*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* *SHIMFIDAR LABARIN* ((1)). Sunan da na taso da shi tun haihuwata shi ne MA’U. Cikakken sunana na usul Nana Asma’u Adam Bebeji. Ma’u ya bi ni ne daga bakin mahaifiya ta Nene tun ina karama. Mahaifi na Malam Adamu bafullatanin garin Bebeji ne, wata babbar alkarya a kananan hukumomin jihar Kano. Yayin da mahaifiya ta Nene Zainabu ta fito daga kauyen Babura ta jihar Jigawa. Nene baka ce amma doguwa kyakkyawa, wadda ta yi tashen manema a zamanin kuruciyar ta, a karshe dai Allah ya yi ta zama rabon mahaifi na, wanda cin kasuwa ne ya kai shi Babura kamar yada ya saba duk ranar kasuwar garin. Ya ganta a kasuwa tana tallan fura, farat daya ta shiga zuciyar sa, ya sa kai da gaske wajen neman aurenta da karfin sa, har Allah ya ba shi sa’a, ya sure ta zuwa mahaifar sa, Bebeji. Sana’ar mahaifi na shi ne kasuwancin goro, da wannan sana’ar ya dogara tun yana saurayi har zuwa shekarun girman sa. Sana’ar goro ta karbe shi don har Shagamu yake zuwa ya auno goro, ya kai shi kasuwannin gari-gari, kuma da ita ne ya raine mu ni da kanwa ta kwalli daya, Arifah. Mu biyu Allah ya bai wa iyayen mu kamar yadda shi ma mahaifinmu su biyu ne kacal a wajen iyayen su, shi da Yayar sa, Adda Kilishi. Tsakanin mahaifi na da Adda Kilishi akwai ratar shekaru masu dan dama, sai da ta yi shekaru bakwai a duniya sannan aka haife shi. Ba zan manta ba Baba ya sha gaya mana yadda Adda ta yi ta wahala da shi yana yaro, duk inda za ta goya shi ta ke ta tafi da shi, sannan ba yaron da ya isa ya taba mata shi. An yi mata auren wuri, wanda ya janyo rabuwar su domin shekarun ta goma sha hudu ta yi manemi daga garin Sokoto, mai suna, Atiku, abokin sa ya zo gani a garin Bebeji suka hadu kuma cikin dan lokaci suka aminta da juna. Iyaye kuma suka amince da nagartar sa bayan dogon bincike suka aura wa Adda Kilishi Atiku Dogon Daji, ya tafi da ita Sokoto garin iyayen sa. A lokacin yana aiki da ma’aikatar sadarwa ta kasa, wato Ministry of Communication and Digital Economy . Alhaji Atiku Dogondaji ya dade yana aiki a can, ko da suka maida shi jihar Rivers, wato Port-Hearcourt bai tafi da iyalin sa ba, a Sokoto ya bar su, Adda ta ba ni labari cewa duk karshen shekara yana daukar hutu ya zauna cikin iyalin sa kuma duk bayan watanni ukku yake zuwa Sokoto. Tun ina goye Adda Kilishi ke hidima da ni, sutura da kayan wasa kamar ba a kauye nake rayuwa ba. Akai-akai Adda ke zuwa daga Sokoto ta yi wa iyayena goma ta arziki, ni kuma ta yi min sayayyar suttura da kayan wasa da ta saba kawo min duk zuwan ta Bebeji. Adda ba ta dogara da mijin ta kadai ba, tunda ya kasance ba ta yi zurfi a karatun zamani ba, tana aji uku na karamar sakandire aka cire ta aka yi mata aure, kuma mijin ba ya bukatar ta ci gaba, ya ce nashi karatun ya ishe su, sai ya ba ta jari ta ke kasuwanci. Sana’ar Adda atamfofi ne da lesissika da mayafai na mata, sana’ar ta karbe ta don har shaguna gare ta manya guda biyu a kasuwar (Dan Jabalu). Tana yo odar kayanta ne daga waje ta zuba a shagunan ta, kuma Allah ya ba ta nasibi sosai a wannan harkar. Iyakar kulawa da tarbiyya muna samunta ni da kanwata Arifah a wajen iyayen mu, da yayar mahaifinmu Adda Kilishi. Kuma haihuwar Arifah bai ture gwamnati na daga wajen Adda ba, gatan da nake samu a wurin ta Arifah ba ta samu. Allah bai yi Arifah mai tsawon rai ba ce, shekarun ta biyar ta kamu da cutar kyanda (bakon-dauro) wadda ta yi ajalin ta. Duk shaquwar da ke tsakani na da Adda ba abin da na tsana irin zuwa wurin ta a Sokoto, ba don komai ba sai don halin ‘ya’yan ta. Babbar wato Nabeelah cin zalina ta ke yi, shi kuma Yaya Maccido (Attahir) mai bin Nabeelah yana da tsanani akan ilimin boko, daga ni har Muhsin autan Adda wanda shi ne tsara na cikin ‘ya’yan ta don shekaru biyu kawai ya bani bakar wuya muke sha a hannun su. Don haka ne daga baya da na yi wayau idan Adda ta zo ta kuma fara shirin tafiya, to fa za a neme ni ne a rasa har sai ta bar gari. Tun ba ta gane ba har ta gane gudun zuwa gidan ta nake. Rannan ta zaunar da ni don jin dalili cikin lallashi, inda na sadda kai na gaya mata gaskiya, karatun Yaya Maccido ne bana so. Maccido ga bulala in ya koyar ba ka iya ba. Ni kuma a rayuwa ta Allah ya halicce ni da kin karatun boko. Ranar da na gaya wa Adda dalili na na kin gidan ta ta dade tana jan hankali na cewa; Maccido so yake mu zamo masu hazaqar karatu irin nasa, mu dinga ciyo kyaututtuka na ban mamaki a makaranta irin wadanda kullum yake ciyowa, mu zamo zakaran gwajin dafi cikin tsararrakin mu kamar yadda yake. Ba da nufin takura mana yake yi ba. Sunan Sultan Of Sokoto Mohammad Attahiru aka sa wa Yaya Maccido, dalilin da ya sa iyayen ke kiransa Maccido ke nan. Mohammad Attahiru shi ne Sarkin Musulmi na goma sha uku a Seat of Caliphate. Iyayen sa na fatan ya dauko halayen sa da soyayyar sa da gudummuwar sa ga addinin musulunci, shi ya sa suka sanya masa sunan sa. Kamar yadda na fada a baya, daga Adda har mahaifina Malam Adamu Allah bai ba su yawan haihuwa ba. Daga ni sai Arifah Allah ya nufe su da haifa wadda ita kuma ba ta yi tsawon rai ba. Ita kuma Adda daga Nabeelah da muke kira Aunty Nabeelah sai Yaya Maccido, bayan haihuwar Maccido sai da Adda ta kwashe shekaru goma sha biyu ba ta sake haihuwa ba, har ana tunanin haihuwar shi ke nan ta kare, sai kuma Allah ya kawo, Muhsin. Duk cikin ‘ya’yan Adda Muhsin shi ne mai kirki, shi ne bai yo halinsu na mugunta, cin zali da takura wa dan Adam ba. Watakila wannan ne dalilin da ya sa na fi shakuwa da shi, watakila kuma don shi ne kusan sa’a na (tsara) na shi ya sa na fi son sa da kaunar sa. Na taso a gaban iyaye na cikin samun ingantacciyar tarbiyyar addinin islama, da kuma samun cikakken gata wanda bai sa ni na kauce wa tarbiyya ba. Allah da ya halicce ni shi ya sanya min kin karatun boko, wahala yake ba ni, bana fahimtar sa ko kadan, kullum ni ce ta-kashin aji, ni ce mai daukar ta karshe a duk jarrabawar da ake yi mana tunda na fara firamare har na gama ta. Kuma da ya kasance iyaye na ma ba masu ilmin zamanin ba ne sai hakan bai taba damun su ba, domin kuwa ina bada himma a karatun islamiyya, itama ban iya hada baki ba saidai hadda, shekaru na goma sha biyu na haddace rabin Alkur’ani. Sauran littattafan addini kuwa idan ina ja ina tarjama a haddace tsammani za ka yi diyar wani shehin malami ce ni. Idan ana maganar kyau na san ba za a lissafa da ni ba. Kyawu na kadaran-kadahan irin na mahaifiya ta. Babu muni, sannan babu kyau na bada labari. Baka ce ni, doguwa, mai dan kauri, wanda kalar fata ta ya fiddo zahirin kasancewa ta cikakkiyar bahaushiyar Kano jikar Barbushe da Tsimbirbira. Gashin kaina yana da cika da karfi, amma babu tsayi, idan aka yarfa min kitso yana da ban sha’awa, domin ba ka ganin kyawun gashina sai idan an yi min sabon kitso kanana. Babu wanda nake bari ya taba min kai sai Nene (sunan da nake kiran mahaifiya ta Zainabu) kuma sunan ya bi bakin kowa, duk shiyyar mu da Nene ake kiranta. Lokaci-lokaci mu kan je Babura inda dangin mahaifiya ta suke, iyayen ta sun dade da rasuwa, amma akwai birbishin dangi na iyayen nata da iyalinsu a raye. Na taso cike da dokin, ranar zuwan Adda Kilishi. Ta kasance uwa mai yawan kyautata mini ta kowanne fanni, ta kasance ‘yar uwa ta gari ga dan uwan ta, wato mahaifi na. Ta zame masa uwa da uban da ba su tashi da su ba. Zumuncin ta abin a bada labari ne, domin ba ta bambanta ni da ‘ya’yan da ta haifa, tun ina mitsitsiya ta na fahimci wannan bangaren na Yayar mahaifi na Kilishi. An ce akwai wadanda zumuncin su shi zai kai su aljannah, bana tantama ciki har da Adda da mahaifina malam Adam, don dai ni tun da nake a duniya ban taba ganin ‘yan uwa masu son juna fisabilillahi kamar su ba. Duk da mahaifi na ba mai karfi ba ne wannan ba ya hana duk sallar idi ya dinka wa Maccido kayan sallah irin wadanda ya dinka wa kansa. Haka nan yana yi masa kiwon tumaki garke guda a nan kangon bayan gidan mu, wadanda ya fara ne da ba shi tunkiya mai ciki, ta yi ta hayayyafa, Maccidon ya ce Baba ya kiwata masa ita, don gidan su ba wajen kiwo. Baba ya soma yi wa Yaya Maccido wannan kiwon ne tun yana da shekaru goma a duniya, Allah kuma ya albarkace su, domin a yanzu sun zama garken awaki na raguna da tunkiyoyi da ‘ya’yan su. Har zuwa yau Baba bai taba gajiya da kiwon da yake yi wa Yaya Maccido ba. Baba ne kurum yake kiransa da sunansa na asali, wato Attahir, amma a bakin ‘yan gidan su da iyayen sa da abokan sa "Maccido" ne a bakin kowa. Ina aji daya a babbar sakandire wadda sau biyu ana min maimacin aji (repeating) kafin in samu in shiga siniya sakandire, a hakan dai nake kukkulla makarantar maganin zama a gida, kada a ce bana karatu. Ni tunda nake ban taba daukar littafin makarantar boko da nufin in duba abin da aka koya min in na dawo gida ba, sannan bana yin aikin gida (home work ko assignment) yadda aka ba ni shi haka ake karbar littafin ba tare da na rubuta ko ‘alif’ ba. Duka na sha shi wajen malamai har ya yi yawan da bana jin shi a jikina, sai a yi min bulala bakwai a tafin hannuna ban yi ko hawaye ba. Sau ba adadi hukumar makarantar mu ta sha kiran mahaifi na a kan matsala ta, abin da yake cewa kullum shi ne, “Watakila Ma’u ba ta da abinci a boko, tunda ta shiga firamare ma har ta gama haka ta ke, ku yi min alfarma ta ci gaba da zuwa makaranta tana shiga aji, in ba ta koyi karatu ba, ta koyi rayuwa da cudanya da jama’a”. Ina mamakin saukin hali irin na mahaifi na. Idan na duba sai in ga ita ma Adda Kilishi ai haka ta ke. Saukin kansu yayi yawa akan 'ya'yan su. A fili suke nuna mana soyayyar su garemu. A daidai wannan lokacin ne rannan na taso daga islamiyya, tun daga nesa na ga santaleliyar motar da ta sanar da ni cewa, Adda ta zo gari, don haka na kara da gudu-gudu, sauri-sauri na isa gida. Amma abin mamaki direban ta Malam Hussaini ne kawai a zauren gidan mu babu walwala ko ta kobo a tare da shi. A gurguje na gaishe shi na afka tsakar gida ina kiran, “Oyoyo Adda”. Sai dai a raina na yi mamakin dalilin da Malam Husaini yau bai yi min kirarin da ya saba yi min ba cikin raha a duk lokacin da muka hadu, wato; “ASMA’U FARA ‘YAR SHEHU”. Ni kuma na kan amsa masa da cewa, “Wannan Asma’un baka ce. Babu digon fari ko dis a jikin ta”. A duk lokacin da na fadi hakan, Malam Hussaini ya yi ta dariya ke nan. Turus! Na ja na tsaya ganin Nene na zuge katuwar jakar matafiya, Baba ma yana tsaye da tasa dirkekiyar jakar yana kara gyara kayan ciki. Fuskokin su sun yi min kama da na Malam Hussainin Adda da ke soro. Wato fuskokin su dauke suke da matukar alhini. Na karasa jiki a sanyaye na ce, “Nene, ina za ku? Ina kuma Adda?” Nene ta dago ta dube ni, fuskarta ba yabo ba fallasa, ta ce, “Ba ta zo ba, mu ne za mu je mata. Je ki ajiye jakar makarantar ki canza kaya ki zo mu tafi, yanzu za mu dauki hanyar Sokoto”. Tunda muka dauki hanyar Sokoto daga Bebeji babu mai magana a cikin motar, Nene da Baba jan carbi kawai suke yi, yayin da Malam Hussaini ke tuki cikin kwarewa da kula da ladubban tuki. Ni dai sai sake-sake nake, ina so in tambayi abin da ya faru, babu fuska, don ko a junansu ba sa hira. Wani mummunan tunani ya fado min a rai, ko dai wani abu ne ya samu Adda? Abin da zai taso Nene da Baba a wannan yammacin zuwa Sokoto, hakika ba karamin abu ba ne. *KYAUTA NE GA TAKORI'S LOUNGE* *SUMAYYAH ABDULKADIR* *(TAKORI)* TUKUICI NE ga makaranta littatafai na. ```Yiwa Kai Hisabi``` ((2)). A wancan lokacin Najeriya lafiya lau, babu matsalar ‘yan fashi, babu ta ‘yan garkuwa da mutane, babu ire-iren wadannan abubuwan. Ina miki bayanin abin da ya faru ne ga ni Asma’u shekaru ashirin da biyu a baya, wani lokaci ne da kasarmu ke zaune lafiya cikin lumana da kwanciyar hankali. Babu irin tunanin da ban yi ba, amma na kasa rike kwakkwara guda daya in ce shi ya faru, wanda ya janyo mana tafiyar dare haka zuwa Sokkoto birnin Shehu. Tsananin addu’ar da Baba da Nene ke yi, shi ya kawo mu Sokkoto lafiya. Addar da nake tunanin wani mummunan abu ya same ta da ita na fara yin tozali a makeken falon ta, sai dai da ganin ta ta ci kuka har ta gode Allah, ta rame ta yi fiyat cikin kwana daya. Sai da muka kwana muka wuni na fahimci abin da ya faru, Baban su Muhsin ne ya yi hatsarin jirgin sama daga Port-heartcourt zuwa Sokoto, ko gawarsa ba su samu ba, an tabbatar yana cikin fasinjojin, jirgin nasu ya fado ne ya kone kurmus. Ya tafi ya barta da marayu guda uku, da tarin dukiyar da ba su san ya ya za su yi da ita ba. Maccido karatu yake a kasar 'Cuba' (country in the Carribean) yayin da Nabeelah ta ke Beirut din Lebanon tana nata karatun, Muhsin ne kawai a gaban ta. Da wannan tashin hankalin su Adda suka wayi gari. Lokacin da ta ga Baba na sai ta daura kai a kafafun sa ta yi ta rasgar kuka. Kuka ta ke mai tsuma zuciya, mai dauke da amon girman maraicin da ya same ta. Alhaji Atiku Dogondaji, miji ne wanda har a aljannah ta ke fatan Allah ya tashe su tare. Ya rike Adda da daraja da mutunci, bai taba la’akari da zurfin ilminsa ya wulakantata ba, ko ya ce zai auro wadda ta yi boko ta fi ta wayewa ba. Ya yi musu komai a rayuwa ita da ‘ya’yan ta, don haka rashin sa tamkar faduwar wani babban gini ne wanda yake katanga abar jingina a gare ta da ‘ya’yan ta. An yanke shawarar ba za a gaya wa Maccido rasuwar mahaifinsa ba, saboda a daidai lokacin jarrabawa yake yi. Amma ranar kwana biyar da afkuwar al’amarin Nabeelah ta iso. Suma ta rika yi ana yayyafa mata ruwa tana farfadowa. Ko ba ka yi wa wannan family din farin sani ba, dole in ka ga halin da suka kasance a wannan loakcin ka tausaya musu. Mai rangwamen damuwa a cikin gidan, Muhsin ne. Ya yi damuwar, amma ta kwana biyu ya ware ya shiga harkokin sa. Duk inda ya yi muna tare, kamar tip da taya. Tun sati daya da rasuwar su Nene suka so komawar mu gida Bebeji, amma Adda ta hana, sai da muka kara sati. Da za mu koma kuma ta ce, ni a nan za'a bar ni. Gidan ya yi mata fadi da yawa, don washegarin ranar Nabeelah ma za ta koma makaranta. Ai kuwa ba kunya na sa kuka kan ba zan zauna ba. Aka yi a ka yi na ce kafata kafar Nene. Da haushi ya ishi Nene, sai ta tsinka min mari. Na kuwa bare baki ina kara rusa kuka. Adda ta jawo ni jikin ta tana lallashi na a lokaci guda kuma tana yi wa Nene fadan saurin hannun ta. Mene ne abin duka? Ta ce, “Ma’u ba za ki zauna da ni ba?” Cikin kuka na ce, “Adda, to yaushe za ki maida ni wajen Nene?” Tana goge min hawaye ta ce, “Insha Allahu idan Nabeelah da Maccido sun gama karatu sun dawo gida zan maida ke wajen Nenen ki Asma’u. Kadaicin ya min yawa, ina bukatar mai debe min kewa, ba kya tausayi na ne Ma'u?” Duk sai jiki na ya yi sanyi, duk da nake yarinya karama na san Adda abin tausayi ce a wannan lokacin, amma na fi so in yi zamana gaban iyaye na, duk da na san zan samu gata da jin dadi ne fiye da wanda nake samu a gidan mu. Ni wannan ba ya gabana, na fi so kullum na bude ido in gan ni gaban Nene na da Baba. A daren ranar a dakin da Nene ta sauka na kwana, mun raba dare tana min fada, ta bari ta koma nasiha. Ta ce, Adda ba ta cancanci abin da na yi mata dazu ba, kauna ce da soyayya ta sa ta ce in zauna a wajen ta, ba don ba ta da ‘ya’ya ba. Ta yi min nuni da halin da Adda ke ciki, tana son wani makusancin ta ne a kusa da ita. Ta ce in zauna gaba gare ta in hidimta mata, in mata biyayya iyakar iyawa ta, don ba ni da wanda ya fi-ta a duniya bayan mahaifi na. A bayan Nene na kwana, manne da jikin ta. Da asuba ma bayan mun yi sallah sai da ta kara lallashi na tare da jaddada min yi wa Adda biyayya da hidimta mata, ta sa min albarka ta ce, “In kin kasa karatun boko kada ki damu, ba shi ne tikitin shiga aljanna ba, wanda ki ka iya shi ne wanda zai tserar da ke ranar gobe kiyama”. Wadannan kalaman na Nene a kan karatu na na boko kullum ina tuna su, suna cire min damuwar nakasu na a kai, suna zame min fitilar rayuwa. Baba ya ce da Adda shi ko su Nabeelah sun dawo, ya riga ya mallaka mata ni har zuwa ranar da za ta yi min aure. Maganganun su duka shi da matar sa Nene masu karya zuciya ne. Amma a wannan lokaci daga ni har Adda ba mu ankara da muhimmancin su ba. Sai a lokacin da aka shimfide mana gawarwakin su a gaban mu. Sun yi hatsari gab da za su shiga garin Talata-Mafara, Malam Hussaini direba hatta kafarsa da hannayensa sun fita daga jikin sa. Sabon tashin hankali irin wanda zuciya ba za ta iya fassarawa ba. Rana ce da ba zan taba mancewa da ita ba a kundin tarihin rayuwata. Ranar da na tabbata marainiya ba uwa ba uba, har fiye da su Muhsin. Rayuwa ta dandana mana wani irin daci ni da Addah, da babu madacin da ya kai dacin sa. Hankali na ya bar jiki na, nutsuwa ta kau mun, kadan ya rage in rasa hankali na. Kwana na uku ina sambatu wanda babu komai a cikin sa sai "Nene da Baba". Shekaru na goma sha hudu a daidai wannan lokacin, ranar da na amsa sunan ‘MARAINIYA’ gaba da baya a cikin wani dan takaitaccen lokaci mai kama da kiftawar ido. *** *** *** Aka ce mutuwa mai tonon asiri, ba mu tabbatar da wannan ba sai lokacin da kannen mijin Adda su biyu Malam Ilya da da Malam Bilya suka zo addu’ar arba’in din dan uwan su. Bayan an shafa addu’a suka kira Adda falon marigayi. Babu kwane-kwane suka ce ta fiddo duk wata takarda da kowanne kobo da ta san marigayin ya bari za su alkinta wa ‘ya’yan sa, har su yi hankalin daukar takalihun dukiyar su. Sannan in ta amince shi malam Bilya zai aure ta don bai kamata a bar gidan ba namiji ba, in yaso sai ya kwaso sauran iyalin sa daga Dogondaji su dawo gidan da zama. Hajiya Kilishi ta dade kanta a kasa ba ta ce komai ba, har suka gama duk wani tsare-tsaren su, wanda babu komai a ciki sai hadama da babakere a cikin rigar zumunci. Lokacin da suka matsa da son jin amsar ta sai ta ce, ita a yanzu ba ta da magana, tana cikin alhinin rashin mijin ta da tilon dan uwanta, babu wani rabon gado a gaban ta, tunda gadon nan dai babu mai shi daga ita sai ‘ya’yan ta. Maganar aure kuwa ita da kara yinsa har abada! Shekarun ta arba’in da takwas ta kusa isa ‘menopause’ ba ta bukatar wani aure a rayuwarta. Za ta yi zaman ‘ya’yanta ne kawai da zaman jiran nata wa’adin. Ba ta da sauran muradi a duniya. Wadannan dattijai ba su hakura ba, bayan wata uku sai da suka sake dawowa suka ce ba ta isa ba, sai ta fiddo komai sun raba wa ‘ya’yan su gado. Saboda gudun rigima da tashin hankali, Adda ta fiddo kananan kadarorin marigayin ta ba su. Suka dauko malaman karya suka yi kasafce-kasafcensu inda suka samfe komai suka mike, suka ce sai yaran sun yi aure sun zauna waje daya za su ba su. Aure kuma tunda ta ce ba a yi ita ta jiyo, da ma taimakon ta za su yi. Su rike mata marayun ta a gaban su. Abin ya hada da rashin ilmi, ban da haka ‘yar dukiyar da suka gani suka gigice ba ta kai ko kwatan-kwatan abin da mutum irin Alhaji Atiku ya mallaka ba. Sun yi waya da Nabeelah a ranar ita da mahaifiyar ta suka yi ta kuka kamar ran su zai fita. Nabeelah ta ce, ita tashin hankalin ta shi ne Maccido na kan hanya, wai surprise zai yi wa Adda shi ya sa bai gaya mata zai zo ba. Duk halin da Adda ke ciki dole ta murmure ta aro juriya ta dora wa kanta. Ta shiga shirin tarbar Maccido. Watanni uku da sati biyu kenan da rasuwar Alhaji Atiku Dogondaji, wanda ya yi daidai da cikar Babana da Nene watanni uku cif a gidan da ke jiran kowanne dan Adam. Har zuwa wannan lokacin ban koma daidai ba, bana doguwar magana daga eh sai a’ah, abinci sai Adda ta sani a gaba shi din ma sai mai ruwa-ruwa idan na ji hanjin cikina na raurawa. Duk wannan lukutin jikin nawa ya zaizaye na koma kamar a bushe ni in fadi. Ni dai na san ina wanka, amma bayan shi ko mai bana shafawa, balle a je ga zancen kwalli da hoda. Adda ce ke takaba, amma kusan tare muke yi. Sati biyu ke nan da gama takabar ta. Sai da ta tabbatar abincin da ta sa mai aikinta Halima ta taimaka mata ta shirya ya kammala a kan tebir sannan ta fada wanka, ta fito ta sanya kaya masu dan haske wadanda rabon ta da sanya su tun mijin ta na raye. Ta fito falo inda ta tadda mu zaune ni da Muhsin, dawowar sa ke nan daga makaranta ko (uniform) bai cire ba ya ce, “Addah, unguwa za ki ne?” Fuskarsa ta nuna jin dadin ganin ta cikin kyakkyawar kama yau. Ta zauna tana fadin, “Ma’u miko min carbi na”. Ba tare da ta bai wa Muhsin amsa ba. Ko gama rufe bakin ta ba ta yi ba suka tsinkayi sautin sallamar sa cikin muryar sa mai kurdawa har cikin kwakwalwar mutum, ta haifar masa da canjin yanayi. Idan diya mace ce ta rikitata, ta haifar mata da kasala wani lokacin har ta rasa control din kanta. (Maccido-Attahir). Gaba dayanmu muka daga kai muka dube shi. Maccido ne daga Cuba, Maccido (Tahir) Atiku Dogondaji, kamar yadda cikakken sunansa yake. Fari ne ba sosai ba, ya fi kyautuwa a kira shi wankan tarwada. Akwai abubuwa da yawa a tare da Maccido da ba duka maza Allah ya mallakawa ba. Yana da wani irin sassanyan kyau, wanda a kallo na farko ba za ka ganshi ba, abin da za ka gani shi ne, ilhama da cikar halitta. Duk inda ake neman maza su amsa sunan su, to a sanya Maccido cikin su, ko shi kadai zai wakilci guda dari. Maccido mutum ne wanda ba shi da fara’a ko kadan, sannan ba ya wasa ga na kasa da shi, very responsible person, sannan ba ya son duk wata harka in dai akwai shiririta a cikin ta. Shi din wani irin mutum ne mai matukar tsantseni da taka-tsan-tsan cikin mu’amalarsa da kowa. Ba ya shiga sabgar da ba tashi ba, kuma ba ya son a shiga tasa. Babban sirrin Maccido shi ne iya daukar wanka da iya diresin, wadanda suka taru suka cakude suka ba shi wata irin kyakkyawar suffa wadda kafin ka samu mai irinta sai an tona. Maccido Taheer ya mallaki duk wasu nagartattun halaye da ake so namiji ya siffantu da su, kai dai barshi da shan kamshi da rashin fara’ar sa. Wani tsalle da muhsin ya yi daga kujerarsa sai ga shi makalkale da Yayansa Maccido, “Brother da ma kana hanya amma shine ba ka gaya mana ba?” Dan murmushi ya yi yana yi wa Adda sannu da gida kamin ya samu gefen kafafun ta ya zauna, ya dora hannunsa kan tafin kafar ta. “Ka sauka lafiya Maccido, ya ya hanya kuma ya ya karatun?” Ya dukar da kai ya ce, “Na zo lafiya Addah, da fatan na same ku lafiya, saidai karatu akwai matsala. Adda na samu carryover har biyu, abin da ban taba samu ba a tarihin karatu na. Wani irin faduwar gaba nake yawan yi. Ga yawan yin zurfi a tunani. Sannan Adda haka kawai sai nake fama da anxiety wanda ban san dalilin sa ba”. Hawaye suka ciko idon Adda, ta kauda kai daga kallon Maccido. Cikin sanyin murya ta ce, “Ka je ka yi wanka da sallah, ka zo ka ci abinci sai mu tattauna ko?. Yanzun akwai gajiyar zaman jirgi tare da kai na sani”. Sai da Maccido ya yi duk abubuwan da Adda ta lissafa sannan ta runtse ido ta gaya masa duk abubuwan da suka faru a bayan sa. Maccido shidewa ya yi na wucin gadi, iyakar firgita da tashin hankali irin wanda dan Adam ke kasancewa a ciki, a lokacin da ya samu labarin gushewar mahaifi. Mahaifin ma irin Alhaji Atiku, wanda shakuwar da ke tsakanin sa da ‘ya’yansa ta zarta ta uba da ‘ya’ya kadai, su ne abokan sa kuma aminan sa. Sannan ya bugu da mutuwar Uncle din sa da maidakin sa Nene, wadanda akwai kyakkyawar alaqa ta soyayya tsakanin su da shi tun haihuwar sa. Adda har zuwan kawunninsa daga Dogondaji da yadda ta kare da su sai da ta labarta masa. Maccido ya yi kuka har ya ba uku-lada. Kwanan sa bakwai ya kulle kan sa a daki, ba ya zuwa ko ina, abinci ma can Muhsin ke kai masa. Hakika ya shiga wani hali wanda biro ba zai iya rubutawa ba. Nabeelah kan kira shi su yi kukan su mai isarsu. Komai na duniya ya fice masa a ka, karatun ma ya soma tunanin kin komawa. Gani yake a yanzu shi ne gatan uwar sa da ‘yan uwan sa. Ga marainiya Ma’u wadda ta karu a cikin su, takalihun ta dole ya dawo hannun sa. Ya kan tuna soyayyar mahaifi na gare shi don haka ya sha alwashin rike ni cikin su kamar yadda zai rike Muhsin. Da kyar Adda ta lallashi Maccido ya koma makaranta bayan karewar hutun sa. Da lallashi da ban-baki, da kalaman karfafa wa Adda tasa shi ya gyara takardun sa. Ya kuma ci gaba da karatu da wata irin himma wadda a baya ba shi da ita. Apart from course din da yake yi, watau "Architecture" sai ya kara da Business Administration, ba don komi ba sai don ya samu sani kan ilmin kasuwanci, ya zo ya tallafi dukiyar da mahaifin su ya wanzar da rayuwar sa ya tara musu. Gaba daya rayuwar sa ya fuskanci neman ilmi ka’in da na’in, don ya san yanzu shi ne kadai gatan da zai yi wa kansa da mahaifiyar sa da marayun ‘yan uwan sa. *TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE* 10/09/2023 *SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* 07030137870 ~HISABIN NAFS~ ((3)) *BAYAN SHEKARU UKU* Abubuwa da yawa na ci gaba sun faru cikin shekaru ukun da suka biyo baya ga iyalin marigayi Atiku Dogondaji. Aunty Nabeelah ta kammala karatun ta da ta ke yi a Beirut (Lebanon) ba ta tashi dawowa ba sai da guzurin miji balarabe dan asalin kasar Lebanon. Sunanshi Fa’iq, malaminta ne a makaranta wanda soyayya mai karfi ta shiga tsakanin su, wannan ya samo asali da matukar kokari irin na Aunty Nabeelah. Ya biyo ta har Sokoto tare da waliyyansa. An kai ruwa rana da su Baffa Bilya kafin su amince su aurar da Nabeelah ga Fa’iq don cewa suka yi in ta tafi bata za ta yi. Sai da Fa’iq ya alkawarta kawo Nabeelah gida duk karshen shekara, haka duk mai son ganinta zai dauki nauyin zuwan sa gare ta, sannan suka amince aka daura auren. Fa’iq ya dau Nabeelah suka koma Beirut. Yaya Maccido ma ya gama nasa karatun ya samu tayin aiki iri-iri da construction companies daban-daban, amma a karshe ya zabi ya yi aiki da Julius Berger Nigeria, suka barshi a babban reshen su na birnin Tarayya, Abuja. Tun daga lokacin ne ganin sa ya yi mana tsauri. Ya tattara duk dukiyar da mahaifin su ya bar musu ya bude musu wani katafaren shopping mall kusa da Al-madina, ya dauki amintattun yara ya zuba, Muhsin ne manajan wajen duk da karancin shekarun sa. Ko dama can Muhsin haziki ne kuma yana da sha'awar kasuwanci. Shi yasa nauyin da Yaya Maccido ya dora masa bai gagare shi ba. Duk wata ribar shagunan na tafiya kai tsaye account din kowannen su adadin hannun jarin sa. Babu abin da ba a samu a mall din tun daga suttura da kayan abinci na kwalam, da duk abin da Dan Adam ke bukata, kasancewar wajen fuskar jama’a ne, nan da nan sunan MACCIDO MALL ya yi fice a garin Sokoto, kayan su unique ne don Adda ta sa hannu tunda tuntuni ta saba da kasuwanci. Allah kuma ya sanya musu albarka a cikin neman su, asirin wannan family a rufe yake ruf, duk yadda suka yi tunanin rayuwa za ta juya musu baya a bayan ran Atiku Dogondaji hakan bai kasance ba, Allah ya bawa Adda Da daya tamkar da goma, wato Maccido (Attahir), wanda a shirye yake ya sadaukar da rayuwar sa don ingantuwar rayuwar mahaifiyar sa da ‘yan uwan sa. A wannan shekarar ne Yaya Maccido ya zo wa da Adda bukatar yana so ya yi aure. Adda ta tambaye shi ko ya samu matar ne? Ya ce, eh, ya samu a can Abuja kanwar abokinsa ce Usman, sunanta Lubabatu. Adda ta ce, “Yan wane gari ne?” Ya ce, “'Yan Birnin Kebbi ne”. Shiru Adda ta yi na dan wani lokaci tana nazari kafin ta ce. “Maccido ba mu da kowa ni da ‘ya’yana, daga Allah sai kai. Matar duk da za ka aura ya kamata ka tantance ta, ka yarda da tarbiyyar ta da dattijantakar gidan da ta fito. Wadda za ta so mu ta zauna da mu tsakani da Allah. Wadda za ta taimaka maka wajen kula da marayun ‘yan uwanka. Ba wadda za ta kawo canji komai kankantar sa cikin abin da ta zo ta taras ba. Idan ka yarda ka amince ita Lubabatun ta mallaki duka wadannan, to muna maraba da ita”. Ya dade yana tauna magananun Addar sa, yana aunawa a bisa ma'auni na hankali da tunanin sa, don ganin ko Lubabatun sa ta mallaki wadannan qualities da Adda ta jero? Ba zai iya cewa ba! Abin da ya sani kawai shi ne, Lubabatu ta yi daidai da ra’ayin sa, ta mallaki duk abubuwan da yake so a diya mace. Ga kyau ga aji, ga gayu kamar rainon sarauniyar Ingila. Sannan ga ta da ilimi don masters ke gare ta. Ba ya tunanin tana da wani aibu don kuwa abotar su da Usman ta dade. Ya san gidan su babban gida ne, sauran halin mutum ai ba za ka sani ba sai in ka zauna da shi. Gadan-gadan Yaya Maccido ya sa kai ga neman auren sa. Har ya je Dogondaji ya gaya wa su Baffa Bilya. Kafin ka ce me ye wannan magana ta kankama. An kai kudi an yi tambaya, har an ba shi mata. Tsakani na da Yaya Maccido da ma tun fil’azal babu sakewa, babu sabo, babu wata doguwar mu’amala mai nisa. Iyakaci na da shi in ya shigo cikin gida ne mu gaishe shi ni da Muhsin ya sa kai ya wuce dakin Adda, in kuma tare da Addar ya same mu, sai in ba su wuri bayan mun gaisa. Wani lokacin Adda kan sa ni in dauko masa abinci daga dining don ba ya son zama a kan tebir ya ci abinci, ya fi so ya zauna gaban Adda