🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *01* Ƴan Sanda ne tsaye a bakin babban titin garin wadanda a kalla sun tasar ma mutum goma, Ko wannen su riƙe yake da makami wato Bindiga,idan nace Bindiga,ina nufin asalin Bindiga lafiyayye,sun riƙe ta da kyau yayin da suka seta wata baƙar mota ƙarama na yayi wanda idan kaji kudin ta sai kayi mamaki, Jira kawai suke motar ta motsa su bata wuta tamkar yanda sugabansu ya umurce su akan haka, Babu wani fara'a ko digon imana a tare da waɗannan fuskokin kuma basa tunanin zasu sassautawa na cikin motan nan in har basu cika umurnin sun fito daga cikin motar sun mika kai tamkar yanda suka buƙata ba. Lekawa nayi cikin motar domin na gano wani shahararren mai laifi ne wanda wuyansa ya gawurta aka tare har haka,me yayi,sannan yanzun a wani irin tashin hankali yake ciki a zaune a cikin motar, Dan haka a hankali na fara lekawa ta cikin tagar, Sai dai kuma abinda na gani ba karamin mamaki da rikitar dani yayi ba,wanda har saida na kara murza ido na domin son tabbatarwa da gaske abinda nake gani haka ne,sai dai kuma ina kara budawa abinda na gani dai shine zaune ba wani ba,wato dai a takaice wata mace ce na gani zaune a mazaunin direba,wacce daga dukkan alamu ba tada wani girman jiki na azo a gani haka kuma daga zaunen da take zaka fahince ta na da tsayi dai dai gwargodo,bana iya ganin komai nata face ta gefen kunnen ta wanda take fari ne sosai irin tas dinnan,haka kuma suman dake gefen kunnenta yayi wani irin kwanciya mai ban mamaki,sai hannunta wanda sanye yake da bakin safar hannu irin mai kamawa,kamar yanda suman kanta yake a nade an mashi dauren donut sai dai a kwai facing cap a kanta,hancinta sanye yake da wani baƙin Nose mask,sai Jacket din dake jikinta shima baki ne mai dogon hannu,da kuma dogon bakin wando,a takaice dai abin da nake iya gani kenan a jikinta wanda ko kalar fakar ƙafarta baka iya gani, Itama wacce take zaune a gefen hagunta irin shigar dake jikinta kenan,sai dai abu ɗaya wanda ya bambanta su,ita wacce take zaune a gefen hagu jikinta rawa yake,sannan kuma ga hawaye dake fita a gefen idanunta,wanda yake fitowa kai tsaye daga cikin idanun nata,daga dukkan alamu a mugun tsorace take,saɓanin wacce ke zaune a mazaunin Direba koda ma ace hankalin ta a tashe yake,to bata nuna alamar da zai baiyana hakan ba,dan wata waka ce ma take saurare a rediyo motar,kuma har tana ɗan binshi tana gyaɗa kai,tana kuma kallon manyar ƴan sandar dake gabansu, Ɗayar ce a matukar firgice ta kalle ta gefenta tace"BIBA shi kenan mun kawo kanmu duniyar da za'a kashemu,waiyo Allah na,wani tsautsayine ya aikeni biyo ki Kasar Gambia🇬🇲,shi kenan Allah ya jikai na" Cikin wata iri yar murya mai matukar sanyi da zaki,wacce take fita a hankali ba tare da hayaniya ko tashin hankali a tare da ita ba,tace"me yasa kin cika surutu ne Ummita "ta faɗa tana kauda kai, Kuka ta fashe da shi" Yanzun BIBA har kina da bakin da zaki ce na cika surutu,yanzun ba ki ganin mutuwa a gaban mu,ke fa kika ce ba wani aiki mai wahala bane zai kawo mu,sai gashi yanzun kinsa ina fuskantar mutuwa kiri_kiri," Juyowa tayi ta kalleta "karki damu Ummita,dama ita rayuwa hanya biyu ce,kanada damar da zaka zabi duk wacce kake so,ko dai ka dauki hanya mai kyau,ko ka ɗauki mara ƙyau,to ni BIBA na ɗauki akasin mai ƙyau" Cikin mamaki mai tattare da tsoro tace"kina nufin mara kyau kika ɗauka? Murmushi ta sake wanda duk da ba gani kake ba saboda face mask amma ya baiyana a cikin kwayar idon ta"harda ke,hanyar dana zaɓar maki kenan"tana gama faɗin haka ta kunna motar tare da taka burki wanda nan take motar ta bada wani sauti irin na lafiyayyun motoci, Juyowa ta yi ta kalli inda Ummita ke zaune"kin iya ruwa? Da sauri ta girgiza kai tana ɗan leƙen babban rafin dake zagaye dasu,domin a saman titi suke wanda ya kasance kasan shi tafkeken rafi ne, "Ki daura Ballet da kyau" Kara cukuikuye Ballet din dake jikinta tayi, wanda dama tun fara tseren su da ƴan sanda a cikin gari ta daura dakyau dan tasan in dai tukin Biba ne tana iya fita ta windo, Wani irin kara motar ke fitowa dashi mai tattare da hayaƙi wanda tuni ya turnike wurin,karan harbi suka fara ji wanda ya fara sauka a kan mota, Kafin Yan sanda su fara gama tantace shin cikin su zata yi kome zata yi kawai cikin ƙwarewa da iya sarrafa sitiyarin mota ta daki wasu dakali da akayi ta gefen titi da karfin gaske wanda ya haddasa ma wurin fashewa kamar yanda gaban motar ta tarwase,sai dai wannan ba damuwar ta bace,kara dawowa baya tayi a ƙaro na biyu,ta fisge motar wanda nan take suke sunduma a cikin wannan tafkeken Rafin daga ita har motar, Duk jami'an daje wurin da gudu suka nufe rafen suna lekawa domin kuwa ba kamin shammatarsu tayi ba,basu taba tsammanin zata iya faɗawa acikin wannan ruwan ba, Wanda ya kasance Oga a wurin ne yayi ƙwallo da wani block dake gefen shi yana faɗin "ohh shet," Daya daga cikin su ne yace"oga yanzun me abinyi domin daga dukkan alamu ta mutu domin motar ta nitse a cikin ruwa" Cikin matsifa yace"koda ace ta mutu ina bukatar gawarta,ina bukatar gawar wannan yarinyar," "Oga tunda ta mutu me zai hana mu bar ma kifaye su cinye" Wani irin lafiyayyen mari ya zuba mai yana cakumo kwalar rigar shi "kasan kuwa me ta sata,kasan me a hannun ta kuwa,to bari kaji,abinda ke hannun ta yafi kuɗi daraja,yafi zinari daraja,dole koda gawarta ne a nemo a cikin wannan ruwan ina bukatar ta" Ya faɗa da ihun takaici yana wurgi dashi gefe,domin yasan idan har ya kama wannan Hatsabibiyar Yar Tsanar to ba karamin warkewa yayi ba daga shi har dangin shi,matsayi kuwa a gwamnati sai wanda ya zaɓa. Kallon sauran yaran shi dake tsaye yayi "aje a dauko injin mai tsamo mota a ruwa a ciro su" Cikin girmamawa suka Sara mai..... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *02* A cikin ruwa kuwa cikin kwarewa ta cire Ballet din dake jikinta sannan ta buɗe wani karamin jakka data ɗauko daga bayan motar,da sauri ta buɗe ta dauko wasu abubuwa guda biyu na zukar numfashi a cikin ruwa mai dauke da wani ɗan ƙaramin contenar na gas,sai glass na ido, shima wanda ke hana ruwa shiga ido, Jawo Ummita tayi ta cire mata bellet wacce ke ƙoƙarin suna saboda ruwan da take shaka, Saka mata abin tayi a hanci,ta goya mata karamin tukunyar,ita ma abinda tayi kenan,sannan ta tallabi Ummita ta fara iyo da ita ta kasan wannan rafin,wanda a ƙalla sai da tayi iyo da ita a wannan ruwan na tsayin mintina Arba'in tsakanin su da inda suka faɗa,sannan suka fito, Zuwa lokacin ita kam Ummita da kyar take numfashi koda ta yi wurgi da abin hancinta,ta cire gilashin daya taimaka mata wanda ya hana ruwa shiga idonta, Kwantawa tayi kawai tana maida numfashi,tare da jira taga kuma me zai faru, Jin motsin tafiya ne yasa ta daga kai tana bin Biba da kallo,wacce taga ta nufi wata Blue mota mai kama da tazi,hannu tasa ta bude bayan motar ta dauko wani lede babba ta daura saman motar, Abu na farko data fara yi shine cire wannan facing cap din dake kanta ta yar a kasa,wanda hakan yasa saida na kusa kwarewa saboda ganin irin zubin hallitar fuskarta,wanda yake fuska ne mai ɗan faɗi,dan ba zaka kira shi da mai tsayi ba,mai dauke wasu irin dara_daran zagayayyun idanu masu matukar haske da girma,cikin kwayar idon kuwa baki ne wuluk yayin da farin yake tamkar tsaftaccen madara,tsabar fari wanda ba karamin kyau yama idanunba,giran idanunta razo_zaro ne tamkar yanda giranta yake a cike mai tattare da wani irin shape yanda kasan an mata kabin gashi baki kirin, Hancinta ba shida irin tsayin nan sosai,sai dai ba zaka kirashi da mara tsayi ba ko gajere,ya dai zauna sosai kamar yanda ya dace da fuskar, sai kuma labbanta masu matukar taushi da tsantsi ma dai-daita,masu matsakaicin faɗi,haka kuma tana da haƙora fari tas wadanda suke ƴan madaidaita yanda kasan na yara,masu matukar jan hankali,kuskar Biba kadai can iya jan hankalin mutum ya shagala ga kallon ta, Jacket din saman jikinta ta cire ba tare da tunanin komai ba ta daga rigar dake kasan jaketa din wanda yake fari ne, Kai jama'a tsarki ya tabbata ga Allah wanda yake makagin dukkakn hilittu, Idan ka kalli tsarin halitar kirjinta wanda yake a cike a cikin Pink din Bireziya ka gangaro zuwa shafaffen cikinta wanda ya haɗe da baya,idanunka suka sauka a saman ɗan ƙaramin ramin Cibiyar ta wanda ya shige canciki, yayin da aka makala wani ɗan ƙarfe mai matukar jan hankali a wurin wanda na tabbatar na zinari ne saboda yanda wurin ke daukar ido,maranta a shafe yake sosai babu alamun tudu ko wani abu, Takalmin ƙafarta ta cire sannan ta cire dogon wandon dake jikinta,ya rage daga ita sai pant,jama'a ba zan iya cewa komai ba sai dai ku kwatanta yanda tsarin halittar kugun Biba yake,sai dai abun da zan iya faɗa shine ba tada mugun Hips madaidaicine mai matukar jan hankali,kamar yanda fatar jikinta yake sumul yanda kasan na tarwada tsabar tsamtsi,babu wani tamurewa ko tattarewa a tare da fatan kamar yanda babu nankarwa ko rakainuwa ne oho,babu shi dai a jikinta, Juyowa tayi ta kalli Ummita wacce ta taso ganin yanda take tube kaya, Jawo ledan tayi ta ciro wasu kaya ta mika mata"kiyi sauri ki saka mubar nan wurin domin nan da minti ishirin jirginmu zai tashi zuwa NIGERIA" Amsar kayan tayi ta warware tana kallon ta"Biba ina kika samu kaya" Ba tare data juyo ba tace"ba nida lokacin amsa maki wannan tambayar kawai kiyi abinda nace in kina buƙatar kasancewa a raye" Bakinta taja ta kulle yayin data hadiye dukkan tambayar da take dashi,idan sunje gida ta jero mata su. Dukansu riga da siket ne na atamfa sai jallabiya irin wacce ake ma lakabi bi After dressing,shi suka saka,sai kuma Sun glass na ido babba wanda ya kusan cinye rabin fuskar tasu, Kayansu ba iri ɗaya bane kowa da irin nashi, Kayan da suka cire ta kwashe ta maida cikin leda,harta daure ledan sai kuma ta sance da sauri ta ciro wandon data cire,hannun ta saka a aljihum wandon ta ciro wani karamin leda,ta buɗe,sai ga wani ɗan ƙaramin Memory Card, Maida wandon tayi cikin ledar sannan ta wurga ledan cikin wannan katon rafin, Motar suka shiga yanzun ma itace a mazaunin direba,kafin ta tayar da motar ne ta mika hannunta ta dauko wani karamin jakkanta wanda yake ɗan madaidaici ne irin na ƴan matan yanzun,buɗewa tayi ta duba passport dinsu,sannan ta ciro wata Android phone ta saka wannan Memory a ciki,ta maida cikin jakkan, Sai da tayi Ribas sannan ta ja motar da karfi suka bar wurin,wanda tafiyar minti goma ya kai su Airport, Lafiya aka gama caje su kafin a basu damar shiga cikin jirgi,wanda gaba ɗayan su a lokacin da suka ji jirgin ya lula sararin samaniya dasu suka sauke ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya,yayin da ita kuma take ƙara damke jakkan dake rike a hannun ta,tana mai fatan saukarsu lafiya.. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *03* Misalin karfe biyar na yamma jirgin su ya sauka a garin Abuja cikin aminci, Suna fitowa daga cikin Airport din tsayawa tayi tana ƙare ma jeren motocin dake wurin kallo,kafin ta sauke idanun ta a kan wata lafiyayyen Mota mai numfashi wanda wani matashi ke jingine a jiki, Kauda kai tayi tana tare taxi da hannun wanda nan take ya tsaya,da sauri Ummita ta buɗe ɗayan gefen ta shiga,dan ba a karamin gajiye take ba, Harta dafa marfin mota zata shiga taji an riƙe marfin,dagowa tayi dan ta ga wani isasshe ne, Kallon sama da ƙasa take masa wato dai wannan saurayin ne na jikin motar nan, Dan murmushi ya sakarmata "Barka da dawowa Biba" Ƙoƙarin shiga mota take yi ba tare da tace masa komai ba, Da sauri ya kara cewa"Sorry ban lura da ku bane,sannan Oga yace na dauko ki" Sai da ta zauna da kyau sannan ta jiyo ta kalleshi"bana bukatar zuwa inda yake yanzun domin a gajiye nake"ta faɗa tana kulle marfin matar, Kasancewar glass a buɗe yake yasa yace"to ki bani sakon na kai masa,domin a matse suke,yanzun haka sun haɗu ke suke jira" Wani banzan kallo ta watsa mashi wanda sai da gabbanshi su kayi sanyi"ko su da suka aikoka basu isa su sa na yi abinda banyi niya ba balle kai ɗan aiken su"kallon direban tayi "muje mana" Ta fada tana jan tsaki, Cikin sauri yace"ga katin Hotel din da zaki sauka,an riga an shirya maki ɗaki, Amma tuni sunyi gaba tunkafin ma ya karasa faɗin abinda ke bakin shi, Shafa kanshi yayi yana tunanin shi ta ina ma zai fara yaje yace ma Minista tace ko shi bai isa ya karɓi abinda ke hannun ta ba,kai lallai wani abu sai Biba, Motar shi ya shiga ya bar wurin. A wani Hotel mai suna Majestic suka sauka,wanda yake ba wani babba bane anan suka kama ɗaki daya ita da Ummita, Suna shiga dakin ta kalle ta "Ummita kiya mana order abinci dan yunwa nake ji" Ta fada tana wurgi da jakkanta kan gado"yauwa ki hado da kayan da zamu saka" "Ba yau zamu koma gida ba" Hanyar wata kofa tabi wanda take da tabbacin bayi yi,"sai zuwa gobe" Ganin ta shige bayin ne yasa ta jawo jakkan data ajiye ta bude, wasu wayoyi ne a ciki kusan guda uku,daya daga ciki ta ɗauka ta buɗe bayan marfin,sai ga sim card a faɗo,ɗauka tayi ta saka acikin wayar sannan ta kunna, Dama kuma su nada Company da suke ordan abinci,nan ta danna masu kira,bugu biyu kuwa aka dauka nan ta faɗi kalan abincin da suke buƙata,sannan ta masu transfer na kuɗi harda kalan kayan sawa da suke bukata, Ta dauki lokaci mai ɗan tsayi kafin ta fito wanka daure da ɗan ƙaramin tawol wanda da kyar ya gama rufe mata mazaune,idan kuma har za tayi kyakkyawar dukawa kuwa to tsaf za'a iya ganin jikin ta, Faɗawa tayi kan gado tana sauke ajiyar zuciya ta jawo filo ta rungume, Ko kafin Ummita ta fito wanka tuni tayi barci, Koda ta fito kallon ta tayi ta girgiza kai,ita dai tamkar wacce ba tada wata damuwa a zuciyar sai dai in bata kwanta da sunan barci ba,nan take kuwa barci zai dauke ta, Ganin haske a wayar ta ne yasa ta dauka ta kara a kunni,cewa kawai tayi"ok"sannan ta kashe wayar, Bata damu da saka wani abu da zai rufe mata jiki ba ta fita a haka daga ita sai karamin tawol ita ma irin na Uwar dakin ta,sai dai ita nata ya danfi sauka duk da bai gama kaiwa guiwa ba,a haka ta buɗe ƙofar dakin da suke ta fita, Kasancewar Hotel din mai dan girma ne kuma ba laifi a kwai mutane kowa na harkan gaban shi,amma duk da haka duk inda ta gifta sai ta ja hankalin jama'a,domin kuwa ita ma ba baya ba wurin ƙira sannan zama da Biba dole ta koyi kyaran jiki, Ba abinda ya shafe ta a haka ta je ta amso kayansu ta dawo dashi, Zama tayi ta ci iya wanda zata iya ci sannan ta ajiyewa ma Biba nata,dan tasan idan tana barci bata son a tayar da ita... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *04* Washegari kuwa basu baro Hotel ɗin ba sai zuwa yamma,dama kuma ya garin Abuja yake in dai yamma tayi da traffic,yau kuma sai abun yayi yawa fiye da kullun, Taja tsaki yafi a kirga ta kalli Direban Texi da ya dauko su"Malam hala dai akwai abinda yake faruwa ne a garin nan yau" Dariya mutumin yayi "hala dai Hajiya baki da labarin yau a garin nan muna da babban baƙo" Ummita ce tace"Babban baƙo kuma,daga ina? Na ga dama ai garin Abuja kullun cikin karɓar baƙi muke,abun dai na yau ne naga yayi yawa" "Ai in fada maki Hajiya yau babban malamin nan wanda ake ji dashi a kasa baki daya shi ne zai kawo mana ziyara a garin Abuja,kuma ga shi jama'a daga ko'ina a faɗin Nigeria zuwa suke domin halarta wannan taron Wa'azin" "Ni kuwa waye wannan malamin" Dariya yayi "Bara dai na faɗa maki sunan da Matasa ke masa laƙabi da shi,wato YOUNG USTAZ" Lumshe ido tayi sakamakon faduwar gaban da taji haka kawai daga jin sunan da aka kira,dama kuma tun tambayar farko data mai bata kara fadin komai ba duk maganar da suke tare da Ummita suke, Maimaita sunan Ummita tayi "Young Ustaz kuma malam,maimakon naji kace Shik wani ko Malam wani" Murmushi yayi"saboda ko ke kika gan shi kinsan ya dace da a kira shi da young din,domin kuwa shi din yaro ne matashi wanda yake ji da ɗanyen ƙuruciya,da kuma baiwar ilimin Addini da Allah ya mashi,hmm young ustaz kenan,duk yanda ake maki bayanin shi to ya fi nan sai dai kin gan shi kawai,yauwa yau ki kasance a gaban talabijin za'a hasko wa'azin,zaki ga yanda tsantsar kyau da kamala ke zuba,za ki ga...... Da sauri ta katse shi saboda ji tayi kamar kanta na juyawa"ya isa haka Malam sauke mu a nan" Tsayawa yayi kuwa suka sauka a bakin wani gida matsakaici mai matsakaicin ƙyau, A kwai mai gadi a ƙofar gidan,wanda yana ganin su ya mike da sauri ya buɗe masu karamin kofa yana gaishe su, Gidan akwai fili sosai ga wurin parking motoci,wanda naga manyan motoci masu matsifar tsada guda uku,kaloli daban-daban, Tsayawa tayi a bakin korido tana jiran Ummita data je dauko makulli a ƙasan wani tukunyar fulawa, Tana daukowa tazo ta buɗe suka shiga, Sake baki nayi ina kallon ikon Allah,domin falon karan kanshi abin kallo ne,dan ba karamin dukiya aka kashe mashi ba,zaka iya yin mamaki ganin irin wannan haɗaɗɗen falon a cikin wannan gidan, Ko wacce wani kofa naga ta buɗe ta shiga wanda daga dukkan alamu nanne ɗakinta, Zama tayi a bakin gado tana sauke ajiyar zuciya, Rinbon ɗin dake kanta ta cire tana ba suman kanta damar zubowa har gadon bayan ta, Ɗayan wayar ta ciro daga cikin jakkan tana saka Sim card din data cire a bayan wayar ta kunna,kafin ta gama kawowa ne naga ta jawo dirowar dake gefen gado ta ciro wani kwali wanda ban gane me a ciki ba sai lokacin dana ga ta zaro karan sigari ɗaya,zaro ido nayi ina jira inga me zatayi dashi, Ban gama mamaki ba kawai sai gani nayi ta kyasta mai wani ɗan abu karamin mai dizai wanda wuta ya fito daga cikin shi, Sakawa tayi a baki ta mishi kyakkyawan riƙo tana zuka a hankali tare da busa hayaƙin ta baki da hanci, Ummita ce ta shigo ɗakin,kallon ta tayi, sai dai babu wani alama na mamaki data nuna dan ganin tana shan taɓa,sai ma cewa da tayi, "Biba yau akwai fita ne? Kafin ta bata amsa ne wayar dake hannun ta ya shiga ƙara,sai dai bata ɗauka ba sai ma kallon Ummita da tayi" Muna da baƙi anjima,ki tabbatar kin kira Sara tazo ta gyara gidan nan dan yayi kura,ki kuma kimtsa kanki" Gyada kai tana kallon wayar Biyu da ake ma three miss call,amma bata ɗauka ba"to Biba,bara to naje na fara gyara jiki na" Bata bata amsa ba sai ɗaukar wayar ta da tayi,wanda tana karawa a kunne naji ta ɗayan gefen ana faɗin "haba Biba ai har kin tayarmin da hankali" Shiru tayi taki magana sai zukan sigarin da take yi tana busar da iska "Biba kin dawo lafiya ya aikin,da fatan an samu nasara" "A ko wani lokaci nasara tana tare da Biba," Dariya yayi yana sauke ajiyar zuciya domin ba karamin daɗi yaji ba dajin wannan sanyayar muryar nata,"tabbas maganar ki haka take Biba,to yanzun yaushe zamu zo mu karɓi kayan" "Ƙarfe goma na dare a gida na"tana gama fadar haka ta kashe wayar, A nashi ɓangaren kuwa,rungume wayar yayi yana wani lumshe ido,Allah ya gani yana matukar kaunar Biba,duk da yasan yanada ya'ya waɗanda suka girma mata,yana da mata har biyu,kyawawa ga ilimi, Sai dai kyan Biba na musamman ne,bai damu da Karuwancin da take yi ba,ko kuma wasu harkallolin da take gudanarwa,ko shaye-shayen da take yi,shi dai in har zata amince ta aure shi wallahi yana iya rabuwa da matan shi domin ita,yana iya mallaka mata duk abinda ya mallaka, Sai dai kash,Biba ba su bane a gabanta,eh dole yace basu bane,domin shi kan shi da yake Minista yasan bashi kaɗai ne ke wannan haukar ba a kanta, Ita mutum ce wacce baka gane asalen ne burin ta a rayuwa,dan haka take da wuyar fahimta, A jiyar zuciya ya sauke yana daga wayar shi domin kiran sauran abonkan harkallolin su domin sanar dasu yau zasu haɗu da Biba a gidan ta...... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *05* Sai da ta ƙarasa zuke sigarin da ke hannun ta sannan ta tashi ta shiga banɗaki, Ruwan wanka ta tara tafashesshe a bahon wankan sai tururi yake, Wani loka dake cikin bayin ta buɗe ta dauko wasu goruna sun kai kala biyar sai wasu robobi guda uku, Wani irin sinadari ne a cikin waɗannan goruna wanda suke ruwa-ruwa,ko wanne sai da ta tsiyaya a cikin wannan ruwan,sanna ta buɗe robobin wanda gayayyaki ne kala kala a ciki,shi ma zubawa tayi,sai roban ƙarshe wanda ta dauko wani busasshen jan ganyen fulawa guda biyu ta wurga a cikin ruwan wanda nan take fulawan ya narke ruwan kuma ya koma wani irin ja mai fitar da wani irin sihirtaccen kamshi mai shiga fata, Fita tayi daga bayin ta jawo kofar, Kayan jikinta ta cire tas ya rage daga ita sai bireziya da pant,ta dauki wani mai a karamin gora ta shefe gaba ɗaya jikinta dashi, Sannan ta dauki wani karamin kafet ta shimfida a zauna,gyaran kumban ƙafarta ta fara yi cikin kulawa,tana shafa masu wani dan mai a kwalba wanda sai da ta kusa minti talatin kafin ta kammala sannan ta koma banɗaki dan tuni ruwan ya huce ya kasance dumi kawai yake dashi,duk wasu tsumin kamshi data saka mashi ya gama jika,dan haka karasa cire ragowar kayan da ke jikinta tayi ta shige cikin ruwan tana nitsewa gaba ɗaya har kanta, Ta jima sosai a bayin kafin ta fito ta shirya cikin wasu doguwar riga fara tas mara nauyi,rigar zan iya cewa ita da babu duk daya gomin kuwa rigar ta sauka har ƙasa,kuma dogon hannu gareshi,sai dai shara_shara ce yanda kasan lariya,sai dai wani dan yadi mai dan kauri wanda ya rufe daga rabin kirji zuwa haƙarƙari,amma cibiya a waje take,sai kuma daga ƙasan mara zuwa ƙasan duwawu suma a rufe suke da wannan yadin mai dan ƙauri,amma daga cinyarta har kasa ana iya gani, Zama tayi kan kushin tana kallon tashoshin waƙoƙin turawa hankalin ta kwance,dan lokacin ma ƙarfe takwas ta wuce, Ji tayi ana ta faman ƙwanƙwasa ƙofa,amma ko kallon wurin ba tayi ba, Ummita ce ta fito daki da sauri ta zo ta buɗe ƙofar tana tambayar waye, Ba tare daya kula ta ba ya shigo cikin falon yana kalle kalle,hango ta da yayi a hakimce saman kushin ne yasa da sauri ya karasa in da take zaune, A kasa ya zauna ya kwashi ƙafafunta ya daura saman cinyarshi yana dan mammatsawa a hankali tare da shafawa,sannan cikin marairaice murya kamar zaiyi kuka yace"Biba ina kika tafi kika barni,kin saka na koma tamkar mahaukaci a garin Abuja ina nimanki,amma kin dawo ko ki nime ni"ya karasa fada yana sumbatar tafin ƙafarta, Bata bashi amsa ba kamar yanda bata hana shi shafar ƙafarta ba, "Biba na yi kewar ki tamkar rayuwa," Matashin saurayin ya faɗa yana tasowa tare da kara tsugunnawa sosai a gabanta yana shakar wani ni'imtaccen kamshi wanda yake ƙara tashi daga jikin ta, Tana kallon shi ya matso da kanshi a hankali ya sumbaci lebbanta, Nan ma bata hanashi ba, Lumshe ido yayi yana sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya,ƙara sumbatar bakinta yayi a karo na biyu yana daura hannun shi a saman kirjinta ya shafa, Hannun shi ta cire daga kan kirjinta sannan ta kauda kanta daga kumbatar da yake mata, Kamar mahaukaci haka yake ƙoƙarin hawa jikin ta,dan wannan kamshin da yake shaka ji yake kamar zai zauce, Dakatar dashi tayi"ya isa haka Habib,ka tafi gida gobe zamu yi magana " Girgiza kai ya shiga yi"dan Allah,dan Allah Biba ki taimaka min,wallahi a matse nake,mayi kewar ki Biba ki taimaki rayuwa ko da romancing dinki ne ki bari nayi,nayi alƙawarin kome kike so zan baki,na maki aikawari " Mikewa tayi tsaye"kayi abinda nace ko kuma kai da ganina sai nan da sati ɗaya" Da sauri ya juya ya bar gidan domin yasan tabbas zata iya aikata abinda tace, Habib ɗa ne ga wani Senator,iyayen shi masu kuɗi ne sosai,shi kuma yana aiki ne a Central Bank,ba karamin kuɗi yake dashi ba, Sun haɗu da Biba ne a wurin wani party a club,ranar tayi shaya_shayen abinda yafi karfin kanta,shine ta bishi gidan shi suka kwana a can,tun daga lokacin yake haukan binta yana mata barin kudi sai dai ko akai bata kawo shi,wani lokaci ne ma in yaci sa'a takan ɗan kula shi, Ɗakinta ta shiga bata tsaya ko ina ba sai durowan dazu data buɗe wannan karon wani sacet din magani naga ta ciro, Daya ta balla ta zauna tana tattaunawa kafin ta kora da ruwa, Ko minti biyar ba ayi ba ta fara jin kanta na juyawa sakamakon kwayar data ci, Wani Albom naga ta jawo a ƙarƙashin gado irin wanda ake saka hotuna a ciki, Buɗe shafin farko tayi,wanda naga tana shafawa hawaye ya fara saukowa daga cikin idanun ta, Taba ta kuma kunnawa,yayin da ta tsayar da idonta a kan hoton wanda bana iya ganin ko fuskar waye, Ta ɗauki lokaci mai tsayi a haka kafin Ummita ta shigo "Biba sun iso tun dazu ke suke jira, Wurge ta kuma yi da Albom din kasan gado kafin tasa hannu ta share hawayen idonta,ta ɗauki wayar ta da hannu daya hannu ɗayan kuma na riƙe da karan sigari ta doshi wani karamin hanyar dake cikin falon ta wanda ya sadata da wani madaidaicin falo hadadde in da wasu Dattijai ke zaune su huɗu suna kiranta, Kallo daya zaka masu ka shaida cewa kuɗi sun zauna tare da hutu. Daya daga cikin su yana dariya ya tashi ya rungume ta a jikin shi "na san zaki iya Biba, shi yasa nace ba wanda ya dace da wannan aikin sama dake Biba" Ita ma dariya tayi tana zama a kan kafar shi bayan ya jata sun zauna saman kushin, Shafa gemun shi tayi"kai dai faɗi gaskiya kawai dai kasan babu wanda zai iya irin wannan kasadar sai Biba shi yasa dole dai aka nime ta" Amsar karan sigarin dake hannun ta yayi ya ajiye a saman wani karamin plate yana shafa bayanta tare da shinshinar hannunta zuwa dokin wuyar ta, Daya daga cikin su ne wanda zuwan shi wurin na biyu kenan ya ce"Haba Alhaji Mansur,wani irin zubar da girma ne haka,wannan ai tayi sa'ar yar cikin ka,ni gaskiya bana son haka, Kawai ta bamu abinda zata bamu mu ce"yana faɗa yana kallon inda Alhaji Abubakar ke zaune yana ta faman dariya suna zolayar Ummita wacce ita ma ke saman jikin shi dare_dare,shida Alhaji Rabi'u, Tashi tayi ta kunna wani karamin talabijin dake jikin bango a wurin,tare da soka wannan Memory din a jikin wani ƙaramin na'ura,ta daddana sai gashi ta kamo wani video, Wani katon mutum ne zaune a bakin gado daga shi sai ɗan garen wanda wanda har ta shafin gabanshi kana gani,babu riga a jikin, ga kuma manyan kwalaben giya a gaban shi sai sha yake yana dariya yana kallon wasu yan mata dake gabanshi,daya daga ita sai pant irin wanda turawa ke sakawa mara amfanin nan da bireziyarshi,daya kuma sikect ne a jikinta irin na Indiya mai faɗi,sai dai yanda kasan lafiya haka yake ɗan kana kallon komai na jikinta ga shi kuma siket din ya nada tsagu ta cinya har Kwankwaso, Sun kunna wata waka na yaren garin sai wani irin rawa take tana guyi tana karkada mashi kirji,sai dai kuma su ƴan matan ba a ganin idon su,sai dai bakinsu kawai kake iya gani, Sai shasshafa tsohon suke har suke cire mashi wannan guntun wandon dake jikin shi ya zamana babu komai a jikin shi, Inda video ya tsaya kenan, Abinda ya faru kuwa a can Gambia,bayan sun gama mai wannan rawar ne Biba ta bashi lemu yasha wanda ta zuba kwaya a ciki, Nan ya tuntsire yana barcin Asara,su kuma suka cire kemera suke wuce, To in da aka samu akasi shine washegari da managan ya zo duba abubuwan da suka faru a dakin manyan bakin su,dan suna yin haka wanda za'a goge a goge wanda za'a barshi a barshi,to anan ne mutumin yagani ta cctv, dace babban Hotel din sun ga abinda ya faru,ɗan shi mutumin babban VIP din su ne,domin kuwa ya fito takaran niman kujerar Shugaban Ƙasa a Gambia, Shine sukayi saurin sanar dashi shi kuma tamkar yayi hauka dan ya tabbatar in wannan video ya fita ya shiga uku,ko fita kofar gida sai ya gagare shi, Shine yaba yan sanda dama su kamo mashi Biba idan kuma sun ga zasu gudu su sake masu wuta,ya masu Alkawarin kome suke so zai basu,har balle Ogan su, Ita kuma Biba tuni tayi amfani da kyakwalwarta wurin fecewa daga Gambia da wannan kemeran.. Kallon su tayi" to gashi dai kamar yanda kuka buƙata aikinku ya kammala,"ta cire Memory ta damka ma Alhaji Mansur, Dukkanin su fuskar su dauke yake da maɗaukakin farin ciki domin kuwa bata san irin Alheri da Alfarma da zasu samu ba saboda wannan video, Kallon ta Alhaji Abubakar yayi"Biba me yasa tunda muke saka ki aiki baki taɓa tambayar mu akan me muyi dashi,ko kuma wani dalili yasa muke haka ba? Takawa take cikin wani irin salo tana juyi tamkar tarwada ta karasa kusa da shi,hannun ta tasa ta ɗan ture shi ya koma ya jingina da jikin kushin ta haye saman ciyarshi,kafinma ya samu damar yi mata magana ta haɗe bakinta da bashi ta shiga sumbatarshi cikin wani salo yayin da hannun ta daya ke bayan kanshi tana shafawa daya kuma ta tura a cikin wandon shi tana juyawa, Ai kafin ka sani sai ga Alhaji Yahuza ya shiga sakin nishi yana ƙara jawo ta,yana lumshe ido, Minti biyu tayi a jikinshi ta sauka gabaɗaya har yana mika hannu yana ƙoƙari riƙe ta, "Ban damu dame zaku aikata dashi ba,domin ni tsarin aiki na kenan indai har zaka biya ni,ya rage naka kasan yanda zakayi da sauran" Wani irin shigiyar dariya gabaɗaya suka kwashe dashi,Alhaji Mansur har da nuna shi, "YAR TSANAR ZINARI kenan me saka Yara shedewa,Tsofaffi kuma ta saka su Suman daɗi," Cikin nuna ko in kula da halin da dattijon ya fara shiga na sha'awa tace"ko da kamar ƙaramar yar da ka haifa ne idan har kasan zaka samu natsuwa da ita sai ka ajiye tsufan ka koma yaro domin ka more sauran lokacin da suka rage maka Alhaji Yahuza" Kallon ta Alhaji Abubakar yayi"Ki bani dama na cikashe maki duk wani gurbi dake zuciyar ki,na aure ki,zan nuna maki gata irin wanda baki taba samu ba" Lumshe ido tayi ta buɗe su akan shi wanda yaji ta ƙara tafiya da zuciyar shi"Ni ƴar tsanar Zinari ce wacce take zagaye da mugayen kunamai masu mugun dafi,duk wanda ya yayi gigin daukar wannan Yar tsanar zinari,to fa wannan dafin ba zai barshi ba,domin mai shiga ciki ne ya lalata zuciya,,shi yasa gara ka bar Yar tsana a inda ka ganta,a kuma matsayin daka ganta,domin ita din ba mai taɓuwa ɓace" Kiran sunan shi tayi"har yanzun ina ga Allah ba hallici wanda zai ciki zurbin zuciya ta ba,kuma ina ga har abada babu, Kuna da Account number na ku turomin sauran kuɗi na" Tana gama faɗar haka ta tashi ta wuce ciki ta barsu a nan idan sun gama tattaunawa su tafi Ummita ta rufe mata kofa,idan kuma tabi daya daga cikin su kwana ne babu abinda ya sha mata kai....... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *06* Babban ɗakin taro ne wanda yake daukan mutane sama da dubu,amma duk da haka a cike yake har ma wasu na niman wurin zama,saboda tsabar cika da akayi domin halartar wannan wa'azin, A kwai wurin zama na Malamai da ban sannan kuma akwai babban TV na bango wanda yake hasko ko wani malami dake wurin dakuma wanda yeke wa'azi alocin,dan kusan Malamai uku ne, Sannan a wurin akwai wurin zaman mata daban na maza daban, Sai dai kuma a bangaren matan abinda zai baka mamaki shine yanda wasu daga cikinsu suka ci ado da kwalliya yanda kasan wadanda zasu je wurin bikin ko kuma gasar kyau ta ƙasa, Lamarin ya ban mamaki,wanda hakan ne ma yasa na shiga wurin matan na zauna dan naji me ke faruwa dasu haka,dan tunda nake halartar wa'azi ban taɓa ganin inda mata suka cika irin na yau ba,kuma suka yi irin wannan kwalliyar. Wata ce daga bayana naji tana ce ma yar uwar ta"waini Allah wallahi zafi ya ishe ni,gashi kwalliyar dana bada kuɗi har dubu biyar ta fara narkewa saboda zafi,shi kuma wanda nayi domin sa ko shigowa bai yi ba" Tsaki wacce ake ma magana taja"ke dai bari yar'uwa,ai ni bakin cikina yanda muka kaso kudi tun daga Sokoto har Abuja saboda mutumin nan,sai gashi naga hadaddun ƴanmata waɗanda suka fimu,wasu fa daga Adamawa,wasu Bauci,ke har daga Zamfara,kinga wadancan yan matan guda uku na wancan layin na kusa da karshe,to wallahi tun daga Ghana suka zo,kuma yawanci abinda ya kawomu daya ne,wato ko Allah zai sa kina da rabon sa'a a rayuwar ki YOUNG USTAZ ya yaba ko soyayya kuyi,inma Allah yayi ki da kashin arziki ya ce yana so zai aureki ai daga ke har dangin ki ku da talauci har tattaɓa kunnen ku,sai dai kuma yawan yammatan dake nan wallahi yau har tsoro suke ban duk in da ka juya,wasuma da kansu suke kawo yayan su" Wanda ake ba labarin ne tace"ke yar uwa kinje wa'azin da yayi a Kaduna kuwa,watancan daya wuce? "A'a ban samu zuwa ba" "Hmmm,ai kuwa ana cikin wa'azi sai ga wata mata ta tashi wai ta ba Young Ustaz sadakan ƴar ta" Zaro ido tayi har tana rike mata hannu "Allah yasa bai karba ba" Dariya tayi"ai wallahi daya karɓa,ni kaina da kaina zan kira Babana yazo ya bada sadaka ta, Sai dai Allah ya so shi,sai godiya ya mata yace tayi haƙuri ba zai iya karɓa ba saboda wani dalili," Ajiyar zuciya ta sauke har da dafe kirji "kai Allah na gode maka" Ji suka yi wani Malami ya fara sanar da Shigowar karamin kuma Babban malamin su wato,Ustaz SORAJ ABDUL BASIR, Aikuwa nan take ɗakin taron ya ɗauke da kabbara wanda yake tashi ta ko wani lungu da sako na cikin ɗakin, Wasu manyan mutane na gani su biyu sun sha bakin kot na maza,fuskar su a turbune,kamar yanda ko wanne su kunnen shi ke manne da abun jin magana, Su biyu a gaba biyu a baya yayin da suka saka wani matashi a tsakiya wanda nake kyautata zaton shine Ustaz din, Dakyar dai na samu nasaran lekawa dan na gano mana wannan mutumin da yan mata da samari ke buri akan shi,shin yama kamannin shi suke ne, Tun daga ƙasa na fara kallo inda ido na suka sauka akan wani haɗaɗɗen takalmi na maza,na yayi irin wanda sai a MBC Action nake gani suna tallan shi,masu matsifar kyau da tsada na fata, ina karawa sama sai na cin karo da wando na farar shadda wanda daga kasan kafa ya Dan matse na samari ya ma farin kafar wani irin kyau Sai hannun shi wanda yake dauke da agogon Azurfa mai matukar ɗaukar ido,da hannun shi wanda yake sanye da zobe kwara daya tal, Sai kuma rigar jikin shi wanda ya kasance ya zaune mashi a jiki sosai kuma iya guiwa ya tsaya mashi,sai dan siririn dizai da aka ma rigar har kasa kuma fari tas,wanda ba karamin kyau da zauna mashi kayan yayi ba. A kanshi na tsayar da kallo na kafin na gangaro fuska, Wato suman kanshi nada ɗan yawa kaɗan sai dai a murmurde yake irin na Asalin Hausawa, Sai dai daga ganin murdewar kasan kamar dai an dan murmurdene ba yin kanta bane,an kyara ta sosai har wani daukar ido take saboda baki,sai dai bai daura hula. Masha Allah baki na ya furta a lokacin da ido na suka sauka a kan nashi,domin kuwa kyau,idan nace kyau ina nufin sosai din nan,to Allah ya bashi,wanda mace bata isa ta tsaya mashi yanga ba in dai akan kyau ne,gashi fari yanda kasan ka taɓa jini ya fito haka yake,ga kwarjinin da haiba da Allah ya mashi, Ko kallon fuskar shi kaɗai kayi sai kaji wani iri a jikin ka, Ni a tunani na zanga wani babban malami ne duk da naji ance young amma ban taba tsammanin zan ga malam da irin wannan shigar ba,ban taɓa tunanin yaro irin haka wanda bai wuce shekaru ishirin da biyar ba zai samu irin wannan tarin ilimin daukaka da girmamawa,kuma abin daure kai gaba ɗaya Al'ummar dake wurin babu wanda ya damu da kalan kayan dake jikin shi,sai ma murna da matasa keyi akan sun samu wata sabuwar wanka a wurin Ustaz yau. Lallai dole ƴan mata su ruɗe, domin yanda kasan wani celebrity haka yake. Tunda ya shigo yake daga ma mutane hannu fuskar shi cike da sanyayyiyar murmushi,har ya zauna a inda aka tanada domin shi, Cikakkiyar Sallamah ya fara masu,wanda nan take dakin taron ya fara amsawa daga bakin mutane mabanbanta, Godiya ya fara ma Allah daya kawo shi wannan garin da kuma irin tarbar da mutanin garin suka mashi, Daganan kuma ya dauki topic daya wanda zai yi magana akai wato ZINA, Tun daga lokacin daya fara magana yana jawo aya ya fassara tare da hadisai kaji gabaɗaya wurin ya ɗauki wani irin shiru wanda ko tari baka ji sai jifa jifa,sai kuma sautin daddarar Kira'an da kuma muryar shi mai saka mutum natsuwa, Cikin harshen Hausa wacce bata fita mashi sosai kamar dai bayajin Hausar sosai,dan wani bi yafi haɗawa da Turanci wanda ba kowane ke gane abinda yake faɗa ba saboda yanda yake furtasu,sai dai duk da haka yana ƙoƙari wurin sassauta turancin shi, Daga karshe yayi magana kuma akan illolin shan giya,kafin ya fara rufe taro da Addu'a sosai,wanda a kalla sun dauki awa uku suna wa'azin,sannan ya sanar dasu sai sun haɗu kuma a wani garin domin gobe zai koma, Kafin mutane su yayyabeshi security din shi su buɗa mai hanya har ya shige moto dan su mai dashi babban Hotel din daya sauka,dan akwai mutanen da zai gana da su kafin tafiyar shi gobe da yamma......... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *07* Tunda ta idar da sallar asuba ta koma ta kwanta ba ita ta tashi ba sai ƙarfe sha ɗaya na safe,wanka ta fara yi sannan ta saka wata doguwar riga na atamfa,rigar bata wani matseta ba kamar yanda bai mata yawa sosai ba,sai dai dinkin ya zauna sosai a jikinta,sai ɗankwali data naɗa wanda kusan rabin sumanta a waje yake,haka kuma mayafin ta baida girma dan madai_daici ne ko nace ɗan ƙarami ne, Tana fitowa ta dauki makullin motar ta sabuwa wanda ajiya da daddare aka bata kyautar shi,sai kuma ta maida ta ajiye tana jan tsaki,da kafa ta tako har bakin Get inda me gadi yake zaune,tana kara waya a kunne,maganar mintuna biyu tayi ta kashe wayar tana karaso in da yake, "Barka da safiya ranki ya daɗe" "Yawa barka,ya aikin naka"ta faɗa tana zama akan bencin dake wurin, " Alhamdulillah Hajiya" Bata ce mashi komai ba kuma ta shiga danne_danne da yawarta kusan mintina goma zuwa sha biyu sai ga wani me Adaidata ya zo ya tsaya da sauri ya fito ya shiga gaida ita cikin girmamawa, Amsawa tayi sannan ta tashi,buɗe karamin jakkan dake hannun ta tayi ta zaro dubu goma ta mika ma tsaho mai mata gadi, Godiya ya shiga yi mata yana saka mata Albarka,a zuciyar shi kuwa yana mata fatan shiriya,domin kuwa ba karamin kyautata mashi take yi ba,kusan ko wani lokaci in dai tana nan to cikin yi mashi kyauta take,kai Allah dai ya shiryata ta koma gaban iyayenta, Shiga cikin Adaidaitan tayi,ya ja suka fito bakin babban titi, Sai lokacin ya ce "Hajiya ina zamu? " Gidan Aunty Babba" Yasan in da take nufi dan haka jan Adaidaitan yayi ya dauki hanya wanda tafiyar mintuna ishirin da biyar ne ya kai su har bakin Tangamemen Get din, Cewa tayi ya tsaya ya jirata a bakin Get,ta fita Tana isa mai gadin yana ganin ta ya shiga dariya tare da washe hakora ya na gaishe ta,tare da bude mata ƙaramin kofar ta shiga, Wato gida ne babba mai hawa uku mai dauke da ɗakuna sama da guda hamsin, Tun daga shiga cikin harabar gidan zaka fara tabbatar ma kanka da wani irin gida ne wannan ,domin kuwa mata ne wanda ke sanye da kaya dai dai son ransu,wasu da riguna iya cinya,wasu sunyi dandali suna zukan shisha pot,yayin da wasu ke buga karta,a ta wani bangare kuma wata haka gani zaune a saman cinyar saurayi ko tsoho a zaune suna sha'anin gaban su, Duk inda ta gifta baka jin tashin komai face na ihun mata da shewarsu suna kiran sunan ta"sai Yar Tsanar Zinari "wannan sunan kawai suke mai maitawa tare da mata kirari,"zinariya abin bege ga kowa,sai dai duk kudinka baka isa ka mallaka ba sai da rabonka,ko da rabon ka,sai dai ka ara amma baka mallaka ba,domin zinari dashen Allah ce"wannan ce kirarin da wasu ke mata,yayin da take daga masu hannu tana tana murmushi, Wani ɗaki wanda yake yafi ko wani daki a wurin girma da kuma ƙwalliya a ƙofa shita shiga batare data damu da yin sallamah ba, Duk juyowa suka yi suka kalle ta kamar yanda ita ma ta kalle su ta watsar tare da zaunawa a kan daya daga cikin kushin din dake wurin kusa da wata mata wacce aƙalla zata kai shekara arba'in da biyar zuwa da uku,amma tasha kwalliya yanda kasan yar shekara talatin ta haɗe cikin wani Les, Kallon baƙin ta tayi waɗanda suke maza ne ta kuma kalli Biba wacce bata da niyar gaida su,karshe ma sai cingan data ciro a jakkanta ta wurga a baki ta shiga tauna,tare da kada ƙafafu, "Biba wani irin rashin tarbiyya ce shigowa wuri babu sallamah? Kallon ta tayi tana tabe baki" Tarbiyata ce a haka" "Ni fa ba haka nake nufi ba,kin dai san ya kamata ki ni me izini kafin shigo ko? " Banga wanda zan ni me izini a wurin shi bane," "To gaisuwa fa,domin su baƙi na ne kuma masu mahimmanci" Ɗan murmushi tayi tare da sauke ƙafarta ta daga masu ƴan yatsun ta"hello gentlemen" Suma sakar mata fuska sukayi suna amsawa, Dafe kai Aunty Babba tayi tare da basu haƙuri ta sallamesu akan sai sun haɗu gobe, Suna fita ta jiyo tana dalla mata harara "tun yaushe nake kiran ki a waya amma baki ɗagawa,ni keke ma wulakanci ko Biba," "Ni fa damuwa ce bani so,to yanzun gani akan me kika ni ma na? " Ina kaso na,naji ance kin je aiki kasar waje ina nawa saƙon " Cikin rashin kunya tace "tunda tare da ke muka je ai dole ki tambaye ni naki kason" "Kar ki manta ni dai na dauraki akan wannan harkar" "Kar ki manta ko da na shigo wannan harkar da arzikina na fara ba a tsiyace na faɗo ba" Ajiyar zuciya ta sauke tana dafe kai,in dai Biba ce ba a cinta a tabarman roba a ƙare lafiya"ok ya isa haka,to yanzun me zan samu? Komawa tayi ta jingina da kyau a kan kushin ɗin "yanzun kika yi magana Uwar karuwai" Karamin filon dake gefen ta ta wurgo mata"Biba bana son iskanci " Ita ma ɗan dariya tayi kaɗan "to ai sunan ki ne" "Ni dai ki bani kaso na" "Oh Allah ke dai da wannan kason naki, ki duba na tura maki ta banki"ta faɗa tana mikewa" Dama ba wani abu bane kika addabi mutum da kira, "A sauka lafiya ni dai tunda na gani" Ko da ta fito tsakar gidan sai da ta masu barin kudi kafin ta fita taba mai gadi na shi ta shige cikin Adaidaitan ya ja, Tunda suka hau kan babban titi suka haɗu da wani irin kuna taccen Go Slow, Sai tsaki take,domin abinda ta fi tsana kenan, Kamar daga sama ta ji ana kiran "Ummu Sallah,Ummu Salma" Juyawa tayi yayin da gabanta ya yi wani irin faduwa wanda sai da ta rintse ido tare da dafe kirjinta, Shikuwa mai kira sai kara kiran sunan yake yana nufo in da take zaune a cikin Adaidaitan, Ganin ya kusa isowa in da take bayan ya fito daga cikin nashi motar ne yasa da sauri ta fito cikin Adaidaitan har jikinta na rawa tace mashi su haɗu a gida, Da sauri ta shiga kutsawa ta cikin motoci domin bata fatan ko da a mafarki ta haɗu da wanda zai kira wannan sunan,dan haka wata mota dake gefen ta baƙa mai baƙin gilashi kawai ta buɗe ta shige tare da mai da kofa ta rufe ba tare data damu da motar waye kuma suwaye a ciki ba, Jingina taye tana dafe kirji tare da kallon mutumin wanda yazo har ta gaban motar da take ciki ya dafe kai yana ƙara kiran sunan "Ummu Salma"yana juye yuye, Lumshe ido tayi tare da katanto duk wani addu'a da yazo bakinta domin saisaituwar buguwar zuciyar ta, Jim kamar motsi a gefen ta ne yasa ta buɗe ido tare da kallon inda ta ji motsin, Mutum ne zaune a gefen ta namijin,ya zuba mata idanun shi masu matukar haske da daukar hankali,kamar yanda furkarshi har wani daukar ido yake, Ita ma kallon shi tayi tana tabe baki tare da harara shi,a hankali kuma ta furta "Maye" Tana juyar da kai, Mamaki ne ya kara kamashi,wai yau shine mace zata shigo ma mota har ta kalli tsabar idanun shi ta kira shi da Maye,karo na farko a rayuwar shi ya samu harara a garin Abuja,aranar da yake shirin barin garin,domin komawa in da ya fito....... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *08* Mai da kanshi yayi ya jingina yana lumshe ido, Yayin da shi kuma Direba yake cigaba da jan motar shi har ya samu suka bar Traffic din, Dafe kai tayi tana jan dogon tsaki,tare da tunanin dole ta bar garin Abuja koda na wani lokaci ne, Dafa kujeran da direba ke zaune ta yi "kai tsaya na sauka a nan" Da sauri ya juyo yana gangarawa gefen titi tare da yin parking,dan ba karamin tsoro da mamaki ganin ta acikin motar da Young Ustaz yake ciki yayi ba,ta yaya ta shiga,ko dama tana ciki ne, Cikin rawar jiki ya fito yana buɗe ta bangaren da Malamin nasu ke zaune,yayin da sauran motocin dake binsu a baya suma suka tsaya, Kallo shi tayi sai dai idanunshi a lumshe suke kamar mai yin bacci,amma ta tabbatar ba bacci yake ba,dan tafiyar da suka yi na ƴan mintuna bai ci ace har mutum yayi barci ba, Bata cikin yana yi mai daɗi,dan haka ce mashi kawai tayi "idan kana ji na ka rage wannan suman na kanka,idan kuma kai kurma ne Allah ya baka lafiya" tana gama fadar haka ta kulle mai kofar mota ta wuce, "Ko ina ruwana ma da suman shi ohh" ta faɗa tana tsallaka titi dayan barayin tare da tare adaidaita ta shige, Tambayar shi suka shiga yi ko yana lafiya, Domin dai sun ga ko da ta fito sai da ta tsaya suka yi magana dashi a nasu fahimtar,amma kuma abin ya basu mamaki domin tunda suke dashi basu taɓa ganin shi da wata mace haka ba balle har su zauna tare,to wacece wannan. Ganin duk irin tambayoyin da suke mai yaki kula su ne yasa dole suka koma cikin motocin sannan suka tada tare da daukar hanyar Airport in da zasu kai shi. Suna isa airport din basu wani jima ba jirginsu ya tashi,ƙarfe biyu ta musu ne a cikin Kano,ko da suka sauka motocin gidan su ne suka zo daukar shi, Suna tsayawa kofar gida ana kiran sallah,dan haka tsayawa sukayi a bakin Get ya sauka dan sun san ka'idar shi, Ya fara Alwallah kenan yaji an ɗan buge kafadarshi ana dariya "Ustaz Suraj an dawo kenan,yau yamma ta nawa ka haɗu da su,domin so nake ka haɗa ni da guda biyu zafafa ko na rage hanya dasu,kasan ku malamai ba a rabaku da eh yane" Ya karasa faɗa yana dariya. Duk maganar da yake yi yana jinshi sai dai bai bashi amsa ba har ya idar da Alwallah ya dago, Kallon shi yayi,shima dai matashi ne wanda a ƙalla zai iya ba Suraj din shekara uku zuwa huɗu,kuma suna da dibar kama sosai da shi,daga gani dai kamar suna da alaƙa sosai da juna, Bai bashi amsa ba ya juya ya shige cikin masallaci dan in dai Ibrahim ne yasaba da irin wannan halin nashi. Shima kuma ganin bai kula shi bane yasa ya fara daura Alwallah kafin Abba ya fito,dan yasan yanzun zai iso masallacin,idan kuma yazo bai gan shi ba zai iya samun matsala. Koda aka idar da sallah kafin ya fita masallaci sai da ya tsaya suka gaggaisa da mutane sannan ya fito, A ƙofar gida ya haɗu da Abbu a tsaye wanda yana ganin shi ya sake murmushi kamar shima yanda ya samu kanshi dayi, Karasawa yayi inda yake yana ƙoƙarin tsugunnawa ya gaisheshi,sai dai kafin ma yakai ga yin haka har ya rungume shi, "Abbu mun same ku lafiya? Ya faɗa shima yana rungume mahaifin na shi. " Lafiya qlau ɗan albarka,ya fama da jama'a? "Alhamdulillah Abbu," Riƙe hannun shi yayi "mu je Ummin ka na jira"tare suka jero suna tafiya yana ɗan mashi tambayoyi game da tafiyar tashi,wanda haka yake matukar mantar dashi damuwar shi,dama kuma shi ba mai bari karamin abu ya tsaya mai a zuciya bane,dan yanada harkoki da yawa a gabanshi shi yasa ba karamin abu bane zai sa kaga ya riƙe ka ko a fuska ne. Gidan babban gida ne sosai mai dauke da manyan bangarori guda biyar, Part din dake tsakiya wato na uku shi suka shiga. Falone babba wanda ya ji kayan alatu na rayuwa dai-dai gwargwado ba a cika komai irin na nuna isa kona Almubazzaranci ba, Sai kamshi ke tashi ta ko ina, Da sallamah suka shiga har tsakiyar falon in da wata yar budurwa ta amsa wacce ba zata wuce shekara goma sha huɗu ba,sanye da hijabi dai dai guiwa,da fara'a ta tare su"oyoyo yaya Suraj,barka da dawowa,Allah yasa kamin tsaraba "ta faɗa tana dariya tare da isowa in da suka zauna shida Abbu, Murmushi ya sakar mata wanda ya kara baiyana kamar dake tsakanin su,cikin kwaikwayonta yace" Oyoyo Rabi'ah, Allah yasa kin ajiye min abin daɗi " Dariya ta saka tana buga ƙafa irin na shagwaba,"ai Ammi ta ajiye maka," Dariya suke mata shida Abbu,wanda yace"kinga ƙyale shi Auta wannan karon harda ne sai an ba tsaraba,ɗan mun gaji da kullun mantawa da mu da akeyi" Karan tafiyar da suka ji ne daga gefen su yasa suka juya, Mace ce kyakkyawa wacce da ka ganta yanda kasan an tsaga kara tsakaninta da Suraj,da kuma ƙanwar shi,abubuwan Abbu kaɗan ne suka kwasa. Da sauri ya tashi ya karasa inda take tare bata kyakkyawar runguma"I miss you Ammi" Shafa bayan shi tayi"baka kai ni ba Baba na," Dagowa yayi ya rike hannun ta ya sumbaci hannun,"Ammi na yunwa nake ji" "Mu je ka ci abinci" "Ammi bari nayi wanka sai nazo na ci" Jinjina kai tayi"ok Allah yama Albarka" "Amin My Ammi" Ya fada yana nufar kofar fita"Abbu sai zuwa anjima " Hannu ya daga mai,"sai ka shigo " Yana fita ta bayan shiyansu yabi inda ya ɓulla ta wani boy's quarter,babba wanda daga dukkan alamu anan samarin gidan suke, Duka kofofin irin wanda zaka saka ɗan kati ne ya buɗe,a kwai kuma inda zaka saka number, Dan haka da katin yayi amfani ya buɗe ƙofar wanda wani ni'imtaccen sanyi ne ya daki hanci na,nayi mamakin ganin garman dakin domin na ɗauka ɗaki daya ne,sai dai babban falo ne madaidaici mai dauke da manya kujeru sai kayan kallo da man yan labulai wanda suka ƙara kawata falon, Sai dakin barcin shi mai hade da bayi, Wanka yayi ya canja kaya,sannan ya fito,sai dai a maimakon ya koma shiyansu sai naga ya shiga daya daga cikin part din dake gidan wanda yake kusa dana farko. Da sallamah ya shigo,in da wata tsohuwa dake zaune a saman babban darduma tana baran gyada ta amsa,"Me gida na barka da dawo," Ya mutse fuska yayi yana zama kusa da ƙafarta "kin min tsufa,ni yarinya karama nake so" "Kai dai faɗi gaskiya kace ka rasa mai sonka, kaga ni ma manegi nake da kai tunda an rasa meso" Dariya ya saka wanda bai yi niya ba,"ni har yanzun banga wacce ta min ba," "Ko dai Aljana ta aure ka ne bamu sani ba Surajo,kai ko dan irin ƴan matan nan da samari keyi kai ban taɓa ganin ka yi ba,to bari Adamu da Auwalu su zo,dole a fara ni ma maka taimako" (Adamu shine sunan Abbu,mahaifin shi,Auwalu kuma Abba,yayan mahaifinsa,baban Ibrahim) Ɓata fuska yayi"dan Allah ki daina ɓata min suna wai Surajo,pls ƴan mata,kuma ni bani da wata Aljana data aure ni,kin ga me zan samu a dakin nan"ya faɗa yana mikewa tare da tashi ya nufe firig dinta,buɗewa yayi yana dudduba abubuwan dake ciki,wani kwanu ya dauko ya dawo ya zauna, Kokarin mika hannu take zata ƙwace "to ka dawo kenan ko,zaka fara caje min dakin kamar kaban ajiya,bani fura ta nan,damawa nayi na sha anjima" Kaucewa yayi yana dariya"ke dai faɗi gaskiya dama ni kika ajiye ma,dan ki kara siye zuciya ta,to karki damu ba yanzun zan yi auren ba,"ya faɗa yana yin Bismillah tare da saka ludayi aciki yana kaiwa baki, Sallamah suka ji daga bakin ƙofa, Kaka ce ta amsa da karfi tana bada izinin shigowa,shi dai a hankali ya amsa, Wata budurwa ce ta shigo kyakkyawa wanda ba zata wuce sha tara ba,sanye da jallabiya baki sai karamin hijabi,hannunta riƙe da Basket da kulolin abinci, Cikin yanga mai haɗe da natsuwa ta shigo,ɗan dukawa tayi"barka da dawowa Yaya Suraj" Hannu kawai ya daga mata,ba tare daya bata amsa ba, Basket din hannun ta kai gaban Kaka ta ajiye "Kaka gashi inji Momy" "To Allah yayi Albarka,je kikai kicin"kallon shi tayi" Surajo ko a zubo maka" Girgiza mata kai yayi ba tare daya bata amsa ba,yana cigaba da kurban furanshi. Tana shiga kicin sai ga wasu ƴan mata su biyu suma sun shigo,sai dai su zasu kai ishirin da uku zuwa da biyu,gai dashi suka yi saku gai da Kaka sannan suka shige cikin dakin kaka, "Yanzun zaka saka a fara min layi a ƙofar daki Sojago,ƙarfi da yaji kasa na samu karin wasu jikokin wanda ba nawa ba,sai dun saboda kai,kai kuma na rasa kanka ace ka rasa wacce ta motsa zuciyar ka sai kace wani Dutse" Wacce ta kai abinci kicin ne ta fito ta zauna kusa da kaka,"yaya Suraj munga wa'azin ka na Abuja yayi kyau sosai " Wani mugun kallon daya sakar mata ne yasa ba shiri ta mai da gyadar dake hannun ta wanda ta diba,tare da tashi sumui_sumui ta shige dakin kakan,in da waɗannan yan matan suke. Kallon shi tayi"Allah raba ka da bakin hali" Rufe kwanun yayi"dana yi me? "Kai kenan baka son mace ta rabe ka,,daga harara sai ka dauri yi masu bakin hali,ta yaya mace zata ji daɗin zama da kai" Hannun ta ya rike tare da sumbatar bayan hannun,"idan na tashi aure sai na baƙi mamaki" "Allah yasa ba mamakin da zai kashe ni zaka bani ba" Dariya kawai yayi yana fita daga shiyan,dan yasan in dai ya zauna to fa yanzun zasu shiga yin zirga-zirgar a cikin falon,daga yan matan gidan har na makota masu shigowa, Shi kuma tsakanin shi da mace sai niman tsari, Shi sam basu gaban shi,basu burge shi,shi yasa duk wacce tayi kuskuren ya gano kina son shi,to kin shiga uku bashi ba raga maki,tsakanin ku harara,amma in kin iya takunki to zaku zauna lafiya,harma ku yi hira,to duk kuma randa yan iskar nashi ke kai,to ranar kowa a gidan kama kanshi yake hatta masu tsaron shi,ɗan shi mutum ne mai matukar sauƙin kai,bai da saurin fushi,ya nada fara'a,sai dai bai son rai ni,wani lokaci kuma haka kawai ranar sai kaga ya dauke wuta,wato ya gimtse fuska duk wanda ya mai to ranar ya shiga uku,domin ya iya bada punishment wanda duk girman mutum sai yayi kuka,shi yasa duk randa suka ganshi a irin wannan yayi kowa yake kama kanshi a gidan babba da yaro.... Yana fitowa daga part din kaka sai ga Direba, cikin girmamawa ya miko mashi wani karamin pos na mata da waya kiran iPhone"Ustaz gashi a cikin mota na gani" Bai amsaba sai tsayawa da yayi yana kallon pos din tare da wayar "ina riƙe pos ne da zaka kawo min? Dukar dakai yayi cikin girmamawa yace" Ba haka nake nufi ba,a yi hakuri,ina ganin na wannan yarinyar ce data shiga motarmu " Ɗan shiru yayi yana nazari dan shi sam yama manta da wata ta shiga motar su dazu,ohh ya tuna,wannan mara kunyar yarinyar,wacce tace mashi maye,harda cewa ya gyara suman kanshi, "Jeka dashi" Yace ma Direban,har kuma mutumin ya juya yana tunanin yanda zai yi da kayan,ko me ya tuna ohho,sai kuma yace "Kawo" aikuwa da sauri mutumin ya kawo mai ya juya ya bar wurin cikin sauri dan karma ya canja ra'ayi. Jujjuya kayan yake a hannu kafin ya nufe dakin shi dasu...... ______Bangaren Biba kuwa... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *08* *Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku* *Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309* *ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865* A gigice ya shigo cikin gidan har yana cin tuntube sabar saurin da yake yi, Ga masu aiki ta ko ina duk in da yabi sai gaida shi suke yi amma sam ba su bane a gaban shi, Burin shi daya shine ya ƙarasa inda masu gidan suke, Tunda ya taka ƙafar shi a babban falon gidan wanda daka ganshi kasan naira tayi kuka ya fara kwalla kiran sunan mutanen gidan daya bayan daya cikin tashin hankali, "Mama! Mama!Abdulrahman! Yaya Abdulmajid! Ina kuke ɗan Allah ku fito! " Daya bayan daya suke fitowa daka shiya mabanbanta a cikin falon, Ita wacce aka kira da Mama wacce ke sanye da Hijabi dogo har ƙasa tare da carbi a hannun ta ne ta kalle shi,"lafiya Abdulmalik? Kallon ta yayi,tare da kallon ƴan uwan shi maza dake tsaye suna jira suji ko lafiya,yake a gargitse haka, A hankali ya buɗe baki ya kira sunan ta"Mama" Amsawa ta kara yi tana kallon ɗan nata wanda yake cikakken saurayi kuma matashi wanda zai kai shekara ishirin da takwas,taga ya fashe da kuka tare da rungume ta, Duk da basu san me ya saka shi kuka haka ba,amma sun san ba karamin abu bane zai saka shi kuka haka,dumin kuwa shine mai ƙarfin zuciya a cikin su,shine mai kwantar masu hankali a ko wani lokaci,tun bayan faruwar wani babban lamari a rayuwar su,wanda shi ne yayi sanadiyar sauya komai na gidan,ya mai da masu da gida tamkar kango wanda babu mutanen dake rayuwa a cikin shi,tun daga lokacin da suna rasa NURUL AINI,wato hasken idaniyar su,mai haska zukatan wannan Alhali gaba ɗaya,sunyi babban saken da ZINARIYAR da suke ji da ita tabar hannun su,wanda suke tunanin da wuya ta kuma dawowa hannun. Abdulmajid da bai da wuyan kuka wanda shine Babban yayan su,ne ya zo ya rungume shi yana hawaye"Me haka Abdulmalik,so kake ka kara tayar mana da hankali,ɗan Allah na rokeka ka faɗa mana damuwar ka,ɗan uwan mu" Dagowa yayi ya kalle su,yayin da wasu hawayen ke kara sauko mai a ido,dukar da kai yayi,sannan ya dago cikin matsanancin rauni yace"Mama na ganta,na ganta yau a garin Abuja " Cikin sauri Abdulrahman ya kara so in da yake"wa ka gani! Wa ka gani yau a Abuja,pls ka faɗa mana" A jiyar zuciya ya sauke me haɗe da kuka,"Yaya,wallahi na rantse Allah wannan karon naga Ummu Salma a garin Abuja, na.... Ganin ta tafi suuu tayi baya tana ƙoƙarin faduwa ne yasa da sauri suka tare ta suna kiran sunan ta a kidime,tare da taimaka mata suka zaunar da ita kan kushin, Kiran sunan daya faɗa ta fara"Salma! Salma,dan Allah ku nimomin Salma kamin in mutu,akwai abinda nake son na faɗa mata,"riko hannun Abdulmalik din tayi"ɗan Allah ka taimake rayuwa ta Abdulmalik ka kai ni wurin Salma,waiyo Allah rayuwata bata amfana min komai ba sai aikin dana sani,na bi son zuciya na cutar da rayuwata da ta ƴa ta,na kai kaina ga halaka bayan nasan cewa halakar ce,ya zanyi da rayuwata,waiyo ya Ubangiji ka yafe min,ka yafe min na tuba" Tsugunawa yayi a gabanta tare da zube guiwoyin shi a ƙasa yana zubar da hawaye mai ciyon gaske,"Mama ina niman gafaranki domin na kasa kawo maki ita,domin kuwa a Traffic na ganta,ko da na kira sunan ta muna haɗa ido da ita ta fita daga adaidaitan da take,na yi niman ta a wurin banganta ba,kwanana biyu a kullum a wurin nake yini ko Allah zai sa na ganta amma banganta ba Mama"ya faɗa yana kifa kanshi a cinyar ta. Dafa kafadar shi Abdulrahman yayi"karka damu Abdulmalik,ko da ace zamu zagaye garin Abuja,insha Allah in dai anan Ummu Salma take sai mun ne mo ta," "Kwarai kuwa" Cewar Abdulmajid,domin kuwa sun san dole zai kasance cikin damuwa,duk cikin su yafi shakuwa da ita sosai, "Mama ɗan Allah ki bar kuka haka,kin ga kada Dady ya tashi yaga idonki ya kumbura haka zai damu,idan kuma yaji batun Salma kin san me zai iya faruwa, pls" Hannu tasa tana sharewa wani na zubowa "na kasa tsayar dasu,a ko wani lokaci ƴar uwar ku na cikin rai na,tunda tabar gida dai dai da sakon daya ban taba manta taba,a ko wani numfashi na cike yake da nadama,da dana sani,ji nake da za'a dawo da lokaci baya,da ban haɗu da miji kamar mahaifinku ba,da dana haɗu dashi dana ki amincewa dashi,kila da kaddarata bata zo a haka ba," Dago kai tayi ta kalle yaranta maza dake zagaye dasu,"a lokacin da kanwar ku ta faɗa min damurta,a matsayina na uwa kamata yayi na nima mata mafita na gari,sai na bata shawara akan tabi ta hanyar da nake bi,!a lokacin kun san me tace min kuwa? Duk kallon ta suke cikin tsananin sanyin jiki mai haɗe matsanancin damuwa irin wanda yake tafiya da kuzari, A lokacin kuka ta fashe dashi tare da rungumeni,tace min Mama kina ban tsoro,wannan kamar ba Mama na ba,dan Allah ki dai na faɗin haka kina ban tsoro, Da wannan hannun nawa na ture ta,na ce mata sai ta nimar ma kanta mafita da kanta,amsar da ta ban shine,na yi dana sanin zuwa duniya a matsayin ƴar ku,da Ace Allah yana ba ya'ya zabi su zabi iyaye,Mama da ban zabe ku keda Dady a matsayin iyaye naba,na kwammace a haife ni a cikin ahalin da basu da komai sai sun fita sunyi bara sannan su ci dani,ba zan taba bi ta hanyar da kuka bi ba ke da Dady,Allah ya isa tsakanin ke dani,da kuma wanda yake a matsayin uba a gare ni,Ubangiji shi zai min hisabi daku ta yanda kuka kawo ni wannan duniyar,: Wannan shine maganar kanwarku dani na karshe,Abdulmalik na tabbatar da haƙƙin ta ba zai bar ni ba,maganarta gaskiya ne,ban cancanci zama uwa ba,dan Allah ku gafarce ni"ta faɗa cikin matsanancin kuka tare da haɗe hannun ta wuri ɗaya. Dukkanin su rungume ta suka yi suna masu kwantar mata da hankila,domin kar hawan jinin ta ya tashi, Da kyar dai suka samu ta yi shiru,yayin da kowannensu ke fama da kuka zuci,domin kuwa Ummu Salma farin cikin su ce,ita ce Nurul Kalbi a gare su. Jin wani ɗan ƙara ne yasa duk suka dago, Mikewa tayi tsaye,tana ɗan share fuska,"ina ga mahaifinku ya tashi,muje ku duba shi" Duk bin bayanta suka yi,suka bi ta cikin wani korido a falon in da yasa dasu da wani karamin falon wanda akwai wani dakin a cikin sa,dakin suka shiga,in da wani farin mutum ke kwance a kan gado an daura mai abun jawo numfashi a hanci,sai na'urorin dake zagaye dashi masu nuna blood pressure,da temperature,sai respretion,din shi, Duk zagaye shi suke yi suna mashi sannu,da ido kawai yake iya amsawa,yana bin su da kallo daya bayan daya,kafin ya saida idanun shi akan matarshi, A hankali ya daga hannun shi ya mika mata, Matsowa tayi tare da kama hannun shi ta riƙe, Cikin dauriya ya ɗan daga abin zukar numfashi,a hankali ya furta "Salma,ta dawo" Da sauri Abdulmalik ya maida masa abin a hancin shi,"Dady ka kwantar da hankalin ka zata dawo,insha Allah zata wo" Mai da ido kawai yayi ya lumshe,bai ƙara ce masu Komai ba har suka bar dakin... *Abuja* Sai da ta sauka a Adaidaita sannan ta shiga niman pos ɗinta, "Ohh, ya Allah,ina ganin na barshi a motar wannan mutumin," Tsaki taja,sannan ta karasa inda me gadi ke zaune,"Audu ka bashi dubu daya idan nashiga ciki kazo ka ansa" "To Hajiya an gama" Daki kuwa ya shiga ya dauko dubu guda ya ba mutumin. Ita kuma tuni ta shiga gida, Dakin ta shige kai tsaye tare da ciro wani madaidacin akwati ta shiga zuba kayanta a ciki, Ummita ce ta shigo,dan su gaisa,sai dai ganin yanda take haɗa kaya a akwati cikin sauri ne yasa ta tsaya tana kallon ta,"tafita zaki yi ne Biba? ba tare data juyo ba ta bata amsa"Eh" "Zuwa ina,ko wani aikin ne ya taso" "Legos zan je,ina ga daga nan zan tafi England ba yanzun zan dawo ba" Cikin sauri ta ƙarasa in da take tare da karɓar takalmin data dauko tana kokarin sawa a jakka,"Biba amma lafiya,tafiya cikin gaggawa haka,kuma ba aiki ba" Dauko wani tayi ta saka"sauri nake yi," "To zan biki" Kafin ta bata amsa ne wayar ita Ummitan yayi kara, Dubawa tayi,wanda ganin me kira ne yasa da sauri ta saki hannun Biba data riƙe tana danna wayar tare da ƙarawa a kunne, Kafin tayi makaga sai cewa aka yi"idan kina tare da ita ki bata " Cikin sauri ta mika ma Biba wayar,tare da faɗin "VIP ne" Bata yi niyar karba ba sai dai jin sunan da aka kira yasa ta amsa tare da karawa a kunnen ta,"ina jin"abinda tace kenan. Daga ɗayan gefen kuwa sai cewa akayi"ki shirya a yau da yamma zaki bi jirgi domin zuwa Kano,akwai aiki mai muhimmanci da za ki yi a can" "Akan waye? Ta tambaya. " YOUNG USTAZ "............ *sai mun haɗu a paid group* 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *10* *Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku* *Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309* *ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865* "Akan waye" Ta tambaya, Ta ɗayan ɓangaren ne aka bata amsa da "YOUNG USTAZ" Shiru tayi yayinda ta shiga tunanin ina ta taɓa jin wannan sunan, Bata son tayi Stressing brain ɗin ta shi yasa ta kara tambayar"waye shi" "Idan kin isa Airport akwai wacce zata baki wani envelope mai dauke da duk wasu bayanai na mutanen gidan wanda ya kamata kisani har da na shi" "Zan iya tafiya da Ummita? Ta tambaya tana kallon Ummita wacce ke haɗe hannun ta alamun roƙo akan zata bita, " A'a domin wannan karon aikin ya banbanta da wanda kuka saba yi,wannan aikin na musamman ne wanda idan har kika samu nasaran cika shi,na maki alƙawarin cikar burin ki a wannan karon,dan haka ke kaɗai zaki tafi,sannan karki dauki kaya ko daya,a airport din matar da zata kawo maki sako zata hado maki da kaya harda wanda zaki canja ki saka,sannan ki yi taka tsantsan Good lock"yana gama fadar haka yawar ya tsinke. Kallon Ummita tayi wacce tayi shiru tana turo baki,dan taji a binda yace,duk da tasan yawancin aikin su da Biba tana matukar shan wahala wanda ba wata wahala bane daya wuce tsoro,saboda Biba yar kasada ce,tana iya siyar da ranta ta jefasu cikin hatsari dan cikar aikin ta,kuma sai tayi cikin ikon Allah kuma ta samu nasara. Komawa tayi ta zauna kusa da Ummita,tana tunanin wani aiki ne haka zai turata wanda zai ce karta dauki ko wani kaya, Ummita ce ta katseta wacce tace"ni kuwa ina na taɓa jin wannan sunan Young USTAZ"jujjuya kai ta shiga yi tana jujjuya sunan a zuciyar ta,ganin ta kasa tunawa ne yasa ta mike,zan fita amma zan dawo kafin lokacin tafiyar taki tayi. "Uhmm" Kawai ta bata amsa tare da komawa ta kwanta,tana tunanin dole ta yi masa wannan aikin ko don samun cikar burinta ita ma. duk yanda taso ta samu tayi barci kafin lokacin tafiyar ta tayi bata samu tayi ba har Ummita ta dawo tasame ta, Tare suka shiga kicin suka yi girkin abinci,sannan suka yi wanke-wanke, Sai da ta ci abinci kafin tashiga banɗaki tayi wanka,koda ta kammala shiryawa biyar saura,dan haka Ummita ce taja mota taimata rakiya har airport, Sai dai bata shiga ba,anan bakin kofa suka rungume juna"ki kula da kanki,Allah ya bada sa'a " "Amin,ke ma ki kula da kanki" Sake juna suka yi "ta yaya zan iya samun ki a waya" "Idan na sauka zan siya waya da sim zan nime ki" Jinjina kai tayi"sai na jiki" Juyawa tayi tashige ciki,yayinda ita kuma ta juya ta shiga, Ta san cewa ba tada komai a hannun na tafiya daga ita sai karamin hand bag wanda ake ratayawa, Ji tayi daga bayanta an taɓa ta,juyowa tayi,sai dai wata mata ce wacce fuskarta ke sanye da nikaf,wani Bag ta damka mata a hannun ta irin na matafiya mai ɗan girma,sai wani envelope fari tare da ta takardun jirginta, Bata ce mata komai ba ta wuce,ita ma bata ko juya ka kalle matarba ta ta saka kanta gaba,kai tsaye banɗaki cikin Airport din ta shiga,buɗe jakkan kayan tayi domin ta ciro wani kayan ta canja tunda yace in ta iso ta canja kaya, Sai da ta kammala ciro kayan jakkan kaf kafin ta tsaya tana masu kallo mamaki,wannan wasu irin kaya ne,ko dai matar nan tayi kuskure ne,amma kuma ta saba in dai har zata aiki ita ke kawo mata jakkan kalan kayan daya kamata ta saka a wurin aikin, Ƙare ma kayan kallo take yi,wasu riga da zani ne kodaddu wanda babu yabo babu fallasa,sai riga da siket wanda bai wuce kala uku ba,suma kuma data ɗaga su wasu manya dasu babu daidai jikinta,suma kuma duk babu sabo,duk da a goge suke, Kai ina wannan ba kayanta bane,dan haka ba zata saka su ba,idan zaje can ta san dole zai nime ta ko ta yaya ne kafin ta fara aikin,amma ba zata saka waɗannan summokaran ba, danƙa bata canja kayan ba ta dauki jakkan ta fito, Duk wani abunda ya kamata tayi sai da tayi kafin a basu dama suka shiga jirgi,wanda in da zata zauna a first class ne, Sai da ta zauna kafin ta dauko wannan Envelope din ta buɗe,paper dake ciki wanda aka naɗe ta ciro tare da buɗe shi, A hankali ta fara karanta bayanai dake ciki,wanda the more tana karantawa the more ɓacin ranta na ƙara baiyana, The worst part of it,shine wai a gidan malamai VIP ya tura ta aiki wannan karon,wanda zata tafi a matsayin mai aiki a cikin gidan, Har da cewa ta saka wannan kayan ta kwantar da hankalin ta ba wanda wani ya saka bane,duka sababbi ne,an zuba masu wani abu ne wanda ya kodar dasu ya maida su tsofaffi,kuma dole sai tayi taka-tsantsan,karta kuskura tayi abinda zai yi exposing dinta,har da wani cewa dole tabar duk wani shaye-shayen da take yi saboda ba karamin gida zata je ba,dole ne ta dauko mashi abinda ya faɗa mata a cikin gidan ta. Tunda take bata taba jin bacin rai ba akan aikin ta irin na yau, wai yau ita Biba ce zata wani gida a matsayin ƴar aiki, A gaskiya da ba dan jirgin su ya tashi ba da ba abinda zai hana ta sauka tace ta fasa wannan aikin,duk da tasan cewa bijirewa VIP ba karamin matsala bane domin shi ɗin mutum ne mai matukar hatsari. Tafiyar ba wani mai dadewa bane suka sauka a garin Kano,wanda tana fitowa airport din taji an kira sunan ta, Juyawa tayi sai ganin wata mata tayi fara tas wacce fatarta yaji bilicin ya gaji,sai taunar cingan take yi, Kai da ganinta kaga yar duniya, Karasowa matar tayi inda take tare da karɓar jakkanta, "Biyo ni" Kawai tace mata tana yin gaba, Bin bayanta tayi har wurin parking in da ta saka jakkan cikin wani adaidaita sannan ta shiga ta zauna, Ganin haka ne yasa ita ma ta shiga,sannan mutumin ya tayar suka bar wurin, Sunyi tafiya mai nisa kafin su isa wani unguwa wanda tun daga bakin layin zaka tabbatar da unguwar talakawa ne,ko ta ina ka juya hayaniya kawai kake ji yana tashi na jama'a, Har kofar wani gida wanda bai da kofa ya, tsaya sannan suka fito, Kuɗi taga ta ciro ta bashi sannan ta ƙara daukar jakkan suka shiga cikin wannan gidan wanda tunda suka shiga ta fara ganin ƴan mata kala-kala yara da manya wasu kallo daya zaka masu ka fahimce daga kauye suke, Wani daki suka shiga daga cikin jirin ɗakunan dake cikin gidan, Wata budurwa ce ta ajiye jakkan gefe ta fita wanda dama suna shigowa cikin gidan ta amsa, Kare ma dakin kallo tayi cikin yanayi ta ɗan kyankyami domin sam gidan bai kwanta mata ba,ita macce ce mai tsafta da son gayu,dan haka gefe ta samu ta ɗan zauna, Cire mayafin ta matar tayi tana wurgi dashi,ruwa ta dibo a kofi ta sha sannan ta ajiye ma Biba a gabanta,wanda ganin kofin ruwan kaɗai yasa ta fara jin tashin zuciya, Zama tayi kusa da ita tana faɗin "wash Allah" Kallo ta tayi "kina jina,ki sake jikin ki domin sai nan da kwana biyu zaki fara aiki a gidan zuwa lokacin mun san dole zasu buƙaci mai aiki" Bata rai tayi "kina nufin zan zauna a nan har na tsayin kwana biyu? " Eh domin dole ne akwai wasu abubuwan da zan koya maki,da kuma karin bayani dangane da halin ko wani mutum na cikin gidan har zuwa bangaren da zaki yi aiki" "Wai a matsayin mai aikin me zanje" "Shara da wanke-wanke,wata kila harda girki" Wani irin zaro ido tayi tana dafe kirji"shara! Ni Biba! Wallahi I hate it,na tsane shara, ta ina kuma na iya girki,? Hannu ta Daura a kai "this is the worst ever" Dariya matar ta fashe dashi...... *waye VIP* *Menene burin Biba* *Shin masu karatu wani irin abu ne Biba zata je daukowa a gidan su Young Ustadz* *wani irin aiki ne koma zata yi a kanshi* *Shin zata samu nasara a kan matashin malamin namu* *Zai gane ta kuwa* *me zai faru a gidan* *Shin tukunna ma zata amince tayi wannan aikin* *wacece BIBA* *Me Asalin ta da labarin ta,me ya fito da ita gida* *shin zata koma kuwa*🤷‍♀️ ohhuuu,ni ma ban sani ba sai mun haɗe a *Paid Group* Taku har kullum Jiddarh Umar🦚. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *11* *Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku* *Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309* *ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865* Dariya matar ta fashe dashi,"ai kuwa haka dai zaki daure kiyi tunda kin riga kin zo,batun girki kuma karki damu yanzun akwai takardar girke-girke kala-kala sai a siya maki ki tafi dashi,dan ina ganin haka zai fi sauƙi " Shiru kawai tayi mata dan gaba ɗaya ranta a jagule yake,ta yaya kamar ita ace wai aikatau zata,kuma a gidan Malamai,ya za'a tasake,dan gaskiya ba zata iya daina shaye-shaye ba,ga wasu kaya kamar na gidan yari wasu manya-manya dasu, Ajiyar zuciya ta sauke tana karewa dakin kallo, Matar ce wacce ko sunan ta bata sani ba tace"bari na saka a kawo maki abinci" Girgiza kai tayi"ki bar shi kawai dan yanzun zan tafi ne" Kallo mamaki take mata"zuwa ina? "Hotel zan kama,ranar da zan tafi aiki zan zo,tunda kin ce sai nan da kwana biyu" Taɓa baki tayi,dama tasan hakan na iya faruwa tun daga ganin farko data mata, "babu matsala,bari na kira mai Adaidaita na ya kai ki" "Ok "kawai ta ce mata, Bata wani jima ba sai ga mai Adaidaita ya iso,ita matar ita ta faɗa mashi sunan Hotel ɗin da zai kai Biba,wanda yana kaita tun daga ganin tsarin ginin tace bai mata ba ya canja mata wani, Aikuwa lafiyayyen Hotel ya kai ta,wanda anan ta sauka kuma taimashi biya mai ƙyau,ta bashi sakon akan ya faɗa ma matar in da ta sauka. _______Tunda ya dawo daga Wa'azi Abuja kwana biyu kenan bai ƙara fita ba,sai Abbu da ya tafi Jos wa'azi. Yau tunda ya dawo masallaci sallah Asuba ya zauna a shiyan Kaka inda anan suke karatun safe zuwa ƙarfe bakwai kafin su tashi sannan ayi shirin Boko, Tunda ya shigo ko wacce ta kama kanta,daga wacce ke turo baki har masu gyangyadi duk natsuwa suka yi, Samun daya daga cikin kushin din falon yayi ya zauna yana jan carbi,yana kallon yanda Malamin su ke biya wa ko wacce,da kuma yanda suke biyawa, Sai da lokacin da suke tashi yayi kafin malamin ya masu addu'a, Ɗaya bayan daya suke gaida shi suna fita,bai amsa ba sai dai ɗan gyada masu kai da yake yi,har suka gama fita, Daya daga cikin jerin ƴan matan da suka fita su uku ne ta dafe kirji tare da sauke a jiyar zuciya, Duk kallon ta suka yi"lafiya kuwa Zainab " Lumshe ido tayi ta buɗe "ke dai bari Sis Bilki wallahi duk sanda naga Yaya Suraj sai naji gabana yana faɗuwa,ban san me yasa ba,amma wallahi bala'in kwarjini yake min" "Lah Ashe bani kaɗai nake jjn haka ba,sai dai wani lokaci haushe yake bani saboda bai sake mana fuska,kullum fuskar shi a haɗe,in dai ba an nuna shi a TV bane yana wa'azi shi ne wani lokaci zaka ga yana murmushi,amma fa su mama cewa suka yi wai yana da fara'a,ni dai bana gani,kufa?ta faɗa tana kallon su. " Hadiza kenan,to bari kiji,ko jiya naga yana ma Khalifa wasa yaron Anti Hajo,mune dai ya rai na,insha Allah sai ya haɗu da mata dai-dai dashi,wacce zata zaunar dashi tace yayi ta dariya shi kaɗai "cewar sis Bilki. Gabaɗayan su dariya suja kwashe dashi kamar wasu sababbin mahaukata,dan maganar Bilki ba karamin dariya ya saka su ba, " Ba Amin ba Bilki,ke a tunanin ki a kwai maccen da zata iya juya wannan,balle har ta kawo mashi hauka,haka ma baki ji abinda yace ma kaka bane a ranar daya dawo,wai shi har yanzun bai ga maccen data iya motsa zuciyar shi ko da kaɗan bane,kin ga ko akwai matsala,ni dai kam zan so naga Allah ya nuna min wannan yarinyar data motsa zuciyar shi,ta saka shi kuka ace,sai mu ga Young Ustadz yana rokon asoshi," Nan ma wata Uwar dariyar suka fashi dashi Zainab harda faduwa sabar dariya, Daga bayan su suka ji ance "idan kun gama gulmar sai ku bani hanya in wuce" Da sauri suka zabura tare da juyawa suna kallon ta suna matsa mata, Ganin zata wuce ne yasa da sauri duk suka riƙo mata hannu "Aunty Maijidda baki dai ji me muka faɗi ba ko? Kallon su tayi daya bayan daya yanda duk suka riƙe ta tare da Zuba mata ido suna jiran su ji me zata ce, " Naji mana? "Me kika ji?Hadiza ta tambaya. " Komai da komai,ina nufin tun daga farko har in da kuka tsaya,yanzun ku sake ni bari naje na sanar dashi domin ya fara Addu'ar niman tsari a kanku" Ƙara cakume ta suka yi suka shiga roƙon ta akan ta rufa masu asiri ba zasu sake ba, "Ok,ok naji ku sake ni,amma duk sanda na karajin kun ma Suraj irin wannan addu'ar ni da kaina zan faɗa mashi" "Insha Allah ba za mu sake ba" "To ku sake ni mana na wuce" Duk sake ta suka yi ta wuce tana girgiza kai,tana jinjina zancen yaran a zuciyar ta,domin gata nan zaune a gida har yanzun ta kasa aure tana zaman jiran shi amma shi ko kallon ta bayayi,kuma kowa a gidan ya sani, Shi kuma yi yake kamar bai san da halittar ta ba acikin gidan,dan haka bata fatan ma a samu macen da har zata motsa masa zuciya,dan a wannan lokacin bata san wani irin hali zata shiga ba,ko kuma me zata iya aikatawaaikatawa ba. Tashi yayi ya shiga cikin ɗakin kaka in da take zaune tana jan carbi,zama yayi kusa da ita ya na tankwashe kafa"barka da safiya tsohuwa" Saida takai karshe sannan ta ajiye carbin "Surajo da fatan ka tashi lafiya? " Alhamdulillah" "Allah ya maka Albarka, ya nuna min auren ka" "Amin tsohuwa" Hararanshi tayi"sai kace yana da niyar yi" Ɗan murmushi yayi "ina da niya mana Tsohuwa," Mikewa yayi Abbu yasa ni aikin duba masa wani littafi bari naje," "In ajiye maka abin kari" "No A'a dan zan fita ne kuma ba zan dawo da wuri ba" "Allah ya tsare,amma ka tabbar ka karya da wuri dai" Murmushi kawai yayi ya fita. Dakin shi ya buɗe ya shiga ajiye carbin hannun shi yayi a inda yake rataye sharbi, Dakin da yake ajiye littatafai ne ya shiga sannan ya fara dudduba littafin,sai dai baya wurin,dirowoyin dakin ya fara jawowa yana dubawa nan ma baya ciki, Tsayawa yayi yana tunanin to ina ya ajiye littafin, Fitowa falo yayi ya jawo wani karamin durowar dake gefen kushin, Tsayawa yayi yana kallon abunda ke ciki wanda shi yana manta dashi, Hannu yasa ya dauko pos din harda wayar, Samun kanshi yayi da zama kan hannun kushin din,haka kawai zuciyar shi ke raya mashi ya kunna wayar, Dubawa yayi yaga wurin kunnawa sannan ya kunna, Kafin ya kawo ne ya buɗe pos ɗin,wanda ATM card dinta ne da aka rubuta Habiba Abdulmajid,sai master card,da kuɗi a ciki yan dubu daya daya,wanda bai damu daya kirga ko nawa bane, wani karamin kwali ya gani ɗan madaidaici,ciro kwalin yayi wanda yana buɗewa sai ganin karan Sigari yayi a ciki,wato Taba,ya jima yana jujjuyawa tare da tunanin yanzun mace ce ke shan wannan abin,tunda dai gashi a jakkanta ya gani,kafin ya maida komai a cikin jakkan ya rufe, Duba wayar yayi babu wani key da aka saka mata,wurin App ya fara dubawa wanda babu wani App a wurin sai irin wanda waya ke zuwa dashi,sai kuma WhatsApp da Facebook, ko TikTok babu a wayar, Komawa baya yayi ya shiga wurin hotuna, To ni dai bansan me yake gani a wurin ba ko kallo sai dai ji da nayi yana sauke numfashi akai-akai,sai kuma naga da sauri ya fita wurin yana kashe wayar gaba daya tare da mai su in da ya dauko, Mikewa yayi ya buɗe firig tare da daukar goran ruwa mara sanyi sosai yashi, Kafin ma ya ajiye goran hannun shine yaji wayar shi na vibration a Aljihu, Yana dubawa ne yaga sunan kanwarshi,ɗauka yayi wanda kafinma yakai ga yin sallamah yaji kukanta da ihunta, Cikin sauri yashiga tambayarta lafiya,meke faruwa, "Yaya, Suraj dan Allah kazo part ɗinmu da sauri Ammi ta zame ta faɗi,kuma ta kasa tashi" Bai ma gama sauraron abinda take fadaba tunda yaji tace Ammi ta faɗi ya fita cikin sauri wanda har yana dan haɗawa da sassarfa ya nufi part ɗinsu. Koda ya shiga falon yaga basu ciki,har zai haura sama yaji kamar kuka a kicin,dan haka can ya nufa, Ta samu ta mike da kyar hannun ta na cikin na Amira sai dai ta kasa ajiye kafar a ƙasa sai cije baki take yi, Da sauri a karasa in da suke yana rikota "Subhanallah,Ammi sannu,ba ki dai ji ciyo ba? Cije baki tayi" Suraj kafa ta,zafi yake min bana iya ajiye ta " Tsugunnawa tayi ya duba kafar wanda yake na hagu ne,Babban yatsar kafar yayi ja har ya fara kumbura, Yana mikewa kawai sai ji Ammi tayi ya dauke ta kamar wata yarinya yana tafiya da ita, "Suraj sauke ni,so kake ka kada ni " Bai kulata ba sai da ya fito da ita falo ya zaunar da ita kan kushin,sannan yace"Ammi bari na kira me kyaran kafa dan kamar kin samu targade ne" Kyara zama tayi tana jinjina mai kai"amma kar ka sanar da Abbu ku dan hankalin shi na iya tashi" "Insha Allah"ya faɗa yana zaro wayar shi a Aljihu. Wata number ya kira wanda bai jima yana ƙara ba aka ɗauka,sallamah kawai yayi yace" Idan ba damuwa ina buƙatar ganin ka a gida yanzun,"ban ji me aka ce mashi ba sai ajiye wayar da naga yayi ya koma wurin Ammi yana mata sannu, Kallon Amira yayi wacce ke hawaye"me ya faru a kicin ɗin? Share hawayen idon ta tayi "Yaya man gyaɗa ta taka shine ta zame" Cikin mamaki yace"man gyaɗa kuma,garin ya man gyaɗa ya zube har ta zame,ko dai gangancinki ne" "Wallahi yaya ban san yanda aka yi ba,amma ko jiya da muka gama girkin dare sai da na share kicin dinnan sannan na goge ko ina nayi wanke-wanke,ni bansan ta in da man gyaɗa ya fito ba har ya zuba a ƙasa,tunda ba a kicin muke ajiye kayan abinci ba" Shiru yayi yana ɗan nazari,ganin bai fahimce ko mai bane yasa yace"is ok, kukan ya isa haka " Jin ana sallamah ne yasa yace mata"je ki dauko ma Ammi Hijabi"shi kuma ya tashi ya fita, Bai wani jima ba ya shigo tare da mutumin,wanda anan ya duba kafar ya kuma tabbatar masa da cewa ta samu targade a babban ɗan yatsa,sai tsagewar kashi ta gefen ƙafar, Sai da ya koma gida yazo da abubuwan da yake bukata kafin ya fara mata ɗaurin kafa wanda ba karamin azaba ta ji ba, Allah dai ya taimaka an samu nasaran kyarawa,sai dai ba daman Kata kafar sosai, A ɗan kwana biyun da tayi wannan ciyon ƙafar aiki kamar zai kashe Amira,wacce ga zuwa makaranta ga kuma islamiya, Hakan ne yasa Kaka da kanta ta bada shawara akan dole a dauki ƴar aiki domin ba ta yanda za'a yi Amira ta iya waɗannan aiyuka ita kaɗai, Duk da Ammi bata soba ba yanda ta iya tunda lalura ne ya kamata wanda dole tana buƙatar mataimakiya, Matar da take kawo masu masu aiki Kaka ta kira ta sanar da ita suna buƙatar me aiki,kamar dai ko wani lokaci mace mai tsafta suke so, Ce mata tayi zuwa yamma za'a kawo ta. _____misalin karfe biyar,zaune take a saman tabarmar da aka shimfida mata,ta turo bakin nan nata gaba,wanda kallo daya zaka mata ka fahimce irin bacin rai dake tare da ita, Matan nan ce naga ta zo ta zauna kusa da ita tana miko mata wata waya Nokia wanda tasha lobali ko marfi ba ta dashi, "Biba karba mana" Kin karɓar wayar tayi tana mai da hannun ta baya kamar wata karamar yarinya, Duk yanda taso ta ɓoye dariyar ta dan karta ƙara tunzura kasawa tayi sai da ta saka dariya,ganin yanda tayi yanda kasan yarinya ƴar shekara shida,ga kayan data saka riga da zani wasu masu kalan tsofaffin,zanin leɓe daya yafi ɗaya kasan ya matse wanda da ƙyar ma in zata iya tafiya dashi,rigar gashi nan babu fasali dan ya mata yawa ajiki, Fuskarta dai yayi wani fari tas dashi mai ban sha'awa,gashi sumul babu wani ɗigon baki ko kurji,idanun ta sun kara haske domin ko kwalli babu,sai ƴan madai_daitan labbanta jawur dasu ta turo su gaba, Idan har kai mai lura ne kallo daya zaka ma hallittar jikin Biba kasan jikinta ba kalan wanda ya saba aikin wahala bane. "Kinga Biba haƙuri zaki yi ki karɓi wannan wayar haka,na saka maki sim a ciki,akwai kuma number ta a ciki,idan kina buƙatar wani abun sai ki sanar dani,kuma ta wannan layin VIP zai neme ki" Amsa tayi ba tare data ce mata komai ba ta mike tana daukar jakkan dake gabanta zata goshi ƙofa, "A'a tsaya kinga sai kin saka hijabi" Ta faɗa tana dauko hajabin dake ajiye a gabanta,tabi bayan ta, Sai da suka shiga Adaidaita sannan ta karɓi hijabin ta saka. "Kinga karki damu,ba wani daɗewa zaki yi a gidan ba,da zaran kin dauko masa abinda yake buƙata shikenan aikin ki a gidan ya kare,ko da kuwa a yau ne,kuma akwai littafin girki a cikin jakkan ki na saka maki,wanda zai taimaka maki" Ita dai bata ce mata komai ba domin bacin randa take ciki ma ya ishe ta, Jin mai Adaidaita ya saya ne yasa ta dago kanta tana kare ma wani tafkeken kofar Get din da suke tsaye,wanda akwai babban masallaci a kofar Get ɗin, Fitowa suka yi daga cikin Adaidaita suka doshi kofar gidan tare da jakkan ta a hannun yayin da take jin bugun zuciyar ta na sauyawa a ko wani taku da tayi...... *Last free page* 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *12* *Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku* *Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309* *ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865* Mai gadi ne ya buɗe masu Get suka shiga bayan sun faɗa mashi wurin Kaka zasu,duk da dama ya santa, Tunda suka shiga gidan take kallon ko ina cikin taka tsantsan,yayin da matar wacce taji yaran gidan na kiranta da A'i take nuna mata da ido waɗannan shiyoyin guda huɗu,"wannan dake kallon Arewa anan zaki yi aiki,sauran kuma duk na Ya'yan Kakar ce,sai na karshe wanda ɗiyarta ke ciki da nata yaran,idan mun shiga wurin tsohuwar dan Allah ki yi mata ladibi sannan waɗannan idanun naki da suke a tsaye ki dinga rusunar dasu"ta faɗa tana turo kofar wani shiya,"kinga kuma ta can baya ne dakin samarin gidan yake" Sallamah tayi a ɗan madaidaicin tsakar gidan wanda yake a share tas, Jin ba'a amsaba yasa suka karasa har kofar shiga cikin falon Kaka, Nan ma wata sallamah tayi,wanda suka ji an amsa masu ta bayan su, Duk juyowa suka yi suna kallon ta,ƴar budurwa ce wacce bata wuce sha tare,kusan tsaran Biba ce,dauke da ninkakkun kayan da aka wanke,alamun ta kwaso ne daga shanya,duk da kayan jikinta ba laifi amma daga dukkan alamu yar aiki ce, Murmushi ta sakar masu"barkar ku da zuwa,wa kuke nima" "Wurin Kaka muka zo tana ciki? " Eh ku shigo"ta faɗa tana shiga gaba,har cikin falon kafin ta nuna masu wurin zama,ta shiga kicin da dauko masu gorunan ruwa tare da kofi,domin yin haka dokar Kaka ne,in dai baƙo zai shigo wurinta, Wani daki tashiga bata jima ba sai gashi ta fito"ku jira tana zuwa" "To mungode ƴan mata" Basu wani jima ba saiga wata kyakkyawar tsohuwa ta fito daga cikin daki,ƙafarta tasha lalli na Hausa,tayi kyau abinta, Da murmushi ta karaso inda suke, Da sauri taga A'I ta tsugunna kasa tana gaishe ta,wanda ita ma ganin hakan ne yasa ta tsugunna, Zama tayi a kushin din dake fuskantar nasu tana dan dariya,"a'a maza ku tashi ku zauna,A'I kinsan bana son irin wannan gaisuwar" Komawa suka yi suka zauna kan kushin, "Ga ta na kawo kaka,da fatan tayi maki" Kallon ta take tun daga sama har kasa tana jinjina kai,"ya sunan ki yan mata"ta tambaya Kanta a duke yake domin matar ta mata kwarjini sosai,"Habiba,amma ana kira na da Biba" "Masha Allah suna mai daɗi,Habiba,shakaranki nawa" "Ishirin nake" Maida kallon ta tayi kan A'I wacce ke addu'a a zuciyar ta akan Allah yasa ta amsheta"wannan din tayi A'I,da fatan ba zamu samu matsala da ita ba" "Insha Allah Kaka domin ita ba tada matsala ga tsafta,na tabbatar sai kin yaba" "Allah yasa,yanzun dai za'a dinga biyanta ta hannun ta ne ko kuwa ke za'a ba" "A'a Kaka kawai ku dinga bata a hannun ta,shi zai fi," Yarinyar dazu ce ta fito zata wuce,kaka ta ce "Nafisa kawo masu abinci" "A'a Kaka a barshi domin sauri nake ina son in shaga kasuwa ne kafin a tashi," "To ba matsala,zubo ma Habiba ita," Kuɗi ta ciro wanda zai iya kaiwa dubu goma taba A'I "gashi kiyi kudin komawa " Amsa tayi tana washe baki"nagode sosai kaka Allah ya biya,ya ƙara lafiya " Cikin sanyin murya tace"kaka nima na koshi" "Ki saki jikin ki sosai damu Habiba,na tabbatar ba zaki yi dana sani ba" Dukar dakai kawai tayi domin haka kawai ta ji matar ta kwanta mata. Sallamah A'I taimasu ta wuce, Daukar waya tayi ta shiga wurin kira,bugu daya aka ɗauka,amsa sallamah tayi"ki turo min Amira " Sai kuma tace "to" Tana sauke wayar. "Iyayenki ƴan wasu gari ne Habiba" "Daura a Katsina" Ta bata amsa domin haka aka tsara mata, "Aikuwa nasan katsina sosai,a wata unguwa" Kafin ta bata amsa ne taji anyi sallamah a bakin ƙofa, Amsawa suka yi,kaka na bada umarni ta shigo, Tana zuwa zama tayi kusa da kaka tana rike hannun ta tana jujjuyawa "Wow kaka hannun nan naki yamin kyau,kamar muyi canje" "Ko dai zamu yi canjen ne,ai ku yaran yanzun kyuya ke hanaku kwalliya" "Ni dai banda ni,idan na samu lokaci zan zo kimin da kanki" "Sake min hannu karki karya ni,ga sabuwar mataimakiya nasa an kawo wacce zata dinga taimaka ma Ammi,kafin taji sauki,idan har ta mata kuma tana iya riƙe ta,idan kuma taga bata butarta zuwa lokacin ni zata dawo shiyana da aiki" Juyowa tayi inda Biba ke zaune tana kallon su,"Wow kaka ina kika samo ƴar aiki mai kyau haka? Tasowa tayi ta dawo kusa da Biba tana shafa fuskarta"Wow,gaskiya kina da kyau,kamar ba yar ƙauye ba" "Ke ni bani son zuba,tashi ki kaita ta gaida Ammi ki kuma nunnuna mata wuraren daya kamata ta sani" Tashi tayi tana rike hannun Biba,wacce ta dauki jakkanta da hannu daya,"muje" Tare suka fito da Amiran wacce take ta zuba mata surutu akan kyanta,ita dai sai dai tayi murmushi, Babban falo ne suka shiga wanda ba laifi komai an zuba shi daidai hankali,cewa tayi"ki ajiye jakkanki anan kafin muji me Ammi zata ce" Ajiye jakkan tayi a gefen kushin suka nufe wani ƙofa,nan ma cewa tayi"tsaya na sanar da ita shigowar mu" Nan ma tsayawa tayi,ita kuma ta shiga ciki, Bata jima ba ta fito fuskarta dauke da murmushi"muje tace ki shigo" Bin bayanta tayi,har cikin wani madaidaicin falo in da anan suka tarad da wata mata kyakkyawan zaune a kan kushin tasha kwalliya sai kamshi take zubawa, Samun kanta tayi da zama a ƙasa tana gaishe ta"ina wuni" Kallon yarinyar take yi cikin kulawa"lafiya ya kike" "Lafiya" "Ya sunan ki" "Habiba,amma ana kira na da Biba" "Daga wani gari kike" "Katsina a Daura" "Yayi kyau,da fatan dai ba kiɗa matsala,domin bana son kazanta ko kadan,ta ko wani bangare ya kasance kina da tsafta,idan har kin kiyaye zamu zauna lafiya" "Insha Allah Hajiya" "Nuna mata ɗakinta Amira,sai ki nuna mata kicin ta daura girkin dare,Sinasir da miyan ganye zata yi,sai ki bata shinkafar da nasa kika jika dazu" "TO Ammi" "Idan kin kammala nuna mata ki zo ki tafi islamiya kafin yayanki ya shigo" Nan ma amsa mata tayi, Tunda taji ance tayi Sinasir taji wani zufa na karyo mata,ita da batama taba jin sunan abinci haka ba,bata ma sanshi ba,shine za'a ce taje tayi, Duk wani surutu da Amira ke yi ba fahimtar ta take ba,har ta nuna mata ɗakinta wanda karamin gado ne kawai a dakin sai sif da kuma bayi a ciki, "Yauwa ki ajiye jakkanki kizo in nuna maki kicin dan zan tafi ne,idan kin kammala sai ki zo ki kyara dakin. Kara fita sukayi ta kaita har babban kicin dinsu ta kuma nuna mata in da kayan abinci suke da komai da komai har da Firig din da suke ajiye nama daban na saka abinsha da ban, Anan ta barta tsaye ta wuce, Komawa ɗaki tayi ta ɗauki waya ta kira number A'I,wacce sai da taimata kira uku kafin ta ɗauka so disgusting,jin tana tambayar waye ne,dan ba makaranta tayi ba,cikin jin haushi tace "Biba ce" "Ohh ya aka yi? " Sun ce nayi Sinasir,ni kuma ban san yanda ake ba" Cikin daga murya tace"ni bana jinki ki daga murya kin san wayar ki sai a hankali " Kara maimaita mata abinda ta ce tayi, "Oh,shinkafar da aka baki jikakke zaki wanke sosai sai ki zuba a Blender ki duba acikin firig in akwai nono mai kyau sai ki zuba kaɗan a cikin shinkafar sai ki niƙa,idan ya yi sai ki juye a kwano ki rufe shi dakyau sai ki ajiye a wuri mai dumi,ko kuma ki rufe da Flannel zuwa mintuna talatin,daga nan sai ki hau suya"nan ta sanar da ita yanda zata soya,miya kuma tace ta duba a cikin jakkanta zata ga littafin girki idan ta duba akwai wanda kalolin miya ne kadai aciki. Da taimakon A'i dana takardan nan ta samu tayi Sinasir da miya,kuma ya fita sosai saboda bata cika wuta ba kamar yanda A'I ta faɗa mata. Koda ta kammala har an fara shiga sallah Magrib,dan haka dakinta ta shiga tayi wanka sannan ta canja kaya tayi sallah,tana idarwa ta koma kicin ta wanke kayan da ta bata ta kuma goge duk inda ta bata, Samun kanta tayi da son dafa shayi irin wanda ta ɗauki lokaci mai tsayi a rayuwarta bata dafa irin shiba,wato shayin da mahaifinta ke matukar so,kullun ita ke dafa mashi a wannan lokacin. Dauko tukunya tayi ta dauraye ta goge,sannan ta daura a gas,sai da ya bushe sannan ta zuba ruwa madaidaici a kai,kayan marmari ta dauko ta yanka shi kanana_kanana sai dai banda kankana da gwanda,ta zuba a ciki,sannan ta kawo kayan kamshi ta zuba,hade da wasu ganyayyakin shayi masu kanshi data gani a store,ta rage wuta sosai dan haka a hankali yake dahuwa, Kulolin abincin data zuba na mutanen gidan ta dauka ta kai in da suke cin abinci,sauran kuma guda biyu ta bar shi a anan ɗan bata san ko na waye ba ne. Sai da aka idar da sallar Isha'i kafin ta juyo shayin ta tace ta zuba a fulas kananu guda biyu, Shayin kawai ta diba ta shige dakin ta, Ammin ce ta fito rike da wani ƙarfe irin wanda masu ciyo a kafa suke amfani dashi, Kicin ta fara shiga ta dudduba domin tabbatar da tsaftar ta,babu komai na datti domin komai a kyare yake saf, Dawowa falo tayi nan ma ta buɗe kulolin abincin ta duba,ba laifi tayi ƙoƙari,ganin fulas ne yasa ta buɗe wanda wani irin kanshi mai matukar daɗi ya ɗaki hancin ta,kofi ta jawo ta zuba kaɗan,kalan shayin ruwan zuma ne farar saƙa,kaiwa bakinta tayi ta kurbi kaɗan tana lumshe ido,domin kamshin fruit ne ya haɗu da kayan ƙanshi sai ya bada wani kamshin na musamman,gashi kuma da zaƙi dai dai mitsali, in kana bukatar suger kana iya karawa, Jinjina kai tayi tana sakin murmushi, Tana kwance tana jujjuya karamin wayar nan a hannun ta,sai ji tayi ana kwankwasa mata kofa ta ji an yi,tashi tayi ta fara buɗe ƙofar,Amira ce ta gani tsaye,"Ammi na kira"komawa tayi ta dauki karamin hijabin ta iya guiwa ta fito falo, Tire Amira ta miko mata wanda yake ɗauke da kuloli sai fulas daya a kai"wannan ki kaima Kaka,ni zan kai ma Yaya nashi" Amsa tayi domin ta gane shiyan, Kasan cewar gidan akwai haske wuta ta ko'ina yasa bata damu da duhun da garin yayi ba, Sai da takai ƙofar falon sannan tayi sallamah,amsawa aka yi, Dan haka jin an amsa ne yasa ta shigo kai tsaye, Maza ta gani zaune wadanda zata iya kira da manyan samari,biyu suna daddana waya yayin da daya kuma suke surutu da Kaka sai dariya suke, Kallo daya taimasu ta kauda kai tana gaida su,sai dai ba wanda ya amsa mata,wanda ba karamin haushi hakan ya bata ba,wai yau ita Biba take magana har ayi kaman ba a san da ita ba, Karasawa tayi wurin kaka cikin girmamawa tace"kaka ina zan ajiye maki abinci " "Ƴar Albarka ajiye anan,jiki kicin gashi can ki dauko min kofi," "To" Ta faɗa tana mikewa tabi hanyar da kaka ta nuna mata, Tana sako kai cikin kicin din shi kuma yana fitowa hannun shi riƙe da kofi mai dauke da ruwan zafi a ciki, Cikin rashin sani suka ci karo wanda kofin ruwan zafin ya faɗi ƙasa yayin da ruwan ya zubar mata a hannu,shi kuma ya zubar mai a ƙafa, Wani irin zafi taji ya sauko tun daga cikin ƙwaƙwalwar ta har yatsun hannun ta,dan haka kafin ma ya ankara dawa yaci karo har ta buɗe baki ta shiga kwara ihu tana yarfe hannu tare da fitowa falo da gudu rike da hunnun tana ihu. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *13* *Wannan Littafina mai suna a sama na kuɗi ne,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku* *Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309* *ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865* Jin ihu ne yasa duk suka maida hankalin su ta ƙofar kicin ɗin, Ganin yanda ta fito a gigice ne yasa Kaka mikewa tana salati tare da kiran sunan"Biba,Biba"amma ina gaba ɗaya ma hankalin ta baya wurin su domin ni man hanya fita kawai take daga Falon domin ta samu ruwan sanyi ta zuba a hannun,dan ko kaɗan bata shiri da ruwan zafi, Nafisa ca data fito ɗaki da sauri kaka tace"Nafisa riƙo ta muji me ya faru" Da sauri ta riƙe mata hannu "sannan Biba,zo ki zauna a nan" Ta faɗa tana zaunar da ita in da Kaka ta nuna mata, Yarfe hannu kawai take tana hawaye"waiyo hannu na,ki bani ruwa" Kaka ce tace"miko ruwa " Da sauri ta bude firig ta dauko goran ruwan sanyi ta buɗe sannan ta mika mata, Tana ƙoƙarin zubawa ne Kaka ta riƙe goran ruwan"karki zuba ruwan sanyi,muga wurin"ta faɗa tana jujjuya hannun wanda tuni wurin yayi ja, "Nafisa ɗauko kwano a banɗaki" Jin takun tafiya a hankali ne yasa suka maida idon su kanshi,shima a hankali yake ɗan dingisa ƙafa in da ruwan zafin ya zubar mai, Maida kallon ta kan Biba tayi "wai me ya faru ne? Cikin muryar kuka ta nuna shi da ɗayan hannun " Wannan ne ya kona ne da ruwan zafi," Ƙara kallon shi suka yi,shi kuma sai ɓata fuska da yayi ya nime wuri ya zauna, Ajiyar zuciya kaka ta sauke"Nurudeen zo dan Allah ka duba mata wannan hannun gashi har yayi ja" Bai ci musu ba,domin kuwa tunda ta fito kicin din idon shi ke kanta har zamanta ƙare mata kallo yake tun daga kan ɗan yatsar ƙafarta har zuwa fuskarta wanda ɗan kukan da tayi yayi ja, Tasowa yayi ya zauna a gefenta,"kawo hannun mu gani " Ba tare da tunanin komai ba ta daura tafin hannun ta saman nashi, Kallon yatsun hannun nata yake wanda suke zaro_zaro,gasu farare tas,ɗan shafa tafin hannun yayi yayin da yaji wani laushi da tsantsi a hannun nata,kai ko fatan ta abin kallo ne,"Sorry "ya faɗa a hankali, Buɗe first aid box,da Nafisa ta kawo yayi yana ciro wani kwalin cream wanda naga an rubuta Ketoconazole a jikin shi,buɗewa yayi ya ciro sannan ya ɗauki cotton Bud's guda daya ya tatsa Cream din a jiki sannan ya shiga shafamata a hankali yana kallon yanda take dan matse ido, Koda ya kammala shafamata cream ɗin bai sake mata hannu ba,sai kallon hannu yake domin ba karamin jan hankalin yake ba. Sai sannu kaka ke mata, Haɗa ido suka yi dashi dake zaune ya wani hakimce yana shan abu a kofi, Harara ta zuba mai,tana ɗauke kai,domin ba karamin haushe ya bata ba,ko sannu bai ce mata ba, Ganin abunda ta mai me yasa ya kauda kai yana jinjina rashin kunyar ta, Dariya Ibrahim yayi yana ajiye wayar hannun shi"ƴan mata ya kike hararar mana Young Ustadz"domin ya ga abinda ta yi,"Kaka ina kika samo yarinya mai kyau haka? "Tubarkarla,mai taimakama Ammi ce,dazu ta zo,gashi Sorajo na ƙoƙarin kona yar mutane" Jin yanda yake shafamata tafin hannu ne yasa ta zare hannun ta a cikin nashi tana kallon shi, Murmushi ya sakar mata, Ibrahim ne ya katse su"ni dai tamin Kaka,me sunan ta" Ɓata fuska tayi"ni fa bana son shashanci," Mikewa yayi tsaye "Tsohuwa sai da safe" "Ba zaka ce mata sannu ba,bancin ka kona ta da ruwan zafi" Bai bata amsa ba yasa kai ya fita, Cikin jin haushi tace "ku tashi ku tafi na sallame ku" Mikewa suka yi suma cewa "tunda laifin wani ya shafe mu sai da safe" Sakawa tayi Nafisa ta rakata har shiyan su sannan ta dawo,dan ita a nan shiyan kaka take kwana, Washe gari da Asuba,tana barci taji wayarta na ƙara kamar zai fasa mata kunne, Tsaki taja tana jawo wayar tare kashewa, Ƙara kira aka yi,wanda sau uku tana kashewa,amma sai ƙara kira ake yi, Ana huɗun ne dai ta ɗauka cikin jin haushin damunta da ake yi tace"pls abar ni in yi barci " Daga ɗayan bangaren taji ance"tashi zaki yi ki fara gyaran falo ki daura abin kari " Cire wayar tayi daga kunnen ta tana duba ko ƙarfe nawa ne "ƙarfe biyar dai dai yanzun" Cikin tsananin gajiyawa da maganar tace"A'i ba zan iya ba barci nake ji" "Dole zaki tashi domin haka aka tsara maki,dole sai kin shiga jikin mutanen gidan kafin ki samu ki cika aikin ki,dan haka tashi ki fara gyaran gida" Ranar haka tayi kyaran falon har kicin tana hawaye,domin Allah ya gani ita wannan aikin azabtar da ita ake,sai da ta kammala har karin safe kafin ƙarfe bakwai, Zuwa lokacin ji take kamar zata faɗi tsabar gajiya da ciyo da jikinta ke yi, Ruwan Tea kawai ta iya sha sannan ta fito harabar gidan, Kalle_kalle tayi,sai dai ba kowa a tsakar gidan,dan haka zagayawa tayi ta baya in da sai gashi tana hangar ɓangaren samarin gidan, Karema tsarin jeren ɗakunan wurin kallo tayi,kafin naga ta nime wani dan dutse nisa kaɗan da wurin ta zauna, Hannu naga tasa kasan hijabinta sai gashi ta ciro karan sigari ɗaya tare da abin kunnawa, Tunda ta saka abiki ta fara zuka har wani lunshe ido take tana jin wani natsuwa na sauko mata,haba ta yaya za'ayi ace wani tabar shaye-shaye,ai gara kawai a cillata rijiya, Jin kamar karan tafiya ne yasa ta dago kai a firgice ta na kallo wurin, Sai dai cikin rashin sa'a idanun su ya faɗa cikin na juna,wanda ba ƙaramin firgita tayi ba....... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *14* *Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku* *Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309* *ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865* Cikin sauri ta maida hannun ta baya tana fuskewa,tare da ɗauke idanunta cikin sana, Shima ɗauke idon shi yayi a kanta yana turo kofar daya buɗe ya shege tare da maidawa ya rufe, Banɗaki ya shiga yayi wanka,sannan ya canja kaya zuwa riga da wando na ratsattsen shadda fari kar,sai ɗaukar ido yake, Yana gama shiri ya fito daga bangaren su,ya nufe shiyan Ammi, Koda yayi sallamah babu kowa a falon dan haka samun wuri yayi ya zauna yana daddanna waya,daga dukkan alamu abu mai muhimmanci yake yi, Sam bata lura da mutum dake zaune a falon ba,da fari dogun tsaki ta fara ja tana rike Kwankwason ta,"waiyo Allah baya na,Allah ya tsina ma VIP,gara aikin komai da wannan"ta faɗa tana komawa kicin, Jin tsinuwar da aka yi yasa ya dago kai dan ganin wacce tayi wannan lafazin a cikin gidan su,domin yasan tsunuwa ba ɗabi'ar su bace,sai dai ko da ya dago bai ga kowa ba,tsirama hanyar kicin din ido yayi na ɗan lokaci kafin yaci gaba da abinda yake yi, Ammi ce ta fito falon domin ta san cewa da safen ne zai wuce dan zai gudanar da wa'azi a Jos, Tunda ta hango shi zaune ta saki murmushi,wato dai ba zai shigo dakin ta ba,domin haka ɗabi'ar shi take,baya taɓa shiga dakin ta da sassafe haka, Jin takun takalmin ta ne yasa ya ajiye wayar hannun shi yana mikewa,karasawa yayi inda take ya riko hannun ta yana sumbata,"Good Morning Ammi" Shafa kanshi tayi"Morning Sweet heart,Allah ya Albarkaci rayuwar ka" "Amin Sweet Ammi"riƙo mata hannu yayi suka zauna kan kushin, Ɗan ɗaga murya kaɗan tayi ta na kiran sunan " Biba,Biba" Da sauri ta fito kicin tana goge hannu tare da amsawa ta karaso in da suke tana amsawa,cikin girmamawa ta tsugunna "Mam gani" "Ɗan Allah ki kawo ma yaro na kofin shayi, amma karki sa madara da Sugar,sannan kar kisa tafasasshen ruwa,ki yi amfani da wanda ya ɗan fara hucewa amma ba sosai ba" "Yes Mam" Ta faɗa tana satar kallon shi, Da sauri ta dukar da kai tana mikewa,a zuciyar ta tana raya,na shiga uku,ba dai wannan bane yaron matar nan oh young ustaz kenan,hakan na nufin akanshi da baban shi zata yi aiki, ya Allah gashi ta gwabsa tun a matakin farko,me yasa da ya zuba mata ruwan zafi bata haƙura ba,Allah ma yasa dazu bai ga tana shan sigari ba,kai data shiga uku in dai wannan aikin ya lalace a wurin Vip. Ta gefen ido yake kallon ta tun lokacin da tsugunna a gaban Ammi har ta koma kicin, "Ammi wace wannan? Ya tambaya yana cigaba da danna waya. " Sabuwar mai taya ni aiki ce wacce kaka ta dauko " "Ammi bana son ta,ki sallame ta,zan sa asamar maki wata mai hankali" Kallon mamaki take mai,domin tunda take dashi wannan ne karo na farko data taba jin yayi magana akan al'amarin daya shafi cikin gida,dan haka ƙara maida hankalin ta tayi kanshi,tare da amsar wayar dake hannun shi wanda yake daddannawa ta ajiye gefe "yaro na,faɗa min,shin akwai wani abin ne,ko ta maka wani laifi nr? Ɗan murmushi ya sakar mata ganin lokaci ɗaya tana ƙoƙarin shiga damuwa" Ammi na,ki kwantar da hankalin ki,babu komai,kuma bata min komai ba,kawai dai bata min bane Ammi,ban yarda da yarinyar ba,kamar akwai abinda take ɓoyewa " Ajiyar zuciya sauke"batai maka ba,kuma kana zarginta " Jinjina kai yayi. "A ganin dana ma yarinyar ban fahinci wani abu tattare da yarinyar ba na damuwa ba,tana da kokarin aiki daidai gwargwado,na yaba da tsaftarta da kuma girkin ta,sai dai ban san Me ka hango ba a tattare da ita wanda yasa harka fara zargin ta,wanda ni ban hango ba,abin mamaki ban taba jin kace wani bai maka ba sai yau,ban sani ba ko zargin da kake mata ne yasa kace bata maka ba,amma dai na san kasan cewa babu kyau kace halittar Allah bai maka ba,kuma insha Allah dana kara samun sauki da yardar Allah zan sallame ta,tunda kaka ce ta kawo ta,dole nayi haƙuri da ita na dan wani lokaci,kuma ni ma zan saka ido a kanta " "Insha Allah zan kiyaye Ammi," Kafin ya kara magana sai gata ta fito hannun ta riƙe da ƙaramin Tea plate mai dauke da ƙaramin kofin shayi, Ajiye mashi tayi a gaban,ba tare data dago ba ta mike zata wuce, Ji tayi ya ce ma mamatshi "ki yi hankali da ita,sannan ki fara kasa ido a kanta,da zaran kinga abinda baki yarda dashi ba dangane da ita ko da kaɗan ne,ki sallame ta,karki damu da kaka ta kawota,ni zanji da komai" Iya nan wakai taji ta karasa shiga kicin, Jingina tayi da kofar kicin ɗin,wato dai daga dukkan alamu da ita yake yi,zargin ta yake yi,kuma ya sanar da mamarshi,Allah yasa bai sanar da ita batun shan tabar ta ba,dole ta fara takatsantsan ta samu ta karasa wannan aikin, Komawa tayi ta bakin ƙofar fitowa ta labe da kyau ta yanda zata iya jin me suke faɗi, "Idan ka tafi yaushe zaka dawo" "Nan da kwana uku insha Allah,domin a local government uku zanyi wa'azi a garin" "Pls Suraj ka dunga saka kayan sanyi,domin kasan yanzun lokacin sanyi ne kuma Jos a kwai sanyi sosai,ka dunga shan ruwan zafi akai_akai,kar ka bari mura ya kamaka kasan yanda yake maka" "Insha Allah Ammi" Ɗan marairaice fuska tayi"gashi Abbu ku bai dawo ba,kai kuma zaka tafi ka barmu ni da kanwar ka,gabaɗaya in baku gidan baya daɗi,pls karka je ka daɗe " Ɗan dariya yayi"karki damu Ammi,Abbu ma zuwa jibi insha Allah zai dawi,so karki damu," Murmushi ta sake tana ɗan daka tsalle kaɗan tare da dunƙule hannun ta"Yes "tafiya zai yi zuwa Jos kuma har na tsayin kwana uku gashi mai gidan ma baya nan," Waiyo daɗi, this is the right time da zan gama wannan aikin na bar wannan gidan kafin su dawo" Cikin jin daɗi ta koma kicin dan karasa kife kayan data gama wanke wa,idonta ne ya sauko a kan inuwar mutum, Ɗan tsayawa tayi jim,tana kallon inuwar,a hankali ta ƙarasa ta jikin windon tana jan labulen windon baya tare da lekawa,tabbas mutum ne ke a lebe a jikin windon,sai dai duk yanda taso ta iya hango wani abu dangane da wanda ke wurin bata iya ganin komai ba, Komawa tayi ta tsaya tana nazari,kenan hakan na nufin labe ake masu,kenan dai ace ba ita kaɗai bace keda buri a akan wannan aikin, Da sauri ta zagaya ta ƙofar kicin din ta fita,sai dai cikin rashin sa'a tana isa sai dai hangar bayan na miji tayi,to waye wannan kuma,lallai akwai matsala dole tayi sauri tayi komai kar ya zamana abin harin su ɗaya, Koda ta koma ta samu harya fita,ita kuma Mam ta koma ɗakin ta, Yanzun ta wata hanya zata bi ta samu ta fara shiga dakin Abbu kafin dakin wannan ɗan rainin hankalin, Dole tana buƙatar sanin komai daga nan zuwa gobe,domin iya lokacin da take dashi kenan,gashi daga dukkan alamu wannan matar bamai bari a shigar mata daki miji bane koda ta hanyar shara. Komawa tayi ta zube kan gado tana runtse ido akan dole sai ƙwaƙwalwarta ta fara aiki, Yana fita daga falon bayan sun yi sallamah da Ammi,wurin parking ya nufa inda yana isa aka buɗe mai kofar mota ya shiga sannan aka maida aka kulle, A hankali motar ya fara tafiya dan barin harabar gidan, Jinginar da kanshi yayi a jikin set yana lumshe ido na wani lokaci, Motar na gama barin gidan direbobi suka hau kan hanya da kyau, Gani na yi ya saki wani lallausar murmushi na gefen baki,wanda ba karamin kyau yayi ba,duk da bansan na Menene ba, Amma a zuciyar shi kuwa rayawa yake lallai wannan karon daga dukkan alamu tarkon shi zaiyi babban kamu,wanda yana ganin ta hanyar wannan Beran ne zai kai ga Asalin abin Farautar shi, Gabaɗaya shiyansu Abbu zagaye yake da Camera ta ko ina har izuwa shiyansu na samar,wanda babu wanda ya san dasu face shi, Wannan karon ya shirya wasan da gaske, Sai dai kuma wannan halitta kallon ta kawai yake,amma tun ganin farko daya mata ya riga ya shaida ita waye, Ya san yana da mantuwa akan abinda ya san baida amfani,idan kuma lokacin amfanin shi yazo yana tunashi,haka ƙwaƙwalwar shi take,dan haka tsaf ya sheda ta,wato dashi zata yi wasa ko,lailai bata san waye shi ba,amma a hankali zai fahimtar da ita ta yanda da ƙafar ta zata bar gidan, Wani murmushin ya kuma saki yana buɗe idon shi,tare da fara ma Annabi kirari a zuciyar shi. *this is just the beginning* *Yanzun Aka Fara* 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *15* *Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku* *Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309* *ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865* *Not edit* Jin an dafata tare da girgiza ta yasa ta dago kai a ɗan razane, "Lafiya Biba tun dazun Ina ta magana amma kinyi zirfi cikin tunani,meke faruwa ne" Ajiyar zuciya ta sauke me ƙarfi tana dafe kirjin ta,"Hmm,babu komai Nafisa,wai ina imagine ne a kan faruwar wani lamari mai tsayi,kin san kuwa a kan waye" Girgiza kai tayi"A'a " "A kan Young Ustaz" Ɗan zaro ido tayi"Young Ustaz kuma? "Eh,wai ina imagine ne yace ma Mam baya so na,bai yarda da ni ba,kinsan wani abin mamaki" Nan ma girgiza kai tayi domin da tafara kulle mata kai, "Wai har ina dab da barin wannan gidan bayan na kammala aikina,amma sai gashi kin tasheni daga mafarki na,naso ace naga yanda abin zai kasance," Kallon ta tayi"me yasa kika min magana? "Ohh yi hakuri,dama nazo wucewa ne na hange ki anan,shi yasa na zo" Matsawa tayi "zauna anan" Zama tayi kusa da ita"na gode " Jin an kara buɗe ƙofa an fito ne yasa ta kalle wurin, Mutumin dazu ne dai ya kuma fitowa ya tafi, "Waye wannan" Kallon wanda ta nuna mata tayi"Yaya Shamsuddeen kenan" "Amma ba'a giddan yake ba ko" "A gidan yake,baƙi taɓa ganin shi a shiyar ku ba? " A'a " "To ai shima yaron Abbu ne,sai dai shi Mamar shi da ban ne," Cikin mamaki take jinjina kai,domin a list ɗin da aka bata babu sunan shi a ciki"to shi ina Mamar shi" "Gaskiya ban sani ba amma dai a yanda naji sun rabu da Abbu" "Me ya raba su? Kallon mamaki take mata" Ya za'ayi in sani" "Oh haka ne,never mind me,amma suna kama sosai da Ustazu,dan dazu ma na ɗauka shi ne,har na tafi mafarkin zaune" Dariya tayi"mafarkin zaune ba,to bani labari akan mafarkin ki," Ita ma dariya tayi"kinsan wani lokaci mutum na zaune haka kurin zai kama imagining wasu abubuwa na faruwa,faɗa min halin Ustazu da yayanshi " Wannan karon ma sai da tayi dariya"ɗan Allah Biba,karki ɓata ma young Ustaz din mu suna,wai ustazu" Tabe baki tayi ba tare da tace komai ba, Mai do fuskarta tayi ta kalle ta"ya cika girman kai,sai ya dinga kallon mutane kasa_kasa" "La aikuwa Yaya Suraj bai da matsala,kawai dai kin mai rashin fahimta ne,kuma kinsan wani lokaci idan ba wai ka zauna da mutum bane baka sanin halin shi,daga shi har Yaya Shamsuddeen wallahi ba su da matsala,ɗan garama yaya Suraj wani lokaci zai dan maka magana,amma shi kuwa Yaya Shamsuddeen da wuya ki ganshi cikin gida," "Waɗancan ɗakunan kuma nasu waye" Nuna mata take da hannu "kinga a gefen na yaya Suraj na Nuriddeen ne,sai na Ibrahim da Salman" "Gidan akwai mutane har haka ne,su kuma ya'yan mutum ɗaya ne su? " A'a,kawai dai bari na miki ƙwari_ƙwari,a yanda dai na sani,ita Kaka da kike gani Mijinta babban malami ne,a hanyar shi na zuwa wa'azi Sudan suka yi hatsarin jirgi ya rasa ran shi, Tana da yara uku maza ɗaya mace, Abba Al-Mustapha shine babba yana da mata daya mai suna Hajiya Rahama,suna da yara uku,Yaya Ibrahim,sai Aunty Hajjo wacce tayi aure yaranta biyu,sai karamar su Zainab, Abba Al-Mustapha Custom ne. Na biyu kuma shine Abbu Sufyan,na faɗa maki ya taɓa aure amma sun rabu da matar wanda suna da yaro ɗaya da ita,shine Shamsuddeen,daga baya kuma ya aure Malama Hafsat wacce ta haifa mashi yara biyu,Yaya Suraj sai ƙanwar su Amira, Abbu Babban malami ne kuma ɗan kasuwa,shi kuma yaya Suraj duk da babban malami ne kamar mahaifin shi amma yana aiki ne da EFCC yana amsan Albashi mai tsoka. Na uku kuma Dady Ahmad shi kuma Soja ne babba,bai cika zama a gida ba yaran shi biyar,Nurudeen,sai Aunty Atika wacce wata biyar kenan da akayi auren ta,sai Aunty maijidda,sai Salman da Bilki " Na huɗun su kuma Goggo Hasiya,ita ta taba aure sai dai a yanda na samu labarin mijinta ya ɓace ba'asan inda yake ba,sai dai wasu na cewa guduwa yayi ya barta da ya'yanta,wasu suce sace shi aka yi,Allah kaɗai yasan gaskiya sai su,tana da yara biyu,Hadiza da Khadija, duk suna zaune ne a nan gidan ita da yaranta,sannan kuma kiyi hankali da ita dan masifaffiya ce na karshe, Sannan ko wani shiya suna da ma'aikata, Wannan shine labarin mutanen gidan,Halin su kuma a hankali zaki fahimce halin ko wanne daga cikin su,sai dai abinda zan faɗa maki shine kiyi hankali da Nurudeen da Ibrahim,domin ba kananan yan son aci duniya bane" "Me kike nufi" "Karki damu a hankali zaki gane me nake nufi" Ajiyar zuciya ta sauke tana mikewa "kinga tashi mu tafi,gashi har after Nine O'Clock na safe,bari na je na fara shirin daura girki,na gode da labarin ki" Dafata tayi "babu damuwa" daga nan kowacce ta wuce ɓangaren da take aiki, Har zata shige daki sai kuma ta dawo ta tsaya a tsakiyar falon tana kare ko'ina kallo,haka kurun zuciyar ta ke raya mata akan ta duba ta gani kar ya kasance tunanin ta na Camera ya zama gaskiya, Kicin ta shiga ta dauko abin cire yanar gizo-gizo tare da dogon kujera, Hawa tayi tana yi kamar mai cire kura amma kuma dubawa take yi, A haka ta gama zagaye lungu da sako na shiyan sai dai ko alamun camera babu, Ɗauko kujerar tare da sandar tayi ta shigo falon tana tsaki,"kai jama'a a duniya ba kada maƙiyi daya wuce zuciyarka," Jin muryar Ammi na kiranta ne yasa da sauri ta juyo tana amsawa, "Je ki Ɓangaren Goggon su ki kira min Amira,ta zo ta tayani gyara dakin Abbu kafin ya iso dan yana hanya,ki ce tayi sauri" "To Mam" Fita tayi tana bin ta inda Nafisa ta nuna mata nan ne ɓangaren goggon su a dazu, Tana isowa ɗan hanyar da ya raba shiyan Goggon da hanyar shiga shiyan Samarin gida ta kusa cin karo da Nurudeen, Da sauri ta matsa baya tana rabewa gefe dan bashi damar wucewa,"Sorry ban kula da kai ba" Murmushi yayi "koda ma kin bige ni kin bi ta kaina ai babu damuwa domin kin isa kiyi" Ita sai bata bashi amsa ba, Ba zato sai ganin shi tayi a gabanta yana daf da ita wanda har suna iya juyo numfashin juna, Riƙo hannun ta yayi yana juyawa cikin wani irin salo irin na mazaje waɗanda suka kware wurin yaudarar zuciyar ƴan mata"Ya hannun naki Bib,da fatan ya dai na maki zafi" Kafin ta buɗe baki ta bashi amsa ne suka ji taku a bayan su, Shi dai bai juya ba,amma ita da sauri ta juya,sai dai ganin mai wutowa ne yasa ta dauke numfashi tana Freezing domin ba karamin bugawa zuciyar ta tayi ba, Ko kallon in da suke bai yi ba,saima raɓawa ta gefen su da yayi ya wuce abun shi, Da ido ta bi shi har ya ɓace ma ganin ta, Ji tayi ya shafa fuskarta,"karki damu da wannan dutsen,shi bashida wata sha'awa a rayuwar shi,kar ki ji tsoro domin ba mu bane a gaban shi" Cikin sauri ta ture shi baya tana matsawa sannan ta juya cikin sauri ta bar wurin, Tana jin gabaɗaya zuciyar ta a jagule, Tura kofar falon tayi tare da yin sallamah,wanda bai fito sosai ba, Jin shiru ne yasa ta shiga cikin falon inda ta tarad wasu yan mata su Uku zaune sai hira suke cikin kwanciyar hankali ga kayan ciye-ciye a gaban su, "Sannun ku,,Amira Ammi na kira"ta faɗa tana juyawa ba tare da ta jira jin amsar su ba, Har ta kusa barin falon taji an daka mata tsawa tare da cewa" Ke jakar ina ce da zaki shigo mana falo babu sallamah,babu gaisuwa kawai sai ki faɗi abinda ke bakinki ki wuce kamar wata Tunkiya " Cikin mamaki ta kalle yarinya da ke fadar wannan mummunan kalami a kanta wacce bata wuce tsaranta ba, wato Zainab,dama haka take da fadin Rai, Nuna kanta tayi da hannun ta"da ni kike"dan ta juya gefe da gefe bata ga kowa ba, Takowa tayi gaban ta "in ba dake ba da wa zanyi,wai me yasa ku ƴan aikin nan kuncika raina mutane ne,ko dan kunga ana sake maku" Hadiza dake zaune ne tace "baƙi ga irin kallon da take maki ba" Amira ce ta tafi "ku kuma da kanunan magana... Kafin ta ƙarasa ne suka ji muryar goggo na fadin " Meke faruwa "tana karasowa inda suke. Cikin shagwaba Zainab tace " Goggo wannan mai aikin ne muna zaune kawai sai shigowa tayi babu sallamah,sai ce mana tayi sannun ku,kamar taganmu a gadon asibiti " "Ni dai matsamin ki ga in wuce" Cewar Amira"goggo na tafi Ammi na kira na" Hannu kawai ta daga mata, Kallon Biba take daga sama har katsa"ya sunan ki,awani bangare kike aiki,nawa ake biyanki " Kallon matar tayi ido cikin ido babu alamun tsoro ko dar a tare da ita"suna na Biba,ina aiki ne a ma Ammin Amira" "Waɗanda kike ma aiki basu faɗa maki matsayina dana ƴaƴana bane a wannan gidan? " Ba'a faɗa min ba" Saukan wani lafiyayyen mari taji a lafiyayyen fatar fuskarta mai taushi wanda nan take shaidan yasunta biyar suka fito kwance a fuskar ta, Nuna ta tayi "amma daga dukkan alamu baki samu tarbiyya daga wurin iyayenki ba,to ki sani idan har bikida tarbiyya ni nan zan tarbiyantar dake, wawuya,jahila,dakikiya kawai,fitar min a shiya,karna kara ganin kafarki a shiyana" Idanun ta sunyi jawur na azaban Marin da tasha wanda tunda take a ba a taɓa Marin ta ba sai yau, Bata son ko kaɗan ta nuna gazawarta ta hanyar zubar da hawaye,shi yasa ta juya kawai zata fita, Dakatar da ita tayi "ke,zo ki basu haƙuri" Juyowa tayi,ta kalle yaran da ake cewa tana ma haƙuri,girgiza kai tayi ta kalli goggo "Never" Ta fadin haka ta bar falon, Juyawa tayi ta kalli ko ina,nima take ta samu inda zai fi mata sirri domin amayar da abinda ta hadiya, Ta gefen ɗakunan samari ta samu dakali ta zauna, Hawaye ne ya fara zuba a hankali a hankali,kafin kuma ta rufe bakinta tana fashewa da kuka mai taba zuciya tana gunji,wanda da kaji yanda sautin kukan ke fita kasan cewa wanda ke yinshi tabbas kuka ne na kadaici da kuma tuno wani abu mai ciyo a rayuwarka irin wanda ka kasa mantawa dashi, Babu abinda ya mata ciyo irin kiranta da jaka, tunkiya,da wannan yarinyar tayi, sai mamarta data kira ta da Jahila,kalmar mara tarbiyya bai mata ciyo ba,domin ta san tun daga lokacin data saka kafa tabar gida,tun daga lokacin ta fita a jerin masu tarbiyya, Duk gatan da suke takama suna samu,to wallahi bai yi koda rabin gatan da take dashi ba,ilimin da suke takama suna dashi na Boko idan suka ji a inda tayi karatu da abinda ta karanta sai kusa haɗiye zuciyar su da mamaki,haka kuma ilimin Addini,sai dai kawai ta ajiye su a gefe ne kawai domin basu da amfani a gare ta,domin tayi Alkawarin duk abu abu wanda ta sanadin iyayenta ta same shi to ta ajiyeshi har abada,ko da menene. Domin koma yaya ne su suka hallakar da rayuwar ta,kai,bama tason ta tuna komai dangane dasu har a badas Ta sanadin su gashi waɗanda basu kai matsayinta ba suna wulantata, Tayi kuka sosai wanda sai da fatan idon ta ya kumbura,idanunta sukayi jawur, Ta kwashe kusan mintuna talatin kafin ta fito wurin dan komawa shayansu, Tana fitowa shi kuma yana jawo kofar dakin shi ya wuce,wanda daga dukkan alamu cikin sauri yake, Taga lokacin da yake kokarin saka katin buɗe ƙofar shi a aljihu,sai da cikin rashin sani katin ya faɗi, shi kuma bai lura ba ya wuce, Ganin ya wuce ne yasa da sauri ta karasa ta dauki katin tana jujjuya shi, Wani irin murmushi ne ya subuce mata wanda nan take ta manta duk wani damuwa daya shiga zuciyar ta a shin mintunan nan, Rungume katin tayi a kirjin ta,tana murmushi,sai kuma ta ciro ta kai baki ta sumbata,tare da lumshe ido jin ta shaki wani ni'imtaccen kanshi "mugu,kai Allah na gode maka,ko na komai in dai na samu na dauko na ɗakin shi a dakin Abbu bazai min wuyan samu ba" Karrama rungume katin tayi wanda tana zuwa ta saka a na'urar,nan take kuwa kofar ta buɗe, Cikin sauri ta shiga ta maida ƙofar ta kulle, "Wow" Ta faɗa tana kallon tsarin falon yanda yake a tsaftace,ko ina sai kamshi yake tashi, Ta jima tana kalle_kalle a dakin kafin ta shiga aikin take mashi kaya,wanda tundaga falon har zuwa ɗakin barcin shi bata ga komai ba, Wani fitowa data jawo a dakin barcin shi,babu komai aciki face damin kuɗi wanda a kalla taga na Country biyar a ciki,harda daloli, Maida durowar tayi ta kulle ba tare data ko taba ba, Cikin mintunan da basu wuce goma sha-biyar ba ta gama hargitsi komai na dakin harta zanin gado a wurge yake a kasa amma bata ga koda alamar abinda take nima ba, Ji tayi ranta ya baci,so take ta ƙara dubawa,sai dai kuma ta riga taja lokaci, Dan haka ta yanke shawarar ta fita kawai wata rana zata ƙara samun dama, Kar ya zo ya Kamata, Kallon dakin tayi yanda gabaɗaya ta fitar dashi kamannin shi, Girgiza kai tayi,data tsaya kyara mashi dakin ya kamata,Gara ta gudu ai ba zai san ko waye ba. Da wannan shawaran tayi amfani ta doshi kofa domin fita,sai dai tana saka kati kofar ya shiga key ya kulle bam, Ƙara kwada sawa tayi bayan ta juya katin ko bata saka dai_dai bane, Sai dai ga mamaki ta duk yanda tayi domin kofar nan ta buɗe taki buɗewa sai ma nuna mata key da yake yi, Tun tana yi da wasa har ta fara tsorata ta hau jan ƙofar tana tura shi iya karfinta ko zai buɗe, Sai dai ina kofa ko motsi bai yi ba, Tsoron ta daya,yanzun idan ya kamata me zata ce mashi ta zo yi dakin shi,ƙila ma asirin ta ya tonu, Wasa_wasa tana cikin wannan halin har awa daya ya shige,har gashi na biyu na ƙoƙarin shudewa, Ga uwar yunwa da ke addabar ta kamar hanjin cikinta zai tsinke, Nan lamarin ya wuce tunanin ta ne yasa kawai ta zauna nan bakin kofar tana fashewa da kukan nadamar shigowa dakin tare da kife kanta a jikin ƙofar tana rusa kuka............ 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *16* *Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku* *Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309* *ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865* Tun tana yi da ɗan ƙarfi har ta koma yi a hankali daga nan barcin wahala ya ɗauke ta wanda bata masan iya adadin lokacin data ɗauka ba, _____koda suka je suka dauko Abbu a filin jirgi zuwa gida,ya daɗe a shiyan Amme suna hira,har Abbu yayi wanka suka ci abinci tare,sai wuraren ƙarfe daya sannan ya fito ya nufi bangaren su,yana jin Ammi na aiken Amira akan taje ta dubo mata Biba tun dazu bata ganta ba,Abinci ma sai tare da ita Amiran suka lalaba suka yi tunda ba makaranta, Ganin ya laluba aljihunshi bai ji katin buɗe ƙofar shi bane yasa kawai ya saka numbobi ya buɗe ƙofar dashi, Yana tura ƙofar yaga ya buɗe kaɗan sannan kamar a kwai abu mai dan nauyi daya tare kofar wanda ya hana shi buɗewa yanda ya kamata, Yana sako kafar shi bayan taku biyu,yaji kafar shi ya sauka a kan abu mai laushi, Da sauri ya daga kafar yana matsawa baya a tsorace dan Allah yasa bai gama sauke kafar shi ba,duk a tunanin shin ajikin mage ya saka kafar shi,shi yasa yaja baya yana kiran sunan Allah,dan ba karamin tsoron mage yake ba. Tsayawa yayi cikin tsananin mamakin ganin ta a wurin yana kallon ta,ya kuma kalli kofar,ta yaya ta shigo ne,ta ina, A hankali ya saka kafa ya tsallake ta, Jin yanda ta sauke wani ajiyar zuciya mai ƙarfi irin wanda ke nuna mutum yana cikin kuka barci ya dauke shi irin shi tayi, Hakan ne yasa ya juyo ya kalle ta ba tare da yayi niya ba, Idon shine wannan karon ya sauka akan fuskar ta,wanda yasha mari,ganin kamar shaidar hannu a fuskar ne yasa a hankali ya kara taku ɗaya daga inda yake zuwa gare ta, Tsura ma fuskar ido yayi,tabbas shaidar mari ne wanda ga alamun kwanciyar yatsu biyar nan a faran fatan fuskar ta,sai kuma idanunta da suka kumbura, Dauke idon shi a kanta yayi wanda nan take kuma suka kara sauka akan yanda falon ya canja kamanni ba kamar yanda ya fita ya bar shi ba, kalle ta yayi ya kalli falon kafin ya shige dakin shi,in da ya iske nan ma haka ɗin ne, Dafe ƙwanƙwaso yayi yana nazarin ɗakin kafin ya fara tattara duk wani abunda aka cire daga muhallin shi yana mai dawa daidai,ganin lokacin sallah Azahar ya gabato ne yasa yashiga bayi yayi wanka,dan daga masallacin yana son ya fita ne. Daga inda take kwance kamar wacce aka tunatar da inda take haka ta Mike a firgice,ba tare data tsaya gama wastsakewa ba ta tura ƙofar dan ganin ko zai buɗe,sai dai cikin tsananin sa'ar ta sai gashi kofar ya buɗe, Ai bata jira komai ba yanda kasan wacce aka kora haka ta tashi ta fita da gudu tana sauke ajiyar zuciya, Ba tare data Ankara ba kawai sai ji tayi taci karo da mutum,tana kokarin faɗuwa shi kuma ya torota yana maida ita tsaye a kan ƙafafun ta, A hankali taji muryar shi yace "ki dinga kula,ki daina guda ɗan bashi da amfani"ya fada yana kare mata kallo,dan gaba ɗaya a hargitse take,gashi ko ɗankwali babu a kanta,ga ido a kumbure, Kallon shi kawai tayi ta saka kai tana yin gaba,dan yanzun bata shi take ba,duk da ta gane shi,wato Shamsuddeen ne. Binta yayi da kallon mamaki,kafin ya kalli ƙofar dayaga ta fito, Baya son zuciyar shi ta raya mashi wani abu,amma kunsan yanda zuciya take,har ya kai bakin kofar dakin shi,ya juya yayi kofar dakin Suraj, Yana tura ƙofar yaji ya buɗe,dan haka shiga yayi, Tsayawa yayi yana karema falon kallo kafin idon shi ya sauka a kan ɗan kwalinta dake yashe ata bakin kofar, Shiru yayi ya zuba ma ɗan kwalin ido, Sai kuma yaji yana son ya shiga cikin dakin, A hankali yake takawa har ya isa bakin ƙofar ɗakin, Kiran sunan shi yayi"Suraj " Daga inda yake zaune a gaban karamin miro yana shafa mai ya amsa yana juyowa, Shi kuma jin an amsa ne yasa ba tare daya jira komai ba ya shigo cikin dakin, Sai kuma naga ya tsaya turus kamar wanda yaga wani abu, Kallon Suraj ɗin yayi wanda yake ɗaure da Tawul iya kugu,jikin shi ba riga daga dukkan alamu kuma daga wanka ya fito, Sai kuma ya kalli kan gado wanda yake a hargitse zanin gadon ya tattare ya koma gefe ɗaya,ga filalla duk sun yi gefe,dan daya gama gyara dakin ya rage saura gado,sai kawai ya wurga filallan a kan gadon kafin yaje ya dawo ba. Ganin yanda yake ƙare ma dakin kallo ne yasa yace"Bismillah zauna,bari na saka kaya" da sauri ya jirgiza kai"A'a ba zama zanyi ba,dama naga kofar ka a buɗe ne shi yasa na leko naga ko kana ciki" "Ina ciki" Juyawa yayi"to bari na tafi"har ya juya sai kuma ya juyo ya kalle shi "amma kuma" Ko tunanin ne yayi oho sai cewa yayi kuma"ba komai barshi "ya faɗa ganin yana kallon shi,ya juya ya fita yana mamakin wannan kuma wani irin sabon lamari ne yake shirin faruwa dasu kuma acikin wannan gidan kuma da wanda ba'a taba tunani ba, Dole ya faɗa ma Kaka,ko kuma ya sanar da Abbu kafin abun yayi tsanani..... *in Allah ya kaimu zanci gaba* 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *17* *Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku* *Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309* *ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865* Allah ya taimake ta koda ta shiga cikin falon babu kowa,cikin sauri ta shige ɗakin ta tana sauke ajiyar zuciya,ko ba komai ta godema Allah da dakin ya buɗe ba tare da mai dakin ya dawo ba, Banɗaki ta shiga tayi wanka sannan ta canja kaya ta fito falo,zuwa lokacin an dan jima da idar da sallar, Tana fitowa anan ta iske Ammi zaune tare da Shamsuddeen sai shi uban gaiyar wanda yake rike da carbi yana ja,shi kuma Shamsuddeen Amira na zuba masa abinci a plate suna dan hira da Ammi, Tana zuwa tsugunnawa tayi a gabansu "Mam barka da Juma'a"sannan ta kalle su cikin dukar dakai tace" Barkan ku da Juma'a " Dago kai Shamsuddeen yayi yana kallon ta, "Yauwa barkarmu da rana mai falala,sai dai kuma ina kika je ne Babi tun dazu na aika cigiyar ki a cikin gidan nan sai dai ace ba'a ganki ba,ina kika je? Wannan karon ba Shamsuddeen ba har ta shi kanshi da idon shi ke lumshe yana jan carbi sai da ya dakata na ɗan wasu lokutan dan jin ne zata ce,yayin da shi kuma Shamsuddeen ɗin yake satar kallon dukkan su, Ba tare da dar ba tace"Mam kiyi haƙuri a lokacin da kika aikeni kiran Amira ne bayan na kirata ina hanyar shigowa saiga kiran Uwar ɗakina akan Mamata ba tada lafiya daga ƙauyen mu har an shigo da ita cikin gari yanzun haka tana Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, Mam kiyi haƙuri hankalina ne ya tashi shi yasa na tafi ba tare da izinin ki ba"ta faɗa tana share guntun hawayen daya zuba a idonta, Idonun shi dasu rufe bai masan yanda akayi suka buɗe ba tsabar mamakin irin karyar da wannan ƴar yarinyar ta haɗa a lokaci ƙanƙani,sai tsintar idanun shi yayi a kanta, Yayin data gefe ɗaya kuma Shamsuddeen ya kusa kamewa a zaune yana tunanin kodai ta manta dazun ya ganta tana fitowa ɗakin ƙanin shi. "Subhanallah,ai ban sani ba dana hada ki da wani kuje tare,yi hakuri bar kuka,insha Allah mamarki zata samu lafiya da yardar Allah, Yanzun ya jikin nata? Jan majina tayi cikin muryar ban tausayi tace" Da sauƙi" "Meke damunta ne har haka" "Likita yace hawan jini ne ke damun ta" "To ba komai kar ki damu,zuwa anjima Shamsuddeen in baka komai sai ka kai ta ku dubo Mamar nata" Da sauri ya girgiza kai"A'a Ammi zuwa ajima zamu fita da Abbu ne sai dai ko Suraj" Jiyowa yayi ya kalli yayan nashi yana bata fuska,wanda shi kuma da sauri ya kauda kai, "To hakan ma yayi,kaga sai kuje kaida Amira ku gaida su" Ba zai iya ci mata musu ba ko kaɗan,kuma ma bancin haka zai so ganin karshen mai ƙarya,"insha Allah Ammi,sai dai kimin hakuri zuwa bayan sallar la'asar sai mu je " "Hakan ma yayi Allah ya kalmu" "Na gode sosai Mam Allah ya biya ki,Allah yasa kifi haka" "Amin kar ki damu,ɗauki ga bakin leda can ki kaima Kaka" Ɗaukar ledae tayi ta fita tana sharan hawaye, Girgiza kai Ammi tayi"yarinya abin tausayi" Duk cikin su ba wanda ya bata amsa. Tana fita kai tsaye shiyan kaka ta shiga inda ta same ta a zaune saman Babban darfuma ta mike ƙafa Nafisa na ja mata, Cikin girmamawa ta gaishe ta tare da ajiye mata ledar a gefe, "Ɗauka ki kai min ɗaki Biba" "To Kaka" Ɗauka tayi ta shiga ɗakin, Tsayawa tayi sake da baki tana kallon ikon Allah,wai dama har yanzun akwai irin wannan Gadon na mutanen da Mai Runfa,lah,ita da labarin shi kawai take ji bata taɓa gani ba, Dakin gabaɗaya tsarin shi da kayan dake ciki duk na mutanen da ne,sai dai komai a tsare yake,kuma a tsaftace, Akan wani teburi ta ajiye ledar ta fito tana murmushi, Zama ta yi a gaban kaka tana tankwashe kafa,"Kaka nikan dakin ki yamin ƙyau sosai " Kallon yarinyar tayi itama ta tana sakar mata murmushi "me ya burge ki a dakin tsohuwa? Cire hannun Nafisa tayi daga kafar Kaka ta shiga matsa mata a hankali tana dannawa" Komai da komai,kinga ni kam har balle wannan gadon naki mai runfa,da kwanunaka,harda kyaryan mai kamar kwanu,kinsan wani abu? Girgiza kai tayi tana jin daɗin matsar ƙafar da take mata,dan har tafi Nafisa iyawa,ta kuma san dai_dai inda yake ma mutum ciyo,"A'a saikin faɗa " "Inda ace mijin da tan aura zai so irin waɗannan kayan ko,da nazo kin ɗan min naki na tafi dashi,ɗan Allah idan kin tashi kyauta da wannan gadon ki bani ina so kinji" Ta fada tana marairace fuska. Dariya sosai Kaka ta saka ganin yanda ta wani marairace fuska ita a dole tana roƙo"in banda ke me zaki yi da kayan tsohuwa" "Ni dai ina so kinji kaka,kuma kullun zan dinga zuwa ina danna maki kafa ina kuma tuna maki dan kar ki manta" Dariya take tana jinjina wauta irin na yarinyar wacce cikin lokaci kankani ta shiga ranta, Abbu ne suka shigo tare da Abba,suma da fara'a a fuskar su jin dariyar tsohuwar tun daga ƙofar falo, Sallamah suka yi tare da shigo bayan kaka ta amsa, Ganin sun zauna kusa da kaka ne yasa ta matsa tana gaida su, Abba ne yace"wacece wannan "ya fada cikin sakin fuska dan shi yana da son wasa da yara. " Sunan ta Biba ina jin baku taba haɗuwa bane,amma a dakin Ammin yara take,bayan tafiyar Abbu Sufyan ne na daukar ma Ammi ita saboda tsautsayin daya same ta" "Godiya muke Uwar ƙwarai" Cewar Abbu yana murmushi, Cikin jin na'uyin dattawan tace"Kaka na tafi sai anjima" "To Ƴar Albarka sai na ganki,kar dai ki manta da Alƙawarin mu" Dariya tayi kasa_kasa"ba zan manta ba" Tana fita Abbu yace"to wani Alkawarin kuma aka yi" Tana dariya ta sanar dasu yanda suka yi da Biba,aikuwa suma ba karamin darawa suka yi ba,daganan suka shiga hira kamar yanda suka saba duk Juma'a,a haka itama Goggon yara tazo ta same su,sai daf da sallar la'asar sannan suka fito shiyan su mazan suka tafi masallaci.... Tana fitowa shiyan kaka komawa tayi shiyan su,a kicin taga abinci a kula ta diba iya cikinta ta shige daki. Sai da taci ta koshi sannan ta mike,juye_juye ta hauyi akan gadon,haka kawai ta rasa meke mata daɗi,ta rasa natsuwarta,komawa ƙasa tayi ta kwanta,sai dai nan ma haka ne,ji take kamar tayi ihu,abinda bata so tayi dai shi ne dole zata yi dan samun kwanciyar hankalin ta,in ba haka ba ji take kamar ta tube kayanta tayi yawo tsirara, Jakkan kayanta ta ciro ta zazzage shi gaba ɗaya,daga can tsakan jakkan naga ta ciro wani dan sacet din magani wanda banga suna a jikin shi ba,guda daya naga ta cire tare da ballashi gida biyu ta saka rabi a baki ba tare data damu ba akan ta kora da ruwa, Har wani jan numfashi take da saukewa tana wani lumshe ido yanda kasan wacce keshan wani abin daɗi, Maida sauran tayi a kasan jakkan shi kuma ballin ta samu leda ta daure shi,harfa ta kusa gama mai da kayan kamar wacce aka tsikara ta kara zazzago kayan ta ciro ballin ta wurga abaki ta tattaune shi,goran ruwan da taci abinci shi ta dauka tasha sannan ta kara mai da kayan, Komawa tayi kan gadon ta kwanta tana kallon sama yayin da taji wani natsuwa da kwanciyar hankali na sauko mata,a hankali ta fara lumshe ido tana budewa,ganin yanda dakin ya fara juya mata a hankali a hankali, A haka ta kasance ita dao ba'a sume ba ita ba'a farke ba,har lokaci ya tafi. Ganin an idar da sallar La'asar ne Ammi tace Amira taje ta sanar ma da Biba akan ta shirya yanzun Suraj din ya mata waya su same shi a bakin get. Koda ta shiga dakin a kwance ta same ta,dan haka karasawa tayi inda take kwance tana tada ita"Biba,Biba,ki tashi wai Ammi ki shirya Yaya Suraj na get yana jiran mu" A hankali ta buɗe idanun ta,waɗanda ba karamin nauyi suka mata ba,da kyar ta iya haɗo ɗan sauran hankalin daya rage mata"to ganinan zuwa" Juyawa tayi ta fita ba tare data lura da halin da take ciki ba, Ita kuma ganin ta fita ne yasa ta tashi da kyar ta shiga ban ɗaki,ruwan sanyi na fanfo ta kunna ta tara kanta,sai da ta gama jikewa sannan ta fito,ita gaba ɗaya jinta taje a 140 komai daidai, Jakkanta ta jawo ta ciro jallabiya baki ta saka,ta tauko zanin Atamfa ta daura asama,sai karamin Baby hijab ta daura a sama,wanda ana ganin bakin jallabiyar da yake da dogon hannu,kuma ta kasan ma zanin bai gama sauka ba,ana ganin baƙin jallabiyar,takalmanta masu kyau ta saka ko nace masu ɗan dama dama acikin wanda A'i ta saka mata, Tana fitowa ƙafarta na gurdewa da takalmin kasancewar sa mai ɗan tudu, Ammi bata falo dan haka tayi wucewar ta,dan ma ko tana falo ba ganewa zata yi ba, A bakin kofar gida ta iske Amira a tsaye wacce tana ganinta ta karasa in da mota ke fake ta buɗe gidan gaba ta shige, Ita ma tana zuwa gidan gaban ta buɗe tana ƙoƙarin zama a kan Amira, Ganin da gaske zauneta zata yi ne yasa da sauri tace"ke Biba baki gani na ne zaki zaune ni" Dakatawa tayi,cikin wani irin yanayi tace"Ke Amira baki gani na ne da ba zaki ce min akwai mutum ba,ni fa bana son iskanci, Ta faɗa tana buɗe ƙofar baya ta shiga ba tare data kulle kofar ba, Kallon juna sukayi ita da Yaya Suraj wanda ya kauda kai, "Mu tafi mana wai me muke jira ne,nifa zafi nake ji, Juyawa tayi ta kalle ta sai gani tayi kofar motar a buɗe," Oh My God,Biba nifa ina da abinyi dan Allah ki kulle ƙofar motar mu tafi " Kallon ƙofar tayi,cikin mamaki tace "wani kofar zan kulle bayan wanda na kulle,ko dai baki gani ne? Kallon yayan nata tayi" Is she ok? Kara kauda kai yayi gefe kamar bai ji ta ba, "Ya ilahi" Ta fita ta rufo kofar da karfi cikin jin haushin Biba wacce tayi wani shiri kamar mai shirin yin Surfe, Jan Mator yayi suka hau kan titi yayin da babu mai yi ma ɗan uwan shi magana kowa da abinda yake sakawa a ran shi, "Ta wani Get zamu shiga" Ya fada a hankali ganin sun kusa isa. Jin ba'a tanka mashi bane yasa cikin jin haushi Amira tace"wai ba da ke ake magana ba Biba? Kamar me magagi cikin ihu wanda sai da ta kusa tsorata su daga shi har Amira tace"ta kofa zamu shiga" Juyawa baya tayi " Biba wannan wani irin hauka ne,ba sai ki yi magana a hankali ba" "Kaji min yarinya,bancin a hankali nayi magana,so kike nayi ihu ne,ni da ban iya ihu ba,a hankali nafi iya magana sai dai ki yi haƙuri," Da karfi ta dafa kujeran da yake zaune"kai Direba kayi gudu damu mana kamar kana tuki,wai ko dai kanada tsohon Basir ne " Kiran sunan Allah ya fara domin kuma ya tabbatar daga dukkan alamu yarinyar nan da wuya in tana da hankali, Ba wanda ya kulata har suka isa cikin Asibitin suka faka mota in da ake ajiyewa, Suna fitowa da kyar ta samu ta tsaya,dan wallahi zuwa lokacin ƙwayar data ci ya gama jukuwa, "Ta ina zamu bi? Cewar Amira tana kalle a cikin Asibitin, Ihu tayi da gudu taje ta rungume wata mata suna dariya tare, Jawo matar tayi ta takawota gaban su" Yaya ga Aunty Jasmine,Malamarmu ce" Gaisawa suka yi da matar cikin mutunci, "Ɗan Allah yaya Kuje bari ingaida yayar ta da aka kwantar zan karaso" Jinjina mata kai kawai yayi, Jan hannun ta malamar tayi suka wuce, Shi tsoron yima yarinyar ma magana yake yi Allah ya gani,balle yanda ta wani kame tana daga hanci, Badan yaso ba yace "mu je wurin Mamar taki" Gaba tayi shidai yana binta a baya,da haka suka shiga cikin Asibitin,shi dai yaga sai wuce bangarori daban-daban suke suna tafiya,wani wurin ma sau biyu suke zagaye shi, Shikan ya gaji da wannan zagayen dan ya lura kamar ma tafiya kawai take yi, "Ke tsaya" Juyowa tayi ta kalle shi, "Wai ina ne wurin" Cikin kallon rashin fahimta tace"ina ne ma za mu je? Wannan karon ko dafe goshinshi yayi,yau Ammi ta haɗa shi da aiki,da ba dan babu yanda za'ayi ya koma ba tare daya cika umurnin ta ba da tun a titi data kira shi da suna Direba yayi wulli da ita,, Cikin bacin rai yace"gaida mahaifiyarki " Dafe kai ita ma tayi"Oh ashe haka ne,nama manta,"yatsarta ta saka abaki tana juye juye"ta ina ne ma hanyar "dan gani take gabaɗaya hanyar ya rarrabe mata, Dan hanyar ya kasu kashi uku ne ko wanne da bangare da zai kai ka, Hannun hagu ta nuna tana dariya " Yauwa,Ustazu nan ne hanyar"ta faɗa tana yin gaba, Ba yanda ya iya dole ya bita har kofar wani daki, Sai da ta ƙwanƙwasa sannan ta cire takalmi ta shiga da sallamah,juyowa tayi ta kalle shi "shigo mana" Babu musu yana hamdala a zuciyar shi koba komai yayi barka ya rabu da Tambelen ta, Dan haka shima da sallamah ya shiga sai dai bai cire takalmi kamar ita ba, Kasa karasa sallamar yayi ganin a inda suke,wanda ba ko ina bane da ya wuce banɗaki, Yanzun banɗaki yarinyar nan ta kawo shi, Cikin tsananin masifar da ba zai iya riƙe kanshi ba awanni lokacin yace"wai ke wata irin mara hankali ce,dama Mamar taki a banɗaki take,sh........... Kafin ya karasa fadar a binda ke bakin shi ta yanka ihu mai ƙarfi tare da fadowa jikin shi tana kankameshi,wanda ba karamin tsorata shi tayi ba dan saura kaɗan su zube ƙasa da ba dan yayi saurin dafe bangon ba,dan a rayuwar shi babu abinda ke saurin tsorata shi irin ihu, ita kuma wannan shedaniyar kamar ta sani sai tsorata shi take........ 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *18* *Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku* *Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309* *ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865* Kokarin ture ta daga jikin shi yake yi amma taki bashi dama,sai ihu take yi tana kuka wanda haka ne yaja hankalin mutanen dake wurin tare Nos, Da sauri ya maida face mask din data cire mashi dan baya son ko kaɗan a san waye shi,wannan ma yana iya zamar mashi abin kunya, Nos din data iso inda suke ne cikin faɗa_faɗa tace"wai meke faruwa anan ne" Da sauri ya cire ta daga jikin shi yana tura ma nos ɗin ita wacce ganin zata faɗi yasa ta rukota jikin shi, Ita kuma cikin gushewar hankali ta cakumi wuyar matar tana nuna mata shi"wannan ne,wallahi shi ne,ya.. Ya... Ganin da gaske shirin zubewa take yasa wata mata dake kusa da ita ta jijjiga ta,dan suna tsoron ko wani mugun abin ya ta"je buɗe idon ki,me ya maki " Ƙara nuna shi tayi da hannu "Mama ta,Mama ta ya sace" Duk mutanen dake wurin cikin tsoro suka zubo masa ido,wanda shima kanshi cikin tsoron yake kallon ta ganin tana shirin jawo masa masifa, Juyawa yayi da shirin barin wurin ta kwalama security kira, Jin an kira security ne yasa ya tsaya, Zuwa lokacin babu abinda yake yi sai kiran sunan Allah a zuciyar shi, domin sam baya buƙatar a san koshi waye, Cikin yanayi na fitar hankali ta kuma cewa"Ku duba min shi,tana nan cikin Aljihun shi ya saka ta,ku caje min shi da kyau" "A'a anya kuwa wannan kanta daya kuwa,Madam Merry ina ga fa kamar mata cikin hankalin ta,ji yanda take magana" Duk kallon ta suka yi domin tabbatarwa, Shi kuma da wannan damar yayi amfani yabar Asibitin yana hamdala dan ko takan Amira bai bi ba. *Bayan Sati ɗaya* Tunda ta dawo gida bata ƙara saka shi a ido ba har yau,haka kuma ta kasa tuna me ya faru a wannan ranar,ita dai kawai tasan ƙwayar da ya kamata ace ta raba guda daya kashi uku ta sha,shine ta shenye guda ɗaya, Sai dai tana iya tuna ta shiga mota zasu Asibiti,amma daga nan bata iya tuno komai,sai farkawa da tayi ta ganta kwance a Gadon asibitin bayan awa biyar. Tsakanin ta da kaka kuwa a kwai shakuwa sosai,dan yanzun duk yamma ita ke mata dannan ƙafa,yayin da suke shan hiran su sosai, Yau ma kamar ko yaushe ne a wurin ta,sun saka Kaka a tsakiya ita da Nafisa sai dariya suke mata tana basu labarin lokacin da zata yi aure irin lallin amare da aka mata,Lallin gida aka saka mata tun daga tafin kafa har zuwa guiwar kafa,shine wai idan zasu yi aure irin shi zata ma kowanne su, Sallamar da akayi ne tare da shogowa shi ya katse su, Cikin jin haushi da ɗan tsawatsawa matar tace "wannan wani irin rashin hankali ne da tarbiyya zaku buɗe baki haka kunata dariya kamar wasu batattu," Kallon Bibi tayi dake kwance samar dadduma "come on,Dalla sauka,dama ku ƴan aikin nan baku iya samun wuri ba,ni bansan me yasa kike haka ba Mama,ai wannan raini ne,ace inda ɗan gida ke zama nan nasu aiki ke zama,kai ku saurare ni,daga yau bana son na ƙara ganin ku a a zaune irin haka,indai ba wani aiki ba," "Kin dai sana'a bana son irin wannan halin Rahama,da masu kuɗi da talaka ai duk na Allah ne,dan haka bana son kina banbacewa ba, " Daga bakin ƙofa taji ance"wlh Mama Gara ta banbance,dan masu aikin yanzun idan ka yi sake sai su ce sune masu gidan kai kuma kai ne ƴan aiki," Nuna Biba tayi"ƴar uwa Kinga waccen yarinyar,duk gidannan babu mara kunya irin ta,kiri_kiri na saka ta abu ace bata yi" Cikin Mamaki ta maimaita kalmar "bata yi" "Kwarai kuwa" Kaka ce ta kuma katse su"ni fa bana son haka,abinda ya wace kuma me na maimaita shi,bana son haka,ku kuma ku tashi ku tafi" Da sauri Nafisa taja hannun ta suka bar falon zuwa cikin ɗakinta, "Wai waye wannan matar? Mikewa tayi saman gado " Wash Allah,wannan da kike gani ita ce Babban Suraka ta wannan gidan,matar Abba Al-Mustapha,Ajiya Rahama, Kin ganta nan halin su daya da Goggon yara,idan ta saka ma mai aiki ido to ko bata so da kanta zata gudu ta bar gidan ba dan ta so ba, Matar ba ta da sauƙi ko kaɗan,yanzun bari kiga,ba dai ta ɗauki fuskarki ba,to kin shiga uku domin ta dinga aikawa a kiraki kenan," Katseta tayi"in dai har zan shiga uku ta sanadin ta to fa sai dai mushiga uku ni da ita,dan in ban huta ba ita ma ba zata huta ba" "To ni dai na faɗa maki gara kiyi a hankali" Dafa Kafadar ta tayi tana mikewa "kowa dai ya bi a hankali domin har yanzun Biba nake" Da yamma ta kammala girkin dare kenen sai ga kira daga Momy Rahama wai tana buƙatar Biba, Dama wanka take shirin shiga sai ga Amira ta zo ta fada mata, Tare da me aikin da aka aika ta zo ta bi,har cikin babban falon su inda me aikin tace ki jira a nan, Kare ma falon kallo take yi tana tabe baki,ba laifi an zuba karya, Ganin ta gaji ne yasa ta ni me guri kan kushin ta zauna tare da daura kafa daya kan ɗaya tana kallon TV dake kunne ana hasko Namomin daji, Salatin data ji daga bayan tane ya ta juya, Karasowa gabanta Hajiya Rahama tayi tana tafa hannu "yanzun ashe da gaske ne abinda Goggon yara ta fada a kan ki" Mikewa tayi tsaye tana ɗan kyara rigar ta, Ibrahim ne ya shigo yana tambayar "Mom lafiya? " Ni da fitsararriyar yarinyar nan ne" Kallon ta yayi "Biba me ya faru" "Ba wannan ba,maza ɗauko abin goge kushin ki koge min inda kika zauna,A'a daka ta,bana son da injin,dauki Soso ki saka ruwa ki goge,yanzun kafin magriba" "Mom ta yaya zata iya goge kushin da hannu,pls mana ba zama kawai tayi ba" Jan hannun shi tayi"bana son ka saka baki akan wannan maganar mu je "ta faɗa tana jan hannun shi suka bar wurin. Ajiyar zuciya ta sauke tana fitowa daga cikin falon domin ganin in da zata samu soso da Bokiti, Ta bayan shiyan ta samu yan aikin shiyan su uku duk sun yi tsurotsuru," Kai ina zan samu Soso da bokiti " "Bari a dauko maki" Dayae ta faɗa, Haɗa mata ruwan da kayan kamashin da ake goge kushin tayi ta mika mata tare da soso, Karba tayi ta koma ciki ta fara goge sabon kushin din da bai yi komai ba, Cikin mintuna biyar ta gama jika kushin ɗin nan sharkaf da ruwa,domin ruwan dake cikin Bokitin sai da ta tabbatar da kushin din ya kusa shanye shi,kaɗan din daya rage garin mikewa ƙafarta ya ture Bokitin ruwan ya zube, Ba tare da damuwa ba ta dauki Bokitin ta fita dashi ta bar shiyan.... Kuyi haƙuri mura ya saka ni a gaba,.. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *19* *Na mai da Littafina mai suna a sama na kuɗi,tare da JAURO,idan kina son daya 300,dari uku,guda biyu kuma da Yar Tsanar Zinari tare da Jauro,dari biyar 500,ko wani daya dari uku* *Hauwa Umar,Zenith Bank, 2284905309* *ko katin waya na MTN,tare da turo shedar biya ta 08141644865* Ihun da taji ne yasa ta zabura da sauri daga saman sallayar da take ta fito, Khalid ne rungume a jikin Zainab yana rusa ihu tare da rike ƙafa, "Lafiya,me ke faruwa? Ta tambaya tana karaso wa wurinsu" Me ya same shi? "Mama,wai waye ya zubar da ruwa ne haka,gashi Khalid ya zame,ni kuma na daura takardu na a saman kushin kalli yanda suke jike kamar na zuba a ruwa" Kallon kafar tayi wanda nan take ya kumbura,ta kalli yanda kushin din ya jike,"kira likita ya duba ƙafar nan " "To Momy" Amsar shi tayi tana ta lallashin shi,har likitan ya zo,nan ya duba shi ya kuma tabbatar da yayi targade, Nan ta ba da baƙi kuwa aka gyara ma yaron kafa wanda take jin kukan shi har cikin zuciyar ta,domin shine jikan ta na farko yaron Aunty Hajo, Ganin yayi barci ne yasa ta fita da kanta tayi shiyan Ammi,wacce ita harma ta shige daki dan lokaci kusan tara saura Tana shigowa Amira ta samu zaune tana daddana laptop,ganin wacce ta shigo ne yasa ta mike tsaye tana mamakin me ya kawo Momy Rahama Shiyan su,dan tasan bata shigowa sai da dalili mai ƙarfi, "Ina ne dakin me aikin ku" Yanda taga tayi magana a dake ne yasa ta nuna mata da hannu, Kai tsaye dakin ta shige, Sai dai bata same ta a ciki ba,jin motsin ruwa a banɗaki ne yasa ta ɗan dakata, Mintuna biyu tsakani sai gata ta fito daure da tawol wanda ya saukar mata har guiwa,suman kanta a jiki wanda yake ja,dan ba za'a saka suman kanta a jerin baƙaƙe ba,yana da tsayi dan ya sauko mata har kafaɗa duk kasancewar shi a jike, Sam bata lora da ita ba,dan hankalin ta na kan wayar ta da taji yana ƙara, Jin saukar abu me nauyi a kanta ne yasa ta dafe wurin tana rintse ido,dan wani irin zafi taji ya ziyarce ta wanda yasa ma ta kasa ihu, Kafin ta dawo haiyacinta ne taji saukar duka a jikin ta na igiyar caja da ke ajiye a wurin, Wannan karan kam ihu ta saka domin zafin ya mata yawa,kun san yanda duka yake ga jikin da yake jikakke,abun babu sauƙi, Saukan bulala kawai take ji a jikinta babu kakkautawa, Tsabar gigicewa yasa ta rasa wake mata irin wannan hukuncin,dan abun yazo mata a ba zata ne,gabaɗaya ta ruɗe, Cikin ikon Allah ta samu sa'a ta hankada Hajiya Rahama wacce take jibgegiyar mace,domin ba karamin ɓace,shi yasa ta samu sa'a ta saka ta a tsakiya, Tagal_tagal tayi sai gashi ta faɗa kan gado, Da gudu ta samu ta fito fallon tana ihu tayi waje,har tana banke Amira wacce take tsaye ta bakin kofa tun jin ihun Biba na farko, Ta juya ne kenan dan zuwa kira Ammi sai ga Biban ta fito da gudu tayi waje yayin da Momy Rahama tabi bayan ta ita ma da gudun wanda take yi kamar zata kifa,dan in da akan ɗan ta ne ko jikan ta babu wanda take jin zata iya ragama, Tana kaiwa tsakiyar gidan ta tsaya cikin tsananin kuka tana kalle_kalle dan ta rasa ina zata je ta tsira a wannan lokacin,ɗan irin raɗaɗin da kanta da jikin ta ke mata bana lafiya bane,dan tunda take a rayuwar ta bata taba fuskarta abu makamancin haka ba, Idonta ne ya tsaya a shiyan Kaka,tana juyawa baya ta hango Momy Rahama saura kaɗan ta cimmata, Zaune suke sun tasa kaka suna zolayar ta wacce take cin naman gasasshiyar Rago,Aunty Maijidda,Yaya Ibrahim,Sulaiman,Bilki,da kuma Suraj wanda yake tsaye ta bakin ƙofar shigowa yana amsa waya, Bata iya gudu sosai saboda jirin data fara gani,ba dukan data mata bane matsalar,abinda ta buga mata akai shine matsalar, Ji yayi an faɗo jikin shi da ƙarfi,sai kuma aka zagaya ta bayan shi aka kankame shi,cikin kuka da kuma murya mai tattare da tsananin tsoro take"Help me! Help me please! " Gabaɗaya hankalinsu ne ya dawo kansu,mamaki suke wacece wannan ,daga ina kuma take haka,domin dai sun ga mutum daga ita sai tawol,duk jikin ta a buɗe yake, Ganin shigowar Momy Rahama tana haki ne yasa suka maida akalar kallon su kanta, "Yauwa Suraj miko min makiran yarinyar nan,yau sai naga ubanda ya ɗaure maki kafa a garin nan" Jin abinda tace ne yasa ta sake shi da sauri,ta juya tana nufan wurin da Kaka ke zaune, Komawa bayanta tayi ta tsugunna ta rike rigarta ta baya "ɗan Allah kaka karki bari ta matso inda nake,kashe ni zata yi,she is a monster" Cikin hasala tace "kam bala'i,ni kike kira da monster? Ta faɗa tana karasowa cikin tsakiyar falon. Da sam bata gane taba,amma jin muryan ta ne yasa ta kira sunan ta dan tabbatarwa" Habiba" Kara rike rigarta tayi da karfi "ɗan Allah gata nan zata zo,ki ce ta tsaya ɗan Allah ki taimake ni" Ranta ne ya baci sosai "wannan wani irin rashin hankali ne Rahama,Me haka zaki biyo yarinya da gudu kamar sa'ar ki,ashe har yanzun baki da hankali ban sani ba" Cikin daga murya tace"Mama amma kinsan abinda yarinyar nan tayi kuwa,ruwafa ta zubar da gangan dan na sakata goge kushin Khalid ya zame yayi targade sai da aka mashi kyaran kashi" "Sai me dan ya faɗi yayi targade,yanzun so kike ki kasheta dan ta saka jikanki yayi targade saboda bakida kunya baki San daraja taba,ace yarinya har ta gudu ta zo shiyana amma ki biyo ta har gabana zaki daka,lallai baki ganin daraja ta" Shiru kawai tayi tana huci, Jawota tayi daga bayanta,ita kuma tana girgiza mata kai tare da kara boyewa, Jawota tayi"is ok,fito " Jawota tayi ta tura mata ita gabanta "gata nan dai sai kashe ta tunda ta taɓa jikanki" Kauda kai tayi"nifa Mama ba haka nake nufin ba,naga duk kin canja maganar "ta faɗa tana barin falon cikin jin haushi tare da kuɗin idonta idon Biba sai ta karya ta, Ganin ta fita ne yasa ta zame tana zama a wurin tare da saka kuka sosai, Ammi ce ta shigo tare da Amira cikin sauri, Gabaki ɗayan su yanda kasan wadanda aka ɗinke ma baki,sai binta da ido da suke yi cikin tausawa,domin ga shatin bulala nan a jikin ta,wanda ya fito rado_rado a jar fatan ta, Da sauri Nafisa ta matso inda take tana kokarin ɗaga ta"Biba tashi muje ki saka kaya,jikin ki abude yake" Fisge hannun ta tayi daga cikin nata"ki ƙyale ni! Bubu inda zanje,yau bazan kwana a garin nan nan ba," "Haba Biba me kike faɗa haka ne? Ga bashi kaka ta hanata tabaki ba,ai ta wuce,tashi muke" Cikin kuka ta ce "baki ga yanda jikin na yayi ba,kalli hannuna,! She is wicked women! What did I do to her! Me na mata,ni ba zan ƙara kwana a gidan nan ba,"ta faɗa tana dafe kanta tare da ɗan rintse ido" Ance gidan malamai akwai tsoron Allah,suna kyautatama kowa,ba suda zalunci,Ashe duka karya ne,su masu son kansu ne,na tabbatar da a wani wurin nake aiki da babu wanda zaimin haka,tunda nake a rayuwata ba'a taba marina ba,sai a gidan nan,ba'a taba duka na ba sai wannan so calling gidan malamai,Nafisa kalli yanda ta bata min jiki na,shikenan na zama mai tambo a jiki,ba zan zauna ba,na gama aikin I am out" Gabaɗaya jikin su ne yayi sanyi,domin tabbas ba'a kyauta mata ba,kuma a yanda sunan su yayi kauri bai kamata a samu irin wannan shaidan daga cikin gidan su ba, Ji tayi an yafa mata abu a jikin ta,wanda ya rufe ruf jikinta gaba ɗaya, Dago ido tayi ta sauke a kan Ammi wacce ke tsugunne a gabanta, "Idan har an zalunce ka,kana da damar da zaka faɗi abinda aka maka,amma suturta jikin ki ya zamo shine abu na farko daya kamata kiyi"ta faɗa tana share mata hawayen dake sauka saman fuskarta, Aunty Maijidda ce cikin tsoro tace " Ammi jini" Duk kallon inda ta nuna suka yi,farin hijabin da Ammi ta yafa mata ne ya fara jikewa da jini wanda yake ɗigowa daga cikin kanta, Ammi na kokarin kai hannu saman hanta ne,taji saukar lallausar hannun shi biyu saman kanta wanda hakan yayi daidai da lunshe ido da tayi tana ganin wani duhu na gifta mata, 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *20* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Salati Kaka ta saka cikin tsoro,domin ko kaɗan bata son tashin hankali tana da saurin rudewa,"inna'lillahi'wa'inna'ilaihi rajiun,ya Ubangiji ka rabani da ganin bakin rana a rayuwa ta,yau me zan gani,kisan kai a gidan nan,"gaba ɗaya ta ruɗe tana kuma kokarin ruɗa su da kalamanta, Ganin bata numfashi ne yasa cikin tsoro ita ma Ammi tace"Shamsuddeen bata numfashi fa" Koƙarin ɗaukarta yake yace "Ammi ki kula da Kaka" Ɗaukarta yayi yana ƙoƙarin barin Falon da ita, Da sauri Nurudeen ya dakatar dashi ta hanyar faɗin "ina kuma zaka kai ta,baka ganin halin da take ciki? Wani mugun kallo ya watsa mashi sannan ya kuma saka kai, Kaka ce tace" Shamsuddeen dawo da ita nan Nura ya duba ta" Cikin tsananin jin haushi ya dawo da ita ya ajiye ta a saman kushin ya juya ta bar falon, Duk da kallo suka bishi,to me shi kuma ya bata mashi rai haka, Kiran sunan shi da kaka tayi ne yasa shi dawo da kallon shi kanta"Sujaro zo ka dauke ta ka kai ta dakina" Kallon wacce ake cewa ya ɗauka yayi yanda take wance babu numfashi,a hankali ya tako in da take kwance ya dauke ta ya shigar da ita dakin kaka,saman karamin gadon kaka ya kwantar da ita, Aunty Maijiddarh ce data biyo shi a baya ta yaye gabaɗaya hijabin da Ammi ta rufa mata wanda ya gama baci da jini"Yaya Suraj ka dafe kanta inda yake fitar da jini" Kauda kai yayi daga kallo ɗaya da yama jikin ta,dan sai lokacin yake ganin irin yanda fatar jikinta yayi,jin muryar Nurudeen yana ƙoƙarin shigowa ne yasa yaja zanin gadon ya rufa mata jikinta gaba ɗaya dashi, "Ki danne mata wurin" Abinda ya faɗa kenan ya bar ɗakin, Kai tsaye in da su Kaka suke ya tsaya ya mata magana,sai kuma ta kwalla kiran sunan Nurudeen wanda ya shiga dakin ko yana ƙoƙarin zame zanin da aka yafa mata,"Fito ga Hauwa'u ta zo,sai ta duba ta" Yi yayi kamar bai ji me tace ba,sai da Maijiddarh tace"Kaka na magana " Tsaki yaja ya fito falon yayin da ita kuma wacce aka kira da Hauwa'u ta shiga dakin, Maijiddarh ita take ta taimaka mata har ta gama mata treatment sannan ta rubata Allurai da magunguna, Duk suna zaune suna jiran fitowar ta, Kai tsaye wurin da yake zaune ta nufa tare miƙa mashi ƙaramin takarda "yallabai an samu nasaran tsayar da jinin sannan na mata duk abinda ya kamata,wadannan magunguna da Allurai ne da za'a siya zan dinga zuwa na mata na kwana uku ne,sannan shatin jikinta ma zai tafi idan tayi amma da cream din dana rubuta," A maimakon ya karba sai kauda kai da yayi ganin duk yanda suka zuba mai ido, Ganin bai da niyar karba ne yasa Ammi tace"kawo takardar " Miƙa mata tayi cikin girmamawa, "Allah ya maki Albarka yarinya,Bilki zo ki ɗauko kuɗi a daki na ki sallame ta mun gede sosai"cewar kaka, Cikin rawar jiki Bilki ke kokarin tashi,sai ji suka yi matar tace" A'a Kaka ki barshi tsakani na da Suraj yafi nan,babu matsala Allah ya bata lafiya " Da Amin suka amsa kafin ta masu sallamah ta fita, Tashi suka ga yayi yabi bayan ta, Ammi ne da Kaka suka shiga dakin, Allah sarki baiwar Allah,a hankali take sauke numfashin wahala,gabaɗaya ta gama basu tausayi, "Ki yi ƙoƙari ki bada a amso maganin da Alluran" "To Kaka,bari na saka a kawo mata kaya saboda idan ta tashi" "Haka ne" Fitowa falo suka yi, Salman ne yace"wai me ya haɗa ta da Momy Rahama? Balki ce ta bashi amsa"wai rashin kunya tai mata,ai ni wallahi ba karamin birge ni tayi ba,dan yarinyar sam ba ta da kunya,haka fa taima goggo rashin kunyar nan,bata San Momy ba kyale ta zata yi ba"ta fada tana mikewa "tunda an gama game bari na ƙara gaba" Haɗa ido suka yi da Nurudeen wanda ya zuba mata harara,kasancewar ta raina shi shiyasa ko akai bata kawo shi ba saima dariya da tayi tana barin falon, Kafin suma su watse, Ranar a shiyan Kaka ta kwana tare da Nafisa,cikin dare ne wani irin zazzafar zazzaɓi ya taso mata wanda jikin ta har wani gab_gab_gab yake yi,yanda kasan wacce zata tashi, Hakan ba karamin tsorata Nafisa tayi ba,gashi bata son ta tayar da kaka saboda ta san tana da hawan jini idan tana barci ba'a tashin ta, Gabaɗaya ta rasa mafita, ta kuma san tabbas idan bata nime taimako ba komai na iya faruwa da Biba, Wani shawara ne ya fado mata,dan haka da sauri ta shiga dakin kaka ta dauko wayar ta, Tama rasa wata number zata kira dan Allah ya gani ba tayi Boko ba,ba zata iya tantance waye ta kira ba ko wa zata kira, Dan haka number data gani a farkon wurin kira ta latsa ma kira,tana kallon Agogo,a lokacin ƙarfe biyu na dare, Kira biyu aka ɗauka,jin muryar wanda yayi sallah ne yasa cikin rawar jiki ta kira sunan shi"Yaya Suraj kai ne? Ta tambaya domin tana buƙatar tabbatarwa, Bai damu da bata amsar tambayar data mai ba sai ma jeho mata nashi tambayar da yayi"ina kaka? "Tana barci" "Lafiya kika kira? " Biba ce ba ta da lafiya "ta fada da sauri jin yana ƙoƙarin ajiye wayar. Dan shiru yayi yana tunanin ma wacce Biba, " Na sani"ya bata amsa dan sai yanzun ya tuna tunda yasan dai a shiyan mutum ɗaya ce ba ta da lafiya,shi baimasan sunan ta ba sai yau. "Yaya wallahi jikinta rawa kawai yake sosai gashi yayi zau,na rasa me zan yi,tsoro nake ji kar wani abu ya same ta" "Ki jika towel da ruwan sanyi ki dinga Gogo mata a jiki" "Yaya nayi hakan amma abin ya fi karfi na dan kamar zata yi jijjiga" Shi mutum ne mai tausayi sosai dan haka mikewa yayi tsaye daga zaunen da yake saman darduma ya fito, Kai tsaye shiyan su ya nufa,sai da ya ƙwanƙwasa sannan tazo ta buɗe mai ya shiga, Nuna mashi Biba tayi wacce take kwance an jibga mata zannuwan gado a jiki,Lokaci-lokaci kuma takan zabura,kai basai ka taba jikin ta ba,ko daga yanayin ta kaɗai ya isa ta shaida maka irin yanda zafin jikinta yayi sama. Yasan ba shida wani taimako da zai iya mata tunda ba aikin shi bane,wayar dake hannun shi ya danna kira wanda sai da ta mai kusan miss call takwas sannan ya ɗauka cikin muryar Barci, Ce mai kawai yayi"kazo shiyan kaka ina jiran ka"ya sauke wayar a kunnen shi. Jin an ambaci sunan kaka ne yasa da sauri ya wastsake ya saka dogon riga ya fito,kai tsaye shiyan na nufa,a buɗe ya samu ƙofar dan haka ahiga yayi,yana ƙoƙarin nufar ƙofar kaka,dan ba karamin ji da tsohuwar suke yi ba,shi yasa lamari in dai nata ne basa wasa dashi ko kaɗan, Ji yayi muryar Nafisa ta ce"Yaya Nurudeen nan zaka wuto " Bin bayanta yayi inda ya taradda Suraj a tsaye,kallon shi yayi,sai dai kafin ma ta mai magana ya nuna mashi gado da ido, Cikin sauri ya karasa inda take kwance tare da yaye bargon ya dafa goshinta, Kallon Nafisa yayi cikin dan yanayin bacin rai tace"garin ya kika bari jikinta yayi zafi har haka,ba kisan tana ita shiga Fit saboda high fever ba" Ita dai bata ce komai addu'ar ta daya Allah yaba Biba lafiya, Yaye duka bargon da aka rufa mata yayi"kara karfin AC" Dan waro ido tayi ganin yanda take rawar sanyi sannan ace ta kara AC"rawar sanyi fa take yi" Wani irin kallo ya wurga mata da sauri ta yi yanda yace tana kallo ikon Allah, Allah yasa dazu kafin Ammi ta tafi sai da ta taimaka ta saka mata dogon wondo da riga shima dogo har kasa mara nauyi amma na barci ne,sai hula,to garin zaburan da take yi ne hulan ya zame wanda nan take suman duk ya baje saman filo,ya rufe mata fuska, Suman baki ne wuluk yanda kasan ta shafa mashi dayis saboda baƙi,ga tsantsi da laushi, A hankali ya kai hannu yana kyara mata suman tare da shafawa yana kallon tushen suman don son tabbatar wa ko nata ne, "Dibo ruwa da towel ki zo kina shafa mata,bari na dauko Alurai wanda zai taimaka mata" Ya karasa faɗa yana barin dakin da sauri, Shi dai tana tsaye rungume da hannu yana kallon dun abinda suke yi,sai dai bai ce masu komai ba, Ba jimawa kuwa sai gashi ya dawo da kayan aiki,cikin kwarewa ya mata duk abinda ta kamata ai mata, Ganin yana ƙoƙarin zama bakin gadon ne yasa yace"Malam tashi mu tafi zasu kulle ƙofa " "Ka tafi kawai idan zazzabin ya sauka zan wuce" "Ba dai ka mata abinda ya kamata ba? " Sosai ma kuwa" "To tashi mu tafi bana son cin musu" Ya fada yana ƙara gimtse fuska,dan ya fara lura da take_taken shi. Ba dan yaso ba ya mike ya nufa kofa harda juyowa ya kara kallon ta,gaskiya wannan Ustazun ya kwabsa mashi,shi da yaso ya zauna yata kalle ta. "Mu je ki kulle ƙofa" Ya fada yana yin gaba, Da sauri Nafisa ta bishi ta kulle kofofin shiyan, Cikin ikon Allah kafin wani lokaci zazzabin ya sauka,ta daina rawan sanyin, Washegari da safe ta ji sauƙi tunda har ta ita tashi tayi sallah,sannan taje ta gaida Kaka wacce ba karamin jin daɗin ganin ta tayi ba,sannan ta koma daki ta kwanta, Kamar yanda suka saba daukar karatu a shiyan kaka dun safiya yauma haka ne,sai dai Yaya Nurudeen ya riga kowa shigowa,shida bai cika zuwa ba, Sai kalle_kalke yake ta ina zai hango ta,ganin sun fara karatu ne yasa ya mike ya doshi dakin Nafisa, Ji yayi muryar Kaka ya dakatar dashi"ina zaka" Shafa kai ta fara ya nuna mata dakin Nafisa "zan dubo mai jiki ne" "Dawo ka zauna dan yanzun ta bar nan,jikin da sauƙi dan har tayi sallah ta kuma zo ta gaida ni,sannan bana son na ƙara ganin irin haka" Ya gane me take nufi wato bata son ya kara cewa zai shiga dakin. Ba dan yaso ba ta dawo ya zauna,can kuma ta tashi ya fita,dan ya lura kaka ba raga mashi za tayi ba,har balle ta gano ƙudirin shi akan yarinyar. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *21* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Misalin karfe takwas da rabi na safe ta tashi tayi wanka da ruwan ɗumi,sosai ta ji daɗin jikin ta,Nafisa ce ta je shiyan Ammi ta karbo mata kayanta,riga da zani ne na Atamfa wanda rigar ya saukar mata har guiwa sai zani, Kasancewar ranar sati ne babu aiki kowa na gida,shi yasa duk ranar ashiyan Kaka suke karin safe,sannan suke cin abinci dare, Shi yasa ma yau duk suka hadu Ana cin abincin safe, Hauwa'u ce ta shigo da sallama,gaisawa suka yi har da Kaka, "Ga wuri ki zauna,Nafisa kawo mata abin kari" Zama tayi tana murmushi domin ba karamin burge ta suka yiba,"kaka na koshi,na gode," "Nafisa kira mata Habiba" Da to ta amsa tana mikewa, Jimawa kaɗan sai gasu sun fito tare,tana biye da ita a baya, Duk da kayan jikinta sun mata yawa zani kuma leɓe daya yafi daya tsayi,ga kuma ɗan kwalin da yafashi kawai tayi akai bata Daura ba,amma ta fito shar da ita,fuskarta ya ƙara haske,yayi fayau da shi, Nuna mata kusa da ita tayi"zauna a nan "zama tayi tana gaida su, Wasu sun amsa wasu basu amsa ba, Tambayar ta matar da ta ji an kira da Hauwa tayi" Kin yi karin safe" Jinjina mata kai tayi"eh" Kaka ce tace"Zainab jeki shiyan Ammi ki anso ledan magunguna " "To kaka"ta faɗa tana fita, " Wai nikam ina Surajo yake ne ko yau ba zai karya ba ne? "Na dai ga kofarshi a kulle" Cewar Salman. Zainab ce ta shigo da leda a hannun ta mika ma Hauwa'u, Amsa tayi ta ciro magunguna ta shiga nuna mata yanda zata sha, Allura ta ciro ta shiga haɗawa,"zamu shiga daki sai na maki Allura zuwa yamma kuma zan dawo sai na maki daya" Numfashi ta sauke sannan ta mike tsaye,kallon kofar fita falon tayi,"ina so in je in gaida Ammi,bari in na dawo sai ki yi min"ta faɗa tana nuna ƙofa, "Da dai kin tsaya sai na maki dan sauri nake zani wurin aiki" Tana kokarin yin magana ne kaka tace"ku shiga daki na sai ku yi " "To Kaka" Cewar Hauwa'u tana mikewa, Ba dan ta so ba tabi bayan ta, Mintina biyu tsakani,sai jin tashin ihu suke,sai kuma gashi ta fito da mugun gudu ɗan kwali a hanu tayi waje,yanda kasan wacce kura ya biyo, Duk da kallo suka bita, Kafin Hauwa'u ta fito ɗakin riƙe da Allura a hannu,tana kiran sunan ta, Kaka ce ta dakatar da ita daga ƙoƙarin binta da take "lafiya?me ya faru? Tsayawa tayi tana dafe ƙwanƙwaso" Wallahi nima ban sani ba kaka,amma ina ga duk yanda akayi tsoron Allura take yi" Yamutse fuska Aunty Maijiddarh tayi"sai dai in iskanci amma me abin tsoro ga Allura" "Wallahi kuwa,ke dai bari kin San idan mutum ya samu wuri babu tsiyan da ba zai shuka ba" Cewar Khadija, Ibrahim ne yace"na ga dai Uwar faɗin ma haka take " Kaka ce ta dakar dasu"bana son rashin girmama abinci,wannan ba ɗabi'a mai kyau bane kana cin abinci kana surutu, Sallamar shi da suka ji ne ya jawo hankalin su, Niman kusa da kaka yayi ya zauna, Da sauri Aunty Maijiddarh ta taso tazo tana kokarin zuba mai kunun kyada dake cikin fulas,da hannu ya mata alama akan ta dakata, Jiki a sanyaye ta tashi ta koma wurin zaman ta, Gaida shi Hauwa'u tayi ya amsa,a takaice, "Zainab maza ku tashi ku kira min Habiba ta bar yarinya tana zaman jiranta" Turo baki tayi"kaka to ai ita ba ƙaramar yarinya ba ce,kawai ita Hauwa'u ta yi wucewar ta jiki magayi,idan ta ji jiki da kanta zata nime a mat... Haɗa ido da suka yi dashi ne yasa ta kasa karasa maganar daje bakinta,cikin sauri ta tashi ta fita, Da kanshi ya zuba kunun a kofi har sai da ya kusa kammalawa sannan suka shigo wai basu ganta ba bata shiyan Ammi, Dan haka kaka tace Hauwa'u ta wuce Nurudeen zai karasa mata Alluran,wanda hakan ba karamin daɗi ya mashi ba. Sallamah ta masu ta wuce, Yana kammalawa tashi yayi ya fita kaka ce ta dakatar dashi"ina zaka kuma baka ci kosai ba" "Sauri nake saboda yau zamu tafi wa'azi Nijar" "Yanzun zaku tafi? " Sai zuwa anjima amma yanzun akwai in da zanje ne" "To Allah ya tsare hanya ya dawo da kai lafiya," Da Amin ya amsa,sannan ya wuce. Har ya saka katin kofa sai yaji kamar yana jin motsin mutum, Dan haka juyawa yayi,sai dai bai ga kowa ba,hango gefen zani yayi, Dan haka a hankali ya taka ya isa in da take zaune a ta lungun dakin su,ta makale ta haɗa kai da guiwa, "What are you doing here? Baki ta buɗe tana ƙoƙarin saka ihu,domin ba karamin tsoro taji ba, Ihun ya makale ne sanda taga wanda ke tsaye a gabanta, Dafe kirji tayi tana sauke numfashi, Cikin jin haushi ta turo baki" Shi ne zaka ba mutum tsoro" Jin kamar takun tafiya ne yasa ta juya baya,Salman ne ke ƙoƙarin bude nashi kofar, Kokarin yin magana yake yi,yaji an riƙe mai ƙafa gam, Juyo da kallon shi kanta yayi,ta tsugunna yanda kasan me niman gafara,gashi ta wani marairaice fuska yanda kasan kyanwa,sai wani rau_rau da ido take yi,"dan Allah karka faɗi in da nake" Jan kafar shi yayi"me yasa? "Bana son Allura" "Bout you are so big to say that" Shagwabe fuska tayi"ni dai dan Allah karka faɗa ma kowa" Jinjina kai yayi,ya juya ya wuce abin shi, Mintuna kaɗan sai ga Ibrahim da Aunty maijiddarh,sai Bilki, Kawai sai ganin mutane tayi tsaye a kanta, Ihu ta kurma yanda kasan wacce za'a yanka ta mike tana ƙoƙarin gudu, Da sauri Aunty maijiddarh ta rukota, Hmmm ranar sunga hauka domin kuwa da kyar suka kai ta shiyan kaka da kuka da ihu,duk yanda aka so ayi Allurar dole hakura aka yi aka kyale ta,dan har da cizon Nurudeen tayi a hannu,gabaɗaya ta hargitsa gida,dole aka kyale ta, Wurin shan magani ba tada matsala domin ko banza ta ci kwaya balle kuma wannan, Bayan sati ɗaya, Sai da taji sauki sosai sannan ta koma shiyan Ammi,bayan kaka ta kira matan gidan tai masu kyakkyawar kashedi akan bata yarda ko da wasa a ƙara cin zarafin wani ɗan aiki a gidan ba,idan kuma aka kuma yi mutun zan haɗu da ita, Wannan dalilin ne yasa ta dan samu sauƙi,dan bata shiga shiyan kowa sai na kaka, Sai dai idan ta haɗu dasu a hanya, Tsakanin ta da yaran gidan kuwa ko kallon banza,dan sai dai su zage ta amma bata gaida su,tunda ba girman ta suka yi ba,har gara Aunty maijiddarh,tunda taga wani lokaci tana da kirki, Zaman gidan gabaɗaya ya isheta domin ko wanda zata yi aiki domin shi bata ganin shi tun wannan ranar daya faɗa ma su Nurudeen in da take,dan ta tabbatar da shi ya faɗa masu. Ganin ƙafar Ammi da sauƙi ne yasa taimata karya akan zata ganin Mahaifiyar ta wai jikin nata ya tashi, Cikin tausayawa ta amince mata sannan ta haɗa mata tsaraba sosai,har da kaka, Ranar da zata tafi ne ta fito wanka kenan sai gashi taga shigowar kira a wayar ta,duk da babu suna kuma yawancin lokuta da numbobi mabanbanta yake kira amma ta fahimce me kira, Dan haka ɗauka tayi, Abu na farko da yace shine"me yasa zaki tafi? Shiru tayi tana mamakin ta yaya akayi yasan zata tafi bayan ko A'i bata san da maganar tafiyar ta ba, "Ina buƙatar hutu" Ta bashi amsa. "Ba dai akan dan abun da ya faru ba? " Me kake nufi? "Nasan komai,na kuma san kin warke,abu ɗaya kawai zai sa na bari ki tafi hutu saboda nasan baya ƙasa,ya tafi Sudan yin wani aiki tare da mahaifinsa,karshen watan nan zasu dawo,ina nufin nan da sati uku,kina da damar da zaki iya hutawa na sati biyu,domin jinyar mahaifiyar taki,ki tabbatar ya dawo ya same ki,sannan a wannan lokacin idan baki yi saurin cika min aiki na ba kome ya biyo baya ki yi kuka da kanki " Cikin tsananin mamaki tace"ar you threaten me? Kai tsaye ya bata amsa da"Yes" Bai jira tace komai ba ya kashe wayar. Kallon wayar dake hannun ta tayi,sabar bacin rai ne yasa ta buga wayar da ƙasa,me yake nufi,threatening ɗin ta yake saboda wani banzan aiki da bata masan amfanin me takardun zasu mai ba,sannan kuma duk halin da take ciki a gidan ya sani,to kodai ba ita kaɗai ɓace take mai aiki, Tsaya ma tukun,ta ji yace ya tafi aiki Sudan tare da Mahaifinsa,bayan kuma ta san Abbu na gida,to wani mahaifi,Something is not right some were,tunda take aiki tare da VIP bata taba ganin yayi serious about wani abu ba kamar wannan aikin, Komawa tayi ta zauna saman gado,ta shiga duniyar nazari,na farko shi dai ba Aljani bane,dole mutum ne,to waye shi,bata taɓa ganin shi ba,amma shi yasan komai game da ita,ta yaya, Dafe kanta tayi,tana buƙatar sanin abubuwa masu yawa,amma kuma ta yaya zata yi hakan, Ajiyan zuciya ta sauke tana jin kanta na daurewa,dan haka tashi tayi ta saka kaya sannan ta dauki Sim card ta jefa a jakka, Ko da ta bar gidan ba wai ta tsaya a nan Kano bane,ko kuma tayi Abuja,kawai Jirgin Legos ta shiga dan gara taje can ta huta,in da anan suka hadu da Ummita. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *22* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Kwanan ta biyu a Legos ranar sun dawo daga cin abinci tana zaune tana danne danne a Laptop sai saki take yi,mikewa zauna tayi ta dafe kanta,kallon Ummita tayi dake zaune tana kallo a TV sai faman dariya take yi, Kiran sunan ta yi"Ummita" Amsawa tayi ba tare data juyo ba, Cikin jin haushi ta wurga mata filo,"dan Allah malama ki juyo " Juyowa tayi tana bata rai ta katse mata kallo"gani" Kyara zama tayi"ni kan baki ganin kamar akwai abinda bai tafiya dai-dai? "A ina kenan? "Wannan aikin da nake yi" "Me kike nufi,kinsan wannan karon ba abinda na sani" A jiyar zuciya ta sauke"da fari aiki akan Young Ustaz da Baban shi,sai kuma na fahimta mijin Goggon shi ya ɓace ba'asan in da yake ba," "Eh to ɓacewa yayi,is a normal thing" Girgiza kai tayi"is not normal,Nafisa tace min Shamsuddeen ba yaron Ammi ba ne mahaifiyar sa sun rabu da Abbu,to shi kuma Ustazu fa? "Yaron Ammi ne da Abbu mana" "Kai ina da wata a kasa,ki duba fa ki ga,karshen magana na da VIP cewa yayi Ustaz ya tafi wani aiki da Baban shi a Sudan,kuma a lokacin Abbu yana gida" "Oh Biba ni dai ban fahimci abun da ke kika fahimta ba,ni dai a gani na da ki bata lokacin ki wurin wannan bincike ba gara ki samar ma kanki mafitar da zai kai ga waɗannan takardun kawai,ayi a wuce wurin" Dan shiru tayi,kafin tace "tabbas a kwai wani abu a kasa,yauwa kin ga matso ki gani" Ta faɗa tana nuna mata fuskar Laptop ɗinta,"kin ga anan sunan mahaifin sa Abu Sufyan,shi kuma yana amfani da Suraj Abdul Basir,waye Abdul Basir? Me yasa yake amfani da wannan sunan a maimakon Abu Sufyan? "Ni dai Biba ki yi a hankali domin na lura wannan aikin ba kamar irin wanda muka saba yi bane" Komawa tayi ta kwanta"in Allah ya yarda idan na koma da zaran ya dawo zan kammala komai na dawo,kin san wani abu kuwa"ta faɗa tana kunna Sigari, "A'a sai kin faɗa? " Da na kammala wannan aikin London zamu koma da zama,gaba ɗaya Nigeria ya ishe ni" Ihu ta saka cikin tsananin jin daɗi ta taso ta rungume ta suna dariya, "Shi yasa nake ji dake Aunty Biba,gashi Alhaji Mansur sai damuna da kira yake akan yaushe zaki dawo," "Kyale dan wahala,ni yanzun bata nasu nake yi ba,so nake kawai naga na kammala wannan aikin in huta" "Ai kuwa sai dai ki yi hakuri dan wallahi na riga na tura masa Address din mu,idan baki ganshi yau ba kya ganshi gobe" Haka dai suka cigaba hiransu, Zamanta a Legos ba karamin daɗi ya mata ba,dan har bata son ta tuna cewa zata koma wannan gidan aikin. Ranar da zata koma aiki har da Kukan zuci sai da tayi,dan ta san zata koma aikin shara kenan da wanke-wanke,. Tana sauka a bakin Get din ta haɗu da A'i tsaye tana jiran ta, Ganin tana ƙoƙarin shigewa ne yasa ta kira sunan ta, Tsayawa tayi tana kallon ta,mika mata wani karamin waya tayi tare da karamin takarda,bata jira tace komai ba ta juya ta wuce, Da kallo ta bita,kafin ita ma ta shige cikin gidan, Sai da ta gaida Ammi wacce tuni ta ji sauƙi,sannan taje shiyan kaka ta gaida ita,sosai tayi farin cikin ganin ta,kafin ta koma shiyan su, Fadawa tayi kan fado tana warware takardar da A'i ta bata, "Karki zurfafa bincike,domin yana iya faɗawa kanki" Ta maimaita maganar ya kai sau nawa,to me taje nufi da zai iya faɗawa kanta, Nannaɗe takardar tayi ta saka cikin kayanta, Amira ce ta zo ta faɗa mata cewar Ammi na kiran ta, Fitowa tayi ta same ta zaune a falo, Tsugunnawa tayi a gefe"Mam,gani" "Alhamdulillah,dama so nake na sanar dake naji sauki,dama Kaka ta kawo kine domin ki taimaka min,kuma yanzun na warke,duk da ban jima dake ba amma naji daɗin aikin ki,Kaka tace na tambaye ki shin kina ganin zaki cigaba da zama damu anan ko zaki koma shiyan kaka? "Zan zauna dake anan Mam," Domin ta san zama anan din ne zai fi bata damar sanin duk abinda take buƙata, "Kin tabba ta? " Eh Mam" Murmushi tayi"shi kenan tashi ki tafi " Godiya ta mata sannan ta koma daki. Da yamma ne taje kaima Kaka Abinci ta ji suna magana Momy Saudat Mamar su Nurudeen,tana magana da Kaka cikin marairaicewa yayin da Aunty maijiddarh ke zaune tana sharan hawaye, "Kaka nasan fa kinsan abun da ke wakana a tsakanin Suraj da Maijiddarh,gabaɗaya taki kula kowa,ta nace sai shi kaɗai take so,duba ki ga yanda duk tabi ta lalace,na rasa yanda zan yi,duk wani hanya da zata bi ta samu shiga a wurin shi ya to shi,ko kiran shi tayi a waya baya ɗagawa,taki cin abinci ba ta da aiki sai kuka" "To ni yanzun Saude me kike son nayi mata? " Kaka Suraj yana jin maganar ki,kome kija faɗa kai zai amince,ni wallahi tsoro ma nake kar yaje can wurin wa'azin shi wata ta samu nasaran aure shi,tunda matan ma yanzun da kansu suke kawo mashi tallan kansu" "Kinsan dai shi ba yaro bane ballantana na takura akan sai yayi abinda nake so,ita maijiddarh ta hakura mana,ko ta samar ma kanta mafita amma ni dai kam ba zan iya mai magana ba" Kuka ta fashe dashi tana rarrafawa gaban kaka"ni dai Kaka ki yi wani abu kai,ni ba zan iya auren kowa ba in ba Yaya Suraj ba,dan Allah ki taimake ni" Shafa fuskarta tayi"ya isa haka,bari ya dawo za'a san abun yi" Rungume kaka tayi babu kunya,tana mata godiya kafin su fito shiyan, Da sauri ta labe ta ƙofar gidan dan ta cikin gida ba wurin da mutum zai labe, Suna fitowa tsayawa suka yi a ƙofar gida,Momy Saudat ce tace"ya kama mu ƙara dagewa akan wannan lamarin,domin na lura da take_taken Goggon ku,so take ta saka Khadijah a wannan lamarin,dan haka wannan karon idan ya dawo ki yi duk yanda za ki yi alakar ku tafi na da ƙarfi,bana son ya tsubuce mana" Tsaki taja"Momy kin san halin Yaya Suraj yanda kika san mai zuciyar dutse haka yake,duk yanda mace za tayi ba ya daga kai ya kalle ta,shi yasa wani lokaci take ban haushi " "To ko zaki hakura? Zaro ido tayi" Rufa min Asiri Momy,wane ni,ai ba irin Suraj bane ake hakura da shi,Allah dai ya dawo dashi lafiya,amma wannan karon dole salon zai canja" Da haka dai suka tafi,in da suka bar ta cikin tsananin mamakin su kuma, Ganin tana kokarin faɗawa tunani ne yasa ta watsar da lamarin ko ma dai menene gara ta cika nata aikin ta bar gidan. Ana gobe zai dawo Ammi ta saka suka shiga kyaran gida,duk da dama ko'ina a kyara yake ko yaushe amma na yau na da ban ne, Ita da kanta taje ta kyara mai dakin shi,bata bari ko Amira ta shiga ba, Ranar da zai dawo ma basu fara shirya abinci ba sai da akayi sallah Azahar,zuwa ƙarfe hudu da rabi gar sun kammala, Wanka tayi ta nime wuri ta kwanta tana karanta littafin girkin da A'i ta bata,tana kuma tunanin hanyar da zata bi domin samun shiga dakin shi. Jin diran motoci a harabar gidan ne yasa ta tashi daga kwancen da take ta buɗe wundan ɗakinta wanda zata iya hangan harabar gidan duk da yayi nisa sosai ba zata iya tantance mutanen dake wurin ba, Motoci ne guda biyar wannan karon,sun ɗan jima daga bisani kuma taga sun guya sun bar gidan, Komawa tayi ta kwanta,tana aiyana ƙila ya dawo ne, Ganin har ƙarfe shida tayi ne yasa ta tashi ta fito daga shiyan su,kamar zata nufa shiyan kaka,sai kuma ta juya tayi hanyar Boys Quetta, Tasan wannan lokacin duk mazan gidan basa nan,dan haka daga tsayen da take ta kunna wutar Sigari ta saka a baki,kyakkyawar zuka ta masa tana busar da hayaƙin tare da lumshe ido, Duk da tasan ba ko yaushe take sha ba,amma a ƙalla a sati tasha sau biyu,to kuma gashi tunda ta dawo ko sau daya bata sha ba sai yau,shi yasa take jinta a sama, Tunda ya nufo sashin su yake jin warin Taba,abinda yafi tsana a rayuwar shi,ko kaɗan baya so, Mamaki ne ya kamashi domin bai taba tunanin a gidan a kwai mai shanta ba,dan bai taɓa jin makamancin warinta ba, Duk da duhun Magriba ya gabato amma yana iya hanyan ko ina na wurin, Idanun shi ne suka sauka a kanta,yanda take busa hayaƙin sama cikin ƙware da kuma yanda ta riƙe a hannu,wannan shi zai tabbatar maka da cewar ita din ba yar koya bace, Gabaɗaya ya kasa yarda da abinda yake gani,Mace! To yana dai ji a labarai, Jikinta ne ta bata kamar ana kallon ta daga ta wani wurin,dan haka da sauri ta shiga juye_juye,sai dai bata ga kowa ba, Ajiyar zuciya tasauke ta yarda karan sagarin ta murje da ƙafa,kafin ta bar wurin. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *23* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Komawa shiyan su tayi,sai da aka yi Sallah Isha'i sannan ta fito zata shiyan Kaka, Ta kusa shiga shiyan ne ta ji an finciko ta anyi baya da ita an jin gina ta jikin bango, Kasancewar wurin akwai ƙarancin haske hakan yasa bata gane ko fuskar waye ba ne,sai da ta ji muryar sa yana sun sunan wuyanta,cikin muryar da zai nuna maka irin shaukin da mutum ke ciki yace"Baby na ina kika tafi kwana da kwanaki,sannan kin dawo kin kuma hana ni ganin fuskar ki" Oh sai yanzun ta dago muryar shi,kauda fuska tayi,domin bata son ta nuna mashi halinta,in ba haka ba,wlh da in ta rike shi sai ya gudu da kafar shi,"Nurudeen bana son haka"ta faɗa tana ƙoƙarin barin wurin, Riƙe mata hannu yayi yana ƙoƙarin jawo ta baya "akwai maganar da nake son na faɗa maki" "To sake ni sai ka faɗa min" "Kina da kyau" "Na sani" Ta bashi amsa kai tsaye, "An taba faɗa maki" "Sosai ma" Murmushi yayi"wannan ba abin mamaki bane idan aka yi duba da cancantar ki" Kafin ta bashi amsa ne suka ji daga bayan su wani sanyayyan murya yace"Excuse me " Ganin wanda yayi magana ne yasa gaba ɗayansu shan jinin jikin su,saboda shi rike yake da hannun ta,cikin sauri ya sake ta,yana matsawa gefe,ita ma haka,amma shi gogan ko a jikin shi,sai ma raɓawa da yayi ta gefen su ya wuce ya bar su da kamshi, Ganin ya shige shiyan Kaka ne yasa da sauri ta juya ta bar wurin,dan Gara kawai ta koma shiyan su,ita bata san Me yasa a duk lokacin da zasu haɗu basa haɗuwa da sa'a ba,yanzun ba sai ya mata kallon mara da'a ba, Wani zuciya nata ne ya bata amsa kai tsaye,dama da'a gare ki,nan take ta saki murmushi,domin rabon ta da wannan kalmar shekara biyar kenan daya wuce. Tana shiga daki faɗawa tayi kan gado tana lumshe ido,kome take tunani?Allah kaɗai yasan abinda ke gudana a zuciyar ta,daga bisani kuma sai naga kamar hawaye na gangarowa daga idanun ta data lumshe,sai dai kafin na tantance sai gani nayi ta kifa fuskarta cikin filo,sai kuma a hankali shesshekar kuka ke tashi,wanda idan ba wai ba ka saurara sosai bane ba zaka taba tsammanin ana yin shi ba,ita wannan ba komai bane a wurinta face abinda ta saba komai tsayin dare sai yishi,in dai wannan kukan ne, Jin alamar kamar za'a shigo ne yasa da sauri ta gyara natsuwar ta,tana goge fuska da sauri, Amira ce ta shigo da sallamah"Biba wai inji Ammi ki fito ki yi wanke-wanke an kama" Mikewa tayi"ok gani nan tafe" Cikin natsuwa take aikinta har ta kammala yanda kasan ba ta da wani damuwa domin fuskarta a washe yake, Ba ta yarda masalarta ko damuwarta ya nuna a fuskar ta,abu ne mai wuya, Wannan tsakanin ta da zuciyar ta ne. Tana kammalawa daki ta shige ta kwanta,dan ta kammala aikinta na yau sai kuma gobe idan Allah ya kaimu, Washegari ma bayan an idar da sallah ne ta fito ta shiga gyaran gidan sannan ta daura break Fast,Waina da Miya tayi,wanda ya ji kayan haɗi, Koda ta kammala har takwas ta wuce,dan haka daki ta koma tayi wanka,dan tana idar da sallah suke gaisawa da Mam, Daukar na kaka tayi ta kai mata, Koda ta dawo bata lura dashi zaune ba,sai da Ammi ta ce"Biba zubo ma Suraj Waina" "Ammi wa yayi Waina? Ya tambaye ta, Kasancewar tasan yana matukar so,cikin murmushi tace" Biba tayi,kuma gashi yayi laushi yanda kake so" Daukar wayar shi dake gefen shi yayi yana mikewa"Ammi ki ce ta barshi kar ta zubo,yau bana jin cin waina " Kallon mamaki take mai,domin tasan yanda yake son waina ko ya ko shi ne sai ya dauki guda daya ya saka Albarka, "Yau kaine baka jin cin waina? Murmushi ya sakar mata" Bari na tafi na gaida Kaka Ammi,zuwa anjima zan shigo" Jin jina kai tayi,tana binshi da kallo, Ita dai tana kicin tana jinsu, Koda yaje shiyan Kaka ma haka ne ta faru,domin tana mai tayi ita ma ce mata yayi baya jin cin masa, Ta gaji da zama ita kaɗai,gashi duk yaran gidan sun tafi makaranta,dan haka fitowa tayi ta zauna ta gefen Barandar su,ganin kamar rana yana son ya takura mata ne yasa ta canja wurin zana zuwa ta takanin shiyan Goggo da Hajiya Rahama,daga inda take zaune tana iya hango duk mai shiga da kuma wanda zai fita, A karamar wayar dake hannun ta take buga game,duk da ba wai daɗin shi yake ji ba, A hankali ta fara jin sautin murya na tashi,cigaba da buga game ɗin ta tayi,iska ne ya kwaso magana ya faɗa kunnen ta,wanda wannan kalmar ce tasa ta natsuwa ta ajiye wayar hannun ta"gabaɗaya ya tare min numfashi,baƙin ruhi ne dashj,ba zai taɓa bari mu ci galaba akan shi ba," Ɗayan da suke magana mai sanye da dogon hijabi har katsa ne ta ji tace"kome yake taƙama dashi,wannan karon abin ba zai taba zuwa yanda zai yi tsammani ba,domin sai yayi kuka da idanun sa yana niman cito,alokacin da babu wani Mahaluki da zai yarda da shi," Tabbas wannan ba muryar mace bane kamar yanda take ganin mutum sanye da hijabi,Namiji ne,amsar da zuciyar ta ya bata kenan,amma yanda yayi shirin mata har da nikabi ba zaka taba kawo hakan a rai ba, To su waye,dukkanin su sun juya mata baya,bata gane wacce macen ba,amma daga dukkan Alamu a gidan take, Ganin jamar zasu juyo ne yasa da sauri ta bar wurin ta koma inda ta taso,zuciyar ta fal da tunani,to waye abin harin su,gaskiya akwai masala koma waye suke hari,ita dai gara tayi ta gama ta koma inda ta fito,dan zaman gidan sam baya mata daɗi ko kaɗan. Tana kallo har mai hijabin yazo ya wuce,ta jima a wurin kafin ta tashi ta koma shiyan su dan locin yin girkin rana yayi, Da yamma tana kammala aikinta shiyan Kaka ta tafi wurin Nafisa,dan ta gaji da zama ita kaɗai,sun sha hira tare da Kaka kafin a kira sallah,su suka shige dakin Nafisa har aka yi Isha'i, Suna jin sanda jikokinta suka fara zuwa gaishe ta,wasu su zauna wasu su wuce, Hadiza ce take ba Zainab labarin wani India film data kalla jiya,gabaɗaya sun karaɗe falon da surutu, Fitowa tayi domin ta ɗaukar ruwan sha,ta buɗe firig kenan ta ji falon ya dauki wani irin shiru yanda kasan ba mutane a cikin shi,sai kuma ta ji sanyayyar muryan nan dai yana sallamah, Sai da Kaka tayi dariya kafin ta amsa, Shigowa yayi ya zauna a gefen ta, Cikin zolaya tace "wai ya naji shiru ne kamar ba mutane a falon" Dago shanyanyun idanun shi yayi ya sauke a kansu,yanda duk suka natsu, Mai da duban shi yayi kan Kaka"Me ya faru? Gabaɗaya sun cika ni da surutu,nayi magana sunce wai suyi shiru kamar babu mutane,to yanzun bansan me ya faru ba naga duk sun natsu kamar babu kowa ma a nan"ta karasa faɗa da murmushi, Aunty Maijiddarh ce cikin salon yanga da makale murya tace"Kaka ai hira suke taya ki" "Ke kuma me ya samu muryar ki na ji ta kamar a shaƙe,ko mura kike yi ne"cewar kaka tana tambayar Maijiddarh domin tasan yanzun dai ta gama magana da muryarta lafiya amma yanzun yanzun kuma ace ya shaƙe, Da yake su ƴan mata ne shi yasa nan take suka fahimci abinda ke faruwa wato make murya tayi,dan tana gaban shi, Ai kuwa mantawa sukayi suka shiga kyalkyata dariya,Zainab harda dukawa "kai Aunty Maijiddarh harda make murya kuma,wallahi ko kyau bai maki ba" Ɗaukar ruwan dake gaban kaka yayi ya ƙafa a kai yayi Bismillah ya shanye, "Biba ɗauko ma Surajo Fura a firij ya sha tunda ya shigo" Amsawa tayi da to sannan ta buɗe firig din da har ta rufe ta jawo kwanun dake ɗauke da lafiyayyen fura da aka dama shi da Kindirmo, Tana daukowa ta kawo gabanshi,sai da ta duka sannan ta ajiye, Har ta juya baya sai ji tayi yace "ke" Duk da ta ji yace ke,amma hakan bai sa ta juyo ba,sai ma cigaba da taku da ke yi, Zainab ce tace"ke Biba baki jin Yaya Suraj na magana" Juyowa tayi ba tare da tace komai ba,hakan ne ya tunzura shi,domin ba abunda ya tsana irin yayi magana a kyale shi,dan ne zuciyar shi yayi,ya nuna ta da yatsa"zo ki dauke wannan abun a gaba na" Ba ita kaɗai ba har ta kaka kallon mamaki take mai, "Ni fa na dama da hannu na, na kuma ajiye maka" Kallon kaka yayi"daga yau in dai har kina son ki ba ni abu na ci ko na nasha,to kar ki ƙara barin masu aiki su taɓa,ko da kuwa ɗauko min ne," "Me yasa" Ta tambaye shi mamakin ta na ƙaruwa, domin abune da bai taba yi ba, Kallon ta yake ido cikin ido"Saboda kazamai ne,and I hate it" Nan take ta ji idanun ta sun cika da hawaye,domin babu wani cin fuska daya wuce wannan,a kalle ka ido cikin ido a kira ka da kalmar da ko haɗa hanya ba ku yi da ita,wato ƙazanta,ganin baida niyar dauke idanun shi a kanta ne yasa ta ɗauke idonta a kanshi,tana ƙoƙarin haɗiye hawayen ta,domin ba zata taba bari su zubo anan ba, "Amma Suraj naga daga Biba har Nafisa duka su suna da tsafta sosai,na yarda da tsaftar sune shi yasa ma suke zaune tare da mu" Mi kewa yayi tsaye yana ƙara daura idon shi akan fuskarta"ki ƙara binciken ta "yana gama faɗar haka ya bar falon, " Waye zan ƙara binci ka"cewar kaka tana kallon shi yana barin falon,sai dai bai bata amsa ba ya wuce. Juyo da kallon ta kan Biba tayi wacce ke tsaye tamkar wacce aka dasa"me ke faruwa "ta tambaye ta, Girgiza kai kawai tayi ta juya ta koma dakin Nafisa, Duk da kallo suka bita,kafin kuma ta maida kallon ta kan kwanun Furan ta, " Mejiddarh zo ki ɗauka kusha tunda shi wanda akai ma gwanin ta ba'a burge shi ba " Riƙe baki tayi"ni! Wallahi Kaka bana sha,haka kurum,tunda kika ga Yaya Suraj ya faɗi haka shi yasan abinda ya gani,kinga na ma wuce"ya faɗa tana ƙoƙarin barin falon, "Zainabu zo ki ɗauka Kuje kusha" Dariya suka saka "a'a tsohuwa ki dai sha abin ki" "To yanzun ni ya kuke son nayi da wannan Furan? Ai tuni duk sun fita sun bar ta cikin Mamakin su,to amma me shi Surajo yaje nufi ne, Fitowar Biba ne yasa ta dago tana kallon ta, Dukawa tayi kaɗan" Kaka na wuce sai da safe" "Zo ki zauna Biba" Ta faɗa tana nuna mata kusa da ita, A hankali ta tako ta zauna kusa da ita ta zauna in da ta nuna mata, "Ki yi hakuri da halin Suraj,shi haka yake,sai dai ina son ki san shi mutum ne mai matukar sauƙin kai,bai cika shiga harkar da ba nashi ba,balle na masu aiki,wannan shine karo na karko da ya taɓa faɗar haka,shi mutum ne mai matukar kyankyami,bansan me ya gani tattare dake ba haka wanda ya saka shi fadar haka,amma dan Allah koma menene ki yi ƙoƙari kiyayewa kin ji? Hadiye hawayenta tayi"insha Allah kaka zan kiyaye " "Yauwa Allah ya maki Albarka" "Amin,sai da safe" "Allah tashe mu lafiya" Tana shiga daki ta saka sakata, Fadawa tayi kan gado tana fashewa da kuka,tunda take a rayuwar ta ba'a taba mata irin makamanciyar wannan abun ba sai yau,babu wanda ya taba faɗa mata haka,a kowani rana tana wanka sau uku a rana,ta goge baki sau uku,a jikinta ba ta barin ko da digon suma ne,in dai batun tsafta ne sai dai ta nuna ma mutum ba dai a nuna mata ba,kayan wanka ta ma odar take yi daga Indiya,amma shine wannan Ustazun saboda baya tsoron Allah zai kalli cikin idanun ta ya fada mata bai yarda da tsaftar ta ba,wannan abu yafi komai bakanta mata rai,kallon idanun ta da yayi, Insha Allah sai ta shayar dashi madaran mamaki,ta yanda zata ga yaya zai yi da rayuwar sa a wannan lokacin, Ranar haka ta kwana cikin baƙin ciki, da Alwashi. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *24* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Washegari haka ta tashi cikin rashin walwala,a haka ta kammala aikin ta na gida,ranar ko shiyan kaka bata shiga ba tana dakin ta,sai da rana ta fito tayi girkin rana,tana kammalawa ta jira in da ake jerawa, Ammi ce ta kira ta dakin ta, Amsawa tayi tana shiga dakin da sallamah,wani kwali ta nuna mata da kuma makulli,"dan Allah dauki wannan kwalin da makullin ki buɗe dakin Abbi ki ajiye wannan a falon sa,yau ƙafan nan so yake ya takura min" Ai ji take gabaɗaya ta nime bacin ranta ta rasa,har ma bata san sanda ta saki wani murmushi ba,"to Ammi" Har takai hannu zata ɗauka sai suka ji sallamar shi,amsawa Ammi tayi,tana faɗin "yauwa ga ɗan Albarka nan ya shigo,kinga barshi Biba bari nasa kawai yakai min" Nan take taji wani kololo ya sauko ya mata saye,wannan fa shi ake kira anga samu anga rashi, "Ammi bari nakai maki kawai" Ta faɗa tana addu'ar Allah ya bata sa'a ta amince, "Jeki abinki ai kina ƙoƙari Allah dai ya maki albarka" Kasa amsawa ma tayi ta fita tana barin dakin cikin tsananin jin haushin shigowar shi,gabaɗaya ya bata mata jin daɗin ta, Dan haka inda suke ajiye su Omo ta nufa ta dauki wani gora da naga an rubuta Fresh a jiki ta buɗe ta zuba da yawa a cikin bokitin da suke morping daki dashi,ta zuba ruwa kaɗan,sannan ta saka mopa ta fito falo da sauri, Ta dai-dai ƙarshen matakala tana tsamo mopa ko matsewan kirki bata yi ba ta saka a ƙasan wurin ta shiga kogewa,ta yanda sai da ta tabbatar wurin ya juku yanda take so sannan ta maida kayan in da ta dauko ta koma gefe ta tsaya ta naɗe hannu, Tunda ya fito daga ɗakin Ammi ta kure shi da ido tana taunar yatsanta a hankali,Allah_Allah take kawai ya sauko, Jikin shi ne ya bashi ana kallon shi,duk da ya saba da kallo domin ba baƙon shi ba,amma yasan a gidan ba mai mai irin wannan kallon mai shiga jiki,dan haka dan juyawa yayi ya kalle ta inda yake jin nan din ne,ai kuwa idanun shi ne suka sauka a kanta,sai dai kuma hankalin ta bawai a kanshi yake ba akan takun da yake yi yake,bin inda idanunta ke kallo yayi,kafin ya dauke kanshi, Faɗi take ai Gara kai ma ka karye ko zan samu damar cika aiki na in huta, Kirgawa take yi saura huɗu,saura uku,saura biyu,saura d.... Ɗan ƙara ta saki tana yarfe hannu jin zafin cizon da tama yatsar ta,tana faɗin kash,ganin a maimakon ya faɗi sai wucewa yayi cikin tafiyar nan nashi na kasaita, Kallon shi tayi ta kalli wurin,to kodai ba ta saka da kyau bane, Cikin hanzari ta karasa wurin domin dubawa,sai dai tana saka ƙafa sai ji tayi tayi baya zuuuu ta zame sai gata tayi zaman yan Bori, Ba ƙaramin zafi taji ba wanda yasa ta saki ƙara,kokarin mikewa take yi,sai dai ta kasa mikewa dan data yunkura sai santsi ya kuma kwasanta, Jin motsi a bayanta ne yasa ta juya,sai ganin shi tayi tsaye rungume da hannu yana kallon ta, Hannu ta shiga miƙa mai,alamun ya taimake ta, Takowa ya fara yi a hankali har ya iso in da take,kallon sakon biyar ya mata da hannun da take mika mashi ya kada kai ya wuce abin shi, Yaune karon farko da bakin ta ya fara furta sunan shi a gaban shi,"Suraj! Suraj,yaya Suraj! "Sai dai ko juyowa ya kalle ta bai yi ba ya yayi wucewar shi, Faɗi take" Mugu,waiyo Allah mazaunai na,"ta faɗa tana dafa duwawun ta,da rarrafe ta samu ta bar wurin,tana masa Allah ya isa,dan bai faɗi ba shine yasa ita ta shige,ta faɗi. Haka ta koma kicin ta kuma hado ruwa ta zo ta goge wurin kar wani ya kuma zamewa tunda wanda ta haɗa ma gadan ya tsallake,amma wallahi bawai ta hakura bane sai ta rama,dan yanzun suka fara, Dafe ƙwanƙwaso tayi tana fadin wash tare da yamutse fuska. Da yamma da kyar take iya mikewa a haka tayi girki,har Ammi na tambayar ta ko lafiya me ta same ta ne,sai cewa tayi zamewa tayi a banɗaki, Nafisa ce ta zo shiyan su wai Kaka na kiran ta,dama lokacin shirin wanke-wanke take yi,dan haka Ammi tace ta tafi ta bar wanke-wanke Amira zata ƙarasa, Suna fitowa,taga yanda aka ƙawata harabar tsakar gidan harda Docuration akai mai da su Balan_balan kore da Ja,wurin yayi kyau saboda ya samu wadataccen haske, haɗu da su Hadiza tsaye ita da Zainab sun sha kwalliya yanda kasan wadanda zasu gidan biki suka yi, Ko kallon banza basu ishe ta ba,suka wuce abin su,sai ma Nafisa ce data gaishe su,ita ko kallon arziki basu ishe ta ba, Kallon Nafisa tayi"yau me za'ayi a gidan nan ne? Dariya tayi "ai yau karin shekaran Yaya Nurudeen da kuma Aunty Maijiddarh,dan a wata irin daya aka haife su,shi yasa suke yi a tare" Cikin mamaki tace"dama gidan malamai haka ana celebration na Birthday? "To su dai suna yi sai dai ba ko yaushe ba,suma da kika ga zasu yi kangara gare su,kuma iyayen su sun daure masu gaba da baya shiyasa," Taɓa baki tayi"shi yasa naga waɗancan masu kama da Ungulun sun sha kwalliya " Dariya sosai Nafisa ta fashe dashi,domin ba karamin dariya abun ya bata ba,wai masu kama da Ungulu, A zaune take saman kushin tana kallon wa'azi a TV,zama tayi kusa da ƙafafunta a ƙasa,"barka da dare Kaka " Juyowa tayi"shine yau baki shigo kin duba ni ba ko Habiba,ko dai fushi kike da ni? Ɗan dariya tayi"A'a Kaka,dama ina shirin na kammala aiki na na shigo ne sai ga kiran ki" "Allah yasa da gaske ne" "Sosai ma" "Kaka to ya naga ke baki shirya ba? " Shirin me kuma" "Na zuwa party mana" Dariya tayi "raba ni da shirme" Nafisa ce ta shigo tana tambayar Kaka"a saka kayan yaji a ruwan shayin dake kan wuta? "A'a barshi kinsan Surajo baya son yaji ko kaɗan,har balle barkono,idan ya nuna kawai ki tace sai a saka a fulas" Da to ta amsa tana wucewa, Hiran su suka cigaba dayi tana danna mata kafa, Daga bisani tace ma kaka bari ta je tayi fitsari,tana shiga dakin Nafisa ta same ta a ciki tana ninke kaya,dan haka fita tayi ta zagaya ta kicin, Ganin karamin fulas mai kyau yasa ta buɗe,ganin shayin ne a ciki yasa da sauri ta shiga dudduba durowoyin kicin ɗin,ganin garin Barkono yasa da sauri ta diba ta zuba a kofi,sannan ta zuba ruwa,yana dan kwantawa ta samu karamin lariya ta tace,sannan ta buɗe karamin fulas din ta zuba kusan rabi a ciki sannan ta mai da komai ta ajiye ta fito, Dawowa falo tayi ta zauna ta cigaba da danna ma kaka ƙafa, Ba jimawa sai kuwa gashi ya shigo shida Salman yana rike da wani karamin jakka a hannun shi, Sai da ya gaida kaka kafin ya zauna, "Kai kuma jakkan waye a hannun ka?cewar Kaka tana kallon Salman, Mai da jakkan gefe yayi" Na yaya Suraj ne" "Salmanu shiga kicin ka dauko ma yayanku ƙaramin fulas da kofi ka kawo mai" Murmushi yayi"yauwa dama shi yasa na biyo Yaya dan in sha "ya faɗa yana shigewa kicin, Ba jimawa sai gashi ya dawo harda kofuna guda biyu a hannun shi, Budewa yayi ya fara zuba ma yayan shi sannan ya miƙa mashi, Ajiye wayar dake hannun shi yayi ya karba kofin yana faɗin " Thank " Kai Kofin bakin shi yayi yana shakan ƙanshin shayin idanun shi a lumshe,sai kuma ya buɗe ya juyo yana fuskantar Kaka, Da sauri ta kauda kai daga haɗa idon da suka yi tana cigaba da matsa ma Kaka kafa, "Waye ya dafa shayin? " Khadija na saka tayi haɗin komai,sai kuma Nafisa dana saka ta tace shayin ta zuba a fulas" Ajiye kofin yayi,ya kalle Salmanu dake ƙoƙarin kai kofin bakin shi"je ka kiramin Khadijah " Ajiye kofin yayi ya fita da sauri dan Allah_Allah yake ta dawo ya shaya shayin ahi, Ba jimawa kuwa sai gashi ta shigo cikin yanga tana wani juyi cikin wani dogon riga na material data saka mai bala'in daukar ido,gashi ta sha makeup sosai, Zama tayi gefen shi dan nisa da shi kaɗan,sai dai kuma ko kallo bata ishe shi ba,dan bai ma juya ya kalli inda take ba "Yaya Suraj gani" Ba tare daya juyo ba yace"kira Nafisa " Ta gane wa yake nufi dan haka a bakin kofar dakin Nafisa ta tsaya ta faɗi mata, Tana dawowa tana kokarin zama ya nuna mata gaban shi,"dawo nan ki tsaya" Nan take gabanta ya yanke ya faɗi,ganin yanda yayi maganar a dake,babu alamar fara'a a fuskar shi,ko wasa,to me tayi,domin ta san duk wanda zai ce ma ya tsaya a gaban shi to ba alkhairi bane,tambayar kanta ta fara tana tunanin abinda tayi a yinin yau, Cikin sanyi jiki ta tako ta tsugunna a banshi tana karanto duk addu'ar dake bakin shi, Kallon Nafisa yayi wacce ta iso tana kokarin dukawa a gefe ya nuna mata gaban shi kusa da Khadija,alamun ta tsaya a wurin ita ma, Sake ƙafar Kaka tayi ta juyo tana jiran taga meke shirin faruwa, Gani tayi ya juyo kanta kafin su haɗa ido da sauri ta kauda kai gefe,amma duk da haka sai da yace"ke ma dawo nan" Da sauri ta juyo tana waro mai dara_daran idanun ta tana buɗe su a kanshi,tare da nuna kanta"Ni? Mai bata amsaba shima sai madaidaitan adanunshi daya sauke a kanta,alamun tabbatar wa, Ita dai Kaka tana kallon ikon Allah, Ganin yanda ya jera su a gaban shi duk su uku...... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *25* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Kallon Salman yayi "ɗauko wani kofin a kicin" Tashi yayi ya dauko mai yana mamakin me zai yi da wani kofi kuma,"dauko shayin ka" Nuna ma Khadija wanda ke cikin kofin yayi,"ɗauka" Cikin sauri ta dauka babu musu, Ɗayan kofin da Salman ya kawo ya nuna ma Nafisa "juye na cikin fulas ki ɗauka"ita ma haka tayi, Shi kuma Salman cikin girmamawa yace"yaya gashi" Nuna Biba yaya,domin shayin kofin Salman yafi nashi yawa"bata" Kallon yayan nashi yayi ya kalli shayin shi da ya kwallafa ma rai,sai dai ba damar tambaya in ba haka ba ya ja ma kanshi,mika ma Biba yayi, Sai dai sam taki karɓa sai ma kauda kai da tayi,kara mika mata Salman yayi amma taki kula shi, Ɗan murmushin gefen baki ya saki wanda lokacin yayi dai-dai da dago kai da tai ta kalle shi,bata san sanda ta furta masha Allah ba a zuciyar ta,tunda take ganin shi bata taba tsayawa ta mai kallo koda sakon goma ba ne sai yau,idan ana maganar kyau da gayu aka zo nan an kai iyaka,fari ne shi sosai irin tas ɗin nan,idanun shi matsakaita ne farare tas dasu,sai dai kuma bakin cikin idanun ba baƙi bane brown ne mai matukar daukar hankali irin wanda ba kowa bane ke iya jure haɗa idanu da shi, Giran shi a cike yake gazar_gazar baki kirin,sai dai ita tunda take bata taba ganin namiji mai tsayin giran ido mai matuƙar jan hankali ba irin nashi,idan yana kallon kasa zaka ɗauka idanun shi a rufe suke kamar dai yanzun da duk umurnin da yake basu hankalin shi nakan wayar da yake dannawa,idan kuma aka gangaro kan Lips din shi,ji tayi tsigar jikin ta na tashi kallon su kawai da tayi,domin gasu yan kanana jawur da su,har wani maiko suke na daukar hankali yanda kasan ya shafa masu man baki, Gaskiya ba shi ba babban baki yanda kasan na mata,zuciyar ta ne ya raya mata ko dai mace Allah ya so ya halicce shi,sai kuma aka yi shi namiji, Sai dai kuma suman kanshi ba mai laushi bane,ko irin mai kwantawar nan a'a,mai ƙarfi ne dan a tsaye yake yashe kyara an aske gefe_da gefe sai kyallin maiko yake yi,gashi baki kirin yanda kasan ta saka bakin abu, Nan take taji kishi ya kamata,wallahi wannan ko tantama bata yi yafita kyau nisa ba kusa ba,haba dan Allah ai dole yayi yanga ya kuma wulakanta mata, Tun ranar farko da ta fara tsayawa kusa dashi take maitan ta gano wani kalan turare yake amfani dashi,sai dai ta kasa gani wani irin kanshi ne wannan, Domin kamshi ne dake fita a hankali_a hankali yake mamaye wurin da yake,sabanin wani turaren da tun mutum na nisa da kai zaka fahimci zuwan shi saboda kamshin turaren shi,amma nashi sai ya iso daf da daf sannan kamshin zai fara tashi yana mamaye wuri har balle idan ace ya zauna ne to ba'a magana,a takaice kamshi ne mai kashe zuciya da saka nasuwa, Ji tayi cikin sanyin muryar nan nashi wanda baya fita da hayaniya yace"idan kin gama ƙare min kallo ki amsa abinda ake baki" Lumshe ido tayi sannan ta buɗe a hankali saboda sai da ya ɗan matso kusa da ita kaɗan sannan yayi maganar,yayin da daddadar ƙanshin dake fitowa daka bakin shi ya dake fuskarta, Ba tare data ce komai ba ta amsa kofin da Salman din ke mika mata,kanta a duke saboda tsare ta da ido da yayi, Nurudeen ne ya shigo da sallamah yana faɗin "Kaka ina kayan dana baki ajiya? Miƙa mashi hannu tayi" Kaga zo ka taimaka min na shiga ciki,tunda an gama wa'azin " Kallon su yayi ya Suraj dake zaune ya daura kafa daya kan daya,nuna su yayi"su kuma waɗannan fa kamar masu niman gafara " "Aikin ɗan uwan ka ne,ni zo ka daga ni" Kallon Biba yayi,sannan yaje ya taimaka ma Kaka ya kai ta daki,sannan ya fito dakin riƙe da leda a hannun shi, A maimakon ya wuce sai niman wuri yayi ya zauna yana kallon su, Kiran sunan ta yayi"Khadija " Da sauri ta amsa"Na'am Yaya" "Ajiye kofin ki wuce,'ya nuna Nafisa" Ke ma tashi ki tafi" Cikin sauri duk suka ajiye kofin suka mike, Ganin haka yasa itama ta ajiye kofin tana kokarin mikewa, Wani irin tsawa daya daka mata sai da taji hanjin cikinta ya kaɗa,"who the hell are you to stand up ? Ba ita kaɗai ba har su kansu basu san sanda suka koma suka tsugunna ba, Domin ba zasu iya tuna randa yayan nasu yayi irin wannan tsawar ba, Lallai yau an tabo shi, Mugun kallon daya sakar masu ne yasa ba shiri suka ƙara mikewa suka bar shiyan gabaɗaya,har ita Nafisa da Salman,domin sun san yau kan Biba sai kuma ta Allah. Nuna mata kofin dake gaban shi yayi"ɗauka ki shanye " Duk da a tsananin tsorace take dashi karo na farko,amma hakan bai hana ta zaro ido ba tana girgiza kai, Cikin sanyi da son sulhunta komai Nurudeen yace"Bro pls kayi haƙuri koma me ta maka ka yafe mata" Nan take ya saki fuska harda sakin dan guntun murmushi yanda kasan ba shi ya gama tsorata su ba yace"is ok ni Bani da damuwa,kawai in kana son na haƙura ta ɗauki shayin nan ta shanye " Kallon Biba yayi wacce tuni ta fara hawaye,saboda ta san Me a cikin shayin wanda gashi har tururi yake na zafi, "Ok zata sha,badai shayin bane matsalar?to zata sha" Ɗaga kafaɗa yayi"ok then" Cikin muryar lallashi ya kira sunan ta"Biba " Allah sarki jikin ta har bari yake ga hawaye duk ya wanke fuska ta juyo tana kallon shi"is ok ya isa,ki kwantar da hankalin ki I am with you,shayi ne kawai zaki sha,dan haka ki ɗauka ki sha sai ki wuce" Da sauri ta girgiza mai, "Me yasa ba zaki sha ba" Ya tambaya Cikin kuka tace"bana shan shayi" Nuna mata kofin dake gabanta yayi"amma wannan ba kalan shayin da kika saba sha ba,wannan yana ƙara lafiya dan haka ki daure ki sha a wuce wurin" Girgiza kai take yi"dan Allah kar ka bari ya saka ni in sha mutuwa zanyi,dan Allah ka taimake ni" "Is ok Baby I will help you" Maida kallon shi kan Suraj yayi wanda gabaɗaya ma hankalin shi bai kansu yana kan aikin da yake yi a waya, "Suraj wai me yasa kake son ka tilasta mata ta sha,tunda bata ra'ayi kamata tayi ka bar ta, ba kowa ke da ra'ayin shan shayi ba har balle irin wannan" Ko kallon su bai yi ba, "Suraj pls ka ajiye wayar nan muyi magana mana," Ya faɗa cikin roƙo dan yasan halin shi idan har yace zai mai garaje yana iya hassala shi, "Me kake buƙata? Ya faɗa ba tare daya ajiye wayar ba, " Dan Allah ka saurare ni dai" Ajiye wayar yayi yana fuskantar shi"ok ina jin ka" "Dan Allah ka bar ta ta wuce" "Idan kana hada ni da Allah kana ƙara ja mata ne" "Sorry na fahimta to ka bar ta ta wuce" "Me yasa dana ce kowa ya dauko shayin ya ɗauka ita taki karɓa? " Me kake nufi? Ba tare daya kalle in da take ba yace"ka tambaye ta" Kallon ta Nurudeen yayi"me yasa baki ɗauka ba? "Bana shan shayi shi yasa" "To kaji me take" "Yauwa kai likita ne ai ko? Jinjina kai yayi" Sosai ma kuwa" "Zaka bari ta mutu a gabanka?ya faɗa yana nuna mashi Biba. " Kai ina har abada,idan akwai hanyar da zan ceceta sai nabi dan ceto ta" "That is good,dan haka ɗauka kisha yanzun kafin na nuna maki asalin waye ni ta yanda ba zaki taɓa manta hakan ba" Ya faɗa cikin tsananin daure fuska babu alamar wasa a ciki, Kokarin magana yake amma sai cewa tayi"idan ba zaka iya jira a nan ta sha ba,ka jira ta a waje idan ta fito ka ceci rayuwar nata" Jin abinda yace ne yasa yayi shiru kawai yana kallon su, Yayin da ita kuma ta dauki kofi cikin kuka tana faɗin "i am Sorry" Sai dai ko kallon ta bai yi ba, Kurba daya taima shayin ai da gudu ta mike ta shiga yarfe hannu ta rufe baki dan ta kasa haɗiye wa, Duk da kallo suke binta,ƙoƙarin zubarwa take yi taji yace"idan har kika zubar zan ƙara maki wani " Da kyar da rintse ido ta haɗiye, Gaban shi ya nuna mata dole ta dawo ta tsugunna,a takaice ranar taga Azaban da tunda Allah ya halicceta bata taɓa tsammanin haɗuwa da irin sa ba,domin ko wani kurba daya ji take kamar zai tafi da numshinta da fatar bakinta harma da maƙoshin ta, Tayi kuka tayi data sani tayi ban haƙuri amma bata taɓa tsammanin rashin imanin shi yakai nan ba, Da Nurudeen ya nuna bacin ranshi sai cewa yayi idan ya kuma magana sai ya kara mata ruwan shayin domin ita da kanta ta haɗa abinda zai kashe ta,ko ƙarya na faɗa? Ya faɗa yana kallon ta yanda miyau ke dalala daga bakin ta, Da sauri ta girgiza kai,Alamar haka ne, "Dan haka idan ba zaka iya jira har ta kammala ba kana iya jira a waje" Gaskiya ba zai iya ba,amma kuma ya tausaya mata,wata kila saboda bata san halin Suraj din bane shi yasa ta yi gangancin yi masa kutse, Tashi yayi ya bar falon. Bai damu da yanayin da take ciki ba sai da ya tabbatar ta shanye shayin dake cikin kofin tas sannan ya mike tsaye,dukowa yayi saitin kunnenta "ki tabbatar da ƙwarin gwiwar ki kafin aiwatarwa" Yana gama faɗar haka yayi ficewar sa ya bar ta nan tana fitar da numfashi da ƙyar, Ko tashi bata iyawa sai da Nafisa da ke kofar gida taga fitowar shi shine ta shiga ta dagata, Amma ina ko tashi bata iyayi,da talla_talla ta taimaka ta kaita shiyan su,dan ji take cikinta kamar ana busa mata wuta a ciki, Ranar bata ga komai ba sai da daddare domin ranar a cikin bayi ta kwana,domin zawo mai azabar yaji ya kamata,tun tana yi tana iya fitowa har ta koma a banɗakun kawai take zaune,ko zaman ma sai dai tayi goho,tun tana iya hawaye har takai bata iyawa,domin abun sai ya haɗe mata ya zama Amai da zawo, Kafin gari ya waye har ta zabge yanda kasan wacce tayi jinyar shekara,ko tashi bata iyayi,ita kanta Ammi data ganta da safe sai da ta tsorata,cikin gaggawa tasa akayi Asibiti da ita,a takaice sai da tayi kwana uku a Asibiti tasha ruwa leda Takwas,dan zawo tayi bana Arziki ba ko zama taba iyawa, Duk numfashi daya cikin tsine ma Suraj take,in Allah ya yarda yace ta tabbatar da ƙwarin gwiwar ta kafin aiwatarwa to sai ta bashi mamaki,sai tasa yayi suman tsaye.. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *26* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Kaka ce tace Nafisa ta tsaya ta yi jinyar ta a Asibiti,ranar data cika kwana biyu kuma sai ga A'i ta zo a matsayin yar uwarta,ta karɓi jinyar har aka sallame ta, Tana zaune kan gado A'i na haɗa kayan su a jakka ta kalle ta"kina buƙatar hutu dan haka na ɗaukar maki izini wurin Uwar ɗakin ki,idan kin ƙara jin sauƙi sai ki koma" "Babu in da zanje ki mai dani can kawai,domin sai na ƙarasa aikin dana fara" Ajiye kofin dake hannun ta tayi ta dago tana kallon ta"a haka ne zaki koma wannan gidan,Gara dai ki bari ki ƙara kwari in ba hakaba karasaki zasu yi" Kauda kai tayi"ko da zan dauki hutu sai na tabbatar na rama abinda akai min" "To wallahi in dai zaki bi shawara ta gara ki bar batun ramuwar nan,domin banga amfanin ta ba,wannan da kike gane tunda har ya iya tsallake tarkon ki ba tare da ko kwarzane ba ki tabbatar yana iya saukar da duk wani hatsari da jiji da kai irin na ƳAR TSANAR ZINARI" "Zamu gani" Ta faɗa cikin kwarin gwiwa, "Ki kalli yanda ya saka acikin kwana uku kika kusa rasa rayuwar ki,kin kuwa ga ma yanda kika koma,gaba ɗaya duk cikar fuskarki ya tsiyaye sai dogon hanci da idanu,to wallahi ki yi a hankali kar a fito mana da gawar ki" Saukowa tayi daga kan gadon Asibitin "idan kin kammala haɗa kayan ki same ni a waje" Ta faɗa tana barin ɗakin, Shiru tayi kawai ta bita da kallo,tausayin yarinyar take yi,domin ta tabbatar da bata san irin girman hatsarin da take saka rayuwar ta aciki ba, Domin ba ita bace mace ta farko da VIP ya bama wannan aikin ba,ita ce ta shida, Gaba ɗayan su sunyi aiki ne a sashi mabanbanta a cikin gidan,sai dai wahalhalun dake tattare da zama acikin gidan ke koransu,wasu basu ma samu damar koda magana bane da shi uban gaiyar,Ustaz,balle su samu damar nufar shiyan mazan gidan,acikin su ma akwai waɗanda ko ganin shi basu taba yi ba agidn, a haka kuma ko waccen su da kalar wahalar da zaisa su bar gidan,sai dai da sun fito da kwana biyu ake niman su a rasu sai bayan wani lokaci aga gawarsu,ba dan komai ba sai dan kawai sun san sirrin abinda ake hari, To amma ita nata lamarin da ban ne tunda gashi har ta samu nasaran sanin wani abu, Ta san ko da tayi nasara VIP ba zai taba barin ta ba, Ajiyar zuciya ta sauke sannan da ɗauki jakkan ta fito, Dole haka ta maida ita gidan ba dan tayi ni ya ba, Ammi ce tace taje daki ta huta ta bata hutun kwana huɗu ta kara hutawa, Sosai tai mata godiya sannan ta koma ɗaki,tana tunanin ta hanyar da zata dauki fansa dan ita bawai zata ƙyale shi bane, Washegari tunda ta tashi,take cikin wani irin yanayi na rashin farin ciki da walwala,zuciyar ta gaba ɗaya zafi yake mata,har balle idan ta tuna yau wace rana ce a gare ta, Ranar ko shiyan kaka bata shiga ba,sai wuraren bayan sallar La'asar sannan ta fito,ta bayan ɗakunan su nan ta je ta samu wuri ta zauna, Fito da kwalin sigarin dake jikin ta tayi ta kunna daya,kafin wani lokaci har ta gama dashi ta kuma kunna wani,a haka sai da tasha kara biyar ba tare da taji komai na daga damuwarta ya rage ba,sabaninda da ƙara daya kawai take sha, Tana ƙoƙarin kunna na shida ne sai ga kira ya shigo karamin wayar ta,dagawa tayi ta kara a kunne ganin me kira, Sunan ta aka kira"Babi " "Ummm" Ta amsa mata, "Ina fata kina lafiya? " Ummm" "Ar you ok" Share wayen daya zubo mata tayi da bayan hannun ta"yes I am fine" Dan shiru ne ya ratsa tsakani kafin kuma tace"karki yi kuka,dan Allah kar kiyi shaye-shaye,don't forget were you ar,karki manta me ya kawo ki,nasan yanda kike ji yanzun saboda yau ne,amma karki bari tuna hakan ya raunata zuciyar ki,karki sha Sigret da yawa" Dan jan majina tayi kaɗan "is really painfull,ji nake kamar zuciya ta zata buga,na kasa manta komai,na kasa anytime i remember is really destroy me,bana son ina tunawa amma it keep coming to my mind and ring is to my head," "Na sani,yanzun me kike yi? " Just setting" "Me a hannun ki? Kallon Sigret din tayi"Segret " "To ki maida shi cikin kwali sannan ki kashe wanda kike sha ki rike sai ki zubar in da ba za'a gani ba" Kamar yanda faɗa mata haka tayi sai dai kwalin na ajiye a gefen ta,"Ummi ta"ta kira sunan ta, "Na'am Biba" "Da zaran na kammala wannan aikin nawa,ba zan kuma yin wani aiki ba,zamu bar kasar nan mu je wani wuri in da babu wanda zai ƙara takura mana,in da ba zamu haɗu da wadanda suka san mu ba balle suyi threatened din mu" "To Biba idan kina son haka ya kasance sai kin watsar da komai kin maida hankali kin cika aikin ki" Share hawayen idonta ta kuma yi"zan yi haka,cikin satin nan duk hanyar da zanbi zan bi domin na kammala" "Yauwa Biba,shi yasa nake son ki,saboda nasan zaki iya" "Thank you for supporting me all the time,and encouraging me,you are my only Family in this world" Daga nata ɓangaren ma share hawaye take yi,ta san halin Biba sarai,ta san matsalarta,kamar yanda ita ma ta san nata,Biba ta dauke ta ta maida ita danginta alokacin da take tsaka da niman taimako,ta bata muhalli,ta maye mata gurbin duk wani abinda ta rasa, Sun maida junan su Ahalin juna,shi yasa ta riga tasan wannan wani irin rana ne a wurin Biba"ke ce farin ciki na,kuma gata na,dan haka ki yi sauri ki kammala ina jiran ki" Jinjina kai tayi"sai munyi waya"tana gama faɗar haka ta sauke wayar. Maida kanta tayi ta jinjinar da jikin iccen,idanun ta a lumshe, Wani irin ni'imtaccen kamshe ne yake shiga hancinta,wanda ta tabbatar da a jikin mutum ɗaya kadai take jin wannan kamshen, Tuna wanene yasa da sauri ta buɗe idanun ta,wanda cikin rashin sa'a sai a cikin nashi, Yana tsaye a gefen ta ya zuba mata ido kamar mai nazarin ta, Da sauri ta ɗauke kai dan ba zata iya jure kallon cikin waɗannan idanun shi ba, Hannu tasa da sauri tana goge ragowar hawayen dake kwance saman fuskarta, Tuna kwalin Segret din dake gefen tane yasa da sauri ta zabura tana daura hannun ta saman kwalin, Ƙara dago ido tayi dan ganin ko yaga kwalin wanda bata fatan haka, Sai dai har yanzun idanun shi na kanta ne bai dauke ba, Kara kauda kai tayi a karo na biyu ta dauke kwalin Segret din cikin dubara ta tura a hijabin jikin ta, Mikewa tayi ba tare data ce mai komai ba tana ƙoƙarin barin wurin, Cikin muryar nan nashi mai ratsa kashi da barko taji yace"wannan ya zamo karo na karshe da zan kuma ganin inuwar ki a tanan ɓangaren "yana gama fadar haka ya juya yayi tafiyar shi cike da mamakin ta,shi fa ya fara zargin Something is not right about this girl,ya dawo daga masallaci ya shiga bayi domin yin wanka,amma gabaɗaya kasawa yayi saboda bayin shi dake warin hayaƙin Segret,domin windon a buɗe yake, Yana lekawa shine ya hango ta. ___________Niger State. Kusan mintuna biyar kenan yana tsaye a kanta amma bata San ma da zuwan nashi ba, Dukawa yayi a hankali ya saka hannun ya amsa Album din dake hannun ta,wanda take kallo tana shafa hotunan ciki, Dago kai tayi ta kalle shi, Hannu yasa ya shiga share mata hawayen dake bin Fuskarta,"har tsayin wani lokaci zaki ɗauka kina zubar da hawaye Mama? Dagowa tayi ta kalle shi da rinannun idanun ta"har zuwa sanda zata dawo cikin rayuwar mu,ko da ta dawo har sai na nime yafiyarta ta kuma yafe min sannan zan iya samun salama " "Mama yau tsayin shekara biyar kenan,rabon da muga farin ciki acikin idanun ki,gashi sanadin yawan kukan da Kike yi idanun ki na son ya samu matsala,dan Allah Mama koda sau daya ne,ko da na rana daya ne muna son muga farin ciki a fuskokin ku,muna son muga dariya a faskarku" "Abdulmajid" Ta kira sunan shi, Rike hannun ta yayi"na'am Mama" "Tun daga ranar da ƙanwarku ta saka kafa tabar wannan gidan ta tafi da duk wani farin ciki namu,kai ma ka sani,ko da nace zan ɓoye bakin ciki na nayi dariya a fili,to is feck,abu ne da bazan iya ba," Share hawayen ta tayi"yaune ranar zagayowar haihuwar ƙanwarku,yaune kuma naran da tayi aure,"idan da ace tana nan kamar shekarun baya,da tunda Asuba zata fara bi ɗakunan ku tana tayar daku akan sai kun bata gift na karin shakara,haka za ku korata waje ku saka sakata a ƙofar ku,amma duk da haka sai ta hanaku barci da buga ƙofa,har sai ta saka kun fito ba tare da dakun shirya ba,koda tayi aure ma haka sai dai tai ta damun ku da waya tunda Asuba,idan kuma kuka kashe wayoyin ku sai ta kirani tana korafi," Dariya yayi kaɗan shima yana share nashi hawayen,"wani lokaci idan na tuna soyayyar dake tsakanin mu Mama,sai naga kome yayi zafi bai kamata Salma tayi irin wannan nisan ba" "Na tabbatar kuma saboda kun danne zuciyar ku ne shi yasa baku tafi kun barni ba,sai dai ku yi haƙuri domin wannan shine tawa Kaddaran," Ta karasa faɗa tana fashewa da kuka, Rungume ta yayi ajikin shi yaya lallashinta sam baya son hawayen ta ya karu,dan haka ɗauko Album din da ya ajiye a gefe yayi ya buɗe "Mama kin ga nan hoton salma ne lokacin tana shekara biyu,a lokacin ta fara iya magana,kin tuna ba tada aiki sai na cizo,ko hannunka ka kuskure yayi hanyar bakin ta saita kai maka cizo,in kuma kaki yarda ta dinga kuka kenan tana binka" Nan take ta shiga shafa hotun murmushi mai tattare da hawaye yana bin fuskarta, Ko a cikin ya'yan ka Ubangiji kan jarabceka da son daya daga cikin su,wanda zaka ji duk kafi son shi,to su nasu gabaɗaya soyayyar akanta ne,domin ita kadai ce mace acikin su hudu. _______Kano 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *27* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* ______________Kano. Ganin ta gaji da zaman tunani ne yasa ta fito falo domin taya Amira yin girki,sai dai koda ta shiga kicin din kin yarda tayi ta bari tayi aiki, wai ta bari ta ƙara jin sauƙi, "To ki bari na taya ki koda ƙyara ganye ne" Ta faɗa tana jawo kujeran kicin din ta zauna, "So kike Ammi taimin faɗa? " To ai tana ɗaki " "Yauwa abunda za'ayi kawai shine ki shiga dakin Abu ki taya ni kyarawa kinga kafin ta sauko kin kammala" Cikin sauri tace "na amince" Dan ji ta yi kamar ta kama kumatum Amira ta sumbace ta, Nuna mata ɗan key din tayi"gashi nan ki ɗauka sai dai ki yi sauri" Daukar makullin tayi,tana barin kincin din da sauri,cikin tsananin zakuwa da kuma Addu'ar Allah yasa ta dace, Tunda ta shiga falon ta dafe Kwankwaso tana ƙare ma ko'ina kallo,ta ina zata fara,daga kan durowoyi ta fara bincike har karkashin kujeru,sai dai duk bata ga komai ba,tana yi tana share dakin tare da gogewa sama sama dan kar a fahimta, Hannu tasa tana ƙoƙarin murda hannun kofar data gani,ta ji daddadar kamshin nan na tashi, Bata juyoba taci gaba da murdawa ko Allah zai sa ya buɗe, Daga bayanta ta ji ance"me kike yi" Tsabar tsoratan da tayi batasan sanda ta yar da tsintsiyar dake hannun ta ba ta makale jikin bango tana dafe kinji, Kallon shi take cikin jin haushi wai me yasa shi baya sallama ne,kawai sai dai kaji kamshin shi, Ƙara jeho mata wani tambayar yayi"what ar you looking for? Ba tare data bashi amsa ba ta raɓa ta gefen shi tana kokarin wucewa,hannun yasa ya kama gefen hijabinta kaɗan "fadamin me kike nima" Kallon shi tayi ta kuma kalli hannun da ya riƙe ta dashi yanda kasan wanda ya rike kashi"gyaran daki nake yi " Sake hijabin yayi,babu abinda daya kona mata rai irin yanda ya dauki abin goge hannu ya goge hannun shi gaba da baya ya wurga a wurin saka shara,wato yanda kasan wanda ya taba kashi, "Nan ba wurin zuwan ki bane kina iya tafiya"ya faɗa yana nufar wurin kofar,tana kallo nan ma sai da ya ƙara gogewa sannan ya saka makulli, Juyawa tayi ta fita daga falon gabaɗaya dan babu abinda ta samu,sai dai yau dinnan sai ta shiga dakin shi,domin ta ji abakin Amira cewa zasu yi wa'azi yau bayan Isha'i a masallacin kofar gida,dan haka yau kam damarta ce. Daki ta koma lokacin ana daf da kiran sallah Magrib,wanka tayi ta saka doguwar riga na bacci iya cinya mai karamin wando a ciki,sai ta daura zani a sama,da hijabi,tana jira ayi sallar Isha'i sannan ta tafi, Sai da ta tabbatar an idar da sallar Isha'i sannan ta fito, Tana fitowa suka hadu da Nafisa a falo,rungume ta tayi"Biba ya jikin naki" "Da sauƙi Nafisa" "Kiyi haƙuri ban samu na koma na duba ki ba,ni ma Baba nane bai da lafiya shine na tafi duba sa" "Ya jikin nashi? " Yaji sauki dama wai Maciji ne ya sare shi a gona,amma Allah ta taimaka gidan mu suna bada maganin,sai zazzabi da yayi" Kankame hannun ta tayi tana jin tsigar gikinta na tashi"waiyo Allah na tsani maciji,kinga ya jikin nashi" "Yaji sauki sosai ko da na dawo,yauwa muje an aiko ni na kira ki ne" "Waye? " Goggo yara" Sam bata son shiga tsabgar matar nan dan haka tace"me zan mata kuma? "Kin ga ba ke kaɗai bace,ina ga zata sakamu aiki ne" Turo baki tayi"duk ma'aikatan gidan nan,sai ni da Bani da lafiya? Jan hannun ta tayi"dan Allah mu tafi kinga dare nayi" Ba dan taso ba tabi bayan ta har shiyan Goggo,in da suka same ta a falo tana kallo, "Yauwa Nafisa ku shiga dakin na ku duba min har kasan gado ni gabaɗaya ma na rasa meke motsi ne a cikin dakin,Allah dai yasa ba bera bane" Dakin suka shiga suka fara dubawa, Motsi taji ai kuwa ihu ta saka tana daka tsalle sai saman gado Dariya Nafisa ta saka"kardar ke ma tsoron beran kike yi? Leken kasa take yi"duba ta nan naji motsin abu" Dariya ta kuma sakawa tana nuna ta"kinga leda ne na taka shine kika ji motsi " Saukowa tayi tana sauke ajiyar zuciya,a haka suka cigaba da dubawa,ganin har takwas da rabi basu gama kwaliman da ta saka suka fara ba yasa ta yanke shawarar fita dan ƙarfe tara ake gama wa'azin, Kallon Nafisa tayi"bari nage nayi fitsari na dawo" "To dan Allah ki yi sauri" Koda ta fita Goggon bata falo Hadiza ce kawai,dan haka bata ce mata komai ba ta fita, Tsayawa tayi ta duba ko akwai mai kallon ta,ganin ba kowa ata wurin yasa da sauri ta nufe shiyan mazan gidan, Tsayawa tayi a ƙofar dakin shi tana kallon ƙofar, Hannu ta saka cikin Aljihun rigar barcinta ta ciro wani ƙaramin kati, Tana mannashi jikin ƙofar cikin sakon goma sai gashi ƙofar ya buɗe, Cikin sauri ta shiga ta maida kofar ta kulle, Kallon dakin take yi yanda yake a kyare tsaf dashi,ga kuma mayataccen ƙanshin nan nashi dake tashi, Hango wasu takardu tayi a saman table,da sauri ta karasa wurin ta shigo buɗewa tana bincikawa,sai dai takardun duk na wani business da yake gudanarwa a Dubai,sai kuma kimanin kudin da zai kai Biliyan biyu a kudin Najeriya, Zaro ido tayi tana mamakin wani irin kasuwanci ne haka, Mai da takardun tayi ta mike tana jawo wani durowa dake wurin,nan ma takardune,tana buɗe wa wani karamin emvelop ya faɗo kasa wanda yake a like,da sauri ta dauka ta saka acikin Aljihunta,dan tunda ta ganshi a like ta san koma menene a ciki me muhimmanci ne, Daukar sauran takardun tayi tana ƙoƙarin kara buɗe su taji motsi daga bayan ta,wanda hakan yasa ta juya da sauri, Hmmm mutuwar tsaye tayi yayin da takardun hannunta suka zame suka faɗi ƙasa, Bugun zuciyar ƙaruwa yake a ko wani sakan,yayin da take jin yanda jinin ta ke hauhawa,idanun ta na ƙoƙarin rufewa sakamakon jirin dake ƙoƙarin ɗaukar ta, Tsaye yake sanye da farin Singlet fari tas a jikin shi,sai dogon wando baki na jins da kuma towel dake rike a hannun shi wanda hakan zai tabbatar maka daga banɗaki yake,saboda ruwan dake jike a fuskar shi, A hankali yake ta kowa yana doso inda take,yayin da take tsaye kamar wacce aka dasa a wurin,sai dai duk taku daya da zaiyi haɗe yake da bugun zuciyar ta,yayin da kamshin shi ke kara mamaye hancin ta,yake kara sanar da ita kusancin su, Yana isowa bai ce mata komai ba ya duka ya kwashe takardun dake zube a bagan ta ya maida su cikin durowar ya kulle,sannan ya dago idanun shi ya zuba acikin nata "kina son na kyale ki? Da sauri ta jinjina kai alamun eh, " Idan na tambaye ki kibani amsa kai tsaye,idan kika min karya kuma zan sani" Kokarin cire idanun ta acikin nashi take yi,sai dai sam yaki bata dama,sai ma kara tsare ta dasu da yayi,wanda ita hakan da yaye shike kara tsorata ta,kallon idanun nashi,jikinta har ya fara daukar ɗumi, "Me kike nima? Idanun ta ne suka ciko da kalla domin yaki bata damar saukar dasu,sai dai ba zata taɓa faɗa masa me tazo nima ba,saboda ka'idar aikin sune a haka, Ji tayi ya ƙara maimaitawa" Me kike nima? "Kuɗi" Ta faɗa cikin rawar murya, Taku daya ya kara daga inda yake ya kara matsowa daf da ita "canja wani dai" "Da gaske kudi nake nima," "Baki yi kama da barauniyar kudi ba Biba,sai dai wani abun daban,faɗa min me wannan? Mamaki ne da tsoro ya kara shigarta dama yasan sunan ta ne, " Idan da ace kudi zaki ɗauka da tun shigowar ki wancan durowar daki buɗe,ko wancan karon da kika shigo ai baki dauki ko sisi ba,kuma kinga kuɗin,dan haka karki ƙara ce min kuɗi " Hawayen dake makale acikin ramin idonta ne ya sauko, yau ta kawo kanta ajalinta, Cikin dakewa tace"kud...... Sai dai duk yanda taso ta karasa kasawa tayi sakamakom wani irin shaka da ya kai ma makogoron ta, Idanun ta nan take suka yo waje,yayinda da numfashin ta taji yana ƙoƙarin tsayawa, "Kafin ki tsaya a gaba na ki tabbatar da kwarin ƙwarin gwiwar ki" Ya karasa faɗa yana tunkuɗe ta,sai da ta bugu da jikin kushin, Tari take yi sosai tana shafa wuyan ta, Hanyar kofa ya nuna mata"ya zamo karo na karshe " Cikin tsananin rudewa ta mike ko takan zanin jikinta da ya kwance ba tayi ba sai ma rike shi da tayi a hannu ta fita da gudu, Tsaye suke ita da Dady da Ibrahim wandanda suke taka mata tana ɗan motsa kafa,dan shi Abbu yana Masallaci shi kewa'azi, Kallon juna suka yi cikin tsananin mamaki,domin kuwa a idanun su ta fito daga cikin dakin da gudu da kuma zani riƙe a hannunta,tazo ta giftasu,tabbas wannan kamshin turaren mutum ɗaya ne,duk gidan shi kaɗai ne me irin wannan kamshin, Riƙe mai hannu tayi"me nake shirin gani? Duk shiru suka yi kafin Ibrahim yayi saurin faɗin "idan da ace ni ne na faɗa da cewa za ku yi sharri nake mashi,to yanzun dai gashi kun gani da idanun ku,har balle Kaka da anyi magana ki ce Surajo babu ruwan shi,to yanzun dai kinga misali,wama yasan me yake aikatawa a garuruwan da yake cewa yana zuwa wa'azi" Dafe kanta tayi tana kiran sunan Allah, Dady ne ya dakatar dashi"to ya isa haka,sauran kuma naji wannan maganar a bakin wani,Kaka ki kwantar da hankalin ki insha Allah zan bincika lamarin naga meke faruwa " "Amadu" Ta kira sunan Dady, "Na'am Mama" "Wata yarinya ce wannan? Da sauri yace" Ai Biba ce" Hararanshi Dady yayi, Maimata sunan take"Habiba" "Ita ce,amma Mama ki kwantar da hankalin ki in sha Allah zan bincike komai,muje mu karasa mutsa ƙafar" Girgiza kai tayi"A'a mayar dani gida" Dole mayar da ita shiyan ta sukayi,domin kamar hankalin ta a tashe yake. __BIBA. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *28* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Tana shiga daki kullewa tayi da key ta fada kan gado tana sauke numfashi,tare da shafa wuyan ta, Goran ruwan dake gefe ta buɗe ta kafa kai sai da ta shanye sannan ta ajiye, Shafa wuyanta tayi tana faɗin "mugu"tare da ciro emvelop ɗin dake ajjihun rigar ta,ita sam shakan da ya mata bata damu ba in dai har zata samu nasaran ɗauko abin harinta, Buɗewa tayi ta shiga warware takardar, Tsurama takardar idanu tayi,*Hadarin dake sararin samaniya yayi baƙi kirin,kuma daf yake da saukar da bakin ruwa mai mugun dafi,da fatan za'a shirya ma ƙwaryar taran shi*. Ta karanta wannan wasikar yafi sau ishirin amma ta kasa fahimtar koda kalma daya me yake nufi,tayi tunani iya tunani amma ta kasa fahimtar komai, Nannaɗe takardar tayi ta maida sannan ta buɗe jakka kayanta ta saka aciki, Komawa tayi kan gado ta kwanta tana lumshe,shakar numfashi tayi tana busarwa,yayin da take jin yanda gabaɗaya jikinta ke tashin kamshim turaren shi,duk da yana da kyau na jan hankali amma sam baya burge ta,saboda bai da tausayi a nata fahimtar,sai dai kuma duk yanda zai yi da ita sai dai yayi,domin kuwa sai ta koma,tana buƙatar komawa,dole ne ta cika aikinta a cikin kwanakin nan ta je ta sami Ummita, Mikewa tayi sam ta cire wannan rigar na jikinta,ta sauya wani sannan ta kwanta. Washegari misalin ƙarfe tara na safe sai ga shi kaka ta aiko a kira ta, Koda taje a zaune ta same ta a falo tana tsinkar Zogale, Zama tayi kusa da ita "Kaka me za ki yi da zogale? Cikin sakin fuska kamar ko yaushe tace" Yau dambu nake jin ci" "Wow kaka ai kuwa ina son danbu,har balle idan aka saka gyaɗa,a lokacin ina gida Mama tana saka wa ana min" Murmushi ta sake "me sunan Maman naki" "Fatima,sunan ta Fatima" Ta faɗa muryar ta dauke da murmurewa, "Kin ji kewar ta sosai kenan? Ta tambaya, " Tamkar rayuwa,wata rana ji nake kamar na buɗe idanu na ganni a gabanta" "Idan har kinji kewar su har haka me zai haka ki dauki hutun sati ɗaya sai kije ki gansu" "Har abada bazan taba zuwa ba" Cikin mamaki ta dago tana kallon ta"me kike nufi " Cikin sauri ta daidaita natsuwarta domin ada ta manta dawa take magana har take shirin sakin layi,da sauri tace"ohh ina nufin ban daɗe da nage gida ba,kinga ko sati ba'a yi ba,bai kamata na koma ba yanzun" Jinjina kai tayi"amma a katsina a wace unguwar kike? Shiru tayi domin tama manta sunan unguwar da A'i ta faɗa mata,dan bata taba zuwa garin ba,juya idanu ta fara tana kokarin tuna sunan wurin, Wayar kaka ne da yayi kara ya dakatar dasu, Ganin ta dauki wayar ne yasa ta sauke ajiyar zuciya tana dafe kirji, Bata wani jima ba ta sauke wayar ta juyo "ina jinki" "Emm,Umm,yauwa kaka dan Allah ki taimaka ki koya min dambu" Ta faɗa a kokarin ta na kawar da maganar,sai dai ta manta wanda ya rigaka kwana ya rigaka tashi, Murmushi kawai Kaka tayi"kina da number A'i? "Eh ina da shi" Mika mata wayar ta tayi "ga shi ki saka min sai ki adana min shi a yawa" Amsa tayi ta saka mata,daga nan suka cigaba da hira hankali kwance,sai zuwa goma da rabi ta koma shiyan su. Bai samu ya shigo gaida kaka da safe ba,sai bayan Sallar Azahar wanda bama a gida yayi shi ba, Suna gaisawa tace"dama ina son magana da kai " Kyara zaman shi yayi saman darduman ta, "Sai dai kafin nan kiramin Amadu a waya idan yana gida bai fita ba yazo" Ya gane wa take nufi,dan haka kiran wayar dady yayi,ai kuwa ya shaida masa ga shi nan zuwa, Bayan wasu yan mintuna sai ga shi ya iso,zaunawa yayi shima yana ƙara gaida kaka dukda basu daɗe da rabuwa ba, Kallon Dady tayi"ina son ka zama shaidar komai shi yasa na saka a kira ka" Jinjina kai yayi"in sha Allah ina tare da ke Kaka" Kiran sunan shi tayi"Surajo " Amsawa yayi da "Na'am" "Shin ka tashi aure ne? Ko ince kana buƙatar aure ne? Kallon mamaki ya shiga yi mata" Kamar ya? Ya tambaya cikin rashin fahimtar in da ya dosa, "Tambayar dana maka shi nake nufi" "Kai muke saurara ka bamu amsa kawai" Cewar Dady, Numfashi yaja ya sauke yana ƙoƙarin daidaita kanta"A'a kaka,bana bukatar aure" "Me yasa" Ta kuma tambayar sa, "Saboda ban shirya ma hakan ba" "Ko da baka shirya ma hakan ba me zai hana ka fara ajiye daya a kusa da kai,na tabbatar da yanzun kana bukatar haka" "Ta yaya nake buƙatar hakan?sam aure baya gabana yanzun" "Na fahimta,amma me zai hana ka yarda cikin satin nan a aura maka yar uwar ka Maijiddarh"cewar kaka, Wannan karon baki buɗe yake kallon su," What? Why? Sai kuma yayi shiru tuna waye Dady a wurin shi da kuma wurin Maijiddarh,domin mahaifinta ne,duk cin fuskar shi ba zai iya yi a gaban shi,amma me dalilin kaka na dauko wannan zancen, "Me ka ga" Dady ya kuma tambaya, Shiru yayi gaba ɗaya ma ya rasa me zai ce, "Kai muke saurare" "Ayi abinda ya kamata" Ya faɗa kasan makoshi, "Ina iya tafiya? Cikin sakin fuska gaba ɗaya suka amsa mai da "eh"tunda sun samu amsar da suke so, Ganin ya fita ne yasa Kaka sakin murmushi" Alhamdulillah tunda ya amince,yanzun abinda nake so sai a fara gudanar da shirye-shiryen tunda yau Lahadi nan da kwana biyar sai a ɗaura auren kowa ya huta" Zuciyar shi wasai domin yasan matarsa yau sai tayi rawar daɗi "to amma Kaka wani hanzari ba gudu ba,yaya za'ayi da batun ita wannan yarinyar,kinga bai kamata ma kwata_kwata su dinga ganin juna ba" Dan shiru tayi kamar mai nazari kafin tace"babu damuwa akan haka,domin nan da kwana biyu zan sallame ta,tunda ita Ammi din ma taji sauƙi" "To shikenan bari naje dan a fara shirye-shiryen da wuri" "To Allah ya maka Albarka" Da Amin ya amsa cikin tsananin farin ciki. Yana fita shiyansu kai tsaye ya nufa,anan yake sanar da iyalan shi kyakkyawar labari wanda sai da Maijiddarh tayi kukan farin ciki, Kafin kace me tuni gida ya hargitse da murna, Ammi ita ma Kaka ke nasar da ita hukunci data yanke,duk da abin bai mata daɗi ba ko kaɗan kuma ya kona ranta haka ta hakura ta ke sakin murmushi ba tare data nuna damuwarta ba,amma a ranta ta san duk inda yake yanzun baya cikin walwala, Aunty Atika Maijiddarh ta kira tan sanar da ita abinda ke faruwa,cikin wayar ta shiga zuba ihun farin ciki,tana taya yar uwarta murna, "Ki ce tun yau na fara kiran ki da Hajiya Maijiddarh" Dariya tayi"kai Aunty Atika " "Dama ina da ƙawa yar Sudan bari na kira ta na maki bukin gyaran jiki" "Ai kuwa da kin taimake ni" "Ke dai ki jira gamu nan zuwa" Daga haka ta sauke wayar tana kuma niman number kawayen ta domin sanar dasu, Itama a bakin Amira ta ji batun Bikin,duk da taji abun a ranta wani iri,amma sai kara ɗaukar ƙuduri tayi akan kafin bikin ta samu abin harinta ta bar gidan,can su kara ta abin su, Tun daga lokacin da aka sanar da wannan bikin basu kara samun hutu ba domin yanda ake ta faman gyaran gida ana sake sabon fenti shiya_shiya, Kuma tundaga lokacin daya shake mata wuya basu kara haɗuwa har yau da ya rage saura ƙwanaki uku bikin shi, Kira ne na gaggawa ya shigo wayar ta daga VIP,sai dai bansa me yake faɗa mata ba amma abu ɗaya kawai naji tace shi ne "me kake nufi da yau Kaka zata sallame ni a aiki" da ganan kuma sai naji tace"yanzun? Sai kuma ta ajiye wayar, Kallon Agogon bango tayi,wanda ya nuna ƙarfe goma na safiyar ranar Talata, Riga da Siket ne a jikinta wanda ya zauna mata cas ajiki dan kayan ma har yaso ya dan matse ta,dan Amira ce ta bata,kuma ta dan fi Amira kiba kaɗan, Bata iya saka ɗankwali ba dama kuma sumanta ta kama shi da ribbon ne,dan haka hijabinta mai dan jirma ta saka ta fita tare da daukar wannan katin na buɗe ƙofa ta nufi shiyan mazan gidan, Tana zuwa ba tare da shakkun komai ba tayi ammafi da katin wurin buɗe ƙofar ta shiga kanta tsaye,ba tare data damu data kulle kofar ba, Kallon ta yake rike da goran ruwa a hannun shi,kamar yadda itama take kare ma shi kallo, Wannan karon babu riga a jikin shi,gaba ɗaya tana kallon farar fatan jikin shi,wanda yake a cike ko ina yake,yayin da alamun ƙarfi ya gama bayyana a jikinshi wanda Kirjinsa babu ɗigon suma ko dis, Ganin kallon da take masa ne yasa cikin tsananin bacin rai wanda ya nunka wanda yake ciki ya nufota a hargitse,"wai ke wata irin jahila c.... Kafin ya karasa faɗa ta shire hijabin jikinta ta yar haɗe da ribbon wanda yayi sanadin saukowar sumanta har gadon bayanta, Yana isowa daf da ita kafin ya ƙarasa faɗin abinda ke bakinsa sai ji yayi ta shige jikinshi tare da bashi kyakkyawar runguma tana haɗe bakinsu wuri ɗaya, Duk yanda yaso ya kwace bakin shi acikin nata ta hana shi ta hayan kin bashi dama,wani irin tsotsa take ma harshen shi,yanda kasan wacce bata San dawa take tare ba.......... 🤭 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *29* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Duk yanda ya so ya kwace bakin shi a cikin nata ta hana shi ta hanyar ƙin bashi dama, Wani irin tsotsa take ma harshen shi yanda kasan wacce bata san dawa take tare ba, Cikin zafin nama da jarumta ya dago ta daga jikin shi,wannan ne karo na farko a rayuwar sa da mace ta samu galaba har haka a kansa,kuma wannan ne karo na farko daya taba ɗaga hannu ya Mari wata mace kamar yanda bai jira komai ba ya sauke mata lafiyayyen Mari a saman farar fatan fuskarta, Hannu yasa ya shiga goge baki tare da jawo tulin Tissue paper ya shiga goge bakinsa dashi,sam hankalin shi baya kanta yana kan yanda zai yi ya taimaka ma kanshi ta hanyar goge najasan data saka mashi, Daukar hijabinta tayi fuskanta fes cikin farin cikin halin da taga ya shiga"ina fatan yanzun na tabbatar maka da ƙwarin gwiwa ta? Ta faɗa tana daga mashi gira daya, Juyawa tayi ta shiga takawa a hankali har wani rausaya take yi tsabar farin ciki,sai da takai bakin kofa sannan ta kuma juyowa"Excuses me" Juyowa yayi da rinannun idanun shi ya sauke a kanta,wanda ita kanta sai da gabanta ya faɗi,amma tsabar tsaurin ido irin na Biba sai sakin murmushi tayi tace"you Smell nice "tana gama fadar haka ta kashe mai ido daya tare da barin ɗakin,wanda Allah ne kaɗai yasan irin juriyar da tayi wurin gudanar da wannan aikin,dan zuciyar ta tsabar zillo ji take kamar zai fito ta baki,dan haka tana fitowa dakin bata jira komai ba ta kwasa a guje sai shiyan su,tana shiga daki ta kulle kofa ta saka Key, Jingina tayi da jikin ƙofar ta na sauke numfashi ɗan ji take makar biyo ta zai yi,zamewa tayi ta zauna a wurin tana tunanin makomar ta,idan har yau Kaka ta kore ta a gidan ya makomar aikin ta,me kuma makomar rayuwar ta. Gabadaya he is speechless yama rasa me ya kamata yayi,ji yake makar yayi hawaye tsabar bakin ciki, Yanzun kenan duk tattalin kanshi da yake yi ya tashi a banza kenan?domin ita ce mace ta farko data fara sumbarta shi,tuna ranar daya fara ganin ta tana shan Segret yayi,da kuma kwana uku da suka wuce,ai nan take yaji hanjin cikin shi ya murda,cikin hanzari ya shiga bayi ya fara kwara Amai tamkar zai amayar da hanjin cikin shi. *Bayan Awa Biyu* Gabaɗaya ta tashi hankalin Aunty Atika da ta zo gaishe ta,saboda tana shigowa ta isketa zaune tana faman rusa kuka,kuma tayi lallashin har ta gaji taki faɗa mata meke faruwa, "Dan Allah Kaka ki faɗa min me ke faruwa,wai ko dai rasuwa aka yi? Fyace majina tayi da tissue paper" Yanzun nan ki kira min yaran nan gaba ɗayan su" "Wasu yara kenan kaka? " Ki kira min Mustafa da Abbu Sufyan da Amadu,ke kowama na gidan nan ki kira min shi yanzun nan babba da yaro ina son ganin su" "Too,Allah dai yasa ba wani abu bane" Daukar wayar ta tayi ta shiga kiran su daya bayan daya,waɗanda ma basu kusa duk cawa suka yi ga sunan zuwa. Kafin wani lokaci ahalin gidan babba da yaro sun halarta a wannan falon,kowa hankali a tashe ganin yanda tsohuwa ta tashi hankalin ta,gashi kuma sai kuka take yi, Da yar dai su Goggo da Hajiya Rahama suka samu tayi shiru, Dagowa tayi ta kalle ko wanne su,sai dai bata ga mutum ɗaya ba,"Ina Sirajo? Ta tambaya tana kallon Nurudeen, "Na kira shi yace gashi nan zuwa" Jinjina kai tayi"Salmanu, Zainabu,Hadiza,Khadija, Bilkisu,Amira,ku tashi ku tafi wannan maganar da zan yi ba naku bane,na iyayen ku ne da yanyin ku" Nanfa suka shiga turo baki dan wallahi ba haka suka so ba,amma ba yanda suka iya dole suka fita, Kallon Maijiddarh tayi"Je ki kira min Habiba" Tashi tayi tana ƙoƙarin fita sai gashi ya shigo,sanye yake da farar shadda a jikin shi,yayi matsifar kyau sai kamshi yake zubawa,sai dai ko kaɗan fuskar shi babu fara'a kuma ya ɗan faɗa kaɗan,dan fuskar shi ya nuna ramar da yayi, Sallamah yayi sannan ya gaida iyayen nashi,ya zauna kusa da Ibrahim, Tunda Maijiddarh ta sanar da ita kiran Kaka gabanta ke matsanancin faɗuwa,wanda ta san bai rasa nasaba da rasa aikinta da zata yi, Sai dai ganin irin taron dake falon ne yasa tsoron karuwa,dan haka bayan ta gaida su wadanda zasu amsa suka amsa sannan ta koma gefe ta rakube. Maida kallon ta kan shi tayi"Sirajo "ta kira sunan shi,domin tunda ya shigo ya zauna kanshi a duke yake, Dago idanun shi yayi wanda har yanzun suke a birkice" Na'am "ya amsa da muryar shi da bata fita sosai, " Ya muka yi da kai a game da bikin ka da Maijiddarh? Shiru yayi yana kallon ta yana son ya fahimci inda maganar ta ya dosa"na ce na Amince" "Me yasa tun farko da kaji kana ra'ayin mace baka faɗa amaka aure ba? Wannan karon kam ya rasa ida zaren maganar ya dosa,dan haka shiru yayi bai ce mata komai ba,tunda bai san me take nufi ba, Kuka ta fashe dashi" Na dauke ka tamkar jika na,harma na fifita ka akan sauran,na nuna maka soyayya har na dauki jika ta ina ƙoƙarin baka a matsayin matar auren ka,ba tare dana duba laifin dana ganka kana aikatawa ba,amma shine ba zaka iya riƙe kanka har nan da kwana uku ba sai ka nuna asalin halin naka" Tofa gabaɗaya maganar kaka ya ɗaure ma kowa kai a wannan wurin face wadanda dama suka san da shirin, Abbu ne yace"me kike nufi da kasa riƙe kai Mama,da kuma wani hali na shi? Cikin kuka ta nunashi da hannun ta"gashi nan ku tambaye shi me yake aikatawa a ɓoye da yar mutane" Duk maida kallon su kanshi suka yi,suna jiran jin karin baya ni,sai dai kanshi a kasa yake domin ji yake kamar kanshi na juyawa,yau me ke shirin faruwa dashi, Ammi da tuni ta fara hawaye tace "Suraj kai muke saurare ka faɗa mana Komai" "Ai ba zai iya faɗa ba amma ku duba abinda ya ke aikatawa kenan" Ta fada tana watso wasu hotunan a tsakiyar falon, Gabaɗaya hankalin duk wanda ke cikin falon tashi yayi,domin kuwa tabbas shi ne ba wani ba,nan take kaji salati ya shiga tashi ta ko ina, Tunda ya daga kai ka kalli hotunan saudaya ya maida kai ya dukar,tabbas yanzun kam yasan meke shirin faruwa dashi, Kukan Ammi ne ya karaɗe falon sosai yayin da cikin gunjin kuka ta nufi shi,rike hannun shi tayi ta duka a gaban shi "Suraj!dan Allah ka ce min ba kai bane wannan,kaci musu,ka ce ba kai bane" Ta fada cikin matsanancin kuka da tashin hankali, Dady ne yace "dama ita tsintacciyar mage bata mage,Allah mun gode maka daka nuna mana wannan sirrin nashi kafin haɗa zuri'a dashi,dan haka na janye baka aure yata,ba zan iya haɗa zuri'a da kai ba" Ammi ce ta riƙe hannun Abbu wanda yake zaune yama kasa cewa komai "dan Allah Sufyan kama ɗan Uwan ka bayani,wannan ba halin ɗan mu bane,wannan ba halin Suraj bane" Sai dai ga mamakin ta sai zame hannun shi yayi daga cikin nata"ɗan ki dai,domin kowa yasan cewa Suraj ba ɗa na bane,ƴaƴa na biyu ne daga Shamsuddeen sai Amira,wanda ina da tabbacin Shamsuddeen ba zai taba aikata hakan ba saboda ya haɗa jini da ni,banga laifin wadanda suke cewa basu karɓar dan wani a matsayin nasu ba,saboda karya bata ma nasu tarbiya,ƙila dai ta ɓangaren ubanshi ya dauko irin wannan halin" "Ai matsalar Auren mace mai ɗa kenan,yanzun ga irin ta nan,ka jawo shi a jiki tamkar naka,amma ji abin kunyar da yazo yake aikatawa,mun gode ma Allah da abun ya tsaya a kan masu aiki bai kai ga ya'yan mu mata ba" Cewar Goggo, Kukan Ammi ne ke kara ƙaruwa"Kufa malamai ne,masana Addini,me yasa kuke faɗin haka,me yasa ba za a ji ta bakin shi ba" "Ammi sai dai kawai in baki son ki yarda da abinda ke gabanki na zahiri,amma ni kai na na sha ganin shi ba sau daya ba,ba sau biyu ba" "Amma me yasa baka taɓa sanar da ni ba Shamsuddeen,me yasa? " Saboda koda na faɗa maki ba yarda zaki yi ba Ammi,kamar dai yanzun ma da ga shaida a gabanki amma baki son ki gasgata " "Ai ku ne baku sani ba,amma ni ba abinda ban sani ba,ko yawon tafiye-tafiye da yake yi na karyan yana zuwa wa'azi ai tare yake zuwa da ƴan matan shi,wasu kuma a can yake samu suna hutawar su" Cewar Ibrahim, "Haɗa jini da Bayahude mutum hatsari ne,komai daren daɗewa sai ya nuna maka halin su na Akuyanci,ni banga laifinshi ba tunda Kakar shi bayahudiya ce wa yasan abinda ta aikata lokacin yarinta,kuma shi dama ƙazanta ai jini yake bi"Hajiya Rahama ta faɗa, Jin maganganun su yake har tsakiyar kanshi,suna mai amsa kuwa,ko wace kallama daya da zasu faɗa ji yake yana shiga cikin jikin shi ya bula zuciyar shi ya shige,zafi yake ji,raɗaɗi yake ji sosai,ji yake kamar yace su tsaya ya huta,su tsaya ya sauke numfashi daya tsayamai a kirji kafin su cigaba,sai dai ya kasa koda ɗaga kai ya kalle su,domin mutanen da yayi rayuwa dasu,ya yarda dasu,yake zaune dasu tamkar ahalin shi sune suke fadar munanan kalamar akanshi,harda wanda yake kira da dan uwa kuma yaya,Shamsuddeen,da kuma wanda ya ɗauka a matsayin Kani,Ibrahim, Yana sauraran yanda Ammin shi ke kuka,duk kuma saboda shi. Maijiddarh wacce tunda taji batun fasa aurenta take kuka ta matso wurin kaka,cikin kuka tace"Kaka kema kinsan ina son shi,ba zan iya rayuwa ba idan bashi,dan Allah kar ki bari a fasa wannan auren ina son shi a haka" Jawota Aunty Atika keyi"kina da hankali kuwa,ba ki ganin abinda ke gaban ki,"ta faɗa tana nuna mata hotunan da har yanzun suke watse a tsakar falon"a haka zaki aure shi,mutum irin shi sam bai dace da zuri'ar wannan gidan ba,kuma koda kin aure shi ba fasa halin shi zai yi ba,dan haka ki dawo hankali ki" Aunty Hajjo ce tana mikewa ta kai mata Lafiyayyen mari a fuskar ta......... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *30* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Aunty Hajjo ce tana mikewa ta kai mata lafiyayyen mari a fuskarta, Duk mai da kallo kansu suka yi,sai dai shi uban gaiyar ko inda suke bai kalla ba,sai ma lumshe idanun shi da yayi gabaɗaya, Nuna ta tayi da ɗan yatsa"ai wannan ita ce babbar munafukar,kuma mai laifin,ta yaya ta aikata abu irin haka sannan ta zauna ba tare da tace komai ba" Dafe kumatunta tayi da taji yana mata raɗaɗi dan wallahi har gara marin da ya mata dazu akan wannan na Aunty Hajjo dan katon hannu gare ta, Tattara hotunan tayi ta watso mata shi a jikinta,"tunda shi dan gidan Yahudawa yaki mana bayani ke sai ki mana bayani akan waɗannan " Hajiya Saude ce tace"kika sani ko tursasa ta yayi? Daukar hotunan take cikin tsananin mamaki wanda ya kasa boyuwa,kallon wanda ke hannun ta yi"wannan lokacin da muka je Asibiti ne" Da sauri Ibrahim yace"ba dai zubar da ciki ba" Duk da halin da take ciki hakan bai hana ta hararanshi ba"tir,tir Allah ya kiyaye duk iskanci na ban taba zubar da ciki ba" Salati yawancin mutanen falon suka saka yayin da Kaka da Ammi suke ci gaba da kuka, "Kenan dama kun daɗe kuna iskanci?wannan karon Shamsuddeen ne ya mata tambayar, Dago kai tayi ta kalle shi,sannan ta maida kallon ta kanshi,idanun shi a lumshe suke,sai dai fuskar nan nashi yayi ja, Wannan ne karo na farko da taji ya bala'in bata tausayi,domin duk maganar da suke faɗi da aibantashin da suke yi bai ce masu komai ba,bai kuma ƙarya tasu ba,Ashe shi ba Asalin jikan kaka bane,kuma ba ɗan Abbu bane,to me yasa zasu mai irin wannan fahimtar lokaci ɗaya haka, "Ke muke saurare" Ya kara faɗa, "Ban taɓa Iskanci da shi ba,asalima babu wani abu ɗaya taba shiga tsakani na dashi sai yau,wannan hoton da kuke gani lokacin da suka raka ni Asibiti ne shida Amira duba Mama ta da bata da lafiya" "To ya akayi ya rungume ki a hoton" Shiru tayi kamar mai nazari,tabbas ma nazarin take yi,domin a ranar da abin ya faru taci kwaya bata cikin hankalin ta"ba zan iya tunawa ba" "Magana ta tabbata kenan,a kwai dai abinda ya kaimu" Nuna ɗayan hoton yayi "wannan ma kamar na yau ne? " Eh tabbas na yau ne,sai dai ba laifin sa bane,ni ce da kaina na sumbace shi ba tare da son ranshi ba" Duka Aunty Atika takai mata"sannu manafuka uwar Karuwai,wato kare shi zaki yi,ta yaya zaki sumbace shi ba da son ranshi ba,kalli fa harda rike mata ƙwanƙwaso" Janye ta Hajiya Rahama tayi"rufamin Asiri kar ki haɗa kashi da ita,domin irin su ba'a faɗa dasu sai su shafa maka zufan su na tsiya " "Abu ɗaya kawai nasan zan masa na karshe a matsayina na wanda yake amsa sunan mahaifin shi,shine aura masa wannan yarinyar a yau ta yanda zai zama ishara a gare shi"cewar Abu Sufyan Tunda aka fara maganar nan wannan ne karo na farko daya buɗe baki yayi magana" Kayi haƙuri Abbu amma ban yarda da wannan auren ba" Salati Goggo ta saka"kai kaji min ɗan duniya,bayan ka gama ɓata masu yarinya shine zaka ce ba zaka aure ta ba,ai kuwa baka isa ba" "Ai dama irin su haka suke,anci moriyar ganga za'a yada koren ta" A zabure ita ma tace"wallahi ban amince ba,ni ba zan aure shi ba," Buge mata baki Aunty Atika tayi"munafuka yi mana shiru" Kallon Ammi Kaka tayi"idanun ɗan ki ya buɗe sosai yanzun,har tsoron yi masa magana nake yi,dan haka ina ga ƙila ke ki nada sauran daraja a idanun shi ki masa magana ko zai amince" Kafin tace komai sai ji suka yi yace "na amince" Ihu ta saka "wallahi ban amince ba,ni dai ba na son shi tafiya ta ma zan yi yanzun" Ta faɗa tana ƙoƙarin mikewa, Aunty Hajjo ta jawota kiiiii ta cillata dakin kaka ta kulle ƙofa "tunda har kwadayin ku yaja maku to sai dai ku karasa da juna" "So nake a ɗaura auren daganan zuwa sallar Magariba,zuwa lokacin Iyayen yarinyar sun iso an masu bayani nasan idan sun ji komai ba zasu ki yarda ba" Ba tare da yace masu komai ba ya mike ya bar falon,kamar yanda suma basu ce mai komai ba sai bakaken maganganu da wasu a ciki ke jifan shi dasu, Yana fitowa bai koma dakin shi ba da kyar ya samu yakai kanshi wurin Parking ya buɗe mota ya shiga, Ganin hakan ne yasa daya daga cikin direbobin gidan yazo ya shiga yana tambayar shi ina zai kai shi, Da kyar ya iya furta kalmar "gida" Ya gane inda yake nufi dan haka jan motar yayi suka bar gidan, Yayin da yake jin numfashin shi kamar zai bar gangan jikin shi. Kuka ta fashe dashi tana zama anan bakin kofa,to me ke shirin faruwa kuma a rayuwar ta a karo na biyu,Aure! Aure fa!dama abinda VIP ke nufi kenan da yace ta je tayi kissing din shi kuma ta bar kofa a buɗe, To waye ya shigo ya ɗauke su hoto,dama ya shirya ma hakan kenan,amma ai baya cikin tsarin aikin su,baya cikin yarjejeniyar su, Cikin sauri ta lalubo number shi a wayar ta tashiga kiran shi,sai da ta kira sau takwas ba tare da kakkautawa ba kafin a ɗauka, Kuka ta fashe dashi"me haka! Me haka! Wannan fa baya cikin yarjejeniyar mu,kokarin aura min shi ake yi,gaskiya a canja wani hanyar " Daga ɗayan bangaren yace"kina da wata hanyar ne daya fi wannan,? Shiru tayi"amma kai ai ba zaka rasa ba" "Haka ne,shi yasa na zabar maki da wannan,domin shine hanya mafi sauki da zai kaiki ga kammala wannan aikin cikin kankanin lokaci" "To auren fa? " Biba me yasa kike abu kamar ba wayayyiya ba,auren ai na baki ne tunda baki son shi,da zaran kin kammala aiki da kaina zansa ya sake ki" "Ni dai ba na son wannan hanyar,domin ka sani a rayuwata babu abunda na tsana sama da Aure,ta sanadin aure komai daya faru dani ya faru,ta sanadin wannan kalmar na gano abinda bai dace nasan dashi ba har abada,idan sai da aure zan cika wannan aikin to na ajiye,na janye" Wani irin shegen dariya ya fashe dashi,irin wanda da ka jishi kasan irin na rashin imani ne"dama nasan irin haka na iya faruwa,shi yasa na shirya ma wannan ranar Biba,ina ga har yanzun ba kisan da wanda kike aiki ba,ai tunda kika fara aiki dole ne saikin ƙarasa,ko kina so ko baki so,bari na tuna maki,ina kika bar ƴar uwar ki Ummita,"ya fada yana ƙara sakin wani dariyar, Gabanta ne ya faɗi "me kake nufi,ina Ummita? " Karki damu,tana hannu na cikin ƙoshin lafiya a yanzun,amma ban dai san daga nan zuwa nan gaba ba idan kika cimin musu,kina iya rasa ta,domin a wurina hakan ba komai bane,dan haka rayuwar ƴar Uwar ki yana hannun ki,idan kin ga dama ki yi wasa dashi idan kuma kinga dama ki cece ta tahanyar kammala aikin dana saka ki" Idan ranta yayi baki to ya baci"idan har wani abu ya samu Ummita ba zan taba barin ka,sai na binciko ko kai waye naga bayan ka " "A'i zata zo yanzun domin mun riga mun shirya wadanda zasu tsaya a matsayin iyayen ki,idan kinga dama ki nuna abinda zai sa a zarge ki,Gara ki kwantar da hankalin ki kiyi komai cikin natsuwa domin nasan babu abinda zaki iya" Yana gama faɗar haka ya kashe wayar, Ihu tayi na bakin ciki tana haɗa wayar da bango,nan take kuwa ya tsarwatse, Dukawa tayi a wurin ta shiga rusa kuka ko zata ji sanyi a zuciyar ta,wannan wani irin ƙaddara ce haka,idan har ta rasa Ummita bata san Me kuma ya rage tayi ba a rayuwata ta,ina zata samu mafita,wani irin tunani ya kamata tayi, Kuka take sosai na rashin sanin mafita. A falo kuwa Kaka ce ta bada number A'i aka kira ta Goggo tai mata bayanin komai,ita ko harda kuka,tace masu yanzun zata sanar na mahaifinta,kuma komai yazo da sauƙi tunda yayan mahaifin Biba aman Kano yake anan kuma yake sa'ar shi, Daganan ne taro ya watse inda mazan suka nufe masallaci dan lokacin sallah Azahar yayi, Mata kuma kowacce ta koma shiyan su. Ko da A'i ta iso gidan Ana daf da kiran sallah la'asar dan ta bata lokaci ne wurin koya ma wadanda suka yi haya yanda zasu yi idan sun zo nan ɗin, Cikin mutumci suka gaisa da Kaka kafin ta nuna Mata dakin Nafisa da Biba ta koma, Ko da ta shiga a kwance ta same ta idanunta a buɗe tana kallon ƙofa, Ganin shigowar A'i ne yasa ta tashi da sauri tazo ta rungume ta tana fashewa da kuka "A'i dan Allah ki taimake ni! Ki taimaki rayuwa ta,ya ɗauki Ummita,idan wani abu ya same ta ba zan iya yafe ma kaina ba! Hannu ta saka mata a baki alamun tayi shiru,zaunar da ita bakin gado tayi,sannan ta maida kofa ta kulle, wayarta ta buɗe ta cire batir sannan ta zauna" Ya saka tiraka a waya ta duk abunda muka faɗa yana iya ji" Share mata hawaye tayi"nasan haka zai fara,kuma abinda yafi haka ma yana iya faruwa idan shi ne," "Me kike nufi A'i" "Shi mutum ne mai matukar hatsari,yanada wayau sosai da basira" "Ta yaya zan iya taimakon ƴar uwa ta,ki taimaka min" "Ki yi hakuri Biba,ban San ta wace hanya zan taimaka maki ba,amma kuma bari na faɗa maki abunda baki sani ba,kila nan gaba hakan na iya taimakon ki" Rike mata hannu tayi"ki faɗamin koma menene" "Bake kadai ce kika fara aiki a wannan gidan ba,kafin ke a kwai mutum shida,acikin su babu wacce tayi nisan da kika yi suke barin aiki,sai dai da sun fito da kwana biyu ake niman su a rasa,sai bayan wasu ƴan ƙwanaki ake tsintar gawar su a wuri mabanbanta" Zaro ido tayi cike da tsoro"me hakan ke nufi? "Kashe su yake yi saboda suntsan komai,kuma kema ina mai tabbatar maki idan har baki kammala wannan aikin ba zai iya kashe ki,haka kuma idan har kika kammala masa aikin shima ba barin ki zai yi ba" A tsorace tace"to me ya kamata nayi,idan na kammala a kashe ni idan ban kammala ba akashe ni,to me zan yi kenan na tsira,ba na son na mutu a hannun wani? "Hanya daya ce kawai zaki iya bi domin ceton kanki dana ƴar Uwar ki" "Dan Allah ki taimaka ki faɗa min A'i" Ajiyar zuciya ta sauke "saboda ina ƙaunar ki tun ganin farko shi yasa na yanke shawarar taimaka maki,sai dai ban sani ba ko abinda zan faɗa haka ne,? Sauke numfashi ta kuma yi" Ki yarda ki aure Suraj,domin shi kadai ne wanda zai iya taimaka maki,shi kadai ne wanda yasan Asalin waye suke takun saƙa dashi,domin ni kai na bansan waye VIP ba,amma ina da tabbaci a kan shi ya sani, Ko ta halin yaya kar ki taba dauko abinda ake buƙata,domin da zaran kin miƙa naki ya ƙare,haka kuma kar ki taɓa kin daukowa,kar ki bari ko ta halin yaya VIP ya zargi wani abu,ki ci gaba da nuna kina kan aiki, Sannan akwai wani gagarumin matsala da zai taso ma Suraj,wanda ba lallai bane ya rayu,abu ɗaya kawai nake son na sanar dake,shine ko ta halin yaya kisan yanda zaki taimaka masa ya rayu,domin fa idan kika bari suka samu nasarar kashe shi to lallai zasu samu damar cimma manufarsu sannan kema su gama dake ko kina so ko baki so, Dan haka daga yanzun sai ki fara tunanin ta hanyar da zaki tseratar da rayuwa uku" Tunda uwata ta haihota duniya bata taba shiga tashin hankali da ruɗani ba irin wannan "A'i wani irin matsala ne wannan da zai taso" "Gaskiya ba na ce ba,domin bansan me suke shiryawa ba,amma nasan koma dai menene to ba ƙarami bane,zai iya kaiwa matakin da za'a rasa rayuwa" Ganin yanda ta shiga damuwa ne yasa ta dafa kafadar ta"ki kwantar da hankalin ki,na tabbatar idan har kika natsu,kika kuma bi komai daki_daki zaki iya cin nasara " "A'a matakin cin nasara ta sufili 0 Zero ne,ba ni da kwarin gwiwa da jarumta" "Idan kika tuna mahimmanci rayuwar ki data ƴar Uwar ki su zasu kasance maki kwarin gwiwa" Ajiyar zuciya ta sauke,amma Allah ya gani gabaɗaya ƙwaƙwalwar ta ya toshe,ta yaya zata iya fuskantar wannan Ustazun ma,ta san yanzun haka duk inda yake ji yake kanar yaga bayanta, "Ni zan wuce amma zuwa anjima zan dawo kafin a ɗaura auren" Jinjina kai kawai tayi,dan ba zata iya ce mata komai ba,tana kallo har ta fita ta jawo mata ƙofar..... *yanzun aka fara* *Jiddarh 🦚ce* 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *31* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Tun daga farkon shigarsu layin Sultan Road Jami'an tsaro ne ta ko ina wanda hakan ne zai tabbatar maka da unguwar bata ƙananan yara ba ce, Tunda Direban daya dauko shi ya shigo layin Jami'an ke tsare shi domin duba wanda ya dauko,domin da mota daya ne suke,kuma sun san duk wanda yake layin da kuma number motar su,da ya tsaya ya sauke glass sun hango wanda ke Hakimce a cikin motar suke Sara mai su basu hanya, A bakin wani haɗaɗɗen bakin Get din wani gida ya tsaya,wanda ni kaina da badan nasan ba yanda za'ayi a ajiye gidan kwali iska bai dauke ba da nace wannan gidan ba hannu ya gina shi ba, Gani nayi Get din ya buɗe da kanshi kafin direban ya shiga da motar ciki,nan ma Get din ne ya kulle kanshi, Wurin Parking motoci ya parkar inda a ƙalla a wurin a kwai motoci sama da guda shida wanda in zai tafi wa'azin dashi suke tafiya,a rufe motocin suke daga dukkan alamu ma an jima ba'a yi amfani dasu ba, Motar su na gama tsayawa wasu mutane su huɗu suka zo suka tsaya suna jiran fitowar sa,yayinda daya daga cikin su ya buɗe ƙofar motar, Daga dukkan alamu masu tsaron gidan ne sai dai dukkanin su karfafa ne a koshe suke, "Yallabai mun iso" Cewar Direban shi, Buɗe Lumsassun idanun nashi yayi wadanda basu da daɗin kallo ko kaɗan, Sannan ya zuro ƙafar shi waje,sai da ya dauki sekon goma sannan ya fito gabaɗaya, Duk rusunar da kai suka yi suka shiga gaishe shi cikin girmamawa, Sai dai ko ɗaga hannun daya saba masu idan ba yajin yin magana basu samu ba,duk randa kuma ƴan arzikin ke kai zai tsaya ya basu hannun su gaisa yana tambayar ya suke, Amma na yau kam da ban ne, Dereban ne ya mike ma daya daga cikin wadanda ke tsaye wayoyin shi daya bari a mota, Amsa yayi ya mika ma na kusa dashi"Bala karɓa ka shigar ma maigida dashi,ka kuma shirya masa abinci,naga kamar yau a gajiye yake,sai dai kabi a hankali karka cika kwaranniya dan yana buƙatar hutu da natsuwa" Wanda aka kira da Bala ne ya amsa da"an gama sarkin gida" Cikin sauri ya bi bayan shugaban nasu wanda tuni har ya kusa isa kofar falon kasancewar a hankali yake takawa, Yana isa naga kofar ya buɗe da kanshi sannan suka shiga ya kulle, Ko ina a gyare yake tsaf dashi sai kamshi ke tashi ta ko ina,haka kuma idan ana maganar tsaruwa da kayan Alatu to babu abinda babu na more rayuwa na zamani acikin falon, Haurawa gidan saman yayi ya buɗe wani daki,ba tare da ya kunna wutar dakin ba ya faɗa kan gado yayi ruf da ciki,numfashi kawai yake fitarwa da sauri_sauri, Ganin bai kunna wutar dakin ba kuma ya kwanta ne yasa ya ajiye masa wayoyin saman durowan dake bakin ƙofa,dan in yace zai shiga ba ganin gabanshi zai yi ba, Fitowa yayi daga falon gabaɗaya,wurin Sarkin Gida ya nufa,dan sunan da suke kiran shi dashi kenan saboda shi ke kula da harkan komai na gidan tun zaman iyayen Suraj har zuwa yau shi yasa suke kiran shi da haka, Zama yayi kusa da shi "ina ga fa akwai Matsala" "Na me kenan,ya kamata kayi ka haɗa abinci" "Bai da amfani domin ko nayi ba iya ci zai yi ba,kai baka lura da halin da yake ciki bane,kuma wutar dakin a kashe yake ya kwanta," Dan shiru yayi kafin yace"bari na kira Sir Farhan " "Gaskiya kam,dan ina ga ba lafiya" Nan take kuwa ya dauki waya ya kira wanda suka kira da Sir Farhan,ban dai san Me ya faɗa masa ba ya dai ce"ok sir"sannan ya sauke wayar, "Kaje kayi girki amma ka Girka abu mai sauƙi ga shi nan zuwa," Tashi yayi ya koma kicin cike da tunanin meke damun Ogan nasu,yasan shi mutum ne mai matukar sauƙin kai da son mutane,shi mutum ne mai taimako duk da aiki suke masa amma yanda yake biyan su yafi karfin kudin aikin su,shi yasa suke matukar jin daɗi zama dashi duk da yana ɗaukar lokaci kafin ya zo,yawancin lokaci a wata sau daya yake zuwa ya duba su ya wuce,wani lokaci kuma idan ya buƙaci hutu to zai yi kwana biyu anan ɗin. Bayan minti talatin sai ga wani mota ya shigo gidan, Tashi sarkin gida yayi ya nufe inda yake ɗan tun shigowar shi layin sai da Security suka kira domin tabbatar da ko an san da zuwan shi, Kyakkyawan saurayi ne shima matashi,zasu zo tsara da Suraj din, Cikin sauri ya fito motar yana tambayan sarkin gida"ina yake? "Yana dakin sama" Bai ce komai ba ya nufi falon,haurawa saman yayi yana shiga ya kunna wutar dakin, Karasa yayi in da yake kwance yana kiran sunan shi"Suraj,Suraj "sai dai ina bai dago ba bai kuma amsa ba, Dafa shi yayi,sai dai ji yayi jikin shi yayi zafi gau dan har yana iya ji a hannun shi,cikin sauri ya juyo dashi,yana ƙara kiran sunan shi, Sai dai a hankali yake buɗe ido shima ba sosai ba, Kyara mashi kwanciya yayi da sauri ya fito dakin ya nufi motar shi,kayan aiki ya kwaso ya dawo a lokacin ya tadda yana ta faman kwara amai, Shi da Bala suka taimaka mai sannan ya masa Allurai ya daura masa drip, Ganin Bala ya fita ne yasa ya kira sunan shi"Suraj,kana jina,in kana jina ka buɗe ido" Buɗe lumsassun idanun shi yayi wadanda suke nuna halin da zuciyar shi ke ciki, "Meke maka ciyo yanzun? A hankali ya motsa Labbanshi" I am fine" "Ka tabbata? Nan ma da ido ya amsa mashi,kafin yace " Were is my Phone? Da sauri ya tashi ya dauko mashi, Amsa yayi ya shigo wurin kira,sai dai video called ya kira,kuma number bata Nijeriya bane, Ringin biyu aka ɗauka,sai dai wani Baturen mutum na gani fuskarshi dauke da murmushi,ya kira sunan Suraj din, Gaisawa suka yi da harshen Turanci,kafin naji yana faɗin"we're is Grandma? "Do you want to see her? " Yes " She is in examination room,give me five minutes " "Is there any progress? Ya tambaya, Ajiyar zuciya mutumin ya sauke" We hope so this time,and don't worry everything we'll be all right dear " "Thank you sir" "I'm sure your grandma will be very proud of you Suraj,and don't forget anything you're so dear to her" Wanna ne karon farko tun faruwar wannan lamarin da naga ya dan saki murmushi kaɗan wanda idan baka lura bane ba lallai ka gane anyi shi ba"Thank you Doctor "daga nan ya sauke wayar, " Akwai abinda baka faɗa min ba,me ke damun ka? Cewar Farhan, "Im ok" "No,you not" Kafin yayi magana ne wayar shi ya shiga kara,sai dai number Dazu ne na kasar waje kuma babu suna dan kamar ba'a yi seving din shi ba, Video call din ne,dan haka ɗauka yayi,sai dai ba fuskar wannan baturen bane yanzun,wani daki ne lafiyayye irin na ƴan gatan majinyata domin daga dukkan alamu a Asibiti ne, Wata tsohuwa ce kwance a saman gadon,duk da kasancewar tsufa ya kamata amma hakan bai ɓoye kyawun da take dashi ba,gata a kwance tamkar kace ta tashi,sai dai kuma tana cikin yanayi ne na doguwar suma, Gani nayi ya tsura mata ido,kafin wani lokaci kuma hawaye ya fara saukowa daga ramin idanun shi,wanda ya kyale su suna zuba ba tare daya goge ba, A hankali bakin shi ke motsi kafin ya furta"Grandma " Dafa hannun shi Farhan yayi"she will be ok In sha Allah " Hannu yasa ya share hawaye idunshi "when?when will she wakeup,?yanzun shekara goma sha ɗaya kenan,har yanzu bata tashi ba" Cikin tsananin tausayi ya kara damke hannun nashi,domin koma menene ya saka shi a cikin wannan yanayin ba kaɗan ba ne,yasan ada yakan yi kuka,amma yanzun ya daina,ba zai iya tuna zanar da ya ganshi haka ba"na San kasan Allah ya kan jarabci bayinsa ta hanyoyi masu yawa ina fata zaka ci wannan jarabawar ta hanyar haƙuri da juriya " Kashe wayar yayi ya ajiye a gefen shi sannan ya dauki dayan,wurin Massege ya shiga ya buɗe sannan ya mika ma Farhan, Amsa yayi yana karanta abin da ke rubuce:i hope you like my present: "Me haka ke nufi? Ya tambaya Lumshe ido yayi ya kara buɗewa tare da furzar da iska daga bakin shi" Yau za'a Daura min Aure"ya karasa faɗa can kasan makoshi, zaro ido yayi sai kuma ya ɗan saka dariyar zulaya "wasa dai kake min? Ganin bai ce masa komai ba,ya kuma cewa" Hi I know you ar joking right? Kauda kai tayi, Hakan ya tabbatar masa ba wasa yake ba"da gaske"ya faɗa da karfi wannan karon "how?when? Where? Who is she? Matsowa inda yayi yake " Dan Allah Suraj ka faɗa min meke faruwa,kasa kaina ya kulle duk ban fahimta ba" Juyowa yayi yana fuskantar shi"idan ka natsu sai na faɗa maka komai " Numfashi ya shiga ja yana busarwa sai da yayi haka sau uku sannan yace"na natsu yanzun faɗa min," "Fassarar abinda wasikar ke nufi,ya samu nasara a kaina wannan karon" "Ta yaya suka samu nasarar ka Suraj,nasan kai mai matukar kiyayewa ne, Allah yasa basu da haɗi da wannan auren daka faɗa? " Shine ma babban matsalar Farhan,wannan karon da hatsabibiyar yarinya na haɗu,ba kamar waɗancan sauran take ba,tana shan Segret ba kaɗan ba,abinda na fi tsana a rayuwata,tsabar saurin ido irin nata yau da safe yarinyar nan har daki na ta biyo ni,and do you no what she did? "What? Ya tambaya, Shafa fuskar shi yayi yana busar da iska"she kiss me" Duk da ganin halin tsananin damuwa da aminin shi ke ciki,da kuma shima damuwar da yake ciki,hakan bai hana shi bushewa da dariya ba,har yana buga katifa,saboda yanda ya faɗi kalmar She Kiss me kamar zai fashe da kuka, Tsabar takaici tsaki kawai yaja yana kauda kai. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *32* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Tsabar takaici tsaki yaja yana kauda kai, Ganin kamar ranshi ya baci ne yasa ya saisaita kanshi "Sorry ba wai ina nufin yin dariya ba ne,gaskiya bata yau ta ba,yanzun shi kenan ta rage maka daraja ta maida kai karamin bazawari" Da sauri ya juya "kamar ya? Haɗiye dariyar shi yayi" First Kiss,first Night,to ta kwace maka first Kiss dinga,kaga ko a tarihi idan aka ce waye ka fara kissing sai dai c..... Cikin jin haushi ya dauki filo ya wurga mashi,a zuciyar shi yana tsine ma wannan Kiss din,domin kuwa ta cuce shi, "Faɗa min ya akayi daga yin Kiss da karfe goma na safe sai kuma batun Daura aure,ina ita mejiddarh,? "Tunda ta fita daga dakina bansan me ya faruba,sai kira daga Kaka,daga nan ne komai ya canja," Nan ya shiga bashi labarin duk abinda ya faru har zuwan shi nan. "Amma Suraj a ganin ka waye ya dauki wannan hoton sannan har ya kai ma Kaka,kenan hakan na nufin bibiyar ku ake kuma wannan shiryayyen lamari ne? " Tun daga farko shiryayye ne,sannan sanin waye mai daukar hoton bashi bane mai muhimmanci,daga shi mai daukar har wanda ya kai ma Kaka dukkan su yan aike ne,matsalar anan shine suna na da ya bata a gidan,ya cire duk wata yardar dake tsakanina da mutanen da nake kallo a matsayin nawa,ya saka mummunar fahimta a tsakanin mu,abinda ke min zafi Ammi! Idan da Ace Pa yana raye,ko kuma Grandma tana nan da hakan ba zai faruba,da ba akai wannan matakin ba,nima da ina da nawa ahalin, Wani lokaci Farhan mutane suna da mantuwa,Amma babu komai lokaci ne zai tunatar dasu komai " Dafa kafadarsa yayi"juriya shine ya kamace ka,ina fata ba zaka taɓa nuna gazawarka a idanun magauta ba? Dan murmushi yayi"cikin juriya nake tsayin shekaru goma sha ɗaya,idan har zan iya z Durewa na tsayin wannan lokacin me zai hana ni juriya har yanzun,na dai san duk abunda yake ma ba zai taba samu ba," "Hakan na nufin kasan waye kenan? To me yasa baza kaishi kasa ba lokaci ɗaya" Wannan karon mamaki ne ya kama ni ganin irin murmushin daya saki,duk tsauri irin na mayunwacin Zaki,idan har zai yi farautar habin harin shi koda yana gabanshi dole ne sai ya fara dukar da kai kafin yakai cafka," "Kana nufin.. Katse shi yayi" Lokaci bai yi ba" "To yanzun ya zaka yi da wannan auren? Kallon Agogon dakin yayi wanda ya nuna ƙarfe biyar da rabi na yamma" Bayan sallah Magrib za'a daura,sai dai bansan yanda suka tsara abin ba,sai dai koma me suka shirya I will accept it,domin hakan ma wani mataki ne na nasara ta wanda su basu san haka ba amma ni na sani" Cikin mamakin abokin nasa yace"me kake nufi da matakin nasarar ka,bayan kace baka son auren kuma ba sonta kake ba,ama ajiye batun so gefe,kasan ita din yar aikin makiyanka ce,ta yaya samunta zai zamar maka matakin nasara" Dan karamin dariya yayi duk da bai fito ba haƙoran shi ne kawai suka bai yana "ka sa ido ka gani,domin yanzun ne Asalin wasan zai fara" Shiru kawai yayi domin gabaɗaya ya rasa gane ina ya dosa,Sallamar Bala ne ya katse su, Shigowa yayi da tire dauke da bowl na abinci da chokali sai goran ruwa da kofi, Amsa Farhan yayi ya mai godiya sannan ya fita, "Yaushe ruwan zai ƙare?ya tambaya. " Zai kai ƙarfe takwas" "Idan lokacin sallah yayi ka cire min idan mun dawo ɗaurin aure sai ka maida min" Kallon mamaki yake mai"zaka je ne? Bai bashi amsa ba sai ma cin abinci daya fara. _________ Kaka ce ta shigo dakin rike da wani leda mai dan girma a hannun ta,ajiyewa tayi a gefen ta tana zama kusa da ita, Ganin bata da niyar yi mata magana ne yasa tace"Kinji haushin hukuncin da muka yanke ne? Dago idanun ta da suka kumbura tayi tare da girgiza kai"kawai dai auren ne bana so,dama ace korata kika yi da hakan yafi min" Rike mata hannu tayi"na yarda da wannan hukuncin ne badan in cutar dake ba,na tabbatar da cewa wata rana sai kin yi alfahari da wannan hukun namu" Shiru kawai tayi bata ce mata komai ba, Mika mata ledar tayi"ki saka wannan kayan domin ƴan awoyi suka rage a ɗaura auren,sannan mahaifiyar ki ta iso munyi magana da A'i ba baza su jimaba zasu iso" "Na gode" "Allah ya Albarkaci rayuwar ki" Dole ne idan har ina son kaiwa karshe na kwantar da hankali nabi komai a hankali, sai dai kuma hankalin nawa yaki kwanciya saboda rashin sanin wani hali Ummita ke ciki,ƙara share hawayen daya sauko mata tayi,wanda hakan ya jawo idanun suka kumbura sosai, Da yar ta iya lallashin zuciyar ta sannan ta sauki lafiyayyen Les din da yaji aiki ta saka,a cikin kayan harda ƴan kunni da Sarkar wuya na zinari,sakawa tayi da takalmim,kayan ruwan Orange color ne da fari,shi yasa kayan ya bala'in yi mata yau,duk da yanda fuskantar babu ko da digon kwalliya amma ta fito yanda kasan ba ita ba,dan dinkin riga da zani ne Bubu irin na yarbawa wanda ake daura zanin a ciki,ɗaurin ɗan kwalin kuma data daura sai ta sauko da suman kanta ta baya,wanda har ya kusa gadon bayanta, Wannan ne karo na farko da tayi shiga mai kyau mai kuma ma'ana tunda ta zo gida, Zura ƙafarta tayi a takalmin wanda yake flat shoe ne fari da kuma madaidaicin mayafi fari,shi kuma a gefen kafardar ta na hagu ta rataya shi,sai turaren data feshe kanta dashi tun daga sama har katsa, Jin yanda aka buɗe ƙofar aka shigo sannan aka maida aka kulle ne yasa ta dago kanta tana kallon ta, Zama tayi kusa da ita cikin sauri ta ce "ina fatan ki zama mai wayau mai kuma rike sirrikan kanki,karki taɓa yarda da kowa koma waye,ki yi taka tsantsan sosai domin ta ko'ina za'a saka ido a kanku" Jin an murda kofar ana ƙoƙarin shigowa ne yasa da sauri ta canja magana"haba ke kuwa Biba wani irin kuka ne haka kika yi,kinga yanda idanun ki suka kunbura kuwa" Wasu mata ne su biyu suka shigo ɗakin,mikewa tayi tana jawo wata acikin su"yauwa Maman Biba kinga yanda idanun ta suka koma kuwa " Kallon matar da aka kira da Maman Biba tayi"Da kaganta kaga zubin yan duniya,sai dai ba tada wayewa sosai,tana isowa rungume Biba tayi"Haka kuma lamari ya kansance Habibatu,me yasa zaki aikata irin haka"ta faɗa tana saka kukan munafirci, Ganin Goggo ta zo tayi tsaye ne yasa dole ta kakaro hawaye"Mama ki yi haƙuri ki yafe min,duk laifi na ne" Ita dayar da suka taho tare nan ta shiga sharan hawaye harda fyace majina, Ganin Goggo ta wuce ne yasa ta saki matar da sauri dan warin zufa take yi irin kuma mai ƙarnin nan, Dan matsawa baya tayi kaɗan tana bata fuska, "Ki ce min Biba ko Habiba,amma banda Habibatu" Washe baki tayi"in dai baki so ai an gama,ni inama ni aka ba wannan aikin in auri dan gidan masu kuɗi ai da kullun da namar kaza zan dinga brush "ta karasa faɗa suna saka dariya. Kaka ce ta saka Nafisa ta kawo masu lafiyayyen Abinci da ta saka aka shirya masu,nan suka shiga ci hannu baka hannu ƙwarya, Jin Ana kiran sallah Magrib ne yasa gabanta faduwa,har aka idar da sallah tana zaune,ba ta iya tashi ta dauro Alwallah tayi sallah ba,ko a sujada kuka take yi,domin wannan lamarin so yake yafi karfin zuciyar ta,a tsorace take,ido rufe take niman wanda zata iya faɗa ma halin da take ciki, Ta idar tana saman darduma sai ga A'i ta kuma shigowa tana rangaɗa guɗa tare da faɗin "An ɗaura,An ɗaura" Maida kanta tayi ta haɗa da gwiwar ta tana karanto duk wani Addu'a da yazo bakin ta,jin irin yanda gabanta ke tsananin faɗuwa,abubuwan da suka faru da ita a baya suna ƙoƙarin dawo mata sabo a cikin ƙwaƙwalwar ta. __________Acan waje kuwa wurin ɗaurin aure.. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *33* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* A masallaci tun ganin lokacin kiran sallah ya kusa Abbu ya kira shi a waya, Yana ɗauka yace"sai na tuna maka da batun ɗaurin aure " Cikin sanyi murya yace"zan zo yanzun nan Abbu" Ba tare da yace komai ba kuma ya kashe wayar,duk da yanda yaji muryar shi wani iri abin ya ɗan taɓa zuciyar shi,dan daga dukkan alamu kamar bai da lafiya,yana son Suraj sosai,domin yaro ne mai matukar biyayya,tunda suke dashi bai taɓa saɓa ma umurnin shi ba,ko yaci masa musu akan wani,kawai dai yau he is very disappointed akan abinda ya aikata,kuma dole ne sai ya nuna mai kuskuren shi a kan haka. Kallon Farhan yayi dake ƙoƙarin cire mashi Drip,"ka fitar min da kayan da zan saka" "An gama ran Ango ya daɗe" Ba tare da yace mai komai ba ya tashi ya shiga banɗaki dan yayi wanka,yana gamawa ya dauro Alwallah gabaɗaya sannan ya fito, Kujeran madubi ya ja ya zauna dan baya jin karfin jikin shi,mai ya shafa kawai sai turaren da ya feshe jikinsa dashi, Kallon kayan dake ajiye saman gado yayi,ƙaramin tsaki yaja sannan ya buɗe durowa ta jawo wani farin Jallabi da farin hula ya saka,sai wani dan karamin Carbi daya riƙe a hannun shi, Tsarki ya tabbata ga Allah,domin yanda kasan wani Balarabe haka ya fito, Tunda yake saukowa daga sama ya buɗe baki yana kallon shi cikin mamaki,ganin yana ƙoƙarin wucewa ba tare da yace mai komai bane yasa da sauri ya tashi ya bi bayan shi "me haka zan gani Suraj,ina kayan dana fito maka dashi? "Basu min ba" Ya bashi amsa a takaice, Nuna shi yayi"ta ya za'a yi kaje ɗaurin auren ka da wannan kayan sai kace mai shirin zuwa bada sallah" Buɗe mota tayi ya zauna a gidan baya ya jawo kofa ya kulle, "To waye zai ja motar ba dai ni ba,ina matsayin abokin ango" Ba tare da yace mai komai ba ya buɗe motar ya fito,kai tsaye motar Farhan dake parke a gefe ya kuma buɗe gidan baya ya shige, Dafe kai yayi yana kallon motar,shi dai duk yanda kayi dashi sai ya bullo maka ta wata hanyar, Buɗe wurin zaman direba yayi ya zauna ya ja motar yana gunguni, Lumshe idanun shi yayi yana jin zuciyar shi na faman yi mashi zafi,har ɓalle idan ya tuna da ita da kuma abinda ta mai,idan har yarinya is capable of doing something like that,to me ne ba zata iya aikatawa ba,wama ya sani ko maza nawa ta haɗa baki dasu irin haka, Tuna hakan kuma da yayi ne yasa yaji zuciyar sa na tashi sosai,da sauri ya dafa Farhan "tsaya" Dan juyowa yayi"me kace" "Ka tsayar da mota" Samun gefen hanya yayi ya parker, Da sauri ya fito ya tsaya a gefe ya shiga Kwara Amai, Sai abun yayi kamar zai tsaya,amma da yayi tunanin Kiss din,nan take Aman ke dawowa har ta hanci yi yake yi, Shi kanshi Farhan abin ya fara damun shi,goran ruwa ya dauko masa ya kuskure baki tare da wanke fuska,sannan ya taimaka masa ya shiga mota, Kallon shi yayi zazzaɓin ƴan awoyi amma duk ya fada,fuskar shi yayi ja idan ka sanshi to zaka shaida bai da lafiya dan ko a muryarsa kana iya shaida hakan "Muje Asibiti? Jirjiza kai yayi kaɗan yana lumshe ido, " Jikin ka ba ƙarfi,kana bukatar Medical attention " "Kai ni masallaci" Yana ƙoƙarin kara yin magana ne wayarsa da ke ta kara tun dazu bai sani ba ya kara daukar kara, Kallon wayar yake yi da sunan Ammi ya fito baro_baro, Sai da yaja numfashi ya busar yana kauda kai kamar ba zai ɗauka ba sannan ya danna wurin amsawa, Sallamah tayi ya amsa "kazo ina son ganin ka" "Idan an fito masallaci zan shigo" "Ok" Kashe wayar kawai yayi, Suna isa lokacin har an fara kiraye-kirayen sallah,mutane nata Daura Alwallah,dan haka masallaci suka shiga,kusa da Abbu dake jan carbi ya samu wuri ya zauna kafin a tayar da sallar, Abbu ya bada sallah har aka idar,bayan Addu'o'i ne ya sanar da daurin aure,kafin aka shiga fitowa da kwandunan goro Sweet da Dabino, Kowa mamaki ya shiga yi irin wannan daurin aure na Ustaz Suraj,kafin kace me nan take mutanen da suka hallaci sallah a wannan masallacin sun fara Daura magana a social media,cikin kankanin lokaci magana ya zagaye gari wasu su ƙaryata wasu kuma su yarda, Ana gama daurin aure dady ya dafa Kafadarsa ba tare da yace komai ba ya fita daga masallacin, Ganin Abbu na magana da mutane yasa ya zame jiki ya bar masallacin ba tare da ya koma ko takan Farhan ba yayi shigewar shi cikin gida, A hankali yake takawo hannun shi dafe da kanshi dake matukar Sara mashi, Ji yayi an riƙo shi ta baya wanda hakan ne yasa ya juyo "me yasa zaka amince ka aure ta bayan kasan ina sonta,me yasa zaka dinga cin amana ta ka zagaya kana bata mata rayuwa,sam bata dace da mutum irin ka ba,ba zan kyale ka ba,sai na saka ka sake ta da bakin ka na aure ta" Ganin bai da niyar ce masa komai ne yasa cikin jin haushi kuma ya sake shi ya wuce, Shi bai ma sani ba idan da akwai ta yanda zai juya komai da ba'a kawo wannan matakin ba,duk da kalaman Nurudeen ɗin ya bashi mamaki jin yana sonta,karamin tsaki yaja kawai tare da nufar shiyan Ammi, Zama yayi kawai a kan kushin yana jan carbi ba tare da ya shiga ciki ba, Amira ce ta fito ta ganshi nan zaune, Kasancewar taga idanun shi a rufe ne yasa ta koma dakin Ammi ta faɗa mata isowar shi,cewa tayi tace ya shigo, Tana fitowa zama tayi kusa dashi"yaya"ta kira sunan shi, Buɗe idanun shi yayi wanda har yanzun suke a firgice ya daura a kanta ba tare da yace mata ko mai ba, "Da gaske ka auri Biba,an daura maka aure da ita yanxun kamar yanda naji a masallaci? " Ummm "ya bata amsa a takaice, Bata fuska tayi tana bata rai" Dama Aunty Maijiddarh ce,yaya Biba fa yar aiki ce ba tayi koda karatun Boko ba,amma Aunty Maijiddarh tayi Degree a bangaren Arabic,gata wayayyiya,amma wannan ko baki kayi ta yaya zata fitar da kai kunya,bana tunanin ma ta iya koda karatun sallah ne,ku malamai wani lokaci ana gaiyatar wurin walima ko wa'azi tare da matan ku,ko kuma su a gaiyace matan naku,gata baƙauyiya ko saka kaya bata iya ba,kalli ma wasu irin manyan kayan da take sakawa kamar wata Goggo,kai kuma duk da kana malami amma kai ɗan zamani ne,ɗan Gaye,gaskiya ni dai yaya an cuce ka sam baku dace ba,bata min ba" Yasan duk abinda ta faɗa gaskiya ne,duk da akwai wata a kasa tsakanin shi da yarinyar ba haka bane zai sa ya bada kofar da ƙannen sa zasu wani samu dama a gare shi"ita din Aunty kice ki dai na fadar haka a kanta" Buɗe baki tayi"Aunty kuma?Allah y..... Katseta yayi"ina Ammi? Tsabar takaicin rashin bata amsa da baiyi ba yasa da hannu kawai ta mai nuni da hanyar dakin Ammi, Bai ce mata komai ba shima ya Mike ya wacewar shi ɗakin, Da sallamah ya shiga,tana zaune saman darduma ta amsa mashi, Shigowa yayi ya zauna dan nisa da ita kaɗan yana tankwashe kafa, Da hannu ta mai alama da ya matso, Matsowa yayi zuwa in da take, Tsira mashi ido tayi na wasu ƴan sakanni,yayin da kanshi ke duke, Hannun ta daya ta daura saman fuskar shi "are you ok? Jinjina kai yayi" I am fine" "But you are not" Dan murmushi ya kakaro "I will be ok in time" Ajiyar zuciya ta sauke"kayi haƙuri wannan ne kawai mafita" "I hate it" "Ni ma haka,sai dai at this stage dole ita kadai zata iya tunda ita ta fara,we have to Trust her,we have no option,you have to endure it,can you do it for me? Ta faɗa idanun ta na cika da hawaye, Hannun ta dake saman fuskar shi ya rike ya sumbata" Insha Allah,for you and grandma" "Thank you and im Sorry it all my fault from the beginning"ta faɗa hawaye na ƙara bin fuskarta, Rungume ta yayi " Haka Allah ya tsara tun farko,ke ma ba yin kanki bane,ya kamata ki bar faɗin haka a yanzun" "Har sai ranar da komai ya zo karshe sannan zan huta" "Komai ya kusa zuwa insha Allah" "Ya kamata ka tafi Asibiti tare da Farhan" "Na ji sauƙi" Girgiza kai tayi"ka kula da kanka shine abu mai muhimmanci" "Zan kula Ammi,"ya faɗa yana ƙoƙarin mikewa, " A ina zaku zauna? "Sai yanda su Abbu suka tsara"ya fada yana mata sallamah tare da barin dakin cike da tunanin me zai je ya tarar dakin Kaka. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *34* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Bakin shi dauke da sallamah ya shiga falon bayan sun amsa mai, Sai da ya zauna kusa da Kaka sannan ya gaishe su,amsawa suka yi ba cikin walwala ba,shiru yayi kawai kanshi a duke ba tare da ya kuma cewa komai ba, Abbu ne ta kalli sauran mutanen dake falon,sannan ya ce"Alhamdulillah Allah mun gode maka daka tsara mana wannan ranar a haka,ina fata wannan ya zamo izina a sauran yaran gida,me kokarin aikata irin wannan kuskuren sai ya kiyaye ya kuma san me zai iya faruwa dashi,kai kuma Suraj mun maka haka ne bawai dan ba musanka ba,sai dan muna son kare mutuncin ka dana wannan gidan shi yasa,sannan iyayen ita yarinya sun zo kuma an daura aure cikin mutunci dan haka dole mu gode ma Allah " Duk jinjina kai suka yi cikin gamsuwa da maganar shi, Dady ne yace"to yanzun ina zai zauna da matarshi " Goggo ce ta amshe maganar da faɗin "me kuma zasu zauna su yi mana a gida?ai shi yanzun ba ƙaramin yaro bane tunda har yasan ya saka mace a ɗaki,dan haka ya tattarata suje can gidan shi su karata tunda Allah ya hore mashi,mu kuma ya bar mu muci gaba daba ya'yan mu tarbiyya yanda ya kamata" "Sosai ma maganar ki gaskiya ce,ni yanzun gashi can an bar yata da jinyar zuciya,dan haka abun ya isa haka,muma a ba ya'yan mu wuri su sha iska"cewar Hajiya Saudat, Abba Mustapha da tunda suke magana bai saka masu baki ba, yadan yi kyaran murya,kiran sunan shi yayi wanda hakan ne yasa kowa yayi shiru yana jira yaji me zai ce "Suraj" Dago kanshi dake duke yayi ya amsa a hankali "Na'am Abba" "Shin ko Kanada abun faɗa" "A'a Abba" "A kan hukuncin da muka ɗauka fa,shin baka ganin bamu maka adalci ba,gashi ko dangin mahaifinka bamu ni ma ba" Dan guntun murmushi ya saki wanda ya ɓoye sirrin dake ranshi,tare da raunin shi,"ku din ma iyaye na ne,duk hukunci da kuka yanke zan karbe sa hannu biyu" "Na gode da girmamamu da ka yi,yanzun ka ɗauki matarka ka tafi da ita gidan ka,idan akwai abunda kake buƙata ka kirani ka sanar da ni" Mikewa yayi,domin dama dauriya ce kawai yake yi,"na gode Abba "sallah ya masu sannan ya fita, Kallon sauran yaran dake falon yayi" Ku tashi ku tafi na sallame ku" Duk tashi sukayi suka fita kowa da kalan abunda yake sakawa a zuciyar shi, Kallon Abbu Sufyan yayi"dazu banji daɗin kalamanka ba sam Sufyan,kai a matsayin uba kake a wajen shi,shi kuma yana maka kallon mahaifi,amma ka bari bacin rai ya rinjaye ka,ka faɗa maganar da sam bata dace da bakin ka ba,ka kushe shi da zuri'ar shi,ka aibantashi a gaban ɗan ka,yayin dashi kuma ka yabe shi da kasancewar shi jinin ka,karka manta ko kai bakafi karfin Allah ya jarabceka ka,ina so kuma ka tuna waye Mahaifin Suraj wacece Kakar shi da kuka kira da jikin yahudawa,kai kanka kasan waye ita,idan da Ace tana kusa,wane kai Sufyan,sai dai kawai kaci Albarkacin Auren mahaifiyar jikanta,Kaka kema kin sani,amma ɗan ƙaramin kuskure ba tare da dogon bincike ba idanun ku sun rufe,a gaskiya kun ban kunya,ba kaɗan ba,ban taba tsammanin a gaban mahaifiyar yaron zaku iya fadar haka ba tamkar ku kuke taimaka mata kamar ta dogara daku,bayan a ko wani lokaci idan taga dama tana iya rabuwa da nan ɗin,idan kana taƙama aƙwai yarinya a tsakanin ku,to kamin ta same ta sai da ta sami wanin ta,"mikewa yayi"ni na tafi sai da safen ku,yauwa kaka ki saka ta fito tabi mijinta dare na yi dan na lura kamar ma ba lafiya gare shi ba"yana fama fadar haka ya fita ya bar su nan zaune cikin tarin nazari, Kaka ce tayi kiran sunan Nafisa dake dakin kakan tana kyara mata wurin kwanciya, Cikin sauri ta zo ta tsugunna "ki ce ma Habiba ta fito mijinta na jiranta" "To kaka" Ajiyar zuciya Abbu Sufyan sa sauke tare da mikewa "Mama sai da safe" "Allah ya tashemu lafiya" Tare da Dady suka fita kowa yayi nashi shiyan, Kai tsaye dakin ta ya nufa bakin shi dauke da sallamah, Har yanzun a zaune take saman darduma sai dai ba komai take yi ba,daga dukkan alamu nazari wani abu take yi, Zama yayi kusa da ita ya yaro hannun ta, Murmushi ta sakar mai kamar babu komai a zuciyar ta,"barka da shigowa" Bai iya bata amsa ba sai dukar da kai da yayi yana tunanin ta ina zai fara"kiyi haƙuri" "Akan me?ta tambaye shi, Jin abinda tace ne yasa ya dago kai" Dan Allah kiyi haƙuri akan abunda ya faru dazu,bai kamata na faɗa abinda na faɗa ba" Girgiza mai kai ta yi,fuskarta a sake tana Daura hannun ta saman nashi,cikin tabbatarwa wanda ya hakan ke sashi shiga shakku tace"A'a,ya ya wuce,ba kayi kuma ko wani kuskure ba,ka tunatar dashi ne matsayin shi a gareka,ba kayi kuskure ba is normal thing" Baki ya buɗe yana ƙoƙarin yin magana ta sanya mashi yatsanta a baki alamun yayi shiru "karka damu da sai ka ban haƙuri,wallahi har cikin raina ban rike ba,kuma na gode maka a bisa haƙuri da kayi dashi na tsayin shekaru har izuwa yau daka aurar dashi,na kuma gode da kuka bashi damar matsawa ko zai kara fahimtar rayuwa,domin yanzun shi ba yaro ba ne,na gode" Rungume ta yayi a jikin shi,sai yanzun yake ainahin danasani akan kalamansa na dazu,yaso ta nuna bacin ranta ta yanda zai bata haƙuri a wuce wurin,amma sai gashi ita ke bashi haƙuri ta bar shi da nauyin zuciya, "Ki bani dama ta ƙarshe" "Har abada ni matar ce idan ba ka yanke Alakar dake tsakanin mu ba,da kanka,ka kwantar da hankali ka har yanzun kallon uba yake maka" Babu yanda ya iya da ita amma She make him fill guilty,in sha Allah da kanshi zai gyara abinda yake ƙoƙarin batawa. *_________* tana zaune kan gado bayan ta gama sauraren duk bayanin da suka tattauna a kai sa ga Nafisa ta shigo, Kallo take kare mata daga sama har kasa "Masha Allah Biba,yanda kikasan kamar ba ke ba,gaskiya ke yar sa'a ce gashi daga zuwa aikin kin yi ram da daya daga cikin yaran gida,dan Allah ni ma ki ban sirrin" Ta faɗa fuskarta dauke da farin ciki, "Wai ba cewa akayi ki kira ni ba? " Umm haka ne,kin ga taso Angon ki na waje yana jiran ki," Ganin ta taso tana kokarin fita ne yasa ta jawota baya"ke tsaya ba haka ake yi ba"Mayafinta dake a kafadarta ta dauka ta yafa mata a kai ta sauko dashi far ya rufe rabin fuska,"wai ina Maman ki da yar uwarta? "Sun wuce" Dan budo ido yayi"ta yaya zasu wuce basu tsaya sun kai ki ba? "Mu a garin mu Ango shi kaɗai yake tafiya da Amaryarsa ba tare da kowa ba," "Wow gaskiya abun yayi kyau,to amma ni dai muje sai na rakaki har bakin mota" "Aukuwa na gode muje" Tare suka fito, Wurin Kaka ta tsugunna tana mata sallamah"karki damu mun riga munyi magana da ƴan uwan ki kuma sun faɗa mana Al'adun ku,shi yasa na ce ki fito ki bin angon ki,sannan batun kayan sawarki na ba Teloli su uku domin ayi saurin haɗawa zuwa gobe,in sha Allah za'a kawo maki kayan Lefen ki" Nan ma godiya tayi mata, "Tashi kije yana jira Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a ta gari" Wannan karon kam bata ce Amin ba dan bata buƙatar ko fatan haɗa zuri'a da shi,dan ba wannan bane a gabanta, "Kaka bari na raka ta wurin mota sai na nawo" "To hakan ma yayi" Tashi suka yi suka fita tana riƙe da hannun ta "Biba dan Allah duk dadin da kika samu karki manta da ni,tunda yanzun kin zama matar manya" "Dan Allah karki dame ni da wannan maganar sai kace wacce zasu tabbata tare" "Me kike nufi,tare zaku tabbata tunda mijinki ne" Girgiza kai tayi"ba zaki gane ba" Ganin sun isa bakin motar ne yasa dole tayi shiru, Kallon Farhan Nafisa tayi dake jingine a jikin mota"dan Allah wani mota zan saka Amarya? Da hannu ya mata nuni da wani karuwar Jeep baka dake ɗan nisa dashi kaɗan, Nufar wurin suka yi yana bin wacce fuskarta ke lulluɓe da kallon nazari,dan daga dukkan alamu doguwa ce sai dai ba can ba,sannan siririya nan ma ba sosai ba,tana da shef sosai duk da a lulluɓe take,to ko ya fuskarta zai kasance tunda yaji abokin nashi yace tana shan sigret,ko ma dai ya take nan ba da jimawa ba zasu haɗu. Buɗe mata gidan baya tayi"ki shiga nan ki zauna,sai da safe ni na tafi" "Na gode Nafisa ba zan kuma manta dake ba" Cikin jin daɗi ta ce"ai kuwa na gode"sannan ta ja mata kofa ta rufe, Kyara zamanta da kyau tayi tana sauke ajiyar zuciya tare da cire mafayin dake lulluɓe a kanta, Wani irin fitinannan kamshi ta ji yana tashi a cikin motar wanda ta saka ta lumshe ido ta buɗe, Jin kamar numfashi a gefen ta ne yasa da sauri ta kalli wurin, Yana zaune idanun shi a lumshe yana jan carbi,yayin da yayi tamkar bai san da mutum a gefen sa ba, Kallon shigar dake jikin shi tayi tana tabe baki,wato da Jallabiya yazo ɗaurin auren shi,ɗan ƙaramin tsaki taja wanda bata yi tunanin ya fito ba, Kamar mai ciyon baki taji yace"wannan ya zama karo na karshe" Da ba dan ta kwantar da hankalin ta ba da bata fahimce me yake nufi ba,magana a gutsurew ba tare da an kai ƙarshen shiba, Farhan ne ya buɗe mazaunin direba ya shiga yana daɗin "Amarya baki laifi ko da kin mari ango" "Ba dai irin wannan ba" Jin abinda tace ne yasa ya dan saki dariya kaɗan,"ke dai faɗi gaskiya Amarya,kin ga dai ga angon naki nan zaune a gefe yana ji,ko zaki gwada? "To kai ɗin me zai hana ka kwada na baka baki" Wannan karon ko dariya yayi sosai"lallai za'a je dake,to ya kuma muka ji da jama'a? "Alhamdulillah" "Allah ya baku zaman haƙuri," "Amin" Tayar da motar yayi suna barin harabar gidan"suna na Farhar " "Ni kuma Biba" "Nice to meet you" Tunanin bata jin Turanci yasa da sauri yace yi haƙuri "ina nufin naji daɗin haɗuwa da ke" "Karka damu ni ma haka" Daganan basu kuma cewa komai ba har suka iso Sultan road, Kamar dazu babban Get din da kanshi ya buɗe suka shiga sannan ya kulle kanshi, Daga kai tayi tana kallon gidan wanda gabaɗaya kusan rabin shi da Glass aka yi shi,ba karya ya haɗu,ta faɗi hakan a zuciyar ta,domin ita a wurin ta ba wannan ne karo na farko data fara ganin ire-iren wadannan gidajen ba,tunda tayi zaman kasan waje kuma ta zagaya kasashe da dama, Ganin uban gaiyar ya fita ba tare da ya ce mata komai ba yayi gaba yana taku dai daya kamar bai son yi, Taji an buɗe mata ƙofar "fito Amarya"cewar Farhar, Fitowa tayi" Na gode " "Mu tafi ciki kafin ya kulle ƙofar" Ita dai bata ce masa komai ba tabi bayan shi har cikin madaidaicin falon, Ganin ya doshi sama ne yasa tabi shi har cikin dakin, A zaune suka same shi a bakin gado dafe da kai, Jin takun tafiyar na mutane biyu ne yasa ba tare daya dago ba yace, "Me ta shigo min a daki " "Me kake nufi? " Kace ta fitar min a daki"ya fada wannan karon yana daura idanun shi akanta, Wanda hakan yayi dai-dai da zame kyalen kanta data kuma yi gabadaya ta rike a hannu, Hakan yayi sanadiyyar baiyanar kyakkyawar fuskarta da yake ƙyalli ba tare da ko digon ƙwalliya ba,haka kuma lallausar sumanta dake kwance a gadon bayanta saboda kalar ɗaurin dankwalin da tayi, Ita ma tana daura nata idanun a cikin nashi...... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *35* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Kafin ta saki wani lallausar murmushi wanda ya baiyana fararen haƙoran ta suke jere tas dasu,sai kuma dimful wanda ya baiyana a gefe ɗaya na kumatun ta, A hankali take takowa da takalmanta masu dan tudu har ta isa gefen da kushin yake tama kanta mazauni a wurin kafin ta juyo da kallon ta kan Farhan wanda yayi suman tsaye yana binta da kallo"Farhan ka faɗa mashi shin ya manta matsayi na ne a wurin shi,dan haka bai da hurumin faɗar haka" Mai da kallon shi kan Suraj yayi"tace baka da hurumin fadar haka" "Ka faɗa mata ta zaɓa wani ɗakin acikin ɗakunan duk wanda ya mata ta zaɓa,amma ba na son tazo inda nake" Kallon ta yayi sai dai kuma ya rasa me zai ce mata,saboda yarinyar ba karamin kwarjini ta mai ba, "Me ya faɗa Farhan"a zuwan ita bata ji me yace ba "Ummm cewa yayi babu komai kina ina zama duk in da ya maki" "Yauwa na gode Farhan" Cikin sauri yace"yaushe na faɗa maka haka,ke tashi ki barmin daki" Turo baki tayi ta tashi tana takawa kamar zata bar ɗakin,juyowa tayi tana dawowa baya kafin ta juyo da gudu ta nufo in da yake, Ko da ya dago kai kafin yace zai motsa sai jinta yayi ta fado jikin shi,gabaɗaya suka zube saman gado a kwance ita tana saman kirjin shi, Kokarin ture ta yake daga jikin shi sai kwantawa tayi da kyau yayin da kirjinta ke gogon nashi, "Idan kayi ƙoƙarin ture ni zan yi abinda baka so" Kauda kai yayi yana furzar da iska,"ɗaga ni" Girgiza kai tayi"a'a " "What do you want? Dan shiru tayi kamar mai tunani sai kuma ta juyo da kallon ta kanshi,yatsa tasa tana zagaye fuskar shi dashi," Do you hate me that much? "Fiye da yanda hankali zai ɗauka" "Har haka? " Ɗaga ni" Sauke hannun ta tayi a fuskar shi "ni ma na tsane ka sosai,fiye da yanda ka tsane ne,sai dai ba yanda zaka yi dani domin na zama matar ka,dolen ka,kuma na zama bindin ka,duk inda zaka tafi tare zamu rika zuwa,ka saka hakan a ranka"tana gama fadar haka ta sauka daga jikin shi ta doshi hanyar da suka shigo ta fita, Dakin dake gefen nashi ta buɗe,nan ma a kyare yake babu abinda babu,dan haka zama tayi nakin gado tana ƙara nazarin dakin. Shigowa yayi yana dan kalle_kalle a ɗakin,"ta wuce ne? "Zo ka mai da min drip" Hannun shi ya kama yana duba inda zai samu jijiya "tana da kyau sosai,na ɗauka zan ganta kamar sauran yan aiki,sai dai ita na daban ce" Bai bashi amsa ba sai ma mai da idanun shi da yayi ya rufe, Ganin haka ne yasa shima ya ja bakin shi yayi shiru,dan ya sani idan har yayi haka ba kara wata maganar zai yi ba,amma dai maganar gaskiya shine ta wuce da tunanin shi,sam bai yi tsammanin haka ba,sai dai daga dukkan alamu ita din ba ƙaramar yar duniya bace,yarinyar idanun ta a buɗe suke,shi wallahi da zai samu irin wannan bai ga abinda zai sa yayi wasa da damar shi ba,sai dai yasan halin Suraj,zai kuwa so yaga yaya wasan nasu zai kasance da yarinyar dan ita kanta hatsabibiya ce, Yana gama saka mashi ya mashi sallamah ya wuce a kan sai sun haɗu gobe. Washegari da safe koda ta farka ƙarfe tara na safe saura,ta jima bata samu tayi barci irin haka ba,dan haka banɗaki ta shiga tayi wanka da kalolin sabulan wanka masu kamshi da ta gani,wanda hakan ne yasa ta jima a cikin banɗaki, Sai da ta tabbatar ta cire duk wani dauɗa da dake jikin ta lungu da tsako sannan ta dauro Alwallah ta fito,buɗe durowar dakin tayi,babu komai a ciki sai kayan maza,cikin Jallabiyoyin shi ta jawo ɗaya haɗe da boxe size ta saka sannan ta yafa gyale tayi sallah, Tana idarwa falo ta fito dan ba karamin yunwa take ji ba, Kallon wurin da ake shirya abinci tayi,ganin manyan kuloli tayi shirye a wurin,dan haka jawo kujera daya tayi ta zauna sannan ta shiga jawo ko wanne gabanta tana dubewa dan ganin me a ciki, Lafiyayyen farfeson kaza ta zuba wanda ya ji sinadirin kanshi da ɗandano,sai kunun kyada, Bata jima da fara ci ba ta ji takun saukowar shi,kallo daya ta mai ta dauke kanta tana ci gaba da taunar tsokar kazanta, Cikin sauri Bala dake biye dashi a baya ya karaso inda take"malama daga ina,wacece ke?me kike yi anan,daga zuwa kuma sai taba abin mutane " Kallon ƙasa da sama ta mai"tashi min a kai karka saka na kware" "Wacece ke" Ajiye naman dake hannun ta tayi,sannan ta karaso inda yake tsaye cikin sakin fuska, "Mijina Abin Alfahari na barka da safiya,ya jikin naka? Kauda kai yayi yaci gaba da takawa zama yayi kan kushin," Bala"ya kira sunan shi, "Idan kuna bukatar wannan abincin ka kwashe,idan kuma baka buƙata ka fitar min dashi" "To me zaka ci uban daki na? " Ka samar min abu mai sauƙi,wannan kuma zata zauna damu na ɗan wani lokaci ka bata abinci yanda ya kamata," Zama tayi kusa dashi tana daura kafa daya kan daya kamar yadda yayi"Bala ni matar mai gidanka ne,dan haka dole ka jirmama ni kamar yanda kake girmama shi" Cikin mamaki yake kallon ubangidan nashi,da mamakin yaushe hakan ya faru,da kuma yaushe yayi aure,sai dai katse mashi tunanin yayi ta hanyar fadin"Barshi"ya yi fitar shi, "Ina sauran ma'aikatan gidan nan? " Suna shiyan su" "Ina bukar ganin su yanzun nan" Bata fuaka yayi dan ya lura kamar so take ta rusa masa gwamnatin shi a wurin ubangidan nashi, "Yanzun suna kan aiki ne" "Kaje ka kira min su idan kuma basu zo ba a bakin aikin ka" Dafe kirji yayi"bakin aiki na kuma,ta nan fa nake samu nake ciyar da iyalai na " "Ba sai ka koma bara ba,dama akwai wanda nayi alƙawarin zam nimar ma aiki,yama fika dacewa da aiki,ka ga yanzun ni ce mata gida sai yanda nayi da mai gidan" Cikin rawar jiki ya juya "bari naje na kira su" "Dawo muyi magana tukunna" Dawowa yayi wannan karon harda tsugunnawa dan ya lura in bai yi hankali ba wannan yarinyar da bata wuce sa'ar kanwar shi ba tana iya mai sage_geduwa gara ya bita a hankali, "Idan har ka yarda zaka min aiki zan kara maka albashi akan wanda ubangidan ka ke baka" "Wani irin aiki,sai dai ki sani in har na cutar da ubangida na ne ba zan karba ba ko nawa zaki ba ni" Dan murmushi tayi"kwantar da hankalin ka dan ni ma ba zan iya cutar dashi ba,sai dai na kare shi,aikin ka shine kawai duk lokacin da kaga zai fita ka sanar dani,in da hali ma har in da zai je " Ji yayi hankalin shi ya ɗan kwanta"in dai wannan ne ba kida damuwa Hajiya " "To kaje ka kira min su gani nan fitowa" "To hajiya" Bayan kamar mintuna goma sai gashi ya dawo"Hajiya suna ƙofar falo" Mikewa tayi ta fito a tsaye ta same su suna jiranta,ba tare da damuwar komai ba ta masu sallah, Amsawa suka yi cike da tunanin wacece ita,domin wannan ne karo na farko da wata mace ta shigo nan ɗin, "Ni suna na Habiba,matar mai gidan ku,nasan zaku yi mamaki,amma ba abin mamaki bane dan jiya aka ɗaura mana aure da shi" Ganin duk sunyi shiru suna mata kallon mamaki ne yasa ta ɗan daga kafaɗa ta "akwai mai abun fada? Girgiza kai sarkin gida yayi" A'a Hajiya " "Well to ni ina da abun faɗa,na farko bana son gulma da kananun magana,sannan ina son girmamawa,ma'ana a dinga bani girma na,na uku kuma ina fata zamu zauna lafiya tare da ku" "In sha Allah Hajiya" "To sai kumin introducing kan ku" Babban cikin su ne ya matso gaba"ni suna na Sarkin Gida,kuma ni ne babban su mai kula da duk wani harka na cikin gidan nan,sai wannan Bala shine mai yi ma uban gida girki,sai kuma direba,da masu kula da tsakar gida ta tsaftar gidan " "Hakan yayi kyau,dan haka kuna iya tafiya" "Mun gode" Suka faɗa a tare, Komawa cikin falon tayi ta zauna tana sauke ajiyar zuciya,wayarta dake hannun ta shiga dannawa tana kwada number Ummita ko Allah zai sa ta sumu,sai dai abu ɗaya kawai ake maimaita mata shine wayar a kashe take, Tsaki taja cike da tunanin a wani hali take ci,gabaɗaya wannan yanayin yana hana ta samun natsuwa, Ji tayi kararrawar kofa yana ƙara alamun ana niman izinin shigowa, Tashi tayi ta buɗe ƙofar, Kallon_kallo suka tsaya suna ma juna kafin Zainab ta buge kafadarta ta shiga ciki,sai Amira sannan Aunty Hajjo dake, Da Bala da sarkin gida ne suka shigo dauke da wasu manyan Akwataiya guda shiga suka jera a tsakar falon sannan suka fita, Mai da kallon ta kansu tayi,sun yi wani zaman taƙama a falon yanda kasan na gidan su, Cikin sakin fuska tace "Aunty Hajjo ina kwana,Amira sannan ku da zuwa" Sai dai duk cikin su ba wanda ya bata amsa, Sherawa tayi ta shiga kicin ta dauki masu gorunan ruwa da lemu, "Kin ga dauke mana a gaba dan ba mu maki kama da wadanda suke ni ma ba" Ita fa ta lura da take taken su,ba su san duk wannan abun da take masu na marmari bane,amma ba komai a hankali zasu san juna, Aunty Hajjo ce tace"wannan ba rigar Suraj bane kika saka" Murmushi ta saki cikin jin kunya tace"da Asuba ne da muka yi wanka tare to shi ne ba ni da kayan da zan saka shine ya saka min nashi" Gabaɗaya miyon bakin su daukewa yayi,wanka fa tace tare da Suraj din kuma har da saka mata kaya,kenan ba dai har yayi wani abu da ita ba,kai Namiji ba shida amana, Ganin halin da suka shiga ne yasa ta saki wani shegen murmushi tana ɗan dago kai, Sai dai cikin rashin sa'a idanun ta ya fada cikin nashi dake tsaye rungume da hannu yana sauraran abinda ta faɗa. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *36* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Ganin irin kallon da yake jifanta dashi ne yasa tayi ɗan tsam kafin kuma ta kyara tsayuwarta tana ɗauke idanun ta cikin nashi"ummm gama Yayan naku ya zo,bari na baku wuri "ta faɗa tana hawa bene ba tare da ta ƙara juyowaba, Dan rigima a maimakon tayi ɗakin ta sai shigewa ɗakin shi tayi ta kwanta saman dago tana juyi" Gaskiya wannan gadon yafi laushi,wancan sai saka ciyon baya,ai sai dai kayi haƙuri amma nan dakin zan dawo da kwana". ___ƙara daure fuska yayi wanda dama yake a cunkushe saboda rashin walwala, Takowa yayi ya zauna a daya daga cikin kujerun, Nan take suka shiga gaida shi,sai dai bai amsa masu ba sai kallon Aunty Hajjo da yayi"barka da Safiya" Bata bashi amsa ba sai ma cikin ɓacin rai da tace"Abinda wannan yarinyar ta faɗa gaskiya ne? Kauda kai yayi be bata amsa ba,to me zai ce mata a gaban kanne shi, "Suraj tambayar ka fa nake yi,ni da nake son su Abba su huce a maida saka ranar ka da Maijiddarh,amma ji abinda yarinyar nan ke fada" "Me zai hana ki bincike ta"yayi maganar kamar ba a bakin shi ya fito ba, " Yaya"Amira ta kira sunan shi cikin jin haushi"dan Allah karka ja mana raini a wurin wannan yarinyar " Wani mugun kallo ya watso mata"ita din Aunty ki ce idan har ni yayan ki ne,kar na kuma jin zancen rashin girmamawa daga gare ki" Mikewa yayi yana dosar hanyar barin falon"bana son kananan magana "ya fada yana karasa faɗa. Ajiyar zuciya ta sauke" Banga me zai hana na kyara ma yarinyar nan zama ba,ku tashi muje " Haka suka bar gidan cikin bacin rai. Sai zuwa ƙarfe biyu data gaji da kwanciya ta fito,shine ta kara cin karo da Akwatunan da suka kawo dazu, Ɗauka tayi ta kai dakin shi ta jera sannan ta shiga budewa,ba laifi an zuba kaya sai dai ba masu irin tsadar nan ba,dan kudi Kaka taba Aunty Hajjo ta hado kayan saboda irin sana'ar da take yi kenan,shine ta zubo waɗannan,gabaɗaya kayan har akwatin idan aka duba kuɗin su basu wuce dubu dari bakwai ba Karamin tsaki taja,ai ko dan kunnen da take sakawa yafi karfin gabaɗaya kayan balle yanzun data samu yancin akanda da take gidan su,dan haka yanzun sai abinda taga dama, Daukar pant daya da Bran tayi sai doguwar riga da takalmi flart shoes ta saka,gyalen dan karamin Jallabiya data saka ta yane kanta dashi, Dubawa tayi cikin kayan kwalli sai dai duk ciki ba kalan product din da take amfani dashi,dan haka man baki kawai ta shafa,ka karamin kyau kayan ya mata ba,dan kalar Ashe ne ma'ana ruwan toka. Tana cikin fesa turare taji shigowar shi,sai dai bata juya ba dan tana iya ganin Reaction ɗin shi ta cikin madubi, Murmushi ta saki tana juyowa cikin takun dai daya ta iso gaban shi "Mijina nayi ƙyau" Ganin baida niyar kulata yasa ta ɗan bata rai "gaskiya Suraj idan ka bata fuska baka cika yin kyau sosai ba,ka dan dinga murmushi mana" Ta karasa faɗa da murmushi a fuskarta, "What ar you doing? Ya tambaya yana karema dakin kallo harda gadon shi da ke hargize, Itama bin dakin da kallo take bi" What? Ta maida masa tambayar shi, Nuni yaimata da akwatunan dake jere da kuma gadon dake a yamutse har zanin gadon ya fado kasa,"what is the meaning of dose thing here? Bata fuska tayi"ai gadon dakin can ne yake saka ciyon baya shi yasa na dawo nan,idan kuma kaima nan ɗin ta maka We can share this room,kaga sai mu dinga kwana tare akan nan zai fi armashi ko? Ta faɗa tana faɗaɗa fara'ar fuskarta, Dafe Kwankwaso yayi yana ɗan furzar da murmushin takaici "what is your name ma again?nunata yayi da yatsa " Habiba,for God sake stop being like a real wife,I now you are just Acting,pretending,please a don't want any trouble, keep pretending like one,but stop coming into my way,I don't like you at all,I think you have to know even living with you is like hell to me,Dan haka kici gaba da aikin dake gabanki amma ki fita harka na,sannan ki tattara ki barmin daki kafin ranki ya ɓaci " Har ya juya zai bar dakin ya kara juyowa "na baki minti biyar" Ya faɗa yana karasa fita, Duk da maganganun shi sun soso mata zuciya nisa ba kusaba,hakan yasa ta lumshe idanun ta na wani lokaci kafin ta buɗe tana ƙoƙarin shanye duk wani ɓacin ranta, Zaciyarta take lallashi,tabbas da ba dan akan aikinta take ba da Suraj bai isa ya faɗa mata irin waɗannan maganganun ba,sai dai zata dinga tuna Ummita wanda hakan ne zai kasance mata ƙwarin guiwa,zata iya jurewa ko dan ita,tayi haƙuri da duk wani abunda zai mata har zuwa sanda zata samu nasara ta fita rayuwar sa,zata dauki ƴar uwarta su koma kasar waje kamar yadda suka tsara,to amma me take da yace tana pretending ne akan komai,ɗan shiru tayi tana nazari,ko da yake yasan basu son juna shi yasa ya faɗi haka,to kuma yace aiki,wani aiki yake nufi,wani zuciya ne ya bata amsa to ko dai yasan aikin da take yi ne,da sauri ta girgiza kai,ina ba zai sani ba,ta yaya ma zai sani,kawai dai yana nufin,shiru tayi to yana nufin me?ajiyar zuciya ta sauke koma dai me yake nufi bashi yake nufin yasan komai ba, Ɗan murmushi ta saki wanda ita kaɗai tasan ciyon da take ji a zuciyar ta dole ta maida shi murmushi, A kwatunanan ta fito dasu ta ajiye a ƙofar dakin ta sannan ta sauko kasa, A falo ta same shi yana waya, Zama tayi tana jira ya kammala sai dai yana ganin ta zauna ya mike yana ƙoƙarin barin wurin ba tare daya katse wayar da yake yi ba, Ganin abunda yayi ne yasa ta tashi tabi bayan shi har zuwa falon gidan na biyu,sai dai jinta a bayan shi yasa ya katse wayar ba tare daya kammala ba ya juyo yana kallon ta"Lafiya? Ya tambaya, Sam ita bata son wannan tsaretan da ido da yake yi,sai kace mai ƙoƙarin daukar wani abu a fuskar ta,bai san irin kwarjinin da yake mata ba,dauriya kawai take yi tana nuna masa gagaranta, Tsuke baki tayi tana juya idanunta a hankali tace"bana son irin wannan kallon" Babu zato taji yace"idan baki da ƙwarin gwiwa jurewa ki daina baiyana" Da sauri ta kuma juyowa, har yanzun kuma idanun shi tsaye suke a kanta,sai dai duk yanda taso fassara yanayin fuskar sa ta kasa,"idan da banida shi da ban shigo rayuwar ka ba" Giranshi daya ya daga"duk juriya irin na mage ba hakan ke nufin zata kai labari ba" "Duk iya farauta irin na Zaki hakan ba yana nufin wata rana zai nime taimako wurin mage ba,sai dai kuma ina mai bashi shawara da yabi takunshi a hankali domin shima gab yake da fadawa hannun mugayen mafarauta,wa ya sani ko mage ce kawai wacce zata iya taimakon shi a wannan lokacin" Ta faɗa tana ƙoƙarin daura nata idanun akan nashi,sai dai tsabar mugunta Inji ta irin nashi sai dauke kanshi yayi a kanta yana canja zance ba tare da ya faɗi komai ba kamar yadda taso,sai cewa yayi"me kike buƙata " Haushi ya bata,amma ita ma sai ta share,ko ba komai a juye zuwa rafi wata rana Tulu zai fashe"ina buƙatar ATM card din ka,zan fita siyayya akwai abinda nake buƙata " "Me yasa sai nawa,in baki da kuɗi ki bar fitar mana" Ya juya zai tafi, Gaban shi tasha tana wani marairaice fuska"Allah sarki kai da malami ne,mai tsoron Allah,kuma kasan haƙƙoƙin miji akan matar shi,ko da ta ƙarya ce,balle namu an shafa fatifa,k.. " Mika mata ATM card din yayi daya ciro a cikin walet"Mage mai kwanciyar ɗaukar rai" Da sauri ta amsa"wata rana Magen ce zata taimake ka" "8487" Ya faɗa yana barin wurin, Jujjuyawa take a hannun ta"Ohho dai ba dai ka bani ba,ka ji a jikin ka"ta fada tana fita falon gabaɗaya, Tsayawa tayi tana kallon motocin dake fake a wurin ajiye mota, Direban gidan ne ya taso da sauri yazo inda take"Hajiya fita zaki yi ne? "Eh ina makullin wannan motar? Ta nuna wani sabuwar mota Maron kolo dake cikin leda alamu ma ba'a taba amfani dashi ba, " Yana wurin Ubangida domin ba'a taba amfani dashi ba" Gaskiya motar ya tafi da imanin ta,taji kewar tuƙi,ji take kamar ta buɗe ta shiga taja,sai dai bata son nuna zalamar ta a fili,dan haka tace"ɗauko ma kulli muje shopping " Da sauri yace"An gama Hajiya " Shi ya buɗe mata ta shiga sannan ya ja suka tafi, Babban wurin siyayya na garin Kano ya kai ta, Farko layin data fara shiga shine na kayan shafa,Glow gold ta dauka man da take shafawa,wanda kudin sa Naira dubu saba'in ne,sai kuma Sabulan wanka na ruwa da turare wanka kala-kala,man baki, da jan baki,sai kuma turaruka inda anan ne tayi ainahin ɓarna da kuɗi, Bangaren kayan sakawa ma ta kwasa ba kaɗan ba,dogayen riguwa jallabiyoyi,dana kanti,ƙananan kaya wanduna da riguwa sai after dress,pant da bran,takalma,Agogo,sarka na wuya da kunne,man wanke kai dana kamshi,a takaice duk wani abunda ta san tana buƙata ko kuma zata buƙata sai da ta siya,dan bayan but din motar sai da aka cika shi da kaya, Har zata fita sai kuma ta tambaye ko akwai inda ake sai da waya a ciki,nan ma nuna mata akayi,lafiyayyen Iphone ta dauka amma na dubu dari da gamsin ta dauka,a cewar ta gaba ta canja wani,sai kuma tayi ɓangaren gyaran jiki,in da anan aka kara kyara mata suma aka wanke kafa da hannu,sannan aka mata ƙunshi a kumbuna na hannu da ƙafa duka ja,dan bata son barin kumbunan ta fari, Ba ita ta fito wurin ba sai kusan biyar na yamma,a gajiye suka dawo gida, Cikin sauri ya buɗe mata ta fito yana ta faman washe baki,dan shikan yau ta burge shi,tunda sau biyu tana aiko mai da abinci bayan haka harda turmin zani biyu masu kyau ta siya ta bashi tace ya kai ma matarshi ko Maman shi,gaskiya ba ta da rowa, A bakin ƙofar falo suka jibga kayan shi kuma Bala yana kwasa yana ajiyewa a ƙofar ɗakinta na sama, Ita kuma tana shigar dasu daki, Sai da ta kammala sannan ta jera komai in da ya dace zuwan lokacin har an tada sallah Magrib,dan haka ƙara kyara dakin tayi ta share ta goge sannan ta shiga wanka, Tana fitowa tayi sallah sannan ta fito dan mai da mashi da ATM card din shi, Sai dai tana tura kofar dakin ta shiga taga gabaɗaya yanda kasan ba dakin ba,domin babu abinda ba'a canja ba na dakin tun daga kan gado har komai na banɗaki data leka,sai ƙamshi dakin ke zubawa kamar na sabuwar Amarya, Tabe taki tayi"kudi na faɗa maka ƙarya "kwalbar turaren data siyo mashi dan karami mai matukar kyau da kamshi ta ajiye mashi nan saman madubi ta fita, Cike da tunanin ya kamata ta fara gudanar da aikinta zuwa gobe da safe idan ya fita,dan yau kam ta gaji... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *37* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Tana shiga daki ta turo kofa ta zauna kan gado, Jakkan data fita dashi dazu ta buɗe,wanda kwalayen Sigari ne guda biyu a ciki,ciro kwali daya tayi ta cire wanda zata sha guda daya sai wani magani data balla guda daya ta raba biyu ta wurga a bakin ta tana tsosa ba tare data damu da dacin shi ba, Sai da ta tabbatar ya narke sannan ta kora da ruwa ta kunna Sigret tana mashi kyakyawar zuka, Tana kammalawa ta tashi ta cire hijabin dake jikin ta da zani ta maida kayan bacci wanda yake ɗan ƙaramin pant ida duwawu sai karamin singileti mai tsansi iya haƙarƙari,gabaɗaya tundaga shafaffen cikin ta har zuwa kasan maran ta a buɗe yake,yayin da Cibiyar ta dake sanye da ɗan kamin makale na zinari wanda zaka yi mamakin ta ina aka bula aka saka shi,dan har wani daukar ido yake yi, Dama gashi suman kanta yasha gyara dan haka ta baje shi a tsakar bayanta yana lilo, Shafe jikinta da turarukan kamshi tayi kamar yanda ta saba in dai har zata kwanta, Jin kanta ya fara nauyi ne yasa ta tashi daga gaban madubi ta haye saman gado taja bargo sannan ta rage hasken wutar dakin sosai, Lumshe ido tayi ta buɗe tana kallon Silin,abubuwa ne da dama suke dawo mata acikin kwakwalwa,ƙara lumshe ido tayi sai ga hawaye ya sauko ta gefen ramin idanun ta, A hankali bakin ta ya furta "Ma" Ba tare da ta karasa ba ta haɗiye sauran a ranta,tana jin wani abu mai matukar girma da ɗaci yana tsaya mata a makoshi, Tasan ita yarinya ce mai matukar Kawazucin iyayenta,har balle Mama,ko ina bata yar da ta je ba tare da ita,sai makaranta daya zama dole,to amma gashi cikin lokaci kankani komai ya sauya,tana rayuwa ba tare dasu ba,tana rayuwa ba tare da tasan halin da suke ciki ba,tana rayuwa ba tare da jin muryar su ko ganin su ba,shin suna raye ko sun mutu, Tunanin hakan ne yasa ta fashe da kuka daga kwancen da take,kuka take sosai kamar wacce aka daka, Rayuwar ta bai da wani amfani,ta shiga duniya ne kawai saboda bakin ciki,tana son taci gaba da gujewa wannan bakin cikin har zuwa ƙarshe,to sai dai ina ne ƙarshen?ta ina zata bi ta kai wannan ƙarshen?ko yaushe a ciki gudu take amma har yanzun bibiyar ta yake yi,duk da ta canja gari,ta canja suna,amma har yau ba abinda ya sauya, Sai dai koda kafin ta kai wannan ƙarshen zata rasa ranta a hanya,ba zata taba juyawa baya ba ga inda ta boro,ba zata taba juyawa ba ɓalle ta ga nisan da tayi,ko da hakan na nufin zata iya fadowa daga saman tsaunin data hau,ba zata taba waiwayarsu ba har abada, Ta dauki lokaci mai tsayi tana kuka kafin daga nan Sarkin iya sata ya dauke ta,wato Barci wanda tayi shi ba dan daɗi ba, Jin yanda jikinta ke ciyo ne ya sakata tashi zaune ba tare data buɗe ido ba,dan ƙwayar data ci tuni ya gama jukuwa, Saukowa tayu daga kan gado ta dawo kasa ta kwanta,nan ma ba daɗi taji ba sai ma mulmula data gama yi ta kara tashi, kai tsaye fita tayi ta nufi ƙofar ɗakin shi wanda yake kallon nata, Turawa tayi ta shiga ba tare data damu da duhun da ɗakin ke dashi ba, Da lalube ta faɗa kan gado tana jawo bargon data ji a shimfede ta shige, Cikin ƙanƙanin lokaci barci mai matukar daɗi yayi awon gaba da ita,dama kuma gashi yanayin garin yau akwai sanyi, Kiran sallah dake shigowa kunnen shine ya tilasta shi ƙoƙarin buɗe ido wanda yake jin yayi masa nauyi, Ɗan shiru yayi yana saurare kamar mai nazarin wani abu, Tabbas yana shakan wani irin kamshi wanda ya san ba daga jikin shi yake fitowa ba,sannan yana jinshi kamar a jikin mutum, Hannu ya miƙa ya kunna wutar dakin gabaɗaya,sannan a hankali ya shiga yaye bargon dake jikin shi, Wani irin zabura da yayi ya faɗo daga saman gado hakan yasa itama ta firgita ta mike tsaye cike da tsoro tana kalle_kallen ko abun gudu ne ita ma ta gudu, Kallo daya ya mata ya kalli kanshi ai dasauri ya runtse idanun shi yana fadin"Bismillah,A'uzu billah,ya haiyu ya Kaiyum" Da sauri ta duro daga saman gadon cike da tsoro ta dawo ta bayan shi ta rike mai hannu,cikin muryar Tsoro tace"Suraj mu gudu,ni tsoro nake ji hala maciji ka gani,dan Allah ka fitar dani "dan ita a rayuwar ta ba abun da take tsoro irin maciji, Ba tare da ya kalli in da take ba yace" Fitar min a daki" Gabaɗaya ma rungume shi tayi ta baya tana kwantar da kanta a bayan shi wanda bai saka riga ba,"A'a babu inda zan je,sai dai in goya ni zaka yi,tsoro maciji nake yi" Duk wani addu'a da ya zo bakin shi faɗi yake a zuciya,ba tare daya dire wani ba yake daukar wanu,rokon Allah kawai yake daya mai tsari da ita da kuma sharrin ta, Da kyar ya iya danne zuciyar shi"ki hau kan gado bari saka kaya sai na fitar dake " Bata ci masa musu ba ta hau kan gadon ta tsaya tana kallon shi har ya saka doguwar Jallabiya ba tare da ya juyo ba ya nuna mata hanyar waje "zoki fita" Makale kafaɗa tayi"Umm Umm" Ranshi ne ya bala'i ɓaci dan haka juyowa yayi yana fuskantar ta dan dai kawai taga bacin rashin,sai dai duk yanda yaso ya jure kallon ta kasawa yayi,saboda yanda gabaɗaya ta turo baki ta narke yanda kasan wata Baby,gashi kuma duk wani motsawa da zata yi sai sharasharan rigarta na sama ya daga wanda hakan ke kara bayyana cikakken Kugun ta,da kuma ramin Cibiyar da ɗan makalen ke ɗaukar hankalin shi, So yake yaga me a wurin,dan bai taba tsammanin ana saka abu a wurin ba,dan bai kasance mai kallon tsiraicin mace ba, Da hannu ya nuna cibiyar nata"me kika saka anan" Kallon inda yake nunawa tayi,ɗaga rigar sama tayi tana kallon shi"me? Ɗauke kai yayi yana jin kanshi na sarawa,kafin ya tako inda take,ba zato taji ya jawota ya daura saman kafaɗa,a bakin ƙofa ya dire ta "ki cire wannan abun na Cibiyar ki" Garam ya maida kofar ya kulle, Ƙwanƙwasawa ta fara tana kiran yazo ya buɗe mata,sai dai bai da alama zai buɗe, Cikin jin haushi ta buga ƙofar ta da ƙofar,sai kuma ta dafe ƙafar tana faɗin"uch"falo ta koma kan kushi ta yi kwanciyar ta,har ya fito ya tafi masallaci ya dawo tana kwance, Ruwan sanyi ya dauko a firig ya buɗe, Ji tayi yanda ruwan sanyin ke ratsa ta yasa ta tashi a firgice tana niman wurin gudu,sai dai rike mata hannu yayi da hannun shi daya,duk yanda taso ta kwace kasawa tayi,haka kuma duk yanda taso ta rungume shi yaki bata dama, Hakan yasa kawai ta sadakar ta tsugunna a gabanshi ta dukar da kai har sai da ya karar da gogar ruwa masu azaban sanyi a kanta, Ji take kamar ta sheke saboda sam bata shiri da sanyi shi yasa ma ko abu mai sanyi bata cika sha ba, Gashi ba kayan ƙwarai ne a jikin ta ba,ga sanyin AC dake ƙara butso sanyin,ta jike sharkaf yayin da sumanta ya rufe mata fuska, Dagota tsaye yayi da hannun shi dake cikin nata, Murmushi ya saki wanda har tana iya jin sautin shi a kunnen ta, Ta kasa buɗe ido saboda ruwan dake diga daga cikin kanta,ga kuma suma daya rufe mata rabin fuska, Hannun ta ya riƙe duka biyu ya daura a saman ƙafar shi, Suman daya rufe mata fuska yasa hannu yana maida mata dashi gefe, Kallon lip din ta yayi yanda yayi jawor yana dan motsawa saboda rawar sanyi da take yi, "Buɗe idanun ki" Kin buɗewa tayi,saboda yanda ranta ke tafasa, Ba zato taji hannun shi a saman boturan maɓallan rigar ta shara_shara na saman, Duk da haka bata buɗe ido ba, sai ma ƙara rintsesu da tayi, Duk Boturan uku ya cire,ya zame hannu rigar zuwa cinyar hannun ta,wanda hakan ya bayyana manyan kirjinta dake cikin ƙaramin rigar, Hannu yasa ya shafi saman kirjin ta sannan ya gangaro ruwa Cibiyar ta inda nan ne yafi ko'ina tsole mashi ido, Shafa wurin yake yana zagaye ƴan yatsun shi, Jin yana ƙoƙarin gangarawa kasan maranta ne yasa ta buɗe rinannun idanun ta a kanshi, Dama kuma duk abinda yake idanun shi na kan fuskarta yana karantar ko wani hawa da saukar numfashin ta,ganin ta buɗe ido ne yasa ya kuma sakin murmushi, "Wannan jikin naki ba komai bane a wuri na face madaddalan datti,in da wasu kazai mai suka gama zub da ƙazantar su a ciki suka tafi,ki sani in dai kece ko da zaki yi yawo tsirara ba zaki taba jan koda digo bane daga cikin hankalin, Domin ni mai tsafta ne,bana hulɗa sai da mutane masu tsafta, Ki kama kanki,karna kuma ganin wannan kazamin jikin naki a inda nake," Ya karasa faɗa yana shafar ƙugun ta,"ke abin tausayi ce,har yanzun baki San komai ba acikin duhu ki ke "juyawa yayi ya barta a wurin yayi shigewar shi ɗaki, Ta jima tsaye a wurin har saida ta ji ƙafarta na niman gagara ɗaukar ta sannan ta taka a hankali ta shige daki tana turo ƙofa, Tun daga lokacin ban kuma jin duriyarta ba. *Bayan Kwana Biyu* Tun bayan faruwar lamarin ta fita harkan shi,bata ƙara barin sun haɗu ba,a duk lokacin data tuna kalaman shi akanta sai ta zubar da hawaye,shi bai san komai ba dangane da ita,me yasa zai ce jikinta matattaran ditti ne,,eh tasan abunda ya faɗa gaskiya ne jikin ta akwai dauda,amma abin ne da ciyo,domin idan da ace tana da damar da zata bar wannan aikin da tuni ta bar shi,da bai kara ganin ta ba har a bada,kuma ko yanzun hakan ne ta ƙudurta a ranta,da zaran aikinta ya kammala zata yi wucewar ta, Shi yasa ma yanzun ta yanke hukuncin fita harkar shi ta ci gaba da lalube cikin duhu ko zata dace, Jin ana ƙwanƙwasa kofar dakin ta ne yasa ta rufe karamin takardar da take rubutu a ciki,ta jefa cikin durowa sannan ta zura karamin hijabi ta fito, Bala ne a tsaye bakin ƙofa "Hajiya kin yi baki a ƙasa" "Su waye? " Kannen megida ne" Daki ta koma dan canjo hijabi sannan ta fito, Khadija ce da Zainab, Ba tare data ce masu komai ba ta zauna a ɗaya daga cikin kushin tana daura kafa daya kan ɗaya, Kamar yanda suke jira ta gaishe su ita ma haka take jira su gaishe ta dan haka tayi burus dasu, Kallon juna suka yi suna jinjina lamarin, Tashi Zainab ta yi ta ajiye mata wani ɗan ƙaramin takarda "address din wurin da za'a walima ne na matan manyan malamai,kina daya daga cikin manyan baƙi,ƙarfe Goma za'a fara,dan haka sai ki same su a can," Tana gama faɗa suka wuce ba tare da sunce mata komai ba, Kallon Agogon bango tayi wanda ya nuna mata ƙarfe goma saura mintuna goma sha-biyar, Karamin tsaki taja tana mikewa tare da ɗaukar takardar, Har zata haura sama sai kuma idonta ya sauka a kan wani ƙofa wanda tunda tazo gidan bata taba shiga ba, Juyawa tayi kawai ta doshi dakin cike da tunanin me a ciki. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *38* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Turo ƙofar dakin tayi wanda yake da duhu,da hasken wayar ta tayi amfani ta kunna wutar dakin, Shiru tayi kawai tana kallon ko ina yanda duk aka rufe kayan dakin da fararen kyalle, Kalle_kalle take yi cike da tunanin ta buɗe ne ta duba ko zata samu wani abu ko kuma ta fita,dan da alama dakin ya tara kura sosai na alamun an daɗe ba'a yi amfani dashi ba, Da kushin ta fara,buɗewa tana yi tana tari saboda kura,ganin zai takura mata ne yasa ta zame ɗan kwalinta ta daure hancinta dashi, Duk wani abunda aka rufe sai da ta buɗe, Dafe kwankwaso tayi tana kallon dakin kafin idon ta ya sauka a kan wani babban Enlargement mai ɗauke da hoton Ahali, A hankali take takawa har ta isa wurin da hoton yake,sai dai saboda tsananin kura ba'a ganin fuskokin wasu,hakan yasa ta saka hannu ta share, Akan wata tsohuwar mata mai kama da Baturiya idanun ta ya fara sauka,tana zaune yayin da wasu Maza su biyu suna zagaye da ita,sai kuma wanda take da tabbacin Suraj ne,dayar matar dake gefe kuma kamar Ammi kamar ba ita ba,tana dai ɗan kokonto,sai kuma ta kasan matar in da nan ma wani mutum ne shima kamar Bature ya rike hannun ta yana dariya, Shiru tayi tana nazarin hoton,to su waye waɗannan,tana buƙatar sanin su,sannan ina suke yanzun, Ɗaukar hoton tayi ta juya baya ko zata ga number gidan hoton kamar yanda sukan saka wani lokaci har ma da sunan gidan hoton, Sai dai duk yanda ta duba bata ga komai ba,hakan yasa ta mai da ta ajiye, Daukar na kusa da shi tayi,baki ta saka tana hure kuran, Tari ta hau yi saboda shaka da tayi, Ajiyewa tayi ta jawo farin kyallen da saka rufe hotunan dashi ta goge,sai dai wannan hoton Suraj dinne da wannan mutumin dake tsugunne gaban Kaka,sai dai kamar ba'a Nigeria aka dauki hoton ba, Haka dai ta dinga cin karo da hotuna na mutanen da take kwadayin sanin su waye su,sai dai tasan a yanzun babu mai bata amsa,dan wanda take da yakini shi zai bata amsa tasan ko ƙwaya taci bata isa ta doshi in da yake ba da wannan zancen, Duba Agogon wayar ta tayi,da sauri ta zari ido ganin ƙarfe goma sha ɗaya harda mintuna ishirin, Maida kayan tayi ta rufe cikin sauri ta bar dakin ta koma daki ta shiga wanka, Tayi ƙoƙarin koma dai menene sai ta nimo amsar su waye waɗannan na jikin hoton, Tana fitowa mai kawai ta shafa sai janbaki pink data ɗan mussika kaɗan sai giran ta data gyara, Doguwar rigar Jallabiya maron kolo ta saka sai hula shima marun kafin ta naɗe karamin ɗan kwalin ta yafa a kanta, Agogo ta makala a hannun ta sai karamin jakka,wani katon gilashi ta saka wanda ya kusa mamaye mata rabin fuska, Masha Allah,sai dai maƙiyi,ko shi sai dai ya kushe dan bakin ciki,domin ta fito a YAR TSANAR ZINARI,tsabar kyau,duk in da ta juya kamshi kawai ke tashi, Kayan ya bala'in mata kyau ne dan Jallabiyar tasha duwatsu wanda ko su abin jan hankali ne, Ta inda ake ajiye makullan mota a durowan falo ta tsaya,kallon keys din tayi,hannu tasa ta dauki wani mai kalan ja ajikin shi dan zuciyar ta ya bata kila na jan motar nan ne, Tana fitowa wurin parkin ta danna makulli sai gashi motar tayi kara, Murmushin ta saki sannan ta doshi motar wanda yake kalan kayanta ta shige,tana sauke ajiyar zuciya,tare da shafa sitiyarin motar, Jin ana kwankwasa Glass din motar ne yasa ta saukar dashi ƙasa, Cikin tsoro direba yace"Hajiya fita zaki yi" "Eh" "Fito sai na kai ki" "A'a ka barshi zan je da kaina" Ganin kamar ya shiga tunani ne yasa kafin ma ya ankara sai gani yayi ta kunna motar ta doshi Get wanda tana zuwa ya buɗe mata ta fita da mugun gudu, Mamaki yake dama ta iya mota ne ko yaya, A'i ta kira akan taimata kwatancen Address din da aka bata, Da taimakon ta dana sign bord,ta isa katafaren dakin taron wanda daga gani ba na wasa bane yanda wurin ke ɗibar mutane,gabaɗaya duk mata ne a dakin domin taron nasu ne,wasu sun zo ne dan jin irin wa'azin matan manyan malamai zasu yi,yayin da dayawa a cikin su sun zo ne domin ganin wata mai sa'a ce ta samu nasarar aure tauraron su, Ita sam bata masan cewa akwai motoci biyu dake biye da ita a baya ba sai da tayi parking tana ƙoƙarin fitowa taji an buɗe mata mota, Kallon mutumin tayi mai sanye da bakin kaya "Malam kai kuma waye? Ta tambaye shi tana karasa fitowa, " Mu masu tsaran lafiyar ki ne,yallabai ya turo mu domin baki kariya " Cikin mamaki tace"wani yallabai,"dan har zuciyar ya fara karkata wani wuri, "Yallabai Suraj" "Suraj" Ta maimaita sunan mamakin ta na ƙaruwa,to me ya same shi zai hada ta da masu tsaro,anya kuwa shine?ta yaya akayi kuma yasan ta fito, "Da yaushe kuke bina"ta kuma jeho ma mutamin tambaya, " Ranki ya daɗe tunda kika fito gida" Ɗaya daga cikin sune shima sanye da baƙaƙen kaya ya iso inda suke"ranki ya daɗe an sanar da isowar ki yanzun ke kaɗai ake jira" To fa sabon salo,ko me yake nufi da duk wannan abun ohho, Cikin takun kasaita ta nufi Hall din tamkar wata Sarauniya,dama ya lafiyar kura yake balle an samu nama,in dai batu ne na iya tafiya tamkar Hawainiya to salo_salo ta iya, Tunda ta doshi Hall din yayi shiru yanda kasan ana jira aga waye zai shigo haka idanun su ke tsaye a kan kofa, Basu kadai ba har da yan gidan su dake zaune a wurin su Aunty Hajjo da Aunty Atuwa,Maijiddarh,da sauran yaran gida mata, Dariya Aunty Atuwa ke yi kasa_kasa tunda taji an sanar da isowar ta, Maijiddarh ce ta zungureta "wai Aunty dariyar me kike gaka tun dazu " "Jira nake naga ta shigo,Allah yasa dai ba katon rigar nan data saba sakawa tasa ba,ai kuwa data kunyatar da Suraj" "Ai shi ya nima,maganin shi kenan,kina tunanin ko hawa stage ƙaramin aiki ne,kalle fa mutanin dake nan an fi dari da hamsin,ko idon wani ya isa tsorata ka,balle ita ƴar ƙauye" "Ke dai bari muga yanda zata kaya"Aunty Atuwa ta faɗa da murmushi a fuska ta, Amira ce kamar zata fashe da kuka ta rike hannu Zainab "ni dai zan fita,ba zan iya jure wannan abun ba" "Ai gara ki tsaya dai muga yanda za'a kare" "Kofa karatu bata yi ba,idan ta hau nan me zata ce,ta ina zata fara" Kofar da malamai ke shigowa da aka buɗe ne ya kuma jan hankalin mutane, Cikin natsuwa ta karasa gaban sauran malaman dake kujeru na musamman ta shiga mika masu hannu tana masu sallamah,yayin da matar dake tsaye da mic take sanar da cewa ga Mata muka Amarya ga Ustaz Suraj,wanda mutane suka fi sani da Young Ustaz, Wannan shi ake kira da kallo ya koma sama,domin ko waɗanda suka santa da kyar suka shaida ta, Zama tayi a kujerar da aka nuna mata, Sannan aka cigaba da wa'azin, Kamar wasa taji an kira sunan ta akan ana buƙatar tayi ma mutane nasiha aka wani abun,suka bata zaɓi, Murmushi kawai ta saki wanda ya ƙara tafiya da zuciyar mutane, Tashi tayi cikin takun nan nata na isa ta amsa mic din, Sallmah ta fara ma mutane kafin ta fara jawabi akan muhimmancin suturta jiki ga mace musulma,yayin da take kawo aya da hadisai tana haɗawa dasu,ta fassara,ta gefe ɗaya kuma takan sako turanci wanda jifa_jifa take yin shi, Hall din yanda kasan mala'ikan mutuwa ya gifta tsabar shiru,ba kajin komai sai hawa da saukar numfashin mutane, Muryanta kadai daya karaɗe wurin abun sauraro ne,har balle kuma idan tana jawo aya da hadisai yanda kasan ba daga bakinta yake fitowa ba, Maganganun ta sun ratsa zuciyar mutane,sun motsa ruhinsu,sun kuma girgiza wasun su,yayin da wasu kuma suka yi mutuwar zaune, Tana kammalawa nan Hall ya cika da kabbara ta ko'ina,yayinda da malamai ke jinjina sa'a irin na Suraj da wayau irin nashi,wato sai da ya zaɓa ya darje ga kyau ga kuma ilimi, Cewa tayi idan da me tambaya yana iya yi domin tana da uzuri zata wuce, Amma ta bada dama tambaya uku kawai zata amsa sauran kuma sauran malamai zasu amsa masu, Mutane uku da suka fara ɗaga hannu aka ba dama, Ta farkon tana cikin masoyan Suraj,dan haka tambayar data fara yi shine akan abunda ke cikin zuciyar ta "Malama Habiba tambaya ta na farko anan shine su waye iyayen ki?ta yaya kika samu nasarar sace zuciyar mutum kamar Young Ustaz Suraj?ko zaki bamu shawara akan muna zamu iya cikin nasara akan wadanda muke so? Wannan shine tambaya ta" Tana gama faɗa ta zauna, Shiru Hall din ya kuma ɗauka kowa ya tsura mata ido yana jiran jin me zata faɗa, Duk da tambaya na farko ya daki zuciyar ta har ya so saka ta girgiza,hakan yasa tayi saurin ƙara kame kanta,sannan ta saki murmushi "well yammata da ace tambata kika yi akan wace ni zan baki amsa,amma duk da haka zan faɗa maki,iyayena sune Suraj,abokai na sune Suraj,ƴan uwa na sune Suraj,dangi na sune Suraj,because Suraj is my husband,he is my Father,My mother,my Aunty,my every thing,that is who I am" Ta karasa faɗa cike da kwarin gwiwa, Kafin kace me Hall ya kara rikicewa da Kabbara harma da ihu da shewa,domin ba karamin burge mutane tayi ba da wannan amsar nata,yayinda wasu da yawa ke ɗaukarta Video,kafin kace me har wannan kalaman nata sun fara zagaye akan social media, Ganin yanda Hall din ya rikice ne yasa kawai tai ma malaman sallah ta fita abunta ita kanta farin ciki ne ya kamata,ba dan komai ba sai dan ganin ta kubuta daga wannan tambayar,ta kuma ba da amsar daya dauke hankalin mutane. __________ya fito daga Asibiti kenan dubo Grandma ya shiga mota zai koma gida sai ga kiran Ammi daga Nigeria,dan tun ranar da suka yi faɗa ya jikata da ruwan sanyi ya bar garin da yamma zuwa Germany duba Grandma da jikinta ya kara tashi, Daukar wayar yayi ya ƙara a kunne yana amsa sallamar ta, Daga ɗayan bangaren tace"Suraj kaga abunda yake faruwa kuwa" "Meke faruwa Ammi" Ya tambaya, Yana iya juyo sautin murmushin ta "hau online yanzun zaka gani" Dayar wayar shi ya dauko ya kunna data,sai ga saƙonni suna ta shigowa, Buɗe wanda ta turo mashi yayi, Tun daga farkon fara wa'azin ta har zuwa tambayar da aka mata da amsar da ta bayar ya kalla, "Son ina tunanin wannan karon mun dace" "Ba hakan ke nufin zamu sake jiki ba" "Haka ne,amma na yaba da kwazon ta,nasan kuma zata iya" "Ina fatan haka,sai dai juriyar ne kamar zai mata wahala" "Ni ma na fahimci haka,amma dai muci gaba da saka ido mu gani" "In sha Allah Ammi" "Ka haɗu da shi kuwa? " Sai daya tunda nazo" "Kayi taka tsantsan Allah ya tsare ka,yaushe saka dawo" "Nan da kwana biyu in sha Allah,in na kara ganin yanda jikin nata ya kasance" "Shikenan Allah ya bata lafiya" Da Amin ya amsa yana sauke wayar, Shiru yayi yana dan nazarin kalaman nata,kara kunna Video din yayi yana kallo, tsayar dashi yayi dai_dai inda take faɗin he is my every thing, Dan guntun murmushi ya saki wanda idan bawai idanun ka na kan fuskar shi bane ba zaka taba Fahimtar yayi shi ba,kafin bakin shi kuma ya furta"this girl ba"sai kuma ya kauda kai yana maida kallon shi akan manyan gine-ginen da suke ta wucewa,can kuma ya kara furta"Stubborn"yana lumshe ido cike da tunanin abunda ya faru dazu, Wato lokacin yana Asibiti aka kira aka sanar dashi batun zuwanta taro da aka gaiyaceta,wanda ya sanar dashi ya so ya hanata zuwa amma yace karya ce komai ya bar komai a hannun shi,duk da ya san manufar gaiyatar ta da akayi wanda ita bata sani ba, Shi ya saka securityn shi suka mata jagora har kuma yanzun da take hanyar komawa gida yana jin komai, Buɗe mashi kofar da baturen direba yayi ne ya tabbatar mashi da sun iso, Hakan yasa ya buɗe idanun shi yana saukewa a makeken gidan wanda kallon shi kadai da tsaruwarshi ya isa ya kara ma mai rai imani, Yayinda shi kuma a nashi bangaren kallon gidan da rayuwa a cikin ta yana tuna mashi da Asalin waye shi ada da kuma yanzun.. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *39* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Wanda ya tuko ta acikin motar data tafi dashi ne kaɗai ya shiga har cikin gidan yayi parking wurin ajiye motoci sannan ya fito ya buɗe mata,dan tayi_tayi su bari ta tuka motar amma suka hana,dole ta shiga baya ta zauna cikin jin haushi har suka iso gida, Tana fita a motar cikin falon ta shige sannan ta wuce dakin ta,cire kayan jikinta tayi ta shiga banɗaki ta watsa ruwa dan sam bata jimirin zafi,in dai zata shiga rana ko yaya ne sai tayi wanka in ta dawo, Tana cikin duba kayan da zata saka ne wani tunani ya faɗo mata, Dan haka cikin hanzari ta kasara shirin cikin doguwar riga mara nauyi sannan ta fito, Akwatunan da aka kawo mata wanda har yanzun suna nan bakin ƙofarta ta sauko da yaɗa wanda bata masan me a ciki ba, Da wayar falo tayi kira akan sarkin gida ya turo mata Bala tana son ganin shi,amsa mata yayi da an gama, Dan haka zama tayi a daya daga cikin kushin din tana bude akwatin wanda hijabaine sai kyalulluka da takalma, Shigowa yayi ya tsugunna a gefe "ranki ya daɗe gani" Buɗe marfin akwatin tayi gabaɗaya ta shiga juya kayan ciki tana yamutsa shi ta yanda yake iya gani komai na ciki, Yamutse fuska tayi"kayannan duk basu min ba"kallon shi tayi"Bala matan ka nawa ne na duba naga ko a wai abinda zai matsu? Ai kuwa nan take ya shiga washe baki yana ƙara leken kayan,ai shi wallahi in dai ta bashi wannan aure kawai zai kara,"Mata ta daya ce amma ina zaune tare da mahaifiyata,amma dai in na samu dama Hajiya zan ƙara ta biyu" Hijabai biyu ta ciro ta ajiye a gaban shi,"gashi sai ka basu kowa dai daya " Da sauri ya jawo su gaban shi ta rungume yana kara washe baki"na gode Uwar daki na,gaskiya Yallabai yayi dacen mace ta gari,ai daga ke babu ƙari " Murmushi ta saki,tana kara ajiye mai sunkin sabulu a gaban shi,"ai babu komai Bala,ai ya faɗa min ka jima kana aiki a gidan nan" "Ah sosai ma kuwa,domin na kai shekara goma sha biyu ina Girka ma maigida abinci" Takalmi ta kuma tura mashi gaban shi "A'a lallai ka daɗe,kace ka zauna da surukarta na" "A'a ban zauna dasu sai dai lokacin Kakan mai gida tana zuwa lokaci-lokaci ta duba shi" Juya ido tayi,tana kara mika mashi wani takalmin"yanzun ta daina zuwa kenan ? Gyara zama yayi"ai in faɗa maki rabona da ita tun wani zuwa da tayi har tati ma maigida girkin irin abincin su na turawa ra zubo mana,tunda nake ban taba cin abinci mai daɗi ba irin wannan " "Ai sun iya girki sosai, to bata ƙara zuwa bane? " A'a bayan komarta da kwana biyu wasu mugayen ƴan ta'adda suka shiga gidan suka harbe ta," Rike baki tayi "su ko me tsohuwa tai masu? " Ai in faɗa maki,a yanda naji wai akwai wani abu mai matukar daraja da suka sata a gidan,kuma wannan abun tun zamanin kakanta ita ma ta gaje shi,to shine suka dauke, Tsayin shekara goma sha ɗaya kenan tana cikin doguwar suma har yau bata farka ba,shi yasa duk bayan wani lokaci maigida yana zuwa ya dubata,ai ina ga ko yanzun ya tafi can ɗin ne ko kuwa? Ya karasa faɗa yana tsare ta da ido, Cikin sauri tace"Eh haka ne,ai muna waya dashi"dan bata son yayi zargin komai, Jakkan ratayawa guda biyu ta mika mai"amma me suka sata a gidan? "Wama ya sani,ni wallahi bansan ko me suka sata ba,amma dai na tabbatar koma menene abu ne mai matukar muhimmanci" Ɗan shiru tayi kamar me tunani"to amma an kama wadanda suka aikata aikin? "A'a har yanzun da nake baki labari babu labarin waɗannan mutanen,sai dai kuma wasu na zargin idan Kakan nashi ta tashi zata San wadanda suka aikata mata haka" To me wannan me muhimmanci da aka sata,su waye kuma suka aikata wannan aiki, Mai da kallon ta kanshi tayi"yama sunan garin da kakan nashi take" "Tana can dai ƙasashen turawa,ba kin ce kuna waya ba,hala bai faɗa maki bane? Dan murmushi ta kakaro" Ya faɗa mun kawai manta sunan garin nayi,yauwa bayan Kakan shi babu wasu yan uwa dake zuwa nan din a wancan lokacin? "Eh kawun shi ne ko waye,kamar dai kanin Kakar shi ne naji yace a wancan lokacin shine yazo sau daya,kuma bai ƙara zuwa ba? Da sauri ta mike tana turo mashi akwatin gaban shi," Ka dauki akwatin duka,duk abinda bai maka ba ka zubar"ta faɗa tana barin wurin, Tsabar daɗi har da rawar murna sai da yayi, Tana shiga daki da sauri ta jawo durowa ta falli takarda ta dauki Biro, Rubutu ta fara kamar haka, Kakan shi,sai kuma sata,alamar tambaya ta saka a wurin,to me aka sata,wani irin abu ne haka,sannan su waye suka aikata satan, Shiru tayi ta shiga dogon nazari,to ita yanzun wannan takardar da aka ce ta dauko me amfanin shi,tabbas takardar ba gida bane,ko kamfani,takarda ne,wani irin buɗe ido tayi kafin a fili ta furta"ba dai yana da Alaka da wancan satan ba"girgiza kai tayi"inaa hakan ba zai yu ba,"har gitsa suman kanta tayi"Ya Allah me yake faruwa ne,shin wani irin aiki nake yi,wa kuma nake ma aiki,"sai dai fa idan har zargin ta zai iya kasancewa gaskita takardar nada Alaƙa da wancan aikin to shi kuma VIP kenan koma waye shi yana da masaniya a kan komai, Ajiyar zuciya ta sauke,kai hakan ba zai taba yuwa ba,ai shi wancan aikin ma shekara goma sha daya,kenan da suka yi fashin, Ita kuma wannan aikin nata data fara har auren bai wuce wata biyu,dan haka ba yanda za'a yi hakan ya faru, Sai dai koma waye VIP sai ta binciko shi duk inda yake a duniya,haka koma menene waɗannan takardun suma sai ta bincikosu domin ta nan ne kawai zata iya samun duk wani amsoshin da take buƙata,kuma shine makamin duk wani yaƙi da zata gabza har ya kai ta ga duk wanda take son gani, Sai dai babban matsalar shine ta yaya zata iya yin haka,ta ina zata samu wannan takardar. Jin karan da wayar ta keyi ne ya dawo da ita daga dan gajeren nazarin da take yi, Ganin me kira ne yasa gaban ta faɗuwa,dan cikin sauri ta ɗauki wayar tana karawa a kunnen ta, "Me kika samu" Abu na farko da aka fara faɗa kenan daga ɗayan ɓangaren, "Ina Ummita? " Me kika samu? Ya kara maimaitawa, Ta lura idan ba har ta bashi amsar tambayar shi bane ba zai taba amsata ba, "har yanzun ina kan bincikawa,amma ban samu komai ba har yanzun,sai dai ina ganin kamar waɗannan takardun basa cikin wannan gidan" Tsaki taji an ja"to me nufinki a tunanin ki,shi din ya fiki wayau nisa ba kusa ba,sai dai ina da tabbacin duk wayau shi yana da lago,shi zaki nimo ki yi amfani dashi har ya kai ga faɗa maki in da suke,domin shi kaɗai yasan in da suke" "Ta yaya zan yi haka? " Ke matar shi ce kin fini sanin haka,na baki nan da kwana biyu,idan banji labari mai daɗi ba kome ya biyo baya sai ki yi maraba dashi,domin nima banda isasshen lokacin" "Ummita fa? " Nan da kwana biyu zaki ganta" Kafin tace wani abu har ya katse kiran,to me yake nufi da nan da kwana biyu zata ganta, Ita kan ta shiga uku,kwana biyu kam ya mata kaɗan ta ina zata fara, Mikewa tayi ta nufin dakin shi,gara ta fara binciken dakin ko zata samu wani abu, Tama yi tunanin zata ga dakin a rufe,sai dai a buɗe yake dan haka shiga tayi ta fara duba duk wani lungu da sako na dakin wanda tayi kusan awa biyu ba tare da taji ta gaji ba,har addu'a take akan Allah yasa ta samu wani abun,sai dai kamar yanda ta hargitsa dakin haka ta kyara dan ba abinda ta samu ko me kankantarsa, Fitowa tayi ta jawo mashi kofa ta zauna nan bakin ƙofa,gabaɗaya ta rasa meke mata daɗi,ta rasa wani kalan tunani zata yi,a haka dai ta ƙarar da wannan ranar batare da yanke me ta kamata tayi ba, Washegari da safe,ƙarfe goma wayar dakin ya shiga ƙara babu kakkautawa, Cikin gigin bacci ta dauka tana karawa a kunne, Muryar Bala taji yana fadin"Hajiya ki sauko kin yi baƙi " "Ohh Bala barci fa nake yi" "Ki yi hakuri ki sauko domin yan uwan Ubangida na ne suka zo,kamar ma harda iyaye" Kashe wayar tayi tana jan tsaki, sannan ta shiga banɗaki tayi wanka cikin gaggawa ta saka doguwar riga na Atamfa wanda yaji aiki, Tunda take saukowa daga saman bene suka kureta da ido,yayin da kamshin turaren ta ke sanar dasu isowar ta gare su, Cikin jirmamawa ta shiga gaida su,duk da wasu sun amsa wasu basu amsa ba, Ganin an kawo masu ruwa da abun motsa baki ne yasa ta zauna ita ma a daya daga cikin kujerun falon, "Sannun isassah,muna saman kushin kina sama babu ko ɗan girmamawa"cewar Hajiya Rahama, Hararan gefe tayi" Momy ai yanzun kin san level ya ƙaru " Duk buɗe baki suka yi suna kallon ta"ah lallai level ya karu,baƙauye ya karo wulaƙanci " "Sosai ma kuwa Goggo tunda gashi Baƙauyen ne ya samu nasarar shiga gidan sarki" Duk sun gane inda ta dosa,dan haka mikewa suka yi "zamu tafi ina Suraj,ko shi yafi ƙarfin fitowa ya gaishe mu" "Barci yake yi domin jiya da daddare yayi aiki ya gaji,bamu yi bacci da wuri ba" Daya bayan daya suka fita suka bar falon ba tare da sun kuma ce mata komai ba,lallai ashe ita din Kura ce mai lulluɓe da fatan Akuya,jiya sun ga Video da aka mata a wurin wa'azi,shine kaka ta haɗa su taimasu faɗa akan ba su je sun dubo Suraj din da matar shi ba,amma ji amma da yar iska ta faɗa masu, Ita kuma suna fita taja ƙaramin tsaki,domin ita wallahi ko kaɗan bata su take yi ba, Wani tunani ne ya faɗo mata dan haka cikin sauri ta tashi ta shige daki,durowa ta buɗe ta shiga duba Asalin Jakkan kayanta ta dauko ta zazzage, Wannan wasiƙar data taɓa satowa a ɗakin shi ta dauko, Jikinta har rawa yake yi wurin lalubar number shi,kira biyu ya ɗauka ba tare da yace komai ba, "Na samu wani abun" Ta faɗa da kwarin gwiwa, "Ina jinki" "Wasika ce dana samu a dakin shi," "Akan inda takardar yake ne? " A'a sai da an ruba *Hadarin dake sararin samaniya yayi baƙi kirin,kuma daf yake da saukar da baƙin ruwa mai mugun dafi, da fatan za'a shirya ma ƙwaryar taran shi* abinda ke cikin wasikar dana samu kenan, Dariya taji ya sheke dashi kafin yace"ai kuwa ruwan ma yafara sauka sai dai bansan ko da wani irin ƙwarya zai iya taran shi ba" "Me kake nufi" "Koma me nike nufi daga nan zuwa gobe zaki ji" "To Ummita fa"ji tayi ya kashe wayar dif yayin da take jin sautin dariyar shi a ranta,haka kawai kuma sai taji gabanta na faduwa kafin wani irin tsoro ya shige ta," Me yake nufi?me zai faru a gobe?ita fa ta lura kamar daga jiya zuwa yau ta rame tsabar fargaba,ƙoƙari tayi ta cire abun arai,sai dai duk yanda tayi ta kasa sai ka ƙara shiga fargaba da take yi, Ganin ta kasa jurewa ne ya ta fito daga falon tana kira Bala, Da sauri ya karaso "Hajiya gani" Ya faɗa cikin girmamawa dan tun kyautar data mashi ya shiga kara girmamata, "Kana da lambar Ubangidan ka na kasar waje? " A'a ba ni da shi sai dai Sarkin gida ba zai rasa ba saboda ko wani abun ya taso" "Yi sauri ka kiramin shi" Har zai fita sai kuma ya juyo"amma baki da number ne Hajiya? "Ohh kai dai da wannan tambayar,to numbobin waya tane suka goge" Dan dariya tayi"ok ok na gane,in ba haka ba ai da sai nayi mamaki"ya karasa faɗa yana fita, Tama kasa zaune ta kasa tsaye,ganin ya jima ne yasa ta fita dan gara ta bishi ta amsa da kanta,dan gani take kamar ko wani dakika ta kara kamar barazana ce a gareta, In da tasan sarkin gidan ya cika zama nan ta nufa,yana ganin ta ya mike yana amsar takardar da yake mika ma Bala, "Hajiya da kanki,ai da sai ki bari na zo" "Kaga sauri nake bani number" Mika mata takardar yayi"wadannan sune numbobin da yake amfani dasu guda uku, Daya na Paris ne,dan yace a kwai aikin da zai tafi yi a can,amma ban san ko yaje ba,in dai yana can to zaki ga number dana rubata Paris,sai biyu kuma na Germany wanda idan yana can shima yafi amfanin da layukan,kuma idan yana nan ma wani lokaci yana amfani da dayar" Da sauri ta juya tana fadin "na gode" Daki ta koma har da saka key,sannan ta zauna ta shiga loda number ta farko a wayar, Har ta kammala tana ƙoƙarin danna kira wani tunani ya fado mata,to yanzun idan ma ta kira shi me zata ce mai,me zata faɗa mashi,me kenan take kokarin aikatawa, Da sauri ta sauke hannun ta daga kan wayar,amma kuma kaso casa'in na zuciyar ta ba karfafa mata guiwar koran shi, Ta ma rasa me zata kama,shin ta kira ko karta kira. *fans Yar tsanar zinari na niman shawara,shin ta kira Suraj ko karta kira shi*..... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *40* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Kafin ta sani sai ji tayi ana Sallamah, Da sauri ta kara wayar a kunne sai dai sam ta kasa magama,dan jin muryar shi kaɗai da tayi yasa taji faduwar gaban ta ya ƙaru a maimakon raguwa, Shima daga nashi ɓangaren jin shiru ne yasa shima yayi shiru yana sauraran yanda take sauke numfashi a hankali, "Idan kinsan ba kida ƙwarin gwiwar yin magana me na kira? Cikin mamakin abinda ya faɗa tace" Ya akayi kan nice " "Tambayar da kika kira kimin kenan? Turo baki tayi" To nama fasa faɗa tunda abinda zaka ce ke nan" "Shiken " Ya faɗa yana ƙoƙarin sauke wayar, "Wait, wai kai mai yasa baka iya lallashin mutum bane?yanzun baka son kaji me zan faɗa?ka sani ko abunda zai amfaneka ne? Dan murmushi taji yayi wanda kaɗan sautin haka ya sauka a kunnen ta," Daga dukkan alamu yau Mage a tsorace take,me ya faru? Dan shiru tayi kamar mai nazarin abin da zata faɗa,ta kwashi kusan mintuna goma ba tare data iya furta komai ba,yayin da shi kuma yayi shiru shima yana sauraren yanda Lokaci-lokaci take sauke numfashi ba tare daya ce mata komai ba kuma bai kashe wayar ba, Sai da ta gaji da saƙawa da warwarewa kafin tace"ina ganin kamar akwai abinda ke shirin faruwa" Jin shiru yayi ba tare da an bata amsa bane yasa ta cire wayar a kunnenta ta duba,ai kuwa har lokacin yana kan layi,hakan yasa ta maida wayar kunnen ta"kana jina kuwa? Nan ma sai da aka dauki ƴan sakanni kafin taji yace"Umm " A hassale tace "to baka ce komai ba? "Ina jinki" "Ai Nasan kana jina" Kamar wanda baya son maganar yace"me zai faru? Wannan karon ta kasa rike bacin ranta dan haka cikin masifa tace "ban sani ba,idan ka ga dama duk in da kake sai ka kiyaye idan kuma ka yi sake ka rasa rayuwar ka kai ka sani"ba tare data jira taji mai zai ce ba ta kashe wayar,dan ba karamin haushi ya bata ba,haka kawai tana ƙoƙarin taga ta ankaran dashi amma ya tsaya yana nuna mata miskilanci,tsaki ta ja,tana ƙoƙarin tashi ne taji saƙo ya shigo wayar ta,kamar ta share sai kuma ta bude "I know you need me a life" Abinda saƙon ya kumtsa kenan, Ta maimaita ya kai sau nawa amma ta rasa gane ina ya dosa, Yinin ranar tayi shine ba'a cikin natsuwa ba,domin hankalin ta a tashe yake,bata san me zai faru da ita ko shi ko Ummita ba,idan har suka ci nasara akan shi kamar sun samu nasara ne a kanta,idan kuma wani abune ya samu Ummita bata masan me zata iya aikatawa ba nan gaba, Abunda ta jima rabonta da tayi shine yau ta tashi tana yi,wato Sallah Nafila wanda rabon da tayi ta kai shekara uku zuwa huɗu. Anashi ɓangaren kuwa yana gama tura mata sakon ya maida kanshi ya jinginar yana rufe idanun shi yana nazarin kalamanta,sai dai baya son ya kawo komai a ran shi, Jin ana kiran Fasinjojin da zasu tafi Nigeria ne yasa ya tashi ya ƙarasa,dan yanzun jinginsu zai tashi,wanda zai sauka ne a Legos, Bayan kammala duk wani bincike aka basu dama suka shiga jirgi,bakin shi dauke da Addu'a,ƙarfe shidda na yamma jirjinsu ya sauka a Legos, Duk yanda yaso ya kwana a gida dole hakura yayi ya kama Hotel saboda ma'aikatan airport din sun tabbatar mashi da babu jirgin Kano sai dai zuwa gobe da safe ƙarfe goma, Dole ya hakura, Babban daki ya kama na kwana daya a babban Hotel din daya sauka,wanka ya fara yi sannan yayi ordan Abinci yaci, Ganin lokacin sallah Isha'i yayi ne yasa ya fito daga dakin bayan ya kulle ya fita domin duba ko akwai inda zai samu masallaci kusa,dan sam baya son yin sallah shi kaɗai a gida ko a daki indai ba ya kama bane, Tafiya yake yana ɗan duddubawa kafin Allah ya taimake shi ya samu,lokacin ana ƙoƙarin tada sallah,duk da yake masallacin na Yarbawa ne hakan be dame shi ba domin Allah daya suke bauta ma,dan haka yabi su Jam'i har aka idar sannan ya koma masaukin shi,har ya kusa isa daki yaji kamar ana magana ana kuka ta wani lungu,kamar dai ya share sai kuma ya matsa ta wurin yana lekawa, Wani mutumin ya gani daga dukkan alamu ma'aikacin wurin ne,dan sanye yake da kaya irin na masu aiki a kicin, Waya yake yana sharban hawaye, Ganin Suraj din tsaye yana kallon shine yasa ya yanke wayar da sauri yana tambayar shi da harshen Turanci,"ko akwai abinda yake buƙata ne? Girgiza mashi kai kawai yayi alamun babu,har mutumin zai wuce sai ya dakatar dashi,yana tambayar shi me ya same shi yake kuka" Kamar bazai faɗa ba amma ganin yanayin Suraj din kamar mai kuɗi kila yana iya tausaya mashi yasa ya faɗa mashi Ƙanwar shi ce ta mutu wata biyu kenan tana Matuwari,shida maman shi dan Baban su ya mutu,kun kasa tara kudin da za'ayi bikin Binne ta,to yanzun gashi a ƙauyen su har an fara yima Mamar shi gori,shi yasa abun ke damun shi,kuma ya roki alfarma wurin aikin shi a bashi rancen dubu hamsin amma sun haka shi"ya karasa faɗa wasu hawayen na zubo mashi, Suraj mutum ne mai tausayi,wanda ba shida rowa ko kyashi,bashi da nuna Ƙabilanci ko Addini,idan zai maka abu da zuciya daya zai maka ya wuce ba tare daya waiyaye abun da ya maka ba, Dan haka cikin tausayawa yace,ba tare daya tambaye shi nawa ne kudin ba,yace"Bani Account number ka" Cikin sauri kuwa ya karanto mashi,rubutawa yayi a wayar ba tare da yace mashi komai ba ya juya yayi tafiyar shi,shima mutumin da kallon mamaki ya bi shi har sanda ya buɗe ƙofar dakin wanda kuma a daidai lokacin yaji Alart, yana dubawa Dubu dari biyu ya gani, Da fari bai yarda ba,sai da ya kara karanta sakon yakai sau biyar sannan ya tabbatar,ai kuwa tsalle ya kama shi kadai yana kukan murna da jin daɗi,bai taba tsammanin a Musulmai akwai mutanen kirki irin wannan mutumin da yaga sunan shi ya bayyana a Account din wai Suraj ba,abinda ƴan uwan shi suka kasa mai,shi kam ba zai taba mantawa da wannan mutumin ba,ai kuwa washegari da safe zai bar garin ya komai ƙauye,dan ƙanwar shi bikin gata za'a mata. Da sallamah ya shiga dakin duk da yasan ba mai amsa mashi,zama yayi kan kushin yana cigaba da jan carbinshi ya ɗauki wasu yan lokuta a haka fakin ya mike,kai tsaye banɗaki ya shiga ya leka sai dai babu komai a ciki,haka kurum yake jin wani irin a jikin shi kamar akwai abinda ba daidaiba a dakin,sannan kamar kanshin dakin ya canja mashi,har kasan gado ya duba sai dai bai ga komai ba, Mikewa yayi yana tunanin gara kawai ya fita ya masu magana a canja mashi ɗaki ko kuma yama bar Hotel din gabaɗaya,dan zuciyar shi ya fara bashi Something is not right some were,Gara ma kawai ya tafi, Har ya kai hannu zai buɗe Sif din kaya yaji ana danna karrawar dake nuna alamu ana buƙatar shigowa,da yaso ya share har ya dauko kayan shi,wanda ba komai bane sai karamin jakkan shi mai ɗauke da wasu takardu nashi, Jin yanda ake danna kararrawar babu kakkautawa ne yasa yaje ya buɗe ƙofar, Tsayawa yayi yana kallon su cikin mamaki yayin da mamakin shi ya karu a sanda daya daga cikin su yaja hannun shi ya saka mashi Ankwa yana fadin"you are under Arrest,Abisa laifin kisan kai" Wannan karon abin yazo mai ata inda bai taba zata ba,kisan kai kuma,kisa fa!inna'lillahi wa'inna ilaihi rajiun,abinda yake ta maimaitawa kenan, Shiga cikin dakin suka yi yayinda sauran mutum uku suka da suke riƙe da shi har cikin dakin, Kallon ikon Allah kawai yake yi,har zuwa sanda daya daga cikinsu ya buɗe Sif din,ta iya yuwa su basu shiga Shock ba,amma kam shi yayi suman wucen gadi yayi, Domin Gawar Mace ce makale a jikin Bangon Sif din yayin da jini ke zuba a jikinta kamar yanzun aka yanka ta,haka kuma an cire idanun ta da Harshen ta, Duk kiran sunan Jijos kawai suke kasancewar su Arna, Ko mintuna biyar ba'a yi ba,sai ga masu binciken gawa da Ƴan gidan Jaridu sun shigo dakin yanda kasan wadanda dama a shirye suke, Nan take aka shiga ɗaukar shi hoto tare da gawar, Abin karin girgiza a wurin shine Jakkan shi da aka buɗe aka samu Idon matar da kuma harshen ta a ciki, Tunda yake bai taba shiga tsananin tsoro da tashin hankali ba irin wannan,da ba ɗan karfin Addu'ar da yake yi ba da tuni shima ya yanke jiki ya faɗi, Daya daga cikin ma'aikatan ne ya ɗaga gabjejen hannun shi ya koda mai lafiyayyen Mari,"dama ku musulmai ba kuda imani,to Asirin ka ya tonu yau" Rintse ido yayi yana jin raɗaɗin marin a saman fuskar shi wanda nan take wurin yayi jawur dashi kasancewar shi farin mutum, Nan suka jawo shi suna cukui_kuye dashi suka fito dashi daga dakin, Bai ma ƙara tabbatar da abinda ke faruwa dashi da gaske bane sai lokacin suka fito dashi wajen Hotel din, Dandazon Yarbawa ne wanda suke dauke da makami akan lallai sai an miko masu shi sun ƙona shi da ranshi, Nan take ƴan sanda suka zagaye shi yayinda jifa ta ko'ina tashi yake yi suna burin dai su same shi, Cikin haka ne wani daya wurgo katon dutse bai tsaya a ko'ina ba sai gefen goshin shi,ai kuwa nan take jini ya balle ya shiga bin gefen fuskar shi, A haka suka jefa shi a cikin motar su suka wuce dashi yayi da shi kuma a nashi bangaren yake ji kamar duniyar ce ta kife gaba daya,ko kuma mafarki ne yake yi ba gaskiya bane,sai dai duk yanda yaso ya farka daga wannan mummunan mafarkin abin ya gagara,domin iduk sanda ya motsa acikin waɗannan maguzawar yake ganin shi zaune a wulaƙanci, Yau shine haka,a garin mutanen da basu san darajar musulmai ba,shi SURAJ ABDUL BASIR, Acikin abinda bai wuce mintuna ishirin ba komai ya canja. Abu kamar wasa babba magana ya kara zama gagarumin magana,domin kafin ka sani gaba ɗaya maganar ya zagaya Nigeria har ta inda baka yi tunani ba,har ta gidan TV da gidajen Rediyo duk in da ka kunna labarin dake zagayawa kenan har ta da social media an haɗa hoton shi dana gawar. ___A lokacin da Shamsuddeen ya shigo cikin tashin hankali yake nuna ma Ammi hoton nan take ta yanke jiki ta faɗi sumammiya domin ko Awa daya basu yi da gama waya dashi ba yake sanar da ita ya sauka lafiya shine kuma yanzun za'a ce haka. Ita da Kaka dole Asibiti aka kai su domin an yayyafa ruwa amma basu farka ba daga dukkan alamu doguwar suma suka yi..... *Tofa wasa farin girki* 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *41* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Tunda ta kammala cin Abinci bayan sallah Isha'i take zaune a falo tana buga Game a waya,badan komai ba dan ya ɗebe mata kadaici,ita ba gwanar kallo bace,haka kuma social media sai tayi kwana da kwanaki ba tare data hau online ba, Ji tayi an buɗe ƙofar an shigo da gudu ana kwala mata kira"Hajiya!Hajiya"dan sam bai lura da ita zaune a falo ba,ita har ma ya bata tsoro, "Bala lafiya?menene haka? Jikin shi rawa kawai yake yi yayinda hawaye bibbiyu ke suka daga cikin idanun shi, Tsoron tane taji ya fara tasiri har cikin zuciyar ta,domin bata taba ganin shi a haka ba,cikin wannan halin," Menene? Ta kuma tambayar shi a tsorace, TV ya nuna mata da hannu,"Mai gida!Oga" Ji tayi gaban ta ya yi wani irin mummunan faduwa,wanda ba zata tuna ranar data ji irin shi ba,"wani abun ya same shi ne? Shi bai masan ta ina zai fara fahimtar da ita abinda ke faruwa ba,dan haka cikin sauri ya dauki rimot dake ajiye a teble ya kunna TV wanda kamar dama jira ake a kunna magana ya ɗauka, yayin da matar ke kan sanar da cewa"Shi dai wannan shahararren Malamin wanda matasa ke masa laƙabi da Young Ustadz an kama shine Dazu da misalin karfe takwas da kwata yana ƙoƙarin tsirewa bayan ya kashe matashiyar budurwar ya kwakwale idanun ta da harshen ta,wacce har yanzun ƴan sanda basu gama kammala bincibe ba akan wacece ita wannan matashiyar sannan wani alaƙa ne a tsakanin su, Yanzun haka dai shi mai laifi yana hannun hukuma domin zanga-zangar da matasa garin Lagos suka tada akan sai hukumar ta mika mashi su sun kashe shi, To masu kallon mu duka_duka anan muka kawo karshen labaran mu sai kuma kun jimu gobe domin jin yanda wannan Al'amarin mai matukar girgizawa zai kasance domin yanzun haka malamai suna kan tattaunawa akan wannan lamarin" A tsaye take amma ji tayi wani irin gizo yana rufe mata idanu,bata iya ganin matar da kuma hoton shi dake gefe tare da gawa, Ragab ta faɗa kan kushi,ta dai ga bakin Bala na motsi yana hawaye amma kuma sam bata jin me yake faɗa, Ruwa masu sanyi a kofi ya miko mata, Ganin ba tada niyar karba ne yasa ya ɗauki hannun ta ya Daura mata kofin a sama,dan ya gama alama ita ma kamar ƙoƙarin suma take yi, Ganin yana mata alama da hannu a kan ta sha ruwan ne yasa ta kafa kai kuwa sai da ta shanye tas sannan ta mika masa Glass cup ɗin, "Bala" Ta kira sunan shi, Da sauri ya amsa, Nuni tai mashi da TV"me matar nan ke faɗa ne,? Kuka ya kuma fashewa dashi sannan ya shiga yi mata karin baya ni,yana kuma faɗin "yanzun haka yanda na samu labari mahaifiyar oga da kakar shi suna gadon Asibiti a kwance rai hannun Allah,ki duba Facebook zaki ƙara samun bayanai dan abun tuni ya zagaya ƙasa" Duk da irin jirin da take gani wanda ba komai ya jawo shiba sai bugun zuciyar ta daya karu fiye da ka'ida sannan ga Shock da abin yazo mata dashi,"Suna wani Asibiti ne? "Suna asibitin Nasarawa" Dafa kushin tayi ta mike "mu je ka kai ni" "To dauko Hijabin ki mu je" "Doguwar riga ce a jikinta mai ƙauri kasancewar ana sanyi sai hula data saka, Ba tare data bashi amsa ba ta fita daga falon tana dosar wurin a jiye motoci, Ganin haka ne yasa da sauri yashiga kwalama direba kira, Kokafin ya iso har ta zauna a mazaunin direba,hannun ta mika mai " Bani key" Yana ƙoƙarin mika mata ne Bala ya amsa da sauri yana hararan shi"kana da hankali kuwa?a haka a wannan halin kake tunanin zata iya tuki da kanta " Juyowa yayi ya kalle ta cikin kwantar da murya yace"Hajiya fito dan Allah a kai ki,kin ga dare ne ga kuma halin da Kike ciki,kuma ba lallai bane k gane Asibitin " Fadin haka ne yasa ta fito ta koma gidan baya ta zauna,tabbas ya faɗi gaskiya domin hankalin ta baya jikin ta,duk da bata zauna tare da shi ba na tsayin lokaci ba amma ta tabbatar shi ba kalan mutumin da za'a ce yayi kisan kai bane,No way,babu ta yanda hakan zai faru,sai dai ita tun jin wannan labarin ta san Shiri ne mai matukar karfi,wanda fito dashi sai Allah, Idan har suka yi nasara a kanshi,to tabbas ta san mutuwarta ce ta ke gabatota, "Dan Allah ka ƙara gudu" "To Hajiya" Cikin mintuna kalilan suka isa katafaren Asibin, Da sauri ta fita duk da bata san ata ina zata gansu ba amma ta tabbatar koma ta ina ne dole suna Emergency, Cikin ikon Allah ma suna Shiga da Nurudeen suka fara cikin karo yana ƙoƙarin fitowa, Cikin sauri ta karasa inda yake tana kiran sunan shi, Ganin ta ne yasa ya dakata yana fuskantar ta,"ina su Ammi,ina kaka?meke faruwa? Ganin yanda duk take a rikice yasa yace"ki kwantar da hankalin ki duk suna lafiya,mu je ki gansu " Bin bayan shi tayi da sauri har suka isa wani kofar daki dake VIP world,in da anan taga sauran mutanen gida kowa ka gani hankalin shi a tashe yake,buɗe mata kofar dakin da Ammi take ciki yayi, Da gudu ta karasa shiga tana rungume Ammi tare da fashewa da kuka, Rungume ta tayi ita ma tana jin hawaye na saukowa daga cikin idanun ta,Allah ya gani tana matukar son ɗanta,bata fata wani abu ya same shi,kamar yanda aka samu nasaran mahaifinshi a samu nashi, Ganin yanda take kuka ne yasa ta shiga shafa bayan ta, Goggo ce data shigo ta dafa kafadar Ammi"kukan ya isa haka,kibar kuka ki kwantar da hankalin ki in sha Allah zai dawo domin yanzun haka Abbu da Dady sun kama hanya ko,dan babu Jirgi,amma duk da haka tafiyar mota zasu yi,da yardar Allah komai zai zo da sauki " Cire jikinta tayi daga na Ammi tana rike hannun ta"Ammi tsoro nake ji,Allah yasa babu abinda suka mai," Gara ma yarinyar tana da sauran karfin da zata iya yin magana,ita tunda aka kawo ta Asibiti har yanzun ta kasa furta komai, Ganin ƙarfe goma na dare yayi ne yasa Goggo tace"ya kamata ki tashi ki koma gida dare nayi" Girgiza kai tayi"tsoro nake ji,kawai zan biku mu can gidan,tunda yanzun za'a ba da sallamah " "Gama takardar sallahar,bari na taimaka ma Ammin Yara dan naga har yanzun jikin nata ba ƙarfi" Tare suka taimaka mata har suka fito aka saka ta a mota suka nufi gida, Har yanzun kuma bata yi magana ba,sai da suka tabbatar ta kwanta sannan suka ja mata kofa suka fito, Goggo ce tace"ki yi ƙoƙari ki dinga shiga kina leka ta,ni zan kwana tare da Kaka," "To,sannan Amira bata shigo ba" "Tana shiyana tare dasu Khadijah,nasan idan ta shigo zata damu Ammi da kuka ne,shi yasa nace tayi zamanta a can dan karta takura mata" "To hakan yayi sai da safe" "Allah ya tashe mu lafiya" Har ta juya sai kuma ta dawo"yauwa,kema karki saka damuwa a ranki,duk da nasan hakan ba mai yiwa bane,amma ki yi ƙoƙari ki danne zuciyar ki,ki kuma taya shi da Addu'a Allah ya baiyana gaskiya,koma menene ya kawo mana ƙarshen shi cikin gaggawa,domin nasan Suraj bazai taɓa aikata haka ba " Tunda take ganin matar bata taba tsammanin tana da sauƙin kai har haka ba,kawai dai dama can rashin fahimta ne, "Na gode sosai Goggo" "Babu komai" Ta faɗa tana fita yayin da ita kuma ta kulle ƙofar, Ɗakinta nada ta shiga,inda take zaune a lokacin da take aiki,har yanzun komai na dakin yana nan,dan haka zama tayi abakin gado tana tunanin ta ina ya kamata ta fara fuskantar wannan lamarin, Karan wayar tane ya dawo da ita daga duniyar nazarin da take kokarin faɗawa, Ganin number kawai yasa gabanta ƙara tsinkewa,karo na farko da taji shakkun daukar wayar shi, Ganin ya kusa katsewa ne yasa ta daga, "Da fatan wannan hanyar zai maki? " Wani hanya kenan?ina fatan ba kada hannu akan wannan labarin "ta tambaya ɗanta tabbatar, " Kin ce baki san hanyar da zaki ja hankalin shi har ya faɗa maki inda takardun suke ba,shi yasa na matsar maki dashi dan kiji daɗin cika aikin ki cikin sauƙi " "Amma me yasa sai ta hanyar kisa,kana ganin zai fito kuwa,batun kisa ba abu mai sauƙi bane" "Wannan ba damuwarki ba ne,kawai dai kiyi abinda ke gabanki" "Ina Ummita? " Idan kin gama aiki da wuri zaki ganta "yana gama fadar haka ya kashe wayar. Sauke wayar tayi a kunne tayi shiruu,yanzun yaya zata yi,sun riga sun samu nasara mataki na farko,ta tabbatar da zaran sun samu wannan takardar daga ita har shi kashe su zasu yi,tana buƙatar shi a raye idan tana son kasancewa a raye,dole ne sai ta kubutar da shi,tana buƙatar haɗuwa da shi sai dai dole zata jira zuwa nan da sati ɗaya taga wani mataki iyayen shi zasu ɗauka. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *42* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Ranar haka ta kwana duba Ammi,sai dai duk shigan da zata yi a zaune zata same ta saman sallaya, Ganin haka ne yasa itama ta dauro Alwala ta shiga yin Nafila har zuwa ƙarfe uku na dare sannan bacci ɓarawo ya ɗauke ta, Washegari da safe tana idar da sallar dakin Ammi ta shiga,har yanzun tana zaune saman sallaya,zama tayi a gefen ta tana jira ta kai karshe,sai dai ganin har yanzun ba ta da niyar tsayawa ne yasa ta dafa hannun ta tare da kiran sunan ta"Ammi"ganin bata dago bane yasa ta kuma kiran sunan ta,wannan karon ido kawai ta dago ta kalle ta da shi ba tare data amsa ba,kuma har lokacin tana jan carbin, "Tabbas kina cikin tashin hankali irin wanda ba zai taba faɗuwa ba,duk yanda zamu shiga cikin tashin hankali ba zai kai rabin wanda kike ciki ba,dukkanin mu mun sani babu ta wani hanyar da zamu saka wannan lamarin yayi sanyi irin ta hanyar Addu'o'i da rokon Allah, Ke mahaifiyarsa ce,addu'ar ki a gare shi ba zai taɓa faduwa kasa banza ba,sai dai kuma be kamata ki yi ta yanda zaki iya cutar da kanki ba,ke din tamkar bango ce a gare shi,idan kuma har kika faɗi to dame zai jingina, Ammi faduwar ki tamkar nasarar ce a gare su,zuciyarki ta zamo tamkar na dutse shine zai nuna jaruntar ɗan ki, Duk da ban zauna dashi na wani lokaci ba,sai dai na fahimta shi mutum ne ba mai tsoro ba,mutum ne mai juriya da tawakkali,na tabbata zai jure,zai kuma kai ga inda yake da burin kai wa, Ya kamata ki samu ki yi wanka sai ki ci abinci ki kwanta ki huta,domin sai Kanada lafiya da kuzari sannan zaka iya fita filin daga har ka gabza faɗa"mikewa tayi"Allah ya kawo mana mafita "har ta kai bakin ƙofa zata fita taji tace" Allah ma ya riga ya kawo mana mafitar" Cikin tsananin mamaki ta juyo tana kallon ta,domin rabon da taji tayi magana tun kan a tafi asibiti,da sauri ta dawo gabanta ta tsuguna"Ammi ina mafitar?menene mafitar? Ajiye carbin dake hannun ta tayi ba tare data fuskance taba tace"Kece mafitar " Zaro ido tayi"ta yaya aka yi na zama mafitar wannan lamarin,ni bansan komai ba"ta faɗa gabanta na faduwa cikin tsoro,don kar azo Ammi ta riga tasan komai,Alhalin itama mafitar take nima, Ganin yanda kamar hankalin ta ya tashi ne yasa ta rike mata hannun "ba abinda kike tunani nake nufi ba,kawai dai ki yarda da ni ke kaɗai ce wacce zaki iya taimakon shi,ki kaɗai ce wacce zata iya fito dashi," "Ammi ta yaya zan yi haka,wallahi bansan wannan hanyar ba,ban San hanyar da zanbi ba," "Kin sani,sai dai duhun da ya lulluɓe maki idanu shi zai hana ki ganin wannan hanyar,duhun daya lulluɓe maki zuciya,shi zai hana ƙwaƙwalwar ki buɗe maki hanyar, Sai dai zan yi haƙuri na jira har zuwa lokacin da duhun zai yaye,haske ya baiyana,har zuwa sanda zaki ƙara karɓar kanki a matsayin yanda kike,har zuwa sanda zaki karɓi kaddaranki a yanda ta zo maki, Zan jira har wannan lokacin" Shiru tayi kawai tana kallon Ammi,domin ko kaɗan bata fahimci me take nufi ba,bata fahimci ina zancen ta ya dosa ba,sai tsintar kanta tayi da kara cewa "yaushe ne wannan lokacin zai zo da kike faɗa? " Ni ma dai ban sani ba,amma na tabbata ya fara matsowa,duk da irin nisan da yayi,karki takura ma kanki da tunanin kalaman da ba zaki taba fahimta ba,sai dai kawai a bu daya zan faɗa maki,idan wannan lokacin yazo,amsar da kanshi zai bibiye ki ba ke zaki bibiye shi ba, Tashi ki tafi zan kwanta na huta kamar yanda kika buƙata" Mikewa tayi jiki a sanyaye ta bar dakin,ita kam koma me Ammi ke nufi ba ta sani ba,amma ta san duk rintsi baza ta taba bari ta mutu a hannun wani ba,to sai dai in haka Allah ya tsara mata, Kyaran gidan ta fara kafin ƙarfe bakwai ta kammala komai har ta haɗa abin ƙari, Jin ana ta ƙwanƙwasa kofar falo ne yasa da sauri ta fito ta buɗe, Bankade ta tayi "wannan ai iskanci ne mutum naji ana buga kofa amma bai iya fitowa ya buɗe ɗan isa,to Allah dai yasan mun san asalin mutum" Ita dai bata ce mata komai ba,amma kuma tana mamakin canji irin na Amira,ta san a da ba haka suke ba,amma tunda ta auri yayanta shi kenan yarinyar tabi ta tsaneta,karamin tsaki taja dan yanzun ba ita ɓace a gaban ta, Daki ta koma dama abinci take ci,tana kammalawa ta haye kan gado ta kwanta,taso ta ɗan yi bacci,sai kuma ta jawo waya ta shiga Facebook,gara ta duba taga ya ake ciki game da lamarin, Har yanzun dai ko ta ina labarinsa ne ke zagayawa, Anan ne ma take gani ashe yarinyar yar Chief Judge ne, Mahaifinta babban Alkali ne akasan,ba Musulmi ba ne,mugun mutu ne,wai yarinyar watan ta hudu bata gida,sun nime ta basu ganta ba,ta samu matsala da mahaifiyar ne shine tayi fushi ta bar gida,, A yanda Uwar ke kuka take faɗa kenan a wani dan Video da ta gani ta buɗe,wai sai an daukar mata haƙƙin yarta,sai sun kashe shi ba zasu taba yarda ba,shi kuma mahaifin yana fadin sai inda karfin shi ya ƙare,zai ga kuma wanda zai tsaya ma yaron,domin yarinyar su biyu kawai suka haifa,daga yayanta Namiji sai ita," Mutane kowa nata fadin Albarkacin bakinsa, Tayi matukar mamaki yanda taji mutane da yawa sun yarda da lamarin sai tsine mashi suke suna Allah wadai da mutum irin shi,har da cewa ai duk dama kyan ɗan maciji ne da dashi,kai ga dai maganganu nan dai wanda kallon su kaɗai zai iya hardasa ma mutum bugawar zuciya, Dan haka sauka tayi kawai a online ɗin tsabar haushi ma sai goge Facebook din tayi gabaɗaya daga kan wayar ta, Bata san Me yasa mutane suke haka ba,basu san farkon labari ba,sai kawai su tashi su fara bada tsakiyar labari ba tare da sun jira sun ga ƙarshen ba. Jin an buɗe ƙofar an Leko ne yasa ta dago tana kallon kofar,haɗa ido suka yi "wai kije shiyan Kaka ana nimanki a can" Tana gama faɗa ta jawo kofar ta kulle, Kallon agogo tayi,har ƙarfe tara na safe tayi,ashe dai ta ɓata lokaci a online, Mikewa tayi ta saka Hijabin ta ƙaramin sannan ta fita, Tunda tayi sallamah ta ɗaga labulen gabanta ke faduwa,domin mutanin gidan suna cikin falon har ta da Ammi, Samun wuri tayi ta zauna gefen Ammi bayan ta gaida su,har da kaka, "Mustapha kira Abbu Sufyan muji ya ake ciki" Cewar kaka, Amsawa yayi ya saka wayar a amsa kuwa, Sai da yayi kira biyu sannan ya ɗauka, Sai ga muryam Abbu ya baiyana,amsa sallamah yayi,kafin su gama gaida juna,"ga Mama"ya faɗa yana mika ma Kaka, Tana amsa yana ƙoƙarin gaida ita ta dakatar dashi"ina Surajo?ya yake?yana cin abinci kuwa? "Mama,wallahi tun ƙarfe bakwai da muka samu muka iso har yanzun sun hana mu ganin shi,sai yawo da hankali suke mana,sai turamu ofisoshi suke yi, Yanzun haka wai sai mun ɗauki lauya sannan zamu iya ganin shi,to munma ce su samar mana lauya amma sai cewa suka yi su badu da wani lauya a ƙasa,sai dai mu samu da kanmu,to yanzun dai abinda muke cike kenan,dan akwai wani abokin mu da muka yi karatu tare,to danshi Lauya ne,yanzun haka yaron yana hanya zai iso sai musan yanda za'ayi" Share hawayen ta tayi"Allah sarki yaron kirki,Allah ya bashi karfin zuciyar cin wannan jarabawar,Allah yasa komai yazo maku da sauƙi " "Mama ki dai na kuka,kin san dai abinda likita yace,dan haka addu'ar ku kawai muke buƙata" Jan majina tana"Allah ya maku Albarka" "Amin yauwa ina ga gashi ya iso bari muyi magana duk yanda ake ciki zaku ji"ya fada yana sauke wayar, " Wani gaskiya Allah zai nuna bancin wanda ya nuna mana yanzun,ina ce ko sati ɗaya ba'a cika ba da aka gama rigima akan Auren shi,wanda shima Allah ne ya tona mai Asiri kika gani da idanun ki,da yake Maijiddarh ba tada rabon shan wahala da ganin bakin ciki sai gashi an fasa an daura da Farkan shi,to yanzun ya aikata halin shi a in da Allah ya tona mai Asiri,sannan ku faɗi haka,wama yasan da haka yake yi duk yawon Wa'azin da yake yi,gaskiya Allah na gode maka daka nuna min komai a baiyane Asirin da ake ɓoyewa ya tonu,d.......... Saukar Marin da taji a fuskarta ne yasa ta dafe kumatunta tare da dago idanunta dan san ganin wani isasshe ne mai zarra da zai mata haka, Kowa na falon tsit sukayi suna mashi kallon mamaki,domin abune da ba'a taba yi ba acikin gidan,balle har a gaban kaka kuma bata ce komai ba, Cikin tsanin mamaki ta kira sunan shi"Mustapha ni ka mara? "Kwarai kuwa an Mare ki,ko zaki rama ne? " To me na maka zaka Mare ni,kan na faɗi gaskiya,idan har ni kun iya rufe baki na zaku iya rufe na mutanen dake waje suna magana ne,ko kuwa zaku dinga binsu da duka ne? "Koma me zamu yi dasu babu ruwan ki,amma ke kuma muna da yanda zamu yi dake,ban taɓa sanin rashin mutuncin ki ya kai har haka ba Saudat sai yau,ace a gaban Uwata,a gaban Mahaifiyar Yaro kike fadin haka dan ba kiɗa imani da hankali" Ya karasa faɗa a tsawace cikin bacin rai, "Haba Abba me yasa zaka Mari Momy bayan kowa nan yasan maganarta gaskiya ne,ya aikata,idan da ace be aikata ba da hakan be faru ba,ga abu a zahiri babu sharri a ciki amma ku baku son ku gani" Mi kewa yayi ya riƙe hannu Hajiya Saude data dafe kumatu "Momy tashi muje"mi kewa yayi tabi bayan ɗanta suka fita,yayin da itama Aunty Hajjo tabi bayan su ta fita, Girgiza kai Kaka keyi kawai, Da sauri ya karaso inda take" dan Allah Mama kiyi haƙuri,Nasan abinda ta faɗa bai kamata ba,in sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa ba" "Me yasa zaka Mari uwa a gaban ya'yanta,so kake yayanka su tsana ka?wannan ba abu mai kyau bane ta aikata,sai ka bari idan kun keɓe ja mata duk abinda kaga dama amma banda duka banda Mari,domin wannan baya daya daga cikin halin kwarai,na tabbatar da idan ma da kyale ta ka yi da tana gama faɗa wucewa zata yi" "Mama kiyi haƙuri zan dinga kiyayewa," "Dan Allah ku bari a gama da wanga jarabawar da ya same mu" Komawa yayi ta zauna, Hajiya Rahama ce ita ma ta mike "to kowa dai ya dibo da zafi bakin shi,dan haka nayi gaba" Tashi yayi ita ma ta yi wucewar ta, Kallon Kaka ta yi,cikin kwana daya gabadaya ta zabge ta yi rama, "Kiyi haƙuri Ammi sannan ki rage damuwa a zuciyar ki,karki bari wani ciyo ya kamaki,addu'a ita ce mafita" Dan murmushi yake ta saki,domin ita ba mahaukaciya ɓace"In sha Allah kaka " Nurudeen ne yace"yanzun haka na bada aikin saukar Kur'anai makarantun goma,har zuwa sanda lamarin zai yi sanyi" "Na gode Nurudeen Allah ya maka Albarka"cewar kaka, " Karki damu kaka,ai Suraj ai ɗan uwa na ne " Karan Wayar Abba ne ya dakatar dasu"yauwa gashi ma sun kuma kira Allah yasa an dace sun samu shiga " Duk da Amin suka amsa, Gyara zama tayi,domin Allah ya gani ita kanta ta matsu ta ji halin da ake ciki..... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *43* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Ɗaukar kiran yayi ya saka a amsa kuwa kamar dazu, Bayan amsa sallamah ne yace"Ya ake ciki Sufyan ? "Gabaɗaya wannan lamarin ya wuce da tunanin mu,domin yaron ya iso shine yake faɗa mana ai in dai a nan garin ne ba za mu taɓa samun lauyan da zai ɗauki case ɗin nan ba,domin gabaɗaya goyon bayan mutumin nan suke yi,idan kuma har wani loya musulmi yace zai karɓa ƙoƙarin koranshi suke yi daga aiki,yanzun haka shima a saboda kawai yace zai amsa wannan Case din an yi Seizing License din shi na Loya, Yanzun gashi har karfe goma amma wallahi mutanen nan yanda kasan basu san da mu ba" Inna'lillahi wa'inna ilaihi rajiun,shine kawai abinda suke ta maimaitawa, "Insha Allah zamu dai ci gaba da jarabawa ko za'a dace,ku kwantar da hankalin ku,sai dai zuwa anjima duk yanda ake ciki zaku jimu" "To shikenan"daganan sallamah suka kuma yi, Nasiha sosai Kaka da Abba suka ma Ammi ciki harda ita sannan aka sallame su akan duk yanda ake ciki anjima za su ji, Suna fitowa tana biye da Ammi a baya,har sun kusa isa falo tace" Ammi ina son zanje can gidan na kwaso kaya" "Kisa Direba ya kaiki,sannan ki zauna a can dan zaman ki a nan baida wani amfani,ƙila zaman ki a can zai iya taimaka maki"tana karasa faɗa tana shigewa falon, Me kuma take nufi da zaman ta anan bai da wani amfani, Dan shiru tayi,to kuma gaskiya ta faɗa fa,duk da ta san abin zai yi kamar bai dame ta bane idan ta koma,amma komawar shi yafi,dan haka ba tare data shiga ciki ba ta juya ta nufi wurin ajiye motoci dan ta san anan zata samu mai kaita gida, Tana zuwa kuwa daya daga cikin direbobin gidan ne ya kai ta har gida sannan ya dawo, Bala ne da sauran ma'aikatan gidan suka shiga jajanta mata,tana amsawa ta shige falo, Yau dinnan ba zata zauna ba duk wani daki na gidan nan sai ta tabbatar data bincika shi, Anan falo ta ajiye Hijabin ta,kai tsaye dakin shi ta shiga ta fara dubawa lungu da saƙo,har ta gado,da dorowar kayan shi sai da ta matsar a tunanin ko zata samu wani ɓoyayyen daki ko ma'adana,sai dai ko fallan takarda bata samu ba a ɗakin, Ba lallai bane ta iya maida dakin yanda yake sai dai kawai tayi iya yin ta tabar saura in ya dawo ya kyara abin shi,ƙila ma lokacin ta daɗe da barin gidan, Ɗayan dakin dake gefen na kasa taje buɗewa,sai dai kamar daga ta ciki aka kulle dan taki buduwa, Ta kwada yin amfani da dan karamin ƙarfe dan kwada ko zai bude amma sai da ya dauke ta kusan awa daya kafin ta iya buɗewa dan ma taki hakura,a cewar ta sai taga me a ciki, Lafiyayyen daki ne,sai dai shima kamar wancan an rufe komai na dakin da farin kyalle wanda hakan ke nuna an jima sosai ba'a yi amfani da dakin ba, Gabaɗaya ta yaye kyallayen tana kare ma ɗakin kallo,daga dukkan alamu dakin mace ce, Durowar kayan ta bude nan ma kayane amma kuma na tsofaffi ne,sai dai kayan yawanci dogayen riguna ne,harda su sarƙoƙi masu matukar tsada,mai da su tayi inda ta dauki su,tana kokarin rufe wurin ne wani karamin fefa ta fado daga ƙasan akwatin sarƙoƙin, Ɗauka tayi ta buɗe ta warware, *Wudil,sabon layi,house no 120,Ilyasu Shehu* Abinda ke rubuce kenan a cikin ɗan ƙaramin takardar kenan, Ba tare da tunanin komai ba ta ɗauke takardar,ta bar ɗakin, *Bayan Kwana biyu* Abubuwa marasa daɗi ne kekan faruwa game da wannan lamarin,domin maganar so yake yafi karfin tunanin su,duk inda suke tunani za su samu lauya abin ya faskara,domin ko da sun samu da zaran ya amsa da kanshi zai dawo yace ya fasa abin yafi karfin shi, Su kuma su Abbu har yanzun an hana su ganinshi,sun rasa yanda zasu yi,domin mutumin ba karamin mugun mutumi bene,duk kuma wanda ya amsa aiki kashedi ake masa da rayuwar sa ko data ahalin shi,dole ya ajiye aikin, Sun ce kuma a cikin kwana na biyar zasu kai shi kotu a yanke mai hukunci tunda sun kasa samun Loya, Su kansu kungiyar malamai sun so a dawo da case din Arewa,sai dai sam uban yarinyar yaki yarda dan haka addu'a kawai suke mashi, Duk waɗannan labaran tana samu ne daga bakin Kaka idan kullun taje gaishe ta, A wana na biyun ne kuma suka samu baki daga South African,Kanin Kaka ne tare da yaran shi uku,Babban dan shi,wanda yake wani gabjeje a kalla zai yi shekara Arba'in da biyar,sai mai bi mashi,sai kuma ƙanwar su mai ishirin da shida, Shi kuma uban ya dan fara manyanta amma yanda kasan yaro haka yake,domin a tsuke yake cikin Kananan kaya,irin mutanin nan ne waɗanda daka gansu kasan budurwar zuciya ce dasu, Ta gama shiri kenan tana ƙoƙarin fita sai ga Bala ya shigo da sauri har suna shirin cin karo,"kai lafiya? "Hajiya baƙi aka yi" Karamin tsaki taja "daga ina" "Kanin kakar Ubangida mu ne,kuma yazo ne tare da nashi ƴaƴan" Shiru ne ya ratsa falon na wani dan lokaci kafin tace"dama idan sun zo anan suke sauka? "Eh to sau daya dai na taba ganin yazo nan kuma shi kadai yazo a wancan lokacin,dan a sannan Kakar Ubangida tana nan" Falon take kare ma kallo,"yanzun ta ina zata sauke su,ita bata cika son tana zama wuri ɗaya da mutanen da bata sani ba gaka, Ajiyar zuciya ta sauke,"da fita zan yi amma mu je " Tare suka fito daga cikin falon ta nufi inda suke cikin takun ta nan mai jan hankali wanda ya riga ya bi mata jiki tun da jimawa ba tare ma data San tana yi ba ko a gaban waye, Su din ma nufarta suke yi sai dai ganin ta kusa karasowa ne yasa suka dakata suna jiran isowar ta, Tunda ta daura idanun ta a kansu zuciyar ta ke tsinkewa,domin bata yi tunanin ganin su a haka ba,manya zarata dasu har uban,sai dai shi kalar shi kamar ba Bature ba,yafi kama da yan American,sabanin yayar shi data gani a hoto wacce take Baturiya sak, Tana isowa ta sakar masu da murmushi mai sanyi tana karasa kusa da wanda take da tabbacin shine Baban su "Welcome to Nigeria Grandpa " Murmushi mutumin shima ya sakar mata yana buɗe mata hannu Alamun zai rungumeta, Ita ma da yake yar duniya ce sai ta rungumeta suka gaisa,sannan ta juyo wurin mazan suma dai irin gaisuwar da suka yi kenan kafin ta masu jagora zuwa cikin falon tana rike da hannun maccen, Nuna masu wurin zama tayi tace suyi haƙuri a gyara masu wurin da zasu zauna, Bala ta aika yayi masu ordering abinci, Matashiyar budurwar ce tace mata"Daughter in low ni tare dake zan zauna" "ba damuwa tashi mu je"cikin sakin fuska tana mika mata hannu, Kama hannun ta tayi suka yi ɗakinta ta nuna mata banɗaki ta kuma cire mata sababbin kayan wanka, Jakkan kayanta kuma ta saka mata a gefe, Sai da Bala ya kowa abinci sannan ta fito daga dakin da tasa ana gyara masu,ta sanar dasu an kammala suna iya shiga kowa daki daya,idan sun kammala ga abincin su nan, Godiya suka mata, Baban su da taji suna kira da Pa ne yace idan sun huta zuwa anjima zata kaisu wurin Maman Suraj, Tana fitowa dakin wayar Ammi ta nima dan gara ta faɗa mata da zuwan su akan ta ganta da baƙi babu sanarwa, Yana ta kara ba'a ɗauka har tayi kira na biyu yana ma shirin tsinkewa taji an ɗauka, Ƙoƙarin yin sallamah take yi taji ance"wai lafiya kike damun ta da ƙira da rana tsaka" Sai da tayi dan jim kafin tace"idan Ammi na kusa ki ba ta waya" "Bana jin zan iya bata,tukunna ma ke wacece da zaki aike ni" Ranta fa ya fara ɓaci da wannan rashin kunyar na yarinyar"Amira,ko kinki ko kinso ni din matar yayanki ne,idan baki karɓe ni ba wannan damuwar ki ne tunda yayanki ya karɓe ni ya kuma haɗa shimfida dani,uwarki ta karɓe ni,idan kin ga dama ki kaimata wayar idan kin ga dama karki bata,wawuya Stupid"tana jin lokacin da zata sauke wayar ana tambayar keda waye ke waya,ta sauke wayar tana faɗin ai Gara na karasa lalata alakar dake tsakanin mu na san cewa bama shiri gabaɗaya, A can ɓangaren kuwa,ji tayi ranta ya bala'in baci har balle ce mata wawuya da stupid ɗin data yi,gashi ta sauke wayar balle ta rama ko za ta ji sanyi, Jin tambayar da Ammi ke mata ne yasa idanun ta cika da Hawaye ta mika mata waya"Habiba ce,wallahi Ammi sai nama yarinyar nan rashin mutunci,cemin da tayi wawuya harda cemin stupid " "Ta birgeni,dama ta haɗa maki da Doluwa tunda baki gane komai ba" "Ammi!" "Yes na,oya tashi ki barmin daki bana son surutu" Cikin jin haushi ta tashi ta bar dakin tana turo baki, Girgiza kai kawai rayi tana ƙara kiran wayar Habiban, Ɗauka tayi da sallamah tana gaida Ammi,ita ma amsawa tayi,sannan tace"kin kira bana kusa" "Eh Ammi dama baki aka yi kuma sun ce zuwa anjima na kawo su wurin ki,so karki ganni da baƙi shi yasa na kira ki" Dan murmushi tayi"na gode Habiba,amma su waye? "Kanin Kakar Suraj ne da yaran shi," "Kanin kakar Suraj? " Eh" "Kin tabbata" "Eh to ni dai yanda Bala ya faɗa min kenan,sannan na taba ganin hoton shi tare da na Kaka" Shiru ne na ɗan wani lokaci ya ratsa wayar wanda har sai da tayi tunanin ko kiran ya katse ne ta shiga fadin Hello, Jin ta sauke numfashi ne yasa tace "ok sai kin zo" "To Ammi" Sauke wayar tayi tama tunanin yaufa ta so taje Wudil,amma ba komai taje gobe. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *44* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Koda suka kammala cin abinci kwanciya suka yi domin su samu su huta, Sai zuwa yamma sannan suka shirya,Direba ya jasu har gidan su Ammi,a falon Kaka akai masu masauki,sannan Ammi tazo suka gaisa,cikin mutumtawa, Kuka Pa ya saka yana yabon Suraj da harshen turanci,ita sam bata ma taɓa tsammanin kaka na jin Turanci ba sai yau,in da take ta bashi haƙuri tana kuma tsanar dashi halin da ake ciki, Cewa yayi Gobe zasu tafi Legos din suje su samu su Abbu dan asan halin da ake ciki, Babu zato ta ji Ammi tace"sai ku tafi tare da Habiba dan ko ba komai ya kamata tana kusa" Cikin sauri ta kalle ta,sai dai kauda kai tayi tana jiran ta ji me kaka zata ce, Kamar zata musa sai kuma tace "to ba damuwa sai su tafi tare" Ita wallahi ba haka taso ba,dan haka tashi tayi tace masu tana zuwa ta koma shiyan Ammi tayi zamanta, Sai da zasu wuce ne Ammi ta saka aka kirata sannan suka tafi, Direba na sauke su ta amsa makullin mota tana kokarin shiga,budurwar da suke kira da Nadiya ce tace "zaki kuma fita ne? " Eh"ta bata amsa, "Zanje " Ta faɗa tana ƙoƙarin zagayawa ta shiga mota, Da sauri ta tada motar"Sorry ana jira na ne yanzun zan dawo"ta faɗa tana fita daga gidan,tunda abun ya zama haka gara ta tafi duk dare ta dawo, Da Marp ta yi amfani ta tafi Wudil, Ranar ba ita ta dawo ba sai ƙarfe kusan sha-biyu na dare,dan ba ƙaramin wahala tasha ba, A matukar gajiye ta shigo gidan kai tsaye ɗakinta ta buɗe wanda tana tura ƙofar hayaƙi ya fara turnike mata fuska, Ƙara hasken wutar dakin tayi tana kallon ta cike da mamaki, Tana zaune a kasa ga kwalin sigari a gabanta ga kullin wiwi irin yanda suke yin shi kamar taba da kuma ƙananan kwalaben giya masu ƙarfi da tsada guda biyu,sai shan abinta take yi cikin kwanciyar hankali, Ganinta kuma bai saka ta fasa abinda take yi ba, Ɗan dariya tayi"Sorry Beb na bata maki daki ko? Shigowa tayi ta faɗa kan gado tana sauke ajiyar zuciya"no is ok" "Thank you" Bata ce mata komai ba sai lumshe ido da tayi tana nazarin maganar da suka yi da Dattijon Mutumin,wanda ya riga ya san da zuwanta,to ta yaya akayi ya san cewa zata zo,tuno irin maganar da suka yi ne yasa jikinta ƙara yin sanyi, Wannan wani irin aiki ne take yi,abun yana kama da ba mutum ɗaya take ma aiki ba, Wannan wani irin rikici ne ta jefa kanta a ciki haka, Jin warin Sigari ta wurin kanta ne tasa ta dago ido tana kallon ta, Mika mata wanda ke hannun ta tayi"wannan yana rage damuwa " Tashi tayi ta sauko katsa ta zauna kusa da ita sannan ta amsa ta fara zuka cikin kwarewa, Dariya ta saka cikin jin daɗi ta shiga faɗin "Ashe ke ma kin iya har haka? "Nama fi nan" "Bari kiga irin yanda muke sha a garinmu" Wani irin wasa da hayaƙin take yi sosai, "Gaskiya naku na daban ne," "Sosai ma kuwa,kuma ina shanye kara shida zuwa takwas a rana" "Kai amma kinsan yawan shanta yana kawo illa" "Ban damu ba,sai dai ina shan maganin da bazata min illa ba" "Haka ne," "Kefa? " Me kenan?ta tambaya, "Guda nawa kike sha a rana,Kwali daya ko biyu" Dariya tayi "ina bai wuce sau daya a sati ba,ina kiyaye lafiya ta" "Amma dai ke matsoraciya ce,to wannan fa?ta fada tana mika mata wiwi, Girgiza kai ta yi" A'a bana shanta ita da giya " "Me yasa? " Kawai dai" "Ki gwada mana? " A'a ke dai sha kawai" "Kina shekara nawa kika fara shaye-shaye? "Goma sha-biyar" "Wow that was so early" Jinjina kai tayi "sosai ma" "Ni sai da na kai 20 years,kuma wani saurayi na ya koya min gashi yanzun mun rabu dashi, he break my heart,ban cin ina son shi sosai" Shafa bayan ta tayi "Sorry ai haka suke ƴar uwa they easily break our heart,ni ma akwai wanda nake so sosai,i eving Love him more than my life,ban taba son wani ba irin yanda nake son shi,but in the end sister,he break my heart more than the way glass use to be break in to pieces,irin yanda bazai taɓa haɗuwa ba har abada,he disappointed me,but babu komai" "Akwai" Girgiza kai tayi"babu" "Idan babu why are you Crying" Shafa kumatunta tayi,ita san bata masan tana hawaye ba,dan murmushi tayi tana share hawayen ta"babu komai,na bar su da Allah "ta faɗa da Hausa wannan karon dan dama da turanci suke magana, " Har yanzun kina son shi? Shiru tayi tana sauraron bugun zuciyar ta"ƙila" "Me hakan ke nufi? " Ban sani ba tukun na" "Ke mutuniyar kirki ce,in faɗa maki wani abu? Lumshe ido tayi ta buɗe tana jin yanda zuciyar ta ke zafi" Ina jinki" Dan matsowa tayi Kusa da ita dai_dai kunnen ta"Be careful with my Father and brother" Razo ido tayi tana shirin yin magana ta daura mata hannu a baki,tare da nuna mata ƙofa da hannu, Bin hannun tayi da kallo inda idon ta ya sauka akan inuwar mutum, "Suna iya kashe mutum,na taba gani kuma suka ce idan na faɗa zasu kashe ni,kema ki yi a hankali"ta raɗa mata a kunne kuma Gabanta ne ya shiga bugawa da karfi,ita ma cikin raɗa ta tace" Yaushe zaku tafi? "Ban sani ba,kin ga manta dasu,ni dai wallahi kin min i Love you" Ta faɗa da ɗan karfi cikin alamar fitar hankali Kwantar da ita gefe tayi"kwanta ki huta"tashi tayi ta nufi bakin kofa duk da har lokacin tana ganin inuwa a wurin,tsoro take ji sai dai ba zata fasa zuwa dubawa ba, Tana bude ƙofar sai dai ba kowa a wurin,dan lellekawa tayi nan ma ba kowa,maida ƙofar tayi ta rufe ta koma ta kwanta bayan ta kashe wutar dakin ta kwanta gefen Nadiya, Agogon wayar ta ta duba ƙarfe biyu na dare har da rabi, Lumshe ido tayi,ji take zuciyar ta kamar an ɗauko dutse mai matuƙar nauyi an Daura mata,abubuwa ne da yawa ke mata yawo a cikin zuciyar ta, Idan ta tuna maganar ta da Wannan dattijon,da kuma hiranta da Nadiya har zuwa kalamanta na karshe sai ta rasa gane ina ne Asalin hanyar daya kamata tabi,sai ta tsince kanta acikin duhu irin wanda Ammi ta faɗa har kuma take mata fatar yayewar shi,to sai dai ta rasa koda ƙaramin hasken da zai haska mata hanya domin taimaka mata wurin niman madaidaiciyar hanya,wanda zai iya bullar da ita,har ta kaita ga fita tarkon da take ganin tamkar ɗana mata shi akayi da gangan aka kuma sakata aiki a kanshi, A wannan daren bacci barawo ne kawai ta samu damar sace zuciya irin nata mai cike da sake sake. Washegari koda ta tashi ƙarfe bakwai har ta wuce,dan haka wanka tayi sannan tayi sallah ta tayarda Nadiya da ƙyar, Fitowa tayi ta ba Bala sako akan ya amso abin kari,sai dai ma har ya riga ya gama girkawa, Pa ne kawai zaune a falo,dan haka cikin girmamawa ta gaishe shi,amsawa yayo cikin sakin fuska,har ma yana tambayarta ƙarfe nawa jirginsu zai tafi, "Ƙarfe tara"ta bashi amsa, " To kiyo kokarin saka Nadiya ta shirya da wuri karta bata mana lokacin " Da to kawai ta amsa mashi sannan ta koma daki, Samun ta tayi har ta kammala wanka tana saka kaya, Zama tayi kusa da ita,"barka da safi Nadiya " Murmushi ta sakar mata"barka,da fatan kin tashi lafiya " "Lafiya,na ma zata baki tashi ba" "Ina son in ga Suraj shi yasa na tashi da wuri," "Idan kin kammala ki fito mu ci abinci" "A'a kuci kawai ni bana cin abinci da safe haka" "Ok"ta fada tana mikewa, Ƙarfe takwas da rabi ta masu ne a filin jirgi,dan haka lokacin nayi jirgin su ya tashi, Cikin lokaci ƙanƙani suka sauka a garin Legas inda Abbu da Dady ne suka tare su, Daki daya aka sauke ta ita da Nadiya a babban Hotel din da suka sauka,sai kuma su kowa daki dai daya. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *45* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Misalin ƙarfe Hudu na yamma, Zaune suke a wani matsakaicin falo,mai ɗauke da jerin kujeru kamar na Dinner table mai zagaye da kujeru shida, Su biyar ne zaune a kan kujerun,daga dukkan alamu akwai wanda suke jira, Hira suke yi jifa_jifa a tsakanin su, Jin an buɗe ƙofar an shigo ne yasa gaba ɗaya suka maida hankali kan kofar,ganin wanda ya shigo ne yasa gabaɗaya suka mike tsaye, Daya daga cikin sune ya karasa inda yake cikin dariya suka rungume juna, "Barka dai Abokina" "Shine Dazu ka nuna kamar baka sanni ba" "Kayi haƙuri kasan irin yanayin da muke ciki a yanzun,dole komai sai munyi da taka-tsantsan," "Hakane kuma" Jawo mashi kujera yayi ya zauna, "Naji yau kwana uku kenan da kuka iso" "Eh haka ne,kasan dole mu riga kowa isowa" Daya daga cikin sune yace"Shugaba har yanzun fa yaron yaki yayi magana " Murmushi mutumin yayi wanda ba zan iya shaida fuskar shi ba saboda ƙarancin haske na ɗakin,"ba zai taɓa magana ba"kallon wanda ke gefen shi yayi"Chip baka da abin faɗa ne? Gyara zama yayi"ni kuwa nake da abin faɗa,domin na sadaukar da yarinya ta domin ƙaruwar mu,kuma ni har yanzun ban ji bayanin da nake son ji" Daya daga cikin su ne ya kuma cewa"amma dai ai ba aikin banza kayi ba,domin ba karamin kuɗi ka karɓa ba akanta,kaga kenan zamu iya cewa tsiyan yarka muka yi da makudan kuɗi kuma ka saka hannu ka karɓi abin ka " "Ku me yasa baku sai da naku ya'yan ba,ka sani duk da kuɗi na karɓa ba karamin Alfarma na ma kungiya ba,Shugaba matsayin da aka min alƙawari? "Ina nan ina aiki akai Ade Bayo,ka kwantar da hankalin ka in dai matsayin Minista ne zaka yi shi,kai dai kawai ka mai da hankali akan batun shiga kotunnan da za'ayi jibi" "Shi kenan Shugaba" Kara tambaya yayi yana juyowa kan wanda Dazu ya kira da abokin shi,ji nake murya shi tamkar na tabajin jin shi a wani wuri,"ya ake ciki batun lauyoyi? "Har yanzun dai ba'a samu wanda zai tsaya masu ba,domin mun toshe duk wannan hanyar,wannan karon abunda muka yi shekaru muna shiryawa shi muke kokarin muga mun kammala a wannan karon,sai dai wannan yaron yana son ya nuna mana taurin kai" Dan dariya yayi"baka tsoron Mahaifiyar ka da matar ka su gane? Shima dariya yayi"ba zasu taba ganewa ba,dama ita ai dan haka tun farkon aka aure ta " Duk shekewa da dariya suka yi, Sannan daya ya kuma cewa"jibi ne shiga koto,chep hukuncin kisa gaba ɗaya zaka yanke mai" "Idan ya yanke mai hukuncin kisa ba tare da faɗa mana komai ba to ya zamu yi kenen" "Karku damu Zinariya dab take da karasa aikin ta ba tare data sani ba" "Ya zamu yi da ita? " Zuwa gobe zamu kara fahimtar da ita karfin mu,dan haka ku kwantar da hankalin ku cigaba da gudanar da komai kamar yanda muka tsara," Duk mikewa suka yi cikin girmamawa"to Shugaba" "Sai mun haɗu a kotu"ya faɗa yana barin dakin suna rake mai baya. ____________daki ne mai matukar duhu wanda mutum ko tafin hannun shi baya iya gani,ta gefe ɗaya kuma baka jin komai sai karan saukar duka,ta ko ina kake ji, An dau lokaci mai dan tsayi kafin kuma naga an bubbude windojin dakin gabaɗaya lokaci ɗaya haske kuma ya baiyana a ɗakin, A tsaye nake rakube a jikin bango amma tsabar firgita bansan sanda ya yanke jiki na faɗi ba,ganin abinda ke tsaye a gaba na, A tsaye yake a tsakiyar ɗakin yayinda hannayen shi ke daure duka a baya a tsakale a wani ƙarfe, Gabaɗaya jikin shi a farfashe yake wani wuri ya tara jini har yayi baƙi,duk fatan jikin shi a fatfashe yake babu kyan gani kasancewar shi farin mutum,fuskar shi gefe ɗaya ya kumbura haka gefen fuskar shi,ya rame fiye da tunani a kwana uku kawai,ya fita kamannin shi,idan aka faɗa maka wannan Suraj ne wlh kana iya musawa, Dago idanun shi yayi wadanda suka canja kala,daga asalin kalan da suke ya daura a kansu, "Ka faɗa mana komai muna iya sake ka kaci gaba da rayuwar ka" Murmushi yayi wanda ba shida daɗin kallo sannan ya tofar da miyau gefe mai tattare da jini"har abada " Ɗayan ne ya sauke numfashi"ko dama baka faɗa ba dab muke da samun abunda ka daɗe kana ɓoyewa " "Ba za ku taɓa samu ba" "Oh haka kake gani?to shikenan kaci gaba da wahalar da kanka,yanzun haka cikin kawa biyu komai zai kammala" Dariya dai ya kuma yi"ita din Mage ce,bata isa ta shiga dajin da damisa kaɗai yake iya shiga yayi shawagi acikin ta ba,ku dai na daura yardar ku da imanin ku a kan haka,domin babu abinda zata iya yi" "Haka kake gani ko,zamu baka mamaki" "Ni ma kuma zan baku mamaki" Kallon juna saka yi cikin mamaki to me yake nufi shi da yake kulle "me kake shiryawa? " Abinda kuka zo tambaya kenan? Dafashi wanda na ji dazun sun kira da Shugaba yayi"mu je kawai,kai kuma zamu ga iya inda taurin kan naka zai kai ka"ya faɗa yana jan hannun shi suka bar wurin,tare da kullo ƙofa. Sai da suka shiga mota sannan ya kalleshi cikin damuwa"me wannan yaron ke nufi? "Kaga karka damu,so kawai yake ya saka mana kokonto a ziciyarmu" "Kasan yaron hatsabibin kanshi ne,shi yasa na ɗan fara damuwa" "Tada mota muje babu abinda ya isa yayi" Taka mota yayi kuwa suka bar wurin. _______________suna fitowa daga dakin wurin cin abinci suka nufa na cikin Hotel ɗin,anan suka ci abinci suna dan taba hira, Ganin shigowar Pa da Dady ne yasa da sauri ta tashi ta karasa inda suke, Tana dan kiran sunan Dady, Tsayawa sukayi ta karaso "Dady yaushe zamu tafi ganin Suraj din? Ɗan jim yayi kafin yace" Kin ga wallahi har yanzun akan abunda muje aiki kenan yata,babban matsalar ma shine rashin loya,shi yasa har yanzun bamu samu damar ganin shi ba" "To yanzun Dady babu wani abinda za'a iya yi? " Ina fa,sai dai mujira mugani zuwa jibi," Pa ne ya miko mata wani ATM"Kim ga karɓi wannan ki rike a hannun ki,anjima kaɗan ku shirya a kwai wani yarona a nan garin zai zo ya kaiku ku ga gari sai ku dan shi iska ke da Nadiya,karki wani saka damuwa a ranki " Amsa tayi tana murmushi,duk da ba wannan bane a gabanta amma ko ba komai ta ji daɗin yanda ya nuna mata kulawa "mun gade Pa" Komawa tayi ta zauna inda suke da Nadiya tana nuna mata katin. Ranar tunda mutumin ya fita dasu basu suka dawo gida ba sai ƙarfe goma na dare,shima ita ta matsa su dawo saboda ta gaji, Suna dawowa wanka tayi kawai ta kwanta dan tun a can suka ci abinci, Nadiya ce ma ta dauki kayan shaye-shayen ta fara, Har baccinta ya fara nisa dan lokacin ƙarfe sha biyu na dare ta ji wayar ta na ƙara, Ba tare data duba waye ba ta dauka ta saka a kunne ba tare data ce komai ba, Ji tayi ance "Biba kina jina? " Ummm "ta faɗa cikin yanayin barci, " Duk abinda kike yi yanzun nan ki baro shi ki taho Abuja,domin kuwa yanzun haka rayuwar Ummita na gagarumin hatsari,tana cikin gidan ki a ɗaure,ba lallai bane takai har zuwa lokacin da zaki iso,amma abu ɗaya shine ko gawarta ki samu nasarar gani,domin idan har suka san kin san inda take kafin ki iso sun dauketa a wurin,karki maimaita maganar a fili domin ana iya jinki" Wani zabura tafi har tana fadowa daga saman gadon,"hello! Hello "amma ina tuni an kashe layin, Jikinta har rawa yake yi wurin ƙara kiran number amma wayar ma ce mata yake wai the number is not exist, Gabaɗaya babu abinda ke mata Ringin akai irin rayuwar ta na cikin haratsari,mutuwa,da kuma kalmar gawa, Dafe kirjinta tayi,tana ambatar sunan a fatar bakinta Ummita, Duk irin tambayar da Nadiya ke mata ganin yanda hankalin ta ke tashi kin bata amsa tayi,tunanin mafita kawai yake yi awanni lokacin,ta san cewa idan har tace sai da safe to lallai lokaci zai kure mata kamar yanda yace, Dan haka ta riga ta tsayar da zuciyarta kome zai faru ko nawa zata kashe yau sai ta isa garin Abuja, Cikin sauri ta cire kayan dake jikinta na barci ta saka doguwar riga na jallabiya ta dauki karamin jakka, Kallon Nadiya tayi da tayi zurum tana kallon ta"idan an kira ki akan ina nake,ki ce masu an kirani Babban Yayana yayi hatsari ya mutu,na tafi" "Da gasken hatsari yayi" Kokarin fita take yi"eh"ta bata amsa tana fita tare da jawo mata ƙofa, Ta san garin Lagos sosai dan ba bakonta bane, Dan haka tana fita mashin ta tara ba tare tayi ciniki dashi ba ta faɗa mashi sunan garejin da zai kaita,dan ta san a can ne kadai zata ita samun motar da zai kaita duk in da zata je, Cikin lokaci kankani suka isa saboda irin gudun data saka yayi,saboda dare ne akwai sauƙin abin hawa, Dubu biyu zata bashi amma dubu biyar ta bashi tayi wucewar ta, Ofishin Shugaban garejin taje ta mai magana akan ta son direban da zai kaita Abuja cikin ƙanƙanin lokacin, Dubu talatin suka ce,amma ga mamakin su sai cewa tayi in dai zai yi sauri ta bashi dubu Sittin, Cikin lokaci kankani aka haɗa ta da lafiyayyen mota da ma kuma wanda zai kaita bayan ta masu transfer, Tunda suka kama hanya mutumin ke zuba wani uban gudu da ita yanda kasan zasu tashi sama,ta san gudun da suke yi ya wuce kima amma ita bashi bane a gaban ta,burinta daya kawai ta ganta a Abuja, Cikin hukuncin Ubangiji sai gashi ƙarfe biyar na Asuba ta masu a cikin garin Abuja,ita take ta nuna mai hanya har ƙofar gidan ta, Tana fita cikin tsananin sauri ta ɗauki makullin gidan inda suke ajiyewa ta buɗe ta buɗe, Na falo ma haka sannan ta shiga, Kunna wutar gidan tayi gaba ɗaya ko ina ya dauke da haske sannan ta shiga duba ɗaki ɗaki tana kiran sunan ta. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *46* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Duk in da take tunanin zata ganta a cikin gidan ta duba bata ganta ba, Cikin sanyin jiki ta dawo falo ta zube anan kasa tana fashewa da kuka, Ummita tamkar kwarin gwiwar ta ce na cigaba da rayuwa a wannan lokacin,tana son Ummita domin sun yi rayuwa da ita na amana,tausayi,da daraja juna, Bata da wani wanda take gani a matsalin dangi irin ta,itace Ahalinta, Idanun ta ne ya sauka a kan labulen da isaka ke kadawa yana dagawa kaɗan kasancewar ta bar kofa a buɗe, Kamar hannun mutum take gani, Da gudu ta tashi ta ita wurin tana kiran sunan ta tare da yaye labulen, Wani irin ihu ta yanka wanda tun daganan sai ganin duhu tayi ya mamaye mata idanu,daganan kuma bata ƙara sanin meke faruwa ba, Bayan awa uku,a hankali ta fara buɗe idanun ta tana kallon silin din dakin, Shiru tayi tana sauraren ƙaran Ac dake tashi,ƙoƙari take ta tuna abinda ke faruwa da ita, Wani irin zabura tayi da karfi saura kaɗan ta fado sai ji tayi an riƙe ta"ki yi a hankali karki ji ciyo" Juyowa tayi ta kalli Nos din dake riƙe da ita"ina ne nan,ina Ummita " "Ki kwantar da hankalin ki nan kina Asibiti ne" "Asibiti? Ta maimaita, " Eh" Da sauri ta sauka daga kan gadon tana cire Butterfly needle da aka saka mata Drip dashi ba tare data damu da zafin da wurin ke mata ba, "Ina Ummita" Rike mata hannu tayi mu je na kaiki," Har ofishin Doctor ta kaita sannan ta mai bayani, Tashi yayi daga kan kujeran da take,yana nuna mata hanya"mu je " Tana biye dashi ya juyo yace"ya kike da ita" "Yar uwa tace" Shiru yayi kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace"iyayen ku fa,dama jira muke ki farka" "Duka sun mutu ba mu da kowa sai mu kaɗai" Ta faɗa mashi dan bata son ya kuma mata wani tambayar, Tura ƙofar dakin yayi ya shiga tana biye dashi sai dai dakatawa yayi kafin su karasa ciki,"naso ace naga wani babba naku,sai dai kin ce ba kuda kowa wanda hakan ke nufin ke zan ma bayanin komai " "Ina Ummita? Numfashi ya sauke" Ina mai baki haƙuri akan rashin da ki kayi,domin sakamakon gwaje-gwaje ya tabbatar mana da cewa yau tsayin kwana biyu kenan ma da bata raye,saboda rashin Oxygen,shi yasa ma har ta fara kunbura, Sam ita bata ma fahimce me yake nufi ba"ina Ummita "ta ƙara maimaita mai,dan ji take kamar kalam shi na dazu ba da ita yake yi ba, Lumshe ido yayi ya buɗe yana matsa mata a hanya" Tana ciki" Bata ma jira ya ƙarasa faɗa ba ta shige cikin dakin da sauri, Kallon gadon dake cikin dakin tayi wanda shi kadai ne a tsakar dakin,akwai kamar mutum kwance a sama sai dai an rufe shi da farin kyalle kamar da gawa, Ta jima tsaye tana kallon gadon kafin a hankali ta fara takawa har ta isa ta wurin kan, Hannu tasa ta yaye zanin da aka rufe fuskar dashi har katsa, Tun daga suman kan take kallo har zuwa yatsar ƙafa, Jin yanda jikinta ke rawa ne yasa ta tsugunna a gaban gawar tana jin yanda hawaye ke diga daga idanunta zuwa katsa, Wani irin kuka ta fashe dashi mai ƙarfi tana riƙe hannu ta,"Ummita!"ta shiga kiran sunan tana kuka mai matukar girgiza zuciya,ba-zata taba manta maganar da sukayi da ita na karshe ba in da take cewa *ke ce farin cika na,kuma gata na,dan haka ki yi sauri ki kammala ina jiran ki* Rungume hannun ta tayi a kirginta"Ummita ke kika ce zaki jira ni,me yasa zanzo yanzun na tarar da gawar ki,why?me yasa,shin baki san ni ma kece farin ciki na ba,me yasa zaki tafi ki barni"kuka take yi sosai tana jin wani irin duhu na mamaye zuciyar ta,wani irin zafi take ji gabaɗaya jikinta har katsan zuciyar ta, Shi kenan Ummita ta mutu kenan ba zata sake tashi ba,ba zasu sake rayuwa wuri ɗaya ba,ba zata sake mata magana ba,yanzun da waye zata dinga zuwa aiki, Kallon gawar tayi,"wani irin mutuwar azaba kika yi yar uwata "ta faɗa tana daura kanta saman kirjin ta, Nos din ce ta zo ta daga ta tana rungume ta," Fatar jikinta bai da karfi saboda zafi,ki yi hakuri yanzun haka ƴan sanda na kan bincike akan ta" "Dan Allah ki taimake ni ki ƙara dubata ko dai bata mutu ba,ina son na faɗa mata zan mai da ita gida wata rana,ina son tayi rayuwar farin ciki kamar kowa,me yasa zata tafi yanzun"ta ƙarasa faɗa cikin tsananin kuka tana dafe kanta" Nayi dana sani akan komai,me yasa lokacin da zan tafi da kika ce zaki je ban tafi dake ba,"komawa tayi wurin gawar ta shiga jijjigata "Ummita,dan Allah ki tashi,please don't live me,me yasa zasu ce kin mutu,I can take it,na rasa kowa nawa,a lokacin da nake farin cikin samun ki nake murnar zan rayu a matsayin me yar uwa me yasa zan rasaki ke ma,? Share hawayen ta tayi" Kin ce na daina kuka,me yasa zaki tafi,ni yanzun na zama ni dai kenan,Ummita " Ji tayi lokaci ɗaya numfashin ta yana ƙoƙarin daukewa kuma, Ganin zata faɗi ne yasa Nos din dake gefe tana taya ta kuka tayi saurin riƙe ta, Da taimakon likitan aka ƙara mai da ita kan gado, Alluran barci mai ƙarfi sukai mata wanda dole zata jima tana yi dan tana buƙatar hutu, Duk da haka kafin barcin yafi karfin ta sai kiran sunan Ummita take yi, Gaskiya sun tausaya mata sosai,domin ta saka yarinyar a rai, Ba ita ta ƙara tashi ba sai ƙarfe biyar na yamma,ta jima a kwance idanun ta biyu,wato abinda zasu mata kenan,ta masu aiki tsayin shekaru shine zasu biyo mata ta wannan hanyar, Tabbas wannan karon sun kai makuran su,kamar yanda bata san waye su ba,haka basu san wacece Biba ba,amma yanzun sun taso da guguwar da ba zasu iya tarewa ba,sai ta baiyanar dasu a idon duniya ɓoyewar da suke yi sai ta baiyana, Yanzun da ita zasu fara Yaƙin ba da Suraj ba,sai ta zame masu ɗan haƙƙin data rai na, Mikewa zaune tayi sannan ta sauko daga saman gadon tana zura takalminta, Tana buɗe ƙofar Nos din na ƙoƙarin shigowa "Miss ya jikin naki? " Da sauƙi dan Allah ki ara min wayar ki" "To ba damuwa" Cirowa tayi ta mika mata wayar,komawa tayi cikin dakin ta zauna bakin gado, Number data san yafi kiranta dashi ta tura masa sako kamar haka:*Naga saƙon ka na gode,ni kuma ku jira nawa zuwan* Goge saƙon tayi tayi sannan ta saka wani number wanda Ringin uku aka ɗauka, "Biba ce" "Biba" Ya faɗa da mamaki kafin da sauri yace kuma"kina ina ne,tunda muka rabu a Legos ban ƙara ganin ki ba,na kira Ummita number ta baya shiga,Biba yaushe zamu haɗu,akwai aiki a katsa fa" "Mu haɗu yanzun zan zo gust house ɗin ka" "Wow to sai mun haɗu ina jiran ji,ko na zo na ɗauke ki ne? " A'a gani nan zuwa"ta kashe wayar, Mikewa tayi ta fito ta kai ma matar wayar ta"zan wuce amma ba zan dawo yanzun ba a saka gawar a Matuware " "Ki tsaya to ki karasa karɓar treatment di ki" Girgiza kai tayi"ina da abin yi"tana gama faɗa ta wuce, Tana fita Adaidaita ta hau ta faɗa masa in da zai kai ta, Suna isa me gadin ne tasa ya ba mutumin kuɗin shi,sannan ta shiga ciki, Gidan ba baƙon ta bane dan haka kai tsaye cikin falon ta shige, Da sauri ya taso ya rungume ta ya ɗaga ta sama yana juyi da ita yana dariya, "Ka sauke ni Mansour" Sauke ta yayi yana rungume da ita,kokarin sumbatar ta yayi ta kauda kai tana zame wa daga jikin shi,samun wuri tayi ta zauna a daya daga cikin kujerun falon, Zama yayi kusa da ita "Beb meke faruwa naga kamar baki cikin farin ciki" Dago fuskantar yayi cikin tashin hankali yace"me ya samu idon ki?kin yi kuka ne?me ya faru,waye ya taɓa ki? Kuka ta fashe dashi tana faɗawa jikin shi,gabaɗaya ta gama tayar mai da hankali saboda irin kukan da take yi,"Ummita ta Mutu,they kill her" Da sauri ya dago ta"me kike nufi da ta mutu? Sake shi tayi tana kyara zama"wani aiki ne na karɓa mai matuƙar rikitarwa,"nan ta shiga bashi labari har na auren da tayi a cikin aiki da kuma abinda ke faruwa da shi da kuma ita,"yanzun haka ana su shirin gobe za'a shiga koto,idan har na bari suka samu nasara akan shi to kamar akai na suka samu,so suke su kashe mu bayan kammala komai,sun hana a samu lauyar da zai tsaya" "Zan samar maku lauya Biba,sai dai nayi baƙin cikin wannan auren,amma dai in komai ya wuce kuka gama wannan rigimar zaki dawo mana ko? Dan Allah ya gani yana bala'in son yarinyar, " Bana son shi,dan haka zan rabu dashi" "Bari na kira shi yazo ya same mu" "A'a bana buƙatar wani Loya,zasu iya mai barazana kamar yanda suka saba,wannan karon kuma ina son na fito masu ne a zahirin koni wacece" "Me kike nufi? " Ina da takardun zama cikakkiya Lauya,sai dai License di na yayi expire,ina buƙatar inyi sabon Registration wanda ba ni da lokacin, Sai dai taimako daya zaka iya min shine a matsayin ka na Babban Ministan birnin taraiya ka saka Amin Ragester cikin awa daya sannan a dauke ni a matsayin lauyar Gwamnati,ta hakan ne zan iya tsaya mashi domin ni babu abinda zan rasa yanzu" "Dama kin yi karatu har haka ne? " Nayi karatun lauya a kasar London,nayi Digree na daya dana biyu duka a can " Buɗe baki yayi yana kallon ta cikin mamaki,domin bai taba tunani ba,"ina takardun naki suke? Wayar shi ta ɗauka ta saka number Google Account dinta ta fito mai da su,mika mashi tayi "gashi nan,sai ka tura masu suyi printing" Amsa yayi yana kallo kafin ya gado yana kallon ta,cikakkiyar result ne mai dauke da shedar kwarewarta a kan Lauya,"Me yasa naga sunan *UMMU SALMA ABDULLAH* Lumshe ido tayi"Asalin sunan kenan " "Kina nufin asalin sunan ki kenan" "Umm" "Biba kuma fa" Ɗaga kafaɗa tayi,"ka yi ƙoƙari a kammala min komai zuwa ƙarfe bakwai zan wuce" Dariya yayi yana jin son yarinyar na ƙara tasiri a zuciyar shi,yanzun da yake gab da sanin ita wacece"zan saka a kaiki da ƙaramin jirgina " "Na gode,ka saka a samomin duk wani abunda nake buƙata zan rubuta maka list,zan zauna anan kafin na tafi" "An gama Hajiya ta," Ganin tana ƙoƙarin shigewa daya daga cikin dakin ne yace"to ko ɗan Kiss ba zan samu ba? "Har yanzun da igiyar auren shi a kaina ka bari idan an warware"ta fada shigewa cikin dakin tare da turo ƙofa, Murmushi yayi kawai ya tashi yana barin gidan, Tana kulle kofar faɗawa tayi kan gado tana fashewa da kuka tare da tura kanta cikin filo, Ada tayi Alkawarin ba zata kara amfani da duk wani abu ɗaya danganci Salma ba,saboda ta tsani ta tuna baya,bata kaunar ta tuna wandanda suka yi silar kawota duniya saboda babban zunubin da suka aikata ma rayuwar ta,taso tayi nisa da komai ta ci gaba da tafiya har abada,sai gashi sanadin wannan aikin yana ƙoƙarin mai da baya,bayan ma sosai irin wanda ta fara mantawa da kaman sa, Bata son ta ji suna ko mai irin nata saboda gudun wancan rayuwar, Jin wayar shi data karɓi daya yana ƙara ne yasa ta duba,shi ne ke kira akan ta turo masa list din dan har an fara mata aikin takardun ta, Dan haka cikin sauri ta rubuta komai ta tura mashi,sannan ta tashi ta shiga banɗaki dan tayi wanka kafin ya aiko mata da kaya ta wuce, Zuciyar ta cike da ƙuduri da kwarin gwiwar ɗaukar fansa. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *47* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Kafin ƙarfe shida na yamma ya kammala mata komai na tafiyar ta an kammala hada mata License nata,sannan ya saka jirgin shi ya dauke ta,wanda ƙarfe takwas ta masu ne garin Lagos, Bata yarda ta sauka a Hotel din da su Abba suke ba,wani ta kama da ban ta kammala shirin ta sannan ta nufe babban Headquarter da taji yake, A babban offishin su aka sauke ta kasancewar ta nuna masu I D card din ta na matsayin cikakkiyar lauyar gwamnati sannan zata tsaya mashi, A lokacin ma Ogan su na gida aka fada mashi,sannan tace tana buƙatar ganin wanda zata kare, Koda suka faɗa mashi dariya kawai yayi"maza ma sun kasa sai ita,ku barta ta shiga" Ai kuwa kira suka yi aciki aka fito dashi karamin falo in da suke ganawa da lauyoyi ko kuma iyalan su, Tunda ta shigo wurin take kallon ko ina da kuma irin jami'an tsaro dake wurin,har aka mata iso aka buɗe mata ƙofar shiga in da yake, Tunda ta shiga take kallon wanda ke zaune fuskarshi na kallon gefe, A hannun shi da suke kumbure idanun ta suka fara sauka,hakan yasa karfin takunta fara raguwa,har ta iso in da yake zaune, Ganin bai juyo bane yasa ta kira sunan shi a hankali dan son tabbatar wa"Suraj" Juyowa yana daura idanun shi a kanta, Da sauri ta dafa kujerar dake kusa da ita, Kamar yanda take kallon shi haka shima yake kallon ta,banbancin shine ita kallon tsoro take mai, Ganin ba ta da niyar natsuwa ne yasa yace"Idan baki da karfin gwiwar gurewa me na baiyana? Tabbatas shi ne, Ji tayi hawayen da take ƙoƙarin rikewa ya sauko, Da sauri ta share da bayan hannun ta,cikin karfin hali ta jawo kujeran dake kusa dashi ta zauna, "What have they do to you? " Tambayar da kika zo ki min kenan? Ganin yanda yake magana da kyar ne yasa ta kasa jurewa ta kifa kanta da kujeran wurin tana fashewa da kuka"ba zan taɓa yafe masu ba!ba zan taɓa barin su ba"ta faɗa cikin kuka, Bai dakatar da ita ba dan haka sai da tayi kuka sosai har sai da taji zuciyarta ya ɗanyi sanyi sannan ta tago,idanun ta sun yi jawur sun kumbura,saboda yinin da tayi tana yin kuka, "Why are you crying? " They killed my friend,she is my everything " "Waye lauyar nawa? Share hawayen idanun ta tayi wandanda suka kasa tsayawa," Ni ce" "Akwai hatsari a aikin ba zaki iya ba" "Na riga na rasa abinda nake karewa,babu wani abunda yayi saura wanda zan rasa" "Wannan hawayen yana nufin gazawa,rashin juriya" "Na yau ne kawai" "To ki saka su tsaya"ya faɗa yana kallon yanda take ƙoƙarin ganin ta Dakar da hawayen ta hanyar shanyewa amma ta kasa,because the more she tried the more hawayen ke kara saukowa, " Ko wata fitar numfashi da aƙwai sauki mai tarin yawa a cikin shi, Kula da ciyo mai matukar zafi ba abu ne mai sauƙi ba, Kada ki yi ƙoƙarin kunna wuta akan abinda zai iya kona ki,sannan kaɗa ki rike takobin ki domin yanka fure kawai, A sanda zaki iya iyo a cikin babban Teku,kada ki bari ruwan hawaye ya rufe maki idanun ki,domin kina iya nitsewa" Mikewa tsaye yayi"sai mun haɗu a Kotu gode "yana gama faɗar haka ya juya ya bar wurin cikin dingishi wanda yake yi yana dafe gefen cikin shi, mikewa itama tayi tana sai saita kanta sannan ta fito cikin wurin ta wuce bayan ta masu sallamah, Hotel din data sauka ta koma,tana shiga daki wayar ta na ƙara,koda ta duba sunan Ammi ta gani,dan haka ɗauka ta yi,sallamah taimata,ita ma ta amsa, "Gobe za'a shiga koto" "Hakane Ammi" "Kin samu ganin shi? " Eh" Dan shiru tayi na wani lokaci"Abbu yace har yanzun basu samu ganin shi ba,sannan basu samu tsayayyen lauya ba" "Zan tsaya a matsayin lauyar shi" Ajiye carbin dake hannun ta tayi,"ya amince? "Ban damu da amincewar shi ba" Jin sautin murmushin ta tayi,"Allah ya bada sa'a " "Me yasa baki yi mamaki ba? " Saboda Nasan zaki iya" "Baki yi mamakin kasancewata lauya ba?me yasa baki tambaya ba? " Saboda akwai wasu abubuwan da har mu mutu bamu isa mu san su ba, Allah ya kare ki,ya kuma saka Ayi walƙiya mai matuƙar haske,abin da ke cikin duhu ya baiyana" Shiru tayi ta kasa cewa komai,maganar su na matuƙar daure mata kai daga na Uwar har na ɗan,shima bai yi mamakin kasancewarta lauya ba,haka bai tambaye komai akai ba,it seems like sun san wani abu game da ita, "Ammi"ta kira sunan ta " Na'am " "Shin kin san koni wacece? Sai da tayi ɗan jim kamar ba zata amsa ba sai kuma tace" Na sani Ummu Salma,na sani tun farko,har ta abinda ke kanki baki sani ba game dake,"ajiyar zuciya ta sake"ina da duk wani amsa da Kike nima,sai dai yanzun ba lokacin da zan amsa maki su bane,abu na farko da zaki yi shine Ceto rayuwar ɗa na,idan har kika dawo min dashi lafiya na miki alkawarin sanar dake abin da baki sani ba" "Amma shi ya sani? "Bai sani ba,babu wanda ya sani," "Wacece ke? Ta tambaya domin ji take kamar bada Ammin take magana ba,a ina ta santa,har ta san Asalin sunan ta,ji take kamar numfashi kawai take yi amma wasu mutane ne ke sarrafa rayuwar ta, " Me yasa kika karbe ni a matsayin mai aikin ki bancin tun farko kin san ko ni wacece? "Ki yarda dani Ummu Salma,ba zan taɓa cutar dake ba,ke dai kawai ki yi yanda nace,domin rayuwar ku a yanzun shi yafi komai muhimmanci" Hawaye ne ya shiga bin idanun ta,meke faruwa da rayuwar ne,jan majina tayi tana ƙoƙarin sai ta kanta "Amma kin san da mutuwar Ummita? " Dazu nake samun labari,very sorry for you lost " "Me yasa zasu mata irin wannan kisan,me yasa" Ta karasa faɗa tana fashewa da kukan data kasa riƙewa ta tsugunna a nan ƙasa tana faman rusa kukan, Hannu tasa ta dafe kirjin ta "ba zan iya daurewa ba,zuciya ta zafi take min kamar an kunna wuta,a duk lokacin dana tuna shi kenan na rasata har a ba da ji nake kamar na mutu ni ma, Rayuta kadai ta rage min a yanzun amma ji nake kanar ita din ma tana hannun wasu ne su ke juya min ita, Yaya zan yi,me ya kamata nayi domin dawo da komai,sai dai komai ya riga da ya bar hannu na,duk da haka bana jin zan iya barin koma waye ke da saka hannu akan wannan lamarin,ina nufin ko waye shi" "Rayuwar ki tana hannun Allah ne da hannun ki ba hannun wani ba,ke kike da damar da zaki juya taki rayuwar Salma,ko wani abu da ki kaga ya faru da bawa to yana da dalili,ko wani dan Adam kuma yana da nashi tarihin mai ƙunshe da abubuwan mamaki da darasi,kamar dai naki, Ina maki fatan nasara akan wannan tseren,idan har akwai abinda kike butaka kina iya tuntuɓa ta"tana gama faɗar haka ta yanke wayar. Wannan shine dare na biyu da ta ci kuka kamar rayuwar ta zai ɗauke a karo na biyu,komai sabo yake dawo mata a cikin ƙwaƙwalwarta, Da fari komai gwanin daɗi,amma daga baya komai ya juya tun daga sanin wani ɓoyayyen gaskiya,ba zata taɓa manta ko ita wacece ba,duk kuwa da irin nisan da tayi da kuma kokarin da tayi, Abu ne mai matukar ciyo sosai,mai kuma kona zuciya ya narkar da ita kamar bata taba wanzuwa ba a jikin ɗan Adam, Tabbas tayi tunani me zurfi a wannan dare,ta kuma ɗauki darasi a mutuwar yar uwarta,shin ta koma in da ta fito ne ko kuma taci gaba da tafiya kamar yanda ta ɗauki kudiri a da. Rufe karamin littafin dake hannun ta tayi tana ajiye biron a gefe, Shafa bayan littafin tayi wanda aka rubuta *MY DESTINY* a jikin bangon littafin, Kallon Agogon bangon dakin tayi wanda ya nuna ƙarfe Uku na dare, Komawa tayi bakin gado ta zauna a kasa tana daura kanta a saman katifar gadon a maimakon ta hau ta kwanta, Daga haka ne bacci barawo yayi awan gaba da ita ba tare data shirya ma hakan ba. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *48* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Washegari tana tashi wanka tayi sannan tayi sallah ta koma ta kwanta tana jawo wayarta ta buɗe data, Bansan me take yi ba amma daga dukkan alamu abu mai muhimmanci take yi,wanda tana yi tana duba agogon dake makale jikin bango lokaci_lokaci saboda ƙarfe goma na safe za'a fara gudanar da nashi shari'ar, Dan haka sai ƙarfe tara sannan ta tashi tayi break Fast wanda tasa aka kawo mata tun dazu, Number Alhaji Mansour ta kira tana sanar dashi ta kammala ya turo mata direban sa yace zai mata aiki, Nan yake sanar da ita ai mutumin yana harabar Hotel din yana jiranta tun ƙarfe takwas na safe, Kashe wayar tayi ba tare data damu da mai godiya ba ta fito, Tsayawa tayi a babban harabar Hotel din tana kallon manyan motocin dake farke a wurin, Ji tayi daga bayanta ana fadin"Hajiya barka da fitowa " Juyowa tayi ta kalli mutumin wanda bai wuce sa'ar yayanta ba,sai dai bata ce mashi komai ba, Da hannu ya mata nuni da inda wani lafiyayyen mota ruwan ƙasa ke parke "Hajiya ga motar can" Bin bayan shi tayi ba tare data jira ya buɗe mata ba ta saka hannu ta buɗe gidan baya tayi zamanta, Shi kuma buɗe mazaunen Direba yayi ya ta da motar suka fita farfajiyar Hotel ɗin, "Hajiya ina zamu tafi? " High court"ta bashi amsa a taƙaice tana kwantar da kanta jikin kujeran motar, Kunsan yanayin Goslow irin na Legos dan haka ko kafin su isa har ƙarfe goma da rabi ake nima,koda suka shiga koton an daɗe da fara gudanar da shari'a, _____Acikin koto kuwa ba'a bari wasu mutane masu yawa sun halarci cikin ba,daga dangin Yarinyar sai kuma nashi dangin,wato su Pa dasu Abbu,Dady,sai Nadiya dake ma su Kaka Video kai tsaye suna kallon abinda ke wakana acikin koton, Haka suma bangaren iyayen yarinyar suma suna da masu kwashe masu,sai dai su kai tsaye suke daurawa a shafikan su na yanar gizo wanda kowa zai iya kallon yanda komai ke gudana, ____A can gida Kano kuwa hankalin su duk a tashe yake,domin gabaɗaya daga manyan gidan iyaye da yara har Ammi a falon kaka suka haɗu suna kallon yanda Lauyan su ke jeho ma Suraj tambaya kuma ya hana shi magana sai dai kawai ya bashi dama in Eh ne yace eh,in A'a ne yace A'a,kuma duka da harshen Turanci suke magana, Kaka ce ta fashe da kuka"kai Allah ya tsine ma wannan jikan bakin tuwo,ta yaya zai hana yaro magana " Kuka Amira ta saka tana dafa Ammi dake kusa da ita wanda Allah kaɗai yasan meke gudana a cikin zuciyar ta"Ammi shi kenan yanzun sun kada yaya Suraj,jibi yanda suke zubo mashi tambaya " "Ai daga ganin yanda wannan lauyan ke jeho tambaya kasan ƙwararre ne, kayar da shi ba abu mai sauƙi bane,gaskiya da wuya akai labari" Cewar Hajiya Saude, "Koma dai menene karfin addu'ar mu na tare da Suraj Allah zai baiyana gaskiya ta inda basuyi zato ba" Goggon yara ta fada, Dafa hannun ta tayi"me yasa zaki karaya tun yanzun,bayan ko asalin shari'ar ba'a fara ba " Duk kallon mamaki suke mata,Ibrahim ne yace"Ammi amma ai har yanyi rabin shari'ar,idan kuma har aka kai karshe ba tare da wani kwakkwaran hujja ba shike nan mun rasa wannan shari'ar " Nuna masa TV tayi"ai ba kai karshe ba,amma ka kalla ka gani" "A'a wacece wannan ta shigo?ku kalla ga wata nan ta shigo sanye da kayan lauyoyi" Duk maida hankalin su kan TV suka kuma yi, _________*Legos* Mai gadin bakin ƙofar babban Hall din ne ya buɗe mata ƙofa bayan ta nuna mashi I.D card ɗinta, Jin an buɗe ƙofar ne yasa Lauyar dakatar da wasu tambayoyin da yake ma Suraj ɗin, Taku take cikin natsuwa tana juyawa tamkar wata Ɗawisu,har ta iso dai dai in da take da damar tsayawa kafin ta cire gilashin dake Idanunta wanda ya kusa rufe rabin fuskarta ta rike a hannun, (Kuyi haƙuri da yanda shari'ar zai zo domin bansan yawancin ka'idojin Kotu ba). Daya daga cikin masunjojin kotu ne ya tashi"Hajiya shin baki san nan kotu bane da zaki shigo kai tsaye tamkar gidan ki? Ba tare data bashi amsa ba ta maida fuskanta kan Alkalan dake zaune su biyu cikin girmamawa irin nasu tace"ina niman afuwa akan jimawar dana ni ban karaso ba,wanda hakan ya faru ne sakamakon cunkoson abun hawa, Ni suna na *Ummu Salma Abdullah Lauyan wanda ake tuhuma* To fa wannan shi ake kira kallo ya koma sama, Nadiya ce ta dafa yayan ta tana kallon Pa"Pa wannan ai daughter Biba ce,matar Suraj " Ɗan rankwashi yayan nata ya sakar mata"ba ita ba ce,ke dai ki yi shiru muji " "Kina iya zama kotu ta maki uziri amma nan gaba ki ki kiyaye" "Na gode ya mai shari'a" Ta faɗa tana zama a kujerar da aka tanada dan su,wanda ta samu lauyoyi biyu a zaune, Lauyan dake magana ne ya cigaba da faɗin "Ya mai shari'a,kamar yanda na gabatar ma da kotu kwararan hujjojin na,ina rokon koto data yi gaggawar yanke ma mai laifi hukunci ba tare da bata wa kotu lokaci ba"sannan ya koma ya zauna Alkalin ne yace" A sakamakon waɗannan hujjojin da Lauyan mai ƙara ya gabatar,koto ta duba kuma ta gamsu dashi,zata kuma yi amfani dashi wurin yanke ma mai laifi hukunci..... Mikewa tsaye tayi tana daga hannu "ya mai girma mai shari'a,a matsayina na Lauyan wanda ake tuhuma ban yarda da hujjojin da Lauyan wanda yake kara ya bayar ba,sannan ina da tambayoyin da nake da bukatar na ma wanda nake karewa a gaban kotu sannan tare da ba da nawa hujjojin kafin a yanke hukunci" Ji yayi kamar ya taso ya shake wannan yarinyar daga saman kujeran da yake zaune,wacece ita da zata bata masu shirin su,daga ina take,shi yasa yaso ya yanke hukunci kai tsaye amma ta katse shi,daga ganin kuma yanda take tana da kwarin gwiwa,domin babu alamar tsoro a tattare da ita ko fargaba,chief ya fada a zuciyar shi,wanda ba shi kaɗai yake raya hakan ba,yasan suna da yawa a koton masu tunani irin nashi,dan daga inda yake zaune yana iya hango bacin rai mai tsanani ƙunshe a fuskar Shugaba, Babu yanda ya iya dan haka dole yace"Kotu ta baki dama" "Na gode mai shari'a" Ta faɗa tana haurawa saman stage din da yake tsaye yana kallon ta tun shigowar ta,duk da ada ya fara cire rai akan zuwan nata, "Malam shin zaka iya faɗa mana Asalin Sunan ka? Ta fada cikin kwarewa da harshen turanci, " Suraj Abdul basir " "Menene Alakarka da Jusica" "Ba ni da wata Alka da ita,asalima ban santa ba" "Idan baka santa ta yaya aka samu gawarta a cikin dakin Hotel din da kake zaune? Zuba mata ido yayi na sakanni,yayin data kauda kanta daga kallon da yake mata, " Ni ma ban sani ba,domin bansan da gawar ba sai da jami'an tsaro suka zo suka bincika " Juyawa tayi gaban Alkalan "ya mai girma mai shari'a,ina son kotu tayi duba da waɗannan takardun binciken da likitoci suka gudanar a kan gawar,wanda ke nuna babu shafin hannun wanda ake zargi akan jikin Jusica,ko kuma wuƙar da aka yi amfani da ita wurin cire wani shashi na jikin ta,ina son koto tayi duba ga wannan ta kara nazari akan wannan batun" Mikewa Lauyan su yayi"ya mai shari'a,Barista Ummu Salama ba ta da wani hujja da zata gabatar ma kotu,so kawai take tayi ma kotu wasa da hankali ta kuma bata ma kotu lokacin " "Ina da dama da zan fada duk abinda zan faɗa kuma kotu ta saurare ni a matsiya na Lauyan under Section 10 a kundin littafin lauyoyi," "Kotu ta baki dama,Barista Wale ka kiyaye" Dole ya koma ya zauna yana hararanta,ƙarama da ita tana ƙoƙarin maida masu da aiki baya, "Yamai shari'a ina rokon kotu ta Bani damar yi na shugaban yan sanda na wannan yanki tambayoyi? " Kotu ta baki dama" Nan matsinjan ya fara shelan mutumin kafin katon Bayaraben ya fito yazo ya tsaya gaban kotun, "Ya sunan ka? " Suna na Akintola " "Malam Akintola ko zaka iya faɗa ma kotu ta yaya ka samu labarin cewa akwai Gawa acikin wannan Hotel din a kuma dakin da wanda ake tuhuma yake ciki" "Eh na samu labari ne daga kiran dana samu" "Muna bukatar jin daga waye ka samu kiran? Ɗan shiru yayi kamar mai nazari kafin yace" Nima ban san ko waye ba kawai dai number ne ya kira ni ya faɗa min,ni kuma naje domin na tabbatar shine na samu abinda na samu" "Ina butar ganin wannan number da aka kira ka dashi" "Wayar ya faɗi,an sace wayar" Jin ji na kai tayi"shin an sace ne ko ya faɗi ? "Ya faɗi ne" "Zaka iya komawa ka zauna" "Na gode" Ya faɗa yana sauke wani ɓoyayyen ajiyar zuciya, "Ya mai shari'a ina butar kotu ta Bani dama domin nayi magana da Manager Hotel" Daya daga cikin masunjojin yace" Manager wannan Hotel din baya nan saka makon wani uziri da ya kama shi ta tafi garin su Jos" Komawa tayi gaban koton"Ya mai shari'a sakamakon rashin kammala haɗa hujjoji na ina rokon wannan koton mai adalcin data ɗaga wannan shari'a daga nan zuwa ranar Ishirin ga watan nan" Ɗayan Alkalin ne yace"sakamakon duba da wannan lamarin da kotu tayi,Kotu ta daga wannan shari'ar daga yau hudu ga watan April shekara ta dubu biyu da ishirin da uku zuwa goma ga wannan watan na April shekara dubu biyu da ishirin da uku"daga nan ya buga wannan ɗan sandan nasu, Duk mikewa suka yi cikin girmamawa, Duk da taso ta samu ƙarin ƙwanaki ta yanda zata yi bincike sosai a kan komai amma shine suka bata kwana shida kawai, Duk da taga sanda suka biyo dashi ta gabanta zasu tafi dashi gakan baisa ta dakata daga haɗa takardun da take yi ba,har suka wuce dashi, Tana fitowa ta samu su Dady suna jiran fitowar ta a harabar wurin 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *49* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Karasawa tayi in da suke tsaye,sai da ta kalli agogon dake hannun ta wanda ya nuna mata ƙarfe goma sha-biyu na rana, "Barka da rana" "Habiba me ke faruwa ne?cewar Abbu, Murmushi ta saki,dama ta san hakan zai faru" Ba wani abu bane Abbu,ku kwantar da hankalin ku na maku Alkawarin idan komai ya lafa an gama wannan shari'ar zan sanar daku komai " Pa ne yace "ki faɗa mana komai yanzun dai,da Ummu Salma muka ji fa kin gabatar da kanki"ya faɗa kamar adan hasale, " Abu mai muhimmanci shine yanda Suraj zai fito,sannan koma menene ya biyo baya, na bar ku lafiya sai mun haɗu a kutu"tana gama fadar haka ta juya ta wuce,dan ba zata manta maganar A'i da tace mata karta yarda da kowa har a cikin gidan, __________*Kano* "Kaka wannan ba Biba ba ce? Duk ƙara kurama TV ido suka yi, " Kanbu,wallahi ita ce,kaka nifa na fara tsoron lamarin yarinyar nan,ki duba yanda tayi mana bazata a wurin taron mata malamai,yanzun kuma Lauya? "Shi yasa naso tun farko na aure ta saboda nasan ita din Materiel ce" Duk kallon mamaki suke mai, "Ka nada hankali Nurudeen? Bata fuska yayi yana kauda kai,dan abinda ya faɗa har cikin zuciyar shi ne, " Ni dai in komai ya wuce a bin cike ta"cewar Hajiya Rahama "Wallahi Momy na fasa zama likita lauya zan karanta,dubi yanda Biba ke zuba Turanci kamar ba a bikinta ya ke fitowa ba"cewar Hadiza, " Ammi me ke faruwa? Ta faɗa tana kallon TV yanda ake zuba challenge, "Koma me ke faruwa lokaci zai nuna" _____________tana shiga mota tace ma direban"muje gidan yari" "To Hajiya" Ya faɗa yana karya kwana, Koda suka isa buɗe mata kofa aka yi aka bata damar yin magana dashi kamar dai jiya a wannan ɗakin, Jan kujera tayi ta zauna suna fuskantar juna, "Ina yini" "Assalamu alaikum" Ya fada, "Oh Assalamu alaikum" "Wa'alaikumussalam,wannan ya zama abu na farko da zaki fara yi aduk sanda muka haɗu" Turo baki tayi"har yana da bakin korafi" "I can hear you" "Akwai abunda nake buƙatar na sani ne? Ganin irin kallon da yake mata ne yasa tace" Ina nufin a matsayina na lauyan ka" "Babu" "Akwai mana,kamar daga lokacin da gawar ya kasance a dakin da kake,ko kuma wani yanayi ko kuma dai abinda kake zargi ko wanda kake zargi, dole za'a samu wani" "Duka babu" Ya faɗa a takaice, Ajiyar zuciya ta sauke tana dafe kumatunta,yayin da hankalin ta ya tafi kan wani nazari na daban, Zame hannun nata yayi daga tagumin da tayi wanda hakan yasa goshinta ya bugu da center table ɗin, Dafe goshinta tayi tana shafawa,cikin jin haushi tace "me haka? Kafaɗa ya daga" What" Mikewa tayi sai kuma ta koma ta zauna da sauri tana sakin murmushi,"yauwa ina Kakan ka take,ina nufin a wani Country take " Shiru yayi kawai yana kallon ta ba tare daya bata amsa ba, Ɗan marairaice fuska tayi"bana son irin wannan kallon pls" Kauda kai yayi yana ɗan lumshe ido kafin yace"me za'a " "So nake kasa a canja mata Asibiti daga in da take,idan so samu ne har likita ka canja mata,idan kuma ka yarda da wannan kana ita daukar shi aiki har zuwa sanda komai zai kammala ya zama na babu wanda yasan in da take" Tambayar daya jeho mata ne yasa ta dakata daga maganar da take yi, "Me yasa zan yarda da ke? Shiru tayi na wasu sakanni yayin da suka shiga musayar kallon na sakanni kafin ta dauke nata idanun" Wannan zabinka ne ka yarda da ni ko akasin haka"busar da iskar bakin ta tayi sannan ta dawo da kallon ta kanshi"ni ba kamar yanda kake gani na nake ba,ko da yake ina dauke da Najasa,haka ne tunda ni din *ƘARUWA CE* kana iya saka Hausar a haka,ta iya yuwa kasan abinda ya shigo da ni rayuwar ka ko baka sani ba,amma ina mai tabbatar maka haɗin kanka shi kawai zai saka mu tsira tare da kai, Idan kuma har mukaci nasara zan bar rayuwar gabaɗaya ba tare da na bar maka wani abinda zaka tuna da ni ba," Jin kalmar data kira kanta dashi kaɗai ya saka zuciyar shi dukawa, "Idan har baki ci nasara ba fa?zaki fita ki bar rayuwata? " Duka daya ne?idan ka yi tunani akai kana iya sakawa a kira ni"ta faɗa tana mikewa, Har ta kusa kaiwa ƙofa ta ji yace"Germany,Berlin, Mitte,Orthopedic Clinic (Campus Charite Mitte) Takardar da ke ajiye a gabanshi da biro ya ɗauka yayi dan rubutun da bai wuce layi uku ba ya turo mata,sannan ya tashi ya wuce, Murmushi ta saki tana bin shi da kallo kafin ta dauki takardan ta fita, Daganan ta wuce cike da tunanin dole gobe zata tafi domin bata da isasshen lokaci. ______karan saukar Mari ne ya karaɗe dan madaidaicin falon, Cikin masifa da tsananin bacin rai yace"i will killed you,me yasa baka faɗa min tun tuni ba sai yanzun,gashi saboda kai aikin da muka yi shekaru muna shiryawa kana kokarin ruguza komai,bayan mun sha matukar wahala kafin mu samu wacce zata iya " Cikin tsoro da rawar jiki ya tsugunna a gabanshi "dan Allah shugaba kamin rai ba zan sake ba,ko da na bar ta Lafiya ta qlau ban San zata mutu ba" Wani marin ya ƙara sauke mashi yana huci,"ita ce yanzun ta tsaya masa a matsayin lauya,bayan kwangilan da muka dauke ta,kalli sakon data turomin"ya faɗa yana nuna ma Abokin nashi saƙon, "Yanzun mu kirata muji me zata faɗa"cewar Chief, Duk na'am suka yi da hakan,dan haka wayar shi da yake kiranta dashi ya ɗauka ya shiga kiran number ta, Sai da yayi ringin uku ba'a dauka,har ya cire rai za'a daga sai gashi yaji an daga, Sai saita kanshi yayi,kafin ya ce" Me haka ke nufi? Daga in da take zaune tana shirya wasu takardu ta bashi amsa"kamar me kenan? Danne duk wani bacin ranshi yake kokarin yi"Ummu Salma," "Suna na ne" "Sunan ki fa?Kotu fa?Barrister?me kike shirin yi ne,me manufar ki na kare wanda kike aiki a kanshi?ina bukatar karin bayani domin kinsan haka baya cikin tsarin aikin mu" Dariya tayi irin mai tsayawa a zuciya na takaici "tsarin aiki fa kace?ohh na manta ashe aikin yana da wani tsari?" Ajiyar zuciya ta sauke tana busar da iska mai zafi daga bakin ta"ina da amsar duk tambayoyin ka,sai dai ba zan amsa maka su ba,da kanka zaka fitar da amsar ta hanyar aiki na, Hmm kai har kana da wani ka'idar aiki,ai tuni na ajiye naka aikin a sanda ka karya alkawarin mu,mun maka aiki na tsayin shekara huɗu,amma ba kaji kunya ko tausayi ba ka kashe Ummi ta,sai dai ka sani wannan shine babban kuskuren da ka yi a cikin aikin ka wanda zai iya mai da maka aikin ka Sifili,kamar yanda bansan ko kai waye ba haka kaima baka san kome a kai na ba,dan haka wasa tsakanina dakai yanzun aka fara, Ba zan taba bari ka samu nasara ba sai na tarwatsa duk wani guziri naka,sai na baiyana ka a idanun kowa" Cikin tsawa mai haɗe da bacin rai yace"ke har wacece ke da kika isa ki bata shirin da ake yi tun kafin ki zo duniya,ke a tunanin ki zaki iya?shin zaki iya wasa da wuta a tsakiyar Teku? "Idan har kai da wuta kake wasa to ni ruwa ce mai matukar sanyi,wannan wutar da kake takama dashi sai na kashe shi na bi ta kanshi" "Zamu gani tsakanin ni da ke,?ki jira yi saƙonni na" Dariya tayi,"babu abinda zaka iya domin ni *YAR TSANAR ZINARI CE* mai tattare da abin mamaki iri-iri, Idan har ka iya to zaka iya taba ni ka zauna lafiya,idan kuma ka bata rawar ka da tsalle to dafi ne dane wanda yafi na maciji hatsari,idan ka shirya rasa rayuwar ka sai a kafta"Ta karasa faɗa tana sauke wayar domin dama ta tsammace abinda yafi haka daga gare shi, A nashi bangaren buga wayar da kasa yayi yana wani irin huci kamar zai yi aman wuta tsabar bacin rai, " Ina son a nimomin duk wani bayani dangane da wannan yarinyar" "An gama Shugaba" Suka fada cikin girmamawa, _______a washegarin da zata tafi bata samu damar wucewa ba,saboda dan tsaikon da aka samu daga Airport,dan haka da yamma ta shirya ta tafi Hotel din da ya sauka,in da abun ya faru, Nuna masu I.D card din ta tayi ta gabatar ma da matar da ke zaune a wurin tarbar baki,"dan Allah ina son in ga footage din 15 ga wannan watan" "Kiyi haƙuri ba ni da damar nuna maki,sai dai zan kira manager duk abinda ya ce zaki ji" "Ok ba damuwa" Daukar waya yarinyar tayi ta shiga kira, Ita dai tana gefe tana jiranta,tana kuma kallon yanayin yarinyar,daga dukkan alamu ba'a dace ba, Tana gamawa tazo in da take"ki yi haƙuri domin tun a wancan ranar Ƴan Sanda sun zo sun wuce shi" "Yan sanda kuma? " Eh" Ajiyar zuciya ta sauke tana dafe ƙwanƙwaso,"ko zaki iya haɗa ni da manager naku,dan akwai tambayar da nake son na mashi" Gyaɗa kai tayi"to bari na kira shi" Bayan yan mintuna sai ga mutumin ya zo,duk da ta dauka ko Bayarabe zata gani sai dai yanayin sarin na shi da yanayin shi zai tabbatar maka da IBO ne, Kamar a hassale yake,yanayin fuskar shi ya nuna haka da yake tambayar yarinyar, Nuna mashi in da take zaune yarinyar tayi, Yana karasowa ya zauna yana kare mata kallo tun daga sama har ƙasa kamar mai nazarin ta, Sanye take da riga da siket wanda siket din har kasa,rigar kuma mai dogon hannu mai botiri, sai ta gaban rigar ta hada ta daure leɓe daya,sai dan karamin Baby Hijab,tayi kyau sosai yanda kasan wacce bata cikin damuwa, Ƙara gyara zama tayi tana daura ƙafa ɗaya kan ɗaya,ita ma tana tsare shi da nata fararen idanun masu matukar han hankali, "Hi" Ta fada "Hy" Nan ta gabatar mashi da kanta da kuma abinda take nima..... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *50* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* "Ina mai baki haƙuri da kuma sanar dake kamar yanda ta faɗa maki haka din ne,domin ƴan sanda sun zo sun tafi da Footage ɗin" Dan kumbura baki tayi tana busar da isa tare da shafa goshin ta, "Karki damu da zaran sun dawo dashi zan kira ki," "Shi kenan na gode,sai dai dan Allah da zaran sun kawo ka kira ni" "Karki samu damu,sai dai baki Bani number da zan kira ki ba" Karamin takarda da biro ta ciro ta yaga ta rubuta mashi suna da number ta bashi, "Sai na jika" Ta faɗa tana wucewa, Taso ace ta riga ƴan sanda rike Footage ɗin,sai dai ba damuwa Allah yasa su dawo dashi akan lokaci, Washegari jirgin London ta bi kwanan ta daya a London ta wuce Germany a nan sai da tayi kwana biyu saboda shirye-shiryen da suka tsaya yi ita da Doctor wanda sai da ta bashi wasikar Suraj ɗin sannan ya yarda suka tafi ITALY kwanan ta daya ta biyo jirgi ta dawo,domin zuwa lokacin hankalin ta ya koma gida ta koma ta harhaɗa wasu hujjojin, A daren da ta sauka Hotel din ta koma ba tare data ko tsaya ta ci abinci ba ko ta huta duk da irin gajiyar data yi, Ba wannan matar rannan ta samu ba dan wannan ce mata ta yi bayanan,dan haka number shi ta laluba da tayi seving, Sai da yayi ringin uku ba'a dauka ba,har ta cire rai zai dauka sai gashi an daga, Cikin magagin barci yake tambayar waye, Faɗa mashi tayi har da ranar da suka haɗu ƙwanaki uku da suka wuce da kuma Alkawarin da ya mata, "Ohh Sorry Madam kiyi haƙuri na manta gashi har nayi tafiya tanzun haka ina Chaina kuma sai nan da kwana biyar zan dawo" "Har kwana biyar?zuwa lokacin ai an shiga kotu,gaskiya ba ni da wannan isasshen lokacin" "To yanzun ya kike son nayi? " Ko akwai dai taimakon da zaka min,idan har Footage din yana kusa kana iya saka wanda kafi yarda dashi ya bani " "Gaskiya ba zai yuba,kin ga ni bacci ma nake ji,ki bari gobe zamu karasa magana" Dif ya katse wayar, Kallon wayar tayi tana jujjuya shi a hannun ta, Yanzun ya zata yi,dole tana buƙatar wani abun na daban,Asalin Footage din kawai zai tabbatar da komai, Ganin zaman ba zai mata bane yasa kawai tayi ordan abinci sannan ta fito ta shiga mota bayan ta karɓa, Duk da a lokacin ƙarfe tara na dare ake nima hakan bai sai ta yi gudu sosai ba da mota kamar yanda ta saba duk da ba cikowar abin hawa, Wani katon Mota irin na kwasan shanaye ne yazo gabanta yana tukin banza,idan ta kauce sai ya kuma shigo ta, A karo na biyu ta je gaucewa kenan ta ji wani motar ya daketa ta baya da karfi ko karin sai saita kanta take ta rike Sitiyarin motar dake ƙoƙarin kauce mata,sai dai kara dukan Motar na bayan yayi,wanda hakan yasa tayi Losing control motar ta faɗa cikin wani karamin Kwalbati, Ganin haka ne yasa suka wuce suka bar wurin, Hanyan mutane basu cika bi ba,wasu dan haka dai_daikun motoci ne masu tafita suka tsaya,sannan aka buɗe motar aka fitar da ita,wanda tun buguwar kanta da Sitiyarin ta Suma, Fito da ita aka yi aka saka ta a motar wani mutum suka yi asibiti mafi kusa da ita, ___________*Niger State* Kusan mintunan shi Arba'in kenan a tsaye a ƙofar gidan amma ya ƙasa shiga, Haɗaɗɗen Namiji ne wanda ya amsa sunan shi,Black Beauty ne dan bakin shi har daukar ido yake,gashi dogo,da ka ganshi kasan cikakken matashi ne mai ji da kuɗi,saboda ko kayan dake jikin shi abin kallon ne dan Farin Shadda ya saka sai daukar ido da walwali take yi, Jin an buɗe ƙofar gidan ne yasa da sauri ya dan matsa baya yana kallon ƙofar, Haɗa ido suka yi da juna,sai dai wanda ya fito daga cikin gidan bai ce mashi komai ba ya raɓa ta gefen shi zai wuce, Cikin sauri ya riƙo hannun shi yana kiran sunan shi tare da marairace fuska "Abdul Majid,dan Allah mana" Fisge hannun shi yake kokarin yi amma yaki saki sai fadin yake dan Allah, Wannan karon a hassale ya juyo "wai me kake so ne da ni?dan Allah ka rabu damu ka bar kofar gidan nan dan bamu kaunar ganin ko da inuwar ka ne,ka fita a rayuwar mu dan Allah kamar yanda ka yi a baya" "Naji amma dan Allah ka bani dama ko sau daya ne na ganta,ina son nayi magana da ita ne" Wani irin kallon takaici ya watsa mai"wa zaka gani? "Ummu Salma,dan Allah ka bani wannan damar" Daga bayansu suka ji an buɗe ƙofar gidan an kuma fitowa, Ture mai hannu yayi"ka bar kofar gidan nan kafin ka saka na maka abinda zaka yi dana sani" Wanda ya fito yanzun ne yace"me haka ka keyi Abdul Majid?so kake ka tara mana mutane a ƙofar gida ? Sake Abdul Majid din yayi ya karaso wurin ɗayan "yau sati na daya kenan kullun sai nazo amma sun ƙi bani dama na ga Ummu Salma,ka taimaka min Abdulrahaman" Kallon dan uwan nashi yayi"ka tafi in da zaka ni zan shiga dashi" Juyawa yayi ya wuce abinshi ranshi na kuna, Kallon matashin yayi yana tura ƙofar gidan "mu shiga *YUSIF* " "Na gode Abdulrahman" Har cikin babban Falon gidan suka shiga da sallamah wanda ba kowa a cikin shi sai sanyi da ƙanshi dake tashi, Nuna mashi daya daga cikin kushin din yayi"zauna bari na kira Mama ku gaisa " Da sauri ya dakatar da shi cikin yanayin tsoro "A'a ba sai ka kira taba,kawai Ummu Salma nake son gani" Bai bashi amsa ba ya shiga wani kofar daya buɗe, Ƙare ma falon kallo yake yana nan kamar yanda ya san shi,sai dai kuma gidan ya mai shiru kamar ba kowa a cikin shi saɓanin da,duk da ƴan aikin da ya gani amma da abin da kamar da ba, Zuba ma makeken hoton ta dake makale a bangon falon ido yayi, Fuskarta ɗauke da murmushi tana kallon wani wurin kamar bata san sanda aka yi hoton ba,amma duk da haka ba ƙaramin fita yayi ba,sai sauran da take tare da yannan ta,su Uku maza ita kaɗai mace,duka suna dariya, A zuciyar shi ya raɗa Happy Family, Jin an buɗe ƙofar ne yasa ya maida kallon shi ƙofar,cikin sauri ya sauka daga saman kushin din ya tsugunna kasa kanshi a ƙasa, Muryanshi har rawa yake wurin gaida ita,"Mama ina wuni barka da fitowa" Bata bashi amsa ba sai ma tsayawa da tayi dan nisa da shi tana ƙare mai kallo yayin da zuciyar ta ke zafi yana tafasa aduk kallon da take ma shi, Danne zuciyar ta tayi ta amsa mashi "Lafiya" Dan shiru suka yi na ƴan mintuna kafin tace"Lafiya dai ko? Ƙara dukar da kai yayi"dan Allah Mama ina son nayi magana da Ummu Salma ne" "Kana iya shiga duniya ka duba mana ita idan har ka ganta ka rukar mana ita ta dawo gida haka" Tana gama fadar haka ta shige dakin ta bar shi, Dago kai yayi ya kalli Abdulrahman "me Mama ke nufi da shiga duniya? Kamar ba zai bashi amsa ba" Tun faruwar wancan lamarin tsakanin ka da Baba komai ya wargaje,kai ka tafi bayan ka rubuta mata takardar saki ba tare daka duba komai ba,ba tare data duba barnan daka aikata ba,ba tare daka duba irin soyayyar da take maka ba,bayan duk abinda kuka aikata wanda shi yayi silan tarwatsewar Ahalin mu,Baba ya samu bugawar zuciya,mukuma mun san tsirrin daya tarwatsa namu zuciyar wanda haka yasa ita Salma kasa jurewa ta bar gida,yau tsayin shekara biyar kenan da faruwar haka,yanzun kana iya tashi kabar mana gida domin ganin ka kaɗai yana taso mana da wani miki ne,kai ne silar faruwar komai dan Allah ka fita rayuwar mu" Hawaye ne ke zuba daga idanun shi yayin da jikin shi yayi sanyi "Na yi danasani yafi a kirga, Nadama nake a kowace safiya a ko wani lokaci,sai dai ɗan Adam bai isa ya mai da hannun agogo baya ba,idan lokacin ya wuce koda da awa daya ne bai isa ya mai da shi baya ba,ina dana sani akan komai dana aikata a wancan lokacin,ina son Salma so mara misaltuwa,a wancan lokacin bam san Me ya shiga kaina ba,son abin duniya da ƙuruciya su suka ja min,ina kallon irin son da take min kamar irin wanda ba zata iya rabuwa da ni ba ne,shi yasa na aikata komai, amma nayi Alkawarin duk in da take zan nimota,zan tabbatar na dawo da ita cikin rayuwar mu koda nawa zan kashe sai na nimo ta" Bai bashi amsa ba yasa kai ya fita dan jin waɗannan maganganun na Yusuf kona mashi rai suke yi,ko da aman wuta yake yi idan har ta dawo ko inda take ba zasu bari yaje ba balle yayi tunanin mai da ita rayuwar shi Kazantacciya. ___________*LEGOS* Koda aka kaita Asibiti bata cikin hayyacinta dan haka da sauri likitoci suka karbe ta,ta samu rauni akai sai da aka nannade kan,sai hannun data samu Targaɗe shima aka daure aka sakala hannun da wani abu mai haɗe da Belet har ta wuyanta hannun ya tsaya a kirjinta, Sai washegari da safe ta bar Asibitin bayan Direban da Alhaji Mansur ya haɗa ta dashi ya gama biyan komai,ba yanda basu yi da ita ba ta zauna ta ƙara hutu amma taki yarda saboda tana ganin aikin dake gabanta, Gida ta koma tayi wanka sannan ta sha magunguna ta dauki jakka da takardun da take buƙata ta fito, Ce ma direban tayi ya kai ta gidan yarin da Suraj yake, "Hajiya ya kamata ki huta" Ya faɗa, Dan wallahi ba karamin jin jiki tayi ba,har fuskarta ta faɗa saboda stress yawan tafiya da rashin natsuwar zuciya, "Idan na dawo zan huta" Ta bashi amsa, Ya ya'iya dole ya tuka ta har in da take bukatar zuwa,nan ma sai da aka dan bata mata lokaci kafin a bata damar ganin shi.... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *51* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Tunda ta shigo cikin wurin ya kafe ta da idanun shi yana ƙare mata kallo tun daga sama har kasa, Turo baki take yi domin irin kallon da ta tsana kenan a cewarta duk masu irin wannan kallon gulma gare su, Jan kujera tayi ta zauna sannan tayi sallamah, Ba tare daya dauke kai ba ya amsa mata, "Ni bana son irin wannan kallon kamar za'a cinye mutum" "Idan har kinsan baki da kwarin gwiwa jurewa me na zuwa" Kauda kai tayi tana hararan gefe "ba sai ka kore ni ba" Ta fada a hankali, "Ina jin ki" Daura jakkan hannun ta tayi saman teburin wurin ta ciro wayar ta, Ƙoƙari take ta kunna amma ta kasa saboda bata saba amfani da hannun hagu ba,hannun dama kuma shine mai ciyo wanda aka nannade, Dagowa tayi ta kalle shi,har yanzun kallon ta yake bai da alamun ma zai yi magana, Haushi ya fara ba,amma tunda har bai ji tausayin ta ba yace ta kawo ya taimaka mata ita kuma ba zata taba cewa ya taimaka mata ba, Dan haka ta Daura wayar a saman teburin ta shiga latsawa dai daya har ya buɗe ta shiga in da take buƙata sannan ta tura mashi a gaban shi, Mai da hankali kan video dake magana yayi,likitan Grandma ne yake mai bayani akan tafiyarsu har kuma garin da suka isa wato ITALY,sai video fuskarta da aka yi tana kwance amma ya tabbatar mashi daga dukkan alamu za'a dace saboda babban Asibiti ne kuma akwai ƙwararrun likitoci a wurin suna kula da ita yanda ya dace, Ganin video ya ƙare ne ya turo mata wayar ta gabanta, Wani karamin takarda ta kara tura mashi"ga address din Asibiti ko da zaka je idan an kammala wannan case din" "Wani tabbaci kike dashi akan za'a gama? " Eh to har yanzun gaskiya ban samu abinda nake nima ba,amma ina saka ran komai zai iya juyawa har yanzun muna da sauran kwana biyu a ƙasa " Lumshe ido yayi ya buɗe bai ce mata komai ba, Zazzage tarkacen dake cikin jakkan ta tayi sai dai ba takardun data kawo domin ya saka hannun, Karamin tsaki taja "ina ga na baro su gida,yanzun dole na dawo gobe" Mikewa yayi yana ƙoƙarin wucewa, "Ina kuma zaka tafi? Juyowa yayi kaɗan" Akwai abinda zan maki ne? "Amma! " Sai kuma tayi shiru"Anyway babu komai " Har yayi taku uku taji ba zata iya jurewa ba dan haka cikin jin haushi ta dauki bairon dake gefenta ta wurga mashi da karfi,ai kuwa cikin sa'a ya sauka a keyar shi, Ko daga kai ta kalle shi ba tayi da dan ita bata masan ya same shi ba tsabar masifar da take yi ita kaɗai "mutum ko tausayi bai da shi,ba zai ma iya cewa me ya same ni ba,sai dai kawai ya kureka da idanun shi kamar wani kunkuru,mtwss ko kunkuru na da ido ne ma oho"ta karasa fada tana daukar jakkanta ta fita ba tare data juya in da yake ba dan ita a tunanin ta tuni ya shige, Ganin ta wuce ne yasa ya sauke wani ɓoyayyen ajiyar zuciya, Yasan koma menene ya same ta baya rasa nasaba da wannan case din,shi yasa tun farko yace ta ajeye case din saboda yana mata gudun irin haka,sai dai tunda ta fara ba shida damar da zai dakatar da ita sai dai kawai ya bita da addu'a Allah ya kare ta, Dukawa yayi ya dauki Bairon ya shige dashi. _________*KANO* "Kaka ya kamata ki saka Biba ta dawo in ya so sai a daukar masa ƙwararre lauya " "Wai idan ta dawo Uwar me zata maka Ibrahim,ni fa ban gane ba,shin zaka samar masa wani lauya a ina,ko ubanka bai iya samu ba sai kai?ni fa bana son haka ka barmu muji da abinda muke ji" "Kaka nifa tsoro nake ji kar ta saka yaya na ya ƙare a gidan yari,Biba fa a matsayin yar aiki take a gidan nan yanzun kuma wai lauya,duk ta ina hakan ya kasance,ko dama dai tana da wani manufa ne na zuwa wannan gidan" Gabaɗaya falon shiru yayi yayinda zuciyar kowa ya koma kan kiyasta masa wacece ita din, Ammi ce ta katse tunanin nasu ta hanyar tacewa"wani irin magana ne haka kike faɗi Amira?koma menene Biba tayi yanzun ba lokacin maida magana da maida tunani baya ba ne tunda har tana iya bakin kokarin ta wurin ganin Yayan ki ya dawo,Lauyoyi nawa ƙwararru aka samu kuma aka roka dan kawai su tsaya masa amma suka kasa,sai ita da take mace ta sadaukar da komai nata domin ta taimaka masa shine har kike da bakin fadin haka?bana son ki zamo mai son zuciya,idan har ba zaki yaba mata ba ki bita da addu'a kar na kuma jin bakin ki a wannan maganar gara ki yi shiru " Dukar da kai tayi"ki yi hakuri Ammi zan kiyaye" "Kwana biyu ma ba'a samun number ita Biba dan na kira naji yanda take amma ban same taba na tambaye su Abbu sunce badi san masaukin data koma ba suma kwana biyu kenan rabonsu da ita" Cewar Nurudeen. "Ka kara kira yanzun ko za'a dace" Cewar Kaka, "Bari na kira " Ammi ta faɗa tana ɗaukar wayar ta, Cikin sa'a kuwa sai gashi ringin biyu aka ɗauka dan Video call ne, "Ammi ina wuni? Bata ma iya amsa mata ba sai kallon ta da take cikin yanayin tashin hankali" Me ya same ki Biba haka a goshi? Dan murmushi tayi ganin yanda duk hankalin ta ya tashi "ba komai Ammi kawai dai na ɗan samu Accident ne ƙarami" "Wannan ai ba karamin bane,kalli yanda dun fuskar ki yasha Plaster" Shafa goshin ta tayi "babu komai ai naji sauki" Kaka ce ta karɓe wayar"ke bani in ganta," Sake mata wayar Ammi tayi,ta san dole akwai wani abu a kasa,zata kira ta suyi magana amma ba anan ba,dole tana buƙatar kaɗaicewa,ba zata so wani abu ya samu yarinyar ba saboda ita ma din tamkar amana take a wurin ta, "Ke Habiba me ya faru dake haka? Sai da tayi dariya" Kaka hatsarin mota na samu amma da sauƙi " "Garin ya haka ta faru,hala dai kin bari ana ta sharara gudu dake ne? " A'a kaka kawai dai tsautsayi ne Allah ya kawo,kuma ma abin da sauƙi tunda targade kawai na samu a hannu sai wannan kujewar na fuska,shima zai warke cikin kwana biyu " "To shi kenan Allah dai ya kiyaye ki ya kuma kare ki dan Allah ki dinga kula" "To Kaka na godewa sai anjima" "Yauwa Allah maku Albarka" Da Amin ta amsa tana kashe wayar. Mikama Ammi wayar ta tayi"yarinya abin tausayi " "Kaka ina da magana " Duk juyowa sukayi kanta, sai dai ita bata damu da suba domin abinda ta ƙudurta sai tayi, "Maijiddarh ta samu mijin aure" "Me kike nufi Hajiya Saude? " Goggon yara abinda kika ji shi nake nufi domin ba zan bar yata tayi ta zama har ta tsofe min a gida ba bayan ta isa aure,tunda Allah ya riga ya nuna mana halin wancan" "Amma ai kamata yayi ki bari koma menene sai ayi bayan fitowar Sujar" "Allah ya kiyaye waye yasan sanda zai fito haka kawai,wallahi ba zan jira ba tunda har na samu ta amince tana son shi" "Kaka ya kamata ki yi mata magana ke ko zata saurare ki" Cewar Goggon yara, "Me kuwa zan ce mata tunda ta riga ta yanke hukunci,kinsan idan zuciya ta bushe Addu'a ce kawai zata iya sanyaya shi har ta mai dashi mai taushi" "To yanzun ma da kike maganar Auren waye zai Daura mata aure bayan Ubannin ta basu nan" "Ai Mustapha na nan shima Ubanta ne dan haka yana da damar da zai Daura mata aure" Kaka ce ta katse su dan su Ammi ko baki basu saka masu ba balle ta fassara su wani iri,ita da Goggon yara ne kawai take yi, "Waye mijin da zata aura? Murmushin shakiyanci tayi" Yauwa Kaka tambayar daya kamata tun farko sumin kenan amma sun tsaya suna Challenging di na" "Ki faɗa min abinda na tambaye ki" "Sunan shi Yusuf,shi din shahararren ɗan kasuwa ne,yawancin kasuwancin shi a kasar waje yake yi" "Iyayen shi fa? " Mutanin Niger state ne" "Menene Nasabar shi dana iyayen shi? " Wai ni kaka duk wannan tambayoyin na menene " "Idan ba kida duka amsar waɗannan tambayoyin to ki nimosu kafin ki zo min da batun aure domin ko ke kafin ki shigo cikin zuri'a ta sai da na tabbatar Nasan ko su waye iyayen ki da kakanin ki,dan haka bana son wata magana tashi ki fitar min a falo" Cikin jin haushi ta tashi ta bar falon yayin da ta bar kowa da saƙar zuci. ____________*LEGOS* Suna kammala waya da su Ammi hawa kan gado kayi ta kwanta dan tana buƙatar hutu, Ranar yini tayi tana barci sallah da cin abinci kadai ke tayar da ita,dan ita kanta ta san idan har bata huta ba tana iya rasa hankalin ta, *Washegari da safe* Karfe takwas yayi mata ne a Gidan yarin domin daganan so take ta koma Hotel ɗin nan akwai binciken da zata yi a karo na karshe, Kamar ko wani lokaci yauma haka ne yana zaune yana jiran shigowarta, Sai da ta mai sallamah sannan ta zauna, jan kujera tayi ta zauna sannan ta buɗe jakka ta ciro takardar ta tura mashi a gaban shi "gashi ka saka hannu" Ja yayi gaban shi ya saka hannu"idan har na fita me kike buƙata? Shiru tayi tana kallon shi na wani lokaci,wato ma tambayar da zai mata kenan,nan take wani tunani ya zo mata,ai kuwa zata yi maganin shi,kare ma fuskar shi kallon take yi kafin ta tsayar da idanun ta akan lips din shi"kome nake bukata zaka Bani? "In dai bai tsaba ma shari'a ba" Murmushi ta sake tana ture jakkan ta gefe ta mike tsaye, A hankali take takowa har ta iso in da yake zaune, Jan kujeran da yake zaune tayi baya sannan ta zauna a saman cinyar shi ba tare da fargaban komai ba a zahiri, Kyara zamanta tayi da kyau a saman cinyan shi,"Kace kome nake buƙata ? Ƙoƙarin kauda kai yake yi tasa ɗan yatsan hannun ta tadawo da fuskar shi ta yanda suke fuskanta juna, Tun daga saman goshinshi ta shiga zagayewa da ɗan yatsar hannun ta har ta gangaro izuwa cikakken giran shi,idanun shi masu matukar jan hankali, Lumshe ido yayi yana jin yanda take yawo da yatsanta saman fuskar shi, Gangarowa ta kuma yi saman lip dinshi inda nan ma sai da ta ɓata sakanni tana zagayeshi kafin yaji saukar nata bakin saman nashi, Kara lumshe nashi idanun yayi, Bata damu da yanayin da zai shiga ba ko yake ciki,ita dai abinda tayi niyar yi mai shi take kokarin aikatawa, Dan haka kama Lip dinshi na sama tayi ta shiga tsotsa a hankali tana mai kokarin kamo harshen shi, Bai hana ta ba sai ma dama da ya bata, Sai da ta gamsu dan kanta sannan ta sake masa baki wanda saura kaɗan ta ciye masa shi, Haɗe goshin su wuri ɗaya tayi ta yanda suke iya shakar numfashin juna, Dago kai tayi ta tsura ma fuskar shi ido na wasu sakanni,duk da idanun shi a lumshe suke baka isa ka fassara a wani irin yanayi yake ciki ba, Ta dai san duk wannan Kiss din data mai ko sau daya bai yi respond ba,bai kuma hana ta ba, Kamar wacce aka tsikara haka ta mike ta dauki jakkan ta ba tare data ƙara kallon inda yake ba ta bar wurin....... *Jiddarh ce* 🦚 *Yanzun aka fara* 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *52* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Tana fita daga wurin mota ta shiga ta zauna a gidan baya"muje " "To Hajiya" Ya fada yana tayarda motar, Ya riga ya san inda zasu je dan ta riga ta sanar dashi tun kafin su fito dan haka kai tsaye Hotel din suka nufa wanda yake da tazara sosai da in da suka baro,karin abin takaici shine yawan Goslow da hanyar, A tafiyar da zaka yi mintuna talatin sai ka bata kusan awanni biyu zuwa uku, Abinda ya bata haushi ya kuma ɓata mata rai shine bayan irin wannan dogon tafiyar da suka sha sai gashi masu gadin bakin Get din shiga wurin sun hana su shiga, Ba irin rokon da bata masu ba har ta I.D card dinta ta nuna masu amma suka ki yarda wai umurni ne na Ogan su, Ta kira Number wancan Inyamurin shi kuma bata shiga wanda daga dukkan alamu blocking din ta yayi, Ko kusa da bakin Get din sun hana su tsayawa,dole dan nisa da Hotel din suka samu wuri suka yi parkin mota, Fitowa tayi daga cikin motar ta jingina da jikin motar ta dafe kai, Tunani take ta ina zata fara,komai ƙoƙari yake ya kwace mata,gashi gobe ne za'a koma kotu sai dai har yanzun komai baya iya samu ba, Ta tabbatar ko yaya ne idan har bata samu wani abun da zata kai ba suna iya yanke mashi hukuncin da suka ga dama wanda bata fatan haka, Ji yayi daga gefen ta ance "Hi" Dagowa tayi ta kalli mutumin shima zubin Yarbawa gare shi, Mai da mai da "Hi" Din shi tayi kafin tace"me kake buƙata "dan a yanda ya tsaya mata daga dukkan alamu akwai magana a bakin shi, Kalle_kallen gefen shi yake" Zamu iya shiga motar ki muyi magana,domin ba na son a gammu tare ni ma'aikacin wannan Hotel din ne "ya faɗa yana nuna mata I.D din shi, Cikin sauri ta buɗe mashi gidan baya" Shiga " Sannan ta zagaya ta shiga"ya kamata mu ɗanyi nisa da nan kaɗan " Jin abinda tace ne yasa Direban dake jiran umurninta ya tayar da motar ya bar layin dasu. Yana parka motar a wani ɗan hanya ya fita a motar ya bar masu wuri, "Ma,Suna na Josif, ni ma'aikaci ne a wannan Hotel ɗin,tun wannan ranar da kika fara zuwa wurin Manager mu na ganki,naso na maki magana amma ban samu dama ba kuma ina jin tsoron a ganni dake dan amma gargaɗi sosai akan ki,sai dai kuma yau ma na ga an hana ki shiga shi yasa nace bari nayi amfani da wannan damar domin ba zan taba manta taimakon da wanda kike karewa yayi min ba,a lokacin da kowa ya juya min baya na rasa yanda zan yi,shine ya taimake ni ba tare daya duba yare na ko Addini na ba wanda gashi har ta sanadin haka na buɗe ma Mama na shago ta na sayar da kaya a ƙofar gida tana samun kuɗin abinci ba tare data jira ni ba ko taci bashi," Ita dai sauraren shi take yi tana kuma mamakin wani taimako ne ya mai haka, "Ranar da abin ya faru ina kicin ina aiki sai gashi Manager ya kira akai mai abinci shida baƙi a Ofishin shi, Ko da na shiga kai abincin suna ta cikin dakin hutawar shi dake cikin Ofishin,har zan juya naji daya daga cikin su yana daɗin Tunda mun samu ya fita daga dakin ya kamata ka saka a hanzarta a shigar da Gawar yarinyar dakin shi ta yanda komai zai yi dai daidai, Jin wannan maganar ne yasa da sauri na ciro wayata na shiga wurin kwasar Video da daukar murya na labe ina ta kwasar su har suka kammala tsara shirin su, Jin za'a fito ne yasa da sauri na fita, Sai dai ban koma wurin aiki na ba na labe a ta bayan kofar baya da naji ta nan za'a shigo da gawar, Sai da na tabbatar na kwashe komai sannan na wuce,sai dai a lokacin ban cewa ɗakin shi aka saka gawar ba,kuma ni ma dalilin da yasa na ɗauka saboda ina son idan na koma gida na kira Manager na masa barazana da wannan Video na samu kudin bikin binne kanwata data mutu, Ana cikin haka sai ga kiran Mom din mu tana faɗi min irin munanan kalaman mutane ƙauyen mu a kanmu,wanda sai da nayi kuka, A wannan lokacin ne Allah ya haɗa mu da shi yaji kukan da nake yi shine ya tambaye ni akan meke damuna,dana faɗa mashi nan take ya amsa account din na ya turamin dubu dari da hamsin, Shi yasa da na ga abinda ya faru dashi ban tura ma Manager Video ba na ajiye domin na san zai taimake shi wurin fitowa"ya faɗa yana mika mata Memory, Tsabar farin ciki ji tayi kamar ta rungume mutumin sai godiya take tayi mai kafin ya fita yayi wucewar shi, Direban ne ya shigo motar"ina zamu Hajiya? "Gida" Ta bashi amsa fuskarta dauke da murmushi. Ranar haka tayi ni cikin tsananin farin ciki domin ta san Allah ne ya kawo mata sauƙi har in da take,jira kawai take gode tayi a shiga kotu. ____________*Washegari* Ƙarfe tara na safe tayi mata ne a cikin kotu dan ma tun ƙarfe bakwai suka fito,to amma saboda yanayi na cikowar abin hawa shi yasa basu iso da wuri ba, Ko da ta isa a haraban babban Kotun ta samu su Pa da Abbu sai Dady, Cikin girmamawa ta gaishe su,suka amsa, Dady ne yace"ƴa ta da fatan an samu wani abun,dan gaba ɗaya hankalin mu a tashe yake yau bamusan yanda shari'ar zata kasance ba" Dan fuskar damuwa ita ma ta nuna"Dady sai dai ku taya mu da addu'a kawai,sai dai abinda Allah tayi" "Haka ne Addu'a kuwa munanan muna taya ku dashi kullun" Cewar Abbu, Hango shi zaune tayi a saman wani ɓENCI hannun shi tsarkafe da Ankwa sai masu tsaron shi dake tsaye suna hira suma dan wurin cike yake da jami'an tsaro, "La gama Suraj din can" "Ai ba zasu barki ki karasa in da yake ba,dan mun yi kokarin haka ko gaisawa muyi dashi amma sun hana" Cewar Pa, "Bari naje na gwada ai ni lauyar shi ce" Bata jira amsar suba ta nufe in da suke, Suna kallon yanda take Challenging da Masu tsaron shi daga karshe suka ga ta karasa in da yake zaune yana kallon su ta zauna fuskarta dauke da murmushi, "Barka da Safiya Malam Suraj" Kim amsa mata yayi, Bata fuska tayi cikin shagwaba tace"ba zaka amsa ba? "Ki fara yin sallamah tukun na" "Ohh na manta tare da Ustazu nake,Assalamu alaika" Amsawa yayi yana kauda kai daga kallon ta, "You look Happy" Dariya ta yi wanda ke ƙara baiyana farin cikin ta"sosai ma domin yau zaka fito" "Kina da tabbaci a kan haka kenan? " Hundred and ten percent " Ganin bai ce komai ba ne yasa tace"to ka juyo mana,ni na fison idan ina magana ana kallo na" Har yanzun din ma kin kallon nata yayi, Ji yayi ta shiga jan hannun shi "ni dai ka juyo,ni dai sai ka kalle ni" Ganin tana shirin ja mai magana ne yasa ya juyo yana daura idanun shi a kanta, Murmushi ta saki"yauwa ko kaifa,to mu koma maganar mu na jiya tunda ina saka ran komai ya kare anan" Ganin kamar bai gane me take nufi bane yasa tace"jiya baka tambaye ni me nake bukatar ba" Dantse Lip dinshi yayi da hokora,wanda ganin abinda yayi ne yasa ta shiga kwasan dariya tana nunashi,shi kuma sai bata fuska yake yi,sai da tayi mai isar ta sannan ta dafa shi"kaga relax,i am not ganna kiss you" Har yanzun bai cire haƙoran ba"da gaske nake yi,kaga bari ma na fada maka abinda nake so" Juyowa yayi yana sake Lip dinshi a hankali ya mai da hankalin shi kanta, Wannan karon a kwai natsuwa a tare da ita wanda hakan ke nuna muhimmancin abinda take son faɗa, *Idan har naci nasara yau ɗin nan zaka rubuta min takardar saki* ?Ta faɗa tana dagowa suna kallon juya cikin idanu.. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *53* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Kamar ba zai ce komai ba dan har ta fara cire rai ga amsar shi, Sai ta ji yace"me yasa kika zaɓi wannan? Ajiyar zuciya mai ɗan ƙarfi ta sake yayin da nan take wani irin damuwa mai tattare da kunci ya lulluɓe kyakkyawar fuskarta mai dauke da dariya "Ada ina son nayi wani irin tafiya ne da babu waiwaye a cikin ta,sai dai kuma duk nisan da nayi sai gashi na tsince kai na a baya,ina nufin a mafarin tafiyar wanda hakan ke nuna dole sai dai na sake sabuwar farawa, Ban damu ba ada,amma kuma yanzun na rasa kwarin gwiwa tun mutuwar Ummita, Na tabbatar a kwai abinda ke jana baya,shi yasa na yanke hukun komawa baya na fuskaci rayuwata dana baro,wacce nake jin tsoro,"dago kai tayi ta kalle shi "a hanya muka haɗu da kai ina kan wannan tafiyar,shi yasa nake son na rabu da kai a wannan hanyar,bana son na tafi da nauyin ka ba tare daka sauke min shi ba,zan koma gida,zan koma wurin iyayena" Dukar da kai tayi tana share hawayen daya ɗigo daga idanun ta"ka yi hakuri komai na wancan auren Karya ne" Ya buɗe baki da shirin yin magana kenan sai ga sako daga masinjan kotu wai su shigo lokacin shari'ar su yayi, Mai da abinda ke zuciyar shi yayi har zuwa sanda zasu fito, Ita ma mikewa tayi"idan mun fito ma karasa magana,dan bazan koma Kano tare da ku ba" Bai bata amsa ba suka fara yin gaba da sojojin kafin ta bi su a baya, Wannan karon ma kamar wancan lokacin ne dan sai da akayi gaisuwa da kuma gabatarwa, Lauyan wanda suka shigar da kara ne ya tashi ya fara magana "ya mai shari'a ina rokon Kotu idan har wannan karon Barrister Ummu Salma ba ta kawo kwakkwaran hujja ba ina rokon Kotu data yanke ma Suraj hukunci kisa kamar yanda yama Jesica,wanda hakan zai zama izina ga masu hali irin nashi da kuma shi kanshi,na gode ya mai shari'a" Ya fada yana zama irin na takama alamun zamu ga yanda zaki yi, Mikewa tayi tsaye ita ma"kamar yanda ɗan uwana Barrister ya faɗa ni kaina ba zan so na bata ma kotu lokaci ba,kuma ina rokon kotu duk wanda yake da hannu a cikin wannan shari'ar kotu ta yi gaggawar kamashi ta mai hukunci,sannan abu na karshe shine ina son gabatar ma kotu da wannan ɗan ƙaramin Video nawa kashin na kuma gabatar da wani shaida " Ɗayan Alkalin ne yace"Kotu ta baki dama" Masinja ne ta amsa ya haɗa a babban kayan kallon dake cikin Kotun wanda nan take video Manager da mutanen da ba'a gane ko su waye ba suna magana har irin kudin da aka bashi,da sanda aka shigar da gawar dakin daya sauka,har karshen video, Kowa jikin shi yayi sanyi da ganin wannan video, "Ya mai shari'a ina rokon kotu ta Bani dama na gabatar da shaidata na biyu" "Kotu ta baki dama" Nan ma gabatar masu da Jusif tayi,in da ta shiga yi mashi tambayoyi yana amsawa har ta kammala, Barrister ne ya tashi yace"ya mai shari'a in ba damuwa ni ma akwai wasu yan tambayoyin da nake son nama Jusif " Nan ma kotu ta bashi dama, Sai dai duk irin tambayoyin da take ma Josif domin ya rudar dashi yaki bashi dama,dan ya kwantar da hankali sosai yana amsa mashi kamar yanda ita ta faɗa mashi hakan na iya faruwa, "Ko zaka iya faɗa ma koto ta yaya kaga sanda suke magana har kaji ka kuma gani? " Kamar yamda na faɗa Abinci aka kira kicin akai shi ne aka ce na ɗauka na kai, shi yasa naji abinda suke faɗa " "Kenan haka na nufin Labe ka yi masu? " Eh to kana iya saka shi a matsayin haka,domin kan ba zan musa ba idan ka ce Labe ne,dan na Labe na dauki su Video domin na yi amfani dashi na samu kuɗin da zan yi bikin birne kanwata,to sai gashi wanda aka ma abin shi ya taimaka min wanda har yanzun ni da mahaifiyata muna cin taimakon,shi yasa ban yi manager barazana da video ba" "Amma kasan kotu zata iya hukunta ka akan abinda kayi,sannan ba kaji a ranka kaci amanar yarenka da ƴan uwanka ka zabi wasu" Dariya yayi kaɗan "Amana fa kace, karka manta na faɗa maka uzurina amma a cikin su ba wanda ya iya taimaka min ko yaji tausayi na har ta dashi manager da nake ma aiki,har vashi na roka su Bani sai a dinga cirewa acikin Albashi na amma suka hana ni,yan uwana sai zagi na suke yi,shi kuma wanda ka kira bare ba tare daya sanni ba ko ya damu kabila ta ko addini na ya taimakamin da kuɗaɗe masu yawa, lta yaya ina da abinda zai taimaka mashi ba zan taimaka ba,ni ban damu da hukuncin da za'a min,in dai har zai fita to zan jure" Mikewa tayi"ya mai shari'a Barrister yana ƙoƙarin sauka kan layi,domin babu in da aka ba da dama akan a hukunta mutum domin yayi Labe,tunda ba'a kamashi da laifin yima Manager barazana ba,ina rokon kotu ta watsar da wannan kalaman na Barrister ta" "Barrister ka kiyaye" Alkali ya faɗa, "Na gode ya mai shari'a" Ya faɗa yana komawa ya zauna,domin cikin ikon Allah duk wani dubara nashi ya kucce, "Sakamakon hujjoji da muka haɗa daga likitoci wanda ke nuna babu shatin hannun Suraj a jikin gawar,da kuma hujjojin da Lauyar shi ta gabatar,wannan Kotun ta wanke Suraj Abdul basir daka zargin da take mai na kisan kai,ta kuma bada dama da a kamo Manager Hotel domin a fara sabuwar shari'a a kanshi" Nan take mutumin ya buga wannan karamin sandar nashi mai fitar da dan sauti, Duk in da masoyan Young Ustadz suke a fadin duniya masu kallon abinda ke faruwa ta online godiya suka shiga yima Allah daya fito masu da matashin malamin su lafiya, Yayin da ta gefe ɗaya kuma hankalin wasu a mugun tashe yake fiye da tunani,dan wannan shi ake kira da rashe ya juya da mujiya ko kuma suce Shari'a saɓanin hankali. Nan take Sojojin suka shiga kwance mashi Ankwa,suna mai ba shi haƙuri,yayin da yana fitowa yan jarida suka lulluɓe shi suna mashi tambayoyi, Ita kuma ta ɗayan ƙofar ta fito dan ba zata iya da wannan cin koson da akayi mai ba idan sun koma Hotel ya huta sa karasa magana, Tana fitowa lokacin taga su kuma sun shiga wani bakin mota katuwa,kamar kuma faɗa suke yi ranshi a ɓace, Tana kallo har matukin motar yaja motar wanda bata sanshi ba,wani tunani ne yazo ranta,to me ke faruwa ai kamata yayi ace taga tsananin farin ciki a fuskar su ba tashin hankali ba da faɗa kamar zasu yi danbe abinda bata taba gani ba,to ko kuma sace su za'a yi, Kai koma menene gara ta bi bayan su, Dan haka cikin sauri ta karasa wurin motar Allah yasa Direba na wurin yana jiranta sai gashi ta iso,nuna mashi motar dake kokarin barin harabar Kotun tayi"Yi sauri kabi wannan motar" "To Hajiya" Nan kuwa ya tayar da motar ya shiga binsu a baya,duk da suna ƙoƙarin ɓace mai amma haka yake ƙoƙarin, Sai da sukayi tafiyar mintuna Arba'in kafin kuma suga sun shiga harabar wani babban gida, Dan haka sauka tayi tace mashi ya jirata tana zuwa, Ita din a wannan harkar ba bakuwa bace,dan haka tana isa tura kofar tayi zata shiga madu gadi suka hanata, "Wa kike nima" "Joj ne yace nazo na same su yanzun" "Bari to na kira shi na sanar dashi zuwan ki" "A'a ba sai ka kira shi ba ni bari na kira shi nace masa ka hana ni shiga amma ka tabbatar da zaran ya fito ka rasa aikin ka" Buɗe mata yayi domin daga gani a tsaye take,dama ga Biba da diri kamar ita ta tsara kanta,"a fito lafiya " Ko kula shi bata yi ba ta shige, Sai dai tana ganin ta kure ma ganin su ta shiga sanɗa a cikin falon tana son ta duba dakin da aka ajiye su, To me haɗin su da Joj kuma Baban Jusica, Wani ƙofa ta dafa tana shirin buɗewa kenan ta ji an buga tebur har sai da ta firgita,kafin ta ji magana ya biyo baya"wannan wani irin shashanci ne,mun yarda da kai akan zakayi wannan shari'ar yanda ya dace,zaka saka shima a kashe shi ashe ma kai a fagen aikin naku ba kowa bane babu abinda ka iya,tunda gashi yar karamar yarinya ta raina maku hankali," Dukawa taga Joj din yayi "ka yi hakuri Shugaba zamu samo wani hanyar da zamu gama dashi," "Hanyar uwar ka hanyar banza,kasan tun tsayin shekara nawa muke jiran wannan ranar sai gashi cikin awa daya kasa komai ya ruguje" Wanda ya juta baya ne ya juyo "yanzun me kake son mu aika,dole sai mun sake wani shirin kenan akan sa" Daga inda take tsaye tana kwashewa a waya saura kaɗan wayar ya zame a hannun ta,domin ganin na farkon da aka kira da shugaba bai tsayar da bugun zuciyar ta ba kamar wannan,dan numfashin ta ma sai da ya tsaya na wucen gadi, "Tunda har kotu ta wanke shi na tabbatar yau zamu koma gida,dan haka za'a shirya gagarimin hatsari wanda dole zai rasa ranshi a ciki,domin ba muna da wani zaɓi a yanzun ko option" Daga bayanta ta ji ance "me kike yi anan" A zabure ta juya tana ɓoye wayar a cikin siket dinta ta baya, Suma duk fitowa sukayi daga dakin suna mata kallon me kike yi anan, In ina ta fara"dama naga kun shiga mota ne da wasu mutane shine na biyoku dan na ɗauka sace ku aka yi" "Biba shin kinji wani abu ne? " Da sauri ta girgiza kai,a'a ni ba abinda naji dan yanzun na shigo" Murmushin yayi"Ke Yar tsana ce mai matukar wayau,wacce dama kuma Dama nake jira wanda zan samu na batar da wannan yar tsanar,sai gashi cikin sauki ta kawo kanta har in da nake," Bata fuska yayi cikin rashin imani yace"Ku kamamin ita" Ai kuwa cikin sauri ƙattan sukayi kanta,tafi kusa da ƙofa dan haka fita tayi da gudu yayin da suke binta a baya,ɗayan dauke yake da katon ƙarfi a hannun shi wanda duk cikin su ya fi su gudu, Cikin sa'a kuwa ganin ba zai iya kamata ba ya daga wannan katon ƙarfen ya buga mata shi sai akan keyar ta, Duk da ta ji wani abu tsuuu daga kanta hakan bai sa ta tsaya ba daga fita gef din da tayi wanda dama ƙafarta daya na ƙoƙarin karasa fita ne ya samu nasarar buga mata, Kafin ta kai bakin motar ne ta ji jikin ta ya fara saki kamar ana kokarin janta baya, Tana shiga ya fisge motar a tsiyace ganin yanda aka biyota ya bar layin dasu, Sai da sukayi tafiya mai dan nisa kafin yaji Kiran sunan shi da take yi"Hashi"da kyar ya iya ji domin da kyar maganar ta fito, "Na'am Hajiya" "Tsaya ka duba min me ke zuba a kaina" "Faka motar yayi gefe ya juyo, Wani irin ihu yayi yana matsawa gefe ganin irin yanda gaba ɗaya ta jike da jini, " Hajiya kina zubar da jini sosai " "Ka kai ni wurin Suraj" Ta faɗa da kyar, "A'a bari mu je Asibiti" "Ka kai ni wurin shi,akwai abinda zan faɗa mashi,dan Allah" Gabaɗaya hankalin shi ya tashi,domin ba karamin jini take zubarwa ba,yanzun ina zai ga Suraj, Yauwa tabbas yana Hotel din da iyayen shi suke,sai dai tafiya ne mai dan tazara ba lallai ta iya jurewa ko takai ba,amma ba yanda ya iya, Haka ya shiga mota shi bai masan kuka yake yi, dan bin hanya yake lungu da sako saboda gujewa cikowar abin hawa ta yanda zai iya isa da wuri,yanayi yana kallon yanda take sauke numfashi a hankali ta madubi 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *54* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Gudu yake zubawa sosai kamar zai tashi sama, Cikin hukunci Allah lokaci kankani ya isa Hotel ɗin,yana yin parkin, motar su Dady na tsayawa ita ma, Da sauri ya karasa wurin da Suraj din ke tsaye yana jiran Dady ya jawo hannun shi domin ya kasa magana sai kuka da take yi, Shi kuma bin shi yayi dan ya lora da motar da yake mai nuni, Da sauri ya buɗe bayan motar inda take kwance "Duba ka gani ban San yanda zan yi ba" Cikin sauri ya kara leka motar da kyau damin tabbatarwa, Salati ya fara yana kiran sunan Ubangiji duk wanda yazo bakin shi, A hankali ya ciro ta yana rungume da ita,ganin yanda jinin ke ƙara fita ne yasa cikin tashin hankali ya shiga kiran sunan Dady, "Me ya same ta,maza saka ta a mota muje asibiti" Shida ita ne a baya kanta na saman cinyarshi ya tattare da rigar shi da ya cire saboda jinin ya tsaya, Shafa fuskanta yake yi yayin da hawaye ke fita daga idanun shi yana sauka saman fuskarta, A hankali ta buɗe idanun ta,wadanda take ji sun ji matukar yi mata nauyi har bata iya ganin shi da kyau, Ƙoƙari take tayi magana amma ji take makoshinta kamar a kwai a binda yazo ya tsaya a wurin, Ganin idanun ta sun dan buɗe ne yasa ya shiga kiran sunan ta wanda take jin shi can da nisa, Bakinta ta buɗe tana kokarin yin magana sai ta kasa fusta komai, Ya fahince so take tayi magana, Girgiza mata mata kai yake"please don't live me Beb!stay with me!I have so many things to tell you please we need you,"ya karasa faɗa yana haɗa goshin shi da nata,yayin da hawayen shi ke sauka saman fuskarta, A hankali yaji saukar hannun ta saman hannun shi dake rungume da ita, Cikin sauri ya kamo hannun ya sumbata yana ci gaba da sha fuskarta,da zaran ya ga zata lumshe ido,da sauri yake dan jijjigata yana kiran kiran sunan ta tare da faɗin "pls don't close you eyes"yan kara matse hannun ta a cikin nashi, Zai iya cewa a wannan lokacin ya manta rabon daya shiga tashin hankali irin na wannan ranar, Duk da yasan ko yaushe komai na iya faruwa dashi ko wani nashi,kai ko lokacin da yaga gawa a matsayin wacce ya kashe bai shiga firgici da tashin hankali ba irin na yanzun,wanda ba komai bane ya jawo haka face ganin ta da yayi lifeless wance a jikin shi, Allah ya gani tsoro yake ji,yana matukar jin tsoron rasata a karo na biyu, Ire-iren sambatun da yake tayi kenan har suka isa asibiti,cikin gaggawa likitoci suka karbe ta emergency,yayin da su kuma suke tsaye sun kasa zama, Gani suke yanda likitocin ke shige da fice a dakin har na tsayin awa daya,kafin wani babban a cikin su ya kira su Ofishin shi, Nuna masu kujerar zama yayi amma cikin su ba wanda ya iya zama, "Doctor ya jikin nata? Ya tambaya muryar shi na rawa, " To yanzun dai ba za mu iya cewa komai ba,domin dai mun yi nasaran tsayar da jikin dake zuba,sannan mun gudanar da bincike wanda ya tabbatar ma na da cewar ta samu tsagewar kashin kai, Dole tana buƙatar aiki na gaggawa idan ba haka ba tana iya rasa rayuwar ta," "Doctor idan har babu wani matsa a fara aikin kawai" "Ba aikin bane matsala akwai wasu matsaloli da za'a iya samu" "Kamar me" "Aiki ne mai makutar hatsari wanda a ko wani lokaci ana iya rasa patient,na biyu idan an samu nasara aikin yana da Complications misali,tana iya rasa ganin ta,ko kuma ta rasa jinta,shi yasa a Nigeria ba ko wani asibiti ake yi wannan aikin ba,amma ke kace? " Me kake nufin da me kace?ba zan taba yarda ai mata aikin da zata rasa idanun ta ko rasa jinta ba,balle akai ga mutuwa,ba zan iya ba" "To yanzun me kake son ayi,dole ne cikin biyu ayi da" "Kawai zan fitar da ita kasan waje,na tabbatar su din zasu iya" "Kaga ka kwantar da hankalin ka domin duk abinda kasar waje zasu mata muma nan muna da kayan aiki muna da kuma ƙwararrun likitoci,kuma duk inda kaje bayanin daya domin Surgery na ƙwaƙwalwa aiki ne mai hatsari balle irin nata da kashin ya tsage" Hawaye ya fara yayin da zuciyar shi ke cike da kunci,yana tuna maganar su na karshe da ita a dazu da take faɗa mashi zata koma gida wurin iyayenta,ta yaya zai iya bari haka ya faru da ita har ta rasa ranta, Rungume shi Dady yayi"ya isa haka addu'a zaka mata ba wai ka kama kuka ba kamar karamin yaro " Shima rungume Dady yayi"bana son na rasa ta " "I know,sai dai ba muna da wani option" "Yaushe za'a aikin? " Nan da awa ishirin da tara,daga nan zuwa gobe da yamma kenen,domin akwai wasu gwaje-gwaje da za'a mata" Jinjina kai yayi"dan Allah ka yi min ƙoƙarin kar ta rasa komai nata,ka yi min Alkawari " "Na maka Alkawarin zan yi iya kokari na,kai ma sai ka dage da addu'a" Hannun shi Dady ya yawo suka fito"tunda har tana karkashin kulawar likitoci kuma ba zasu bari a ganta ba,ya kamata kaje gida ka yi wanka ka huta" "A'a ba zan iya tafiya ba Dady" "Ba nason musu tashi muje" Suna fitowa suka hadu da Hashim da sauri ya karasa in da yake"me ya faru dazu,wa ya aikata mata haka? "Ban sani ba nima,amma abu ɗaya na sani shine daga Kotu dazu ina tsaye sai gashi tazo ta same ni wai na bi wancan bakin motar,shine na bi su har wani unguwa tace nayi parking a gefe zata shiga ta fito, Daganan dai Nasan ta shiga amma bansan me ya faru ba sai ganin ta nayi ta fito da gudu wasu maza na binta tana shiga mota ni kuma naja,shine tace na kawota wurin ka akwai maganar da zata fada maka,iya abinda na sani kenan " Lumshe rinannun idanun shi yayi ba tare da yace komai ba ya juya ya buɗe mota yashiga,in da Dady ke jiran shi,wallahi wallahi duk mai hannu a cikin wannan lamarin koshi waye ba zai taba barin su ba,domin idan har ta sanadiyar shi wani abu ya same ta ba zai yafe ma kanshi ba, Dafe zuciyar shi yayi dake mai zafi,idan har ya tuna rabuwar su da kuma abinda ta mai a jiya sai yaji hankalin shi ya ƙara tashi, Har Dady ya tayar da mota yace masa yana zuwa,kiran Hashim yayi "Ina jakkan ta,a wani Hotel take zaune? " Ba Hotel take zaune ba a gidan Oga na take zaune" Cikin mamakin daya kasa boyuwa yace"gidan oganka kuma"fuskar shi na nuna wani yanayi, "Eh amma shi yana Abuja ita kaɗai ce a nan," Nan ya faɗa mashi sunan unguwar da number gidan,sai jakkan ta daya miko mashi, Jan motar Dady yayi suka bar Asibitin zuciyar shi cike da tunanin me take son ta faɗa mashi. Suna shiga Hotel din Dady ya amsar mashi makullin daki kusa da nasu ya bashi, Wanka yayi ya sauya kayan jikin shi, Sannan ya kunna wayar shi da suka mai da mashi, Number Ammi ya duba ya danna ma kira, Ai kuwa makar dama jira take yi ta dauka da sallamah, Sunan shi ta kira domin son tabbatar da ko da gaske din shine"Suraj " Ji yayi idanun shi sun cika da hawaye"Na'am Ammi" "Alhamdulillah,Allah na gode maka Alhamdulillah, yau zaku dawo ko? " Umm um "ya faɗa yana share hawayen shi, Dan shiru tayi kafin tace" Me ya faru,na yana ji kamar kana kuka,why are you Crying? "Ammi tsoro nake ji" "Nasan duk abinda ya girgiza wannan zuciyar har ya samu nasarar tsorata shi ba ƙarami ba ne,faɗa min me ya faru ? " Nan ya shiga sanar da ita abinda ke faruwa har karshe kamar yanda Hashim ya sanar dashi" "To su waye ta gani ta bi,me kuma ya faru a cikin gidan,me take son ta fada maka? " Ammi koma dai menene ba karami bani na tabbata" "Gobe zan zo insha Allah zan biyo jirgi,sannan ka kwantar da hankalin ka insha Allah zata ji sauki za'a dace" "Allah yasa Ammi" Daganan sallamah suka yi ya kashe wayar ya kwanta,sai dai duk yanda ya so yayi barci ko ya huta kasawa yayi,dan haka tashi yayi ya jawo jakkan ta ya buɗe,hannu ya saka a ciki sai gashi ya ciro wayar ta,sannan ya zazzage jakkan gaba ɗaya saman gado, Takardu ne a ciki sai man baki da sauran kayan kwalliya dai na mata,sai makullin gida, mai da komai yayi cikin jakkan ya adana, Ranar bai samu yayi bacci ba domin kukan shi da godiyar shi ya rinka mikawa ga Allah, Ba ya so ya rasa ta ko ta rasa wani ɓangare na jikin ta, Washegari ma ko kafin su Abbu su tashi bacci shi har ya wuce Asibiti,sai da suka duba dakin shi a kulle shine suka kira shi ya sanar dasu ai tun ƙarfe bakwai na safe yana Asibiti, Abbu ne yace"ka kuwa karya " Dan shiru yayi kafin yace"yanzun zan karya dan na ga akwai wurin cin abinci a asibitin " Cikin yana yi na dan faɗa faɗa yace"kasan ƙarfe nawa yanzun kuwa? Kallon agogon hannun shi yayi wanda ya nuna ƙarfe goma da rabi na safe "Sorry Abbu" "To ka dai dinga kiyayewa muma gamu nan zuwa" "To sai kun iso" Ya faɗa yana sauke wayar, Lekawa yayi ta glass din dake tsakanin su a I.C.U,tana kwance yanda kasan gawa babu ta inda take motsi sai na'urorin dake aiki a kanta wanda har saman kanta aka mammanna wasu karafe ƙanana, Ji yayi an dafa shi daga baya, Juyawa yayi,ganin Doctor ne yasa ya sauke numfashi, "Kana son ka shiga ka ganta? Girgiza kai tayi" Ba sai na shiga ba" "Ka tabbata? " Umm,yaushe za'a shiga aikin? "Nan da ƙarfe biyar na yamma" Lumshe ido yayi ya buɗe waɗanda yake ji sun mai matukar nauyi "ina fatan dacewa" "Da yardar Allah" "Zan je na dawo zuwa anjima" "Ba damuwa ranka ya daɗe" Juyawa yayi ya wuce,sai da ya je yaci abinci sannan kai tsaye ya wuce unguwar da Hashim ya mai kwatance,har ƙofar gidan kuwa aka kaishi, Da makullin daya dauko a jakkan ta dashi yayi amfani ya buɗe har cikin falon, Sai da ya gama ƙare ma falon kallo wanda yake tsaf sannan ya shiga dakin da ya gani a buɗe, Daga dukkan alamu a nan take kwana,dan ga dakin nan da kayan ta har a saman kushin,daga dukkan alamu bata kyara dakin ba ta fita, Gaban madubi ya tsaya wanda ke dauke da man shafawarta sai turarukan jiki, Daukar daya yayi ya buɗe ya fesa a iska ya lumshe ido yana shakar ƙamshin,tabbas shi ta saka shekaran jiya data zauna a jikin shi, Wani takarda mai ɗan girma ya gani a saman madubin,bangon littafin ya ja hankalin shi har ya shafa littafin, Haka kawai yaji yana son buɗewa yaga me a rubuce, Bin umarnin zuciyar shi yayi ya buɗe wanda shafin farko kyakkyawar rubutunta wanda yake jere bisa tsari yaga an rubuta *MY DESTINY* ( *Kaddarata* )da manyan harafi, Ya dau sakanni yana mai maita sunan a zuciyar shi kafin ya buɗe shafi na biyu, Abinda ya gani a rubuce ne yasa ya mai da takardar ya rufe ya ɗauka sannan ya rufe gidan ya koma Hotel din daya sauka, Yana shiga daki hawa saman gado yayi ya zauna tare da kara buɗe littafin wanda daga dukkan alamu tarihin asalin rayuwar ta ne a ciki wanda shi kanshi zai so yaji wacece asalin Biba da kuma Ummu Salma,me alakar dake tsakanin suna biyun nan,menene ya faru da rayuwar su da kuma kaddaran dake bibiyar su..... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *55* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Shafi na biyu daya bude a cikin littafin,ya shiga bin abinda ke rubuce daki daki makar haka:A ranar Laraba sha biyu ga watan Agusta shekara ta dubu biyu da ishirin da huɗu,da misan ƙarfe goma na safe,iska ne mai matukar daɗi ke kadawa yayinda tsuntsaye ke tashi daga wannan bishiyar zuwa wannan,ta gefe ɗaya kuma idan har na kalli gajimare abin na matukar kayatar dani,saboda ina son kallon sararin samaniya ko dai lokacin haɗari ko kuwa lokacin da taurari ke baiyana,na kan tsince kai na cikin tsananin farin ciki kamar yau, Tafiya nake ina juyawa yayin da kaina ke kallon sama,sabanin sauran mutane dake tafiya suna kallon gabansu ko gefe, Ji nayi cikin zafin nama da karfi an jawo ni baya,wanda sai da nayi tangal_tangal kafin na tsaya da kafafuna, Cikin masifa ya fara faɗa "wai ke wata irin yarinya ce da magana daya baya mata,ta yaya zaki saka kai a Titi ba tare da kin duba ba,kalla yanzun saura kaɗan mota tabi ta kanki amma ko sani baki yi ba" "Na sani Mana yaya" "Kin sani shine zaki shiga titi haka? Dafa shi tayi" To me yasa zan wani damu da kallon Titi ba yan ina tare da ku" "Me kike nufi" "Ga ka ga Yaya Abdulmajid,ai kune ido na bana bukatar yin amfani da nawa" Karamin tsaki ya ja yana jinjina shirme irin na Ummu Salma " Jan kunnen ta yayi da ƙarfi "ai kuwa shi yasa baki gajiya da faɗawa kwalbati" Ihu ta saka tana kiran sunan "Ya Majid" Da sauri wanda aka kira da Majid din ya juyo yana sallamar Abokan shi da suke tare ya karaso in da suke"me ya faru "ya tambaye dan uwan nashi dake ke rike da kunnen ta har yanzun, " Sauran kaɗan mota ya bige ta" "Kai kana ina har mota zai bige ta,hankalin ka na ina,shi yasa nace ai ka bita a baya kana kallon hanya," Kwace ta yayi"sake ta ai duk laifin ka ne" Buɗe baki yayi yana bin su da kallon mamaki,duk da wannan ba shine bane karo na farko ba,in dai zata fita sai an haɗa ta da wani a cikin su,saboda tsabar kanta bai iya tsayawa wuri daya,idan kuwa ka bari taji ciyo ka shiga uku ko a wurin mama da sauran su, Yana biye dasu a baya har suka shiga cikin unguwar su wanda yake na matsakaita ƙarfi ne, Tunda suka shiga layin su duk inda suka gifta in da akwai manya a wurin sai sun gaida su, Su kuma suna amsawa cikin sakin fuska, Da haka har naga sun doshi Get din wani makeken gida wanda kaf unguwar babu gida mai girma da tsaruwa irin shi, Kwankwasa karamin ƙofar gidan suka yi sai gashi mai gadi ya fito ya buɗe masu, Ko asalin cikin gidan abin kallo ne ba sai na tsaya faɗa maku ba, Tana ganin sun shiga cikin gidan ta fisge hannun ta da gudu ta karasa cikin falon gidan tana kiran sunan Mama babu kakkautawa, Cikin sauri ta fito daga kicin hannun ta rike da Cokalin miya, Dafe Kwankwaso tayi tana kare masu kallo, Itama dafe kwankwaso tayi tana kallon Mama tana kyafkyafta ido,ganin Mama na ma Ya Abdul majid signal akan ya kamo mata ita ne yasa ta zabura zata gudu dakin ta,duk bin bayanta suka yi yayin da suka shiga zagayen falon suna dariya,har Mama ta samu nasarar kamata a ɗaura a kafaɗa tayi kicin da ita, A wannan lokacin shekara ta goma sha huɗu a duniya,ba ta da wani nauyi sai tsayi, Wurwurga kafa ta fara tana rokon Mama "dan Allah bana karki shigar da ni kicin,bana son kicin" "Ni kuma bana son kira kamar wata batatta" "Mama kiyi haƙuri ba zan kara kiran ki ba" Direta tayi a gaban sink din kayan wanke-wanke, "ga aikin ki nan" Turo baki tayi tana fashewa da kuka,dan ita a rayuwa ba aikin data tsana irin ace tayi shara tayi wanke-wanke,kallon Abdul Majid da Abdulmalik take tana mika masu hannu, Dan marairaice fuska Abdul Majid yayi"Mama na taya ta? Girgiza kai tayi "No" "Pls Mama,let us help our little sister" "Kuje ku kyara min dakin Baban ku yanzun" Badan sun so ba dole suka tafi, Ganin sun wuce ne yasa dole tayi shiru domin ta san a wannan lokacin Mama ba kula ta zata yi ba, Dan haka Safar hannu dasuke amfani dashi wurin wanke-wanke ta saka sannan ta buɗe fanfo ta fara, Kiran da aka ma Mama a waya ne yasa ta dauka tana barin kicin din, Kamar jira suke ta fita sai ga Abdulmajid ya shigo "kawo safar hannu" Zarewa tayi ta bashi,nan da nan kuwa ya shiga taya ta wankewa tana daurayewa har suka kusa kammalawa, Jin takun tafiyar Mama ne yasa da gudu ya fita kicin din ya bar ta bayan ya cire safar, Da sauri ta maida shi a hannun ta tana ƙara marairaice fuska, Kallon kayan tayi ta kalle ta"ke waye yazo ya tayi ki" Kumbura baki tayi"babu kowa" Girgiza kai tayi domin tasan karya take yi,wannan saurin ba nata ba ne, Sai da ta saka ta kammala ta wanke wurin sannan ta bari ta fita, Ɗakinta ta shiga wanda ya ji ado da kayan more rayuwa irin na matasan yan mata waɗanda ake ji dasu, Hayewa tayi saman kushin ta ɗauki wayarta tana buga game, Ba adau wani lokaci ba sai ji tayi ana ƙwanƙwasa mata ƙofa, "Come in" Ta fada da ƙarfi, Turo kofar Mama tayi"ki fito ki ci abinci" "Na koshi" "Bana son jin haka maza ta so mu je" Ajiye wayar tayi ta fito,ko da suka fito har yannin ta sun fito ko suna zaune sai Baba da shima shigowarshi kenan, Da gudu ta karasa inda yake ta rike hannun shi"Baba na barka da fitowa" Murmushi yake saki "barka mai gimbiya,da fatan kin tashi lafiya" "Lafiya glau" Zama suka yi a saman babban Darduma na falon,duk barka da fitowa suka mai, Mama ce ta zuba ma kowa abincin kari, Cikin natsuwa suke ci babu mai magana har suka kammala ita ta kwashe kayan ta mai da su kicin sannan mai aiki tazo ta wanke, Dawowa falon tayi ta zauna a tsakiyar yannin ta,"Baba ina son in siya wani takalmi dana gani ana tallah a online " "Nawa zai maki? " Dubu hamsin " "Zan tura maki,ke ma ban manta da Alkawarin mu ba"ya faɗa yana kallon Mama, Kiran da aka mashi a waya ne ya katse su, Sun dai ji yace" Shigo" Ba jimawa kuwa sai ga wani matashin saurayi ya shigo cikin falon da sallamah,daga dukkan alamu shi din ɗan gidan matsakaita ne daga ganin yanayin kayan jikin shi,kana kuma iya saka shi a sahun talaka amma ba tubus ba, Kyakkyawa ne baki ba laifi dan alokacin rashin kuɗi ya hana kyan shi fitowa, Dukawa yayi ya tsugunna har kasa yana gaida su,Baba da Mama ne suka amsa mashi sannan ya gaida su da suke kallon shi dan ba Kasafai Baba ke bari wani ya shigo har cikin falon shi haka ba, "Wannan shine *Yusuf*,shekaran jiya ya fara aiki a kamfani na na Suger" Kallon yaron Mama ta kara yi,nan take fara'ar dake fuskanta ya ɓace "gaskiya wannan yayi ƙarami" "Na dauki wadanda basu kai shi komai ba kuma sun iya balle shi,kuma a matakin manager zan Daura shi" "Allah ba da sa'a ta faɗa tana mikewa tare da barin wurin, Sallamar shi Baba yayi akan ya jira shi a waje yanzun zai fito. Ranar ƙarfe hudu suka kuma zuwa islamiya wanda da ma hakan yake duk ranar sati da Lahadi sau biyu suke zuwa islamiya, Tana zaune a aji ana karɓar hardansu na Kur'ani sai ga Malam babba ya aiko a kira ta, Sai da malamin dake ajin ya karɓi hardan ta sannan ya bari ta fita,domin haka dokar su take,to yanzun haka tana izufi Arba'in da biyu ne a harda, Tana shiga ofishin shi da sallamah ta gaida shi cikin Girmamawa, Nuna mata gefen shi yayi"Me alaƙar ki da waɗannan " Kallon su take daya bayan daya kafin ta zare ido tana kokarin karasa kusa da ɗayan, Dakatar da ita yayi"baƙi Bani amsa ba" "Malam wannan yaya na ne,sai wannan kuma saurayi na ne" Kallon ta sauran Malam dake ofishin suka yi, Daya daga ciki ne yace"kai jama'a lallai duniya ta zo ƙarshe,yanzun ke ƴar ƙarama dake har kinsan ki nuna wani a matsayin saurayin ki ba tare da kinji kunyar idanun mu ba? Bata fuska tayi"Malam to ai naga ku kuke faɗa mana ƙarya haramun ne,yanzun kuma dan na faɗi gaskiya sai ace nayi rashin kunya?dama fadar gaskiya na zama rashin kunya lallai duniya ta zo karshe"ta faɗa tana dafe gemunta da hannu, Dariya Malam babban yayi,dan yanda ta karasa maganar dole ya baka dariya,kallon su yayi"me ya hada ku faɗa a kanta" Ɗayan yaron ne da bai wuce shekaru sha biyar ba yace"Malam muna hira ne a ajin mu shine kowa ke fadin sunan budurwa shi,ni kuma da aka tambaye ni na kira sunan ta,shine fa ya taso ya ƙoda min Mari wai akan wani dalili zan ce ita duburewa ta ce " Maida kallon shi kan Abdulmajid Malam babba yayi"da gaske hakan ne ya faru? Dukar da kai yayi "haka ne Malam" "Yaya" ta kira sunan shi cikin jin haushin abinda ya aikata, Dagowa yayi yana hararan ta"Do you tell me? "Amma ai dama zan faɗa maka" "To be mun ba" "But I Love him" "Sama da ni? Lokaci ɗaya kuma ta saki murmushi ta tako har gaban shi ta rungume shi" Ai kai rayuwata ce,duk kuma abinda rai bai so ai barin shi yafi" "Da gaske" Jinjina mashi kai tayi "sosai,dan haka karka kara faɗa da wani" Murmushi ya saki shima"good Girl " Sake shi tayi"Malam kayi haƙuri yaya na bazai ƙara faɗa ba," "Ke ce bakin shi? " Umm "ta fada maimakon ta cewa A'a, Dan waro ido yayi" Umm" Shiru ta mai dan wannan tambayar Malam Buhari ne dama kuma shi ba shiri suke yi ba, "Ku biyo ni dole zaku karɓi hukunci domin makaranta ba wurin wasa bane,ba kuma wurin dambe ba ne" Tashi suka yi suka bi bayan shi har ofishin shi,ganin ya dauko ƙato bulala ne yasa ba shiri ta shiga rokon shi akan dan Allah yayi haƙuri karya Duke yayan ta, "Ki koma aji domin dole sai an hukun tasu". 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *56* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Kin tafiya tayi ta tsaya a wurin har Malam Buhari ya dauko bulala ya shiga zuba ma Yaya Abdulmajid,a duk bulalan da zai sauka a jikin shi ji nake tamkar a jiki na yake sauka,shi ake duka amma ni make faman zuba kuka shi kuma yana faman faɗin "ya isa haka ai babu zafi ma,ki dai na kuka" Shi kuma mugun malamin sai ƙara dukarmin yaya yake yi, Jin irin kukan da nake yi har da hadawa da ihu ne yasa Malam babba ya fito daga ofishin shi yace dukan ya isa haka ya bar su, Dole ya bar su badan ya so haka ba,dan yaran haka kawai suke bashi haushi saboda yanda yake ganin su ko yaushe a tare, "Malam ban fa yi mashi wani bulala ba,kawai makirci ne irin na wannan yarinya ita kullun haka take in dai za'a daki daya daga cikin yannin ta sai ta zo ta tasa mutum da kuka kamar ana yanka su" Murmushi Malam babba yayi yana kallon yanda take cigaba da kuka tana duba tafin hannun yayan nata,shi kuma sai cewa yake"ai hannun ba yamin zafi,ki bar kuka haka" "Tashi ku koma aji" Mikewa suka yi suka fita sai da ya raka ta har bakin ajinsu ya tabbatar ta shiga sannan ya koma nashi ajin, Ko da aka tashi islamiya tare suka jero sun saka ta a tsakiya kamar ko yaushe, Abdulrahman ne yace"wai ke yaushe zaki daina wannan fushin ne,na ga shi wanda aka daka har ya hakura amma ke sai fushi kike yi" "Yaya wallahi malamin nan haushi yake bani,kome nashi na mugunta ne,amma bari sai nayi maganin shi" "Me zaki mashi? Cewar Abdulmalik, " Sirri ne" "Don't just go and do anything stupid" In ji Abdulrahman, Kin bashi amsa tayi sai ma ƙara sauri da tayi ta yi gaba ta bar su,dole da sauri suka bi ta, A ƙofar gida suka haɗu da Yusuf yana zaune, Yana ganin su ya tashi ya mika masu hannu suka gaisa, Abdulrahman ne yace"me kake yi a ƙofar gida? "Ba komai kawai dai na shigo ne mu gaisa Mama tace kuna islamiya" "To ai daka zauna ciki,shigo mu je" Bin su ciki yayi sai da suka shaida ma Mama sun dawo kafin su shiga nasu falon dashi, Tana gama cire kaya dakin su ta shiga bayan ta canja wani,zama tayi cikin su suka shiga yin hira, Kallon Yusuf tayi "Ka iya game? " Wani iri? "Motal comebat" Girgiza kai yayi"A'a " "Yana da daɗi sosai bari na koya maka" Jona TV tayi ta haɗa da kayan game,nan suka shiga bugawa tana yi tana nuna mashi, Sai da lokacin sallah yayi sannan suka fita masallaci ita kuma ta shige daki, Washegari tunda Asuba ƙarfe biyar kafin ayi sallah ta tashi bacci ko wanka bata yi ba ta buɗe ƙofa ta nufe shiyansu,bubbuga masu ƙofa ta fara da karfi tana kiran Ya Abdulrahman,ya Abdulmajid,ya Abdulmalik,haka ta shiga kira tana buda ƙofa wanda ƙaran haka ne ya tayar da Baba ya fito yana haskawa dan jin ko lafiya, Ganin ita ce yasa yace"Gimbiya lafiya?me kike yi a nan yanzun" Turo baki tayi cikin jin haushin kyale ta da sukayi tace"Baba yau fa Birthday dina so nake su bani kyautar karin shekara" Dafe goshi yayi"My gimbiya yanzun fa ƙarfe biyar na asuba tayi,ko sallah ba'a yi ba,ki je ciki idan gari ya waye zasu baki " "Ba zasu bani" "I promise you zasu baki" Juyawa tayi ta shige cikin shiyansu ta bar wurin, Girgiza kai kawai yayi yana kwankwasa masu kofa sau daya tare da kiran sunan su, Nan take kuwa sai gashi ko wanne yana buɗe ƙofar dakin shi yana fitowa, Kallon su yayi"Amma kuna jin kanwar ku ko? Hamma Abdulrahman yayi"Baba wallahi she is really Stoburn" "Lokacin sallah yayi sai ku fito mu tafi masallaci" "To Baba" Koda suka dawo masallaci da zasu kulle kofa daga mai saka filo ya toshe kunne shi sai mai saka Earpis a kunne, dan kawai kar su ji damun da zata masu, Sai dai fa duk da haka ƙarfe bakwai na safe na cika ta dauki katon sanda ta shiga bugun kofar su dashi tana kiran sunan su, Ganin ba su da niyar buɗewa ne yasa da kuka ta nufi cikin gida dakin Mama wacce take kwance tana waya, Kwantawa tayi kusa da ita tana cigaba da kuka wanda ganin haka yasa ta ajiye wayar"me ya faru? "Mama su Yaya sun ƙi tashi su ban Happy birthday" Kallon agogon bangon ɗaki tayi "ƙarfe bakwai yanzun,ki bari idan sun tashi zasu baki" "Wancan karon ma haka suka min fa Mama,ni dai yanzun sun daina so na" "Salma pls barci nake ji kin ji Sweet heart" Sauka tayi akan gadon tana barin ɗakin ta shige nata ta kulle ƙofa, Komawa tayi ta kwanta kan gado tana jin haushin abinda suka mata,daga haka barci ya ƙara kwashe ta, Ba ita ta farka ba sai ƙarfe goma saura,banɗaki ta shiga tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga na Les ruwan ƙwai da fari, Ba karamin kyau kayan ya mata ba,sai Mayafin data yafa,ta fito shar da ita yanda kasan wata Ƴar Tsanar Zinari, Ji tayi an Kwankwasa mata ƙofa,dama kuma tana shirin buɗewa ne dan haka buɗewa tayi, Ji tayi abu mai ƙyalli ya zubo mata a kai yayin da yannin ta ke tsaye a gabanta suna mata waƙar Happy birthday to you, Duk irin yanda take jin haushin su ganin yanda suke murmushi da dariya yasa ba shiri itama ta saki dariya tana kama ƙananan fulawar dake sauka a jikin ta, Hannun ta Abdulmajid ya jawo suka gangaro da ita ƙasa,anan ta tarad da Mama rike da katon cake tana jiran isowar ta an kunna kendu a jikin shi, Karamin wuƙa ya mika mata ta amsa,suna mata waka ta yanka cake ɗin, Mama ta fara saka ma abaki kafin ta shiga saka masu daya bayan daya,sai Yusuf dake gefen shima yana murmushi dan ba karamin burge shi suke yi ba ta saka mashi shima a baki. Wannan shine asalin rayuwar su mai ɗauke da farin ciki da annashuwa, A hankali shakuwa ke ƙara shiga tsanin su da Yusuf wanda take kira da Game partner saboda duk lokacin da yazo gidan suna tare suna buga game yana biye ma duk wani shirmenta,kamar yanda yannin ta ke mata, Wata biyu da cikar ta shekara goma sha-biyar takardar nima mata jam'i ya fito a London wanda anan zata karanta Lauya na tsayin shekara biyu, Koda Baba ya kawo mata takardar a maimakon yaga farin ciki shimfide a fuskarta sai damuwa daya hango,yayi tambayar duniya amma sai ce mashi take babu komai,karshe ma sai tashi tayi ta fito daga falon shi wanda a bakin ƙofar fita ne suka haɗu da Yusuf yana ƙoƙarin shiga wurin Baba, Kallon shi tayi na sakan ni kafin ta ɗauke kai tayi wucewar ta, A cikin yan watannin nan da yayi tare da su,ta lura ba karamin ji dashi Baba yake yi ba,yanda yake ma Yusuf ko su Yaya baya masu haka,idan har Yusuf zai ce yana son abu to cikin rawar jiki kuwa zai ɗauka ya bashi har ma fiye da yanda ya tambaya, Shida iyayen shi Baba ya basu wani tankamemen gida wanda babu abinda babu a ciki,sannan ga Mota lafiyayye ya siya mashi,amma su yaya tun yaushe suke bin shi ya sai masu mota yaƙi sai dai duk inda zasu Direba ya kai su, A babban falo taci karo da Yaya Abdulmajid,rike ta yayi"ke kuma tunanin me kike kina tafiya? Kallon hanyar data fito tayi "na fara jin haushin Yusuf" Ta faɗa tana tura baki, Kama baki yayi yana dafe kwankwaso"ke kuma da ya maki me? "Kalli fa yanda yake shiga dakin Baba kai tsaye yanda kasan wani Baban shi" Rankwashi ya sake mata a kai"to ai Baban shi ne tunda yaron aikin shine,kin ga ban son gulma je ki faɗa ma Baba masu karɓar sadaka suna waje suna jira " Dafe kanta tayi tana bata fuska "ba zan je ba ka je da kanka" Ta faɗa tana rugawa da gudu tayi hanyar dakin Mama, Girgiza kai yayi "kyuya ko?zamu haɗu da ke" Ya faɗa yana wucewa dan sanar dashi,domin Al'adar shine yin sadaka a ko wani yamma,daga wurare ma mutane kanzo karɓar wannan sadakar nashi,shi yasa mutanen unguwar su ke girmama shi sosai, Dakin Mama ta shiga da sallamah ta same ta a zaune kamar ko yaushe ita kenan yawancin lokaci cikin amsa waya,sam Mama bata gajiya da amsa waya, Zama tayi kusa da ita "Mama" Sallamah tayi da wanda take wayar ta juyo kanta"ya akayi Sweet heart? Miƙa mata takardar tayi, "Na menene? " Na makaranta ne a London " Nan take ta sake murmushi ta jawota ta rungume "Oh Sweet heart congrat yaushe ne tafiyar? " Nan da sati biyu " Ganin yanda tayi maganar cikin damuwa ne yasa ta ƙara kallon ta"me ya faru,ya naga kamar you ar not happy " Ai kuwa kamar dama jira take ai mata wannan tambayar ta fashe da kuka wanda yi take ba kakkautawa, Duk ta tashi hankalin Mama sai aikin lallashi take yi, Da kyar ta samu tayi shiru ta natsu, "Faɗa min meke faruwa" "Mama ke kika ce duk abun dake damuna a should feel free to tell you" Jinjina kai tayi"sosai ma faɗa min ko ma menene I will be here for you " Share hawayen idon ta tayi da yaƙe dai na zuba. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *57* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* "Mama ina ganin ina da karfin sha'awa" Zaro ido tati cikin mamakin jin abunda yarta ta faɗa "Ƙarfin sha'awa kuma Salma? Shiru tayi ta dukar da kai tana murza ƴan yatsun ta, Ajiyar zuciya ta sauke tana ƙoƙarin saisaita kanta" Ta yaya kika san haka,i mean ya kike ji a jikin ki? Ganin taki cewa komai ne yasa ta riƙo hannayen da take murzawa "ba na ce zan taimaka maki ba,dan haka faɗa min " Dan rintse ido tayi ta buɗe,tana jin kunyar yanda zata faɗa,sai dai ba ta da wanda zata ni ma shawara ne sai ita Maman,domin duk rashin kunyar ta ba zata iya tunkarar daya daga cikin yannin ta maza ta nime shawarar shi ba,ko yanzun ma abun yana son yafi karfin ta ne "Idan har zan kalli wani namiji na kan ji tsigar jiki na yana tashi,sai kuma in ji ina son in rungume shi,haka kuma idan na kalli film naga mace da namiji sun yi Kiss ji nake kamar na samu wani kusa da ni da zai min,jiki na sai ya dinga kaikayi ta ciki wani lokaci har jikewa nake yi ta cikin pant di na,hankali na tashi yake" "Har da yannin ki kina jin haka a kansu? Da sauri ta girgiza kai" Su bana jin komai a kansu ko kaɗan " Dan shiru Mama tayi tana nazarin maganarta tabbas sha'awar ne,to sai dai ya zata yi da ita, "Mama baki ce komai ba? " Salma tunani mafita nake yi" "Mama ina da mafita" Kallon ta tafi ta zuba mata ido na wani lokaci kafin tace "wani iri? " Mama na yanke shawarar aure zan yi" "Aure!aure fa kika ce Salma?yanzun ke har kinsan aure? Dukar da kai tayi" Ni dai aure nake so " Tama rasa me zata ce mata sai ido data zuba mata"shekaran ki nawa ma? "Goma sha biyar" "And you want to get marriage at this age? Shiru tayi bata bata amsa ba, "Answer me girl" Kara marairaice fuska tayi"Mama ni dai duk hukuncin da zaki yanke dan Allah kumin aure " Dafe kai tayi kafin ta kuma cewa"to wa zaki aura? Kai tsaye ta bata amsa wanda sai da tayi dana sanin faɗin hakan domin tunda suke da Mama bata taɓa yi mata tashin hankali ba irin na yau "Mama Yusuf nake so,shi nake so na aura " Wani irin zabura da tayi tare da faɗin "What" Sai da ta matsa baya,domin kamar abin yazo ma Mama a bazata ne, "Yusuf fa kika ce" Shiru tayi tana zazzare ido, "Wasa dai kike yi ko? " Umm um,i Love him i want to married him" Cikin tsananin faɗa da rufewar ido tace"ba dai a gidan ba,in banda rashin hankali da rashin sannan ciyon kai me zaki yi da wannan yaron,to bari kiji in dai har ina raye ba zaki taba auren wannan yaron ba har a bada ba dai Yusuf ba,wato zaman da yake yi cikin ku bana arziki bane yana zuwa ne dan ya hore maku kunne,to ba dai a gidan nan ba zai koya maku bakin hali da mummunan ɗabi'a ba,kar na kuma jin kin yi maganar aure a gidan nan balle maganar shi,kuma tafiya karatu dole ne,tashi ki barmin daki mahaukaciyar banza" Da kuka ta tashi ta bar dakin tana mai matukar jin zafin abinda Mama ta faɗa akan Yusuf, Ranar yi ni tayi kuka a daki wanda sai da idanun ta suka kumbura shi yasa ko abinci dare bata fito ci ba, *Ban sani ba ashe wannan shine mafarin komai,Ashe Mama ta san abinda ni ban sani ba game dashi,amma a wannan lokacin yarinta da ƙuruciya sun hanani ganin komai sai ma laifin Mama da nake gani* buɗe shafi na gaba yayi. Ganin har sun kammala cin abincin dare ban fito ba gashi basu ji Mama tayi magana ba yasa Ya Abdulmalik cewa"Mama lafiya banga autar ki ta fito cin abinci ba? Kauda kai tayi"ƙila ta ko shi ne,idan yunwar cikinta ya isheta zata fito" Duk kallon_kallo suka shiga yi ma junan su,abinda bai taba faruwa ba,kome Salma tai mata da zaran lokacin cin abinci yayi taga bata fito ba da kanta zata shiga lallashi har sai ta lallabata ta fito ta ci, "Mama wani abun ya faru ne? Abdulrahman ya tambaya tana ajiye chokalin hannun shi, " Kamar me kenan? "Tsakanin ke da Salma" Itama ajiye nata chokalin tayi"ku saurare ne,daga yau sai yau bana son na ƙara ganin ku tare da wannan yaron " "Wani yaro" Cewar Abdulmajid, "Yusuf,bana son na kuma ganin ku tare,ko a gida ko a waje," Duk shiru suka yi suna mata kallon mamaki, "Mama dan Allah idan har wani abu ya faru ne ki faɗa mana" Mikewa ta yi "na dai faɗa maku,idan ana son zaman lafiya a gidan nan sai a kiyaye" Tana gama faɗa ta yi shigewar ta daki ta barsu nan zaune baki sake, "To me yake faruwa" "Wa ma ya sani,ku tashi muje mu duba Salma" Mikewa sukayi suna masu bin shawarar Abdulrahman, Sai da suka ƙwanƙwasa ƙofar har sau uku suna sallamah ba'a amsa ba,jin shirun yayi yawa ne yasa suka tura ƙofar suka shiga, Tana zaune a tsakiyar gado rungume da filo tana sauke ajiyar zuciya irin na wanda yayi kuka ya gaji, Da sauri suka ƙarasa inda take cikin tashin hankali suke tambayar ta me ta faru,me yasa take kuka, Rungume Abdulmajid tayi tana ƙara fashewa da wani sabon kukan, Shafa bayan ta ya hau yi"Ya isa haka nan,yayi,kinga jikin ki har ya fara zafi," "Yaya me laifi na ma Mama,kawai ɗan nace ina son shi? Kallon juna suka yi" Waye kika ce mata kina so? "I am just feeling somehow,I want to get married and I tell her cewa Yusuf nake son aure,shine Mama take ta yi min ihu tana faɗa wai Yusuf ba mutumin kirki ba ne,in dai tana raye ba zata taɓa bari na aure shi ba" Ta kara fada tana saka sabon kuka, Duk shiru sukayi suna tunanin wannan lamarin, Abdulrahman ne yace"but the Yusuf I know is not a bad person, ko kuwa? Ya tambaya yana kallon sauran ƴan uwan nashi, "Gaskiya ne" Dago ta yayi yana share mata hawaye "kin ga ki kwantar da hankalin ki insha Allah zamu samar maki mafita" "But Mama tace sai dai bayan ranta,ya ya zan yi? "But Girl I think you are to small for marriage,domin abinda na sani there are so many complications about marriage,sannan a wannan kananan shekarun naki how are you going to handle them, ta yaya,ni fa ina ganin Mama ta na da dalili" Duk shiru suka yi suna sauraren shi, "But Abdulrahman tana son shi" "Is doesn't matter ko tana son shi,abun nufi shine ya rayuwar ta zai kasance,bancin haka makaranta fa zata tafi London nan da sati biyu,ta yaya zata dauko zancen aure bancin shekaranta sha biyar" Karfin kukanta ta kara tana maida kanta saman filo "Ku fita I don't wanna see you," Dafa ta Abdulmajid yayi"tunda dai har kina son shi ni dai ina bayan ki,tashi ki faɗa min dama kun jima kuna soyayya ne? Tashi tayi zaune tana girgiza kai"a'a is one side love " Duk zaro ido suka yi"Uhhh " Jinjina masu kai tayi "Yes,I never get a chance to tell him" "Amma shine kike cewa zaki aure shi,kin faɗa mashi ne? Abdulmalik ya tambaye ta wannan karon, "Kawai ni Mama na faɗa ma kafin na fada mashi" Dafe goshi Abdulrahman yayi "ohh God,gashi nan bay this your stupid action kinsa Mama ta tsane yaro,to yanzun sai ki faɗa mana me kike son ayi" Kai tsaye tace"Aure,auren shi nake son yi" Zuba tagumi yayi yana sauraren wannan haukar na yar uwar tasu"zuwa yaushe kike son auren? "Kafin na tafi London,idan ya so sai mu tafi tare dashi" Mikewa tsaye yayi daga saman gadon nata"Abdulmajid jeka ɗebo mata abinci taci,ke kuma ki kwantar da hankalin ki zamu fara shawo kan Mama kafin mu tunkare Baba da maganar,sannan zuwa anjima zanje gidan su Yusuf din sai mu yi magana dashi a can" Ai kuwa nan take farin ciki ya mamaye duk wani bacin rai na fuskarta "Na gode ya Abdulrahman" Ko kulata bai karayi ba ya fita, Abdulmajid ne ya kawo mata abinci tana ci suna hira har da Abdulmalik har saida suka tabbatar da ta ko shi kafin su bar dakin. A falon su suka same shi zaune yana waya wanda daga dukkan alamu da Yusuf din yake waya,sai da ha kammala sannan ya ajiye wayar ya kalle su"Abdulmajid kai zamu tafi gidan su Yusuf da kai, Kai kuma Abdulmalik ka zauna har mu dawo" "Ba damuwa sai kun dawo amma dai karku daɗe domin kun ga takwas da rabi ya wuce" "Ok" Kawai suka ce mai suja fita, Ba da direban gida suka je ba,dan basu ma son Mama ta san sun fita,dan haka suna barin Get din gidan suka tare Adaidaita suka shiga, Har kofar gidan Yusuf ya kai su sannan suka sallame shi ya wuce, Me gadin gidan ya san su dan haka ko da suka Kwankwasa ya buɗe yaga sune bai hana su shiga ba sai gaida su cikin girmamawa da yayi, Suna shiga ciki a ƙofar falon su wurin da aka zuba kujeru dan hutawa suka same shi, Sai da suka ja kujera suka zauna sannan suka shiga gaisawa kamar yanda suka saba, Dariya yayi"yau kune a gidan namu da daddare,hala daga wani wuri kuke? "A'a daga gida dai" "Wow kace today was my lucky day,to bari na kawo maku abun motsa baki"ya mike yana faɗin "ina Game partner di na da Abdulmalik suke ke? "no bar shi kawai dama akwai magana mai muhimmanci daya kawo mu,su suna gida" Komawa yayi ya zauna yana tunanin wani irin magana ne da zai fito dasu gida yanzun haka,shi yasa yayi mamakin daya gansu a wannan lokacin,"ina jin ku" Furzar da iska Abdulrahman yayi kafin yace "Me tsakanin ka da Ummu Salma? 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *58* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Maimaita tambayar yayi "meke tsani na da ita? " Umm" Dan shiru yayi yana nazarin wani irin tambaya ne wannan sannan da wani amsa ya dace ya basu,"maganar gaskiya ban gane inda wannan tambayar ta dosa ba,dan nasan babu komai tsakanin ni da ita,kawai dai ina mata kallon kanwata ce kamar yanda kuke mata,that's all" Kallon Abdulmajid yayi"That's so bad "cewar Abdulrahman Jinjina kai yayi"nan da sati biyu zata wuce karatu London" "Wow that's Nice,gaskiya na taya ta murna sosai" Ƙara kallon juna suka yi,kafin yaci gaba da faɗin "sai dai akwai ɗan matsala" Shiru yayi yana sauraren su,"matsalar me? "Taki yarda da batun tafiyar domin wai aure take so,idan har ba'a mata aureba ba zata tafi ba" Dan waro ido yayi"aure fa,da yaushe ta isa aure bayan shekar ta goma sha biyar,kai gaskiya Salma da rigima take,yanzun ita wa take so ta aura,ko dama tana da saurayi ne?ya faɗa yana tsare su da ido, "Maganar gaskiya bamu sani ba sai yau a dazu,sannan da muka tambaye ta sai cewa tayi kai take so,mun tambaye ta ko dama kuna soyayya ne tace a'a ita bata taɓa faɗa maka ba,kuma tana can ta tayar da hankalin ta sai kuka take yi shi yasa muka ce bari mu zo mu same ka" Kamar wasu marasa hankali haka yake kallon su,nuna kanshi yayi "ni Yusuf din tace tana so? " Eh kai tace,dan ko mu munyi mamaki" Girgiza kai yayi"gaskiya ni bana ra'ayin soyayya da mace bare kuma Ummu Salma,ba zai taɓa bari ba" "Waye ba zai bari" Cewar Abdulrahman, Kai tsaye ya basu amsa "Baban ku,ko ya sani ne? Ya mai da masu da tambayar, " Bai sani ba,amma bana jin za'a samu matsala ta nashi bangaren " Wani irin murmushi yayi wanda suka kasa gane kanshi da manufar shi "to ai anan babban matsalar take,domin ba zai taba yarda ba" "To me yasa wai kuke ganin rashin yuwar haka,daga kai har Mama,yanzun kuma kai ka faɗi haka,ko dai akwai abunda bamu sani bane dangane da kai Yusuf? " Abdulmajid kenan,babu wani bu,sai dai ko da ace ma su sun yarda ni ba zan yarda ba" Wannan karon kalaman shi ya fara basu haushe "me a tattare da Salma da har zaka ce kai ba zaka yarda da Aurenta,na tabbatar idan kyau kake butaka to tana dashi,idan kuma kuɗi ne ko tarbiyya kaima kasan duk gidan su ka zo,ko me babban magana akan wannan lamarin" "Babu wani babban lamari amma kasan shi aure abu ne na ra'ayi to ni kuma Allah bai Daura min wannan ra'ayi ba,kuyi haƙuri sannan ku ba ƙanwar ku haƙuri ta nime wani ta aura" Yana gama gadar haka ya tashi ya shige cikin gida ya bar su nan zaune a baranda, Kallon juna suka yi suna jinjina wulakanci irin na Yusuf wanda basu taba tsammanin haka daga gareshi ba,sun dauka zai amshesu da hannu biyu sannan yayi farin ciki akan lamarin ya nuna jin daɗin shi,sai gashi ya nuna masu saɓanin haka, "Tashi mu tafi" Mikewa yayi suka fito sannan suka samu abin hawa ya maida su har ƙofar gida, Suna shiga shiyan su zama suka yi a nan falo saman kushin in da Abdulmalik ke zaman jiran su, Yana jin shigowar su ya tare su"Kun same shi? Ya kuke yi dashi? Dama soyayya suke yi ko? Dafa kafadarshi Abdulmajid yayi"duk yanda kake tunanin abun ba haka yake ba" Zaro ido waje yayi"kamar ya? "Zauna kaji" Nan suka shiga ba shi lamarin duk yanda suka yi da Yusuf din har wutowar su,"yanzun ban san yanda zamu yi da Salma ba,kasan ita matum ce mai tsayawa akan magana daya har balle a kan abinda take so,yanzun duk wani shawara da zamu bata ba ɗauka zatayi ba," "To me zai hana mu same Baba da maganar" In ji Abdulrahman. "A'a yayi sauri Gara dai mu fara dai-dai ta kansu tsakanin shi da ita sannan mu shawo kan Mama tukun na kafin Baba" "Hakan yayi, yanzun mu je mu kwanta kun ga har ƙarfe goma tayi gobe ma san abun yi" Da wannan shawarar suka tsayar in da kowa ya shige ɗakin shi ya kwanta kowa zuciyar shi cike da nimar mafiya ma kanwar su. Washegari ta riga kowa fitowa wanda ita kanta Mama sai da tayi mamakin fitowar ta,domin ba ta zata ba, Cikin sakin fuska ta gaida Mama,wacce ta kasa yin shiru "what the occasion" Dan dariya tayi kaɗan "babu komai Mama,kawai dai ina cikin farin ciki ne" A tunanin ta ko ta hakura da maganar su na jiya ne dan haka tace"ai gara da kika cire shi a ranki domin hakan zai fi maki" Girgiza kai tayi"A'a ban cire shi a rai na ba,kawai dai sun min Alkawarin taimaka min ne" "Su yannin naki? Ta tambaya cikin mamaki, " Umm "ta fada tana haɗa shayi, Bata ce mata komai ba har sai da ta tabbatar ta karasa shan shayin ta sannan ta kalle ta" Bana son ki saka yakinin ki da yawa a kansu,domin haka zai iya cutar dake,abu na biyu ko da ni na amince ki sani mahaifinki ba zai taɓa yarda ba ballantana ni ma kuma ba zan taba yarda ba" Ji tayi nan take duk wani kwarin gwiwa data tashi dashi Mama ta sare shi"me yasa baki son Yusuf,me yayi maki da kika tane shi har haka Mama Yusuf fa is a normal gay,yana aiki a kamfanin Baba,ana biyan shi Albashi wanda na tabbatar da zai iya riƙe mu,to Mama me kuma ake buƙata,na tabbatar da idan da Ace tun farko bai da tarbiyya Baba ba zai taɓa yarda ya shigo dashi cikin gidan nan ba,ke ma kin sani" Kallon ta kawai take yi tana kuma jinjina irin fahimtar ta da kuma yarda da tayi da mahaifinta,tabbas data san shi waye da bata faɗi haka ba,dan haka ba tare data bata amsa ba ta mike ta shige daki abunta, Da kallo ta bita cikin mamakin abunda tayi,ta dauko magana sannan bata karasa ba ta wuce, Dan haka tashi tayi ta bita daki,in da ta same ta tsaye da waya a hannu daga dukkan alamu kira take kokarin yi, Kallon ta tayi"lafiya? "Mama baki ce komai ba? Zama tayi bakin gado" Me kuma kike son na faɗa maki Salma wanda zaki fahimce ni? "Kin ce kar na ji kunya a duk lokacin da nake da wani buƙata ko niman taimako na zo na same ki a matsayin ki na mahaifiyata zaki taya ni samun mafita,amma sai gashi a karon farko kina kokarin jefa rayuwa ta cikin hatsari ta hanyar hana ni aure" Dafe goshinta tayi ta dan murza tana busar da iska cikin tsanin damuwa da lokaci guda ya baiyana a fuskarta "ina maki gudun aikata wani babban kuskure wanda zai ta bibiyar rayuwar ki na tsayin har a bada Salma! Ina maki gudun tafka babban kuskure irin wanda na aikata a baya!ina maki gudun rayuwa mara tabbas,kokonta da bullewa Salma! Bawai ban fahimci halin da Kike ciki bane,kawai dai ina tsoron halin da zaki shiga ne,domin duk irin nunin da zan maki,ba zaki taba fahimtar komai ba domin idanun ki a rufe suke wanda ni kaina bana fatan abunda zai buɗe maki su har abada balle ki fuskanci abunda ke gaban ki,sai dai ki sani auren wannan yaron da zaki dauko ma kanki tamkar mutum ne ya faɗa rami sannan yaci gaba da haka ramin wai a kokarin shi na fitowa har wata rana wannan ramin yayi zurfin da zai fado ya danne shi, Ni idan da ace wani kika kawo ba shi ba wallahi zan yi farin ciki dashi na kuma taya ki karbar shi,amma Yusuf har abada ba zan taba karɓar shiba,domin kokin aure shi ba zaki taba samun abunda kike nima ba" Kama hannun ta tayi duka biyu ta haɗa wuri ɗaya"ɗan Allah ki fahimce ni Salma,ki canja wani zaɓin zan taimaka maki kin ji? A hankali ta zame hannun ta a cikin nata"Mama ki yi hakuri duk yanda naso na natsu na fahimce ki na kasa,domin har yanzun baki ba ni wani kwakkwaran hujja ba da zai hana ni son shi,dan haka ki yi hakuri har yanzun ina kan baka na Yusuf shine zaɓi na"tana gama fadar haka ta tashi ta bar mata ɗakin " Da kallo ta bita,sai dai wannan karon zuciyar ta cike yake da rauni ganin irin kuskuren da yarta ke kokarin tafkawa a rayuwar ta,sai dai ko zasu kai ruwa rana ne ba zata taɓa bari hakan ya faru ba.... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *59* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Ganin lokacin tashin Baba yayi ne yasa suka shiga dakin shi da sallamah, Cikin farin cikin ganin yaran nashi ya amsa yana sakar masu murmushi,zama suka yi kan kushin "Baba muna da magana" Ajiye Turaren da yake fesawa yayi ya dawo ya zauna a daya daga cikin kujerun da suke zagaye a dakin, yana fuskantar su,ganin yanda suka ba maganar da zasu faɗa Muhimmanci suka natsu, Yasa yace"Ina jin ku" Ajiyar zuciyar Abdulmajid ya sauke kafin ya fara magana "Baba Salma ta faɗa maka ra'ayin ta game da tafiya makaranta? " A'a,wani abun tace maku ne? "Ta samu Mama jiya da maganar cewa ita bata son tafiya karatu London ba tare da Aure ba,ina nufin wai aure take so" Dan shiru yayi na dan wani lokaci alamun nazari kafin ya ce"tunda har ta zaɓi haka to ba matsala ba ne,da ace taje tana aikata wani abu bayan idon mu gara da ta faɗa kun ga sai ai mata abun da take so,in yaso sai su tafi tare da mijin ta,ko ba haka ba? Kallon juna suke yi suna sakin murmushin nasara domin basu ɗauka lamarin na wurin Baba zai zo masu da sauƙi ba,"haka ne Baba" "To dama tana da wanda take so ne,ko kuma ta tsayar? " Eh tana dashi Baba,sai dai kuma data fadama Mama sai cewa tayi sai dai bayan ranta dan bata isa ta aure shi ba," "Wannan ai maganar banza ne,bayan yarinya na son shi kuma har ta faɗa,so take ta saka ta a wani hali ko kuma so take na mata auren dole,karku damu zan fahimtar da ita amma kan aure sai an yi tunda suna son juna,tukunna ma waye yaron,waye mahaifin shi? " Baba ai ka riga ka san shi,Yusuf ne me zuwa nan gidan " Dan jim yayi kafin kuma kamar wanda aka tsikara tace"ba dai Yusuf ba? "Shi Baba" Nan take wani irin zufa mai matukar sanyi ya shiga fito mai daga jiki ta ko'ina,hankalin shi ya tashi yayin da yaji wani abu ya tsaya mai a rai"ba dai Yusuf ba,dama amanata zai ci yana soyayya da ƴar tawa bayan duk abinda nake ma shi bai ishe shi ba" Kallon tsoro da mamaki suke mai,sai suke ganin kamar ba shi ba,yanzun fa ya amince amma kuma yake yi kamar bai gane me suke nufi ba, "Baba dama soyayyar bari daya ne" "Kamar ya? " Shi baya son ta ita ce ke son shi,dama so muke ka faɗa ma iyayen shi ko zasu shawo kan shi " Wani irin ajiyar zuciya mai matukar ƙarfi ya sauke wanda yasa sai da suka kara shan jinin jikinsu da wannan lamarin,gashi har share zufa yake yi yayin da idanun shi suka yi ja "to tunda baya son ta ai ba dole bane,ba sai ta nime wani ba,ni ban damu ba ko ma waye ta kawo zan aura mata amma banda Yusuf" "Baba amma fa yanzun ka nuna amincewar ka me ya faru,shin me yasa baku son ta auri Yusuf,ko dai akwai wani abu dangane dashi ne wanda ya kamata mu sani,? Kara share zufan daya karyo mashi yayi" Kawai dai ku bata shawara tabi shawarar mahaifiyarta,ku tashi ku tafi sannan bana son na kuma jin irin makamancin wannan maganar a gidan nan on dai akanta ne da Yusuf " Cikin sanyi jiki da kokonton iyayen nasu suka fito daga dakin Baba yayin da suka samu Mama a falo zaune tana kallo a zahiri,amma idan ka fahimce ta da kyau ba kallon take yi ba kawai idanun ta ne a kan TV, Duk zama suka yi kusa da ita,yayin da Abdulmalik ya dafa kafadarshi ta,"yin dogon nazari yana haifar da damuwa Mama" Juyowa tayi tana ɗan lumshe ido"kanwar ku ke ƙoƙarin haifar ma da rayuwar mu da damuwa gaba ɗaya " Matsowa Abdulrahman yayi cikin damuwa"Mama dan Allah ko dai akwai abunda kuke ɓoye ma na ne game da Yusuf ke da Baba banda baku son mu sani? "Me ka gane Abdulrahman,shin wani abun ya faru ne? " Mama munje mun samu Baba da maganar Yusuf da Salma,da fari ya yarda ya amince kafin sanin Yusuf take so,amma daga jin shine taje so,shima ya tashi hankalin shi ya nuna rashin yardar shi,Mama ko dai Yusuf yaron Baba ne bamu sani ba? Kallon yaran nata take yi yanda duk suka tsira mata ido suna jiran karan bayani, Girgiza kai tayi"Shi ba ɗan mahaifinku bane,domin mahaifinku ba shida wani ɗa a duniya,kuma na tabbatar da mata basu gaban shi, Kawai dai akwai dalilin da yasa bamu amince da wannan auren ba,sannan ɗan Allah karku tambaye ni domin ba faɗa maku zan yi ba har abada kamar yanda shima mahaifin naku ba zai taɓa yarda ba har da shi kanshi Yusuf ɗin,domin shi yasan dalilin, Abu na gaba shine kusan yanda zaku shawo kan kanwar ku ta bar wannan maganar ta canja wani"tashi tayi ta koma daki ta turo ƙofa, Cakuɗe gashin kanshi Abdulmajid yayi"ohhhh,this doesn't make sense,kai na ya dau zafi,so nake na san wannan dalilin" "Ni ma haka wallahi" Cewar Abdulmalik, "Ku tashi mu je mu sami Yusuf tunda Mama tace ya sani sai mu rokeshi ta faɗa ma na" Da haka suka bar gida,sai dai ko da suka je gidan su Maman shi ke shaida masu ya fita sai dai ba zai jima ba, dan haka suka zauna zaman jiran shi, Ya ɗauki kusan awa daya kafin ya dawo,ko da ya gansu bai wani nuna zumudin zuwan nasu ba kamar sauran lokutan da suka saba zuwa har ya rasa ina zai ajiye su, Jan kure yayi ya zauna yana miƙa masu hannu suka gaisa,"kun jima da zuwa ne? "Eh amma ba sosai ba" "Ai da kun kira ni" "No ba damuwa tunda gashi ka dawo" Cewar Abdulrahman "Da fatan kuna lafiya" Ya tambaye su, dan wannan karon dukansu su uku ne suka zo, "Lafiya ƙalau,dama dai akan maganar jiya ne Yusuf,sai dai abin mamaki kamar yanda kace iyayen mu ba zasu yarda sai gashi hakan ne ya kasance dan har yanzun dukansu sun ƙi amincewa saboda wani dalili nasu wanda mu ba mu sani ba amma kuma kai kasani,shine muke rokon ka ko zaka iya faɗa mana ne yasa dukka suka ki amincewa da kai,menene dalili " Ɗan dariya yayi wanda ya basu mamaki domin basu ga wani abun dariya ba acikin wannan maganar"shi Baban da Maman naku basu faɗa maku ba? Ya faɗa yana Daura kafa daya kan daya, "Sun ƙi faɗa shi yasa muka zo ko zaka faɗa mana" "Ai ba zasu iya faɗa maku ba,domin sirrin su ne" "Dan Allah ka faɗa mana,menene wannan sirrin Yusuf" Cewar Abdulmajid cikin zakuwa, Girgiza kai yayi"Umm umm,domin ƙwaƙwalwan ku da zuciyar ku ba za su iya ɗauka ba,May be ma zuciyar dayanka yana iya bugawa,dan haka"Let the sleeping dogs lie"(abar kaza cikin gashin ta) "A'a Gara dai a fige ta" "Kun ga ni iyaye na ada talawaka ne,saboda iyayen ku ne muka samu rufin Asiri har muka samu muhalli na kuma samu abun yi,ƙila shi yasa suke ganin rashin dacewar na aure ƴar su,ni ma kuma bai dace na aure ƴar mai gida na ba,kun ga gara dai da kasance ayi Cut your coat according to your clothes(dai_dai ruwa dai_dai tsaki) ku samar mata wani kawai " "Wannan ba hujja bace Yusuf,kuma baka faɗa mana har yanzun ainahin dalilin ba"cewar Abdulmalik, Ajiyar zuciyar ya sauke,yana mikewa tsaye" Kun ga ku tashi" Duk kallon shi suke yi cikin rashin fahimta, "Ku tashi mana" Mikewa tsaye suka yi suna jira su ji me zai ce, "Wannan ya zamo karo na karshe da zaku ƙara takowa gidan mu da sunan yi min maganar wata mace,bana ra'ayin ta,bana ra'ayin ƙanwar ku,bana sonta a takaice,ina fatan kun fahimta,dan haka ku zo ku fita" Ya fada yana nu a masu hanya, Cikin tsananin jin zafin wulaƙancin da ya masu Abdulmajid ya shako wuyan rigar shi "kai har kayi kyau da arzikin da zaka ce baka son kanwar mu,in banda rigima da rashin sanin ciyon kai irin na Salma me zata yi da jaki mara hankali wanda bai san abun arziki ba irin ka,ko an faɗa maka muma muna son ka ne,ko kuma muna son ƙanwar mu ta aure mutum irin ka,daga yau idan ka ƙara ganin mu a ƙofar gidan ku duk abinda kaka dama ka mana,Stupid"ya faɗa yana ture shi gefe, Bayan Abdulrahman ya samu nasaran cire hannun shi a wuyan Yusuf din wanda yake ta faman shafa makoshi da tari dan ba karamin shaka yayi mai ba,dama ya sani ko lokacin da yake zuwa gidan su duk cikin su babu wanda ya kai Abdulmajid zuciya, Ko kallon su bai yi ba ya juya fuuu ya fita a gidan,dama wannan karon da mota suka zo dan haka buɗe gidan baya yayi ya shiga ya zauna yana hadiyar zuciya,dan babu abinda yafi bashi haushi irin yanda ya fito a gaban fuskar su yace baya son Salma,wannan abun ya ƙona mashi rai, Ko suka iso suka shiga mota ba wanda yace ma ɗan uwan shi komai har suka isa gida, Ya rigasu sauka a motar dan haka gani suka yi kai tsaye ya shige cikin gida, Da sauri,suma bin shi suka yi,sai dai kafin su isa garya shige dakin Salma ya turo ƙofa, Dole sai komawa falo suka yi suka zauna suna zaman jiran fitowar shi, A zaune ya same ta tana danne_danne a waya, Tsayawa yayi a kanta yana huci, Dago kai tayi tana kallon shi,sai dai bata ce mashi komai ba, "We need to talk" "What happen" "Ba zaki aure wannan yaron ba" "Wa kenan? " Wanda kike so" Yusuf " "Koma waye ba zaki aure shi ba,yanzun kam ina bayan su da Baba" "Yaya" Ta kira sunan shi tana mamakin me ya faru daya hassalashi haka, "Ido na fa ya kalla yace min baya son kanwata,wani irin cin fuska ne yafi haka,idan har kina ganin girman mu da darajan mu a matsayin mu na yannin ki yi ki fitar harkar yaron nan,in aure kike so akwai mazajen da suka fi shi komai wallahi zamu tsaya miki har sai kin aure shi,na maki aikawari" Kallon shi take ido cikin ido"me zai hana kamin wannan alƙawarin wurin ganin na aure wanda nake so?Yaya ba wai ina son Yusuf bane dan in canja ra'ayi a kanshi a ko wani lokaci,A'a kawai ina son shi ne domin na aure shi,kayi haƙuri kome zaka ce ba zan canja ra'ayi ba" "Hakan na nufin kin zaɓe ki bijire mana akan shi?kin zaɓe shi kenan a kan mu? Ya faɗa yana kallon ta, Lumshe ido tayi ta buɗe tana kokarin yin magana ya katse ta" Tunda haka kike zaɓar ma rayuwar ki shikenan,mu dai ba zamu maki mugun fata ba saboda ke kanwarmu ne,amma ki sani ko me ya biyo baya a tsakanin ki da shi karki nufo mu"yana gama faɗan haka ya juya ya bar ɗakin, Tabe baki tayi tana faɗin "what ever" *Ban sani ba ashe hakan da nayi tamkar na caka ma ciki na wuƙa ne* . 