[11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: *👑YARIMA ABDUL-MALIK 👑* *💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫* *Story & written* *By* *Yusrah Musa Abubakar* *(Mrs Al'ameen Ahmed)* *Dedicated to Zarah Musa Dan Adam* *In the name of Allah the beneficent and the most merciful* *Be good be helpful everybody will like 💗 u* *Page 1* Abuja fct babban birnin tarayya, misalin karfe shida na safe, hadari ne sosai ya taso garin ya bada kala mai kyau. Sakamakon rana bata fito ba, gashi ana kada iska mai ni'ima. Wani kayattaccen layi ne, yasha kwalta mai kyau, sai walwali yake, gashi an kawata shi da fitilu masu d'aukar hankali. Tun daga farkon anguwar zaka san ba anguwar masu karamin karfi bace, yadda tsarin ta yake da tafka tafkan gidaje na alfarma. Wani kyakkyawan gida ne, mai dogon gini ya gaji da kyau. Kuma ko ba'a fada maka ba kasan gidan sarauta ne, saboda yanayin zanukan jikin gidan da tambarin masarauta. Dai-dai wannan lokacin, wasu matane uku ne, ri'ke da wani mutum da kayan fadawa a jikin su. A yanayin rikon da sukai masa zasan laifi yai suka kamoshi. A kofar tangame man get d'in gidan suka tsaya. Tare da 'kwan'kwasawa. Ganin haka yasa nace, bari na bisu, domin naga meke faruwa fadar. Irin tsaruwar gidan bata lokacine, tafiya ce mai tsawo sukai, sannan suka tsaya a wata iriyar kofa ta glass. Da alama wani suke jira. Sun kai minti goma a gurin, kafin suka hango shi tafe ta cikin glass d'in, da sauri suka bud'e kofar, cikin girmamawa suka duka masa. Wai wai wai, masha Allah. Zan kad'i, wani kyakkyawan saurayi ne, fari tas dashi. Ya fito sanye da kayan army, wand'an da su kai matukar bala'in yin masa kyau. Umh da gani babu tambaya, wannan shine yarima Abdul-malik. Zare glass d'in idon shi yai, tare da zuba wa wanda aka kamo ido, tabd'i. Ni dai kauda fuska ta nai, dan wadannan razanannun idon na sa bazan iya kallonsu ba, wata firgitacciyar tsawa ya daka. Wanda ba mai laifin ba, hatta fadawan sai da suka tsorata. kowa yai zaman dabas a kasa, jiki na rawa,😂cikin fada ya fara magana" suraj na yarda dakai, shine zaka min haka? sai ka fada min uban waye ya baka poised, yace ka zuba min cikin abin sha, ko kuma ka karasa rayuwarka a gidan yari". Kuka wanda aka kira da suraj keyi, amma ko kashe shi zaiyi bazai taba fada masa wanda ya bashi gubar ba. Ganin yadda jikinsa ke rawa, ya kasa mgn ya musu nuni da cewa, su tafi da shi su tambaye shi har sai ya basu amsa. Mikewa sukai, cikin girmamawa. suka tafi dashi, yana wani irin kuka. Dan yasan Allah ne ka d'ai yasan irin azabar da zai sha a gurinsu. Gashin kansa yake shafawa cikin dunbin tunani to waye zai bada poised a bashi? waye keson ganin bayanshi? ganin ya kasa samun amsa yasa ya fito a part d'in, cikin wani irin taku ya nufi palon kakan sa, lokacin daya shiga dukkan ahlin gidan suna zaune a palon. Amma banda maman sa, dan bata wurin du'kawa yai, cikin girmamawa a gaban mai martaba. cikin tsananin so mai martaba ya riko hannun sa, yana murmushi. A duniya yana son Abdul-malik matuka a ransa. Kowa fuskarsa da walwala, banda Yahanasu da takejin duk duniya ba wanda take 'ki kamar sa. Wani irin firgitaccen kallo take binsa da. Ganin yadda mai martaba yake lailaya shi kamar jariri. Mai martaba ne ya fara magana "Muhammad ina fatan baka da wata matsala?" murmishi yai cikin jin dadin kular da mai martaba ke bashi yace "bana bukatan komai". kallonsa mai martaba yai "ka tabbata?" kai ya d'aga yana sakin wani kayattaccen murmishi. Ganin yadda yaha tai da fuskarta ita da mahmud kamar anyi musu mutuwa. Abban mahmud shima dake kallon Yariman cikin kauna yace "idan akwai matsala ka fada min baba na, kasan ban san ganin ka cikin damuwa" tun kafin yai mgn yaha ta tare shi da fadin "haba mai sai kace wani yaro, sai tambayar sa kake, ai yana da hankali idan yana da matsalar zai fada. Idan adalci ne, ai ga mahmud meyasa shi baka tambaye shi ko yana da matsala ba?" Murmishi abban mahmud yai yana kallonta, yace "ai in dai lamarin baba na ne, ni yafi gold a gurina. Ina ji dashi, ina ririta shi tamkar raina". Cikin bacin rai, yaha ke duban yarima kamar ana 'kara hura mata wutar 'kiyayyar sa a ranta. Kallon mahmud tai "tashi mu tafi" mi'kewa su kai, suka fita a dakin. Da kallo abba ya bisu yana mamakin wacce irin mace yake aure kamar yaha mara tunani haka Allah ya sau wa'ke. Duk ranar data kai shi bango zata sha mamakinsa. Mi'kewa Yarima yai yana musu sallama ya fita, suna sa mai albarka. Part d'in maama d'in sa ya shiga, don kwata kwata idan bai ganta ba baya samun nutsuwa, yana shiga palon ya hangota kishingide, ganin sa da tai yasa ta mi'kewa zaune, tana tarar sa da murmushin kauna. Bako kunya yana zuwa ya kwanta a jikin ta. Hannu tasa a suman kansa tana shafawa, cikin murya mai sanayi tace "baby baka rabo da rigima har yanzun jinka kake yaro, kafa girma kosai ka fara ganin naka yaran zaka san ka girma?" mi'kewa zaune yai yana rike mata hannu a hankali yace "I love u my sweet momy fatan kin tashi lafiya? kuma ba wata matsala?" dariya tambayar ta bata tace "wato baby na fahimce ka, tambayar dasu mai martaba suke maka yau kuma ni ka kewa?" 'Kara rike hannunta yai cikin shagwaba yace "haba mama, kin san yadda nake jinki a raina ke d'aya ce tamkar da dubu. Dukkan wata soyayya da kulawata a gareki take ina matukar son ki my mah". Murmushi tai cikin jin dad'i tace "na sani ba wanda kake so sama dani Allah yama albarka, sannan kuma kaci abinci? abinda baka so nace dagowa yai yana ganin ta kureshi da kallo yasa yace " eh zanci idan na koma" har lokacin kallonsa take tace "oh da gaske? toni ban yarda ba tashi muje ga abinci can kaci kada ulcer ta kama min kai". Bata fuska yai irin baya so d'innan, mama tace "bazan barka ka tafi ba sai kaci ko kad'an ne," shiru yai yana karya wuya ya koma kalar tausayi dan ta barshi ya tafi. kiran sa akai a waya ya d'aga yana son kwacewa daga rikon datai masa amma taki sakin sa baiwace ta shigo da abincin ta ajiye sauke wayan yai yana kallon abincin ya dauke kai daukan spoon in tayi tana dibowa takai saitin bakinsa. Yai saurin rufe ido ganin idan ta biyeshi ba ci zaiyi ba ta aje spoon in tamai durar karfi da yaji. Batun yaha kuwa suna komawa part d'ita ita da mahmud ta soma zagaya palor cikin taikaici, zama Mahmud yai cikin jan tsuka yace "wai dan Allah umma me yasa abba na yake min haka? kamar ba shine ya haifeni ba. Gaba d'aya ya tattare soyayyar sa, ya dorata akan Abdul-malik. kafin ya kira sunana sau d'aya, ya kira nasa sau goma. gaskiya na gaji". yaha ce ta juyo tare da cewa " af kwantar da hankalinka mahmud, na kusa daukar mataki kowama ya huta, amma kafin nan sai mun san yadda zamuyi mu shiga jikinsa. Kaga daga nan hakan mu yacimma ruwa, sai mu kashe shi ta ruwan sanyi, ba tare da an zarge muba. shine aure zanje gaban mai martaba nace ya kawo lokacin daya kamata ace ya aje iyali, idan har mai martaba ya yarda zan fadi yarinyar daya kamata ace ya aura" Mahmud da hankalinsa yadan tashi yace "to wacce zaki zaba masa idan mai martaba ya amince?" zama tai tana kalln sa, tace "ina nufin hajara yar gidan yaya, kasan ta kusa zuwa". Mi'kewa mahmud yai" what umma hajara fa? aa da sake, abinda na dade ina mafarkin samu" yaha tace "kamarya? yace "haba amma ai kinsan nike son wannan yarinyar, gky ban amince a bashi ita ba". Dafa shi yaha tai tace "karka damu mahmud zanyi maka bayani, ba kana son ganin bayan Abdul-malik ba? to ai dole sai ta wannan hanyar ce ka d'ai zamubi mu samu nasara, yanzu idan mukace zamu kasheshi ba wani dalili. Hakan zaiyi mana wuya, amma idan ya auri hajara zata she'ke mana shi, ba tare da munsha wahala ba. Kuma ba mai zargin mu, kaga zamu dawo mune da fada a gurin mai martaba idan ya zama babu shi. Kayi tunani ta wanna hanya ce ka d'ai zamu iya shafe shi, mu batar da tarihin sa har abada." Cikin gamsuwa mahmud yace "kuma haka ne fa, kinga riba biyu zan samu, an kashe shi, kuma na auri wacce nake so" cikin jin dadi yaha tace "shiyasa nake yinka. Akwai fahimta, yanzu kaje ka tafi hospital kada lokaci ya kure ma, kuma ka sake tunani akan abin dana fad'a maka," tana kaiwa nan ta wuce shima mi'kewa yai ya fita. *** Kano farawa, wata budurwace tafe a wannan anguwa ita ka d'ai, kyakkyawa ce ta ajin farko, kuma yanayin kayan dake jikinta bazai nuna maka cewa yar talakawa bace, sai dai ba haka abin yake ba muje zuwa mahaukaci yahau kura. Wani gida ta bud'a ta shiga, amma iya yanayin sa zai nuna maka cewa gidan hayane, da wata tsohuwa suka hadu zata fita a gidan cikn tausayawa ta kalleta tana cewa "sannu kinji zainab, ki 'kara hakuri komai mai wucewa ne, ki daina sa tunani a ranki in Allah ya yarda wata rana zakiga ribar hakurin ki." Murmushin karfin hali zainab tai tana daga mata kai tace "ngd da kulawarki inna, sai kin dawo Allah ya tsare amin" inna tace tana ficewa. Ita kuma ta shiga gidan, bangare biyu na inna da nasu. Da sallama ta shiga tanai wa matar dake zaune a gaban kuloli sannu da gida, ko cira kai batai ba balle ta sa ran zata bata amsa. Wuce wa tai ta shiga d'akin ta tana tunanin yaushe ne zata samu canjin rayuwa? rashin iyaye baiyi ba, gashi batasan kowa nata ba, balle ta koma wurin su. Mahaifanta sun rasu bata san danginta ba, sai hjy bilki kishiyar maman ta, wannan wacce irin rayuwa ce ta tsinci kanta a ciki? goge hawayen fuskar ta tai jin bilki na kwalla mata kira, cikin sauri ta fito tana cewa "gani umma". Tsaki taja "wato zainab wuyanki ya fara 'kwari ko? sbd ke tinkiya ce kullum sai nayi da baki na akan fita da abinci shago saboda kin gado bakin halin uwarki, to wallahi wuya zaki sha a gurina" kuka zainab keyi dan idan akwai abin data tsana a duniya shine ka zagar mata mahaifa. Bilki tace "inye hamshakiya danna zaki uwarki kike kuka? to ko tana raye zan zageta balle tana bayan kasa, ke dalla tashi ki fitamin da kayan sana'a ta, dan wallahi kikamin kwashe duka zaki mi'kewa tai ta f ara diban kulolin tana fita dasu, tana shago taga Tanimu ya sauke hindu a mota dan girgiza kai tai cikin takaici, sai bayan la'asar ta koma cikin gida duk da abincin ya kare tun wuri, zaman ta a wajen yafi mata alkairi. Bata kud'in tai dai-dai Hindu ta shiga da bakar leda a hannunta, ta mi'kawa Bilki tana cewa "wanka zanyi in anjima Tanimu zai zo" kallon Zainab tai "ke jeki d'ebo mata ruwa za tai ba'ko, ba irin ki bace mai bakin jini, kuma ki dawo ki dafa mata wannan kazar" 'Kala zainab bata ce ba, ta d'au bokiti tana fita a gidan, bayan ta d'ebo tana shigo wa gidan a zaure suka hadu da Bashir, yana ganin ta cikin murna yace "masoyiya ta dama ke nazo nema, ya gida?" kallon sa tai, cikin takaici taja tsuka, zata wuce ya jawo hijab d'inta. bokitn ya fad'o ya fashe WASH ALLAH GASKIYA KUNA KOKARI 😥 [11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: 👑YARIMA ABDUL-MALIK 👑 💫 *ANNURI WRITER'S ASSOCIATION* 💫 By YUSRAHMS ABUBAKAR #YMA Dedicated to Maman khaleel Safiyya Aliyu Ina matukar godiya da nuna kaunarki a gareni MY FEEDOH may Allah bless you and your household wannan page din naki ke daya har zuwa page 20 mallakar kine. *If you go to the river dont swim 🏊 it can carry you away 🏃. Page 2 Da gudu Bilki ta fito ganin abinda daya faru yasa tace kan ubancan amma Zainab anyi muguwar yarinya sbd bakin hali saida kika karasa min bokiti to wallahi baki isa ba saikin biyani mayya kawai mitsiyaciya ta karasa maganar tana janta ciki hakuri Zainab ke bata amma wani irin gigitaccen Mari ta sauke mata saida ta durkusa har kasa bisa kafafunta saboda azaba wanda hakan yai daidai da shigowar Inna da sauri ta karaso tana dago Zainab din dake kuka fuskarta tayi ja wani irin kallo taima Bilki mai nuna cewa wata rana zaki nadama tace amma wallah Bilki baki da da'a sau nawa zan fada miki ki daina dora hannunki akan yarinyar nan rashin iyaye fa ba hauka bane kinsan irin bala'in da kike kwasarma kanki kinsan hukuncin mai zaluntar maraya me yasa baki da tunani ko kadan ina tsorace miki ranar da zaki kuka da idanunki Zainab ba yarinyar da za'a wulakanta bace duk abinda ya sameki ki kuka da kanki na fada miki. Kallon sama da kasa Bilki ke mata tunda ta fara magana sannan tace ahayye nanaye kaji mace da kwarton munafirci meye ruwanki a ciki amma ba laifinki bane da alama yunwa kike ji ga dusa can idan kin gama ci kije ki sha ruwa munafikar tsohuwa kawai tana kaiwa nan ta wuce ta koma ciki. Da kallon suka bita inda sabo kuma Inna ta saba da wulakancin Bilki ba tun yauba hannun Zainab ta rike tace muje dakina Zainaba ki huta kinji ki ta hakuri komai mai wucewa ne Allah ya jikan Umar da Khadija ameen Zainab ta furta cikin damuwa amma ko babu komai tana samun sauki idan Inna ta wuni a gida. Yau Yarima ke shirin zuwa kano gurin kakarsa zaune suke a palor mama ta kalleshi tace gaskiya babyna kana da kyau kamar balarabe "harka shirya kenan"? Da kai ya bata amsa taci gaba da cewa Allah ya kare min kai baby inaji a jikina kamar zuwanka gurin ammi alkairi ne tamkar zaka hadu da wani abu dazai saka farin ciki kuma ya zamo maka garkuwa a rayuwarka. Ido ya zuba mata bayan ya gama jin jawabinta yai murmushi har dimple dinsa na lotsawa amma baiyi magana ba mikewa mama tai tana kire hannunsa suka fita har mota tai masa rakiya kafin ta koma. Lokacin daya dayai perking da mota a harabar gidan da mamaki Mustapha dake tsaye kafar shiga palor yake kallon motar da tunanin waye a ciki bai kare mamaki ba Yarima ya fito yana gyara agogon hannunshi domin shi kadai ya bata shi mutum ne wanda baya bukatar takurar wasu fadawa ko bayi duk inda zaije shi kadai yake zuwa ko driver baya bukata. Dagowa yai sukai ido biyu da Mustapha wani ihu yai yana rungumeshi cikin nuna tsantsar murna yace abokina kaine dama zan ganka kwana kusa gaskiya nayi kewarka yaushe raban da mu hadu kusan shekara biyu fa murmushi Yarima yai yana kallon shi yace sorry ba gani yau nazo muje ciki na gaji inason na huta shiga sukai wata farar mace ta dago tana kallonsu tace dama saida tunani na ya bani tunda naji Mustapha na ihu yana cewa abokina nace nasan kaine ba wanda zaizo yayi wannan haukan sai kai ta karasa maganar da murmushi. Rungumeta Yarima yai a rayuwarsa yana matukar son ammi Mustapha ne ya fara dariya yana cewa wato Abdul-malik har yanzu baka janye wannan dabi'ar taka ba yanzu runguma ce gaisuwa dagowa yarima yai yana kallon ammi alamar ta tanka Musty yace malam bafa zakazo ka sanya tsohuwata magana ba ka baro taka acan tana hutawa zaka wani takura min tawa harararsa Yarima yai kafin ya mike yana cewa muje na gaji inason na huta bani da lokacin ka wucewa sukai yana cewa ammi bari ya dan huta. Zainab ce zaune a tsakar gida tana hada kunun aya Bilki ta fito a daki tana cewa Zainab me kikeyi anan? dagowa ta tana kallonta tace kunun aya nake hadawa [11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: Innalillahi dan Allah amin afuwa ban gama typing ba nayi sanding. *👑Yarima Abdul-malik 👑* #Yusrah m Abubakar Yusrahmusa65@gmail.com *💫ANNURI WRITES ASSOCIATION💫* *Page 3 Tana kallota tace "kunun aya nake hadawa". Kudi ta mika mata jeki sayo min kayan miya bari na rika dura miki to Zainab tace tana amsar kudin tasa hijab ta fita a gidan Aliya ce ta shigo tana cewa, a'a Bilki harda kunun aya kika koma yine? Um lallai liyafa taci gaba ta karasa maganar tana zama a kujerar da Zainab ta tashi sai a sannan Bilki tai magana "a'a ba nawa bane na Zainab ne makaranta zata tafi dashi jin haka yasa Aliya tabe baki tace wallahi shiyasa duk yarinyar nan tabi ta rainaki ashe guri ta samu kina mata bauta Bilki zatai mgn Zainab ta dawo dan haka tai shiru aje kayan miyan tai tana dauka jakanta ta fita a gidan haduwa sukai da hindu a karshen layin anguwar suna tsaye da wani bata ko kalli gurinsu ba ta tsaida napep ta shiga. A shirye suka fito shida Musty zai rakashi makaranta dan lecturer ne ammi ce ta kalli Yarima cikin wasa tace me soja zaije yi makaranta karfa ka firgita dalibai dan murmushi yai yana kallonta yace, dama ana gane soja ne ko baisa kaya ba? Dariya Musty yai ana ganewa mana musamman rashin fara'arka. Mikewa yai yace to naji muje tunda ban sako dakai ba fita sukai suna shiga mota basu zame ko'ina ba sai makaranta babu yadda Musty baiyi ba akan ya karasa office dinsa amma yaki yace ya barshi anan idan yana bukata zai biyoshi hade rai Musty yai zaiyi magana Yarima yace masa "sorry"cikin haushi yace a'a uban sorry dan iska kawai wucesa yai shi kuma ya tsaya jikin motar yana waya da mama kamar saida akazo saitin kunnensa aka kwalla kiran Zainab wallahi ki tsaya kibani abuna idan na kama ki zaki sani haka kawai xuciyarsa ta tunzura shi ya kalli inda ake maganar idonsa ne ya sauka akan Zainab dake tsaye tana dariya rike da fefa a hannunta tana kalla alamar karantawa take wani irin kallo ya bita dashi cikin mamakin da baisan yayi hakan ba. Karasowa waccen din tayi zata kama ta sukayi wani lungu da gudu dan dafe kirjinshi yai tare da runtse ido Musty ne ya dafa shi bai dago ba cikin mamaki yace abokina yadai meke faruwa? Shiru yarima yai ba tare daya bashi amsa ba saima shiga mota dayai abin ne ya daurewa Musty kai dan haka shima shiga yai daidai zaiyiwa motar key ya kuma cewa Abdul-malik wai dan Allah meke damunka naga gabadaya ka canja ba haka muka taho ba kodai kayi gamo ne? Wata uwar harara Yarima ya sakar masa batare da yace kala ba rabuwa dashi Musty yai dan ba amsa zai samu ba. Koda suka koma gida ma kasa samun nutsuwa yai daya rufe ido ita yake gani lokacin da take dariya gabadaya ko abinci bai samu yaci ba har dare. Bayan kwana biyar yau weekend ne Zainab tana zaune a daki taji muryar bashir ya shigo yana cewa masoyiyata ina kike? Ga kayan marmari na kawo miki da gudu Bilki ta fito daga daki har tana tuntube ta karbe ledar hannunsa tana cewa kai wanne irin banza ne ai ba ita zaka kawowa ba ni zaka kawowa tunda nice uwar 'ya cikin muryar yan kwaya bashir yace gaskiya ni kullum sai karbe min kudi kike kuma kinki fada min yaushe ne auren zama Bilki tai tana bare ayaba tace kwantar da hankalinka an kusa kadai kaci gaba da kawo kudi aure da Zainab kamar anyi ne shigowar hindu kenan ta karasa maganar tana cewa kwarai kan zamu sha biki ankon yi shirunka maraya zamuyi😂 amarya kuma sai ta dinka azari lilo da takalmi silifa dariya gabadaya sukai Zainab dake sauraronsu ta girgiza kai tana neman tsari daga sharrinsu 😡. Yau Monday har Musty ya gama shiri Yarima na kwance yana kallonsa juyowa yai yana kallon sa yace wai malam lafiyarka kalau ko junnu suka shafeka gabadaya ka bi ka sauya to nidai tashi ka shirya ka rakani makaranta. Mikewa Yarima yai yana daukar towel yace jeka bazani ba gida zan tafi zaro ido Musty yai kai da kace zakai saki uku daga daya kace wai tafiya zakai shiga toilet yai yana cewa eh idan kuma zaka hana to dariya Musty yai ni asuwa kare da gudun layya ka gaishe min da aunty na yana kaiwa nan ya fita. Cikin minti goma ya gama shiri sama sama yai sallama da ammi ya kama hanyen Abuja lokacin daya isa gida tararsa harda mai martaba kamar zai mayar dashi ciki wani irin abune ya tsayawa Yaha a makoshi dakyar take hadiyar yawu ganin yadda kowa yake rawar kafa akansa barin gurin tai kamar zata tashi sama tana shiga part dinta tafara kaiwa da komowa ta ciji yatsanta yafi sau a kirga harsai da yatsan ya fidda jini bata sani ba saboda zafin da takeji a ranta daga waya tai tana kira bugu daya aka dauka cikin tsawa ta soma mgn hajara nace kizo kinki ko kinsan irin halin da nake ciki kuwa na baki nan da jibi ina son ganinki cikin Abuja bansan shashanci daga can dayan bangaren hajara tace wai umma meke damunki naga da ko nazo ko kar nazo baki damu ba gaskiya bani da lokaci a yanzu tana fadin haka ta katse kiran tsaki Yaha tai dai dai lokacin da Mahmud ya fito daga part dinsa yana mika alamar daga bacci ya tashi kallonsa tai cikin takaici tace sakaran banza ba dole kai bakin jini ba tunda bakasan ciwon kanka ba shashasha😁kallonta Mahmud keyi yace me kuma nayi daga tashina kefa abin laifi bayai miki kadan wata uwar harara ta sakar masa cikin san huce haushinta tace uwarka da ubanka kaimini dariya Mahmud yai yana cewa ke da Abba kenan shiru Yaha tai ta zuba masa ido cikin takaici bata sake magana ba. Yarima kuwa sai daya huta gajiya ya tafi gurin mama fara'arta ce tamasa maraba rungumeta yai yana cewa fatan alkairi gareki momy na su ammi na gaishe ki da wannan yaron. Wane yaro kuma badai Mustapha kake nufi ba dan wannan babanka ne tunda kanina ne shagwabe fuska yai to amma aina fishi "eh komai kayi ba finsa ba shidin uncle dinka ne" Tab aikwa bazai samu ba, dan shiru yai zuwa can yace mamina zanyi tafiya gobe zan dawo nan da wata uku kallonsa tai tana cewa Allah ya tsare min kai babyna zamewa yai ya kwanta akan cinyarta yace ameen mom nagode da addu'arki. Washe gari tun sha biyu ya gama shirinsa cikin kayan soja yaje sallama da mai martaba a gabansa ya durkusa yai kneel down yana cire hular kansa hannu mai martaba ya dora akan nasa yana jero addu'a ana amsawa saida ya gama masa ya mike yana rungumeshi cikin jin dadi kafin yaje ya rungume dadynshi albarka sosai ya samu kafin ya shiga motar da zatai masa rakiya zuwa airport. Bilki ce ta fito daga daki tana kwalla kiran Zainab jin shuru yasa ta leka dakin ganin bata nan tace lallai yarinyar nan uwar raini ce bari zata dawo duk gidan uban wanda taje ma. Zainab ce zaune gaban wani tsoho kallonsa tai tace dan Allah kaka Abdullahi abbana bai taba fada maka labarin danginsa ba? Kai ya jinjina cikin tausayawa yace Zainab tunda nake da Umar bai taba fada min asalinsa ba saidai a yanayinsa idan yai wani abun zakiga tamkar shidin jinin sarauta ne amma bani da tabbaci akan hakan hakanan Khadija ma bansan asalinta ba tsintar ta nai kawai bata cikin hankalinta nai mata magani ta warke amma dana tambaye ta ko tasan danginta tace a'a ta mantasu har tabar duniya kuwa bata tuno suba. Kuka Zainab ke yi harda shashsheka sosai Abdullahi ke tausayin Zainab saidai ba yadda zasuyi nasiha ya mata kafin yace ta tashi ta tafi gida. Bayan sati daya tafe suke daga farkon layinsu zasu tafi gida ba wanda ke magana Zainab ce ta kalli Fatima tace wai nikam lafiyanki kalau? Sauke ajiyar zuciya tai tana cewa inafa lafiya zuciya ta nason jefani a tsaka mai wuya wani take so dan murmushi Zainab tai tana cewa wakenan babu boye boye ta fada mata cewa uncle Mustapha take so sai dai tana tsoron kada ya gane ya kore ta danko lecture yake musu tana yawan hada ido dashi. Yar dariya Zainab tai tace bawani korarki dazai tunda ni muna mutumci dashi idan zanje gurinsa zamuna tafiya tare sai ku saba dashi ko ya kikace murmushi Fati tai cikin jin dadi tace nagode Zainab dai dai sun karaso anguwar su kowa ya shige gida. Da sallama ta shiga Hindu dake wanki tace gadontsiya andawo daga yawan tambadancin kenan gaban ta Zainab ta karasa tace idan harni tsiyace kema haka baki da bakin da zaki fada min magana ki kiyayeni na fada miki ki guji ranar da zaki kaini bango zakisha mamakin matakin dazan dauka a kanki dan wallahi saina dumama miki jiki da duka. Mikewa hindu tai tana cin kwalarta tace ke nikike fada ma mgn haka kwarai yaushe kika samu wannan damar kan mage ya waye ko to wallahi zanci uwarki wani irin mari Zainab ta dauketa dashi sai da taga taurarin azaba ✨ cikin bacin rai tace kar ki kuskura wannan kazamin bakin naki ya kara zagarmin uwa dan akanta zaki ga anahin wace Zainab Umar zan iyayin abinda ba'ai zato ba tana fadin haka ta tureta tai gaba mamaki ne da tsoro suka bayyana a fuskar Hindu bata taba zato cewa Zainab nada baki haka ba shigowar Bilki kenan ganin yadda Hindu ta zubawa guri daya ido tace ke kuma lafiya? Kai Hindu ta girgiza cikin takaici tace bakomai ta koma gun wankinta kira Bilki ta kwalawa Zainab fitowa tai cikic fada tace ina kikaje yau? Da ladabi Zainab tace makaranta naje wata uwar harara ta mata bance ki zauna a gida shine dan ban isa ba kika fita wato na kasheki ko? Kai Zainab ta girgiza kiyi hakuri Keda hakurin kunci gwafar ubanku tashi dora min miya ni kada lokaci ya kure mikewa tai ta shiga kitchen. 