yana ci suna hira. Wannan ita ce alakar da ke tsakani na da Yayana Maccido. Shekaru biyu baya, Adda ta sa ya kai ni wata sakandire ta kudi na dora karatu na. A halin yanzu ina aji biyar na babbar sakandire. Kada ku dauka ko yanzu akwai soyayya tsakani na da boko, har yanzu ina nan jiya i yau, don ma dai Muhsin ba ya bari na haka. Kullum da yamma sai ya sa na dauko littafi na ya tisa min abin da aka koya mini. Amma kan ba ya daukar komai. Kullum ni ce ta karshen aji ko ta biyun karshe. An so a yi min repeating a shekarar da zan shiga SS 2, Adda ta je har makarantar da kanta ta bude bakin jaka, ta kuma ba su hakuri. Ita dai burin ta in samu ko da kwalin kammala sakandire ne, ko da ba zan shiga jami’a ba. Bikin yaya Maccido ya zo, aka yi biki na kece raini a Sokoto da Abuja. Bikin diyar Sanator Abdu Gwadabe.... Lubabatu Abdu Gwadabe da Arch. Attahir Atiku Dogondaji. Yaya Maccido ya sayi apartment a Gwarimpa mai daki uku da falo. Ranar na ji yana gaya wa Adda iyayen amarya sun ce gidan ya musu kadan, ya je ya kama haya a Maitama mai faluka uku suke so. Adda ta kalle shi a shekeke! Ta ce, “Ko bayan raina ban yarda ka zauna gidan haya ba, alhalin kana da naka. Ni ban yarda da rainin arziki ba. In za su zauna a wanda Allah ya ba ka shi ke nan, in bai musu ba, to fa babu dole ta yi ta zama a gaban iyayen ta”. An kai ruwa rana kafin su yarda su je su yi jeren. Muna kitchen ni da Addah muna hada abincin dare, na ji Adda tana kwafa. Kafin cikin takaici ta ce, “Ma’u, tun ba a je ko’ina ba na fara sunsuno gagarumar matsala cikin auren Maccido, sai dai Allah ya kade fitina”. Nan ta ke ba ni labarin maganar gida. Na ce, “Ni kuwa tunda na ga matar rai na yake son ta Adda, kyakkyawa ce sosai, ga ta da gashi har kafadun ta”. Adda ta harare ni, ta ce, “Ai nan ku ka fi kauri ‘ya’yan zamani, kyale-kyalen duniya, wanda dukkan shi mai gushewa ne. Amma mutanen da suka fito fili suka raina arzikin ka, ai babu alamun alheri a tattare da su”. Ranar lahadi aka kawo amarya Sokoto. An yi wa baki abinci na alfarma wanda zai ishe su komin yawan su. Bangaren Maccido na gidan aka sauke su wanda Yaya Maccido ya gyara sosai. Sai dare suka shigo da amaryar wajen Adda tana tare da abokan arzikin ta da mutanen Dogondaji, aka yi abin da ake kira ‘amana', aka yi addu’o’i na nema wa ma’auratan zaman lafiya da zuri’a dayyiba sannan suka koma sashen Yaya Maccido. Washegari ‘yan rakiya suka juya Birnin Kebbi, sai amarya da ‘yar aikin ta wata budurwa banufiya. Kwana uku na yi ina hidimar su don duk abin da za su ci Adda ta dora shi a wuya na. Ta kan ce "in dai a kan girki ne ba ni da haufi a kanki Ma’u. Ko Maccido ya sara miki duk miskilanin sa, ya ce, kin iya girki sosai”. Da daddare bayan na shigar musu da dinner na yi sallama dakin Aunty Lubabatu. Tana gaban madubi tana kwalliya, da alama daga wanka ta fito. Gashin nan da nake so ya sha gyara sai sheki yake a dokin wuyan ta. Ta amsa min sallamar ba tare da ta juyo ba daga shafa hodar da ta ke yi. Na ce, “Aunty zan je in kwanta ne, ban sani ba ko da abin da ku ke so bayan abinci?” Ta ce, “Ina son gasassun ‘yan shilla wallahi, bana son cin abinci da daddare”. Na yi dan jim! Kafin na ce, “Ga shi ba mu da ‘yan shilla sai manyan kaji, ko in nemi karama a ciki in gasa miki?” Ta yamutse fuska, ta ce, “Kai anya? Barshi kawai in Tahir ya dawo ya nemo min. Na gode”. Na koma sassan mu can na samu Muhsin yana kallon kwallo a falo. Ya ce, “Ma’u me ku ka dafa ne?” Na ce, “Sai abin da ka ke so. Abinci har kala uku na yi wa amare”. Ya kyabe baki, ya ce, “Ni fa sam wannan matar Yaya Maccidon ba ta yi min ba. Mace ba fara’a ba haba-haba da jama'a. Ko da na kissa ne. jiya fa da na shiga ina jin shi yana yi mata bayanin ko wane ne ni, amma sai cewa ta yi, "sannu fah!" (Ya fada yana kwaikwayon muryar ta), daga haka ta ta kara kallona ba”. Na yi dariya na ce, “Yanzu kuma duk abin da na sha wahala na girka mata ta ce ba ta so, ya yi nauyi, gasassun ‘yan shilla ta ke so, kuma ba mu da su”. Ya ce, “Mijin ta ya zo ya nemo mata. Ni gara su tattara su tafi su bar mana gida. Haka kawai a dinga sa ki wahala, ke girkau ce?” Adda ta leko daga kofar dakinta da hijab a kanta, da alama sallah ta idar, ta yi masa dakuwa, ta ce, “Ungo nan. Kun zauna kuna gulma, akwai sa’anku cikin su? Na ce akwai sa’an ku?” Ba shiri daga ni har Muhsin muka bar falon, kowa ya yi dakin sa. Na canza kayan jiki na na sa na barci na canza bedsheet dina, ina kokarin bude labulaye don rage karfin A.C da ta cika dakin, na ga Yaya Maccido na shigowa cikin motar sa kirar Cadillac. Sai na samu kaina da son tsayawa in ga fitowar sa don ni dai haka kawai yake burge ni, ga kyau ga wata irin nutsuwa, ga aji, sannan ga wani irin kwarjini na musamman da Ubangiji ya mallaka masa. Ya fito sanye cikin shadda filtex fara kal! Sai walainiya ta ke yi cikin hasken farin kwan fitilar da ya haske harabar adana motocin, hannayen sa rike da fararen ledoji. Kai tsaye cikin kasaitaccen takun sa ya wuce ta gefen tagar daki na zuwa cikin gida. Wajen Adda ya fara zuwa kamar yadda ya saba bai jima ba na ga wucewar sa zuwa nasu sassan, wanda dole ta gaban tagar daki na za'a wuce. Iska ta kado min sassanyan turarensa Escada Magnetism. Na samu kaina da fadawa bisa kwayar kujerar sofa da ke daki na yayin da wani tunani ya bakunce ni. “Matar sa ta yi sa’a”. “Matar sa is a lucky person”. “Matarsa ta ji dadi a rayuwar ta”. A lokaci guda na tambayi kaina dalilin wannan bahagon tunanin? Inda ba tare da bata lokaci ba zuciya ta ta halarto min da amsa; “Yaya Maccido yana BURGE NI!”. Kwan fitilar da na kashe aka kunna, haske ya gauraye dakin. Adda na gani rike da daya daga cikin ledojin da Yaya Maccido ya shigo da su. Ta ce, “Ma’u, kin yi barci ne?” Na yunkura na tashi zaune, na ce, “Ina shiri dai Addah”. Ta miko min ledar hannun ta, “Ungo nan ki ci, gasassun ‘yan shilla ne Yayan ku ya kawo min. Ni ba iya cin su na yi ba, ko za ki iya ci?” Na karba tare da yin godiya, ta juya ta fita tana jaddada min yin addu’o’i kafin na kwanta. Na bude ledar kamshin naman ya buge ni wanda ya ji kayan kamshi. Wato shi auren haka yake da maida mace ‘yar gata, ko me ta ke so mijin ta zai mata, zai nemo mata komai runtsi. To ni yaushe nawa auren zai zo? Wane ne nawa mijin? Yaushe zan isa auren? Tambayoyin da nake yi wa kaina ke nan wadanda ba ni da amsar su. Na san dai rayuwar Yayan mu Maccido da matar sa Lubabatu ta darsa min kwadayin yin aure a zuciyata. ***** Satinsu biyu suka tattara suka wuce Abuja. A satin nan guda biyu mun fahimci da yawa daga halayen amaryar tamu. Don kuwa ba ta zuwa ta gaida Adda in har ba Maccidon ne ya sako ta a gaba suka shigo tare ba. Sannan ni da Muhsin da muke matsayin kannen mijin ta ba mu ishe ta kallo ba. Ni ta ma fi ba ni matsayin ‘yar aikin gidan ganin yadda ta ke sa ni ayyuka cikin gadara da bada umarni. Mun fahimci dai tana da girman kai, sannan ba ta shigo gidan da niyyar gina kyakkyawar mu’amala tsakanin ta da mu ba. Adda ma bayan gaisuwa babu abin da ke hada su. Gane hakan da Muhsin ya yi sai ya yi gaggawar janye jikin sa daga gare ta. Ni da alhakin kula da abincin ta ke wuyana dole na ci gaba da shiga sashen nata akai-akai har suka gama kwanakinsu suka wuce birnin tarayyah. Ranar da suka tafi Muhsin ke fadin, shi wallahi gidan ya fi masa dadi. Na ce, “Ni kuma kewar su nake, ko banza ina koyon dressing, ina kallon gayu ina kwaikwaya”. Tsaki ya yi, ya ce, “Allah ya sauwake miki Ma’u”. Tunda su Yaya suka tafi tsakanin shi da kowa sai dai waya. Adda ta ke kokanta min rannan muna girki, “Yayan ku yau watannin shi hudu bai zo ba, shi da a da karkari ya yi sati biyu, kodayake ya yi aure, nauyi ya karu masa, kuma dai yana kiran waya. Amma ya dace ya zo haka don lissafin mall ya fi karfin Muhsinu, jiya yake gaya min an samu batan wasu kudade masu yawa, kuma yana zargin akantocin mall don sun ga yanzu babu idon Maccido”. Yadda ta ke maganar cikin sanyin jiki da sanyin murya dole ta ba ka tausayi. Na rasa abin da zan ce wanda zai kwantar wa da Adda hankali, amma tabbas Yaya Maccido tunda ya yi aure ya manta da mu, ya dauke kafar sa daga cikin gidan su. Ban san dalili ba, amma na san hakan is unfair don ka yi aure ka daina zuwa ganin mahaifiyar ka da marayun kannen ka. Wasa-wasa sai da Yaya Maccido ya kwashe watanni tara ba zuwa ba aike. Wayar ma da yake kira sai ya yi sati bai yi ba. Ba dama Muhsin ya yi korafi, yanzu Adda za ta ce tunda yana lafiya cikin iyalin sa alhamdulillah. Amma ni na sani Adda na cikin matsananciyar damuwa, ba ta son dasa wa Muhsin damuwar da za ta sa ya daina girmama Yayanshi ne. Duk ta rame ta rage walwala. Sai dai kuma ta kara karfi wajen ibada. Sosai Muhsin ya zage ya dora wa kansa nauyin da Yayansa ya sauke na kula da mall da duk wasu kudi da ke shigowa. Kuma akantocin da ya kama da yi wa shagon almundahana ya sallame su nan take, don haka sauran suka shiga taitayin su, duk da haka abubuwa da yawa na fin karfin sa in aka yi la'akari da karancin shekarun sa. Aunty Nabeelah ce ta kira Adda a waya daga Beirut, bayan sun gaisa sai ta kanga mata kukan jariri a waya. Zo ki ga farin ciki wajen Adda a fili ta dinga fadin, “Masha Allah, tabarakallah. Mace ko namiji?” Nanilah ta ce "namiji ne, Atiku (Aasim)". Wani hawaye ya digo daga idon Addah, kewar Baban nasu ta zo mata. Tun tafiyar Maccido da kin zuwansa sai yau ne ta san hawayen da ta zubar a kan Maccido ne. in lissafin da ta ke yi daidai ne watannin auren Maccido goma sha daya, wanda a ciki bai fi sau uku ta sa shi a idanunta. Nabeelah ta ce, “Adda ya wajen su Maccido? Ni tunda ya yi aure ya manta da ni, ya daina kira na, ni in na kira shi koyaushe ya ce min yana kan uzuri zai kira ni, kuma a karshe sai dai ni in kara kiran, amma ba zai taba kira na ba. Matar kuma sau uku ina kiran ta, amma yadda ta karba min ban ji dadi ba sam, shi ya sa ban sake ba”. Adda ta nisa ta ce, “Allah ya raya min maigida na. Maccido kuma ki yi masa uzuri kin san yanayin aikin nasa, ba waje daya yake zaune ba, koyaushe yana kan furojat (project)". Nabeelah ta bar zancen don bai gamshe ta ba, ta ce, “Muna kan hanya zuwa jibi insha Allah, gara in zo in wankan ganyen runhu da darbejiya hankalina zai fi kwanciya duk da a asibiti an ce ba sai na yi ba”. Adda ta ce, “Rabu da su, ku zo ku yi wankanku ku sha ruwan zafi ku gasu. Allah ya kawo ku lafiya”. *TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE* Nan muka shiga shirin zuwan Aunty Nabeelah, hatta ganyen da za ta yi wankan da shi an tsinko an jibge, an sayo runhu da duk abin da za su bukata, tare za mu zauna a daki na in ji Addah, don tun asali da ma dakin ta ne na gaje. Aunty Nabeelah ta iso da kyakkyawan balaraben jaririn ta. Tun ranar da suka zo yaron ya shiga raina sabida kyawunsa, kai ka ce ni aka haifa wa jaririn nan, koyaushe yana bayana a goye. Sau uku kawai Adda ta yi masa wanka na koya na karbe ni nake yi masa safe da yamma, in cancara masa kwalliya da kayan sa masu kyau. Aunty Nabeelah na kiranshi Aasim, to sai mu ma duka muka kama. Satin su biyu Aunty Nabeelah na lura da abubuwa. Babu Maccido babu wayar sa bayan ta gaya masa ta haihu, kuma ta zo gida. Sannan ta lura komai Muhsin ke wa Adda wadanda a baya Yayan ke yi. Sannan Adda ba ta yi mata zancen sa, ko ita ta dauko zancensa Addah za ta waske. Me za ta ce wa Nabeelah? Maccido tunda ya yi aure ya samu mata ba ta kara ganinsa ba tun watanni ukun farko, ko me? Ba ta so ta zama uwar miji mai korafi, sannan ta san Nabeelah na da zafi ba ta so ta fahimci komai. Ina goye da Aasim ina zagaye dakin da shi don mu samu ya yi bacci sai rigimar dare yake yi. Aunty Nabeelah da ke zaune gefen gado tana gyaran kayan Aasim ta ce, “Ma’u zo nan”. Na karaso inda ta ke, ta ajiye rigar yaron da ke hannun ta, ta ce, “In tambaye ki mana? Za ki gaya min gaskiya?” Na ce, “In har na sani Aunty Nabeelah zan gaya miki”. Ta ce, “A wata sau nawa Maccido ke zuwa gida?” Na jinjina kai ina dan tunani cikin lissafi. “Auren Yaya Maccido ai ya shekara, amma sau uku ya taba zuwa ba, shima bai kwana ba, tunda suka bar nan da amaryar sa, kuma yanzu an doshi watanni goma da zuwan nasa”. Nabeelah ta zaro ido a kaina kamar ni ce Maccidon, sai kuma ta boye razanar ta da mamakin ta, ta hanyar lumshe idanunta, ta ce, “Kada ki gaya wa Adda na tambaye ki komai”. Kai na girgiza, “Insha Allahu”. Daga ranar Aunty Nabeelah ba ta kara kiran Yaya Maccido a waya ba, sannan ba ta kara yi wa Adda zancen sa ba. Na ga dai suna yawan kebewa ita da Muhsin suna magana. Wankan wata daya ta yi sun murmure sun yi kyau da kiba, ita da Aasim. A ranar da suka cika kwanaki talatin ta ce da Adda ita fa ta gama wanka, za ta je yawon arba’in Abuja, tunda ta zo ba ta ga dan uwan ta ba. Za ka iya ganin yadda Adda ta sunkuyar da kai, tsufan ta ya fara bayyana sakamakon damuwar da ta ke ciki. Ta kasa ce da Nabeelah kada ta je tunda Nabeelah za ta nemi ba’asin hakan, amma a zahiri ba ta so ta je din. So ta ke ta ci gaba da sanya wa Maccido idanu ba tare da sun bibiye shi ba har ta ga iya gudun ruwansa. Ashe da ma a wajen ‘ya’yan yanzu mace na maye gurbin mahaifiya da shakikai? Adda ta ce, “Da ma Dogondaji ki ka tafi wajen dangin ki, da ya fi miki, bana so ki je ki dora musu hidima”. Aunty Nabeelah ta yi wani irin murmushi ta ce da Addah, “Can din ma zan je in na dawo kafin in koma. Bar ni in duba dan uwana rabin raina”. Adda sai ta mike da nufin barin wajen, Aunty Nabeelah ta ce, “Ina neman alfarmar rakiyar Ma’u, kin san ta fi ni iya kula da Aasim”. Addah ta ce, “Lala-lalah! Ma’u ba ta taba tafiya mai nisa ba, kuma kin sani ba hutu suka yi ba”. Aunty ta marairaice, “Don Allah Addah wallahi zan kular miki da Ma’un ki, insha Allahu lafiya za mu je mu dawo, kuma gobe juma’a za mu tafi mu dawo lahadi. Zan koya mata karatun da ya wuce ta na islamiyyar". Muhsin ma ya saka baki. “Ai ni in babu Ma’u babu ni a tafiyar, na fi so kullum tana gefe na in ina tuki, don ma ba ni da kudi ne da na fara biyan Adda toshin Ma’u”. Ya fada yana sosa keya da mukullin motar shi. Dariya Aunty ta yi, ta ce, “Da kun bada perfect match gaskiya. Kai 18 years, ita 16 years, ku tara ‘ya’ya before 20 years ku cika wa Addah daki da su su taya ta hira”. Na galla masa harara tare da zumburo baki, “Allah ya sauwake in aure ka, me zan yi da dan ball?” Ya ce, “Yarinya ball aji ce yanzu, da Adda za ta ba ni dama da har Manchester sai na je na buga ball”. Adda ta yi tsaki, “Ku bana cikin shiririta, kada in kara jin wannan maganar, dukkan ku yara ne kuma karatu nake so ku yi, in ba za ka taimaka mata wajen ganin ta maida kai ga karatu ba, to kada in kara jin wannan maganar”. “Mun tuba Adda, mun bi Allah mun bi ki!”. In ji Muhsin. “Addah, don Allah mu tafi da ita?” In ji Aunty Nabeelah tana marairaicewa. “Ku je Allah ya kiyaye hanya. Amma don Allah Nabeelah ki kama girman ki, kada ki je ki yi halin yara na sanki sarai”. Murmushi mai ciwo ta yi, ta ce, “Insha Allahu Adda zumunci ne kawai zai kai mu”. Tuni na tsallake su na tafi na soma hada mana kaya. Aunty Nabeelah ta shigo ta tadda ni har na zuge jakar ta da tawa da ta Aasim. Ta ce, “Aiki ga mai kare ka…” Dariya na yi, na ce, “Don ba ki san yadda nake son zuwa Abuja ba ne Aunty Nabeelah, in ga Aunty Lubabatu mai gashi. Sosai nake son ta wallahi”. Aunty ta ce, “Wace ce haka?” “Matar Yaya Maccido mana!”. Tsaki ta yi, ta ce, “Allah ya shirye ki Ma’u”. Ba mu isa Abuja ba sai yamma lis, duk da cewa mun yi asubanci, kuma gudu sosai Muhsin yake yi. Gaba daya mun yi wujiga-wujiga. Aasim sai tsala kuka yake yi sabida gajiya da ciwon jiki. Muhsin ya dauke kan motar ya shiga unguwar Gwarimpa, gidajen su Yaya Maccido na daga farko-farkon unguwar. Bai tsaya ba sai a kofar apartment din wanda ke dauke da fenti ruwan madara da ruwan kasa. Kananan gidaje ne a cikin estate masu kyau da tsari. Kusa da Cadillac din Yaya Maccido Muhsin ya adana motar sa, sannan ya kashe. Gabadaya muka yi hamdala ta godiya ga Allah da ya nufe mu da isowa lafiya. Aunty ta ciro wayar ta a jaka saura kadan cajin wayar ya muta, ta kira lambar Yaya Maccido. Sai da ta yi ta burari tana sake kira ba tare da ta kosa ba, kamin ta samu ya daga wayar da sassanyar sallama a bakin sa. “Ga mu a kofar gida”. Kawai ta fada ba tare da ta amsa sallamar da ya yi mata ba. Ya ce, “Kofar wane gidan?” A gajarce ta ce, “Naka”. Ta kashe wayar tare da jefa ta cikin jakar hannunta. Muna ganin sanda aka zuge labulen falon aka tabbatar akwai bakuwar mota a kofar gidan, kafin entrance door din ta bude. Yaya Maccido ya fito sanye da jallabiyya fara kal mai gajeren hannu, kafarsa slippers ne mai kalar fari shi ma. Ido na kura wa Yaya Maccido, yana karasowa inda muke. Zuciyata na ji tana bugawa da sauri-sauri (at a speedy level) sakamakon ganin wata irin rama da baki da ya yi. A lokacin da ya iso gaban motar mu ba zan iya ci gaba da kallon shi ba, runtse idanuna na yi na sunkuyar da kaina ina tambayar kaina, wace irin rashin lafiya ya yi haka? Ita kanta Aunty Nabeelah jikin ta ya yi sanyi, ta yi saurin balle murfin motar ta fito ta rufe ta jingina jikin motar tare da harde hannayenta a kirji tana kallon shi yana doso ta. Muhsin ma ya fito, amma ni sai na gyara zamana ina kallonsu daya bayan daya. Ya iso gaban Nabeelah kamar za su hade don kusancin da ke tsakanin su, ya ce, “Baki haka unexpected?” Duk wani tanadi da Nabeelah ta yi na cin mutuncin Attahir ta neme shi ta rasa. Duk wasu muggan kalami da ta shirya fada masa sun subuce daga bakin ta. Kallon sa kawai ta ke kafin ta kai hannu ta dafa kafadar sa. “Maccido!” Ta fada a hankali. Dan murmushi ya yi kafin ya ce, “Nabeelah, ya ya za ku taso tun daga Sokoto amma ki kasa kira na ki fada min?” Ta lumshe idon ta a hankali ta ce, “Saboda ba ma so ka san za mu zo. It is a surprize visit”. Kama hannayenta biyu ya yi ya ce, "I appreciate. How is ADDAH?” Cikin raunin murya Nabeelah ta ce, “Do you still remember her? Ba ka neman ta ko a waya Maccido!” Maccido ya girgiza kai idanun sa sun kada, ya ce, “She is always in mind, na zama busy ne kwana biyu. Shekaran jiya muka dawo daga Egypt na kai Lubabatu ganin likita”. Aunty Nabeelah ta gyada kai, “Ya yi kyau, mu karasa ciki ko? Don a gajiye muke”. Juyawa ya yi kadan yana kallon falon nasa kamar mai tsoron ko ana kallon su, kafin ya ce, “Ku jira in sanar da matar gidan, bai kamata ta gan ku katsahan ba”. Ya juya da saurin sa, Nabeelah ta girgiza kai tana bin sa da kallon tsoro da mamaki, a ranta tana kakabin al’amarin nan mai kama da mafarki. To tsoron matar tasa ya ke yi ko me? Ta gaza fahimtar komai, wai Maccido ne wannan? Kanin ta vibrant and energetic? Gabadaya ya zabge kamar an zabtare shi, ya yi sanyi kamar ba shi ba. Muhsin kam ai bai jira an dawo daga yi masa ison ba ya bude booth ya fiddo jakunkunan mu ya cicciba ya yi gaba da su yana fadin, “Ma’u fito kin ji! In mun shiga ba izni a koro mu”. Na zunkuda goyona sannan na fito. Daga matar har mijin sai ganin mu suka yi mun murdo kofa muna shigowa, kowannen mu dauke da sallama a bakin sa. Cirko-cirko muka same su shi da Lubabatun kamar zakaru, da alama ko ma me suke cewa ba cikin dadin rai ba ne. Wani kallo ta yi mana kamar ta ga kashi, sannan ta juya ta yi masa kallon za mu gamu ne, ta yunkura da kyar da tirtsetsen cikinta ta bar falon zuwa dakin ta. Ko kallon Aunty Nabeelah dake shigowa bata tsaya yi ba. A rayuwar Attahir Atiku Dogondaji, bai taba jin ya muzanta a gaban Yayar shi da kannen shi irin yau ba. Ni dai ina daga gefe sai faman jijjiga Aasim da ke goye a baya na nake. An ce namiji har kullum namiji ne, shi ya sa Yaya Maccido ya sunkuya ya dauki jakar Aunty da tawa ya ce mu biyo shi, yayin da baby bag din Aasim ke hannuna. Wani daki ya bude a falon ya ce mu shigo. Daki ne mai tsananin kyau ya sha furnitures na alfarma da shimfidar gado mai laushi. Ya juya cikin jin nauyi ya ce da Aunty Nabeelah. “Zan je na kai Muhsin hotel na samo muku abin da za ku ci, babu dakin da zai iya sauka a nan”. Aunty ta ce, “A gaskiya ni bana cin abincin sayarwa sai wanda aka sarrafa a gida”. Ya jefar da kai gefe, ya ce, “To ba mu yi ba, ko ba kya ganin ta yi nauyi ne, yaushe za ta shiga kitchen ta yi muku wani girki a daren nab?” Aunty ta kyabe baki, ta ce, “ba matsala, in dai akwai kayan girkin, yanzun nan Ma’u za ta dafa mana”. Shi sai a lokacin ma ya lura da ni da ke gefe ina fama da baby. Ya dan dube ni na ‘yan sakanni a ran sa ya ce, “Ta yi tsawo, ta kara girma”. “Ba ki gaji ba za ki iya girki?” Ya fada yana kallon bangaren da nake. “Babu komai, zan iya”. Na bada amsa cikin girmamawa. “Okey, mu je in nuna miki komai”. Na mika wa Aunty Aasim, na bi bayan shi muka fita. Wani rantsattsen kitchen ya kai ni, komai tafiyayye kuma rantsattse, sai dai tsaftar kitchen din da sauki. Ya nuna min freezer da fridge ya ce, “Komai ki ke nema za ki samu”. Sannan ya bude wani labule da ya raba kitchen din biyu. Kayan abinci ne katan-katan da abincin gwangwani nau’i-nau’i, ya nuna min bangaren spices da maggi, sannan ya dago ya dube ni by mistake muka hada ido. “Ki dafa har da ni”. Kai na gyada, ya fita ya bar min madafin. Samun kaina na yi da bin bayan sa da kallo, wani irin kallo na tausayi da kaunar ‘yan uwantaka. Masculine turaren sa mai sanyi har zuwa lokacin bai bar kicin din ba. Ajiyar zuciya na yi bayan fitar sa, na dau madaidaiciyar tukunya na aza bisa wuta. A raina ina cewa, jallop din cous-cous zan yi da farfesun kifi kawai ya fi sauri. Na zo shigowa dakin don in tambayi Aunty ko zaben da na yi mana ya yi mata? Na ji tashin muryar ta a bakin kofa cikin bacin rai tana fadin. “Yanzu a matsayi na na Yayar ka uwa daya uba daya, tarbar da matar ka za ta yi min ke nan? Ta yi min kallon banza ta shige daki, to me na tare mata? Ko zuwana ne ya bata mata rai, ko kuwa ba ka gaya mata ko ni din wace ce dinka ba? In ba ta so a rabe ta kaima sai ta hana ka rabar kowa naka? Uwar da ta haife ka Maccido tunda ka yi aure ta daina ganin ka? No wonder na ga duk ka fige kamar kazar mayu, to ko dai ita mayya ce ta ke lashe ka ba ta so a ankara sai ta gama cinye ka tas? Ta kaiwa uwarka kasusuwan ka? Attahir let me tell you what you forgot… Addah ba ta da kowa sai mu, ba ta bukatar komai a wannan stage din na rayuwar ta sai mu da kulawar mu. Idan ka biye wa wannan annamimiyar wuta za ta kai ka billahillazee… Na gama fahimtar babu mutunci da imani cikin al’amarin ta. Bari ka ji in gaya maka, in ma asiri ta ke maka, ko tsoron ta ka ke ji da ka watsar da kowa naka ka kamata, to mu zuba mu da ita shege ka fasa! Ta zo gidan da ba a san asiri ba, amma an iya dungura goshi a yi sujjadah. Tunda ka zabe ta a kan mahaifiyar ka ka je mun yafe mata kai, amma zamu kai kara wajen Allah. Dadin abun ba kai kadai Adda ta haifa ba… Allah ya kai mu gobe za mu yi asubanci mu koma inda muka fito, in yaso ta yi gunduwa-gunduwa da kai ta sa a tukunya ta dafa ta cinye…”. Ta fashe da matsanancin kuka, wanda ya sa ni saurin ja da baya na koma kitchen gabana na faduwa. Ban taba jin Nabeelah na magana cikin zafin rai irin yau ba. Jikina har rawa ya ke yi in na tuna babban mutum irin Yaya Maccido take yi wa wannan fadan. **SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* 07030137870 * ~HISABIN NAFS~ ((5)). Har na gama girkin na dauko shi zuwa daki suna nan a yadda na bar su. Kai da ganin Yaya Maccido ka ga wanda damuwar duniya ta yi wa rubdugu. Yana zaune gaban Aunty kan sa a sunkuye. Ban san dai me ya ke gaya mata ba, amma na ga alamun ta sauko daga fushin ta sun koma magana ta fahimta. Ta ce, “To wannan bakin da ramar da ka ke yi na mene ne? Matar taka ba ta ba ka abinci ne ko mene ne?” Ganin shigwa ta ya sa bai ba ta amsa ba. Ta maido dubanta gare ni, ta ce. “Kawo abincin nan Asma’u”. Na karasa gabanta na ajiye katon tray din ta ce, “Sannu kin ji, Allah ya yi miki albarka”. Ta dau plate da serving spoon ta yi serving Yaya, ta loda masa abincin sosai ta tura masa, sannan ta zuba wa Muhsin, ni da ita kuma ta hada mana a faranti daya. Tunda Yaya Maccido ya soma cin abinci bai dago kansa ba. Kafin ka ce me ye wannan ya tashi da farantin. Aunty na kallonsa ta kasan ido cike da tausayi, ta ce. “Ko a kara maka?” Ya ce, “I’m okey, zuba dai in kai wa Lubabatu ita ma ba ta ci abincin dare ba”. Wani kallon banza Aunty ta yi masa, ta ce, “An hana, ba za a bayar ba, na karfi ne ku zo ku kwata”. Murmushi Maccido ya yi, wanda ke kara masa kyau a duk sanda ya yi shi, ya mike yana fadin. “Bari in bar ku ku huta, inda abin da ku ke so da babu a gidan ku fada da safe sai a sayo”. Suka fita shi da Muhsin, kowanne jiki ba kwari. Aunty ta dauka da safe Lubabatu za ta shigo ta gaishe ta, amma shiru ka ke ji ba ita ba karin kumallon mu. Shi ma maigidan ba mu gan shi ba. Bayan na yi wa Aasim wanka, na shirya shi ta ce in shiga madafi in sama mana abin da za mu ci. Ran Aunty Nabeelah a matukar bace yake, ban taba ganin ta cikin fushi haka ba. Na shiga kicin ina tunanin abin da zan sama mana mai dan sauki, na jona ruwan tea a kettle na debi dankali na soma ferewa. Ina cikin aikin na ji taku an nufo madafin. Kafin matar gidan ta bayyana cikin kwalliya ta kasaita, kamshin turaren ta duk ya bade kicin din. Ta yi min wani sakaren kallo ta ce. “Ke kuma wace ce haka za ki shigo min kitchen babu neman izni babu komai? Ko haka ake yi a kauyen ku?” Na sunkuyar da kai rike da dankali a hannu. Ta nuna min hanya, “Wuce ki ba ni waje gayyar na ayya kawai”. Ba musu na ajiye wuka da dankali na fice. Aunty na gyaran kayan mu lokacin da na shiga, ta daga ido ta dube ni, ta ce, “Har kin gama?” Kaina a kasa na ce, “Ta koro ni”. Kafin in rufe baki sai gata ta shigo daga bakin kofa ta tsaya tana taunar cingam rakakas! Rakakas! Ta ce da Aunty, “Sannun ku da zuwa, jiya kun zo ina jin barci, kuma zuwan naku ba notice”. Aunty ta daga ido tana kallon ta kawai”. Ta ce, “Mai aiki za ta zo yanzu sai ta dafa muku abincin, wannan yarinyar ta fiya gidadanci ko kunna gass ba ta iya ba”. Ba ta jira cewar Aunty Nabeelah ba, wadda ta daga kai a fusace zata mayar mata, amma nan da nan gargadin Adda ya shigo cikin kan ta, Lubabatu ta yi wucewar ta. Abinka da cikin jego, Aunty yunwa ta ke ji sosai, amma haka ta yi juriya. Yaya Maccido ya shigo ya sha wanka ya dauki walwali cikin shadda getzner. Da na kalle shi sau daya, ban kara marmarin maimaitawa ba, sakamakon cewa kwarjini, haiba da kamalar sa masu cika idanu ne. Ba kowacce mace ce zata iya jurar hada idanu da Maccido ba. Ko gama gaisawa da Aunty ba su yi ba, a gurguje ya ce, “Zan kai Lubabatu asibiti, wai tun jiya ba ta ji motsin baby ba”. Aunty ta hadiye malolon bacin ranta ta ce, “Hakan yana da kyau, sai kun dawo”. Sai bayan wajen awa daya da fitar su wajejen karfe goma na safe muka ji motsin ana share-share. Zuwa lokacin yunwa ta ci ta cinye mu. Har karfe sha daya na safe ba breakfast din da aka ce ‘yar aiki za ta zo ta ba mu. Yunwa ta ci mu ta cinye don mu a gida karfe takwas mun karya kumallo. Aunty na kwance tana bai wa Aasim nono, ni kuma na yi wanka ina shiryawa. Ta dau wayarta ta kira Muhsin. “Muhsin, kana ina ne?” Ya ce, “Aunty ina hotel din da Yaya ya kai ni, na shirya yanzu zan taho”. Ta ce, “To don Allah ka tsaya ka samar mana wani abu a hanya, har yanzu ba mu karya ba”. Bai tsaya bincike ba, ya ce, “To, in sha Allahu”. Muhsin ya iso mana da takeaway muka zauna muka ci mu duka uku. Shiru-shiru babu masu gidan har bayan azahar. Aunty ta ce da Muhsin ya tashi mu kama hanya, ita ba za ta kuma kwanan gidan Maccido ba. Muhsin ya yi ta tausar ta, ya ce, yanzu in mun tafi tafiyar dare za mu yi, ta yi hakuri goben da muka yi da Addah za mu koma mu yi asubanci mu kama hanya. Masu gidan ba su shigo ba sai karfe hudu na rana. Yaya Maccido rike da manyan ledoji, Lubabatu ta biyo bayansa ta kalli Aunty da murmushin keta ta ce, “Sannun ku fah!” Aunty ba ta amsa mata ba, ta ce, “Mun biya gidan friend dita ne daga asibitin, ina fatan Rose ta ba ku abinci?” Daga ni har Aunty babu wanda ya amsa ganin haka ya sa ta tura katon cikin ta ta yi gaba tana yi wa Yaya wani shu’umin kallo. “Dear ina jiran ka in kun gama, ka tausa min kafafun nan, ka ga duk sun kumbura”. Ta wuce ba tare da ta kara kallon kowa ba. Shi kuma kunyar Aunty ta hana shi amsawa. Ya ajiye ledojin hannun sa ya zauna kusa da ‘yar uwar sa, sannan ya janyo su ya soma bubbudewa. Sayayya ce ya yo mana har da ta banza, kowa ledar sa daban. Sannan ya mika wa Aunty ledar takeaway din gasassun kaji da fresh milk, ya ce, “Ku ci da hakuri, Lubabatu ta ce ba ta so Asma’u na shigar mata kitchen jiya ta lalata mata abubuwa”. Aunty ba ta san sanda ta kira sunansa da karfi. “Attahir!” Da sauri ya dube ta, ta ce, “Kicin din nata ya ci abu kazan-kazan uban sa! Ma’u ba faqiriya ba ce, ba ta kuma fito daga fatararren gida ba. Bar ganin dazu ta kira ta bagidajiya ta kuma kore ta daga kitchen na yi shiru, to ba tsoro ba ne, gudun magana ne, gidan ku kuma yanzu za mu bar muku shi ba sai anjima ba. Insha Allahu wani cikinmu bai sake takowa gidan ka Maccido, mun bar wa Lubabatu! Sannan ina mai shawartar ka da ka dage a kan ibadah, ka gyara ibadar ka. Akwai gyara a cikin mu’amalarka da Ubangijin ka. Wallahi Maccido ba kalau matar nan ta barka ba. Gidanka kuma yanzu za mu bar shi ba sai an jima ba, ko kai ka saura da wa Addah, daga yau ta yafe ka, mu uku mun ishe ta za mu yi mata komai. Sai dai ka kasance cikin kokonton hanyar shigar ka aljannah”. Aunty ta mike ta sunkuci Aasim tana hawaye. Muhsin ya ce, “Aunty don Allah ki yi hakuri da yau da goben duk daya ne, ki dauki abubuwa da sauki, abin duk bai kai ga haka ba”. Yaya Maccido kansa na kasa bai ce komai ba. Ya rasa abin da yake masa dadi, ya rasa me suke yi shi da Lubabatu wanda yake fusata Aunty haka. Shi bai ga laifin Lubabatu ba tunda gidan ta suka zo suka same ta babu sanarwa. Ya san Lubabatu ba ta karbar wasu baki in ba nata ba, ai ta yi kokari ma da karbar da ta yi musun, a dai halinta da ya sani. “Ku yi hakuri, abun bai kai haka ba, Lubabatu fa ta yi kokari da har ta bar ku kuka kwana gidan nan, ita bata karbar baki in ba ita ta gayyato su ba.”