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *60* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Tun daga wannan lokacin kowa na gidan ya fitar harkarta,babu mai shiga lamarin ta,kuma hakan ba wai ya dameta bane,abinda zai ba mutum mamaki shine duk wannan haukar da take yi bata taɓa tunkarar Yusuf din da maganar soyayya ba, Tun abun baya damunta tana ganin kamar na dan lokaci ne har abun ya fara damunta,domin tunda take a rayuwar ta bata yini daya ba batare da tayi magana da yannin taba,gashi yanzun idan har suna cin abinci ta fito to kowa tashi yake ya bar mata wuri,haka kuma idan har suna zaune suna hira ta shigo to duk nan take zasu haɗe fuska babu mai ƙara magana kuma har sai ta gaji da zama ta tashi,ko kuma su sudinga tashi dai daya, Wannan abun da suke mata ba karmin ciyo yake mata ba,dan haka a kwana na uku sai taki fitowa karin safe,har suka kammala bata fitowa,Lokaci-lokaci suna kallon ƙofar ɗakin ta,sai dai ba wanda yace komai har suka kammala suka tashi, Da lokaci girkin rana yayi Mama ta fito ta shiga kicin,kallon kulolin abincin tayi,kiran mai masu wanke-wanke tayi ta nuna mata kayan"me yasa ba'a wanke waɗannan kayan ba,tun na karin safe bayan kin San ban son ajiye kayan wanke-wanke? Dukar da kai matar tayi cikin girmamawa"Ummu Salma ce bata fito taci abinci safe ba,shi yasa na bar shi ko zata fito " "Ta zo ta ci? Ta kuma tambaya, Girgiza kai tayi" A'a bata fito ba" Ɗan shiru tayi kafin ta kuma kallon ta"amma kin je kin mata magana kuwa? "Eh naje na mata magana amma sai cewa tayi na fita ba zata ci ba" Tabe baki tayi"cikin ta,idan yunwa ya dame ta ai ta fito"har ta juya sai kuma da sauri ta kara juyowa "amma dai lafiyar ta glau ko da kika shiga? " Eh lafiyar ta kalau domin tana zaune ne a falo tana danna waya" "Ki dafa shinkafa fari da wake da miya,amma a miyar kar a saka Nama,a dafa kwai sai a ɗaura a sama" "To Hajiya an gama" Matar ta faɗa cikin girmamawa, Hakan ne kuma ya kuma faruwa lokacin cin abincin rana,nan ma bata fito ba har suka kammala,kuma ko in da suke zama a falo suna kallo ta zo ta same su nan ma har suka gaji da zama suka fita basu ganta ba, A lokacin cin abincin dare ne suna zaune har da Baba,Abdulrahman ya kasa daurewa,kallon Mama tayi"Mama wai Salma na gidan nan kuwa? "Tana nan me ka gani? " Naga duk yau ban ganta bane tun safe har wurin cin abinci " "Kila bata jin cin abincin ne shi yasa ka ga bata fito ba" "Amma daxu fa da rana na tambaye masu aiki suka shaida min bata ci abincin safe ba dana rana,kuma gashi na dare ma bata fito ba,kin San Salma tana da Ulcer " Cewar Abdulmajid, Ba tare da Baba yace masu komai ba ya mike ya doshi dakin Salma,duk da kallo suka bishi,bayan kamar mintuna uku sai gashi ta fito cikin tashin hankali dauke da ita hannu kamar gawa tana jijjiga ta tare da kiran sunan ta,sai dai ina ko motsi bata yi sannan gashi duk jikinta amai ne, Suma zabura suka yi suka bi bayan shi,amma ko kula su bai yi ba dan kafin ma su ƙarasa in da yake har ya saka ta a mota taja motar sun fita gidan, Cikin tashin hankali Mama tace"Abdulrahman dauko min makullin mota yanzun nan" "Mama yana hannun direba" Cikin ihu tace"na mota na nace ka ɗauko min" Ganin kamar shima a ruɗe yake yasa da gudu Abdulmalik yaje dakin ta ya dauko mata makullin, Ita ta tuka su har Asibitin da suke zuwa ganin likita, Koda ta isa ana ƙoƙarin Daura mata ruwa shi kuma Baba na tsaye ko kallon su bai yi ba, Kokarin karasawa in da take suke ya dakatar dasu"ku dakata" Duk tsayawa suka yi suna mashi kallon mamaki, "Ina zaku je?wa zaku je dubawa? Kasa bashi amsa suka yi, " A lokacin da kuka tabbatar da bata ci abincin safe ba amatsakin na uwarta me ya kamata kiyi?sannan da kika ga bata fito ko da falo ba shima me ya kamata kiyi,har iyau bata fito cin abincin dare ba shima me ya kamata kiyi,?duk babu abinda kika yi saboda ba ita bace a gaban ki ko? Hawaye ta fara,cikin sanyin jiki take kokarin yin magana ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu"ba kida wani uzurin da zaki fada min" "Baba" Cewar Abdulmajid, "Karka kira suna na,a da ina ɗauka ko bayan rai na zaku iya kula da kanwar ku ashe na yi kuskure,na yi kuskure ina ɗauka kuna mata ƙauna fiye da kanku,ban sani ba sai yanzun,amma ba komai kun ma kanku,domin tun da abin ya zama haka Gara kawai na aura mata Yusuf na mallaka masa wani kaso daga cikin dukiya ta tayanda zai iya kula min da ita ko bayan rai na" Wani irin ihu Mama ta saka tana cakumo wuyar rigar shi,Inna'lillahi wainna'ilaihirajiun,domin abune da tunda suke tare da iyayen su basu taɓa ganin makamancin haka ya faru ba a gidan su,duk gaba ɗaya cikin tsoro suka ja baya, "Wallahi ba ka isa ba,ba dai Yusuf ba,wannan ba zan yarda ba,so kake ka cuce rayuwar ta kamar yanda ka cuci nawa rayuwar! So kake ta kare wurin aikata aikin da zata din ga danasani!a da nayi tunanin ba zaka taɓa yarda ba tunda kasan komai,ba zaka taɓa bari ba,amma shine da kanka kake faɗin haka?ban taba sanin baka kaunata da zuri'a taba sai yau,kuma Salma yata ce Ni na haifa abuna dan haka ko da zata mutu ba zata taɓa auren wannan yaron ba" "To ai kuwa zan ga uban da ya isa yasa a fasa,dan haka ki ma je gidan ku na sake ki saki daya" Babu alamar tsoro ko dana sani sai ma ƙoƙarin ƙara shaƙe mai wuya da take yi"ba saki daya ba,Allah yasa kamin saki goma ba zan taɓa yarda da wannan auren ba" "Tunda haƙa kika ce to na.... " Cikin sauri Abdulrahman ya kulle mai baki yana fashewa da kuka tare da girgiza kai"dan Allah! Dan Allah Baba ya isa haka ba sai ka ƙara cewa komai ba" "So kuke mu tsane ƴar uwar mu,wannan abun da kuke yi duk saboda auren wannan Yusuf din ne,abinda ba mu taɓa ganin kun yi ba sai gashi yau kun yi shi kuma a gaban jama'a,tir da wannan auren daga ita har shi Fuck them" Cewar Abdulmajid yana barin Asibitin domin dama shi zuciyar tsiya ne dashi, Zame hannun tayi daga jikin shi tana kallon shi a karo na farko wanda sai lokacin hawaye ya sauko a idanun ta"kaji daɗi!yanzun ai kaji daɗi "tana gama fadar haka ta juya ta bar Asibitin tana tafiya tana sharan hawaye ba tare da ta damu da kallon ta da mutane ke yi ba. Dogon tsaki yaja ba tare daya kalle su ba ya shige dakin da take kwance, Jawo kujera yayi ya zauna yana shafa kanta,barci take yi tana sauke numfashin wahala,a zahiri ya furta "Allah kadai yasan iya wahalar da kika sha,in dai Yusuf ne sai dai tayi duk abinda zata yi amma sai kin aure shi,idan ya so sai... Shiru yayi yana busar da iska ba tare da ya karasa faɗar abinda ke bakin shi ba, A haka ya zauna da ita har sai da ta farka bayan barcin awa uku da tasha. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *61* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* A hankali ta fara buɗe idanun ta da suke mata nauyi,ganin yanda yake zaune yana ɗan gyan-gyadi ne yasa ta kira sunan shi a hankali "Baba" Buɗe ido yayi da sauri yana gyara zaman shi tare da ƙara riƙe hannun ta"sannu Salma,kin tashi?ya jikin naki?meke maki ciyo yanzun? Dafe gefen kanta tayi tana ɗan lumshe ido "Baba kai na,kaina na ciyo" "To bari na kira Doctor ina zuwa" Da sauri ya sake hannun ta ya fita,ba jimawa sai gashi ya shigo tare da wani Doctor dake bin shi a baya, Dubata likitan yayi sannan ya dawo da kallon shi kan Baba"babu wani damuwa nan da lokaci kaɗan ciyon kan zai sauka,sannan zuwa anjima zaku iya komawa gida,sai dai a dai na bari tana zama da yunwa,sannan ta rage cin soyayyen abu" "Insha Allah za'a kiyaye likita" Ganin likitan ya wuce ne yasa ta kalle shi"Baba ina su Mama da Yaya? Komawa yayi ya zauna"ki kyale su,yanzun ba su ba ne a gaban mu,ki fara samun sauƙi shine abu mai muhimmanci,sannan ba dai kina son Yusuf ba? Jinjina kai tayi, "To karki damu zan aura maki shi cikin satin nan matuƙar zaki iya haƙuri dashi" Bata masan sanda ta saki laulausar murmushi ba"zan iya Baba,you are the best father in the world" Murmushi shima ya mai da mata,yana raya abubuwa da yawa a ran shi game da wannan lamarin, Shi ya zauna da ita har drip din da aka saka mata ya kare aka cere sannan aka sallame su, Ko da suka koma gida bata tarad da kowa ba kuma bata damu ba,saboda ta san yanzun ba harkar ta suke shiga ba,kila ma sun kwanta ko,tunda a lokacin ƙarfe goma sha ɗaya na dare, Sai da tayi wanka da ruwan dumi sannan ta kwanta kan gado tana sauke numfashi yayin da take jin wani irin farin ciki yana ratsa zuciyar ta, Lumshe ido tayi tana tunanin irin rayuwar da zasu gudanar tsakanin ita da Yusuf, Zuwa can kuma wani tunani ne ya fado ranta,shine me yasa take son Yusuf,ƙara lunkumewa tayi a cikin makeken gadon ta yayin da ta shiga tuno abubuwa masu yawa a kanshi,wanda idan da ace za ta zauna ta natsu tayi nazari data fahimce irin haukar data ke yi,sai sam ko kaɗan bata gani ba sai ma ƙara son kasancewa dashi da take ji yana ƙaruwa a zuciyar ta, Da ire-iren waɗannan tunanin barci ya dauke ta. Washegari da safe sai da ta makara wurin yin sallah Asuba, Tana zaune saman darduma tana karatun Kur'ani sai ga Abdulrahman ya shigo dakin da sallah, Ganin tana karatu ne yasa ya nime gefen ta ya zauna yana jira ta idar, Addu'a tayi suka shafa tare, Juyowa tayi in da yake zaune"barka da safiya Ya Abdul " Duk da fuskar shi ya bayyana damuwar dake cikin zuciyar shi hakan bai hana shi ɗan sakar mata murmushi ba" Ya jikin naki? "Naji sauki sosai" "Allah ya ƙara maki lafiya" Da Amin ta amsa, "Kiyi haƙuri bamusan rashin lafiya kike yi ba,mun ɗauka kawai baki son cin abincin ne shi yasa ba mu je mun duba ki ba,ina fata zaki yafe ma yannin ki" "Yaya har yanzun fa Mama bata zo ta duba ni ba,haka ma su Yaya,ta yaya zanji daɗi,a can Asibiti ina tunanin idan na farka zan ganku tare da ni,amma banga ko mutum ɗaya daga cikin ku ba,ban ji daɗi ba,ko dai kun tsane ni ne,kun dai na sona akan kawai na nuna zaɓi na" "Ba haka bane Salma,kiyi haƙuri ke ma kinsa ko me kika mana ba za mu taɓa tsanar ki ba,kuma koda Baba ya kaiki Asibiti mun je,mun biku har da Mama,sai dai fushin da yayi ne yasa ya hana mu shiga mu ganki,shi yasa muka dawo gida" "To amma Mama fa,kalli fa har gari ya fara haske amma ko lekowa bata yi ba" "Ai bata kwana a gida ba" " Oh tafiya tayi ta bar ni? Tana fada idanun ta na kawo ruwa, "Ba tafiya ta yi ba,a jiya ne aka kira ta akan jikin Maman ta ya motsa,shine ta tafi ta duba ta" Ya faɗa mata haka ne kawai domin ba zai iya ce mata saboda ita iyayen su suka sami matsala ba, "Su yaya Abdulmajid fa? " Zuwa anjima duk zaki gansu,sannan yanzun ki samu ki kwanta ki huta zuwa anjima sai mu tafi ki buda Mama" Jinjina kai tayi"to yaya" Daganan sallama ya mata ya fita. Sai zuwa ƙarfe goma ta tashi,sai dai har yanzun basu shigo ba,amma ga kulolin abinci nan a jere an ajiye mata, Kaɗan ta iya ci kafin ta fito daga ɗakin, Kallon ƙofar Mama tayi dake a buɗe,kamar ta shiga kamar kar ta shiga,tayi kewar su,tana son ganin su, A hankali take takawa har ta isa bakin ƙofar sannan ta ɗaga labule ta shiga, Dakin ba kowa a ciki gashi a gyare,kofar banɗaki ta buɗe shima a bushe yake alamun ba'a yi amfani dashi ba, To ina Mama ta je ne,ko dai tana falo ne ko kocin, Fitowa tayi ta nufi kicin,sai dai bata ciki sai ma'aikata, Kallon daya daga ciki tayi"Mama Ladidi ina Mama na? "Wallahi tunda safe dana zo ban ganta ba,ni ma na duba dakin ta dan na gaishe ta sai dai bata ciki" Ba tare data ce mata komai ba ta nufi dakin Baba,sai da tayi sallamah ya bata damar shigowa sannan ta shiga, Zama tayi a gefe shi yana turo baki, "Me ya faru" Ya tambaye ta, "Baba ina Mama taje ne tunda safe haka? " Tana gidan su" "Gidan su ta maimaita" "Ummm" "Ko dai kaka ce ba tada lafiya" "Kila" Ya bata amsa a takaice, Mikewa tayi"bari na bita na duba jikin kaka " Bai bata amsa ba sai ma cewa da yayi"ki dawo da wuri " "To Baba" Daganan fita tayi ta koma daki ta shirya kafin ta saka direba ya kai ta gidan kakannin ta dake Bosso, Gidan su da gidan sarki bai da nisa daka wuce Bosso clinic sai gidan, A ƙofar gidan ta haɗu da Yaya Abdulmajid zai fito, Kallon ta yayi yana tsayawa"Ya jikin naki? Ya tambaya fuskar shi babu walwala, "Na ji sauki" Ta faɗa tana raɓawa ta gefen shi ta wuce,dan haushin shi take ji, Da sallamah ta shiga cikin gidan duk suna zaune a dakin Kaka,daga dukkan alamu hira suke yi,dan har da kanwar Mama Aunty Hulaira, "A'a lale da zuwan babbar mace" Turo baki tayi tana zuwa kai tsaye wurin Aunty Hulaira ta zauna a jikin ta"ina kwana Mama Hulaira " Dariya tayi tana shafa kanta"lafiya qlau Ummu Salma,ya karatu? "Yau naga iya shege,yanzun ke ko Uwar ki ta isa ta shigo nan ba tare data gaida ni ba balle ke Salamatu"cewar Kaka, Gwalo tai mata tana makale kafaɗa" Ba dai zan gaishe ki ba tunda ba wurin ki na zo ba,ina Mama ta? Cikin jin haushi tace"gata nan na makala a wuya " Dariya Aunty Hulaira ke masu"ku dai duk in da kuka haɗu baku gajiya da faɗa " Cikin shakwaba tace"Aunty Hulaira ina Mama? "Ta je Unguwar Biri tun dazu gidan Aunty Hadiza,na san ba zata jima ba zata dawo tunda ta jima da zuwa" Kallon kaka tayi"wai me yasa ake kiran unguwar da unguwar Biri,ko dai Birai ne a unguwar? "Ki bari idan Uwarki ta dawo sai ki tambaye ta" "Aunty Hulaira,kin ga kaka tana zagi na ko? " Dan mai garinku ba sai ta rama maki ba" "Da zaran Mama ta dawo wucewa zamu yi,dama so kike ki ba mutane wahala shi yasa kawai kika kwanta wai ba kida lafiya" "Ta yaya zata koma babu inda zata je har sai mahaifinki mai taurin kai ya janye maganar auren ki" Buɗe baki tayi cikin mamaki tace"ba dai yaji Mama tayi ba? "Ai wannan yafi yaji tunda tun a asibiti ya dirka mata saki daya dan ta faɗi gaskiya" Dafe kirji tayi"saki!shi Baban nawa ne ya saki Mama? "Oh!to ai sai kiyi,jiya kin ganta a gida ne? Girgiza kai tayi, " To dama jira nake ki zo naji dalilin da saboda wani banzan soyayya naki zaki raba auren iyayen ki da aka gina shekara ishirin " Jikinta ne yayi sanyi sosai,domin bata taba tsammanin lamarin ya kai har haka ba. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *62* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Share hawayen dake bin idanun ta tayi"ban taba tsammanin lamarin zai kai haka ba tsakanin Baba da Mama,ni son tsakani da Allah na ke ma Yusuf kaka,ba wai soyayyar sha'awa bace ko ta wani abu,Allah ne ya Daura min,gashi ta sanadi na auren iyaye na yana ƙoƙarin rabuwa,idan har haka ya faru ba zan taɓa yafe ma kaina ba" Ganin yanda take kuka ne yasa Aunty Hulaira ta jawota jikinta"ya isa haka ba laifin ki bane,haka Allah ya tsara kuma duk abinda Allah zai tsara mana zai same mu ba mu isa mu kauce masa ba,so wannan ma mu ɗauke shi a matsayin haka"ta faɗa tana share mata hawaye, "Shi yasa na ga su yaya suna jin haushi na" "Yo ba dole su ji haushin ki ba sun ga kina ƙoƙarin sakawa a saki Uwar su" "Kaka dan Allah ki kyale yarinya ta huta kin ga ba lafiya ne da ita ba," Tabe baki tayi"ku dai kuka sani, Wai ni kan Salamatu in tambaye ki? Bata bata amsa ba sai ido data Daura mata wanda hakan ke nuna tana jinta, "Shi wannan yaron da kika nace ma anya ba Asiri ya maki ba" Aunty Hulaira ce tace "Asiri kuma Kaka? " To ki duba ki ga,in ba aikin asiri ba ta yaya za'a yi ace yarinya ta bijirema kowa,bata jin shawaran kowa saboda shi,ki duba ki ga fa har auren uwarta take kokarin kashewa amma baki ji tace ta fasa ba,ko kin fasa? Ta faɗa tana tambayar ta Ita fa wannan tsohuwar mugun surunta ke sakawa bata son zuwa gidan,cikin jin haushi tace"ba Asiriba kome zaki ce ina son Yusuf kuma ba zan fasa ba,sai dai zan roki Baba Mama ta dawo" "Wai shi din ma ɗan gidan uban waye ne? Aunty Hulaira ce tace" A jiya dai Aunty Fatima ta ce min yaron aikin Baban ta ne,shi ya samar mai komai har ta gidan da suke ciki,to yanzun haka a jiya yace zai ɗibar mai kaso mai yawa a cikin dukiyar shi wanda zai dinga kula da ita Salmar" Abin mamaki,sai gashi nan take kuwa tsohuwa ta shiga washe baki"ai to in haka ne kenen abun ma da sauƙi tunda ba cikin talauci da kunci zaku zauna ba,tunda mahaifin naki ya ji ya gani zai iya, to in banda ma abin Fatima me na tayar da hankali har haka,bari to zo ai kuwa yanzun zata tattara ta bar min gida" Sallamah suka ji sannan lokaci ɗaya tana tambayar"wa zai bar gida? "Ke mana,domin ni yanda kika min bayani ina daukar yaron matsiyaci ne ashe ubanta yace zai masu komai" Ita ba ta san sai yaushe bane idanun Kaka zasu dawo dai-dai akan kuɗi,gabaɗaya rayuwar ta idan kana son faranta mata to ka dauko harkar Arziki,duk har da saboda wannan shegen son kudin nata ta jefa ta cikin wannan yanayin da take ciki, Mai da kallon ta kan Salma tayi"bi yo ni" Tashi tayi tabi bayan ta zuwa ɗakin kaka data shiga. Tana zaune kan gado,nuna mata kusa da ita tayi alamun ta zauna a wurin, Zama tayi tana kallon fuskar mahaifiyar nata wanda a ɗan tsakanin kwana biyun nan ta rame sosai,sai dai ita bata lura ba sai yanzun, "Ummu Salma" Ta kira sunan ta, Kanta a duke ta amsa da "na'am" Domin kunyar haɗa ido take da ita,saboda gashi saboda ita auren ta na ƙoƙarin mutuwa, "Dado kanki ki kalle ni" Girgiza kai tayi hawaye na kara sauko mata"Mama dan Allah ki yi hakuri,ban San abinda ya faru tsakanin da Baba kenen ba saboda ni" "Koma me ya faru dani wannan ba damuwarki bane,tsanina dashi ne,ni tambaya nake son na maki wanda zai kasance tambaya ce ta ƙarshe tsakanina dake a kan Yusuf" Dagowa tayi tana kallon mahaifiyar nata, Jinjina mata kai tayi"Ummu Salma"ta kira sunan ta a natse Sai dai bata iya amsawa ba saboda yanda zuciyarta ke bugawa dan bata San wani irin tambaya mahaifiyar nata zata mata ba, "A yau kina da damar da zaki sauya Kaddaranki,ki sauya rayuwar ki gabaɗaya,idan har zaki jure ma zuciyar ki kibar zabin ranki,ki dauki dayan ɓangaren," Ta faɗa tana kallon ta, Ganin har ƴan mintuna sun shuɗe ne yasa tace"kina ji a ranki kin zabi Yusuf kenan? Nan ma shiru tayi, "Ki faɗa min abinda ke ranki Salma ba zan maki dole ba,kuma na maki alkawarin duk hukuncin da kika yanke a wannan lokacin to na karɓa" "Mama kiyi haƙuri har yanzun na kasa cire shi a raina" Nan take wani hawaye mai matuƙar zafi ta sauko daga cikin idanun nata,yayin da ta ji zuciyarta ya mata nauyi Kamar an daura dutse, Cikin sauri ta dafa hannun ta"Mama kuka kike yi dan na zaɓe Yusuf,Mama k..... Yatsa ta saka mata a baki alamun tayi shiru,tana girgiza mata kai,"Salma sai yau na tabbatar da Allah baka taɓa mashi wayau ko dubara,na yarda da hakan tunda gashi tsayin shekaru muna ta kokarin keɓe ku daga irin wannan amma sai gashi sai da Allah ya jarabcemu ta hanyar da bamu yi tsammani ba," "To Mama me yasa kike kuka? " Ba zaki taɓa gane me yasa nake kuka ba Salma sai nan da lokaci mai karasowa,domin kuwa lokacin yazo,karasowa kawai ya rage,lokacin zaki fahimci abinda nake maki gudu,lokacin zaki fahimci illar hanyar da kika zaɓa,yayin da babu hanyar juyawa baya,kuma babu Alkalamin da zai goge haka daga cikin rayuwar ki da ƙwaƙwalwar ki,abinda nake ma gudu kenan Salma,ranar da zaki kasa jurewa,ina matukar tsoron amsar da zan baki,shi yasa tun kina da sauran dama nake roƙon ki daki janye batun wannan yaron" Ganin irin yanda mahaifiyar nata ke hawaye wanda ke nuna asalin tsoron ta ne yasa ita ma nata hawayen kara yin yawa"Mama ki yi haƙuri " Shafa kanta tayi"Allah ya maki Albarka,ya baki haƙuri da juriya a duk halin da kika tsinci kanki" "Amin Mama" "Shi kenan tashi mu koma gida,dama nayi magana da Baban ku ko" "Da gaske zaki koma me Mama? Dan dakatawa tayi tana share fuskarta" Eh," Rungume mahaifiyar nata tayi tana dariyar farin ciki, Suna fitowa bata ko kalli in da kakar nata ke zaune ba ta saka kai zata fita,ji tayi tana faɗin "A sauka lafiya,Uwar soyayya" Dan juyowa tayi kaɗan tana dariya kafin ta ƙarasa fita daga gidan, Direban daya kawo ta shi ya mai da su gida, Tun daga lokacin basu kara tayar mata da zancen shi Yusuf ba,sai dai sun sake mata fuska sun koma tamkar babu abinda ya faru,Baba kawai ke sanar da ita cewar sun yi magana da iyayen Yusuf sati mai zuwa za'a daura auren su,washegari kuma zasu tafi London din tare, Ranar farin ciki kamar zai sheketa,ƴan uwanta sun tayata murnar samun muradin zuciyar ta,amma Mama ko kallon in da suke bata yi ba,kuma har ya kasance yau da ya rage saura kwana uku ɗaurin aure Mama bata ce mata komai ba dan gane da gyaran jikin amare da ake yi, Aunty Hulaira ce ma ta kira ta take ce mata ko an gama bata magungunan mata data karbo kuwa, Tace ita ba abinda aka bata,in ba maganin sanyi ba da Mama ta bata, Taga bacin rai sosai a fuskar kanwar Maman nata,dan haka bin bayanta tayi ta tsaya a ƙofa bata shiga ba ganin yanda ita Aunty Hulaira ta shiga dakin Mama a hassale, Tana ji take tambayar Mama"Aunty Fatima ina maganin dana siya ki ba Salma" "Wani magani? Ta tambaya, " Na kayan mata" "Oh yana nan" "Me kike nufi da yana nan,kin san irin kudin dana kashe domin hado waɗannan magungunan kuwa,sannan ace yarinya biki har saura kwana uku ba'a fara bata komai ba,haba sai kace wacce ba tada gata,ke in ba zaki bata ba Bani su nan na fara bata" Girgiza kai tayi"shi yasa tun farko na ce maki karki siya,amma baki karɓi shawarata ba,Salma ba zata sha wannan maganin ba" Katse ta tayi"zata sha mana domin abune da zai taimaka wurin ɗaga darajar mace" "Ba zaki gane me nake nufi bane Hulaira,Salma bata dace da shan maganin mata ba,domin idan har tasha ina mai tabbatar maki za'a samu babban matsala irin wanda bana fata,ko yanzun ya ta kare,da kanta fa take sanar da ni irin karfin sha'awar da take dashi,to ina ga tasha wani kayan mata," "To ai hakan abu mai kyau ne,kin ga su sabbin aure ne,sannan suma mazan yanzun ba haka suke zama ba,idan tasha sai kiga komai yazo masu yanda ya dace" Dafe goshinta tayi,domin ta tabbatar idan zata kwana yi masu bayani ba fahimtar ta zasu yi ba,"na maki alƙawarin idan aka kaita ɗakinta da sati biyu ba tare da an samu wani matsala ba to da kaina zan kai mata kayan matar har inda take,na maki alkawari amma dan Allah karki kuma cewa komai "ta faɗa da alamun roƙo, Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi" Shikenan ba damuwa na yarda dake,sai dai dan Allah Aunty Fatima ki cire komai a ranki dangane da wannan aure kawai ki masu fatan zaman lafiya,da samun ya'ya na gari" Maganar ta na karshe ne ya sata ɗan yin murmushin takaici "Ya'ya,Umm,to!Allah ya basu masu Albarka" "Yauwa ko kefa,Amin" Da hakan zancen ka kare suka dauko wani hira, Ita kuma juyawa tayi ta wuce tana tunanin dalilin da zai hana Mana bata maganin yanzun har sai nan da sati biyu wai kuma shima in ba matsala,Umm ta rike maganin ta domin ita kam tuni suka yi ciniki da wata mata a online mai sai da kayan mata yau kuma kayan zai iso tun daga Sokoto,in ita ba zata gyarata ba ai Gara ta gyara kanta. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *63* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Duk wannan haukar da take yi tun daga farko har zuwa yau da yake ɗaurin auren ta basu taɓa yin waya da Yusuf ba,komai Baba ke mata,dan haka ita abun be dameta ba, Ranar Sati da misalin karfe goma na safe aka ɗaura auren,wanda ya samu halarta manyan mutane daga wurare daban-daban,domin a garin Minna mahaifinta ba ɓoyayyen mutum bane, Kasancewa yanda auren yazo da kuma yanda yan uwan basu so yasa ba'a yi wani program ba,sai gagarumin Dinner da Baba ta shirya masu a Lebo Kutigi,da karfe takwas na dare, To fa shine suka haɗu a cikin motar da aka shigo ɗaukarta dashi da zasu tafi wurin Dinner, Tayi shiga na Alfarma,tayi kyau na ban mamaki,yanda kasan ba a kasar Nijeriya ba,kasancewar ta Fara tas,yayin da kayan dake jikinta na doguwar riga ya kasance ruwar toka mai haɗe da dan karamin hijabi,shima Kot ne a jikin shi ruwan toka, Tunda aka buɗe mata marfin mota ta shiga aka maida aka kulle,ta juyo tana fuskantar shi,domin bata San da wani irin fuska zai tarbe ta ba, Shima ita yake kallo kamar mai nazarin wani abu,kafin kuma lokaci guda ya sakar mata da murmushi,ya mika mata hannun shi alamun ta riƙe, Wani irin ɓoyayyen ajiyar zuciya ta sauke tana daura hannun ta a saman nashi, "Kin yi kyau sosai Beauty" Juya idanun ta tayi cikin tsananin farin ciki tace"na ɗauka ba zan samu irin wannan tarbar daga gareka ba" Sumbatar hannun ta yayi "nariga nama Mahaifinki Alkawarin zan kula dake na mai dake gimbiya a gida na" "Kana nufin Baba? " Eh Baban mu,Kin San yanzun ya zama namu har da ni" Dariya ta saki cikin jin daɗi, Da haka suka isa wurin Dinner aka gudanar da komai cikin kwanciyar hankali da wadata,aka kuma rabu cikin Arziki,yayin da suka yi sallamah da mutane da dama domin gobe da safe ƙarfe takwas jirginsu zai tashi zuwa London. Sai da ya ajiye ta a gida sannan shi kuma direba ya mai da shi gida, Har ta yi wanka ta kwanta dan lokacin ƙarfe sha-biyu na dare ake nima sai gashi ta ji an turo kifar dakin ta, Daga kai tayi ta kalle ta,ganin wacce ta shigo ne yasa ta mike zaune tana kiran sunan ta"Mama" Dan murmushin yake ta sakar mata tana zama kusa da ita, Kallon mahaifiyar nata tayi yanda idanun ta suka kumbura alamun ta ci kuka,to ko ita da take amarya ta lura ba tayi kuka ba kamar yanda Mama tayi, Shafa kanta tayi"ba kiyi barci ba? "Tanzun na fito wanka shi ne na kwanta" "How was the party? Murmushi ta saki" Komai ya tafi dai-dai " "That good" Dan shiru sukayi na dan lokaci,kafin ta katse shi tun da faɗin "gobe d safe zaku tafi" "Eh haka Baba yace" Ajiyar zuciya ta sauke a karo na ba adadi "Nasan ba lallai bane gobe na samu lokacin da zamu yi magana shi yasa na shigo yanzun dak da Nasan kin gaji" Girgiza kai tayi "is ok Mama ina ji" Lumshe ido tayi ta bude kafin ta fara da kiran sunan ta,"Ummu Salma" Kasa amsawa tayi sai zuba ma Mama ido da tayi "Ina son a ko wani lokaci ki dinga tunawa kina da Mahaifiya mai ƙaunar ki,da yanni maza masu son ki,kina da Ahali masu matukar kaunar ki,ko me zai faru dake ki dinga tunawa dasu kuma zasu tsaya maki a ko wani hali,idan har kina niman wanda zaki fadama damuwarki ni mahaifiyar ki ina nan,zan saurareki na kuma baki mafita," "Mama wani abun zai faru ne?ta tambaya cikin dan yanayi na tsoro, Rike hannayen ta tayi" Babu abinda zai faru,kawai dai ina faɗa maki ne saboda karki manta damu, Abu na gaba,shine mai muhimmanci,Salma banda bincikan mijiki,karki cika bincike akan lamuran shi,ki yi hakuri da duk abinda kika gani domin ke kika zaɓa,kuma dauriya da juriya da dauke kai ya zama dole a gare ki,a duk lokacin da kika ji zuciyar ki na rayo maki wasu abubuwa ki yi sauri ki kama kiran sunan Allah domin shi kaɗai ne zai taimake mu," Shiru kawai tayi tana sauraren wannan nasiha na Mama wanda kwata_kwata bata gane kanshi ba,bata gane in da ta dosa ba,ita a nata tunanin nasiha ya kamata ta mata akan yanda zata kula da tsafta da girki da kuma kyaran jiki ta yanda zata rinka dauke hankali mijinta,sai gashi tana mata Nasiha kamar wacce zata shiga rayuwar kunci, Ganin irin kallon da ƴar nata ke mata ne yasa ta kuma shafa kanta"na San yanzun baki gane mai nake nufi ba,amma a hankali zaki gane,ki kwanta ki huta sai da safe"ta faɗa tana sumbatar ta agoshi, "Ok Ma," Ta faɗa tana gyara kwanciyar ta yayin da Mama ta kashe mata wutar dakin ta fita. Washegari suna idar da sallar Asuba Baba ya haɗa su daku har da yannin ta ya masu nasiha akan su rike zumunci,su haɗa kan Ya'yan su,koda yana da rai ko beda rai, Kallon Salma yayi cikin zolaya yake faɗin "Gimbiya idan kin haihu wani suna zaki saka ma ɗan ki" Dariya tayi tana juya ido"Baba idan na haifi ɗa namiji zan saka masa sunan Muhammad,saboda sunan Manzon Allah,kuma suna yana tasiri sosai akan yaro " "Laa to ba zaki saka suna na ba" Da sauri Mama tace"A'a tunda har suna na tasiri akan yaro ai Gara dai Muhammad ɗin," "Mama to ai sunan Baba ma yana da kyau,tunda shima sunan ɗan Manzon Allah gare shi,Abdullahi" Girgiza kai tayi tana canja zancen"to idan mace ce fa"ta tambaye ta, "Umm,to zan saka mata Nana Habiba,ina son sunan sosai" "Sai na kira ta da BIBA" Dukan wasa takai masa"kai Yaya Abdulmajid me kuma Biba,ni Nana Habiba nace " "Kunga ni idan na yi aure sunan Mama da Baba zan saka ma yara na" "A'a,bamu bukatar haka,kawai ku saka masu wani sunan amma ba namu ba" Bata fuska yayi"Mama" Murmushi tayi"eh"kallon Baba tayi daya zuba mata ido,domin shi ya fahimci inda zancen ta ya dosa,sai dai su yaran ba zasu taɓa ganewaba,sai dai ko kaɗan bai ga laifin ta ba,ƙoƙari take a matsayinta na uwa taga ta inganta rayuwar ahalinta,"ko ba haka ba Baban su? Ta faɗa tana tsare shi da ido, Jinjina kai yayi"no need,kawai kome kuka haifa Allah ya albarkaci rayuwar su " Da Amin suka amsa, Daganan tashi sukayi domin su yi wanka su shirya su rakata filin jirgi, Zuwa ƙarfe bakwai da rabi suka baro gida gabaɗayan su,har da Mama da Baba,dasu Aunty Hulaira yan rakiya, A can suka sami Yusuf da ƴan uwan shi suna jiran isowar su, Gaisawa suka yi cikin mutunci sannan Yaya Abdulrahman ya amsa Tikitin su ya shiga gudanar masu da komai har zuwa lokacin da jirgin su zai tashi, A lokacin da zata wuce bata wani damu ba,sai lokacin data kalli idon yannin ta sannan ta fara hawaye,domin tasan zata yi kewar su,sai dai in sun kawo mata ziyara,amma ita da dawowa sai nan da shekara biyu idan ta kammala karatun ta, Komawa baya tayi ta rungume su daya bayan daya tana,a kan Abdulmajid ta tsaya tana rike da hannun shi"Yaya kayi haƙuri " Shima share hawayen shi yayi "we are all with you" Rungume shi ta kuma yi"na gode " Shafa kanta yayi"Allah ya albarkaci rayuwar auren ki" Da Amin ta amsa ta kara rungume Aunty Hulaira da Mama har ma da Baba,kafin su shiga inda Asalin zasu shiga jirgi yayinda Yusuf ke rike da hannun ta,*Ban sani ba sallamar da nayi dasu a wannan lokacin na haɗa ne gabaɗaya har da farin cikina na bar masu a nan,yayin da na fara taka matakalar jirgi haɗe da wani mataki na littafin ƙaddaran rayuwata,tun daga wannan lokacin da ba zan taɓa mantawa da shi ba komai ya fara juyawa,a ranar Lahadi ƙarfe takwas daidai,* Kujerana na kusa da nashi ne,dan haka hannun mu na cikin na juna domin shi wannan ne karo na farko daya taɓa shiga jirgi,ni kuma ba zan ma iya tuna adadin sau nawa na shiga ba, A haka har jirgin mu ya sauka a birnin London. Address din da Baba ya bani dashi nayi amfani na tare Taxi na faɗa masa ya kaimu,duk wannan abin yana riƙe da hannu na,saboda shi baisan gari ba,kuma zuwan shi na farko kenan wannan ƙasar, Har bakin tangamemen Apartment din mu aka sauke mu,wuri ne ba kaɗan ba,dan gidan zai tasarma hawa goma sha biyar,dan lambar dakin mu shine na dari da goma sha uku,muna hawa na tara ne, Dan Linta mukayi amfani zuwa sama,in da ƙofofi ne a jere wasu na kallon wasu,sai dai idan ka shiga cikin dakin zaka ɗauka wani duniya ne ka shiga,domin babu abinda babu,katon Falo da dakuna biyu wurin wanki da shanya,barandar shan iska,da kuma wurin girki,har da dan wani wuri da akayi domin hutawa,gaskiya dakin ya haɗu,komai akwai shi a cikin, ɗaki daya ta dauka sannan ta nuna mai nashi,"ga ɗakin nan,kayi wanka ka huta zan mana ordan abinci,zuwa gobe Monday zamu fara shiga School,domin mu karasa abinda za mu yi sai mu fara ɗaukar karatu" "To Allah ya kai mu" Ya faɗa, Juyawa tayi ta koma nata dakin data zaba,sai da tayi ordan abinci kafin ta shiga wanka,dan ɗakin akwai na'uran saka ɗumi adaki, Bayan wasu mintuna ne karrawar kofar ya shiga ƙara,ita ta fito ta buɗe ta amsa abincin ta bashi kuɗin shi sannan kulle kofar,a saman Dinner Table, ta koma daki domin ta shirya, Riga da ƙaramin wando ta saka iya cinya,a lokacin idan ka kalle ta ba zaka so ko da kyafta ido kayi ba,saboda yanda rayi matukar kyau yanda kasan wata Bebi, Kwankwasa mashi kofa tayi haɗe da yin sallamah ta shiga ba tare da ta jira ya amsa ba, A lokacin ya kammalawa saka gajeren wondo irin na maza wanda yake saukowa zuwa guiwa na shan iska,yana rike da Sinlet fari yana ƙoƙarin sakawa ta shigo, Da sauri ya manna rigar a kirjin shi ya rufewa tare da kauda kai,"ki je ina saka kaya idan na gama zan fito" Turo baki tayi tana ƙara matsowa inda yake"ai kai Mijina ne yanzun babu abinda zaka ɓoye min" Amsar karamar rigar dake hannun shi tayi tana warwarewa,taimaka mashi tayi ya saka rigunan duka,"ni ba zan ɓoye maka komai na jiki na ba domin yanzun da daba daya bane" Bai bata amsa ba sai ma cewa da yayi "mu je" Tare suka fito suna zaune,ita ta saka masu a plate daya ta kuma hana shi saka hannu sai ma diba da take yi tana bashi a baki,tun yana ɗan kau kauda kai har dai ya zage yana karba,sannan shima yana saka mata a baki tana ci, Sai dai abunda ya fara bata mamaki koda yake ta mai izini saboda ƙila lokacin shine na farko daya fara keɓancewa da mace,domin ko alamar burgewa ko jan hankali bata gani tare da shiba akan wannan shigar nata,ko a idanun shi bata gani ba. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *64* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Suna kammala cin abincin ta kwashe kayan ta kai kicin wanda zata saka ashara kuma ta saka, Ko da ta fito baya falon dan haka dakin shi ta leka,yana kwance kan gado daga dukkan alamu waya yake yi,dan haka ita ma fitowa tayi ta koma nata dakin ta kira wayar Mama domin shaida masu sun sauka lafiya, Bayan ta gama kiraye-kirayen wayarta ne ta kwanta daga nan barci ne mai matukar daɗi ya ɗauke ta,wanda ba ita ta tashi ba sai daf da magriba,cikin sauri ta ƙara yin wanka da ruwan zafi dan jikinta ya sake sannan ta jero sallolin da ake binta,a haka ta zauna har lokacin sallah Isha'i yati sannan tayi, Jin karar TV tun Dazu ne yasa ta fito falon, Yana zaune yana kallon Boll a wani tashar, Zama tayi kusa dashi tana daura kanta a samar kafadarshi,"partner yunwa nake ji" Zame kanta yayi daga jikin shi yana dan matsawa kaɗan "ki yi mana ordan abinci dan nima yunwa nake ji" Ƙara matso shi tayi tana riƙe hannun shi,"shine baka tayar da ni ba? "Naga kin ji daɗin barci ne shi yasa," "To bari na baka number su koda wani lokaci idan kana bukatar abinci sai ka nime su" Hannun shi ya cire cikin nata yana mika mata wayar shi dake gefen shi, Amsa tayi ta saka mai sannan tayi seving, Lura da tayi kamar baya son tana taɓa shi ne yasa ta kyale shi,koda suka kammala cin abinci daki ya koma,duk yanda taso tajashi da hira, Ita ma bata jima tana kallon ba ta kashe kayan kallon ta koma daki, Ta dauka idan ta shiga daki zai biyo ta su kwana tare kamar yanda taga sauran sababbin ma'aurata ke yi,sai dai shi ko kofar ɗakinta bata jin ya taɓa,gashi kuma maganin da taje ta dinga banka ma cikinta wanda ta siya a ɓoye ya fara mata aiki,dan da kyar ma ta iya barci, Washegari da safe tana idar da sallah dakin shi ta shiga,yana kwance saman gado yayi dai daya yana sharar baccin shi hankali kwance,ji take kamar ta fada kamshi ta rungume shi, Ajiyar zuciya kawai take saukewa, Jan bargon tayi tana kiran sunan shi a hankali, Da kyar ta samu ya tashi"tashi ka shirya kasan yau zamu shiga makaranta" Shi sam yama manta da wanin karatu,dan nashi bangaren kasuwanci zai karanta,amma duk makaranta daya ne sai dai kowa da Department din shi, Tashi zaune yayi yana yamutse fuska "ki je ki shirya ganinan fitowa" Fita tayi dakin tana jinjina nauyin barci irin nashi, Wanka tayi ta shirya cikin doguwar riga na jallabiya baki sai karamin mayafi data naɗe kanta da shi, Fitowa tayi riƙe da karamin jakka a hannun ta,dayan hannun kuma makullaine, Cira wasu daga cikin shi tayi ta mika mashi"ga makullin dakin ka,wannan kuma na gida ne sai ka riƙe ɗaya,nima na riƙe data saura kuma zamu ajiye saboda tsaro,ko mantuwa " "Ok" Kawai ya fada, "Idan mun fita sai mu tsaya ka ci abinci" Dagowa yayi ya kalle ta"ke fa " Wannan ne karo na farko tun zuwan su jiya daya mata tambayar dake nuna alamun an damu da mutum, Dan haka murmushi tayi"ni sai zuwa ƙarfe goma zan karya " "Ok to nima ba wai ina karya da wuri bane,ki bari idan zaki cin abinci sai ki kira ni" Jinjina kai tayi, Koda suka isa katafaren makarantar tare da mutumin ba Baba ya hada su shi ya taimaka masu sukayi komai,sannan aka tura dan sako ya kai kowannensu Department din shi har kuma ajinsu,sannan aka nuna masu dakin karatu na ɗaliban, Babu abun da yafi mata daɗi sai ganin cewar ƴan ajinsu basu da yawa basu wuce su goma sha ɗaya ba, Kujeran ta a kusa da na wata yarinya me suna Suba yake,ita ƴar ƙasar Rasha ne,balarabiya, Mika mata hannu tayi suka gaisa take fada mata sunan ta,da kuma garin su,ganin yanda tayi shiga kamar wata yar uwar su balarabiya,ta kuma yi mamakin jin cewar ita ƴar Nijeriya ce, Koda suka kammala darasi ƙarfe sha biyu na rana,kallon agogon hannun ta tayi"lokaci ya tafi,ni zan wuce sai mun haɗu gobe" Daga mata hannu tayi,"karki manta gobe ƙarfe biyu na rana muke da darasi" "Insha Allah" Ta faɗa tana cigaba da tafiya tare da ciro wayarta a cikin jakka,number shi ta shiga kira,sai dai sai da yayi kara kusan sau uku sannan aka ɗauka,"kana ina ne"shine tambayar data fara mashi, Dan shiru yayi kafin taku ta ji yace"ina wani wuri " "Acikin makaranta? Ta kuma tambayar shi, " A'a na bi wani aboki na ne zan karba abu a wurin shi,amma ba jimawa zan yi ba yanzun zan dawo,kin koma gida ne? "A'a yanzun muka gama lecture,dama na kira ne na tambayeka ko kun kammala sannan kaci abinci? " Eh karki damu na ci abinci,ki tsaya ki siya kici sai ki wuce gida," "Ok sai ka dawo" Kit ta ji an kashe wayar ba tare da ya bata amsa ba,gyaɗa kai tayi tana mamaki da yaushe yayi aboki daga fara zuwa makaranta yau har kuma zai bi shi gida,koda yake su maza ne sunada saurin sabo da juna, Da wannan tunanin tabar makaranta ta tsaya a wurin cin abinci ta ci sannan ta wuce gida. Wanka tayi ta sauya kaya sannan ta shiga gyaran gidan nasu,har ɗakin shi sai da ta kyara tayi moping sannan ta fito da kayan daya cire ta saka a abin wanke kaya ta shanya, Ko kafin ta kammala ƙarfe uku tayi,dama ta riga tayi sallah dan haka wanka tayi, Jin motsi a falo ne yasa ta fito daure da tawul, Kallon shi take yi yana daura wani leda daya shigo dashi a saman tebur, "Ka dawo" Ta faɗa tana karasa fitowa, Kallo daya ya mata ya ɗauke kai "eh na dawo,ga fruits na siyo,naga kina so" Murmushi tayi"Thank you"ta faɗa tana ƙoƙarin karasawa inda yake,sai dai kafin ta karaso har ya doshi dakin shi, Tura baki tayi tana jin wani iri a zuciyar ta,shi wai me yasa baya nuna ɗoki a kanta,baya nuna yana ra'ayin ta kamar sauran amare,sai ma gudunta da taga yanayi, Jin wayarta na ƙara ne yasa da sauri ta koma daki tana ɗaukar wayar, Ganin sunan Mama a rubuce ne yasa ta ɗauka da sallamah, Amsawa tayi cikin sakin fuska"Amarya ya kike" "Mama" Ta kira sunan ta a shagwabe,"ko dai na cemin amarya " "Me yasa zan daina ce maki amarya,tukun na ma ya naji kamar ranki a ɓace yake? " Ba komai kawai dai yanzun na dawo makaranta na gaji ne,kin San kuma bana shiri da yunwa,wallahi har na fara jin kewar gida " Dariya Mama ta saka"in banda abinki ba sai ku yi odar ba,ina shi mijin naki? "Ya shiga wanka dan tare muka dawo,yauwa gashi ya fito,bye Mama i Love you" Kit ta kashe wayar tana zama bakin gado,tama rasa wani irin tunani ya kamata tayi, Tashi tayi ta saka kaya ta fito ta shiga kicin,dan yau ita zata masu girkin dare tunda suna da komai a kicin, A haka suke wannan zaman har yau da suka cika kwanaki huɗu da zuwa garin,babu wani abu ɗaya canja a tsakan zaman takewar su,baya wani nuna damuwar shi a kanta ko abinda ya shafeta,idan ya dawo yana kunshe a daki yana kallo a wayar shi,ita bata masan Uwar me yake kallo ba,amma da zaran ya ganta ta shigo da sauri yake kife wayar,idan kuwa ka gansu tare to abinci suke ci, Ta gefe ɗaya kuma gashi maganin da ta sha sai nukurkusar ta yake yi,da kyar take iya samun barci da daddare, Kamar dai kyau tsabar nauyin da maranta keyi mata tasa ta zauna tana sharan hawaye,dumin duk wani hanya da zata bi domin karkato da hankalin shi kanta tayi amma abun baiyi aiki ba,idan yaga ma kamar zata matsa mashi sai ya shige ɗaki ya kulle ƙofa, Karan da wayarta ke yi ne yasa ta share hawaye tana jawo wayar,ganin sunan Mama ne yasa ta sai saita natsuwar ta tana ƙara wayar a kunne, "Barka da Dare Mama" "Barka dai Salma ya kike" Ji tayi wani hawayen ya sauko mata saboda jin yanda maran ke ƙara tsungulinta "ina lafiya Mama" Dan shiru tayi na wani lokaci kafin ta ce "ina mijin naki? " Yana daki " "Me ya same ki? Kara share hawayen ta tayi" Babu komai " "I expect more than this,dan haka faɗamin,zan iya taimaka maki da shawara,karki boyemin komai" Bata masan santa ta fashe da kuka ba,kun san yanda lamarin yake,tsakanin uwa da ɗa sai Allah, Dan haka sai da ta bari taci kuka ta dan kanta har zuciyar ta yayi sanyi kafin tace"fadamin yanzun meke faruwa" "Mama ki yi haƙuri,ana sauran kwana uku aure na naji maganar da kuka yi keda Aunty Hulaira akan kayan Mata,ki yi haƙuri bansan me kika gani ba,ban kuma san dalilin ki ba na kin bani nasha,amma shine na ɗauka ko dan baki son aure na da Yusuf ne shi yasa kika hanani,shine na haɗu da wata mata a online yar Sokoto na siya kayan mata a wurin ta,a washegari aka kawo min saboda na zuba mata kuɗi, Yanzun kuma gashi tunda muka zo babu abinda ya shiga tsakanin mu,Mama marana ciyo yake min kamar ya fashe"ta karasa faɗa tana saka sabon kuka. Ajiyar zuciya ta sauke "kina jina Salma" "Ummm" "Ina son ki natsu ki saurari abinda zan faɗa maki,a duk lokacin da kika ji kina bukatar mijinki karki saka kunya a lamarin,domin shi mijinki ne duk abinda kika mai ba abin kunya bane,ki je ki same shi ki faɗa mashi you need him,kina bukatarshi,karki ji kunya,ina nufin ko wani lokaci,domin irin su in kina zaune dasu ba zaki taɓa burge su ba," "Mama kenan ba zan taɓa birge Yusuf ba kome zan mai,ina ƙoƙari kullun in share gida in yi girki sannan in wanke masa kaya,amma kuma duk da haka ba zan taba burge shi ba? Bata son ta bata tsoro ko ta sare mata guiwa,amma maganar gaskiya shine abinda ta faɗa,ba zata taɓa burge shiba,"Sweet heart kina jina? "Umm". 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *65* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* "Daga yau karki kuma yin komai domin ki birge shi,ban yarda ki dinga yin wanki ba,ba laifi idan kin yi aikin gida kin gyara masa daki,amma banda wanki, Yanzun yana ina ne? " Yana dakin shi" "Tashi ki je ki same shi a dakin ki faɗa mashi kina bukatar shi" "Mama ta yaya a matsayina na mace zan fara kai kaina wurin mijina,shin kina ganin hakan ba zai zamar min abun magana ba? " In dai a wurin sune hakan ba komai bane,ki yarda dani hakan ne kawai mafita a gare ki,ba wai ina nufin daga yau shikenan ki rabu dashi ba dan kin samu abinda kike so,ki yi tunanin ai zai biyo ki,ba zai taba binki ba,tashi kawai ki tafi,da safe ki kirani "dif ta kashe wayar ba tare da ta jira ta ji me zata ce ba. A gaskiya tana buƙatar shi yanzun,idan har bata yi yanda Mama tace ba,to ba lallai bane ta iya kaiwa wayewar gari, Dan haka tashi tayi ta saka kayan barci marasa nauyi farare sannan ta doshi dakin shi, Allah yasa yau ƙofar a buɗe take,saboda yasan bata cika shigowa ɗakin da daddare ba, Yana kwance yau ma kamar ko wani lokaci yana kallon a waya,kanshi na saman filo ya daga wayar sama, Duk sallamar da tayi bai ji ba domin daga dukkan alamu yayi nisa wurin kallon abinda ke cikin wayar, Dan girgiza mashi kafa tayi tana kiran sunan shi, Cikin sauri ya kife wayar yana zabura, Wannan ne karo na farko da ta fara ganin bacin ranshi, cikin fushi da jin haushi yace"wannan wani irin rashin hankali ne da rashin tarbiyya,wani irin hauka ne zaki shigo min daki babu sallamah,"dafe goshinshi yayi "shi yasa auren yaran masu kuɗi matsala ne," Tsaki ya kuma ja Karo na farko da tsoron shi ya fara shiga zuciyar ta,bata son ihu,dan nan take hankalin ta ke tashi, A tsorace ta matsa baya tana kallon shi"na yi sallamah har sau uku baka ji ba" "Karya kike yi,ni kurma ne da zaki ce kin yi sallamah banji ba,karya kike yi" Ita yarinya ce sosai a lokacin,domin shekaranta goma sha biyar a lokacin,amma duk da haka tasan ciyon kanta,bata kaunar ace mata karya take yi,sai taga kamar an muzanta ta ne, Juyawa tayi kawai ta bar dakin tana fashewa da kuka,domin abun ya bata mata rai, Daki ta shiga ta turo ƙofar ta kashe wuta tana cigaba da kuka, Dafe kai yana tunanin kar taje kuma ta sanar da mahaifiyarta,dan yasan idan mahaifinta ne ba zasu samu matsala sosai ba, Kila akwai abinda take so, Dan haka fitowa yayi ya shiga ɗakinta,ganin wutar dakin a kashe yake yasa ya mika hannu ya kunna wutar, Karasa yayi in da take kwance kan gado ya rungumota jikin shi"i am Sorry Baby,ki yi hakuri ba zan sake maki ihu ba" "Ka fita kawai ni bana son ganin ka" "Ki yi hakuri kinji ai nace ba zan sake ba" Da wannan damar tayi amfani wurin baiyana masa manufarta ta hanyar haɗe bakin su wurin daya, To tana iya daurewa ta kira wannan daren da First Night din ta,amma ba wai dan ranta yaso ba,domin kwata_kwata bai wuce minti goma ba yayi releasing a jikin ta,kuma ya sauka ba tare da damuwar ta gamsu ko bata gamsu ba, Ita a yanda ma take daukar daren sai gashi ba haka yazo mata ba, Ganin ya saka kayan shi ya fita ne yasa dole ta tashi ta haɗa ruwan dumi ta shiga sannan tayi wanka, A maimakon ta ji zuciyarta yayi sanyi sai ji tayi wani abu ya tsaya mata a wuya,dan haka dunkulewa tayi a wuri ɗaya ta fara kuka ko zata ji sanyi a ranta. Washegari koda ta fito har ya riga ta fita,dan haka kyaran gida tayi sannan ta wuce makaranta, A hankali lokaci ke tafiya yayin da dare ke yi kafin ka sani gari ya waye, Wanda a haka suka wayi gari suna da shekara daya harda watanni biyar a wannan garin,domin kuwa har sun fara lissafin lokacin komar su gida, A cikin wannan lokacin ta fuskanci matsaloli masu tarin yawa na rayuwa, Domin kuwa zata iya rantsewa sau uku kaɗai Yusuf yayi mu'amalar aure da ita,shima kuma kamar bada son ranshi yake haka da ita ba,tayi mashi rokon duniya akan idan yanada matsala ne ya yarda suje suga likita,amma ya ki amincewa, Wani lokaci sai yayi kwana biyu zuwa uku baya kwana gida,a haka kuma bata isa tayi korafin ba,zai fara faɗa da tayar da jijiyoyin wuya, Sam bata jin daɗin rayuwarta,wanda da wannan damar ne ƙawarta Suba tayi amfani ta fara koya mata harkar shaye-shaye,tun daga shan Sigari har zuwa tauna Kwaya,in da Allah ya taimaka dai shine basu shan giya, Kuma har yau idan har ta kira Mama ta fada mata halin da take ciki sai dai ta ce taci gaba da addu'a, Ranar da suka kammala makarantar su aka basu takardun kammala karatu,in da ta samu kyautuka masu tari yawa kasancewar ta First Class, Ba zata taɓa mantawa da wannan ranar ba a rayuwar ta, Abinda ya faru kuwa a lokacin shine Yaya Abdulrahman baida lafiya sosai har yakai ga an saka masa bututun shaƙar numfashi,wannan dalilin ya hana daga gida babu wanda yazo mata, duk da ba daɗi sai dai bata ji haushin su, Abinda ya ɓata mata rai shine rashin halarta Yusuf wurin har aka gama ta dawo gida, Kiran number Mama tayi tana tambayar ta mai jiki, "Da sauƙi ta amsa mata" "Mama ki gaishe shi idan ya farka" "Zai ji" Dan shiru suka yi na sakanni,kafin tace "Mama,dan Allah ko zaki ma Yusuf magana da kanki ko zai yarda muga likita tunda cikin satin nan zamu dawo," "Salma ke ma kisan ban cika son shiga harkar mijin ki ba,ki bari idan kun dawo koma dai menene sai mu yi magana" "Dan Allah Mama,ni dai nafi son kawai ki mai magana mu ga likita anan" Numfashi ta sauke"to kai mashi wayar" Dariya ta saka"na gode Mama" Koda ta shiga dakin shi yana wanka,"Mama bari zan kira ki zuwa anjima domin yana wanka yanzun" Da to ta amsa tana kashe wayar, Ita kuma zama tyi anan bakin gado tana tunanin yanda zasu kare da Mama,Allah dai yasa ya amince,ai kuwa da ta ji daɗi, Hannunta ne taje ajiyewa shine ya sauka a kan wayar shi dake ajiye, Murmushi tayi tana juyo da fuskar wayar"shi kenan bai da aiki sai kallo a waya,ji yanda ya kife waya salon mutum ya zauna a sama sekrim ya fashe y.......... Sauran maganar nata ya makale ne sakamakon wani irin mugun gani da tayi a rayuwar ta wanda har yau yake mata gizo a kwakwalwarta,har a bada bata fatan tuna abinda ta gani a wannan wayar, Domin kuwa Video ne hannun ta ya danna ya shiga play, Fuskar Baba ne a bayyane yana tsaye haihuwar uwar shi tare da Yusuf da ke kwance yana mika mashi hannu alamun yazo gare shi, Yanda kasan mata da miji,sumbatar juna suke yi suna shafa jikin juna,yayin da lokacin daya Baba ya shiga aikata Madigo da Yusuf ta baya,suna masu kururuwan jin daɗi, Haka ma video na gaba,wanda sai da tayi playing uku duk su biyu ne a daki mabanbanta suna aikata Luwaɗi, Daga zaunen da take ne ta ji idanun ta na ƙoƙarin rufewa,jin alamun zai fito ne yasa da sauri ta ajiye wayar tana fita daga dakin a daddafe saboda duhun da take gani, Da kyar ta iya kai kanta ɗakin ta zauna a kasa ba tare da ma ta san cewar a kasar take ba, Tunda take a rayuwar ta bata tsammanin duka su biyu zasu iya aikata haka ba, Mijin aurenta da mahaifinta, Duk yanda taso ta ƙaryata kanta kasawa tayi,haka kuma duk yanda taso ta gasgata kanta nan ma kasawa tayi, Tsabar tashin hankalin da ta shiga ko kiran Mama bata iya ɗauka ba,a ranar tai ma kanta buking din jirgin Nijeriya wanda gobe zai tashi ƙarfe tara na safe, Ranar duk iya sata irin na barci kasa ɗaukarta yayi,domin idanunta kuwa kafin wayewar gari sun kumbura,haka kuma a lokacin da za'a auna jinin ta to zai iya kaiwa ɗari biyu, ji take zuciyarta ya mata wani irin nauyi har numfashinta bai iya fita da kyau, Sai dai bata damu ba, da halin da take ciki dan haka ko ta kanshi bata bi ba,ƙarfe takwas na safe ya mata ne a airport,ita bata ma kaunar ta ganshi domin hankalin ta tashi zai ƙara yi,nimar wanda zai karyata mata lamarin take yi,dan haka tana buƙatar Mama,tana son tayi magana da ita, dan baza taɓa iya ɓoye mata wannan lamarin mai girma ba. Ƙarfe tara jirginsu ya shilla a sararin samaniya. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *66* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Jirgin su na sauka,Adaidaita ta tare ya kawota har cikin unguwar su, A baki Get tace ya tsaya sannan ta ciro kuɗi ta bashi,ko tsayawa karɓar canji ba tayi ba ta buɗe Get ta shige, Megadi na ganinta ya taso cikin rawar jiki da murna zai tare ta,sai dai ko takanshi bata iya yi ba sai ma sake mashi aƙwati da tayi ta karasa cikin gida tana kwalla kiran sunan Mama, Daya daga cikin masu aikin gidan ne take sanar da ita ba kowa a gidan domin duk suna Asibiti wurin Abdulrahman, Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi da tana ƙoƙarin danne duk wani damuwa dake ranta,sai dai wannan lamarin ba irin wanda zata iya jurewa ba na,Oh shiyasa wato bai da ra'ayi akan mata ko, Dakin Mama ta shiga ta watsa ruwa sannan ta canja kaya,sai dai a kwana ɗayan nan kawai idan ka ga irin ramar da tayi zaka yi tunanin ko tayi shekara ne tana ciyo, Ta dauko mayafi tana ƙoƙarin fitowa ta tafi Asibitin sai ga Mama ta shigo, Tsayawa tayi baki buɗe tana mata kallon mamaki"ke ce kuwa da gaske" Nan take ta ji komai ya ƙara dawo mata saboda,raunin da take kokarin ɓoyewa ne ya baiyana, Da sauri Mama ta rungume ta tana shafa bayan ta "ina Yusuf din yake? " Na baro shi a can London" "Kika taho nan ke kaɗai?ko dai faɗa kuka yi ne? Girgiza kai tayi cikin tsananin kuka tace" Mama!na ga Baba da Yusuf a waya" Kasa karasawa tayi sai yanke jiki da tayi ta faɗi,dan nan take numfashin ta ya ɗauke, Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana,domin ihu Mama ta fara tana kira sunan ta,abinda ya kuma bata tsoro shine ganin jini na fita daga kasa ta, Kasancewar Mama mace mai jiki yasa ta dauke ta da kanta ta saka a mota,direba ne yaja suka tafi Asibiti,inda anan ne aka karbe ta aka shigar da ita dakin taimakon gaggawa, Sai bayan awa daya da rabi likita ya fito, Anan yake sanar da Mama cewar sai dai suyi haƙuri domin cikin dake jikinta dan sati takwas ya fita,sannan sun mata wankin ciki,yanzun haka tana dakin hutu suna iya zuwa su ganta, Kuka Mama ta fara tana riƙe hannun Baba wanda isowar shi kenan ya samu likita na wannan bayanin, Lallashinta ya fara yi "idan har kina kuka haka ita kuma me ya kama tayi kenan,ya isa haka zo mushiga mu duba ta" Tare suka shiga dakin da take kwance ita kaɗai,idanun ta a buɗe suke yayin da take kallon sama, Jin an buɗe ƙofa ne yasa ta maida kallon ta kan ƙofa,ganin shine yasa ta lumshe ido tana ƙoƙarin koran abinda ke zuwa mata a cikin ƙwaƙwalwa, Da sauri suka karasa inda take,rike hannun ta yayi"Salma kina lafiya?ya jikin naki?yanzun me yake maki ciyo? A hankali ta zame hannun ta a cikin nashi,"Mama ina Yusuf " Ajiyar zuciya ta sauke"karki zamu yana hanya,sun riga sunyi magana da Baban ku,ya shaida mashi kina nan" "Me likita yace" Ta tambaya yayin da maganarta ke fita a hankali, Kallon juna suka yi sai dai sun kasa faɗa mata,ba tare data ce masu komai ba ta juya baya yayin da take jin hawaye masu zafi na ƙara wanke mata fuska, Ganin haka ne yasa suka mike suka fita tare da jawo mata ƙofa dan ta samu ta huta, Ganin sun fita ne yasa ta fashe da kuka sosai ko zata ɗan ji sanyi,ita a rayuwar ta bata San wani irin so take ma Yusuf ba,wannan abun da ta gani koda ace na karya ne yaci ace ta tsane shi,amma ta kasa,sai ji ma da tayi tana son ganin shi,ita ta san wannan shine babban jarabawar ta soyayyar Yusuf, Ta jima tana kuka kafin barci mai nauyi ya ɗauke ta, Ƙarfe hudu na yamma aka sallame su suka dawo gida,dan Mama ce ta tsaya da ita sai Yaya Abdulmajid, Da taimakon Mama ta zauna a kan gado,tana ya mutse fuska,dan har yanzun tana jin murdawar ciki, Har Mama zata fita ta kira sunan ta,"Mama" Juyowa tayi, nuna mata kusa da ita tayi alamun ta zauna, Dawowa tayi ta zauna kusa da ita, "Mama,kinsan me na gani a wayar Yusuf? Girgiza mata kai tayi, " Video Baba na gani tare da Yusuf suna aikata barna,dukkanin su babu kaya ajikin su Mama,Luwaɗi suke aikatawa "share hawayen daya zubo mata tayi" Na kasa yarda,Baba ba zai taɓa aikata haka ba ko Mama?abu ne da Allah ya ya tsine ma masu yi,kuma duk mai yi Allah zai haɗa sa da mutanen Annabi Lut,aci gaba da azabtar dasu har ranar tashin kiyama,Mama saboda Luwaɗi Ubangiji kan iya juya kasa ya kife ta,Nasan Baba ba zai yi haka ba,balle da Mijina " Rungumeta tayi yayin da taji wani irin tashin hankali na karyo mata,abinda take mata gudu kenan a wancan lokacin amma ita bata fahimtaba, Dago fuskarta tayi suna fuskantar juna"kina jina ba? Jinjina kai tayi tana ƙoƙarin rike kukan dake ƙoƙarin kucce mata, "Kina son mijinki har yanzun? " Mama na kasa daina son Yusuf,duk da baya kyauta ma rayuwata na kasa tsanar shi,gani nake idan har babu shi ba zan iya rayuwa ba" "Bansan wani irin so kike mashi ba,in da ace zaki iya hakura dashi da sai nace ki hakura dashi Allah ya zaɓa maki wanda ya fi shi" Girgiza kai tayi"ba zan iya ba Mama" "Allah ya riga yayi ki mai ƙarfi sha'awa,shi kuma bashi da ra'ayi akan mace,zamanku akwai cutarwa mai tarin yawa Salma,sai dai hanya daya ce wacce za ku bi daga ke har shi ku zauna lafiya cikin kwanciyar hankali ba tare dakun rabu ba" Dago jajayen idanunta tayi tana kallon mahaifiyar nata"wani hanya ne Mama? "Zan faɗa maki,amma ki bari sai gaki gani ga kuma Yusuf" "To yaushe zai zo? " Ai na faɗa maki yana hanya na tabbatar zuwa anjima zaki ganshi,bari na hado maki shayi sai ki sha kafin a kammala abinci,ni zanje na duba yayan ki a asibiti" "Ki ce Ina gaida shi Mama,sannan yayi sauri ya ji sauki gobe Birthday dina" Murmushi tayi tana shafa kanta"baki manta ba" "Umm" A ranar ma koda Yusuf din ya iso da wuri bai zo ya duba ta ba duk da Baba ya faɗa mashi batun zubewar cikinta,sai ƙarfe tara na dare, Duk da bata jin daɗin jikinta a haka ta ƙara yin wanka ta dan shirya sannan ta fito falo in da yake zaune, Hmm jama'a kuɗi yayi,domin kuwa idan kasan Yusuf ada yanzun in ka ganshi ba lallai bane ka gane shi, Zama tayi kusa dashi,tana ƙoƙarin ɓoye damuwar dake fuskarta "barka da isowa" Ko kallon inda take be yi ba"Baban ki ya faɗa min abinda ya faru dake,Ashe ciki gare ki,to Allah ya kyauta,sai dai ki sani nayi farinciki zubewar shi domin ban tashi ajiye yara ba" "Yanzun duk wannan tafiyar da kayi dan ka faɗa min haka ne? Sallamar Mama ne ya kase shi daga amsar da zai bata, " Yusuf video dana gani a wayar ka kai da Baba na menene? Dagowa yayi ya kalle ta ta kuma kalli Mama da ta zauna"me abinda kika gani? Share hawayen da ya sauko mata tayi,"Mama ki fada mashi ya min ƙarin bayani " "Ai ba sai na maki karin bayani ba,itama tana iya maki tunda ta san komai" "Kunga yanzun ba wannan maganar ba,ke Salma ki bar dauko wannan maganar,domin ba na son na sake jin shi a bakin ki,ni da nake son na samar maki mafita ta yanda zaki zauna da mijin ki lafiya,dan Allah ki natsu ki ban hankalin ki" Shiru tayi kawai tana kallon Mama,domin ita ta ma rasa me suka maida ita, "Kuna jina,hanyar da naga zai fi maku shine mai zai hana ke Salma ki yarda da wani namiji,ina nufin a duk sanda buƙatar ki na ɗa namiji ya taso ki ni me wani namijin ya sauke maki,tunda shi mijin ki bai da sha'awa,ko ya ka gani Yusuf? Dariya ya fashe dashi sosai har da tafa hannu"kai lallai Mama ƙwaƙwalwar ki na ja,ni tuntuni da wannan shawarar kika ba mu ai da abin bai kai haka ba,gaskiya in dai ni ne wallahi ba matsala na amince da wannan shawarar " Ji tayi kamar bugun zuciyar ta zai fito tsabar yanda yake harbawa,ji take kamar bata fahimce in da zancen su ya dosa ba"Mama me kuke nufi,Zina fa kenan,so kuke ke da Yusuf nayi zina da auren shi a kai na,? "To me a cikin,ba gashi shi ya amince ba,ko kina da wata hanyar ne bayan wannan? " Inna'lillahiwainna'ilaihirajiun"abinda take ta maimaitawa kenan,domin ji take kamar kanta na juyawa, "Mama keda bakinki kuke cewa na aikata zina da aurena,?Yusuf da amincewar ka,?" Kara kallon su take da kyau dan so take ta tabbatar ko da gaske sune ɗin a gabanta, "Ke ba Mama ta ba ce,ba maman dana sani bace! Nayi dana sanin kasancewarki uwa a gare ni,Gara ace wasu matsiyata ne iyayena baku ba,na y...... Saukar lafiyayyen mari ta ji a saman fuskarta,, nuna kanta tayi cikin tsananin bacin rai"do you think is easy for me na fada maki haka? Ni fa mahaifiyarki ce,y...... Wani Envelop ya ciro a Aljihun shi ya wurga mata"idan har ba zaki bi wannan hanyar ba,banga anfani zaman mu ba,domin ba na son takura,gashinan takardar saki ne,na sake ki saki biyu" Daga zaunen da take ba ta san sanda ta zamo kasa ba,ta ma saka cewa komai,sai binsu da ido da take yi har ya juya ya bar dakin, Cikin jin haushi Mama tace"ai yanzun sai ki samar ma kanki mafita"ta juya ita ma ta bar dakin........ Hmmmm. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *67* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Ta ma kasa yin kuka,zuciyar ta nauyi ya mata,yayin da idanunta ke ganin dishi_dishi, Da kyar ta iya mikewa,da bin bango ta isa shiyan mazan gidan, Ganin falon su a buɗe ne yasa ta shiga,Abdulmajid ne zaune yana cin abinci, Ganin yanda ta shigo ne tasa ya Mike da sauri yana isa in da take "me ya faru,ke da bakida lafiya da sai ki kirani a waya, Mika mashi takardar hannun ta tayi,amsa yayi yana fadin" na menene? Ganin bata bashi amsa bane yasa ya buɗe yana karantawa,sai kuma ya saki murmushi"kai amma na ta yaki murna,at list yanzun zaki dawo hankalin ki,gaskiya naji daɗi " Hawayen da suka kasa fitowa ne suka sauko "Yaya,Yusuf yaci amana ta, y..... " Kinga dakata,ai kome ya maki ke kika ja,wani irin bayani ne ba mu maki ba a kanshi,karki manta na faɗa maki komai zai faru tsakanin ke da shi karma ki nufoni da batun dan haka ke ta shafa,ina fatan yanzun zaki yi hankali" Juyawa tayi inda take jin motsin Abdulmalik, Shima girgiza kai yayi"kinga je ki kwanta zamu yi magana da safe,dan ni yanzun ta lafiyar Abdulrahman muke ba naki ba" A haka ta juya ta fito sai dai ba ta shiga cikin gidan ba,domin ji take gabaɗaya duniya ya mata zafi,bata taɓa tsammanin zata haɗu da irin wannan lokacin a rayuwar ta ba data roki Allah ya dauki ranta tun kafin yau. Ta kusan kai ƙarfe biyu na dare zaune a wurin,ta ci kuka har ta gode Allah kafin ta tashi ta koma cikin gidan, Ko da ta shiga daki ma kasa kwanciya tayi,sai zama da tayi a kasa,da tayi tunanin zata iya samun sauki a wurin Ƴan uwanta,sai gashi sun nuna mata sabanin tunanin ta,ita kuma wanda take gani tamkar majingina a wurin ta,sai gashi ita ke kokarin turata wuta,yanzun Hope din ta daya ne shine Baba,so take ta ganshi ta faɗa mashi komai ko zai karya ta mata,ya kuma samar mata mafita, Jira kawai take gari ya waye, ta san ƙarfe takwas take dawowa. A haka ta zauna idanun ta a bushe ar garin Allah ya waye,ganin ƙarfe tatwas da mintuna goma ne yasa ta fito,babu kowa a falon nasu masu aiki sun kammala gyara,dan haka dakin shi ta nufa kai tsaye, Har ta kai hannu zata tura kofar dakin ta ji hayaniya na tashi yana fitowa daga cikin dakin, Dakatawa tayi sai kuma ta juya zata koma,dan ta san Mama ce a dakin,yanzun kam bata shirya haɗuwa da ita ba, Sai dai jin an kira sunan Yusuf ne yasa ta daka, Baba ne ke faɗin"dan ya sake ta me na bacin rai a ciki,bai mata ƙoƙari ba,saboda ni ne fa ya amince ya aureta har yake zaune da ita, " "Amma shine zai sakar min yarinya a gaba na,wallahi karya yake bari mu haɗu dan abin ba zai mai daɗi ba" "Karma ki fara,domin kin San yanda nake son Yusuf ina iya yin komai akan shi,har ta ke ina iya rabuwa dake" "In dai akan waɗannan ƴan iskan abokan harkallanka ne ai kasaba" "Ni bansan in da yarinyar nan ta gado irin wannan jarabar ba na tsiya,ke me yasa ba zaki koya mata irin yanda kike yi ba" "Me nake yi? " Kin dai san ba zan taba bari Yusuf ya haihu ba,ki bata shawara tabi ta hanyar da kike bi,idan tana son yara ko nawa ne taje ta haifa zamu karba " "Wai me yasa baka da adalci ne a rayuwar ka,kana son yanda ka bata min rayuwa na bata rayuwar yata,saboda ba kai ka haifa min ita ba,na tabbatar ubanta ba zai taba son haka ba" Dariya ta ji ya fashe dashi sosai kafin yace"sannu,yanzun ke a yanda kike idan aka ce ki faɗi waye uban Abdulrahman zaki faɗa,balle na sauran yaran naki,na tabbatar ko wanne da ubanshi,ita wannan yar gwal din naki Nasan ko kashe ki za'ayi ba kisan wanda ya maki cikinta ba,saboda tsabar mazajen da kika bi" "Me ka maida ni,ko da yake koma me na zama ai kai ne Sila tunda baka biya min buƙata na sai dai kace na nime wasu mazan tunda kai maza ƴan uwan ka kake bi, Kuma yara na duk nasan Ubannin su,ita Salma ne dai kawai ba zan iya gane waye mahaifinta ba,kuma koma waye bai da amfani tunda kai kaji zaka iya karɓar ya'yan dan kawai ka ɗauke zargin mutane a kanka, Kaga bama wannan ba,yanzu ya zamu yi da batun Yusuf? "Ki bar batun Yusuf,domin ba zan iya hakura dashi ba ko nan da can,Gara da auren ya mutu,ki je can ki san yanda za ki yi da ita" Da rarrafe ta karasa shiga cikin daki,banɗaki ta shiga ta dinga kwara amai kamar zata amayar da kayan cikin ta, *ban taba sanin cewar ni ƴar Zina bace sai yau!a zinan ma ba'asan waye yayi ciki na ba!haka kuma yanni na maza suma duk ba Baba bane ya haife su,Mama zina take yi!Baba kuma Madigo!harda mijina!sun ciyar damu da haramun!sun tufatar damu da haramun!sun saka munyi ilimi da haramun!wannan dalilin ne yasa na ajiye duk wani abu da nasan su suka yi min,sai wanda na siya da kuɗi na,shi kaɗai na dauka,a wannan lokacin ban ƙara awa daya ba acikin gidan na ajiye ma su Mama wasika na bar gida,wannan shine dalilin da yasa nayi nisa da rayuwar su,na bar masu komai nasu,domin ba zan iya jurewa ba,ba zan iya ba,idan na zauna tare dasu bayan nasan zunubin da suke aikatawa mutuwa zan yi* *rayuwata ba ta da wani amfani tunda ni ƴar zina ce,Gara na karar da rayuwata a hanya,gara nabi wasu mazan,sai dai ba zan taɓa haihuwa ba,balle na haifi ƴar da zata maimaita irin abunda mahaifiyata ta aikata,ni ma kuma na aikata,na yi Alkawarin ba zan kara waiwayar su ba har a bada* Ban shiga harkar bin maza a tsiyace ba,ba kuma ko wani namiji nake bi ba,na canja suna na daga Ummu Salma zuwa BIBA, Da Abuja na fara,a haka aka Bani kyautar gida,in da anan nake zaune,na fara ma manyan mutane aiki ne shekara biyu data wuce,ina samun manyan kuɗaɗe, Ana haka ne na haɗu da Ummita,wacce ita kuma kishiyar uwa tai mata Asiri ta sakata bin maza,a haka ta samu ciki shine mahaifinta ya kore ta, Yarinya ce mai hankali,muna zaune tare muna gudanar da rayuwar mu,ita ta kasance min ƴar uwa,ina son Ummita sosai. VIP ya fara bani aiki shekara daya da ya wuce a waya,ban sanshi ba,sai dai shi ya sanni, Yana biya na kuɗi sosai a lokacin,domin ba ni da wani damuwa dashi, Sai dai wannan karon ya bani wani aiki mai matukar wahala da hatsari, *daganan ta fara rubuta duk wani abunda akai mata wanda ya mata dadi da wanda bai mata dadi ba a gidan su* Idanun shi ya tsaya a in da ta rubuta *Yau Suraj ya ce min ina dauke da kazanta a jiki na!shi bai san gaba ɗaya ta kazanta bace?Umm,maganar shi ya min ciyo sosai,har ma nayi kuka,shi bai sai komai ba game da rayuwata,wama ya fada mashi ni Mage ce,Suraj Mugu ne,bayan yasan ina tsoron maciji shine zai fitar da ni dakin shi* Shafi na karshe a cikin littafin shine in da take faɗin *Ummita ta mutu,sun kashe ummita,ba ni da kowa yanzun!sai dai ba zan taɓa kyale su ba sai na ɗauki fansa ko da zan rasa raina,na riga nama Ummita alkawarin wata rana zan maida ita gida,me yasa zata tafi ta barni* *idan har Suraj ya fito a yau ina son ya rubuta min saki na domin na tafi,ina son na bar rayuwar su,na karasa fadana da kaina,idan har na samu nasara,zan koma gida bayan shakara Biyar,ina son na ga fuskar iyaye na,ina son na tambaye Mama ko Allah zai sa ta gane waye mahaifina,ina son nayi nasara a wannan shari'ar* *Ammi ta san ko ni wacece,ta san abinda ban sani ba game da kaina,me ta sani a kaina,ina son in sani* *cigaban labari* Rufe littafin yayi yana sauke ajiyar zuciya,"za mu yi nasara tare,ba zan taba rabuwa dake ba Ummu Salma,domin ke wata bangare ce na rayuwa ta " Jin karan wayar shi ne yasa ya zaro shi daga cikin aljihu,ganin number Ammi ne yasa ya ɗauka da sauri, "Suraj muna Airport mun sauka lafiya,a wani Asibiti Kuke? Shi sam yama manta da batun zuwan ta,wannan labarin ya dauke mai hankali" Ku tsaya Ammi gani nan zuwa" "To kayi sauri dai" Yana sauke wayar ya dauki littafin sannan ya jawo kofar ya kara kullewa,ya kulle gidan sannan ya nufi Airport rike da takardan a hannu. Yana isa ita kaɗai ya samu a zaune tana jiranshi, Karasa kusa da ita tayi yana yi mata sallamah, Amsawa tayi tana mikewa tsaye tare da rungume shi,shima bai yi kasa a guiwa ba wurin maida mata da kyakkyawar runguma, Sai fadin "Alhamdullah" Take yi, Sake shi tayi tana shafa fuskar shi,da wurin idon shi in da yayi dan baki alamu duka ne yasa wurin baki ko buguwa"kana lafiya? Sumbatar hannun ta yayi"ina lafiya amma,sai dai kuma ita din bansan me zai faru da ita ba,ba na son ta rasa komai nata" "Da Allah muka dogara,na tabbatar da ba zai taɓa zamar damu ba,yanzun muje ka kai ni in duba ta" "Ammi ki bari na kaiki ki huta" Girgiza kai tayi"muje dai kawai,domin hankali na ba zai taɓa kwanciya ba har sai na ganta" Ba yanda ya iya dole Asibitin suka tafi tare, Da Abbu suka fara haɗuwa wanda ba karamin jin daɗin ganin Matar tashi yayi ba,dan ba karamin kewarta yayi ba. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *68* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Bai damu Suraj din dake wurin ba sai ma rungume ta da yayi"barka da isowa" Dan dariya tayi tana kokarin zamewa daga jikin shi "yaron mu na kallon" Ta faɗa cikin raɗa, Shima cikin raɗan yake ce mata"shima ta matar shi yake yi" Jin muryar Dady na kyaran murya ta bayan su ne yasa ya sake ta da sauri yana dan waskewa, Dariya yayi"sannu da isowa Ammin yara,tunda baki ganmu ba" Cikin jin kunya ta kara gaida shi"sannun ku da Ƙoƙari,Allah ya biya ku" "Ki dai na fadar haka domin shima Suraj ai ɗan mu ne,yanzun dai sai dai mu yi fatan Allah ya tsare na gaba,sannan ita kuma matar shi Allah ya tashi kafadar ta" Duk da Amin suka amsa, Abbu na riƙe da hannun ta har bakin ƙofar I.C.U in da take ciki, Shima yana tsaye ta Glass din yana kallon ta,yayin da zuciyar shi keta ruwaito mashi abubuwa da yawa a kanta, Dafa kafadarsa tayi"insha Allah zata ji sauƙi " Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon ta"I Hope so" "Yanzun me likita yace? " Yau za'a mata aiki,amma na roƙi Alfarma ko za'a iya maida ita Kano,in ya so sai ayi aikin a can, ni ko nawa ne zan ɗauki nauyi,domin ina ganin hankalin mu zai fi kwanciya,sannan zata fi samun kulawa" Jinjina kai tayi "tabbas kayi tunani,yanzun me suka ce,hakan yai yu? "Eh amma zasu amfani da private jet ne na wannan Asibitin sai a tafi da ita," Rike hannun ta yayi"kiyi haƙuri Ammi na baki wahala" Girgiza kai tayi"duk wahalar da zan sha bai kai kashi ɗaya ba cikin wanda kake fuskanta,buri na dai shine Allah ya tashi kafadar su" "Amin" "Ammi muje ki ci abinci kafin lokacin tafiyar mu tayi" "Da yake yau Alhamin ina azumi" Murmushi yayi "haka ne Ammi na manta" Abbu ne ya karaso,dan dama yana barin ta tare da Suraj suka fita da Dady"lokacin tafiya yayi "Ammi gashi kina isowa zaki juya" "Babu komai" "Yauwa to mu je,domin ke zaki bimu ne mu tafi tare,shi Suraj sai ya biyo jirgin Asibiti da mara lafiyar" "To ba damuwa" Dan juyawa tayi "tunda na iso banga Pa ba dasu Nadiya? " Nima tunda muka rabu a kotu ba mu haɗu ba,sai dai ya kirani yake shaida min wani uzirin gaggawa ya taso masu zasu tafi,sannan yace na faɗa maki yana tayaki murnar fitowar Suraj,amma in sun samu lokaci zasu dawo" "To ba damuwa Allah ya tsare" "Amin" Suka amsa. Tare suka fito daga cikin Asibitin ya masu rakiya har wurin parking suka shiga mota sannan ya koma cikin Asibitin. Yana shiga ya samu har sun canja mata kaya an kuma Daura ta a wani gado suna ƙoƙarin fitowa da ita, Da sauri ya ƙarasa in da suke,yana rike hannun ta da yaga ya sauko, Lumshe ido yayi ya buɗe yana sauke numfashi kafin ya maida mata hannu saman cikinta yana gyara rufan da aka mata da wani tsaftataccen zanin gado, Ko a cikin jirgi yana zaune kusa da ita yana karanto mata addu'o'i, Kusa da ita ya zauna yana tsura ma kyakkyawar fuskarta ido,yana kallon yanda numfashin ta ke hawa da sauka ta cikin oxygen, Hannu yasa a hankali ya shafa gefen fuskarta,yana ƙara jawo mata hular kanta wanda ya dan zame kaɗan aka ganin lallausar sunan kanta wanda yake baki kirin ya kuma kwanta sosai. Daya daga cikin likitocin da suke cikin jirgin ne wanda duk abinda yake yana kallon shi yana murmushi yace"you Love her a lot" Shima murmushi ya sakar mashi kawai ba tare da yace komai. Ƙarfe Biyu na rana tai masu ne a cikin garin Kano, wanda kai tsaye a cikin babban Asibitin su jirgin yayi Landing, Wasu manya daga cikin Asibitin wadanda suka san da zuwansu su suka tsaya suka tare su,har aka shigar da ita dakin da ya kamata aka saita komai sannan suka fito, Babban likitan da zai yi aiki ne ya dafa kafadar sa"Abokina ka kwantar da hankalin ka,ka je gida ka huta domin kai ma daga dukkan alamu kana bukatar hutu,karka ka bari Stress ya yarda kai,domin kai kaɗai ne zaka iya kula da matar ka,shi yasa nake son yanzun kaje gida kayi wanka ka huta ka ci abinci sannan ka samu isasshen bacci,tunda sai karfe tara na ayi aikin nata,mun matsar da shi ne saboda tafiyar da muka yi,ka ga kafin lokacin ka huta harka dawo" Shi kanshi yasan yana buƙatar hutu,domin tunda ya fito wannan abun ya faru da ita bai samu natsuwar zuciya ba,"na gode sosai Doctor,zan tafi amma dan Allah idan wani abu ya taso ka sanar da ni " "Karka damu" Daganan yana fitowa abin hawa ya tara ya kaishi har ƙofar gida,Allah yasa duk mutane suna cikin masallaci suna Sallah dan ba'a idar ba, Shigewa cikin gida kawai yayi bayan ya sallami mai Adaidaita, ,nan ma ko da ya shiga bai ci karo da kowa ba har ya buɗe dakin shi ya shiga ya maida ƙofa, Tsayawa yayi yana ƙare ma dakin kallo, Komai a gyare yake tsaf,sai Ni'imtaccen kamshi ke tashi,wanda ya san wannan aikin ammi ne,tunda kullun da kanta ke shigowa ta kyara ɗakin, Idanun shi ne suka tsaya a daidai tsakiyar falon, Wani tunani ne lokaci ɗaya yazo ya gilma ta zuciyar shi, wanda ya saka sai da yaji tsigar jikin shi na tashi, Ba komai ya tuna ba face ranar data sumbace shi a tsakiyar falon, Da sauri ya shiga kiran sunan Allah,yana ƙoƙarin kauda wannan tunanin daga zuciyar shi, A hankali yake takawa har ya ƙarasa shigewa cikin ɗakin, Littafin dake Aljihun shi ya ciro, Shafa littafin yake kafin ya buɗe wani durowa mai numbobi wanda in baka lura ba zaka ɗauka ma abin zama ne, Saka littafin a ciki yayi ya maida ya kulle,sannan ya shiga wanka, Ya jima a banɗaki kafin ya fito ya saka kaya ya kwanta,dan tun a Asibiti yayi sallah kafin ya fito dan masallacin can suna riga na kofar gidan su Sallah, Yayi ƙoƙarin ganin ya cire komai a ran shi kodan ya samu ya huta sosai ta yanda zai iya kula da ita kamar yanda Doctor ya faɗa, Kuma Alhamdulillah yana kwanciya barci ne mai matukar nauyi ya ɗauke shi. Jin yanda wayarshi ke ta ƙara ne yasa ya buɗe idanun shi da kyar wadanda sukai mashi nauyi, Addu'ar tashi daga bacci yayi kafin ya mika hannu ya jawo wayar, Kallon Screen din yayi,ganin sunan me kira ne ta saka ya dauki wayar yana sallamah, Daga ɗayan ɓangaren amsawa tayi"kana ina?tundazu mun iso bamu gan kaba,gashi kaka ta damu" "Ammi barci nake yi amma gani nan shigowa" "Yauwa to maza ka tashi domin har ƙarfe biyar tayi" Da sauri ya maida kallon shi kan agogon bango yana zabura,dan ko Sallah la'asar bai yi ba, Cikin sauri yayi wanka domin ya kara samun karfin jiki sannan ya shirya cikin wani farin shadda wanda yasha maiko,ya gyara suman kanshi wanda sai da ya rage sama_sama saboda cika, Yana idar da sallah fitowa yayi daga dakin yana jawo ƙofa, Ji yayi ance"Yaya Suraj " Juyawa yayi yana kallon me kira ba tare daya ce mai komai ba, A hankali yake matsowa in da yake tsaye,hannu yakai a hankali ya dan taɓa shi"kai ne kuwa"ya fada kamar mai kokonto, Mintsinin shi yayi a kafaɗa wanda hakan yasa ya saki ihu yayi tsalle ya rungume shi yana dariya yana faɗin "shine,wallahi shine ashe" Dariya shima yayi wannan karo yana raba shi da jikin shi "Salman so kake ka karya ni" Kuka kuma ya fashe da shi yana rike hannun shi"yaya Suraj,wallahi na ɗauka shi kenan ba za mu kara ganin ka ba" Shafa kanshi yayi yana dan murmushi "to ba gani ba, me na kuka? " Gani nake yi kamar mafarki nake yi" Ganin ya fara tafiya ne yasa da sauri ya riƙe shi yana zaro ido"ina kuma zaka" "Zan koma in da na fito ne" "Ina kenan" Ya tambaya da sauri "Duniya ta,domin dama mafarki kake yi" Dafa kafadarshi yayi"ya kamata ka farka haka nan in ba so kake ka bini ba"ya karasa faɗa yana zame hannun shi cikin da Salman ɗin, Ganin kiran Ammi na ƙara shigowa wayar shi shine yasa da sauri yayi gaba ya bar shi nan tsaye yana tunanin shin da gaske mafarki yake yi ko kuwa idanun shi biyu. Kai tsaye shiyan Kaka ya nufa inda suke zaune suna jiranshi. Tun isan shi shiyan ya fahimce falon a cike yake,kasancewar yanda hayaniya ke tashi da muka yawan takalmar dake zube a ƙofar ɗakin,domin ita bata barin a shigar mata da takalmi falo, Zame takalmin kafar shi yayi ya daga ƙaramin labulen dake rufe a kofa wanda yake shara_shara,bakinshi dauki da sallamah, Kalifa yaron Aunty Atika shi ya fara ganin shi,dan yawanci hankalin su ya dauke ne a kan hiran da suke yi, Jin yanda yayi ihun kiran sunan "Uncle Suraj" da yanda ya tashi da gudu ya nufo wurin shi ne ya janyo hankalin su dawowar kan wanda ke tsaye a bakin kofar yana dariya yayin da yake juyi da yaron a hannun shi, Basu taɓa tsammanin sun yi kewarshi har haka ba sai yau da suke ganin shi,basu taba tsammanin dariyar shi na saka su nishaɗi ba sai yanzun da suke ganin shi tsaye a gabansu yana dariya, Kai jama'a rayuwa kenan,yayin da wasu ke tsananin murnar ganin ka da ci gaban ka,to wani idan ya ganka ji yake kamar ya kashe ka,amma kuma a zahiri nunawa yake kamar yafi kowa murnar ganin naka(Allah kara bamu da makiyan ɓoye). 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *69* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Kamar dama jira su khadija ke yi ya sauke kalifa suka taso suma da gudu suka rungume shi,sai kuma Amira ta fara kuka,ganin haka ne yasa suma suka fara kuka, Har yanzun dai murmushi ne a fuskarshi, "kukan na menene ba gashi na dawo ba" Ƙara kan_kame shi suka yi,Kaka ce ta hau faɗa "yau ga ja'iran yara,so kuke ku yarda shi,ku sake shi muma mu samu mu ganshi mana" Sake shi suka yi yayin daya cigaba da taku har gaban Kaka in da take zaune tana jin kamar ta tashi ta taro shi,sai dai ciyon kafa ya mata cikas, Yana isa gabanta tsugunnawa yayi yana kamo hannayen ta ya sumbata"Kaka" Hawaye ta shiga zubarwa "Allah mun gode maka da ka dawo mana da wannan yaron hannun mu lafiya ba tare da dubaran mu ba,Surajo Allah ya ƙara tsare ka,ya tona Asirin masu hannu a wannan lamarin" "Amin Kaka,ya karfar ki? " Ƙafa da sauƙi sai godiyar Allah "leken bayan shi take yi" Ina ita Habiba,ya banganta ba? Shiru yayi bai iya bata amsa ba sai ma mikewa da yaki ya nufe in da Ibrahim yake ya mika mashi hannu,kafin ya ba Shamsuddeen sai Nurudeen,duk masabaha suka yi suna mashi barka da dawowa, Idanun shi ne suka sauka a kan Maijiddarh wacce duk inda yayi take bin shi da ido, Duke kan shi yayi kafin ya gaida su Hajiya Saude,da Goggon yara,duk Allah ya tsare suka mai, "Yanzun Suraj shi kenan magana ta ƙare? Cewar Momy Saude, " Ya ƙare mana,idan bai kare ba zaki ganshi ne a nan,ai duk munafunci irin na mutum bai isa yayi abinda Allah bai yi ba"kaka ta faɗa wacce dama kamar jira take yi, "Ah ni fa bawai ina nufin wani abu bane,dama tunani nake yi tunda ya dawo kuma ni har yanzun ban gama bincike a kan wannan Yusuf din ba d...... Katse ta kaka tayi ta hanyar kara tambayar shi a karo na biyu" Wai ni Surajo na tambaye ka ina Habiba baka Bani amsa ba har yanzun" Kallon Ammi yayi wacce ta mai magana da ido, Juyawa yayi kan Kaka"ki yi haƙuri Kaka,tana Asibiti yanzun haka" "Me ya same ta,Allah yasa ba hannun bane ya matsa mata? Furzar da iska yayi cikin yanayi na dan damuwa yace" Ba hannun bane,domin yanzun haka aiki za'a mata zuwa anjima " Dafe kirji tayi tana salati "wani irin ciyo ne haka ya same ta da za'a mata aiki" "Jiya ne da aka fito koto,a yanda nake samun labari daga bakin durebanta wai taga wasu sun fito daga cikin koton sun shiga mota,to shine tace ya bi bayan su da ita,suna zuwa ta bar shi a waje ita kuma ta shiga cikin gidan,to bansan waye ta gani ta bi ba, ko kuma me ta ji a can,kawai dai sai gani yayi ta fito da gudu wasu na binta,ashe garin gudu sun samu nasaran buga mata ƙarfe a kai,"cewar Ammi "Yaya to wasu mutane ne waɗannan? Sannan me tai masu"cewar Khadijah "Koma dai me tai masu wannan karon sun zaɓi hanya mara bullewa" "Idan har kasan ba zaka iya kula da ita har haka ba me na bari ta shiga cikin rigimarka? Nurudeen ya fada cikin yanayi na jin haushi, "Kasan ko su waye ne?gaskiya ko su waye basu kyauta ba" "Umm na sani" Ya faɗa yana sauke idanun shi akan Shamsuddeen, "Kaka zan fita zai dai zuwa anjima" "Ka faɗa mana wani Asibiti ne sai mu je mu dubata" Cewar Goggo, "A'a Goggo ki bari zuwa gobe sai kuje ku dubata saboda yanzun ko kunje ba za ku samu damar ganin ta ba" "To ba damuwa Allah ya kaimu ya kuma bata lafiya" Da Amin ya amsa yana fita. Yana fitowa kai tsaye shiyan Ammi ya nufa,har ya kusa isa yaji daga bayan shi ana kiran kiran sunan shi, Tsayawa yayi yana jiran karasowar ta, "Ya aka yi Maijiddarh? Matsowa tayi ta gefen shi ana ana dukar da kai" Yaya Suraj nayi farin cikin dawowar ka sosai" "Na gode" "Yauwa ya jikin Habiba? " Da sauƙi Alhamdulillah" Ganin tayi shiru ne kamar wacce bata da abun faɗa yace"ina iya wucewa" "Eh,amma anjima zan zo Asibiti na dubata" "Ok ba damuwa sai kin zo" Ya faɗa yana karasa shigewa cikin falon, Da kallo ta bi shi tana jin tamkar tace ya tsaya,sai dai tasan a yanzun ba tada wannan damar,amma zata jira har zuwa sanda zata samu dama. Yana shiga shiyan Ammi tsayawa yayi a babban falon su yana tsura ma hoton da sukayi gaba dayan su ido wanda harda Shamsuddeen a ciki, Ji yayi daga bayan shi an dafa shi, Juyowa yayi yana ganin ita ce ta rungume ta, Ita ma rungume shin tayi tana Hamdala ga Allah maɗaukakin sarki, Hannun shi taja suka shiga har cikin dakin ta sannan ta maida kofa ta rufe, Zaunawa tayi saman gado yayin da ya zauna a kujeran dake gefen ta,domin baya taba yarda ta zauna mata a saman gado,duk da yasan ba nan suke kwana tare da Abbu ba. "Shin an samu nasara kuwa? Lumshe ido yayi ya buɗe" Ammi an samu fiye da baya" Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi"kayi haƙuri Suraj na saka ka damuwa da yawa sanadin wannan aiki,sai dai ka sani dole sai ka sadaukar da wani abu kamin ka sami wani abun, A lokacin dana samu karin bayani akan wannan shirin nasu hankali na ya tashi sosai,na rasa ta wani hanya zan bi domin tseratar da kai,ka yi hakuri shi yasa na juya wasan ta yanda basu yi tsammani ba,sai dai gashi ta sanadin haka the innocent soul is suffering,ina fatan zaka yafe min? Rike hannun ta yayi"ba kiyi komai ba Ammi,kin yi ne dan ki taimaki rayuwar ɗan ki,and na tabbatar da she will understand you,fata na yanzun Allah ya bata lafiya" "Amin ya haiyu ya kaiyum " Ya tsanshi biyu ya saka a cikin idanunshi yai gashi ya ciro wani dan abu kamar leda fari tas wanda ya hade da kwayar ido,baka iya sammanin ya saka abu a ido,buɗe wani karamin contena yayi ya saka wannan ledar idanun guda biyu, wanda nan take asalin kwayawar idanun shi suka baiyana, Rufewa yayi ya mika ma Ammi"komai yana cikin nan,yanzun abu ɗaya ya rage mana mu kammala haɗa hujja " "Shima dab muke da cimma shi,sai dai ya maganar iyayenta? Busar da iska yayi yana shafa fuskar shi" Ada nayi tunanin kiran kiran su,amma dai yanxun ina ganin gara mu bari idan an yi aikin ta samu lafiya" "Eh hakan yayi,yanzun yaushe zaka koma Asibitin? " Sai bayan Sallah Magrib" "Ok Allah ya kai mu" Da Amin ya amsa yana tashi, Daganan gidan shi ya nufa inda anan su Bala suka saka sabon kukan murnar ganin Ubangidan nasu. *Bayan wasu Awanni* Yana fitowa masallaci ko gida bai koma ba ya wuce Asibiti, Yana yin parking mota kiran Dr na shigowa wayar shi, Ɗauka yayi yana karawa a kunne, Daga ɗayan ɓangaren yace"kana ina sir Suraj? "Gani a cikin Asibiti" "To kayi sauri ka same ni a ofishi na" Ba tare daya ce komai ba ya sauke wayar,yana karasa shiga cikin Asibitin, Yana isa ofishin ƙwanƙwasa kofar yayi domin mutumin ba Musulmi bane, Umurnin shiga aka bashi sannan ya shiga, Nuna mashi wurin zama yayi"zauna" Zaunawa tayi"ina fatan babu wani matsala? "A'a da sauƙi dai,dama jini muke nima saboda aikin da za'a shiga da ita,shine nake son na tambaye ka,shin a saka mata jinin siyarwa,ko kuma a family za'a samu wanda zai yi donating blood" "In dai wannan ne babu damuwa zan yi donating blood dina saboda ni (O-) negative ne" "Yauwa to yanzun zamu tafi LAB domin a fara ɗiban jinin ka a duba,sai a duba nata jinin ita ma" Mikewa yayi"to mu je,yanzun saura awa nawa a shiga aikin" "Saura dai mintuna talatin" Tare suka jera har Lab din in da anan ka ja jinin shi suka fara gwadawa,shi kuma yana zaune a reception,har suka je dakin da take suka dibo jinin ta, Yana dai zaune yana danne _danne a wayar shi yaga wanda yazo ya dibi jinin ta ya fito da sauri,kafin wani lokaci kuma sai ga wasu manya daga yan Lab din sun zo sun shiga, Yana dai zaune yana lokacin_lokaci yana duba agogo,a haka sai gashi har an kwashe kusan mintuna ishirin, Likitan da zai mata aiki ne ya ga anje an kira tare da wasu likitocin ma, Hakan ne yasa a jiye wayar a gefe yana tunanin ko lafiya,gashi lokaci na ta kurewa, Dr Daniyal ne ya fito jiki a sanyaye yazo in da yake, Shima yana ganin shi ya mike tsaye, Dafa kafadarshi yayi"mu je Lab akwai abinda nake son nuna maka " Jinjina kai yayi yana bin bayan shi "da fatan dai lafiya? Bai bashi amsa ba har suka shiga ciki,sai dai ba ta inda aka diba jinin shi ba ne,wannan wani madaidaitan falo ne,mai dauke da kujeru sai kuma likitocin dake zaune a wurin su uku ko wanne fuskar shi dauke da damuwa, Nuna mashi wurin zama sukayi ya zauna, Sannan daya daga cikin su ya fara magana kamar haka"Malam Suraj Abdulbasir,matarka ita ce Ummu Salma Abdullah " "Haka ne" Ajiyar zuciya likitan ya sauke"muna son mu sanar da kai cewar cuta ba mutuwa bane,sannan duk wani cutar da Allah ya saukar dashi sai da ya saukar da magani,sai dai wani lokaci kafin mu fahimce maganin ne sai ya dauke mu shekaru masu yawa," Katseshi yayi"ka fada min meke faruwa kai tsaye " Daukar Rimot din wani karamin TV yayi dake jikin bango ya danna,sai gashi wasu irin abu na yawa a cikin TV,kamar dai a saka mai a cikin ruwa yanda yanda yaje rabewa yana hadewa, Nuni ya mashi da TV"wannan shine gwajin jinin Matar ka da muka yi,wanda ya tabbatar mana da tana dauke da *LEUKEMIA* *CANCER OF THE BLOOD* wanda ya nuna a cikin jinin ta sakamakon kwajin da muka je yi tsakanin jinin ka da nata. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *70* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Gabaɗaya karamin falon shiru ya ɗauka na sakanni yanda kasan babu mutane a cikin shi, Sai da suka ƙara maimaita mai maganar ganin kamar baida niyar cewa komai, "Rayuwa da mutuwa duka na Allah ne,nasan cewar tun daga lokacin da aka hallicci ɗan Adam Allah ya riga ya dibar masa iya numfashin da zai shaka a rayuwar sa, Bai isa ya kara ƙofa da ja daya bane" Dago idanun shi yayi wanda suka sauya daga farin da suke zuwa wani yanayi da baka isa ka fassara halin da zuciyar shi ke ciki ba,yanayi ne da duk wani bawa mai tawakkali da karfin imani kan tsince kansa a ciki a duk lokacin da wata masifa ko jarabawa ta same shi. "Hakan na nufin lokacin rasa ta yayi? " A'a ba haka lamarin yake ba Sir Suraj,wasu mutane sun dauka da zaran ance mutum na dauke da ciyon Cancer shi kenan lokacin mutuwar shi yayi,abun kuma ba haka yake ba,yanzun an samu cigaba a duniya fiye da yanda mutum ke tunani,kullum sababbin lamari ƙara fitowa suke yi,ka ga kamar na Matar ka,ya zama matsalarta biyu ne,wanda nake ganin idan har muka shawo kan matsalar zata samu lafiya ta koma dai-dai kanar da" Ganin bai ce komai ba ne yasa yaci gaba da bayani kamar haka,yana matsar da hoton dake jikin TV zuwa wani, "Wannan hoton Kidney ta ne,wanda ya nuna mana saboda rashin functioning yanda ya kamata ya janyo wannan Leukemia ɗin, Ɗan Adam yana iya amfani da Kidney daya kuma ya rayu,to sai dai ita dama a sakamakon binciken da muka yi ya nuna an taba mata aikin Kidney har an cire daya,da daya take amfani,wanda shima yanzun ya samu matsala ta sanadiyar shan kwayoyin da take yi ko wani lokaci,sannan da shan taba,ma'ana Sigari,duk da illar sigarin ba sosai bane dan bai kai kwayar da take ci yawa ba" Hannun yasa yana shafa gaban goshinshi da yaji yana mashi ciyo lokacin daya,ba tare daya dago ba yace"me abin yi yanzun? "To da farko dai dole muna buƙatar wanda zai iya Donating blood cell,sai ayi abinda ake kira da *STEM CELL TRANSPLANT* kafin nan kuma ita kuma za'a mata *Chemotherapy* is to kill the blood forming cell, Idan har an kammala an samu nasara,sannan ne zamu mata asalin Surgery na kai da kuma Kidney Transplant" "Yaushe ne za'a fara gudanar da aikin? " Eh aikin ba shine matsalar ba,matsalar shine wanda nasu cell din zai dace da juna wanda zai iya bata kyauta ko kuma dai a siya,sai kuma batun Kidney,duka ba abu bane mai sauƙin samu nan kusa,dan haka dai zamu cigaba da daurata a cikin Coma har sanda za'a mata aikin in an samu" Mikewa tsaye yayi"na gode "ba tare daya jira cewarsu su ba ya fito daga ɗakin, Har yayi taku uku yaji an kira sunan shi, Ji yayi kamar ba zai tsaya ba,sai kuma ya juyo,da sauri Dr din ya karaso in da yake" Wucewa zaka yi" "Umm" Ya bashi amsa yana kauda kai, "Mu je ka ganta" "No"ya faɗa kamar mai ciyon baki, Cikin mamaki yace " No fa kace,I thought you care so much,kuma zaka so ganin ta" "Zan iya tafiya,domin inada abun yi" Kasa ba shi amsa yayi,sai ma rakashi da ido da yayi har ya bulle ma ganin shi, Shifa a nashi tunanin yanda yaga ya nuna damuwa sosai a Legas a ranar farko da aka kawota,hankalin shi a tashe,sai yake tunanin zai iyayin komai domin ita,yanzun ma yana tunanin wannan maganar da suka faɗa mashi sai sun rike shi,amma sai gashi yana nuna kamar abin bai dame shi ba,shifa bai gane ba, Ganin kanshi na ƙoƙarin kullewa ne yasa ya gyaɗa kai yana wucewa. Yana fitowa daga cikin Asibitin kai tsaye wurin parking mota ya nufa inda ya ajiya Motar shi,ji yake zuciyar shi na mashi wani irin zafi da raɗaɗi,a maimakon daya shiga ya tayar da motar ya wuce,sai kunna AC da yayi ya rufe Glass ya haɗa kai da Sitiyarin motar, Ya dauki lokaci mai tsayi a zaune a cikin motar da ana tunanin samun mafita wanda aƙalla yayi awa daya zaune kafin ya yanke shawarar da zuciyar shi yafi tsayawa a kai kafin ya tada mota yabar Harabar Asibitin, Kai tsaye gidan shi dake Sultan Road ya nufa, Yana shiga daki zama yayi a baƙin gado yayin da hannun shi ke riƙe da waya ya tsura ma wata number ido kamar mai shirin tantance wani abu, Ajiyar zuciya ya sauke a karo na ba adadi kafin ya danna number cike da fata iri-iri, Sai da wayar yayi Ringim sau biyu sannan aka ɗauka da Sallamah, Amsawa yayi cikin muryar nan nashi mai matuƙar sanyi,"Ina magana ne da *Abdulmajid* ? "Eh dashi ne,pls waye ke magana? Shiru ne ya ratsa wayar na ɗan wani lokaci wanda har sai da ya ƙara maimaita tambayar kafin ya buɗe baki kamar wanda aka tilasta yace" Kana magana ne da Suraj Abdul basir " Tun daga nan ban kuma sanin me yake faɗi ba saboda yanda yake magana a hankali, Sun dauki lokaci mai dan tsayi yana magana kafin naji yace"Sai kun iso "ya sauke wayar ya koma ya kwanta yana lumshe ido,wanda Allah ne kaɗai yasan me ke gudana a ran shi. Ranar a gidan ya kwana,yayin da yanda yaga rana haka yaga dare,sai dai banbancin shine bai bata lokacin shi a banza ba,domin Alwallah ya dauro yana mika kukan shi da godiyar shi a wurin Allah mai yin yanda ya so. Bashi ya kwanta ba sai bayan ya dawo daga sallar Asuba sannan bacci ya dauke shi, Jin yanda wayar shi ke ta ƙara ne ya tayar dashi daga nauyayyen baccin da yake yi, A hankali yake buɗe idanun shi yana lumshewa har sai da ya tabbatar da ganin shi ya dawo dai-dai sannan ya mike zaune,nan ma bai tashi kai tsaye ba saboda yasan illar dake tattare da mutum yana farkawa daga bacci yayi saurin tashi, Sai da ya ƙara mintuna uku kafin ya mike tsaye ya nufi ban ɗaki, Wanka yayi cikin sauri ya shirya cikin Kananan kaya da jaket na maza wanda kayan ba karamin fitowa dashi sukayi ba,sai baƙin facing cap daya saka saman lafiyayyen gyararren gashin kanshi,wanda yasha Kalolin mayuka masu matukar kamshi, Turaren shi mai matukar sanyin kamshi ya fesa sannan ya mai da ya ajiye, Fuskar nan nashi har wani ƙyalli yake da ɗaukar ido,yayin da kwarjinin shi yake karuwa a duk lokacin da zaka daura idanun ka a kanshi, Ko kaɗan yau babu fara'a a fuskarshi,domin yau yan halin na kusa, Agogon Azirfar dake ajiye gaban madubi ya ɗauka ya saka a hannun shi sannan ya fito bayan ya ɗauki makullin daya daga cikin sabbin motocin dake fake a cikin gidan a wani keɓantaccen wurin wanda in dai ba lura kayi ba da wuya ka gane a kwai wannan garejin a gidan, Wata Musulman mota baka katuwa mai numfashi ya buɗe,wanda sai ƙyalli da daukar ido irin na niman magana yake yi, Irin motar nan ne da manyan masu kuɗin Larabawa zaka ga suna hawa,saboda su basu son karamin mota,to irin ta ne, Kunnawa yayi ya tayar sannan ya bar harabar gidan cikin kwarewa,da iya sarrafata, Tunda ya shigo layin unguwar duk in da ya gefta kallon mitar ake yi,wasu har leke suke yi suga a ina zai tsaya, Bai shigar da motar cikin gida ba dan yasan ba jimawa zai yi a ciki ba zai fito shi yasa ya faka ta a waje, Duk suna tsaye a ƙofar gidan wasu a zaune,kasancewar a kwai ɗaurin auren da aka gama gabatarwa yanzun, Kallon motar kawai suke yi suna jira suga wani hamshaki ne zai fito daga ciki,sai dai tsayin sakanni ba'a buɗe ba,kai babu ma wata alama da zai nuna maka na cikin motar nada niyar fitowa, Kallon Nurudeen yayi"gaskiya duk me wannan motar ba karamin tarawa yayi ba,wata biyu kenan da akayi Lunching dinta a Saudiyya" Ɗayan gayen dake tare dasu ne yace"ai Ibrahim ni wallahi ko wanke wannan motar aka bani na kwana daya an gama min ko mai " Duka ya kai mashi yana dariya, Shi dai nurudeen bai basu amsa ba,ya dai zuba ma motar ido ne kawai,domin kusan wata shida kenan tunda aka fara tallar motar ya fara tara kuɗi domin siyan ta sai dai ko rabin rabi har yanzun bai hada ba,duk da Dream Car din shi ne sai dai ya fara cire rai,dan yasan sama tayi ma yaro nisa,kai shi bai ma ɗauka a Nigeria an samu wanda ya shigo da ita ba sai yanzun da yake ganin ta a gaban shi, Lallai ko waye mai wannan motar to ba karamin kusa bane ko dai a gwamnati ko kuma a wani masarautar,shi jira kawai yake yaga waye a cikin ta. Sai da ya gama amsa wayar da yake yi kafin ya buɗe marfin motar ya sako kafar shi mai ɗauke da takalmi but farare sabon dizai wanda ba sai an faɗa maka ba kasan bana sawar yara bane, Karasa fitowa yayi ya maida ƙofar motar ya kulle hannun shi riƙe da wayar shi ya doshi hanyar shiga cikin gida yayin da ya cire facing cap ɗin dake saman kanshi. Duk da kallon Mamaki suka raka shi har ya bulle ma ganin su ba tare dashi yasan ma suna yi ba, Basu kadai ba duk wani wanda hankalin shi ke kan fakawar wannan motar sai da yayi mamakin ganin wanda ya fito,domin sun san cewa a rayuwarshi shi mutum ne ba mai fariya ba,da wuya kaga ma yana tuka mota da kanshi,in ma zai tuka to sai dai ya shiga na matsakaita kuɗi,dan har akwai wata rana da Ibrahim ya taɓa mai gatse,akan cewar mu dai munji ance kun gaji dukiya sai dai ko kadan banga alama ba,ƙila ma faɗi ne irin na mutane,domin meshi ai baya taɓa ɓoyewa, A lokacin girgiza kai kawai yayi ya wuce ba tare da ya ce mashi komai ba, Da hannu yayi nuni"wannan ba Suraj bane? Kafin su bashi amsa ne sai ga Dady ya iso in da suke"waye ya ajiye wannan motar a nan?ko anyi baƙo ne? Girgiza kai Nurudeen yayi cikin disashewar murya yace"Suraj ne" Shima sai da ya kara kallon motar na saƙonni kafin ya juya ya doshi cikin gida. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *71* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Cikin natsuwa yake tafiya tamkar wanda baida wani damuwa a zuciyar,ya doshi shiyan Kaka, Da Sallamah ya shiga, tana ganin shi ta shiga washe baki tana dariya wanda hakan ya saka shi murmusawa, Da sauri Khadija ta tashi daga inda take zaune kasancewar yawancin lokuta yafi zama a nan wurin, "Yaya ga wuri" Bai amsa mata ba sai ma zaunawa da yayi kusa da Kaka, "Tsohuwa barka da safiya" "Da fatan ka tashi lafiya,? Bai bata amsa ba sai ma cewa da yayi" Me zan samu na ci? Kallon Mejiddarh tayi data yi zaune ta tsira mashi ido kamar taga sabon hallita, Dauke idonta tayi a kan ta tace"ke Balki dauko ma Surajo Kunun tsamiya yana nan cikin fulas a kicin" Da sauri ta mike ta nufi kicin din domin dauko masa, Khadija ce ta mike tabi bayanta "bari na taimaka mata wurin dauko kulan kosai da kofi" Ba wanda ya bata amsa har ta shige ita ma, Karo suka ci da sauri ta karasa shiga tana jawota baya"ke kinga abinda na gani? Hararanta tayi"ke dai Khadijah anyi Uwar gulma,yanzun har kin ga wani abu" Dariya ta saka,sai kuma ta toshe bakinta da sauri tana zaro ido"ba ki lura da kallon da Aunty maijiddarh take masa ba? "Wani irin kallo kenan? Duka takai mata a kafaɗa" Irin kallon dan Allah ka kula ni " Juya ido tayi"ina lura da komai,shima kuma yau naga kamar yan miskilancin sun motsa baki ga yanda ko amsa gaisuwar mu bai yi ba? Kafin ta bata amsa ne suka ji muryar Kaka na fadin"wai Kunun yaki daukuwa ne? A tare suka amsa da faɗin "gani nan zuwa" Rike mata hannu tayi tana kashe mata ido"sai dai fa ya haɗu Balki babu karya,yau na daban ne" Fisge hannun ta tayi tana yin gaba tare da fadin "ba kida hankali tunda so kike ya sheke mu" Ajiye mai fulas din tayi a gaban shi sannan ta tsugunna ta tsiyaya mashi, Ba tare da ya ce mata komai ba ya ɗauka ya fara sha a hankali, Shigowar su Ibrahim da Nurudeen ne yasa ya dan daga kai ya masu kallo daya sannan ya dauke kai yana cigaba da kurban kunan shi, Wanda hakan da yayi ba karamin tsayama daya daga cikin su a rai yayi ba, "Ya jikin Habiba Surajo?an samu an mata aikin kuwa? Jujjuya kofin dake hannun shi yake yi wanda ya kusa kammalawa" Ba ayi ba " Cikin nuna damuwa tace"me yasa,ko an fasa aikin ne? Ajiye kofin yayi"ba'a fasa ba za ayi amma ba yanzun ba," Ganin tana shirin ƙara jeho mashi wani tambayar ne yasa yace"akwai wasu gwaje_gwajen da ya kamata su kara yi mata,da zaran sun kammala za ayi" Ibrahim ne yace "Bro gaskiya motar nan daka shigo da ita ta cije ni" Kallon rashin fahimta yake mashi, Dariya yayi kaɗan "ina nufin motar ya haɗu,kasan nawa naji kudinta kuwa,ai ban dauka an samu wanda ya shigo da ita Nigeria ba saboda wata biyu kenan da ya fito kuma a Saudiya aka yi Lunching din ta" Ganin bai da niyar gama jawabin shine yasa ya mike yana faɗin "Kaka zan fita sai zuwa anjima" "To Allah ya tsare Surajo" "In zo ka rage min hanya"ya tambaya dan kawai ya shiga motar ya kafa tarihi a cewar shi, Bai bashi amsa ba har sai da ya kusa barin falon sannan yace" Ba yau ba" Dariya su Khadijah suka saka ganin yanda ya ɓata fuska,harara ya dalla masu"bakuda hankali baku san irin motar da nake magana ba ne? "Ni kan wani irin mota ne haka da har zaka yi marmarin hawa bayan duk irin motocin dake cikin gidan nan" Karamin tsaki yaja "bari dai na nuna maku abinda nake magana akai," Nan ya ciro waya ya bude data cikin yan mintuna yayi downloading hoton motar sannan ya mika ma Maijidda"kalli mota ki gani tamkar wani jirgin ruwa" Amsa ta yi tana dubawa yayin da take yin kasa da hoton domin duba kudin mitar, Ai babu shiri ta buɗe ido cikin tsananin mamaki, "Kaka kin ga kudin motar nan kuwa? Yanzun irin motar nan Yaya Suraj ya ke dashi? " Ita ma ya hau yau,idan har bai wuce ba kina fita kofar gida zaki ganta fake " Fisge wayar Balki taki"ku bamu mu kashe kwarkwatan ido" Shigowar Hajiya Saude ne ya katse su wacce ke tambayar "cin mu sun ne ake yi? Balki ce ta mika mata wayar" Momy kalli motar da yaya Suraj yake da,kalli kuɗin motar, Idan har yana da kudin siyan wannan motar to wani irin kuɗi kenan yake dashi " Amsar wayar tayi tana dubawa"yanzun Suraj ne yake da irin wannan motar? "Sosai ma kuwa" Hararan shi tayi tana mika mai wayar"karyan banza,yaushe yayi wannan Arziƙin,waye Ubanshi?me kuma ya mutu ya bar mai da har zai mallaki irin wannan motar,sai dai in yana haɗawa da wata hanyar ne na ƙarƙashin ƙasa wanda bamu sani ba" Ta karasa faɗa tana zama a daya daga cikin kugerun falon. Dariyar da Kaka tayi ne tana girgiza kai ya maido hankalin su kanta, Kallon ta tayi tana jinjina kalamanta "kika ce waye uban Surajo Saude?sannan kika ce Ina yaga kudin siyan wannan motar?to bari na sanar dake wani ɗan ƙaramin abu da baki sani ba game da Ahalin sa,Kakan shi,a wancan lokacin hamshakin mai kuɗi ne wanda idan ma baizo na daya ba a masu kudin kasar MARDESH to zai zo na biyu,domin Allah ya Azurta wannan Ahalin da dukiya na ban mamaki,sai dai kuma su jarabawar su shine Allah bai yi su da samun Ya'ya ba,yawancin su ba su da haihuwa wanda suke matukar so,kafin a samu haihuwar uban Surajo ba karamin wahala suka shaba wurin rokon Allah,kakan shi ya mutu ya barma kakar shi mace dukiya wanda dana auren dangi suka yi ba mai nuna ma wani arziki,ita kuma dan da take dashi ya mutu ya bar mata jika ƙwaya daya tal,wanda shine magajin duk wani abunda suka mallaka a duniya, Dan ma Allah ya tsare shi Surajo ba mai nuna komai bane ai da baku isa ku haɗa mazauni da ku ba,ko a yanzun iya Business nashi da Allah ya hore mashi kun san abunda ya mallaka a kasashen duniya,"ƙaramin tsaki taja tana mikewa "kawai dai kuna ganin mutane ne kuna wulakanta su ba tare da kunsan iya baiwar da Allah ya masu ba,sannan har kuke mamaki dan kun gan shi ya hau wannan motar da kudinta a wurin ko cikin chokali bai kai ba" Ta karasa faɗa tana shigewa dakin ta,ta bar su nan zaune cikin mutuwar jiki. Kallon Maijidda tayi yayin da suka haɗa idanu,sai dai ba wanda yace komai yayin da jira kawai suke su keɓe dole akwai magana,dole ne ma, Hajiya Saude ce ta fara tashi ta bar dakin. _____________yana fita daga shiyan Kaka kai tsaye shiyan Ammin shi ya shiga,tana zaune a falo tare da Amira dake ta faman ja mata ƙafa, Amsa Sallamar shi tayi fuskarta dauke da fara'a na farin cikin ganin ɗan nata, Zama yayi saman shimfidaddiyar darduma dake zagaye da kalon a maimakon zama kan kushin yana karbar ƙafarta da Amira ke matsawa, Ita ma ganin haka yasa ta sakar mashi tana gaida shi ta bar falon falon ta nufe shiyan Goggo, "Barka da safiya Ammi" "Da fatan ka tashi lafiya? " Alhamdulillah" Shiru ne ya ratsa falon na ɗan wani lokaci kafin ta katse shirun ta hanyar faɗin "ya jikin nata? " Alhamdulillah " Ajiyar zuciya ta sauke wanda ke nuna damuwar da take ciki"yanzun dole sai mun jira? "Umm" Girgiza kai tayi"sun iso? "Eh tun dazu,suna masauki " "Kaje ka kai su,zuwa anjima zamu haɗu" Cigaba yayi da mammatsa mata kafa"insha Allah " Sai da ya kammala sannan ya mata sallamah ya fita domin zuwa Hotel din da ya saka suka sauka. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *72* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Yana fakawa a harabar Hotal din ya fito daga cikin motar,sai dai bai shiga ba dan sam baya ra'ayin shigar, Daukar wayar shi yayi ya shiga wurin kira,kafin naji ya amsa Sallamah,sai kuma yace"gani a harabar "sai kuma ya sauke wayar yana sauke ajiyar zuciya tare da jingina a jikin motar, Ganin duk wanda yazo wucewa sai ya kalle shi wasu harda juyowa ne yasa ya saka facing cap din dake hannun shi ya saukar dashi da kyau ta yanda ba zaka iya ganin idanun shi ba, Tunda suka fito suke waige_waige ko zasu hango shi, Sai dai rashin sanin kamannin shi yasa dole sai da Abdulmajid ya ƙara kira yana jira yaga ta in da zai hango shi, Inda yake tsaye yana iya hanzo zaratan samari masu jini a jiki wadanda ke dan jujjuyawa alamun nimar wani,hannu ya daga masu daga in da yake "ka juya damar ka gani nan ina daga maku hannu" Da sauri ya juya,ai kuwa yana hango shi yace"mu je gashi can" Tun daga nisa suke kare mai kallo tun daga kan takalmin kafarshi har zuwa bakin hular dake kanshi wanda bai basu damar ganin fuskar shi ba,face farin fatar hannun shi dake baiyane saboda rigar hannun ta ba mai tsayi bane wanda hakan zai tabbatar ma da mai kallonshi shi din fari ne tas,sai kuma zaro_zaron yatsun hannun shi dake dauke da zobe guda daya, Suna isowa inda yake hannu ya mika masu tare da kara masu Sallamah cikakkiya, Amsawa suka yi suma sannan suka yi musabaha, Bude masu kofar baya yayi "Bismillah" Sai da suka kalli juna kafin dai su shiga kamar yanda yayi masu nuni, Juya sitiyari yayi ya bar cikin Hotel din dasu, Tunda suka dauki hanya babu wanda yace ma ɗan uwansa komai,kowa da abinda yake rayawa a zuciyar shi, Ganin an dube masu wani katon Get ne yasa suka ɗaga kai suna kallon zanen rubutun dake rubuce wanda aka rubuta da manyan harafi,*Jiddarh Hospital* Asibitin makekene na gasken gaske,domin Asibitin hawa biyar ne bayan kuma wasu manyan ɓangarori dake gefe,gashi ta ko ina ka juya yaji ado da furanni koraye masu saka nishaɗi da sanyaya zuciya, Ta ɗayan gefen kuma babban wurin ajiye motoci ne in da anan yayi parking sannan suka fito, Yana gaba suna biye dashi a baya har suka doshi wani babban wuri da suka ga an rubuta Restaurant, Suna shiga ya saka hannu ya zame hullan dake kanshi ba tare daya juyo ba ya nufe wurin wani mutum dake tsaye a babban teburi wanda daga dukkan alamu daga nan ake ajiye odar, Su dai basu san meya faɗa ma mutumin ba,sun dai ga cikin girmamawa da rawar jiki yake amsa mashi kamin ya fito yaje ya buɗe masu wani kofa dake cikin babban wurin cin abincin, Sai lokacin ya juyo inda suke tsaye"Bismillah " Kalmar da ya kara fitowa bakin shi kenan,yayin da su kuma kowa da abinda yake rayawa a ran shi game da wannan fuskar, Bin bayan shi sukayi har cikin wani karamin falo wanda ya ji kujeru manya da kayan kallo,daga dukkan alamu daki na musamman ne, Zazzaunawa suka yi suna kara nazarin dakin,cikin lokaci kankani aka cika masu gaba da kayan motsa baki,sai dai ba wanda ya taɓa komai domin ba shi bane a gaban su kamar yanda shi ma ya sani, Murmushi ya saki mai sanyi wanda sai lokacin suke ƙara ganin asalin baiwar kyau da Allah ya mashi, "Ni Suna na Suraj kamar yanda na faɗa ma Abdulmaj a waya,sannan ni Miji ne ga ƙanwar ku Ummu Salma,shima kamar yanda na faɗa masa" Dan shiru yayi na sakanni kafin cikin sanyi muryar nan nashi mai fita a natse yaci gaba da faɗin "Nasan duk abinda ya faru da ita a baya,har dalilin barin ta gida,sai dai kuma a lokacin da zuciyar ta yayi sanyi take jin zata iya karɓar ƙaddarar ta,a lokacin shi kuma Ubangiji yayi nashi ikon ta haɗu da hatsari wanda ba na ce ba,idan ta farka zata faɗa mana me ya faru a wancan ranar,sai dai har yanzun bata farka ba tana hali ne na doguwar suma, Na so a ce ba zan sanar daku ba har sai ta samu sauƙi,sai dai na kasa domin kome yana hannun Allah ne ba hannu na ba,shi yasa na yanke shawar gaiyatarku nan domin ku ga kanwar ku"ya karasa fada yana dago kai domin sanin a wani hali suke ciki. Hawaye ke sauka daga cikin idanun su babu kakkautawa,yayin da Abdulmajid ya sauko daga saman kushin ɗin da yake ya karaso in da yake,tsugunnawa yayi akan gwuiwowin shi ya rike hannun Suraj"Bawan Allah duk da ban sanka ba,ban San a ina ka haɗu da kanwar mu ba!sai dai muna matukar yi maka godiya da kasancewarka mijinta!muna matukar maka godiya da karɓar ta da kayi bayan sanin kome dangane da ita!muna kuma gode kama daka tuna damu a matsayin ƴan uwan ta a wannan lokacin!wallahi tun jiya daka faɗa mana ba mu kara samun rintsawa ba da natsuwa!dan Allah ka kaimu mu ga ƙanwar mu" Mikewa yayi yana mikar dashi"kai tamkar yaya kake a gare ni,dan Allah ka tashi, tunda har ka ga na kira ka ai dole ne na kaiku in da take " Share hawayen fuskar su suka yi suna ƙara yi mashi godiya, Tare suka fito suka nufi asalin cikin Asibitin, Abin mamaki duk inda suka bi a cikin Asibitin cikin girmamawa zaka ga manyan likitoci na gaida shi a haka har suka isa hawa na biyar in da anan take kwance, Wasu Nurs ne da suka zo giftawa suna biye da wata Doctor a baya suka ga ta gaida shi cikin girmamawa amma hannu kawai ya daga mata ya wuce,dan ya gaji da ansa gaisuwa tun daga hawa na daya, Duk da kallo suka bishi,yayin da daya daga cikin su tace "Ma wannan sabon likita ne? Murmushi ta saki tana bin bayan shi da kallo har suka bulle ma ganin ta, Girgiza masu kai tayi" Umm umm" "Ba likita bane shine muka ga kin gaishe shi cikin girmamawa" "Ba likita bane,shi ɗin jarumin Miji ne da duk wata mace zata yi alfaharin kasancewar sa miji a gare ta,shi din jarumin miji ne da sai mace mai sa'a zata taka matsayin amsa sunan matarsa,shi din jarumin miji ne da zai iya yin komai domin matar sa,shi din jarumin miji ne da zai iya sadaukar da ko nawa ne domin iyalansa,shi din shine Young Ustadz karamin su babban su," Cikin tsananin mamaki suke kara bin hanyar da kallo kamar zasu kuma ganin shi "Waiyo Allah gaskiya ashe yafi kyau a fili,kai kaga mutum kamar bugun injin" Dayar ce tace"to me yake yi a asibiti? "A jiya aka kawo matar shi ba ta da lafita daga Legas,amma kunsan wani abun mamaki? Duk girgizar kai suka yi, " A jiya da daddaren ya siya wannan Asibitin a kan miliyoyin kudi,ya kuma ƙara ma duk wani likita dake aiki a wannan Asibitin Albashi,duk da akwai kayan aikin da za'a ma matar shi aiki sai da ya kara yin odar wasu daga ƙasashen waje sababbi na zamani wadanda a kanta za'a fara aiki dasu,kunsan irin farin cikin da duk wani likita dake Asibitin nan yake ciki saboda shi?maganar gaskiya munji daɗin kawo wannan Zinariyar matar tashi wannan Asibitin,dan haka daga yanzun duk inda kuka gan shi ya zamo abin girmamawa a wurin ku,domin mutane da yawa zasu amfana saboda shi" Dayar ce ta rungume hannu a kirji cikin shauki take faɗin "waiyo Allah ina ma ace ni ce wannan matar tashi,dana tsula tsiya a duniya" "Sai kuma Allah yayi ko me sharan gidan shi baki zama ba,com on Jare kuxo mu tafi" Bin bayanta suka yi suna masu fadar abubuwa da dama a kanshi,yayin da shi kuma ko sanin suna yi bai yi ba. _____daga bakin kofar suka tsaya suna kallon kanwar tasu dake wance bata da maraba da gawa face ta hanya daya wato numfashi wanda yake fita a hankali, Hankalin su ya tashi sosai da ganin halin da take ciki,duk yanda suka so su daure ma zuciyarsu kasawa suka yi,sai da suka dinga zubar da hawaye yayin da abubuwa masu yawan gaske ke dawo masu a ransu game da rayuwar su na baya daya shuɗe,lallai dan Adam ba abakin komai yake ba, Basu jima sosai a wurin ba yace su tafi domin ko da ma sun tsaya babu wani abunda zasu iya yi mata,dan haka dole suka fito suka bar ta ba dan ransu yaso ba, Yanzun ma a motar shi suke sai dai bai nufe Hotel din da suka sauka da suba sai gidan shi daya kai su, Abdulrahman ne yace"Kanin mu nan ina ne" Murmushi yayi jin sunan da ya kira shi dashi"nan gida na ne " "Ai da ka maida mu Hotel kawai" Cewar Abdulmalik "Ta yaya zaku zo har in da kanwar ku take ba tare da kun shiga gidan ta ba,duk da bata ciki na tabbatar zata ji daɗi idan tasan anan kuka sauka,ni ma kuma zanfi samun natsuwa" Kallon juna suka yi suna sakin murmushin farin ciki,domin kan lallai sun yarda yanzun Ummu Salma tayi aure kuma ta samu miji, Bin bayan shi suka yi har cikin babban falon gidan. Duk zaunawa suka yi a falon suka kara kallon gidan, "Ya su Mama " Ya tambaya, "Kamar yanda ka roka akan kar mu faɗa masu tukunna shi yasa basu san mun zo nan ba" "Dama nafi bukatar ku fara ganin halin da yar uwar ku ke ciki saboda ku zasu fi su iya jurewa" Abdulmalik ne yace"kani ni kam kana min kama da wani malami bari dai ka gani"nan ya ciro wayar shi ya kunna video din wa'azin Young ustaz mika ma Abdulrahman yayi"kalla ka gani kamar har ta baci " Amsa yayi ya kalli na wayar ya kalli shi yanda yake zaune yana kallon su hankali kwance, "Shine mana,kanin mu ai kai ne ko? Ya tambaya domin son tabbatarwa " Ni ne" Mamakin su ne ya saka boyuwa ikon Allah,"To Babban Malami irin ka a ina ka haɗu da Biba gashi har kunyi aure" Dan murmushi yayi"is a long Story,idan ta tashi zata faɗa maku" "Allah yasa ta manta da komai ta yafe mana"Abdulmajid ya fada cikin damuwa, " Karka damu Allah ya bata lafiya " Duk da Amin suka Amsa, Tambayar shi suyi game da bayanin likita akan lafiyar ta, Bai ɓoye masu komai ba ya sanar dasu har kuma da irin aikin da take buta, "Abbas Mama ta faɗa mana lokacin Salma na da shekara biyar a duniya tayi fama da ciyon koda sosai wanda sai da cire Mama daya aka saka mata"cewar Abdulmalik "In dai har Salma zata samu lafiya a shirye muke damu bada Kodar mu domin a saka mata" Kanin mu,dan Allah ka mai da mu Asibiti likita ya gwada mu ya gani a cikin mu duk na wanda ya mata a shirye muke damu bada har ta da jinin da take bukata" Shiru yayi dai ba tare daya basu amsa ba tamkar dai mai nazarin kalaman su. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *73* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Sai zuwa yamma sannan suka kara komawa Asibiti domin a gwada su,dan lokacin da Dr ya basu kenan. Abdulrahman ne ya fara shiga aka gwada shi,su kuma suna zaune a babban ofishin likita suna jira,sannan da aka kammala yi masu gwaje-gwajen daya kamata sannan suka koma gida dan sai zuwa gode sakamako zai fito, _______A gidan kuwa,suna barin shiyan Kaka part din su suka shiga, Zama tayi sharaf saman kushin tana sauke numfashin takaicin mahaifiyar nata, Itama zama tayi kusa da ita"yanzun ya zamu yi" Cikin jin haushi ta juyo tana fuskantar ta"akan me kenan? "Akan wannan yaron mana Suraj,nasan kin San me nake nufi" Ji tayi ranta na ƙara ɓaci "yanzun ni Momy me kike son in yi ne,ina ce tun farko sai da na faɗa maku ina son shi haka nan,amma ke da Aunty Atika babu irin zagin da baku mai ba,har da Marina sai da kika yi,bayan ni na hango ma kaina irin rayuwar da baku hango ba,gashi a karan banza kun saka wata yar aiki cikin daula,sannan yanzun kina tambaya ta akan me zamu yi? Mekewa tayi ta bar falon tana faɗin "sai ki san yanda za ki yi" Da kallo ta bita baki buɗe "ki zo mu samu mafita" Sai dai ko kulata ba tayi ba tayi shigewar ta, Dan shiru tayi tana nazarin maganar Kaka,in dai kuwa haka ne to dole ne Yusuf ya janye dan ko ana ha maza ha mata wallahi ba zata bari wannan daular ta wuce su ba. _______karfe tara na dare ne suka kara komawa Asibiti tare domin jin sakamakon gwajin da aka yi. Yanzun ma kamar dazu ne sune zaune a ofishin Babban likitan,sai dai wannan karon bashi kaɗai bane su uku ne, Dan haka cikin kwantar da murya suka shiga yi masu bayani akan an samu jinin Abdulmalik zai dauki nata,batun koda ma haka na Abdulmajid zai mata, Wannan bayanin ba karamin farin ciki ya saka su ba, "Dr yanzun zuwa yaushe za'a gudanar da aikin?ya tambaya, " Nan d kwana biyu,domin zuwa gode kayan da kayi mana oder zasu iso,dan haka sai mun tsaya mun kwada su yanda ya kamata" "Babu damuwa Allah ya kaimu" Da Amin suka amsa, "Sai dai batun STEM Transplant zuwa gobe da yamma za'a yi mata shi,domin mun duba cigaban da aka fara samu ta wannan ɓangaren" Cewar ɗayan Dr ɗin. "Babu damu a shirye muke a ko wani lokaci" Daga nan suna fitowa gida suka koma domin Ammi ta kira akan ita ma tana hanya domin zuwa ta gana dasu. Tun a harabar gidan suka shaida isowarta dan ganin baƙuwar mota a wurin parking, A falon kuwa suna saka ƙafa wani daddadan kamshi na musamman ya ziyarci hancin, Kalle_kalle yake a falon ganin yanda ko ina yayi fes,duk da falon a kyare yake a ko wani lokaci domin ma'aikatan gidan na ƙoƙari,amma gyaran mace dana namiji ba daya bane, Fitowa tayi daga cikin hannun ta ɗauke da wasu hadaddun kuloli yayinda Bala ke biye da ita a baya shima yana dauke da sauran kayan, Da sauri ya amshi kayan dake hannun ta yana murmushin farin ciki "Ammi sannu da zuwa" "Yauwa har kun dawo" "Umm" Ya faɗa yana ajiye kulan a table, Cikin girmamawa suka shiga gaishe ta, Amsawa tayi cikin dakin fuska tana nuna masu wurin zama, "Ya kuka tsaya a tsaye,ku zauna mana" Zaunawa sukayi "Ammi mun same ku lafiya" "Lafiya qlau,ya iyayen naku" "Suna nan lafiya" "Ya jikin Baban naku,da sauƙi kuwa ko har yanzun sai a hankali" Wannan karon kallon juna suka yi cikin mamaki,ya akayi tasan da jikin Baban su har haka, Ganin sun dan shiga yana yi na mamaki ne yasa ta kuma cewa"karku damu hakan ba abin mamaki bane,domin na San iyayen ku shekaru ishirin da biyu data wuce" Wannan karon ko Abdulmajid kasa ɓoye mamakin shi yayi"Ammi a ina kika san iyayen mu,sannan gashi kuma Ummu Salma tana auren danki,amma kuma baƙi taba niman itayen ta ba,ko dai dama kin riga kin San ko ita din wacece?amma baki nime mu ba? Wannan karon kam murmushi tayi domin tambayoyin yaron sun mata,tana son mutum me confidence,"batun sani iyayen ku ba abu ne daya shafe kuba,wata kila nan gaba kadan ku na iya sanin a ina muka san juna,ita kuma Salma tun farko nasan ita din wacece,sannan maganar kiran ku ko maida ita gida kuma kun san ba abu bane da zai yu a wancan lokacin,domin zuciyarta bata gama karɓar kaddaran daya same ta ba,yanzun kuma da ta ji tana iya yafe maku ta karbe ku a matsayin ƴan uwa shine ta haɗu da wannan tsautsatin,shi yasa ma har Ɗa na ya kira ku domin ku ganta" Duk shiru suka yi domin sun kasa tabbatar da manufar wannan matar,sai dai koma menene zasu jira har sanda ƴar uwar su zata farfado, Nuna masu abincin dake gabansu tayi"kuci abinci kar yayi sanyi" Cikin natsuwa suke cin abincin har suka kammala, Mikewa tayi tana kallon su"ku kwantar da hankalin ku insha Allah ƙanwar ku zata samu lafiya,sannan ku dauka tamkar a nan gida kuke" Haɗa baki suka yi wurin faɗin "mun gode" Sallamah ta masu yayin da Suraj ya rakota har bakin mota inda Direbanshi dama ya dauko ta shi kuma zai maida ita, Buɗe jakkan dake hannun ta tayi ta ciro wani dan karamin Kit fari ta miƙa mashi"na riga na gama haɗa komai na cikin wannan so yanzun kana iya haɗa shi da sauran" Amsa yayi yana buɗewa,wannan farin abun ne daya ciro a cikin idon shi wanda ta bata a wancan ranar,a takaice Cameran ido"to Ammi" Ajiyar zuciya ta sauke tana shafa fuskar shi "Allah ya albarkaci rayuwarka," Lip din shi ne kawai ya motsa wanda ke nuna alamun ya amsa, Sai da ya tabbatar sun bar cikin harabar gidan sannan ya koma ciki. Har sun shiga dakin da ya basu, Ƙofar dakin ta naga ya buɗe ya shiga, Dakin a gyare yake fes kamar akwai mutum a ciki, Sif din kayanta ya buɗe wanda yake babba ne sai ba sosai ba amma mutum zai iya shiga ciki ya tsaya tsaf, Kallon kayanta dake jere yayi,sai kamshi suke yi,lumshe ido yayi yana buɗewa, Hannun shi manna a jikin sif din wanda nan take muryar naga wurin ya kawo haske yayin da muryar computer ya fara magana "welcom maste" Scanning tafin hannun shi wurin yayi,kafin kuma lokaci ɗaya naga kamar an tura kayan cikin sif din gefe shi kuma inda nan take yayi kasa,ma'ana wurin Elevator ne, Tafiyar mintuna biyu sai gashi ya tsaya tsaf,bude ƙofar yayi ya fito, wanda wurin wani kayataccen wuri ne mai ƙunshe da nau'ikan na'ura na Cumpute kala-kala,komai na dakin fari ne sol mai matuƙar jan hankali,gashi a gyare shi ma wurin yake, Buɗe wani kofar da akayi aka shigo ne yasa na mai da hankali wurin, Bala ne ya shigo hannun shi rike da jug dan madaidaici mai matukar kyau wanda zaka iya ganin ma abinda ke ciki, Murmushi ya saki ganin uban gidan nashi"barka da shigowa Yallabai " A hankali ya taka har gaban waɗannan computers ɗin,wani soket ya dannan nan take gabaɗayan su suka kawo wuta,"ya iyalanka? "Suna nan lafiya yallabai" Zaunawa yayi a saman kuyera yayin da ya buɗe dan akwatin da Ammin shi ta bashi ya ciro wannan abun idon ya Daura a wani kwalba,ya jima yana danne_danne cikin kwarewa da sanin kan na'uran,sai da ya gama sannan ya shire ya mai dashi cikin akwatin,danne_danne yaci gaba dayi na tsayin lokacin wanda a ƙalla yayi kusan awa biyu, Kallon agogo yayi wanda ya nuna ƙarfe sha ɗaya na dare, Mikewa tsaye yayi yana miƙa tare da lanƙwasa wuya jin yanda ya riƙe masa, Daukar jug din shayin da Bala ya ajiye mashi yayi yana tsiyayawa a ƙaramin cup, A kan wasu jerin kushin masu matukar kyau da tsaruwa ya zauna yana mike kafa,cikin natsuwa yake kurban shayin yana dan lumshe ido yayin da yake kallon Screen din computer dake haska video cikin gidan tun daga ranar da yayi tafiya har zuwan su Pa da dauko wasikar da tayi ɗayan dakin,a takaice babu abinda bai gani ba har zuwa ranar da suka bar gidan, Lumshe ido yayi a karo na ba adadi kamar mai jin bacci yana sauke su a kan hotonta,wanda take tsaye a harabar gidan dan daga dukkan alamu bata san da hoton ba, Na ranar da taje taron wa'azin matan manyan malamai ne, A yanda yake zaune yana kallon hoton yana sauke numfashi a hankali zai tabbatar maka da yana cikin wani yanayi wanda kallon shi dai bai isa yasa ka tantance a wani halin yake cikin ba,kallo ne irin na wanda ake ma mutumin da aka dade ana tsumayen shi,ta ɗayan bangaren kuma kallo ne irin iya matukar kewar ki,idan kuma har ka kara natsuwa da kyau hankalin ka zai iya baka cewar babu daya acikin biyun waɗannan kallon,domin kallo ne da ina matukar jin haushi ki,koma dai wani irin kallo yake ma hoton shi kaɗai yasan sirrin dake cikin zuciyar shi. Ganin ƙarfe daya na dare yayi ne yasa ya mike yana kashe komai na dakin tare da barin wurin ta hanyar daya shigo. *bayan kwana biyu* Alhamdulillah an samu anyi STEM Transplant din lafiya,kuma likitoci sunyi Observing dinta na awa Arba'in da kwas ba tare da wata matsala ba,sannan a yau suke saka ran ƙarfe goma na safe za'a mata kidney Transplant din. Tunda ya tashi wanka kawai yayi ya fito tare da nufar shiyan Kaka,domin a nan gidan ya kwana yau ba a gidan shi ba dan su Abdulmajid suna tare da Abdulrahman a Asibiti. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *74* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Da sallamah ya shiga shiyan kaka wacce ke zaune tana gyangyadi, Murmushi ne ya subuce ya juya ya fita dan baya son ya takura mata, A hankali yake takawa cikin tafiyar nan nashi tamkar na mai tausayin taka kasa, Har ya baro shiyan kaka yaji daga bayan shi ana kiran sunan shi wanda hakan ya tilasta mashi juyawa, Da hannun take mai alamar da yazo, Babu musu ya isa in da take tsaye tana sakar masa murmushi, Cikin girmamawa wacce take ɗabi'ar shi yace"Momy in kwana? "Lafiya qlau Suraj,hala fita zaka yi da safe haka? " Umm"kawai yace yana mamakin tsayar da shi da tayi,dan gaskiya bai cika shiga lamarin Momy Saudat ba domin yasan a matsayin data ɗauke shi,ita da Momy Rahama. "Kaga dama kuwa akwai maganar da nake son muyi dai in ba damuwa ko zamu iya shiga ciki? Kallon ta yayi ya kalli kofar falon ta da take nuna mai yana mai da kanshi ga Agogon Azurfan dake hannun shi,ganin yana da dan sauran lokaci ne ta saka ya sauke ajiyar zuciya " Ba damuwa Momy " Tana gaba yana biye da ita har cikin babban falonta wanda take a kyare tsaf,dan ita ma Momy Saudat mace ce mai tsafta, Nuna masa kushin tayi"zauna bari na saka a kawo maka abun kari" "A'a na gode" Bata saurare shi ba ta shiga kwala kiran maijiddarh,wacce bata san yana ciki ba ta shigo tana tura baki da fadin"Momy lafiya k... Maganar ta tsaya ne a ƙasan maƙoshinta dalilin ganin wanda bata yi tsammanin gani ba musamman zaune a falon su, "Kawo ma Yayan ku abun kari" Da sauri ta juya tana fadin to, Cikin mintunan da basu wuce biyar ba sai gata ta shigo dauke da tire ta ajiye a gaban shi, Sannan ta nime gefen ta zauna tana satar kallon shi kasa_kasa, Sai take ganin yau ya ƙara mata kwarjini sosai musamman da yake cikin shigar jampa na wani farin yadi mai matukar laushi fari tar wanda daga ganin shi kasan ba na karin kuɗi bane musamman yanda ya lafe a jikin shi, Ta gefe ɗaya kuwa suman shi har daukar ido yake tsabar baki da ƙyalli da yake yi yanda kasan wanda ya shafa ma dayis, Sai hakan ya ƙara fito da ainahin kyawun da Allah ya masa da wani irin ƙwarjini mai cika wuri irin na wadanda suka rike sallah da Salati, Ganin har mintuna biyar sun ƙara shuɗewa babu wanda yace komai,shi kuma yana zaune tamkar wani hamshaki, "Suraj kaci abinci mana" Ƙara duban Agogo yayi "Momy bana karin safe da wuri" "To ko ruwa ba zaka sha ba" Dan kauda kai yayi domin shi tunda yake su tayin abinci kamar na yau bai taɓa haɗa su ba,dan haka ba tare da ya kuma ce mata komai ba ya dauki koran ruwa ya buɗe ya tsiyaya a kofi yayi Bismillah yayi kurba daya ya ajiye. Ganin yana shirin mikewa yasa da sauri tace"ya jikin matar taka? "Da sauƙi" Ya faɗa ciki_ciki dan zaman sa anan din ya fara gunduran sa, "Emmm dama a ina batun lamarin ka da Maijiddarh ya tsaya? Wannan karon kallon ta yake sosai" Kamar wani lamari kenan? Ya mai da mata da tambayar, Ganin yanda ya zuba mata idanu ne yasa ta danji zuciyar ta na rawa,amma idan ta tuna me take son tayi sai taji ta kuma samun kwarin gwiwa,"ina nufin lamarin auren ka da Maijiddarh,kaga tunda ka dawo kuma komai ya wuce to me zai hana a maida saka ranar na,kaga mu ko yanzun ka shirya a yau ɗin nan ma ana iya daura maku aure,ko me ka gani? Ta fada tana da sare shi itama da nashi idanun. Wani irin laulausar murmushi ya saki,irin mai tsayawa a rai,ya mike tsaye,juyawa yayi in da Maijiddarh take zaune kafin ya dawo da ɗuban shi kan ta"gaskiya Momy is not a good idea haɗa jini da jinin yahudawa,,sannan na ma matata Alkawarin ba zan taɓa mata kishiya ba,kin san wani abu kuwa? Shiru kawai tayi tana kallon shi cikin tsananin mamaki domin bata taba tsammanin zai iya maida mata magana har haka ba, Ci gaba yayi da faɗin "na kuma faɗa mata idan har a shekarar auren mu na farko ta haifarmin Baby to duk abinda na mallaka ya zama nasu,and I tell her that I Love her ita kaɗai,kinga Momy yin maganar Maijiddarh yanzun kamar cin amanar ta ne,wanda haka baya daya daga cikin hali na,dan haka ina mai baku haƙuri Allah ya bata miji na gari"yana gama fadar haka ya juya yayi fitarsa yayin daya barsu nan zaune tamkar wadanda aka zare ba jijiya, Yana fitowa falon ya saki wani ɓoyayyen ajiyar zuciya tare da shafa kanshi yana busar da iska ta bakin shi,sai kuma ya saki murmushi tuna irin halin da ya baro su a ciki,tabe baki yayi lokaci guda yana fadin a ranshi when did I tell her that I Love her oho,ko ta yaya ma zan iya haɗa jiki da wannan yarinyar har ta haifa mashi ya'ya oho ya ba kanshi amsa yana daga kafaɗa da faɗin "aure zan yi " Tunda ya doso wurin parkin din security din shi suka mike tare da buɗe ma shi kofar wani lafiyayyen farin mota a cikin gerin mitoci uku dake jire suna jiran shi. *____________Asibiti* Kira ne ya shigo wayar Abdulmalik wanda tun jiya ake ta dun shi da kira amma yaki dagawa kasancewar shi sam baya son ɗaga baƙuwar number, Tsaki yaja yana faɗin "wannan ko maye ne haka zai ganni ya barni" "Kai dawa? Cewar Abdulmajid dake ƙoƙarin mika ma Abdulrahman kofin shayin daya hada mashi, " Wallahi tun jiya wani number ya azabeni da kira" "To ja ɗauka mana,ka sani ko wani ne da ka sani,ni bansan me yasa kake da irin wannan ra'ayin ba,irin kune idan mutum na niman taimako har a kashe shi baku sani ba saboda wannan ɗabi'ar" Dariya sukayi shida Abdulrahman dake kurban shayin shi, "Yama katse bari a ƙara kira sai na ɗaga" Bai ma gama rufe baki ba kuwa sai gashi an ƙara ƙiran,ɗauka yayi tare da yin sallamah,sai dai jin muryar wanda ke magana ne yasa da sauri ya saka wayar a amsa kuwa ta yanda duk zasu iya jin abinda na cikin wayar ke faɗa, "Hello,Hello Abdulmalik kana jina Yusuf ne" "Wani Yusuf? Ya tambaya kamar bai gane me magana ba, " Yusuf mijin Salma" "Oh kana nufin tsohon mijin Salma? " Kaga ba nida lokacin wannan yanzun haka ina Kano na gano Asibitin da salma take ba ta da lafiya sai dai an hana ni shiga dakin da take,dama na maku alkawarin ai duk inda take zan nimota,yanzun haka gani a gaban dakin,dan haka kuna iya zuwa a yau ku dubata ku gani" Duk shiru suka yi suna sauraren shi har ya kai karshe"yanzun kai kana kofar dakin Salma ne? "Eh" Ya bashi amsa, "To ina zuwa" Yana fadar haka ya kashe wayar yana kallon su "hmmm lallai Yusuf,hala shi bai san yanzun sama tayi ma yaro nisa ba ne? " To me zaka yi da kace ya jira ka? Ɗan dariya yayi yana kallon agogon dake manne a jikin bangon dakin,"nasan yanzun haka Suraj ya kusa isowa,"mikewa yayi"bari naje na manna mai hauka,domin yanzun ne lokacin ramuwar gaiya " "Kai dai ka yi a hankali kasan sai za'a ma aiki,karkaje ka yi wani dogon magana" Bai gama sauraran su ba ya fita yana dariya kasa_kasa. ___________A babban haraban Asibitin motocin suka yi parking,daya daga cikin security din ne ya buɗe mashi ƙofa,har ya sako ƙafa daya waje yaji wayar shi na ƙara,dan dakatawa yayi gani number da take kiran shi, Sai da yayi ɗan jim kafin ya ɗauka wayar,sai dai bai yi sallamah ba kasancewar ya san da wanda yake magana, Daga ɗayan bangaren ne aka kira sunan shi cikin harshen Turanci "Suraj Albishirinka? Murmushi yayi jin abinda yace ya san tabbas akwai labari mai daɗi kenan" Goro fari kar Dr" Kamar a mafarki yaji yace mai "Kakar ka ta tashi " Shiru ne ya rasa wayar har tsayin mintuna biyu, Ya san dama za'a rina "kana jina Suraj" Wani dogon ajiyar zuciya yaja yana saukewa yanayin da yaji idanun shi na cika da hawayen da bai san ko na menene ba"Umm" "Da gaske nake yi ta farka bayan dogon suma na tsayin shekaru goma sha ɗaya,sannan munyi observing din ta babu wani damu sai dai dan wanda ba'a rasa shima cikin lokaci ƙanƙani zata dawo dai-dai domin nan a kwai kayan aiki sosai wanda zai taimaka mata har jijiyoyin ta su sake," Murmushi ya sake wanda ke fita tare da hawayen dake sauka a fuskar shi "ina take? " Tana barci a yanzun haka amma daga nan zuwa awanni uku zata tashi,zan haɗa ka da ita,sannan yaushe zaka shigo domin tana buƙatar ka a kusa da ita? "Nan da awanni goma " Murmushi shima yayi daga nashi bangaren "sai mun ganka" Daga nan ya sauke wayar, Hannun ya daga yana kwararo ma Ubangiji yabo da kirari domin ya dawo mashi da ran da ya daɗe da fara cirewa a lokacin da bai yi tsammani ba, Karasa fitowa yayi yana saisaita yana yin sa,a yanzun burinsa daya ne shine yaga fuskar kakar tasa, Tafiya yake yi cikin yanayin da zai nuna maka shi din lafiyayye namiji ne mai jini a jika,da kuma takama da kuruciyar sa,yayinda security din shi ke taka masa baya suna doshi cikin Asibitin....... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *76* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Murmushi kawai suka yi, "Karku damu babu wata matsala tattare da ita" Cewar likitan da ya gama dubata, Godiya suka yi masu sannan suka wuce. Kaka ce da ta kasa hakura tace"Abdulrahman ko?ta faɗa tana nuna shi, Girgiza kai yayi"A'a Abdulmajid " "Yauwa Abdulmajid me yasa tunda kuka zo baku shigo cikin gida ba,sannan a ina kuke zaune? "Da fari a Hotel muka sauka,amma sai Suraj ya matsa sai mun koma gidan shi," Kallon su tayi tana kara kallon Biba dake kwance "daga dukkan alamu ku ba matsiyata bane balle ace sabida hakan Biba ke aikatau,ko dai akwai wani dalili ne? Duk kallon Nurudeen suke suna tunanin amsar daya dace su bashi, " Tabbas maganar daka faɗa gaskiya ne,sai dai ka sani ita wacce kuke kira da Biba ba shi bane asalin sunan ta,Sunan ta shine Ummu Salma Abdullah,yace yar gata kamar sauran yan gatan yaran da iyayensu ke ji dashi,ita din sanyin idanun ahalin mu ne,abu ɗaya kawai zan iya faɗa maku Kaka"ya juyo yana fuskantar Kaka"tsayin Shekara biyar kenan da muka kwashe muna nimanta bayan barin ta gida,cikin ikon Allah kwanaki uku da suka wuce muka samu kira daga mijinta Suraj,ya faɗa mana yasan komai game da ita,sannan a lokacin da take jin cewar ya kamata ta koma wurin iyayenta da yan'uwan ta,sai gashi ta haɗu da wannan hatsarin, dan haka Kaka muna masu matukar baku haƙuri akan ɓoye maku ita wacece da Salma tayi,sannan muna matukar gode maku akan riƙe ta da kuka yi hannun biyu,Ubangiji ya albarkaci rayuwar ahalunku,sannan Kaka kiyi haƙuri dama muna shirin zuwa har gida wurin ki idan munga ta farka lafiya ita da ɗan uwan mu,da fatan zaki yafe mana? Murmushi ta saki yana rike hannayen su,"babu komai Allah ya yafe mana ya muka bata lafiya" Da Amin suka amsa, Balki ce tace"me yasa to ta bar gida"ta faɗa tana tsare Abdulmajid da ido, "Idar har ta tashi in har tana da ra'ayin faɗa maku zata faɗa," Tabe baki tayi"to ai shikenan" Murmushi yayi yana rayawa a rashi wannan sai an yi tsiwa, Nurudeen ya ɗan kara kallon dakin kafin yace"ina Suraj din yake? "Dazu tafiyar gaggawa ya taso mai kuma ya tafi"Abdulmajid ya basu amsa, " Bayan anyi ma matar shi aiki ba zai iya tsayawa ta farka ba,yanzun har a kwai tafiyar da yafi matarsa muhimmanci? Duk shiru suka yi an ma rasa mai bashi amsa, "Ai ya kira ni ya faɗa min,kuma na tabbatar da koma menene ba karamin abu bane" cewar kaka, Ba tare daya ce komai ba ya juya ya bar dakin, "Mu zamu tafi amma dai zuwa gobe zaku shigo ku dubamu ko? " Insha Allah Kaka" Har bakin mota suka raka su sannan suka dawo ciki. Basu jima da tafiya ba ta farka,nan ma sai da likitoci suka ƙara dubata suka tabbatar da cewa babu wata matsala sannan suka wuce suna masu matuƙar farin ciki,sannan da gindaya ma yanninta abinda ya kama tayi da wanda bai kamata tayi ba a yanzun. Tunda ta buɗe idanun ta take bin ko ina da idanun ta,da take ganin kamar mafarki take yi ko kuma tayi wani irin tafiya ne mai matukar nisa wanda har yanzun bata dawo ba,ko kuwa ta dawo ne, Duk in da suka bi da ido kawai take bin su, Ji tayi an riƙe mata hannu,tare da kiran sunan ta"Salma " shin da gaske da sunan data manta an taɓa kiranta dashi yanzun dashi aka kira ta, Tsira mashi ido tayi tana buɗewa yayin dake lumshewa duk a lokaci ɗaya, Ganin yanda hawaye ke fita daga cikin idanun su ne yasa a hankali ta kwada kiran sunan su dan son tabbatar da ko da gaske su din ne zaune a gabanta, "Yaya Abdulmajid" Ta furta a hankali, Kara matse hannun ta suka yi cikin nasu yayin da Abdulrahman ya kara fashewa da kuka"dan Allah ki yafe mana kanwar mu" "Da gaske ku ne? " Mu ne,Salma!mu ne" Mai da idanun ta tayi tana lumshewa jin ta gaji da magana, "Yaushe kuka zo? Ganin tamkar ta gaji da maganar ne yasa yace" Muna nan tare da ke,ki samu ki huta zuwa da safe zamu karasa magana " Tun tana kallon su har bacci mai nauyi ya kara dauke ta, Sanin dokar Asibitin na ba'a kwana da mara lafiya ne yasa dole ganin baccin ta yayi nisa suka koma masaukin su bayan sun duba Abdulmalik. Washegari kuwa koda suka shigo cikin Asibitin ƙarfe takwas na safe,dan lokaci ne ake bari a ga masara lafiya, Tana zaune a saman gadon ta an ɗan dago da gadon ta yanda zata fi jin daɗin zama,idanun ta a lumshe suke sai dai ba barci take yi ba, Jin sallamar muryoyin da take dokin ji ne yasa ta buɗe manyan idanun da suka shanye saboda ciyo tana daurawa a kansu, Su kansu kallon ta suke yi cikin tsananin bege da kewa,domin shekaru biyar ba wasa bane, Tabbas suna,domin a jiya gani take tamkar mafarki kawai take yi, Gani suke yanzun da ta bude ido kuma ta tashi zaune sai tai masu girma,sai suke ganin tamkar ba wannan yar kanwar tasu ɓace wacce suke kula da ita a duk lokacin da take tafiya,sai suke ganin tamkar ba ita bace take zama a cikin su suke wasa tare da dariya tare,suke kuma dauke duk wani kuruya da hauka bana,yau sau suke ganin ta fita masu daban tamkar dai an canja ta, Jin hawaye ya sauko daga cikin idanun ta ne yasa tayi sauri saka hannu tana sharewa,sai dai kuma sun kasa tsayawa sai ma ci gaba da zuba da suka ci gaba da yi, A hankali suka ta kowa suna karasowa in da take zaune,gabaɗaya durkusa suka yi a gaban ta suna masu fashewa da kuka, "Dan Allah ki ga farcen mu Salma,tabbas mu masu laifi ne a gare ki,ki yafe mana a matsayin mu na ƴan adam ajizai" Kara share hawayen idonta tayi,lokaci ɗaya kuma tana sakin murmushi tare da dafa hannu su dake saman nata, "A wancan lokacin naji babu dadi sosai musamman idan na tuna wadanda nake tunanin zasu kasance bango a gare ni,su suka fara watsamin kasa a ido,sai naji na ƙara tunzura da son na kuma yin nisa daku sosai, nisa irin wanda kona waiwaya babu abinda zan gani,sai dai cikin ikon Allah sai gashi na dawo farko,sai dai dan Allah ina roƙon ku akan abar abinda daya wuce,zai maida shi tamkar wani mugun mafarki ne dana taɓa yi a cikin barci na,kuma na tashi,dan Allah karku kuma niman yafiyata " Gabaɗaya duk rungume ta suka yi suna masu hawayen farin ciki, "Ina Abdulmalik? " Nan suka shiga bata labarin ai shi ya bada koda aka saka mata dan haka yana ɗayan dakin na kusa da ita" "Yaya amma ya akayi kuka san inda nake? " Ai mijinki ne ya kira Abdulmajid ya faɗa mashi in da kike,sannan yace in zamu zo karmu zo dasu Mama saboda halin da kike ciki,koda zamu faɗa masu mu fara barin kiji sauƙi " Wannan karon ko mamakin ta ne ya kasa boyuwa "ta yaya aka yi ya sanku har ya san number Ya Abdulmajid,sannan ya kira? " Ya ce mana ya san komai akanki har da dalilin barin ki gida" "In ji shi" "Tabbas haka yace ranar da muka iso garin nan" Shiru tayi kawai yayin da zuciyarta ta shiga tunanin dame_dame ya sani game da ita da yake kiran ya san komai game da ita, Katse mata tunani Abdulrahman yayi da fadin "mijin ki mutumin kirki ne,ya karbe mu hannu bibbiyu,ban taɓa tunanin Allah zai haɗa ki da mutumin kirki irin wannan Salma,ya san mutunci da dattako,muna fatan Allah ya bar ku tare" Bata bashi amsa ba sai ma cewa da tayi"ina yake? Hannu Abdulmajid ya saka a Aljihu ya ciro wani Emvelop ƙarami ya mika mata"yace idan kin tashi a baki" Amsa tayi tana warwarewa,tsirama rubutun shi ido tayi,yanda suka kwanta sosai a jikin takarda gwanin ban sha'awa,: *Assalamu alaikum,ina maki fatan samun lafiya mai ɗorewa,tafiya ya kamani,ki kula da kanki*: Kara kallon wasikar tayi tana kara juyawa ko akwai wani rubutun ta baya da bata karanta ba,ganin babu komai ne yasa cikin yatsine fuska tace"Yaya iyakar wasikar kenan? "Eh" Cikin jin haushi ta dangwaran da wasiƙar a durowar wurin, Kallon juna suka yi suna tambayar juna da ido ko lafiya, Jin hayaniya na tashi daga bakin kofa ne yasa suka fita dan su duba ko lafiya, Ganin wanda ke tsaye ne yasa Abdulrahman kallon Abdulmajid "ya zamu yi dashi" Murmushi yayi yada dafa kafadarsa tare da faɗa masa wani maganar a kunni wanda banji ba sai gani nayi shima ya saki murmushi "to ai ba komai" Kallon security wurin sukayi"ku bar shi ya shigo domin shima dan uwa ne" Shi kanshi kallon mamaki yake masu domin bai taba tsammanin jin haka daga bakin suba,ji yayi wani sanyi ya lullube shi. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *77* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Hanya suka buɗa mashi"shigo mana,ka kuma tsaya kamar wani baƙo " Murmushi yayi yana karasowa cikin ɗakin "na gode" Jin muryar shi kaɗai ba ƙaramin saka mata bugun zuciya yayi ba,dan har sai da taji kanta ya sara, Kamar yanda take kallon shi shima haka yake kallon ta,yayin da abubuwa da yawa suke dawo masu, Wani irin abu ne taji ya sauko ya tsaya mata a zuciya,kauda kai tayi gefe,ji take kamar ta ɓace ta bar wurin,bata son tuno wasu abubuwan da suke dawo mata,sai dai tunda har ya kawo kanshi gare ta a wannan lokacin,bai kamata ta nuna gazawar ta ba,zata tayi amfani da wannan damar wurin nuna masu jiya da yau ba ɗaya bane, A hankali ya karaso baki n gadon da take,harshen shi har tuntuɓe yake yi wurin faɗin "Partner ya jikin naki? Sai da tayi tamkar ba zata kula shi ba kafin ta amsa " Alhamdulillah " Ji yayi duk ta kara mashi kwarjini,sai yake jin shakkar yi mata magana kuma,dan gani yake tamkar ba Salman daya sani shekara biyar baya bane,wannan ta daban ce,duk da akan gadon jinya take da ka kalle ta kasan ita din macece mai aji, Ganin ko kallon in da yake ba tayi ba yasa cikin sanyi jiki ya koma ya zauna kan kushin kusa da Abdulmajid da suka yi tamkar basu san da zaman shi ba, "Abdulrahman nace ba,amma idan ta ji sauki zata koma Minna ne tare damu ko? Wani kallon banzar ya watsa mashi" Ban sani ba amma gaka gata ai kana iya tambayarta " Juyawa yayi ya kalle ta sai kuma ya dauke kanshi ba tare daya ce mata komai, A hakan sai da suka yi zaman mintuna Ishirin babu wanda ya ƙara cewa komai,asali ma dakin kamar babu kowa acikin shi, Jin yanda ya tsargu ne yasa ya tashi "zanje na dawo anjima" Babu wanda ya bashi amsa har ya bar ɗakin, Juyowa tayi kansu"Yaya" Dukansu lokaci ɗaya suku amsa suna juyowa, "Kar a ƙara barin shi ya shigo" "Me yasa? Abdulrahman ya tambayeta, " Kodai har yanzun kina son shi ne? Abdulmajid ya ƙara jefa mata wani tambayar, Ji tayi zuciyar na wani irin tafarfasa da suya,ta ma rasa wani amsa ya kamata ta basu,dan haka komawa kawai tayi ta kwanta ta juya masu baya ba tare da tace masu komai ba, Kollo juna suka yi suna tabe baki, Har sun cire rai akan zata sake yi masu magana,sai cewa tayi"yaushe yace zai dawo? "Waye? " Suraj" "Ina ce ya fada maki komai a cikin wasiƙar,' Juyowa tayi daga kwancen da take,cikin shagwabe fuska tace" Yaya,ni dai in kun dai na sona ku tashi ku tafi" Makale dariyar dake taso masu suka yi, "Oh Sorry ba haka bane,ta yaya zamu dai na son hasken idaniyar mu,Kin ga bai faɗa mana komai ba illa fada mana cewar tafiya ta kama shi,sannan ya bamu wasika mu baki" "Amma shine baku hana shi tafiya ba? Wannan karon ko buɗe baki suka yi suna mata kallon mamaki, Ganin kallon da suke mata ne yasa ta kyaf_kyafta idanu tana ɗan turo baki gaba," To me yasa zaku bari ya tafi ya bar ƙanwar ku a kwance rai a hannun Allah? "To me zamu masa? " Well I don't now kawai dai naga bai kamata bane,sannan ko irin ku tambaye shi yaushe zai dawo baku yi ba,I am disappointed with you gay " Da hannu ya nuna ta"you.. Maida kanta tayi ta kwantar tana kulle ido, Ganin daga kulle ido bacce ya kwashe ta ne yasa suka fito suka komawa wurin Abdulmalik, *Bayan Sati Ɗaya* Alhamdulillah jiki ya fara warwarewa dan har ta fara dan takawa,sai dai abubuwa da yawa sun faru koma dai in ce suna kan faruwa,domin kullun sai Yusuf ya zo Asibiti sai dai ba mai hana shi shiga wurin ta,amma in ya shigo kuma babu mai kula shi har ya gaji ya fito,ba zai sa gobe kuma yaki dawowa ba, Kamar yanda suka ma Kaka Alkawarin zasu je,basu samu zuwa ba dan sun roki Suraj ya basu number ta kuma ya basu,Abbulrahman ne ya kira ta da kanshi,ya bata haƙuri akan idan Salma da Abdulmalik sun ji sauki zasu taho tare, Ta yarda kuma tai masu fatan samun sauƙi, Ta bangare Ammi kuwa kullun sai ta zo ta dubata,sai dai kamar yanda bata ce ma Biba komai ba haka ita ma bata ce mata komai ba,jira kawai take ta kara samun karfin jikin ta lokacin zata ji daɗin fuskantar kowa, Babu ma abinda ke bata haushi irin rashin jin Suraj,ko a waya bai nime ta ba,sai dai kawai wani lokaci taga suna waya da daya daga cikin yannin ta,amma ko irin da wasa yace a bata bai yi ba,ai kuwa tana kule dashi,kuma zasu haɗu,dan jira ce take dashi. Washegari da safe tunda ta tashi tayi sallah ta koma ta kwanta, Cikin barci take jin kamar dariya na tashi sama_sama ne yasa a hankali ta shiga buɗe idonun ta,sai dai bata juyo in da suke ba, A hankali take jin wani irin kanshi mai matukar sanyi yana mamaye hancen ta,wanda take da tabbacin a jikin mutum ɗaya ne kawai take jin irin wannan kamshi, Lumshe ido tayi ta buɗe tana jin yanda bugun zuciyarta ke kara karfi wurin harbawa, Kasancewar ta juya masu baya ne yasa basu san da farkawarta ba,a hankali ta juyo tana fuskantar su, Su huɗu ne zaune a cikin kujerun dake zagaye a tsakiyar wani dan madaidaicin charting table, Hira suke yi cikin kwanciyar hankali wanda daga dukkan alamu hiran ba karamin daɗi yake masu ba,dan sai sakin murmushi suke yi,wani lokaci ma har darawa suke yi, Tunda take dashi zata iya cewa bata taba ganin dariyar shi ba,murmushi ma bazata iya tuna when last ta ganshi yana yi ba, Gani tayi ya kara mata tsayi duk da a zaune yake,fuskar shi ta ƙara haske da kyau musamman yanzun da yake dariya,wani lokaci ma har tafawa taga sunayi da Abdulmalik dake zaune a gefen sa, Tun dazun yake jin alamun ajikin shi ana kallon shi, Ita kuma data ga kamar zai kallo in da take sai ta lumshe ido da sauri, Wannan karon shammatar ta yayi dan sai da ya bari ta gama sake jiki sai kawai sintar idanun shi tayi cikin nata tsamo_tsamo, Ga mamakin ta sai gani tayi ya sakar mata murmushi yana mikewa tare da faɗin "kin tashi? Kuma har yanzun idanun shi na cikin nata ne yaki bata damar da zata cire nata idanun saboda wani irin kaifaffen kallo ne yake jinfanta dashi mai kashe gaɓoɓi, Tsayawa yayi a gabanta yayin da hannun shi ke zube a cikin aljihun shi, Gani tayi yannin nata suna fita ɗaya bayan daya tare da jawo masu kofa, Cire idanun nashi yayi cikin nata yana sassauta kallon da yake mata, zama yayi a gefen ta suna fuskantar juna daga kwancen da take, Maida idanun nata tayi ta lumshe, Babu zato taji saukar hannun shi yana zagaye fuskarta,yana kallon yanda take kara matse idanun ta,da gaske bata son buɗe ido ta kalle shi, "Buɗe idan ki" Turo bakin ta tayi tana motsawa a hankali sai dai baya iya jin me take faɗa, "Ina son muyi magana" "Kawai ka fada ina jinka" Ji tayi wani irin sanyayyen sanyi mai haɗe da kamshi yana sauka a saman fuskanta, A hankali ta fara motsa idanun ta kamar zata buɗe,sai kuma tayi kokarin juyawa gefe,sai dai ya riga ya saka hannun shi a gefenta ta yanda ko kaɗan bata da chance din juyawa, Dole bude shanyayyun idanun ta tayi tana daurawa a cikin nashi tare da haɗe fuska,domin ta lura in bata nuna mai har yanzun a Biban ta take ba to ba ƙaramin raini bane zai shiga tsakanin su,😎 Kuma tsabar dai nimar magana duk da ta buɗe idon bai daina busa mata iska ba,abunma har da gaiya,dan ji take kamar zata shede, Babu sallamar ko nimar izinin shigowa kawai ganin shi suka yi ya faɗo cikin dakin kai tsaye,yayin da waya ke makale a kunnen shi yana faɗin "zan dawo mana,in dai wannan ne karka samu damuwa do....... Maganar ta makale ne cikin makoshin shi sakamakon.... Bai ma karasa tunanin dake zuciyar shi ba sai gani kawai yayi ya karasa dan tazaran dake tsanin fuskokin su wanda dama bai wuce inch daya ba, Ita kanta sai da ta shiga Shock da daukewar numfashi domin abune da tunda take dashi bata taba tsammanin haka daga gare shi ba, A nashi bangaren kuwa yaji irin shigowar da yayi,sai dai bai juya ba,bai kuma damu da sanin ko waye ya shigo ba,sai dai ko ma waye yasan darajar niman izini kafin shiga wuri, Daura bakin shi kawai yayi saman nata ba tare da ya tsotsa ba,yayinda idanun su ke yawo a cikin na juna, Bai masan sanda dankareren wayar dake a sakale a kafadarsa ya zame ya faɗi a kasa ba,ji kake tasss karan tarwatsewar wayar, Ji yayi kafafunshi na minan gagaran ɗaukar shi,yayin da numfashin shi ke yi tamkar zai dauke sabar yanda zuciyar shi ke ci da wutar kishi, Cikin zafin rai ya juya ya bar dakin tare da bugo kofar da ƙarfi, Wanda har sai da ya jishi a tsakiyar kanshi, Lumshe idanu yayi yana kokarin cire bakin shi daga nata, Sai dai kuma nan take wani abu ya gefta zuciyar ta wanda yasa babu shiri ta buɗe bakin ta tana kamo lip din shi na kasa tare da sakala hannayen ta duka biyu a wuyan shi,tana kara ci gaba da tsosan bakin shi cikin kwarewa,yayin da idanun su ke cikin na juna........ 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *78* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Wannan karon ma kamar waccan karon ne dan ko kaɗan bai da ba gudunmawa ba,sai ma hannun ta daya zame a hankali daga saman wuyan shi yana cire bakin shi a cikin nata, Kallon sakon biyar ya mata sannan ya mike tsaye yana sai-saita natsuwarsa, "Me kike son faɗa min a wancan ranar? Kauda idanunta tayi daga cikin nashi" Duk abinda kake son sani ka duba a cikin waya ta " Gani tayi ya zari Tissue paper dake ajiye ya shiga goge lips din shi dashi a hankali yana yi yana Kollon ta kamar yanda ita ma ta buɗe idanu tana kallon shi, "Wannan ya zamo karo na karshe da zaki ƙara aikatamin haka ba tare da izini na ba" Maganar tasa ta zo mata a bazata,tare da yanayin action din shi,bata taɓa tunanin yau har a kwai namijin da zaiji Kyankyamin haɗa baki da ita ba,har yakai ga matakin goge bakin, duk da cewa duk Kiss din da take ma shi aciki babu wanda tayi masa domin nishaɗi,,duka da gaiya take yi masa su,duk da takanji shi a jikinta kasancewarsa lafiyayyen namiji,ko yanzun tayi masa haka ne kawai saboda ta san yanda baya son ta rabi jikin shi,sannan gashi har da kanshi dan ya kuntata ma wani shine yake iya daura lip din shi saman nata,shi yasa ta kara sa masa amma ba wai dan wani manufa ba sai dan kawai taga wani yanayi zai shiga, Nan take taji zuciyarta ta raunana,yayinda kalamansa da Action dinsa suka mata zafi fiye da komai a wannan lokacin, har tana jin idanun ta na kawo hawayen bacin rai wanda bata basu damar sun sauka ba, "Bana bukatar izinin ka domin aikata abinda nake so" Kallon ta yayi yanda take kokarin shanye hawayen idanun ta, "Ina Alkawarin da kamin a ƙoto?yau ina son ka bani takardar saki na,domin duk wani abu dake tsakanin mu ya riga ya kare tun a koto" Jin yayi shiru ba shida alamun bata amsa ne yasa ta dago kai tana kallon shi, Kauda kai yayi daga kallon ta yana dosar kofar fita"har yanzun da saura dan bai riga ya kare ba," Dafa hannun kofa yayi ya juyo yana kallon ta"nan da kwana biyu idan an sallame ki zaki koma wurin Ammi har zuwa sanda komai zai kammala,idan yaso daga baya sai nayi tunanin yanda zan yi dake"yana gama faɗin haka ya fita tare da rufo mata ƙofa, Hawayen da take rikewa ne ya koma kuka jin abinda yace"wallahi baka isa ba,babu inda zan kona,garin mu zan wuce,baka isa kace sai ka yi tunanin yanda zakayi dani ba tunda ni ba kaya bane,kuma sai ka sake ni dan rainin hankali "ta faɗa cikin jin zafin abinda yayi mata yanzun,Allah ma ya sota ba kaunar shi take yi ba balle ta mutu da takaici,dan haka rabuwa dashi ya zama dole ko yana so ko baya so. __________yana fitowa ɗakin ajiyar zuciya ya sauke,yana dan yatsine fuska,dakin da suke zaune yayi noking tare da sallamah, Amsawa suka yi yayin da Abdulmalik ke yar dariya kasa_kasa, "Yayan mu me kake ma dariya? Kafin ya bashi amsa sai gani kawai suka yi ya shigo a harzike har wani huci yake yi, " Kai karamin dan iska ne,domin a iskan cin ma baka taka kara ka karye ba,har ni zaka nuna ma salon duniyanci?ni!!!! Giran ya dage yana mashi kallon kai kuma wanene "Malam daga dukkan alamu kana da ƙarancin ilimin addini,da tarbiya"Juyawa yayi in da suke" Ni zan wuce sai mun yi waya" A tare suka mai addu'ar Allah ya tsare, Ganin da gaske kokarin gefta shi yake yi ne yasa cikin kasa dai-daita fushi ya finciko shi baya"ina kake tunanin zaka je,"kafin yace zai bashi amsa sai jin saukar naushi yayi a gefen cikin shi,from no where, A tsaye yake amma bai san sanda ya dafe wurin ba yana dukawa,domin nan take yaji wani irin jiri na daukar idanun shi tare da raɗaɗi, Cikin tashin hankali da gigita sukayo kanshi suna ƙoƙarin daga shi,sai dai ya kasa mikewa tsaye sosai yana dafe da gefen cikin shi, Lafiyayyen Mari Abdulrahman ya sauke mashi yana cakumar kwalar shi"ban taba sanin har yanzun ba kada hankali ba sai yau,so kake ka kashe shi? "Idan na kashe shi sai me?me zaku iya yi?ka sani gabaɗayan ku a tafin hannu na kuke,? Ganin yanda su Abdulmajid suka tallaboshi suna ƙoƙarin zaunar dashi kan kushin ne yasa ya nuna shi da yatsa" A haka kuke tunanin zai iya da kanwarku da take harija?a haka?naushi daya ne fa na masa amma duba yanda ya zama kamar wanda na ma dukkan mutuwa,"fisgar kanshi yayi daga hannun Abdulrahman yana ƙara kallon shi yanda yake sauke numfashi yana dan rintse idanu "ka sani kafin ka san komai na jikin ta na riga ka sani,kuma Salma har yanzun ni take so ba wani raggo irin ka ba,bari ma na faɗa maku abinda baku sani ba,tun wancan lokacin a shekaron biyar da suka wuce na maida auren mu da Salma,tun kafin ta gama iddah k...... Basu san tashi shi ba domin hankalinsu nakan wannan mummunan zancen da yake kokarin bijiro da shi, Sai ganin shi kawai suka yi shake da wuyan Yusif din,wanda yaji nan take numfashin ahi na ƙoƙarin barin gangar jikinsa, Buga bayan shi yayi da jikin bango yayin da yake mashi kallon sama da kasa,"na lura har yanzun you are stuck in that fucking five years,sannan ka sani wannan ya zamo karo na karshe a rayuwar ka da zaka ƙara fadin irin makamanciyar wannan maganar a kanta, Ganin da gaske kokarin suma yake yi ne yasa suka cire shi a hannun ahi,nan take ya shiga tarin wahala yana shafa wuya,bai taba tsammanin yaron yanada karfin da zai iya shake mai makoshi lokaci ɗaya yaji kamar zai mutu ba sai yau,shi kadai yasan irin shakar da yasha,shi kaɗai yasan irin wutar fitinar da ya hango a cikin idanun yaron, Ganin ya kara mikewa kamar zai yi kanshi ne yasa cikin sauri ya buɗe ƙofar dakin ya fita,yana shafa wuya, Kara zaunar dashi Abdulmajid yayi suna kallon yanda yake huci dan yau mutumin ba karamin kona mashi rai kalamanshi suka yi ba,wallahi ba shi ba da yake yi dan ita,har ta da ita sai ya hukunta,kyaleta kawai yake yi amma bari ta ji sauƙi, Dafa kafadarshi Abdulmalik yayi"dan Allah ka yi hakuri ka sassauta ma zuciyarka ko dan lafiyar ka,kaga yanzun ma jini na fita ya kamata muje a duba wurin in ba wata matsala" "Haka ne," Busar da iska yayi yana lunshe birkitattun idanun shi da lokaci ɗaya suka canja daga farin da suke zuwa yanayin jaja,kallon idanun shi ma kaɗai ya isa ya sanar da kai irin tafasar da yake yi a ciki, "A'a I am ok,nan da mintuna goma jirgin mu zai tashi,idan na je can zan ci gaba da ganin likita domin na ma Grandma alkawari" Duk shiru suka yi ba dan sun so ba"dan Allah kayi haƙuri" Dan murmushi ya sakar masu ganin yanda duk hankalin su ya tashi, "Karku damu babu wani matsala"ya fada yana kiran waya akan a kawo mashi wani riga,yana gama canjawa ya mike ya masu sallamah, " Mu je mu raka kanin mu" Gyaɗa mashi kai kawai yayi,tare suka fito har wurin parking,yana ƙoƙarin shiga mota ya dakata yana juyowa "dan Allah kar a kara barin shi ya shiga inda take" Tare suka saki murmushi domin sun fahimce wanda yake nufi, "karka samu damuwa" Koda ya shiga motar ma jin jinginar da kanshi yayi yana rintse ido tare da dafe wurin,sai dai duk irin raɗaɗin da wurin yake masa idan har ya tuna kalaman Yusuf akanta sai yaji raɗaɗin zuciyarsa ta shafe wannan, Cikin kankanin lokaci suka isa Airport, Niman wuri yayi ya zauna yayin da daya daga cikin security din shi ne ke kokarin kammala masa abinda ba'a rasa ba, ___________Asibitin kuwa, Suna ganin motar ta bar harabar Asibitin suka koma ciki,sai dai wannan lokacin ɗakin da take ciki suka nufa kai tsaye, Jin shigowar su ne yasa da sauri ta shiga share hawayen da ke idanun ta, "Umm hmm kukan rabuwa da masoyi ake yi?Abdulmalik ya faɗa da sigar zolaya, Zama kusa da ita Abdulrahman yayi yana mika mata waya" Karɓi ki kira shi " Dago jikakkun idanun ta tayi a kanshi"waye ?ta tambaya kamar bata gane wa yake nufi ba, "Mijinki,domin sun samu matsala da Yusuf yanzun nan,kuma ya tafi ranshi a matukar ɓace duk da bai nuna ba,sannan ki faɗa masa ya kula da kansa dan Allah sosai" Kallon mamaki take mai yanda yake zaro mata zance"to me yasa zan faɗa masa haka? "Saboda mijin ki ne,kuma akanki komai ya faru,ni dai sam hankali na bai kwanta ba da yanayin da yake ciki" "Yaya to ni baka ga yanayin da nake ciki bane na bacin rai,ai Allah ne ma ya kama min shi" Ta faɗa tana juya masu baya, Ranshi ne yaji ya fara ɓaci dan haka cikin yanayin fada_faɗa yace"kin san halin da yake ciki kuwa,wai me yasa har yanzun ba zaki nuna mana cewar kin yi hankali ba,mijin ki ne fa,karki saka raina ya baci dake a yanxun " Kukan da take kokarin rikewa ne ya kucce mata,ai kuwa nan ta shiga rerawa,domin abin ya mata yawa a cewar ta,ga mari ga tsinka jakka,bayan yanzun ya gama gasa mata maganar banza,sannan kuma shi dan an bata mashi rai sai su zo suce sai ta kira shi, Dafe goshi yayi yana mikewa tare da barin ɗakin, Abdulmajid ne ya dawo gabanta tare da rike mata hannu, Cikin kuka tana ƙoƙarin kwace hannun ta daga cikin nashi tace"kunfi son shi yanzun a kai na" Share mata hawaye yayi "ke din yar uwarmu ce,abin Alfaharin mu,ki sani babu wani wanda muke so sama dake,kawai dai ba muso son da muke maki ya rufe mana ido ya hanamu dauraki a kan hanya madaidaiciya,shi din mijin ki ne,wanda ya samu rauni saboda ke,ki sani abinda ya maki ba kowa bane zai iya yi maki shi a rayuwa,ko da kuwa mu da muke yannin ki,shi yasa ba mu so ki yi wani abun da zai nuna rashin godiya ko girmamawa a gare shi,dan Allah kiyi yanda muka ce" Turo baki ta shiga yi"me yamin wanda ku baku min ba?kuma bancin haka ai kome yayi ni ban sa shiba" "Na dai ji,amma dan Allah ga wayar ki kira shi,"ya faɗa yana daura mata waya a hannu ya tashi suka fita shi da Abdulmalik, Share hawayen fuskarta tayi tana jan hanci,bala'in haushin shi take ji,Allah ma ya gani zata kira shi ne kawai saboda su ba dan shi ba, Kiran number dake saman wayar tayi,sai da yayi ringin biyu sannan aka ɗauka, Ji tayi cikin sanyin murya wanda yafi na ko wani lokaci sanyi yayi sallamah, Ɓoyayyen ajiyar zuciya ta sauke tana kumbura baki tare da amsawa ciki_ciki kamar wacce aka shake ma mako shi, Shiru yayi bai ƙara cewa komai ba yayin da yake sauraren yanda take sauke ajiyar zuciya akai akai, "Har yanzun baki gama kukan ba ne? Ya faɗa a hankali tamkar mai raɗa,wanda da ba dan wayar tana akan kunnen ta bane da bata ji me yace ba, " Baka kai matsayin da zan maka kuka ba" "Abinda kika kira ki faɗa min kenan? Ji tayi wani abu mai kama da ɓacin rai ya mata tsaye a wuya,ta rasa wani irin raini hankali Suraj ke dashi, Cikin jin haushi tace" A'a,sako na kira na faɗa maka,wai ance in ce ka kula da kanka"tana gama fadar haka ta yanke kiran ba tare data jira jin ta bakin shi ba dan karma ya ƙara sako mata wani abun bacin ran, Jin ta katse kiran ne yasa ya sauke wayar yana dan lumshe ido"marakunyar ƙarya"ya faɗa a ranshi yana mikewa jin an sanar da lokacin shigar su jirgi yayi........ 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *79* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* *Bayan Kwana biyar* Tun daga wannan lokacin bata ƙara saka shi a ido ba har yar yau da aka sallame ta, Suna cikin motar da zai maida su gida sai gani tayi sun doshi hanyar gida kaka Da sauri ta juyowa"Yaya ina ce Airport zamu wuce daga Asibiti? "Me zamu yi a Airport?Abdulmalik ya mai da mata da tambayar, " Gida mana,ina ɗauka Minna zamu koma a yau" Wannan karon Abdulrahman ne ya bata amsa"mijinki ya buƙaci da a maida ke wurin mahaifiyar sa kafin ya dawo" "To ku kuma fa? " Mu yanzun haka jirgim mu na kasa zuwa ƙarfe hudu zamu wuce" Aikuwa kamin ya gama rufe baki ta fashe da kuka tana kankame hannun shi"ni dai wallahi ban yarda ba,babu in da zaku je ku barni,kafar ku ƙafa na,babu in da zan zauna ni gida zan je," Shafa kanta yayi shima yana jin babu daɗi a ranshi,dan maganar gaskiya yaso su wuce da ita,sai dai ba zai iya rokon Suraj wannan alfarmar ba,ya lura yana da dalilin yin haka,sannan ko wannan Alfarmar daya masu na sake kasancewa da ƙanwarsu ai ya masu, "Ki ƙwantar da hankalin ki,ai ba cewa akayi ba zaki je gidan ba,cewa yayi ki jira shi idan ya dawo sai ku taho tare" Girgiza kai ta shiga yi tana cigaba kuka"ni dai a'a,yaushe ma nasan sanda zai dawo, Yaya dan Allah ku tafi dani,ina son in ga Mama da su Baba dan Allah " Yanda take kuka kuma duk sai ta tashi hankalin su,nan suka shiga lallashi amma sam ta nuna bata san da wannan yaren ba, Koda motar tayi parkin a harabar gidan fita kawai tayi wuce shiyan Ammi ta bar su nan tsaye sake da baki suna kallon ta, Ko da ta shiga falon Amira ce kawai zaune dan ita ko lura da ita bata yi ba ta shige dakinta na da tana kullo kofar har da saka key tana ci gaba da kuka, Ya Abdulrahman "baka ganin ya kamata muma Suraj magana yayi haƙuri ya bari mu tafi da Salma? " Me yasa? "Wallahi ta bala'in bani tausayi,na tabbatar da tana jin kewar su Mama ne sosai kuma ta saka ran da ganin su" Ajiyar zuciya ya saukar"ba zamu bari son kanmu yayi tasiri a zuciyar mu ba,na tabbatar tunda ya faɗi haka yana da dalili,kuma tunda har ya iya kawomu gare ta na tabbatar da zai kai ta gare mu ita ma,dan haka mu ƙara haƙuri" Ganin wasu yan mata na ƙoƙarin geftawa ne yasa ya dan daga murya kaɗan yana faɗin "Assalamu Alaikum" Juyowa suka yi suna amsawa, "Muje su mana jagora cikin gidan" Kallon samarin dake doso su suka yi "Bilki kamar yannin Biba" "Ta yaya kikasan ko sune? " Saboda ban manta fuskar na tsakiyar ba" Kallon shi da kyau Khadija tayi tana dan mun tsinin ta"ya haɗu " Juya ido tayi tana "ke ba haka nake nufi ba" Suna karasowa,gaida su suka yi kafin tace "wa kuke nima? Abdulmajid dake tsakiya ne ta bata amsa" Ko zaku mana jagora zuwa wurin kaka" "Eh babu matsala mu je" Suna baya ƴan matan na gaba har shiyan Kaka, Tsayawa suka yi a ƙofa har sai da suka shiga suka nimar masu izini wurin kaka, "Wai ku shigo" Cewar Khadijah data fito, Ita kaɗai ce a ɗakin sai su Balki da ke ciki tare da Nafisa,suma suna cikin gaisawa da Kakan suka fito suka wuce daga dukkan alamu wani wurin zasu, "Ya masu jikin?ta tambaya, " Duk sunji sauki Kaka,dan ita Salma ma ina ga tana shiyan Ammi" "Hakan yayi Allah ya ƙara masu lafiya"Abincin dake gabansu wanda Nafisa ta kawo ta nuna masu" Kuci Abinci " "To Kaka mun gode" Sun san halin tsofaffi basu son su baka abu kaki ci,dan haka suka buɗe kulolin wanda lafiyayyen dambun shinkafa ne a ciki yaji kayan haɗi, Dama shi Abdulmajid yana matukar son dambu,dan haka ko suka ci kaɗan shi ya karasa sauran sannan ta kora da ruwa, Dariya kaka ke masa ganin yanda ya keta santin dambun,har da tambayarsa ko a karo masa, Yace ta ko shi, Sun dan jima a gidan kaɗan sai da suka bata labarin duk abinda ya faru,sai dai kuma ba komai suka faɗa mata ba saboda wannan sirrin Ahalinsu ne,wanda suke fatan ya kasance a binne har abada, Sai dai basu ɓoye mata batun auren Yusuf da ita Salman ba, Da zasu tafi ta rako su har bakin falo,duk da sun so tayi zamanta saboda ƙafar ta, Sawa tayi Nafisa ta kai su shiyan Ammi, Nan ma sai da akai masu iso sannan suka shiga,ita sai lokacin ma ta san cewar Salma na gidan, Basu wani jima a shiyan ba suka tashi zasu tafi,bayan Ammi ta masu Alkawarin zuwa har gida idan Suraj ya kammala abinda yake yi zasu taho tare da Biba, "Bari na kira naku ita kuyi sallamah" "A'a Ammi ki bar ta domin wani rigimar zata saka" "To shikenan" Ita ma ta rakasu bayan Alkhairin data masu sosai ga kuma na Kaka da suka samu shima,gaskiya hankalin su ya kwanta sosai da mutanen. Bayan tafiyar su ne Ammi ta nufi kofar dakin ta,ƙwanƙwasawa ta shiga yi a hankali tana kiran sunan ta, Jin muryar Ammi ne yasa dole ta taso tazo ta buɗe ƙofar tana kauda kanta gefe,dan bata son Ammi taga waɗannan kumburarrun idanun, Murmushi tayi tana karasa shiga tare da zama a gefen gado,nuna mata kusa da ita tayi"zo ki zauna" A hankali take takowa kanta a kasa dan Allah ya gani tana girmama matar kuma kunyar ta take ji, A maimakon zama saman gadon in da ta nuna mata sai zaunawa tayi a kasa kusa da ƙafafunta,cikin sanyin murya tace"Ammi ina wuni" "Lafiya qlau Salma ya jikin naki" "Da sauƙi" Ta faɗa tana share hawayen da yaki tsayawa, "Har yanzun kukan ne? Ita dai shiru tayi bata bata amsa ba, Hannun ta tari ko cikin nata,cikin kwantar da murya irin na wanda ake rarrashi ta shiga yi mata nasiha mai ratsa jiki,akan Kaddara da kuma yarda da ita" Kaddara wata aba ce da Ubangiji ke Daura ma bawa domin ya gwada karfin imanin shi,Salma duk wani bawa mai imani da zaki gani a ɗoron duniya tabbas yana fuskantar tashi ƙaddarar,wani za'a jarabce shine ta hanyar Ya'yan shi,wasu ta Matan shi,wasu kuma ta yan uwa ko ya'yan yan'uwa ko kuma miji, Duka dame zamu kira shi?kaddara wanda muke fatan mu cinye ta hanya mai kyau, Ke Allah ya jarabce kine ta hanyoyi uku,na faro mijin ki,na biyu mahaifinki,na uku kuma mahaifiyar ki,amma sai gashi a lokacin daya kin manta da Allah da ya jarabce ki yana sane dake ba kuma ya manta dake bane,kin zabi hanyar saba mashi,a maimakon komawa gare shi,kin manta cewar duk in da kika je kika dawo dole wurin shi zaki koma in da yake jiran ki a madaka domin amsa tambayoyi,kin yi zina,me zaki ce masa akan haka Salma,idan da ace a wancan ranar kin mutu ba tare da kin tuba ba me zaki ce masa Salma? Lallai Allah yana son ki da rahama da har ya nufe ki da tashi ba tare da kin samu wani nakaso ba,wannan na nuna wata dama ce da Ubangiji ya kara baki domin ganin kin share wannan kuskuren da kika aikata,shin me zaki yi game da haka? Ina mai baki shawara da ki yi gaggawar watsar da komai ki fuskanci rayuwarki,ki kuma ga Allah ki nime yafiyar shi,domin shi gwanine a fagen yafiya,ki dage da yin istigfari ina ganin hakan zai fi idan har kika karɓi kaddara ki da hannu biyu" Tunda Ammi ta fara magana take kuka tana kuma auna kuraruran ta da lafukanta, Rungume Ammin tayi tana ci gaba da kuka"tabbas na aikata laifi mai tarin yawa wanda na aikata cikin sani ba cikin rashin sani ba,domin rufewar ido dana zuciya,ina ganin tamkar babu wani wanda yake cikin kuncin rayuwa sama dani,shin kina ganin idan na nime yafiyar Allah zai yafe min? "Me zai hana,ai shi Allah mai yin gafara ne,dan haka zai gafarta maki,ke dai kawai ki tsarkake zuciyar ki,ki kuma tabbatar ba zaki ƙara komama zunu banki ba" "Nayi Alkawari Ammi,in sha Allah daga yau na cire komai a raina,sai dai kuma VIP,ba lallai bane ya barni,sannan Suraj.... Yatsa ta saka mata a baki," Karki damu da wannan domin Suraj zai ji da komai" "Ta yaya aka yi kuka san da batun VIP Ammi,naga shima Suraj yawancin abubuwa baya mamaki a kansu,sannan dama kin san da aikin da ya kawo ni gidan nan tun farko me yasa kika amshe ni?sannan ya akayi kika sani? Murmushi mai ciyo a saki,wanda iyakar shi fatan bakin ta, " Abu ne da aka fara shekaru goma sha ɗaya data wuce,har i zuwa yau,kin ga mu ba abin mamaki bane a gare mu,har balle kamar yanda suke tunanin sun san ko wani motsi na mu,to muma kusan haka ne,duk da ba duka ba, Tun kafin zuwan ki wannan gidan nasan da batun turo ki,a lokacin da suke niman har yar shigo dake cikin gidan a lokaci na basu hanya ta hanyar zubar da man gyada na zame har samu targade a kafa,ta hakan ne suka samu damar shigo dake, Sun saka kina masu aiki cikin duhu ba tare da sun san ta gefe ɗaya muna muna amfani dake ba,nasan ba zaki manta wanda ya kiraki yake shaida maki ki yi maza ki bar Legas ki koma Abuja domin rayuwar Ummita na a cikin hatsari,tabbas shima yaron mijin ki ne,wanda yake bibiyar dum wani motsi nasu har ma da naki, Sannan shi karan kanshi wanda yake saka ki aiki da sunan VIP,da kuma mutanen dake zagaye dashi dukansu yanzun a tafin hannun mu suke,Domin yanzun Kaka ta farka,dama ita ce cikon shaidar mu,kuma ta tashi," Tunda Ammi ta fara magana ta kafe ta da ido,cikin tsananin mamaki,wato a cikin wannan wasan dai ita ce katin wasan da kowa ke bugawa yanda yaga dama ba tare da sanin ta ba,"da yaushe ta tashi" "Ranar da za'a maki aiki,yanzun haka mijin ki na can" Lumshe ido tayi ta buɗe "baki bani amsar yanda akayi kija sanni ba,har kome dan gane dani,ina son sanin komai" "Zaki sani sai dai ba yanzun ba,amma na maki Alƙawarin zan warware maki komai a gaban mahaifiyar ki,a lokacin da muka haɗu,sannan nan da kwana Takwas da za'a shiga ƙoto domin Kaka ta shigar da kara a yanzun haka,amma a London za'a yi shari'ar domin a can komai ya faro" "Amma an kama su ne? " Ummm to wannan dai yana hannun mijin ki,sai yanda ya tsara,amma a nasu bangaren basu san yasan komai ba" "Ammi please waye VIP" Ta tambaya tana tsare ta da ido, Girgiza mata kai tayi"bana ce ba,amma mu jira har zuwa lokacin da za'a shiga kotu,da idanun ki zaki ga ko ma waye,dan idan na faɗa maki ba lallai ki iya yarda ba" Tana shirin ƙara jeho mata wani tambayar ta Daura mata yatsa a baki"shiiii no more question,sannan da zaran kome ya kare zamu mai da ke gida,sai dai ina son in zaki koma ki koma cikin mutunci da kyawun gani,dan haka zuwa anjima zamu fara kyaran jikin ki"tana gama fadar haka ta tashi ta fita tana kara jawo mata ƙofa, Gabaɗaya zuciyarta bata mata daɗi,wato a wannan wasan ita ce a tsakiya,kuma a duhu,amfani dukan su biyu suka yi da ita wurin cin ma burin su harda Suraj,wato tun farko yasan komai,gashi sanadin wannan wasan nasu Ummita ta rasa rayuwar ta har abada,ita ma kuma Allah ne yayi da sauran shan ruwan ta a duniya,da yanzun kuma ba wannan labarin ake yi ba,ita ce babbar mai asara a cikin su,domin ta baro gidan su da komai nata,ta kuma zabe hanyar da take ganin zai fi mata sauki bata san rami take tura kanta ba, Amma babu komai ko yanzun ta koyi darasi a kan wannan aikin,dan haka zata bi shawarar Ammi ta koma ga Allah da niman tuba,sannan da an gama wannan shari'ar zata koma gida taci gaba da rayuwar ta cikin yannin ta da iyayenta,zata manta da komai ta fara gina sabuwar rayuwar ta, Da wannan tunanin ta tsayar da zuciyar ta wuri ɗaya....... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *80* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Da Sallamah ta shigo dakin hannun ta rike da tiren kuloli,ajiyewa tayi a gefe ba tare data ce mata komai ba,ita ma din dai tana zaune ne a in da Ammi ta barta tun dazu, Ganin har tana shirin fita bata dago ta kalle ta ba yasa ta ɗan dakata"ya jikin naki? Kara kauda kai tayi tana kwantar dashi saman gado "da sauki" "Allah ƙara lafiya" Ta faɗa tana fita,ita a da bata son Biba ko kadan tunda ta aure yayan ta,kuma ba tada ilimi,sai gashi cikin lokaci ƙanƙani ta shayar dasu mamaki,ashe da gaskiyar hausawa da suke cewa duk yanda kake ganin mutum karka taba raina shi saboda baka San irin baiwar da Allah ya mai ba. Bata maci abincin ba sai da tayi barci ta tashi,sannan ta watsa ruwa,ganin lokacin sallah la'asar yayi ne yasa ta dauro Alwallah tayi sallah,ko da ta idar zaman yin istigfari tayi,har kusan ƙarfe biyar da wani abu,sannan ta shafa addu'a ta tashi,dan sau biyu Ammi na aikowa a leko ko ta gama,sai da ta ci abinci sannan ta fita,ganin bata falo ne yasa ta nufe dakin ta, Sallamah ta yi,daga ciki aka amsa tare da tambayar"Biba ce" "Eh ni ce" "Shigo" Shigowa tayi,nuna mata kan kushin tayi "zauna" Zaunawa tayu tana kare ma dakin kallo wanda yake a kyare tsaf a ko wani lokaci,ga kamshe mai ni'ima da ke tashi,domin Ammi macece mai matukar tsafta da son kamshi, Wani dan karamin jakka ta dauko ta zauna kusa da ita tana fito da kayan dake cikin jakkan, Wasu madaidaitan robobi ne masu kyau a ajiye a gabanta, Nuna mata su ta shiga yi data bayan daya, Wannan sabulun wanka ne,dashi zaki rinka yin wanka,wannan kuma man shafawa ne,sai wannan shi kuma zaki dinga cire kwaya daya kina sha ɗaya da safe daya da yamma,wannan kuma ki maida shi ruwan shanki,ba shida wani illa ko side effect,sai wannan turaren da shi kuma na tsugunnawa ne sai na jiki,a duk lokacin da zaki yi amfani dashi za'a kawo maki kaskon,dan Allah ki dage ki yi yanda nace,wanda baki gane ba zaki ga komai a rubuce "ta faɗa tana maida su cikin jakkan tare da mika mata, Amsa tayi" Na gode sosai Ammi" "Ki yi ƙoƙari ki shiga ki gaida Kaka" "To" Ta fada tana tashi, Daki ta kai kayan ta ajiye sannan ta ɗauki ƙaramin hijabi ta saka sannan ta fita, A hankali take takawa dan ji take kamar iska zai dauke ta saboda rashin nauyin jiki, Tana dab da shiga shi yana taji an riƙo mata hannu, Zabura tayi tana dan matsawa baya kaɗan dan ta dan tsorata, "Oh Sorry na baki tsoro " Kallon shi take yi tare da kokarin janye hannun ta,sai dai yaƙi saki, "me haka Nurudeen sake min hannu" Ajiyar zuciya ya sauke"Thank God baki manta suna na ba" "Ka sake ni bana son haka,idan wani ya ganmu fa" "Ai nafi son ma a ganmu kin ga sai a saka wannan hoton mijin naki ya sake ki ni kuma na aure ki" Daga bayan su suka yi an ce"sakar mata hannu" Duk juyawa suka yi,ganin wanda yayi maganar ne yasa da sauri ya sakar mata hannu, Ba tare data ƙara kallon su ba ta saka kai ta shige, Ita gabaɗaya daga shi Nurudeen din har Shamsuddeen,tun lokacin da shi Shamsuddeen din ya bada shaidar karya a gaban su kaka a kan ita da Suraj ta ji ya fita ranta,ɗan girman da take ganin shi dashi duk ta zube, Da fara'a Kaka ta tare ta "Habiba ya jikin naki" Zama tayi kusa da ita"na ji sauki Kaka sai kewar ki da nake yi" Dariya tayi "ke dai faɗi gaskiya,ko dai kewar mijin ki kike yi" Nan take ta bata fuska tana shirin yin magana kenan suka haɗa ido Maijiddarh dake zaune, Nan take ta canja salo zuwa yanayin shagwaba "ban cin ya tafi ya barni da kewar shi,ni fushi nake dashi" Dariya kaka ta saka"ke da ba kida lafiya ina zai dauke ki yai ta yawo dake"wayar ta dake gefe ne ya shiga ƙara,ɗauka tayi tana miƙa ma ta"dubamin wake kira,dan ban fito da Glass ba, Ganin sunan me kira kaɗai sai da yasa zuciyar ta girgiza"Suraj ne" "Yauwa dan Halak ke nan,to ɗauki wayar" Girgiza kai tayi"A'a ai ke ya kira,ni kin ga ma bari naje amma anjima zan dawo " Karɓa tayi tana karawa a kunne tana dariya, Daga can ɓangaren yake tambayar "kaka dariyar me kike yi" "Ni da matar ka mana,wai fushi take da kai" Dan murmushi ta saki "me tace na mata? " Ka kira ta ka tambaye ta" Dariya yayi "ke dai na baki wannan damar ki lallasar min ita" "Ja'iri ya jikin Nana A'isha" "Da sauƙi,gata ku gaisa"ya faɗa yana karama Kakar shi wayar a kunne, _________kwance take saman gado tana rusar kuka,tunda ta dawo shiyan kaka yanzun kusan mintuna talatin kenan tana abu daya,babu abinda yake kara tada mata hankali shine ganin yanda Biba ta zama jaruma akan idanun kowa, Jin shigowar Momy bai sa ta tsagaita daga kukan da take yi ba, Zama tayi a bakin gadon tana dagota "zauna muyi magana" Kokarin komawa kwance take yi"ni dai ki kyale ni,babu wani maganar da zamu yi da ke" Wannan karon cikin jin haushi ta ce"idan baki saurare ni ba ta yaya zamu samu mafita? Ƙara dagota zaune tayi, "Yanzun shi Yusuf ya kuke ciki akan maganar shi? Jan majina tayi tana sheshsheka"idan na kira wayar shi baya ɗauka,karshe ma sai turomin saƙo yayi cewar ni ba iri ajin shi bace,saboda ya lura ni ban waye ba ban San Me duniya ke ciki ba," "Tsinanne,shi har ya isa yace haka akanki,ki kyale shi shi yake da asara" Kara fashewa tayi da kuka"ni yanzun shi kenan haka zan zauna ban yi aure ba,shi kenan nayi Two Zero,gashi Suraj yayi min nisa ko ganin shi bana samun damar yi,har Gara da,wallahi Momy kin cuce ni duk ke kika lalata komai " Tama rasa me zata ce mata,wani shawara ya kamata ta bata wanda zuciyar ta zai yi sanyi,tun ba yanzun ba ta san cewar ta kwafsa da ya,sai dai bata son ta nuna gazawarta a gaban yar ta,"kin ga kiyi haƙuri bari zan kira Atika zamu samu mafita"a haka ta samu ta shawo kanta da kyar ta yi shiru. *Bayan sati ɗaya* A cikin kwanaki bakwai idan ka ga Biba kallo daya zaka mata ka shaida tabbas ta dawo haiyacinta,ta kuma koma asalin Biban ta, Domin duk wani rama da kodewa da tayi sai da ta ciko, Ammi kullun cikin bata haɗin danyen madara da na namar kaza take,gashi man da ta bata ya taimaka wurin goge mata fatar jiki,dan har wani tsantsi take yi,cikin turarukan da take sawa tayi har da gashi, ita karan kanta wani lokaci idan ta kalli kanta a madubi tana jinjina ma kayan tare da mamakin in da Ammi ta samo su,dan wani irin fitinannan kanshi ke fita a jinta wanda hatta fitsari idan tayi shi ji take a ciki,har mamaki matsewarta take yi,dan ko kaɗan yatsar ta bai iya wuce kofar wurin,ga wani irin ruwa sake fita,wani lokaci har tsoro abin ke bata yanda yake fita,ita karan kanta ta san ta samu canji da yawa a jikin ta,farin ta ya karu fiye da da,har wani kashe ido take da ƙyalli na musamman,lallai bata san da wani baki ya kamata ta gode ma Ammi ba,babu in da take zuwa sai gaida Kaka sai kuma zaman istigfari wanda a yanzun yawancin lokuta zaka ganta da ƙaramin charbi irin mai batir din nan tana dannawa. Ammi ce ta buɗe ƙofar ta shigo "har yanzun baki kammala shiryawa ba,kin san saura yan mintuna jirginmu ya tashi" Juyowa tayi fuskarta dauke da murmushi "na kammala Ammi yanzun takalmi kawai zan saka" "To ki yi sauri dai dan ke kadai muke jira"ta ƙarasa faɗa tana fita, "To" Ita da Ammi ne kawai zasu tafi,dan Amira zata zauna ne a wurin Goggon yara,dan haka Shamsuddeen shi ya kai su har Airport bayan sunyi sallamah da su Kaka, Ko lokacin da jirgi ke lulawa sararin samaniya lumshe ido tayi tana jero addu'a,kwata-kwata bana jin yin wannan tafiyar,ba dan komai ba sai don bata son haɗuwa dashi,ita da ma ace za'abi nata da Ammi ta barta anan idan har aka gama shari'ar sai su dawo su mai da ita gida,sam bata shirya tarbon wulakanci ba irin nashi,ta tabbatar idan har sun haɗu sai yayi abinda zai ɓata mata rai sannan hankalin shi yake kwanciya, Ganin tunanin yana ƙoƙarin yi mata yawa ne yasa ta maida hankalin ta wurin jan charbin da take yi,daga haka har bacci ya kwashe ta, Sai da jirgin su ya sauka sannan Ammi ta tayar da ita suka fito,wani irin sanyi ake yi mai matukar shiga jiki da ratsa kashi,Glass din dake cikin jakkanta ta ciro ta saka a idon ta,wanda ba karamin kyau da ƙara fito da ita yayi ba,dama gashi riga da Siket ne na Atamfa a jikin ta mai kalan ja,sai After dress data saka fara tas mai tsansi shara_shara mara nauyi,sai karamin jakka mai dogon tsarka wanda ake sakalawa a kafaɗa dan ƙarami wanda baici ya ɗauki waya biyu ba,sai ta fito yanda kasan ƴar tsanar zinari, Ammi ce a gaba ita tana biye da ita a baya jaye da dan madaidaicin Aƙwati, Sam bai lura da ita ba sai da ya rungume Ammi yana murmushin farin ciki "welcome Ammi" "Thank you My Dear" Cikin yanayin shagwaba wanda ba ta san ya iya ba ya shafa cikin shi"Ammi yunwa nake ji,nayi kewar girkin ki," "Nikam babu abinda zan kara girka maka tunda ga matarka nan ta maka" Yana shirin kara yin magana ne idanun shi suka sauka akan ta,duk da akwai Glass mai duhu a idanun ta hakan bai hana shi ganin kwayar idanun ta data cire a kanshi tana ƙara kauda kai, Gefen lips din shi ya dan ciza yana shafa kai tare da kara kallon ta daga sama har kasa cikin kallon nan nashi na gefen ido, "Ni dai muge sanyi nake ji" Maida hankali yayi kan Ammi yana rike hannun ta"muje to" Tana biye dasu a baya har wurin parking mota inda ya buɗe ma Ammi gidan baya ta shiga,ya mai da kofar ya kulle,da makulli yayi amfani ya danna,nan take but din motar ya buɗe,saka akwatin tayi ta kulle sannan ta zagaya ta buɗe gidan baya kusa da Ammi ta zauna ba tare data kalli koda in da yake ba,tayi alkawarin har su bar garin ba zata taɓa shiga har Karshi ba, Da kallon mamaki yake binta dashi a ran shi,wanda ko kaɗan bai nuna ba a fili,wato shi zata nuna ma miskilanci,ai kuwa sai ta san dame yi take yi, Buɗe mazaunin direba yayi ya zauna,yana tayar da motar....... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *81* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Tsanin su da Airport din akwai nisa,duk da lafiyayyun titina da ke shimfide sai da ya dauke su tsayin mintuna talatin sannan suka iso wani babban gida lafiyayye mai hawa uku,gidan babba ne kam, A wurin ajiye motoci yayi parking,kai ko harabar gidan abun kallo ne ba sai na tsaya yi maku bayani ba,tana biye dasu tana ƙare ma ko'ina na gidan kallo wanda ba karamin jan hankalin ta yayi ba,tana matukar son Fure,a ko'ina taga fulawa tana iya tsayawa ta kalla domin yana saka ta farin ciki, Ji tayi an riƙo hannun ta,kallon Ammi tayi dake sakar mata murmushi "ki dinga kallon gaban ki" Sai lokacin ta lura ashe step ne a wurin da bata lura dashi ba,ƙila da faduwa zata yi, "na gode Ammi" Tana rike da hannun ta har suka shiga cikin makeken falon wanda nan take wani dumi mai matuƙar daɗi mai hade da kamshi ya shiga mamaye hancin su da jikin su baƙi daya, Dukkanin su kallon falon suke cike da tunani mabanbanta a zuciyar su, Ji suka yi wani murya mai taushi yana musu marhaba da zuwa cike da farin ciki, Mai da kallon su suka yi kan tsohuwar da ake turowa zaune a saman keke,wacce ke cikin shiga na mutumci yayin da kwarjininta ke fita tare da murmushin da take saki, Hannu ta buɗe ma Ammi wacce tuni ta fara hawaye, Da sauri ta karasa in da take ta tsugunna tare da rungumeta tana fashewa da kuka,ita kanta tsohuwar kuka ta saka domin sun riga sun jima da cire ran sake saduwa a duniya,sai gashi yau Allah yayi sun hau ido da ido,duk da suna magana a waya amma ba kamar yau ba da suke jin dumin juna, "Ummi ki yafe min" Daga inda take tsaye hawaye take yi wani na bin wani,dan ba ƙaramin tausayi suka bata ba,ita ko yaya ne bata son taga babban mutum yana kuka, Gani tayi an mika mata handkerchief fari tas,amsa tayi tana goge hawayenta dashi har da fyace hanci dashi duk da ba komai a cikin hancin, Jin muryar shi tayi daf da ita yana faɗin "why ar you Crying? Ba tare data kalleshi ba tace" I am just happy that she overcome it" Nuni Ammi tai mata da Biba"ga matar Jikan ki Ummi,yarinyar kirki ce" Gani tayi itama matar ta buɗe mata hannu tana mata alamar ta zo,babu musu kuwa ta karasa gareta ta rungume ta, "Ohh Grandma kukan ya isa haka in ba so kike mu koma Asibiti ba" Dakuwa tai masa tana dariya mai haɗe da kuka. Sake su tayi cikin murmushin farin ciki tace"kuje kuyi wanka sai ku sauko mu ci abinci"kallon shi tayi"ka tafi da matarka dakin ka" Dagowa tayi ta kalle wanda shima yayi dai dai da ita din yake kallo,ganin bai da niyar cewa komai ne yasa tace"ni tare da Ammi zan zauna" Grandma ce ta girgiza kai"a'a ƴar Albarka ki zauna kawai da mijin domin nan gidan ki,gashi kuma kun jima baku haɗu ba" Babu damar cin musu,dan haka tashi tayi tabi bayan shi, A hawa na biyu ma wani duniyar ne na daban,ga ɗakuna nan na alfarma, Daya daga ciki ya nuna mata"ki shiga wannan"ya faɗa ya juya yana ƙoƙarin bude na kusa dashi, "Kaya na fa? Ba tare daya juyo ba yace" Za'a kawo maki" Bin kofar daya shiga ya kullo da kallo tayi sai kuma ta tabe baki"hakan ma yafi "ta faɗa tana shiga dakin,faɗawa tayi kan gado tana sauke numfashi,komai na dakin fari ne tas har ta labulaiya, Jin ana kwankwasa kofa ne yasa ta tashi ta je ta buɗe, Wata mata ce mai sanye da kaya irin na masu aiki,dan tun a hawa na dawa ta ga masu irin kayan,daga dukkan alamu akwai ma'aikata da yawa a gidan, Cikin girmamawa ta gaishe ta tare da fada mata ina zata ajiye kayan, Karba akwatin tayi tana sallamar matar, Ajiye akwatin tayi sannan ta shiga wanka,ko da ta fito sai da tasha magungunan ta data zo dashi sannan ta shirya,har ta zauna sai gashi an aiko data fito suci abinci, Wurin cin abincin ma bata ganshi ba,dan haka ba karamin daɗi ta ji ba,cikin saki jiki suka gama cin abinci suna hira da Grandma,bata taba dauka matar nada sakin fuska da barkwanci irin haka ba,ranar tare suka yini har dare,sallah kawai ke tada su,hirace ta an daɗe ba'a haɗu ba. Har zata kwanta taji tana ra'ayin shan ruwan Lipton saboda sanyin da akeyi,dan haka fitowa tayi ta nufi kicin din ƙasa, Koda ta haɗa Lipton din jan daya daga cikin kujerun kicin tayi ta zauna,bata san wani irin Lipton bane amma ba karamin daɗin ya mata ba,lumshe ido yayi tana kurba a hankali har ta kusa kammalawa, Jikinta ne ya bata kamar akwai mutum kusa da ita,yayin da wannan kamshin mai sanyi daɗi yake shiga duk wani kusurwa na hancinta,wanda hakan ke tabbatar mata da kusancin ta da wanda take tunani, Da sauri ta buɗe idanun ta,sai kuma ta saki ƙara a lokacin daya tana yarfe hannu,saboda ruwan Lipton din daya zubar mata a hannun sanadin zaburan da tayi, Babu zato sai jin saukar lallausar hannun shi tayi saman nata,matso da hannun yayi ya shiga busa mata iskar bakin shi mai matukar sanyi yake yi a hannun tare da faɗin "Sorry,Sorry" Kuka ta saka jin yanda hannun ke radade,wanda bana komai bane sai na raki,dan bata kaunar abinda zai taɓa mata lafiyar jiki, Matso da ita jikin shi yayi a haka ya buɗe sink ya kunna ruwa ya tara hannun ruwa na sauka a kai, "Hannun yana zafi har yanzun? Jinjina mai kai tayi, Da yatsan shi yayi amfani wurin dago habar ta" Kalle ni" Dago jikakkun idanun ta tayi tana daurawa a kanshi, "Akira likita? Sai lokacin ta tuna a gaban waye take,dan haka cikin sauri ta fiske hannun ta dake cikin na shi,ba tare data ce mai komai ba ta juya tayi tafiyar ta, Sai dai taku biyu kawai tayi sai ji tayi ya riƙe hannunta ta baya,kafin ta gama tantance dalilin shi nayin haka,sai jinta tayi jingine a jikin shi yayin daya rankafo ta bayan ta,ya zagaye cafaffen cikinta da hannayen shi, kanshi kuma saman kafadarta,tana jin yanda yake busa mata numfashin shi da goga hancin shi a jikin fatar jikin ta, Ai kuwa nan take taji wani carrr tsigar jikin ta ya tashi,wasu irin abu na faman mata yawo a jiki, Hannunta ta Daura saman nashi tana ƙoƙarin zame hannun shi,sai dai sam yaki sakin ta sai ma kara matse ta da yake yi"ka sani in wuce bana so!me haka kake min"ta faɗa cikin haushi, "Har yanzu fushi kike yi dani? " Ban sani ba dan Allah Suraj ka sake ni"ɗan ihu ta saka jin wani irin Kiss daya sakar mata a kafaɗa mai shiga jiki, Kuka ta saki lokaci ɗaya na takaici jin sautin murmushin daya saki,wato da gangan yake yi, "Fada min fushi kike yi da ni? Cikin kuka tace" Ko na faɗa maka me zaka yi,ni ka sake ni" "Haƙuri zan baki mana,so kike Allah ya kamani saboda fushin ki? " Ai kuwa in da wannan ne Allah ya gama kamaka dashi" Ba tare data san sanda ya ɗaga rigar nata ba sai jin hannun shi tayi yana yawo a fatar cikin ta,wanda yasa dole sai da ta rintse ido tana jin yanda yake zagaye ramin Cibiyar ta yana wasa za karamin Pin ɗin zinari dake makale a wurin, Daga ita har shi wani irin numfashi suka sauke a tare, Cikin wani irin murya mai tattare da kasala ya furta mata kalmar"I .. am.. Sorry "a cikin kunnen,Yana goga lip din shi a kunnen,dan wani irin fitinannan kanshi ne yake shaka daga jikinta mai tada hankali, Kankame hannun shi tayi da ƙarfi,dan ji take kamar zata zube kasa" Please"ta furta a wahalce, "Ummm" Ya faɗa yana sakin ta lokaci ɗaya tare da barin kicin din ba tare da ya yarda ya kalli in da take ba, Ganin fitar shi ne yasa cikin sauri ta data teburin wurin tana tsugunnawa,ta jima a haka kafin ta lallaba ta koma dakin ta tana kulle kofa har da key, Kai tsaye banɗaki ta nufa tana sakar ma kanta ruwa ko zata ji sanyin bijire mata da gangan jikinta ke shirin yi,yana hasaso abinda ba zai taba yuwa ba,ita kanta tasan ko taki dole sai ta haɗa da wankan tsarki,dan tun rungumar farko daya mata ta ji yanda wasu ruwa masu dumi suka balle mata,wannan wani irin yanayi ne........... Hmmmm ni kan ina daga gefe na ce kila maganin Ammi ke aiki😜to bari dai mu gani ko za'a iya jurewa 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *82* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Washegari da safe tana idar da Sallah ta shiga dakin Grandma ta gaida ita,sai dakin Ammi nan ma sai da ta dan jima dan ta samu tana karatun Kur'ani ne,bayan ta idar ne suka gaisa,har ta isa kofa zata fata,dan so take ta kwanta dan jiya Allah ya gani ba tayi wani baccin kirki ba,saboda ciyon mara,ita ba lokacin Al'adan ta balle tace shine,da yar ta samu tayi bacci gab da Asuba,shi yasa take sauri yanzun taje ta kwanta, Kiran sunan ta da Ammi tayi ne ta dakatar da ita ta juyo tana amsawa, "Ki shirya da wuri domin zuwa ƙarfe tara zamu fita" "Insha Allah Ammi" Gyada mata kai tayi,hakan yasa ta fita tana jawo mata kofa, Tana saurawa shi kuma yana saukowa sanye da Jallabiya fari a jikin shi sai karamin hula fari dake kanshi,yanda kasan wani matashin Balaraben,kallo daya tai masa ta kauda kai,shi ma bai kula taba yayi ci gaba da saukowa kamar bai ganta ba,sun gefta juna da step biyu ya dakata yana juyawa baya"na ce ba" Kin kulashi tayi duk da taji shi,taci gaba da takunta, Sai dai ko step uku bata karaba cikin rashin sani ta taka doguwar rigar dake jikinta ai kuwa nan take tayi baya gaba ɗaya tana shirin faɗuwa,duk yanda taso ta kama kasa ta tsaya abin ya gagara,ta tabbatar da idan har bisa tsautsayi keyarta ta kai kasa to babu lallai na zata kara tashi a wannan rayuwar,domin ta san dinkin dake kanta ya gama kwancewa bama shi kadai ba kan gaba ɗaya ya gama tashi aiki,saboda step din nada yawa, Ta dai jita ta faɗa jikin abu mai laushi idanunta a lumshe,sai dai ko kusa bata gwada bude ido ba,dan ta sadakar mala'ika yayi sama da ita ko, Ai kuma jin anyi saman da ita ne yasa ta kara sake jiki gabadaya kamar mawa sumammiya,koda yake zamu iya kiranta da haka tunda da gasken suman wucen gadi tayi, A hankali yake tafiya da ita a hannun shi yana kuma kallon yanda take sauke numfashin a hankali wanda hakan ke nuna masa da bugun zuciyarta yayi ƙasa, A maimakon shiga da ita dakin ta,sai tura kofar dakin shi da ƙafa yayi ya shiga,ya maida,kan gado ya shimfidar da ita a hankali kamar wata karamar yarinya,ya dauki filo ya daura kanta, Zame doguwar rigar jallabiyar jikinta yayi,wanda yayi sanadiyar bai yanar yar karamar rigar baccin dake jikinta iya cinya, Kallo daya ya mata ya dauke idanun shi a jikinta ya maida a fuskarta, Shafa fuskar yake a hankali tare da kiran sunan ta"Bebin bude idon ki" "Um Umm" Dukawa yayi saitin kunnenta "buɗe ido ki gani" "Na mutu ne? Bai bata amsa ba sai tafin ƙafar ta daya kama ya shiga murzawa da dan ƙarfi yanda zafin ke ratsata a hankali hakan ya tilasta mata buɗe idanunta,kallon shi take na ɗan wani lokaci kafin kuma ta kalli dakin sai zame ƙafarta tayi tana sauka,ba tare data ɗauki rigar ta ba tace" Thank"ta yi fatar ta, Girgiza kai yayi yana mikewa canja kaya yayi ya fita, Ita kuma tana shiga daki fadawa tayi kan gado tana sauke numfashi daga nan bacci ne ya dauke ta, Ba ita ta tashi ba sai da Ammi ta aiko daya daga cikin masu aiki a tayar da ita ta shirya, Da kyar ta buɗe ido ganin ƙarfe tara da rabi ne yasa babu shiri ta tashi zaune,sai kuma ta mike tana nufar banɗaki da gudu, Cikin kankanin lokaci ta yi wanka ta shirya cikin doguwar riga na jallabiya,sai rigar sanyi mai nauyi da Ammi ta aika mata dashi, Koda ta sauko duk suna falo harda Grandma, Kallon Agogo Ammi tayi"yi sauri ki karya,kin san nan basu daukar African time " "To Ammi" Cikin sauri ta dauki ruwan shayin da aka haɗa mata wanda ya dan sha iska,tana kurba tana tura soyayyen ƙwai, "Ammi muje na gama" Ta faɗa ta karɓar keken da Grandma ke zaune tana turata a hankali, Su suka taimaka mata ta shiga mota sannan Driba ya ja su, A bakin wani tangamemen Kotu wanda ya amsa sunan sa suka parkar a wurin parking, Koda suka shiga a wani babban ofishi suka zauna,ko minti goma ba su yi ba aka ce su shigo za'a fara kowa ya halarta, A wasu manyan kujeru Alkalaine dattawa guda biyar, Sai kuma wadanda bata sansu ba,amma abinda ya bata mamaki shine ganin Pa,Nadiya,da sauran yannin ta,sai Abbu,Shamsuddeen,Dady,Abba,Nurudeen,kai ikon Allah, Dan can ba kaman nan bame da a cika koto,wannan shari'ar irin na Family ne kawai, Kallon Ammi tayi"kalli su Abbu yaushe suka zo? "Ki natsu" Ta faɗa ba tare data kalli in da suke ba, Kallon mamaki take mata,sai dai bata ce komai ba, Wani ne ya tashi da takarda a hannu ya fara magana kamar haka"wannan shari'a ce da aka fara shekara goma sha ɗaya da suka wuce,amma saboda rashin hujja da kuma rashin lafiyar ɗayan daga cikin hujjoji yasa yasa aka daga shari'ar har ta samu sauƙi,to yanzun gashi Allah yayi ta tashi cikin aminci,kamar yanda aka fara to yanzun za'a daura daga in da aka tsaya,sai kuma wasu daga cikin nan waɗanda aka gaiyato su a bisa yardar gwamnatin garin su,tare da wakilan gwamnatin,suma sun iso ne a safiyar yau" Daya daga cikin Alkalan ne yace "Dr Aisha ko zaki iya fitowa ki kara fada mana abinda ya faru shekaru goma sha ɗaya baya" Ammi ce ta tashi ta tura Grandma zuwa stage,ita sai dube dube take ko zata hango Suraj,sai dai sam ta kasa ganin shi, Dole ta mai da hankali kan Grandma da zata fara magana. Da farko Ahalin mu sun kasance daya daga cikin sanannun mutane a garin Mardesh,saboda Arzikin da Allah ya basu,sai dai kuma Allah bai yi su da haihuwa ba,shi yasa idan har aka samu haihuwa a zuri'ar akanyi sati ana shagali, Ahalinmu basu yarda da auren bare,sai dai auren haɗi, Mahaifina ya auri mahaifiyata mai suna Mariya,a lokacin baya auren haɗi ne kuma ba sonta yake yi ba,sai da suka shekara goma da aure sannan Allah ya basu haihuwa na,ina da shekaru bawai a duniya,wani aiki na buɗe sabon Company su ya kaishi South Africa,anan ya haɗu da wata yarinya mai suna Linda,sunyi soyayya sosai da ita,ba tare da aure ba ƙaddara ciki ya shiga,sai da ta haihu sannan ne dangi suka samu labari,a lokacin an yi tsiya sosai domin cewa sukayi zasu kore shi acikin dangin mu,Mariya da Hassan,dan uwan mahaifina su suka tsaya mashi,sannan dangi suka hakura,da Sharadin zai musuluntar da ita ya aure ta,kasancewar yana sonta shi yasa ya amince,mahaifiyata tayi zaman hakura dasu sosai saboda mahaifina kiri kiri yake nuna yafi son Pa a kaina,sai dai mahaifiyata bata nuna komai ba,a lokacin dana cika shekara goma ta tara mahaifiyata ta rasu,mutuwar da ta girgiza mahaifina domin zazzaɓin sati ɗaya tayi,sai dai ko sannu bai ce mata ba,saboda a tunanin shi zata tashi,ya manta cewa mutuwa bata sanarwa,yayi daya sanin rashin kyautata mata,ko sau daya bai taba furta mata kalmar so ba, Ba na son zama tare da Linda,dan haka na koma digan dan uwan Baba na Hassan na zauna tare da matarshi da kuma yar shi mai shekaru goma, Ana cikin haka mahaifina ya fitar min da miji mai suna Usman,babu gardama na amince kasancewar sa mutum mai nagarta kuma ya san abinda yake yi, Inada shakara biyu a gidan miji na kammala master's dina na fara aiki, Bayan shekaru shida da aure na mahaifina ya kamu da ciyo mai tsanani a lokacin Pa yana da kusan shekara goma sha takwas a duniya, Mahaifina yayi kira na nida mijina, Dana same shi ne ya nuna min wani akwati ƙarami dake gefen shi yace na ɗauka na buɗe,ina buɗe sai ganin dutsen Diamond na yi tare da wani takarda,a kalla ko a wanan lokacin kuɗin Diamond din ya haura biliyoyin kuɗi, Tambayar shi nayi Baba wannan na menene, Sai cewa yayi tunda ya auri mahaifiyata bai taba mata komai ba,nima haka,wannan Diamond din dukiyar daya mallaka tare da gadon da mahaifiyata ta barmin ne ya haɗa ya siya wannan dashi,dan haka ya mallaka min shi har duniya ta nade, Nati kuka sosai na kuma gode masa,a lokacin Linda dake labe da ɗanta ta fito ta nuna Babana akan wannan abinda yayi cin amana ne,to su mai ya bar masu,girgiza kai kawai yayi ya ce ya bar mata Company shi na garinsu,sai kuma wannan gidan da yake ciki ta je ta rayu ita da ɗanta,sai kuma kuɗaɗen da bansan adadin su ba daya basu, Ni dai mun wuce tare da mijin na,ba'a dau kwana biyu ba Allah ya mai rasuwa, Bayan kwana biyu da rasuwar shi ta tattara ita ɗanta suka koma Sauth Africa, Ko wata hudu ba ayi da rasuwar mahaifina ba Allah ya bani ciki,nayi farin ciki sosai na kuma yi kukan murna, Yan wata tara na haifi dana mai suna Abdul basir, Yaro ne wanda ya taso da natsuwa da hankali,ga tausayi, Ta gefe ɗaya kuma yarinyar Kanin Baba na Hassan tayi auren Shamsiya, Abdul basir nada shekaru biyar Shamsiya ta haihu,in da a wurin haihuwa Allah ya mata rasuwa,mutuwarta ta girgiza dangi sosai,nayi kuka kamar me,domin mun shaku sosai da Shansiya,hakan yasa na roƙi mijinta wanda yake matsayin Ɗan'uwa a gari saboda auren dangi ne ita,akan su ba ni yar ina son zan kula da ita,babu musu aka gabi,saboda dukkan mu daya ne,sai dai da Sharadin ba zan taba shayar da ita Nono ba saboda auratayya na iya shiga tsakani,cikin sauri na Amince,bayan kwanaki biyar yarinya taci suna Hafsan (Ammi kenan) na riƙe Hafsat a matsayin ƴar dana haifa,kusan tare da Abdul basit muka yi rainon ta,dan barci kadai ke raba su har girma,dan saboda ita yaki yarda yaje wani gari yin karatu, Shi kuma bangaren kanina lokaci lokaci na kan je na duba shi,shima ya zama babban mutum har yayi aure, Lokaci ne yayi tafiya mai matukar nisa wanda a hankali har Allah ya nuna min girmar yarana Hafsat da Abdul,wanda tana da shakara goma sha takwas ta nuna babu wanda take so sama da ya'yanta,idan bashi ba bata jin zata aure wani,mukan dama abinda muke so kenan,ai kuwa ba'a dauki lokaci ba aka ɗaura masu aure,sai dai suna zaune ne tare da ni a nan garin Mardesh, A lokacin da muka fara fuskantar barazana ta farko shine a lokacin da Hafsat ta haife Suraj,yana da wata biyu,aka kara turo min wasika akan na bayar da wannan Diamond din dana mallaka a wurin Baba na ko a kashe iyalaina, Da fari na shashantar da maganar,amma da abun ya kai har cikin gidan da nake ake shiga a ajiye mun wasika duk yawan Jami'an tsaro yasa na fara tsorata,na faɗa ma mijina,shine ya bada shawara akan mu dauke takardar Diamond ɗin wanda idan har mutum yayi nasarar satan Diamond din in babu wannan takardar na shaidar mallaka babu ta yanda za'ayi ya iya fitar dashi ko da tsayin shakara nawa ne,haka kuma ko fasashi akayi to tabbas wurin siyarwa da kwaji sai an gane na Ahalin mu ne, Dan haka muka tattara muka dawo garin London da zama har da su Hafsat,shi kuma takardar muka bada ajiyar shi ba tare da sanin kowa ba haɗe da Diamond ɗin, Tun daga lokacin sai muka samu sauƙin komai har sai da jikana Suraj ya kai shakara goma, Wata rana na dawo gida daga wurin aiki na taradda Hafsat zaune a falona tana kuka, Hankali na ya tashi dan haka da sauri na karasa in da take na rungume ta ina tambayar ta lafiya, Cikin kuka take sanar dani cewar Abdul basit yana cin amanar ta ba zata iya zama dashi ba ya sake ta, Jin wannan kalmar daga bakinta yasa hankali na yayi kololuwa wurin tashi,domin saki abu ne da ba'a taba yi ba a dangin mu, A lokacin nayi rarrashin duniya amma taki hakura,na kira shi shima nayi tambaya har nayi fushi yaki ya fada min abinda ya faru,sai ma kuka da yake yi akan na riƙe ta tayi hakura ba zai iya rayuwa babu ita ba, A lokacin da nayi kokarin kara bata haƙuri sai nuna min hotunan shi tayi wanda yake tare da mata cikin tsiraici,abin yasa zuciyata girgiza,sai kuma kalmar da ta faɗa na cewar idan har ina kallon ta a matsayin Ƴar dana haifa na saka ya sake ta, Juyowa nayi gare shi,cikin mutuwar zuciya dana gangan jiki,sai dai kafin ince mashi wani abu,ya buɗe baki da kyar cikin kuja ya furta mata ya sake ta saki ɗaya,sannan ya tashi ya fita,tunda ya bar gidan bai ƙara dawowa ba,sai dai muna waya dashi lokaci-lokaci,bayan tayi Idda da watanni biyar wanda har lokacin muna tare kuma babu abinda ya canja a tsakanin,ta kawo mana wani a matsayin wanda take so wanda ni bansan in da ta haɗu dashi ba,wato Abbu Safwan,nasan zata fuskanci matsala daga wurin dangin mu,amma da taimakona ta aure shi,duk da har raina ba wai ina kaunar shi ba ne, A ranar da aka ɗaura auren su a ranar aka sace Suraj... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *83* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Hankalin mu ya kai kololuwa wurin tashi,lungu da tsako yan sanda nima suke sai dai babu labari,Kakanshi ne yace ai mu kwantar da hankalin mu ayi trackin din Suraj ta hanyar zoben dake hannu shi wanda ya bashi a matsayin kwatar karin shekara, Da wannan muka yi amfani wurin gane in da suka kai shi a cikin wani sohon gini na wani unguwa,ba karamin fafatawa akayi da yan sanda da barayin ba kafin su samu nasarar dauko shi,inda suka kashe mutum biyu cikin barayin,suka kuma kama mutum daya, Da ka tambaye shi dalilin kama Suraj din sai cewa yayi suma kwangilar sace shi aka basu,kuma basu san wanda ya saka su ba,abinda da yasa kuma suka karɓi aikin saboda na kuɗi ne masu yawa aka saka a kan duk kungiyar data samu sa'ar sato shi, Wannan bayanin nasu yasa Hafsat ska kuka tare da roƙo na akan dan Allah na basu Suraj su tafi dashi Nigeria,ba zan iya hana ta ba saboda ina matukar son ta,duk da muma na jin yanda zamu rabu da jikan mu,ta gefe ɗaya kuma ga mahaifinsa,sai dai shima ko ba komai Hafsat kanwa ce a gare shi,zai iya yin komai domin faranta mata,shi yasa ko da na faɗa masa hukuncin daya yanke bai Musa ba,domin dama shi ba mai jayayya bane a gare ni, Dan haka a washegari ranar suka wuce dashi, Sai da tayi wata biyar hudu sannan muka kwaso muka zo dubata har da Abdul basit,a gidan da muka saka aka yi mana ana muka sauka, Munyi farin cikin ganin ta ita da Suraj cikin farin ciki da ƙoshin lafiya,gata kuma har Allah ya azurta ta da samun ciki, Mun kai wata biyu a garin sannan muka koma London,bamu kara dawowa ba sai ta haihu, A gaka rayuwa ke tafiya mana sai dai kuma shi Abdul basit yaki yarda ko kadan yayi wani aure,idan yaga na damu sai yace mai nike buta aduniya daya jika,kuma gashi sun bani shi da Hafsat,in yi hakuri ahi ba zai iya aure ba tunda har Hafsat bata iya zama dashi ba,to babu macen da zata iya zama dashi, Haka kuma idan nace to ya fada min gaskiyar lamarin shi da ita,nasan shi ba mai niman mata ba ne,me ya faru,sai yace shima bai sani ba,amma yaji daɗi da nuna yardar da nayi dashi,Hafsat kuma bai san in da ta samu waɗannan hotuna ba,sai dai yasan komai dadewa gaskiya zata yi halinta ko yana raye ko baya raye,idan ya faɗi hakan na kan kwabe shi da fadin ina zai je ya bar ni, Wani narar Alhamis da ba zan taba mantawa ba, Abdul basit ya shigo garin daga Airport zuwa gida aka dauke shi,sannan aka kira mu akan in har muna son ɗan mu dole mu amso wannan Diamond din mu kawo gida,idan kuma muka daka faɗa ma Jami'an tsaro to tabbas zasu kashe shi, Dan mu yafi mana komai da muka mallaka,dan haka cikin rawar jiki muka je Banki bayan dogon cike cike muka amso sannan muka dawo gida, sai dai kafin mu shiga ciki sai ga kira daga Hafsatkamar ba zan ɗauka ba,sai kuma na dauka,cikin Kuka take shaida min Abbu Safwan yaci amanar mu,tambayar ta na shiga yi akan wani amana ne yaci,na daiji ta ambaci sunan Abdul basit daganan mijina ya karɓe wayar ya kashe tare da faɗin yanzun ba lokacin wannan maganar bane, ,muna shiga falo anan muka same shi daure da saman kujera sun masa jina jina,yayin da fuskokinsu ke sanye a cikin bakin safa, Mutum shida ne,sannan muryoyin su ba asalin nasu bane sun yi amfani da abin canja murya, Cikin kuka na isa gare shi ya rungume shi una kuka,ina kuma rokon da su kyale mu ga abinda suke bukata nan,sai dai cikin rashin imani babban su yana karbar akwatin Diamond din a hannun Usman ya harbe shi a tsakiyar goshi, Wani irin razanannan ƙara na fasa,sai ina ƙoƙarin barin jikin Abdul basit naji ya kira suna na,abu ɗaya ya faɗa min shine Ummi Suraj,kafin ya karasa shima sai saukar harbi naji a jikinshi ta ko'ina,na ruɗe,na rasa wurin waye zan tafi,shi wurin mijina da nake ganin shi kwance acikin jini babu rai,ko kuma wurin dana da yake zaune cikin jini wanda yake zuba kamar an yanka dabba, Kamar yanda nake kallon idanun Abdul basit dake kallo na a haka har idanun suka lumshe alamun rai yayi halin sa, Na rasa hankali na domin sai kiran sunan su nake yi,da wannan suka yi amfani wurin ganin sun buga min ƙarfe a ciki a maimakon harbi,a cewarsu ba zasu yi asaran bulet din su ba wurin karasa ni, wannan ma kawai ya ishe ni,nan suka wuce suka barni,ba tare da sun san Allah ya yi ba zan mutu a hannun su ba,sun kashe min miji da dana a gaban ido na,sai dai kuma duk da haka na gane mutum data a cikin su,wanda yake tunanin idan yayi badda kama ba zan iya shaida shi ba,sai dai ina rokon Koto da kafin na faɗi waye wannan ina son ba ma Hafsat dama ta fito ta faɗi abinda ta sani game da wannan lamarin. Kowa ka gani a cikin koton jikin shi yayi sanyi yayin da dayawa a cikin su hawaye suke yi na tausayin matar,ta ɗayan bangaren kuna idan ka juya zaka ga waɗansu sai sharan zufa suke yi,duk sanyi irin na garin,domin basu taba tsammanin irin wannan ranar zata zo masu da wuri ba,acikin bazata, babu wani tashin hankali da ya wuce irin wannan kisan a gaban idan ka,har balle a ce mutane masu muhimmanci a gare ka, Nan daya daga cikin Alkalan yace Hafsat ta fito, A hankali Ammi ta fito wacce idanun ta sun yi jajir saboda kuka dan tunda Grandma ta fara bada labari take kuka domin tuna irin zama na amana da suka yi da Abdul basit da irin soyayyar da ya nuna mata,ita ce zata masa laifi amma dan kawai a zauna lafiya shi zai bata haƙuri ya haɗa harda lallashi,ko kadan baya son abinda zai taɓa ta,ba zata taɓa yafe ma duk wani mai hannu a cikin kisan shi ba koda waye kuwa,share hawayenta tayi tana tsayawa a kan stage, "Kamar yanda Ummi ta faɗa kun san komai daya faru har aure na da Abbu Safwan,A lokacin dana kira Ummi a wannan ranar naji wani sirri dan gane dashi wanda ya tashi hankali na har na kasa daurewa na kira ta, Abinda ya faru kuwa shine na kammala girki rana shi kuma yana dakin shi wanda tunda nake dashi ban taba shiga dakin ba,idan na tambaye shi me a cikin ɗakin n sai yace min ai takardu ne kawai a ciki,ni kuma ban kawo komai a raina ba, To naje faɗa mashi cewar na kanmala abinci shine na samu tana cikin wannan dakin kuna kofar a buɗe take,dan haka ba tare da tunanin komai ba na kutsa kai,dai-dai lokacin shi kuma yana waya yana faɗin, Ku kashe Abdul basit din,domin na lura har yanzun hankalin ta na kamshi,karku damu da batun takardun domin nasan ita da ɗanta sun san inda takardun yake,zan ci gaba da lallabasu har su kawo min shi cikin hannu na, Sai kuma ya kuma cewa ai wannan dalilin ne yasa nake matukar girmamaka Oga,domin cikin ruwan sanyi ka saka ta rabu da mijinta ta hanyar hotunan karya,gashi yanzun ka aura min Jari domin ita din jari ne a gare ni,ai in faɗa maka ko yanzun kasuwa ta tashi dan koli yaci riba, Jikina na rawa na juya na bar dakin ina kuka shine na fita ta baya cikin tsananin tashin hankali na kira Ummi dan in shaida mata, Na fara mata magana shine ta kashi wayar na kira na kira kuma ban samu ba,nan na tsugunna ina ta rusar kuka na rashin sanin abin yi, Daga baya na naji ance"kin gane gaskiya kenan ko? Cikin firgita na Dago kai ina kallon shi,ba kowa bane face mijin Goggon yara,wato Habib mijin kanwar su, Na tsorata da ganin shi,saboda babu abinda ke haɗa ni dashi sai gaisuwa, Cikin kwantar da murya yace ki yarda dani ni nasan komai tun kafin auran ki,ni cikakken dan jarida ne,kuma aboki ga mijin ki sai dai ganin hanyar daya zaɓa ne yasa bama shiri dashi, Cikin kuka nace ya taimaka min na gudu na koma garin mu,bana son zama dashi, Dariya yayi sannan yace lallai ashe so kike ki mutu ke da dan ki,domin duk in da kika shiga a wannan duniyar sai sun nimo ku saboda wannan takardar,sai dai daki tura makiyin ki nisa ai gara ki jawoshi kusa,ki zauna tare dashi ta hakan ne kawai zaki iya tsira,idan har kin amince zan taimake ki" Da wannan shawarar na yarda domin ba ni da hanyar daya wuce haka,a kuma wannan ranar na samu labarin mutuwar su da fadawar Ummi doguwar suna, Nayi kuka na tashin hankali wanda naji kamar na kashe kaina nima,sai dai idan na tuna Suraj dole nake dakatawa,ni ce silar komai,ni najawo komai,idan da ace ban amince da waɗannan hotunan da na gani ba kula da hakan bata faru ba, Habib shi ya bani shawara kar na ce zan je na zauna tare da Ummi in zauna tare da Safwan kin dinga bibiyar rayuwar shi ina tara hujjoji ta yanda zan san duk wani mai hannu a ciki,in kuma raini dana, Ana cikin haka ne wata rana ya kira ni akan nazo wani wurin hutawa na same shi,to anan ne na iske shi da wata mata da yarinya yar shekara biyar suna zaune,gaisawa muka yi da matar har na dauki yarinyar ina mata wasa da tambayar me sunan ta,nan matar wacce daga gani kasan yar duniya ce ta bani amsa da Salma,ko minti biyar basu kara ba naji tace mai su sun tafi Minna sai ya zo, Bayan wucewar ta ne nake tambayar shi me haɗin shi da irin waɗannan matar,shine yake bani labari a kan matar matar aure ce,sai dai shi ya aikata babban kuskuren da bai taɓa ɗauka zai yi shi ba a rayuwar shi,ita taja hankalin shi suna tarayya tare,sannan wannan yarinyar da nake gani yar shice,sunan ta Ummi Salma,anan ya bani Address din garinsu da gidan da suke, Cikin jin haushin abinda ya aikata nace masa me yake buƙata nayi da wannan address din,a lokacin murmushin yayi mai tattare da damu yace,kawai dai na baki ne saboda wata rana,ko da bana nan komai daɗewa dan Allah ki duba ta,ba sai ta san komai ba game dani,amma dai bana son tayi rayuwa irin na mahaifiyarta,daganan ya bani wani karamin Envelop,wannan duk wani abinda na bincika ne na kuma samu,sai dai kina iya ci gaba da bincike daga in da na tsaya, Ko godiya ban mai ba tsabar haushin tarayya da matar aure da ya fadamin yayi na wuce,wannan shine gani na dashi na karshe shima domin tun daga lokaci shima aka ni me shi aka rasa,wasu suce ya gudu ne saboda matar shi,wasu suce ya mutu me a wani wuri,Allah kadai yasan abinda ya faru dashi, Bayan faruwar haka dole na ajiye duk wasu makamaina na mai da hankali wurin ganin na inganta rayuwar Dana ta yanda zai zamo jajirtacce,domin ba zan iya faɗan ni kaɗai ba,ina bukatar matayi,sai dai kowa ba abun yarda ba ne, A lokacin da Suraj ya kammala karatu a lokacin muka soma fuskantar wani matsalar domin ta ko'ina aiko mana da yan leken asiri ake yi,sai dai ina saka shi yana iya baƙin ƙoƙarin shi wurin kauce masu, Ana haka wata rana za shi wa'azin Niger State na roki alfarman akan ya duba min Yar Habib na bashi Address din da ya bani, Bayan yaje da kwana biyu sai gashi ya dawo min da labarin sun tashi daga wannan Address din amma yayi ƙoƙarin ganin ya same su,kuma a ranar aka ɗaura ma yarinyar aure,har ma ya taho min da hoton ta,nayi farin ciki sosai,sai lokacin ya tambaye ni wacece ita,ban faɗa mashi komai ba na dai ce mashi wata ce,ganin ban son faɗa mashi ne ya bar maganar, Bayan wani lokaci sai gashi wata rana ya kawomin wani post da su ATM card sai kwalin sigari,cikin yanayin kokonto ya nuna min,Ammi wannan kamar yarinyar da kika sa nayi bincike a kanta, Amsa nayi na duba,tabbas ita ce,sai dai ganin wannan sunan ta Biba yasa na ni ma na shiga kokonto,na dai karɓi kayan na bar maganar, Na samu labarin cewa suna ƙoƙarin kawo mana wani mai aikin dana bincika sai na gane ita din ce zata shigo,a nan ne nasa shi ya fara min bincike akan ka,har na gano tabbas ita ce, Ta gefe ɗaya kuma na gane ba kowa bane yake turo su face Abbu Safwan,shi ne VIP,shine ke saka su komai,sai dai shima kuma yana da Oga,sannan da haɗin bakin danshi Shamsuddeen,dashi aka haɗa baki wurin yi ma Suraj sharrin kisa a legos,sannan da taimakon shi wurin yin munakisa Suraj ya auri Biba,duk da saka hannun shi,sannan Abbu Safwan yana tare da matar shi mahaifiyar Shamsuddeen,amma a idanun duniya gani ake sun rabu,yanzun haka duk wani shaida daya kamata mu haɗa mun haɗa har da na hatsarin daya faru da Ummi,na gode. Kara_kara_kara,ai kuwa zan so kuga yanda koto ya rikice,kowa kallon dan uwan shi yake hankali tashe,yayin da dage gefe ɗaya kuma zufa ya shiga jika wasu,wannan ba kamar koton Nigeria bane,wannan suna amfani ne da karfin hujja da dokoki, Ta gefe ɗaya kuma tunda ta dukar da kai take hawaye,domin tabbatar bata taba tsammanin kaddara zai kai ta nan ba,mahaifinta shine mijin goggon yara,sannan Abbu shine VIP sannan shi ya kashe Ummi ta,tabbas sai yanzun ta tuna shine ya buga mata ƙarfe a kai,sakamakon haka yasa ta manta komai daya faru a wancan ranar sai wayarta wanda tace Suraj ya nima, Dago kai tayi ta kalli in da yake........ 