan ganin kwana biyu da baa bashi maganin ciwonsa ya daina tashi,shine nake tunanin ko maganar ta mutanene da suke cewa ciwon nasa ba asibiti ne shiyasa na tambayeka".. Wata irin ajiyar zuciya ya sauke batare da ya sani ba Wanda a kunnen ummaty yayi ta wanan Karon sai taga jikinsa yayi sanyi ya dubeta "ba wani Abu bane yasa nace kibar zuwa gidan gabaki daya banaso ki shaku da yaron har sarki ya ce zai aura Miki shi bayan kinada ranki da lafiyarki cukakkiyar mutum kamar kowa shiyasa "...a sanyaye yayi maganar take itama dabara ta Fado Mata, "Idan har wanan shine tunaninka baba,ka kwantar da hankalinka,Babu wata soyayya tsakanina dashi,Babu wata shakuwa a tsakanina dashi da zaisa in yarda in amince da zancen aurensa Yana nakasasshe,dik wani Abu da Zanyi Masa inayi Masa ne tsakani da Allah don insamu Lada...Dan Kuma amimcim dake tsakaninka da Mai martaba shiyasa kawai"....Tai maganar tana duban yanayinsa....wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarsa Jin furucin da ummaty tayi dikda can kasan zucuyarsa a firgice yake da tambayar da tayi Masa da farko.... "Shikenan na amince Miki ki cigaba da kula dashi,kamar yadda kikeyi din"...murmushin nasara tayi ta durkusa har kasa tace "nagode baba Allah ya saka da alheri Allah ya Kara girma"... "Ameeen"yace Yana Mai Zama a tabarmar dake kofar daki...har ta wuce ta dawo "baba inasu innah?" "Taje gaisuwar mutuwa gidan malam madu da'nsa ya fada rijiya dazun Allah yayi Masa rasuwa" "Allah sarki Allah ya jikansa" "Ameen" Tasa Kai tayi hanyar dakinta rike da Jakarta zuciyarta cike da farin ciki na samun nasara da tayi cikin sauki..... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS* *DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* ********** kuka kawai yakeyi Yana murkususu a cikin daki fasawansa suna danne dashi sai faman zufa yakeyi ,yadda yake ji a cikin jikin nasa wanan karon ya wuce misali.....abinda ya kwana biyu bai Yi ba shikeson samunsa Amma da yake yanada sauran karfi Allah ya bashi ikon karatun alkurani a bakinsa dik surar da ta fito bakinsa karantawa takeyi da adduoi kala kala ...kafafuwansa da hannuwansa sai lankwashewa sukeyi tamkar ana juyasu.... Dik yadda yusha'u yaso ya Kira iyayen nasa kin yarda yayi mutum daya kawai ya yarda Akira Masa itace gimbiya rumana....kallon yusha'u yayi cikin tsananin ciwo dakyar ya furta "kiramum ummah"...da sauri yusha'u yabawa lawal umarnin Kiran gimbiya rumana shi Kuma ya cigaba da rikesa Yana jijjigasa Yana tofa Masa adduoi... Sanye take da hijjabinta har kasa ta shigo hankali a tashe "Yaya dai zainul Dan ummah?menene yake damunka?jikin ne?"dik a firgice take maganar ta karasa cikin dakin ta janyosa jikinta.. "Ummah jikina ciwo ko Ina hannuna kamar ana kakkaryamun shi kafafuwana"cikin tsananin ciwo yake maganar dakyar yana cije lebensa ga rawa da jikinsa yakeyi... Kuka ta fashe dashi Tana shafa ko Ina a jikinsa "Yi shiru Dan ummah kaji Allah zai baka lafiya insha allahu Allah zai kawo karshen wahalar taka zatazo da izinin Allah"ta tallabo shi Tana sharar hawaye....can kasan zuciyarta kuwa tamkar ta taka rawa takeji wani farin ciki ne ya lullubeta,tabbas ummaty ta bashi maganin Nan tunda haka ta kasance taji dadin hakan....towel ta janyo kusa da shi ta dubi yusha'u dake tsaye "dibo mun ruwa Mai Dan sanyi insa Masa a jikinsa naji jikin nasa yayi zafi" jiki na rawa ya nufi toilet ya Shiga Nan da Nan ya samu Yar roba Mai kyau ya dibo ruwa ya kawo ta Shiga tsoma towel din ciki tana matsewa Tana shafa Masa a jikinsa,shi kuwa adduoi kawai yakeyi cikin zuciyarsa dik da azabar da yake Sha.... ******** Ta Dade zaune a dadduma bayan sallahr asuba tana zuba adduoi akan abinda ta gudura a ranta Akan Allah ya Bata nasara ya dafa Mata,Tai adduoi sosai sanan ta janyo Dan karamin alkuraninta ta bude ta karanta suratul yaseen kamar yadda ta Saba ko wace asuba tayi sanan Ta rufe da addua ta shafa.... Jakarta dake nesa da ita kadan ta janyo ta Ciro gorar maganin ta ajiye a gabanta,...kirrrrr tayi da idonta tana kallon gorar maganin tunanin lokacin da mahaifinta ya daina Bata maganin zainul abideen takeyi da lokacin da gimbiya ta soma Bata magani tabawa zainul abideen......dafe kanta tayi zuciyarta na tsananta bugawa idan har Bata manta ba mahaifinta ya daina Bata magani da sati daya gimbiya ta cigaba da Bata magani tabawa zainul abideen....sanan abun mamakin da gora iri daya Babu banbanci,shin menene alakar gimbiya rumana da mahaifinta?shine babban abinda ya kamata ta fara bimcikawa yanzun Amma ta Yaya?ta cije lebenta.....sanan menene kudurin gimbiya rumana akan zainul abideen haka ?...tayaya zatasamu wadanan amsoshin waye zai Bata wanan amsar? Wata zuciya ke ayyana Mata "amsoshinki gabaki daya suna shawarar da kika yankewa Kanki Yi a jiya?ta wanan hanyar kadai Zaki samu amsarki tare da samun mafita cikin wanan lamarin"...abinda zuciyarta ke fada Mata kenan....ajiyar zuciya ta sauke tare da zurfafawa tunaninta da shirinta da takeyi akan gimbiya rumana....wanan karon murmushi ummaty tayi ta gyada kanta cike da karfin gwiwa...... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* *HASKE WRITERS* *ASSO💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY😍*[1/23, 11:05 AM] 😍SLIMZY😍: 21 ******** Hankalinsu na kan katon tv plasma din da yake patlorn bakajin sautin komi sai karar fanka sai AC da suka kureta karshe ko Ina ya dauki sanyi dik hankulansu na kan American film din da suke kallo ....can gefe warisah ce zaune kunnenta makale da waya tanayi tana lumshe idanuwanta da alama tana Jin dadin wayar da takeyi....a hankali ta turo kofar falon bakinta dauke da sallama dukkansu Babu Wanda ya kula da ita balle yasan tayi sallama ko batayi ba har ta iso tsakiyar patlorn zata ketare ta wuce sashen zainul abideen,...kallon banza warisah ta bi ta dashi sanan ta katse wayar da takeyi tace cikin tsawa "dalla malama dakata"....cakkkk ummaty ta tsaya kamar an dasata "Baki iya sallama bane ballantana musamu arzikin gaisuwa?"...Tai maganar tana dagowa daga kishingiden da take.... wanan karon juyar da kanta ummaty tayi da niyyar wucewa,warisah ta Kara Kara dakatar da ita a Karo na biyu "Halan ke dabbar Ina ce da anayi Miki magana kina kokarin wucewa?ko kurma ce ke?" "Nayi sallama har sau uku ba kuji bane"Tai maganar ranta a tsananin bace Amma sai ta danne ta kakalo murmushi... Mtswwww warisah taja tsaki ta zauna tana fadin "komi akayi da jaki sai yaci Kara"...itadai ummaty Bata ce komiba tasa Kai Tai shigewarta ko karasa wucewa batayi ba taji sautin muryar zahira tana fadin "turaren jikinta kamar na Yan bori wallahi dik ta cika Mana parlor Bari kugani"...ta Mike Tai hanyar window tana kokarin zuge labule tsuki warisah taja ta dubi baiwarsu dake rakube a gefe "ke hinde jeki ki hado mana turaren wuta kisa a wajen Nan dik ya dume da warin talauci" Dukkansu Yan Matan dake parlon dariya sukeyi sosai Banda mutum daya wadda ta dubesu Rai a bace tace "haba Dan Allah wanan ba Yi bane wallahi ba girmanku bane,yarinya batayi muku komiba dik kunbi kum tsamgwameta fisabilillahi?" Wani kallo warisah ta watsawa Mai maganar sanan tace "hafsaht ke dama ai ko da yaushe bamu San daidai ba kece kikasan dai dai Kuma kike kaunar mutane koh?Wai shin ma Ina ruwanki Dan antaba wanan kucakar?" "To ku ma Ina ruwanku da ita idan ba sa Ido ba?mtsww sai shegen kishin tsiya " "Kishin uban me zaayi da wanan jakar?"zahirah tace a fusace "Kishi kuke tafiku kyau Kuma ya zainul ita yakeso zai aura"...yadda Tai maganar yasa su dukkansu shekewa da wata irin dariya suna rike ciki har suna hada Baki wajen fadin"tabdijan wanan zamuyi kishi Dan tafimu kyau?farar fata dai,maganar ya zainul Kuma mun bar Mata indai wanan ne" Takaici ne ya Kara lullube hafsat ta Mike tsaye ta rike kugu "insha allahu wata Rana cikinku sai an samu wadanda sukai fada Akan ya zainul Bari dai yasamu lafiya "tana Gama fadin haka ta fice a fusace suka bita da hayaniya tamkar zasu tsaga dakin.... ********* Zaune take gefen gadon zainul abideen rike da hannunsa fuskarta samm Babu walwala ko kadan Tai shiru tana Kare Masa kallo yadda ya rame daga Daren jiya zuwa wayewar gari,....murza Masa hannuwansa takeyi da yatsunta Yana Kara lumshe idanuwansa da alama yanajin dadin yadda takeyi Masa,...cikin wata iriyar murya a dashe yace "ummaty kina Sona?"...da sauri ta saki hannun ta kalleshi a tsorace gabanta yayi mummunan faduwa....Bata taba tunani ko a mafarki zataji wanan kalmar daga bakinsa ba Koko zaiyi Mata wanan tambayar da taji dirarta cikin zuciyarta,....gabaki daya a rude take ta kasa magana jikinta ne ya soma rawa....shi kuwa ya zuba Mata manyan idanuwansa. Farare Tass ya kasa kunne yaji me zatace ,sai kawai tasunkuyar da kanta kasa jikinta bai daina rawa ba....sosai taso bashi dariya dik da yadda yakejin jikin nasa Babu Dadi bai hanasa yin murmushi ba yace "kinyi shiru?tunda bazaki amsa ba mubar maganar kawai ammah ga hannuna rikemun ki cigaba da yadda kikemun inajin dadin hakan"...a hankali yadan dago hannunsa dikda nauyin da hannun yakeyi Masa yau itace Rana ta farko daya dagasa sosai Amma Yana rawa Kar Karrrr Karrrr.....shiru tayi ta kasa dago kanta sai zuciyarta dake bugawa tamkar zata fasa kirjinta ta fito....dakyar ta Dan dago idanuwanta ta kalli hannun da yake Mika Mata,Dan haka sai ta tsinci kanta da dago hannunta a hankali ta ruko hannunsa masu shegen taushi kamar auduga ta rike ta Shiga Yi Masa kamar yadda ya Umar ceta....wani Abu ne ke yawo a ilahirin jikinta tamkar shocking take taji wata irin kasala na neman saukar Mata...dakyar ta iya motsawa ta dago kanta suka hada Ido ya lumshe Mata idanuwansa Wanda suka sa lokaci daya jikinta ya karasa mutuwa wani irin bakon yanayi fiye da Koda yaushe taji a cikin jikinta....suna cikin wanan yanayin aka bude kofa hade da sallama da sauri Tai kokarin kwace hannunta sai kawai taji Allah ya bashi ikon riketa gammm rukon da bazata iya kwacewa ba... Karasowa tayi cikin dakin tana sanye da doguwar rigar Abaya baka Tasha kwalliya Tai masifar kyau sai kamshi take zubawa bayi ne biye da ita sunkai biyar ko wacce da abinda take rike dashi haka ta nemi waje ta tsaya Amma idanuwanta karr Akan hannuwansu da take kallo....daya daga cikin bayi ce ta zube a kasa tace "barka da war haka zainul abideen Dan sarki jikan sarki magajin sarki...da daya tamkar da dubu a dik fadin wanan masarautar ,dik wani namiji a bayanka yake Dan Kaine magajin sarki.....ranka ya Dade Yar sarkin kudu ce ta kawo ziyara wanan masarautar gimbiya maryama diyar sarauniya zainab aminiya ga gimbiya rumanah ummanka,tun jiya ta sauka a wanan gida Mai albarka Amma kasantuwar ta gaji batasamu tazo bangaren magajin sarki Dan duba jikin nasa ba Allah yaja zamaninka ,Allah ya Kara maka lafiya ya kawo karshen wahalarka"....har wanan baiwa ta Gama magana idanuwan zainul abideen a lumshe suke Saida yaji shiru sanan ya budesu hade da sakin lallausan murmushi....itama murmushin ta maida Masa sanan cikin siririyar muryarta tace "barka da warhaka ya zainul" Gyada Mata Kai yayi sanan ya bude Baki a hankali yace "barkanki dai maryama".... "Ya jikin naka?"Tai tambayar a takaice.... "Da sauki"kawai yace hade da rufe idanuwansa yanajin dadin rikon da ummaty Tai Masa....ta dauki lokaci sanan tace"Allah ya Kara sauki" Dukkan su dake dakin sukace "ameeen"...batare da Bata lokaci ba ta saci kallon zainul da idanuwansa ke rufe tamkar me bacci ta kalli ummaty ta Dan tabe Baki ta juya Tai hanyar fita Yan rakiyarta suka take Mata baya... Kamshin turarenta ne ya gauraye ko Ina yasasu saurin diban inda sukejin kamshin,ko kallonsu batayi ba Tai gaba abinta bayi na biye da ita,dukkansu basusan shigowarta ba sunbar patlorn lokacin da ta shigo Dan haka kowa kallon mamaki yake bin ta dashi Allah Allah suke Tai nisa suyi magana , Jikin zahira har rawa yakeyi wajen fadin "tabdijan Amma fa ta hadu"...wani kallo warisah da hafsat sukai Mata hafsat ta dauke kanta warisah ce ta kasa hakuri tace"kedai Taiwa kyau ni batamunba batafini kyau ba"tana fadin haka ta Mike ta fice abinta.... ******** Ganin yayi bacci yasata mikewa a hankali ta zare hannunta daga nasa ta tsaya tsaye Kansa tana murmushi ta girgiza kanta ta juya a hankali take takun nata Dan kada ta tasheshi Koda taje kofa a hankali taja kofar ta sulale Tai cikin gida.... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN* *BAYANI 08166177830 KO 07084161619* ********* Firar dankali tsohuwar keyi a ta bayan babban dakin girki na cikin masarautar tana zaune kan kujerar ta sanye da kaya irin na manyan kuyangi tsofaffi wadanda suka Dade a cikin gidan har suka hayayyafa a ciki Kaya ne irin na gargajiya irin na saki na da Wanda tsofaffi ke sawa kalar blue kamar Koda yaushe a jikinta ta dukufa tana firar dankalin turawa ummaty ta karaso wajen da faraarta hade da sallama tace "assalamualaikum baba kande" "Waalaikumussalam ummaty barkanki da zuwa "baba kande tace fuskarta dauke da faraa tana cigaba da firar dankalinta... Gefen baba kande karamin benci ne ummaty ta gyara ta zauna "baabah dankali kiketa ferewa haka da laasar din Nan?" "Ehh wallahi Wai bakin can Yan Mata sukeso a soya musu Wai bazasuci tuwon shinkafa ba daddare shine akace infere insa a ruwa sai inbawa Mai suyar da yamma sai ta soya musu"... Dan Bata fuska ummaty tayi tace "shine sai a saki?" "Ya Zanyi ummaty?ai aikinmune bauta gidan Nan shekara da shekaru karki wani damu kinji" "Toh Bari in tayaki muna Yar hirarmu ko Yar tsohuwar?" Dariya sukai gabaki daya ummaty ta dauki wuka ta dau dankali ta Shiga ferewa....sun dau minti biyar a hakan ummaty tace "baabah nabar zainul yanata bacci a daki nayo Nan muyi Hira kafin ya tashi yasa rigima har ummansa taji takirani taimun fada"Tai maganar tana dariya... Jinjina Kai baba kande tayi ta cigaba da firar dankalinta tana Yar dariya...."ammah kinsan wani Abu baabah?" Baba ta dago Kai tana kallon ummaty alamar tana sauraronta... Ummaty ta cigaba da magana "dik gidan Nan Babu Wanda yakei ummah rumanah son ya zainul tana matukar ji dashi sosai wani lokacin har tausayi take bani sai kiga tamkar ta cire ciwon ta maida jikinta idan ciwonsa ya tashi....kwanakin Nan tana Shiga damuwa sosai akansa"... Jinjina Kai babah kande tayi ta dubi ummaty tana rike da dankali tace "yarinya ce ke ummaty" "Babah bangane ba me kike nufi?"... "Karki damu Zaki fahimci abinda nake nufi Nan gaba,Zaki fahimci tsananin soyayyar da gimbiya rumana keyiwa zainul abideen sanan Zaki San komi dangane da yaron da mahaifinsa da mahaifiyarsa...." Cikin rashin fahimta da tsananin fargaba ummaty ke kallon baba kande tana sauraronta...shiru tayi na Dan lokaci tana nazarin kalaman babah kande Wanda ta ninke ta Dasu a baibai....Bata fahimci komiba a furucin dik yadda taso ta kasa....cije lebenta tayi Tana son Karin bayani Amma zuciyarta ta haneta da hakan Dan kada baabah kande ta fahimci wani Abu ....sai kawai Tai murmushi tace"tsohuwa ni ban fahimci wanan furucin naki ba wallahi kinyimun magana da yare irin naku na tsofaffi"ta turo Baki gaba... "Ba lallai bane yaro ya fahimci yaren tsofaffi tunda shekarunsa basukai hakan ba,musamman ke me kananan shekaru wadda bakisan komi a cikin wanan duniyar ba,ballantana kisan abinda ke ninke a karkashin kasa a gidan sarauta...gidan sarautar ma babba Mai iyalai kala kala daban daban....Nan gaba kadan idan kinkasance me wayau da kaifin basira Zaki iya fahimtar Killin dake kwrkashi. Kasa".... Tunda baabah kande ta soma rattabo wanan kalaman ummaty ta kafeta da Ido tana nazarin....ta tsinci wasu kalmomi biyu zuwa uku Amma zataso Karin bayani akansu...sanan tunda baabah kande ta furta hakan kenan tasan sirrin cikin gidan Kuma tasan sirrin gimbiya rumana kenan?.....ajiyar zuciya ummaty ta sauke batare da tace komiba ta kalli babah kande suka hada Ido sukai wa juna murmushi....firar dankalin takeyi tana tunani indai haka ne ko anzo wajen tasamu abinda takeso.....tasamu inda zata samu kadan daga cikin abinda take nema....tabbas tasan yanzun ne zasu fara Wasa itada gimbiya rumana dikda batasani ba cikin ita da ita Wanda zaiyi nasara....murmushi tayi kawai ta dire wakar hannunta ta dubi babah kande "Bari inje nasan ya zainul ya tashi yanzun".... Gyada Mata Kai baba kande tayi Tana murmushi ta bita da kallo...ummaty ta bace Mata ta sauke ajiyar zuciya tace a fili "ummaty Allah ya taimakeki akan wanan bakar muguwar ya kawo karshen makircinta insha allahu komi zai warware....da yardar Allah zansa Miki hannu Koda a boye ne..... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *HASKE WRITERS ASSO💡* *SLIMZY😍* [1/23, 11:06 AM] 😍SLIMZY😍: 22 Kwance take Akan makeken gadonta Mai shegen kyau da tsada,kallo daya zakayiwa dakin kasan cewar naira tayi kuka a wanan dakin saboda yadda aka kawatashi da kayan kyale kyale na rayuwar duniya,dikda Babu wadataccen haske a cikin dakin Amma kana iya kallon komi dake ciki saboda dumm light ce a kunne,murginawa tayi ta kwanta rigingine tana kallon ceiling din dakin gashinta baje Akan pillow Dina....dik minti da zuciyarta ke bugawa tana bugawa ne da tunaninsa ,yau kadai da ta gansa ta rasa abinda yakeyi Mata Dadi ta kasa sukuni dikda cewar ba yau tasaba ganinsa ba Amma yadda ta ganta Yana nunar Mata da cewar ya soma samun lafiya,wani irin kyau da kwarjini yayi Mata Wanda be taba Yi Mata shi ba,...runtse idanuwanta tayi ta budesu hade da canja direction din kwanciya...shin menene nata na tunaninsa? menene hadinta dashi?da zuciyarta zata kasa sukuni sai tunaninsa idanuwanta Babu Wanda suke hasko Mata sai kyakkyawar fuskarsa Mai dauke da tsadadden murmushinsa?...tsaki tayi ta janyo wayarta ta kunna data kawai ta Shiga Instagram Dan ta kauda abinda takeji a ranta..... ******* "Ni Kam warisah kinsan cewar Ina kwadayin hadaki aure da yaron Nan zainul abideen?" Zumbur warisah ta Mike tana bin mahaifiyarta da wani irin mugun kallo lokaci daya ta soma numfarfashi saboda yadda zuciyarta ke bugawa sauri da sauri...."momy kinsan me kike fada kuwa?kodai kinyi batan Baki ne yasa kika Fadi wanan kalmar?kinsan wa kike cewar kina kwadayin in auresa kuwa?musakin momy?" "Dan ubanki kinfi karfin auren nasa ne kike nufi ko me?daga nayi magana ki Mike kina wani numfarfashi kamar wata zakanya?Koko dukana kike Shirin Yi inci ubanki daddaren Nan,ke warisah nagaji da wulakanci da iskamcim da kikeyi akan yaron Nan kinaji na koh?to ki fita idona in rufe kinji na fada Miki,Dan hakan kibini a hankali Ina fadawa yayah Mai martaba wanan maganar amincewa zaiyi kuma ba jiran amincewarki zamuyi ba gara ma ki saurara tunda ba cewa nayi ayi aurenba",.... Yadda hajiya kubrah ke masifa ya Kara kular da warisah dake tsaye ta zunguro Baki gaba hannunta rike da wayarta,tsabar tsananin bakin ciki batasan lokacin da ta fashe da kuka Tai hanyar dakinta ba, Hajiya kubrah ta bita da kallon mamaki har ta bacewa ganinta,girgiza kanta tayi hade da mikewa tabi bayan Yar lelen tata don ta lallasheta.... ******** Kuryar daki gimbiya rumana ke ciki suna magana kuss kuss da yarta ta biyu halima baka iya sauraron hirar da sukeyi komi kasa kunnenka ,...sosai suke magana Mai muhimmanci baba kande tana gefe,minti minti takan girgiza kanta cike da al'ajabi.... Juyowa gimbiya rumana tayi ta dubi baba kande wadda ke durkushe Akan gwiwoyinta kamar Mai rokom gafara kanta a kasa cike da ladabi dikda tsufanta,"kande"..gimbiya rumana ta Kira sunanta Kai tsaye, "Kinsan ke amintacciya ta ce cikin amintattun kuyangina da bayi na dake cikin gidan Nan koh"...baba kande ta gyada kanta 'haka yake uwargijiyata" "To inaso maganar Nan da nayi a binneta a cikin dakin Nan banaso inji ko burbushinta a wani waje,dikda nasan kedin ko wacece Kuma nayi sirri dake da dama ban taba jinsu ko sau daya ba ban Kuma Baki taba tonamun asiri ba shekara da shekaru Dan hakan nakeso maganar Nan ta Zama sirri inkara Jan kunnenki sosai Akan maganar da kikaji munyi" "Insha allahu Zaki sameni Mai sirri kamar Koda yaushe uwargijiyata Allah yaja zamaninki ya Kara girma gimbiya rumana uwar zahrau"gyada Kai gimbiya rumana tayi cike da gamsuwa sanan ta juyo ta kalli halima wadda keta hura hanci tana yatsine yatsine kamar uwarta,ita dama halima ko a cikin yaran gidan kafin tayi aure tafi kowa Nuna Isa da mulki sanan da ita ake fada da bayi da kuyangin gidan,komi nata irin na gimbiya rumana harta kamanninsu,Abu daya gimbiya rumana Tai Mata zarra dashi a Hali shine tanada faraa sosai sabanin halima da Bata dariya ko kadan sanan tazo ta auri Dan sarkin wata masarautar sai mulki da Isa da takama ya hadu,wanan yasa gimbiya rumana ke matukar ji da halima take alfahari da tana auren Dan sarki wanan yasa gimbiya rumana bataso yaran gimbiya bilkisu su samu daukaka kamar yaranta komi so takeyi ace yaranta sunfi...Dan haka take amfani da kissa da makirci da tsafi wajen juya hankalin kowa a wanan masarautar ciki kuwa harda uwar Mai martaba hajiya Kaka... Shiru halima tayi na Dan wani lokaci sanan ta dubi mahaifiyarta cike da yanga da sarauta dakyar ta bude bakinta tace"ummah idan akai hakan kina ganin shine mafita?" "Kwarai kuwa halima shine mafita,Kinga zamu jefi tsuntsu biyu da dutse daya,Kinga ummaty diyar sarkin dawaki tanayi mun aiki batare da ta sani ba Kuma inada tabbacin har yanzun Bata fahimci wani abuba dikda kwanaki yarinyar Naga kamar taso ta dagoni Amma nayi amfani da karfin iko da mulki na kifar da shegiyar yarinyar nan,inaso aikin Nan da ya kammala zansa a kasheta ko a batarmun da ita gabaki daya cikin ruwan sanyi Kuma ubanta be Isa ya ce wani Abu ba saboda akwai sirririka da dama Wanda Nima na sani nashi akan Mai martaba" Yatsina fuska halima tayi "akan Mai martaba Kuma" "Kwarai da gaske ko ke bakiyi mamakin yadda Mai martaba ya bawa sarkin dawaki muhimmanci fiye da waziri da sarkin aska ba?to juyar Masa da hankali yayi inda dik abinda yace shi akeyi a wanan masarautar infada Miki"... Jinjina Kai kawai halima tayi hade da kishingida da kilisa ta runtse idanuwanta....ganin hakan yssa gimbiya rumana yin shiru Dan tasan alamu ne na halima tagaji da surutu,Dan halima bameson yawan surutu da hayaniya bace so dayawa ko magana Mai muhimmanci kakeyi da ita saidai ehh ko ah ah Kota girgiza Kai kawai Dan haka tai shiru hade da janyo babban farantin fruits dake gabansu ta dauko ayaba ta mikawa babah kande tace "baremun"... ******* Sai wajen laasar halima Tai Shirin zuwa fadar sarki wajen mahaifinta Amma sai gimbiya rumana Tai Mata umarni da suje suga jikin zainul abideen idan yaso daga can sai taje fada wajen mahaifin nata.... Sunnah tv take zaune tana kallon waazin malam tukur almannar hannunta rike da carbi tana azkhar din bayan sallar laasar sukai sallama cikin patlorn tare da kuyangi biyu biye Dasu, Zubewa kuyangin sukayi gaban gimbiya bilkisu suka kawo gaisuwa ta amsa musu hade da sakin murmushi ta dubi halima dake gefe sanye da alkyabba baka Mai adon golden a jiki Mai shegen kyau da tsada "halimah yaushe kika shigo ne"shine tambayar da gimbiya bilkisu Tai Mata fuska dauke da kulawa... Murmushi halima tayi "ammiey ban Dade da shigowa ba wallahi nace Bari inzo ingaisheki ummah Kuma tace zatazo ganin autanta zainul" Murmushi gimbiya bilkisu tayi tace "to Kinga baban naki ne?" "Ehh yanzun idan Naga jikin brother zan wuce fada ingansa da zuwan na musamman danshi ne' "Lafiya dai ko?" "Lafiya Lau ammiey,inasu fiyya da afee uwar rigima ayshah nasan tana sokoto hutu koh?" "Dik suna wancen patlorn harsu musaddik suna Hira"...gyada Kai halima tayi tare da mikewa tsaye "ammiey Bari mu Shiga" Jinjina Kai gimbiya bilkisu tayi hade da murmushi tana bin halima da kallo,har cikin zuciyarta tana tsananin kaunar halima fiye da kowa cikin yaran gidan saboda natsuwarta da kamun Kai uwa uba mulki da take dashi da Jan aji ,yasa take kaunar halima... Jin alamar motsi yasa ummaty fahimtar zaa shigo duba zainul Dan takun da taji ya wuce na mutum daya take zuciyarta ta ayyana Mata gimbiya rumana ce da tawagarta,Bata Gama tunani ba suka kutso Kai cikin dakin,ganin wadda suke tare yasa ummaty saurin sunkuyar da Kai Dan kada su hada Ido da halima ta watsa Mata wanan kallon na wulanci data Saba, Gefen gadon halima ta tsaya ta Mika hannunta ta ruko hannun zainul "my little brother ya jikin"tace tana kallonsa, Murmushi yayi "jiki da sauki bayan kwana biyu bakizo kin ganniba"Yana maganar harshensa na Dan hardewa.. "Sorry brother kaji prince ne ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa London yasa ban samu na leko gidan ba saboda can munata hidindimu wallahi yanzun ma saboda Inga jikin naka nazo ko su samir da sabreen banzo da su ba, Muhammad ma bacci yayi nasa driver ya kawoni yanzun zan koma nace Bari inzo inganka kaji my lil brother" Miyau ne yadan gangaro Masa ta gefen fuskarsa rabonsa da hakan tun kafin ciwonsa ya tashi shekaran jiya Dan hakan sai gimbiya rumana ta dubi ummaty "ummaty Baki ganin miyau ya gangaro Masa gefen fuska bazaki goge ba?"..Satan kallon zainul ummaty tayi batare da gimbiya rumana ta lura ba sai kawai taga ummaty ta turo Baki gaba hade da hararar inda zainul yake dik a idon gimbiya rumana da halima ta juya taje ta dau karamin towel tazo daidai fuskarsa taga idanuwansa a lumshe sai tasa towel din a hankali tana gogewa kamar tana taba kashi ta cillar dashi gefe....mamaki ne da al'ajabin ummaty ya lullube gimbiya rumana Amma ta kasa magana Halima ce ta katse shirun"brother"ta Kira sunansa ya bude Ido a hankali... "Kaga nazo maka da kilishi zansa babah kande ta kawo maka harda yougourt na siya maka"...murmushi yayi cike da faraa yace a hankali "nagode".... Sun Dan jima kafin halima tayiwa zainul sallama ta nufi sashen Mai martaba... Ummaty kuwa suna fita ta gyarawa zainul abideen kwanciya ta gyara Masa fuskarsa ta fito da ruwan adduwarta daya jikasa da ganyen magarya ta dibo a Kofi ta tallafosa jikinta ta Mika Masa Babu musu ya kwalkwale hade da rufe idanuwansa da yakejin bacci sosai...baai minti biyar ba yayi bacci,kamar jira takeyi ta fice Tai inda babah kande take... ********* Wajen zaman nasu Nan ta sameta ita kadai ta rafka tagumi,har ummaty ta zauna babah kande Bata saniba,Saida ummaty ta Dan dabota "Baba kande wai tunanin me kikeyi ne har nazo Baki saniba?"...a tsorace babah kande ta juyo ganin ummaty ce yasa ta sauke ajiyar zuciya "ammah anyi ja'irar yarinya saikizo ki tsoratani?" Turo Baki ummaty tayi Tana gyara hijjabinta "to ba tunanin marigayi mijinki kikeyiba bakisan nazo ba"...sosai tabawa baba kande dariya yadda Tai maganar,itakuwa ummaty dama hakan takeso saitace "bani labarin tunanin me kikeyi?" Wanan karon canja fuska baba kande tayi "tunanin rayuwa nakeyi yarnaj,yadda rayuwa ta canja ta tabarbare ake zaluncu kala kala akecin amanar zaman tare" "Ban ganeba baba kande fahimtardani"""" Ajiyar zuciya baba kande tayi "ummaty na amince da hankalinki da natsuwarki yasa zan gutsira Miki kadan daga cikin abinda nasani game da gidan Nan saboda inaso a cikin kwanakin Nan idan Allah ya nufa ki ceto wanan yaron zainul abideen Nima insha allahu zanbaki gudun mawa da goyon baya dari bisa dari da taimako da zan amso Miki kala kala ganin munsamu nasara' Wani farin ciki ne ya lullube ummaty duka jikinta ji takeyi kamar an watsa Mata ruwan sanyi Amma saita boye farin cikin nata Dan kada babah kande ta fahimci tasan wani Abu tunda so takeyi ta kyankyasa Mata komi... Ruko hannunta baba kande tayi "kafin inbaki labari da sirrikan gidan Nan zan fada Miki wata magana da ja jiyo a sashen gimbiya rumana Wanda tunda nake da ita ban taba fallasa sirrinta ba....Amma banaso kiyi mamaki ko ki tsorata kinji?"ummaty ta gyada Kai cike da kosawa.... "Na jiyo gimbiya rumana da yarta halima suna tattaunawa akan sun samu sabon Malami Wanda zaakai zainul abideen wajensa da sunan Yi Masa magani a nakasta rayuwarsa batare da kowa ya fahimta ba,Dan yanzun haka halima taje fada wajen sarki zaafada Masa a juyar Masa da hankali a karasa nakassa zainul abideen dikda a kwance yake so akeyi ya rasa hankalinsa gabaki daya"...zumbur ummaty ta Mike cike da tashin hankali tana kallon babah kande a rude, "Nace kada ki tsorata ki saurareni tsaff ingama Mana insha allahu munada mafita"...bakin ummaty na rawa jikinta nayi muryarta har hardewa takeyi "baabah kande "ta Kira sunanta dai dai Nan wata baiwa ta karaso wajen sai suka canja hirar "ummaty gimbiya rumana na bukatar ganinki a sashenta" Takaici ne ya lullube ummaty na Bata gamajimzance ba ankirata ba lallai su hadu ba Dan yamma tayi sai kawai ta bude Baki zatayi magana babah kande ta rigata ta hanyar fadin "gatanan zuwa,ummaty je Kiran uwargijiyata"Dan hakan ba musu ummaty ta wuce hankalinta a tashe... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* ******* Gefen carpet ta zauna kamar yadda ta Saba "gani ranki yadade" Cike da kulawa murya kasa kasa gimbiya rumana tace "ummaty Kinga nakiraki koh"...ummaty tagyada Kai, "Dazun ne Naga kinyiwa yarona abinda banji Dadi ba yasa nakiraki intambayeki dalilinki nayin hakan kamar kina kyamarsa bayan ba hakan kikeyi Masa ba"...murmushi ummaty tayi har zuciyarta taji Dadi tarkon da ta Dana ya Kama gimbiya rumana Dan hakan saita daure fuskarta,ta nisa hade da sauke ajiyar zuciya "ranki ya Dade ba kyamarsa nakeyi ba,kawai dai Nima nafara gajiya da jinyar ne, masifar haushi yake bani wallahi banida yadda Zanyi ne yasa nake zuwa ramki ya Dade Amma na gaji"ummaty kawai sai ta saki kuka hawaye Sharrrr sharrr a fuskarta ta cigaba da Fadi cikin kuka "kiyi hakuri ranki ya Dade idan na Bata Miki Rai saboda danki ne" Wani sanyin dadi ne ya lullube gimbiya rumana jin furucin ummaty Akan zainul abideen wato tagaji dashi?Kai taji dadin wanan lamarin tabbas yazun tasan hakarta zata cimma ruwa Dan dik abinda tace Yar tayi zatayi babu musu... Ita kuwa ummaty kasan zuciyarta tamkar ya Kama da wuta takeji dikda tasan tarkon da ta danawa gimbiya ya kamata Kuma zata yarda da ita dari bisa dari yanzun.....dik ta kosa ta fita taje wajen baabah kande su karasa maganarsu Dan yanzun tasan ta Gama da gimbiya yanzun Target dinta na gaba kawai zata Dora..... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *HASKE WRITERS* *ASSO💡* *SLIMZY😍* [1/23, 11:10 AM] 😍SLIMZY😍: 23 Sauri sauri ta fito sashen gimbiya rumana har tana hardewa kamar zata Fadi kasa,bayin dake zagaye da sashenta suna kaiwa da komowa suka bi ummaty da kallo hade da girgiza Kai,...daya daga cikinsu ta kalle Yar uwarta murya kasa kasa tace "uwaliya ko Kinga wanan yarinyar kullum sai na ga gilmawarta a sashen gimbiya rumana ko me take zuwa Yi oho" Wawwaigawa wadda aka Kira da uwaliya tayi sanan Tai kasa da murya tace "saade indai wanan ne ni ba kwanan Nan na soma gani ba koma menene zai bayyana Nan bada jimawa ba,babban abinda ya bani mamaki ma jiya fa na gansu tare da babah kande?" Dafe kirji saade tayi "wace baba kande?"sai Kuma ta tabe baki hade da girgiza Kai cike da tsaigumi tace "su kadai sukasan me suke kullawa" "Idan tayi wari zamuji,yanzun idan kanason kanka da arziki da mutunci ka Kama bawan Allah ka kayi shiru kasa Ido ka baza kunnuwa"suka tafa hade da sakin dariya.. "Umm Bari kigani inje inyi abinda gimbiya tace kafin ya nemeni kinsan halinta"a tare suka juya suka watse wajen kowa yayi hanyarshi... Duban duniyar Nan ummaty tayi bataga baba kande ba hankalinta ba karamin tashi yayi ba gashi yamma tayi batare da ta so hakan ba haka ta hakura ta juya a sanyaye ta nufi sashen gimbiya bilkisu Dan ganin halin da zainul abideen yake ciki.... ******** Durkushe take a babbar fadar sarki gaban Mai martaba mahaifinta gefe daya gimbiya rumana ce zaune tana kada kafafuwanta fuskarta dauke da murmushi ta dubi halima tace "halima ya dai akwai magana ne Naga kinyi shiru tamkar kinada bukatar wani Abu" Gyara Zama halima tayi hade da gyaran murya tace "dama nazo wajen abbah ne da wata magana dangane da lil bro zainul" Jin hakan yasa Mai martaba maida hankalinsa sosai kan halima, "Au Ashe zuwan ba namu bane,zuwan na mahaifinki ne da d'an uwanki to sai ki fada mishi ai ba kiyi shiru durkushe ba" Murmushin manya Mai martaba yayi cike da zolaya ya dubi gimbiya rumana 'yanzun dai kishi kikayi saboda d'iyata tace wajena tazo miyi magana ba wajenki ba koh" Farrr tayi da idanuwanta tana murmushin kasaita baiwarta nayi Mata fifita a hankali sanan tace cike da kissa "to ai gatanan ga ka koh?saima nabaku wuri idan sirri ne,saidai Abu daya zaisa inzauna don maganar ta shafi yarona shiyasa"...dukkansu dariya sukayi sanan Mai martaba ya dubi halima hade da maida hankalinsa sosai "Ina sauraronki sadiya" "Ranka ya Dade Akan maganar ciwo zainul ne nazoda wata muhimmiyar magana,...maganar ciwonsa ne nake ganin ya Dace zuwa yanzun a nema Masa maganin gargajiya" Mai martaba ya gyada Kansa cike da gamsuwa da maganar da halima tayi,ita Kuma ta cigaba da maganarta "akwai wani Malami Wanda ya kware Akan harkar magungunan gargajiya Dana musulunci Wanda prince ya sanshi shine yake bani labarin cewar shine ya warkar da kanin mahaifinsa lokacinda ya samu tabin hankali,zuwa biyu kwata kwata akayi yasamu lafiya,shine nace ya hadani dashi Zanyi maka maganar idan har ka amince a dauki zainul abideen akaisa can ko Allah zaisa mudace ko zai Mike da kafafuwansa" Gimbiya rumana ta karbe zancen cike da farin ciki "alhamdulillahi Kai naji dadin wanan labari Allah yasa karshen wahalar yaron Nan ne tazo"... Shiruuuu Mai martaba yayi na Dan wani lokaci Yana nazari,yayinda zuciyoyin su suke bugawa sauri da sauri cike da faduwar gaba suna sauraron amsar da zataa fito daga cikin bakinsa...kimanin minti goma Sha biyar bece wani Abu ba sai cannnn yayi Yar gyaran murya yace "halimatu saadiya naji zancenki naji shawararki Kuma ya yaba da ita....saidai ni bana gaggawar yanke shawarar batare da nayi nazari akanta ba Kuma nayi shawara da abokanan shawarata.... Gimbiya rumana bataso hakan ba zuciyarta batayi Mata Dadi ba taso ace ya amince take batare da Bata lokaci ba,Amma Bata baci ba tasan yadda zata bullowa lamarin Dan hakan sai ta dubesa "ranka ya Dade ya kamata ka duba lamarin yaron Nan kasan halin da yake ciki shekara da shekaru,watakila warakarsa ce tazo ,watakila wahalarsa tazo karshene yasa Allah ya bawa halima ikon zuwa gareka da maganar...Dan Allah abbam zainul a duba lamarin Nan na yarona a nemawa magajin babansa magani Shima ya samu lafiya kamar kowa"cike da damuwa take maganar tamkar zatayi kuka,...tausayin ya ne ya lullube Mai martaba sai kawai ya gyada Mata Kai tare da cewa"zaa duba ki kwantar da hankalinki uwar zainul abideen" "Magajin babansa Kuma ba"cewar gimbiya rumana tana dariya....Nan suka kauda maganar suka dauko wata hirar,Saida aka Kira magriba sanan halima Tai haramar tafiya gidanta.... ******** *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS* *DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* ********* "Ke ummaty lafiyarki kuwa tunda kika dawo gidan Nan kike Abu zabure zabure kina magana ke kadai kamar wata zautacciya?" Dan furgita ummaty tayi hade da juyowa ta dubi innarta dake gefenta ta kafeta da Ido sai kawai ta sakar Mata lallausan murmushi ta Dora kanta a cinyarta tana turo Baki "Kai innah nifa ba magana nakeyi nikadai ba" "Karya nayi Miki kenan?ko Kuma baa kusa Dani kike maganar ba wani waje kikeyi daban,meye yake damunki ne haka " "Innah wallahi Babu komi kawaidai banajin dadin Raina ne kwana biyu tun Akan maganar auren da baabah yace zaimum dik hankalina ya tashi" Murmushi innah tayi "ke Kuma bakison maganar aure koh?idan an barki haka Zaki zauna kenan ko ummaty?ai aure ya Zama Dole kiyishi komi Daren dadewa Amma dai kiyi tunani Akan hakan tunda bazaki dawwama a gabanmu ba ko? Gyada Mata Kai ummaty tayi jiki a sanyaye,tace "toh innah"ta kwantar da kanta a cinyarta ta sake lulawa cikin duniyar tunani.....babban tashin hankali ke Shirin fuskantosu matukar abinda babah kande ta fada gaskiya ne to zaa samu babbar matsala,...hanyar da zaa rusa ginin tafiyar shine abin dubawa Dan tasani tabbas yanzun Mai martaba bashida wani buri da ya wuce yaga zainul abideen ya warke ya taka da kafafuwansa,Kuma ta tabbatarwa kanta da cewar zasuyi amfani da makirci da kissa cikin ruwan sanyi zasu shawo kan Mai martaba akam yabari akai zainul abideen wajen magani,Kuma ana kaisa shikenan dik Shirin da tayi ya koma baya komi zai lalace....idanuwanta suka kada sukai jajir...kanta yayi zafi zuciyarta Babu abinda takeyi sai bugawa sauri da sauri...shin me ya kamata tayi shiri Akan hakan ganin tafiyar ta ruguje?zuciyarta ke ayyana Mata Tai amfani da mahaifinta Amma take wata zuciyar ta kwabeta da hakan Dan zargin da takeyi akwai makarkashiya tsakanin mahaifinta da gimbiya rumana saboda yadda tunaninta yake Bata dikda Bata Gama gasgata hakan ba hasashe takeyi tare da lalube cikin duhu....runtse idanuwanta tayi tamkar Mai bacci,Amma a zahiri zuciyarta tana can wata duniyar ta daban,ji takeyi tamkar ta bude idonta taga gari ya waye Dan ta samu babah kande Akan wanan maganar.... ********* Tun sassafe ummaty ta tashi saboda rashin samun isasshem bacci da batayi ba Daren jiya,da bacci ya sure ta take farkawa saboda mugayen mafarkai da takeyi da gimbiya rumana hankalinta ba karamin tashi yayi da hakan ba yasa ta Mike cikin Daren tayi sallolin nafila tana kaiwa Allah kukanta akan samun nasara da rinjaye Akan gimbiya rumana tana zaune Akan sallaya har akai sallahr asuba Dan hakan batasamu bacci ba yasa ta tashi idanuwanta sun kumbura ga ciwon Kai da take fama dashi sosai... Ayyukanta na gida tayisu a gaggauce wanke wanke da shara hade da gyaran daki dama ta Dora ruwanta akan murhu kafin ta Gama Dan haka tana Gama aikinta ta surka ruwanta ta dauki bokiti tayi bayin wanka .... ********* Mai martaba ne zaune a fadarsa zagaye dashi waziri ne,sarkin dawaki da sarkin aska yau harda maga takaddar fada dukkansu sun hallara saboda Kiran gaggawa da Mai martaba yayi .... Gyaran murya Mai martaba yayi sanan ya fara maganar dalilin tarasu a wanan lokaci...komi ya kwashe dangane da maganar ciwon zainul da Kuma shawarar da halima ta kawo na kaisa a nema Masa magani shine yake neman shawararsu....take waziri ya amshi maganar kafin kowa yace wani Abu yace cike da zumudi "alhamdulillahi ranka ya Dade wanan shawara tayi ya kamata gaskiya a duba lamarin yaron Nan Dan sarki jikan sarki a cikin wanan Hali na rashin lafiya Wanda ya Dace tun tuni ayi wani Abu akai ai ni harga Allah naji dadin wanan shawara" Sarkin aska ma cikin tsananin murna da farin ciki yayi naam da maganar da Mai martaba ya kawo Banda sarkin dawaki Wanda yayi sumar zaune tunda Mai martaba ya rattabo wanan zancen hanakalimsa yayi kololuwar tashi Dan yasan Babu tantama wanan makircin na gimbiya rumana ne da halima su suka hadashi don suga bayan zainul,baisan lokacin da zufa ke keto Masa ta ko Ina a jikinsa ba har ya manta a inda yake zaune Saida ya tsinkayo muryar Mai martaba yanayi Masa magana "sarkin dawaki menene shawararka Akam wanan lamarin?"ya jeho Masa tambaya idanuwansa akansa... ******** Idanuwanta a rufe ta Fado cikin gidan kamar wadda aka korota sai waige waige takeyi kamar Mara gaskiya burinta be wuce su hadu da baabah kande ba Dan haka Bata ma Yi hanyar sashin gimbiya bilkisu ba sai tabi ta wata karamar hanyar da zata sadaka da bayan kitchen da inda bayi na gidan suke taruwa da kuyangi,tasan zata iya samunta a wajen saidai Bata so kuyangin gidan su fahimci akwai wata alaka tsakaninta da baabah kande Dan gudun gulma....saita makale jikin katamga tana leke ko zata hangota,....ta bayanta aka dafa kafadarta Wanda yasata sumar tsaye batare da ta waigo ba,...gabanta ya tsananta faduwa Amma hakan be hanata jarumtar juyowa a hankali taga waye ya dafa kafadarta ya ganta a makale a wanan wajen ba,ganin babah kande yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya hade da dafe kirji tana sauke numfashi a hankali...... *WANAN LITTAFIN NA KUDINE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *HASKE WRITERS* *ASSO💡* *SLIMZY😍* [1/23, 11:11 AM] 😍SLIMZY😍: 24 Shiru kowa yayi Yana sauraron shawarar da sarkin dawaki zai bada wadda dukkansu sunsan cewar dik abinda yace dashi Mai martaba ke amfani,Dan ko waziri Yana matsayin waziri ne Amma Mai martaba baya amfani da maganarsa kamar yadda yake amfani da ta sarkin dawaki ballantana wani galadima Wanda tuni sarki yayi fatali da lamarinsa... Gyaran murya sarkin dawaki yayi tare da tattaro dik wata jarumta tasa yace "a bisa shawarar da kowa ya bada da wadda sarki ya kawo wadda gimbiya halima ta bada to a gaskiya nidai tawa Tasha bamban da ta kowa"dukkansu sukai saurin dagowa suna Bim sarkin dawaki da kallon mamaki da al'ajabi shi kuwa Mai martaba maida hankalinsa yayi sosai Yana gyada Kansa hade da cewa "umhmm sarkin dawaki muna sauraronka meye shawarar taka?" "A bisa alamu da suka Nuna na jikin wanan yaro zainul abideen alamu sun Nuna Yana samun sauki sosai magungunan da aka canjo Masa ake basa na asibiti sun karbesa Kuma ana samun cigaba sosai a jikin nasa,yaron yayi lafiya sosai ya murmure tamkar ba shi ba,abinda ya rage Masa be wuci samun kafarsa ba Dan yadda na lura har magana yanayi sosai Dan hakan nake ganin idan aka kaishi wajen masu maganin Nan ba lallai bane maganin ya karbi jikin nasa a bisa dalili ko sanadim hakan sai ya kawo rikicewar jikin nasa ni a ganina a Kara Masa lokaci zuwa ya gama Shan magungunansa na asibiti mugani ranka ya Dade"...sosai Mai martaba ya gamsu da bayanin da sarkin dawaki ya bashi Dan haka ya gyada Kansa ya juyo ga sashen da waziri ke zaune ya kasa kunne yaji me sarki zaice..."a bisa kwakkwarar hujja da sarkin dawaki ya kawo Kuma shawarar tasa Mai kyau ce inaga zamuyi amfani da shawarar tasa mugani zuwa Nan da wata uku"... A tare suka hada Baki "Allah ya Kara mishi lafiya ranka ya Dade"gyada Kai kawai Mai martaba keyi batare da ya amsa ba daga waziri har sarkin aska rasa bakin magana sukayi kowa da abinda ke cikin zuciyarsa har Allah Allah sukeyi su fita a tare a fadar su zanta,kasa hakuri waziri yayi ya dubi sarkin aska bayan sunfito suka tsaya can nesa da fadar damuwa ce dauke da fuskarsa yace "sarkin aska Anya wanan mutumin Babu wani Abu da yake shukawa a wanan masarautar kuwa?wanan Abu akwai mamaki tsantsa da al'ajabi...dubafa kagani ko akan rashin lafiyar yaron Nan zainul shekara da shekaru ace ana Abu daya sarkin dawaki shi ke dakatar da Mai martaba akam dik wata shawarar arziki da zaa bada sai ya kawo cikas a ciki?Anya wanan tafiyar Babu wata kulalliya da manakisa kuwa?" "Hmmm waziri kenan ni ai abun ne ya isheni kaga na kasa ko kwakkwaran motsi har ya Gama rattabo iyayinsa nasan Mai martaba bayansa zaibi shiyasa ban tsaya dogon bayani ba nace shawarar tayi Dan nasan ko munce wani Abu bazai amfani dashi ba sai abinda sarkin dawaki yace gara karma in Bata bakina" Cikin tsananin bacin Rai waziri Yama rasa abinda zaice cewa kawai yayi "Allah ya kyauta toh"... "Ameeen "yace kawai ya juya abinda cike da bacin rai.... ******** "Baabah kande wallahi harga Allah kinbani tsoro bakiji yadda zuciyata ke harbawa ba"ta turo Baki,....dariya sosai babah kande tayi "kagamum ja'irar yarinya sai kace Kinga dodo ko wata aljanah zakice na Baki tsoro?" "Umm babah kande ni dik ba wanan ba kinsan yadda na Shiga tsananin damuwa daga jiya zuwa yau?"hmmm Allah ko baccin kirki banyi ba tunani kawai nakeyi akan abinda zai biyo baya ba Dan gimbiya inhar hakan ta kasance to tabbas ta mamayeni" "Ki kwantar da hankalinki ummaty inaji a jikina Babu abinda zaisamu zainul abideen alfarmar annabi da alkurani domin Allah zai kareshi tunda bashida hakkinsu ko kadan Dan haka kibi komi a hankali Banda garaje sanan babbar shawarar da zam Baki shine kiyi taka tsantsan Akan komi zakiyi karki kuskura ki hada Kai da kowa wajen wanan tafiyar karkice Zaki nemi mataimaki bayan Allah domin zaa iya Gina Miki rijiya ki fada....Kinga gimbiya rumana?macece shedaniya ga wayau zata iya amfani da wata damar Dan sanin sirrinki da asirin ki gabaki daya bazaki San yadda zatasamu komiba saidai ki wayi gari cikin masifa baa fata Dan haka ki iya takunki ummaty" Sosai jikin ummaty yayi sanyi da kalaman baba kande,iska Mai zafin gaske ta hurar daga bakinta sanan tace cikin sanyin murya "baabah kande insha allahu Zanyi yadda kikace Kuma da izinin Allah fatana be wuce gimbiya ta wayi gari zainul ya taka da kafafuwansa ba insha allahu yanzun Ina cikin tsananin damuwa damgane da abin Nan data bullo dashi"ta dubi babah kande tamkar zatayi kuka, Tausayinta ne ya lullube babah kande "ki kwantar da hankalinki nace Miki akwai wani shiri Dana shirya a zuciyata matukar hakan ya kasance ,balle Ina fatan Allah ya kawo sanadim da zaa fasa wanan shiri nasu... ******* Masifa sosai gimbiya rumana ke zazzagawa hannunta makale da waya "halima kinji abinda Mai martaba yace kuwa?ya Bata mun shiri ya Gama Dani wallahi " Daga can bangaren halima tace cike da Isa "Mai yace ne ummah dik kikabi kika tashi hankalinki haka?" "Cewa yayi ya yanke shawarar bazaakai zainul abideen wajen Mai magani ba tunda kwana biyu ya samu lafiya da alamu maganin asibiti ne ya karbeshi"tana Gama maganar ta Danna speaker ta ajiye wayar gefen gado tana huci,.. Shiru halima tayi sanan tayi gyaran murya "Niko idan haka ne wanan dik ba abin tashin hankali bane ummah tunda already munada hanyoyi da zaa cutar Mana dashi cikin ruwan sanyi ummah,yanzun ne ma ya kamata ki kwantar da hankalinki tunda ita kanta yarinyar da muke amfani da ita tafara bijirewa?" Tsaki gimbiya rumana tayi cike da takaici "bijirewa kamar yaaya?" "Kai ummah ki kwantar da hankalinki Mana?bijirewa tunda ta soma gajiya da jinyar tashi tunda da Kanki kika bani labarin yadda kukayi da ita ranan to Kinga idan hakan ne me zaisa ki damu?wallahi nasan yarinyar Nan ko kasheshi kikace tayi Nan gaba kadan zatayi tunda tafara sauya Masa" Shiruu gimbiya rumana tayi Tana sauraron Amon sautin muryar halima wadda ke magana cikin natsuwa cike da hikima da kwabtarwa da mahaifiyar tata hankali Dan haka sai gimbiya ta danji sanyi a zuciyarta dikda yadda zuciyarta ke tafasa hankan be hanata samun sassauci ba Jin kalaman da halima keyi Dan haka sai ta cije lebenta tace "haka yake halima Dan ni kaina nayi mamaki sosai da yarinyar ta canja lokaci daya ko kunyar idona bataji ba take fadamin ta gaji da jinyar zainul wallahi da wani ya fadamin bazan taba yarda ba,Amma Babu damuwa idan sunsan wata Basu San wata ba zanja ummaty sosai a jikina muyi tafiyar Nan tare,idan Naga ta saki jiki ta bada hadin Kai to tabbas zan bankade sirrika tsaf infada Mata nasan amincewa zatayi zan iya ce Mata ma zainul ba Dan Mai martaba bane a waje akai cikinsa aka laka Masa Dan haka ta taimakeni ta Tai Maki me martaba Kuma tsaf zata yarda Kinga ba zainul abideen kadainba hatta uwarsa idan nace ta kasheta kasheta zatayi"dariya suka Sanya a waya a tare cike da nishadi lokaci daya gimbiya rumana ta nemi bakin cikin da take ciki ta rasa Dan haka ta hadiyi mugun miyau tace "Bari ma kigani yanzun zanjen sashen nasu ince najeyi musu Hira Dan yarinyar ta Kara sakin jiki' "Shiyasa nake sonki ummah"...murmushin Jin Dadi gimbiya tayi sukai sallama ta ajiye wayar... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS* *DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* ********* Yau da kanta ta kunna Masa karatun alkurani wajen awa daya Yana saurare sanan ta cire Masa gudun kar wani ya gani Kuma da kanta ta tofesa da adduoi sosai sanan ta gyara Masa jikinsa ta shimfidar dashi ,dik abinda takeyi Yana bin ta da wani irin kallo Mai tattare da shauki da so hade da tsananin kauna ...kujerarta ta janyo ta jata can nesa dashi tana Shirin Zama ya bude Baki a hankali yace "ummaty ya kika zauna nesa Dani?ki dawo kusa Dani in rinka kallonki sosai ko zanji Dadi kinji?" Gabanta ne ya Fadi Dan ita tasan dalilinta na yin hakan Dan haka sai ta kakalo murmushi "nikam nafiso in zauna Dan nesa da Kai sosai Dan nafi hango asalin kyawun yayan nawa Kuma bana gajiya da kallonka"murmushi kawai yayi zaice wani Abu aka turo kofar dakin dukkansu sukabi kofar da kallo da sallamarta ta shigo fuskanan dauke da faraa "ah ah yayadai autan ummah jikin ne?"..cike da shagwaba yace "ba jikin bane ummah ba ummaty bace yanzun ta daina Zama kusa Dani sai nesa nesa"yace Yana bin ummaty da kallo cike da shagwaba, "Ah ah ke Kuma ummaty haka akeyi sai kibar Dan ummah shikadai ki koma gefe"cewar gimbiya tana kallon ummaty, Cike da dabara ummaty ta dubi zainul taga Baya kallonta sai ta tabe Baki hade da zabga Masa harara Mai cike da tsana da takaici sanan ta dubi gimbiya rumana tana yak'e sai ta sunkuyar da kanta 'wallahi ba gudunsa nakeyi ba ummah shine din ya cika rigima ki kyalesa kawai rigimarsa ce"...jinjina Kai gimbiya rumana keyi zuciyarta fal farin ciki tamkar ta taka rawa ganin irin abinda ummaty keyi Masa tabbas hakan ya Nuna Mata zahiri yarinyar kinsa takeyi yanzun,Dan haka sai ta soma fadam karya "haba ummaty banason haka adaina kyale Dan ummah shi kadai ana komawa gefe,Kinga fa ba lafiya gareshi ba," Turo Baki ummaty tayi hade da tabe bakin tana kunkunin karya ciki ciki ganin idonsa baya kanta....sai tayi murmushi "zaa gyara ranki ya Dade insha allahu" "Kular da baiwarta ta shigo rike da ita ta nunawa ummaty da yatsa "ga farfesun kayan ciki Nan da nasa akayi mishi yaji kayan yaji Kuma ya dahu sosai yadda zai iyaci ba tare da yasha wahala ba kisa a plate idan ya huce ki bashi Bari inje zamu fita da yarana fiyya da afeee zamuje siyayyar makaranta su afee zasu koma Monday zata Shiga SS1 to ta tubure Wai bazata da driver da bayi ba da ummanta zata kinsan Yar rigima ce" Dariya ummaty kawai tayi ta sunkuyar da Kai har gimbiya ta Gama Yar hirarta ta fice zuciyarta fari tasssss Fatarta keda wuya ummaty ta sunkuto kujerarta ta dawo kusa da zainul abideen,Yana ganin hakan ya runtse a idanuwansa hade da daura fuskarsa shi a Nan Dole yayi fushi....murmushi tayi Masa cike da tausayinsa zuciyarta ta karaya sosai ya Bata tausayi Dan haka Bata tsaya komiba ta ruko hannunsa gammm ya Shiga kici kicin kwacewa,Amma ya kasa saboda rashin karfin nasa Dan haka sai kawai yayi shiru Yana Jin yadda take murza Yan yatsunsa yanajin wani Abu nayi Masa yawo a cikin jikinsa...."ya zainul"ta Kira sunansa cikin wata irin siga da murya Mai zakin gaske Wanda yasashi daskarewa a kwancen da yake,ganin baiyi wani kwakkwaran motsi ba yasa ta cigaba da magana "afuwan ya zainul kaji?kayi hakuri nisantar ka da nayi kaji?nayi laifi sosai Amma bazan sake ba dikda inada kwàkkwaran dalilina na yin hakan"ta karasa maganar tamkar zatayi kuka...shiru yayi bece Mata komiba,har ta cire Rai da zaice wani Abu saita tsinkayi muryarsa "menene dalilinki nayin hakan bayan ba haka kika Saba ba?" Tambayar da yayi Mata jiki a sanyaye yasa jikinta karayin sanyi idanuwanta suka ciko da hawaye Amma ta danne dakyar ta bude Baki Tai magana "kayi hakuri ya zainul bazan sake ba,dalilina na yin hakan shine idan ka lura mafi yawancin daidai wanan lokacin ammiey da ummah sukan shigo su kawo maka ziyara watarana ma harda Mai martaba,to a gaskiya kusan sau uku kenan suna tarar damu a yanayin da yake sani nakejin kunya matuka shiyasa kaga daidai wanan lokacin nakan jamye har sai sun shigo sun tafi Dan inajin tsananin kunyarsu sosai kada ace banida kunya"ta karashe maganar a shagwabe... murmushi yayi Wanda har Saida fararen hakoransa suka bayyyana sai ya jinjina Kansa sosai "naji sarkin kunya,Kuma na hakura da na dauka wani Abu ne har zuciyata ta soma yimun waswasi"ya kafeta da idanuwansa,da sauri ta sadda kanta kasa tana murmushi ...wani sanyi na ratsata samun dabara da tayi cikin sauki.... Yau ma Koda ta fito zata tafi gida Saida ta duba baabah kande inda suke Zama Bata ganta ba Dan haka kawai saita wuce gida abinta... ******* Zaune suke bayan sallahr isha'i sungama cin abinci suna zaune ne kan tabarma Babu wuta suna Dan Shan iska innarta da baban nata suna Hira sama sama,itama kuwa nata tunanin takeyi ta kulla wancam ta kwance wancen hardai dabara ta Fado Mata tace "baabah Dan Allah inason kayi mun wani Abu" "Me kikeso ummaty fadamun"da sauri ya amsa Mata Yana mai maida hankali akanta sosai, Wasa da yatsanta ta shigayi batare da tace komiba "kiyi magana Mana ummaty kinyi shiru me kikeso?" "Waya nakeso ka siyamun babah Dan Allah" Sai ya daura fuskarsa wanan karon "ah ah ummaty ya mukai dake akan maganar waya?Ina nace bazan sai Miki waya ba sai kinyi aure?Dan haka kima kauda maganar siyan wayar Nan yanzun ki kawo wata bukatar banson Jin wanan Kar Kuma kice zakimun musu"badan ranta yaso ba ta Kama bakinta Tai shiru Amma kasan zuciyarta ji takeyi tamkar ta fashe da kuka.... Maida kanta tayi gefe zuciyarta nayi Mata suya...wani bangare na zuciyarta ke fada Mata "me zai Hana ki fadawa gimbiya ta siya Miki wayar?ai idan ita ta siya mahaifinki bazaija da hukuncinta ba Kinga kin jefi tsuntsu biyu da dutse daya"...murmushin jim dadi tayi na wanan shawarar dan haka ta kwantar da kanta jikin bango ta jingina tana ayyanawa zuciyarta abubuwa kala kala.....minti minti takan sauke murmushi Wanda ita kadai tasan dalilin murmushin... *Wasa ya soma fa Bari* *muga waye da nasara....*🤥🤥😁 *Team gimbiya rumana🏃🏻‍♀* *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *HASKE WRITERS* *ASSO💡* *SLIMZY😍* [1/23, 11:11 AM] 😍SLIMZY😍: 25 ******* Da shirinta tsaf tazo na yadda zata tunkari gimbiya rumana ta juya mata tunani batare da wata matsala ba Dan haka yau ko sashen zainul abideen Bata soma zuwa ba sashen gimbiya rumana ta nufa direct kanta tsaye batare da wata shakkaba... Zaune take Akan babbar daddumar dake shimfide a tsakiyar patlornta tana breakfast kayan ciye ciye ne na alfarma lafiyayyen abinci ne a gabanta ta tsakuri wanan ta tsakuri wancan, karfe Sha daya da minti goma ne na safe ummaty tayi sallama cikin babban patlorn ,da sauri gimbiya ta dago manyan idanuwanta ta saukesu akanta suka hada Ido Wanda take ummaty taji faduwar gaba saboda kwarjini da tayi mata ta sunkuyar da kanta tana takowa a hankali,ita kuwa gimbiya rumana ganin ummaty yasata sauke faraa s fuskarta da dariyarta take fadin "ah ah kags d'iyata ummaty yau da wuri akazo gaisheni dama zan aika nemanki sai gaki kinzo" Karasa Zama ummaty tayi Tana Dan yake a fuskarta "barka da tashi ranki ya Dade" "Barkanki dai ummaty ya innar Taki?da babanki suna dai lafiya koh?" "Lafiyarsu kalau "tace hade da sadda kanta kasa tana Dan murmushi... "Ummaty matso ki karya nasan kila bakici wani abuba kika fito saboda sauri kizo wajen rigimammen Nan Dan ummah" Dan Bata fuska tayi ummaty hade da fadin "wallahi nskoshi ummah," Kallonta sosai gimbiya rumana keyi tana nazarin fuskarta sanan tace"ummaty yadai naga kin Bata fuskarki hakan?kodai akwai wata damuwa ce", Kara natsuwa ummaty tayi Tai shiru tamkar zata fashe da kuka ta soma magana cike da ladabi"ranki ya Dade kinsan yau da gobe sai Allah Kuma batabar komiba "...,gimbiya rumana ta gyada kanta "haka ne ummaty menene Ina sauraronki"ta maida hankali sosai kan ummaty, "Kawai dai gajiya ce nafara gajiya da jinyar Nan ranki yadade inaso Nima in natsu a gidanmu Kinga kullum Kara girma nakeyi Kuma iyayena ko basuyi mun magana ba bazasu so inzauna hakan batare da nasamu miji nayi aureba,ranki ya Dade bazan boye Miki ba zainul danki ne bansan ya zakijiba Amma nagaji da jinyar Nan dik ya siremun wani irin haushinsa nakeji"ta karasa maganar tana zubar da hawaye ta Dan dago idanuwanta jike da hawaye ta dubi gimbiya ta sadda kanta kasa tana sharar hawaye...sosai ta hango tsantsar yadda a fuskar gimbiya rumana...ga yadda ta maida hankalinta sosai akanta da yadda tayi da fuskarta tana sauraronta...a zahiri ummaty sharbar kuka takeyi Amma kasan zuciyarta wani irin farin ciki ne kwance saboda burinta be wuce gimbiya rumana ta gama yarda da itaba yadda zata gudanar da aikinta cikin sauki.... Ajiyar zuciya gimbiya rumana ta sauke Dadi cike da cikinta Amma sai ta danne gudun kada ummaty ta fahimci wani Abu "haba ummaty kiyi hakuri Mana har musamu yasamu sauki?Kinga yanzun akan Shan maganinsa yake Kuma kece nasamu kike taimaka Masa har ya warke Dan Allah ki Kara hakuri kinji ummaty nasan jinya Babu Dadi kiyi hakuri kinji" Share hawayenta ummaty tayi "ranki ya Dade kullum bada maganin Nan nakeyi Amma Babu sauki ranki ya Dade har na soma gajiya wallahi wasu abubuwan inayinsu ne donke Dan iyayensa musamman ke da kikemun alheri kikasan inayi"... Dadi ne sosai ya Kama gimbiya rumana "yauwa ummaty ko kefa to kiyi hakuri ki cigaba dayi ko Dan ni din kinji?kinsan magani ba daga farawa ake warkewa ba sai an daure,Kinga ga wani maganin ma ankawo dama nace idan kinzo zan aika kiranki kizo sai kibashi" "Ranki ya Dade naso ace inada wayar sadarwa idan dik abinda kikeso ki kirani saiki fadamun da ki rinka aikawa kirana tunda kince bakyaso kowa yasan kina Taimakonsa a fili sai bayan ya warke ansamu biyan bukata koh?Kinga idan kina aikawa kirana may be a fahimci wani Abu Amma shawara ce" Kasa boye farin cikinta gimbiya tayi jikinta har rawa yakeyi "daama inataso intambayeki ko kinada waya Ashe Baki da ita budurwa kamarki Babu waya?be yuwuwa tunda afnan Ma auta tanada ita saike budurwa dakee?,zan aika zuwa yamma kafin kitafi a kawo Miki waya"... Zaro idanuwa ummaty tayi "ranki ya Dade babana yace sainayi aure fada zaimun ki rufamin asiri" Murmushin kasaita gimbiya rumana tayi "inajinki kamar Yar Dana Haifa Dan haka kome Zanyi Miki kyautatawa ce kema kinamun Kuma inajin Dadi... kibarni da sarkin dawaki nasan yadda zan bullo Masa"...tsoron fadan mahaifinta takeyi Amma saita danne tana addua cikin zuciyarta Allah yasa kada yace ita tasa aka sai Mata....ita kuwa gimbiya rumana kissima yadda zata bullowa sarkin dawaki takeyi yadda zata furgitashi batare da yayi wani tunani ba... Janyo gorar maganin ummaty tayi ta Dan yatsina fuska "ranki ya Dade ni wallahi dama kinzo munje tare Kinga muna Hira sai inbashi maganin a matsayin ruwa yadda zaki Dan zauna zanji Dadi"..satar kallon gimbiya tayi sai taga tayi murmushi "kema kin iya rigima ummaty to ai idan mukaje tare zai fahimci wani Abu" Ummaty tana sane tace hakan Dan gimbiya rumana ta Kara yarda da amincewa da ita,ta Kuma ga alamar hakan yadda gimbiya dik ta rude jikinta sai rawa yakeyi fuskar Nan dauke da farin ciki Wanda ta kasa boyewa...turo Baki ummaty tayi hade da mikewa 'bari inje ummah nasan Yana can Yana nemana"..ta danyi tsaki ta dauki gorar magani tasa a hijabi "ummah sai anjima" ",Toh ummaty kibiyo idan Zaki tafi gida"... Ummaty na fita gimbiya rumana ta janyo wayarta ta Kira waya da alamar shago takira tana tambayarsu wayar da suke da ita a kasa zata Aiko driver da kudi ya karba...tana gama wayar number sarkin dawaki tayi dialing... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* ******* Bata karasa fitowa sashen gimbiya Ba sukai kicibis a hanya da baabah kande batace Mata komiba hannunta ta Kama ta jata sukai wata hanya Dan nesa kadan shiru Babu kowa sai dawaki dake kuka a wajen, Gora ta Ciro a hannunta daga hijjabinta ta dubi ummaty tana waige waige "kalli gorar Nan",da sauri ummaty ta kalla ta xaro Ido hade da Dan furgita ta Ciro ta cikin nata hijabin taga Babu banbanci a kidime tace "babah kande wanan gorar fa?iri daya ce data hannuna" Gyada mata Kai babah kande tayi Tana murmushi "ki kwantar da hankalinki nasamota ne a dakin gimbiya saboda mu rinka musayar magani Koda kinje Zaki iya Ciro wanan ta hannuna ki bashi memakom waccan,nayi ma wanan sheda yadda bazaki makuwa ba wanan ruwan na maganine adduoi ne sosai na tsari da karya sihiri shi Zaki bashi memakon na hannunki" Sosai ummaty ta rude "menene faidar samun gorar iri daya?" "Ummaty ke yarinya ce bakisan gimbiya rumana ba tanada masifar wayau dikda Naga alamun ta yarda dake Amma hakan bazai Hana Tasa ai mata gadinki ba Kinga koda Tasaka a sa Miki Ido zaaga ai gorar ce kike bashi maganin Kinga bazaa ganeba ,dikda kema kinada basira da hikima Amma zata iya Miki wayau Dan ta wuce dik inda kike zato,kibar ganin daga ke Sai ita kukeyi zata iya sa Miki Ido ta ko wani siga", Ajiyar zuciya ummaty ta sauke ",lallai nagodewa Allah da ya hadani dake babah kande,gaskiya kinfini hikima kinfini basira dikda kin tsufa,Koda yake kin haifeni Dole ne kifini hangen nesa" ",Kema da Taki basirar da hikimarki domin samun gimbiya ta yarda da mutum take ba karamin Abu bane Dan dik inda kika bullo mata tanada wayau zatasa Miki Ido sai daga karshe ta Nuna Miki tasan komi Dan hakan kika taka tsantsan", ",Insha allahu baabah kande idan tasan wata batasan wataba yanzun haka zata saimun abinda zan yaketa dashi batare da ta Ankara ba", "Mekenan Yar Nan?" "Wayar salula babah kande,kedai zanbaki labarin yadda zaayi yanzun Bari inje Dan nasan bawan Allahn can Yana can Yana jirana, zaice wanan ta canja besan shi nakeson cetowa ba" ",To adaiyi a a hankali kizo Kuma mu tattauna akan wayar " "Insha allahu natafi sainazo"ta juya da sauri tabar baabah kande wajen tana bin ta da kallo tausayi yarinyar take Bata harga Allah shiyasa tasa mata hannu Dan anason jefata a halaka batasani ba harda ubanta...ta kada Kai kawai tabar wajen... ******* Sarkin dawaki s firgice ya nufo gidan Mai martaba Jin Kiran gimbiya na gaggawa gabaki daya a tsure take dik tunaninsa tasan shi ya warware tafiyar Kai zainul wajen Mai magani Dan haka hantar cikinsa a kade ya iso gidan.. gaba daya ya furgita da lamarin gimbiya ga babban tashin hankalinsa besan me yarsa takesonyi da waya ba da takeso a siya mata waya Rana tsaka a haka ya karasa sashen da suka Saba haduwa da gimbiya rumana.... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *HASKE WRITERS ASSO💡* *SLIMZY😍* [1/23, 11:12 AM] 😍SLIMZY😍: 26 Ko wannensu shiru yayi Yana sauraron abinda Dan uwansa zaice,musamman sarkin dawaki Wanda zuciyarsa ke harbawa tamkar ta fasa kirjinsa ta fito... gabaki daya ya zabge ya rame sosai kamar Wanda yake rashin lafiya, danasani da nadamar abubuwan da suka aikata shida gimbiya rumana kawai ya sashi wanan ramar ta Babu gaira Babu dalili... gyaran murya tayi cike da izzah da Isa irinta masu mulki ta kada kanta kadan fuskar Nan kamar Koda yaushe dauke da murmushin Nan nata Mai tsada Wanda ya kasance dabiarta ce hakan..."sarkin dawaki kaji Kira daga sama ko?daga gimbiya rumana wadda ta kasance ta hannun damanka a baya yanzun Kuma kake gudunta ko ganinta baka kaunar Yi koh?"hmmmm ta sauke lallausan murmushi "bedameni ba saboda nasamu nasara na Kuma cinmma burina ko ince Ina gab da cin ma burina Dan Ina hango nasara Nan kusa kadan tunda Yar taka itace ta kasance babbar aminiyata yanzun ta hannun damana nake juyata yadda na gadama batare da tamun gaddama ba,dikda itama a tafin hannuna take Dan yanzun dik motsinta zan Sanya idanuwana gaba da baya Dan a rinka bibiyar takunta dikda na yarda da ita Dan ita din yarinya ce mara wayau shiyasa nayi nasarar saurin juyar da hankalinta"... hannu tasa ta dauko kofin lemo dake gabanta ta Dan kurba kadan ta ajiye sanan ta nufasa tana me binsa da kallo yadda ya firgice Babu abinda yakeyi sai zufa... "Kiranka nayi inbaka umarni Akan inaso kabar ummaty da waya domin nicenan nace tafara tuntubarka da maganar waya kace bazata rikeba har saitayi aure menene dalilinka na hakan" Wani bakin ciki ne ya rufe Masa idanuwa ya Mike a haukace "saboda y'ata ce ko yarki ce?kece kika haifamun ita da zan bada umarni kizo kina tambayata kina Shirin gindaya mun sharadi?saboda son Rai da son zuciya irin naki?saboda rashin Imani da tsoron Allah ,kin isheni kin zamewa rayuwata bala'i gabaki daya kinsani a rudani to Bari kiji wanan karon baki isaba wallahi zan fito fili insanarwa da ummaty ko kedin wacece"...wata uwar tsawa ta daka mishi hade da mikewa tsaye a haukace "sarkin dawaki!!!ya isheka da yimun tsawa,ko ka manta a gaban wadda kakene?in tuna maka?ka manta a gaban gimbiya rumana kake har kake daga murya sama Akan tata?to ka Shiga taitayinka tun kafin insaka fadawa su fitar dakai can bayan gari su dauremun Kai a jikin dutse su farfasa maka jiki da bulala,su shafa maka gishiri su gana maka azaba Mai radadi"ta karashe maganar tana huci hade da nunasa da yatsa tana huci kirjinta Yana hawa Yana sauka....shiru sarkin dawaki yayi batare da yace komiba sai bugawa da zuciyarsa keyi sauri da sauri ta cigaba da magana "maganar kaje ka fadawa ummaty koni wacece ka Dade baka fada mataba sarkin dawaki ni zanfi so kasanar da ita hakan Amma idan katashi ka hada da kanka yadda zatayi danasanin zamowa daga cikin tsatsonka yadda zataji tsanarka fiye da kowa a rayuwa...Ina rokonka kada ka fasa yin wanan mugun gangancin Wanda guguwar ajali ke dibarka,a kashe abinda zan sanar dakai shine umarni ne wanan baka Isa ka ketare ba Dan haka zan siyawa ummaty waya karka kuskura kayi yunkurin karbar wayar Nan a hannunta kaji na fada maka,shashasha tashi ka fice kabani waje"... Babah kande dake makale Tana sauraron hirarsu duka Jin sarkin dawaki zai fito tayi wuff ta fada wani daki dake gefe Wanda Babu komi ciki sai abincin doki....makalewa tayi jikin bango har ya wuce besan da mutum a wajenba...sosai baabah kande ta furgita kwarai da Jin hirarsu tabbas tasan da saka hannun gimbiya wajen rashin lafiyar zainul Amma Bata taba tunanin akwai sarkin dawaki ciki ba mahaifin ummaty... baabah kande ta tsorata matuka da wanan hirar da taji wato kenan da mahaifinta ake amfani da ita wajen jefata cikin halaka ba tare da tasani ba "innalillahi wa Inna ilaihi rajiun tabdijan"tasa hannu ta goge zufar da takeyi ta gyara daurin Dan kwalinta dake Shirin faduwa...tabdijan akwai gwarama, Yaya ummaty zataji idan tasan da saka hannun mahaifinta a ciwon zainul?ya Mai martaba zaiji ranan da dik wanan kwai me wari ya fashe cewar babban me bashi shawara a fada ya dauka shine babban makiyinsa...tabbas wanan shi ake cewa makashinka Yana tare da Kai...dik na sarkin dawaki me sauki ne Akan gimbiya rumana da Mai martaba keji da ita saboda yadda take kaunar gudan jininsa zainul abideen...girgiza Kai kawai baabah kande tayi jiki Babu kwari ta fito tana Jan kafa a hankali har ta fice ta kofar baya.... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS* *DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* ********* tun bayan da ta shafa Masa ruwan adduar da baabah kande ta Bata yasha Kuma ta shasshafa Masa a jikinsa yayi bacci tana zaune s gefenta tana kissima abubuwa da dama a cikin zuciyarsa tana kallon yadda yakeyin bacci Yana fuzge fizge tamkar wani Abu na fita a jikinsa minti minti yakan sauke atishawa da karfin gaske mikewa tayi ta tsaya akansa tana tofa Masa adduoi fuskarta dauke da damuwa dik tayi bakim Kirin saboda damuwar da ta tsinci kanta ciki.... ******* Kurrrr da Ido yayi mata Yana aika Mata sakkonin soyayya ta cikin kwayar idanuwanta yayinda itama ta kafesa da Ido ta kasa kauda idanuwanta cikin nasa fuskarta dauke da murmushi Mai kayatarwa...kashe Mata Ido daya yayi Wanda da sauri tasa hannu ta rufe idanuwanta tana dariya...."yayadai my princess kika rufemin fuskarki wadda ita kadai nake kallo injini cikin wata Duniya wadda ban taba tsintar kaina cikinta ba" Mikewa tayi hannunta har yanzun rufe a fuskarta tana kokarin barin wajen yasa hannu ya riko hannunta ta Shiga kici kicin kwacewa "Kai ya zainul dik ka bani kunya wallahi"Tai maganar cike da shagwaba... "Haba wareeh idan kintafi ya kikeso inyi kawo hannunki kiji yadda zuciyata ke bugawa "yakai hannunta kirjinsa daidai zuciyarsa...Jin yadda kirjinsa ke harbawa yasata saurin bude idanuwants aikuwa take idanuwansu suka hadu wani Abu taji ya soketa a kirji tamkar kibiya tayi baya zata Fadi ya fizgota ta fada kirjinsa... Zumbur ta Mike daga kan gadonta rike da gefen kirjinta Wanda taji Yana sokawa kamar yadda taji a mafarkinta ga zufa da ta jike dashin tamkar an kwara mata ruwa,...lumshe idanuwanta tayi zuciyarta na ci gaba da bugawa ta budesu Akan agogon bangon dake manne a dakinta karfe hudu saura minti biyar na laasar...a hankali ta bude bakinta tana dafe da kirjinta "mafarki nayi?da sallar laasar da tsakiyar ranan Nan ba dare ba?"...daidai Nan hajiya kubrah ta turo kofar dakin bakinta dauke da sallama, hango Yar tata da tayi zaune yasa tun kafin ta karaso take fadin "Ashe kintashi ma,na turo a tasheki akace kinata bacci sai nace a kyaleki"shiru warisah batace komiba idonta na tsaye waje daya ta lula duniyar tunani, Tabata uwar tayi "ke lafiyanki kuwa?" "Momy mafarki nayi"Tai maganar a sanyaye... "To kindaiyi addua da kika tashi koh?sai Kuma ki Mike kiyi sallah" "Momy mafarkin ya zainul nayi"...cakkk hajiya kubura ta tsaya tana kokarin fita da , takai seconds ashirin sanan tayi murmushi ta kada Kai ta fice dakin ba tare da tacewa warisah komiba... A sanyaye tayi alwala tazo ta tada kabbarar sallah tanayi Amma hankalinta baya waje daya a daddafe ta idar da sallar ta zauna kan dadduma dik jikinta ya mutu da ta rufe idanuwanta sai zainul take gani yanayi mata irin murmushin da yakeyi mata a mafarki ga zuciyarta dake hautsunawa tamkar zata fito kirjinta..."Allah yasadai ba ciwon zuciya bane yake Shirin kamata na Yan mintuna... Turo kofar akayi da sauri ta dago Kai dikda taji kamshin turaren nasa tasan ko waye ,kyakkyawan saurayi ne ajin farko ya shigo dakin fuskarsa Babu yabo Babu fallasa ya dubeta "ke warisah dazun na tambayeki Baki bani amsa ba" Turo Baki tadanyi "ya haris bansan mezance makaba dikda idan na fahimceka wadda kake tambayar wacece din ummaty ce me jinyar ya zainul Yar sarkin dawaki, shikenan"..murmushin gefen fuska yayi yasa hannu ya shafa gashin kasa "well kince yau zamu koma ingaida Mai martaba ya kamata muje koh?Kuma Inga jikin na zainul abideen,Allah sarki aminina tun muna yara Allah ya bashi lafiya" Ameen tace kirjinta Yana bugawa "Bari in shirya ya haris sai mu dauki zahira muje koh?"..ya gyada mata Kai ya juya Yana takunsa na takama da Isa,har ya Kai kofa ya juyo "idan munje zan ganta?" Tadan zaro idanuwa"ita wacee?" Sai ya basar "share kawai"yace ya fice ta bishi da kallo tana tabe Baki... ******* Sabuwar waya galleliya gimbiya rumana ta Kira ummaty ta bata Tai Mata godiya sosai ta fito cike da farin ciki tayi wajen aminiyar tata babah kande "babah kande Kinga wayar Nan kafin inje gida zanje wajen likitan waya na unguwar mu ya koyamin ita ya saitamun recording cikinta sanan ya nunamin abubuwa sosai" Gyada Mata Kai babah kande tayi Tana murmushi "hakan nada kyau ummaty yanzun ayi haramar tafiya gida dare zai Miki a hanya gashi kince Zaki biya wani waje" "Sainaje wajen ya zainul munyi sallama,yanzun zantafi baabah kada ki manta kince idan nazo gobe Zaki sanar Dani tarihin gidan Nan da mu kanmu yadda muka taso" "Insha allahu ummaty Allah dai ya kaimu goben da Rai da lafiya" "Ameen tace"ta Mike ta tafi... ******** Jin alamar da mutane dakin yasata faduwar gaba dikda batasan kosu waye ciki ba,ta Dade a kofar dakin sanan ta tura kofar hade da sallama a bakinta...binsu takeyi daya bayan daya sanan ta sadda kanta kasa ta gaida ya haris Wanda besan tanayi ba ya shagala wajen kallonta...Shima Kuma zainul idonsa kirrr Akan su duka Yana binsu da wani irin kallo..... Warisah kuwa tabe Baki tayi ta kauda kanta gefe saboda bakin ciki...... *WANAN LITTAFIN NA KUDINE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *HASKE WRITERS ASSO💡* *SLIMZY😍* [1/23, 11:12 AM] 😍SLIMZY😍: 27 Kallon da haris ke bin ta dashi yasa dik ta tsargu sanan babban abinda yake Bata mamaki be wuce warisah da ta gani zaune kusa da ya zainul ba hannunta rike da cup din da yake Shan ruwa dashi da alama Shan ruwan tayi,dago idanuwanta tayi a Karo na farko ta saci kallon gefen da warisah ke zaune taga yadda take Yi tamkar ba itaba sanan ta juyar da dubanta ga gefenta kararff suka hada dashi a Karo na uku dakyar tayi karfi da jikinta ta Mike tsaye cikin sassanyar muryarta ta dubi zainul abideen sukai Ido hudu ta sakar Masa wani lallausan murmushi sai kawai ya cije lebensa Yana kallonta "ya zainul zan tafi sai Allah ya kaimu goben"ta tsaresa da Ido... Wani irin Abu ne yaji yanayi masa yawo a cikin jikinsa da wata irin kasala da ta saukar Masa dakyar ya sauke ajiyar zuciya yace "to ummaty sai Allah ya kaimu kifa zo da wuri kinji" Gyada Masa Kai tayi Tana murmushi "angama ranka ya Dade insha allahu"..Shima gyada mata Kai yayi Yana murmushi sai kawai ta dauki Jakarta tayi hanyar fita,har ta Kai kofa ya haris yayi saurin fadin "mu baxaayi Mana sallama ba "cakk ta tsaya gabanta na tsananin faduwa Wanda batasan dalilin hakan ba,sai kawai ta juyo a hankali ta sakar Masa murmushi "to sai anjimanku a gaida momy"...lumshe idanuwansa yayi batare da yace komiba tasa Kai ta fita... Wani tsaki warisah ta sauke ta kauda kanta gefe zuciyarta nayi Mata tsananin zafi na takaicin ummaty da wutar tsanarta dake Kara ruruwa cikin zuciyarta.. "Abokina Amma jikin Nan naka yayi kyau gaskiya nayi matukar farin cikin ganinka a wanan yanayin Allah ya Nuna mana ks taka da kafafuwanka"yasa hannu ya dauki banana tana barewa "Insha allahu zan samu sauki haris ,inajin dadin jikina sosai Ina matukar alfahari da wanan yarinyar da kake gani tabbas banida kamarta a fadin duniyar Nan"...wani kallo warisah ta wurgo Masa cike da haushin abinda yace...Wai wanan kucakar yake cewa bashida kamarta ?mtswww wata zuciyar tace toke warisah idan hakan ne menene naki ciki?kodai sonsa kikeyi..take ta Shiga girgiza Kai a zuciyarta tana fadin ah ah ah Allah ya kyauta,.wani kallo haris yayi Mata"ke meye hakan kamar wata Mara hankali kina zancen zuci kina kada Kai tamkar wata sabon kamu" .zumburo Baki tayi ta Mike fuuuuu tana tafe tana kunkuni ta fice dakin ta bugo kofar dakin...shiko zainul Allah Allah yakeyi ta fita Dama Dan ganinta yakeyi tamkar wata bakar macijiya gefensa wani irin tsanarta ce ke yawo cikin jinin jikinsa,Abu daya ya hanasa korarta ganin tare take da yayanta da badan hakan ba dababu abinda zaisa ya barta Tai second cikin dakinsa...kauda tunaninta tayiy hade da Dan tsaki ya juyo ga haris Wanda ke famar daddana waya da alama chat ya Shiga yanayi.... ******* Har karfe bakwai na magriba tana gurin Hassan Mai shago Yana famar tattaba wayar ya Shiga Nan ya fita can dik wani Abu da take bukata ya saita Mata a cikin wayar sanan cikin kankanin lokaci ya koya Mata dik wani Abu da take bukata,sosai take murna tare da Jin wani nishadi a cikin zuciyarta dikda yadda take tsoron zuwa gida da wayar ga dare da tayi Dan haka Yana gamawa sauri sauri ta sallameshi ta karbi wayar ta Miki hanyar gidansu..... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* "Assalamualaikum"...Tai sallamar muryarta na rawa ...."ke ummaty dakata Nan,daga gidan ubanwa kike a daidai wanan lokacin ?"ya daka mata tsawa wadda ta haifar mata da faduwar gaba lokaci daya hantar cikinta ta kada,ji takeyi tamkar ta saki fitsari s inda take a tsaye,kafafuwanta ne suka soma rawa bakinta na rawa muryarta na sarkewa ta dubesa a tsorace "baabah...daga gidan Mai martaba nake wajen ya zainul"Tai mgnr a tsorace... "Daidai wanan lokacin ne zakice daga gidan Mai martaba kike?ummaty me kikeso ki Zama?wallahi ki Shiga hankalinki idan ba haka ba zan matukar Saba Miki ,kalli lokaci karfe bakwai da minti goma har anyi magriba Baki shigo ba kincemun daga gidan Mai martaba kike koh?to ki kama Kanki tun kafin in hanaki zuwa gidan Mai martaba gabaki daya" "Kayi hakuri baba insha allahu baxaa Kuma ba"Tai maganar tana sunkuyar da kanta kasa jikinta sai rawa yakeyi...wani irin kallo yake bin ta dashi daga Sama har kasa idanuwansa suka sauka Akan ledar wayar dake hannunta.... gabansa ne ya Fadi ya dago Kai ya dubeta da kyau sanan yace "kwalin menene a hannunki?"ya jefa Mata wanan tambayar,. A rikice ta dubesa bakinta Yana rawa "umm...umm...babah dama ummah rumana ta siyamun waya dazun tare da afnan"Tai maganar a tsorace.. Girgiza Kansa kawai yayi batare da yace wani Abu ba yasa Kai ya fice... Kada Kai kawai innah tayi fuskarta Babu yabo Babu fallasa ts kalli ummaty dake tsaye kamar an dasata sanan ta kauda Kai cike da bacin Rai tamkar bazata ce wani Abu ba ,ita kanta ummaty Tasha jinin jikinta yadda innar tata tayi mata "ummaty me kikeso ki Zama ne?gabaki daya lokaci kankani kinaso ki canja halayenki ki rinka betawa mahaifinki Rai ko ummaty?kina ganin kin kyauta kenan?haba ummaty kin bani mamaki gaskiya banji Dadi ba karki kuskura kice Zaki sauya idan kika sauya bazakiji dadin mahaifinki ba da ni kaina nafada Miki",tana Gama maganar ta juya ta dauki Dan karamin bokiti da muciya a ciki ta nufi kitchen,..tsaye take hawaye na gudu a idanuwanta zuciyarta ta karaya da kalaman innarta,gabaki daya jikinta yayi sanyi har batasan lokacinda ta Soma kuka a tsaye ba tasa hannu ta share hawayenta sansn taja kafarta ta shige dakinta tana sharar hawaye.... ******** Dik juyi idan yayi cikin dakinsa muryarta ce takeyi Masa yawo a cikin Kai Babu abinda yafi burgesa a tattare da yarinyar Wanda ya wuce murmushinta da manyan fararen idanuwanta wadanda sukeyi tamkar suna Jin bacci...dago Kansa yayi ya dubi agogon bango dake manne a dakinsa karfe takwas da Rabi dai dai ya Mike ya zauna Akan gadonsa Yana sanye da farar singlet da dogon wandonsa jeans....hannunsa ya Mika ya dauki rigarsa ya zura ya dauki wayarsa dake gefe da makullensa dake gefen gadonsa ya kwasa ya fice daga sashensa ya bullo ta kofar baya ya nufi parking space ...yasa key ya bude motar ya Shiga shirruuuu yayi bayan ya rufe kofar yana tunanin yadda zaayi yaje wajenta to idan yaje yace Mata mene?Yaya zaayi ya samu gidansu?ya furzar da isaka Mai zafi daga bakinsa yayiwa motarsa key ya fice gidan a guje batare da sanin inda ya nufa ba haka yake toki minti minti yakan ja tsaki shi kadai zuciyarsa sai Kara azslzalarsa takeyi da wutar kaunarta..... ******* Gabaki daya hankalinta yaki kwanciya tunanin yadda zaayi ta fito ta sanarwa da ummaty kudurinta akan zainul abideen kawai takeyi Dan gabaki daya ta Gama kololuwar tunani Akan kawai ta fito ta sanarwa da yarinyar kudurinta dan wanan wahalar da takeyi shekara da shekaru ta Isa ta kasa kasheshi shi a wahale ita a wahale gara kawai tunda ummaty ta Nuna gajiyarta akan jinyar tasa gara ta sanar Mata da su kasheshi kawai ita ta huta da jinya itama ta ciwwa burinta...da wanan tunanin ta kwana tare da kosawa ummaty ta iso gidan Dan ta sanar Mata da bukatar ta... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* *HASKE WRITERS* *ASSO💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY😍* [1/23, 11:13 AM] 😍SLIMZY😍: 28 Tafe yake Yana tuki cikin kwanciyar hankali gabaki idanuwansa akan tukin da yakeyi suke a zahiri Amma hankalinsa gabaki daya ya karkata akan yarinyar gabaki daya ya rasa natsuwarsa tun ranan da ya fara sanyata cikin idanuwansa yanzun menene abunyi?zuciyarsa ke tambayarsa shin gidansu yarinyar zakaje daddaren Nan?idan kaje kace mata mene? gabansa ya Fadi sai kawai ya Kar kata kan motarsa ya canja hanya ya dauki hanyar GRA gidan anty Zahra be dau lokaci ba ya iso gidan yayi horn Mai gadi ya leko da Kansa yana kallon kotar haris ya Kara horn da karfi ya haske masa Ido da gudu ya ruga ya wangale masa gate din,ya take motar ya Shiga s guje "barka da zuwa ranka ya Dade" komi bece Masa ba ya kulle motarsa ya barsa Nan tsaye ya kada Kansa ya koma maxauninsa kan benci... Kallon tv yaran sukeyi lokacin da yayi sallama cikin patlorn a guje suka ruga suka rungumeshi suna ihun "oyoyo oyoyo uncle haris ya dawo " "Welcome back uncle haris"cewar Yar Macen ya dagata sama Yana dariya "oyoyo surayya Ashe kin gane uncle haris"...ya ruko hannunsu suka karaso patlorn saiga Zahra ta fito rike da nuaiym a hannunta "ah ah haris Ashe Kaine nakejin ihun su surayya " Shafa Kansa yayi "nine anty Zahra" Da faraar ta takaraso patlorn ta Mika Masa nuaiym tana fadin "su haris manyan gayu yau Kaine a gidana yaushe rabo?" "Kai anty ai Ina zuwa sosai kawaidai so kike kiyimun sharri"sukasa dariya tare,Kiran me aikinta tayi ta kawo Masa kayan motsa Baki da kular abinci ta dire Masa a karamin table din dake gabansa....yanaci suna Hira sama sama har ya gama... "Hmmm haris kodai daga wajen zance kake?"Tai maganar cike da tsokana... Shafa Kansa yayi "anty ni ai Banda budurwa yanzun ne dai nasamu" "Kai Dan Allah haris?kace zamusha biki alhamdulillahi Kaine namiji na farko da zaka fara aure a family dinmu gaskiya naji Dadi"Tai maganar cike da zumudi... "Kaga anty Zahra harkin fara maganar aure bayan ban gabatarwa da yarinyar Ina sonta ba yanzun haka na fito da niyyar zuwa gidan ne nafasa Dan bansan mezance Mata ba idan naje" Dariya sosai anty Zahra tayi "Kai haris dadina dakai shirme?au baka fada mata ba?Yar gidan waye to?a Ina take?" Shiru yayi Yana shafa Kansa sanan yayi murmushin gefen fuska "ummm ummaty ce yarinyar sarkin dawaki", Dafe kirji anty Zahra tayi hade da zaro Ido "ummaty haris?" Kallonta yakeyi fuskarsa Babu yabo Babu fallasa "batayi bane anty Zahra?" "Ah ah haris wallahi tayi nayi mamaki ne da kace kana son ummaty naganka Dan gayu kana son social life ita Kuma yarinyar akwai kunya da natsuwa gashi Bata fiye gayu ba,Amma naji dadin wanan maganar wallahi zainul nayi mata shaawa saboda yadda take wahala dashi Amma kaga auren zainul be kamaceta ba wallahi saboda lalurarsa kaje ka nemi soyayyarta Allah ya shige Mana gaba" Farin ciki ne ya lullube haris har fuskarsa ya kasa boyewa "anty Zahra nagode Amma su mama nakeji fa" "Karka damu Mai martaba zai tsaya maka Nima Kuma Ina tare da Kai" "Nagode anty Zahra Bari inzo inkoma dare nayi" Mikewa tayi tallabe da nuaiym tace "bazaka jira abbansu ya shigo ku gaisa ba ya kusa fa?" "Nidai ah ah kya gaisheshi zan dawo jibi insha allahu", "Ok"har wajen mota ta rakashi sukai sallama Tayo cikin gida cike da zumudin wanan labari... ******* Da karfin jiki sosai zainul ya tashi shi Kansa Yana mamakin Kansa farin cikin da yake tsintar Kansa cikin wadanan kwanakin baya misaltuwa zaune yake Akan wheel chair dinsa shi Kansa mamakin yadda akayi yake rike da cup a hannunsa batare da ya Fadi ba yakeyi da Kansa yakai bakinsa dikda hannun nasa Yana Dan rawa yasha ruwa a hankali ya dawo da hannun ya rike kallon jikinsa yakeyi fuskarsa dauke da murmushi... kafafuwansa yake Dan motsawa da yatsunsa a bakinsa ya ambaci kalmar "alhamdulillahi "...lallai bashi da bakin da zai godewa ummaty dashi saidai yayi Mata addua Dan Babu musu magungunan da take basa a kwanakin Nan suke warkar dashi da kudurar Allah...kada Kansa kawai yakeyi zuciyarsa na ayyana Masa abubuwa da dama waigawa yayi gefensa kadan ya hangi MP3 din da ta kawo Masa yake kwana saurare ya lumshe idonsa ya bude take taji Yana Jin kwadayin dakko mp din Amma Babu Wanda zai dauko Masa zuciyarsa ke ayyana Masa ka gwada mikewa tsaye mana?zaka iya daukowa da kanka ka gwada... gabansa na faduwa ya Dora hannuwansa biyu Akan hannun wheel chair din ya dafa sosai hannuwansa na rawa a hankali yake kokarin yunkurawa Yana numfarfashi Sama sama dai dai Nan ta turo kofar sai kawai ya karasa mikewa kafarsa na tsananin rawa... daskarewa ummaty tayi s tsaye dafe da kirjinta idanuwanta tamkar zasu Fado kasa tana binsa da kallo Yana sanye da purple din shadda da hula yayi masifar kyau ta dauki seconds talatin kafin ta furta "ya zainul Kaine s tsaye?I can't believe alhamdulillahi ya ilahi"murna sosai takeyi kafin ta Ankara yayi baya ya zauna a kujerar saboda kafarsa dake rawa...da gudu tayi Kansa zata rukosa taga ya fada kan kujerar sai ta sauke sassanyar ajiyar zuciya murmushi ya hau yi Mata ita kuwa tsananin farin ciki ya hanata magana... Kashe mata Ido daya yayi "yadai ummaty" Sai kawai ta janyo kujera ta zauna nesa dashi kadan ta kafesa da Ido...cikin mintuna hawayen farin ciki suka Shiga sauka a kumatunta...Wanda batasan tansyinsu ba lokaci daya Kuma murmushi yaki gushewa daga fuskarta "ummaty kuka Kuma?menene?umm?ai ban Fadi ba ko?Kinga na fara tsayawa Amma kafafuwana rawa sukeyi ummaty"...yadda yayi maganar ya Kara Bata tausayi ga wani kyau dake fita daga fuskarsa da kwarjini na daban fiye da ko yaushe uwa uba shaddar jikinsa da Tai matukar karbarsa.... "Kukan farin ciki nakeyi ya zainul...nayi matukar Jin dadin ganinka a tsaye da kafafuwanka gani nakeyi tamkar a mafarki ne ya zainul Kaine a tsaye? alhamdulillahi....Allah ya Kara maka lafiya ya zainul...naji Dadi sosai" "Ummaty ke Zanyi wa godiya keda kika jajirce wajen nema mun magani da kula Dani,abinda iyayena suka kasa fahimta ke kika fahimta,tabbas nadade da tunanin ciwo na bana asibiti bane Amma baba ya kasa ganewa...banida bakin da zan gode Miki saidai incee Allah ya Saka Miki da alheri ummaty...Kuma Ina ganin maganin da kike bani yanzun shi ya sa naji sauki haka sosai cikin kankanin lokaci" Wani murmushin Jin Dadi tayi zuciyarta Tana godewa Allah da ya hadata da baabah kande cikin kankanin lokaci suka samu wanan ci gaban "alhamdulillahi ya zainul Allah ya Kara lafiya".. Murmushi ya sauke mata Wanda ya Kara narkar Mata da zuciya yace "ameen ummaty"... ******* Kasantuwar yau jumaa yasa dukkansu sukazo gida da iyalansu kamar yadda al'adar gidan take da halima da Zahra ne yaran ummah rumana zaune gefen mahaifiyarsu Alan katuwar dadduma suna taba Hira sama sama gimbiya rumana sai wani Shan kamshi takeyi tana magana da kyar tamkar Dole da alamu yau sarautar ta Mata ta motsa.... Cikin zumudi anty Zahra ta dubi halima tace "albishirinki halima jiya saiga haris a gidana daddare" "Kai Dan Allah kice yazo Miki ziyara,ai haris akwai mutunci idan ya gadama" "Shegen ba gidana yayi niyyar zuwaba budurwa ya samu Wai be fada Mata Yana sonta ba da gidansu zaije Amma ya kasa zuwa sai kawai yayo gidana kiji shirme"dukkansu sukasa dariya sai lokacin gimbiya rumana tasa musu Baki "haris kenan iyayen girman Kai dama zaiyi budurwa wanan yaron" "Ai ummah budurwar ma Yar cikin gidace Amma ya kasa gaya Mata ba wata bace ummaty ce" "Ummaty!"gimbiya rumana da halima har rige rigen fada sukeyi...take hankalin gimbiya rumana ya tashi ta gyara Zama Tana sauraron Zahra "itafa ummah Amma indai dagaske yake sonta yayi Mata Dan tanada hankali sosai gata kyakkyawa zanso ya aurentan" Tabe Baki halims tayi ta dubi mahaifiyarta suka hada Ido sai Kuma halima ta hau dariyar yak'e "wallahi kuwa ni kaina zanso ta auri haris kodan ta bar zainul itama ta huta da jinyar Dan ko warkewa zainul yayi bazai aureta ba" "Saboda menee? "Tana matsayin Yar sarkin dawaki?bama Yar waziri ba ko galadima sauki sauki tabdijan"... Bataji dadin yadda halima tayi maganar ba sai kawai ta dauki nuaiym ta fita Dan ta shimfidesu kamar jira takeyi su fita gimbiya rumana a fusace tace 'kinji wani bala'i ko" Dariya halima tayi "shine daidai ummah ai kawai ko wani bekai maganar Nan gaban Mai martaba ba kiyi kokarin kaiwa dan shine cigabanmu da samun nasararmu da zarar ummaty ta auri haris karasa zainul ba wani Abu bane" Cikin rashin fahimta gimbiya rumana tace "meye dalilinki na hakan" "Zamu tattauna ummah xaki fahimci inda na dosa Amma ko labarin auren ummaty da haris zainul yaji to tabbas bakin ciki zai ksrasasa Dan ko ba komi nasan ya kamu da sonsa Koda yarinyar Bata sonsa Dan hakan kija haris a jiki kikai maganar wajen sarki akwai nasara", ",To idan ummaty batason haris dinfa?" "Bazataki shi ba,saboda haris hadadde sanan ummaty bazata iya Musa maganarki Kota Mai martaba ba"..jinjina Kai gimbiya rumana tayi zuciyarta cike da tunani barkadai... ******* Sauri sauri suketa aiki tun safe saboda yau jumaa abinci kala kala ya kamata ayi saboda Baki Dan haka baabah kande batasan wainar da ake toyawa ba a sashen gimbiya tana wajen masu aiki Tana duddubawa dikda jikinta Yana Bata anyi magana Mai muhimmanci da ya kamata ta saurara... A Nan ummaty ta sameta take shaida mata ci gaban da aka samu dangane da maganin da take karbo Masa sosai baabah kande tayi farin ciki da Jin hakan Amma zuciyarta nayi mata rauni da zarar zainul ya warke to tsugunu Bata Kare ba ummaty ce zata Shiga uku... "Baabah ya naga fuskarki ta canja kamar bakya farin ciki"ummaty ta tambayeta cike da damuwa... Gudun kada yarinyar ta fahimci wani Abu yasa ta sakin fuska tana fadin "ai Dole inyi farin ciki diyar albarka kawai dai kaina ke ciwo ga aiki tun safe mukeyi" "Haka ne Bari inje in duba ya zainul ko ya tashi Dan ni zan kaishi fadar sarki idan an sakko masallaci"tana gama Fadin haka ta wuce baabah kande ta bita da kallo cike da tausayi.... ******** Haris zaune gefen musaddik Yana daddana wayarsa yasha kwalliya cikin farar shadda da bakar hula yayi matukar kyau sosai hannunsa rike da farar wayarsa iPhone 11 hankalinsa na kan wayar kowa na zazzaune Yan Matan ma sunsha ado suna Yar hirarsu a gefe can gefe iysyensu ne kannen me martaba suna tasu hirar bangaren hagu Kuma su Zahra ne ke tsokanar hajiya Kaka....sarkin fada ne yayi yekuwa tare da neman izinin zaa shigo cikin fadar... sarki ya amince aikuwa ya bude musu kofa tana ture dashi a wheel chair da sallama bakinta suka shigo kowa ya bisu da kallo musamman zainul abideen da yayi masifar kyau ga Yar kiba yayi Yana sanye da farar shadda da bakar hula irinta jikin haris sai walkiya yakeyi tamkar ya Mike ya taka da kafafuwansa...sumar zaune warisah tayi tunda ta shaki kamshin turarensa zuciyarta ta buga take taji wani Abu ya caketa s kirji ya rufe idanuwanta kawai fuskarsa take gani a mafarkinta yanayi Mata tsadadden murmushin Nan nasa...Jan numfashinta tayi ta sauke ta dauki mintuna a hakan kafin ta bude idanuwanta wadanda suka canja launi suka kankance.... Haris kuwa irin kallon da yake bin ummaty dashi yasa hafsat zungurin zahira ta Nuna Mata suna kada Kai suna murmushi ita kanta anty Zahra radawa halima tayi a kunne "dubi mutuminki"ta juyo ta Ganshi kusan kowa yaga yadda yake bin ta da kallo ... hajiya kubrah kuwa tayi kicin kicin da fuska har ummaty ta fice dakyar ya dawo hankalinsa karaf suka hada Ido da mahaifiyarsa ta watsa Mai harara.... Abinci aka Shiga zuzzubawa ummah rumana da kanta ta Mike cike da iyayi "Bari in bawa yarona abinci Dan nasan Babu me yimun Kara"murmushi Mai martaba yayi "to ai kema Baki jira ayi Miki karar ai da kin tsaya kingani nasan kubrah zatayi Miki"...dukkansu sukasa dariya. Gefensa tai masauki rike da plate din jelof da nama da cokali sai murmushi zainul keyi sai kawai ya Mika Mata hannu "ummah zan iyaci da kaina"ta zaro Ido tana kallonsa "ah ah zaka Bata jikinka zainul" "Allah ummah xan iya kawo kigani"Mai martaba kuwa sai faraa yakeyi Yana kallonsu itama gimbiya bilkisu hankalinta na kan Dan nata "Kawo ummah kigani Allah zan iya"cike da shagwaba yayi maganar Yana Bata fuska tamkar yaro karami... Haris yayi murmushi "ummah kibashi Mana kuna maidamun brothet yaro bayan ya girma kuma alhamdulillahi Yana samun lafiya" Sai kawai gimbiya rumana ta mika Masa da bismillah a bakinsa ya karba batare da plate din ya Fadi ba kowa zaro Ido yakeyi cike da mamaki Babu Wanda yayi magana Amma hankalin kowa na Kansa a hankali ya dibo abincin dikda jikinsa na Dan rawa yakai bakinsa tsananin farin ciki yasa Mai martaba tafi Yana fadin "alhamdulillahi"kowa sai murna da sowa ciki kuwa harda warisah wadda takeji tamkar taje ta rungumesa a guje zahira ta karasa ta rungumesa ta baya "yaayah yafara samun sauki alhamdulillahi"...wani kallo warisah ke bin zahira dashi tamkar ta shaketa...ita kuwa zahira kasa sakinsa tayi saboda yadda kamshin jikinsa ke fusgarta tanajin wani irin nishadi cikin zuciyarta....gimbiya bilkisu har kwallar farin ciki Saida tayi....haka ya rinka cin abincun Yana faraa saboda yadda kowa ke murna... Kuka sosai gimbiya rumana keyi tana godewa Allah yaronta ya samu lafiya har hajiya Kaka Saida ta lallasheta tace farin ciki zatayi tayi dariya haka ta rungume zainul Tana shafa Kansa.... A haka aka karasa cin abincin kowa cike da farin ciki shiko haris Allah Allah yakeyi a gama saboda ya Kai zainul sashensa Dan yaga ummaty ko zai samu saidah cikin zuciyarsa.... *WANAN LITTAFIN NA KUDINE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* sosai haris ke jan ummaty da Hira da tsokana tun Bata kulasa har ta sake dashi Tana bashi amsa da dariya sosai yayinda zainul ke gefe kamar ya fashe da kuka bini bini haris ya sako zainul cikin maganarsu bakin ciki yasa zainul lumshe Ido Yana baccin karya..."muje ki rakani ladan dariyar da nasaki Dan Dole ki biyani dariyar da nasaki"yayi maganar cike da barkwanci Cikin faraa tace "indai wanan ne me sauki ne muje"ta Mike ya Mike ya dubi zainul "laa yayi bacci idan ya tashi kice natafi"ta gyada Masa Kai ta dauki wayarta tabiyo bayansa...yanajin karar rufe kofarsu ya bude idanuwansa da sukai jajir ya bi kofar da kallo cike da takaici.... Har mota ta rakasa ya bukaci numberta dakyar ta basa Saida ta Gama ja Masa aji sanan ta koma shi Kuma ya wuce... Tana sako kafarta cikin gidan Kiran gimbiya rumana ya shigo wayarta dikda number ta gani tasan itace Dan daga ita sai haris keda numberta....wani irin faduwar gaba ta tsinci kanta tana bin Kiran da kallo har ya tsinke sai a Karo na biyu ya Danna recieve ta Kara a kunne a sanyaye tace"assalamualaikum barka da yammaci ranki ya Dade" "Barkanki dai ummaty kintafi ne ko kina Nan?" Dan yatsina fuska ummaty tayi Tana tsaye "Ina Nan ranki ya Dade" "Ina bukatar ganinki yanzun a sashina zamuyi magana Mai muhimmanci"...Tana Gama maganar ta kashe batare da jiran cewarta ba Dan hakan ummaty tabi wayar da kallo tana nazari...sanan tayi murmushi ta Shiga danne danne Nan da Nan ta Shiga recording sanan tayi sashen gimbiya rumana..... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* *TEAM...UMMATY/HARIS*🏃🏻‍♀ *Team gimbiya rumana*🤥 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *HASKE WRITERS ASSO💡* *SLIMZY😍* [1/23, 11:18 AM] 😍SLIMZY😍: 29 A tsaye ta sameta tana kallon window dakinta hannuwanta rungume a bayanta....cakkk ummaty ta tsaya daga kofar dakin gabanta na tsananin faduwa dakyar ta hadiye wani mugun miyau ta furta "assalamualaikum"batare da ta karasa shigowa dakinba, A hankali gimbiya rumana ta juyo fuskarta dauke da damuwa ta saukewa ummaty idanuwanta wadanda suka canja kala sukai jajir tamkar wadda tayi kuka,kallonta takeyi ido cikin Ido yayinda kirjin ummaty ya cigaba da bugu sauri da sauri....tsoro ya cikata tamkar ta saki fitsari takeji a wajen saboda tsananin tsorata da tayi da yanayin na gimbiya rumana addua ta shigayi cikin zuciyarta hade da tasbihi kala kala Tana mai neman tsari da Sharrin gimbiya rumana...katse mata tunani tayi ta hanyar Kiran sunanta da wata iriyar murya bakinta har Yana sarkewa ",ummaty"....dammm gabanta ya Fadi ta dago Kai da sauri bakinta Yana karkarwa ta amsa "na'aaam ranki ya Dade" "Ya kika tsaya daga bakin kofa kamar wadda zaa cinye ki shigo Mana"...jikin ummaty na tsananin rawa kafafuwanta dakyar take dagasu ta tako a hankali tana tafiya gimbiya rumana na bin yadda jikinta ke rawa da idanu har ta karaso tsakiyar falon ta durkusa Akan gwiwoyinta ta sunkuyar da kanta...cije lebe gimbiya tayi cike da takaici sanan tayi gyaran murya ta matso daf da ummaty "ummaty ya Naga dik kin tsorata kin furgita lokaci daya kafafuwanki har rawa sukeyi"ta jefa mata tambaya Tana bin yanayin nata da kallo... "Ummaty yanayin ki Yana Nuna min tamkar akwai wani Abu da kikeyi Wanda bakyaso insani dik a rude kike"... Zaro Ido ummaty tayi hade da dafe kirji"haba ranki ya Dade?Nina Isa inyi wani Abu batare da sanin uwata uwargijiyata ba ?Babu wani Abu Wanda Zanyi shi batare da sanin kiba ranki ya Dade farin cikinki shine farin cikina banida wani aiki Wanda ya wuce bin umarninki ko wani iri ne ranki ya Dade wane ni?" Murmushin Jin Dadi gimbiya rumana ta sauke hade da sassanyar ajiyar zuciya "kin tabbatar dik abinda nasaki Zaki iya yinsa?kin tabbatar idan na bude Miki sirrin zuciyata Zaki rike mun Amana bazakici amanata ba ummaty kin tabbatar Zaki kasance tare Dani har karshen rayuwarmu Babu abinda zai Shiga tsakanina dake na cutarwa ummaty?Zaki taimakeni ta ko wani Hali ummaty?"ta karasa maganar muryarta Tana rawa tamkar zatayi kuka ita kanta kalaman gimbiya rumana da yadda muryarta ke rawa sun sanyaya mata jiki sun karya Mata zuciya har idanuwanta suka ciko da hawaye...tasa hannu ta share batare da gimbiya ta ganiba Amma bangaren zuciyarta ta tuna mata da niyyarta na kubutar da zainul da sauran zuriar gidan daga muguntarta lokaci daya tausayin gimbiya ya gushe cikin zuciyarta ta Kara samun karfin gwiwa....style tayi tamkar Tana duba agogo ta tabbatar da wayarta tana kan recording taji wani sanyin dadi cikin zuciyarta na burinta dake Shirin cika...gyaran muryar gimbiya ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tsunduma tayi furgigit ta dago kanta taga ita take kallo ta sadda kanta kasa zuciyarta na tsananin harbawa..."ranki ya Dade Babu wani Abu Wanda Zaki umarceni inyi Miki shi banyishiba a lokacin da kikeso domin inajinki tamkar uwar data haifeni Kinga kuwa uwata Bata Isa ta bani umarni in kalli idonta ince baxanyi Mata shiba bazan iyaba ranki ya Dade dik wani abinda kikeso ki fadeshi Kai tsaye batare da wani tunaniba Zaki sameni me gaskiya da rukon Amana ranki ya Dade", "Kin tabbata?" Gyada mata Kai tayi"insha allahu ranki ya Dade"...mstsowa tayi kusa da ummaty ta zauna daf da ita har numfashinsu Yana Karo da juna... "Ummaty Abu na farko shine inaso infito fili insaki aiki Akan zainul abideen saboda Naga boye boyen bazai yuwuba hada kanmu nidake shi zaisa inci nasara har incinma burina Akan bukatata,ko nawa ne daga naira daya zuwa million dari zsn Baki inhar zakisa mun hannu mu salwantar da rayuwar zainul abideen" A firgice ummaty ta dago Tana kallon gimbiya rumana dikda batayi mamaki da wanan maganar daga bakinta ba a zahiri dama abinda take expecting kenan Amma s fili saita nuna mata furgici hade da zaro Ido take tasa hannu tana murza idanuwanta Wai alamar ko mafarki takeyi....rukota gimbiya rumana tayi yadda taga dik ta firgice tamkar zararriya batare da sanin cewar ummaty pretending kawai takeyi ba "cool down ummaty ki kwantar da hankalinki,nasan zakiyi mamaki akan wanan maganar da kikaji daga bakina nasan bakiyi zaton haka ba saboda yadda zainul yake a wajena koh?"