. Yaya Maccido ya fada cikin sanyin murya. Aunty zama ta yi a kasa tana kuka riris, fuskar ta cikin kafafun ta. Bayan ta dangwara min Aasim akan cinya ta. Tausayin Maccido kawai ta ke ji. Kafin a samu mutumin kirki mai son ‘yan uwan sa da karrama al'amarin su a baya irin Maccido abun mai wuya ne. Kafin a samu mutum mai kula da mahaifiya da tsantseni cikin mu’amalarsa da ita irin Attahir sai an yi sa’ar gaske. Rana daya daga yin aure ya zubar da duka wadannan halayen nasa. Mace ta canja shi, canjin da ta kasa ganewa. Jikin Maccido ya yi mugun sanyi, shi ma nasa idon suka cicciko da kwallah. Amma kokari ya ke ya maida su. Rokon Aunty ya soma yi a kan ta yi hakuri, idan ya bata mata rai, bai yi da gangan ba. Ba zan iya jure kallon wannan abun tausayi ba, babban mutum kaman Yaya Maccido na hawaye a gabana. Don haka na mike tsam na yi toilet dauke da Aasim ba tare da sun ankara da tashina ba. Zama na yi a gefen kwamin wanka ina hawaye ni ma rungume da yaron, na tausaya wa halin da suka samu kan su. Ban san yaya suka yi suka ciwo kan Aunty Nabeelah ta yarda sai gobe da asubah mu tafi ba. Sai da na tabbatar Yaya Maccido ya bar dakin sannan na fito. Muhsin ya bi ni da kallo har na samu gefen gado na zauna. “Ma’u na, Ma’un Addah, wa ya taba mun ke?” Ya yi maganar cikin raha irin tasa, amma ko kadan ba ta ba mu rahar ba ni da Aunty. Dole ya tashi ya bar mana dakin, Aunty Nabeela ta dauki wayar ta da ke tsuwwa suka canza harshe ita da Fa’iq din ta. Sai larabci suke zumbudawa abin ya yi matukar burge ni. Na ce a raina, ina ma ni ma in auri Balarabe irin mijin Nabeelah? Shi ba zai yi min gorin boko da ban iya ba! Ba zai damu ba don ban iya karatun boko ba. Duk da dai yanzu a Sokoto ba kamar Bebeji ba, ba laifi ina tsintar ‘yan abubuwa da ba za a rasa ba sabida koyarwar Muhsin da dagewar sa wajen ganin ba a yi min maimaicin aji ba. Sai ga Aunty na kyalkyatar dariya da mijin ta kamar ba ita ce ke kuka yanzu ba, yayin da ni kuma na shiga hidimar Aasim. Canza masa diaper na yi na hada masa madarar sa na dauke shi na soma ba shi. Bayan sallar isha Aunty ta ce in tattara mana komai namu tun yanzu kada mu makara da safe. Wajen karfe tara na dare Yaya Maccido ya shigo dakin, a yanzun kananan kaya ne a jikinsa shat da wando, samfurin Tommy Hilfiger ruwan bula mai haske da mai turuwa, duk da ya rame daga yadda yake a baya kyansa yana nan bai je ko’ina ba, sannan daukan wankan sa sai abin da ya yi gaba. Ya dube ni ina jijjiga Aasim, ya ce, “Ke kullum ba kya zama ne sai da yaro a hannun ki? Ki bar mata dan ta mana ko tare ku ka haife shi?” Aunty Nabeelah ta galla masa harara, ta ce, “Ai ita ta san darajar na gaba da ita, ta kuma san nata shi ne nata. Hidimar da ta ke da dan uwanta ba zai gajiyar da ita ba”. Murmushi ya yi ya zauna dab da ita, don ya san magana ta gaya masa, duk dakin ya amshi bakuncin turaren sa obsession (by CK). Har wani lumshe ido na yi don dadin turaren Yaya. Ya san Aunty Nabeelah bakar magana ta gaya masa, ya rasa laifin da ya yi mai zafi da yake fusata ta haka. Iyakar iyawar sa ya ba ta hakuri dazu kuma ya amsa laifin da take tuhumar sa da shi na watsar da Addah, ya mata alkawarin zai zo ya ga Addah, ya ba ta hakurin rashin zuwan sa da rashin kiran ta, shima ya rasa abinda ya ke hana shi shiga Sokoto, ji yake kamar bazai gane hanyar garin ba, ya fada mata sau da dama ya sha kama hanya amma sai kawai ya ji shi ya karya kan mota ya dawo gida, ya bata hakuri yadda ya kamata amma duk bayan dakika Aunty Nabeelah sake sabunta laifinsa take ya koma sabo fil! Ta lura shi sam ba ya ganin girman abin da ya yi, ya yi admitting ya yi laifin ne ganin bacin ranta mai tsanani, ban da haka ai ya san Adda lafiya ta ke tunda yana gaishe ta a waya, ta san kuma irin commitments dinsa. Ko ita Addar ba ta korafi sai ita sarkin fushi da fushin wani. Ya dube ni kadan, “Ki je ki dafa mana wani abun mu ci, matar gidan ta jima da yin barci, ba zata san kin shiga kitchen din ba, but be careful kada ki bata mata wani abun ta gane kin shiga”. Wani bala'in haushi ya kama Aunty, ta ce, “Ba za ta dafa ba, na ce ba za ta dafa ba din balle ku ce ta lalata muku cooker gass, ko ku ce mata bagidajiya. Ka je ka ci gaba da ci a inda ka saba ci kafin mu zo, na tabbata matar nan azabtar da kai take da yunwa ko makaho ya shafa ka ya san wannan, mu da abincin gidan ka haihata-haihata Maccido. Wanda muka ci ma Allah ya amfana”. Ya jefar da kai gefe zara-zaran gassun idonsa na lumshewa, ya ce. “Wai Yaya Nabeelah me ya sa duk kin bi kin tsane ni yanzu? A baya ba mai so na irin Yayata Nabeelah, ba wanda ya isa ya taba mata ni. Amma tunda ki ka zo ban samu tattausar kalma ko daya daga bakin ki ba, a haka ki ke so mu rabu ki koma inda sai na shekara ban gan ki ba?” Zuciyar Nabeelah ta dan sassauta, kalaman bakin sa sun bata tausayi, kowa ya san Tahir is her favourite brother, so ta ke ta fahimtar da shi kuren sa ya kuma fahimci wannan matar da ya aura ba alkhairi ba ce a gare shi, amma ya ki ya gane inda ta dosa. Kwata-kwata baya ganin laifin matar nan tasa, ko aibun ta. Ba kuma za ta fito fili ta fada ba, Adda ta hane ta da tada tarzoma. Saboda Allah a matsayin ta na Yayar mijin ta uwa daya uba daya ba kanwar sa ba, wadda ba ta taba zuwa gidan ba ko sau daya, ta cananci irin tarbar da ta yi mata? Ko sau daya ba ta bata abinci ba, sau daya ta zo ta gaishe ta daga bakin kofa ta gaya ma Ma’u magana, ba su kara ganin ta ba. Babban bacin ran Aunty Nabeelah irin rayuwar da ta fahimci ana yi a gidan, ko abinci ba'a ba shi, matar gidan ce master, shi subordinate. Amma ko a jikin sa. *TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE & TAKORITES* *SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI (07030137870)* ((6))Ta sauke numfashi a hankali, yanzun a cikin kallon da ta ke yi masa akwai sassauci da kauna. “Attahir!”. Ta kirayi sunansa a hankali. Ya dago kyawawan idanunsa ya dube ta. “Me ya sa ka wannan ramar?” Dan murmushi ya yi, ya ce, “Yanayin aikin mu ne kawai da ba hutu”. Ba tare da ta yarda ba, ta ce, “Addah yaushe za ka je ka ganta?” “Insha Allah idan Lubabatu ta haihu, zuwa next month za ta shiga EDD dinta, za mu taho gabadaya”. “Allah ya raba lafiya”. Ya amsa da, “Ameen”. Hannu ya sa a aljihunsa ya zaro bandiran kudi har guda hudu ya dora ma Aunty bisa cinyar ta. “Ga shi ku sha mai, wannan yarinyar a saya mata wani abu kada Adda ta ce ban ba ta komai ba”. Aunty ta ce, “Sunanta ASMA’U ba wannan yarinyar ba. Ta gode”. Sallamar mu da Yaya Maccido ke nan. Bayan ya koma dakin barcin su da kamar mintuna talatin Aunty tace inje in dauko mata kofi a kitchen din zata sha magani. A hankali na bude kofa na fita ina taku cikin sanda kada su ga na shigar musu kitchen, na dauko kofin na dawo zan wuce ta kofar dakin da suke naji tashin muryar Yaya, kamar an ce da ni in tsaya.... kawai na tsaya jin yana magana kamar zai yi kuka. "Amma Lubabatu kina tsoron gamuwar ki da Allah kuwa? Tun shekaranjiya nake bin ki akan ki bani hakki na kina wulakanta ni, kawai saboda 'yan uwa na sun zo gidan ki, ke su waye ba kya kawowa daga gidan ku na taba nuna miki bacin rai ko bakin halin da kike nuna min? Kinsan dai bani da kamar su duk fadin duniya dole su zo inda nake. Lubabatu in ban zo wajen ki ba matan titi kike so inje in nema? Kin san dai ina jure komai cikin tarin wulakancin ki, amma banda wannan horon naki.... Don Allah Lubabatu ki min rai...zan iya mutuwa kafin safe....". Ji nayi ya karasa maganar muryar sa na rawa. Yana rufe baki ta bishi da mugun tsaki. "Ai na gaya maka this is your punishment, gobe ka sake basu fuskar zuwar mana gida, wannan Nabilar mai idanun munafurci a cikin idon ta na gane bata kauna ta. To sai dai ta mutu amma bata isa ta fidda ni daga gidana ba don ni wargi ce daidai kungurun kowa, wallahi ta dade bata zo ganin kwaf gida na ba......". "Duk na ji Sweetheart, mun yi miki laifi nida 'yan uwa na, but pls don't punish me that way......Bani da wannan juriyar kin sani.....". Da dan banzan sauri na daga kafa na bar wajen zuwa dakin mu, jiki na babu inda ba ya rawa, ban san me yake rokon ta yi masa ba amma na san bai kamata ba tsayawar da na yi. Kwana na yi da abun a raina, yana ci min rai, ashe Yaya Maccido duk kwarjinin nan nasa a cikin gida kwallo ake da shi kamar ball ko gare-gare abin wasan yara? Sai na samu kaina da mugun jin haushin Lubabatu, don ta samu Allah ya bata miji kamar Maccido shine take wulakanta shi? To ita meye matsalar ta da 'yan uwan sa ne? Me muka tare mata??? Bani da wanda zan gayawa abinda na ji ba tare da yayi min fada ba, don haka na bar abun a raina amma ya kasa bace min a zuci. Washegari ba mu sa Lubabatu a idon mu ba har muka shiga mota, Yaya kam tunda ya dawo masallaci bai koma nasu dakin ba yana tare da mu har muka shiga mota. Kamar ba za su rabu ba shi da ‘yan uwan sa, haka Muhsin ya ja motar ya bar Yaya with nostalgia (begen gida). Tunda muka kamo hanya Aunty da Muhsin ke tattaunawa a kan abin da suka gano gidan dan uwan nasu. Ina ji suna shawarwarin abin da za su fada wa Adda da wanda ba za su fada mata ba. Tunda aka fita garin Abuja barci ya yi awon gaba da ni. Ba ni na farka ba, sai da muka shiga Kaduna. Mun wuni sur! A kan hanya, sallah kadai ke tsaida mu. Sai kuma in mun samu gidan cin abinci mai kyau mu tsaya mu saya. Har Allah ya kawo mu gida Sokoto lafiya. *** *** *** Allah sarki Adda! Murnar da ta yi na dawowarmu lafiya tana da yawa. Bayan kwana uku muka shirya muka raka Aunty Nabeelah Dogondaji wajen dangin mahaifin su, ba mu kwana ba a ranar muka dawo, Aunty Nabeelah ta soma shirin koma wa Beirut. Ana gobe za su tafi na sha kuka sabida Aasim, Aunty tana ta tsonakata wai ya kamata Addah ta yi min aure in je in haifo mata yaro mu yi ta raino. Addah ta ce, “Mai auren Ma’u ai sai ya shirya, don da sisin gwal za a biya ni sadakinta”. Washegari Aunty ta koma Lebanon. Ranar wata lahadi na dawo Tahfiz na ga wata bakuwar tsaleliyar mota a kofar gidan mu. Sai sheki da daukar ido take yi. Wannan ya tabbatar min baki ne muka yi. Ban bi ta falo ba ta kofar kicin na bi zuwa daki na na cire hijab na canza kayan jiki na daga uniform zuwa na gida, na kishingida ina hutawa kafin lokacin sallar magriba ya yi. Kukan jariri na ji duk ya cika gidan, ba shiri na zabura na fito don tantance daga inda nake jin kukan. A daidai kofar shiga falon muka gabza karo saura kadan na fadi, na yi saurin kama marikin kofa. A hankali na cira kai don ganin da wa na gabza karo, idanuna suka sauka a kan Yaya Maccido. Yana sanye da wata danyar shadda milk colour wadda aka yi wa aiki da zare ruwan kasa turarre, kansa da hula ita ma ruwan kasar ce. Ba laifi wanan karon ya dan yi haske, amma ramar sa tana nan, kuma kyawun halittar sa koyaushe kamar karuwa yake. Kallon sa na tsaya yi na kasa cewa komai. It’s exactly one year rabon sa da gidan nan, don haka zuwan na shi ya dan sa ni a kokonton anya shi ne? Tsaki ya yi ya wuce yana fadin, “Be careful in kina tafiya mana!”. Wani irin lumshe ido na yi wanda ban san lokacin da na yi shi ba. Kamshin turaren Yaya Maccido da nake matukar so har cikin tsokar zuciyata. Ina nan tsaye na kasa tabuka komai, Addah ta fito za ta wuce ta same ni a wurin a tsaye. “Me ki ke yi tsaye a bakin kofa? Ki shiga mana? Kin yi ‘ya, tun dazu suka sauka”. “Adda, waye ya haihu?” Ta ce, “Lubabatu”. Da hanzari na na fada falon Adda, ido na ya sauka a kan Aunty Lubabatu rungume da jaririyar ta. Ta sha kwalliya kamar wata matar gwamna ba matar Maccido ba. Tana gani na ta sha bula. Na karasa da farin ciki na ina fadin. “Aunty sannun ku da zuwa, ba ni babyn in gan ta”. Kamar ba za ta bayar ba, sai kuma ga Yaya Maccido ya sako kai falon, sai ta miko min ita. Na zauna a gefe rike da cute jaririyar ina ta kallon ta. Tsabar farin ciki na manta cewa Yaya Maccido ba abokin hira ta ba ne, amma ban san sanda na ce, “Wallahi Yaya da kai baby ta ke kama, komai da komai”. Zan iya cewa, wannan ne karo na farko da Yaya Maccido ya yi min murmushi a duniya, tare da cewa, “Ni kuma tun sanda aka haife ta da ke ta ke yi min kama, musamman hancin ku”. Na washe baki, dadi kashe ni!. Aunty lubabatu ta balla min harara, shi ma ta balla masa tasa, ta ce, “Allah ya sauwake. Ni ‘ya ta ba ta kama da kowa daga uwar ta sai uban ta”. Fuskar Yaya Maccido ta muzanta da kalaman Lubabatu, amma bai ce komai ba, ni kuma uwar ‘yan kankanba na mike zan tafi da baby daki na. Da sauri Aunty Lubabatu ta ce, “Kawo ta…”. Yaya ya dago kai daga kan wayar sa ya dan dube ni, ya ce, “Je ki da ita, in ta yi kuka kya kawo ta…”. Ai kafin ya rufe baki na yi waje, rungume da baby, ina ji Yaya na fadin. “Wannan abin da ki ke yi Lubabatu ba daidai ba ne. Kanwata ce fa!” Duk da ban kalle ta ba na san gatsine da kyabe bakin da na lura tun zuwan mu gidan ta dabi’ar ta ce ta yi. Ta ce, “Ai fa na ga Muhsin ne ya sha nono ya sakar mata. Ni irin wadannan jajibe-jajiben dangin bana yarda da su. Gara ma ka canza mata suna daga kanwar ka zuwa dangin-dangaro". Da sauri na karasa ficewa ban san amsar da Yaya Maccido ya ba ta ba. Na wuce ta kicin inda Addah ta tsaya tare da Hawwa mai aikinta suna hada wa su Yaya abinci. Adda ta dube ni ta ce, “Taufa! An yi ‘ya yau raino sai inda mai ya kare”. Dariya na yi na wuce zuwa daki na ina ta lelen ‘ya ta. Ji nake kamar ni na haife ta. Kuma wani ikon Allah sama da wajen awanni biyu ba ta yi min kuka ba sai baccinta ta ke a gado na. Kafin uwar ta ta biyo sawunta ta amshe abar ta wai za ta ba ta nono. A bakin Adda na ji sunan yarinyar Ihsan. An ce tsakanin Da da mahaifi sai Allah, wannan haka yake, duk laifin nan da Yaya Maccido ya yi wa Addah farin cikin ganinsa da na haihuwar Ihsan ya shafe komai. Sai nan-nan ta ke da su, ta ce min sati biyu za su yi. Ni da Hawwa ne muka je muka gyara ko’ina na sassan Yaya Maccido muka shigar musu da kayan su da duk abin da za su bukata. A zaman nan nasu na sati biyu na aikatu sosai da hidimar abincin su da rainon Ihsan. Uwar ta na yakice ni, tana min kora da hali, tana nesan ta ni da ‘yar ta, amma ni din kamar mayya na like wa Ihsan. Ko ba komai yarinyar jini na ce, kuma son yara a jini na yake, shi ya sa sam bana damuwa da wulakancin Lubabatu, har wankin kayan Ihsan ni nake yi in shanya, in sun bushe in kwashe in shigar mata da su. Canza mata diaper akai-akai da yawan ba ta ruwan zam-zam da Adda ta ce a dinga ba ta, duk da uwar ta bata so a bata ruwa.. Suna gama sati biyun su suka hada inasu-inasu suka koma Abuja. Dama kamar akan kaya suke. Gidan mu ya koma yadda yake, don kewar yarinyar komawa na yi kamar an yi min mutuwa. Muhsin ya yi ta tsokana ta, wai in rabu da Adda mu yi auren mu, mu haifo namu a daina yi mana kwalele da ‘ya’yan mutane. Na ci gaba da zuwa makaranta da Tahfiz da yamma. Daga aji biyar Muhsin ya bar sakandire, ya zana Waec da jamb, kuma cikin ikon Allah ya haye. Ya samu gurbin karatu a jami’ar DanFodiyo inda zai yi nazarin tsimi da tanadi (Economics). Ni kuma a sannan na shiga aji shidda da kyar da sudin ludayi. A wannan lokacin makerin budurci ya gama kera ni. Na zama budurwa sosai, amma ba ni da cika ido, ga ni nan ‘yar daidai, komai nawa ya yi daidai da inda Ubangiji ya halicce shi. Ni kaina na san babu ni a jerin kyawawan mata, amma ina kokarin gyara kaina irin na ‘yammatan da suka san ciwon kan su. Addah kan ce, kwarai na ke da tsafta kamar Nabeelah, kuma kamanni na da Nene yanzu sun fi na baya fitowa sosai. Tun zuwan su Yaya Maccido lokacin haihuwar Ihsan da komawar su ba mu kara jin duriyar su ba. Adda na lissafe da watanni daidai har guda goma sha biyar. Da farko yana kokarin kiran waya lokaci-lokaci ya gaishe ta har ya kanga mata gwalantun Ihsan a wayar, amma daga baya wayar ma ta gagara. Lubabatu kuwa ba ta taba kiran Addah ba ko don gaisuwa tun auren ta da Yaya. A yadda take-taken ta ya nuna shi ne, ita irin matan nan ce wadanda in sun auri namiji shi kadai suka aura. Ba ruwan su da kowa nasa including wadanda suka yi silar zuwan shi duniya. Amma duk da haka yana kula da MACCIDO MALL daga can inda yake, lokacin da Muhsin ya samu gurbin karatu a Danfodiyo abubuwan za su yi masa yawa, don haka ya nemi Yayan da ya nemo masa mataimaki amintacce, wanda zai iya handling dukkan ayyukansa na manager. Akwai wani abokin yaya da suka yi karatun sakandire tare da ya biyo ta hannunsa yana so Yayan ya samar masa aiki tun da jimawa. A wannan lokacin sai ya nemo shi. Bayan dogon bincike da amincewa juna dukkanin su, ya yarda zai zama mataimakin Muhsin. Al-Qasim Ka’oje ke nan, wanda shigowarsa cikin harkar mall ba mall din kadai ya taimakawa ba. A sannu ya shiga ran Addah sabida hankalin sa da nutsuwar sa. Ga shi da biyayya kamar ita ta haife shi, sai ya shigo sosai cikin harkokin gidan mu yake taimakawa ta kowanne fanni, sannan ya zama tamkar wakilin Yaya Maccido wajen harkokin cikin gida, da kula da gidan don Muhsin yanzu ta kansa yake a jami'a. Shi Al-qasim yana yawan kiran Yaya Maccido su yi magana, ba ya jira sai Yayan ya neme shi, duk abin da ake ciki a kan harkar kasuwancin da abin da Adda ke bukata yana kokari ya ga ya sanar da shi tunda ganin sa yanzu ya gagare mu. Al-qasim shi yake kai Adda asibiti yanzu sakamakon ciwon sugar da hawan jini da ya same ta rana daya. Yawanci in zai kai ta ganin likita da safe suke zuwa, lokacin ni ina makaranta. Har cefanen wata na gidan Al-Qasim ke yo wa, wataran a aljihunsa yake sayo abubuwa ya kawo, musamman fruits, mutum ne shi mai yawan ALHERI sosai, ga shi da ilmi don Muhsin ya ce min masters gare shi, kuma a yanzu haka yana karatu part-time na PhD dinsa a Open University. Tun shigowar Al-Qasim al’amuran gidanmu abubuwa da yawa suka gyaru mana, matsaloli da yawa suka kau. Addah kullum ce min ta ke, “Na yi dan da ya maye min gurbin Maccido!”. Ni haka kawai ban cika sakewa ba idan yana gidan. Ya cika kallo, ni kuma bana son kallo. Daga baya na lura ni kadai yake yawaita kallon. Wannan abu na matukar kular da ni, a kan me zai maida ni dubarudu ba dama in zauna sai ya debi lunkuma-lunkuman idanun sa ya yi ta lafta mini yana maida ni unease? Rannan na yi wa Adda korafi. “Wannan dan naki ya cika kallo wallahi”. Adda sai cewa ta yi, “Ke da wane idon ki ka kalle shi, har ki ka san ya cika kallo?” Yau bayan ya tashi daga mall ya zo gidan kamar yadda ya saba da manyan ledoji a hannun sa, ya yi sallama ya shigo falon, daga ni sai Adda muna kallon talabijin. Addah ce ta amsa, ni kam a zuci na amsa. Na kalle shi sau daya na dauke kai, a raina ina fadin, “Ga fa duba-rudu ya iso”. *TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES* https://www.arewabooks.com/book?id=6329c8029b3e7782f077921d YIWA KAI HISABI Har gaban Adda ya karasa ya tsugunna ya gaishe ta, sannan ya aje mata ledojin da ya shigo da su masu tambarin ‘Maccido mall’, kayan amfanin gida ne da ya kan debo mata a shagon su da toiletries da abincin gwangwani iri-iri. ‘Yar karamar ledar da ta rage a hannun sa ya iso gare ni ya aza min bisa handle din kujerar da nake zaune, “Autar Adda ga tsaraba na yo miki daga mall”. Dauka na yi na bude babu ko an gode, sabida yadda yake ba ni haushi da kallon sa, amma ganin choculates ‘yan uban-ubansu masu tsada ban san sanda bakina ya bude ya yi godiyar ba. Na fiddo mars da kit-kat na bude na gutsira kunnena har motsi yake. Adda ta ce, “Ki dai sha kadan, kin san lokacin watan ki ya kusa, kada ki zo kina min murkususun nan naki”. Wata kunya ta kama ni, na saci kallon Al-Qasim, sai na ga bai ma gane zancen da Addah ke yi din ba. Zama ya yi bisa centre carpet daga gefen Addah yana yi mata bayanin ribar da ake ta samu a wannan shekarar. Rannan kafin ya shiga mall ya zo gidan da sassafe yana sauri, bayan sun gaisa da Addah ya tambaye ta, ko na tashi daga barci? Addah ta ce, bari ta dubo ni. Ta same ni tashina ke nan ina shirin shiga wanka, ta ce, “Ma’u zo mana, Al-Qasim yana nemanki”. Na zumburo baki, “Duba-Rudu za ki ce Addah!”. Dakuwa ta yi min, “Ungo naki, bana son raini wa na gaba. Kada in kara ji kin ce masa Dubarudun nan, ke da wane idanun ki ke dubansa har ki ka san yana duban naki?” Sake zumburo baki na yi, na daura zani bisa rigar barci na na dora hijabin sallah ta na bi bayan Addah. Yana tsaye tsakiyar falon rike da kwamfutar kan cinya (laptop) a kunne. Ya yi kwalliyar sa tsaf yadda ya saba. A perfect gentleman. Ina fitowa ya tako zuwa gare ni da saurin sa muka game a tsakiyar falon. Ya ce, “Yauwa kanwata, kin fito?” Na gyada kai. Ya sake matsowa da laptop din. “Wani dan taimako za ki yi min, ai kin iya microsoft excel ko?” Cikin jin kunyar kada in bada kaina in na ce ban iya ba, ban ma san mece ce ita din ba, na gyada masa kai kawai. “Yauwa! Please Master ya kira ni Abuja yanzun nan (Yaya Maccido), ga shi ina da muhimman bayanan da ban shigar cikin kwamfuta ba. Ga su a rubuce bisa sheet din nan don Allah daga yanzu zuwa dare ki shasshigar min”. Ya miko min takardun da kwamfutar. Ban yi kasa a gwiwa ba na karba. Ya yi min murmushi tare da godiya. Ya ce, “Me zan kawo miki?” Na ce, “Babu komai, ka gaida min Ihsan kawai”. “Za ta ji, insha Allah”. Da haka ya yi mana sallama ya tafi. Na koma daki na aje (laptop) bisa gado na na zuba mata ido ita da takardun. Kwata-kwata ba abin da na fahimta. Wannan shi ne karshen tozarci idan Al-Qasim saurayin da ke ji da kansa ya fahimci zero nake a boko. Duk kidifirin da na ke masa ai dariya zai koma yi min tunda (empty-head) gare ni. Wasu hawaye suka ciko idanu na, na ce bari in yi wanka in zo in jagwalgwala abin da ya sauwaka, da babu gara ba dadi. Bayan na yi wanka doguwar riga kawai na saka na zo na dinga danne-danne a kwamfuta, shiga nan fita can ban san sunan komai ba, ko abin da nake yi daidai ne ko ba daidai ne ba. Har azahar ina abu daya. Sai da Addah ta turo Hauwa ta gaya min ga Nabeelah a waya, sannan na rufe kwamfutar ba tare da na yi switching off ba, sai da cajin ta ya kare ta kashe kanta. Sai da Al-Qasim ya yi kwana biyu a Abuja sannan ya dawo, don shi ne ke kula da sabon ginin wani mall din ko ko Plaza da Yaya Maccido ke yi a Abuja. Wanda ba shi da maraba da na Sokoto a komai.. Da daddare ya zo gidan suka gaisa da Addah. Tunda na ganshi gabana ya fadi don tunda na aje kwamfutar sa ban kara bi ta kanta ba, ko dan caji ban sa mata ba. Ya dube ni da murmushi, ya ce, “Ihsan na gaishe ki tayi ba ki masha Allah ga shi tana gudun ta ko’ina”. Na yi murmushi sosai, na ce, “Oh my daughter”. Ya ce, “Maza a dauko min aikin da na sa ki, Master na jira in tura masa yanzu”. Ba musu na mike kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, na dauko kayan sa na kawo masa. Ya karba yana shirin kunnawa ya ce, “Ya? Babu caji ne?” Na ce, “Ban saka ba”. Na fuske abuna, don ma kada ya kara yi min wata tambayar. Da kansa ya tashi ya je ya jona ya bata lokaci ta kama sannan ya kunna. A hankali yake duba abubuwa da aikin da ya sa ni Nana Asma’u in yi masa. Duk wasu muhimman applications masu dauke da bayanai masu muhimmanci na goge masa su. Da ya shiga excel don ganin aikin da ya sa ni sai ya tarar na cika raws din da sunana Asma’u Adam Bebeji da kuma ABCDEFG. Mamaki, takaici, tu’ajjibi suka taru suka lullube Al-Qasim Ka'oje. Me hakan ke nufi? Ba ta iya ba ko shakiyanci ne ta jaza mai asara haka? Amma ai ‘yar makaranta ce, ajin karshe a sakandire, makarantar ma mai aji da mukami, ko last week shi Adda ta tura ya biya (school-fees) dinta kudi na gugar wuri masu yawa. Kada dai a ce asarar kudin tara ake yi a kan Asma'u? Amma da yake mai ilmi ne bai nuna komai a fuskar sa ba. Ya dauko murmushin karfin hali ya dora wa kyakkyawar fuskar sa. “Ma’un Adda, na ga aiki ya yi kyau fa na gode”. Na saki baki ina kallonsa, “ABCD fa na rubuta maka. Ni ma su kadai na iya, shi ya sa na rubuta maka su sai kuma sunana”. Adda ta rage sautin talabijin ta bada attention dinta ga hirar mu. “Al-Qasim wai me ye?” Ya ce, “Adda aiki na bai wa Ma’un ki ta taya ni, sabida Master ya kira ni Abuja da sauri, shi ne aka rubuta min Asma’u Bebeji maimakon aikin nawa, aka kuma yi min ciko da ABCD aka ba ni alakoro da goge min duk wasu muhimman bayanai da ke cikin kwamfuta”. Adda ta juya tana sakin dariya. Dariyar da ta kular da ni na tashi na bar musu falon. Sai da Adda ta yi dariyar ta ma'ishi sannan ta ce, “Wa ya aike ka? Kuma ba ka tambaya ta iya ko ba ta iya ba kawai sai ka ba ta?” Ya langwabar da kai cike da takaici, ya ce, “Sai da na fara tambayar ta fa ta ce ta iya”. Adda ta sake yin dariya ta ce, “Ma’u da ka ke ganinta kanta babu komai na karatun boko. Tunda aka haife ta haka take, sunan zuwa makarantar ta "jeka-na-yi-ka". Ina tsammanin daga sakandire ta gama shiga aji don ba za ta iya karatun jami’a ba”. Maganar ta doki Al-Qasim sosai, domin kuwa shi so na yake, so na hakika. Wanda yake fatan ya kai mu ga siradin aure ya samu tsatso daga gare ni. In haka ne to me zan koya wa ‘ya’yan sa idan yayi kasadar aure na? Ya dubi Adda fuskar sa dauke da tausayi da soyayyar Asma’u. Ya ce, “Akwai abin yi akai Adda, ba haka za'a kyale ta ba. Ni na san irin matsalar ta. Tana da Learning Disability, tana bukatar koyarwa ta musamman (Special Education). Insha Allahu Ma’u za ta yi karatu kamar kowa har matsayin da ya fi degree sai ta taka”. Ba karamin jin dadin kalaman sa kan Ma’un ta Adda ta yi ba. Rana ta farko da wani ya taba ba ta ‘hope’ kan karatun Ma’u. malamanta cewa suke, jaka ce, wasa ne kawai a kanta. A daren ya kira Master dinsa (Yaya Maccido). Rana ta farko da ya taba yi masa magana a kan kanwar sa Ma’u. Maccido ya tuna Adda ta taba yi masa magana kwatankwacin wannan a kan Asma’un. Ya bada shawarwarin da yake ganin in an bi za'a taimaka mata ta rubuta WAEC wannan shekarar ta shiga jami’a. Yaya Maccido ya dora alhakin komai a wuyan sa ya ce, a ciri kudi ko nawa ne a dauki nauyin karatun nata. Zuwa wannan lokacin Addah ta dangana a kan Maccido, ta yarda ta haifi Maccido ne, amma Lubabatu ta haifamawa. Tsakanin ta da shi sai aiken kudi wanda ita ba ta bukata sam. Abinda ta ke samu a kason ta na mall har ya fi karfin bukatun ta. Nabeelah dai ta ce, ta dage da addu’a akwai abin da ya juyar da kwakwalwar Maccido daga kansu. Al-Qasim ya sanar da Addah shawarar da suka yi da Maccido na daukarwa Ma’u malami na musamman wanda ya yi specializing a kan learning disability zai fara karantar da ita watanni shidda kafin su zana waec. Ba karamin dadi Adda ta ji ba da wannan gudunmuwa ta Al-Qasim ga Ma’u. Ta yanar gizo Al-Qasim ya sa cigiyar Malamin Ma’u. Cikin watanni biyu aka samu, amma daga jami’ar Danfodiyo zai je kullum wajen Ma’un. Sai da suka gama komai Maccido ya dunkule albashin sa na duka watanni shiddan da zai yi yana koyar da Ma’u ya ba wa Al-Qasim ya ba shi. A ka sa ranar da zai fara zuwa. A harabar gidan nan ma’adanar motoci akwai rumfa a nan za mu dinga zama. Al-Qasim ya sayo blackboard, duster da marker wa malamin. Sai da aka gama komai Addah ta zaunar da ni ta yi min bayani yadda zan fahimta. Ina wuta in jefa Al-Qasim?! Lallai ya cika Duba-Rudu, wato har kwakwalwar tawa sai da ya sa madubin Duba-Rudunsa ya hango maganin ta. Ni ina ruwana da shi? Me ya yi ruwansa da harkata? Da haka kawai zai zo ya sa a takura min? Zama na yi gaban Adda ina share hawayen abin nan da Al-Qasim yayi min, Addah tana lallashi na tare da fadin Al-Qasim alheri