WRITING BY HIS ECCELLENCIY NOVELS GROUP.. 'YAR KWALLIYA Page 1-5 March 07, 2018 'YAR KWALLIYA .. Bismillahirrahmanir Rahim . Wannan kirki raren labarine nayi shi dan fada karwa da nisha dan tarwa ban yishi dan wani ko wata ba Written by Jabeer.. . Wata yarin yace 'yar shekara 15 kafa fururu komai babu fuska kuma tasha Jan baki da hoda harda gazal ta fallo da gudu kanta daukeda tulo tadebo ruwa a guje ta fada gida Tana shiga ta saki tulun yafadi ya fashe Nidai gaskiya bazan yar daba hikenan ni banda kata bus hine fa ya bini har inda zan debo ruwafa inna yana cemin *YAR* *KWALLIYA* kafa ba mai fuska tasha ado hine nakamahi da danbe na fasa mihi baki hine dan bahida kunya ya biyoni gida Yasin bazan yarda ba inna kalli yanda bakina yake zubar jini inna Abu muguwace wlh Kayi hakuri kaji kaima da naka ina ruwanka da tsokanar ta kuma kasani sarai bazata barkaba Au abinda zaki ce kenan to shi kenan zan turo me rama min Kayi hakuri mana kai baka jin hakurine Ina kotsayawa beyiba yatafi Inna ki barhi ki barhi nace kaje ka kawo bindiga karhe kenan Yanzu Abu Wannan rayuwar kika zaba to shikenan zandena tsare miki wlh tinda ke bakida hakuri yanzu Wannan gabjejen kato kika kama da fada Inna hinefa ya nemi tso kanata fa Yanzu ruwan da kika debo ma gashi kin fasa tulon kaini inna ina zansa kaina Inna Wannan fa laifin tulun kine ina ruwanhi dani nan naso na ajiye hi hine ya fadi ya fahe sai hakuri Kamarya sai hakuri Abu girkifa zan Dora yanzu ya kikiso ayi To ni kome ma za ayi ayi tuludai yafahe nikuma na gaji bazan iya komawaba . Kin isa komawa kamar kinyi kin gama ga wani tulun can jeki dauka kidebo wani ruwan Kai inna kinemo wani ya debo kinga janbaki da hudana ya kare sonake na zagaya baya na siyo I dan har baki debo ruwan nan ba ba inda zaki Abu kin jini da kyau hikenan zan debo Abu ta dauki tulun tatafi Rake yauwa bari naga maya finda ke daure a kugunta ta kwance ta Ciro Hamsin ta mika wa me rake Yabata rake da canji tana tafe tana sha harta karasa rafi Yauwa wana kama wato jiya kika watsa min kasa kika gudu ko yanzu wana kama cewar Abu Ke Abu kinga diban ruwa aka turoni ba fada ba matsa na wuce cewar binta Ke binta me kike nufi ni wasa aka turoni kenan bari kiga wasa cewar Abu Hannu tasa ta ture tulun dake kan binta yafadi kasa yafashe Yauwa kinga wasa nan nafasa banza ko kinada abinyi ne Kaiiii ni kika fasawa tulu wallahi kinyi karya saina rama Abu kome kike takama dashi kin tara kin samu ni binta saina gyara miki zama Binta na gama fada tasa kafa ta daki tulun Abu yafashe Nanfa Abu ta daka tsalle ta dire ta kamo wuyan Binta suka kama fada da kyar aka rabasu Aina fada miki Abu ni Binta nice dai dai ke saina gyara miki zama Tohi kenan idan baki gyara min zamaba nizan gyara miki kuma saikin biyani tuluna kona daka ki a gurin nan wlh Allah ko Abu bazan biya ba kiyi abinda kika gadama koda me kika zo ni Binta na fiki haka kikace ko to hikenan Kallon ta Abu take tana gyada kai da buga kafa Banga wanda ze fi karfinaba ni Abu wai saiwata banza bazara iskar damuna binta wlh kintarowa kanki aradu da ka Hannun ta Abu ta kama ta sakar mata cizo dagudu tabar wajan Binta tabi bayanta da gudu haka suka yanka cikin unguwa dagudu harzuwa gidansu Abu Abu ta boye a bayan inna Inna ki matsa Wannan fadan ba naki bane kimiko min Abu na nuna mata abinda binta zata iya ni kika ciza dai ko cewar Binta Yar gidan marasa tsoro mekikeyi a bayana aina fada miki ni nadena bada hakuri kinga Binta gata nan zoki mata abinda kike so cewar inna Gadan gadan Binta tataho Kinga Binta tsaya Abu ina ruwan dana aikeki kidebo cewar inna Inna asara kika aika dankuwa ni Binta nice nan na fasa tulun *'YAR KWALLIYA* tafasa min nawa shine nima na rama wata tsiyarce cewar Binta Ahh babu bakomai kinyi daidai yanzudai kiyi hakuri Binta kibari idan tafito kuyita takare mutuwama tana tsoron idon ma haifi cewar inna Inna kenan kince haka ko to ina waje ba inda zanje kekuma Abu zaki fito kisameni hoda bawanka kidinga Wanka idan zakiyi kwalliya Binta tajuya ta fita Inna ki matsa kibar ni da ita kina jin metake cemin Karya tayi Abu gaskiya tafada yau kwananki nawa rabonki da kwanka Inna batun wankan nan kibarhi aikyan kwalliya kayihi batateda wankaba gawani kamhin turare na musamman dayake tahi a jikina gahi turaren babu a