[3/8, 12:45 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) MIKIYA WRITERS ASSOCIATION 1 Iskar hadarin dake kaɗawa ba ta saka na yi yunƙurin tashi don kwashe abubuwan dake tsakar gidana ba, saboda gudun kar ruwa ya sauko. Ina nan zaune kamar an dasa bishiya ban ko motsa ba, ina ta kuncewa da saƙa yadda za a yi ni ma na zamo ɗaya daga cikin fitattun mata na wani group ɗin WhatsApp da nake ciki. Ganin wankin hula yana ƙoƙarin kai ni dare ya sa na sauke wani wahalallen numfashi tare da miƙewa na fara kintse-kintse. Ina yi ina tunanin da wani hamshaƙin mai kuɗin nake aure ko gida mai tsakar gida ba zan yi rayuwa a cikinsa ba, bare na yi fargabar kar ruwa ya taɓa mini abubuwan amfani. Bayan na gama na shiga ƙaramin falona na zauna na kishingiɗa akan kujerar zaman mutum biyu. Kallon ko ina nake yi a ɗakin ina bitar kayan cikinsa kamar ba nawa da na saba gani kullum ba. Kujeru ne kawai saiti da labulaye, sai ƙaramar TV ta ƙasa. Ban san lokacin da na ja wani dogon tsaki ba lokacin da hoton wata Hajiya da ta turo ɗazu ya faɗo mini a rai, wanda aka ɗauke ta a gaban tamtsamemiyar TV'n bango dake cikin wani rantsatstsen falo. A karo na barkatai cikina ya murɗa saboda yunwar dake ƙwaƙular hanjina, tsabar karanta wasiƙar jakin da na tsaya ina yi ko abincin rana ban ci ba, ga shi Magriba ta kawo kai. Ba don son raina ba sai don ban da zaɓi na miƙe na zubo shinkafa da waken da na girka na zuba mata mai ishashshe, ga salad da tumatir a gefe da yajina da ya ji magi. Cikin takaici na fara cakuɗa ta ina keɓe fuska kamar na ga kashi. "Ko ɗan kifi babu akai balle ƙwai." Na faɗa a fili ina tuno haɗaɗɗun girkunan da matan group ɗin nan suke turowa, wanda yake wadatuwa da lafiyayyen nama. A maimakon kidahumar ƙwaƙwalwata ta tuno mini waɗanda ba su da shi, waɗanda da za su gan ni za su ce dama ni ce su, waɗanda kullum suke kwana su tashi da fargabar abin da za su ci. Haka na tuttura abincin na tashi na je na kwanko hannuna, ina ƙoƙarin komawa ɗaki yarana maza guda biyu Sultan da Safyan suka shigo da gudu bakinsu ɗauke da sallama. Bin su na yi da kallo ganin yadda uniform ɗinsu ya yi datti, komai dare ko gobe da safe sai na wanke musu kafin su kuma sakawa. Hasasowa na yi da matar mai kuɗi ce ni kamar matan cikin group ɗin nan da sai dai masu wanki su wanke musu. Cikin rige-rige suka zo suka rungume ni kowa na ƙoƙarin karanta mini abin da aka koya musu a islamiyya. Zare su na yi daga jikina, cikin tsawa da zare ido na ce. "Mene haka? Ba ku da hankali ne?" Bi na kawai suka yi da ido don hakan baƙon al'amari ne a gare su. Ni kuwa gare ni haushin mahaifinsu da nake ji ne ya shafe su, na baƙincikin bai zo a mai kuɗi ba. Ina shiga ɗaki suka biyo ni jikinsu duk a sanyaye. Kamar yadda mahaifinsu ya horar da su idan sun yi mini laifi su ba ni haƙuri haka Sultan ya dube ni ya ce. "Mami mun yi miki laifi ne? Ko gudun da kika hana mu muka yi ne ya ɓata miki rai?" Kallon shi na yi kafin na yi magana Safyan ya riga ni da faɗin. "Ni ban yi ba Mami, Yaya ne ko?" Numfashi na sauke tare da janyo su jikina na ce. "Kuna yi wa Abba addu'ar Allah ya ba shi kuɗi mu koma ƙaton gida kuwa?" Bi na da ido kawai Sultan ya yi, Safyan ne ya ce. "Irin gidansu Zuhura?" Da sauri na ce. "Eh, ko ba kwa so?" Sufyan ya ce. "Muna so." Shafa kansa na yi ina murmushi na ce. "Yawwa yaron kirki, mu ma mu zama ƴan gayu yanda mutane za su dinga sha'awar mu, mu dinga cin abinci kullum da nama da kaji." Cikin tsallen murna ya ce. "Eh Mami." A hankali Sultan ya ce. "Mami amma da ba kya cewa mu yi wannan addu'ar, haka kawai kike cewa mu ce Allah ya buɗa wa Abba." Na ce. "To yanzu ku fara, don in ma bai yi kuɗin ba barin shi za mu yi mu je mu samu wanda zai kai mu ƙaton gidan, don ba zan ci gaba da rayuwa a wannan akurkin ba." Bi na kawai suka yi da kallo don ba su gane abin da nake nufi ba. Bayan na cire musu uniform na zuba musu abinci suka fara ci na fita na ɗauro alwala na dawo parlour'n don tayar da Sallah. Ina tsaki na kunna torchlight ƴar madaidaiciya wadda ake yi mata chaji saboda babu Nepa. Cikin raina ina tunano yadda matan cikin group ɗin nan suke labarin kodayaushe suna samun Nepa a unguwanninsu, saboda ta masu hannu da shuni ce, idan ma an ɗauke za a tayar da inji ko kuma a kunna solar. Idar da Sallahta ya yi daidai da shigowar kira cikin wayata. Sultan ne ya miƙo mini na karɓa na duba mai kiran, ɗaya daga cikin members ɗin group ɗinmu ce ta kira ni, wadda muka fi mutunci da ita saboda sunanmu ɗaya. Ɗagawa na yi tare da yin sallama. Ba ta amsa ba saboda maganar da take yi, daga yadda na ji tana bayar da umarnin a kwashe kajin da mijinta ya zo da su a saka a fridge na san da mai aikinta take. Wani yawu na haɗiye tare da tambayar kaina yaushe ni ma zan gan ni a wannan level ɗin? "Namesake." Na ji muryar Maman Nasma ta faɗa. Cikin fara'a kamar tana gabana na ce. "Na'am, kin gama maganar ne?" Ta ce. "Eh, ya gida? Ya sa Sultan da Dad ɗinsu?" Na ce. "Duk suna lafiya, ya su Nasma da Abul?" Ta ce. "Alhamdulillah, yanzu ma suka hau sama gurin Dadinsu, ya dawo sun tafi karɓar chocolate." Na ce. "Ayya." Kawai. Ta ce. "Ban gan ki online ba ne, na ga kuma an ci gaba da gabatar da kai a group kowa yana turo pic ɗinsa da na yara, shi ne na ce bari na taɓo ki na ce ki zo ki ba mu naki, na san yadda muryar nan taki take da zaƙi zankaɗeɗiyar mace za mu gani." Yaƙe na yi na ce. "Toh shikenan, bari na hau yanzu na tura, su Safyan ne suka dawo daga islamiyya na tsaya sallamar su, da na gama na yi Sallah, shi ya sa ban hau ba." Daga haka muka yi sallama na katse wayar. Shiru na yi ina jujjuya ƴar akwalar wayata a hannuna, wadda kuɗinta ko dubu ashirin ba zai yi ba. Uzurin da na ba wa Maman Nasma ba shi ya hana ni hawa online ba, chaji ne ishashshe ban da shi, kuma ba tabbas ɗin kawo Nepa, ga fitilarmu idan chaji ya ƙare sai dai na koma haskawa da ta wayata. Dogon tsaki na ja cikin takaici na kunna data, direct WhatsApp na shiga cikin group ɗin *Zumuncinmu* na fara kallon hotunan da aka tutturo, hannuna har rawa yake gurin bubbuɗewa. Zuƙa-zuƙan mata kawai nake gani a haɗaɗɗun background, na wannan yana wane na wannan. Na ga yadda ake ta wow wow tare comments. Fita na yi na shiga gallery na fara duba nawa hotunan da na yarana wanda duk aka yi su da wayar hannuna, sai na gan mu wasu dususu kamar almajirai. Jinjina kai na yi na ce. "Taɓɗijan! Yanzu ta yaya zan tura wannan hotunan? Ai ko karen hauka ne ya cize ni ba zan soma ba." Ficewa na yi na koma WhatsApp na shiga group ɗin, tagging ɗina na ga an yiyyi akan na tura nawa, don sun gan ni online. Cikin tsinkewar zuci da sanyin gwiwa na ce zan tura musu yanzu, bayan na bibbi pictures ɗin da aka turo da. 'Masha Allah.' Direct ta group ɗin na shiga gallery na fara bin pics ɗin cikin wayata ɗaya bayan ɗaya, akan na wata ƙawata da muka yi secondary school tare da take auren mai kuɗi na tsayar da idona. Tana sanye cikin abaya mai kyau a gaban ka'aba, a ƙasa mai tsarki aka yi mata hoton, last zuwan da suka yi Umrah da mai gidanta ne ta turo mini hoton. A take zuciyata ta ba ni umarnin na tura musu shi kawai na ce ni ce, ba tare da nazari ko tsoron abin da zai je ya dawo ba na danna shi ya cika screen ɗin wayar. "To ni ma ga ni, ina yi wa kowa fatan Alkhairi." Na rubuta caption da haka tare da turawa.......✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 12:45 PM] Bahaushiya👍: Drama section ko comment section ba a tura littafi can comment kawai da surutu za a zuba https://chat.whatsapp.com/J0sit2lZquWHwDxJaARjR3 *YI WA KAI* MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) 2 Dif! Wayar ta ɗauke babu chaji, dogon tsaki na ja na dangwarar da ita a kan dardumar da nake kai. Dama na san hakan za ta iya faruwa, shi ya sa na ƙi hawa online ɗin tun ɗazu. "Mamy me ya faru kike ta tsaki yau?" Cewar Sultan da ya miƙe da plate ɗin abincin da suka gama ci a hannunsa. A kufule na ce. "Ubanka ne Sarkin tambaya ɗan gidan tanbai." Cikin rawar murya kamar zai yi kuka ya ce. "Ki yi haƙuri don Allah." Ban ce komai ba amma jikina ya yi sanyi, miƙewa na yi na ce. "Ku je ku yi alwala ku zo ku yi Sallah, kar ku manta da addu'ar da na ce ku yi wa Abba kun ji yaran kirki." Gyaɗa mini kai suka yi suka fice a tare bayan Safyan ya ɗaukar musu fitila. Kwanciya na yi a maimakon zikiri da na saba yi a irin wannan lokacin, na fara tunanin da ban san ranar gama shi ba, babban takaicina rashin sanin pic ɗin da na tura ya tafi ko bai tafi ba. A haka mijina ya shigo ya same ni. Duk da ban kalli fuskarsa ba amma na san ɗauke take da murmushin da yake shigowa da shi a kullum, a zuci na amsa masa sallamar da ya yi, saɓanin da da nake tashi da hanzari na tarɓe shi. Kunna torchlight ɗin wayarsa keypad ya yi yana faɗin. "Ina ƴar aljannar tawa take ne?" Harara na zabga masa a duhu tare da jan tsaki a zuciyata na rufe idona, cikin raina ina tambayar kaina me ya rufe mini ido lokacin da ina budurwa na amince na aure shi? Ban kai ga ba wa kaina amsa ba na ji yana faɗin. "Subhanallahi! Hafsah ba dai ba ki da lafiya ba?" Saboda in dai ba cuta nake ba, ba ya taɓa zuwa ya tarar da ni a kwance a irin wannan lokacin. Buɗe idona na yi tare da tashi zaune kamar an yi mini dole na ce. "Sannu da zuwa." "Yawwa, me yake damun ki?" Ya yi maganar yana taɓa goshina, muryarsa da alamun ruɗewar da yake yi a duk lokacin da ban da lafiya. Ture hannunsa na yi na ce. "Babu komai." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Kin tabbata my love?" Wani kallo na yi masa tare da faɗin. "Sai aukin soyayya amma babu ko sisi." Yadda na yi maganar dama na san ba zai ji abin da na ce ba. Zama ya yi a kusa da ni yana ƙoƙarin janyo ni jikinsa ya ce. "Ban ji me kika ce ba." Na ce. "Cewa na yi ƙalau nake." Ya ce. "Amma me ya sa na gan ki a haka? Don Allah ki faɗa mini idan ba ki da lafiya mu je chemist ɗin Kamilu ya duba ki." "Lafiyata fa ƙalau." Na faɗa cikin zunɓura baki. Tsayawa kawai ya yi yana kallo na, daga baya ya sauke numfashi ya tashi ya fita daga falon. Raka shi na yi da wani mugun kallo, a fili na ce. "Wai chemist? In ma cutar nake da gaske ba za a kai ni asibiti ba sai wani chemist." Ranar da su Maman Nasma suke zancen family doctor a group ce ta faɗo mini a rai, ƙwafa na ja na koma na kwanta ina wadaran auran talaka a cikin raina. Ina jin shi suna ta hira da ƴaƴansa a tsakar gida, suna biya masa karatun da aka yi musu a makaranta, yana gyara musu inda suka yi kuskure. Tare suka je masallaci suka yi sallar isha'i. Bayan sun dawo ya ƙara tisa ni a gaba da tambayar abin da yake damu na cikin kulawa, banza na yi da shi na juya masa baya. Ya bar ni na ji da rashin chajin wayata ma amma ya bi ya ishe ni, na san yanzu ana can ana ta shan hira a group. Gabaɗaya sai ya tashi hankalinsa, ya dinga lallaɓa ni da roƙon na faɗa masa idan wani laifin ya yi mini ya ba ni haƙuri, sai da na gaji da magiyara sannan na ce masa gajiya ce kawai take damu na. Ko rufe baki ban gama yi ba ya tashi ya ɗauko mini maganin gajiya da ruwa a cup ya kawo mini na sha, sannan ya ce su Sultan su mammatsa mini ƙafata shi zai fita ya wanke musu uniform da takalma. Sai da ya yi wanke-wanken kwanukan da muka ɓata ya dawo ɗakin. Sannu ya yi mini tare da faɗa mini abubuwan da ya yi, na ɗaga masa kai kawai cikin ƙosawa. Bai zauna ba ko ya nemi abinci ya kama su Safyan ya yi musu wanka shi ma ya yi. Ya kai su ɗakinsu ya shirya su ya kwantar da su. A lokacin aka kawo wutar nepa, cikin tsananin farinciki na miƙe na rarumi wayata na nufi socket na soka chaji. Daidai lokacin ya dawo falon yana faɗin. "Bari na goge wa su Sultan uniform ɗin da na wanke yanzu, da safe kin huta aikin ya yi miki sauƙi, ga ruwan wanka can na haɗa miki, ko ba za ki iya zuwa toilet ɗin ba na kai ki?" Kallon shi na yi ba yabo ba fallasa na ce. "Zan iya, ka zo ka ci abinci, na ga tunda ka dawo ko ruwa ba ka sha ba." Ya ce. "Zan ci ne, so nake na gama duk ayyukan don gobe ki samu hutu da bacci ishashshe, kar gajiya ta ƙara damar mini ke." Taɓe baki na yi a raina na ce. 'Hutun ai na banza ne tunda ba a gidan da ya amsa sunan gidan hutu nake ba.' Daga haka na miƙe na fice daga falon. Bayan na fito daga wanka na zarce ɗakin baccinmu, ina cikin shiryawa na ga wata ƙaramar baƙar leda a kan mudubi. Ɗauka na yi na duba abin da yake cikinta, biscuit ne ɗan goma-goma guda biyar da alawa ita ma guda biyar ɗin. Na su Sultan ne da yake siyo musu kullum, idan za su school na ba su bibbiyu, islamiyya ma haka. Taɓe baki na yi na mayar na ajiye. A fili na ce. "Aikin kenan, kullum siyayyar yara ba ta wuce ta Naira ɗari, wasu kuwa komai katan-katan ake dire wa ƴaƴansu, abubuwa masu tsada ma ba ƴan goma da biyar ba." Har na gama shirina ban daina mita ni kaɗai a cikin raina ba, don ban da wani buri a duniya a yanzu da ya wuce na buɗe ido na gan ni a cikin ƙaton gida, mai ɗauke da komai na kayan alatu da abubuwan more rayuwa irin wanda matan cikin group ɗinmu suke ciki. Idona gabaɗaya ya rufe, babu abin da ƙwaƙwalwata take ganewa sai wannan tunanin. Da na koma falo ko sannu ban yi wa Anas ba na zauna na janyo wayata na kunna. Hakan bai hana shi duba na ba cikin murmurshi tare da faɗin. "Kin yi kyau autar matana." Haɗe rai na yi na ce. "Ka faɗa ne kawai don na ji daɗi, amma ka san ba a kyau sai da kayan kyau." Cak ya tsaya da gugar da yake ya zuba mini ido, cikin wani irin yanayi ya ce. "Me yake damun ki ne yau Hafsah? Ban gane me kike nufi da wannan maganar ba? A da idan na ce kin yi kyau murmushi kike yi tare da yi mini godiya ki kuma ba ni tukuci da abin da kika san ina matuƙar so." Cikin ko in kula da yanayin da na gan shi na ce. "Lokacin ban gane halin da duniya take ciki ba ne sai yanzu." "Wanne hali kuma? Ai ƙara saka ni a duhu kika yi." Ya tambaya fuskarsa da alamun damuwa. "Ka ci gaba da abin da kake yi kawai." Na faɗa hankalina akan wayata lokacin da na shiga cikin group ɗinmu. Bai kuma magana ba ya ci gaba da gugarsa, hakan ya yi mini daɗi, don ko ya yi ma ba tanka masa zan yi ba. Chat ɗin da aka yi ba na nan na fara bi, na ga wanda ba su tura pic ɗinsu ba duk sun tutturo, nawa wanda na tura kuma bai tafi ba. Ban ce komai ba na fita daga cikin group ɗin, Na buɗe saƙon Maman Nasma da ta yi mini ta private. 'Takwara ina kika shige ne? Don Allah ki zo ki ba mu hoton nan naki, ko rawar ganin ki kike mana?' Na karanta abin da ta ce a cikin raina, reply na yi mata na tura, sai na ga bai yi tick alamar ya tafi ba. Kashe datata na yi na ƙara kunnawa amma still ya ƙi tafiya. Fita na yi na duba data balance ɗina, sai na ga ashe ta ƙare ne, dama tun yamma da na duba saura kaɗan. Dogon tsaki na ja na ajiye wayar. 'Kai bawa daga wannan sai wannan, Ubangiji ka raba mu da tsiya da talauci.' Na faɗi haka ƙasa-ƙasa tare da miƙewa na bar falon, ina ganin Anas yana bi na da wani irin kallo wanda na san na zallar mamakin sabbin ɗabi'un da bai san ni da su ba ne. Juyi kawai nake a kan gadona cikin rashin sanin mafita, ina tsoron kar na tura hoton Sa'adatu ƙawata na je wata ta san ta a cikin group ɗin, ko kuma tsautsayi ya sa mu haɗu da wata a zahiri ta ga ba ni ba ce. Ni kuma gaskiya ba zan iya tura hotona da na yi da wayata ba, saboda rashin fitarsa da rashin haɗaɗɗen background, sai yanzu nake jin daɗi ma da hoton bai tafi ba. Don duk waɗanda suka turo hotunansu kowacce da kyan ganin ta, alamun da manyan wayoyi suka yi ba jagwal irin tawa ba. 'Ko dai gidan Sa'adatun kawai zan shirya na je gobe ta yi mini hoton a gidanta na tura musu?' Na tambayi kaina cikin tantama don na san ba lallai ya bar ni ba, saboda ban san me ya sa ba, ba wani son alaƙata da ita yake ba. Tashi zaune na yi ina bin ƙaramin ɗakin nawa da kallo, hoton wata Maman Fa'iz ne ya faɗo mini a rai, wanda aka yi mata a gaban mudubin ɗakinta, ta cikin mirror tamfatsetsan gadonta na ƙasar waje ya fito, ga ɗakin daga ga ni ƙato ne. Saukar da idona na yi a kan wardrobe ɗinmu, wadda na san a irin gidansu Maman Fa'iz ko a ɗakin mai gadi ba za a saka irinta ba. Komawa na yi na kwanta, saboda tsabar tunani kaina har wani juya mini yake yi. A lokacin Anas ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, na amsa masa ciki-ciki. Bai damu ba ya dube ni cikin kulawa tare da faɗin. "Ya kika kwanta kuma ba ki saki net ba? Duk da akwai Nepa ai sauro yana yawo." Na ce. "Zan saki ne." Yana sakin net ɗin ya ce. "Kin je kin tofa wa su Sultan addu'a ne?" Cikin ƙosawa da maganar tasa na ce. "Eh." Ya ce. "To bari na kakkashe ƙwaiƙwaye na zo mu yi magana, don wannan yanayin da kike ciki na san ba ƙalau ba my love." Baki kawai na taɓe ban ce komai ba, ya gama abin da zai yi ya hawo kan gadon ya ja ni jikinsa ya ce. "Don girman Allah ki faɗa mini abin da yake damun ki, wallahi ganin ki a haka gabaɗaya ya hautsina zuciyata." Na ce. "Ba komai fa, ka yi baccinka kawai." Ƙasa ya yi da murya kamar kodayaushe idan yana rarrashi na ya ce. "Ba ma haka da ke, kar mu fara a yau, kin san babu yadda za a yi na iya yin bacci kina cikin ɓacin rai, ko kun samu saɓani da wani ne ta waya? Na ga da tana hannunki kina ta tsaki." Hararar shi na yi na ce. "Ko ɗaya, tunda na ce maka babu komai ka ƙyale ni mana!" Shiru ya yi kawai, duk da duhu ne amma na san kallo na ya tsaya yana yi. Barin jikinsa na yi na koma can ƙarshen gado ina jan tsaki a cikin zuciyata. Don ni gabaɗaya gani nake shi ne matsalata, da ya zo a mai kuɗi ai da yanzu ba na cikin fargabar fita kunya a cikin group ɗinmu. Ina jin shi yana sassauke numfashi na yi banza da shi. Na san abu biyu ne ya haɗar masa, baƙon halin da na tsiro da shi da kuma tabbacin rashin samun haɗin kaina da zai yi idan ya buƙace ni, don ba ƙaramin tanadi ya yi wa wannan daren ba, saboda yau da safe na yi wankan tsarkin hailar da na yi kwanaki biyar ina yi, tun kafin ya fita yake ɗoki, da rana ma da ya muka yi wayar da muka saba yi kullum idan ya fita sai da ya yi mini zancen. Na ɗauka ya haƙura amma sai na tsinkayi muryarsa a raunane yana faɗin. "Shikenan Hafsah tunda haka kika zaɓa, ba zan takura ki dole sai kin faɗa mini abin da yake faruwa ba tunda kin ɓoye, amma don Allah ki daina bayyana ɓacin ranki, kin fi kowa sanin yadda hakan yake taɓa ni sosai ya kuma sanya ni a cikin damuwa, ba ki ji yadda nake ji a cikin raina ba, gabaɗaya na rasa nutsuwata, don Allah ki yi mini wannan alfarmar." Ture tausayinsa dake ƙoƙarin mamaye ni na yi na ce. "Shikenan, in sha Allah zan yi hakan." Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi tare da faɗin. "Na gode tawan, Allah ya yi miki albarka ya ji ƙan Umma, ya raya mana su Sultan, ya kawo ƙannensu dozen masu albarka." Ya ƙarashe maganar cikin sigar tsokana. A daƙike na ce. "Amin." Ban yi niyyar tanka masa ba, amma don ya ƙyale ni na samu na yi tunanin sama wa kaina mafita na biye masa muka yi magana. Sai dai abin da nake so ɗin bai samu ba, don jin shi kawai na yi a jikina a maimakon na ga yana shirin yin bacci. 'Mutum sai jarabar tsiya amma ba ko sisi.' Na faɗi haka a cikin raina cikin takaici da haushin shi da yake ƙara cika mini zuciya.......✍️ *Zeey Kumurya ✍️* [3/8, 1:34 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) 3. Washegari bayan na yi sallar asuba na koma na kwanta duk da ba bacci nake ji ba, don ban saba yin shi a irin wannan lokacin ba. Kuma na san su Sultan za su tafi school, amma rashin data ya sa duk takaici da ɓacin rai ya cika mini zuciya. Bayan Anas ya gama karatun Alkur'ani da azkar ya dube ni ya ce. "Wai har yanzu wannan yanayin bai bar ki ba? Ba mun gama magana jiya ba?" Fuska babu walwala na ce. "Na ce maka akwai wata matsalar ne?" Ya ce. "A'a, alamu dai kawai na gani." Siririn tsaki na ja na juya masa baya. Bai ce komai ba ya tashi ya fita, ina jiyo shi suna buruntu shi da ƴaƴansa. Har bakwai na safe ta wuce ina inda nake ban ko motsa ba, na ɗora da daga inda na tsaya a tunanin da ya aure ni. A lokacin su Sultan suka shigo ɗakin bakinsu ɗauke da sallama, juyowa na yi na kalle su tare da amsa musu, ganin jikinsu da ruwa alamun wanka ya yi musu ya sa tilas na tashi na fara shafa musu mai. Bayan sun gaishe ni Sultan ya ce. "Mami ba ki da lafiya ne yau ba ki fita kin yi mana girki ba?" Gyaɗa masa kai kawai na yi. Cikin marairacewa Safyan ya taɓa goshina ya ce. "Sannu Mamina, kin sha magani?" Shafa kansa na yi na ce. "Ai ban da maganin ciwona a yanzu, amma idan kuna addu'ar da na ce shi ne maganin zai samu." Sultan yana saka wandonsa ya ce. "To mene yake miki ciwo?" 'Talauci.' Na faɗa a cikin raina. A fili kuwa ban ce komai ba. Tare muka fita parlour, na tarar har Anas ya dama mana kunu ya siyo ƙosai, yana kallo na ya ce. "Zuba musu su ci mu tafi, sun kusa latti, bari na yi wanka kafin su gama." Kamar wadda ya faɗawa mutuwa haka na ɗaga masa kai fuskata a cuskune. Duk da ba na kallon fuskarsa amma na san tsayawa ya yi yana kallo na, kamar ban san yana yi ba na tsugunna na fara tsiyaya kunun a ƙananan cup. Ina jin shi ya ja dogon numfashi sannan ya fita, raka bayan shi na yi da harara. Na Kunna wayata ina dube-dube ya dawo ya shige ɗaki, ya ƙara fitowa kamar mai neman wani abu ya koma. Na san me ya sa ya yi hakan, a tunaninsa ko ban gan shi ba ne ko kuma tuni yake yi mini, saboda ya saba kullum ni nake shirya shi tsaf. Bayan ya gama ya fito ya kama hannun su Sultan ya tafi kai su school. Ina tunanin ranar da mafarkina na ganin lokacin da drivers za su dinga kai su Sultan school a haɗaɗɗiyar mota na fita tsakar gida, na gan shi fes har shara ya yi, da ma kuma kusan kullum shi yake yi, don tun ina amarya indai yana gida tare muke yin aiki, yanzu kuma da hidimar su Safyan ta ƙaro sai muke raba aikin, shi ya yi shara da wankin toilet ni kuma na yi wanke-wanke da abun kari da gyaran ɗaki. Idan kuma ba zai fita da wuri ba har wanke-wanken yake yi da dama kunu ko tafasa ruwan tea, ni kuma na shirya su Sultan. Cups ɗin da yaran suka ɓata na wanke na koma ɗaki na fara gyarawa. A haka ya dawo ya same ni, yana duba time ya ce. "Mu je mu karya kar ƙosan ya ƙara yin sanyi." Ɗan yamutsa fuska na yi na ce. "Ba na jin yunwa, ka je ka ci kawai." Fuskarsa da maɗaukakin mamaki ya ce. "Hafsah! Wai kina cikin hayyacinki kuwa? Ni ne fa Anas mijinki amma kike yi mini irin wannan abubuwan, me yake damun ki ne?" Ban ce komai ba na ci gaba da aikina, duk da na san hakan ba ƙaramin ƙular da shi zai yi ba, don ya tsani yana yi wa mutum magana yay masa shiru. Ganin ya ƙi fita na juya na kalle shi na ce. "Ka yi haƙuri, mu je mu ci abincin." Girgiza kai kawai ya yi ya fice daga ɗakin. Ina son mijina da ƴaƴana, kuma ba na son ɓacin ransa, amma burina na son zama hamshaƙiyar mace matar mai kuɗi ya canza mini komai a cikin raina, don a yanzu ban da wani fata sama da haka. Kuma gabaɗaya a da ban san ana irin wannan rayuwar kuɗin ba, saboda a cikin talakawa na tashi a nan na rayu, ina dai jin labarin masu kuɗi, amma ban taɓa tunanin jin daɗin rayuwarsu ya kai haka ba sai a SANADIN WAYA. Zuciyata ta kwaɗaitu matuƙa da irin wannan rayuwar. Duk wani rarrashi da nasiha sai da Anas ya mini kafin ya fita, hakan ya sa na ɗan saki raina, muka rabu lafiya kamar yadda muka saba kullum. Fitar shi babu jimawa message ɗin kati ya shigo wayata, da ma na faɗa masa ban da data ne, ya ce yana fita zai tura mini. Da rawar jiki na loda katin na siya data, har wani zuƙo jikina yake yi mini saboda zumuɗin shiga group ɗinmu na ga abin da aka yi da ba na nan. Hirarraki burjik na tarar an yi, a hankali na fara bi tun daga farkon inda na yi offline. Rabin hirar ta yabon hotunan juna ce, daga nan aka fara zancen kaya, lace ɗin jikin wata ne ɗaya daga cikin admin ta ce sun yi ankon shi a wani biki, kuɗinsa dubu ɗari biyu da wani abu. Zaro ido na yi na koma kan pic ɗin matar na yi zooming na ƙara kallon kayan da kyau, a anko kawai an yi na sama da 200k? Ina kuma ga normal kayan sakawa na gida ko na Sallah? Ci gaba da bin hirar na yi, na ga wadda ta saka kayan tana faɗar kuɗin ɗinkin da aka yi mata 30k. Haka dai nai ta bi ina kallon hirar tare da haɗiyar yawu, jin yadda suke zancen maƙudan kuɗaɗe a kayan sakawa kawai da takalmi da jaka. Abin da ya fi komai ɗaukar hankalina videon bikin da wadda ta ce sun yi ankon lace ɗin ta turo. Wani haɗaɗɗen hall  ne da ban taɓa jin labarin irinsa ba a rayuwata balle na gani. Ga hamshaƙan mata sun kame a kan kujeru, wuya da kunnuwansu duk gwala-gwalai ne. Na maimaita kallon videon babu adadi, kamar na yi tsalle na faɗa cikin wayar saboda yadda abun ya yi mugun ƙayatar da ni. Wasu mahaukatan kuɗaɗe ake liƙawa kamar ana watsa duwatsu. Ba don na gaji da kallon videon ba na haƙura na koma na ci gaba da bin chat ɗin nasu, don tsabar kallo sai da na haddace duk wani abu da ake yi a cikin videon da maganganun mc. A cikin hirar na ji wata ta ce ta ga bikin a Instagram, daga nan aka fara zancen ƙayatattun bukukuwan da ake ɗorawa a manhajar ire-iren waɗannan da ma wanda suka fi su. A take na ji ina son na shiga Instagram ɗin ni ma na gani. Da wannan zumuɗin na fita daga Whatsapp na koma play store na ɗauko app ɗin, bayan ya gama installing na yi ƙoƙarin buɗewa amma ya ƙi saboda ban da email account, ga shi ban san ta yadda zan buɗe shi ba. Na koma group ɗin da nufin na tambaye su ko sun sani amma sai na ga kamar ajina zai zube, hakan ya sa na fasa na miƙe na zari hijabina na rufe gida na fita. Wani gida a layinmu dake da wadatuwar samari na je suka buɗe mini a nan take, na yi musu godiya cikin tsananin farinciki sannan na dawo gida.  Zaman dirshan na yi a tsakar ɗaki ina kallon video's a Instagram baki buɗe, ashe ko rabin tsaruwa da haɗuwar bukukuwan ba su fasalta ba a group ɗin. Ban ajiye wayata ba har sai da na ga sun daina buɗewa, alamun datata ta ƙare. Ni da take yi mini kwana shida amma yau a cikin awanni ta ƙare, ashe shiga kowane apps a social media ɗin ma sai masu kuɗi, kullum ina ji suna ta zancen apps kala-kala, ashe ba ƙaramin data suke jibgawa a wayoyinsu ba. Wannan tunanin ya ƙara girmamar burina a cikin raina, na ji a yanzu babu abin da nake so sama da na ga na je irin waɗannan bukukuwan, ko kuma ya kasance an yi akan wani nawa ko wanda na sani da za a gayyace ni, duk da zan fi so a ce a bikina shagalin ya kasance. Tunanin ƴar walimar da aka yi lokacin aurena ya sa ni jan dogon tsaki tare da cizon yatsa. Sai sha biyu na rana saura na iya tashi na ɗaura girki, ina aikin ina imagining ranar da zan gan ni a cikin irin manyan haɗaɗɗun halls ɗin bikin da na gani, ni ma na tura a group ɗinmu aita mun fatan alkhairi da yaba bikin. Don yadda aka yiwa wadda ta turo sun yi bikin Allah ya sanya alkhairi abun ya burge ni matuƙa, don na san da irin namu gajari-gajari ta turo ba ballai a kula ba, amma wannan kowa sai rububin yi mata fatan alkhairi yake yi. Lokacin da su Sultan suka dawo ban kammala girki ba, kuma ba na jin na taɓa yin hakan in dai ba cuta nake ba, kafin su dawo na gama komai, amma yau sai da suka makara a islamiyya. Na dinga mita ni kaɗai ina cewa. "Da matar mai kuɗi ce ni ina za a samu wannan matsalar? Ina daga kwance kamar matan cikin group ɗinmu ina latsa waya masu aiki za su yi komai su gama, throughout suna online saboda ba sa aiki a gidajensu, amma ni hura gawayi ma kaɗai ya ishe ni, Allah ka kawo mini karshen wannan wahala da jarabar, don sai a yanzu na fuskanci auren talaka ba ƙaramin jidali ba ne." Na ƙarashe maganar kamar wadda take cikin wani mugun tsananin taskun rayuwar.......✍️ *Zeey Kumurya* [3/8, 1:34 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) 4. Bayan na yi wanka na fita na siyo kati, fita biyu kenan a yau ba tare da izinin mijina ba, abin da ban taɓa yi ba kenan a rayuwar aurena. Na yi sa'a ina dawowa ana kawo NEPA, da ma chajina ya yi ƙasa sosai wayar tana gaf da mutuwa. Sai da na saka ta a chaji sannan na loda katin na siya data, direct Instagram na hau na ɗora daga inda na tsaya. Nai ta ganin abubuwa kala-kala, sai da aka kira sallar la'asar sannan na tashi. Ina idarwa na koma kan wayar, amma wannan karon Whatsapp na shiga, replying messages na fara yi sannan na shiga group ɗinmu. Na tarar sun ƙara cika shi da hira kamar marasa aikin yi, haushi ne ya kama ni, don na tsani a yi hira ba na nan. Sallama na yi tare da gaishe da kowa da kowa, waɗanda suke online suka amsa mini tare da yi mini ƙorafin kwana biyu ba na leƙowa gidan, na ce abubuwa ne suka ɓoye ni. Cikin zolaya Maman Nasma ta mun voice da faɗin. "Ko dai Oga ya ɗauke ki kun tafi sabon honeymoon ne? Shi ya sa kika manta da mu saboda kina can kina ƙonewa." Yaƙe na yi na ba ta amsa da faɗin. "Ba haka ba ne." A raina kuwa na ce, 'Wannan ai sai mazajenku masu zuciyar yi.' Daga nan na yi sama na fara bitar chats ɗinsu. Na ga an yi maganar za a yi taro, tare da shawarwarin yadda taron zai kasance. Ƙarshe dai an yanke shawarar za a haɗa kuɗi a yi abinci sannan za a fitar da anko, kuma har mayafi duk iri ɗaya suke so a saka. Inda za a yi taron kuma a gidan ɗaya cikin admin ne. Majority sun yi amanna da wannan shawarar, don haka sai aka bar ta a matsaya. Aka yanke kuɗin da za a bayar 5k, sai kuma atamfa anjima za a turo wadda za a yi tare da price ɗinta ita da mayafi. Yadda kowa ya aminta da abun da murnar taron da suke na san maganar ba ta wasa ba ce. Ban da zaɓi ni ma haka na nuna amincewata tare da fatan Allah ya nuna mana lokacin. Sai da daddare da Abban Sultan ya dawo na samu damar yin karatun Alkur'ani, da ma kusan kullum sai mun yi a tare kafin mu kwanta, da rana kuma duk Sallar da na yi ba na tashi sai na karanta ko da shafi biyar ne, amma yau ko buɗe Alkur'anin ban yi ba, saboda duk kusan wunin nawa akan waya na ƙarar da shi. *One week later* Zaune nake a tsakar gida na yi tagumi ina tunanin inda zan samo kuɗin atamfar ankon taron group ɗinmu, atamfar 12k ce, sai kuɗin ɗinki da na mayafi, ga takalmi da jaka duk ina son na je da sababbi masu tsada, yadda zan fito cas da ni kamar kowa don kar a raina ni. A kullum idan Anas zai fita yana ajiye mini Naira ɗari ya ce ko zan ji sha'awar wani abun na siya, ko in an kawo talla, saboda ba ya ba ni kuɗin cefane, komai shi yake siyowa, hatta kayan miya, daddawa, kuka da kanwa. To ita nake tarawa idan ina buƙatar wani abun na siya ba sai na tambaye shi ba, duk haka sai na daɗe ban siya abu da kuɗin ba, don ko unguwa zan je yana ba ni kuɗin mota, in haihuwa aka yi ko biki a dangi yana ba ni abin da zan kai na gudunmawa daidai ƙarfinsa. Ganin ƴan group ɗinmu kowa na tura kuɗinsa ya sa a cikin kuɗin da nake da shi dubu bakwai da wani abu na je p.o.s ba tare da sanin Abban Sultan ba na ba da aka tura mini, sauran da ya rage kuma duk na ƙarar da shi a siyan data, don wuni nake a Instagram ina kalle-kalle, hakan ya sa wayata ta ƙara rakwaɓewa, rashin riƙon chajinta ya ƙaru saboda yawan caji, da ya ƙare zan jona idan akwai NEPA, idan babu kuma sai na miƙa ta gurin masu chaji. Yanke shawara na yi zan tuntuɓi Abban Sultan yau da batun, taron yana ƙara matsowa kar na je lokaci ƙure don a tsayar da date ƙarshen watan da muke ciki. Ni kuma na ƙudurce wa raina duk runtsi duk wuya sai na yi ankon na kuma je taron, saboda har wanda ba ƴan Kano ba ma za su zo, bare ni da nake cikinsa, a tsarina har waya nake son canzawa kafin lokacin, gudun kar na je da ta hannuna a raina ni. Bayan ya dawo mun gama komai yara sun yi bacci na tunkare shi da maganar kaina tsaye na ce. "Abban Sufyan bikin ƙawar nan tawa fa Naja za a yi." Na san in na ce masa taron group ne ba zai taɓa bari na, na je ba. Da fara'a ya ce. "Masha Allah, Naja lokaci ya yi kenan? Allah ya sanya alkhairi, yaushe ne?" Na ce. "Ƙarshen watan nan ne, shi ya sa ma na ce bari na sanar maka, don an fitar da anko tuntuni, kuma mai ɗan tsada ce atamfar." Murmushi ya yi ya ce. "Ubangiji zai kawo yadda za a yi, ba za ta gagara ba in sha Allahu, ai Naja mutum ce mai zumunci kuma mai yi, don haka dole mu rama wa kura aniyarta." Na ce. "Haka ne kam." Ya ce. "Nawa ce atamfar?" Gyara zama na yi na fara yi masa lissafi. "Atamfar 12k ce, sai kuɗin ɗinki don mai kyau nake so a mun 5k, sai mayafi da jaka da takalmi, sabbi nake son sakawa kuma masu ɗan kyau, na tambaya kowane six-six thousand ne, sai casual make up da zan yi, amma ita ban san kuɗinta ba sai na tambayo. Sannan kuma ina son ka canza mini waya kafin ranar bikin, tawa duk ta rakwaɓe ta zama jagwal." Wani irin kallo na ga ya bi ni da shi da na kasa tantance ko na mene ne, wajen 2 minutes kafin ya numfasa ya ce. "Hafsah! Kin san lissafin da kika mun kuwa? Kusan 100k fa tunda yanzu wayoyi tsada suke yi, ko kin manta waye ni da sana'ar da nake?" Ɓata fuska na yi na ce. "Na sani, kuma na san ba ka rasa kuɗin da za ka yi mini duk abubuwan da na ce ba." Ya ce. "Haka ne, tabbas ban rasa ba, amma na rasa wadda zan ɗauko na ba ki, ki yi wannan buƙatun, domin wadatata ba ta kai haka ba, ke ma kin sani. Na yi mamakin wannan lissafin naki matuƙa da gaske, domin ba ki taɓa zuwar mini da buƙata mai girman wannan ba." Na ce. "Kamawa ta yi yanzun ma na zo maka da itan, ka san wace Naja a gurina da irin abubuwan da ta yi mini, lokacin bikinmu wacce hidima ce ba ta yi da jikinta da aljihunta ba?" Girgiza kai ya yi ya ce. "Na sani, ita ma kuma in sha Allah ba za mu ƙi yi mata ba, amma daidai ƙarfinmu, zan siya miki atamfa na ba ki kuɗin ɗinki dubu uku, takalmi da jaka da mayafi kuma ki yi amfani da naki na da." Cikin takaici na dube shi na ce. "Yanzu kana da kuɗin amma ba za ka siya mini ba?" Ya ce. "Eh, kuɗina na siyan abincin da za mu ci ne da sauran buƙatu, ga Sallah ta kusa, term ya zo ƙarshe zan biya kuɗin makarantar su Sultan, both boko da islamiyya. Ban san ki da kafiya da naci ba, kar ki koya a yanzu please." Girgiza kai na yi na ce. "Taɓ!" Tare da tashi na fice daga ɗakin. Parlour na je na kwanta akan kujerara zuciyata cike da baƙinciki, kusan matan group ɗinmu duka sun gama siyan komai na fitar taron, kuma kowacce cewa take mijinta ne ya siya mata, amma ni nawa mijin kamar a kansa aka ƙare fatara da tsiya ya ce ba zai iya ba. Tsaki na ja tare da ayyana irin kalolin rashin mutuncin da zan fara shuka masa, matuƙar ya dage da gaske ba zai ba ni kuɗaɗen nan ba. A parlour na kwana, abin da ba mu taɓa yi ba kenan wato raba shimfiɗa don mun samu saɓani, na kuma san ba ya son hakan shi ya sa na yi da gayya. Bayan Sallar Asuba ya same ni a inda na yi Sallah ya ce. "Yanzu dan na ce ba zan yi miki abin da ban da halin yi ba, shi ne kika kwana a nan? Mun samu saɓani kala-kala wanda suka fi wannan amma ba ki taɓa haka ba sai yau, me ya sa Hafsah? Me ya sa kike ɗauko wasu halaye da ban san ki da su kike yi? A Kwanakin nan gabaɗaya na daina gane kanki, duk kin canza, hatta kula da yaranki ma duk kin rage, mene matsalar ne?" Banza na yi da shi na ƙara haɗe raina kamar ban taɓa dariya ba, ina jin takaicin yadda a kodayaushe yake nuna ya damu da damuwata, amma kuma ba zai iya fitar da ni kunya ba. "Magana fa nake miki." "Babu komai." Na ba shi amsa ciki-ciki. "Amma kin san ba na san magana a dunƙule ko? Ina tambayar ki kina cewa babu komai, alhalin kuma da akwai." Yadda ya yi maganar na gane ya fara fusata, hakan bai sa na sakko ba, don da ma abin da nake so kenan na ɓata masa rai. Bai ƙara magana ba ya fice ya bar mini parlour'n. Na bi shi da harara tare da taɓe baki, don na san ba iya dogon fushi zai yi da ni ba, har inda nake zai zo ya same ni ya rarrashe ni......✍️ *Zeey Kumurya* [3/8, 1:36 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) 5. *BRIGHT PENS...* _suna mara ba da masu buƙatar a tallata musu kasuwancinsu, masu siyar da turarruka, kayan sawa, magani komai da komai, cikin sauƙi za a tallata musu a cikin duka littafan guda uku🤙🏼 *CUTARWA, MUNAFUKIN MIJI, YI WA KAI*_ Tsari👯🏻‍♀️ Duk page ɗaya 200 Duka littafin kuma 600 Shafi biyar a littafi ɗaya 1000 A littafai uku kuma 3000 Domin ƙarfin bayani sai a yi wa wannan number magana 08164069385🤙🏼👯🏻‍♀️🫶🫶🏼 Shi ya tafasa ruwan zafi suka sha tea da bread, ko tsinke ban ɗauke ba har ya dawo daga kai su Sultan school ya karya ya ɗauraye cups ɗin da suka ɓata ya gyara gurin. 300 ya ajiye mini ya ce idan mai kifi ya kawo na siya na saka a miya, ga kayan miya can ya taho da shi ya ajiye a kitchen. Motsi ban yi ba balle na tanka masa har ya fice daga gidan. Ranar haka muka ƙara kwana kowa zuciyarsa babu daɗi, don da ya dawo ko sannu da zuwa ban yi masa ba, na dai yi girki saboda cikina da ƴaƴana. A haka kwanaki uku suka shuɗe babu wata jituwa a tsakaninmu, duk yadda ya so mu sulhunta ni kuma na ƙi, magana dubu in zai yi ba zan tanka ba, yara ma idan yana nan ba na sakar musu fuska, idan suka ishe ni da magana na daka musu tsawa na hantare su. Hakan ba ƙaramin ɓata masa rai yake yi ba, kuma ina yi ne duk dan na takale shi amma ba ya kula ni. Makwanci kuma tuni na raba mana da ma, tun ranar a parlour nake kwana ko a ɗakin su Sultan. Yau ya siyo mana kayan abinci da sabulun wanka da na wanki, ya haɗo da wani turare da ya san ina so, ya kawo mini har gabana ya ajiye, amma na ƙi ko ɗaga kai na kalle shi bare na ce na gode. Kasancewar Friday ce su Sultan suna gida, shi kuma da ma idan ya dawo daga masallaci ba ya kuma fita, zai zauna mu yi karatu ko hira ko mu fita unguwa tare. Ina ɗakin su Sultan a kwance ina kallon haɗaɗɗun girke-girken da aka turo a group ɗinmu, da yake Juma'a ce majority abinciccikan gargajiya suka yi, ban da haɗiyar yawu babu abin da nake yi, saboda kusan kowanne da zuƙu-zuƙun nama a kansa. "Garin daɗi na nesa." Na faɗa kamar zan fashe da kuka, dafadukar da na yi yau ce ta faɗo mini a rai, wadda ba ta da maraba da ta gidan bikin ƙauye a gurina. Tsaki na ja na tashi zaune tare da ajiye wayar hannuna. Duk wani abun gayu da abinci da ake turawa ni ban taɓa turawa ba, ina tsoron kar hakan ya sa su gane talaka nake aure su raina ni. Kowa yana taɓuka abun arziƙi a group ɗin amma ban da ni, komai ni ce koma baya. Ga shi an san ni sosai, ina daga cikin mutum biyar da suka fi kowa magana a gidan, shi ya sa ko daɗewa na yi ban hau online ba sai su yi ta cikiya ta, a yanzu ma sai da Maman Nasma da Aunty Billy mai group ɗin suka yi tagging ɗina, suka ce ni rowar abincin nake musu ne da ban turo nawa ba? Ƙaryar na je unguwa na yi musu. Tagumi na yi na fara tunanin ko tashi zan yi na yi dambu ne na tura musu? Tunda ina da gyaɗa da zogalen da ya siyo ɗazu, saboda yana son miyar zogale shi ya sa duk lokacin da zai siyo kayan abinci sai ya haɗo da shi. Murmushi na yi na miƙe ina faɗin. "Haka za a yi." Duk da ba a nan gizo yake saƙar ba, tunda ban da wayar da zan ɗauki hoton dambun ya fito ya yi tar kamar nasu, da haɗaɗɗun food flak's ɗin da zan zuba irin nasu, kuma su akan dinning suke jerawa su ɗauki hoto su turo, ni kuwa gidana ko tiles babu sai ledar tsakar ɗaki. Gwauron numfashi na ja na koma na zauna saboda tunawa da na yi shinkafar da zan yi amfani da ita ma ita kanta sai na yi zaman tsincewa, ba kamar su da sai dai kawai su saka abu su kamfata a cikin buhu su wanke su dafa ba. Takaici goma ashirin da hamsin duk suka cika mini zuciya. Tsabar tunanin ranar da mafarkina zai zama gaskiya ban san Sultan ya shigo ɗakin yana ta sallama ba sai da ya taɓa ni. A fusace na doka masa tsawa tare da faɗin. "Mene ne?" A firgice ya ɗan ja baya idanunsa cike da ƙwalla ya ce. "Abba ne ya ce ki shirya mu je gidan Kawu." Tsaki na ja na ce. "Ka ce masa bana jin daɗi." Yadda yaron ya yi sororo yana kallo na cikin hawaye sai jikina na fara yin sanyi, na ji kamar na zubar da makaman yaƙina na haƙura da batun zuwa taron gabaɗaya, na rungumi ƴaƴana da mijina kawai mu koma rayuwarmu kamar da. Janyo shi na yi jikina cikin sanyin murya na ce. "Kar ka yi kuka yaron kirki, I'm sorry na yi maka tsawa." Cikin kuka ya ce. "Mamy kin daina son mu yanzu, kullum sai dai ki yi ta yi mana faɗa da tsawa." Kansa na shafa na ce. "Ai uwa ba ta taɓa daina son ɗanta har abada my son." Bai kuma magana ba har na share masa hawayen fuskarsa, ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Kin daina yi mana faɗa ko?" Ɗaga masa kai na yi ina murmushin da suka kwana biyu ba su gan shi a fuskata ba. Ta window na hango Abban Sultan tsaye yana kallon mu, ɗauke kai na yi tare da ture Sultan daga jikina. Fita yaron ya yi shi kuma ya shigo, muryarsa da alamun maɗaukakin ɓacin rai ya ce. "Duk abin da za ki yi ya tsaya iya kaina Hafsah, amma ban da ƴaƴana, ba za ki tusa musu damuwa a cikin zuciya tun suna ƙanana ba." Haɗe rai na yi sosai na ce. "Ai ni ba ƴa ba ce da kai kake cusa mini damuwar." "Me nake miki? Me na rage ki da shi a zamanmu?" Ya tambaya a kaushashe. Ɗage kafaɗa na yi tare da taɓe baki ban ce komai ba. "Tambayar ki nake yi fa." Numfashi na sauke na ce. "Babu komai." A fusace ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya fasa ya juya ya fita, na raka shi da harara. Wayata na janyo na kunna data na ɗora daga inda na tsaya, hirar taron da za mu yi kawai ake yi a group ɗinmu, hakan ya ƙara dugunzuma hankalina, domin ranakun taron da suka rage ba su fi goma ba, ga shi abubuwan da nake yi ya sa ba mu ƙara zancen ƙaryar bikin Naja da na cewa Abban Sultan za a yi ba, bare ya ba ni ko iya kuɗin da ya alƙawarta ne, har yanzu bayan 5k ɗin taron da na tura ban ƙara wani shiri akai ba, saboda ba ni da ko sisi. Na ja tsaki ya fi cikin kwando na rashin mafita. Bayan Magriba ina zaune a parlour ina chatting da ƙawayena na ga messages suna ta shigowa na group ɗinmu na *Zumuncinmu*, da sauri na shiga group ɗin don ganin abin da ake tattaunawa akai. Da message ɗin wata Maman Ayman na fara cin karo, ta turo video na wata tsaleliyar waya a cikin kwalinta kamfanin iphone. Ban san lokacin da na tashi zaune daga kwancen da nake ba saboda tafiya da ni da wayar ta yi. Babu abin da ya fi jan hankalina sama da cewar da ta yi mijinta ne ya siya mata saboda yadda ta ci burin taron da za mu yi, don ta je da sabuwar waya ta sha pictures. Ci gaba da bin chat ɗinsu na yi ina karantawa da saurarar voice note, congrats akai ta yi mata, daga baya kuma aka koma maganar kuɗin wayar, wanda ba ƙaramin gigita ni suka yi ba saboda yawan su da na ji. 