yake nufi na da shi. Rana ta farko da Malamin ya zo an kai ruwa rana kafin in yarda in fita. Amma a rana ta biyu, ni da kaina na fita babu bacin rai. Wannan ya samo asali ne sabida hanyar da Malamin ke bi wajen koyar da ni (so much persuasive, caring with endurance). Cikin sati daya sai ga ni ina bai wa Addah da Muhsin labarin Malam Sa’ad ba a taba malami mashahuri irin shi a duniya ba. Muhsin ya yi dariya ya ce, “Ai daga yau mun daina Hausa a gidannan, turancewa kawai za mu rika yi ni da Ma’una”. Da taimakon Malam Sa’ad, da bada karfin gwiwar dan uwana Muhsin, tare da jajircewar Al-Qasim Ka’oje, na fara fahimtar ilmin boko tare da ganewa ashe shi din abu ne mai sauki, kallon tsoro nake masa. Ko wata daya ba a cika ba turanci mai kyau ya soma zama a bakina. ****** BAYAN WATANNI SHIDDA Bayan watanni shidda na zana waec, neco da jamb da taimakon Malam Sa’ad ta karkashin kasa. To sai dai ko da sakamako ya fito ban ci jamb din ba, ita ma waec din credit hudu na samu. Duka gidan babu wanda bai jinjina min ba tare da tabbatar min da cewa, na yi abin kirki, na yi kokari kada in bari gwiwa ta ta sage. In bari shekara mai zuwa in sake maimaitawa. Al-Qasim kuma ya ce, kafin zagayowar shekarar za mu ci gaba da karatu da Malam Sa’ad, kuma zai dinga koyar da ni ilmin na’ura mai kwakwalwa. Ya sayo dankareriyar kwamfutar kan cinya laptop ya kawo min matsayin gudunmuwar sa. Zuwa wannan lokacin kowa ya gama fahimtar inda Al-Qasim ya sa gaba a kaina. Ni din ce dai ban taba sanya wa raina komai ba, na dauka yana hidima da ni ne kawai a matsayin aikin sa da yake karbar albashi a kai kamar yadda ya ke kula da komai na gidan. Domin zuwa yanzu ya zama personal assistant din Yaya Maccido, wanda duniya ta gama bude wa kofofin arziki ko ta ina. Ya zama babban director a Julius Berger, ya dade da barin gidan sa na Gwarimpa ya gina wani a Apo. Sun koma shi da gimbiyar tasa da ‘yar su wadda aka ce ta kusan haihuwar cikinta na biyu. Duniya ta yi mata yadda ta ke so, komai ya yi acan-acan. Maccido ya zama nata ita kadai, daga ita sai ‘ya’yan da ta ke zubo masa. Na san a rayuwa in Adda na da damuwa, to ta Maccido ce, wanda ya cire ta daga kan hanyarsa. Tsakanin ta da shi gaisuwa a waya sai kuma in ya bushi iska ya leko bayan watanni masu yawa. Ita kuwa Lubabatun ma tun zuwansu haihuwar Ihsan ba ta kara zuwa Sokoto ba. Ta zama Abuja -Woman, daidai da burin ta. Ranar wata asabar Yaya Maccido ya bugo wa Adda waya ya sanar da ita haihuwar Lubabatu, an samu da namiji. Yanzu haka suna can gidansu Lubabatun ita da yaran a garin Birnin Kebbi a can za ta yi wanka. Yaya ko tunanin ya dauko su ita da jaririyar ya kawo wa Addah ta ga jikan ta bai yi ba, sai a hoto ya turo mana hoton sa. Aunty Nabeelah rannan da suka yi waya da Adda bata san ina toilet din ta ina jin su ba, ina ji tana share hawaye tana labarta mata irin banzatar da itan da Maccido ya yi, tsakanin ta da shi sai waya, ba ta isa ya tako ta ganshi ba balle ‘ya’yan sa. Aunty Nabeelah ta ce, “Addah ke ma kina da laifi, tunda na ga take-taken yarinyar nan Lubabatu tun farko na nusar da ke kan ki dauki mataki, ki kuma sa a taya ki da addu’a a kan Maccido, amma ki ka ce ke ba za ki yi kutse cikin rayuwar sa da iyalin sa ba. Sannan ba za ki sa wani ya yi miki addu’a a kan dan da ki ka haifa ba. To Addah zamani ya canza... Kina barci ana yi miki minshari, dan hakin da ki ka raina sai ya tsole miki ido. Sai yanzu da abubuwa suka fi karfin control za ki koka? Ai kawai ki ci gaba da hakurin ki kuma dage da addu’a, amma Maccido ya yi mana nisa”. Aunty Nabeelah ta fada tana share hawaye ita ma. Tana tuna kuruciyar su mai dadi da kanin ta Maccido. Tun daga ranar damuwa ta ci gaba da taba lafiyar Addah a hankali-a-hankali. Ta soma ciwuka a tsaitsaye tana danne shi da karfin ran ta. Kullum jarumta ta ke ta nuna cewa lafiyar ta kalau, amma a zahirin gaskiya ba ta da lafiya. Muhsin da ya zo weekend don yanzu ya tattara ya koma hostel ya takura mata kan ta je asibiti, ta dage ita lafiyarta kalau, amma kuma kullum a kwance ta ke wuni a daki, ko falo ba ta iya fitowa. Al-Qasim ma ya yi ya yi a je asibiti, amma Addah ta ki. Ciwo sosai ya ci karfin Addah wanda aka rasa gane kansa da gindin sa, ya zamana ko sallah ba ta iya yi sai a zaune. Al-Qasim ne ya dauko likita mace ya kawo har gida don ta duba ta. Likitar ta dudduba ta, sannan ta dauki jinin ta ta ce akwai gwaje-gwajen da za ta yi a asibiti kafin ta san hakikanin me ke damunta. Ta takurawa Addah aka wuce da ita asibiti don cikin ta da za a yi wa scanning sabida kukan ciwon ciki da ta soma yi. Kafin result din gwaje-gwajen Addah ya fito Addah ta daina shaida wanda ke kanta. Daga ni har Muhsin da Al-Qasim mun kasance cikin madaukakin tashin hankali. Hankalin mu bai kara tashi ba sai da sakamakon gwajin ya fito inda suka sanar da mu Addah na fama da ciwon koda ne. Akwai bukatar a yi gaggawar yi mata aiki a cire stones daga cikin kodar ta. https://www.arewabooks.com/book?id=6329c8029b3e7782f077921d Na kwantar da kaina jikin gadon da Adda ke kwance ba ta san wanda ke kanta ba. Shesshekar kuka nake yi a hankali cikin rauni da karaya nake fadin, “Adda, Allah ya tashi kafadun ki, Allah ya ba ki lafiya Addah… Ba ni da kowa sai Allah da ya halicce ni, sai ke…” Kuka nake yi mai motsa zuciyar duk wani mai saurare da muryar da ke nuna maraici na. Alamun zaman mutum na ji a kujerar da ke kusa da tawa, hanci na ya surnano min wani lallausar kamshi na turaren obsession (by CK). Hannu ya kai a hankali ya kama hannun Addah wanda babu karin ruwa a jiki. A hankali na dago ina bin shi da kallo, kallon da a sannu yake sauya kala yana komawa na kiyayya… na tsane shi, na tsane shi don na san duk matsalolin da Addah ke fama da su na hawan jini da yawan bacin rai shi ne sila. He is very selfish… kansa kawai ya sani da shaidaniyar matar sa. Ko kusa bai zame wa Addah sanyin idaniya ba, haihuwar sa ba ta kare ta da komai ba sai tulin bacin rai. Ta dauki soyayyar sa da damuwa da lamarin sa ta aza a ranta har ya yi mata illah. Rabon da mu ganshi yau watanni bakwai ke nan, sai yanzu da ya ji an ce Addar na gargarar mutuwa shi ne ya wani kwaso jiki ya zo. To me ya zo ya yi mata? Ko ya zo ne don bakin cikin sa ya karasar da ita zuwa kushewar ta? Ban san sanda na saki wani mugun tsaki ba. Na ji na tsani Yaya Maccido sakamakon treatment din sa ga Addah. Tsana mai yawa, wadda ta cire min burgenin da yake a baya. Na mike zan bar wajen, kallon mamaki Yaya Maccido ya bi ni da shi, na san tantama ya ke kan tsakin da ya ji, da shi nake ko da wa? To in ba da shi nake ba da wa nake? Mu biyu ne kacal a dakin, sai Adda da ke kwance rai kwakwai-mutu-kwakwai. Wannan ba lokacin da zai tsaya yana tantance Ma’u ta yi masa tsaki ba ne ko a'ah. Ya zo ne da kyakkyawar niyya ta YI WA KAN SA HISABI tsakanin sa da Addar sa, tare da yin repenting manyan kura-kuran sa. Repenting din da zai baiwa kowa mamaki. Ya kuma wanke zuciyar kowa nasa. Ya amincewa kansa bai kasance Da mai farantawa mahaifiyar sa ba. Ya kasance cikin wani irin ajizanci na lokaci mai tsawo. Amma yanzu jin kan sa yake kamar wanda aka tasa daga nannauyan barci. Ya yarda tunda ya auri Lubabatu ya canza akalar rayuwar sa bakidaya. A yanzu kam ya yarda Lubabatu ba ta jan shi ga hanyar da zai samu rahmar Allah. Ya tabbata Addah ta yi hakuri a kansa hakurin da iyaye da yawa ba za su yi shi ba a kan ‘ya’yan da suka haifa. Yana rokon Allah ya ara masa dama ya gyara kuskuren sa, ta hanyar da ba wanda yayi tsammani, ko da wannan shi ne abu na karshe da zai aiwatar a duniya. Hannun Adda ya kama ya rike gam! Hawaye na fita daga idanun sa. Daidai lokacin da likita da nurse suka murdo kofar suka shigo, ni kuma ina bayan su. Na je ne na kira su don su cire mata karin ruwan da ya kare su daura mata wani. Kallo daya na yi wa Yaya Maccido na fahimci kuka yake yi. Na kyabe baki a raina ina fadin, “Daga baya ke nan!” ....wai sadaka da bazawara. Ko ganinsa idanuna ba sa son yi, saboda yadda tsanar sa ta lullube min zuciya, har cikin kokon raina. Gefen gadon Addah na koma na tsaya na harde hannaye na a kirji, na kuma tokare kafata daya a jikin bango. Ko kallon inda yake bana yi, addu’a kawai nake wa Addah cikin raina. Ina ji yana magana da likitan kan ya tattara masa bayanan komai na Adda, nan da kwana uku zai fita da ita Jeddah - Saudi-Arabia a yi mata aikin a can. A raina na ce, ‘Ta baya ta rago’. Bayan fitar likitan ya dan saci kallon inda nake tsaye. Cikin taushin murya ya ce, “Ba kwa bukatar wani abu? Zan je gida in dawo”. Na zumburi baki, “Ba abin da muke bukata, in ma akwai Muhsin zai kawo idan zai zo”. Ya dan tsura min ido kamar mai son tantance tone din murya ta mai alamun akwai fusata a ciki. Kyabe baki ya yi, ya mike ya fice a ransa yana fadin, ko me na yi masa shi ya ja wa kansa da ya kula ni, bayan ya lura yau fizga nake kamar mai bugun aljannu. Yana komawa gida sashen sa ya nufa, ya yi wanka, ya yi sallah ya canza kaya marasa nauyi ya kishingida a sofa bed. Wayarsa ya dauka ya kira Aunty Nabeelah. Sun dade suna magana wata irin doguwar magana mai kama da doguwar jayayya, daga karshe Nabeelah kuka ta koma yi masa a wayar tana sanya mishi albarka. Ta ce, komai dare ya tafi Dogondaji, ita kuma za ta kira Bebeji. Washegari Al-Qasim Yaya ya sa ya dauke ni muka tafi immigration don yin fasfo, don Yaya ya ce da ni za a tafi Jeddan. Cikin kwana daya fasfo ya fito aka shigar da neman visa na Addah kuma aka sabunta shi. Ranar da za mu tafi tun dare na hada duk abin da zan bukata, washegari ambulance ce ta dauki Adda zuwa filin jirgi. Ni da Yaya kuma muna motar Al-Qasim, bai koma gida ba sai da ya tabbatar jirgin da muka shiga na emirate mai zuwa Saudi-Arabia ya bar kasa. Yau sai na ga Al-Qasim ya zame min kalar tausayi, he look pale. Na nemi Muhsin na rasa tun jiya, ba inda ban duba ba ban ganshi ba, a jiya da safe dai ya ce min zai dan yi balaguro, amma ba jimawa zai yi ba sai dai har mu tafi wata kilan ba za mu hadu ba. Aunty Nabeelah ta kira ni ta wayar Yaya ba da son ransa ba ya ba ni wayar muna gab da tashi ta ce, “Ki ce alhamdulillah, subhanallah sau uku”. Na yi yadda ta ce. A daidai lokacin dana gama fadar hakan ne naji gabana ya tsinke ya yi mugun faduwa, dai-dai lokacin da daqiqar agogon hannu na ta nuna karfe sha daya na safe, kirji na ya hau yin wani balli-balli har sau uku. Sai ta ce cikin sautin murmushi. “Safe journey my lovely Sis, ki kula da kan ki, ki kula da Addah, zan iske ku a Jeddah next week Insha Allah!" ****** JEDDAH, SAUDI-ARABIA Yau ni Ma’un Nene ce a filin jirgin saman Sarki Abdul’aziz dake birnin Jeddah. Duk da jinya ce ta kawo ni, na yi farin cikin kasancewa ta a kasa mai tsarki. Daga filin jirgi motar asibitin Doctoor Sulyman Faqeeh ce ta kwashe mu zuwa asibiti, inda likitoci suka rufu a kan Addah suka ba mu daki V.I.P kamar yadda Yaya Maccido ya zaba. Kyawun dakin ya isa, kamar kana gidan ka. Ba abinda babu. Har da ciki da falo, talabijin, A.C, firji, da duk abin da dan Adam zai bukata. Tunda aka shigo da mu dakin ban kara ganin Yaya Maccido ba, yana can wajen management din asibitin. Haka tunda muka taho wata kalma ba ta hada ni da shi ba. Sai in na samu faraga in harare shi son raina in dauke kai. Aka ce aikin banza wai harara a duhu, don Maccido bai san ina yi ba, don kuwa ban ishe shi kallo ba. Duk da cewa ga kujera ta ga tasa, har kafadun mu na gugar na juna. Earpiece ya sa a kunnen sa yana sauraron kira’ar Abdurrahman Sudaith, daga baya ban san me yake yi ba sakamakon bacci da ya dauke ni bayan mun ci abinci. Har muka sauka a Jeddah ina barci. Na gane an zo ne ta hanyar hannun Yaya da na ji ya zagaye ni yana unfastening belt dina. Saura kadan numfashi na ya dauke sakamakon dumin numfashin sa da ya sauka a wuya na. Na galla masa harara, a raina na ce ko ina ruwansa da ni? Oho! Meye business din sa da saka belt dina da cirewa? Bai san na yi ba, don kuwa bai ma kalle ni ba. Na nisa daga zuzzurfan tunanin da na fada, daidai lokacin da aka turo kofar dakin namu aka shigo. Yaya ne, hannun sa rike da ledojin da na fahimci abinci ne ya sayo. A take akuyar ciki na ta motsa, don kuwa rabo na da abinci tun na cikin jirgi. Zama ya yi a kujera ya ja karamin tebir gaban sa ya daura ya bude ya soma cin kentucky fried chicken din da ya shigo da ita, yana yi yana korawa da lemon Pepsi mai sanyi. Na saci kallon sa tare da hadiyar yawu, mukut! Ko ya tuna da ni ya miko min dayar ledar, amma mutumin nan ban ishe shi kallo ba. Ya cinye kazar sa tas! Ya fiddo waya ya kira inda daga sunan Sweetie na fahimci shi da matar sa ne. Sauran hirarrakin kasa sauraro na yi, don ban saba jin irin su a rayuwa ta ba, sai na mike na sa silifas da zummar barin dakin. A raina ina ta mamakin Yaya, ashe da ma yana magana haka? Na ce a raina, bari in fita in dan zaga ko zan samu abin da zan saya in ci. Na tuna ko sisi ba ni da shi. Idona ya cicciko da kwalla, na fita jikin barandar dakin na tsaya ina kallon shige da ficen motoci, a lokaci guda ina share siraran hawaye daga idona. Ni ban san kaddarar da ta jefa ni hada tafiya irin wannan da Yaya Maccido ba. Mutumin da uwar sa ma ba ta dame shi ba, wace ce ni da hakki na zai dada shi da kasa? Wani balarabe ne ya zo inda nake ya tsaya ganin ina kuka yake tambayata cikin larabci ko akwai taimakon da nake nema? Daga ni har shi ba mu ga sanda Yaya ya fito ba, sai jin hannun sa na yi cikin nawa yana yi wa Balaraben godiya, ya ja ni muka koma daki. A kujera ya dangwarar da ni, ya tsaya a kaina. Kallo yake kare min daga sama har kasa, kafin cikin kaushin murya ya magantu da cewa. “What’s wrong with you?” Girgiza kai na yi hawaye na bilbilowa daga ido na, hawayen da bansan yadda zanyi in tsayar da su ba, me yake so in ce masa? Horon yunwa da ya fara yi min ne ba zan iya dauka ba? Ko kuwa bana son jin ni da shi mun kadaice a wuri guda irin haka, babu mutum na uku a tsakanin mu ban saba ba? Hawaye na suka kara yawa. Murmushi ya yi, ya dauko ledar KFC ya aje a gabana, da kansa ya bude min ya bincire min hancin gwangwanin fanta. Ya ce, “In kin yi hakuri ai ba zan ci in hana ki ba, ina magana da Madam dina ne, daga yau kada ki kara fita waje ba tare da ni ba, larabawan nan ba hankali ne da su ba”. Na kasa cin komai sabida ya tsaya min a ka. Ya gane hakan, amma ya ki matsawa, kallo na yake daga sama har kasa, ka ar yau ya soma gani na a gaban sa, kallon da na tabbatar Yaya Maccido bai taba yi min kwatankwancin sa ba tunda aka haife ni, bai taba yi min kallo na biyu ba, amma yau kallon da yake yi min har ya zarce ka’idar musulunci. Yanke shawara na yi a raina, gara in shige toilet, don in kubutar da kaina daga wadannan mayatattun idanun na Maccido. Ina mikewa na yi taku biyu sai ji na yi ya fizgo ni na fada jikin sa. Kadan ya rage in saki fitsari sabida razana da tsabar firgita. Rungume ni sosai Maccido ya yi yana sakin wata irin ajiyar zuciya, abin da ya dauke ni ya shilla wata duniya da ban taba ziyarta ba ke nan. Duniyar da ta fi kama da ta yawo a kan gajimare, domin har bayana yake bubbugawa da hannunsa daya, yayin da ya sarke na hagun cikin nawa. Tunda nake ban taba jin lallausar hannu irin na Maccido ba. Ganin komai nake kamar cikin mafarki, amma nan take kwakwalwata ta koma cikin hankalin ta. Adda ta sha gaya min, duk namijin da zai nemi taba jiki na, to dan iska ne, kuma ba mutuin kirki ba ne, in guje shi kuma in zo in gaya mata. Da karfin gaske na janye jiki na daga cikin na Maccido na zura toilet a guje na banko kofar. A jikin sink na tsaya ina regaining consciousness tare da hango abin da ya faru cikin dakikar da ba ta wuce goma ba. Ni ce rungume jikin Yaya Maccido ba mafarki na yi ba, al’amarin mai kama da almara ya faru da gaske. Kamshin turaren da jiki na ya koma yi na obsession (by CK) ya kara tabbatar min da hakan. “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Na ambata har sau uku. Da ma malamin islamiyyar mu ya ce, “Idan mace da namiji suka kebe, to tabbas shaidan ne na ukun su”. Wato don ya ga babu idon kowa a kan mu shi ne zai aikata wannan zaluncin a gare ni? Zan kuwa ba shi mamaki, duk girman sa da ke idanuna wanda da ma yanzu rawa yake, sabida tsanar dana yi masa akan laifuffukan sa ga Addah zan yakice shi in nuna masa na san abin da nake yi, kuma na san mutuncin kaina. Ina masa kallon mutumin kirki ashe shi ma in ya samu faraga dan duniya ne? Ina jin bude kofar sa da fitar sa, na wanke fuskata a sink na fito. Kazar na dauka na gyara zama na afka mata babu sassauci. Addah na wani daki na musamman suna kula da ita, sai dare suka turo ta bisa gado zuwa dakin mu suka kwantar da ita a kan gado. Da alama ta sha alluran barci don barci ta ke yi sadidan. Ban kara ganin Yaya Maccido ba sai karfe tara na dare agogonsu na can. Ya canza kayan jikin sa, da alama wanka ya yi. Ina daidai kan Addah rike da hannun ta sanda ya shigo, ledojin hannun sa ya ajiye ya karaso inda muke. Na kuwa tattare fuska na hade girar sama da ta kasa. “Ba ta tashi ba?” Ya tambaye ni. Juyar da fuska na yi wani gefen ban ce masa komai ba. Ya ja kujera ya zauna a gaban Addah yana karanto addu’o’i yana tofa mata. “Ga abinci can ki je ki ci”. “Na koshi”. Na yi saurin bada amsa. Ya daga fararen idanunsa ya kalle ni, kallon sakan biyu, kafin ya ce cikin muryar bada umarni. “Asma’u, na ce ki je ki ci abinci”. Sai na samu kaina da kasa musawa wannan karon, domin ya murde fuska ya koma Maccidon sa da na sani. Shinkafa ce da gasasshiyar qibdah (hanta), na zauna na soma ci ba don yunwa ba, sai don bana son wata magana kowace iri ce ta sake hada ni da Maccido. Wayar sa ce ta yi kara, sai ya dauka ya yi magana, sai na ga ya kalle ni ya wani bata rai, kafin ya ce, “Zo ki karba”. Na tsame hannuna daga cikin abincin na je na amshi wayar na kara a kunnena. Aunty Nabeelah ce. “Hello Ma’u, ya ku ka sauka, ya kuma jikin Addah?” Na ce, “Aunty lafiya kalau. Addah dai tunda muka zo suke mata allurar barci wai sai jibi za a yi aikin”. Ta ce, “Ina nan ina shirin tahowa, sai nan da kwana shidda. Ki yi hakuri da Maccido kin ji?” Dan murmushi na yi, na ce, “Aunty ke ma kin san ba wani shiri muke ba, me ya sa aka hado ni da shi, bayan ga Muhsin?” Aunty Nabeelah ta yi ajiyar zuciyar da na jiyo ta, ta ce, “Sabida shi ne babba. Abin da zai yi Muhsin ba zai iya ba. Sannan kin ga yana so ya yi amfani da damar ya yi repenting kurakuran sa ne. Ya kula da mahaifiyar sa. Alhamdulillah tunda mun samu Allah ya juyo mana da hankalin sa sai mu ba shi dama. Shi ma ya samu ladan mahaifiyar sa da yake ta batawa. Kin ga dukkan ayyukan da ke gabansa ya ajiye su ya taho, kuma za ku kwashe a kalla wata guda bayan aikin Addah kamar yadda likitocin suka ce. Ke dai tsakaninki da shi ai gaisuwa ce, sai kuma ki yi masa biyayya tunda gaba yake da ke”. Na so in ce, “Aunty dazu ba rungume ni ya yi ba… kuma hakan haramun ne”. Amma ina dago idanuna na dubi saitin da yake, sai na ga ya kafe ni da ido yana min kallon mind yourself. Kafin ma in yi magana Aunty Nabeelah ta ce, “Baban Aasim ya shigo, zan kira ki gobe insha Allahu”. **SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* 07030137870 * *YIWA KAI HISABI* ((9)). Na mike na kai ma Yaya Maccido wayar sa, ya ce, “Gobe zan hada miki waya, way ata ta daina shiga hannun ki bakauyiya kawai, kada ki lalata min. Dubi duk kin shafa min maiko a jiki”. Ni dai ban ce komai ba, na je toilet na wanko hannuna da bakina. Sanda na fito yana shirin barin dakin. Ya ce, “Zan je supermarket me ki ke so?” Kaina a kasa na ce, “Sai dai in rubuta maka”. Ya jingina da kofar dakin, ya ce, “Ok, hurry”. Jakata na jawo, na dauko jotter da biro. Da rubutuna mai kama da na ‘yan firamare na rubuta masa duk abin da nake bukata, pad ce ta karshe wadda na rubuta ina runtse ido cike da kunyar kaina. Ya karba yana dubawa, sai da ya tattara hankalin sa ya gane abin da na rubuta. Ya sa takardar a aljihun sa ya fice. Niki-niki ya dawo da ledoji, har ma abin da ban ce ba in dai ya san zai min amfani a zaman da za mu yi, ya siyo min. sannan ya sayo min ice-cream. Hannuna da nashi ya miko min ledar ice-cream din, ya ce, “Ki sha, ko ki sa a fridge kada ya yi melting (kada ya narke)”. Har raina na ji dadin karamcin da ya yi min, na kuma ce a raina, ashe Yaya in ya ga dama yana da kirki? Har karfe goma sha dayan dare yana zaune yana ta buge-bugen waya, har Ihsan sai da ya yi magana da ita. Kamar in ce ya ba ni yarinyar, sai kuma dai na yi shiru. Ina ji ya yi magana da Al-Qasim da Muhsin. Ban san me Muhsin ya ce masa ba, ya ce, “Wallahi ba zan ba ta waya ta ba, maiko ta ke shafa min, gobe zan hada mata tata sai ku yi ta yi”. Ya mike yana kallo na kai tsaye daga tsakiyar idanun sa. “Zan je na kwanta Asma’u, sai da safe”. Yadda ya siranta muryar shi ya ba ni mamaki. Na dago a hankali sai ido na cikin nasa. Da sauri na kawar da kai sabida ba zan iya jure kallon da nake gani cikin idon sa ba. Mamaki da tu’ajjibi kamar su kashe ni. “Sai da safe Asma’u”. Ya sake fada da irin muryar dazun, sannan ba tare da ya jira amsawa ta ba ya juya ya fita, ya rufe min kofar. Gani na yi in na zauna ina mamakin Yaya Maccido mai halaye irin na wahainiya, to kuwa zan kwana a zaune. Yau na wuni da Maccidon da ban taba wuni da shi shekaru goma sha tara ba. Yau na ga bangarori da yawa na Maccido, wadanda ban taba sani ba. Karewa ma yau har a jikin Maccido na kwanta. Na girgiza kai tare da mikewa na dauro alwala, na zo na dasa sallah, sai dai kuma na rasa abu na biyu da zan roki Ubangiji bayan samun lafiyar Addah. Sabida tunani na na yau bakidaya Maccido Tahir ya cukurkuda shi. A gaban Addah na kwana, zaune a kan kujera kaina bisa gadon ta, hannu na rike da hannun ta. A haka barci mai nauyi ya dauke ni, sai kiran sallar asubahi na tsinkaya daga dan nesa da mu. A hankali na zame hannuna daga na Addah wadda ke ta barci, amma ta kan motsa lokaci zuwa lokaci. Na gyara mata kwanciya sannan na dauro alwala na tada sallah. Da na fito na tadda nurses da doctors sun shigo suna kanta, don haka sallahta na tayar. Fatan mu Allah ya sa a yi aikin nan cikin sa’a. Sai karfe takwas Yaya Maccido ya shigo, a hannunsa ledojin karin kumallon mu ne. Ciki-ciki ya yi sallama, ni ma ciki-cikin na amsa masa. Kai tsaye wajen Addah ya dosa wadda ta bude ido tana kallon mu tarr! Amma ba ta iya ce mana komai, sai wasu siraran hawaye da suka biyo ta gefen idon ta. Gaba dayan mu muka yi kanta da sauri ni da Yaya, ya ce, “Addah, me ki ke so?” Ni kuma na ce, “Addah, ina yake miki ciwo? Ko in kira likita?” Girgiza kai ta yi, sannan a hankali ta lumshe idanun ta. Kafin ta kai hannu ta kama hannuna ta dauke kanta daga duban Maccido. Ya kara dawowa saitin da ta maida fuskar ta. Addah ta sake dauke kai daga gare shi, wannan abu ya tada hankalin Maccido kamar ya fashe da kuka. A kan gwiwoyin sa ya gurfana ya kama hannun Addah ya kankame ya soma magana cikin rawar murya. “Addah…. Na sani… ni din mai babban laifi ne… laifin da ya cancanci kowanne irin hukunci daga gare ki. Sai dai kuma ina so ki sani, na gane kure na, a yau kuma ga ni na zo na gurfana a gaban ki ina mai neman yafiya da afuwar ki. Ina mai daukar miki alkawarin ba zan sake yin nesa da ke ba. Na sani cewa, na ba wa neman duniya da hidimar iyali na muhimmanci fiye da ke a baya. Ina rokonki Addah ba don hali na ba, ki yi duba ga dumbin alfarmomin ku na iyaye ga mu ‘ya’yan ku ki yafe min Addah, ki ba ni dama in gyara kuskurena ta hanyar da hakan ba za ta sake faruwa ba. Na zo miki da kyakkyawan albishir Addah, wanda na tabbata zaki ji dadin sa, duk don in wanke laifi na daga zuciyar ki, wanda nake so ki dubi alkhairin da ke cikin sa ki yafe min Addah…” Hawaye ya zubo daga idanun Addah, ba ita kadai ba, dukkan mu babu wanda hawaye bai zubowa ba. Ni dai nawa na tausayin su ne su duka, da farin cikin kalaman da yake gaya wa Addah a yau, na kuma tabbata nadamar nan da yake fadin ya yi, da gaske ya yi ta. Domin za ka iya ganin ta zane baro-baro cikin fararen kwayar idanun sa, wadanda suka rine da hawaye suka koma light brown masu sheki, sai walainiya suke cikin duhun labulayen dakin da kuma hasken fitila da ba a kunna ba. Addah ba ta yi wani nuni da ke nuna ta yi na’am da kalaman bakin sa ba, ko ta san me yake fadi, a hankali ta lumshe idon ta ta koma barci. Ni kuma na koma gefe na dau daya daga cikin ledojin abincin da ya zo da su na soma ci. Ina ganinsa ya ja kujera gaban Addah ya zauna yana kallon ta with so much affection, ba ya ko kiftawa. Sai da wayarsa ta yi kara ya tashi, ya fita don ba ya so maganar sa ta tada Addah daga barcin da ta samu. Sai bayan azahar ya fita, ya dawo sanye da jallabiya mai gajeran hannu ruwan madara, wadda na tabbata a nan garin ya saye ta. Kamshin jikin sa ya canza daga turaren obsession ya koma amfani da oud abyad. Bakin balaraben Saudiyyah Yaya Maccido ya koma daga zallar baturen sa na baya. ‘Yar farar ledar da ke hannunsa ya miko min. Hannu biyu na sa na karba da na fahimci kwalin karamar waya ce iphone mai shegen kyau da tsada. Na ce, “Yaya, na gode. Amma ban san ya ake amfani da ita ba”. “Ki koya a hankali". Kawai ya ce ya karasa yana taba wuyan Addah. Sai juya waya nake a hannu na, ina mamakin wai wannan tsaleliyar wayar tawa ce ni Ma'u. Ko Muhsin da Al-Qasim tasu ba ta kai aji da mukamin tawa ba. Sai ji na yi kira ya shigo cikin wayar. Da sauri na ce, “Yaya…”. Sai kuma na yi shiru ganin ya juyo yana harara ta. Wayar na mika masa ya nuna min inda zan danna, na yi maza na amsa fuskata fal murmushi da na ji Aunty Nabeelah ce. “Larabawan Jeddah, ya ku ka kwana? Kaifa haalikum! Ya jikin Addah?” Na ce, “Alhamdu lillah aunty, bikhairin wa aafiyah, ya ya Aasim?” Ta ce, “Ai ya shiga kindergarten yanzu ba zaman gida. Maccido ya gaya min ya saya miki waya”. “Eh Aunty, ki taya ni godiya, ni in na yi masa magana harara ta yake yi”. Dariya Aunty Nabeelah ta yi, ta ce, “Harara as in how?” Na ce, “Harara sosai, kamar wadda ta yi masa laifi”. A hankali nake magana yadda na tabbatar ba ya ji na. A rashin sani na yana da karfin ji, tsaf yake jin duk abin da nake fada a kansa. Aunty dai ba ta bar dariya ba, ta ce, “Ina fata dai yana kyautata miki, duk abin da ki ke so yana sayo miki?” Na san in na ce Yaya ba ya yi min abubuwan da ta ambata din na yi masa karya, watakila har Allah ya tsaida ni hisabi da shi a kan hakan. Don haka na ce da Aunty Nabeelah, “Ba ni da wannan matsalar da shi, ya sayo min komai har da wanda ban ce ina so ba, yana da alkhairi sosai”. Murmushi Nabeelah ta yi, ta ce, “To masha Allah, don’t mind hararar sa tunda dai ita ce kadai matsalar sa”. Ba jimawa kiran Muhsin ya shigo, na amsa da kaina don na rike inda Yaya ya nuna min dazun. Ya ce, “Ma’u na ta yi waya, ta zama babbar yarinya, ya jikin Addah kuma ya aka ji da sabon wuri?” Na ce, “Wato da karamar yarinya ce tunda ba ni da waya ko?” Ya ce, “Eh mana!”