😍Ana tare in sha Allah yan group din ANNURI W A gaisuwa ta a gareku da bata da iyaka. INDO KINA RAINA CAN CIKI BA WANDA ZAI TADDOKI. ONE LOVE 💋❤ *Mrs Al'ameen Ahmed ce* [11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: (*() *) 8:18Am typing 📲 👑YARIMA ABDUL-MALIK 👑 💫Annuri Writer's Association💫 Story and written Yusrah Musa Abubakar Always be watchful dont take risks don't try to get lost try to protect your life always. Manzon Allah (s*a*w) Ya mana nasiha cewa muso juna mu rike gaskiya da amana sannan mu raya zumunci hanya ce ta aljannah duk makiyin zumunci bazaya kusanci ceto ba. Muna sonka fiye da rai da iyaye da dukiya. #Y M ABUBAKAR# *Page 4 Yaha ce zaune a palor tana waya cikin fada tace "yanzu yaya kamar ni da girmana na daga waya na kira Hajara amma yarinyar nan tamin rashin kunya tana nufin ban isa da ita ba kome yanzu idan na kira ta a waya bata dagawa dan kawai ina son ta zo shine sai ta bata min rai dan Allah yaya ka turo min ita tazo". Sai daya gama sauraronta ta gama sannan yace "ita Hajaran ce bata daga wayanki amma shikenan zan same ta saidai a yanzu bata da lokacin zuwa gurin ki domin jarrabawa suke taya kuwa zata zo miki saidai ki bari sai su gama". Dan shiru Yaha tai zuwa can tace "shikenan yaya amma dan Allah tana gamawa ka turo min ita tazo ni zan sai mata makaranta anan inyaso sai taci gaba da karatunta". Mamaki ne ya kama yaya yasan Yaha dasan kudi lallai abinda Hajaran zatai mata babba ne dan haka zai bibiyi koma menene Yahan take shiryawa daga haka ya mata sallama. Tsawon wata guda kenan Yaha na zuba ido amma babu Hajara babu alamarta yauma zaune suke tace "ka gani ko Mahmud yar iskar yarinyar nan tana so ta bata mana shirin mu" tabe baki Mahmud yai yana cewa amma dai Umma ai kinsan taurin kan yarinyar nan ko tunda yanzun Abdulmalik din bayanan ki bari mugani kafin ya dawo ko za ta zo". Jinjina kai "tayi kuma haka nefa to bari mu gani zuwa dawowar tasa idan ma bata zoba da kaina zanje har maidugurin in taho da ita". Yau da wuri su Zainab suka shiga jarabawa amma basu fito da wuri ba, a hanyarsu ta dawowa gida tafe suke da Fati Zainab tace "kai wallahi jarabawar yau tai wuya mun dauki dogon lokaci dariya Fati tai tana cewa to dama karatun likata wasa kema lokaci zaizo da zaki fara operation zaki ga ribar wuyar da kika sha". Duka Zainab takai mata inji ubanwa niko allura bazan iyaba balle operation". Har lokacin dariya Fati ke mata zatai magana Zainab ta katseta da fadin "kinga ni dan Allah muyi sauri karki jamin jarabar umma dan nasan tanacan tana jira na". Bayan kwana goma yau Yarima zai dawo amma babu wanda ya sani suna zaune a palon mai martaba kamar daga sama suka ganshi ya shiga palon cikin kasaitacciyar sallamarsa da wani irin murmushi a fuskarsa Abba ne ya kalleshi yana cewa "babana yaushe ka dawo"?har lokacin murmushinsa na nan yace "sorry Abba nayi shigowan dare ne". Ya fada yana kallon mama datai masa alamar jinjina da hannu. Mai martaba da farin cikinsa ya kasa boyuwa yace "matso kusa dani mana Muhammad yaushe rabona dakai" mikewa Yarima yai yana karasawa rungumeshi yai cikin so yace "Allah ya maka albarka Abdul-malik" "amin" duka suka amsa banda Yaha data Mike ta fice a palon tana zuwa part dinta ta kira Hajara tana dagawa cikin 'kunar rai Yaha tace ''waike wacce irin yarinya ce nace kizo kinki ko zan fita a hanyarki fa cikin tabe baki Hajara tace "towai dan Allah umma idan na zo me zanyi miki"? Cikin fada Yaha tace uwarki zaki min kizo mana ai zaki gan___dif taji an kashe wata uwar ashar ta saki tana jifa da wayan. Hhhh! mai son waya jama'a saidai taci screen 😂. Zainab kan angama jarrabawa kuma sakamakonsu ya fito ansamu abinda ake so dan haka tacewa Fati ta rakata zataiwa uncle Mustapha godiya Fati tace "nima daga can na ganoshi"dariya Zainab ke mata har suka shiga napep. Don Allah ayi hakuri bani da caji in sha Allahu zuwa jimawa zan karasa muku page din. Ana tare 😍💋 [11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: Hhhhhhhh gani na biyu ku fito ku kashe kwarkwatar idonku😆 Yarima ya tafi kano ko me zai faru muje zuwa. #YUSRAHMS# Zaune Zainab take a kofar daki Bashir ya shigo Bilki dake kitchen ta fito da sauri tana karbar ledar hannunsa ta dauko masa kujerar roba ya zauna yana dauko kudi a aljihunsa yace "ga kudin sadakin na samo ranar juma'ar nan nake so a daura mana aure na samu gurin zama a wani bariki"cike da rudewa Zainab ta dago tana kallon Bilki hawaye na zuba a idonta 😢kallon kudin Bilki tai tace "nawa ne "? Bashir dake kallon Zainab yana murmushi yace "dubu biyar ne"hade rai Bilki tai "gaskiya ni bazan karbi dubu biyar ba kaje ka kawo min dubu ishirin indai kana so a daura"Bashir yace "to wannan dinma kinsan da yadda na samu akuya na sata sannan nasiyar ta na kawo miki"harararsa Bilki tai lallai ashe baka son auren shiyasa kake jada ni malam kaje ka cikato kudi ka kawo idan ba haka ba sai dai a fasa"kada kai Bashir yai yace "shikenan zan ciko to rike wannan din"mikewa Bilki tai batare data karba ba tace "a'a jeka da abinka a jumlace nake son kudin"mikewa yai yana fita a gidan Bilki dake cin kifin daya kawo ta kalli Zainab "ga irin kayan mijin naki idan zaki ci"takaicine ya kama Zainab sai kawai ta fashe da kuka baki sake Bilki ke kallonta tace "munafika ba gata zanyi miki ba". Zaune suke a palon ammi Mustapha yace "wai ni Abdul-malik na tambaye ka mana yaushe zakai aure"? Wata uwar harara ya samu daga Yariman amma bai samu amsa ba cikin tsokana Musty yace "ya ina tambayar ka zaka wani rabu dani"kallo mai nuna ina ruwanka dani ya kuma yimasa dariya Musty yai yana cewa "da ruwana man ina matsayin baban ango don Allah Abdul-malik yaushe zakai aure"? Mikewa Yarima yai yana cewa "ranar da ka zaba min dan sa ido kawai banason takurawa malam ka rabu dani na huta" yana fadin haka yai waje dariya Musty yai yana daga murya yace "oho dai komai daren dadewa zamu ga gwanar taka ai". Koda safe da kamar zai cewa Musty bazai rakashi ba sai kuma wannan yarinyar ta fado masa a rai don haka yace suje a hanya Musty ke ce masa "i have found a girl i want marry amma sai ta kara girma"ta tafar sauke Yarima baice ba har suka karasa makarantar. Zainab ce ta fito daga wanka cikin sauri ta gama shiri ta fita a gidan don tana son taiwa uncle Mustapha godiyar nauyin karatunta daya dauka Yarima dake tsaye jikin mota jin ya gaji yasa yai niyar shiga office din Musty yadan huta yana cikin tafiya ba zato yaji yayi gware da abu da sauri ya dago yaga wanne banzanne yake tafiya kansa a sama 😜idonsa ne ya kalli fuskar Zainab datai baya zata fadi cikin sauri ya riko hannunta yana jawo ta donkar taje kasa cikin tsoro tai saurin rike masa riga tana kife kanta a kirjinshi jiki na rawa tai shiru zuwa wani lokaci da nutsuwarta ta dawo jinta jikin mutum yasa da sauri taja baya tana zaro ido 🙊tace "dan Allah kayi hakuri ban kula bane"idan dutsi zaiyi magana shima yayi ganin yadda take a tsorace yasa ya tabe baki ya juya yana wucewa ajiyan xuciya ta sauke daidai Musty ya iso yace "a'a Zainab Umar tsohuwar daliba ziyara kika kawo mana ne"?. Cikin ladabi Zainab ta gaida shi sannan tana "uncle dama nazo nai maka godiya ne"katseta yai daga haka yace ba komai Zainab aiyiwa kaine ina kika baro kawarki Fatima Sulaiman"? Da sauri ta kalleshi cikin mamaki tace "tana gida ai basan na taho ba "ok yayi idan kin koma kice ina gaishe ta, fitowa sukai suna dan hira anan yake ce mata yana son Fati zaizo ta rakashi gidansu wai murna gurin Zainab kamar itace ta samu masoyi har jikin mota ta rakoshi Yarima na ciki yana kallon su da mamakin dama Musty ya santa a yadda yake gani kamar shakuwace mai karfi a tsakaninsu sallama sukai ta wuce shi kuma ya shiga mota suka kama hanyar gida suna cikin tafiya Yarima yace "na tambaye ka dan Allah"? Da mamaki Musty yace "Allah yasa nasani na baka amsa"kai Yarima ya jinjina yace "wancan yarinyar da kuke magana wacece ita"? Cikin zolaya Musty yace itace yarinyar da nake ce maka ina sonta"Yarima dake duba waya baisan lokacin da yace "WHAT"ba wanda yasa Musty binsa da kallon mamaki yace "menene"? "Batai bane"? Kai Yarima ya girgiza baiyi magana ba zuwa can ya kasa hakuri yace "to amma tasan kana sonta"? A yadda yai maganar saida yabama Musty dariya yace "kaifa da wasa nake maka kawarta dai dai nake so ita wannan idan kaji labarinta sai ka tausaya mata"kallonsa Yarima keyi cikin mamaki ya gaji da magana amma yana so yasan labarin nata dan haka yacewa Musty to amma banga wata alama data nuna min 'yar talaka bace"? Dariya Musty yai "kai waya fada maka ba maganar fariya ba ni na dau nauyin karatunta hatta kayan sawarta a wuya na yake tunda muka hadu da ita sunanta Zainab Umar____tsaf ya fada masa iya duk abinda ya sani game da ita shiru Yarima yai har saida Musty ya dafa shi amma bai dago ba kuma har suka je gida hakan nan ya rasa sukuni gani yake yanzu ma kila Bilki na mata abinda Musty ya fada masa. Washe gari Zainab ta tafi sayo kayan miya kenan Aliya ta shigo gidan da magana a bakinta ko gaisawa basuyi ba ta fara fadin "Bilki me kike kallo za'a haifa miki shege a gida ki gamu da surutun mutane"cikin rashin fahimta tace "kamar ya"? Aliya taci gaba da cewa jiya nadiya na dawowa daga makaranta tace min taga Zainab ta shiga motar wani saurayi sunbar anguwar nan dama nace kila baki sani ba a matsayina na kawarki nake fada miki kisan matsayin da zaki dauka dan zainab ta fara fin karfinki"salati Bilki keyi tun dazun tace yanzu Zainab keda ciki ban sani ba bari ta dawo saita fadamin a gidan uban wanda ta dauko"jin haka yasa Aliya tace "ki dau mataki kan ni natafi sauri nake"tana fadin haka tai waje. Babu jimawa Zainab ta dawo mikewa Bilki "tai zonan Zainab dama bin maza kike"? Cikin mmk Zainab ke kallon ta tace "wallahi tallahi karya ake min umma"mari Bilki ta dauketa dashi tana dukanta ta ko'ina tace za'ai miki karyane annamimiya dama na dade ina zargin haka kuma wallahi yau sai kin bar gidan nan inyaso sai kiji dadin karuwancin"kuka Zainab keyi sosai gashi inna batanan taje gida dakinta Bilki ta shiga ta fara cillo mata kayanta waje waje cikin kuka Zainab tace "dan Allah umma kiyi hakuri idan kika koreni ina zan tafi "? 😭Bilki data gama watso komai waje tace duk gidan uban wanda zaki ma ni bai shafeni kafin na fito daga daki kibar gidan nan dan wallahi sainai miki dukan mutuwa"jakar takardun makarantar ta kawai ta dauka ta fita tana kuka a zauren gidan ta zauna tana ciki kuka Bashir ya shigo ganin ta haka yace "masoyiyata ke da waye ubanwa ya saki kuka"? Bata kullashi ciki ya wuce jin Bilki tace "dani ce nan"Korarta nai domin tana bin maza "Bashir dake kallonta yace kuma kudina fa da kika ci"? Cikin ko in kula tace kabita ka kamota sai kazo ga daki ka fanshi kudinka"jin haka yasa Bashir juyawa da gudu yai zaure ashe itama Zainab din tajiyo dan haka a guje ta bazama Bashir daya fito hangota dayai acan nesa yasa shi kara gudunsa kafin sakan har ya cimmata ganin ya kusa da ita ta kara gudunta amma sai dayai nasarar rike hijab dinta taci mugun tuntube ta fadi kasa wani uban ihu tai ta mike tsaye zai sake riketa ta hankada shi ya fadi kafin ya tashi ta kuma zubawa a guje ko gabanta bata gani harta iso bakin titi babu zato taji mota tai sama da ita wani razanannan ihu tai ta dawo kasa a sume Cike da rudewa mai motar ya fito wa zan gani Yarima Abdul-malik ne cikin sauri ya ciccibeta yasa ta a mota dan ya kaita asibiti ya shiga yama motar key cikin gaggawa. 😋 Um abin yazo sabuwar duniya sabuwar rayuwa sabin yan uwa da kuma sabon muhalli 😀 😀 Ina sonki 'yar uwata Naja'atu Musa Abubakar Zarah musa dan adam kina rai na Maman khaleel bani da bakin godiya a gareki saidai kawai nace ina sonki ❤ *YUSRAHMS ABUBAKAR * Mrs Al'ameen Ahmed ce 💋Everything about you is so good but one things is wrong that you are not mind. 💞INDO ke ta daban ce 🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒 Wallahi ana tare yan uwa 🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒 [11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: *👑Yarima Abdul-malik 👑* #Yusrah m Abubakar # *💫ANNURI WRITES ASSOCIATION💫* *Umh! The parrot that speakers * *True love never end in the world 🌏 Ina matukar godiya a gareku masoya Allah yabar zumunci *INDO ABLA'S DA RABI'AHH may Allah help and bless you anywhere you are. *Mrs Al'ameen Ahmed * Banda kamar ku. Fatima musa Abubakar Abubakar musa Abubakar. *Page 5 Bashir daya karaso ganin abinda daya faru yasashi juyawa a 360 ya koma gurin Bilki hankali tashe yana shiga Bilki ta mike tsaye tana cewa "ina take"? Bashir dake haki kamar ransa zai fita dakyar yace "wani mai mota ne ya bigeta kuma ya dauke ta sun tafini yanzu ya zanyi"? Cikin harara Bilki tace "ya zakai kuwa banda hakuri"wani irin kallo ya mata daya sata kusan sakin fitsari yace "me kike nufi dan kinga ina shaye shaye sai akace miki bansan ciwon kaina ba kome"? Shiru Bilki tai ta zuba masa ido yaci gaba da cewa to bazai yuwu ba cikin biyu ki zabi daya ko ki biyani kudina ko ki bani hindu a madadin Zainab". Mikewa Bilki tai kan ubancan tabdijan amma wallahi baka da hankali hindun 'yar riko zan dauka na baka me zancewa iyayenta to waima kana dan kwaya ubanwa zai dau 'yarsa ya baka tun wuri kasan inda dare ya maka Hindu ba sa'arka bace tafi karfin kazami dan jagaliya irinka kudin ka kuma da kake mgn na cinye bazan biya ba ka dau mataki idan ka isa". Tunda ta fara magana Bashir ke kallon ta har takai aya jin zata raina masa hankali yace "haka kika ce "? Itama cikin fushi take kallonsa tace "eh ko akwai abinda zaka iya ne "? Kai ya jinjina kafin ya daga hannunsa dauketa da mari a firgice ta dago zatai mgn ya kuma wanka mata wani cikin bacin rai yahau dukanta kamar Allah ne ya aiko shi Hindu dake sauraronsu tun dazu ganin zai kashe Bilkin da duka ta mike a guje ta dauko itace tazo zata buga masa ya hankade ta ta fadi kasa kafin ya cilla Bilki daki ya jawo kofa ya rufe yana cewa Hindu "a kanki zan fanshi kudi na "wani ihu Hindu tai amma ba maceci. Bilki dake daki ta leko ta window tana cewa "wallahi Bashir idan ka taba yarinyar nan kotu ce zata raba mu"ko kallo inda take baiyi ba yaja Hindun dayan daki ya rufo kofa. Hmmm indai zaka gina rabin mugunta kayi dai dai kai don it may be kaine zaka fada. Bilki kuka take tana buga kofa kamar zatai hauka musamman yadda taji muryar Hindu na fita kamar wanda take gargarar mutuwa fitowa Bashir yai yana bude Bilki yace "nidin ba mahaukaci bane kamar yadda kike dauka ta nasan me nake kuma bangama fashe kudina ba in anjima zan dawo" yana kaiwa nan yai waje hannu Bilki ta dora a ka tana cewa Allah ya isa mugu tsinanne baza ka gama da duniya lafiya ba azzalumi. Hhhh wai yau Bilki ce me kiran wani azzalumi. Musty ne ya fito yana mika cikin mmk yake kallon Yarima don jiya haryai bacci bai dawo ba zama yai kusa dashi yana cewa "wai jiya ina kaje ne tun yamma na rasaka nayi tunanin ma ko gida ka tafi dan nasan ba karamin aikin ka bane"shiru ya masa zuwa can yace "yarinyar na bige jiya a mota shiyasa ban dawo da wuri ba yanzu ma inaso zan koma asibitin ne"kallonsa Musty yai yace "ok Allah ya rufa asiri bari na shirya sai muje tare"kai Yarima ya girgiza "no need "da mmk Musty yace "me kake nufi "? Mikewa yai batare daya bashi amsa ba yace "let me go i don't want be late"? Ko tsayawa yaji me Musty zaice baiyi ba ya wuce domin a yanzu ma yasa an zo daga Abuja an dauke ta domin a kara duba lafiyarta shima zuwa jimawa zai tafi. Sai dare ya isa gida ba wanda yasan ya dawo ko hutawa baiyi ba jakarta dake kusa dashi ya dauko yana budewa ganin takardu ne yasa ya mayar sai wani photo daya sashi kusan kwaruwa da ganinsa cikin mamaki ya zubawa photon ido idan ba mafarki yake yi ba kuma ba idonsa ne ke nuna masa hakanba tabbas wannan matar ta jikin photon tana matukar kama da mamansa dan farko ma yai zaton itace sai daya kalla dakyau sannan ya gane ba ita bace shiru yai ciki mmk to wacece wannan yarinyar daya buge wacece wannan matar dake kama da mahaifiyarsa shiru yai ba amsa dan haka dole ya hakura ya kwanta bacci wanda kusan rabi da rabine. Asuba nayi dayai sallah yabar masarautar bai yarda an ganshi ba dan baya bukatar hakan. Kwanan Zainab biyu a asibiti kuma alhmdllh babu abida daya sameta saidan kurjewa mamaki ne ya isheta ganin inda take tasan dai asibiti ne to kenan mai motar daya bige tane ya kawo ta tana cikin wannan tunanin likita ya shigo yana cewa "to alhmdllh yau muka baki sallama wanda ya kawoki yanzu zaizo ku tafi "kai Zainab ta daga tace "nagode "fita likitan yai da kamar minti goma taji anyi sallama da wata irin murya data sata dagowa da sauri ganin waye shima idonsa a kanta cikin wani irin mmk da yake neman sheke masa tunaninsa bai zauna ba ya tsaya a bakin gadon yana harde hannuwansa a kirji kawai ya kasa mgn. Dan sauke nufashi yai yana kallon ta yace "amma kina matsayin mace kike irin wannan gudun a layi ina zakije"? Umh daga haduwa sai tambaya maimakon ace ya jiki sunkuyar da kai tai cikin sanyi tace "wani ya biyo ni"wani? "Me kika masa"? Cikin kuka tace kishiyar ummi nace tamin sharri kuma ta koreni shine tace ya biyo ni wai ya fanshi kudinsa da taci"tambayar ta ya kuma yi cewa "yanzu idan na mayar dake kano zaki koma gurinta"? Kai ta girgiza tace "idan naje ma bazata barni na shiga gidan ba ni kuma bansan inda zanje ba a matsayina na mace ina tsoron a keta min mutunci na idan kasan wani gidan marayu na rokeka ka kaini can na zauna". Shiru yai ya zuba mata ido yana tunani a zuciyarsa yace "to ni yanzu ya zanyi da ita"? cikin sanyin nazari yace "to ko masarauta zan kaita kila zasu samu mafita"jin zuciyarsa ta amince da hakan yace "ok taso juyawa yai ya fita ta mike tana bin bayanshi har jikin mota suka karasa ya shiga yana ce mata ta shiga daya site din sannan ya kama hanya wani dankareran gida ya kaita amma akwai tsaro har cikin bedroom ya karasar da ita yana ce mata ga toilet nan idan tana bukatar wanka ta zauna yana dawowa mmk ne ya kamata ita da tace ya kaita gidan marayu sai ya kawota wannan kyakkyawan gidan zama tai bakin gado tana kara kallon dakin da kyau. Kwananta biyu a gidan amma bata kara ganinsa ba saidai komai ta bukata zata samu. Shigarsa gurin mai martaba kenan yaga yadda mai martaba ke kallon shi abin ya bashi mmk amma sai ya dake ya mike zai tafi yaji muryar mai martaba yace "Muhammad wacce yarinyar ka ajiye a gidanka"? labari yazo min cewa kana ajiye mata a gidanka saidai ban gamsu ba don ba halin ka bane, mene gaskiyar al'amari "? Cikin mmk Yarima ya kalli mai martaba kafin ya juyar da kallonsa saitin Yaha wani irin shu'umin murmushi yaci karo dashi a furkarta nan take ya harbo jirgin ya kalli mai martaba yana cewa "ni kaina bani da labari akan hakan kakana kila so kawai ake a hada ni dakai kasan ba halina bane"kai mai martaba ya jinjina cikin gamsuwa yace "Muhammad nikaina ban yarda ba nasan sharri ne akai ma tashi kaje Allah yama albarka"murmushi Yarima yai yana kallon Yaha ya mata alama da tasa batasan lokacin da tace "kuturun ubacan ni kakewa haka"? Cikin haushi Abba yace "ke kuma da uban wa "? Shiru tai cikin takaicin ganin yadda Yariman ya nuna kamar badashi take ba hakan na nufin yamai da ita mahaukaciya a cikin mutane Mikewa yai har lokacin da murmushin sa ya fita a palon ya bar Yaha kamar ta dora hannu aka tai kurma ihun takaicin sa. Bai zauna a masarautar ba can gidansa ya koma dan bai kamata ya barta ita daya ba, bayan sallar isha yana zaune a palor yaji an bude get din gidan ko kafin yai wani yunkuri yaga su mai martaba sun shigo dukkansu zama sukai ba wanda yai mgn mai martaba yasa wadanda yazo dasu su goma su shiga gidan su bincike masa ko'ina wani irin faduwa gaban yarima yai amma ko kadan bai nuna ba sun jima suna binkice suka fito cikin girmamawa suka ce basuga kowa ba hamdala kowa yake a gun banda Yaha dan itace ta kara hura wutar ya kamata a zo a bincika gidan cikin jin dadi mai martaba yace "madalla da yaro na gari yanzu kan zargin mu akanka ya wanke Allah ya kara shirya mana kai", fatan baka shiga damuwar ganinmu dakai ba shiri ba"? Murmushi Yarima yai "kakana komai kukai ai kun isane kuma kuna sona shiyasa hankalinku yaki kwaciya sai da kuka tabbatar"mikewa mai martaba yai yace cewa su tashi su tafi har jikin mota ya raka su kafin ya dawo gidan direct dakin Zainab din ya shiga a jikin window ya ganta tsaye cikin mamaki yake kallon ta da alamar tambaya dan zama ta tace "naji abinda ake fada a palon shine na shiga toilet