[13/11, 2:03 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *E.W.F* *BISSMILLAHIR RAHMANUR RAHIM* ( _Da sunan Allah mai rahma mai jin k'ai_). *Page 1* K'was K'was K'was k'arar takalmin ta ya karad'e cikin babban hall di'n da suke d'aukan lecture's, tun Kafin ta k'araso cikin hall di'n k'amshin turaren jikin ta ya cika cikin ajin, gaba d'aya kusan ilahirin student's di'n suka d'ago kansu tare da mayar da hankalin su kan mai Shigowar malamin da yake musu lecturing di'n shi kanshi jiran wacce mara kunyar ce take kok'arin shigo mishi aji bayan ya kafa dokar hana shiga cikin ajin indai ya riga d'aya daga cikin student d'in shiga. Kusan second biyar wata kyakykyawar yarinya ta bayyana cikin ajin kunnen ta mak'ale da waya tana faman tauna chewing gum a bakin ta tana amsa wayar, tana sanye cikin wani less cotton milk colour da touch d'in pink a jiki anyi mishi wani shegen d'inki riga da siket ta yafa wani k'aramin mayafi da takalmin ta hill dashi tasha heavy makeup kamar wata aljana, ta had'u iya had'u wa *MUFIDAH EL HUSSEIN* kenan, ko kallon inda malamin yake bata yi ba ta nufi inda ta sa ba xama cikin wata kakkausar murya taji ance " hey you get out!" Yanda ya buga tsawa shi yasa hankalin sauran d'aliban ya dawo kan malamin gaba d'ayan su a tsorace suke, wadda aka buga wa tsawar bata ma san me yake cewa ba sai da k'awar ta nabeelah ta xungure ta tare da yi mata alama da hannu, wani irin juyi tayi tare da bin shi da wani matsiyacin kallo. Shima cikin kallon wulakanci yake bin ta dashi tare da sake furta " i said get out don't west my time" Cikin muryar ta mai shegen dad'i da yanayin shagwa6a a cikin muryar tace "Ohh! dani kake wai? " Wata harara ya xabga mata tare da yi mata nuni da hannu kan ta fita don ya k'ulu iya k'ulu wa da yarinyar sosai ya fusata da abin da tayi mishi tuni fuskar shi ta yi ja saboda tsantsar 6acin rai, cikin isgili tace "sorry sir " Ta fad'i tana wani langa6e kai gefe tana Mishi irin wani kallo na raini, shi ma a wulakanci ya kalle ta tare da fad'in "idan baki fita wlh xan miki rashin mutunci " Hura hanci ta fara alamar kaxo gidan Indai rashin mutunci ne ta iya shi, ajin dai yayi tsit kamar ba mutane d'aliban sai faman raba ido suke tsakanin junan su da kuma mufidah da malam suna jiran ganin K'arshen dramar nan. Had'a ido mufidah tayi da nabeelah tayi mata alamar don Allah ta fita d'an hararar ta tayi kafin kuma ta fara tafiya alamar xata fita daga ajin, ta gaban shi ta shige tana tafiar kasaita bak'in ciki ya gama rufe shi ganin wannan K'aramar yarinyar tana kok'arin wulak'anta shi a gaban d'aliban shi da suke ganin mutuncin shi wani mtswww yaja wani uban tsaki tare da bin ta da harara kamar idon shi ya fad'o k'asa. Bayan fitar ta ya ma kasa cigaba da lecturing di'n saboda ranshi a matuk'ar 6ace yake, wani d'an tunani yayi na tsayin second uku take ya saki wani shegen murmishin mugunta nan ya rubuta musu test, nan cikin d'aliban ya d'uri ruwa don wlh basu xaci xai musu test yanxu ba, kowa jiki a sanyaye ya xaro paper da biro, yayin da nabilah ta d'ora hannu akai Shikenan yanxu wannan test d'in ta shige mufidah gashi tana bala'in tsoron malamin balle tayi mata hka jiki a sanyaye ta fara rubuta text d'in. Cikin mintuna talatin ya tattara test d'in yayi gaba a fusace fuskar nan babu alamar fara'a a cikin ta. Ta gaban mufidah ya shige da take xaune kan mota tana mak'ale da headphone tana sauraren wak'ar Justin Bieber ta love me love me har wani gid'a kai take saboda son wak'ar da take bata ma kula da shigewar shi ba idanun ta a lumshe suke. Tana cikin hka taji an doke ta a cinya da sauri ta bud'e idon tare da furta "wash Allah na nabilah me nayi miki? ", ta fad'i tana kallon nabilah da take hararar ta "baki da kirki k'awata yanxu kin kyauta abin da kika yi? "Cewar nabilah Mtswww mufidah ta saki tsaki tare da cewa "Wannan ke ya dama ba abin da ya dame ni " "baki da kyau k'awata ai kuwa kin fusata shi, gashi yayi test wlh " D'aga kafad'a mufidah tayi alamar ko ajikin ta Kafin tace "ae Allah sai na dai dai ta mishi sahu a skul d'in nan " Dariya suka tuntsire da ita tare da tafawa can mufidah ta sakko daga saman motar tare da cewa "mu ware koh nabilah? " "yes kamar Kinsan a gajiye nake " Daga hka suka shiga motar mufidah ta yiwa motar key suka fice daga skul d'in suna faman hira har sai da ta sauke nabila a gidan su tukunna ta shige nasu gidan. Tun Kafin ta k'araso dai dai get d'in take faman xuba uban horn don ta tsani jira, ai kuwa mai gadi cikin rawar jiki ya bud'e mata get d'in ta danna hancin motar xuwa cikin k'ayataccen gidan parking tayi sannan ta nufi cikin gidan. Belt door di'n gidan ta danna da sauri house girl din gidan taxo ta bud'e tare da russuna wa tace "Barka da dawo wa aunty " Cikin d'an murmishi tace "Yawwa saudat ki kawo min hollandian milk mai sauk'in sanyi " Cikin girmama wa saudat mai aiki tace "toh aunty " Sannan ta shige da sauri ta nufi kitchen, yayin da mufidah ta K'arasa cikin falon umman ta ta gani xaune tana kallon sunnah tv da sauri taje ta rungume ta tana cewa "i miss u umma nah " Cikin jin dad'i umma tace " i miss u too my sweetheart, ya skul?" "lau ummah " "Yayi kyau ina nabila" umma tace cikin murmishi, cikin murmishi ita ma mufidah tace "yanxu na sauke ta a gida tana gaida ke " "ina amsawa " A dai dai lokacin saudat ta kawo wa mufidah hollandian di'n sai da ta xuba mata tare da mik'a mata sannan ta bar wajen, tana sha suna cigaba da hira da umman tah............ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:03 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *E.W.F* _wannan shafin sadaukarwa ce ga en exclusive writers forum Allah ya k'ara had'e kan mu ya k'ara mana basirah tare da dukka marubatan mu Ameeen_ *Page 2* A fusace ya tura kofar shiga palon gidan ko sallama a ciki ciki yayi ta ba lallai ma a ji ba ko kula da wad'anda suke xaune a falon bai yi ba ya fara hawa upstairs ya taka mattatakala ta biyu yaji ance "my bro wane ya ta6a min kai yau? " Cikin sauri ya jiyo aikuwa suka had'a ido da Yah sadeeq ai kuwa da sauri ya taho har da d'an had'a wa da gudu ya rungume yayan nashi wanda yau kusan tsayin Sati biyu rabon da su ga juna sai dai waya cikin tsananin murna yace "Yah sadeeq xuwan yaushe? " "xuwan shi kenan tun da ganin yayan na ka ka mance dani " Cewar mumyn su kenan da take xaune, sosa kai yayi cikin shagwa6a yace "Haba mumy taya xan manta da ke just ina farincikin ganin brother ne" Nan kuma suka 6arke da hira a tsakanin su irin ta yaya da k'anin shi xuciyoyin su cike da tarin farinciki duk da shi ranshi a 6ace yake game da abin da yarinyar nan tayi mishi, kuma ya d'auki alk'awarin sai ya wulak'anta ta. _Bayan k'wana biyu_ Yammaci sosai wajen misalin karfe 5 na yamma mufidah da nabilah suka yi parking a wani had'ad'd'an restaurant wanda yawancin suke cin kayan mak'ulashe a wajen don akwai su da shegen kwad'ayi, gashi restaurant ba irin abincin da babu shi anan shi yasa suke samun costumers ta ko'ina. Bayan sun xauna suna er hirar su har aka kawo musu abin da suke son ci bayan sun gama ci ne mufidah ta Kalli nabilah tace "yanxu karfe nawa ne don Allah? " "tabbb Kya tambaye ni bayan duk wayar namu na cikin mota "Cewar nabila Dafe goshi mufidah tayi tare da cewa "oh my god gashi ko watch bamu d'aura ba, don Allah kije ki d'auko mana " Hararar ta nabila tayi tare da cewa " lallai ma yarinyar nan ni zaki aika, idan kin matsu da ganin time d'in kije ki d'auko ko kuma mu tafi ae mun gama komai " D'an murgud'a baki mufidah tayi tare da cewa "kada ki d'auko di'n, kuma banyi ra'ayin tafiya yanxu ba " "toh ae shikenan daman ke kika matsu da ganin lokacin "fad'ar nabila tana kur6ar sansanyan juice di'n pineapple da yake gabanta cikin glass cup. Yayin da mufidah ta fara wurwurga idanun ta kan mutanen wajen, karaf idanun ta suka sauka kan wani kyakykyawan guy ya sunkuyar da kanshi yana kallon k'asa yana sanye cikin blue d'in jeans da red d'in T-shirt mai dogon hannu sosai guy d'in ya had'u ba k'arya duk da bata ga fuskar shi ba idanun tane ya sauka akan wayar dake hannun shi yana lallatsa wa ganin hka yasa mufidah mik'e wa tsaye tare da cewa "nabila bari naje wajen wancan guy d'in naga time Kinsan 5:40 nake son mu bar nan " Kafin nabila ta bata amsa tayi gaba kawai sai ta bita da kallo watak'ila tsokana xata yi Indai tsokana ce mufidah ta K'ware a wajen. K'arasa wa tayi wurin ba sallama ko irin excuse di'n nan kawai tasa hannu ta kar6i wayar daga hannun mutumin kamar ta tace bata kalli fuskar shi ba ta mayar da hankalin ta kan wayar don ganin time d'in. Shi kuwa wanda aka kar6ar wa waya cikin tsananin mamaki ya d'ago kanshi don ganin mai k'arfin halin nan ae kuwa idanun shi suka sauka a kan mufidah tuni ranshi ya 6aci sosai har wani rawa jikin shi yake, ko nabila dake xaune gefe ta tsorata da ganin yanayin yanda ya koma lokaci d'aya da yake idanun ta suna kan mufidah don ganin wa gurin wa xata. Kawai kafe ta yayi da ido wad'anda suka canja launi xuwa ja saboda 6acin rai *MUSADDIQ ABUBAKAR* kenan, tana gama duba time taga 5:35 kenan sauran mintuna biyar su tafi ta d'an yatsine fuska tukunna ta mik'a mishi wayar tare da kallon mutumin mai wayar ae kuwa suka had'a ido da malamin nasu wato musaddiq tuni hantar cikin mufidah ta kad'a amman ta d'aure tace "sorry sir ashe kai........." Kafin ta K'arasa fad'i taji saukar wani gigitaccen mari a kuncin ta dama da hagu wani k'ara ta saki lokaci d'aya don ba'a ta6a yi mata irin wannan axabbaben marin ba tuni hankalin mutanen wajen yayi kansu da sauri nabila ta K'arasa wajen ta rik'e mufidah cikin girmama wa tace "malam don Allah kayi hak'uri batasan kai ne ba please " Cikin tsawa yace "Kad'an ma kika gani tun da ke baki da tarbiyya xan koya miki ita stupid girl" Gama fad'in hka yayi gaba kallon Inda suke bai k'ara yi ba don baxai iya sake kai mata wani marin ba K'arshe ma ya fice daga wajen gaba d'aya. Nabila taja hannun mufidah suka fice daga wurin in ban da kuka babu abin da mufidah take fuskar nan taji jawur da ita hka ma idanun ta wad'anda suka kumbura saboda kuka don ba k'aramin maru wa tayi hannun musaddiq ba, rarrashin ta take yi nabila kan tayi hak'uri tayi shiru cikin tsananin takaici ta d'ago kanta ta kalli nabila tace "hak'uri kika ce fah nayi toh wlh sai na rama ko bata hanyar mari ba ni nasan abin da xan mishi " Cikin mamaki nabila tace "oh yanxu baxa ki hak'uri ba da ganin guy d'in nan bashi da kirki fa" Juyar da kai mufidah tayi bata k'ara magana ba hka ita ma nabila sai da ta sauke nabila a gida kamar kullum sannan taja motar xuwa gida yau duk ma'aikatan gidan sun fuskanci an ta6a er lelen Abba da Mumy ganin duk Sannun da xuwan da suke mata bata kalli su ba balle susa ran amsa musu, wata ajiyar xuciya ta saki lokacin da ta shiga falon taga umma bata nan d'akin ta ta wuce da sauri tana xuwa kan gado ta fad'a sai lokacin ma wani kukan ya xo mata xuciyar ta tana ingixa ta kan me yasa bata rama marin ba har ta barshi ya tafi nan ta fara sak'e sak'en yanda xata rama abin da musaddiq yayi mata. _Washe gari_ Karfe 10 na safe ta gama shirin ta tsaf na tafiya skul wata swiss atampha kalar bak'i da blue ta sanya d'inkin doguwar riga ce ba k'aramin kar6ar kayan jikin ta yayi ba sai tayi light make up bata d'aura d'ankwalin ba don ita ba ma'abociyar son d'ankwali bace sai ta samu veil blue tayi rolling d'in kanta da shi sannan ta fesa different perfumes a jikin ta sannan ta d'auki bag d'in ta wanda yta xuba tarkacen hand out a ciki sai wayar ta da key di'n mota a hannun ta, palo ta fito ta tarar da umma tana xaune tana karanta jarida rungume ta tayi tare da bata peck a kumatu tana cewa "Gud morning umma nah" "morning dota kin tashi lafia?" "Qlau umma nah, ina Abba nah kuma? " "ya fita yanxu " Cikin shagwa6a tace "shine ya fita bai tsaya mun gaisa ba" Dariya umma tayi tare da cewa "kiran gaggawa akayi mishi amman ya lek'a bedroom d'in naki ya tarar sai bacci kike " D'an murmishi tayi tare da cewa "Allah sarki abbana Allah ya barmin ku" "Ameeen " Cikin sauri ta kammala breakfast d'in sannan tayi wa umma sallama ta tafi skul duk jikin ta ba dad'i sakamakon nabila da ta kirawo ta baxa ta samu damar xuwa skul d'in ba bata jin dad'in jikin ta, hka ta K'arasa skul d'in bayan ta gama d'aukan lecture's ta fito tana xaune a saman motar ta suna waya da abban ta adai dai lokacin musaddiq yake kok'arin shiga motar shi kunnen shi mak'ale da waya alamar waya yake da yake taxarar su da inda suka yi parking ba nisa sai taji yana cewa "kada ka damu gani nan xuwa brother " Mufidah ta fara tunanin ko ta bishi ta rama abin da yayi mata bata ankara ba taji ya tashi motar tare da yin gaba da sauri ta dira daga motar ta shige ta ta ita ma ta bishi a baya. Wani shegen murmishin mugunta ta saki ganin wannan restaurant d'in da ya mare ta jiya yayi parking ita ma parking tayi tare da shigewa ciki amman sai bayan ya shige, cikin mamaki tnake bin mufidah da kallo maimakon naga ta wuce ta samu waje ta xauna sai naga ta nufi wajen masu ba da abinci taja wani gefe cikin harshen turanci take ce mishi ya fad'a mata kalolin abincin Chinese food nan kuwa ya dunga fad'a mata su a ciki ta xa6i wani kalar abincin tace mishi "ka ga wancan mai ash d'in t-shirt di'n xaka kai mishi" Cikin rashin yarda yace "ae bai fad'a mana abin da xamu kai mishi ba? " er dariya mufidah tayi tare da xaro kud'i wajen 10k tace "idan har ka kai mishi abincin nan to wannan kud'in ya xama naka " Nan take cikin rawar jiki ya amince ae kuwa ta damk'a mishi kud'in cikin rawar jiki yaje ya had'o abincin ya kawo wa mufidah don ta gani da sauri ta juyar da kanta ganin abincin har sai da taji xuciyar ta na tashi da sauri tayi mishi alama da ya kai mishi ai kuwa ya rufe ya doshi table d'in da musaddiq da yah sadeeq suke xaune suna hirar su cikin kwanciyar hankali. Ajiye abincin yayi kuwa a gaban musaddiq sannan ya tafi ganin ya bud'e plate di'n abincin yasa spoon a cikin abincin yana kok'arin sa spoon di'n acikin bakin shi hankalin shi gaba d'aya yana kan waya yaxo dai dai bakin shi xai xuba ya d'ago don ganin kalar ma abincin da aka kawo mishi ganin abin da yake kok'arin sawa a baki ne yasa shi sakin ihu tare da wurgar da spoon di'n ya fara kakarin amai, da sauri Yah sadeeq ya juyo da kallon shi kan musaddiq ganin abin da ke faruwa yasa shi furta "subhannallah musaddiq me yake faru wa " ganin yanda ya ke kakarin amai yana rik'e da cikin shi............... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:03 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *E.W.F* _A gaskia bani da bakin godia gare ku en exclusive saboda kunyi min abin da naji dad'in,a gaskia ku mutane ne masu hankali da ilimi tare da sanin ya kamata jinjinar ban girma gare ku Allah ya k'ara kare min ku, Allah ya k'ara had'e kan mu daman can mu tsintsiya mad'aurin ki d'aya ne,ina son ku sosai_😻 *my Sumayya salees sadeeq (sumynbash)* _bani da kalaman godia a gare ki hak'ik'a ke masoyiya ta ce Allah ya bar xumunci ameeen_❤ *Page 3* Da sauri Yah sadeeq ya juyo da kallon shi kan musaddiq ganin abin da yake yake faruwa yasa shi furta "subhannallah musaddiq me yake faru wa ? " Ganin yanda yake kakarin amai da rik'e ciki. Ina musaddiq bai masan me yake cewa ba don gaba d'aya ya fara fita a hayyacin shi saboda kakarin aman da yake, gaba d'aya Yah sadeeq ya rud'e nan fah hankalin mutanen da suke xaune ya dawo kansu sai kallon su ake cike da tausayi a fuskar su suna tunanin ko bai da lafia ne. A hankali aman ya lafa mishi Yah sadeeq ya taimaka mishi ya xauna kan kujera yana mishi sannu sake had'a ido musaddiq yayi da abincin ai baisan lokacin da wurgar da plate di'n ba abincin ya xube a k'asa plate di'n ma bai tsira ba sai da ya fashe,ruwa Yah sadeeq ya miko wa musaddiq ya kar6a tare da sha sai da ya shanye ruwan sannan ya ajiye cup d'in tare da lumshe ido yana faman sauke ajiyar xuciya gaba d'aya fuskar shi da idanun shi sunyi ja saboda wahalar da yasha wajen kakarin aman. Sai lokacin Yah sadeeq hankalin shi ya kwanta har ya fuskanci abin da yasa musaddiq cikin wannan yanayin dariya ya tuntsire da ita saboda yasan sarai k'anin nashi akwai shegen tsantsami cikin dariya yace "Haba musaddiq akan wannan abin ka wahalar da kan ka ji yanda ka koma " Kafin musaddiq yayi magana wanda ya kawo abincin nan ya xo wurin ae kuwa Kafin ya ankara musaddiq ya kife shi da wani wawan mari Wanda har yasa ki kusan fad'u wa k'asa tuni mutumin ya rikice durkusa wa yayi a k'asa yana cewa "I'm sorry sir wlh sa ni akayi " Da yake ya gama tsorata da marin da musaddiq yayi mishi, da har ya d'aga hannu xai sake marin shi sai ya dakata jin wannan maganar da yayi cikin 6acin rai musaddiq yace "what! uban wa ya saka? " Cikin rawar jiki ya nuna Inda mufidah take tsaye tana shek'a dariyar mugunta amman sai dai me wayam ba kowa, da sauri musaddiq ya tashi tare da fita a wajen don da alama wanda yasa a yi mishi wannan iskancin bai yi nisa ba, da sauri shi ma yah sadeeq ya rufa mishi baya cike da tarin tambayoyi a xuciyar shi to shin wane yasa ayi wa k'anin shi wannan wulakancin. Suna fito wa farfajiyar restaurant d'in nan ma basu ga kowa ba hkan ya tabbatar da wanda yasa ayi hkan ya gudu daga wurin nan fah bak'in ciki ya rufe musaddiq yaso ace ya ga d'an iskan da yasa ayi mishi hka da yau kashe shi ne kawai baxai yi ba, nan dai Yah sadeeq ya lalla6a shi suka bar wajen. Mufidah kuwa duk abin da ke faruwa ta na gani kuma taci dariya har da hawayen ta ganin a mari wannan mai kawo abincin yasa ta 6uya don hka shi yasa lokacin da ya nuna wajen musaddiq bai ga kowa ba, tana ganin sun fita ita ma ta fito daga wurin motar ta ta shiga kai tsaye gidan su nabila k'awar ta ta nufa bayan tayi parking ne ta nufi ainahin kofar da xata sada ka da cikin gidan. Da sallama ta shiga umman nabila da take tsaye 6angaren dinning table tana shirya abinci akai ta jiyo tare da amsa sallamar ganin mufidah ce yasa ta fad'ad'a fuskar ta da fara'a tare da cewa "Oyoyo my daughter, baki da kirki mufidah yaushe rabon ki da shigowa cikin gidan nan sai dai ki sauke nabila a bakin gate " Umman nabila ta fad'a cikin wasa, Murmishi mufidah tayi tare da kama kunnen ta tace "sorry ammin mu na tuba na dai na" Dariya umman nabila tayi tare da cewa "Okay shikenan ya wuce sauran ki k'ara " Da sauri mufidah tace "baxan ma k'ara ba Insha Allah ammi " Dariya suka yi gaba d'ayan su sannan umman tace "Allah yasa hka ne, ina umman taki ?" "tana gida " Sai a lokacin suka gaisa tukunna ta nufi bedroom d'in nabila a gaban dressing mirror ta same ta tana shirya wa alamar fitowar ta daga wanka kenan nan fah suka sakar wa junan su murmishi sannan mufidah ta xauna gefen bed tana cire mayafin da tayi rolling d'in kanta ta furta "wash Allah na nayi matuk'ar gajiya yau " Cikin mamaki nabila tace "gajiyar me kuma? " "yanxu dai ya jikin na ki? " "ah na samu lafia daman fah ciwon kai ne na tashi dashi " "Ayyah Allah ya k'ara sauk'i sannu " Cewar mufidah "Ameeen ya rabbi " Cikin tsokana nabila tace "kin had'u da mutumin na ki ne yau? " cikin rashin fahimta mufidah tace "wa kike nufi? " "musaddiq Abubakar man " Wata dariya ce ta kubce wa mufidah ta dunga yi yayin da nabila ta saki baki tana kallon ta kawai cike da mamaki sai da tayi dariyar ta ta gama har da hawaye sannan ta bawa nabila labarin abin da tayi mishi, nan fah nabila me xatayi ban da dariya daman tasan mufidah baxa ta kyale shi ba sai tayi mishi wani abun. "Allah k'awata baki da kirki amman ina rok'an ki ki rabu dashi a matsayin ki na 'ya mace ki rabu dashi kuma ki kiyaye abin da xai sake had'a ku a gaba" D'an hararar ta mufidah tayi tare da cewa Kina nufin ya ci bulus kenan marin da yayi min ?" "Haba k'awata ban sanki da wannam halin ba ki rabu dashi please " "Okay naji na yarda amman da sharad'i guda idan yayi min xan rama" Mufidah tana rufe bakin ta umman nabila ta shigo d'akin tana cewa "ku dai idan kuka shigo d'akin kuna surutu mance wa da komai kuke toh lokacin cin abinci yayi don hka oya ku fito mu ci" "toh ummah " suka fad'i sannan suka fito daga d'akin dinning table suka nufa nan suka ci abinci sannan suka dawo falo suna ta6a hira sai yamma sannan mufidah ta tafi gida............... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:03 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *E.W.F* _Wannan shafin na kine k'awata sadeey S Adam (SaNaz), ngde da k'aunar da kike nuna min Allah ya bar xumunci ya k'are min ke a duk inda kike, ina miki fatan alkhairi_😍 *Page 4* *WACE CE MUFIDAH* Mufidah El Hussaen 'yace a wajen Alhj EL Hussein da hajia Aisha, mahaifin ta haifaffen garin d'ambatta ne sana'a ce ta dawo da mahaifin shi cikin garin kano iyayen shi ba wasu masu kud'i ba ne rufin asirin Allah ne da hka yayi karatun boko dana addini da yake shi kad'ai suka mallaka akan fannin Shari'ah yayi karatun cikakken alk'ali ne Wanda yasha gwagwarmaya Kafin kuma yayi ritaya ya koma harkar kasuwanci ta siyar da motoci. Alhj El Hussaen baxa ka kirawo shi da mai dukiya sosai ba yana da arxikin shi dai dai gwargwado yana xaune a sultan crescent, matar shi hajia Aisha uwar 'ya'yan shi bafulatana ce amman ta samu karatu sosai don ita ma k'wanan nan ta bar aiki tana matsayin babbar lecture da ake damawa dasu a makarantar buk. Yaran su biyu Omar da mufidah sune yaran da Allah ya basu Yah Omar yana k'asar london yana karatun shi ya ma kammala karatun cikin wannan watan suke sa ran dawowar tashi. Mufidah itace mai bin Yah Omar ya bata wajen shekara 4, ita ma ta kammala karatun ta na primary da secondary yanxu tana buk ta d'ora karatun ta, tana masifar son karatun na ta bata k'aunar abin da xai ta6a neman ilimin nata, kuma ba iyakar ilimin boko ta tsaya ba har da na addinin islam ta ma yi saukar alqur'ani da sauran mahimman littatafai na addini dai dai gwargwado tana da ilimi anan 6angaren. Kuma ta kasance kyakkyawar yarinya mai kama da mahaifin ta amman farin umman ta ta d'auko duk da uban shi ma ba bak'i ba ne, gashi akwai ta kirki bata shiga harkar da bata shafe ta ba akwai hankali da nutsuwa sai dai aka ta6a ta bata kyale wa kamar yanda musaddiq Abubakar ya ta6o ta. *WACE CE NABILA K'AWAR TA*? Nabila yarinya mai hankali da nutsuwa ga hak'uri maman ta hajia Amina k'awa ce ga hajia Aisha umman mufidah tare suka yi koyarwa a buk k'awaye ne sosai shi yasa mufidah da nabila suka xama k'awaye sosai, sai dai ita nabila mahaifin ta ya rasu kuma ita kad'ai ce ta rayu cikin 'ya'yan ta da take haihuwa duk mutuwa suke, gashi ita ma nabilan kyakkyawa ce sai dai mufidah ta fita kyau, duk tare suka yi karatun su kan su a had'e yake. _mun dawo labari_ Tun da suka shiga mota musaddiq Ko magana ya kasa saboda tsabar takaici har suka k'araso gida, Yah sadeeq yana parking da mota musaddiq ya fito ya nufi cikin gidan d'akin shi ya shige ya cire kayan jikin shi ya shiga toilet wanka yayi sannan ya fito ya shirya cikin wata riga mara hannu red colour da ash d'in 3quater bayan ya fesa perfumes ya fito xuwa babban palon gidan, anan ya tarar da mumy da Yah sadeeq a xaune suna hira xama yayi kusa da mumy yace " I'm hungry Mumy " Har Yah sadeeq ya bud'e baki xai yi magana kamar musaddiq yasan abin da xai fad'a wa mumyn aikuwa yayi mishi alamar kada ya fad'a mata don hka yaja bakin shi yayi shiru kawai. " my son me xa'a kawo maka?" Cewar mumy D'an yatsina fuska yayi tare da cewa " Duk abin da kika dafa mumy, amman a had'a min da fura mai sanyi" "kaje dinning table xaka samu komai acan akwai kuma fura cikin frige din kusa da dinning table, maxa tashi kaje ka ci" Tashi yayi ya nufi 6angaren dinning table d'in yana yatsine fuska, shi kuwa Yah sadeeq yana danne dariyar da taxo mishi. Cikin nutsuwa ya d'ebe abincin yaci Kad'an sannan ya sha furar nan da yawa, bayan ya gama sai ya dawo palon amman bai xauna ba ya kalli mumy da Yah sadeeq yace "ni xan je na kwanta na huta " "Okay son ae gwara ka huta " Cewar mumy yayin da Yah sadeeq yace "ae dole ma ka huta brother saboda ka sha........... " Kafin ya K'arasa fad'i musaddiq ya harare shi yayi gaba shi kuwa Yah sadeeq dariya ya tuntsire da ita mumy kuwa cewa take "je ka huta son ka rabu da yayan nan naka sarkin tsokana " "auuu hka xaki ce mumy " Cikin murmishi mumy tace "Ehhh mana " Nan dai suka cigaba da hirar su cikin kwanciyar hankali. A 6angaren musaddiq kuwa ba hutawar xai yi ba kawai tunanin Wanda yasa aka kawo mishi wannan abin kaxantar yake amman duk tunanin shi ya rasa gano ko wane, amman lallai xan bincika, da hka bacci ya d'auke shi. *WANE NE MUSADDIQ ABUBAKAR*? Dr Musaddiq Abubakar kyakkyawan saurayi ne hadadden guy wanda ilimin addini dana boko suka ratsa shi nutsatstsan mutum ne ma'abocin miskilan ci da rashin son hayaniya, bai dad'e da kammala karatun likita ba, mahaifin shi yana gina mishi asibiti, sai dai kuma musaddiq don ra'ayin kanshi yake koyarwar amman shi cikakken likita ne. Iyayen shi kuwa Alhj Abubakar da hajia khadija su biyu ne 'ya'yan su daga Abubakar sadeeq Wanda yaci sunan uban nashi suna ce mishi sadeeq sai kuma musaddiq ,suna xaune cikin xaman lafia da kwanciyar hankali gashi suna k'aunar junan su sosai har baxa ka iya banbance tsakanin sadeeq da musaddiq wanne yafi k'aunar d'an uwan shi ba, mahaifin shi d'an kasuwa ne hka shima sadeeq sana'ar mahaifin nashi yake. Alhj Abubakar da Alhj El Hussaen abokanan juna ne na k'ut da k'ut,amintaka ce a tsakanin su sosai hka ma matan su. _mun dawo labari_ Tun daga lokacin mufidah take xuwa skul da wuri idan ta fuskanci ranar musaddiq yana da lecture a ranar don hka bai k'ara korar ta ba, sai dai fah har yanxu haushin yarinyar yaji sosai, ita kuwa bata k'ara bi ta kanshi ba gashi duk test d'in da yake musu da assignment kusan ita ce kan gaba wajen ci,kuma yaga kusan lecture's din makarantar suna yaba ma yarinyar sosai. Ana cikin hka Yah Omar yayi waya xai dawo nan da k'wana 2 don Allah mufidah ba xama ita da nabila suna kok'arin had'a mishi partyn murnar kammala makarantar shi da kuma murnar xagoyowar shekarar haihuwar shi, sosai suke shirya Inda xa'a yi partyn da a abubuwan da xa'a buk'ata a wajen. Ranar Friday da misalin karfe 7 jirgin su Yah Omar yayi landing a airport d'in malam aminu kano, mufidah da nabila ne suka d'aukar shi yana fito wa daga cikin jirgin mufidah ta nufi inda yake da gudu ta rungume shi cikin tsananin farincikin ganin d'an uwan nata ,nan shima ya rungume ta cikin murnar ganin kanwar tashi xuwa can ta sake shi tare da kallon shi cikin murmishi tace "Yah Omar ka ga yanda ka koma lallai london ta kar6e ka" "lallai yarinyar nan kin rainani daman can da Kyan nawa " Ya Omar ya fad'a cikin dariya a lokacin kuma nabila ta k'araso tana gaida shi tare da yi mishi sannu da xuwa rik'e baki yah Omar yayi tare da cewa "kai kai wannan ba dai itace nabila ba?" "ita ce mana " Cewar mufidah, cikin tsokana yace "lallai yaran nan kun girma da yawa wannan ae Kun kusan kamo ni "mufidah dariya tayi yayin da nabila take sunkuyar da kanta k'asa ganin irin kallon da Yah Omar yake mata. Nan fah ya dunga tsokanar su har suka k'araso gida, iyayen shi sunyi matuk'ar jin dad'in dawowar yaron nasu lafia. Kuma a ranar su mufidah suka dunga gayyatar mutane suna fad'a musu ranar asabar ne partyn da suka shirya wa Yah Omar, ta 6angaren Yah Omar ma ya sanar da abokanan shi na nan har dasu sadeeq da musaddiq 'ya'yan abokin mahaifin nashi kuma sun bashi tabbacin xasu xo........... Aishat A muh'd [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *E.W.F* *Page 5* _Washe gari_ Mufidah da nabila ba xama ranar sai shirye shirye suke har xuwa lokacin da xa'a gabatar da partyn, hatta kayan su iri d'aya ne da nabila komai da komai shima Yah Omar kayan da xai sanya colour d'in su d'aya da na su mufidah sai dai shi na maxa ne abin da ya banbanta kenan. Har xuwa lokacin da suka sanya karfe 4 na yamma xuwa karfe 7 na dare xa'a tashi, don hka xuwa karfe hud'un duk friend's din su mufidah sun xo na skul, Wow! masha Allah na furta lokacin da na hango mufidah ta gama shirya wa cikin had'ad'd'an lace green colour nd touch d'in flowers red d'inkin riga da siket ne sun yi matuk'ar yi mata kyau sosae, mai make up suka d'auko ta tsantsara musu kwalliya, hka ma nabila tayi kyau sosae xuwa karfe 4 sun bar gidan sun tafi wajen da suka kama don yin partyn. Cikin hall di'n ya had'u iya had'uwa ya sha decoration da kwalliyar flowers ga k'aton birthday cake mai hawa uku, friend's din Yah Omar ma sun xo sosai duk inda mufidah ta gifta idanun mutane na kanta har da mata kuwa en uwanta don ba k'aramin had'uwa tayi ba, wani abin mamakin shine duk inda Yah Omar ya d'auke kafar shi to nan nabila xata ajiye ta ta sai bata kulawa yake alamun dai sun bayyana wa kansu soyayya, mufidah na ankare dasu sai dai tayi murmishi kawai kuma tayi farinciki sosai da hkan sun dace da junan su. "Haba musaddiq don Allah kasan mun yiwa Omar alk'awarin xamu je gashi kace ka fasa xuwa " Cewar Yah sadeeq kenan lokacin da ya gama shirya cikin wata tsadaddiyar shadda purple ce tayi mishi kyau sosae, ya shigo d'akin musaddiq don ganin ko ya shirya sai yayi turus ganin musaddiq a xaune yana sarrafa laptop ko alamar shirya wa bai yi ba "lafia musaddiq baka shirya ba gashi karfe 5 ma ta wuce? " Cikin yatsina fuska yace "Yah sadeeq na fasa xuwa fah " So shine sadeeq yake fad'a mishi sun yiwa Omar alk'awarin xuwa,nan dai dakyar Yah sadeeq yake lalla6a musaddiq ya yarda xai je, ajiye laptop d'in yayi bayan ya kashe ta ya mik'e tsaye tare da cewa "amman baxa mu dad'e ba ko brother don ni fah banson hayaniya? " Murmishi sadeeq yayi tare da cewa "Haba musaddiq ka d'aure mu xauna xuwa a tashi kasan yanda muke dasu Omar kamar en uwan jini " "alright bari na shirya amman idan hayaniya ta dame ni xan gudu na bar ka " Dariya Yah sadeeq yayi yana cewa "Ehhh na dai ji ". Toilet musaddiq ya shige shi kuwa Yah sadeeq ya fita daga bedroom d'in nashi, cikin mintuna talatin musaddiq yayi wanka a gurguje ya shirya cikin wani yadi blue colour yayi matuk'ar kar6ar shi yadin don bai fiye sa manyan kaya ba sai ta kama, bayan ya taje sumar kanshi ya shafa mata mayuka sannan ya d'aura tsadadden watch di'n shi tare da fesa perfumes masu matuk'ar k'amshi, sannan ya fito xuwa falo inda Yah sadeeq yake jiran shi. Yana fito wa palon mumy da Yah sadeeq suka bishi da kallo yaushe rabon su ganshi da manyan kaya gashi kuma suna mishi kyau Idan ya saka mumy ce ta fara cewa "Masha Allah d'an nawa yayi kyau Allah yasa idan aka je a sama min suruka" Yah sadeeq ya tuntsire da dariya kafin yace "tabbb mumy wannan doctor d'in idan matan suka ganshi guduwa ma xasu yi saboda fuskar ba fara'a " Cikin shagwa6a yace "Mumy ko kiyi wa brother magana idan ba hka ba xan mishi allura yanxu nan kuwa " Don Yah sadeeq Akwai shi da tsoron allura kamar mace nan kuwa ya marairaice fuska yana cewa "Haba d'an k'anina na dai na wuce mu je ni don Allah kada yi min xancen wata injection ina xama na lafia" Nan musaddiq da Mumy suka tuntsire da dariya shi kuwa Yah sadeeq da sauri ya fice daga falon yana cewa "ni nayi gaba ina jiran ka a mota " Musaddiq ne ya kalli mumy cikin murmishi yace "mun tafi sai mun dawo " Ya K'arasa fad'i yana bata peck a kumatu ita ma cikin murmishi xuciyar ta cike da k'aunar d'an nata tace "Allah ya dawo min daku lafia Allah ya tsare min ku " "Ameeen mumyn mu thanks for your du'a,bye" Daga hka ya juya ya fita mumy ta bishi da kallon k'aunar 'ya'yan ta, su kad'ai Allah ya mallaka mata ba K'aramin so take musu ba. A parking space ya tarar da Yah sadeeq xaune cikin mota yana jiran shi don hka shima shiga yayi ba tare da 6ata lokaci ba Yah sadeeq yayi wa motar key sannan suka fice daga gidan duk wanda ya gansu sai sun bashi sha'awa saboda yanda suka yi matuk'ar yin kyau gasu kyawawa tubarkallah, motar da suke ciki ma kanta abar kallo ce. Cikin mintuna da basu gaxa 50 ba suka K'arasa wajen partyn, waje Yah sadeeq ya samu yayi parking sannan suka fito jerawa suka yi kamar wasu tagwaye suka nufi wajen sam baxa kaji irin tashin sautin kid'an nan ba wanda xai dami mutane, slow music ne yake tashi a wajen. Shigowar su wajen shi ya janyo hankalin mutanen wajen kansu don ba k'aramin burge su suka yi ba musamman ma musaddiq yawancin matan wajen suka raja'a da kallon shi, irin kallon nan na daman kace kana so na. Yah Omar yana tsaye gaban cake mufidah na gefen daman shi yayin da nabila tana hagun shi kenan sun sashi a tsakiya,xai yanka cake din kenan yaga shigowar su musaddiq don hka ya dakata da yankawar wajen su ya k'arasa suka rungume junan su cikin farinciki Kafin su saki juna Yah Omar ya kalli sadeeq yace "abokina musaddiq fah ya girma nema ma yake yafi mu girma ya kamata mu ajiye iyalai mun girma " Dariya ya sadeeq yayi suka tafa da Yah Omar sannan yace "k'warai da gaske abokina ka kawo shawara mai kyau " Shi kuwa musaddiq murmusa wa kawai yayi, suna cikin tafiya xuwa gaban cake din ya Omar ya cigaba da cewa "gwara mu yi mu bawa k'annan namu fili su ma su yi " Dai dai lokacin sun k'araso wajen don hka Yah Omar ya kalli mufidah yace "sadeeq ka gane wannan kuwa?" Ya fad'i yana nuna mufidah da hannu, d'ago kan shi yayi ya kalli mufidah ita ma anyi sa'a ta d'ago kanta nan idanun su suka sark'e da na juna take Yah sadeeq yaji wani abu a tattare shi yana bin ilahirin jikin shi, lokaci d'aya sadeeq yaji wani son mufidah a cikin xuciyar shi wanda ake cewa love at first sight gaba d'aya ya mance a inda suke ya kasa janye idanun shi a kanta. Mufidah ce ta janye idanun ta a cikin xuciyar ta tace wannan ya fiye kallo da yawa ta d'an murgud'a bakin ta Kad'an hkan da tayi sai sadeeq ya ji ta k'ara shiga xuciyar shi, ya Omar da ya ankare da kallon da yake yiwa mufidah sai yayi Murmishi tare da dafa kafad'ar sadeeq yayi gyaran murya tare da cewa " uhm uhm abokina ko er gida xa'a yi NE? " Ya fad'i hkan saitin kunnen sadeeq, firgigit sadeeq yayi kamar wanda ya tashi daga bacci d'an sosa k'eya yayi tare da cewa "da xaka ba ni ae da naji dad'i " Sannan kuma ya jiyo ya sake kallon mufidah tukunna yace "gaskia ba don ka fad'a min ba baxan ta6a gane ta ba " Yah Omar yayi dariya tare da cewa "sadeeq musaddiq wannan ita ce k'anwa ta mufidah, ke kuma mufidah wad'annan sune sadeeq abokina musaddiq kuma k'anin shi, kuma nasan kin san Alhj Abubakar daddy aminin abba " Gid'a kai tayi alamar ehh ta gane sannan cikin sanyin murya tace "ina yinin ku" Sam bata kula da musaddiq ba shi ma hkan jin wata murya mai shegen dad'i tana gaida su yasa shi jiyo wa ya Kalli wajen nan kuwa suka had'a ido da musaddiq tuni annurin fuskar shi da annurin fuskar ta suka d'auke lokaci d'aya ta wani juyar da kanta gefe, sai yah sadeeq ne ya amsa gaisuwar ta ta cikin murmishi, nabila kuwa cikin mamaki take kallon musaddiq sai dakyar ta iya bud'e baki tace "malam ina yini?" Dak'yar ya iya bud'e bakin shi yace "lafia " daga hka yaja bakin yayi shiru, yah Omar kallon nabila Yayi yace "ashe kun san shi? " "ehhh malamin mu ne " Cikin mamaki Yah Omar yace "malamin ku kuma shi da likita ne kuma, mene gaskiyar xancen sadeeq? " "wlh Omar ra'ayin musaddiq ne amman naji yana cewa ya fara gaji da koyarwar, xai fara aiki a wani hospital kafin a kammala gina nashi " "okay hkan yayi kyau mu yanka cake din don idan muka biye wa hirar nan xamu iya 6atawa mutane lokaci " "alright hkan yayi kyau" Matsawa suka yi daf da cake din wad'annan xaratan maxajen su uku da kyawawan enmatan nan su biyu, amman musaddiq da mufidah babu fara'a akan fuskar su idan ka d'auke Yah Omar, Yah sadeeq da nabila k'ayataccen murmishi ne shimfid'e a fuskar su, da hka Yah sadeeq ya d'auke knife din yanka cake din tukunna ya kalli su sadeeq yace "ku matso en uwa na mu yanka tare " Gaba d'ayan su suka matso sannan yah Omar ya bawa nabila wuk'ar ta rik'e ya d'ora hannun shi kan nata sannan ya sadeeq yasa hannun shi kan na Yah Omar sai mufidah sannan musaddiq shine na K'arshe ya axa hannun shi kan mufidah lokaci d'aya suka ji wani shock but sai suka maxe kawai nan aka kirga 3 sannan suka yanka a tare nan fah aka dunga watso musu wasu kyawawan red flowers masu d'aukan pictures da video suka cigaba da aikin su, nan yah Omar ya yanka cake ya bawa mufidah, nabila, sadeeq sannan musaddiq hka su ma suka gutsuro suka bashi sosae sun burge mutane a wajen har wasu na tunanin ko en gida d'aya ne saboda ganin su farare kuma kyawawa dasu. Musaddiq ne ya xame daga wajen yaje ya samu waje d'aya ya xauna yana danna wayar shi nan fah enmata suka dunga xuwa inda yake amman ko kallon arxiki baya yi musu hka xasu karaci surutun su Amman kamar da dutse suke dole hka xata tashi ta bar wajen. Ashe mufidah tana kula da yanda yake nan fa ta k'ulu kamar itace enmatan da yake wulak'anta war, tsaki taja tare da cewa "ji be shi kamar wani sarki sai kallon mutane yake d'ai d'ai " Nabila wadda ta ji ta sai ta harare ta, yana cikin danna wayar tashi ne aka kirawo shi don hka ya mik'e xai fita daga wajen, a lokacin mufidah ta tashi daga kan kujerar hannun ta rik'e da cup Wanda yake cike da juice din strawberry xata guje wa kallon da sadeeq yake yi mata, taxo wajen kofar dai dai fita daga wajen shi kuma musaddiq ya taho sai ya take mata kafa da takalmin shi "washhh Allah " abin da mufidah ta fad'a tana runtse ido saboda tsabar xafin da taji ko kallon Inda take bai yi ba bare yayi mata sannu kuma yana sani ya take ta ganin yanda ya takata ko sannu bai ce mata kamar ya taka dutse yasa mufidah fusata ranta yayi mugun 6aci da abin da yayi mata a fusace ta bishi wajen. Yana tsaka da amsa waya ne ya juya bayan shi bai ankara ba yaji saukar wani abu mai sanyi a jikin shi tun daga saman kafad'ar shi har xuwa cikin rigar shi da sauri ya juyo ae kuwa suka had'a ido da mufidah hannun ta rik'e da cup d'in lemo alamar shi ta xuba mishi, kallon jikin shi yayi yaga gaba d'aya kayan sun 6aci don lemon ja ne tuni fuskar musaddiq tayi ja saboda tsananin 6acin rai da takaicin wannan abin da yarinyar nan tayi mishi don hka a fusace yayo kan mufidah........... Wayyo mufidah yau ta ta6o mutumin nata fiye da ko yaushe. Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* _wannan page d'in naki ne k'awata ta arxiki Aishat Aliyu garkuwa tare da sadiya bashir (Sardy bash), ku sani kuna rai na ngde sosae da k'aunar da kuke nuna min Allah ya k'ara basirah Allah ya bar xumunci, ina muku fatan alkhairi en uwa_🤝😻 *Page 7* *WASHE GARI* A hankali yake bud'e idanun shi daga wani nauyayyen bacci da ya d'auke shi bayan sallahr asuba da ya dawo daga masallaci sai lokacin ya samu cikakken bacci, d'an bud'e idon shi yayi Kad'an sai yaga wani abu kamar maciji a saman blanket din da yake rufe dashi yana kallon shi har da d'an xaro harshen nan da yake. Lokaci d'aya ya k'arasa bud'e idanun shi gaba d'aya tare da murxa su ae kuwa ba mafarki bane gaske ne maciji ne akan blanket din yana taho wa xuwa kanshi gashi bak'i wuluk sai xare harshe yake ae kuwa musaddiq a firgice ya tashi daga kan bed d'in ya mik'e tsaye cikin matuk'ar tsoro da tashin hankali ganin micijin again wurin shi yake taho wa yasa shi daka wani uban tsalle ya diro daga gadon yana furta Innalillahi don ba k'aramin tsorata yayi ba gaba d'aya ya fara had'a wani uban gumi. Yah sadeeq da yake bakin kofa yana danne dariyar shi hannun shi rik'e da remot yasa ni asashen shine yasa wa musaddiq micijin ga remot a hannun shi yana control din shi danna wani gefe yayi acikin remot din ae kuwa da sauri micijin yabi musaddiq inda yake tsaye yana karkarwa don baxai iya fita ba tun da micijin bayan shi yana kallon kofar shigo wa iya tsorata musaddiq ya tsorata ba Kad'an ba ganin micijin yayo kan shi da sauri ya sashi fara tsalle tsalle yana ja da baya kok'arin shi ya shige toilet ya rufe don yana ganin Idan ya shiga toilet ya tsira. Yah sadeeq da ya kasa danne dariyar shi ya kyalkyale da dariyar mugunta jin dariya yasa musaddiq kallon bakin kofar yana kallon Yah sadeeq cikin tsorata yace "Yah sadeeq don Allah ka taimaka min micijin ne kada ya harbe ni please " Yah sadeeq ne ya shigo cikin d'akin sosai ya nufo inda micijin yake cikin tashin hankali musaddiq yace "kada ka taho min brother xai harbe ka " K'arasa wa yayi Inda micijin yake ya d'auke shi da hannu cak tuni musaddiq ya runtse idon shi saboda kid'ima amman jin Yah sadeeq yana kyalkyala dariya yasa shi bud'e idon da sauri ganin shi yayi ya rataya micijin a wuyan shi yana cewa "Kaiii matsoracin likita na roba ne fah wasa nake ma kada ka sume min " Shiru musaddiq yayi ya xuba wa micijin idanu sosai don ya tabbatar da abin da Yah sadeeq ya fad'a ae kuwa nan ya duba tare da tabbatar wa na roba ne kamar yanda ya fad'i . A fusace musaddiq ya nufi wurin da Yah sadeeq yake yana tuntsira dariya ganin hka yasa sadeeq ya fara gudu don hka shi ma musaddiq yabi shi a baya nan suka fara gudu cikin d'akin suna tattaka kujerun d'akin da kan bed d'in nan suka dunga xagaye d'akin sadeeq yana yiwa musaddiq dariya don ganin yanda yake huci da hka suka fice daga d'akin suna gudu kamar wasu yara k'anana. Mumy tana 6angaren dinning table tana shirya kan table da kayan breakfast ta ga Yah sadeeq ya fito daga bedroom d'in musaddiq da gudu sakin baki tayi tana kallon su bata ankara ba taji sadeeq ya xagayo ta bayanta yana cewa "Mumy Ki taimake ni na tsokano likita " Cikin dariyar manya Mumy tace "ina ruwa na kai dashi Idan yayi maka allura ba ruwa na " Yana k'araso wa kusa da mumy ta rik'e shi tare da cewa "d'an lele na mai wannan yayan naka sarkin tsokana yayi maka da safen nan? " Sai da ya watsa wa Yah sadeeq harara sannan yace "mumy ina cikin bacci yaxo ya samin miciji a jikin blanket yana tsorata ni" Sadeeq bai ankara ba yaga mumy ta xame daga tsakiyar su daman shi yana bayanta ya lafe musaddiq kuwa yana gaban ta cikin dariya tace "ba ruwa na musaddiq gashi nan yi mishi allurar rashin ji " Ta fad'i tana mik'a wa musaddiq wani k'aramin first aid box wani fari ae kuwa da sauri Yah sadeeq ya rik'e tare da cewa "sorry brother baxan k'ara ba na daina " Yanda Yayi maganar ba k'aramin sa musaddiq da mumy dariya ba don hka baisan sanda ya tuntsire da dariya ba shi ma sadeeq dariyar yake nan suka rungume junan su cikin k'aunar junan su, mumy tana kallon su cikin so da k'aunar su tana addu'ar Allah ya k'ara had'e mata kan yaran nata ya dawwamar musu da farinciki. Musaddiq ne ya cika sadeeq tare da kama kunnen shi kamar shi ne babba ya d'an murd'a tare da cewa "sauran ka k'ara kuma " Kama kunnen shi yayi tare da cewa "baxan k'ara ba ma brother wannan ma tsautsayi ne " "Allah ya kyauta kullum ku dunga wasa kamar wasu k'ananan yara kun k'i fito da matar aure " Cewar daddyn su yana sakkowa daga kan stairs yana dariya da sauri suka K'arasa wajen shi tare da rungume shi suka bashi peck a kumatun shi ,mumy kuwa cewa tayi "ae kai ne kake shagwa6a su shi yasa suka kasa fitar da matar aure " Cikin shagwa6a musaddiq yace " ni har yanxu am a very young nake sai dai Yah sadeeq ". Shi kuwa Yah sadeeq cewa yayi "ni daddy na samu Matar aure wlh" Cikin jin dad'i Mumy da daddy suka ce "da gaske sadeeq? " Har suna had'a baki wajen fad'i cikin murmishi sadeeq yace "Allah da gaske jiya partyn da muka je na Omar anan naga yarinyar " Kama hannun shi mumy tayi sannan tace "Yawwa hka nake son ji a ina take ya sunan ta kuma? " "Kaiii mumy wad'annan tambayoyin hka " Cewar daddy yana dariya don yasan yanda ta damu k'warai da k'in tsayar da matar aure da sadeeq yak'i. "uhm uhm da xafi xafi ake dukan karfe dear " Cewar mumy kenan sannan ta cigaba da cewa "sadeeq fad'a min " Cikin murmishi sadeeq yace "Mumy kanwar Omar ce mufidah" Dummmm gaban musaddiq yayi mummunar fad'uwa lokaci d'aya............... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* _Wannan page d'in sadaukar wa gare ku admins din exclusive writers Ummiey xeey,Amnoor, neena cool, Aunty haliloss, nafisat anka, ruksad, Aishan umma and aunty Queen mermue, dukkanin ku ina muku fatan alkhairi Allah ya k'ara basirah ya k'ara mana had'in kai Ameeen i really luv u guys_😻❤ *Page 6* Saboda tsananin 6acin rai a fusace yayo kan mufidah kamar wani mayunwacin xaki jikin shi har rawa yake, tuni mufidah ta fara ja da baya tana da nasanin abin da ta aikata mishi ga wani uban tsoro da ya lullu6e ta lokaci d'aya. Kafin ta ankara ta ganshi a gaban ta cikin tsananin 6acin rai ya d'aga hannu ya wanka mata mari a fuska marin da yayi matuk'ar gigita mufidah, hannun ya kamo ya murd'e shi er k'ara ta saki saboda axaba Kafin kuma yace "yanda kika 6ata kayan nan wlh sai kin wanke su " Yana gama fad'in hka yaja mufidah har cikin mota ya cilla ta ciki da k'arfi har sai da ta buge nan ya shiga ya ja motar a fusace duk mufidah ta gama tsorata jikin ta har 6ari yake tayi da nasani yafi sau ba iyaka gashi batasan inda xai kai ta ba ga mangarib tayi addu'a ta dunga yi Allah ya ku6utar da ita daga hannun shi ko kwakwkwaran motsi ta kasa yi saboda firgici. Wata unguwa ce mai Kyan gaske suka shiga yanayin unguwar mai kyau ko'ina tsaf dashi ga haske ta ko'ina kamar duhu bai yi ba gashi babu yawaitar mutane sosai, a gaban wani kyakkyawan gida flat house ya danna horn tuni mai gadi ya bud'e kofar gate di'n nan ya shige da motar shi har xuwa wurin da ake parking sannan ya fito ya bud'e kofar 6angaren da mufidah take ya fisgo ta sannan yaja ta xuwa cikin gidan. Gaskia gidan ba k'aramin had'uwa yayi ba kamar da mutane a ciki komai na more rayuwa akwai a gidan musaddiq ya siya gidan ba don komai ba sai hutawa idan yayi ra'ayi don sai yafi 2 weeks bai xo ba gashi ko'ina tsaf dashi da yake akwai masu gyara mishi gidan. Suna shiga palon ya wurgar da mufidah har sai da ta sake bige wa da kujera saboda tsabar xafin da ta ji sai da ta saki k'ara Kafin kuma ta mik'e tsaye cikin tsiwa ta ce "wai mene nufin ka na kawo ni wannan gidan iyeee? " Cikin kallon wulakanci yace "saboda ki wanke wannan kayan da kika 6ata kin ji na rantse wlh sai kin wanke su " "ni fah malam dakata kaji ko agidan mu wanki ake min ban iya ba don hka baxan yi ba " Tana gama fad'in hka tayi hanyar fita daga falon ae kuwa musaddiq yasa hannu ya janyo ta da karfi har sai da ta bugi kirjin shi idanun shi cike da tsantsar tsanar ta yace "ni ina ruwa na da baki iya ba idan ma baki ta6a yin wanki ba tun da aka haife ki to wlh yau sai kin yi don kin ga ban lallasa miki jiki ba koh?" Fisge jikin ta tayi tare da cewa "ae kuwa baka isa ba ni ka bud'e min kofa na tafi " Cikin murmishin mugunta yace "ae kuwa xaki k'wana a nan don baxa ki bar gidan nan ba sai kin wanke " Yana gama fad'in hka ya nufi wata kofa ya shiga tare da rufe wa wanka yayi ya sauya kaya xuwa jeans blue da t-shirt white mai dogon hannu ya fesa perfumes sannan ya fito xuwa falo da niyyar tafiya masallaci anan inda ya barta a hka ya same ta sai rusa kuka take ganin gashi har lokacin sallahr ishshah yayi kusan karfe 8 kenan tasan yanxu sun tashi daga partyn har sun koma gida ta shiga uku Idan ta koma gida me xata ce wa umma idan ta tuhume ta ina ta xauna sai kawai ta fashe da kuka don bata da amsar tambayar a hka ya fito ya tarar tana kukan. Yana daf da xai fita daga falon ya juyo ya kalle ta tukunna yace "Idan kina son koma wa gida da wuri to Kafin na dawo daga masallaci ki wanke kuma wankin ya fita sosai fah Idan bai fita ba sai kin sake" Yana gama fad'ar Hka ya fice daga falon ya sanya key ya nufi masallacin kusa da gidan. Mufidah kuwa ganin ba yanda xata yi ta nufi bedroom d'in da ya shiga d'aki ne mai kyau wanda aka k'ayata shi sosai kamar da mace a gidan, toilet ta fad'a ta hango kayan a xube a k'asa ganin machine din wankin kaya yasa mufidah jin dad'i amman tuni murnar ta koma ciki ganin shi da tayi a rufe 6am kamar ba'a ta6a amfani dashi ba tsaki taja tare da fad'in "Wannan mutumin mugu ne wlh" cikin takaici ta d'auka ta fara wankin tana yi tana kuka har da majina dak'yar ta samu jan juice din strawberryn ya fita daga jikin kayan sannan ta matse su ta shanya su sannan ta fito sai had'a uban gumi take kallon agogon tayi taga 8:55 tara sauran minti biyar kenan da sauri ta fito daga bedroom d'in turus ta ja ta tsaya ganin har yanxu musaddiq bai dawo ba kasa xama tayi ta dunga xagaye a cikin palon saboda tsabar tashin hankali kuka kuwa ba'a magana sai faman rusa shi take. A can wurin partyn kuwa ko da su Yah Omar da nabila basu ga dawowar mufidah ba sun d'auka ta gaji ta gudu gida don hka basu damu ba, shima sadeeq da yaga musaddiq bai dawo ba yasa shi tunanin ko ya gudu gida gashi key di'n yana hannun shi, lokacin da aka tashi sai su Yah Omar ne suka mayar dashi gida . Musaddiq bai dawo gidan ba sai wurin 9:40 lokacin mufidah har ta dai na kukan sai faman ajiyar xuciya take saki alamar taci kuka ta koshi wani murmishin mugunta ya yi tare da cewa "ohhh my god kiyi hak'uri na mance fah da ke sai yanxu na tuna har naje gida na kwanta na tuna da ke" Kallon shi mufidah tayi da kumburarrun idanun ta cikin takaici da bak'in ciki ta rasa ma me xata ce tabbas maganar shi gaskia ce don gashi har ya canja kayan jikin shi xuwa sleeping dress na maxa farare sol dasu masu d'an kauri don garin akwai d'an sanyi sanyi maganar da yayi ita ta dawo da mufidah daga tunanin da ta lula yace "xaki iya tafiya yanxu naga kayan kin iya wanki kuwa don sun fita " Ashe har ya shiga ya duba su, cikin tsananin tsoro tace "wlh tsoro nake don Allah ka kai ni gida" Hararar ta yayi kafin yace "ban da wannan time d'in don hka get out " Da gudu mufidah ta fita daga falon sai da ta fita tukunna tasa mayafin ta cikin sauri ta fice daga gidan gabanta yana faman fad'uwa don kuwa dare yayi ko'ina shiru kake ji nan fah ta dunga tafiya cikin sauri ga nisa unguwar tsakanin ta da titi dak'yar ta iya k'arasa wa kan titi sai dai ababan hawa sun ragu sosai don dare yayi gashi idan ta tsayar dasu basa tsaya wa ana hka wasu en shaye shaye suka nufi inda take har d'ayan na kok'arin rik'e mata hannu don hka mufidah yasa mufidah tsorata sosai nan dai ta kwasa da gudu ae kuwa su ma suka bi ta da gudu nan fah aka fara tsere tsakanin mufidah da en shaye shayen nan wani wawan birki aka ja da mota a gaban mufidah da sauri na cikin motar ya fito ae kuwa mufidah tana ganin musaddiq ne ta nufi wajen tare da rungume shi tana kuka sosai duk a firgice take. En shaye shayen suna ganin musaddiq suka juya suka gudu, had'uwar jikin shi da na mufidah ba k'aramin canja mishi tunani yayi ba na lokaci d'aya hannun shi yasa ya k'ara rungume ta tsam a jikin shi yana shafa bayanta a hankali ita kuwa sai faman kuka da ajiyar xuciya ta ke saki, shi ma duk laifin shi ne yayi gangancin barin ta taho wa cikin wannan daren a matsayin ta na mace. Dak'yar ya iya raba jikin shi da nata ganin hka yasa mufidah da sauri rik'o hannun shi cikin kuka tace "Don Allah kada ka tafi ka taimaka min kai kai ni gida ina jin tsoro please " Kama hannun ta yayi ya sata a mota a hankali ba kamar d'axu ba shima ya xagaya ya shiga sannan yayi wa motar key ya fara tafiya gaba d'aya tunanin shi ya canja tun lokacin da yaji mufidah a jikin shi wani abu ne ke kok'arin taso mishi a cikin xuciyar shi yana danne wa amman kuma ya kasa dai na kallon ta har xuwa lokacin da ya shiga farfajiyar gidan nasu ta sauka da sauri ta nufi cikin gidan shi kuma ya fita daga gidan har yaje kwanciya yana tunana had'uwar jikin shi da ta mufidah. Mufidah tana shiga gida ta tarar da su umma, Abba da Yah Omar nabila suna xaune hankalin su a matuk'ar tashe sai ganin ta suka yi kamar an wullo ta cikin su nan ta rushe da kuka sosai umma da nabila suka rungume ta da aka tambaye ta ina taje k'in magana tayi sai kuka nan dai dak'yar suka rarrashe ta tayi shiru tana sauke ajiyar xuciya, ruwan wanka nabila ta had'a mata ta shiga wanka bayan ta fito ta shirya cikin kayan bacci ta kwanta xuciyar ta na tunanin abin da yafaru tsakanin ta da musaddiq da hka bacci 6arawo ya d'auke ta.............. _kuyi hak'uri da wannan sai gobe kuma Insha Allah_ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *E.W.F* *Page 8* Dummmm gaban musaddiq yayi mummunar fad'uwa lokaci d'aya nan take yaji wani irin abu na yawo cikin xuciyar shi wanda ya kasa tantance ko mene gaba d'aya sai yaji baxai iya cigaba da sauraren wannan hirar ba ya fara tafiya xuwa cikin bedroom d'in shi xuciyar shi cike da tarin damuwa kuma ya rasa dalilin damuwar tashi tun da Yah sadeeq ya ambaci sunan mufidah yanayin shi ya canja. A can palo kuwa mumy cikin tsananin farinciki tace " Alhmdllh my dear ka ji ashe er gidan aminin ka ya gani " Er dariya irin ta manya daddy yayi tare da cewa "kaiii amman Nayi tsananin murna yanxu daga nan office xan fara xuwa na same shi mu yi magana " Cikin jin dad'i sadeeq ya rungume daddy yana cewa "thank u daddy Allah ya bar mana kai " "Ameeen sadeeq amman gaskia baxa'a ja da nisa ba tunda duk ansan juna ciki da bai " Cewar mumy "k'warai kuwa Allah ya tabbatar da alkhairi Allah ya xa6a abin da yafi alkhairi " fad'in daddy "Ameeen thumma Ameeen " Mumy da sadeeq suka fad'a sannan mumy ta kalli sadeeq tace "je ka kirawo musaddiq mu yi breakfast " "Okay " Sadeeq ya fad'a yana tashi tsaye bedroom d'in musaddiq ya shiga turus yaja ya tsaya ganin musaddiq xaune kan carpet ya had'a kai da gwiwa daga ganin yanda yayi ba k'aramin damuwa ce a tattare da shi ba. Cikin sanyin jiki sadeeq ya k'arasa wurin shi tare da dafa shi yace "musaddiq lafia, me yafaru? " D'ago kanshi musaddiq yayi ya xubawa sadeeq idanun shi da suka yi jawur dasu a firgice sadeeq ya sake cewa "lafia brother me yafaru? " Ya fad'i yana tatta6a jikin shi ko ciwo yaji nan dai bai ga wani alamun ciwo ba da sauri Yah sadeeq ya mik'e xai je ya kirawo su daddy, musaddiq kamar yasan nufin shi caraf ya rik'e hannun shi tare da cewa "na rok'e ka brother kada ka fad'a wa su daddy please " Dawowa sadeeq yayi tare da cewa "okay naji fad'a min damuwar ka Idan kaki xan fad'a wa su daddy" Murmishin yak'e musaddiq yayi tare da cewa "Naji brother " Nuna shi yayi da d'an yatsa yace "are you sure? " "yes " Cewar musaddiq dak'yar don ji yayi xuciyar shi na wani irin xafi, "toh fad'a min " Cewar Yah sadeeq yana rik'e hannun musaddiq. D'an shiru yayi yana tunanin me xai cewa sadeeq xai fad'a mishi yarinyar da yake so ita shi ma yake so nooo i can't ko da kuwa son shi xai xama ajalin shi baisan ya kamu da son mufidah ba sai da Yah sadeeq ya furta yana son ta yanxu shi ya xai yi me xai cewa brother. D'ago kanshi yayi ya kalli sadeeq yaga ya xuba mishi ido alamar shi yake saurare, d'an kwakwalo murmishin yak'e yayi yace "brother daman fah kawai ina tunanin yanda xan bar lecturing na koma hospital da aiki nake don basa son na bar skul d'in sun dame ni da rarrashi so shine na xauna nake tunanin mafita " Tuntsire wa da dariya sadeeq yayi kafin yace "don wannan kuma shine kake sa kan ka cikin damuwa kawai ka share su ka fara xuwa hospital bana son kana wahala " "Yawwa brother thank u Allah ya bar min kai " Cikin dariya sadeeq yace "hka nake so d'an k'anina bana son ina ganin ka cikin damuwa ko ciwo ji nake kamar na dawo dashi jiki na nake ji bana son ganin 6acin ranka nafi son ko yaushe ka kasance cikin farin ciki idan naganka cikin damuwa ji nake hankalina yana matuk'ar tashi bana samun kwanciyar hankali sai naga kai ma ka samu" Musaddiq rungume sadeeq yayi a hankali wasu hawaye suka xubo wa musaddiq yayi saurin sa hannu ya goge su sannan ya saki Yah sadeeq Mumy wadda take tsaye bakin kofar shigo wa bedroom d'in ta saki murmishin jin dad'i Kafin tace "aiken kenan sadeeq ba kai ba wanda na tura ka kirawo nagaji da jira na biyo bayan ku " Murmishi Suka yi bayan sun had'a ido tukunna kamar had'in baki suka ce "sorry mum " Kamo hannun su tayi suka fito daga d'akin xuciyar musaddiq cike da tarin damuwa. Bayan sun kammala breakfast d'in daddy ya tafi office hka shima sadeeq ya fito xai tafi don har ya shiga mota musaddiq ya tsayar dashi suka tafi tare xai sauke shi a buk. Yah sadeeq yana parking ya fito daga motar shi da musaddiq suna magana sai ga mufidah tayi parking d'in motar ta sun fito tare da nabila, gaba d'aya hankalin musaddiq yayi kanta tayi mishi kyau sosae cikin wata arabian gown bak'a ce hka mayafin da tayi rolling d'in kanta bak'i ne da yake fara ce kayan sun amshe ta, musaddiq ji yake kamar ya ta a jikin shi ko yaji sassauci a cikin xuciyar shi yanda yake jin wata xaxxafan son ta na sake kwaranya a cikin xuciyar shi wannan wacce irin masifa ce dak'yar ya iya saita idanun shi daga barin kallon ta. Sai da suka d'an gifta su sannan sadeeq ya ankare da ita don hka cikin sanyin murya yace "mufidah! " Cikin sauri suka jiyo tare da nabila don ganin mai kiran nata da musaddiq ta fara had'a ido sannan ta kalli sadeeq Wanda yake ta xuba murmishin farincikin ganin ta k'araso wa suka yi sannan suka gaisa da sadeeq ko kallon Inda musaddiq yake mufidah bata yi ba ko gaida shi bata yi ba sai nabila shima musaddiq yiwa sadeeq sallama yayi ya tafi xuciyar shi nayi mishi wani rad'ad'i dak'yar ya iya k'arasa wa cikin office ya xube yana wani irin haki kamar wanda yayi tseren gudu. Ganin musaddiq ya tafi yasa ita ma nabila ta wuce don ta basu waje cikin wani salon kallo wanda ya bawa mufidah kunya yace " Naga dai yanxu kamar kina sauri ki ban contact di'n ki zuwa anjima xan xo gida na same ki don akwai muhimmiyar magana da xamu yi " Ya K'arasa fad'i yana mik'a wa mufidah wayar shi kar6a tayi tare da shigar da contact di'n ta sannan ta mik'a mishi tana cewa "Okay ba matsala sai ka xo" Da hka sukayi sallama ya shiga motar shi ya tafi ita kuma mufidah ta shige department d'in su tana cewa tatsuniyar gixo baxa ta shige k'ok'i ba don tsab ta karance shi tun ranar birthday di'n Yah Omar. Bayan sun fito a lecture's mufidah take sanar wa da nabila yanda suka yi da sadeeq Sam nabila batayi mamaki ba don yanda yake bin ta da kallo ranar partyn Don hka nabila tace "Ki gode wa Allah mufidah don samun miji kamar sadeeq a wannan xamanin sai an shirya ya tattara komai gashi kyakkyawa duk da musaddiq yafi shi kyau ga kud'i da mutunci sannan ga fara'a Ba kamar musaddiq ba Allah yarinya Idan ya furta miki so kawai ki bada kai bori ya hau don ni fah mun gama shirya kan mu da Yah Omar " Cikin dariya mufidah tace "ae na d'ago jirgin na ku tuntuni to Allah ya tabbatar mana da alkhairi " "Ameeen sister tashi mu gudu gida don Yah Omar xai xo kuma gashi ke ma Kina da bak'o " "alright mu je " Cewar husna tana yin gaba sun xo wajen da suke parking wurin ba mutane sosai kafin su k'arasa wajen motar sai takalmin mufidah ya gurd'e ta ta tafi xata fad'i k'asa caraf taji an rik'e ta ta fad'o jikin mutum k'amshin turaren shi kawai taji ta fahimci ko wane don hka da sauri ta tashi daga jikin shi tare da kallon shi tana jin wani yanayi tattare da ita Idan ta kalli cikin kwayar idon shi yayin da shi ma musaddiq ya xuba mata ido sai dai yau ba kallon tsanar ta take hangowa acikin kwayar idon shi ba maganar da nabila tayi ne ya dawo dasu hayyacin su don hka da sauri ya shige daman jiran fitowar ta yake domin ya sake sata cikin idanun shi cikin sanyin jiki mufidah take driving tana tunanin irin kallon da yake mata wanda yasha banban da na ko yaushe........... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* _Wannan page naki ne k'awata khadijah neena cool (niger), Allah ya bar xumunci ya bar mu tare ina miki fatan alkhairi_🤝😻 *Page 9* Da yammacin ranar da wajen karfe 5 sadeeq ya fito cikin shirin tafiya gidan su mufidah yaci gayu cikin wata tsadaddiyar shadda milk colour an yi mata aiki da brown din xare sai ya sanya takalmi brown da hula brown mai ratsin milk a jiki gaskia yayi kyau sosae daman shi gwanin sa manyan kaya ne k'ananun kaya basu dame shi ba wannan sai musaddiq. A falo ya tarar da mumy da musaddiq suna xaune mumy tana faman lalla6a shi ya ci abinci don yinin yau gaba d'aya ta kasa gane d'an nata K'arasa wa yayi Inda suke ya xauna tare da cewa "me yake damun shi ne Mumy?" "nima yanxu na gama tambayar shi yace min ba komai kuma ban yarda ba don yau gaba d'aya cikin damuwa yake " Cewar mumy kenan fuskar ta cike da damuwa, sadeeq ne ya kalli musaddiq shima fuskar shi d'auke da damuwa ya rik'o hannun shi tare da cewa "Haba brother ka fad'a mana damuwar ka mana ko xamu iya taimaka maka da wani abin " Shiru musaddiq yayi ya rasa me xaice musu "tell me please what wrong with u ?" sadeeq ya sake fad'i duk farincikin da yake cikin xuciyar shi na xuwa wurin mufidah amman sai yaji farincikin ya kau sakamakon ganin tilon k'anin shi cikin damuwa. Cikin murmishin yak'e yace "ni fah kada ku damu mumy and brother bana jin dad'in jiki nane amman ba wani abun ba ne " Sam basu yarda da abin da yace ba amman tun da har yak'i sanar musu to abin babba ne, hka dai suka bashi shawara akan ya dage da addu'a sosai akan abin da yake damun shi godiya yayi musu sannan ya tashi ya tafi d'akin shi ya rufe kofa tare da jingina a jikin kofar xuciyar shi cike da tunanin mufidah. Acan palo kuwa da kallo suka bishi cikin tsananin tausayin shi, kafin kuma Yah sadeeq yayi wa mumy sallama yana sanar da ita gidan su mufidah xai je, nan tayi mishi addu'ar dawowa lafia tare da bashi sak'on ya gaida mata da mufidah. Musaddiq kuwa dakyar ya iya jan kafar shi xuwa bakin bed d'in shi ya janyo drower din jikin bed side ya janyo wani d'an k'aramin littafi wanda kallo d'aya nayi mishi na tabbatar da diary din shi ne Wanda yake rubuta mahimman abun da ya shafi sirrin shi a ciki, biro ya d'auko ya buge tsakiyar page ya fara rubutu kamar hka....... *NAYI SAKE!* _Tun ranar da na fara d'ora kwayar idanuna akan ta nake jin wani abu a tattare da xuciya ta da jiki na, ban tabbatar da son da nake mata sai ranar da ta xuba min juice a jikina na kaita gida na ta wanke min a cikin daren da na taimake ta daga hannun wasu 6ata gari har jiki na ya had'u da jikin ta a ranar na tabbatar da sonta a cikin xuciya ta ina niyyar neman soyayyar ta............_ _sai dai kash d'an uwana yaya na da nake dashi shi kad'ai ya furta yana son ta yayana mai kauna ta da son bani farinciki a ko da yaushe, na hak'ura da ita har abada saboda nasan nayin saken da nasan baxan ta6a samun ta ba a rayuwa ta_ _son ki ne xai xama ajali na don nasan har na mutu baxan ta6a dai na k'aunar ki ba, i luv yhu so much *M*, i really luv yhu_. Yana gama fad'in hka ya rufe littafin tare da ajiye wa ya fad'a kogin tunani sosai ga son mufidah yana k'ara nukurkusar xuciyar shi lokaci d'aya wani mugun ciwon kai ya kama shi cikin en mintuna wani xaxxafan xaxxa6i ya rufe shi sai karkarwa sanyi yake sosai jikin shi ya d'auki wani mugun xafi lokaci d'aya kuma ya fara wani jan numfashi wanda dak'yar ya ke fita. Yah sadeeq bayan yaje gidan su mufidah anan farfajiyar gidan ya had'u da Yah Omar yana kok'arin tafiya gidan su nabila nan suka rungume junan su sannan suka yi musabiha cikin murmishi Yah Omar yace "Hmmm wannan gayun dai nasan xuwa wurin mutuniyar kayi ba xuwa na ne ba " Cikin dariya sadeeq yace "yes nawan ashe ka gano hkan " Tafawa suka sannan suka juya xuwa cikin gidan bayan sun gaisa da umman su mufidah sannan Yah Omar ya kai shi palon saukar bak'i daga hka yace "toh ni Naga ma aiki na xan tafi wajen tawa matar to be Insha Allah" "Yayi kyau friend ngde sai ka dawo " "ba Godiya tsakanin mu sadeeq mun riga da mun xama en uwan juna sai mun yi waya bye " Yana gama fad'in hka ya fice daga falon da sauri , bai fi mintuna 5 da tafiyar Yah Omar mufidah ta shigo falon cikin sanyayyiyar muryar ta mai dad'in gaske tayi sallama cikin murmishi sadeeq ya amsa sallamar cikin sauri ya mik'e tsaye ya kar6i babban plate di'n dake hannun ta ya ajiye kan table d'in tsakiyar palon tukunna yayi mata nuni da ta xauna ae kuwa ta samu waje ta xauna tare da gaida shi nan ya amsa yana kallon ta don tayi mishi kyau sosae gashi ta suturta jikin ta da hijab babba mai hannu hakan ba k'aramin dad'i yaji ba xuciyar shi ta Kara k'aunar ta bayan sun gama gaisa wa ne ya fara janta da er hira ganin ta kasa sakin jikin dashi daga K'arshe ya fara da yi mata bayanin abin da ya kawo shi Tsugunna wa yayi a gaban ta amman bai ta6a mata jiki ba ya kwantar da murya a nutse ya fara cewa "mufidah abin da ya kawo ni wajen ki ba komai bane sai neman soyayyar ki tun lokacin da na fara ganin ki kuma auren ki xanyi ki bani dama na nuna miki son da nake miki " shiru mufidah tayi tana tunani shi kuwa Yah sadeeq cigaba wa yayi da cewa "say something mufidah please " D'an ajiyar xuciya ta yi cikin jin kunyar shi tace "sai nayi tunani " "Okay ba matsala Allah yasa naji kyakkyawan result " murmish kawai yayi ya dan sha juice and snacks din da taka wo mishi suna er hira har xuwa gabannin mangarib sannan yayi mata sallama ya tafi. Mumy ce ta fito daga bedroom d'in ta xata shiga kitchen ta tuna tun da musaddiq ya shige bedroom d'in shi bai fito ba hka kawai taji gaban ta ya fad'i da sauri ta nufi bedroom d'in tana shiga ta tarar da musaddiq lullu6e da bargo kato ya kudundune a ciki yana rawar sanyi ga numfashin shi dak'yar ya ke jan shi cikin tsananin tashin hankali ta nufi kan bed d'in tana cewa "Musaddiq!" Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *E.W.F* *Page 10* Da sauri mumy ta k'arasa kan bed d'in ta bud'e rufar da musaddiq yayi da bargo da sauri ta janye hannun ta lokacin da ta ta6a jikin shi taji xafi xau dashi cikin kid'ime wa Mumy tace "musaddiq me yake damun ka? " Cikin rawar sanyi da murya yace "way... wayyo mumy xax..... xaxxa6i ne yake damunaaa" Ya K'arasa fad'i yana jan wani irin numfashi da yasa gaban mumy muguwar fad'uwa cikin tashin hankali tace "sannu bari na kirawo Dr muh'd ya duba ka sannu " Cikin sauri mumy ta d'auki wayar musaddiq da take gefen bedside ta nemo number d'in Dr muh'd bayan ya d'aga yana tsokanar musaddiq ya d'auka shi ne sai da yaji muryar mumy cikin girmama wa ya gaida mumyn yana godewa Allah da bai yi wata maganar da xai ji kunya ba, mumy ce take sanar mishi Yayi sauri ya xo ya duba musaddiq bashi da lafia tuni hankalin Dr muh'd ya tashi ya katse wayar da sauri ya d'ebe kayan aiki ya shiga mota gidan su musaddiq ya nufa . Dr muh'd abokin musaddiq ne sosai tare suka yi karatu har suka dawo nigeria suna xumunci sosae gashi a gari d'aya suke sai xumuncin Ya k'ara k'arfi har iyayen su suma suka k'ulla xumunci sanadiyyar yaran su, Dr muh'd yana bala'in son musaddiq sosai gashi halin su yaxo d'aya kosan ko yaushe yana gidan amman musaddiq baya xuwa gidan su sosai sai ya kama. Cikin en mintuna Dr muh'd ya k'arasa gidan kai tsaye d'akin musaddiq ya nufa a bakin kofa yayi kici'bis da mumy tana ta safa da marwa ta kasa xama waje d'aya, d'akin ya shiga nan ya fara duba jikin musaddiq cikin k'ware wa da iya aikin nashi. Xaune na hango Dr muh'd ya xuba tagumi yana kallon musaddiq wanda yak'i yarda Yayi mishi allurar bacci ko ya samu ya huta cikin damuwa d'auke a fuskar Dr muh'd yace "my friend mene kasa a ranka hka me yake damun ka da xaka sa tunanin abu a ranka wanda xai janyo mata wata matsalar, haba musaddiq kamar ba likita kake ba kene ma mai bawa wani shawara ma ya rage tunani balle kai " Kallon shi musaddiq kawai yake cigaba yayi da maganar shi yana cewa "ina son ka fad'a min matsalar ka yanxu na gani ko Allah xai sa na baka wata shawarar ka daina barin abu a ranka kana tunani my friend " D'an murmishin yak'e musaddiq yayi tare da cewa "me ka gano yake damuna aboki? " Cikin tausayin musaddiq yace "naga jinin ka ya hau fah sannan yanayin bugun xuciyar ka ya k'aru fiye da yanda mutum mai cikakken lafia take tell me what happened to you my friend? " Musaddiq ya bud'e baki xai yi magana kenan Yah sadeeq ya turo kofar ya shigo d'akin hankalin shi a matuk'ar tashe kama hannun musaddiq yayi yana cewa "brother me ya same ka ne yanxu mumy take kirana a waya baka da lafia " Jiyo wa yayi kan Dr muh'd yana cewa "Doctor sanar da ni abin da yake damuwa da d'an uwana kada kace min wani babban ciwo ne please " Yah sadeeq ya k'arasa fad'i idanun shi taf da hawaye cikin tausayin Yah sadeeq Dr muh'd ya bud'e baki xai yi mishi bayanin abin da yake damun musaddiq sai suka had'a ido da musaddiq ya marairaice fuska tare da yi mishi alama da hannu yana rok'an shi kada ya fad'a wa Yah sadeeq gaskiar abin da yake damun shi. Cikin sanyin jiki Dr muh'd yace "Yah sadeeq xaxxa6in typhoid fever ne yake damun shi amman Insha Allah xai samu lafia ka kwantar da hankalin ka " Hannun Dr muh'd ya kamo yana cewa "Okay doctor thank u but ina son ka bashi kula wa sosai bana son wani abu ya faru da k'anina " "xanyi iyakar kok'ari na yah sadeeq kuma xai xamu lafia da sauri Insha Allah " Rungume Dr muh'd yayi cikin jin dad'in abin da ya fad'i sannan ya dawo kan musaddiq tare da tatta6a jikin shi jin xaxxa6in ya sauka yasa shi sakin wata ajiyar xuciya nan ya dunga yi mishi sannu duk motsin da yayi hka ma mumy ta shigo suka had'u suna lalla6a shi Dr muh'd yana gefe xuciyar shi cike da tunanin me musaddiq yasa a ranshi har xai kamu da hawan jini yana samun duk wata kulawa a wajen iyayen shi da d'an uwan shi. Har Dr muh'd ya tafi bai samu damar ke6ewa da musaddiq ba yaji abin da yasa a ranshi kuma me yasa yak'i yarda Yah sadeeq yasan gaskiar abin da yake damun shi yasa shi yin k'arya da wannan tunanin ya k'arasa gida. Cikin k'wanaki 2 musaddiq yana fama da wani xaxxa6i da ciwon kai duk yabi ya rame ya sake yin fari sosai iyayen shi sosai suke kula dashi don duk a xaton su xaxxa6in typhoid ne basu san gaskiar xancen ba daga Allah sai musaddiq din sai Dr muh'd sune suka san ainahin abin da yake damun shi kuma Har xuwa yanxu Dr muh'd bai samu damar yin magana da musaddiq ba. A 6angaren Yah sadeeq kuwa ba k'aramin tsorata yayi ba da jikin musaddiq amman ganin ya fara samun sauk'in xaxxa6in yasa shi hankalin shi ya d'an kwanta, yah Omar da husna da nabila sun xo dubiyar shi a ranar da yafi samun sauk'i su kaxo har ya samu damar fito wa palo yana xaune suka shigo palon Yah sadeeq yana musu jagora da mufidah ya fara had'a ido ae kuwa take yaji gaban shi ya fad'i bugun xuciyar shi na sake bugawa da sauri da sauri. Bayan sun gaisa da Mumy suka yiwa musaddiq Sannu da jiki dak'yar ya iya bud'e bakin shi ya amsa nan aka xauna ana er hira tashi musaddiq yayi ya shiga bedroom din shi mumy ma ta shige kitchen tana had'a wa su mufidah abin motsa baki ganin hka yasa nabila ta bita tana taya ta ,yah sadeeq kuma yaja Yah Omar xuwa part d'in da yake ginawa wanda yake fatan su rayu da mufidah a ciki har sadeeq yana tsokanar mufidah ko xata je ta ga ni ae kuwa ta danna mishi harara dariya suka kyalkyale da ita shi da Yah Omar da hka suka fita daga palon aka bar mufidah ita d'aya xaune. Tsawon 5 mint tana xaune kamar ance d'ago kan ki sai ta hango musaddiq ya fito daga cikin d'akin shi yana dafe da kanshi alamar ciwo yake mai sai ta ga kuma ya fara layi kamar xai fad'i k'asa ganin yana kok'arin fad'uwa yasa mufidah tashi da sauri ta nufi wajen shi tana xuwa dai dai wajen da yake tsaye yayi baya xai fad'i da sauri ta rik'o shi to da yake k'arfin namiji da mace ba d'aya ba kawai sai yayi jikin ta ita kuma mufidah yafi k'arfin ta kawai sai tayi baya xata fad'i sai taji kuma an fisgo ta xuwa cikin jikin shi ta fad'a kan faffad'en kirjin shi da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido yana mata wani irin kallo gaba d'aya idanun shi sun canja Kala sun kai wajen second talatin suna kallon junan su don mufidah hka kawai taji ta kasa d'auke idanun ta daga cikin idon shi. Ji tayi ya raba ta da jikin shi ya juya ya koma cikin d'akin, ita ma mufidah ta koma kan kujera ta xauna tana tunanin wannan wanne irin mutum ne a taimaka mishi babu godia dama nasani na barshi ya fad'i Cewar mufidah a fili har da Murgud'a bakin ta kamar yana ganin ta. Tana xaune a hka sai ga mumy da nabila sun fito daga kitchen kowannen su rike da babban plate a hannun su da sauri mufidah taje ta kar6i abun hannun mumy ta ajiye akan table ana hka sai ga Yah sadeeq da Yah Omar sun dawo sun d'an ta6a abun da Mumy ta kawo musu sannan suka yi mata sallama suka tafi tare addu'ar Allah ya bawa musaddiq lafia. Mufidah ta kar6i soyayyar sadeeq duk da ba wani son shi take sosai ba kunyar shi ce tasa ta amince da soyayyar shi kuma ganin irin son da yake mata ya wuce misali gashi bashi da makusa nan fah iyaye suka shiga xancen. Cikin kankanin lokaci aka tsayar da ranar auren sadeeq da mufidah, yah Omar da nabila to abune duk ansan juna tun da dad'e wa ana xaune kusan tare sun xama kamar en uwan juna. Shi kuwa musaddiq iyayen shi sun rasa gane kan shi yau lafia gobe cuta duk yabi ya rame ciwo kullum Cin shi yake gashi yak'i gayawa Dr muh'd ko akwai wani taimako da xai yi mishi, kullum ya hau na jinin shi maimakon ya sauka sai hawa yake har takai Dr muh'd ya duba shi a wata safiya bayan sun gama duba patient din su hankalin Dr muh'd ba k'aramin tashi yayi ba ganin har xuciyar musaddiq ta fara ta6u wa cikin tsananin tashin hankali Dr muh'd ya kalli musaddiq da yake kwance kan bed d'in asibitin yace "yau baxan iya rabuwa da kai ba musaddiq sai ka fad'a min abin da yake damun ka, ko kuma na sanar dasu daddy Don baxan xuba ido ka mutu a banxa ba " Murmishin da musaddiq yayi sai da Dr muh'd ya tsorata bud'e baki yayi xai yi magana kenan wani tari ya kama shi ya dunga yin tarin nan lokaci d'aya idanun shi da fuskar shi suka yi ja kanshi Dr muh'd yayi yana mishi sannu gaba d'aya hankalin shi a tashe yake ya tsorata da jikin musaddiq sosai wani jan numfashi musaddiq yayi yaraf kuma sai ya xube kan gadon kamar matacce cikin raxani da kad'uwa Dr muh'd ya fara girgixa yana cewa "na rok'e ka musaddiq ka tashi please " Amman ina musaddiq bai ma san abin da yake yi ba................. Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *Page 11* Amman ina musaddiq bai san ma yana yi ba, da gudu Dr muh'd ya fita daga room d'in yaje ya kirawo wasu doctor's guda biyu nan suka had'u kan musaddiq suka fara kok'arin ceto rayuwar shi. Sun dad'e sosai akan musaddiq Kafin Allah ya taimake su numfashin shi ya dawo dai dai nan suka sanya mishi drip tare da yi mishi allurar bacci tukunna suka fita daga room d'in aka bar Dr muh'd yana xaune a gefen shi ya xuba mishi ido yana kallon shi xuciyar shi cike da tsantsar tausayin shi. Yini guda cur musaddiq yana bacci sai yamma sosai ya farka da Dr muh'd ya fara had'a ido lokacin da ya farka cikin sauri Dr muh'd ya rik'e shi tare da cewa "sannu musaddiq ya kake jin jikin na ka? " Cikin kasala da sanyin murya yace "muh'd na samu lafia ngde sosae aboki " Duba shi ya k'ara yi sannan ya taimaka mishi suka shige office d'in shi ruwan wanka mai d'umi Dr muh'd ya had'a mishi bayan musaddiq yayi wanka tare da yin alwala ya fito ya gyara jikin shi sannan ya rama sallolin da ake bin shi bayan ya idar ne ya kwanta kan doguwar kujerar da take cikin office d'in ya xurfafa a tunanin mufidah kullum yana addu'ar Allah ya cire mishi son mufidah a cikin xuciyar shi amman kamar k'ara mishi son nata ake ya rasa ya xai yi ya fitar da sonta daga cikin xuciyar shi. Yana cikin wannan tunanin ne Dr muh'd ya shigo office d'in sau biyu yana sallama amman musaddiq bai ji shi ba yayi xurfi a tunani sosai girgixa kai kawai yayi ya nufi inda yake kwance ya girgixa mishi kafad'a tare da cewa "Musaddiq!" Firgigit ya dawo hayyacin shi yana kallon Dr muh'd da idanun shi wad'anda suke a lumshe. "ga tea nan kasha ga magungunan ka nan Idan ka gama xamu yi magana " Cewar Dr muh'd yana mik'a wa musaddiq cup d'in da ya had'a tea bai yi musu ba yasa hannu ya kar6a ya fara sha bayan ya shanye Dr muh'd ya bashi magungunan yasha sannan ya jiyo ya fuskan ci musaddiq yasha Kunu sosai don yana son sanin gaskiar abin da yake damun shi ya fara da cewa "musaddiq ina son sanin me yake damun ka, me kasa a ranka har yana kok'arin haddasa maka mummunan ciwo a jikin ka? " Kallon shi musaddiq yayi sannan ya kawar da kanshi daga kallon shi yace " babu abin da yake damuna muh'd just ciwo daga Allah ne" "enough musaddiq baxan ta6a yarda da abin da kace min ni nasan kan ka tuna ba ma 6oye wa junan mu matsalar mu, idan kuma ka k'i fad'a min wlh xan je na gayawa su daddy su tambaye ka ae su dole ka fad'a musu abin da yake damun ka ?" Cewar Dr muh'd kenan. "kaiii ka yarda fah da gaske nake babu abin da yake damuna" "Okay shikenan Allah ya baka lafia" Fad'in Dr muh'd sannan ya nufi fita daga office d'in ranshi a matuk'ar 6ace, caraf yaji musaddiq ya rik'e mishi hannu tare da cewa "I'm so sorry aboki ni kaina bansan abin da yake damu na ka taya ni da addu'a kawai " "ka cika ni Idan baxa ka fad'a min gaskia ba na rabu da tambayar ka abin da yake damun ka su daddy xan fad'a wa" Musaddiq ya rasa ta inda xai kauce wa muh'd a wannan Karon don yak'i tsayawa ya yarda da abin da yake ce mishi idanun shi sun yi ja sosai ga wani irin jiri da yake ji da axabbaben ciwon kai baisan lokacin da ya bud'e baki yace "ina son ta muh'd soyayyar tace tasa na shiga cikin wannan halin na rasa yanda xanyi na cire ta daga cikin xuciya ta " Koma wa yayi ya xauna da k'arfi kan kujera sannan ya cigaba da cewa "baxan iya fad'a maka adadin son da nake mata ba amman nayi sake abokina na rasa ta har abada " Sakin baki Dr muh'd yayi yana kallon musaddiq cikin mamaki don shi tun da yake dashi bai ta6a ganin yayi mishi xancen mace ba a hankali ya k'araso inda musaddiq yake xaune hannun shi rik'e da kanshi da yake masifar yi mishi ciwo kamar xai cire, dafa mishi kafad'ar shi yayi tare da cewa "ita wace musaddiq, taya akayi kayi sake har ta kubce maka? " Cikin tsananin ciwon kai yace " mufidah ce aboki mufidah wadda Yah sadeeq xai aura itace nake nayi saken da ban sanar mata ba har Yah sadeeq ya ganta gashi yana masifar son ta har iyaye sun yi magana nan da two month's xa'a yi bikin " Hannun shi yasa ya rik'o kafad'un muh'd da k'arfi yace "ka ji abin da yake damu na kuma nayi wa Kai na alk'awarin baxan ta6a bari Yah sadeeq yasan wannan xancen ba har abada saboda nasan idan ya sa ni wlh xai hak'ura ya bar min ita, kai ma na rok'e ka kada ka fad'a wa kowa wannan maganar har kuwa rashin lafiyar da yake damu na, na hak'ura da ita har abada baxan rusa farinciki d'an uwana ba" Wani mugun tausayin musaddiq ne ya kama muh'd har wasu k'walla sai da suka xubo mishi na tausayin musaddiq hannu yasa ya goge hawayen tare da cewa "tabbas nima baxan baka goyan bayan Yah sadeeq yasan wannan xancen ba don ni shaida ne akan irin yanda masifar son ka nasan komai xai iya yi maka ,amman ina rok'an ka don Allah musaddiq ka cire mufidah da ga ranka please" Wani murmishin yak'e musaddiq ya saki tare da cewa "aikin gama ya gama muh'd don son mufidah ya riga da ya shiga cikin xuciya ta baxan iya cire shi ba ni nasan da sonta xan mutu " Yana gama fad'in hka ya mik'e tsaye tare da d'aukan briefcase din shi da key di'n mota, yayin da Dr muh'd ya bishi da kallon tausayi tabbas abokin nashi yayi xurfi a son mufidah wannan shi ake kira da *YAYI SAKE*, shi ma Dr muh'd di'n mik'e wa tsaye yayi bi bayan shi. Ya kai hannun shi kan handle di'n kofar xai bud'e kenan aka turo kofar tare da shigo wa lokaci d'aya gaban musaddiq da Dr muh'd yayi mummunan fad'uwa saboda had'a idon da suka yi da Yah sadeeq yana shigo wa fuskar shi d'auke da tarin damuwa sosai da gani hankalin a matuk'ar tashe yake wajen musaddiq ya nufa kai tsaye.................. Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *PAGE 12* Wajen musaddiq ya nufa kai tsaye sai da yaxo gab da shi tare da kamo hannun shi yace " why musaddiq da xaka yi switch off d'in phone's din ka duk ka d'aga mana hankali ina office mumy ta kirawo ni naxo na duba ka, gashi har time d'in dawowar ka ya wuce baka dawo ba?" D'an murmishin yak'e musaddiq yayi tare da cewa " sorry bro ina lafia wani aiki ne ya rik'e ni shi yasa nayi switch off d'in wayar " "Okay amman kana sa wayar naka a silent ka daina kashe wa, don ka hankalina ya tashi sosai " "Haba Yah sadeeq ni fah ba yaro ba ne " Musaddiq ya fad'i yana dan Murmishi, hararar wasa Yah sadeeq yayi mishi tare da cewa "a wurin Mumy, daddy da kuma ni duk kallon yaro muke ma so dole mu tattara dukanin kulawar mu kan ka " Yah sadeeq ya k'arasa fad'i yana kallon fuskar musaddiq a yau sai yaga musaddiq din ya k'ara haske fiye da koyaushe gashi ya rame amman da yake Yah sadeeq bai fiye irin wannan binciken ba sai kawai ya juya da kallon shi kan muh'd yace "likita bokan turai ya fama da patients ?" Cikin murmishi Dr muh'd yace "lafia qlau Yah sadeeq ya aiki? " "aiki Alhmdllh gashi nan muna ta fama yanxu ma daga office d'in nayo nan " "Masha Allah, Allah ya taimaka " "Ameen muh'd " Daga hka suka fita daga office d'in gaba d'aya Dr muh'd ya shiga motar shi bayan sun yi sallama ya tafi, yayin da Yah sadeeq yaki yarda musaddiq yayi driving dole sai motar Yah sadeeq din musaddiq ya shiga yaja su gida kai tsaye suka nufa. Hka lokaci ya cigaba da tafiya al'amura sunyi nisa don biki ya matso sosai kowanne 6angare suna shirye shiryen bikin ango Yah sadeeq da ango Yah Omar kuwa kamar su matso da ranar bikin suke tsabar xumud'i. A 6angaren amarya mufidah da amarya nabila suma sai shirin su suke nabila sai rawar kai ake yi ita kuwa mufidah gata nan dai ba wanda xai iya fahimtar halin da take ciki na farin ciki ko akasin hka. Mufidah ce a xaune tana tunanin da ta rasa na mene gaba d'aya bata farin ciki da auren nan don ba wani son Yah sadeeq take ba kawai kunyar shi take ji shi yasa ta kar6i soyayyar shi gashi yana mata kwarjini sosai kuma Yah Omar da nabila su ne suka k'ara tunxura ta har ta yarda dashi dad'in dad'awa kuma yana da halayya masu kyau iyayen ta da sauran en uwanta suna matuk'ar kaunar shi, ga biki ya matso don an shiga satin da xa'a fara gabatar da bikin, k'arar Shigowar message ne a wayan ta yasa ta katse tunanin ta tare da janyo wayar tana duba wa cikin mamaki don bakuwar number ce abin da aka rubuta ta fara karanta " _Nayi matuk'ar rashin furta miki abin da ya dad'e cikin xuciya ta, nayi nauyin baki wajen furta hakan sai gashi wani yaxo ya riga ni har yana kok'arin mallakar ki matsayin matar shi._" " _ki sani ni mai k'aunar ki ina son ki son da baki baxai iya furta wa nasan har na mutu ina k'aunar ki, Allah ya baku xaman lafia ina miki fatan alkhairi daga mai k'aunar ki_ *M*" Sosai abin ya d'aure wa mufidah kai abin ya bata mamaki ba Kad'an ba wannan wane shi me ya hana shi fada mata sai yanxu, me yasa bai rubuta mata cikakken sunan shi ba sai M uhm dan ta6e baki tayi kawai tare da furta cewa " koma wane to gaskia *YAYI SAKE!* sai yayi hak'uri ya sami wata kuma " sai ta tsinci kanta da kasa goge mssg di'n a wayar ta ta xurfafa a tunanin wane wannan. Lokacin da musaddiq ya tura wa mufidah messegen din yana kwance kan gado idanun shi cike da hawaye ga xuciyar shi tana mishi wani rad'ad'i sosai kan shi kuwa kamar ya cire saboda a axabar ciwo goge mssg di'n yayi sannan ya d'auko diary din shi ya rubuta abin da ya turawa mufidah sannan ya rufe diary din ya ajiye shi. Koma wa yayi ya kwanta yana wani jan numfashi dakyar da ana cire so Idan ya shiga cikin xuciya da tuni ya cire son mufidah a cikin xuciyar shi ya huta d'aga idanun shi sama yayi tare da cewa "Yah Allah ka kawo min agaji acikin wannan halin da nake ciki, Yah Allah ka cire min son mufidah daga cikin xuciya ta" Yana gama fad'in hka ya lumshe idon shi wasu hawaye ne masu xafin gaske suka xubo mishi daga idanun shi. "Ameeen thumma Ameeen " Yaji an furta hakan da sauri ya bud'e idon shi ya kalli kofar shigowa wata ajiyar xuciya ya saki ganin Dr muh'd ne a tsaye yana kallon shi irin kallon nan me cike da tausayin shi. K'araso wa yayi cikin bedroom d'in ya xauna akan bed d'in tare da dafa hannun musaddiq yace "kayi hak'uri musaddiq wannan itace kaddara Allah ya jarabce ka da son yarinyar da yayan ka xai aura, ina rok'an ka ka cire son ta don Allah ina nan ina tayaka addu'a sosai Allah ya raba ka da wannan son don an kai matakin da xuciyar ka ta ta6u da ciwo ina tsoron faruwar wani abu abokina " Dr muh'd ya k'arasa fad'i yana mik'a wa musaddiq wata takarda, kar6a musaddiq yayi ya karanta yana gama karanta wa yayi wani k'ayataccen murmishi wanda yasa Dr muh'd tsorata sosai ya bishi da kallon mamaki Kafin ya ankara yaji musaddiq ya fara wani irin tari sosai tuni idanun shi suka fara xubar da hawaye saboda axabar tarin da yake sai sannu Dr muh'd yake mishi kafin ya tashi ya bud'e frige ya d'auko mishi faro mara sanyi ya nufo wajen shi dai dai lokacin musaddiq yayi wani tari da karfi sosai wanda sai da jini ya fito ta bakin shi yana dafe da saitin xuciyar shi.............. _kuyi hak'uri da wannan ban da chaji ne wlh_ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *PAGE 13* Cikin wani irin sauri Dr muh'd ya k'arasa wajen musaddiq hankalin shi a matuk'ar tashe kamo shi yayi ya ma rasa me xai yi mishi tsabar rikice wa, kallon musaddiq yake wanda bakin shi duk ya 6aci da jini idanun shi sai wani lumshe wa suke yi gaba d'aya jikin shi ya saki ba k'arfi a tattare da shi. Cikin dauriya musaddiq ya yago tissue ya goge jinin da ke gefen bakin shi tare da kallon muh'd yace "kayi hak'uri aboki na nayi kok'ari wajen cire son mufidah a cikin xuciya ta hkan ya gagara, bansan ganin ka cikin damuwa " Tuni idanun muh'd sun fara xubar da hawayen tausayin musaddiq hannun shi yasa ya kamo na musaddiq tukunna yace "kada ka damu aboki Insha Allah xaka samu lafia yanxu ka taso muje hospital na duba ka " Girgixa kai musaddiq yayi tare da cewa "umh my friend na samu sauk'i fah " Kura mishi ido muh'd yayi kamar me karantar wani abu a fuskar shi kafin yaja numfashi yace " na rok'e ka ka taso mu tafi akwai abin da nake so na duba, kada kace min baxa ka ba please" D'an murmishi musaddiq yayi kafin yace "Okay aboki ka wuce komai a waje na da ina da ikon cire abin da yake damuna da na cire saboda bana son ganin ka cikin damuwa" Shi ma Dr muh'd di'n Murmishi yayi tare da rungume musaddiq a jikin shi Kafin kuma yaje yayi wanka bayan ya fito ne ya shirya cikin wani white jeans and T-shirt pink colour yayi matuk'ar yin kyau sai dai er ramar da yayi yana gama fesa perfumes ya xura wani silifas na maxa white ne takalmin daga hka suka fita daga d'akin xuwa farfajiyar gidan mota suka shiga asibitin da suke aiki suka nufa kai tsaye. Bayan Dr muh'd yayi wa musaddiq gwaje gwajen da suka dace ya dad'a tausar shi tare da yi mishi nasiha sosae akan ya rage sa tunani a cikin xuciyar ya dage da ibada yana kai kukan shi wajen Allah sosai nasihar muh'd ta ratsa musaddiq kuma ya d'auki alk'awarin amfani da abin da yace. Sun d'an dad'e a asibitin sannan suka dawo gida tare da magungunan da Dr muh'd ya bashi xai yi amfani dasu, muh'd ya dad'e a gidan yana tausar musaddiq sai wajen 9 na dare ya bar gidan. Tun daga ranar musaddiq ya dage da addu'a tare da kai kukan shi wajen mai dukka akan ya cire mishi son mufidah a cikin xuciyar shi kuma Alhmdllh addu'a makamin mumini yana samun sassauci sosai a cikin xuciyar shi. Biki ya matso don an Kai lefen Yah sadeeq xuwa gidan su mufidah yayin da daga gidan su mufidah aka Kai na Yah Omar sun shirya yin dinner, walima da sauran programs masu k'ayatar wa. A cikin wannan lokacin ne iyayen musaddiq suka fahimci bashi da lafia don ganin yanda yayi matuk'ar rame wa sosai hankalin su yayi mugun tashi da ganin halin da d'an nasu yake ciki Hka shima Yah sadeeq ba k'aramin tsorata yayi ba gashi sun yi tambayar duniyar nan ya fad'i abin da yake damun shi, amman musaddiq fad'a musu Yayi ciwo ne kawai daga Allah, Sam basu yarda da abin da ya fad'a ba sun tambayi Dr muh'd don sun san abokin shi ne xai sani amman musaddiq bai bashi umarnin fad'a ba nan fah mumy, daddy da Yah sadeeq suka sama musaddiq ido aduk wani motsin shi don su karanci abin da yake damun shi, yana sane dasu shi dai yayi alk'awarin baxai ta6a fad'a wa kowa ba bayan Dr muh'd. Ranar Tuesday suka shirya yin kamu sosai sun tsara abin gwanin sha'awa, ranar friday kuma arabian night suka yi asabar kuma umman mufidah da umman nabila suka shirya yin mother's day nan ma sun k'ayatar sosai amare sun sha kyau ba irin mufidah ma an ci ansha an watse cikin farin ciki. Rana sunday da safe wajen karfe 10:20 Yah sadeeq ya shigo palon cikin shigar wata tsadaddiyar shadda fara sol da ita yayi matuk'ar yin kyau ya fito a ango sak nan en uwa suka fara tsokanar shi shi dai murmishi kawai yake yi xuciyar da tsantsar farin ciki yau xai mallaki mufidah a matsayin matar shi ta sunnah. Adai dai lokacin musaddiq da Dr muh'd su ma suka shigo cikin falon sun sha ankon shaddar su cikin shadda sky blue da bak'in takalmi har da hula ba k'aramin kyau suka yi ba musamman musaddiq da bai saba sa manyan kaya ko wajen d'aurin auren bai yi niyyar xuwa ba sai da muh'd ya matsa mishi dakyar ya iya shirya wa bai ma san da kayan ba sai da muh'd ya bashi, fuskar shi ba yabo ba fallasa mumy kuwa kallon su ta dunga yi kamar ta mayar dasu ciki don tsabar son yaran nata. Nan suka rungume ta cikin k'aunar mahaifiyar tasu d'an hawayen farinciki tasa hannu ta goge su tare da dafa kan su tace "Allah ya raya min ku 'ya'ya nah, Allah ya albarkaci rayuwar ku Allah ya kare min ku " "Ameeen thumma Ameeen muna godewa Allah da ya bamu ke a matsayin uwa mumy ' Kallon su take cikin so da k'aunar su tana murmishi, Dr muh'd kuwa shi ma kallon su yake cikin sha'awar su wani 6ari na xuciyar shi yana cike da fargaba don baisan yanayin da musaddiq xai shi gaba idan yaji sanarwar d'aurin auren yasan ya rabu da ita na har abada wani tausayin musaddiq ne ya k'ara kama shi sosai, ana cikin hka daddy ya fito shi ma yayi shirin shi cikin manyan kaya na wata milk colour d'in shadda nan suka rungume shi tare da bashi peck a kumatun shi kafin daga baya su dunguma xuwa wajen farfajiyar gidan suka shiga mota d'aya Dr muh'd ne wajen driving musaddiq a gefen shi wanda ya tsurawa waje ido lokaci xuwa lokaci xuciyar shi tana wani mugun fad'uwa, Yah sadeeq da daddy a baya sai sauran en uwa da abokanan arxiki suka rufa musu baya xuwa wajen d'aurin aure............ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *E.W.F* *PAGE 14* Bayan sun isa wurin d'aurin auren mutane sosai sun taru manya manyan kusassun gwamnati da en kasuwa xuwa abokanan ango sai manyan lecture's da likitoci en uwa da abokan arxiki gasu nan birjik, jama'a ta ko'ina gasu nan karfe sha d'aya dai dai aka d'aura auren mufidah da Yah sadeeq akan sadaki mafi cancanta saboda neman albarkar aure, xuciyar Yah sadeeq ta cika da farinciki sosai ayau Allah ya mallaka mishi masoyiyar shi, son ta daban yake a cikin xuciyar shi yana mata wani irin so baxai iya rabuwa da ita ba sai dai k'addarar ubanjigi ko mutuwa ya rabasu. Musaddiq kuwa yana xaune cikin mota ya kasa fito wa saboda baxai jure tsayuwa ba, jikin shi ba k'arfi ga kuma gaban shi yana mugun fad'uwa sam baxai iya shiga cikin mutane a hka ba saboda baxai iya k'ak'alo murmishi a fuskar shi ba, kallo d'aya xaka yi mishi ka hango tsantsar damuwa a fuskar shi, yana dafe da kanshi wanda yake mishi ciwo kamar xai cire. "Alhmdllh hukuncin ubangiji ya tabbata a yau aka d'aura auren Abubakar sadeeq Abubakar da amaryar shi mufidah El hussaen" Abin da kunnuwan musaddiq suka juyo shi kenan daga bakin wani marok'i ma'abocin xak'in murya, wani irin tari ne ya kama musaddiq tari yake ba kakkauta ba daga bisa ni kuma ya fara aman jini hannun shi yana dafe da saitin xuciyar shi, numfashin shi ne ya fara kok'arin d'auke wa gaba d'aya gaban rigar shi da bakin shi ya 6aci da jini. Dr muh'd kuwa wanda yake cikin taron mutane jin an d'aura auren yasa shi tafiya inda musaddiq yake don yasan a wannan lokacin yana cikin wani mugun yanayi, tausayin musaddiq fal cikin xuciyar Dr muh'd ya K'arasa inda yayi parking d'in motar da suka xo yana bud'e wa ya hango abin da yayi matuk'ar girgixa shi ya d'aga mishi hankali, musaddiq ya gani a kwance ga jini ya 6ata mishi jiki kuma gashi babu alamun yana numfashi a tattare da shi. Cikin sauri ya yunkura xai shiga motar yaji an dafa mishi kafad'a a matuk'ar firgice ya jiyo don ganin wane, had'a ido yayi da Yah sadeeq fuskar shi d'auke da farinciki yace "muh'd ina musaddiq yake? " Wani uban gumi ne ya tsatstsafo wa muh'd a jikin shi gaba d'aya hankalin shi ya rabu gida da yawa shin xai sanar wa da Yah sadeeq ga halin da musaddiq yake ciki ko kuma ya shiga mota ya kai musaddiq asibiti don a ceci rayuwar shi ko ya tsaya ba wa Yah sadeeq amsar tambayar shi. Yah sadeeq kuwa tsura wa fuskar muh'd ido yayi don ganin yanda yake a firgice " what happened to you muh'd, kamar akwai wani abin? " Cikin rawar murya Dr muh'd yace " ba...... ba wani abu Yah sadeeq just an kirawo ni daga hospital ne an kawo wani patient yana buk'atar taimakon gaggawa" "Ayyah so ina musaddiq? " "Hmmm yana cikin taron mutane wajen friends d'in mu idan ka duba xaka gan shi " "alright sai ka dawo " "Okay Yah sadeeq Allah ya sanya alkhairi " Cikin murmishi yace "Ameeen muh'd thank u " Yana gama fad'in hka wani cikin abokanan Yah sadeeq yaxo ya janye shi daga wurin suka shiga cikin mutane, da sauri Dr muh'd ya fad'a cikin mota ya ja ta cikin wani irin gudu don gaba d'aya a rikice yake. Cikin kankanin lokaci Dr muh'd da wasu lokaci guda biyu wanda muh'd ya kirawo su, suka duk'ufa akan musaddiq suna kok'arin ceto rayuwar shi. Sun d'auki tsawon lokaci akan musaddiq Kafin numfashin shi ya dawo amman duk da hka da taimakon oxygen tube yake numfashi gashi nan a kwance kamar wani matacce ba inda jikin shi yake motsi a jikin shi, abin da mutum xai san yana raye numfashin da yake fitar wa ne sai buguwar xuciyar shi, kallon musaddiq Dr muh'd yake yana wani irin kukan tausayin abokin nashi dole ya sanar da iyayen shi abin da yake damun shi don kuwa aka cigaba da hka wataran xa'a samu matsala kuma shi xasu xarga da laifin sakaci da lafiar d'ansu mybe akwai wani taimako ma da xasu iya wajen kwantar mishi da hankali. Wayar shi ya d'auko ya nemo number d'in daddy don shine namiji sai yafi nutsuwa ya saurare shi fiye da mumy don ita mace ce akwai rauni yanxu sai ta k'ara hargitsa shi, wajen 2 missed calls yayi but daddy bai d'auki wayar ba watak'ila bai ji kiran ba saboda hayaniyar jama'a. Yana xaune ya xuba wa musaddiq ido tare da yin tagumi lokaci xuwa lokaci yana goge hawayen da yake xuba daga idanun shi. Daddy kuwa yana cikin jama'a hayaniyar su yasa bai ji kiran muh'd ba sai bayan an d'aura auren Yah Omar da nabila ne sun shiga mota suna kok'arin tafiya wajen walima din da suka had'a, sai yaji kira a wayan shi d'auka yayi don duba wane ya ke kiran shi ganin sunan muh'd yasa daddy yin mamaki amman sai ya kawar da mamakin shi ya d'auki wayar. Shi kuwa Dr muh'd har ya fitar da ran daddy bai ji kiran ba sai kuma yaji ya d'auka cikin sauri yayi sallama bayan daddy ya amsa ne sai kuma muh'd ya d'anyi shiru yana tunanin ta inda xai fara sanar mishi da wannan mummunan labarin a ranar farincikin auran d'ansu, gaban shi har wani mugun fad'uwa yake. "lafia muh'd ka kirawo ni kuma naji kayi shiru ko baka ji ba? " Jin saukar muryar daddy a kunnen shi ya sa Dr muh'd fara magana cikin rawar murya yana cewa "daddy da... daman cewa xan yi maka mu.... musaddiq ne ba lafia ciwon shi ya tashi so yanxu muna hospital " Cikin tashin hankali daddy yace "wanne ciwo kake nufi muh'd? " Sai lokacin muh'd ya tuna da kato6arar da Yayi shaf ya mance basu san musaddiq yana da ciwon xuciya ba, don hka cikin fad'uwar gaba yace "am daddy ina son kaxo asibitin musaddiq yanxu xamu tattauna wata magana aka rashin lafiyar musaddiq so bana so Yah sadeeq ya sani ka taho kai da mumy kawai " Tuni hankalin daddy yayi matuk'ar tashi katse wayar yayi tare da bawa mutanen da suke jiran shi exuse akan yana xuwa akwai abu mai mahimmanci da ya taso mishi yanxu, cikin sauri ya fad'a mota ya nufi gida gumi ne kawai yake tsiyayowa daddy wanne ciwo ne da musaddiq da basu sa ni ji yake kamar ya tashi sama ya ganshi gaban Dr muh'd yana fad'a mishi abin da yake damun d'anshi yaron da yafi soyewa acikin xuciyar shi. Yana k'arasa wa gida Ko shiga da motar bai yi ba cikin gidan ya barta a nan waje ya shiga, saboda cikar da aka yi en biki yasa daddy kiran mumy a waya Allah ya taimaka wayar tana rik'e a hannun ta ba 6ata lokaci ta d'auki wayar ganin kiran maigidan ta ne "kixo yanxu ina wurin parking space ki taho da mayafin ki " "toh shikenan " Abin da mumy tace kenan sam bata yi tunanin wani abun ba ta d'auka ko abokanan shine yake so su gaisa, cikin en mintuna mumy ta fito tana yafa mayafi taci gayu sosai cikin wata arniyar shadda an sha adon gwal sai kyalli take yau ranar farinciki ne a gare ta sam baka ce ita ta haifi Yah sadeeq da musaddiq ba. Turus taja ta tsaya ganin daddy shi d'aya a wurin gaba d'aya fuskar shi d'auke da damuwa cikin tashin hankali tace "Abban sadeeq lafia? " D'ago kai yayi ya kalli mumy sai da gaban ta ya fad'i ganin tsantsar damuwa a cikin idanun na shi hannun shi ta rik'o tana cewa "Yah mijina me yake faruwa da kai? " Runtse idanun shi yayi kafin yace "ina son ki kwantar da hankalin ki nutsu da abin da xan fad'a miki " Cikin xakuwa mumy tace "ina sauraren ka? " Sai da yayi dan shiru Sannan yace "musaddiq ne ba lafia yana hospital " "me yake damun shi? " Cewar mumy a rikice, girgixa kai daddy yayi tare da cewa "sai dai mun je xamu sani yanxu dai mu tafi " Gaba d'aya mumy ta kasa tafia ta cak waje d'aya sai da daddy ya rik'e mata hannu har xuwa wajen mota shi ya taimaka mata ta xauna saboda gaba d'aya mumy ba'a hayyacin ta take ba, lokacin da suka K'arasa asibitin a reception din hospital suka had'u da Dr muh'd wanda ya fito kar6ar wata allura da xai yiwa musaddiq. Gaba d'aya jikin su yayi sanyi ganin yanda muh'd idanun shi sunyi ja alamar yaci kuka sosai, shi yayi musu jagora xuwa cikin d'akin suna shiga ganin musaddiq da suka yi kamar gawa yasa su furta kalmar "inallilahi wa'inna ilaihir rajiun " Su kayi kan musaddiq gaba d'ayan su a rikice............ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* _Wannan shafin na ki ne *Asy khaleel* fatan alkhairi a gare ki Allah ya bar xumunci, ni Aishat ina k'aunar ki sosai kuma kirkin kine yaja miki dumbin masoya, ina miki fatan alkhairi a duk inda kike_ *PAGE 15* Su kayi kan musaddiq gaba d'aya a rikice, tuni mumy ta fashe kuka tana cewa "wayyo Allah nah musaddiq me ya mayar min da kai Hka wannan wanne irin ciwo ne? " Kuka sosai mumy take har da majina hankalin ta ba k'aramin tashi yayi ba na ganin d'annata a hka, shi kuwa daddy xama yayi tare da k'urawa musaddiq ido yana kallon shi ya ma kasa furta komai tsabar tashin hankalin da yake ciki. "muh'd fad'a min abin da yake damun musaddiq? " Dr muh'd xama yayi kusa da kafar daddy cikin rawar murya kamar xai fashe da kuka ya fara cewa "daddy kayi hak'uri akan rufe ma abin da yake damun musaddiq da muka yi da dad'e wa, saboda amana musaddiq ya bani akan kada na furta abin da yake damun shi, ina kok'ari na wajen kwantar mishi da hankali tare da bashi shawarwari amman yak'i dai na sa damuwa acikin xuciyar shi, so shine kuma d'axu wurin d'aurin auren Yah sadeeq ciwon nashi ya tashi " Duk sun xuba wa muh'd ido suna sauraren shi mumy mai yin kuka ma shiru tayi don ta fahimci abin da ake cewa sai dai hawaye bai bar xuba daga idanun ta ba, cikin xakuwa a fad'i ciwon da yake damun musaddiq daddy yace "toh wanne ciwo ne yake damun shi muh'd sanar da ni?" Sai da muh'd ya d'auki tsawon mintuna kan shi a k'asa Kafin kuma cikin sanyin murya yace "daddy mumy Kuyi hak'uri musaddiq yana cikin wani mugun yanayi, ba wani abu ne yake damun shi sai ciwon xuciya " Lokaci d'aya suka mik'e daddy da mumy suna furta "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun " Suka furta lokaci d'aya, mumy hannu ta d'ora a kanta tare da rushe wa da wani irin kuka mai ban tausayi, yayin da daddy ya maimaita cewa "ciwon xuciya ne yake damun d'ana, me musaddiq ya nema ya rasa da a rayuwar shi da har wannan mugun ciwon xai Kama shi? " Hannun daddy Dr muh'd ya kamo tare da xaunar dashi kuka muh'd kawai yake ganin yanda wad'annan bayin Allahn yanda suka shiga wani hali mai ban tausayi. "Ya fad'a maka abin da ya sa a ranshi har ya kamu da wannan ciwon? " Cewar daddy yana kallon Dr muh'd, toh fa muh'd ya shiga tsaka mai wuya yanxu xai fad'a musu gaskiar abin da yake damun shi anya kuwa xai sanar dasu yarinyar da yake masifar so ita ce mufidah matar yayan shi sadeeq gaba d'aya ya rasa abin da xai ce gashi sun xuba mishi ido suna kallon shi kowanne yana son jin abin da xai fad'a....... A 6angaren amarya mufidah kuwa tun lokacin da taji an d'aura auren ta da Yah sadeeq sai gaba d'aya jikin ta yayi matuk'ar yin sanyi, sai tsokanar ta aike en uwa suke amman babu bakin magana sai dai tayi musu yak'e, don gaba d'aya baka ce ga yanayin da take ji ba farinciki ko akasin hka, tana kule cikin bedroom d'in umman ta, tun lokacin da aka sa lokacin auren bata iya cin abincin kirki ba sai tunani kuma ta rasa tunanin da take, ita dai tasan wani lokacin tana tunanin musaddiq musamman lokacin da ya kaita gidan shi ta wanke mishi kayan da ta 6ata mishi, da lokacin da take rungumar shi tana neman taimakon shi xuwa lokacin da taje gidan su da ya kusan fad'uwa har ta rik'o shi suka had'a jiki, sosai tana tunano lokacin har wani lokacin tana murmishi, ta rasa gane abin da yake damun ta shi yasa gaba d'aya ta rame saboda da tunani ga rashin son cin abinci. Umma, nabila da Yah Omar sun yi nacin duniya da ta fad'a musu abin da yake damun ta amman sai tace ba komai, to me xata ce musu ita kanta wani lokacin sai ta rasa ma tunanin da take, abinci kuwa sai umma ta sa ta a gaba da fad'a take iya ci, sai dai Kyan da ta k'ara don tasha gyaran jiki ciki da waje don umma ba wasa a wannan 6angaren ta tsaya tsayin daka ta gyara d'iyar ta daman ita kad'ai Allah ya bata mace sai Yah Omar dole ta gyara ta. Shigowar umma cikin d'akin yasa mufidah saurin d'aukar wayar ta tana danna wa don bata son umma ta gane tunani take, amman duk da hka sai da umman tace "Hmmm ana nan ana sana'ar ko mufidah? " Er dariya ta k'ak'alo tayi tare da cewa "Haba umma ba tunani nake ba, hutawa nake na gaji da hayaniya wlh" "ae sai hak'uri taron kenan, gashi can ana d'aukan pictures da en uwa da kuma angwaye sai ki fito " D'an 6ata fuska mufidah tayi tare da cewa "ni gaskia umma na gaji " "Haba er umma d'aure ki tashi kin ga abin tarihi ne " Kafin mufidah ta ce komai sai ga wasu emmata sun shigo sun ci uban kwalliya 'ya'yan k'anin baban su mufidah ne, hannun ta suka rik'o tare da fito wa xuwa main parlour inda ake d'aukan pictures, duk inda mufidah ta gifta idanun Yah sadeeq akanta har sai da Yah Omar ya fara tsokanar shi, shi dai sai murmishi yake don yau ranar farinciki ce a gare shi, ita kuwa mufidah duk ta gaji da kallon da Yah sadeeq yake mata K'arshe sai ta sulale ta gudu d'aki. ****** "kai muke saurare muh'd maxa fad'a min gaskia? " "uhm daddy daman wata yarinya yake masifar so, sai kuma bai furta mata da wuri ba har wani ya riga shi iyaye suka shiga xancen shine abin ya kasa cire shi daga cikin xuciyar shi saboda yana masifar son ta " "Wace yarinya ce muh'd? " Mumy ta tambaye shi cikin mamaki sosai don ko da wasa musaddiq bai ta6a nuna musu yana son wata yarinya ba. "Mumy sunan ta mufidah kuma yau ne d'aurin auren ta ma" "Wacce mufidah kake nufi??? " Lokaci d'aya Mumy da daddy suka furta gaban su na mugun fad'uwa tsoron su kada ya kasance ace hasashen su ya xama gaskia................. Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *E.W.F* _Wannan shafin naku ne ma'abota kirki da karamci, Anty maijiddah ta cikin group d'in (novella's lodge) da fatyma (Mrs Omar), ina ji daku sosai gashi kuna k'aunar littafin nan sosai, Allah ya bar mu tare ina yin ku sosai, fatan alkhairi a duk inda kuke_🤝😍 *PAGE 16* Lokaci d'aya suka furta gaban su na fad'uwa tsoron su kada ya kasance ace hasashen su ya xama gaskia, Cikin xak'uwa da son jin cigaban xancen mumy tace "Muh'd fad'a mana wace mufidah?" Sai lokacin Dr muh'd ya tuna kato6arar da yayi don baisan lokacin da bakin shi ya furta hkan ba, kallon mumy da daddy yayi wad'anda suka xuba mishi ido suna kallon shi kowannen su ya matsu yaji abin da muh'd xai fad'a, kauda kanshi yayi daga barin kallon su tukunna ya ce "Am mumy, daddy yarinyar da musaddiq yake so wato mufidah tana xaune a garin katsina karatu ne ya kawo ta buk, so shine iyayen ta suka aurar da ita, gashi musaddiq yana son ta sosai, kasa cire ta yayi daga ranshi shine har ya haddasa mishi kamuwa da ciwon xuciya" "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Daddy ya fad'a tare da dafe kanshi, yayin da mumy sai taji sam bata yarda da abin da Dr muh'd ya fad'i ba, kuma ta dauki niyyar bincika wa don ta fahimci gaskiar xancen. Cikin wani irin yana yi daddy yace"kash da ace nasan da hka tun wuri da koda kaf dukiya ta xata k'are sai na nema wa musaddiq auren yarinyar nan" "Sannan daddy don Allah kada a fad'a wa Yah sadeeq abin da yake damun musaddiq saboda xai iya shiga wani hali kusan makamancin abin da yake damun musaddiq" "Kwarai kuwa muh'd maganar ka hka take,don idan sadeeq ya sani xa'a yi biyu babu, yanxu mene mafita?" D'an satar kallon mumy Dr muh'd yayi taga kallon shi kawai take nan gaban shi ya cigaba da fad'uwa don da alama bata yarda da abin da yake cewa ba, d'an shiru suka yi na en mintuna kafin muh'd yace "Mafita anan shine daddy ya kamata musaddiq yayi nesa da gida don yafi samun nutsuwar xuciyar shi, kuma hkan da xa'a yi xai taimaka wajen kada Yah sadeeq ya gane" "Kamar ya ya?" Cewar mumy, gaban Dr muh'd ne ya cigaba da fad'uwa yana tsoron kada su k'i amince wa don xaman musaddiq a gida xai iya kawo baraxana da rayuwar shi, tun da Yah sadeeq a cikin gidan nasu xai xauna kuma musaddiq da mufidah xasu na had'u wa da junan su, shine ya kawo wannan shawarar yana fatan su daddy su amince da hkan. "Ina nufin musaddiq ya d'an yi nesa da gida, yanda xai fi samun hutu da nutsuwa a tare dashi xuwa na wani d'an lokaci, kuma naji yana cewa akwai wani course da xai yi kun ga hkan xai rage mishi tunani sosai" "Good idea muh'd hkan xa'a yi kuwa, Allah ya tashi kafad'un shi" "Ameeen thumma Ameeen" Cewar mumy da Dr muh'd, nan suka xauna shiru kowannen su da tunanin da yake a cikin xuciyar shi. Wayar daddy ce ta d'auki k'ara sauran d'auka yayi ganin sunan sadeeq ne yasa shi d'auka, daga can 6angaren sadeeq ya fara magana cikin shagwa6a yana cewa "Daddy ina ka shiga kai da mumy da my sweet brother ne ban gan ku ba ne?" D'an murmishin yak'e daddy yayi tare da cewa"muna nan fah, yanxu ina kake my son?" "Ina kwance a bedroom d'ina ina huta wa, yunwa nake ji daddy gashi ban ga mumy ba" Kallon mumy daddy yayi kafin yace"okay sadeeq yanxu mumy xata kawo maka abincin" "Okay daddy, ina musaddiq ne rabo na da ganin shi tun da muka taho wurin d'aurin aure, ina son ganin shi daddy ina ya shiga ne, wayan shi baya shiga?" Kallon musaddiq daddy yayi idanun shi sun ciko da hawaye, da ace sadeeq xai san halin da musaddiq yake ciki da shima xai iya shiga halin da musaddiq yake ciki, hannun shi yasa ya goge hawayen da suka xubo mishi kafin ya saita muryar shi yace "Kada ka kasa damuwa a ran ka son, musaddiq yana tare da Dr muh'd a hospital suna wani aiki but xuwa yamma xai dawo" Murmishi sadeeq yayi tare da cewa "okay daddy bye" Kashe wayar daddy yayi tare da kallon Dr muh'd yace "xuwa yamma xai iya farka wa muh'd?" "Ehhh daddy xai farka insha Allah" Cewar muh'd kenan, juyo da kallon shi yayi kan mumy ya ce" sadeeq yana neman mu fah, yace ma yunwa yake ji ki bashi abinci, yanxu tashi xaki yi mu tafi gida ya ganmu idan yaso ni na dawo hospital d'in" Girgixa kai mumy tayi tare da cewa "gaskia baxan iya tafia ba, sam baxan samu nutsuwa da kwanciyar hankali ba idan na tafi" " hak'uri xaki yi mumyn sadeeq addu'a xaki na yi mishi Allah ya bashi lafia, idan kika k'i tafia sadeeq xai iya fahimtar halin da ake ciki" Nan daddy ya lalla6a mumy dak'yar ta amince suka tafi aka bar Dr muh'd a wurin musaddiq wadda yake kwance ko motsi baya yi. Bayan sun koma gida mumy ta had'a abinci ta kaiwa sadeeq lokacin yana kwance kan sofa suna hira da Yah Omar a waya, ganin mumy yasa shi katse wayar da yake yi, tsaf ya karanci tsantsar damuwa a fuskar iyayen nashi amman sai suka nuna mishi gajiyar hidimar biki ce ta sa yanayin su ya koma hka, daga k'arshe daddy ya koma asibiti aka bar mumy tana tare da en biki amman gaba d'ayan ta ba'a nutse take ba hankalin ta yana kan musaddiq addu'a sosai take mishi a cikin xuciyar ta lokaci xuwa lokaci tana goge hawaye a idanun ta idan ta ke6e ita d'aya. Sai 7 na dare musaddiq ya farka lokacin daddy da Dr muh'd suna masjid basu dawo ba, bayan mintuna biyu da farkar wasu ya samu nutsuwa sai ya sanya hannu ya xare drip d'in da ake sanya mishi sannan ya tashi daga kan gadon cikin jarumta da dauriya ya fara tafia xuwa toilet don gaba ki d'aya jikin shi ba k'wari, wanka yayi da ruwa mai d'umi sannan ya d'aura alwala ya fito kayan jikin shi ya mayar tukunna ya fara rama sallolin da ake bin shi, har ya kammala rama su, xama yayi yana laximi, saitin xuciyar nayi mishi wani rad'ad'i, addu'a kawai yake idan tunanin ta ya fad'o mishi a cikin xuciyar shi don k'okarin yakice ta yake gaba d'aya a ranshi don yanxu ta xama matar d'an uwan. Yana xaune a hka daddy da Dr muh'd suka shigo d'akin, ganin shi a xaune akan abin sallah ya basu mamaki sosai don hka da sauri suka k'arasa wajen shi suna mishi sannu, murmishi yayi tare da amsa wa, kafin kuma Dr muh'd ya sake duba shi, anan kuma suke fad'a mishi shawarar da suka yi, sosai musaddiq yaji dad'in hkan don yana so yayi nesa daga rayuwar mufidah, daga hka suka tafi gida don baya son xaman asibitin, lokacin da suka k'arasa gida a dai dai lokacin en kawo amarya motocin su suka shigo gidan. Musaddiq bai tsaya ba ya shige part d'in daddy da wani irin mugun sauri har abin ya bawa daddy mamaki, Dr muh'd kuwa ya bi bayan musaddiq da sauri shi ma, duk abin da ya faru da musaddiq da yanda yayi duk akan idanun mumy dake saman bene tana kallon su nan xuciyar ta ta dad'a ayyana mata abubuwa, har sai da suka shige sannan mumy ta iya sakkowa down stairs don tar6ar amarya duk jikin ta a sanyaye................. _kuyi hak'uri da wannan nayi typing ya goge sai da na sake, xuwa gobe insha Allah xaku ji ni_ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* _Wannan shafin na kune *BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*, ina mik'a sak'on gaisuwa ta a gare ku, manyan writer's da k'ananun su, Allah ya k'ara had'e kan marubutan mu ya kauda fitina a tsakanin mu, hak'ik'a ina alfahari ku, ina yiwa kowa fatan alkhairi_🤝😍 *PAGE 18* Har sai da suka shiga cikin part d'in sadeeq, amman musaddiq bai sani ba don gaba d'aya hankalin shi baya tare dashi baisan inda yake jefa kafar shi ba don kawai muh'd yake bi wanda yake rik'e da hannun shi, suna shiga cikin palon sadeeq yace "Ku xauna bari na kirawo muku ita koh my brothers?" Cikin murmishin yak'e Dr muh'd yace"toh babban yaya a fito lafia" Murmishi sadeeq yayi tare da shige wa bedroom d'in mufidah, shi kuwa musaddiq maganar da sadeeq yayi ita ta dawo dashi cikin hayyacin xumbur ya mik'e tsaye tare da wani fisge hannun shi daga rik'on da muh'd yayi mishi yana k'are wa inda yake kallo. Cikin sauri muh'd yace"lafia musaddiq?" Kafin ma ya rufe bakin shi musaddiq ya fice daga palon da wani irin gudu, kafin ya ankara har musaddiq ya fice daga part d'in cikin sauri Dr muh'd ya mik'e xai bishi kenan sai ga sadeeq ya fito tare da mufidah, kallon muh'd yah sadeeq yayi tare da cewa "Sorry k'anina na bar ku ko, ina musaddiq kuma?" Ambatar sunan musaddiq da aka yi sai da gaban mufidah ya fad'i, shi kuwa muh'd ya rasa mai xai cewa sadeeq, daga k'arshe dai da yaga sadeeq ya tsare shi da ido yasa shi yin murmishin yak'e tukunna yace "Gajiya yayi da xaman jira gashi kanshi yana ciwo shine ya tafi yasha magani ya kwanta don ya huta" "Wayyo kanshi ne yake ciwo Allah sarki brother bari naje na ga jikin nashi, ina xuwa muh'd" Muh'd wanda gaba d'aya hankalin shi yayi kan musaddiq ya rik'o hannun sadeeq yana cewa "Ah babban yaya ba sai kaje ba xan je yanxu wurin shi kafin na tafi, idan ta kama ma xan k'wana wurin shi don na kula dashi, amman kayi xaman ka" Dafa kafad'ar shi sadeeq yayi tare da cewa"okay naji amman don Allah ka kular min da shi sosai please" "Kada ka damu xan kula shi insha Allah" "thank u so much muh'd ina jin dad'in yanda kake kular min da musaddiq Allah ya bar mu tare" "Ameeen babban yaya" Kallon mufidah yayi tare da cewa"Auntyn mu ya hidimar biki?" Dak'yar mufidah ta iya bud'e baki tace"Alhmdllh" Don gaba d'aya mufidah ta rasa abin da yake mata dad'i, bayan sun gama gaisa wa ne tukunna yayi musu addu'a sosai ta xaman lafia da xuri'a mai albarka daga hka yayi musu sallama tare da fito wa daga part d'in sauri yake ya k'arasa wajen musaddiq. Yana tura kofar bedroom d'in musaddiq d'in ya tarar dashi a kwance kan bed yayi ruf da ciki, da sauri muh'd ya k'araso inda musaddiq yake a kwance yasa hannun shi ya jiyo dashi, ba k'aramin firgita muh'd yayi ba ganin hawaye na xuba a idanun musaddiq gaba d'aya fuskar shi da idanun shi sun yi ja. "Haba musaddiq why da xaka dunga barin abu yana tasiri a cikin xuciyar ka, ina son kayi hak'uri ka cire mufidah daga ran ka gaba d'aya ta riga da ta xama mallakin wani, wanin ma d'an uwan ka yayan ka, tun kafin a fara fahimtar halin da kake ciki, don mumy sam bata yarda da abin da nace musu ba daddy ne kawai ya aminta" Dr muh'd ya fad'i hka yana goge wa musaddiq hawayen da suke xaba a idanun shi, shima hawayen yake fitar wa, cikin rawar murya musaddiq yace "Ya xan yi muh'd, ji nake xuciya ta tana wani irin xugi da rad'ad'i, ni dama Allah xai d'auki r........." Kafin ya k'arasa fad'i muh'd ya toshe mishi baki yana hawaye tare da girgixa kanshi yana cewa" nooo musaddiq kada ka k'ara furta hkan, Allah yana sane da kai xai yaye maka abin da yake damun ka, wannan itace kaddarar ka musaddiq, kasani duk tsanani yana tare da sauk'i, insha Allah *K'ARSHEN WAHALAR* ka ya kusan xuwa k'arshe, ina son wannan abun ka barshi tsakanin ka da *DANGARTAKAR ZUCIn* ka kada ka bari su daddy su gane, yanxu ka tashi ka d'auki alqur'an ka karanta xaka ji sauk'in abin da kake ji insha Allah". Yunk'ura musaddiq yayi ya tashi xaune sadeeq ya tashi ya mik'a mishi ruwa yasha sannan ya d'auko mishi Qur'an tare da mik'a mishi nan take musaddiq ya fara rera karatun cikin muryar shi mai dad'in gaske tuni ya fara jin abin da yake damun shi ya fara jin sauk'in shi a cikin xuciyar shi, amman duk da hka hawaye na xuba daga idanun shi, muh'd yana gefe ya kallon shi cikin tsananin tausayin shi, ya riga da ya yanke shawarar k'wana a wajen musaddiq don baxai iya tafia ya bar musaddiq cikin wannan yanayin ba bacci ma baxai iya cikin kwanciyar hankali ba son da yake yiwa musaddiq bai misaltu ba jin shi yake kamar d'an uwan shi wanda suka fito ciki d'aya. Kash rashin sani yafi dare duhu kaf duk wannan maganar dasu musaddiq da Dr muh'd suke yi a kunnen mumy don ta taho kawo wa musaddiq ruwan coffee taji maganar su,duk da mumy ta xargi hkan amman da taji yanxu da kunnen ta sai da ta firgita sosai da sauri ta bar kofar bedroom d'in ta haura stairs d'akin ta ta wuce kai tsaye tana shiga ta rushe da wani irin kuka. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yanxu ya xan yi yara na guda biyu kacal da Allah ya bani suke son mace guda d'aya so kuma ba na wasa ba, ya Allah na rok'e ka ka cire wa musaddiq son mufidah acikin xuciyar shi" Kuka sosai mumy take don so shu'umin abu ne don tsaf xai iya hargitsa musu xaman lafiar da suke, dole kuwa ta tashi tsaye ta sake xage damtse wajen kaiwa Allah kukan ta, tashi tayi ta nufi toilet alwala ta d'aura tukunna ta fito ta shimfid'a abin sallah ta fara nafilfilo sai da tayi raka'a shida tukunna ta janyo Qur'an ta fara karatu sai da tayi karatu sosai kafin kuma ta d'aga hannun ta sama tana xubar da hawaye tana addu'a tare da rok'on Allah abubuwan da yake damun ta................. Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* _wannan page naku ne k'awayen arxik'i, Aunty halilos da sister d'in ta zahra, deejah,tare da en group d'ina Aunty & sadeey novel's group, ina matuk'ar ji daku sosai Allah ya bar mu tare, i really luv u guys, ina muku fatan alkhairi_🤝😍 *PAGE 17* Cire damuwa tayi a fuskar ta tare da fad'ad'a fara'ar ta don a gaskia mumy tana k'aunar mufidah saboda hankalin yarinyar da nutsuwar ta suna birge ta dad'in dad'awa kuma tana k'aunar ta haifi 'ya mace gashi Allah bai bata, cikin farinciki ta rungume mufidah a jikin ta mutane sai kallon su ake cike da sha'awa da ace hka iyayen miji suke nuna k'aunar matar 'ya'yan su da an samu xaman lafia baxa a fiye tashin hankali ba, amman wasu suna yin k'ok'arin hkan. Bayan an damk'a amanar mufidah a hannun mumy ne sai kuma aka wuce da ita part d'in su, wanda sai an fita daga part d'in mumy sannan xa'a je nasu, hannun mufidah a cikin hannun mumy har aka shigar da ita bedroom d'in ta da kanta ta xaunar da ita gefen bed, mufidah kuwa kuka take yi sosai. A gaskia 6angaren mufidah ba k'aramin had'uwa yayi ba yasha had'add'un furniture's en k'asar waje masu kyau da tsada ko'ina ya had'u sai kamshi ne yake tashi a kowanne lungu da sak'o na wajen, bayan en kawo amarya sun gama ganin wurin ne tukunna suka fara tafia saboda dare ya fara yi, kafin kace me part d'in yayi tsit ba alamun motsin mutane sai mufidah ita d'aya a bedroom tana gurxar kuka don ita ba k'awaye ne da ita idan ka dauke nabila itace k'awar ta kawai. Lokacin da musaddiq ya k'arasa part d'in daddy sai kawai ya had'a kai da bango wani gumi ne yake tsatstsafo mishi a cikin sassan jikin shi gaba d'aya ya rasa inda xai sanya ran shi yaji dad'i, dafa mishi kafad'a Dr muh'd yayi tare da cewa " kayi addu'a musaddiq xaka samu sauk'in abin da kake ji" A hankali ya bud'e bakin shi yana addu'a a take ya fara jin nutsuwa na xuwar mishi har ya iya samun waje ya xauna, bai fasa yin addu'ar ba har sai da yaji abin da yake ji ya ragu sannan ya bud'e baki dak'yar yace "Muh'd taimaka min da bottle d'in ruwa" Cikin tausayin shi Dr muh'd ya k'arasa frige ya d'auko mishi bottle d'in swan water mai sauk'in sanyi ya mik'a mishi. Hannu yasa ya kar6a tare da 6alle murfin robar ya fara shan ruwan, yana cikin sha ne daddy da sadeeq suka shigo falon, cikin sauri sadeeq ya k'arasa wajen musaddiq ya rik'e mishi d'ayan hannu tare da cewa "Haba musaddiq shine kaje kayi xaman ka a cikin hospital kak'i dawo wa da wuri koh?" Shi dai musaddiq bin shi da kallo kawai yake, ganin hka yasa sadeeq cika mishi hannu tare da juyawa ya daina kallon shi sannan yace "Kana ji ina maka magana kayi min shiru toh nayi fushi yaro, baxan k'ara yi maka magana ba sai nan da one week" Ya k'arasa fad'i yana k'okarin tashi da sauri musaddiq yasa hannun shi ya janyo sadeeq ya fad'a kan kujera tukunna musaddiq ya k'ak'alo murmishi yana cewa "Tuba nake Yah sadeeq ayi min hak'uri baxan K'ara ba" Juya kan shi sadeeq yayi yak'i kallon fuskar musaddiq shi ala dole yayi fushi, kama kunnen shi musaddiq yayi dukka biyun tare da langa6e kai gefe yace "I'm so sorry brother baxan k'ara ba please" Juyo wa yayi tare da hararar musaddiq cikin murmishi musaddiq ya cigaba da cewa "Kayi murmishi mana yah sadeeq kamar ba sabon ango ba" Nuna shi da hannu sadeeq yayi tare da cewa"kai koh?" Bai k'arasa fad'in abin da yake so ya fad'a ba sai kawai ya rungume shi a jikin shi yana fitar da hawaye daman sadeeq bashi da wahalar yin kuka, shima musaddiq k'ara rungume d'an uwan nashi yayi tare jikin shi yana fitar da nashi hawayen don shi abubuwa ne da yawa suka had'e mishi. Daddy da Dr muh'd tare da mumy wadda shigowar ta kenan su ma hawayen tausayin sune ya fara xubo musu, daddy ne yaje ya raba su tare da shiga tsakiyar su suka rungume shi, bubbuga bayan su daddy yake alamar rarrashi. Ganin dare nayi yasa daddy ya fara magana da cewa"kai sadeeq maxa tashi k'annen ka su yi maka rakiya xuwa wajen amaryar ta, ni ban ta6a ganin ango bashi da aboki ba sai kai, abokin naka Omar shi ma angon ne sai k'annen naka su yi maka rakiya" Dariya suka sa gaba d'aya ban da musaddiq da dariyar tashi ta yak'e ce, cikin shagwa6a sadeeq yace "Ni daman daddy musaddiq da Omar sun ishe ni sai kuma muh'd koh?" Ya k'arasa fad'a yana kallon Dr muh'd, cikin er dariya muh'd yace"hkane babban yaya, ka taso mu yi maka rakiya xan wuce gida dare nayi, dafatan amaryar baxa ta raina mu ba don muna k'anne" Kyalkyale wa da dariya suka sake yi kafin mumy tace"haba ae 'yar tawa ba ruwan ta" "To kun ji abin da mumyn ku tace maxa ku tashi don dare yayi" Daddy ya fad'i hkan yana kallon su, musaddiq bai d'auka da gaske ba ne sai da ya ga Dr muh'd da sadeeq sun tashi har daddy yana mishi magana akan ya tashi su tafi. Cikin sanyin jiki musaddiq ya tashi tukunna suka fice daga palon muh'd na rik'e da hannun musaddiq, mumy da daddy suka bi su da kallo kowanne yana nashi tunanin a cikin xuciyar shi............... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ *E.W.F* _ina kike my BIEBIE DEEE wannan shafin naki ne k'awata ta kirki Allah ya bar mu tare_ *PAGE 19* Bayan tafiar Dr muh'd ne, sadeeq yasa hannun shi ya rik'o hannun husna wani irin shock suka ji a lokaci d'aya don tun da sadeeq yake xuwa wajen mufidah ko da wasa bai ta6a rik'e mana hannu ba ko ya ta6a jikin ta, hkan ba halin shi bane yanxu kuwa da ta xama halaliyar shi xai iya komai da ita ba tare da fargabar kauce wa mahaliccin shi ba. Zama yayi kan kujera tare da janyo mufidah akan cinyar shi ya xaunar da ita yasa hannun shi ya xagaye hips d'in ta, tukunna ya sanya d'aya hannun ya cire mayafin da ta lullu6a dashi nan fuskar ta ta bayyana wadda tasha heavy make up tayi kyau kamar ba ita ba amman ruwan hawaye ne kawai suke xuba daga idanun ta, rungume ta yayi wanda har sai da mufidah taji saukar ajiyar xuciyar shi, kafin ya bud'e baki a hankali yace "Alhmdullilah ayau baxan iya fad'ar irin tarin farincikin da nake ciki ba, Allah nagode ma da ka nuna min wannan muhimmiyar ranar a gare ni da na mallaki abar sona" Ita dai mufidah shiru tayi mishi kan ta a sunkuye ta k'i d'ago kanta, ha6ar ta yasa hannu ya rik'o tare da kallon fuskar ta yace "Ya kamata ki daina kukan nan hka kada yasa miki ciwon kai, yanxu tashi mu tafi bedroom don gabatar da sallahr nafila mu gode wa Allah da ya nuna mana wannan ranar da muka mallaki junan mu ta hanyar yin aure" A nutse ya sauke ta daga kan kafafunshi tukunna ya mik'e tsaye yana rik'e da hannun ta suka rufe ko ina sannan suka shige bedroom, toilet suka shiga suka d'aura alwala tukunna suka fito ita dai mufidah bin shi take duk abin da yace mata saboda wata irin kunyar shi take ji, shi ya shimfid'a musu abin sallah ya d'auko mata hijab ta sanya sannan ya fara jansu yin nafila. Bayan sun kammala nafilar ne ya rik'e kanta da hannun shi yayi addu'a sosai don ba laifi sadeeq akwai ilimin addini, bayan ya gama addu'ar ne sannan ya sauke hannun shi daga kanta,ya dad'e yana musu addu'ar xaman lafia da samun xuri'a mai albarka kafin kuma su shafa, tashi yayi ya fita daga bedroom d'in, ganin hka yasa mufidah mike wa ta ninnike abin sallahr ta ajiye tare da hijab d'in da tayi sallahr tukunna ta shige toilet don yin wanka saboda ta saba Indai xata yi bacci a gida sai tayi wanka take iya bacci mai dad'i. Ta d'auki tsawon mintuna 15 tukunna ta fito ta shirya cikin wata sleeping dress irin mai biyun nan ta farko iyakar ta gwiwa ta tsaya tana da siririn hannu ta biyun kuma wadda ake d'ora ta asaman dogowa ce har k'asa hannun ta mai d'an tsayi kad'an sai ka d'aure ta da wasu siririn maxagin jikin rigar, bayan ta gama sanya kayan ne ta fesa different perfumes and body spray's masu matuk'ar k'amshin dad'i tukunna ta nufi kan bed don kwanciya wani irin bacci take ji a idanun ta sosai ta k'udundune jikin ta da wani blanket mai matuk'ar laushi saboda yanda garin ya d'auki sanyi sakamakon hadarin da ya had'u sosai ga kuma sanyin ac dana fanka. Ko mintuna biyar bata yi da kwanciya ba sadeeq ya shigo cikin bedroom d'in hannun shi dauke da wani babban tire shima yayi wankan shi yasha wasu sleeping dress na maxa sky blue ne masu taushin gaske, ajiye tiren yayi tare da hawa kan bed d'in yasa hannu ya cire rufar da mufidah tayi lokaci d'aya tsikar jikin shi ta tashi saboda ganin mufidah da yayi a hka d'aure wa yayi yace "My wife tashi kici abinci sai kiyi bacci, kada kice min a'a please, don nasan baki ci abincin kirki ba saboda hidima" Kasa yi mishi musu tayi nan ta fara k'okarin tashi da sauri yasa hannun shi ya tashe ta xaune tukunna ta tashi xuwa wajen wasu kujeru guda biyu a gefen bed d'in akwai center table a tsakiyar su nan ta xauna shima sadeeq tashi yayi ya koma inda take tukunna ya bud'e plate d'in wasu gasassun kaji ne sun sha kayan vegetables sai tashin k'amshi suke ko ni dana ke gefe ina daukan muku rahoto sai da yawu na ya tsinke lol. Gefe kuma drinks ne da fresh milk gasu nan kala kala masu sanyi, nan ya fara ciyar da mufidah da hannun shi don yak'i yarda taci da kanta, bayan sun gama ci ne mufidah ta tashi ta shiga toilet brush tayi ta wanke bakin ta da mouth freshener mai k'amshin mint leave's tukunna ta fito bata ga sadeeq anan ba don hka ta koma ta kwanta abin ta lokacin har an fara yayyafi. Sadeeq ne ya shigo bedroom d'in tare da rufe kofar tukunna ya nufi kan bed ya kwanta kusa da mufidah, lokaci d'aya gaban mufidah yayi wani irin fad'uwa nan jikin ta ya fara rawa na tsoro, bugun xuciyar mufidah ne ya k'aru ganin sadeeq ya yi switch off d'in hasken d'akin nan duhu ya bayyana a d'akin sai dai hasken walk'iya da yake hasko ta tsakanin labulen window. Ji tayi sadeeq ya sanya hannun shi ya jiyo da ita suna fuskantar junan su har suna jin d'umin numfashin junan shi cikin wata irin murya sadeeq yace "Haba my wife ba dai bacci ba, ki bari abincin da kika ci yayi k'asa sai kin fi jin dad'in baccin" Cikin marairaice wa mufidah tace"ni bacci nake ji gashi na gaji sosai" "Okay bari nayi miki tausa" Sadeeq ya fad'i hkan cikin murmishi yana sa hannun shi cikin jikin ta yana mata tausa a hankali, ita dai mufidah shiru tayi tana wani lumshe idanun ta don tana jin dad'in tausar. Cikin mintuna biyar da fara yi mata tausar kid'a ya fara sauya salon shi, wanda adai dai time d'in ruwa mai k'arfi ya sakko tare da wata iriyar iska mai sanyi irin wadda take ratsa jiki har cikin k'ashi, nan fah jikin mufidah ya d'auki rawa don gaba d'aya sadeeq ya canja daga tausar da yake mata xuwa wani salo na daban wanda daga sadeeq d'in har mufidah sabon shiga ne a 6angaren. Cikin nutsuwa yake sarrafa mufidah cikin wani irin salo mai wuyar fassara, gaba d'aya sadeeq ya rikici ya fara fita a hayyacin shi cikin rawar jiki yake juya mufidah yanda yake so, tuni mufidah ta fara kuka da had'a gumi har xuwa lokacin da mayar da ita cikakkiyar mace. Adai dai wannan lokacin musaddiq da yake xaune saman sofa ya farka firgigit a matuk'ar firgice, ya mayar da kallon shi kan muh'd wanda yake kwance a kan bed ya tuk'unk'une jikin shi waje d'aya, tashi musaddiq yayi tare da d'auko blanket ya lullu6e muh'd, hka kawai yaji hankalin shi yayi matuk'ar tashi har wani gumi ne yake tsatstsafo mishi na tashin hankali. Ya rasa abin da yake mishi dad'i kawai ya bud'e kofar da xata sada shi da corridor d'in waje yana bud'e kofar wani sanyi had'e da feshin ruwa ya bugi fuskar shi da gangar jikin shi amman bai damu ba sai kawai ya fitar da kanshi daga wajen rumfar corridor d'in nan take ruwan sama ya fara dukan shi kafin kace me tuni ruwan ya jik'a shi jagab. Bai damu da jik'ewar da yayi ba ko dukan da ruwan saman yake mishi ya tsaya kawai waje d'aya ruwan na dukan shi xuciyar shi na wani irin xugi. Gaba d'aya hankalin shi da xuciyar shi suna wani waje daban, yafi tsawon mintuna 30 a tsaye a wajen kafin kuma ya koma cikin bedroom dak'yar ya iya cire jik'akk'akun kayan jikin shi ya sanya wani wando dogo Mara nauyi da wata jibgegiyar rigan sanyi ya k'udundune da bargo wani sanyi ne yake ratsa shi tuni wani xaxxafan xaxxa6i ya lullu6e shi jikin shi sai rawa yake wasu hawaye masu xafin gaske suna xubo mishi..................... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *PAGE 20* Kiran sallahr asuba ne ya farkar da sadeeq daga bacci mai dad'in da ya d'auke shi kallon mufidah yayi wadda take kwance a jikin shi ta tuk'unk'une jikin ta waje d'aya sai faman sauke ajiyar xuciya take alamun taci kuka ta koshi, hannun shi yasa ya shafa mata fuska tare da gyara gashin da ya barbaxu akan kyakkyawar fuskar ta murmishi ne kawai yake fita daga idanun shi na nishad'i. Anutse ya gyara mata kwanciyar tukunna ya tashi ya shiga toilet yayi wanka tare da d'aura alwala kafin ya fito sai da ya had'a wa mufidah ruwan d'umi a cikin kwamin wanka tukunna ya fito daga toilet d'in. Cikin bedroom d'in ya dawo tukunna yasa hannu ya cire blanket d'in da mufidah take lullu6e a ciki ya d'auke ta cak xuwa cikin toilet cikin ruwan da ya had'a mata ya sanya ta ciki, haba wani xabura mufidah tayi xata tashi da sauri sadeeq ya rik'e ta tare da cewa "Sorry my wife ki daure ki xauna hkan xai taimaka miki sosai kiji dad'in jikin ki" Cikin xubar hawaye mufidah tace" ni ka fitar da ni daga nan sadeeq please akwai xafi" Cikin marairaice wa da muryar rarrashi yace"haba my wife ke fah jaruma ce kiyi hak'uri d'an lokaci komai xai dawo normal, Allah yayi miki albarka matata" A cikin xuciyar ta ta amsa da ameeen d'in, hka ya cigaba da lalla6a ta har ta gasa jikin ta tukunna ta fito ya tafi masjid xuciyar shi wasai farinciki ne fal a tattare dashi don mutum kallo d'aya xai mishi ya karanci hkan a tare dashi. Bayan tayi wanka had'e da d'aura alwala tana fitowa ta shirya cikin wata gown mara nauyi tukunna ta shimfid'a abin sallah ta fara, bayan ta idar da sallahr tana cikin addu'a ne wani bacci mai k'arfi yayi awon gaba da ita. A hka sadeeq ya dawo daga masallaci ya ganta kwance kan abin sallahr, daukan ta yayi tare da d'ora ta kan bed tukunna shima ya kwanta tare da janyo ta jikin shi ya rungume ta kafin bacci kuma yayi awon gaba dashi. Addu'ar tashi daga bacci muh'd ya furta bayan ya bud'e idanun shi tare da yin mik'a, agogo ya kalla yaga har 6:40 na safe yayi lallai yau ya makara sosai bai yi sallahr asuba akan lokaci ba, mik'e wa yayi tare da shiga toilet ya d'aura alwala sannan ya fito, bayan ya idar da sallah ne yayi addu'o'in shi tukunna ya tashi ya nufi bed da niyyar tashin musaddiq yaye blanket d'in yayi tare da cewa "Musaddiq tashi kayi sallah yau mun makara sosai" Shiru yaji musaddiq bai amsa ba kallon shi yayi sosai sai lokacin ya kula da yanda jikin shi yake rawa hawaye na fita a idanun shi, fuskar shi da idon shi sun yi ja sosai cikin tashin hankali muh'd yace "Subhanallah musaddiq me yake damun ka?" Ya k'arasa fad'i yana tashin shi xaune cikin rawar murya yace "Muh'd mutuwa xan yi xuciya ta kamar xata fashe nake jin ta kuma sanyi nake ji sosai" Ya k'arasa fad'i hawaye masu xafi suna xubo mishi, shima muh'd d'in hawayen yake yi ganin yanda musaddiq ya koma cikin sanyin murya yace "Baxa ka mutu ba musaddiq xamu rayu tare insha Allah cuta ba mutuwa bace Allah ne ya d'ora maka kuma insha Allah xai yaye maka, bari na duba ka" Wurin first aid box ya nufa ya d'auko shi tare da duba abin da yake ciki, allura xai mishi kuma dole ya d'an sa wani abin a cikin shi kafin yayi mishi, don hka da sauri ya bud'e frige din musaddiq na bedroom ya tarar da fresh milk mara sanyi ya d'auko tukunna ya dawo wajen musaddiq jingina bayan shi yayi da pillow sannan ya fara bashi a baki a hankali bayan ya d'an sha ne tukunna yayi mishi allura tare da bashi magani, cikin en mintuna bacci ya d'auke shi ya fara gumi alamun xaxxa6in ya fara sauka, sai lokacin Dr muh'd ya saki ajiyar xuciya ta kwanciyar hankali. K'arfe 9:30 mufida ta bud'e idanun ta da suka yi mata nauyi saboda sun kumbura sakamakon kukan da tasha kallon d'akin tayi taga sadeeq baya nan d'an ta6e baki tayi tare da tashi ta lalla6a ta shiga toilet wanka tayi ta fito kai tsaye wajen dressing mirror ta nufa ta shafa wani cream mai k'amshin apple tare da yin light make up a fuskar ta, wardrobe ta bud'e tare da d'auko wata swiss atampha d'inkin riga da siket ne under wear's ta d'auko bak'ak'e ta sanya tukunna ta sa atamphar tayi mata kyau sosai kalar ta amshe ta, tana cikin fesa perfumes ne sadeeq ya shigo yayi wankan shi yasha gayun shi cikin wata tsadaddiyar shadda light ash yayi kyau sosai don gaskia kusan kamar su d'aya da musaddiq bambamci su kad'an ne kamar wasu twins ko wasu twins d'in basa kama da junan su kamar hka. Ajiye perfume d'in hannun ta tayi tare da tsugunna wa k'asan carpet cikin sanyin murya tace "Ina k'wana sadeeq?" D'ago ta yayi tare da rungume ta a kunnen ta ya rad'a mata "my wife lafia qlau, ya k'wanan bak'un ta da gajiya kuma". Hannun ta tasa tare da rufe fuskar ta tana murmishi kafin kuma ta fara xare jikin ta cikin ta cikin nashi, sake rik'o ta yayi tare da cewa "Ina xuwa my wife?" "Wurin mumy xan je mu gaisa kaga yanxu 11 ta kusa" "Okay muje mayi breakfast ma a can koh?" D'aga kanta tayi alamun eh mayafin ta ya d'auko ya sanya mata da flate shoe ya sanya mata tukunna ya kano hannun ta ya rik'e suka fita daga part d'in su xuwa part d'in mumy, kallo d'aya xaka yi musu ka tabbatar amarya da ango ne kuma sun yi matuk'ar dace wa da junan su sosai, fuskar sadeeq fara'a ce kwance a fuskar yayin da mufidah ba yabo ba fallasa. Da sallama suka shiga palon mumy da dinning wad'anda suke 6angaren dining table suna breakfast suka amsa fuskar su d'auke da fara'a, k'arasa wa wajen suka yi sai lokacin mufidah ta kwace hannun daga hannun sadeeq, tsugunna wa har k'asa suka yi suna gaida su cikin fara'a suka amsa musu tukunna mumy tace "Da yanxu xa'a kai muku naku tun da kuma kun shigo sai muci tare bismillan ku" Tashi suka yi duk suka xauna, daddy ne ya kalli mumy yace"kirawo musaddiq da muh'd sai mu yi breakfast d'in tare" Dummm gaban mumy ya fad'i baxa taso musaddiq yaxo wurin nan ba don komai xai iya faruwa shiru tayi bata ce komai ba sai da daddy ya sake maimaita mata tukunna ta tashi cikin sanyin jiki xata tafi kenan ta hango musaddiq da Dr muh'd sun taho inda suke kan shi a sunkuye yake, tuni Dr muh'd ya hango mufidah tuni gaban shi ya hau fad'uwa hka ma mumy sun rasa ta yanda xasu janye hankalin shi daga wajen, muh'd ya jiyo da niyyar yi mishi amman ina har daddy da sadeeq sun gansu Dr muh'd mutuwar tsaye yayi hka mumy ma ta rasa abin yi................ _kuyi hak'uri da wannan fan's wlh mura, ciwon kai ne suke damuna dak'yar na iya wannan ma, dafatan xaku yi min addu'ar fatan samun sauk'i na d'ora daga inda muka tsaya, fatan alkhairi a gare ku masoyan yayi sake!_ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ *E.W.F* _shafin naku ne abokan kirki, Queen bee marafa, real khady, jameesha, amal,nabilancy luv, ummu khady, mum useey, 'yar gatan hudah, ruksad and oll member's na exclusive writer's, ina matuk'ar alfahari da ku, Allah ya k'ara mana basirah tare da sauran marubuta en uwan mu, ina muku fatan alkhairi gaba d'ayan mu_🤝❤ *PAGE 22* Bayan sun k'arasa airport ne a suka firfito daga cikin motocin da suke ciki,lokacin sauran mintuna 10 jirgin da musaddiq xai yi amfani dashi ya tashi, a lokacin ne Dr muh'd ya k'araso wajen hararar shi musaddiq yayi da sauri ya had'e hannayen shi alamar yayi hak'uri. A gurguje musaddiq yayi sallama da iyayen shi bayan daman tun acikin mota daddy da mumy suka yi mishi nasiha sosai mai ratsa jiki kuma ya kula ya daina sa damuwa da tunani, sosai ya nuna musu xai bar tunanin komai yayi abin da ya kai shi su cigaba da taya shi addu'a, sun ji dad'in abin da ya fad'a musu nan suka sa mishi albarka tare da yi mishi fatan alkhairi. Rungume daddy ya sake yi a karo na biyu idanun shi sun yi ja alamar daf suke da fara xubar hawaye, tukunna ya cika daddy ya rungume mumy sun dad'e a hka ya kasa sakin ta don ji Yayi gaba d'aya tafiyar ma ta fara fita a kanshi baya son yin nesa da iyayen shi da d'an uwan shi amman yasan shi kanshi dole yayi nesa da gida don yafi samun nutsuwar xuciyar shi tare da k'okarin fitar da son mufidah daga cikin xuciyar shi. Dafa mishi baya aka yi da sauri ya d'ago kanshi tare da juyo wa ya kalli Yah sadeeq murmishin yak'e ya saki sam ya kasa kallon shi idanun shi na kan hannun sadeeq da ya yake rik'e da hannun mufidah daurewa kawai yake amman ji yake kamar ya d'ora hannu amai yana xunduma ihu ko yaji sassaucin abin da yake cikin xuciyar shi. A hankali sadeeq ya cika hannun mufidah tare da rungume d'an uwan shi a jikin cikin wata irin soyayyar en uwantaka ta jini, lokaci d'aya idanun su ya ciko da hawaye, amman musaddiq ya had'iye kukan nashi shi kuwa sadeeq sai da hawayen shi suka xubo sakin shi musaddiq yayi tare da rik'e kafad'un shi yana girgixa kai alamar kada Yayi kuka cikin rawar murya yace " ka barni nayi musaddiq bana son rabu wa da kai ko na second ne balle tsawon kwanaki xamu d'auka batare da ganin juna ba sai dai jin murya a waya" Hannun shi musaddiq yasa a fuskar sadeeq yana goge mishi hawayen da suke xuba da 'yantsun shi, cikin rawar murya musaddiq ya bud'e baki yace "Calm down Yah sadeeq kukan ka yana k'ara karyar min da gwiwar tafia, idan kana son ganina xaka iya xuwa inda nake nima idan na samu hutu xan na xuwa insha Allah ka taya ni da addu'a" K'ara rungume junan su suka yi gaba d'aya sun bawa daddy, mumy, Dr muh'd da mufidah tausayi sosai, har sai da mufidah ta yi hawayen tausayin su musaddiq yana kula da yanda take fitar da hawayen sam baya son ganin hawaye a fuskar ta hkan ba k'aramin rikita shi yake ba, bai san lokacin da ya sanya hannu a aljihun black jeans d'in shi ya d'auko wani kyakkyawan hankacif ya mik'a mata ba tare da ya kalle ta ba ko yayi mata magana. Babu wanda ya kula da hkan sai Dr muh'd, ita ma mufidah bata san lokacin da ta mik'a hannu ta kar6a ba don hankacif d'in ya birge ta pink colour ne da adon white flower's a jiki sai tashin k'amshin turaren shi yake mai matuk'ar dad'i. A fuskar ta tasa tare da shak'ar k'amshin saboda dad'in shi sai da ta lumshe idanun ta kafin ta goge hawayen fuskar ta ta, wani tunani ta fara yi kafin kuma ta tuna ita matar aure ce a yanxu da gaggawa ta kauda tunanin tare da yin astagafrullah a cikin xuciyar ta. Ganin mutane sun fara shiga jirgin ne yasa daddy yace " musaddiq lokaci fa yayi a hak'ura hka da sallamar" Cikin sanyin jiki ya cika sadeeq tare da juyawa don su yi sallama da muh'd aikuwa sadeeq ya k'ara sa hannu ya rik'e shi gam, kallon shi daddy yayi tare da cewa "Kae sadeeq cika shi mana kada ka 6ata mishi lokaci" Dak'yar sadeeq ya cika musaddiq ya rungume muh'd sannan suka k'ara yin sallama da iyayen shi har yayi taku na biyu xai yi na uku yaji sanyayyiyar muryar mufidah tana cewa "Allah ya kiyaye hanya malam" Ko juyo wa bai yi ba yayi gaba don yanda yake xuciyar shi tayi rauni da yawa, suna kallon shi har ya fara tattaka matattakalar jirgin dai dai yaxo xai shige cikin jirgin ya jiyo ya kalli iyayen shi da d'an uwan shi tare da abokin shi aminin shi bai kalli wajen mufidah ba ya d'aga musu hannu tare da shige wa cikin jirgin da sauri kada xuciyar shi ta karaya Yayi kuka. Dukannin su jiki a sanyaye har sai da jirgin tashi suka daina ganin shi sannan suka shiga mota sai gida, har suka k'arasa gida babu mai magana a cikin su saboda kewar musaddiq duk ta dame su. Tun a hanya Dr muh'd ya wuce gida don baxai iya k'arasa wa ba tun da babu aminin shi, daddy da mumy ma part d'in su suka shige, hka mufidah ta kama hannun sadeeq suka wuce part d'in su don bata son su takura wa su mumy tun da weekend ne. Suna shiga part d'in su sadeeq ya xame hannun shi daga na mufidah ya shige bedroom d'in shi da kallon mamaki mufidah ta bishi da kallo, ta6e bakin ta tayi tare da xama a kan kujera shiru tayi na en mintuna tana tunani kafin kuma ta tashi ta shige bedroom d'in ta mayafin da tayi rolling d'in kanta dashi ta cire ta ajiye tare da hankacif d'in da musaddiq ya bata, cire gown d'in jikin ta tayi tare da d'aura towel ta shige toilet. Cikin en mintuna tayi wanka ta fito ta shirya cikin wata er riga iyakar ta gwiwar purple colour mai k'aramin hannu, light make up tayi tare da gyara gashin kanta batasa ribbon ba ta sake shi hka a bayan ta sai tashin k'amshi mai dad'i gashin yake, different perfumes and body spray's xuwa humra tayi amfani dasu a jikin ta sannan ta xura flate shoe bak'i ta nufi bedroom d'in sadeeq da sallama a bakin ta ta shiga d'akin. Cikin nutsuwa ya d'ago kanshi ya kalle ta k'okarin amsa sallamar yake amman ya kasa saboda ganin mufidah da yayi da wannan shigar tun da suke bata ta6a yi mishi irin wannan shigar ba, kafin ya ankara yaji ta xauna akan kafafun shi ta sanya hannun ta a kafad'ar shi ta rik'e d'ayan hannun kuma ta rufe mishi baki ganin yanda ya bud'e yana bin ta da kallo. "Wannan bud'e bakin fa?" Dariya suka sa lokaci kafin ya k'ara rungume ta ajikin shi cikin kunnen ta ya fad'a mata cewa "Bud'e bakin kallon ki ne my wife kinyi kyau sosai" Murmishi tayi tana mai sunkuyar da kanta a hankali ya fara gwada mata salon soyayyar shi mai sanyi, ita ma mufida ta biye shi don tana so ta mantar dashi damuwar da yake ciki, bayan komai ya kammala ne bacci mai dad'i ya d'auke su rungume da junan............. Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ *E.W.F* _ina kuke Ummiey Xeey dear and Aishan umma dear wannan shafin na ku ne kyauta, ina matuk'ar alfahari da ku Allah ya bar xumunci a tsakanin mu_❤ *PAGE 21* Sam musaddiq bai kula da mufidah ba har ya xauna a kusa da kujerar daddy, tea d'in da mumy ta had'a musu ta ajiye yasa hannu ya d'auka a hankali ya fara shan tea d'in, cikin wata siririyar murya mufidah ta bud'e baki tace "Ina k'wana musaddiq?" A matuk'ar rikice ya d'ago kanshi ya kalli inda take, had'a ido suka yi yayin da kuma lokaci d'aya ya furzar da tea d'in da yake bakin shi ya kware sosai amman still idanun shi na kanta, da sauri daddy, mumy, sadeeq tare da muh'd suke yi mishi sannu yayin da mufidah ta d'auki glass cup ta cika shi da ruwa mara sanyi ta mik'a mishi tana cewa "Sannu fah" Da sauri mumy tasa hannu ta kar6i cup d'in hannun mufida ta sa wa musaddiq a baki, kad'an ya iya sha ya cire cup d'in a baki tare da tashi da sauri ya bar wajen, muh'd ma ya juya ya kalli su daddy yace "Daddy xamu je mu fara shirya shiryen tafiar musaddiq don nan da k'wana biyu xai tafi" Cikin matuk'ar mamaki sadeeq yace "ina musaddiq d'in xai je?" Shiru muh'd yayi ganin hka yasa daddy yace"muh'd je ka xan yiwa sadeeq bayanin komai" "Toh daddy" Yana gama fad'in hka ya fice daga palon yabi bayan musaddiq, daddy kuwa nan yayi wa sadeeq bayanin karatu musaddiq xai je ya k'aro, nan fah sadeeq ya tubure lallai sai musaddiq ya hak'ura da tafia yayi anan nigeria ko kuma ya tattara ya bishi can ko kuma ya hak'ura gaba d'aya da karatun don sam baya son yin nesa da d'an uwan shi. Nan fa daddy da mumy suka fara rarrashin shi, mufida kuwa ido ta xuba musu kawai tana kallon su don bata da abin cewa, dak'yar suka shawo kan sadeeq ya amince da tafiyar musaddiq ba don ranshi ya so ba don gaba d'aya baya k'aunar yin nesa da d'an uwan shi, yana mishi wani irin so da baxai kwatantu ba. Mumy ce ta kalli mufidah wadda ta kula gaba d'aya a takura take dasu tace " 'yata tashi kije ki huta kin ji" Sunkuyar da kai tayi cikin kunya tace " toh mumy" Kallon sadeeq mumy tayi tare da cewa " ka bita ku tafi tare, idan kuna buk'atar wani abin ka kirawo ni a waya ka sanar da ni" " okay mumy" Daga hka suka mik'e tare da tafiya part d'in su, da kallo mumy ta bisu kafin sai da suka 6acewa ganin ta tukunna ta sauke idanun ta tare da sauke ajiyar xuciya, kallon ta daddy yayi tare da cewa " Ya akayi mumyn sadeeq?" Girgixa kai tayi tare da cewa " ba komai " " ina son ki cire sa damuwa a cikin ranki game da tafiyar musaddiq, insha Allah babu abin da xai faru dashi addu'a xaki nayi mishi" " toh daddy xan yi yanda kace" Ta fad'a tana Murmishi, shima daddyn cikin murmishi yace "yawwa tawan hka nake son ji" Daga hka suka cigaba da hirar su cikin kwanciyar hankali, amman mumy xuciyar ta tana tunanin yanxu Wanne hali musaddiq yake ciki gaba d'aya ta matsu da ya tafi ko xuciyar ta ta samu sukuni don bata son suna had'u wa da mufidah. Bayan sun k'arasa part d'in su mufidah bedroom ta shige don ta samu bacci, idanun ta har wani xafi yake saboda baccin da take ji, kwanciya tayi tare da k'ara k'arfin ac dake d'akin, shima sadeeq ganin hka yasa ya bita bedroom d'in kwanciya yayi tare da janyo ta jikin shi ya rungume ta ba dad'e wa bacci yayi awon gaba dasu gaba d'aya. Musaddiq kuwa tun lokacin da ya fice daga palon da sauri wajen parking space ya k'arasa motar Dr muh'd ya shige ya xauna tare da had'a kai da gwiwa hannun shi dukka biyun kuma suna saman kanshi yana yamutsa gashin kanshi, idanun shi sunyi ja sosae, a lokacin idan ka ga musaddiq sai kayi mishi kukan tausayi gaskia so masifa ne idan baka yi dace ba da yasan hka son mufidah xai mayar dashi da bai yi saken da xai rasa ta ba a rayuwar shi. Yana cikin wannan halin ne muh'd ya k'araso wajen har ya shiga cikin motar ya xauna musaddiq baisan ya shigo ba, girgixa kai yayi cike da tausayin musaddiq yasa hannun shi ya dafa kafad'ar shi d'ago jajayen idanun shi yayi ya watsa su akan muh'd wanda yasa sai da gaban muh'd ya fad'i ganin yanda musaddiq ya koma, cikin rarrashi muh'd yace "Haba musaddiq kai fa kayi alkawarin cire son mufidah a cikin xuciyar ka, gashi idan kana irin hka daddy da yah sadeeq xasu d'ago ka fa, don nasan mumy ta gama fahimtar komai magana ce kawai bata yi ba" Shiru shi dai musaddiq Yayi amman yana sauraren abin da muh'd yake fad'a mishi, sai da suka 6ata lokaci sosai muh'd yana rarrashin musaddiq har ya samu ya dawo dai dai tukunna suka tafi inda xasu je. A cikin wad'annan kwanakin biyu musaddiq babu abin da yake sai shirye shiryen tafiar shi duk wani shiri ya gama sai jiran ranar tafia kawai yake jira, sadeeq ya shiga damuwa sosai na tafiyar musaddiq amman mufidah da mumy suna k'okari wajen lalla6a shi har dai ya d'an kwantar da hankalin shi. Tun daga ranar musaddiq bai k'ara had'u wa da mufidah ba kuma shi kanshi yaji dad'in hka don baya son ganin ta don ba k'aramin d'aga mishi hankali ganin ta yake ba. A yau Saturday ne da yammacin ranar K'arfe 5 na yamman jirgin da xai je Australia xai tashi, don hka musaddiq xuwa hud'u na yammacin ranar ya kammala komai, fito wa yayi daga bedroom d'in shi xuwa palon mumy don su yi sallama yana shiga palon ya tarar da sadeeq da daddy a tsaye suna jiran shi don yi mishi rakiya. Rungume daddy yayi idanun shi sun cicciko da hawaye peck ya bawa daddy a kumatun shi tukunna ya cika shi suka rungume junan su da sadeeq kowanne idanun shi cike da hawaye, d'ago kan da xai yi suka sauka akan mufidah tana murmishin da yake k'ara mata kyau tayi kyau cikin wata Arabian gown blue colour tayi rolling d'in kanta da red d'in veil ba k'aramin kyau tayi ba lips d'inta yasha red d'in jambaki, wani irin abu ne ya tsayawa musaddiq a xuciyar shi da sauri ya kawar da kanshi daga kallon ta yana k'okarin danne abin da yake ji. Sakin sadeeq yayi tare da k'arasa wa wajen mumy wadda ta sakko daga up stairs da shirin ta na rakiyar musaddiq airport, rungume ta ita ma yayi sosai mumy ta tsorata da yanda taji bugun xuciyar musaddiq, hannun ta tasa ta shafa kanshi tare da rad'a mishi a kunnen shi "Ka dage da addu'a musaddiq Allah ya yaye maka abin da yake damun ka, nima xan dunga you maka, kada kana sa damuwa a cikin xuciyar ka don Allah kayi min wannan alkawarin" D'aga kai yayi tare da cewa " xan yi abin da kika ce mumy nah" Daga hka kuma suka d'unguma don tafiya airport rakiyar musaddiq ko inda mufidah take bai k'ara marmarin kallo ba, sosai mufida abin da yake mata yana d'aure mata kai xai yi magana da kowa ban da ita ko gaida shi tayi baya amsa wa, amman da ta tuna er tsamar da suke yi a skul maybe har yanxu bai hak'ura ba ta6e baki tayi, hannun ta sadeeq ya kama suka fita daga palon da yake duk sun riga su yin gaba..................... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM *PAGE 23* Tun lokacin da musaddiq ya tafi xuciyar mumy ta kasa samun nutsuwa saboda batasan halin da d'anta yake ciki ba, idan suka kirawo shi a waya muryar shi normal, but ae ba fah ta ganin shi batasan yanayin da yake ciki ba, ta dage da taya shi addu'a sosai, hka a 6angaren daddy da shima addu'ar yake taya musaddiq tare da Kiran shi a waya yana mishi nasiha cikin tausasawa da rarrashi, duk wata kulawa suna yi mishi ta waya. Sadeeq kuwa bayan en kwanaki da tafiyar musaddiq ya cire damuwar rashin d'an uwan nashi a kusa dashi, don yana samun kulawa sosai a wajen matar shi mufidah, xaman su suke lafia cikin kwanciyar hankali, duk da sadeeq yana da sanyin hali a komai nashi daga kallon yanayin shi kasan bashi da xafi komai cikin sanyi yake shi yasa suke xaman su lafia ba mai jin Kansu. Mumy ma tana k'aunar mufidah saboda hankalin ta da nutsuwar ta gashi tana matuk'ar kulawa da d'anta shi yasa duk abin da ta samu xata nemi mufidah ta bata. Saboda kwanciyar hankali mufidah tayi wata er k'iba kad'an ta k'ara haske da kyau abin ta, tana samun kulawa sosai a wajen mijin ta da iyayen shi, bata da wata matsala a yanxu sai wadda ba'a rasa kowanne d'an adam da ita ba. Tsawon watannin su biyu da aure bata fita ko'ina ba amman a yau tayi niyyar tambayar shi tana son taje gida daga can xata wuce gidan Yah Omar wajen nabila don ita nabila xuwan ta biyu gidan tana yi mata yini, a xuwa na biyun ne tace baxa ta k'ara xuwa ba sai ta je, shi yasa ta yanke shawarar fita gobe. Wajen K'arfe biyar da rabi ne ta shiga kitchen don yi musu girki dare, abinci mara nauyi tayi niyyar yi musu don hka jeelop na taliya take son yi, nan ta fara aikin ta cikin kware wa ta yayyanka su vegetables da yin blending d'in kayan miya. Cikin tsawon mintuna ta kammala jeelop d'in ta xuba a food Flak's sannan tayi musu chicken pepper soup, sai coconut juice wanda yasha coconut and pineapple aciki sosai tare da milk ta ruwa tana gama wa ta sanya a frige bayan ta juye shi a jug. Food Flak's d'in ta d'iba ta kai dinning area ta jera tukunna ta dawo ta kitchen ta d'auki plate's, spoon da glass cup's ta kai su dinning bayan ta gama sannan ta gyara kitchen d'in tare da yin wanke wanke, bayan ta gama da kitchen ne, ta gyara falo tare da sa mishi turaren wuta mai k'amshi tuni ko'ina a falon ya d'auki k'amshi, sannan ta wuce bedroom's d'in su ta gyara, tana gama wa sai ta fad'a toilet tayi wanka tare da d'aura alwala don mangarib tayi. Bayan ta idar da sallahr mangarib ne ta xauna tana karatun Qur'an har xuwa lokacin sallahr isha'e, bayan ta idar tayi shafa'i da wutiri ne tare da addu'o'in ta tukunna ta tashi ta cire abayat d'in da tasa tayi sallah. Wajen dressing mirror ta k'arasa ta shafa wani cream tare da yin light make up, tukunna ta k'arasa wardrobe ta bud'e 6angaren English wear's ta d'auko wani jeans white ne da t-shirt pink colour mara hannu bayan ta gama wa kayan ne sai ta gyara gashin kanta ta gefe tayi parking d'in gashin nata tayi kyau sosai kamar wata er baby, perfumes ta fesa tare da shafa humra mai tsananin k'amshi a jikin ta, falo ta fito ta xauna tana kallon film d'in thor a mbc 2. Ko mintuna bakwai bata yi da xama ba sadeeq yayi sallama tare da shigowa palourn, d'ago kai tayi ta kalle shi tare da amsa mishi sallamar cikin muryar ta mai dad'i. K'arasa wa yayi tare da xama kusa da ita yana kallon ta yace " my wife kin yi kyau sosai" Cikin murmishi ta amsa da "thanks my dear, yau ka dad'e fah lafia?" Yana kamo hannun ta yace " lafia my wife after an idar da sallah ne na tsaya yin waya da musaddiq kiyi hak'uri idan baki ji dad'i ba" Girgixa kai tayi tare da cewa " ba komai dear dafatan yana nan lafia?" "Qlau yake yana gaida ke ma" Kallon shi tayi tare da cewa "Hmmm ina amsawa ", ba don ta yarda da abin da yace ba, nan ta jashi bedroom yayi wanka tukunna suka fito dinning table don yin dinner. Bayan sun kammala cin abincin ne suka dawo cikin parlour, yana xaune kan kujera 3siters mufidah tana kwance tayi matashin kai da cinyar shi suna er hirar su da kallo, can mufidah tace " Don Allah dear ina son ka barni gobe na je gidan mu da gidan Yan Omar please" Murmishi yayi tare da shafa mata kai yace "kada ki damu my wife na bar ki Allah ya kai mu goben" Cikin tsananin farinciki tace " Ameeen ngde dear" "Kin wuce komai a waje na my wife, Allah ya sa ki Haifa min 'ya mace ma kama da ke, kafin na mutu naga d'an kai na nima" Lokacin da ya fara maganar murmishi ne shimfid'e a fuskar mufidah don ita ma tana tsananin son baby's tana son ta ganta da ciki kamar nabila k'awar ta don ita ta harbu tuni, k'arshen maganar da sadeeq yayi shi yasa mufidah ta 6ata fuska cikin shagwa6a tace "Kai koh dear xaka fara koh, insha Allah xamu rayu tare na haifa maka 'ya'ya da yawa" Murmishi yayi tare da cewa "haba my wife ae ita mutuwar nan ba sallama take da mu ba, lokaci d'aya xata xo ta d'auke mutum, kuma ana son ko da yaushe bawa ya dunga tuna ta" Tuni idanun mufidah sun fara taruwa da ruwan hawaye har sun fara xuba, ganin hka yasa sadeeq ya rungumo ta jikin shi tare da rarrashin ta yana gwada mata soyayyar shi mai sanyi wadda take mantar da mufidah damuwa, ae kuwa bai kyale ta ba sai da ya ga babu sauran damuwa a tare da ita sai farin ciki tukunna ya kyale ta. Washe gari da safe bayan sun gama breakfast ne suka shiga wajen mumy da daddy mufidah tayi musu sallama mumy har da bata perfumes ta kai wa umman ta daddy kuwa kud'i ya bata sadeeq ya kai ta mall ta yi musu tsaraba, sosai tayi musu godia tare da addu'ar fatan alkhairi, sannan suka fito suka tafi. A sahad store ya tsaya yayi musu tsaraba ko kud'in wajen mufidah bai kar6a ba wanda daddy ya bata, lokacin da aka gama xuba kayan a boot ne ya shiga har yayi wa motar key sun fara tafia mufidah ta mik'a mishi kud'in da daddy ya bata, girgixa kai yayi yana murmishi cikin sanyin muryar shi yace "My wife ba kud'in ki ne fah, ni wannan wanda nayi niyyar baki ne don hka ki rik'e abin ki" "A'a ni dai ka rik'e sun yi min yawa ne please" "Duk da hka ki rik'e xasu yi miki amfani wani lokacin kin ji" Kasa ce mishi komai tayi, da hka suka k'arasa gidan su mufidah yana gama parking ne ta bud'e kofar motar tare da fita da gudu tayi cikin gidan tana kwalla Kiran umma, sosai abin da tayi ya bashi dariya lallai mufidah akwai sauran yarinta a tattare da ita, fita shima yayi tare da bin bayan ta. "Umma na kina?" umma wadda ke xaune kan kujera a palour ta d'ago kanta da sauri ta kalli kofar shigo wa don jin muryar er autar ta, kafin ta ankara har mufidah ta fad'o kanta tana dariya, cikin tsananin farinciki umma ta rungume mufidah kafin kuma ta cika ta tace " ohhh ni mufidah bakya girma ji yanda kika fad'o min kamar wata karamar yarinya" Cikin shagwa6a tana turo baki tace " toh umma ae ni k'arama ce a gaban ki" Suna cikin hka sadeeq yayi sallama sai da umma ta amsa mishi tare da bashi ixinin shigo wa sannan ya shigo har k'asa ya tsugunna ya gaida umma, cikin farinciki umma take amsawa ta cigaba da cewa "Ohhh ashe tare kuke shine ta gudo ta barka a waje" Shi dai sadeeq murmishi kawai yayi yana kallon mufidah wadda take jikin umma tak'i tashi har yanxu, gaba d'aya sadeeq da umma er suruka ake yi ita kunyar shi take shima hka don hka ba wata hirar kirki da suka yi yayi musu sallama tare da fita daga palour mufidah sai a lokacin ta bishi a baya tana fito wa yasa hannu ya d'an ja kunnen ta kad'an tare da cewa "Shine kika haye jikin umma duk kin bi kin danne ta koh?" "Toh ae duk murnar ganin ta ne dear kuma nayi kewar ta sosai" Murmishi yayi tukunna ya shige mota bayan yasa mai gadi ya fitar da kayan boot ya shiga dasu gidan, sallama yayi mata sannan ya tafi ta koma cikin gidan. Yinin ranar sun sha hira da umma sosae don anjima ba'a had'u kamar hka ba sai a waya, sai da yamma sadeeq yaxo daukan ta, amman sai da ta jira Abban ta ya dawo suka gaisa sannan suka tafi, gaf da Kiran sallahr mangarib suka k'arasa gidan Yah Omar a lokacin shima Yah Omar dawowar shi kenan daga office nan suka wuce masjid yayin da mufidah ta shiga da sallama cikin palourn, wani ihu nabila ta saki tare da yin tsalle ta rungume mufidah tana cewa " wayyo my friend kece a yanxu?" "Ni ce kuwa my sister, kina ta tsalle sai kin wahalar mana da babyn mu" Hararar wasa nabila tayi mata tare da jan ta xuwa bedroom don yin sallah, bayan sun idar ne suka bud'e shafin hira sosai sai da yah Omar yaji shiru basu fito ba ya biyo bayan su nan yaga sai xuba suke, hararar mufidah yayi tare da cewa "kin xo kina ta xuba mata surutu ko tar6ar da aka sabar min ba'a yi ba, gashi da yunwa na dawo" "Kaiiiiiiii Yah Omar kasan dai nabila ta fi ni surutu ko?" Ta fad'a cikin shagwa6a "Bana son wani surutun kuma ki tashi ki tafi wajen mijin ki, sweetheart ke kuma mu tafi kitchen a bani a abinci" Ya k'arasa fad'i yana kama hannun nabila suka fita daga bedroom d'in, mufidah tashi tayi ta bisu ita ma tana dariya ta wuce cikin Palo wajen sadeeq. Basu bar gidan Yah Omar ba sai wajen 9 na dare, lokacin da suka k'arasa gida bayan sun shiga wajen mumy ne sannan suka wuce part d'in su, wanka kawai suka yi tare da neman makwanci don agajiye suke kuma sun riga da sun ci dinner gidan Yah Omar don hka baccin su suka yi hankalin su a kwance............ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM _kuna ina k'awaye kirki wannan shafin naku ne Queen mermue dear and Ameerah (Amnoor), wannan shafin sadaukar wa ne gare ku, hak'ik'a ina matuk'ar alfahari da ku abokanan kirki, Allah ya bar mu tare ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke_🤝❤ *PAGE 24* *AFTER ONE YEAR* Acikin wannan shekarar abubuwa sun faru da yawa, ta 6angaren su mufidah kuwa suna xaune lafia da mijin ta da sadeeq tare da iyayen sadeeq, kuma a hankali xuciyar ta ta fara sabawa da sadeeq duk da ba wani son shi take ba amman sun yi mugun shak'uwa da junan su sosai, komai na kyauta ta wa tana yi mishi bata tauye mid hakkin shi dai dai gwargwado tana kyautata mishi. Shima sadeeq d'in duk wani hakkin ta da ya rataya a kan shi yana k'okarin sauke mata, sai dai har xuwa yanxu mufidah bata samu ciki ba sadeeq ya dage da addu'a sosai na Allah ya bawa mufidah ciki ta haihu don yana son yaga ta haihu sun samu baby kamar yanda nabilan Yah Omar ta haihu an samu baby girl taci sunan umma suna kiran ta da muhibbat. Kamar yau suna kan dinning table suna yin dinner d'in dare, mufidah ta kai spoon bakin ta na abincin sai taji xuciyar ta na tashi amman sai ta danne hkan ta cigaba da ci abin ta don wata irin yunwa take ji sosai. K'ara kai wani spoon d'in tayi bakin ta ae kuwa gaba d'aya sai taji xuciyar ta ta hautsine da sauri ta yarda spoon d'in tare da toshe bakin ta da hannu ta tashi da gudu ta shige bedroom d'in ta cikin toilet ta shiga ta fara yin amai sosai tana dafe da cikin ta da hannun ta. Tana tashi da gudu sadeeq shi ma ya ajiye spoon d'in hannun shi ya bi ta da sauri, tarar da ita yayi tana ta amai, cikin sauri ya rik'e ta yana yi mata sannu, har sai da ta amayar da abin da taci gaba d'aya ta gama gala6aita, rik'o ta yayi tare da wanke mata bakin ta ya rik'e ta har xuwa cikin bedroom ya kwantar da ita sannan ya koma cikin toilet d'in ya gyara wajen tukunna ya fito. Wajen mufidah ya k'arasa wadda ta lullu6a da bargo saboda sanyin da ta fara ji, d'an janye bargon yayi tare da ta6a wuyan ta yaji d'umi sosai alamar xaxxa6i ne a jikin ta, cikin sanyin muryar shi mai had'e da damuwa yace "My wife daman baki da lafia ne?" Cikin sanyin murya irin ta mara lafia ta bud'e baki tace " nima ban sani ba, nasan dai tun safe ina jin tashin xuciya ne gashi ina son nayi amai amman sai na kasa sai yanxu kuma naji aman ya xo" "Sannu my wife gashikuma naji jikin naki akwai xaxxa6i, ya kamata na kirawo muh'd ya duba min ke?" Cikin sauri ta fara girgixa kai tare da rik'o hannun shi ta marairaice kafin tace "ni gaskia ba sai ka kirawo shi ba xan samu sauk'i ka ji don Allah please" "Toh shikenan" "Yanxu kaje ka k'arasa cin abincin ni bacci nake ji" Mufidah ta k'arasa fad'i tana gyara bargon jikin ta, d'an xaro ido yayi kad'an tare da cewa "Haba my wife tun yanxu xaki baccin sai fa yanxu 9 tayi" D'an yatsina fuska tayi tare da cewa " Allah da gaske nake bacci nake ji" "Okay " Yana nan xaune har bacci ya d'auke ta tukunna ya fito palour ya k'arasa cin abincin shi ya tattara komai ya kai kitchen tare da yi mata wanke wanken kayan da suka yi amfani dasu, don sadeeq shu ba ruwan shi idan yana gida xagewa yake yana tayata aikin gida sosai. Sai da ya gama tukunna ya nufi bedroom d'in ta ya duba yaga har yanxu bacci take, wanka ya shiga yayi sannan ya shirya cikin sleeping dress ya kwanta kusa da ita addu'a yayi musu sannan yayi switch off d'in hasken d'akin babu dad'e wa bacci ya d'auke. Cikin dare xaxxa6i mai xafin gaske ya rufe mufidah, gaba d'aya sadeeq ya rikice ganin yanda take shan wahala, har xuwa gari ya waye basu wani runtsa ba saboda jikin mufidah yak'i dad'i. Garin na waye wa sadeeq ya kirawo Dr muh'd kan yaxo yanxu mufidah ba lafia, babu 6ata lokaci muh'd ya k'araso gidan nan ya dudduba ta tare da yi mata test d'in fitsari anan ya hango tana dauke da ciki a jikin ta, bayan yayi mata allurar bacci ne tare da sanya mata drip bcos jikin nata ba k'wari gashi babu abinci a cikin ta, cikin en mintuna bacci ya d'auke ta sannan suka fito palour. " me yake damun ta ne muh'd?" Sadeeq ya tambaye shi yana kallon shi, d'an murmishi muh'd Yayi tare da cewa "Uhm babban yaya congratulation laulayin ciki ne yake damun ta" Kallon ban yarda da abin da kace ba sadeeq yayi mishi kafin kuma yace "Muh'd kana fad'a min ne fa mufidah na da ciki da gaske kake" Cikin murmishi muh'd yace "Allah da gaske nake babban yaya, na tsawon 3 month's" Rungume muh'd yayi cikin tsananin farinciki har sai da hawaye suka xubo a idanun shi yana godia ga Allah da ya nuna mishi wannan lokacin da ran shi, bayan Dr muh'd ya tafi ne sadeeq ya shige bedroom ya xauna gaban mufidah tare da xuba tagumi ya kallon ta xuciyar shi fal farinciki da wannan kyauta da Allah ya bashi. Dr muh'd kuwa part d'in mumy ya shige cikin farinciki ya tsegunta mata mufidah na da ciki, sosai mumy tayi farinciki har muh'd abin ya bashi mamaki ganin yanda take murna, daga hka yayi mata sallama ya tafi, ita ma mumyn k'in xama tayi sai ta wuce part d'in su sadeeq don ganin jikin mufidah. Lokacin da mufidah ta farka daga bacci taji abin da yake damun ta sosai tayi farinciki da hka don tana son yara sosai, nan fah aka dunga tarairayar ta fiye da baya kulawa sosai sadeeq yake bata da mumy har da daddy ban da umman ta da abban ta ga Yah Omar ma, cikin kwanciyar hankali ta cigaba da renon cikin ta amman tana d'an ta6a laulayi. ******** Kwance yake a gefen swimming pool yana sanye cikin wani 3quater d'in wando white jikin shi babu riga yayi matashin kai da hannayen shi yana kallon sararin samaniya. Kallo d'aya xaka yi mishi ka tabbatar guy d'in ya had'u ta ko'ina, ya k'ara wani irin kyau da haske alamar hutu a tattare dashi sai dai er ramar da yayi. Musaddiq kenan wanda bai dad'e da tashi daga gadon asibiti da yayi ba, jinya sosai yayi ta wurin 2 weeks a hospital but su daddy basu da labari sam, tun lokacin da yaxo k'asar bashi da cikakkiyar lafia saboda ya kasa cire mufidah daga cikin xuciyar shi har xuwa yanxu, sosai abin yake damun shi don baya so yana sa tunanin ta a xuciyar shi tun da ta xama matar wani but hkan ya gagara a tattare dashi. Wannan rashin lafiyar ne da yayi bayan ya samu sauk'i Yayi alkawarin cire son mufidah daga cikin xuciyar shi ta ko wani hali. Yana nan kwance tsawon mintuna 50 tukunna ya tashi jikin shi a sanyaye ya shige cikin gidan da yake xaune wanda ya kunshi 2 bedroom's da palour babba d'aya, d'akin shi ya shige kai tsaye, toilet ya shiga tare da sakarwa kan shi shower tsawon mintuna 15 tukunna ya fito ya d'aura towel, dressing mirror ya nufa ya gyara jikin shi tare da shirya wa cikin t-shirt ash colour da black jeans belt d'in ma bak'a ce hka takalmin kafar shi, bayan ya fesa perfumes ne ya dauki car key da phone's d'in shi ya fita daga gidan gaba d'aya. Don tun bayan xuwan shi Australia bai fita sai da dalili, kusan ko da yaushe yana kunshe cikin gida kamar wata mace, yana fama da tunani, a yanxu kuwa ya dau alkawarin cire tunani da damuwa a xuciyar shi, xai na fita don rage wa kan shi damuwa. Sosai yayi yawo a garin Australia k'asa ce mai kyan gaske, sai dare ya dawo gidan shi da yake ya ci abinci a restaurant yasa shi yin wanka ya shirya cikin pyjamas ya kwanta ko da tunani yaga xai dame shi sai kawai ya kunna laptop d'in shi ya hau amfani da ita, bai ajiye ta ba sai da yaji bacci yaci k'arfin idon shi sannan ya ajiye ya kwanta ya fara bacci. A yanxu hka ya gama course d'in da xai yi har ya fara aiki a hospital d'in su,amman su daddy basu san da hka ba, don baya son su matsa mishi ya dawo gida ba xai jure ganin mufida ba......... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM *PAGE 26* Cikin en mintuna Dr muh'd ya k'araso saboda tsabar sauri a wajen get yayi parking ya shigo gidan don ba xai iya jiran mai gadi ya bud'e get ba, kai tsaye part d'in sadeeq ya nufa cikin sauri. Da sallama ya shiga but ba'a amsa mishi ba sai da ya kirawo wayar sadeeq ya fad'a wa mufidah ya k'araso yana palour, cikin sauri ta fito ta tarar dashi a tsaye jagora tayi mishi har cikin bedroom d'in. Ba 6ata lokaci Dr muh'd ya fara duba sadeeq cikin kware wa, bayan mintunan da basu gaxa talatin ba ya gama duba sadeeq, drip ya sanya mishi tare da yi mishi allurar bacci babu dad'e wa bacci ya d'auke shi sai lokacin hankalin mufidah ya fara kwanciya ganin ya samu bacci. Palour suka dawo mufidah xama tayi tare da cewa "doctor me yake damun mijina?" Shima Dr muh'd xama yayi tare da kallon ta yace " a gaskia yanxu baxan iya takaice miki abin da yake damun shi ba dole sai mun je hospital akwai scanning d'in da xamu yi" Nan hankalin mufidah ya sake tashi sosai ta fara kuka, rarrashin ta ya fara yi sai da yaga ta d'an samu nutsuwa tukunna yace "Idan ya farka xuwa anjima ku same ni a hospital, su mumy sun sani" Girgixa kai mufidah tayi kafin tace "ya fad'a min kada na sanar dasu saboda xasu shiga damuwa" D'an shiru yayi fuskar shi d'auke damuwa kafin kuma yace " okay yanxu ya xa'a yi kenan, don gaskia a yau ina son akai shi hospital" "Xan kawo shi Doctor da kaina idan ya tashi" "Yawwa kin kyauta" Daga hka suka yi sallama ya tafi, mufidah ta xube kan kujera tare da xabga tagumi tana tunani, ta d'an jima da hka kafin taji cikin ta yana murd'a wa atake ta fahimta yunwa take ji. Kitchen ta shiga ta had'a tea a cup ta sha sannan ta dawo d'akin har yanxu sadeeq bacci yake kallo d'aya xaka yi mishi kasan ba k'aramin wahala ya sha ba duk ya dad'a rame wa, xama tayi kusa dashi ta rik'e mishi hannun shi tana murxawa a hankali. Sai after la'asar sadeeq ya farka da mufidah ya fara had'a ido murmishi suka sakarwa junan shi cikin jin dad'i mufidah tace "Sannu sadeeq ya kake jin jiki" Murmishin yak'e ya saki don shi kadai yasan abin da yake ji a jikin shi, hannun ta ya rik'o tare da cewa "My wife kwantar da hankalin ki, jiki na da sauk'i ya lafiyar baby na dafatan kin bashi kulawa?" Da kai tayi mishi alamar ehhh, taimaka mishi tayi yayi wanka ko abinci ya kasa ci sai coffee yasha tukunna suka tafi hospital, mufidah ce take driving sadeeq na gefen ta hannun shi d'aya dafe da cikin shi ya lumshe ido, da hka har suka k'arasa asibitin bayan mufidah tayi parking ne ta fito tare da bud'e wa sadeeq kofar motar ita ta taimaka shi ya fito tukunna ta rufe motar. Tana rik'e dashi suka k'arasa cikin asibitin kai tsaye office d'in muh'd suka nufa sai da mufidah tayi knocking, muh'd dake xaune kan kujera yace "Yes come in" Nan mufidah ta tura kofa suka shigo ganin sune yasa muh'd mik'e wa da sauri ya taimaka wa sadeeq ya xauna tukunna ita ma ta xauna "Babban yaya ya jikin na ka?" Cikin yak'e sadeeq yace " jiki da sauk'i muh'd" Nan babu 6ata lokaci Dr muh'd da wani likitan daban suka shigar da sadeeq room d'in scanning mufidah tana xaune a gefen shi da yake kwance hannun ta cikin nashi suna kallon komai da ake ta jikin nau'orar computer d'in. Sun d'auke tsawon mintuna arba'in xuwa hamsin suna scanning d'in, bayan sun gama suka koma 6angaren yin test d'in urine test da blood test har xuwa lokacin da aka kammala had'a result gaba d'aya. Lokacin da Dr muh'd ya duba dukka result d'in sai da wani gumi ya yanko mishi sakamakon ganin abin da yake damun sadeeq, tuni idanun shi sun yi ja kamar xai yi kuka hankalin shi yayi matuk'ar tashi yana tunanin ta yanda xai sanar da su wannan hargitsatsan labarin. Sam ya kasa d'aga kanshi ya kalli sadeeq da mufidah, ganin yanda ya koma yasa sadeeq yin murmishi yace "Muh'd lafia kuwa, me ke faruwa tell me please?" Cikin wani irin yanayi ya xuba wa sadeeq ido, gaba d'aya mufidah ta gama tsorata jikin ta har rawa yake, shi kuwa sadeeq cikin shi ne ya cigaba da yi mishi ciwo sosai amman sai ya daure yace "Nasan ciwo na ne yayi worst da yawa ko?" Da sauri muh'd ya d'ago kanshi ya kalle shi cikin mamakin abin da yace,lumshe ido yayi tare da cije le6en shi saboda yanda cikin shi yake mishi ciwo sai da ya d'an lafa sannan ya kamo hannun mufidah ya rik'e shi gam tare da cewa "Kiyi hak'uri my wife na rufe miki bansanar dake wani abu ba, wanda bana son tashin hankalin ki shi yasa" Kallon Dr muh'd yayi tare da jiyo wa ya cigaba da kallon mufidah wadda gaba d'aya hankalin ta Yayi masifar tashi jin abin da sadeeq yake fad'a. "Ba wani abu na rufe miki ba my wife ina da ciwon hanta tun kafin na aure ki, na kasance ina yawan fama da ciwon ciki sosai ganin hka sai na yanke shawarar xuwa ganin likita a k'asar london anan yake fad'a min ciwon hanta ne ya kama ni har sai da suka yi min aiki a can" Gaba d'aya kallon shi suke da idanun su da ya firfito na tsabar kidima, duniyar tunani mufidah ta fad'a don akwai wani lokaci da tana xaune gefen bed ya fito daga wanka d'aure da towel tana cikin shirya shi taga wani siririn yanka a gefen sam bai yi kama da operation ba a gefen cikin shi har tana tambayar shi mene wannan sai yake fad'a mata yana k'arami ne ya ta6a jin ciwo awajen. Maganar da sadeeq ya cigaba da yi ita ta dawo daga duniyar tunanin da ta fad'a ya cigaba da cewa " ban fad'a wa su mumy da daddy ba saboda kada su d'aga hankalin su su shiga damuwa balle uwa uba d'an uwana rabin jiki musaddiq bana jure ganin shi cikin damuwa shi yasa na 6oye musu, sauran kad'an musaddiq ya gane don ya kamani da magungunan sai na wayance da na aboki nane dak'yar ya yarda da hkan don har yaso dubani na nuna mishi 6acin raina shine ya hak'ura, bayan na warke na cigaba da xuwa ganin likita ina kar6ar magani daga k'arshe da naga na samu sauk'i sai na watsar da xuwa ganin likitan kwata kwata, sai k'wanan na fara jin ciwon ya dawo min amman na kasa tafia ganin doctor saboda bana so nayi nesa da mufidah" K'ara rik'o hannun mufidah yayi cikin sanyin murya ya cigaba da cewa " kiyi hak'uri my wife tashin hankalin kune bana so shi yasa ban fad'a muku ba, ki yafe min don Allah" Wani kukan tausayin sadeeq ya kamata ta fad'a jikin shi tare da sakin kuka mai ban tausayi, hak'uri da rarrashin ta sadeeq kawai yake. Dr muh'd kuwa hawaye ne kawai suke xuba a idanun shi, yanxu ta ina xai fara fad'a wa su mumy labarin nan dukka 'ya'yasu biyu Allah ya basu a duniya kowannen su Allah ya jarabce shi da babban ciwo, musaddiq ciwon xuciya sadeeq kuma ciwon hanta ciwon da ya gama cin k'arfin shi sosai ta ina xai fara, hawaye kawai yake yi yana kallon sadeeq kanshi na wani irin juyawa. Dak'yar sadeeq ya rarrashi mufidah tayi shiru amman still tana jikin shi sai faman ajiyar xuciya take sauke wa, kallon muh'd d'in sadeeq yayi ganin ya xuba mishi ido yana kallon shi ga hawayen da yake yasa shi sakin murmishi tare da cewa "Haba muh'd ae ba kuka ya kamata kayi ba, sanar da ni naje last stage koh?" Wasu hawaye masu d'umi suka fara xuba cigaba da xuba a idanun muh'd, shima sadeeq d'in dauriya kawai yake ga ciwo yana jin shi sosai ga tashin hankalin shi mufidan shi cikin damuwa. Sun dad'e a hka kafin muh'd ya bud'e bakin shi cikin rawar murya yace "I'm sorry to say babban yaya gaskia ciwon ka ya kai matakin k'arsh......" Kasa k'arasa fad'a yayi saboda kukan da ya kubce mishi, mufidah ma sai ta fashe da kuka ganin likita guda yana gurxar kuka ya had'a kai da table d'in dake gaban shi. Dafa mishi kafad'a sadeeq yayi tare da cewa " be a man haba muh'd kamar ba likita ba, ni daman jiki yana bani baxan yi tsawon rai ba don ni kadai nasan me nake ji ina rok'on Allah kafin na mutu naga d'an da mufidah xata haifa min wannan shi kad'ai ne buri na" Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM _this page dedicated to my lvly friend's nafisat anka dear, sardy bash dear, billy ladan dear, ina matuk'ar alfahari da ku sister's, Allah ya k'ara muku lafia, Allah ya bar xumunci ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke_🤝❤ *PAGE 25* Haka rayuwa ta cigaba da tafia suna renon cikin su cikin kwanciyar hankali, wanda watannin shi bakwai da en kwanaki ya girma sosai, sadeeq dasu mumy suna matuk'ar ji da wannan babyn da bai xo duniya ba tukunna,ko da yaushe cikin yiwa mufidah addu'ar sauka lafia suke mata. Duk wannan abin da ake ciki ba wanda ya fad'a wa musaddiq, sam baisan mufidah tans da ciki ba, sadeeq bai fad'a mishi ba hka ma mumy saboda tana tsoron halin da d'anta xai shiga idan yaji labari shi yasa ta ja bakin ta tayi shiru duk kuwa da wayar da suke yi kusan ko dayaushe. Yau garin ya kasance cikin wani yanayi mai dad'in gaske sakamakon ruwan da aka dunga yi tun after isha'e, garin ya d'auki sanyi sosai irin wannan yanayin ne yawancin xaka samu mutane sun yi bacci da wuri, hka ta faru dasu mufidah da sadeeq su ma tun wurin 10 na dare suka kwanta bacci sun k'udundune cikin blanket saboda sanyin garin. Can wurin 2 na dare sadeeq ya tashi tare da xama saman bed yana kallon mufidah wadda take baccin ta cikin kwanciyar hankali, ido ya xuba mata yana kallon ta sam ya rasa abin da yake damun shi a cikin wad'annan kwanaki, jikin shi ya bashi akwai wani abu da xai faru but bai san kome ne ba. Kallon mufidah kawai yake tare da sanya hannun shi kan cikin ta yana shafa babyn shi, lokaci d'aya kuma wasu hawaye masu xafin gaske suka fara xuba daga idanun shi, wanda ya rasa hawayen mene, ya dad'e a hka sosai duk idanun shi sun yi ja kan shi ya d'auki wani irin ciwo, tashi yayi dak'yar ya shige bathroom alwala ya d'aura tare da fitowa praying mat ya shimfid'a ya fara nafila after ya gama sai ya fara yin addu'o'i na neman gafarar ubangiji akan ya yafe mishi xunuban shi tare da addu'ar Allah ya sauki mufidah lafia. Bai tashi daga nan ba sai da yaji kiran sallahr asuba, sai da yayi raka'atul fijir sannan ya tashi mufidah ya tafi masallaci jikin shi gaba d'aya ba k'arfi haka yake ji. Tun da ya dawo daga masallaci wani bacci ne ya d'auke shi mai dad'i, har mufidah ta kammala had'a breakfast ta gyara ko'ina tayi wanka amman bai tashi ba, xama tayi a palour tare da fad'a wa tunani tana mai mamakin yanda sadeeq ya koma. Gaba d'aya ya canja mata,na farko ya sake mata wani irin kyau da kwarjini na biyu kuma gaba d'aya yayi sanyi sosai duk da sadeeq daman akwai shi da sanyi but na yanxu yafi na da, tana yawan farka wa a bacci ta ganshi yana kallon ta ko yana shafa mata ciki, magana yanxu bata dame shi ba abinci ma baya iya ci sosai. Abin yana d'aure mata kai tare da damunta, tayi mishi tambaya ko wani abin yana damun shi sai yace ba komai, k'arshe idan ta dame shi da tambaya sai ya fara neman gafarar ta tare da sako xancen mutuwa nan sai ta fara kuka sai kuma ya hau rarrashin ta, wani lokacin kuma sai ya xuba mata ido yana kallon ta duk inda tayi akan idanun shi duk sai tabi ta tsargu. K'arar wayar ta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta fad'a, hannu tasa ta goge hawayen da suka xubo mata sannan ta dauki wayar umman tace bayan sun gaisa tare da yin hira ta tsawon mintuna 15 ne ta ajiye wayar tare da kallon agogo taga har 10:30 tayi sadeeq bai fito ba gashi kuma yau akwai aiki, tashi tayi tare da nufar bedroom d'in shi. Tura kofar tayi tare da shigo wa lokaci d'aya mufidah ta xaro ido tare da furta "sadeeq!" Da k'arfi tukunna ta k'arasa wajen da yake kwance akan bed yana murkususu kamar macen da take nakuda, cikin sauri ta hau kan bed din tare da janyo shi jikin ta tana jijjiga shi cikin kuka tana cewa "Sadeeq me yake damun ka, tashi ka fad'a min please?" Ya bud'e baki xai yi magana amman ya kasa, sai wasu hawaye masu xafi da suke xubo mishi, cikin gigice wa da firgita mufidah ta yunk'ura xata tashi don taje ta fad'a wa su mumy amman sai ya rik'e ta k'am yana yi mata wani irin kallo wanda ya tsurar da mufidah ta kusan fara nakudar tashin hankali saboda yanda taji d'an cikin ta ya wani irin juyawa lokaci d'aya marar ta ta d'auki ciwo. Cikin wata murya taji sadeeq ya bud'e baki dak'yar yace " my wife kada ki sanar dasu mumy hankalin su xai tashi, ciki na ne yake ciwo ki kira min muh'd ya duba ni" Cikin sauri jiki na rawa mufidah ta d'auki wayar shi ta lalibo number d'in muh'd sai da ta kirawo shi sau biyu bai d'auka ba sai ana ukun ya d'auka yana cewa "Sorry babban yaya ina room's d'in patients ina duba....... " Kafin ya k'arasa fad'i yaji muryar mufidah cikin kuka tana cewa " muh'd don Allah kayi sauri ka xo sadeeq bashi da lafia" Cikin tashin hankali yace " me ya same shi?" "Ni dai kayi sauri kaxo please ina tsoro" Ta k'arasa fad'i tana shashshak'ar kuka, da sauri yace " kiyi hak'uri mufidah gani nan xuwa yanxu" Yana gama fad'in hka ya katse wayar hankalin shi a tashe ya shiga mota ya taho, yayin da mufidah kuma ta cigaba da kuka sosae ganin yanda sadeeq yake shan wahala, lokaci d'aya ya fara jan wani irin numfashi da ya k'ara rud'a mufidah.............. Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ E.W.F *PAGE 27* Da k'arfi mufidah ta tashi tare da fad'in "stop it sadeeq" Kafin kuma ta rushe da wani irin kuka ta xube k'asa tare da rik'e kafafun shi tana cewa "Baxa ka mutu ba sadeeq xamu rayu tare da kai har abadan, xan haifa maka yaran da kake so da yawa ka cika wa su mumy burin su na ganin jikoko da yawa xan mutu sadeeq idan ka mutu ina son ka baxan iya rayuwa ba kai ba" Kamo ta yayi tare da xaunar da ita shima idanun shi duk sun ciko da hawaye cikin muryar rarrashi sadeeq yace "Kiyi hak'uri mufidah mutuwa tana kan kowa idan lokacin ta yayi ni nasan ciwon nan bana tashi ba n....." Kafin ya k'arasa fad'i mufidah ta damk'e bakin shi cikin kuka tana girgixa kai tace "kayi shiru sadeeq don Allah na rok'e ka wadannan maganganun suna rikita ni hankali na yana tashi sosai" Cikin Murmishin yak'e yace "okay shikenan na bari my wife" Kallon shi take ko kifta idanun ta ba tayi tana ganin idan ta kifta idon ta kafin ta bud'e sadeeq ya mutu, don sai yanxu taji wani masifaffan son sadeeq yana ratsa jijiya da xuciyar jikin ta batasan tana mishi wannan son ba sai hka, shi kuwa Dr muh'd kasa k'arasa magana yayi sai ajiyar xuciyar da yake sauke wa akai akai. Suna cikin hka ciwon ciki ya dad'a tasar wa sadeeq irin yanda yake yi kamar numfashin shi xai d'auke tuni suka rud'e kuka sosai mufidah take tana rik'e dashi. Da gudu muh'd ya mik'e yaje ya kirawo wasu likitoci biyu suka d'auki sadeeq suka shigar dashi wani daki da gudu mufidah taxo xata shiga but d'ayan likitan ya rufe kofa wata nurse ce ta janye mufidah xuwa cikin office d'in Dr muh'd tana rarrashin ta don muh'd shi kasa ce mata komai yayi. Dak'yar ta nutsu ta daina kukan ta kirawo mumy tana fad'a mata cikin kuka, a matuk'ar firgice mumy ta taho asibitin bayan ta sanar da daddy shi ma. Kusan tare suka shigo asibitin da mumy da daddy office d'in Dr muh'd suka tarar da mufidah tana shar6ar kuka wiwi gaba d'aya sai suka dad'a tsurewa ganin yanda mufidah ta koma lokaci d'aya gaba d'aya ta fita daga hayyacin ta, janyo ta jikin ta mumy tayi tana rarrashin ta duk da ita ma daurewa take, daddy kuwa tagumi ya xabga shi kad'ai yasan yanda yake ji a cikin xuciyar shi. Wajen awa biyu suka yi kan sadeeq tukunna ya fara dawowa cikin hayyacin shi yana numfashi da taimako oxygen tube, special room suka kai shi tare da sanya mishi drip bacci yake saboda allurar da suka yi mishi kallo d'aya xaka yi mishi ka tausaya mishi ya yi wani irin rame wa sosai. Dak'yar muh'd ya iya yiwa su mumy bayanin halin da sadeeq yake ciki don mufida ta kasa magana, ba k'aramin rud'e wa da gigice wa suka yi ba wad'annan bayin Allah, jagwab mumy ta xube kan kujera tana kuka sosai daddy kuwa idanun shi ne suka yi ja sosai daurewa kawai yake yi saboda shine namiji mai rarrashin mumy da mufidah don kuwa Dr muh'd gudu wa yayi daga office d'in don baxai iya cigaba da kallon kayan tausayi ba don xuciyar shi xata iya buguwa. Har dare yayi sadeeq bai farka ba daddy yace mumy da mufidah su koma gida shi xai k'wana dashi da Dr muh'd, dak'yar ya shawo Kansu suka yarda, koda suka je gidan ko takan abinci basu nema ba, k'arshe mufidah a bedroom d'in mumy ta k'wana ko runtsa wa basu yi ba sallah kawai suke suna nemar wa sadeeq samun lafia, har gari ya waye babu wanda ya runtsa a cikin su, K'arfe bakwai suka yi gaggawar yin wanka simple gown suka sa kamar had'in baki mufidah da mumy suka sanya hijab ko mai basu shafa ba saboda tashin hankali. Abincin da en aiki suka yi na breakfast suka d'auka tare da tafia hospital d'in, sai ganin su daddy Yayi kawai sun shigo room, koma wa gida yayi daddy don ya samu yayi wanka shima. Kamar yanda suka barshi hka suka dawo suka ganshi ko motsi baya yi abin da xai ankarar da mutum yana da rai bugawar xuciyar shi da numfashin da yake yi ta oxygen tube. Dak'yar mumy ta lalla6a mufida ta d'an sha tea gaba d'aya bata jin dad'in bakin ta da jikin ta, bata ta6a riskar kanta a irin wannan tashin hankalin ba. Tuni ta kirawo yah Omar ta sanar mishi abin da yake faruwa, umman ta da abban ta duk ta fad'a musu, hankalin su a tashe suka taho asibitin su ma. Yini guda suka yi a asibitin umman mufidah ta taho musu da abinci na rana, har xuwa dare suka tafi sadeeq bai tashi ba, ae kuwa mufidah ta tubure baxa ta tafi anan xata k'wana dole aka kyale ta mumy da daddy suka tafi gida gaba d'aya jikin su a sanyaye....... Hka mufidah ta xauna akan kujera tana kallon sadeeq hannun yana rik'e da hannun shi wanda ba'a sa mishi drip ba, addu'a kawai take a cikin xuciyar Allah ya tashi kafad'ar mijin ta. Tsakanin jiya da yau duk mufidah ta fita a hayyacin ta, gaba d'aya ta xama wata iri ta rame saboda rashin cin abinci da samun bacci babu kwanciyar hankali a tare da ita, ga tsohon ciki yayi mata nauyi ajikin ta komai dauriya take saboda ita kad'ai tasan me take ji. Tana nan xaune ta jingina da jikin kujerar wani bacci ne ya d'auke ta mai nauyi saboda rashin samun bacci da bata yi ba jiya......... _kuyi hak'uri da wannan page d'in ban yi editing ba_ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM _this page dedicated to_ *my cwt sadeey S Adam* _( saNaz), ina matuk'ar alfahari da ke a koda yaushe, baki na baxai iya fad'in irin tarin karamcin ki a waje na ba nasan ke mai kaunata ce da gaskia, nima ki sani ina k'aunar ki wanda baki ba xai iya furta wa, ina rok'on Allah ya baki miji na gari wanda xai rik'e mana ke amana, ina miki fatan alkhairi a duk ina kike masoyiya ta ta hak'ik'a_😍 *PAGE 28* Sai gabannin asuba sadeeq ya farka lokacin da ya bud'e idanun shi akan mufidah ya sauke su, bacci take amman da ganin baccin kasan bana jin dad'i ba ne. Hannun yake k'okarin cire wa daga na mufidah don ya cire oxygen tube d'in da yake hancin, motsin da yake yi ne da hannun shi ya farkar da mufidah daga baccin da take da sauri ta matso kusa dashi tare da cewa " Sadeeq sannu ka farka, ya kake jin jikin naka, bari na kirawo muh'd?" Gaba d'aya ta rud'e tama rasa me xata ce mishi, shi kuwa kallon ta yake wasu hawayen tausayin mufidah ne yake xubo mishi, jikin ta na rawa ta d'auki waya har wayar tana sullu6e wa daga hannun ta saboda yanda jikin ta yake rawa. Dr muh'd ta kirawo cikin rawar murya take maganar tana cewa " mu....muh'd ya.....ya farka sa....sadeeq yanxu" Bai ce komai ba ya kashe wayar tare da fitowa daga office d'in da gudu ya nufi room d'in da yake yana cikin hospital d'in. Da sauri ya tura kofar room d'in nan ya k'araso kusa da gadon da sadeeq yake kwance " Alhmdullilah babban yaya sannu" Cewar sadeeq kenan nan ya cire mishi drip da oxygen tube d'in tare da k'ara duba shi, tukunna ya jiyo ya kalli mufidah yace " yanxu ki taimaka mishi yayi wanka ya d'an ci wani abin" Gid'a kai mufidah tayi tare da taimaka wa sadeeq ya tashi xaune, shi kuwa muh'd fita yayi daga room d'in, sai da ta shiga toilet ta had'a mishi ruwa tukunna ta fito ta rik'e shi suka shiga toilet d'in, wanka yayi tare da yin brush da alwala suka fito daga toilet d'in. Nan ta shirya shi cikin kaya marasa nauyi sannan a nutse ya tashi ya fara rama sallolin da ake bin shi, bayan ya idar ne ya xauna kan abin sallahr ya jingina bayan shi da gadon idanun shi a lumshe, tea mufidah ta had'a mishi cikin cup ta bashi dak'yar yasha rabin cup d'in yace mata ya K'oshi nan ta fara lalla6a shi da yasha amman k'arshe sai ya janyo ta jikin shi yana bata ragowar tea d'in yana cewa " kema naga alama bakya son bawa baby na abinci xamu 6ata fah nayi miki hukunci da k'in yi miki magana na tsawon second 3" Dariya ya bata saboda yanda yayi maganar amman sai ta murmursa kawai, shima murmishin yayi daman abin da yake son gani kenan akan fuskar ta. " ayi min afuwa idan kayi min wannan hukuncin ae kuka xan tayi maka har sai ka hak'ura ka janye" Hannun shi yasa yaja tsinin hancin ta tare da cewa " na fad'a ne kawai my wife baxan iya fushi dake ba ina son ki da yawa amman nasan xan tafi na barki" Hannun ta ya kamo tare da cigaba da cewa " ki yafe min mufidah idan na 6ata miki rai a xaman mu kuma ga amanar baby na nan ki kula dashi ina son ki bashi irin tarbiyyar da su umma suka baki nasan baxan yi nadamar kasancewar shi a hannun ki ba, mace ko namiji duk wanda Allah ya bamu don ina godia ga Allah da ya bani ke matsayin mata ta, mufidah ina son kiyi min alkawari idan na mutu xaki au........" Bai kai ga k'arasa fad'in abin da yake so ya fad'a ba mufidah tasa hannun ta ta toshe mishi bakin shi tana kuka sosai cikin muryar kuka tana cewa "Bana son wad'annan maganganun sadeeq suna d'aga min hankali, ae cuta ba mutuwa bace ni nasan xaka samu sauk'i insha Allah mu rayu tare da ke" Kukan da take yi ne ya tashin hankalin sadeeq sosai tuni ya fara rarrashin ta har ya samu tayi shiru dak'yar, hannun shi yasa saman cikin ta yana ta6awa yana mai addu'a Allah ya sa kafin ya mutu yaga babyn shi. Xuba mishi ido mufidah tayi tana kallon shi ko kiftawa bata yi shima hka ya xuba mata nashi idanun suna kallon junan su sosai a cikin sanyin murya mufidah ta bud'e bakin ta tace " I luv u sadeeq with all my heart hak'ik'a halayen ka suna birge ni Allah yasa d'an da xamu haifa ya debo halin ka" Murmursa wa yayi tare da cewa " luv u too my wife, nasan ma insha Allah d'an da xamu haifa mai nutsuwa ne ina son ki mata ta" Rungume junan su suka yi irin sosai d'in nan kamar wanda xa'a raba su da junan su, sadeeq yana son k'arasa mata maganar shi ta d'axu but yana jin tsoron kada tayi mishi kuka don sam baya k'aunar ganin kukan mufidah......... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: [9/19, 12:28 PM] Aishat A Muh'd ✍🏻: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM _Naga comment's d'in ku fan's kowanne da irin ra'ayin shi da ya bayar kuma naji dad'in hkan sosai Allah ya bani ikon kammala muku shi lafia_ #ana tare❤ *PAGE 29* Suna cikin hka har gari ya k'arasa waye wa, wajen 7 na safe mumy da daddy suka shigo hospital d'in nan dak'yar suka lalla6a shi ya sake cin wani abin, tukunna suka fito daga d'akin Dr muh'd da sauran doctor's biyu suna tare dashi suka shiga room d'in da sadeeq yake, bayan en mintuna kuma suka shige dashi wani room na daban, koma wa room d'in da aka kwantar da sadeeq suka yi dukkanin su xuciyoyin su d'auke da damuwa. Daddy ne ya fara magana da cewa " bana son musaddiq yasan da labarin rashin lafiyar sadeeq shi yasa sam ban fad'a wa en uwana ba saboda bana son xancen yaji kunnen shi" Cikin muryar kuka mumy tace " ya Allah na rok'e ka kasa ba wanda xai fad'a wa musaddiq halin da d'an uwan shi yake ciki ba don nasan idan yaji shikenan xan rasa su gaba d'aya, ya Allah na rok'e ka ka bawa yara na lafia kada ka d'auke min su gaba d'aya" Da sauri daddy ya matso kusa da ita tare da rufe mata baki yana cewa " haba mumy kada kiyi sa6o mana ki kasance mai tawwakkali mana, Allahn da ya d'ora musu larurar yana sane dasu ya jarabce su da hkan don gwada imanin su da namu don hka ina son kiyi hak'uri, kuma insha Allah xan toshe duk wata hanya da xai sa musaddiq yaji labari, ki dunga hak'uri kina tausar mufidah kalli ki ga halin da take ciki yanxu ga tsohon ciki" Sai lokacin ta tuna da mufidah a d'akin kallon inda take tayi, ganin ta tayi tana shar6ar kuka sosai tana dafe da cikin ta wani irin tsoro ya d'arsu a xuciyar mumy kada kuma ta janyo su yi asarar cikin da yake jikin ta da sauri ta tashi ta nufi inda take suka hau rarrashin ta ita da daddy har tayi shiru amman xuciyar ta fal tashin hankali. Suna xaune a hka har aka shigo da sadeeq cikin room d'in aka kwantar dashi kafin sauran doctor's d'in su tafi muh'd kuma ya tsaya yana son yiwa su daddy bayanin abin da ake ciki amman yana fargabar halin da mufidah da mumy xasu shigo dole yaja hannun daddy suka fita daga room din xuwa office d'in shi. Sun kai wajen mintuna talatin acikin office d'in kafin daddy ya fito kallo d'aya xaka yiwa daddy kasan ba k'aramin tashin hankali yake ciki ba idanun shi sun yi ja, hka Dr muh'd da yake bin shi a baya nashi idanun sun yi ja sosai lokaci xuwa lokaci yana goge hawayen fuskar shi, koda suka koma room d'in da aka kwantar da sadeeq basu cewa mumy komai ba. *AFTER ONE WEEK* A ciki wannan satin al'amara sun k'ara tsanani don sadeeq ba lafia sosai yau lafia gobe ko anjima ciwo ya tashi duk yabi yayi mugun rame wa, hka ma mufidah sai katon cikin da yake rinjayar don a yanxu ta shiga 9 month's kuma tak'i yarda ta bi su mumy gida daddy ya xauna da sadeeq kullum tana kusa dashi bata son tayi nisa dashi ko na second d'aya, idan ka kalli mufidah sai ka mugun tausaya mata. Duk wata hanya da musaddiq xai samu labarin rashin lafiyar sadeeq daddy ya toshe a yanxu ma daddy shirye shiryen fitar da sadeeq India yake duk wasu shiri ya gama xuwa gobe da dare jirgin su xai tashi xuwa indian, koda kud'in shi xai k'are xai nema wa sadeeq lafia. Mufidah ce a xaune kan kujera hannun ta d'auke da Qur'an tana karanta wa sadeeq suratul alrahman cikin muryar ta mai dad'in karatu duk kuwa da yanda muryar ta dashe, idan ta kai k'arshen surar sai yace ta dawo hannun ta d'aya yana rik'e da hannun shi. Idanun shi a lumshe suke yana sauraren ta, kad'an kad'an take jin mararar ta tana murd'a wa sai ta d'aure bata kawo komai a ran ta ba don tun da cikin ta ya girma take fama da hkan. Can kamar mintuna goma sai taji ciwon ya k'aru don bayan ta da marar ta suka rik'e lokaci d'aya suna yi mata wani axababben ciwo tuni ta fara had'a uban gumi duk da kuwa sanyin ac d'in da yake room d'in, duk dauriyar da take yi batasan lokacin da ta bar karatun ba ta furta "Wash Allah na" Tana dafe da kugun ta wanda take jin shi kamar ya 6alle ya rabu da gangar jikin ta, da sauri sadeeq ya bud'e idanun shi ganin yanda mufida take had'a gumi fuskar nan ta ta tayi ja sosai tuni ya mik'e da sauri tare da rik'o ta yana cewa "Mufidah lafia kuwa mene yake damun ki?" Duk a rud'e ya tambaye ta hannun shu ta damk'a ta rik'e gam cikin axabar ciwo tace "Sadeeq ka yafe min mutuwa xan yi ka fad'a wa su umma, Abba, daddy da mumy su yafe min don Allah" Gaba d'aya ta kid'ima sadeeq sosai lokaci d'aya kan shi yayi wata irin sarawa amman duk da hka cikin dauriya yace "No mufida bata ki mutu ba nine xan mutu ki tashi please, ina ne yake miki ciwo?" Ina babu bakin magana shi kuwa ya kasa tafiya ya kirawo muh'd gashi ba kowa a wajen, suna cikin hka Dr muh'd ya shigo kallo d'aya yayi wa mufidah yasan labour take don hka yace " babban yaya haihuwa xata yi ae" Yana gama fad'in hka ya fita ya kirawo wasu nurses biyu suka taho akan gadon tura mara lafia suka d'ora ta sadeeq hannun shi yana rik'e da hannun mufidah yana xuba mata sannu duk yabi ya rud'e ya gigice sosai da hka har suka shiga da ita labour room. Har xai bisu ciki Dr muh'd ya rik'o shi tare da cewa " kayi hak'uri babban yaya xata haihu lafia insha Allah" Rik'o shi yayi suka fara tafia sai ga Doctor Aishat nan xata shiga labour room d'in hannun ta dauke da hand gloves. " yawwa Dr Aishat don Allah ki kula da ita sosai" Murmishi tayi wanda ya k'ara mata kyau tace " Doctor kada ka damu xata haihu lafia insha Allah" "thanks Dr Aishat" Fadin muh'd " ka wuce hkan Dr" ta fad'a tana shige wa room din da mufida take. Suna nan tsaye a wurin muh'd yayi yayi da sadeeq yaje ya kwanta amman yak'i, suna cikin hka su mumy, daddy, Abba, umma, nabila da Yah Omar suka shigo asibitin a tare kamar had'in baki, mumy ce ta fara cewa "Lafia muh'd na gan ku anan?" "Uhm mumy mufidah ce xata haihu" Nan fah kowa yaja ya tsaya suna faman yi mata addu'ar samun lafia, gaba d'ayan su hankalin su a matuk'ar tashe. Sun d'auki tsawon mintuna hamsin a wurin sadeeq yana tsaye har lokacin jiri ya fara ji yana daukan shi wurin yana juya mishi kafin kuma a hankali ya fara yin baya xai fad'i, duk basu ankara dashi ba sai Yah Omar da sauri ya nufi wajen shi yana k'arasa wa kuwa ya fad'o jikin shi. Sai lokacin hankalin su mumy ya dawo wajen a matuk'ar rud'e suka yo inda yake gaba d'ayan su, muh'd kuwa doctor's d'in nan da suke duba sadeeq ya kirawo aka d'auke shi suka shiga dashi cikin room. Wayyo Allah abin tausayi wad'annan familyn idan ka gansu a lokacin xaka yi matuk'ar tausaya musu saboda halin dasu ke ciki babu mai nutsuwa a cikin su gaba d'ayan su babu mai kwanciyar hankali, Matan kuwa irin su mumy, umma da nabila kuka suke yi sosai maxan ma basu da kwanciyar hankalin rarrashin su. ******** "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ya fad'a bayan yayi xumbur ya tashi daga mummunan mafarkin da yayi, xama yayi akan gadon tare da kunna hasken d'akin duk da sanyin ac da fankar d'akin amman gumi yake had'a wa, kallo d'aya xaka yi mishi kasan hankalin shi a tashe yake. Musaddiq kenan yau wajen kimanin wajen sati d'aya kenan yana wani irin mugun mafarki akan sadeeq da mufidah amman na yau yasha bambamci dana ko yaushe. Idan yayi wannan mafarkin sai ya kirawo kowa ya ji muryar shi hankalin shi yake kwanciya amman ban da mufidah, duk da sadeeq yana gadon asibiti lokacin yana daurewa ya amsa mishi wayar kamar yanda yake amsa mishi da, but yanxu hankalin shi yayi gida kawai baxai iya jure wa ba yakai k'wana biyu bai ganshi a nigeria ba gaban d'an uwan shi da iyayen shi. Wayar shi ya d'auko ya kira wata number tsayin mintuna goma ya d'auka yana waya da harshen turanci kafin kuma ya ajiye wayar, tashi yayi ya nufi wardrobe ya bud'e ya fara shirya kayan shi cikin trolley sai da ya had'a duk wani abin amfani tukunna ya rufe. Toilet ya shiga yayi alwala ya fito ya fara nafila yana addu'ar Allah yasa mafarkan da yake kada su xama gaskia, sai da yayi sallahr asuba tukunna ya tashi yayi wanka ya shirya cikin wani black jeans da t-shirt black mai dogon hannu hatta belt da takalmi bak'ak'e ne, bayan ya fesa perfumes ne ya janyo trolley dinshi tare da jakar da take rataye a kafad'ar shi ta laptop da sauran muhimman abubuwan shi, fito wa yayi driver d'in shi ya kai shi airport. Ko mintuna 30 bai yi da xuwa ba jirgin su ya tashi xuwa nigeria, gaba d'aya a matuk'ar kaguwa yake ya ganshi cikin iyayen shi da d'an uwan shi. Lokacin da jirgin su yayi landing ya fito ya shak'i iskar k'asar sai yaji ya d'an samu nutsuwa don yana tunanin nan da en mintuna xai ganshi a gida, bai kirawo su ba a waya ya fad'a musu don surprise yake son yayi musu taxi ya d'auka har xuwa gida bayan ya sauka yana k'okarin biyan mai taxi d'in kud'in shi sai ga mai gadi nan ya fito cikin mamaki yake kallon musaddiq kafin kuma cikin girmama wa ya gaida shi, maigdin ne yace "Yalla6ai as gaba d'aya en gidan basa nan suna asibiti" A firgice musaddiq ya kalli maigadin yace " lafia, wane bashi da lafia?" Sai lokacin maigadin yayi da nasanin fad'a wa musaddiq don daddy ya gargad'e su da hkan, cikin ina ina yace "Bansan wanda bashi da lafiyar ba yalla6ai sai dai kaje suna can asibitin da alhj ya Gina maka" Kafin ya k'arasa fad'i musaddiq yace "d'auki trolley d'in nan ka shigar min dashi gida" Cikin rawar jiki maigadin ya d'auki trolley ya shige, shi kuma musaddiq ya shiga taxi d'in ya fad'a mishi inda xai kai shi............ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: [9/19, 3:54 PM] Aishat A Muh'd ✍🏻: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ E.W.F _lokacin da Allah ya sakkowa da bawan shi wata jarabta ya kasance cikin furta innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yayi ta maimaita har sai ya samu nutsuwa, ita rayuwa da muke ganin ta kowanne mutum da irin tashi kaddarar don hka mu kasance cikin takatsantsan da rayuwa da bautawa Allah tare da kiyaye dokokin shi don idan mutuwa ta tashi xuwa daukan mutum ba shawara ake dashi ba, don kowanne ita yake jira tun da Allah swt yana cewa cikin suratul imran (kullu nafsin xa'iqatul ma'ut) kowanne mai rai xai d'and'ani d'acin mutuwa, don hka ina kira a gare ku da mu kyautata mu'amalar da mutane domin ka samu shaida mai kyau a bakunan mutane, sannan mu dage da aikata alkhairi da karatun al'Qur'an, addu'o'i, nafilfilo, istigfari, salatin annabi da sauran su, a dunga kyautata iyaye ana musu biyayya, idan kina da aure ana yiwa miji biyayya, ana yawaita yin xumunci da axumin nafila da sadaka, Allah yasa mu dace duniya da lahira, Ameeen thumma Ameeen_. *PAGE 30* Ba k'aramin wahala mufidah tasha ba kafin Allah ya taimake ta ta haihu bayan sun gyara babyn Dr Aishat sai da tayi wa mufidah d'inki don ba k'aramin k'aruwa tayi ba don tubarkallah babyn k'atuwa da ita sai da ta duba ta ita da babyn ta tabbatar suna cikin koshin lafia tukunna suka fito a tare da sanar dasu mumy an sauka lafia an samu baby girl, sosai sun yi murna nan suka kar6i babyn har suka shiga room d'in mufidah da take kwance tana huta wa suna mata sannu, duk bata amsa ba sai ma bud'ar bakin ta tace "Mumy ina sadeeq?" Shiru mumy tayi ta kasa magana ganin hka yasa mufidah yunk'ura ta tashi xaune dak'yar saboda d'inkin da aka yi mata cikin tashin hankali ta kuma cewa "Ina sadeeq ne ina tambayar ku kun yi shiru?" Abba ne yayi k'arfin cewa "ki kwantar da hankalin ki mufidah ciwon shi ne ya tashi likitoci suna kan shi suna duba shi" Hawaye ne masu xafin gaske suka xubo daga idanun ta komawa tayi ta xauna tana kuka k'asa k'asa acikin xuciyar ta kuma addu'ar samun sauk'i take yi wa sadeeq, duk d'akin anyi shiru kamar ba mutane babu wanda yayi iya yunkurin rarrashin mufidah sai nabila. A can kuma room din da sadeeq yake likitoci sun dukufa akan shi wajen ceto rayuwar shi, ana cikin hka nau'orar da take nuna yanda numfashin mutum yake tafiya tare da bugawar xuciya ta fara yin k'asa, a firgice muh'd ya kalli yanayin numfashin shi ya ga yana sauka har xuwa 50 tuni muh'd ya rud'e cikin rawar murya yake cewa "Babban yaya kalle ni kada ka mutu please gashi mufidah ta haifa maka baby girl" Kallon shi sadeeq ya tsaya yi kafin kuma yana jan wani numfashi dak'yar yace "Muh'd taimaka ka d'auko min babyn na gani don Allah" Cikin rawar murya yake cewa "to...to ina xuwa kada ka tafi ka barmu" murmishi sadeeq yayi mishi na d'aga kanshi, da wani irin gudu Dr muh'd ya fice ya shiga room d'in da mufidah take ciki ya banka kofar da k'arfi ya shiga gaba d'aya su mumy sun firgita da ganin shigowar muh'd bai bi ta Kansu ba ya d'auki babyn ya fita da ita da sauri su ma suka bi bayan shi har da mufidah wadda dak'yar take tafia nabila na rik'e da ita. Tuni muh'd ya shige room din kafin su mumy su k'araso an rufe kofar dole suka tsaya hankalin su a matuk'ar tashe. Da sauri muh'd ya k'arasa wajen gadon yana nuna wa sadeeq babyn, bai da ikon daukan ta saboda drip d'in da yake hannun shi hannun shi yasa ya shafi fuskar ta xuwa kanta kafin dak'yar ya furta "Allah ya raya min ke ya albarkaci rayuwar ki Nana khadijah" Kallon muh'd yayi tare da yin wani irin murmishi da sake tsurar da muh'd ya bud'e bakin shi dak'yar yace "Muh'd ina son ka kular min da musaddiq, mumy, daddy, mufidah da kuma 'yata don nasan ke mutum ne nagari, ka rokar min yafiya wajen iyaye na da d'an uwana da matata da duk wasu abokanan hurd'ata, kace su yafe min Alhmdullilah nasan ba me bina bashi yanxu tun kafin ciwon yaci k'arfina na biya kowanne ma'aikacin company na kud'in su, daga k'arshe muh'd ina son ka daukar min alkawari guda d'aya" Tari ne ya sark'e shi yana yi sosai gaba d'aya doctor's d'in nan biyu hawaye ne yake xuba a idanun su na tausayi, muh'd kuwa kuka yake wiwi cikin rawar murya ya ce "Fad'i alkawarin ka babban yaya insha Allah xan cika maka shi" Sai da tarin ya lafa kafin yace "ina son kada ka bari kowanne namiji ya aure mufidah sai musaddiq d'ina don nasan xai kular min da ita da d'an da na haifa don Allah muh'd ka cika min wannan burin" Cikin kuka ya rik'e hannun sadeeq yace "na d'auki alkawari babban yaya xan cika maka shi amman baxa ka mutu ba xamu rayu tare da kai ka tashi please" Murmishi sadeeq yayi bai k'ara magana ba sai wasu hawaye da suke xuba a idanun shi yana kallon 'yarshi a hannun sadeeq tana bacci. D'aya daga cikin likitoci ne yace " muh'd numfashin shi yayi kasa sosai na 20 fah " A wani irin xabura muh'd ya kai idanun shi kan nau'orar mai nuna yanayin numfashin mutum kafin yayi wani yunkuri yaji sadeeq yana furta Kalmar shahada lokaci d'aya kuma nau'orar nan ta ba da sautin d'il d'il d'il sai kuma ta d'auke, a lokacin shima sadeeq ya gama furta Kalmar shahada shikenan mai raba wa ta raba kullu nafsin xa'iqatul ma'ut (kowanne mai rai sai ya d'and'ani d'acin ta). Lokaci d'aya fuskar shi ta d'auki wani haske tayi kyau sosai a sake fuskar nan tashi kamar a kira shi ya tashi, ja da baya muh'd ya fara yi da sauri d'ayan likitan ya kar6i jaririyar daga hannun muh'd ganin yana k'okarin sakin ta, girgixa kai yake yana hawaye kafin ya dawo jikin gadon yana rik'e sadeeq yana cewa "No no sadeeq kada ka tafi ka barmu don Allah ka tashi please" Ina sadeeq ko motsi bai yi ba, xube wa yayi k'asa ya hau kuka sosai likitoci nan suna rarrashin shin shi d'ayan ne ya rufe jikin sadeeq da wani farin mayafi har xuwa fuskar shi. Xumbur muh'd ya mik'e yana kuka ya fito daga d'akin da gudu kici6is yayi da su mumy, daddy, mufidah, Abba, umma, Yah Omar da nabila a tsaye suna jiran fitowar su ganin muh'd yana kuka yasa su xuciyoyin su suka tsinke da fargaba. Shi kuwa muh'd kasa magana yake sai kuka ta ina xai dubi idanun wad'annan bayin Allah ya furta musu sadeeq ya mutu kawai sai gani suka yi ya bar wajen da gudu yana kuka ko ina muh'd ya shige sai ayi ta kallon shi ganin babban likita kamar muh'd yana kuka. Yaxo dai dai shiga office d'in shi suka yi karo da wani d'ago kan shi da xai yi suka had'a ido da musaddiq dukannin su kallon juna suke cike da tashin hankali, musaddiq wanda yaga muh'd yana kuka ya fara tunanin me yasa shi kuka hka, duk da yanda gaban musaddiq yake fad'uwa yayi yunkurin bud'e baki yayi wa muh'd magana amman ina tuni muh'd ya shige office yasa key a jiki tare da jingina a jikin kofar ya na wani irin kuka mai ban tausayi. Har musaddiq xai bi bayan muh'd sai ya hango mumyn shi don hka sai ya nufi wajen gaban shi na matuk'ar fad'uwa. Lokacin da likitocin suka ga muh'd ya fita sai d'aya ya turo gawar sadeeq d'ayan kuma yana rik'e da babyn suka turo kofar suka fito fuskar su babu walwala ko kad'an idanun su sunyi ja sosai ganin an lullu6e mutum da farin mayafi har kanshi lokaci d'aya mumy ta fashe da kuka tana cewa "Shikenan sadeeq d'ina ya mutu innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Nan fah waje ya hargitse da kuka d'ayan likitan ne ya mik'a wa nabila babyn ta kar6a ita ma tana kuka sosai. Cikin dauriya Dr yace "I'm so sorry Allah ya kar6i ran yalla6ai sadeeq" Jin abin da likitan yace yasa mufidah tayi baya ta xube a sume. A lokacin musaddiq ya k'araso wajen ganin su mumy suna kuka babu wanda ya kula dashi a wajen, jaririyar ya hango a hannun nabila kuma bai ga mufidah don tuni ta xube a sume wasu nurse's sun d'auke ta don yi mata taimako gaggawa, sai kawai xuciyar shi ta bashi mufidah ce ta mutu wajen haihuwa take gaban shi ya fad'i ya nufi wajen gawar sadeeq wadda take a lullu6e, sai lokacin su daddy suka ankara dashi kafin su tsayar dashi ya sanya hannun shi yana k'okarin bud'e mayafin............. _ina jiran comment's d'in ku fan's_ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: [9/20, 10:47 AM] Aishat A Muh'd ✍🏻: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM *PAGE 31* Sai lokacin su daddy suka ankara dashi kafin su yi wani yunkurin na tsayar dashi tuni ya k'arasa wajen ya sanya hannun shi kan mayafin yana janye shi a hankali xuciyar shi na wani irin bugawa. Yana gama janye mayafin fuskar sadeeq ta bayyana kamar an kirawo shi ya amsa, daskarewa musaddiq yayi a tsayen ko kwakkwaran motsi ya kasa lokacin bugun xuciyar shi ya tsanan ta sosai fiye da d'axu mintuna uku yayi a hkan kafin kuma ya bud'e bakin shi da k'arfi ya furta " Yah sadeeq!" Lokaci d'aya kuma idanun shi suka fara rufe wa kafin kuma yayi baya ya sulale a k'asa a sume. Da gudu su daddy suka yi kanshi, mumy kuwa kuka take tana furta " shikenan musaddiq nasan shima yabi d'an uwan nashi ya Allah ka bani hak'urin rashin su" Kafin ta xube ita ma akan kujera tana shashshak'ar kuka cikin xuciyar ta tana karanta innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Allahumma arjurrni fil musubati wa'akbarni min khairul minha da sauran addu'ar da taxo xuciyar ta gaba d'aya ta wani xabge ta rame lokaci d'aya saboda tsabar tashin hankali. Dr muh'd kuwa bud'e kofar office d'in yayi kad'an yaga musaddiq baya nan don hka sai ya fito ya nufi inda suke idanun shi na xubar hawaye, yana k'arasa wa ya hango musaddiq a k'asa a sume su daddy da Abba suna k'okarin daukan shi, a rud'e ya k'arasa wajen da gudu ya cakumi jikin musaddiq yana kuka yana cewa "No musaddiq kada ka bishi kai ma nima xuciya ta xata buga na bi ku baxan jure rashin ka ba" Maganganun da muh'd yake shi ya sake tsinka xuciyoyin su daddy yana rik'e da musaddiq yana kuka sosai dak'yar Yah Omar ya rik'e muh'd aka shigar da musaddiq emergency room don ceto rayuwar shi. A cikin ambulance aka sanya gawar sadeeq daddy da Abba suna xaune kusa da gawar, umma, mumy, nabila da jaririyar kuma suka shiga motar Yah Omar suka nufo gida domin sada shi da gidan shi na gaskia, mumy babu uhm babu uhm uhm hawaye ne kawai yake fita a idon ta xuciyar ta tana wani irin xugi da rad'ad'i. An samu nasarar farfad'owar mufidah Dr Aishat tana k'okarin yi mata allurar bacci don ta huta amman mufidah tak'i yarda cikin kuka take cewa "Doctor na rok'e ki da kada kiyi min allurar bacci ki bar ni naje na yiwa mijina kallon k'arshe don nasan baxan k'ara ganin shi ba sai a photo" Wani mugun tausayin ta ne ya kama Dr Aishat don hka ta dafa kafad'ar ta tana cewa "Baxan miki ba mufidah amman ina son ki bar kukan nan addu'a yanxu sadeeq yafi bukata fiye da komai a wajen ki kin ji" Gid'a kai tayi nan ta kamo hannun ta suka fito daga room d'in. Musaddiq ma an samu ya farfad'o yana bud'e idanun shi komai ya dawo mishi sabo don hka ya yunk'ura ya tashi yana jin wani jiri da axababben ciwon kai ga xuciyar shi da take mishi xugi yana dafe da saitin xuciyar ya layi ya nufi kofa xai fita a lokacin muh'd shima ya murd'a handle d'in kofar ya shigo suka tsaya kallon kallon tsakanin su, ganin musaddiq yana yin baya xai fad'i cikin xafin nama muh'd ya rik'e shi cikin wata irin murya yace "Muh'd da gaske ne Yah sadeeq ya tafi ya barni, kace mishi ya dawo ina bukatar kasance wa dashi dama nine na mutu ba Yah sadeeq ba baxan iya jurar rashin shi ba nima xan bishi muh'd ya Allah nima ka d'auki rai na huta da......" Cikin kuka muh'd ya toshe wa musaddiq bakin shi don yasan baya cikin hayyacin shi, " kadai na fad'in hka musaddiq Allahn da ya bamu shi ya kar6i abin shi yanxu addu'ar mu kad'ai Yah sadeeq yake bukata ka taso yanxu mu je gida" Yana rik'e dashi suka fito har farfajiyar asibitin a lokacin kuma Dr Aishat ta sanya mufidah a motar ta xata kai ta gida sai gasu sun fito don hka sai kawai muh'd ya sanya musaddiq a bayan motar shima ya shiga ya xauna kusa dashi don baxai iya driven yanxu ba. Nan Dr Aishat ta ja motar ta suka fita daga asibitin, karatun Qur'an ta kunna cikin motar don samun nutsuwa ae kuwa duk shiru suka yi suna sauraren karatun Qur'an d'in da hka har suka k'arasa gida. Dak'yar suka samu damar shiga gidan saboda yanda mutane suka cika tun daga farkon layin ka shigo motoci ne da mutane damk'am har xuwa cikin k'atuwar farfajiyar gidan, don cikin lokaci k'ank'ani mutuwar SADEEQ ABUBAKAR ta kewaya ko'ina a fad'in sassan nigeria xuwa kasashen ketare don sadeeq mutum ne managarci, hankali, tausayi, taimako babu ruwan shi kowa na shine gashi da sanyin hali ga fara'a kai yabo dai sadeeq yasha shi daga bakunan mutane, shi yasa duk wanda yaji mutuwar ba k'aramin girgixa shi take ba wasu har da kukan su. A cikin palon daddy aka yi wa sadeeq wanka aka had'e shi kuma daddy da abban mufidah sai babban aminin shi abokin shi Yah Omar suka had'e shi shi likkafani suna yi suna xubar hawaye mai k'una. Bayan sun gama ne aka kirawo mumy don tayi mishi addu'a lokacin da mumy taga sadeeq a hka kusan sumewa tayi numfashin ta ya fara yin sama har daddy xai fitar da ita daga palourn sai kuma ta fara yi mishi addu'ar samun dace wa da rahmar ubangiji daga k'arshe kuma ta ce "Sadeeq na yafe maka a matsayi na na mahaifiyar ka Allah yayi maka rahma yasa aljanna ce makomar ka" Tana gama fad'in hka tayi shiru sai kuma ga mufidah da musaddiq nan tare da muh'd sun shigo palon suma. Musaddiq xama yayi a k'asa kusa dashi ya xuba mishi ido kawai yana kallon shi kamar wanda bai ta6a ganin shi ba sai yau hawaye ma sun dai NA fita a idanun shi sai *K'UNAR XUCi* (littafin ummu safwan), da yake yi. Muh'd ne yayi k'okarin yi mishi addu'a shima hawaye na xuba a idon shi, mufidah kuwa kuka take sosai ta kasa bud'e bakin ta tayi mishi, har xuwa lokacin da su daddy, Abba, Yah Omar da muh'd suka fara k'okarin d'aga makarar da sadeeq yake ciki. Sai lokacin mufidah ta rik'e makarar k'am tana cewa " bai fa mutu ba yayi min alkawarin xamu rayu da juna ku dawo da shi" Kuka take sosai tana sumbatu kamar mai ta6in hankali dak'yar mumy da umma suka janye ta aikuwa suna sakin ta ta xura da gudu ta kuma rik'e makarar tana surutai sosai ta bawa mutanen wajen tausayi don koma wa tayi kamar wata mahaukaciya sabon shiga. Wannan karon mumy kasa rik'e ta tayi sai umma ce da Dr Aishat suka rik'e ta nabila kuwa jaririyar ce ta tashi tana kuka shine take jijjiga ta a kafad'ar ta tana kallon mufidah tana kukan tausayin kawar ta ta. Suna rik'e ta sai kuwa tayi baya ta xube a sume nan suka d'auke ta xuwa bedroom d'in mumy nan Dr Aishat ta fara k'okarin ceto rayuwar ta bayan ta farfad'o tayi mata allurar bacci. Shi kuwa musaddiq har aka fita da gawar sadeeq yana xaune a wurin ya kasa motsi duk kukan da mufidah take da surutun da take bai san ana yi ba, xuwa can kuma ya mik'e xumbur ya fito lokacin har sanya sadeeq cikin mota don da d'an nisa tsakanin su da mak'abartar cikin sauri ya shiga ya xauna kusa da makarar muh'd yana kusa dashi. Lokacin da aka sanya sadeeq cikin kabari daddy ne da musaddiq suka sanya shi a cikin an fara xuba k'asa akan shi sai lokacin musaddiq ya dawo cikin hayyacin shi sai gani akayi kawai ya xube saman kabarin a sume nan aka d'auke shi aka sanya shi a mota aka nufi gida dashi don bashi taimakon gaggawa. Mutane sun fara tafia a mak'abartar amman daddy ya kasa tafiya kawai yayi xaman dirshe cikin k'asa gaban kabarin sadeeq yana shafa saman kabarin dak'yar Abba da Yah Omar suka janye shi tare da sashi a mota suka tafi gida.......... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM *PAGE 32* Bayan sun dawo gida Dr muh'd allurar bacci yayi wa musaddiq bayan ya farfad'o daga suman da yayi, tukunna ya fito xuwa farfajiyar gidan inda su daddy suke kar6ar ta'axiyya, gefe d'aya ya samu ya xauna yana aikin tunani lallai rai ba'a abakin komai yake ba lokacin da Allah yaso kar6ar abin shi ba wanda ya isa ya hana kamar d'axu ne da safe suka gama shan hira da sadeeq yanxu kuwa baya nan ya tafi tafiyar da har abadan baxai sake jinshi ko ganin shi ba a duniyar wayyo rayuwa Allah yasa mu dace Allah Yayi mana kyakkyawan k'arshe Ameeen, tunanin da muh'd yake yi kawai idanun shi suna hasko mishi fuskar sadeeq kunnuwan shi suna jiyo mishi muryar sadeeq lokaci d'aya hawaye masu xafin gaske suka xubo mishi. Damuwar da muh'd ya shiga sai kace wani d'an uwan shi shak'i k'in shi ya rasu, Allah ne ya had'a su da musaddiq har suka yi mugun sabo har suka rikid'e suka koma aminan juna na sosai da sosai k'aunar su yake da xuciya d'aya son su yake so irin mara algus d'in nan a ciki, wad'annan tunanin yake har xuwa lokacin da aka kirawo sallahr axahar suka tafi masallaci. A6angaren su mumy kuwa abin dai sai du'a'i don ko magana bata iya yi a yanxu ta daina kuka sai na xuci idanun ta sun ja sosai tana xaune cikin bedroom d'in ta akan abin sallah tana rik'e da carbi tana addu'a bayan ta idar da sallah, addu'ar samun dace da rahmar ubangiji take yiwa sadeeq tana fatan d'anta ya dace da albarkatun da suke wannan ranar ta alhamis, tana matuk'ar k'aunar 'ya'yan bata son abin da xai ta6a mata su sai gashi mutuwa mai yankan kauna ta raba rabuwa ta har abada shikenan baxa ta kara ganin sadeeq d'in ta ba, mutuwa kenan mai raba d'a da mahaifiyar shi. Nabila kuwa tana tare da mufidah duk da har yanxu bacci take bata farka ba, jaririyar ma tayi bacci ta kwantar da ita bayan ta gama d'ura mata madarar jarirai, kallon k'awar ta take tana mai tausayin ta mutuwar miji babu dad'i ko dad'e wa basu yi don basu fi shekara biyu da aure ba suna kan ganiyar cin soyayyar su sai gashi mutuwa taxo ta raba hawaye ne suke xuba sosai a idanun ta na tausayin mufidah. Sai da dare allurar baccin ta saki mufidah lokacin da ta bud'e idanun ta ta ganta a d'akin mumy a lokacin komai ya dawo mata cikin kwakwalwar ta hawaye ne suke xuba a idanun ta jin abin take kamar a mafarki wai sadeeq ya mutu anya ba tsokanar ta suke ba, kuma ae ta ganshi acikin makara har aka d'auke shi aka fita dashi da gaske ne sadeeq ya tafi ya barki da 'yarshi, wayyo sadeeq me yasa ka tafi ka barmu a lokacin da nafi buk'atar ka ni da 'yarka Allah ka jik'an sadeeq d'ina ka gafarta mishi. Tana cikin hka nabila ta ankara da ta tashi don hka nan ta dunga rarrashin ta da nasiha akan tayi hak'uri ta yarda da kaddara Allah ya kaddara sadeeq lokacin Yayi addu'ar samun rahmar ubangiji xata na mishi abin da yafi bukata kenan. Dak'yar ta lalla6a ta ta watsa ruwa duk idanun nan sun kumbura sun kod'e saboda tsabar xubar hawaye wata simple gown nabilah ta d'auko ta bata ta saka tukunna ta rama sallolin da ake bin ta, k'ememe mufidah tak'i cin abinci sai da nabilah da umma suka takura mata tukunna tasha tea cikin cup d'aya ba don taso ba duk bakin ta babu dad'i, sai lokacin nabilah ta mik'o mata jaririyar don ta shayar da ita an yi mata wankan ta fes an sanya kayan ta tayi tsab idanun nan nata a bud'e gaba d'aya sai kalle kalle take abin ta. Kura mata ido mufidah tayi sai taga ta koma kamannin sadeeq tsab, kallon ta take idanun ta suna xubar hawaye suna d'isa a fuskar jaririyar cikin raunin murya da sanyi tace " kin ga baban ki ya tafi ya bar mu da kewar shi tafiya ta har abada kinxo duniyar shi kuma yana barin ta gaba d'aya, bakisan baban ki ba kuma baxa ki ta6a ganin shi ba har abada sai a photo ya tafi wajen da ba'a dawowa idan aka tafi mahaifin ki mutumin kirki ne sosai babu ruwan shi yana son ki tun kafin kixo duniyar nasan har mutuwa ta d'auke shi bai gan ki ba kuma ganin ki shine burin shi na k'arshe kuma....." Toshe mata bakin ta nabilah tayi ganin maganar tayi yawa kuma bata da alamar tsayawa, tana kuka tace " haba mufidah ki daina irin wad'annan maganganun ita me ta sani da xaki sata a gaba kina surutu nace miki a yanxu soyayyar da xaki nuna wa sadeeq ita ce addu'ar na rok'e ki kiyi shiru kina karyar min da xuciya" Wani murmishin yak'e mufidah tayi idanun nan har yanxu hawaye ne suke xuba kafin ta ce " nabilah baki san abin da nake ji bane da kinsani da....." Da sauri nabilah ta katse ta tare da cewa " nasan da hka mufidah amman kiyi addu'a xaki ji sauk'in koma mene" Daga hka suka yi shiru mufidah tana shayar da babyn ta ta kura mata ido tayi tana kallon ta xuciyar ta cike da tausayin Kansu don tasan sun yi rashi ba kad'an ba. Musaddiq kuwa shima acikin daren ya farka lokacin da ya tashi Dr muh'd yana xaune a sofa ya buga tagumi, d'ago kanshi yayi suka had'a ido da musaddiq da sauri ya sanya hannun shi ya goge hawayen fuskar shi tare da tashi ya matsa kusa da musaddiq yana cewa "Sannu musaddiq ka tashi, me yake damun ka yanxu ba inda yake maka ciwo?" Muh'd ya jero wa musaddiq duk wad'annan tambayoyin cikin muryar shi mai rawa, kallon shi musaddiq kawai yake ba tare da yayi mishi magana ba, kallon da yake mishi kamar yau ya ta6a ganin shi har muh'd ya tsorata da irin kallon da yake mishi, hannun shi yasa ya ta6a shi amman ko motsi bai yi ba kuma yak'i dai na kallon shi rasa me xaice mishi yayi kawai ya samu waje ya xauna kusa dashi. Xuwa can sai yaga ya tashi xumbur ya mik'e ya shige toilet bin bayan shi da kallo muh'd yayi yana girgixa kanshi wasu kwalla suna xubo mishi tausayin musaddiq, mufidah, mumy da daddy yake yi sosai. Musaddiq yana shiga toilet ya cire kayan jikin shi ya sakarwa kanshi shower kafin kuma ya tsugunna a wajen yana wani irin kuka mai ban tausayi ga ruwa mai sanyi yana xuba a jikin shi ya rasa me yake mishi dad'i da gaske ne ashe Yah sadeeq ya mutu ya barshi shi kad'ai ba wa ba k'ani shi d'aya tilo wajen su mumy ta ina xai ji dad'in rayuwa babu d'an uwa rabin jikin shi, kuka sosai ya shashi a toilet kafin ya kashe shower d'in ya d'aura alwala ya fito. A tsaye ya tarar da muh'd sai safa da marwa yake don baisan a wane yanayi musaddiq yake acikin toilet d'in da tuni ya shiga saboda mugun dad'ewar da Yayi a ciki da kallo muh'd ya bishi ganin ya xura jallabiya ya fara rama sallolin da ake bin shi. Bayan ya idar ne muh'd yayi dashi don yaci abinci amman ko magana bai yi mishi dole hka ya hak'ura ya barshi yana kallon shi ganin yanda ya had'a kai da gwiwa. A cikin wannan dare musaddiq, mufidah, mumy,daddy,Yah Omar da muh'd babu wanda ya samu ya runtsa yayi bacci xuciyoyin su cikin alhinin rashin managarcin mutum suke ma'abocin kirki da karamci ba ruwan shi bai d'auki rayuwa da xafi sanyin hali ne dashi wanda Indai mutum yayi xama mintuna dashi sai yaji k'aunar shi a cikin xuciyar shi balle su da suka kwashe tsawon shekaru tare da shi, wannan daren dare ne da baxa su ta6a mantawa dashi acikin kundin rayuwar su ba, dare ne da suka kasance cikin tsananin kewar sadeeq kewar da basu ta6a jin irin ta a tattare dasu ba saboda sun san sun rabu da ganin shi har abadan, suna fatan Allah ya had'a su cikin aljannatul firdaus su kasance a tare, rayuwa kenan rayuwa mai cike da tarin kaddara acikin ta babu bawan da ya isa ya tsallake tashi kaddarar, rayuwa mai cike da tarin k'alubale a cikin ta, rayuwa mai cike da tarin ni'imomin da rahmomin ubangiji,Allah yasa mu dace da rahmar ubangiji ta duniya da lahira Ameeen ya rabbil alameen.......... _kuyi hak'uri da wannan fan's ban da chaji ne sai kuma gobe idan Allah ya kaimu_ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: [9/26, 5:44 PM] Aishat A Muh'd ✍🏻: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM _Happy birthday my Ummiey Xeey dear, ina taya ki murnar karin shekara wannan shafin sadaukar wa ne gare ki don taya ki murna, Allah ya k'aro shekaru masu albarka ya baki miji na gari mu xo Kaduna musha biki._Ameeen. *PAGE 33* Har garin Allah ya waye xuciyoyin su cike da alhinin rashin sadeeq wani lokacin ji suke kamar ba mutuwa Yayi ba xai dawo xuwa anjima, musaddiq da wani irin mugun xaxxa6i ya tashi ajikin shi da ciwon kai mai tsananin gaske wanda dak'yar yake iya bud'e idon shi, ga rashin cin abinci rabon shi da yasa wani abin abakin shi tun jiya yana cikin jirgi da yasha coffee kawai. Dr muh'd ne ya tsaya sosai akan shi har xuwa yamma xaxxa6in kamar k'ara mishi ake yak'i sauka idan ka kalli musaddiq a time d'in sai ya baka tausayi Yayi masifar rame wa sosai abu ne yake cin shi a xuciya ga yak'i fitar da kukan waje sai na xuci kawai yake sai da kaji yana wani jan numfashi tare da sauke ajiyar xuciya. Wannan yanin gaba d'ayan su sun yi shi cikin wani mawuyacin hali musamman musaddiq da mufidah har gwara mufidah ana takura mata taci abinci saboda shayar da babyn, musaddiq kuwa muh'd ne yake fama dashi wajen cin abinci amman yak'i kar6a yaci mumy ma k'in xuwa ganin shi tayi don baxa ta jure ganin d'an nata da yanxu ya rage mata ba cikin wannan halin, tasan musaddiq mutuwar sadeeq sai tafi ta6a shi fiye da kowa idan aka yi la'akari da yanda suka yi mugun shak'uwa da junan shi, addu'a kawai take mishi Allah ya sanyaya mishi xuciyar shi ya bashi hak'urin jure rashin d'an uwan shi. *AFTER 7 DAY'S* Anyi kwanaki bakwai da rasuwar sadeeq a yanxu, ranar da ya cika kwanaki 7 a ranar daddy yaxo sanya wa jaririyar suna da yake duk suna palon gaba d'ayan su idan ka d'auke musaddiq wanda yake can a d'akin shi yana shan bacci sakamakon allurar baccin da ake mishi. Kallon mufidah daddy yayi tare da cewa "mufidah ko da akwai sunan da kike ra'ayi a sanya mata?" Girgixa kai mufidah tayi tana xubar da hawaye kafin ta bud'e baki murya na rawa tace "Daddy duk wanda ka sanya mata yayi ban da wani xa6i" Har daddy ya bud'e baki xai yi magana da sauri muh'd yace "Daddy kafin Yah sadeeq ya rasu lokacin da na kai mishi babyn naji ya furta Allah ya raya ki NANA KHADIJAH ina tunanin shine sunan da yake so" Da sauri mufidah ta kalli muh'd cikin mamaki lokaci d'aya taji wani d'an sanyi a cikin xuciyar ta jin sadeeq yaga babyn kafin ya mutu. "Masha Allah kenan sunan mumyn shi kenan to Allah ya raya mana NANA KHADIJAH, Allah ya albarkaci rayuwar ta ya jik'an mahaifin ta da rahma" Cewar daddy kenan. "Ameeen thumma Ameeen" Gaba d'aya falon aka amsa idanun su ya cicciko da hawaye, nan daddy yayi mata hud'uba da khadijah tukunna aka yiwa sadeeq addu'a sosai sannan aka watse. A ranar umman su mufidah da nabilah Yah Omar suka wuce gida aka bar mufidah a wajen mumy, bayan nabilah ta bata shawara akan ana kiran khadijah da Afnan saboda sunan mumy ne, mufidah ta sha kuka sosai lokacin da su umma suka tafi dak'yar mumy ta rarrashe ta tayi shiru, xuciyar ta tana kewar sadeeq kusan kullum da pic d'in shi take k'wana rungume a jikin ta duk dare sai ta xubar da hawayen rashin sadeeq tasan baxa ta ta6a samun miji irin sadeeq ba gaba d'aya ma ita ta sawa xuciyar ta ba xata yi aure ba xata xauna ta kula da Afnan d'in su ita kad'ai ta ishe ta xata xauna ta jira yi har mutuwar taxo ta d'auke ta taje can ta had'u da sadeeq d'in ta. Musaddiq ma gaba d'aya ya xama wani iri abinci sai an rarrashe yake ciki kullum yana cikin daki a kwance yana faman tunanin rayuwar su ta da tare da d'an uwan shi, mumy ce ta sawa xuciyar ta jarumta wajen rarrashin mufidah da musaddiq. ******* Haka rayuwa ta mik'a ta cigaba da tafiya a hankali suka fara saba wa da rashin sadeeq addu'a ce kullum cikin yi mishi suke xuciyoyin su sun fara sanyi, da hka kwanaki suke tafiya sannu a hankali har sadeeq yayi k'wana 40 da mutuwa a ranar an yi sadaka da karatun alQur'an da addu'o'i akan Allah y rahma mishi a ranar mufidah tasha kuka sosai don a ranar ta tabbatar sun fa rabu da sadeeq har abada. Duk wannan xaman da suke gida d'aya tsakanin musaddiq da mufidah basu had'u da junan su kowannen su yana cikin bedroom basa fito wa. Lokaci yana ja kwanaki suna tafiya har xuwa lokacin da sadeeq ya samu kimanin wata uku da rasuwa, Afnan tayi wayo sosai kamannin ta da mahaifin ta yana sake fitowa sosai a kusan koda yaushe tana hannun musaddiq idan ya xuba mata ido yana kallon ta ko kiftawa baya son yi don gani yake kamar suna tare da d'an uwan shi sadeeq, kullum idan mumy tayi mata wankan safe xata kawo mishi ita ta yini a wurin shi sai dai lokacin cin abincin ta yayi mumy taxo ta kar6e ta don sam baya sha'awar fitowa abin yana damun mumy da daddy da muh'd gashi ya Tara wata gashi a fuskar shi sosai yak'i xuwa a gyara mishi muh'd ma yayi yayi dashi don ya ma gyara mishi yak'i yarda dukannin su a tsorace suke kada shima yabi bayan d'an uwan nashi, don gaba d'aya musaddiq ya koma kamar bashi ba daman gashi miskilin gaske a yanxu kuwa gwara da sau dubu akan yanxu sai ku kusan yini tare amman baxai bud'e baki yayi maka magana ba sai dai yayi ta bin ka da kallo kamar yau ya fara ganin ka.......... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM *PAGE 34* Kamar yau ranar juma'a wanda Yayi dai dai da watanni biyar da rasuwar sadeeq, abin da musaddiq yake mumy ta gaji da ganin shi cikin hka don hka tun safe bayan ta gama abin breakfast ta d'auki nashi ta nufi bedroom d'in shi da sallama ta shiga but kamar koyaushe bai amsa ba and kuma yana kwance still kan bed yayi rigingine yana tunani. Mumy kallon d'an nata tayi cikin tausayin shi ajiye breakfast d'in tayi tare da k'arasa wa inda yake ta xauna tare da dafashi tace "Musaddiq tashi xaune" Ba musu ya tashi ya xauna tare da d'ora kanshi saman kafad'ar ta shafa bayan shi take tana cewa "Musaddiq na gaji da ganin hka cikin wannan halin ina son ka sawa xuciyar hka hak'urin rashin sadeeq, ganin hka yana d'aga min hankali kai kad'ai ne ka rage min yanxu idan baka sawa xuciyar ka hak'uri ba xaka iya samun matsala ka fison ka dunga ganin mu cikin tashin hankali koh?" Girgixa kai yayi tare da d'ago kanshi yana kallon mumyn wadda take fitar da hawaye, hannun shi yasa yana goge mata hawayen shima kuma hawayen yake yana girgixa mata kai cikin rawar murya yace "I'm so sorry mumy Yah sadeeq ya tafi ya bar mu na kasa yarda ya mutu ji nake kamar xai dawo gare ni, bana son ganin ki cikin tashin hankali ki dai na kuka don Allah mumy" "Idan har kana so na daina damuwa to kayi hak'uri da rashin sadeeq ka d'auki hkan a daman Allah ne ya bamu aron shi xuwa wani lokacin gashi kuma ya d'auki abin shi ka cire damuwa a ranka addu'a sadeeq yafi bukata shine abin da xamu yi mishi mu nuna mishi mu masu son shi ne" "Okay mumy xan yi abin da kike so" Cikin hawayen da take ta fara dariya tana cewa "Da gaske musaddiq xaka koma kamar da?" Wani murmishi yayi wanda rabon shi da yayi an dad'e kafin yace "I promise mumy xan dawo miki kamar Yah sadeeq" Rungume shi mumy tayi tana mai jin dad'in yanda yau ya bata had'in kai nan ta cigaba da yi mishi nasiha cikin sigar rarrashi kafin daga k'arshe ta shiga toilet ta had'a mishi ruwa mai d'umi a bathtub tukunna ta d'ebo kayan aski ta xauna ta gyara mishi fuskar shi fes, tuni musaddiq ya rikid'e ya koma musaddiq d'in shi na da bayan ta gama yi mishi ya shiga toilet yayi wanka sosai wanda rabon shi da yayi irin wannan wankan tun kafin sadeeq ya rasu. Bayan ya fito ne ya shirya jikin shi cikin wani lallausan yadi sky blue wanda yayi matuk'ar kar6ar shi yana cikin fesa perfumes ya hango wani pix d'in su da suka yi shi da sadeeq ta mirror suna dariya pic d'in yayi matuk'ar yin kyau sosai, hawaye ne ya cicciko a idanun shi bai bari sun xuba ba ya d'aure ya rik'e su hannun shi yasa ya shafa mirror d'in tare da cewa "Yah sadeeq ka tafi ka bar ni, ina matuk'ar kewar ka " Ya k'arasa fad'i muryar shi na rawa sosai kamar xai fashe da kuka, yana cikin hka mumy ta shigo bedroom d'in da sauri ya dai dai ta nutsuwar shi don yayi mata alkawarin daina sa damuwa a xuciyar shi. Dad'i ne sosai ya kama mumy ganin d'an nata ya fito fes dashi ya dawo musaddiq d'in shi rungume shi tayi tana shafa kanshi tana cewa "Naji dad'in ganin ka a hka musaddiq Allah yayi maka albarka ya jik'an sadeeq" "Ameeen mumy na" "Yanxu sauran ka breakfast kasha magani sai ka mu fita palour daddy yana jiran mu" Cewar mumy kenan idon ta akan shi tana son ganin yanayin yanda ya kar6i maganar ta ta. Murmishi ya d'an yi kafin yace " okay mumy" Nan ta fara bashi abincin a baki har yaci ya K'oshi wanda rabon da yayi wannan cin abincin har ya mance bayan ya gama ci ta bashi maganin shi ya sha tukunna suka fito xuwa palon daddy. Ba k'aramin dad'i daddy yayi ba ganin musaddiq a hka nan shima nasiha sosai yayi mishi nan suka xauna hira har xuwa lokacin tafiya masallaci yayi don yau juma'a tare suka tafi da daddy. Mufidah ce na hango a bedroom tana k'okarin sanya hijab a jikin ta tana sanye da wata atampha tayi kyau kam don ma har yanxu bata ciko daga ramar da tayi ba, sauri take tana shirya wa don yau gida take son xuwa tuni ta gama shirya Afnan tana Palo hannun mumy. Bayan ta fesa perfumes mara k'arfi a jikin ta ta fito xuwa falo, ko make up bata yi ba but duk da hka tayi kyau don kyanta natural ne. A nutse ta fito tana tafiyar ta har xuwa Palo nan ta kar6i Afnan a hannun mumy suka yi mata sallama ta jiyo tana k'okarin bud'e kofar palon adai dai time d'in musaddiq ya sanya hannun shi kan handle d'in kofar ya bud'e gware suka yi da kan su saboda shi musaddiq ya d'an rakwafo kanshi gwaren nan irin na unexpected ne shi yasa suka ji xafin sosai har sai da mufidah ta d'an saki k'ara tana dafe goshin. Wanda hkan yasa Afnan ku6uce wa daga hannun ta tayi k'asa sauran kad'an ta fad'i cikin xafin nama musaddiq ya taro ta da hannun shi lokaci d'aya Afnan ta tsandara ihu don ta tsorata sosai ta fara kuka, wani kallo musaddiq yayi wa mufidah wanda ya d'an tsorata ta tare da ja da baya don kada ya kawo mata bugu sai wani huci yake. A tare mumy da daddy suka k'araso wajen suna tambayar su lafia, cikin fusata musaddiq yace " mumy wajen sakacin ta ne yasa ta kusan fad'uwa" " anya kuwa musaddiq sai dai tsautsayi?" Mumy ta fad'i hkan tana kar6ar Afnan tana rarrashin ta har sai da tayi shiru. "Ina xasu je ne?" Cewar daddy, " gida mufidah xata je" Mumy ta bashi amsa, kallon musaddiq yayi wanda yake k'okarin barin wajen yace "Musaddiq ka kai ta gidan ni yanxu xan sake fita da driver " Kafin yace komai daddy ya bar wajen, mumy ma mik'a wa mufidah Afnan tayi tare da cewa "Sai kun dawo ki gaida min su xan shigo anjima da dare sai mu dawo tare" Tana gama fad'in hka ta wuce ita ma, aka bar mufidah da musaddiq a tsaye, wanda shi tsabar mamakin abin da daddy ne yace ya hana shi kwakkwaran motsi, ita ma mufidan taji babu dad'i don sam bata so daddy yace ya kai su ba haushin musaddiq take ji sosai wai ya wani ce saboda sakaci na xan yarda Afnan kamar wata 'yar shi. Kwafa tayi tare da jan d'an siririn tsaki, shima tsakin yaja har ya bud'e baki xai yi magana ko mai ya tuna sai yayi shiru tare da fita daga palon a fusace............. Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: [9/27, 11:24 AM] Aishat A Muh'd ✍🏻: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM *PAGE 35* A fusace ya fita daga palon xuwa farfajiyar gidan motar da suka fita masallaci da daddy Ita ya shiga ya xauna yana jiran ta gaba d'aya ranshi yayi masifar 6aci akan abin da daddy yace yana nan xaune sai faman doka tsaki yake shi kad'ai. Mufidah sai da ta kwashi tsawon mintuna tukunna ta fara k'okarin fito wa daga palon, kallon ta yake tana taho wa ranshi ya k'ara 6aci sosai ganin yanda ta shanya shi sai da tayi ra'ayi sannan ta fito kau da kanshi yayi daga barin kallon ta yana jan tsaki. A nutse ta sanya hannun ta ta bud'e kofar motar ta xauna babu wanda yayi wa wani magana a tsakanin su yayi wa motar key ya fita daga gidan kowannen su fuskar shi a d'aure, har suka karasa gidan su mufidah a kofar gate d'in ya yi parking ba tare da ya kalle ta ba ko yayi magana. Haushi ya sake turnik'e mufidah wato a waje ma xai ajiye ta baxai shigar da ita d'an tsaki taja tare da bud'e kofar motar ta fita sannan ta buga mishi murfin kofar da k'arfi har sai da musaddiq ya d'an tsorata ya kallo inda take amman wayam bai ganta ba har ta shige cikin gidan. "Lallai yarinyar nan ashe har yanxu akwai raini atsakanin mu da ita ae kuwa xan koya mata hankali" Ya fad'a yana jan tsaki can kuma har yayi wa motar key ya fara tafiya sai kawai ya furta a fili "Xan kyale ta saboda darajar Yah sadeeq, but dole na kar6e Afnan daga hannun ta kada ta koya mata tsiwa da rashin kunya". Mufidah kuwa cike da jin haushin musaddiq ta k'arasa cikin palour tare da kwalla wa umma kira tana cewa "Umma na kina ina?" Da sauri umma ta fito daga kitchen jin muryar mufidah ae kuwa tana ganin ta suka rungume junan su cikin tsananin farinciki sai mufidah taji duk 6acin ran ta ya kau sai farinciki. Sakin ta umma tayi tana kar6ar Afnan tace " Masha Allah Afnan sai girma take ga kamannin ta da mahaifin ta sak kamar yayi kaki ya xubar" Tuni idanun mufida sun ciko da hawaye jin umma ta ta6o mata wani abun, ganin yanda lokaci d'aya mufidah ta canja yanayin ta cikin damuwa daga farincikin da take yasa umma ta rik'o ta suka xauna cikin sigar rarrashi da nasiha tace "Haba mufidah bana son ganin ki cikin wannan yanayin ke har yanxu baki sa wa xuciyar ki hak'urin sadeeq ba ya kamata ki hak'ura kina mishi addu'a kin ji" "Toh umma shikenan" Ta fad'i hka muryar ta na rawa. "Wane ya kawo ku kuma?" Cewar umma don tana so ta bagarar da wancen xancen, d'an ta6e baki mufidan tayi tare da cewa " Hmmm musaddiq ne daddy yace ya kawo mu" "Okay, yasu hajia khadijahn?" "Suna nan Qlau tace na gaida ke anjima xata shigo" D'an shiru umma tayi ta fad'a tunani jin tayi shiru yasa mufidah d'ago kanta tace "Umma lafia, me ya faru?" " uhm mufidah wai so suke mu bar miki so ae sun xo da ita daddyn su sadeeq na nuna gaskiya ni ban amince ba tun da nima ba wasu 'ya'yan ne da ni ba da yawa nima ku biyu kad'ai Allah ya ba mu, yanxu kuwa da nayi tunani sai naga kema d'in ba wani dad'e wa xaki yi da wajen su ba aure xaki yi, kuma Omar da abban ku sun ce na hak'ura na bar ki saboda mutanen suna da karamci sosai" Tun da umma ta fara magana mufidah take bin ta da kallo hankalin ta a tashe sam ita xama gidan su sadeeq bata so yanxun ma a dole take xaune saboda tana yawan tuna wa da sadeeq, kunyar mumyn ce ta hana ta dawowa gida, sannan ita ma sam bata da ra'ayin aure gaba d'aya a tsarin ta. "Kin ga Omar ya fara yin gini acan 6angaren xasu dawo nan saboda kawai don na barki wajen su kuma yanxu na amince da hkan, ke dai ki cigaba da yi mishi biyayya ki d'auke su tamkar iyayen ki kuma ki cigaba da tsare mutuncin kan ki har xuwa lokacin da Allah xai fito miki da wani mijin na gari". Gaba d'aya hirar ta gunduri mufidah jin yanda umma take mata xancen aure kawai sai ta silale ta gudu bedroom d'in ta, da kallo umma ta bita tun ba yanxu ba ta fuskan ci mufidah bata son ayi mata maganar aure sam, girgixa kai tayi tare da tashi ta goya Afnan a bayan ta don tayi bacci ta shige kitchen tana cigaba da ayyukan ta. Sai yammaci bayan la'asar mufidah ta fito daga bedroom d'in xuwa Palo kallo d'aya umma tayi mata tasan tayi kuka, nan ta xauna tana cin abinci suna er hira da umma har daga k'arshe kuma suka shiga kitchen tare don shirya abincin dare. Sai bayan wurin 8 na dare mumy taxo da sallama ta shigo palon umma da mufidah wadda take shayar da afnan suka amsa mata kafin su rufe bakin su muryar musaddiq ta doki kunnen mufidah yana sallama, fuskar nan tashi a d'aure da gani kasan dole aka yi mishi ya shigo. Da sauri mufidah ta gyara rigar ta haushi ya kamata taya ya xai shigo musu Palo direct ba tare da an bashi ixinin shigo wa ba, sai wani hararar shi take, Afnan kuwa jin an raba ta da abincin ta yasa ta saki kuka don bata koshi ba, jikin shi har wani rawa yake jin kukan ta kafin su ankara har ya tsallake mumy ya wuce gaban mufidah ya kar6i Afnan d'ora ta a kafad'ar shi yayi yana jijjigata harara ya watsa wa mufidah kafin ya dawo ya xauna kusa da mumy yana cigaba da jijjiga Afnan. Da kallo umma da mumy suka bishi ita kuwa mufidah bedroom ta shige tana wani cika tana batsewa, sai lokacin hankalin shi ya dawo kan umma ae kuwa kunya ta kamashi don bai xaci tana palon, sosa kai ya hau yi kafin ya iya bud'e baki ya gaida ita. Hararar shi mumy tayi tana cewa "sai yanxu ka kula da ita kenan" dariya umma ta d'an yi tare da cewa " ba komai hajia khadijah kukan 'yar tashi ne ya rud'a shi" Shi dai musaddiq bai k'ara magana ba hankalin shi ya mayar kan Afnan yana yi mata wasa, suna cikin hka daddy, abba da yah Omar suka shigo nan aka gaisa tukunna aka nufi dinning table don cin abinci. Umma da kanta ta kirawo mufidah ta fito tana wani 6ata rai don musaddiq shine a kusa da kujerar da xata xauna, sai da ta gaida su Abba, daddy da yah Omar sannan ta fara serving d'in kowa ta xuba wa kowa dai dai yanda xai ishe ka musaddiq kuwa don mugunta sai da ta cika mishi plate taf da abinci har sai da yayi tsini wanda kowa ya kalli xuba abincin kasan don dole ta xuba. Ba wanda yayi magana sai abincin suka fara ci ita xama tayi tana cin nata hankali kwance, musaddiq kuwa bai san me ake ciki ba don danne danne yake kawai a wayar shi ba tare da ya kalli plate d'in da aka xuba mishi jellop d'in cous cous ba ya sanya hannun shi ya janyo don gaba d'aya k'amshin ya cika mishi ciki sai yaji plate d'in yayi d'an nauyi d'ago kan da xai yi yayi ido biyu da tulin uban abincin da mufidah ta xuba mishi.............. Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM *PAGE 36* Ranshi ne ya 6aci sosai ganin rainin hankalin da mufidah tayi mishi don yasan ita ce xata aikata hkan, daddy ne ya kalle shi ganin yanda yasha mur yana kallon abinci danne dariyar shi yayi tare da cewa "Musaddiq lafia kuwa, Ka tsaya baka fara cin abincin ba?". Girgixa kai yayi kafin kuma yace " daddy wannan abincin yayi min yawa ko rabi baxan iya ci ba fah" Ya k'arasa fad'i yana huci, hararar mufidah yah Omar da umma suka yi aikuwa ta turo baki gaba ta wani waske kamar ba ita tayi ba, Abba ne yace " kaci ka barshi musaddiq " Janyo abincin yayi yana wani cin magani don kawai abincin ya yi mishi kyau a fuska gashi kamshin shi sai dukan hancin shi yake yasan idan yayi xuciya ya hak'ura da ci bai yiwa kanshi adalci ba, don hka yayi bismillah ya fara ci lumshe idanun shi yayi saboda tsabar dad'in da abincin yayi mishi, hka ya cigaba da ci amman idan ka kalle shi baxa ka gane yana jin dad'in abincin ba ko akasin hka don yanda yabi ya d'aure fuska. Bayan sun gama ci ne nan suka fara maganar da ta kawo su, su mumy da daddy kenan babu 6ata lokaci umma da Abba suka amince da xaman mufidah a gidan nasu, saboda dad'i sai da mumy ta rungume umma nan suka yi ta godia. Basu bar gidan ba sai wurin 10 na dare gaba d'aya lokacin jikin mufidah a sanyaye har suka k'arasa gida don ita da xa'a bi ta ra'ayin ta baxa ta xauna a gidan ba. Hka mufidah ta cigaba xama a gidan ba inda take xuwa daga gidan su sai gidan yah Omar shima tun daga lokacin da ya kammala ginin shi ya dawo gidan da xama shikenan, gaba d'aya mufidah ta gaji da xaman wuri d'aya tun da ta gama karatun ta yanxu aiki take ra'ayin fara wa amman tana jin nauyin tunkarar su mumy da xancen tayi shiru kawai ta dage da addu'a. Musaddiq kuwa sam baya shiga harkar mufidah ko magana ba Yayi mata idan ma tana wajen yaxo xai bar wurin sam ko kallon ta baya yi, tuni ya yanke lokacin da xai koma Australian don baxai jure xama gida d'aya da mufidah ba kwata kwata ga kewar d'an uwan shi da take damun shi don ma Dr muh'd yana debe mishi kewa, nan ya samu daddy da xancen ba 6ata lokaci daddy ya amince da hkan don yanxu ya daina takurawa musaddiq tun lokacin da yaji yana da ciwon xuciya idan ma abin bai yi mishi ba cikin rarrashi da nasiha yake mishi. Mumy ce ma ta d'an nuna k'in amincewar ta da komawar tashi amman cikin lallami da dad'in baki yayi mata har ta amince amman da sharad'i nan da 6 month's ya dawo ya sami mata yayi aure nan ya amince da hkan kuwa. Cikin kwanaki uku ya gama shirin shi ya d'aga xuwa k'asar Australian xuciyar shi tana cike da kewar mumyn shi, daddy, Yah sadeeq d'in shi, Dr muh'd aminin shi da kuma Afnan don tafiyar da yayi shi da agan shi ya dawo xa'a dad'e don so yake komai ya wuce a xuciyar shi ya samu kwanciyar hankali da nutsuwa. Bayan tafiyar musaddiq da two month's daddy ya bawa mufidah office a asibitin musaddiq a matsayin medical Doctor don fannin da ta karanta kenan a skul. Ba k'aramin farinciki mufidah tayi ba don ta gaji da xaman wuri d'aya, cikin k'ank'anin lokaci komai ya fara canja wa a wajen ta yanxu ta rage tunani sosai yawancin ma sai xata yi bacci kewar sadeeq take damun ta, Dr muh'd ma yaji dad'i sosai da aikin mufidah da ta fara kullum tare suke tafiya hka shiya ke dawo da ita gida, sosai ya sama ta ido don baya son yaga ta fara soyayya da wani don yana son cika alkawarin da yayi wa Yah sadeeq, shima kuma ya kula mufidan bata kula kowa bata da wannan ra'ayin kuma yaji dad'in hkan sosai. Gashi an kusan kwashe shekara da rasuwar sadeeq amman muh'd bai ta6a jin ko da wasa musaddiq yayi mishi xancen mufidah ba. Abin yana bashi mamaki har takai akwai lokacin da yayi mishi magana akan mufidah nan musaddiq ya birkice yana yiwa muh'd masifa taya ya xai aure mufidah matar da yayan shi ya aura ace shima xai aura nan ya dau fushi da muh'd sosai ya daina daukan wayar shi abin sosai ya dami muh'd don wannan karon kusan shine na farko rigimar da suka yi. Dak'yar musaddiq ya hak'ura shima sai da muh'd d'in yaje har Australian tukunna ya hak'ura suka cigaba da mu'amalar su kamar da tun daga lokacin muh'd bai k'ara yi mishi maganar mufidah ba............ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM *PAGE 37* *AFTER 2 YEAR'S* A cikin wad'annan shekarun abubuwa da yawa sun faru a cikin ta, mumy, daddy,mufidah da musaddiq sun fara saba wa da rashin sadeeq acikin xuciyoyin su ,sun riga da sun sawa axuciyar su wanda ya mutu baxai ta6a dawowa ba sun rabu da ganin shi har abada sai dai a picture daman hka rayuwa take cikin ta cike da kaddarori na rayuwar d'an adam . Mumy kusan ko dayaushe cikin waya take da musaddiq tana mai tak'ura mishi ya dawo gida ya samu mata don yayi aure, amman musaddiq baya mai da hankali kan abin da mumy take fad'a mishi don shi sam baxai iya dawowa nigeria yanxu ba don baya son tunawa da abin da ya wuce acikin rayuwar shi komawar shi nigeria kuwa yana ganin mufidah hkan ba k'aramin dad'a taso mishi abin da ya shige xai yi ba, kuma ya riga da ya sanya wa xuciyar shi hakurin rashin mufidah tun lokacin da Yah sadeeq ya aure ta baya son ya dawo sai lokacin da ta samu miji tayi aure ta bar gidansu,shi yasa yake kauce wa xancen mumy duk da yana kewar iyayen nashi da muh'd tare da afnan yarinya jin ta yake tamkar sadeeq d'in shi. Wani irin son ta yake a cikin xuciyar shi irin son nan da ko d'an da haifa ba lallai yayi mishi irin wannan son ba shi yasa kusan koyaushe cikin turo mata kayayyakin sawa da na wasa yana son ganin ta cikin farinciki sosai kulawa sosai yake bata duk da basa kusa da juna kuwa. Afnan ta xama 'yar gata gaba da baya kowanne 6angare cikin bata kulawa ake da nuna mata soyayya sosai, afnan yarinyar akwai ta da hak'uri kamar mahaifin ta sadeeq ga fara'a. Kamar yau rana ce ta week end mufidah bata da xuwa hospital tana kwance kan bed cikin bedroom d'in ta baccin ta take cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ,da ganin yanda take baccin kasan ba k'aramin jin dad'in shi take ba. Afnan ce ta turo kofar bedroom d'in ta shigo tana sanye cikin wata pink gown iya gwiwar ta an gyara mata gashin ta da ribbons pink and white colour. D'ago kanta da tayi bansan lokacin da na furta subhanallah tabarakallahu ahsanin kaliqeen saboda tsabar kama da sadeeq da tayi ,ja tayi ta tsaya ganin mufidah tana baccin ta ita da ta taxo don ta duba ta ga ta shirya su tafi gidan umma. Wani 'yar dariya ta saki a hankali tana toshe bakin ta don kada sautin dariyar ta ya tashi mufidah tace "Tabbb mumy ma har yanxu bacci take bata tashi ba" Ta k'arasa fad'in hka tana yatsina fuska kad'an , nufar kan bed din tayi ta hau tare da sanya d'an yatsan ta d'aya cikin kunnen mufidah tana yin motsi dashi. Hannun ta mufidah tasa xata sa a kunnen don jin motsin da take ji aciki, da sauri afnan ta xare d'an yatsan nata tana dariya k'asa k'asa don ganin mufidah ta gyara kwanciyar ta tare da komawa baccin ta hankali kwance. Ganin hka yasa afnan ta kai bakin ta dai dai kunnen mufidah tace " Mamee na wake up" Da k'arfi ta fad'i hkan ae kuwa a firgice mufidah ta tashi sauke ajiyar numfashi don ba k'aramin tsorata tayi ba ,dariya afnan ta kwashe da ita tare da cewa "Mamee na kin fiye tsoro nice fah" Hararar ta mufidah tayi tare da d'aure fuska hannun ta tasa ta kama kunnen ta da d'an k'arfi tare da cewa "Afnan how many times da xan miki magana ki daina yi min ihu a kunne idan ina bacci, kina son na dunga tashi da headache koh?" Girgixa kai afnan tayi tana mai yin raurau da idanun ta alamar gaf take da ta rushe da kuka ta marairace fuska tace "Sorry mamee na daina " K'ara hararar ta mufidah tayi tana kokarin tashi da sauri afnan ta rik'o hannun mufidah sannan ta kama kunnen ta dukka biyun tace "I'm so sorry mamee na please baxan k'ara ba" Duk tabi ta wani damu don sam bata son ganin tayi wa mameen nata laifi tana mata fad'a, kallon ta mufidah tayi sai taji wani mugun tausayin ta batasan lokacin da ta rungume ta ba tsam a jikin ta, tana mai jin wani irin sabon sonta na k'ara shiga cikin xuciyar ta. "Mamee kin hak'ura?" Cewar afnan murmishi mufidah tayi tare da cewa "Na hak'ura afnan baxan iya fushi da ke ba " Kallon mufidah take wadda ta sauka daga kan bed tana tsaye ita kuma afnan tana kan bed din tace "Mamee an fasa xuwa gidan umma ne?" Hancin ta mufidah ta kamo tana d'an ja tace "Sarkin son xuwa gidan umma xamu je bari na shirya ko?" "Yawwa mamee na thank u " Gaba d'aya suka sanya dariya sannan mufidah ta shige cikin toilet xuciyar ta cike da kaunar 'yar ta ta. Cikin en mintuna tayi wankan sannan ta fito ta fara gyara jikin ta suna hirar su da afnan har ta kammala shirya was cikin wata black arabiyan gown mai adon flower's golden a jiki tayi kyau sosai da yake mufidah fara ce kalar ta kar6i fatar ta, ba wani kwalliya tayi ba daga powder sai wet lips mai k'amshin apple bayan ta fesa perfume's ne a jikin ta ta rik'e hannun afnan suka fito xuwa down stair's, d'ayan hannun nata yana rik'e da car key and phone nata . Tun kafin su k'araso cikin palourn mumy take kallon su xuciyar ta cike da farinciki fuskar ta ma bata 6oye yanayin da take ciki ba saboda yanda take murmishi idanun ta akan su har suka karaso cikin parlour. Gaida mumy mufidah tayi bayan sun gama gaisa wa ne ta nufi dinning area ta fara breakfast, bayan ta gama suka yiwa mumy sallama suka tafi. A nutse take driving har suka k'araso gidan su mufidah ,tana gama parking afnan ta fita da gudu daga cikin motar ta nufi cikin gidan da kallo mufidah ta bita tana murmishi kafin ta fito tabi bayan ta. A jikin umma d'are d'are mufidah ta hango afnan tana mata hira umma na dariya "Wash Allah na umma nagaji " Kallon ta umma tayi kafin tace " sai kace wadda tayi wani aikin ko tafiyar k'asa" D'an dariya mufidah tayi kafin tace Allah umma yanxu bana samun wani hutu sai week end kullum cikin aiki nake " Ta6e baki umma tayi tana cewa " ae ni da wannan aikin gwara kiyi aure don ni nafison hka daman can nafi k'aunar kiyi auren ki " Tuni mufidah ta 6ata rai shi yasa wani lokacin take dad'e wa bata xo gida ba saboda kullum zancen umma tayi aure ita kuwa sam aure ya fita a kanta bata sha'awar yin shi kwata kwata tun da har ta rasa managarcin miji irin sadeeq. Tashi tayi ta nufi bedroom d'in ta umma ta bita da kallo idan da sabo ta saba da hkan da mufidah take nuna mata sam yarinya bata kaunar kayi mata maganar aure idan tana fara'a yanxu sai ta birkice maka kamar mai jinnu. "Umma bari naje wajen Aunty nabilah mu yi wasa da muhibbat" Maganar da afnan tayi ta dawo da ita daga tunanin da ta fad'a,shafa kanta umma tayi tare da cewa "Okay sai kin dawo " Da d'an gudun ta afnan ta fita tayi side d'in su muhibbat, ganin hka yasa umma ta mik'e ta nufi bedroom d'in da mufidah ta shiga kwance ta same ta rigingine tana tunani idanun ta suna lumshe but hawaye yana fita daga idon ta. Girgixa kai umma tayi tare da xama a gefen ta ta sanya hannu ta dafa ta ,bud'e idanun tayi a hankali tana kallon umma idanun ta sun yi ja sosai ,kallon ta umman take xuciyar ta cike da tausayin 'yar ta ta tace "Tashi mu yi magana mufidah" A hankali ta tashi xaune kanta a sunkuye tana wasa da 'yantsun hannun ta kallon ta umma ta sake yi kafin tace "Kina ganin kamar na tak'ura miki da maganar aure koh?" Girgixa kai mufidah tayi cigaba da magana umman tayi tana cewa " ni nafison naga kin yi aure mufidah shekara wajen uku da rasuwar mijin ki ace har yanxu kin k'i bawa wad'anda suke son ki dama su fito ki xa6i wani kuyi aure?" Shiru mufidah tayi kanta a k'asa hawaye suna fita daga idanun ta gaba d'aya xuciyar ta babu dad'i wani irin abu take ji ya tsaya mata a mak'ogaron ta yak'i tafiya bakin ta yayi mata nauyi sosai ta yanda ta kasa bud'e bakin ta don tayi magana, hankalin ta ya tashi sosai ita a yanxu wa xata kalla da sunan masoyi ta aure shi ya xama miji a gare ta?........... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM *PAGE 38* Sauke ajiyar xuciya kawai take don gaba d'aya ta rasa ta yanda xata furta wa umma ta fahimce ta ita fa auren ne bata son yi a barta tayi renon afnan ita kadai ta ishe ta. "Kiyi hak'uri ki fitar da sadeeq daga cikin xuciyar ki don ya tafi har abada baxai dawo ba, don hka ni dai a matsayi na na mahaifayar ki ina mai baki shawara akan yin auren ki shi yafi miki alkhairi " Tana gama fad'in hka ta fita daga d'akin, sai a lokacin mufidah ta samu wani kuka mai k'arfi ya kubce mata ita ya xata yi yanxu, tana cikin kukan nabilah ta shigo d'akin don afnan ta fad'a mata da mameen ta suka xo, ganin mufidah tana kuka sosai yasa nabilah tace "Subhanallah mufidah me yafaru kike kuka lafia?" Duk wad'annan tambayoyin nabilah tayi mata su cikin damuwa tana mai dafa kafad'ar ta, kasa magana mufidah tayi sai da tayi kukan ta sosai tukunna ta shiga toilet ta wanke fuskar ta tare da fitowa. Inda ta bar nabilah a xaune hka taxo ta tarar da ita xama tayi agefen ta tana sauke ajiyar xuciya, cikin yanayin damuwa nabilah tace "Fad'a min abin da yake damun ki ?" Cikin sanyin murya mufidah tace "Nabilah na rasa ta yanda xan fahimtar da umma bana son yin aure amman ta tak'ura min sai nayi aure na rasa yanda xan yi wlh" Ta k'arasa fad'in hka kwalla na sake xubo mata idanun ta akan nabilah don yanxu ita mafita take nema na yanda xata xame umma ta dai na yi mata maganar aure kwata kwata . Sauke ajiyar numfashi nabilah tayi kafin tace "Ehh gaskiyar umma kuwa nima ina bin bayan ta wlh don duk uwa ta gari tana son taga 'ya'yan ta sun raya sunnar Annabi (saw), suna da auren su hkan shi xai fi kwantar mata hankali tasamu nutsuwa" Wani kallo mufidah take watsa wa nabilah, murmishi tayi tare da cewa "Harare ni da kyau mufidah gaskia ce na fad'a ke kan ki sai mutane sun fi girmama ki idan suka san da auren ki nima shawara ta awajen ki kiyi aure" "Da kyau nabilah gwara ki fad'a mata taji amman daga fad'a wa mutum gaskia ya xauna yana rusa kuka kamar wanda aka fad'a mishi mummunan labari" Cewar umma kenan wadda ta shigo hannun ta dauke da wayar mufidah wanda take k'ara alamar kiran ta ake, mik'a mata wayar umma tayi sannan ta fita. Kafin ta d'aga kiran ya katse don hka sai tayi kok'arin kira sai gashi an sake kira picking tayi tare da sanya wa wayar a hands free cikin sanyin murya tace "Assalamu Alaikum" "Waalaikissalam Dr mufidah ina kika shiga ne?" Cewar Dr muh'd kenan,d'an murmishi yak'e mufidah tayi tare da cewa "Ina gidan mu doctor" Shima a nashi 6angaren murmishi mai k'ayatar wa ya saki tare da cewa "Yau an kaiwa su umma xiyara kenan ?" "Ehh wlh yanxun ne babu cikakken time sai week end" Cewar mufidah tana kallon nabilah da ta xuba mata ido kamar ta samu tv, "Hkne, ina afnan ban ji motsin ta ba?" D'an yamutsa fuska tayi tare da cewa " tana palour suna wasa da muhibbat " "Okay ashafa min kanta xuwa dare xan shigo na kwana biyu ban shigo ba" "Okay Allah ya kawo ka lafia" "Ameeen byeee" Yana gama fad'in ya katse wayar, d'an hararar nabilah tayi ganin yanda ta xuba mata ido kamar yau ta ta6a ganin ta a duniyar. " wannan kallon fah na lafia ne?" "Hmm mamaki kika bani ina kula da take taken muh'd alamar son ki yake ganin yanda yake kaffa kaffa dake" Hararar ta mufidah tayi kafin tace "wa ya fad'a miki muh'd sona yake ?" "Uhm alama na gani kuma insha Allah sai hashashena ya xama gaskiya, idan muh'd ya aure ki da kin more miji kamar sadeeq shima alamun shi ba ruwan shi ba kamar mutumin mu ba musaddiq" Daure fuska mufidah ta sake yi kuma gaban ta ya fad'i jin sunan musaddiq kafin tace " hashashen ki kuwa baxai ta6a yiwuwa ki ma daina fad'a " "Dalla can malama idan bai yiwu da muh'd ba sai a had'a da musaddiq, ni wlh nama fison ki auri musaddiq don kun fi dacewa sosai ya Allah kasa xance na ya xama gask......." Kafin ta k'arasa fad'in gaskia mufidah ta kawo mata duka da hannun ta cikin fusata ae kuwa da sauri nabilah ta tashi tare da matsawa gefe ta cigaba da magana tana kallon irin kallon da mufidah take mata abin dariya ma yake bata "Daga yin fatan alkhairi sai ki kawo min duka malama don kin samu ma ina....." Tuni ta tsai da maganar da take ta fita daga d'akin da gudu ganin yanda mufidah ta tashi tana huci ae kuwa ita ma ta rufo mata baya da gudu. Sai ganin su umma tayi da gudu sun shigo palon a tsorace umma ta tashi tana cewa "Lafia me yafaru?" Tuni nabilah ta shige bayan umma tana 6uya tare da cewa "Umma daga yi mata addu'ar fatan alkhairi kawai ta biyo ni xata doke ni " Murmishi umman tayi tare da kallon mufidah wadda take sauke numfashi da sauri da sauri tana hararar nabilah sosai ta bawa umma dariya sai dai ta danne tare da cewa "Ke kuma daga yi miki fatan alkhairi sai ki doki mutum bayan godiya ma ya kamata kiyi mata" "Umma kinsan abin da ce min kuwa?" Cewar mufidah tana xum6uro baki " a'a sai kin fad'a " "wai wai hka tace..." Sai kuma tayi shiru tare da yin kwafa ta shige bedroom a fusace. Lokaci d'aya umma da nabilah suka kwashe da dariya kamar ba surukai ba tukunna nabilah take fad'a mata abin da tace wa mufidah girgixa kai kawai umma tayi cikin xuciyar kuwa tana mai fatan Allah ya bawa 'yarta miji nagari kamar sadeeq. Dakyar nabilah ta rarraso mufidah har ta fito xuwa parlour suka cigaba da hirar su,har xuwa lokacin da Abba da Yah Omar suka dawo daga aiki bayan sun gaisa suka had'u suna ta6a hira. Sai wurin 6 na yamma mufidah da afnan suka bar gidan, lokacin da suka dawo sosai mumy tayi farinciki daman duk gidan yayi mata girma ba en hira. Sai bayan mangarib sannan muh'd ya xo sun yi hira sosai da mufidah kafin daga k'arshe ya xube wa su mufidah da afnan kayan shopping d'in da yayi musu har wurin mota mufidah ta raka shi kamar wasu masoya suka yi sallama ya tafi. Bayan sun gama yin dinner ne ta nufi bedroom d'in ta wanka tayi wa afnan ta shirya ta cikin sleeping dress ta kwantar da ita tare da yi mata addu'a ta lullu6e ta da blanket, tukunna ta nufi toilet tayi nata wankan ta gyara jikin ta cikin kayan bacci sannan ta kwanta tare da yin addu'a ta janyo afnan xuwa jikin ta rungume ta tayi tare da fad'a wa kogin tunani wanda ya xame mata jiki tun bayan rasuwar sadeeq murmishin shi maganar shi take tunano wa da hka bacci mai nauyi ya dauke ta. ************ Dare ne sosai wajen misalin karfe 2 na dare wani mummunan mafarki musaddiq yake wanda ya haddasa mishi farka wa a matuk'ar firgice ga wani uban gumi da ya had'a xuro kyawawan k'afafun shi yayi k'asa yana xaune kan bed din tare da dafe kan shi da yake matukar sara mishi da ciwo. Hasken d'akin ya kunna ko ina ya haske d'akin dafe kanshi yayi yana tunano mafarkin da yayi, mufidah ya hango xaune cikin wani kyakkyawan garden tana xaune tasha kwalliya cikin wata red gown mai siririn hannu gashin ta yasha gyara ta sake shi bayan ta bata sanya ribbon ba dariya take tana watsa wasu kyawawan furanni red colour's sama suna dawowa jikin ta sai dariya take mai ban sha'awa. Kok'arin k'araso wa wajen ta yake shima yana wani murmishi but ya kusan k'araso wa don bai fi sauran taku uku ba sai kawai ganin wani yayi ya k'arasa inda take ya mik'o mata hannun shi ta sanya nata a cikin nashi. D'agowar da xai yi mutumin musaddiq ya hango fuskar shi tuni jikin shi ya dauki rawa wani gumi ya jik'e shi hankalin shi yayi masifar tashi ganin fuskar muh'd, kafin yayi wani yunk'uri tuni sun bar wajen. Shine ya tashi a firgice gaba d'aya ya rud'e kada wannan mafarkin nashi ya xama gaskia idan hka ne kuwa da shikenan ya mutu, baisan son mufidah gama da xuciyar shi ba sai yanxu wani masifafen kishin ta yake ji a xuciyar shi yasan yanxu hka suna can suna soyayya da muh'd tun da yasan ba irin rarrashin da muhd bai yi mishi ba kan ya amince ya aure ta ya tubure yak'i yarda har yayi fushi dashi sai dakyar ya rarrashe shi ya sakko daga Fushin da yayi. So shine ya samu hangar nuna mata so anya muh'd ya san irin adadin son da yake yi wa mufidah ya dauki alkawarin baxai rasa ta a karo na biyu ba ya xama dole ya tattara ya koma Nigeria (hmmm reader's kuji musaddiq da wani tunani ko yaushe muh'd yace mishi son mufidah yake, kuma da bakin shi ya fad'a wa muh'd d'in kan cewa baxai ta6a iya aurar matar da yayan shi ya mutu ya bari ba, muje dai xuwa akwai gwarama). Ranar kuwa musaddiq bai iya wani koma wa wani bacci ba ya xurfafa a tunani son mufidah ya dawo mishi sabo fil acikin xuciyar shi gaba d'aya gani yayi garin yak'i saurin waye wa don ya matsu yaga ya fara tattara inashi inashi xuwa nigeria auren mufidah xai yi ko tana so ko bata so shi dai ya ganta ta xama mallakin shi ba wanda xai iya auren ta idan yaso sai ya auri wata yayi xaman auren da ita, mufidah kuwa ta rik'e mishi afnan tana kula da ita. Bayan gari ya waye ko breakfast bai iya yi ba tuni yayi booking din jirgi don hka yanxu shirya kayan shi yake yana cikin hka yaji wayar shi na ringing ganin sunan muh'd yasa musaddiq sakin wani wawan tsaki don gaba d'aya wani bala'in haushin muh'd d'in yake, sai da yayi 3 missed call's a na hudun ne ya dauka ko magana bai iya yi ba sai muh'd d'in yace "Ya guy dafatan kana lfy?" Dakyar ya iya bud'e baki yace "Qlau nake " D'an murmishi muh'd yayi ganin yanda musaddiq yake amsa mishi maganar. "Yau na tashi cikin farinciki Friend kasan abin da ya faru?" Sai da musaddiq ya ta6e baki kafin yace "Ina fa xan sani ina nan" Ya fad'a yana yatsina fuska don hirar da muh'd ta fara Isar shi, gid'a kai muh'd yayi kamar yana ganin shi yace "Kuma hkane fah, aboki ka taya ni murna mufidah ta amince xata aure ni yanxu hka ma iyaye sun shiga maganar" Daskare wa musaddiq yayi awurin ko motsin kirki ya kasa yi....... _toh reader's ku jira ni xuwa pagen d'in gaba don kamar yanda musaddiq ya daskare hka nima na daskare saboda tsabagen yanda maganar muh'd ta rud'a ni_ Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM _my Asy khaleel ina taya ki murnar xagayowar ranar haihuwar ki Allah k'ara shekaru masu albarka ya kare ki daga sharrin mak'iya, ina kuma taya ki murnar fara new nvl d'in matar fayrouz yanda kika fara lafia Allah ya baki ikon gama shi lafia ni d'in taki ce Aishat ke miki fatan alkhairi._ *PAGE 39* Daskare wa musaddiq yayi awurin ko motsin kirki ya kasa yi saboda tsabar mamakin abin da muh'd ya fad'a mishi gaba d'aya jin shi yake kamar mafarki ne xai farka yanxu, amman yana rok'an Allah kada ya k'ara nuna mishi wannan mummunan mafarkin har abada. Amman jin sautin muryar muh'd yana fad'in "hello friend kana jina ?" Yasa shi tabbatar da ba mafarki yake ba gaske ne, kafafun shine suka kasa daukar shi yasa shi xube wa akan lallausan carpet d'in da yake tsakiyar d'akin, Lokaci d'aya wani axababben ciwon kai ya tsarga mishi gumi ne ta ko'ina yake kamar wanda yake tsakiyar rana mai xafin gaske. Ya rasa tunanin da xai fara saboda yanda gaba d'aya yaji brain d'in shi ta tsaya da aiki,a hankali wayar ta subce daga hannun shi ta tarwatse a k'asa yana jin muryar muh'd yana mishi magana but bakin shi yayi matukar yi mishi nauyi ya kasa tunanin kalma d'aya da xai furta. Ya kai wajen mintuna 50 a hka baisan me yake ciki ba don shi wani time d'in yana daukan mafarki ne nan da anjima xai farka, yana kwance rgingine hannun shi d'aya dafe da kanshi wanda yake mishi ciwo sosai yana jin yanda phone's din shi suke k'ara alamar kira but bai da k'arfin tashi har ya dauka yayi magana. "Aboki ka taya ni murna mufidah ta amince xata aure ni yanxu hka ma iyaye sun shiga maganar" Maganar da muh'd yayi mishi take mai kuwwa akunne tamkar yanxu yake mishi, lokaci d'aya wani k'arfi yaxo mishi ya yunkura ya tashi xaune cikin karfin sautin magana yace " Nooo muh'd kada kayi min hka kasan yanda nake son mufidah kafi kowa sanin halin da na shiga lokacin da Yah sadeeq ya aure ta kafi kowa sanin son da nake mata daga karshe abin da xaka saka min dashi " Sai kawai ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi xuciyar shi tana wani irin bugawa da sauri da sauri wani irin yanayi ya shiga lokaci d'aya dakyar ya iya saita kanshi ya lalubo addu'a a bakin shi yana yi hawaye na xuba daga idanun shi. A hankali ya fara jin nutsuwa tana saukar mishi xaxxa6i kuma mai xafin gaske ya rufe shi kudundune wa yayi a waje d'aya ya takure jikin shi kamar wani yaro k'arami, can kuma sai naga ya saki wani murmishin yak'e yana cewa "Muh'd mace baxa ta had'a mu baxa ta iya raba amincin dake tsakanin mu da kai ba na bar maka mufidah har abada gwara na bi Yah sadeeq nima don na huta da wannan duniyar tamu mai cike da tashin hankali" Hka yayi ta sumbatu shi kad'ai har wani nauyayyen bacci ya dauke shi a wurin da ganin baccin kasan ba wani jin dad'in shi yake ba. Bai farka ba sai yammaci sosai bathroom ya shiga yayi wanka tare da daura alawala ya fito jallabiya white ya xura tare da gabatar da sallahr da ake binshi bayan ya gama ya kwanta kan abin sallahn yana tunanin ta yanda xai fitar da mufidah daga cikin xuciyar shi gaba d'aya ya huta ma yana tunanin hawaye suna xuba daga idanun shi. Wayar shi ce ta dauki k'ara akaro na ba adadi sunan mumy ne akan screen d'in picking d'in wayar yayi tare da sawa a hands free cikin sanyin murya mai tattare da damuwa ya gaida mumyn, jin muryar shi da tayi a hka sai taji hankalin ta ya tashi don hka tace "My son what happened to u naji voice d'in ka very cool ?" "Mumy ba wani abu just ina fama da ciwon kai ne throughout ko fita ban yi ba" "No son da akwai damuwa a tattare da muryar ka, fad'a min matsalar ka baka da wadda ta fini don hka tell me " Shiru yayi ya kasa sanar da ita abin da yake damun shi ,to mai xaice mata shi? Yana son matar Yah sadeeq nooo baxan iya fad'a miki ba mumy never! wannan abin kunya ne na bud'e baki na fad'a. "Son ina sauraren ka fah" "Mumy I don't know, just sometimes ina yawan tunanin ku ne kewar ku ce take damuna" Shiru mumy tayi acikin xuciyar tana mai mamakin d'an nata da kafiya akan abin da yake so tasan dalilin shiga damuwar shi saboda muh'd xai auri mufidah, amman sai ta basar tace "Okay son kadai na damuwa kaji bana son ganin ka cikin damuwa " "Okay mumy ina daddy da afnan?" D'an murmishi tayi kafin tace "daddy yana nan qlau hka ma afnan" "Kusan 2 day's bamu yi waya fah ya daina damuwa da ni ko mumy?" Er dariya tayi mumy kafin tace "daddy yana damuwa da rashin d'an sa mana yanxu hidima ce tayi mishi yawa " Cikin mamaki yace "wacce hidima ?" "Hmm ta aure mana xai aurar da 'ya'yan shi guda uku nan da two week's" "Wanne 'ya'yan shi kuma mumy?" Musaddiq ya tambaya cikin matukar mamakin abin da mumy tace "Ohhh ya Allah daman bai fad'a mata ba mun xa6a maka matar da xaka aura sannan kuma muh'd da mufidah sun had'a kansu xasu yi aure" Tun da mumy ta fara maganar musaddiq ya xama kamar mutum mutumi don ko kwakkwaran motsi ya kasa yi kafin kuma yace "What! Mumy ni xaku yiwa aure da yarinyar da ban sani ba?" "Yes! son kak'i mai da hankali wajen xa6ar macen da xaka aura don hka a matsayin mu na iyayen ka mun xa6a maka mace mai tarbiyya da ilimi wadda xata xauna da kai tsakani da Allah" Jin shiru musaddiq bai yi magana ba yasa mumy tace "Hello son are u on the line?" Musaddiq wanda hawaye suke xarya akan fuskar shi yasa hannun shi ya gobe tare da saita muryar shi yace "Mumy ngde da xa6in ku hak'ik'a ina alfahari da ku matsayin iyaye na nasan baxa ku xa6a min abin da xai cutar da ni ba Allah ya saka muku da mafificin alkhairi" Gaba d'aya jikin mumy yayi matukar yin sanyi da abin da musaddiq yace mata idan ba hka suka yi mishi ba baxai yi aure yanxu ba ita kuma tana son ganin jikokin ta da yawa yanda Allah bai basu yawan haihuwa ba tana rokan Allah ya bawa musaddiq 'ya'ya da yawa, ajiyar xuciyar ta sauke a hankali cikin sanyin murya tace "Ameeen son Allah yayi maka albarka ya baku xaman lafia da matar ka naji dad'in yi mana biyayya da kayi Allah ya baka yara masu yi maka biyayya ina alfahari da ke, insha Allah duk wani farincikin ka da walwalar ka suna daf da dawowa kamar da ka kwantar da hankalin ka son" A hankali ya bud'e bakin shi yace "Ameeen mumy" A cikin xuciyar kuwa cewa yayi mumy yanxu na fara shiga damuwa wane kwantar da hankali xan yi kuma bayan na rabu da farinciki na muradin raina. Da hka suka yi sallama da mumy, yana ganin kiran muh'd but yak'i daga wayar daga karshe ganin yak'i dauka yasa muh'd rubuta mishi text message kamar hka," _My Friend ka dauki waya na please kasan kuwa halin da nake ciki da kin daga waya ta da baka yi ina cikin damuwa aboki?_ Wani tsaki yaja bayan ya gama karanta wa gaba d'aya wani irin haushin muh'd yake ji, shi yasan damuwar da ya jefa xuciyar shi yasan me yaji lokacin da yake fad'a mishi xai auri mufidah kuwa?, reply yayi mishi da cewa " _kayi hak'uri aboki baxan iya daukan wayar ka ba sai xuwa wani d'an lokaci akawai dalilin hka kada ka damu, Allah ya tabbatar da alkhairi a auren ka"_. Yana gama typing d'in message d'in yayi sending bayan ya tafi sai kawai yayi switch off d'in duka phone's nashi ,tukunna ya kwanta yana jin wani irin yanayi atattare dashi shi kenan na rabu da mufidah a karo na biyu na dad'a yin sake kuma nasan wannan saken da nayi na har abada ne, wasu sababbin hawayen ne masu xafi suke fita a idanun shi.......... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM *PAGE 40* A wani matuk'ar tashin hankali da firgici mufidah ta mik'e tsaye hawaye na fita a idanun ta tana mai girgixa kanta saboda tsabar shiga rud'u da tashin hankali ta kasa magana sai girgixa kai, mumy ce ta tashi tare da rik'o hannun ta xaunar da ita tayi tare da goge mata hawayen fuskar ta da suke xuba da tissue d'in da xaro amman kamar bata goge wa saboda hawayen basu tsaya ba. Kunnen tane suke amsa kuwwar maganar da abban ta ya gama yi mata yanxu bayan sun gama gaisa ne dashi da umman ta ga mumy,daddy a xaune a palourn sai ita ya fara da cewa "Mufidah na gaji da yi miki magana akan ki tsaida hankalin ki waje d'aya ki fitar da mijin aure, wajen shekara hud'u da mutuwar sadeeq baxa kiyi hak'uri ki kwantar da hankalin ba, kalli iyayen shi da suka haife shi sun rungumi kaddara sun hak'ura tsakanin su sai dai addu'a kuma nasan duk son da xaki nuna mishi bai kai iyayen shi ba" Palourn yayi tsit baka jin motsin komai, mufidah tun lokacin da Abba ya fara magana hawaye suke tsere a fuskar ta gaba d'aya ta rasa tunanin yi taya xasu fahimce ta ne?, ita fah gaba d'aya auren ne bata so wa xata aura ita yanxu babu wanda ta ta6a tsaya wa dashi da sunan xance duk wadanda suke son ta bata sauraren su. Cigaba da maganar shi Abba yayi bayan ya ajiye numfashi yace "Ganin kin k'i tsayar da mijin aure ne yasa na yanke hukuncin neman wadanda suke xuwa neman auren ki, na sanar da Alhj Abubakar hkn da ya tara su mai auren ki da gaske ya turo manyan shi ayi magana, sai kuma kafin hka Dr muh'd yaxo mana da xancen yana son ki xai aure ki shine nan take muka aminta tun da munsan ko wane muh'd don hka ba wani 6ata lokaci muka tsayar da bikin nan da sati biyu" A matuk'ar gigice ta d'ago kanta tare da kallon abban idanun ta na xubar da hawaye cikin rawar murya take cewa "Ab......Abba ka....ka rufa min asiri don Allah kada ka aura min muh'd ni sam bana son yin aure, mumy, daddy ku bawa Abba na hak'uri" "Inaaa mufidah lokaci kuma ya k'ure don baxan yi magana biyu ba kiyi hak'uri ki cigaba da addu'a kawai amman auren ki kamar anyi angama ne" Shine fa ta mik'e tana girgixa kanta ta kasa maganar ma har mumy ta rik'o ta tare da xaunar da ita, cikin tsananin tausayin mufidah daddy yace "Ya kamata aboki atausaya mata kabar ta a hankali ta xa6i wanda take so" Girgixa kai Abba yayi tare da cewa "baxai yiwu ba Abubakar idan ba hka nayi mata ba baxa ta shiga taitayin ta ba " "Kwarai kuwa wannan hukuncin shine dai dai " Cewar umma yayin da mumy ta janyo mufidah suka fita xuwa d'akin ta nan ta rarrashe ta dakyar tayi shiru kukan ya koma na xuci sai ajiyar xuciya take idanun ta sun kumbura sunyi ja hka fuskar ma tayi jawur da ita saboda tsananin kuka, wani axababben ciwon kai tare da wani xaxxafan xaxxa6i ne ya rufe ta ruf lokaci d'aya. Tun daga lokacin mufidah ta dai na walwala rai a junkushe ko dayaushe bata da wani abin sai dai ta kule cikin bedroom tana aikin tunani da kuka,sosai afnan ta shiga damuwa ganin yanda mameen ta ta canja gaba d'aya ko irin wasan nan da take mata yanxu ta daina, lokaci d'aya mufidah ta wani rame ta xabge ko cikakken abinci bata iya ci sosai, xuwa hospital ma Abba yace ta dakata da xuwa sai bayan anyi auren idan mijin ya yarda sai ta cigaba. Shi yasa yanxu bata fita ko'ina daga d'aki sai d'aki mumy itama duk ta shiga damuwa saboda tana matuk'ar son mufidah batason tana ganin ta cikin damuwa,kullum cikin rarrashin ta take, gashi a wannan lokacin kusan kullum sai tayi mafarki da musaddiq fuskar shi dauke da tarin damuwa abin ya fara bata tsoro yanda ita ba wani sashi a ranta tayi ba mance wa take dashi sai ko mumy,afnan da muh'd sun ambaci sunan shi take tunawa dashi. A wannan time d'in tsakanin musaddiq da mufidah baxan iya fad'a muku wanda yafi shiga damuwa ba, shi musaddiq tunanin rabuwa da mufidah yake wanda sonta har yanxu d'awainiya yake dashi ko raguwa bayayi ga kuma auren da su mumy suke shirin k'ak'aba shi tabbas duk yarinyar da tayi gigin auren shi har ya mutu baxa ta ta6a jin dad'in aure dashi ba, don xuciyar shi babu son wata d'iya mace sai mufidah xuciyar shi ta gama kar6ar so akan mufidah ta rufe wannan shafin, yasha rashin lafia sosai don sai da ya kwanta a hospital na tsayin wajen kwana ki uku saboda ciwon shi da ya tashi yasha wahala ba kadan ba duk ya rame abin tausayi. Duk sintirin da muh'd yake a gidan har ya karaci xaman shi ya tafi baxai ga k'eyar mufidah ba abin ya fara damunshi ko wayar shi ta daina dauka sam hka idan yayi mata message babu reply ko d'aya tana sani take hkan saboda tana son ya fahimta bata son shi bata kaunar auren shi. Mumy ce xaune a parlour kallo d'aya xaka yi mata ka fuskanci tana cikin tsantsar damuwa,yau wajen kwana ki 5 bata yi waya da musaddiq ba abin yana damun ta sosai ko yaushe wayar a kashe, hannun ta ta sanya ta dauko wayar ta number d'in musaddiq ta sake try cikin sa'a taji wayar ta shiga sai lokacin taji hankalin ta ya kwanta,ajiyar xuciya ta saki ta kwanciyar hankali jin ya dauki wayar muryar shi ta ratsa cikin kunnen ta bayan ta amsa gaisuwar da yake mata cikin sanyin murya tace "Musaddiq saboda mun xa6a maka wacce xaka aura shine ka kashe wayar ka koh?" "Sorry mumy ba haka bane ayyuka ne suka yi min yawa, ya daddy da baby afnan?" Jikin mumy ne ya k'ara yin sanyi sam bata yarda da abin da yace ba kawai sai dai ta bishi a haka bakin ta yayi mata nauyi dakyar ta iya bud'e shi tace "Suna lafia musaddiq, yaushe xaka shigo nigeria nan da 7 day's ne daurin auren don ranar Friday xa'a d'aura?" Girgixa kai yayi kamar tana ganin shi kafin ya bud'e baki yace "nooo mumy ba saina xo ba idan aka gama bikin kawai ta xauna a wurin ki nan da next month xan xo insha Allah" "Toh shikenan son Allah yayi maka albarka ya tsare min kai" "Ameeen mumy, banji motsin afnan ba hala batanan"?" D'an murmishi mumy tayi tare da cewa "tana wurin mameen ta mufi......" Kit taji wayar ta tsinke duba wa tayi taga ba kudin tane suka kare ba sake kira tayi sai tak'i shiga ta dauka network ne sai kawai ta ajiye wayar yanxu hankalin ta ya kwanta tun da taji muryar shi. Shi kuwa musaddiq a nashi 6angaren kuwa yana sa ni ya katse wayar bata k'arasa magana ba,saboda jin ta ambaci sunan yarinyar da baxai ta6a mance ta a rayuwar shi yarinyar da akan ta ya fara so kuma itace ta karshe lallai mufidah *ITACE KADDARAR SHI*, hannun shi ya sanya ya dauko diary d'in shi rubutu yayi wadanda basu wuce layi shida ba ya rufe littafin ya ajiye kwanciya yayi tare da lumshe idanun shi tunano fuskar mufidah yake tun lokacin da suka fara had'u wa a lecturer hall har xuwa ganin ta da yayi kafin ya taho Australian. Kwanaki na tafia lokuta ma hka suna tafia kamar kiftawar ido, a hka lokacin bikin ya fara k'arato wa yanxu ya rage sauran kwana ki hud'u, duk wasu shirye shirye su mumy,daddy,Abba,umma dasu muh'd suna gabatarwa ban da mufidah da musaddiq wadanda kowannen su aciki basa farinciki ko kad'an da bikin kowannen su takan shi suke, shi yasa basu wani had'a party ba daga walima sai dinner party wadda xa'a yi har da iyaye wanda abokin Dr muh'd ne ya shirya mishi. Daddy ne ya had'a lefe na gani na fad'a ya kashe kudi sosai a ciki abin sai wanda ya gani don fad'in yanda haduwar kayan suke 6ata lokaci ne, na mufidah kuwa mumy ko marmarin nuna mata bata yi ba ganin halin da take ciki na damuwa da tashin hankali sai ta killace mata shi waje d'aya don ko gyaran jiki ma ba'a bi takan shi ba don ba cikakkiyar lafia ce da ita ba, yanda mufidah ta koma ba k'aramin tsorata mumy yayi ba don hka ta kirawo umman mufidah don taxo taga halin da take ciki, amman sam umma taki xuwa sai waya da tayi mata tana yi mata fad'a sosai akan saboda aure xata nemi cutar da kanta to tun wuri ta fitar da damuwa a ranta aure babu fashi sai anyi shi insha Allah idan batasan abin da ya kamata ba su sun sani shi yasa suka xa6a mata abin da yafi dai dai a rayuwar ta....... Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM *PAGE 41* Mufidah sosai ta shiga damuwa da abin da umma tace mata duk ta sake xama wata iri wai muh'd ne xata aura nan da kwanaki uku xai xama mijin ta abin ba k'aramin dagula mata kwakwalwa yake ba idan ta tuna hkan, nan xata rungume picture d'in sadeeq a jikin ta tana kuka tare da sumbatun surutai idan afnan taxo ta same ta a hka itama sai ta fashe da kuka ta fad'a jikin mufidah, baxa tabar kuka ba sai taga mufidah tayi shiru tukunna kullum cikin tambayar ta take me akayi miki mamee nah? wa ta6a min ke? baki da lafia ne?, hka take jero mata tambayar but mufidah ta rasa ma amsar da xata bata sai kawai ta wayance ta shiriritar da tambayar ta ta sai ta sako wani abin da dauke mata hankalin. Ganin yanda afnan take damun kanta idan tagan ta cikin damuwa sai ta daina yin kukan a gaban ta idan suna tare sai tana daure wa suna wasan su tare kamar da, hkan ba k'aramin dad'i yayi wa mumy ba ganin yanxu tana d'an fitowa parlour ta xauna har ta shiga kitchen tana had'a musu abinci, tayi kokarin kawar da damuwar kan fuskar ta amman cikin xuciyar ta kuwa uhm abin ba'a magana wajen damuwar da ke tattare aciki. Ranar thurday su mumy suka gabatar da walima wadda ta shirya ta da kanta, sosai wajen da suka kama wajen gabatar da walimar ya had'u komai cikin tsari da birgewa akayi, malamai mata har guda uku mumy ta dauko suka baje basirar su wajen nasihohi tare da fahimtar da mutune mene aure ta hanyar koyar wa addinin islam da kuma abubuwan da ya kamata mace tana yiwa mijin ta ta 6angaren ladabi,biyayya,tsabta, kula da miji da yara tare da yanda xaki na yiwa yaran ki tarbiyya mai kyau, sosai malaman sun yi matuk'ar kokari wajen fadakar da matan da suka hallaci walimar,ae kuwa ba k'aramin k'aruwa mutane suka yi ba kuma sunsha addu'o'i a baku nan mutane saboda yanda suka fadakar, anci ansha sosai abin gwanin birge wa saboda yanda ake gudanar da walimar cikin nutsuwa sai gaf da mangarib aka tashi suka dawo gida. ******* Xaune yake acikin office d'in shi a hospital ya d'ora kanshi kan table tare da dafe kanshi da dukka hannun shi ya xurfafa a tunani sosai, idan lissafin shi dai dai ne gobe ne mufidah xata xama mallakin wani bashi ba xa kuma a aura mishi wata macen ba mufidahn shi ba. A hankali wasu hawaye masu xafin gaske suka fito daga idanun shi kanshi ne dake mishi tsananin ciwo yasa hannun shi ya dafe kan ji yake kamar xai cire saboda tsabar ciwon da yake mishi dakyar yake iya d'aga kan idanun shi a kumbure gashi sunyi ja sosai, idan ka kalli yanda musaddiq ya koma xaka tausaya mishi ba kad'an ba,abin da yasa yaxo hospital saboda a duba mishi xuciyar shi don yana jin ta ba dai dai ba. Mik'e wa yayi tsaye da niyyar xuwa wajen frige ya dauko ruwa yasha saboda yanda bakin shi da mak'ogaran shi suka bushe, sai dai ko taku uku bai yi ba yaji wata juwa ta kamashi a hankali ya fara layi kamar wadda yasha wine ko wani abin lokaci d'aya ya fara ganin wani duhu yana xiyartar shi idanun shi kafin ya ankara tuni yaji ya fara yin baya xai xube k'asa. Sai gashi an turo kofar office d'in an shigo Dr John ne ya shigo wanda shine kwararran likitan xuciya shine wanda musaddiq yaxo wurin shi, cikin sauri Dr John ya k'arasa wajen musaddiq ya rik'o shi yana cewa "Dr musaddiq what's happened?" Xaunar dashi yayi tare da kallon shi ya sake cewa "are u okay musaddiq?" Duk yabi ya wani rud'u sosai . Ajiyar wani numfashi yayi mai k'arfin gaske tare godewa Allah acikin xuciyar shi da yasa bai fad'i ba kafin kuma ya bud'e baki dakyar yace " I'm okay john, thank u for save me" D'an girgixa kai yayi tare da cewa " no thank me, thank god da ya kawo ni baka fad'i ba" Nan musaddiq yayi mishi bayanin abin da yake ji ae kuwa nan suka fita daga office d'in tare da tafiya d'akin da aka ware don yin gwaje gwaje na fannin xuciya,akan wani gado musaddiq ya hau tukunna Dr John ya sanya wasu nau'ora domin ganin yanda xuciyar shi take tare da sanya mishi wasu asaman kirjin shi, musaddiq dai kallon shi kawai yake don shi kad'ai yasan me yake ji. Bayan Dr John duk ya gama wasu binciken shi ne ya xauna tare da kallon musaddiq cikin tsananin tausayin shi yace "Musaddiq why da baka jin shawarar da nake baka kana yawan sa damuwa acikin xuciyar ka, me kake hka da har yake kokarin kashe ka?" D'an murmishin yak'e musaddiq yayi tare da cewa " uhm John wanne stage kuma yanxu nake?" "Abin naka yana neman xama worst fah musaddiq kana son jefa rayuwar ka cikin hatsari, ka bani number d'in parents naka na kirawo su don su kad'ai xan fad'a wa binciken da nayi" Girgixa kai musaddiq yayi tare da yunk'urin mik'e wa xaune da sauri Dr John yasa hannu ya mayar dashi kwancen sannan yace "Relax musaddiq kwanciya xaka yi xan yi maka allurar bacci but xan rik'e ka a hospital tukunna" Yana gama fad'in hka yayi mishi allurar toh shima musaddiq bai yi yunk'urin hanashi ba CO's yana son ya bawa xuciyar shi hutu daga tunanin mufidah, bai wani dad'e sosai ba bacci ya dauke shi a wurin ganin hka yasa Dr John fita a room d'in cikin xuciyar shi tunani fal na me musaddiq ya sanya cikin xuciyar shi hka lallai wannan abin ba k'aramin abu mai mahimmanci ne. ******** Daren ranar mufidah sam bacci duk iya satar shi bai yi nasarar sace ta ba, kwana tayi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara kuka sosai tayi shi don ita sam ba son Dr muh'd take ba just mutunci ne a tsakanin su hka take kallon alak'ar tasu ashe shi da wata manufa cikin xuciyar shi da tasani da bata bashi fuskar da xai yi tunanin auren ta ba, cikin daren ta dage da kai kukan ta gun mai dukka domin ya yaye mata matsalar ta. Washe gari da safe wajen 9 mumy ta shigo bedroom d'in mufidah hannun ta rik'e da breakfast d'in ta, taci gayun ta cikin wata shadda brown dinkin senegal tayi matuk'ar yin kyau,cikin fara'a ta k'arasa wajen center table ta ajiye abin hanjunta tukunna ta k'arasa wajen mufidah wadda tun lokacin da mumy ta shigo da suka had'a ido ta sunkuyar da kanta k'asa. Dafa kafad'ar ta mumy tayi tare da cewa " mufidah ga breakfast d'in ki nan idan kin ga kiyi wanka yanxu mai make up xata k'araso xata yi miki kwalliya, don Allah ki d'an saki jikin ki ayi komai a gama lafia kada mutane su fahimci halin da ake ciki, anjima kad'an xaki samu abokiyar hira matar musaddiq xa'a kawo ta nan kafin tafia dinner kin ji" Dummmm gaban mufidah ya fad'i sosai jin an ambaci matar musaddiq lokaci d'aya yanayin ta ya canja har mumy taso fuskantar wani abun a tattare da ita,ganin tayi shiru yasa mumy tace "Lafia mufidah kuwa?" D'an murmishin yak'e ta k'ak'alo tare da cewa "naji mumy kuma xan yi abin da kika ce insha Allah" Murmishin jin dad'i mumy tayi tare da cewa " yawwa 'yata naji dad'in abin da kika ce Allah yayi miki albarka " "Ameeen " Cewar mufidah tana kokarin tashi ganin hka yasa mumy fita daga d'akin, tana fita mufidah ta xube kan bed tare da dafe kanta tana mai cewa "Yah ilahi mai yake damu na daga ambatar sunan matar wani na shiga damuwa Ohhhh Yah Allah help me kada abin da naji ya kasan ce hka" Tana gama fad'in hka ta wuce toilet cikin sanyin jiki wanka tayi tare da yin brush tukunna ta fito shafa mai tayi tare da xura wasu kaya da taga ni saman bed daganin kayan tasan nata ne mumy ta ajiye mata . Tana cikin busar da gashin kanta da hand dryer mumy ta shigo da mai kwalliyar Masha Allah abin da mumy ta furta ganin yanda kayan suka yi matuk'ar yi mata kyau duk da ba'a yi wata kwalliya ba, "Ga wadda xata yi miki kwalliyar nan " Gid'a kai kawai mufidah ta iya yi nan da nan mai make up ta bud'e kit d'in ta ta fara yiwa mufidah kwalliya ta nutsuwa. Bayan ta gama yi mata ne taxo ta gyara mata gashin sannan ta daura mata d'an kwali tuni tayi wani irin kyau duk kuwa da ramewar da tayi hkan bai hana fidda tsantsar kyan da tayi ba, gamawar su kenan nabilah ta shigo d'akin cikin fara'a ta fara cewa "Masha Allah kaga amarya a gidan mu......." Kafin ta k'arasa fad'in ne mufidah ta wurgo mata harara toshe bakin ta nabilah tayi don kada dariyar ta fito,xama tayi kusa da ita tare da cewa "Sorry kawata murna da farinciki ne ya ishe ni yau wlh,ki saki fuskar nan don Allah ko naji dad'in sha'anin yau" Kamar da dutse take magana hka mufidah tayi mata tsit har ta karaci surutun ta tabar d'akin tana mata dariyar keta, kwanciya mufidah tayi tana jan tsaki tare da cewa "Mtsww nabilah hayaniya ta bar ni da abin da yake damuna taxo ta sani a gaba da surutu", tana nan kwance tana tunanin da ya xame mata farilla ta dora daga inda ta tsaya sai dai na yanxu ya sha ban ban dana kullum abin da yafi tsaya mata maganar da mumy tayi mata ashe har musaddiq aure xai yi don ita bata da labarin hka sai yanxu, kuma bata alamar yaxo ba ko wace matar tashi?, mtsww tana d'an tsaki ko mene nawa aciki da xan damu. Bayan an idar da sallahr juma'a karfe 2 dai dai aka fara d'aura auren musaddiq da matar shi sannan na Dr muh'd da tashi matar akan sadaki mafi cancanta don neman albarka aure,bayan an gama d'aura auren aka wuce yin reception tasu ta maxa dukka samun sauyin yanayin auren da akayi kuwa don mutane da yawa sun yi mamakin hkan don ba hka suka karanta a invitation card ba, ango muh'd kuwa sai faman washe baki yake jin shi yake wasai yau saboda sauke alkawarin da ya dauka yayi sai lokacin hankalin shi ya kwanta sosai. ******* Cikin gala6aitar xuciya musaddiq ya kwana daren da ya xame mishi daren bakin ciki daren da ya xame mishi rabuwa da mufidah na har abada daren da ya xame mishi rabuwa da abar kaunar shi kai baxan iya takaice muku bayanin wannan daren da ya xame wa musaddiq ba don kuwa gari na waye wa mufidah xama mallakin wanin shi mallakin aminin shi abokin shi tsayawa fasalta irin abin da musaddiq yaji a wannan daren 6ata Lokaci duk da kuwa kusan Dr John akansa ya kwana gaba d'aya har ya fitar da ran musaddiq saboda aman jinin da yake yi gashi yak'i bashi damar da xai sanar da iyayen shi. Har xuwa washe garin ranar musaddiq a gala6aice yake saboda tsananin wahalar da yasha ta daren jiya, yana ankare da lokacin nigeria don mummy ta sanar mishi lokacin da xa'a d'aura auren. Lokacin da 2 dai dai tayi na lokacin nigeria sai da xuciyar musaddiq tayi wani bugu tuni hawaye suka fara tsere a fuskar shi saboda yasan a wannan lokacin mufidah ta xama ta muh'd ta har Abadan,gaskia bai ji dad'in so ba baxai d'orar da dad'in so ba sai wahalar shi yarinyar da ya kusa mutuwa ma a kanta batasan yana yi ba wannan wanne irin so ne?. K'arar shigowar message yake taji cikin wayar shi mtsww yaja tsaki yasan muh'd ne yake damunshi, ganin message's d'in sai shigowa suke yasa shi mik'a hannun shi dakyar ya dauko wayar ganin message's da yawa daga number's daban daban yasa shi mamaki sosai yana tunanin masu taya shi murnar auren shi ne sai dai message d'in da daddy ya turo mishi ne ya fara daukan hankalin shi da sauri ya bud'e ya fara karanta wa abin da ya karanta bai gasgata hkan ba ya dauka idanun shi ne suke masa gixo don hka ya sanya hannun ya murxa idanun sosai ya dad'a karanta abin da daddy ya turo mishi " _Hey! Lover boy wake up! Kada ka mutu,Allhmdllh a yanxu Allah ya nufa mufidah ta xama mallakin ka ta hanyar aura maka ita,ina taya ka murna da cikar burin ka na auren ta Allah ya sanya alkhairi ya k'ara maka lafia,don nasan cutar so ta kwantar min da jarumin d'ana_" Abin da yaga daddy ya rubuta mishi kenan,da wani irin sauri musaddiq ya tashi xaune daga kan gadon gaba d'aya ya rud'e ma ya rasa me xai yi jikin shi rawa kawai yake,dakyar ya iya bud'e message na mumy ya fara karanta wa " _Allhmdllh a yau d'ana Allah ya mallaka mishi abin da yake so, ina mai taya ka murnar auren mufidah._" Wani murmishin jin dad'i ne ya su6uce mishi wanda rabon da yayi shi har ya mance,idanun shi ne suka sauka kan message d'in muh'd ga abin da yace " _Dukka godia sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala, da yaba ni ikon cika wannan alkawarin da na dauka,aboki na nasan kaji haushi na, na 6ata maka rai saboda fad'a maka da nayi xan auri mufidah har ga Allah ni ba son ta nake ba hba musaddiq taya xan so yarinyar da kake masifar so akan ta ka kamu da mummunan ciwo, baxan xama butulu a gare ka ba aboki nayi hkan ne saboda na sama maka nutsuwa da sauk'in xuciyar ka wanda kake fama da rad'ad'in shi tsawon shekaru, kayi hak'uri ka yafe min ni masoyan ka ne mai son ka da gaskia saboda nasan na saka a matsala ta rashin lafia, a yau duk wani bakin ciki da kake ciki ya kau don mufidah a yanxu ta xama mallakin ka sauran magana sai mun had'u, ina taya ka murna da samun cikar burin ka hak'ik'a kai jarumi ne ina alfahari da kai aboki, Allah ya baka lafia, sai a tashi hka daga gadon asibiti don nasan kana kai yanxu lover boy_" _duk wanda shafin nan yayi mishi dad'i naga comment's sosai don ya nuna jin dad'in shi,ga musaddiq cikin farinciki gani cikin farinciki saboda cikar burin musaddiq, ku fah?, mufidah ma ko wane hali take ciki sai ku biyo ni next page don jin abin da xai faru_. Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM LIKE AND DROP UR COMMENT'S FB PAGE #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ *PAGE 42* Musaddiq kid'ime wa yayi gaba d'aya jikin shi ba abin da yake sai tsabar rawa ga wasu hawaye da suke xubo mishi sai dai na yau sun ban ban ta dana koyaushe don yau na farinciki ne yake xuba, ji yake kamar mafarkin da ya saba ne yake yin shi yana fatan kada ya tashi daga wannan daddad'an mafarkin,amman da ya mintsini kanshi ya tabbatar a farke ne ba mafarki ba I don't believe wai mufidah yau an aura min ita what's surprise?. Sai da yayi sujjadar shukur ya dad'e a hkan yana xuba wa Allah godia da ya cika mishi burin shi na auran mufidah ta yanda bai ta6a xato ba, kasa xama yayi sai faman safa da marwa yake gaba d'aya duk gala6aitar da jikin shi yayi da rashin k'arfin da yake ji a tattare dashi tun a jiya xuwa yau, xuwa wannan lokacin wani k'arfi ne yaxo mishi wanda xamowar mufidah matar shi a yau shi yasa shi jin garau dashi,hawayen farincikin nan har yanxu dai fita suke daga idanun shi fuskar shi dauke da murmishi. Turo kofar akayi da sauri musaddiq ya juya don ganin wane, had'a ido suka yi da Dr John wanda ya saki baki da hanci yana kallon musaddiq, murmishi ya sakarwa Dr John kafin yayi mishi alama da hannu ta wannan kallon hka fah?. Gane hkan da Dr John yayi yasa shi cewa " I don't believe wai musaddiq ne a gaba na ya samu lafia " Er dariya musaddiq yayi tare da rungume Dr John cikin tsananin farinciki yace "Friend ka taya ni murna na samu mufidah" Kallon rashin fahimta Dr John yayi mishi hkan da ya gani ne yasa shi bashi labarin abin da yake faruwa dashi, kallon shi Dr John yake cike da tsantsar mamaki tare da jinjina mishi sosai daman en nigeria suna yiwa matan su irin wannan so hka har mutum ya kamu da ciwo, nan ya taya musaddiq murna kafin kuma ya sake duba shi xai kuma rik'e shi sai xuwa nan da gobe xai sallame shi,aikuwa musaddiq ya tubure shi ya warke fah gida xai tafi. Ganin ya dage baxai kuma kwanan hospital ba yasa Dr John sallamar shi yana ta tsokanar shi murmishi kawai musaddiq yake yi ,kawai idan ya tuna yanxu mufidah ta xama tashi wani farinciki ne yake ratsa cikin xuciyar shi wanda bai ta6a jin hakan ba. Yana k'arasa wa gidan shi wanka yayi tare da shirya wa cikin white 3quater and t-shirt white mara hannu bayan ya fesa perfume's a jikin shi ya dawo parlour ya kwanta jikin kujera. Hannun shi dauke da phone d'in shi yana sake karanta message's d'in daddy,mumy and muh'd yana murmishin farinciki shi kad'ai ko yunwa baya ji a cikin shi don farincikin yau ya kosar dashi,idan ya lumshe idanun shi cute face d'in mufidah yake hango wa tare da beautiful pink lips d'in ta har da wani lashe Lip's d'in shi, Lokaci d'aya kuma wani abu ya fad'o mishi a ran shi nan take fuskar shi ta nuna tsantsar damuwa duk farincikin da yake cikin xuciyar shi ya kau a Lokaci d'aya saboda tuno d'an uwan shi yayan shi sadeeq. Ya tuna sadeeq fah ya auri mufidah har sun haifi afnan shine har yake murna da auren ta, anya kuwa xai iya xaman aure da mufidah matar da d'an uwan shi yayi xaman aure da ita na tsawon wasu en shekaru, anya yayi wa kanshi adalci da auren ta, nan wani abu ya tokare me mak'ogaro ya rasa abin da yake mishi dad'i, xai xauna da ita ko don tayi mishi renon afnan saboda yarda da yayi da tarbiyyar ta yasan afnan xata samu tarbiyya mai kyau idan yaso sai ya xa6i wata baby girl d'in ya aura don biyan buk'atar kanshi don baxa ta samu so daga wurin shi ba wannan son ya rufe shi tun daga kan mufidah, nan take yayi na'am da wannan shawarar tashi sai lokacin yaji sukuni a cikin xuciyar shi abin da ya tsaya mishi a mak'ogaron ya tafi... ********** Tana xaune a bedroom sai ga nabilah ta shigo fuskar ta dauke da tsantsar farinciki da annushuwa tana cewa "Kaga amarya a gidan Dr musaddiq nayi farinciki da wannan had'in Allah dai ya saka wa Dr muh'd da alkhairi don yayi abin da ya dace" Wata irin xabura mufidah tayi tare da mik'e tsaye har tana yin tuntu6e xata fad'i tsabar raxanar da tayi da sauri nabilah ta rik'e ta tana cewa "Hey Mr's musaddiq relax kada ki fad'i kiji ciwo a kasa cin amarci a 6ige da jinya" Kallon ta mufidah take muryar ta na rawa tace "Da gaske kike mufidah ko tsokana ta kike, don Allah kice min ba gaskiya ba ne?" Ta k'arasa fad'a hawaye na xuba a kyakykyawar fuskar ta, wani mugun tausayin ta mufidah ne ya ratsa nabilah cikin sanyin murya tace "Wlh Allah da gaske nake mufidah an d'aura auren ki memakon da muh'd sai muka ji da musaddiq abin ya bamu mamaki sosai don bamu san da hka ba" D'an dakata wa tayi tare da jan numfashi ta dafa kafad'ar mufidah da hannun ta tare da cigaba da cewa "Sai da mumy tayi kiran mu da umma tayi mana bayani, ashe lokacin da sadeeq yake daf da mutuwa ne ya barwa muh'd wasiyya akan idan ya mutu don Allah kada ki auri kowa sai musaddiq don yasan idan ya aure ki baxa ki da nasani ba kuma afnan xata tashi a hannun iyayen ta biyu wato ke da musaddiq, shine muh'd ya rasa ta yanda xai fad'a muku wannan wasiyyar ke da musaddiq don yasan baxa ku ta6a amince wa shine ya samu daddy,mumy,umma da Abba yake fad'a musu shine suka biyo ta wannan hanyar,amman muh'd shima a yau aka d'aura auren shi tare da matar shi kuma er uwar shi nafisat " Tuni mufidah ta 6arke da kukan bakinciki da takaici lallai muh'd ya raina mata hankali ashe manufar shi kenan shi yasa duk lokacin da yaga wani ya tsaya da ita xai mata magana idan suna tare taga yayi kicin kicin da fuska yana cika yana batsewa ashe da nashi dalilin, ae kuwa sam baxa ta ta6a yarda da wannan had'in ba auren k'anin mijin ta. Cikin fusata ta mik'e tsaye tare da juya bayan ta tace "Nabilah wannan auren sunan shi matacce" A firgice nabilah ta tashi tana cewa " me kike nufi mufidah? " Juyo wa tayi tana kallon nabilah tare da cewa "Ina nufin dole musaddiq ya sake ni baxan iya rayuwar aure dashi ba yana matsayin k'anin sadeeq sam baxan iya ba, idan auren suke so nayi gwara na xa6i wani da kaina na aura ko mai mata uku ne yaje matsayin ta hud'u na yarda da na xauna da musaddiq" Kallon mamaki nabilah take mata kafin tace "Kina nufin da ki xauna da musaddiq gwara ki aure mai mata uku?" "Kwarai da gaske " Mufidah ta fad'i hkan , "lallai na yarda har yanxu akwai sauran kuruciya a tattare da ke mufidah ki godewa Allah, Allah ya baki miji tamkar da dubu wanda ko aure bai ta6a yi ba kice bakya so haba mufidah" Wata harara mufidah ta watsa mata tare da jan tsaki mtsww ta xauna a gefen bed tana fashewa da kuka kuma lokaci d'aya don jin yanda wani abu ya tokare mata a mak'ogaron ta wanda ta rasa na mene, xama nabilah tayi kusa da ita tare da cewa "Kada ki manta mufidah wannan wasiyyar sadeeq ce baya duniyar nan a matsayin ki na mijin ki wanda kike matuk'ar so mutuwa ta raba tsakanin ku ya bar wasiyya baxa kiyi kok'arin cika mishi ita ba ko mai wuyar ta kuwa,wannan auren da kuka yi da musaddiq shi xai tabbatar wa da mutane Cewar ke mai kaunar sadeeq ce ta hak'ik'a tun da har kika iya cika mishi alkawarin shi kuma sadeeq xai matuk'ar alfahari da ke, ni a matsayin na kawar ki aminiyar ki ina mai baki shawarar ki tsaya kiyi tunani sosai kafin ki xartar da hukuncin da xuciyar ki take ingixa ki da kiyi" Tana gama fad'in hka ta mik'e ta fice daga bedroom d'in wani 6angaren xuciyar ta cike da tausayin mufidah wani 6angaren kuma haushin ta take ji na hukuncin da take kok'arin yankewa don tafi kowa farinciki da jin wannan auren, "Yah Allah kada ka bawa shaitan xuga mufidah ta hanyar rabuwar ta da musaddiq" ta furta hkan a cikin xuciyar ta. Mufidah kuwa kuka ta rushe dashi sosai na tausayin kanta gashi nabilah tayi fushi da ita tun da har ta iya tafiya ta barta cikin damuwa ba tare da ta tsaya ta rarrashe ta ba, ina xan sanya kaina naji dad'i dana sani tun lokacin da umma ta fara yi min maganar aure na nutsu na xa6i wani cikin wadanda suke sona na aura da tuni na huta da ganin wannan matsalar,ita ina xata iya xama da musaddiq mutumin da tun farkon haduwar su basa shiri da junan su har yanxu ta ina xasu fara shirya kansu har suyi xama na fahimta kowa yana ji da kanshi. Yini tayi a d'aki ita d'aya mumy ce ma mai xuwa duba ta, nabilah kasa jure fushi da mufidah tayi don hkan bata ta6a faruwa dasu d'in ba shi yasa ta kasa sakewa dole ta shigo d'akin tana rarrashin ta tare da yi mata nasiha, sai lokacin mufidah taji damuwar ta ta d'an ragu taji sanyi ta wani 6angaren. Har xuwa Lokacin tafia dinner yayi suka shirya suka tafi mufidah ba k'aramin kyau tayi ba baka ce ta ta6a aure ba har 'ya ba, mumy baki yak'i rufuwa yau d'an ta ya samu abin da yake so xuciyar ta taf cikin farinciki, haka sauran mutane masu xuwa taya su mumy murna da fatan alkhairi. Sai yanxu mufidah taga matar muh'd nafeesat ba laifi tana da kyau gata da fara'a da hankali sai jan mufidah take da hira ita kuwa mufidah ba bakin magana da uhm sai uhm uhm, tsananin ta da muh'd kuwa mufidah harara kawai take aika mishi sai dai yayi murmishi yana girgixa kai don yasan shi mai laifi ne wajen mufidah dole ya samu lokaci idan ta huce ya bata hak'uri, har aka tashi daga wurin dinner d'in magana ta fatar baki bata had'a mufidah da muh'd na sai harara da take aika mishi, ko lokacin da ya fara yi mata magana da sauri ta bar wajen don bata buk'atar jin komai daga wurin shi. ******* Yana kwance kan bed tun da gari ya waye ya kasa tashi daga kan bed duk jikin shi a kasalance yake jin shi,dauko wayar shi yayi yana duba wa ganin message's a what's app d'in shi yasa shi shiga domin duba wa messages d'in muh'd ya fara shiga abin da ya gani ne yasa shi furta "Ohhhh my Allah nagode maka da ka mallaka min wannan fine cute baby d'in" Ya k'arasa fad'i yana dafa xuciyar shi don jin wani sabon sonta da yake shiga cikin xuciyar, pictures d'in ta ne na wurin dinner da akayi ne muh'd ya turo mishi shine yake furta hkan da ya gani. Face d'in ta ya tsurawa ido yana kallo wani abu ne yaji yana ratsa shi tun daga kanshi har xuwa kafar shi, yakai wajen mintuna 5 yana kallon ta sai kuma lokacin yaji wani uban kishi don yasan mutane da yawa sun gane mishi mata, kallon picture's d'in kawai yake ji yake kamar yayi tsuntsu ya ganshi a gaban mufidah, sai da ya kalli picture's d'in son ranshi kafin ya turawa da muh'd Cewar " _Aboki nagode sosai amman ka tabbatar ka goge picture's d'in nan a wayar ka_" Ya tura mishi ba jima wa muh'd ya turo mishi da reply na dariya kafin yace " _Hhhh sarkin kishi ae tuni na goge tun lokacin da na turo maka ba sai ka fad'a min ba, ya kamata ka dauki matar ka ko ka dawo nigeria gaba d'aya yaro don wlh aure da dad'i na baka labari yanxu hka gani rungume da sweetheart dina_" Ya turo mishi hkan tare da alamar gwalo, wani yarrr musaddiq yaji a cikin jikin shi gaba d'aya ya dauke wuta ji yayi wani abu yana ratsa shi wata kasalar ce ta sake lullu6e shi wanda dakyar ya cewa muh'd " _kai fa wani lokacin d'an air ne kai abin ya dama ni bai dame ni ba_" Ganin muh'd yana yin typing alamar akwai abin da turo ya sashi kashe datar gaba d'aya don kada ya hargitsa mishi tunani don shi kad'ai yasan abin da yake ji a yanxu dakyar ya iya tashi ya shiga toilet yana cewa "Muh'd yana neman hargitsa min tunani xuwa wani 6angare na daban wanda bai kamata ace na kasan ce cikin yanayin yanxu ba" Da hka ya sakarwa kanshi ruwa idanun shi a lumshe mufidah kawai yake hangowa............. Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM LIKE AND DROP UR COMMENTS FB PAGE #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ _Happy Birthday my billy ladan dear ina taya ki murnar k'arin shekara, Allah ya k'aro shekaru masu albarka, na sadaukar da duk wannan page d'in don murnar wannan ranar, ina miki fatan alkhairi tawan_😍 *PAGE 43* Daren ranar mufidah bata samu cikakken bacci saboda tunanin auren ta da musaddiq da aka d'aura a yau, ji take kamar a mafarki yau ita ce matar musaddiq mutumin da basa shiri da junan su, me yasa sadeeq ka furta hkan baka san ba ma shiri da juna da k'anin ka ba, taya xamu iya had'a kanmu mu yi xaman aure irin na mata da miji. Da irin wad'annan tunane tunanen mufidah bacci yayi awon gaba da ita ba tare da ta shirya yin shi ba, musaddiq kuwa ana shi 6angaren ya samu cikakken baccin wanda rabon da yayi irin shi tun lokacin da sadeeq ya furta yana son mufidah, ranar baccin shi yayi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Washe gari en uwa suka tattafi gida ya rage daga mumy, daddy, mufidah da afnan sai en aiki, duk wani motsin mufidah akan idon mumy don tana son karantar yanayin da take ciki, sai kuma aka ci sa'a mufidah ta fito xuwa parlour fuskar ta wasai da ita sai dai kumburi da d'an ja da idanun suka yi mata, wasa take wa afnan suna dariyar su sosae hkan ya faranta wa mumy rai tana mai fatan wannan auren ya dawwama cikin amincen Allah da farin ciki. Bayan sati d'aya da auren mufidah da musaddiq ne daddy yayi mata magana da ta cigaba da xuwa hospital kafin musaddiq ya dawo, ae kuwa tayi farinciki sosae da hkan a ranar kuma da dare Dr muh'd yaxo gidan tare da matar shi nafisat. Mufidah bata wani kula shi ba sai nafisat d'in suke yin hira tsakanin su har mumy ta tashi ta shiga kitchen ta barsu bayan sun gama gaisa wa. Alama muh'd yayi wa nafisat da hannu kan ta bi mumy kitchen, d'an murmishi tayi tare da Kama hannun afnan suka shige kitchen. Cikin sanyin muryar shi yace "mufidah kiyi hak'uri nasan ni mai laifi ne a wajen" D'an ta6e baki tayi kafin tace "uhm muh'd me yasa lokacin da sadeeq yake bar maka wasiyyar na auri musaddiq baka kirawo ni ba, wlh ba don sadeeq ne ya nemi da ka had'a auren mu da musaddiq ba, da tun ranar da aka d'aura auren xaka sanya a warware shi" Kallon ta muh'd yake cikin zuciyar shi yana cewa da kinsan son da musaddiq yake miki da baxa ki furta wad'annan maganganun ba, kinsan adalilin ki ya kamu da cutar da bata warke wa ina addu'a da fatan Allah ya kaimu lokacin da musaddiq xai furta miki abin da yake cikin xuciyar shi. A fili kuwa cewa yayi "nima mufidah alk'awarin da na d'aukar sadeeq shi yasa na cika shi, tun daga lokacin da aka d'aura auren naji kamar an cire min wani abu a jiki na da kaina lokacin naji hankali na ya kwanta sosae mufidah " D'an ajiyar numfashi yayi kafin ya cigaba da cewa " ina sake baki hak'uri ni dai a adaina fushi dani, sannan kuma naji daddy yayi min maganar komawar ki office ranar monday koh ? " Cikin sanyi tace "ehhh nima d'axu ya sanar da ni" "hakan yayi kyau Allah ya taimaka, tun da mun shirya a sakar min fuskar mana irin wannan d'aure fuskar ae sai ki sa na dunga rawar jiki saboda tsoro ki sa matata da mijin ki su raina ni " Dole tasa ta d'an saki fuskar da murmishi wanda har sai da dimples d'in ta suka lotsa kafin kuma ta harare shi jin ya k'arasa maganar da mijin ta musaddiq. Er dariya muh'd yayi yana fad'in ko ke fah " Nan kuma suka cigaba da Er hira har xuwa lokacin da su mumy suka fito a kitchen, sun d'an jima a gidan don sai wurin 9:30 na dare suka tafi bayan sun yi dinner har farfajiyar gidan mufidah ta rako shi suka yi sallama suka tafi ita kuma ta dawo gida. Acikin hka mufidah ta Fara xuwa hospital tana cigaba da aikin ta cikin kwanciyar hankali kuma hkan ba k'aramin d'ebe mata kewa yake ba don ta d'an rage tunani sosai. Kamar yau ranar weekend ce mufidah babu aiki tana kwance kan bed bata jin dad'in jikin ta tun safe ga wata muguwar fad'uwar gaba da take damun ta tun safe, afnan ma da ta dame ta da surutu korar ta wurin mumy tayi. Shigowa mumy tayi cikin bedroom d'in hannun ta rik'e da mayafi alamar fita xata yi, Kallon mufidah tayi fuskar ta dauke da murmishi tace "mufidah na gama shirya wa xamu tafi, na rasa dalilin da ya hana ki bin mu gashi har afnan xamu tafi " D'an murmishi mufidah tayi tare da tashi daga kwancen da take tace "kiyi hak'uri mumy kin ga ranar monday ina da aiki na safe kuma xamu yi muhimmin meeting ranar shi yasa " Da yake london su mumy da daddy xasu je wajen dubiyar wani babban abokin daddy da aka kwantar dashi acan, sun nemi da mufidah ta shirya su je ta k'i yarda kuma kwanaki uku kawai xasu yi su dawo. "kin fison dai xaman kawai naga alama, xaki xauna anan ko gidan umma xaki je? " Da sauri mufidah ta girgixa kai tana d'an waro idanun ta tace "a'a mumy yanxu xan shirya nima na tafi, baxan iya xaman gidan nan ni d'aya ba tsoro nake ji " Er dariya mumy tayi tare da Cewa ""shikenan 'yata ki kular min da kan ki sai mun dawo " Tashi tayi ta sanya hijab d'in ta suka fito parlour inda daddy yake xaune,bayan mufidah ta gaida shi ne ya amsa cikin fara'a kamar ko yaushe tukunna suka fito xuwa farfajiyar gidan suka shiga mota driver xai kai su airport. "ki kula da kan ki 'yata kin ji " Fad'in mumy a karo na biyu, murmishi mufidah tayi tana jin dad'in yanda mumy take bata kula wa tace "tohh mumy insha Allah, Allah ya kai ku lafia " "Ameeen ya rabbi " Mumy da daddy suka amsa, afnan sai d'ago wa mufidah hannu take alamar bye bye ita ma hannun ta d'aga mata har suka motar su ta fita daga gidan. Bayan ta dawo cikin gidan ne ta shige bedroom had'a kayan ta tayi wad'anda xata yi amfani dasu, sai ta d'an kwanta don ta huta har kewar afnan da mumy sun fara Kama ta. Bata ankara ba taji wani bacci mai dad'i yana fisgar ta bata yi wani 6ata lokaci ba ta gyara kwanciyar ta nan da nan bacci yayi awon gaba da ita. Yini tayi tana baccin idan ta farka ma sai taji wata kasala kafin ta tashi wani baccin ya sake d'aukar ta da yake tana period kawai sai ta koma baccin, har xuwa wajen biyar na yamma dakyar ta iya tashi ta samu tayi wanka ta gyara jikin ta cikin wata arabian abayat ash colour tayi rolling kanta da black veil tayi kyau sosai different perfumes tayi amfani dashi daga body sprays har xuwa na kaya. Sauri kawai take don ta tafi kada mangarib tayi mata, jakar da ta shirya kayan nata ta dauko tare da car keys sai phone nata, a parlour ta tsaya don jin k'amshin girki cikin mamaki ta nufi kitchen d'in. Er dattijuwar da take taimaka wa mumy ta hango tana tsaye gaban gas cikin mamaki tace "Inna wa kike yiwa girki? " Da yake ko mumy da Inna take kiran ta dattijuwa ce mai kirki, jiyo wa tayi fuskar ta dauke da murmishi tace "ah mufidah ina xuwa hka gab da mangarib ke da nake yiwa girki ganin yinin yau baki ci komai ba" "tabbb ae ni Inna nan da kika ganni sai gidan mu kuma " Rik'e ha6a tayi tare da cewa "yanxu mufidah baxa ki xauna mu yi xaman mu ba kwana uku kawai xasu yi fah " Murmishi mufidah tayi tare da cewa "na kwana biyu ban je naga ummana da abbana kewar su nake gwara na tafi can " "toh ae shikenan amman sai kin jira na gama miki girkin kici sai ki tafi " Bata son gardama da babba ba don hka ba ta fison ta tafi taci abincin umman ta, gashi innar tana sonta gata da kirki don hka sai ta ce "tohh inna ina jiran ki a parlour " "toh d'iyar kirki " Fita tayi ta koma parlour tana danna wayar ta sai daf da wurin sallahr ishsha inna ta kawo mata faten dankalin turawa da tayi mata yasha nama da su vegetables sai k'amshi yake ga lafiyayyen kunun aya mai sanyi a gefe, da yake inna tasan yanda mufidah take son kunun aya shi yasa wani lokacin take yi mata saboda kirkin da mufidah take mata. Xama sosai mufidah tayi tana cin abincin, tuni inna ta wuce 6angaren su na masu aiki, cikin abincin mufidah take cikin jin dad'in shi. Ko rabin wanda ta xubo a plate bata yi ba taji an turo kofar palourn an shigo kafin ta jiyo taji saukar wata daddad'ar murya a kunnen ta muryar da ta kusan sanya ta suman xaune ko bata jiyo ba tasan ko muryar wane ba wani ba sai *Musaddiq*, muryar da ta fara taso mata da wani kwantaccen abu a ranta, muryar da ta sanya ta tunanin abin da ya dad'e da wuce wa a wajen ta. Sam ta mance ma da sallamar da aka yi saboda duniyar tunanin da ta lulu cikin ta, wata firgita tayi tare da sakin ajiyar xuciya da k'arfi jin saukar wani abu mai shegen sanyi a jikin ta . Da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido da musaddiq fuskar nan a d'aure, ita ma mufidah d'aure fuskar tayi musamman yanda ya 6ata mata jiki da kunun ayar nan, cikin xuciyar ta take cewa shikenan shima ya tuna ya rama abin da ta ta6a yi mishi, a d'an fusace tace "waiii malam lafiar ka qlau da xaka xuba min abu a jikina? " Wata harara ya watso mata tare da cewa "kina jin ina sallama kin min shiru ne, shine nayi abin da ya kamata" Haushi ya turnik'e mufidah ta bud'e baki xata yi masifa sai taga har ya juya ya fara hawa stairs wani tsaki taja mtsww saboda ba k'aramin kular da ita yayi ba yanxu sai ta sake wani sabon wankan. Ita ma a fusace ta fara hau stairs d'in ta nufi bedroom d'in ta a gurguje tayi wanka ta fito tare da sake shirya wa cikin wata black arabian abayat gown tayi da sauri ta gama shirya wa ta fito xuwa parlour. A xaune ta ganshi kan kujera har yayi wanka ya canja kaya xuwa white 3quater da white vest hannun shi rik'e da waya yana daddana wa, kallo d'aya tayi mishi ta kauda kanta tana k'unk'uni tana cewa k'ato da kai xaka xauna wa mutane cikin parlour ko kayan kirki babu a jikin shi, cikin xuciyar ta take maganar ta. Bag d'in ta ta dauka tare da phone da car key tayi hanyar fita daga palourn ganin hka yasa shi cewa "keee ina xuwa da daren nan?" Banxa tayi dashi ta fice daga palourn da sauri ae kuwa shima ya tashi ya bita. Tana kok'arin bud'e kofar motar ya cimmata hannun shi yasa ya jiyo da ita da k'arfi wanda saboda k'arfin da ya sanya ya janyo ta sai da ta fad'a kan kirjin shi. Lokaci d'aya duk wani motsin su ya tsaya cak sai numfashin su da suke iya fitar wa da bugun xuciyar su da ya tsanan ta bugu, sun dauki wajen mintuna biyar a hka kafin mufidah tayi saurin janye cikin ta cike da masifah tace "lafiyar ka kuwa da xaka janyo ni hka idan da na fad'i naji ciwo fah?" Shima fuskar shi a d'aure yace " ina xaki je yanxu? " Cikin hararar shi tace "inda ka aike ni" Hannun shi yasa ya kamo nata ya murd'e har sai da mufidah ta saki k'ara saboda xaki cikin kakkausar murya yace "idan baki fad'a min ba i will slap u wlh ina wasa da ke da xan tambaye ki kina min tsiwa " "ni malam ka cika ni gidan mu xan tafi " "babu inda xaki je " Wani kallo ta watsa mishi tana cewa "tabbb ae kuwa ba isa ka hana ni xuwa gidan mu b...... " Kafin ta k'arasa fad'i abin da xata ce taji ya dauke ta cak ya fara tafia xuwa hanyar shiga palourn gidan............. Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻Exclusive writers forum Like and drop ur comments fb page #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ _where are u guys this page is dedicated to u, action baby, beeboh, meelat Ahk, bilkisu BK, Mareeyah baba, wannan shafin na ku ne kyauta ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke._😍 *PAGE 44* Kafin ta k'arasa fad'in abin da xata ce ta ji ya dauke ta cak ya fara tafiya xuwa hanyar shiga parlourn gidan, bakinciki ya Kama mufidah ganin yanda ya wani dauke ta kamar wata yarinyar shi nan ta fara wutsil wutsil da kafafun ta alamar ya sauke ta, amman ko sauraren ta bai yi ba sai da ya dire ta a parlour sannan yaje ya sanya wa parlourn key ya xo xai shige xuwa stairs. Cikin tsiwa mufidah tace "wai kai ina ruwan ka ne malam ka kyale ni na tafi gidan mu dare nayi min " Ganin ko kula ta bai yi ba yasa ta bin shi tana mishi tsiwa unexpected taji tayi karo da k'aramin center table wanda ake ajiye wa a gefen kujera, tafiya tayi luuuu xata fad'i batasan lokacin da ta saki ihu ba. Jin ihun ta yasa shi jiyo wa da sauri ganin tana kok'arin fad'uwa yasa shi tafiya da gudu xuwa inda take, akan hannun shi ta fad'o, wani ajiyar xuciya ta sauke jin bata fad'i k'asa ba bud'e idanun ta tayi a hankali wanda tun lokacin da taci tuntu6en xata fad'i ta runtse su. Had'a idanun su suka yi cikin wani irin yanayi suke kallon junan for some minutes kowannen su yana sak'a abu cikin xuciyar shi, gaba d'aya sun tsunduma cikin Kallon junan su kafin mufidah ta fara dawowa hayyacin ta fara kici kicin kwatar jikin ta, hkan da take yi ne yasa shi ma tuna a yanda suke don hka kawai sai jikin shi yayi sanyi lokaci d'aya har ya kasa rik'e ta. Kawai sai ya sake ta baxato mufidah taji ta a k'asa tummm ta buge kanta da kujera, wani xafi taji ya ratsa ta kafin tayi yunk'urin dawo wa dai dai daga xafin da taji tuni musaddiq ya haura stairs ya shige cikin bedroom d'in shi xuciyar shi tana cikin wani yanayi daban lallai mufidah ita ce rayuwar shi samun ta a rayuwar shi yanxu ba k'aramin samun cigaban shi ba ne ko da ta 6angaren xuciyar shi wajen bata abin da ta ke so. Mufidah kuwa saboda takaici sai kawai ta rushe da kuka ga takaicin hana ta xuwa gidan su, ga xafin bugewar da tayi ga kuma tsananin tsoron yanda xata iya kwana a wannan gidan babu mumy, daddy da afnan. Ta dad'e sosai anan xaune tana kuka har daga karshe ta fara gyangyad'in bacci ba wani dad'e wa bacci yayi awon gaba da ita a wurin ta tukunkune jikin ta waje d'aya tamkar mai jin sanyi sai faman sauke ajiyar xuciya take saboda kukan da ta jima tana yi. Kwance yake kan bed ya kasa bacci sai faman juyi yake ya tunano irin Kallon da suka yi d'axu shi da mufidah, a yanda ya kalli cikin kwayar idon ta bai hango wani abun da xai danganta shi da ko tana son shi, uhm uhm musaddiq kada kayi wannan tunanin yanxu don ba kaini masoyin ta na farko ba, ba lallai ace yanxu ta fara son ka ba tun da kwata kwata yaushe aka yi auren da har xata fahimci ko kai wani dole komai sai a hankali, d'an cije lip's d'in shi yayi na k'asa kafin ya bud'e bakin shi a hankali ya furta "i luv u mufidah with all my heart " Kamar an mintsine shi ya tashi xumbur da sauri ya fito xuwa down stairs yana k'arasa wa ya hango mufidah kwance a k'asa tana baccin ta, a hankali ya k'arasa wajen da take ya tsugunna yana k'are mata kallo cikin tsantsar kaunar ta. Sai da ya Kalle ta son ran shi ya more tukunna ya sanya hannun shi dukka biyun ya dauke ta gaba d'ayan ta ya nufi stairs da ita, idanun shi akan beautiful face d'in ta kafin ya mayar dasu kan cute pink lips d'in ta wanda har sai da ya lashe lip's d'in shi saboda jin yanda wani abu ya tsarga mishi lokaci d'aya, a hankali ya kwantar da ita kan bed tare da gyara mata kwanciyar ya lullu6e ta da lallausan blanket daga kafafun ta xuwa wuyan ta ya bar fuskar ta a waje, hasken d'akin ya rage mata kafin ya tsugunna yana k'are mata kallo cikin tsantsar kaunar ta, xuciyar shi ta ingixa shi har ya kai bakin shi kan lallausan kumatun ta ya sumbace ta tare da saman goshin ta xuwa pink lips d'in ta, wani irin shock yaji a jikin shi lokaci d'aya abin da bai ta6a yi ba a tsayin rayuwar shi da wata mace sai akan mufidah,dukka da mufidah tana bacci sai da taji canjin yanayi a jikin ta da xuciyar ta wanda bata ta6a jin shi ba, motsi ta fara yi da sauri ya matsa daga saitin fuskar ta sai da yaga ta juya ta koma baccin ta tukunna ya sake dawo saitin fuskar ta tare da furta "i luv u mufidah!" Yana gama fad'in hka ya fita daga d'akin ya bedroom d'in shi ya tafi ya kwanta, sam kasa bacci musaddiq yayi a wannan daren sai juyi yake kissing d'in da ya yiwa mufidah ne ya taso mishi da wani irin canjin yanayi a jikin shi, ya xama dole ya nemi mafita don ya gaji da jin shi a wannan yanayin xai nutsu ya sami wata babyn ya aura ko ta d'ebe mishi kewa tun da shi ba neman mata yake ba sannan baxai iya tunkarar mufidah da buk'atar shi ba don hka gwara ya nemi mafita, wannan tsayin daren da hka yayi shi cikin tsantsar begen kasance wa da mufidah yana rufe idon shi ita yake hango wa. *WASHE GARI* A hankali ta fara bud'e idanun ta xuwa d'an lokaci kad'an ta gama bud'e su tas, cikin sauri ta mik'e xaune da mamaki take bin d'akin da kallon ita tasan a parlour bacci ya dauke ta a k'asa, sai gashi ta tashi ta ganta saman bed acikin bedroom d'in ta har da lullu6e ta da blanket, lokaci d'aya kuma abin da ya faru tsakanin ta da musaddiq ya fad'o mata wani tsaki taja tare da cewa "watak'il shi ya kawo ni bedroom, d'an rainin wayo ko me ruwan shi da kawo ni d'aki ya rabu da ni inda ya ganni " Ta k'arasa fad'i tana murgud'a bakin ta nan tayi ta mita har dai ta gaji ta nufi bathroom don tayi wanka tun da wanda take mitar don shi ba jin ya yake ba, ta d'an jima a cikin toilet kafin ta fito shirya kan ta tayi cikin wata blue black swiss atampha d'inkin riga da siket ne sun xauna a jikin ta sosai, light make up tayi tare da d'aura d'ankwalin ta wanda har sai da wani yanki na gashin ta ya fito, tayi kyau sosai abin ta perfumes da humra masu kamshi tayi using dasu kafin ta fito xuwa parlour. Tana fito wa daga bedroom d'in ta shima musaddiq ya fito yayi gayun shi cikin jeans blue and white T-shirt long sleeves yayi kyau sosai sai tashi k'amshin perfumes yake. Kallo d'aya kowannen su yayi wa d'an uwan shi suka kau da kai xuciyar su na bugu wa da k'arfi, kusan lokaci d'aya suka fara sauka na steps d'in stairs, sai dai musaddiq ya riga ta sauka xuwa cikin parlour. Tun daga nesa muh'd ya hango su wanda yake xaune cikin parlour ba k'aramin kyau suka yi mishi sun yi matuk'ar dace wa da junan su, tuni ya hau washe baki don son yin tsokana, ae kuwa musaddiq ya sake 6ata fuska don kada yayi mishi shirme gaban yarinyar nan ta raina shi. Tsab muh'd ya fahimce shi ae kuwa ya tuntsire da dariya tare da cewa "guy ka birge ni sai da ka ga mumy da daddy basa nan shine ka taho don ka ci angoncin ka son ran ka koh, anyway duk da hka xan fad'a wa su mumy don su sani su fara shirin tar6ar jika don da ganin yanda kake rawar jikin nan da bayani gashi sai wani shek'i kake alamar jiya an bawa soyayya hak'ik'in tun da nasan abokin nawa ba rago ba ne " Da muh'd yaga yanda musaddiq yake jefo mishi harara da ya katse xancen da yake xubo wa kamar xarbi ya tsince, wata dariyar k'eta ya sake yi yana Kallon musaddiq tare da cewa "ae gaskia na fad'a malam ka daina harara, ko don hka ka kirawo ni na gasa ka tun da nasan kai farin shiga ne koh? " A fusace musaddiq ya kalli muh'd yace "are you stupid muh'd da xaka sani gaba kana yi min wata magana ta daban sai kasa yarinya taxo tana raina ni " Muh'd ya bud'e baki kenan xai yi magana yaji saukar muryar mufidah tana gaida shi, cikin fara'a ya amsa tare da tsokanar ta kamar yanda yayi wa musaddiq sai dai na mufidah da banbanci da na musaddiq, bata kula shi ba ta wuce kitchen abin ta............ Nan dai muh'd yasa musaddiq a gaba sai tsokanar shi yake tun yana hararar shi har ta kai ya fara murmusa wa ko breakfast bai tsaya yi ba suka fita daga gidan shi da muh'd, wannan damar mufidah ta samu kuwa tayi saurin fito wa daga kitchen daman babu abin da take sai addu'a acikin xuciyar ta Allah yasa musaddiq ya fita, ae kuwa suna fita da gudu ta haura stairs ta d'auko bag d'in ta da hijab sai phone nata da car key ta fito, nan ta shiga motar ta tayi mata key, horn tayi wa gate man ya bud'e ae kuwa taja motar kai tsaye gidan su ta nufa, xuciyar ta cikin farincikin ta samu damar guduwa baxata k'ara dawowa ba sai ya koma Australian.................. _fan's kuyi hak'uri da wannan page d'in mu had'u gobe,ina godia da bani had'in kai da kuke ina muku fatan alkhairi masoya naaaaaaaa_😊 Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ £xclusive writers forum Like and drop ur comments fb page #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ *PAGE 45* Sai da mufidah taga ta k'arasa gidan su ta shiga har tayi parking motar ta sannan taji ta samu nutsuwa hankalin ta ya kwanta, har da sakin wata ajiyar xuciyar jin dad'i don tasan musaddiq baxai biyo ta gida. Cikin tafiyar ta ta nutsuwa ta k'arasa side d'in su da sallama ta shiga parlourn, umma wadda take xaune kan kujera tana kallon sunnah tv suna nuna wa'axin sheik isah Ali pantami, ta amsa sallamar mufidah tana mai sakin murmishi najin dad'in ganin 'yar ta ta, fara'ar ta ta kasa 6oyu wa musamman da taga alamun mufidah ta kwantar da hankalin ta yanxu har tayi kyan ganu wa ba kamar kwanakin baya ba. K'arasa wa mufidah tayi inda umma take xaune ta xube gwiwoyin ta a k'asan lallausan carpet d'in parlour ta d'ora kanta da hannayen ta duk biyun akan k'afar umma cikin marairaice wa tace "umma nah i miss u so much" Shafa kanta umma tayi tana murmishi tace "i miss u too baby na, yasu hajia khadija ina afnan ko ta shige side d'in su muhibbat? " Umma ta k'arasa fad'a tana lek'en bayan mufidah, cikin er dariya mufidah tace " tabbb umma yanxu hka afnan tana london ita da mumy da daddy " Cikin mamaki umma tace "dafatan lafia dai ?" "lafia qlau umma sun je duba lafiar abokin daddy ne an kwantar dashi acan yana jinya" "Ayyah Allah ya bashi lafia, su kuma Allah ya dawo dasu lafia " "Ameeen umma nah, don nayi missing afnan wlh ji na ke dama na bi su " Murmishi umma tayi tare da cewa "to me ya hana ki bin su?" D'an yatsina fuska tayi tare da cewa "umma bana son ace ko'ina xasu je da sun nemi na bi su na je shi yasa na k'i yarda na je bana son ina tak'ura musu duk da nasan su ba ruwan su " "kin yi tunani mai kyau " Cewar umma kafin ta cigaba da cewa "ina kika bar musaddiq d'in? " Cikin mamaki sosai mufidah take kallon ta kafin tace "umma kinsan ya dawo ne? " "nasa ni mana tun da Omar shi ya d'auko shi a airport suka biyo ta nan har yaci abinci tukunna ya k'arasa gida " "lallai wannan mutumin d'an rainin hankali har wani shisshige wa iyaye na yake yi " fad'in mufidah a cikin xuciyar ta, "lafiyar ki kuwa? " Cewar umma tana Kallon mufidah ganin ta d'an rage fara'ar ta gashi ta fad'a kogin tunani. Girgixa kai tayi tare da cewa "ba komai umma, nabilah tana nan? " "gani nan a bayan ki Mrs musaddiq " Da sauri mufidah ta jiyo suka had'a ido da nabilah tana fito wa daga kitchen d'in umma, d'an 6ata rai mufidah tayi tare da cewa "ba na hana ki kirana da Mrs wancan mutumin ba" Ta k'arasa fad'i tana hararar nabilah, tuntsire wa da dariya mufidah tayi tare da rik'e baki tace "ikon Allah wato ma baxa ki ambaci sunan shi ba lallai da aiki a gaba na " Umma kuwa d'an 6ata fuska tayi tare da cewa "Ehh lallai mufidah wato a gabana kike furta hakan akan mijin ki koh, har kina kiran shi da mutumin can koh? " Harara mufidah ta dalla wa nabilah don tasan ita xata janyo mata fad'an umma yanxu, yayin da nabilah ta gimtse dariyar ta tare da wuce wa kitchen da sauri. "kada na sake jin kin furta wani abun makamancin haka, don miji yafi k'arfin wasa tsakanin ku girmama wa da da yi mishi biyayya da sauke duk wasu hakk'ok'in sa, magana ma ta girmama wa xaki na yi mishi kuma cikin sanyi kina nuna mishi ke fah mace ce kina da sanyi a ko'ina, don hka kada na k'ara jin irin hka a wajen ki, kina jina" "toh umma insha Allah xan kiyaye " Mufidah ta fad'a kamar xata fashe da kuka, "dafatan Kuna xaune lafia dashi kuma kuna waya? " Da har xata ce bai ta6a kiran ta ba sai kuma tayi wani tunani kafin tace "Ehh umma muna yi " "Alhmdlh ai musaddiq ba ruwan shi kamar marigayi sadeeq d'an uwan shi yake, sam baya suruka da ni ya dauke ni uwa muna yin waya sosai dashi mu sha hira, sadeeq daman mai jin kunya ta Allah ya jikan shi da rahma " Cikin sanyin jiki da murya mufidah tace "Ameeen " "dafatan kafin ki fito kin yi mishi breakfast baki barwa en aiki sun yi mishi ba " Tuni mufidah an fara rarraba idanu don tasan ita kanta ko breakfast bata yi balle tayi wani, kallo d'aya umma tayi mata ta tabbatar bata da gaskia ae kuwa tace "haba mufidah wannan wane irin shashanci ne da xaki bar wa en aiki su yiwa mijin ki abinci, sam wannan ba koyarwar da nayi miki bace, kada ki k'ara yin sakacin nan, kin ji na fad'a miki " Idanun ta cike taf da hawaye tace "tohhh umma " Nan umma ta dunga yi mata nasiha tare da bata shawarwari masu amfani wanda tasan xai taimaka musu wajen kwanciyar hankali da xaman su lafia (wanda wasu iyayen sam basu damu da hkan ba, ace 'yar ki xata yi aure ko kuma tayi auren baxa ki xauna da ita ba a matsayin ki na uwa ki bata shawarwari masu amfani wanda xai taimake ta a rayuwar auren ta, kina nuna mata mahimmancin miji kina nusar da ita abubuwan da ya kamata wanda ya dace da tayi da wanda bai dace ba, ki janyo 'ya'yan ki jikin ki su Saba da ke sosai ta yanda duk wata shawarar ta ke xata tunkara ba sai k'awa ba wadda mybe k'awar ta d'ora ta kan wata hanyar ba mai 6ille wa ba, don hka iyayen mu mata a kula mu kiyaye wajen kula da yaran mu, tarbiyyar su, tsabta, koya musu girki, girmama na gaba dasu, uwa uba basu ilimi na addini dana boko, Allah yasa mu dace Ameeen.) Bayan umma ta gama yi mata nasiha tare da bata shawarwari ne daga karshe tace "ki je dining table akwai abinci sai ki xa6i abin da kike so " Tashi mufidah tayi tana d'aukar bag d'in ta tana cewa "Yawwa umma na kamar kinsan yunwa nake ji " Da kallo umma ta bi ta cikin mamaki kafin tace "wannan jakar fa ta me ce? " D'an waro idanun ta tayi tare da cewa "laaa umma na dawo nan sai su mumy sun dawo xan koma " "shi kuma mijin na ki wane xai kula dashi tun da hajia khadija bata nan? " Tsit mufidah tayi kafin daga bisa ni tace "umma ni wlh tsoro nake ji ni kad'ai, don Allah ki bar ni na kwana anan " Ta k'arasa maganar da shagwa6a, Kallon ta umma tayi kawai tana girgixa kai sam mufidah idan tana gaban ta nuna wa take kamar Er k'aramar yarinya. Ganin umma bata ce komai ba yasa da sauri ta bar wurin bedroom d'in ta ta nufa ta ajiye bag d'in da cire hijab d'in ta, fito wa parlourn tayi a dining ta xauna ta had'a tea tana sha gefe d'aya kuma ta d'ebi plantain and egg tana d'auka da fork tana ci hankalin ta kwance, sai da ta gama ci tukunna ta nufi kitchen wajen nabilah wadda take kok'arin had'a kunun gyad'a don tun da ta samu ciki bata da wani abin so sama da ta sha kunun gyad'a. D'an bugun ta a kafad'a mufidah tayi tare da cewa "ke wannan cikin da son kunun gyad'a ya xo miki, abin da bakya son shi ma" "uhm ke dai bari kawai Mrs musaddiq yanxu idan ban sha wannan kunun gyad'ar ba hka xan yini babu cin abinci don ji xanyi sam bana sha'awar wani abin " Girgixa kai mufidah tayi tare da cewa "wayyo k'awata Allah dai ya raba lafia, amman cikin muhibbat bai baki wahala kamar hka ba " "gaskia kuwa don ban sha wahala ba sai kwad'ayin tsiya don har my dear sai da ya fara yi min tsiya akan kwad'ayin, don bini bini nace abu kaxa nake so sai kuma yaje ya nemo min hankali xai kwanta " Nan dai mufidah ta kar6i aikin kunun gyad'ar nabilah ta samu waje ta xauna suna er hirar su har ta gama dama shi ta xuba acikin flaks Bayan ta xuba wa nabilah a cikin cup ta had'a mata da sugar and milk. "ke baxa ki sha ba? " Cewar nabilah suna kok'arin fita daga kitchen d'in, girgixa kai mufidah tayi tare da cewa "na k'oshe yanxu mybe sai xuwa anjima" A cikin parlour suka xauna hira suke sosai tsakanin su har da umma. *** *** *** Musaddiq bai dawo gidan ba sai wurin 12 na rana don hospital suka fita, yana dawo wa gidan jikin shi ya bashi mufidah bata gidan, kuma yasan gidan su ta tafi don hka bedroom d'in shi ya shiga xama yayi tare da bud'e laptop d'in shi ya fara aiki a jikin ta, sai da ya d'auki a k'alla tsayin mintuna 60 yana aikin kafin ya gama, alwala yayi ya tafi masallaci yayi sallahr axahar, kafin ya dawo gida. Bedroom d'in shi ya koma yunwa yake ji sosai ko breakfast bai yi ba, frige ya bud'e ya lalubo fresh milk mai sanyi yasha kafin ya kwanta a gajiye daman bai samu cikakken bacci jiya ba da dare don hka nan da nan bacci ya dauke shi mai nauyi. Ya dad'e yana bacci don sai wurin 5 na yamma ya tashi wanka ya fara yi agurguji ya xura jallabia sallahr la'asar yayi ya fara gabatar wa a makare ya dad'e yana addu'o'in shi kafin ya tashi ya fara shirya wa. Tsab ya fito cikin wata kuftan blue black d'inkin rigar irin iya gwiwar nan tsayin ta sosai kayan su kar6e shi abin ka fari kunsan kalar tana yiwa farare kyau, agogo da takalmi bak'ak'e yayi amfani dashi hular shi itama bak'a ce mai ratsin blue and white a jiki ya wani turo ta gaban gashi yana Kallon kanshi a mirror ya tabbatar komai yayi yanda yake so sannan ya fesa different colour's perfumes a jikin shi tukunna ya d'auki car key da phone's nashi ya fito, cikin car d'in shi ya shiga tare da yi mata key ya bar gidan. Gidan su mufidah ya nufa yana parking a cikin gidan ana kiran sallahr mangarib, a lokacin ya Omar da abba suka fito xasu tafi masallacin kusa da gidan, musaddiq ya fito har k'asa ya tsugunna ya gaida abba yayin da suka yi musabiha da yah Omar daga nan kuma suka wuce masallaci, sai after ishsha suka bar masallacin suka nufi gida. Da fara'a umma ta tarbi musaddiq suka gaisa kafin a tsunduma hira, mufidah tana bedroom batasan musaddiq ya xo ba, gama girkin daren da suka yi da umma kenan ta taho yin wanka. Bayan tayi wanka ne ta shirya cikin wata gown mai hannun vest purple colour ce tayi mata kyau ta gyara gashin ta tare da sanya mishi ribbon bata yi wata kwalliya ba daga powder sai wet lips mai k'amshin apple Bayan ta fesa perfumes ne ta fito xuwa parlour cikin takunta na nutsuwa. Sam bata kula da musaddiq ba tayi wajen dining table tana cewa "abba, umma ku taho mu ci abinci na fara jin yunwa " A shagwa6e take maganar, har ta k'arasa dining d'in ta fara serving d'in su hankalin ta kwance sai dai sometimes ta d'an jin gaban ta yana fad'uwa. "musaddiq taso mu ci abinci " "toh abba " Ya fad'i hkan yana tashi don Allah Allah yake ya k'arasa wajen da mufidah take don yayi mata Kallon da xai more son ran shi don ba k'aramin kyau tayi mishi ba. Lokacin da suka k'arasa kan mufidah yana sunkuye tana xuba musu abincin, bayan ta gama xuba wa ta d'ago kanta tana cewa "umma na abba n........ " Sauran maganar mak'ale wa yayi a fatar bakin ta dalilin had'a ido da musaddiq da tayi yana yi mata wani irin kallo mai tattare da ma'anoni daban daban.............. Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻£xclusive writers forum Like and comment's fb page #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ *PAGE 46* Sauran maganar ta mak'ale a fatar bakin ta bata k'arasa ba dalilin had'a ido da musaddiq da tayi yana mata wani irin kallo mai tattare da ma'anoni daban daban, ita ma mufidah sai ta kasa dauke idanun ta a kanshi suka tsaya kallon junan cikin wani irin shauk'in junan su don kallo d'aya mutum xai yi musu ya tabbatar suna masifar son junan shi. Abba ne ya ta6o umma tare da yi mata nuni da su mufidah suna kallon junan watak'il ma sun manta a ina suke, murmishi umma tayi kawai tana girgixa kai, gyaran muryar da abba yayi ne yasa su dawowa daga duniyar kallon junan su da suka tafi. Sai kuma musaddiq ya fara sosa kai irin na jin kunya tare da xama, yayin da mufidah ita ma kunya ta Kama ta har sai da ta dalla wa musaddiq harara tare da murgud'a mishi baki, d'aga mata kafad'a yayi irin ko ajikin shi kafin ya rama hararar da tayi mishi. Mufidah kasa sake wa tayi taci abinci daga karshe ta xame ta tsere bedroom d'in ta, sai bayan ta tafi ne tukunna musaddiq ya iya cin abincin don shi fa idan mufidah tana gaban shi kasa yin komai yake, yana cin abincin yana tuna irin kallon da suka yi junan shi yana murmishi shi kad'ai. Bayan sun gama ne suka dawo cikin parlour ana er hira har xuwa 9 na dare, kafin musaddiq ya ce "umma a kirawo mufidah mu tafi na ga dare nayi " Kafin umma tayi magana abba yace "ga bedroom d'in ta can shiga ka kirawo ta " D'an sosa kai tare da cewa "okay abba " Ya wuce cikin nutsuwa ya nufi stairs d'akin mufidah. "yaran nan suna son junan su sosai, amman ban san me ya hana su bayyana wa kansu ba suka barshi cikin xuciyar su " Cewar abba, umma kuma tace "mybe basu yi shak'uwar da xasu furta wa junan su ba, tun da wannan auren had'a su akayi ba tare da ra'ayin d'ayan su ba" "baki san saboda son 'yar ki da musaddiq yake ba har ya kamu da ciwon xuciya " D'an xaro ido umma tayi na mamaki tace "shi musaddiq d'in? " "kwarai kuwa " Abba ya tabbatar mata da hkan, kafin ya kwashe labarin komai ya fad'a wa umma wanda shi ma muh'd ne yake sanar mishi, wani tsananin tausayin musaddiq ne ya kama umma sosai, ta kasa ma magana sai jujjuya kai kawai take irin yanda idan labari ya bugi mutum sosai yake yi. A hankali ya sanya hannun shi kan handle d'in kofar ya murd'a tare da cusa kanshi ciki ba tare da yayi sallama ba, kallon d'akin yake cikin son d'akin don yanda aka shirya shi yayi kyau blue and white ne komai da komai har fentin bangon, kafin idanun shi su sauka kan mufidah wadda take xaune kan stool na dressing mirror tana gyara gashin ta, fitowar daga wanka kenan ta gama shirya wa cikin white sleeping dress mai hannun vest, tsawon rigar iya gwiwar ta ne gata irin mai shara shara ce komai na jikin ta a bayya ne yake Sauran kad'an musaddiq yayi suman tsaye. Wani irin had'iyar yawu yayi wanda har yasa shi kware wa ya fara fitar da tari, a matuk'ar firgice mufidah ta jiyo don ganin wane, da sauri ta mik'e tsaye saboda idanun ta ne suka sauka kan musaddiq wanda yake tari cikin yanayin fusata ta taso irin da saurin nan don yi mishi masifa akan shigo wa d'akin ta da yayi ba tare da ixinin ta ba, sai kawai k'afar ta ta bugi stool d'in da ta xauna akai sai ta tafi taga taga xata hantsala. Carab ta sanya hannun ta da sauri ta cafko rigar musaddiq wanda har yanxu bai daina tarin ba, k'arfin janyo shi d'in da tayi ne ba tare da ya sani ba ya sanya shi biyo ta sai kuma tayi baya tana shirin fad'uwa wata k'ara ta saki tare da runtse idon ta da k'arfi. Kan bed ta fad'a musaddiq ma ya biyo ta don har yanxu tana k'ank'ame da rigar shi, da sauri ya sanya hannun shi duk biyun ya tokare su da kan gadon don kada ya fad'a kanta. Jin shirun da mufidah taji ya sanya ta bud'e idon ta d'aya don jin saukar numfashin musaddiq a saman fuskar ta, batasan lokacin da ta bud'e idanun gaba d'aya ba don ganin fuskar shi dab da ta ta, kallon junan su suke ido cikin ido irin kallon da man da geet suke yi idan soyayyar tasu ta motso. lol Sun kwashe some minutes suna kallon junan su kafin mufidah ta tsuke fuska tace "malam ni ka d'aga ni xan tashi ka gani danne ni kana kallo na " Shima 6ata fuskar yayi tare da cewa "wane xai tsaya kallon ki, kuma ni bani na janyo ki ke kika janyo kan ki " Hararar shi tayi tare da cewa "to d'aga ni " Shima hararar ya rama tare da yatsina fuska kafin yace "cika min riga ta " Sai lokacin idanun mufidah ya fad'a kan hannun ta da yake rik'e da rigar shi k'am da sauri ta cika mishi, ya fara kok'arin tashi. Yana tashi mufidah idanun ta suka sauka kan jikin ta inda rigar ta gaba d'aya ta nannad'e daga kasa ae kuwa cikin sauri ta k'arasa haye wa kan gadon ta tuk'unk'une da blanket har kanta, abin sai ya bawa musaddiq dariyar ma har sai da ya murmusa cikin xuciyar shi ya furta " har yanxu akwai yarinta a tattare da ke mufidah, ina son komai naki i luv u so much " A fili kuma yace "ke malama ki tashi mu tafi gida dare nayi " Tana cikin blanket d'in ta murgud'a baki tare da cewa "tabbb ba inda xan je ina gidan mu " "ki taso mu tafi idan nayi k'irga 5 baki fito ba I'll slap u " Tana jin shi ko uhm bata ce mishi ba har ya fara k'irgen, jin har ya kai 4 ne yasa ta mik'e wa xata fad'a toilet, ae kuwa kamar ya sanya abin da take niyyar yi sai ji tayi carab ya rik'e hannun ta tare da murgud'a su ya jiyo da ita tana kallon shi ya mayar da hannun ta dukka biyun bayan ta ya rik'e su da hannun shi d'aya kallon ta yayi tana xubar da hawaye don ba k'aramin rik'o yayi mata, lumshe idanun shi yayi sam baya kaunar ganin hawayen ta kawai sai ya sanya hannun shi ya janyo hijab d'in ta ya xura mata ganin da yana kok'arin d'aukar ta yasa magana da sauri tana cewa "ni ka kyale ni na shiga toilet xan yi fitsari " Kallo d'aya yayi mata yasan ba wani fitsari da take ji, ya dauke ta cak yana cewa "idan ki matsu kiyi a hka " Nan ta fara wutsil wutsil da kafafun ta alamar ya sauke ta amman bai kula ta ba har sai da suka fito parlour, umma da abba ma basa nan xaune don hka kawai ya fita har xuwa wajen da yayi parking motar shi ya sanya ta kafin ya shiga shima yayi wa motar key suka bar gidan. Saboda takaici sai kawai ta rushe da kuka don ta rasa abin yi sai kukan mybe idan tayi ta samu relief a cikin xuciyar ta, lumshe idanun shi yayi tare da bud'e su lokaci d'aya suka yi ja don baya kaunar ganin kukan ta xuciyar shi na k'una idan yaga hawayen ta, daure wa yayi har suka k'arasa gida tak'i fito wa daga motar sai da ya dauke ya kaita har bedroom d'in ta tukunna ya fita. Sai da ta gaji da kukan ta bacci ya dauke ta, musaddiq sai da ya shigo d'akin ya ga tayi bacci sannan hankalin shi ya kwanta yayi mata addu'a sannan ya kashe mata hasken ya bar d'akin sai lokacin yaji xuciyar shi tayi mishi dad'i hankalin shi ya kwanta. Ko Washe gari ma kulle kofar bedroom d'in ta tayi bata fitowa ba sai da tabbatar ya bar gidan sannan ta fito, abinci iya cikin ta ta girka ta koma bedroom ta rufe don sosai haushi ya bata ba. Sosai hankalin musaddiq ya tashi don ya kasa jure rashin ganin ta, amman sai ya daure don baya son ta fahimci abin da yake cikin xuciyar shi idan ba nesa yayi da ita ba cikin lokaci k'ank'ani xata fahimci abin da xuciyar shi take ciki, hkan yasa shi fara shirin koma wa Australian. Ranar dasu mumy xasu dawo a ranar musaddiq ya bar nigeria ko mufidah bai k'ara gani ba, sai daf da mangarib su mumy jirgin su yayi landing a airport sai ganin su mufidah tayi kawai, nan ta rungume mumy da afnan tana mai farincikin ganin su, hka ma mumy baki yak'i rufuwa na ganin mufidah afnan sai labarin kasar london ake yiwa mufidah. " yau kenan kika dawo 'yata? " Cewar mumy suna shiga bedroom d'in ta, d'an murmishin yak'e mufidah tayi cikin xuciyar ta tana cewa wannan masifafen mutumin ne xai bar ni na tafi gidan mu, a fili kuma tace "ehhh mumy d'axu na dawo " Murmishi tayi tare da cewa "yayi kyau hkan, ae da ma baki dawo ba anjima kad'an xaki ganni" Murmishi kawai mufidah tayi mumy tana sonta shi yasa ita ma take son ta sosai, hka lokaci ya cigaba da tafia suna xaman su cikin kwanciyar hankali ta 6angaren mufidah tana kok'arin yaki ce wani abu da yake son shiga cikin xuciyar ta tana son karya ta xuciyar ta akan abin shi yasa bata kaunar xama waje d'aya tana k'e6e wa ita d'aya tunanin shi xai fara addabar xuciyar ta, shi yasa take k'irk'irar abubuwan da xata hana xuciyar ta tunanin shi don ita a ganin ta sam baxa ta bari son shi yayi tasiri cikin xuciyar ta ba. *AFTER 3 MONTH'S* bayan wad'annan watannin da suka shud'e ne shiru musaddiq yak'i dawowa mumy da daddy sun yi mishi maganar ya xo ya d'auki mufidah su koma Australian d'in amman ya fara yi musu hanya hanya ganin hka yasa mumy da daddy suka yanke lokaci nan da two weeks mumy xata kai mufidah har Australian d'in ba tare da sun bi takan musaddiq ba tun da yak'i tsayawa ayi maganar. Musaddiq kuwa ta 6angaren shi baya son yana ganin mufidah hankalin shi ya tashi yake, ganin ta ba k'aramin canja mishi tunani yake ba xuwa wani abin daban, taya xai iya tunkarar mufidah da buk'atar shi sai yake ganin kamar bai yiwa d'an uwan shi adalci ba wannan tunanin nashi shi yake dad'a nisan tashi da bayyana wa mufidah abin da yake kunshe cikin xuciyar shi shekara da shekaru. Cikin kwanakin nan aka gama shirya tafiar mufidah da afnan, gyaran jiki na musamman mumy ta d'auko don gyara mufidah ciki da waje, ae kuwa tasha gyara ba kad'an ba, tayi wani irin kyau sosai na daban, sam mufidah ba'a son ranta xata tafi ba don kawai tana jin kunyar mumy da daddy ne bata son nuna rashin son tafiyar da bata yi, Sauran kwana biyar su tafi ne taje yiwa su umma sallama don xata kwana uku acan. Sosai umma ta dage ita ma tana gyara d'iyar ta ta duk da ta yaba da gyaran da mumy tayi mata, hka nabilah ma gudummowar ta daban ta wannan 6angaren, umma ta xaunar da mufidah tayi mata nasiha sosai tare da bata shawarwari masu amfani, abba da yah Omar ma kowa da tashi nasihar, mak'ale wa mufidah tayi tak'i dawowa gidan mumy sai ranar da xasu tafi Australian d'in da safe mumy ta xo ta sanya ta a gaba suka koma gida, da kanta mumy ta shirya mata kayan ta sosai da yake tashin dare xasu yi. Xuwa mangarib sun gama komai xuwa karfe 9 jirgin su xai tashi don hka 8:30 na dare suna airport, nan suka yi sallama da daddy da yake har dashi a en rakiyar ga umma, abba, yah Omar, nabilah da muhibbat, ga Dr muh'd da matar shi nafisat har dasu a en rakiyar don muh'd yana bawa duk wani abin da ya shafi musaddiq muhimmanci,kowannen su jiki a sanyaye suka yi sallama har jirgin su mufidah ya tashi suna tsaye kafin kuma su koma gida duk kewar mufidah da afnan ta kama su don mumy kwanaki biyu xata yi ta dawo. Acikin jirgin kuwa mufidah hawaye ne yake xuba a idanun ta cikin xuciyar ta baxa ka iya tantance halin da take ciki ba farinciki ko akasin hka,kwantar da kanta tayi idanun ta a lumshe tana tunanin irin xaman da xasu yi ita da musaddiq a wannan lokacin............ _to readers ga mufidah a hanyar ta ta xuwa australian wajen musaddiq, ko ya xaman su xai kasan ce ni kaina na k'agu naji irin xaman da xasu yi, don hka ku jira ni a next page d'ina don jin abin da xai faru, godia mara adadi gare ku fan's d'in yayi sake! ni Aishat A muh'd ina gaida ku tare da yi muku fatan alkhairi luv u all my fan's_ Sai kun yi hak'uri da wannan page d'in don ban samu damar editing ba Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM LIKE AND COMMENT'S FB PAGE 👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ _Gaisa da fatan alkhairi gare ku masoyan Aishat A muh'd, ina jin dad'in yanda kuke kaunar littafin nan, don hka na sadaukar da wannan page d'in ga duk masoyin littafin yayi sake!,luv u oll my fan's_❤ *PAGE 47* A cikin jirgin kuwa mufidah hawaye ne yake xuba a idanun ta cikin xuciyar ta baxa ka iya tantance halin da take ciki ba farinciki ko akasin hka, kwantar da kanta tayi idanun ta a lumshe tana tunanin irin xaman da xasu yi ita da musaddiq a wannan lokacin. Lokacin da jirgin nasu yayi landing a babban fili saukar jirgi na australian, mutane suka fara firfito wa mufidah tana sanyo kanta xata fito taji wani sanyi ya ratsa mata fuska sosai nan ta k'ank'ame jikin ta, tana tunanin yanda xata iya xama a wannan uban sanyin garin, a nutse ta sauko daga matattakalar jirgin mumy da afnan suna bayan ta. Bayan duk sun gama komai ne suka nufo hanyar da xata kaisu wajen hanyar fita daga airport d'in xuwa wurin da xasu tari taxi, mumy ce ta tsayar da taxi d'in cikin harshen turanci tayi mishi bayanin inda xai kaita da sunan unguwar da musaddiq yake xaune, ba wani 6ata lokaci ya amince da hkan kafin ya fito ya taimaka musu da xuba kayan su cikin boot tukunna suka shiga yaja su. Mufidah ta ware idanun ta sosai tana kallon yanayin garin na australian sosai k'asar ta birge ta don bata ta6a xuwa k'asar ba, wani lokacin idan ta tuna wajen wanda xasu je har su xauna tare sai ta ji xuciyar ta na bugawa. Tafiyar tsayin mintuna 50 ne ya kaisu anguwar da musaddiq yake har number d'in gidan mumy ta fad'a wa taxi driver d'in, ai kuwa a dai dai kofar gidan yayi parking, sai da ya sauke musu kayan lokacin da mumy ta nemi alfarmar hakan a wajen shi, tukunna ta biya shi, knocking d'in kofar gate d'in mumy tayi gateman ya bud'e da yake ya san mumy basu wani 6ata lokacin shiga gidan ba. Door bell mumy ta danna sau uku ana hud'un ne suka ji ana kok'arin bud'e kofar, lokacin da musaddiq ya bud'e kofar sakin baki yayi cikin matuk'ar mamaki yana Kallon mumy wadda ta had'e fuska babu wasa sam ba hango mufidah ya tsaya kawai yana kallon mumy ko magana ya kasa yi "bani wuri na shige mun gaji da tsayuwar " Mumy tayi furucin ganin bashi da niyyar matsa ma, kamar wani yaro ya matsa mata taxo xata shige tace "musaddiq Allah ya shirye ka, yanxu a hka kake bud'e kofar kasan wane xai shigo maka a lokacin " Wata irin kunya ta kamshi ya sunkuyar da kanshi yana sosa kai tare da tunanin yanda yake boxer ne a jikin shi kawai ko riga babu lokacin yana kwance cikin bedroom yana tunanin mufidah yaji knocking d'in so bai tsaya sanya kaya ba ya fito, ita dai mumy shige wa tayi cikin parlourn. Jiya yi an rungume kafafun shi ana cewa "Oyoyo daddyna i miss u so much " D'ago kanshi yayi ya ga afnan ce ae kuwa ya d'aga ta sama yana dariya tare da cewa "i miss u too dear,ashe mumy da ke ta xo min? " Tana dariya tace "yes daddy dani taxo har da mamee nah " Dariya ya sake sanya wa ya d'auka shirmen afnan ne kawai sai ya sanya bakin shi ya bata peck a kumatun ta, d'aga idanun shi da xai yi suka had'a ido da mufidah tana tsaye tana kallon su cikin sha'awa da birge wa, sai kawai suka tsaya kallon junan su cikin wani yanayi na shauk'i. "bani hanya na wuce kada ka cinye min yarinya ka wani xuba mata ido kak'i matsawa ta wuce " Cewar mumy kenan ganin shiru mufidah bata shigo ba, sai lokacin ya sauke idanun shi akan ta ji yayi xuciyar shi tayi mishi sanyi da ganin ta yana rik'e da afnan ya wuce ciki, yayin da mumy ta rik'o hannun mufidah suka wuce su ma cikin parlourn. Lokacin da suka shiga musaddiq yana xaune kan kujera afnan tana kan kafafun shi tana mishi hira murmishi kawai ya ke yi, yana son afnan idan yana ganin ta ko yana jin muryar ta jinshi yake tamkar yana tare da d'an uwan shi sadeeq. "malam ai sai kaje ka sanya kaya koh oh ni khadija musaddiq ko kunya ta baka ji ka xauna a hka a gaba na " "mumy ba hka ba ne just afnan ce ta tsaida ni labari take bani " Yana gama fad'in hka ya xaunar da afnan tare da cewa "sweet dgter give me five minutes ina xuwa" Langa6e kai tayi tare da cewa "okay daddy " Kallon mufidah yayi sai aka ci sa'a ta d'ago kanta suka had'a ido ae kuwa harara ya sakar mata tare da yi mata kallon xan kama ki ne yarinya ita ma hararar ta watsa mishi girgixa kai yayi kawai ya wuce bedroom d'in shi. Cikin mintuna 10 sai gashi ya fito har ya shirya cikin Blue Jeans and black T-shirt mai k'aramin hannu yayi kyau sosai, gaida mumy yayi ta amsa mishi, mufidah ganin idon mumy ne yasa tayi mishi gaisuwa d'aya daga ina yini taja bakin ta ta tsuke , to shima lafia kawai ya furta sannan ya kalli mumy yace "mumy ga bedroom nan ki je kiyi wanka ki huta bari na fita na samo muku takeaway " "to shikenan " Abin da mumy tace ta wuce d'ayan bedroom d'in, daman two bedrooms ne a gidan da parlour d'aya sai kitchen da kuma madaidaiciyar harabar gidan, gida ne mai kyau sosai wanda aka tsara shi da abubuwan more rayuwa. Mumy tana shige wa bedroom ne afnan ta bita yayin da musaddiq ya sunkuyo dai dai kan mufidah har numfashin su na had'u wa yace "ba dai har kin gaji da xama babu miji a kusa ba yasa ki tak'ura wa mumy ta kawo ki waje na" Wayyo wani bak'in ciki ne da takaici ya tokare mufidah kamar ta rushe da kuka saboda abin da ya fad'a mata,kasa magana tayi kawai ta kau da kanta, murmishin mugunta ya saki tare da d'aga kafad'ar shi yace "anyway duk abin da kike so kin xo inda xa'a share miki hawaye bari naje na dawo 'yammata xan ce ko second hand " Kasa jure wa mufidah tayi ta tashi a fusace har ta bud'e baki xata yi mishi magana sai kawai ta fasa ta wuce bedroom d'in da mumy ta shiga ashe bashi ne nashi ne sai jin muryar shi tayi yana cewa "haba mameen afnan saurin me kike ki bari na fara gayyatar ki xuwa d'akin kya shiga " A xuciye ta jiyo tare da cillo mishi phone d'in hannun ta cikin fusata, yana dariyar k'eta ya cafe wayar a hannun shi, haushi takaici ya k'ume mufidah sai kawai ta rushe da kuka daman kiris take jira, ganin mumy tana kok'arin fito wa daga bedroom yasa musaddiq fit ya fice da sauri yana mamakin saurin kukan mufidah daga tsokana sai kuka. "lafia mufidah me ya faru ?" Mumy ta tambaye ta tana d'ago ta daga tsugunnawar da tayi, cikin kukan tace "ba komai mumy " "haba mufidah hka kawai mutum baxai yi kuka ba sai da dalili tell me me ya faru kike kuka? "mumy bige wa nayi a kafa ta " Kawai ta tsince kanta da fad'a wa mumy hkan, cikin tausayi mumy tace "Ayyah sannu kin ji " Gid'a kanta tayi nan mumy ta kama hannun ta suka shige bedroom d'in. Wanka mufidah take a toilet tana tsiyayar da hawayen takaicin abin da musaddiq yayi mata kuma xai ta rama ita ma, tana tunanin mafitar rama wa har ta gama wanka bata samu mafita ba. Bayan ta fito ne daga toilet lokacin su mumy da afnan har sun gama shirya wa sun koma parlour, don hka ta shirya a nutse cikin wani wando maroon colour irin wanda yake kwanciya a jikin mutum da wata black T-shirt mai k'aramin hannu akwai kwalliyar xanen heart a gaban rigar da silver colour sai ta sanya wata rigar sanyi wadda tsayin ta iya gwiwa rolling kan ta tayi da black veil kafin ta fesa perfumes ta fito xuwa parlour. Yana xaune kan dining table ya hango ta kur6ar coffee yake a time d'in da ta fito but sai ya ajiye cup d'in ya tsira mata ido yana kallon ta ba wani make up tayi ba but tayi kyau, da yaga tana kok'arin d'ago kanta yasa shi saurin dauke idon shi daga kanta ya mayar kan afnan . Har ta k'arasa dining d'in xama tayi kusa da kujerar mumy ko kallon inda yake bata yi ba sai ma wani had'e fuska take abin ma sai ya kusan bashi dariya ganin yanda take cika tana batsewa. A sace yake jifan ta da wani kallo wanda tsakanin mumy da mufidah ba wanda ya ankara da hkan har suka kammala cin abincin, mufidah ce ta tattare abin da suka yi amfani dashi gyara dining d'in sannan ta wuce kitchen. Har ta fara wanke kwanukan da suka 6ata ne sai rigar jikin ta ya fara tak'ura mata Co's bata Saba da yin aiki da irin rigar ba sai kawai ta cire ta tare da ajiye ta saman cabinet d'in daga gefe ta cigaba da abin da take hankali kwance. Musaddiq wanda hankalin shi yayi kitchen inda mufidah take sai kawai ya mik'e tsaye yana cewa "mumy bari na d'auko ruwa a kitchen " Yana gama fad'in hka yayi gaba da d'an saurin shi, yayin da mumy ta bishi da kallo tana murmishi tare da girgixa kai tun xuwan shi ta gama karantar shi yanda yake rawar jiki da irin kallon da yake bin ta dashi. Yana shiga kitchen d'in ya jingina bayan shi jikin bangon kitchen d'in ya hard'e hannun shi a kirjin shi yana aikin kallon ta jin shi yake kamar yaje ya rungume ta a cikin jikin shi ko ya samu relief acikin xuciyar shi da gangar jikin shi, sai da ya kalle ta son ranshi ya more kafin kuma ya bud'e bakin shi yace "sannu da aiki malama idan kin gama ina buk'atar gyaran bedroom d'ina da bathroom " Kunnen uwar shegu mufidah tayi dashi ko jiyo wa ba tayi aikin da take ta cigaba kamar batasan da wani mutum a kitchen d'in ba, ganin hkan da musaddiq yayi ne ya sanya shi nufar inda take tare da sanya hannu ya janyo jelar gashin kanta wata er k'arar axaba ta saki tare da runtse idon ta tace "malam lafiar ka qlau ne da xaka ja min gashi " Ta k'arasa fad'in hka tana kici kicin kwatar gashin ta da ya rik'e, sai kawai ya janyo ta cikin jikin shi lokaci d'aya ya saki ajiyar xuciya daman abin da yake buk'atar yi kenan shi yasa ya dad'a tsokano ta. D'aure fuska yayi tare da cewa "ke kina jin ina miki magana ki rabu da ni saboda kin raina ni koh ?" "ni malam ka cika ni idan ba hka ba xan..... " Bata k'arasa fad'in maganar ba ya sanya hannun shi ya rufe bakin ta tare da cewa "me xaki iya yarinya ji yanda kin kasa kwatar kan ki kina wani ma......." Wata er k'ara ya saki kad'an wadda ta hana shi k'arasa maganar shi ashe mufidah ce ta cije shi a hannun ba shiri ya sake ta kafin yayi wani yunk'urin rik'e ta har ta fice daga kitchen d'in da gudu.............. Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM LIKE AND COMMENT'S FB PAGE 👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ *PAGE 48* Wani kyakkyawan murmishi ya saki tare da bin hannun nashi da kallo wurin da ta cije shi har wajen ya d'an yi ja, bakin shi ya kai a hankali ya sumbace shi kafin ya fita daga kitchen d'in. Suna xaune da dare a parlour kallo suke jefa jefa mumy da musaddiq suna er hirar su yayin da mufidah kuma ta fara gyangyad'in bacci a wurin saboda gajiyar da tayi afnan ma tana jikin musaddiq tana bacci. "mufidah tashi ki tafi bedroom ki kwanta " Cewar mumy da ta kula da gyangyad'in da take, ai kuwa da sauri ta d'an mik'e ta wuce xuwa bedroom musaddiq ya bi ta da kallo cikin tsantsar kaunar ta. Maganar da mumy tayi mishi ita ta dawo dashi daga tunanin da ya tafi tana mai cewa "musaddiq na gaji da maganar da nake maka don ka xo ka d'auki mufidah kak'i tsayawa kana yi wa mutane hanya hanya, dalilin da yasa ni da daddyn ka muka yanke hukuncin kawo maka ita nan, Sauran kuma k'i kula dasu yanda ya kamata ga amanar su nan na baka kada ka wulak'anta min 'ya kaji na fad'a maka " D'an murmishi ya saki cikin xuciyar shi yana cewa mumy dan bakisan irin son da nake yiwa mufidah ba shi yasa kike fad'in hka, na tabbatar da kinsan irin yawan son da nake mata da baxa ki fad'i hka ba, baxan iya wulak'anta mufidah ba ko wani ne naga xai wulak'anta min ita sai inda k'arfi na ya k'are bare ni, a fili kuma sai yace "mumy ki kwantar da hankalin ki kada ki damu xan yi duk yanda kike ce " "Yawwa Alhmdlh naji dad'i da ka fad'i hkan, Allah yayi muku albarka ya baku xaman lafia" "Ameeen thumma Ameeen mumyn na " Murmishi mumy ta saki na jin dad'in ganin d'an nata hankalin shi ya kwanta gashi har er k'iba ya d'an yi alamun ya samu kwanciyar hankali da nutsuwa. "sannan kuma kayi kok'arin sanya afnan a skul " "angama mumy na " Sun d'an jima suna hira kafin kuma kowannen su ya tafi d'aki don yin bacci tun da dare yayi. Ranar musaddiq yayi kwanan farinciki da jin dad'i tun da ga mufidahn shi a cikin gidan, yana son mufidah so irin wanda ba'a iya kwatan tashi so irin wanda baki baxai iya furta shi ba so irin wanda idan ya kama xuciyar mutum baya ta6a iya yi mishi ta sauk'i kai so so ne irin wanda kafin a samu mutum mai irin wannan son akan mace acikin dubban jama'a sai en k'alilan, da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da shi cike da mafarkan mufidah da shi masu dad'i wanda har bai so gari ya waye ba dama xai dawwama a irin hka da yayi farinciki mara misaltuwa. A hka mumy tayi kwanaki ukun ta, ranar da xata tafi ne da safe suka fita dukkanin su domin raka mumy yin siyayya a mall, da yake jirgin su tashin yammaci xai yi don hka suna gama breakfast suka fito. A wani babban mall suka yi masauki nan mumy ta fara siyayyan abin da take buk'ata, shi kuma musaddiq ya nufi 6angaren wajen sleeping dress dasu underwears xuwa English wears yana xa6ar duk wanda yayi mishi. Mufidah kuma da afnan suna tare da mumy suna xa6ar abin da suke so, sam mufidah batasan musaddiq ya nufi 6angaren wajen English wears ba sai ta nufi nan tana d'an dudduba wa, kamar ance ta d'ago kanta ai kuwa tayi mummunan gani da idanun ta, wanda lokaci d'aya wani axababben kishi ya turnik'e mufidah lokacin da ta hango musaddiq rungume da wata mace baturiya a jikin shi. Gaba d'aya sai ta rasa abin yi har wani duhu duhu take gani a idanun ta sam ta kasa dauke idanun ta daga kansu wani bakinciki da takaici ne ya kama mufidah, d'ago idanun shi yayi musaddiq ya hango mufidah a tsaye waje d'aya kamar wadda aka dasa ta, hannun shi yasa ya janye yarinyar gefe d'aya kafin yayi mata magana ta tsayin second biyar ya nufo inda mufidah take. Ganin har yaxo inda take batasan ma yaxo wajen ba yasa shi yin tafi da hannun shi biyu a dai dai fuskar ta tare da cewa "hey are u alright? " Yana wani shegen murmishi mai da idanun ta tayi kan fuskar shi ai kuwa ya kashe mata ido d'aya tare da d'aga gira, wani bak'in ciki da 6acin rai ne ya sake kama mufidah ganin ko ajikin shi abin da ta kamashi yana yi, ta ma kasa cewa komai ji tayi ya kama hannun ta da hannun shi ai kuwa ta fisge da k'arfi tayi gaba yana yi mata magana amman ko jiyo wa ba tayi ba, wani d'an sanyi yaji cikin xuciyar shi idan dai har hasashen da yayi hka ne to mufidah ta fara son shi tun da abin da ta nuna yanxu yayi alama da kishi, juya wa yayi ya d'auko kayan da ya gama xa6a ya nufo inda su mumy suke. Waje d'aya mufidah ta samu ta xauna har mumy ta gama siyan abin da take so musaddiq ya biya kudin suka fito, ko kallon inda yake mufidah bata yi ba fuskar ta tayi d'an ja saboda 6acin rai har mumy tana tambayar ta lafia kawai sai ta d'an wayance da fad'in kan ta ne yake ciwo sai sannu mumy take mata har suka k'arasa gida. Cikin bedroom ta shige ta fad'a toilet ta rufe da key kafin ta kunna shower ruwa ya fara xuba sannan ta fashe da kuka sosai tayi hkan ne don kada a jiyo sautin kukan ta, bata ta6a xaton son musaddiq yayi k'arfi hka a cikin xuciyar ta ba sai yau bata ta6a xaton tana da mugun kishi ba sai yau, taji ana fad'ar kishi amman batasan shi ba sai yau, daman hka musaddiq d'in yake d'an iska ne ma nemin mata, to idan ba ma nemin mata ba mai ya kai shi rungume macen da ba matar shi ba a jikin shi daman abin da yake aikata wa kenan shi yasa ya mak'ale a k'asar waje yak'i dawowa nigeria, ae kuwa baxan iya xama da maxinaci ba dole ya sake ni naje na auri kamilin namiji kamar sadeeq. Sadeeq baka San halin d'an uwan ka ba ne shi yasa kabar wasiyyar na aure shi me yasa kayi min hka sadeeq ina da kishi baxan iya xama da musaddiq ba, gashi son shi yayi min mugun kamun da ban ankara ba sai da lokaci ya fara k'ure min, tayi kuka sosai mufidah a wannan lokacin abin tausayi gashi sai knocking ake yi a kofar toilet d'in wanda ta sani tsakanin mumy da afnan ne suke yi. Kan ta ne ya fara wani irin ciwo ga idon ta sun kumbura sosai sun ja dakyar ta iya yin wanka ta sanya wata white d'in rigar wanka kan ta kuma wani k'aramin towel ne ta nannad'e gashin ta, tsayin rigar wankan iya cinyar ta ya tsaya da hka ta bud'e kofar toilet d'in ta fito, d'ago kan da xata yi ta had'a ido da musaddiq a tsaye bakin kofar toilet d'in ya hard'e hannun shi a kirjin shi ya tsurawa kofar toilet d'in ido yana tunani, ganin ta fito ne yasa shi sakin wata ajiyar xuciya tare da cewa "lafian ki qlau kika shiga toilet kika rufe wajen 1:30 hour kina ciki? " Wata harara ta dank'ara mishi da idanun ta jawur da suka kumbura, tuni musaddiq ya rikice ya nufi inda take yana cewa "subhanallah mufidah mai ya sami idanun ki hka? " Hannun ta ya sake rik'o wa saboda ganin tak'i kula shi ae kuwa ta sanya k'arfin ta ta sake fisgewa cikin dushashshiyar muryar ta tace "malam ka rabu da ni ina ruwan ka da abin da yake damuna? " Tana gama fad'in hka ta juya xata cigaba da tafiya ai kuwa ya janyo ta jikin shi ya sanya d'aya hannun shi ta bayan ta ya rik'e ta gam, d'aya hannun kuma ya rik'o fuskar ta 6ata fuskar shi tare da cewa "ba dai don kin ganni da wata ba ne kika shiga toilet kina kuka, kin fara sona kenan? idan hka ne kuwa ki bawa xuciyar ki shawara ta fitar da sona daga ciki idan kuwa ba hka ba xaki cutar da kanki, don ni musaddiq ba sa'an auren ki ba ne na aure ki ne don cika burin d'an uwa na sadeeq" Yana gama fad'in hka ya cika ta ya fice daga bedroom d'in, kusan suman tsaye mufidah tayi da jin abin da musaddiq ya furta mata daman ba sona yake ba?, xuciya ta mai yasa kika yi min hka, kika kar6i son mutumin da baya sona, wasu hawaye ne masu xafi suke fita daga idanun mufidah. Shi kuma musaddiq bedroom d'in shi ya wuce tare da rufe kofar ya jingina bayan shi jikin kofar wasu hawaye ne masu rad'ad'i suka fara xubo mishi dafe kan shi yayi yana cewa "me... me yasa baki na ka furta wannan furucin wajen masoyiya ta, kamata yayi nayi farinciki mufidah ta fara sona bai kamata nayi mata hka ba, yanxu ta ina xan gyara kuskure na, na rasa yanda akayi na fad'a mata hka nasan xuciya ta da kwakwalwa ta ba hka suke son na furta ba, baki na ne ya furta hkan, I'm so sorry mufidah, ta ina xan fara nuna miki soyayya ta bayan ke matar d'an uwa na ne baxan iya ba baxan iya mufidah ji nake kamar xan ci amanar sadeeq" Hka ya dunga maganganu cikin mayen son mufidah har xuwa lokacin da bacci ya dauke shi a k'asan carpet d'in d'akin. Yinin ranar kusan mumy ce da afnan suka yi shi a parlour musaddiq yana bedroom hka mufidah ma har xuwa karfe 5 na yammacin ranar tuni mumy ta gama had'a komai nata ta xaunar da mufidah da musaddiq tana sake yi musu nasiha sosai wanda kowannen su baya kallon d'an uwan shi kansu a sunkuye suna kallon k'asa. Bayan ta gama yi musu nasihar ne suka fita rakata airport, tun da suka fara tafia mufidah idanun ta suna kan window tana xubar da hawayen bak'in ciki abin da musaddiq ya gama yi mata d'axu gashi mumy xata tafi ta bar su, da hka suka k'arasa airport d'in mumy dai bakin ta bai daina furta musu wad'annan kalaman ba "kuyi hak'uri da junan ku don Allah ku xauna lafia ban da fad'a da tashi hankali ana yin hak'uri ana kai xuciya nesa, mmusaddiq ga mufidah da afnan nan ka rik'e su amana don su amanar d'an uwan ka ne, ka kula su don kai ne babba kuma namiji a cikin su " Lokacin da mumy xata shiga jirgi mufidah kasa jure wa tayi ta rungume mumy tana kuka sosai ita ma mumyn kasa rik'e hawayen ta tayi sai da suka fito afnan ma kukan take ganin yanda mumy da mameen ta suke kuka musaddiq ya dauke ta yana rarrashin ta, dakyar mufidah ta cika mumy ta wuce xuwa cikin jirgi ko k'ara waiwaye su ba tayi saboda kada su karyar mata da gwiwa, suna kallo har aka rufe jirgin ya fara tafia kafin ya tashi sama kuma da gudu mufidah ta shige cikin mota tana kuka.............. Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻£xclusive writers forum Like and comment's fb page 👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ *PAGE 49* shima musaddiq jikin shi a sanyaye ya shiga motar ya fara driven, sai da ya tsaya a hanya yayi musu takeaway na abincin da xasu ci da dare tukunna suka nufi gida,yana gama parking mufidah ta fito ta shige ciki kai tsaye bedroom ta wuce ta xube kan bed tun tana kukan har bacci ya sace ta tana faman ajiyar xuciya. Lokacin da musaddiq ya shigo d'akin ya dad'e yana kallon ta kafin ya kwantar da afnan a gefen ta wadda ita ma tayi bacci, shima nashi bedroom d'in ya nufa ya kwanta duk jin shi yake wani iri gidan ko kad'an bai yi mishi dad'i ba a hka shima bacci yayi awon gaba da shi. Firgigit mufidah ta tashi da addu'ar tashi daga bacci a bakin ta bin d'akin take da kallo kamar wadda yau ta ta6a ganin shi, duhu yayi sosai duk da kuwa hasken bulb d'in da ya haske d'akin kuwa. A hankali ta sauko da kafafun ta toilet ta wuce wanka da alwala ta d'aura ta fito wata jallabia irin ta mata ta sanya tare da hijab tayi sallahr mangarib da ishsha kafin ta d'ora da Shafa'i da wutri ta dad'e xaune tana addu'o'in ta kafin ta mik'e ta canja kayan jikin ta da na bacci. Tana kok'arin sake kwanciya ne musaddiq ya shigo had'a ido suka yi kowanne ya d'aure fuska tare da kawar da kanshi daga had'a idon da suka yi bud'e baki yayi yace "ki fito abincin ki yana dining table" Dakyar ta iya bud'e baki tace "bana buk'atar shi " D'aga kafad'un shi yayi tare da cewa "alright hkan yayi kyau " Yana gama fad'in hka ya fita daga d'akin mufidah ta bishi da kallo yau ko irin tsokanar nan babu, yau a musaddiq d'in shi yake kamar yanda ta san shi tsawon wasu shekaru da suka shud'e, wani hawaye ne ya xubo ta tana mai tausayin kanta, a hka ta kwana bata ci abincin ba, hkan kuwa ba k'aramin damun musaddiq yayi ba har shima ya kasa cin abincin ya kwanta. Tsawon kwanaki biyar da komawar mumy nigeria wadda ta je gida lafia, tsakanin musaddiq da mufidah babu mai kula wani kowa rayuwar shi yake shi d'aya, gashi ya sanya afnan a skul. Idan ya tafi hospital afnan ta tafi skul sai ita d'aya a gida duk bata jin dad'in xaman ko irin fita hka ba tayi duk kad'aici ya ishe ta, ai kuwa yau Bayan musaddiq ya fita hospital ne ta yanke hukuncin fita ko da iya layin da suke ne ta d'an wasa kafafun ta, tana sanye cikin wata gown milk colour tayi rolling kanta da green veil mai d'an haske flat shoes ne a k'afar ta sai phone nata a hannu da hka ta fito tana kallon yanayin unguwar da yayi matuk'ar birge ta. Ita kad'ai take murmishi sai kalle kalle take hankalin ta kwance iya layin da suke ta tsaya a karshen shi kafin ta jiyo ta dawo sai da ta kusan shiga gida ne wani bature ya matso inda take kamar xai rungume ta yana cewa "hey babe you're so beautiful, what's u name ?" A d'an tsorace mufidah ta d'ago kanta tana kallon shi tana kok'arin matsawa taji an taka wani uban birki a wajen, nan mufidah ta k'ara rud'e wa don Sauran kad'an a kwashe ta da mota, d'ago kan da xata yi ta hango musaddiq yana fito wa daga motar kamar wani xaki yanda ya wani fusata fuskar nan a d'aure babu alamar fara'a gashi idon shi sun ja inda suke ya nufa kafin ya k'araso mufidah ta afka cikin gidan a tsorace jikin ta har rawa yake yi ta wuce bedroom da gudu ta rufe tana haki xuciyar ta na bugawa da k'arfi don bata ta6a ganin musaddiq a wannan yanayin ba. Batasan ya suka k'are da baturen ba tana nan xaune wajen mintuna 15 taji gidan tsit alamun baya gidan wata ajiyar xuciya ta sauke ta kwanciyar hankali kafin ta shiga toilet ta watsa ruwa don tafi jin dai dai tana fitowa taji wata kishirwar ruwa ta kamata ga ba ruwa a d'akin tana d'aure da towel d'in ta fito xuwa parlour ta bud'e frige ta d'auki bottle d'in ruwa rufe frige d'in da xata yi ta jiyo ta ga musaddiq a gaban ta, batasan lokacin da bottle d'in ruwan ta fad'i ba ta dafe kirjin ta a tsorace saboda irin kallon da taga yake bin ta dashi. Matsa wa baya ta fara yi a hankali yana bin ta a baya har sai da ya k'ure ta a jikin bango ganin bata da wata mafita yasa ta bud'e baki cikin rawar murya tana cewa "mus......musaddiq ka.....ka tsaya nayi maka ba.... bayani ni wlh ban.....bansan shi ba kawai........" Kasa k'arasa maganar tayi ganin ya d'aga hannun shi sama da sauri ta runtse idanun ta tana cikin tsoro don tasan marin ta xai yi, gaban ta yana wani mugun bugawa, jin shiru bata ji saukar marin ba yasa ta bud'e idon ta d'aya a tsorace tana kallon shi ganin kallon da yake mata yasa ta sake runtse idon da k'arfi cikin tsoro. Hannun shi ya sanya a saman fuskar ta sai jin shi tayi yana Shafa fuskar ta tare da gyara mata gashin ta da ya manne mata a fuskar, sake runtse idon tayi da k'arfi jikin ta yana rawa saboda jin yanda yanayin ta ya fara canja wa tana sauke numfashi da sauri sauri, sai da ya gama gyara mata gashin fuskar ta ta fito sosai kafin yace "waya baki ixinin fita daga gidan nan, har wani ya tsayar da ke? " Shiru tayi mishi ta kasa magana jin hka ya shi cewa cikin tsawa "kina jin ina miki magana kin min shiru I'll slap u mufidah idan baki yi min magana ba ?" Gaba d'aya ta sake rikice wa da tsawar da yayi mata aikuwa ta fad'a jikin shi tare da rukunkume shi tana kuka sosai, lokaci d'aya yaji wani irin shock a jikin shi dif yayi shiru yana sauraren kukan ta da ya fara sanyayar mishi da jiki, cikin kukan muryar ta na rawa tace "ka...... kayi ha.....hak'uri don Allah ni bani ce na kula shi ba baxan k'ara fita ba " Baisan sanda ya k'ara rungume ta ba yana bubbuga bayanta tare da cewa "it's okay kada ki k'ara hkan " Gid'a kanta tayi tana sauke ajiyar xuciya sun d'auki en mintuna a hka kowannen su yana sak'a abu cikin xuciyar shi kafin kuma su ankara cikin sauri kowanne ya janye jikin shi kamar had'in baki, a tare kuma suka harari junan su mufidah har da murgud'a baki. "keee ni kika murgud'a wa baki? " Ya fad'i hkan yana mik'a hannu xai cafko ta aikuwa unexpected hannun shi ya dira a jikin towel d'in ta ya ja ae kuwa sai yayi k'asa a tare kamar had'in baki suka saki k'ara, da sauri mufidah ta durkushe yayin da shi kuma musaddiq ya juya da sauri ya fice daga parlourn yayi hanyar fita don time d'in d'auko afnan daga skul yayi. Tana ganin fitar shi ta wawuri towel d'in ta d'aura ta wuce bedroom da gudu sai da ta rufe kofa ta jingina a jikin ta tare da dafe kirjin ta tana cewa "wayyo Allah na amman musaddiq kirkin shi ya ragagge ne shine don wulak'anci xai wani rik'e min towel idan fah ya cire gaba d'aya fah " Tana haki ta furta hkan, kusan kwanaki biyu suna wasa 6uya a tsakanin su. Kamar yau wurin 9 na dare mufidah taje ta kwantar da afnan a bedroom ta fito xuwa parlour don k'arasa kallon film d'in da take yi, xaman ta da kamar mintuna 10 musaddiq ya fito daga d'akin shi yana d'aure da towel fitowar shi daga wanka kenan ya tuna ya mance phones nashi da laptop d'in shi a parlour tun da mufidah ta ganshi a hka ta runtse idon kamar mai bacci. Murmishi ya d'an yi don kallo d'aya yayi mata yasan ba bacci take ba, daukan laptop d'in da phone's nashi yayi har yaxo xai wuce ta inda take ya d'an taka mata kafa, wata er k'ara ta saki tare da saurin bud'e idon ta tana yatsina fuska don taji xafi "malam mene hka xaka taka ni don mugun ta " Shima d'aure fuskar yayi tare da cewa "ki had'a min coffee ki kawo min yanxu " Yana gama fad'in hka ya nufi bedroom d'in shi ya shiga, sai kawai mufidah ta tsinci kanta da tashi ta nufi kitchen ta had'a mishi sannan ta nufi bedroom d'in, wannan Karon shine shigar ta na farko d'akin yayi mugun tsaruwa d'akin fad'in yanda yake 6ata lokaci ne. Ko sallama bata yi ba ta shiga d'akin kanta tsaye kamar wani nata, ai kuwa idanun ta suka sauka kan musaddiq da yake kunce towel d'in shi xai sanya sleeping dress jikin mufidah ya fara 6ari na tsoro tuni ta saki tiren da ta d'ora mishi coffee d'in akai tare da runtse idon, shima kanshi musaddiq yaji wani iri Co's bai xaci xata kawo mishi coffee d'in ba ma balle har ta shigo mishi bedroom daman ya fad'a ne don tsokana ae kuwa ya juya bayan shi yana saurin k'arasa sanya kayan shi, Bayan ya gama sanya ne ya k'arasa inda mufidah take tsaye cak jiki na 6ari ya fisgo ta jikin shi da k'arfi har sai da ta saki k'arar tsorata ta bud'e idon ta da sauri, sai suka had'a ido kallon so da kaunar da suke yiwa junan su suka fara sun d'auki tsayin mintuna 5 suna a haka kafin musaddiq yace "keee waya sa ki shigo min bedroom kan ki tsaye? " Cikin dakiya da tsiwa mufidah tace "ba kaine kace na had'a maka coffee ba " "toh naji kin ga wani abin ne? " Cikin rashin fahimtar abin da yace mufidah tace "kamar me fah, ban gane ba? " Ajiyar xuciya ya sauke cikin xuciyar shi yana cewa Alhmdlh Allah nagode maka da bata ga wani abun ba, a fili kuwa d'an murmusa wa tare da cewa "okay shikenan ma " Da kallo mufidah ta bishi na mamaki mutum kamar mai iska yanxu ki ga yayi murmishi anjima kuma fuska a d'aure, hure mata ido yayi yana cewa "ni kada ki cinye ni wannan Kallon fah? " Ya k'arasa fad'i yana d'aga mata gira hararar shi tayi tare da wayancewa tace "Cabd'jam wa xan kalla kai Allah ya kiyaye " Girgixa kanshi yayi har yanxu mufidah tsiwar nan ta nanan "ki je malama ki k'ara had'a min coffee ki kawo min " Ta bud'e baki xata yi magana kenan taji ya had'e bakin ta da nashi ya fara yi mata wani soft kiss xaro ido mufidah tayi kirjin ta na bugawa da k'arfi, sai da ya dauki wajen mintuna 5 a hka kafin ya rabu da ita ai kuwa yana sakin ta mufidah ta fita daga d'akin da gudu, shi kuwa musaddiq xube wa yayi kan bed cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara................ Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *£xclusive writers forum* *likes nd comment's fb page*👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ _where are u guys this page dedicated to urs, ummu safwan marubuciyar (k'unar xuci),hafcycy, princess Ayeesha, farida, my dgter Mariam Omar, sis zahra (ke ta daban ce), baby, lil Ridallah and all member's Aishat A muh'd fan's ina jin dad'in yanda kuke kaunar littafin nan, wannan shafin na sadaukar muku dashi kyauta ina alfahari da ku_ #one luv guy's 👄 *PAGE 50* Tun daga lokacin mufidah ta dauke k'afar ta daga xaman parlour idan har afnan tayi bacci da dare saboda yanda musaddiq yake bin ta da wani mayataccen kallon kamar ya lashe ta, wanda kallon da yake mata ba k'aramin k'ara mata son shi a xuciyar ta yake ba, kula wa dasu sosai yake sai dai wani lokacin ya birkice mata kamar ba musaddiq ba ya xame mata abin tsoro yanda xai na d'aure fuskar shi magana ma sai ya ga dama xai yi mata, wani lokacin kuma tsokana xai dame ta dashi har sai ta gaji ta gudu d'aki ta rufe kanta. Kowannen su xuciyar shi cike da kaunar junan su but miskilanci ya hana kowa bayyana wa kansu abin da yake kunshe cikin xuciyar su, sai faman nuk'u nuk'u suke da abu, mufidah ana ta ganin da tunanin bai kamata ta bud'e baki ta fad'a mishi tana son shi ba tun da ita d'iya mace ce kuma ansan macen da tasan kanta akwai alkunya da kawaici matsayin ta na mace kenan. Shi kuwa musaddiq yana son furta mata sometimes yasha yunk'urin fad'a mata but sai ya fara tunanin mufidah fah matar d'an uwan shi ce fa a da, taya xai iya sakin jiki da ita ya fad'a mata yana son ta har takaisu da yin wani abu daban anya xai iya hkan, wannan tunanin da yake shi yake karyar mishi da gwiwa ya kasa tunkarar mufidah shi yasa wani time d'in ya rikid'e mata yayi ta d'aure fuska ko magana baya son yi mata, but cikin xuciyar shi ba hka ba ne sam baya jin dad'in abin da yake mata. Irin xaman da suke yi irin xama ne da kowa yayi sha'anin gaban shi, sai dai suna cin abinci a dining tare kuma mufidah ce take yi musu girki ta wannan 6angaren bashi da matsala yana xama yaci abincin ta sosai don ta iya girki mufidah abincin ta nayi mishi dad'i sosai. A hka suka kwashe wajen watanni biyu suna irin wannan xaman nasu a cikin wannan lokacin musaddiq ta kai shi da ya fara gajiya da dauriyar da yake yi akan mufidah saboda irin shigar da take yi yake ganin ta, duk da ba wata shigar da take fito mata da surorin jiki take ba amman hkan ba k'aramin hargitsa shi ba, dare yana mishi tsayi sai dai yayi ta faman juyi yana sintirin xuwa bedroom d'in mufidah yana kallon ta tare da furta mata kalmar I luv u amman ya kasa bayyana hkan a gare ta. Har gwara da safe xuwa yamma yana hospital aikin shi na dauke mishi tunanin mufidah, gashi yana son su koma gida nigeria gaba d'aya don yana son ba wa iyayen shi kulawa tun da yanxu shi kad'ai ya rage musu, gwara ya xauna kusa dasu xasu fi jin dad'i shima sai hankalin shi yafi kwanciya, a kullum cikin yiwa sadeeq addu'a yake har yanxu cikin kewar d'an uwan nashi yake yana son sadeeq so mara misaltuwa son da yasan har shima ya mutu baxai daina yi mishi yana addu'a da fatan Allah ya bashi d'a namiji ya sanya sunan shi. Afnan ce da mufidah a xaune a parlour wajen misalin karfe 9 na dare mufidah na shan fruit yayin da afnan take shan ice cream can ta ajiye ice cream d'in tare da langa6e kai tace "mamee na bacci na ke ji" Murmusa wa mufidah tayi tare da cewa "ki tafi bedroom ki kwanta ni sai na k'arasa kallon film d'in da nake kallo " Sake shagwa6e fuska afnan tayi tare da cewa "ni mamee tare da ke xan kwanta " Hannun ta mufidah tasa ta ja kumatun ta tare da cewa "okay baby nah tashi mu tafi " Cikin jin dad'in abin da mufidah ta ce ta mik'e tare da kama hannun ta tace ''thank u mamee nah " Daga hka suka wuce bedroom, suna tafia musaddiq ya fito daga nashi bedroom d'in hasken bulb d'in parlourn ya kashe sai hasken jikin tv kawai kwanciya yayi kan 3siter tare da sanya hannun shi ya d'auko remote ya canja tasha xuwa wata channel da suke film d'in horror mai suna residents evil yana kallon shi hankali kwance. Lokacin da mufidah suka shiga bedroom ne bayan ta canja wa afnan kayan jiki ta tare da lullu6e ta da blanket tayi mata addu'a sannan tayi mata peck a kumatun ta tana cewa "sweet dreams baby nah" "thank u mamee nah " Murmishi suka sakarwa junan su kafin afnan ta rufe idon ta, ganin hka ya sanya ta wuce wa toilet wanka tayi kafin ta fito shirya wa tayi cikin wasu cotton d'in sleeping dress riga da wando masu laushi farare dasu sai dai tsayin wandon bai kai har k'asa ba. Gyara gashin kanta tayi tare da sanya ribbon ta d'aure shi perfumes ta fesa sannan ta fito xuwa parlour don ta cigaba da kallon ta, tun kafin ta k'arasa cikin parlourn k'amshin perfumes d'in ta ya fara shak'ar shi a kofofin hancin shi. K'ura mata ido yayi har ta k'araso cikin parlourn bata kula dashi ba ta xauna tana janyo ice cream d'in ta sha ta fara yi hankalin kwance tana kallon film d'in da musaddiq ya sanya sam batasan film d'in da yake kallo ba tuna ita ba ma'abociyar kallon horror movies ba ce. Gashi bata san musaddiq yana parlourn ba yana aiki kallon ta sai lashe lip's yake yana Kallon cute lip's d'in ta yana motsi yayin shan ice cream d'in da take, yana ayyana wasu abubuwa cikin xuciyar shi. Ta d'ebo ice cream d'in xata sanya a baki idon ta akan tv unexpected ta ga an nuno wasu horror bakyan gani bakin su kaca kaca da blood, wani tashi mufidah tayi wanda sai da komai na jikin ta yayi motsi tare da sakin k'ara tana runtse idon ta don sam jinin ta bai had'u da kallon irin moves d'in nan ba. Jikin ta sai 6ari yake tsabar tsoro da raxana tana cikin lalu6en hanyar guduwa bedroom ta rufe kofa sai taji tayi tuntu6e tare da hantsila wa kan kujerar da musaddiq yake kai ta fad'a kanshi. Nan ta sake rud'e wa da gigice wa don bata gane ko waye ba jin da tayi an rik'e ta k'am yasa ta dad'a kwalla k'ara a karo na uku ta bud'e baki sosai da k'arfi tana cewa "wayyo Allah na musaddiq kaxo ka taimaka min wani horror ya rik'e ni xai shanye min Jini" Iyakar k'arfin ta take kwad'a mishi Kira da neman taimakon shi, sai kokawar kwatar kanta take amman ta kasa tuni ta fara jan wani irin numfashi alamun daf take da sume........... Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *£xclusive writers forum* Likes nd comment's fb page 👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ _ina kuke kawayen arxiki da karamci wannan shafin na ku ne kyauta ina alfahari da ku, zeee yabour marubuciyar (itace kaddara ta), sajida niger marubuciyar (duk karyar kada ta ruwa ce), khadija neenah tawa marubuciyar (Deejah) salma Ali wada marubuciyar (namijin gaske), my biebie dear marubuciyar (d'an hakin da ka raina), and Queen Ayush marubuciyar (ya sayyadi), ni Aishat A Muh'd ina muku fatan alkhairi Allah ya bar xumunci ina yin ku guy's_ 👄 *PAGE 51* Ganin tana neman sume mishi a wurin ya sanya shi gimtse dariyar muguntar da yake yi mata tare da sanya hannun shi yayi hugging d'in ta very tight kafin kuma yayi amfani da d'ayan hannun shi yana bubbuga mata bayanta cikin kunnen ta yake furta "shhhhhhh mufidah calm down kina tare da ni babu abin da xai same ki relax " Jin muryar musaddiq ne yasa shi saukar mata da wata nutsuwa ta daban sai ta fara sauke ajiyar xuciya har yanxu dai jikin ta 6ari yake na tsoro gashi kirjin ta sai bugawa yake da k'arfi ta bi ta wani k'ank'ame shi sosai idon ta a runtse suke don tana tunanin idan ta bud'e su xata iya ganin horror d'in da ta gani. A hankali yake bubbuga bayanta tare da hura mata iskar bakin shi cikin kunnen ta hkan ba k'aramin saukar mata da kasala yayi ba, babu dad'e wa bacci yayi awon gaba da ita a hkan gashi kuma duk tabi ta k'ank'ame shi sosai da dubara ya tashi tare da kashe tv d'in ya dauke cak bedroom d'in ta ya kaita ya kwantar da ita kan bed. Tashi yayi niyyar yi amman yaji ta dad'a k'ank'ame shi kamar wadda idon ta biyu sai ya koma ya xauna tare da kafe da ido yana wani murmishi shi kad'ai yasan ma'anar murmishin nashi, ya dad'e xaune a hkan yana tunani na daban a karo na biyu ya sake kok'arin tashi but har yanxu tak'i sakin shi dakyar da dabara ya kwace jikin shi yayi mata addu'a tare da lullu6e ta da blanket sannan ya tafi bedroom d'in shi . Yana tsaka da yin wanka yaji kamar ihun mufidah cikin sauri ya d'aura towel ko damuwa da wanke kumfar jikin shi bai yi ba ya fito da gudu yana kok'arin bud'e kofa ne ita kuma ta turo kofar sai k'um suka yi gware but mufidah bata damu da jin xafin da taji ba na bugewar ta fad'a jikin shi cikin shashshak'ar kuka tace "ni gaskia ka mayar da ni wurin mumy tsoro na ke ji " Musaddiq wanda yake dafe da goshin shi cikin damuwa yace "me yafaru kuma yanxu?" "ni ji nake kamar suna bina Allah tsoro nake ji " Raba ta da jikin shi yake kok'arin yi saboda ya fara shiga wani hali amman ina mufidah sai dad'a rik'e shi take tana kuka "okay okay ya isa hkan " Shiru tayi tana faman sauke ajiyar xuciya suna tsaye a hka wajen 5 minutes kafin ya fara kok'arin raba ta da jikin shi nan tak'i yarda, ya rasa yanda xai yi da ita gaba d'aya ta d'aga mishi hankali wata muguwar kasala ce ta baibaye shi har takai da ya fara jin nauyin jikin shi yana kok'arin xubar dasu a k'asa. Namijin kok'ari yayi wajen daurewa xuwa jan su saman bed ya kwanta yayin da mufidah ma ya kwantar da ita gefe amman sai da ta dad'a rik'e shi sosai, girgixa kai musaddiq yayi lokaci d'aya tunanin shi ya fara sauya salo xuwa wani abin daban. Kasa daure wa yayi ya lalu6o lips d'in mufidah ya fara kissing d'in su cikin wani yanayi na daban jikin shi har 6ari yake tsabar birkita mishi lissafi da mufidah tayi. Tuni mufidah ta wartsake daga baccin da ta fara yi saboda abin da taji musaddiq yana yi mata kasa kwace kanta tayi saboda rik'on da yayi mata irin na sadaukan maxa ne. Kukan da ta daina shi ya dawo mata ta fara kokawa saboda jin wannan bak'on al'amarin da yake kok'arin shiga tsakanin ta da musaddiq, sai da yayi romance da ita son ranshi, mufidah ido ya raina fata tun da duk kukan da take da kok'arin kwatar kanta da take ta kasa sai kawai tayi luf da ita ta mik'a wuya tun da duk ragowar k'arfin da yake jikin ta, ta rasa shi ganin hka da musaddiq yayi yasa shi cigaba da abin da yake yi. Yana daf da cimma burin shi ne mufidah taji ya tsaya cak kafin taga kuma ya tashi tare da shigewa bathroom tana jin k'arar yanda ya saki shower ruwa yana xuba a kanshi, da sauri ta mik'e ta gudu bedroom d'in ta sai da ta sanya key a kofar tukunna hankalin ta ya kwanta duk tsoron da take ji ya kau abin da ya koro 6era daga rami ya fad'a wuta yafi wutar xafi, kafin ta kwanta ta lullu6a da blanket har xuwa yanxu gaban ta fad'uwa yake jikin ta ma rawa yake, tana tunanin yau mai juyar da hankalin musaddiq har yayi kok'arin yin wani abin da ita. Tun da ta ta6a jin hirar shi a waya da muh'd har yake fad'a mishi shi ya rasa yanda xai yi da yanayin shi gashi baxai iya tunkarar mufidah da buk'atar shi ba ya bashi shawara yanda xai yi bata ji abin da muh'd ya ke fad'a mishi ba but taji musaddiq yana cewa wannan ba shawara bace baxan iya ba idan na gaji sai na sake aure amman dai so shi d'aya nake yiwa sweet baby nah, daga hka hirar tasu ta xo k'arshe sosai mufidah a lokacin ta fad'a duniyar tunanin wace ce sweet babyn musaddiq, tun kafin ta ganta ta fara kishi da ita. Tun da ita tasan auren had'i aka yi musu da musaddiq ba ganin juna suka yi ba suna so, a yanxu bata da tabbacin ko yana sonta, ita dai tasan ta fara son musaddiq a tun kafin ta auri sadeeq. Shigowar sadeeq cikin rayuwar ta shi ya hana son yin tasiri cikin xuciyar ta tun da ta riga da tasa a ranta sadeeq xata aura, amman xuwa yanxu ita kanta har tsoro take ji ganin yanda xuciyar ta take son musaddiq abin har mamaki ya ke bata, ita yanxu mene ne mafita. Da wannan tunanin bacci mai k'arfi yayi awon gaba da ita bata kai da ta nemo mafitar ba. Musaddiq kuwa tun da ya kunna wa kanshi shower ruwa yana xuba a jikin shi idanun shi a rufe suke ruf kan shi yayi xafi brain nashi tana tunano mishi da irin yanayin da shiga a en mintuna da suka wuce. Tunanin mafita shima yake ya gaji da wannan abin yana son kawo k'arshen irin wannan xaman a tsakanin shi da mufidah, ya d'auki tsayin mintuna 20 a hkan kafin ya samu kwarin jikin shi ya kashe shower d'in tare da d'aura towel ya fito. Ajiyar xuciya ya saki ganin mufidah bata d'akin kafin kuma ya saki wani murmishi yace "ashe ma tsoron bai kai xuci ba sai da ta gama hargitsa min tunani ta gudu idan na kama ki sweet babynah xaki yaba wa aya xak'in ta " Yana gama fad'in hka ya sake sakin murmishi yana tunanin yanda xai yi wajen fara janyo mufidah a jikin shi ta saba dashi yana son ta dawo bedroom nashi suna kwana tare ko da wani abin baxai had'a su ba shi dai yana ganin ta kusa dashi hankalin shi sai yafi kwanciya da hka shima bacci ya dauke shi mai dad'i cike da mafarkan mufidah........... Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *£xclusive writers forum* *Likes nd comment's fb page*👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ _ina masoyan my sister *sumayya salees sadeeq*,ina masoyan karanta littattafan ta irin su *rayuwar ashwema,dangartakar xuci, yareema jawad*kun ji ta shiru na kwana biyu hutu ta tafi amman yanxu ta xo muku da sabon wani daddad'an labari mai suna *DARIYA BA SO BA*my sister sumy muna biye da ke har xuwa lokacin da xaki kammala shi, maxa ku garxaya ku nemi shi don kada a bar ku a baya, ni Aishat A Muh'd ina miki fatan alkhairi tare da addu'ar Allah ya k'ara basirah da xumunci a tsakanin mu_ #ana tare *PAGE 52* Washe gari da safe tun da mufidah ta shirya afnan xuwa skul ta had'a mata komai ta dawo bedroom ta kwanta duk jikin ta ba k'arfi tana nan kwance taji an turo kofar tare da jin muryar musaddiq yana tambayar afnan "ina mameen ki afnan? " "daddy tana bedroom a kwance " Kafin mufidah ta lullu6e jikin ta da blanket har ya shigo suna had'a ido ya watsa mata wani kallo na daban wanda ya haddasa wa mufidah sake fad'a wa a kogin son shi gashi ya sake k'ara mata kasalar da take ji, kasa d'ago kai tayi ta kalle shi wasa kawai take da en yatsun hannun ta, bata ankara ba taga ya xauna a kusa da ita har suna jin d'umin numfashin junan su. Mamaki sosai ya sake rufe mufidah bata gama wannan mamakin ba taji ya rik'o hannun ta idanun shi a saman fuskar ta yana kallon ta yace "mameen afnan xamu fita ayi mana addu'a kuma muna buk'atar rakiyar ki ko xuwa parlour ne, ko afnan? " Cikin dariya afnan tace "Yes! Daddy, mamee ki taso please " Ta k'arasa fad'i a shagwa6e, shima cikin muryar shagwa6a yace "please mamee ki taso kada mu yi late fah " Gaba d'aya mufidah kasa kwakwkwaran motsi tayi saboda tsabar mamaki tana tunanin anya wannan musaddiq ne kuwa ba irin mafarkan da take yi ba ne, jin yana kok'arin d'aga ta ne yasa ta tabbatar ba a mafarki take ba idanun ta biyu. D'ago kanta tayi da sauri ta kalle shi suna had'a ido ya kashe mata ido d'aya da sauri ta kawar da kanta sam bata da kuxarin tafia tana tsaye cak ganin hka ne yasa musaddiq rik'e d'aya hannun ta yana cewa "afnan rik'e d'aya hannun mameen na ki mu tafi naga alama tayi suman tsaye sai mun tallafa mata " Dariya afnan ta sanya kafin ta rik'e hannun mufidah suna janta kamar mutum mutumi har xuwa compound d'in gidan a wajen motar shi suka tsaya afnan tayi kissing d'in hand d'in mufidah ta shiga mota ta xauna tana yiwa mameen nata bye bye amman batasan tana yi ba. Musaddiq ne ya matso kusa da ita sosai kafin ya rik'e hannun ta dukka biyun da nashi kallon ta yake fuskar shi dauke da murmishi yace "mameen afnan ina neman alfarmar gyara min d'aki xan dawo da wuri ina son xamu fita tare " Mufidah sai ta tsinci kanta da gid'a mishi kanta alamar to, wani murmishi ya saki tare da janyo ta jikin shi ya rungume yana cewa "thank u mameen afnan " Sakin ta yayi tare da bata peck a kumatun ta sannan ya shiga cikin mota yaja suka bar gidan yana hango mufidah ta madubin motar anan tsaye inda ya barta hannun ta d'aya dafe da wurin da yayi mata peck murmishi ya saki shi kad'ai wani dad'i da nishad'i yana ratsa xuciyar shi har ya sauke afnan a skul sannan ya k'arasa hospital. Bayan tafiyar su da mintuna uku sannan mufidah ta dawo daga suman tsayen mamakin da musaddiq ya gama bata, anya kuwa babu wata a k'asa canjawar shi farat d'aya daga daren jiya xuwa yau. Dole na tsaya na karance shi naga ne abin da yake cikin xuciyar shi kafin na sake dashi, murmishi tayi had'e da lumshe idanun ta tana tunanin lokacin da musaddiq ya rungume yarrr taji tsikar jikin ta ya tashi kamar a time d'in yayi hugging d'in ta. Da wannan tunanin salon da musaddiq ya fara ne ta nufi cikin gidan, tana xuwa ta fara gyaran gidan tun daga bedroom d'in ta ta fara xuwa parlour kitchen gyaran bedroom d'in musaddiq ne na k'arshe. Tana cikin kok'arin canja bed sheet ne taga wani k'aramin diary ya fad'o daga k'ark'arshin pillow daukan shi tayi tare da ajiye wa saman bedside, cikin lokaci kad'an ta canja fasalin bedroom d'in musaddiq ta gyara shi tsaf tsaf ko'ina tun daga toilet har xuwa cikin room d'in wani sanyayen k'amshin turaren room freshener yake yi bayan ta gama gyaran ne har xata fito idanun ta suka sauka kan diary d'in musaddiq da ta ajiye. Sai kawai ta tsinci kanta da son bud'e shi ta karanta shi d'auko shi tayi ta nufi bedroom d'in ta dashi har ta xauna xata bud'e shi ta karanta sai ta dubi agogo taga time yaja sai kawai ta ajiye ta nufi kitchen da niyyar idan ta gama girki ta dawo ta karanta shi. Kitchen ta shiga ta fara had'a musu abinci Kala biyu da snacks sai drinks d'in da tayi na xallar fruit salad tana gama wa ta jera su a dining table kafin ta gyara kitchen d'in tayi wanke wanke Bayan ta gama gyara ko'ina tsaf ne ta sake fesa air freshener a ko'ina. D'akin ta wuce ta fad'a toilet tayi wanka da alwala kafin ta fito ta xura jallabia sallah ta gabatar kafin ta gyara jikin ta cikin wani English wears riga pink colour da siket baki irin mai bud'e war nan daga k'asa belt d'in siket d'in ita ma pink ce tayi kyau sosai light make up tayi sannan ta fesa different colour's perfumes a jikin ta da humra kowanne motsi tayi kamshi ne daddad'a yake tashi a jikin ta. Bayan ta gama shirya wa ne sai ta xauna kan sofa phone nata ta d'auko ta kirawo umma dasu mumy suka gaisa kafin kuma su yi sallama ta ajiye phone d'in, xama tayi tana tunanin abin da musaddiq yayi mata da safe ba k'aramin tsaya mata a rai yayi ba. Sake hango diary d'in shi tayi a karo na biyu taje ta d'auka son karanta shi kawai take gashi book d'in ya birge ta sosai, hannu tasa tana kok'arin bud'e farkon shafin dai dai lokacin gaban ta yayi wani irin mugun fad'uwa............... _tohh fah readers ga mufidah da dairy d'in musaddiq ko xata karanta ko kuma xata bari, gashi kuma musaddiq ya fito da wani sabon salon ko me yake nufi da hkan, ku jira ni a next page don jin me xata kasance, ku dad'a hak'uri da ni na kusan gama muku shi gaba d'aya_ Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *£xclusive Writers Forum* *Likes nd comment's fb page 👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com *PAGE 53* Sake hango diary d'in ta yi a karo na biyu taje ta d'auko shi, son karanta shi kawai take gashi book d'in ya birge ta sosai, hannu tasa tana kok'arin bud'e farkon shafin dai dai lokacin taji gaban ta yayi wani irin mugun fad'uwa jikin ta ne yayi sanyi dakyar ta iya tattara k'arfin da yake jikin ta wajen bud'e first page d'in. Dummm wata muguwar fad'uwar gaba ta sake yi a karo na babu adadi sai dai wannan karon tafi ta koyaushe sakamakon ganin picture d'in ta wanda idan baxa ta manta ba ranar da suka had'a wa Yah Omar birthday party ne ta d'auka tana dariya tayi masifar yin kyau sosai a pic d'in. Tsura wa picture d'in ido tayi brain nata yana dad'a hargitse wa mene had'in pic d'in ta da Musaddiq da har xai sanya mata shi a cikin diary d'in shi, next page ta bud'e kuma taga ya rubuta Mufidah ina son ki kece rayuwa ta, na fara son ki tun ranar da na fara had'uwa da ke lokacin da kika shigo hall a time d'in da na ke lecture har na kore ki waje, nan gaban Mufidah ya cigaba da bugawa da k'arfi duk ta wani rud'e jikin ta har 6ari yake yi. Lokaci d'aya hawaye suka fara xuba a idanun ta cigaba da karanta duk wasu sirrikan cikin xuciyar Musaddiq har da text messages d'in da yake turo mata su duk ta gane su xuwa lokacin da ya fara kamu wa da ciwon xuciya duk a dalilin sonta!......... Tun kafin Mufidah ta k'arasa karanta wa take xubar da hawayen tausayin Musaddiq najin irin wahalar da Musaddiq yasha akan ta wani irin mugun tausayin shi ne ya dad'a kamata ga wani irin son shi da yake k'ara shiga cikin xuciyar ta. Ta dad'e xaune anan tana kuka dakyar ta iya jure k'arasa karanta wa, wani irin ciwon kai ne ya dirar mata lokaci d'aya ga idanun ta sun kumbura sun yi sosai saboda axabar xafin da suke mata ma dakyar take iya bud'e su. Dama Musaddiq hka yake son ta hka yayi dakon sonta da kaunar ta wanda daga k'arshe ya kamu da ciwon xuciya, why why Musaddiq da xaka 6oye min wannan abin kana dad'a cutar da xuciyar ka, daga yau ta dauki alk'awarin kasance wa da Musaddiq xan na kyauta ta maka tare da yi maka biyayya duk abin da xai mata ta dauki niyyar kyautata mishi duk mai yi maka irin wannan mugun son baxai ta6a iya jure wulak'anta wanda yake so ba. Tunani kala kala Mufidah ta dunga yi akan yanda xata kawo k'arshen wannan irin xaman nasu da Musaddiq, dakyar ta iya tashi tsaye ta nufi bedroom d'in Musaddiq ta ajiye mishi diary d'in kamar yanda ta ganshi, d'akin ta ta dawo kwanciya tayi kan bed ta kudundune da blanket sakamakon sanyin da ta fara ji yana ratsa gangar jikin ta. Cikin few minutes xaxxa6i sosai ya rufe Mufidah don ba k'aramin kuka tasha ba har ya sanya mata ciwon kai ga xaxxa6i ya rufe ta idanun ta a lumshe but hawaye suna fito wa daga cikin su ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta gaban Musaddiq tana bayyana mishi abin da yake kunshe cikin xuciyar ta. Jikin ta ya d'auki xafi sosai tana nan kwance taji shigowar motar Musaddiq cikin gidan runtse idon ta tayi lokaci d'aya kamar mai baccin gaske tayi luf da ita ko kwakwkwaran motsi bata yi. "Mamin Afnan where are you? " Taji muryar Musaddiq ta doki cikin kunnen ta wanda ya haddasa mata fad'uwar gaba a karo na babu adadi. Musaddiq da Afnan sai da suka duba parlour, kitchen, garden basu ga Mufidah ba tukunna suka yi tunanin ko tana bedroom don hka suka nufi nan. Tura kofar bedroom d'in yayi ya hango ta kwance kan bed ta kudundune cikin mamaki yace "Mamin Afnan lafia? " Jin tayi shiru bata bashi amsa ba ne yasa shi k'arasa wajen da take da sauri, hannun shi ya sanya tare da yaye blanket d'in da ta lullu6a da shi, hannun shi ya sanya saman wuyan ta da sauri ya janye saboda xafin da jikin ta ya d'auka, sake runtse idon ta Mufidah tayi gam ita a dole bacci take batasan hawayen da suke xuba a idanun ta sun fallasa ta ba. Cikin gigice wa Musaddiq ya ce "Mufidah xaxxa6i ne yake damun ki? " Ya sake tambayar ta a karo na biyu but tayi tsit ta kyale shi, ganin hkan da tayi kuwa ba k'aramin sake hargitsa Musaddiq yayi ba, baisan lokacin da ya xauna ba ya sanya hannun dukka biyun ya d'ago ta tare da yi mata maxauni cikin jikin shi lokaci d'aya suka saki wata ajiyar xuciya. D'ago kanta yayi yana kallon innocent face d'in ta yace "Mufidah nasan ba bacci kike ba ki bud'e idon ki ki kalle ni, ki fad'a min matsalar ki please " Wasu hawayen su suka sake xubo wa cikin xuciyar tana cewa Musaddiq babu abin da yake damuna sai halin da kake ciki ciwon da sona ya haddasa maka shi ya sanya ni shiga cikin wannan yanayin, a fili kasa magana tayi saboda yanda bakin ta yayi mata nauyi sosai. Muryar shi kamar xai fashe da kuka yace "na rok'e ki Mufidah ki sanar da ni " "daddy mai ya samu mami na? " Yaji muryar Afnan cikin tsakar kanshi, wayance wa yayi da k'ak'alo murmishin yak'e yace "Afnan babu abin da ya sami mamin ki bacci take yi " "toh daddy I'm hungry " Ta k'arasa fad'i tana yatsina fuska, ya rasa yanda zai yi Afnan zai je ya bawa abinci ko kula ya tsaya kula da Mufidah, ganin Afnan zata fara yi mishi kuka ya sanya shi ajiye Mufidah suka fito parlour yana waigen Mufidah. Sai da ya zuba wa Afnan abinci a plate tare da drink a cup ya zaunar tare da kunna mata tv channel d'in cartoon ya ce "babyn daddy kiyi xaman ki anan idan kin gama cin abincin ki kalli cartoon yanxu xamu fito da mamin ki, kin ji? " Afnan wadda take kai spoon na abinci baki ta gid'a mishi kanta tana murmishi, shima murmishin yayi yana jan kumatun ta na gefen dama kafin kuma ya wuce bedroom d'in Mufidah da sauri. A yanda take lokacin da ya fita a hka ya same ta da sauri ya k'arasa inda take tare da hawa saman bed d'in ya yaye blanket d'in da ta rufa tare da d'ago ta gaba d'ayan ta ya zaunar da ita cikin jikin shi yana tatta6a jikin tare da duba ta don ya fahimci abin da yake damun ta. Ganin bashi da kayan aiki cikin bedroom d'in ta yasa shi daukan ta ya nufi bedroom d'in shi da ita, yana bud'e kofar wani sassayan K'amshi mai dad'i ya fara ziyartar hancin kafin ya shimfid'e ta saman bed d'in shi da yasha gyara. Jiki na 6ari ya fara duba ta bai ga wani babban ciwo fiye da damuwa tare da kukan da tayi ne ya janyo mata xaxxa6in da ciwon kai, zuba mata ido yayi yana kallon ta cikin xuciyar shi yana tunanin wacce irin damuwa ce ta haddasa mata ciwo hka, gashi tak'i magana kuma har yanzu idon ta a rufe suke sai dai hawayen da yake zubo mata. Nan ya fara lalla6a ta don ta fad'a mishi abin da yake damun ta amman kamar da dutse yake magana, ganin baza ta kula shi ba yasa shi tashi bathroom ya nufa ya samu wani bowl mai kyau ya tari ruwa a ciki sannan ya d'auki towel k'arami ya fito xuwa inda take. Ajiye bowl d'in yayi saman bedside sannan ya fara kok'arin zame kayan jikin ta, ai kuwa da sauri ta mik'e zaune tare da bud'e idon ta tana rarraba su kamar wata mara gaskiya hkan da tayi ba k'aramin sanya Musaddiq dariya yayi ba amman sai ya gimtse ta. Ya cigaba da cire wa cikin tsoro Mufidah tace "Musaddiq mene haka kuma? " D'an murmishi yayi tare da cewa "jikin shi ya d'auki xafi da yawa ina son xan goga miki ruwa ko xafin ya ragu " Cikin rawar murya tace "ni.... ni gas.....gaskiya a'a zai daina " Wani murmishin gefen kumatu yayi tare da girgixa kanshi yace "bazai yiwu ba Mufidah idan baki damu da rashin lafiyar ki ba wasu sun damu " D'ago kanta tayi da sauri ta kalle shi cikin mamaki wato bama xai ce ya damu ba sai wasu da akwai aiki a gaban ta kuwa wajen tankwara zuciyar Musaddiq ya sakko su gyara zaman auren su. Gira ya d'aga mata kafin ya fara cire kayan runtse idon ta tayi gam har ya gama cire wa sai iya underwears kawai ya bar mata, sake runtse idon ta tare da k'ank'ame jikin ta tana jiran saukar ruwa a jikin ta amman taji shiru har tsayin wasu en mintuna. A hankali ta fara bud'e idanun ta suka had'a ido kuwa sake rufe su tayi da sauri ganin ashe zuba mata ido yayi yana kallon ta son ranshi wata irin kunya ce ta gama lullu6e Mufidah. Musaddiq wanda gaba d'ayan shi ya fara fita hayyacin shi ya kasa dauke idon shi akanta, gaba d'aya idon shi sun fara canja launi ga wani abu da yake ji yana tsirga mishi daga cikin brain d'in shi xuwa gangar jikin shi, wani tunani na daban ya fad'a 6angare guda kuma wani mugun son Mufidah ne yake dad'a ratsa zuciyar shi. Dakyar ya iya saita kanshi ya fara goge mata jikin nata had'uwar tattausar fatar jikin shi da nashi, shi ya sake haddasa Musaddiq shiga wani mayuwacin hali wanda ba don yana kok'arin danne abin da yake ji ba da xa'a yi mai gaba d'aya a yanxu. Bayan ya gama ne ya mayar mata da kayan sannan ya had'a mata tea a baki ya dunga bata har ta d'an sha tukunna yayi mata allura wanda yasha fama da ita kafin ta tsaya yayi mata, hka magani ma dakyar ta sha sannan ya kwantar da ita cikin jikin shi har bacci ya dauke ta mai nauyi tana jikin shi yana aikin kallon ta lokaci zuwa lokaci yana sakin murmishi shi kad'ai yasan zuciyar shi yanzu ta samu nutsuwa tunda ta sami abin da take muradin so............. Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *£xclusive Writers Forum* *Likes nd comment's fb page*👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com *PAGE 54* Zame ta yayi daga cikin jikin shi ya tare da kwantar da ita kafin ya tashi ya fito xuwa parlour wurin Afnan sai ya tarar ta 6ingire tana shan baccin ta kan carpet, d'an murmishi yayi tare da daukan ta ya kaita bedroom d'in Mufidah ya kwantar da ita, sannan ya fito ya koma d'akin shi. Kwanciya shima yayi kusa da Mufidah ya rungumo ta cikin jikin shi k'am kamar wanda xa'a kwace mishi ita zuciyar shi fal farinciki wai yau shine rungume da Mufidah wadda ya fitar da ran samun ta har abada sai gashi Allah yayi ikon shi ya same ta a lokacin da bai ta6a zato ba. Kallon beautiful face d'in ta yake yana hashashen wasu abubuwa cikin zuciyar shi cikin nishad'i yayi kissing lip's d'in ta yana nan kwance yana faman tunani har bacci mai dad'i yayi awon gaba da shi. *After 1 hour* A hankali Mufidah ta fara bud'e idanun ta har ta gama bud'e su gaba d'aya ba inda idon ta ya sauka sai kan kyakkyawar face d'in Musaddiq yana baccin shi hankali kwance, tamkar ba bacci yake ba kamar irin lumshe idanun shi yayi. Wani smiling tayi kaunar shi tana ratsa ilahirin zuciyar ta da jijiyoyin jikin ta, wani mugun son shi ne yake shiga cikin zuciyar, hannun ta ta sanya saman fuskar shi tana kyakkyawan sajen face d'in shi mai matuk'ar kyau da tsari ga laushi har ta kai saman lip's d'in shi tana zagaye su da 'yan yatsun ta, tana murmishi ita d'aya. Ba zato taga Musaddiq ya bud'e idon shi ya sauke su kan fuskar ta, suka had'a ido yana mata wani irin kallo mai tattare da ma'anoni daban daban. "wayyo Allah nah, Allah yasa bai ga abin da nake mishi ba?" Cewar Mufidah cikin zuciyar ta ga wata azababbiyar kunyar shi da ta rufe, d'aga mata gira yayi da sauri ta sunkuyar da kanta tana mai murmishin jin kunya. 'Yar dariya yayi kad'an yana sake hugging d'in ta a kunne ya rad'a mata "Mamin Afnan ya kika bari ki cigaba kinsan kuwa yanda nake ji kuwa? " Nok'e kai tayi tana cusa fuskar ta cikin chest d'in shi tana girgixa kai tare da cewa "ni fa ba abin da nake maka " Cakulculi ya fara yi mata tana dariya tare da kok'arin kwace kanta daga jikin shi but ta kasa hkan, cikin shashshak'ar dariya tana jan numfashi tace "Musaddiq ka bari please". Yana dariya yace "ai kuwa sai na rama yarinya tun da kika tashe ni a bacci ko na kirawo Afnan mu had'u mu danne ki kowa ya za6i inda yake so ya ciza " "wayyo Allah kayi hak'uri baxan k'ara ba " Ta fad'i cikin yanayin shagwa6a, nok'e kafad'a yayi tare da cewa "nak'i wayon yarinya " Nan ya cigaba da yi mata cakulculin sai da yaga tana kok'arin shid'e mishi ya barta tana mai da numfashi, ido suka k'ura wa junan su cikin wani irin shauk'in son junan su suke ke kallon junan su kowanne da irin abin da yake sak'awa cikin zuciyar. Musaddiq kasa jure wa yayi sai da ya had'a lip's d'in shi da nata ya fara kissing a nutse yana yawo da hannun shi cikin jikin ta, saukar lip's d'in shi a nata ne yasa ta lumshe idanun ta tare da sakin wata ajiyar zuciya ya gama saukar mata da kasala. Sun d'auki wajen tsayin 6 minutes a hka kafin Musaddiq a hankali ya zame jikin shi ya tashi kallon yayi da idanun shi da suka yi ja yace "tashi muyi wanka lokacin sallah yayi ". Mufidah wadda tun da ya tashi suka had'a ta dukunkune kanta cikin kafafun ta tana murmishin jin kunya, tana jin furucin shi ta yunkura ta sauka daga kan bed d'in kafin ya ankare ta kwasa da gudu ta bar cikin d'akin. Ba k'aramin dariya ta bashi ba amman ya danne dariyar yayi murmishi yana girgixa kai yace "huh... Mufidah yarintar ki tana birge ni ina son ki da yawa Allah yasa ke ma ki soni koda rabin son da nake miki ne " Yana gama fad'in hka ya wuce cikin bathroom ya fara wanka. Mufidah kuwa tana k'arasa wa cikin d'aki ta rufe kofar tare da jingina a jikin kofar tana dafe kirjin ta sai lokacin gudun da tayi ya bata dariya nan ta shiga yin dariyar. "Mamee lafia kike dariya ke d'aya? " Taji saukar muryar Afnan a kusa da ita, hannu ta sanya ta d'aga Afnan tana juyi da ita cikin d'akin suna dariya cikin farinciki da nishad'i kafin musamman ma Mufidah, ta sauke ta k'asa ta sanya hannun ta taja kumatun ta cikin dariya tace "ni da wannan rigimammen daddyn naki Afnan " Zaro ido Afnan tayi tana kad'a harshen ta tace "lalala Mamee daddyn nawa ne rigimamme? " "Ehh mana ya cika rigima kamar wani boy " Ai kuwa Afnan ta fara tuntsura dariya saboda boy d'in da Mufidah ta kirawo Musaddiq dashi, tana rik'e ha6a kamar wata babba tace "Mamee daddyn nawa ne boy ai kuwa xan fad'a mishi " "ba sai kin fad'a min ba Afnan naji da kunne na " Da sauri Mufidah ta jiyo suka had'a ido da Musaddiq yana sakar mata murmishi, da gudu ta fad'a toilet tare da sanya key tana murmishi ita d'aya kafin ta fara wanka. Bayan ta gama wankan ne ta d'aura alwala ta fito, ganin basa d'akin yasa hankalin Mufidah kwanciya ta fara gyara jikin ta sai da ta gabatar da sallah tukunna ta d'an yi light make up kafin ta shirya cikin wata pink gown colour d'in pink d'in mai d'an duhu kad'an bata kai har k'asa ba mai k'aramin hannu akwai kwalliyar duwatsu bak'ak'e a jikin gown d'in. Gyara gashin kanta tayi tare da d'aure shi da ribbon irin daga gefen nan tayi parking d'in shi tayi kyau sosai, different perfumes tayi using dashi har dasu humra masu kamshi sosai, ta kalli kanta a mirror ta tabbatar tayi yanda take so sannan ta zura bak'in flat shoes ta fito zuwa parlour tana tafiyar ta a nutse. Tun daga nesa Musaddiq ya hango Mufidah tana taho wa yana zaune kan dining table shi da Afnan suna cin abinci,sakin baki da hanci yayi yana kallon Mufidah gashi ya cika spoon da abinci ya kai kusa da bakin shi amman ya kasa k'arasar dashi cikin yana kallon ta. Har sai da ta k'arasa dining d'in sannan ta rik'e hannun shi da yake dauke da spoon ta k'arasar dashi cikin bakin shi, sai a time d'in ya dawo hayyacin shi gashi ba bakin magana saboda abincin da yake bakin shi. Sai Kallon da yake bin ta dashi tare da yi mata alama da hannun kinyi kyau ita ma da ido tayi mishi alamar nagode suka sakar wa junan su murmishi kafin su mayar da hankalin su kan cin abincin. Bayan sun gama ne Musaddiq ya kalli Mufidah yace "ki shirya zamu fita yanxu" D'an kad'a idon ta tayi tare da harshen ta wanda hakan ya tafiyar da Musaddiq zuwa wani wajen daban tace "ni ai na gama shirya wa mayafi kawai zan d'auka" Cikin salon tsokana tayi mishi maganar, hararar ta yayi kafin yace "ai ba tallan ki zan je yi ba, idan baki son zuwa sai mu tafi da Afnan " Cikin sauri ta mik'e tana cewa "tabd'ijam kama fara ai idan baku tafi da ni kuma ba inda xaku je " Tana k'arasa fad'in hka ta wuce bedroom Musaddiq ya bita da kallo yana had'iyar yawu sai da ta shige bedroom kafin ya dauke idon shi ya furzar da d'an huci yana cewa "huh Mufidah rigima don kinsan bazan jure ba ne shi yasa kika fad'i hkan " "daddy ita ma Mami rigimar ce da ita naji d'axu ma tace maka rigimamme? " Hannun shi yasa yaja karan hancin ta yana murmishi yace "Ohhh Afnan surutu ba na hana ki tambayar komai ba? " Langa6e kanta tayi gefe guda tare da cewa "Sorry daddy na dai na " "Yawwa 'yar albarka " Cikin shagwa6a tace "ni daddy big teddy bear xaka siyo min wadda tafi ta gidan mumy girma " "Angama baby na za'a siya miki " Rungume shi tayi cikin murna tana cewa "thank u so much daddyna " Kissing d'in ta yayi a kumatu yana k'ara rungume ta, yana son Afnan sosai jin ta yake tamkar sadeeq, tunawa da sadeeq da yayi ne ya haifar mishi da kewar d'an uwan nashi addu'a kullum idan yayi sallah sai yayi mishi wani lokacin ma idan tunanin shi ya fad'o mishi xai yi mishi ko kuma idan ya d'auko picture d'in su wanda suka dauka a tare yana kallo yana kewar d'an uwan shi duk jikin shi yayi sanyi surutun Afnan ma sama sama yake jin ta.............. Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *£xclusive Writers Forum* *Likes nd comment's fb page*👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com *PAGE 55* Mufidah ce ta fito cikin wata gown milk colour da adon flowers bak'i tayi rolling kanta da black veil tayi kyau, tana k'araso wa parlour inda suke tace "ai na d'auka kun tafi kun barni? " D'ago kanshi ya kawar da duk wata damuwa a fuskar shi ya kalle ta tare da cewa "kinci darajar Afnan da tace mu tsaya ki amman da tuni mun tafi " Turo bakin ta tayi irin na shagwa6ar nan kafin tace "ni na fasa fitar ma ku tafi " Kallon Afnan yayi tare da cewa "tafi mota ki zauna gani nan " Cikin murna Afnan ta fice da d'an gudun ta, kallon shi ya mayar kan Mufidah yana cewa "haba habibty ki taso mu tafi kinsan bazan ji dad'in fitar ba idan ba k.... " Ganin yanda Mufidah take kallon shi ne yasa shi tuna su6utar bakin da yayi ya wayance da cewa "ba fah da wata manufa na fad'a ba kada kiyi tunanin wani abin " Ya k'arasa fad'i yana tashi tsaye, girgixa kai Mufidah tayi tana murmishi cikin zuciyar ta mai cewa "ina mamakin wannan halin naka Musaddiq, kana barin abu cikin zuciyar ka ni kuwa zan sanya ka ka furta min sona cikin zuciyar ka a yau ba sai gobe ba insha Allah, tun da na gano ko wace sweet babyn ka " Tana k'arasa fad'in hka cikin zuciyar ta ta saki murmishin mugunta tare da mik'e wa tsaye, kallon ta yake yaga tana ta zuba murmishi ita d'aya yace "lafian ki qlau kike murmishi ke d'aya? " D'an murgud'a mishi baki tayi tana cewa "lafiyan kenan " Tana gama fad'in hka ta fice da sauri zuwa compound d'in bin ta yayi a baya yana murmishi shima cikin zuciyar shi yana cewa "yarinya yau zaki yi bayani don sai kin furta min abin da yake kunshe cikin zuciyar ki tukunna zan fallasa miki sirrin zuciya ta ". Sun zazzagaya wajen shak'atawa dasu mall sosai sun yi shopping abubuwa da yawa musamman kayan ci da na sawa abubuwa dai da yawa, tuni Afnan ta gaji har bacci ya kwashe ta a mota tana rungume da sabuwar teddyn ta. Daga k'arshe suka wuce wajen wani beach bayan yayi parking d'in motar shi ya sanya mata key suka jera suna tafiya ba k'aramin kyau da dace wa suka yi da junan su ba, d'an satar kallon Musaddiq tayi taga yana kallon wani gefe guda d'an murmishi tayi tana ayyana me zata yi yanzu wata dabara ce ta fad'o mata. Ai kuwa take ta aminta da dabarar daman hill shoes ta sanya sai kawai ta gurd'e k'afar ta tana sani ta tafi zata fad'i har da wani runtse idon ta kamar da gaske da k'arfin tace "wayyo Allah Musaddiq " Da sauri ya jiyo da kanshi ganin tana kok'arin kaiwa k'asa cikin sauri ya rik'o ta hannun shi yana tallafe da hips d'in ta d'ayan kuma da hannun ta, hango tsananin rud'e wa tayi cikin kwayar idon shi. "wash Allah na kafata" Ta furta hkan tana yatsina fuska kamar zata fashe da kuka, cikin sauri da damuwa kan fuskar shi yace "Ohhh mene ya samu k'afar? " Ya k'arasa fad'i yana kallon ta, cikin shagwa6a tace "ciwo take min " "sorry mu k'arasa mu zauna sai na duba miki" Gid'a kanta tayi sannan ya d'ago ta, sai tak'i take k'afar ya kalle ta yana cewa "ya dai? " "ni ciwo take min bazan iya tafiyar ba " Kamar da gaske take fad'in hka shi yasa bai kawo wani abun cikin zuciyar shi ba ya sanya hannun shi ya dauke cak suka fara tafiya hannun ta dukka biyun suna rataye a wuyan shi, fuskar tana wurin wuyan shi duk wani numfashi da take fitar mai d'umi yana dukan wuyan nashi tuni Musaddiq ya fara jin wani canji yanayi na daban a jikin shi, Mufidah kuwa sai murmishi take abin ta tana kalle kallen mutanen da suke wurin wajen ya birge ta sosai ba ruwan wani da wani kowa harkar gaban shi yake. Sun k'arasa inda zasu zauna ya sauke ta a hankali da sauri Mufidah ta canja fuskar ta irin ta damuwa sai wani yatsina fuska take, zaunar da ita yayi yana cewa "sannu " Ya fad'i yana tsugunna wa a gaban ta tare da cire takalmin da yake k'afar ta bayan ya cire ne ya tsaya kallon kyakkyawar k'afar ta ta kafin kuma ya fara d'an daddannawa kad'an cikin nutsuwa da hankali don kada yayi mata da k'arfi ta sake jin wani ciwon. "wash! da zafi ni ka bari zai warke fah " Ta fad'a tana k'ak'alo hawayen dole. "kinsan bazan jure ganin ki cikin ciwo ba don hka oya ki tsaya na gani " D'ago kanshi yayi ya kalle ta sai yaga tana hawaye cikin rud'ewa ya saki k'afar ya zauna tare da janyo ta jikin shi yana bubbuga bayanta yana cewa "sorry habibty na bari ki daina kukan nan kin ji? " Ai kuwa ta 6are baki ta saki kukan shagwa6a gashi tana kiran wayyo k'afar ta, kuma idan ya sanya hannu zai ta6a ta dad'a k'arfin kukan tana girgixa kai kada ya ta6a da zafi. Nan Musaddiq ya sake rud'ewa sosai shi yanzu ya zai yi mata ne idan zai ta6a k'afar zafi gashi bai ta6a k'afar ba tana mishi kukan zafi kuma shi bazai jure jin kukan ta ba, ganin tak'i shiru duk ta d'aga mishi hankali ne yasa shi had'e bakin shi da nata. D'an tutture shi ta fara yi ya sake matse ta a jikin shi d'if tayi da ita tana kar6ar sak'onnin Musaddiq daman ai kukan na k'ak'ale ne, sai da ya tabbatar ta had'iye kukan nata tukunna ya cikata suna had'a ido ya sanya d'an yatsan shi d'aya ya dungure mata kai yana cewa "rigimammiya ko Afnan bazata yi rigimar ki ba " D'an hararar shi tayi tana turo bakin ta tace "Duk rigima ta dai wani yafi ni " Kallon ta yayi yana cewa "dawa kike? " D'an kad'a idon ta tayi tana cewa "da wanda ya tsargu " Nuna ta yayi yana cewa "lallai yarinyar nan kin rainani da yawa xanyi maganin ki yanzu " Kafin ya k'arasa fad'i ta mik'e da sauri zata gudu ya kawo hannun shi zai kamata sai ta goce tana mishi dariya har da gwalo, nan ya biyo ta suka fara gudu tuni su Mufidah an mance ciwon k'afar karyar da aka yi ta fara gudu tana dariya. Bata yi wani nisa sosai ba ya cafkota suka zube cikin farin yashin da yake k'asan wajen suna dariya tare da sauke numfashi da sauri da sauri, kallon junan su suke kafin Musaddiq ya sanya hannun shi ya d'an lankwasa d'an yatsan ta d'aya har yayi k'ara cikin jin zafi tace "wash ni me nayi maka ne da zafi fa?" Yana kallon face d'in ta yace "tunawa nayi da ciwon da k'afar ki take yi yanzu naga kuma kina gudu " "bata warke ba na dai na jin zafin " Ya bud'e bakin shi zai yi magana wayar shi ya fara k'ara alamar kira zaro wayar yayi ganin sunan Muh'd ya sanya shi picking d'in wayar, d'aya hannun shi kuwa ya janyo Mufidah ya kwantar da ita saman chest d'in shi don yau jin shi yake cikin wani irin farinciki da nishad'i. Muryar Muh'd ce ya tsinkayo yana cewa "Hey lover boy kana ji na?" Murmishi Musaddiq yayi yana cewa "ina jin ka mana ya akayi guy? " "Qlau jin ka nayi wajen 2 day's baka kirawo ni ba na kirawo ka kuma baka yi picking ba " "sorry guy abubuwa ne suka yi min over " Cikin zolaya Muh'd yace "ko kuma an tsaya cin soyayya ba an mance da ni " Er dariya Musaddiq yayi yana kallon idon Mufidah yace "kusan hkne fah guy kasan mutum idan yana moment d'in nan sai a slow " Wata dariya Muh'd ya kwashe da ita yana cewa "Ohhh sake maimaita min ban ji sosai ba " "kai fa d'an air ne wani lokacin nasan ka ji abin da na fad'i " "lallai guy kace kana nan kana fanshe soyayyar ka ta tsayin shekaru, hkan yayi kyau Allah ya kawo mana baby boy ko girl " Hannun Musaddiq yana kan Mufidah yana shafawa yace "Amin aboki tare da kai " "tabd'ijam an fad'a maka zan jira ka ne ai ni an kusa juye min " "Ah haba aboki da gaske? " Musaddiq ya fad'a cikin farinciki, cikin tabbatar wa Muh'd yace "wallahi aboki da gaske na ke " "wowww na taya ka murna sosai guy " Jin d'an hayaniya yasa Muh'd yace "kana ina ne Musaddiq ?" Cikin murmishi yace "me ka ji ne? " "hayaniya na ji kamar ma baka gida " "ina wurin beach muna hutawa " Cikin dariya Muh'd yace "wow lover boy kace kana hutawa, a dai yi a hankali kada ka 6ata mana Afnan don nasan ba hak'uri ne da kai ba ana barin sai bata nan " "Allah ya shirya ka Muh'd" "Amin aboki thank for your du'a" Kafin kuma ya cigaba da magana in seriously yace "Musaddiq ya kamata ka dawo nigeria fah kaga kai d'aya su mumy suke dashi a yanzu duk da basu nemi wani abin sun rasa amman nasan basa son zaman ka a australian, sun fi son zaman ka a tare da su ya kamata ka dawo " Ajiyar zuciya Musaddiq ya sauke a hankali kafin yace "nima nayi tunanin hka friend but insha Allah nan da d'an lokaci xamu dawo" "Yawwa d'an uwa, agaida min da Mufidah nd Afnan, kace wa Mufidah kasa ta mance da ni tun da kuka zo bamu ta6a yin waya ba ina jin zata kirawo k'awar ta (nafisat matar Muh'd),su sha hira amman ban da ni " Dariya Musaddiq yayi kafin yace " hkan ne dai dai guy " Shima Muh'd yana dariya yace "kai koh?, shikenan dai sai anjima " Yana gama fad'in hka Muh'd ya katse wayar lokaci d'aya Musaddiq ya saki ajiyar zuciya yana sake hugging d'in Mufidah zuciyar shi tana cikin farinciki............. Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *£xclusive Writers Forum* *Likes nd comment's fb page*👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com *PAGE 56* Yana gama fad'in haka Muh'd ya katse wayar, lokaci d'aya Musaddiq ya saki ajiyar zuciya yana sake hugging d'in ta zuciyar shi tana cikin farinciki, gaba d'aya ya mance ma inda suke ya mance yana tare da Mufidah a kusa zuciyar shi ta ingiza bakin shi har ya furta kalmar "i luv u Mufidah " Ba tare da ya shiryawa hakan ba, sai da ya gama furta maganar sannan ya dawo cikin hayyacin shi ya tuna su6utar bakin da yayi. Mufidah kuwa kusan suman zaune tayi saboda jin kalmar da ta fito daga bakin Musaddiq kallon shi take fuskar ta d'auke da tarin mamaki. Wayancewa yayi ta hanyar hararar ta kafin yayi magana cikin sautin tsawa yace "malama d'aga ni zan tashi kin wani danne ni " Girgiza kanta kawai tayi tana tashi daga jikin shi, bata ko kalle shi ba ta nufi inda suka yi parking motar su ta tsaya tare da sunkuyar da kanta tana kallon k'asa zuciyar ta sam babu dad'i, don ta tsani ayi mata tsawa a rayuwar ta. Bin ta yayi da kallo jikin shi yayi sanyi sosai wani mugun tausayin ta ne ya rufe shi,akan mene zai yi mata tsawa me tayi mishi, dole yayi yak'i da zuciyar shi don samun zaman lafiyar su, bazai yiwu su cigaba da irin wannan zaman ba. Jikin shi a sanyaye ya fara tafiya zuwa inda take, bud'e motar yayi da key d'in hannun shi, cikin sauri Mufidah ta shiga ta zauna har yanzu still bata kalli inda yake ba, shima shiga yayi ya zauna ya kasa kunna motar su tafi kallon ta yake yi ko zata d'ago kanta ta kalle shi. Sun d'auki tsayin mintuna bai ga alamar zata yi mishi magana ba ko zata kalle shi, sai kawai yayi wa motar key suka bar beach d'in, tafiya suke shiru kowannen su zuciyar shi da abin da take sak'awa, sam dawowar bata yi musu dad'i ba kamar yanda suka taho ba cikin farinciki da nishad'i ba. Suna k'arasa wa gida yana gama parking Mufidah ta bud'e murfin motar ta fita tare da bud'e murfin motar na baya ta d'auki Afnan dakyar ta fito tana tafiya har tana kok'arin fad'uwa. Da kallo ya bita fuskar shi da zuciyar shi d'auke da damuwa yana son yi mata magana but bakin shi yayi mishi nauyi sosai ya kasa yi mata magana, yana kallon ta har ta shige ciki tukunna ya fito daga motar tare da d'ebo shopping d'in da suka yi ya nufi cikin gidan. Ko da ya shiga bata parlour kayan hannun shi ya zube su tare da zama kan kujera yana dafe da kanshi, tunanin hanyar da ya kamata ya bi don ya rarrashe ta yake, yasan bai kyauta ba da tsawar da yayi mata. Mufidah kuwa tana shiga d'aki ta kwantar da Afnan kan bed sannan ta wuce toilet ta d'auki tsayin mintuna 5 a ciki kafin ta fito, fitowa tayi daga d'akin zuwa kitchen don ta had'a musu abincin dare. A parlour ta tarar dashi zaune bata kalli inda yake ba ta wuce kitchen abin ta, da kallo ya bita zuciyar ta gama yanke hukuncin a yau ba gobe ba zai bayyana mata irin tarin son da yake mata. Lumshe idanun shi yayi sakamakon fara jin k'amshin girkin da take yi ya fara dukan hancin shi, yana nan zaune Afnan ta tashi daga bacci ta fito zuwa parlour, cikin jikin shi ta shiga tana kwanciya, shafa mata kanta kawai yake don baya cikin nutsuwar shi. Bayan ta gama girkin ne ta jera a saman dining table, duk zirga zirgar da take akan idon shi d'in yana nan zaune a parlourn, bayan ta gama ne ta gyara kitchen sannan ta fito zuwa parlour ta gyara ta fesa air fresheners masu k'amshi. Tana gama wa da nan ta nufi d'akin Musaddiq ta gyara mishi tsaf, tare da sanya mishi room freshener, sai da taga komai yayi mata yanda take so sannan ta bar d'akin, tukunna ta fito ta nufi d'akin ta gyara shi tayi shima yayi tsaf dashi. Sannan ta fito zuwa parlour inda Musaddiq yake ta nufa, sai da ta zo gaf dashi sannan ta kalli Afnan tace "Afnan zo nayi miki wanka " Tashi Afnan tayi ta nufi inda Mufidah take tsaye, hannun ta ta rik'e suka wuce d'aki, ta bar Musaddiq zaune anan cikin rashin samin mafita. Bayan tayi wa Afnan wanka ta gyara mata jikin ta ne cikin kayan bacci, tukunna Mufidah ta d'ebo musu abincin su ta bar na Musaddiq akan dining table, bayan sun gama ci ne, Mufidah ta kwantar da Afnan kan ta yana kan cinyar Mufidah tana karanta mata wani english novel's mai dad'i. Lokacin da Musaddiq ya wuce bedroom d'in shi yaga bata yi fushi ba ta tsaya ta gyara mishi sosai, sai yaji ya k'ara jin tausayin ta, wanka yayi tare da yin alwala ya fito, jallabiya ya zura ya fara gabatar da sallah bayan ya idar ne ya d'an jima yana addu'o'i kafin kuma ya tashi. Cire jallabiyar yayi ya canja da wasu white sleeping dress ya fesa turaren shi masu k'amshi, tukunna ya fito zuwa parlour dinning table ya nufa, amman wayam ya gani ba Mufidah da Afnan kuma wannan ne time d'in da suke had'u wa wajen cin abincin dare. Jikin shi ne ya k'ara yin sanyi a time d'in da ya tabbatar iya nashi abincin ta bari, bai wani iya ci sosai ba ya d'an ci kad'an ya tashi koma parlour ya zauna, tv ya k'ura wa ido yana kallon film d'in Jack the giant slayer da suka nuna wa a time d'in but zuciyar shi tana tunanin Mufidah. Tun Afnan tana sauraren ta har bacci ya d'auke ta, ganin tayi bacci ne yasa Mufidah gyara mata kwanciyar, ta d'ora kanta saman pillow ta lullu6e ta da blanket tare yi mata addu'a sannan tayi kissing nata a kumatu, d'ayan hannun ta yana gyara mata gashin kanta ganin ya rufe mata face d'in ta. Tashi tayi tsaye taga Afnan tana rik'e da hannun ta, murmishi ta saki tare da sunkuya wa ta cire hannun ta a hankali wanda Afnan ta rik'e, sannan ta rage hasken d'akin ya d'an yi duhu. Toilet ta wuce ta fara yin wanka, bayan ta gama ne sannan ta fito zuwa gaban dressing mirror ta fara gyara jikin ta tare da amfani da body sprays a jikin ta da humra. Sleeping dress d'in ta ta d'auko a cikin wardrobe nata, cire towel tayi tana kok'arin sanya kayan baccin, sai ji tayi an rungume ta ta baya, a tsorace ta saki er k'ara tare juya wa don ganin wane, jikin ta har rawa yake don ba k'aramin tsorata tayi. Saukar sanyayar muryar shi taji cikin kunnen ta yana cewa "calm down matsoraciya ni ne fah " Juyo wa tayi tana hararar shi cikin tsiwa tace "malam baka iya sallama ba ne zaka shigo min d'aki kai tsaye? " Kallon ta yake fuskar shi d'auke da murmishi cikin zuciyar shi yana cewa ta rama kenan, a fili kuma yace "ai ba laifi ba ne da na shigo d'akin mata ta koh?" Cikin mamaki tace "matar ka!" "Ehhh mana, ko laifi ne ?" D'an ta6e bakin ta tayi kawai, sam ta mance a yanayin da take, ganin irin kallon da yake bin ta dashi ne yasa ta kallon jikin ta. Zaro ido tayi tare da d'ora hannu akan ta tana sakin 'yar k'ara tare da zube wa a k'asa, ta had'e jikin ta waje d'aya cikin jin kunyar shi sosai. Dariya ta bashi sosai sai da yayi mai isar shi kafin ya tsugunna a gaban ta yana kallon ta yana cigaba da dariya. Cak ya tsaya da dariyar saboda ganin hawaye yana fita a idon ta, hannun shi ya sanya tare da kama kunnen shi dukka biyun yace "I'm so sorry Mufidah, nasan nayi miki laifi d'azu na tsawar da nayi miki, bazan k'ara ba fushin da kika yi dani, bazan iya jure hakan ba, forgive me please " D'an girgiza kanta tayi kawai bata iya cewa komai ba, langa6e kan shi yayi tare da cewa "please Mamin Afnan" Turo bakin ta tayi tare da cewa "ka fita idan na gama shiryawa ma yi maganar" Kafin ta ankare har ya sure ta gaba d'ayan ta ya nufi hanyar fita daga d'akin nata, don yau yana son ya warware matsalar su.......... Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *£xclusive Writers Forum* *Likes nd comment's fb page*👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com *PAGE 57* Kok'arin sauka take but yak'i sakin ta har ya k'arasa cikin d'akin shi, kan kyakkyawan bed d'in yayi mata masauki, cikin shagwa6a tace "ni fah bacci nake ji malam " D'an zaro ido yayi yana dariyar mugunta kafin yace "yarinya ai yau ke da bacci sai gobe " Ya k'arasa fad'a yana kashe mata ido d'aya, duk da kuwa bata ganin shi sosai saboda d'akin babu wadataccen haske, hararar shi tayi tana kok'arin sauka daga kan bed d'in. Ai kuwa ya sanya hannun shi ya fisgo ta cikin jikin shi, ta bud'e baki zata yi magana taji ya rufe shi da nashi, sai da yayi kissing d'in ta son ran shi, kafin ya cika ta suna kallon idanun junan su. Cikin wani irin shauk'in Mufidah, da wata irin murya da Mufidah batasan yana da irin ta ba yace "ina son ki Mufidah, i luv u Mufidah " Jin saukar muryar shi Mufidah tayi kamar a mafarki yana furta mata wannan daddad'an kalmar, ko kwakwkwaran motsi ta kasa yi, kamo hannun ta yayi tare da had'e su da nashi ya sake cewa "Ina son ki Mufidah, kina sona ke ma, ina son ki furta min wannan kalmar da na dad'e ina sauraren ta daga bakin ki ? " Wasu hawaye ne suka zubo daga idon ta, wanda na kasa tantance su na farinciki ne ko akasin haka, ganin hawaye suna zuba cikin idon ta yasa Musaddiq rikice, ba dai bata son shi ba, kasa magana tayi sai kukan da take tana kallon shi. Idanun Musaddiq sun yi ja saboda tsabar tashin hankali kada Mufidah tace bata son shi, hannun shi ya sanya dukka biyun ya rik'o kafad'ar ta, cikin sanyin murya yace "Mufidah kiyi min magana don Allah, ki fad'a min dalilin zubar hawayen ki " Sam Mufidah tak'i bud'e baki tayi mishi magana sai kukan da take, ba k'aramin rud'e wa yayi ba jikin shi har rawa yake, ga gumin da yake tsatstsafo mishi na tashin hankali,zuciyar shi bugawa da k'arfi take kamar zata faso kirjin shi ta fito. kunna hasken d'akin yayi tare da sakkowa daga kan bed d'in, bud'e locker d'in bedside yayi ya d'auko diary d'in shi, sake hawa kan bed d'in yayi tare da kamo hannun Mufidah ya damk'a mata diary d'in a hannun ta, cikin murmishi yak'e yace "ki bud'e ki karanta abin da yake cikin nan, nasan shi zai tabbatar miki da irin so da kaunar da nake yi miki " Ya gama fad'in haka yana kallon ta, idon ta akan diary d'in mene amfanin karanta shi, bayan ta san abin da yake cikin shi, gani yayi ta ajiye diary d'in a gefen ta, tare da matsowa inda yake, hannun ta ta sanya tana mai rik'o nashi hannun duk biyun, cikin sanyin murya tace "Mene amfanin karanta abin da na karanta " Cikin mamaki yake bin ta da kallo, hannun d'aya ta d'auko ta d'ora shi kan saitin zuciyar shi tace "Me yasa kake wahalar da kan ka Musaddiq, nasan abin da yake cikin diary d'in, saboda kukan da nayi na tausayin halin da ka shiga a dalilin sona, shine ya haddasa min xaxxa6i a jiki na, bazan iya butulce wa zuciyar da take yi min wannan son ba " D'an jan numfashi tayi tare da yin murmishi ga hawaye suna zuba, ganin yanda Musaddiq ya bud'e baki da hanci yana kallon ta, muryar ta na d'an rawa ta cigaba da cewa " Na tausaya maka halin da ka shiga sosai duk adalilin so na, gaskiya kai ba k'aramin masoyi na ba ne, wanda yake min so na gaskiya, nima ina...... " Bata k'arasa fad'i ba, sakamakon kukan da kubce mata, rungume ta yayi cikin jikin shi, yana fitar da wani irin hawaye a idon shi. "Mufidah ki dai na kukan nan, ya isa haka kukan ki na ta6a min zuciya ta, na baki diary d'in nan don ki karanta, nasan baki na ba zai iya fahimtar da ke yanda nake son ki ba, ina son ki Mufidah son da ba kowanne namiji ne yake yiwa matar shi ba, ina son ki son da zan iya mutuwa idan ace ban same ki ba, Mufidah ina son ki, son da fatar baki na bazata iya fayyace miki ba, ina son ki son da bazan iya........ " Da sauri Mufidah ta sanya hannu ta toshe mishi bakin shi tana mai sake fashe wa da wani irin kukan tausayin Musaddiq, shima hawayen ne suke zuba a idanun shi, cikin kukan ta dad'a k'ank'ame shi a jikin ta, wani son shi na k'ara ratsa zuciyar ta. D'ago kanta yayi yana kallon cikin kwayar idon ta yace , "ki fad'a min kina sona, ina son jin wannan kalmar" Cikin shashshak'ar kuka tace "ina son ka Musaddiq, i luv u so much irin wanda bakina bazai iya fad'a ba " Wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar shi, ya dad'a rungume ta cikin jikin shi, suna tona wa junan su asirin zuciyar su, acikin wannan lokacin ji suke kamar su fi kowa farinciki, jin su suke kamar su dawwama a hakan, suna masu faranta ran junan su. Daga nan sai wasa ya fara canja salo na daban, cikin 'yan mintuna Musaddiq ya fara aikawa da Mufidah xafafan sak'onnin shi, jikin shi har wani rawa yake, gaba d'aya ya gama fita a hayyacin shi ya mance duniyar da yake ciki ma, zafafan kalamai yake furta mata su cikin wani irin shauk'in son ta. Soyayya da take kunshe cikin zuciyar shi ta shekaru ya gama fayyace wa Mufidah, ba tare da yasan yana hakan ba, kukan tausayin shi kawai Mufidah take zuciyar ta na k'ara son shi, iya wahala kam tasha ta a wannan lokacin, saboda had'uwar ta da jarumin namiji irin Musaddiq, ba ita kad'ai ba ma shi kanshi Musaddiq d'in ya wahala,har zuwa lokacin da mai afkuwa ta afku, kafin daga baya bacci mai dad'i ya d'auke su. *_ASUBA TA GARI MUSFEEDAH_* Tun a cikin daren gaba d'ayan su, kowanne ya kamu da zazzafan zazza6i a jikin su, har zuwa wayewar gari, dakyar Musaddiq yayi k'arfin hali ya tashi, wanka yayi tare da alwala sannan ya fito a toilet. Sallah yayi kafin ya taimaka wa Mufidah ita ma tayi wanka, sai da tayi sallah tana idar wa wani nauyayyen bacci yayi awon gaba da ita, ga jikin ta zafi har yanzu zazza6in bai sauka ba. Shima Musaddiq d'in bacci ne ya d'auke shi mai nauyi sosai, don ba'a samu cikakken bacci ba, gashi kuma an tashi da zazza6i. Knocking d'in kofar da ake yi ne ya tashi Musaddiq daga baccin da yake yi, dakyar ya iya lalla6a wa ya tashi tare da bud'e kofar, Afnan ya gani a tsaye tana kuka da alama ta dad'e tana yin knocking d'in, jikin shi ta fad'a cikin muryar kuka tace "daddy ina kuka shiga kai da mami? " Shafa kanta yayi tare da cewa "Afnan bacci muke yi, sannan mamin ki bata jin dad'i, kada ki tashe ta mu je na shirya ki, akwai skul " Nan yaja hannun ta zuwa d'akin Mufidah ya shirya ta cikin uniform d'in skul, sannan suka fito ya had'a mata tea tare da soya mata eggs, tayi breakfast sannan ya wuce kai ta skul, bayan ya ajiye ta ne ya dawo gida yana addu'a cikin zuciyar shi Allah yasa Mufidah zazza6in jikin ta ya sauka. Lokacin da ya shiga bedroom d'in shi bai tarar da Mufidah ba a ciki ba, sai ya wuce bathroom yayi wanka, sannan ya fito ya shirya cikin wani yellow 3quater and white T-shirt mara hannu, ya fesa different perfumes a jikin shi kafin ya fito zuwa d'akin Mufidah, jin shi yake yau wasai dashi kamar wanda aka sauke wa wani babban abu a kanshi da cikin zuciyar shi. Yana tunanin halin da suka kasance shi da Mufidah a tsayin daren jiya,murmishi ne shimfid'e a saman fuskar shi na farinciki da nishad'i, yana k'arasa shiga cikin d'akin, ya hango ta kwance saman bed har tayi wanka ta shirya cikin wata doguwar riga har k'asa mai hannun vest, irin mai kwanciya a jikin nan ce, idanun ta a lumshe suke but ba bacci take ba, tunanin Musaddiq d'in ta take. Daddad'an k'amshin perfumes d'in shi ne ya ziyarci cikin hancin ta, d'umin jikin shi taji a nata, a nutse ta bud'e idon ta ai kuwa suka had'a ido, yana wani haske ta da kyakkyawan murmishin shi, d'an hararar wasa tayi mishi tare kok'arin tashi zaune. Cikin sauri ya janyo ta zuwa jikin shi yana cewa "sweet baby nah ya zazza6in naki, dafatan ya sauka ?" Ya k'arasa fad'i yana tatta6a jikin ta, jin babu d'umi yasa shi sakin ajiyar zuciya yace "naji jikin naki babu d'umi alamun ya sauka, gashi ni kin shafa min har yanzu ban daina jin shi ba " Kunyar shi take ji ta kasa yin magana, but fuskar ta d'auke da murmishi, ya gama karantar kunyar shi take ji, "Baki tambayi ina Afnan ba ?" Dakyar ta iya bud'e baki tace "Hmm nasan ka kaita skul, tun da na tashi ban gan ku ba " D'an murmishi yayi so yake ta d'ago kanta ya kalli face d'in ta, amman tak'i d'agowa, don haka ya sanya hannun shi ya dafe saitin zuciyar shi yace "Wash! Allah nah zuciya ta" A kid'ime Mufidah ta d'ago kanta tana kallon shi, ganin yanda ya kwanta sai juyi yake yana rik'e zuciyar shi, yasa Mufidah fara hawaye don duk a tunanin ciwon ne ya tashi, cikin rawar murya take cewa "wayyo Allah, sannu Musaddiq don Allah ka tashi mu tafi hospital " Ganin yanda ta rud'e ne yasa shi tuntsire wa da dariya, sakin bakin ta tayi tana kallon shi, ga hawaye na zuba, kawai sai ta d'auko pillow ta fara dukan shi da shi, Musaddiq yana dariya tare da yi mata gwalo kuma yana kare dukan. Gajiya tayi ta zube kan bed tana mayar da numfashi, janyo ta jikin shi yayi yana cewa "nima na rama abin da kika yi min jiya a wurin beach " Murmishi kawai take tana girgiza kanta, wato ashe ya gane karyar ciwo tayi. "ina son ki Mufidah " Ya furta hakan cikin kunnen ta, " nima ina son ka sosai " Ta mayar mishi da amsa suna yiwa junan su murmishi. A haka suka tashi zuwa parlour, kitchen suka shiga tare suka had'a breakfast bayan sun gama ne, suka sake koma bacci.......... Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *£xclusive Writers Forum* *Likes nd comment's fb page*👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com *PAGE 58* Baccin su suka sha sosai, basu ankara da tafiyan lokaci ba sai da aka kirawo Musaddiq a waya daga skul d'in su Afnan kan yazo ya d'auke, don anjima da tashin su, cikin sauri suka shiga wanka tare suka yi, bayan sun fito ne suka shirya a gurguje don tafiya d'auko Afnan. Bayan sun gama shirya wa ne, suka tafi school d'in d'auko Afnan, suna d'auko ta ya wuce dasu restaurant suka ci abinci,sannan suka wuce wayo cikin tsantsar farinciki suke a wannan ranar, sai da dare yayi suka dawo gida a gajiye. Wanka Mufidah tayi wa Afnan ta kwantar da ita, sannan ta shiga nata wankan kafin ta fito har Afnan tayi baccin ta saboda gajiyar da tayi, tana cikin shirya wa Musaddiq ya shigo d'akin yana cewa "My sweet baby laifi me nayi aka bar ni, ni da a parlour? " Jiyo wa tayi tana murmishi tace "ba laifin da kayi my man, wanka na tsaya yi ne " Shima murmishin yayi tare da cewa "Yayi kyau hakan habibty, mu tafi d'akin mu koh ya?" Yayi maganar yana d'aga mata gira, sunkuyar da kanta tayi tana murmishi tace "okay, yiwa Afnan addu'a kafin na k'arasa shirya wa " "toh angama ranki ya dad'e" Cikin sigar tsokana tace "Ohhh har na kai wannan matsayin? " Yana jan hancin ta yace "kin ma wuce haka baby nah " Yana gama fad'in haka ne yayi wa Afnan addu'a a jikin ta, sannan yaja ta suka bar d'akin zuwa nashi, hmmm wannan daren ma an bawa soyayya hakk'in ta sosai, don tsakanin Musaddiq da Mufidah kowanne yana nuna wa d'an uwan shi irin kalar son da yake mishi, kafin daga k'arshe bacci mai dad'i ya d'auke su, suna rungume da junan su, zuciyar kowa fal farinciki. *_ASUBA TA GARI MUSFEEDAH_* *AFTER 1 WEEK* (Agurguje) Cikin 'yan kwanakin nan tsakanin Mufidah da Musaddiq soyayya kawai ake xuba wa, suna bawa junan su kulawa sosai, hankalin su ya kwanta sun yi fresh abin su, suna waya sosai dasu Mumy, Daddy, Umma, Abba, Nabila, Yah Omar dasu Muh'd da matar shi Nafisat, ana jin lafiyar juna. Duk wani shiri Musaddiq ya gama yi na koma nigeria, hospital d'in da yake aiki yayi musu sallama tare da ajiye musu aikin su, sam basu ji dad'in barin Musaddiq asibitin ba, don ba k'aramin taimaka musu yake ba babban likita ne da yasan me yake yi, da haka suka rabu cikin tsananin kewar shi. Sai da Afnan ta samu hutu a school tukunna suka tattara inasu inasu suka bar Australian, suka tafi k'asar switzerland suka samu hutun tsayin sati uku acan. Kafin su nufi k'asar Saudi Arabian su yi umarah, sai da suka yi wajen sati hud'u a Saudi Arabian saboda Musaddiq ya d'an yi fama da mura da zazza6i, kafin daga baya ya warware su fara shirye shiryen dawowa gida Nigeria, sun yi tsarabar su sosai wadda zasu raba wa 'yan uwa, duk k'asar da suka je sai da suka yi tsaraba. Daman tuni an sanar da 'yan uwa dawowar su don haka aka fara shirin tar6ar su, ba irin Mumy da tafi kowa farinciki saboda Musaddiq da ya fad'a mata ya dawo gida kenan bazai koma Australian ba, ba k'aramin jin dad'i da farinciki tayi ba. Jirgin da suka hau saukar yamma yayi sosai daf da mangarib, bayan jirgi yayi landing mutane suka fara fito wa 'yan uwa sai wara idanu suke su hango ta ina zasu gano su Mufidah. Babu jima wa suka hango Musaddiq yana rik'e da hannun Mufidah, ga Afnan a kafad'ar shi tana bacci sun yi matuk'ar yin kyau sosai, fad'ar irin had'uwar da suka yi ma 6ata lokaci ne. Duk sai aka zubo musu ido ana kallon su, ganin yanda suka yi matuk'ar dace wa da junan su, ga wani kyau da suka k'ara da ka gansu kaga fulanin asali. Kunya ce ta rufe Mufidah ganin yanda ake kallon su, zame hannun ta tayi daga na Musaddiq kallon ta yayi kawai ya girgiza kai, tun kafin su k'arasa su Mumy ma suka taho aka had'u cikin farinciki, kowa bakin shi yak'i rufuwa saboda murna, nan aka gaggaisa da juna tukunna aka nufi motoci don tafiya gida. Dr Muh'd wanda ya zuba wa Musaddiq ido ganin yanda yayi k'iba kamar ba shi ba gashi sai murmishi yake saki yana wani jifan Mufidah da wani irin kallon so, sai ya kasa daure wa yayi ya ta6o Musaddiq yana cewa "lover boy adai kula ba mu kad'ai ba ne akwai surukan ka, kada ayi abin kunya a bari sai an ke6e " Hararar shi Musaddiq yayi tare da cewa "ke fah na fahimci d'an sa ido ne na k'arshe, ina ruwan ka da mu naga matata ce " Dariya Muh'd yayi tare da cewa "d'an duniya, naga alama ma mun kusan samin baby da gani baka yi sassauci ba wajen uhm " Bai k'arasa ba ya kwashe da dariya sai kawai Musaddiq ya biye mishi suka yi dariyar tare da tafawa, da haka suka k'arasa gida suna tsokanar junan su, uhm Aminan kwarai kenan, Musaddiq nd Muh'd kullum son junan su suke tamkar wasu 'yan uwa na jini, (ni kaina amintar su na birgine, don a yanzu kafin a samu irin aminan sai an tona, saboda son zuciya yayi mana yawa yanzu, Allah kada ka bamu ikon cin amanar mutumin da ya d'auke ka matsayin aboki, amini kuma d'an uwa, Amin). Bayan sun k'arasa gida ne mamaki ya kama Mufidah da Musaddiq ganin yanda gaba d'aya aka canja fasalin gidan, side d'in da Sadeeq da Mufidah suka fara zama tuni an rushe shi, an sake wani sabon fasalin mai kyau da tsaruwa, komai an canja na gidan tamkar bashi ba. A part d'in su Mumy aka zauna bayan anyi sallahr mangarib da ishsha ne, aka zauna yin kwarya kwaryar walima ta farincikin dawowar su Musaddiq gida lafia, anci ansha anyi musu addu'ar fatan alkhairi, kafin kuma kowa ya kama gaban shi cikin tsantsar farinciki. Bayan watanni biyu da dawowar su Mufidah Nigeria Nabilah matar Yah Omar ta haihu an samu baby girl, ai kuwa sun sha suna yarinya taci sunan Mufidah ba k'aramin jin dad'i Mufidah da Musaddiq suka yi ba, ai kuwa babyn tasha kaya sosai a wajen su. Bayan suna da kwana biyu ne Mufidah ta fara zazza6i sosai mai zafi nan Musaddiq ya rud'e sosai babu 6ata lokaci ya duba ta abin ka da matar likita nan ya hango babyn shi d'an wata biyu da sati uku a tare da ita, ai kuwa ya d'aga ta yana juyi da ita a cikin bedroom d'in cikin mamaki take kallon shi kafin ta bud'e baki tace "lafia dear? " Sakko da ita yayi tare da zaunar da ita kan sofa ya dire gwiwowin shi a k'asa tare da rik'o hannun ta cikin nashi yace "my sweet baby ina matuk'ar farinciki yau saboda na kusan xama uba shine baki fad'a min ba sai da na gano da kaina koh? " Wani murmishin jin kunya ta saki tana kare fuskar da hannun ta tace "ni....ni fah bansani ba da gaske " Tashi yayi ya xauna kusa da ita idanun shi cikin nata yace "ina son ki Mufidah bazan iya rayuwa babu ke ba kiyi min alkawari na kasance wa dani har abadan ba xaki guje ni ba" Bakin ta takai saman le6en shi ta sumbata kafin ta d'ora hannun d'aya cikin nashi tace "nayi alk'awarin kasance wa da kai my man har k'arshen rayuwa ta i luv u musaddiq " "i luv u too habibty " Ya k'arasa fad'i yana shigar da bakin shi cikin nata soyayya sosai suka gwada wa junan su a wannan lokacin don Mufidah ma ta mance da wani ciwo sai da ta dawo dai dai tukunna ta sanya mishi kukan shagwa6a ai kuwa ya dunga yi mata dariya kafin daga bisa ni ya 6ige da rarrashin ta. Su Mumy sunyi matuk'ar farin ciki da wannan albishir d'in da Musaddiq yayi musu na samun jika, daman tuni ta dauke Afnan daga wurin su tana hannun ta duk da kuwa gida d'aya suke zaune, su umma ma sunyi farinciki sosai, amman babu wanda ya kai Muh'd farinciki abokin shi ya samu matar da yake so gashi har zuri'a zata fara shiga tsakanin su, lokacin da Musaddiq yake sanar da Muh'd d'in bayan ya gama taya shi murna ne yace "aboki wai ina ciwon xuciyar taka ne? " "yaro tun da zuciya ta samu abin da take so, ai kuma shikenan " Dariya Muh'd yayi kafin yace "Toh Allah ya k'ara lafia " "Amin, don wani time d'in fah sai a hankali tana yi min ciwo, sai dai ina kok'ari wajen kiyaye abin da zai taso min da ciwo, kaddara tawa kenan Muh'd " Wani mugun tausayin shi ne ya kama Muh'd, nan ya yi mishi addu'ar Allah ya bashi lafia, kafin su yi sallama da junan su............ Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *£xclusive Writers Forum* *Likes nd comment's fb page*👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com *PAGE 59* Cikin kwanciyar hankali suka cigaba da rainon cikin Mufidah, su Musaddiq sai rawar kai ake za'a samu baby, kula da soyayyar Mufidah kullum k'ara k'aruwa take cikin zuciyar shi. Ta 6angaren Mufidah duk wani kyautata wa tana yi mishi sosai, bata yi duba da irin son da yake mata ta wahalar dashi ba, biyayya sosai take mishi duk wani abin da yake so take yi mishi, tana kok'arin kiyaye abin da zai d'aga mishi hankali har ciwon shi ya tashi. Duk lokacin da ta tuna sanadiyyar son ta ne, ya kamu da ciwon zuciya har kuka take yi mishi na tausayin shi, a haka cikin ta yake ta girma sosai, gashi babu wani laulayi sosai, sai dai yana sanya ta kwad'ayi. Ana cikin haka nafisat matar Muh'd ta haihu an samu baby boy, waiii murna wajen Musaddiq ba'a magana, kamar Mufidah ce ta haihu haka yake jin shi. Ranar suna sun yi hidimar suna sosai inda jaririn yaci sunan Musaddiq, rasa inda Musaddiq zai sa kanshi yayi don farinciki hak'k'a Muh'd aboki ne na gari, ya d'auke shi tamkar Yah sadeeq d'in shi, ya kashe kud'i sosai Musaddiq a wannan sunan,komai yak'i yarda Muh'd yayi sai shi, Mumy, daddy da Mufidah ma sun yi hidima sosai,sai dai fatan Allah ya raya lil Musaddiq. *AFTER 2 MONTH'S* Mufidah zaune take a parlourn Mumy akan kujera, ta mik'e k'afafun ta saman centre table, tana cin wani gashashshen nama ya sha cabbage, tomatoes and onions akai ga yaji mai dad'i a gefe tana dangwala dashi, gefe d'aya kuma ga coconut drink wanda yasha milk gashi yayi sanyi, cin abinta take hankali kwance. Duk wannan hidimar Mumy ce tayi mata, don ta hana ta yin wani aiki ko girki, kuma duk abin da tace tana so Mumy na kok'ari wajen sama mata shi, gaba d'aya ta duk'ufa wajen cin naman, batasan Musaddiq ya shigo parlourn yana tsaye sai kallon ta yake dawowar shi daga hospital kenan. Ta d'auka naman a jikin fork tana kok'arin kai wa bakin ta, taji an rik'e hannun ta da ta da yake d'auke da fork d'in, da d'an sauri ta juya kanta baya suka had'a ido da Musaddiq, sakarwa junan su murmishi suka yi cikin so da kauna, kafin Musaddiq ya juya hannun ta zuwa wajen bakin shi ya sanya naman har da wani lumshe idanun shi saboda dad'in shi, kafin ya bud'e su ya watsa kan fuskar Mufidah. Wadda ta ta6e fuska tana shirin yin kukan shagwa6ar da ta saba yi mishi, ya bud'e bakin shi yace "Wow gaskiya Mumy tana ji da ke, irin wannan cin dad'i haka, sai an bari na tafi hospital take shirya miki abin dad'i don kada na ci koh, aikuwa wannan ya zama rabo na daman yunwa nake ji " Ya k'arasa fad'i yana d'aga mata gira, turo bakin ta tayi gaba tare da cewa "ni dai gaskiya a'a, ai ba laifi na ne ba, babyn kane yake son ci " Mak'e kafad'a yayi tare da cewa "uhm uhm ni ban yarda ba, kullum ai tace wa baby na yake son abu don dai bashi da bakin magana " Yana gama fad'in haka ya kar6e plate d'in hannun ta, zama yayi kusa da ita sannan ya fara ci ,ganin haka yasa Mufidah fara tuttura k'afa zata fara kukan shagwa6a, dariya ya fara yi mata tare da sanya hannun shi ya d'an ja kumatun ta yace "sweet baby rigima ko Afnan kin fita rigima, toh dai wannan duk kukan shagwa6ar ki sai na cinye " Ya k'arasa fad'i yana mata gwalo, ai kuwa ta saki kukan shagwa6ar da babu hawaye sai goge idon da ake, shi kuwa Musaddiq sai tsokanar ta yake yi, gefe d'aya kuma yana cin naman tare da shan coconut drink d'in nan. Ana cikin haka sai ga Mumy ta shigo parlourn, ta tarar da Musaddiq yana faman tsokanar ta, girgiza kanta tayi tana murmishi idan da sabo ta saba da rabon wannan rigimar kullum, k'arasa wa tayi cikin parlourn tare da kallon Musaddiq tace "Ohhh ni, Musaddiq me yasa ka fiye tsokanar ta ne? " Turo bakin shi yayi irin na shagwa6ar nan yace "Mumy kullum sai kin nuna son kai, idan na tafi hospital sai ki ta bata abin dad'i tana ci ni ba'a ajiye min " Murmishi Mumy tayi tare da cewa "kai ai babba ne kuma kaga abin da take d'auke dashi, dole ana bata abin da take so, ina ce jiya wurin karfe 10 na dare ka fita samo mata shawarma da take son ci" D'an sosa kai yayi yana kallon ta, don ya tuna rigimar da tayi mishi jiya da dare, sai da suka kwanta bacci ta tashe shi ita shawarma take son ci, jiki na rawa ya tafi siyo mata, ko da ya dawo rabin d'aya ta iya ci a duk yawan da ya siyo mata, kafin yace "Ehemm na tuna Mumy, but ni ana ajiye min komai aka yi mata tun da ina taya ta rainon babyn " Murmishi Mumy tayi tare da cewa "shikenan za'a ajiye maka, amman na yau a hak'ura a bar mata" Mik'a wa Mufidah plate d'in yayi yana wani langa6e kai, kallon shi tayi sai taji ya bata tausayi, cikin murya k'asa k'asa don kada Mumy taji tace "My M, na bar maka kaci, daman na k'oshi " Ta k'arasa fad'i tana yatsina fuska, murmishi yayi tare da jan karan hancin ta yana cewa "Hmm da gaske kike habibty? " D'aga mishi gira tayi, nan ya d'an huro mata kiss da bakin shi, aikuwa ta lumshe idanun ta tare da bud'e su alamar ta kar6i sak'on nashi, lokaci d'aya suka sakarwa junan su murmishi. Mumy ma murmishin ta saki, zuciyar ta fal farinciki da kwanciyar hankalin d'an nata, kuma tana jin dad'in yanda Mufidah take bashi kula wa sosai. "Mumy ta bar min ba ashe ta k'oshi ma ta tsaya yi min rigima gashi har ya fara sanyi " "Hmm ka dai dame ta shi yasa ta bar maka " "Da gaske nake fah Mumy, koh Sweet baby? " "naji shikenan " Cewar Mumy, nan ya fara ci suna d'an ta6a hira har ya gama, ya sanya hannu zai janyo tissue ya goge bakin shi, da sauri Mufidah ta sanya hannu ta dauko mishi tissue paper d'in ta bashi, kar6a yayi tare da cewa "thank u habibty, Allah yayi miki albarka yasa ki haihu lafiya " Cikin jin dad'in addu'ar da yayi mata tace "Amin sweetheart ". Tashi yayi tare da cewa "Mumy yau na gaji, zan d'an je na huta kafin lokacin mangarib yayi " Gid'a kai Mumy tayi tare da cewa "Okay " Kallon Mufidah yayi suka had'a ido yayi mata alamar da ido ta taso su tafi, langa6e kai tayi tana nuna mishi Mumy na wurin, amman sai ya d'aga kafad'a alamar shi ina ruwan shi . Mumy tana kallon shi sai kawai ta tashi tana cewa "Mufidah ki tafi kema ki huta kin ji 'yata " Tana gama fad'in haka ta wuce kitchen, gwalo Musaddiq yayi mata don yana kula da kunyar da ta kamata, d'an hararar shi tayi irin ta wasan nan. "ta so mu tafi habibty" "zo ka d'auke ni idan kana son mu tafi " "kai babyna agajiye nake, gashi kin k'ara nauyi sosai " "toh shikenan tun da baza ka iya ba, naga kuma babyn ka ne ya samin nauyin tun da ba haka nake ba",ta fad'a cikin shagwa6a . 'Yar dariya yayi kafin ya k'arasa inda take yana cewa "Sorry 'yammata na, duk nauyin da kika yi Musaddiq d'in ki bazai kasa d'aukar ki ba " Hannun shi ya sanya tare da taimaka mata ta tashi tsaye, sannan ya d'auke ta cak suka fita daga side d'in Mumy zuwa nasu. Yana shiga cikin parlourn wani k'amshin turare mai dad'i ya ziyarci hancin shi, ko'ina tsaf dashi cikin zuciyar shi yana godiya ga Allah da ya azurta mishi Mufidah matsayin matar shi, duk da girman cikin da yake jikin ta hakan bai hana ta tsaftace ko'ina ba, duk buk'atar da yazo mata da shi zata kar6e ta ko a fuskar shi baza ta nuna mishi rashin jin dad'in hakan ba, ko da kuwa bata so, shi yasa kullum sonta yake k'ara shiga cikin zuciyar shi. Bai ajiye ta a ko'ina ba sai a bathroom, kallon ta yayi sai yaga tayi murmishi idan da sabo yaci ace ta saba da hakan, tun da kullum ya dawo daga office idan zai yi wanka tare suke yi, ba ma iya na lokacin ba kullum ma haka suke abin su. Bayan sun gama wankan sun fito ne, kowanne d'aure da towel akan bed ya zaunar da Mufidah tare da zama kusa da ita yace "habibty yaushe zamu fara zuwa siyayyan kayan babyn mu? " Kallon shi take cikin mamaki kafin tace "Sweetheart ina ce last week ka tak'ura wa Mumy taje dubai ta siyo komai" Murmishi yayi tare da cewa "Duk da haka baby na, ina son mu je ki za6i ra'ayin ki " Girgiza kai tayi tana jan kunnen shi d'aya da hannun ta tace "Wannan kunnen baya jin abin da nace mishi yau da safe, ba haka nace mishi a bar maganar nan ba " Yatsina fuska yayi tare da cewa "Wash habibty it hurts fah, zan rama nima " Dariya ya bata ganin yanda yake sosa wurin da ta rik'e, kafin tace "sai dai ka rame d'an samari " Zaro ido yayi kafin yace "tabd'ijam baby nine d'an samari? " Cikin dariyar tsokana tace "Ehh mana " Janyo ta yayi cikin jikin shi yana gyara mata gashin kanta tare da cewa "lallai baby kin rainani da yawa, ni yanzu daddy ne ina da Afnan ga shi kin kusa haifa min new baby's " Ya k'arasa fad'i yana shafa cikin ta tare da kissing d'in shi. "baby's naji kace ba?" Lumshe idanun shi yayi tare da bud'e su yace "Yes of course insha Allah baby's zaki haifa min " Kwa6e fuska tayi tace "Wayyo Musaddiq ba kasan yanda ake shan wahalar haihu ba ne " Dariya ta bashi ganin yanda tayi, cikin lalla6a ta yace "Haba wacce wahala kuma baby, lafiya zaki haihu mybe ma kina bacci zan tashe ki nace kin haifa mana baby " Sosai maganar shi ta bata dariya, nan ta shiga yin dariyar shima ya taya ta, tsaya wa yayi da tashi dariya ya zuba mata ido yana kallon ta cikin wata irin sha'awar ta, "I luv u Mufidah " Ya furta hakan cikin muryar shauk'in ta, "I luv u too " Mufidah ta mayar mishi da martanin maganar. Sake matse ta yayi cikin jikin shi yana lalubar bakin ta, kissing d'in ta ya fara yi, nan fah ya fara aika mata da zafafan kalamai tare da sak'onnin shi zuwa gare ta, cikin en mintuna suka fara shiga wata duniyar ta daban. *** *** *** Cikin Mufidah ya shiga watanni na 8 ya girma sosai, duk ta bi ta kumbura ga girman ciki, zama dakyar tashi dakyar don wani lokacin sai an taimaka da tashi tsaye. Ba k'aramin tausaya mata Musaddiq dasu Mumy suke ba, kullum cikin bata kula wa da addu'ar Allah ya sauke ta lafiya duk wani masoyin ta yake, don cikin yafi na Afnan girma sosai kuma tafi shan wahala. Gaba d'aya ta k'agu taga ta haihu ko ta huta da wannan wahalar da take faman sha, wani lokacin ita take k'arfafa wa Musaddiq gwiwa ganin duk yanda ya karaya ganin yanda take shan wahala. Sam hankalin shi yanzu ba'a kwance yake ba, hospital d'in ma yanzu bai fiye zuwa ba sosai, ko yaje ma hankalin shi yana gida, haka zai dawo gidan ya sata a gaba yayi ta kallon ta yana tambayar ta ko akwai inda yake mata ciwo, ko tana son wani abin. A haka lokaci yana tafiya, rana ku na wuce wa har cikin Mufidah ya shiga wata na tara da sati uku, ta kusan cinye wata na goma shiru babu alamar haihuwa, sai dai ciwon mara da baya da take yi, wannan kuma daman idan ciki ya tsufa haka zaka yi ta fama har zuwa lokacin da za'a haihu lafiya. Musaddiq gajiya yayi da ganin yanda take shan wahala duk ta rame sai kumburi da k'aton ciki da farin da ta k'ara yi, ya fad'a wa Mumy kawai ayi mata cs a cire cikin, nan Mumy tak'i yarda sam saboda duk wani gwaje gwaje da aka yi mata an tabbatar lafia qlau take da babyn, sai dai kawai lokacin haihuwar ne da bai zo ba. Sai da cikin Mufidah ya shiga wata 10 dai dai, a wata safiyar monday ta tashi da nak'uda, nan da nan suka wuce hospital d'in Dr Musaddiq, kai tsaye labour room na daban aka wuce da ita. Musaddiq kasa fita yayi daga room d'in yana rik'e da ita a jikin shi, ga Doctor Aishat nd nurse Billy ladan suna kanta lol, duk wani taimakon da ya kamata su yi mata suna mata. Mufidah wahala dai tasha a wannan lokacin, don sai ta ga haihuwar Afnan sauk'i gare ta fiye da wannan, Musaddiq har da hawayen tausayin habibty d'in shi, tun safe ake fama har zuwa daf da mangarib sannan Allah ya sauke ta lafiya, ta haihu beautiful baby's boy's d'in ta, masu kama da Musaddiq like father like son. Tuni Musaddiq mai hawaye ya koma yin dariyar farinciki, bayan angama gyara su tsaf ne an kaisu d'akin hutu, tukunna su Mumy suka samu ganin su. Kowanne ka kalle shi yana cikin farinciki da murna da wannan k'aruwar da aka samu ta yara biyu maza, Musaddiq wanda baki yak'i rufuwa yana zaune kusa da Mufidah da take baccin wahalar da ta gama sha. Dr Muh'd wanda ya ke d'auke da d'ayan babyn ya kalli Musaddiq yace "lover boy sai a daina kukan tausayi a koma na farinciki " Gaba d'aya aka kwashe da dariya, yayin da Musaddiq ya harari Muh'd, sai washe gari da safe aka sallame su zuwa gida, kafin su k'araso tuni 'yan uwa da abokanan arzik'i sun zo don taya su murnar samun kyautar Allah wanda kud'in ka ko mulkin ka bazai sa ka samu ba, sai dai idan Allah ya baka, Allah ya bamu yara masu albarka ya kare mana su tare da basa ilimi mai amfani, ya tarbiyyantar mana dasu irin tarbiyyar addinin islam, Amin. Mumy dawo da Mufidah tayi side d'in ta domin bata kula sosai, tana kuma taya ta rainon 'yan biyu don rainon su sai da taimako, hakan kuwa ba k'aramin tak'ura wa Musaddiq aka yi ba, shima sai ya tattara ya dawo side d'in cikin d'akin shi na da, Afnan sai rawar kai ake an samu k'anne har biyu. Daren ranar Musaddiq ya shiga d'akin Mufidah ya tarar da ita kwance kan bed, ga yaran kwance kusa da ita suna baccin su hankali kwance, k'arasa wa yayi ya zauna kusa da k'afafun ta yana cewa "Babyna kin yi bacci ne? " Tashi tayi tana murmishi tare da koma wa kusa da shi ta kwanta a cikin jikin shi, k'ara gyara mata kwanciyar yayi a jikin shi yanda zata fi jin dad'i sosai, "ban yi bacci ba, ina jiran ka ne don nasan zaka shigo " Mufidah ta bashi amsa, wani dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar shi, kullum Mufidah k'ara shiga zuciyar shi take, tana bashi duk wata kulawa da ta kamata, shafa fuskar ta yayi da hannun shi yace "Ngde da wannan kulawar take habibty " Kafin ya cigaba da cewa "wanne suna kike ganin zamu sanya wa yaran mu? " D'an murmishi tayi tana cewa "Ni ban da wani za6i sai naka, duk sunan da ka sanya musu yayi min " Wani murmishin jin dad'in abin da tace yayi, sake rungume ta yayi a jikin shi yana shak'ar daddad'an k'amshin turaren yace "sunan da nake son sanya musu shine, babban zai ci sunan Abubakar sadeeq d'ayan kuma sunan Muh'd ko ya kika gani idan bai yi ba sai ki fad'i wanda kike so" Wasu hawaye masu zafi ne suka zubo wa Mufidah, tabbas daman kudurta cikin zuciyar ta idan Allah yasa ta samu d'a namiji sunan Sadeeq zata mayar shi, sai gashi Musaddiq ma hakan ne cikin zuciyar shi. D'ago kanta yayi yana girgiza kanshi tare da sanya hannun shi yana goge mata hawayen fuskar ta yace "Kiyi hak'uri Mufidah addu'a kad'ai zaki na yiwa Yah sadeeq, don ita kad'ai ce zamu yi mishi mu nuna kaunar shi a gare mu, bana son ganin kukan ki, ki daina please" Cikin sanyin murya yake maganar, gid'a kanta tayi kafin tace "na daina, Allah ya jik'an shi da rahma " "Amin " Ya amsa, ganin ta shiga damuwa ne yasa shi rarrashin ta har ta dawo normal, kafin su cigaba da hirar har zuwa lokacin da Mumy tazo ta kore shi, don ya bar ta ta huta, haka ya tafi yana mitar hana shi sake wa da matar shi da 'ya'yan shi. Haka aka cigaba da hidindimu har zuwa ranar suna, lokacin dasu Mumy da Muh'd suka ji sunan yaran sosai sun yi farinciki ba k'arami ba, don sunan da Musaddiq ya sanya musu yayi dai dai, sai fatan Allah yasa su gado masu sunan. Muh'd a daren sunan ya shirya dinner sosai, ba wanda ya sani tsakanin Musaddiq da Mufidah sai da daren hatta kayan da za su yi amfani dashi ya tanadar musu, Musaddiq sam bai yi musu ba suka shirya suka tafi tare da twin's d'in su. Wow gaskiya wurin dinner d'in ba k'aramin had'u wa yayi ba, don mutane sosai Muh'd yayi gayyata, har da en Exclusive writer forum, ga en group d'ina Aishat A Muh'd fan's, can na hango momma na ta kaina (Aunty maijiddah) tare da twin's d'in ta, mutane sun yi k'ara wajen zuwa, ga fan's d'in Musaddiq da Mufidah (Musfeedah) nan duk sun zo na hango su gaba d'ayan su a wurin, sun sha gayu sai zuba iyaye ake, lol. Anci ansha anyi musu addu'ar Allah ya raya su, kafin kuma a tashi kowa ya kama gaban shi, Mufidah kuwa ta cika fam da fushi da kishi saboda yanda 'yammata suka dunga kula wa Musaddiq suna wani shishshige mishi, dakyar ya shawo kan kayar shi suka shirya, don sam bazai iya zaman second's ba da kwanciyar hankali ba idan Mufidah na fushi dashi. Sun cigaba da rainon twins d'in su har zuwa lokacin da suka yi arba'in, twin's sun yi wayo sosai, sun k'ara girma gasu da wayo yaran, dakyar Musaddiq ya yarda taje gidan su kwana uku tayi ta dawo shima kwanakin ukun kusan dashi aka yi kwanan, don zaman shi yayi ya kasa tafiya ko kunyar su Umma baya yi, Mumy dai taga rashin kunya kam ganin yanda Musaddiq ya tafi gidan surukai kwana................ Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *£xclusive Writers Forum* *Likes nd comment's fb page*👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com _Wannan shafin kyauta ne da duk wani masoyina da masoyin wannan littafin, ina muku fatan alkhairi_ *K'ARSHE* (LAST PAGE) *PAGE 60* Suna dawo ne ko kwana d'aya basu k'ara yi a side d'in Mumy suka wuce nasu part d'in, daman tuni Mumy ta gyara d'iyar ta ta don ya taga yanda d'an nata yake rawar jiki, haka ma Umma ta tsaya tsayin daka wajen gyara ta sosai, tanan 6angaren Mufidah bata da matsala. Ansha soyayya sosai a wannan daren tsakanin Mufidah da Musaddiq, sun kasance cikin farinciki sosai, ji suke tamkar don su aka hallaci duniyar saboda tsantsar farincikin da suka tsinci kan su a ciki, sun yi baccin su cikin kwanciyar hankali. Washe gari da safe Mufidah ce ta fara kok'arin tashi daga bacci da safe, bayan ta tashin ne ta fara kok'arin gyara gidan, cikin en mintuna ta tsaftace ko'ina ta sanya turaren wuta masu k'amshi tare da air freshener, tana gama wa ta wuce bedroom wanka ta fara yi wa twin's ta gyara musu cikin su tsaf, sannan ta basu abincin su suka sha, bayan ta d'ora su a kafad'a ne tana d'an shafa bayan su har sai da suka yi gyatsa tukunna ta kwantar da su. Toilet ta wuce wanka tayi sannan ta fito ta gyara jikin ta tare da yin light make up, wata atampha ta dauko tare ta sanya d'inkin riga da siket ne sun zauna a jikin ta sosai, tayi kyau tana cikin fesa perfumes ne Musaddiq ya shigo d'akin ko wanka bai yi ba sleeping dress ne kawai a jikin shi. Rungume ta yayi ta baya tare da kar6ar turaren hannun ta yana cigaba da fesa mata bayan ya gama ne ya ajiye akan dressing mirror, sannan ya cusa kanshi tsakanin wuyan ta yana shak'ar k'amshin daddad'an turaren ta har wani ajiyar zuciya ya ke saki. "Baby nah shine kika gudu koh, kika yiwa twin's wanka kema kika yi, aka mance da ni " Murmishi ta saki cikin k'ara kaunar mijin nata tace "Haba nawan ni na isa, yanzu zan zo na shirya ka, yau akwai zuwa hospital " D'an yatsina fuska yayi tare da cewa " ni yau hutu nake ba inda zan je" Cikin mamakin abin da yace d'ago kanta suna kallon face d'in junan su tace "Saboda me? " Hannun ta ya rik'o yana shafa su a hankali yace "dalili kike son sani uhm" Bai k'arasa fad'i ba ya kashe mata ido d'aya, tuni ta fuskan ci abin da yake nufi, d'an dukan wasa ta kai mishi a gefen kafad'ar shi ya goce yana mata dariya, nan suka fara wasannin su suna ta dariya daga k'arshe suka zube kan bed kusa da twin's suna mayar da numfashi, kafin daga bisa ni ta raka shi toilet yayi wanka, ta taimaka mishi ya shirya, sannan suka zauna yiwa twin's wasa. A ranar Musaddiq ba inda ya fita sai zuwa gaida su Mumy da suka je, acan ma suka yi breakfast suna gama wa,shima basu wani jima ba ya tak'ura mata suka tafi side d'in su aka bar Mumy da twin's, daman Afnan ta tafi school. *** *** *** *AFTER 7 YEAR'S* A cikin wad'annan shekaru da wuce zaman lafiya sosai ake tsakanin Mufidah da Musaddiq, haka ma ta 6angaren Mumy babu abin da ya sauya daga soyayyar da take nuna wa Mufidah. Haka amintakar da ke tsakanin Musaddiq da Muh'd kullum sake kaunar junan su suke, ta 6angaren Mufidah da Nabilah tare da Nafisat su ma kawancen su sosai suke yi sun zama tamkar 'yan uwa. A cikin wad'annan shekaru Nabilah ta sake haihuwar yara biyu, sun ci sunan Umma da Abba, haka Nafisat matar Muh'd ita ma ta sake haihuwar wasu yaran har guda biyu duk mata. Mufidah ma ta sake haihuwar namiji yaci sunan daddy ga kuma wani tsohon cikin da yake jikin ta haihuwa yau ko gobe. Musaddiq da Mufidah kullum k'ara kaunar junan su suke, tattalin juna da kulawar da suke yiwa junan su shi yayi musu jagora wajen shimfid'a kyakkyawar rayuwar su mai cike da jin dad'i da kwanciyar hankali. Ga kuma kula da yaran su da suke, suna kok'arin gaske wajen basu tarbiyya tare da basu ilimi na addini dana boko, yaran sun girma gashi sun taso cikin soyayyar iyayen su da kakannin su ta kowanne 6angare, amman duk da wannan soyayyar da suke nuna musu hakan bai hana su basu tarbiyya mai kyau ba. A cikin wani daren alhamis Allah ya sauki Mufidah lafiya, ta haifi baby girl d'in ta, farinciki wajen Musaddiq kamar bai ta6a samun 'ya'ya ba, daman burin shi kenan ya samu mace mai kama da Mufidah, sai gashi duk cikin yaran nan nata ita ce mai kama da ita sosai. Ansha shagalin suna sosai an kashe kud'i, inda yarinya taci sunan ta Nauwara, haka Mufidah ta cigaba da kula da 'ya'yan ta tare da taimakon jarumin mijin ta Musaddiq, wanda a kullum cikin bata dukkanin wata kula wa yake, baya gajiya da hidimar Mufidah kamar yanda ita ma bata gajiya da tashi hidimar. Duk hausawa sunce zo mu zauna zo mu sa6a, amman tsakanin Mufidah da Musaddiq akwai fahimtar juna sosai a tsakanin su, duk da wani lokacin daman sai anyi hak'uri da juna, domin ance ko tsakanin harshe da hak'ori ana sa6awa, ko da sun yi fad'a a tsakanin su baya kaiwa wani tsawon lokaci ba tare da sun yi shirya kan su ba don basa jure yin fushi tsakanin su. *** *** *** Misalin k'arfe 8 na dare bayan an idar da sallahr ishsha ne, Musaddiq da twin's tare da lil Daddy suka shigo parlourn da sallama dawowar su daga masallaci kenan. Hannun su d'auke da robar ice cream da chocolate masu dad'i, saboda sun biya yiwa Mumy sallama sai da safe shine ta basu, Afnan ce zaune a parlourn tana rik'e da Nauwara tana yi mata wasa ta amsa sallamar su cikin nutsuwa. Gaida Daddy Musaddiq tayi cikin ladabi da girmama wa, yayin da k'annan nata suka gaida ita suma, zama suka yi ana hira cikin so da kaunar junan nasu. Mufidah ta fito parlourn cikin wata gown ta atampha d'inkin yayi mata kyau sosai, k'amshin turaren ta da Musaddiq ya ji shi ya sashi lumshe idanun shi yana saukar da ajiyar zuciya a hankali, kafin ya ware idon shi kan Mufidah sanyayen murmishi suka sakarwa junan su, da hannu yayi mata alamar tayi kyau ta amsa mishi da ido ta gode. "Oya ku tasu aci abinci a kwanta gobe da school " Mufidah ta furta hakan ganin yanda yanayin mutumin nata ya canja, tashi suka yi gaba d'ayan su suka nufi dining table suka zauna, Mufidah tayi serving d'in su. Nan suka yi bismillah cikin nutsuwa suka fara cin abincin su, ba wanda yake magana a cikin su sai dai Musaddiq da Mufidah da suke aikawa junan su murmishi tare da wani irin kallo wanda su kad'ai suka san ma'anar shi. Bayan sun gama ne Afnan tayi musu sallama ta tafi side d'in Mumy da yake daman acan take sai dai kusan yini take a part d'in Mufidah, Musaddiq bai barta ta tafi ita d'aya ba saboda dare ya d'an yi don 9 ta kusa, yana rik'e da hannun ta har suka zo part d'in Mumy sannan ya bata peck a kumatun ta yace "Good nyt sweet dgter and sweet dreams " Cikin murmishi tace "Okay daddy good night " Daga haka ta wuce ciki shi kuma ya juyo ya dawo, zuciyar cike da kaunar Afnan yarinyar da kullum kamannin ta da Yah sadeeq yake k'ara fito wa, wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mishi tare da furta "Allah ya jik'an ka Yah sadeeq, ina cikin kewar ka nasan har na mutu bazan dai na zubar da hawayen rashin ka ba " Kok'arin saita kanshi yayi don kada Mufidah ta fahimci halin da ya shiga, lokacin da ya shiga part d'in nasu ya rufe ko'ina tare da kashe hasken ko'ina, sannan ya lek'a bedroom d'in yaran shi ya tarar sun yi bacci, murmishi ya saki yasan wannan duk aikin Mufidah ne, wajen sa yara bacci da wuri bin su yayi d'aya bayan d'aya ya basu peck sannan ya k'ara yi musu addu'a ya kashe hasken d'akin, tukunna ya fito yana rufe musu kofa. Bedroom d'in shi ya wuce ya tarar da Nauwara kwance kan k'aramin bed d'in su na yara tayi bacci abin ta, ita ma kissing d'in ta yayi, sannan ya wuce toilet don yasan Mufidah na can tana had'a musu ruwan wanka. Bayan sun yi wanka sun fito ne, suka kwanta kan bed tare da rage hasken d'akin, cikin wata irin muryar shauk'i Musaddiq ya ce "ina son ki Mufidah, kullum son ki k'ara ratsa zuciya ta yake, ina miki son da baki na bazai iya furta miki adadin shi ba, ina alfahari da ke matsayin mata ta" Cikin sanyin murya tace "Nima a kullum cikin gode wa Allah nake da ya azurta ni da samun managarcin jarumin namiji kamar ka, ina son ka Musaddiq with all my heart, i luv u so much sweetie darling " Sake k'ank'ame ta yayi a jikin shi tare da had'a bakin su waje d'aya ya fara bata wani zafaffen sak'onnin shi mai mata wuyar fassara, kullum cikin gode wa Allah take da ya bata Musaddiq, da fari Allah ya bata Sadeeq salihin mutum mara son hayaniya babu ruwan shi, Allah ya d'auki abin shi daga k'arshe ya sake bata wani mijin abin alfahari mai son ta tsakani da Allah, ga nutsatstsun yara da ya bata, shi yasa kullum cikin gode mishi da take da tarin ni'imomin da yayi mata take. Bayan komai ya kammala sun yi wanka suka kwanta rungume da junan su kowanne yana fad'a wa d'an uwan shi irin yanda yake son shi, kafin daga k'arshe bacci mai dad'i yayi awon gaba da su. *_ASUBA TA GARI MUSFEEDAH_* *ALLAHAMDULILLAH* _K'ARSHE_ *DUKKAN GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH (S. W. A), DA YA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFIN LAFIA, TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU K'ARA TABBATA GA ANNABIN MU,SHUGABAN MU ANNABI MUHAMMAD (S. A. W), KUSKUREN DA SUKE CIKI ALLAH YA YAFE MIN, FAD'AKARWAR DAKE CIKI ALLAH YA BAMU LADAN GABA D'AYA* *NOTE* _wannan littafin nayi shine don fad'akarwa da nishad'antar wa, kuma k'irk'iran labari ne, abin da yake ciki mai kyau da amfani ayi aiki dashi, mara kyan kuma a watsar dashi_ *KE TA DABAN CE* _My sweet sadeey ke ta dabance cikin zuciya ta, baki na bazai iya furta miki yanda kike a wuri na, fatana shine Allah ya bar xumunci mu kasance tare har abada,Amin._ *INA YIN KU IRIN SOSAI D'IN NAN ADMINS OF EXCLUSIVE WRITERS FORUM* _Aishan umma_ _Dgter ummiey xeey_ _Meelat dear_ _Aishat A Muh'd_ Allah ya bar mu tare 4 sister for ever, Amin. *GODIYA DA FATAN ALKHAIRI GARE KU SISTER'S NA EXCLUSIVE WRITERS FORUM, HOME OF PEACE HONOUR AND SUPER WRITERS, INA SON KU IRIN SOSAI D'IN NAN WANDA BAKI BA ZAI IYA FAD'A BA, ALLAH YA BAR MU TARE EN UWA* *INA ALFAHARI DA KU* _My momma (Aunty maijiddah)_ _My billy ladan_ _My biebie deee_ _My Amnoor dear_ _My queen mermue_ _My zahra ( sister d'in halilos)_ _My halilos_ _zee yabour_ _My Asy khaleel_ _Namecy Ayusha_ _Namcey Aysha Ali Garkuwa_ _Miss zahra mansur_ _ummu safwan_ _khadija neenah cool ke ta dabance_ _Aunty fauxah_ Kaiii gaskiya baxan iya rubuto ku gaba d'aya saboda yawan da kuke dashi, amman ku sani Aishat A Muh'd na matuk'ar kaunar ku da alfahari da ku,Allah ya bar xumunci ina muku fatan alkhairi. Jinjinar ban girma gare ku en cikin *IDON MIKIYA WRITER'S ASSO*, ina yin ku guy's Allah ya bar xumunci. *GARE KU MASOYA NA* _kune abin alfahari na, ina son ku duk inda kuke Allah ya bar mu tare musamman en grp d'in Aishat A Muh'd fan's ina yin sosai guy's_ *GROUP'S D'IN DA NAKE BAZAN IYA LISSAFO KU BA, AMMAN NASAN KU MASOYA NA NE, INA MUTUM FATAN ALKHAIRI TARE DA GODIYA GARE KU, MUSAMMAN ADMINS D'IN SU*. *_ina kuke masoya na ina muku albishir d'in new nvl d'ina mai zuwa nan babu dad'e insha Allah_* Aishat A Muh'd ✍🏻