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *84* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* "Daya daga cikin Alkalan ne yace ko zamu iya ganin shaidun da kuke dasu? Suraj dake zaune a gefe ne ya tashi ya mika kudi mai dauke da duk wani baya nai da suke buƙata,video din shi sakawa a kayi yayin da komai ya fara baiyana kamar film,duk wani shiri da suka gabatar da abinda Pa ya shiya,shi ne silar komai shi kuma ya Daura su akan hanyar da suke, Kotu ne ta bukaci in akwai mai magana acikin su sai yayi, Abbu Sufyan ne ya fito cikin hawaye ya fara magana,tabbas nasan son zuciya shi ya kai ni ga wannan halin da nake ciki,Pa abokina ne tare dashi muka yi karatu a can Sauth Africa,shi ya nime taimakona tare da nuna min hoton Hafsat,ni kuma tunda na ganta da kuma jin irin kudin da zan samu na amince da aikin,tabbas na aikata kuskure wanda nasan baza taba yafe min ba,nasan da zaran mun koma ba ni da damar da zan sake ganin ta har na nime tafiyarta duk da nasan ba yafe min zata yi ba,ina rokon gafaran ku" Cewa akayi ko Pa yana da magana, Shi babu alamun dana sani ko dar tare dashi,sai cewa yayi"ai Baba shi ya ja maki domin shi yara nuna banbanci tsakanin ni da ke,ni da nake namiji ne yasa bai Bani wannan kyautar ba sai ke,dan haka ko yanzu na fito sai na ga bayanki,kuma Diamond yana wuri na ba zan taba fadar inda yake ba"ya karasa faɗa yana nuna Grandma, Cikin kuka Nadiya ta mike"ni na San inda yake zan faɗa komai zan fada maku in da yake,Pa na yi dana sanin kasancewar ka mahaifi a gare ni,tana gama fadar haka tabar Koton da gudu tana kuka, Mai shari'ar ne ya buga wannan sandar yana fadin a natsu, Ganin yanda Pa ke kiran sunan Nadiya da fadin sai ya kashe ta idan ta faɗi wani abu, Sai da aka natsu sannan yaci gaba da faɗin "abisa ƙwararrun hujjoji wannan Koton ta yanke ma Pa hukuncin rataya,tare da mukarrabansa, Shi kuma Abbu Sufyan saboda haɗa hannu dashi zamu mika shi ga hukumar kasar shi domin ta zartar masu da hunci shi da Danshi, Sannan hukuma zata yi ƙoƙari wurin ganin ta dawo ma da Dr Aisha dutsen Diamond din ta na gado, Daga Su Nurudeen dasu Dady duk kuka suke yi ganin yanda aka saka ma Abbu Sufyan sarka,babu tonon asiri da yafi wannan, Da sauri Dady ya karasa in da Ammi ke tsaye" Dan Allah Ammi ki yi hakuri a sassauta ma Dan uwan mu,ki yafe masa" Kallo data taimasa ta kauda kai,"ku bari idan na dawo Nijeriya zamu magana " Tana gama fadae haka ta shiga tura Grandma a keken ta suka bar wurin yayin da Biba ke biye dasu a baya. Tunda suka isa gida ta shiga daki kulle kofa ta kwanta tana faman rusa kuka,zuciyar ta zafi yake yi,ji take kamar ta samu wani abu wanda zai gusar mata da hankali ta sha,ba tada komai sai dai kuma ta riga ta tuba ga Allah,ranar haka ta yini idanun ta sun kumbura saboda kuka gaba ɗaya bata cikin walwala,ko da Ammi ta aiko akan ta sauko su ci Abinci cewa tayi ta ko shi,ganin har yamma bata fito bane yasa ta shigo dakin da kanta, Zama tayi a bakin gado in da take kwance,sai dai ba bacci take yi ba, Shafa kanta tayi"kina fushi ne a kan kin faɗa maki da nayi? Girgiza kai tayi hawaye na sake saukowa daga cikin ramin idanun ta, "To faɗa min menene? Dafe kirjinta tayi" Ammi zuciyata zafi take yi,gani nake kuma kamar ba zan iya yafe ma Baba da Mama ba,saboda shi ya gefe ta acikin wannan halin,ita kuma a maimakon ta bar shi sai ta zabi hanyar da ya bata,wani irin zunubi ne wannan,sun bata mana rayuwa,wanda duniya take ma kallon mahaifinmu da ban asalin iyayen mu daban,ta yaya zuciya zata ta ba daukar haka,ji nake kamar na mutu" Cikin sauri ta rufe mata baki,tana girgiza mata kai "ko wani dan Adam da kika gani yana da nashi tarihin,wanda idan aka tambaye shi da za'a mai da lokaci baya me zaka goge a rayuwar ka,zai fada maki nashi kuskuren, Na tabbatar da mahaifiyarki ma haka yake a gare ta,kamar dai ni,idan da ace lokaci na komawa baya,da babu a binda zai raba ni da Abdul basit,kome yayi ba zan taba rabuwa dashi ba,kinsan wani abu dake min ciyo? Girgiza kai tayi, "Ko lokacin da suka zo sunan Amira ban yarda na haɗu dashi ba,saboda har lokacin haushin shi naje ji,rabon da in ga fuskarsa tun zuwansa Nijeriya na farko duba Suraj wanda suka zo da Ummi,ba zan taɓa manta murmushin shi ba,mai dauke da ma'anoni" Dan shiru tayi ita ma tana goge hawayen idon ta tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, "Sai dai babu ta yanda zamu mai da hannun agogo baya,dole ne mu karɓi kaddara,mu ajiye aikin dana sani da muka yi ta hanyar kyautatawa,karmu bari damuwa da dana sani su runjaye rayuwar mu,muna bukatar cigaba,na san ba zamu taba mantawa ba,sai dai ina fatan ya zamo lokaci-lokaci zamu dinga tunawa saboda ya zamo izina a gare mu"hannun ta tari ko "tashi mu je ki ci abinci" Tashi tayi ta rungyme ta gaba ɗaya "na gode,da kika bari na zauna tare dake bayan kin san ki ni wacece,na gode da kika bani damar auren ɗan ki duk da kinsan irin abinda nake aikatawa," Shafa kanta tayi"ke din Amana ta ce" Dagowa tayi "amma banji kun ce komai ba game dashi,ko dai ya mutu ne? Girgiza kai tayi" Bai mutu ba,sun boye shi ne suna ta azabtar dashi tsayin waɗannan shekarun,yanzun haka yana Asibiti a Nigeria,in nuna maki hoton shi ne? Da sauri ta ce "a'a" Tana sauka daga kan gadon. Ita ma bata ƙara ce mata komai ba ta biyo bayan ta,ita ta zuba mata abinci sai dai kaɗan ta iya ci saboda rashin daɗin baki,dole Ammi ta kyale ta,tunda ko ba komai ta danci kaɗan ɗin. Sai da tayi sallah Isha'i wanda ta jima tana kai kukanta a wurin Allah sannan ta tashi ta yaɗa ruwan wanka,da kalolin turaren da Ammi ta bata,tana matukar son kamshi har balle idan zuciyarta babu dadi,hakan yasa ta zuwa ruwan turaren da yawa a cikin ruwan wanka,ita karan kanta tana jin yanda yake hawa mata kai,amma hakan bai dake ta ba,in da zata samu Relief kawai take nima,haka ma ha turaraw jiki,magungunanta ta diba ta sha,na ruwan ma kaɗan ya rage shine ta juye ra shanye, Tana kammalawa hawa tayi kan gado ta kwanta tana dunkulewa,so take tayi bacci amma ta kasa,tunani ne yake zuwa mata ta ko ina daki daki,kafin kuma a hankali ciyon mara ya fara,domin bata san illar Overdose da tayi na turaruka da kuma magani ba,a tunanin ta ai normal ne, Tun tana ɗaukar abin da wasa har taji yana so yafi ƙarfinta,ganin juyeyuye ba zai mata ba,yasa dole ta sauko ta nufi kicin domin haɗa ruwan lifton ko Allah zai sa ya sake, Kallon agogo falo na daya tayi da ya buga ƙarfe goma, Da kyar ta ita zuba ruwan zafi a cup daga cikin ƙaramin fulas,tsugunnawa tayi a wurin tana dafe mara,ji take kamar ana karta mata wani abu,wani irin yanayi take jin kanta wanda bata isa tace meke damunta ba, Tun shigowar ta kicin din yana zaune,dan haka duk nurkususun da take yi yana kallon ta, Mikewa yayi ya karaso inda take ya tsunguna tare da kiran sunan ta, Jin muryar shi ne yasa ta gado kai tana zuba mashi rikitattun idanun ta, "Me ke damun ki? Ya tambaya, Sai da ta lumshe ido ta bude kafin a hankali ta fusta"Mara" "Kin ci wani abu ne? Bata ba shi amsa ba sai ma mikewa da tayi dafe da ciki tana kokarin barin wurin,da Allah kaɗai yasan yanda take ji, Rikota yayi ta dawo daf dashi,kare mata kallo yake yi daga tsayen da suke,ringa bacci mai kauri ne a jikin ta na doguwar riga,sai dai babu komai na siglate a cikin ta domin yana iya ganin kan nipple din ta daga cikin rigar,dauke idon shi yayi daga nan, Shi ba yaro ba ne,ko ba komai zai girme mata da kusan shekara biyar ko bakwai, "Kina bukatar taimako na? Kafin ta bashi amsa sai ji tayi ya ɗauke ta tamkar wata ƴar tsana yayi sama da ita,kwantar da kanta tayi a saman faffadan kinjinshi,tana shakan kamshin shi, Ita dai bata san a wani daki suka shiga ba,ta daiji ya kwantar da ita saman gado sannan ya rufu a kanta, Tsira tama ido yayi yana kallon fuskar ta dake daf da nashi,yanda take ta faman lumshe ido da buɗewa,tana kuma sauke numfashi da dan sauri_sauri, Ba zata iya jurewa ba,yau in ma ya kama ta mai FYAƊE ne sai taimasa, Dan haka ba tare da tunanin komai ba ta cire hannun shi daya masu rumfa ta mirgina,sai gashi ya dawo kasa ita kuma tana saman shi, Idanun shi dake cikin nata take kokarin janyewa,sai dai yaki bata dama, Cikin sanyi murya ta fuska"i am Sorry " "Can you do it? Wannan tambayar ne kuma bata gane in da ya dosa ba,dan haka ba tare data damu data sanin ba ta hade bakin su wuri daya,ta san ba zai taba respond ba,dan haka a hankali take sumbatar shi,yana tsutsan duk wani lungu da sako na cikin bakin in da ta san kai tsaye zai iya ta da masa da nashi fitinar, Kokarin cire bakinta take cikin nashi,sai dai ga nata mamakin sai ji tayi lokaci ɗaya ya juye da ita ta dawo kasa shi kuma ya dawo sama,wannan shi ake kira da kallo ya koma sama,domin wani irin sumbatar ta ya shiga shi yana tsotson harshenta, Lokaci yada ya dogo yaga cire rigar dake jikin shi,daga in da take wance ya zame rigar dake jikin ta,tana kallon yanda jikin shi ke rawa, Hmmm abune da bata taba zata ba,domin kuwa a wannan daren ta shayar da ita abunda bata taba tsammani ba,ya kuma tabbatar mata da maza suna suka tara,domin tun tana daukar lamarin shi da wasa tana ganin zata iya,sai gashi cikin abinda bai wuce awa daya ba ta fara rokon ya sauka ta gaji,domin yasa tayi release har sau uku a lokaci ɗaya,duk wani gaba na jikin ta ya saki, Ganin yanda tayi laushi ne yasa ya duko ta saitin kunnen ta"Bebin " Da kyar ta iya buɗe idanun ta da suka yi laushi a kanshi, Murmushi ya sakar mata "ban goshi ba" Wani irin zaro idanun tayi tana kokarin zabura,"dame? "Dake" Ganin shirin sauka take daga kan gadon yasa ya maida ita ya kwantar,yana kwantawa a gefenta tare da yasha maranta da ɗayan hannun shi,"sai da na tambaye can you don it,kina nuna zaki iya,ni kuma matsalar ban idan na fara ban san abinda ake kira gajiya ba,kin ga nj ko sau daya ban gamsu ba,amma ke gar kin yi uku,this is not fear,ni dai sai nayi" Kuka ta fashe dashi tana kai masa duka a kirji "ai ban taba sanin kai mugu bane sai yau Suraj,so kake na mutu? Light kiss ya sakar mata a lip,yana share mata ƴan hawayen da suka sauko" Kefa da kanki kike ikirarin ke Harija ce,ko dai dama baki samu dai-dai dake ba ne "rungumeta yayi tsam a jikin shi yana murmushi," Abar ma wannan maganar" Daga haka da salo ya ƙara sauyawa,domin duk yanda taso ta noke taki ba da haɗin kai sai da yasan yanda yayi ya tasar mata da wani sabon sha'awar ta hanyan wasanni, Ranar taga fitina wanda ya zarta tunanin ta,dan sai da ya kaita makura,tayi roƙo tayi kuka akan ta gaji ya kyale ta amma bai saurara mata ba sai da ya tabbatar da shi kanshi ya gamsu iya gamsu ta yanda sai da ya siyaye duk wani abunda ke dankare a mararsa, Dariya ne ya nime subuce masa a lokacin da ya kalle ta yaga yanda tayi rashe rashe tana sauke numfashin wahala,ko yatsarta bata iya dagawa, Ban daki ya shiga ya haɗa masu ruwan dumi,sannan ya zo ya dauke ta, Jin ta a ruwan zafi ne yasa ta buɗe ido tana fashewa kuka,tasan ko bata yage ba to taji rauni,dan sai rintse ido take yi, Jawota jikin shi yayi ya rungunme "kina so na kara ne,idan baki gamsu ba ni a shirye nake" "Kawai ka kashe ni ka huta kawai" Sumbatar wuyanta yayi yana kyara mata suma gefe,"idan na kasheki waye zai dauki nauyi na? "Daga yau babu ni babu kai,karka kara nuna ka sanni,mugu mai fuska biyu" Wannan karon kam ya kasa rike dariyar sa sai da yayi,wanda haushin haka yasa ta fasa kuka tana kokarin kwace jikinta a nashi,sai dai yaki sake ta,"ki saka a ranki yanzun zamu fara,domin babu daga ƙafa,bana son ciyon mara yaci gaba da kamamin ke Bebin,"ya faɗa yana sunsunan gefen wuyanta,domin wannan ƙanshin nata ba karamin kara tayar mai da hankali yake ba, Da kyar ya bar ta tayi wanka sannan suka yi wankan tsarki,ya riga ta fitowa saboda yana son ya kyara in da zasu kwanta, Wurin takawa har da hawayen bakin ciki take yi jin yanda ƙafarta ya rike yake mata zafi,tun da take biye_biyen ta bata taba haɗuwa da mutum dan duniya ba irin Suraj,yau taga sital har da wanda bata taba sani ba,juyata take ta yanda yaga dama,ita da take ikirarin yi masa Fyaɗe sai gashi cikin sauƙi ya juya da ita,gashi tafiya ma nima yake ya gagare,wallahi in dai haka ne babu shi babu ita,zuwa gobe ma komawa Nigeria zatayi domin dama ba son shi take yi ba,aiki ya kawo ta kuma komai ya zo karshe,komawa gida zata yi tana buƙatar ganin iyayen ta da yan'uwa ta,tana son taga Mama dan haka ba zata zauna dashi ba......... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *85* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Tana fitowa daga banɗaki sanye ta iske shi da jallabiya yana zaune a bakin gado, Ganin ta yasa ya mike cikin takunnan nashi na nasuwa ya tsaya a gabanta,sai da ya gama kare mata kallo tun daga sama har kasa kamar mai minan wani abu ajikin,dan wannan kallo na shi har ya fara bata tsoro, Turo baki tayi cikin jin haushi "to me kuma kake kallo na" Daga gira daya yayi "me yasa ba zan kalli abu na ba" "Babu wani abun ka anan,ni ka matsamin,wallahi da nasan kai lalatacce ne ai da ba zan taba amincewa na aure ka ba" Dariya maganarta ta bashi,yanzun fisabilillahi tsakanin ita dashi waye lalatacce,"yanzun dan na taimaka maki shine kike fadin haka?na tabbatar da idan da ban taimaka maki ba ƙila da fyaɗe zaki min" Zaro ido tayi tana matsawa kamar taga abin tsoro,cikin in in na ta shiga faɗin "ni me me yasa to zan maka fyaɗe,kaɗai ji tsoron Allah Suraj" Bude baki yayi yana mata kallon zargi tare da nuna ta"kardai ki ce abinda ki kayi niyar yi min kenan? Da sauri ta juya tana ƙoƙarin barin dakin"ni kalle ka kato da kai ta yaya zan maka hakan" Bin bayanta ya shiga yi "faɗa min gaskiya dai" Ganin kofar a kulle ne yasa kawai ta haye saman gado tana lulluɓe kanta da bargo "ka ƙyale ni" Dariya ya shiga yi"to tashi wallahi zan tsaya ba zan maki gardama ba har ki gama" "Live me alone" Yaye bargon yayi yana dagota gaba ɗaya ya zaunar,"kina da Alwallah? "Hmmm" "Sauko ga kayan ki na dauko maki ki saka sai mu yi sallah" "Ni ba zan iya tsayuwa ba kafa na ciyo yake min" "Don't be a lazy girl" Cikin shagwabar da bata san tana yi ba har da murza kafa ta shiga faɗin "to ba kai bane ka ji min ciyo,ni ko tashi ba zan iya yi ba" Shafa fuskar ta yake yi murmushi ya kasa daukewa a fuskar shi"to bari na duba,kin ga da an kara yi sai ki saba lokaci ɗaya" Da sauri ta sauko kan gado,ba tare da tace masa komai ba ta saka kayan da ya ajiye mata da hijabin, Sallah ya jasu raka'a biyu,sannan ya jero masu addu'o'i sosai,bata yi mamaki ba kasancewar ta san waye shi, Koda suka shafa cewa yayi ta hau gado ta kwanta,dama jira take yi dan haka hijabi kawai ta cire ta haye gado,tun tana kallon shi yanda yake jero nafila har bacci ya kwashe ta. Da Asuba ma kafin tayi sallah sai da ta kuma shiga ruwan zafi,sannan ta dauro Alwallah tayi sallah,tana idarwa kuma tayi kan gado ta lunkume domin ko kadan bacci bai ishe ta ba, Baccin ta bai yi wani nisa ba,ta fara jin wani baƙon yanayi na ziyartar ta,ta ko'ina jikin ta karɓar sako yake yi,tun tana ɗaukar abin kamar a mafarki har lamarin yasa ta buɗe ido, Jin kanshi a kirji ta yasa da sauri tayi ƙoƙarin ja baya,sai dai kara rungume ta yayi yana ci gaba da abinda yake yi, Gabaɗayan su numfashi kawai suke saukewa,so take ta kwace jikinta ta hanashi sai dai ta kasa domin jikin ta ya riga yayi na'am da abinda ke faruwa, Da kyar ta iya dago kanshi,suna fuskantar juna,cikin kasewar murya tace"pls... Ya isa haka... Bacci nake ji" Haɗe goshin su yayi wuri ɗaya ya shiga sunbartar ta a hankali yana yi yana kallon idon ta,so yake ya tabbatar yanda yake a tsume ya tsuma ta, Ganin da kanta ta amsa ragamar ne yasa yace"can you do it? Kankame shi tayi ba tare da ta bashi amsa ba,dama kuma abinda yake jira kenan, Bayan shudewar wasu mintuna,baka jin komai sai gunjin kukan ta, Shi kuma yana tsugunne a gabanta rike da hannun ta yayin da take daure da ƙaramin towel kanta ma daure da daya,daga dukkan alamu wanka ta fito, "Kin ga a hankali fa na yi,kuma ke kika bani dama,sai da na tambaye ki can you do it kika bani go a heard,har da bude min ƙafa... " Cikin kuka ta kai mashi duka a kirji "mugu,ai dama da gangan kayi,sai da ka bari na fita haiyacina sannan zaka tambaye ni?sannan ko na ce a'a faɗi min tsakanin ka da Allah kyale ni zaka yi? Ta faɗa tana tsare shi da jikakkun idanun shi, Dan shafa kai yayi" Eh to kila," "Eh to kila,wato ba kada tabbaci,gashi yanzun ka jawo min zama gurguwa,ni dai ba zan iya zama da kai ba" Tashi yayi ya zauna kusa da ita"is ok ba zan kara ba,sai dai a duk lokacin da zan ganni tare dake ni kadai,kasa riƙe kai na nake yi" Juyowa tayi ta kalle shi"to me yasa a baya baka min haka?sannan me yasa sai yanzun?ni dai nasan ba haka kake ba,ko dai kasha wani abun ne" Mikewa tsaye yayi yana kara mikar da ita "idan da Ace na sha wani abun da ko tashi na tabbatar da bazaki iya yi ba,ko dai kina so in kwada ne? Cikin sauri ta girgiza kai, Jan hannun ta yayi suka fara takawa,taku biyu ta tsaya tana yarfe hannu " Ba zan iya ba" "Zaki iya,mu koma ban daki na kara taimaka miki,kiyi iya kokarin ki wurin ganin kin ɗaure,saboda yau zaki tafi Nigeria,idan kuma har Ammi ta lura ba zata bari ki tafi yau ba" Ai bata san sanda ta tsaya da kyau ba,wani irin gwarin gwiwa mai haɗe da farin ciki ne ya lulluɓe ta,ko ba komai yau zata rabu da azabar nan nashi,kwana daya kawai da suka yi tare ya fitine rayuwar ta,ya hanata barci,ita duk abinda zai shiga tsakanin ta da bacci bata kaunar shi, Rashin ganin fara'a a fuskar shi bai dame ta ba,tunda dai har zata wuce shi ya sani,cikin zumu di tace"karfe nawa jirgin zai tashi? "Takwas" Kwalalo ido tayi ganin bakwai da kwata,cikin sauri ta juya ta koma ban dakin,zaman minti biyar tayi a ruwan zafi dan tana buƙatar shi,Allah ya gani ita ta san raɗaɗin da take ji, Ko da ta fito baya ɗakin,dan haka dakin ta shiga,sai dai turus ta tsaya ganin akwati a tsakiyar dakin alamun an shirya kaya, Jin motsi bayanta ne yasa ta juyo tana bin shi da kallo,hannun shi riƙe yake da wani madaidaicin tray mai dauke da kofin shayi sai plate din abinci, Ajiyewa yayi sannan ya kalle ta "zo ki karya kar yayi sanyi,na riga na haɗa maki kaya tun dazu" A hankali ta tako har in da yake ta zauna a gefe tana ƙoƙarin daukar chokali, Amsa yayi a hannu ta ya diba yakai mata baki,ganin taki karɓa ta tsaya tana Kollon shi ne yasa yace"upen your mouth" A hankali ta buɗe bakin ta ya saka mata,a haka har ta kusa kammalawa,ta kasa rike tambayar dake ranta "Do you Love me? Shima dagowa yayi ya mata kallon sakan uku kai tsaye ya bata amsa da" No" Dan zaro ido tayi"to Why i you feeding me? "Do you want me to Love you? Shi ma ya jefa mata nashi tambayar, Ɗan hararanshi tayi tana kama hannun tare da tura chokalin a bakin ta, sai da ta hadiye sannan ta bashi amsa" No need,saboda ni ma ba son ka nake yi ba,ka ga zamu rabu cikin sauki " "Waye yace maki zamu rabu? Cikin mamaki take kallon shi" Saboda ba mu son juna" Mikewa yayi dauke da tray "hakan bai da amfani,ki shirya ki same ni a kasa" Ya kasara faɗa yana barin ɗakin, Dan shiru tayi na wasu mintuna"to me yake nufi"karamin tsaki taja shi ya sani. Cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala shiryawa cikin doguwar riga na jallabiya sai karamin Baby hijab data Daura saman rigar sanyin ta,fuskarta yayi wani irin Fresh dashi har wani daukar ido take yi,babu digon kwalliya a fuskarta ko kwalli yau bata shafa ba sai man baki, Ganin baya falon ne yasa ta fara shiga dakin Grandma,anan ta tarad dasu zaune har da Ammi, Cikin girmamawa ta gaida su, Amsawa suka yi cikin kulawa Grandma tace"zaki tafi kenan? "Eh Grandma" "To adai ta haƙuri da rayuwa,duk wani abinda zaki je ki tarad ina fata ki karbe sa da hannu bibbiyu,dama kuma haka Ubangiji ya kadarto,ba laifinki bane suma kuma ba laifin su bane,inda taje muma muna nan tafe idan lokacin mu yayi" Ji tayi gabanta yayi wani irin faduwa wanda nan take taji duk wani zumudi da farin ciki da take ji ya yaye a lokaci daya,cikin sanyin murya ta ce"Grandma waye ya rasu? Juyawa tayi ta kalli in da yake zaune,girgiza mata kai yayi, "Ohh babu kowa kawai dai magana nake yi,kin ga tashi kuje karki makara" "Insha Allah nan da kwanaki uku munanan tafe" "To Ammi" Ta fada tana mikewa, Koda suka fito yana biye da ita,yayin da kayanta an riga da an saka a bayan mota ko, Tunda ta shiga gidan gaba ta zauna bata ƙara faɗin komai ba,tayi wani irin shiru babu abinda take saurara face bugun zuciyar ta, Kallon ta yayi ganin ko sit belet bata saka ba,dan haka dan rankafowa yayi ya saka mata, Har suka isa Airport bata ce masa ba sai dai binsa da take yi duk in da yayi,har ya kammala mata duk wani abinda yayi saura, Jan hannun ta yayi suka zauna a daya daga cikin kujerun dake wurin, Kafin yace wani abu ta riga shi "fada min waye ya mutu" Ta faɗa tana tsareshi da idanun ta,"Nasan kai tsaye haka kawai ba zaka ce na shirya na tafi gida ba koda kuwa baka sona " Hannayen ta duka biyu ya haɗa ya riƙe cikin nashi yana murzawa a hankali yayin da yake kallon idanun nata,sai dai ya kasa furta mata komai, Hawaye ne suka shiga saukowa daga ramin idanun ta,"Abdulrahman ne? A hankali ya girgiza mata kai, "Abdulmalik? Nan ma girgiza mata kai yayi, " Abdulmajid ne? Nan ma girgiza kai ya kuma yi, So take ta furta suna na gaba amma ta kasa,tsoro take ji,tsoro take ji akan abinda kunnuwanta tasu jiye mata, Jawota kirjin shi yayi ya rungume ta gaba ɗaya, Kuka ta fashe dashi sosai tana kara kankame shi tare da kara cusa kanta a kirjin shi,"na fasa zuwa,ba zan je ba" Dago ta yayi yana share mata hawayen fuskarta wanda suka kasa tsayawa da hannun shi,"look at me" Girgiza kai tayi tana kara dukar da kai, Dago fuskar ta yayi"kalle ni Bebin" Dago rinannun idanun ta tayi ta zuba masa, "I Trust you,no matter what comes I no you will overcome it,na maki Alkawarin nan da kwana uku zan zo,do you want me to come?ya faɗa da alamun tambaya, A hankali ta jinjina kai, Mai da ita kirjin shi yayi ya rungume yana shafa bayanta" That is my Girl " Dagota yayi ya bata light kiss a goshi kafin ya mike rike da hannun ta jin ana faɗar lokacin shiga jirgin su yayi,har iyakar in da zai iya rakata yaje sai da yaga ta shige kafin ya juya ya koma,cike da jimamin halin da zata sake shiga idan ta isa gida, Wannan hukunci ne na Ubangiji wanda babu wanda ya isa yayi hakan bayan shi......... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *87* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Jirgin su a Abuja ya sauka,tana fitowa daga Airport ganin motoci tayi jere kusan guda uku,tayi mamakin ganin Bala sosai, Akwatin hannun ta ya ansa cikin girmamawa yace"barka da isowa Uwar ɗaki na" Murmushi ne ya kucce mata,domin ko ba komai ta ji daɗin ganin wanda ta sani,"Bala kana lafiya? "Lafiya qlau nake"ya faɗa yana buɗe mata motar tsakiya, Sai da ta daidaita zaman ta sannan ta juyo" Me kazo yi anan? "Tarbar ki muka zo yi" Dan waro ido tayi"tun daga Kano? "Muhimmancin ki a wurin shugaba ya kawo hakan" Tabe taki tayi tana mai da kanta ta jinginar, Ganin haka yasa shima ta saki murmushi yana shiga dayar motar tare da bada umarni tafiya, Tafiyar awa daya da rabi ne ya shigo dasu garin Minna,kallon ko'ina take yi kamar yau ta taɓa shigowa garin,hannu ta saka ta dafe kirjinta jin yanda bugun zuciyar ta ke tsananta bugawa,addu'a kawai take yi akan Allah yasa yanda ta tafi ta bar kowa lafiya a cikin gidan Allah yasa ta same su lafiya, Jin tsayuwar mota ga ƙarar buɗe Get ne ya dawo da ita cikin hayyacinta,da sauri ta ƙara buɗe idon ta ganin in da suke,wato a harabar gidan su,mamaki take yi dama sun san gidan ne,sai dai mamakin ya tsaya ne a lokacin da taga mutane ta ko'ina a cikin gidan,sannan duk wanda zaka gani baya cikin daɗin rai, Kamar yanda yawancin hankalin mutane dake zazzaune saman tabarmi ya dawo kan waɗannan jerin motocin haka ita ma hankalin ta yake kansu,sai da ta kasa fito,kuma bata da shirin fitowa, Abdulrahman ne ya fito daga cikin gidan da sauri sai Aunty Hulaira dake biye dashi,kallo daya zaka masu ka shaida rashin natsuwa a tare dasu, Ganin isowar su ne yasa Bala bude ƙofar motar da take ciki, Lekawa Aunty Hulaira tayi tana kiran sunan ta,"Ummu Salma! Ita din ma kallon kanwar mahaifiyar ta tayi,ganin yanda take ƙoƙarin son ɓoye hawayen da ya kasa tsayawa a idonta ne yasa ta kasa ce mata komai sai binta da kallo da take yi, Hannun ta ruko ta na fitowa da ita, "Ina Mama?shine tambayar da ya fito daga bakin ta, Kallon juna sukayi,sai dai babu wanda ya bata amsa,sai ma jan hannun ta da tayi suka doshi cikin gidan, Duk in da tabi da kallo kawai mutane ke bin ta,duk da basu san Me ya faru ba amma sun san cewar ta daɗe bata gida,a tunanin su kila tana zaune ne a kasar waje, Kale_kale ta hau yi a falon,ganin babu wacce take nima ne yasa ta nufi dakin Mama,sai dai har bayi ta leka babu kowa,dakin Baba ma ta shiga,shima baya ciki,duk wannan nimar da take masu babu wanda da dakatar da ita kamar yanda babu wanda yace mata komai, Cikin tashin hankali ta fito falo in da duk suke tsaye cirko cirko ta riko hannun Abdulmajid "Yaya!ina Baba da Mama? Cikin sauri Aunty Hulaira ta rungume ta tana saka kuka" Kiyi haƙuri Salma,wanda ya fimu son ta ya karɓi abin shi," Ji tayi kamar mata fahince me take nufi ba,dan haka zane jikin ta daga na ta tayi"Aunty ni fa ban gane in da maganar ki ta dosa ba" Tana ƙoƙarin yin magana Abdulrahman ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu,sannan ya kama hannun Salma"biyo ni " Bin bayan shi tayi har suka zauna a daya daga cikin kujerun dakin, "Mama takasance cikin jiran ki na tsayin waɗannan shekarun da suka wuce,kulun cikin kuka take rike da hoton ki tana begen sake kasancewa dake domin ta nime tafiyar ki,sai dai Allah bai yi fuskokin ku zasu sake haɗuwa ba har izuwa numfashin ta na karshe,har i zuwa lokacin kuma sunan ki ka dai take kira, Tayi data sanin abubuwan data aikata a baya,tayi data sanin biyewa son zuciya, Muna roƙon ki a matsayin ki na ƴar uwar mu da ki yafe ma mahaifiyar mu kawo ki wannan duniyar da tayi bata hanyar da Ubangiji ya shardanta mata ba,mu mun jima da yafe masu" Ta kasa kuka ta kasa zubar da hawaye,jin idanun ta take suna mata raɗaɗi kamar ana zuba mata barkono, "Ina Mama?shine tambayar data ƙara gefa masu yayin da take daura idanun ta a kanshi, Ji yayi gaban shi ya ɗan faɗi,ganin yanda idanu ta sukayi ja yanda kasan wanda jini ke ƙoƙarin kwantawa a ciki,tsoro yake yi kar ta zo ta cutar da kanta, " A yau da karfe hudu na Asuba Allah ya karɓa abin shi" Wani irin shiru ne ya ratsa falon,jira suke suga tayi kuka ko ta saka salati,sai dai ko daya ba ta yi ba sai ma dukar da kai da tayi, "Baba fa? " Yana Asibiti a kwance,tunda ya samu labarin rasuwarta" Mikewa tayi tsaye"mu je ka kai ni wurin shi" "Ki bari ki huta ko ruwa fa baki sha ba" Wani irin kallo ta jefa mashi,ba tare da tace komai ba tayi gaba yana biye da ita a baya, Tana fitowa gaisuwa mutane suka shiga yi mata,sai dai babu wanda ta amsa sai shi dake bayan ta ne yake karbawa, A wurin parking ne ta iske su Bala zaune suna cin abinci,ganin ta yasa duk suka mike,da hannu tai masa alama a kan yazo,cikin sauri kuwa ya ajiye plate dun dake hannun shi ya iso in da take, Kallon Agogon hannun ta tayi"ƙarfe biyu yanzun,zamu iya komawa Abuja ku kwana gobe sai ku koma Kano,idan kuma har zaku iya tafiya Kano a yau kuna iya wucewa na gode" Dukar da kai yayi dan sai yake ganin ta kara masa kwarjini har balle da babu wani digon fara'a a fuskar ta, "Ubangida na yace mu tsaya dake,duk in da zaki muna iya kai ki,sannan akwai gidan saukar bakin sa a nan garin a can zamu sauka" "Bana bukatar ku,ku faɗa masa ni nace ku wuce damun ba komawa zan yi ba" Tana gama fadar haka ta buɗe motar da Abdulmajid ke ciki,ba tare da ta kara kallon in da suke ba, Tunda taga sun doshi hanya har sun wuce Tunga ta san I.B.B Hospital zasu nufa kenan,hakan na nufin jikin shi yayi tsani kenan, Mai da kanta tayi jikin windo tana hadiyar wani abu mai ɗaci da tauri da ya tsaya mata a makoshi. Har suka isa Asibitin babu wanda yayi magana a cikin su, Shi ya buɗe mata kofa ta fito sannan suka shiga ciki,a wani daki na musamman aka kwantar dashi shi kaɗai, Buɗe ƙofar yayi suka shi,sai dai kasa karasawa tayi in da take hango mutum kwance sanye da Oxygen, Janyo hannun ta yayi har bakin gadon, "Roƙon Allah yake yi a koda yaushe a kan kar ta ɗauki rayuwar shi ba tare da ya ganki ba,gashi yau Allah yayi kin dawo" Ita kanta ba zata iya shaida me take ji ba a zuciyar ta,lallai duniya ba bakin komai take ba,yanzun Baba da ta sani tsayayyen mutum mai nagarta da lafiya shine ya zama haka,shine kwance a nan kamar wani tsumma,shine haka ya koma kamar mai ciyon kanjamau,har tana iya ganin kashin awazan shi, Lallai Ubangiji ba'a mashi isgili,yanzun ina lafiyar da yake takama da ita,ina kuɗin da yake takama da shi,ina ɗaukakar da yake ganin yana dashi,yau gashi kwance duk abinda yake takama dashi ba su isa su mai maganin komai ba. Numfashin ta har wani rawa taji yanayi, Ganin kamar jiri yana ɗibar ta ne yasa ya dauko kujera ya ajiye mata tare da zaunar da ita gaban gado yana ɗaukar hannun Baba dake ajiye ya damka a cikin hannun ta, "Ki yi masa magana zai jiki"ya faɗa yana barin dakin tare da bar mata dakin, Ta kwashi mintunan da ita kanta bata san adadin lokacin da ta bata ba a zaune, tana riƙe da hannun shi,jin yana motsawa ne yasa ta daura idanun ta a kanshi,a hankali har ya gama buɗe idanun shi, " Baba! Lumshe ido yayi yana buɗewa, "Baba! Ta ƙara kiran sunan shi a hankali, Jiyowa yayi ya tsira mats idanu,dan kara matse hannun nashi tayi" Salma ce" Ta cikin oxygen din ya maimaita abinda ya faɗa,kokari yake yi ya cire oxygen din sai dai ya kasa, Taimaka mashi tayi ya cire,ta daga gadon kaɗan, Ƙara rike hannun ta yayi,"kin dawo ne? Jinjina mashi kai tayi"ka yafe min Baba"ta faɗa tana dukar da kai, Da kyar yake iya magana,kai da gani kasan yana jin jiki,"na gode ma Allah da ya nuna min dawowar ki,tabbas na cutar da rayuwar mahaifiyarku da naku,gashi ta tafi ta barni,ki yafe min" Girgiza mai kai tayi "Baba na yafe maku kai da Mama har cikin zuciya ta,ina roƙon Allah ya bar mana kai ko zamu samu sanyi" Hawaye ne ke yawo a idon shi "ko haka Allah ya dauki raina na gode Salma,ina maki fatan nasara da farin ciki a rayuwar ki" "A'a zaka rayu damu" "Ina mijin ki,Abdulrahman ya fada min kin yi aure,nayi farin ciki" "Baba zan mai da maka oxygen numfashin ka yana katsewa" Girgiza kai yayi"ki bari nayi magana dake" "A'a idan ka huta zuwa anjima zamu yi magana,na maka Alkawari" Ba dan ya so ba ta mai da mashi, Ranar sai dare suka bar Asibitin, Acikin mota ne ya kalle ta"me yasa ba ki yi kuka ba" Ajiyar zuciya ta sauke tana jinginar da kanta jikin Glass"na kasa" "Ya kamata ki yi domin gudun abin da zai iya haifar maki" "Ji nake zuciyata ta zama kamar dutse,kamar Baba wani jini dake yawo a ciki,wata kila ni ma lokaci na yana dab ne" Bai bata amsa ba sai ma girgiza kai da yayi,dole tana buƙatar kuka ko ta yaya ne,shi shaida ne akan yanda suka Shaku da Mama,sannan ace yau bata duniya amma ko hawaye bata zubar ba,Allah kaɗai yasan irin ƙonewar da take yi a ciki, Yanayin parking a cikin gidan,ta fito ta shige ciki,tunda bata ga motocin su Bala ba ta san sun wuce kenan, Dakin Mama ta buɗe ta shiga, Aunty Hulairaw ce ta biyo bayan ta"Ki yi wanka bari na kawo maki abinci " Girgiza kai tayi"bana buƙata,hutu nake so" "Amma kin san bai kamata ki zauna da yunwa ba ko? Cikin tsananin damuwa ta juyo gare ta" Dan Allah!ina son in huta,ki ajiye zan ɗauka anjima " Fita tayi kawai tana jawo mata ƙofa,gaskiya akwai matsala,ita kan ba zata bari haka kawai ka kashe kanta ba,gara ta faɗama Abdulrahman ya kira mijinta ya faɗa mashi........ 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *87* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Tana shirin kiran shi kenan sai gata ta fito"Aunty Hulaira,zan sha Tea " Ajiye wayar tayi"yauwa to bari na haɗa maki"cikin yan mintina ta haɗa mata shayi mai ƙauri,ta kuna zaunar da ita anan falo kasancer sauran yan uwa na ɗayan falon, Sai da ta tabbatar ta sha sannan ta shiga yi mata nasiha, Washegari ma bata zauna a gida ba tana Asibiti wurin Baba,wanda ba karamin daɗi hakan ya masa ba,domin ko ba komai ganin ta ya rage kaso casa'in na damuwar shi, Ranar ma sai dare Abdulmalik ya komar da ita gida,su kansu hankalin su yafi kwanciya akan ta zauna a nan din suna ganin hankalin ta ba zai kwanta ba, A ranar ƙarfe uku na dare suka samu kiran gaggawa daga Asibiti, Inna'illahi wa'inna'ilaihi rajiun,kafin su isa Allah ya amshi abin shi,a wannan ranar na Laraba sha huɗu ga watan shida shekara ta dubu biyu da ishirin da uku, Mutuwar data kara girgiza su da kara masu imani, Basu faɗa mata ba sai da aka dawo da gawar ƙarfe takwas na safe, Abdulrahman ne ya jawo Aunty Hulaira gefe"kin faɗa mata kuwa? Dafe kanta tayi"na kasa,ina tunanin irin halin da zata shiga,har yanzun taki kuka akan na Mama,ka duba ka gani acikin kwana biyun nan yanda ta koma,gabaɗaya tayi rama yanka kasan wacce ke ciyo,bata cin abinci,haka kuma bata bacci,yanzun idan na faɗa mata abinda ya faru bansan me zai same ta ba" "Dole ne zamu faɗa mata ko ba komai dole tayi sallamah da shi,bari naje na same ta" Ɗakin ya shiga da sallamah,a zaune ya same ta a bakin gado bata dago ba sai dai ta amsa, Ya dan jima tsaye a kanta sai dai ya rasa ta yanda zai fada mata, "Salma" Ya kira sunan ta, "Na'am" Ta amsa masa,ya kira ta ya kai sau uku tana amsa mashi sai dai ya kasa fadar komai, Dago shanyayyun idanun ta tayi wandan suka zurma acikin kwanakin da basu gaza biyu zuwa uku ba,tunda yau din ne sadaka ukun Mama, "Yau mun karasa zama marayu gabaki daya ko yaya? Sai da ya dan zabura,kafin kuma ya sukar da kai, Mai da kanta tayi kasa" Na rika na sani tun lokacin da kuka bar gida ƙarfe uku na dare cikin tashin hankali,na sani! Sai dai ka sani ni ba zan zamo maku damuwa ba,ni musulma ce na san hakan ƙaddara tace wanda ban isa in guje mata ba" Rungume ta yayi yana fashewa da kuka,domin shi kam bai da karfin zuciya, Sai da yayi kuka sosai tana jin shi amma ita ta kasa yin kukan, Aunty Hulaira ce ta shigo ta daga ta"mu je ku sallame shi saboda lokacin yayi da za'a mika shi dakin shi na gaskiya " Ganin kamar tana layi ne yasa ta riƙe mata hannu,a haka har suka shiga dakin shi da anan aka wantar da gawar wanda fuska kawai ya rage a ɗaure, Duk zama sukaya suka zagaye shi, Addu'a kowa ya shiga yi mashi da fatan samun da cewa,Abdulmalik da Abdulrahman ne hawaye ke zarya a idanun su,yayin data mai da idanun ta kan Abdulmajid da idanun shi suka yi ja suka kumbura alamun shima yaci kukan,sai ita da take yi wani irin nauyi a zuciyar ta,yayin da idanun ta suka shige ciki sannan suka yi ja yanda kasan wacce yaji ya shigar ma ido haka take jin suna mata raɗaɗi, Kallon dakin take yi yayin da rayuwar su ke sake dawo mata acikin ƙwaƙwalwar ta,da yanda suka mu'amala dashi a cikin wannan dakin,yau kuma shine yake bankwana da wannan dakin,a hankali ta fara ji fitar numfashin ta na nimar gagaran ta,dakin kuma na juya ma a lokacin daya, Ta dai ji an rungumi ta ana salati,daga nan bata ƙara sanin abinda ya faru bayan nan ba. *Washegari* A hanka ta fara buɗe idanun ta,dakin take ganin yana mata dishi_dishi,kanta na dan sarawa kaɗan, Hannu takai tana ƙoƙarin dafa kan,sai jin saukar lallausar hannu taji saman goshin ta sannan a hankali ana mata massage,hakan yasa ta mai da idanun ta ta kulle,an dauki mintuna ana mata kafin taji an saya sannan an daga gadon da take sama kaɗan,hakan yasa ta kara dube idanun ta,jin tayi an zauna kusa da ita sannan an riƙe hannun ta, Kokari take da idanun ta wurin son tantance wanda ke zaune kusa da ita, Cikin shakakkiyar muryarta da baya fita sosai ta kira sunan shi domin son tabbatar da ko shi din ne "Suraj" Sumbatar hannun ta dake cikin nashi yayi"Bebin " "Zan sha ruwa" Goran ruwa dake ajiye ya ɗauka tare da kofi wanda ke ajiye a cikin Basket din da aka saka kulolin abinci,tsiyaya mata ruwan yayi ya da gata baki daya ya jinginar a jikin shi,ma'ana rabin jikin ta yana saman nashi, Ƙafa mata kofin ruwan yayi,kirɓa biyu ya bari tayi ya cire kofin ya ajiye, "Zan kara ruwan" Girgiza mata kai yayi"zai saki ciyon ciki,ki bari an jima sai ki sha" Komar da kanta tayi ta jinginar a kafadarsa idanun ta lumshe,kamar minti biyu tayi wani irin zabura wanda da badan ya riƙe ta ba cikin zafin nama, da babu abinda zai hana ta faɗowa har ma taji ciyo, "Baba" Sunan da ya fito bakin ta kenan,tana ƙoƙarin sauka daka jikin shi, Duk yanda yaso ta nutsu kin natsuwa tayi sai kokawar sauka take yi,gashi jini har ya fara biyo Cannula dake hannun ta da aka saka mata drip, Hakan yasa ya daka mata tsawa wanda sai da dakin ya ɗauka,ai kuma nan take ta natsu jin yanda jikin ta ya amsa wani riƙo da ya maka, Cikin fushi yace"so kike ki kashe kanki?idan wani abu ya same ki fa?ance baki cin abinci,baki bacci,sannan baki yi kuka,me kike son ki zama? Ita ma cikin muryar kuka tana kwace hannun ta daga nashi"ya same mana,ina rukan ka dani " "Naji ina zaki je? " Babu ruwan ka da in da zanje " Kin bari ta sauka yayi"idan har ba zaki faɗamin in da zaki ba, ni kuma ba zan bari ki tashi ba" Duk yanda taso kwace kanta kasawa tayi domin da hannu daya kawai ya rike mata hannu,"kalle ni" Dago jajayen idanun ta tayi ta saka cikin nashi, "Maman ki ta mutu kwanaki hudu da suka wuce,jiya kuma Baban ki shima ya mutu,dukkan su ba zasu dawo ba,kin zama marainiya,wacce ba tada uwa ba tada uba" Ganin yanda ta nasu tana kallon shi ne yasa ya sake mata hannu yana furzar da ajiyar zuciya,"sun tafi in da ba zasu taba dawowa ba,sun tafi in da babu wani abunda zaki iya yi domin su dawo,haka Allah yaga dama,bai kadarta zaki haɗu da ita ba,ba zaki iya yin komai akan haka ba,zuciyar ki zafi kawai zata ci gaba daya,idanun ki kuma zasu ci gaba da yin ja,wanda hakan ke nuna rashin karɓar ƙaddarar ki,kinki ki karɓi ƙaddara,so kike ki nuna ma Ubangiji ke mai taurin kai ce, ko kuma ke mai taurin zuciya ce,b..... Gani yayi hawaye sharrr ya sauko daga cikin idanun ta, Ɓoyayyen ajiyar zuciya ya sauke "wannan shi ake nufi da taushi,idan har zuciyar ka ta kuntata,har ka samu ka saka tayi laushi,to zaka samu sassauci,har ka iya ɗaukar ƙaddara,s.... Duka ta kai nasa a kirji tana fashewa da kuka" Waye ya faɗa maka ban karɓi kaddara ba?kai ba kasa halin da zuciyar mutum ke shiga ba idan ya rasa wanda yake muradin gani,kai baka san wannan kuncin ba"ta kara fada tana kara karfin kukan ta, Zame hannun ta daga saman kirjin shi yayi ya jawo fito ya daura mata saman cinya sannan ya tashi ya bar dakin,dama wannan shine burin shi, Ta yi kuka iya yanda take jin hawayen sun tsaya,ta zubar sadu ko zata samu sa ida a zuciya, Koda ya fita bai yi nisa da dakin ba,asali ma jin gina yayi a ƙofar dakin yana sauraran yanda take kuka mai tsuma zuciya, A nata ɓangare kara matse filon dake cinyarta tayi,ji take komai na dawo mata sabo har ta da mutuwar Mama,shi kenan ta rasa su har a bada kamar yanda yace. Koda Abdulmajid da Ammi suka zo,cewa yayi tana kuka su barta tayi kawai kar su shiga,su koma gida shi zai dawo da ita, Abdulmajid ne yace"ya kamata kai ma kaje ka huta,tun jiya da kuka iso kana nan Asibiti tare da ita,gashi har kwana ka yi anan,kai ka koma da Ammi idan ta gama kukan zan dawo da ita" Girgiza kai yayi"she is my responsibility,hakki na ne kaje kawai " Ammi ne tace"mu je Abdulmajid,rai iya" "To Ammi" Yana kallon suka wuce,sai kyara zaman shi yayi, A jiya sun iso ƙarfe tara na safe dan sun samu halartar jana'izar shi,saboda jirgi suka biyu, Anan suka samu ana ƙoƙarin kaita Asibiti,Aunty Hulaira da wasu mata su biyu ne suka kai ta,su sai da suka dawo Makabarta sannan suka tafi dubata a Asibiti, Su sun koma gida saboda karɓar gaisuwa shi kuma ta tsaya da ita, to bata farkaba tun jiya sai yanzun,duk da an samu ta farfaɗo daga dogon suman data tafi,sai suka kara yi mata allurar bacci saboda ta samu ta huta. Ta dauki kusan Awa daya tana kuka kafin tayi shiru dan kanta tana sauke ajiyar zuciya,fuskar ta gaba daya ya kumbura yayi ja,abinka da farar mace, Buɗe ƙofar dakin yayi ya shigo da sallamah,zama yayi bakim gadon in da take zaune sanye da hijabi, "How ar you filling? " Better "Ɗan dagowa tayi ta kalle shi kaɗan" Thank you" Bai bata amsa ba sai na riƙo hannun ta da yayi yana mikar da ita"mu je gida? Kai ta gyada mashi, Yana riƙe da hannun ta suka fito bai damu dak in da suka gibta kallon da ake masu ba,shi ya buɗe mata gidan baya ta shiga sannan shima ya zagaya ya shiga,Bala ya ja su, Idanun ta a lumshe suke shi yasa bata san hanyar da suka bi ba sai jin tsayuwar mota da tayi, Shi ya ƙara buɗe mata,sai da ta fito take bin harabar gidan d kallon kafin ta juyo in da yake,cikin shakakken muryarta tace"nan ina ne? Tana kara kollon ko ina, Bai bata amsa ba sai ma ɗaukarta da yayi kamar wata karamar yarinya ya nufi tangamemen gidan da suke fuskanta,ba tare da ya damu da ma'aikatan shi da ke wurin ba..... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *88* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Ba ta da karfin da zata ce zata ci musu ko ta tsaya jayayya dashi,dan haka kwantar da kanta tayi a saman faffadar kirjin shi, Kofar wani daki ya buɗe ya shiga,kai tsaye banɗaki ya shigar da ita, Zaunar da ita yayi a saman wani kujera dake a cikin lafiyayyen bandakin,tsaftacecce kuma, Buɗe idanun ta tayi tana bin shi da kallo yanda yake haɗa mata ruwan wanka da zuba duk wani abinda yasan zai taimaka mata wurin saukar da gajiya, Dawowa yayi ya da gata tsaye, Hijabin dake jikin ta yake kokarin zamewa ta riƙe "me zaka yi? Zuba mata idanun shi yayi,kafin ya busar da iska yana riƙo hannun ta," Taimaka maki zan yi,ba wani abu ba,ki yarda da ni " Ta san shi ta kuma san shi ba mutum bane mai cutarwa,yana da tsayawa akan maganar shi,dan haka a hankali ta saki hijabin ta data kanainaye, Kanta na katsa,tana jin yanda yake zame duk wani sutura dake jikin ta,sai da ya rage daga ita sai pant da bran,zagayawa yayi ta bayan ta,jin saukar hannun shi a saman maɓallan bran din ta ne yasa ta ɗan ja numfashi, Daya bayan daya yake ɓalle maɓallan guda uku har ya kammala, Da sauri ta dafe kirjinta d hannu ta yanda bran din bai faɗi ba, Zagayowa ya kuma yi ya tsaya a gabanta,ba tare da ya kalli fuskarta ba ya saka hannun shi duka biyu a saman kafadar ya shiga zame hannun a hankali har ya gangaro,ganin bata cire hanun ba,shi kuma bai daga hannun shi a wurin ba ne yasa dole ta zana hannu tana kara yin kasa da kanta, Cirewa yayi ya ajiye,sai dai tun daga nan kuma sai ya kasa yin komai,sai tsayawa da yayi yana kare mata kallo,ita kuma da gangan ta ki kare jikinta,to me zata ɓoye shi, Ganin ta fara gajiya da tsayuwar ne yasa a hankali ta raba ta gefen shi ta shige cikin bahon wanka, Lunshe idanun shi yayi da dan ƙarfi ya buɗe,ba tare da ya kalli in da take ba ya bar bayin, Ta jima a cikin sannan ta fito,sai dai baya cikin dakin wani irin sanyi ta ji ya ratsata lokaci ɗaya,lokacin data daura ƙafarta a tals din dakin dan ba karamin sanyi ya ɗauka ba,ga na AC dake busowa, Har cikin kwakwalwarta take jinshi, Cikin sauri ta haye kan gado ta jawo bargo ta shige ta dungule. Ya dauki lokaci sai kuma gashi ya shi ya shigo dakin dauke da tiren abinci da kuma ledan magungunan da aka amsu, Ajiye tiren yayi ya nufi bayi,sai dai bata ciki,fitowa yayi yana tunanin ina kuma ta shiga ne, Idanun shi ya sauka a kan gado,yanda mutum ke dunkule yana rawar sanyi, Da sauri ya hau kan gadon yana yaye bargon, Tallabota jikin shi yayi yana jin yanda jikinta ya dauko wani zafi,"Bebin,upon your Eye" Ƙara shigewa jikin shi ta yi tana faɗin "Suraj!sanyi na ke ji,ka rufe ni" Cikin rawar murya, Kankameta yayi"is ok" Ciro wayar shi dake cikin Aljihu yayi ya shiga Laluben number Farhan,kira biyu ya ɗauka, Cikin zolaya yake faɗin "Angon Biba bada kanka a sare" Karamin tsaki ya ja"jikin ta ya kara yin zafi,wani taimako zan bata " "Ba yanzun kuka dawo Asibiti ba? Ya tambaya saboda sun yi waya kafin farkawar ta, " Eh" "Ok ka kwantar da hankalin ka,ba wani abu bane,yanzun ina take? " Gata nan" "To samu ruwan sanyi amma ba ina nufin na firig ba,ka saka towel karami kana shafa mata a jiki gaba daya,idan kuma har zuwa lokacin bai sauka ba,kai kayi amfani da jikin ka" "Kamar ya? " Kai ban son iskanci"ya faɗa yana sauke wayar, Kallon ta yayi yanda ta kanainaye shi,a jiyar zuciya ya sauke yana kwantar da ita da kyau, Kamar yanda yace haka yi mata sai dai har zuwa lokacin idan yayi sanyi sai kuma ya kara zafi, Karshe rigar dake jikin shi ya cire ya cire mata towel din dake jikin ta ya rungumeta yana jin yanda zafin ke ratsa shi, Tsayin awanni biyu da ta samu bacci a jikin shi ba karamin jigata yayi ba,dan ko rintsawa bai iya yi ba,ganin lokacin sallah na gabatowa yasa a hankali yayi ƙoƙarin zameta daga jikin shi,sai ji tayi ta kara kankameshi,mai da kanshi yayi ya kwantar na tsayin mintuna biyar kafin ya ƙara ƙoƙarin gwadawa ta hanyar zame hannayen ta data zagayeshi dashi, A hankali ta buɗe idanun ta wadanda suka sauya sukayi dishi_dishi,"please don't live me"tana kara komawa jikin shi, Ajiyar zuciya ya sauke,yana shafa kanta,"i will never live you,never " Dago kanta tayi tana kallon shi"kayi Alkawari" Sumbatar goshin ta yayi"i promised,na maki Alkawari " Ajiyar zuciya ta sauki na samun natsuwa,tana sakala yatsun su wuri ɗaya tana juyawa"ina jin kewar Mama sosai,da ace tun a wancan ranar nazo da mun haɗu da ita,har ma muyi magana,sai dai.. sai dai.. Kasa karasa fada tayi jin yanda kuka ke ƙoƙarin sarke ta,kokarin cire hanun ta take yi cikin nashi,sai dai yaƙe sakin nata hannun ta, "Koda ma ace kin zo wancan ranar,kin kuma haɗu da ita,ba lallai bane ta iya yi maki magana kamar yanda kike so,saboda haka Allah ya tsara,yanzun haka babu abinda tafi buƙata daga gare ki wanda zaki nuna mata soyayya har ta san kina yi sana da Addu'a,shi kaɗai zaki dinga mata wanda zai isa gare ta,har da shi Baba,ko ba komai ya raine ki na tsayin shekaru goma sha biyar,ba tare da gajiyawar shi ba,kuma cike da kulawa da tattali,shi ma ya cancanci addu'a daga gare ki," Kuka ta fashe dashi,"shi kenan ba ni da kowa " "A'a ki na da ni,sannan ga yannin ki,ba za mu taba barin wani abu ya same ki ba" Dago jikakkun idanun ta tayi,cikin kuka ta tace"Amma ba ka so na,ta yaya zan iya rayuwa da mutumin da baya so na,kuma ni ma ba na son shi,ta yaya zan yi farin ciki,ta y.... Haɗe bakin ta da nashi yayi a hankali yake sumbatar ta, Haɗe goshin su yayi wuri ɗaya suna shakar numfashin juna,"zan kula dake na baki farin ciki na tsayin rayuwata,baki bukatar soyayya domin duk abinda kike buƙata kin samu "harshen shi ya saka ya shiga lashi duk wani ruwan hawaye dake saman fuskarta,sai da ya tabbatar ya kashe komai sannan ya gangaro wuyanta, Jin yanda yake sun sunar wuyan yana sauke mata numfashi yasa ta dago fuskar shi," Me yasa ka ce bana bukatar soyayya?ni soyayya ita na zaɓa a kan komai,ka mai da ni gida" Kwantowa yayi a jikin ta,"ki bari zuwa anjima" Dan ture shi tayi tana ƙoƙarin mirginawa "me yasa kake son mai da jiki na wurin hutawarka,kai ma ɗaukar jiki na kake yi wurin hutu kamar yanda waɗancan mutane suka ɗauka, Babu soyayya a tsakanin mu,ka kyale ni na tafi,ina son nayi rayuwar natsuwa ne yanzun,ina son na bar komai dana samu a wancan hanyar a baya,ciki har da kai,dan Allah"ta karasa faɗa tana sauka kan gadon, Kallon mamaki yake mata,da jin irin kalaman dake fitowa daga bakin ta,yanzun har shi Suraj zata faɗa ma haka,har shi zata kalli idon shi tace saboda jikinta yake tare da ita,tana kuma mashi kallon daya daga cikin mutanen da suka amfana da jikin ta, Ba tare da yace komai ba ya sauka daga saman gadon ya nufi ban ɗaki,ya jima sosai a ciki dan har ta gaji da jiranshi ta zuba abinci ta ci bai fito ba, Yana fitowa kuma bai kalli in da take ba ya fita,babu jimawa kuna sai ga shi ya shigo da leda babban a hannu,ajiyewa yayi saman gado,fuskarshi a cunkushe take yanda baka isa ka shaida yanayin da yake ciki ba,sai dai idanun shi da suka yi wani iri, "Ga kaya nan ki saka,idan kin kammala ki same ni a falo,zan mai da ke gida" "Na gode" "Umm" Ya fada yana barin ɗakin....... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *89* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Tana kammala shiryawa ta fito,a falon ta same shi yana amsa waya,zama tayi a gefen shi har ya kammala, Juyowa yayi fuskar shi dauke da dan murmushi "muje ko? Jinjina nashi kai tayi tana mikewa, Tare suka jero hannun shi na zube cikin aljihun wandon shi, Idan ka kallesu yanda suke taku a hankali yanda kasan wata da zara,sun bala'in dacewa da juna, " Akwai in da ke miki ciyo ne? Kallon shi tayj"Umm um,naji sauki yanzun sosai " Ajiyar zuciya ya sauke "that is good" Buɗe mata gidan gaba yayi ta shiga sannan ya zagaya ya zauna a mazaunin direba, A hankali yake tuka motar ba tare da gudu ko garaje ba,"Kasan gidan mu ne? Ba tare da ya kalli in da take ba yace "um" Jin haka yasa ta ja bakinta tayi shiru,dan ta fahimce ƴan miskilancin suna kusa, Cikin kankanin lokaci sai gasu a bakin Get din gidan su,mai gadi na ganin shi ya buɗe masu Get suka shiga, Tare suka fito sai dai ita gaba tayi ganin ya tsaya da Yaya Abdulmajid suna gaisawa, Tana shiga falo Turus ta tsaya ganin mutanen da bata taba tsammanin gani ba,wato yan Group din Yar Tsanar Zinari Fans group, Da gudu ta karasa ta rungume Ummunas tana fashewa da kuka,ita ma rungume ta tayi tana shafa bayan ta,cikin taushin murya ta shiga lallashin ta tana mata nasiha "ni ba zan hana ki kuka ba,domin duk wanda kaji yace yi ma mamaci kuka babu kyau to bai rasa wani mukusanci nashi bane,abinda kawai ba a so shine yin na fitar kima,kiyi haƙuri wannan wata jarabawa ce data same ki,kuma muna maki fatan zaki cinye ta" Dagowa tayi daga jikin ta tana share hawaye,"Addu'ar ki shi suka fi bukatar a yanzun"cewar Ummuhaidar, "Gaskiya ne komai yayi zafi addu'a ne magani,ki duba ki ga dukkan mu saboda ke muka zo nan" Cewar Bareerah Umar, "kalli ga Salma,ga DeejAysh,ga Ummu husna,kin ga harda Rx_Aryamn tana nan,duk da aiyukan da suke dashi haka suka ajiye domin ke saboda suzo su sanyaya zuciyar ki," Murmushi mai dauke da hawaye ne suka sauko mata,"Ummunas banga Salmancy da A.I Bauchi da Fatety ba,ko dai basu samu zuwa bane? "Sun zo,ina ga suna waje suna magana da Suraj ne dan sunce shima ya cancanci gaisuwa" Sallamar da suka ji ya saka su juyawa,fara'ar fuskokin su ne ya karu ganin tawagar Kungiyar Moonlight writers,wato kungiyar su na Marubuta tare da yan fans group dinsu, Queen Nasma ce a gaba,domin ita ce shugaba kuma jagoran wannan kungiyar mai Albarka,wanda ya hada manya kuma haziƙan marubata, Cikin girmamawa da mutunta juna aka shiga gaisawa tare da musayar ta'aziyya, Ko gama zama ba su yiba sai ga sallamar yan Fans group din FAKIRI yayin da shugaban su Khadijah Umar ta jagorance ce,tare suke da Fans din Sardauna,Allah sarki ƴan Amana, Wannan zuwan nasu ba karamin farin ciki da daɗi ya mata ba,domin mutane ne da suka zo daga mabanbanta yanki a fadin kasar,har ma da wajen kasar,kuma duk saboda ita suka zo,gaskiya in bata gode ma Allah ba bata san Me zata yi ba, Aunty Fati Uwar Abulkhairi ita ta fara lura da babu Uwar mijin ta,dan haka mikewa tayi tana dan lekawa tare da fadin"wai jama'a ina Jiddarh Umar? Daga bakin kofa suka ji ta amsa da "gani nan" Masha Allah kake jin yana fitowa daga bakin mutane,domin sanye take cikin leshi dinkin doguwar riga na bubu wanda ba karamin kyau ya mata ba,gata dama doguwa mai dogon gashi har gadon baya,ga dogon hanci har baki,ido farare tamkar madara,dan ko Biba da take mace sai da ta juya ta kara kallon ta tsabar kyau yanda kasan ba a duniyar mutane ba,kamar dai a duniyar Novel (ni ma na ɗana,ehe basu Biba kadai suke da kyau ba😜) Cikin tsananin farin ciki ta kara so ta rungume Biba tare da mata gaisuwar rasuwa,sannan cikin girmamawa ta gaida shugaban kungiyoyi da manyan su, Abinci lafiyayye Biba ta saka aka kawo masu,cikin har da su farfesun kaji da kayan shaye-shaye kala_kala, Dukkan su kowa yana ji da kanshi domin mutane ne masu aji da class, Nikam ganin basu da niyar taba komai ne yasa na juya na kalli Maman Abu,"Sirika idan zaki ci Bismillah idan kuma zaki tsaya yanga ni dai na yi nan"kafin su ankara sai ganin Jiddarh Umar suka yi ta zauna tare da takwashe kafa tashiga buɗe plate,duk wanda ya mata shi take jawowa gaban ta, Ganin da gaske ci take hankali kwance ya saka masu sha'awar ci suma suka fara ci, Queen ce ta danja gefen mayafin ta "Jiddarh" Juyowa nayi"umm "domin ba zan iya amsawa ba saboda baki na cike yake da namar kaza, " Me haka,dan Allah karki bada ƴan Moonligh mana" 'Gaskiya sai dai kiyi haƙuri Queen,ba zan iya ma kai na bakin ciki ba,haka kawai kana kallon abu kana son ci sai ka tsaye kana hadiye miyau saboda wani abu wai shi aji,gaskiya ni dai in kan abinci ne ba ni da aji,domin duk in da naje aka ba ni in har yamin zan ci ne,babu ruwa na ehe " "Dama nasan you ar very Stoburn" Tura baki nayi na ci gaba da kwasan girki na, Rx_Aryamn ce tace"Jiddarh ki bar naman nan haka,kin san ba lafiyar kirji gare ki ba,kuma likita ya hana ki cin soyayyen abu,salon ki ci yanzun an jima ki kama nishi da faɗin zaki mutu" "Ai sai dai ki yi hakuri likita,domin rayuwa bashi yuwa sai da soyayyen abu,ta yaya za'ayi in gani in kyale,gaskiya ci zan yi idan ciyo ya taso a sha magana asha wahala,idan an warke a ɗaura daga in da aka tsaya" "To karma dai ki nime ni anjima idan abun naki ya motsa" Sahibar Moonlight ce ta katse mu ta hanyar fadin "jiddarh naji ance ke yar Kano ce? " A'a ni ba yar Kano ba ce,ni yar Niger state ce" "Niger? " Ni fa bance Niger ba,ina nufin Niger State a garin Minna " "Wow abun mamaki,wai dama a Minna a kwai marubuta? " Akwai mana,ban san me yasa mutane wani bi suke raina baiwar da Allah yama dan adam ba,sau da yawa sai kiga mutane suna fadin ai gabaɗaya marubuta a Kano suke,alhalin basu san a garin da suke ma akwai ba,dan haka nake Alfaharin kasancewata yar Niger state " Murmushi ne dauke a fuskar su "gaskiya ne Jiddarh,yanzun dai tunda kin gama ya kamata a kira mana Ammi da Aunty Hulaira mu masu gaisuwa,daganan sai mu fita mu ma Suraj shima gaisuwa" "Haka ne" Duk suka amsa, Ammi ma ta ji dadin zuwan su sosai dan malama Amina Jibrin ta group din Fakiri ita ta bayar da Addu'a sosai tare da wa'azi mai ratsa jiki, A waje ma gaisuwa suka ma Suraj da su Ya Abdulmalik,har bakin Get Biba ta raka su kafin ta dawo, Ganin ta wuce ne Salmancy ta kalle mu"ni kuwa sai nake ganin kamar a kwai damuwa a idanun Suraj,ko baku lura da haka ba? "Ke dai Salmancy Allah ya shirye ki,baki iya gani ki yi shiru" Cewar Bareera Umar, "Allah da gaske nake ji" Girgiza kai Ummunas tayi,bata dai ce masu komai ba ita da Ummuhaidar, "DeejAysh baku gani ba? Busar da iska tayi ta baki" Ta ya za'ayi in gani bayan hankalina yana kan kallon baiwar kyan da Allah ya mashi" "Kuka sani ko damuwar mutuwar ce har yanzun a ran shi" Cewar fatity, "To me zai hana mu tambaye Jiddarh Umar" "Dadi na dake kanki na ja Salma" Ummuhusna ta fada, Jawo ni baya suka yi "faɗa mana meke damun Young Ustaz ne haka? Kallon su take ita ma kamar yanda suka zuba mata ido,dan har dariya sun so bata" To ta yaya zan sani,kawai dai ku jira ku gani koma dai meke damun shi ai da kanshi zai faɗa ko,ni ta yaya ma za'a yi in sani" "Saboda ke ce Alkalin wasan" Gira daya na daga,"a naku ganin ba,ni kuma a nawa bangaren hannu na shine Alkalin wasan,domin ban isa yanke hukunci ba sai lokacin da nake kan buga wasan,ma'ana sai lokacin dana dauki waya,dan haka mu jira mu gani,Allah sarki gaskiya Biba ta ban tausayi " Karamin tsaki sis Khadijah taja"ai ke kika sani,ni kunga tafiya ta ga Baban Hamnat can ya zo daukata " Sallamah suka mata ta wuce, A takaice dai da dai_daiya matan auren mazajen su ke ta zuwa suna ɗaukar su har ya rage daga ni sai Fatity, Ganin yanda ta yi shiru be yasa na dafa ta"ya dai mutuniyar" "Jiddarh aure zan yi" Ba karamin dariya maganar ta ya ba ni ba,ai kuwa sai da na dara"me yasa sai yanzun? Kafin ta ba ni amsa ne sai ga kiran Sultan di na ya shigo waya,dan haka ba tare dana saurare ta ba na daga mata hannu ina daukau wayar tare da shigewa cikin Adaidaita sahun dana tare, Murmushi tayi itama tana ɗaga min hannu........ *wannan shafin na sadaukar dashi ga yan group din Yar tsanar zinari,da Moonlight writers,sai group din Fakiri,wadanda na kira da wadanda ban samu na kira ba,ina matukar Alfahari da ku* *Love you all* 😘 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *90* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* *Sadaukarwa ga* Mummys Girl Maman Amira(Kaduna) Maman masoyi Hassana Muhammad Ummeeh Maman Ummi Khadija Barau ~Chawa Madame Anass Nana Aisha Maman Abdul, Na sadaukar da wannan shafin gare ku,Allah ya Albarkaci rayuwarku dana Ahalinku. Ko da ta koma falo har ma'aikatan gidan sun kusa kammala gyaran falon,dan haka kai tsaye dakin da Ammi ta sauka ta shiga, Tana ganin ta kuwa ta mika mata hannu,amsa tayi ta zauna kusa da ita, "Ya jikin naki? Dan dukar da kai tayi" Naji sauki sosai Ammi" "Alhamsulillah" Dan shiru ne ya ratsa dakin na sakon ni,kafin tace"ki yi hakuri haka Allah ya kadar ta ba zaku haɗu ba "nan ta shiga yi mata nasiha mai matukar sanyaya jiki,tana kara tsoratata akan tsoron Allah da bauta masa,cire damuwa da maida komai ba komai ba,muhimmancin hakuri," Ina fata zaki yi aiki da abinda na faɗa maki? Share guntun hawayen ta tayi tana jin yanda zuciyarta ke sanyi tana kara samun natsuwa"na gode sosai Ammi insha Allah zan yi iya ƙoƙari na" "Allah ya maki Albarka,ya baki zuri'a na gari" "Amin"cikin sanyin murya tace" Ammi ina Abbu,kin koma Kano ne,yasu Kaka? Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi,"ayanda naji Kaka tana kwance a Asibiti,amma jikin da sauƙi yanzun,Ashe tun randa ake shari'ar Nurudeen ya kwasa ya tura ma mahaifiyarshi,shine ita muka ta je ta nuna ma Kaka,wacce nan take ta yanke jiki,ita ma Goggon yara sai da aka saka mata ruwa saboda hawan jinjin ta ya tashi,jin Yayan ta ne ya kashe mijinta" Dan zabura tayi "ya mutu ne? Dafa kafadar ta tayi" Bayan sun kamashi da shekara uku shine ciyo ya kama shi wanda yayi sanadin rayuwar sa" Duk da bata sanshi ba,taso ace ko da sau daya ne ta gan shi, "Karki damu,nasan me kike tunani,Goggon yara macece mai sauƙin kai,sai dai tana da faɗa,baka sanin sauƙin ta sai ka zauna tare da ita,yanzun haka ta san komai game dake,sannan ashirye take data karɓe ki a mayin ya,a cewarta ke baki aikata mata komai ba,kuma ba laifin ki bane da kika zo duniya a haka,itama tayi kuka sosai tace kuma in nima mata gafarar ki,duk abinda tayi maki ki yafe mata" Girgiza kai tayi"ni dama ban rike ta ba Ammi,kuma bata min komai ba,na gode da karbata da tayi,ina mata jaje da fatan Alkhairi " "Hakan da kika yi shine dai-dai Salma,domin Allah yana son masu hakuri, Shi kuma Abbu yanzun haka yana gidan yari,domin washegarin dawowar ki suka turo shi nan tare da kwararrun hujjoji,yanzun haka an yanke mashi hukuncin rama gidan yari har karshen rayuwar shi tare da aiki mai tsanani,Salma gabaɗaya ya bata rayukan ahalin nan,idan kin je gidan yanda kika san babu mutane saboda rashin kwanciyar hankali da farin ciki" Katseta tayi"Ammi kin je ne? "Naje na duba Kaka,na tabbatar mata da ta kwantar da hankalin ta ni ban rike ta ba a rai na,kawai wanda yayi laifi ne ake hukuntawa,domin abinda yayi ba irin wanda za'a iya yafe mashi bane,ya aure ni bayan raba ni da mijina da yayi,yasan komai sannan ya tsaya yana cuta ta,yana da mata amma bai taba fada min ba,abubuwa marasa dadi Salma,ina matukar son mijina amma haka sukayi amma da kishi na suka raba mu,suka kuma kashe min su,ta yaya zan iya yafe ma mutum irin wannan,tsayin shekarun dana zauna dashi na zauna ne cikin kunci,rashin tabbas da dana sani tun farko,to amma ya zan yi,dole in jira har zuwa lokaci,lokacin daya dace"busar da iska tayi"na gode ma Allah da komai ya zo karshe,dazu da muka yi waya da Goggon yara tace zuwa gobe za'a sallami Kaka,mu kuma zuwa gobe idan anyi sadakar uku zan koma London saboda Mama" Ji tayi jikinta yayi sanyi idanun ta sun taru da hawaye "Ammi amma dai zaki dawo ko? Riko hannun ta tayi" Acan zan zauna saboda Ummi,ita ma tana buƙata ta,sai dai tunda kuna nan zan dunga zuwa lokaci-lokaci in duba ku,sannan ga waya zamu dinga yi kullun karki damu"ta faɗa tana rungume ta. Ranar bata ƙara saka shi a ido ba har ta kwanta kwanta bacci, Cikin magagin bacci ne ta ji wayarta na kara,sai dai saboda gajiya da kuma rashin son yin magana a waya da daddare yasa kawai ta kashe wayar ba tare data duba mai kira ba. Washegari ne da karfe goma na safe aka gudanar da Addu'ar sadakar uku na Baba wanda aka haɗa da na bakwai din Mama, Bayan kammala Addu'ar sai da suka kammala sallamar baki sannan ya kira ta awaya dan yana son zai wuce ne,ganin ba'a ɗauka bane ya kira layin Ammi,bugu biyu ta dauka da sallamah, Amsawa yayi yana faɗin "Ammi dan Allah in akwai wani kusa dake ki kice a faɗa ma Salma ta kira ni a waya" "Babu kowa kusa dani,sai dai in ni zanje na faɗa mata" Dan murmushi yayi"wane ni na aiki Abin alfahari na " Itama murmushi tayi"na maka uzuri,yauwa ƴar albarka kaga gata ma ta shigo" Yana jin sanda ta mika mata wayar tana faɗa mata ga mijin ki zai yi magana dake, Amsar wayar tayi tana barin dakin,sannan ta saka a kunni, "Hello" "Ki same ni a dakin Abdurrahman" Kallon wayar tayi ganin ga katse,karamin tsaki taja tana komawa ta kai ma Ammi wayar ta, 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *91* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Kamar yanda ya faɗa a dakin Ya Abdul-rahman ta same shi,sanye yake da ƙananan kaya a jikin shi,ta lura ya ɗan yi rama,hannun shi na rike da waya kamar ko wani lokaci, Zama tayi kusa da shi "barka da safiya" "Kin tashi lafiya" "Lafiya qlau" Ajiye wayar yayi yana fuskantar ta"yau zamu wuce " "Umm haka naji Ammi ta ce" "Yaushe zaki dawo" Dan shiru tayi tana dauke idanun ta a kanshi,"na riga na faɗa maka bazan koma ba,dan Allah ka sauwake min" Ba tare da ya kuma ce mata komai ba ya tashi ya fita, Da kallo ta bi shi,ita ba taga wani dalili da zai saka yaki rabuwa da ita ba,tunda ba wai sun shaku bane,koma dai ne zai yi sai dai yayi amma fa ba zata taba komawa rayuwar shi ba, Itama tashi tayi ta fita, Ranar ma sai a bakin Aunty Hulaira taji cewar ya wuce, Dan ita Ammi sai da akayi sallah Azahar sannan ta wuce,saboda zata kwana a Abuja gobe tabi jirgi zuwa London. Kwana biyu da yin sadaka baƙi na nisa dana kusa duk suka gidajen su,gida ya rage daga ita sai Aunty Hulaira sai kuma mazan, Kaka ce tace bata yarda Aunty Hulaira ta barta ta zauna a gidan ita kaɗai ba sai dai su dawo Bosso,dan in tana can ita kadai hankalin ta ba zai taɓa kwanciya ba, Suma su Abdulmalik sun yi na'am da hakan, Ita kuma sam ba ta so haka ba,tafi buƙatar zama ita ja dai akan zama da Kaka,dan ita Allah ya mata surutu ne,to amma ya ta iya dole ta tattara suka kwasa zuwa Bosso, Yau tsayin kwana biyar kenan da komawarta gidan kaka,wanda yake dai-dai da sati ɗaya rabon da suyi waya dashi,ranar sadakar uku, Jin yanda Kaka ke kwalla kiran sunan ta ne yasa dole ta tashi ta fito tana turo baki, A bakin kofa ta tsaya ba tare da ta iso inda suke zaune saman tabarma ba"gani" "Ai na ganki,wai ke meke damun ki ne,ace ayi mutum baya sakewa da mutane kullun shi kenan ƙunshe a ɗaki kamar Daudauwa,maza zo ki zauna ki sha iska,irin haka ba shi ke sakawa kafa mutum ya nukushe ba? Dariya Aunty Hulaira ta saka" Haba Mama sai kace wata tumatur ko Kankana" "Yo me marabin su da ita" "Kin ga Salma,zo ki zauna kisha iska qyale Mama" Takowa tayi ta zauna saman tabarmar "ni wallahi na gaji da zama haka" "Au duniya ta zo karshe,wato dai faɗa mana kike kin gaji damu gidan mijin ki zaki koma" Zaro ido tayi"ni da Kaka ba haka nace ba,Aunty Hulaira ni fa kishi ga tsakani ni da Kaka,dan na lura tunda nazo gidan nan ba ta da aiki sai ja na da faɗa " Hannu ta saka ta rufe baki,dan wannan fadan nasu yafi karfin ta, "Uwata an kai maki karata banji duka ba" "Umm,ina zuwa bari naje nasha ruwa"ta fada tana barin wurin,dan wannan faɗar na Kaka da Salma in sun fara sai su saka ka rasa abin faɗa, Ganin ta wuce ne yasa ita ma tashi ta bar ta zaune duk da tana jin irin kiran da take mata, Tana shiga daki taji wayarta na ƙara,ko kafin ta karasa ta dauka wayar ya katse wani kiran ya ƙara shigowa,dauka tayi na nazarin number,saboda number na kasar waje ne, Tasan kila Ammi ce,dan haka ta dauka da Sallamah, Jin shiru ne yasa ta kuma maimaita sallamar,tana kara tattara natsuwarta,domin haka kawai taji jikinta na bata ba Ammi bace,sunan shi da zuciyarta ta kama ne yasa tace"idan har kasan ba kada ƙwarin gwiwa magana me na kira? Daga cikin wayar tana jin yanda ya sauke ajiyar zuciya,kafin ya amsa mata sallamar, Dama kuma yanzun kaka ta gama bata haushi,cikin yanayi na masifa_masifa kamar wacce dama jira take ya kira ta sauke mashi tace"dama ai kai ɗan kyaluwa ne,kana jina ina ta sallamah amma ka kasa amsawa,kawai dan a saka bakin mutum ciyo," Jin tayi shiru ne yasa ya kyara zaman shi a ƙasan ya yake zaune saman lafiyayyen darduma,"na baki hakuri ne? Ya tambaya, Waiyo Allah aikuwa ji tayi kamar ya ƙoda mata mari "ban sani ba,ta yaya za kayi laifi sannan har ka tsaya tambayar ko ka bada hakuri ne,ban sani ba,sannan kar ka ƙara kira na" Kit ta kashe wayar, A nashi bangaren rike wayar yayi a hannu yana tunanin to lafiya,irin wannan masifa haka me ya same ta,ko dai shi ne ya bata mata rai, Dafe goshin shi yayi yana murzawa,ko tambayar da yake so ya mata bata bashi dama ba, Number Abdulmalik ya kira,bugu daya kuwa ya ɗauka,cikin girmamawa suka gaisa, Dan Allah ko zaka turo min Address din Kaka,da Account number na Salma" "Ok babu damuwa Bani minti biyar" Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gashi ya turo mashi, Godiya ya mashi,sannan ya kashe ya kira number Bala. Ana ta bangaren tana gama wayar Aunty Hulaira ce ta shigo "taso muje ki raka ni Baipass" "Ina ne kuma Baipass? " Ohh Allah na gode maka,yarinya kamar ba garin Minna aka haife ki ba" "Kinsan Baba baya bari muna zuwa ko'ina shi yasa" "Haka ne,sai dai Baipass din bai da nisa sosai da nan,da ta wurin Al_Amin bread zamu je," "Wurin wa? " Zamu kaiwa Hajiya Kaya ne,sannan Amina ma ta dawo daga Dubai jiya,kila kiga abinda ya maki a can " Mikewa tayi tana ƙoƙarin cire rigar jikin ta domin ta canja, Ganin haka ne yasa ta fita ta bar mata dakin dan ta san halinta yanzun ba kunya ne da ita ba tsaf sai ta kwabe kaya a gabanta babu kunya, Suna fitowa kaka ta kalle da ɗan ƙaramin gyalenta raka ni ganta,ai kuwa tace bata fita dashi,in dai har ba zata saka hijabi ba sai dai ta fasa fitar, Allah sarki har da hawayen ta kuwa,amma ya zata yi da kaka tunda tana son fita dale ta saka babban hijabi iya guiwa,kalar navy blue,ba karamin kyau ya mata ba, Adaidaita suka samu a bakin Bosso Clinic suka shiga, Kallon hanya kawai take yi tana jin daɗi yanda take shakar iska, Hankalin ta ne yayi nisa wurin kallon wani babban makarantar Sakondiri mai hade da wuraren wasanni manya,filin kwallon ma yanda aka kawatashi kadai abin sha'awa ne, Nuna ma Aunty Hulaira tayi"nan ina ne? "Ahmadu Bahago secondary School" "Amma gaskiya Babba ne" "Sosai ma kuwa" Juyowa tayi"yaushe zamu je kasuwa? "Me zaki yi a kasuwa? " Kawai dai ina son zuwa ne,kuma ma ai ba a rasa abun siya a kasuwa" "Sai dai zuwa ran Lahadi lokacin babu cikowar mutane sai mu je" "Allah ya kaimu" Har ta ƙofar gidan aka sauke su,wurin gidan Aimajirai,wadanda gasunan suna ta karatu, Kallon yaran take cike da burgewa,domin fes suke babu wani alamun datti a jikinsu yanda kasan ba Almajirai ba,suna riƙe da Allunan su, Murmushi kawai take siki, "Lafiyar ki kuwa kike murmushi ke kaɗai? Muma mata yaran tayi" Sun burge ni ne,yauwa Aunty mu je na basu sadaka duk da ban fito da kuɗi ba" Ai kuwa bin bayanta tayi,sai da suka gaisa da Malamin sannan ta ciro yan dubu dubu dake pos dinta wanda zasu kai goma koma sufi ta mika mashi,"Malam gashi aima yara sadaka" Dodiya ya shiga yi mata tare da saka mata Albarka, "Malam iyaye na sun rasu dan Allah ka saka su a cikin Addu'ar ku koda ta yau ce kaɗai" "Insha Allah za'a saka su yarinya,Allah ya barbarkaci rayuwar ku" Da Amin suka amsa, Tafiya kaɗan suka isa gidan saboda abinda hawa baya iya hawa ta wurin, Sosai Hajiya ta ji daɗi dan har zungumeta sai da tayi, Amina ita tayi masu girki,yarinyar nada matukar kirki da son mutane ga hiri yanda kasan ta daɗe da sanin Salma,dama ita Hulaira yar gida ce,saboda Hajiya tana matsayin yarinyar Kaka ce, Ranar sai dare suka dawo dan a can suka yi sallah Isha'i,, Ba kamin daɗin wannan fitar ta ji ba,ko ba komai ta siya kaya sosai a wurin Amina,dogayen riguna na yayi,da jakukkuna,sai wani sarka da Agogo,kayan sun mata kyau sosai,haka ma ita ta zaɓar ma Aunty Hulaira,ta kuma biya kudin nan take ta hanyar trasfer. Suna shiga gida daki ta shige ta cire kaya,kasancewar a kwai bayi a dakin Aunty Hulaira shiyasa ta shiga ciki ta jona ruwan zafi tayi wanka, Tana cikin saka kaya Aunty ta shigo"zaki ƙara abinci? Girgiza kai tayi"na koshi sosai " "To Kaka na kira" "Um hmm"sai da ta kammala shiryawa sannan ta shiga dakin Kaka, Zaune take tana tana saukaren labaran da ake yi a gidan rediyon prestige, Zama tayi kusa da ita" Gani tsohuwa" "Uwa ki ma tsohuwa ce tunda ajiye irin ki" "Amma ai bata kai ki tsufa ba,kinga fada min abinda zaki faɗa min dan ni barci nake ji" "Ai sai ki shake mako shi ki fito da maganar" Tabe baki tayi ta na hayewa kan gado ta kwanta,"idan na fara bacci kuma karki ta dani " "Dazu Ɗan Albarka ya aiko mana da kayan abinci da abun sha kala-kala,suna nan a kicin wallahi har babu wurin sakawa dole wasu a dakin baki aka jibga,ko shinfa kadai buhu goma,wannan ai sai ya shakara muna ci, bancin jarkokin manja dana man gyada, in... Katse ta tayi"Oh dama dan ki faɗa min haka kika hana ni kwanciya,ni kinga sai da safe" "Oh ba zaki tambaya waye ya kawo kayan ba,to Mijin ki ne sai ki masa godiya idan ya kira" "Ai ba ni na saka shi ya kawo ba,idan dan Allah yayi baya bukatar godiya" Duka ta zuba mata a cinya,"wallahi ki fita ido na in rufe " Ihu tayi tana durowa daga kan gadon"na fasa kwana anan ɗin " "Dama ban gaiyace ki ba" Wurga mata wani karamin jakka tayi"kashi nan wai a baki" Dauka tayi ta fita ba tare data ce mata komai ba tana gunguni, Zama tayi kan gado ta buɗe dan karamin jakkan,ATM card ne sai karamin wasiƙa,da kayi rubutu wanda bai wuce layi biyu zuwa uku ba, *idan kina buƙatar wani abu ki yi anfani da wannan katin* Tsaki taja tana wurga jakkan cikin jakkan ratayawar ta,kome ya mai da ita Oh ho,ya zo ya same ta. Komawa tayi ta kwanta kusa da Aunty Hulaira tana ja masu bargo.. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *92* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* *Bayan watanni biyu* Zaune yake a bakin ruwa yayin da ƙafafun shi ke cikin ruwan yana dan motsa su lokaci-lokaci, Yana kallon yanda iska ke kada ruwa,yayin da iskan ke ratsa duk wani sassa na jikin shi,wanda hakan ke kara saukar mashi da kasala, Duk da yaji sanda ya zauna kusa dashi hakan bai sa ya juyo ya kalle shi ba,duk da kuwa sunan shi daya kira, "Suraj"sanin yana jinshi amsawar ne kawai bai yi niya ba yasa yaci gaba da faɗin" Shin kana kallon kan ka a madubi kuwa?wai ko so kake yi damuwa da shauki su kayar da kai?duk da nasan dama kai ba mai jiki ba ne,amma duk da haka ka rame ka rage walwala,kafi son zama kai kaɗai fiye da zama cikin mutane,wai me damuwar ka,a tunani na ni da kai mun zama daya,ina iya faɗa maka damuwa ta,kai ma kuma ka faɗa min naka,amma wannan lokacin kana nuna min ni ba kowa bane a gareka,haka ne? Lumshe ido yayi yana fesar da iska mai zafi daga bakin shi,yasan maganar Faisal gaskiya ne,bashi da wanda zai tunkara da wannan damuwar,Ammi ma kyale shi tayi,taki cewa komai, Juyowa yayi suna fuskantar juna"Salma ce" Shiru yayi yana nazarin wacece ma Salma,sai can ƙwaƙwalwar shi ta kamomai hoton ta"Oh matarka? Ganin bai bashi amsa bane yasa da sauri ya kuma cewa"me ya same ta,ina fatan ba wani abu ba ne " Kauda kai tayi kamar mai jin nauyin abinda zai dafa "taki dawowa,a duk lokacin da zan mata maganar dawowa da faɗa muke rabuwa,ta koyi wasu dabi'u wanda ba nata ba ta Daura ma ranta,Yawan faɗa,da saurin fushi,komai ka yi a wurin ta kaifi ne," Shafa goshin shi yayi"na rasa yanda zan yi da ita," "To Ammi fa? " Taki saka baki,wai sai dai in yi duk yanda zan yi" Dafa kafadarshi yayi "ban taba tunanin akwai macen da zata saka ka tagumi ba haka" "Ban taba tunanin zan haɗu da mace irin ta ba " Wannan karon kam sai da ya dara,"Be a Man" "Idan na kira a waya da tana ɗauka ko masifa ne tayi,amma yanzun kusan sati ɗaya taki ɗaukar waya na" "To ka kira yannin ta mana" Girgiza kai yayi"a'a,hakan kuskure ne" Kyara zama yayi"ni kan Suraj ka taba furta ma yarinyar na cewar kana son ta? "Kamar ya in ce Ina son ta? " Kamar dai haka ko kuna waya,ko kuna zaune tun can baya har yanzun ka taba furta mata I Love you? Lumshe ido yayi ya buɗe"faɗin haka bai da amfani " Zaro ido yayi"me yasa,ko dai baka son ta ne? Shiru yayi kamar mai nazarin abin faɗa yayin da ya tsira mashi ido kamar a fuskar shi zai ciro amsa, Ganin shirun yana niman yin yawa ne yasa ya kara maimaita mai tambayar, "Ummm,fadin ina son ki ko ina son ka ba wani abu bane mai amfani,zama wuri ɗaya da yin rayuwa tare shi zai tabbatar da abinda ke zuciyar ka harma da irin muhimmanci da matsayi da abokin rayuwar naka ke dashi a gareka," "Banki ta abinda ka faɗa ba,sai dai ka sani yawancin mata sun fi son ko da yaushe kana faɗa masu cewar kana son su,kuma suna da matukar muhimmanci a rayuwar ka,ta yu ita matarka tana ɗaya daga cikin irin jerin waɗannan matan,amma kuma kai saboda wani ra'ayi naka baka taɓa faɗa mata cewar kana son ta ba,ko ka taɓa? Girgiza kai yayi" Ai naga ita ba yarinya bace" Dafe kai yayi yana dan girgiza shi "Oh My God!Suraj,ni fa abin da nake ta kokarin in faɗa maka shine su mata komai girman su da tsufan su tamkar yara haka ƙwaƙwalwar su take,suna son su ji ana faɗa masu cewar su masu kyau ne,kamshi na da daɗi,idan sun yi kwalliya kuma ace sun yi kyau,sannan a fada masu ana son su,suna son kalamai masu daɗi da kwantar da hankali,kamar yanda suke son kayan daɗi,idan har zaka iya saukar da kai to ka gwada " "Kana ganin hakan zai yi amfani? " Idan har ita mai ra'ayin soyayya ce to hakan zai yi amfani " "Ka yankar min tiket na Kano" "Kano kuma?ko dai Niger? " A'a ina son in je in duba Kaka ne" "Shi kenan". *washegari* Kamar yanda ya faɗa mashi kuwa haka yayi dan zuwa ƙarfe goma na safe jirgin su ya tashi daga nan Legas zuwa Kano, A gidan shi ya sauka,sai da ya huta zuwa Azahar sannan ya nufi gida, A bakin Get ya haɗu Nurudeen,tsawa yayi ya bashi hannu suka yi musabaha, Tambaya shi yake"yaushe ka dawo? "Dazu,ya garin? " Lafiya qlau,hala wurin mutuniyar kazo? Dan murmushi yayi"kasan dole sai ana yi ana leko ta" "Gaskiya kam,to mushiga ciki" Tare suka jera suna dan tattaunawa har shiyan kaka,domin yanzun duk sun zubar da makaman su,saboda sun san yanzun ko kusa shi ba abin rainawarsu ba,dan nasabarshi ma har yafi nasu, Ba karamin daɗi Kaka ta ji ba har da hawayen farin ciki,dukda ta san yana yawan shigowa ya dubata,amma ta ji kewar shi saboda a da kullun ai suna tare in dai ba ya tafi wani wurin ba,ko yayi tafiya zuwa wa'azi, Goggon yara ce ta shigo dauke da kulolin abinci a hannun ta,ajiyewa tayi tana faɗin "kai kuma yaushe a gari? Cikin girmamawa kamar ko yaushe ya shiga gaida ita, Amsawa tayi tana fadin bari a zubo maka abinci, " Ai kuwa dama yunwa nake ji,gashi kaka ko ruwa bata Bani ba" "Ja'iri ai daɗin ganin ka ne yasa ni sha'afa,jin ga zubo mashi" Da waya kuwa ta zuba mashi,yana cikin ci ne Salman ya shigo,sabar ɗokin ganin shi saura kaɗan ya barar mai da abinci, "Wai kai yaushe za ka yi hankali? " Yaya ai in ina ganin ka ba zan taɓa yin hankali ba"ya faɗa yana zama kusa da shi, Girgiza kai kawai yayi yana kallon Nurudeen da ya mai da hankalin shi wurin daddanna waya,"yaushe ne bikin naka" Dagowa yayi ya kalle shi"Malam da saura,dan har yanzun bamu gama daidaitawa da yarinyar ba" "To kadai yi ƙoƙari,so muke ka yi Azumi da mata bana" Tabe baki yayi, "Ina Ibrahim ne? " Yana wurin aiki" Goggon ce ta katse shi"ina yarinya ta? Ya san wacce take nufi"tana Minna" "Gaskiya dai ta kamata ta dawo dakin ta haka,kun yi magana da ita kuwa? " Eh gobe zani can din ma" "In dai har zata dawo ka kawo mana ita" "Insha Allah" Ya jima sosai suna hira kafin ya masu Sallamah akan zai fita zuwa anjima zai dawo,dan so yake yaje gidan yari ya duba Abbu. 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *93* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* Ba tare da wani matsala ba yana zuwa Gidan Yari aka bar shi ya shiga har zuwa wurin da suke ganawa da baƙi, Zaman mintuna biyar zuwa bakwai yayi sai ga shi ya shigo, Mikewa tsaye yayi har sanda ya kara so, Cikin girmamawa kamar ko yaushe ya gaida shi, Amsawa yayi cikin sanyi murya yana zama kanshi a kasa, Shima zama yayi suna fuskantar juna"Abbu!"sai kuma yayi shiru ya rasa me zai ce,Abbu Sufyan mutum ne da yake matukar girmamawa kodan son da yake ma Ammi,ko dan daurashi da yayi akan tarbiya na gari,sai dai lafinshi babba ne,laifin kisan kai ba karamin abu bane, "Ka yafe min Suraj!nasan na aikata kura-kurai masu yawa a rayuwata waɗanda a matsayina na masani,na take sani na nayi abinda nake so,na bi son zuciya,gashi a in da na ƙare" Ya fada yana fashewa da kuka, Duk yanda zuciyar shi takai ga motsawa yaki yarda ya zubar da hawaye,sai dai idanun shi da suka yi ja, "Ni na yafe maka Abbu ko dan Kanwata Amira,amma ka sani Allah baya yafe laifin wani sai in shi yace ya yafe maka, Mutanen da kuka kashe fa yaya za ku yi dasu?waɗanda kuka yi sanadiyar mutuwar su fa?iyalansu da kuka saka cikin halin damuwa,zullumi da bakin ciki fa Abbu?yaya za ka yi da nasu haƙƙin?"furzar da iskar bakin shi yayi,"Na roki Ammi da Grand ma,akan su yafe maka,sun yafe maka,domin rashin yafe maka ma babu abinda zai kara masu ko sai ma ya rage su,naso ace ko da sau daya ne ta zo ta ganka kamar yanda ka roka,sai dai taki yarda,ni kuma ba zan iya tilasta mata ba," Kuka yake yi sosai,wallahi_wallahi har ga Allah yayi nadamar abinda ya aikata, Mikewa yayi"ina maka fatan samun sassauci daga wurin Allah" Ya juya ya wuce,duk da ya so ya duba Shamsuddeen sai dai ba zai iya ba,saboda zuciyar shi ya riga yayi sanyi da ganin yanda Babban malami kamar Abbu Sufyan ya tafka babban kuskuren da yanzun yake kuka da na dama,lallai duniya budurwar Wawa ce,sai yanzun ya kara yarda da maganar Hausawa. Sai zuwa Yamma ya koma Gidan Kaka,in da anan take sanar dashi ai Maijiddarh za tayi auren wata mai kamawa,zata auri daya daga cikin Alarammomin da suke fita dasu wa'azin,mutumin matan shi biyu ita ce ta uku, Hajiya Saudat kamar za tayi hauka tsabar tashin hankali har da yaji, Amma babu wanda ya kulata da kanta ta gaji ta dawo, Addu'ar samun zaman lafiya kawai ya mata, A daren ne da zai wuce yaba Salman kyautar makullin mutar nan nashi,ai kuwa tsabar daɗi har da kukan farin ciki,duk wani ahali na gidan da ya samu labarin wannan kyautar sai da ya jinjina ma Suraj. Washegari jirgin safe yabi zuwa Minna, A gidan shi ya sauka,sai zuwa da yamma sannan ya shigo Bosso, Yaro ya aika aimasa iso, Tana jin sunan wanda aka faɗa tace maza ace ya shigo, Yana shigo har ƙasa ya tsugunna ya gaishe ta, Cikin jin daɗi ta amsa tana nuna masa babban tabarmar data shimfida masa har da darduma,a gindin icce,kasancewar ana ɗan taɓa zafi a garin, Tambayar shi take ya mutanen gida,cikin sakin fuska yake amsa mata, Dama ta riga ta gama girki,dan haka zubo mashi lafiyayyen Gurasa tayi a plate wanda yaji kayan haɗi da ganyayyaki kabeji,salat,karas,har da yankakken tumatur,ga dakan kulin yaji tafarnuwa da citta, Ai kuwa sake jiki yayi yaci sosai dan har ya manta rabon da yaci irin wannan abinci,gaskiya yayi missing Ammi, Ganin ya cinye ne yasa Kaka tace ko a kara mashi,girgiza kai yayi yana Hamda, Kasancewar ta mace mai surutu gata da iya jan mutane da hira yasa cikin lokaci kankani ta saka ya sake da ita,hira suke sosai har da dariya, "Mutuniyar taka ta fita motsa jiki,yau da kyar na nasamu na korata tabi Hulaira,kullum ba tada aiki sai kwanciya,idan dare yayi kuma ta hana kowa bacci wai jikin ta na ciyo, Shi yasa na tura su Tudun Fulani can kusa da Dam,gidan yar kanwa ta Mariya,maman Hafsat da Haidar," "Ko ba tada lafiya ne dai Kaka" "Kyale ta shegen taka ne kawai,yau kuma akwai labari" Ko gama rufe baki ba tayi ba sai ganin ta sukayi ta shigo babu ko sallamah ta shiga cilli da takalman ƙafarta,da dingishi ta karaso ta dauke ruwan goran dake gaban shi ta ƙafa kai,sai da ta shanye tas sannan ta ajiye goran, Aunty Hulaira ce ta shigo tana kyalkyalan dariya, "Ke kuma me haka zaki shigo ma mutane gida babu sallamah? Dan waiwaigawa tayi ta jawo kujera ta zauna kusa da kaka tana mika mata ƙafa" Danna min ƙafa " "Ko uwa ki bata Hulaira bata isa ba balle ke" Ai kuwa kafin su ce me sai hawaye sharr ta fara, Salati kaka ta saka"ke Hulaira zo ki gane min ikon Allah,Suraj kalli lalaci irin na matarka me aka mata yanzun take ma mutane kuka? Ita sai lokacin ma idanun ta ya sauka a kanshi daya zuba mata ido,ai kuwa harara ta zuba mashi tana ci gaba da matso hayawan ta, Aunty Hulaira ce ta maso"me ya same ki? "Aunty ƙafa ta kamar zai karye ciyo yake min,gashi kaka taki ja min kafa" "Taso muje na ja maki" Girgiza kai tayi"ba zan iya ba,"dan tsakani da Allah ji take ƙafafun ta kamar basa jikin ta, Kwanun dake gefen ta ta jawo tana buɗewa "Kaka kin yi mana gurasa kuwa? Girgizar kai kawai Aunty Hulaira tayi tana amsa gaisuwar ta da Suraj yake yi, Ganin gurasa a kwanu yasa ta saki murmushi" Ina Balango yake" "Ai baki ban kuɗi ba" Ture kwanun tayi tana turo baki "to ni dai ba zan ci gurasa ba babu tsire ba" "Eh,ai kuwa gurasar mu za tayi auki" Cikin sanyi murya yace "muce na siya maki" Hararanshi tayi"bana so" "Ai kuwa kin ma kanki domin babu me siyo maki" Mikewa yayi "kaka zan tafi sai zuwa anjima" "To ɗan Albarka sai ka shigo,dan Allah ka din ga haƙuri da ita na ga ko gaisheka ba tayi ba,ita wannan cikin nata da jarabar masifa yazo mata" Da sauri ya jiyu yana kallon ta,kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru bai ce komai, Ganin da gaske tafiyar zai yi ba tare da ya ce mata zai siyo ba yasa tace"ka siyo min Balango" "Idan har kina so ki tashi muje," "Ki tashi mana ai babu nisa da kun siyo sai ku dawo" Cewar kaka, Allah ya gani tana son cin Balango,dan tun safe dashi ta tashi a rai, Ba tada zabi mikewa tayi tana takawa a hankali tana dan rmatse ido,saboda hawa tsaunin da suka yi duk ƙafarta ciyo yake yi ya mata tsami,dan har dingisawa take yi, Shiya buɗe mata gidan gaba dan ta shiga,amma sai ki tayi ta bude gidan baya ta shiga ta zauna, Girgizar kai yayi ya buɗe mazaunin direba ya shiga ya tayar da mota, Yana hawa babban titi ya dawo wayar shi,ta dai ji alamun yana magana amma bata San Me yake faɗa ba, Jiyowa dan wai gawa baya kaɗan yayi"ina ake sai da Balango? "Wurin masallaci Juma'a" Cigaba da tuki yayi,sai dai maimakon ya karasa sai kwanan Sitadiyon Junshon ya bi kai tsaye Asibitin Loko ya shiga da motar, Kallon shi take yi tana kallon Asibitin, Buɗe mata kofar yayi "fito" "Me zamu yi a Asibiti? " Ni zaki raka saboda bana jin daɗi " Kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta fito tabi bayan shi, Ofishin Babban likita suka fara shiga gaisawa suka yi da mutumin"Ustadz Suraj ko? "Eh" "Barka da zuwa,muje Malam" Shi ya masu jagora har babban ɗakin da ake Sikainin, Da kanshi ya ƙyara gadon yanda zata ji daɗin kwanciya, Nuna mata gadon yayi"Madam Bismillah " Kafin ta gama tantance me yake nufi sai ji tayi ya dagata cak ya kwantar saman gado, Zaro ido tayi tana ƙoƙarin sauka da sauri ya mai da ita"please" "Me za'a min? Hannu ya tura cikin hijabin ta yana sakawa cikin rigarta tana jin yanda yake shafa cikin ta," So nake duba min meke cikin nan" Kara yunkurawa tayi"da izinin wa,ni dai sake ni in tashi" Dan marairaice fuska yayi"dan Allah Bebin,ba wani abu bane dubawa ne" Likitan ne yace"Madam ba wani abu bane dan Allah ki bari a duba" Komawa tayi ta kwanta tana kauda kai, Tana ji ya daga hijabin ya daga rigar ma,sannan ya kara zamo da siket sakar marar ta, Shafa marar yake yana tunanin anya abinda kaka ta faɗa gaskiya ne kuwa,saboda sam cikin ba shida alamun akwai abu a ciki,saboda yanda yake shafe, "Malam ka dan cire hannun ka a wurin" "Oh Sorry" Ya faɗa yana murmushi, Nurse ce ta shafa mata wani dan mai a wurin mai sanyi sannan ta daura wani ɗan na'ura tana zagaye marar dashi, Jin an danna kasan maran da dan ƙarfi ne yasa ta saki ƙara dana matse hannun shi dake cikin nata,dan tun da aka fara ta ne matsar ido kasancewar tana dan jin zafi, "Ki mata a hankali mana"cewar likitan " Sorry,sannan "ya shiga fada yana shafa hannun ta, Goge mata ciki tayi sannan ta saukar mata da riga" An gama Madam" Tashi zaune tayi tana kokarin sauka ya kama ƙafarta yana matso da kujeran shi gaban gadon ya Daura kafar saman cinyanshi, A hankali ya shiga matsa mata kafar yana dan daddannawa, Ba ta ci musu ba saboda kafar damun ta yake yi, Mai da kanta tayi ta kwantar tana lunshe ido dan ba karamin daɗi matsar kafar ke mata ba, Cikin burgewa likitan ke kallon su yana yan rubuce rubucen shi a wani takarda har ya kammala, Mika mashi yayi"Malam Suraj gashi an kammala " Karba yayi yana godiya,tare da warware takardar, Tun daga sama ya fara dubawa komai lafiya har zuwa wata cikin wanda ya nuna wata sati takwas da kwana biyar, Tunda ya fara karanta yake murmushi har ya kammala,tashi yayi ya rungume ta,dan tuni har ta fara gyangyadi, Ture shi take kokarin yi"me haka ka sake ni" Sake ta yayi yana dariya"na gode sosai da wannan kyau da Allah ya Bani ta sanadiyar kiina rokon Allah ya sauke ki lafiya" Ba tare da ta kula shi ba ta sauka tana saka takalmin kafar ta, Ɗaukarta yayi kamar wata karamar yarinya,ba tare da ya damu da kallon su da mutane ke yi ba ya gaba da ita,ta san ko tace ya sauke ta ba sauke ta zai yi ba dan haka bata tsaya wahalar da bakin ta ba, A gidan gaba ya saka ta ya mai da marfi ya rufe sannan ya shiga ya tayarda mota, Sai da suka kai in da ake sayarda Balango sannan yayi parking ya sauka ya shiya da waya kuwa dan na dubu goma ya siya, Har suka isa gida bata ce mashi komai ba, Ganin sun shiga Zauren gidan tana ƙoƙarin shigewa ne yasa ya dakatar da ita,dan yasan in dai har ta shiga ba fitowa zata yi ba, "Bebin ki shirya mu koma gida gobe,dan Allah ki ba ni dama na kula dake da Baby na dake tare dake har a bada" Fisge hannun ta tayi daga cikin nashi"ba zan taba komawa gidan ka ba,bana son ka na faɗa maka kamar yan da baka sona,ina haɗa ka da Allah daka sake ni Suraj,Nasan ka san girman Allah " "Wallahi ban taɓa maki karya ba Salma,Allah shine shaida na,amma ban taba faɗa maki cewar bana son ki ba,ina matukar son ki,ina kaunar ki" Katse shi tayi"me yasa sai yanzun zaka faɗa min?me yasa tun dama baka faɗa min ba?ko dan yanzun kasan cewar ina dauke da gudan jinin ka shi yasa? Girgizar kai yayi"A'a Salma ba haka bane,ni a tunani na faɗa maki hakan bai da wani amfani,nuna maki soyayya shine yafi,dan Allah ki Bani dama na nuna maki wannan soyayya ta hanyar kulawa da rayuwar ki,ki Bani dama na killace na nuna maki asalin waye ni,ki Bani wannan damar" "Ba zan iya ba,kafin ka tafi gobe ka aikomin da takardar saki na"kokarin wucewa take yi ya riko ta, Kasancewar yanda jikin shi ke rawa saboda tashin hankali daya tsince kanshi yasa tana ture shi yayi baya saura kaɗan ya faɗi, Ji yayi an riƙe shi,bai damu da ya juya ba yayi kokarin kara binta,sai dai riko shi aka kuma yi hakan yasa ya juya, Abdulmajid dake tsaye idanun shi sun yi jawur ya matso gaban su ba tare da wata_wata ba ya dauke ta damari sai da kusa kifuwa a kasa, Zabura yayi yana ƙoƙari taro ya dakatar dashi da hannu"ka tafi gida Suraj,gode zamu yi magana " "Marinta fa ka yi Abdulmajid,ba ita kaɗai ɓace,me yasa zaka Mare ta? " Na sani,amma ka tafi,ina son nayi magana da ita a matsayi na Yayan ta ne" Dafe goshin shi yayi,yana kallon yanda take kuka dafe da kumatun ta,jin kukan yake har cikin zuciyar shi, "idan har danni ne na yafe mata duk abinda tace,kuma ban yi fushi ba kamar yarda banji haushi ba,dan Allah kamin Alkawarin ba ko goshin ta ba zaka kuma dungura ba" "Na maka Alkawari" "Na gode" Ya faɗa yana barin gidan,sam zaciyar shi babu daɗi akan wannan marin da aka mata. A nasu bangaren kuwa yana ganin wucewar shi ya juyo kanta.......... 🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂 Story & Writing By JIDDARH UMAR 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ *Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba* *94* *Paid book* *300₦* *Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309* *mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865* A nashi bangaren kuwa yana ganin wucewar shi ya juyo kanta, "Kin bani kunya!ban taba tunanin har yanzun ba kiyi nadama abubuwan da suka faru da rayuwar ki ba sai yau!ban taɓa tunanin son zuciyar ki ya kai nan ba sai yau!mijin ki!mijin ki fa kike kallon idanun shi ki ce mashi baya ki son shi ya sake ki!Ashe iatigfarin da kike yi na karya ne!tuban da kike ikirarin kin yi ashe duk na fadar fatan baki ne!tunda gashi ko kadan baki nuna ma Allah godiya ba akan baiwar samun rahamar da ya maki,tunda gashi har kina da bakin da zaki kalli mutumin da Allah ya halarta maki zama dashi kina fadin ya sake ki!Wa'iyazubillah,kalmar da Al'arshin Ubangiji ke girgiza aduk sanda aka ambace shi,sannan kike fadin mijin ki ya sake ki,wallahi Salma ba ki da godiyar Allah,na tabbatar da idan bawan Allah nan ya sake yi ba zaki taba samun ko da mashin shini bane balle a kai ga batun Aure,kuma sai Allah ya jarabceki akan hakkin shi,"busar da iska yayi yana huci"idan har yanzun zuciyar ki na kan Yusuf ne to ki cire,domin wannan karon idan har kika zabe shi to babu mu babu ke har a bada,tunda baki San Alkhairin dake tare da ke ba,wallahi salma ki gode ma Allah,biyo ni ki ga wani abun mamaki" Tunda ya fara magana take kuka,bin bayan shi tayi har bakin motar shi ta bude ta shiga kamar yanda taga shima yayi, Har cikin motar Kuka take yi tana ƙara jin tsanar kasancewa da Suraj a rayuwar ta,in dai tun yanzun taraiyarsu zai zamar mata barazana a rayuwa to gaba bata San Me zai faru ba, Gani tayi sun shiga cikin Asibitin General Hospital Minna, Yana yin parking suka fito,ita dai tana biye dashi har cikin wani word suka shiga in da kana dosan dakin wani irin karni da wari da za fara ji,duk da tsafta irin na Asibiti, Tsayawa yayi a bakin kofa ya ciro Nose marks ya mika mata "saka a hancin ki" Amsa tayi ta saka sannan suka shiga dakin, Tun da suka saka kafa taji kanta ya sara,ganin mutane kwance tamkar masu ciyon kanjamau sabar rama da kashin jikin su daya fito,wasu ko numfashi kirki basu iya yi,ga wari na masifa dan ko majinyaci daya baya tare dasu, Abakin wani gado suka tsaya,in da wani tsohon mutum ke kwance yana fitar da numfashi da kyar ko riga babu a jikin shi,wallahi har tsoron kallon fuskar shi take yi yanda fuskar ya rame kana iya ganin duk wani kashi na fuskar,ga ido da yayi zuru_zuru, Cikin sauri ta riko hannu Abdulmajid tana dan komawa ta gefen shi, Nuna mata mutum yayi"kinsan waye wannan? Girgiza kai tayi, "Kara kallon shi da kyau ki gani" Tsira mashi ido tayi sai dai sam ta kasa gane shi, Nan ma kara girgiza kai tayi, "To wannan da kike gani Yusuf ne,Yusuf dai da kika sani tsohon mijin ki shine," Wani irin zaro ido tayi tana kara zuba mai ido,sai yanzun abin ya zo zuciyar ta,tabbas shine, Muryarta har rawa yake yi wurin fadin "Yaya me ya same shi? " Abinda ya shuka ne yake girba,Salma shi yasa nace Allah yana son ki,domin ya gama maki duk rahama da zai maki,amma kina ƙoƙarin yi ma kanki mummunan hisabi, Ki duba irin jinyar da Baba yayi duk da baƙi nan,komai sai an mashi,har zuwa karshen rayuwar shi yayi mutuwa irin ta rashin jin daɗi wannan ma wani ishara ce,ki duba mutuwar Mama da ko haɗuwa Allah bai nufa za ku yi ba duk da irin burin haɗuwar da kuka ci ma juna,ko samu taga fuskar ki ta nime yafiyar ki ba tayi ba,sannan ki duba wannan na gaban ki na yanzun,ko magana baya iya yi,gabaɗaya wurin bahayarshi ya zazzago kashi baya iya tsayawa,fitsari baya iya tsayawa,wurin tsutsotsi ne kawai ke fita suna rarake wurin,shi kuma ke zaki ce a kanshi, Ke kuma me ya same ki Salma,Ubangiji ba tsoronki yake yi ba da kika tafi yawon duniya da sunan fushi kina ta aikata barna,amma bai hukunta ki ba sai ma ya baki miji na gari wanda zai iya sadaukar da komai domin ke, Kin san ma kuwa cewar shi ya bada Kodar shi daya aka sai ya maki" Da sauri ta gado jikakkun idanunta ta daura a kanshi, "Kwarai kuwa,domin a lokacin an duba namu a ciki babu wanda ya maki,kuma idan har aka bata lokaci to kina iya rasa ranki saboda coyon dake kanki,shi ya yace zai baki nashi ba tare da tunanin komai ba,kuma ya bada, Kin ma san irin rashin lafiya da yayi a lokacin,domin kuwa wannan da kike gani a kwance so yayi ya kashe shi ta hanyar dukan shi a ciki, Kiyi tunanin irin raɗaɗi da azabar daya fuskanta,A ranar da za'ayi aikin a ranar Kakar shi da tayi shekara goma sha ɗaya a kwance a ranar ta tashi,ranar da suka dauki tsayin shekaru suna addu'a da fatan zuwan ta,amma haka ya hakura ya kwanta aka yanka jikin shi aka cire wani bangare nashi mai muhimmanci aka saka maki,ba tare da sanin shin zai kara buɗe ido ko bazai iya ba,ko kuma shima tafiyar ke nan,ya watsar da komai nashi da burin shi ya zaɓe ki, What sannan har kike fadin baya son ki dan kawai bai faɗa maki cewar yana son ki ba, Wallah kin ban kunya!kin bani kunya Salma! Amma fa babu komai rayuwa ce kuma duniya ce ta isa kowa riga da zani,amma ki tuna da wannan misalin dake gaban ki,yanzun zabi ya rage naki"har ya juya ya juyo ganin yanda take sharbar kuka"muje na kaiki gida" Bin bayanshi tayi,har cikin mota yana jin yanda take rusa kuka sai dai ko alamar dakatar da ita bai yi ba,gara tayi ko zai taimaka wurin dawo da ita haoyacin ta, A ƙofar gida ya ajiye tana fita yaja motar shi ya bar kofar gidan. Babu kowa a tsakar gidan dan haka dakinsu ta shiga ta zauna ta lungun gado tana cigaba da kuka, Ganin Yusuf a yau a haka kuma ya matukar tayar mata da hankali,Yusef dan gayu mutum mai ji da iya wanka da saka kaya,yau sai gashi kwance ko riga babu,duk irin kudin da yake kashe ma fatar jikin shi sai gashi yau fatar ta mutu ta yakushe ko gane shi ba'a yi, To yanzun ina duniyar daya nime,ina arzikin da ya tara,ina kuma lafiyar da yake takama da shi,duk basu amfana masa komai ba,gashi kwance tamkar gawa,zai tayi yabar komai, Suraj zuciyar ta ya ambaci sunan,tabbas Allah ya bata shine domin ya kara gwada imanin ta,sai gashi duhun kai yana nima ya kai ta ga aikata aikin da na sani, Idan har zata tuna irin zaman ta da tayi da Yusuf da kuma kwana daya kawai da tayi da Suraj sai yanzun take ganin Allah ne ya amsa addu'ar ta ta bata miji wanda zai iya da ita har ma ya fita saboda ya tsayar da ita a wuri da,amma makantar zuci ya shafi ido, Tabbas ta cancanci da a kira ta da bulu mara godiyar Allah, Ya kamata tun yanzun ta koma hankalinta ta nuna godiyar ta ga Allah kafin ita ma lokaci ya kure mata ta tafi tana nadamar rayuwar ta. Sai lokacin sallah ta fito tayi Alwallah tayi sallah, Ganin har lokacin bata zo ta dauki abinci bane yasa Kaka ta tashi ta shigo dakin, A zaune take har lokacin saman darduma, Zama tayi a bakin gado tana fuskantar ta tunda ba komai take yi dan ba carbi take ja ba, Duk da Abdulmajid ya kira ya faɗa mata yanda suka yi amma tana buƙatar jin ta bakin ta, "Me ya same ki? " Yau zanbi Suraj gobe zamu koma tare dashi" Wani irin murmushi ta saki mai sanyi"Alhamdulillah,Allah mun gode maka,na yi farin ciki sosai da wannan hukuncin da kika yanke,ina kuma fata zaki karɓi mijinki hannu biyu ki yi masa biyayya domin samun Aljannar ki,ta hakan ne kawai zaki iya nuna ma Allah godiyar ki ta hanyar yin bauta a gare shi,domin aure ma yana daga cikin bautar Ubangiji," Kara share hawayen ta tayi"na gode Kaka da hakurin da kike tayi da ni" Saukowa tayi ta rungume ta"ke din dole ta ce dole ne nayi haƙuri dake,ina maki fatan samun farin ciki a rayuwar ki Ummu Salma" Ita ma rungume Kaka tayi"na gode Kaka" Auty Hulaira ce ta shigo nan ta tared dasu a haka, Zolayar su ta shiga yi,kafin daga baya su sakata a tsakiya suna mata nasiha,dan ita Aunty Hulaira shekara biyu kenan da ta dawo gida dan mijin ta rasuwa yayi kuma Allah bai taba basu haihuwa ba,yanzun nan ne ma ta tsayar da wani sai dai shi saurayi ne kuma haka ya nace sai ita,kuma ƴan uwan shi sun yi na'am da ita, Tare ta zubo masu Gurasa a plate da Balango sai kayan ganye suka shiga ci suna janta da hira dan kawai su ɗebe mata kewa,dan a wannan stage din da take ciki ba a buƙatar wani abu da zai dame rayuwar ta, Su suka haɗa mata kayan ta wuri ɗaya a cikin babban akwati,sannan Kaka ta kira mata yannin ta,har da Abdulmajid ta nime tafiyarsu akan bata masu rai da tayi tun lokacin auren ta na farko da Yusuf har i zuwa yau,ta kuma kara da masu godiya akan dawo da ita hanya da suke ƙoƙarin yi a ko yaushe, Sun yi farin ciki sosai sun kuma yi mata fatan Alkhairi, "To sauran ku Allah yasa ina da rabon ganin auren ku" Cewar kaka, "Insha Allah zaki gani har ma ki goya tattaɓa kunne"duk dariya suka saka jin amsar da Abdulmalik ya bata, " Yauwa ni fa na samu mata,dama jira nake komai ya daidaita ayi magana " Duk kallon sa suka yi, "Shi yasa nake son ka yaya Abdulmajid nasanka ba kada sanya,a ina take?cewar Salma, " Ai Balki ce ta Kano yar gidan Gaggon yara " Baki ta buɗe "da yaushe kuka haɗu,yanzun idan ka kaure yarinyar nan kana nufin dole nace mata Aunty" "Sosai ma kuwa,ai tun lokacin jinyar ki muka dunki" "Kuma tana son ka? " Sosai ma kuwa,ban cin haka ai har da mamarta muna waya tana yawan tambayar ki,ta kuma shaida min in har da gaske nake yi na kwantar da hankali na ta bani " Duk dariyar farin ciki suke yi, "To kai fa Abdulrahman? " Yarinyar limamin unguwar mu ce,Nusaiba " Duk hamdala suka saka, Abdulmalik ne kafin ma a juyo kanshi yace "ni fa kar ma a tambaye ni domin har yanzun ina kan bincikawa ne" Dariya ya basu"Allah ya tayaka zaɓar na gari" "Yaunzun Abunda za'ayi zan kira kanne na maza zasu zo a gudanar da bincike sannan a shiga gida ayi magana" Da haka suka tsayar da maganar sannan aka dauko wani hirar,anan suka ci abinci dare bayan sallar Magrib sannan suka wuce bayan sun sallame ta. Sai da ta idar da sallah Magrib sannan ta kira number shi,wanda bugu biyu ya ɗauka da sallamah, Amsawa tayi "idan ka idar da Sallah Isha'i ka zo " "Ina fatan lafiya? " Lafiya glau kai dai kazo" "To shi kenan sai na zo" "Um hmm" Ta faɗa ta na sauke wayar. Tun ƙarfe takwas take jiran kiran shi har sai takwas da rabi ya kira dan sai da ya idar da jan carbi, Shi yasa yana kira ta dauka cikin jin haushi tace"Me ne" Murmushi ya saki domin ya haminci haushi ta ji,to ya zai yi da ita dole sai haƙuri ya san ba laifin ta bane wannan yawan fushin da jin haushi, "Yi haƙuri gimbiya gani a ƙofar gida" "Na riga na kwanta sai gobe" "Dan Allah kiyi haƙuri ki taimake ni,yau ba zan iya bacci ba idan ban gan ki ba" Dan shiru tayi tana sauraren yanda yake magiya kafin tace "gani nan zuwa" Sai da ta dauki lokaci dan kanta tana tsaye kofar gida yana kira kafin taga sun fito ita da Aunty Hulaira dake janye da katon Akwati,da sauri ya karasa ya amsa"Aunty ina zaku" "Akwatin matar ka ce,yau dai Allah yayi wai binka zata yi" Wato ido yayi yana kallon ta,dauke kai tayi kamar bata ganshi ba, "Kai da kata na ka bita a hankali domin kasan ba ita kadai ba,ina maku fatan Alkhairi da fatan sauka lafiya," Ji yayi kamar ya rungume Aunty Hulaira tsabar murna"na gode sosai Aunty,Allah ya biya ku" Da Amin ta amsa tana shegewa gida tare da daga masu hannu, Murmushi ya saki yana buɗe mata gidan gaba, Shiga tayi ya mai da kofar ya kulle, Har suka bar unguwar bata ce mashi komai ba,sai da suka hau babban titi sannan ya dan juyo "kina bukatar wani abu ne? " Fruits" "Ok" A ta bakin titi ya tsaya ya tsiya masu sannan suka kara kama hanyar gidan shi dake unguwar Bosso Lokos, Dama kuma ta san gidan, Yana parking a harabar gidan ya buɗe ya fito sannan ya buɗe in da take,kamar wata karamar yarinya haka ya dauke ta ba tare daya dire ta ba har cikin daki saman gado ya zaunar da ita, Fita ya kuma yi ya shigo da akwatin kayanta ledar kuma ya kai kicin,yayyanka fruit din yayi ta yanda zata ji daɗin sha sannan ya dauko, Tsayawa yayi rike da tire a hannu yana kallon yanda ta jinginar da kanta jikin gado idanun ta a lumshe alamun barci na son ɗaukarta, Murmushi ya samu kanshi da saki,domin aduk sanda ya tuna gudan jinin shi na tare da ita sai ya ji wani irin farin ciki mara misaltuwa tare da ƙaunarta na ratsa zuciyar shi, Ajiye tire din yayi a hankali sannan ya taka zuwa in da take, Zube guiwowin shi yayi a kasa ya tura hannun shi cikin rigarta yana shafa marar ta, Ɗan zabura tayi tana sauke ajiyar zuciya tare da kyara zama, "Sorry na tsorata ki" Bata ce mai komai ba sai kokarin cire hannun shi tayi daga cikin ta, Tashi yayi ya hau kan gadon gaba ɗaya ya jawota kan gadon yana kwantar da ita tare da karasa cire mata karamin kyalen dake kanta, Rigarta ya tattara ya mai da shi saman kirjinta tana saka hannun shi a tsakanin siket dinta ya jawo shi kasa, Tsira ma shaffen cikin ta idanun yayi,yana kure in da yaga ya ɗanyi tudu kaɗan idanu na kusan mintuna goma kafin a hankali ya kai hannun shi sai tin wurin yana dan shafa wurin,sai kuma ya duka ya sakar mata Kiss a wurin,yana kankame ta hanyar zagaye hannun shi gabaɗaya ta bayanda kanshi kuma saman cikin ta"Allah ya Albarkaci rayuwar ki,ya faranta maki kamar yanda kika faranta min,ya yafe maki kura-kuran ki har abada ya saka Aljanna ce makomar ki" Hannu tasa ta shiga shafa lallausar suman kanshi"ya kuma barni tare da kai har karshe rayuwata " Da sauri ya sake ta yana dagowa "da gaske kike kina son Allah ya barmu tare? Jinjina mashi kai tayi tana rungume shi tare da saka kuka" Dan Allah ka yafe min akan duk abinda na maka,nasan na faɗa maka maganganu marasa daɗi wadanda Allah zai iya tuhuma ta,na maka alkawarin ba zan sake ba dan Allah ka yafe min" Shafa bayan ta ya shiga yi"shiii ya isa haka,ni dama ban taba rike ki a raina ba,na san kuma idan nayi haƙuri komai mai wucewa ne zaki fahimta,dan haka tun tuni yake yafe maki" "Ni dai kace ka yafe min" "Na yafe maki duk abinda kika min da kuma wanda zaki min nan gaba,Allah ya yafe mana baki daya" Ƙara rungume shi tayi"na gode Zauji " "Kin tabbatar ni din Zaujin ki ne? " Kai rayuwata ta ce" Sunbatar goshin ta yayi yana sauko da ita,tare suka sha fruit din sannan ya mai da kayan kicin, Ranar tare suka yi kwanan farin ciki,babu wani da ya shiga tsakanin su sai dai kyakkyawar runguma daya mata har gari ya waye, Haka washegari ko tsinke bai bari ta dauka shi yake mata komai har ta wanka shi ya mata ya shirya ta, A ranar ta ga wani abu wai shi tarairaya,ko kwakkwarar motsi tayi sai ya tambaya mai take so, Jirgin yamma suka bi zuwa Abuja daga nan suka tafi London, Da yaba Ammi takardar Sikainin din ta gani har da kukan farin ciki ita da Grandma, Kwanan ta biyu tare dasu ya zo ya dauke ta ya maida gidan shi dake nan bayan dogon gargaɗi da bayani daga Ammi akan ya rinka binta a hankali, Rayuwar ta koma tamkar na wata Sarauniya,domin ta ko wani bangare ba karamin kula take samu ba,har balle da cikin ta ya kai wata biyar lokacin ya fito sosai kana ganin shi, Sau biyu ta zo Nigeria a lokacin bikin yanninta sai kuma lokacin da Amira ta kammala makaranta,a nan Kano a dakin Goggon yara ta sauka, Dawowar su da sati biyu aka rataye Pa,Allah sarki rayuwa shi kuma a inda nashi babin ya kare kenan, Bayan wata huɗu sai gashi Allah ya sauke ta lafiya in da haifi ɗan ta namiji mai matukar kama da mahaifinshi,tun a Asibiti yama danshi Huɗuba da Abdulbasit wanda zasu rika kira da (Abid) kasancewar sunan mahaifinsa, Grandma da Ammi har da Kukan murna,wannan dama shine burin su, Tunda aka haifi yaro sun dauki son duniya sun daura mashi,har balle Ammi ko ƙara bata yi sai tace ai yayan ta ne, Yan Nigeria ma sun zo Suna ciki har da Maijiddarh,Allah sarki ita ma da nata cikin,sai fatan sauka lafiya, Sai da sukayi sati ɗaya sannan suka dawo da goma sha tara na Arziki,domin sunje gidan Arziki sun ga inda aka gaji Arziki a bar Arziki, Sai da tayi Arba'in bayan haɗi da tsumi na musamman da Ammi tai mata sannan ta bashi matar shi suka koma gidan su,cike da sharadin kullun za'a kawo mata Yayanta ta ganshi, Ganin yanda Suraj din ke yi masu zarya a gida kamar zai sace ƴar mutane, Randa ta koma kuwa data shiga hannun shi sai da tayi har sai da idanun ta suka kumbura,saboda ya nuna mata tsakanin ta dashi babu sassauci,domin kwanakin daya ɗauka yana haƙuri sai da fanshe shi, Sai da komai ya lafa sannan ya rungume ta yana aikin lallashi, "Ke rayuwata ce Bebin,ba zan iya rayuwa ba babu ke,ina mai rokonki da kiyi haƙuri da ni da kuma halina,ban taba jin haka game da wata mace ba face ke,shi yasa bana iya riƙe kai na a duk lokacin da nake tare dake" Shafa fuskar shi take yi tana jin wani shaukin shi na kara taso mata"kai din jarumi ne a cikin jarumai,a duk lokacin da naso nuna jarumta ta a gabanka sai naji ni ba kowa ɓace face YAR TSANAR KA wacce zaka juya kayi yanda ranka yake so da ita,ina matukar Alfahari da kai" Mumushi ya saki wanda ya bayyana fararen jerarrun haƙoran shi,yana ƙara matso da ita jikin shi"soyayyarki kullum takan narka tunani na acikin shaukin iske goben rayuwata a tare dake, tamkar jini ina da bukatar a ko da yaushe ki kasance a cikin jiki na, Sabanin haka kuma,hakika zan azabtu sau lokacin da yawa, Haka kuma da soyayya nauyi ce ga jiki,tabbas dana roƙi Allah ya hukunta jiki na ya zamo mafi nagarta iya dauka domin kada na bada rauni yayin tafiyar da soyayyar ki, Kece ƙaddara mafi daraja wacce farashin ki baya taɓa faduwa a rayuwata,kullum hauhawa kike sama tamkar shekaru na Bebin,ina matukar son k.... Haɗe bakin su tayi wuri ɗaya domin ƙwaƙwalwar ta ba zata iya jurewa sauraron waɗannan tausasan kalaman dake fitowa bakin shi ba,masu saka ta jin shaukin soyayyar shi dake kokarin fasa kinjin ta ya fito, Cire bakin ta tayi cikin nashi tana haɗe goshin su wuri ɗaya"ina matukar kaunar ka Zauji" Kara hade bakin su yayi yana jawo masu bargo, Ni ma kuma ganin haka yasa na fito dakin tare da jawo masu kofa ina ma Abid fatan samun kani a wannan daren. *Alhamdulillah ina ma Allah godiya da ya bani ikon kammala wannan littafin na yar tsanar zinari a wannan lokacin a kuma wannan ranar, abin kirkin dake ciki Allah ya bamu ikon amfani dashi,wanda bai da amfani kuma Allah ya yafe mana kura-kuran mu Amin* Sai mun haɗu a sabon littafi na mai suna *Ayi dai mu gani* wanda zai zo a matsayin na kyauta,wato free book. Godiya ta musamman ga paid group din YAR TSANAR ZINARI, na gode da haƙurin ku Allah ya sadamu da Alkahiri Amin...