su kuma da suka zo iya budawa sukai ganin ba kowa suka rufe ni kuma ina bayan murfin toilet din"ajiyar zuciya ya sauke "shikenan good night "yana fadin haka ya fita a dakin ita kuma ta kwanta. Gari na wayewa yace ta shirya zasu wani guri saida ta gama komai ta fito ta sameshi a mota mintina kalilan suka iso inda zasu cikin mamaki Zainab ke kallon masarautar a ranta tace kodai dan sarki ne, to amma me zasuyi anan? ganin ya wuce ta yasa tabi bayansa tana kalle kalle kamar 'beran kauye yaje birni bai zame ko'ina ba sai asalin babban palon mai martaba kuma yau gabadaya ahlin suna can bai tsaya ko'ina ba sai gaban mai martaba ya durkusa ya kwashi gaisuwa cikin mmk mai martaba yake kallon Zainab yace "Muhammad daga ina ka samo wannan"? Cikin ladabi ya fara fada musu komai har kuwa zaman datai a gidansa shiru palon ya dauka kowa na kallon Zainab cikin tausayawa banda Yaha da haka kawai taji tsanarta lokaci guda ta diram mata arai. Mai martaba ne ya kalli Zainab yana cewa "ke yarinya daga ina kika fito? mene gaskiyar labarinki,? kada kiyi mana karya ke 'yar waye? Zainab da kanta ke sunkuye tun dazu muryata na rawa ta fara basu labari kowa ji yake tsumin jikinsa na tashi dajin labarin yayin da ita kuma take kukan tuna mahifanta. Lallai kam taga rayuwa ace bakasan dangin ka ba ko daya wanne irin hali zaka shiga. Mai martaba daya gama tunani yace "to yanzu mene shawararku akan wannan al'amarin domin abune mai girma"? Abban Mahmud ne yace ai inaga ba abinda zamuyi daya wuce mu rike ta anan tamkar 'yar da muka haifa idan shawara ta tayi, "amma ranka ya dade me kace"? Mai martaba yace "haka shine dai dai Ibrahim nima abinda nake tunani kenan idan ma mun barta ta tafi babu inda zataje, to amma a cikin ku waye zai riketa kai ko Yusuf "? Abba yace "a'a nizan riketa sai ta zauna a gurin Yahanasu duk abinda take so zata samu". Gyara zama Yaha tai tana cewa "gaskiya nidai bazan riketa ba tunda Hajara ta kusa zuwa taya zan rikesu har su biyu kawai bansan yarinya ba daga ta fada muku karyarta ko da sharri tazo wa yasani sai a nemi a likamin ita ni dai bazanyi rikon wannan tsintacciyar magen ba"tana fadin haka ta mike ta fice a palon. Da mmk mai martaba yace "Ibrahim dama matarka bata da kirki a gabana take iya fadar bakaken mgn haka"? Cikin ladabi Abba yace "ayi hakuri ranka ya dade amin afuwa"dadyn Yarima mai martaba ya kalla yace "Yusuf kai na baka ita daga yau kaine mahaifinta duk wani nauyin ta akanka yake"cikin girmamawa yace "to ranka ya dade godiya nake "kallon mama yai yana mata alama dan murmushi tai tana jinjina kai kafin ta mike tana cewa "yata tashi muje"mikewa Zainab tai tana goge hawayen maganar da Yaha ta fada akanta suka fita Yarima ma sallama ya musu yana fita domin shi kasar ma zai bari. Mama na rike da hannunta har part dinta ta rakata wani bangare daban tace ta zauna tana zuwa ba'a jima ba ta dawo tare wata budurwa zamatai tana kallon Zainab tace "ranki ya dade dama Yarima Abdul-malik nada kanwa wallahi suna kama"? Murmushi mama lokacin zata fita tace "kedai yi mata lalle kawai ina dawowa yanzu"lalle ta fara zana mata mai kyau saida aka gama sannan aka fara yimata kitso tab masha Allah sai wanda ya ganta bayan angama komai tai wanka mama ta kawo mata kaya tasa ta fita palo. Dagowa mama tai tana murmushi tace "dota zo ki zauna ga abinci nan zama Zainab tai tana sunkuyar da kanta tace "nagode mama Allah ya saka da alkairi" har lokacin murmushi mama keyi Yarima ya shigo cikin shirinsa alamar lokacin tafiyarsa yayi mikewa mama tai tana riko hannunsa tace baby harka shirya,? yaushe kuma zaka dawo"? Zama yai yana lankwasar da kai yace "bazan wuce wata biyu ba kawai"zaro ido mama tai "baby wai watan nan jinta kake kamar sati naga alama dadi kake ji idan ka tafi ka barni amma yanzu tunda muna da wata babyn shikenan kaje kai shekara ma"cikin shagwaba yace "haba mama kar muyi haka dake am first and last"cikin zolaya mama tace "tab waya fada ma"? Gara ka sake shiri dan kaidin yanzu babban yayane"yunkurawa yai zai tashi ta rike shi tana dariya tace "baby tsaya kaci abinci" dan bata fuska yai ganin ta dauko cikin lallami tace "ci ko spoon biyar ne sai ka tafi kaji babyna" tana fada masa magana mai dadi ta samu yaci abinci kafin ya tafi Zainab kan dataga irin lallabashin da mama keyi kamar yariri yasa ta zaro ido aranta tace "tabdijan shagwababbe". Sati uku da tafiyar Yarima Hajara ta zo murna gurin Yaha kamar ta maida ita ciki duk abinda tace yanzu za'ai mata shi. Abinda aka samai rana me karewa ne yau gida kacame yake da murna yarima zai dawo dan Hajara ma gabadaya ta kasa nutsuwa sai kaiwa da komowa take abinci kala Kala tasa aka mata na saukarsa a palon Yaha ta ajiye tana cewa bari taje tai wanka Yaha batai mata magana ba domin abinda ke damunta daban Abba da Dady sun tafi masarautar Bauchi mai martaba ya aikesu kawai ji take hankalinta bai kwanta da hakan ba da tafiyar da sukai. Da yamma Yarima iso gida murna abin ba mgn kamar yadda aka saba tararsa koda yaushe yauma haka saida ya gaisa da mai martaba sannan ya shiga part dinsa don hutawa yana palo Hajara ta shigo da wadanda suke dauke da abincin suna ajiyewa sukai waje sai daya gama daura agogon hannunshi ya nufi hanyar fita shan gabansa tai tace "haba Abdul-malik mene haka"? Da mamaki yake kallon ta ita kuma wannan lfy uban me tazoyi nan cikin danjin haushi yace "ban guri idan kika kara shigowa part din nan saikin gane kurenki"cikin nuna isa Hajara tace "malam bafa zaiyuwu ka wulakanta niba dan kawai ina sonka bashi yake nufin kana da ikon da zakai min kowanne cin fuska ba"kallon ta yake cike da tsana danshi wannan me kama da tabaryar ba abinda zaiyi da ita zagaye mata yai zai fice ta jawo hannunsa tana cewa "wallahi fa baka isa ka fita a palon nan ba sai ka saurare ni ko anfada maka nidin sa'ar____bata karasa ba tai shiru jin wani lafiyayyen mari ya sauka a kumatunta ba arziki ta sake shi ko karasa kallonta baiyi ba ya fice yana jan tsuka kuka Hajara ta fice dashi tana komawa guri Yaha harda birgima a kasa wai marinta yai hankali tashe Yaha tace "ya mareki"? Amma wannan yaro anyi mara tarbiyya kinga daina kukan aure ke dashi kamar an daura ne"share hawaye tai "wallahi umma ko baya sona dole ya aureni "Yaha tace af kwantar da hankalinki nace miki nasan abinda zanyi. Part din mama ya nufa dai dai zai shiga yaji Zainab na waya dan dakatawa yai jin tace "ina jinka nufin ka wai kazo gidanmu, tab a'a gaskiya zan dai fada maka amma ba yanzu ba saina tambayi mamana da dadyna idan sun amince zan sanar dakai sai kaz______jitai an zare wayar afirgice ta dago ganin wanda batai zato ba yasata rudewa ga wani abu da take hangowa cikin idanunsa da batasan me zata kira shi ba tsawa ya daka mata cewa da ubanwa take mgn shiru tai mama dake bedroom batasan meyake faruwa ba jin karar Zainab yasa ta fito da gudu da mmk take kallon Zainab datai kneel down a gaban Yarima tana kuka shi kuma yana tsaye ya zuba mata ido karasowa mama tai tana daga zainab din cikin mamaki tace "baby lafiya? meya faru? Idansa nakan Zainab din yace "yaushe wannan yarinyar ta fara hira da samari cikin wayarki a ina ta sansu?"? Da sabon mmk mama tace "Zainab din"? Bai sake magana ba ya juya ya fita a part lallashinta mama tai sannan ta kama hannunta suka shiga ciki. Washe gari suna zaune ana firar yaushe gamo su Abba sun dawo mai martaba ya kalli Yarima yana cewa "Muhammad ya kamata ace yanzun kayi aure kana da iyali kaima ko ba haka ba, kaga aure shine darajar kowanne mutum ya kamata kayi"sunkuyar dakai Yarima yai baiyi mgn ba alamar bai shirya ba mmk ne ya kama mai martaba amma sai yace "to shikenan Muhammad tashi kaje"mikewa yai yana fita Yaha tai gyaran murya tace "ranka ya dade ai wannan mai sauki ne Hajara ta dade tana sonshi saboda shi ta dawo nan da zama ta jona karatunta ta dade tana cemin na fada nace mata a'a". Shiru palon ya dauka zuwa can mai martaba yace "kai Yusuf ya kake gani domin danka ne kaine mahaifinsa"? Cikin ladabi dady yace "a'a duk hukuncin dakayanke dai dai ne kai da kaya ai duk mallakar wuya ne"zuciyar mama tafasa take tun lokacin da Yaha ta fara mgn tasan akwai wani abu data kulla a cikin wannan abin Abba kam cewa yai "a'a a bari tukuna aji ta bakinsa idan ya amince shikenan "karaf Yaha tace "to shiyai kansa duk umarnin da aka bashi dole zaibi"mama so take tayi magana ta kasa mai martaba yace "shikenan zamuje medigurin in sha Allahu" Abba kan bai amince ba ya kuma cewa "gaskiya ya kamata a fara tambayar_____ tarar numfashinsa Yaha tai "ya kake jada maganar mai martaba ai ya gama yanke hukunci" tana fadin haka ta tashi ta fice a palon tana shiga part dinta ta sheke da dariya tana cewa "lokacin ki ya fara Yaha wallahi Abdul-malik sai na mayar dakai gawa. Mama na shiga palon ta taga Yarima a zaune alamar yayi nisa cikin tunani dafa shi tai ya dago ganin mama ce yashi rungumeta jin zuciyarsa kamar zata fito waje cikin kwantar masa da hankali mama tace "baby kayi hakuri in Allah ya yarda abu mara kyau bazai taba samun ka ba kaga yanzu fitowa ta daga palon Mai martaba yace zasuje maidiguri a nema maka auren Hajara ni kuma wallahi harga Allah yarinyar nan batai min ba ko kadan". Zabura Yarima yai jin abinda maman tace wai shi za'a aurawa waccan mahaukaciyar yarinyar to ba gara ya mutu baiyi aure ba wayar dake hannunsa yai wurgi da ita cikin sakan ya burkicewa mama shigowar dady kenan ganin abinda yake faruwa da sauri ya karaso yana tambayar lfy maimakon ya bashi amsa sai yai baya luuuuu zai fadi cikin sauri dady ya tare shi har ya suma cikin gaggawa mama ta debo ruwa suka hau shafa masa Zainab na gefe tana kallo sauke ajiyan zuciya yai yana bude idonsa sai kuma ya sake rufewa girgiza shi dady yai amma ya kara suma dan haka yaci gaba da shafa masa ruwan har ya samu ya farfado kalmar farko daya ambata shine "Zainab ke nake so ba wata ba kada ki bari wani ya shiga tsakanin mu"shiru sukai jin abinda yake fada Zainab kan da sauri tabar gurin cikin faduwar gaba kallon dady mama tai sai kawai sukai murmushi a tare dady yace "tunda haka ne da kansa zaije ya fadawa mai martaba ga wacce yake so ba yazo yana suma ba "dariya sukai dai dai lokacin daya bude idonsa ya tashi zaune ganin duk jikinsa ruwa yasa yace "lafiya "? Mama tace "kai zamu tambaya lafiya kazo harda suma"cikin mmk ya kalleta "suma dai "? Dady dake masa dariya tun dazu yace "babana karka tsaya bata lokaci kaje ka samu mai martaba da kanka kace ga wacce kake so zai fahimceka tunda abokin kane "shiru Yarima yai bayan ya gama tuna abida ya faru yace "nifa bance inason wata ba"wani kallo dady ya masa yana cewa "naga alama tashi kaje tunda baka ce kana son wata ba muma ai bakaji munce kana son wata ba "mama data bishi da kallo tace baby Allah ya shirye ka bata fuska yai ya fita a palon ko takalmi bai dauka ba haka ya tafi part dinshi. Hhhhh wasa ne Gaisuwa dai maman khaleepha Allah ya kara zumunci. INDO ina godiya sosai Allah ya barmu tare. ABLA'S ke ta daban ce. RABI'AHH kina raina har bansan yadda zance ba. MRS TSARI wannan sai Naja'atu Musa Abubakar. # ## ### #### ##### #YUSRAHMS ABUBAKAR # Mrs Al'ameen Ahmed ce. [11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: (*() *) (*()*) 📲Typing 👑YARIMA ABDUL-MALIK 👑 💫ANNURI WRITING ASSOCIATION💫 Dedicated to Safiyya Aliyu & Zarah Musa #YUSRAHMS ABUBAKAR Moral lesson If people care for you, you also show care for them. MANZON ALLAH (S*A*W) You are unique, the first and the last, no success without you, you are the mirror of life, you are everything, you are the answer to every question, you have no limit YA RASULULLAH. *Page 6 Mikewa mama tai bayan ficewar Yarima ta shiga part din da Zainab take a bakin gado ta same ta ganin mama yasa ta sunkuyar da kai murmushi mama tai tana zama ta rike hannunta ta soma mgn "dota kinji abinda ya faru ba sai na sake yi miki bayani ba shin kin amincewa babyna zaki aure shi eh ko a'a? kada ki ji kunyata fada min gaskiyar abinda ke ranki idan baki amince ba babu mai yi miki dole kara sunkuyar da kai Zainab tai ta kasa mgn gabanta na faduwa ganin tai shiru mama dake kallonta tace "haka yana nufin baki amincewa baby ba baki sonshi"? Cikin sauri ta girgiza kai muryan ta na rawa tace "amince zan aureshi halaccin dayai min bansan dame zan saka masa ba daya wuce nai abinda ya nema yanzun zanyi masa biyayya bazan saba masa ba zai sameni mai ladabi a gareshi"rungumeta mama tai cikin jin dadi tana sa mata albarka. Ba yadda mama batai da Yarima ba akan yaje ya samu mai martaba amma yai kirmishishi yaki zuwa ganin idan ta biye mai wankin hula zai kaisu dare yasa ita da dady sukaje gurin mai martaba ba wani boye boye suka fada masa komai mai martaba da shima haushin angama mgn da iyayen Hajara yasa yace "to meyasa tun wuri baizo ya fada min ba gashi yanzu an karba masa auren wata to saidai ya hada su duka biyun ya aura ya tafi dasu sbd bazai yiwu mu mayar musu da magana ba "amincewa sukai duk da mama bata ji dadin hakan ba to amma ba yadda zasuyi suna nan zaune ya shigo fuskarnan a matukar murtuke dan ya kasa boye damuwarsa mai martaba dake kallon shi yace "Muhammad kayi hakuri nasan zakaji babu dadi amma kasan mu idan munyi alkawari bama canjawa ina so ka cire damuwar komai a ranka in Allah ya yarda zakaga riba da nasara a gabanka"numfashi ya sauke ba tare dayai mgn ba har kuwa suka bar gurin mai martaba ba wanda yaji muryar sa suna shiga palor mama ta kalleshi tana cewa "baby me yasa bakaje gurin mai martaba kayi masa bayani ba gashi yanzu ka jawa kanka auren mata biyu dan me kaki zuwa tun ranar da abin ya faru"? Shiru yai babu amsa dan shi kadai yasan abinda zuciyarsa ta shirya masa. Yau saura kwana goma Yarima ya bar kasar mai martaba kuma yace bai amince ba ya gaji da ganinsa ba aure sai dai ayi bikin cikin kwana goman din daya rage ya tafi dasu sbd idan ya tafi ba'a san ranar dawowarsa ba Yarima ya firgita lokacin daya ji wannan mgn amma sai ya dake bai cewa kowa komai ba har saida ya basu mmk musamman daya nuna rashin damuwarsa akan mata biyun dazai aura Yaha kan dataji labarin wai Yarima zai auri Zainab yar karamar hauka tai dan gani take bazatai nasara ba Zainab tamkar barazana ce a rayuwar ta musamman dataji ance iya na Zainab din za'a daura ita Hajara saiya dawo tunda karatu take babu kunya taje gaban mai martaba da kukan ta tace a daura harda Hajara karatu baifi aure ba duk sanda suka dawo taci gaba mai martaba yayi mmk ganin irin kukan da take amma sai yace mata shikenan za'a daura farin ciki kamar ta mike tayi rawa a gaban sa. Yarima baiso mai martaba ya amincewa Yaha ba amma sai yai burus da zancen. musamman mama ta dauko mai gyaran jiki ake kula da Zainab tayi kyau tai fresh abinta har mmk take idan taje gaban mirror kamar ba ita ba. Yaha ce zaune a palor kamar a mafarki taga Yarima ya shigo ba tare daya kulata ba yai hanyar dakin Hajara da sauri Yaha ta mike tana cewa "malam me zakayo anan kayi ajiya ne"? Batare daya juyo ba yace "niko nai ajiye tunda gurin mata ta nazo bai shafe kiba idan kuma so kike ki ganewa idon ki abinda yafi karfinki saiki shigo"yana fadin haka ya bude kofa ya shiga takaicine ya kama Yaha to uban me zaiyiwa Hajaran da har zata shiga ta tuno abinda daya fada mata tajuya zuwa palo tana jiran fitowar sa, Hajara dake kwance cikin mmk ta mike zaune tana zaro ido waje tace "lafiya "? Harde hannu yai yana kallonta yace "lfy nazo Duba lafiyar mata nane ko tana cikin farin ciki "da sabon mmk ta kuma zuba masa ido cikin jin dadi anya kuwa ba mafarki take ba Abdul-malik ne yazo duba ko tana lfy katse shirun yai da cewa bani number abbanki zan kira shi mu gaisa a matsayinsa na suruki na baban mata ta kuma uwar 'ya'ya na ya kare maganar da dage mata gira alamar ita yake jira jiki na rawa ta dauko waya tana cewa "gashi dauki"hade rai yai "fado min "fada masa tai sannan yace "tnk my wife take care good night "bai saurari wani abu daga gare ta ba yai waje dan bukatar sa ta biya ko kafin Hajara ta fito har ya fice Yaha ce ta tare ta "ke lfy ina zakije "? Ihu Hajara tai tana rungumeta tace "umma ki tayani murna Abdul-malik da kansa yanzu ya kira ni da matarsa wallahi umma ya fara sona"cikin mmk Yaha ke kallon ta amma batai mgn ba dan ita hankalinta bai kwanta da zuwansa ba gani take kamar wani abu yake shiryawa. Ranar alhamis masarauta ta cika tab da baki na sauran wasu masarautun Yaha tayi mamakin rashin ganin dangin su na masarautar maidiguri amma data kira abban Hajara sai yace mata duk gobe zasu zo kafin ayi daurin aure sai sannan hankalinta ya kwanta. Yaha na zaune taga wata budurwa ta shigo tana karewa part din kallo kamar mai duban tsafta mikewa tai tana kallonta tace "wace ke me kike nema anan ko kinyi batan kai ne idan ma makancewa kikai to maza ki saitawa kanki hanya ba nan ne part din da ake bikin ba har kike wa mutane kallon banza daga ina kika fito"? Dan murmushi tai tana duban yaha tace "ni bakuwa ce munzo biki daga masarautar Bauchi sunana Salmah part din Ibrahim Abban Mahmud nake nema"cikin faduwar gaba Yaha ta kuma bude ido a kanta tace "nan ne lfy"? Kai Salmah ta girgiza ba tare datai mgn ba ta juya ta fice a part din kasa zama Yaha tai tana tunanin ita kuma wannan ubanwa ya aiko ta amma tafi zargin Amina ce (mama) tana cikin zagaya palo Abba ya shigo tararsa tai da cewa "Ibrahim wacce yarinyar daka turo tazo ta min wulakanci"? Ko kallon ta Abba baiyi ba ya wuce da gudu tasha gabansa tana huci tace "me kake boyemin wacce ita "? Kallo mai ma'ana da yawa Abba yai mata kafin yace "i think ta fada miki sunanta Salmah daga masarautar Bauchi right nine na turo ta domin baki zo da part din daga masarautar kuba kuma kada ki sake ki rufe kofa dan anan tace min zasu kwana "wata ashar ta saki batare data shirya ba tahau masifar me yake nufi da haka amma ko ta kanta baibi ba ya fice abinsa haka ta karaci kumfan baki ita kadai tai shiru. Yarima yana zaune Musty ya kira shi cikin tashin hankali ya soma mgn "Abdul-malik me nake gani wacce wannan yarinyar da zaka aura dazu ina zaune Aunty ta turo min photon wedding dinku kamar Zainab nake gani wai dama tana gunka amma sbd rashin mutunci kaki ka sanar dani ka barni ina ta shan wahalar nemanta please ka bani amsa"? Murmushi Yarima yai yana cewa "amma alamu sun nuna kanka baya ja wannan zaka kalla kace wata zee dinka ko ka fara makancewa ne kalli sunanta mana ba Malika Ibrahim ka gani ba suna nawa Zainab din taka take amfani dashi"? Kara kure photon Musty yai da kallo wallahi abinda kawai wannan zata fi Zainab haske da kiba sai yanayin hutu, sake kallon Yarima yai cikin marairaicewa yace "please Abdul-malik na roke ka idan itace ka fada min na daina shan wuyar nemanta"wata harara ya samu maimakon amsa sannan yace masa "zakasan ba ita bace sai ranar da kuka hadu, malam ina da baki please zan koma gurinsu good night"bai bari Musty yace komai ba ya kashe camerar da yake video call ne suke Musty kan ji yake tamkar yai tsuntsuwa ya dawo Nigeria kodan ya gani da idonsa cewa ba Zainab bace dan ya kasa yarda gashi ko ranar tahowa bai saka ba haka nan dole ya hakura. Hhhhhhhh rana fa bata karya ina masoya ku fito mu kwashi shoki dan abin yazo inji mai fadar aurensa yace gobene fa. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 #Yusrah Musa Abubakar Ina INDO ku matso kusa yau zamuje Abuja diban gara ABLA'S hanzar ta lalala ina RABI'AHH ai tafiyar bazata yuwu ba idan babu ke, sai kunzo mukan mun dau katuwar gana masgon mu munyi gaba dan ba jira 🏃‍♀️kar muje ayi ba mu 😜. Washe gari da yanayi mai kyau gidan sarauta ya tashi kowa murna yake musamman bangaren mai martaba dasu mama abin bana magana bane sai wanda ya gani dan nikan na gani amman bazan fada ba. Saida akai sallar juma'a sannan aka fara hidimar daura auren daya samu halattar manyan mutane masu martaba saida komai ya kammala Yarima ya tashi daga cikin abokansa ya matsa gurin mai martaba cikin rada yace "kakana kabar dayan daurin auren munyi magana da babanta ya amince tunda wata hudu kawai zanyi idan na dawo sai ayi na 'yar sa inaga zaifi da ace tana matar aure kuma tana yawon zuwa makaranta ba'a gidan miji take ba, amma me kace kakana"? Kai mai martaba ya jinjina cikin gamsuwa yace "kwarai gaskiyar ka kayi tunani mai kyau haka shine dai dai Allah ya maka albarka"wani irin murmushi Yarima yai ganin yaci nasara ta ko'ina dady tun dazu yana hankalce dashi ganin bayan sun gama maganar sai murmushi yake yasa ya jashi gefe yana masa kallon tuhuma yace "kai me ka fadawa mai martaba? dan haka kawai naji ban yarda dakai ba"? Cikin yar shagwaba baya ko kunyar mutane ya wani narke a jikin dady yana cewa "nifa babu abinda nace masa kawai munyi magana ne "kallonsa dady yai "to daga min jiki karka karasa ni kasan na fara tsufa"yar dariya Yarima yai yana kallon sa bai kara mgn ba ya sake shi yana komawa gurin abokan shi suka dau hanyar gida. Cikin tashin hankali Yaha ta shiga part din Yarima ganin sa a palor yasa cikin tsawa tace "kai Abdul-malik! "Da mamaki Yarima ya dago yana kallonta cikin bacin rai ta soma mgn "wannan wanne irin rashin mutunci ne kayi dan kawai ka bakanta min shine sai da kasan yadda kai aka fasa daura na Hajara dan mugunta harda wani saika dawo wallahi baka isa ba azzalumi kawai" ta karasa mgnr kamar zatai kuka har lokacin kallonta yake cikin natsuwar tsokana yace "haba umma ki rika shan ruwan sanyi zaki sawa kanki ciwon kai da wannan ihun da kike ga guri zauna muyi mgn mene abin daga hankali aiba cewa nai bazan aure ta ba"wani irin kallon takaici Yaha take binsa dashi jin abinda yake fada tace "nice nake ihun kenan ka mayar dani kare kome "? Dan murmushi yai yana cewa a'a ko daya wa? Ni na isa nace miki kare amma bari na gyara miki ba kare zakice ba sai dai kice karya tunda ke mace ce kin gane bazanyi abinda zai takura ni ba na rufe wannan layin kamar yadda kofa ta riga ta kulle kuma dakin da matukar duhu akwatin sirrin na tantame shi da igiya bamai ganin wani abu daga cikin sa har abada "tunda ya fara magana Yaha ke kallon sa da mmk dan bata taba ganin sa yayi doguwar mgn ba sai yau gashi ya caccaka mata mgn kuma ya fuske kamar bai fadi komai ba wani zazzafan numfashi take fitarwa mai cike da kuna dakyar tace "me kake nufi ban gane ma'anar wannan sakalkalen maganar da kake min ba wai kai me kadau kanka? har yaushe ka girma? waye kai? Kai tsaye Yarima yace mata "I'm if you know sannan i'm not if you doesn't know ina fatan yanzu kin gane to zaki iya fecewa "wata tsawa ta daka wanda tasa shi saurin toshe kunne yana mikewa ya rike hannunta ya fara tafiya da ita saida suka fito a part dinshi ta fara kokarin kwace hannunta dan juyawa yai yana kallonta yace "idan kikai haka a gaban bayinki kiyi fada da danki mutuncinki zai zube dan haka ki nutsu"ci gaba yai da tafiya da ita kamar wata yarinya. Tab Yaha kam ko gabanta bata gani sbd bacin rai har gaban mai martaba ya kaita sannan ya sakar mata hannu da mmk kowa ke kallon su mai martaba ne ya fara magana "Muhammad daga ina haka ina fatan lfy"? Kai Yarima ya jinjina lfy kakana dama umma ce taje min tayani murna taimin addu'ar dana ji dadinta shine nace nima bari na kaita gurin babban abokina ta karbi tata addu'ar "murmushi mai martaba yai "hake Muhammad naji dadi kuwa Allah ya miki albarka Yahanasu"sbd bakin ciki Yaha durkusawa tai a gun tana fashewa da kuka dan ta kasa rike shi da mmk mai martaba yace "a'a lafiya kuma"? Yarima dake murmushi yace "ai kakana farin cikin addu'ar da kai mata ne yasa ta kuka tasan albarka zatai mata zobe a jikinta murnarta ta kasa rikewa gaskiya umma ta nuna jin dadinta akan auren nan kakana a kara bata wata albarkar ko tasamu tadan tsatso naga duk ta rame sai kace itace amaryar"dakuwa hajiya tai masa tana cewa "gidan ku ba ummarka bace ka maida ita kakar ka "bai sake mgn ba ya juya yabar palon yana murmushi ko ba komai gaba zata kiyayi rike girman ta dan hausawa sunyi karin magana cewa "any old man that don't fear to ride on donkey, donkey will not fear to throw the old man to the ground". Yana komawa part din sa ko zama baiyi ba Musty ya kira shi kin dagawa yai saida ta katse sannan yabi kiran nasa Musty na dagawa cikin tsokana Yarima yace "malam wai meye ka dame ni ko yaudin ma kira na kai akan na fito maka da Zainab dinka sbd ka mayar dani dan yankan kai ko"?nidai shawara zan baka ka daina wahalar da kanka ba samun ta zakai ba dan kila ita ta shafe babinka a rayuwa kuma bari kaji idan ka sake kira na kana tuhuma ta akan batan Zainab zansa a kulle min kai aita dimar ka saika fadi inda na kaita"cikin haushi Musty yace prince, prince kasan Allah ka kiyaye ni ubawa zakasa ya kulle ni kasan yadda nake jin yarinyar nan a raina kuwa? kasan irin matsayin dana dauke ta da zakace haka"? Gyara zama yarima yai "na sani mana zai wuce malami da dalibarsa, kuma naji ka dage sai prince kake kira fatan ba dani kake ba? dan ni bashi bane"Musty yace "inji ubanwa kai bashi bane "yarima dake duba wasu kaya yace "ok to fada min mene ma'anar prince "? Musty ya ci gaba da cewa "a boy of royal birth, the son of a king like you "tabe baki Yarima yai "malam ba shi bane just kira ni Abdul-malik Yusuf dina shine sunana, kuma nidai ina sake tabbatar maka da cewa kai da Zainab kunyi hannun riga ba lallai ka sake ganin ta ba "yana kaiwa nan ya datse kiran tsaki Musty yai "wallahi Abdul-malik anyi dan iskan mutum in kaga na hakura da neman Zainab to saidai in bana numfashi. Zaune duka familyn suke a gaban mai martaba yana musu nasiha da addu'ar fatan alkairi sannan yace idan Hajara ta gama karatu lokacin ya dawo a daura, Yaha kan ta cika tayi dam so take tayi mgn ta kasa sai juya hannu take ta matsu taga Yarima baya duniya gashi yazo ya auri mara asali yar tsuntuwa cikin dakewa tace "ranka ya dade Yarima dan dangi ne iyaye da kakanu me zamu cewa 'yayan su nan gaba idan suka taso akace musu uwarsu bata da dangi yar tsuntuwa c_____bata karasa ba Abba ya daka mata tsawa tai shiru wanda shi kanshi mai martaba yaji haushin mgnr data fada amma sai yai burus da ita ya kalli sauran yan palon yace "Yahanasu kinyi mgn mai kyau wacce za'ai duba a cikin ta amma ina so ki sani ko nan gaba idan aka tambaye ki waye mahaifin Zainab kice Yusuf ne mahaifiyar ta kuma kice Amina ce idan yayun ta ake nema kice Abdul-malik da Mahmud idan kanin mahaifinta akazo nema ga Ibrahim kakanu kuma da kike mgn akai mune ni da Aisha idan kuma gaba daya danginta ake nema kice mune ina fatan yanzu kan kin fahimta"shiru Yaha tai kanta ne kawai yadau caji ta rasa wanne irin so sukewa Zainab a gidan nan babu wanda ya sake mgn Abba ya rufe taro da addu'a sannan kowa ya mike ya fita da sauri Hajiya ta biyo Yarima tana cewa "kai naji ana cewa ranar monday zaku tafi ka tabbata ka bar mana saidar kimar matar ka idan kuma ba haka ba Wallahi sai ranar da kayi da kubar masarautar nan kaji na fada maka "juyawa yai yana kallonta yace "kinsan Allah ki fita idona ba ruwanki da wannan shafin ganin dama tane "harararsa tai sannu baba Yakubu baka isa ba to sai kayi ko ka hakura da tafiyar, idan kuma kaine baka da lafiya fada min inji sai a nemo maka magani"? "tafiya ya farayi yana cewa "eh bani da lafiya"Hajiya dake dariya tace "karya kake ". Mama ce zaune Zainab na gaban ta tasha kwalliya da kayan ado iri daban daban hadi take mata tana sha kuma tana mata nasiha da hakuri domin tunda Yaha tace bata da dangi take kuka ta rasa wacce kalar rayuwa ta tsinci kanta a ciki ace duka bangare biyun bakasan ko daya ba suna nan jakadiya tai sallama tana cewa "ranki ya dade inji Hajiya lokaci yayi"wani irin faduwa gaban Zainab yai wanda dama kukanta a kusa yake sai kawai taci gaba dayin abinta mikar ta mama tai tana rike hannunta tace "kiyi hakuri dota muje dama nayi alkawari ko ba baby kika aura ba nice zan raka ki har dakin mijin ki "tafe suke da masu take musu baya har part din yarima ta kai ta kuma yi mata nasiha sannan ta mata sai da safe ta fita tana murmushi. Shiru Zainab ta zauna tana tunanin ta inda zata fara neman dangin ta kodan gorin da ake mata zata tsaya tsayin daka ta samo su ko ta samu salama a rayuwar ta. Jin karar bude kofa yasa ta dago da sauri Yarima ne ya fito daga wanka dauke kanta tai jikin ta na daukar tsuma ba tare daya kalleta ba yace "u'r welcome"shiru tai jikin ta na tsananta rawa batasan me yake ba domin kanta a sunkuye yake sai jitai an mikar da ita tsaye yana cire mata alkabbar jikinta aiko kuka ta saki harda shashsheka Yarima dake kallon ta yace "what "? Kasa mgn tai sai kokarin tsayar da kukan da take gira ya dage yana mata wani irin kallo dake mugun firgita ta cikin wani irin yanayi yace "kar ki damu da mgnr Hajiya indai kika biye ma wannan tsohuwar ba zaki abin arziki ba ki kwantar da hankalinki babu wanda zaiga first night din mu sai munbar kasar jeki dauro alwala zamuyi nafila"sakin ta yai yana fita daga dakin cikin sauri ta shiga toilet din har tayo alwalar ta fito bai dawo ba . Zama tai cikin minti biyu ya dawo tare da wata tsararriyar abayat mai kyau da gyalen ta ya bata ta saka yaja musu sallah cikin nutsuwa da kyakkyawar addu'a mai shiga rai kafin ya mike yana cewa "kizo ga gado ki kwanta good night" ya haye abinsa yana jan bargo duk da haka kin tashi tai saida ta dade sannan ta mike tana cire abayar ta hau gadon kwanciya tai a bayan sa tana kallon gashin dake kwance jikin sa dan shi mutum ne mai ni'imar gashi dan taba kwanceccen gashin kansa tai ganin yadan motsa da sauri ta janye hannunta cikin fargaba juyowa yai yana murmushi yace "yada tashi kuma madam ina cikin bacci na "dan hade rai tai batai mgn ba shima hade nasa ran yai yana cewa "ni da kika tsokana ban hade miki rai ba saike to bari kiga wani abu"wutar dakin ya kashe yana matso da ita kusa dashi. Abin yayi kyau yaukan na gama typing see you next time. Taku har kullum *Mrs Al'ameen Ahmed * [11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: 👑Yarima Abdul-malik 👑 💫ANNURI WRITING ASSOCIATION 💫 Dedicated to Zarah Musa Safiyya Aliyu #YUSRAHMS ABUBAKAR ANNURI WRITING ASSOCIATION i know everything about you is so good but one things is wrong that you are not mind wannan haka yake ana matukar tare. *Page 7 Kamar zatai kuka cikin rawar murya tace "dan Allah kayi hakuri "kara hade rai yayi yana kallonta yace "me yasa baza ki gane ba nima banyi niyya ba kinajin abinda Hajiya tace bazan bar masarautar nan ba harsai na ajiye musu saidar kimar ki kiyi tunanin abinda kowa zaiyi zato idan muka tafi a haka bazasu taba yarda da mu ba kuma kinsan kina da makiya a gidan nan sun nuna miki kansu basai na fada miki suba kamata yai ki bani hadin kai kuma ki basu mmk"kai ta girgiza cikin tashin hankali tace a'a dan Allah karkayi "kallon mmk ya mata yana cewa "nikam ina son na bar nan kodan aikina amma tunda kin kasa fahimta ta shikenan" fincike rigar baccinta yai dama bamai hannu bace wasu yan zararruka ne suka rike ta ihu ta fasa tana tura shi zata tashi ya rike ta tamau ya hada bakin su yana bata kyakkyawan kiss wanda ya kusan sheke mata numfashinta gabadaya a cikin yan mintuna da basu da yawa ya gama burkita mata tunanin ta bata iya gane komai kawai ni'ima ce taji tana shigarta wacce baza iya gane meke faruwa ba lokaci guda a firgice taso kwacewa amma ko kadan bata samu dama ba kuka ta fara tana rokon sa akan ya bari ko sauraronta baiyi ba gyara ta yai yadda bazai cutar da ita ba ya soma shigarta wacce ba shiri ta saki wani gigitaccen ihu jin kamar zata mutu kara sakin ihun tai kamar muryar ta zai fashe tana kuka da kiran mama nikam bari na koma waje duk da naga yan annuri sun cika kofar bedroom din suna leke wasu ta window babu abinda zaku gani kawai ku hakura. Bayan wani lokaci yarima ya fito daga wanka ya shirya cikin kayan bacci kamar yadda ya saba gadon ya koma yana taba ta jin batai motsi ba yasa ya kunna fitila yana kai duban sa inda take kwance ganin ta suma yasa ya dauke ta yana shiga toilet da ita kukan tane kadai ke tashi zuwa can suka fito tunani ya fara taya zaije part din mama ya dauko mata kayan bacci ganin ba dama yasa suka kwanta a haka. Da asuba ma saida ya kuma gasa mata jiki wannan karon kasa kukan ma tayi dan azaba doguwar riga mai hade da mayafi ya dauko mata tun daga saudia ya sayo ta shekaru biyar da suka wuce kuma yayi alkawari matar daya aura da ita zatai sallar asubar daren farkon su tana zaune akan abin sallah bayan ya tafi masallaci bata iyayin sallar ba sai a zaune gashi so take ta koma bacci tsoro ya hana ta dan so take ta koma gurin mama tace ta fasa auren bazata bishi ba. Lokacin daya shiga gun su mai martaba a sama sama ya gaisa dasu yabar palon wanda hakan dayai ya tabbatarwa kowa ya angonce musamman Yaha da taji tamkar hawayen ta su fara zuba a gurin sam bata so Yarima yai doguwar rayuwar dazai hayayyafa son mai martaba zai koma kan yayansa wanda baza taso hakan ba so take Mahmud ya zama shi kadai suke kallo amma tana ganin kamar hakan bazai samu ba. Mama na part din ta tasa aje a taho mata da Zainab kamar yadda ta basu umarni haka suka taho da ita sun rirrike ta da kyar take daga kafa duk inda suka gifta bayi ne ke zubewa suna gaisuwa har suka iso gun mama murmushi mama tai tana kallonta tace "sannu kinji dota Allah ya miki albarka ya baku zuri'a ta gari sunkuyar da kai Zainab tai hawaye na sauko mata so take tacewa mama ta fasa auren amma ta kasa mgn kyakkyawan gyara mama tasa akai mata wanda saida taji gara na Yariman ma yafi sauki akan nasu bayan sun gama shirya ta gurin mama suka dawo da ita suna fita a palon a gaba mama ta sata sai taci abinci idan ta gama ga hadin magunguna nan ta sha dakyar take cusawa har lokacin jikinta rawa yake suna haka Yarima ya shigo bako kunya ya zauna kusa da mama yana kwantar da kansa a jikinta yace "fatan kin tashi lfy momyna "dago shi mama tai tana murmushi tace "lfy na tashi babyna fatan kaci abinci "? Bata fuska yai jin abinda maman tace ganin haka yasa taci gaba da cewa "daman na sani ga abinci wanne kake son ci "shiru yai dan haka tadau spoon tana debowa tace "amsa mana babyna "kalar tausayi ya koma yana kallonta a shagwabe kai mama ta girgiza dan saidai tamai abinda ta saba dura Zainab abin har daure mata kai yake tunda tazo gidan nan bata taba ganin yaci abinci dan kanshi ba saidai a masa dura mikewa yai bayan mama ta gama bashi ya shiga bedroom din ta jin kamar zaiyi amai itama tashi tai tana cewa Zainab "dota kema kici abincin nan idan ba haka ba zan miki dura kamar yadda naiwa baby bari in dawo "fita tai Zainab na zaune Yarima ya fito yana kallonta yace "wai ke baki iya gaisuwa ba ko nayi miki laifi ne yau din "? Dagowa Zainab tai ganin idonsa a kanta yasa tai saurin dauke kai tana mikewa tai hanyar bedroom din ta da kallo ya bita kamar zaiyi dariya sai kuma yace "dan gurgu dawo ki zauna ni tafiya zanyi idan kunya ta kike ji "rabuwa dashi tai ta shige ciki shi kuma ya mike yana fita a part din. Kyauta mai matukar girma Zainab ta samu a gurin familyn gidan dan Yaha ma dole saida ta bada sarkar da ta ajiye sbd auren Hajara kamar ta kurma ihu lokacin data mikawa jakadiya ranar kusan kasa bacci tai kuka kam dama tayi shi tunda aka fice da sarkar daga part dinta sarka ce ta lu'u lu'u kowa yayi mmkn wannan kyauta ta Yahanasu da hajiya na sa mata albarka kuka ta kama sbd bakin ciki amma sai tace dadin addu'ar hajiyan ce ta sata kuka. Cikin kwana biyun daya rage su tafi ba karamin gyara tasha ba har mmk take idan taga yadda mama ke kula da ita batai tunanin zata sake samun irin wannan gatan ba tun bayan rasuwar mahaifanta dan abbanta mutum ne wanda ya iya soyayyar yaron sa ya kuma bashi tarbiyya ta shikimammiyar hanya shi yasa ta tashi da nutsuwar ta Umar mutum ne wanda yasan abinda yake ba hayaniya a rayuwarsa. Ana gobe zasu tafi mama na part dinta suna zaune tana mata nasiha Yarima ya kira mama a waya bayan ta daga yace "am mama ina son paper da biro "da mmk mama tace "me zakai dasu kuma wa zanbawa ya kawo maka"? Dan kasa yai da murya yace "please ki bawa dotar ki ta kawo min dan Allah ina jira "mama dake kallon Zainab data zaro ido tace "baby mgn muke da ita zan turo wani ya kawo maka ko kazo da kanka ka karba"cikin shagwaba yace "haba mah dina yanzu zata dawo tana kawo min kinsan bansan koda wanne lokaci a rika shigowa inda nake dan Allah ki bari ta kawo min"ok dota je ki kaiwa baby paper da biro ki dawo yanzu sai mu karasa maganar "murmushi yai lokacin da mama tace haka kafin ya kashe kiran mikewa Zainab tai jikin ta na rawa tasa hijab ta fita dare ne amma kamar rana sbd hasken fitilun daya haska ko'ina a masarautar bayi ne keta ayyukansu wasu na zaune suna dan hira dai dai zata shiga part din taji anja hijab dinta da sauri ta juyo dan dama a tsorace take cikin mmk take kallon Hajara data rike mata kamar tana da gadon sa tun batai mgn ba taji Hajaran tace ke yar tsuntuwa uban me zaki a wannan part din idan bakin saba da karuwanci ba ko kunya bakiji ba ki sato jiki ki taho yawon kwartanci anyi asara dai kodan ba laifinki bane laifin wadancan bakaken munafikan naki da suke goya miki baya duk zanci uwar________bata iya karasawa ba jin wani irin gigitaccen Mari ya sauka akan fuskarta cikin fushi Zainab ta soma mgn"me kike daukar kanki an fada miki kowa sa'an rainin kine? duk abinda kika taka na fiki ki sani kinyi tsararo baki kai ba naji ni ba jinin sarauta bace amma inason kisan cewa ko ke da kika kasance jinin sarautar a yanzu aka jera tsakanin ni da ke kinsan wa yafi dacewa da wannan sunan idan har bakya kallon fuskar ki a mudubi gobe ki fara dan ko kadan bakya kama da jinin sarauta kinfi kama da jinin farauta ina miki gargadi daf da duka ni yanzun ba sa'ar yinki bace na zarcewa tunanin ki idan kika kara tara ta da irin wannan banzar mgnr jikin ki ne zai fada miki kuma bamai daukar mataki a kaina na daki banza juyawa tai tana kallon mahmud daya zuba musu ido tace "yaya Mahmud kai ya kamata ka fada mata wacce ni idan bata sani ba tunda bakuwa ce "dariya ce ta kama Mahmud ganin yadda Hajara kebin Zainab da kallo yace "mantawa nai amma yanzu ai ta gane wace ke "mai da kallo sa yayi gurin Hajara yana cewa "madam kinga sakamakon tauri kai sai kizo mu wuce dan ba iya rama marin ki zaki ba "wata ashar Hajara ta sakar masa tana kara shan gaban Zainab tace "ke ai ban gama dake ba gidan uban wa zaki saina tattaka ki a gurin nan yadda gaba idan kin hangoni zaki sauya hanya da wuri "wani irin kallo Zainab ke mata batare data sake magana ba ta janye ta gefe tana wucewa karo tai da mutum da sauri tai baya dan batai tunanin Yarima bane saida taji ya dauke ta tagane dan ba mai wannan ikon idan bashi ba bude kofa yai ya shiga tare da rufowa wanda yasa Hajara fasa ihu tana dukan Mahmud dan shi ta fito rakawa wani gun da tasan zata ga wannan abin da bata fito ba ganin yadda bayi suke kallon ta yasa ta daina dukan Mahmud ta soma dankara musu zagi ba arziki suka baje wasu na dry wasu na Allah ya kara. Hajara suna komawa part din Yaha ta kama kuka cikin tashin hankali Yaha tace "menene me akai miki "? Cikin kuka Hajaran tace "ba Mahmud bane yace na raka shi shine muka hadu da Zainab a gabansa ta mareni amma sai ya kamai mun dariya wai maganin tsokana ta "bacin raine karara a fuskar Yaha tace "ta mare ki lallai ta mari ajalinta kai kuma dan ubanka mara kishin zuci a gaban ka wata banza mara asali ta mari yar uwarka amma sbd matacciyar zuciya baka tattaka taba kayi koli koli da ita shashasha baka da wani amfani "wucewa Mahmud yai zuwa part din shi yana cewa "akan me zan daki yar mutane tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa yake duka wallahi nan gaba ko cewa kikai Hajara ga Zainab zoki mata duka to saidai ita Hajaran taki taci duka nima fa wani san inason gaskiya banga laifin taba data mareta itan kinji irin maganganun data rika fadawa zainab din itama ta rama tace batai kama da jinin sarauta tafi kama da jinin farauta kuma kalli Hajaran ki gani sai kace 'yar gidan masu kiwon karnuka "ya karasa maganar yana dry cikin hangulowa Yaha tace uban ta ne yake kama da jinin farauta shegiya tsintacciyar kan hanya kawai mara asali wa ya sani ma ko shegiya ce tazo ta samu guri tayiwa mutane karya san ranta kila ma bata da iyaye yar karuwa ce ". Uhm Yaha kenan manya maganin karagar kasa. Yarima kam suna shiga ya dire ta akan gado yana mika mata hannu alamar ta bashi paper cikin sauri ta mika masa duk ta kadandane sbd daukan ta dayai ta matse ta a hannunta dagowa yai yana kallonta yace "aikin lalata pepan bazai rubutu ba, wai dama kin iya fada haka ashe dage na aura ba sani ba shikenan na huta zaki iyayin fada da makiyanki yanzu zaki koma ki kawo min wata pepan ne "? Shiru tai fin minti biyar taki mgn rabuwa da ita yayi ya dauko sabon littafi ya yagi pepan ya fara rubutu zaro ido Zainab tai me hakan ke nufi dama yana da littafi ma dan yasa ta wahala ne saida ya gama rubutun sa tsaf sannan ya linke pepar yana ajiyewa ya juyo inda take zaune yace "me kike jira ko anan zaki kwana na kira mama na sanar da ita kince zaku hadu da safe "? Cikin sauri ta girgiza kai tana sauka a gadon tare ta yai batare dayai mgn ba ya cire hijab din dake jikin ta jan hannunta yayi suka koma bakin gadon yace "dama ba peper zaki kawo min ba kwana kawai zaki taya ni tsoro nakeji "duk da tashin hankalin da take ciki saida ta dago tana masa kallon mmkn da shima yaga hakan gira ya dage yana mata kallon so what dan marairaicewa tai kamar zatai kuka kuma ta kasa mgn tana ji tana gani ya daga waya ya kira mama yace tsoro yake ji Zainab zata taya shi kwana mama har kwarewa tai sbd mmk dakyar tace saida safe saboda kwaruwar datai murmushi yai bai sake bi tan hawayen da take ba ya dauke ta suka hau gadon yana kashe fitilan dakin. Saida safe zeey tsiyata da sabon shiga kenan barawo da sallama wai shishshigi malami da rabon giya. Washe gari tunda Zainab ta koma part din mama ta kasa hada ido da ita mama yi tai kamar batasan me take ba taci gaba da hada mata kayanta sai bayan sallar la'asar suka bar masarautar bayan sunsha dunbin addu'o'i a gurin su mai martaba mama dai jitai kamar sun tafi da ranta saboda kewa. Sautin kukan Hajara ne kadai ke tashi a bedroom din Yahanasu cikin kuka take cewa "wallahi umma bazan yarda ba nima na fasa karatun auren nake so ni Abdul-malik nake so wacce bata da asali ma ta same shi balle ni jinin sarauta gaba da baya dan Allah kije ki samu mai martaba nima a daura nawa na bisu London din "cikin lallashi Yaha tace "kinga Hajara ki kwantar da hankalin ki wata hudu tamkar kwana hudu ne aure kuma zaki aure shi dan Zainab ba matar sa bace kashe ta zamuyi ke kadai zaki zauna baki da kishiya amma saikin nutsu "kara volume din kukan ta tayi "ni wallahi bazan yarda ba kije kawai kuyi mgn da su mai martaba "cikin bacin rai Yaha ta mike tana cewa "dan ubanki bazan jeba kije da kanki tunda ban isa na fada miki ba bakyajin shawara sai kije ki karata ko ki kashe kanki aishi gaba takai shi dama bason aurenki yake ba ranar juma'ar nan akanki tun daka part dinsa yake jana tamkar ya sayo sabuwar akuya a kasuwa har gaban mai martaba yamin rashin mutumci saida naji kamar na hadiyi zuciya na mutu dan bakin ciki idan kika kuma yimin mgnr sa indai ba dawowa yai ba saikin tattara kayan ki kin koma gida "tana fadin haka tai hanyar fita a bedroom din cikin kunkuni Hajara tace "wallahi ba wanda ya isa ya sani nabar masarautar nan a yanzu ko mai martaba ne saidai in na auri Abdul-malik "juyowa Yaha tai tana kallonta tace "zaki ci ubanki shegiya duk kin bata fuskar ki da mai"da harara Hajara ta bita tana cewa "wa yace idan ban shafa man nayi fari ba yarima ko kallo ban ishe shi ba "? Banza Yaha ta mata ta fice tsaki Hajara tai tana goge hawayen fuskar ta ta gyara kwanciya tana cewa "ba hakura nai ba dakai Abdul-malik saina aure ka. Aiki gamai yinka mukan yan kallo ne. Su Yarima basu sauka ba sai cikin dare dagowa yai da niyyar yiwa Zainab mgn yaga ashe ita bacci ma take abinta cire mata bel din yayi ya dauke ta a haka yake saukowa daga matakalar jirgin sosai aka zo tarar sa abokai da mutanen arziki babu bata lokaci suka wuce bayan ya shiga mota har gida sukai masa rakiya yakai Zainab daki yazo suka gaggaisa kafin ya musu saida safe ya koma wanka yai ya dauro alwala yayi sallar isha da ake binsa yasa kayan bacci ya kwanta. Koda asuba ya riga ta tashi sai da yai alwala sannan ya tashe ta zaune ta mike bata lura da yanayin jikin ta ba sai data sauka a gadon zaro ido tai tana kallon shi batare daya kalle ta ba yace "kije kiyi alwala ki rama sallar