...ummaty ta gyada Kai hannunta dafe da kirjinta har zuwa lokacin jikinta be bar rawa ba.... *WANAN LITTAFIN NA KUDINE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* "dik wata soyayya da zakiga ni rumana Ina nunawa zainul abideen to ba soyayyar komi bace face ta karya,banida wani buri a duniya Wanda ya wuce ni rumana Inga gawar zainul abideen a kwance Dan bana kaunarsa harabada bazan taba kaunarsa ba nayi nayi in rabasa da duniyar gabaki daya nakasa shine na biyo ta wanan hanyar na nakassa rayuwarsa nakeso tunda na kasa kasheshi ya Kare rayuwarsa a kwance,to yanzun babban tashin hankalina be wuce ganinsa ya fara warkewa ba shiyasa nakeso mu hada Kai dake mu shekasa lahira ki taimakeni ummaty banaso yaron Nan ya warke ya gaji sarautar garin Nan shine babban bakin cikina kiji tausayina Kinga ni ban haifi da namiji ba"Tana kaiwa Nan ta fashewa ummaty da kuka ta Sanya gwiwowinta a kasa a gabanta.. ummaty kuwa dake zaune tayi sandare take taji duniyar na jujjuya mata tamkar wadda Tasha kayan maye...Amma ganin gimbiya rumana gabanta Tana rokonta yasa ta tattaro jarumta tayi saurin rukota tana kokarin xaunar da ita "haba ummah darajarki da martabarki ta wuce kiyi durkuso a gaban ko waye ballantana ni ranki ya Dade umarni ya kamata kibani ba rokoba Dan kinfi karfin hakan,ni kaina neman maraba nakeyi domin nagaji Dan haka ki kwantar da hankalinki zamu yardar da kwallon mangwaro mu huta da kuda"....tsananin farin ciki yasa gimbiya rumana rungume ummaty a jikinta tana shasshekar kuka...... ******* Tafe take Tana hurga kafa domin tunda ta fito daga gidan Mai martaba ta kasa sukuni tunani kawai takeyi Babu kakkautawa lallai duniya Babu gaskiya yanzun da wata ce ita saboda kwadayin abin duniya zata bada hadin Kai wajen cutar da Dan uwanta musulmi?gimbiya rumana ta Bata mamaki matuka taci amanar gimbiya bilkisu kuma taci amanar Mai martaba koda yake batayi mamaki ba domin Dan Adam a wanan rayuwar ba abin yarda bane zaiyi abinda yafi haka mutum Sai Allah...aikuwa idan hakan ne to tabbas zata shayar da ita mamaki Dan saita tona mata asiri ta maidata abar kwatance...da wanan tunanin ta shawo kwanar hanyar gidansu,tun daga nesa take kallon dalleliyar motar Tana tunanin waye ta sani da irin waccan motar wadda ke kofar gidansu s Parke?harta karaso ta kasa tunawa Dan hakan ganin ba kowa yasa tasanya Kai cikin gidansu hade da sallama....turuss tayi tsaye tana binsa da kallo zaune Akan tabarma gefen Inna yanacin latas tsayawa tayi Tana kallonsa mamaki ya hanata magana shiko cike da barkwanci yace "ummaty kinyi mamakin ganina a Nan na rigaki zuwa koh?kin manta kece kikacemun innah latas zatayi shiyasa na rigaki zuwa na cinye duka"ya karasa maganar Yana daga mata gira daya, Saroro tayi tana cigaba da kallonsa,...innah kuwa dariya tayi sosai sanan ta dubi ummaty "ke Kuma inbazaki shigo ba ki koma saikace haris din ne Baki saniba kin wani tsaya kina kallonmu"...jiki Babu kwari ta shigo cikin gidan ta wuce dakinta ta barsu Nan zaune suna hirarsu... Koda sarkin dawaki ya dawo sallar magriba farin ciki yayi sosai da ganin haris yazo Wai saboda ummaty...addua ya shigayi cikin zuciyarsa Wanda ya barwa Kansa ita kawai.... ******* Sosai hankalin halima ya tashi Tana rike da Muhammad "ummah gaskiya kin tafka babban kuskure na saurin yadda da wanan yarinyar har kika kwashe sirrinki kika fada mata ummah meyasa?"halima ta dafe Kai cike da bacin Rai... Girgiza kafa gimbiya rumana tayi Tana murmushin kasaita "ki kwantar da hankalinki sanin Kanki ne kusan Rabin maaikatan gidan Nan sun San koni wacece Amma shekara da shekaru Babu Wanda yayi yunkurin tonamin asiri Dan haka nasaka Mata matakan tsaro hagu da dama gabas da yamma kudu da arewa sanan na Dana mata tarko da su yusha'u Dan haka idan tayi yunkurin tonamin asiri itace zata kwana cikin balain... "Waye yusha'u Kuma ummah"halima tace hade da yatsina fuska... "Masu gadin zainul abideen masu kula dashi tuntuni sukai yunkurin tona mata asiri Wai sunganta Tana bawa zainul magani nina hanasu...sanan akwai makamai dayawa dana tanada saboda tsaro"... Ajiyar zuciya halima tayi zuciyarta na ayyana Mata abubuwa da dama..... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *HASKE WRITERS ASSO💡* *SLIMZY😍* [1/23, 11:37 AM] 😍SLIMZY😍: 30 Kallonta halima ta sakeyi fuska dauke da damuwa a Karo na biyu wanan karon furzar da iska tayi Mai zafi daga bakinta hade da yatsina fuska "well ummah tunda kince haka baxanja da hukuncinki ba baxanja da maganarki ba Amma tabbas inaji a jikina shigo shigo Babu zurfi yarinyar Nan takeyi Miki dikda nasan kedin wacece xan kwantar da hankalina Inga yadda wasan naku zai kasance dikda jinina a kunbata yake".... Girgiza Kai gimbiya rumana keyi cike da mulki Yana hura kafafen hancinta,lokaci daya ta saki wata arniyar dariya Mai dauke da tsantsar mugunta "kisa Ido kiga yadda wasan zai kasance dikda yadda kikeji a jikin naki nikam ba haka nakeji ba domin inaji a jikina ta rigada ta shigo hannuna na d'ana Mata tarko fitarta Abu ne me yuwuwa Dan haka Bari kigani"....ta juyo da dubanta gefe da gefe Babu kowa sai ta mika hannunta jikin wani switch dake makale a bango ta Danna kararrawa cikin seconds saiga hansa'u ta shigo jikinta na rawa ta zube a kasa "tuba nakeyi ranki ya Dade na rashin samuna a kusa har kika Danna kararrawa na fita kenan kika Danna Inna fatan hakan be batawa uwargijiyata Rai ba" Murmushin gefen fuska "karki damu hansa'u nice na bukaci kiyi nisa saboda inason ganawa da Yar taawa, yanzun Kuma na bukaci ganinki kikazo akan lokaci Dan hakan ba laifi bane,...ba wanan surutun nakiraki kiyimun ba"...da sauri hansa'u ta Kara zubewa kasa sosai "me kikeda bukata uwargijiyata intashi intafi in aiwatar dashi yanzun Nan,me kikeso a kawo Miki yanzun in garzawa Koda wata masarautar ne in tabbatar na kawo Miki shi a mallaki shi?banida wani amfani Wanda ya wuce in bautawa gimbiya matar sarki Kuma uwargidan sarki,aiki komi wuyarsa komi hadarinsa Zanyi mikishi a cikin seconds din da Basu wuce goma ba domin kedin adalace Allah ya Kara Miki lafiya da nisan kwana uwar Fatima Zahra da gimbiya halimatussaaadiya na gaisheki"....sosai gimbiya rumana ke kada Kai tare da Jin dadin kirari irin Wanda hansa'u takeyi mata kanta Yana Kara girma Tana Jin kanta on top tanajin ta dara dik Matan duniya.... "Bawani abu nake bukataba face inaso kiyimun aiki nasan kin kware a wanan fannin wajen sawa dik wani Mai shige da fice a cikin masarautar Nan idanuwa,Dan hakan nake umarrarki da inaso ki bibiyi rayuwar ummaty Ido,dik wani shige da fice nata,dik inda Tasa kafa da muamalarta inaso ya zamana akan idanuwanki takeyi idan so samune Ina bukatar kisamu rahoto har fannin bilkisu mahaifiyar zainul abideen ki rinka kawomin,idan kikaimun hakan yadda ya kamata kinada sadaki Mai tsoka Dan haka na Baki wanan aikin".... "Indan wanan aikin Mai saukine uwargijiyata fatana da burina bai wuce inganki cikin farin ciki ba Dan hakan zaayi Miki wanan"... ******** "Wai ke Kam menene haka dik kikabi yau kika firgice kamar wadda wani Abu ke damunta?bini bini kinyi tagumi tun bayan dawowarki kike hakan Kuma ganin haris ne a gidan kiketa hakan"innah keyiwa ummaty magana tana zaune gefenta a tabarma bayan sallar isha'i... "Babukomi innah kawai dai nayi mamakin zuwan nasa Nan gidan ne tunda ban taba ganinsa ba a Nan gidan din sanan harda hidimar siyo Mana kayan abinci shine dik naji wani iri" Murmushi innah tayi wanan lokacin "ummaty kenan gaskiya haris mutumin kirki ne kece dai bakisan hakan ba kuma tun ainihi daman ni nasanshi lokacin muna Zama cikin gidan sarki wajena yake wuni idan ya dawo makaranta" "Amma innah ban taba ganinsa ba fa"Tai maganar cike da shagwaba... "To ke yaushe kike wuni a wajena kina sashen gimbiya bilki wajen zainul Kinga bazaki sanshiba Dan haka indan wanan ne ki kwantar da hankalinki"...sarkin dawaki dake cikin dakinsa Yana jiyo tattaunawarsu ya bude labulen dakinsa ya fito Yana fadin "Amma ga dukkan alamu akwai wani Abu da haris yakeso tare damu yasa kikaga Yana wanan rawan jikin saboda nasan halin yaron yarone Mai natsuwa da Kamala sanan akwai abubuwa da na lura dashi dangane da yaron daga shigowarsa" Murmushi innah tayi tana sunkuyar dakai cike da kunya Dan ta fahimci abinda sarkin dawaki ke nufi,..ya cigaba da magana "kinsan ance idan kaga Kare Yana shinshina takalmi to dauka zaiyi Dan hakan indai hasashe na da abinda na hango na fahimta gaskiya ne to tabbas sainafi kowa farin ciki da hakan" Itadai ummaty kanta daurewa yayi Dan dik maganar da iyayen nata keyi Bata fahimta ba kallonsu kawai takeyi daya bayan daya kamar tv tana sauraren tattaunawarsu... ********* Hajiya kubrah mahaifiyar haris da warisah ce zaune s parlor yaran nata zagaye da ita suna cin abinci cikin kwanciyar hankali sunayi suna kallon tv misalin karfe Tara saura na dare "ni Kam momy nakosa daddy ya dawo daga London din Nan daya tafi yanzun idan ban manta a kirgana ba saura sati biyu ya dawo ko momy" "Ehh Dole ka kosa Mana tunda kaima kadawo gida kanason kaga mahaifinka shiyasa,Wai inama kaje ne sai yanzun ka shigo kasan tun kana kasar Nan banason yawon dare kaida ba abokai gareka ba "ta dubeshi fuska a Nan daure, Hannu yasa Yana shafa sumar Kansa hade da sauke lallausan murmushi batare da yace komiba,ta kafesa da idanuwanta...sai wanan lokacin warisah ta dago Kai ta dubesu hade da tabe Baki kamar bazatayi magana ba sai Kuma tace "hmmm yaayah kenan nasan inda kaje wallahi,bazai wuce gidan sarkin dawaki ba wajen ummaty " "Wace ummatyn?"momy ta dafe kirji hade da zaro idanuwa... "Ummaty Mana Yar sarkin dawaki?me kula da ta zainul Mana can yaje" Wani mugun miyau ta hadiye hade da hurga masa wani mugun kallo "Sannu haris wato can kaje koh?shiyasa kwana biyu kuke kuss kusss kaida Yar uwarka ko Ashe abinda kuke kullawa kenan,sanan haba biri yayi Kama da mutum dik na fahimci komi dangane da kallon da kake bin ta dashi dazun a gidan Mai martaba, nasan dik wani mahaluki ya fahimci inda ka dosa to wallahi baka isaba Dan bazaka kwasomin Yar talakawa ba dubeka fa?ka tuna da Yar dakake Shirin nema kayi kadan" Wani kallo ya watsawa warisah suka hada Ido ta sadda kanta kasa cike da faduwar gaba dama yasan zaayi hakan shiyasa yaso mahaifinsa ne zai fara Jin labarin Nan Dan yasan zai Mara Masa baya shi baya kyamar talakawa,Amma tunda haka ne zaisamu Mai martaba akan maganar kafin yanaji Yana gani ya rasata... "Wato Ina magana kayi shiru ka kyaleni mahaukaciya na magana ko?kake nufi kome" Idanuwansa a kasa ya motsa bakinsa a hankali "kiyi hakuri"shine abinda yace ya Mike ya fice daga patlorn ta bishi da kallo... "Ke Kuma me kikeso kicemun tun jiya nake binki kifada mun damuwarki kike ramewa cikin kwana kin Nan kinki fadamin jiya na sake binki kince Zaki fadamin Baki fada munba,oya Ina jinki" Kwalla ce ta ciko a idanuwanta ta cije lebenta Dan kada ta zubo mata uwarta ta fahimci halin da take ciki Wanda daga ita sai zuciyarta ta bar mawa, Bata shirya tona asirin zuciyarta ba yanzun...sai kawai ta dauki cup din tea dinta batare da tacewa momy komiba ta fice a patlorn tayi hanyar dakinta...kallon mamaki da al'ajabi momy ke bin ta dashi har ta bacewa ganinta,sai kawai ta janyo wayarta ta Shiga dialing wata number... ****** Bayan kwanaki hudu kusan kullum cikin kwana kin Nan haris sai yaje wajen ummaty Kuma tare da hidimomi kala kala bai Kuma Nuna mata dalilinsa na yin hakan ba bai Kuma taba Nuna mata alamar Yana sonta ba ko a fuskarsa saidai kawai yayita tsokanarta yanayi mata barkwanci kala kala Wanda dabiarsa ce matukar Yana jinyin wasan...ganin hakan yasa ta Dan saki jiki dashi ba dukkanba,a cikin kwanakin Kuma zainul ya samu sauki sosai fiye da da Dan ya koma normal mutum dinsa da taimakon magunguna da baabah kande take kawowa suna canjawa zainul suna bashi,yanzun har tsayawa yakeyi da kafafuwansa Amma baya iya daga kaafarsa saboda tanayi Masa nauyi sosai... Hankalin gimbiya rumana yafi Koda yaushe tashi musamman yau data dawo daga ziyartar zainul abideen ta ga yadda ya koma ta furgita kwarai ta Kuma lura da yadda mahaifinsa ke rawar kafa da tsananin farin ciki akan hakan musamman yau da sukaje tare....ta rasa inda matsalar take ta tabbatar wa da kanta cewar ummaty tana bawa zainul abideen magani Dan hansa'u Tana kawo mata rahoto akan hakan,har yusha'u Yana kawo mata rahoto sosai Shima to ta Ina matsalar take?shin daga bokanta ne Koko daga waye?Dole ne yau tasa bokanta yayi bincike Akan wanan mummunan balain da yake tunkaro ta Dan haka zuciyarta ta karkata Akan ta shirya ta ziyarci kauyen da kanta yau.... Cikin kankanin lokaci ta shiryawa tafiyar zuwa kauyen na bokanta tare da hansa'u da wata baiwarta amintacciyarta ta boye Wanda ba kowa yasanta ba.... ******* Ummaty gabaki daya batajin dadin ranta a yau minti minti gabanta Yana faduwa Wanda batasan dalilin hakan ba Tana zaune gaban zainul abideen hankalinta gabaki daya ya karkata wani waje shi Kuma gogan dik wani motsi nata akan idonsa takeyi yanajin wani shauki dangane da ita Yana fusgarsa dik seconds soyayyarta karuwa takeyi a cikin zuciyarsa, Tayi zurfi cikin tunanin mafita Dan ta rigada ta fahimci akwai matsala dangane da gimbiya rumana ta fara fahimtar zainul ya samu lafiya,ita kanta bataso ta fahimci hakan ba Amma Babu yadda zaayi ta hanasa Nuna samun lafiyarsa saboda besan meke faruwaba idan har tayi gigin sanar Masa to tabbas batasan me hakan zai biyo bayaba Dan haka take adduar samun mafita "Ummaa...ty"ya Kira sunanta cikin wata irin siga Wanda ita kanta Saida taji wani Abu ya tsarga Mata tun daga saman kanta zuwa tafin kafafuwanta,dakyar ta hadiyi miyau ta amsa can kasan makoshinta"naam"ta maida hankalinta garesa, "Cikin kwanakin Nan na rasa abinda yake damunki ummaty Kuma dik Wanda ya ganki yasan akwai damuwa tattare dake kina boyemun hakan ne saboda ban cancanta kifadamun ba ko"ya kafeta da isanuwansa da wani irin kallo me dauke da sakwanni kala kala, Muryarta na rawa zuciyarta na bugawa sauri da sauri tace"ka cancanta kasani sanan matsayinka ya wuce dik wani Abu daya dangani ummaty"ta kifta Masa idanuwa Tana murmushi,Shima murmushin ya maida mata "idan har hakan ne Ina bukatar sani" "Akwai lokaci da zaiyi Wanda zan sanar maka Dan haka ka kwantar da hankalinka" "Shikenan Allah ya kawo wanan lokacin"...ameen tace hade da sauke sassanyar ajiyar zuciya,kallo ya bita dashi Yana matukar tausayinta dikda besan dalilin hakan ba".... ********** Wani kallo takeyiwa musaddik ji takeyi tamkar ta shakesa saboda tsananin kiyayya,da yasan yadda take kiyayyarsa da be ko kusanto inda take ba ita dik abinda ya dameta ya dameta Dan haka kauda kanta tayi gefe guda ya cigaba da magana "warisah zuwa yanzun ya kamata kibani dama domin bayyanawa zuriar gidan Nan abinda yake tsakanina dake Dan idan banyi wasaba soyayyarki tana iya kaini kabari"...yadda ta kafesa da Ido Shima haka yake kallonta ita kuwa tunda ya soma magana fuskarsa ta rikide mata ta koma ta zainul abideen har ya Gama tayi nisa cikin tunani hade da kallonsa shiko zuciyarsa ce ke wani irin bugawa jira kawai yakeyi ta amince masa Dan yagama yarda da cewar Tana sonsa kenan tunda take binsa da kallo Mai dauke da soyayya "kiyi magana masoyiyata" Sai lokacin ta dawo daga duniyar tunanin da take ta saki wani mugun tsaki ta Mike daga palon tayi hanyar dakinta tana tafe Yana bin maxaunanta da kallo kirar jikinta kadai ya Isa dik namijin daya kalleta ya Kara kallonta...iska Mai zafin gaske ya furzar daga bakin sa zuciyarsa nayi Masa tsananin Kuna... Kan gadonta ta fada ta fashe da kukan takaici kullum abinda takeji dangane dashi karuwa yakeyi Kuma kullum sai yazo Mata cikin mafarkin ta Wanda tarasa dalilin wanan bakon al'amarin....hannu tasa ta share hawayenta ko giyar wake Tasha bazata tunkari zainul abideen ta fada Masa tana sonsa ba Dan ita kanta tasan yadda ya tsaneta bazai saurarenta ba zuciyarsa da ruhinsa na wajen ummaty ....hannu Tasa ta dafe gefen zuciyarta dake yi mata azabar ciwo...ga Dan uwanta na tsananin son ummaty wanan wace irin iftilai ke Shirin fada musu....ga mahaifiyarsu Bata son ummaty mafita daya ce tafadawa mahaifiyarta tana son zainul Dan tabar haris ya Suri ummaty da wuri tabar mata shi...to tayaya ita da ta daukarwa zuciyarta alkawarin boye sirrin dake cikinta tayi nisa cikin tunani batasan mahaifiyartata ta shigo dakin ta zauna gefen gado Tana fuskantar ta ba sai ji tayi an ruko hannunta ta matukar tsorata hakan yasa da sauri ta juyo da fuskarta sharbe da hawaye sukai Ido hudu da mahaifiyarta ta fada jikinta hade da sakin marayan kuka Mai ban tausayi...ta rungumota jikinta Tana shafa kanta... ****** Shirin tafiya gida takeyi yau da wuri tun karfe uku na Rana "meyasa kike tunanin akwai abinda zai raba zumuncina dake ummaty ?" Murmushi kawai tayi batare da tace komiba sai kawai ta dauki Jakarta ta Mike tsaye "zan wuce"ta sauke Masa murmushi kallo kawai yake bin ta dashi cike da al'ajabi Dan haka be ja da itaba yace "to Allah ya tsare sai gobe kenan",ta kada Masa Kai idanuwanta cike da kwalla batare da ya gani ba ta sa Kai ta fice....sauri takeyi har tazo daidai sashin gimbiya rumana ta tsaya ta Dan kalla Tana son ganin baabah kande Amma batajin zata iya ganinta yau Dan haka saita sa kanta ta fice.... ******* Sosai boka yakeyi mata bayanin komi da abinda ke Shirin faruwa cike da tashin hankali take sauraronsa har ya Gama....dakyar ta hadiyi miyau a bakinta Wanda yayi Mata dacin gaske saboda tsananin takaici da tashin hankali...kullin magani ya dauko ya kwance ya dubashi cikin ruwa Tana binsa da kallo har maganin ya jika ya tashesa ya zuba a gora sanan ya dauko wani ruwan magani ya zuba ciki ya jijjiga yasa murfi ya rufe sanan ya dubeta "wanan maganin matukar ta bashi shi ya Sha to ya tashi aiki ki matsa mata kiyi mata barazana sanan ki Nuna mata kinsan shirinta dikda inaji a jikina da wuya ku kwashe lafiya nayi iya bimcikena da bugun kasa wajen gane waye dayan da ke taimakonta nakasa ganewa da alama shima da shirinsa" "Bazai wuce mahaifinta ba tunda dama ya fara yimun gaddama Akan hakan shine ya bullo da haka to wallahi sai na shayar Dasu mamaki dukkansu sainayi sanadiyyar su gabaki dayansu tunda ka tabbatar mun cewar da wuya ya Kara kwanciya to zan Basu mamaki"cike da bacin Rai take maganar da kunar Rai.... Haka ta amshi maganin cike da tashin hankali ta baro wajen boka tamkar mahaukaciya dik komi ya tsaya Mata tunanin yadda zatayi kawai takeyi da yadda zata dauki fansa Akan sarkin dawaki Wanda take zargin shike taimakon ummaty...😂😂😂 ****** Baabah kande hankalinta a tashe yake tunda ta saurari tattaunawar gimbiya rumana da yarta a waya take tunanin yadda zataga ummaty kafin su hadu da gimbiya rumana tun safiyar yau take dakonta Amma inaaa Bata ganta ba sai kawai hangen gilmawarta tayi cikin sashen gimbiya rumana Tana biye da hansa'u wadda akasa Tai kiranta.... *WANAN LITTAFIN NA KUDINE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI ,08166177830 KO 07084161619* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *HASKE WRITERS ASSO💡* *Dan Allah kuyi hakuri wayata ke hauka kwana biyu da kukaji shiru yanzun komi normal insha allahu zakujini akai akai* *SLIMZY😍* [1/23, 11:38 AM] 😍SLIMZY😍: 31 Cakk ta tsaya ganin yanayin fuskar gimbiya rumana Babu annuri Nan da Nan jikinta ya dauki Bari da rawa tamkar mazari a hankali ta jingina da jikin bangon dakin Tana sauke numfashi a hankali,yadda zuciyarta ke bugawa ita kanta tabawa kanta tsoro Dan iyakacin tsorata ta gama tsorata,...ita kuwa ogar takowa tayi a hankali ta karaso har inda take ta tsaya Tana bin ta da kallo Mai cike da tuhuma da zargin...hannu takai jikin kofar Tasa makulli aikuwa take hantar cikin ummaty ta Kara kadawa ji takeyi tamkar ta saki fitsari a inda take, Hannunta tasa ta dago habar ummaty idonta cikin nata "kunyi gangancin cin amanata keda ubanki ummaty,saurin me kukeyi haka ganin kunga bayana?meyasa kika Bari mahaifinki yayi galaba akanki kuka hada Kai kuke ganin zakuci amanata ku zauna lafiya?" Cikin rashin fahimta inda ta dosa ummaty ke kallonta dikda tsoro daya cika mata zuciya be hanata yin karfin halin wurga mata tambaya ba "ranki ya Dade ban fahimci maganarki ba da kike cewa nida mahaifina munci amanarki kibani haske akan maganar Allah ya Baki yawan Rai"...ta karashe maganar muryarta na tsananin rawa... Wata uwar tsawa gimbiya rumana ta daka mata ",ke dakata muna fuka zakice mahaifinki be sanar dake cewar maganin da kike bawa zainul abideen tun farko ba maganin da yake sashi ciwo bane?dikda a wancan lokacin ke Kanki bakisan maganin menene kike bashi ba Amma na tabbatar a kwanakin baya da yayi mun tawaye ya sanar dake Kona menene shiyasa yanzun kuka hada Kai wajen ganin kun warkar da zainul abideen ni Kuma nawa asirin ya tonu ko?to karya kukeyi dukkanku wallahi nafiku tsafi malamina yafi naku Kuma sarkin dawaki na sanar dashi tun a kwanakin baya yayi kuskuren da betaba yinsa ba ya jefa Kansa cikin danasani Mara amfani Dan nasha sanar dashi asirina bazai taba tonuwa ba saidai nashi wallahi"....idanuwan ummaty gabaki daya sun ciko da kwalla sunyi jajir Jin furucin da gimbiya rumana keyi tabbas tunaninta da zarginta yau ya tabbata na cewa da mahaifinta ake hada Baki wajen ganin bayan zainul abideen.... innalillahi wa Inna ilaihi rajiun shine abinda ta furta a zuciyarta ta runtse idanuwanta da karfi wasu zafafan hawaye suna gudu daga idanuwanta zuwa kuncinta...wani irin bala'i ne wanan yake Shirin tunkaro su? mahaifinta beyi mata adalci ba yayi sanadiyyar jefata cikin masifar da fitar da ita Sai Allah daya halicceta....wayyooo Allah inama mafarki takeyi da idan ta tashi daga mafarkin Nan bazata Kara kwanciya ba harabada...wayyooo Allah kaiconta...ta cije lebenta da karfin gaske har Saida yayi jini sanan ta bude idanuwanta ta saukesu akan fuskar gimbiya rumana wadda ta hada Rai tamkar tunda Allah ya halicceta Bata taba murmushi ba....sai kawai ta zube a gaban gimbiya rumana ta fashe da wani irin kuka Mai ciwo hade da ban tausayi ta ruko kafafuwan gimbiya "ranki ya Dade ban taba danasanin zuwana duniya ba kamar yau inama ace wanan abun daya faru a mafarkine ba gaske ba?menayi muku haka kuka jefani cikin halaka kuka zabi tsomani cikin wanan balain"...ta rushe da kuka Mai karfin gaske Tana rike da kafar gimbiya rumana wadda ko gezau batayi ba dikda kuka Mai ban tausayi da ummaty keyi tana gurfane rike da kafafuwanta...sun dauki minti goma a haka bakajin sautin komi sai shesshekar kukan ummaty dakyar gimbiya rumana ta sauke numfashi ta soma magana wadda har ummaty ta cire Rai da zatace wani Abu "karki kuka da kowa ki kuka da ubanki sarkin dawaki Dan shikadai ne babban aminina tun kafin a haifeki,tun kafin kisan zakizo duniya dik wani kulli dashi muke kullawa Kuma shi ya kawo shawarar amfani dake wajen bawa zainul magani saboda zuciyata Bata aminta da insaka wani yayimun ba gudun kada asamu matsala,sanan kece kawai Zaki bawa zainul Abu ya ci dubada yadda kuka taso kuke kaunar juna dubada yadda ya yarda dake kuka shaku da juna shiyasa kika zamo cikin wanan abun sai gashi ke kina tunanin kedin me wayauce bayan bakida wayaun komi kwaya nawa kike?dududu shekararki goma Sha bakwai a duniya har kike tunani yiwa Yar shekara hamsin wayau?hmmm kinyi gangancin Dan hakan yanzun haka kinada dama ta karshe a wurina wadda idan Kinga Zaki iya to idan bazaki iyaba banki kowa ya kwana a ciki ba"ta makale kafadarta fuskarta dauke da murmushi..... Mikewa tsaye ummaty tayi fuskarta jike da hawaye Tana kallon gimbiya rumana cike da takaici "Fadi damar data rage a gareni indai bazata jefani cikin wata masifar ba ko ta haddasamun damuwa da ciwon da bazai warkeba a zuciyata zan iya yinsa..." Cike da kasaita take takawa har ta karasa jikin wardrobe dinta ta bude wata bakar Leda ta dauko Mai dauke da gorar magani ciki ta dagata Sama tana bin gorar da kallo sanan ta sauke lallausan murmushi ta juyo ta tako har wajenda ummaty ke tsaye itama ta tsaya,murmushi ta Kara saukewa a fuskarta ta daga gorar daidai fuskar ummaty,wadda gabanta ke tsananin faduwa tana karewa gorar kallo cike da tsoro..."wanan shine abinda zai fiddaki cikin matsalar da kike Shirin fadawa,idan har kika bawa zainul wanan maganin ya Sha bukatata ta biya to tabbas zan fiddaki cikin wanan Kullin Koda Nan gaba ne bazan taba saki ciki ba ummaty ki ceci Kanki ki ceci rayuwar iyayenki data zuriarku Baki daya kibawa zainul maganin Nan yau ayita takare idan ba haka ba Ina Mai tabbatar Miki komi Yana iya faruwa,Abu na karshe da zan sanar Miki shine idan kikace Zaki yaudareni to wallahi wallahi zakisha mamakina idan kingadama kije Kiki bashi kiyi dik yadda kikeso Amma idanuwana sunkai dubu akanki dik abinda kikeyi ko numfashi kika sauke me karfi sai an sanarmun Dan haka dabara ta rage ga Mai Shiga rijiya karbi"ta Mika mata gorar hannunta na rawa ta karba hawaye kuwa tamkar an bude pampo zuciyarta na Raya Mata abubuwa da dama ga recording tayi dik na maganganunsu Amma batasan ta yadda zaayi ta fidda kanta ba....ita kuwa gimbiya makulli tasa ta bude kofa tayi Mata nuni da ta fita...... *WANAN LITTAFIN NA KUDINE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* ********** tallabe take da warisah a jikinta wadda jikinta yayi zafi Rau alamar zazzabi cike da tashin hankali hajiya kubrah ta dubi Yar tata "ke warisah Wai bazaki fadamin abinda yake damunki ba so kikeyi ki mutu?wa kikedashi Wanda ya fini?Wanda kike ganin Zaki iya fadawa damuwarki bayan ni?dik yadda naso ki fadamin kinki fadamin dubi dik yadda kika koma fisabilliahi kifadamun ko menene damuwarki d'iyata Allah zai Miki maganinta Zanyi Miki"...ta karashe maganar cikin sigar lallashi, Maimakon tace wani Abu sai kawai ta lumshe idonta tana murmushi,hawaye na gangarowa ta gefen idanuwanta masun zafin gaske a hankali ta daga hannunta ta dafe gefen kirjinta batare da tayi magana ba zuciyarta na gargadinta da kada ta Fadi abinda ke damunta idan haka ne har gara taje ta tari zainul ta sanar dashi dikda tanaji a jikinta bazai taba sauraronta ba .... Jijiigata momy keyi da kyar ta bude idanuwanta wadanda suka canja kala sukai jajir hankalin momy ba karamin tashi yayiba warisat dinta ce dik ta canja haka?meke faruwa da yarinyar take boye mata Wanda yakesata tsananin Rama ga fari da take karawa da kyau na daukar hankali...dik yadda hajiya kubrah Tai lallashi fafur warisah Taki fada mata damuwarta saima mikewa da tayi ta fada toilet Dan tayi wanka...ta dauki lokaci cikin toilet kafin ta fito inda tabar hajiya kubrah Nan ta sameta ta rafka tagumi sai kawai Tai mata murmushi ta karasa gaban mirror dinta ta Shiga shafa mayuka kala kala masu dadin kamshi da turarruka ta shirya tsaf cikin doguwar rigar jallabiya red Mai stones masu daukar Ido ta yane kanta da gyalenta ta kawo maroon din janbaki ta shafa Sama sama ta zizara kwalli a manyan idanuwanta Wanda Tai masifar kyau tamkar ba ita ba....sallamar ya haris ce ta dakatar da ita daga maganar da Tai Shirin Yi ya nemi gefen gado ya zauna sanan ya kalli warisah ya tabe Baki cikin sigar tsokana yace "ko kyau"ta turo Baki "Dama fa Kai zanje nema naji kamar kana cewa xaka Shiga gidan sarki" "Ehh,ya akai"yace hade da tamke fuskarsa, "Dama Ina son zuwa ne in duba jikin ya zainul"daga momy har haris kallonta sukai cike da mamaki sai Kuma suka basar haris yace "to muje kada ki Bata min lokaci"... "Momy sai mundawo I love you kinji"cewar warisah tana murmushi tana kallon momy itama murmushin ta maida mata "a gaida bilkisu da rumana inaga zan sameku da yamma can", ",Owk momy"suka hada Baki tare suka daga mata hannu suka fice dakin ta bisu cike da kallon so da kauna..... ********* Dik wani shiri hansa'u da yusha'u sunyi shi Suna makale suna kallon cikin dakin zainul abideen rikeda camera yusha'u ya dubi hansa'u suka hada Ido lokacin da ummaty ta Ciro gorar magani idanuwanta taff da hawaye.... "Ya zainul ga maganinka zakasha?idan bazaka sha ba bazan takuraka ba"tayi maganar ne don zainul yace Baya Sha, "Mezai hanani Sha ummaty?maganin Nan ba yau kika soma bani ba ban Isa ince baxan Sha ba Dole insha bani"...ya karasa maganar Yana kallonta,...gabanta na tsananin faduwa ta Ciro gorar tana kallo, Daga inda suke labe "yusha'u wanan ba gorar da gimbiya tabawa ummaty bace mu cika aiki kawai mu dauki wajen da ta bashi mu ruga mu sanarwa da gimbiya bilkisu halin da ake ciki". "Kin tabbatar ba ita bace?"ta gyada Masa Kai murya kasa kasa "wallahi ba ita bace"... Tanaji tana gani ta Mika Masa gorar ya rike ta rike ya Shiga kwankwadar ruwan maganin da gimbiya tabawa ummaty har yasha rabi tari ya sarkesa cike da tashin hankali ta rike gorar tanayi Masa sannu.... Suna Gama sanar mata da Nuna mata videon gimbiya bilkisu da fiyya suka Mike s kidime suka runtuma a guje zuwa sashen zainul abideen cikin tsananin tashin hankali , Bankado kofar da akayi ce ummaty ta Mike a kidime gorar ruwan maganin da sauran suka Fadi jikinta suka watse....shiko zainul na kwance shame shame Babu alamar numfashi s guje gimbiya ta shake ummaty "asirinki ya tonu munafukar Allah lallai mutum Sai Allah dama kece silar ciwosa?" Dafe kirji warisah tayi daga kofar dakin da suka shigo tare da haris ...... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *HASKE WRITERS* *ASSO💡* *SLIMZY😍* [1/23, 11:40 AM] 😍SLIMZY😍: 32 Kakkafe idanuwan ummaty sukayi saboda yadda gimbiya bilkisu ta shaketa ta Shiga kakari tamkar wadda zata sheka lahira cikin azama haris yayi kansu da sauri ya ruko hannun gimbiya bilkisu "ammiey ki tsaya Zaki kasheta kinsassauta rukon Nan kada yarinyar Nan ta bakunci lahira Dan Allah" Idanuwa jajir take bin haris da kallo hawaye taf ciki "menene amfanin makashinka Yana tare da Kai haris?ko kasan cewa shekara da shekaru nake zargin akwai Wanda yake kullawa yaron Nan wanan masifar inata addua yau Rana tsaka Allah ya Toni asirinta na tsaneki na tsaneki ummaty allah ya tsine Miki albarka bakida wani amfani a wanan duniyar Wanda ya wuce in kasheki matsiyaciya dangin matsiyata"...kan haris daurewa yayi saboda furucin da gimbiya bilkisu keyi Amma hakan be hanasa sa karfinsa wajen kwatar ummaty ba cikin kankanin lokaci ya fizgota ta fada jikinsa sumammiya safiyya wadda ke tsaye a gefe saboda tsananin zuciya Tai kukan Kura tayi kan ummaty,wata uwar tsawa haris ya daka Ma safiya 'ke dakata kina hauka ne?meye haka?meye ribar Yi Mata taron dangi idan aka kasheta wani sabon laifi ne"Yana maganar cike da fushi Yana rungume da ummaty wadda ke numfashi Sama sama idanuwanta a rufe hawaye masu dumi ke bin gefen fuskarta.... Gimbiya rumana a firgice ta shigo sashin tana zarar idanuwa zuciyarta na bugawa fat fat saboda furgici Amma ganin halin da ake ciki ta danne sai kawai tayi kan zainul abideen tana sharar hawaye "Allah sarki Dan ummah ni dik ba ta kowa nakeyi ba ta yarona nakeyi ta ran magajin sarki nakeyi shi kadai gareni idan aka kashemun shi an cuceni"tana rusa kuka musaddik ne ya shigo da sauri ya sunkuci zainul abideen a kafadarsa yayi sashin Mai martaba dashi be tsaya ko Inaba sai bedroom din sarki Nan ya shimfide shi ya bude windows hade da kunna fanka saboda yadda yake fidda numfashi tamkar me ciwon asthma kimfaffaki ke fita daga bakinsa.... Gabaki daya gida ya rikice Nan da Nan dangi duka fara hallara gidan sarki harda Yan kallo na nesa Dana kusa cikin gari ya dauka cikin mintuna da Basu wuce goma Sha biyar ba labari ya karade garin da kewaye cewar angano Wanda yayi silar ciwon Magajin sarki ummaty Yar gidan sarkin dawaki wasu suna yarda da maganar wasu Basu yarda da cewar ummaty zata aikata hakan ba duba da kananun shekarunta.... ******** Cikin awa daya fada ta cika dankammm har Babu wajen Zama xuriar gidan Mai martaba kowa ya iso da labari ya cin Masa harda sarkin dawaki Wanda Yana kasuwa akayi Masa Kiran gaggawa Wanda ko da ya karaso cikin fadar ya tarar da mahaifiyar ummaty ta rigashi isowa yadda yaga wuri makil da mutane ya tabbatarwa da Kansa shikenan tafaru takare (Billy galadanci)Wai anyiwa Mai Dami daya sata dama yasan ko ba Dade ko banjima akwai wanan ranan,Jin yakeyi tamkar ya saki fitsari lokacin da ya hada Ido da gimbiya bilkisu ta watsa Masa wani kallo Mai tattare da tsana da kyama besan lokacin da ya sadda Kansa kasa ba Yana ambatar sunayen Allah s zuciyarsa... Hawaye ne kawai ke gudu a fuskar innah wadda ta rasa abin cewa ji takeyi tamkar ta hadiyi zuciya ta mutu Dan bakin ciki ta tabbatar wa da kanta sharri akayiwa ummaty ba gaskiya bane wanan labarin da ake yadawa... Zaman sarkin dawaki a fada shi ya hargitsa fadar aka soma CeCe kuce surutu hade da zage zage kawai ke tashi har kusan minti biyar.... Mai martaba Iya tashin hankali ya tsinci kansa ciki shiya haifar masa da kasa cewa komi saidai sauke ajiyar zuciya kawai da yakeyi minti minti yakan kada Kashi saboda tsananin mamaki da kunar Rai.... Dakyar ya daidaita Kansa yayi gyaran murya Wanda yasa fadar yin tsittt tamkar Babu wata halitta Mai Rai dake cikinta kowa yayi shiru Yana sauraren me Mai martaba zaice dangane da wanan lamarin Mai cike da ban mamaki... "Farko dai Babu abinda zance saidai ince "innalillahi wa Inna ilaihi rajiun dangane da wanan lamari daya faru Mai cike da dumbin ban mamaki da al'ajabi ko a mafarkina ban taba zato ko tunanin haka zata faru ta fannin Wanda nafi yarda dashi ba a duniya wato sarkin dawaki...ummaty dai Bata Kai shekarun da zata aikata wanan taasar ba ita kadai Saida saka hannun wani a ciki tunda bincike ya Nuna cewar ta Dade tana bashi maganin Nan nuni da wanan video dake cikin wayar yusha'u"... Take yusha'u yayi playing video din daidai inda ummaty ke fadin zainul inbaka maganin naka kasha ne Koko sai anjima....Nan take muryar zainul ta cika fada inda yake cewar ummaty Akan me zanki Shan maganin da kindade kina bani shi ?aibanida wani zabi daya wuce Shan wanan maganin ummaty... Nan fada ta kacame da surutu kala kala da kyar sarkin fada yayi tsawa kowa yayi shiru Yana jiran hukuncin Mai martaba... "Banida wani hukunci Wanda zan zatar Akan hakan face na yanke alakata da ahalin sarkin dawaki da dik wata zuria tasa na barranta Dasu ko a lahira bana fatan Allah ya hada fuskokin mu Dasu domin dik Wanda zaiyi Mana wanan cin amanar Yana daidai da yasa a halakamu" Kuka ummaty ta rushe dashi harda shassheka ta Shiga waige waige tamkar zararriya wayarta take nema Amma Bata ganta ba zabura tayi zata ruga aguje innah ta rukota Tana kuka "ranka ya Dade wallahi bani bace bani bace banida hannu a wanan lamarin" Wani zabura hajiya Kaka tayi jikinta har rawa yakeyi cike da tsana da takaici tace "bake bace to uban waye munafuka?ga sheda kuru kuru kice bake bace mudai kawai anci amanar mu Kuma Allah yayi Mana sakayya insha allahu zainul abideen da kaina zan cigaba dayi Masa magani zai warke Sarai Kuma zai taka da kafarsa babban abinda zan sanar muku shine wallahi idan yaron Nan be farfado ba ya taka da kafafuwansa ba to dagake har uwarki da ubanki sai kun bakunci lahira sai nasa an tsireku munafukan Allah marasa kaunar Allah asirinku ya tonu"...tunda hajiya Kaka ta soma magana ummaty ta kafeta da idanuwa hawaye na gudu a fuskarta dakyar ta juyar da kanta suka hada Ido da gimbiya rumana wadda keta sharar kwallar makirci ita an cuceta takasa magana.. kada Kai kawai ummaty tayi ta danyi murmushi cike da takaici....Mai martaba ya cigaba da magana "inaso ku tattara komi naku ku koma bayan garin Nan kuje can da Zama domin ko ganinku bana sonyi na tsaneku na tsani dik wani Abu daya dangance ku har zuwa lokacin da zan nemeku Dan kaina"... Waziri da sarkin aska ji sukeyi tamkar su zuba ruwa a kasa su Sha saboda farin ciki...Dama irin wanan ranan suke jira... Dik wanan hukuncin da Mai martaba ya yanke ba haka gimbiya bilkisu tasoba so tayi kawai Mai martaba ya yanke musu hukuncin kisaa....shi kuwa sarkin dawaki tunda ya sunkuyar da Kansa ya kasa cewa komi sai zufa da take keto Masa ta ko Ina idanuwansa sunyi jajir haka ya dago Kai ya dubi ummaty suna hada Ido ta runtse idanuwa saboda wani irin bakin ciki da ya taso Mata mahaifinta ne Amma bakinkirin take ganinsa ....innah kuwa yadda take sharbar kuka ne kadai zai baka tausayi idanuwanta sun kumbura sunyi jajir ga wani irin tukukin zafi da take ji cikin kirjinta ...Mai martaba ne ya bada umarni da a fidda Mai su daga cikin fada Yana Gama fadin haka ya Mike yayi hanyar dakinsa inda aka kwantar da zainul abideen aka kunna Masa karatun alkurani bacci ya daukesa.... Warisah da zahira da safiyya harda afnan suna zagaye da Dan uwan nasu ko wanne cikin tsananin tashin hankali yake sai fifita sukeyi masa lokacinda Mai martaba ya Shiga ya Basu umarni da su fita Babu musu ko wacce ta fita jiki Babu kwari....tsaye yayi Akan Dan nasa Yana Kare Masa kallo soyayyarsa na yawo cikin jinin jikinsa wani irin tausayinsa ke ratsa sa ta ko Ina...shi Kansa Mai martaba baisan lokacinda kwalla ta cika a Ramin idanuwansa ba ya cigaba da kallon zainul Yana shafa Masa Kai..... ******** *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* Isowarsu gida keda wuya suka zube Akan tabarma daga innah har ummaty dik sun fita hayyacinsu cikin kankanin lokaci,sarkin dawaki jikin katamga ya tsaya ya kifa Kansa batare da yace komiba,...ganin hakan yasa innah cikin kuka take fadin "malam tunda wanan bala'i ya fada Mana cikin dakikun da suka wuce bakace komiba har a gaban Mai martaba ka kasa magana,Dan Allah malam kace wani Abu Mana kasan ummaty bazata aikata hakan ba"tasa hijjabinta tana goge fuskarta wasu hawayen na gudu, Mikewa ummaty tayi a zabure cike da takaici ta Zame Dan kwalin kanta sumar kanta dake kwance ta bayyana ta cije lebenta tana fuskantar inda mahaifinta ke tsaye "innah Babu abinda baba zaice domin dik abinda ya samemu shine sanadi".. Cikin kuka innah ke duban ummaty "kina hauka ne ummaty kinsan me kike fada kuwa?kinaso kice min abinda ake zargi hakan ne Kuma malam yasani?" Murmushin takaici ummaty tayi tasa hannu ta share hawayen fuskarta ta sauke numfashi "ya sani innah domin shine silar komi shi ya jefani cikin wanan halin na tsinuwar mutane da laana" "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"shine abinda Inna ke furtawa tana kallon ummaty cike da son Karin bayani....take ummaty ta kwashe komi dangane da abinda ya faru Wanda ta sani da maganganun da gimbiya rumana ta fada Mata a yau ta kwashe ta fadawa mahaifiyarta... Sosai innah ta girgiza da lamarin dakyar take kada kanta saboda tsananin takaici "malam ka cucemu ka haincemu malam ka cutar da yarka kasata cikin mummunan Hali,kayi Mata pentin da me wanketa sai Allah ka shafa Mata bakin jini... innalillahi wa Inna ilaihi rajiun,Dole zaman cikin garin Nan ya gagaremu Koda sarki ya bamu umarnin Zama bamu Isa mu zauna ba saboda abubuwan da zamu fuskanta,....sanan ko menene ummaty Bata Isa ta fallasa asirin gimbiya rumana ba wadda falladuwar asirinta sai Allah shi kadai ne zai Tona Mata asiri da izinin Allah"... Kuka sarkin dawaki yakeyi cike da nadamar abinda ya aikata a baya take ya zube Akan gwiwoyinsa a gaban iyalin nasa Yana rokar gafararsu Akan abinda yayi Sharrin shaidan ne Yana kuka da hawayensa....dukkansu kuka sukeyi cike da takaici,ummaty tausayin mahaifinta ne ya lullubeta tasan cewar gimbiya rumana tayi amfani da makirci ne wajen samun galaba akansa dikda batasan ainihin tarihi da labarin komiba.... Haka tasa dankalinta tana sharewa mahaifinta idanuwa Tana girgiza Kai "baxan taba yafewa kaina ba,bazan taba iya jure ganin mahaifina Yana zubar da hawaye a gabana ba harabada komi girman laifin da zaimun Koda yakai dutsen uhudu girma Zan yafe Masa kayi shiru mahaifina na yafe maka harabada"....ta fashe da kuka ta fada jikin mahaifinta tana shasshekar kuka ya rungumeta tsamm innah ta taso daga inda take ta karaso wajensu suka rungume juna suna kuka... Turo kofar gidan yasasu juyawa a tare suna kallon hanyar kofar gidan cike da faduwar gaba.. haris ne ya shigo gidan cikin kananun kaya masu shegen kyau wadanda sukai matukar amsar jikin nasa fuskarsa Babu yabo Babu fallasa,kallo daya zakayi Masa kasan cewar Yana cikin tsananin damuwa.....Bata dauke idanuwanta ba daga Kansa har ya karaso inda suke ya tsugunna a gabansu,....hannunsa ya zura aljihunsa ya Ciro farin karamin towel Mai shegen kamshi ya Kai fuskarta ya Shiga goge Mata hawayen da Yana gogewa wasu na sauka ko kifta ido batayi wajen kallonsa "banaso insake ganin hawaye a wanan kyakkyawar fuskar Taki ummu Salma Dan Basu kamaceki ba,inaji a jikina cewar wanan abun daya sameki kaddara ce hade da makirci aka kulla Miki Dan ban yarda ba innocent ummaty zata aikata hakan"...kuka ta fashe dashi "ya haris wallahi summa tallahi bani bace na aikata hakan bazan taba aikatawa zainul wanan mummunan aikin ba banida hannu cikin wanan aikin Babu Wanda zai yarda Dani Amma nasan zainul shikadai zai fiddani cikin lamarin Nan sai Allah "...kada Kansa kawai yakeyi idanuwansa sunyi jajir dakyar ya furzar da iska Mai zafi daga bakinsa ya juyo ya dubi sarkin dawaki cike da jimami da tausayawa "baba ka kwantar da hankalinka,insha allahu gaskiya zatayi halinta da izinin Allah kaji" Kada Masa Kai sarkin dawaki yayi zuciyarsa cunkushe da tsananin bakin ciki....shiruu sukayi kusan minti talatin bakajin sautin komi sai shasshekar kukan ummaty wadda har muryarta ta disashe kamanninta gabaki daya ya canja ta fita hayyacinta... Gyaran murya haris yayi "baba idan bazaku damu ba Zan kwasheku a gidan Nan in kaiku wani gidana da na siya can wajen gari Babu Wanda yasan dashi in ajiyeku a wajen ku zauna har muddin Rai sanan inaso in maida ummaty ta koma karatu Koda karatun Nan na bangaren lafiya tayi inaganin hakan zaifi kafin komi ya daidaita Kuma ku kwantar da hankalinku dik runtsi dik wahala Ina tare daku baba Dan girman Allah kada kuce ah ah nabaku kwana uku kuyi shawara abinda kuka zartar saiku sanar Dani"....tunda ya soma magana sarkin dawaki ke kallonsa batare da yace komiba har ya Gama itama inner batace komiba shiru tayi ...ya Dade zaune basuce komiba har yayi musu sallama da nufin zai dawo washe gari.... ******** Tsaye tsaye suke akansa lokacinda malamin da aka Kira yayi Masa adduoi aka shafa masa me hade da ganyen magarya da ayatushifa aka bashi dakyar aka samu ya farfado bakinsa dauke da salati da Kiran sunayen Allah....lokaci daya yake bin kowa da kallo a dakin daya bayan daya da sauri gimbiya rumana ta rungumesa cikin tsananin farin ciki "alhamdulillahi Dan ummah ya farfado na godewa Allah Ashe kanada sauran Shan ruwa a duniya yarona,watakila warakar ka ce tazo kanada sauran numfashinda zaka haifamun jikoki"cikin tsananin farin ciki take maganar tana Kara rungumesa sosai...runtse idanuwansa yayi saboda yadda jikinsa yayi Masa nauyi babu karfi tamkar an cire Masa lakka...cikin karfin Hali ya kalli gimbiya bilkisu wadda take hawayen farin ciki yayi murmushin sanan yace "ammiey Ina ummaty?,ta tafi Bata jirani na tashi ba koh?"ya marairaice Yana tambayarta..... *HASKE WRITERS ASSO💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY😍* [1/23, 11:41 AM] 😍SLIMZY😍: 33 Shiru kowa yayi a dakin suna kallonsa batare da sunce mishi wani Abu ba sai ya lumshe idanuwansa ya Kara budesu a kan sister dinshi halima "maman samir Ina ummaty ta tafi gida ko?Dan Allah idan ta tafi a je a kiramun ita inason ganinta sosai"cikin sigar shagwaba yake maganar, Anty Zahra dake gefe rungume da Muhammad ta share hawayen da ya gangaro mata daga idanuwanta tausayin Dan uwanta ya cika Mata zuciya itadai ta kasa cewa komi tun bayan faduwar hakan domin zuciyarta Bata aminta da zancen ba Allah kadai ya baiwa Kansa sani,a tare suka tako zuwa gaban makeken gadon da yake kwance suka tsaya itada halima,karfin Hali anty Zahra tayi ta ruko hannunsa tana murzawa cikin sigar lallashi "lil brooo"ta Kira sunansa cikin sanyin murya da sauri ya dubeta Yana murmushi "naam anty Zahra"...cigaba tayi da murza hannuwansa "kaga ka daina Kiran sunan ummaty kaji baxaka sake ganin ummaty ba kaji broo kayi hakuri"...cikin rashin fahimta yake dubanta zuciyarsa cike da tsoro me kalamanta suke nufi?ya ma zaayi ace bazai sake ganinta ba yarinyar da ta Zame kasa jigon rayuwarsa jinin jikinsa?...kodai mutuwa tayi gabansa ya yanke ya Fadi ya Shiga girgiza Kansa inaaa hakan ma bazai yuwu ba da kyar ya motsa harshensa dakeyi Masa nauyi cikin sarkewar murya yace "Akan me zaace hakan?wani Abu ya faru ne?"ya Watso wata tambayar a Karo na biyu....kowa a dakin kallon kallo yakeyi sai gimbiya rumana wadda Tai karfin halin kwashe dik abinda ya faru ta sanar dashi ...da hukuncin da Mai martaba ya dauka sanan ta Dora da "Kar insake Jin zancen wanan azzakumar yarinyar a bakinka kaji na fada maka macuciya ce kaji?ka cireta a zuciyarka ka manta da ita tunda Allah yayi Mana arzikin Bata kashe ka ba"Tai maganar Tana shafa Kansa.... Dummmm yaji Kansa yayi Masa gabaki daya network din Kansa ya dauke dakin ya Shiga jujjuya Masa tamkar ana wurgasa sama ana jehosa kasa yakeji ga mummunan faduwar gaba daya darsu a kirjinsa cikin seconds da Basu wuce talatin ba wasu siraran hawaye suka Shiga gudu daga idanuwansa Wanda ya kafesu Akan fankar Sama ko kiftawa bayayi.... Ganin hakan yasa halima tabe Baki batare da kowa ya lura ba ta Dora da cewar "Dole kayi kuka lil broo Amma hakanan zakayi hakuri domin ummaty ta cutar dakai shekara da shekaru saidai Allah ya saka maka ka kwantar da hankalinka ka daina kuka ciwonka yazo karshe insha allahu Allah zai baka lafiya".... Wani kululun bakin ciki ne ya tokare wuyan gimbiya bilkisu wadda takeji tamkar ta Dora hannu akai ta fashe da ihu saboda takaici ko sunan ummaty gimbiya bilkisu Bata bukatar ji Dan dik duniya da zaa Bata wuka ta kashe wani to mutum na farko da zata kashe shine ummaty da zuriarta gabaki daya taci amanarsu Kuma insha Allahu sai sunga sakayya da wuri sanan ta Gama yadda da kowa a fadin duniyar Nan...tayi zurfi cikin tunani lokacin da aka turo kofar dakin hade da yin sallama...haris ne ya shigo da hajiya Kaka wadda gabaki daya jikinta babu kwari tun bayan faduwar hakan,....kallon zainul takeyi yadda hawaye ke gudu a fuskarsa take itama idanuwanta suka cicciko da kwalla Dan kallo daya zakayi Masa ya baka tausayi....haris ya xauna gefen gadon ya ruko hannun zainul yaji hannunsa zafi Rau ya dubesa kadan ya kauda Kansa "zainul ka kwantar da hankalinka ka duba halin da kake ciki kaji?wanan Abu saidai mubarwa Allah kawai Amma tariga tafaru ta kuma Kare"...sai lokacin zainul ya kifta idanuwansa ya juyo da kallonsa ga haris...."wallahi haris na rantse da Girman Allah banaji ummaty zata aikata abinda ake zarginta dashi,yarinyar Nan tayi iya bakin kokarinta wajen kulawa Dani Bata taba guduna ba,kashina,fitsarina,dik wata kazanta tawa itace shekara kusan nawa tana wanan dawainiyar?tun lokacin Bata kasheni ba sai yanzun?....Yan uwana inace wasu har guduna sukeyi saboda kazantata Amma ita Bata gujemin ba idan har nayi mata hakan tabbas nayi mata butulci Kuma Allah zai saka mata"... A fusace gimbiya bilkisu ta soma magana cikin kumfar Baki "ko Kuma Kai Allah ya saka makaba sakaran banza,sakaran wofi" Gimbiya rumana ta karbe zancen "haba bilkisu meye hakan kikeyi?kibishi a hankali Mana tunda kinsan halin da yake ciki sanan kada kiga laifinsa Dan yayi wanan sambatun Sam baa hayyacinsa yake ba bakisan iya rubutun da aka bashi yasha ba ta shanyesa Dole mu cigaba dayi Masa addua mubisa a hankali" Kuka sosai zainul yakeyi tamkar karamin yaro cikin kukan ne yake fadin"inhar maganar da kuke fada gaskiya ne na bazan sake ganin ummatyba to tabbas ku shirya dan nan bada jimawa ba abinda kuke gudun zai sameni Dan zan iya rasa Raina a kowani irin lokaci yarinyar Nan itace rayuwata itace jinin jikina itace komi nawa"tari ya sarkesa ya dafe gefen kirjinsa tamkar Wanda zai sheka lahira, Bakinciki ne yasa gimbiya bilkisu mikewa tabar dakin Dan ji takeyi tamkar ta shake zainul saboda takaicin maganganunsa,... Rukosa haris yayi Yana lallashinsa dikda can kasan zucuyarsa wani irin kishi ketaso Masa akan ummaty ji yakeyi tamkar ya shake zainul yakeji saboda kishi bayajin xai iya hakuri da ummaty shi Kansa Koda duniyar gabaki daya xata juya Masa baya Yana Nan tare da abarsa as far as iyayenta zasu aura mishi ita zaiyi rayuwa dagashi sai ita Dan haka dakyar ya busar da wata Isaka Mai zafin gaske daga bakinsa Nan da Nan jijiyoyin Kansa suka fito a saman goshinsa badan yaso ba haka yayita lallashinsa saboda wani bangare na zucuyarsa na matukar ji da zainul abideen Dan Yana kaunarsa Shima... Tana isowa sashinta ta Kira malamin da Mai martaba yasa aka kawo Dan yayiwa zainul magani ta Kira sa a wayar cewar tanason ganinsa akwai maganar da takeso su tattauna...cikin kankanin lokaci baiwarta lubabatu ta sanar da ita zuwan na malamin inda akai Masa masauki a babban patlornta... Sanye take da alkyabbar ta baka Mai tsadar gaske Tana rike da wayar ta pito patlorn tana taku dai dai,...malam zubair Yana ganinta ya zube kasa Yana kawo gaisuwa 'barka da yamma ranki ya Dade Allah yaja zamaninki sai Kuma naji Kiran gaggawa daga gareki Ina fatan ba jikin nasa bane ya tashi" Girgiza Kai tayi fuska dauke da damuwa "allah ya gafarta malam ba jikin bane wata damuwa ce nakeson fada maka ko Allah zai sa kanada maganinta Allah yayi Mana maganin damuwar mu" "To Allah yasa dai lafiya" "Wasu maganganu ne yaron Nan ya farka Dasu dangane da makirar yarinyar can wadda Sam banji dadinsu ba sun matukar batamun Rai "...Nan ta kwashe dik yadda sukai da zainul bayan farfadowarsa sanan ta Dora da "malam inaso a rinka bashi rubutu Wanda zai mantar dashi yarinyar Nan gabaki daya koma yaji ya tsaneta Dan samm Babu abinda na tsana a rayuwata sama da ko Jin sunan yarinyar Nan malam ka taimakeni"Tai maganar cike da damuwa... Shiru malam yayi Yana nazarin maganganun gimbiya bilkisu ya dauki minti goma sanan ya sauke ajiyar zuciya cike da alhini yace "ranki ya Dade wanan lamari na yaron Nan abin dubawa ne gaskiya sanan maganar rabasa da yarinyar Nan farar daya daga faruwar lamari bazai taba yuwuwa ba sai a hankali saboda kunsan yadda sabo yake da shakuwa musamman da kukace sun taso tare komi tare sukeyi Dole sai a hankali sanan Zanyi istihara Akan lamarin domin annabi SAW shi Kansa yanayin istihara na neman zabin Allah da rinjaye Dan hakan ki kwantar da hankalinki bazai gagaraba".... Ajiyar zuciya gimbiya bilkisu tayi fuska dauke da damuwa "to malam a duba lamarin sanan nagode sosai Allah ya saka da alheri"...sukai sallama da malam ta bashi kyautar kudi sanan ya tafi.... ****** 2pm Na dare zaune take Akan sallayar sallarta tana adduoi Tana kuka hade da yiwa Allah kirari akan Allah ya bayyana gaskiya cikin gaggawa rokon Allah kawai takeyi tana Kiran sunayen Allah.... Tana zaune kan dadduma zazzabi Mai zafi ya rufeta ga ciwon Kai Mai tsananin gaske Wanda takeji tun bayan faruwar lamarin.... Hawaye kawai ke gudu a fuskarta hade da shasshekar kuka ga wata iriyar yunwa da takeji gabaki daya rabinta da abinci tun safiyar jiya, shasshekar kukanta ne ya tada innah ta Mike da sauri ta nufi dakin ummaty tana mutsike Ido dikda ita kanta bacci barawo ne ya saceta saboda tsananin damuwa..."haba ummaty saiki tashi cikin dare kina koke koke?umm kiyi tawakalli ga Allah kinji ki roki Allah ya bayyana gaskiya sanan ya sanyaya Miki zuciyarki kinji?banaso damuwar hakan ta haifar Miki da wata lalura kinji ummu Salma?"cikin sigar lallashi take maganar, Dago Kai ummaty tayi fuskarta sharkaf da hawaye da gumi hade da majina tsabar kuka idanuwanta sun kankance ga zugi da sukeyi mata shasshekar kuka takeyi tana kallon innah "yanzun innah shikenan rabuwata da ya zainul tazo kenan?shikenan ta hakan zamu rabu idan ma zamu rabu?ya zainul yaji abinda ya faru yanzun nasani...Amma nasan shi yasan koni wacece bazai aminta da Zan cutar dashi ba...Allah sarki banida sauran wani Dan uwa a duniya"... Tausayinta ne ya lullube innah ta Shiga sharar hawayen da batasan suna zuba ba "kinadashi ummaty kingafa haris Shima Dan uwanki ne Kuma Yana kaunarki Shima inhar baya kaunarmu da hakan ta faru bazai biyomu har ya lallashemu ba,kingani ga Kuma abinda yace karki kuskura kice bakida Dan uwa a gabansa bazaiji dadiba kinji ki rungumi kaddarar da Allah ya jeho Mana da hannu biyu biyu sai Allah ya kawo Mana mafita,Kinga annabi ma yace Yana daga cikar imanin mutum shine yadda da kaddarar Mai kyau da Mara kyau me zaisa bazakiyi koyi da annabi ba kibi maganar daya fada umm?"...kuka ummaty takeyi ta fada jikin innah ta rungumeta ta cigaba da lallashinta ga jikinta yayi zafi Rau har asuba suna zaune waje daya Saida aka Kira sallar asuba sanan sukayo alwala din gabatar da sallar asuba.... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* ******** misalin karfe Tara na Rana tana kwance kan tabarma kanta akan cinyar innah Tana fama da ita akan ta tashi taci abinci Taki tashi sai ajiyar zuciya take saukewa minti minti ga jikinta da yayi zafi sosai har kanajin hucin zazzabinta, Haris ne ya shigo bakinsa dauke da sallama Yana sanye cikin kayan sanyi track suit jajaye Riga da wando sun matukar karbarsa innah ta amsa Masa sallamar cike da kulawa ya tsugunna a gabanta "innah barka da tashi, antashi lafiya?" "Lafiya Lau haris ya dawainiya Allah ya saka da alheri yayi albarka".. "Ameen"yace Yana sadda Kansa kasa minti minti yakan dago idonsa ya Saci kallon ummaty wadda ta lumshe idanuwanta tamkar me bacci,.. "Innah ummaty bacci takeyi ne?" "Ehh inaganin Dan jiya daddare bamuyi bacci ba,kwana mukai batayi bacci ba tanata koke koke ga jikinta yayi zafi sosai zazzabi ke damunta bansan ya Zanyi da itaba"... Cije lebensa yayi ya busar da iskar bakinsa "innah sai a hankali zuciyarta Babu Dadi ne nazo ne inji shawarar da kuka yanke Dan nasa har anfara gyaran gidan"... "Toh shikenan Allah yayi albarka Babu damuwa insha allahu zamu zauna can din .." "Zuwa gobe zanzo in kwasheku in maidaku can din Bari inje in Nemo Mata magunguna in dawo" "To haris Allah ya saka maka da alheri"... "Ameen innah" Wasu hawaye ne masu dumi ke gudu a fuskarta dikda idanuwanta a rufe suke Tana sauraron dik tattaunawarsu... ****** Juyin duniyar Nan anyiwa zainul magana tun tashinsa yaki kula kowa tamkar kurma haka ya koma musu gashi tun jiya beci komiba ,har idan aka matsa Masa da magana sai ya sa kuka tamkar karamin yaro bakaramin tashin hankali iyayensa suka Shiga ba na wanan lamari musamman Mai martaba Wanda yayi iya bakin kokarinsa akan zainul Amma yaki koda kallonsa ne hakan Nan badan sunso ba kowa ya bashi waje... Baiwar gimbiya bilkisu ce ta turo kofar bakinta dauke da sallama ta shigo sanan ta tura kofar,...gefen wheel chair din da yake zaune ta zube a kasa dik kawo gaisuwar da takeyi be amsa ba kusan minti biyar da kyar tayi shahada ta bude Baki taace "ranka ya Dade dama jiya bakada lafiya dangane da abinda ya faru shine na tsinci wayar ummaty to ummah naso Kai mawa saidai nace Bari inkawo maka idan kace akai sai akai"...da sauri ya juyo gareta Yana kallonta har ta karasa zancenta yayi shiru bece komiba har ta fidda Rai zaiyi magana sanan ya mikar da hannunsa "mikomim wayar" Babu musu ta Mika masa wayar ya karba, Gabaki daya ya maida hankalinsa kan wayar yayi kurrr da Ido Yana kallonta tamkar ummaty yake gani a gabansa har lubabatu ta Mike ta Kai kofa zata fice ya dakatar da ita da sauri ta tsugunna a wajen "Kar inji labarin cewar wayar ummaty tana hannuna idan har naji to tabbas kece kika fadeta Dan haka wanaan wayar itace zata debemun kewar masoyiyata"...Yana Gama magana ya daga Mata Kai alamar ta tafi ta Mike da sassarfa ta fita sukai kicibis da warisah xata Shiga wajensa.... ******* "Dik yadda zaayi ki tabbatar kin samomin wayar Nan a hannun yarinyar Nan Dan ban yadda da ita ba gabaki daya hankalina be kwanta da cewan da tayi in mallaka Mata wayaba"cike da tashin hankali take fadawa hansa'u wanan lamari.... Jijjiga Kai hansa'u takeyi cike da alhinin wanan maganar da uwargijiyata ke fada Mata zuciyarta cunkushe da tunanin yadda zata bullowa lamarin ta karbo..... *HASKE WRITERS ASSO💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY😍* [1/23, 11:42 AM] 😍SLIMZY😍: 34 Jiki a sanyaye ta shigo dakin bakinta dauke da sallama,kamar wadda takejin tsoro haka ta rakube daga gefe ta sadda kanta kasa gabanta na tsananta faduwa,...shiko wani mugun kallo yake jifanta dashi tun shigowarta dakin kusan minti goma Babu Wanda ya cewa Dan uwansa uffan yasa warisah sadakarwa bakinta na karkarwa "barka da tashi ya zainul ,ya jikin?fatan kasamu lafiya"ta dago manyan idanuwanta ta sauke Masa su,...wata muguwar harara da ya watsa Mata itace tasa hantar cikinta wani irin kuwwa Amma saita daure,ko tanka Mata beyiba ya maida Kansa gefe suna Nan zaune malam zubair ya shigo hannunsa dauke da robar ruwan addua na rubutu da yayo Masa Shima sallamar yayi ya shigo dakyar zainul ya bude Baki ya amsa Masa ciki ciki,malam zubairu bedamu da hakan ba ya cigaba da magana "ranka ya Dade ya karfin jikin? fatan kasamu lafiya, yanzun me kakeji?"ya Watso Masa tambaya Yana maida hankali Kansa, Dakyar zainul ya bude Baki tamkar me ciwo a bakin yace "da sauki Babu abinda ke damuna"yace a takaice... Gyada Kai malam yayi cike da gamsuwa "Masha allahu ga ruwan addua na kawo da turare Wanda Zan shafa maka hade yake da habbatusauda da zaitun ciki anjima da yamma Ma zanzo in shafa maka safe da yamma"... batare da yace komiba ya gyada Masa Kai,...sai kawai ya juya sashen da warisah ke zaune ta sadda kanta kasa Tana Wasa da yatsunta cikin daga murya hade da tsawa yace "ke uban me kikemun a daki har yanzun Baki fitaba?"...a firgice ta dago Dara daran idanuwanta Tana kallonsa "Ina magana kin kafeni da Ido tamkar wata mayya?xaki fita ko sai na Kira fadawa sun fiddaki?"...take idanuwanta suka kawo ruwa ta Mike jiki Babu kwari Tai hanyar fita,dakyar take Jan kafarta har ta Kai kofa ta juyo ta kallesa taga shi yake bin ta da mugun kallo, haka ta rufo kofar ta tsaya ta baya ta danne bayanta da jikin kofar Tana maida numfashi hawaye na sauka daga idanuwanta....shiru tayi tsaye har wajen minti arbain tana tsaye wajen Saida taji alamar motsi zaa fito sanan tayi saurin barin wajen..... ******** Koda suke fito da kaya daga gidan haka jamaa sukai cirko cirko kofar gidan cike da tsaigumi wasu na murna wasu har zubda hawaye sukeyi cike da jimami da tausayinsu dik yadda makota sukaso da su ji inda zasu koma Babu Wanda suka fadawa dakyar ummaty ta fito ta Shiga motar abokin Haris al'ameen Wanda sukazo tare dik zazzabi take fama dashi gashi ta zabge ta rame sosai.....tayi fari sosai ta cikin glass take kallon unguwar Tana zubda hawaye cike da takaici haka suka tattara sukabar unguwar.... Gida ne Mai kyau Dan karamin daidai zamansu da Dan madaidaicin parlor Mai kujeru set daya da dining area yayi kyau sosai tare sukai gyaran gidan da haris da al'ameen har suka Gama sanan suka fice tare... "Innah nikam bansan da wani Baki zamuyi wa haris godiya ba" .jinjina Kai innah tayi "wallahi kuwa hidimar tayi yawa ummaty nikaina narasa bakin magana saidai muce Allah ya saka mishi da alheri" Kwalla ce ta ciko a idanuwan ummaty ta marairaice "innah yanzun shikenan bazan sake ganin ya zainul ba?wallahi nadamu jiya har mafarkinsa nayi bansan halin da yake ciki ba innah Allah sarki Babu me tayashi Hira innah"....shiru innah tayi tana sauraronta tausayin Yar tata ya Kara kamata sai ta danne Dan kada ta karya mata zuciya "hakuri zakiyi ummaty kiyi addua idan kinada rabon Kara rayuwa dashi zakiyi ummaty Koda zumunci ne Dan zainul abideen yanzun yafi karfinka kinji?"...gyada mata Kai ummaty tayi Tana share kwallar dake zubo Mata dai dai Nan haris yayi sallama hannunsa dauke da take away biyu da drinks da sallamarsa ya shigo innah ta karba Masa cike da kulawa.... ******* Bayan sati daya da faruwar lamarin cikin kankanin lokaci zainul abideen ya warke tasss sai Dan abinda baa rasa ba domin yanzun da kafafuwansa yake takawa kowa sai Sam barka yakeyi.. Ta fannin gimbiya rumana kuwa ta Gama haukacewa hade da furgicewa dik Wanda tasa binciken ummaty baa samu inda suke ba gashi abubuwa sunyi mata yawa ta rame sosai ta danyi Baki tunda ta ziyarci wajen bokanta ya sanar da ita ta tabbatar da ta samu yarinyar Nan domin Nan da kankanin lokaci asiri zai iya tonuwa... Cikin tsananin tashin hankali take duban yusha'u Wanda yake durkushe a gabanta "yusha'u idan har kasamomin inda ummaty take to tabbas nayi maka alkawarin gida harda kujerar makka matukar ansamu abinda akeso ka kokarta" "Ranki ya Dade dik garin Nan Babu inda ban leka ba neman su Amma bansame suba hatta unguwar da suka Bari nayi bincike Babu Wanda yasan inda suka koma ranki ya Dade dikda an tabbatar mun ba garin suka Bari ba" Sintiri ta shigayi cikin patlorn tana shawagi dik ta fita hayyacinta babban tashin hankali take ciki tasani tabbas bokanta bai taba buga kasa ya fada Mata karya ba to yanzun menene abunyi?" ******* Shigowar haris ya Sanya momy dago idanuwanta ta cikin farin glashi tana watsa Masa harara sanan ta kalli agogon hannunta "karfe nawa yanzun haris?daga Ina kake?shin Wai ma in tambayeka kasamu aikine yasa cikin sati dayan Nan baka wuni a cikin gidan Nan?idan ka fita tun safe sai dare bansan gidan uban da kake zuwaba"tayi kwafa, . Shafa Kansa ya shigayi ya sani bashi da ta cewa Dan beda gaskiya Dan haka sai ya kaskantar da muryarsa "kiyi hakuri momy wallahi kwana biyun Nan muna can inda al'ameen yake gini muna lura da wajen kinsan ya kusa sure momy" "Ya kusa aure kaikuma kana Nan kana binsa zarau zarau kamar wani lagwani Kai bakada niyyar auren kenan ko?to ka Shiga taitayinka nafada maka ban hanaka bin abokinka harkoki ba Amma ka sama Mana namu lokacin kana gani yau saura kwana hudu abbanku ya dawo ya Dace ayi Masa shiri Amma baka samu lokaci ba balle mu zanta" "Kiyi hakuri momy andaina kinji ranki ya Dade"ya rike kunnuwansa yanayi mata dariya ta Kai Masa bugun Wasa ya goce yayi hanyar dakinsa Yana dariya.... ********* Zaune yake cikin Riga da wando jeans da polo shirt blue sun matukar karbar jikinsa saye yake da facing cap hannunsa rike da wayar ummaty ya Shiga gallary dinta hoto kwaya d'aya ne ciki Wanda ta dauki kanta da bakar Riga tayi masifar kyau ya kure hoton da idanuwa minti minti yakan sauke ajiyar zuciya....jujjuya wayar ya shigayi wani tunani ne ya darsu Masa cikin zuciya shin waye ya siyawa ummaty wanan wayar?shi ya fara zo Masa Dan Yana ganinta da wayar a kwanakin Nan Amma be taba tambayarta ba ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yaji motsin shigowa Dan hakan sai kawai ya jefa wayar cikin aljihunsa amminsa ce ta shigo dakin ta nemi waje ta zauna fuskarta dauke da damuwa.... "Zainul abideen"ta Kira sunansa cikin sanyin murya... Memakon ya amsa sai kawai ya dubeta ya maida hankali kanta hade da kafeta da idanuwa alamar Yana sauraronta... "Shin zaman da kakeyi hakan Kai kadai batare da kowa ba kana ganin bazai haifar maka da wani ciwonba?gashi ka gayyato damuwa ka sawa rayuwarka da zuciyarka abbanka yace tunda ka samu lafiya matukar baka Kori damuwa ka gayyato farin ciki ba aure zaiyi maka,kila matar ta sama maka farin ciki"... Murmushin gefen kumatu yayi "ammiey ya zaayi ku ganni farin ciki bayan da kanku kuka rabani da farin cikin?...damuwa ko bani na gayyato ta ba itace tazo da kanta ta samawa kanta mazauni a gurbin da farin cikin ya tafi,bani da wani farin ciki Wanda ya wuce samun ummaty a kusa Dani inhar bansameta ba to tabbas nagama dariya harabada" Kallonsa kawai takeyi zuciyarta Babu Dadi samm ta rasa yadda zatayi da zainul Akan wanan mayyar yarinyar...kallonsa takeyi Shima kallon nata yakeyi cikin kankanin lokaci idanuwansa suka canja kala sukai jajir "ammiey ki tallafi rayuwata ayi bincike Akan wanan lamarin Dan zuciyata na fadamin sharri akai Mata" "Ba sharri akai Mata ba zainul gaskiya ce domin Kai da kanka kaga video din da kanka ya Dace ka yarda kodan wadanan hujjojin" Cike da takaici yace "ammiey baxan taba yarda ba bazan taba amincewa ummaty zata cutar Dani ba ammiey ku duba wanan lamarin ku dawo da ita gareni"... Mikewa tsaye tayi "sai kayi ai nidai nafada maka gaskiya idan kaga zaka dauka ka dauka idan damuwar zaka cigaba bismillah"Tai tafiyarta cikin fushi ta bugo kofar... Iska ya kaiwa naushi cike da takaici ta Mike Shima yayi hanyar waje... Kicibis yayi da ita a hanyar shigowa sashin tana ganinsa gabanta ya Fadi yadda ya daura fuskarsa tun daga nesa yake watsa Mata kallo tamkar yaga Kashi da sauri tace "ya zainul Ina yini wajenka nazo dama" "Uban me Zanyi Miki?ke waini saan wasanki ne warisah ki Shiga hankalinki idan ba haka ba zanbaki mamaki"Yana Gama fadin haka yayi gaba abinsa ta bisa da kallo idanuwanta cike da hawaye ga bugun zuciyarta daya tsananta ta Sanya hannu gefen zuciyarta ta dafe ta soma tafiya.... Driver ya nema Nan da Nan sai gashi ta zo"fita Dani zakayi zuwa sabuwar unguwa a hankali nakeso ka taka Dani inaso Inga gari ne".... ****** Sanye take da hijjabinta a parlor ta tadda haris zaune Yana cin shin kafa da wake suna hada Ido ya kashe Mata Ido daya ta Dan hararesa "sai Kuma Ina?"yace Yana kallonta... "Nidai ya haris fita Zanyi in zagayo ta titi don nagaji da zaman gidan Nan wallahi kafafuna dik sunyi tsami," Murmushi yayi Mata "kijirani ingama muje to" Kada Kai tayi "na hutar dakai ka zauna da mama a gida yanzun Zan dawo Dan na rigada na shirya ban iya jiranka"Tai maganar cike da shagwaba... Tabe Baki yayi cikin sigar tsokana "kije Zanyi Hira da innah ta Kuma karki Dade"ya kashe Mata Ido...itadai innah sai murmushi takeyi. "Naji insha allahu saina dawo"...har ta Kai kofa ya bita ya rada Mata wani Abu ta rufe idanuwanta tana dariya ta fice..... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* *HASKE WRITERS ASSO💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY😍* [1/23, 11:43 AM] 😍SLIMZY😍: 35 Tafe take gefen titi hankalinta gabaki daya Yana can wani waje ga gaban da ya tsananta faduwa minti minti takan juya gefe da gefen hanya tana waige waige....ko Ina shiru ne wajen sai kukan tsuntsaye ga gidaje rerassss masu shegen kyau tamkar ba cikin garin da sukeba haka kawai ta tsinci kanta cikin tsananin nishadi Wanda rabinta da hakan tun kwana goma da suka wuce... Tafe suke a mota ya tsurawa titi Ido tamkar wani ba kauye minti minti yakan sauke ajiyar zuciya wadda besan dalilinta ba,...juyowa yayi da Kansa gefensa na dama ya tsurawa gefen Ido tun daga nesa yake hangen tafiyarta da bayan hijjabinta Wanda ya Sanya shi saurin saka hannunsa ya murza idonsa ya budesa tamkar Wanda ya tashi daga bacci Kara murzar idonsa yakeyi Yana kallonta sosai ko a mafarki yaga kirar jikinta ko a cikin kurgumin duhu ne inhar zaa haskata to tabbas sai ya ganeta har sukazo gaffff da ita da sauri ya dubi driver cikin daga murya yace "tsayasaaaaaa Dan liti"a tsorace yaja burki "ranka ya Dade me kake bukata?kayi hakuri Ina gudu ko,? Ko ta kan Dan liti beyiba ya fito a guje ya ruga gareta tana Shirin tsallaka titi ya ruko hijjabinta...cikin azama ta juyo da niyyar ganin ko wani Dan rainin wayau ne ya shakota sukai Ido hudu....cakkk ta tsaya dik wata hanya ta sadarwa dake jikinta Saida ta tsaya,,,,kallon juna sukeyi Ido cikin Ido ko kiftawa basayi....runtse idanuwanta ta shigayi tana furta "idan mafarki nakeyi bana fatan Allah ya farkar Dani daga wanan mafarkin me niima da Dadi .....gani ga ya zainul....Allah karka farkar Dani daga mafarkin Nan"...tana magana idanuwanta a runtse...hawaye na sauka daga cikin idanuwanta,...shiko tsaye yayi Yana kallon yadda bakinta ke motsawa,zucuyarsa na Kara bugu tamkar ana kada ganga ga wani mugun tausayinta daya lullubesa idanuwansa gabaki daya sun canja launi sun dauki lokaci Mai tsawo a haka ganin da gaske takeyi batada niyyar bude idanuwanta gani takeyi tamkar baccin takeyi yasashi matsawa daffff da ita ya Shiga hura Mata iskar bakinsa Mai sanyi da kamshin minti da ya gama tsotsa...a hankali take bude idanuwanta a Kansa ba tare da ta daina zubar hawaye ba...."kukan me kikeyi ummaty?...Ashe inada Rabon sake ganinki a duniya?" Girgiza Kai tayi "gani nakeyi kamar mafarki nakeyi ya zainul ji nakeyi tamkar baa cikin duniyar da nake rayuwa bace,kuka na biyu ne na farko dai na farin cikin ganinka tsaye da kafafuwanka a doron kasa Babu wanan nakasar danasani Allah ya cikamun burina na samun lafiyarka dikda bani nayi sanadinta ba,...babban bakin cikina be wuce ka farka an sanar maka da mugun labarin cewar ga abubuwan Dana aikata maka ba shekara da shekaru...wallahi summa tallahi ya zainul ban..."rufe mata Baki yayi ganin dik yadda ta dimauce kuka Yana neman cin karfinta ba...girgiza Kansa ya shigayi alamar ta bar kukan ya sa hannu ya Shiga share Mata hawaye Yana jifanta da wani irin mayen kallo Wanda ke Kara narkar Mata da zuciya...ruko hannunta yayi Babu musu tabi bayansa har cikin mota yayi musu masauki a baya,ta gilashin mota sukai Ido hudu da Dan liti yace "bamu waje"..cikin azama Dan liti ya bude mota ya fice ya barsu ciki ya rufo musu kofofin motar... "Share hawayenki"yace Mata Yana daura fuskarsa tamkar be taba dariya ba,kallonsa takeyi Ido cikin Ido ganin ya tsareta da Ido yasanya ta sadda kanta kasa ga wani mugun kwarjini da yayi Mata yadda ya tsare gida tamkar ba zainul abideen din da ta sani ba gabaki daya ya canja yayi mugun kyau ga sarauta da yake takama da ita..."idan kika Kara yimun asarar hawayenki ummaty Allah sai na ladabtar dake Dan Babu abinda na tsana dik duniyar Nan sama da ganin hawayenki sanan Babu abinda nake kauna kamar kyakkyawan murmushin Nan naki wadda yake bayyana ainihin kyawu da Allah yayi Miki....inaso ki kwantar da hankalinki Akan maganar da take yawo a gari cewan kin nemi hallakani Allah beyi ba nasani na tabbatar ummu salmata Yar aljannah ce ko cinnaka bazaki taba kashewa ba balle Dan mutum na yarda dake na amince dake dari bisa dari kinji?"...murmushi ta sauke hade da ajiyar zuciya Mai nauyi take ta tsinci kanta cikin tsananin nishadi Wanda ya haifar Mata da murmushi Wanda ya kasa gushewa daga fuskarta...ganin Bata da niyyar dago fuskarta yasanya shi sa hannunsa a habarta ya dago fuskarta suka hada Ido ta runtse Ido tanajin bugun zuciyarta na tsananta....dayan hannunsa yasanya ya shafo fuskarta tun daga goshinta har zuwa lips dinta Yana yawo da yatsansa...Yana kallo yadda kirjinta ke sama da kasa alamar bugun zuciyarta ya tsananta Dan haka murmushin gefen fuska yayi yanajin wata iriyar kasala na shigarsa tun daga Kansa har tafin kafarsa..ita kanta Bata taba tsintar kanta cikin wanan yanayin ba Mara misaltuwa wani irin Abu ke Yi Mata yawo cikin jiki tamkar magana disu...dukkansu sun shagaltu kusan minti goma Sha biyar sanan yayi gyaran murya ya saki habarta Wanda yasata sauri rufe fuskarta da tafukan hannayenta... "Ummaty Ina sonki"ya furta cikin wata irin murya wadda batasanshi da ita ba,...da sauri ta kallesa ya kashe Mata Ido hade da dage girarsa sama Babu alamar Wasa a fuskarsa ya cigaba da magana "zakice bakisan Ina sonki bane?Koko kinaso kicemun ke Baki Sona ummu Salma,...hmmmm look wallahi summa tallahi Ina sonki Ina kaunarki Kuma banajin akwai abinda zai rabani dake dik runtsi dik wuya....na shiryawa gagarumin yaki ko wani irine ummaty indai akanki ne sanan idan Allah ya kaimu gobe Zan sanarwa da Mai martaba muradina" Tsoro ne ya cikata yadda yake maganar Amma kwarjinin da yayi Mata ya hanata cewar komi sai gyada kanta kawai takeyi cike da faduwar gaba..dago Kai tayi ta cikin glass din motar Tana duban waje taga gari har ya soma duhu alamar magriba tayi ta dubesa cikin marairaicewa "ya zainul magriba tayi inaso inje gida" "Kinaso kije gida Koko muje Inga inda kike?"..take tsoro ya cikata tunawa da tayi haris Yana gidansu sanan bataso yarima zainul yasan cewar haris ne ya Basu wajen Zama da kyar ta hadiyi mugun miyau ta tattaro dik wata natsuwarta tana yake tace "ya zainul baba bayaso kowa yasan inda muka koma Ina ganin idan har ya ganmu zaiga kamar nice na biyoka na kawoka gidanmu"...wani irin kallo yake watsa mata Wanda ya sata Babu shiri ta Shiga taitayinta "nayi Imani da Allah baba Dan ya ganni a gidansa bazai taba korata ba domin Nima da'nsa ne kamar yadda kike yarsa Dan haka gyara Zama zakiyi ki Nuna mana hanya....sauke glass yayi ya yafito Dan liti dake gefen titi yanata rawar sanyi,a guje ya rugo ya zube a kasa "gani ranka ya Dade" "Shigo ka jamu ummaty zata Nuna maka hanya"...da sauri ya zagaya maxaunin driver ya tada mota suka dau hanya... *WANAN LITTAFIN NA KUDINE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*... minti minti yakan kalli agogon wayarsa Yana duban lokaci har yanzun Bata dawo ba cike da damuwa ya dubi innah wadda ke zaune tana Jan carbi yace "innah har yanzun ummaty Bata shigo ba kaddai tayi makuwar hanya" "Bazatayi makuwa ba haris ai ummaty akwai ganuwar hanya inaga dai kila ta biya wani wajene"...gyada Kansa kawai yayi badan zucuyarsa ta aminta da fitar Nan tata ba fatansa da burinsaa Allah yasadai ba wani bane ya tareta Nan take taji wani kishi ya rufesa...zaiyi magana kenan wayarsa ta Shiga ruri Yana dagowa yaga sweet momy ... gabansa ne ya Fadi yasan zaisha fada Dan tun safe ya baro gida be komaba gashi mahaifinsa yau zai dawo lallai ya tafka babban laifi hakanan ya daure ya Danna recieve ya Kara a kunnensa "hello sweet heart"yace cike da zolaya "Dik inda kake kazo gida Nanda minti goma Dan daddynka ya dawo tun dazun baka a gida idan ba haka ba saina sassaba maka shasha Sha kawai"ta kashe wayar cike da bacin Rai...bin wayar yayi da kallo ya tabe Baki gefe daya farin ciki ne ya cikasa na zai samu muradin ransa ummaty Dan yau baa kwana be fadawa mahaifinsa maganarta ba kuma yasan zai Goya mishi baya Dan haka mikewa yayi ya dubi innah "innah Bari inje gida momy na kirana daddynmu ya dawo daga London" "Kai Masha allahu to a gaida gida ayi Masa sannu da zuwa kaji" "Insha allahu zaiji innah" "Ga ummatyn Bata dawo ba har yanzun" .cije Baki yayi beso hakan ba Dan bayaji yau zai runtsa yadda be ganta sunyi sallama ba hakanan yayi hanyar kofar gidan,Yana fitowa yaja motarsa a guje ya bar kofar gidan daidai kwanar fita unguwar sukai clashing da motar yarima....kallo haris yabi motar dashi tamkar yasan motar saidai an tada kura baya iya hango lambar motar balle yasan waye.... Har kofar gida suka kawota sun Dade cikin motar suna musayar kalamai masu sanyi da ratsa zuciyar masiya ta bude kofar motar zata fita ya fizgota ta fada jikinsa ya kafeta da wani mayen kallo da narkakken idanuwansa a hankali ta Shiga kwace jikinta saboda yadda taji kasala na neman rufeta shi Kansa jikinsa a sake yake fitarta kawai ya gani a guje Tana murmushi shafa Kansa yayi Shima yana murmushin hade da lumshe shanyayyun idanuwansa.... ******** "Kace yarinyar Yar sarkin dawaki ce?"dady ke tambayar haris bayan ya Gama rattabo mishi labari Dan haka da sauri ta kada Kansa.. Murmushi irin na manya daddy yayi "to alhamdulillahi indai yarinyar da kake magana ce tanada tarbiyya ummu Salma sanan shi Kansa sarkin dawaki mutumin kirki ne Dan haka Zan sameshi da maganar zuwa jibi.."farin ciki ne ya lullube haris har baya iya rufe bakinsa saboda farin ciki...yayita wa daddynsa godiya ,dik maganar da sukeyi momy batasan wainar da ake toyawa ba koda tayi sallama ta shigo patlorn shiru haris yayi gudun kada taji Aiko dady ya Shiga zayyano Mata.... ******** Zazzabi me zafi ya rufeta a kuryar daki ta rasa yadda zatayi dik maganin duniya Tasha Amma yaki sauka ga mugun ciwon kirji gefe daya da take fama dashi kusan sati uku kenan Taki fadawa kowa dik ta rame ta fita hayyacinta...wayarta ta janyo ta Shiga foldern din hotuna ta bude wasu hotunansa ne guda biyu Wanda haris yayi Masa gab da zaiji sauki ta bude tana kallo tana murmushi warisah kenan wadda ciwon soyayya ke neman yin ajalinta ta shagala wajen kallon hotonsa Wanda ya zame mata kamar aikinyi bataci Bata Sha sai an tsareta...tari ne ya taso mata taitayi da sauri ta fada toilet Jin tamkar zatayi amai tarin bai sauka ba taji wani Abu na taso Mata daga makogwaro ta kakoshi kasa tamkar majina zaro Ido tayi lokacin da tayi tozali da gudan jini....ta kara kako wani Shima jinin ne innalillahi wa Inna ilaihi rajiun...Nan da Nan idanuwanta suka cicciko da hawaye daidai Nan momy ta turo kofar toilet din ta shigo tana Kiran sunan warisah..... *HASKE WRITERS ASSO💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY😍* [1/23, 11:43 AM] 😍SLIMZY😍: 36 "Innalillahi wa innah ilaihi rajiun shine abinda hajiya kubrah ke furtawa jikinta na tsananin rawa ta shiga cikin toilet din ta ruke warisah wadda dik ta galabaita saboda amai ga wata irin Rama da tayi wadda ita kanta bata lurada hakan ba sai yau "warisah meke damunki babyna?meyasameki haka?"..cikin tashin hankali takeyi mata tambayar...gaban warisah ne ya fadi cike da tsoro ta kalli fuskar momy sai ta kauda kanta gefe Dan bata shirya sanar mata da ta dade da hakan ba kuma Bata shirya fallasa sirrin zuciyarta ba Dan haka sai kawai dabara ta Fado mata ta danyi tari kadan sanan a wahale tace "momy wallahi wani irin tari ne nake fama dashi idan na Soma sai nayi amai kuma harda jini ciki inaga mura ce tayi mummunan kamani"..cikin rashin yarda momy ke kallon kwayar idanun warisah Tana so ta hango wani Abu Amma dik yadda ta Kai ga karantar ta takasa hango karya a kwayar idanun nata cikin mutuwaar jiki momy tace "Amma wanan wani irin tari ne kikeyi hadda jini guda guda da Dan yawa hakan?nasan cewar inhar mutum na tari me jini to zaiyishi Amma bada jini sosai ba naga naki yayi yawa shikenan Bari muje asibiti gobe idan Allah ya kaimu sai a Baki maganin taarin kinji?"gyada mata Kai warisah tayi fuskarta dauke da murmushi na dole har yanzun momy rike da ita take haka suka fito toilet din Tana karantar yanayin yartata Wanda samm Bata yarda zancen warisah ba koma menene dai zata kaita asibiti kuma likita zai bincike mata ita... ******* Wajen karfe daya na dare juyi takeyi kawai Amma bacci ya kasa daukanta gabaki daya hankalinta na wajen shi dik motsinta da bugun zuciyarta hade da saukan numfashinta Tana yinsu ne tare da soyayyar zainul abideen wadda take yawo a cikin jinin jikinta da b'argonta...gyara kwanciyarta tayi ta Mika hannunta gefen drawer din gadon ta ta janyo wayarta ta shiga typing massage jikinta har rawa takeyi.... It's seems like I can do without u ya zainul I luv u beyond ur expectations save my life...it's warisah....ta dade Tana karanta massage din tamkar bazata tura ba haka tayi shahada ta tura massage din hade da runtse ido... Wayarsa ce tayi haske alamar massage ya shigo lokacin Yana zaune kan dadduma ya idar da sallah Yana tasbihi da rokon Allah gefensa alkurani ne me girma a kusa dashi wayar tasa take,Dan haka da sauri ya dauki wayar ganin wanene yayi Masa massage da wanan Daren zuciyarsa na darrrr darrr ya bude massage din ganin bakuwar number ce yasashi saurin fara karantawa...Saida ya Kare karantawa ya tabe bakinsa ya wulla wayar kan gado hade da dafa kansa cike da takaici ya rasa yadda zaiyi da wanan yarinyar kamar mayya metake nufi da wanan massage din?shine zatacewa ya ceci rayuwarta?Aiko indai soyayyarshi ce to gaskiya Yana tsammanin zata mutu,...zuciyarsa ke ayyana Masa Anya yarinyar nan zata barshi yasha ruwa?ta barsa da abinda yakeji Mana a jikinsa na rashin masoyiyarsa a tare dashi lokacin da yafi bukatarta?...inaga idan har be yi mata mummunan rashin mutunci ba bazata sakar Masa Mara yayi fitsari ba Yana neman mafita akan ummaty Tana kokarin hasa mishi wata sabuwar wuta...Dan tsaki yayi hade da yin auzubillahi minasshaidanin rajim..ya Kori shaidan sanan ya janyo alkuraninsa ya bude suratul yaseen Yana karantawa.... ******** Ko kafin safiya jikin warisah yayi zafi sosai Amma Bata fadawa kowa ba sai aukin Shan magunguna da takeyi Wanda ba likita ya rubuta mata ba yau ma hakan ta kasance kusan karfe goma na safe Tana nade cikin bargo rike da waya tana jiran tsammanin massage dinta Koda na zagi ne tasamu taji sanyi... A parlor hajiya kubrah ta shirya tsaf cikin leshinta me kyaun gaske da tsada suna breakfast itada daddy mahaifinsu soyayye Irish da kwai da pepe soup din kayan ciki suke breakfast dashi....a yangance take cin abincin lokacin da daddy ya kurbi tea ya ajiye cup ya dubeta yace "momyn Yara wai Ina babyna ne?tunda na dawo sau daya na ganta,yanzun gashi muna breakfast ban ganta ba Ina ta shiga ne?ko tana gidan Mai martaba ne?" "Tun jiya nakeson sanar dakai batada lafiya yanzun haka Shirin da nayi kenan da nagama breakfast zanje in lallabeta taci ko kadan ne inkaita likita ya cajemun ita dikda tace tana fama da tari" "Toh hakan nada kyau nima idan an sakko masallaci anjima Zan dauki alhaji madu muje nemawa Dana aure" Cikin rashin fahimta momy ke kallon daddy Wanda ke aika pepe soup bakinsa "ban gane nemawa Danka aureba,Dan alhaji madu ne zaiyi aure?" Nisawa yayi kadan "ai alhaji madu bashi da yaro namiji karami ne Ina nufin haris Mana ya samu matar aure" "Wai haris nawa kake nufi?tabdijan wacece matar da har ni besanar Dani ba Kai ya sanar da Kai?wato inda baka fadamin ba sai kun gama abinku zanji kenan" "Ummu Salma ce diyar sarkin dawaki"... Wani irin zabura tayi ta Mike daga zaunen da take ta tsaya da kafafuwanta jikinta har rawa yakeyi ta bude Baki zatayi magana daidai nan haris ya shigo Aiko tayi kansa da masifa "munafuki dama abinda kake kullawa kenan yasa idan ka fita sai dare kake dawowa?yarinyar da ta nemi kashe Dan uwanka da badan Allah yasa Yana da kwana gaba ba da yanzun ya bakunci lahira ita zaka kwasomin a matsayin sirika?uwar jikokina?wanan karya ne wallahi ni bazan taba hada jini da kaskantattun talakawa kamar iyalin sarkin dawaki ba wlhy baka Isa ba"..neman waje haris yayi ya zauna batare da yace komiba,daddy ne ya dubeta a kaikaice fuskarsa babu walwala "Hajiya kubrah kinsan abinda kike fada kuwa?har kikewa Allah izgilancin bazaki hada jini da talaka ba?Allah kike fadawa koni?Ina Allah ne ya haliccesu talakawa yayoki me arziki?to Baki isaba idan kinada iko da haris nima inada iko da shi tunda nine ubansa ni Zan nema Masa auren ko?to idan Kinga baaayi auren nan ba Allah ne beyiba shasha Sha"...makullin mota ya dauka ya fice haris ya take Masa baya suka barta nan tana babatun masifa.... ********* Dik yadda likita yaso ya duba warisah kuka ta sa mishi a dakin ganin likita babu yadda yaso haka ya kyaleta,sanan ta rokeshi akan ya rufa mata asiri kar ya fadawa mahaifiyarta sosai tabawa doctor Abdul tausayi har zata fita ya karbi number wayarta ya rubuta mata magunguna kamar yadda ta bukata ya Bata ta fice dakyar take taka kafarta ta samu momy a reception nan ma ta tsula mata wata karyar haka momy tabi maganarta suka fito dama driver su yake jira Koda suka shiga motar ce Masa tayi ya kaita gidan sarki....babu musu ya tada mota suka dau hanya.... ******** "Tarba me kyau sarkin dawaki yayiwa iyayen haris inda suka gama komi har kudin nagani inaso suka bada sanan suka tafi cike da jin dadin karamcin da dattijon yayi musu.. Tagumi ummaty ta rafka minti minti takan sauke ajiyar zuciya ita kadai tasan zullumin da take ciki batama Isa ta furtawa haris Bata sonsa ba saboda yayi musu halacci. Da ba dik namiji ba ya tallafi rayuwarsu da yanzun basusan inda suke ba tunda gidan da suke ciki kansa nasa ne to Amma ya zatayi da soyayyar zainul abideen Wanda ta ginu akanta tun batasan kanta ba?soyayyar da ta kasance itace rayuwarta ita kanta?....Anya bataci amanar zainul abideen ba?...to haris fa Wanda babu dare babu rana yake kan hidima dasu?yau ya zatayi da baba idan zainul yazo kofar gidansu?idan Bata manta ba yau yace zaizo wajenta idan an sakko masallacin jumaa ,kuma batajin zataki fita wajen sanyin idaniyarta Wanda tun jiya take mafarkin haduwarsu ta yau adduarta daya Allah kada yasa haris yazo sai zainul yazo ya tafi Dan haka ma zata zauna gaf da gate dinsu Dan taji zuwansa Dan haka yar farar kujera ta dauko ta Baro parkorn...dik yanayinta innah na lura da ita Dan haka Koda ta dauki kujera ta nufi waje innah na biye da ita har ta sa kujera zata zauna Inna ta katse ta, "Waike ummaty dik yanayinki ya nuna kamar kinada damuwa a tattare dake kamar bakya farin ciki da wanan baiwa da Allah yayi miki kin zauna sai tunane tunane kikeyi ko me kike tunani oho"...nisawa ummaty tayi ta sauke ajiyar zuciya "innah wallahi Ina cikin damuwa " "Tamene?" "Damuwata ya zainul kamar banyi Masa adalci ba" Sarkin dawaki ya karbe zancen "maganar banza maganar wofi ke har yaushe Zaki San cewar wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa?idan mafarki kikeyi ki farka Dan zainul yafi karfinki ke ko cewa yayi Yana sonki ban bashi ke Mara tunani kawai kin manta halacci irin na haris Koh?kina kokarin yi Masa butulci tun kafin akai ko Ina to Baki isaba wawuya kawai"shigewarsa ciki yayi innah tabi bayansa tana kada Kai nan suka bar ummaty Tana zubda hawaye.... Tana nan zaune ta rafka tagumi tana tunane tunane yaro ya shigo har zai wuce tayi saurin tararsa "Kai Ina zakaje?" "Wai ummaty tazo inji wani a waje".. Saida ta lalleka sanan tayi kasa da murya kadan "je kace ganinan zuwa". Da sauri yaron ya juya Yana fita ta leka ciki taga Inna ta maida hankalinta kan tv tayi wufff ta fice harta fita dabara ta Fado Mata ta dawo tace haris ne yazo zai wuce sauri yakeyi Bari ta Gandhi innah tace to ta fice.... Yana sanye cikin dakakkiyar shadda light blue gezna sai zuba kamshi yakeyi na turarruka kala kala Karin hularsa ya zauna akansa dasss ga sajensa da ya kawata fuskarsa Wanda ya fito da ainihin kyawu nasa irin na Fulani.... Da sallamarta ta shigo motar dik fuskarta babu walwala Amma kallon da tayi Masa kadai batasan lokacin da ta sauke ajiyar zuciya ba,sun dauki mintuna kafin ta katse Shirun da "barka da yammaci takawa"...beko amsata ba ya jeho mata tambaya a Karo na farko "Fuskarki babu walwala tamkar wani Abu Yana damunki akwai wani Abu ne?"ya tsareta da idanuwansa dake kara narkar mata da zuciya... Kwalla ce ta ciko a idanuwanta tai narai narai da ido "wai an kawo kudin nagani inaso nawa baba kuma ya amsa" "Wani me gangancin ne ya keso ya shiga gonar da ba tasa ba?ko waye kuwa yayi tsaurin ido don wallahi ummu Salma tawa ce ni kadai"yayi maganar cike da Isa da izzah Yana shafar sajensa fuskarsa dauke da murmushi... Hawayene suka sulalo Mata a fuska yayi saurin ruko kanta ya shiga share Mata hawaye batare da yace komi ba da kyar ya furta "shhhhhhhh banason hawayen kiyi shiru kinji ya Isa"cikin sigar lallashi yayi maganar Amma fuskar nan a daure tamkar ba zainul din da ta saniba dik ya canja ..hakanan batada zabin daya wuce bun umarninsa ta share hawayen suka shiga hirarsu ta masoya..... ******** Baabah kande ce labe jikin kofa tana sauraron hirar gimbiya rumana da hansa'u "kin tabbatar kin zuba gubar nan cikin abincin zainul abideen?Dan inaso yau ba sai gobe ba ya bakunci lahira ko kuma ya koma gidan jiya" . Kara saurarawa baabah kande tayi cike da fargaba wani abincin aka zubawa magani to?"Bata karashe tunani ba ta tsinkayo muryar hansa'u "a cikin burabusko nasa da farfesun Naman Kai kinsan su yafi so nasan inhar abincin nan ya Isa sashensa to babu abinda zai hanasa cinshi" "Yauwa hansa'u nagode tashi kije da ya shigo ki fadamin zanje sashen nasa da kaina sai Naga yaci abincin"...jinjina Kai baabah kande tayi a fili ta furta "Allah yasa ya zama silar tonon asirinki"...ta juya Tana tunanin yadda zata bullowa lamarin... *WANAN LITTAFIN NA KUDINE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* ******** Tana fitowa motar zainul motar haris nayin parking a kofar gidan Dan haka shidai zainul yaga mota besan Kota waye ba Amma tunaninsa ya basa kila gidan da suke Basu kadai bane kila BQ. Suke shi kawai ya kawo a ransa Dan haka yaja motarsa yayi gaba Dan ko yan rakiya be daukaba gudun gulma.... Wani kallon haris ke watsawa ummaty cike da bacin Rai hade da tsananin kishi ita kanta ta lura da hakan shiyasa ma ta basar Bata nuna ta furgita da ganinsa ba dikda ta tsorata ainin Dan bataso su hadu da zainul Dan haka dakewa tayi ta murje idonta "barka da isowa ya haris Ashe kana hanya?"ta kauda kanta taki hada ido dashi... A dakile ya amsa da "ehh"kawai yasa kansa yayi cikin gida tana biye dashi gabanta na dukan Tara tara😂😂😂😂 ******* Tun daga hanya ya lalubi wayar ummaty dake aljihunsa wadda yaje da niyyar Bata ya manta sai kawai ya shiga dube dube direct sashensa ya wuce hannunsa rike da hularsa...uwale ce a sashen tana goge goge ya kalleta kadan "ajiye goge gogen nan ki fice inada bukatar hutawa"... "Ranka ya dade ga abinci nan a table burabusko da miyar ganye sai farfesun Naman Kai"...lumshe idanuwansa yayi cike da nishadi ya nuna Mata hanya ta fice da sauri ta fice ta rufo Masa kofa ....tana fita yasa key...a hanya tai kicibis da gimbiya rumana tana tafe tana takunta tamkar bazata taka kasa ba tai hanyar sashen zainul..... *HASKE WRITERS ASSO💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY😍* [1/23, 11:44 AM] 😍SLIMZY😍: 37 Bude kulolin abincin yayi wani daddadan kamshi ya dake hancinsa Wanda ya sashi shakar numfashi sama ya sauke hade da lumshe shabyayyun idanuwansa Wanda suke tamkar na Mata Koda yaushe a lumshe suke tamkar wani me jin bacci Dan haka juyowa yayi zuwa fridge dinsa ya bude ya Ciro lemo da ruwa ya Dora akan centre table sanan ya dubi agogo har bakwai ta gota,dafe goshinsa yayi tunawa da yayi beyi sallahr magriba ba ya wuce bedroom dinsa ya zare wandon jikinsa ya fada toilet Dan ya dauro alwala.... Bayan ya idar da sallah ya fito parlor ya kunna tv ya dauko kulolin abincin ya budesu ya zuba da kansa a plate ya Soma ci da Bismillah sosai burabusco din yayi Masa Dadi Yana ci Yana lumshe idanuwansa ya bude wayar ummaty ya Shiga bincike dik inda ya Shiga empty ne har ya Shiga play store....audios ya gani sunfi goma ya kada kansa hade da murmushi "ummaty kenan baiwar Allah kaf wayar nan Babu wata Waka sai audios din karatun alkurani"...batare da wani tunani ba ya bude audio guda daya.... ******** Sosai haris ya Bata tausayi yadda yanayinsa ya canja Koda suka Shiga cikin gida innah ta kofsa mata Dan tambayarsa tayi shida akace xai wuce shine ya shigo cikin gidan kuma?...juyowa yayi ya kalli ummaty take kunya ta lullubeta ta sadda kanta kasa jiki a sanyaye sai kawai ya cije lebensa zuciyarsa nayi Masa lugude ya tattaro dik wata jarumta gudun kada innah ta fahinci wani Abu yace "innah har na karya Kan mota Zan tafi kawai sai naji inaso in shigo in ganki mu gaisa inci tuwon darenki"...murmushi innah tayi ta kauda kanta gefe Dan yanzun kunyar haris takeyi tunda ya zamo surikinta Kujerar Roba ya janyo ya zauna sanan ya kalli ummaty wadda ke tsaye kamar an dasata ta kasa dago idanunta saboda kunya tayi Dan murmushi ke kin amshi soja ne da kika tsaya tsaye kusan awa guda?ki zauna Mana?ko Baki gaji da tsayuwar bane Captain ummu Salma"yayi maganar cike da zolaya Yana sane yayi hakan Dan ya fahinci kunya ce ta lullubeta, Turo Baki gaba tayi ta Dan hararesa sanan ta dubi innah "innah kinji me ya haris ke cemin ko?wai Captain ummu Salma"...maimakon innah tai magana yunkurawa tayi ta Mike tai hanyar sashin sarkin dawaki "kunfi kusa Kinga tafiyata ni"Tai shigewarta ta barsu nan.. Taku uku tayi zatayi gaba ya ruko hannunta ta tsaya cakkkk "Ina zakije bakiyimun bayayanin waye yazo wajen ki kika fita batare da izinina ba?waye wanan yake Shirin yin karambanin kawo kansa wajen matar wani?hmmmm ummaty kenan to ki sanar dashi tun wuri ya Kama gabansa Dan bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane kina ji Koh"...kici kici. Kwace hannunsa daga garesa ya rike ta kammm Yana Yi Mata wani irin kallo hade da aika Mata sakwanni kala kala.... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* ******** jijiyoyin kansa gabaki daya sun mimmike idanuwansa sunyi jajir ya Mike tsaye jikinsa har rawa yakeyi Yana sauraron wanan audios din da wanan ya Shiga ya gama wanan ya fita...dafe kansa yayi saboda yadda dakin yake juya Masa a guje tamkar Yana gudu cikin mota ...I can't believe....ummahhhhh ya kwalla Kara Yana juye juye cikin dakin.... ******** Ummaty ce kwance Kan cinyar innarta bayan tafiyar haris innar nayi Mata Susa cikin kanta tana sauraron redio "innah nikam inaso inji tarihin mu da tarihin muamalar mu da gidan sarki"...kada Kai innah tayi tana mamakin yadda ummaty ke bibiyarta akan wanan lamarin Amma ya zama dole yau ta sanar da ita Koda ba duka bane...... *HASKE WRITERS ASSO...💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY😍* [1/23, 11:44 AM] 😍SLIMZY😍: 38 Shekarun baya da suka wuce..... Sarki Muhammad shine mahaifi ga zainul abideen kamar yadda kika sani yanada Yara shida sakamakon matansa biyu ne,gimbiya rumana itace ta farko cikin matansa tanada Yara biyu da sarki Muhammad Zahra itace ta farko sai halima wadda ke bi Mata....gimbiya rumana ta kasance komenene sarki ita yake sawa a gaba saboda yadda yake balain Sonta Yan uwansa Suma suke Sonta kamar yadda kika sani kannen sarki biyu Mata da hajiya kubra mahaifiyar haris da warisah sai hajiya shaawah itace mahaifiyar zahira musaddik da hafsat....sun tun bayan haihuwar halima Allah be sake bawa gimbiya rumana haihuwa ba sunyi yawo asibiti asibiti wajen masu magunguna amsar dai daya CE lafiyarta kalau Allah ne be kawo ba Dan halima ta kusan zama budurwa kafin kwatsam sarki ya bukaci Kara aure,wanan Abu ba karamin tadawa gimbiya rumana hankali yayi ba lokacin da taji cewar sarki zaiyi aure Babu Wanda besan wanan tashin hankali na uwar gidan sarki ba dik fadin garin nan da masarautar nan saboda yadda ta tada hankulan jamaa....sarki da ahalinsa da mahaifiyarsa suka cigaba da shirye shiryen biki dikda sarki Yana kwantarwa da gimbiya rumana hankali Akan wanan aure da yake so yayi... Cikin kankanin lokaci kuwa aka fara shagulgulan auren sarki da bilkisu diyar sarkin agadaz a wanan lokacin shiyasa zakiga bilkisu tana da tata sarautar da izza saboda itama daga gidan sarauta ta fito....lokacin da aka kawo gimbiya bilkisu gidan sarki basa Shiri da gimbiya rumana ko kadan basa zama inuwa daya cikin kankanin lokaci ta mallake dangin mijin kaf basayi da amarya sai ita hatta mahaifiyar sarki hajiya Kaka sai abinda gimbiya rumana tace takeyi saboda yadda take zuba mulki a cikin gidan,dik wanan baya damun gimbiya bilkisu harkar gabanta takeyi kawai batare da tasan Allah yayi gimbiya rumana a wajen ba....cikin wata uku da auren gimbiya bilkisu kwatsam labari ya karade masarautar cewar ai amaryar sarki na dauke da juna biyu..fadan farin cikin da sarki yayi a wanan lokacin baaa magana haka yayita kyauta Yana rabawa talakawansa hatta mu dake zaune a gidan a da shine sanariyyar da ya bamu kyautar wanan gidan muke zaune ciki Wanda muka baro....gimbiya rumana Koda taji labari sai batayi hauka yadda ake tunani ba Dan kawai gani akai ta Kama farin ciki kuma tabi gimbiya bilkisu suka shirya kamar basu ba dik wata kula da akewa me ciki gimbiya rumana keyiwa kishiyarta tun Bata saki jiki da itaba har ta saki komi ya wuce lokacin ciki nata girma Masha allahu...sosai sarki ya dukufa wajen adduar samun magaji bashi da wani buri daya wuce gimbiya bilkisu ta haifi namiji Dan haka akaita azumi Ana sadaka da rokon Allah na Allah ya sauketa lafiya yasa ta haifi da namiji....wata Tara ciff alkawarin Allah ya cika inda gimbiya bilkisu ta haifo da namiji Kato Mai cike da koshin lafiya da hakora biyu na kasa aka haifesa wanan yasa jamaa akai ta tururuwar zuwa kallon wanan baiwa da Allah yayiwa wanan yaro.....soyayyar duniya sarki ya dorawa wanan yaro Ana haihuwarsa ya Sanya Masa suna Muhammadul zainul abideen akaita shagalin suna inda rukonsa da komi nasa yake hannun gimbiya rumana komi ita takeyi Masa yadda take sonsa bazaki taba cewar ba ita ta haifesa ba komi ita keyi Masa tsakaninsa da gimbiya bilkisu tabashi no-no haka rayuwa taci gaba inda gimbiya bilkisu ta Kara samun wani ciki a nan ta haifo safiyya wadda suke Kira fiyya lokacin zainul nada shekara hudu a duniya nan ma akaita shagali bayan ita ta Kara haihuwar ayshah lokacin zainul nada shekara takwas bayan haihuwar Aysha ne na haifeki kema inda tin bayan haihuwarki Ina zuwa gidan aikace aikace zainul ke makalemun yayita Wasa dake har yakam cemin Allah yasa ammiey idan zata sake haihuwa ta haifo kyakkyawa me kamar ummaty innah saidai inyi Masa dariya kawai shike renonki komi shi yake Miki har ta Kai dik in banje gidansu ba zaizo har nan gidan da kansa da haka har ya koya Miki tafiya da karfin tsiya Dan mikar dake yakeyi yayita tafiya dake kema kuma lokacin inhar zainul zai karbeki to ko nice na Mika hannu bakya yadda tare kuke Wasa a sashin gimbiya rumana wataran har wanka can kikeyi ita ke kula daku a tare sakamakon haka yasa gimbiya rumana ke Shiri da mahaifinki komi na yau dakullum shi take Kira idan zaayi yayi a gidan sarki.... Shiru innah tayi tana kallon ummaty wadda Tai kasake tana sauraron yadda Inna ke kwararo Mata labari dikda labarin da take Bata sama sama ne bawai cikakke take Bata ba a dunkule take Bata labarin... "Innah kinyi shiru kici gaba Mana"cikin sigar shagwaba Tai maganar....Jan numfashi innah tayi ta sauke sanan ta Dora da "kwatsam wata Rana da bazamu mance ba aka wayi gari da zainul ya kamu da wanan ciwon Wanda kikai wayau kika sanshi da shi an Shiga cikin tsananin tashin hankali a wanan nahiyyar dik wani Wanda ya kwana ya tashi a cikin garin nan ranan Saida ya tausayawa wanan yaro saboda zainul na mutanene yaro ne me farin jini ga tarbiyya uwa uba ga son mutane dikda yanada miskilanci sosai be cika son magana ba Amma baya wulakanta Dan Adam shiyasa ciwon nasa ya girgiza alummar Babu Wanda zai Baki tausayi kamar ammiey mahaifiyarsa wadda take dauke da tsohon cikin afnan lokacin haihuwa yau ko gobe wanan balai da kaddara ta sauko Masa baya iya ko mikewa yadda dai kika girma kika gansa to hakan ne Yana wanan ciwon kikesa rigima zai ankaiki wajen yaayah kamar yadda kike kiransa a wanan lokacin haka rayuwa ta kasance iyayensa basuda kwanciyar hankali kullum suna hanyar asibiti musamman gimbiya rumana wadda dik ta fita hayyacinta saboda ciwon zainul Amma kullum abin gaba yakeyi memakon baya Ana haka gimbiya bilkisu ta haifi ummul khairi wadda suke Kira da afnan sakamakon sunan kakarta ta wajen uba akasa Mata....haka rayuwa ta kasance kulllum gimbiya rumana ke kula da zainul da masu hidimarsa kina manne dashi baya cin abinci komi sai kina tare dashi a hakan har kika girma kika tsincu kanki kece me kula dashi abinda nasani kenan a takaice.... Dakyar ummaty ta hadiyi wani kakkauran miyau Wanda ya tarun Mata "Amma innah kuma Babu Wanda ya taba tunanin cewar gimbiya rumana itace tayiwa ya zainul asiri?" "Babu Wanda ya taba tunani Dan har yanzun banajin idan Zaki hadiyi kurani wajen cewar itace silar ciwonsa a yarda a yarda Babu Wanda zai yarda saboda yadda ta shiga ran me martaba yadda take mutuwar son zainul abideen banaji akwai abinda zaisa su yarda Dan haka kiyi shiru da bakinki har Allah ya kawo karshenta a gidan" Ajiyar zuciya ummaty tayi cike da zullumi da tunani inama ace zaasamu recording din da ta dauka na gimbiya rumana?wadda muryarta ce Babu Wanda zai karyata hakan?inama ace Allah zai tona asirinta cikin kankanin lokaci ta daina cutar mutanen cikin gidan tanayi musu kisan mummuke?tonuwar asirin gimbiya rumana shine kawai zai zama cikar burinsu ita da zainul abideen na kasancewa a karkashin inuwa daya wato maaurata,to ya zatayi da haris?...lumshe idanuwanta tayi abubuwa da dama sunayi Mata yawo akai.... ******** Tamkar wani mahaukaci haka ya fad'a fadar sarki Yana tangadi cikin tsananin tashin hankali ga fuskarsa ta canja saboda kuka da yayi shi kadai a daki....hannunsa rike da wayar ya Kara volume lokacin da ya karasa gaban sarki ya Mika Masa ya fadi kasa ragwaf....gimbiya rumana Tai saurin fadin "d'an ummah lafiyanka kuwa meye haka shaye shaye ka farayi?"dafe kansa yayi saboda yadda kansa ke Sara Masa...diffff gimbiya rumana tayi lokacin da taji sautin muryarta tana fadin "ummaty matukar bakiyi abinda nace ba kin aiwatar da umarnina ba to kisani zansa reshe ya juye da mujiya Dan asirinki zai Tonu kowa zai tsaneki ko kinyi bayanim cewar Nike saki kike bawa zainul magani ciwonsa na tashi Babu Wanda zai yarda...Dan haka ki gaggauta zuwa ki bashi maganin nan Dan na Matsu da Inga gawar zainul abideen a kwance shine cikar burina yadda ban haifi namijiba Babu wani yaro da zaizo ya rayu a wanan masarautar ya kuma gaji mulki matukar Ina numfashi"....dibbbb sarki yayi Yana saurare yayinda fadar yayi tamkar an dauke wuta haka recording din nan ya rinka Shiga wanan ya fita wanan juyi kawai me martaba keyi Yana zufa Babu makawa ko tantama wanan muryar gimbiya rumana ce....mikewa tsaye gimbiya rumana keyi jikinta na tsananin Bari tamkar ansa Mata mazari...."lallai wanan makircin shiryayye ne yanzun na gano inda aka dosa wato an hada Kai a kulla min sharri Dan aga karshena ko to in Allah ya yarda ummaty da sarkin dawaki bazakuci nasara ba"tana maganar zufa na gudu a fuskarta bakinta na rawa tamkar mejin sanyi.... Ciki. Dasasshiyar murya zainul yace "Babu Wanda zaiyi Miki sharri ummah wanan muryarki ce ummah Ashe bakya Sona?Ashe son karya kikemun ummah kasheni kikeson Yi" Cikin tsawa gimbiya rumana ke fadin "dakata zainul abideen wato anje anbaka ka Sha ansa maka a abinci kaci sun mallakeka an hada Kai dakai wajen zuwa a kullamin sharri ko?waye yace maka Zan kasheka?... Daidai nan baabah kande ta sawo Kai cikin fadar hannunta dauke da kulolin abinci Wanda Tai musaya da akasawa zainul magani a ciki....dama da niyyar kawowa sarki take na idan ta Musa ace taci taci....shine ta shigo ta tarar da wanan TAK'ADDAMAR...."Babu karya a cikin lamarin cewar kinason kashe zainul abideen ranki ya dade gimbiya rumana dama KO zainul be zo fada ba to inada niyyar kawo wanan abincin da kikasawa magani kikabawa baiwarki kikace takai Masa yaci ya mutu...."...juyawa gimbiya rumana tayi sashin da take jiyo wanan muryar sukai ido hudu da baabah kande tana karasowa... *DAN ALLAH KUYIMIN UZURI ABUBUWA SUNAYI MANA YAWA BAFA RUBUTU KADAI SHINE AIKINMU BA DOLE AKWAI HARKOKIN YAU DA KULLUM KUYI HAKURI BABU DADI MUTUM YASA KUDI YA SIYA YAZO BAA POSTING TAFIYA NAYI KWANAKI SHIYASA AMMA NA DAWO INSHA ALLAHU ZAMU KARE LAFIYA....INA KAUNARKU FISABILILLAH....* *HASKE WRITERS ASSO💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 SLIMZY😍 [1/23, 11:44 AM] 😍SLIMZY😍: 39 Wata irin zufa ce kawai take karyowa gimbiya rumana tamkar Ana watsa Mata ruwa lokaci daya faduwar gaba ta ziyarceta lokacin da ta tunada furucin da boka yayi Mata lokacin da taje wajenshi..."gargadi na karshe shine zanyi Miki gimbiya Akan yaron nan nafada Miki ki hakura yaron nan yanada tsawancin kwana idan da badan haka ba iya tsafi da magungunan da muke Baki kike gabza Masa sun Isa ace ya sheka lahira Amma sai wahala kawai yakeyi batare da ya mutu ba yanzun kinje kinyi sake ya warke to Ina me tabbatar Miki tunda ya taka kafarsa a doron kasa Babu wani Abu Wanda zakiyi Masa Wanda zai kamasa a halin yanzun idan kikace Zaki matsawa lamarin yaron to tabbas kece Zaki kwana a ciki Dan asirinki zai Tonu Amma tunda kin matsa ga wanan kisa mishi a abinci muddun yayi Koda cokali ne to bazai Kara second a duniya ba idan ko ya Kara to wahala zai tayi daga karshe ya mutu Dan tsafataccen magani ne"....runtse idanuwanta tayi jiri na neman dibanta take ta fara ganin kowa biyu biyu a cikin fada Wanda dabadan ta tsaida kafarta a kasa ba Babu abinda zai Hana ta cin kasa....wata irin kwarin gwiwa tasamu Dan bazata taba Bari asirinta ya Tonu ba dikda cewar Babu Wanda be saurari muryarta ba Amma zata iya karyatawa... Zubewa tayi a kasa yaraf ta fashe da matsanancin kuka Mai ban tausayi "Allah sarki nidama nasan dik abinda zanyi Ana nan Ana bina da bita da kulli dik soyayyar da nakeyi maka zainul abideen saboda son da kakewa mace ka watsawa idanuwanka toka kun hada Baki anje ansa muryata a computer anzo zaa kullamin sharri saboda ni ban haifi da namijiba saboda gudun kada kace zaka aureta in tona muku asiri dik iskancin da kake fakewa da ciwo kanayi da ita?haba zainul"kuka takeyi Babu kakkautawa... Shiko zainul a fusace ya Mike tamkar mayunwacin xaki saboda yadda zuciya ta ciyosa yayi inda take gadan gadan "dakata zainul abideen karka fara kaji na fada maka"mahaifiyarsa ta daka Masa uwar tsawa a Karo na farko sanan ta yunkura daga mazauninta tana taku cike da izzah da sarauta ta karaso inda gimbiya rumana ke zube a kasa tana faman kuka....zagayeta gimbiya bilkisu ta shigayi takai ta kawo inda gaban gimbiya rumana ya Shiga dokawa tamkar Ana buga Mata guduma..."banyi mamakin jin wanan voice note dinba rumana Dan nasan cewa inhar rumanan da nasani ce farkon zuwa na gidan nan to zata aikata abinda yafi hakan sai kika kwantar da kanki kikai Mana kisan mummuke kikai Mana zagom kasa kika kwantar da kanki kika nunamin zallar makirci da kisisina Koda yake dik Wanda ya rigaka bacci dama zai rigaka tashi kuma dik yadda mutum ya girmeka to ya girmeka Koda da second ne sai yayi maka wayau wallahi tallahi ko kaffara bazanyi ba wanan muryarki ce kuma babu karya a cikin ta sanan wayar nan na taba ganinta a hannun ummaty bada dadewa ba wanan asiri ya Tonu" "Bilkisu har kinada bakin da zakicemun Nina nemi cutar da danki?menene hujjarki?" "Koda banida wata cikakkiyar hujja wadanan kalaman naki sukadai sun Isa"...cikin azama gimbiya rumana ta Mike jikinta har rawa takeyi tana Shirin shararawa gimbiya bilkisu Mari da sauri ta rike hannunta sai yanzun sarki ya samu damar hadiyan miyaun da ya tsaya Masa a makogoronsa tun bayan sauraran wanan recording din Jinsa yakeyi tamkar ba a cikin duniyar da ya Saba rayuwaba mamaki da al'ajabi su suka hanasa magana dikda cewar Yana ko kwanto Akan muryar daya saurara ta bakin nata ne cewar xaa iya sa murya a computer a canja cikin sauki tunda yanzun ansami wayewa cikin wanan duniyar Amma waccan baiwar allahr fa tsohuwa dattijuwa wadda ta dauki shekaru tare dasu tanayi musu hidima kuma ga abinda tace?idan hakan ne zaiyi amfani da maganar baabah kande ya watsar data zainul abideen tunda ba hotonta bane Babu cikakkiyar hujja Dan haka Mai martaba yayi gyaran murya saboda yadda fada ta kaure da hayaniya baka iya jin kowa a wajen kowa kokari yakeyi ya fadi albarkacin bakinsa Dan haka ya Soma magana cikin muryarsa Mai cikar Kamala da dattako "banason hayaniya a cikin fada ta dik Wanda ya sake magana zanyiwa dogarawa umarni su fitarmun dashi su hukuntashi da bulala ashirin ko waye kuwa"...Dan haka nan da nan fada Tai tsit kowa sai kallon kallo yakeyi hatta da bayi wadanda suke cikin fadar zare ido kawai sukeyi kowa ya baza kunnuwa...sarki ya cigaba da magana "wanan lamari da zainul yazo dashi na saurara abune Mai matukar wuyar shaani domin hakan zata iya faruwa ko akasin haka tunda ba hoto Mika gani ba murya ce muka saurara Dan haka bamuda ikon saurin yanke hukunci ko yadda da abinda mukaji"...da sauri gimbiya rumana ta dubi mai martaba cikin tsananin kosawa ta kada Kai kawai tadanji sanyi cikin ranta...Mai martaba ya cigaba da magana "Dan haka sheda ta biyu zamuyi amfanida ita itace wadda waccen kuyamga tsohuwa ta gabatar Mana da cewar rumana Tana kokarin kashe zainul abideen ta hanyar sanyawa zainul guba a abinci Dan haka yanzun zaayita ta Kare ga fili ga Mai Doki Wanda keda nasara"...cikin rashin fahimtar abinda sarki ke nufi yasanya kowa juyawa a tare suna kallonsa Banda gimbiya rumana wadda ta gama fahimtar abinda yake nufi take ta saki fitsari ta cikin alkyabbar dake jikinta batare da kowa ya fahinci hakanba,cikinta ya Shiga kugi da murdawa nan da nan taji wani irin zawo Yana yunkuro Mata idan Tai kwakkwaran numfashi Shima zata iya sakinsa a jikinta saboda yadda hantar cikinta da yayan hanjinta ke jujjuyawa lokaci daya....ga gumi dake karyo Mata ta ko wani sako na jikinta tana tsaye tamkar wadda aka dasa a wajen kowa kallon yanayinta yakeyi Yana kada Kai....kallo daya zakayi Mata ka hango tsantsar tashin hankali da tsoro cikin kwayar idonta...mai martaba ne ya katse shirun da cewa "kande"...da sauri ta zube a kasa hannunta rike da katin paranti me dauke da kuloli"Allah ya taimakeka" "Ki ajiye parantin nan ki dauki karamin plate cikin kayan abincina gasu can kizo ki zuzzuba dik wani abinci dake cikin kulolin hannunki ki ajiyesu a tsakar fadar nan inaso in tabbatar da gaskiyar gimbiya rumana matukar ta yadda taci abincin nan to tabbas itadin me gaskiya ce kuma batare da wani Abu ya sameta ba zamu Bata awa daya mugani"....kafafuwanta ne Suka Shiga karkarwa tamkar wadda ake watsawa ruwan kankara lokacin hunturu....gimbiya bilkisu ta sauke wani lallausan murmushi Wanda har wushiryata ta bayyana ta kiftawa gimbiya rumana ido.... Cikin minti biyar baabah kande ta zuba burabusko da miyat kayan ciki da alyyaho a plate sai kamshi yakeyi ta kuma tako har inda gimbiya rumana take ta durkusa har kasan ta ajiye hade da cewa "gashi ranki ya dade umarnin Mai martaba ne"...ta yunkura ta Mike ta Kara komawa sashin da take tsaye ta tsaya hade da sunkuyar da kanta kasa.... Kusan minti goma Sha biyar gimbiya rumana Bata motsa daga inda take ba sai faduwar gaba da take famanyi...tsawa Mai martaba ya daka Mata Wanda yasata turkudewa tayi kamar zata Fadi kasa sanan ta yunkura ta Mike jikinta na rawa ta dauki plate din ta rike cokali....gara taci abincin kawai Dan idan ma bataciba asirinta tonuwa zaiyi ya nuna cewar ta aikata idan ko taci shikenan idan ma mutuwar ne ta zabi ta mutu da wanan abun kunyar da ta daukowa kanta sakamakon son zuciya....take tabi shawarar zuciyarta ta dibi burabusko a cokali takai bakinta....baabah kande mamaki ne ya lullubeta hansa'u baiwarta dake gefe itama hantar cikinta a Kade take....kirrrr sarki yayi da idonsa akanta yadda take cin abincin jikinta na rawa dakyar tayi cokali biyu ta somaji hanjim cikinta tamkar Ana kamasu Ana kukkulesu tamkar Ana yayyakansu da wuka ta rike cikinta tana wani irin juyi a tsaye tamkar Ana Wana gwangwani..... WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WADANAN NUMBES DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619 *HASKE WRITERS ASSO💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY✍🏼* [1/23, 11:48 AM] 😍SLIMZY😍: 40 Faduwa kasa gimbiya rumana tayi tana juyi a tsakar carpet din dake malale a fadar yayinda zufa ta shaga tsattsafowa a ko Ina a jikinta hatta alkyabbar dake jikinta Saida ta jike sharkaf tamkar an watsa Mata ruwa kallonta kowa yakeyi tamkar an kunna tv yayinda wajen yayi tsit komi Bakaji sai saukar numfashi cikin mintuna da basu wuce biyar ba nan da nan ta fita hayyacinta lips dinta sukai Kore sharerrr kwayar idanuwanta ma suka canja kala zuwa kalar Kore daga sarki har gimbiya bilkisu Saida suka furgita ganin yadda ta canja kala nan da nan shi kansa zainul abideen mutuwar tsaye yayi a wajen dakyar ya iya zura hannunsa cikin aljihun wandonsa ya lalubo number yayi dialing ya Kara a kunne cikin seconds akai recieving daga can bangaren wadda ya Kira ta karba da "hello lil brooo ya akayi meye labari" Murya a dishe yace "anty Zahra idan kinada lokaci kizo gida yanzun idan ilkinshigo kizo fada direct"...yadda yayi maganar yasa hantar cikinta kadawa ta zaro ido tamkar Yana ganinta a kidime tace "bros wani Abu ya faru ne?mekefaruwa ka fadamin"....bayida karfin da zai Kara magana dan haka kashe wayar yayi dibbbbv....daga can bangaren Zahra jikinta ya kwashi rawa tasan Babu lafiya ko a yanayin da taji muryar Dan uwan nata to Allah yasa ba jikin bane shine abinda ya Fado Mata a Rai... Gimbiya bilkisu ta dubi zainul "meyasa ka kirata?" "Ammiey gara Dana kirata ayi komi a gabanta Dan kar wani Abu ya biyo baya aga kamar an cutar musu da mahaifiya"... Tun tana Shure Shure ta daina ga wani irin tari da takeyi da tayi amai ke bulbulowa daga cikinta Kore sharrr hade da jini jini...dik wani mahaluki Wanda ke cikin fadar Saida ya girgiza ganin yadda gimbiya rumana ta koma cikin kankanin lokaci numfashima dakyar take saukewa....kallo daya Mai martaba yayi Mata ya kauda kansa gefe ya juya abinsa dakyar ya dubi mutanen dake wajen yace "kowa yaje yayi sallah ya dawo don lokacin sallar ishai yayi"...Babu Wanda yayi musu da daidai da daidai suka Shiga zare jikinsu kowa ya watse a fadar akabar gimbiya rumana kwance wajen Bata iya kwakkwaran motsi.... ******** Shiko zainul Yana fitowa fada Mai makon yayi masallaci parking space yayi ya Shiga yayiwa motar key da kansa dikda ba kwarewa yayi a motar ba bayan warkewarsa ne aka koya Masa....Amma cikin kwarewa yake murza motar a titi har unguwarsu ummaty Yana karasa parking kofar gidan ko kashe motar beyi ba yayi cikin gidan da sauri... Kwance take gefen innah tayi nisa cikin tunani kamar saga sama sukaji sallamar mutum ko kafin su amsa sun ganshi dibbb a gabansu...a zabure innah ta Mike tana karewa zainul abideen kallo kafin tasa hannunta ta murza idanuwanta ta bude...murmushin karfin Hali yayi yace "nine innah nine zainul abideen" "Zainul meya kawoka gidan nan daddaren nan sanan waye ya nuna maka inda muke?"cike da tashin hankali innah ke jefa Masa tambayoyi "Nadade da sanin inda kuke innah,yanzun haka inaso ku bini kuka abin al'ajabin da yake faruwa a cikin gidanmu"...ko kafin innah tayi magana sarkin dawaki ya karbe zancen "su bika Ina?Babu inda zasu bika daddaren nan ka dauki kafarka kaima kabar gidan nan tunban sassaba maka ba kafin ka janyo Mana wani balain muna zaune lafiya"...furzar da iskar bakinsa yayi me zafi idanuwansa sunyi jajir "baba inaso kuzo kuga sakamakon sharri da akayi muku yanzun haka dik abinda yake faruwa a masarautar mu asiri ya Tonu ko sallah banyi ba nazo tafiya daku Dan Allah ku daure ku bini"...shiru yayi sarkin dawaki dik yadda yaso da ya kartawa zainul rashin mutunci kasawa yayi saboda yadda yaron yayi Masa kwarjini sanan koma menene akayi musu ai shi yaja kuma ba yaron bane yayi bashi bane sila....jikinsa ne yayi Sanyi ya dubi innah da ummaty wadda ke faman zare ido yace "ku dauko mayafinku muje"...innah zatayi magana sarkin dawaki ya katseta ba haka taso ba Amma Bata da zabin da ya wuce bin umarnin mijinta.... ******** Hansa'u wadda dik ta tsure baiwar gimbiya rumana da komi tare suke kissimawa ta Shiga hada kayanta a Ghana most go da zarar kowa ya koma fada ta setawa kanta kafa kawai a bayanta taji anyi magana "hansa'u Ina kike Shirin zuwa kika hada wadanan faggon kayan?" A furgice ta dago ganin uwale ce yar uwarta baiwa yasata saukar da ajiyar zuciya tana zazzare idanuwa "uwale ki rufa min asiri Dan Allah banaso masifar nan ta bare Dani Dan tana gab so nakeyi da angama tafiya fadar sarki in gudu kawai"...murmushin keta uwale tayiwa hansa'u "to ai Mai martaba ya bada umarnin kar Wanda aka Bari ya fita gidan nan daganan zuwa gobe da yamma saboda zai yanke hukunci Akan dik Wanda yakeda sa hannu wajen cutar da jininsa da Wanda keda alaka da gimbiya rumana Dan haka ki sauke kayanki da kika Dora akai kike Shirin guduwa matukar kinada gaskiya Babu abinda Mai martaba zaiyi Miki"...kuuuuuuu cikin hansa'u ya karta take taji zawo ya taso Mata Tai jifa da jakar kayanta tayi waje a guje rike da duwawunta saboda yadda kashi ya matseta....dik yadda uwale taso daurewa dariya Saida ya kufce Mata nan ta fadi Tai dariya Mai isarta harda hawaye Tana nan hansa'u ya dawo ido zuruzuru kamar an kwashewa karya y'a y'a.... uwale tace "ke nake jira muje fadar tare tun kafin sarki yayi Mana hukunci"...neman kuka tayi ta rasa sai zazzare ido kawai hansa'u keyi uwale na gaba tana biye da ita... ******* A tare motoci uku sukai parking a kofar gidan sarki da motar zainul data anty Zahra da mijinta sai haris Wanda ya dauko hajiya kubura da warisah ya biya ya dauko hajiya Kaka da zahira wadda ke gidan hajiya Kaka....dakyar ummaty ta sako kafa ta fito daga motar zainul saboda kunyar haris data lullubeta....innah da sarkin dawaki dake bayan bota Yana Gama parking suka fito ita kuwa dakyar ta sako kafa ta fito daidai nan sukai ido hudu da haris Wanda ya bisu da wani irin kallo Mai cike da mamaki da tuhuma ta wani bangaren kuwa kishi ne ya taso ya lullubesa nan da nan idonsa suka kankamce...warisah ko kallo daya Tai musu ta kauda kanta saboda wani irin kyau da sukai Mata sun matukar dacewa itama zuciyarta ce taji Tana barazanar tarwatsewa Dan haka da sauri taja hannun zaheera dake yakewa zainul Baki bemasan tanayi ba sukai gaba Babu mecewa kowa komi haka suka nufi fada zuga guda lokacin kowa ya hallara ita dama anty Zahra da mijinta sun Riga kowa Shiga.... Ganin mahaifiyarta warwass a kasa yasata karasawa inda take a rude tana rukota koda ta dago gimbiya rumana ta kalli fuskarta abinda ta ganine ya furhitata yasanyata saurin sakin kanta kasa ta kume ta Mike a furgice "ummah meyasameki menene haka yake fito Miki a fuskarki"....jin haka yasa wadanda ke kusa da wajen daga Kai suna dogon wuya suna leke cikin kankanin lokaci wasu kananan kuraje masu ruwa su yayyabe fuskar gimbiya rumana caba caba dik Wanda ya kalla sai tsigar jikinsa ta tashi ga Kore sharrr da fuskar tayi....zainul na shigowa kallo ya koma kansu dagashi har sarkin dawaki har innah da ummaty take fada ta kaure da surutu....kowa na fadan albarkacin bakinsa wata tsawa Mai martaba yayi take kowa yayi shiru ya Shiga taitayinsa nan Mai martaba ya Soma magana "dik abinda kace zaka ginashi Akan turbar karya da son zuciya da mugunta da k'eta to tabbas komi Daren dadewa sai asirinka ya Tonu Koda a karkashin kasa kakeyi sai ya fito sanan dik Wanda zai Gina Ramin mugunta ya ginashi daidai kwaurinsa watakila ya fada da mutum shine kadai abinda Zan iya fada Dan abun ya dauremin Kai ya zarce tunanina ban taba tunani ko zaton haka ba sai gashi ta inda bana tunani tanan ya bullo sanan bincike ya nuna cewar akwai masu taimaka mata wajen aikata hakan kuma Basu kowa bane sai bayinta wadanda ke gefenta ciki kuwa harda hansa'u"...Dan haka hukuncin da Zan yanke harda hansa'u da yushau Mai kula da zainul...Dan haka gimbiya rumana nata hukuncin kenan cin guba da tayi shine daidai da ita a tunaninta bazai cutar da itaba Dan haka ni na saketa saki uku sanan ta Barmun gida na gobe gobe n nan sanan hansa'u da yushau na yanke musu hukuncin zama a gidan yarin wanan masarautar na tsawon shekara goma ciffffff sanan banaso su Kara awa daya cikin gidan nan batare da ankaisu can ba sanan ni na wanke sarkin dawaki da ahalinsa gabaki daya kuma zam biyasu diyyar sharri da akayi musu batare da hakkinsu ba bayan hakan banida abinda zance saidai ince Allah ubangiji yayi Mana sakayya Akan dik Wanda ya cutar damu Allah ya maida Masa da abinda sanan a karshe na bawa sarkin dawaki da iyalensa sashin gimbiya rumana su zauna halak malak"...Mikewa yayi cike da bakin ciki furucun Mai martaba yasa Babu Wanda Bai zubar da hawaye a wajenba musamman ummaty wadda take kuka tana murmushi na farin ciki yayinda ita kanta hajiya Kaka kukan tasa ta tako har inda ummaty ta rungumeta a jikinta "kiyafemun kinji jikata"....sharewa hajiya Kaka hawaye ummaty tayi "haba hajiya ba laifinki bane rashin fahimta ne na yafe Miki"....dik Wanda yake wajen jikinsa yayi sanyi ta wani bangaren tausayin Zahra ne ya cikasu yadda take kuka rungume da mahaifitartata tana trying number halima Amma Taki shiga....gimbiya bilkisu kuwa bayan Mai martaba tabi abinta....har inda take tsaye haris ya karaso fuskarsa a daure tamkar be taba dariya ba ya kalli agogo hannunsa karshe Sha daya da wani Abu na dare cike da izzah ya Bata umarni "ummaty muje inkaiki gida kedasu innah koma menene gobe a karasa banaso ki Kara Shiga motar wani"...yadda yake mgnar take binsa da kallo cike da faduwar gaba...ta dayan bangaren kuma zainul yace ta jirashi yayi sallar ishai ya kaisu gashi shine ya daukosu ya zatayi...... *WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619* *HASKE WRITERS ASSO💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY✍🏼* [1/23, 11:49 AM] 😍SLIMZY😍: 41 Batada zabi haka ta juya ta dubi innah a sanyaye ta ce "innah keda babah kubi motar ya zainul Bari inje haris ya saukeni Naga neman magana yakeyi"Sarai innah ta fahinci ummaty sai kawai tayi murmushi "toh shikenan Amma kar ya tsaya dake ko Ina ya kawoki gida kinji Koh"ummaty ta gyada Mata Kai....batada zabi haka ta nufi motar haris Wanda tasan tsabar rigima yakeji Dan Haka tana Shiga zainul na fitowa hannunsa rike da makullin mota yaga lokacin da ta shige motar haris sai ya basar kawai ya karaso wajensu innah "innah muje in saukeku dare yayi sosai" .sarkin dawaki dake gefe besan wainar da ake toyawa ba ya Shiga waige waige bega ummaty ba "innah ummaty tayi?ko nan takesoh kwana?" "Haris ya dauketa a motarsa sunyi gaba sun rigamu tafiya tun dazun".. wani mugun kishi ne ya tasowa zainul yaji zuciyarsa na bugawa fat fat...dannewa yayi dik yadda yakeji Amma haka yayiwa motar keyi ya bar kofar gidan... Yadda haris ke driving tamkar bazasu tafi ba har motar su zainul tazo ta wucesu fiiiiii....murmushi haris yayi Dan Haka yakeso itakuwa ummaty bakin ciki ne ya Kara lullubeta "Wai ya Naga kana driving a haka?bayan kasan dare yayi?kana gani har motarsu innah tazo ta wuce Tamu?kana kuma Jin lokacin da innah tace karka tsaya Dani ko Ina zata iya min fada"cike da takaici Tai maganar kmr ta shakeshi...dariya ya Sanya Mata wadda ta Kara sata kuluwa batare da ta ce komi ba sai harara da ta watsa Masa .."Ashe kin iya masifa,to masifarki ce zatasa inyi sauri?hmmm so kikeyi muyi sauri muje ki hadu da masoyinki ko?to da kike cewa innah zatayi Miki fada ko kin manta cewar ni mijinki ne tunda kudin aurena na gidanku?kuma innah tasan cewar nidai ba Dan iska bane balle Dan Haka wallahi idan kikace Zaki Kara cewar wani Abu dangane da yadda nake tafiya parking zanyi mu kwana a nan sai asuba"...wani irin mugun haushinsa da takaicinsa ne ya lullubeta taji kuka na kokarin kwace mata ita tayi Masa halacci tayi gudun bacin ransa shine zaiyi Mata Haka Dan ya bakanta Mata Rai?dik yadda taso da danne zuciyarta Saida hawaye ya sauko a idanuwanta lokacin da ta dubi agogon wayar innah dake hannunta karfe shabiyu da minti ashirin na dare.....tana cikin tunani taga giftawar motar zainul a guje ta dawo ta bi motar da kallo Bata Ankara ba haris yaja motar da wani irin karfin gaske Wanda Saida tayi gaba kamar zata bugu ta dawo...ya Shiga sharara gudu a titin...faduwar gaba ce ta ziyarceta yadda yakeyi da motar kamar zai tashi sama ta juyo ta kallesa idonta tafff da hawaye yadda taga ya tsare gida yasa ta hadiye wani miyon bakin ciki ta hadiye kukan...Sarai ta fahinci inda ya dosa wato dama yayi hakan ne Dan kada ta hadu da zainul?sai da yaga wucewarsa sanan ya Soma gudun fanfalaki da ita?....Bata bawa kanta amsa ba kawai ji tayi mota ta tsaya tai furgigit ta juya taga sun kawo sai kukan karnuka kakeji a ko Ina Dan Haka batai wata wata ba ta bude kofar motar ta saka kafarta ya ruko hannunta ta juyo da sauri "saurin me kikeyi ba kiyi sallama da mijinki ba?ko fushi kikeyi Dani?"ya tsareta da ido da yasa ta sunkuyar da Kai kasa ta girgiza Kai "ah ah dare yayi ya haris Bari inje" "Naji Zaki tafin Amma sai kinyimun murmushi"harara ta watsa Masa ya fashe Mata da dariya Dan Dole Saida tayi dariya sanan yace "kuma da wuri zanzo gidan nan gobe Dan ban goyi bayar ku koma gidan sarki ba tunda aka iya muku korar Kare dik halarcin da kukayi nan gaba ba fata akeyi ba wani Abu ya faru a Kara korarku Dan Haka nan gidan na canja takaddun sunan gidan tuni na mallakawa baba"...Baki bude take kallonsa kafin ta kwace hannunta tayi cikin gida da gudu ya bita da kallo Yana shafa kansa...da kyar ya tada mota yabar kofar gidan.... ******** Zahra ce zaune rungume da mahaifiyarta wadda gabaki daya cikin kankanin lokaci Allah ya saukar da ikonsa akanta gabaki daya kamanninta sun canja ta koma masakiya complete tamkar ba gimbiya rumana ba wadda cikin awanni goma da suka wuce take cikin koshin lafiya tamkar ba gimbiya rumana wadda ta kasance kyakkyawar mace meji da mulki da iko ba... Tabbas annabi yayi gaskiya da yace Dan Adam Tara yake be cika gomaba kuma Babu wani Dan Adam da ake gamawa halitta sai ranan da ya koma ga ubangijinsa tabbas ga ishara ta sauka Akan gimbiya rumana... Jan numfashi Zahra tayi ta sauke tana cigaba da rera kuka tamkar wadda akaiwa mutuwa kasantuwar anan baban nuaiym ya barta...dakyar gimbiya rumana ta motsa bakinta saboda yadda takeso tayi magana ga mugun kishin ruwa da takeji ganin yadda take mutsu mutsu yasa Zahra riketa da kyau ta tallabota hade da kafeta da idanuwa da kyar ta iya furta "zansha ruwa"...ta rufe bakinta.. da sauri Zahra ta kwantar da kanta ta Mike taje ta zaro gorar swan water a cikin fridge ya dawo da sauri ta bude ta tallabo kanta tace "gashi ummah bude bakin Kisha"... Tari ne ya sarke gimbiya rumana tun kafin ta Sha ruwan ta Shiga gwaro amai me kumfa kumfa Kore sharerrr da shi a wahale takeyin Aman tamkar ranta xai fita,tausayin mahaifiyarta ne ya lullubeta ta rungumeta sosai daidai nan yaronta dake bacci ya farka haka ta kwantar da ita ta ruga ta daukeshi ta rungume ta Shiga jijjigashi a tsaye tanayi tana waigen mahaifiyarta wadda ke sambatu kamar haka "niba ni bilkisu tayiwa asiri ta Shiga tsakanina da mijina Koh?...wato zainul abideen ya warke zai gaji sarauta to Basu isaba kuma wallahi Bari inji sauki saina Rama abinda sukayi min harda magani aka bani naci Koh?to wallahi dik sai sunci ubansu" ...haka taita maganganu marasa Kan gado har bacci ya dauketa" ******** Kiran sallar farko zainul abideen ya tashi yayi nafilfili kamar yadda ya Saba har akayi sallar asuba sanan ya gabatar da sallah da azhkhar dinsa ya fito sanye da jallabiya ya nufi sashin mahaifinsa ya Shiga zaune ta taddasu Kan dadduma shida mahaifiyarsa sun idar da sallar asuba kamar yadda ya Saba...ya tsugunna har kasa ya gaidasu cike da kulawa sanan ya shedawa mahaifiyarsa zai fita "Ina zakaje zainul da asuban nan?" "Zansa aje a kwashewa su ummaty kayansu yanzun zaifi" "Inaga zainul ai abari gari ya waye Koh?" Murmushi Mai martaba yayi ya sako musu Baki "ah ah kibarshi yaje kinsan ance da zafi zafi ake bugun karfe"..Sarai ta fahimci abinda yake nufi itama dariyar tayi ta cigaba da Jan carbinta ta dagawa zainul Kai alamar ya tafi...ya Mike ya fice... ******* Ummaty na azhkar din safe kamar saga sama taga mutum sanye da farar jallabiya hakan ta tsorata ta taja da baya kadan tana zaro ido "ya zainul daga Ina kake da safiyar nan?"be Bata amsar abinda ta tambayesa ba ya ce 'banaso ku Kara cikakkiyar awa daya cikin gidan nan ga mota nan a waje na kawo zata kwashi kayanku wadanda kukeso"gaba yayi ya barta nan a zaune ya nufi dakin da yake tunanin nan ne na sarkin dawaki...shima yayi mamakin ganin zainul ya shaida Masa abinda ya kawosa beyi Masa musu ba ya shaidawa innah itama Shiri ta shigayi suka Shiga shirye shirye ummaty kuwa dik yadda taso ta hada ido dashi ko zataji sanyi ya ki Bata dama kauda kansa yakeyi dikda shima Babu abinda yake bukata sama da ganin kwayar idanuwanta Amma takaicin abinda tayi jiya shi ya sa wani kishi ke damunsa yayi hakan ne Dan ya kuntatawa haris Dan yasan tabbas zaizo zai kuma tarar da basa nan sai yaga ta iskanci.... Tsaye yake jikin Shiga kofar gidan ya juya baya ta tako har inda yake ta tsaya gabanta na tsananin faduwa ga wani tsoronsa da ya cikata "ya zainul"ta kirasa muryarta na rawa..."menene Ina jinki"....yace a takaice cikin wata irin dakakkiyar murya ..kasa cewa komi tayi kawai ta rakube gefensa ta wuce hawaye na sauka a idanuwanta wani irin ciwo yakeji ya ga ummaty a wanan halin baya kaunar ganin hawayenta saidai Dole ya dau mataki kanta Dan ta Bata Masa Rai.... Ko kafin bakwai sun Gama kwashe Kaya tas sun nufo gidan Mai martaba da Kaya Niki Niki nan zainul ya zage dashi aka Shiga kwashe kayan zuwa cikin gidan da maaikatan cikin gidan ******** Zaune suke suna breakfast shida daddynsa a parlor ,daddy ya nisa yace "haris inaso kafin inkoma Italy ayi bikinka menene shirye shiryen ka?".. Dadi ne ya lullube haris bakinsa ya kasa rufuwa ya durkusar da kansa cike da kunya Yana jujjuya cokali cikin tea shiru yayi sanan yace "daddy nima hakan nakeso wallahi tunda ankai kudi sai ayi maganar aure ayi shirye shirye daddy da kayan akwati ko?sai a tsaida Rana " "Ehh hakan nakeso Bari Zan Kira abbanka da mukaje tare mu koma gobe Akan maganar yanzun zanyi maka transfer din million biyar cikin account Dinka sai ka dauki kanwarka kuje siyayyar Kaya idan Basu isaba Zan Kara muku"...hajiya kubra ce ta shigo parlorn jiki a sanyaye tun jiya ta rasa abinda keyi Mata dadi ta nemi kujera ta zauna "alhaji saidai inji Kuna maganar aure daga Kai sai Danka Baku sani cikin lamarinku yanzun haris ne zai dau