. Na yi dariya na ce, “Addah gobe da safe za a yi aikin ta, sai a ci gaba da taya mu addu’a. Ashe Baban Ihsan ba laifi yana da kirki, kai dai bar shi da harare-harare”. Dariya Muhsin ya saki, ya ce, “Allah ko? In ya ji ki ya kwace wayar sa babu ruwa na”. Na ce, “Ina Al-Qasim?” “Ga shi a gefe na”. “Ba shi mana mu gaisa”. “Ya ce ba zai yi magana da ke ba”. Cikin mamaki na ce, “Sabida me?” Muhsin ya yi wani irin murmushi, ya ce, “Abin sirri ne. Ki shafa min kafar Addah in samu albarkar ta”. Har muka kashe waya ni da Muhsin ina ta mamakin wai yau Al-Qasim ne ya ce ba zai yi magana da ni ba, ni din da a da ba wanda yake son kulawa iri na. Duk da share shin da na ke yi. To me na yi masa??? Haka muka kare wunin ranar ni da Yaya kowa na danne-danne a wayar sa. Idan mun yi kuskuren hada ido ya harare ni. Sosai na takura da zama da shi a dakin. Lokaci-lokaci nurses da doctors na shigowa su yi aikin su a kan Addah. Da aka kira magriba ya fita, bai dawo ba sai da aka idar da sallar isha. Hannunsa rike da abincin da za mu ci. Ya zauna yana cin nasa, ni kuma na adana nawa don bana jin yunwa. Sai karfe goma na dare ya mike zai tafi. A lokacin ina waya da Muhsin yana ta ba ni labarin abubuwan da ke faruwa a gida da mall. A fusace Yaya Maccido ya ce, “Wallahi in ba ki daina hirar wofi da Muhsin ba zan raba ki da wayar nan, don shi ba shi da hankali gobe za'a yi wa uwar sa aiki mai matukar hatsari, amma ya zauna yana surutun banza maimakon ya je masallaci ya yi ta addu’a. Ke kuma shashasha shi ne ki ka biye masa. Kashe wayar nan ki je ki yi alwallah ki kama abin da ya fi alkhairi”. Da sauri na kashe ba tare da na yi wa Muhsin sallama ba. Yaya Maccido bai san halin Muhsin ba ne. Shi ba shi da sa abu a rai, ko sanda mahaifin su ya rasu makokin kwanaki biyu ya yi ya ci gaba da harkokin sa da abokan sa. Har polo suka je ranar sadakar ukun Baban su. Naturally haka halinsa yake, ba abin da ke daga masa hankali. Washegari tun karfe bakwai na safe Yaya Maccido ya iso, ya yi wanka ya yi fresh da shi. Ya zuba wata farar voile mara nauyi, wadda aka yi wa dinki tazarce, links din hannunshi da botiran kayan na silver ne, ya yi matukar kyau kamar saurayi mai tashen ashirin da takwas. Ni ma na shirya cikin bakaken jallabiya na nade kaina da mayafin su. Karfe takwas daidai na safe aka shiga da Addah dakin tiyata inda za'a yi mata aiki don raba ta da kidney stones. Ni da Yaya dafe da gadon da aka gungurata a kai har zuwa kofar theatre room din. Muka dawo jikin tagar dakin muka jingina, zuciyar kowannen mu ta yi nauyi. Ban san tunanin da Yaya ya yi ba, sai ji na yi ya kama hannu na ya rike gam! Kafin ya ja ni mu soma tafiya. Sai bin sa nake tamkar rakumi da akala, mamaki na neman zauta ni. Ajrah (taxi) ya tare mana a bakin titi, ya ce a kai mu birnin Meccah. Muna bayan mota mai Ajrah na ta sharara gudu daga Jeddah zuwa Meccah. Ban tambayi Yaya komai ba don na fahimci yana cikin wani hali na aikin nan da za'a yi wa Addah. Na fahimci babban tashin hankalin sa bai san matsayin sa ba, Addah ba ta yafe masa da bakin ta ba, idan ta mutu ta bar shi, ina zai sa ransa? Sai da muka isa Haraam yake gaya min dawafi za mu yi, bakwai sau bakwai, mu roka wa Addah samun lafiya. A sanyaye na ce, “Mu yi umrah kawai gabadaya mu huta”. Ya ce, “Na fi so in yi umrah tare da Addah, amma mu fara din, in Allah ya tashi kafadun ta sai mu dawo tare mu sake yi”. Mun yi umrah, mun yi safah da marwah, mun yi nawaafil a maqama Ibraheema Musally, sannan mun yi dawafi bakwai sau bakwai mun yi wa Addah addu’a wadda muka sakankance an amsa kawai, sabida alkawarin Ubangiji ne, duk wanda ya zo da bukatar sa wannan wajen ya sakankance cewa an amsa. Ko abinci ba mu iya mun ci ba muka sake hawa Ajrah muka dawo Jeddah. A lokacin muka samu an yi aikin lafiya. A fili na saki hamdala, Yaya ya yi wata irin ajiyar zuciya. An kai Addah daki na musamman inda za ta zauna tsawon kwana bakwai ba tare da kowa ya shiga ba sai likitocin ta. Duka kulawar ta tana wuyan malaman jinyar asibitin. Mu da ganin Addah sai bayan kwana bakwai. Dakin mu na farko muka koma inda Yaya Maccido ya umarce ni da in tattara komai nawa mu wuce masaukin sa. Mu da dawowa nan sai bayan kwana bakwai din, amma zai dinga zuwa kullum da safe ya ji ci gaba da ake samu a lafiyar Addah. Ina tattara kayana, amma hankali na ya rabu biyu. Hotel fa za mu koma daga ni sai Yaya! Wannan ko a musulunci ba mu da hurumin sa ko da ciki daya muka fito, dukkan mu baligai ne. Dai-dai misali inada ilmin addini na. To bai ba ni damar da zan yi masa tambaya ba, don haka na rika bin umarnin sa in ga irin hankalin sa. Ai kuwa na ga abin da ya hargitsa min hankali domin kuwa na fahimci dakin da ya sauka a Al-Jamjoum Fundak nan ya kawo ni. Ya aje jakunkunan mu ya juyo ya dube ni na ci uban birki a bakin kofa. Wani miskilin murmushi Attahir ya yi, ya ce, “In kin gaji da tsayuwar, sai ki shigo ki rufe kofar”. Ya shige toilet abinsa. *TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES* *SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* *07030137870* ```HISABIN NAFS``` ((10)). Da na ga tsayuwar ba za ta kai ni ba, duk kafafuna sun sage, dole na ja jiki zuwa cikin dakin. Kujerar farko na samu na dofana jikina kamar a ce kyat! In zura a sittin. Da na ji motsin kofar toilet har wata irin firgita na yi. Wai an ce makaho bai san ana kallon sa ba sai an taba shi, ya kamata in yi wa Yaya magana watakila ya manta cewa, dukkannin mu baligai ne, sannan kuma ba muharraman juna ba. “.....Yaya sai na ga kamar bai dace mu sauka daki daya ba”. Na fada a matukar darare, kamar wadda ke tsoron furta maganar tata. Yana shimfida darduma zai tada sallah ba tare da ya juyo ba, ya ce, “Allah koh?” Sai kawai ya kabbara sallahr sa. Na yi mutuwar zaune da al’amuran Maccido Taheer, masu neman hauhawar da jini na. Domin bayan ya idar da sallah abinci ya ja ya soma ci, bayan ya gama ya nufi closet yana kokarin sauya kayan jikin sa. Da sauri na mike na yi hanyar kofa a lokacin da na fahimci Yaya Maccido rigar sa yake cirewa. Runtse idanu na na yi, wani irin gam! Na karasa ga kofar da lalube. Maccido na kallona yana murmushi sosai, ya ce, “Asma’u!”. Tsayawa na yi daga tafiyar laluben da nake yi, amma ban juyo ba. illahirin jikina rawa yake yi. Ban san sanda ya tako ya cimmani ba daga shi sai farar singileti da dogon wando. Hannaye na biyu ya kama da duka hannayen sa hagu da dama, ya ce, “Bude idanun ki ki dube ni”. Na dan motsa idanun yayin da yawu ya kafe a baki na. “Open your eyes ki dube ni”. Girgiza kai na shiga yi, hawaye na zubo min. “Bai kamata ba Yaya!”. Ya kara matsowa gabana saura kadan ya hade space din da ke tsakanin mu. Ya ce, “What are you afraid of (me ki ke tsoro)?” Shiru na yi na kasa amsawa, ni kaina ban san me nake tsoron ba, kawai dai na san bai kamata ba mu zauna daki daya ni da shi. Hatta wannan closeness din da ya assasa a tsakanin mu na san mun keta hurumin Ubangiji. Jin na yi shiru ban amsa ba ya kai hannu ya dafa kafaduna guda biyu, murya can kasa, ya ce, “Asma’u. I’m your brother ba zan cutar da ke ba. Ina so ki sa a ran ki cewa, kina cikin amanata. Na dauko ki ne cikin amana, kuma cikin amanar zan mayar da ke hannun Addar ki. Idan har kin amince da hakan ki bude ido ki dube ni”. Dole kowa Yaya Maccido ke wa magana da wannan muryar tasa ya yi masa abin da yake so. Wata irin kasala muryar tasa ta saukar min, hadi da faman murza yatsu na da yake yi su suka taru suka birkita ni. Ko’ina a jikina rawa yake yi, amma a hakan na yi kokarin na bude ido na dube shi don dai ya yarda na amince ba zai cutar da ni din ba. Abin da na hango cikin idanun sa mai girma da zurfi ne da ya shallake tunanin mu. Ai ba shiri na maida idon nawa na lumshe su, shi kuma da wata irin azama ya rungume ni kam-kam a jikin shi. “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel...”. Na furta da karfin da ya sa ba shiri Yaya ya sake ni. Sai na durkushe a wurin na soma kuka. Kukan da ban san dalilin yin sa ba. Na dai san Yaya ya sa mun yi abin da bai dace ba, ya keta alfarmar Ubangiji sabida sakacin sa da gangan. Ina ga mun kwana a daki daya? Ni gabadaya ma ya canza min, kamar ba Maccidon da na sani ba, handsome, giant, mijin Lubabatu. Wannan ya koma Tahir mai shekaru ashirin da biyar ba wanda ya ajiye ‘ya’ya biyu ba. Ganin kukan ba zai kai ni ko’ina ba, don Yaya barin gabana ya yi ya shiga jona kettle zai dafa (gahwah-Al-arabiyyah), bai kara bi ta kaina ba. Jakunkuna na guda biyu na jawo na durfafi kofa, gara in je ko kofar dakin da Addah ke kwance ne in dinga kwana, amma ba da ni za a yi wannan katobarar ba. Tunda dai na rike sunan asibitin magana ta kare. Na murda kofa na sake murdawa, amma ko gezau! Ta ki buduwa. Ban san sanda ya isa ya murza mata mukulli ya zare ba. A jikin kofar na sulale na zauna ina kuka. Kukan da na tabbatar in har da imani a zuciyar sa dole ya tausaya wa halin da na ke ciki. Ilai kuwa kukan nawa ya dame shi. Ya hana shi nutsuwa. Ya ce, “Asma’u ki yi min shiru. Ki bar ganin ina lallaba ki. To me ki ke tunanin zan yi miki in mun kwana daki daya? Ko kuwa kina so ne ki ce min kin san akwai wata mu’amala tsakanin mace da namiji wanda ni ban san shi ba?” Kukana ya makale jin abin da ya ce, in ma ban sani ba ai yau ga shi ya nuna min akwai din. Ya taso ya baro gahwah din da yake sha zuwa inda nake, har yanzu singlet dinsa ce fara kal a jikin shi da dogon wandon kayan da ya cire. Hannu ya miko min ina daga zaune. “Hold my hand and get up!". Ya fada da muryar da na kasa amincewa ta Yaya Maccido ce. Maccidon nan Ma’abocin izza da kasaita a cikin kannen sa, wanda tsakani na da shi sai hange daga nesa. Sai na kasa resisting wannan lallashin nasa. A hankali na sanya hannuna cikin nasa. Ya mikar da ni tsaye ya ja ni zuwa three seater din da ya taso, muka zauna kusa da juna. Shayin gahwah din da ya hada a dan kankanin kofin tangaran din Larabawa ya nufo baki na da shi. Juyar da kai na yi alamar ba zan sha ba. Ci gaba ya yi da shan abin sa, sai da ya gama ya ce. “Now, listen, mu yi magana ta fahimta irin ta Yaya da kanwar sa. Ki lissafo min duk abubuwan da ba kya so a zaman mu, na yi miki alkawarin zan kiyaye. Don gaskiya aljihuna ya yi kasa sosai, ba ni da kudin da zan kama miki wani dakin”. Shiru na yi ina nazarin kalaman sa, babu alamun wasa a fuskar sa, ko da ma can shi ba ma’abocin wasan ba ne. Sai dai na san ya fada ne kawai don ya ji dadin bakin sa, da kuma wani dalili nasa na daban amma ba don bashi da kudin kama min daki ba. Amma da hankalin sa saboda Allah me ya sa zai yi haka? Me ya sa ya san tun farko bai shiryawa tafiyar ba ya dauko ni? Ni ina duba ya kamata ne, ko da nake karama ashe na fi shi hankali. Don dai ni ban taba jin irin wannan katobarar ba. “Ke nake sauraro, ina so zan kwanta”. “Kada ka kuma zuwa kusa da ni, kada ka kara taba ko farce na even by mistake”. Ban san sanda na fadi hakan ba, na manta ko da wa nake magana, tsabar bacin rai yasa na manta wanene Maccido. Ga mamakina murmushi ya yi, ya ce, “Su ke nan sharuddan naki?” Kai na gyada masa. Na ce. “Sauran matsalolin zan san yadda zan yi da kaya na. Ubangiji ya sani ba ni da laifi”. “Consider it done. Don haka kwantar da hankalin ki. I will not dare touch you again. Yanzu mu yi shirin kwanciya kaina ya fara ciwo, kin sa ni magana da yawa”. To amma kwanciyar Yaya za'a yi ta? Gadon dakin guda daya ne. Karasawa na yi na dauki pillow daya na jefa a kan three seater na kwanta, ko kayan jikina ban canza ba. Rana ta farko ke nan tunda na yi wayo da na kwana ba da kayan barci ba. Ina kallon shi ta kasan ido na ya je closet ya canza kayan jikin shi zuwa pajamas bayan ya rage wutar dakin ya bar dim light. “Amma da kin koma gadon ko? Kin bar min nan din wuyan ki zai yi ciwo”. Na dan bude ido na kalli saitin da yake ina auna yadda tsayin shi zai yi occupying three seater, ai kuwa sai dai ya yi ciwon baya. “Na ci kankanta, na bar maka”. Murmushi ya yi mai sauti ya dauko quilt din gadon ya rufa mini. Sannan ya karasa gadon ya kwanta. Da asubah shi ya tashe ni da alama shi har ya dauro alwalla, na je na dauro na zo na same shi bai tayar ba yana jira na. Shi ya ja mu sallar muka yi jam’i cikin daki. Yana gaba na ina bayan sa bayan mun idar. Wata irin nutsuwa da gamsuwa na ji a rai na irin wanda ban taba ji ba a rayuwata, a lokacin da na gabatar da ibadah. Sai na daga hannuwa ina kwararo addu’a na nemawa Addah lafiya dauwamammiya, sannan na yi wa kai na ta gama wa da duniya lafiya. Bayan wannan ba ni da wani buri don ni a rayuwata ban taba hango wa kaina AURE ba, na san ina son yara, amma na mutane, don ni kam ma bana lissafa kaina a sahun mata. Ni din ba kowa ba ce face Asma’u ‘yar Addah, kanwar Nabeelah Maman Aasim, autar Nene Zainabu. Kamar akwai wani exception tsakani na da sauran mata (ni din ban cika mace ba) watakila da na cika mace da wani da namiji ya taba cewa yana sona, bakin jini na kam ya wuce misali. Yau da na kasance kusa da Maccido, cikin wani kyakkyawan yanayi, sai zuciya ta ta karkace, ta zarme, ta soma son kwatanta ni da mata ‘yan uwana, musamman wadanda ke gidan aure, ashe contentment din da suke samu ke nan in suna tare da mazajen su? Gari ya soma haske, ni da Yaya babu wanda ya motsa, muna nan zaune a inda muka yi sallah kowa da irin tunanin da yake yi a zuciyarsa. Wani yanayi ne na nutsuwa da ban san yadda zan kwatantashi ba ban kuma taba tsintar kaina a ciki ba. Bana so ko kuda ya gifta ta gabana don kada ya katse min bakin abubuwan da nake ji a raina. Don kada Yaya ya tashi daga gabana, ji na yi tamkar ya zame min garkuwa daga duk abin da zai iya cutar da ni. Yaya ne ya fara tashi, sabida lokaci ya ja sosai. Toilet ya wuce kai tsaye. Wanka ya shiga, yayin da na soma tattare kayan da suke watse a kasa, na maida dakin neat. Ya fito sanye da rigar tawul ta wanka ya daure igiyar daga tsakiyar cikinsa. Kallo daya na yi masa ban kara marmarin maimaitawa ba domin kuwa kirjinsa na hango wanda ke rufe luf! Cikin lallausar suma baka sidik. Shi ma dai me ya sa yake saka irin wadannan kayan a gabana? Ai bai kamata ba. Ko da yake na dade da fahimtar shi bai san ya kamata ba. Tun da ya farlanta mana zaman daki guda din, da sai ya dau kayan sa a hannu ya shiga toilet ya canza tunda ya ce zaman namu tare ya zama dole. Dan gajeren tsaki na yi hadi da zunburo baki, wanda ban san cewa ya shiga kunnen Yaya ba. Na juya na ba shi baya ganin ya fiddo kaya zai saka. “Are you pouting at me (ni ki ke zumburo wa baki)?” Na yi saurin girgiza kai tare da cewa cikin karkarwar murya, “Amma Yaya sai na ga zai fi dacewa ka dinga saka kaya a toilet”. Ina jin sautin murmushin sa, ya ce, “gashi ni ban iya takura wa kaina ba, ko ba komai na san daga ni sai kanwata a dakin”. Kamar in ce masa, ai ni ba Nabeelah ba ce, sai na yi tunanin zai ja zancen zuwa wata ma’anar daban, don haka na ja baki na na yi shiru. Sai goma na safe muka gama breakfast, wanda aka shigo mana da shi daga hotel din. Yaya ya isa ga madubin dogon yaro yana murza hula a kansa, sai da ya tabbatar ta zauna sosai, sannan ya dauki turarukansa biyu yana fesawa (obsession da oud abyad) da ya saya a nan Jeddah. Ya gama ya juyo inda nake na yi tagumi, domin haka kawai nake fama da yawan faduwar gaba da kasala. “Zan je asibiti Asma’u, daga nan zan je wajen wani abokina a King Abdul-Aziz University, sai wajen azahar zan dawo. Za su shigo miki da abincin rana”. Na marairaice, “Yaya don Allah zan bika, in son sanin halin da Addah ke ciki”. “Ko mun je ba za su bari mu ganta ba, ki yi hakuri ki yi zaman ki. Idan Nabeelah ta zo sai ku dinga zuwa duk inda ku ke so tare. Ba da son raina ba na hakura, na ce, “To ka sayo min KFC”. “Ita kadai?” “Eh”. “To sai na dawo, take care”. Wani irin dadi na ji a raina, ashe haka mata ke ji idan suka samu kulawa ko da ta fatar baki ce daga mazan su? Sai azahar din kuwa ya dawo, ya kawo min KFC mai zafi da Laban mai sanyi. Daga nan ya kara ficewa bai dawo ba sai dare. Yau ma irin kwanjiyar jiya muka yi, ina kan kujera yana tsakiyar gado, ina jin shi yana ta kiraye-kirayen waya da daddare. Ya kira matarsa sun sha hira, amma bai zurfafa hirar ba, sannan ya sassauta kalaman sa. Duk da haka sai na samu kaina da matukar jin haushin Lubabatu, bayan a zahiri ita ya kamata ta ji haushi na ina nan ina more mata miji, har da kwana daki daya da shi babu sidi ba sadada. Idan har ta san muna taren ke nan, na fi kyautata zaton bai gaya mata da ni aka yi tafiyar ba ma, don lafiya-lafiya suke hirarsu. Washegari ya ce min zai je cikin jami’a wajen Musbahu abokinsa, lakcara ne a can. Rokon sa na yi ta yi a kan zan bi shi har dai ya yarda, amma ya ce sai na sa niqaab. Ina ta zumburar baki na sa niqab din muka jera ni da Yaya muka fito. Mai Ajrah ya shigar da mu har cikin King Abdul-Aziz University, daga nan muka taka zuwa ofis din abokin nasa. Mai fara’a da shi, baki mai zubin Mallawa. Ya ce da Yaya, “Maccido yau ba kai ne bakona ba, Madam ce, don haka ita zan fara yi wa barka da zuwa”. Yaya ya ce, “Musbahu ka ki aure ko? Har mun tara yara kana nan a tuzurun ka”. Murmushi ya yi, ya ce, “In za ka ba ni kanwar nan taka me zai hana in biya sadaki kafin ku koma Nigeria?” (Na dage niqaab dina sama don in sha iska shi ne har Musbahu ya ga fuskata). Na juya na kalli Yaya sai na ga duk annurin fuskar sa ya kau, kuma bai bi ta kan zancen Musbahu ba. Tun daga nan in muka hada ido sai ya yi ta dalla min harara. A karshe ma hirar ta ki dadi, ya ce da Musbahu za mu koma, yana so ya shiga asibiti. Tunda muka hawo ajrah Yaya ya soma fada, fada yake yi tamkar ya kai hannun shi jiki na. “Na ce ba za ki biyo ni ba ki ka kafe min kahon naci, ashe don ki zo ki tallata wa maza fuskar ki ne. In ba haka ba me ye na cire niqaabin a gaban maza? Ko an ce da ke in kin yi hakuri har gida Allah ba zai kawo miki mijin aure ba?” Fadan yaya sai ya koma ba ni dariya, amma na san ko giyar wake na sha ban isa na yi ta ba a yadda yake matukar fusacen nan. Kadan ya rage ya kai min mari. Saboda Allah ina ruwana da wani niqaabi ni ba matar kowa ba, ba ‘yar takari ba? Na hadiye dariya ta ban yi ta ba, don na lura ba karamin fusata ya yi ba. Yau ko ‘yar KFC din bai saya mana ba, tunda na bata masa rai. Ya rantse ya sake rantsewa ba zai kuma zuwa ko'ina da ni ba, in dankare a dakin hotel. A hankali cikin ‘yan kwanakin da muka yi tare nake ta fahimtar wane ne Attahir (Maccido)? Sanin da tunda aka haife ni nake zuwa gidan su har rasuwar iyaye na da dawowata gidan su gabadaya ban taba yi masa ba. Na lakance shi, wata irin lakanta da bana jin ko matar shi da ya kwashe shekaru biyar tare da ita ta yi masa irin ta. Na san irin abubuwan amfanin sa kama daga suttura, turare, bath kit (kayan wanka) kayan askinsa (shaving kit) na Arganavita. Na san duk irin abincin da ya fi so da abin shan sa, na san likes and dislikes din sa. Na gane halayen sa ciki da ba. Na lakance shi karshen lakanta, ta yadda na tabbata ranar komawar mu gida tabbas zan kasance cikin kewar sa. A baya ina masa kallon wani mutum mai izza da girman kai, ina masa kallon mai wasu irin baudaddun halaye da suka sha bamban da na mutane. A dan zaman nan namu cikin birnin Jeddah sai na gane Yaya Attahir Maccido yana daga cikin kariman mutane; wato mutane ma’abota kirki da karamci ga duk wanda zama ya hada su da shi na dan lokaci mai tsawo. Babban abin da ke burge ni da Yayan namu shi ne; tsaftarsa, ba ya kwanciya sai ya yi wanka, haka in ya fita ya dawo sai ya yi, in ya sa kaya sau daya ba ya maimaita su sai an wanke an goge. Bai cika sanya kananan kaya ba sai in a gida zai zauna. Kusan kullum cikin shaddoji, voile da yaddidikan filtex masu karshen tsada da aka yi wa dinki tazarce yake rayuwar sa. Dinkunan sa kullum simple, ba'a cika su da ado, amma in ka duba links dinsu za ka samu masu daraja ne sosai. Zan iya kwana in wuni ina fasalta muku wane ne Maccido? Don haka na bar wa mai karatu sauran, ya gane cewa Attahir is classique, perfect, decent and genius. Ta yadda in na zauna sai in yi ta kintace da hasashen Lubabatu wace irin sa’ar zuwa duniya ta yi? Gobe ne Aunty Nabeelah za ta sauka a Jeddah, kuma a gobe ne za a bar mu mu ga Addah, don haka don zumudi yau barci na ragagge ne. Yaya Maccido ko barcin sa ya shaka har da minshari. Tun asubah bayan mun idar da sallah na fada wanka, ganin rawar jikin da nake yau sai ya shiga bata lokaci yana yi min yanga yadda yake so, na ce mu fita tun bakwai sabida Nabeelah sha daya na safe za ta sauka. Tunda akwai tazara tsakanin cikin gari da airport. Yaya Maccido ya ce, tabdi ai shi bacci ma zai koma, sannan sai ya tashi zai yi wanka. Ya shige cikin quilt ya bar ni a zaune kamar na fashe da kuka. Haka na daure na kyale shi na zauna ban da aikin duba agogo ba abinda nake yi. Karfe tara na kure karar talabijin don dai ta tashe shi. Ya tashi yana yamutsa fuska ya shige toilet. Nan ma sai da ya ci rabin awa ya fito ya shiga shiryawa lakakai-lakakai. Na shige cikin duvet yadda nake yi duk lokacin da na fahimci zai canza kaya, tunda shi hakan ba damuwar sa ba ne. Ya dau turare yana fesawa na mike na rataya jaka ta na nufi kofa zan saka takalmi. Amma sai Yaya ya ce, wai shi sai ya karya kumallo. Hawayen da ke makale tun dazu na bari suka zubo kawai. Ya kama baki yana min dariya, wai Nabeelah ko uwata ce sai haka. Ganin na ki zama na babbake a bakin kofa ina ta share hawaye, ya hakura da cin abincin ya zura takalmin shi tare da daukar wayoyin shi guda biyu ya zuba a aljihun shi, ya ce. “Mu je don Allah, kada ki sa ni in kware da wadannan kananan idanun naki”. A Ajrah (taxi) muka tafi filin jirgi bayan ya tabbatar na maka niqaabi sai ka ce mutanen takari. Muna zuwa jirgin wanda ya taso daga Lebanon yana sauka. Sai da aka bata lokaci kafin Aunty Nabeelah ta iske mu, da gudu na sheka na rungume ta. Aasim da ke gefe ya shiga ture ni yana kiran sunan Babar sa. Dariya muka yi, na rusuna na sunkuce shi dan lukuti da shi, kamar ba jaririn da na sha rainon sa ba. Sai Larabci yake yi accent din Lebanon. Yaya ya tura trolley din ta muka nufi inda taxi suke. Yaya da mai Ajrah suna gidan gaba, ni da Aunty Nabeelah da Aasim muna baya, sai kallo na ta ke yi kamar yau ta fara gani na. Tana yi tana murmushi. Wanda na kasa gane ma'anar sa. Na ce, “Aunty, wannan kallon fa?” “Ina kallon yadda kani na ya iya kiwo ne, gabadaya kin yi kyau. Kin zama kamar balarabiyar Maghrib”. Na rufe fuska ina dariya, na ce, “Aunty ai kullum fada muke yi”. Wani takadarin murmushi ta yi, ta ce, “za ku yi mai dalili ne, wannan na rashin dalili ku ke yi”. Ban dai gane abinda Aunty Nabeelah ke nufi da hakan da ta ce ba. Daidai lokacin da muka shiga farfajiyar asibitin Doctor Sulayman Faqeeh. Tun kafin Yaya Maccido ya fito na bude kofar bangare na na fice dauke da Aasim. Ina kallon su suka tsaya gefe suna magana wadda ban san me suke tattaunawa ba. Daga baya suka shigo muka jera gabadaya zuwa dakin V.I.P da aka sake maida Addah. Ina murda kofar dakin gabana ya yi wani irin muguwar yankewa ya fadi, sakamakon kalmar shahada da na jiyo Addah na furtawa cikin wata irin murya da ban taba jinta da ita ba. *TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES* *SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI 07030137870* ```HISABIN NAFS``` (YIWA KAI HISABI) Adda muka taras na zaune a kan gado, jingine da filo sai salati take a fili, salatin da tun daga waje ya tsorata mu, ya sa muka karaso dakin da gudun mu. Na karasa da hanzari na rungume Addah ta. Hawayen farin ciki na zubo min. Farin cikin ganin cewa lafiyar ta kalau. Ga ta zaune akan kafafun ta. Amma tabbas salatin da muka tsinkayo tun daga waje tana rafkawa ya bala'in tsinka mana zuciya dukkan mu. “Ma’u na, Ma’un Addah, sannu da kokari kin ji? Allah ya baki ladan jinya”. “Adda, yau farin ciki zai kashe ni, kin samu lafiya, Allah abin godiya”. Aunty Nabeelah da Yaya Maccido suka karaso gaban gadon, Aasim yana hannun Yaya Maccido, idanun Maccido duk sun raina fata. A sanyaye ya ce, “Addah, sannu da jiki, Allah ya sa kaffara ne, Allah ya kara lafiya”. Ta amsa ba yabo ba fallasa tana mai kawar da kai daga gare shi. Tare da daure fuska. Aunty Nabeelah ta kama hannun Yaya Maccido ta rike cikin nata ta ja shi suka karasa gaban gadon Addah. Su duka biyun suka tsugunna a gaban ta bisa gwiwoyin su. Cikin sanyin murya Nabeelah ta soma magana da tattausar muryar da duk mai imani dole ya tsaya ya saurare ta. “Addah, Maccido ya yi laifi, laifi kan laifi kam ya yi shi. Tun kina alkunya har bacin ran ya fito fili, ya kuma shafi lafiyar ki. Maccido mutum ne dan adam kuma ajizi kamar kowa, wanda bai fi karfin sharrin shaidan da rudin duniya ba, har ma da iblisanci irin na mata. Addah yau ga Maccidon ki a gaban ki, ya kawo kan sa matsayin mai laifi a gare ki, yana mai amsa dukkan laifukan sa. Fatan sa kawai ki yi hakuri ki manta komai, ki yafe masa. Ki kuma ba shi dama ya gyara kurakuren sa. Tun ranar da ya iso ya same ki cikin halin da ki ke ciki, sakamakon wayar da Muhsin ya yi masa, tun kafin lokacin dama yana cikin damuwa da nadamar da ya rasa ta yadda zai bi ya gyara wannan kuskuren na kaurace miki, ya ce shi kansa in za'a kashe shi bai san dalili ba, ya shiga tunanin hanyar da zai wanke zuciyar ki, ya kuma zama kullum ko ba ya nan wani bangare nasa yana tare da ke wanda zai hana ki yin kewar sa da tunanin sa ko iyalin sa. A kan haka ne Maccido ya yanke shawarar auren Ma’u, Asma’un ki….”. Daga ni har Adda da ta sunkuyar da kai a firgice muka dago muka dubi Aunty Nabeelah. Wata irin firgita da ban taba yin irin ta a rayuwa ta ba. Idanu na suka yo waje bakidaya ina son jin ainihin me Aunty Nabeelah ke nufi??? Ba ta damu da reaction din mu ni da Addah ba ta ci gaba da bayanin ta hankali kwance, murmushi dauke bisa kyakkyawar kamilalliyar fuskar ta. "A ranar da ya kira ni ya gaya min, na ce ban yarda ba in har ya san ba son Ma’u yake ba, ya kyale ta a hankali za ta samu mijin ta. Sannan Ma’u yarinya ce ba za ta iya zama da kishiya ba. Balle hamshakiya irin matar sa, wadda uwar sa ma ba ta dauke ta a bakin komai ba. Maccido ya gaya min duka hujjojin sa kuma na amince da su. Ya ce bai zo neman auren Ma’u don ya faranta miki kadai ba, sai don yana bukatar karin auren sabida matsalolin cikin gida da yake fuskanta daga matar sa, sannan ya hanga ya duba babu wadda zai aura ya wanke zuciyar ki, ya yi miki ramakon duk abin da ki ka rasa daga suruka da jikokin da ba a bari kin shaqu da su ba irin ASMA’U. A takaice ma dai a kan karan-kansa yana son ta Addah, tuntuni, tun tana kankanuwa. Lokacin da yake son yin aure bata isa aure ba, shi ya sa ya nemo aure a waje, amma wannan niyyar tana nan cikin ran sa. Na gamsu da dukkan bayanan sa Addah, ya kuma ce min zai dauke ki zuwa asibiti a Jeddah, yana so a daura aure kafin ku tafi don Ma’u ce mai jinyar ki, kuma bai kamata ya tafi da Ma’u irin wannan tafiyar babu aure tsakanin su ba. Na ce hakan ba zai zamo gaggawa ba? Ya ce ai shi so yake duk ranar da ki ka bude ido, ki gan shi da Ma’u matsayin matar sa, watakila ya ci alfarmar hakan ki yafe mishi dimbin laifukan sa gare ki. Adda kin ji yadda muka yi da Maccido. Na amince da duk abin da ya ce, na ce ya je ya samu Baffa Bilya ya gaya masa komai, sai su je Bebeji su nemi Malam Ayuba da ki ke yawan ba ni labari, wanda ki ka ce shi ne aminin Baban Ma’u tun daga kuruciya har girma. Su kai masa sadaki a daura aure. Muhsin shi ya jagoranci su Baba Bilya zuwa Bebeji, ba su sha wahalar samun sa ba duk da ya tsufa, bayani kadan suka yi masa ya sa kukan farin ciki sabida wannan karramawa da suka yi masa na ba shi waliccin auren Ma’u. Shi ya ja su zuwa gidan Hakimin Bebeji ya yi masa bayanin Ma’u, shi ma sosai ya ji dadi, don ya ce Baban Ma’u mutumin sa ne, duk Juma’ah sai ya zo ya gaishe shi. Kasancewar ranar juma’a ce sai Hakimi ya bada sanarwa cewa bayan sallar juma’a akwai daurin auren ‘yar Malam Adamu mai goro. Aka yi daurin auren cikin farin ciki na zukata masu yawa, Baban su Ma’u ya sha yabo da addu’a daga bakin jama’ar garin Bebeji kamar yadda Muhsin ya labarta mini”. Ta sa hannu cikin jakar hannunta ta fiddo wani dan akwati tana murmushi, ta dora wa Addah a kan cinyar ta, “...Addah ga sadakin Ma’u. Muhsin ya gaya mini kin sha ce masa 'sisinan gwal' shi ne sadakin Ma’un ki…”. Ta bude akwatin ta kama tafin hannun Addah ta dora mata. Kuka ne ya kubuce wa Addah Kilishi, ta kamo hannun Nabeelah ta kamo na Maccido ta ja su jikin ta ta rungume su. “Allah ya yi muku albarka baki dayan ku, yau na san na haifi ‘ya’ya, wadanda ko bayan raina za su rike min marainiyar ‘yar dan uwana da amana da daraja da kauna. Barakallahu fi-kum”. Ta sake kecewa da kukan farin ciki. A hankali ba tare da sun ankara ba na dinga ja da baya a hankali, har na bude kofa na fice daga dakin. Da sauri-sauri nake tafiya a gefen titi bana ko ganin gabana, ina tafe ina kuka da hawaye shabe-shabe ban damu in share ba. Ban damu da kallon da mutane suke min ba. Ni na ce ina son Yaya Maccido? Ko kuwa shi ke nan don ya maida ni kaza yana neman hanyar shiryawa da mahaifiyar shi sai ya kare a kaina? Ni me zan ci da mai mata da ‘ya’ya? Allah na tuba kuma mijin Lubabatu? In rasa wanda zan aura in auren zan yi sai ragowar wata? Ai wallahi ko auren zan yi ni ma sai dai na auri yaro, kuma balarabe irin na Aunty Nabeelah… mijina ni ni kadai, ba mijin wata ba. Ban da karya mai mace kamar Lubabatu, me zai ci da ni, in ba yaudara da rainin hankali ba??? Tunanin da nake ta yi ke nan ina tafe ina gursheken kuka, ban ankara ba na ga wata farar ajrah ta sha gabana, saura kadan ta take kafafu na. Yaya Maccido da Nabeelah ne suka bude kofofin motar suka fito suka sha gabana, na dage riga ta zan taka da gudu, Maccido ya damke ni. "Ke kina da hankali kuwa? Ko kin dauka a Nigeria ki ke?” “Daga turu na fito”. Na fada cikin karajin kuka ina fiffizgewa daga hannun sa. Aunty Nabeelah cikin mamaki ta ce, “Ma’u ba za ki nutsu ba? Kina so ki jawo mana jami’an tsaro ne?” Hararar ta na yi da jikakkun idanuna, na ce, “Ai komai ke ce sila, kin bi bayan kanin ki kun zalunce ni, ni na ce miki ina son shi? Akalla a ba ni hakki na na dan Adam a tuntube ni kafin a daura min aure? Ko kuwa don shi shi ne shafaffe da mai, ya gama yi wa Adda cin kashin sa sannan ya zo ya yi abin da yake so a kaina?” Ji ka ke taaas! Yaya Maccido ya dauke ni da wani lafiyayyen mari. Na sa hannu na dafe kunci na ina jin kamar fatar fuskata ta daye. “Ashe ba ki da kunya? Auntyn ki ke gaya wa haka? An aure ki ba da sanin nakin ba, don Allah ki je ki maka ni a kotu a fidda miki hakkin naki”. Na rushe da kuka. “Don an ga ni marainiya ce ba uwa ba uba… wayyo Nene, wayyo Baba…...”