da ake binki kar lokaci ya kure "waje ya fita zuwa masallaci ita kuma ta dauro alwala ta sa kaya ta fara gabatar da sallah ta kuma yiwa Allah godiya da sauyin rayuwar dayai mata bacci ta koma bayan sallar asuba kafin gari ya waye, karfe 10amta tashi tai wanka saida gama komai taje saka kaya taga babu wanda mama ta sako mata ko daya dubawa ta farayi ganin ba wanda yai mata yasa ta zauna shiru a gaban akwatin har ya tashi a nasa baccin yai wanka ya shirya cikin kayan soja ya gama komai tana zaune dan kallonta yai yana kallon akwatin yace "sauri ki shiya ke nake jira ina da meeting kada ki bata min lokaci "kamar zatai kuka tace kayan babu wanda zansa wannan kuma na arna ne "ba shiri ya dago yana kallonta kayan ya fara dubawa yana cewa "daga yau sune kayan sawar ki atamfa ko lace kin baro su a Nigeria "ya karasa maganar yana dauko wata bakar doguwar riga yace "sa wannan mu gani ko na arnan ne "turo baki tai "wallahi ni bazan iya sa wannan kayan ba "jin abinda tace yasa ya mike tsaye yana takawa inda take da sauri ta jada baya kanta farga yasa hannu ya jawota ta fado jikin sa daure fuska yai yace "yaushe na fara wasa dake "? Tsoro ne ya kamata ta soma bashi hakuri shareta yai yana sa mata rigar da yake fara ce sai bakar rigar ta mata mugun kyau sosai rigar ta nuna shape dinta saidai itama tsaga tun daga cinya har kasa kuma ta gaba ma kusan rabin kirjinta a waje ta baya ma kusan rabin bayan ta a waje tsayawa yai yana kare mata kallo cikin sauri tai niyyar juya masa baya ya rike hannuwanta yaci gaba da kare mata kallo runtse ido tai cikin kunya ganin ta rufe ido yasa yace "bude idonki "kara kullewa tai da yake a gaban mirror suke saiya juyar da ita yana zagaya hannunsa a cikin ta yace "baki jiba "? Kin budewa tai amma jin ya daura hannunsa a saman kirjinta yasa cikin sauri ta bude ta mudubin suka hada ido ganin har lokacin kallonta yake sai kawai ta sunkuyar da kanta jan hannunta yai suka sauka stairs yace "ke bakya jin mgn ko? zanyi maganin ki ne bari dare yayi"batai magana ba har suka sauko dinning shake da kayan abinci kala Kala zama sukai Zainab kam Yarima ta zubawa ido taga yau daba mama daya zaici abinci ga mmkn ta mint tea ya hada a mini cup yana sha ganin ta kure shi da kallo yasa ya daga mata gira alamar tambaya kai ta girgiza tana ci gaba dacin abincin ta saida suka hada ya mike ya wanke bakin sa yana fita a gida Zainab daki ta koma suna waya da mama tambayar ta mama tai yaya jikin ta da sauri ta kashe kiran tana rufe ido kamar maman na gurin . Da dare hartai bacci bai dawo ba sai da safe ta ganshi ko takwas batai ba yasa ta shiya suka tafi wani kayattaccen guri ga mmkn ta makaranta ce bata sake tsinkewa ba da Yarima yace zata dora karatun ta saida taga ya fito da takardun makarantar ta abin yai mugun bata mamaki bata tambaye shi ba saida suka dawo gida ta kalleshi tace cewa "a ina ka samu takardun makaranta na dady ya tambaye amma nace masa sun fadi "dan kallon ta yai "au dama kina mgn ai na dauka kurma na aura "rufe fuska tai tana dariya yace "lokacin dana bige ki a mota naga jakan ga sauran abubuwan ciki" mika mata yai ta karba tana kallon photon ummanta wanda lokaci guda ta shiga yanayi shima ya fahimci damuwar da take ciki dan haka ya dau abarsa sukai daki ya matar da ita duk abinda ke damun ta. Hayaniya inna dake daki ta jiyo da sauri ta fito duk zaton ta koda Zainab ne dan yau ta dawo daga garin su shigowar ta kenan ko hutawa batai ba da sauri ta karaso ganin Bashir ya shakewa Bilki wuya cikin tashin hankali inna tace "dan Allah Bashari sake ta bari kada kai kisan kai "sakinta Bashir yai yana huci yace "wallahi kinci darajar wannan tsohuwar da yau saidai ki kwanan lahira "mmk ne ya kama inna amma batai magana ba dan sunfi kusa juyawa tai zata bar gurin da sauri Bilki ta rike ta tana kuka tace "dan Allah inna kimin rai ki hana bashir zuwa gidan nan wallahi zai kashe ni "wani kallo inna ke binta dashi domin a iya sanin ta tun kafin tazo bashir ke zuwa gidan nan amma yau rana tsaka take neman a hana shi zuwa lallai akwai mgn Bashir da tun dazu yake kallon Bilki sai yanzun ya mayar da kallonsa gun inna yana cewa "danfa inajin kunyar kine na kyale ta amma yau da sai naga ta daina motsi dana barta dan ta raina min hankali shekara ta nawa tana cin kudina amma danta kori Zainab shine zatai min halin yan duniya, duk abinda kikeji dashi na fiki iskancin da barikin sai na ga iya kwarewar ki "ya kasara mgnr yana kai mata naushi da sauri ta koma bayan inna wacce taji maganar kamar saukar aradu wai Bilki ta kori Zainab juyawa tai tace "da gaske Bilki kin kori yarinyar nan? wai me tamiki haka a rayuwa da bakya kaunar ta da alkairi yanzu kinsan a wanne hali take ko abinda ya sameta gaskiya ke butulu ce da Umar yasan zaki wulakanta bayan sa daya fadawa yarinyar nan asalin sa ko bayan ransa taje ta same su hakkin Zainab bazai taba barinki ba har kabarin ki da nasan abinda kika aikata kenan bazan fito ba inya so Basharin ya kashe ki ni wannan gara na sauya gidan haya dan idan naci gaba da zama anan wata rana harni za'a kashe a kakalo masifarki "tana kaiwa nan ta wuce tana takaicin yanzu ina Zainab din take a wanne yanayi take ganin Bilki ta biyo ta yasa ta karasa daki da sauri tana rufo kofa cikin bacin rai kuka Bilki keyi Bashir kuma yai fitar sa a gidan kallon Hindu dake kwance ga ciki ya fara fita tai sai kawai ta durkusa tana kuka yanzu me zata cewa iyayen yarinyar nan, nikam nace oho. Fati ce kwance a daki duk ta rame saboda damuwar batan Zainab hjy Asma'u ta shigo tana cewa "Fatima dan Allah ki hakuri haka ki dau dangana ya zamuyi da kaddara ta riga fata tun farko saida nacewa baba Abdullahi ya bani Zainab nai rainonta amma yace aa bai kamata a karbe ta daga hannun Bilkisu ba gashi yanzu abinda ya biyo baya kinga kiyi hakuri in Allah ya yarda za'a ganta tashi kici abinci "mikewa zaune tai tana karban plate din kwata kwata bata so haka ba sai lokacin farin cikin su za'a tarwatsa musu rayuwa. Masha Allah bintu Musa Abubakar ta gama typing yau cikin yardar ubangiji sai Allah ya tashe mu lafiya gobe zamu ci gaba. *Mrs Al'ameen Ahmed ce * [11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: Typing 📲 👑Yarima Abdul-malik 👑 💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫 #Mrs Al'ameen Ahmed ce *Allah dakai ne nina dogara, kaine kake min dukka sutura, duka halitta kai take jira, ya mai sifar girma da gagara. 🅿️8️⃣ An gama komai na mgnr auren Abba da Salmah jikar sarkin bauchi ba wanda ya sani a cikin Yaha da mama saida biki ya rage kwana goma suka ji mai martaba na zancen kai akwatuna da za'ai wai Yaha kam ba kunya a gaban mai martaba taci kwalar Abba tana kururuwa da kuka tana faduwa kasa dan Allah mai martaba ya hana Abba karya mata kishiya kukan ta saida ya firgita kowa amma ido da ido Abba yace babu abinda dazai hana shi yin wannan auren sai mutuwa lokacin daya fadi haka ihu Yaha tai ta yanki jiki ta fadi a sume sai asibiti aka kaita. Kishi kumallon mu inji masu magana. Yarima na palor suna waya da Mustapha Musty yake ce masa "Abdul-malik idan na gama abinda nake inason zan biyo tanan na kawo muku ziyara naga matar ka mu gaisa"Yarima dake kallon Zainab data dago itama tana kallon shi ya maida hankalin sa kan wayar da yake yana cewa "no thank basai kazo ba ba bukatar ku hadu yanzu ka bari sai lokaci yayi idan kuma kai asarar kudin ka kazo to zan hana abarka ka shigo gidan kaga kazo a banza gara ka wuce Nigeria daga nan zaku hadu wata rana "cikin haushi Musty yace "wai dan Allah Abdul-malik me yasa kake min haka? kasan Allah idan muka hadu saina shuka ma rashin mutunci sbd bakin ciki matar taka ma baka so na gani saika dafa ta ka cinye "murmushi Yarima yayi yana matso da Zainab kusa da shi yace "saika shuka rashin mutuncin naka yanzu kaga kafin mu hadu ya girma, cinyewa kuma bazan cinye ta ba amma bari na mata abinda da zakaji "kiss ya sakar mata kumatun dama da hagu wanda yasa Musty kashe kiran yana dariya yace "Allah Abdul-malik baida kunya ko kadan. Kallonsa Zainab tayi tana "dawa kake waya "? rungumeta yayi yana cewa "da wani uncle dina ne yake damu na ya cika takura kamar gidan haya "dan matsawa baya Zainab tayi ganin mai musu aiki ta fito a kitchen tace "ga siana ta fito ka sake ni "dagowa yayi yana kallonta yace "mene ruwan ta damu ke kike naki yi bahaushiya kawai"dukawa siana tai tana gaida su ba kunya saida Yarima yai kissing bakin Zainab sannan ya amsa wanda saida Zainab taji tamkar ta nutse a kasa babu ruwansa sau tari Siana na palon sai yaita zuba soyayyar sa cikin shagwaba Zainab tace "dan Allah ka bari wannan ai saita raina ni"kallonta yayi yana murmushi ya maimaita kalmar saita raina ni lallai Zainab akwai son girma siana a kalla zatai 27 years take kiran zata raina ta ita mai 20 mikewa yai yana daukar ta yace "haka ne zata raina ki anan muje inda bazata gani ba na baki wani abu mai kyau "ya fada yana wucewa da ita. Duk tunanin Yaha idan Abba yaga wannan kukan datai da ramewa zai janye mgnr auren sa amma sai taga yaci gaba da hidimar sa ko a silifas dinshi wanda hakan ba karamin daga mata hankali yayi ba ko akwatuna dayai mata cewa tai bata so yakai wacce take bukata ba tare daya nuna damuwa akan abinda tace ba ya hade su da wanda za'a kai bauchi Yaha tayi kukan bakin ciki harta godewa Allah amma Abba yai kamar baisan me take ba dan ya gaji da halin ta gara ya auro wacce tasan abinda takeyi duk da kasantuwar ta yarinya dan Salmah bazata wuce 25 ba sai kyau da diri. Hhhh Abba banga laifin ka ba yan ANNURI shoki zamu diba ranar daurin aure. Yaha na zaune duk abin duniya ya dame ta gashi Hajara ta fara gagarar ta bata isa da ita ba duk wannan ma bashi bane abin daya fi mugun daga mata hankali yau ake daurin auren Abba gida tab yake da baki Yarima shima yazo amma banda Zainab acan ya barta. Cikin harara yaha kebin dangin Salmah da suke kai kawo a part din da Salman zata zauna zuwa part Abba ji take kamar ta kunna wuta kowa ya kone ayi mutuwar kasko jin gidan ya kacame da algaita da kirari yasa jiki na rawa Yaha tasa hijab ta fita turus tai ganin an bude mota amarya ta fito a lullube ihu ta zunduma tana kuka ta juya part dinta da gudu shewa wasu daga cikin yan kawo amarya sukai suna cewa "lallai aiki ga mai yinka kishaya dai tazo kuma baza a mayar ta ba dan Salmah ita da Ibrahim mutu ka raba haka zaki ganta haka zaki barta dan tafi karfinki gaba da baya "yaha na shiga bedroom dinta taga Hajara na rawa Mahmud na mata liki da kayan anko a jikin sa hannu ta daga ta wanka mai mari tare da daukar wayar tasa daya kunna wakar ta buga ta a jikin bango ganin bata fashe ba taci gaba da dokawa saida screen din wayar yai damage sannan ta cillar da ita cikin masifa tace "so kuke ku kashe ni dame zanji daku koda wadancan tsinannun masu kama da aljanu zaku cika min kunne mitsiyatan yara "tabe baki Hajara tai tana cewa "umma meyai zafi bafa mune muka karo miki kishiya ba mijin ki ne aishi zakije kiwa ba mu yan gayyar sodi ba "kanta Yaha tai tana cewa "dan ubanki ni kike fadawa mgn mitsiyaciya "ganin ta nufo ta aguje ta fita daga dakin tana dariya sannan ta leko tace "umma baki sun shigo da amarya suna jiran ki a palor zasu baki amanar ta ki rika mata wanki da guga kina dafa mata abinci da sharar part dinta "ashar Yaha ta sakar mata daidai Mahmud zai fita tasha gaban sa ganin ya dauka mata ATM tace "gidan ubanwa zaka kaimin atm "? kallonta yai yana cewa "haba umma kiji wata tambaya ki fasa min waya kuma ki tambayi me zanyi da atm dinki kudin wayata zan cira na sayo wata million daya ne da dubu dari biyu ba yawa karamar kika fasa min bani code din zan tafi "banza tayi dashi ta gefen ta ya wuce yana cewa "ok na manta ashe last moon na ciro miki kudi a account naki code din 1834 ne ni na wuce "fita yai yabar Yaha ta rasa inda zata dura kanta. Wayyo abin tausayi 😔abin dariya 😂. Bayan wata hudu da auren Abba komai ya fara sauki ba kamar da ba. Yarima na zaune suna video call da mama Zainab ta fito tana saukowa daga stairs da mini riga a jikinta dan yanzu inba kananun kaya tasa ba ita ma bata jin dadi purple din din riga ce ta matse ta sosai tayi kyau ta kara kiba da haske cup ta dauka tana hada kyakkyawar madara ta zauna a dinning tana sha. Yarima dakewa mama murmushi ya dago yana kallonta da hannu ya mata alama tazo mikewa tai tana zuwa inda yake jawota yayi yana zaunar da ita akan kafar shi yace "mama ga dotar taki da kike nema yanzu ta tashi a bacci sai ki tambaye ta basai na zama jakada ba "zaro ido Zainab tai dan ita batai tunanin waya yake ba ga mama free tana kallonta da sauri ta mike ya maida ita yana cewa "mgn fa zakuyi ina zaki kuma "? kasa daga ido Zainab tai ta kalli mama sbd kunya mama kuwa cike da wani irin mamakin dayasa taji kanta na juyawa take kallon Zainab tana cewa "baby wai dama dota ciki ne da ita amma baka fada min ba"? dan kallon Zainab yayi yana cewa mama "sorry mom dinna mantawa nai "cikin farin ciki mama tace "to mezai hana ka dawo da ita nan idan ta haihu saita dawo tunda yanzun nan ammi ta kira ni take cemin an tsayar da ranar auren Mustapha kaga gara ta haihu a gabana"bata fuska Yarima yai jin abinda mama tace cikin shagwaba yace "a'a dan Allah mama abar zuwan nan lokacin dawowar mu Nigeria baiyi ba anan din ma za'a kula da ita "mama da tun dazu Zainab take kallo mmkn ta ya kasa karewa ganin cikin ma yayi wayo sosai tace "to baby shikenan Allah ya sauke ta lf, amma zaka zo bikin Mustaphan ai"? dan shiru yai sai kuma yace "gaskiya bazan samu zuwa ina da aiyuka bayan haka banzan iya tahowa na barta ita kadai ba amma zan kira shi zamu yi mgn"to mama tace tana kallon Zainab da tunda suka fara mgn bata iya dagowa ba tace "dota kinki mgn ko yaushe ne haihuwan "? tashi Zainab tai da sauri tabar wurin dariya mama tai tana cewa "dan Allah baby ka kula min da yarinyar nan ina sonta sosai "insha Allahu yarima yace bayan sunyi sallama ya kira Musty suna waya yana bashi hakurin cewa bazai samu damar zuwa ba madam tayi nauyi dariya Musty yayi "naji to dan iska basai ka fada min tayi nauyi ba kawai kace bata da lfy malam kai baka iya fulatanci ba "yarima yace akan me zan iya bayan bashi bane ka taya ni da addu'ar Allah ya sauke ta lfy na samu kyakkyawar baby nai kama da ita "rike baki Musty yai "lallai prince ka wuce ma tunani na to Allah ya kawo yan biyu "ameen Yarima yace "kamin addu'a mai kyau ni inada son yara ko yan goma ne Allah ya kawo su dan haka sai anjima ka dame ni "dariya Musty yayi daidai zai kashe wayar yace "sannu uban yan sharri sai anjima nima gurin tawa abar kaunar zan tafi na tsaya kana bata min lokaci "sallama sukai. Yau anan zan tsaya ayi hakuri typing din baida yawa aiki zanyi ne. *Mrs Al'ameen Ahmed * Dukka muradi baya cika saiyai bara a gurin ka mai duka dakai makaskanci ya daukaka kaine kasa ka'aba a garin makka. Manzon Allah (s.a. w) a farkon bukata ta kaunar ka itace abinda na roka. #Yusrah Musa Abubakar. [11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲 *👑YARIMA ABDUL-MALIK*👑 *💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION*💫 WHATSAPP NO:+2349055273614 *#YUSRAHMS ABUBAKAR*# *🌹TAMBARIN 👉🏻YMA DUTSE*🌹 🅿️9️⃣ Zaune suke a gaban mai martaba kowa yana sauraron Yahanasu domin itace ta kawo korafi cikin muryar tausayi tace "ranka ya dade ni kuwa kuna jin labarin Yarima naga kowa ya manta da shi ba'a zancen sa kamar wanda yabar duniyar". Cikin bacin rai mama tace "da ace kowa ya manta dashi uwa bazata manta da danta ba balle dukkan mu muna waya dashi kuma yana halin lafiya Yahanasu ina son ki tsaya iya matsayin ki ba ruwan da maganar sa akan zai dawo ko bazai dawo ba kinga Yaha bana son shishshigi malami a wajen rabon giya shiru mama tayi dan ta manta ma ita a gaban mai martaba suke haushi ne ya kama ta. Yaha kuwa kallonta kawai take ta kasa mgn Abba da shima yaji haushin maganar Yahan yace "towai ke ina ruwan ki mene naki na tambayar anajin labarin sa"? Dan shiru tai kamar bazatai magana ba sai kuma tace "naji lokacin dazai tafi ance wata hudu zaiyi ya dawo amma gashi har mun shiga wata na goma da tafiyar sa gashi bansan ina mgnr Hajara ta kwana ba domin shi muke jira Yaya ma ya kira ni nace masa ya kusa dawowa kodan ba laifinsa bane tunda ya tafi da wacce ta fishi sanin gari idonta a tsaye yak____tsawa Abba ya daka mata zaikai mata bugu dady ya rike shi. Kokarin kwacewa yake cikin fushi yace"dan Allah ya ka barni wannan mara mutuncin bansan tsautsayin da yasa na aure ta Yahanasu sam bata dace dani ba yanzu sbd hassada wannan yarinyar zata kalla tace wai idonta a tsaye yake tana nufin ba yarinyar kwarai bace kenan"dady hakuri yake bawa Abba dan baya so abin yai nisa idan ya burkice bamai iya saita shi akan dadi. Mama kan farin ciki tayi dan ko ba komai Abba na hana Yaha aikata wasu abubuwan taso dady ya sake shi ya nuna mata abinda ta fada tayi karya ba haka bane. Salmah da tun dazu take kallon su dan batasan kowa ba tsakanin Yarima da Zainab sai labarin su da take ji tace"eh ya kamata a nuna mata kuskuren ta duk da banga yarinyar ba a iya zaman da mukai da Yahanasu nasan halin ta na kushe abin da bata ra'ayi na tabbata abinda ta fada akan ta ba gaskiya bane kuyi tunani tana so ya auri yar yayan ta ai bazata so matar saba idan ma ta sota saidai son fuska biyu dan Allah a duba dakyau kada a zargi yarinyar nan". Abba dake hararar Yaha yace "keda kikasan gaskiya kenan amma ita ai ba tsoron Allah take ba "dady yace Ibrahim kayi shiru haka a gaban mai martaba kuke fa kokun manta?ya kamata ku nutsu"dukkan su shiru sukai mai martaba da tun dazu yake binsu da kallo sai yanzu yai magana "to Ibrahim dina idan ka gama fadan saikai mana addu'a shedan din daya shigo ya fita" ya fada yana murmushi dariya sukai dan ko kadan mai martaba bai nuna bacin rai da abinda ya faru yanzu ba. Addu'a Abba yayi bayan an shafa mai martaba ya fara magana "to alhmdllh na fahimci inda Yahanasu ta dosa nufin ta lokaci yayi daya kamata ace Muhammad ya dawo anyi biki kamar yadda aka tsara na gamsu da wannan amma ban amince ba kar na sakejin an soki matar Muhammad domin yarinya ce mai tarbiyya. Hajiya ta dora da cewa "wallahi kam gaskiya yarinyar nan bata da gurin kushe nida a barshi da matar sa ma karya wani kara aure a takura masa. Mai martaba yace "a'a Aishatu mun riga mun karbi masa auren ta a gurin mahaifanta dan haka baza a fasa ba saidai idan ba matar sa bace. Abba zaiyi mgn dady yace "Ibrahim kaga kayi hakuri Allah ya zaba mana mafi alkari"duka suka ce amin mama da batai niyyar fada musu cewa Zainab nada ciki ba ta rike sirrin a zuciyarta so take a musu ba zata saidai kawai su ga sun dawo musu da baby amma yanzu ta yanke shawarar fada musu lokacin da kowa yaji labarin hamdala yake da farin ciki. Banda Yaha data mike tana fita a palon cike da kaduwa abinda take gudu ya faru idonta a rufe ta shiga part dinta a bedroom ta samu Hajara na kwalliya cikin barin rai ta kama watsi da kayan tana cewa "asararriya ni incan ina nema miki lafiya ke kina nan kina kwalliya gidan ubanwa zakije amma dai ba fita zaki ba "? . Rike kugu tai tana jijjiga tace "wai dan Allah umma ina ruwan ki da sabga tane? nifa na tsani sa ido aikin banz____bata karasa ba Yaha ta wanka mata mari cikin fusata tace "yanzun Hajara abin naki yakai ace ni Yahanasu kanwar ubanki zaki iya zagi na wallahi daga yau baki isa ki kara fita daga masarautar nan ba tunda an baku hutu har sai Abdul-malik ya dawo gidan ubanwa kike zuwa kullum a cikin garin? wa kika sani"?. Kuka Hajara ta fashe da shi tana fita daga bedroom din tace "na rantse da Allah baki isa ba sai naje duk inda nake so kuma sanda naga dama baki da ikon hana ni "cikin kunan rai Yaha ta bita da kallo ji take kamar ta kama ta tayi ta duka har sai ta daina motsi. Anyi bikin Mustapha lafiya an gama duk abinda akai saida Musty ya turawa Yarima ba yadda Zainab batai dashi ba akan ya bata tagani fur yaki domin yasan komai zai dame idan ta gani yana gama gani ya goge dan karta dauka baya nan ta gani. A London kan masha Allah zama suke cikin walwala ba karamin kyau sukai ba musamman Zainab da yanzu cikin ta ya tsufa suna zaune a palor doorbell yai kara mikewa Yarima yayi yana budewa wani soja ne cikin girmamawa ya masa rada juyawa Yarima yayi yana kallon Zainab da alaman damuwa a tattare dashi komawa yayi maimakon ya zauna sai yai upstairs mmk ne ya kama Zainab gashi ita yanzu tafiya wuya take mata balle ta bishi. Tana zaune can sai gashi yana saukowa da kayan sojoji a jikinsa yana gyara bindigar hannunsa mikewa Zainab tayi tana kallonsa da sabon mmk tace "ina zakaje"? shiru bai bata amsa ba har wata mace baturiya ta shigo Yarima ya mata bayyanin yana so ta zauna anan tare da Zainab kafin su dawo zasuje Russia kwana goma zasuyi. Amsa masa matar tayi da fara'a domin dama suna mutunci sosai dashi juyawa yayi suna fuskantar juna da Zainab ganin yadda hawaye yake zuba a idon ta yasa yaji tamkar ya fasa tafiyar yadau excuse baisan wanne kalar lallashi zai mata ba sai kawai ya juya cikin dakewar xuciya zai fice daga palon dan duk jarumtar mutum soyayya rauni take sashi. Sunan da Zainab bata taba kiransa dashi ba yau ta kira da karfi cikin kuka tace "Abdul-malik! "cak ya tsaya amma bai juyo ba ganin haka yasa Zainab ta karasa inda yake tana rungumeshi ta baya cikin kuka tace "dan Allah karka tafi ka barni"xuciyarsa babu dadi ya juyo da ita zuwa gaban shi yana goge mata hawayen yace"kiyi hakuri kwana goma ne ba dadewa zamuyi ba zan dawo gare ki in Allah ya yarda ki kwantar da hankalin ki kada babyna shima yaji momyn shi na kuka kinji"kaita daga masa shi kuma ya bude kofa yana fita ko waiwayen ta baiyi ba wani irin kuka ne ya kuma zuwa mata ta kifa kanta jikin kofar tana yi matsowa kusa da ita matar tayi tana bata hakuri da kwantar mata da hankali dakyar ta samu tayi shiru suka koma cikin palon. Yau masarauta cike take da murna domin Salmah nada juna biyu ba karamin farin ciki akai ba musamman Abba daya fidda rai da haihuwa. Zaune Salmah take a palonta sai ganin Yahanasu tai kamar an cillo ta da mmk Salmah ke kallon ta ita kuma wannan lfy jitai Yaha tace"ke tun wuri ki nemawa cikin nan ubanshi dan saidai indashi kika zo dama kina kama da masu yawon tambadanci. Mikewa Salmah tayi tana