https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC 💘 ZAƁIN ZUCIYA💔 THE HEART'S CHOICE BY NARNAH ƘANWAR SOJA Birthday Gift Novel by Sayeedan Adda July queen Leo 🌙 Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM PAGE 1 best on true life story INTRODUCTION "When the heart chooses, even silence speaks. And when love travels far, memories walk back home." a cikin rayuwa, wasu soyayya na zuwa da sauƙi – kamar iska da ke busowa daga arewa; wasu kuma na zo da wuya – kamar ambaliya da ta hana ruwa kwarara. Wannan littafi, ZAƁIN ZUCIYA, ba kawai labari ba ne — wata zuciya ce da ta zaɓa ta ƙi mantuwa, ko da nisan da ya zo, ko da shiru ne ya maye gurbin saƙo. It's a story of distance and nearness of souls. a tale of rauni, of waiting, and of choosing again and again a wannan littafi: Zamu haɗu da zuciyar da ta kasa mantawa da wanda ta zaɓa Zamu shiga duniyar da soyayya ke jure nesa, jure sabani, kuma tana da ƙaƙƙarfan fata Zamu fahimci cewa ba kowanne zaɓi ne mai sauƙi ba, amma wasu zaɓuɓɓuka na zuciya ba su da musanya 🎉 Happy Birthday to Me July Girl Special 🎂✨ Wannan novel an rubuta shi ne a matsayin kyauta na musamman ga kaina — a matsayin wata ƙauna da nake yarda da ita, ko da kuwa ta zo da ciwo. Na zaɓi na baku labarin zuciya Na zaɓi in ba zuciya murya. Na zaɓi “ZAƁIN ZUCIYA” – saboda ba kowa ke fahimtar irin zaɓin da zuciya ke yi ba, sai wacce ta taɓa ƙauna da rauni. Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words. Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌 **************"""""""""""""""""" A RAINY NIGHT IN JULY “Some hearts don’t forget – they just grow quiet.” Ƙarar ruwan sama ne ke bugun tagar ɗakin, kamar yana son shiga don ya ce mata: "Ina jin zafin ki." Ɗakin ba mai fadi bane, amma cike da natsuwa tagar gidan karama ne, amma tsafta da kamshi na lavender ya karade ko ina. An shimfiɗa farin farar bed sheet, wani dogon hula mai launin kore a gefe, da na'urar wayarta a gefen pillow – sai hasken screen ɗin da ke yawo da sunansa: Best Choice "Still Online..." A gefen mirror ɗin da ke bango, tana zaune – Ƴar shekara 21 amma idanunta na ɗauke da sirrin shekaru goma sha biyar da suka shude. Black beauty ce – fari ba sosai, amma fata ce mai ɗaukar haske. Lips ɗinta kamar rubutattun baitai – thin and sweetly dark, kamar an zana. Idanunta manya, dogaye, masu cike da tambayoyi da sirri. Gashin kanta yana da tsawo, sai dai ta na yawan ɗaure shi da bun ko kuma ta ɗaure da kyalle mai soft floral prints. “Why am I the one still waiting?” ta furta a hankali, kamar tana tambayar tagar, ko wataƙila zuciyarta ce. Sunan ta Ammatullah ba don suna yana da kyau ba kawai, sai don yana da ma’ana: wacce take ba da zuciya gaba ɗaya idan ta ƙauna. Ba ƙaramin so ta yi masa ba – saurayin da zuciyarta ta zaɓa. kuma yanzu, a cikin watan da aka haife ta, watan da duniya ke yi mata barka, ita kuma tana jin komai yayi shiru amman ko magana bai mata ba duk da yasan wanan muhimmancin rana a garita . Shiru mai nauyi, shiru mai wuyar fassara. She wiped a few stubborn tears that escaped her eyes, but her chest… it was a battlefield. A war between silence and screams. Suddenly, her body gave in — her knees curled to her chest as she collapsed on the bed, Hannu biyu biyu tasa ta toshi bakin ta tana ihu kamar ana tsibtar da ita da wuka tana amballiyar jini .. Ammatullah burst into tears. Not the soft sobs of a broken girl… But the deep, painful cries of someone who had lost her future — because to her, Nashwan was everything. “Why…? Why me?” ta furta da raɗa, cikin kuka mai kauri da tsananin ciwo. “Ya za a yi ace ni ce nake ƙauna da gaske, but he’s the one who moved on so fast?” “Na rasa komai…” ta furta a hankali, kamar tana magana da numfashin zuciyarta. “Shine farkon zaɓina, kuma shi ɗaya ne nake so…” tasa hannun ta a kirjinta kamar zata turo numfashin ta cikin ta. Zuciyarta na fizgewa da ciwon da ba a ganinsa, sai dai a ji shi. “Shi ya kamata ya tuna ni yau…” ta ce, hawaye na gangarowa. “…amma sai yau ne ya zabi ya manta da ni.” Wayar ta zame daga hannunta ta faɗi ƙasa. Zuciyarta na ta kai da kawowa, tsakanin mantawa da tunawa, tsakanin fata da fargaba. Tsakar dare, a cikin daki mai shiru, zaɓin zuciyarta ya ci gaba da hukunta ta. “Some wounds don't bleed, they echo in silence.” “He was my first love…” Zuciyarta ta furta kamar wata ƙaramar murya daga ciki. “…and he left me with a silence that screams louder than his goodbye.” tana jin zuciyarta na fizgewa da dukan da ba ta da ƙarfi akai. Tana jin kowane message notification kamar fata, ana wishing nata happy birthday amma ba shi bane. Sai take jin kamar duniya gaba ɗaya ta barta — a ranar da ita ce birthday month ɗinta, Nashwan ya zabi ya manta da ita. Bacci mai wahala ne ya kwashe ta, idanunta cike da hawaye, zuciyarta a hargitse. Ba wai saboda ba ta so ta manta dashi ba, amma saboda zuciyarta ta zaɓa shi – kuma zuciyar tana da taurin kai fiye da kwakwalwa. "First love never leaves… it just buries itself deeper." Narnah ƙanwar soja ✍️ https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC 💘 ZAƁIN ZUCIYA💔 THE HEART'S CHOICE BY NARNAH ƘANWAR SOJA Birthday Gift Novel by Sayeedan Adda July queen Leo 🌙 Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM PAGE 2 best on true life story INTRODUCTION 07/7/2025 "When the heart chooses, even silence speaks. And when love travels far, memories walk back home." a cikin rayuwa, wasu soyayya na zuwa da sauƙi – kamar iska da ke busowa daga arewa; wasu kuma na zo da wuya – kamar ambaliya da ta hana ruwa kwarara. Wannan littafi, ZAƁIN ZUCIYA, ba kawai labari ba ne — wata zuciya ce da ta zaɓa ta ƙi mantuwa, ko da nisan da ya zo, ko da shiru ne ya maye gurbin saƙo It's a story of distance and nearness of souls. a tale of rauni, of waiting, and of choosing again and again a wannan littafi zamu haɗu da zuciyar da ta kasa mantawa da wanda ta zaɓa, zamu shiga duniyar da soyayya ke jure nesa, jure sabani, kuma tana da ƙaƙƙarfan fata zamu fahimci cewa ba kowanne zaɓi ne mai sauƙi ba, amma wasu zaɓuɓɓuka na zuciya ba su da musanya 🎉 Happy Birthday to Me July Girl Special 🎂✨ Na sadaukar da wanan littafin wa karan kaina kasancewar sa a watan haihuwa ta July.. Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words. Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌 **************""""""""""""""""" The Quiet Hope Safiyar Asabar ce, kirar sallar Asuba ta farko ce ta farka da ita – sautin muryar mai ƙira kamar yana faɗin sunanta bata tashi da walwala ba, amma zuciyarta tana ɗauke da wata dabara guda ɗaya: Ta sake duba Nashwan... Cikin addu’ar zuciya, da kalmomin da ba a jin su sai Allah, ta lalloɓo wayarta a gefen matashin kai, idonta ya kumbura, idon mai kuka amma idon mai fata. “ko ya tuba da shiru?” ta tambayi zuciyarta. “ko kuwa ya tuna yau?” ta hau WhatsApp da sauri kamar wani numfashi ne ke jiran ta a can. Tayi scroll har ta isa inda sunansa ke rubuce da wani ƙaramin emoji. Nashwan 💞 last seen 1:30am. Tayi wani lumshewa da ido. Ta ji kamar wani abu mai sanyi ya sulale a zuciyarta — sanyi mai ciwo, mai nauyi. Shiru. Babu reply. Babu "Hi". babu "Ina kwana sai nothing. Ta maida wayar tana zubar da numfashi mai dumi, ta saka a charger ta fita zuwa barandar gidan su. Sanyi ne ke yawo a iska, yana shafan fuskarta kamar yana ce mata, “Ki kwantar da hankali, ko da zuciya bata so.” Jikinta a lullube da doguwar riga ta shadda mai launin blue mai sanyi, hannayenta a jike da ruwan dare. Ta ɗauki buta, ta zuba ruwa, sannan ta nufi bayangida. A lokacin da ruwan farko ya sauka jikinta, ta rintse ido – kamar tana jin an wanke mata damuwa, ko da kuwa ɗaya daga cikinsu ne. Sannan ta fito a hankali, numfashinta ya sauya kadan, sai ta nufi inda za ta yi alwala. hannu na biye da ruwa mai sanyi, zuciya na biye da addu’ar da ba a furta ba. “Ya Allah... idan har ina cikin zaɓin zuciyarsa, ka ƙarfafa shi da magana. Idan kuma bana ciki... ka ƙarfafa ni da mantuwa.” Tana shiga ɗaki, jikin ta da sanyi na waje, zuciyarta da dumin damuwa — ta shimfiɗa sallaya da nutsuwa, kamar wacce ta saba mayar da damuwa sallah tayi niyya da nutsuwa. Sallah ta faraAllahu Akbar… Ruwa na gangarowa daga idonta ba tare da kuka ba – addu’a ce ke zuwa da hawaye. Tana sujada tana furta sunan wanda bata son ambata, amma zuciyarta ba ta ƙi yi masa addu’a ba. Bayan ta idar da sallah, ta zauna cikin nutsuwa kamar mai jiran saƙo daga sama. Sai ta ɗaga hannu, idanu a rufe. “Ya Allah… idan so ne, ka sa ya yi halin soyayya. Idan jarabawa ce, ka sa in zama mai hakuri. Idan kaddara ce, ka sa zuciya ta karɓa.” Da take juyawa don ɗaukar Qur’ani, sai idonta ya sauka a kan ƙaramar ƙanwarta Safiya, tana ta mirgina a kan gadon gefe kamar wacce ake ƙoƙarin tashi da ƙarfin hali. “Safiya!” ta kira da ƙara kaɗan, “Asuba tayi! Tashi ki gabatar da sallah kafin Sarki bacci ya mamaye ki gaba ɗaya.” Ta ƙara ɗan ƙara da dariya, "Duk yaƙin da na yi da bacci jiya, ke kina nan kina 'kwashe bachi' kamar a sace ki a sa ki a buhu." Safiya ta buɗe ido da firgici, tana goge fuska da hannunta, “Adda Amatu… Yaƙi? Me ya faru?” Kamar wacce ta tashi daga duniyar mafarki, tana duban fuskar yayarta da ke ɗauke da wata irin haske mai rauni. Amatu ta murmusa, ta ɗan lumshe ido, sai kuma ta ɗan dariya – dariyar da ta fi kuka ciwo "babu komai, safiya zuciya ce kawai… tana ƙoƙarin doke duhun dare." Ta ɗauki Qur’ani mai tsarki, ta buɗe shi a hankali, ta ɗora hannunta sama da shafin, sannan ta fara karatu da muryar da ke sanyi amma cike da ƙarfin ruhi “Wa innaka la'ala khuluqin 'azeem…” Hasken safe ya fara shigowa ta taga. Rana ba ta bayyana sosai ba tukuna — amma karatun ta yana bayyana haske a ɗakin. Kalmar Allah tana ratsawa da hancin lavender da na tunanin Nashwan da har yanzu ba ya magana "Zuciya dai tana karatu... kuma tana jiran amsa daga sama ko daga nesa." Karfe shidda da rabi, fitilar safe na cika ɗakin da kwarjinin launin ruwa, zuciyar