warisah su je siyayyar kayan aure inada Rai" "To momyn yara ai gani nayi bakison auren kince Babu ruwanki shiyasa kawai nace muyi nida yarona".murmushi tayi wanan karon "to yanzun da ruwana a tsundumani dumu dumu ciki"...wani Dadi ne ya lullube haris ya rungume momy Yana dariya cikin zolaya ta dungure Masa Kai "kaga ja'irin yaro wato ka gaji da zama da momy aure kakeso Koh?"dukkansu sukasa dariya cike da farin ciki suka cigaba da breakfast dinsu a tare... "Ina babyna ne Wai"daddy ya tambayi momy... "Warisah bacci takeyi ninarasa meke damun wanan yarinyar inaga wajen likita Zan maidata Dan nagaji" "Gaskiya momy"cewar haris Yana Kai farfesu bakinsa.. ******* Tryin number halima Zahra ta karayi ganin yadda gimbiya rumana ke numfarfashi ta nufi wajen mahaifinta yaki sauraronta so takeyi akaita asibiti Amma yaki tayi Kira na biyu kenan taji sallamar halima cikin dakin...ta shigo sanye da hijabi fuskarta a kumbure idanuwanta sunyi jajir yaranta biye da ita da sumayya da samir sanye da kayan sanyi.... Kallo Zahra Kebin halima dashi Baki bude har ta shigo...cakkkk ta tsaya halima tana bin mahaifiyarta da kallo cike da mamaki da tsoro ta zaro ido zatayi magana samir ya ce "laaaa ummu dubi ojuju"ya kwashe da dariya Yana tabo Yar uwarsa... . "Meya samu ummah ?ya na ganku a wanan sashin da Babu kowa?na shigo uwale tacemin Kuna nan?" Takaici ne ya lullube Zahra ta Shiga zayyanowa halima abinda ta sani daga farko har karshe "innalillahi wa innah ilaihi rajiun...na Shiga uku ni halima wanan wace irin bakar Rana CE nagani a daidai wanan lokacin jiya nima muka samu matsala da prince da mahaifiyarsa ta ce sai ya sakeni jiya shine ya sakeni harda duka".. wata irin zabura Zahra tayi ta Dora hannu aka "nashiga uku na lalace wace irin mummunar kaddara ce ta samemu?" ******" Parking haris yayi a kofar gidan ya kashe mota ya fito Yana sanye da track suit kansa da hular sanye me rubutun later U a jiki ya nufi kofar gidan saidai Kato padluck da ya ganine ya sanyashi yayi turus yayi maza ya Ciro wayarsa ya kalli agogo karfe Sha daya da Rabi....Ina sukaje?....ya tambayi kansa cike da tashin hankali zuciyarsa ce ta Raya Masa Kila suna gidan Mai martaba.....ya juya kawai ya nufi motarsa ya Shiga ya tadata ya bar kofar gidan.... *KUYI HAKURI DAN ALLAH BANI DA BAKIN DA ZANBAKU HAKURI AKAN WANAN LAMARI WALLAHI KWANA BIYU BANI DA LAFIYA NE SAI A HANKALI SANYI YAZO SHIYASA KUKE JINA SHIRU WALLAHI...AMMA INSHA ALLAHU SAURAN PAGES DIN NAN DA YARAGE ZAKUJII* *HASKE WRITERS ASSO💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY😍* [1/23, 11:50 AM] 😍SLIMZY😍: 42 Tarba suka samu ta musamman daga bangaren gimbiya bilkisu wadda dama tasan tun bayan fitar zainul can ya nufa ko baa fada mataba shiyasa ko kafin su iso an gyara sashen gimbiya rumana dikda dama ba wani Abu ya sameshiba sanan anyi breakfast dasu abinci kala kala aka Shiga shigowa dashi sashen gimbiya rumana Wanda ya kasance yanzun sashen sarkin dawaki da iyalensa....Baki bude innah take bin bayi da kuyangi ganin yadda wanan ya shigo wanan ya fita da abinci kala kala...kallon ummaty tayi suka hada ido ummaty ta sakar Mata murmushi tana Jin wani irin sanyi a cikin zuciyarta da wata natsuwa ta musamman data tsinci kanta ciki "Niko wanan abincin da ake shigowa dashi ummaty ai yayi yawa Ina zamu kaishi daga Baki na sai naki saina babanku?"itadai ummaty murmushi tayi batare da tace komi ba...janyo plates innah tayi tana Shirin serving dinsu wata baiwa ta shigo da sauri ta amshi plate din "ranki ya dade ba aikinki bane wanan hidimar tawa ce sunana iklima nice Mai aikin na sashen dik abinda kuke bukata nice zanyi muku"...innah galala tayi tana bin iklima da kallo wadda ta cigaba da aikinta tayi serving dinsu abinci kowa ta dire Masa a gabansa...tea ummaty ta dauka ta kurba ta ajiye cup din kenan haris yayi sallama cikin dakin Saida gabanta ya fadi da sukai ido hudu ta kauda kanta....innah da ke zaune sai faraa takeyi ta dubi haris "ah ah harisu sai kaje can baka ganmu ba ko?wallahi zainul abideen tun asuba ya je ya kwasomu kamar masu Shirin barin gari"...murmushi haris ya kakalo ya Dan tsugunna "innah Ina kwana" "Lafiya kalau haris ya maman naka?" "Lafiyansu kalau tace a gaisheku"...ya koma kujera ya zauna Yana jifan ummaty da wani irin shu,umin kallo ita ko gabaki daya ta rikice da kyar take cusa abincin a cikinta...innah ce ta katse shirun "haris a zuba maka abincin ka karya Mana"...siririyar ajiyar zuciya ya sauke "na karya innah kafin na fito" "Toh shikenan"ta Mike ta bar musu parlorn ta nufi daya daga cikin dakunan....tasowa yayi daga inda yake zaune ya dawo daf da ummaty ya zauna Yana fuskantar ta da wani irin mayen kallo ko kifta idanuwansa bayayi,dik ta takura da irin kallon da yakeyi Mata ga wani irin bugawa da zuciyarta keyi...turo Baki kadan tayi ta jefa Masa harara ta dakko cup din tea zata Kai bakinta ya rike da sauri tai Masa wani irin kallo "ka rike mun cup Ina cin abinci idan tea din yayi Sanyi bazan iya Sha ba"kallonta kawai yakeyi batare da yayi magana ba,daga labulen dakin da akayi ne yasasu duka su biyun juyowa a tare hannun haris na jikin cup din ummaty....zainul ne tsaye a bakin kofar murmushi yayi "sorry bros na shigo banyi muku sallama ba hope banyi laiifi ba "ya karashe maganar Yana murmushin gefen fuska,gyada Masa Kai haris yayi shima Yana murmushin "yanzun nake Shirin shigowa wajenka dama idan na gama da nan din" "Owk sai ka shigo"zainul yace a takaice sanan yayiwa ummaty wani irin kallo ya fice,...Ido ta bishi da shi har ya bace Bata sani ba Saida haris ya Dan tabo ta sanan Tai furgigit ta dawo da hankalinta tana sauke numfashi..cije lebe haris yayi cike da kishi yace "ummaty nasan zuciyarki Bata tare Dani gangan jikinki ce take tare Dani sanan inaji a jikina bakya Sona ummaty"a sanyaye yayi maganar Yana furzar da iska daga bakinsa Tausayinsa ne ya lullubeta ta dubesa da Lulu eyes dinta "meyasa zakace haka ya haris bayan kana Shirin aurena sanan kace bana sonka?" "Bakya Sona kinadai tausayina ummaty sanan kona aureki gangar jikinki kawai zan aura amma ruhinki da zuciyarki tana can wani waje daban"...mikewa yayi ya zura hannunsa cikin aljihunsa sanan yace"yau su daddy sukace sunaso suzo a tsaida ranar aurena dake so nazo in shaidawa baba ne kuma Naga kamar Baya nan Amma ki shaidawa innah" Dakyar ta hadiye miyon da ya makale Mata a makoshi tace "toh"hanyar waje yayi ta bishi da kallo ya fice ko waigenta beyi ba,wani irin kuka ne ya taso Mata ta toshe bakinta ta fada Kan kujera tana rera kuka Mara sauti.... ******** Dik wani bincike likita yayi iya kokarinsa wajen binciken abinda ke damun gimbiya rumana wadda halima da Zahra sukai sammakon barin gidan da ita batare da kowa ya sani ba dik sun fita hayyacinnsu sun tsorata da yanayin mahaifiyar tasu,gashi Basu da wasu dangi ta bangaren mahaifiyarsu Wanda suke jituwa dasu,dik Wanda suka Kira suka shaida Masa abinda ke faruwa saidai yace Allah ya sauwake ko yace Ina mulkin da sarautar?Ina dukiya?meyasa bazasuyi Mata maganiba a yanzun?amsar kenan...halima ta share hawaye cike da nadama da tsananin damuwa ta dubi doctor dake ta rubuce rubuce a file din gimbiya rumana "likita yanzun Babu wani taimako da zaka iya Yi Mata Wanda zata samu relief ko yaya ne?musamman wanan Aman da takeyi Mai wari ga shakuwa da take fama,ni kurajen da sukai Mata kaca kaca Basu dameniba kamar wadanan abubuwan?" Ajiye rubutun likita yayi ya fuskancesu duka su biyun yadda suka fita hayyacinsu ga damuwa karara a fuskarsu"Babu abinda Zan iya Yi Mata Wanda ya wuce kwayar maganin da na Baku ku rinka Bata shine kawai mafita shima zugi da radadi kawai zai cire Mata da Koda yaushe da zata kasance cikin bacci saboda yadda Naga tana sambatu kamar Mai tabin hankali kuma munyi gwaji a kwakwalwarta lafiya Lau Dan haka Babu abinda zan iya Wanda ya wuce hakan"... Hawaye ne ya gangarowa Zahra tace"likita why not kayi addmiting dinta a nan har ta Dan samu sauki?" "Sorry to say ranki ya dade gaskiya bazan iyaba saboda idan kin lura babban asibiti ne nan da ake kawo marasa lafiya daban daban sanan bamu gano cutar dake damunta ba balle musan yadda zamu magance kada tazo ta shafi wadanda ke kwance a asibitn Kinga anbata goma biyar Bata gyaru ba Dan haka ga wanan takaddar"ya Mika masu da sauri halima ta karba ta karanta takaddar sallama ce ya Basu sanan ya Mike "inada patient suna jirana a waje zasu fara shigowa ganina Dan Allah zaku iya tafiya"ya nuna musu kofa...mikewa Zahra tayi tana gyara goyonta cike da takaici "muje halima" Fitowa sukayi suna Jan kafa da kyar har dakin da gimbiya rumana ke kwance tana ta sharar baccin wahala...kallonta kawai sukeyi bacci takeyi Amma yadda take sauke numfashi tamkar Mai asthma ga manyan kuraje da sukai bulu bulu cike da fuskarta gwanin kyama haka suka tasheta ta tashi a furgice da wanan sambatun kamar kullum "an daura zainul abideen a gadon mulki Koh?insha Allah bazai hau sarautar nan ba"dukkansu kallo suke bin ta dashi kawai cike da takaicin maganganunta...dakyar suka kamata suka nufi waje da ita asibitin cike yake da mutane dik inda suka bulla kallonsu akeyi harda leke masu tausayi nayi masu toshe hanci da rufe idanuwa sunayi har suka iso wajen motarsu da kansu suka shigar da ita cikin mota halima ta koma mazaunin driver Zahra na gefenta rungume da yaronta dake ta sharba bacci..."Ina muka nufa ya Zahra?" "Gidan hajiya dake bayan gari inda ta siya kwanaki din nan can xamuje tunda abbah yace be bukatar ganinta a gidansa idan yaso sai ku zauna tare ko nasan abban samir insha allahu zai maidaki zanyiwa daddy magana ya kirashi ayi sulhu"kada Kai halima tayi taja motar a guje suka bar harabar asibitin.... ******** Mai martaba yayi gyaran murya bayan gimbiya bilkisu ta gama Koro Masa shawarar da tazo da ita gefe zainul abideen ne zaune yasha shada fara kall da bakar hula ya sadda kansa a kasa.. "Shawarar da kika kawo bilkisu naji dadinta ta a aurawa zainul abideen ummaty yayi hakan,dama tunanin da nakeyi kenan tunda yarinyar nan itace tayi wahala da yaron nan kusan ince itace silar samun lafiyarsa dikda dama na fahimci akwai soyayya da shakuwa a tsakaninsu kawai a Zan nemi sarkin dawaki da maganar yau bayan sallar ishai inji ya zamuyi ba lokaci zamu dauka ba sati daya ne KACAL zamusa a gudanar da hidimar" Murmushin Jin Dadi gimbiya bilkisu tayi "dama fiyya nuradeeen ya Aiko Akan a nema Masa izinin aurenta Dan sarkin agadaz shine nace idan har sun shirya kawai Kai musu izini su turo a gudanar da bikin gabaki daya"..jinjina Kai Mai martaba yayi cike da nishadi "Masha allahu, alhamdulillahi sanan dama yaron nan musaddik na hango masa warisah tunda dadewa idan hakan ne dik a hadasu ayi musu aure auta afnan kawai zata rage" Dariya suka bawa zainul kawai ya Mike ya fice dik suka bishi da kallo cike da kaunar Dan nasu...."bilkisu Amma kinsan zainul abideen Dani yake Kama ko?sai yanzun da ya samu lafiya na hango tsantsar kamarmu" "Amma ai akwai abinda ya dakko nawa ba duka yake Kama da Kai ba"Tai maganar cike da zolaya dukkansu dariya sukasa cikin farin ciki..."zansa a sanarwa sarkin dawaki Kiran nawa bayan ishai" "Toh Allah ya kaimu ya Kara girma ranka ya dade" "Ameeen ranki ya dade"yayi maganar Yana dariya... ******** "Inaga tunda bayan sallar laasar kace zasuzo maganar tsaida ranar ya kamata a sanarwa da mutanen gidan nan tunda mundawo nan kada muyi Abu da ka ko?"..sarkin dawaki zaiyi magana iklima Tai sallama ta shigo ta zube a kasa "ranka ya dade sakon Kiran gaggawa daga Mai martaba cewar Yana bukatar ganawa dakai bayan sallar ishai a fadarsa"... A tsorace sarkin dawaki bakinsa har rawa yakeyi yace "to iklima jeki "ta Mike ta fice...kallon innah yayi "bazan Bari har wanan lokacin ba zanje yanzun inji dalilin Kiran inaga zaifi ko?tunda yanzun din ba wani Abu nakeyi ba?" "Ehh kaje din Allah yasa muji alheri" "Ameen 'ya Mike Yana gyara babbar rigarsa yayi waje..... *HASKE WRITERS ASSO💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 Rashin wuta da rashin comments dinku ke hanani typing wlhy Amma kuyi hakuri nasan nidin me laifice wlhy wanan dalilan suke hanani typing kaduna sai a hankali wutar nepa saura pages uku insha allah SLIMZY✍🏼 [1/23, 11:52 AM] 😍SLIMZY😍: 43 Gurfane sarkin dawaki yake a gaban Mai martaba Yana kwararo Masa dalilin nasa na kiransa sanan ya Dora da cewar "Babu wata sakayya wadda zaayiwa ummaty dangane da hidimar da tayi da yaron nan zainul abideen face a daura Masa aure da ita tunda alamu sun nuna cewar suna son junansu dukkansu su biyun tun suna Yara shiyasa na yanke shawara da mahaifiyar yaron da yaron Akan in tuntubeka Akan maganar nan ta auren yaran inasu inji daga bakinka yuwuwar hakan tunda gashi Dan uwan yaron nan haris ance an nema Masa aure shiyasa nakeso dukkansu a hadasu ayi auren gabaki daya".. Ko kafin Mai martaba ya Gama Koro bayaninsa sarkin dawaki ya jike da gumi tun daga kansa har jikinsa ga mamaki da al'ajabi da yayi Akan maganar Wai ummatynsa ce zata auri Dan sarki?shi kanshi sarkin da kansa yake nemawa dansa auren ummaty?...to da wani Baki zai sanarwa da Mai martaba cewar an bada auren ummaty ga Dan uwan zainul abideen tunda Basu sanar dasu hakan ba?...shiru sarkin dawaki yayi ya kasa magana har Mai martaba yayi gyaran murya yace "sarkin dawaki kayi shiru da maganar,bakace komi ba ko akwai wata damuwa ne?idan an rigada anbawa wani aurenta ba wani Abu bane zainul sai ya hakura ya auri Yar uwarsa warisah"...gaban zainul ne ya fadi Wanda ya kunno Kai zai shigo wajen mahaifinsa Jin furucin da mahaifinsa yakeyi ba karamin tada Masa hankali yayiba da sauri ya shigo fadar har kafarsa na hardewa fuskarsa Babu annuri take maganar da sukayi da haris ta Fado masa hakan ne yasa shi jin Dan sanyi a zuciyarsa... Cike da ladabi ya gaida sarkin dawaki ya nemi gefe guda ya zauna ya sadda kansa ka'sa Yana sauraron Mai sarkin dawaki zaice... Harshensa a daure yace "ranka ya dade banida wata magana wadda zanyi Akan maganar nan dik hukuncin daka yanke daidaine saidai akwai alfarma daya da nakeso ka bani " "Ina sauraronka Fadi alfarmarka sarkin dawaki"... "Ehh inaso zuwa dare zanzo anjima nan din mu tattauna wata magana da haris da zainul abideen"...murmushi zainul abideen yayi ya zaro waya a aljihunsa ya Shiga daddanawa "Babukomi sarkin dawaki Allah ya kaimu"Mai martaba yace cike da murmushi irin na manya Dan ya harbo inda maganar sarkin dawaki ta nufa dama Yana hasashen hakan.... ******** Hawayene kawai yake sauka a idanuwan ummaty a parlor gefenta innarta ce da mahaifinta Wanda ke zaune kusa da ita ya rafka tagumi "ummaty meyasa tun farko kinsan akwai soyayya a tsakaninki da zainul abideen kikabawa haris dama har ya turo iyayensa?sanan kuma abun mamaki ma mahaifiyarsa kanwace wajen Mai martaba Amma Basu San da maganar ba?ni wallahi bansan ta yadda Zan bullowa wanan lamarin ba Dan gaskiya bazan iyawa Mai martaba musu ba sanan bazan kuma iya butulcewa haris ba idan abun yafi karfina haka nan zaa daura Miki aure da haris" Cikin shasshekar kuka ummaty ke fadin "baba babukomi dik abinda Allah yayi Mai kyaune Zan rungumesa hannu biyu biyu matukar hakan shine alheri" Ajiyar zuciya innah ta sauke "to Allah ya zaba Mana abinda yafi alheri" "Ameeen sarkin dawaki ya amshe dashi cike da damuwa...mikewa ummaty tayi jiki Babu kwari tana sharar hawaye ta fada dakin kwananta ta rufo kofa ta Sanya key ta fada Kan gadonta ta saki wani irin kuka Mara sauti.... *******" "Amma Kai haris kana ganin hakan da kayi kayiwa kanka adalci kenan"cewar hajiya kubura cike da damuwa... Cije lebensa yayi cike ya saki Dan murmushi kadan "tun daga ranan da nasa ummaty a idanuwa na naji Ina matukar kaunar yarinyar fiye da tunanin me tunani momy Amma nasan cewar bazan sameta ba duba da yadda suka shaku da kanina zainul abideen dik wani Abu da nakeyi na nuna so da tsantsar kishi banaso ta fahimci komi ne momy Amma wallahi har cikin zuciyata kanina nakeyiwa kamu badan komi ba sai Dan lokacin da suka bar gidansu nasan matukar suka koma garinsu to zaa iya Yi Mata aure a can shiyasa nayi amfani da wanan damar nasa abbah ya nema mun aurenta saboda nasan cewar abbah yanada fahimta sanan kuma yasan cewar bazanyi Abu Dan cutar da wani ba wallahi summa tallahi yarinyar tanada Shiga Rai Amma wallahi tallahi Dan uwana nayiwa kamunta Dan kada ya rasata abbah Dan haka Ina rokonku Akan ku gafarta min abinda nayi kuma na tattauna da zainul abideen din dazun mun hadu na rokesa alfarmar kada ummaty tasan cewar badani zaa daura auren ba sai ranan auren ayi Mata surprise saboda yadda take sonsa take kaunarsa nasan zatayi mamaki sosai ko a yadda nake nuna kishi akanta akansa wallahi be Kai zuciyata ba"...murmushin manya abbah yayi ya dubi haris Wanda ya dasawa zancensa Aya "lallai ka cika d'an halas yarona Allah ubangiji ya saka maka da alheri Allah yayi maka albarka Amma akwai wani kamu da ni kaina yanzun na hasaso maka"...dariya hajiya kubura keyi tana kallonsu cike da kauna,.. "Abbah wani irin kamu ne kayimun haka?" "Why not ka karbi Aysha ko zaheera?ka auri daya daga cikinsu inhar bazaa takuraka ba"..murmushi haris ya sauke har dimple dinsa ya lotsa "abbah na sauki Aysha kanwar fiyya ashmah ko?" Hajiya kubura ta kada Kai cike da Jin Dadi "Kai Masha allahu munada bukukuwa a gidan mu alhamdulillahi nasan Mai martaba zaiyi matukar farin ciki da Jin hakan" "Warisah Kam tunda aka Soma zancen bikin ta da musaddik shikenan ta ware ta daina ciwo ko momy?ni Naga bana ganinta kwana biyu" Dariya sukasa dukkansu hajiya kubura ta amshe zancen "kaji Dan nema kasawa yarinyata Ido haris,warisah taga abin bazaiyuwu bane ta saki jiki don kwanaki Ina ganin take takenta nasan zainul abideen takeso Amma nayi burus da ita Dan nasan bazai yuwuba zainul basa Shiri aurensu ko anyi bazaiyi karko ba shiyasa na kauda kaina a lamarin Amma nasan ko ciwace ciwacen da takeyi na soyayya ne"...murmushi daddy yayi ya zaro waya a aljihunsa ya Kira abokinsa dake aiki a maaikatar alhazai bugu daya ya dauka daga can bangaren yace "ranka ya dade" "Ibrahim Ina bukatar kujerar makka ta mutum goma Sha biyu idan zaa samu Zan biya kudin zuwa gobe" "Ranka ya dade baa Gama biyan kudi ba dama zaku iya biya insha allahu " "Nagode"daddy ya kashe waya ya dubi haris "hajjin bana da ku zaaje da matayenku duka" "Mungode abbah Allah ya Kara girma" "Ameeen"suka amsa a tare suka cigaba da Hira zainul ya Kira haris a waya ya tashi ya fice.... ******* Mai martaba da kansa yasa aka kaishi gidan mahaifiyarsa wadda ke kofar kudu maso arewa.tarba ta musamman tasa akayiwa Dan nata da abinci kala kala na gargajiya irin Wanda tasan yanaso tasa maaikatan ta suka cika Masa table dashi dik abincin da aka kawo tuwo miyar kuka da man Shanu kawai yakeci Yana Hira da hajiya Kaka nan yake sanar da ita da maganar bikin da ake Shirin Yi cikin kwana goma masu zuwa,farin ciki wajen hajiya Kaka baa magana bakinta yaki rufuwa sai hakorin makan bakinta ke walkiya "naji Dadi Kai Masha allahu Allah yasa alheri yasa munada Rai zaayi Kai naji Dadi matuka " "Iyayen nurudeen na wajen safiyya sun turo maganar aure da sadakinta million daya da Rabi suka kawo da kujerar makka sanan warisah ma ta wajen kubura da musaddik angama komi sai zahira da yazeed abokin musaddik yayan nata tare zaayi" Dadi wajen hajiya Kaka kamar zata taka rawa saboda farin ciki take ta Shiga hailala tana godewa Allah suka cigaba da Hira da d'an nata daya tilo... **** Tunda ta Shiga ta kwanta a daki Taki bude kofa bugun duniyar nan innah tayi ummaty Taki bude kofa sai kuka kawai takeyi tana shassheka ga kanta da yake masifar ciwo yake Sara Mata....wayar innah ce tayi ringing dake gefenta Tai saurin juyawa tana hawaye ta dubi wayar sunan haris ta gani gabanta ya yanke ya fadi badai yazo wajenta ba ta tambayi kanta da sauri ta Mike ta zauna Kan gado ta share hawayenta ta Danna recieve ta Kara a kunnenta hade da sallama..... *HASKE WRITERS ASSO💡* 💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞 *SLIMZY😍* [1/23, 11:52 AM] 😍SLIMZY😍: 44 A sanyaye Tai sallamar,daga inda yake ya sauke lallausan murmushi ya dubi zainul dake rike da hannunsa a gefensa ya sakar Masa murmushi shima murmushin ya sakar Masa sannan haris yayi gyaran murya ya Soma magana "ya dai amaryata ya naji muryarki a haka ko bakida lafiya ne?make damunki umm?"....hawaye ne ya sauko a idanuwanta ta sa hannu ta share cikin sarkewar murya tace "babukomi kawai dai kaina ne yake ciwo" "Ayya sannu Allah ya Baki lafiya, dama nida kanina ne zainul Kuma abokina kamar yadda kikasani shine mukazo zai tambayeki me kike bukatar ayi na biki saboda munaso musan naki shirye shiryen"...girgiza Kai tayi kamar Yana ganinta wasu sababbin hawaye na zubowa "bana bukatar komi a bikina sai walima walimar ma nasan da Yan uwanku zaayi saboda ni banida kawaye gaskiya so kaga Babu amfani kenan kubarshi kawai tunda bani kadai zaayi bikinba sai sauran suyi nasu walimar idan yaso sai mu halarci wajen"...yadda take maganar a marairaice tana Jan hanci ya tabbatar musu da kuka ummaty takeyi Dan haka dakyar haris ya saisaita kansa yadda dariya ke neman kwace Masa ya toshe bakinsa sanan yace "toh shikenan Amma gaskiya mun rigada munzo sashen ku ta baya ki leko kawai Inga fuskarki inji Dadi kinji matas"...Yana Gama fadin haka ya datse wayar be jira me zatace ba,shida zainul suka tuntsire da dariya zainul ya Dan bugi kafadarsa "haris banason iskanci kaji ko ya zaka zauna kana sa min matata kuka?Anya Zan iya jure ganinta a wanan yanayin ban fallasa abinda ke cikin zuciyata ba?" "To majnun sarkin soyayya ?ko kunyata ma Bakaji kake fadin irin wanan kalaman a gabana da katon kanka"...zaiyi magana yaji alamar kamar Ana tahowa take dukkansu suka saisaita kansu,...zainul abideen gefe ya koma Yana fuskantar baya shiko haris shi yake fuskantar inda zata bullo....ta dade Tana lekensu gabanta na tsananin faduwa kafin ta daurewa zuciyarta ta fito sanye da dogon hijabinta maroon har kasa fuskarta tayi fayau ta Kara fari sosai idanuwanta sun Dan fada kadan sai doguwar fuskarta dakyar ta tako ta karaso inda suke bakinta dauke da sallama Kai a kasa ta tsaya gefe,...juyowa sosai haris yayi Yana fuskantarta hade da murmushi "dik kukan rabuwa da innar ne haka ummaty?nifa banaso a kaimun ke a rame".... Juyowa zainul abideen yayi karaf ya amshe zancen "kaifa bakada kunya ka Bari akai maka ita Mana sai wani zumudi kakeyi bayan kayiwa wasu overtaken...hmmmm nimadai Allah yasa inada tawa matar Kuma Ina son abuna"...yaddai Tai saurin dagowa ne yasa dukkansu suka zuba Mata ido a tare ,da sauri ta sunkuyar da kanta gabanta na tsananin faduwa ita kanta kunya taji na kasa daurewa da tayi... Murmushi suka sakarwa juna haris yayi gyaran murya "Bari muje baby dama nazo ne Inga kyakkyawar fuskar nan naganki Kuma naji Dadi sai kinjimu Dan Mai martaba ance yana nemanmu Bari muje"...be jira cewarta ba ya tabo kafadar zainul "muje ko"..tsaye tayi ta bi bayan zainul abideen da kallo yadda ya juya ko kallonta beyi ba har suka fice a gidan,durkushewa tayi a kasa tana kuka Mai ban tausayi,iklima ce tazo ta dagota tana lallashinta ta Shiga da ita ciki.... ******** Iska Mai zafin gaske ya furzar lokacin da suka fito gidan anty Zahra aka shaida Masa cewar ai Bata zama kullum tana zuwa jinyar mahaifiyarta,...tausayin Zahra ne ya lullubesa saboda Babu ruwanta a rayuwa batada matsala Saar mahaifiya da Yar uwa tagari ba tambayar kansa yayi inda suke yanzun saboda yanaso ya sanar da Yan uwansa maganar bikin Dan maimartaba da ammiey ko ta kansu beyi sabgogin biki kawai sukeyi ana kashe kudi,.. Ganin shirun yayi yawa yasa haris zungurarsa "muje Mana"shafa kansa yayi ya dubi haris da jajayen idanuwansa "tunanin inda zansamu su anty Zahra nakeyi Dan akwai rashin dacewa inhar baa sanar musu da maganar bikin nan ba" "Muje zainul nasan inda suke Dan na taba ganin halima ta bullo daga sashen tana driving a motarta idan yaso ko tambaya ne sai muyi"..tada motar zainul yayi ya ja a guje sukabar unguwar... Tafiyar minti talatin ta sadasu da unguwar da haris yake kwatantawa zainul gefe suka samu sukai parking motarsu suka fito,hangen mutane tsuraru sukayi suna alwala a kofar wani gida Mai Kama da gidan sarauta sarauta pentin gidan,sai haris yace "Bari musamu mutanen can muyi tambaya ko akwai Wanda ya sani"...shidai zainul gabansa kawai ke tsananin faduwa bece komiba yabiyo bayan haris har kofar gidan,zasuyi magana kenan aka fito da gawa daga cikin gidan halima ta fito a guje tana kuka wasu mata suka rukota tana fizgewa tana Mika hannu "wayyoo ummah kin mutu kinbarmu ummah akwai ranan da zamu budi Ido dama ki mutu kibarmu a cikin wanan duniyar?kaicona ummah Allah ya yafe Miki kura kuranki"matan ne suka rirruke halima sukai ciki da ita,...kallon kallo haris sukeyi shida zainul ko wanne cikin su al'ajabi da tsoron Allah ya lullubesa,...zainul kuwa mutuwar tsaye yayi Yana bin makarar da kallo har aka ajiye gefe,..."ummah rumana ce ta rasu fa"cewar haris muryarsa na sarkewa....hawaye ne ya ciko a idanuwan zainul abideen zuciyarsa a karye ya kalli haris ya share hawayen da ya zubo Masa "muje me bi sallar gawa tunda yanzun mukai azahar munada alwala Koh?"...gyada Masa Ido haris yayi da jajayen idanuwansa suka taka har inda akaja sahu nan da nan suka kabbara salla sukabi sallar gawa.... Har inda aka bizneta zainul da haris Saida sukaje dasu akayi komi sukai Mata addua sosai,zainul yasha kuka tamkar wani mace tsoron duniya da tsoron Allah ya Kara lullube zuciyarsa haka suka biyo ayarin mutane suka dawo,..."mu Shiga cikin gidan"suka Shiga a tare bakinsu dauke da sallama zahar na gefe tana shayar da yaronta tana kuka su zainul suka shigo dukkansu a tare suka Mike tsaye da halima da Zahra suka taho a guje suka rungume kanin nasu suna kuka Mai ban tausayi haris gefe ya koma Yana sharar hawaye saboda tausayinsu dik halima tayi Baki ta fita hayyacinta ga Babu miji da samir da sumayya da sabreen yaranta suna wajen mahaifinsu inda yaran suna hannunta zata danji sanyi a ranta.... Gefe suka koma da zainul da haris da halima da Zahra suka Shiga tattaunawa da maida yadda akayi da yadda gimbiya rumana ke amayo tsutsotsi da kana na kana nan tsokokin cikinta da suka zagwanye abun Babu Dadi haris ne ya Basu shawara akan idan anyi uku su dawo gida tunda Basu sukaiwa Mai martaba laifi ba kuma Zahra tanada aure halima ce zata zo su Roki sarki tare ya yafe Mata ta dawo gidan ubanta da zama da wanan shawarar suka gamsu suka rabu cikin kaunar Dan uwan nasu,har wajen mota suka rakasu suna daga musu hannu tare da ce musu gobe ma zasu zo....haka suka bar wajen cike da alhini. ******* Dawowarsu zainul gida da fadin rasuwar gimbiya rumana ba karamin girgiza masarautar yayi ba kowa da kowa ya Shiga taitayinsa musamman maaikatan gidan Wanda sukasan yadda gimbiya rumana ke zuba mulki da Isa,... *Tsokaci* lallai duniya baa bakin komi take ba Kuma abinda ka shuka shi kake girbewa ko wani Dan adam besan yadda karshensa zatayi ba kasan farkonka bakasan karshenka ba shiyasa ake tunasar damu kullum mutuwa ta kanzo maka a lokacin da bakayi tunani ba baka San yadda zata riskeka ba Kayi kokari ka aikata Mai kyau kodan kwanciyar kabari da tashin alkiyama Wanda ranan yauma tubulassara'ir ranan tonon asiri ga ko wani Dan adam inma ka shuka Mai kyau ko akasin haka a fili Kayi ko a boye baka saniba ranan agaban kowa zaayi hisabi kowa nafsi nafsi kowa kokari yakeyi ya karbi littafinsa da hannun dama Allah ubangiji yasa mu karbi littafinmu da hannun Dana muna faraa cikin yantattun bayi daga wuta zuwa aljannah Allah karya bamu ikon cutarda Dan uwanmu musulmi ameen Hatta gimbiya bilkisu Saida ta zubar da hawaye Jin labarin mutuwar gimbiya rumana Wanda ya tariyo Mata rayuwar da sukayi a baya yau Ina take? Mai martaba kansa ya Tara jamaar gidan akayi saukar alkurani akayi Mata addua jiki Babu kwari ciki hardasu ummaty wadda Tai kuka kamar zata mutu tare da yafewa gimbiya rumana dik abinda tayi mata fatan itama Allah ya yafe Mata..... ********* Ana gobe biki halima da Zahra sukazo wajen mahaifinsu suka rokawa mahaifiyarsu gafara halima ta Roki mahaifinta Akan ya yafe Mata batasha wahala ba ya yafe Mata hatta ammiey taji dadin dawowarsu cikin family dama halima muruniyarta ce Dan haka sashinta tabata dakinsu fiyya aka Shiga gyarawa tunda dukkansu aure zasuyi Afnan ce kawai zata rage.... Hajiya kubra da mamansu zahira hajiya hadiza dik tattarowa sukayi suka dawo gidan Mai martaba inda aketa gudanar da Shirin biki gida ya cika makil da Baki na nesa Dana kusa ga Kuma nadin sarautar zainul abideen wadda zaayi bayan angama daurin aure sarki zaiyi murabus ya huta ya Dora dansa daya tilo a karagar mulki, Bangaren su ummaty kuwa Yan kauyensu sun bayyana su gwaggo kuluwa dik sunzo ita kanta ummatyn batada lokaci kullum cikin zuwa gyaran jiki sukeyi gidan hajiya jummai Mai gyaran amare inda gimbiya bilkisu ta biya makudan kudade wajen gyaran amare,a nan ne Ashma da warisah da zahira da fiyya suke sanar Mata ai ashmah ce zata auri haris itace zata auri zainul Wasa da hankali kawai akeyi Mata,....ummaty jinta takeyi a wata sabuwar duniya Mai cike da Jin Dadi da nishadi Bata taba tunanin ko a mafarki zata auri Dan sarki Wanda ke Shirin zama sarki ba uwa uba ta koma matar sarkin kansa alhamdulillahi da wanan baiwa da niimah da Allah yayi Mata..... Bangaren angwaye baa barsu a baya ba Komi tare sukeyi dik inda zasuje tare suke zuwa kamar wasu Yan biyar kowa sai Sam barka yakeyi..... "******* Karfe goma Sha daya aka Soma daura aure inda aka daura auren haris da Aysha (ashmah)fsrko tunda shine babba sai "musaddik da warisah, sai zainul abideen da ummaty ,nurudeen da safiyya...sai a karshe aka daura na yazeed da zahira....bayan angama daura aure ne kuma aka Shiga cikin nadin sarautar zainul abideen inda dubban jamaa da sarakunan masarautu dayawa suka halarta...a nan zainul ke shaidawa jamaa cewar ya bawa baba kande mukamin zama jakadiyyarsa muddin Rai.... ******** Bayan magriba Kuma aka tafi zuwa dinner inda Zahra da halima suka hadawa amaren suka Kuma gayyaci kowa da kowa zuwa wajen,...naira Kam tayi kuka sosai a wajen nan abinci kala kala Babu Wanda Babu kowa farin ciki yakeyi hajiya kubra da gimbiya bilkisu da hajiya hadiza da Zahra da halima akwansu kala daya ne leshi sky blue da head dinsu silver amare dukkansu lace dinsu golden ne sai head dinsu silver dukkansu Komi nasu iri daya ne an cashe a wajen an rabashe afnan ta rasa inda zatasa rayuwarta saboda Murna dik inda ka waiga zaka hangeta suna kashe hoto itada anty nafisah kanwar ammiey .... ******** Estate guda kowa da gidansa Mai martaba ya bada cikin gidajensa da estate estate Wanda yake dashi cikin gari kowa da sashensa sanan ko wace amarya ankaita sashenta....motarsu zainul ce ta kunno Kai motoci uku ne suka shigo dik angwaye ne a ciki driver's suka jawosu ... Ko wanne fuskarsa dauke da faraa haris yace "dare nayi nasan amaryata tsoro gareta Bari in garzaya Kar inbar abuna ita kadai"dariya sukasa dukkansu sukai sallama da juna kowa ya nufi sashensa... Zainul yasha Nadi fadawa na biye dashi har kofar Shiga ya bude kofa kenan ya juyo ya kallesu "ba a nan zaku kwanaba kuje gidan Mai martaba kafin a gyara naku sashen Saida safe"ya rufe kofar ya barsu tsaye suna kallon juna..... Sanye take da alkyabbarta Mai ruwan Zuma kanta durkushe tana Wasa da yatsunta da suka Sha lalle ya tsaya Yana Kare Mata kallo...kamshin turarensa ya daki hancinta ta dago Kai a hankali ta sauke idonta cikin nasa suka hada Ido Yana cikin Nadi da farar malum malum yayi masifar kyau ta kasa dauke idonta daga garesa har ya karaso gabanta Bata saniba ya Hura Mata iska ta lumshe idanuwa zata boye fuskarta ya dauketa cakkkk ya Shiga juyi da ita cikin dakin ya sabata a kafadarsa Yana juwa da ita dukkansu dariya sukeyi sosai a take ya direta kasa ya rungumeta tsammmmm suna dariya ..... **Tammat bihamdullah nan nakawo karshen labarina naso inraba page din sai nayi kawai guda* *daya Dan Allah Ina rokonku gafara na rashin posting akaikai wallahi ba haka nakeyi ba wanan* **karon akasi akasamu Dan haka nake rokon gafara daga gareku nagode* **kwarai da kauna Allah ya saka muku da* *mafificin alheri......* *** **HANKALINA BAYA KWANCE SHIYASA BAKUJINI BA INADA* *MARALAFIYA DAN ALLAH KUSATA A ADDUA ALLAH YA BATA LAFIYA YA* *SAUKETA LAFIYA* *SLIMZY✍🏼* *