murmushi tazo har gaban Yahanasu tace"ke dallacan gafara gefe ke asuwa nasan duk abinda zaki fada ta haushi ta biyo ciki kuma ba ni nabawa kaina ba Allah ya bani idan kuma zaki ja da ikonsa ne to bismillah dan na fahimci ke bakar muguwar jahila ce ". Daga hannu Yaha tayi zata mareta Salmah ta rike hannun tana mata kallon baki isa ba tace"humm yau ga hauka dangi dangi ke harkin isa wannan kazamin hannun naki ya taba min fuska never in history wallahi daga yau kada ki kuskura ki kara marmarin taba ni idan kuma kin dauka wasa ne ki jarraba saina dumama miki jiki da duka"tana fadin haka ta ture ta gefe ta wuce. Da kallo Yaha ta bita ji take kamar ta fasa ihu dan takaici wannan yarinyar da bata fi sa'ar Mahmud ba idan takai ma amma har ita take bugawa warning zama tayi akan kujera tana kada kafa. Hajara dake kallon su tun dazu ta sheke da dariya tana nuna Yaha a kule Yahanasu tace "dan uwarki me kike ma dariya"? tsayawa da dariyar Hajara tayi tana cewa"gani nayi duk iya makircin ki da feleken ki da fallin ki ya kare gashi kishiyar ki har take fada miki mgn sbd ta mayar dake sakarya". Mikewa Yaha tayi a fusace tai kanta tana cewa "mitsiyaciya ni zaki cewa sakarya wallahi kika bari na kama ki saina fasa miki jiki". Da gudu Hajara ta fice tana dariya tace "kaji min umma da wani cin zali mai zazzabi daban mai shan magani daban nasan kishiyar ki kike son fadawa wadannan maganganun bazaki iya ba sbd kina tsoron duka shine kika fake da guzuma kike zakin karsana wallahi babu abinda kika isa kimin". Abu kamar wasa yau Yarima kwanan su 21 da tafiya amma babu alamar su gashi kotayi kiransa a waya saidai taji a kashe gabadaya tasa damuwa a ranta bata ko iya sakewa taci abinci. Zaune take misalin karfe 1pm na dare ta kasa bacci tunani ya hana ta sakat waya ta daga da niyyar ta gwada kiransa ko zatai sa'a ta shiga batasan lokacin data cillar da wayar ba ta saki wata kara tana kiran aunty Feshen. Buturiyar dake dakin kusa da ita jin kalar kiran da take mata yasa tasan ba lafiya ba da sauri ta shigo dakin ganin halin da Zainab din ke ciki kuma dama Yarima ya mata bayani cewa koda bata da fly ga number wayar asibiti ta kira cikin gaggawa ta koma dakinta tana kiran number daya bata cewa suzo Zainab ba lafiya. Dawowa tayi gurin Zainab dake ta murkususu a kasa jin doorbell yayi kara yasa ta tashi da sauri ta fita taje ta bude musu. Cikin gaggawa suke hawa stairs din tunda suka fara hawa suke jin kukan baby da alama ta haihu suna shiga suka ga katon baby boy fatsi tar dashi sai kuka yake ita ma kuma tana cikin mawuyacin hali. A rikice suka daga ta suna shiga toilet da ita Feshen kuma taji da yaron komai cikin sauri sauri suke yinsa bayan sun gyara ta suka fito da ita suka wuce asibiti bayan Feshen ta gama shirya yaron cikin kyawawan kaya. Ayyuririiiiii mun samu baby boy yan Annuri ku shirya zuwa London ya same ku zamu sha shagali👻. Kwanan ta biyu a asibiti suka dawo gida kuma jikin ta alhmdllh yayi ragal tayi tafiya, madara mai kama da nono ko dan basai nace babyn yai kama da Yarima ba dama hausawa sunce kyan da ya gaji uban sa to nan ma haka ne. Zainab na zaune tana kallon babynta cikin farin ciki taji kamshin turaren da ko tana kabari yakai mata ziyara zata shaida da sauri ta dago dan tabbatar da abinda taji gaskiya ne. Yarima ne tsaye bakin kofar bedroom din ya zuba mata ido yana murmushi mai burgewa mikewa tayi cikin farin cikin ganin sa taje ta rungumeshi saurin dago da ita yai yana kallonta yace "ina cikin"? dariya ta saki tana nuna masa gadon kallon sa yakai inda take nuna masa aikam sai ya sake bude ido akan babyn yana karasawa ya dauke shi cikin nuna tsantsan murna ya kalleta yana cewa "thank u my wife na gode kinmin komai Allah ya barmu tare "amin Zainab tace tana zama kusa dashi Yarima dake kallon babyn yace"beautiful like diamond, yaushe aka haife shi"? Zainab na kallon fuskarsa tace "yau kwana hudu"hada su yai da babyn ya rungume cikin dadin murya yace"sorry babyna daddyn ka ya tafi ya barka ko ayimin afuwa dole ce ta sani nasan kayi hakuri "dariya Zainab tayi tana cewa "kuma yanzu idan kaji yace babu komai daddyna fa yaya zakayi"? Murmushi Yarima yayi yana ajiye babyn ya cire kayan sa zai shiga wanka yace mata "me zanyi kuwa bayan farin cikin na samu yaro dan baiwa"yana kaiwa na ya shige toilet. Lokacin daya fito Zainab na waya da mama ba kunya yazo ya zauna ya fara zubawa mama shagwaba baki bude Zainab ke kallon shi ko sai yaushe zai daina yiwa mama shagwaba? wata zuciyar tace mata sai ranar daya fara ganin nasa yaran suna yi masa kila ya daina Yarima ya saka ma babyn sunan mahaifin mama Ahmad mama tayi farin ciki sosai dajin wannan sunan. Musty ne ya kira shi a waya cewa za suzo suna mama ta kira shi tace masa matar sa ta haihu maimakon Yarima ya bashi amsa sai yace "may be nima ban sani ba "da mmk Musty yace "kamar ya baka sani ba ina tare kuke? kaga prince bana son iskanci mene wai kake min boyan matar ka baka so na ganta kamar mara gaskiya sunan ma dazan zo sai kamin bakin ciki"tabe baki Yarima yayi yace "kaifa baza ka gane min mata yanzu ba sai lokacin dana diba ya cika dan wallahi idan ma ka rakito matar ka kuka zo zansa a hana ku shigowa saidai kuyi honey moon ku juya idan baby ne zan turo maka shi a waya ka gani"cikin haushi Musty yace "bana so ka hada har babyn ka dafa su ka cinye dan iska kawai "yana fadin haka ya kashe kiran murmushi Zainab tayi tana cewa "kana takurawa uncle din nan naka dan Allah ka barshi man yazo"kallonta Yarima yayi yace "ke rabu dashi dan rainin hankali". Hindu ma an haihu Bashir kuwa baya ma gari yafi wata da barin kano Bilki tayi kuka ha saida hawan jini ya hauta mahaifanta Hindi kan sunyi da nasani har ba iyaka dan saida sukai shari'a da Bilki anan sauran dan abin hannunta duk ya kare dakyar ta samu kawarta Aliyah ta bata rancen kudi zata dora jari daga baya ta biya ta amma kafin ta bata saida ta mata tas ta gama kwashe mata sauran ragowar albarkar data rage mata halin mummunar kawa kenan rusawa mutum rayuwa. Allah ya tsare mu👏 A gurguje bayan wani dogon lokaci mai tsaho Ahmad yayi girma abinsa sai shagwaba kamar abinci dama barewa bata gudu danta yayi rarrafe. Suna zaune a palor da dare Yarima ya rasa yadda zaiyi da Ahmad ya dame shi ya cika masa kunne dole tasa ya mike yana goyon sa ya fara zagaya palon har said yayi bacci sannan ya kira Siana ta dauke shi ta saka masa kayan bacci. Zainab dake kallon shi tun dazu tana son tayi dariya tace "kadan ka gani tunda haka ka rika yiwa mama shagwaba abinda bakai mata bama gashi kai anai maka "harara Yarima ya cilla mata yana cewa "ina ruwan ki so ne ya kawo haka"shiru Zainab tayi tana dariya. Shekarar Ahmad hudu suka shirya zuwa Nigeria lokacin Zainab nada wani cikin murna gurin Zainab zata koma Nigeria bayan shekara biyar rabon ta da ita a daren dakyar tayi bacci dan farin cikin gobe kamar iyanzu suna tare da mama. Washe gari gabadaya masarauta ta dauka Yarima zai dawo dan Hajara ba'a barta a baya ba da kanta taje kitchen ta tsaya akan girkin da akewa Yarima bayan an gama komai part din Yaha tasa aka kaima kafin ya sauka ita kuma ta wuce bedroom dan ta shirya. Yahanasu dake labe ganin Hajara ta wuce yasa ta fito tana bude kulolin abincin ta barbade da guba ta mayar a hankali ta rufe cikin sanda ta koma part dinta tana dariyar farin ciki tasan yau duk tsiya burinta zai cika Yarima bazai sake rayuwa a duniya ba. Tunda ta zuba tabar palon ba wanda ya shigo dawowar Mahmud kenan daga hospital ya dauko yunwa da gajiya ganin kuloli yasa shi fasa hucewa ya zauna yana budawa yunwa yakeji sosai dan haka ya dau plate yana diban abincin ya wuce dashi part dinsa zaici acan. Ko wanka baiyi ba saida yaci abincin sannan yayi wanka ya shirya ya wuce garden dan yadan huta yaji ana Yarima zai dawo ma so yake su hadu ya fada masa gaskiyar dalilin dayasa umma take so ya auri Hajara dan ya gaji da wannan shashancin gara su daidaita da dan uwansa gaba ba abune mai kyau ba. Gaskiya ne Mahmud gaba babu kyau. ⛔ Fadawan dake gadi a garden ne sukaji nishi yana fita kamar an shake wani za'a kashe da manyan fitilu masu haske suka fara dubawa can suka hango Mahmud kwance cikin tsoro sukace "waye wannan "? bai iya mgn ba sai hannu da yake daga musu daya daga ciki ne ya dan gane shi yace "ai kamar Yarima Mahmud nake gani "zuba ido sukai sosai suka gane shine cikin sauri sukai kansa suna salati suka daukeshi zuwa fada. Suna shiga palon mai martaba cikin firgici kowa ya mike tsaye ana tambayar mai ya faru cikin girmamawa fadawan suka fadi inda suka ganshi gabadaya salati kowa yake to mai ya samu Mahmud din. Saukar su Yarima kenan yace Zainab ta wuce part din mama da Ahmad su huta zaije gurin mai martaba yayi mmkn ganin gidan a hargitse bai tambayi kowa ba direct palon mai martaba ya shiga ganin palon a cike yasa shi leka inda aka zagaye. Mahmud ya gani cikin mawuyacin hali ga Yaha na kuka kamar zatai hauka cikin sauri yai kneel down a kusa da Mahmud dasu dady ke rike dashi ga jini na fita ta hancinsa. Durkusawa Yarima yayi yana girgiza shi yace "Mahmud lfy me ya faru dakai haka meke damun ka? bude ido Mahmud yayi dan tunda aka kawo shi yaki budewa ganin Yarima ne da gaske yasa ya fara kokarin barin jikin dady rungumeshi Yarima yayi cikin tashin hankali yace"me ya faru da kaine dan uwana "? idan Mahmud na zubar da hawaye yace"yayana dan Allah kayi hakuri ka yafe min tunda na taso mgnr arziki bata taba hada ni dakai ba kuma duk umma ce sila tace ba sona kake ba dan Allah ka yafe ni kada na mutu da alhakin zumunci a kaina". Yarima duk a rude yake dan baya ma jin abinda Mahmud din ke fada masa kallon dady yayi yana cewa "dady ya kamata akaishi asibit_____bai karasa ba yaji yan falon suna salati girgiza shi Yarima keyi yana taba kirjin shi yace"Mahmud dan Allah ka tashi kada ka tafi ka barni". Matsowa mai martaba yayi cikin dauriya yace"Muhammad kayi hakuri Mahmud ya riga mu gidan gaskiya yanzu kaunar da zaka nuna masa yayi farin ciki itace addu'a. Mikewa Yarima yayi yana girgiza kai ya kasa mgn ba zato suka ga ya fadi kasa a sume a rude mai martaba yayi kansa ganin zai rasa biyu. Dady dake durkushe shida Abba a gaban Mahmud yace "Mahmud fa ba mutuwa yayi mu kaishi asibiti tukuna "mikewa yayi wasu na taimaka masa ya fita da Mahmud aka sashi a mota suka wuce asibiti dan a tabbatar ya mutu ko yana da rai. *Mrs Al'ameen Ahmed* Be with me at always my lover's. Ina gaisuwa sosai INDO da HAJARA ABLA'S Allah yabar kauna. Maman khaleel ke ta daban ce. #🌹YMA DUTSE 🌹# *#Ana takai tawa za'ai makurar alfarma tajul-izzullahil-a'ala mai girma*#. *#Komai idan aka bamu saidan daya na dayan da ba'a ji na biyunsa ba*#. *#Mai alfarma abin yabo dan Allah Annabi kula da mu*#. [11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲 *👑Yarima Abdul-malik*👑 *ANNURI WRITER'S ASSOCIATION*💫 *#Yusrah Musa Abubakar*# 🅿🔟 Da gudu Aliyah ta shigo gidan Bilki kamar an jefo ta tana huci ta soma kwalla kiran Bilki a razane ta fito daga daki tana cewa"haba dan Allah Aliyah wanne irin abu ne? wannan ai saiki sa hawan jini na ya tahi irin wannan kira haka kamar wacce ciwon hauka ya kamata". Cikin bacin rai Aliyah tace "oh abinda zaki ce kenan sbd baki gaji mutunci ba zuwa nayi ki bani kudina dana ara miki dan wallahi bazan yarda ki lumar min dashi ba idan kuma ba haka ba zamu hade a gaban hukuma". Kallon mmk Bilki ke mata tace"yanzu Aliya duk irin mutuncin da muke dake ni kike fada ma wai zamu hadu a gaban hukuma akan wata shegiya dubu ishirin to bazan biya dama matsalar bakar kawa kenan sai dai ta kaita halaka ta baro Allah ya isa tsakani na dake". Kallon banza Aliyah tayi mata tana cewa"yauga munafikar mace ni kin manta abinda kikai min na miki dare kika min rana nifa na hada auren ki da Umar amma sbd baki san halacci ba ni kuma kike dan waken zagaye gurin mijina kamar ba tare da ke muke yawaon ba saida kika sa ya sake ni dama nace saina dau fansa shiyasa na turo Bashir a boye yazo ya jone dake dan nasan halin san zuciyar ki duk wata shawara Bashir dani yake kafin ya aikata kuma ko Zainab da yace ki aura masa ni nace yace haka idan kin gama cin kudin sa da sunan zaki bashi Zainab nace masa idan anje gurin daurin aure yace da Hindu za'a daura ba Zainab ba shiyasa na zuga ki kika kore ta sannan nasa ya wargaza rayuwar Hindun da bakya so ta wulakanta yanzu fada min tsakanin nida ke waye ya samu nasara akan wani kuma wallahi saikin biya ni kudi na kinji na fada miki". Bilki data gama kulewa da maganganun Aliyah cikin bacin rai tace"bazan biya ba mitsiyaciya makira Allah ya isa ban yafe miki ba tsinanniyar mace ni nadauki duk yarda ta na baki ina miki kallon mai sona bansan da makiyiyata nake kawance ba bankadaddiya yar tasha karamar 'yar iska wallahi duk abida kika taka na fiki nima din kafar baya ce". Shakota Aliyah tayi tana cewa"idan kika sake zagi na wallahi saina zubar miki da hakora akwai mitsiyaciya bankadaddiya irin ki bari na nuna miki kala ta banga mai ceton ki ba yau ko ni ko ke". Kara shake ta Aliyah tayi tana matse ta a jikin bango dan Aliyah irin mayan matan nan ne gabadaya idon Bilki yayi jawur dan wuya Inna ce ta fito a daki zata tafi gidan da take aiki ta jiyo fadan nasu zuwa tayi tana cewa"a'a meke faruwa haka dan Allah Aliyah bari sake ta ba girman ku bane ace kuna fada". Sakinta Aliyah tayi tana cewa "kinci darajar inna amma yau dasai kin gane kuren ki"ta fada tana nufar kofa zata fice bilki dake binta da kallon tsana tace"karya kike baki isa naci darajar wani ba nafi karfin haka"a fusace Aliyah ta juyo tace "au haka kika ce? to bari naga abinda kika fi karfi "tare ta inna tayi tana janta zuwa waje tace"dan Allah Aliyah ku bari kije ki tafi zata biya ki kudin ki"wucewa Aliya tayi batare da ta sake mgn ba inna ma ta kama haryar ta tana mmkn wanne irin kawance ne wannan kamar a film. Alhmdllh su dady sunkai Mahmud asibiti kuma an tabbatar musu bai mutu ba, ba karamin farin ciki sukai saidai gubar tayi masa illa sosai. Yarima tun suman dayai bai farfado ba saida safe yana tashi a firgice ya soma kwalla kiran Mahmud dakyar mai martaba ya shawo kansa ya fahimci bai mutu ba yana asibiti sai sannan ya samu nutsuwa. Zainab dama batasan abinda ke faruwa ba dan jiya tana shiga part din mama da bata ganta ba bata kawo komai ba dama ta gaji kawai shirin bacci tayi saida safe mama take fada mata ba karamin tsora tayi ba da kuma mmkn waye zai bawa Mahmud guba a fadin masarautar nan. Mai martaba wannan karon ya shirya tsaf akan za'a tsanan ta mugun binkice sai an gano wanda yasa aka bawa Mahmud guba da wanda yasa aka bawa Yarima guba dan idan yai sake za'a karar masa da ahli yana kallo. Bayan wata daya komai yayi sauki musamman jikin Mahmud dan da harya daina tafiya ma daga baya ya zo yana dan takawa. Dukkan familyn suna asibiti gurin Mahmud Yarima daya shigo yana waya dan duban Mahmud yayi yana sauke wayar ya zauna a kusa dashi yana rike hannunsa cikin murmushi yace "dan uwana yaya jikin naka yanzu kana jin alamar wani rashin dadi a jikin ka ko a'a fada min idan kanaji zan fita dakai waje a sake duba ka"? . Dagowa Mahmud yayi yana kallon Yaha data tsaya can bakin kofa kamar mara gaskiya ya girgiza kai yana cewa "bana jin komai ina jina kamar yadda nake da dan Allah yayana kayi hakuri da irin zaman da mukai a baya nayi kuskure dana kasa gane cewa kana sona bansan rudanin da shedan ya jefa ni ba ka yafe min "ya fada hawaye na zuba a idonsa abinda kowa ya juma bai gani ba. Rungumeshi Yarima yayi yace cewa "Mahmud nine ya kamata na baka hakuri kasantuwa ta babba na jaka a jikina tun farko amma banyi hakan ba laifi nane yanzu ne ya kamata mu gyara kuskuren mu"kallon mai martaba yayi"kakana kasa mana albarka tare da addu'ar kanmu ya hadu kenan har abada"murmushi mai martaba yayi cikin jin dadi yace"Allah ya muku albarka jikanu na Allah yasa kun dore kenan"ameen su dady suka amsa gabadaya cikin jin dadi. kuka Yaha ta fashe da shi tana durkusawa a gaban mai martaba tace"ranka ya nice ya kamata a yiwa hukunci lokacin daya kamata ace kunsan gaskiyar komai game da abinda da nake aikatawa kuma ku yafe min ba kowa ne ya bawa Sujara guba ya sawa Yarima a cikin abinsha ba bayan ni sannan gubar da Mahmud yaci ma nice na zuba cikin abincin da za'a sauki Yarima dashi sai Mahmud yaci"juyawa tayi tana kallon mama tace dan Allah kema Amina ki yafe min zubar miki ciki danai sau biyu batare da ansan nice ba naso zubda na Yariman ma abun yaki yuwuwa sbd Allah yayi saiya rayu a duniya na sani ke ba kishiya ta bace amma na dauke ki da zafi na hana zaman auren ki yayi dadi tun a farko dan Allah ki yafe min "ta karasa maganar cikin tsananin kuka tana hade hannunta guri daya alamar neman gafara. Tabbas mama bazata manta ba akan zubda cikin nan sun samu sabani sosai da dady har yace idan bata son haihuwa dashi ne ta fada masa sai yasan matsayin sa a gurin ta. Kowa kamewa yayi ya kasa mgn kawai kallonta suke da kuma mmkn maganar data fada Abba kam baba wata neman shawara ko sauraro yace taje ya sake ta cikin kuka Yaha ta soma bashi hakuri hankali tashe dan tana matukar son Abba, rufe idonsa yayi yace "idan har na kirga uku na bude baki bacewa gani na ba saina dau mummunan mataki akanki Yahanasu"fara kirgawa yayi Yaha dake durkushe cikin kuka tace "dan Allah ku bashi hakuri ya mayar dani wallahi na tuba"jin yace biyu yasa dayake tasan halinsa ta mike tana fita da gudu daga room din babu wanda yasa musu baki cikin sha'aninsu dan hakan shine yafi cancanta da ita. Mai martaba cewa yayi a sallami Mahmud kawai su tafi tare dashi gida hakan kuwa akai kuma ko kadan Mahmud bai nuna damuwa da Abba ya saki Yahanasu ba domin hakan shine daidai a gareta. Lokacin da zasu shiga masarautar daidai nan motar Yaha ke fita alamar tayi gidan su. Uhmm sauka lafiya. Bayan ya kwanaki komai ya lafa Zainab ta haihu an kuma samun namiji Yarima ya saka mai sunan mahaifinta Umar ba karamar murna tayi ba Salmah itama ta haihu namiji abindai kwanin sha'awa ansawa yaron suna Fauzan. Suna zaune a palon mama Zainab tasaka Ahmad a gaba yaci abinci yaki karshe saita karfi ta bashi mama dake zaune da mmk tace"dota wai shima baya cin abinci da kansa saidai a bashi kamar babansa"? murmushi Zainab tayi tana cewa "wallahi kullum haka nake fama ni harna gaji ma bacci nan bazaiyi ba sai ya goye shi ai shagwabar dayai miki shima ake masa kuma har ta zarce wacce yayi". Dariya mama tayi daidai Yarima ya shigo ya sakar wa Zainab harara don yaji abin da tace zama yayi zaifara aikinsa Zainab tace" a rika sara dai ana duba bakin gatari "kallonta yayi tamai signa da ido cewa Ahmad na kallon shi wani kallo ya mata yana cewa"mah dina kina jinta fa idan banyi miki shagwaba wa zanwa a duniyar nan"? murmushi mama tai "gaskiya ne baby amma ya kamata ka daina tunda kaima yanzun anayi maka shagwaba ba taka bace saidai kace kayi da". Hade gira yayi yana cewa "shikenan na daina naji na girma "kallonsa mama tayi "oh baby rigima wasa nake maka har yanzun a gurina kai yaro ne"murmushi yayi"yana kara hararar Zainab yace "shiyasa nake sonki mamana nasan dama bakya yimin kallon babba har yanzu ni yaro ne"shafa kansa mama tayi tace "kai yaro sosai bani da wani bayanka, yauwa baby ina son gobe zamuje kano gurin ammi ko zaka samu dama sai muje tare?"