. Yaya Maccido bai tsaya sauraro na ba da kwarmaton da nake yi, don har na fara tara musu mutane, ya danna ni a motar da suka zo, Aunty ta shigo mai motar ya ja. Na ga za a wuce asibiti ba su shiga ba na kara rusa kuka. "Ni ku sauke ni wajen Addah, babu ni babu ku. Ai ba zaman ku nake ba”. Aunty dai kallona kawai ta ke tana mamaki, in wani ya ce mata ni ce wannan ba idanun ta ne ya gane mata ba, lallai za ta musa. Ashe haka nake?? Hotel din mu muka nufa, Aunty Nabeelah ta kama hannuna muka fito har zuwa lokacin kuka nake yi wurjanjan. A reception muka jira Yaya Maccido ya je ya kama wa Aunty daki ya dawo muka rankaya ta cikin lifter zuwa sama. Ya bude dakin muka shiga dukkan mu, Aunty ta zaunar da ni a gefen gado. Ta zauna kusa da ni, yayin da Yaya ya tafi kujera ya zauna. Ta kira sunana a tausashe, “Asma’u!”. Ban amsa ba, amma na dago na kalle ta da rinannun idanu na da suka kada suka yi jajawur. “Kina so ki mayar da farin cikin Adda bakin ciki?” Da sauri na girgiza kai ta ce, “To why this? In kin bi komai a hankali ai ni mai yi miki duk abin da ki ke so ce. Maccido bai isa ya shiga tsakanin mu ba, ki kwantar da hankalin ki, ki gaya min duk abin da ki ke so na yi miki alkawarin in bai fi karfin iko na ba zan yi miki”. Ai jin haka na ce, “Aunty kawai ki ce masa ya sake ni, wallahi bana son shi!”. Aunty tana hadiye dariyar da ta zo mata ganin Yaya Maccido ya yi tsumuu! Ta ce, “Saboda me ba kya son nasa?” Babu ko kunya na ce, “Ni me zan yi da shi? Mutumin da matar sa da ‘ya’yan sa watakila ma ya fara furfura”. Duk yadda Aunty ke hadiye dariyar ta sai da ta sake ta wannan karon. Ni kuwa na ci magani, don zuciya ta daya nake magana, ta daura hannunta bisa nawa ta ce, “Ma’u ba kyau cin fuskar miji fa!”. Na zumburo baki na ce, “Kada ki kara cewa miji na, mijin Lubabatu dai, ni me zan ci da shi? Wallahi Balarabe nake so irin naki”. Da sauri yaya Maccido ya mike ya bar dakin, fuskar sa kamar hadarin da ya nausa ya yi gabas. Aunty Nabeelah ta dinga kyalkyala dariya, ta ma rasa me za ta ce mini. Na mike ina fadin, “Aunty tashi raka ni dakin sa in kwaso kayana, da ma kamar a kan kaya nake zaune a dakin. Don ya raina min hankali ya ce ba shi da kudin kama daki biyu, ina ya samo na wanda ya kama wannan?” Aunty ta ce, “Um-umh Ma’u, an dai gama shan soyayya shi ne don an gan ni za a wani ce za'a kwaso kaya? To ba da ni ba, ba ruwana”. Kuka na sa mata da karfi ina fadin, “Ni wallahi babu soyayyar da mukai, kullum fada muke yi! Kuma ba gado daya muke kwana ba”. Ta ce, “Fadan soyayya ba?” Na ce, “Wallahi na kiyayya”. Aunty ta koma serious ta ce, “Ma’u, ki nutsu mu yi maganar fahimta. Maccido yanzu ko kin ki ko kin so mijin ki ne, duk kuma abin da ki ka yi masa na kyautatawa ko akasin ta, mala’iku suna rubutawa. Don haka ki shiga hankalin ki, in ke wata mai wayo ce wannan tafiyar dama ce ki ka samu da za ki mori mijin ki ke kadai, ki shiga jikin sa, ki mantar da shi kowacce diya mace. Amma don sakarci har kin fara zancen a raba daki. Ma’u miji ne Allah ya kashe ya ba ki daga sama don haka kar ki yi wa Allah butulci. Wallahil azeem Maccido na son ki, sai da na shaidi wannan kafin in yarda in shige masa gaba ga auren ki. Ga shi dan uwan ki, wanda ya san ciwon ki, ya san mutuncin iyayen ki. Na miki alkawarin muddin ina raye ba za ki taba da na sanin auren Maccido ba. Ma’u ba kya jin tausayin Addah? Ba za ki so ki zama tsanin da Dan ta zai dawo gare ta ba? Ki haifa mata jikoki ki bata ta raina a daina yi mata rowar ‘ya’yan Maccido? Ma’u in ba ki yi wa Addah wannan aikin ba, wa zai yi mata shi da zuciya daya?” Jiki na ya dan yi sanyi da kalaman Aunty Nabeela. Amma hakan ba zai taba sawa in karbi wannan auren ba. Ta dora hannu a kan kafadata ta ja ni jikin ta a hankali cikin sigar rarrashi. “Maccido abun tausayi ne Ma’u, saura kadan mace ta kai shi wuta. Ki zama mai aikin jihadin ceton soyayyar uwa da Da. Ba ruwan ki da matar sa, tana Abuja kina Sokoto, me zai dame ki da ita?” Zuwa wannan lokacin Aunty Nabeelah ta dan kashe min jiki. Abin da na ki yarda da shi har yanzu shi ne Maccido na so na. Zan yi kokari in gane hakan da kaina komai daren dadewa kafin in yarda da hasashen Aunty Nabeelah. Ta mike ta ce, “Ban zo don in rashe ba, na zo ne don in karbe ki jinya, ke kuma ki yi amarci yadda ya kamata. Mu je toilet da kaina zan yi miki dilka da halawa, sannan in yi miki wankan turaren da na zo da shi takanas, sabida ke”. Duk abin da ta fada din kuwa sai da ta yi min. Ina kumburi ina komai sai kara kwantar min da hankali ta ke yi da tausasan kalami da misalai kala-kala. Ta dauko wasu tablets masu kama da magungunan supplement ta ba ni, ta ce in hadiye su. Sai da ta tsaya a kaina ta mika min ruwa, ta tabbatar na hadiye din. Ta bude jakarta ta fiddo wani lallausan swiss lace da aka yi wa dinki senegalese ta ce su zan sanya, sannan ta sake feshe ni da turare ta yi min daurin kai very cute da shi. Ta ja baya ta kalle ni sosai ta ce, "saura light make up". Dan karamin akwatin kwalliya ta dauko a kayanta ta zaunar da ni a gabanta ta yi min sassaukan make-up. Albarka ta shiga sanya min kamar wata uwa ta sannan ta kama hannu na bayan ta rufa min babban gyale kalar adon leshin ta kira wayar hannun ta. “Kana ina Maccido?". A kasalance ya ba ta amsa, “Ina daki, kaina ke ciwo, sai dare zan maida ku wajen Addah din, may be kafin nan na samu kan ya sarara min”. “Nawa ne lambar dakin naku?” “104”. Daga haka ta maida wayar jakar ta, ta kama hannuna muka fita. *TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES* Ta lifter muka bi zuwa kofar dakin. Ni dai kallon komai nake kamar a majigi. Majigin ma na cikin mafarki. Wai yau ni ce Aunty Nabeelah zata kai dakin miji. Mijin kuma Maccido, Maccidon ma wanda na sani, na yi wa farin sani, wanda a baya ban taba mafarkin wata alaka a tsakanin mu bayan gaisuwa ba. To shi sha’anin Ubangiji haka ya ke. Matar mutum kabarin sa, ashe Allah ya riga ya rubuta min Attahir a matsayin miji, babu makawar hakan komai daren dadewa. Ina wannan tunanin Yaya Maccido ya bude kofar da Aunty ta kwankwasa masa. Yana budewa kuma ya koma ciki ba tare da ya dube mu ba. Wata irin kyakkyawar jallabiya ce a jikinsa kalar coffee, da alama wanka ya sake bayan baro mu da ya yi a masaukin Aunty Nabeelah. Ni da Aunty muka zauna a kan seater yayin da ya koma gefen gado ya zauna ya dafe kansa, da alama a kwance yake kafin shigowar mu, Aunty ta kira sunan sa na yanka, “Attahir, ga amanar kanwa ta Asma’u na kawo maka. Ina rokon Allah ya taya ka riko. Asma’u ga amanar kanina Tahir na damka a hannun ki. Allah ya tallafa miki wajen yi masa biyayya, Ya ba ku zuri’a masu albarka". Hawaye suka gangaro daga idanu na. Na tabbata wata sabuwar rayuwa ce mai cike da kalubale zan fara daga yau, wadda ban san me zan je in tarar a cikin ta ba, ban san ya ta ke ba. Girma ya hau ni, a lokacin da ban shirya masa ba. Kyale hawayen na yi suka yi ta zuba abin su, ba tare da na tare su ba. Ko na share su. Aunty ta mike za ta fita, ai ban san lokacin da ni ma na mike na bi ta ba. Ta dakata ta kama ni tana girgiza min kai, ni ma na shiga girgiza mata. I just cannot, bayan sani da na yi cewa shi din yanzu yana da wani mafificin matsayi a gare ni. “Idan ba za ki zauna a dakin mijin ki ba, gobe zan koma inda na fito in bar muku kasar gabadaya”. Kuka nasa mata, wani irin kuka mai cin rai, wanda ya taho da karfi tun daga karkashin zuciyata, na ce, “Aunty me ya sa za ki min haka? Yaya ne fa, shi din Yaya na ne. Ba zan iya wata rayuwa ta daban da shi ba, bayan wadda muka riga muka taso a cikin ta”. “Ma’u, Allah bai haramta ba, baku sha nono guda ba, na rantse ko ki zauna ko na koma Beirut gobe”. Ina ji ina gani Aunty ta juya ta fita, tunda ta rantse min, na koma jikin kofa na jingina da ita in shesshekar kuka. Yaya ya taso ya rufe kofar dakin da key ko kallo na bai yi ba, ya koma ya kwanta. Ya ja quilt ya kudunduna a cikin sa. Sai da na yi kuka na ma’ishi babu mai lallashi na. Abin da ban sani ba Yaya Maccido ta kansa yake, domin zazzabi ne da ciwon kai suka rufe shi. Ina ji ya dauki waya ya kira Aunty Nabeelah, ya ce ta dauki ajrah ta koma asibiti ba zai iya fitowa ba, kansa ya matsa masa. A daidai lokacin aka kira sallar magriba, Yaya ya mike ya shiga toilet, na yi amfani da wannan damar na tuje daurin da Aunty ta yi min, kwalliyar dama duk ta dame da hawaye da majina. Na san ta yi min su ne don in burge Yaya, ni kuma ban shirya zama matsayin matar sa ba ma, balle in nemi kauna aminci daga gare shi. Ya fito ya shimfida darduma har zai tayar da sallah ya ga ba ni da niyyar tashi anan inda suka barni, sannan sautin kuka na bai bar fita a hankali ba. Yana ci masa rai, yana azabtar da zuciyar sa. Ya dafe goshin sa da hannun daman sa cikin raunin murya ya ce, “Ki yi wa Allah ki yi min shiru, I’m having headache”. Muryar sa kawai na ji na yarda ba shi da lafiya din da gaske. Amma ko kadan ban ji ya ba ni tausayi ba. Tunda kukan ne ba ya so, ni kuma yanzu na fara shi, in yaso in ya gaji ya kira Aunty ta zo ta tafi da ni. Don haka na kara sautin gunjin kuka na ya koma kamar na fitar rai. Takowa ya yi a hankali ya zo har inda nake. Ga dukkan mamakina, hannuna ya ja zuwa three seater, ina tirjewa ina komai, ya zaunar da ni sannan shi ma ya zauna gefe na, kafadun mu na gugar na juna. “Asma’u!”. Yaya Maccido ya kira sunana da tattausar muryar sa da ta gama yin rauni, ga ciwo ga damuwa. “Me ki ke so in yi miki mu zauna lafiya?” As if ba Maccido ke magana ba, the voice is so soft, babu diya macen da bazata tausasawa zuciya ba. Na ja shessheka na fyace hanci na, na ce, “A kan me za ka aure ni ba da sani na ba? Ni kaza ce? Ko kuwa 'yar tsana ce? Ni na ce ina son ka? You are never my choice. Ban taba mafarkin auren mai mata ba. Kana da rayuwar ka inada tawa, don me zaka dauko ni ka tsunduma ni cikin taka ba tare da sani da amincewa ta ba?” Maccido ya zuqi numfashi ya fesar. Ko maganata tayi masa ciwo hakan bai nuna akan kyakkyawar fuskar sa ba, a hankali ya ce. “Na dauka an wuce wannan wurin tuntuni? Tunda aikin gama ya gama? Aure ya riga ya dauru, da amincewar wanin mu ko babu. Neman maslaha ce a gaban mu yanzu?” Shiru na yi masa. Ina tauna maganar tasa a raina. “To in wannan ne laifi na ina ba ki hakuri. Kodayake kin ce ba kya sona ne saboda na miki tsufa, Balarabe ki ke so ko Asma’u? Ni kuma nace mai zai hana ki ba ni dama mu gani ni da Balaraben wa ya fi iya soyayya?" Ya dago habata da hannun daman sa ya dubi yadda hawaye suke gudu akan kunci na, kafin in yi aune na ji taushin bakin Yaya Maccido cikin nawa. Wani irin kissing dina ya shiga yi kamar zai cinye ni, duk hawayen fuskata sai da ya bi su emotionally ya dauke su tas! Babu wata gaba ta jiki na da ba ta amshi sakon sassanyar sensual kiss da Attahir ke aikawa ba. Wani yanayi ne da ban taba tsintar kaina a ciki ba, ban san akwai shi ba. Ban san sanda na lumshe idanu na ba ina jin abinda tun da uwata ta kawo ni duniya ban taba ji ba. Yaya Maccido ya sa hannayen sa duka ya sake rike ni da wani irin riko da na yi tsammanin har abada ba zai sake ni ba. It was kind of gentle romance wanda ya goge duk wata hadda da ke kaina ya soma cusa sababbin karatun da Maccido-Attahir ke kawowa. Kiran sallahr maghriba da aka yi shi ya cece ni daga hannun Yaya, kasancewar sa mai muhimmanta kiran sallah fiye da komai a rayuwar sa, ya bi ni da lumsassun idanun sa wadanda ba sa ko buduwa a wannan lokacin. Mikewa na yi ba tare da na iya hada ido da shi ba sabida kunya da takaicin kaina, na yi toilet na rufe kaina. Na jingina baya na da kofar bandakin ina hawaye. Bakin cikin kaina duk ya kama ni kan yadda na sakarwa Yaya jiki kamar mai zaman jiran hakan daga gare shi. Tabbas in aka ci gaba da irin wannan tafiyar ba za'a je ko’ina ba Attahir zai goge mini lissafin duk da ke kaina, in manta da duk wasu laifuka da nake zargin shi da yi mana ni da Addah. Cikin mutuwar jiki na daura alwala na fito. A kwance na same shi saman gado kafafunsa na kasa. Jin motsi na ya sa ya yunkura ya mike, kallo na ya yi yana murmushi ya ce, “Jira ni in zo mu yi jam’i tunda kin warware min alwalar kin ji dadi”. Ban ce masa komai ba, amma na zauna jiran nasa. Bayan mun idar da sallahr magriba da isha muka yi shafa'i da wutri. Sannan Yaya ya ce, za mu yi wata nafilar raka’a biyu don nema wa auren mu albarka. Tunda ibada ce ai bani da ja. Da muka idar ya gama addu’o’in shi ya ce min zai je downstairs ya samo maganin headache in na ji yunwa in jira shi yanzu zai dawo”. Ko kula shi ban yi ba. Yana fita na sauya kayana zuwa na barci na shige cikin quilt na kudundune. Ba jimawa barci ya yi awon gaba da ni don gabadaya a gajiye nake. Ga kukan dana sha, wanda nima ya sabbaba min ciwon kan. Lokacin da Yaya Maccido ya dawo samu na ya yi ina barci bilhaqqi a kan kujera yadda muka saba. Zama ya yi a gaban kujerar ya dora hannu a kan wuya na da goshi na. Nan ya ji zafin da suka dauka. A hankali na bude ido, sai idanu na cikin na Attahir. “Tashi ki ci abinci”. Ya fada with care. “Bana jin yunwa”. Na ba shi amsa ina mai turo baki, tare da sake lumshe ido na. “To tashi ko Haleeb ki sha, sai ki sha magani, you have some fever and headache kema”. Girgiza masa kai na yi cikin nauyin barci. “Don Allah Yaya ka kyale ni, wallahi na koshi, kuma ni lafiya ta kalau”. Ya rankwafo daidai saitin kunne na. Har ina jin hucin sassanyan numfashin sa. Kasa-kasa ya ce. “To ni kuma ya ya za ki yi da ni Asma’u? Kwana bakwai ko takwas ke nan ina hakuri, ina kauda kai, alhalin na san cewa ina tare da matata ta sunnah ne, halali na. Asma’u I will not force you to be with me, in ba ki amince ba zan hakura, har zuwa lokacin da za ki karbe ni a matsayin miji, koda hakan na nufin zan cutu. Fata na daya ne ki yarda cewa I really love you”. Yadda yake maganar loving and romantic kamar ba Yaya Maccido ba. Da wata irin lallausar murya da na kasa amincewa ta Yayanmu Maccido ce. Maccidon nan ma'abocin kasaita da fadin rai kamar na basarake. Na bude ido a hankali, don dai in tabbatar da wanda nake magana, idanu na suka sauka cikin nasa. Yana durkushe a gabana ina kwance saman kujera. Ko kadan ban ji tausayin shi ba duk da cewa he looked so pale a yanayin da yake maganar. Na ga cewa in nayi wasa, Yaya zai yi galaba a kaina, domin wani sashe na zuciya ta ya fara darsa min tausayin sa, alhalin ko kusa ban yarda da wannan soyayyar tasa ta dare daya ba. Abinda na yarda da shi shine Attahir ya aure ni ne don ya shirya da mahaifiyar sa, ya wanke laifin da yayi mata using me as an instrument, amma ba don so ba. So daya ne, kuma na san matar sa yake wa. Kowa ma shaida ne akan hakan. Cewa yana matukar son Lubabatu ta yadda har ya zabe ta akan mahaifiyar shi. Yana da target din sa na aure na wanda bazan taba amincewa yayi galaba da ni ba. "Yaya in ka sake taba ni, bayan wanda ka yi dazu na kyale ka, wallahi zan haura ta taga in fada in mutu in huta, ya fiye min da in amince ka nakasta min rayuwa. Wallahi ba so na kake ba, ka aureni ne don ka cika burin ran ka, wanda kai kadai ka san shi. Gara in mutu, da in baka abinda kake nema daga gare ni". Na karasa da kuka wurjanjan, Yaya Maccido ya rasa abinda zai ce min, kuma kwarai kalamaina suka yi masa zafi. A sanyaye ya ce. "Na ji Asma'u kuma na gode, amma ki yi min alfarma ki koma gadon, ni ki bar min kujerar. Zan tabbatar miki ban aure ki don abinda kike tunani ba, baki da abinda zaki bani Asma'u, wanda sauran matan duniya dana tsallake su na zabe ki basu da shi. Ki rike duk abinda kike taqama dashi, ki ajiyewa Balarabe. Tashi koma gadon ki bar min kujerar". Wai kuma sai na ji kalaman sa sun min zafi. Kin tashi na yi sai da ya daka min tsawa, na tashi ina cuno baki na koma gadon dakin, gadon da ban taba hawa ba tun zuwan mu sai yau. Ya rage hasken fitila, maimakon ya kwanta kamar yadda na yi tsammani sai naga ya koma gefe ya shimfida darduma ya tada sallah. Yadda ya raba daren bai yi barci ba haka nima, na kwana ina tunanin wannan al'amari mai kama da almara da ya same ni rana daya, "auren Yaya Maccido" tamkar kiftawar ido, wanda ko cikin mafarki, ban taba kawowa rayuwata ba. *TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES* *SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* 07030137870 *SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* *YIWA KAI HISABI* ((13)). Washegari a dakin ban da kuka ba abinda nake yi kwance akan gado. Tun asubah dana yi sallah na koma gado na kudundune na bude sabon shafin kuka, zuciyata ta kasa karbar wanan al'amarin da sauki har zuwa yanzu. A jiya na dauka mafarki nake, idan gari ya waye zan farka in ga ba haka bane. Amma da garin Allah ya waye, na tabbatar babu zancen mafarki cikin aure na da Maccido. Don haka na bude sabon shafin kuka. Har karfe goma na safe ina abu daya, Yaya yana kwance a doguwar kujera yana fama da ciwon kansa da zazzabi. Ya kama kansa bai shiga sha'ani na ba. Ko asibiti yau ya kasa fita. Banza yayi min kamar bai san ina yi ba. Daga ni har shi ba wanda ya dubi abincin karin kumallon da aka kawo mana. Sai wajejen azahar ya ga bani da niyyar tashi balle in yi wanka, ya samu yayi wanka ya shirya amma idanun sa jazur sabida zazzabi da ciwon kai, ya dube ni a wahale da murya mara amo ya ce. "In kin ga dama ki tashi ki shirya mu tafi asibiti, ina jiran ki". Ai jin za'a tafi wajen Addah, nan da nan na mike na fada wanka a gurguje, da na fito ko mai ban shafa ba na zuba Abayat dina baka wuluk na nade kaina da veil din ta, ina so in ce masa na shirya, amma bana so ya ji amon murya ta, ya dauka ko na fara saduda da auren sa ne, yana zaune tallabe da kansa da yake jin kamar zai fice daga gangar jikin sa sabida tsabar ciwo. Ko kadan ban ji tausayin sa ba, a raina nace alhaki na ne ya kama shi yake ta ciwo ba wani abu ba. Shi da kan sa ya fahimci na shirya din ya mike yayi gaba na bi bayan sa. Sanda muka iso Adda na cin abincin ta na musamman wanda asibitin ke bata, Aunty Nabeelah na gefen ta tana yi mata hira suna dariyar su, Aasim na barci a kan kujera. Dukkan su kallon mu suka yi admiringly Aunty na fadin, “Me ku ka zo yi? Ba na ce yau ka bari sai dare ku zo ba?” Yaya ya karasa gaban Addah ya kama hannunta ya sumbata ya ce, “Barka da rana Addah, ya karfin jiki?” “Jiki sai hamdala, kullum lafiya karuwa ta ke, na gode Allah ya yi muku albarka bakidayan ku”. Ya juya ga Aunty ya ce "nima zan ga Doctor ne, shi yasa muka fito, jiya da fever da headache na kwana sosai, amma yanzu da sauki, bari in je in dawo". Ina ta hararar Yaya, amma ya ki yarda ya kalle ni. Aunty ta ce, “ko dan paracetamol baka sha ba?" Ya ce "bana shan magani ban ga likita ba, ina zuwa yanzu". Ya juya ya fita, suka bi shi da kallo fuskokin su dauke da 'yar damuwa. Addah ta juyo gare ni ta ce, “Ma’u dawo nan kusa da ni”. Na koma kusa da Adda na zauna, na ce, “Bari in kira Muhsin ku gaisa Adda, kwana biyu ba mu gaisa da shi ba". Na hau neman waya ta a jaka ta amma sai na tuna na baro ta a daki tana caji. Sai da Yaya ya dawo rike da ledar magungun sa don kada Adda ta fahimci bama magana na yi ta maza na ce. “Yaya ba ni aron wayar ka”. Ba tare da na yarda mun hada ido ba. Ya daga idanunsa da suka kada sabida zafin zazzabi ya dube ni, karo na farko da muka hada ido tun daren jiya, jikina na ji ya yi bala'in sanyi, cikin sanyin murya ya ce. “Ki shafa min maiko?” Da sauri na nuna masa tafukan hannu na. “Allah ka ga hannuna sumul yake”. Addah ta ce, “In za ka ba ta, ka ba ta, bana son jan rai”. Ya ciro ta daga aljihun gaban rigar shi ya miko min. Ina laluben lambar Muhsin kira ya shigo wayar. ‘My Wife’ shi ne sunan da ke yawo a fuskar wayar. Ban san lokacin da na katse kiran ba, aka sake kira na katse shi, haka ta ci gaba da jerawa mijin ta kira ina katsewa babu dalili. Kuma da yake wayar a silent ta ke, Yaya bai san ina yi ba. Ni kaina bansan dalili na na yin hakan ba, ji nayi nan duniya ba wanda nake jin haushi irin Lubabatu. Yaya ya fita don ya nemo mana abinci, na ja gefe na bar Addah da Aunty suna hirar su, na tsinci kadan daga hirar tasu hirar kayan lefe ne da kayan daki da za'a yi min wanda Aunty za ta je Abu-Dhabi ta auno komai zuwa Nigeria. Na shiga gallery din Yaya babu komai sai hoton iyalin sa. Inda na gane shi ba mai yawan daukar hoto ba ne. Duk wani hoto na Lubabatu sai da na goge shi tas, amma ban goge na yaran ba, haka wanda suka dauka shi da ita duk sai da na bi na yi marking na goge tas. Cike da mamakin karfin hali irin nawa. Yaya ya shigo da ledojin abincin 'Mud’am Furouj Faqeeh', Aunty ta karba ta shimfida ledar cin abinci a kasa wadda suke hadowa cikin abincin, ta juye komai bisa ledar ta ce mu zo mu ci mu duka. Ita da ma Addah ba ta cin komai sai wanda aka ba ta a asibiti bisa ka’ida. Muka sauka mu uku muka zauna bisa kilishi muna cin abinci, Addah sai kallon mu ta ke yi zuciyar ta na yi mata dadi. Haka take so ta gan mu, haka take buri. Wato Allah ya hada mata kan marayun ta. Ta roki Allah cikin zuciyar ta ya kara hada kan mu, ya kara soyayya da kaunar juna a tsakanin mu. Aunty ta ce da Addah, “Auren Maccido da Ma’u shi ne YI WA KAI HISABI. Maccido ya yi laifi, kuma ya yi wa kansa hisabi da auren Ma'u. Hisabin da ya yi wa kowa dadi. Allah ya sa albarka a auren ku, Ya kade fitina, Ya hada kan matan ka, Ya ba ka ikon yin adalci a tsakanin su”. Yaya da sauri ya amsa, “Amin-amin Yaya Nabeelah. Kin manta ba ki ce Allah ya kawo wa Addah yara kurkusa ba”. Da sauri na bar cin abincin na sunne kaina cikin gwiwoyi na, Aunty ta harare shi ta ce, “Ai muna da yara, Ihsan da Ahsan, duk da rowar su ku ke yi wa Addah”. Ya ce, “Ai shi ya sa na ce ki yi addu’a Allah ya kawo wadanda za su zauna kusa da ita, har sai tana korar su tana cewa, sun ishe ta”. Addah ta ce, “Ni ba zan taba korar su ba”. Haka suka yi ta hirarsu suna nishadi, Yaya ya sha magungunan sa bayan mun gama cin abinci, na yi addu’a cikin raina, Allah ya sa wannan farin cikin da ke kan fuskokin su ya dore har karshen rayuwar su, don na lura wannan shine farin cikin Addah, wato hadin kan 'ya'yan ta. Tunda Yaya ya dawo sallar isha Addah ta ce mu tashi mu tafi, duk wannan sakewar da ke tsakani na da Addah yanzu ta kau, kunyar ta nake ji sosai. Muka yi musu sallama, sannan muka fito muka tari Ajrah muka koma hotel. Ina tsaye jikin mudubin dogon yaro ina kallon ramar dana yi cikin kwana daya kacal, na ji shi yana waya yana fadin, “Na kashe miki waya? Da yaushe aka yi hakan? To shi ke nan tunda haka kika ce na kashe din, don Allah kada ki fasa tafiyar, dawowa ta kuma babu rana sai uwata ta samu lafiya”. Ya jefa wayar gefe yana tsaki. Sai kuma ya dauko ta ya shiga binciken ta, ya shiga call log din sa, gallery din sa da akwatin sakonninsa nan ya fahimci komai. Kaina a kasa irin na marasa gaskiya na bi ta gaban sa zan wuce, sai ji na yi Yaya ya damko ni, na ce, “Wayyo Allah na, zaka karya ni" Ya ce, “Sannun ki, wato shi ne ki ka hada ni fada da matata ko? Ki ka goge min texts din ta da hotunan ta masu sanyaya min zuciya daga bakaken kalaman ki, bayan ke kin ce ba kya so na? To a wane dalili? Ina son sani". Na yi fuska sosai, sai ka rantse da Allah ba ni na yi ba, nace "a wane dalili kuwa? Kawai gani na yi sun cika wayar ba space. Amma ka yi hakuri, ni daga kai har ita ba kwa gaba na". Wani irin miskilin murumushi Yaya Maccido yayi. Ya girgiza kai yana ta mamaki, wai ‘yar wannan Asma’un ta san kishi, tun yanzu ma ke nan, ranar da suka hadu ashe ya shirya abin da a baya bai taba tunani ba. Bai ce min komai ba ya sake ni yana ta murmushi wanda na kasa gane dalilin yin sa. Irin kwanciyar jiya, ita aka yi yau ma, yana kujera ina gado, ya tada kai da hannayen sa. Ya lumshe ido yana tunanin ta inda zai bullowa wannan hutsuwar Asma'un. *** *** *** Yau ma sai azahar muka shiga asibiti, jikin Addah sai hamdala yau ta sauko daga gadon ta je toilet da kanta, duk da har yanzu a zaune ta ke sallah. Yaya Maccido ya ce da Addah da Aunty tunda jikin Addah ya yi kyau gobe ni da shi za mu tafi ziyarah Madeenah. Za mu yi kwanaki bakwai. Aunty na dariya ta ce, “Ka fadi gaskiya dai, ziyara ko honeymooning?” Ba kunya Yaya Maccido ya ce, “Duka biyun, ai ana jifan tsutsu biyu da dutse daya”. Na dago kai gabana na dukan uku-uku jin abinda Yaya ya ce, bansan sanda na ce "gaskiya Adda ni ba inda zani". Addah ta ce "ba'a kin zuwa Ziyarar Ma'aiki, burin kowanne musulmi kenan, kiyi hakuri ku je". Haka tayi ta lallashi na har na amince zan je amma ta gargadi Yaya kan kada ya takura min kan duk abinda na ce bana so. A daren Yaya da kansa ya hada mana gabadaya kayan mu, don ba lallai in mun dawo mu sake sauka a dakin ba. Yaya Maccido ya yi mana shatar lafiyayyar mota, wadda za ta kai mu har Madeenah. Tafiya zuwa Madeenatul Munawwarah daga birnin Jeddah ba tafiya ce mai sauki ba, mun wuni sur a hanya, sai dai dadin abun akwai mud’ams (gidajen cin abinci) a kan hanya ta yadda matafiyi ba zai jigata ba. Sai dare muka shiga Madinah, yaya Maccido ya kama mana masauki a hotel din Dar At-Taqwa wanda ke kusa da Masjid Al-Nabawy. Ba abin da muka iya sai ramuwar barci sabida gajiya, kasancewar mun yi duk sallolin mu a kan hanya, sai asubah muka taka a kafa zuwa masallaci mai alfarma, muka samu sallar asubah. A kan idona aka bude Raudha na kukkutsa yadda kowa ke yi na gabatar da sallar nafila raka'a biyu. Allah ka kara wa Manzonmu darajah da fadhilah da waseelah, ameen. Kasancewar wajen maza daban na mata daban, ba mu kara haduwa ni da Yaya ba. Sai bayan sallahr azuhur a daki. Ya shigo mana da shinkafa-kaza da juices, laban da haleeb muka ci muka yi kat, sannan ne muka sake wanka muka koma masallaci muka samu sallar la’asar. Karfe hudu da rabi muka koma hotel Yaya ya ce, yanzu za mu kai ziyara ne wurare masu albarka, masu tsohon tarihi a musulunci. Mun je Masjid Quba, Uhud Mountain, Baqi’a, da Masjidil Qiblatayni, sannan muka je Dar Al-madinah Meseum muka ga kayan tarihi. Washegari kuma Yaya ya kai ni shahararren shagon sutturar nan na manya da yara, wato Majma’al Qimmah. A kokarin Yaya na ganin ya faranta min, na daina kumburi da fushin dana ke yi masa ya ce in sayi duk abin da nake so a shagon. Da farko na ce bana son komai, daga baya na yi wani tunani. Kayan yara na fara dauka masu kyau da nagarta, mace da namiji, Ahsan da Ihsan na sai wa, sai kuma Aasim din Aunty Nabeelah. Na daukar wa Muhsin jallabiyyu masu kyau da turare irin wadanda na ga Yaya ya saya yana sakawa. Har Al-Qasim na yi wa tsaraba. Yaya bai san me na debo ba sai da aka zo biyan kudi. Ya ce, “Duk wadannan uban kayan ina za ki kai su?” Nan na dan saki fuska nayi masa bayani, don dai in samu ya biya duka, amma ban gaya masa da na Al-Qasim ba, na ga alama ya ji dadi sosai da tsarabar su Ahsan, amma sai ya ce, “In suka haura kilo din kayan da aka yarje miki ke za ki biya kudin awo ba ruwa na”. Zumburo baki na yi, na ce masa, "na yarda" Tun daga ranar ba mu kara zuwa ko’ina ba sai Masjid Nabawy, kowacce sallahr farillah ba ta wuce mu a masallaci. Zaman mu Madinah kadaran-kadahan tsakani na da Yaya Maccido, duk yadda Yaya ya so ya rarrashe ni ya samu kaina mu shirya mu mori amarcin mu kamar yadda ya zo da niyya na ki yarda da hakan, ba na tashi tada bori da kuka na sai dare ya yi, abinda na san Yaya ba ya so ko kadan, kuma yana kokarin kiyaye umarnin Addah da ta ce kada ya sake ya takura min. Sannan da kokarin sa na son nuna min ba dalilin da yasa ya aure ni kenan ba kamar yadda ya fada min a baya. Shi yasa Yaya ya saka min ido na cigaba da yi masa duk abinda naga dama. Tare da wasu dalilan da dama bayan wadannan, su suka taru suka sa Yaya ya daga min kafa, ya kyale ni bai kara bijiro da neman wani abu da ya danganci aure daga gare ni ba. Duk wani sauke kai da namiji zai iya don ya samu hadin kan matar sa da yake matukar so Yaya Maccido ya yi a Madinah, sai dai ba ya samun martanin komai daga gare ni ko kadan. Banza na ke masa har sai ya gaji ya rabu da ni. Da rana zamu wuni lafiya wataran har 'yar hira ina yarda mu yi, musamman in su Aunty Nabeelah sun bugo waya. Sai dare yayi zaka gane ba masoyan gaske bane, domin kuwa kai da kafa muke kwana, har gobe kallon Yaya Maccido nake matsayin Yaya na yadda yake a baya ba abinda ya canza a idanu na. Kuma na gaya masa, na kara gaya masa ba zan taba son shi ba, so irin na aure, he's never my choice. Balarabe na ke so kuma yaro. Ba zan taba son shi ba. Tun kalamai na suna baiwa Yaya haushi har sun koma bashi dariya, wani lokacin in muna tafiya a cikin gari, ya ga wani kyakkyawan balaraben sai ya