Amatu na jiran sautin da ke iya canza dukkan yanayin rana ɗaya saiga notification ɗin wayarta ya yi tsetsen haske. Ta kalle shi da idon da ke nuna gajiya da ƙuntatawa hankalinta ya yi raye; ko Nashwan ne? ko kuma har yanzu yana da zuciyar barin ta cikin shiru? A hankali ta matsa yatsanta, ta buɗe screen ɗin wayar Tecno Pop 8 ɗinta. Credit Alert. ₦50,000. Narration: "Happy birthday my Amatu." murmushi ya bayyana a fuskarta – ba irin na farin ciki ba – murmushi ne mai ɗauke da ciwo, kamar wanda aka lulluɓe da kyalle mai ɗumi da ciwon fatan rai, "kai nake so, ba kuɗinka ba..." ta furta a zuciyarta da wata irin murya mai kama da kuka da dariya. Ba tare da jinkiri ba, ta matsa lambar Nashwan kiran farko—ya wuce na biyu—ya tsallake na uku—ya ƙi karɓa. kafin ta samu damar cire wayar daga kunne, sai kira ya dawo. Zazzaggar muryarsa, mai kama da busar sarewa mai ƙayatarwa, ta cika kunnenta da wani sauti mai sanyi kamar ana karanta wata waka daga nesa “My dear… kin tashi lafiya?” muryarsa cike take da nutsuwa da laushin murya mai wuyar mantawa kamar yana cin amanar zuciyarta ne, yana lalube inda ta fi rauni. Amatu ta haɗiye yawu, ta yi kokarin gyara murya, amma har lokacin zuciyarta na harbawa da ƙarfi. “lafiya lau Nashwan na tashi lafiya, sai dai... last night broke me in pieces.” ta ce da murya mai sanyi, cikin wani irin nauyin zuciya da rashin iya boye gaskiyar da ke kwance a ranta. Ya yi shiru na dan lokaci kamar yana hadiye abin da bai so ya furta ba. “I'm sorry baby… I just— I didn’t know how to face you. I was hurting too. You mean more to me than you’ll ever understand.” kalmar "baby" da "you mean more to me" sun karyar da wani ƙaramin bangon da zuciyarta ta gina da hawaye jiya. ta juya gefen gado, ta jingina da bango, idonta cike da hawaye amma baki na dariya. “I didn’t ask for your money, Nashwan. I asked for you your presence... your voice... just you.” kamar ta goge fuskar allon don ta ganshi a zahiri. “I know I was a coward amma ina so ki sani: wallahi kina cikin zuciyata fiye da yadda nake cikin tawa. I miss you every moment I breathe.” Kalmarsa ta shige jikinta kamar ruwan zafi a sanyi, ta narke cikin soyayyar da ta kasa kare kanta daga gare ta. “So… yanzu fa? What do we do?” ta tambaya da dariya mai sauƙin gaske, tana kokarin boye tsoron da zuciyarta ke yi. “We fight. For us. For love. For what we started.” Ya furta da wata irin karfi da tabbatarwa. “And right now, all I want is to hear your voice until the sun sets.” ta ƙara lumshe idonta, ta ce: “Then talk, Nashwan. I’ll listen… even if the world goes silent, I’ll still hear your heartbeat through your words.” Wayar ba za ta katse ba soyayya na tafiya cikin wayar tamkar jini da jijiya sun bar duniya a waje, sun ɓullo sabuwar hanyar da zata iya zama mafita ko mafarki mai rai. TSOKACI Zan bar ku da ɗan tambaya: Shin soyayyarsu zata jure gwagwarmayar da ke gabanta, ko kuwa Nashwan na da wani sirri da ba a tona ba tukuna? Kuyi min uzuri na rashin posting kwana biyu ina sunƙullar aurar da ɗiyata ce ina muku fatan alheri a kodayaushe daga yau posting zai fara zuwa muku a cikin ranakun mako biyar ina godiya sosai da addu'a da fatan alheri da kuka nuna min a wanan kwanakin mujee zuwa sabon littafi Mai taken masoya da soyayyar nisa , sabbin jarumai IRRIN NASHWAN , AMATULLAH Shin soyayyar su cikakkiya ce ko kuwa burin Amatu da wanan zazzafan soyayyar da ta ɗaurawa namiji ɗaya takk a rayuwar ta bazai cika ba ? Ku chigaba da kasancewa cikin alƙamin...... Narnah ƙanwar soja ✍️✍️ https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC 💘 ZAƁIN ZUCIYA💔 THE HEART'S CHOICE BY NARNAH ƘANWAR SOJA Birthday Gift Novel by Sayeedan Adda July queen Leo 🌙 Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM PAGE 3 & 4 best on true life story INTRODUCTION 11/7/2025 "When the heart chooses, even silence speaks. And when love travels far, memories walk back home." a cikin rayuwa, wasu soyayya na zuwa da sauƙi – kamar iska da ke busowa daga arewa; wasu kuma na zo da wuya – kamar ambaliya da ta hana ruwa kwarara. Wannan littafi, ZAƁIN ZUCIYA, ba kawai labari ba ne — wata zuciya ce da ta zaɓa ta ƙi mantuwa, ko da nisan da ya zo, ko da shiru ne ya maye gurbin saƙo It's a story of distance and nearness of souls. a tale of rauni, of waiting, and of choosing again and again a wannan littafi zamu haɗu da zuciyar da ta kasa mantawa da wanda ta zaɓa, zamu shiga duniyar da soyayya ke jure nesa, jure sabani, kuma tana da ƙaƙƙarfan fata zamu fahimci cewa ba kowanne zaɓi ne mai sauƙi ba, amma wasu zaɓuɓɓuka na zuciya ba su da musanya 🎉 Happy Birthday to Me July Girl Special 🎂✨ Na sadaukar da wanan littafin wa karan kaina kasancewar sa a watan haihuwa ta July.. Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words. Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌 Bayan sun datse wayar, Amatu ta lumshe ido tana sauke wata ajiyar zuciya da ta fito daga zurfin ruhinta, kamar wacce aka saukar daga dutsen damuwa. “Muryar Nashwan… kawai taji ta, duk wata ƙunci sai ya shige. Ina son shi, so da ban taɓa yiwa wani ba shi nake yiwa addu'a cikin dare da safiya murya sa kaɗai na isar da farin ciki cikin zuciyata.” Ta furta da wani irin ƙanƙanin murya mai sanyi, hannayenta a cike da rawar sanyi da tunani wani irin so ne da ba ya buƙatar kyauta, ba ya jiran reply—kawai kasancewar shi ne abun girmamawa da mafarki. Cikin wannan nutsuwar da shauƙi, sai ga Mama ta shigo. Macce ce kamila, ba za ta haura shekara arba’in ba, mace mai sanyin fuska da sautin tafiya mai kwantar da hankali. Amatu ta sauko daga katifa tana gaishe da ita, safiya na gefe tana gyara lilo da dariyar kwanciyar hankali. An samu ruwa da safe, dusar gajimare da daddadan sanyin iska ya lullube garin su uku suka fita wajen gida domin ɗaukar aikin safe kamar yadda suka saba. A cikin shirin tafiya aiki, Amatu ta shiga bayi tayi wanka, ta fesa turaruka masu daɗin ƙamshi, sannan ta zaɓi kaya farare—suit mai sauƙi da lafiyayyen hijabi. Da ta fito sai shape ɗinta ya bayyana da salo: ta cika cika ta kwanta kwanta, amma cike da modesty da kamun kai a gabanta na madubi, ta tsaya tana kallon kanta, hannunta na dafa ƙirji kamar tana tambayar zuciyarta ita wacce ce. WACCECE AMATULLULAH...? Amatullulah ’yar mace mai kamun kai da imani ta fito daga gida na natsuwa da tarbiyya, amma rayuwa ta koya mata yadda ake zaune da hawaye a fuska da dariya a zuciya. tana da murmushi da zai iya warkar da zuciya mai ciwo, da idanu masu taushi kamar ruwa mai nutsuwa. ba ta da hayaniya, ba ta da surutu, amma idan ta kalle ka da idonta, zaka fahimci cewa akwai sirri da zurfi da ta ɓoye. tana aiki a asibiti, ƙaramin matsayi ne – health care assistant – amma zuciyarta girma take da tausayi da kulawa. A duk ranakun da take fuskantar wahala, bata taɓa fushi da Ubangiji ba. Soyayyarta da Nashwan wata labari ce ta silent devotion, tana iya hakuri da komai saboda shi. Amatu ba mace bace da za ka gane da fari, dole sai ka tsaya ka zurfafa—sai ka fahimta a hankali. Akwai wani abu a cikin shigarta, cikin tafiyarta, cikin yadda take kallon madubi tana tambayar kanta: “Shin ni ce ta cancanci soyayyar sa?” Toh, ita ce. Amatullulah ce. Wacce Nashwan ke mafarki da ita wacce rayuwa ta so tayi wa rauni, amma zuciyarta ta ƙi karɓar karyewa. AMATULLULAH YUSUF LABARAN Amatullah Yusuf Labaran, kyakkyawar budurwa mai cike da nutsuwa da kunya, ta fito daga karamin gida mai tarin daraja da tarbiyya. Ita ƴar asalin Borno ce, daga unguwar Gwange, wato ɗaya daga cikin tsofaffin unguwanni masu cike da tarihinta da rayuwar talakawa a birnin Maiduguri. Unguwar da take cike da ɓoyayyun daraja—duk da talaucin da ya bayyana a bango da ƙofar gida, akwai arzikin zuciya da girmamawa a cikin iyalanta. Unguwar da ko ruwan famfo ya ƙi fitowa, mutane ke da zuciyar taimako da hakuri da juna. Malam Yusuf Labaran mahaifin Amatu, mutum ne mai ilimi da ɗabi’a. Ba shi da yawa a aljihunsa, amma ya cika da basira da tarbiyyar da ya tura wa ‘ya’yansa. Ma’aikacin gwamnati ne—malami a makarantar sakandire ta gwamnati. Rayuwar malam Yusuf ba mai cike da kwaɗayi ba ce; sai dai koyarwa da addu’a da fatan ‘ya’yansa su rayu cikin nasara da tsoron Allah. Yana da yara uku: 1. Mahir Yusuf Shi ne babba a cikin ‘yan uwansa. Yana da shekaru 23 a duniya. Dalibi ne mai hazaka a jami’ar University of Maiduguri, sashen Computer Science. Kamar mahaifinsa, yana da nutsuwa da hangen nesa. Slsai dai Mahir ya fi son ya fita daga ƙungiyar talauci da ɗan karen aikin gwamnati—yana mafarkin kafa IT Company ɗinsa, domin ceto iyayensa daga wahalar rayuwa. 2. Amatullulah Yusuf Tana cikin matsakaicin shekaru, shekarar ta ashirin kenan ɗiyar da malam Yusuf ke alfahari da ita. Budurwa ce mai hankali da kamun kai, tana aiki a babban asibitin gwamnati – General Specialist Hospital, Maiduguri – a matsayin karamar nurse (healthcare assistant). Ta saba da sanyi da zafin asibiti. Idonta ya saba da ganin hawaye, amma zuciyarta bata saba da bari ta bayyana nata ba. Tana da kwarjini, da hali mai jan hankali. Duk wanda ya sadata da ita yana gane cewa akwai zurfin hankali da farin ciki mai ɓoyuwa a cikin sirrinta. Shi ya sa Nashwan bai gushe da soyayyarta ba – ko da yake zuciyarta tana cike da shakku da mafarki. 