? kai Yarima ya jinjina "in sha Allahu "yana kallon Zainab yace "to sarkin hada mutum da mamansa sai aje ayi shiri tun wuri basai goben ba". Kashe masa ido tayi tace"ai ba hadi bane gaskiya ce na fada "tana fadin haka ta mike tana daukar Umar ta wuce part dinsa dan ta shirya musu kayan tafiya. Washe gari tun wuri suka shirya Zainab murnarta da yawa dan tayi niyyar zataje makaranta taga uncle Mustapha da kuma anguwarsu gurin Fati da Inna dan bata lissafi da Bilki. Suna shiga palon ammi mama ce a gaba Zainab na biye da ita cikin murmushi ammi ke kallon mama da farin ciki zatai mgn idonta ya sauka akan Zainab a firgice ta mike tana nuna ta da yatsa murya na rawa tace "Amina a ina kika samo wannan "?da mmk mama tace"matar baby ce ammi lafiya "? cikin tashin hankali ammi ke girgiza kai tace "Amina duk inda yarinyar nan ta fito jinin Khadija nace kalli kamar mana dakyau jini baya buya"zubawa Zainab ido mama tayi cikin wani irin yanayi ta kasa mgn. Yarima dake tsaye dama yasan haka zata faru karasowa yayi yana nuna photon yace"ammi itafa kinga mahaifiyar ta "karbar photon ammi tayi tana kallo kuka ne kawai ya kwace mata a wannan lokacin mama da itama cikin mmk take kallo tace"dota a ina kika samo wannan photon "? Zainab da duk jikin ta yayi sanyi dakyar tace"mahaifiya tace"mikewa tsaye mama tayi cikin zaro ido tace "Khadijan dama itace ta haife ki? kedin jini nace 'yar gidan kanwa ta uwa daya uba daya ban sani ba innalillahi wa inna ilaihi raji'u"shine kadai kalmar da mama ke iya maimatawa ammi kam babu bakin mgn sai hawaye daya ki tsayawa. Mustapha shigowar sa kenan yaga Zainab a firgice yace"Zainab Umar dama kina nan"? Kallonsa ammi tayi "ka santa ne"? kai ya jinjina Fati dake bayanshi itama ta kame dan mmk gani take kamar a mafarki ba Zainab ce a zahiri ba. Cikin magiya ammi tace wa Zainab "dan Allah ki fada min inda Khadija na take naje na ganta"Zainab da itama yanzun ta kasa rike nata kukan tace"ta dade da rasuwa tun ina shekara 12 salati ammi keyi tana cewa "shikenan Khadija sallamar karshe mukai dake zaki tafi makaranta ashe shine rabuwa ta dake saidai naga jininki Allah yaji kanki da rahma"sun dade ba mai iya lallashin wani saida kowa ya daina kukan dan kansa. Mustaphan ya bada labarin abinda ya sani game da ita fati ita ce ta bada dan cikakken bayani cewa. *Mrs Al'ameen Ahmed ce* Love for ever yan ANNURI 😍🍒ana tare. [11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲 *👑Yarima Abdul-malik*👑 *ANNURI WRITER'S ASSOCIATION*💫 *#YUSRAHMS ABUBAKAR*# 🅿️1️⃣1️⃣ Fati ce ta bada dan bayani kadan game da zuwan Khadija anguwar su kamar yadda taji ummanta na fada tace"kaka Abdullahi yace wata rana suna zaune da Umar suka hango ta tafe tun daga nesa har ta karaso kusa a yanayin ta bai nuna tasan inda take nufa ba ganin haka yasa kaka Abdullahi yai kiran matar sa cewa tazo ta rike ta a zaton idan suka bata abinci taci zasu samu dan wani bayani daga bakin ta amma shiru sai kaka Abdullahi ya soma shawarar yi mata magani a zaton sa sammu ne daga baya dayai mata maganin ya fahimci cewa ba maganin gargajiya cutarta ke bukata ba yayi shawara da Umar suka kaita asibiti aka fara yi mata magani domin a yadda bincike ya nuna allura ce aka mata dan ta manta komai na rayuwarta ta baya anyi nasara ta dawo hankalinta amma da aka tambaye ta danginta ko gidan su da wani abu data tuno tace batasan komai ba a haka ta zauna a gidan kaka Abdullahi zuwa wani lokaci kafin Umar ya bukaci aurenta kaka Abdullahi ya bashi da kudin sadakinta ya kara nasa kudin akai ya mata kayan daki dukda Umar yana da mace Bilkisu a haka suke zaune har bayan an haifi Zainab da shekara 12 duka ta rasa mahaifanta ta koma rayuwa cikin wahala a hannun Bilki wannan shi kadai na sani a labarin Khadija ki ammi"Fati ta karasa maganar cikin sauke numfashi dan ganin yadda jikin kowannen su yayi. Babu mai mgn ammi tace"tabbas Habiba ta cuce ni ta rabani da farin ciki na biyu a lokaci daya a ranar da zata mutu ta nemi gafara ta cewa itace silar batan Khadija sbd taga irin son da Ahmad yake mata sai tasau tsanar duniya ta dora mata har tayi sanadin barinta gidan nan bayan ta tafi makaranta tasa aka dauke ta a mota tare da yi mata allurar da zata manta komai nata da naji haka ban fidda rai da zan ganta ba koda ba a cikin hankalinta bane amma hakan bai samu ba shi kansa Ahmad dayaji abinda Habiba ta fada kafin mutuwar ta ya tsoma masa zuciya ya kuma tayar masa da hankali dahar yasa ciwon hawan jini ya kama shi wanda shine ajalinsa Habiba ta cutar damu shikenan yanzu nida Khadija saidai naga jininta"ta fada tana share hawayen dake kara zubo mata. Ganin duk guri ya rude yasa Yarima rike hannun Zainab suka bar palon dan ta samu nutsuwa dan indai tana gurin suna kallonta abin ne zaiyi ta yimusu gizo ne. Ameen 👏🌹🌺 [11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲 *👑Yarima Abdul-malik*👑 *#Mrs Al'ameen Ahmad#* 🅿️1️⃣2️⃣ Washe gari tun wuri ammi tace suje gurin kaka Abdullahi domin yi masa godiyar abinda ya musu na maganin Khadija da rike ta dayayi tamkar 'yar daya haifa lokacin da kaka Abdullahi ya gansu kuma suka mai bayani ya jinjina al'amarin yayi farin ciki ya kuma yi mmk dayaga cewa iyayen Mustapha mijin jikarsa Fatima sune kakanun Zainab babu wanda ya taba tunanin hakan zata kasance. Hjy Asma'u kan harda rawar farin ciki tayi a gaban su suna ta yi mata dariya Asma'u tace"sau dubu idan zan bude ido naga danginki Zainab to sai nayi rawar jin dadi "murmushi Zainab tayi tana cewa "dan Allah inason naje gurin umma "tsayawa Asma'u tayi tana kallon ta tace "badai kina nufin kije gurin Bilki ba mai zakiyo mata kin manta duk abinda data miki kenan "? Cikin marairaicewa Zainab tace"dan Allah ina so na ganta ne kawai "hararar ta Fati tayi tace"da yake abin arziki ta miki ba shiyasa zaki nemeta "banza Zainab ta mata tana kallon Asma'u tace"abinda ta min ya riga ya wuce nidai ina so naje mu gaisa"girgiza kai Asma'u tayi tana cewa "Bilki dai ko kinje bazaki same taba domin jiya 'yan sanda suka zo har gida suka kamata kawarta Aliyah ce tayi kararta akan ta cinye mata kudi kuma ba ita kadai ba mutane da yawa ta narkar musu da kudi dan haka tana bayan kanta saidai idan candin zakije". Cikin damuwa Zainab tace "eh fati tashi ki rakani zan biya kudin a fito da ita "Fati dake duba waya tace "bazanje zo ki daura min igiya a kafa sai kijani kikai watan tsoron ki bai kama ba 'yar me abin duka kawai"shiru Zainab tayi tana tunani zuwa wani lokaci tace"to rakani gurin inna "Asma'u dake shirin barin gun tace "inna ta sauya anguwa tabar nan wasu yan hayar ne a gidan "dole Zainab ta hakura dan an gama kure ta tana gani suka bar anguwar kamar zatai kuka domin taso zuwa gidan sosai dan Asma'u taki barinta ne. Kwanan su biyar amma Zainab bata samu damar ganin Bilki ba dan Yarima ya hanata zuwa dole tabar batun suna zaune a palon ammi ana fira su Ahmad suka fito shida Rufaida 'yar gidan Mustapha zama sukai a kusa da fati mama tace"dota hadawa yaran nan kayan breakfast tunda sun tashi"to Zainab tace tana bude kulolin tana kallon Ahmad tace"boy wanne kake so "? dauke kai yayi daga kallon kulolin alamar babu mama da hankalinta ke kanshi tace"me kake nufi bazaka ci ba"? daga kai yayi yana cewa"grandy nifa bana cin wannan nafi son tart "harararsa Zainab tayi tana cewa "kafi son tart ba a London kake ba idan na karajin bakinka ya kira tart din nan saina rushe ma wadannan kananan hakoran"Ahmad daya rike kunnansa tunda Zainab ta soma fada alamar ya tuba yace"mum nifa yau azumi nake"ba shiri Zainab ta kau da kai tana murmushi jin abinda yace dariya mama tayi tana cewa "baby ka masa mgn ko zaici "cikin shagwaba Yarima yace"haba dai ki barshi yayi koma lokacinsa ne ko my boy"? dariya gabadaya akai ganin yadda yake shagwaba san ransa a gaban yayansa . Zainab ta hada tea tana jawo ahmad ganin yana shirin guduwa tace"zan saba makafa boy ka bude min bakin ka "kuka ya fara sai data zazzare masa ido sannan ta samu ya soma sha Mustapha yace "nifa ban gane ba naga tunda kuka zo gidan nan baya cin abinci da kansa sai kin dura masa meyasa haka"? kallon Yarima Zainab tayi alamar in fasa kwan aikuwa ya cillo mata harara rufe baki tayi tana dariya tace"ka tambayi old man dinshi zai baka amsa abinda dayasa baya cin abinci da kansa "cikin haushi Yarima yace "kinga ki kiyaye ni"kallonsa Musty yayi "kaga malam daga ance na tambaye ka shine abun fushi"Yarima dake harararsa yace"ban sako dakai ba uban 'yan shishshigi da mata ta nake"dariya Musty yayi"gaskiya ne dadyn boy wannan action din naka yayi, aunty me yasa yaron na bayacin abinci da kansa"? mama tace "nima ban sani ba a gurin babansa ya gada shima har yayi aure dura nake masa"dariya sosai Musty keyi cikin tsokana yace"saidai hakan fa ashe gado ne baka da laifi yaro gaskiya prince Allah ya shirye ka kaidin dan asara sai kace wani baru sai ana maka dura "banza Yarima ya masa mama ce tace"bansan iskanci fa Mustapha aiba laifi bane danna bashi abinci a baki gata ne ya kawo haka"danne dariyar Musty yayi yace"haka ne aunty ayimin afuwa". Ahmad da shagwabar shi ya nufi gurin Yarima yana cewa"dadyna mum ta cika min cikina zai fashe"Yarima yasan mai Ahmad yake nufi mikewa yayi yana goyonsa ya fara yawo dashi a palon Zainab dake dariya tace"wannan abin yana bani sugar "a kule Yarima yayo kanta tayi tsalle ta koma kusa da ammi musty yace"gaskiya kai mugu ne daga tace haka rama abinda kaiwa aunty yake yi "yarima baiyi masa mgn ba ya dire Ahmad zai zauna kenan farouq ma ya mika masa hannu ganin suna neman karasa shi yace"ku tashi muje kusha ice cream "cikin murna suka mike harsu Rufaida suka tafi washe gari sukai shiri suka koma Abuja bayan sunbar su ammi da kewar su. Yaha kam dakyar Abba ya dawo da ita bayan sa bakin mai martaba sannan ya hakura suna zaune a palor mai martaba ya kalli Yarima yana cewa "Muhammad lokaci yayi daya kamata ace an daura maka dayan auren ka ko"? wani irin faduwa gaban Zainab yayi ta dago cikin tashin hankali tana kallon Yarima da shima ita ya kalla yana Murmushi dan yaga yadda zatai ganin murmushi yake kamar abin bai dame shiba ta dauke kai daga kallonsa tana hadiye abinda ya tsaya mata yake neman hanata yin kyakkyawan numfashi . Yarima da har yanzu murmushi yake ya kalli mai martaba yana cewa "kakana mun gama mgn da dan uwana jiya ya sameni akan cewa dama tun farko shine yake sonta ni kuma inason dan uwana sosai shiyasa na bar masa ita fatan kakan zaiyi farin ciki da jin haka"? Murmushi mai martaba yayi yana kallon Mahmud yace"shikenan duka daya kuke Mahmud mai yasa tun wuri bakai mgn cewa kaine kake sonta ba da tun a wancen lokacin an hada naku auren dana Muhammad amma yanzun ma bata baci ba za'ai muku Allah yasa albarka "ameen sukace wani numfashi Zainab ta sauke tana kallon Yarima daya daga mata gira ta sakar masa harara tana mikewa tabar falon sun dade suna tattaunawa kafin kowa yayi part dinsa. Direct Yarima part din mama ya shiga dan yafi tunanin Zainab nacan zama yayi a palor yana waya da Abeed abokinsa fitowar Zainab kenan ya dago yana kallon ta tare da aje wayar sbd wata irin kwalliya data tsara ta daukar hankali tasa doguwar riga baka mai adon farin fulawa kanta ba kwali tayi parking zama tayi a kusa dashi tana murmushi tace "yadai soulmate nayi kyau ne"? kallonta kawai yake ya kasa mgn kara matsowa tayi kusa dashi tana dora hannunta a kafadar shi ta matso da fuskarta jikin tashi sosai ganin yadda ya rude yasa ta tallafo fuskarsa tana hada bakin su. Wai bari na rufe idona🫣 karna makance. Saida suka dau lokaci a haka kafin ta sake shi dakyar ya saita kanshi yana zamewa ya kwanta akan cinyarta yana rufe ido ita kuma take kallonsa tsantsan kyan sa da yake dashi tare da dora yatsarta akan lips dinsa tana shafawa bude ido yayi yana kallonta yace "i love u you're the one who make me happy you're the one i want keep i love u so much"murmushi tayi cikin jin dadi tace"i love u too my soulmate "mikewa zaune yayi suna facing juna wani irin yanayi suka shiga na shauki kowa yana son gwada ma dan uwan sa irin son da yake masa hannunta ta zagaya a wuyansa shi kuma ya zagaya nasa zuwa bayanta yana shirin kissing dinta mama tace"baby maza tashi ku tafi inda kuka nufa "matsawa Zainab tayi da sauri daga jikinsa amma saiya kara riketa. Cikin mmk mama tace "wai baby kun manta a inda kuke ne yanzu da kuma dadyn kune fa yaya zakuyi"? cikin mazewa Yarima yace "idan da shine cewa zaiyi Allah ya muku albarka "mama tace "lallai baby lamarinka yafi karfina harda ke dota kika biye masa"? Zainab data juya baya tana dariya tace" soulmate dan gyara min zip dina mama karki damu mudin abu daya ne a haka muke"ganin yadda mama ta zuba musu ido yasa suka dawo kusa da ita Zainab na cewa "sai maman mu Allah ya bar mana ke"kai mama ta girgiza tana cewa "Allah ya shirye ku". Bayan sati biyu akai bikin Mahmud Yarima ne yayi masa wali ba karamin farin ciki su Abba sukai ba dan hatta lefe Yarima ne ya hada masa rakiya kuwa har daki ya musu nasiha sosai sannan shima ya koma gurin zezensa. Komawar su London ta kama gobe suna gurin mai martaba ana zaune Salmah ta shigo cikin tashin hankali kowa mikewa yayi ana tambayar ta kuka tasa tana durkusa a gun tace"yanzu mamina ta kirani a waya yayan mahaifina ya rasu dazu "mai martaba yace "subhanallahi kamisu ne mai rasuwar"? kai Salmah ta daga tana cewa"eh shine"dubansu mai martaba yayi cikin damuwa yace "kowa yayi shiri babu wanda za'a bari mu tafi bauchi "amsawa sukai kowa na fita Yarima na shiga part dinshi yaga Zainab ta fito a wanka kallonta yayi yana zama yace"sauri ki shirya wani guri zamuje ina su boy"? da mmk ta kalleshi amma batai mgn saida ta shirya tace boy na part din mama "mikewa yayi suna fita bata kara tsinkewa ba sai data ga tafiyar harda su mai martaba gashi babu halin tambaya haka suka fita zuwa airport ba bata lokaci suka nufi Bauchi . *Mrs Al'ameen Ahmad ce*🌹. [11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲 *👑Yarima Abdul-malik*👑 *💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION*💫 *#YUSRAHMS ABUBAKAR*# Dedicated to Maman khaleel Zarah Musa d'an Adam 🅿️1️⃣3️⃣ Lokacin da suka sauka masarautar makil suka sameta da mutane kyakkyawar tarba suka samu daga gurin sarki bayan sunyi masa ta'aziyya Salmah ta karasa ciki dasu mama domin su samu wurin zama su huta har dare Zainab na zuba ido ko zataga Ahmad amma shiru duk hankalinta ya tashi domin itafa tun a gida rabonta dashi bayan tayi masa wanka bata sake ganin sa ba iya Farouq ne a gurinta. Salmah na cikin fada gun iyayenta bayan ta kawowa su mama komai tace bari ta shiga ciki ba'a jima ba ta dawo tare da maminta tana cewa "mami gasu ku gaisa lokacin da suka shiga gurin Addah bakya nan shiyasa nace bari na kira ki" zama tayi sukai gaisawar mutunci dasu mama inda take kallon Zainab cikin mmk tana kama da wani data sani saidai ta manta waye mai kama da irin wannan fuskar sallama ta musu tana fita zainab nason tambayar mama ina Ahmad ta kasa haka ta hakura dakyar tayi bacci. Washe gari tun asuba wayoyi keta ringing wanda shine silar tashin dukkan su mama a bacci sukai sallah bayan gari yayi haske mama ke tambayar Zainab "dota waye yake kiran waya da asuba "? dan murmushi Zainab tayi tace"soulmate ne "kafin mama tayi mgn Hajara tace"nima wallahi Mahmud yake ta kirana"mama data dago tana kallon su tace"kai kunji yaya da rashin hankali mai zakuyi musu"? Zainab tace "kila ko son ganinmu suke kinsan tun jiya fa "da sauri mama ta kalleta ba shiri tana cewa "kwarai dota sannunki da kokari to babu inda zakuje"ji tayi daga bayansu ance"mu gamu munzo ai"ido mama ta zaro tana kallon su tace "yauga wani hauka uban me kuka zoyi nandin dama ba gurin su mai martaba zaku tafi ba mema ya biyo daku tanan din"? da hannu Mahmud ya nuna mata Hajara yana cewa minti daya kawai shaf shaf "mikewa mama tayi tana nuna musu kofar fita tace"maza kubi nan kafin na kira muku Ibrahim "dan hade rai Yarima yayi yana kallon Zainab alamar minti daya ta girgiza masa kai tana nuna mama kwafa yayi yana jan hannun Mahmud yace"zo muje kyale su akwai gaba"mama tace "yauwa kufi ruwa gudu "suna fita mama tace "kuma saura naji kunje saimun koma gida ku rabu dasu "dariya Zainab tayi tace "da aiki suda zasu tafi gobe mukwa sai anyi bakwai "mama dake kokarin kiran ammi tace "ko dubu zamuyi haka zasu hakura". Ranar da akayi uku gabadaya ana tare guri guda a palor harda su mai martaba domin tafiya zasuyi addu'a akeyi kowa na amsawa da ameen bayan an shafa aka sake gaisawa da ta'aziyya sai sannan Zainab taga Ahmad kwana uku rabonta dashi mama na kallonta harda sauke ajiyan zuciya kamar zatai mata dariya zeey masoyan yaya. Addah ce tace"amma dai bayau zaku tafi ba? ku bari sai gobe dan Allah "Salmah tace"eh yau zasu tafi gabadaya domin ba'a bar kowa acan ba sai wakilai "Farouq daya hango Ahmad ya fara kokawar kwacewa a hannun Zainab ya tafi gurinsa ita kuma taki sakinsa kuka ya fara mama tace"dota ki barshi ya je mana ba gurin dadynsa zaijeba"? shiru Zainab tayi Addah ta mike tana cewa "da alama wannan jikar tawa akwai kunya kodai fabulatana c______cikin firgici Addah ta kasa karasa maganar tana kallon Zainab da mmk tace "ranka ya dade kalli wannan yarinyar "ba moddibo ba kowa na palon Zainab ya zubawa ido harda su mai martaba dansu fahimci abinda yake faruwa me Addah ke nufi. Mikewa moddibo yayi yana Karasowa gurin da Zainab take zaune saida ya kare mata kallo ya juya inda Addah take yana cewa "alhmdllh abinda na dade ina nema abinda kullum nake alfahari dashi nake mafarki da kwadayin gamuwa dashi zinaren da a kowacce rana yake sheki a idona abinda ya kasance shine nutsuwar zuciyata kuma farin ciki na ya iso gareni lokacin da ban taba tunanin zan ganshi ko na sameshi ba wannan yarinyar duk inda kika fito ke jinin Umar dina ce idan har ba gizo idona kemin ba da abinda nake muradi kuma ba rudewa nayi ba tabbas ke 'yar Umar dinace "ya karasa maganar yana kallon Addah da hankalinta yayi mugun tashi ba zato taji kuka yazo mata cikin damuwa tace"koma menene kaine silar batan Umar ai da halin daya tsinci kansa a ciki mai yasa ka kasa masa hakuri ka fahimce shi tun a wancan lokacin akan laifin da baikai ya kawo ba ka iya cewa yabar maka masarauta shekara talatin kenan babu ko alamarsa yanzu da yarsa tazo maka har gida ai ka nemeshi "ta karasa maganar dakyar sbd yadda muryarta ke shakewa zainab kallonsu kawai take inda taji zuciyarta ta girgiza lokacin da Addah ta ambaci Umar shine ya tsorata ta. Moddibo hakuri kawai yake bawa Addah don yasan bai kyauta ba mai martaba dake kallon su dukda maganar ta cikin gida ce amma tunda abin ya hado da Zainab dole ne suma suyi mgn dan haka yace suna neman karin bayani shiru palon yayi ana sauraron moddibo ganin kowa shi yake kallo yasa ya sauke numfashi yana cewa "gaskiya da na rike sirrin a zuciya ta amma yanzun dole na fada kowa yaji dalilin dayasa umar yabar cikin ahlinsa nine sila shiru moddibo yayi ya kasa magana gabadaya kansa ya dau caji ji yake kamar kada ya fada amma kodan ya wanke laifinsa a gurin yarsa ya fada musu. *Mrs Al'ameen Ahmad ce*🌹 YA RASULULLAH Ka saita bayi akan hanya ta islama a koyarwar ka harda ladabin sanya takalma abinci kwa kar a cishi sai ansa hannun dama bismillah ayi baza a ci da shaidan ba. Ya shugaba kasan abinda dake xuciyata ko a munbari ko a ayari kana ko a halin kadaita banda kai aya sayyidil khalki Yusrah banda sauran bukata ka cika burika na akan ka rainon Halimatus-sadiyyah. Gaisuwa mai tarin yawa Indo Abla's Rabi'ahh Bichi my Feedoh and maman khaleel ❤4ever. [11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲 *👑Yarima Abdul-malik*👑 *ANNURI WRITER'S ASSOCIATION*💫 @YUSRAHMS ABUBAKAR# 🅿️1️⃣4️⃣ Cikin nutsuwar damuwa Moddibo ya fara musu bayani"dalilin dayasa Umar yabar gida shine na tashi zan kaiwa sarkin Gombe ziyara sai Umar yace yana son muje tare dashi Umar shine auta na kuma inaji dashi ina sonsa fiye da sauran yarana muka tafi tare dashi ina farin cikin ganin sarki ya yaba da hankalinsa da nutsuwar sa sai ya sameni akan yana son zai bawa Umar auren yarsa da murna ta na amshi mgn amma dana same shi akan ga abinda sarki yace kansa tsaye yace wallahi baya sonta ranar dama ana gobe zamu dawo gida ne Umar haka ya daga min hankali sai mun taho a ranar sbd wannan mgn ko fada kin komawa yayi sbd kada kunyar sarki tasa ya amince babu irin lallashin daban masa ba dakyar na samu yaje yaga yarinyar amma duk da haka yaki yarda ". Shiru modibbo yayi zuwa wani lokaci har kowa ya fidda rai bazai sake mgn sai kuma sukaji yace "bayan mun dawo gida da wata daya sakon sarki ya same ni akan idan mun gama daidaitawa da Umar shi a shirye yake banyi kasa a gwiwa ba gani ga Zainab (Addah) na sake samunsa akan mgnr amma dai batun daya ne baya sonta shi ba yanzu zaiyi aure ba raina ya baci dajin haka nasan Umar yaro ne mai biyayya amma a wannan lokacin ya juya min baya idan ina lallahin sa sai naga tamkar kara hura masa wutar kiyayyar yarinyar nake yi a xuciyarsa wannan abinda yayi ya bakanta min sai ya nayi masa barazana da cewa saidai ya bar masarauta ya kama gabansa indai bazai fidda ni kunya ba". Banyi tunanin idan nace haka zai tafi ba amma sbd kiyayyar yarinyar a jininsa take saiya amince ya barmu akan ya aure ta ya kama hanya batare da kowa ya sani ba hatta kayan jikinsa saida ya sauya su yasa na talakawa kwarai da kar ayi masa kallon wani kuma ya rufe fuskarshi domin kowa ya sanshi bai dauki ko tsinke daga cikin dukiyarsa ba tana nan har yanzu ina jiran ranar da zanga jininsa domin dukiya ta dansa ce ". Cikin dare yabar gida amma labari bai sameni ba saida gari ya waye sosai wasu fadawa da suka gane shi suka zo sukace min Umar yabar gida jiya da dare lokacin da suka iske ni da wannan mgn nasa abi bayansa na baza mutane ta ko'ina cewa su bishi a boye suga inda zaije wadanda suka shiga kano neman sa sune suka zomin da labarin cewa Umar nacan ya sauka a wata anguwa farawa gurin wani malamin addini da naji haka zuciya ta tayi sanyi kuma hankali na ya dan kwanta nasa wasu boyayyun mutane suke kula min da duk wani motsinsa har yayi shakara guda a kano ko murmushi Umar yayi sai sun fada min ance yayi aure a cikin wannan shekara dayan". Bayan auren sa da wata biyar suna zaune shida malamin suka tsinci wata budurwa data kasance bata cikin hankalinta har suka fara yi mata magani ta samu lafiya itama umar ya aure ta mamaki ne ya kamani da naji ya auri mace har biyu bayan kin auren ne yasa yabar gida lokacin da masu kula min dashi suka zomin da labarin Allah ya azurta Umar dina da samun haihuwa daga sabuwar matarsa nayi matukar farin ciki kuma nasan tunda haka ta faru zai nemi ya dawo gida amma baiyi hakan ba har shekaru takwas suka wuce baida niya da naga haka saina kudura a zuciyata zanje da kaina na taho dashi ". Rana mafi muni a gurina shine ranar da masu suka lura dashi suka zomin da bakin labarin cewa mota ta buge Umar kuma tun a gurin ya mutu nayi kuka nayi bakin ciki har sai da hawan jini ya same ni nayi jinya sosai a wannan lokacin wanda ko Zainabu ban fadawa ba gudun abunda zai faru da ita nabar sirrin mutuwar a zuciyata nayi tunanin zan warke da wuri nasa aje kano a taho min da iyalansa suzo suga danginsa amma abun nawa sai gaba yake karshe sai kasar waje aka fita dani don a nema min magani shikenan karshen rabo na dajin labarin su kenan wannan kuma shine dalilin barin Umar gida da rayuwar da yayi ". Kuka sosai modibbo keyi ya duka bisa gwiwoyin sa a gaban Zainab yana rike hannunta yace"ina neman gafararki jikata lallai nayi kuskure kuma nidin mai laifi ne a gareki ina roko ki yafe min nayi miki ba daidai ba bansan wacce kalar rayuwa kika samu kanki ba bayan rasuwar Umar ki gafarce ni " kuka Zainab ta kama tana girgiza kai gaba daya ta kasa mgn dukkan sauran ahlin modibbo ma kuka suke da wadanda suka san Umar da jikanun da basu sanshi ba sosai moddibo ya bawa Zainab hakuri yaki tashi gaban ta har saida tace ta yafe shi. Kallon Yahanasu mama tayi tana mata alamar kin gani ko babu wanda bashi da dangi saidai kaddara ta raba shi dasu sunkuyar dakai Yaha tayi cikin kunya dan komai na masarautar yafi nasu lallai tayi kuskure dole ta nemi gafarar Zainab abinda ta mata. Bayan komai ya lafa sosai modibbo yayiwa mai martaba godiya da rike masa jika da yayi hannu biyu babu kyama mai martaba ya nuna masa babu komai yiwa kaine ba karamin farin ciki modibbo yayi ba ganin Ahmad da Umar ga kuma Yarima mijinta aka gabatar masa da mama cewa yayar mahaifiyar Zainab ce uwa daya uba daya yayi godiya har ya rasa inda zaisa kanka yaji daidai . Mama ta taya Zainab farin ciki ganin ta samu dangin mahaifin ta Yaha kam da kukan ta tanemi gafarar Zainab ita kuma ta nuna mata komai ya wuce dama can bata rike ta ba. Azahar nayi sukai shirin komawa Abuja amma sai modibbo yace abar Zainab ta musu kwana biyu daga baya za'a kawo ta mai martaba ya amince duba da suma suna bukatar ta a halin yanzu bayan sunyi sallama aka musu rakiya zuwa airport har da Ahmad da umar suka tafi domin Zainab din ta samu nutsuwa sosai kuma ta fahimci su modibbon Yarima kuwa ba'a mgn hade rai yayi zaiyi magana mama ta janyi shi dole ya hakura. Iya tsantsan gata Zainab