ce "Asma'u to ko wannan ya yi? Tunda Maccido bashi da sa'a?" Hararar sa nake kawai in kau da kai, don na lura ya maida ni mahaukaciya. Daga ni har Yaya mun yi sumul a kwanaki bakwai, kamar da ka taba mu jini zai yi tsartuwa, mun zama wanke hannu ka taba, tabbas kasar Saudiyyah rahma ce ga kowanne musulmi. Kwanan mu bakwai muka tattaro kayan mu muka dawo Makkah. Wannan karon a hilton na kusa da haraam Yaya ya kama mana karamin daki kwana uku. Muka sake yin umrah muka yi dawafin godiya ga Allah a bisa duk rahamomin da ya yi mana, muka gode maSa lafiyar da ya dube mu Ya baiwa Addah. Muka kara rokon Sa Ya rufa mana asiri duniya da lahira, Ya dawwamar da mu cikin kwanciyar hankali, arziki da zama lafiya. Mun ziyarci Abraj Al-Bait Towers a Makkah. Kwanan mu uku muka dawo Jeddah, muka samu Addah ta murmure tana harkokin ta kamar bata taba kwanciya ba. Tun daga ranar da muka dawo na ki bin Yaya mu koma masaukin mu nace ni jinya na zo kuma ita zan yi da Addah zan zauna, Addah bata yi wata-wata ba ta ce Yaya ya kyale mata 'yar ta, dama bata shirya tarewa ta nan kusa ba. Yaya Maccido ya yi fushi sosai ya rabu da ni ko dakin ya shigo baya kula ni balle ya kalli inda nake. Wai kuma sai hakan ya soma sanya ni a damuwa. Duk da haka ban bishi ba, na cigaba da zama na wurin Addah. Nabeelah bata ce komai ba. Bayan sati daya da dawowar mu muka soma shirin dawowa gida, bayan an baiwa Addah sallama. Da sharadin zuwa check-up bayan watanni shidda. Saura kwana biyu mu taho Aunty Nabeelah ta koma Beirut. Inda bayan sati biyu za ta tafi Abu-Dhabi ta hado lefena da kayan daki, kamar yadda Yaya ya bata kwangila, sannan ta iske mu a gida da kayan. Adda dai ta ce tarewa ta ba rana ba wata. Ranar laraba ta shekarar dubu biyu da goma (2010) jirgin Emirate ya dawo da mu gida, ta Abuja muka sauka, da Addah cikin koshin lafiya mu kuma cikin kwanciyar hankali. **SADAUKARWA GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES* *SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* *07030137870* * SOKOTO, NIGERIA. Mun dawo mun samu gidan tsaf! Hawwa ta gyare ko’ina, Muhsin da Al-qasim su suka dauko mu daga filin jirgi. Muhsin na ta kururuta tsabar canzawar da muka yi daga mu har Addah. Al-Qasim ya canza min bakidaya domin ko gaisuwa ta da kyar ya amsa, sai da Addah ta ce da shi, “Ana gaishe ka”. Bayan na tabbata ya ji din. Abin bai min dadi ba ko kadan, domin akwai sabo a tsakanin mu a baya. Daga baya na ga to me zai dame ni don Al-Qasim ya ki amsa gaisuwa ta? Ai da da yanzu ba daya ba ne. Ni din yanzu matar aure ce ina da special miji na a gefe. Murmushi na yi wa kai na ni kadai, a rai na na ce "kamar gaske" mijin da ko gaisuwa babu tsakanin mu??? Ni kaina na san ba zan iya cewa bana son Yaya ba, na laluba a fadin kirji na da zuciya ta na rasa space na kiyayyar Maccido, sai dai wani kwantaccen so wanda ban taba sanin da shi ba sai yanzu dana ke da tabbacin ni matar sa ce, domin ba tun yau ba Maccido ke burge ni, na ke yiwa kai na addu'a da fatan samun miji kamar sa. Baya ga laifin da ya yi min na aure na ba da sani da amincewa ta ba, na kasa manta biris din da yayi da Adda akan mace, duk da ita ta yafe masa suna sabgar su ta Da da uwa kamar da. Sannan wani irin kishi ke nukurkusa ta a kan Maccido, wanda ban taba sanin ina da shi ba, sai yanzu da ya zama miji na na zama matar sa. Kishin Lubabatu! Tunda kuwa ta riga ni mallakar Attahir da komai nasa. Ta riga ni haifa mishi 'ya'ya, shi yasa na tattara kishin hakan da haushin hakan da bacin rai na duka na dora akan Maccidon, ta sigar kafewa akan ni bana son shi ko kadan. A ranar da muka dawo da daddare bayan mun ci abincin da Hawwa ta tanadar mana Yaya ya dube ni kadan ta kasan ido ina zaune jikin Addah. Ya ce. “Asma’u, dauki kayan mu ki shigar da su sassan mu, da wuri zan kwanta, don gobe sammako zan yi zuwa Abuja, ayyuka sun tarar min fiye da kima, ga wadancan sun dame ni da waya”. Na gane matar sa yake nufi, ban ce komai ba na yunkura da nufin daukar babbar jakar sa. Addah ta ce, “Ke Ma'u, koma ki zauna, in ga kafar ki ta taka sassan nan, sai ran ki ya baci. Babu wanda ya san da auran ku, ba'a yi miki jere ba, ba'a shirya ki ba, ba a raka ki gidan miji ba, kawai sai ki kwashi jiki ki shiga dakin miji don ke akuya ce ko? Ko don kin ga na bar ki kin bi shi Madinah? Wannan ai ibadah ce, ba kuma wanda ya isa ya hana ibadah musaman ta hajji da umarah”. Na koma na zauna cike da kunya ina fadin, “Da ma fa kayan zan kai masa kawai Adda ba zama zan yi ba”. Addah ta harare ni, “Sannu tattabara sarkin soyayya, Muhsin ya kai masa, ke da shiga sassan nan sai Nabeelah ta dawo, ta yi miki jere. Mun shaidawa 'yan uwa da abokan arziki auren ku. An yi ko walima ce. Wuce daki na ki kwanta kafin in bata miki rai”. Ta gaban Yaya Maccido na wuce ina zumburo baki, Adda bata yi min adalci ba, ni kwata-kwata ba nufi na kenan ba, na yi niyyar kai masa kayan ne ma albarkacin idon ta, kada ta gane ba wani shiri tsakanin mu, ba nufi na in tare dakin Yaya ba, ina ganin yadda ya sunkuyar da kai, na wuce, ya bi ni da kallo, a karo na farko duk sai ya ba ni tausayi. Addah ma ba ta wani jima ba ta shigo, sabida duk a gajiye muke. Muna shirin kwanciya Yaya Maccido ya kara shigowa, daga bakin kofa ya tsaya hannayen sa cikin aljihu, fuskar sa dauke da damuwa tsantsa domin shi yau ya shirya angoncewa. Bai taba tsammanin hukuncin da Addah zata yi kenan ba, Allah ya gani ya yi hakurin da ba duk maza ne zasu iya ba. Amma Addah na kokarin karya masa juriyar sa. Da ya san hukuncin da zata yi kenan, ai da bai yi hakurin da ya yi ta yi ba. “Asmau ina ki ka saka min cajar waya ta ne?” Ya fada daga bakin kofa hannayen sa zube cikin aljihu, looking upset. Na rasa wacce cajar waya yake nufi, don ni ban dauka ba, don haka na ce, “Ka duba cikin karamar trolley din ka, can na zuba komai". Ya ce, “Ni ban san wata karamar trolley ba, in za ki dauko ki dauko min, ina falo”. Addah ta ce, “Maccido ko ka fi kowa naci, yau ba kai ba hada daki da Ma’u, ka bace min da gani ko in sabar muku dukkanin ku”. Cikin kunkuni ya ce, “Haba Addah? Daga neman charger? Na tafi ku kwana lafiya. Ba nufi na kenan ba". Addah ta yi murmushi ta ce, “Allah ya tashe mu lafiya”. Sosai Yaya Maccido ya shaqa, yayi fushi sosai, ya juya yana fadin, “Na tafi Addah, ki yi ta ajiyar 'yar ki a daki, in na ga ta uku sai in kara, tunda Allah ya bani dama”. Ta kara sakin murmushi ta ce, “ko biyu ne ma ka karo, ni dai tunda Ma'u na ta shiga, kowa ma kake so kayi ta kawowa’. Attahir ya dago lumsassun idanun sa muka hada ido, ya sakar min harara ganin ina dariyar su ciki-ciki, bayan shi ya fada ne don mu ji haushi ni da Addah, yayin da ni kuma na lumshe masa nawa idanun cikin wata irin siga wanda bansan lokacin da na yi hakan ba... Da sauri ya juya ya fice ya bar dakin. Washegari tun kan mu tashi Yaya da Al-Qasim wanda zai tuka shi sun yi sammako sun kama hanyar Abuja. Da kayan mu suka iso na ba wa Muhsin tsarabar sa tare da ta Al-Qasim, na ce, “Ni na rasa abin da na yi wa Al-Qasim tunda muka dawo ba ya yarda mu gaisa”. Muhsin ya dinga kyalkyala dariya, ya ce, “Kishi ya ke Ogan sa ya kasa shi. Wai ke kina nufin ba ki taba sanin Al-Qasim son ki ya ke yi ba?” Baki sake na ke kallon Muhsin, "So? Wane irin so?” Ya ce, “So na aure, so na soyayya. Ya dade yana son ki, ya gama burin auren ki, ya jinkirta ne zuwa ki gama lesson din ki ki sake waec don kar ya raba miki hankali. Sai kawai ga wannan sharp-shooter din ya zo rana daya ya yi masa kamshin mutuwa ya sure ki kamar kiftawar ido, kin ga ko ai dole ya yi kishi”. Mamaki ya hana ni cewa komai, don dai ni ko da wasa ban taba kawo hakan a raina ba, kuma ban taba ganin wata alama daga gare shi mai nuna hakan ba. Sai na ji tausayin shi ya kama ni, na ce, “Muhsin zan masa addu’a Allah ya ba shi wadda ta fi ni, kuma don Allah ka ba shi wannan tsarabar. Ba zan taba mancewa da taimakon da ya yi min ba a rayuwa, shi ne silar da na fara gane karatu, har na yi developing hope a cikinsa. Shi din mutumin kirki ne ko don yadda yake kula da Adda da komai na gidan nan. Da ina da kanwa da na ba shi”. Muhsin ya ce, “A kunnen Yaya”. Na ce, “Ka yi sauri kada kuda ya riga ka, in ya kore shi ai komai kanka zai dawo. Yanzu kuwa ka samu kana karatun ka a nutse babu stress a kan ka”. Tun tafiyar Yaya na koma ba fuss ba ass! Ban san na saba da shi ba, ban san na shaqu da shi ba, ban san zan yi kewar sa ba, bansan soyayyar sa ta shige ni a dan zamqn da muka yi tare a Jeddah ba sai da ya tafi ya bar ni. Ya kuma daina kira na. Duk na zama wata irin sukuku! Soyayyar Yaya Maccido sai kara shiga ruhi na ta ke a hankali tana kassara ni, tana karar da kuzari na, tana tafiyar da duk wata walwala ta a cikin gida. Adda ta kasa gane kaina, tambayar duniyar nan ta yi na ce ni ba abinda ke damu na, akai-akai ina ji yana kiran Addah amma ni ko sau daya bai kira ni ba. Wannan abu ya dame ni matuka. Wani lokacin sai na dauki waya da niyyar kiran sa sai in fasa, gudun ko yana tare da matar sa. Yau ma ina zaune gefen Addah ina cin abincin dare Yaya ya kira wayar Addah, ina ji suka gaisa suka cigaba da hira, har suka yi sallama ban ji Yaya ya neme ni ba, itama Addah bata ce gani a kusa ba. Hawaye ne na ji zasu bada ni, don haka na tsame hannu na daga cikin tuwon na mike na yi uwardakin Addah, kwanciya na yi rigingine akan gadon Addah ina hawaye, zuciyata na wani irin suya. Ban ji shigowar Addah da zaman ta a gefe na ba, sai sunana da na ji ta kira. "Ma'u me yake damun ki? Duka a kwanakin nan ina lura da ke cikin damuwa kike" "babu komai Addah kai na ne kawai yake ciwo" murmushi Addah ta yi, ga mamaki na sai cewa ta yi "in shi bai kira ki ba, ke ba saivki kira shi ba? Ba mijin ki ba ne? Maccido tun yana yaro mai son kulawa ne, mai son a bashi girma, sai kin tashi tsaye sosai wajen kula da shi, in ba haka ba zaki sha wahalar sa. Ungo nan kira shi da kan ki ki gaishe shi" ta miko min wayar ta. Girgiza kai na yi "Addah in yana kusa da matar sa fa? Kika sani ko ya gaya mata auren mu ko bai fada ba? Bana so in ja masa matsala" Addah ta daure fuska sosai ta ce "na ce ki kira shi, kada ki yi musu da ni Ma'u". A sanyaye na karbi wayar daga hannun Addah, bata bar wajen ba sai da ta tabbatar na kira lambar Yaya har ta fara ringing. Kayan sallahr ta ta dauka ta bar dakin. Ga dai waya ta shiga, kuma Yaya Maccido ya dauka, amma sai na kasa magana. Shi da kan sa ya gaji da shirun ya gane ba Adda ba ce ni ce, ya ce "Asma'u yau kin tuno ni?" Hawaye suka ciko ido na, na ce "kullum ma ina tuna ka" "ban yarda ba Asma'u, da kina tuna ni da kin neme ni, you don't care for me anymore. Duk a cikin rashin son ne? Ranar da zan taho ko sallama baki zo mun yi ba, duk yadda zan yi in ja ki a jiki don ki sake da ni ki kuma karbe ni a matsayin miji na yi Asma'u, ban san me ya sa ba kyaso na ba". Hawayen dake cike a idona suka idasa gangarowa akan kundukuki na, sabida yadda Yaya Maccido ya ke maganar, dole ya raunata zuciyar diya mace, balle mai saurin kuka iri na, da kyar na iya cewa "Yaya ni ban fada ba...." "kin fada Asma'u, ba sau daya ba ba sau biyu ba akan ido na, ba kya so na balarabe kike so, kuma na yi miki tsufa, hmmm, Nabeelah ma shaida ce kan kin fadi hakan" "ka yi hakuri Yaya na tuba, wasa nake yi, na tuba na bi Allah na bi ka". Dariya ya yi ya ce "baki duba kan nawa kin gani ba fa ko akwai furfura ko babu, kike saurin janye maganar ki. Ni dai na san ina son Asma'u, ko ita tafi kowa tsufa a duniya. Zan tabbatar miki da hakan duk ranar da kika bani dama". Zuciya ta ta yi wani irin sanyi daga kuncin da ta ke ciki a baya, sakamakon kalaman Yaya Maccido "amma Yaya me ya sa ba ka kira na? Tunda ka tafi ko sau daya baka kira ni ba" na fada cikin shagwabar da ban san ina da ita ba. Yaya ya ce "because i want to confirm if you care for me or not, yanzun ma ban tabbatar da hakan ba idan ba na gani a zahiri ba" "me zan yi Yaya ka yarda na damu da kai fiye da yadda kake tsammani?" "Ki yarda ki tare a dakin ki da zarar na zo, shine kawai zai tabbatar min kin damu da ni Asma'u, kin kuma karbe ni a matsayin mijin da Allah ya zaba miki, kin san na yi hakuri ko? Hakurin da maza da dama iri na ba za su iya ba". Kunya ce ta kama ni na kai tafin hannu na na rufe fuskata tamkar Maccido yana gaba na. Domin na gane hakurin da yake nufi ya yi, Nace "Yaya ni ba ruwa na sai abinda Addah ta ce" "ai na san bakin ku daya ke da Addar taki, duk cikin ku babu mai tausayi na, shikenan, kada ku zarge ni in na nemo mata ta uku". Wani dunkulallen abu ne ya zo ya tsaya min a kahon zucci, wuta ta dauke min, nace "Yaya....." "ki bar ce min Yayan nan, ni ba Yayan ki bane yanzu, nafi so na ji kin ce Maccido" "bazan iya ba Yaya, because i respect you much,..... don Allah kada ka kara zancen auren nan....zuciya ta za ta buga Yaya!" Ina jiyo sautin murmushin Maccido, "Then sai kiyi kokari ki zama cikakkiyar matar aure in ba haka ba aure ba fashi, ba daya ba har biyu. Na yi aure don ina bukatar kara aure amma sai gasa ni kuke Asma'u, yaya kike so in yi da rai na?" Murya ta na rawa na ce "Yaya in ka daina maganar kara aure ko me kake so zan yi maka" Yaya Maccido yayi murmushin da na jiyo tashin sa cikin wayar ya ce "promise?" "Yes, i promised" "to ki shirya min tarba ta musamman, ranar Juma'a ina tafe insha Allah" "Allah ya kawo ka lafiya Yaya" "call me Maccido, ko sau daya ne please Asma'u" na kai tafukana na rufe fuskata, wani irin feelings na fizgar zuciyata zuwa gare shi, "ba zan iya ba Yaya, don Allah ka yi hakuri" "ban yi hakurin ba Asma'u, na bi ki bashi, idan nazo sai kin fadi 'Maccido' a kunne na na ji" "na yi alkawari Yaya in ka zo ga ni ga ka zan fada" duk dai don in samu ya zo din, na yi kewar sa yadda harshe na ba zai iya bayyanawa ba. Yaya Maccido ya ce "kina ta daukar alkawarin da ba zaki iya cikawa ba, first of all kin yi alkawarin yi min duk abinda na ke so, sannan kin yi alkawarin zaki kira ni da sunana a gabana. Well, don ke zan kamo hanya Asma'u don haka i expect a very warm reception from you" Murmushi na yi na canza position din rikon wayar daga dama zuwa hagu, ji nake tamkar in shiga cikin wayar in tadda Attahir, gaskiyar sa ne ina ta daukan alkawarurrukan da bani da tabbacin zan iya cika su ga ni ga shi, yanzu ma don ba na ganin sa ne. Shigowar Addah ya sa nayi maza na kashe wayar ba tare da mun yi sallama da Yaya ba, ban gayawa Addah Yaya ya ce zai zo Juma'ah ba sabida kunya. Addah ta ce "Ma'u kashe wayar nan haka ki je ki kwanta, Allah ya tashe mu lfy". Da wani matsanancin farin-ciki na kwana yau. Kwana na yi da tunanin Yayana-Mijina Attahir, yau na tabbata nima ina daga cikin mata masu sa'ar zuwa duniya, ban rako sauran mata ba kamar yadda a da nake tsammani. Washegari da safe muna karyawa ni da Addah a dining Al-Qasim ya shigo gidan, ya dau wanka da karin hula kamar yadda ya saba, gaban Addah ya zo ya tsugunna ya gaishe ta, Adda ta amsa cikin far'a tareda yi masa tayin kosai da kunun da muke sha, ya dauki kosai daya a warmer ya kai bakin sa. Na ce "Yaya Al-Qasim ina kwana?" Bai juyo ya dube ni ba ya amsa ciki-ciki. Sannan ya fadawa Adda sakon da ya kawo shi. Ya bata wasu kudade masu yawa cikin leda da ya karbo mata daga banki yayi mana sallama ba tare da ya ko dubi sashen da na ke ba ya fita. A rai na nace "ka mutu da bakin ran ka, ni bani da case da kai". A daren ranar ma raba dare muka yi muna hira ni da Yaya. Wani abun in ya fada kamar in nitse kasa don kunya. A rai na in yi ta mamaki har in tambayi kai na anya Maccido ne wannan? Cikin kwanaki biyun nan Yaya Maccido ya bi ya sukurkuta ni da soyayyar sa, ba abinda na ke so irin in bude ido in gan shi gabana. Amma na san ganin nasa shine abu mafi wahala gare ni a halin yanzu, bani da idon da zan dubi Yaya Maccido, idan na tuna irin hirarrakin da ke fita daga bakin sa. Washegari Juma'ah har karfe goma na safe ban fita falo ba, Adda ta aiko Hawwa kira na in karya kumallo har sau biyu ina cewa gani nan, amma ko motsawa daga bargo na na kasa. Fargaba ce fal a rai na game da zuwan Yaya don na san na yi masa alkawarirrikan da na san bazan iya cikawa ba. Kuma na san rigima ce kawai za ta kawo shi. Wajejen karfe sha daya Adda ta shigo har dakin da kanta ta same ni, tace "Ma'u lafiyar ki kuwa? Kin san Maccido na hanya shine tun jiya baki sanar da ni ba?" Kara shigewa na yi cikin bargo na nace "ni ban sani ba Adda". Harara ta tayi ta ce "kada ki sani din, ki tashi a bargon nan haka ki nemar masa abinda zai ci, kin san ba ya son abincin 'yan aiki ni kuma yau ba dadin jiki na nake ji ba" cike da fargaba na bude bargon na ce "Adda ina ke miki ciwo?" In da abun da ke daga min hankali a duniya, to ciwon Adda ne. Ko da kuwa na farce ne. Adda ta ce "ba wani abu bane babba, dan zazzabi nake ji, amma na yi wa Al-Qasim waya zai taho min da magani anjima". Ta juya ta fita tana fadin "na fada miki ki bar gadon nan haka ki tashi ki nemar masa abin da zai ci, ki kuma nemi wani abu ki sa a cikin ki". Tsaye nake jikin island din kicin ina tunanin me zan dafawa Yaya? A karshe na yanke shawarar gasa masa kifi manyan karfasa da Al-Qasim ya kawo jiya, nan na soma hada spices din cire karni da kayan hadin da zan wa kifin, sannan na dora ruwan zafi a wuta da nufin in yi masa tuwon acca da miyar egusi. Aikin da ya dauke ni awanni biyu, sannan ne na samu na yi wanka, na ci abinci, sassaukar kwalliya na yi don kada Adda ta gane ina dokin zuwan Yaya Maccido a yau fiye da kowacce rana a rayuwa ta. *TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES* *SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* 07030137870 Maccido-Tahir ba shi ya iso ba sai gefen magriba, ya shigo a gajiye likis rataye da babbar rigar sa da wayoyin sa biyu a hannun sa. Tun da naji muryar sa na kule a uwar dakin Adda amma har can sassanyan masculine turaren sa obsession ya bi ni yana sanar da ni zuwan sa. Duk abin da suke fadi shi da Adda ina ji, hirar iyalin sa suke yi da hirar 'Maccido Mall' na Abuja da plaza din sa. Yana gaya mata irin nasarorin da ake ta samu da kalubalen da suke fuskanta. Ko motsi na Maccido bai ji a gidan nan ba don haka sai zuba ido yake yi don ganin ta inda zan bullo, amma ya yi kawaici bai tambayi Adda ba har lokacin sallah yayi duk suka tashi daga hirar, ya fita masallaci Adda kuma ta shigo dakin don ta daura alwalla a toilet din ta da ke cikin dakin. Nan ta same ni a kwance bisa gadon ta, ta ce "amma Ma'u an yi shashasha, yanzu mijin na ki ya kamo hanya tun daga Abuja har Sokoto saboda ke, shine kika buya uwar daki? To abincin wa zai kai masa?" Na mike daga kwanciyar na ce "Adda ni ba waje na ya zo ba fa, abincin yana dining na ajiye tun dazu" Adda ta ce "wannan kandararren girkin naki? Maccido ba zai ci shi ba, gara ki je ki dumama masa a microwave, na tabbata a haka kika ajiye shi" na fita ina fadin "toh Adda zan dumama, amma sai na yi sallah". Da na idar da sallah na kwashe abincin nayi kitchen na kunna na'urar dumama abinci, ba jimawa na gama na mayar dining. Ina kokarin barin bangaren cin abincin Yaya Maccido ya shigo falon. Wata irin kunya ce ta kama ni kamar in narke a gun, kamar yau na fara ganin Maccido, na yi kasa da kai, ban san yaushe Yaya ya tako ya iso gaba na ba. Ratar da ke tsakanin mu bai fi taku biyu ba. Ya kira suna na a hankali "Asma'u" amma na kasa dagowa. Hannu ya sa ya dago haba ta ban san sanda na rufe idanu na ba. "Me zan samu Asma'u ga ni na zo? Kin sani kuma sabida ke na zo? Ina alkawarin mu?" Motsin kofa muka ji duk muka juya a tare, Al-Qasim ne ya shigo da sauri ya koma yana fadin "excuse me please......". Yaya ya yi murmushi ya ja hannu na muka bar falon zuwa daki na. Rufe kofar yayi da mukullin dake jikin ta ya ja ni muka zauna a gefen gado na. Ni dai iya abinda zan iya tantancewa kenan sai tsintar kaina nayi a hannun Yaya Maccido yana sarrafa ni duk ta yadda ya ke so. Al'amuran na Yaya sai gaba suke yi suna kara rikita duk wata nutsuwa da na mallaka. Kwata-kwata ya manta a inda muke waje ne da kowanne lokaci Adda ke iya shigowa. Ilai kuwa ba'a jima ba Adda ta soma kwankwasa kofar dakin tana kiran suna na. Ba karamin rudewa nayi ba na kwace kai na daga hannun Yaya. A hankali ya ce "relax Asma'u, Adda ta san kina tare da mijin ki ne, ki nutsu ki kwantar da hankalin ki" Ina! Mikewa na yi jiki na rawa har sai da na baiwa Maccido dariya. Da gudu na shige toilet don bazan iya facing Adda ba despite all those hot kisses daga Dan ta Maccido. Gani na ke kamar da ta ganni zata hango abinda ya faru. Shi kuwa Yayan kansa tsaye ya karasa ya bude kofar. Hararar sa Adda ta yi sannan ta ce "turomin Ma'un" daga haka ta bar bakin kofar. Da kuka na fito ina fadin "Yaya me yasa ka shigo min daki? Yanzu da wane ido zan dubi Adda?" Dariya sosai na bashi ya kwaikwayi murya ta ya ce "da idon da kika sanya mata Da a daki kina ta sumbata" na kara rushewa da kuka, Yaya ya janyo ni a hankali ya sanya cikin jikin sa, ya lullube ni da tsayi da fadin sa. Ya dora habar sa tsakiyar kaina. A hankali ya ke bubbuga baya na da hannun sa, ya ce. "Ban san me Adda ke nufi da ni ba, ta ce sai ta ga dama zaki tare, ni kuma hakuri na ya kare Asma'u" zamewa na yi daga jikin sa zan fice da sauri har ina tuntube. Kunya kamar in yi yaya. Da sauri Yaya Maccido ya sha gaba na, looking at me affectionately. "Ina alkawarin da mu kai na cewa in na zo za ki ce min Maccido?" Tafuka na nasa na rufe fuska ta ga hawaye shabe-shabe "don Allah Yaya ka yi hakuri" ya ce " ai baki isa ba, ba ki zuwa ko nan da can sai kin cika alkawarin nan, Maccido ko Attahir, sai kin fadi guda daya". Ganin da gaske Yaya ya ke bazai barni in fita ba ga Adda na can tana jira na dole na runtse ido na ce "Attahir, ka bude min kofa in fita" da murmushi mai kyau Yaya ya ke kallo na kafin ya ce "saura daya alkawarin". Zaro ido na yi waje don na tuna alkawarin da na yi masa, wanda giyar so ta kwashe ni na yi masa a waya wanda sirri ne a tsakanin mu, bayan kuma alkawari ne dana san bazan taba iya cika shi ba. Ina ji ina gani Yaya ya cigaba da hargitsa duniya ta yadda ya ke so ya ke muradi da wata irin zazzafar soyayya. Ya dauke ni ya shilla a duniyar da shi kadai ya san irin ta. Al'amarin da ya dauke mu lokaci mai tsaho. Gabadaya mun manta da kiran Adda, itama bata kara zuwa ba, amma tana can cike da fargaba da tsoro, tsoron kada Attahir ya tabbatar da auren sa gaban ta. Ta dade da fahimtar ba wani abu da ya shiga tsakaninmu a Jeddah, haka har muka je Madinah muka dawo. Soyayyah ce 'yar usli mai tsafta Attahir ke gwadawa Ma'u, soyayyar da ya tabbatar wata diya mace bata taba samu daga gare shi ba. Shi da kansa ya ankarar da kan sa cewa... this is not the right place.... and not the right time... dole ya kyale ni na fita wajen Addah duk ba cikin nutsuwa ta ba. Kallo daya ta yi min ta dauke kanta tace in je in yi serving Yaya abinci tun da ya iso bai ci komai ba, daga haka ta bar mana falon da ta ga Yaya Maccido na fitowa shima. Adda na shiga dakin ta Aunty Nabeelah ta kira, ta ce ta zo haka su yi shirin tarewar Ma'u. Ita bazata iya da mu ba. Attahir ya zo muna ta mata rashin kunya a gida, Aunty ta yi dariya sosai ta ce insha Allah tana tafe sati mai zuwa. Yaya na gama cin abinci Al-Qasim yayi sallama kan sa a kasa. "Come and join us" inji Yaya. Sosa kai ya shiga yi cike da kunyar abinda idanun sa suka gane masa dazu "I'm okey Master". Yaya ya goge bakin sa da tissue ya mike ya dube ni na sunkuyar da kai, ya ce. "Zan ga Al-Qasim ki shiga daga ciki". Har karfe goma na dare suna tare a falon suna lissafe-lissafe da kasafce-kasafcen su cikin kwamfuta. Da barci ya fara fizga ta Yaya bai shigo ba na mike na ce "Adda zan je in kwanta barci nake ji". Gadon ta ta nuna min "yi a nan, yau anan za ki kwana". Ban gane hausar Adda ba sai da Yaya Maccido ya zo yana yi mata sallama zai je ya huta, ya ce "Asma'u har ta koma dakin ta ta kwanta ne?" Adda ta yi fuska ta ce tana cikin daki na tana barci" Yaya ya tsaya ya kasa tafiya, ta sake hade fuska ta ce "wani abu?" Da sauri ya juya yana fadin "mu kwana lafiya Adda, dama sako zan bata" Adda tayi murmushi ta ce "da safe ka bata". A zuciyar ta ta ce "ba dai a gabana ba, ka yi hakuri har in kawo maka ita". Ina ganin kiran Yaya nata shigowa na ki dagawa sabida kunyar Adda. Washegari Yaya da fushi ya shigo gidan, da na gaishe shi sama-sama ya amsa, Adda ta yi masa tayin karin kumallo ya ce ba yanzu ba. Daga baya ya kira Al-Qasim ya zo ya dauke shi suka tafi mall. Bai dawo ba sai can yamma. Ya same mu nida Adda muna girkin dare a kicin. A jikin cabinet din kicin din ya tsaya fuska a daure ya ce "Adda sannu da gida" ta ce "kai kuma sannu da yawo ba ci ba sha. Ma'u shirya masa abincin gashi har na rana ya kusa tadda na dare" juyar da kai yayi gefe ya ce da Adda "ni ba na jin yunwa, gobe da sassafe zan wuce Adda saboda Monday in shiga ofis akan lokaci". Adda ta ce. "Allah ya kai mu lafiya". Zuciyata ta yi ba dadi da biris din da Yaya yayi da ni, da kuma jin gobe zai koma. A sanyaye na ce "sannu da dawowa Yaya". Harara ta ya yi ya bar kicin din, Adda tace "wuce ki bishi falo ku gaisa sosai ki bar min aikin, na ga alama fushi ya ke yi, ban san tsakanin ni da ke wa ya yi laifin ba". Murmushi na yi. Na wanke hannu na a sink na tsane da karamin tawul, sannan na bi bayan Yaya. Ban same shi a falo ba, haka dakin Adda na duba ban gan shi ba. Kwata-kwata ban kawo yana daki na ba, na shiga kai na tsaye da niyyar in dauki waya in kira shi inji inda ya ke. Anan na sameshi zaune bakin gado na ya hada tagumi da hannuwa bibbiyu. A hankali na taka na isa kusa da shi na zauna. Lokacin da ya juyo muka hada ido, sai da zuciyata ta girgiza da abinda na hango cikin idanun sa. It's nothing but pure love wanda babu surki a cikin sa. Gabadaya ya kara rikita mu daga ni har shi da deep kisses din sa masu tsayawa a zuci. Al'amuran sa masu ban mamaki ne. Ban iya fadin halin da Yaya Maccido ke ciki a wannan lokacin, gabadaya ya manta da fushin da yake yi. Adda ta taho dauke da tray ta shiryo masa abincin ta biyo shi da shi ganin har zuwa lokacin bai shigo ya ci ba, abin ki da uwa akan cikin dan ta. Da bata gan shi a falo ba ko dakin ta ta nufo daki na da abincin. Ai kuwa Adda ta yi kyakkyawan gani. Mu dai sai ji muka yi an ja kofa an rufe. Abinda ya maido da hankulan mu daga ni har Yaya. Na kife fuska cikin tafuka na na rasa inda zan sa kai na. Shi kuwa Yaya murmushi ya yi, ya mike yana gyara karin hular sa. "...... Asma'u that's what i want ai, ta san cewa ina bukatar mata ta...kada abin nata ya koma daukar hakki". Sai da ya kara jimawa kafin ya bar dakin kamar ba zai tafi ba. Ban san yaya suka kare ba shi da Adda. Ni kam har washegari da safe da Yaya ya shigo don yi min sallama zai wuce ina cikin bargo kudundune na kasa fitowa, balle in hada ido da Adda. Yanzu ne na san Adda ta zame min suruka ta hakika, na kuma san abinda ya sa kunya da nauyi ke shiga tsakanin mata da iyayen mijin su. Bayan tafiyar Yaya wuni guda sur ina kaucewa haduwa da Adda cikin gidan, na zama daga daki sai daki. Ita da kanta da ta gaji da rashin gani na ta biyo ni da abinci har daki. Sai da na yi kwana uku ina buyar wa Adda kafin na saki jiki na mu cigaba da harkokin mu cikin gidan kamar yadda muka saba. Yaya Maccido in bai kira ni sau hudu ba a rana zai kira ni sau uku. A wannan dan tsukin ba abinda Adda ke yi irin tsananta Addu'a a kai na da Maccido, tana mai godewa Allah da Maccidon ta ya dawo mata, har ma fiye da baya. Yadda ya ke kula da ita da dukkan al'amuran ta da lafiyar ta sai ya ke tuna mata da mahaifin sa marigayi Alh. Atiku Dogondaji. Kullum addu'a take yi tana karawa kan Allah ya zaunar da mu lafiya, ya kara soyayyar Ma'u a zuciyar Attahir, ya kare mata shi daga dukkan abin ki, da sharrin duk wani mai sharri. ****** Kamar yadda Addah ta ce, sai ta hada mana kasaitacciyar walima don wadanda ba su samu labarin auren ba cikin ‘yan uwa da abokan arziki su sani. Don haka da ta fahimci Yaya hakurin sa ya kare dole ta soma aikawa mutanen arzikin ta, ‘yan uwan su Yaya na Dogondaji, abokan arziki na Bebeji wadanda suka yi zaman mutunci da iyaye na. Ta tada dan aike har garin Babura ta jihar Jigawa ko za'a samu saura cikin dangin mahaifiya ta Nene Zainabu. Dan aiken Adda ya dawo da kyakkyawan labarin an samu mata uku wadanda suka tabbatar masa suna da alaka da Zainabu matar Adamu Bebeji, daga gidan dagacin Babura aka raka shi wajen Inna Asabe, wadda kanwa ce ga kakar Zainabu, sai Abuwa wadda mahaifiyar su Nene ce ta rike ta har ta yi mata aure duk da babu alakar jini a tsakanin su. Sai Jummai matar Baban Nene, amma ta tsufa sosai ba za ta iya zuwa ba, amma Inna Asabe da Abuwa sun tabbata