'Wayar kawai aka siya da waɗannan maƙudan kuɗin?' Na tambayi kaina a kiɗime. Ban kai ga samun amsa ba na ƙara cin karo da wani abun da ya ruɗa zuciyata, Maman Nasma ce ita kuma ta turo tsaleliyar mota ta ce mijinta ya siya mata a yau ɗin nan. Hannuna har rawa yake yi gurin yin zooming ɗin motar yadda zan fi ganin ta da kyau. Ko a kan titi ban taɓa ganin motar da ta tafi da imanina irinta ba. Na kwashe mintunan da ban san adadinsu ba ina aikin kallon mota da waya, sannan na haƙura ba don na gaji ba na yi musu fatan alkhairi kamar kowa. Ina ƙoƙarin fita daga group ɗin na ga Admin ta yi tagging ɗina ta ce. "Maman Sultan ke kaɗai ce ba ki siya atamfa ba fa har yanzu, ga shi lokacin abun yana ta gabatowa, kar ki rasa ɗinki fa." Wata matsananciyar kunya ce ta lulluɓe ni, lokaci ɗaya na ji gumi ya fara tsatstsafo mini kamar sabuwar ɓarauniyar da aka kama dumu-dumu tana sata, ga shi na rasa amsar da zan ba ta. Ina nan zaune kamar an dasa dutse na ga Maman Nasmah ta ba ta amsa da faɗin. "Sorry Admin, account ɗinta ne ya samu matsala shi ya sa ba ta turo ba, ta faɗa mini da muka yi waya ɗazu. Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke ganin abin da ta ce, ko kusa tunanin faɗar hakan bai zo mini ba, to account ɗin ma ba ni da shi, ban san ya abubuwan suke ba bare na shirya maganar da za ta saka a yarda. Fita na yi daga cikin group ɗin ban ce komai ba, ina ƙoƙarin barin Whatsapp ɗin gabaɗaya na ga Maman Nasmah ta mini magana ta pc, buɗewa na yi na ga ta ce ta tura kudin atamfata, na bar shi ba sai na biya ba. Wani irin farinciki da murna ne suka lulluɓe ni, ban san lokacin da na yi mata voice note cikin rawar jiki na dinga kwarara mata godiya ba, na manta sha'af ni ma pretending nake ni matar mai kuɗi ce kamar su, reply ɗin da ta yi mini da faɗin. "Mene abin godiya akan 15k Maman Sultan? Kamar wadda na ba wa 15 millions?" Shi ya dawo da ni cikin nutsuwata daga gigicewar murnar da na yi. Takaici ne ya lulluɓe ni na bayar da kaina da na yi, don duk wanda ya saurari voice ɗin da na yi mata zai gane ba ƙaramar ruɗewar farinciki na yi ba. Nuna mata na yi ai shi alkhairi ba ya kaɗan, don haka dole na yi murna, daga nan na kashe data ina jin zuciyata cikin yanayi biyu, na farincikin biya mini kuɗin atamfar da Maman Nasmah ta yi da kuma fargabar Allah ya sa kar abin da na yi ya sa ta gane ni matar talaka ce. Fitowar Abban Sultan daga ɗaki ya katse mini tunanin da nake yi, ban ko motsa ba bare na nuna na san da wanzuwar shi a gurin har ya zauna a kujerar da take fuskanta ta. "Magana na zo mu yi Hafsah." Na ji ya faɗa ba yabo fallasa. Kai kawai na ɗaga na kalle shi ban ce komai ba. Bai damu ba don ban ga alamar hakan a fuskarsa ba ya ce. "Tun shekaran jiya nake ta son na ba ki kuɗin da kika ce za ki yi amfani da su a bikin Naja, amma ganin kin ƙi ba ni fuskar ma da za mu yi magana ya sa kawai na kira ta na ce ta tura mini account number ɗinta na tura mata kuɗin ankon sai ta bayar a kawo miki, amma sai na ji saɓanin abin da kika faɗa mini daga gare ta, ta tabbatar mini babu wani bikinta da za a yi. Hafsah me za ki yi da kuɗi da har kika zaɓi yi mini ƙarya don na ba ki? Abin da ba ki taɓa yi mini ba, me na rage ki da shi a zaman mu?" Ya ƙarashe maganar muryarsa na bayyana fusatar da ya yi da abubuwana. Da sauri na ɗaga kai na kalle shi, wata irin kunya da takaici masu tsanani ne suka lulluɓe ni, kamar na fasa ihu saboda jin ya gano ƙarya da na yi masa. Duk yadda na so ɓoye halin da nake ciki don kar ya gane amma na kasa, haɗe rai na yi tare da ƙoƙarin yin pretending ɗin ni gaskiya na faɗa masa, ɗaga mini hannu ya yi fuskarsa ɗauke da madaukakin ɓacin ran da na jima ban gani a tattare shi ba ya ce. "Don Allah! Na haɗa ki da girman Allah ki faɗa mini Gaskiyar abin da yake damun ki Hafsah, ki faɗa mini mene matsalar da ta saka kika aro wasu sabbin halayen da ba naki ba kike aikatawa, wanda ba za su amfani rayuwarki da komai ba sai dai ma su kai ki ga hallaka? Kin canza mini kin canza wa ƴaƴanki, kin daina yi musu walwala, girki sai kin ga dama kike yi, haƙƙina kuwa an kusa sati rabon da ki ba ni, kuma da iliminki kin san hakan ba daidai ba ne, ba ki da abokin hira a kodayaushe yanzu sai wayarki, na zura miki ido na ga iya gudun ruwanki amma na ga abin naki ba na ƙare ba ne, don haka yanzu na zo masalaha nake nema, don Allah ki yi haƙuri da ko ma mene ne ki zo mu koma rayuwarmu kamar da, mai cike da farinciki da ƙaunar juna." Ya ƙarashe maganar tare da matsowa daf da ni ya kama hannuna a cikin nasa ya fara murzawa, ina jin sassanyar ajiyar zuciyar da ya sauke. Ban ce komai ba sai ƙasa da na yi da kaina, bakinsa a daidai satin kunnena cikin sassanyar murya ya ce. "Please my love! Ko don su Sultan ba don ni ba." Ban san me ya ba na ji jikina ya yi wani irin yi mini sanyi ba, kai kawai na ɗaga masa don na kasa sarrafa harshena gurin furuci. Murmushi ya yi tare da rungume ni a ƙirjinsa ya ce. "Na gode sosai Ummu Sultan ɗita." A hankali na motsa leɓɓena na ce "Ni ma na gode." Ban gama rufe su ba ya ɗora bakinsa a kansu, kiran sallar isha'i ya sa ya sake ni ya tashi, har lokacin murmushi yake wanda yake bayyana tsananin farincikin da yake ciki, duk da gangar jikinsa ta daɗe da alamta mini hakan, ta hanyar yadda ya dinga sakin ajiyar zuciya da abubuwan da ya yi mini cikin rawar jiki. "Zan je masallaci, ki yi mini tanadi kafin na dawo." Ya faɗa tare da ficewa ba tare da ya jira amsa ta ba. Dogon numfashi na ja na sauke cikin wani irin yanayi da ban san ya zan fasalta shi ba, ina son mijina sosai so mai tsanani, kamar yadda na san bayan mahaifana babu mai so na sama da shi a duniyar nan. Yadda ya zauna a gabana da farko cikin ɓacin rai kawai na tuno, amma cikin lokaci kaɗan ya haƙura ba tare da na ba shi haƙuri ba, ya mayar da laifin kansa duk da tarin wanda na yi masa, ya ba ni haƙuri a madadin ni na ba shi, ƙaryar da na yi masa ma da ya fahimci na ji kunya sai ya bar maganar. Anya kuwa irin mijina suna da yawa a duniya? Ba na jin akwai matar da za ta fi ni dacen miji mai kulawa da nuna tsantsar soyayya a zamanin nan, ga shi da tarin ilimin addini da aiki da shi, a kodayaushe shi mai ƙoƙarin ganin ya kyautata mana ne. 'Da ya zo a mai kuɗi da sai jin daɗi da farincikinmu ya ninka haka.' Wani sashi na zuciyata ya ce mini haka. Gyaɗa kai na yi kamar mai magana da wani na ce. "Tabbas haka ne, domin kuwa kuɗi shi ne kaso ma fi rinjaye na jin daɗin rayuwa." Tunanin kar a ɗauke wuta ga wayata babu chaji ya sa na miƙe na soka, sannan na fita waje don yin alwala. Ina kan darduma suka dawo shi da su Sultan, da gudu suka shigo ɗakin Sufyan ya faɗa kan cinyata yana faɗin. "Mami mun dawo." Kansa na shafa na ce. "Ka kusa karya mini cinya Babana, ko kai ba ka san ka girma ba ne yanzu?" "Ta ina zai sani tun da kin ƙi yi masa ƙani?" Abban Sultan da ke tsaye yana kallon mu hannunsa harɗe a ƙirjinsa ya faɗi haka. Kallon shi na yi na juya masa ido na ce. "Ai daga kai ne." Ya ce. "Ko?" Na gyaɗa masa kai kawai. Murmushinsa ya yi mai kyau bai ce komai ba. Shi ya yi wa Sufyan wanka bayan mun ci abinci, ya kwantar da su da wuri tun kafin lokacin da suka saba kwanciya. Duk wani abu da ya kamata na yi a lokacin shi ya yi, ni dai ina zaune ina ta sana'ar tawa wato tunani. A haka ya dawo ɗakin ya same ni, bayan ya zauna a kusa da ni ya dube ni a tsanake ya ce. "Tun ɗazu na lura da yanayinki Hafsah kamar kina cikin damuwa sakamakon abin da na faɗa miki, ko kuma kina jin kunyar abin da kika aitata. To in dai ni ne komai ya wuce, ba zan ƙara taho da maganar ba in sha Allah, ki kwantar da hankalinki ki saki jikinki mu koma kamar da, kuɗaɗen da kika tambaye ni kuma duk da ban san me za ki yi da su ba, amma na san tunda kika tambaya kina da buƙatar su, don haka da yardar Allah jibi zan ba ki 5k, sai ki yi amfanin da za ki yi da ita." Cikin farincikin samun kuɗin ɗinkin da nake ta tunanin ta yadda zan samu idan Maman Nasmah ta aiko mini da atamfar na saki ajiyar zuciya. Fuskata ɗauke da yalwataccen murmushin da na daɗe ban yi ba na ce. "Na gode sosai mijina." Yana murmushin shi ma ya ce. "Babu komai ƴar aljannatah, duk abin da kike so a duniyar nan ba zan taɓa ƙin yi miki ba matuƙar bai fi ƙarfina ba." Daga haka muka shiga fagen da muka daɗe rabon mu da shi, sai a lokacin na gane ni ma ba ƙaramar kewar shi na yi ba. Bayan komai ya lafa ya yi bacci na ji ni ba zan iya baccin ba idan ban kunna data na ga halin da group ɗinmu yake ciki ba da abubuwan da aka tattauna, ina son group ɗin sosai, ba ma ni kaɗai ba, duk wanda yake cikinsa yana mugun son shi, saboda gida ne mai matuƙar shiga rai, kullum cikin hira muke kamar ƴan'uwan juna ba haɗuwar media ba. A hankali na zare jikina daga na Anas na sauka daga kan gadon na fita parlour na ɗauki wayata, zama na yi a kan kujera na kunna data. Messages na gani sama da goma Maman Nasmah ta yi mini, da sauri na shiga na fara dubawa. Hoton Atamfa ta turo mini ta ce ga shi har ta je gidan admin ta karɓo mun, sai kuma hotunan da suka yi a gidan admin ɗin da video. Cikin rawar jiki na buɗe na shiga kalla. Sai da zuciyata ta yi wani zillo tsabar haɗuwa da tsaruwar parlour'n da aka yi musu wani video, kusan gabaɗaya parlour'n sai da ya fito, saboda juyin da Maman Nasmah take yi da wayar tana cewa "Yau dai ga ni a gidan Aunty Billy Admin." Cikin dariya. Parlour ne wanda ya gama tsaruwa tun daga kan ginin shi da irin ƙawar da aka yi masa, da kuma kayan alatun da aka wadata shi da su, wanda kallon su kaɗai ma ya isa ya saka mutum farinciki. Wani ɗan ƙundulen abu da ya tsaya mini a maƙoshi na haɗiye tare da ɗaga kaina na bi akurkin parlourna da kallo kasancewar da akwai NEPA har lokacin, hakan ya sa na ji wani abu mai ɗaci yana yi mini yawo a ƙirji. "Dole ne fa duk rintse duk wuya ni ma na fara rayuwa a irin waɗannan tafka-tafkan gidajen nan kusa, ko ta halin ƙaƙa." Na faɗa a fili kamar zan rusa kuka. Sauran hotunan na ci gaba da kallo, har da wanda suka yi a farfajiyar gidan, iya motocin da suke fito ta cikin hoton sun kai shida a cikin wata ƴar rumfa, ga wasu irin fitulu da suka haskaka gurin tamkar rana. Abayoyi duka a jikinsu, wanda ko ba a faɗa ba na san masu tsada ne, ga shi sun dace da jikinsu ɗan kuɓul irin na masu hannu da shin. Voice ɗinta wanda shi ne last a cikin messages ɗin da ta mun ba ƙaramin razana zuciyata ya yi ba. Idanuna na waro waje kamar zan zubar da su a ƙasa na ƙara maimaita saurara don jin ko kunnena ne bai ji mini daidai ba, amma still abin da na ji da farko shi ya ƙara mamaye masarrafar jina...✍️ *Zeey Kumurya ✍️* [3/8, 1:36 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) 6. Gwauron numfashi na ja na sauke lokacin da nake ƙara saurarar voice ɗin a karo na uku. "Maman Sultan ki ba ni address ɗin gidanki zan kawo miki atamfar taki da kaina." Shi ne abin da kunnuwana suke jiye mini Maman Nasmah ta faɗa. Girgiza kai na yi na ce. "Taɓ! Karen hauka ne ya cize ni da zan bari ki zo wannan akurkin gidan nawa da ko mai aikinki na san gidansu ya fi shi kyau nesa ba kusa ba." Tunanin ƙaryar da zan sharara mata kawai na fara yi. Ban kai ga yi mata reply ba na ga ta ce ko kuma na turo Driverna ko mai delivery ya karɓar mini. Ajiyar zuciya na sauke cikin jin daɗi, duk da hakan ma akwai yiyuwar asirina ya iya tonuwa, tunda ban da Driver bare wani mai delivery. Reply na yi mata da duk yadda ta yi daidai ne. Ta ce tom shikenan na turo address ɗin nawa kawai ta ba wa drivernta ya kawo mini. Citson yatsa na yi na fara tunanin ƙaryar da zan shirga mata. 'Ki ba ta address ɗin gidan Shamsiyya kawai, sai ta tura drivern nata can a matsayin nan ne gidanki.' Wani sashe na zuciyata ya ba ni wannan shawarar. Murmushi na yi tare da haɗe yatsuna biyu na ɗana na ce. "Yes!" Saboda Gidan Shamsiyya babba ne sosai shi ma, duk da a yanda nake hasashen gidajen ƴan group ɗinmu ba zai kai su ba, amma babu laifi, ya fi dai wannan akurkin namu. Jikina na mazari saboda kar Maman Nasmah ta ga na daɗe ban yi mata reply ba na yi searching numbern Shamsiyya na tambaye ta tana gida gobe? Idan tana nan zan zo. Na yi sa'a tana online, kuma ina yi mata message ta ba ni amsa da. "Ayya ba na nan, mun yi tafiya Dubai da baban su Zuhura." Tagumi na yi cikin rashin jin daɗi na yi musu fatan dawowa lafiya, a raina na ce. 'Ku kuka yi auren jin daɗi Shamsiyya, mazajenku kullum cikin ɗaukar ku, ku tafi yawon shaƙatawa ƙasashen waje suke, mu kuwa namu ƙauye ma idan za a je a ga dangi sai an yi wata ana shirye-shirye da tara ɗan kuɗin mota. Saboda rashin zuciya, kowa yana fita ya nemi kuɗaɗe masu yawa amma ban da irin mazajenmu, da ba sa burin yin tarin arziƙin da za su zama hamshaƙai, sai dai ɗan wanda za a ci abinci a kwanta a makwanci duk munin shi da rashin kyan shi.' Tsaki na ja na koma chat ɗin Maman Nasmah na ce mata ba na nan mun yi tafiya Abuja sai jibi za mu dawo, amma zan ba ta address ɗin gidansu mai aikina ta aika akai a atamfar can, idan ɗan aiken ya je ya tura yaro ya ce ga shi a ba wa Salamatu. Na tura mata da address ɗin gidana a matsayin nan ne gidansu mai aikina. Ta ce tom shikenan babu damuwa. Kamar an sauke mini wani dutse mai nauyi da ya danne mini ƙirjina haka na ji, ganin na samun mafita, don haka kawai ba za ta zo ta ga gidana ta raina ni ba, in sha Allah sai mun koma tsamfatsetsen gida irin nasu kafin wata a group ɗin ta ƙara buƙatar zuwa gidana, saboda ba wannan ne karon farko da aka buƙata ba tunda na ce ni ma ƴar Kano ce. Mun ci gaba da chatting da Maman Nasmah, ta ce na tura mata numbern mai aikin tawa, kar drivern nata ya kasa gane kwatancen, idan ya kakare sai ya kira ta. Ƙaryar ba ta da waya na yi mata. Emogin mamaki ta tura mini tare da faɗin. "Haba Hajiya Hafsah, kamar ke a ce mai aikinki ba ta da waya? Gaskiya ki siya mata." Murmushin yaƙe na yi kamar tana gabana ta ce. "Na siya mata fa ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba tana siyarwa, kin san halin mutane marasa ƙarfi, da sun ji rashi ko mene nasu ɗauka suke su siyar." Ta ce. "Haka ne, amma dai ki ƙara siya mata ko don irin haka." Na ce. "in sha Allah, kawai da ma na bari ta ɗan jigatu ne saboda kar ta kuma siyarwa." Daga nan muka shiga hirar taron da za mu yi, ta tutturo mini agogo, ɗanƙareriyar sarƙa da ɗan'kunne na gold, haɗaɗɗen takalmi da rantsatstsiyar jakar da ta siya duka sababbi saboda taron ta ce ni ma na siya irinsu, mu yi komai iri ɗaya ranar. Jiya mijinta ya ba ta kuɗin ita ma duk ta siya. Tsam na yi a zaune ina rarraba ido, don na san ko gidan da muke zaune zan siyar kuɗinsa ba zai sai mini wannan kayan ba. Jikina a saɓule na ce mata zan siya in sha Allah, ba ta jira na tambaye ta ba ta turo mini price ɗin kowane. Kusan rikitowa na yi daga kan kujerar da nake kai saboda yawan kuɗin da na lissafa. Millions kusan biyar, a iya kayan sakawar rana ɗaya kawai. "Wanda ya ba da wannan kuɗin wanne irin kuɗi ne da shi, shi kuwa? Me yake yi yake samun kuɗi da Anas ba zai iya yi ba?" Na tambayi kaina a ruɗe. Zuciyata ce ta ba ni amsa da 'Rashin zuciya ne ya hana shi mana.' Dungurar da wayata na yi ina jin kamar na haushi bango tsabar takaicin irin mijin da na aura talaka. Da na san haka masu kuɗi suke hutawa da unguwar masu kuɗi nai ta zuwa da ina budurwa, da wani mai kuɗin ne zai gan ni ya aure, ni ma na yi rayuwar hutu da jin daɗi da kwanciyar hankali, na saka abin da nake so na ci wanda nake so a duk lokacin da na so. Dukan kaina na yi ina jin kamar na fashe da kuka. Miƙewa na yi ina tunanin abin da zan yi kafin ranar taron na samu kuɗin siyen abubuwa irin na Maman Nasmah ko da ba duka ba. A haka na koma ɗaki na dinga zarya, a ƙarshe na samu mafita biyu kafin na kwanta. Ta farko zan takura wa Anas akan ina buƙatar kuɗaɗe, ya je ya nemo mini a duk inda suke, ai su ma mazajen su Maman Nasman mutane ne kamar shi, kuma nema suke yi ba da kuɗin aka halicce su ba, don haka shi ma dole ya samo ya ba ni. Ta biyu kuma idan ya ƙi zan ce Shamsiyya ta ara mini duk abin da zan saka ranar, sai na cewa Maman Nasmah kawai gani na yi Abban Sultan ya siyo mini su. Da wannan tunanin na samu na iya bacci, duk da na raba dare kafin ya ɗauke ni. Washegari na tashi cikin farinciki da ɗokin kawo mini atamfar da za a yi, hakan ya sa na yi ayyukana na gida cikin walwala tare da Anas. Bayan su Sultan sun wuce tahfiz saboda weekend ne Abbansu ya yi wanka ya shirya cikin kayan da yake zuwa aikin fenti da su, sana'arsa da ma fentin ne, ranar da babu aiki kuma zaman shago yake yi wa ubangidansu. Yana ƙoƙarin fita ganin kiran da ake ta yi masa a waya na dube shi na ce. "Wai wa yake kiran ka ne?" Yana duba ƴar wayar tasa ya ce. "Su Halliru ne mana, kin san su idan za mu je aiki idan ban fito ba sun ta kira na kenan, dole su sai dai mu fita tare." Ba yabo ba fallasa na ce. "Tom shikenan sai ka dawo." Ya ce. "Za mu iya kaiwa bayan Magriba, saboda gidan da za mu yi aiki babba ne sosai, kuma duk da haka ba za mu gama a yau ba." Gyara zama na yi na ce. "Ku yi ta zuwa tafka-tafkan gidaje aiki, ba ya burge ku ne ku ji da ma ku ne kuke rayuwa a cikinsa?" Murmushi ya yi ya ce. "Ai babu wanda daula ba ta burgewa a duniyar nan, sai dai idan Ubangiji bai ba ka ba sai ka yi haƙuri ka gode masa, tare da fatan ya ba ka a lahira." Taɓe baki na yi yadda ba zai gane ba na ce. "Amma duk da haka ai za ku yi ta kallon gidan ku ce da ma ku ne a ciki ko?" Ya ce. "A'a, a saboda me? Kowa inda Ubangiji ya ajiye shi nan ya so ya gan shi fa, don wani inda kake shi kuma nan yake fatan da ma shi ne a gurin, ai mu sai dai kawai mu ce Alhamdullillah, tunda Ubangiji ya bar mu da lafiyarmu da za mu nemi kuɗinmu na halal ai ya ga yi mana komai." Kamar na rufe shi da duka tsabar takaici da baƙinciki, wato shi ko damun shi manyan gidajen ba sa yi bare ya yi burin gina su watarana, shi komai da an yi magana ya ce kaza-kaza shi sarkin tawakkali, to ai Allan da kansa ya ce tashi in taimake ka. Ban ƙara magana ba har ya fita, yana ta cewa yau babu rakiya ne na yi masa banza. Ƙarfe goma da mintuna na ɗora girki saboda kar su Safwan su dawo 12 ban gama abinci ba. Bayan na gama na gyara kitchen ɗin ina shirin yin wanka na ji ana knocking, ganin sha biyu da mintuna na san su Sultan ne suka dawo, da sauri na nufi ƙofar na buɗe ina faɗin. "Wannan bugun ƙof...." Maƙalewa maganar ta yi a inda ban sani ba saboda ganin wadda ko a mafarki na gan ta sai na gane ta, duk da ba mu taɓa haɗuwa a zahiri ba. Wani irin abu na ji yana yawo a cikin jinina dunƙule-dunƙule saboda tsanani mamaki, ruɗewa gami da razani. Lokaci ɗaya na ji kaina ya fara juyawa saboda matsananciyar ɗimautar da na shiga. "Maman Nasmah!" Na furta a fili tare da dafe ƙirjina, idanuwa gabaɗaya sun yo waje kamar za su faɗo ƙasa, tsabar firgici.........✍️ *Zeey Kumurya* [3/8, 1:37 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) 7. Murmushi ta sakar mini tare da faɗin. "Na'am." Ji na yi kamar babu sauran jini a jikina saboda jirin da yake kwasa ta, dafe bango na yi tare da cize leɓena cikin rashin mafita. 'Komai zai faru kar ki nuna mata ke ce wadda kuke chat, ki dage a matsayin ke mai aikinta ce kawai, tunda ba ta taɓa ganin ki ba ko a hoto.' Zuciyata ta ba ni wannan shawarar wadda na yi na'am da ita. 'To amma sunanta da kika ambata fa?' Wata zuciyar ta tambaye ni. Numfashi na sauke tare da ƙaƙaro murmushin yaƙe don kar ta gane da wani abu na ce. "Sannu da zuwa, mu shiga ciki ko?" Har lokacin fuskarta ɗauke da murmushi ta ce. "Toh." Sai a lokacin na lura da su Sultan da ke tsaye suna kallon mu, gabana ne ya faɗi don wanzuwar su a gidan tare da Maman Nasmah zai iya tona mini asiri, ban san lokacin da suka shigo ba, da tana ɗaki ma suka shigo maƙota zan tura su, har sai ta tafi sai na je na ɗauko su. Tsabar yadda ƙafata ta sage da ƙyar na iya ɗaga ta na bi bayansu, don har sun yi gaba ita da su Sultan. Mayar da ƙofar gidan na yi na rufe bayan na gama leƙen rantsatstsiyar motar da nake da tabbacin a cikinta ta zo, don ita ce ma wadda ta turo a group mijinta ya siya mata. Jikina a saɓule kamar zan fasa ihu na koma cikin gidan, na tarar da su tsaye a tsakar gida Sufyan yana nuna mata parlour yana cewa. "Nan ne inda Mami take kai baƙi, ki shiga." Kamar na janyo shi na rufe shi da duka haka na ji, na rasa mafita da abin yi, ga shi Maman Nasmah har yanzu ba ta ce komai da zai nuna ta gane ni ko ba ta gane ni ba. Ba don na so ba sai don ban da zaɓi na yi mata jagora zuwa cikin parlour'n. Gabaɗaya ƙamshinta mai daɗin shaƙa ya buɗaɗe gidan tun daga soro. Fuskarta a sake sosai muka gaisa, ko kaɗan ban ga alamar ƙyama ko raini a tattare da ita ba, hakan ya sa na ji zuciyata ta ɗan fara sanyi. Ga shi ta ja yarana sosai a jikinta, don Sufyan tunda ta zauna yake kan cinyarta. Ƙare mata kallo kawai nake ta ƙasan ido, fara ce tas kuma tana da ɗan jiki, maroon abaya ce a jikinta mai matuƙar kyau, ta yi rolling da mayafinta, yatsun hannunta guda ukun tsakiya kowanne sanye da zoben gold hagu da dama. Fatarta sai sheƙi take na zallar hutu da jin daɗi. Cikin lokaci ƙanƙani na tabbatar wa da kaina Maman Nasmah matar hamshaƙin mai kuɗin ce kamar yadda na daɗe ina hasashe. Ba don na gaji da kallon ta ba don ba ƙaramin kyau ta yi mini ba na miƙe na ce bari na kawo mata ruwa. Sosai ta burge ni, na ji da ma ni ce nake a matsayin da take. Kallon kaina na yi bayan na fito tsakar gida, zanin jikina duk ya yi baƙin gawayi, ga shi sai ƙaurin ledar da na hura wuta nake yi, gabaɗaya dai na yi kaca-kaca. "Wannan wacce irin baƙar rana ce a gare ni da ta zaɓi mu haɗu da Maman Nasmah a cikinta? Ya Allah idan mafarki nake ka sa na farka, me ya sa sai da nake a wannan hargitsen za mu haɗu?" Na faɗa a fili tare da ɗora hannuna akai, hawayen baƙinciki da takaici na zuba daga idona. Ban taɓa jin kunya matsananciya irin wannan ba a rayuwata. Kitchen na yi saurin nufa jin kamar za ta fito, abinci nake son zuba mata amma ina kunyar ba ta abin da na dafa, don taliyar Hausa ce da manja da yaji, sai salad da na yanka. "Bari na ɗauko kaya a mota." Na ji muryarta ta faɗi haka, saurin share hawayena na yi na ce. "To." Kafin ta dawo na shiga ɗakina na sauya kaya a gaggauce, wani lace na saka wanda Abban Sultan ya ɗinka mini sallar da ta wuce, shi ne ƙarshen ƙurewar adaka a cikin kayana. Na bulbula turare na ɗan yi ɗaurin ɗankwali mai kyau. Amma duk da haka da na fito sai na gan ni kamar almajira a kanta. Fahimtar tana jin zafi saboda babu nepa ya sa na ɗage labulen window da na ƙofa. Ta ba ni atamfar da wasu tarin kayayyaki a leda ta ce na ba wa yara, a ɗarare nake da ita, ko haɗa ido na kasa yarda mu yi. Ban taɓa sanin haka ƙarya take da kunya ba idan aka kama mutum sai a yau, duk da ita ba ta nuna mini komai ba, sai ma hira da take ta ja na, kuma ko da wasa ba ta kama sunana ba ko na su Sultan, kuma ba ta yi mini maganar group ɗinmu ba kwata-kwata balle na taron da za mu yi. Amma duk haka a ruɗe nake, Allah -Allah nake ta tafi ko na samu nutsuwa na yi tunanin mafita, tsabar rikicewa ko ruwa ban ba ta ba. Abinci da ma ba zan iya ba ta wanda na yi ba, saboda kar abin kunyar ya yi mini yawa. Tana kokarin tafiya na ji an buɗo ƙofar gidan an shigo, wata mummunar faɗuwar gaba ce na ji ta ziyarce ni, saboda na san Anas ne kawai yake da wannan ikon, idan kuwa shi ya dawo na shiga uku na kaɗe har ganyena. Domin ba zan so Maman Nasmah ta gan shi a matsayin mijina ba, abin kunyar sai ya yi mini yawa ai. "Ƴar aljannatah!" Na ji muryarsa da ba ta da maraba da saukar dalma a kan ƙirjina a wannan yanayin da nake ciki yana kira na." Ban amsa ba har ya yi ƙoƙarin shigowa ɗakin fuskarsa ɗauke da yalwataccen murmushi. Tun daga kansa har tafin ƙafarsa kalolin fenti ne kamar wanda ya yi birgima a cikinsu. Satar kallon Maman Nasmah na yi na ga ta ƙura masa ido. Na san a cikin ranta tana ta cewa wannan abin ne mijina? Na san ko almajirinta ya fi shi kyan gani, ga shi sana'arsa ta bayyana kanta a jikinsa, yanda ko mahaukaci ne ya shafa shi sai ya sani. 'Ni kam na ga ta kaina, yau ruwa ya ƙare wa ɗan kada.' Addu'a nake ta yi Ubangiji ya sa mafarki nake, don ganin Anas da ta yi ya fi zuwan gidan da yadda ta same ni saka ni a cikin tashin hankali. Na gama tsara ƙaryar da zan shirga mata bayan ta tafi, amma dawowar shi ta wargaza komai, domin ban ga uban abin da zan ce mata ta yarda ba kuma, tunda ta ga mijina da sana'ar yake. Duk yadda ya so control ɗin kaina kar na nuna komai amma na kasa, zuciyata cunkushe da baƙinciki na dube shi na ce. "Me ya dawo da kai?" Idanunsa a kaina yana mun wani irin kallo ya ce. "Tunaninki ne ya addabi zuciyata ya hana ta sukuni, fahimtar ba zan taɓa samun nutsuwa ba idan ban gan ki ba ya sa tilas na bar aikin na zo na gan ki na koma." Ya ƙarashe maganar tare da kashe mini ido. Wani irin ƙululun takaici ne ya ƙara cika ni, maganganunsa ko kaɗan ba su burge ni ba, kamar ya watsa mini garwashi haka na ji su. Harara kawai nake banka masa ƙasa-ƙasa lokacin da suke gaisawa da Maman Nasmah. Tsabar bayar da kai a tsakar gida ya zauna maimakon ya shiga ɗakin su Sultan ya ɓuya. Ƙwafa na yi a ciki-ciki na miƙe ina ƙaƙalo murmushi ganin Maman Nasmah ta miƙe ita ma, ƙoƙarin danne kukan da yake son kwace mini na yi na ce. "Har za ki tafi? Ki bari na gama abinci ki ci mana." Sai a lokacin na tuna ko ruwa ban kawo mata ba. Murmushi ta yi ta ce. "Babu komai wallahi, na gode ma a hakan." Ina gaba tana bi na a baya, har da rusunawarta da za ta yi wa Abban Sultan sallama. Ni kwa ko kallon shi ban yi ba, duk da ina jin shi yana mun magana. Har ƙofar gida na raka ta, na ga ashe tare da driver suke. Shi ya fito da sauri ya buɗe mata bayan motar ta shiga. A raina na ce. 'Kuɗi kenan, mai saka ai ta bauta maka ko da ba ka da sarauta.' Sai da suka bar layin na koma cikin gida bayan na saki ajiyar zuciya, ina cika ina batsewa na nufi kan Anas kamar zan fashe. Kafin na yi magana ya riga ni da faɗin. "Wace ce wannan?" "Ban sani ba." Na faɗa a zafafe kamar zan kai masa duka. Cikin mamaki ya ɗago yana kallo na baki buɗe. Kukan da yake ci na tun ɗazu na saki na ce. "Mene na dawowa yanzu bayan da ka ce sai Magriba? Kawai ka zo ka zubar mini da mutunci da ƙima a gabanta, jibi kayan jikinka da yadda kake, kowa sai ya san mijina fenti yake!" Miƙewa ya yi fuskarsa a haɗe ya ce. "Kunya kika ji don ta gan ni a haka Hafsah? Shi ne har da kuka?" Harara na zabga masa na ce. "Idan kunya ce kaɗai ma ai da sauƙi." Numfashi ya sauke ya ce. "A tunanina abin alfaharinki ne a gan ni a wajen neman halal ɗina ba haram ba, yanzu a misali a ce faɗowa gidan na yi da gudu ana bi na ana na yi mini ihun ɓarawo fa? Za ki so ta ga haka?" "Eh wallahi! In dai a cikin kyakkyawar shiga kake da ba za ta bayyana talaucinka sosai ba, idan ya so na ce mata sharri aka yi maka." Na faɗi haka ina ƙara rushewa da kuka tare da shigewa ɗaki, duk da ba na kallon shi amma na san bi na ya yi da na mujiya. Tsayawa Anas ya yi sakato kamar wani shashasha yana kallon ƙofar ɗakin kamar tana gurin, mamaki da al'ajabin Hafsah sun hana shi magana, ya rasa ma abin da zai ce mata. Ba ya jin tana cikin hayyacinta gaskiya, don waɗannan abubuwan ba halinta ba ne. Girgiza kai ya yi tare da kama haɓa ya ce. "Anya ba zan kira a yi mata roƙiyya ba kuwa? A gani ko aljanu ne suka shafar mini ita, don wannan lamuran nata sun wuce hankali." Bin bayanta ya yi don ƙara tabbatarwa da kansa koma mene ne yake damun matar tasa. Maman Nasmah tana shiga mota ta fashe da dariyar da take ta cin ta cikin rashin damuwa da kallon da drivernta yake mata, ba ƙaramin dauriya ta yi ba da ba ta ƙyaƙyace a gaban Hafsah ba. Ta daɗe da gano ita talaka ce, saboda in dai za a yi maganar wani abu na gayu ko masu kuɗi ba ta saka baki, kuma ta gwada ta da abubuwa da yawa da suka ƙara tabbatar mata da zargin ta. Amma duk da haka ba ta yi tunanin talaucin nata ya kai haka ba, don a lokacin da suka yi parking a ƙofar gidan ta kalli gidan da unguwar ta yarda gidan masu aiki ne, saboda ita a tarihin rayuwarta ma ba ta taɓa shigowa irin unguwannin nan ba, idan ta yi sa'a direbanta ya san unguwar sosai. Ta inda ta gane gidan Hafsah ne tun kafin ta shiga, su Sultan ta gani sun dawo daga makaranta, ta tambaye su sunansu suka faɗa mata, ta ce mamansu tana cikin gidan suka ce eh, kuma farkon sanin ta da Hafsah hoton Sufyan ne akan dp ɗinta, hakan ya sa tana ganin su ta gane su. Tana sane ta ƙi nuna wa Hafsah ta gane ta ko ba ta gane ta ba, ta bar ta a cikin duhu don ta ji idan sun yi chatting anjima me za ta ce mata. Dariya ta ƙara kwashewa da ita saboda tuno yadda Hafsah ta yi tsumu-tsumu kamar an tsoma kaza a ruwan zafi, tana lura da yadda take ta share zufa a goshinta, da dibibicewar da ta yi. Kasancewar Hafsah talaka ba zai saka ta rabu da ita ba, don haka kawai Allah ya haɗa jininsu, ta ji tana son ta. Amma a yau da ta gan ta a gidanta sai ta gane dalilin da ya sa ƙaddara ta haɗa su tun farko. Numfashi ta sauke tare da lumshe idonta tana tuno Anas da murmushin da ya yi wa Hafsah lokacin da ya shigo, irin namijin da ta rayu da burin samu mai cikar zati da kamala. Tun daga sallamar da ya yi kafin ta gan shi gabanta ya faɗi, da ta gan shi kuma sai komai ya kwance mata, ta kasa ɗauke idonta daga kansa. Babban abin da ya ƙara fizgar ta a kansa soyayyar da ta ga ya nuna wa Hafsah. Kashe idon da ya yi wa Hafsah da kallon da yake bin ta shi kuwa sai da ya saka tsigar jikinta ta tashi. To a hakan ma jikinsa duk da fenti ina ga ya kintsa ya yi fes? Ta san sai ta kusa zaucewa. Lafewa ta yi a jikin kujera tana hasaso ita yake yi wa wannan kallon, tabbas ta san sai ta kusa sumewa. A rayuwarta tana bala'in son namjin da ya iya soyayya da kulawa, amma ita nata mijin da shi da katako ba su da maraba, don tana iya yin watanni ma ba ta saka shi a idonta ko ta ji muryarsa ba. Amma in dai dukiya ce yana da ita har da ta hauka, a iya kuɗin da ya mallaka mata in za ta yi kyautar 10 million ko motsi ba za su yi ba, balle kuma shi uban gayyar. Ban da kadarori da ya mallaka mata. Ta gane Hafsah ba ta so ta ga mijinta ba, ita kuma ganin shi kawai da ta yi ba ƙaramin tsintar dami a kala ba ne a gurinta. Wata irin zazzafar soyayyar shi ce ta ji tana mamaye zuciyarta. Ta yi haƙurin zama da mijinta na shekara takwas, amma a wannan karon dole za ta rabu da shi, domin ba irin mu'amalar da take da sauran maza ta ji tana son yi da Anas ba, son shi take, so take su yi rayuwa a matsayin miji da mata, ko ta samu farinciki da cikar burinta a rayuwa ita ma. Kuma sannan ta bar mummunar hanyar da take kai, ta bin wasu mazan da aurenta bisa sahalewar mijinta, kasancewar shi ɗan luwaɗi da bokansa ya haramta masa mu'amla da mace sai dai namiji ɗan'uwansa. Kuɗaɗen da ta mallaka sun ishe su yin duk irin rayuwar da take so ita da Anas. Dogon numfashi ta ja ta sauke a karo na barkatai, matsaloli biyu ne za su yi mata katanga daga samun cikar burinta nan kusa, na farko ta a yadda za a yi ta samu kan Anas ya amince da ita, na biyu kuma yadda za ta raba su da Hafsah, don a matsanancin son shi da ya yi mata kamun farat ɗaya ba za ta iya sharing ɗinsa da wata ba, nata ita kaɗai take son ya zama har ƙarshen rayuwarta. Kuma ko mene za ta yi don ganin ta mallaki Anas, saboda ita kaɗai ta san me take ji a game da shi, daga lokacin da ƙwayar idonta ta sauka a kansa zuwa yanzu......✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:37 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) 8. Ina durƙushe na kifa kaina a jikin gado ina runtumar kuka kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwar uwarta na ji ya shigo, ƙara volume na yi ba tare da ɗago ba balle ya saka ran zan saurare shi. Ina jin shi yana zauna a gefen gado kusa da kaina. Matsawa na yi tare da ƙoƙarin tashi na bar ɗakin na ji ya ruƙo ni, ƙoƙarin ƙwacewa na yi amma ya nuna mini shi namiji ne, ya riƙe ni gam ya mayar da ni na zauna a fusace. Cikin taushin murya ya ce. "Ki yi shiru don Allah Hafsah mu yi magana, mene ne haka? Wannan kukan na mene?" Tsaki na ja na ce. "Don Allah, don darajar iyayenka ka ƙyale ni Anas, ba na son magana a yanzu." Ya ce. "Na ji zan ƙyale ki, amma don Allah ki bar wannan kukan da kike yi mara amfani, ko dan su Sultan da suke jin ki." Na ce. "To." Kawai, tare da share hawayena, duk da na san dole wasu sai sun zuɓo. Ni kaɗai na san halin baƙinciki da takaicin da nake ciki, kamar nai ta zunduma ihu haka nake ji. Babban tashin hankalina ban san me zai biyo baya ba a gurin Maman Nasmah da yadda ta zo ta gan ni, ina tsoron ta faɗa wa wasu ƴan group ɗinmu. Wunin yau gabaɗaya haka na yi shi sukuku, zuciyata a cunkushe da jin haushin Anas. Tun bayan da na dawo daga rakiyar Maman Nasmah na kashe wayata, har dare ban kunnata ba, duk da yadda zuciyata take ta azalzalata na kunna na ji me Maman Nasmah za ta ce mini, na ji matsayin da ta ajiye ni, na Salamatu mai aiki ko kuma Hafsah Maman Sultan. Tsabar abin duniya ya bi ya dame ni ko ruwa ban kai bakina ba. Hakan ya sa nake ji na wani iri kamar mai cuta, ƙirjina har zafi yake mini. Maman Nasmah kuwa bayan ta koma gidanta ta ci gaba da saƙawa da warwarar hanyar da za ta bi ta mallaki Anas, a ƙarshe ta yanke wasu shawarwari, abu na farko da za ta fara yi shi ne ta raba shi da Hafsah, na biyu kuma za ta saka a yi mata binkice akan shi, sai ta fara da bin iyayensa da ƴan'uwansa ta yi musu alkhairi, bayan ta tabbatar ta karɓu a gurinsu sai ta bayyana masa manufarta, yadda ko da ya ƙi amincewa wani nasa zai yi masa dole ya amince, fatanta kawai ya kasance mahaifansa suna raye, don idan da su komai sai ya fi tafiyar mata daidai. Tun yamma take kiran wayar Hafsah a kashe, don ta fara aiwatar da aikinta a kanta, domin da zafi-zafi ake dukan ƙarfe, ba za ta tsaya kuma garin kallon ruwa kwaɗo ya yi mata ƙafa ba. Ina kwance a kan dardumar da na yi sallar Magriba Anas ya dawo. Ban ko kalle shi ba, har ya yi wanka ya je masallaci sallar isha'i ya dawo. Da kansa ya zuba abinci ya ci, na dinga kallon shi ina jin kamar na je na samu fuskarsa nai ta mari, ya na cin taliya da manja da yaji amma kamar mai cin wani haɗaɗɗen abincin da ya ji nama, sai wani lumshe ido yake yana zurƙuma lauma. Ban san lokacin da na ja wani dogon tsaki ba. Bayan ya gama ya dube ni ya ce. "Wace ce ta zo ɗazu?" Kamar na share shi, amma yadda na ji ya yi magana babu alamun wasa ya sa a ƙufule na ce. "Sai yanzu za ka tambaya? Me ya sa tunda ka gan ta ba ka tambaye ta, ta ba ka amsa da kanta ba?" "Saboda ke nake da hurumin tambaya, ke kika kawo ta gidana." Tashi zaune na yi cikin tsiwa na ce. "Ina gidan yake? Har kake wani ƙafafa kana cewa gidanka?" Na ƙarashe maganar ina keɓe baki. Girgiza kai ya yi ya ce. "Ki ba ni amsa kawai, kar ki tunzura ni, na yi miki abin da ba ki taɓa zato ba." 'Ka yi mana' Na faɗa a cikin raina, amma a fili sai na ce. "Ƙawata ce." Ya ce. "Ya yi, amma ya aka yi ban san ta ba tunda muke da ke?" Na ce. "Allah ne bai yi ba." Daga haka na tashi na shige ɗaki. Anas ya bi ta da kallo, har yanzu tantama yake akan anya Hafsah ita kaɗai ce kuwa? Saboda tun sanin da ya yi mata bai san ta da irin waɗannan halayen ba, ya san dai tana da fushi idan aka yi mata abu, amma bayan wannan bai san wani hali nata mara kyau ba. Kuma shi abin da yake ƙara ɗaure masa kai rashin sanin dalilin da ya sa take masa hakan, a iya sanin shi bai san ya yi mata wani laifin ba, bare ya ce ko shi ne dalili. A ɗazu bayan ya koma gurin aiki yay ta tunane-tunane, shi mutum ne da ba ya son zargi ko ƙala wa mutum abin da ba shi da tabbas a kan shi. Hakan ya sa ya ƙi alaƙanta abubuwan Hafsah da matar da ya gani ɗazu, duk da wani sashe na zuciyarsa yana ta faɗa masa wataƙila ya na da nasaba da hakan, ya dinga tambayar kansa wacce mata ce ita da har Hafsah take kunyar ta gan shi a matsayin mijinta. Numfashi ya sauke cikin rashin sanin abun yi, makamancin haka bai taɓa faruwa a tsakaninsu da Hafsah ba tunda suka yi aure, shi ya sa abin ya dame shi matuƙa, ya rasa tudun da zai dafa wanda zai taimaka masa ya gano hasken da zai fitar da shi daga duhun da yake ciki. Yana son matarsa so mai tsanani, ba ya son abin da zai shiga tsakaninsu ko yaya yake. A parlour'n ya goce ya kwanta, don so yake ya ga iya gudun ruwan Hafsah. Duk yadda na so yau ba zan kunna wayata gabaɗaya ba amma na kasa, wajen tara da mintuna na ɗauko na kunna cikin dokawar zuci. Bayan na kunna data direct Whatsapp na shiga na duba group ɗinmu. Duk yawan messages ɗin da na tarar sai da na bi ɗaya bayan ɗaya na ga babu inda aka yi maganata, kuma da Maman Nasmah aka sha duk hirar da aka yi. Ƙaƙƙafar ajiyar zuciya na sauke, don ni duk a tunanina za ta faɗa musu ta zo gidana ta ga ni matar talaka ce. Fita na yi ba tare da na ce ƙala ba, duk da na gagga an yi cikiyata. Ta private na ga Maman Nasmah ta mini saƙo har uku, cikin faɗuwar gaba na buɗe. Na ga ta ce. Ta kikkira ni a kashe, da fatan lafiya. Na ce mata lafiya ƙalau. Ina mamakin yadda kodayaushe tana online, ko dan su ƴan gata ne komai sai dai a yi musu? Ba kamar mu da muke wuni cikin wahalar ayyukan gida ba. Ta mun reply da. 'Masha Allah.' Danne zuciyata na yi na ce mata da fatan ta je gida lafiya? Ba ta ba ni amsa ba, sai ta kira ni. Na ɗaga cikin mutuwar jiki, ji na nake kamar wadda ta yi wa Sarki ƙarya aka kama ta. Sallama ta mun na amsa Idanuna cike da hawaye. "Allah ya sa ba kya tare da baban Sultan na kira ki da daddare." Na ce. "Eh ba ma tare." Ta ce. "Har Salamatu ta faɗa miki na kai mata atamfar kenan? Don ni tun kafin na ƙarasa gidan nata nake kiran wayarki a kashe, ko tana da wani layin naki ne?" Maimakon na yi murna Maman Nasmah ba ta gane ni ce ba sai na ji saɓanin haka, wato tsabar a mawuyacin halin da ta gan ni da mai aiki na yi mata kama? Cikin danne kukan da ya taho mini na ce. "Ai ni kika tarar ba Salamatu ba." Ban san me ya sa na ji na zaɓi kawai na faɗa mata gaskiya ba. Kamar za ta fasa mini dodon kunne saboda ƙaraji na ji ta ce. "What? Ke kuma Namecy? Ke ce wannan matar duk a yagule a wahale?" Hawaye na zuba daga idona na ce. "Ni ce." "Taɓ! Amma gaskiya jin ki ya fi ganin ki, muryarki mai daɗi da sanyi babu wanda zai yi tunanin a wannan gidan kike rayuwa gaskiya, I'm sorry idan kin ji babu daɗi, mamaki ne ya kusa kashe ni." "Babu komai, shi ya sa na kasa bayyana muku wace ce ni saboda kar a raina ni." Na faɗi haka cikin son wanke kaina. Ta ce. "Kin yi farar dabara kam, don aka gane haka kike ba ƙaramar wulaƙantacciya za a mayar da ke ba, Allah ya taimake ki mun haɗu kafin ranar taro." Na ce. "Taimakon me? Ai yadda kika gan ni su ma haka za su gan ni ranar." Ta ce. "Haba, never kina da ni ki je a haka, zan aiko miki mayukan shafawa masu tsada wanda za su gyara miki fata kafin ranar, da turaruka da sabulan wanka, da jaka da mayafi da takalmin da za ki saka ranar, ke har da sarƙa da ɗan'kunne gold da kuɗin da za ki yi liƙi a gurin. Kina da ni ai ba za ki taɓa kunyata ba ƙawata." Wani tsalle na doka daga zaunen da nake ina jin kamar an yaye mini duka damuwata na ce. "Gold fa kika ce?" Ta ce. "To mene ne a ciki? Me aka yi aka yi wani gold? Ke dai kawai ki kwantar da hankalinki tawan, har gurin makeup zan kai ki a yi miki." A rikice na ce. "Wayyo daɗi, kamar kuwa kin san tunda aka fara maganar taron nan tunanin yadda zan yi na fito fes kawai nake yi, na god..." "Babu godiya a tsakaninmu ai Namesy, kin fi ƙarfin komai a gurina, da kin faɗa mini ma tun da ai da ba wannan zancen ake ba, wani tunani ne ma ya faɗo mini yanzu a rai, kawai zan haɗa ki da mai mun gyaran jiki ta yi miki na amare na sati ɗaya, yadda za ki fi yin kyau da sheƙi ranar taron, har ƙunshi ma za ta yi miki." Ƙasa jurewa na yi na tashi da wayar ƙare a kunnena na fara taka rawar murna, da na san haka Maman Nasmah take da kirki kuma take so na da tuni ba na faɗa mata gaskiya ba. Tsabar farinciki rasa abin cewa na yi. Sai da ta ce ko ba na jin ta sannan cikin dariya na ce. "Farinciki ne ya hana ni magana." Ta ce. "To za ki je gyaran jikin na kira ta yanzu na sanar mata?" Na ce. "Me zai hana? Ubangiji ya so ni da rahama na butulce." Ta ce. "Okay, amma tun safe sai dare za ki koma gida fa." Da sauri na ce. "Kai! Duka satin kuma?" Ta ce. "Eh, mene a ciki?" Na ce. "Baban Sultan ne da ƙyar ya yarda gaskiya." Ta ce. "Saboda ba ya son ci gabanki? Bai ba ki kuɗi kin yi ba kuma za ki yi ya hana ki? Idan kika yi kyan ai shi ma zai ji daɗi, ki ce masa gyaran jiki ne ba wani abu ba." Na ce. "Duk da haka, da ƙyar ya bari, na san halin shi, zai ce ga yara ga kula da gida ba zan fita na wuni a waje ba." Ta ce. "Caɓdijan! Gaskiya matan talakawa kuna ƙoƙari, ko da yake da ma an ce talaka akwai baƙar zuciya da mugunta. Ni mijina duk inda na ce masa zan je ba ya hana ni, kuma ya ba ni kuɗin da zan yi amfani da shi ko nawa ne. Sorry sis, amma kuna ƙoƙari fa, ga talauci ga mulkin mallaka." Numfashi na sauke kamar zan yi kuka na ce. "Hmmm, to ya za mu yi?" Ta ce. "Ai ni ba zan iya ba, kuma ku ma har da laifinku, ku kuke nuna musu lako-lako tun farko, miji ba wata uwar yake muku ba, amma ku yi ta yi musu biyayya, yanzun dai duk yadda za ki yi ki samu ki je gyaran jikin nan gaskiya, idan ba haka ba ranar taro ki tashi kamar almajira a cikinmu, idan kuma ki ka ƙi zuwa kowa zai gano ki, saboda da ma ana ta complain kwana biyu kin ja baya a group, ni kankaro miki mutunci nake son yi. Da safe zan faɗa miki yadda muka yi da mai gyaran jikin na tura miki address ɗinta." Daga haka muka yi sallama ta katse wayar. Tagumi na rafka ina bitar maganganun Maman Nasmah, musamman na ƙarshe. Wato mu matan talakawa mu ne a wahale? Mu mazaje suke takurawa, su kuwa komai suke so barin su ake yi su yi, ga kuma rayuwar ƴanci da wadata. Na san Anas da bala'in kulle, abu in ba na dole ko na dangi ba bai fiya bari na zuwa ba, ya fi son duk inda za ni mu je tare saboda kishin tsiya, shi ya sa nake ta tunanin ta yadda zan faɗa masa zuwa wannan taron namu, ga kuma gyaran jiki da ya kunno kai, amma dai zan fara tambayar shi na ji abin da zai ce, idan ya hana ni na yi ficewa ta, don gaskiya Maman Nasmah ta faɗa, mu muke yi musu lako-lako, shi ya sa suke mana yadda suka so. A ɓangaren Maman Nasmah kuwa murmushi ta yi ganin cikin sauƙi ta fara samun nasara, za ta ƙara jan Hafsah a jikinta ta nuna mata ita mai ƙaunar ta ce tsakani da Allah, tare da yi mata tarin alkhairi wanda zai saka ta ƙara sakin jiki da ita. A hankali a hankali tai ta bugar cikinta tana faɗa mata abubuwan da Anas yake so da wanda ba ya so, ta tunzura ta, ta yi masa wanda ba ya so ta hana ta yin wanda yake so. Tunda a iya wayar suka yi yau ta lura ƙaramar ƙwaƙwalwa ce da ita, ban da haka ta yaya don ta ce mata ta gan ta a yagule a wahalce za ta yarda? Ai ko makaho ya shafa su ita da ƴaƴanta zai gane babu wahala a tattare da su, don babu yadda za a yi a ga Hafsah a ce a gidanta take rayuwa. Ana ganin ta an ga mai rayuwa cikin rufin asiri, kuma babu inda za ta shiga a raina ta, don daga gani mijinta yana da kula, ba sa tare da yunwa ko rashi na daidai ƙarfinsu. Amma ita saboda kidahuma ce ba ta fuskanci hakan ba, don haka za ta yi amfani da son kuɗin da dogon burinta ta cimma nata burin........✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:38 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) 9. Washegari na tashi cikin tsananin farinciki mara misaltuwa, ni kaɗai na dinga sakin murmushi ina imagining rawa da murnar da zan yi idan saƙon da Maman Nasmah ta ce za ta kawo mini ya ƙaraso. Ga ni nake kamar a mafarki, idan na tuna wai har da sarƙar gold za ta haɗo mun, sarƙa fa? Ba ma ɗan'kunne ko zobe ba. Gaskiya watan arziƙina ne ya tsaya. Na dinga kallon kaina ina hasaso ni sanye da ɗanƙareriyar sarƙa tana zuba walwali. Ƙarfe bakwai na safe na ga ta mun text na address ɗin gidan mai gyaran jikin, ta ce na je ƙarfe tara tana jira na. Cikin zumuɗi na koma parlour inda Anas yake shirya su Sultan na zauna a kan kujera, fuskata ba yabo ba fallasa na ce. "Abban Sultan zan fara zuwa gyaran jiki yau, na ga fatata duk ta yanƙwane." Kallo na ya yi cikin mamaki sannan ya ce wa Sultan. "Ɗauki abincin naku ku je ɗakinku ku ci." Suka amsa tare ɗauka suka fice suna satar kallo na. Anas ya maido da hankalinsa gare ni tare da faɗin. "Ina jin ki, ban gane me kike nufi ba?" Kaina tsaye na ce. "Cewa na yi zan je gyaran jiki anjima, za a yi mini na sati ɗaya." Cikin rashin fahimta ya ce. "Wai wanne irin gyaran jiki? Da ma kina zuwa ne ban sani ba? Har yanzu ban fahimce ki ba Hafsah?" Cikin hasala na ce. "Da Hausa fa nake yi maka maganar nan, gyaran jiki dai wanda ake yi wa mata su yi kyau fatarsu tai ta sheƙi da fitar da ƙamshi, da kake tambaya kuma da ina yi, ba na yi, yanzu zan fara." Wani kallo da ban taɓa ganin ya yi mini irinsa ba ya wurga mini tare da faɗin. "Shi ne kuma sai a yau ɗin za ki je za ki faɗa mun? To ban shirya ba gaskiya." Tsaki na ja a cikin raina na ce. 'Sarkin tsiya aminin talauci, to ba cewa zan yi ka ba ni kuɗin ba.' "Ba kai za ka biya ba ai, ni zan biya da kaina." Na faɗi haka ina huhhura hanci. "A ina kika samu kuɗin?" "Allah ne ya ba ni." "To ba za ki je ba." Ya faɗa a fusace tare miƙewa ya bar mini parlour'n. Da wani matsiyacin kallo na raka shi, ƙwafa na ja na miƙe kamar zan kifa na ɗauko wayata na kira Maman Nasmah, ringing biyu ta ɗaga, muryarta da alamun bacci ta ce. "Kin ga saƙona kenan?" Na ce. "Eh, ki yi haƙuri na tashe ki a bacci." Ta ce. "Ba komai, Kin tambayi mijin naki?" Na ce. "Hmm." Tare da faɗa mata duk yadda muka yi da shi. Cikin kwakwazo ta ce. "Wannan miji naki ba dai baƙar zuciya ba wallahi, ni fa tunda na gan shi yana yi miki wani murmushin gefen baki na san mugu ne, ban da haka mene na hana ki wani fita?" Kamar zan yi kuka na ce. "Kulle ne da shi da ma, ko bayani ban gama yi masa ba ya tashi ya bar ni, in dai ba tare za mu fita ba bai fiya bari na fita ba, wai shi kishi." "Kin gani ba, muguntar kenan ai, shi yana fita yana watayawa kullum amma ke yana barin ki a gida a dunkume, saboda kar ki fita ki....." Jin motsin shi na yi saurin katse da faɗin. "Ina zuwa, ga shi nan." Ban jira amsar ta ba na datse kiran. Murmushin mugunta Maman Nasmah ta yi ta ce. "Jaka, haka zan ta zura ki na kai ki na baro, miji irin naki ai abin so ne, mai kishin iyalinsa da tsare mutuncinsu, ban da mahaukaciya ce ke da ma wanne mijin arziƙi ne za ka ce masa za ka fara fita wani gyaran jiki rana tsaka ya bar ka? In sha Allahu kafin taron nan sai na yi sanadin da zai miki ko saki ɗaya ne, daga nan na fara plan B ɗina." Ta lumshe idonta tare da rungume pillown da yake ƙirjinta, wani irin son Anas sabo na fizgar ta, mutumin da ko sunansa ba ta sani ba, amma soyayyar shi ta mata mugun gamu, saboda yadda tunaninsa ya addabe ta ko lokacin yin wasu abubuwan ba ta samu yi ba a daren jiya, raba dare ta yi tana ta juyi a gado tare da hasaso irin soyayyar da take fatan su yi. Tana ganin ɗaya daga cikin mazan da take hulɗa su yana ta kiran ta amma ta ƙi ɗagawa, domin daga lokacin da ta yi tozali da Anas duk mazan duniya suka koma mata tamkar mata ƴan'uwanta, shi kaɗai take gani a Namiji. Fatanta kawai Allah ya sa mijinta ya dawo a cikin satin nan, ta rura masa wuta ya ba ta takardarta, ta yi ta yi ta gama iddarta a ɗaura mata aure da masoyinta. Komai take yi fuskarsa kawai take gani a cikin idanuwanta da murmushin da yake yi wa Hafsah. Numfashi ta sauke tare da mirginawa tana murmushi ta ce. "Ina son ka sosai mijin Hafsah Maman Sultan a yanzu, nan gaba kaɗan kuma mijin Hafsat Maman kyawawan ƴaƴan da za ta haifa maka masu kama da kai." Ido na bi shi da shi bayan ya shigo ɗakin, cikin tsoron ko ya ji wayar da nake yi, don babu abin da ya tsana a rayuwarsa sama da wani abu ya faru a tsakaninmu na faɗa wa wani, mutum ne shi mai son sirri sosai. Shi ya sa tun da muke da shi bai taɓa kai ƙara ta gida ba da sunan na yi masa wani laifin. Yana cire jallabiyar jikinsa na ƙarasa kusa da shi fuska a murtuke na ce. "Wai don Allah Anas me ya sa kake mun irin wannan abubuwan ne? Akan me za ka hana ni zuwa gyaran jikin nan?" Ba tare da ya kalle ni ba ya ce. "Saboda na isa." Kallon sama da ƙasa na yi masa na ce. "Yanzu kai ba abin jin daɗinka ba ne zan je a gyara ni?" Ya ce. "Ba shi ne damuwata ba, inda kika samo kuɗin zuwan nake son sani." A wulaƙance na ce. "Oh, saboda ga ƴar matsiyata dangin matalauta ko? Wadda wani nawa ba zai iya ba ni kuɗi ba." Kallon takaici kawai ya mun ya juya ya fita, na bi shi da harara. Kiran Maman Nasmah na ƙara yi na faɗa mata komai. Cikin faɗa ta ce. "Wai wannan mijin naki shi ne autan maza ne da kike ta lallaɓa shi haka? Maman Sultan kar dai ki ce mini ke ma mata kika rako duniya?" Na ce. "Ban gane ba?" Ta ce. "Ai ba za ki gane ba, ni kawai ki faɗa mini idan gyaran jikin ne ba kya so na saka ta dawo mini da kuɗina." Cikin rawar baki na ce. "Wallahi ina so, kawai ban san fita ba da izninsa ba ne." Ta ce. "To sannu doluwa, idan akan maganar kuɗi ne ki ce masa ƙawarki ce kuka haɗu a social media ta ba ki, ba shikenan ba ya ji abin da yake so?" Shiru na yi, don na san hakan ma wata sabuwar fitinar ce. Fahimtar hakan ya sa Maman Nasmah ta ce. "Ko me zai yi ki faɗa masa haka, don maza ba a yi musu lako-lako, ni ban ma taɓa ganin mace mai tsoron miji irinki ba ko a labari, ko a cikin group ɗinmu ai za ki ga kowacce tana faɗa watayawarta take yi son ranta a gidanta, ke kaɗai ce fa kike cikin wannan rayuwar ƙuncin, ki zage ki ƙwatarwa kanki ƴanci, idan ba haka ba taron ma hana ki zuwa zai yi. Don haka duk abin da zai ce ki yi ficewarki, kar ki raga masa, ba a raga wa maza yanzu ko kaɗan." Cikin rashin mafita na ce "Toh shikenan." Daga haka muka yi sallama. Zama na yi ina bitar maganganun Maman Nasmah, tabbas duk abin da ta faɗa gaskiya ne, su da mazajensu ma suke hamshaƙan masu kuɗi ba sa tsoron su sai ni matar talaka. Yanda matan group ɗinmu suke watayawarsu abin ba ƙaramin burge ni yake ba, sai na ji suna cewa duk inda suke so zuwa suke. Don haka ni ma daga yanzu na ɗaura ɗamarar yin duk abin da na ga dama, na daina shayin Anas, bari ya dawo daga kai su Sultan school, zan nuna masa wargi ce ni daidai ƙugunsa. Da wannan tunanin na tashi na fara shirin tafiya gidan mai gyaran jikin. Har na sha tea ɗin da ya tafasa da bread na yi wanka bai dawo ba. Ina cikin shiryawa ya shigo, sai da kammala komai na ɗauki jakata da mayafi na nufi ƙofa fuskata a murtuke, ba tare na ce masa ƙala ba. "Babu inda za ki je fa wallahi Hafsah." Ya faɗa yana tare hanya. A haƙiƙance na ce. "Wai saboda me? Idan kuɗin ne dole sai ka ji wa ya ba ni to ƙawata ce da ta zo jiya." Yana ƙara babbake hanya ya ce. "A ina take? Mene ne alaƙarki da ita?" Kaina tsaye na ce. "A group na Whatsapp muka haɗu." Cikin matsanancin ɓacin rai ya ce. "Ban san ta ba, ban san irinta ba, ban san wace ce ita ba, ba zai yiwu haka kawai ta ɗauki kuɗi ta ba ki ni kuma na bar ki, ki yi amfani da shi ba, don haka ki mayar mata da abinta!" A zazafe na mayar masa da raddi da faɗin. "Wallahi ba zan mayar ba, kai ba ka ba ni ba, ita da yake mijinta mai zuciya ne da son faranta wa iyalinsa ya ba ta har ta sammun a ciki sannan kuma ka ce na mayar saboda mutunta? Su mazansu ga kuɗi ga ba matsi, sai kai talaka ne za ka hana ni rawar gaban hantsi? To wallahi bari ka ji Anas, ban ga abin da zai hana ni zuwa gyaran jikin nan ba, saboda taro za mu yi a group ɗinmu, kowacce mijinta ya ba ta kuɗi don ta fito fes sai ni ce zan tafi a duƙun-duƙun? To ba zai yiwu ba." Na ƙarashe maganar kamar zan kai masa duka, zugar Maman Nasmah na ƙara tunzura ni na ci gaba da faffaɗa masa maganganu ya gane ba na tsoron shi a yanzu, amma na danne na ƙyale shi haka ba don halin shi ba. Tsananin mamaki da al'ajabi su suka saka Anas sandarewa a tsaye, ya kasa ƙwaƙƙwaran motsi, hakan ya ba ni damar raɓawa ta gefen shi na fice. Na kai tsakiyar tsakar gida na ji muryarsa cikin matsanancin ɓacin ran da ban taɓa jin shi a cikinsa ba, don muryarsa har rawa take yana faɗin. "Wallahi! Wallahi! Wallahi idan kika ɗaga ƙafa kika fita daga gidan nan a bakin aurenki!".......✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:38 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* *BRIGH PENS* (FREE BATCH) 10. Cak na tsaya kamar an kafe ni, don furucin a bakin aurenki da ya yi ba ƙaramin dukan zuciyata ya yi ba. Kamar na koma na fasa fitar, amma sai na ji ba zan iya ba, hakan ya sa kawai na ci gaba da tafiyata ba tare da na waiga ba, duk da na ji motsin fitowarsa tsakar gidan. Idan akwai abin da nake da tabbaci cikakke a kansa to shi ne son da Anas yake mini, na san ba zai taɓa iya rabuwa da ni ba, wannan maganar tasa ma ya yi ta ne kawai a matsayin hargagi, amma na san ba har cikin zuciyarsa take ba. Idan ma har cikin ran nasa ne matsalar shi ce ba tawa ba, don kamar yadda Maman Nasmah ta faɗa idan ina nuna ba na tsoron shi sai ya fi shayi na. Na shafe kusan mintuna talatin kafin na ƙarasa gidan mai gyaran jikin saboda akwai nisa daga unguwarmu, ina zuwa babu ɓata lokaci ta fara gudanar da aikinta, ta na yi tana ba ni labarin kuɗin Maman Nasmah da na mijinta, don akan wannan gyaran jikin nawa ma sai da ta ninka mata kuɗin sau uku akan yadda take yi. Sai na ji ina ma ni ce ake labarin kuɗina da na mijina, na dinga addu'ar Allah ya nuna mini ranar ni ma zan zama irin haka, a dinga labarina da kwatance da ni. Sai yamma lis na baro gidan, matar tana ta yabon kyan fatata, ni kuwa gani nake murnar kuɗin da aka ba ta ne kawai ya sa take ta koɗa ni, babu wani kyan fata da nake da shi kamar yadda Maman Nasmah ta faɗa. Yau Anas ko fita bai yi ba, takaici da mamakin Hafsah sun saka ya zauna yay ta tunane-tunane, hakan ya haifar masa da ciwon kai. Bai taɓa zaton zai ce wa Hafsah idan ta yi abu a bakin aurenta za ta aikata ba. Shi ya dafa musu abincin rana ya yi sauran aikace-aikacen gidan. Sai bayan Magriba na koma gida, na tarar ba ya nan sai su Sultan kaɗai a parlour suna homework. Da gudu suka taso suka rungume ni, Sufyan ya ce. "Mami ina kika je? Muna ta neman ki, kin tafi kin bar mu." Kayan hannuna wanda Maman Nasmah ta aiko mini da shi na ajiye a kan kujera na ce. "Unguwa na je, ku ƙarasa aikin naku na ba ku kayan daɗi." Da murna ya koma ya ci gaba. Sultan ya ce. "Mami na zubo miki abinci? Abba ya dafa mana macaroni." Na ce. "To bari na shiga na ajiye kayan nan na fito." Sufyan ya ce. "Za ki biya mana karatu yau ko Mami? Idan mun iya ki yi mana tatsuniya irin na ranar nan." Na ce. "To." Kawai. Sai da na yi Sallah sannan na baje kayan na dudduba, duk abin da ta lissafa za ta ba ni babu wanda ta manta ba ta sako ba, har da kuɗi 30k wai na transport zuwa gidan gyaran jiki, kuma ta ce gobe na tafi da atamfata za ta aiko a karɓa akai mini ɗinki. Ina ɗaga sarƙar gold ɗin da na shafe mintuna ina lailaya ta na ce. "Allah ka saka wa wannan mata da alkhairi, ka ba ni ikon faranta mata kamar yadda ta faranta mini a yau." Kamar zan zauce haka nake ji tsabar farinciki, na ƙara tabbatarwa Maman Nasmah masoyiyata ce ta haƙiƙa, don ta gama yi mini komai, tunda ta fitar da ni kunyar zuwa taron nan. Sai da na gama tsallena da rawar murnar daɗi na kira ta don na yi mata godiya, har lokacin kuma Anas bai dawo ba. Bayan mun gaisa ta ce. "Ya aka yi ya bar ki kika je kuma?" Ina murmushi na ce. "Shawararki na bi ai, na nuna masa bai isa ba, shi ne har da cewa idan na fita a bakin aure na." Maman Nasmah ta ce. "Gara da kika yi masa haka, ki ci gaba da ƙwatar wa kanki ƴanci, kar ki bari takaicin Namiji ya kar ki, namijin ma wani banza talaka da ko ɗawainiyarki bai gama iya ɗaukewa." Shiru na yi don ba na jin daɗin yadda take yawan zagin Anas da aibata shi, duk da wani lokacin idan na yi nazari gaskiya ta faɗa, amma mijina ne duk lalacewar shi, kuma ina son shi a haka. "To da kika dawo me ya ce kuma?" Ta katse shirun nawa da faɗar haka. Na ce. "Ba ya nan na dawo, har yanzu kuma bai dawo ba." Ta ce. "To kar dai ki raga masa, ni shawara nake ba ki wadda za ta fishshe ki, don so nake na ga kina rayuwa mai inganci, idan ya faɗa miki ɗaya ki mayar masa da goma zafafa, kar ki ƙara yarda ki kuma irin rayuwar bayan da kuka yi da shi, wani ladabi da biyayya duk ki zubar da su a gefe, ki daina wannan aikin wahalar da na zo na tarar da ke kina yi kin yi ciɗin-ciɗin kamar wadda aka haƙo daga rami, yadda kika ga na zo gidanki haka nake zama kodayaushe a gidana, ina daga kwance masu aiki ne suke yi mini komai. To akan me zan kashe kaina? Haka kawai na yi baƙi watarana su gan ni a ƙazance, ai abin kunya ne." Na ce. "Haka ne, na gode sosai, zan yi duk yadda kika ce." Daga haka muka yi sallama na katse wayar. Kayan ciye-ciyen da ta kawo jiya shi muka ci ni da su Sultan, na yi musu wanka na kwantar da su, sai murna suke yau na ja su a jiki kamar yadda muka saba a da. Har wajen sha ɗaya Anas bai dawo ba, har na kwanta na ji na kasa bacci, don ba ya taɓa kaiwa haka a waje, bare kuma ya fita ba na nan ya bar yara kaɗai a gidan. Ina ƙoƙarin kiran shi a waya ya shigo. Kamar babu abin da ya faru na ɓacin rai a tsakaninmu kafin na fita haka ya mun magana, ya sanar mini jiran shagon dare ya yi wa mai gidansu tunda bai samu ya yi na rana ba. Ganin haka na nuna masa kayan da Maman Nasmah ta ba ni, amma ban da sarƙar gold ɗin, saboda kar ya yi magana. Bai nuna ɓacin ransa ba ya ce Allah ya sanya alkhairi. Na yi mamakin shi sosai, don na ɗauka zai yi mini bala'i ne. Washegari da na ce masa zan koma gidan gyaran jikin bai hana ni ba, ya dai roƙe ni akan kar na yi dare irin na jiya, na ce masa in sha Allah. Sai da na yi abincin rana na kai maƙota da uniform ɗin islamiyyar su Sultan sannan na tafi. Tun ƙarfe bakwai na ga Maman Nasmah tana ta kira na, amma saboda aiki ban samu sukunin kiran ta ba, sai da na hau napep. Ta na ɗagawa ta ce. "Ya kuka yi da faƙirin mijin naki? Shi nake ta kiran ki na ji amma ba ki ɗauka ba." Cikin mamakin yadda yanzu kullum muka yi waya ko chat sai ta ji me yake wakana tsakani na da Anas na ce. "Me ya sa kika damu ne?" Ta ce. "Saboda ina son na ji halin da kike ciki mana na ba ki shawarar da za ta fishshe ki, ni fa tamkar ƙanwata da muke ciki ɗaya haka na ɗauke ki, kullum da ke kwana nake tashi, wannan mulkin mallakar da yake yi miki ji nake kamar ni ake wa wallahi." Cikin jin daɗi da ƙara yarda da soyayyar ta a gare ni na ce. "Allah Sarki ƙawata, to ki kwantar da hankalinki, don komai ya wuce a tsakaninmu ni da shi, ba ki ga yadda ya mun jiya ba, faran-faran, yau ma tare muka fito, bai hana ni ba." Kamar wadda ta firgita haka na ji ta yi magana da faɗin. "Ban gane ba! Bai ce miki komai akan daɗewar da kika yi ba?" Na ce. "Bai ce ba, kawai dai ya ce kar na daɗe yau." "Kuma kin nuna masa kayan da na ba ki?" Na ce. "Eh." Shiru na ji ta yi na wasu sakanni, daga baya ta ce. "Kin ga shawarar da nake ba ki ta yi aiki ko? Da kin ci gaba da yi masa lako-lakon nan da tuni jiya ya ƙare miki tijara, amma abin da nake so da ke kar hakan ya sa ki koma masa kamar da fa, idan ba haka ba zai ci gaba da juya ki kamar waina ne, yanzu kin saka masa tsoron ki a cikin zuciya, ya gane ko babu shi za ki iya rayuwa, tunda har ya yi miki barazana da saki kuma kika shallake, to haka ake yi wa maza a zauna lafiya da su, idan kuma kika ce za ki raga musu sai su mayar da ke baiwa, dabba ma ta fi ki daraja a gurinsu." Cikin gamsuwa da maganganunta na ce. "Tabbas haka ne, don da a da ne Anas ya hana ni abu na yi sai ya saɓa mini sosai, amma jiya har da haƙuri ya ba ni, ai na faɗa miki yana tsananin so na, ba zai taɓa iya rabuwa da ni ba." "Yawwa, to ki yi amfani da wannan son ki gara shi kamar taya, ke ma ki shigo samun mu manyan mata isassu a gidajensu, za ki ga yadda zai na rawar jiki a kanki da yi miki biyayya." Bayan mun gama wayar na yi shiru ina nazartar maganganun ta, tabbas duk abin da ta faɗa gaskiya ne, na yi kuma amanna da su, duk da na yi niyyar mu koma kamar yadda muke a da ni da Anas, don da ma dalilin da ya saka nake yi masa duk wani rashin mutunci saboda ba zai fitar da ni kunya ba ne, amma tunda na samu duk wani abu da nake buƙata na fitar taronmu ban da wata sauran damuwa. Kasa zaune ko tsaye Maman Nasmah ta yi bayan sun gama wayar, ko kaɗan ba haka ta so ji ba, ta so a ce Anas ya na dawowa ya yi wa Hafsah fata-fata ya kore ta a daren, hakan ya ƙara tabbatar mata ba ƙaramin so yake yi wa Hafsan ba kamar yadda ta faɗa. Dole ne ta ƙara ƙaimi da dagewa gurin ziga Hafsah da nuna mata mijinta ba kowa ba ne face talaka mara daraja, za ta yi amfani da son rayuwar kuɗin da Hafsah take da shi ta cimma burinta. Wani murmushi ta saki lokacin da wata idea ta to mata cikin kwanyarta kamar an zira mata ita. A fili ta ce. "Duk rintsi duk wahala dole na mallaki mijinki Maman Sultan!" Da daddare da muka kuma waya da Maman Nasmah ta ce na takura wa Anas ya siya mini sabuwar waya kafin ranar taro, kowa yana turo abin da mijinsa ya yi masa a group amma ban da ni, saboda nawa mijin ya fi kowa fatara sai ya kasa tsinana mini komai. Ya na dawowa ko bari ban yi ya zauna ba na ce. "Abban Sultan taron da na ce maka za mu yi fa saura kwana biyar, kuma gaskiya ni ina buƙatar sabuwar waya kafin ranar." Ya ce. "Ba mun gama wannan maganar ba Hafsah?" A harzuƙe na ce. "Ba wani mun gama, ni kawai ka siya mini." Ya ce. "Zancen kike so." Masifa na shiga surfa masa kamar wata uwarsa, ta inda nake shiga ba ta nan nake fita ba. Na dinga jifan shi da kausasan kalamai. Bai ce mini ƙala ba har na gaji don kaina na yi shiru ina huci. Ina hawa online a lokacin na ga an ci gaba da turo abubuwa, kowacce ta na cewa mijinta ya siya mata kaza, ya ba ta kaza, ya kawo mata kaza. Hakan ya ƙara tunzura ni, na dinga Allah wadai da auren Anas, don da na san haka masu kuɗi suke bauta wa matansu da ko sama da ƙasa za su haɗe ba zan auri talaka ba. Ga shi ana ta tagged ɗina ana cewa ni ina nawa abubuwan? Rashin abin cewa ya sa ba na yi musu reply. Duk wata tijara da rashin mutunci babu wadda ban yi wa Abban Sultan ba akan ƙin siyo mini wayar da ya yi, na daina aikin komai a gidan, tsakani na da su Sufyan sai hantara da zagi, musamman idan yana gidan, amma duk da haka ko ɗaga kai bai taɓa yi ya kalle ni ba bare ya tanka, duk da ina ganin tsantsar ɓacin rai a kan fuskarsa. Yau ya kama saura kwana biyu taronmu, da daddare bayan na dawo daga gidan gyaran jiki ina zaune a gefen gado ina kallon fatata yadda ta yi wani irin kyau da sheƙi abun gwanin burgewa. Kallon yadda jikina ya koma kaɗai ya na saka ni a cikin matuƙar nishaɗi. Kiran Maman Nasmah ne ya shigo wayata, da murmushi na ɗaga tare da yin sallama, bayan ta amsa na ce. "Ya shirye-shirye?" Ta ce. "Shirye-shirye Alhamdulillah, ai mu mun gama komai, rana kawai muke jira." Na ce. "Masha Allah, Allah ya nuna mana wannan rana dai da rai da lafiya, mu sha shagali mu mori bidirin tanadin da aka yi mata." Ta ce. "Amin, amma dai ya kawo miki wayar?" Na ce. "Hmm, ina fa! Ai da ƙyar ya siya mini, ko tanka ni ba ya yi fa." Ta ce. "Taɓ, kowa kuwa da sabuwar waya zai je gurin nan, daga mai ta million sai mai ta sama da haka, ke kaɗai ce za ki tashi da jagwal." Cikin yaƙe na ce. "In sha Allah ni ma da sabuwa zan zo, bari ya dawo gidan." Ta ce. "Allah ya sa, ki san dai duk yadda za ki yi ya siya miki atou." Na ce. "In sha Allah." Daga haka muka yi sallama ta kashe wayar. Miƙewa na yi na fara zarya a ɗakin, ina tunanin hanyar da zan bi na samu waya mai tsada irinta ƴan group ɗinmu, na ƙulla na ƙunce amma ban da wata hanya sai Anas ɗin dai. Citson yatsa na yi na ce. "Oh Allah, ni Hafsah wacce ƙaddara ce ta kai ni auren mara zuciyar da ba zai iya nemo kuɗin da zai wadata ni da shi ba? Ya mayar da ni zarra a cikin mata ni ma kamar su Maman Nasmah." Tsaki na ja na koma na zauna tare da rafka tagumi. A haka ya dawo ya same ni, na tarɓe shi da kallon banza tare da jan dogon tsaki. Bayan ya rage kayan jikinsa ya na ƙoƙarin barin ɗakin na yi tsalle na sha gabansa, ina bin shi da wulaƙantaccen kallo na ce. "Anas don Allah wai kai wanne irin mutum ne? Ko babu zuciya a ƙirjinka ne da za ka yi amfani da ita ka nemo kuɗi a duk inda suke ka yi mini abin da nake da muraɗi?" Numfashi ya sauke tare da ƙoƙarin raɓawa ta gefena ya fita amma na ƙara tare hanyar, ina hawaye na ce. "Wai mahaukaciya ka mayar da ni a gidan nan ne da sai nai ta maka magana ka ƙi Kula Ni?" "To ai ba ki da maraba da ita." Ya faɗa fuskarsa ba yabo ba fallasa. Bai jira amsata ba ya ci gaba da magana da faɗin. "Duk abin da za ki yi da cin mutuncin da za ki mun na yi wa kaina alƙawarin ba zan kula ki ba, bare na biye miki, har ki yi ki gama." Ƙugu na riƙe a harzuƙe na ce. "Ai ban da ranar ganawa idan har ba za ka yi mini abin da nake so ba, na gaji da zama sai dai na ga a yi wa wasu abubuwa ni ba a min, alhalin su ma mazajen nasu mutane ne kamar kai, ba fin ka suka yi da komai ba, abin da suke yi suke samun kuɗi kai ma za ka iya." Girgiza kai ya yi cikin tsantsar takaici ya ce."Allah ya ganar da ke Hafsah, amma ba zan gajiya da yi miki wannan addu'ar ba." Ina ƙoƙarin ƙara yin wata maganar ya hankaɗe ni ya fice, ƙwafa na yi na koma na zauna ina jijjiga jiki. Sabbin wayoyi da motocin da ƴan group ɗinmu suka tutturo mazajensu sun siya musu sai gizo suke mun a cikin kaina, babban abin da ya fi ɗaga mini hankali yadda duk wadda ta turo abu wani sashi na gidanta ya fito sai na gan shi haɗaɗɗe ginin zamani, wani parking space ma kaɗai sai a saka gidana a ciki ya zauna har da ragowa. Gabaɗaya Anas da duk wata kyautatawa, kulawa da soyayyar da yake min sun fice mini a rai, rayuwar gidan kuɗi da jin daɗi kawai nake hange. Na tabbata yadda nake kwana da wuni da tunanin ranar da mafarkina zai zama gaske idan aka auna jinina ba ƙaramin hawa za a ga ya yi ba. Duk yadda na so mu yi fitina da Anas a daren nan amma ya ƙi biye mini, ƙarshe ma ficewa ya yi ya bar mini ɗakin ya koma nasu Sultan. Da Asuba ina tashi na ɗora daga inda na tsaya, na dinga watsi da kayan ɗakina ina jifan shi da shi, tare da gasa masa duk maganar da ta fito daga bakina. Don hankalina a matuƙar tashe yake na ganin har ana i gobe taronmu amma ban mallaki sabuwar waya ba, kuma kamar yadda Maman Nasmah ta faɗa duk kyawun da zan yi a gurin, da tsadar kayan da zan saka a banza za su tashi idan ban da rantsatstsiyar waya, saboda akwai video da za a yi mana wanda kowa zai ɗaga wayarsa a ciki, so ake mu tashi kan media a taron nan namu, ai ta yawo da videos da pictures ɗinmu, mu zama topic of discussion a ranar, shi ya sa aka ce kowacce ta sako gold. Don haka duk rintsi duk wahala ba zan bari na zamo takashin baya ba, dole duk abin da za a yi ya zamto ina gaba-gaba. Yau idan na je gidan gyaran jiki shi ne za a mun lalle, amma saboda zullumin rashin waya ya sa har 8 ta wuce ban fara shirin tafiya ba. Ina kwance ina aikin kallon hotunan wayoyin da fiye da rabin ƴan group ɗin suka turo a tsakanin shekaran jiya da jiya Abban Sultan ya shigo ɗakin. Kamar an tsikare ni na tashi zaune na dirga daga kan gadon a haukace na je gabansa na haska masa rakwaɓaɓɓen screen ɗin wayata na ce. "Kalli yadda ake abin arziƙi, kalli irin wayoyin da mazajen wasu suka sissiya musu, ni kam Anas anya ka na so na kuwa? Gobe ne abin nan amma ka fitar da ni kunya abu ya gagara." Tankwaɓar da wayar ya yi ya ce. "Ban taɓa sanin ba ki da hankali ba Hafsah sai yanzu, kin taɓa ganin mutum ba shi da gashin wance ya ce sai ya yi irin kitsonta? Kin san kuɗin da mazajen nasu suke da shi ne?" Ina huci na ce. "Ai ba da kuɗin suka zo duniya ba, nema suka yi, kai ma sai ka fita ka nemo a duk inda suke." Murmushin takaici ya yi ya ce. "Kin yi nisa my love, ba za ki taɓa jin kira ba, abu ɗaya nake fata shi ne Allah ya sa ki je ki ga mazajen nasu ba su da wani abu da suke nema ido rufe, wanda ni kuma ina da shi, na san daga nan za ki dawo cikin hayyacinki." Wulaƙantaccen kallo na bi shi da shi, ina keɓe fuska kamar na ga kashi na ce. "Har akwai wani abu da talaka yake da shi da mai arziƙi zai rasa? Ai kuɗi babu abin da ba sa samar wa mutum a duniya." Girgiza kai ya yi ya ce. "Kamar yadda Ubangiji yake raba arziƙi ga wanda ya so haka yake raba lafiya da sauran baiwa ga bayinsa, don ka na da kuɗi bai zama lallai ka na da lafiya ko kuma wani abu mai muhimmanci a rayuwarka ba, na san ba za ki taɓa gane duk wani abu da zan faɗa miki ba a yanzu, balle ki yarda da ni, saboda nausawar da kika yi a cikin wani tunani na banza da wofi. Shi ya sa na tattara ki na watsar na zuba miki ido ki yi duk abin da za ki yi ki gama, zan dai ci gaba da yi miki addu'ar Ubangiji ya ganar da ke cikin gaggawa." Wawan tsaki na ja tare da galla masa harara, ina jin kamar na kikkifa masa mari. Bai ko kalle ni ba ya ɗauki abin da zai ɗauka ya fice. Rashin sanin abin yi ya sa na tafi inda na ajiye kayan da Maman Nasmah ta ba ni don na ɗauka na tasa su a gaba na kalla kamar yadda nake yi kullum ko zan ji sanyi a raina. Sai dai me? Neman duniya babu wanda ban yi ba amma babu su babu alamar su, gabaɗaya na ƙara hargitsa ɗakin, na yi wa komai filla-filla, amma ko alamar abu mai kama da su ban gani ba. A haukace na fita parlour ina sharce zufa na duba amma nan ma babu, kitchen, toilet, ɗakin su Sultan, soro babu inda ban duba ba amma ban gan su ba, har bokitin da nake zuba shara sai da na zazzage a ƙasa na duba. Amma kaya suka ce ɗauke mu inda kika ajiye....✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:39 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *11.* Cikin matuƙar gigita da ɗimauta na koma ɗaki kamar wadda ta rasa duk danginta, na ƙara duba ko'ina har inda kayan ba za su shiga ba amma still ba ta sauya zani ba. Tamkar ledar da ke narkewa a wuta haka na zube a tsakar ɗakina na baje a kwance ina sakin numfashin wahala. "Na shiga uku! Su kuwa kayan ina suka shige? Idan har ta tabbata ɓata suka yi na gama kaɗewa har ganyena!" Na faɗi haka a fili ina ɗora hannuna akai daga kwancen da nake. Kamar ɓeran da ya hangi kyanwa haka na miƙe zumbur na fara laluben inda na cilla wayata, da ƙyar na gano ta a cikin kayan sawarmu da na yi musu ɗaiɗai a tsakar ɗakin kamar na rabon gado. Wani farfar na ga tana yi, a hakan na lalubo numbern Anas na yi Dialing. Sai da ta kusa katsewa ya ɗaga bakinsa ɗauke da sallama. Ban bari ya ƙarasa ba bare na amsa na ce. "Anas ka ɗaukar mini kayan nan da matar nan ta ba ni ka sauya musu gurin ajiya ne?" Ajiyar zuciya na ji ya sauke bai ce komai ma. A harzuƙe na ce. "Magana fa nake yi maka." Yana sauke numfashi ya ce. "Relief nake samu, don yadda kika yi magana cikin tashin hankali na ɗauka mutuwa za ki faɗa mini an yi." Cikin ƙufula na ce. "To ba gara mutuwar da wannan rasa kayan da na yi ba, kayana fa Anas wanda zan yi fitar kunya da su gobe? Don girman Allah da darajar su Inna idan ka gan su ko kai ɓoye ka dawo ka ba ni! Don Allah ba don ni ba, wallahi idan ta tabbata kayan nan sun ɓata zuciyata za ta iya bugawa." Na ƙarashe maganar tare da fashewa da kuka. Cikin lallami da son kwantar mini da hankali ya ce. "Ki nutsu dai ki duba su da kyau Hafsah, don ni tun ranar da kika nuna mini su ko ƙyallin ledar da suke ciki ban ƙara gani ba, don haka suna gidan, tunda babu mai shigowa bare ya ɗauka." A ruɗe na ce. "Ba sa nan, wallahi na duba ko'ina har toilet da cikin bola ban gan su ba, ba sa nan fa Abban Sultan, don Allah ka taimake ni ka zo ka taya ni dubawa, ko idona ne ya makance daga ganin su." Ya ce. "Tom shikenan gani nan." Na ce. "Yawwa, ka yi sauri." Daga haka na kashe wayar. Duk da gajiyar da na yi sai da na ci gaba da bincike kafin ya ƙaraso. Ina cikin yi tunanin kiran Maman Nasmah na sanar mata halin da ake ciki ya faɗo mini, da sauri na ɗauki wayar na kira ta, kamar mai dakon kiran ta ɗaga da sauri, don ni ko ringing ban ji ta yi ba. Ina share hawayen da ya yi male-male a kan fuskata na ce. "Takwara ina cikin tashin hankali, ban ga kayan da kika ba ni ba gabaɗayansu." Cikin mamaki ta ce. "Kamar ya ba ki gan su ba? Wanne kaya ma tukunna?" Na ce. "Wanda zan saka gobe mana? Komai da komai ɗin da kika aiko mun da shi fa, har sarƙar gold ɗin!" Numfashi ta sauke ta ce. "To ai ni ban ga abun damuwa ba a nan tunda kin san wa zai ɗauka?" Da sauri na ce. "Sai dai in aljanu ne, amma ko Abban Sultan bai san inda na ajiye su ba, saboda ɓoyo nake yi musu kamar na ganin mutuwa." Ta ce. "To ko na ganin ƙiyama ne ga shi nan mijinki ya gani ya sace." "Sata kuma?" "Eh mana, to idan ba shi ba wa zai ɗauka? Su Sultan ƴaƴanki ƙanana ko kuma kin yi wani baƙon ne a gidan ban sani ba?" Cikin ɗaurewar kai na ce. "Babu wanda ya shigo gidan ma tunda kika kawo kayan bare baƙon zama, daga ni sai mijina da ƴaƴana a gidan, kuma na kira shi tun ɗazu na tambaye shi ya ce ko ganin su bai yi ba, balle ya ɗauka, Abban Sultan ba ya ƙarya, da ya ɗauka zai faɗa mini wallahi, ko da wasa yake mini yadda ya ji hankalina ya yi mugun tashi zai ce shi ya ɗauka." Dariya na ji ta sheƙe da ita kamar sabon kamu, tana dariyar ta ce. "Lallai Namecy har yanzu da sauran ki a karatun ɗa namiji, to bari ki ji, ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba shi ya sace kayan zai je ya siyar, ƙila ma ya daɗe da cin kasuwarsu, ke kina nan kina cewa ba zai ɗauka ba." Girgiza kaina na fara yi cikin tantamar abin da ta ce, don ko kusa ban kawo Anas zai ɗauki kayan nan da niyyar sata ba, saboda shi mutum ne da kayan wani bai dame shi ba kwata-kwata, tun farkon aurenmu idan zan samu duniya ba ta gabansa, kuma ba ma ni ba, naturally ɗinsa kayan wani ba ya gabansa, ban taɓa jin ya mun zancen abin wani yana burge shi ba, bare ya roƙa, mutum ne shi mai wadatar zuci, abinsa na karan kansa kawai ya sani, da shi yake amfani. Zan shaide shi a wannan fannin. A sanyaye na ce. "Anas ba zai mun sata ba Maman Nasmah." A zafafe ta ce. "Ke kika sace abinki kenan ko kuma kayan su suka ɗauke kansu? Wai ke wacce iriya ce ne? Ina ganin ki kamar mace mai wayo ashe ba haka ba ne? Ki nemi abu ki rasa a gida kuma daga ke sai shi amma ki dinga cewa ba shi ya ɗauka ba, ki yi tunani da ƙwaƙwalwarki mana, kin ce babu wanda ya shigo gidan ma tunda na ba ki kayan bare a ce ko shi ya ɗauka. Ina nuna miki Annabi kina runtse ido, ga abu a fili amma shegen son miji ya sa kin baɗa wa idonki toka kin ƙi gani. To ki karkaɗe kunnanki ki saurare ni da kyau, mijinki shi ya ɗauke kayan nan ya siyar babu ko tantama, ko ki yarda ko kar ki yarda. An faɗa miki ana yarda da maza ne yanzu, idan da akwai abin da ya fi komai rashin tabbas l a duniyar nan to namiji ne. Kin faɗa mini inda kike ɓoye kayan can bayan wardrobe ɗinku ne, idan ba wanda ya san da gurin a ɗakin ba ta yaya za a ɗauki kayan? Aiko ɓarawo ne ma duk ƙwarewar shi a sata ba zai yi tunanin da abu a gurin ba, sannan kuma a yadda kika faɗa mini mijin naki ya ƙyale ki kina yin abin da kike so ya isa ya sa ki gane wata gadar zaren yake shirya miki, ya yi miki lumbu-lumbu ya kwashe kayan. Kin san tsadar kuɗin sarƙar nan kuwa? Ya na ganin shi bai mallaki kuɗinta ba ke kin mallaka ai ko don baƙinciki da hassada ya ɗauke. Na san halin mazaje irin naki talakawa da yawa, kullum matansu cikin kawo mana complain suke idan sun zo neman taimako, talaka akwai baƙar zuciya da mugun hali, ba sa so su ga matansu sun fi su cigaba, don haka tun wuri gara ki farka daga mummunan bacci da kike ki san abin yi." Shiru na yi ina nazarin maganganunta, wani ɓarin na zuciyata ya yarda da ita, wani kuma ya na jaddada mini ko duniya da abin da yake cikinta na mallaka Anas ba zai taɓa ɗaukar mini ko tsinke ba, idan ban ba shi ba. Cikin rashin sanin wanne ɓangare na zuciyar tawa zan bi na ce. "Bai taɓa ɗaukar mini abu ba fa, gaskiya ba shi ya ɗauka ba, sai dai in....." "To waye?" Maman Nasmah ta katse ni cikin kufula. Ban ba ta amsa ba ta ci gaba da faɗin. "Da kike cewa bai taɓa ɗaukar miki abu ba kin taɓa mallakar abun miliyoyi ne? Million ai ba dubu ba ce, da zan faɗa miki price ɗin sarƙar nan sai kin riƙe baki, mantawa na yi ma ban haɗo miki da receipt ɗinta ba. Ni gaskiya nake faɗa miki, saboda na ga so ya rufe miki ido, mutum ba ya son cigabanki ya ga kin samu abin duniya ya sace amma kina yabon shi, just common waya ya siya miki ya kasa saboda maƙo amma kike tunanin ba zai ɗauki abin miliyoyi ba, wa ya sani ma ko ya daɗe da yin cinikinta sai yau ya fake ki ya ɗauka ya kai aka ba shi kuɗin, ina nuna miki haske kina ƙara luluƙa kanki cikin duhu. Amma tunda kin ƙi ganewa bari na ƙyale ki, gaba idan ya kuma tafka miki wata babbar satar kya yarda don dole a lokacin da dare ya yi miki, tunda na nusar da ke tun farko don ki yi wa tufkar hanci amma kin ƙi fahimta." A razane na miƙe tsaye daga zaunen da nake, don zuwa yanzu na fuskanci gaskiya Maman Nasmah take faɗa mini, idan na yi la'akari da yadda yau Anas bai dawo gida ba daga kai su Sultan tahfiz, alhalin ko karyawa da wanka bai yi ba, kuma hakan ba ɗabi'ar shi ba ce, tabbacin ya tafi siyar da kayan kenan. Jijjiga kai na yi ina jin kamar zuciyata za ta fashe na ce. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Me ya sa Anas zai mun haka? Sai ana i gobe taronmu zai mun wannan tozarcin?" "Baƙin halin talaka kenan, ke kuwa kya fita a gan ki fess sanye da ɗanƙareriyar sarƙar gold shi kuma yana fama da kaya duk fenti?" "To wallahi bai isa ba! Bari ya dawo gidan sai ya fito mini da kayana." Maman Nasmah ta ce. "Atou, ki zage ki zabga masa rashin mutunci da tijara ya fito miki da kayanki, kar ki sake ki raga masa ko na sisi, wannan miji naki ai jaraba ne, ga tsiya ga sata, ban da ƙaddara ai kin wuce ajinsa, yadda kike Black beauty ɗin nan ai da manyan alhazawa kika dace, kwata-kwata ba ki yi dace da miji ba." Rasa abin cewa na yi saboda tsabar baƙinciki da takaici, cikin kuka na ce. "Na gode sosai Maman Nasmah, zuwanki cikin rayuwata alkhairi ne, tunda ga shi kina fayyace mini abubuwan da ban taɓa tunanin za su faru ba, na gode da nusar da ni ɗin nan kika yi." Ta ce. "Haba, mene na godiya, ai na faɗa miki tamkar ƴar'uwata ta jini haka na ɗauke ki, don haka babu godiya a tsakaninmu, abin da nake so da ke kawai duk wani abu da ya shige miki duhu ki faɗa mini zan ba ki shawara in sha Allah." Na ce. "Na gode, zan kira ki anjima na faɗa miki duk yadda muka yi da shi." Ta ce. "Allah ya kai mu, ina ƙara jaddada miki dai kar ki raga masa fa, ki buɗe masa wuta ya fito miki da kayanki." Na ce. "In sha Allahu." Tare da kashe wayar na yi cilli da ita cikin ƙunar zuci kamar ita ce Anas ɗin. Wani irin tafarfasa da turirin bala'i ne kawai yake kai kawo a cikinta. Maganganun Maman Nasmah sun yi zaman kafaffen rodi a cikin zuciyata, na yi amanna da yarda da su ɗari bisa ɗari, don a yanzu ko tantama ba na yi Abban Sultan ne ya sace mini kayana. Rasa inda zan saka kaina na ji daɗi na yi, na dinga safa da marwa daga tsakar gida zuwa ɗaki kamar zautacciya, filin zuciyata cike da tanadin tulin buhunhunan tijara da rashin mutuncin da zan zazzage a kan Anas. Ina bakin ƙofar soro na haɗa kaina da bango na ji an buɗe ƙofar gidan an shigo, kamar wadda ta ga abin tsoro haka na ɗago kaina da sauri na bi shi da mugun kallo, ban amsa sallamar da ya yi ba na fara magana cikin ɗaga murya. "Ina kayana? Kar ka ce mini komai kawai ka fito mun da kayana." Sororo ya yi yana kallo na cikin rashin fahimta, fuskarsa ɗauke da maɗaukakin mamaki ya ce. "Rashin kayan ne ya zautar da ke haka kike sunbatu marasa kan gado?" A fusace na ce. "Idan akwai abin da ya fi mahaukaciya ka kira ni da shi ma Anas bai dame ni ba, abin da na sani kawai wallahi sai ka dawo mun da abuna, ka je duk inda ka kai ma ko ka siyar da ka sata ka karɓo k...." "Sata kuma? Ni kike alaƙantawa da sata yau? Me zan yi miki da kayanki? Me za su ƙare ni da shi?" Ya yi maganar yana nuna kansa cikin ɓacin rai. Ɗage kafaɗa na yi na ce. "Oho maka, ka na tsammanin ba zan gane kai ba ne ka sata? Daga ni sai kai a gidan idan ba kai ba wa zai ɗauka?" Girgiza kai ya yi cikin takaici ya ce. "Wallahi Hafsah inda kika ajiye kayanki ma ban sani ba bare na ɗauka, rantsuwa ba ɗabi'ata ba ce kin sani, amma na rantse miki da zatin Allah ba ni na ɗaukar miki kayanki ba, ki dai tuna ko kin cilla su wani gurin kin manta, ban da haka wa zai ɗaukar miki? Wa ma ya shigo gidan?" "Kai mana!" Na faɗa ina zabga masa harara. Numfashi ya sauke ya ce. "Da farko na ɗauka da wasa kike da kika nuna kike zargi, amma yanzu ban ga alamar hakan a tattare da ke ba, ban taɓa tunanin akwai ranar da za ta zo a rayuwarmu ki alaƙanta ni da sata ba, kin fi kowa sani na da abin da zan aikata da wanda ba zan yi ba, ban san me na yi miki ba Hafsah kika zaɓi ki ta ɓata mini rai, kar ki kai ni bango na yanke hukuncin da duk ba zai mana daɗi ba." Baki na taɓe na ce. "An yi walƙiya na ga duk wasu mugayen halinka da a da son ka ya rufe mini ido ba na gani, don haka ko me za ka yi ka daɗe ba ka yi ba, ƙarƙari ka ce za ka sake ni ko? To idan ba ka sani ba ma ka sani shi na fi buƙata a yanzu, don in na rabu da kai wanda ya fi ka komai da komai zan aura." Taune leɓensa ya yi yana hucin ɓacin rai ya ce. "Huɗubar da suke yi miki kenan?" Na ce. "Oho maka, ni dai yanzu ba dogon surutu na nema ba, kawai ka fito mini da kayana, don ba ka siya mini ba, ba ka isa ka ɗauke wanda aka ba ni ba wallahi." Ya ce. "Sai ki yi ta yi, Allah ne shaidata kuma shi zai bayyana gaskiya." Cikin zaƙalƙala na riƙe ƙugu na ce. "Aikin banza, gayyar tsiya kawai da rashin zuciyata, ban da mugun hali babu abin da mutum ya iya, ko da yake an ce gado ba karambani ba ai, tunda ba ka tashi ka ga ana yi a gidanku ba ai kai ma ba ka yi a gidanka ba." Cak ya tsaya daga ƙoƙarin shiga ɗakin da yake, ya juyo ya zuba mini idanunsa da suka yi jajir ɗin bacin rai, muryarsa na rawa ya ce. "Hafsah! Me kike nufi?" Ba tare da tsoro ko dogon nazarin sakamakon da maganata za ta janyo ba na ce. "Abin da yake akwai shi nake nufi, wanda ya kasa riƙe ɗansa ya turo shi almajiranci ta yaya zai iya kula da matarsa har ya yi mata duk abin da take so? Ka ga kenan ba a ƙasa ka ɗauka ba." Jikinsa har tsuma yake saboda tsananin fushi da ɓacin rai, don da farko na ɗauka duka ne zai yi idan ya ƙaraso inda nake, amma sai na ga ya kama hannayena ya damƙe a cikin nasa, muryarsa kamar mai shirin fashewa da kuka ya ce. "Cin mutuncin har da iyayena da suke ƙasa Hafsah? Kar ki fara don Allah! Kar ki fara abin da zuciyata ba za ta ɗauka ba wato sako iyayena a cikin sabgar mu, don ba zan jure ba, zuciyata za ta iya tunzura ni na aikata abin da ban yi niyya ba, kar ki bari mu yi asarar juna saboda wasu can da ba ki san su ba, ba ki san da alkhairi suke nufin ki ko da sharri ba. Please na roƙe ki ko dan su Sultan, ina son ki, ban shirya rabuwa da ke. Kuma kar ki manta yanzu igiyar aurenmu saura biyu, furucin da na yi a baya na idan kika fita a bakin aurenki ya riga ya tabbata saboda kin fitan, na shiga tashin hankali a sanadin hakan, amma ke na ga ko a jikinki, to don girman Allah kar ki bari saura biyun ma su tsinke mana." Dogon tsaki na ja tare da fizge hannuna, ko kaɗan ban ji tausayinsa ko kuma na ji kalamansa sun ratsa ni ba, sai ma wani irin haushin shi da ya ƙara rufe ni, musamman da na tuno gobe ne taronmu, kuma shi nake zargi da sace abubuwan da za su saka na zama tauraruwa a taron, da kuma baƙincikin ƙin siyo mini wayar da ya yi, alhalin matan group ɗinmu komai suke so mazajensu suna yi musu cikin gaggawa. Ga uwa uba huɗubar Maman Nasmah, da ta dinga jaddada mini na tabbatar na matuƙar ɓata masa rai, ya ji babu daɗi shi ma kamar yadda na ji. Cikin son ƙara ƙona masa rai na ce. "Ai da ma wanzami ba ya son jarfa, to tunda ba ka so in dinga taɓa maka Iyaye, ka sake ni na je na auri wanda zai so ni, ya gatanta ni, ya yi mini duk abin da nake so a duniya, mai kuɗi ba faƙiri irinka ba." Bai ce komai ba ya juya kamar zai tashi sama alamun ba ya son ci gaba da jin maganganun da nake yi. Jikinsa sai kyarmar tsantsar ɓacin rai yake. Da sauri na bi bayansa na riƙo rigarsa, cikin fitsara na ce. "Na gaji! Na gaji da wannan takaicin naka! Ka sawwaƙe mini idan ka cika ɗan halak a cikin Binta da Musa!" Ban san lokacin da ya juyo ba sai ji kawai na yi ya ɗauke ni da wani wawan mari da ya saka ni kifawa. Da sauri na dafe kuncina tare da ɗaga kaina na kalle shi ina hawaye. Sai na ga shi ma nasa idanun da suka kaɗa suka yi jajir cike suke da ƙwalla, muryarsa a dashe saboda tsananin tashin hankali da ɓacin rai ya ce. "Ki je na sake ki Hafsah!".......✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:39 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGH PENS* (FREE BATCH) 12. Tamkar saukar aradu da ka haka na ji furucin nasa a tsakiyar kaina, wani irin abu mai zafi da zugi ya baƙunci zuciyata. Lokaci ɗaya na nemi zafin marin da ya mini na rasa, saboda wanda nake ji a cikin zuciyata sakamakon sakin da ya mun ya ninninka shi. Da ma haka sakin yake? Haka mata suke ji idan aka yi musu shi ko da su suka nema? Ji na yi duniyar tana juya mini, na daina fahimtar komai na wucen gadi. Sama-sama na ji muryar Naja ƙawata da ban san lokacin da ta shigo gidan ba tana rafka salati, tare da ƙarasowa ta kama ni a inda na ƙame kamar mutummutumi ta shigar da ni parlour ta zaunar a kan kujera. Ko da wasa ban taɓa tunanin ko me zan yi wa Anas zai iya saki na ba, na ɗauka ko da zan dinga yankar naman jikinsa ina gasawa saboda azabtarwa ba zai iya rabuwa da ni ba, saboda matsananciyar soyayyar da na san yana mini. Numfarfashi kawai nake yi. Naja da ke riƙe ni har lokacin tana sallallami ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Hafsah me ya faru? Me ya haɗa ku da Abban Sultan? Don Allah ki ce abin da suka ziyarci kunnena lokacin da na shigo gidan nan ƙarya ne, kunnen nawa ne bai ji mini daidai ba." Girgiza kaina na yi ina hawaye na ce. "Daidai ki ji Naja'atu, kuma ni na buƙaci hakan da kaina." Ja baya ta yi a ruɗe ta ce. "Subhanallahi! Me ya yi zafi har haka ke kuwa? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Da na san abin da zan tarar kenan da wallahi ba zan zo ba." Gimtse baki na yi tare da share hawayena na ƙwace daga riƙon da ta yi mini na dafe kaina tare da lumshe idona. A hankali a hankali na ji zafin sakin yana raguwa daga cikin raina, ina kallon Naja da ta ishe ni da tambayar sanin ba'asi na ce. "Me ya sa kika damu ne haka? Mene a ciki don na rabu da Anas?" Kallon mara hankali ta mun ta ce. "Ba don na gan ki fes kin ƙara fresh da kyau ba da sai na ce kina cikin mayen hauka ne, na zo na tarar da ku cikin tashin hankali ke da mijinki har ya sake ki sannan kuma ki ce me ya sa zan damu?" Murmushi na yi don a yanzu ba ta Anas da sakin ya yi mini nake ba, duk da ina jin ɗacin abun matuƙa a cikin raina, taron da za mu yi gobe da abin da zan saka shi ne kawai danuwata. "Me ya sa idan na kikkira ki ba kya ɗagawa? Idan na yi miki magana a Whatsapp ba kya dubawa bare ki mun reply?" Hararar ta na yi na ce. "Saboda kin gama kunce mini zani a kasuwa mana, na yi ƙarya da ke amma kika ce wa Anas ba ki san zancen ba." Gyara zama ta yi ta ce. "Shi ne dalilin da ya sa nake ta kiran naki ai, na ji dalilin da ya sa kika aikata hakan." Baki na taɓe na ce. "Ya riga ya wuce ai." Na ƙarashe maganar ina miƙewa don fara haɗa kayana na bar wa Anas akurkin gidansa. Naja da har lokacin na lura a cikin ruɗu take ta kamo hannuna kamar za ta yi kuka ta ce. "Hafsah kin bar ni a cikin duhu fa, don girman Allah ki faɗa mini abin da yake faruwa, na ga kin ware kamar ba wadda take cikin zullumi ba." Komawa na yi na zauna don na labarta mata duk abin da yake faruwa, saboda Naja ta wuce ƙawa ko aminiya a gurina, ta zamo ƴar'uwa da ba zan iya ɓoye mata komai nawa ba. Cikin takaici na ce. "Naja Anas ba so na yake yi ba kamar yadda yake pretending, na yi da na sanin auren shi." A zabure ta ce. "Kamar ya? Ban gane ba?" Tsaki na ja na ce. "Matan da mazajensu suke son su, suke yi musu duk abin da suke so a lokacin da suke so bayan wadata su da suka yi da komai na more rayuwa suna can daban, amma ni ko kusa ba na cikinsu, ba na cikin mata masu sa'a da ake kwatance da su, ake sha'awar su, ake burin samun mazaje irin nasu." Na ƙarashe maganar kamar zan fashe da kuka. Galala ta yi tana kallo na ba ta ce komai ba. Numfashi na sauke na ce. "Ba ki gane me nake nufi ba ko? Yanzu zan ganar da ke." Ban jira amsarta ba na kwashe labarin komai na faɗa mata. A matuƙar gigice na ga ta miƙewa kamar wadda na faɗawa ranar mutuwarta, tana nuna ni da hannu ta ce. "A'uzubillah! Hafsah da ma ba ki da hankali? Ashe mahaukaciya ce ke ban sani ba?" Haɗe rai na yi na ce. "Haukan uban me na yi?" A fusace ta ce. "Ban sani ba, wallahi ba don na kai zuciyata nesa ba da sai na kikkifa miki mari, kamar na rufe ki da duka haka nake ji, I'm speechless! Na rasa me zan ce miki, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Ta ƙarashe maganar tare da dafe kanta. Tsaki na ja ban ce komai ba. Komawa ta yi ta zauna tana bi na da wani irin kallo, idanunta cike da hawaye ta fara magana da faɗin. "Ko a mafarki aka ce mini za ki aikata wannan tafkeken haukan da jahilcin ba zan taɓa yarda ba, yaushe kika haukace Hafsah? Yaushe kika daina amfani da ƙwaƙwalwarki wajen yin al'amuranki? Ina iliminki na addininki yake? Kin watsar saboda son duniya da hangen dala ko?" Shiru na yi ban ce komai ba. Kamar za ta rufe ni da duka ta ce. "Kin ba ni matuƙar mamaki da kunya, akan wani banzan group kika bari salihin miji irin Anas ya yi miki har saki biyu? Saura igiya ɗaya fa a tsakaninku yanzu? Saboda wasu tsinannu Hafsah!" Ta ƙarashe maganar cikin ƙaraji. Kallon banza na yi mata na ce. "Saboda sun haska mini abin da ban sani ba na rayuwa shi ne suka zama tsinannu? Ki yi mini duk zagin da za ki mini amma ban da su, don ni sun gama yi mini komai a rayuwa." "Sun gama kam, tunda sun cuce ki sun kashe miki aure, su kuma suna can zaune lafiya ƙalau da mazajensu." Naja ta faɗa tana jifa na da wani mugun kallo. Cikin tsagalgala na ce. "Ai su mazajensu ba talakawa ba ne, kuma da ma irin gidajensu ai ba a fatan a fita." Ta ce. "Haka ne, duk da na ga alamar kin yi nisa amma ba zan ƙi faɗa miki gaskiya ba, da tunatar da ke abin da gidahumar ƙwaƙwalwarki ta mantar da ke ba. Hafsah tun kina ƴar ƙarama a zanin goyo mahaifinki ya rasu, mahaifiyarki kuma bayan kin ɗan girma ba ki fi shekara uku ba ita ma ta bi bayan shi, daga lokacin aka dawo da ke gurin Kawu ya riƙe ki. Kawu ya yi miki riƙo na tsakani da Allah tamkar ƴar da ya haifa a cikinsa, kuma ya nuna miki soyayya saboda bai taɓa haihuwa ba, sanadiyyar hakan Gwaggo matarsa ta tsane ki, ta gana miki azaba. Ba sai na tuna miki irin uƙubar da kika sha a gurinta ba, saboda kin fi kowa sani. Yanzu idan kika bar nan kika koma gida a matsayin bazawara ya kike tunanin zamanku zai kaya ke da Gwaggo? Kina budurwa ma ba ta so ki ba balle a yanzu? Ko kin mata da wannan? Kuma idan ba gidan ba, ba ki da gurin zuwa, tunda dangin mahaifiyarki suna can Lafiya, tsakaninki da su waya ce ko chat, ba ki taɓa zuwa ba, su ma ban da lokacin bikinki ba su taɓa zuwa kun haɗu ba, can kike tunanin za ki je ki yi zawarcin a haka? Ba su saba da ke ba, ba ki taɓa zuwar musu ba, kawai sai su gan ki rana tsaka ki ce musu aurenki ne ya mutu kika koma? Ki yi aiki da hankalinki ki yi tunanin abin da zai fishshe ki, takamaiman gurin da za ki je ki zauna ma ki ji daɗi ba ki da shi idan kin bar nan ɗin, amma a haka kika kashe aurenki?" Shiru na yi don maganganunta sun fara ratsa ni, amma duk da haka ba su saka na ji zan saduda ba. Ganin haka ta ci gaba da magana da faɗin. "Abu na biyu kuma, samun mijin da yake son ka tsakani da Allah ma kamar yadda Anas yake son ki a wannan zamanin wahala yake, ya so ki tun kina ƴar ficiciyarki, ba ki san kanki ba, bare ki yi kwalliya da za a ce ita ta ja hankalinsa gare ki, kuma a lokacin ko alamar zama budurwa ba ki fara ba, bare ya ce ya ga kyanki ko jikinki ya so ki don su, hasalima a cikin rayuwar wahala da ƙuncin rayuwa ya gan ki, ya fara da jin tausayinki daga nan ya rikiɗe ya koma soyayya. Babu gatanta kin da bai yi ba tun kina gida har zuwa aurenku daidai ƙarfin ikonsa. Soyayya, kulawa, darajawa, babu wanda bai nuna miki ba. Ya taya ki aikin gida, ya kai ki unguwa da kansa, ya ɗauke miki dukkan wata ɗawainiyarki, da kika haifi ƴaƴa bai canza miki ba kamar yadda wasu mazan suke yi, ya rungume ku ke da yaranki kuka ci gaba da rayuwa cikin farinciki da annushuwa. Anas bai taɓa ragar ki da komai ba, to me kike nema a gurin miji da ya fi wannan? Me kike da buƙata? Ke ba matsalar kishiya, ba ta uwar miji, ba ta ƙannensa ko yayye ba, miji ba ya dukanki, ba ya cin mutuncinki bare zagi. Amma saboda hauka ki dinga hangen na wasu can da ba ki san irin taskun rayuwar da suke ciki ba, wallahi Maman Sultan daɗi ne ya yi miki yawa, da kuma kin samu Anas ɗin mai haƙuri. Da ma an ce samu mai saka hauka." Baki na zunɓura na ce. "Hmm, duk waɗannan bayanan naki kin san dai na fi ki sanin da su ko?" Ta ce. "Eh, amma ba kya duba su ai." Na ce. "Eh, saboda ni yanzu ba su ne a gabana ba." Naja da take jin kamar ta rufe ni da duka ta ce. "Ƙaton gida da hawa manyan motoci su ne a gabanki ko? Ki faɗa mini matar da kika sani da always mijinta ne yake saka mata data da katin da za ta yi waya, idan za ta je unguwa ko'ina ne ya ba ta transport, na tabbata da za ki cikiya kafin ki samu ɗaya sai kin samu 50 da ba a yi musu. Ke fa tsabar daɗi ko sana'a ba ki taɓa gwadawa ba, saboda ba ki da buƙatar komai, yi miki ake kina daga kwance ƴar gata. Kuma ko ma ba wannan ba, kwanciyar hankali ya fi komai a rayuwar nan, ka ci ka sha, ka yi ibada ba wani tension ka yi baccinka, me ya fi wannan daɗi? Anas shi ne gatanki, shi ne suturarki, shi ne rufin asirinki, ko kaffara ba zan yi ba idan kika rabu da Anas ba za ki taɓa samun miji kamar shi ba, don irinsu a yanzu ba su da yawa, sun yi ƙaranci." Da sauri na ce. "Zan samu wanda ya fi shi mana, sosai ma." Murmushin takaici ta yi ta ce. "Ban san lokacin da kika koma mayyar kuɗi ba, idan kuɗi kike nufin za ki samu wanda ya fi Anas za ki samu sosai ma, amma samun mai nagartar shi ne zai yi miki wahala. Ana cewa mazan aure sun yi ƙaranci, ba ƙaranci suka yi ba, samun nagari nagartacce ne ya yi wahala. Kin gan ni nan, ban rasa mijin aure wanda zai aure ni ba, amma na rasa nagartacce wanda nake da yaƙiyin zai riƙe ni saboda Allah ya kyautata mini, wanda ya san ma mene ne auren, don matsalar da take damun mu yanzu majority ana auren ne kawai ba don an san mene ne shi ba, ba don an ɗauke shi ibada ba, ana yin shi ne don wata buƙata, ko a bi kyau, ko kuɗi, ko neman ɗaukaka, ko dan a ce mutum ya yi auren shi ma, gabaɗaya ba ga matan ba, ba ga mazan ba, duk an daina aure saboda Allah da bauta masa, ƙalilan ne masu yi don haka. Wasu kuma ilimin zaman auren ma da yadda za su tafiyar da junansu a zamantakewar auren ne ba su da shi. Rimi-rimi za ki ga mutum ya zo mini da gaske da niyyar aure, amma daga mun yi dogon zama zan gane ba za mu zauna inuwa ɗaya ba, masu kuɗin da masu kyan da talakawan duk suna zuwa, amma samun nagartaccen a ciki ya yi wahala, saboda Juma'ar da za ta yi kyawu tun daga Laraba ake gane ta. Maza na gari sun yi wahala Hafsah, ki riƙe mijinki gagam wallahi, idan ba haka ba za ki yi da na sani mara amfani, za ki yi nadama a lokacin da time ya ƙure miki, za ki yi saki na dafe. Yanzu da za ki yi shela ki fadi halin Abban Sultan ki ce idan da mai son shi za ki bari ta aure shi sai kin ga mata dubu sun zo, kuma da kike ta cewa talauci ai shi ba talaka ba ne, yana da rufin asirinsa, bai taɓa gazawa ba tunda kuka yi aure. Na ga gidan hayar da kuka fara zama kafin Allah ya hore masa ku yi naku, abokan hayar taku sha'awar ku suka dinga yi, yadda yake kula da ke da tattalin ki, ya ba ki lokacinsa. Mama kullum cikin sam barka take yi miki, kullum aka tashi zance aka ce maza sun zama ƴan kansu yanzu sai ta bayar da misali da ku, ta ce ƙawar Naja kuwa ta yi dace da mijin marainiya, Allah ka ba wa ƴaƴanmu irinsa." Baki na taɓe don ni gabaɗaya hankalina yana kan yadda za a yi na fito fes a taronmu na ce. "Sai faɗar alkhairinsa kike amma ban ji kin faɗi aibunsa ko ɗaya ba, mutumin da yake zuba mun uban kulle, kamar wata kayan kadara." Numfashi ta sauke ta ce. "Alkhairin nasa ne ya fi aibun yawa, kulle kuma tabbas na san yana da shi, kuma da ma ai ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, amma duk da haka ai ba ya hana ki zuwa biki ko sunan dangi da na maƙota, duk abin da ya faru na jaje yana barin ki, ki je, fita ce haka barkatai babu dalili yake hanawa, ko so kike ya bar ki kina wuni a maƙota da gantali a unguwa?" Hararar ta na yi na ce. "Ban sani ba, tunda ba ke ake turkewa a gidan kamar akuya ba ai dole ki ce haka. Nan gidan Maman Sadik ga baki ga hanci, jikin gidana amma sai na yi watanni ban je mata ba, tun suna shigowa su har sun gaji sun daina saboda ba na zuwa." "To me za ki je ki yi musu? Na ga Asma'u cousin ɗita da suka zuna a bayan layin nan yabon ki ta dinga yi, lokacin da aka yi wani faɗa har da zuwa police station, a saboda irin yawon gulmace-gulmacen nan da ake yi na bin gidan maƙota kullum, ta ce kin huta abinki, ko me za a yi na tashin hankali babu ke a ciki, asirinki a rufe. Amma ke kin raina hakan ko?" Na ce. "Ai shi saboda kar na fita na ga halin da duniya da take ciki ne ya sa yake kullen, kar kuma na ga yadda maza suke bauta wa matansu tunda shi ba ya yi." Naja ta ce. "Ko? To kar ki nutsu ki san inda yake yi miki ciwo, duk da zan yi miki uzurin rashin sanin halin da duniya take ciki, na rayuwar ƙarya da packaging da mutane suka ɗaura wa kansu, shi ya sa kike ganin kamar su waɗancan matan komai gaskiya suke faɗa. Tunda babbar wayar ma ba ki daɗe da fara riƙe ta ba." Cikin ƙosawa da jawabanta na ce. "Su fa ba maƙaryata ba ne, saboda sun sassan gidajen juna suna zumunci, idan ƙarya suke ai ba za su bari a je inda suke ba." Jinjina kai ta yi ta ce. "Ni fa ban ce ba masu kuɗi ba ne, amma ba zai yiwu a ce duka group ɗin ke kaɗai ce talaka kamar yadda kike faɗa ba, kuma masu kuɗi wanda suka tashi a cikinsa ba za su yi irin wannan banzar rayuwar ba, ta komai naka sai ka tura a group an gani, ka yi son a sani, sai dai ko ƴan taka haye ne ƴaƴan Malam Shehu suka auri masu kuɗi, shi ne ba a saba da rayuwar ba ake nuna wa duniya, ko kuma duk packaging ne kashe kai ake a yi abin ƙaryar. Kuma ko da ma masu kuɗin ne kina da tabbacin kowacce tana zaune lafiya cikin kwanciyar hankali kamar ki? Wata ƙila mijinta mai duka ne, wani ɗan shaye-shaye, wani mai bin mata ko maza, wani ma kuɗin ba na halak ba ne, ba ki san ta yadda suke samun su ba." Ɗaga mata hannu na yi na ce. "Kar ki yi musu mugun fata kuma." Murmushi ta sake yi ta ce. "Misali kawai nake ba ki, ba wai ina nufin hakan ba ne, kawai dai ina faɗa miki ne don na san ba za a rasa ba. And lastly yanzu ƙwarya ta bi ƙwarya ake yi, idan kina tunanin za ki kashe aurenki ki fita ki auri mai kuɗi to kin yaudari kanki, don kowa ɗan'uwansa yake aure, talaka sai talaka mai kuɗi sai mai kuɗi, sai dai ikon Allah da tsananin rabo ne yake saka mai kuɗi ya auri talaka." Miƙewa na yi a fusace na ce. "Ya ishe ki haka wannan cin fuskar da kike mun!" Ita ma miƙewar ta yi ta ce. "Idan na ci miki fuska ai kaina na ciwa Hafsah, gaskiya nake faɗa miki, kuma da ma an ce ɗaci gare ta, ki zauna, ki nutsu, ki yi nazari da kyau don Allah, ko don ƴaƴanki da ke kanki. Zan kira Anas mu yi magana da shi idan na koma gida, zan ce masa ni na hana ki tafiya, na san ba zai ƙi mayar da ke ɗakinki ba in sha Allah. Duk da na ga ransa a matuƙar ɓace ya bar gidan nan lokacin da na shigo, don ba na jin ma ya lura da ni. Please ƙawata ki watsar da mutanen can, ki manta da su, ki bar group ɗin ki goge numbers ɗinsu, ke ki canza sim ma gabaɗaya yadda ko sun kira ba su same ki ba, idan ba haka ba wallahi za su kai ki su baro." Na ce. "Na ji na gode." Bi na kawai ta tsaya tana yi da kallo na wasu sakanni. A sanyaye ta ce. "Idan kika bar Anas ba shi kaɗai kika butulcewa ba, har da ubangijin da ya tsamo ki daga cikin jarrabawar rayuwa, ke kuma kike ƙoƙarin siyen ta da kuɗinki. Kina da iliminki na addini daidai gwargwado, kin san arziƙi da talauci duk na Allah ne, a kullum Ubangiji cikin raba arziƙi yake da ƙwace shi, babu wanda aka haifa da dukiya, kowa da kika gani a nan gidan duniya ya samu kuma a nan zai bar shi. Don haka wannan kaɗai ya ishe ki darasi a rayuwa. Ƴaƴa da miji na gari da lafiya su ne babban arziƙi a duniyar nan, kuma duk Ubangiji ya ba ki su, maimakon ki gode masa sai ki raina?" Shiru na yi don zuwa yanzu maganganunta sun fara ratsa ni sosai, ganin haka ta dafa kafaɗata ta ce. "Zan tafi, ina fatan za ki yi amfani da dukkan shawarwarin da na ba ki, sannan kuma don girman Allah kar ki ƙara kwatanta haukan zagin Anas, bare ki taɓo iyayensa, ina jiye miki siyen ticket ɗin wutar jahannama da hannunki, tunda kin san hukuncin mai aikata abubuwan da kike yi a musulunci. Don haka idan kunne ya ji jiki ya tsira!" Daga haka ta ɗauki jakarta ta juya ta fice. Kasa kataɓus na yi na bi bayanta da kallo kawai cikin mutuwar jiki, gabaɗaya ta gama ɗaure ni da jijiyoyin jikina. Na shafe kusan mintuna biyar kafin na ja ƙafata na shiga ɗaki. Ringing na tarar wayata tana yi, na ƙarasa na lalubo ta na duba na ga har kiran ya katse, missed call sama da 10 na tarar na Maman Nasmah. Ban yi yunƙurin bin ta ba don na san ban da ishashshen katin da za mu yi doguwar magana. Wani kiran nata ne ya ƙara shigowa, tsayawa kawai na yi na ƙura wa wayar ido, zuciyata na kokwanton na ɗaga ko kar na ɗaga? Na bi shawarar Naja na fita daga group ɗin na manta da su na ci gaba da rayuwata kamar da, ko kuma na ci gaba da zama a cikinsu da burin kasancewa kamar su ko ta halin yaya?........✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:40 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *13.* Ban gama yanke shawara ba shi ma kiran ya katse, ko 1 second ba a yi ba wani ya ƙara shigowa. Ɗagawa na yi cikin son jin dalilin wannan uban kiran da take zabga mini. Cikin faɗa kamar wata uwata ta ce. "Ina kika ajiye wayar ne nake ta kiran ki ba ki ɗauka ba?" Ba yabo ba fallasa na ce. "Ina parlour ne, wayar kuma tana ɗaki." Ta ce. "Okay, ya kuka yi da shi? Ya dawo miki da kayan naki?" Numfashi na sauke na ce. "A'a, ya ce ba shi ya ɗauka ba, na haƙura kawai na bar wa Allah." Cikin zuzuta ta ce. "Kin ce gobe ya ƙara ɗauka kenan? Shikenan kin buɗe masa ƙofar jidar miki abubuwa, ina nan na kasa sukuni saboda tunanin halin baƙincikin da kike ciki ashe ke har kin ware? Tsabar yadda na damu da abun ko abinci ban iya ci ba tunda kika faɗa mini." A sanyaye na ce. "To ya zan yi? Na yi bala'in na yi masifar, ƙarshe har saki na ya yi fa." "Saki kuma?" Na ji ta faɗa a yanayin da na kasa tantance na murna ne ko kuma na ruɗu ne, saboda yadda ta yi kamar za ta fasa mini dodon kunne. Na ce. "Eh, kin ga ya zama biyu kenan, da na farkon nan da ya ce idan na fita a bakin aure na, na ɗauka baraza ce kawai ya yi, ashe da gaske yake." Cikin karsashi ta ce. "To shi ne me? Ai akan gaskiyarki kike, kuma duk abin da ya faru shi ne ya janyo da ya ƙi kula da ke ya yi miki dukkan abin da kike so, ƙarshe ya ƙara miki da sata." Shiru na yi ban ce komai ba, don na rasa abin faɗi. Cikin sassauta murya ta ce. "Amma ki kwantar da hankalinki, ki zo gidana yanzu, ga ɗinkinki nan an kawo ki zo ki karɓa, duk abubuwan da aka sace kuma zan ƙara ba ki sabbi, har wayar ma duk zan siya miki sabuwa dal, idan da wadda kike so sai ki faɗa a kawo ta, idan kuma ba ki da choice zan ce a kawo miki irin ta hannuna." Cikin farinciki na ce. "Da gaske za ki ƙara ba ni kayan, har da sarƙar gold ɗin?" Ta ce. "Mene a ciki? Yanzu ina yi wa Hubby waya zai saka a kawo komai, wannan ba komai ba ne ai a gurinsa, kuma ko me na ce masa ina so babu ɓata lokaci yake mun, so kar ki wani damu. Ina son ki fito fes kamar kowa ke ma a gobe." Dogon numfashi na ja na sauke na ce. "Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ya ƙara buɗi, ya bar ƙauna tsakaninki da mijinki." Ba ta amsa ba ta ce. "Ki yi maza ki zo, yanzu zan tura miki address ɗin." A gaggauce na shirya cikin doguwar rigar atamfa cikin zumuɗi. Jikina har tsuko yake saboda farinciki. Na yi niyyar bin shawarar Naja, amma sake ba ni kayan da Maman Nasmah ta ce za ta yi ya sa na manta da wata Naja'atu da batunta ma gabaɗaya. Ban damu da rashin dawowar su Sultan ba har biyu saura na fice daga gidan. Na samu mai napep muka tsadance ya kai ni har ƙofar gidan Maman Nasmah. Tun daga farkon unguwar tasu na tabbatar wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, saboda maka-makan gidajen da na fara tozali da su, sakin baki na yi ina ba wa na mujiyata abinci. Gabaɗaya sai na ƙara raina kaina. Muna tafe ina waya da ita tana faɗa mini inda zan na cewa mai napep ɗin ya bi. A bakin wani ƙatoton gida muka tsaya. Da sauri na zuro kaina kamar zan faɗo ina ƙare masa kallo, ban san lokacin da bakina ya furta. "Aljannar duniya." Ba. Sai da drivern ya mini magana sannan na dawo cikin hayyacina na fita na sallame shi. Ban san ya zan iya fasalta girma da ƙawatuwar gidan Maman Nasmah ba tun daga waje ma. Don ko tantama ba na yi idan na ɗaga kaina na ce zan hango ƙarshen tsayinsa sai ɗankwalin kaina ya faɗi. Ina nan tsaye da baki a buɗe aka buɗe ƙaramar ƙofar makeken gate ɗin gida, wani matashi ne ya ƙaraso inda nake ya ce. "Ke ce baƙuwar Hajiya?" Ɗaga masa kai na yi don ruɗewar da na yi ta hana ni magana. Ya yi gaba na bi bayan shi ina tuntuɓe saboda kalle-kalle. Mun yi tafiyar mintuna biyar kafin mu kai inda part ɗinta yake. Ya danna wani abu da ban san mene ne ba, babu jimawa aka buɗe ƙofar da ita ma ɗaukar ido take ya ce na shiga. Zan cire takalmi yarinyar da ta buɗe ƙofar ta ce na shigo da shi. Duk yadda na so sakaya ƙauyancina amma sai da ya bayyana kansa, saboda tsintar kaina da na yi a wani tsamfatsetsen parlour, wanda ya wadatu da fitilu masu wasu wani irin ƙyalƙyali da haske. Ajiyar zuciya na sauke na lumshe idona tare da ƙara baza hancina, don sake shaƙar sassanyan ƙamshin da yake tashi a parlourn a wadace. A iya tunanina ban taɓa tsammanin za a samu kamar wannan falon a Nigeria ba sai dai a ƙasar waje. Sai da muka wuce faluka uku, a na huɗu wanda yake upstairs muka tarar da Maman Nasmah. Fuskarta ɗauke da fara'a sosai ta taso ta rungume ni tare da yi mini sannu da zuwa. Na amsa cikin yaƙe, don ko mai aikinta da ta yi mini jagora ta fi ni kyan gani, don daga gani suturar jikinta ma ta fi tawa tsada. Ta zaunar da ni bayan ta baya wa yarinyar umarnin ta kawo mini drinks. Tana ta jana da hira amma na kasa sakin jikina, satar kallon parlour'n kawai nake ina faɗin. "ALLAHUMMA ARZUƘUNI" A cikin raina. Ita kanta sai na ga ta ƙara yi mini kyau fiye da ganin farko da yi mata, yadda ta hakimce a kan kujera cikin shiga ta alfarma tana latsa waya a gayance ba ƙaramin burge ni ya yi ba. Hakan ya ƙara girmamar burina na son rayuwar kuɗi da hutu. Ta wata ƙofa da ke cikin parlour'n ta shigar da ni inda dinning yake shi kaɗai da zan ci abinci, haɗuwar gurin da tsaruwar shi da kyawun dinning ba za su faɗu ba, food flaks ɗin da aka zuba abincin ma kaɗai abin kallo ne. A taƙaice dai duk yadda nake tunanin girma da ƙawatuwar gidan Maman Nasmah ya wuce nan, don tamkar rainon daji haka na koma saboda ƙauyanci. Bayan na yi Sallah ina zaune a bedroom ɗin da ta kai ni ta shigo ta ce. "Kamar kina  cikin damuwa ko?" Na ce mata. "A'a babu komai." Baki ta taɓe ta ce. "Ai ko kin ɓoye fuskarki ta fallasa ki, kuma na san ba zai wuce akan wancan mijin naki ba ne, da zuwa yanzu ya kamata a ce kin gane ba son ki yake ba, tunda har akan abu ƙanƙani ya iya sakin ki." Girgiza kai na yi na ce. "Wallahi ba shi ba ne, don yanzu da shi da babu duk ɗaya ne a gurina." Murmushi ta yi ta ce. "Ko ke fa, anjima za a kawo kayan naki, yanzu mai lalle ta zo tana parlour, mu je ta yi mana ko iya baƙi ne, tunda time ya ƙure ba damar yin ja." Na ce. "Tom shikenan." Ana yi mini lallen Maman Nasmah tana ƙara kushe Anas da aibata shi, da nuna mini ko ya dawo ya ce na koma kar na yarda, ni dai na yi shiru ban ce komai ba, don har yanzu zafin sakin bai bar sukar zuciyata ba. A ɓangaren Maman Nasmah kuwa wani irin farinciki da annashuwa take ji, duk da a plan ɗinta saki uku take so Anas ya yi wa Hafsah kafin ta shiga cikin rayuwarsa, ta yadda babu aure a tsakaninsu kenan bare ya ce zai mayar da ita. Tana lura da yadda ta ɗimauce da ganin gidanta, ta dinga murmushi a ranta tana faɗin. 'Kina burin kasancewa a cikin irin wannan daular, ni kuma ina burin kasancewa da mijinki da kike ganin shi a banza, wanda duk wannan daular da nake ciki ta kasa gamsar da ni da sanya ni a cikin farinciki, saboda rashin samun abokin rayuwa kamar shi.' Sai da Naja ta koma gida ta huta sannan ta kira Anas, duk da halin tashin hankalin da yake ciki da zazzaɓin da ya rufe shi lokaci ɗaya amma da sauri ya ɗaga yana fatan Allah ya sa zancen Hafsah za ta yi masa, saboda duk da abin da ta yi masa ko kaɗan son ta bai ragu a cikin zuciyarsa ba. Bayan Naja ta yi sallama ya amsa ta ce. "Abban Sultan idan babu damuwa ina son don Allah mu yi wata magana ne da kai, idan kana free yanzu, in kuma kana abu idan ka gama sai ka kira ni." Ya ce. "A'a babu abin da nake yi, ina sauraren ki." Ta ce. "To Masha Allah, ɗazu na zo gidanka na riski wani mummunan al'amari da bai mun daɗi ba ko kaɗan wallahi, ya kuma saka ni a cikin tashin hankali mara misaltuwa, kana nan ma na zo, amma saboda yanayin da kake ciki na san da ƙyar idan ka gan ni. Hafsah ta faɗa mini komai da yake faruwa, na yi mata faɗa sosai tare da ba ta shawarwari, kuma na ga alamar ta ɗauka daga yanayin yadda jikinta ya yi sanyi. Shi ya sa na kira na roƙi alfarmarka, akan don Allah ka yi haƙuri ba don halinta ba, ka mayar da ita ɗakinta, saboda tana gidan ma a can na baro ta, na hana ta tafiya." Numfashi ya sauke ya ce. "Anya kuwa Hafsah za ta risina? Don abubuwanta sun daina ba ni mamaki yanzu sai dai tsoro. Don da farko ma na yi tunanin ba ta cikin hayyacinta ne, sai daga baya na gane tsantsar iskanci ne da burin shirme da ruɗin shaiɗan." Naja ta ce. "In sha Allahu ba za ta sake ba, ka yi haƙuri, ta faɗa mini komai babu abin da ta ɓoye mun, amma ni na yi mata uzuri, saboda rashin mai ba ta shawara da ƙarancin wayewa sun taka muhimmiyar rawa a wajen habbaƙa al'amarin nan, amma komai ya zo ƙarshe in sha Allahu, zan kawo Mama da kaina har gidan ta ƙara yi mata faɗa, ba na son Kawu ya ji zancen nan, don kansa duk son da yake yi mata sai ya kusa balla ta." Ya ce. "Tom shikenan Naja, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, amma da na so na bar ta, ta je gida ta huta, idan ta gaji da zaman gidan ne." Naja ta ce. "A'a fa, da yardar mai duka komai ya zo ƙarshe, kuma kai ma da ka sani ka ƙwace wayar tata ka karya sim ɗin da ka fuskanci inda matsalar take. Da may be abun bai yi tsamari haka ba."  Ya ce. "To ai ba ta bari mun yi magana ma ta fahimta ba bare na gane inda matsalar take, sai dai kawai ɗan abun da na fahimta daga maganganunta na baya da gugar zanan da ta dinga mun, da zuwan wata ƙawarta gidan." Cikin takaici Naja ta ce. "Allah ya kyauta ya ƙara ganar da ita, Da iliminta amma na rasa inda ta ajiye shi ta ɗauki kishiyarsa." Ya ce. "Ni ma mamakin da nake yi kenan, don ban taɓa zaton za ta iya ambaton sunan mahaifana ƙarara ta haɗa kuma da cin mutunci ba." "Ka yi haƙuri, na san ta yi hauka da wauta, kuma ta ɓata maka rai matuƙa, amma ka taimaka ka mayar da ita, ba na son na ga kun rabu wallahi, ba na son ta yi asarar miji irinka." Runtse idonsa ya yi don har lokacin muryar Hafsah ba ta daina yi masa kuwwa a kunne ba, a sanyaye ya ce. "Shikenan na mayar da ita, Allah ya sa ta yi nadamar abubuwan da ta aikata har cikin zuciyarta." Ajiyar zuciya Naja ta sauke ta ce. "Amin ya rabb, na gode sosai da ka fahimci ni da kuma wannan alfarmar da ka mun, Ubangiji ya ƙara muku zaman lafiya da kwanciyar hankali, Allah ya kaɗe fitina a tsakaninku da sharrin shaiɗan, ya sa makamancin hakan ba za ta kuma faruwa ba." Ya ce. "Amin ya hayyu ya ƙayyum, ke ma Allah ya ba ki miji na gari." Murmushi ta yi ta yi masa sallama ta katse wayar. Shiru ya yi yana tunanin rayuwarsu ta da shi da Hafsah, ya so rabuwa da ita na har abada ko don ya nuna mata daraja da ƙimar da iyayensa suke da shi a wajensa, amma darajar su Sultan da kyautatawar da ta yi masa a da su saka sanya ya amince ya mayar da ita. Amma ba zai koma gidan ba a yau, su Sultan ma ba zai mayar da su ba, don da ma da ya ɗauko su ɗazu daga tahfiz gidan wani abokinsa ya kai su, ya ce musu Hafsan ta je unguwa ne. Ya san Naja za ta kira ta, ta faɗa mata duk yadda suka yi, zai gani idan za ta neme shi, inda da gaske ta yi nadamar abubuwan da ta yi masan. Bayan Magriba na ce wa Maman Nasmah zan koma gida, don na san zuwa yanzu Naja sun yi magana da Anas kamar yadda ta alƙawarta, kuma na san ba zai ƙi mayar da ni ba, duk da ba ni da tabbas, don ban taɓa yi masa irin ko da makamancin irin wannan laifin ba na taɓa mahaifansa. Ga shi wayata ta ɗauke ta ƙi kunnuwa gabaɗaya, bare na kira ta ko ita ta kira ni. Hana ni tafiya Maman Nasmah ta yi, ta dinga yi mini faɗa kamar za ta ari baki, wai shi bai neme ni ba, bai mayar da ni ba amma zan komar da kaina saboda zubar da aji da rashin sanin ciwon kai, ta takura sai na kwana a gidanta, gobe inda an gama komai sai na tafi. Don dole ba don son raina ba na amince. A daren muka je saloon aka yi mana wankin kai da na ƙafa, aka kuma kawo mini kayana da sabuwar waya kamar yadda ta faɗa, har da kuɗin liƙi sabbin ƴan ɗari biyar-biyar. Farinciki, murna da ɗoki suka saka na manta da Anas da babinsa, na ci gaba da shirin taronmu da za mu cashe mu raƙashe a gobe. Kallon Hafsah kawai Maman Nasmah take tana yi mata murmushin mugunta a zuciyarta, saboda ita kaɗai ta san me ta shirya mata a wannan kwanan da za ta yi a gidanta.......✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:40 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *14.* Har sha biyu na dare ta wuce ban yi bacci ba, ina zaune a tsakiyar makeken gadon da nake na tasa kayana a gaba ina aikin kallon su, sai jujjuya dalleliyar wayar nake a hannuna ina sakin murmushi. "Allah ka cika mini burina, ka nuna mini ranar da ni ma zan yi kyauta ga wani ninkin ba ninkin ɗin wannan." Na yi maganar ina bin bedroom ɗin da ya kusa rabin gidana gabaɗaya a girma da kallo. Gado, wardrobe, mudubi duk suna gefe ko rabin ɗakin ba su ci ba. Ƙuntataccen ɗakina na tuna, wanda space ɗinsa da ya rage bai fi ya ci ƙaramar tabarma biyu ba. Tsaki na ja na tattara kayan ba don na gaji da ganin su ba na kwanta. Sai na ji kuma na kasa baccin, duk da juyin da nake yi a gadon ina bararrajewa son raina. Tashi na yi na rage hasken ko shi ya hana baccin ɗauka ta. Amma still ya ƙi zuwa, tunanin Anas da su Sultan na ji ya cika zuciyata, wata irin kewar su da ban taɓa zaton yin ta ba ta ziyarce ni. Duk yadda na so na yakice su amma abu ya ci tura. Taune leɓena na yi ina ayyana da dare bai yi sosai ba sai na koma gidana a yau, don na gane ba zan taɓa iya rayuwa babu mijina da ƴaƴana ba, ko kuɗin da nake so da shi nake son mu yi ba wai mu rabu ma, amma shi ya ƙi gane hakan bare ya ba ni haɗin kai. Da ƙyar na samu bacci ya ɗauke ni lokacin da dare ya kusa rabawa. Washegari bayan na yi sallar asuba na koma bacci, sai bayan 10 na tashi muka fara shirin tafiya taronmu. Mai kwalliya ta musamman ce ta zo ta yi mana har gida ni da Maman Nasmah. Zuwa bayan azhar mun gama shiryawa cikin ankonmu. Na daɗe ina kallon kaina a mudubi saboda ba ƙaramin kyau na yi ba ni kaina na sani. Maman Nasmah ta dinga yi mini hoto a wayarta, don tawa har yanzu ba a kunna ta ba, ni ban iya using iphone ba ita kuma ta ce sai mun nutsu za ta saita mini komai. A wata luntsumemiyar mota mai numfashi muka tafi gidan Aunty Billy, muna baya driver yana gaba shi kaɗai. Sosai harabar gidan da aka yi wa decoration ya yi kyau, mun tarar da sama da mutum 20 a gidan sun zo. Da gudu wasu suka taho suka rungume Maman Nasmah, ta nuna musu ni, suka ce ko da ba ta faɗa ba sun san ni ce, saboda sun san duk inda suka gan ta za su gan ni a gurin, tunda kowa ya san ita ce babbar ƙawata a group ɗin. Zagewa na yi aka shiga hada-hada da ni, ina jin kaina kamar kowa tunda na saka gold da sauran kayan kwalliya masu tsada. Sama da mutane 60 ne suka halarci taron, kuma duk ƴan group ɗin namu ne, kowacce kuma ta saka anko, ta yi ɗinki mai tsada da sarƙar gold ɗin da aka ce. Sosai muka yi kyau kamar yadda muke fata. An ci an sha, an yi rawa an cashe an tattauna, abin gwanin ban burgewa. Hakan sai ya ƙara mini son group ɗin sosai, na ji ko me za a yi ba zan fita daga cikinsa ba. Mun sha hotuna da video kamar ba gobe. Sai da aka kusa tashi Maman Nasmah ta saka mini sim ɗina a cikin sabuwar wayar, ta nuna mini yadda zan yi kira da wasu ƴan abubuwan, sauran kuma ta ce sai mun koma gida za ta nuna mini. Kaf matan da suka zo taron babu wadda ta kai ni duhu, saboda kowacce sai na gan ta fara ƙal, waɗanda ba fararen sosai ba kuma duk sun fi ni haske, duk da gyaran jikin da aka mun, alaƙanta hakan na yi da don su matan masu kuɗi ne ni kuma matar talaka ce. Messages na gani da numbern Naja, na farko ta ce tana ta kira na a kashe, na biyu kuma ta ce ina ina? Ta zo gidan ba na nan, alamun tun jiya ta yi su kenan. Sai yau da ta ƙara cewa ta je da safe ba na nan, sai na ƙarshe kuma wanda da alama ba ta daɗe da yin shi ba, ta ce duk inda nake na koma gidana don Anas ya mayar da ni tun jiya, idan ba haka ba za ta je ta faɗa wa Kawu duk abin da yake faruwa. A tsorace na bar filin rawar da muke na ja Maman Nasmah gefe na ce. "Ni fa tafiya gida zan yi yanzu, na ga Magriba ta kusa." Kallon sama da ƙasa ta yi mini ta ce. "Saboda me? Ya kira ni ne? Ba gidana za ki koma ba da ma?" Girgiza kaina na yi cikin fargaba na ce. "Bai kira ni ba, amma ƙawata ta yi mini text ta ce ya mayar da ni." Tsaki ta ja ta ce. "Ita ƙawar taki ya aka yi ta sani?" In brief na ba ta labarin tattaunawar da muka yi da Naja. Tafa hannuwa ta yi ta ce. "Shi ne kike wannan rawar jikin komawar? Bai kira ki da kansa ba tun jiya amma daga an yi miki text an ce ya mayar da ke duk kika gigice haka? Hafsah wai wacce iriya ce ke ne? Akan namiji? Namjin ma talaka." Kamar zan yi kuka na ce. "Ba haka ba ne, ina tsoron ƙawar tawa ta faɗa wa Babana ne." Taɓe baki ta yi ta ce. "To bari ki ji, ita ƙawar taki ita ce babbar munafuka kuma maƙiyiyarki, saboda ba ta son ki da arziƙi, da tana son ki da arziƙi ba za ta ce ki rabu da mu ba, bayan kin faɗa mata yadda muke da irin kyautar da na yi miki, amma saboda tana baƙincikin ki yi mu'almala da masu kuɗin da ita ba ta yi shi ya sa ta ba ki wannan gurguwar shawarar, za ta ce kar ki fara gayu ki bar ta a baya." Girgiza kai na yi na ce. "Naja ƙawata ce ta haƙiƙa tun muna yara, tana so na da son ci gabana sosai, ba za ta taɓa yi mini abu don hassada ba gaskiya, kawai dai tana faɗa mini tata fahimtar ne." A sheƙe kamar kashi ta saki baki tana kallo na, kafin ta jijjiga kai ta ce. "Taɓɗijan! Amma gaskiya ba ki san halin da duniya take ciki ba, to ki je ki tambaya ki ce kaf yanzu a rayuwa wa ya fi rashin amana da nuna hassada, za a faɗa miki a ce aminiya ce. Tun yaushe aka daina ƙawancen tsakani da Allah, kowa zuciya da tsatsa burinsa ya ga ya fi ɗan'uwansa ci gaba. Idan kuma kina tantama akan maganata ki je ki ce mata ta auri miji talaka kamar naki, za ki ji abin da za ta ce, wanda zai nuna ba ta so, amma ke tana danƙwarar da ke akan ki zauna." Jinjina kai na yi, zan yi magana Aunty Billy da ta ƙaraso inda nake ta riga ni da faɗin. "Ku ce aminai kuna nan kuna zantawa?" Murmushi muka yi duk da nawa na yaƙe ne. Ta ce. "Ku zo mu je ku gaisa da Ogana, ya dawo yanzun nan, ya gaisa da kowa ban da ku." Maman Nasmah ta ce. "Shi ya sa na ga bakinki ya ƙi rufuwa, ashe rabin ran kika gani." Ta ce. "Bari ke dai, har ya ƙara mini da kuɗin liƙi." Faɗaɗa fara'a Maman Nasmah ta yi ta ce. "Ai na sani da ma, ni da na san dawar garin, duk dawowa da ma kin ce da kyauta yake yi miki sallama, kamar nawa mai gidan, shi ma yana dawowa zai ce ungo." Dariya suka kwashe da ita tare da tafawa suka yi gaba. Na bi su abaya kamar saniyar ware, a raina ina faɗin. 'Wato su mazajen nasu da kuɗi suke tarɓar su kullum? Gaskiya matan masu kuɗi suna shanawa da yawa, ga ƙaton gida, ga abinci lafiyayye, ga sutura mai tsada, ga hawa mota da sauran abubuwan more rayuwa." Wani part ɗin muka shiga daban ba inda ta kai mu da za mu yi Sallah ba, ba ƙaramin dauriya na yi ba gurin ɓoye ƙauyancina, saboda haɗuwa da tsaruwar shi. Na kasa gane tsakanin gidan Maman Nasmah da na Aunty Billy wanne ya fi kyau da girma, saboda kowanne ya kai duk inda ake son gida ya kai a tsaruwa. Cikin fara'a kamar ya san mu muka gaisa da mijin nata, ta ƙasan ido na ƙare masa kallo. Irin alhazawan nan ne da kuɗi da hutu suka zauna a jikinsu, ga shi ɗan dumurmuri ya sha babbar riga cikin kaya na alfarma. Irin dai mijin da mace ba za ta ji kunyar nuna shi ba ko a ina ne. Anas ne ya faɗo mini a rai, na ja tsaki ƙasa-ƙasa, tare da addu'ar kar Allah ya kawo ranar da wata a group ɗinmu za ta ƙara ganin shi a matsayin mijina bayan Maman Nasmah. Don abin kunya ne a gare ni. Bayan mun fito Maman Nasmah ta ce mini. "Wai tafiyar za ki yi da gaske na ga kina abu kamar a ce ƙyet! Ki gudu?" Ɗaga mata kai na yi ban ce komai ba. Aunty Billy ta ce. "Saboda me? Ki bari a tashi mana, ba wani ɗadewa za a kuma yi ba fa, ana yin Magriba DJ zai tafi." Kafin na yi magana Maman Nasmah ta yi karaf ta ce. "Mijinta ne ya kira ta yaron ta babu lafiya, shi ya sa." Ajiyar zuciya na sauke ina ƙara jin son ta a raina, saboda duk yadda za ta yi kar asirina ya tonu sai ta yi. Aunty Billy ta ce. "Ayya, Allah ya ba shi lafiya, bari na zo to ina zuwa." Bayan ta bar gurin Maman Nasmah ta ce. "Ki yi tafiyar ki kar ki yi wa kowa sallama tunda kin nace, saboda su Maman Suhail tun jiya suke ce mini ina ne gidanki za su je, yanzu idan suka ji za ki tafi bin ki za su yi. Gobe idan Allah ya kai mu da safe sai ki zo gidana, zan saka wani a cikin my driver's ya kai ki ɗaya daga cikin guest house ɗinmu, ki zauna a can a matsayin nan ne gidanki, sai su zo nan su same ki, idan za ku tafi zan haɗa miki da wadataccen abincin da zai isa a ci da drinks. Zan ba su address ɗin yanzu idan sun tambaye ni ina ne gidanki. Bana son su je ainihin gidanki su raina ki ne, shi ya sa na yi wannan dabarar." Ban san lokacin da na rungume ta ba tsabar farinciki na ce. "Ya Allah! Na rasa da bakin ma da zan gode miki wallahi, duk abin da za ki yi ki kankaro mini mutunci kin san shi." Tana murmushi bayan ta raba ni da jikinta ta ce. "Ƙauna ce ta kawo hakan, ke dai duk abin da na ce ki yi kawai ki bi, don ba zan taɓa cutar da ke ba." Cikin zumuɗi na ce. "Na tabbatar da hakan takwara, Allah ya bar mu tare." Ta ce. "Amin." Kayan ciye-ciye da abinci da lemuka Aunty Billy ta haɗo ta ba ni, na yi musu sallama na tafi cikin sauri, don na ga Naja ta fara doka mini kira. Allah ya taimake ni ina fita titi na samu mai napep, ya ce zai kai ni har gida a 2k. Ban tsaya ja'inja ba na shiga, saboda ina da ishashshen kuɗi a hannuna ragowar na liƙin da Maman Nasmah ta ba ni. Mun fara tafiya mai napep ɗin ya ce. "Hajiya ga wata mota tana bin mu a baya, ko kin san su ne?" Girgiza kai na yi na ce. "A'a." Ya ce. "To dai wannan mu take bi, amma bari na shiga ta layuka don na tabbatar, idan mu yake bi zai shigo shi ma." Na ce. "To." Don ni hankalina gabaɗaya ya yi gida, burina kawai na gan ni a cikinsa, don ba na son maganar abin da yake faruwa ta je kunnen Kawu, na san na lahira sai ya fi ni jin daɗi a gurinsa. Da gudu motar da take bin bayanmu ta zo ta wuce mu ta tsaya a gabanmu. Cikin faɗuwar gaba na ce. "Innalillahi! Su waye wannan? Me suke nema a gurinmu?" "Sai Allah." Mai napep ya faɗa a tsorace bayan ya tsayar da babur ɗin. Fita ya yi ya je suka yi magana, ina ta leƙen su a tsorace na ga ya dawo ya ce. "Hajiya ke suka biyo, da ma daga layin da kika fito na ga su ma sun fito." Dafe ƙirji na yi a firgice na ce. "Na shiga uku! Me zan yi musu to?" Yana murmushi ya ce. "Ki je ki ji, amma na tabbatar ba cutar da ke za su yi ba." A tsorace na kalle shi na ce. "Ko dai bakinku ɗaya da su?" Ya ce. "Wallahi ban ma taɓa ganin su ba sai yau, ki daure ki je, sun ce ba jimawa za ki yi ba." Girgiza kai na hau yi na ce. "Ka shigo ka ja mu kawai mu tafi, ni sauri nake babu inda zan je." "Ko mun juya sai sun kuma bin mu, ki je kawai ki ji me za su ce ki dawo, don Allah!" Ya yi maganar cikin roƙo. Ina kallon layin da babu kowa sai mu kaɗai na ce. "Wai maza ne ma ko mata?" Ya ce. "Mata ne." Ajiyar zuciya na sauke na fita ina waige-waige a tsorace, sai a lokacin na lura da sababbin kuɗin da suke hannunsa, tabbacin cin hanci suka ba shi, shi ya sa ya dage sai na je. Kamar kar na ƙarasa, saboda haka kawai na ji zuciyata tana bugawa. Tsayawa na yi cak a gaba da napep ɗin amma ban ƙarasa inda motar take ba. A hankali na ga an buɗe front seat an fito, damm! Ƙirjina ya buga da ƙarfi bayan na yi tozali da mai fitowar........