3. Safiya Yusuf Ta fi kowa ƙuruciya. Yarinya ce mai shekaru 15, tana cikin shirin zana Junior WAEC. Safiya yarinya ce mai wayo da surutu, tana da dariyar da ke sa uwarta ta manta da gajiyar duniya. Ita ce abar birgewa a gidan malam Yusuf. Tana sha’awar ilimi, tana kuma alfahari da Amatullah—wani lokaci har tana kwatanta kanta da ita a gaban madubi. Gidan Malam Yusuf ba kawai alfarma ya ƙunsa ba, sai darajar mutunci. Gidan da ko da turmi da tabarya ke yi da ƙyar, ana ci da albarka, ana kwana da aminci. Wani guri ne da so da addu’a su ke wakiltar arziki. Amatullulah ce farar goro a cikin ruwan dare. Ita ce zuciyar mahaifinta ke alfahari da ita. Ita ce tauraruwa a cikin gidan da ba ya da wutar lantarki amma ke da hasken zuciya. Ita ce jini da numfashin labarinmu. Bayan Amatullah ta fito daga ɗakin su, ta shiga tsakiyar gidan tana gyara ɗan gyambon hijabinta. Mama Rabi ta dubeta da murmushi, ta furta mata addu’ar fatan alheri da karewa daga sharrin hanya da mutane. “Allah ya tabbatar da alkhairi a yau, ya tsareki da alkawarin sa, Amatu,” Mama ta ce cikin muryar da ke cike da ƙauna da kulawa. Amatullah ta lumshe ido, ta amsa da "Amin Mama," sannan ta shige ƙofar gida cikin nutsuwa da sanyin safe mai daɗi, fuskarta a lullube da kwarjini na mace tagari. Ta tsaya bakin titi tana duba gefen hanya don samun abinda zai kaita hospital. Cikin sauri sai wata karamar napep mai kyalli ta tsaya gabanta, ɗan saurayin dake ciki ya leƙo da fara'a da sallama: “Assalamu Alaikum kyakkyawar halitta daga Ubangijin halitta amince ya tabbata a garinki.” Amatullah ta tsaya cak, zuciyarta na karanto sunan da bata ji ba tukuna, amma muryar da kunnenta ya tsinta ya janyo ta juya da hanzari. Ta sakar da dan guntun murmushi Habibu Saurayin da kullum baya gajiya da bin diddigin soyayyarta, kamar yaro da kuka yakan cusa kansa a cikin zuciyarta. Yana da shegen kawaici da zafin so, wanda ke jan hankali ko da a hankali take tafiya. “Lafiya dai Yaya Habibu?” ta ce cikin ladabi da kasaita, tana mai gyara jakar ta a kafada. “Lafiya kalau, nurse Amatu nace na kawo ki aiki yau, ko?” Ya ce yana ƙoƙarin bude kofar gefen napep ɗin cikin ladabi. Ta daga hannu cikin girmamawa amma da takama, “A’a Yaya Habibu, na gode wallahi. Ka daina wahalar da kanka, ni dai na saba zuwa da kaina.” Habibu ya dan sunkuyar da kai, ba tare da nuna damuwa ba, sai murmushi yayi da cewa: “Ai in har wahala ce ke kawo ganin fuskarki safe da safe, wallahi zan ɗauke ta a matsayin ni’ima ne daga sama.” Amatullah tayi dariya kadan, ta kauda kai cikin jin nauyi, sannan ta ce: “Nagode Yaya, Allah ya saka da alkhairi.” Sai ta juya cikin nutsuwa, ta nufi wata babbar motar haya da ta tsaya daga nesa. Habibu kuwa ya bita da kallo har sai da ya fice daga gani, yana kallon fuskarta kamar ana rubuta soyayya da alkalami a zuciyar sa. Tana cikin motar, fuskarta a window, tana kallon yadda iska ke jefa ganyen bishiyu cikin sanyi da natsuwa. A cikin zuciyarta, kalmomi ne ke yawo, kamar ana karanta su daga wani ɗan karamin littafi da ba kowa ke da damar budewa ba. "Ina ma ace Nashwan yana bani lokaci kamar yadda Yaya Habibu ke bani. Ina ma ace duk wata mace zata samu namiji daya damu da ita da zuciyarsa gaba ɗaya… to da kowacce mace daɗin rayuwa ne nata." Ta sauke ajiyar zuciya, sannan wayarta ta fara ringing. Ta zaro ta daga jakarta – Baba ne Sai ta dan lumshe ido kafin ta ɗaga ta kara a kunne. “Baba, barka da safe,” ta ce cikin natsuwa. “Kin fita ne kenan Amatu?” “Eh Baba, ina hanya yanzu.” “To Mama tace kana bachi , Zan dawo da wuri sai muyi magana.” “To ‘yata, Allah ya kiyaye hanya.” Ta katse wayar tana murmushi, zuciyarta na taune ƙaunar da iyayenta ke nuna mata – soyayyar da ke da tsafta da fatan alheri. Bayan ta isa asibiti, ta sauka a hankali, ta gyara veil dinta sannan ta nufi gaban babban ofishin su. Da zarar ta sa kafa a ciki, sautin murya da gaisuwa ya karade ofishin: “Happy birthday Amatu!” Kawayenta da abokan aikin ta suka taso suna rungumeta da murna da dariya. Ta ce da sanyi: “Oh my God! Kun tuna? Thank you so much everyone... Wallahi I didn’t expect it.” Daga nan sai su zauna tare da ƙawarta ta fi kusa da ita – Layla – wacce ko da yaushe tana tsaye mata kamar ‘yar uwa. Layla ta ce: “Wallahi yau sai mun saka miki wani abu, Amatu. Enough of this modest birthday every year!” Suka fara hira, cike da dariya da zolaya, kafin su nufi reception don karɓar jerin sunayen marasa lafiya da za su duba. “To Layla, yau ni da ke jan jini, ko?” Amatu ta ce tana gyara gloves ɗinta. “Eh mana, ko kina ta birthday, ai jinin mutane ba zai tsaya ba,” Layla ta amsa da dariya. Bayan an kammala duba marasa lafiya, Amatu ta miƙe da gajiya amma fuskarta na ɗauke da murmushi mai nutsuwa. Ta cire gloves ɗinta, ta wanke hannunta sannan ta ɗauki jakar ta a hankali, tana nufar ƙofar fita daga asibitin. Yayin da take tafiya, tana jin sauyin iska da hargitsin zuciya—saboda shi. Ta zaro wayarta domin kira. Sunanta biyu: “Nashwan”. Ta matsa kiran farko... ringing... babu ɗauka. Ta kara na biyu... "Missed call". Zuciyarta ta dan yi sanyi, kamar ruwa mai sanyi da aka jika makera. "Wai me yasa yake nesa da ni haka? na cancanci kulawa..." Bata gama tunani ba sai wayarta ta kara, Habibu ne—kamar kullum, girmansa a cikin zuciyarta bai wuce soyayya ba amma bai da gajiya da ƙoƙari. Sai kawai ta danna ɗaya cikin kiran goma da ya shigo a da. Muryarsa mai taushi ta karade kunnenta: “Assalamu Alaikum Amatu, ya aiki?” “Lafiya kalau yaya Habibu, sannu da kokari...” “Na dade ina kiran ki ne, ina so in gaida ki kafin ki koma gida.” “Ah, ai gani nan zan taho, Allah ya saka da alheri.” Ta kashe wayar tana jin tausayi. Habibu mutum ne mai hakuri da nuna kauna, sai dai zuciyarta bata nan gaba ɗaya a wurin sa. Tana son wani, amma wanda bata da tabbacin ya fi son ta. Da ƙarfe shida da rabi na yamma, lokacin rana na neman bacewa da iska mai sanyi tana hura gefen veil ɗinta, ta fito daga asibiti da takunta mai cike da natsuwa da ɗacin zuciya. Sai kawai ta hango Habibu a bakin titi, yana tsaye a gefen napep dinsa kamar yadda ya saba, idonsa cike da kulawa da kaunar da bai iya ɓoyewa. “Bismillah Amatu,” ya ce da ɗan murmushi. Ba tare da musu ba, ta shiga. Babu hayaniya a tsakanin su, sai sanyi da nutsuwa da ke bayyana daga kallon sa. Yana tuka napep ɗin da hankali kamar yana ɗauke da zoben zinariya a ciki. Ya kai ta har kofar gidansu, ya tsaya, ya ce: “Allah ya hutar da gajiyar ki, ki huta lafiya Amatu.” Ta kalli shi tana murmushi, da murmushin da ke tsakanin gaisuwa da alhini, sannan ta ce: “Na gode sosai, Allah ya saka da alheri, yaya Habibu.” Ta juya ta shige gida cikin nutsuwa, amma zuciyarta ba ta da kwanciya. Daya yana nuna ƙauna, ɗaya yana ɓacewa kamar hayaki cikin iska...... Amin uzuri don Allah na rashin posting da rashin time na buɗe group da reply a private message a chigaba da haƙuri in sha Allah komai zai dai dai ta na gode https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC 💘 ZAƁIN ZUCIYA💔 THE HEART'S CHOICE BY NARNAH ƘANWAR SOJA 🎉 Happy Birthday to Me July Girl Special 🎂✨ Na sadaukar da wanan littafin wa karan kaina kasancewar sa a watan haihuwa ta July.. Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words. Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌 Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM PAGE 5 & 6 best on true life story INTRODUCTION 16 /7/2025 "When the heart chooses, even silence speaks. Bayan sallar Ishaa, gidan ya lullube da natsuwa da sanyin dare. Safiya na gefen Mama suna gyara kwanon abincin da suka ci tuwon masara da miya kuɓewa mai ɗan yaji, wanda Amatu ke matuƙar so. Baba na zaune a jikin kujera yana duba littafin karatun sa, zuciyarsa cikin shiru, kamar yana nazarin wani abu. Sai kawai Amatu ta fito da ƙaramar jaka daga cikin daki, ta buɗe ta fito da zunzurutun kuɗi na Naira dubu hamsin, ta miƙa masa da girmamawa da murmushin ƙauna: “Baba, ga wannan. Dan Allah ka karɓa, nasan zaka yi amfani da shi da albarka.” Baba ya karɓa yana kallon kuɗin da ta miƙa, sai ya ɗan jinjina kai da murmushi. “Wannan duk name Amatu? Ina kika samo kuɗin nan haka kamar mai albarkar hatsi?” Amatu ta ɗan yi ƙasa da murya tana murmushi cikin jin kunya: “Nashwan ne Baba. Ya turo min a matsayin kyautar birthday. Kullum haka yake min, ba ya taɓa barin ranar ta wuce haka kawai.” Baba ya kalli Amatu sosai, kamar yana nazarin fuskarta da zuciyarta a lokaci guda, sai ya furta: “Ikon Allah. Shi Nashwan kam baya gajiya. Kuɗin da ya aiko miki da su, wallahi shine albashi na gaba ɗaya a wata. Na yaba da irin karamcin sa. Amma…” ya tsaya yana jinjina kai sannan ya ce da tsantsar tausayi da damuwa: “Sai dai me, ke Amatu... sai yaushe zai turo kansa? Ina jin tsoron kada wannan juyin zuciya ya zame miki juyin rayuwa. Idan har yana sonki da gaske, me zai hana ya taho ya gabatar da kansa? Ya zo ya gaishe mu, mu san iyayensa, su san mu? Ni nake fatan hakan... ba wai zuba ido muna jiran sakon waya da alert ba.” Amatu ta yi shiru, zuciyarta cike da ruɗani. Tana son Nashwan fiye da kowa, amma tambayar Baba tana da nauyi har yanzu, Nashwan bai taɓa fitowa fili da maganar aure ba ya cika da kyaututtuka da kulawa, amma shiru kan abinda take mafarki da fata... Baba ya ƙarasa da faɗar cikin murya mai sanyi: “Na fi son yazo ya ce min da bakinsa, ‘Baba na zo neman Amatullah, ku bani dama’ — haka kawai zuciyata zata huta da murmushi.” Amatu ta ɗan sunkuyar da kai, tana wasa da yatsun hannunta, zuciyarta na faɗin: “Ya Allah ka shiryar da Nashwan ya gane muhimmancin hakan...” Ta koma ɗaki, lokaci ya kusa da ƙarfe goma na dare. Tana cikin shirin kwanciya, rigar bacci jikinta, fuska a gajiye amma zuciya na yawan tunani. Wayarta ta yi tsit, sai kawai ta hango missed call ɗin Nashwan har sau biyu. Ta ɗan jiyo numfashinta cikin damuwa, tana mamakin dalilin kiransa a wannan lokaci. “Ina ma ba za’a gama da kiraye-kirayen dare ba...” Ta furta a hankali, sai kawai wayar ta ƙara ringing. Da kyar ta ɗaga, muryarta cike da gajiya da sha’awar bacci: “Hello…” agefe guda, muryar Nashwan ta karade kunne da sanyi da nutsuwa, kamar mai ɗauke da busar sarewa mai sanyi da tsantsar natsuwa. “My Amatu, kin tashi lafiya? Na gaji da rana, wallahi sai yanzu nake samun kansa.” Amatu ta lumshe ido, murya a sakakke: “Lafiya lau, na ga missed call naka. Nayi zaton ka manta dani ne…” ya ɗan murmura, muryarsa na ɗauke da raɗa: “Kamar ya manta dake? Ai ke ce zuciyata. Kawai ne nayi busy sosai yau, kin san aikin nan... amma a duk inda nake, wallahi ke na ke tunani.” Sukayi hirar da bata fi minti biyar ba, amma kamar zasu baje da soyayya. Sai