za su zo in har za a dauki nauyin kai su Sokoto. Wannan bai damu Addah ba, burin ta ya kasance ina cikin dangin uwa da uba, don haka ta yi alkawarin tura direba ya dauko su tun daga Babura har Sokoto. Kafin Aunty Nabeelah ta iso, kayan da ta auno ne suka fara isowa. Bayan kwana biyu ta biyo bayan su, Yaya tunda ya tafi bai kira ni ba yana ta fushin sa amma yana kiran Adda, yanzu kam Adda har gajiya take da wayar Yaya, Allah kenan, dama ya ce yana tare da su hakuri. A satin nan kwata-kwata ban cika lafiya ba, ciwon fargabar aure ake cewa ko me? Kai ka ce wani waje za'a kaini ba cikin gidan mu ba, ji nake kamar zan yi da Adda, na dai san rayuwar kuruciya ta kare mini, ina dai daurewa ne ganin hankalin kowa yana kan hidimar da ya sa gaba. Aunty Nabeelah ke tambayar Yaya Maccido ko ya gaya wa Lubabatu maganar auren sa? Kai tsaye ya ce, Bai gaya mata ba, ya fi so sai na tare tukunna, sabida ya san halin ta ba za ta bar shi ya zauna lafiya ba. Shi kuma yanzu ayyuka sun masa yawa, ga na kamfanin su ga kasuwancin malls din su. Wadda a yanzu ya fadada na Abujan ya kara gina plaza a kusa da waccan, ya bada hayar shagunan. Aunty ta ce, “Gara ka fada mata, in ta samo labarin a wani wuri abun ba zai yi muku dadi ba. Kuma ka hada mata kayan fadar kishiya, ko ka ba ta kudin a hannun ta”. Duk da haka Maccido bai yi wa Lubabatu zancen ba don suna ‘yar dadi kwana biyun nan tunda ya dawo, ta yi missing dinsa sosai, don bai taba tafiya ya dade haka ba tare da ita ba. Aunty Nabeelah da kawayenta na Sokoto suka shiga sassan Maccido na cikin gidan, suka sa aka fidda komai, da ma babu abin da yake mallakin Lubabatu, ba ta zo da komai nata Sokoto ba, don ta san ba wurin zaman ta ba ne, sai dai ta zo da yawo in ta ga dama. Zo ki ga inda ake jere mai aji, da ma kuma Yaya Maccido ya sa an yi furnishing gidan gaba daya, har bangaren Addah. Gida ya koma tamkar sabo, kai ka ce ba a taba zama a cikinsa ba. Bayan sun gama kafin, Adda ta sa malamai suka yi saukar alqur’ani a cikinsa. Washegari aka yi kasaitacciyar walimar da Addah ta shirya ta mata zallah, aka yi laccoci masu muhimmanci, sannan aka yi ta rabon kabakin takeaway da sovaneours, kowa ya tafi gida very excited don bai taba zuwa walima mai albarka irin wannan ba. *YIWA KAI HISABI* *SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)* Bayan sun gama kafin, Adda ta sa malamai suka yi saukar alqur’ani a cikinsa. Washegari aka yi kasaitacciyar walimar da Addah ta shirya ta mata zallah, aka yi laccoci masu muhimmanci, sannan aka yi ta rabon kabakin takeaway da sovaneours, kowa ya tafi gida very excited don bai taba zuwa walima mai albarka irin wannan ba. Da daddare ne mutanen Bebeji matar Malam Ayuba, wato Inna Kubra da mutanen Babura su biyu da aminiyar Adda Hajiya Wasila suka raka ni dakina. Ina kuka sosai kamar ba cikin gidan za a bar ni ba. Addah don farin ciki sai hawaye ta ke yi, ta shige kuryar dakin ta ta yi wa Allah sujjada da ya nuna mata wannan rana. Wani dadadden buri da ta ke da shi, amma ba ta taba furtawa ba don tabbacin rashin yuwuwar sa. Yau ga Ubangiji kunfa-yakun ya ba cika mata burin ta wanda ba ta taba daga hannu akai da nufin rokon shi ba. Sai dai ta ce ya zaba mafi alkhairi. Kowa ya watse ya bar ni ni kadai, da ma ni ba gwanar kawaye ba. Kuma ba lafiya ce ta ishe ni ba. Zazzabin ma kara zafi yake yi. Na kira Aunty a waya na roke ta ta ba ni Aasim mu kwana tare. Ta ce, “A’ah ba zai yiwu ba, in koyi zaman gidan miji ni kadai, kuma sun yi waya da Yaya Maccido yana kan hanya, sai dai zai kai goma na dare bai iso ba”. Gaba na ne naji ya yi wani mugun faduwa babu dalili, kamar yau zan fara ganin Maccidon. A daddafe na yi sallar isha, ko shafa’i da wutri na kasa yi sabida yadda jikina lokaci daya ya rikice. Wayata na dauko na kira Aunty Nabeelah cikin muryar rashin lafiya, na ce, “Aunty ki zo, saura kadan na mutu”. Ta ce, “Assha! Bar kira wa kanki mutuwa, ba ku gama cikawa Adda daki da ‘ya’yan da ku ka yi mata alkawari ba. Sannu kin ji, stress ne kawai da fargabar da kika sa wa ran ki”. Kafin minti biyar sai ga ta ta shigo da gorar ruwa da kwayar magani, ta ba ni na sha, ta ce in kwanta in yi isasshen barci zuwa gobe zan ji garau. Sai da na kwanta ta rufe ni da quilt, sannan ta juya ta fita. Lokacin da Yaya Maccido ya iso na yi nisa a barci na, tun a cikin gida Aunty ta gaya masa ya kula da ni bana jin dadi, amma dai ta ba ni magani na ji sauki har na yi barci. With concern ya ce, “Ko asibiti za mu je?” “Ba sai kun je a daren nan ba, kuna iya bari sai Monday ma in raka ta bayan ka tafi, na tabbata zata ji sauki zuwa gobe stress ne da fargabar aure. "Fargabar aure?" Yaya ya tambaya. Murmushi ta yi ta ce "normally 'yammata suna yin hakan in za'a musu aure, ita bata san za'a mata auren ba sai yanzu take nata fargaban". Sanda Yaya ya shigo ban sani ba, ya kulle ko’ina, ya saki curtains ya je dakinsa ya yi wanka yana yaba yadda gidan ya koma cikin ransa. Ya san duka aikin Nabeelah ne, akwai ta da iya style, ga iya zaben abu mai kyau. Sai da ya kimtsa tsaf shirin barci ya fesa turaren sa obsession bisa pajamas din shi, ango sosai, sannan ya nufo nawa dakin, bayan ya kashe wutar falo. A hankali ya zauna a gefen gadon daidai kaina, yana kallon yadda nake barci cikin nutsuwa, numfashina na sauka a hankali. Ya dora hannu saman goshina da wuyana ya ji temperature din ya sauka. Ina jin sa ya russuna ya sumbaci baki na softly, da murmushi ya ce “sleeping beauty”. Tare da gyara min quilt din da nake rufe da shi, ya yi light off ya shige cikin quilt din shi ma ya kwanta, ya jawo ni a hankali ya shigar cikin jikin sa, hancin sa yana daidai tsakiyar gashin kaina. A haka muka yi barci, wani barci mai dadin da ban taba irinsa ba. Ya nemi fushin da yake ta yi ya rasa, tunda finally Adda ta yi masa abinda ya ke so ta bashi Ma'un sa. Da asubah bayan mun yi sallah Yaya bai yi la’akari da halin da nake ciki ba. Da lallashi, da ban baki da zakakan kalamai ya samu abin da yake so, ya karbe budurci na cikin girma da daraja, komai ya faru very soft and gentle, he didn't hurt me anymore, ya yi ta sa min albarka. Ba yadda bai yi ba mu je asibiti a washegari ganin yadda na galabaita amma na ki. Ragowar kwanaki biyun da yayi ba abinda yake yi sai jinya ta, hatta Adda da Aunty Nabeelah tarairayata suke ta yi, Adda da abinici mai gina jiki Nabeelah da shigowa akai-akai tana duba halin da nake ciki da tabbatar da na sha magani. Kwanansa uku ya koma ba don ya so ba, da niyyar yau yana komawa zai gaya wa Lubabatu auren sa, kada sai na haihu sannan ta sani, ya kara wani laifin. **** Ba laifi ya samu tarba daidai gwargwado daga Madam din tasa, amma ‘ya’yan sa sun fi murnar dawowar sa. Bai damu ba don ya san haka take canza fuska duk lokacin da ya je Sokoton da yake zuwa yanzu akai-akai. Ya daga Ahsan yana sumbatar sa, yaron ya shiga ransa sosai sabida kamannin shi da ke ga yaron. Suna cin abinci, wanda ta sa mai aikinta ta yi masa, ta ce, “Na ga wasu kayan yara msu kyau a cikin kayanka, a ina ka saya musu?” Ya dan dube ta yana son tuno wane kaya ne? Lokaci daya zuciyar sa ta hasko masa Ma’u a shagon Majma’al Qimmah. Tana zabowa Ihsan da Ahsan kaya. Wani ni'imtaccen murmushi ya yi wanda bai san ya yi ba, sannan ya sosa kansa yana ta murmushin dai ya ce. “Nasu ne”. "Wa ya ba su? Gaskiya ko waye ya iya zaben kayan yara, i'm sure ba kai ka zabo ba”. Ya sake sakin murmushi, ya ce, "Ko? Ashe ni ma na iya zabi?” Ba ta gane me yake nufi ba, ta ci gaba da cin abincin ta. Sai da suka kammala ya dauko wayar sa yana danne-danne. Ba jimawa Lubabatu ta karbi alert din kudi masu yawan da bai taba ba ta kamar su ba. Da mamaki ta dago tana masa murmushi. “Sweetie, wannan kyauta haka? Lallai an bude sabuwar plaza da kafar dama, sai kawai in sayar da motata in cika in sayi latest model. Yana mamakin ta ya ce, “Ba kya tambayar ko na mene ne kawai daga ganin kudi ba neman karin bayani sai kashewa?” Ta ce, “Bayanin me zan nema? Na san dai ba mistake ka yi ba”. Ya gyada kai, “Eh ba mistake na yi ba, naki ne, na fadar kishiya ne, ki sayi duk abin da ki ke so, na ga ya fi in sayo miki kaya tunda ba kya rabo da dinkin sabon kaya”. Lubabatu ta yi tsai da iadanunta tana duban shi, sai da ya yi shiru sannan ta ce, “Attahir, me ka ke fada ne? Kamar kishiya fa ka ce?” With affirmation ya gyada mata kansa, “Eh na yi aure Lubabatu, kusan wata uku da suka wuce”. Lubabatu ta yamutsa fuska, ta ce, “Idan wasa ka ke ka bari, bana son irin wannan wasan ka sani”. Ya dauko wayarsa ya shiga lalube a gallery har ya budo hoton da yake so ya tura mata wayar gaban ta. Da farko kamar ba za ta dauka ba, sai kuma ta sanya hannu ta dauka. Hotonsa ne shi da Ma’u, selfie ne ya dauke su a Hilton na makka, hannayensa zagaye da wuyanta, fuskokin su na nuna irin farin cikin da suke ciki, sannan akwai alamun soyayyar da ke cikin idanun Attahir dadaddiyar ajiya ce, wato ba ta yau ba ce. Wani irin ihu Lubabatu ta saki tare da hada wayar Attahir da bango, ta kuwa tarwatse nan da nan kowanne part ya kama gabansa. Ba karamar razana Ihsan da Ahsan suka yi ba. Lubabatu ta yi kukan kura ta yi kan Attahir, “Gara in kashe ka kafin ka kashe ni…”. Wuyansa ta kai wa damka, duk kokarinsa na bambare hannayenta daga jikinsa ya kasa. Ya ce, “Lubabatu kashe ni, ya fi min alkhairi da inda ki ke leading rayuwata… kin raba ni da uwata kin raba ni da ‘yan uwana, kina kokarin ja na jahannama. Kada ki dauka duk shige-shigen da ki ke yi domin ki halakar da ni ban sani ba. Na yi shiru ne ba don tsoro ba sai don ni ma ina da nawa target din. Wanda shi ne auren ‘yar uwata, yawon bin bokaye don Allah kar ki fasa ki ci gaba, wa man yatawakkal alallahi fa huwa hasbuhu. Na auri ‘yar uwa ta Asma’u, ruwan ki ne ki kama girman ki mu zauna lafiya ruwanki ne ki hana kanki kwanciyar hankali, ki ci gaba da shige-shigen da zai fishshe ki. Rana dubu ta barawo… rana daya ta mai kaya. Ban auri Asma’u da nufin tozarta ki ba, sai don ra’ayin kaina da samawa mahaifiyata farin cikin da ki ka kasa bata, girman da ki ka kasa bata, da ‘ya’yan da ki ke rowanta mata. For your good information ku biyu ne matana yanzu. Ba ni da niyyar hada ku gida daya a halin yanzu, amma ban san me gobe za ta haifar ba…”. “Ubanka za ta haifar Attahir, na ce ubanka za ta haifar. Ka yi kadan ka yi min wannan tozarcin. Ka je gida an tsaface ka an hada ka da wannan dangin dangaron don a ga bayana, to uban kuturu ya yi kadan wallahi. Na fi karfin in hada miji da kowa balle wanan ‘yar matsiyatan. Ban da soyayya kai ka san ba ka isa ka aure ni ba. To haka nake so ka sa a ranka ni kadai za ka rayu da ni da an ki da an so. Ka gaya wa Nabeelah ni murucin kan dutse ce, ban fito ba sai da na shirya, don na san duk wannan munafurcin nata ne. Idan ka ga ka rayu da wata mace ba ni ba, to ka tabbata a lahira ne, in ka yi dacen shiga aljanna kenan...”. Hankade ta ya yi ya mike don ya lura ta soma fita daga saiti, kwayar idonta bakidaya sun juye. Taku ya soma yi zai wuce zuwa dakinsa don ba ya so ya sake tanka mata. Ya gama fadin mata duk abin da yake son fada mata shekara da shekaru ya kasa. Tsoro da dabaibayin da ke kansa bai ba shi dama ba. Yanzun ma har mamakin kansa yake, yadda rana daya ya juye ya koma Maccidonsa na ainahi. Bai san cewa sujjadar UWA ba ce cikin talatainin dare da zafin hawayenta da jajircewar ta wajen kai wa Allah kukanta ba tare da gazawa ko gaggawa ga son saukar ijaba ba. Lubabatu ta dauki kofin da ya gama shan shayi da shi ta wulwula shi zuwa ka Maccido. Bai same shi a ko’ina ba sai a keyarsa. Ya tarwatse a wajen wanda hakan ya yi sanadiyyar nutsewar wani bangare na kwalbar cikin tsokar naman kansa, jini kuma ya balle kamar an kwance famfo. Ihsan ta saki kuka ganin jini na zuba daga kan Babanta, ta yi kansa tana kiran sunansa. Hannunta ya kama sannan ya kai hannu ya dafe wajen ya juyo ya dubi Lubabatu. “You are just wasting your time, bakin alkalami ya riga ya bushe, don kuwa Asma’u da kusa haifa wa Ahsan kannai”. Ya suri mukullin motarsa kan kujera ya sunkuya ya dauki Ahsan da ke ta kuka ya kama hannun Ihsan suka fice. Bangaren mai rainonsu ya kai su, ya ce ta kula da su zuwa safe. Sai salati ta ke ganin jini na malala daga kansa. Take ta hada biyu da uku ya ba ta ma’ana, ko dai Madam zai yi wa kishiya ne? A kan yadda ta san uwar dakin nata a kan kishi har da su ‘yan aiki za ta aikata fin haka. Ya dauki mota jiri na dibansa zuwa private clinic mafi kusa, aka yi masa treating ciwon aka cire wadda ta nitse, sannan aka yi masa dinki. Kin komawa gidan ya yi sai sha biyu na dare, a tunaninsa ta yi barci, amma yana shiga falo ya jiyo tashin muryarta tana waya cikin kuka… “Yadda ki ka rusa rayuwa ta Allah ya rusa ta ki Nabeelah. Allah ya sa balaraben ya sako ki. Ki gaya wa uwarku na ci dubu sai ceto, na dade da sanin mugun nufinta a kaina da wannan mummunar yarinyar da ta ajiye a gabanta… to na ga aure na shaida ina jiran ganin ranar shigowar ta gidana, wallahi sai dai ku dauki gawar ta inyaso ni ma a kashe ni…”. Banka kofar ya yi ya shiga dakin, wayarsa ce a hannunta. Ya fizge wayar ya duba ya ga kiran na tafiya, kuma sunan Aunty Nabeelah ne. Ya daga hannu ya wanka mata mari, ya sake wanka mata. “Nabeelah sa’ar ki ce? Yayata uwa daya uba daya?” Ya kankance ido yana mata wani kallo da ba ta taba gani cikin kwayar idon sa ba. “Uwata ki ke bai wa wannan sakon Lubabatu? Uwar da ta kawo miki ni duniya na shagaltu wajen bauta miki na manta da ita, amma ba ta taba korafi a kanki ba, sai ni don na yi auren da duk cikin su babu wanda ya sanya ni? To ina so ki sani na auri Asma’u ne don ina sonta ba don wani cikin su ya cusa min ita ba. Ke kuma na aure ki ne don kare kaina daga zina, amma tun farko Asma’u nake so ba ta isa aure a sanda ni na isa ba. Hope this information is enough and clear ki yi deciding za ki iya ci gaba da zama da ni ko a’ah?" Lubabatu ta yi masa wani sakaran kallo, “Ina zan je? Ai aurenmu takalmin kaza ne, da ma haka ake so in tafi, don na tsokale wa kowa ido, to ba inda zan je, zama daram. Zaman yakin kwatar kai, inyaso mai karfi ya kwace Maccidon. Kada ka dauka soyayya ce za ta zaunar da ni. Zan zauna ne don in hana ku kwanciyar hankali in kuntata rayuwar ku yadda ku ka kuntata tawa…”. Murmushi ya yi irin na mazan da suka san kansu. “Karyar banza karyar wofi, kin ce soyayyar ta kare ko?” Ya fada yana takowa zuwa inda ta ke. Ta gane abin da yake shirin yi wanda kuma a take zai wargaza dukkan karfin zuciyar ta. Sai ta yi wuf! Ta kasan hannunsa ta fice dakin da gudu tana kuka. Attahir ya yi murmushi wa kansa ya daga murya yadda za ta jiyo shi. “Ai na so ki tsaya a tantance aya da tsakuwa, ta nan za mu gane ta inda karewar soyayyar ya fara. Kin ci darajar haihuwar ‘ya’ya biyu, wallahi yau da sai na kumbura miki mukamikin da ke wa Yayata rashin kunya”. Tun daga wannan ranar gidan ya rikice ya koma wani dan karamin sansanin yaki. Lubabatu ta hana shi kwanciyar hankali ko na second daya. Duk kayan amfaninsa ta lalata, ta kwankwatsa kayan kallo da glassan windows, ta zama kamar wata sabuwar mahaukaciya. ‘Ya’yanta ba ruwan ta da su, komai nasu ya koma hannun mai rainonsu, abinci sai dai ya saya a waje ya kuma ci a wajen in yana so ya tsirga masa. Abubuwa suka taru suka addabi Attahir, ga hidimar mall ga ta Maccido Plaza, ga ta ‘ya’yansa in ya dawo gida, sannan ga tarin ayyuka a ofis. A daidai wannan lokacin ne kuma Julius Berger Nigeria suka kara masa matsayi zuwa construction manager, ya ga cewa in ya ci gaba da rayuwa da Lubabatu a haka watarana stress za ya kayar da shi, don haka ya gaya wa yayanta Usman duk halin da yake ciki da ita, shi kuma bai yi wata-wata ba ya gaya wa Baban su. Lubabatu ta gama tsiyatakunta na yau inda ta debi ruwa bokiti-bokiti ta kwara a gadon Attahir ta fito za ta koma dakinta, ta ji sallamar Babanta da yayanta Usman. Tana ganin su gabanta ya fadi, don ta san Babanta ba ya zuwa gidajen su. Jikin ta ya ba ta Attahir ya gaji ya kai karar ta ne. Ilai kuwa, Usman ya fiddo sharbebiyar bulala daga leda ya mika wa Baban, za ta gudu Usman ya damko ta. Baban ya yi mata dukan kawo wuka, ya lallasata ko’ina a jikinta ya yi birdin-birdin, sannan ya koro mata warning din cewa, idan ta kai Attahir bango ya sake ta, kada ta sake ta doso gidansa. Daga wannan lokacin ne Maccido ya samu saukin Lubabatu, amma sai ta daina shiga duk wata sabgarsa, ta maida shi shi da babu duk daya cikin gidan, sannan ta guntule alakarta da ‘ya’yanta, ta bar wa mai raino. Don haka ne gidan duk ya zame masa kurkuku, Allah-Allah yake ya samu sarari ya arce Sokoto. Ni ma din ba ya samun wata kulawa daga gare ni a waya, ina can ina fama da kaina, imagine laulayin ciki mai wahala, gaskiyar Muhsin Yayan sa is a sharp shooter. Karshe sai dakin Adda na koma da zama gabadaya, don Aunty Nabeelah ta dade da komawa Lebanon. Kafin ta tafi ta ba mu labarin wayar cin mutunci da Lubabatu ta yi mata, duk da Maccido ya ba ta hakuri, Adda kuma ta ce kada ta kula ta zafin kishi ke damunta, ta yi haushin kaza huce kan dami. Ranar wata juma’a ya samu sararin ayyukansa. Ya sa Nanny Maria ta hada masa duka kayan yaran a babbar trolley dinsu. Lubabatu na daki tana ta kitsa sharri a waya da kawaye ya kwashe yaran ya taho da su Sokoto ba da saninta ba. Ba ta gane ba sa gidan ba sai yamma lis, jin shirun su ya yi yawa, da ko ba za ta kula su ba sai sun shigo inda ta ke. Ta kwala wa Maria kira ta zo, “Ina yara ban ji motsin su ba?” Maria ta ce, “Oga ya kwashe su ya tafi da su tun safe ba su dawo ba, kayan su duka ya kwashe”. Lubabatu ta zame wa Maria kamar zautacciya, Maria ta sha mari hagu da dama kan don me tun lokacin ba ta zo ta gaya mata ba ta bari aka kwashe mata ‘ya’ya aka kai wa makiyanta? Ta je daga yau ta sallame ta. *TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES* *SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* SOKOTO Ihsan ce a gaba, Ahsan ya biyo bayanta sanan babansu. Suka yi sallama a dakin Adda. Zaune nake tsakiyar gadon Adda na yi rashe-rashe ina cin gugguru. A tare ni da Adda muka dubi kofa don ganin masu shigowa. Yaya Maccido da na yi masa kallo daya kasa dauke ido na yi a kansa. Gabadaya ya rame ya yi duhu, mutumin da watanni uku da suka gabata kamar ka taba fatarsa jini ya yi tsartuwa. Hannu na bude wa Ihsan ina kiranta, Adda kuma Ahsan ta ke kokarin dauka. Farin cikin ta ya gaza boyuwa. Ta kara amincewa Allah sami’ud du’a’I ya dawo mata Maccidon ta da ta haifa, ba mai kama da shi a baya ba. Yaran duk suka lafe jikin Baban su alamar ba su zuwa ba su san mu ba. Da wayo da cakulet da pop-corn na samu Ihsan ta yarda ta zo kusa da ni, na jawo ta jiki na zuciyata kamar takarda. Yau ba ni da abin da zan biya Yaya Maccido. Ahsan kuwa da Adda ta matsa da son daukarsa, kuka ya saka yana kiran Mamansa. Yaya ya ce, “Ahsan my mum? Ba za ka je wajen Mamana ba?” Adda ta mike ta soma hidima da su, shayi ta fara hada musu mai kauri kafin ta cika gabansu da lafiyayyen abinci wanda na dafa wa Yaya domin ya yi waya ya ce yana hanya, amma bai gaya mini tare da yaran yake ba. Ya ce "Surprise yake so ya yi wa kowa”. Hawwa Adda ta tura ta gyara sashenmu tun kafin isowar Yaya, don ba ta bari na in yi aikin komai. Girkin ma don na Yaya Maccido ne shi ya sa ta bar ni na yi da kaina. Yaya Maccido da Adda sai hira suke cikin nishadi. Na kama hannun Ihsan na dauki Ahsan wanda zuwa yanzu ya soma warewa. Na ce, “Addah za mu je a yi wanka, Hawwa ta shigo min da jakar kayan su”. Addah ta ce, “A dai yi wankan a dawo min da su nan, yau ga kafada ta ga tasu za mu kwana, ki je ki ji da mijinki ya debo hanya ya zo ki ce rainon ‘ya’ya za ki yi, shi kuma wa zai yi nasa rainon?” Kunya ta kama ni na fice da sauri tare da yaran. A falo muka yi karo da Muhsin ya ce, “Lallai yau za a yi ruwa da kankara ‘ya’yan Abuja ne a gidan mu?” Na ce, “To ga su dai ka gansu, ka zo ka sayo musu pampers”. Na yi musu wanka da ruwa mai dumi, Ihsan na ta yi min hira. Shi Ahsan bai iya magana sosai ba. Hawwa ta kawo min kayansu na sa musu, na gyara wa Ihsan gashinta, nan suka yi shar duk suka yi kyan gani. Muna hira da Ihsan barci ya dauke su a jikina. A haka Yaya Maccido ya cimmana. Daga bakin kofa ya tsaya yana bina da wani sassanyan kallo. Yafito ni ya yi da hannun sa, ya yi min alamar in zo gare shi. Na yi masa nuni da yaran da ke jiki na. Karasowa ya yi ya dauke su su duka biyun a kafadunsa yana fada kasa-kasa don kada ya tada su, “This is cheating!”. Na ce, “Don Allah Yaya ka bar su mu kwana”. Hararar da ya yi min ta nuna ina bata baki na ne kawai. Wajen Adda ya kai su ya dawo. Kafin ya gama abin da yake a falo na hada masa ruwan wanka na zuba turaren wankansa a ciki na desire dunhill. Muna kwance kalmashe cikin jikin juna bayan al’amura sun daidaita a tsakanin mu, na kai hannu cikin sumar Attahir ina cakudawa sannu a hankali. Cikin muryar da ke nuna damuwa na ce, “Yaya ka rame, at the same time ka yi baki”. Idanunsa a lumshe ya ce, “Don ma ba a kawo miki gawa ta ba? Amma Lubabatu kashe ni ne kawai ba ta yi ba, in haka ake kishi Allah wadaran kishin mata. This is insane. Ranar da zan miki taki kishiyar ashe ke ma daina so na za ki yi?” Hannu na ya kai kan tudun wani dinki a kasan kansa. Cikin damuwa na ce, “Wannan fa?” Ya ce, “Duk a cikin punishment dina na kara aure ne”. Cike da tausayi na ce, “Yaya kishin mata kala-kala ne, I can never hurt you like this don ka yi min kishiya, zan yi fushi da kai for the mean time in daina yi maka magana, but I can never ever hurt or insult you…”. Yaya Maccido ya shigar da ni cikin jikinsa sosai ya rungume ni. “Balle ma ba zan yi ba Asma’u. Da a ce ke na fara samu ba zan yi mata biyu ba. You are more than enough to every husband. Darajar yaran nan nake dubawa shi ya sa har na daure na ci gaba da zama da Lubabatu cikin mugun yanayin da ko makiyana bana masa fatan auren mace irin ta’. Tausayin Yaya ya kama ni, na sani tun fil’azal shi ba mai son tashin hankali ba ne. Na soma kissing dinsa lightly duk dai don in mantar da shi bacin ran da yake ciki. Daga nan muka manta komai sai hanyar da za mu faranta ran juna. Kullum ya zo gare ni tamfar ba mu taba kusantar juna ba haka muke komawa. Soyayyar kamar ana mata ban ruwa, tana dada yin yado da rassa. A hankali zuciyata ta gama macewa a son mijina Attahir, wani irin so da ban san iyakar sa ba. Yaya ya tafi ya bar Ihsan da Ahsan tare da mu, sosai nake kula da yaran, kwana biyu suka ware suka saki jiki da mu, Muhsin na fita da su in ya dawo ya sawo musu ice-cream, ai kuwa nan da nan suka makale masa, su ce min Aunty su ce wa Adda Granny kamar yadda Muhsin ya koyar da su. Al-Qaseem ya zo ya gaya wa Addah ya samu matar aure, za a je masa tambaya, ‘yar garin Zamfara ce, Addah ta ce in an fidda ranar zuwan ya sanar da ita za ta je insha Allahu. A gajiye Attahir ya iso gida, falmaran din suit din jikin sa a hannu da jakar macbook din sa ya fito daga mota ya rufe ya taka zuwa cikin gida. Tun jiya da daddare da ya dawo ba su hadu da uwargidan ba, sanda ya dawo ba ta sani ba sannan da sassafe kafin ta fito ya wuce ofis. Yana shigowa da ita ya fara tozali zaune a tsakiyar three seater. Kallo daya ya yi mata ya kauda kai yana mamakin wai wannan matar sa ‘yar kwalisa wanke hannu ka taba Lubabatu ce, ta koma kamar wadda aka kwanto daga turu, ta yi baki ta rame kamar ba ita ba. Kayan jikinta ya gane tun wadanda ya ganta da su ne ranar da zai tafi Sokoto. Lokaci na farko da tausayinta ya dan tsirga masa, ya sa kafa ya wuce ta zuwa dakin sa ba tare da ya ce da ita komai ba. Yana shiga dakin ya tsaya jikin gado ya soma loosing tie din wuyan shi. Bankado kofar dakin ta yi ta fado kamar an jefo ta. A firgice ya juya suka yi ido hudu. Cikin kakkausar murya ta ce. “Attahir ina ka kai min ‘ya’ya na?” Ya juyo tare da dan kura mata ido, sannan ya juya ya ci gaba da abin da yake yi. Hakan ya kara fusata ta, wato ma bai san tana magana ba. Takowa ta yi har gabansa ta kama kwalar rigarsa ta girgiza shi cikin yanayin fita hayyaci. “Wallahi ko ka ba ni ‘ya’yana ko shari’a ta raba mu”. Trying hard to control his temper ya ce “Sake ni Lubabatu tun muna shaida juna, bana so tsautsayi ya sa na kara kai hannu a jikin ki, in har ba arziki ne ya kawo ki ba kar ki kuma gigin shigo min daki”. Lubabatu ta sake shi ganin yadda idanun sa ke mata kallon da ta tabbatar yana nufin abin da yake cewa. Ta sulale a gaban shi ta fasa wani irin gigitaccen kuka, ta ce, “Tsakani na da kai yau ke nan Tahir, sabida ka auri ‘yar gidan ku? Duk soyayyar da na shayar da kai ka manta? Duk wahalar da na yi maka ta daukar ciki da haihuwa sakamako na ke nan? Me ka gano a jikin wannan yarinyar wanda ba ni da wanda ya fi shi? Shin soyayya ta gare ka tun ba ka da komai ta cancanci wannan butulcin? Me na yi maka a rayuwa banda so da kauna da za ka yi min wannan sakayyar?” Ta ci gaba da kuka mai nuna komai ya fara kare mata, dabara, izza, masifar da bala’in gabadaya sun kare mata. Saboda wannan Tahir din da ke gabanta ta tabbata sabon Attahir ne ba wanda ta danne shekaru biyar yana mata biyayya da bauta ba. An ce tsakanin mace da miji sai Allah. Sai ya samu kansa da jin tausayin ta. Ya san Lubabatu na son sa, kuma son ne yake take duk abin da ta ke yi, wanda a haukanta shi zai dawo mata da abin da ta rasa a Tahir din. Yana son Lubabatu domin soyayyar ce ta sa ya aure ta, amma in ya tuna yadda ta shiga tsakanin sa da kowa nasa tunda ya aure ta, sai ta yi bakikkirin a idanun sa. Hannunta ya kama ya mikar da ita, ya ja ta suka zauna tare a bakin gado. Wani tsami-tsami da bashi-bashi da ke tashi daga jikin ta ya naushi hancin sa. Da kyar ya hadiye miyau, ya ce, “Lubabatu ke ce kuwa? Yaushe rabon ki da wanka? Now, ba ni da magana da ke sai kin je kin yi wanka, ki fesa turare sannan ki zo mu tattauna. Amma ki sa a ranki Asma’u ta riga ta zama wani bangare nawa, dole ki karbi wannan gaskiyar, idan har kina so mu yi magana ta fahimta ni da ke”. Maganganun sa ba karamin tunzura Lubabatu suka kara yi ba, wai yau ita Attahir ke cewa tana wari, sabida ya auri 'yar cikin sa, har me wannan bagidajiyar zata gaya mata? Kodayake ta san da gaske tana bashin, rabon ta da wanka har ta manta. Jiki ba kwari ta mike ta bi umarnin sa. Tana fita ya zaro wayarsa daga aljihun wandonsa. Bugu daya na daga ya ce, “Asma’u ko ki neme ni ki ji ya na iso gida ko?” Na yi kasa da murya na ce, “Ayya Yayana. Wayar tawa ce Ahsan ya tsoma min a bokitin ruwa, wai zai wanke min. Da kyar Muhsin ya samu aka gyaro ta yanzu. Amma ka san kana raina ko? Kuma addu’ata a kowacce sallar farillahta ita ce Allah ya kare min kai a duk inda ka ke”. Attahir ya lumshe ido, muryata na kara kashe masa jiki, ya ce, “na gode da wannan addu’a taki Asma’u na, hope my soldier is kicking very well, kuma Ahsan da Ihsan ba sa damunsa? I’m missing you terribly… idan na ce kewa ina nufin ta komai…”. Murmushi na yi na ce, “Yaya na gode, kai ma ka san in na ce I LOVE YOU is not enough to express the feelings…”. Maccido sai daga kai ya yi ya ga Lubabatu a kansa tana huci kamar mesa. Kafin ya yi aune ta fizge wayar daga hannunsa ta rotsa ta da kasa. Har ga Allah ya so ya yi sulhu da ita a wannan daren don ta samu sanyi a zuciyar ta ko ya ya ne, amma abin da ta yi din nan ba karamin fusata shi ya yi ba. Ya daga hannu zai kai mata mari, ya yi maza ya taro hannun nasa. Ya rike hannun da zai kai marin da hannun hagunsa ya koma gefen gadon sa ya zauna. “Fice min daga daki, kafin ki sa a kwashe ki a wheel-borrow yanzun nan, tunda ba tare muka hada kudi muka gina dakin ba”. Wani dogon tsaki ta ja, sannan ta juya tana fadin, “Aikin banza. An dai ji kunya wallahi, kanwar da aka gama yi wa muzurai shekara da shekaru, rana daya ake ce wa I love you don yada girma da bunsuranci. Yarinyar da ko fasali babu, ‘yar cin arziki kawai. Wallahi Attahir ka fadi babu nauyi". Ganin ya taso zai cimmata ta kara da gudu ta bar dakin, ta shige nata ta banko kofa. Rayuwar Yaya da Lubabatun sa ke nan. Sai abubuwa sun yi kamar za su gyaru sai ya kuntuka mata abin da zai sa ta kara birkicewa. Duk abin da yake yi akan Asmau ba yana yi don ya tsokane ta bane sai don shi kansa bai san ya ya aka yi yake zama Romeo ba in dai yana tare da Asma’u a waya. Ita kuma gata da labe, kalaman da Lubabatu ba ta iya jure wa jin su, kuma ta kasa daina yi masa labe ga duk wayar da zai yi ko da ba Asma’u ya kira ba. Mamaki yake, sau tari ya ce "Lubabatu ashe haka ki ke? Ashe iblishiya ce ban sani ba? Shin a kanki aka fara kishiya? To sai dai ki kashe kanki, kuma Asma’u ta shigo gidan. Amma masifar ki, jidalin ki, bala’in ki, haukan ki da rashin hankalin ki ba abin da zai sa, ba abin da zai hana”.