✍️ *Zeey Kumurya* [3/8, 1:40 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *15.* Namiji na gani, saɓanin abin da mai napep ɗin ya ce mini. A fusace na juya na koma na ce masa. "Ka ce mata ne, ya kuma na ga maza?" Ya ce. "Ki yi haƙuri, na yi musu alƙawarin zan fito da ke ne, shi ya sa na ce miki mata ne, don na san idan na ce maza ne bai zama lallai ki je ba." Tsaki na ja na ce. "Matar aure ce fa ni! Idan matarka ce za ka so wasu su tare ta?" Cikin lallami ya ce. "Ki yi haƙuri don Allah, idan ba hakan ba na yi na san ba za su taɓa daina bin mu ba, ki je sai ki yi musu bayani, na san za su ƙyale ki." Numfashi na sauke tare da dafe kaina na koma, kaina a ƙasa na ƙarasa inda mutumin yake na ce. "Ga ni Malam ya aka yi?" Murmushi ya yi mai sauti ya ce. "Sannu ƴan mata." Da sauri na ɗago don jin kamar na san shi, kallon tsaf na yi masa, lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarta ta tuno mini shi, mijin Aunty Billy ne. Cikin mamaki na ce. "Alhaji! Lafiya?" "Lafiya ƙalau mai inganci ma kuwa." Ya faɗa yana murmushi tare da bi na da wani irin kallo. Ajiyar zuciya na sauke ban ce komai ba, ina jira na ji ya ce matarsa ce ta aiko shi, sai na ji ya ce. "Ban san yanzu za ki tafi ba ai da na fito da ke na kai ki gida, don zaman da na yi jiran nake ku tashi daga taron na mayar da ke gida da kaina." Murmushin ƙarfin hali na yi na ce. "Babu komai ma ai Alhaji, na gode." Ya ce. "To mu je mu sauke ki ko? Sai mu ƙarasa tattaunawa a cikin motar." Cikin ɗaurewar kai na ce. "Tattauanawa kuma akan me? Na ɗauka ai Aunty Billy ce ta ba ka saƙo ka kawo mini?" Yana gyara tsayuwarsa ya ce. "Saƙon kaina ne ya kawo ni ba na Bilki ba, hasalima ba ta san zan biyo ki ba." Waro ido na yi kawai don na rasa abin cewa. Ci gaba da magana ya yi da faɗin. "Tunda kuka shigo na yi tozali da ke gabaɗaya na rasa sukuni, kuna fita na kira ɗaya daga cikin yarana na gidan na yi masa kwatancenki na ce ya sa mini ido a kanki, shi ya sanar mini da fitarki yanzu, a gaggauce na biyo bayanki don kar ki tsere mini, Allah ya taimake ni muna fitowa na ga lokacin da kike hawa napep, shi ne muka biyo bayanku." Cikin ruɗewa don ba gama fahimtar abin da yake nufi na yi ba na ce. "Akan me to? Ni fa matar aure ce." Murmushi ya kuma yi ya ce. "Wannan ba matsala ba ce, kawai yardarki nake nema, sai mu dinga komai a sirrance. Zan wadata ki da kuɗi, na siya miki motar hawa duk irin wacce kike so, sannan zan dinga yi miki komai da kike buƙata, matuƙar kika amince da ni." A gigice na ce. "Wacce irin mu'amala za mu yi alhalin ina matar aure? Ka fahimtar da ni har yanzu ban gane mai kake nufi ba." "Calm down Baby, na ga duk kin ruɗe, ba wani abin wahala ba ne ba fa, kawai na gan ki na ji kin mun ne, kin tafi da hankalina sosai da ba zan iya haƙura da ke ba. So I decided kawai duk lokacin da nake gari zan kira ki sai mu haɗu a hotel, mu yi some hours na sallame ki, ki wuce gida, ba kwana za ki dinga yi ba tunda kin ce kina da aure." Wani jiri na ji yana kwasa ta, don duk da bai fito ƙarara ya bayyana mini ba, na gane me yake nufi. Kallon shi kawai na tsaya ina yi, ga shi dai mutum har mutum cikin kaya na kamala amma bai da halin arziƙi ashe. Girgiza kai na yi na ce. "Ba haka nake ba Alhaji, kuma gaskiya ba zan iya abin da kake nufi ba." Murmushi ya yi bai ce komai ba ya zaro wani kati ya miƙo mini tare da faɗin. "Ba zan tursasa miki sai kin amince a yanzu ba, amma ga card ɗina nan, ki je ki yi shawara, abin da kika yanke sai ki kira ni ki sanar mini. Ki ba ni account number ɗinki yanzu na saka miki 1 million ki saka kati." Zaro na yi tare da girgiza kaina, ba tare da na karɓi card ɗin ba na ce. "Ban da account." Daga haka na juya cikin sauri na shige napep ɗin tare da baiwa direban umarnin ya ja mu tafi." Bai yi musu ba ya kunna ya ja muka bar gurin. Har muka je gida zuciyata bugawa take, gabaɗaya kaina ya kulle, mamaki da al'ajabin mijin Aunty Billy sun suka kashe ni. Gefe guda kuma ina ta jinjina million ɗayan da ya ce zai ba ni wai kawai na saka kati da ita? Lallai ba ƙaramin kuɗi ne da shi ba, sai dai babu halin ƙwarai. A ƙofar gidana na tarar da Naja a tsaye tana latsa waya. Da mamaki nake duban ta bayan na sauka daga napep, har na ƙarasa kusa da ita ba ta ɗago ba, ga dukkan alamu ba ta gane ni ba duk da akwai wutar nepa. Fuskata babu walwala na ce. "Ga ni, sai ki faɗa mini abin da za ki mini da kika azalalo ni na taho." Ta ɗauki sakanni tana kallo na bayan ta ɗago kanta ba ta ce komai ba, sai can ta numfasa ta ce. "Hafsah ke ce a haka mayafi a gefen kafaɗa? Ba da ban kin yi magana na shaida muryarki ba da ko bangaza ta kika yi ba zan gane ki ba, saboda yadda gabaɗaya kika canza." Jujjuya jikina na yi na ce. "Ya ranki?" Ta jijjiga kai sannan ta ce. "Sai da kika je taron kenan?" Na ce. "Na je ɗin." "Me kika ƙaru da shi to don Allah ?" Ta yi maganar cikin takaici. "Abubuwa da yawa mana, na je na ga masu kuɗi na shiga manyan gidaje, ko banza na kafa tarihi, ga kayan ƙawar da aka ba ni na saka a jikina, ban da haɗaɗɗen abincin da na ci da wanda na yo guzurinsa." Kallo na kawai take yi kamar wadda na canza mata, tsaki na ja na ce. "Kin saka ni a gaba da kallo, wai mene haka ne?" A sanyaye ta ce. "Babu komai, ga shi nan kuwa kin yi kyau abinki." Sarƙar wuyana na riƙo ina jin kaina ya ƙara kumbura na ce. "Kayan kyan ne suka saka na yi kyan ai, har da sarƙar gold fa." Kama haɓa ta yi ta ce. "Allah ya ƙara arziƙi Hajiya Hafsah, ni dai abin da zan faɗa miki duk daular da za ki je ki gano kar ki ƙara raina ƙoƙarin Anas, arziƙi ne a rayuwa kowa da yadda Ubangiji ya ga da ma ya ba shi, ke kina hangen wasu, wani kuma yana can yana hangen ki, yana cewa da ma shi ne ke." Baki na taɓe na ce. "Kuɗi abin so ne fa, ba zan taɓa daina son irin rayuwar ƙawayena da fatan kasancewa kamar su ba har abada." Ta ce. "Tom shikenan, amma ki sani hakan tamkar yake da ki ɗauki wuƙa ki daɓa wa cikinki ne, matuƙar kina tare da waɗannan matan da ba ajinki ba ne, saboda rabuwa da su shi ne kawai masalaha a gare ki." "Abin da ba zai taɓa yiyuwa ba kuwa kenan." Na faɗa cikin haƙiƙancewa. Gyaɗa kai ta yi ta ce. "Allah ya taimaka, ga fili ga mai doki." "Saura sukuwa mai kyau in sha Allah." Na faɗa cikin tarar numfashi. Murmushin takaici ta yi ta ce. "Ni zan wuce, da ma so nake na tabbatar da kin dawo kafin na tafi, don ba na son na ƙara jin kunya a gurin mijinki, jiya na gama yi masa daɗin bakin kin canza amma kika ba ni kunya, ya zo yau ya tarar ba ki dawo ba." Cikin gatse na ce. "Allah ya kiyaye." Daga haka na buɗe ƙofar gidana na shige. Naja ta bi ta da kallo kawai, cikin ranta tana addu'ar Ubangiji ya dawo da ƙawar tata cikin hayyacinta da gaggawa, don ta ga alamar ta yi nisan da ba ta jin kira. Ba ta bar ƙofar gidan sai da ta kira Anas ta sanar masa dawowar da Hafsah, ta kusa awa biyu a zaune a ƙofar gidan kafin Hafsah ta dawo, saboda hankalinta ba zai taɓa kwanciya ba idan ba ganin dawowarta ta yi ba, saboda ba ta son Anas ya ƙara zuwa ba ta dawo ba, don ta san hakan zai iya ƙara janyo musu wata matsalar. Ita kuma abin da take gudu kenan, ba ta son ƙawar tata ta yi rashin nagartaccen miji, shi ya sa ta ɗaukar wa kanta alƙawarin duk yadda za ta yi wajen ganin ba su rabu ba za ta yi iya yin ta da yardar Allah. Ina shiga cikin gida ana ɗauke NEPA, wani irin ƙunci da takaici ne suka cika ni, na tuno tunda na je gidan Maman Nasmah ko motsi wutarsu ba ta yi ba, haka ma gidan Aunty Billy. Tsaki na yi na zaro sabuwar wayata na kunna fitila na haska gidan. Kayan hannuna na fara kaiwa kitchen sannan na shiga toilet na yi alwala na yi Sallah. Bayan na idar na zauna bitar abubuwan more rayuwar da na gano, babban abin da ya fi burge ni yadda idan mutum zai shiga unguwar su Maman Nasmah sai an tsayar da shi a bakin gate ɗin ginin da ya zagaye unguwar, an tambaye shi gidan wanda zai je ya kira shi sun yi magana da security ɗin. Sabga cikin mutunci da arziƙi dai. A cikin gidanta kuwa babu wani abu mara kyau da ƙayatarwa, toilet kaɗai ya isa ɗauke wa mutum dukkanin damuwarsa saboda tsananin kyansa, ga fanfon ruwan sanyi daban na ruwan zafi daban. Gabaɗaya yanzu da na gan ni a gidana sai na ji duk na ƙuntata, kamar ba na samun wadataccen nunfashi ma tsabar ƙanƙantar gidan. Sai wajen goma ya shigo gidan shi da su Sultan, bai kula ni ba, ni ma ko kallon shi ban yi ba. Na ɗauki abincin da na taho da shi muka ci tare da ƴaƴana, muna ci suna labarin gidan da suka je, bayan na gama shan uwar tambayar ina na je na tafi na bar su. Ni kaɗai na kwanta a ɗakina don Anas ko parlour'n bai shigo ba, na gane nufin shi, so yake na je na ba shi haƙuri, ni kuma abin da bai isa ba kenan a yanzu, don ba zan iya fama da talauci da faɗin rai ba. Kusan raba dare muka yi muna hira da Maman Nasmah, ta ba ni labarin abubuwan da aka tattauna bayan na taho, ni kuma na faɗa mata yadda muka kasance da Abban Sultan. Ta ce ko za mu shekara a haka kar na sake na ba shi haƙuri, don ita mijinta tunda suke ba ta taɓa ba shi haƙuri don ta yi masa laifi ba, ko ita ce mara gaskiya shi yake bin ta yana lallaɓa ta. Ina ta son na ba ta labarin biyo nin da mijin Aunty Billy ya yi amma har ta sauka daga online ban faɗa mata ba. Yau ma sai na ji na kasa bacci, saboda yadda gadona tun na aure yake ta ƙarar tsufa, ga katifar duk ta lotse, ta wani gurin har layi-layin katakon karagar gadon ana jiyowa. Luntsumemen gadon da na kwana a kai jiya kawai nake tunowa, na san da shi ne da tuni bacci ya ɗauke ni yadda na kwaso gajiyar nan. Tashi zaune na yi ina firfita saboda zafin da ya addabe ni da sauron da yake ta mun kuwwa a kunne duk da na ɗaura net. Na san in dai ba nepa aka kawo ba, ba zan taɓa iya bacci a cikin wannan izayar ba. Jiya na kasa bacci saboda kewar ƴaƴana da mijina duk da ina cikin ɗakin da babu wani abu na wahala zai hana ka bacci, yau kuma ga ni a tare da iyalin nawa, amma azabar sauro da zafi sun hana ni bacci. Kenan da a irin gidansu Maman Nasmah nake tare da ƴaƴana da mijina babu abin da zai dame ni bare ya hana ni bacci? Jinjina kaina na yi ina ayyanawa a raina ko ta halin ƙaƙa sai mun bar gidan nan mun koma wani ƙato wanda ya haɗa komai na rayuwa nan kusa, don na gane kamar yadda ba zan iya rayuwa ba su Sultan ba haka ba zan iya ci gaba da zama a cikin talauci da ƙuncin rayuwa ba. Tilas ko ni ko Anas mu nemo kuɗi ko a ina ne mu yalwata rayuwarmu. 'To amma ni a ina zan samo?' Zuciyata ta yi mini wannan tambayar. Mijin Aunty Billy da one million ɗin da ya ce zai ba ni don kawai na saka kati ne ya faɗo mini a rai, tamkar shi ne amsar tambayar da zuciyata ta yi mini........✍️ *Zeey Kumurya* [3/8, 1:41 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGH PENS* (FREE BATCH) *16.* Saurin girgiza kaina na yi. A fili na ce. "Ba zan iya yin abin da yake buƙata ba, ina kuma roƙon Ubangiji ya tsare ni da aikata hakan har abada. Zan nemi wata hanyar dai daban."  Ci gaba na yi saƙawa da kwancewa har bacci ya ɗauke ni. Washegari bayan sallar asuba na janyo wayata na hau online, har su Sultan suka tafi school ban sauka ba bare na yi yunƙurin yin aikin gida. Shi ya shirya su ya yi musu komai, tsakani na da su gaishe nin kawai da suka zo suka yi na amsa ne. Kafin ya dawo daga kai su na fita na ɗauko ragowar abincin jiya don na fara jin yunwa na ci na yi wanka na shirya. Ina zaune a bakin gado Anas ya shigo ɗakin ya buɗe wardrobe, kamar na share shi kamar yadda ya yi mini sai na fasa na ce. "Ina kwana?" Ba tare da ya juyo ya kalle ni ba ya ce. "Lafiya ƙalau." Ban san me ya hau kaina ba na tsinci kalmar haƙuri ta subce daga bakina zuwa gare shi, don ganin da na yi masa yanzu sai na ji wata irin kewa da son kasancewa da shi sun baibaye ni. Duk yadda na so ɗaurewa amma na kasa, sai da na bayyana masa abin da yake nuƙurƙusa ta. Bai ƙi ba ya biye mini ba tare da ya nuna mini wani abu na ɓacin rai ko kaɗan ba. Sosai ya nuna mini soyayyar da na yi wa kaina buƙulun samun ta na tsawon kwanaki, ni kaina na san samun namjin da ya iya soyayya da taraiyar mace kamar Anas zai yi wahala. Wajen ƙarfe sha daya ya shirya ya fita a gaggauce saboda makarar da ya yi. Ya na ficewa na bi bayansa zuwa gidan Maman Nasmah saboda uban kiran da take doka mini. Ina zuwa gidan nata ko zama ban yi ba ta dube ni cikin faɗa ta ce. "Wai me kika tsaya yi a gidan ne? Ina ta kiran ki kika ƙi ɗauka, kin san kuma dalilin kiran." A ladabce na ce mata. "Ki yi haƙuri, bari na yi sai ya fita, don yanzu ma ko tambayar shi ban yi ba na fito." Baki ta taɓe ta ce. "Aikin kenan, tsoron miji kamar wani mala'ika, sai ki je ku tafi, don su Maman Suhail suna ta kira na wai za su taho, ke ma sun kikkira ki ba ki ɗauka ba." Na ce. "Eh, duk na ga missed call ɗin da ina hanya." Sai da ta ba ni wata abaya mai kyau sabuwa na saka sannan muka tafi, don cewa ta yi kayan jikina ba su yi ba, marasa tsada ne, duk da ƙurewar adakar da nake ganin na yi. Madaidaicin gida ne mai kyau guest house ɗin nasu, sama da ƙasa ne, ga shi ya sha kayan furnitures masu kyau da tsada. Sai na ji da ma zai zama gidan nawa a gaske, don ko iya shi na samu burina ya gama cika. Kusan su goma ne suka zo, muka sha hira da hotuna. Na dinga kai wa da komowa ina jin kaina na kumbura. Akwai komai na amfani a gidan, kuma fes muka tarar da shi kamar mutane suna rayuwa kullum da kullum a cikinsa. Abinci da drinks ɗin da Maman Nasmah ta aiko sun wadata sosai, don har ragowa suka yi. Sai yamma lis suka tafi, ni kuma sai bayan Magriba na bar gidan ba don na so ba na koma gidan Maman Nasmah. A gaggauce na yi mata sallama na wuce gida, bayan ta nace sai na kwana ni kuma na ƙi. Don na ga Abban Sultan yana ta kira na. A gidan na tarar da shi ya cika ya yi fam, na yi sallama ya amsa ciki-ciki. Sai da su Sufyan suka koma ɗakinsu na dube shi na ce. "Ka yi haƙuri don Allah, wani babban uzuri ne ya fitar da ni." Jinjina kai ya yi ya ce. "Shi ne kuma ya sa kika ƙi neman iznina? Kika je kika kai har dare? Kin san yaran nan za su dawo daga school amma ba ki damu da halin da za su shiga ba idan sun dawo ba kya nan? Ba ruwanki sabgar gabanki ce kawai ta dame ki." Ɓata fuska na yi na ce. "Yanzu fisabilillahi daga dawowata sai ka tarɓe ni da faɗa? Ko hutawa ai ka bari na yi, kuma ba ka san lafiya nake ba ko ba lafiya ba." Cikin takaici ya ce. "Na san ƙalau kike Hafsah, a zatona maganganun da muka yi ɗazu komai ya wuce, za ki yar da sabbin halayen da kika tsiro ki zo mu koma rayuwarmu kamar da, amma tunda har yanzu da saura ki ci gaba, sai dai ina so ki sani ba zan ɗauki wannan gantalin yawon da kika tsiro da shi ba." Daga haka ya miƙe ya fice daga ɗakin. Raka shi na yi da harara tare da jan dogon tsaki, don ni ta gidan da na baro mai AC da wutar nepa kodayaushe nake ba ta shi ba. Bayan na yi Sallah na kira Maman Nasmah muka sha hira, na dinga kwarara mata godiyar fitar da ni kunyar da ta yi, har za mu yi sallama na tsayar da ita na ba ta labarin duk yadda muka yi da mijin Aunty Billy. Shiru ta yi har na yi tunanin ko kiran ya katse ne sannan ta ce. "Hmmm, ai shiru kawai na yi miki na ji ko za ki mun zancen da kanki, don bayan an tashi daga taron ya bi ni har gida ni ma. Har na tsorata ya ce ya kwantar da hankalina, wadda ya gan mu tare ya gani yake na so, kuma da aure yake son ki shi da gaske yake, saboda bai taɓa tunanin matar aure ce ke ba, shi ne ya ce bari ya gwada ki da farko ya ga irinki, don tun kafin magana ta yi nisa gara ya san irin matar da zai aura." Ajiyar zuciya na sauke na ce. "Haba, ni fa na yi mamaki sosai, na ce ga shi kamar kamilalle ashe ba haka ba ne." Da sauri ta ce. "Taɓ, ai mutumin kirki ne sosai, don ko a unguwarsu ba ki ga yadda ake yabon shi ba, ga shi da kyauta da sadaka, kawai ya yi hakan ne don ya gwada ki, ai ya faɗa mini komai bai ɓoye mini ba." Na ce. "Allah Sarki, har ina munana masa zato." Dariya ta yi ta ce. "Ai kuwa kin ɗauki haƙƙin shi, don son tsakani da Allah yake yi miki, so na gaskiya. Saboda a maganganunsa na fahimci ba ƙaramin so yake yi miki ba, ga dukkan alamu ya kamu da yawa." Na ce. "Uhm, shi ya sa abin da yake ta damu na, ni kaɗai na dinga cewa ya san ina tare da matarsa ya yi mini maganar banza, ko tsoron na faɗa mata bai ji ba." Da sauri ta ce. "To kin gani? Wannan ma kaɗai ya ishe ki gane ba halinsa ba ne, don ba haka ƴan iskan mazan suke ba, daga ganin ki ya fara yi miki magana wadda ba ta kamata ba, ba tare da ya san wace ce ke ba, kuma a sanadiyyar matarsa ya san ki. Ai ƴan iskan sai sun ja mutum a jiki sannan suke bayyana musu buƙatarsu." Na ce. "Haka ne kuma." Ta ce. "To yanzu dabara ta rage wa mai shiga rijiya, ke ce wuƙa da nama suke hannunki, don wannan wata gwaggwaɓar dama ce da kika samu ta cikar burinki cikin sauƙi." Cikin rashin fahimta na ce. "Ban gane ba, kamar yaya?" "Ya kamata ki gane kuwa, saboda abin a zahiri yake, ki rabu da wannan faƙirin mijin naki ki zo ki auri mijin Aunty Billy, ki zama matar mai kuɗi ke ma kamar yadda kike fata." Dafe ƙirji na yi cikin zaro ido waje na ce. "Na kashe aurena kenan?" Ta ce. "Eh mana, mene a ciki to?" Na ce. "Gaskiya da akwai damuwa, ina son mijina kuma ban san rabuwa da shi da ƴaƴana, sannan kuma na rasa wa zan aura sai mijin Aunty Billy? Duk yadda muke da ita?" Tsaki ta yi ta ce. "Daɗina da ke ƙwaƙwalwarki ba kodayaushe take ja ba, ai idan kun rabun da ƴaƴanki za ki tafi ba barin su za ki yi ba, wannan mijin naki kuma mene abin damuwa a rabuwa da shi? Kin samu dama amma kina ƙoƙarin yin wasa da ita. Idan kin auri mutumin nan ba ƙaramin hutawa za ki yi ba, ki wataya son ranki, ƙasashen waje kuwa duk wadda kike so ita za ki je ki shana a lokacin da kike so. Aunty Billy kuma duk yadda muke da ita ai bai kai yadda muke da ke ba, ina son ganin kin ci gaba ke ma a rayuwa kin zamto kamar mu, don haka akan wata can Billy ba zan ƙi taimakonki ba. Ki tsaya ki yi tunani da kyau kar ki yi wa kanki sagegeduwa, mutumin yana da bala'in kuɗi, kuma a zuwan da ya yi muka zanta ba ƙaramin son ki na fuskanci yana yi ba, da na ce masa kina da aure ba ki ga yadda ya ruɗe ba." Numfashi na sauke ina hasaso kaina a ƙaton gida matsayin mallakina, ina hawa mota driver yana ja na, ga suturu na alfarma da zan dinga sakawa. Na tuno tarin masu aikin Aunty Billy, na san ni ma idan na aure shi haka zai ɗibar mini su, su dinga mun komai ina daga kwance. Jin na yi shiru ya sa ta ce. "Bari na bar ki, ki yi tunani, amma ni da za ki ɗauki shawarata da kin amince kawai, sai ki bar komai a hannuna, na san me zan tsara na faɗa masa. Ƙarin abun daɗin kuma bai taɓa haihuwa ba, matsalar kuma daga Aunty Billyn ne ba daga shi ba, don mun taɓa maganar da ita. Kin ga da kin je kin fara haihuwa zai ɗauki son duniya ya ɗora miki ke da ƴaƴan, da ma ga shi ke uwar maza ce, sai ki ta haifa masa su, dukiyarsa da komai nasa su zama mallakinsu." Cikin ɗaurewar kai na ce. "Yanzu ni na rasa ta cewa ma, amma ki ba ni zuwa dare, zan yanke shawara." Ta ce. "Tom shikenan Allah ya kai mu." Bayan mun gama wayar na miƙe na fara safa da marwa ina saƙawa da kuncewa. Tabbas Maman Nasmah gaskiya ta faɗa mini, wannan wata dama ce da na samu, amma inda matsalar take Kawu nake ji da hukuncin da zai ɗauka a kaina idan ya san ni na kashe aure na, sai kuma kallon da ƴan group ɗinmu za su yi mini idan suka ji labarin na auri mijin Aunty Billy, da ita kanta ma. Amma duk wannan bai kai son rayuwar kuɗin da nake yi tasiri a cikin raina ba, don sosai nake ji a jikina na kusa kaiwa matakin da nake so na zama matar hamshaƙi. Hango mutumin kawai nake da cikar kamalarsa da yadda kuɗi ya bayyana ko ta ina a jikinsa, alamun ya jiƙu a cikinsa. A ɓangaren Maman Nasmah kuwa tsalle ta doka cikin farincikin murnar samun wani chance ɗin a sauƙaƙe na raba Hafsah da Anas. Za ta yi amfani da hakan tai ta ƙara cusa mata son rayuwar gidan kuɗi har ta yi nasarar raba sun. A cikin mazan da take hulɗa da su za ta haɗa ta da guda ɗaya su dinga waya da chatting a matsayin shi ne mijin Aunty Billy. Don ba ƙaramin daɗi ta ji ba da Hafsah ta ce mata ba ta karɓi card ɗinsa ba, bare ta kira shi ya ci gaba da yi mata maganar banza asirinta ya tonu na ƙaryar da ta zabga mata. Ita kanta ba ƙaramin kaɗuwa ta yi da ta ji mijin Aunty Billy ya bi Hafsan, kuma tsabar ƙwanƙwararre ne shi ya bayyana mata manufarsa ba tare da tsoron komai ba. Murmushi ta yi a fili ta ce. "Ashe ba namu mazajen ne kaɗai bunsuraye ba." Za ta ci gaba da nuna wa Hafsah son ta take yi tsakani da Allah da kuma burin taimakon ta, yadda duk abin da ta ce mata ta aikata za ta yi ba tare da jinkiri ba. Wuni na yi ina abu ɗaya wato tunanin mafita, a ƙarshe na yanke shawarar amincewa da abin da Maman Nasmah ta faɗa, na rabuwa da Anas na fita na auri mai kuɗi irin mijin da nake fata da burin samu. Idona ya rufe gabaɗaya, ƙaton gida da rawuwar jin daɗi kawai nake hangowa, na manta da ƙalubalen da za su biyo bayan faruwar hakan. Da kaina na kira ta na sanar mata na amince, ta nuna mini ta ji daɗi sosai, don mutumin mai suna Alhaji Kyauta ya ƙara kiran ta a kaina, ta ce masa wasa take yi masa ba ni da aure za ta haɗa mu. Na nuna mata ba zan iya mu'almala da shi da aure na ba, ta san abin da za ta faɗa masa kafin na rabu da Anas sai mu fara magana a lokacin. Ta ce tom shikenan babu damuwa, amma na yi komai cikin sauri kar a ja lokaci, na ce mata in sha Allah. Tun daga ranar na fara sauke wa Abban Sultan tsibiri-tsibirin kwandon rashin mutunci da tijara, wulaƙancin yau daban na gobe daban. Duk abin da na san ba ya so shi nake yi, wanda yake so kuma na daina yi. Ci gaba da maganganun abubuwan kuɗi da turo su a group ɗinmu shi yake ƙara tunzura ni, don na sha alwashin ba zan bari wani taron da za mu kuma yi ya zo ina cikin wannan akurkin gidan ba. Saboda an tsayar da cewar duk bayan wata shida za mu dinga yin taron, amma ba za a sake yi a gida ba sai dai a kama guri..........✍️ *Zeey Kumurya✍️* [3/8, 1:41 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGH PENS* (FREE BATCH) *17.* Yau ta kama Laraba, wanda ya yi daidai da watanni uku da fara takun saƙar mu da Anas. Ina zaune a ɗaki da hantsi ina chatting tare da kallon su Sultan da suke ball a tsakar gida, da yake ana cikin hutu ne babu school. Ƙara kishingiɗewa na yi cikin jin daɗin hirar da muke yi a group ɗinmu. Don yanzu ban da matsalar data, Maman Nasmah tana saka mini ishashshiya tare da kati, chaji ma ban da matsalar shi saboda ta aiko mini da sabuwar power bank. Wani video Aunty Billy ta turo, da sauri na yi loading na buɗe, don yanzu duk wani motsinta akan idona yake. Wani haɗaɗɗen gida ne da ya gaji da tsaruwa gurin gini da kayan alatun da suka ƙara ƙawata shi. Gidan mai hawa uku ne, bedrooms da parlourn cikinsa kuwa kasa ƙirga su na yi, kuma kowanne da kaya a cikinsa. Na maimaita kalla ya yi sau biyar sannan na haƙura ba don na gaji da kalla ba. Abin da na ga ta rubuta ne ya saka ni tashi zaune a zabure ba tare da na shirya ba. Sake watching video ɗin na yi cikin zazzaro ido kamar zan saka su a cikin wayar. Ina nuna gidan da ɗan'yatsana na ce. "Kan uba! Da gaske ko da wasa?" Ban kai ga samun amsa ba kiran Maman Nasmah ya shigo, cikin rawar jiki na ɗaga. Ba tare da mun gaisa ba ta ce. "Kin ga abin da Aunty Billy ta turo?" Da rawar murya na ce. "Gidan da ta turo ta ce za su koma a Abuja ita da mijinta?" Ta ce. "Eh, kin ga abin da nake faɗa miki ko? Kina nan zaune sai ta gama tatike shi, wannan uban gidan ko ni mijina ba shi da kamar shi, ki yi ki yi ki bar gidan talakan nan amma abu ya gagara, na tabbata da tuni yanzu ke za ki shiga gidan, don yana ta damu na akan maganarki, ko ɗazu da safe ma ya kira ni, kuma ya ce da an yi auren naku Abujan zai kai ki." Wani yawu na haɗiye mai ɗaci cikin takaici na ce. "To ya zan yi? Anas ya ƙi saki na, na yi masa tijarar, na yi bala'in amma ya ƙi, ba fa na yin komai a gidan shi yake yi, sai ya kai shabiyun dare bai yi bacci ba yana ta kujiba-kujiba da aikin gida." Maman Nasmah ta ce. "Taɓ! Amma wannan mijin naki wanne Iri ne shi? Kamar ba zuciya a ƙirjinsa?" Na ce. "Bala'in haƙuri ne da shi, kuma idan bai ga damar yin abu ba babu wanda ya isa ya saka shi, kuma yana so na sosai, da ma na san da wahala ya iya rabuwa da ni." A zafafe ta ce. "Ba wani so, da yana son ki ai da ya yi miki duk abin da kike so, kawai dai ya san idan kuka rabu ba zai samu wadda zai dinga cuta ya dunkume a gida kamar ki ba ne, shi ya sa. Ni dai abin da na kira na faɗa miki ki yi sauri ki dage ku rabu a cikin satin nan, ki san duk yadda za ki yi ku rabu a wuce gurin. Saboda na gaji da yi wa Alhaji Kyauta ƙarya, kullum ta yau daban ta gobe daban, don ya ce mini shi aure yake da buƙata cikin gaggawa, idan abin nan ba zai yiyu ba ya haƙura kawai ya nemi wata." Da sauri na ce. "A'a, ba ni iya yau zuwa gobe kacal, na san me zan yi." Ta ce. "Ya fi miki dai." Bayan mun gama wayar na ci gaba da kallon gidan ina hasaso kaina a ciki, da tuni ni ce zan wataya a cikinsa amma Anas ya yi mini buƙulu, ƙwafa na yi ina ayyana abin da zan yi masa yau idan ya dawo, wanda na san duk nacin shi dole ya rabu da ni. Ina nan zaune na ji an buga gida, Sultan ya je ya buɗe suka dawo tare da mai bugun, Naja ce, kuma da alama daga gurin aiki take, don sanye take cikin fararen kaya na nurses. Ba yabo ba fallasa na amsa mata sallamar da ta yi. Bayan ta shigo ta yi wa kanta mazauni ta ce. "Hajiya Hafsah, ana ta sana'ar ne? Don na ga yanzu U are always online, ko garin ma ba kya ji." Fari na yi da ido tare da faɗin. "Na kusa zama Hajiyar dai in sha Allah." Ta ce. "To Ubangiji ya tabbatar ya nuna mana lokacin, da fatan kin gama fushin da kike yi da ni?" Yamutsa fuska na yi na ce. "Fushi kuma? Akan me?" Ta ce. "Eh mana, tun daga ranar da na zo ɗin nan shikenan ba kira, ba magana a chat bare ki zo gida kuma." Taɓe fuska na yi na ce. "Au babu komai to, Allah ne kawai bai nufa ba." Ba ta ba ni amsa ba sai wayar hannuna da na ɗaga ta ƙura wa ido, kamar wadda ta ga abin tsoro haka ta nuna wayar ta ce. "Hafsah! A ina kika samu wannan Iphone 14 ɗin?" Jujjuya wayar na yi na ce. "Tsohon zance, tun yaushe na yi ta, wata ƙawata ce da take auren hamshaƙin mai kuɗi ce ta siya mini, ta ce idan mijinta ya dawo ma za ta saka ya siya mini 15." Kamar Naja za ta yi kuka ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Hafsah kina da hankali kuwa? Da kika karɓi wannan wayar mai tsada kin tabbatar saboda Allah ba da wata manufar ta baki ba? Kin ma ce wanda ta ba ki da farko an sace, ganin kayan kika yi ko kuma wasu ta ƙara siya miki?" A gadarance na ce. "Wasu ta sake siya." Shiru ta yi na wasu sakanni sannan ta ce. "Anya ba da wata manufar ta yi miki wannan kyautar ba? Hafsah ki dinga tunani da ƙwaƙwalwarki fa, kar son duniya da ruɗun shaiɗan su kai ki su baro." Tsaki na ja na ce. "Babu wata manufa sai ta alkhairi, kuɗi ne kawai da su, wannan ai ba wani abu ba ne a gurinsu." Ban jira cewar ta ba na buɗe wayata na koma kusa da ita na fara nunnuna mata abubuwan da suke turowa a group ɗin, tare da ba ta labarin gidajen waɗanda na je na gano. Tana kallon gidan da Aunty Billy ta turo ta ce. "Don Allah na tambaye ki mana?" Na ce. "Ina jin ki?" "Wa ya saka ki a group ɗin nan? Yaya aka yi kika tsinci kanki a cikinsa?" Murmushi na yi na ce. "Ke ma ya burge ki ko? Ai group ɗin nan yana da shiga rai, duk wanda ya zauna a cikinsa ba ya iya fita, ga shi mutanen ciki duk ƴan gayu ne masu haɗin ka..." A ƙufule ta katse ni da faɗin. "Ni ba wannan na tambaye ki ba, yadda aka yi kika kasance a group ɗin nake son ji." Tashi na yi na koma inda nake da farko sannan na ce. "Wata ƙawata ce da muka yi islamiyya tare, ta turo link ɗin a group ɗinmu na ƴan'ajinmu, a nan na gani na shiga." Naja ta ce. "To ita ƙawar taki har yanzu tana cikin group ɗin?" Na ce. "A'a, kamar a ranar da na shiga ma ta fita, da muka haɗu kwanaki ta ce mini wayarta ce ta lalace, duk wanda muka shiga tare ma sun fice, sun ce ba za su iya da uban suturun da ake yi a group ɗin ba." "Sai ke da rabon wahala yake jan ki shi ya sa kika zauna ko?" Ta faɗa cikin faɗa da ɗaga murya. A fusace na ce. "Ke Naja! Haifa ta kika yi ne da za ki dinga yi mini magana cikin faɗa da tsawa? Na gaji da abubuwan da kike mini, ki ƙyale ni, babu ruwanki da rayuwata, ki fita daga sabgata, ki tsaya iya matsayinki." Jinjina kai ta yi ta ce. "Na ji, amma ko da wannan ne karo na ƙarshe da zan faɗa miki gaskiya sai na faɗa miki." "To ba na so." Na faɗa cikin ƙaraji. Miƙewa ta yi tare da cillo mini wayata, a sanyaye ta ce. "Idan har kina cikin group ɗin nan ba za ki taɓa ganin duk wata gwanintar da Anas zai yi miki ba, saboda abubuwan da suke turowa na mahaukatan kudi, wanda duk da ban sani ba, rabi da ƙwata duk ƙarya ne. Amma irinki masu ƙaramar ƙwaƙwalwa ba za su gane hakan ba. Ko za ki ƙi ji, ko za ki ƙi amfani da shawarata ba zan fasa faɗa miki gaskiya ba. Anas namiji ne ɗaya tamkar da dubu, idan kika yi gangancin rabuwa da shi za ki yi danasani mara amfani, a lokacin da time ya ƙure miki." Tsaki na ja na ce. "To ko Anas ɗin za ki aura ne Naja? Tunda na ga kullum cikin yabon shi kike." Murmushi ta yi mai ciwo ta ce. "Tabbas da zan samu miji mai nagarta kamar Anas babu abin da zai hana ni auren shi, ko da kuwa ni zan dinga cikon kuɗin cefane, in dai ba shi da hali ne ba mugunta ba ce. Amma Anas babu aure a tsakanina da shi har abada, saboda kin riga da kin yi mana katangar ƙarfe da hakan. Ki saka a ranki har abada ni Naja ko da kin mutu ba zan taɓa auren mijinki ba. Gaskiya ce kawai nake faɗa miki." Taɓe baki na yi na ce. "Ba wani nan, kawai don dai talaka ne shi ya sa ba za ki aure shi ba, amma da mai kuɗi ne sanda za ki auren shi ma wa ya sani?" Cikin takaici ta ce. "Ke ce kuɗi yake gabanki, abin da ba ki sani ba ma ni zuwa na yi na faɗa miki an kawo kuɗina tun last month, an saka biki nan da 3 months." A sheƙe na ce. "Allah ya sanya alkhairi." Ta ce. "Amin na gode, duk da a wulaƙance kika amsa, saboda ina ɗora ki a turbar gaskiya, ki je ki ci gaba, ai ta ɗora ki a kan keken ɓera, KANKI ZA KI YI WA ba wani ba, don ba zan fasa maimaita miki ba ki da wani gata a duniyar nan bayan Ubangijin da ya halicce ki sama da Anas ba." Cikin ƙosasa da surutunta na ce. "Shi gatan ne da shi? Yanda ba ni da kowa shi ma hakan yake." Tana gyara zaman jakarta a kafaɗarta ta ce. "Shi namiji ne, ba shi da matsalar neman matallafi a rayuwa kamar ke, zai iya yin rayuwarsa shi kaɗai ma a cikin gidansa, amma ke kuwa a matsayinki na mace dole sai kina ƙarƙashin wani!" Tsaki na kuma ja ban tanka mata ba. Ta ce. "Hmm, Hafsah kenan, yau ni kike wa haka akan wasu can haɗuwar jiya-jiya?" Na ce. "Na yi ɗin, hurumin da ba naki ba da kika shiga shi ya janyo miki." Ta ce. "Haka ne, kowa rai ya yi wa daɗi babu kamar mai shi, in sha Allah daga yau ba zan ƙara yi miki magana akan wannan rayuwar da kika ɗaukar wa kanki ba." Cikin kora da hali na ce. "Ya fi miki alkhairi, ki sakar mini mara ki bar ni na yi rayuwata yadda na ga dama." Sallama ta mun ta tafi bayan ta ƙara yi mini bitar maganganunta da kwata-kwata ba su da mazauni a gurina, don tamkar amahin shata haka na ɗauke su. Ban da ƙona mini rai ma babu abin da suke yi. Na fara yarda da maganar Maman Nasmah da ta ce hassada da baƙincikin mu'amalata da ƴan gayu take yi. Wunin yau cikin tufka da warwara na yi shi, don ko girkin rana ban yi ba, na jiƙa wa su Sufyan garin kwaki suka sha suka wuce islamiyya. Da suka dawo kuma na ba su ragowar abincin da suka ci da safe, na ce musu idan uban nasu ya dawo ya nemo musu abin da za su ci da daddare ko ya dafa musu. Ni kuma na ci biscuit ɗin da na siya da yawa na ajiye saboda da irin haka, na kora da ruwa. Daf da Magriba na ɗauko bola na wargatsa a tsakar gida da soro, na ɗebi ruwa na kwara a kai. Da kaina na fita ƙofar gida na ɗebo ƙasa na tila akai. Na yi hakan ne saboda Anas, don na san ba ƙaramin ɓaci ransa zai yi ba idan ya zo ya tarar da gidan a haka, saboda ba ya son ƙazanta ko kaɗan a rayuwarsa, ga shi da ƙyanƙyami, kuma kafin ya fita sai da ya share gidan tas. Toilet kuwa da Sufyan ya yi bayangida hana shi flushing na yi, na ƙara damalmala bakin masan na bar shi a haka, duk saboda ya gani ransa ya ɓaci. Da ƙyar Sultan ya iya yin alwala, sai kakkame jikinsa yake ya na ɓata fuska cikin ƙyanƙyami. Sufyan kuma ya na fitowa daga ɗaki ya kama bakinsa ya ce. "Mami wa ya yi mana wannan ƙazantar a gida?" Na ce. "Ban sani ba don ubanka." Jijjiga kai ya yi yana keɓe baki ya ce. "Taɓ, idan Abba ya dawo zai yi faɗa, ki yi sauri ki gyara kar ya zo ya gani." Ban kuma tanka masa har ya ƙaraci surutunsa ya yi shiru, Sultan kuwa da ya san ni na yi bai ce komai ba. Bayan ya idar da alwalar ya ɗauko tsintsiya zai fara shara na ƙwace na kora shi waje. Tare da suka dawo da Baban nasu, ina daga ɗakin su Sultan na ji yana cewa. "Mene wannan kuma a gidan kamar kwata ?" Daga nan ban san ya aka yi ba sai ji na yi ya faɗi tim a cikin cakwalin. Da sauri na fito na haske shi, ganin shi na yi kwance male-male, ƙoƙarin tashi ya yi cikin hanzari, ban san lokacin da wata irin dariya ta ƙwace mini ba, saboda tozalin da na yi da fuskarsa ta yi dagaje-dagaje da ruwa da ƙasa da bolar da na zubar.........✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:42 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *18.* https://chat.whatsapp.com/EDdhJ4RW54T88HqTwLQWI2 Cikin sauri ya miƙe tsaye zumbur, ledar da ta harɗe masa takalmi ta yi sanadiyar faɗuwar shi ya zare ya nufi bakin toilet yana hucin ɓacin rai ba tare da dube ni ba. Yaran sai sannu suke yi masa kamar za su yi kuka, ni kuma na ci gaba da dariya har da riƙe ciki. Fuskarsa ya wanke tare da cire rigar jikinsa da duk ta ɓaci ya bar singlet kawai. Ya shiga toilet zai cilla ta a cikin bucket ya ci karo da aika-aikar da na yi. Sultan da ya bi shi da wayarsa yana haska masa ya yi saurin toshe hancinsa tare da dawowa baya da sauri. Shi kuwa kakarin amai ya fara. Raina fes kamar takarda na koma ɗaki ina faɗin. "Kaɗan ma ka gani, ba dai ka nace ka ƙi rabuwa da ni ba? Yanzu ka fara ganin abubuwa." Ina jiyo su suka gyara tsakar gidan da toilet ɗin, ban ko matsa ba har suka gama facaka da ruwansu, ina kan sana'ar tawa wato chatting. A lokacin ya hura wuta ya ɗumama musu ruwan wanka suka yi dukansu. Bayan ya gama dube-duben shi ko zai ga na yi girki ya ga ban yi ba ya fice daga gidan. Sai kusan sha ɗaya ya dawo, har time ɗin yaran ba su yi bacci ba. Daga yadda na ji suna murna da ƙarar ledar da na ji na san wani abin cin ya siyo musu. Bayan sun yi bacci ya shigo ya kwanta, ban ce masa komai ba na fita na shiga kitchen, don yunwa ta fara nuƙurƙusata. Jikina na rawa na buɗe ledar da na gani a kan kanta wanda ƙamshin abin da yake cikinta ya gama buɗaɗe ni na ga banɗashen gurasa ne suka ci suka rage. Zaman ɗabaro na yi a ƙasa na fara ci hannu baka hannu ƙwarya. Sai da na cinye tas na yi gyatsa sannan na tashi na sha ruwa. Ruwan zafin da na gani a flaks na juye na yi wanka. Ina sauke ajiyar zuciyar jin daɗin jikina na koma ɗaki, lokacin ƙarfe ɗaya saura. Ina cikin shiri aka kawo nepa, hakan ya sa na ƙura wa Anas ido da ya yi ɗaiɗai yana bacci hankalinsa kwance. Wani irin takaici da baƙinciki ne ya turniƙe ni, saboda na fuskanci duk abin da zan yi masa ba ya damun shi, sai dai ni kullum ya bar ni cikin damuwa da tunanin mafita. Ƙwafa na yi na miƙe na je na ɗebo ruwa a waje wanda ya yi sanyi kasancewar sanyi ya busa na dawo na hau gadon na yaye bargon da ya lulluɓa na sheƙa masa tun daga fuska har wajen cikinsa. A firgice ya tashi har yana tuntsirar da ni na kusa faɗawa ƙasa cikin kakkarwa. Ina sauke numfashi na ce. "Anas Musa Shu'aibu ka yi wa girman iyayenka ka sauwaƙe mini wannan ƙaddararren auren naka, na ce maka na gaji, ba na son ka, ba na son ci gaba da zama da kai. Ko ana dole ne? Ka yi zuciya mana, ko ba ka da ita ne?" Ya na jifa na da wani irin kallo ya ce. "Ba tsoron rabuwa nake yi da ke ba, ina duba Kawu da su Sultan ne kawai, don tun ina ɗaukar abin naki yarinta da shirme yanzu na gane zallar iskanci ne. Na yi miki zuru na zuba miki ido duk ba kya gani, a kanki har ƙara yawan tsaiwar dare na yi, kowacce Sallah da addu'ar Ubangiji ya shirya ki nake farawa, amma ban ga alamar lamarin naki na ƙare ba ne. Duk abin da za ki yi don ki ɓata mini rai ina sane, dannewa kawai nake yi ba na biye miki amma...." Dogon tsaki na ja na katse shi da faɗin. "Ni ba wani dogon jawabi na nemi ka yi mini ba, kawai saki nake buƙata daga gare ka, tunda kai ka kasa yi mini abin da nake so, ka kasa wadata ni, sai ka saka wanda zai iya yi yana can yana jira na ya ɗauka." Idanunsa jajir alamar ba ƙaramar tafasa zuciyarsa take yi ba ya ce. "In sha Allah a yau zan rabu da ke Hafsah ko ƴar gold ce ke. Na sake ki! Na sake ki!" Ba tare da na damu da dare ne ba na saki shewa tare da kwaso shoki daga zaunen da nake, duk da wani irin abu mai nauyi da ya ji ya tokare mini ƙirjina. Guɗa na rangaɗa na ce. "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Yau na rabu da auren jaraba da ƙaddara." Bai ce komai ba ya tashi ya fice fuuu kamar zai tashi sama. Na raka shi da mugun kallo. Korar duk wata damuwa da ke ƙoƙarin kawo mini ziyara na yi na tashi na fara haɗa kayana. Ji nake kamar na kira Maman Nasmah a daren nan na sanar mata wannan daddaɗan albishir ɗin. Ko kaɗan ban bari zafin sakin ya yi tasiri a zuciyata ba, Alhaji Kyauta da daular da zai mayar da ni kawai nake hangowa, don ko Kawu ba na ji don na gama tsara abin da zan faɗa masa. Da layi kamar wanda ya bugu Anas ya ƙarasa ɗakin su Sufyan da jan ƙafa ya tura ƙofa a hankali saboda kar su farka ya shiga ya zube a kan dandaryar ledar tsakar ɗakin, yana sassauke numfarfashi da sauri da sauri. Ganin komai yake tamkar a mafarki, bai taɓa tunanin haka za ta faru a tsakaninsu da Hafsah ba. Ko da wasa bai taɓa kawo za su rabu ba idan ba sanadin mutuwa ba. Bai taɓa budurwa ba sai a kanta, daga itan kuma bai ƙara yi ba. Bai san ya zai fara shirin rayuwa da wata macen da ba ita ba. Ƴaƴansa ya kalla da suke kwance suna bacci, wani irin tausayinsu ne ya tsirga masa a cikin zuciya, don ya san zafi da ƙunar yin rayuwa ba tare da UWA ba. Babban tashin hankalinsa inda zai kai su a riƙe su ko kuma matar da zai samu ta riƙe su tsakani da Allah. Don ko sama da ƙasa za su haɗe ba zai taɓa ba wa Hafsah su ta tafi gidan wani da su a matsayin agololi ba. Duk yadda ya yi kar aurensu ya ƙare gabaɗaya ya yi amma sai da Hafsah ta ƙure shi, duk da ya riga ya saka wa ransa hakan rubutaccen abu ne da Ubangiji ya rubuta sai ya faru. Runtse idonsa ya yi yana tuno wayar da suka yi da Naja ɗazu, yadda ta dinga roƙon shi akan ya ƙwace wayar Hafsah ko na wucen gadi ne, sannan ya hana ta fita bare ta je shaiɗanun ƙawayen nata su ƙara ba ta wata, ko hakan zai sa ta hankalta ta dawo cikin hayyacinta. Ya gama tsara yadda zai yi a gobe wanda yake ganin shi ne mafitar da zai sauya komai ashe yana nasa ne Allah na nasa bai sani ba. Ba ƙaramin ɓaci ransa ya yi ba da dattin da Hafsah ta baza ta kacaccala gidan ɗazu, amma duk ya shanye saboda ba ya so ya ɓata plan ɗinsa. Dafe kansa ya yi cikin ƙololuwar tashin hankali yana maimaita "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" A fili. Don shi su Sultan kawai yake ji a faruwar wannan al'amarin. Baccin da bai ƙara komawa ba kenan ya ƙarashe sauran dare a zaune. Duk yadda na so bacci ya ɗauke ni bayan na gama haɗa kayan amma ya ƙi zuwa, na dinga tsaki ni kaina cikin takaicin rashin baccin. Wayata na soka a chaji na dinga playing videon sabon gidan Aunty Billy nai ta kalla. Hakan ya sanyaya mini rai, na ji kamar na zuƙo watanni ukun da zan yi na idda, don ba ƙaramin ƙaguwa na yi na gan ni ina rayuwa a irin gidajen nan ba. Tun daga lokacin da Anas ya furta ya ƙarashe ragowar sakin da ya rage mana jikina yake ta rawar da ban san dalilinta ba har safiya. Ni dai na san ban bari sakin ya dame ni ba, amma na rasa me ya sa wani abu mai nauyi yay tsayuwar kafaffiyar bishiya a cikin zuciyata ba. Har gari ya waye Anas bai dawo daga masallaci ba shi da su Sultan, murmushi na yi don na fahimci manufarsa ba zai dawo ba har sai ya tabbatar na bar gidan, saboda kar na ce zan tafi da su. Bai san ma ba zan ce hakan ba, don Kawu ba ƙarfi ne da shi ba yanzu ba zan je na ɗora masa wahala ba, sai na yi aurena zan karɓe su, a lokacin ne dole ya ba ni su ko ya ƙi ko ya so. Kafin takwas na tattara na bar masa akurkin gidansa. Duk da zuciyata na ta azalzalata na kira Maman Nasmah na faɗa mata, amma na ƙi saboda so nake sai na fara gamawa da Kawu tukunna. A soro na tarar da shi kamar yadda na yi zato, saboda tunda ya fara ciwon ƙafa nan ne ya koma mazauninsa a kodayaushe saboda masu zuwa dubiya, sai dare ya yi yake lallaɓawa ya koma cikin gida. Kaina a ƙasa na yi sallama bayan na mayar da fuskata kalar tausayi. Ya amsa cikin fara'a, sai dai gani na janye da ƙaton akwati kuma babu yara ya sa fara'ar tasa ɗaukewa cak tare da fara bi na da kallo mai alamar tambaya. Bayan na tsugunna na gaishe shi ya amsa tare da faɗin. "Lafiya kuwa Hansatu?" Kukan ƙarya na fashe da shi ban ce komai ba. A ruɗe ya ce. "Ba kuka za ki yi ba, bayani za ki mun? Me ya faru na gan ki da wannan ƙatuwar jaka haka? Ina yaran da Anas ɗin?" Cikin sheshsheƙa na ce. "Kawu Anas ya sake ni har saki uku." "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Sa..sa...saki uku fa kika ce?" Ya faɗa kamar zai miƙe, da alama ya manta da lalurar da yake tattare da ita. Ƙara sakin gunjin kuka na yi na ce. "Eh." Salati kawai ya shiga rafkawa cikin tashin hankali, kamar zai yi kuka ya ce. "Hansatu garin yaya haka ta faru? Me kika yi da kika tunzura yaron kirki mai haƙuri ya yi miki wannan arangizon sakin? Jiya-jiya nake cewa Lami kwana biyu shiru ba ki zo ba ke da yara, da ina da ƙafa da na je na yi bikon ku, ko wani laifin muka yi muku, tunda shi yana zuwa, ko wancan satin ma ya zo da kayan dubiyarsa rigijib, kuma bai ce mini wata matsala tana faruwa a tsakaninku ba, bare na ce ko ita ce sila." Cikin makirci na ce. "Babu abin da na yi masa, kawai wata bazawara ce ta shiga rayuwarsa ta asirce shi ta tarwatsa mana farincikinmu, kusan shekara kenan wulaƙancin yau daban na gobe daban Abban Sultan yake mun, ya hana ni abinci ya dake ni ya zage ni ya kore ni, amma duk na daure na shanye. Sau biyu yana saki na amma na ƙi tafiya bare na faɗa wa wani, sai jiya cikin dare ya cikashe mini na ukun tare da yi mini korar kare, sai a wani kango na samu na raɓa kafin gari ya waye. Wai aurensu ya kusa da bazawarar na fice na ba shi guri zai saka ta, kuma ya ƙwace ƴaƴan ya hana ni tahowa da su." Na ƙarashe maganar ina ƙara fashewa da kuka. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Hasbunallah! Subhanallahi! Wanne irin al'amari ne wannan mara daɗin ji? Lallai bawa ba ya taɓa ƙaucewa ƙaddarar shi, Ubangiji ya sa haka shi ya fi alkhairi. Amma duk da haka zan kira Malam Anas ɗin na ji ta bakinsa." Ya yi maganar cikin matsanancin tashin hankali. Gwaggo da ke leɓe tana sauraren mu tun zuwana ta faɗo soron tare da yin farat ta ce. "Kar ka soma kiran shi, ai aikin gama ya riga da ya gama tunda ya yi saki har uku, ka ƙyale shi ya je can ya ƙarata. Na ji duk abubuwan da kuka tattauna ai." Cikin jin daɗin maganar tata duk da na san farinciki take da sakin na ce. "Ni ma haka na gani, saboda ko ka kira shi ba za ta sauya zani ba, kuma yaran ma na san ƙauye ya tafi ya kai su, ba bayarwa zai yi ba." A sanyaye Kawu ya ce. "Shikenan, Ubangiji ya fi mu sanin abin da yake nufi da faruwar wannan al'amarin, Allah ya sa haka shi ya fi alkhairi. Amma ban da kin ce ba ya cikin hayyacinsa da ba zan taɓa yarda yaron kirki kamar Anas ne ya aikata haka ba." Gwaggo ta ce. "To ya za a yi, tunda mai duka ya yi ƙarshen auren kenan, sai dai kawai mu yi addu'ar Allah ya kawo mata wani na gari." Gyaɗa kai Kawu ya yi bai ce komai ba, tabbacin abun ba ƙaramin girgiza zuciyarsa ya yi ba. Da hannu ya mun alamar na tashi na shiga ciki, bayan ya tambaye ni Abban Sultan ya ba ni shaida na ce a'a. Ina lura da Gwaggo kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha don farinciki, don tun can baƙinciki take da yadda muke zaune lafiya da Anas. Murmushi na yi bayan na shiga ɗakina tun na da kafin na yi aure na ce. "Ki yi ta murnarki, ta kusa koma miki baƙinciki, don wanda zan aura ya fi Anas komai da komai." Sai da na gyara ɗakin don ba zai zaunu ba, saboda karikicen da yake cikinsa. Na haɗe wa Gwaggo shirginta a gefe na ɗauki tabarma a ɗakin Kawu na shimfiɗa, sannan na kira Maman Nasmah cikin ɗoki. Ringing biyu ta ɗaga.......✍️ *Zeey Kumurya ✍️ [3/8, 1:42 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGH PENS* (FREE BATCH) *19.* Cikin zumuɗi na ce. "Ta faru ta ƙare!" Cikin rashin fahimta ta ce. "Ban gane ba, ko ya sake kin?" Ina dariya na ce. "Tun cikin daren jiya ma, yanzu haka ina gidanmu." Wata shewa na ji ta saka mai haɗe da ihun murna tare da faɗin. "Don Allah da gaske kike?" Na ce. "Wallahi Allah." Cikin dariya ta ce. "Alhamdulillah! Ni na tabbata na fi ki farinciki da faruwar al'amarin nan, yanzu za ki huta ki wataya ke ma kamar mu." Na ce. "Allah ya nufa ya yarda ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda." Ta ce. "Danmadaƙyar kenan, sakin ukun ne dai ko?" Da sauri na ce. "Ko gargada babu." Dariya ta kuma sheƙewa da ita sannan ta ce. "To Ma sha Allah, yanzu nan da three months kina gama idda zan haɗa ki da Alhaji Kyauta, ku fara shan soyayya." Cikin farinciki na ce. "In sha Allahu." Daga haka muka yi sallama ina murmushi, a muryar Maman Nasmah kaɗai na gane ba ƙaramin farinciki take ba, kamar ma ta fi ni. Hakan ya ƙara mini son ta da yarda da ita a cikin raina, domin mai son ka ne kaɗai zai damu da damuwar ka tamkar tasa, idan abin farinciki kuma ya faru ya fi ka nuna murnarsa. Maman kuwa tsabar daɗin da ta ji rabon kuɗi ta dinga yi wa masu aikinta, ta rasa ina za ta saka ranta don farinciki. Ta san duk inda Anas yake yanzu yana cikin ƙololuwar ɓacin rai da takaicin Hafsah. Don haka za ta yi amfani da wannan damar ta kai kanta gare shi, ta nuna masa soyayya da kulawa, ta share masa hawayen baƙinciki jakar matarsa, za ta je masa a mutuniyar kirki mai kamewa. Babban abin da zai yi mata cikas aurenta, rabon ta da mijin nata kuma kusan watanni biyar baya kenan, shi ma a lokacin da ya zo kwana ɗaya tak ya yi ya ƙara gaba. Ko time ɗin da za su yi magana ba ta samu ba bare ta je masa da buƙatarta. Ita a yanzu ko ƙasar da yake ma ba ta sani ba, bare ta kira shi su yi magana. Tsakaninta da shi kawai kuɗin da yake sakawa a tura mata duk wata ne, sai lokaci zuwa lokaci idan ta je kamfanunnunwansa ta samu information a kansa cikin wayo da dabarar kar ma'aikatan nasa su gane ita da banza duk ɗaya ne a gurinsa, sun ma fita muhimmanci. Tunda su ba a sati ba su yi magana ba saboda sabgar kasuwancinsa. Hafsah kuma ta san yadda za ta yi da ita akan ƙaryar da ta dinga zabga mata a game da mijin Aunty Billy, ta san me za ta yi yadda asirinta ba zai tonu ba. Tun da Hafsah suka shiga cikin gida Kawu ya nisa a cikin tunani, ya kasa yarda Anas ne da wannan ɗanyen aikin, tunda Hafsah ta ce masa asiri aka yi masa amma yana tantama. Hakan ya sa ya janyo ƴar wayarsa ya lalubo numbern Anas ɗin ya kira, sai dai ba ta shiga aka sanar masa a kashe take. Ya kira ya fi sau goma, daga baya ya haƙura ya ajiye wayar, a ransa yana faɗin. 'Allah ya kyauta.' Ina zaune wajen goma Gwaggo ta shigo ta ce. "Ki taso ga wanke-wanke can ki yi da sharar tsakar gida, kuma gidan babu abin kari tunda uban naki ba ya fita yake yi ya nemo ba, sai dai ki fitar da kuɗinki ki siya." Ɓata fuska na yi na ce. "To." A shaƙe. Ina gungunin daga zuwa na za a fara takura mini na tashi na fitar tsakar gidan da ya yi buɗuɗu da ƙura da ledodi. Da ma kafin na yi aure ni nake komai na gidan, saboda Gwaggo irin matan nan ne masu mugun son jiki, ba ta son motsa jikinta ko kaɗan, ta fi son kullum tai ta jibgewa kamar kayan wanki. Ina toshe hanci saboda ƙura na share tsakar gidan da wata ficiciyar tsintsiya da ta sagar mini da hannu. Bayan na gama na wanke toilet, masan gargajiya ce kuma ta cika ta yi hani'an kamar kashin ciki zai fara malala, ga shi a buɗe take fayau babu ko ɗan murfi. Ina gamawa na dinga kwara amai, saboda ƙyanƙyami da uban warin da na shaƙa. Kallo na kawai Gwaggo take ta na taɓe baki, ba sannu bare na gode. A ranar na ce wa Kawu a samo masu kwasar masai su kwashe zan biya, don ba zan iya rayuwa da wannan toilet ɗin ba. Ya dinga saka mini albarka tare da tarin addu'oi. Saboda kullum da takaicin lalacewar banɗakin yake kwana yake tashi, ba shi da halin gyarawa ne kawai ya saka bai gyara tuntuni ba. Amma sai da ya tambaye ni ina na samu kuɗin? Bayan na ce har abinci Anas daina ba ni ya yi. Ƙarya na yi masa na ce wani abu na siyar a cikin kayan ɗakina, sai jiya aka kawo mun kuɗin na taho da shi. Washegari da safe na je na kwaso barguna da zanin gado saboda shimfiɗa, don ba zan iya kwanan kan tabarma zalla ba. Daga yadda na ga gidan na gane bai dawo ba tun fitar da ya yi, tabbacin ƙauyen ya tafi kenan. Haka rayuwa ta ci gaba da garawa, kwata-kwata bana jin daɗin zaman gidan Kawu saboda Gwaggo, ga shi komai ni nake yi da kuɗina, hakan ya sa duk kuɗaɗen hannuna suka ƙare karaf. Yau da safe bayan na gama duka aikin gidan da tulliƙar wankin kayan Gwaggo na je soro gurin Kawu. Bayan mun gaisa na marairace na ce. "Kawu ina son zuwa asibiti anjima, kwana biyu ciwon kai da na ƙirji ya dame ni." Cikin jimantawa ya ce. "Subhanallahi! Hansatu kar ki bari damuwa ta saka miki wani ciwon fa, ki yi haƙuri ki daure ki fawwala wa Allah komai, na san abin da ciwo, kuma dole ki damu ko don ƴaƴanki da ba sa gabanki." Hawayen ƙarya na fara ban ce komai ba, ya dinga yi mini nasiha sannan ya ce na tashi na tafi. Cikin farinciki da murna na shirya na fita. Direct gidan wata dilalliya a unguwarmu na je, na faɗa mata ina son zan siyar da kayana. Ta ce mu je ta gan su. Bayan ta gani ta yi musu kuɗi, ban tsaya ciniki ba na ce ta bayar kawai duk da tayin wulaƙanci ta yi musu, ga shi kuma sun sha jiki da ma kuɗin ba na kirki ba ne. Rabin kuɗin ta ba ni ta ce za ta cika sauran daga baya. Gidan gabaɗaya ya yi ƙura ya fice daga hayyacinsa, na dinga tambayar kaina ni kaɗai ina Anas ya tafi da har yanzu bai dawo ba? Ina ya kai mini su Sultan da kewar su take ta damu na? Rashin amsa ya saka ni taɓe bakina, na ci gaba da sabgogina. Har katifata na siyar, saboda babu amfanin da za ta mun, tunda wanda zan aura yana da arziƙi shi zai yi komai kamar yadda Maman Nasmah ta faɗa. Kawu kuma da ma na riga na yi masa ƙaryar na siyar komai nawa. Sai yamma lis na koma gida cikin farincikin samun ƴan kuɗaɗe. Sai dai kuɗin ba su fi sati ba suka ƙare, ciyar da kai da su labulun wanka da na wanki ba wasa ba ne. Ƙara komawa gidana na yi na tsitstsinci wasu abubuwan na ƙara siyarwa. Wasa farin girki, kafin na gama idda sai da na siyar da kusan komai nawa, kayan sakawa da ɗan abin da ba za a rasa ba ne kawai suka yi saura. Ƙarshe har wayar hannuna na siyar na siya wata ba kamfanin iphone ba, shi ne ma na ɗan samu kuɗi masu tsoka a hannuna. Yau Juma'a, wadda ta yi daidai da gama iddata. Cikin tsananin farinciki na tashi ina jin zuciyata fes kamar an yi mini bushara da gidan aljanna. Kafin Kawu ya fita soro ya janyo ƙafa ya zo ƙofar ɗakina ya ce. "Hansatu yau lafiya ba ki fito ba har yanzu?" Na ce. "Lafiya ƙalau Kawu, ina kwana?" Ya ce. "Lafiya lau, yau kin kammala idda ko?" Na ce. "Eh, kwana ɗari ba goma ya tabbata." Cikin jimami ya ce. "Kullum da lamarin nan nake kwana nake tashi, har yanzu zuciyata rawa take yi, gani nake kamar mafarki nake zan farka. Ga shi ina ta kiran shi Anas ba na samun shi, bare na roƙe shi ya taimaka ko da sau ɗaya ne ya kawo miki yaranki ki gan su, raba uwa da ɗa ba daɗi." Ban ce komai ba na fara sheshsheƙar ƙarya, irin abin yana damuwa ɗin nan sosai. Cikin tausayawa ya ce. "Ki ci gaba da haƙuri ki ta addu'a, in sha Allah hakan alkhairi ne, Allah ya kawo miki wani mijin na gari wanda ya fi shi." Ina jan hanci na ce. "Ai ni Kawu ba zan sake wani auren ba, a haka zan ta zama, na haƙura, saboda ban san ƙalubalen ƙara fuskanta ba a cikinsa." Da sauri ya ce. "Ashsha! Kar ki ce haka, ai komai ya faru da bawa da sanin Ubangiji, za ki ji daɗi ki yi farinciki a gaba in dai ba ki da haƙƙin shi. Ke dai ki ta addu'a kawai, amma kar ki kuma faɗar haka." Na ce. "To Kawu." Bayan ya tafi na kira Maman Nasmah, bayan mun gaisa na ce. "Yau Allah ya yi aure da mara kwabo, na kammala idda, da ma a addinance tun last week na yi jini uku na gama, na bari na cikashe kwanakin ne saboda lissafin mutane." Ta ce. "Bar kan ki, na taya ki murna." Na ce. "Bari ke dai, ya maganarmu?" Ta ce. "Hmm, abu fa ya lalace." Cikin faɗuwar gaba na ce. "Ban gane ba!" Ta ce. "Hmm, ashe tuntuni Alhaji Kyauta ya gaji da jira ya yi auren shi, yanzu haka suna can honeymoon ma shi da amaryar tasa." Wani irin jiri na ji yana kwasa ta daga zaunen da nake. Cikin matuƙar razani gami da firgici na ce. "Na shiga uku! Yanzu sai da na kashe auren nawa shi kuma zai ce a'a, da can me ya sa bai faɗa ba?" Cikin son kwantar mini da hankali ta ce. "Mene abin damuwa to?" Kamar zan fashe da kuka na ce. "Akwai mana, don Allah ki roƙe shi ko a ta uku ne ya daure ya aure ni, wallahi ko kaɗan ba na jin daɗin zaman gidan nan namu, ga yarana ina son na ɗauko su." Ta ce. "Ai kin fi ƙarfin zama da kishiyoyi biyu, ɗayar ma a plan ɗina kina shiga za ki fitar da ita. Rasa Alhaji Kyauta ba abin ɗaga hankali ba ne, maza masu kuɗi hamshaƙai suna nan da yawa a duniya, akwai wani abokin mijina matarsa ta rasu last year, yana ta damu na, na samo masa mata amma na mayar da abun wasa, har yanzu kuma bai yi aure ba. Don haka yanzu sai na haɗa ku, don ko shekaran jiya ma ya yi mini maganar, ba shi da matsala ko kaɗan, kuma yana da bala'in kuɗi." "Ya kai mijin Aunty Billy?" Na katse ta da faɗin haka. Tsaki ta ja ta ce. "Ya ma fi shi, ki bari na haɗa ku za ki gasgasta ni, yanzu zan tura masa hotunki da lambarki, ke ma na tura miki nasa." Cikin zumuɗi na ce. "Na ji daɗi amma, gaskiya ban san da bakin da zan gode miki ba, kin gama yi mini komai a duniyar nan." Murmushi ta yi mai sauti ta ce. "Kar ki damu ƙawata, matuƙar ina raye ba za ki taɓa zubar da hawaye ba. Abin da ba ki sani ba ma, wallahi ko mijina ne zan bar miki ki aure shi, ni dai ki yi farinciki kawai shi ne burina." Cikin mamaki na zaro ido kamar tana gabana tare da faɗin. "Mijinki fa kika ce?" Ta ce. "Eh, mene ne a ciki, kin wuce haka a gurina ai, kuma kar ki ji zancen wasa, ko a yanzu kika ce kina son shi wallahi za ki aure shi, idan kuma ba ki yarda ba ki gwada ki gani." Jinjina kai na yi na ce. "A'a, ko a mafarki ba zan taɓa auren mijinki ba har abada, mu ma bar wannan maganar." Dariya ta yi ta ce. "Kin ji an ɗaga taro sai bayan Sallah ko? Saboda azumi ya ƙarato." Na ce. "Eh, ai na ji daɗin haka, saboda kafin lokacin in sha Allah ina gidana na alfarma." Ta ce. "Ko tantama babu tawan." Mun daɗe muna tattaunawa akan yadda abubuwa za su wakana sannan muka yi sallama, zuciyata cike da so da ƙaunar Maman Nasmah, tamkar ƴar'uwata da muka fito ciki ɗaya haka nake jin ta, tunda da za ta iya sadaukar da komai nata saboda ni. Bayan na gama duka ayyukan gidan saboda sababin Gwaggo na yi wanka, ina shiryawa na ji ƙarar shigowar message. Da sauri na janyo wayar na duba, don a zatona lambar mutumin Maman Nasmah ta turo mini. Amma sai na ga lambar Anas ce. Ban san me ya sa ba na ji zuciyata ta doka, jikina na mazari na buɗe amma sai na ga babu komai, ba abin da aka rubuta. Umarnin kiran shi zuciyata ta ba ni, bijire mata na yi cikin takaicin yadda na damu, cikin haushi na ja tsaki tare da taɓe baki ina faɗin. "Goge lambarsa ma zan yi, kar zamanta a cikin wayata ya shafa mini salalan tsiyar talauci." Bayan Azhar na karɓo wayata daga chaji na ga an kikkira ni da baƙuwar number har two missed call. Bin bayan kiran na yi, tana shiga na ji an katse an kira. Kafin na yi magana na ji wata irin murya mai sanyi da kamewa ta yi sallama. Amsawa na yi tare da faɗin. "Wa ke magana?" Bai amsa ba ya ce. "Da fatan ina magana da tauraruwa mai hasken da ya haskake zuciyata tun kafin na gan ta a zahiri?" Shiru na yi ina maimaita kalamansa a cikin raina, sai da ya ƙara magana sannan na ce. "Ai gabaɗaya ka sani a duhu ne, har na fara tunanin ko wrong number ka kira." Murmushi ya yi mai sauti wanda na ji shi har cikin kaina ya ce. "Ai zuciya ba ta taɓa mistake akan dukkanin abu mai muhimmanci a gare ta, ke ce wadda nake nema Hafsah." Ya yi shiru na wasu sakanni alamar ba ya iya dogon zance sannan ya ci gaba da magana. "Sunana Mansur Ibrahim Idonnera, ƙawarki takwararki ce ta ba ni numbernki, tunda ta tura mini hotunki na gani na rasa sukunina gabaɗaya, tun lokacin har yanzu ina kwance ina ta tunaninki ne kawai, sai yanzu da kika ɗaga na ji wannan zazzaƙar muryar taki na ji na fara samun nutsuwa." Ƙaƙƙarfar ajiyar na sauke, da ma ina ta addu'a Allah ya sa shi ne wanda Maman Nasmah ta ce za ta haɗa mu, don muryarsa kaɗai ta tabbatar da yanayinsa, yadda yake magana a kasalance yana jan numfashi ba ƙaramin burge ni ya yi ba, daga ji babu tambaya jiƙaƙƙe a can ƙasan tekun kuɗaɗe, ga sunansa kuma da ya ƙara tabbatar mini da haka. Murmushi na yi tare da kwanciya don wayar ta fi armashi na ce. "Duk wannan yabon ni kaɗai?" Ya ce. "Kin fi gaban haka ma zinariyar mata, yanzu dai ki sanar mini na karɓu ko sai na ƙara zage damtse kar zuciyata ta buga." Siririyar dariya na saki tare da ƙanƙame wayar ban ce komai ba. "Dariya mai daɗi da saka nishaɗi." Ya faɗa ƙasa-ƙasa kamar mai raɗa. Hakan ya haifar mini da tashin tsigar jiki. Lumshe idona na yi na ce. "Idan akwai abin da ya fi karɓuwa ma ka yi shi a gurina." Ya ce. "Wow, thank you, dole na bayar da tukuicin amsar nan." Murmushi na yi na ce. "Ai kai ne tukuicin." Ya ce. "Bayan ni ma akwai buƙatar wani, ki tura mini account number ɗinki na saka mini tukuicin, ko kuma ki faɗa mini wani abun da kike so na saka a kawo miki." Cikin jin daɗi na ce. "Na gode, amma account ɗina ba ya aiki yanzu." Don ba zan ce ban da shi gabaɗaya ba ya raina ni." Ya ce. "Zinariya guda ba account kuma nake zaune, bari na kira wani na haɗa ku, sai ki je bank ɗinsu ya buɗe miki duk lokacin da kike so, ni yanzu ba na Nigeria ne amma da ni zan zo na kai ki da kaina." Na ce. "Babu komai, hakan ma ni ce da godiya." Daga haka muka yi sallama bayan ya ce zai tura mini kati. Ina ta rawar murna na samu irin mijin da nake so message ya shigo wayata, ina dubawa na ga credit ne na 20k, murza idona na yi don ƙara tabbatarwa ko shi ne bai ganar mini daidai ba, amma still haka na gani. Waro ido na yi na yi tare da dafe ƙirjina na ce. "Katin dubu ashirin? Katin waya na kira kawai!" Gabaɗaya sai na ruɗe na susuce, na kira Maman Nasmah na sanar mata ba ta ɗaga ba. Sai na hau online na shiga chat ɗinmu, na ga ta tuttura mini hotunan Mansur, cikin azarɓaɓi na buɗe cike da matsuwar son ganin yadda kamanninsa da komai nasa za su kasance........✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:42 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGHT PENS* FREE BATCH *20.* Ƙura wa hoton farko da na buɗe ido na yi, ina bin kowacce gaba ta jikinsa da kallo ɗaya bayan ɗaya. Baƙi ne amma mai haske ba mai duhu ba, kuma yana da ƙiba, sannan ba matashi ba ne kamar yadda na yi tunani don ya fara manyanta, amma a muryarsa da yadda yake magana na ɗauka bai fi matashi ɗan 35 years ba. Hannunsa da ya fi fuskarsa haske sosai tabbacin hutu na kalla ina murmushi. Daga yanayin suturar jikinsa da gurin da aka yi masa hoton kaɗai ma ya gamsar da ni. Ci gaba da kallon sauran na yi, wasu ma duk a ƙasashen waje ya ɗauka. Reply na yi mata da thanks kawai na fita daga chat ɗin. Wani irin fayau nake jin zuciyata kamar an wanke mini ita da tsintar wannan dami a kalan da na yi. Da yamma na je gurin masu siyar da kati na yi musu transfer ɗin na 15k suka ba ni kuɗin, daga nan shagon masu siyar da mayuka na je na siya mai ɗan kyau da sabulu da turare, dan so nake na fara gyara jikina kafin ya zo mu haɗu. Ina son na je gidan Maman Nasmah saboda mu fi tattauanawa yadda yakamata amma ina tsoron Kawu, don ɗan nan da can idan na ce za ni da ƙyar yake bari na. Tun wayar da muka yi da Mansur ba mu kuma waya ba har sai washegari da safe, ya kira ni ya ce ayyuka ne suka yi masa waya, muna gama wayar shi ma kamar jiya ya turo mini da credit na 20k. Da ma jiya da muka yi chat da Maman Nasmah na faɗa mata ta ce ai shi bai mayar da 20k kuɗi ba, indai Idonnera ne yanzu na fara ganin ɓarin kuɗi. Ranar Monday na yi wa Kawu ƙaryar zan koma asibiti, ciwon kai da na ƙirji sun ƙara dawo mini, ya dinga yi mini faɗa da nasiha akan na cire damuwa a cikin raina, na zama mai tawakkali, don shi duk a zaton shi damuwar sakin ce take sanya mini ciwon. Na ce masa in sha Allah zan rage, sannan ya bar ni na tafi. Banki na je aka buɗe mini account, ina zuwa ban wani tsaya bin layi ba, saboda wanda Mansur ya haɗa ni da shi, shi ya zo ya shigar da ni ya yi mini komai. Bayan an gama na kira shi, bai ɗaga ba kamar yadda na yi zato ya katse ya kira da kansa. "Ranki ya daɗe." Ya faɗa cikin sanyin muryarsa. Murmushi na yi na ce. "Tare da naka, an kammala komai shi ne na kira na sanar maka." Ya ce. "Ma sha Allah, yanzu na ji ni daidai, amma da Madam babu account babu hanyar da zan tura mata kuɗin da za ta siya kayan kwalliya ta mun ai ba kanta." Dariya na yi na ce. "To dole kai sai ka tura mini kuɗi?" Ya ce. "Mene amfaninsu idan ban ba ki ba? Kin ga kwana ukun a takure na yi su saboda ban tura miki kuɗi ba, don haka yanzu turo mini account number ɗin kawai na fara tura miki kuɗin powder kafin na zo." Cikin farinciki na ce. "An gama." Tare da katse kiran na tura masa. Tabbas sai yanzu na samu namiji irin wanda ya dace da ni, mai buɗaɗɗen hannu ba irin Anas matsolo ba, tsabar so da tarin dukiya har matsuwa ya yi ma ya tura mini kuɗi. Ƙarar shigowar message ya saka ni saurin duba wayata, yawan kuɗin da na gani ya saka ni zaro ido ina ƙara bitar zirukan, idan ba idona ne yake yi mini gizo ba one million na gani. Ban gama tantacewa kiransa ya shigo. Cikin azarɓaɓi na ɗaga, na ce. "Na ga alert, Ranka ya daɗe ai kuɗin sun yi yawa." Cikin dariya ya ce. "One million ɗin? Ai ni kira na yi na ji idan ba za ta isa ba na ƙaro." Na ce. "A'a, ta yi yawa ma na go...." "Babu godiya a tsakaninmu, don haka daga yau kar ki kuma, million kuma ki shirya tarɓar ta, don kin kusa fara kyautar ta nan kusa ba ma a ba ki ba, don haka ki daina cewa ta yi yawa." Ya katse ni da faɗin haka. Ƙara dashare bakina na yi don tun ɗazu ya ƙi rufuwa na ce. "Tom shikenan my dear, Allah ya ƙara arziƙi da wadata." Ya ce. "Amin, ki jira a nan bank ɗin yanzu zan turo ɗaya daga cikin yarana ya kai ki shopping Mall ki zaɓi duk abin da kike so, kafin na dawo mu je tare." Danne ruɗun da nake ciki na yi na ce. "To." Daga haka muka yi sallama. Ni kaɗai na dinga murmushi, na manta a cikin mutane nake, don gabaɗaya na kasa control ɗin gigicewar da kuɗin suka saka na yi. Har yaron nasa ya zo muka tafi ban daina kallon alert ɗin ina murmushi ba. Ƙara ruɗewa na yi bayan na shiga cikin motar da ya zo da ita, don ba ƙaramar haɗuwa ta yi ba. Wani haɗaɗɗen guri ya kai ni, ya ce na ɗauki duk abin da nake so, Oga ya bayar da maƙudan kuɗaɗe. Na yi dariya kawai ban ce masa komai ba. Zagewa na yi ban yi wa kaina ƙauro ba na jibgi kaya, ina ganin na loda da yawa amma yaron ya ce sun yi kaɗan ya ƙara ɗibar mini wasu. Da muka je gurin biyan kuɗi na ji kuɗin kayan ba ƙaramin girgiza na yi ba, amma shi ko a jikinsa ya zaro ATM ya ba da aka zara muka taho. Rashin sanin ta yadda zan shiga gida da uban kayan ya sa na ce ya kai ni bayan layinmu, na kai su ajiya gidan wata mata da muke mutunci da ita. Bayan mun ƙarasa na shiga na yi mata bayani ta ce. "Inyee, su Hafsah har an fara zaurawan ne?" Murmushi na yi tare da ƙirƙirar abin da zan faɗa mata, don ba zan nuna ina son shi ba a ce da ma muna tare tun da, ko kuma a gane plan ɗina. Cikin ɓata rai alamar ba na so na ce. "Wallahi kuwa Maman Sabir, daga na je asibiti wani mutumi yay ta bi na da naci da magiyar na ba shi lambata, bayan na ba shi kuma ya ƙi ƙyale ni wai sai ya kawo ni gida, shi ne ya tsaya a wani guri ya yi mini siyayya, na ce ba zan karɓa ba amma ya nace, har ƙaryar ni matar aure ce fa na yi masa amma ya ƙi yarda." Ta ce. "To ai abin farinciki ne wannan, sai ayi ta addu'a Ubangiji ya sa da shi za a yi idan da alkhairi." Na ce. "Gaskiya ni ban shirya aure yanzu ba, ko zan ƙara aure ba yanzu ba." Ta ce. "A'a kar ki yi wannan gangancin, domin kuwa dama ce Allah ya ba ki, ai haka abin yake da ma, mace tana yin idda za ki ga maza sun fara tururuwar zuwa mata, kamar waɗanda ake sanarwa." Na ce. "To Allah ya kyauta, bari na je na dawo." Cikin tsokana ta ce. "To ki gaishe shi ki ce in ji surukarsa." Na yi dariya kawai ban ce komai ba. Mun ci gaba da shan soyayya ni da Alhaji Mansur Idonnera, idan muka fara waya har mantawa nake yi kati ake zara saboda daɗewa, ga shi kuma ya ce mini ba ya ƙasar, wani tsari yake yi da duk ƙasar da ka je da sim ɗinka za ka yi amfani, amma ba ƙaramin kuɗi ake ɗauka ba. Idan mun gama wayar mu ɗora da chatting. Sati ɗaya da haɗuwarmu amma kullum sai ya tura mini credit ɗin 20k ya ce na saka data. Hakan ya sa ni kasancewa a cikin nishaɗin da ban taɓa riskar kaina a ciki ba, tare da ƙara mantawa da Anas, su Sultan ne kullum sai na tuna su, amma shi ma ban bari yana damu na ba. Na ƙara tabbatarwa kuɗi su ne jin daɗin rayuwa, su ne gishirin zaman duniya kamar yadda ake yi musu kirari, su ne farincikin komai a rayuwa. Yau Friday yau muka yi da shi zai zo mu haɗu, duk da ina murnar ganin shi amma da fargabar yadda zan sanar da Kawu batun shi na tashi. Ba na so ya yi zargin wani abu ko ya saka ayar tambaya a kaina, don mutum ne shi mai zurfin tunani da nazari. Ina zaune bayan an sakko daga masallaci na samu mafita, akwai wata kamar Yaya take a gurin shi, zan ce masa zan je gidanta na gaishe ta, idan ya so sai Alhaji Mansur ya je can mu haɗu. Don na san ita ba za ta hana ba, musamman idan ya zo ta ga mai kuɗi ne, don irin matan nan ne masu azababben son kuɗi. Cikin murna na shirya, bayan na rufe na ɗakina na yi wa Gwaggo sallama na fita. Na tsugunna a soro na ce. "Sannu Kawu, ya jikin?" Ya ce. "Da sauƙi Alhamdulillah." Na ce. "Allah ya ƙara afuwa." Ya ce. "Amin ya rabb." Kaina a ƙasa na ce. "Da ma gidan Inna Habi nake son zuwa na gaishe ta." Ya ce. "Da kuwa kin kyauta, ga shi kuwa Juma'a ce ga ladan Zumunci, ki je Allah ya kiyaye, ki gaishe ta." Na ce. "Za ta ji." Har na miƙe ya tsayar da ni da faɗin. "To kina da kuɗin mota?" Na ce. "Eh Kawu." Ya ce. "Kar fa ki yi tafiyar ƙafa, idan ba ki da shi ki faɗa na ba ki." Na ce. "Ina da shi wallahi." Ya ce. "Toh shikenan Allah ya kiyaye hanya, kar ki dare amma." Na ce. "To." Duk ci da kaina ɗin da nake yi Kawu bai sani ba, don shi duk a zaton shi Gwaggo ce take ciyar da ni a cikin abincin siyarwarta, saboda duk ƙi na da take yi da muguntar da yi mini a baya ba ta taɓa nunawa a gabansa, yi take kamar za ta lashe ni saboda soyayya idan a gaban idonsa ne, shi ya sa har yau bai gane makircinta ba, ni kuma ban taɓa faɗa masa ba. Na san ko da ba kullum ba zai taɓa zama bai ba ta kuɗin cefane da abin da za a dafa ba, ƙeta ce kawai ta saka ba za tana ba ni abincin ba. Ni kuma ban damu ba tunda Allah ya rufa mini asiri, kuma ba jimawa zan yi a gidan ba zan tafi gidana na alfarma. Kawu kuwa da kallon tausayi ya bi bayan Hafsah har ta fice, ya yi alƙawarin duk inda ta tambaye shi za ta je ba zai hana ta ba, amma ba wai zai bar ta tai ta gantali ko'ina ba ne. Saboda ya san fitar ce take ɗan ɗeɓe mata kewar halin ƙuncin da take ciki. Da sallama na shiga gidan Inna Habi, na tarar da ita a zaune a tsakar gida tana dakan daddawar miya. Ba yabo ba fallasa ta amsa mini, don ba wani kula Kawu take ba saboda talaka ne, don ita indai kaga ta shigewa wa mutum to yana da maiƙon da za ta lasa ne. Tsugunnawa na yi har ƙasa na ce. "Ina yini Inna?" Ta ce. "Lafiya ƙalau, ya Baban naki da jiki?" Na ce. "Da sauƙi Alhamdulillah." Ta ce. "Ma sha Allah, Allah ya ƙara sauƙi. Har kin yi idda ko?" Na ce. "Eh, tun wancan satin ma." Ta ce. "To Allah ya sa haka shi ya fi alkhairi, ya kawo miki wani mijin na gari, ga tabarma can je ki zauna, bari na kawo miki ruwa." Na ce. "To Inna." Bayan an yi la'asar na share mata tsakar gida da ɗaki, ta gama abinci ta zuba mini muna ƴar hira. A lokacin na sako mata zancen Mansur, ina kallon wayata da message ɗinsa ya shigo na ja tsaki. Inna ta ce. "Ke kuma lafiya kike jan tsuka ke kaɗai?" Ɓata fuska na yi na ce. "Wani ne ya dame ni wallahi, wai dole sai ya zo mun haɗu yau." Ta ce. "Wane ne? A ina kuma kuka haɗu?" Yadda na faɗa wa Maman Sabir haka na zayyana mata ita ma." Haɓa ta kama ta ce. "To shi ne me? Mene abin damuwa? Ki tsaya ki saurare shi, ki bar shi ya zo. Ki cire wancan tsohon mijin naki daga ranki ki fuskanci abin da yake gabanki." A shagwaɓe na ce. "Inna yana da kuɗi daga gani mutumin, ni kuma gaskiya ba na son irin masu mahaukatan kuɗin nan." Dundu ta ɗaka mini ta ce. "Ku ji mini sakarar yarinya kai, Allah ya kawo miki tsuntsu daga sama gashashshe za ki butulce masa, wa yake ƙin kuɗi? Ai kuɗi abin so ne, tashi ki je masa ki share seat room ki ƙara gyara shi, ki zo ki karɓi turaren wuta ki saka, sai ku yi zancen a can." Ina murmushi na tashi cikin farincikin haƙata ta cimma ruwa, da ma na san ina cewa mai kuɗi ne za ta goya mini baya, kuma da ma a gurinta kaɗai nake tunanin samun haɗin kai cikin ruwan sanyi. Address ɗin gidan na tura masa, da ma text ɗin da ya yi mini kafin na yi mata maganarsa akan yana jiran address ɗin ne. Sai da ta saka na sake sabon wanka na yi kwalliya, ta ba ni turare na fesa. Bayan Magriba ya yi mini text ga shi a ƙofar gidan, inda Allah ya taimake ni mota tana shiga cikin layin. Da zan fita ta ce. "Ki sakar masa fuska fa, kar ki cukule ki yi dinkum, kin ji na faɗa miki." Na ce. "To Inna." Da na fita na yi zaton zai fito daga motar ne, sai ga bai yi hakan sai horn ma da ya danna. Ina murmushi na ƙarasa gurin motar na buɗe front seat, zuciyata cike da kewar shi, don yau kwata-kwata ba mu yi waya ba sai dai chat, saboda yana cikin hayaniya ya jejje companies ɗinsa don ganin yadda abubuwa suke tafiya.......✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:43 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *21.* Idanunsa ƙir a kaina fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce. "Welcome Madam, ban san sunan da zan ba wa ranar yau ba saboda tsananin farincikin da nake ciki." Ban ba shi amsa ba har sai da na zauna na rufo motar sannan na ce. "Ya na ji muryarka a dashe? Ba dai mura ce ta kama mini kai ba?" Ya ce. "Ita ce mana, wannan zirga-zirgar da na yi ce ta saka." Na ce. "Sannu Allah ya ƙara sauƙi." Ya ce. "Amin ya rabb, ashe Camera rage miki kyau take yi, a fili kin fi kyau sosai." Fari na yi masa da ido na ce. "Kai ma haka ai, Ina yini? Ko gaisawa ba ka bari mun yi ba." Ya ce. "Ana ta kai wa yake ta kaya? Gabaɗaya ni kin ruɗa ni ne ai, gaskiya dole na samu wata gwaggwaɓar kyauta na yi wa Maman Nasmah, saboda haɗa ni da tauraruwar matan da ta yi." Na yi dariya kawai ina ƙare masa kallo, ƙamshinsa mai daɗi da sanyin AC na ratsa ni. Mun daɗe muna hira, da zai tafi ya raka ni har bakin soro, ya ce na kira Inna ya gaishe ta, bayan sun gaisa ya ba ta kuɗi, ni ma da zai wuce ya ba ni bandir ɗin ƴan ɗari biyar. Da murna Inna ta rungume ni bayan na koma, tana dariya ta ce. "Yanzu kika yi miji, ai irin waɗannan kullum su muke addu'a da fatan ku samu, rabon arziƙi ne ya sa kika baro gidan wancan matsolon." Na ce. "Haka ni ma na ce, amma ni Inna Kawu kawai nake ji, don shi Alhajin ya ce ba ya so bikinmu ya kai azumi." Dafa kafaɗata ta yi ta ce. "Kwantar da hankalinki, saboda yanzun nan ma na kira shi na ce masa a nan za ki kwana, gobe da kaina zan je na yi masa bayani, na gama shirya duk abin da zan ce masa, ke ma anjima zan faɗa miki, yadda bakinmu ba zai zama biyu ba, yanzu bari na siyo mana tsire mu ci, wancan tuwon a ba wa almajirai shi kawai." Ina murmushi na ce. "To Gwaggo sai kin dawo." Kusan raba dare muka yi muna tsara yadda abubuwa za su kasance, ni kuwa zuciyata fes na yi amanna da duk ƙaryar da Inna za ta faɗa wa Kawu, don ko ban yi bincike akan Mansur ba na san ba zaɓan tumin dare ba ne, saboda na yi amanna Maman Nasmah ba za ta taɓa haɗa ni da wanda ba ta aminta da shi ba. Washegari wajen ƙarfe goma muka koma gida tare da Inna, bayan mun gaisa da Kawu na shige ciki na bar su tare, cikin raina ina addu'ar Allah ya sa kar ya ba mu matsala a cikin auren nan, don na san halinsa tsaf zai ce a'a idan ya ji irin kuɗin da Alhaji Mansur yake da shi. A tsanake Inna ta dubi Kawu ta ce. "Ɗan'lami magana nake tafe da ita mai muhimmanci fa." Kawu ya ce. "To ina sauraren ki Yaya Habi." Ta ce. "Yawwa, yarinyar nan Hafsah jiya da ta je wani ƙanin mijin maƙociyarmu ya gan ta ya ce yana so, babban mutum ne mai hankali da kowa yake yabon shi, matarsa ce ta rasu shekara ɗaya da suka wuce, bai sake aure ba har yanzu kuma bai taɓa haihuwa ba." Gyara zama sosai Kawu ya yi ya ce. "A ina yake? Mene ne kuma sana'arsa?" Inna Habi ta ce. "Ɗan kasuwa ne, sauran bayani kuma idan ya zo duk zai yi maka da bakinsa, don shi a yadda muka yi magana jiya a ƙage yake, kafin azumi yake son a yi komai idan mai duka ya nufa." Jinjina kai ya yi ya ce. "Amma Yaya kamar ya yi kusa yarinyar nan ta sake aure kafin azumi, don har yanzu tana cikin damuwar mutuwar wancan auren nata, da bari muka yi ta huta sosai, radadi da zafin abun ya bar cikin ranta." Da sauri Inna ta ce. "Wanne hutu kuma? Ai ba ta buƙatar wani hutu, idan ta yi auren ai shi ne abin zai fi saurin barin cikin ranta ta manta da wani Anas, kai dai kawai ka yi mata addu'a, ƙila rabon wasu ƴaƴan da ba na wancan ba ne ya fito da ita. Kuma ita ma fa ta amince da na yi mata magana." Kawu ya ce. "Hafsan da kanta?" Ta ce. "Ita fa." Numfashi ya sauke ya ce. "To Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ki ce ya zo mu zanta, idan har ta amince da shi kuma ba shi da wani aibu da za a hana shi aure shikenan, sai a yi." Cikin farinciki ta ce. "Yawwa, ko kai fa, ai ita bazawa ba a buƙatar yin jinkiri a lamarin aurenta." Da Inna ta sanar mini yadda suka yi ba ƙaramin murna na yi ba, a lokacin Kawu ya kira ki ya tambaye ni zan iya yin aure yanzu? Kuma ina son wanda Inna ta zo masa da batunsa? Tun kafin ya gan shi gara ya ji ra'ayina. Kaina a ƙasa na amsa da na amince. Ya yi mana addu'a tare da fatan alkhairi. A ɗokance na kira Alhaji Mansur bayan na koma cikin gida na ce. "Kawu ya ce duk lokacin da ka shirya ka zo yana son ganin ka." Muryarsa ɗauke da farinciki ya ce. "Kai amma na ji daɗi, Alhamdulillah! Ai ni a shirye nake, anjima da daddare in sha Allahu zan zo." Ina murmushi na ce. "Sai ka zo, zan sanar masa, amma don Allah zan roƙe ka wata alfarma." Ya ce. "Faɗi kanki tsaye darling." Na ce. "Yawwa, idan ka zo gurin Kawu don Allah kar ka ba shi ko taro har ku tafi, hakan zai fi sakawa ya fi amincewa da kai." Murmushi ya yi mai sauti ya ce. "Shikenan, duk da abin yana da matuƙar wahala a gurina, don ni ban san me ya sa ba hannu har ƙaiƙayi yake wajen yin kyauta, bare kuma Babana guda na je har gabansa na kasa ba shi kuɗi, anya zan iya kuwa?" A shagwaɓe na ce. "Please my Man." Cikin marairacewa ya ce. "Ya zan yi, yadda kika ce ai haka za a yi." Na ce. "Yawwa thank you." Inna Habi ce ta sanar wa Kawu zuwan Alhaji Mansur Idonnera, har dare kuma ba ta tafi ba, ta ce sai sun zo ta ji yadda aka yi. Gwaggo dai da ido kawai take bin mu. Kamar yadda ya alƙawarta bayan isha'i suka zo, na ce masa su shiga soron kawai, don kunya nake ji na tsallake Kawu da sunan na fita zance. Hakan ya sa har suka tafi ba mu haɗu ba, sai waya muka yi ya mun sallama, yana ta yabon yadda Kawu ya tarɓe su. Shi ma Kawun yabon nasu ya yi ta yi, ina jin shi yana cewa Inna. "Ma sha Allah, yaron akwai tarin ilimin addini sosai, magana da komai nasa cikin nutsuwa da ilimi yake yi." Washe baki ta yi ta ce. "Ka gani ba, ka ga abin da nake faɗa maka ai." Ya ce. "Na gani kam, yanzu mun gama magana na ce ya turo manyansa neman izini kafin ta fara fita gurin shi, sai su fahimci juna." Inna ta ce. "Hakan ya yi, Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Ya ce. "Amin ya hayyu ya ƙayyum." Kwana uku a tsakani Mansur ya turo magabatansa suka kawo kuɗin aure da sadaki, Kawu da wani abokinsa da maƙotanmu guda biyu ne suka karɓa, duk da Kawu bai so haka ba, don shi tambaya kawai suka ce masa za a yi ban da kawo kuɗi, ya yi niyyar ƙin karɓa amma ragowar suka ce a karɓa kawai, yarinya ta samu miji ba a toshe ta ba. An sanya biki sati biyu kacal, wanda ya kama saura kwana uku azumi a lokacin. Duk wanda Kawu yake da tabbaci a kansa ya saka ya yi masa bincike akan Alhaji Mansur, kuma Alhamdulillah ta ko'ina sakamako mai kyau ake kawo masa. Hakan ya sa hankalinsa ya kwanta ya bi abin da addu'a kawai. Sosai nake shirin bikina, duk da ban da ɗan tayi sai Maman Nasmah da Inna Habi. Don Naja tun ban fi kwana biyu da dawowa gida ba na yi blocked ɗinta a ko'ina da na san za ta same ni, don wani irin haushin ta nake ji. Na kuma ƙudurce a raina ba zan nema ta ba har sai na yi aure, na kira na sanar mata ta zo ta ga irin mijin da na aura da gidan da nake. Ƴan group ɗinmu babu wanda ya san aure na ya mutu bare ya san zan sake wani auren, da ma haka muka tsara ni da Maman Nasmah, ba za su taɓa sani ba, shi ya sa babu wanda na gayyata, haka ma ƙawayena da ƴan unguwar da na zauna, duk ban faɗa musu ba. Kuɗi sosai Idonnera yake tuttula mini na hidimar biki, amma ko sau ɗaya ban taɓa bari Kawu ya sani ba. Na je an yi mini gyaran jiki, na haɗa wa kaina lefe a gidan Inna, na sissiya abincin da za a dafa ranar bikin. Kayan ɗaki da na kitchen da ma ko tsinke ba zan tafi da shi ba, ya riga da ya siya komai. Amma Kawu bai san da batun ba, don wata gonarsa ya ɗaga ya siyar ya ba wa Inna Habi kuɗin ya ce a yi mini komai da su. Ta nuna masa kuma an siya suna nan a gidanta, har jeren ƙarya ta ce masa an tafi ana i jibi ɗaurin auren. Tun daga zuwan da Mansur ya yi na farkon nan sau ɗaya ya ƙara dawowa, saboda ayyuka da abubuwa da suka sha masa kai. Ina ta hidima amma zuciyata cike take da kewar ƴaƴana, na so zuwa har ƙauyen su Anas na kwaso abuna, amma sanin Kawu ba zai yarda ba ya sa na bari sai na tare bayan na gama cin amarci na je na ɗauko su ko ta halin ƙaƙa. Ranar Juma'a ɗaurin auren ya kama, ranar Alhamis na je aka yarfa mini kitso tare da rangaɗa mini ƙunshi. Bayan an gama na tura masa da hotunansu, sai ya ce ba su fita ba sosai, Camerar da na yi amfani da ita ba ta da kyau, bari ya turo a kawo mini waya, da ma yana ta son ya sauya mini kuma ya sha'afa. A daren ya aiko wani yaronsa ya kawo mini sabbin wayoyi, keypad da iphone. Ita kanta keypad ɗin ban taɓa ganin irinta ba, mai kyau ce sosai kuma daga gani babu tambaya da kuɗi mai yawa aka siye ta. Ban yi amfani da su ba na ce sai Allah ya kai mu gobe bayan na tare a gidana. Washegari ta kasance rana mafi girma da tarihi a rayuwata, rana mai ɗumbin farinciki da murnar cikar burina. Duk da ban yi gayya ba amma gidan cike yake da mutane, don ita Gwaggo ta yi, ƴan'uwanta da na Kawu da maƙota. Dangin mahaifiyata kuwa babu wanda ya zo, sun ce abun ya zo a ƙurarren lokaci, sai aike suka yi mini tare da alƙawarin daga baya za su zo su ga gidan nawa. Ƙarfe biyu na rana aka ɗaura aurena da Alhaji Mansur Ibrahim Idonnera, a babban masallacin juma'ar unguwarmu. Bakina ya ƙi rufuwa saboda farinciki, na je aka yi mini makeup mai kyau, na shirya cikin wani tsadadden lace milk color. Maman Nasmah ta zo amma ba ta jima ba ta tafi, saboda za ta je gidansu Ango, don su a event ma suke yinin ba a gida ba. Mansur ya so na je, amma na ce masa a'a don na san Kawu ba zai taɓa bari ba. Yadda nake cikin nishaɗi da walwala haka ma ango yake, bini-bini ya kira ni ya ce ya rasa ina zai saka kansa saboda farinciki, kamar ya zauce haka nake ji. Murmushi kawai nake yi masa. Saboda yadda ya nuna ya ƙagu a kai ni ya sa ana yin sallar la'asar aka tafi kai ni, bayan Kawu ya yi mini doguwar nasiha mai ratsa jiki. Mota ɗaya kacal ya kawo kamar yadda na ce masa, saboda har yanzu Kawu bai san mai kuɗi ba ne sosai, sadaki da kuɗin aure duk kuɗi kaɗan na ce masa ya bayar. Daga Inna Habi sai wata ƙanwarta da wata maƙociyarmu aka tafi kai ni, unguwar da nisa daga tamu, hakan ya sa sai daf da Magriba muka ƙarasa. Tun daga farkon unguwar muka fara cin karo da tafka-tafkan gidajen, wanda tsabar tsaruwar su kamar za su yi magana. Ta cikin mayafi nake ƙare wa ko'ina kallo. Layinka unguwar kowane shafe yake da titi luwai-luwai, a bakinsa kuma an saka gate. Future house ɗin da nake fata dai nan aka kai ni. Ban san ta yanda zan iya fasalta girma, kyau, da haɗuwar gidan da aka kai ni ba, don duk tunanin mai tunani ya wuce nan. A wani ƙaton ɗaki na alfarma da ke hawa na uku a gidan aka ajiye ni, su Inna suna yin sallar Magriba suka yi mini sallama suka tafi suka bar ni daga ni sai halina.........✍️ *Zeey Kumurya ✍️* [3/8, 1:43 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGH PENS* FREE BATCH *22.