Amatu ta nutsu ta faɗa masa: “Baba ya karɓi kuɗin da ka turo, kuma ya ji daɗi sosai. Yace duk da farin ciki da jin dadin karamcin ka, yana tambaya sai yaushe zaka gabatar da kanka.” Shiru ya biyo bayan kalmarta na ƴan dakiku. Sai daga baya Nashwan ya sauke ajiyar zuciya sannan ya furta da gaskiya: “Soyayya ta da ke ba wasa ba ce, Amatu. Wallahi da gaske nake. Amma akwai abubuwa da nake gyarawa yanzu, sai dai insha Allahu—nan da shekara mai zuwa, zan turo iyayena. Zan zo da kaina, mu gama magana cikin mutunci.” Zuciyar Amatu ta cika da farin ciki da fargaba a lokaci guda. Shekara guda? Haka za ta jira? Amma a lokaci guda, ta ji kwanciyar hankali da yadda ya furta kalmomin, ba da wasar magana ba, ba da ɗoki na banza ba. Da karamin murmushi ta ce: “Na yarda. Na karɓa. In Allah ya yarda, zan jira har sai lokacin nan.” Nashwan ya ce da ƙayatarwa: “Kuma har lokacin nan, soyayyata ba zata gushe ba. Na fi ƙaunar ki fiye da na kaina, Amatu.” ta saki ajiyar zuciya, murya a raɗa: “Ni ma ina son ka Nashwan... fiye da yanda zan iya faɗi.” Wayar ta kashe ne da salati da addu’a daga gare shi. Ta zuba wayar a gefe, ta lumshe ido da murmushi a fuska. Zuciyarta ta nitsar da wani irin sanyi — sanyi mai ɗauke da fata, ƙauna da alkawarin gobe... Washegari... Tun karfe bakwai da rabi Amatullah ta tashi, jikinta na da sauƙi, zuciyarta cike da kwanciyar hankali da farin ciki na soyayya. Tana gab da isa bakin titi sai Habibu ya zo kamar yadda ya saba da napep nasa. Ta shiga ba tare da wata damuwa ba, amma a zuciyarta tana jin sanyi... Nashwan dai ya saka haske a rayuwarta. Da suka isa asibiti, ta faɗa Layla rai a ɗumɗum. Bayan sun gama shiryawa a office, suna cikin sassanyar rana, suka zauna a gefen taga suna ɗan hutawa kafin fara aikin rana. Layla ta lura da murmushin Amatu, da wata annuri a fuskarta da ba kasafai ake gani ba. “A’ah ke dai yau kamar an baki labari mai daɗi. Me ke faruwa ne da wannan murmushin sirri?” Layla ta tambaya tana ƙara matsowa kusa da ita. Amatu ta lumshe ido tana ɗan kallon taga, sai ta juya da ɗan shafa sumar kanta tace: “Layla... Nashwan zai turo iyayensa — amma ba yanzu ba, sai shekara mai zuwa.” Layla ta zaro ido, ta rike hannunta cike da sha’awa da farin ciki: “Shekara mai zuwa?! Subhanallah, ke wallahi wannan albishir ne! me kika ce masa?” “Na ce zan jira shi duk da lokacin yana da nisa, amma kalmarsa ta daɗe da natsuwar sa sun saka na yarda. Soyayyarsa ta fi ni’imtar zuciyata.” Layla ta fashe da dariya tana girgiza kai: “Ke dai kina cikin naki duniya Amatu, Allah ya tabbatar da alkhairi. Wallahi Nashwan yana da kirki. Amma dan Allah... wato bazai yi tun da wuri ba kenan?” Amatu ta nisa “Yace yana gyara wasu abubuwa ne. Na fahimta kuma na yarda. Na fi son abu ya zo da tsari da cikar mutunci fiye da sauri ba tare da shiri ba.” Layla ta jinjina kai, tana murmushi: “Toh ai Allah ya sanya alkhairi. Amma sai ki shirya kyau-kyau da addu’a. Zaman jira yana buƙatar haƙuri da jajircewa.” “Na shirya,” Amatu ta amsa a hankali, “In har zan samu Nashwan a ƙarshen jirana — to na yarda da komai.” Suka ci gaba da hira cikin nutsuwa da kwanciyar rai. Soyayya ta gaske ke kera zuciyar Amatu, tana girgiza tunaninta da fatan gobe. Kuma da ƙawarta Layla a gefenta, sai ta ji kamar rayuwar ta na gyarowa cikin salo mai tsafta da albarka... SHIN WANAN JIRAR NA AMATULLAH ZAI HAIFAR DA ƊA MAI IDO SHIN NASHWAN ZAI CIKA ALƘAWARIN SA. LALLAI NASHWAN SHINE ZAƁIN ZUCIYA AMATULLAH MUCEE GABA DA KASANTUWA ANA MIN UZURI DA RASHIN ISASSHEN POSTING A KOYAUSHE FATAN ALHERI 🥳🎊 https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC 💘 ZAƁIN ZUCIYA💔 THE HEART'S CHOICE BY NARNAH ƘANWAR SOJA 🎉 Happy Birthday to Me July Girl Special 🎂✨ Na sadaukar da wanan littafin wa karan kaina kasancewar sa a watan haihuwa ta July.. Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words. Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌 Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM PAGE 7 & 8 best on true life story INTRODUCTION 19 /7/2025 "When the heart chooses, even silence speaks WAYE NASHWAN? Nashwan Ahmad saurayi ne mai kamala da nagarta. Kyakkyawan hali da sauƙin kai sun zame masa tufafi, zuciyarsa cike take da girmamawa da kula da wanda yake so. Tunanin sa mai zurfi ne, ba mai yawan magana bane amma idan ya furta kalma, zata dumi zuciyar mai sauraro. Asalin sa daga jihar Kaduna, amma rayuwar sa ta kai shi ko’ina. A lokacin da Amatu ke secondary school, shine ya zo National Youth Service (NYSC) a makarantar su. Zuciyoyinsu sun haɗu a wancan lokacin — soyayya mai tsafta, mai nasaba da kulawa da mutunci ta kulla tsakaninsu. Daga wancan rana har yau — shekaru uku kenan — soyayyar nan na raye cikin nutsuwa da girmamawa. Ba su cika haɗuwa da juna ba, amma kowacce tattaunawa tana da ma'ana. Yanzu Nashwan na da shekaru 30, yana aiki da wata Company mai zaman kanta dake Kaduna, kuma albashinsa na wata-wata na kai kimanin Naira dubu dari biyu (₦200,000). Duk da karancin ganawa da Amatu, Nashwan baya daina tura mata kyaututtuka, sakonnin ƙarfafa gwiwa da addu'o'in da ke tafiyar da rayuwar mace mai tsari. Sau huɗu kacal ya zo gun Amatu cikin shekaru uku, amma kowanne zuwan yana cike da ma’ana, girmamawa da soyayya. Yana kula da ita fiye da yadda yawancin maza ke kula da matan da suke tare da su kullum a zuciyar Amatu, Nashwan shine hasken da ke tafiyar da daren rayuwarta, kuma soyayyarsa shine mafita da kwanciyar ranta. BACK TO STORY BAYAN WANI LOKACI Karfe tara da mintuna goma sha biyu na dare. Amatu na kwance a kan gadonta, zuciyarta cike da fargaba da tambayoyi. Tana kallon last seen na Nashwan a WhatsApp – online yanzu yanzu ya sauka. "Shiru? tun safe ba text, ba kira, sai na ganka online kana faman hira da wasu amma ni kamar ba na cikin rayuwarka..." Tayi ajiyar zuciya, tana tura sako: "Nashwan, gaskiya bana jin daɗi. Duk da ina ƙoƙari na fahimce ka, har yanzu bana ganin ka fahimce ni. Soyayya ba kyauta ba ce kawai, tana bukatar kulawa da kalma mai daɗi a rana, kirar da zata sa ranka ya lafa. Me yasa kana yin kamar babu ni?" Bayan mintuna shida, sai gashi ya kira. Da ƙyar ta ɗauka. Murya ta cike da shakku da gajiya. "My Amatu... na san ba kya farin ciki, amma wallahi aikin ne... bana da lokaci fa, kinsan aikinmu..." "Ayyukan duniya ba su fi zuciyar da ke son ka ba!" Ta katse shi cikin murya mai sanyi da raɗa. "Duk da nisan da ke tsakanin mu, ina tsammanin zan fi ka ƙauna — ba don kyauta ba, ba don suna ba — sai don ina ganin ka a zuciyata fiye da yadda kake kallona." Shiru yayi, kamar yana narkar da kalmomin. Sannan yace: "Kin fi karfin komai a rayuwata Amatu. Amma ba koyaushe nake da lokacin da zan yi magana ba." ta numfasa, hawaye na gangarowa: "Ba na son auren da zai zama kamar daɗaɗɗen suna ne kawai. Ina son rayuwa da wanda zai damu da rashin saƙona, ba kawai ganin saƙona ba. Nashwan, ka dawo da kulawarka kafin zuciyata ta gaji da jiranka." Kamar wani yayi masa tsawa, Nashwan ya daɗe cikin shiru. Sannan ya furta: "Zan gyara. Kuma zan tabbatar da cewa kina da gaskiya. Tabbas, kina da gaskiya fiye da shiru na." Beep... ya katse kiran. Amma a zuciyarta, tana jin zafi mai sanyi — na soyayya da yawan jira. "Ina son Nashwan. Ina son sa fiye da yadda nake son ganin kaina cikin madubi. Amma duk zuciyar da ake soyayya da ita tana bukatar kulawa. Ina jira in ga ko zai cika alkawuran da yazo da su bayan wannan ƙorafi. Zuciyata na ƙauna, amma tana gajiya..." Sati biyu kenan. Ƙwarya-ƙwarya. Tun ranar da Amatu ta furta “Zuciyata na gajiya da jira”, Nashwan bai sake kiran ta ba, balle ya aiko da wani saƙo. Ba text, ba missed call — kamar soyayyar da suka ginaye akan lokaci da kulawa ta dusashe cikin iska mai sanyi da gajiya. Amatu na zaune a ɗaki, zuciyarta a haɗe da wayarta. Sau dubu a rana tana duba ko Nashwan ya aiko da text ta kira sa ba adadi ta mai text shiru ta mai magana a online ya buɗe shiru ba amsar shiru shiru mai nauyi kamar dutse. WhatsApp: Last seen: Online 10 minutes ago. “Yana lafiya? Ko yana tare da wani ne yanzu? Ko kuwa hakan kawai dabi’arsa ce – idan mun yi faɗa sai ya shude kamar ba mu taɓa soyayya ba?” Zuciyarta na bugawa da ƙara. Kowanne tick na saƙon da ta sake karanta a baya kamar ƙarar dukan zuciya ne ke sake tuna mata da yadda ake ji idan ka fi ƙaunar wanda bai damu ba. Tana kwance da fuska a mayafi, kwalla na ta faman gangarowa. Sai ta furta a hankali cikin numfashi mai nauyi: “Ina missing dinka, Nashwan... ko da baka missing dina ba.” Tayi ƙoƙarin cire shi daga tunaninta, ta mayar da hankali kan aikin ta, sai dai duk inda taje, kamar murya da kamshin Nashwan na biye da ita ne. Tana ganin sa a online, tana hango username ɗinsa, tana jin zuciyarta na amsa sautin sunansa — amma daga shi, shiru… shiru mai cike da tambayoyi. "Shin da gaske so ya tsaya ne? Ko yana kokarin hukunta ni ne da shiru? Ko kuwa... ya gaji da ni? Amma me nayi da har sai haka?” SOYAYYA GAMUN JINI NANARH KANWAR SOJA ✍️✍️✍️✍️ https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC 💘 ZAƁIN ZUCIYA💔 THE HEART'S CHOICE BY NARNAH ƘANWAR SOJA 🎉 Happy Birthday to Me July Girl Special 🎂✨ Na sadaukar da wanan littafin wa karan kaina kasancewar sa a watan haihuwa ta July.. Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words. Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌 Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM PAGE 9 / 10 best on true life story 21 /7/2025 "When the heart chooses, even silence speaks Kwatsam, zuciya ta gama jurewa. Amatu ta kama wayarta da hannu mai rawar zuciya ta danna sunansa. Bayan ƙarar kira sau biyu, ya ɗaga. “Hello…” Muryarsa kamar ba daɗin ji. Ita kuwa ba ta tsaya gaisuwa ba, sai dai ƙorafi mai sa kwalla: “Nashwan, me na maka ne har three weeks baka kira ni ba? Me nayi da zaka rika yin online amma ba zaka tambaye ni lafiyata ba? Ko zuciyata bata da daraja ne a gurinka?” sai shiru ya biyo baya. daga can Nashwan yace a sanyaye: “Amatu... aikin nan da nake ciki ba sauki bane. Wallahi kullum ina yinta har dare. Amma gashi yanzu na tura miki dubu goma, don ki Hai napep zuwa asibiti Sai transfer alert ya shigo. Gaskiya, ya turo. Amatu ta lumshe ido, zuciyarta ba ta cikin kudin. Sai tace da wani yanayi mai cike da taushi da zafi: “Ni ba kudi nake so ba Nashwan, ina so ka bani lokaci. Ko da minti goma ne kullum, ka tuna da ni. So na ba sabulun wanka bane da zaka manta idan ka fita.” “Ni ina son ka Nashwan, fiye da karfina ma. Amma kamar ina soyayya da bango. Zuciyata na ƙonewa.” shi kuwa ya sake shiru. Sai yace: “To... zan duba, zan gyara. Ki bani lokaci.” Washegari Da safe kamar kullum tana jiran kira ko sako, sai gashi ya kira. Da farko ta ɗauka farin ciki zai biyo, amma... “Amatu, na baki minti biyar. Duk abinda kike da shi a ranki, ki fadi yanzu. Ina aiki ne.” Zuciyarta tayi wani irin nauyi. Kamar ta furta: “Ina son ka Nashwan… amma bazan iya soyayya da mutum da agogo ba.” sai ta fara magana cikin kuka mai saukar hankali... “Zuciyata Ba Takarda Bace” Yana cewa “Amatu, na baki minti biyar. Duk abinda kike da shi a ranki, ki faɗi yanzu. Ina aiki ne.” Amatu ta dafe kirjinta kamar zuciyarta na neman tsagewa. Amma ta ja numfashi, ta fara da nutsuwa: “Nashwan, ka tuna lokacin da muke tare a makaranta? Kana bani lokaci fiye da abincin ka. Ka tuna da kalaman da kake faɗa min? Ina ƙaunar ka Nashwan, har yanzu. Amma yanzu kamar ni ce kadai nake tafiyar da soyayyar nan…” “Kullum sai dai ni na kira, ni na yi rubutu. Ka shiga online, amma ko ‘Hi’ ba zaka turo ba. Wannan ba soyayya ba ce, Nashwan. Ni ma ina da zuciya. Bana son mu rabu… amma ina jin kamar ni kadai ce a cikin wannan dangantaka.” Shiru. Can kuwa… ihun Nashwan ya buga a kunne kamar karar roka. “To me kike so ne yanzu? Kina takura min ne fa, Amatu! Ko ina aiki ba zaki fahimta ba? Sai kace ni bawa ne naki?! Wai wannan ce soyayya? Ko fursuna kike son ni na zama??” Wayar ta dauki tsawa kamar hayaki yana fita daga kunne. Amatu ta kasa magana. Kamar rana ta ɓace daga duniyarta. Daga nan sai “call ended”. Ya katse wayar. ta sunkuyar da kanta, hawaye suka gangaro kamar ruwan damina. “So na ba ya isar da ni gareka… amma kuma ka manta ni mutum ce.” - “Ni Ma Mutum Ce” "Meye laifina?" "Laifina kawai shine ina son shi?" "Ni ma mutum ce, ba dutse ba. Macce ce mai rauni, da zuciya mai sauƙin kamuwa da so." "Sai don na nuna mai so na, shi ne zai ce min minti biyar nake da su? Minti biyar! Kamar ina roƙon lokaci daga wani wanda ya mallaki numfashina yana jan min tsaki a waya ." "Shin haka soyayya take? ko kuwa ni ce ban dace ba?" "Yanzu sai na fuskanci cewa soyayya tana da laifi idan mace ce ta fara nuna gaskiya." "Yana online, yana dariya da duniya. ni kuma ina nan ina fama da ƙuncin da soyayyarsa ta jefa ni." "Ko da ace na yi kuskure, ba zan cancanci wannan wulakanci ba." "Wani lokaci nakan tambayi kaina, idan son shi laifi ne, to me yasa zuciyata ke dukan shi ba kowa ba?" Tunda suka yi fadan nan, Amatu ta soma jin wani irin ƙorafi daga zuciyarta—na so da na zafi. Duk lokacin da ta ga Nashwan online, zuciyarta na harbawa, idonta na kallo cikin fatan cewa wataƙila zai turo saƙo ko ya kira, ya ce “Ina sonki, na tuba.” Amma babu. Shiru. Sai ta yanke shawarar cewa zata ja baya. Soyayya ba wai azaba bace da za a cigaba da jurewa ba tare da kulawa ba. Ita ma tana da daraja. A ranar Laraba, ta ga missed call nasa guda daya. Da niyyar komawa kira, sai ta tsaya. “Idan har ni kadai ke ƙoƙarin ceto wannan dangantaka... to ai ni ba itacen gicciyewa bace.” Ta share kiran. Ta tafi asibiti kamar kullum. Tayi murmushi da ma’aikata, ta yi aiki da gamsuwa. Amma duk da haka, a zuciyarta akwai rana mai yawan guguwa da ƙura—ƙuruciyar soyayya ke hura mata ƙonawa. Layla ta lura. Ta juyo ta ce mata da salo mai tausayawa: “Amatu, kin fara zama kamar wacce ke cikin soyayya da namijin da ya manta da ita.” Amatu ta yi murmushi, ya cika da hawaye. “Ni dai Layla, soyayya ta kai ni ƙololuwa... amma rashin mutunci bazan jure ba. A zuciyata har yanzu ina sonsa—amma bazan bar kaina na ci gaba da wulakanci ba. Ni mace ce, mai daraja.” Layla ta matso ta rungume ta. “Kina da kyau, hankalinki kwarai da gaske. Idan soyayya zata ci ki—ki ci gaba da ja baya. Idan zai gane kuskurensa, zai dawo. Idan kuma ba haka ba... Allah zai baki wanda yafi shi daraja da kulawa.” SHIN KUNA TUNANIN AMATULLULAH TAJA BAYA DAGA MASOYIN TA WAI SOYAYYAR NISA HAKA YAKI DA AZABA SHIN KUN TAƁA HAƊUWA DA MASOYI YANA WANI GARI KINA WANI GARI DISTANCE RELATIONSHIP YA ZAMA MATSALARKU SHIN NASHWAN ME KE FARUWA DA ZUCIYAR SA AKAN AMATULLAH DUK DA CEWA YASO TA SOYAYYA MAI TSANANI MUJEEE ZUWA BARE MUGA DA GASKE KO AMATU TAYI HANKALI ZATA JAH CLASS NATA INA TSORON KAR CLASS NIN DAI YA ZUBE NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️✍️✍️ Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words. Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌 Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story Kwatsam, zuciya ta gama jurewa. Amatu ta kama wayarta da hannu mai rawar zuciya ta danna sunansa. Bayan ƙarar kira sau biyu, ya ɗaga. “Hello…” Muryarsa kamar ba daɗin ji. Ita kuwa ba ta tsaya gaisuwa ba, sai dai ƙorafi mai sa kwalla: “Nashwan, me na maka ne har three weeks baka kira ni ba? Me nayi da zaka rika yin online amma ba zaka tambaye ni lafiyata ba? Ko zuciyata bata da daraja ne a gurinka?” sai shiru ya biyo baya. daga can Nashwan yace a sanyaye: “Amatu... aikin nan da nake ciki ba sauki bane. Wallahi kullum ina yinta har dare. Amma gashi yanzu na tura miki dubu goma, don ki Hai napep zuwa asibiti Sai transfer alert ya shigo. Gaskiya, ya turo. Amatu ta lumshe ido, zuciyarta ba ta cikin kudin. Sai tace da wani yanayi mai cike da taushi da zafi: “Ni ba kudi nake so ba Nashwan, ina so ka bani lokaci. Ko da minti goma ne kullum, ka tuna da ni. So na ba sabulun wanka bane da zaka manta idan ka fita.” “Ni ina son ka Nashwan, fiye da karfina ma. Amma kamar ina soyayya da bango. Zuciyata na ƙonewa.” shi kuwa ya sake shiru. Sai yace: “To... zan duba, zan gyara. Ki bani lokaci.” Washegari Da safe kamar kullum tana jiran kira ko sako, sai gashi ya kira. Da farko ta ɗauka farin ciki zai biyo, amma... “Amatu, na baki minti biyar. Duk abinda kike da shi a ranki, ki fadi yanzu. Ina aiki ne.” Zuciyarta tayi wani irin nauyi. Kamar ta furta: “Ina son ka Nashwan… amma bazan iya soyayya da mutum da agogo ba.” sai ta fara magana cikin kuka mai saukar hankali... “Zuciyata Ba Takarda Bace” Yana cewa “Amatu, na baki minti biyar. Duk abinda kike da shi a ranki, ki faɗi yanzu. Ina aiki ne.” Amatu ta dafe kirjinta kamar zuciyarta na neman tsagewa. Amma ta ja numfashi, ta fara da nutsuwa: “Nashwan, ka tuna lokacin da muke tare a makaranta? Kana bani lokaci fiye da abincin ka. Ka tuna da kalaman da kake faɗa min? Ina ƙaunar ka Nashwan, har yanzu. Amma yanzu kamar ni ce kadai nake tafiyar da soyayyar nan…” “Kullum sai dai ni na kira, ni na yi rubutu. Ka shiga online, amma ko ‘Hi’ ba zaka turo ba. Wannan ba soyayya ba ce, Nashwan. Ni ma ina da zuciya. Bana son mu rabu… amma ina jin kamar ni kadai ce a cikin wannan dangantaka.” Shiru. Can kuwa… ihun Nashwan ya buga a kunne kamar karar roka. “To me kike so ne yanzu? Kina takura min ne fa, Amatu! Ko ina aiki ba zaki fahimta ba? Sai kace ni bawa ne naki?! Wai wannan ce soyayya? Ko fursuna kike son ni na zama??” Wayar ta dauki tsawa kamar hayaki yana fita daga kunne. Amatu ta kasa magana. Kamar rana ta ɓace daga duniyarta. Daga nan sai “call ended”. Ya katse wayar. ta sunkuyar da kanta, hawaye suka gangaro kamar ruwan damina. “So na ba ya isar da ni gareka… amma kuma ka manta ni mutum ce.” - “Ni Ma Mutum Ce” "Meye laifina?" "Laifina kawai shine ina son shi?" "Ni ma mutum ce, ba dutse ba. Macce ce mai rauni, da zuciya mai sauƙin kamuwa da so." "Sai don na nuna mai so na, shi ne zai ce min minti biyar nake da su? Minti biyar! Kamar ina roƙon lokaci daga wani wanda ya mallaki numfashina yana jan min tsaki a waya ." "Shin haka soyayya take? ko kuwa ni ce ban dace ba?" "Yanzu sai na fuskanci cewa soyayya tana da laifi idan mace ce ta fara nuna gaskiya." "Yana online, yana dariya da duniya. ni kuma ina nan ina fama da ƙuncin da soyayyarsa ta jefa ni." "Ko da ace na yi kuskure, ba zan cancanci wannan wulakanci ba." "Wani lokaci nakan tambayi kaina, idan son shi laifi ne, to me yasa zuciyata ke dukan shi ba kowa ba?" Tunda suka yi fadan nan, Amatu ta soma jin wani irin ƙorafi daga zuciyarta—na so da na zafi. Duk lokacin da ta ga Nashwan online, zuciyarta na harbawa, idonta na kallo cikin fatan cewa wataƙila zai turo saƙo ko ya kira, ya ce “Ina sonki, na tuba.” Amma babu. Shiru. Sai ta yanke shawarar cewa zata ja baya. Soyayya ba wai azaba bace da za a cigaba da jurewa ba tare da kulawa ba. Ita ma tana da daraja. A ranar Laraba, ta ga missed call nasa guda daya. Da niyyar komawa kira, sai ta tsaya. “Idan har ni kadai ke ƙoƙarin ceto wannan dangantaka... to ai ni ba itacen gicciyewa bace.” Ta share kiran. Ta tafi asibiti kamar kullum. Tayi murmushi da ma’aikata, ta yi aiki da gamsuwa. Amma duk da haka, a zuciyarta akwai rana mai yawan guguwa da ƙura—ƙuruciyar soyayya ke hura mata ƙonawa. Layla ta lura. Ta juyo ta ce mata da salo mai tausayawa: “Amatu, kin fara zama kamar wacce ke cikin soyayya da namijin da ya manta da ita.” Amatu ta yi murmushi, ya cika da hawaye. “Ni dai Layla, soyayya ta kai ni ƙololuwa... amma rashin mutunci bazan jure ba. A zuciyata har yanzu ina sonsa—amma bazan bar kaina na ci gaba da wulakanci ba. Ni mace ce, mai daraja.” Layla ta matso ta rungume ta. “Kina da kyau, hankalinki kwarai da gaske. Idan soyayya zata ci ki—ki ci gaba da ja baya. Idan zai gane kuskurensa, zai dawo. Idan kuma ba haka ba... Allah zai baki wanda yafi shi daraja da kulawa.” SHIN KUNA TUNANIN AMATULLULAH TAJA BAYA DAGA MASOYIN TA WAI SOYAYYAR NISA HAKA YAKI DA AZABA SHIN