na gani daga gurin kowa kamar basu da jikanu haka suke mata gata kuma ko da wasa bata fada musu irin zaman da sukai da Bilki ba domin ita ba mai tsegumi bace. Haka rayuwa take tafiya har Zainab tayi wata guda a bauchi ta saba da kowa kuma ta gane kowa abin mamaki babu wanda ya kula tana da ciki saida tudunsa ya fara fita anan taga sabon gata tamkar yarinyar goye suka maida ta har dariya take idan sukai mata wani abun data cika wata biyu modibbo yace ya kamata ta koma gurin mijinta domin kar su shiga hakkinsa. Ranar da zata tafi bayan ta gama shiri tana shiga gurin modibbo saida tayi tuntube sbd mamaki Yarima ta gani zaune suna zance da Addah yaci uban wanka kamar ka sace shi ka gudu suna hada ido suka ji kamar su rungumi juna saidai ba hali. Nasiha sosai suka mata tare da damka dukkan wata dukiyar Umar a hannun Yarima tunda shine mijinta dole shine mai alhakin kula mata da dukiyar da suka zo tafiya Zainab kuka take ita bazata tafi yau ba Yarima dake kallonta a ransa yace ji wannan yarinyar tana neman dora min hawan jini dakyar ta yarda suka tafi har airport tana kuka bata daina ba shi kuma bai hana taba yace gara ta morewa sabon da sukai haka suka zo Abuja ko mgn batai masa ba saboda dariyar da yake mata. Anan ma kamar wata bakuwa haka suka tarbe ta kowa na murnar dawowar ta bayan an gama gaisawa part din Yarima suka shiga duk abin nan bai lura tana da ciki ba saida ta cire hijab din jikin ta sannan ya gani matsawa yayi kusa da ita yana dora hannunsa akan cikin dagowa tayi tana kallonsa ya daga mata gira alamar yadai. Dan hade rai tayi domin ita fushi take dashi ganin yadda take kallonsa ya jawota jikinsa yana rungumeta cikin kasa da murya sosai yace"wato ciki gareki amma kika ki fada min don karna gaisa da my little one dina to Allah ya kama ki sorry baby yanzun kuwa zaka gaisa da dadynka"bata fuska tayi jin abinda yace ta soma yaja baya tana cewa "nifa bani da lafiya "kallonta yayi yace"oh da gaske haka mara lafiya yake nuna karfi daman ji yadda kike girgiza jikin ki fa kuma kice baki da lafiya yarinya baki isa ba bari nayo wanka kiga abinda zai faru "yana fadin haka ya shige toilet da gudunta tayi hanyar fita amma sai taji a kule tsayawa tayi a bakin kofar harya fito kallonsa tayi a marairaice tace"don Allah soulmate ka bude min kofa kaya kawai zan dauko a part din mama na dawo bani dasu anan"murmushin mugunta ya mata yana nuna mata kan gado kalla tayi taga sabin kaya iya ganin ta kuma duka nata ne kamar zatai kuka take kallonsa har lokacin murmushi yake yace"yadai mumyn baby na akwai magana"harararsa tayi tana daukar towel ta wuce domin tayi wanka. Lokacin data fito kin karasawa gaban mirron tayi ta toge daga bakin kofar bathroom din tana kallonshi tace"soulmate dan Allah ka rabu dani na tafi iya gaisawa zamuyi da mama saina dawo "wani mayan kallo ya mata dayasa yawun da zata hadiya ya sarketa ta hau tari da sauri ya miki yana bude fridge ya dauko mata ruwa ta sha dagowa tayi tana harararsa tace"dama so kake na kwaru shiyasa kake min irin wannan kallon"murmushi yayi yana daukarta yace "tsiyata dake duk abinda ya sameki saiki camfa kice nine to bari mu gani idan da gaskene abinda kika fada"direta yayi akan gadon ta mike zata sauka ya riketa yana cewa"abinda yasa zan nuna miki nayi kewarki yanzu sbd lokacin da zamu taho dasu mai martaba ina kallo kina min dariya na share don nasan akwai ranar dazan rike ki ba mai cetonki shiyasa nima na gama tara ki sai yau maman baby dina"kiss ya sauke mata wanda ba zato yaso fitar ta a hankalinta ba shiri ta rungumeshi tana kwantar da kanta akan kirjinshi zagaye hannunsa yayi a bayan ta tare da cire towel din dake jikinta ya fara bata zafafan abubuwa masu rudar da kwakwalwa gabadaya sun manta komai sun shiga cikin shaukin farantawa junan su wand ba karamin kewa sukai ba kasa rabuwa da juna sukai sunajin tamkar su dauwama a haka Yarima kan ya nuna mata yadda ake missing don har saida tayi kuka ya rabu da ita. Washe gari suka je asibiti akai mata scanning kuma an tabbatar yan biyu ne maza wai murna dama ba'a mgn ba kunya Yarima yana kallon dasu mai martaba a gurin amma ya rungumi dady yana masa albishir ba iya su mama ba hatta mai martaba saida ya masa dariya. Cikin tsokana Hajiya tace"baban mazaje wato gasa kake dani don kaga yayana duk maza kaima kake haifar maza ko"? hade rai Yarima yana kallonta zaiyi magana yaji mama tace"amma baby tafiyar da zakayi kai kadai zaka koma daga baya idan ta haihu ta biyo ka "? ba kunya ya tada rigimar tare zasu tafi mama tace bai isa ba mai martaba yace ta barsu su tafi dole ta hakura tun dare suka gama shiri washe gari kamar wanda ake korarsu tun wuri suka wuce mama har mamakin wannan sammakon nasu tayi. Ba karamar tarba suka samu ba gun aunty Feshen ba tayi murnar dawowar su har ba iyaka ta rungume Ahmad tana masa barka da dawowa duk da yaso manta ta. Karfe shida Umar na harabar gidan da ball a hannunsa wata buturiyar yarinya ta shigo da murnar ta tana tambayarsa ina Ahmad. Umar ya riga yasan halin Ahmad don haka ya sheka mata karya cewa sun fita da dadynsu tare fita tayi tana ce masa idan ya dawo tana nemansa zata dawo fitowar Ahmad kenan Umar ya fesa masa July nazo nemansa. Ahmad dake rike da wani kyakkyawan agogo yana shirin budeshi a kwallinsa yace"me kace mata"? dariya Umar yayi yana cewa"nace kun fita kaida dadynmu shine ta tafi amma wai zata dawo kana da farin jini"harararsa Ahmad yayi yana cewa"rufe min baki haka kada wani yaji muje mum tace na kira ka "juyawa sukai suna shiga ciki gidan dariya sosai Umar keyi abin na cinsa kuma ya kasa fada Zainab tace"bansan haukan ka rufa ma mutane baki "rufe baki Umar yayi yana kallon Ahmed daya zuba masa ido dan yasan dashi yake yace"mum juliana ce tazo neman sa "matsowa Ahmad yayi zai rike shi yana cewa "wannan munafiki mum karya yake bata zo nema na ba "Zainab tace"to naji zo zauna inma tazo neman ka mizaka mata share abbana tsokana yau yake ji da ita. 🌹Mrs Al'ameen Ahmad* Aminci ga mufitahul jannatun na'ima. Aminci ga kiblar bayi a ran kiyama. Aminci ga mai shiryawa cikin salama . Aminci ga duk mai matsayi dakai ya samu . Aminci ga duk mai girma dakai ya samu . Aminci ga duk mai daraja dakai ya samu. Aminci ga fatuhul-akbar aya imamu Yusrah Musa ce tare dani da gaisuwa ta. 👏🍒🍒🍒🍒🍒. [11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲 *👑Yarima Abdul-malik*👑 *ANNURI WRITER'S ASSOCIATION*💫 #Yusrah Musa Abubakar Dedicated to Maman khaleel Zarah Musa 🅿️1️⃣5️⃣ Satin su uku da komawa London Ahmad da Farouq suka fara zuwa makaranta Zainab ma wata babbar makarantar Yarima ya sai mata don ta sake kwarewa akan fannin couse din aikin likitanci. Salmah na da ciki itada Hajara mama ke fada ma Zainab harda murnarta zata je Nigeria amma Yarima yace ko airport baza taje ba ta dauka wasa yake saida suka haihu taga ya dauki iya Ahmad sun tafi harda kukanta amma yayi kamar baisan me take ba itama tayi fushi dashi daya kirata a waya taki dagawa har ya dawo kuwa, duka mace suka haifa 'yar Salmah taci sunan hajiya Aisha 'yar Mahmud taci sunan Zainab suna ce mata Amra. Bayan yan watanni Zainab ta haihu 'yan biyu maza murna dama ba'a mgn kamar yadda Yarima yace haka yayi ranar suna sukaci sunan dady Yusuf da Abba Ibrahim su Fati kam anzo suna sai farin ciki ake don Musty cewa yayi daga nan zasuyi honey moon dinsu kullum sai sun fita shida Fati sunga gari Zainab cikin tsokana tace "Allah idan kikai wasa kafin ku koma zaki jewa da ammi tsaraba dan naga abin naku ya wuce gona da iri "Fati dake dariya tace" to dafa me kike tunani sai kuje suna "harararta Zainab tayi zatai mgn mama ta karaso gurin sai kawai tai shiru. Ahmad da Farouq kullum sai sun fita da Rufaidah ya nuna mata abubuwa har mama na tsokanar sa tace"babana kodai son rufaida kake? idan 'yar gida za'a yi shikenan mun huta "tun kafin Ahmad yayi mgn Farouq yace"tab that mean war kenan wallahi idan July ta ganta akwai yaki domin a school din mu ba wacce take kula shi sun san halin ta tsoron July suke masifaffiya ce sosai"duka Ahmad ya kai masa cikin hade rai yace "karya yake grandy ni July ba sonta nake ba ko sallah fa yan gidan su basayi me zanyi da kirista"ya fada yana kaiwa Farouq wani sabon dukan. Murmushi mama tayi tana cewa "to kinji fa dota danki nada farin jini tun yana yaro ya fara tara masoya gashi har kin samu suruka wai July ". Dariya Zainab tayi tace"akwai wata 'yar bayan gidan mu itama sonshi take sunanta sweety ai inaga kawai idan zaku tafi zai biku yayi karatun shi acan daga baya ya dawo muma hankalin mu zaifi kwanciya". Bata fuska Ahmad yayi yana cewa "nifa mum karya yake min ba wacce take sona". Fati tace"dama nasan sharrin zeey ne rabu da ita me zakai dasu ga Rufaida kawarka ita kake so"kin mgn Ahmad yayi mama tace "a'a ku kyale min babana shi babu wacce yake so tashi tafi kada su takura min kai su hana kayi karatu "mikewa yayi yana barin gurin ganin Farouq zai bishi ya dau sandan da suke buga ball yana nuna shi yace"idan ka biyu ni "dariya Farouq yayi yace"to wazai jefo maka kwallon da zaka buga idan ban biyo kaba"banza ya masa ya wuce da gudu shima Farouq din ya bishi don kar yasawa kofar lock. Haka rayuwa taci gaba da tafiya lokacin Fati itama ta kusa saukewa amma Zainab bata sa rai da zuwa ba don tasan Yarima bazai barta ba. Batasan ma anyi haihuwar ba sai ana gobe zasu tafi yace tayi shiri fati ta samu yan biyu murna agun Zainab kamar ya mata albishir da aljannah harda wani abokin Yarima mai suna Abeed da matarsa suka tafi yace yana so yaga yadda Nigeria take itakam Zainab bata taba ganin sa ba amma musulmi ne. Ba karamar tarba suka samu agun mama ba yaran kuwa gabadaya suna gurin mai martaba Salmah da ta shigo tana musu barka da zuwa dariya Zainab tayi tana kallonta tace"wallahi Salmah yaranki duka da Abba suke kama "Salmah data harareta tace "to dani kike so suyi kama ai akace kyan da ya gaji ubansa oho dai kema nakin da dadynsu suke kama "dariya mama ta musu tace "yau kuma shirmen da zakuyi kenan"? Salmah tace"dan Allah gane min hanya aunty wai makaho yaso gulma abinda na fada gaskiya ne"mama tace"a'a ni babu ruwana karma ku sako dani". Washe gari suka wuce kano aka debi garar suna inda namijin yaci suna Abdul-malik macen Zainab anan take cikin tsokana fati tace"sai mu rika ce musu baby da dota". Wata uwar harara Zainab ta bata tana fada harda kufan baki dama tasan tsokana tasa suka saka sunan su wallahi bazai yiwu suna kirar mata sunan miji ba. Musty yace"ni Abdul-malik dane a gurina dan haka boy ma zan rika cewa yaron"fati na dariya ganin yadda Zainab ta tsime tace"hum haba dota arziki nefa kayi bako ya yanka ka mene dan munce haka kudin yayan mune"duka Zainab takai mata cikin haushi. Satin su biyu a kano Zainab tace zata wuce bauchi gurin su Addah ta bawa mama su Ahmad ta koma dasu Abuja mama tace a'a taje dasu suma agansu tare da Salmah suka wuce babbar karba modibbo yayi musu Yarima sbd ya baro Abeed a Abuja da yayi kwana daya sai ya tafi ya barsu daga baya zasu taho. Da tayi sati biyu itama ta koma Abuja dan Salmah ta riga ta tafiya komawar ta da kwana uku sukai shirin tafiya london Mahmud a gaban kowa yadau Amra yace ya bawa Yarima kyautar ta kowa yayi mmk saidai sunsan da dakuma yanzu ba daya bane godiya sosai Yarima ya masa ya kuma karba hannu biyu . Tun dare Yarima yacewa Abeed zai wuce dasu Ahmad london su zauna a gurin sa kafin su karaso yana son Zainab zatayi hajj ne. Zainab basan sunyi haka da Abeed ba tunda Yarima bai fada mata saudia zasu tafi ba saida washe gari suka je airport taga abu saba'in hankalinta. Cikin mamaki tace"soulmate ya naga haka? ina kuma zamuje naga ka bawa Abeed yaran gabadaya "? bai bata amsa ba sai gurin Abeed dayaje sukai mgn kasa kasa sannan ya dawo inda take ganin yadda tayi da fuska yasa Yarima yayi murmushi tana kallo jirjinsu ya tashi ta dauka wasa yake mata amma sai taga ko a jikin sa. @Mrs Al'ameen Ahmad. [11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲 👑Yarima Abdul-malik 👑 💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫 Dedicated to ❤Maman Khaleel Zarah Musa dan Adam #YUSRAHMS ABUBAKAR # 🅿️1️⃣6️⃣ Kuka ta fara yi masa ganin ana kallonta yasa yace"haba princess so kake mutane su dauka sato ki nayi? kinsan Abeed balle kice zai sayar miki da yara". Cikin shagwaba tace"to ba kana jina ina tambayar ka ba ka rabu dani kuma kasan aida zafi raba d'a da uwarsa" Yarima dake kallonta ganin da gaske take maganarta yace "to princess koda ma ace Abeed sayar dasu zaiyi ai ba damuwa tunda zaki sake haifa min wasu bibiyu sau biyar kinga goma kenan har sun ninka na da ". Make kafada tayi tana cewa "nidai a'a bana son wasu ni yayana nake so dan bazan samu kyawawa kamar su ba". "Tab waye ya fada miki zaki samu finsu ma kalli mana ai dadyn sune kyakkyawan ". Kai ta girgiza "nifa bana so kawai kace masa ya kaiwa aunty Feshen yaran kafin mu koma danni ban yarda dashi ba"murmushi Yarima yayi cikin tsokana yace"Allah yasa kafin mu koma ya sayar dasu sai naga yadda zakiyi kodan gaba ta kaimu shikenan mun dawo sabi dal kamar amarya da ango wani ma inya kalle mu sai yayi tunanin honey moon zamuje "rabuwa tayi dashi karshe daya dameta sai kawai ta toshe kunne karma taji me yake ce mata. Sai dare suka sauka ga mamakin ta wani matashin balarabe ne yazo ya dauke su kuma taji suna larabci da Yarima ko a mafarki batai tunanin ya iya ba. Matarsa da farin ciki ta karbe su sakamakon tasan Yarima shekaru da suka wuce liyafa mai girma aka hada musu Zainab kam saida turanci suka gaisa ashe abokin Yarima ne a US suka hadu sunansa Aliyu shima yaransa biyu Aynul-hayat da Afrahim sun juma suna hirar yaushe gamo Aliyu na tambayar sa ina yaransa yace suna London suma sunzo yin sallah ne. Bayan sunyi hajji ma basu tafi ba saida suka sake kwanaki Zainab harda rama tayi sbd tunanin su Ahmad ranar da zasu tafi murna kamar tayi fuffuke ta ganta a London haka taji Yarima na hankalce da ita amma baiyi mgn ba dan a yadda yaga tana zumudin nan saiya hora ta kafin ta gansu. Lokacin da suka isa London karfe biyar bayan sunyi wanka sun huta Zainab ta tayar da rigima tana cewa " tunda mun dawo kaje ka karbo su ko ka bani adireshin gidan Abeed din ni naje da kaina na taho dasu" Yarima kememe yace" ba zanje ba kuma bazan baki wani address ba sai sanda Abeed yayi ra'ayi dan kansa ya kawo su idan kuma yace yana son su zauna a gurin sa na bar masa su kawai saiki haifa min wasu". Jin abinda ya fada yasa ta fara masa kuka amma ya rabu da ita ta dauka wasa ne abin nasa taga an shafe kwana goma da dawowar su Yarima yayi kirmishishi abinsa tana masa mgnr yara zaice ya barwa Jesmin da Abeed gara ta ware ta haifi wasu. Abeed kam baisan sun dawo ba har sukai wata guda dan duk wata hanya da zasu hadu saida Yarima yasan yadda yayi baya bi iya tashin hankali ta shiga karshe sai mama ta kira a waya. Cikin kuka tace"mama dan Allah kiwa soulmate fada kawai ya kama yabawa abeed yaran duka idan na masa maganar yaje ya karbo su sai yace wai bazai kyauta ya karbe ba ya riga ya bawa Abeed su gara na ware na haifi wasu ki jishi fa mama kyautar yara har hudu ga amra ta biyar dan kawai baisan zafin haihuwa ba". Ba mama kawai ba dady dake jin abinda Zainab din ke fada domin hand free mama tayi saida yayi dariya yace"dota in banda abinki aida wasa yake miki shi dinne zai iya kyautar da har biyar idan kika rabu da shi zai dawo miki dasu ganin kin damu ne yasa yake miki yawo da hankali ". Zainab tace"Allah dady idan na rabu shi shikenan ni dasu bada wasa yake ba dana masa zancen zaice karna dame shi akwai mutumin da yayi kyautar yaya goma kuma ya haifi wasu balle ni mai hudu". Murmushi mama tayi tace"dota har yanzu kin kasa gane halin baby ki kyale shi ki daina masa mgn da kansa zai dawo miki dasu ta ruwan sanyi "Zainab tace"wallahi mama idan na rabu dashi shikenan ni da su har abada"dariya sukai mata jin abinda tace dady yace"gaskiyar ki dota ki ta masa naci har ya gaji ya dawo miki dasu kinji ko". Shiru Zainab tai mama cikin tsokana tace"to mukam ba abinda zamuce saidai Allah ya mayar da alkairi "tana fadin haka ta kashe wayar tana dariya tace"kaji dota da wani shirme babyn ne zai iya kyautar da balle ba guda daya ba lallai da anyi ruwa harda Kankara". Murmushi dady yayi"zan kira shi naji dalilin maida yaran can kinsan shakuwar uwa da d'anta mama tace"babyn da zasu tafi nace ya barmin babana amma ya rufe ido ya tafi da kayansa balle ya bawa wani "dady yace"dama dan baza ta gane bane ta riga ta rude bari zan kira shi lallai ya maida mata karanta". Bani da chaji👉🏻📱 *🌹Mrs Al'ameen Ahmad*. [11/25, 5:29 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲 👑Yarima Abdul-malik 👑 *ANNURI WRITER'S ASSOCIATION*💫 *@Yusrah M Abubakar* 🅿️1️⃣7️⃣ Watan su Ahmad biyu sannan Yarima yaje ya karbosu murna kam Zainab tayi ta kara har saida taso bawa Yarima dariya ya dan kalleta yana murmushi yace"momyn twins dina sai hankali ya kwanta gasu nan na dawo miki dasu sai rigima ta kare"ya fada yana kallonta harararsa tayi tana hada yaran ta suka bar palon. Mikewa Yarima yayi yana bin bayansu yace "a'a wallahi baki isa ki raba yara da dadynsu ba gara na biku bansan kus-kus din da za'a saka musu ba dan naga kina min kallon uku saura sisi". Yanzu komai alhmdllh zainab an zama likita babban asibiti Yarima ya gina mata da kwararrun ma'aikata wadanda suka san abinda suke yi nan da nan ta shahara kowa ya santa ta zama hamshakiya babbar mace. Bilki duniya ta nuna mata halinta tayi kuka tayi nadama musamman ranar da Hajiya Asma'u taje har gidanta ta fada mata Zainab ta samu danginta kuma tana cikin kyakkyawar rayuwa abin yabawa tayi bakin ciki rashin haduwa da Zainab har ta gode Allah amma tasan zai wuya idan zasu sake haduwa a duniya. Hajara ta sake haihuwar namiji Mahmud yasa sunan Yarima kowa yayi farin ciki kuma sunzo suna Yarima yayi bajinta sosai a bikin sunan ya zubar da naira ta mmk su mai martaba sun cika da murna ganin komai ya zama daidai yanzu babu wata matsala Yaha dama ba'a magana an shiryu ta gane gaskiya idan kaga suna wasa da dariya da kowa sai abin ya baka mamaki. Zaune suke a palor suna hira cikin nishadi Farouq ne ya shigo yana dariya da alama daga makaranta suke yayin da Ahmad ya biyo bayansa rike da hannun Amra yana harararsa karasowa palon sukai. Amra tace"mummy yau wasu a makaranta sukai fada akan bros dina harda baki aka fasawa wata a cikin su tana ta kuka"da mamaki Zainab tace"su waye suke fadan a kanka? kaga fa bansan iskanci ka daina shiga safgar yaran mutane kana sawa suna fada yaudin su waye sukai fadan"?. Shiru Ahmad yayi baiyi magana ba amma ya cika yayi fam dashi kamar zaiyi bindiga cikin tsokana Amra dake gaban fridge tana tsiyaya juice tace"wai sonshi suke da friend daya ma cewa tayi duk wacce bata daina kula shiba saita zo da wuka makaranta ta kashe ta". Zaro ido Zainab tayi tana cewa "subhanallahi abin yayi yawa yayan su waye ne wannan wai Ahmad ba kai nake tambaya ba ka bani amsa "wani tagumi Ahmad yayi yana kallon Zainab yace"mum karya fa take ba wanda yayi fada a school din mu ". Cikin sauri Farouq ya dawo kusa da Zainab yana cewa "wallahi mumy ba karya Amra take ba kinsan July ta gidansu Elijah? kai Zainab ta daga Farouq yaci gaba "to itace suke fada da pretty kowa son bros take shine angeli tace duk yarinyar da taga ta sake masa mgn sai ta zubar mata da hakora". Zainab tace"ina abin bai kainan ba gara a sauya masa makaranta ba zafi"Amra tace "mum ranar ma viki sunyi fada da nazi dakyar aka raba su"kallon Yarima Zainab tayi taga ko a jikinsa". Tace "kana jin mufa dan Allah kawai a sauya masa school ni bana son tashin hankali ko kuma a mayar dashi gurin mama yayi karatun sa acan muma hankalin mu zaifi kwanciya". Murmushi Yarima yayi yana kallonta yace"babu inda boy dina zaije yana nan tare da 'yan uwanshi dan wasu yara na fada akanshi duk haukan su suke mai zaiyi da kirista idan ya tashi aure a mutum biyu zai zabi daya ko dai ya auri 'yar gidan Abeed minat ko kuma 'yar gidan Aliyu Aynul-hayat amma ba wata viki nazi da zai so. Dariya Farouq yayi yana kallon Ahmad yace"ni kuwa dama nace sultana Aisha nake so bros kuma na zaba masa Aynul-hayat tunda balarabiya ce"Zainab tace"a'a duka biyun zai aura shikenan ina da suruka baturiya da balarabiya"bata fuska Ahmad yayi yana mikewa yabar palon Farouq yabi bayansa shi da Amra akabar iya twins. Yarima dake kallon Zainab yace"kinyi waya da small mum dina suna lafiya"? cikin rashin fahimta Zainab tace"wacce haka"Yarima yace"matar Mustapha nake nufi shidin tunda uncle dina ne"Zainab dake shirin tashi ta koma ta zauna tana cewa "na fita fa ko lokacin da muke zuwa makaranta na girmeta". Murmushi Yarima yayi"albishirin ki ko shekara dubu kikai a duniya dole kice mata mama tunda babanki Mustapha ta aura inta kama kika tashi gaida ita ki rika durkusawa kamar yadda kike wa mama da dady" . Zainab tace"tab aikwa ba zata samu ba wuce nan"mikewa tayi zata tafi ya rike ta yana cewa "haba princess fushi kike dani soulmate dinki guda tafiya zaki ki barni"kafa ta fara bubbugawa cikin shagwaba tace"nidai a'a sake ni tunda ni yyarinya ce". Kara rungumeta yayi yace"haba mummyn boy waye yace ke yarinya ce bayan kina da zaratan samari har hudu kaga mum din Ahmad gatan Farouq ummin twins gaskiya ina mutuwar sonki mamata kin gama min komai a rayuwa burina Allah ya barmu tare ni da ke". Murmushi tayi tana cewa"nice ya kamata na maka gdy domin ka taimaka min a lokacin da nake cikin kuncin rayuwa kayi tattalina ka kareni daga makiyana kaban abinda har abada wata mace bazata samu ba kayi min kyautar xuciyarka bani da wata kalma dazan iya gode maka kawai saidai nace ina matukar kaunar bazan guje ka ba muna tare har karshen rayuwata soulmate ". Juyowa yayi da ita suna fuskantar juna cikin jin dadi kowa ke kallon dan uwanshi murmushi suka saki tare suna kara rungume juna daidai su Ahmad sun fito suka mike suna karasawa dining cikin farin ciki gasu ga zuri'ar su. *🌹ALHMDLLH* *Masha Allah* *Ya Rabbi salli ala sahibul mukami Annabin da mai sonsa bai zama a hammi sa alihi da sahabban sa zul kirami a'alal ula duk makiyin su ya makanta*. #YUSRAHMS ABUBAKAR # Ana tare 'yan ANNURI gaisuwa mara adadi. *Mrs Al'ameen Ahmad ce* . ❤🌹