* Yaye mayafin fuskata na yi ina murmushi na shiga bin ɗakin da nake da kallo. A hankali na miƙe na fara shafa ƙaton gadon da duk girman shi a ɗan gefen ɗakin yake. Daga baya na koma gurin wardrobe da madubi, na daɗe a tsaye kafin na fita ƙaton parlour'n da ya ji komai na more rayuwa. Wani tsalle na doka cikin tsananin farinciki, yau ni ce a gidan da nake mafarkin kasancewa a cikinsa matsayin mallakina? Tsabar zumuɗi har wani irin tsiko nake jin jikina yana mun. Ɗayan bedroom ɗin da ke manne da wanda na fito na shiga, shi ma kamar shi yake a komai da komai, banbancinsu kawai kowanne furnitures da kalar shi. Ban wani jima ba na fita, ƙofar da na gani tana facing ɗina na shiga, haɗaɗɗen dinning area na yi tozali da shi. Cike da ƙauyanci na je na fara tattaɓa abubuwan ina sunbatu ni kaɗai. Daga nan da na fita hawa na biyu na sauka, shi kuma ƙaton parlour ne kawai da ya ji komai, sai kitchen da toilet a cikinsa. Sai da na leƙa ko'ina sannan na sauka ƙasa. Shi kuma kamar hawa na uku yake, parlour, da two bedrooms kowanne da toilet a cikinsa, sai kitchen da dinning area. Gabaɗaya komai na gidan sabo ne, ko'ina kuma kalarsa daban. Ta window na leƙa na hango wasu apartments ɗin daban daga can nesa, amma duk da ban je na gani ba na san wanda nake ciki duk ya fi su girma. Sai da na gama kalle-kallen nawa zan koma can saman na ga wata ƙofar daban ta cikin parlour'n, da sauri na je na buɗe, sai na ga wani parlourn ne daban shi ma, mai kyau amma bai kai sauran girma ba, da toilet a cikinsa. Ban jima ba na koma saboda kar Ango ya shigo ya tarar da ni a ji kunya. Bayan na zauna na ɗauko jakata na ɗauki wayata na duba time, sai na ga ƙarfe goma na dare ma ta wuce. Cikin mamakin abin da ya hana Mansur zuwa har lokacin na kira shi. Har missed call uku na yi masa amma bai ɗauka ba. Ban kawo komai a raina ba na ci gaba da santin gidana, sai wajen 11 na tuna ko sallar Magriba ban yi ba. Da sauri na miƙe na shiga haɗaɗɗen toilet ɗin ɗakin don ɗauro alwala, da ƙyar na iya kunna fanfo na yi na fito. Bayan na idar na ciro sabbin wayoyina daga kwali na jona su a chaji. Tsohuwar kuma hoton shi na lalubo na shiga kalla don ya ɗebe mini kewa. Abin da ya fi burge ni da shi yadda bai taɓa kyara ta ko nuna mini ƙyama ba kasancewata talaka, da kuma tunda muke da shi bai taɓa yi mini maganar banza ba, duk da ya san ni bazawara ce, kamar yadda aka ce wasu mazan suna yi ko da auren mace za su yi. Hakan ya ƙara mini ganin girman da darajar shi, na tabbatar so na tsakani da Allah yake yi mini. Har sha biyu ta wuce ina zaune a gurin, zuwa lokacin na fara fargabar ko ba lafiya ba? Yadda ya nuna mini ya matsu a kawo masa ni, amma fiye da awa biyar da kawo nin babu shi babu dalilin shi, sannan ina ta kiran shi bai ɗauka ba, shi kuma bai kira ni ko ya yi mini text ya sanar mini abin da yake faruwa ba. Sai da gyangyaɗi ya fara ɗiba ta sannan na tashi na koma kan gadon na kwanta, gabana na dukan tara-tara. Tun ina ɗaukar abin wasa har na ga ya wuce hankali ganin har 2 bai shigo ba. Na dinga kiran shi da tura masa text amma shiru. Duk da tarin gajiyar da ke addaba ta amma sai na kasa bacci, sai wajen asuba wani wahalallen bacci ya kwashe ni, wanda cikinsa na dinga mafarkai wai wani mugun abin ne ya samu mijina. A firgice na farka ina faɗin. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Gabaɗayana na yi sharkaf da gumi. Jin kamar ana buga ƙofar ɗakin ya sa na tashi sauri na je na buɗe, cikin raina ina addu'ar Allah ya sa shi ne. Saɓanin abin da na yi zato na tarar, wata yarinya ce tsaye a bakin ƙofar, kanta a ƙasa ta ce. "Ina kwana Hajiya?" Ina zazzare ido na ce. "Lafiya ƙalau." Cike da ladabi ta ce. "Mu ne masu aikinki da alhaji ya ce a samo, sauran suna ƙasa, mun kammala abin kari ne na ce bari na zo na sanar miki." Kallon ta na yi na gan ta a tsabtace take babu ƙazanta a tattare da ita, numfashi na sauke na ce. "Ok, a cikin gidan nan kuka kwana ne?" Ta ce. "A'a yau muka zo, amma maigadi ya nuna mana ɓangarenmu da za mu dinga kwana mun kai kayanmu can." Gyaɗa kai na yi na ce. "Ya sunanki?" Ta ce. "Laure." Na ce. "To sannun ki, je ki na gode." Har ta juya na kira ta, ta dawo tare da rusunawa, umarni na ba ta akan ta kira mini maigadin. Sai da na yi sallar asuba don lokacin kusan goma saura sannan na sauka ƙasan, na tarar da shi zaune akan carpet. Kamar zai yi sujjada saboda duƙawa ya ce. "Barka da fitowa ranki ya daɗe." Hakan ya fasa mini kai, na zauna a kan kujera tare da harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya. Ban amsa masa ba na ce. "Maigidan nan ya shigo jiya ne?" Ya ce. "A'a, ai da ma ya sanar mini ba zai kwana a gidan ba, wani uzuri ne ya tasar masa ya yi ƴar tafiya, amma ba zai jima ba zai dawo, na ɗauka ya sanar miki ne ma." Ajiyar zuciya na sauke jin yana lafiya ƙalau, amma me ya sa ni bai faɗa mini zai yi tafiya ba? Kuma wanne irin uzuri ne da har ya fi kasancewarmu a daren farkon aurenmu muhimmanci? Ya zaɓi ya je ya yi shi, ni kuma ya bar ni na kwana ni kaɗai ƙwallin ƙwal, babu waya babu komai? Rashin mai ba ni amsa ya sa na sallami maigadin. Hankalina ya ɗan kwanta da na ji lafiya lau yake, hakan ya sa na saka masu aiki suka kawo mini abinci na karya. Bayan na gama suka kwashe kayan. Wajen sha biyu na yi wanka na shirya na fita harabar gidan don ba wa idona abinci, duk yadda na dinga ganin girman gidan Maman Nasmah da na Aunty Billy wannan ya fi shi, don kafin na gama zagaye shi sai da ƙafafuna suka yi liƙis da gajiya. Part ɗin masu aiki maza daban na mata daban, ɗakin gateman da toilet ɗinsa shi ma daban, sai wasu extra parts guda biyu. Ga swimming pool da garden mai kyau da ya ƙawatu. Har bayan azhar ina ta kiran layin Idonnera ba ya ɗauka, tun ina yi masa uzuri har abun ya fara damu na, don abincin rana ma kasa cin shi na yi. Duk tasirin farinciki da murnar kasancewa ta a gidan da na daɗe ina mafarkin kasancewa a cikinsa sai na neme su na rasa. Na ji mijina kawai nake son gani mu sha soyayya, ya ba ni dukkanin kulawar da ya ce ya tanadar mini. Da yamma Inna ta aiko wasu ƴan'uwanmu da kayan lefena, suka zo suka dinga kwakwazo da zuzuta gidana gami da santi. Ban bari sun gane halin da nake ciki ba, da suka tambaye ni ina angon na ce musu bai jima da fita ba. Sun yi abinci sun yi nak, amma da za su tafi har da ƙara yin gurin shi, saboda sun gan shi available. A cikin kuɗin hannuna na ba su 10k, na saka ɗaya daga cikin driver's ɗin ya mayar da su gida. Har raba ban iya cin abinci ba. Na dinga tambayar kaina wacce irin amarya ce ni? Har na kwana na wuni ko muryar ango ban ji ba bare na saka shi a idona. Ga shi ina ta kiran Maman Nasmah layinta ba ya tafiya ita ma. Na hau online na yi mata magana not respond, ban ga ma alamar ta hau ba har na gaji na sauka. Daren yau ko rintsawa ban yi ba. Washegari ana yin Sallah na kasa haƙuri na kira mai gadi, na ce masa anya lafiya kuwa Alhaji yake? Amsar da ya ba ni ce ta kusa saka ni suman tsaye, wai ƙalau yake, ai da ma ko kwana biyu ba ya yi a ƙasar nan, idan ya tafi kuma yana yin watanni, amma tunda da ni yanzu may be ya daina daɗewa. Duk da haka ban ji hankalina ya kwanta hundred percent ba, don a soyayyar da ya nuna mini da zumuɗin kasancewa da ni na san ba ƙaramin abu ne ya hana shi zuwa gare ni ba. Haƙuri na ba wa kaina tare da yi masa uzurin wani babban abin ne ya riƙe shi. A ranar na mayar da komai nawa kan sabuwar wayata, na yi videon gidana da abincin da masu aiki suka girka na tura a group ɗinmu, na ce ga shi a saka mini albarka mun tashi mun koma sabon gida. Ai kuwa na ga ruwan comments kamar yadda nake burin gani a baya. Zan wuni a kwance ina kallo ko chatting, ga masu aiki za su yi mini komai, ga ƙaton gida da kayan alatu, ga ishashshen kuɗi a hannu da account ɗina, zan saka datar ko nawa nake so na shiga social media na yi kalle-kallena, ga abinci sai wanda na zaɓa zan ci, nama cikin freezer, drinks kala-kala a cikin fridge, zan yi video a background mai kyau na saka a status, mutane sui ta wow wow, amma rashin miji da rashin sanin halin da yake ciki ya sa na kasa farinciki da walwala. Duk yadda na zo tanƙwara zuciyata ta kasance a cikin nishaɗin samun abin da take da buri amma abu ya gagara. A haka har na yi sati da tarewa. Wani abu da ya ƙara ɗaure mini kai babu wanda ya zo ya ce yau shi ɗan'uwan maigidan ne, daga ni sai masu aiki muke rayuwa. Ga Maman Nasmah ita ma har lokacin wayarta ba ta shiga, kuma ba ta hawa online. Har yunƙurin zuwa gidanta na yi, amma rashin address da kuma ba zan gane ba ya saka na fasa, don duk zuwan da na yi masu napep kawai nake nunawa address ɗin su kai ni, yanzu kuma ban da wanda ta turo mini, don tun a waccar tsohuwar wayar tawa ne. Ga shi ban san sunan mijinta ba, bare na faɗawa wani a cikin ma'aikatan gidan ya kai ni, tunda abokin Mansur ne ba za su kasa sani ba. Yau idan an kai azumi huɗu, da rana ina zaune a ɗakina ina karatun Alkur'ani da na manta rabon na yi, hawaye ne yana zuba a kan kuncina, wani irin abu mai ɗaci da maƙaƙi ne ya tsaya mini a ƙirji, ga kewar su Sultan da ta cika mini zuciya a kwanakin nan. Rufe kur'anin na yi na rushe da kuka. Wacce irin amarya ce ni mara daraja da har an yi sati guda amma ango bai zo ya gan ni ba? Na tambayi kaina cikin takaici. Abin da yake ƙara baƙanta mini rai kullum sai na tambayi gateman ya tabbatar mini da Mansur yana nan ƙalau cikin ƙoshin lafiya. Bayan na yi kukan mai isata na tashi na haye kan gado, saboda jin maganin baccin da na sha da asuba ya fara aiki, rashin bacci ya sa na ba da aka siyo mini da yawa, kullum idan aka sha ruwa sai na sha nake iya bacci, haka ma bayan sahur. Cikin baccin na ji ana lalubata, a firgice na farka jin ana ƙoƙarin haɗe mini ruwan ciki da katifar gadon, Allah ya ba ni sa'a na wancakalar da ko ma waye tare da tashi zaune ina ƙoƙarin kurma ihu. Wanda na yi tozali da shi ya sa na fasa, ƙura masa ido na yi cikin wata irin mummunar faɗuwar gaba. Muryata na rawa na ce. "Mansur!" Bai amsa ba sai ƙara kusanto ni da ya yi, daga shi sai gajeren wando. A ruɗe na ja baya na mannu da fuskar gado fahimtar abin da yake nufi. Jikina na rawa na ce. "Na shiga uku! Mansur azumi fa ake yi, ko ka manta ne?" Cakuma ta ya yi cikin wata ƙatuwar murya ya ce. "Ke kika san azumin." Tare da fara raba ni da kayan jikina. Duk yadda na so ƙwace kaina amma na kasa, don ƙarfi ya gwada gurin matse ni. Ba yadda ya bi da ni kamar dabba babu wasan komai ne abin damuwata ba, azumin da ke bakinmu da yadda yake ƙoƙarin amfani da ni ta baya shi ne babban tashin hankalina. Yana daf da cimma burinsa Allah ya ba ni sa'a na ƙara hankaɗe shi a karo na biyu cikin zafin nama. Kamar an yi cilli da ni na yi tsalle na bar kan gadon na koma gefe, jikina na kyarma cikin razani na ce. "Mene haka? Me kake shirin aikatawa? Laifi biyu? Ga azumi ga kuma ta gurin da ubangiji ya haramta." Na ƙarashe maganar cikin kuka. Tsaki ya ja ya ce. "Duk ke kika san wannan, ni kawai abin da na sani buƙatata ta biya." Ido na ƙura masa cikin kokawa da numfashina cikin dokawar zuci, tabbas wannan shi ne wanda Maman Nasmah ta tura mini pictures ɗinsa, shi ne ya zo gidanmu zance har sau biyu, shi ne kuma aka ɗaura mana aure da shi, ya zo ranar ɗaurin aure aka yi mana hotuna. Amma ba wannan muryar tasa ce muke waya da ita ba, waccan mai daɗin sauraro da magana cikin taushi ce, wannan kuma ƙatotuwa ce mai hawa kai a maimakon ta kwantar da zuciya. To me hakan yake nufi? Muryar ce ta canza ko kuma me? Na tambayi kaina cikin tsananin ruɗewar rashin sanin wanne iri miji na aura da yake ƙoƙarin aikata manyan laifuka ga Allah da ni matarsa ta sunna a cikin wannan wata mai girma da tarin falala? Wanda kowa burin shi ya nemi rabauta da samun dacewa a gurin mahaliccinsa.........✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:44 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGH PENS* (FREE BATCH) *23.* Miƙewa tsaye ya yi ya ɗora ƙafarsa ɗaya a kan gadon tare da gwiwar hannunsa a kanta, yana murmushin mugunta ya ce. "Na manta fa, ashe ban yi miki bayanin wane ni ba." Ban ce komai ba na ci gaba da ja baya a tsorace, ƙirjina na dokawa da ƙarfin gaske. Taku ya yi ya ya fuskanto ni, fuskarsa a haɗe kamar ba shi ya gama murmushi ba ya ce. "Kamar yadda aka ce miki sunana Mansur Ibrahim Idonnera, don ba zan na ce miki ba, saboda ba da ni kike yin duk chat ɗin da kika yi da waya ba." Waro ido na yi a firgice na ce. "Ban gane ba, waye kai ɗin? Me ka shirya mini da ka shigo cikin rayuwata?" Kamar ba zai yi magana ba sai daga can ya ce. "Ban da lokacin kaina ma bare wanda zan ba wa wani, hakan ya sa na yi nesa da dangina, sakamakon yawan ƙorafin da nake sha daga gurinsu. Na yi aure aure sun fi goma amma matan ba sa iya zama, duk da sai an kai ruwa rana nake iya sakin su. Lokacin da Hafsat matar abokina ta zo mini da maganarki ba ƙaramin farinciki na yi ba, domin ke ce daidai irin macen da ko ta ƙarfin tuwo dole ta zauna a matsayin matata, ta kare mini mutuncina tare da ɗauke hankalin mutane daga zargin wasu abubuwan." Cikin rashin fahimta na ce. "Saboda me dole sai irina? To ni ma wallahi ba zan zauna ka dinga wannan rayuwar dabbobin da ni ba, dole ka sake ni!" Dariya ya fashe da ita ya ce. "Ai har abada ni da ke mutu ka raba, za ki zauna a nan gidan ki ci gaba da yi mini gadin shi, idan ma wannan ɗin ya yi miki kaɗan zan iya canza miki wani, kuɗi kuma ba ki da matsalar shi, amma samun lokacina da yin wata mu'amala ta aure a tsakaninmu babu. Idan za ki tuna duk lokacin da zan zo mu haɗu muryata a dashe take, ina yi miki ƙaryar ina mura, to babu murar da nake yi, kawai bana son ki gane ba da ni kike waya da chat ba ne, da wani yarona na haɗa ku yadda za ki fi aminta da ni, don ni ban da lokacin wata soyayya. Iyayen da na yi amfani da su a gurin auren ki ba na gaskiya ba ne, wasu daban na samu na hayo, sannan kuma ranar da kika ce babanki yana son gani na, ba ni na je ba, Abdurrahman ne wanda kuke soyayya da shi a matsayin ni, da fatan kin fahimta?" Girgiza kaina na shiga yi ina fatan a ce mafarki nake, wani irin jiri ne yake ɗiɓa ta, kwata-kwata ban gane me yake nufi ba, na kasa gane inda maganganunsa suka dosa. Durƙushewa na yi tare da fashewa da kuka. Yana murmushin mugunta ya ce. "Akwai kuɗi! Ga ƙaton gida da motoci kala-kala, ki kwantar da hankalinki ki kwashi arziƙi kawai, ki mora ki fantama, ko da ma ba abin da kike so ba kenan?" Kallon shi kawai na ɗago ina yi amma na kasa cewa komai. Kafaɗa ya ɗage tare da faɗin. "And kuma idan amfanin da zan dinga yi da ke ta baya ba zai gamsar da ke ba, kina da right ɗin hulɗa da duk namijin da kike so, idan ma ke za ki dinga biyansa zan ɗauki nauyin hakan, don ba zan tauye ki ba." Ya ƙarashe maganar tare da nufo inda nake. Duk da halin ruɗun da ya fara taɓa mini ƙwaƙwalwa da na shiga, amma haka na miƙe fahimtar mugun nufinsa again na shige toilet na sakawa ƙofa key tare da jingina a jikinta ina sauke wahalallen numfashi. Har lokacin gabaɗaya maganganunsa suna amsa kuwwa a cikin kaina, ina jin shi yana ta ƙoƙarin buɗe ƙofar amma Allah bai ba shi sa'a ba har ya gaji ya tafi. Ajiyar zuciya na sauke na yi zaman ƴan bori a tsakar toilet ɗin. Tambayar kaina na dinga yi tsakanin Maman Nasmah da Mansur wa ya yaudare ni? Shi ya ɓoye mata gaskiyar halinsa ko kuma ita ma ta sani ta munafurce ni? A fili na ba wa kaina amsa da faɗin. "Ba ta sani ba, soyayyar da take yi mini na yi amanna ba za ta taɓa cutar da ni ba, ta haɗa ni da shi don na samu ingantacciyar rayuwa ashe gurɓatacciya zan samu. Tabbas da ta san yana yin wannan mummunan abun da ba za ta taɓa bari ya aure ni ba." Babu abin da ya fi ɗaga mini hankali sama da cewar ya yi ina da right ɗin hulɗa da wasu mazan, kuma da aurensa a kaina, hakan na nufin ba ya kishi na, ya aure ni ne kawai saboda na zama kariya a gare shi kamar yadda ya faɗa. A toilet ɗin na ƙarasa sauran wunin ranar, damuwa da tsananta wa kaina tunani suka taro suka haifar mini da wani irin matsanancin ciwon kai da jiri. Sai da aka kira Magriba na samu na lallaɓa na fita, ruwa kawai na ɗauka a fridge na sha na faɗa gado na kwanta tare da runtse idona. Tunanin Anas da tarin soyayya da kulawar da ya nuna mini a lokacin amarcinmu na fara tunawa, lokaci mai daɗi da sanya nishaɗi a zuƙata gami da wuyar mantawa. Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga zarya a kan kuncina. Ina ji ana ta buga mini ƙofa amma na kasa tashi na buɗe, duk da na san ba zai wuce masu aiki ba ne. Har aka yi isha'i ina kwance a cikin wani irin yanayi. Tunawar da na yi ban yi sallolin wunin nan gabaɗaya ba ya sa na tashi cikin sauri na je na yi alwala na fara ramawa a zaune, don ba zan iya tsayuwa ba. Bayan na idar na lallaɓa na fita parlour, na tarar an shirya mini lafiyayyun kayan buɗa baki, an jera su a kan center table, baki na taɓe bayan na gama bubbuɗewa. Duk haɗuwar lafiyayyun abincin ko kaɗan ba su burge ni ba, sai ma wani ɗaci da na ji ya ƙara cika mini zuciya. Zama na yi a kan carpet ina ƙarewa falon kallo, so nake na tursasa zuciyata ta yi accepting wannan sabuwar rayuwar da na tsinci kaina a ciki amma ta ƙi, da na tuno Mansur ɗan luwaɗi ne sai na ji komai ya kwance mini. Zuciyata a ƙuntace na tashi na koma ɗaki na ɗauki wayata na ƙara trying nunbern Maman Nasmah, amma har yanzu a kashe take. Data na kunna na hau Whatsapp, nan ma ba ta hau ba. Kamar na tambaya a group ɗin ko da mai wata nunbern tata sai kuma na fasa. So nake na yi sharing wannan damuwar tawa da wani ko zan ji sanyi a raina, musamman ma ita, sai dai tunda na yi auren nan da Kawu kawai nake waya, shi kuma ko karen hauka ne ya cize ni ba zan yi masa wannan zancen ba, shi da takaimaiman wanda na aura ma bai sani ba, ta ina zan fara yi masa bayanin mun ɓoye masa mai kuɗi na aura ni da Inna Habi bare har mu zo kan wannan gaɓar? Naja ce ta faɗo mini a rai, na manta har numbernta na goge sai da na duba na ga babu. Cikin takaici na cillar da wayar tare da fashewa da kukan rashin sanin abin yi, har baccin wahala ya kwashe ni ban sani ba. Wajen Asuba na farka, a firgice na tashi zaune saboda tozali da na yi da Mansur yana waya. Zuba masa ido na yi ina sauraren abin da yake cewa fuskarsa ɗauke da farinciki. "Eh yanzu na sallame shi, yaron ya yi sosai ai, irin wanda na ce kuma aka samo, na ji daɗin shi ba kaɗan ba Alhaji Labaran, ga shi ɗan shawalwali bai san komai ba, ni na fara sha'anin da shi." Ya yi shiru alamar yana saurare, daga baya ya kwashe da dariya tare da faɗin. "Kar ka damu, idan zan dawo zan taho da shi kai ma ka ɗana, don nawa ne shi kaɗai ba yarda zan yi mu dinga sharing ba." Da sauri na toshe kunnena fahimtar inda zancen nasu ya dosa, ina maimaita Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un a cikin raina, abin da nake jin labarin shi, nake ganin kamar ba ya faruwa saboda munin shi, amma yau ni nake rayuwa da wanda yake aikata shi. Ganin ya gama wayar na dube shi na ce. "Tir da halinka wallahi, ga ka kamar wani kamilalle ashe ba na Allah ba ne, kana da damar auren duk kalar matan da kake so har huɗu, amma gara ka dinga saɓon Allah ka....." "Ke!" Ya daka mini razananniyar ƙara. Hakan ya tilasta mini yin shiru ba tare da na shirya ba. Yana nuna ni da hannunsa ya ce. "Ki tsaya iya matsayinki, babu ruwanki da rayuwata da abin da nake aikatawa, kuɗi kika gani kika aure ni, to idan ma ba ki sani ba ki sani wannan abun shi ne silar duk wani arziƙina, kuma yanzu na fara kamar yadda ban da ranar dainawa. Sai kuma abu na ƙarshe da nake son sanar miki, kuskuren da za ki yi a rayuwarki shi ne ki yi gigin sanar da wani wannan sirrin nawa. Ina son ki sani idan za ki shekara kina faɗa babu wanda zai yarda da ke, kuma hakan daidai yake da siya wa kanki tikitin uƙubar rayuwa. Mafita a gare ki kawai ita ce ki zauna ki ci arziƙi, ki rufe mini sirrina ki bi ni da ido kawai." Ya ƙarashe maganar tare da janyo locker jikin mudubi, kuɗi ne cike a cikinta maƙil, nuna mini ya yi ya ce. "Ga shi nan naki ne, sannan duk wata za ki dinga ganin alert, kuma kar ki ga yau na ƙyale ki, ba wani na haƙura da ke ba ne, idan nan dawowa gare ki." Ban iya ba shi amsa ba saboda tsantsar rashin imani da tausayin da nake gani a kan fuskarsa. Bai damu da rashin maganata ba ya ci gaba da faɗin. "Ba ki da kowa ba ki da wani gata, danginku duka matsiyata ne, don haka ki taimaki talaucinku ki iya bakinki, ina fatan idan kunne ya ji jiki ya tsira." Tamkar mutum-mutumi haka na zama, na dinga bin shi da ido kawai a tsorace. Kayan jikinsa ya cire tas ya saka jallabiya kawai, kunnensa kare da waya yana faɗin. "Ka ƙaraso? To gani nan." Ya fita. Girgiza kai na yi don ko bai faɗa ba na san wani abokin shashancin nasa ne ya zo ya tafi gurin shi. Wani irin tsoron shi na ji yana mamaye ni. Ban yi sahur ba na zarce da azumi, don ko ruwa bana marmarin sha saboda ɗacin da bakina yake mun. Gari na fara haske Idonnera ya bar gidan ba tare ya yi mini sallama ba, sai bayan tafiyarsa na ji a bakin gateman da ya zo tambaya ta idan da akwai abin da ya ƙare a cikin kayan abinci za a siyo. Bayan kwana uku ina tsaye a gaban mudubi ina kallon uwar ramar da na yi, a hankali na yi ƙasa da idona na sauke su akan himulin kuɗin da Mansur ya bar mini. Na rasa me ya sa zuciyata ta kasa yin farinciki da mallakar su, so nake na cire damuwar komai a cikin raina amma abu ya gagara. Idan na tuna furucin shi da ya tabbatar mini da duk kuɗin nan nasa ba ta halattacciyar hanya ya same su ba sai na ji ko ruwan gidan na kasa sha, musamman idan na tuna da hukuncin jikin da aka ciyar, aka shayar, aka tufatar da haramun da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da ya ce mana, sai na ji komai na gidan ya ƙara fice mini daga rai. Ga rashin cin abinci da ya haifar mini da wani irin ciwon ciki da na ƙirji. A cikin kwanakin da ba su yi ashirin ba na gane ba kowane kuɗi ne farinciki da jin daɗin duniya ba kamar yadda Naja ta sha faɗa mini. Ga ni dai a gidan kuɗi da ya ji komai na more rayuwa, ga kuɗin kuma a gabana mallakina ina da damar yin yadda na so da su amma na kasa samun farinciki da sukunin zuciya tunda na shige shi. Girgiza kaina na yi na fice daga ɗakin, don ba ƙaramin gajiya na yi da wannan rayuwar kaɗaicin ba, ko da masu aikina ne gara na je na yi hira ko zan ji sanyi a raina. A parlour'n tsakiya muka ci karo da Laraba, ta rusina ta gaishe ni tare da faɗin. "Hajiya kin yi baƙo a ƙasa." Cikin mamaki na ce. "Baƙo! Waye?" Ta ce. "Ban sani ba, amma dai namiji ne tare da yara maza guda biyu a hannunsa." "Kuma ya ce gurina ya zo?" Ta ce. "Eh, Maman Sultan ya ce ma, wai idan na ce miki haka za ki fi gane ke yake nufi." Haka kawai na ji gabana ya faɗi tun kafin na ga ko waye, ban ce komai ba na nufi ƙofa na fita, na manta ko mayafi babu a jikina. Tun ranar da aka kai Hafsah Maman Nasmah ta cire sim ɗinta ta ajiye, saboda ta san dole za ta neme ta a waya, ita kuma ba a wannan lokacin take son su zanta ba, ta fi son sai ta jigata tukuna, duk wani shirin aurenta ita ta shirya wa Alhaji Mansur yadda zai yi. Duk da burinta ya cika na raba ta da Anas amma ba za ta ƙyale ta haka ba, don so take ta yi wa rayuwarta babbar illar da kowa sai ya guje ta. Saboda haushin ta take ji na fara mallakar Anas da ta yi kafin ita, da kuma irin mugun son da yake yi mata. Akwai abokan mijinta da yawa waɗanda idan ta yi musu tallan Hafsah ba za su ƙi ba, amma saboda ta fuskanci bayan halin mazansu na luwaɗi Alhaji Mansur yana da wani mugun abun shi a karan kansa, ta fuskanci hakan ne ta yadda duk matan da zai aura ba sa iya zama, komai uban kuɗi da zai mallaka musu kuwa. Kuma ita ta ce ya bayyana wa Hafsah mummunan halinsa, saɓanin ita da sauran matan abokan mijin nasu da sai dai su fuskanta da kansu, ko kuma idan tafiya ta yi tafiya mazajen su bayyana musu, amma ba daga kai su ba. Ta yi hakan ne duk don kawai Hafsan ta rasa farinciki tun tana Amarya, ta kasa samun nutsuwar da ta ci kuɗin da take ta fatan samu, bare ta tara wani abun da za ta tsira da shi a gaba. Murmushi ta yi bayan ta tuno next tuggun da take haɗa wa Hafsah. Waɗanda ta saka su yi mata aiki akan Anas sun sanar mata ya dawo har ma ya je gurin aiki yau. Hakan ya sa ta shirya cikin zumbulelen hijab da niƙab, ta ɗauki Alkur'ani na sauka mai izifi bibbiyu ta nufi gurin aikin nasu don fara aiwatar da shirinta, zuciyarta cike da fatan samun nasara.......✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:44 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) *24.* Cikin ɗoki ta shiga bayan mota, direban da zai kai ta ya ja suka fice daga gidan. Wani irin nishaɗi take ji yana mamaye dukkan zuciyarta tun kafin ta gan shi, ba ta taɓa son abu kamar yadda take son shi ba a rayuwarta, sau ɗaya ta taɓa ganin shi a zahiri, amma a kodayaushe cikin yi mata gizo yake a cikin ranta. Idan farinciki yana kisa tabbas ranar da aka ce ta zama matarsa za ta iya mutuwa. Ko da wasa ba ta taɓa tunanin za ta so wani mutum haka ba, don ba ta taɓa ma yin soyayya ba a rayuwarta, saboda tana gama secondary school babanta ya aura mata mijinta na yanzu, ba ta son shi, amma ganin irin kuɗin da yake da shi ya sa ta amince da auren nasa. A lokacin da ta gane halin shi ba ƙaramin bori ta yi akan ya sake ta ba, amma da ya toshe mata baki da uban kuɗi sai ta haƙura ta ci gaba da zama a haka. Ko da wasa ba ta bari iyayenta sun san halinsa ba har suka koma ga mahaliccinsu. Numfashi ta sauke cikin jinjina wauta da rashin rabo irin na Hafsah, na yadda idanunta suka rufe ta kasa gane qualities ɗin da Anas yake tattare da su, wanda dubban maza suka rasa a wannan zamanin. Duk da ita hakan gaba ya kai ta ita. A daidai ƙofar shagon ogansu Anas drivern ya yi parking. Tana murmushi ta cikin niƙab ɗinta ta buɗe murfin motar ta fita. Mutanen da ta gani a bakin shagon ta nufa tare da yi musu sallama. Bayan sun amsa ta yaye niƙab ɗin ta ce. "Don Allah Malam Anas nake nema." Da sauri ɗaya daga cikinsu ya ce. "Idan aiki za a yi miki za mu iya yi mu ma, ba lallai sai shi ba." Murmushi ta yi, cikin ranta ta ce. 'Wannan aikin shi kaɗai zai iya yi mini shi duk duniyar nan.' Wani daga cikinsu ya ce. "Ƙwarai Hajiya, mu da shi ai duk ɗaya ne." Idanunta a kan shagon nasu da ba ta iya hango cikinsa sosai ta ce. "Yanzu dai yana nan ko ba ya nan? Idan aiki ne ba ku da damuwa, gabaɗaya tare za ku yi." Washe bakinsu da ya bushe raƙau saboda azumi suka yi suka ce. "Ƙarasa ciki ki tambayi Oga." Ba ta kuma magana ba ta tafi a ɗokance. Bayan sun gaisa ta tambaye shi Anas ya ce. "Ayya, Malam Anas mai mutane, duk wanda ya yi wa aiki sai ya dawo, ga shi kuma kin tari gurbi Hajiya, don ɗazun nan ya bar nan, ya zo yi mana sallama tare da sanar mana ya bar aiki." A ɗan rikice ta ce. "Subhanallah! Saboda me?" Cikin jimami ya ce. "Ban sani ba gaskiya, amma ya ce mana wani ƙwaƙƙwaran dalili ne ya saka mu yi haƙuri." Da sauri ta ce. "To yanzu don Allah a ina zan same shi?" Ya ce. "Ban sani ba wallahi, don ya ce mana zai bar garin ne gabaɗaya." A ruɗe Maman Nasmah ta ce. "Innalillahi! To ya tafi ina?" Cikin mamakin yadda ta rikice Oga ya ce. "Lafiya dai ko Hajiya? Ina fata ba kuɗin aiki kuka biya shi ba kuma ya tafi da su." Girgiza kai kawai ta yi amma ta gaza cewa komai. Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin. "Yawwa, don na san Anas ba halinsa ba ne wannan, ba a taɓa kama shi da abu makamancin haka ba." Tattaro dukkanin sauran nutsuwa da dauriyar da suke ƙoƙarin tarwatse mata ta yi ta ce. "To zan iya samun nunbern wayarsa?" Ya ce. "A'a, ba ma shi da waya yanzu gaskiya, ta da kuma ba ta aiki." Ta ce. "Shikenan, na gode sosai Malam, sai anjima." Ba ta jira cewar shi ba ta juya ta fita a rikice. Oga ya bi ta da kallo, haka kawai ya ji matar ba ta yi masa ba, yana da nunbern Anas, ya ce mata babu ne saboda bai san me za ta yi da ita ba. Tana ji mutanen bakin shagon suna cewa. "Hajiya yaushe za a yi miki aikin?" Amma ta yi banza ta wuce fuuu, ta rasa me ya sa ba ta da sa'a akan Anas, duk lokacin da take murnar abu ya zo daf sai ya koma baya, masu yi mata aiki a kansa sun ce ba ƙaramar wahala suke sha ba, da ƙyar suke samun information a kansa. Ita ba ta taɓa tunanin talaka zai yi wahalar gani haka ba, ta ɗauka available suke a kodayaushe kamar ledar pure water. Kamar tai ta zunduma ihu ko za ta ji daɗi haka take ji, ga shi ƙarin damuwarta bayan ta gama wannan fighting ɗin akwai wani a gaba, na neman yardarsa da kuma na rabuwa da mijinta. Jiki a saɓule na ƙarasa parlourn na zauna ina ƙare wa baƙon da aka ce na yi kallo shi da yaran gabansa. Yana bi na da wani irin shu'umin kallo ya ce. "Sannu da fitowa ranki ya daɗe." Na ce. "Yawwa sannu, an ce kana nema na." Bai ba ni amsa ba sai da ya tura yaran waje sannan ya ce. "Haka ne, gurinki na zo." Gyara zama na yi na ce. "Sai dai ban gane ka ba." "Da ma ba ki san ni ba bare ki gane ni babbar mace." Ya yi maganar yana zunkuɗowa daga kan kujerar da yake. Ban ce komai ba na bi shi da ido kawai, hakan ya sa ya ci gaba da faɗin. "Sunana Faisal, mijinki Alh. Mansur shi ya turo ni don na ɗeɓe miki kewa, na taho da yara ne saboda na ɗauke hankalin ma'aikatan gidan nan daga zargin wani abu, zan zauna a matsayin ni ɗan'uwanki na kawo miki yara ziyara su yi Sallah a nan." Cikin rashin fahimta na ce. "Ban gane me kake nufi ba, ɗebe kewa kamar ya?" Wani munafukin murmushi ya yi tare da tashi ya dawo hannun kujerar da nake, cike da duniyanci ya ce. "Haba Madam, sai na yi gwari-gwari sannan za ki gane? Mu huta mu mori junanmu a bed nake nufi." Ya ƙarashe maganar tare da ɗage mini gira gami da kashe ido. Nemar komai nawa da zan iya sarrafa kaina na yi saboda ɗimaucewa, sai bayan wasu sakanni na fara dawowa daidai, idanuna ƙyam a kansa na ce. "Idan na fahimce ka zina kake nufin mu dinga aikatawa?" Ya ce. "Yeah ƴar gari." A fusace na miƙe ina jin wani abu ya tokare mini ƙirji, nuna shi na yi cikin ƙaraji na ce. "Ni ba ƴar'iska mahaukaciya ba ce da zan aikata zina a ɗakin aurena, kuma tsabar dabbanci da hauka a cikin watan Ramadan, da azumi a bakunanmu kake furta wannan asararren zancen, to ka tattara ka bar mini gida kamar yadda ka shigo, ba da ni za a yi wannan jahilcin ba." Miƙewa ya yi ya ce. "Calm down Bab, ba yanzu za mu yi ba da ma ai, sai an sha ruwa." Cikin hargagi na ce. "Ko haɗiye shi za a yi ba sha ba sai ka bar gidan nan, get out!" Na ƙarashe maganar ina nuna masa ƙofa. Murmushi ya yi ya ce. "Abin duk ba na zafi ba ne babbar yarinya, wannan harkar mun saba yin ta da sauran matan Alhaji, tunda shi ba lafiya ce da shi ba sai ya kawo muku irinmu ku dinga rage zafi, saboda kar ya cutar da ku, kuma ko da kin samu ciki kin haihu zai yi accepting abin da kika haifa a matsayin ɗan cikinsa, zai yi masa hidima ya yi masa komai, ƙarshe idan ya mutu ma har gadonsa zai ci, babu wanda zai sani." Ban iya kuma magana ba saboda yadda zuciyata take tafarfasa na fice daga parlour'n ina haɗa hanya, ikon Allah ne ya kai ni parlona, na faɗa kan kujera da ruf da ciki, hannuna riƙe da kaina da nake jin yana mun wani irin tururi kamar zai tarwatse. Wannan wacce irin ƙazamar rayuwa ce mai cike da jagwala-jagwala, a ce mijinka na sunna shi zai turo maka gwarton da za ku dinga lalata a cikin gidansa? Har gwarton yana proud da ko ka samu ciki zai riƙe shi a matsayin ɗansa. Na rasa sunan da zan kira wannan ƙaddararren auren nawa, rayuwar jin daɗi da watayawar da nake so ga ta nan na samu, amma farinciki da walwala gabaɗaya sun ƙaurace mini kamar yadda rai yake barin gangar jiki, ba kuma na ganin alamar ko burbuɗin dawowar su, matuƙar ba sakin raina zan yi na amince da rayuwar da na saka mata sunan JIN DAƊI A DUNIYA, SHAN WUYA A LAHIRA ba. Faisal kuwa da kallo ya bi Hafsah, bayan ta fice ya taɓe baki tare da komawa ya zauna. Wayarsa ya ɗauko daga aljihun gaban rigarsa ya fara ƙoƙarin kiran Maman Nasmah. Wadda ita ta turo shi, bayan ta gama tsara masa duk abubuwan da zai ce wa Hafsah. Amma saboda kar sunanta ya fito sai ta ce masa ya ce mai gidan ne ya turo shi, don ta san Hafsah za ta yarda da hakan tunda ta san halin mijinta, kuma babu wata hanya da za ta same shi nan kusa bare ta yi masa magana akan lamarin, kafin ya dawo garin kuma ta san ta gama samun abin da take nema. Faisal ɗaya daga cikin yaran da take hulɗa da su ne. Tana zaune tunanin Anas ya addabe ta kiran Faisal ya shigo wayarta. Tsaki ta ja ta ɗauki wayar da niyyar yin reject sai ta ga shi ne, da sauri ta ɗaga ta kara a kunnenta. Kafin ta yi magana ya riga ta da faɗin. "Madam an samu matsala fa." Ta ce. "Matsalar me kuma?" Ya ce. "Ta ƙi amincewa fa, kuma a yanayinta gaskiya za ta yi wuyar sha'ani." Ɓata fuska ta yi ta ce. "Na sani da ma, duk da wawancinta tana da tsatsttsauran ra'ayi akan addini, amma a hakan za ka shawo kanta, ina ƙwarewarka a sace zuciyar mace da yaudara suke? Ko mu kaɗai kake yi wa?" Dariya ya yi ya ce. "Kin san wargi ma guri yake samu, ku da ita da banbanci ai, duk iskancin mutum sai ya samu guri yake iya baje shi." Ta ce. "Na ji, ni dai ka samu ka yi duk yadda za ka yi ko da sau ɗaya ne ta amince." Da sauri ya ce. "Dole na ma ai, don na matuƙar yabawa da ita." Taɓe baki ta yi ta ce. "Ta nan ka fi kauri da ma, saura ka je garin azarɓaɓi ka manta da abin da na saka ka." Ya ce. "Ba zan taɓa mantawa ba, jira nake dare ya yi na saita, da komai ya kammala kawai sai dai ki ga na tura miki." "Good, fatan nasara." Ya ce. "Ki saka a ranki ta tabbata, kamar an yi an gama." Ta ce. "Allah ya sa." Tare ka katse kiran. Numfashi ta sauke cikin takaici, ga rashin samun Anas ga Hafsah ma tana ƙoƙarin ba ta matsala. A yanzu burikanta biyu ne, na farko ta mallaki Anas, na biyu kuma ta ɓata Hafsah a idonsa, ya daina ganin darajarta ko kaɗan ya kuma ƙara tsanar ta, ta yadda ko da ba ta da aure a gaba ba zai yi gigin mayar da ita ba. Duk da a yadda suka yi alƙawari da Mansur duk rintsi duk wuya ba zai rabu da Hafsah ba, sai dai in mutuwa ya yi, wanda ba ta fatan hakan nan kusa. Sai da na yi kwana uku ko ƙofar ɗakina ba na takawa, sai dai masu aiki su kawo mini komai su dawo su ɗauke. Duk da uban sintirin aiken da Faisal yake yi, ƙarshe da na gaji sai na buga wa masu aikin da yake aikowa warning, na ce kar su ƙara dawo mini da zancen shi. Ban yi yunƙurin korar shi daga gidan ba tunda maigidan ya san da zamansa, na bar shi ya gaji don karan kansa ya ƙara mai. Yau Sallah saura kwana biyar, ina kwance a ɗaki na tasa uban tsadaddun kayan sakawana a gaba ina kallo, sarƙoƙin gold's ɗin da wata mata ta kawo jiya na ɗaga, ta ce Alhaji ne ya turo ta, ta kawo mini na yi kwalliyar Sallah da su, a gurinta yake siya wa matansa kodayaushe. Ko kaɗan kayan ba su burge ni ba, ajiye ta na yi ina girgiza kai. Duk da uban kayan lefen da ya ba ni na siya sai da ya aiko mini da kayan Sallah, tunda na jibge su ma ko kuma kallon su ban yi ba sai yau na kwaso na duba. Ajiye sarƙoƙin na yi a kan kayan na ɗauki wayata na shiga Camera, Lokacin da nake ta fata da burin zuwan shi ga shi ya zo mun, mafarkina ya cika na ganin na tara abu na bajinta irin haka na ɗauka na tura a group ɗinmu na ce ga shi ni ma mijina ya siya mini kamar yadda kowa yake yi, amma na rasa me ya sa bana farinciki kamar su, su da walwala da nishaɗi a cikin muryoyinsu a lokacin da suka videon, alamun suna cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Dangwarar da wayar na yi ina jin wani irin ƙunci a cikin zuciyata, so nake na fita daga gidan nan ko na awanni ne na sha iska, amma da na ce wa Kawu zan je na gaishe shi hanawa ya yi, ya ce na bari sai Sallah, ya yi wuri na fara fita yanzu. A hankali na ɗago kaina jin ana knocking, ban motsa ba na ba da umarnin shigowa. Laraba ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama, na amsa kamar mara lafiya. Jug ɗin hannunta da ke cike da kunun aya ta ajiye a gabana tare da faɗin. "Ga shi Hajiya na kammala." Na ce. "Sannu." Tare da janyo shi a zalamance na bude, ko tsiyayawa ban yi a cup ba na fara sha, kasancewar na sha azumi sai yau na yi tsarki na ɗora ya ba ni wahala, shi ya sa na saka a haɗa mini kunun ayar mai sanyi don na sanyaya maƙoshina. Ajiyar zuciya na sauke bayan na dire jug ɗin, ina jin yadda sanyin ke ratsa ƙirjina. Bayan wasu mintuna ina son na tashi na yi Sallah amma na ji kasa, jikina ya yi mun wani iri kamar ba nawa ba, kwanciya na yi akan kayan gabana saboda yadda nake jin kamar iska za ta ɗaga ni daga zaunen da nake saboda rashin ƙwari, ko ɗanyatsana kasa motsawa na yi, ni ba mai bacci ba, ni ba matacciya ko sumammiya ba. Fuskar Faisal ɗauke da murmushin nasara ya kira Maman Nasmah, tana ɗagawa ya ce. "Yes! Na ci kuɗina." Cikin murna ta ce. "An yi nasara ne?" Ya ce. "Eh, yanzu mai aikin ta gama faɗa mini har ta sha drink ɗin, maganin da na ba ta, ta zuba mata kuma sha yanzu magani yanzu ne, na san tuni ya fara aiki, nawa aikin ne kawai ya rage." "Amma ba ya saka bacci dai ko? Don na fi son a ce idanunta biyu tar." Ya ce. "Ba ya sakawa, kawai jikinta ne zai yi weak, ba za ta iya komai ba sai yadda aka yi da ita." Ta ce. "Yawwa, haka nake so, ka yi sauri ka je, sai na ji feedback, saura kuma garin zumuɗi ka manta da yin videon, don na ji duk ka wani gigice." Dariyar ƙeta ya yi ya ce. "Kar ki ga liafina, Beb ɗin ce ta haɗu ta ko'ina, za a amfana da ita." Tsaki ta ja cikin kishi ta ce. "Ni dai ga abin da na ce maka." Daga haka ta katse kiran. Da murmushi a kan fuskarsa ya nufi sama inda Hafsah take, wanda already Laraba ta riga ta buɗe masa kowacce ƙofa da za ta sada shi da ciki, tutturawa kawai zai yi ya shige.......✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:44 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGH PENS* (FREE BATCH) *25.* Laure da ke laɓe a bayan labule ta yi saurin barin parlour'n ta bi bayan shi cikin tashin hankali, duk da ba ta san me yake shirin aikatawa ba amma ta san ba alkhairi ba ne. Tun lokacin da ta ga sun keɓe suna ƙusƙus shi da Laraba ta saka musu ido, hakan ya sa yanzu tana ganin Laraban za ta shiga parlour'n da ya mayar da shi kamar nasa ta bi bayanta ba tare da sun ankara da ita ba. A ruɗe ta zagaya ta ƙofar kitchen da gudu ta riga shi hawa upstairs na biyu, tana rufe ƙofa tana jiyo takun tafiyarsa yana hawowa, hakan ya sa ta ƙara ƙarfin gudun nata, da haki ta shiga bedroom ɗin da Hafsah take ta fara laluben key, a kan drawer ta hango shi, da sauri ta ɗauka har tana tuntuɓe ta kulle ƙofar ta bar shi a jiki. Dogon numfashi ta ja ta sauke tare da sakin ajiyar zuciya, idanunta akan Hafsah da ba ta da maraba da matacciya. Matar da ba ta taɓa wulaƙanta su ko yi musu wani cin mutunci ba kamar yadda wasu matan suke yi idan ana aiki a ƙarƙarshinsu, ta sakar musu komai na gidan su yi yadda suke so, ko dan wannan ba za ta taɓa bari a cutar da ita ba. Tana jin shi yana ta murɗa handle ɗin ɗakin. Cikin mamaki Faisal yake tura ƙofar kamar zai karyata. Ganin ko motsi ba ta yi ba ya ja tsaki tare da sauka ƙasa a fusace ya fara ƙwala wa Laraba kira. A gigice ta fito tana waige-waige ta ce. "Ga ni yallaɓai." Kamar zai rufe ta da duka ya ce. "Kika ce duk kin buɗe ƙofofin? Ya aka yi kuma na je na ji ɗakin nata a rufe?" Da sauri ta ce. "Wallahi na buɗe, sai dai ko ba ɗakin da take ciki ka je ba." Tsaki ya ƙara ja ya ce. "Ba shi ne na farko ba?" Ta ce. "Shi ne." Taune lip ɗinsa ya yi tare da yamutsa fuska, kamar yay ta naushin iska haka yake ji saboda takaici, a ƙufule ya ce. "Ko dai ba ki zuba mata maganin ba ne ƙarya kika yi mini?" A tsorace ta ce. "Na zuba mata, kuma ta sha, a yadda na baro ta ma ya fara aiki a jikinta." Harara ya zabga mata ya ce. "Dalla wuce ki ba ni guri, sakarya kawai." Baki ta zunɓura ta bar masa parlour'n. Yana huci ya ɗauko wayarsa ya kira Maman Nasmah ya sanar mata halin da ake ciki. Cikin baƙinciki ta ce. "Me ya sa haka ne wai? Me ya sa nasara ta yi mini ƙaura a game da Hafsah? Ka koma ka saka ido sosai, don dole akwai abin da ya faru, ba haka kawai aka samu akasi ba." Cikin ƙunar zucin ganin samu da rashin da ya yi ya ce. "Na fi ki takaicin abun nan wallahi, don ƙofar ɗakin aka rufe da key ta ciki, kin ga babu yadda za a yi ta buɗu ta waje kenan, sai dai in ɓalla ta za a yi." Kamar za ta yi kuka ta ce. "Ba fa zan karaya ba, sai aikin nan ya yiyu ko ta halin yaya, ka samo wata hanyar da za mu cimma burin mu kafin Sallah, don maigidan za su iya dawowa a kowane lokaci, gara ka yi abin da za ka yi ka tattara ka bar gidan." Ya ce. "In sha Allah za mu yi nasara, don ba zan taɓa bari duk zaman da na yi a gidan nan ya tashi a banza ba." Ba ta ce komai ba ta kashe wayar don takaici. Tun ina ganin dishi-dishi har na daina ganin komai, ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai can cikin dare na farka a firgice. Salati na rafka tare da tashi zaune, hakan ya farkar da Laure da ke zaune a ƙasa tana bacci. Da mamaki na dube ta bayan na latsa wayata na ga lokaci na ce. "Laure?" Ta ce. "Na'am Hajiya." Numfashi na sauke ina jin jikina wani irin lagwab kamar an yi mini duka, ga kaina da ke sara mini. Ina rarraba ido bayan na gama tuno abin da ya faru kafin hankalina ya gushe, na ce. "Lafiya? Me kike yi a nan a wannan daren? Me ya same ni?" A raunane ta ce. "Ban sani ba Hajiya, kawai hakan da na yi shi ne kariya a gare ki, ki yi haƙuri don ban san yadda zan yi miki bayani ki gane ba." "Kariyar me?" Na tambaya a gigice. Shiru ta yi ba ta ce komai ba, a tsawace na ce. "Ki yi mini bayanin mana, ina sauraren ki." Kanta a ƙasa ta ce. "Wannan baƙon da ya ce shi ƙaninki ne, shi ne ya faki idonmu ya zuba miki abu a cikin kunun ayar da Laraba ta kawo miki, bai san na gan shi ba, a lokacin na rasa mafita, sai bayan da kika sha na samu na shigo, na tarar da ke cikin wani irin yanayi, duk da na ruɗe amma ban fita ba, don na fuskanci ɗakin yake son shigowa ya yi wani abun." Jijjiga kai na shiga yi cikin matuƙar mamaki, don na gane nufin Faisal a kaina. A tsorace kamar za ta yi kuka ta ce. "Amma don Allah Hajiya kar ki ce ni na faɗa miki." Cikin ƙaunar yarinya na tashi na koma kusa da ita na kama hannunta na ce. "Ko zancen ba zan yi masa ba, bare sunanki ya fito a ciki, kawai zan yi takatsantsan da shi daga yanzu, na gode sosai, na kuma ji daɗin taimako na da kika yi." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Babu komai Hajiya." Jikina fayau na tashi ina tunanin mafita, babu abin da zan yi wa Faisal face na haɗa shi da Allah kawai, shi zai yi mini maganinsa. Tun daga ranar na koma yin duk wani abu da zan ci da kaina, ina gamawa na tattara na kai ɗaki na kulle. Saura kwana biyu sallah na kira mai kitso da ƙunshi ta yi mini, ranar sallah na shirya driver ya kai ni masallaci na yi idi. Kamar kar na baro masallacin, saboda ganin hada-hadar mutane ba ƙaramin sanyaya mini zuciya ya yi ba. Ina komawa gida aka aiko wani almajiri ya kawo mini abincin sallah ya ce ga shi daga maƙota. Na karɓa na ce an gode bayan ya yi mini kwatancen gidan. Tsabar halin da nake ciki ma na manta da ana yin wani abincin salla, don a kwanakin nan sosai tunanin su Sultan da kewar su ya addabi zuciyata, hakan ya sa na ƙara lalacewa duk na rame. Washegari na shirya na je na gaishe da Kawu, daga nan na tafi gidan Inna Habi na yini, don ba ƙaramin ɗasawa muke yi yanzu da ita ba. Ta dinga nan-nan da ni tana cewa ciki ne da ni, ramar da na yi daga gani ta laulayi ce, ni dai na bi ta da ido kawai, a raina ina cewa. 'Ba ki san dawar garin ba ne.' Sai murna take na kusa haihuwa a gidan mai kuɗi. Sai bayan isha'i na koma gida, kamar kar na tafi, don kwana na so yi Inna Habi ta hana ni, duk da na ce mata ba ya gari ya yi tafiya. Rayuwa ta ci gaba da juyin wainar ƴar koyo da ni a gidan Alhaji Mansur Idonnera, na ja watanni huɗu amma babu shi babu dalilin shi, ba waya ba chat, sai dai aiken kuɗi kawai. Ban san haka nake da buƙatar namiji da kulawar shi ba sai a wannan lokacin, ga shi babu wanda nake da shi da zan faɗa masa damuwata ya ba ni shawara, Maman Nasmah har sau biyu ina zuwa unguwarsu ina bulayi amma ban yi dacen samun gidanta ba. Har a group ɗinmu na yi cikiyarta, su ma suka ce neman ta suke yi. Ranar wata Lahadi ina zaune na tasa TV a gaba da sunan kallo, amma babu abin da nake fahimta wanda ake yi a ciki. Knocking aka yi na bayar da umarnin shigowa, Laura ce. Cikin ladabi ta ce. "Hajiya kin yi baƙuwa." Da mamaki na ce. "Baƙuwa kuma?" Don tunda na zo gidan babu wanda ya taɓa zuwa, ko nawa ko nasa. Cikin fatan ya kasance Maman Nasmah ce na ce. "Je ki shigo da ita." Tare suka dawo da matar, na bi ta da kallo don ban san ta ba. Fuskarta ɗauke da fara'a ta ce. "Sannu da hutawa." Murmushi na yi na ce. "Yawwa, Bismillah ki zauna mana." Tare da ba wa Laure umarnin ta kawo mata abin taɓi. Bayan mun gaisa ta ce. "Kin ga baƙuwar fuska ko? Maƙociyarki ce, tun lokacin da aka kawo ki nake ta zuba idon ganin amarya za ta shigo a gaisa na ji shiru, yau dai na cewa maigidan bari na shigo mu gaisa, haƙƙin maƙota ba a rayu ba a san juna ba." Na ce. "Allah Sarki, kin kuwa kyauta, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ina ta son na shishshiga ɗin kuma Allah ne bai nufa ba." Ta ce. "Babu komai, ni gani ai na zo." Murmushi na yi na ce. "Kin samu ladan, Allah ya bar zumunci." Ta ce. "Amin." Da na tambaye ta ina ne gidan nata, ta yi mini kwatance sai na ga ashe ita ta aiko mini da abincin Sallah kwanaki. Mun taɓa hira da ita, hakan ya sa na ji daɗi kamar an rage mini damuwar da take damu na. Washegari sai ta ƙara dawowa tare da yaranta masu kyau mace da namiji, har ta bar su suka ɗan jima a gurina. Yara masu da hankali da shiga rai. Bayan kwana biyu ta ƙara zuwa muka gaisa, ta ce amma tunda na ƙi zuwa ba za ta ƙara zuwa ba ita ma. Hakan ya sa ni ma na fara shigar mata. A hankali a hankali muka fara sabawa da ita, tana da kirki sosai, ga ta da addini da sanin darajar ɗan'adam.  Yau ta zo muna cikin hira ta dube ni ta ce. "Aunty Amarya ni kuwa ina so na yi miki wata tambaya, Allah ya sa ba zan yi miki shishshigi ba." Tattara hankalina na yi duka a kanta na ce. "Ina sauraren ki Maman Hanif, ki yi mini duk tambayar da kike so, babu wani shishshigi da za ki yi, ai ni da ke mun zama ɗaya." Numfashi ta sauke ta ce. "Tun ranar da na fara ganin ki na lura kamar akwai wani abu da yake damun ki, daga ranar har zuwa yau kuma kullum a haka nake ganin ki, ba wai ina son jin sirrinki ba ne, ina so na ji ne kawai ko zan iya ba ki shawarar da za ta zamo miki mafita, saboda ni ba na ƙaunar na ga mutum a cikin damuwa ko kaɗan, musamman wanda nake tare da shi." Numfashi na sauke jin ta sosa mini inda yake yi mun ƙaiƙaiyi, a raunane na ce. "Tabbas akwai abin da yake damu na, wanda ya girmi ƙwaƙwalwata na kasa samun mafita." Ido kawai ta zuba mini alamun ni take saurare. Gyara zama na yi na ce. "Matsalar gidan aure ce, mijina ne matsalata!" Waro ido ta yi ta ce. "A yadda kike a cikin wannan gidan idan za ki kwana kina cewa kina cikin damuwa wani ba zai taɓa yarda ba, saboda babu abin da babu na more rayuwa, duk da duniya cike take da ƙalubale, kuma mai ɗaki shi kaɗai ya san inda yake yi masa yoyo." Jijjiga kai na yi tare da gimtse baki na ce. "Tabbas haka ne, don ni ma kafin na shigo gidan abin da zuciyata take faɗa mini kenan, sai daga baya na gane ashe hangen dala ba shiga birni ba ne, ashe kuɗi ba shi ne farincikin da jin daɗin rayuwa ba." Girgiza kai ta yi ta ce. "Ba zan ce abin da kika faɗa ba daidai ba ne, amma akwai masu kuɗin da Alhamdulillah ga dukiyar ga kuma kwanciyar hankali." Da sauri na ce. "Kuma kuɗin na halal ne ba haram." Murmushi ta yi ta ce. "Sosai ma, yadda a talakawa akwai na gari da na banza haka ma a masu kuɗin akwai. Kamar yadda akwai wanda Ubangiji ya ba su duniya da lahira. Bari na ba ki misali da ni karan kaina, kin je gidana kin ga yadda nake, Alhamdullillah mijina yana da rufin asiri daidai gwargwado, don duk shekara Hajj da Umrah ba sa wuce shi, kuma tsaftatacciyar sana'a yake yi, ɗan kasuwa ne, kuma mutum ne mai tarin ilimin addini da na zamani." "Kuma yana ba ki kulawa yadda ya kamata?" Ta jinjina kai ta ce. "Sosai ma, yana taya ni ayyukan gida, yana ba ni lokaci mu yi hira, har lokacin koya mini karatun addini ni da yara ya ware mana, kuma duk wasu buƙatunmu na rayuwa yana yi mana daidai ƙarfinsa, a zamanmu ba ya muzguna mini, ba ya cutar da ni, rayuwa muke yi mai cike da annashuwa, Alhamdullillah shi ne kawai abin da nake cewa game da mijin da Allah ya ba ni." Cike da sha'awar irin rayuwarta na ce. "Ma sha Allah, da ma ba duka aka taru a ka zama ɗaya ba, amma da har na saka a raina rayuwar kuɗi babu jin daɗi a cikinta, ko kuma idan da jin daɗin kuɗin ba na halak ba ne." Ta ce. "To cire ma tun wuri, ai shi arziƙi yalwa ce daga Ubangiji yake yalwata bayinsa da shi, ba zai yiyu ba kuma a ce duk wanda ya ba wa ba ta hanyar halak ya nufa ya samu ba ko kuma ya hana shi jin daɗin rayuwa ba, kawai dai ya danganta da rayuwa ta zo wa kowane bawa daga ubangijins." Shiru na yi cikin gamsuwa da bayaninta, wato ni ce ban yi dace ba kenan? Yadda ta siffanta mijinta exactly irin Anas, banbancin su kawai shi takala ne, mijinta kuma mai kuɗi ne. Babu mamaki ƴan group ɗinmu ma duk sun yi dacen, shi ya suke yin rayuwarsu normal cikin farinciki, hakan na nufin da zan rabu da Mansur ni ma zan iya yin dace da miji mai kuɗi kuma nagartacce a gaba . Katse mini tunani ta yi da faɗin. "Mun shiga wata hirar daban, ba ki faɗa mini matsalar taki ba." Numfashi na sauke kamar zan yi kuka na ce. "Rashin kulawar miji shi ne babbar matsala! Ya wadata ni da komai na more rayuwa, amma kwata-kwata ba shi da lokacina, tunda muka yi aure sau ɗaya ya taɓa zuwa ya kwana ɗaya tak ya tafi." Na ƙarashe maganar ina jin kamar an yaye mini wani abu da ya tokare mini ƙirji, saboda yau na samu chance na faɗa wa wani damuwata. "Tafiye-tafiye yake yi kenan?" Gyaɗa mata kai na yi. Ta ce. "To me ya sa ba za ki dinga bin shi ba tunda kina takura?" Idona cike da ƙwalla na ce. "Ya ƙi yarda ai." Cikin jimantawa ta ce. "To ki yi haƙuri ki karɓi ƙaddarar ki kawai, ki ta addu'a da shawo kansa har ya haƙura ya dinga tafiya da ke." Girgiza kai na yi a raina na ce. 'Ba za ki gane ba ne.' A fili kuwa sai na ce. "Ba zai taɓa yarda ba wallahi, kuma ni idan a haka za a ci gaba tafi ba zan taɓa farinciki ba har abada." Cikin tausayawa ta ce. "Subhanallahi! Kar ki ce haka, ki ci gaba da addu'a, in sha Allah komai zai warware, addu'a tana saurin canza abubuwa." Ta ba ni shawarwari sosai tare da alƙawarin za ta kawo mini wasu addu'oi na dinga yi, in sha Allah za su daidai mini al'amurana. Ta dalilin Maman Muhsin na san wasu maƙotan namu, a ciki na haɗu da wata da jinina ya haɗu da nata sosai mai suna Karima, duk da unguwar ba irin wanda muka taso ba ne, nan kowa rayuwarsa yake yi, sai abu ya faru ake ɗan leƙa mutum, amma duk da haka ina shiri da su biyun nan sosai. Duk da na samu waɗanda suke ɗebe mini kewa amma damuwa ta kasa bari na, wata shida da aurenmu amma har yanzu Mansur bai ƙara zuwa ba, ni kaɗai sai na zauna nai ta tunanin ina yake tafiya ya daɗe haka? Anya kuwa zan iya ci gaba da rayuwa a wannan yanayin? Duk yadda na so tursasa zuciyata ta haƙura amma ta ƙi aminta, kulawa da tattali kawai take buƙata. Gabaɗaya na ƙara bushewa kamar mai cutar ƙanjamau. Na yi nisa a cikin tunanin da ya aure ni na ji an dafa kafaɗata. A zabure na ɗago, ajiyar zuciya na sauke ganin Karima ce. Bayan ta zauna a kusa da ni ta ce. "Ki yi haƙuri na tsorata ki." Yaƙe na yi na ce. "Ah..babu komai." "Tunanin me kike yi?" Ta tambaye ni tana bi na da kallo. Ƙasa na yi da kaina don ji nake kamar na saka kuka ko zan ji sassauci a cikin zuciyata. Ba ta damu da shirun da na yi ba ta ce. "Me zai dame ki har ki yi nisa a cikin tunani haka, na shigo ina ta sallama amma duk ba ki ji ba?" Maimakon na ba ta amsa sai na fara hawaye, ban saba da damuwa ba a rayuwata, don ko takurar Gwaggo ba ta kai wannan tsanani ba a gurina, hakan ya sa na kasa jure mata, raunina yake bayyana ga duk wanda zai tambayi abin da yake damu na." Gyara zama ta yi tana fuskanta ta, ta ce. "Na san abin da yake damun ki Hafsah, saboda matar da mijinki ya saka last kafin ya aure ki cousin ɗita ce." Da sauri na kalle ta kamar ban fahimci me ta ce ba. Gyaɗa kai ta yi ta ce. "Kin yi mamaki ko?" Na ce. "Eh." Muskutawa ta yi ta ce. "Ban jima da tarewa a unguwar nan ba, don kin riga ni ma zuwa, tunda muka zo na ga gidan nan aka ce da mace a ciki na fara tausaya mata tun kafin na gan ta, don na san duk wata ƙazanta da halin maigidan. Cousin ɗin tawa ita ta fara zama a gidan nan, yana sabon shi, ba ki ga yadda aka dinga yi mata murna ba lokacin aurensu, na dace da irin mijin da ta yi. Sai dai ko shekara ba ta yi ba ya sake ta, familynmu aka dinga zuzutun ita kuwa me ya fitar da ita daga wannan gidan hutun? Sai dai kawai ta ce kwanan auren ne ya ƙare, da haka ta rufe bakin mutane, amma ni ta faɗa mini komai ba ta ɓoye mini ba da yake muna shiri sosai." Tana rufe baki ta latsa wayarta ta nemo hotunansu tare ta nuna mini, jikina na rawa na karɓa na gani. Tabbas Alhaji Mansur Idonnera ne da wata, ya washe baki kamar mijin arziƙi, sai hotun ita da amaryar ne da shi duk a ranar. Tana karɓar wayar bayan na gama gani ta ce. "Ba zan tambaye ki abin da ya kai ki auren shi ba, don na san ƙaddara ce, saboda in dai ba sani ka yi ba, babu yadda za a yi ka ce ba mutumin ƙwarai ba ne." Da sauri na ce. "Wallahi haka ne, siffar mutanen kirki gare shi." Halayen shi ta fara lissafa mini wanda na sani da wanda ban sani ba, hakan ya tabbatar mini da gaske take ta shan shi ciki da bai. Ina kuka na ce. "Don Allah ki faɗa mini yadda cousin ɗin taki ta yi ta rabu da shi, wallahi na gaji da auren nan, so nake ya sauwaƙe mini kawai, na gaji! Ba zan iya ba!" Miƙewa tsaye ta yi ta ce. "Ba ta faɗa mini wannan ba, amma akwai shawarar da zan ba ki, wadda matuƙar kika bi ta babu makawa sai mijinki ya sake ki cikin ruwan sanyi ba tare da kun kai ruwa rana ba." Maganata har harɗewa take gurin azarɓaɓin cewa. "Don Allah ki taimake ni ki faɗa mini." "Yanzu kuwa." Ta faɗi haka tare da komawa ta zauna ta fuskance ni da kyau...........✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:45 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGH PENS* (FREE BATCH) *26.* Kallon kowacce kusurwa ta ɗakin ta yi sannan ta yi ƙasa da murya ta ce. "Kafin na ce komai, babu CCTV camera a parlourn nan?" Ina bin bango da kallo na ce. "Ban sani ba, amma kamar babu." Miƙewa ta yi ta ce. "Tashi mu je bedroom ɗinki dai, sai hankalina ya fi kwanciya." Ban ce komai ba na miƙe ta bi ni a baya. Bayan mun shiga mun zauna ta ce. "Bari na kira Zuhura video call, don ki fi tabbatar da abin da na faɗa, ki kuma fi yarda da ni." "Wace ce Zuhura?" Na tambaya ina mayar da numfashi. Ba ta ba ni amsa ba, ta yi latse-latse a wayarta, bayan ta yi ringing an ɗaga ta yafito ni da hannu, na leƙa na ga wadda ta nuna mini hotonta tare da mijina ce fuskarta ta bayyana a kan screen ɗin wayar, gaisawa kawai suka yi ta katse kiran. Hawayen fuskata da ya fara bushewa na goge na ce. "Na riga na yarda da ke tun a fari, ki faɗa mun hanyar da zan bi na rabu da wannan ƙaddararren auren shi ne kawai damuwata." Taune lip ɗinta ta yi ta ce. "Ba ni da yaƙini ɗari bisa ɗari abin da zan faɗa miki zai saka auren ki ya mutu, amma ina da tabbacin idan kin yi komai cikin nutsuwa da wayo da dabara to tabbas za mu yi nasara. Abin ba wani mai wahala ba ne, kawai idan ya dawo ki saki jikinki da shi, ki nuna masa kin yi accepting rayuwar gidansa, ka da ki sake ko da wasa ki nuna wata alama da zai gane plan kika shirya." Jinjina kai na yi na ce. "In sha Allah." "Good!" Ta faɗa tare da sauke da numfashi sannan ta ci gaba da magana. "Ki ba shi abinci da abin sha da kanki, a cikin drink ɗin zan kawo miki wata ƙwaya ki saka masa, wadda za ta bugar da shi ya fita daga hayyacinsa." Waro ido na yi na ce. "Bugarwa kuma?" With confidence ta ce. "Eh mana, amma ba maye zai yi irin na mashaya ba, kawai za ta hau masa kai  ne, ya yi ta abubuwa ba tare da ya sani ba. A lokacin za ki yi amfani da wannan damar, ki ɗauko biro da takarda, ki ba shi ya rubuta miki saki har uku, ki kuma saka ya furta da bakinsa ki yi record, don ya zama hujja." Cikin ɗaurewar kai na ce. "Ban gane ba? Mene ne hukuncin sakin a musulunci? Duk abin da zan yi ba na so ya shafi addinina fa?" Murmushi ta yi ta ce. "A addinance kin saku, saboda ko asiri aka yi wa namiji ya saki matarsa malamai sun ce sakin ya yi, haka ma wanda ya sha abun bugarwa." Cikin tantama na ce. "Wannan ai shi ya sha don karan kansa ya bugu, akwai banbanci da saka masa aka yi ba bisa son ransa ba." "Amma babu banbanci da wanda aka yi wa asiri ko?" Shiru na yi ina nazari, zuciyata tana son karɓar abin da Karima ta zo mini da shi, amma kuma ba na son a yi sakin ina murna kuma daga baya a zo a samu matsala, ko kuma shi ya dage bai sake ni ba. Dafa kafaɗata ta yi cikin karya harshe ta ce. "Kar ki ji tantama ko ɗar a cikin ranki, wallahi indai kika yi yadda na ce kin saku, amma idan zuciyarki ba ta aminta ba za ki iya tambayar malamai ki ji." Wahalallen numfashi na sauke na ce. "Na gamsu mana, kawai ina tunanin matsayin abin da zan aikata ya yake a gurin Ubangiji, ina da zunubi ko ban da shi?" Cikin ƙarfafa gwiwa ta ce. "Ba ki da zunubi, saboda mijinki ba mijin aure ba ne, kina da ƙaƙƙarfar hujjar da idan kika kai shi kotu musulunci ya ba da damar alƙali ya raba aurenku, kawai don ya fi ki power ne ya sa ko kin kai shi ƙarar ba za ki yi nasara ba, wannan abin da na faɗa miki shi ne kawai mafita a gare ki." Shiru na yi don gabaɗaya na rasa ta cewa, kaina ya kulle ban ma san matsayar da zan yanke akan al'amarin ba. Miƙewa ta yi ta ce. "Ki yi tunani, amma ki sani ba zan taɓa faɗa miki abin da ba shi ba ne ko kuma wanda zai cutar da ke ba, taimakon ki kawai zan yi saboda Allah, don a yadda Zuhura ta ba ni labarin baƙinciki da ƙuncin da ta shiga a gidan nan ko maƙiyina ba na fatan ya kasance a cikinsa." Tashi na yi ni ma na ce. "Na gode sosai Aunty Kareema, kuma na ji daɗin da ba zai misaltu ba, Allah ya saka miki da alkhairi da wannan hanyar da kika samar mini, in sha Allah zan yi duk yadda kika ce, ba zan ba ki kunya ba." Murmushi ta yi ta ce. "Babu komai Aunty Hafsah, ko babu wata alaƙa a tsakaninmu na gan ki a cikin wannan halin zan taimaka miki, bare kuma yadda muke da ke. Ki jajirce ki cire tsoro da fargaba, yadda duk wayonsa ba zai taɓa gano ki ba, idan har kin amince za ki yi zan kawo miki ƙwayar da za ki zuba masa ki ajiye har ya dawo ɗin." Da sauri na ce. "Na amince, don ni kawai burina a yanzu na bar gidan nan." Ta ce. "In sha Allah Ubangiji zai ba ki nasara, ai ya ga zuciyarmu, niyyar alkhairi muka yi ba na sharri ba, don a munin abin da mijinki yake aikatawa zama da shi ya haramta, ko abota da fasiƙi Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya hana, bare kuma zaman aure da shi." Cikin gamsuwa na ce. "Haka ne, amma ya zan yi da shi bayan ya dawo cikin hankalinsa? Kin san a jahilcinsa ko babu aure a tsakaninmu ba zai ƙi mu ci gaba da zama a haka ba, tunda da ma don na zame masa garkuwa da kare mutunci kawai ya ajiye ni." "Kar ki damu da wannan, idan cikin dare kika samu damar aiwatar da plan ɗin kar ki nuna masa komai sai da safe, idan kuma da rana ne ko yamma ta kwana gidan sauƙi, kawai ki kira ni a waya, za mu shigo ni da mijina, sai ki fara pretending ɗin ruɗewar ya sake ki kina faɗa mana, na san ba zai nuna ba haka ba ne, gudun kar a gane shi mutumin banza ne, don idan ya musa kika nuna takarda ga kuma voice ɗinsa da kika yi record za a tuhume shi ya aka yi haka ta faru? Na san ba zai taɓa cewa ke kika shirya sakin ba ko kuma abu ya sha ya bugu, saboda idan ke ce kowa zai gane akwai wani ɓoyayyen abu kenan, idan kuma buguwa ya yi za a ce shaye-shaye yake yi da ma." Komawa na yi na zauna saboda jirin da na ji yana kwasa ta, a raunane na ce. "Ya Allah! To Ubangiji ya sa yadda muka tsara komai ya tafin mana daidai kar a samu tangarɗa, amma abin da kamar wuya, musamman yadda ya san ba san zama da shi nake yi ba." Watsa hannunta ta yi ta ce. "Wannan kuma ya rage naki, dabara ta rage ga mai shiga rijiya, ke za ki san yadda za ki yi ki yi masa abin da zai aminta da gaske har cikin ranki kin haƙura za ki zauna da shi, ki yi amfani da baiwar ki ta mace da Allah ya hore mana ta kissa da kisisina." Jinjina kai na yi na ce. "Na fahimta, da yardar Allah zan yi iya yina." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Allah ya ba da sa'a, ya tabbatar mana da nasara." Na amsa da. "Amin." Daga haka muka yi sallama. Tun bayan da ta tafi na zauna nai ta ƙullawa da kuncewa. Tunda na zo gidan ban taɓa jin nutsuwa ta saukar mini a zuciya ba sai yau, na ji kamar har an yi sakin an gama. Washegari na fara aiwatar da abin da na tsara, na kwashe duka kuɗaɗen da ya bar mini na ɓoye, na fara yin kwalliya sosai yadda idan ya dawo zai fi aminta na kwantar da hankalina. Na je aka yi mini kitso da ƙunshi, na siya garin kunun sabaya da na ga ana tallah na fara sha. Cikin sati biyu na fara sauyawa, na murje na yi kyau. Duk da cikin raina fargaba ce fal amma haka na danne ta, ban bari ta yi tasiri ba bare ta saka ni rama. Sati uku da yin maganarmu da Kareema sai ga shi tsubul ga shi an jeho shi da safe, a lokacin ina kwance a parlourn ƙasa ina kallo. Dam! Ƙirjina ya buga, cikin faɗuwar gaba na tashi zaune ina ƙirƙiro murmushin da bai kai zuci ba. Fuskata a sake na kama Haɓa na ce. "Zuwa babu sanarwa? Sannu da zuwa." Kallo na ya yi ba yabo ba fallasa ya ce. "Yawwa." Tare da wucewa ya nufi sama. Ajiyar zuciya na sauke cikin sanyin jiki na miƙe na bi bayansa don fara aiwatar da plan ɗina. A ɗakin kusa da nawa na tarar da shi yana waya. A raina na ce. 'Tsabar jaraba ko zama bai yi ba har ya fara ƙaddararriyar wayar da na lura ba shi da aikin da ya fi ta idan yana gida.' Wani kallo ya mun bayan ya gama ya ce. "Lafiya?" Fuskata ɗauke da yalwataccen murmushi na yi fari na ce. "Don mace ta zo gurin mijinta sai a tambaye ta a ce lafiya?" Taɓe baki ya yi ya ci gaba da sabgoginsa. Hakan bai sa na karaya ba, na ƙarasa kusa da shi na ce. "Ka yi haƙuri idan kana ganin kamar na takura maka, na san idan ka fita ne bai zama lallai na sake ganin ka nan kusa ba, ni kuma akwai maganar da nake son mu yi da kai." Ba yabo ba fallasa ya ce. "Ina jin ki." Numfashi na sauke na ce. "So nake ko sau ɗaya ne ka tsaya mu yi hoto tare." Yamutsa fuska ya yi ya ce. "Akan me? Ke ni fa ban da lokacin wannan shirme-shirmen." Karyar da murya na yi na ce. "Na sani, amma hakan mafita ne a gurinmu gabaɗaya, idan muna yin hotuna ana gani babu wanda zai gane irin zaman da muke yi, kowa ya san kai mijina ne ni matarka ce, kullum aka zo gidana ba a ganin ka, ba a taɓa ganin mu ko tare ba ko da a hoto ne, me kake tunanin zai zo zuƙatan mutane? Za a gane ni da masu aikin da ka ajiye ɗaya muke, gadin gida kawai nake yi kamar yadda abun yake." Ɗage kafaɗa ya yi ya ce. "Shikenan ɗauko wayar taki ki yi mana ki yi ki fice, ina buƙatar kaɗaici don akwai abin da zan yi." Wani abu da ya tsaya mini a maƙoshi na haɗiye na ce. "Kafin mu yi hoton na fi son sai na fara fatanta maka rai, yadda nishaɗin zai bayyana har a kan fuskarsa." Tsaki ya ja alamar na fara isar shi ya ce. "Na hutacce ki, don ni babu wani abu da za ki yi ya faranta mini rai, idan za ki ɗauki hoton ki ɗauka ni ki daina ɓata mini lokaci a banza." "Har abin da kake yi da jinsin naka ba zan iya yi maka ba?" Na tambaya cikin danne tsoron da yake ƙara mamaye dukkan zuciyata. Ƙura mini ido ya yi, ni kuma na dinga murmushi tare da addu'ar Ubangiji ya sa kar ya gano ni. Fuskarsa a tamke ya ce. "Me ya canza miki ra'ayi?" Kallon gefen ido na yi masa na ce. "Kaɗaici, na ci abinci mai kyau, na sha abin sha mai kyau, ina rayuwa a guri mai kyau, me kake tunanin jikina zai fara buƙata bayan wannan?" Watsa hannunsa ya yi ya ce. "Amma na ba ki damar yin mu'amala da duk namijin da kike so ko?" Girgiza kai na yi na ce. "Na sani, amma kishin kaina da na aurena ba zai bar ni na aikata hakan ba, kai dai da kake mijina kawai nake da buƙata, kuma ko ta kowacce hanya ce zan amince maka." Murmushi ya yi ya ce. "Da ma da shirina na ko ki amince ko kar ki amince sai na yi nake tafe, amma tunda kin samar wa kanki masalaha ki je ɗakinki ina nan zuwa idan na gama abin da nake yi." Miƙewa na yi na ce. "Ina jiran ka." Daga fice na bar shi. A kan carpet na zube a parlour ina sakin ajiyar zuciya, wani irin bugu zuciyata take mini kamar za ta fasa ƙirjina ta fito, sosai nake tsoron tarwatsewar plan ɗinmu, don shi ma tantirin ɗan'duniya ne idonsa tar yake kallo na. Na daɗe a zaune kafin na ba wa kaina ƙwarin gwiwar tashi na ɗauko juice na jefa ƙwayar da Kareema ta kawo mini na jijjiga na mayar na rufe na saka a cikin fridge ɗin ɗakina. Sai wajen ƙarfe uku ya shigo, lokacin ban jima da fitowa daga wanka ba. Cikin faɗuwar gaba na dube shi na ce. "Sai yanzu?" Gyaɗa mini kai ya yi tare da fara cire kayan jikinsa. Addu'ar neman tsari na shiga yi a cikin raina, don a wannan gaɓar dole ɗaya a cikinmu ne zai yi nasara, ko ni na yi nasara ko kuma shi ya samu damar aiwatar da mummunar ta'adarsa a kaina. Tunanin yadda zan gabatar masa da abinci da juice ɗin ba tare da ya yi zargin wani abu ba na fara yi, har ya kammala cire kayan ya tunkaro ni ban samu wata matsaya ba, sosai fargaba, tsoro da firgicin kar na je garin neman riga na rasa ido suka cika zuciyata.........✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:45 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGH PENS* (FREE BATCH) *27.* Tuno yadda Kareema ta dinga jaddada mini sai na cire tsoro da fargaba na ari juriya da wayo sannan zan yi nasara na yi. Hakan ya sa na aro jarumta da dakiya na sunkuyar da kaina ƙasa na fara tarin ƙarya da dukkan ƙarfina. Galala ya dube ni ya ce. "Mene ne haka?" Cikin shaƙaƙƙiyar murya ina tarin kaɗan-kaɗan na ce. "Ulcerta ce ta tasar mini, da ma haka take yi time to time." Na ƙarasa maganar ina lumshe idona. Cikin takaici ya ce. "Me ya sa ba ki nemi magani ba? Ina nunbern my family doctor ɗin da na tura miki na ce idan ba ki da lafiya ki kira shi?" A wahalce kamar ciwon gaske na ce. "Bayan na baro ɗakinka bacci na yi ne, sai yanzu na tashi na yi wanka, rashin cin abinci ne." Bai ce komai ba ya samu gefen gado ya zauna. Sai da na gama sassauke numfarfashina sannan na tashi na zubo abinci, na sako spoon biyu. A gabansa na ajiye na ce. "Sakko mu ji." Fuskarsa babu fara'a ya ce. "Na ƙoshi." Karyar da murya na yi na ce. "Ka ƙara ci mana, yau ne fa farkon amarcinmu, ko ka taɓa ganin inda amarya ta ci abinci ita kaɗai ba tare da angonta ba?" Taɓe ya yi ya ce. "Ai ni ba irin sauran angwayen ba ne kin sani." Ƙara marairacewa na yi na ce. "Please, ko kaɗan ne ka ci." Tsaki ya ja ya sauko yana faɗin. "Ban taɓa auren macen da ta yi mini haka ba sai ke, anya kuwa haka kika bar ni?" Murmushi na yi na ce. "Babu abin da na yi maka, kawai ni ɗin ce ƴar baiwa." Ƙura mini jajayen idonsa ya yi, har lokacin spoon ɗin kawai ya riƙe bai kai abincin bakinsa ba, tabbacin akwai abin da yake nazari. Ban bari ko da wasa wani abu ya bayyana akan fuskata ba, ban kuma ƙara yi masa maganar ya ci abincin ba gudun kar ya yi wani tunanin daban. Sai ma ƙasa da na yi da kaina na ci gaba da cin abincina, cikin mamakin yadda har yanzu bai nemi wani abu ya suturce jikinsa ba, kuma hankalinsa kwance yake sha'aninsa, ya bar ni da aikin kau da kai. Sai day na kusa cinyewa ya yi three spoon. Hakan ya sa na tashi da sauri na zuba masa juice a glass cup, ya ɗauka ya ɗiɗɗike, na ƙara masa ya ƙara shanyewa. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, na tattara kayan na fice da shi ba tare da na sha drink ɗin ba. Na yi kusan five minutes kafin na dawo ɗakin, ina taku bugun zuciyata yana ƙaruwa da sauri da sauri saboda fargabar abin da zan je na tarar. Har na mayar da ƙofa na rufe ban kalli inda yake ba, kaina a ƙasa na ƙarasa bakin gadon. Ina neman taimakon Ubangiji a cikin raina na ɗago na kalle shi, kallon da na ga ya yi mini ne ya saka ni jin mummunar faɗuwar gaba. Kafin na yi magana na ga ya nuna ni da hannu tare da faɗin. "Keee! Me kika ba ni ne na ji kaina yana juyawa?" Daga yadda ya yi maganar na san maganin ya fara aiki kenan. Ban ce komai ba na ja baya na ɗauki wayata tare da tsayawa ina kallon shi yadda ya riƙe kansa yana yin wasu irin abubuwa. Jikina har rawa yake saboda rashin sanin takamaiman abin da nake ji, tsoron abin da zai biyo baya ko farincikin samun nasara ne ban sani ba? Kamar mai tafiya a kan ruwa haka na ja ƙafata na koma gabansa na ce. "Mansur." Ya ce. "Uhm." Tare ware jajayen idonsa a kaina. "Ka san ni? Idan ka san ni wace ce ni a gurinka" Na tambaye shi ina nuna kaina. Ya ce. "Eh mana, matata ce ke." Ina sauke ajiyar zuciya na ce. "So nake ka sake ni, ka ce na sake ki Hafsah har sau uku." Baya ya yi ya kwanta ya ce. "Ba zan faɗa ba ɗin, banza kawai." Ban karaya ba na ce. "Sai ka faɗa, saboda ni bana son ka, ba na ƙaunar zama da kai." Hannunsa riƙe da kansa ya ce. "Kaina zai tarwatse, ki cire mini abin da kika sa mun a cikinsa." Sai da na ɗauko takarda da biron da already na tanade su na miƙa masa na ce. "To sai ka yarda za ka rubuta duk abin da na ce maka, in ba haka ba, ba zan cire maka ba." Da sauri ya karɓa ya ce. "Me kike so na rubuta? Zan rubuta, in dai za ki cire mini wannan abun daga cikin jikina!" "Saki, ka rubuta ni Mansur Ibrahim Idonnera na saki matata Hafsah har saki uku." Na faɗa cikin tarar numfashi. Kamar ɗan koyo haka ya riƙe pen ɗin ya rubuta ya cillo mini." Ban ɗauka ba na danna record cikin rawar jiki, muryata ɗauke da kukan ƙarya na ce. "Me ka rubuta? Ka faɗa da bakinka na ji." "Na sake ki! Na sake ki! Na sake ki! Tunda kashe ni kike son yi, kin zuba mini tsutsa a kaina sai yawo take mun." Ya faɗa slowly tare da lumshe idonsa gabaɗaya. Wata irin ajiyar zuciya na sauke kamar zuciyar za ta daina aiki, na yi saved ɗin recorded da tun a gurin cewa na sake ki na uku da ya yi na yi stopping ɗinsa, ban bari sauran maganar tasa ta fito a ciki ba. Hannuna kamar ana kaɗa mazari saboda rawa na ɗauki takardar na linke na miƙe. Bin sa na yi da kallo, ya yi ɗaiɗai a kwance kamar gawa, ƙirjinsa da yake ɗagwa da sautin numfashinsa shi ya tabbatar mini a raye yake. Tamkar mai tafiya a kan wuta Saboda sauri haka na bar bedroom ɗin na fice parlour, a kan tiles na zube ina mayar da numfashi kamar wadda na sha tseren gudu. Tamkar a mafarki haka nake ganin faruwar al'amarin, ji na yi kaina yana juya mini, dafe shi na yi ina maimaita Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un a fili. Na rasa me ma zan yi? Barin gidan ko kuma jiran ya farko ya dawo cikin hayyacinsa? Wani irin tsoro da ban taɓa tsintar kaina a cikin irinsa ba ne ya lulluɓe ni, na fargabar kar ya mutu ko kuma wani abun ya same shi na shiga uku. Ban san lokacin da na ɗauka zaune a gurin ba kafin na tashi na koma ɗakin, a gurguje na ɗauki jakata da na gama haɗa duk wani abu mai muhimmanci nawa na fice, har lokacin yana nan yadda na bar shi. Ɗakinsu Lami na je na zauna, suka bi ni da kallo amma babu halin tambaya. Ko ta kansu ban bi ba na kira Kareema a ruɗe na ce. "Na kammala komai fa, kuma successfully yadda muka tsara." "Alhamdulillah! Na taya ki murna sosai wallahi, Ubangiji ya ba ki wani na gari." Ta faɗa cikin farinciki. Ban amsa ba na ce. "Ni halin da na baro shi ne hankalina bai kwanta da shi ba, ina tsoron kar wani abu ya same shi." Ta ce. "Babu abin da zai faru, nan da mintuna za ki ga ya miƙe, sai da na tabbatar da ingancin ƙwayar sannan na siyo ta, wallahi Hafsah ba ƙaramin shiri na yi ba saboda kawai na taimake ki." Cikin ƴar nutsuwar da na fara samu na ce. "Shikenan, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi." Ta ce. "Amin, ki kwantar da hankalinki fa, na ji duk a ruɗe kike, bari na je na ɗauko Maman Hanif mu shigo tare." Na ce. "Kar ya gane haɗa baki fa muka yi abin ya shafe ku?" Murmushi ta yi mai sauti ta ce. "Kar ki damu, komai cikin dabara da wayo za mu yi, ke dai kawai da ya fito ki kira ni." Na ce. "Tom shikenan." Tare da katse wayar. Runtse idona na yi na dafe ƙirjina saboda bugun da yake yi mini kamar zai bar jikina. Addu'a kawai nake a cikin raina, don ban taɓa shiga tashin hankali irin wannan ba a rayuwata. Na rasa sunan da zan kira wannan ƙaddararren auren da yin shi ya zamar mini bala'i, saki kuma yana ƙoƙarin saka mini ciwon zuciya saboda fargaba. Kamar na yi tsuntsuwa na gan ni a gidan Kawu haka nake ji. Daf da Magriba na hango shi yana saukowa ta windown da na yaye labule saboda ganin wajen, lokaci ɗaya ajiyar zuciya da faɗuwar gaba suka yi mini rufdugu. Cikin azama na kira Kareema na sanar mata, ta ce suna bakin gate ga su nan shigowa. Ina zare ido kamar mara gaskiya na tashi na fita, bayan na ƙanƙame wayata da takardar sakin. A bakin ƙofa na tsaya a ɗarare ina kallon shi, tsaf da shi ya sha babbar riga, kamar mutumin ƙwarai. Wani mugun kallo ya jefe ni da shi ya ce. "Well-done! Ƴar matsiyata, sannun ki da ƙoƙarin ha'intata." Mannewa na yi a jikin ƙofar na fara rarraba ido ban ce komai ba. Yatsun hannunsa ya harɓa suka bayar da sautin daf-daf sannan ya ce. "Ba zan kula ki ba a nan a gaban masu aikin gidana, saboda kar mutuncina ya zube, amma za ki yi mini bayanin abin da kika saka mini da dalili anjima." Daga haka ya nufi ƙofar barin parlour'n, kafin ya ƙarasa doorbell ta fara ƙara, Laure da ke kitchen ta fito a guje ta je ta buɗe bayan ta yi mana sannu, babu wanda ya amsa mata. Kareema ce ta fara shigowa, sai mijinta sai Maman Hanif. Kallo ɗaya na yi musu na sunkuyar da kaina ƙasa. Da fara'a ya tarɓe su kamar ba shi ya gama yi mini magana cikin hargagi da murtukewar fuska yanzu ba. Shi ya ba su gurin zama, suka gaisa cikin mutuntawa. Daga inda nake na gaishe su, Mijin Kareema yana duban shi ya ce. "Ɗazu da safe zan fita na ga shigowarka, da na dawo na tsaya na tambayi maigadi kai ne maigidan? Ya ce eh, yau ka dawo. Shi ne na ce idan na huta zan shigo mu gaisa, tunda na tare ba mu taɓa haɗuwa ba, kuma gidana ne na bayan naka." Murmushi Mansur ya yi ya ce. "Allah Sarki, ka kyauta kuwa, na gode sosai." Ya nuna Kareema ya ce. "Wannan ce mai ɗakin tawa, wannan kuma ta nan gidan jikin gidanka ce, mun fito muka haɗu da ita za ta shigo ita ma." Sheshsheƙar kukana ce ta hana shi maganar da ya buɗe baki zai yi, da sauri Maman Hanif ta ce. "Kamar kuka ko?" Kareema ta ce. "Eh, Aunty Amarya ce kuma take yi, lafiya?" Ta ƙarashe maganar idanunta a kaina. Cikin pretending ina cikin matsanancin tashin hankali na ɗora hannuna akai na ce. "Don Allah ku ba shi haƙuri, ni na ba shi ya ƙi haƙura, ku taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ku!" Cikin mamaki Maman Hanif ta ce. "A'a, me ya faru? Ba rakiya za ki yi masa ba da ma ganin kun da muka yi?" Girgiza kai na yi na tashi a haukace na cilla mata takardar hannuna na ce. "Duba ki gani, wai ya sake ni, kuma ban da kowa, ban da wani sauran gata sai shi, don darajar Allah ku ce masa ya mayar da ni. Ya ɗauki wani matakin a kaina kowanne ne zan jure amma ban da wannan, ba zan iya ɗauka ba, ya yi mini tsauri da yawa." A firgice ta miƙe ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Har saki uku!" Tashi ya yi shi ma ya ce. "What?" Tare da tsare ni da ido cikin wani irin yanayi. Sai a lokacin mijin Kareema ya yi magana ya ce. "Subhanallahi! Ashsha! Saki kuma? Alhaji me ya yi zafi?" Karɓar takardar Kareema ta yi fuskarta ɗauke da tashin hankali ta ce. "Ko dai ba ki gani daidai ba ne Aunty Hafsah?" "Zan fi kowa farinciki idan haka ne, shi ya sa na ba ku, ku duba ku gani ko idona ne yake yi mini gizo." Na faɗa ina ƙara rushewa da kuka. Dafe kanta ta yi tana salati, Maman Hanif da sosai ruɗu ya bayyana a kan fuskarta ta ce. "I'm speechless!" Satar kallon Idonnera na yi na ga ko motsi ya kasa yi, alamun suman tsaye ya yi saboda tsananin mamaki. A hankali na sauke numfashi tare da ɗauke idona daga kansa, mijin Aunty Kareema da ya karɓi takardar ya duba ya ce. "Aikin gama ya riga da ya gama, har saki uku! Irin wanda Allah ba ya so, garin yaya haka ta faru Alhaji? Da na san abin da za mu tarar kenan da ba mu shigo ba." Dogon numfashi ya ja ya sauke, yana karɓar takardar tare da dubawa ya ce. "Ƙaddara ce kawai, ka san aure rai ne da shi, idan Ubangiji ya rubuta ya ƙare ko second ɗaya ba zai ƙara ba sai an rabu, ko ana so ko ba a so." Mijin Kareema ya ce. "Haka ne, Allah ya sa mu dace mu fi ƙarfin zuciyarmu, har an shiga sallar Magriba, mu za mu tafi Allah ya kiyaye gaba." Zubewa na yi a ƙasa na ɗora hannu aka, ina kuka na ce. "Kar ku tafi ku bar ni ba ku saka ya mayar da ni ba don Allah." Cikin tausayawa Maman Hanif ta kama ni ta miƙar da ni tsaye, tana gyara mini hijabin jikina ta ce. "Ki yi haƙuri, ki yadda da ƙaddara, shi ne cikas imani." Ban ce komai ba na ci gaba da kukan da babu yadda za a yi mutum ya ce ba har cikin zuciyata yake ba. Sosai na hangi mamaki da ruɗu da shock a fuskar Alhaji Mansur, bi na kawai yake yi da wani irin kallo da na kasa gane ma'anarsa. Bai kuma magana ba ya juya ya fita bayan ya yar da takardar. Lallami da ban baki Maman Hanif tai ta mun kamar za ta yi kuka, sai haƙuri take ba ni, gami da yi mini nasiha. Kareema kuwa ba ta koma gida ba sai da ta tabbatar na bar unguwar, ko tsinke ban ɗauka ba daga ni sai jakata, ko kayan sakawa ban bi ta kansu ba, ni dai tunda burina ya cika ji nake kamar an tsunduma ni a cikin aljanna, sai godiya ga Allah kawai nake yi. Kawu da ke riƙe da takardar sakin bayan na yi masa bayani ya ja gwauron numfashi ya ce. "Na rasa abin cewa saboda tsabar kiɗima, abin da zan ce kawai Ubangiji ya ba mu ikon cinye wannan jarrabar gabaɗayanmu, Allah ya sa haka shi ya fi alkhairi, ya tsayar iya haka." Na ce. "Amin, Kawu har yanzu ba a kawo su Sultan ba ko?" Ya ce. "Hmm, sai haƙuri, jarrabawa ce, ki ta addu'a kawai kar ki gaza, fatanmu kawai Allah ya sa suna cikin kulawa da ƙoshin lafiya." Cike da kewa da ƙaunar ƴaƴana na ce. "Amin." Sosai nake cikin farincikin yar da ƙwallon mangwaron da na yi na huta da ƙuda, ina jin Gwaggo tana ta ya da habaici amma ban bi ta kanta ba. Juyi na yi a kan tabarmar da nake kai ina ji na sakayau, gabaɗaya damuwar da ke danƙare a cikin raina ta tafi. Ɗanmitsitsin ɗakin da nake ciki a yanzu mai ɗauke da tarkace ya fi mini tangamemen da na baro mai cike da kayan alatu. Ban san da bakin da zan gode wa Kareema ba, na wannan farar dabarar da ta samar mini. Ban taɓa zaton kuma abun zai zo da sauƙi haka ba, duk da na san addu'ar da na dage da ita ba dare ba rana ce ta sanya Ubangiji ya taimake ni ya ba ni nasara. Wajen ƙarfe goma Kareema ta kira ni, bayan mun gaisa ta ce. "Ya kike je gida?" Na ce. "Lafiya ƙalau Alhamdulillah, na gode na gode, na rasa ma abin da zan ce miki saboda farinciki." Dariya ta yi ta ce. "Babu komai ai,kar ki damu, ni kaina nan murna nake yi miki ba kaɗan ba, barkanki, kin tsallake rijiya da baya, wai yaushe ma ya dawo ne?" Na ce. "Yau fa, ga shi cikin ikon Allah an yi komai an gama, gaskiya kina da basira sosai, ni ina zan yi tunanin yin haka? Kuma abin da ya ba ni mamaki yadda bai musa ba, ko record ɗin ma ban saka ba ya amince ya yi sakin." Ta ce. "Ai ya san dalili, ya riga ya gane ke kika haɗa komai, shi ya sa ba zai ce ƙala ba." A raunane na ce. "Allah ya sa kar ya ce zai yi mini wani abun da zai cutar da ni a matsayin ɗaukar fansa." "In sha Allah babu abin da zai iya, ai kuma an riga an gama, wata mai tsautsayin kawai zai nema ya ƙara aura, ba ni labarin yadda lamarin yakasance, ya aka yi ya sha drink ɗin ne?" Kwashe labarin komai na yi na ba ta. Cikin dariya ta ce. "Amma ke ma fa kina da wayo, kin yi ƙoƙari sosai, ga kukan da kika yi kamar gaske, gaskiya za ki iya acting, kamar a Film fa." Dariya na yi na ce. "Mene ma ba zan ba, yadda nake gudun mutuwata haka nake gudun gidan nan, ba ki ji yadda nake ji na ba yanzu, farinciki mara misaltuwa." Ta ce. "Ma sha Allah, Maman Hanif ta ɗauka ƙin sakin kike da gaske, ta damu sosai." Na ce. "Allah Sarki baiwar Allah, mijinki fa? Ya san komai?" Ta ce. "Eh, na ɗan tsakura masa, shi ne ya ce mu je ba matsala, ya san me zai masa da ba zai kawo komai a ransa ba, ban san ya aka yi ya san yau ya dawo ba, amma na fi tunanin maigadi ya tambaya kamar yadda ya faɗa." Na ce. "To an gode, kun yi jihadi Allah ya ba da lada." Ta ce. "Amin ya hayyu ya ƙayyum, wannan miji naku ai ba na zama ba ne, Allah ya raba mu da zuri'armu da irinsu." Na ce. "Amin." Daga haka muka yi sallama ta ce da safe ma yi waya. Daren wannan ranar shi ma ban runtsa ba, na dinga tunanin Anas da kulawar shi a gare ni, duk yadda na so kawar da tunanin amma na kasa. Na dinga tambayar kaina me kuma zai faru da ni a gaba? Wacce irin rayuwa zan shiga kuma? Zawarci ko kuma wani auren zan yi? Na yi auren kuɗin amma gara gidan talatan da na guda sau dubu a kansa, amma duk da haka har yanzu ina nan da burina, musamman idan na tuna maganganun Maman Hanif da ta ce masu kuɗin na gari suna nan da yawa, ko dan kar a ce na ci baya ba zan auri talaka ba a gaba, sai mai hali amma sai na zaɓa na darje da na ƙwarai. Kamar mafarki na yi na farka haka nake ganin aurena da Idonnera, na saka a raina ko a cikin masu kuɗin shi ne ba na gari ba, wataƙila a gaba na yi dace. Har Faisal da ban san lokacin da ya bar gidan ba sai da na tuno. Addu'ar fatan shiriya na yi musu na watsar da lamarinsu. Washegari da safe Gwaggo Habi ta zo ta dinga yi mini faɗa kamar za ta dake ni, da kaicon barin da na yi mai kuɗi kamar Idonnera ya sake ni, ban ji nauyinta ba na ce ba shi da lafiya ne, don ko idda ma ban da ita a kaina. Da ta ji haka ne ta sauko, amma duk da haka sai ta ce ban da jaraba irin ta yaran zamani da na zauna a hakan ai, tunda ga kuɗi ba sai na yi haƙuri ba. Na ce shi ya sauwaƙe mini da kansa saboda kar ya dinga cutar da ni. Wajen azhar sai ga direba da kayan sakawata niƙi-niƙi, wai Alhaji ne ya aiko shi da su. Hakan ya ƙara kwantar mini da hankali, na tabbatar ya haƙura kenan, na yi nasara. Da daddare ina zaune na yi tagumi ina tunanin rayuwa da yadda ta zo mini kira ya shigo cikin wayata. Ko kallon ta ban yi bare na ɗauka, ƙishirwar son ganin ƴaƴana ita ta fi komai damu na a yanzu, na yi mamaki sosai da har yanzu Anas bai kawo su ba, ji nake kamar na tafi ƙauyen nasu na je na gano su. Gefe guda kuma ina tunanin inda Maman Nasmah ta shiga da ta yi wannan ɓatan dabon, ba ƙaramin son mu haɗu na ba ta labarin abubuwan da suke faruwa nake yi ba. Ganin an ƙi daina kiran ya sa na janyo wayar na duba, baƙuwar number ce, hakan ya sa na ɗan yi jim kafin na ɗaga bakina ɗauke da sallama. Muryar Alhaji Mansur na ji ba tare da ya amsa ba yana faɗin. "Sannu ƴar matsiyata, kin yi ƙoƙari fa sosai da tarkon da kika haɗa mini, ga shi kin yi nasara ya kama ni. Na daɗe ina mamakin yadda aka yi kika iya ƙirƙirar wannan dabarar, to abin da na kira faɗa miki shi ne, har yanzu a tafin hannuna kike, kuma tanadin uƙubar rayuwar da na tanadar miki da ƙuncin da zan saka ki a ciki sai kin ji gara zaman gidan nawa da kike gudu sau miliyan da shi, don haka ki shirya, sai kin yi nadama da danasanin rainin hankalin da kika yi mini. Sai na wulaƙanta rayuwarki na ɗaiɗaita ta, nan ba da jimawa za ki yi bankwana da farinciki na har abada. Ba ki da kowa ba ki da komai, bare ki samu mai tsaya miki, za ki gane kin tsokano tsuliyar dodo. Kuma ki sani duk inda za ki shiga a faɗin duniyar nan ba za ki taɓa tsere mini ba, ko'ina sai na saka an ƙwaƙulo mini ke. Bayan na gama illata ki na saka a bazar da ke, kin fi kowa sanin ba ki da wanda zai iya ja da ni a kaf danginku da mutanen da kika sani, bare ki yi tunanin kai ni ƙara." Ya ja tsaki cikin tsananin ɓacin rai sannan ya ci gaba da faɗin. "Ba a taɓa raina mini hankali irin wannan ba, amma kanki kika yi wa ba ni ba, don ba zan taɓa bari ki ƙara wani jin dadi ba a rayuwarki har abada!" Daga haka ya kashe wayar........✍️ _*ALHAMDULILLAH! Sai kuma Ubangiji ya kai mu bayan Sallah zan ci gaba, Allah ya nuna mana watan Ramadan lafiya, ya karɓi dukkan ibadunmu, ya sa mu yi su lafiya mu gama lafiya.*_🙏🥰❤️ *Zeey Kumurya*✍️