KUN TAƁA HAƊUWA DA MASOYI YANA WANI GARI KINA WANI GARI DISTANCE RELATIONSHIP YA ZAMA MATSALARKU SHIN NASHWAN ME KE FARUWA DA ZUCIYAR SA AKAN AMATULLAH DUK DA CEWA YASO TA SOYAYYA MAI TSANANI MUJEEE ZUWA BARE MUGA DA GASKE KO AMATU TAYI HANKALI ZATA JAH CLASS NATA INA TSORON KAR CLASS NIN DAI YA ZUBE NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️✍️✍️https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC 💘 ZAƁIN ZUCIYA💔 THE HEART'S CHOICE BY NARNAH ƘANWAR SOJA 🎉 Happy Birthday to Me July Girl Special 🎂✨ Na sadaukar da wanan littafin wa karan kaina kasancewar sa a watan haihuwa ta July.. DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM PAGE 11 / 12 24 /7/2025 "When the heart chooses, even silence speaks Kamar da, rayuwa tana tafiya. Amatu ta koma aikinta da natsuwa, ta kara jin dadin zama da kanta. Duk da cewa ta ja baya da Nashwan, amma zuciyarta—ita bata fasa ji ba. Sai dai kwatsam rana guda... Ta buɗe WhatsApp, tana duba Status don kawar da gajiya. Sai wani hoto ya buɗo mata ido: Nashwan da wata yarinya sun zauna a kusa da juna fuskar budurwar an rufe ta da emoji, amma jikin rubutun status ɗin: “HAPPINESS IS LOADING...” Gaba ɗaya jikin Amatu ya kakkarye. Kamar fitar zuciyarta ke neman gaske numfashinta ya fara rikicewa. wayar ta zame daga hannunta ta faɗi kasa da ƙarar da ta tada hankalin Mama a ɗakin ciki. “Amatu! Lafiya ke? Subhanallah!” Da sauri Mama ta karaso, ta tarar da ita kwance, shiru, ba motsi kamar wacce aka cire rai. Mama ta zuba mata ruwa, tana kiran sunanta: “Amatu! Diyar Mama! Ki tashi! ki daina tsorata ni!” Amma ba amsa. Sai zuciyar Mama ta fara bugawa da ƙarfi. Da sauri ta ɗauki wayarta ta kira Baba: “Mallam ! Ka kira Mahir da Safiya su dawo yanzu! Amatu ta suma, na rasa me ke faruwa! muna buƙatar zuwa asibiti yanzu!” A lokacin weekend ne, Mahir yana gida bai jima ba, sai aka ɗauke Amatu cikin mota, kai tsaye zuwa babban asibiti—Specialist Hospital Maiduguri Zuciya da take jin so, tana jin daci. Ta ja baya, amma zuciya ba kwalta bace da za a murɗa ba. So ya sauya mata duniya, Nashwan ya bar mata ciwo maimakon kulawa. Asibitin ya yi shiru da yamma. Amatu na kwance a gado, idanunta na kallon sama—ba komai a cikin su face yawu na hawaye. Drip yana sauka da sannu... kwayar ruwa, kamar kwayar damuwa, tana ratsa jijiyoyin jikinta. Mama na gefenta, tana karanta addu’a a hankali, tana share kwalla da saƙon zuciya mai nauyi. “Ciwon zuciya da kake gani ba sai ta fashe ba...” Amatu na cikin tunani, idanu sun cika da hawaye. Da suka sallame ta, suka koma gida da dare, tana cikin shiru kamar macce bata da baki. Bayan wanka da sallah, ta zauna a kan katifarta ta buɗe wayarta. Ta shafe fuskar wayar da yatsa kamar tana son share wani ɓacin ciki. Ta goge number Nashwan ta share history. ta share dukkan chats nasu. Ta cire hoton sa da suka ɗauka tare. Ta cire sunan sa daga zuciyarta… ko da hakan ya fi wuya. Kukan da ta yi ba na banza bane, sai dai kukan soyayya da aka raina. Ta dora hannu a kirji tana faɗin: “Ni Amatu… na tafi da zuciyata. Na riga na yafe, amma bazan manta ba. Nashwan, kai ne zabin zuciyata, amma ka ruguza ta. So na gare ka ya zarce yanda zan iya fassara shi da baki. Har shekaru uku, ban taba kiran wani sunan da ka fi ba. Ka kasance abokina, masoyina, mafarkina… kuma yanzu, ka zame mini ciwo.” Ta sauke numfashi, ta lumshe ido, tana cigaba da magana da karamin murya mai rauni: “Duk abinda ka zagaye, Nashwan… wallahi ba zaka samu zuciyar da ta rike ka kamar tawa ba. Ba zaka sake samun wanda zai dinga jira ka cikin shiru da hakuri ba. Ni ce ragin da baka darajanta ba—Allah zai sakamin.” “Ka raina amana. Wannan zalunci ne a soyayya amma ni zan tashi. Zuciyata ta mutu, amma zan haife sabuwa—ba don kai ba, don kaina ne.” “Yau da Gobe” Watanni shida... Watanni shida tun ranar da ta share komai, ta watsar da zuciyar da ta gama fasa, ta dawo da kanta daga rikicin da so ya jefa ta. Watanni shida da hawaye suka daina fita a ido, suka koma ɓoye a zuciya. Sai dai so—so kam, yana nan. Kamar rubutun da ba zai goge ba, yana kwance a ɓangaren zuciyarta da ba kowa ke gani ba. Amatu ta gama sadaukar da soyayyarta. Sai dai abin mamaki, ko da sakon “Ina kwana” Nashwan bai sake turo ba. Sai labari ya iso—labari mai nauyi. Nashwan ya yi aure. Ya auri wata. Wata daban. Wacce ba ita bace ta jira shi na shekaru uku. Ta kalli labarin a shafin Instagram, fuskar su cike da farin ciki. Amatu ta lumshe idanu. ba kuka tayi ba... kawai ta yi shiru. Shiru mai nauyin lallaba zuciya. Wanan rana kamar yadda aka saba, Baba ya ajiye ta daga aiki. Sunyi shiru suna kallon hanya har suka iso kofar gida. Yana shirin tafiya kenan sai ya tsaya, ya kalleta da kulawa, yana da murmushi mai cike da tausayi amma da ƙuduri. “Amatu, kin girma kin jure fiye da kima. Amma yanzu lokaci ne na sabuwar hanya. Duk mazan a duniya ba Nashwan ba ne. Kuma duniya ba zata tsaya ba. Ke mace ce mai daraja—kin cancanci samun miji nagari. Don haka... ki fito da wanda zuciyarki ke yarda da shi, kafin nan da wata uku. Ba dole sai yau ba, amma ki yarda da kanki, ki buɗe zuciyar ki ga dama. So bai ƙare ba—ya canza ne.” Jan kunne ne, amma da tausayi. Ta sauke kai, amma zuciyarta na tashi. Wata murya a cikin ta na cewa: “Ina zan fara? shin akwai wani da zai ɗauki wannan zuciya da aka fasa, ya ƙawata ta?” Sai dai lokaci—lokaci na iya warkar da kowace zuciya, har ta sake yin fari kamar sabuwa. Wata rana... wata rana mai kyau, za ta kalli kanta a madubi ta ce: “Na tsira. Kuma na dace.” NARNAH ƘANWAR SOJA https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC 💘 ZAƁIN ZUCIYA💔 THE HEART'S CHOICE BY NARNAH ƘANWAR SOJA 🎉 Happy Birthday to Me July Girl Special 🎂✨ Na sadaukar da wanan littafin wa karan kaina kasancewar sa a watan haihuwa ta July.. DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM PAGE 13 / 14 25 /7/2025 "When the heart chooses, even silence speaks Ta shiga ɗaki , zuciyarta na tsalle da rauni, zuciyarta na rawa da zafi ta zube kan gado kamar wacce aka cire wa rai kuka ya biyo baya kuka ba wai na ɓarna ba—na yanke ƙauna daga wanda ta so fiye da komai tana hawaye tana ce wa kanta: “me nayi masa? so na ne laifi? menene nayi da bai ishe shi ba?” babu amsa kamar yadda kwanaki suka wuce babu dalilin cin amanar ta kamar yadda soyayya ta juya ba tare da gargaɗi ba. Amma yau... Amatu ta farka. Ta fara jin wani sabon numfashi mai sanyi yana fito daga ɓangaren zuciyarta da ya daɗe da toshewa ta share hawayen ta, ta yi shiru. sannan ta miƙe cikin kasala, ta ɗauro alwala, ta shimfiɗa dadduma, ta zauna gwiwa biyu ƙasa... da murya mai sanyi da firgici tace: “Ya Allah, kai Ka fi sanin duk wani abu da zuciyata ke ɓoyewa. ka bani ƙarfin zuciya, Ka goge hawayena. Idan har akwai wanda yafi Nashwan alheri a rayuwata, ka kusanto min shi. Ka rabani da wanda bai cancanta da ni ba, ko ina ƙoƙarin ganin yana min ka bani soyayya da zata warkar da ni, ba wadda zata rusa ni ba...” Sai ta lumshe ido... Addu’a ta fara karɓar mata wuri, ta fara busar da ciwon da soyayya ta bar mata. Zuciyarta ta ce “Ba zan rufe kaina daga soyayya ba zan jira wacce zata fito da ni daga wannan duhu. Amma ba zan sake jefa kaina ba, sai idan zuciyata ta amince, kuma addu’ata ta ce: ‘Amin.’” *********NASHWAN********** Gidan da aka ƙawata da kayan alatu, gado mai faɗi da labule masu sheƙi, amma Nashwan bai jin kwanciyar hankali. A kwanaki talatin da auren sa da Azeeza, komai yana kamar mafarki mara tushe. Tana da kyau — kwalliyarta na kama zuciyar ido, murya mai sanyi, motsinta na janyo hankali. Amma komai na waje ne, ba ta da ƙamshin hankali irin na Amatu. zuciyarsa na cike da rudani duk lokacin da ya zauna, da zarar yayi shiru, sautin muryar Amatu ke dawo masa... “Kai ne zabin zuciyata… amma ka ruguza ta.” Ya shake kansa da tafin hannu kamar mai son korar sautin daga kai. Amma ba zai iya ba. Azeeza, sabuwar amaryar sa, bata da sanin asalin namijin da ta aura. Ita dai ta fahimta wannan mutumin mai kuɗi ne, mai natsuwa, wanda ya zo da soyayya da buri. Ita kuma ta tafi da hoto—bata faɗa masa gaskiyar rayuwarta ba. Har sai wata rana bayan wata guda, Nashwan ya dawo gida da wuri. Yana daga cikin dakin su, yana gyara laptop ɗinsa. Sai wayar Azeeza ta faɗi kasa ta buɗe ganin ba pincode ta shiga gallery kai tsaye hotuna suka bayyana. Hotuna ne na Azeeza da wasu maza daban-daban — cikin wuri mai duhu, da tufafi na fallasa. Wasu hotunan suna dauke da bayani kamar: "VIP Client 🖤 — Night to remember." "Dubai night, ₦500k richer." Nashwan ya zuba idanu hannunsa ya daina motsi zuciyarsa ta buga — kamar wacce ta ji bugun karshe ya kira sunanta da sauti mara daɗi: “Azeeza…” tana fitowa da sauri, fuska cike da murmushi amma murmushin ya tsaya da taga fuskar Nashwan da gallery a budewa ya miƙa mata wayar “kamar ba ke ba ce a nan, ko? ko dai akwai wata 'yar uwarki da ta dace da ke sosai?” Azeeza ta tsaya — shiru kamar dutse ba ta da amsa. “Na tambaye ki saboda so na ke ki gaya min da baki ke gaya min, ke wacece?ni fa so nayi aure, ba na saya ba...” hawayen Azeeza ya fara sauka, amma Nashwan bai daga girma ba. “Kin yaudare ni Azeeza na nemi sabuwar rayuwa, amma na fada cikin hadari. Ke ‘yar bariki ce da kika san ni zan iya sauya rayuwarki — kin rufe gaskiya da kwalliya. amma komai ya kare yanzu.” Zuciyarsa ta kulle ba sabo bane, ba laifi ne — kaddara ce ta bijiro da girmanta. yana cikin shiru, hawaye bai sauko daga idonsa ba — sai tunani: "Amatu... da gaske na bar mace kamar ke, na zo na tara karyar duniya duk abinda macce ta mallaka kin mallake sa menene a cikin wayewa na ƴan matan yanzu da ya rufe min ido da barikanci na bar asalin tarbiyyar aure ?" ya kama kansa da hannu biyu, ya dora a gwiwarsa, yana faɗin: “Me nayi wa kaina? Amatu... yanzu na fahimta.” "WAIWAYE" Zuciya tana da nisa fiye da tunani. Idan ta ji ciwo, tana komawa baya — tana tono tarihin da aka binne da so da sakaci. Nashwan na zaune a ɗakin falonsa, AC na busa sanyi, amma hawaye na zafi ke sauka daga idonsa. Ya makale cikin tunani — waiwaye sun fara mamaye zuciyarsa. “Ta yaya hakan ya faru? ina na fara kuskure?” ya lumshe ido... komai ya dawo daga farko. Ranar Farko... Wani taron kamfani ne na shekara-shekara, Corporate Gala a babban dakin taro na Oriental Hotel, Lagos. Nashwan ya halarta da wasu daga ofishinsu. Duk da ya zo da niyyar tafiya da wuri, wani ƙamshi ne ya ja hankalinsa. Turaren Azeeza. Mai ƙamshi kamar hadin jasmine da vanilla, mai sa zuciya rawar jiki ya waiwayo... sai idonsa ya sauka a kanta wata budurwa ce cikin rigar t shirt fara da wando baƙi sumarta a daure, kwalliyar ta ɗauke ido — ta haɗu! Suna haɗa ido, ta saki murmushi. Murmushin da ya dora masa alaka kai tsaye da zuciyarsa. A lokacin, ya manta da Amatu, ya manta da soyayyar da ya jima yana tinkaho da ita. Yayi kamar yana sane — amma zuciyarsa tayi yawo. Kissa da kissisina suka shiga daga wannan rana duk wani barikanci Azezza tayi mai anan taki ya fara tunanin yana duhu yanzu ya haɗu da macce da ta iya soyayya da faranta rai na masoyi Ta fara “checking on you, handsome,” ta fara aiki da kalmomi masu lulluɓin so, ta zame mai saniya da murya mai lallashi. kwana biyu... ya fara aika mata “sweet dreams.” kwana bakwai... ya fara kiranta da “my princess . my world. my future wife ” har ya aike da zabin zuciyarsa gareta—ido rufe. Yanzu... Yanzu yana zaune shi kaɗai, Azeeza tana ɗakin gefe tana kuka da ban-haƙuri, amma shi hawaye ne ke zuba daga idonsa. Yana tunani "Amatu ce ta tsaya tare da ni duk lokacin da na rasa kai na. Ita ce ta dinga hakuri, har lokacin da zuciyarta ta mutu tana riƙe da ni me ya sa ban gane darajarta ba har sai yanzu ta so Ni tsakanin ta da Allah kuma ittace ZAƁIN ZUCIYA ta ba kokkonta she is my first love soyayyar da muka gina da tsoron Allah da lamarin iyayyye da hanuna na rusa shi a sanadin Azezza shin me yafaru sani ba manta abada ƙauna ta ?" Ya dafa kansa, yana jin nauyin gangancin da ya aikata. Fuskar Amatu na bayyana a gaban sa — tana dariya a lokacin da ya bata gift ɗin farko, tana kuka lokacin da ya ƙi amsarta, tana shiru lokacin da ya fara canjawa. “Na cutar da ita na rasa ita.l na rasa kaina...” ya faɗi ƙasa a guiwowinsa, yana ambato sunanta da murya mai rauni: “Amatu...” KOWACCE SOYAYYA AKWAI KALUBALE A ASALIN LABARIN ZAƁIN ZUCIYA NASHWAN BAI TUBA BA HAR YANZU AMMAN YA ƘARA DAWOWA GUN AMATU YA BATA LABARIN RAYUWAR SA KUMA YAI MATA WASA DA HANKALI TA DOMIN YANA KIRAR TA YA TABBATAR MATA DA CEWA YANA SONTA HAR MA ZAI DAWO A BASHI AUREN TA DOMIN YA GANE KUSKURE SA . A WANAN LOKACIN AMATULLAH TA MANTA DA CIWO NA BAYA DOMIN SOYAYYA BA ƘARYA BANE TA SAKI MAYAR DA HANKALI AKAN SA KWATSAM YA KIRA TA YACE IYAYEN SA SUNKAI SADAKIN WATA YARINYA DABAN BA ITA BA ANAN TA TSUNDUMA IHU DA GUGUWA. DOMIN TABBAS YA MUNAFURCHI TA YA KARYA MATA ZUCIYA YA DAWO HAR TA SANAR DA IYAYYEN TA SAI DAI YANZU GASHI YA DAWO DA CEWA ZAƁIN IYAYYE SA YA AURA DAGA NAN TA ZAGI SA A ZUCIYAR TA TABGAYYYAWA ALLAH KUMA TA GOGGE SA HAR ABADA YANZU NASHWAN YAYI AURE AMMAN AMATULLAH NA NAN TA KASA MANCEWA DA ABINDA NASHWAN YA MATA KUMA BATA SAMU WANDA ZUCIYAR TA TA AMINCE DASHI BA DON HAKA MUNA MIKI ADDU'A ALLAH YA KAWO MIJI NAGARI ƳAR UWA KIMA ALLAH YA BAYYANA MIKI SARKIN KE .. ZAN ƘARA SA LITTAFIN DA SALO NA DON ANAN LABARIN TA YA ƘARE INA FATAN KUN FAHIMTA ALƘALAMIN NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️ ✍️ https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC 💘 ZAƁIN ZUCIYA💔 THE HEART'S CHOICE BY NARNAH ƘANWAR SOJA PAGE 15 / 16 26 /7/2025 "When the heart chooses, even silence speaks.. 🎂 BIRTHDAY DEDICATION – 26th July 🎂 “Rayuwar Amatu” An sadaukar da wannan littafi ga marubuciya Sayeeda a ranar zagayowar ranar haihuwarta 26th July. Littafin da ke ɗauke da rayuwa, ƙaddara, juriya da soyayya ta gaskiya — ya dace da zuciyar wacce ta rubuta shi: Mai naci, mai hangen nesa, da zuciyar da ta ƙunshi ƙwazon mace ta musamman. “Soyayya ta gaskiya kamar kyandir ce — tana iya rufta da rana, amma dumin ta yana nan har abada.” Happy Birthday, Sayeeda! Wannan littafi naki ne, kuma soyayyar kalamanki zata cigaba da rayuwa! ✨📚💝 GAISUWA Ga ɗan uwa Najeeb Allah ya saka da dubbun alkaire ɗam gidan Mama Allah ya bar zumunci Nagode.( Ina chan ina bachi dare ƙarfe sha biyu na daren jita ashe yana ta wishing na birthday na Jazzakkalllahu kairan ). GAISUWA Zuwa ga mutanen Yobe Naji daɗin saƙon ku kuma Allah ya saka da alheri Rabbi ya bar zumunci Nagode ************** Da safe da asuba ta kusa fita, Nashwan ya tashi daga bacci cikin jiri na nauyin damuwa bai iya runtsa da dare ba idanunsa sun kumbura — hawaye ne suka sha gajiya. Ya yi wanka, ya sa kayan shiru masu kamun kai — ba kayan boss ba, kayan mutum mai tozarta zuciya ( lol ) Ya fito zuwa falon gidan iyayensa da sassafe, Hajiya maman sa na zaune da Alhaji suna shan shayi da suka gan shi, Hajiya ta ɗaga kai cikin mamaki. “Kai Nashwan, lafiya da safe haka? me ya same ka?” ya durƙusa gaban su — abu da bai taɓa yi ba. “Don Allah... ku gafarce ni. Ku yafe min abin da nayi cikin duhun zuciya.” Alhaji da Hajiya suka zuba masa ido da damuwa, Alhaji yana girgiza kai “Nashwan, me kake nufi?” Ya dafe kansa da hannuwa biyu, kamar wanda ke jin nauyin duniya a cikin kansa ya sauke numfashi, sannan ya fara bayani... “Na aure mace ba tare da sanin cikakkiyar asalin ta ba. Azeeza ba wadda kuke zato ba ce ta yaudare ni da kyan fata, da ƙamshi, da wayo. Na shagala... Na bar Amatu, wadda ta tsaya dani tsawon shekaru, wadda nake da tabbacin so ta gaskiya ce... saboda kissa.” Hajiya ta runtse ido, tana kokarin shanye hawayenta. Alhaji ya gyara zama cikin juyayi da takaici. “Yanzu me kake so Nashwan ga abinda muke gayayama tun farko amman kaje kayi auren ka bada son mu ba wanan shine sakkayar iyayye ?” Ya ɗago kai, yana kallon su da idanu cike da nadama. “Bazan iya cigaba da zama da Azeeza ba. Na gwammace in ci mutunci na da gaskiya, in rabu da ita cikin kwanciyar hankali bana ƙi ta, amma bana iya daraja auren da aka gina bisa ƙarya.” “Don haka... don Allah ku taimake ni. Ku raka ni Maiduguri zan nemi Amatu... idan har zata saurare ni wallahi... a duk duniya, babu wata mace da ta kai ta mutunci da amanar zuciya. Na gane, na girma... kuma yanzu na shirya.” Hajiya ta share hawayenta da dankwali, ta ce da murya mai laushi: “Nashwan... wauta ce tafi kowa da saurin komowa gida. Idan har kana da niyyar gyara, to nima ina tare da kai.” Alhaji ya sauke numfashi mai nauyi, sannan ya ce: “Sai ka nemi sadaki naka. Auren da ya rasa gaskiya, to ginshikinsa ya riga ya rushe. amma Nashwan... ka sani: Amatu ba ta sauƙi. Idan har ka je gareta, to ka tafi da zuciyar gaskiya, ba da launin da ka zo da shi ba farko.” Ya gyada kai da hawaye — yana jin cewa rayuwarsa na da wata hanya ta sake farawa... amma sai ya dawo daga inda ya bar gaskiya. MAIDUGURI Garin ya lafa, rana na shirin fāɗuwa, iska tana busa sannu a hankali kamar tana fassara sabon shafi a rayuwar mutane. Motar Nashwan da iyayensa ta tsaya kai tsaye dai-dai zauren gidan su Amatu. Gidansu ya yi kyau, shuke-shuke a gefen titi, ƙofar ba’a rufe ba—alamun karɓa zuciyar Nashwan tana tashi da sauri kamar agogon da ya kai minti na ƙarshe. “Na dawo gida... first love never broken... Amatu zata gan ni, zata rungume ni, ta yafe min…” ya fito daga motar da sauri, kai tsaye cikin harabar gidan. Yana shirin shiga, kwatsam... Tana zaune a ƙasan zaure cikin wata shadda mai kyau, kanta a ƙasa, ta na wasa da zoben hannunta – kamar mai jiran magana mai daɗi. Fuskar ta faɗaɗe da kwanciyar hankali, har tana ɗan murmushi a gabanta kuma... wani saurayi ne. Tsafta, fara’a, nutsuwa — Habibu. Hannunsa na daure da agogo mai ƙyalli, yana kallon Amatu da irin kallon da Nashwan ya taɓa yi mata shekaru uku da suka wuce... lokacin da bai san darajarta ba. Zuciyar Nashwan ta tsaya. Jikinsa ya ɗauki zafi. Ido ya rufe da fari sai bugu! – zuciyarsa ta murɗa kamar an buɗe murhu. “Wannan saurayin fa? Amatu tana wasa da zobe fa? Wannan fa murmushewar soyayya ce?!” Da gudu ya karaso! ba wata magana, ba izini, ya chafko wuyar saurayin! “Kai wanene?! waye kai da zaka zauna da ita?!” Kowa ya yi turus. Amatu ta miƙe da sauri, cikin firgici, da ramar da ba a saba gani ba: “Nashwan??! wannan hauka ne! ka saki shi! me kake tunanin kake yi shine mijin da iyaye na suka zaɓa min ?!” Habibu bai ce uffan ba – sai ya ɗan ƙwace hannunsa da natsuwa ya dafa wuyarsa, sannan ya ce da Nashwan da murmushi mai ƙayatarwa amma da kwarjini: “Kishi ne da kake yi? Ko hauka ne da ya biyo kuskurenka?” Nashwan ya tsaya—ido cike da hawayen da ba za su sauko ba fuskar Amatu ta tsananta, ta fuskance shi cikin murya mai ƙarfi da taushi a lokaci guda: Nan ta zuba mai idanun cikin ido bugun numfashi su ya tsaya chakk na wasu mintuna “Na jira ka... shekaru. Amma kai ka je ka zaɓi wata ka ajiye ni kamar tsintacciya. Yanzu kuma ka dawo da idanu da rikici? Ka dawo da hannu, ba da so ba? Na yafe maka, Nashwan – amma ni fa yanzu na girma ne...” “...Sabuwar soyayya da ba ta da gurguwar kafa irin ta farko.” Hajiya da Alhaji sun iso daga baya, suka tsaya suna kallon abin da ke faruwa cikin alhini da kunya Alhaji ya furta da murya mai sanyi: “Na ce maka, ba kowace ƙofa ake dawowa da sauƙi ba.” Nashwan ya durƙusa — ba don wani ya hana shi ba, don zuciyarsa ta karye. Zuciyar da ya bari a baranda, yanzu tana hannun wani mai tsaro da kulawa. Yana kallo ta faɗa cikin wani harabar da bai da izinin shigowa da wucewa. Amatu ta gudu! Tana kuka kamar ruwan sama, ta shige gida hannunta na riƙe da kirjin ta. Zuciyarta tana bugawa da ƙarfi, soyayyar Nashwan ta sake dawowa – sabuwa, sabuwa fiye da yadda ta fara... “Shin zai iya dawo da ni? ko kuwa wancan ta riga ta mallake sa?” Kallon Nashwan da ya zo cikin kwarin guiwa da kukansa, da kishi da nadama... ya girgiza ta. Amma Habibu, wanda ya tsaya a kanta a lokacin da take cikin fanko da duhu – shi ne haskenta yanzu. Sai ga Baban Amatu ya fito, ya tsaya yana kallon Hayaki da Nashwan da iyayensa. Kallon ɗan-da-ta da hanzari, yana fahimtar komai kafin a faɗa masa komai. Habibu ya matso da ladabi, ya gaishe shi da salama da girmamawa.Baban Amatu ya buɗe ƙofa ya ce: “Ku shigo maza ku shigo da ku da zuciyarku – wannan ba gidan sabani bane, gidan fahimta ne.” Suka shigo daga nan aka basu ruwa, aka zauna. Nashwan yana durƙushe gaban su, kuka na fito daga idonsa kamar karamin yaro. “Don Allah Baba... don Allah! na kuskure. na bari soyayya ta gaskiya don cutar zuciyata. Amma yanzu na gane – Amatu ce ‘yar aljannata don Allah a dawo min da ita!” Baban Amatu ya ɗauki numfashi. Ya kalli Nashwan, ya kalli iyayensa, sannan ya juyar da idanunsa ga Habibu wanda ya zauna da tawali’u, amma fuskarsa cike da damuwa. Sai ya ce “Nashwan, na ji kuma ka kawo ƙara tare da kuka. ka aiko da zuciyar ka da tausayi.” > “Amma...” ya kalli cikin gida, sai ya ce: “Amatu ta fara mantuwa da kai tana shigowa daga duhu zuwa haske. Ta fara ƙaunar wani wanda ya tsaya da ita a lokacin da rayuwa ta mata nisa.” Burinmu ba auren shi ba ne, burinmu farin cikin ta ne. Idan har har yanzu tana iya jure maka, to ka shawo kanta, ka dawo da ita. Amma ka sani – wannan karon fa, kai da kanka zaka neme ta, ka lalle ta, ka lallaba ta. Kuma ka girmama ta… idan kuwa ba haka ba, ka daina kawo kanka.” “Amma... Idan har ka iya shawo kanta, da gaske ba da salo ba – na yarda. Ita ce zata zaɓa. Mu zamu kula, idan ta amince, zamu sasanta... a ɗaura auren ku.” Shiru. Nashwan ya saki wani kuka mai zurfi. Gaba ɗaya gidan ya shiru sai aka ji ƙarar ƙafa... Amatu ta fito daga ɗakin ta. Ido jajir, fuska cike da kwanciyar hankali. Kallon Nashwan ta yi. Ta kalli Habibu. Sai ta ce: “Na saurari kowa… Amma yanzu lokaci ne na sauraron zuciyata.” NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️✍️ https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC 💘 ZAƁIN ZUCIYA💔 THE HEART'S CHOICE BY NARNAH ƘANWAR SOJA PAGE 15 / 16 26 /7/2025 "When the heart chooses, even silence speaks.. 🎂 BIRTHDAY DEDICATION – 26th July 🎂 “Rayuwar Amatu” An sadaukar da wannan littafi ga marubuciya Sayeeda a ranar zagayowar ranar haihuwarta 26th July. Littafin da ke ɗauke da rayuwa, ƙaddara, juriya da soyayya ta gaskiya — ya dace da zuciyar wacce ta rubuta shi: Mai naci, mai hangen nesa, da zuciyar da ta ƙunshi ƙwazon mace ta musamman. “Soyayya ta gaskiya kamar kyandir ce — tana iya rufta da rana, amma dumin ta yana nan har abada.” Happy Birthday, Sayeeda! Wannan littafi naki ne, kuma soyayyar kalamanki zata cigaba da rayuwa! ✨📚💝 GAISUWA Ga ɗan uwa Najeeb Allah ya saka da dubbun alkaire ɗam gidan Mama Allah ya bar zumunci Nagode.( Ina chan ina bachi dare ƙarfe sha biyu na daren jita ashe yana ta wishing na birthday na Jazzakkalllahu kairan ). GAISUWA Zuwa ga mutanen Yobe Naji daɗin saƙon ku kuma Allah ya saka da alheri Rabbi ya bar zumunci Nagode Kallon Nashwan ta yi. Ta kalli Habibu. Sai ta ce: “Na saurari kowa… Amma yanzu lokaci ne na sauraron zuciyata.” Miƙewa yayi daga inda yake durgushe ya zuba guiwar sa duka biyu a ƙasa ya dafa hannun sa akan yatsun ƙafan Amatu wanda yayi sillar sanya ta cikin shork ba kaɗan ba , idon sa ya ɗago sama nan sunaye four eye's da juna " Don Allah Amatullah ke buɗe idon ke da kyau cikin nawa Wallahi inasonki , inasonki, inasonki,kicce zaɓin zuciya ta kice ganaganr jikin RUHI BIYU a guna kicce MADOBIN IDO NA Amattullah inasonki fiyyeda soyayyar Munir da Khadija ( MIJIN MAGE ) kisani na mallaka miki zuciya tace da amana na tabbatar bazaki rushe min amana ta ba don ki ɗin kin kasance HANYAR RUWA ne mai gudanar da dukkan tsaftattacen tamkar tsaftarr RAYUWAR UMMAH soyayyar ke gaskiya ne a dukkan nin hankali na da zuciya ta a koyaushe sonki ƙara zama yakiye tamkar FARASHIN SO yana hauhawa tamkar zuciyar maccen da takasance MAI CIKI CE , ke fittilar haske ce dake fittar da DUHU CIKIN HASKE kin gama mammaye zuciyarta tabbas bayan yafewa kaina wulakanta soyayyar ke da nayi baya ba ba'a sanina hakan ya faru ba ke yarda da zuciya ta da kallamai na , nine NASHWAN naki , kar koyar tunani akwai wata macce a duniyar nan da zatasa na manta da wanan kyakkyawar halitta da Allah ya bani tun fill azal ke Sarauniya tace sarautar ke ta zarci wata chan wai PRINCESS RAHILAT ina sonki sonda baxan iya haɗawa da AHLIN LAASHKAR BA shin kin san da cewa BAYAN WATA akwai wani haske da zai iya zarce KAƊANGAREN BAKIN TULU tabbas akwai zafi da raɗaɗin rashin mutuntukka dole zuciya tasha wahala a ƙaddarar RUHIN MARAICE Amman kisani cewa duk da cewa hawaye da tausayi kansa ace MASHIƘIYYA CE amman ta azabtar da zuciya ce bawai don zan barki ba lallai ke ta musamman ce kinye BIYAYYYA GA UWA da uba kin jira, kin jure wulakanta Amman kisani I LOVE U , FIRST LOVE NEVER DIE ,,, EVEN IN SILENT EVEN IN DARK AND HURT I WILL STILL LOVE U , U ARE MY CHOICE PLEASE FORGET AND FOGIVE ME saboda darajar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ♥️ Shiru dukka sukaye tabbas soyayya gaskiya ce shi kansa Habibu sun kunyar da kansa yayi domin ganin asalin masoya suna sun junan su tamkar babo kowa a gun "duk son da zanwa Amatu nasan bazata so ne kamar Nashwan ba domin shine Zavin zuciya ta "kowa sai da ya tausaya mai ganin hawaye a idon cikakkakken namiji a durgushe,, Mahaifin ta ne ya duƙar da kansa ƙasa yana jiran amsar Amatuu da tunanin kar ta zubar mai da mutunci sa idan har baya zaɓi Nashwan a karo na biyu ba tabbas basai me zaice musu ba .. Hannu yasa ta share hawaye da yake zuba a idon ta ta ɗaura da cewa “So yana da ƙarfi fiye da ɓacin rai. Ni na yafe maka Nashwan… kuma zuciyata ta kasa mantawa da kai. Zuciyata ce ta dawo ta gaya min cewa kaine ZAƁIN ZUCIYA ta don girman Allah ka riqi ne amana da gaskiya ta faɗa haka tana miƙa mai hannun ta biyu biyu cikin zama yasa hannun sa a hanun ta na miki Alƙawarin in Sha Allah bazan baki kunya ba ne naki ne har abada .... Wannan kalma ta girgiza kowa a dakin. Nashwan da Amatu sun sake sabawa da juna. Ya kawo lefen nadama da alkawura. Ana gaban iyaye, Amatu ta saka masa zobe da murmushi cike da annuri kiran “Zuciyata ta dawo gida” ya mamaye gari. Habibu ya yi murmushi mai cike da fahimta, ya ce: “Idan wani zai sace zuciyar ki, to Allah ya zuba albarka. Ina fatan farin cikin ki har abada.” mahaifin Amatu, cikin tsantsar jin daɗi, ya ce da Habibu: “Kaje kazo da iyayen ka na baka auren Safiya. Ita ce ta dace da mutuncin ka.” A ƙarshe: Habibu ya auri Safiya, ƙanwar Amatu, cikin koshin lafiya da soyayya mai tsafta. BANGON ƘARSHEN SHAFI Farin Ciki da Tsarin Allah “So na gaskiya baya mutuwa, sai dai a gwada shi da raɗaɗi. Idan ya jure to shi ne rayuwa.” Zabin Zuciya “Duk inda soyayya ta rayu, albarka na yawo.” Yau ƙauyen Baggale ya cika da farin ciki, mutane daga nesa da kusa sun taru domin shaidar auren Amatu da Nashwan tare da auren Safiya da Habibu. Gida biyu, soyayya biyu, amma albarka guda ɗaya. Kallon Amatu a dakin amarya sai ka rantse wata sarautar sama ce ta sauka. Fuskarta na sheƙi kamar safiyar Litinin mata suka zagaye ta suna ɗora mata kyakkyawar fure, idanunta cike da murmushin "na ƙarshe, na gaske." Safiya kuma — mai sauƙin kai da nutsuwa — tayi kyau da dinkin Shadda milk white, tana murmushi da hankali kamar wacce aka shayar da madarar soyayya. Hajiya maman Nashwan na kuka da dariya a lokaci guda, tana cewa: “Na samu yarinya mai amana, mai kunya, mai haƙuri – kamar Amatu babu! Na gode Allah.” A fagen biki, Nashwan ya durƙusa gaban Amatu yana mikar da zobensa: “Na yi kuskure, amma soyayya ta gaskiya bata taba lalacewa. First love never dies – kuma ke ce nawa.” ta amsa da murmushin da ke cike da zuciya da kwanciyar rai: “Zan zauna a zuciyar ka a matsayin wacce ka fara gani da idon soyayya.” Habibu kuwa yana kallo Safiya kamar kyautar Allah da ya zo da ita daga sama. Ya ce da ita cikin sanyi: “Kin maye gurbinta ba da haske ba… sai da annuri. Kuma zan girmama ki har abada.” Amarya da angwaye biyu suka fito hannun juna motoci sun yanka hula, yara suna yawo da “kululun goro,” amarya tana raye-raye da zumudi. TSOKACI NA “Rayuwa na juyawa, ƙaddara na da kalar sa. Amma wanda aka rubuta a zuciyarka, ba zai bace ba.” ************ Bayan sun iso Kaduna, aka shigo da su gidan Amatu gidan da aka gina domin ita, gidan da soyayya zata zauna kamar alƙalami cikin ink. Sashin nata kamar aljanna ce: tabarma mai launin shudi da zinariya, labulen satin milk white, furen roses a kowane kusurwa, da kyandiran romantic suna walƙiya da daddadan ƙamshi wani kiɗan light na soyayya yana kunne kamar ana busa saƙo ne daga zuciya zuwa zuciya. Nashwan ya durƙusa a gaban Amatu, hannunsa ya dafe nata, idanunsa sun cika da hawaye masu zafi amma daɗi: “Na ɗan rasa ki, na kusa rasa rayuwa amma Allah ya kawo ki mini har gida. Zuciyata ta daina bugawa a baya, yanzu ke ce kukan numfashina na kasa bayyana yadda nake jin ki – sai dai in ce: ki bar ni na mutu a cikin soyayyarki.” Amatu ta dafe kafadarsa, ta ce cikin sanyi: “ zuciyata ta yi wahala Nashwan. Ta sha hawaye da raɗaɗi. Amma duk da haka, zuciyata bata yarda da wani ba – sai kai.” Suka rungume juna… kamar su guda ɗaya ne da aka raba da ƙarfin duniya. Cikin dare aka shige sashin honeymoon, inda zuma ta haɗu da miya Nashwan ya ce: “Na ƙaunace ki a duk yanayinki, Amatu. ki zama matar zuciyata, mai rabona da kwanciyar raina. Duk inda kika zauna, can ne gidana.” Ya sumbaci goshinta, ta rufe idanunta da murmushi. ta ce da shi cikin ɗari-ɗari: “Ka rikeni da gaskiya, ka rungumeni da aminci. In har soyayya za ta rayu, sai da amana kuma kai na yarda da kai.” sai kyandir ya kashe da kansa… wata ta rufe sararin sama… soyayya ta kulle kofa... Ganin babo haske a ɗakin su da zan kawo muku rahoto nagaji da jira kawai na ajiye alƙalamin nawa a cikin labarin su na baza hijjabi na na kama hanyar Yola don naga tawa mahaifiyar Alhamdullah 💕 ALHAMDULLAH ALHAMDULLAH ALHAMDULLAH