kasuwa me yafi raina shine zan tsaya inta batawa kaina lokaci wajan yin kwanka Dalla rufemin baki kazamar banza kazamar hufi ina kyau Anan *HODA BA WANKA* Baki tabude ta gir_giza kai ta dunkule hannu inna harda ke yasin duk wanda yasake ce min hoda ba wanka na dena raga mihi yasin cewar Abu Yanzu da kika dunkule hannu damben zakiyi dani nima cewar inna Jifa tayi da takalmin kafarta ta debo kayan Kwalliya ta zube a gabanta tadauki Wannan tashafa ta ajiye takalli kanta a madubi tayi dariya . Inna jiya da naje dan dali aka dinga tambaya waye yafesa turare nayi shiru tsabar kanhin turaren jikina hanci suka toshe Niko kayan nan ma bacanzasu zanyi ba Wanka kuwa nadena Kaza kankida motsi afakaice suka zageki baki saniba ba abinda kikeyi sai bugawa kitemaka ki ajiye kayan kwalliya kiyi Wanka kekanki zakiji dadi Tab tab aaah waii saidai wata Abun badai niba wanka nida hi munyi hannun Riga inna kifara sabon lissafi daga nan harranar sallah nida Wanka Haka kikace to Allah yashigoda yayanki da malam su insun isa dake Sa saki kiyi tinda ni kin rainani dan Allah ji yanda kika cika mana gida da tsami cewar inna Kinji ko inna kinji irin kamhin turarena ko hakama wani saurayi yajiyo kamhin yace yana sona nace bana son hi ni fako inna har bana son fita dik inda nabi ansan nice saboda turturarena cewar Abu Waiyoo waiyoo tasa kafa tayi koli da kayan kwalliya inna ban fada mikiba yau ake cin kasuwar gangare natafi Tayi fice warta Badan Allah yasa akwai sauran ruwa agidan nan ba da Abu ta gama dani cewar Inna Tafiya take a hankali tana tafiya tana yanga acewarta tafi kowa haduwa ga turaren jikinta yafi na kowa kanshi tana tafe tana cin gyada hannun takuma rikeda sandar rake ga wuwar danmara tasha a kugunta binda na labe tana kallon ta Abu nakara sowa inda Binta take Binta tariketa Wana kama yasin saina dagargaza bakinki zan kyaleki yanzu ina inna take balle kibuye a bayanta cewar Binta Yasin Binta kanki baya aiki kalli yanda kika rike min Riga a gaban mutane gasamari a gefe kalan ki zubarmin da mutunci a idonsu haba kidena abinda kuda zebiki Karsan kuda nice mangoro kobakijiba cewar Binta Janyota tayi zata daka bashiri ta saketa tatoshe hanci Abu dagaskene abinda ake fada kenan Wannan warin daga ina lallai kinci sunan ki huda ba Wanka sammin raken mana Abu taraba shi2 ta bata Yauwa nagode gyadar fa Tadiba tace Gahi kibarni zaki rakani cewar Abu Eh ni yanzu kawarkice gaskiya kinada hankali Abu Dariya tayi tace ko nasani suna tafe suna shirme harsuka siyo suka dawo . Atare suka shiga gidan Inna na ganinsu ta fara salati Abu mekika kuma yiwa Binta cewar inna Inna ai yanzu Binta tazama kawata cewar Abu Ina baze yiyuba ban yardaba wlh dama ya kike bare ankaraki da binta waye besan bintaba cewar inna Kinga Binta jeki gida zanzo na same ki cewar Abu To inna sai anjima cewar Binta Sallama Alaikum inna ina wuni Lpy kalau Nura sannu dazuwa kaga Abu tayi sabuwar kawa mara aji irinta Ke Abu yatoshe hanci inna meya yake bugawa haka cewar Nura Wacce inbanda *'YAR KWALLIYA* Fari Abu tayi da ido tareda juyawa New writer's Taku husba'ahfama . Yaya Nura a hekaima kaji kanhin tiraren nawa Dalla kanshi ko wari kazama kawai dubi yanda gidan nan yadauki warin jikin ki Wari karyama kenan Yasin kanhi kaji cewar Abu Yau sai kinyi Wanka bazan iya zama dake kina wariba wlh inna bani ruwan nan na kusa dake cewar Nura Banga abinda zesa nayi wanka ba Yasin kalan kanhin turarena ya tafi Nura ya dauki ruwan yasa a bandaki yakai mata soso da sabulo ya karyo bulala yarike Shiga kiyi wanka Yaya Nura ina ganin gir manka fa cewar Abu Yadaga bulala bashiri ta fada bandaki tayi zamanta Kayi ka gaji yaya ba wankan da zanyi cewar Abu Tana tawasa da ruwan kamar tana wanka tawanke fuska da kafa da hannu Kate makeni ina fitowa zan cika fukata da KWALLIYA na raka Binta tallar gurjiya hahhh Tabude ta fito ta harareshi tashige daki tayi KWALLIYA ta tafi gidansu Binta taje tasamu Binta ta fito tallar gurjiya A hanyarsu na tafiya Abu tayi ido4 dawata taci ado da KWALLIYA tayi kyau sosai harta bace Abu na kallon ta Ke mekike kallo cewar Binta Kinga yanda tayi kyau tafi yanta kayanta komai yayi Nanfa Abu tashiga yin irin tafiyar Kibar Wannan abin Abu kinsan daga ina take cewar Binta A'a cewar Abu Daga birni take haka suke tasu KWALLIYAR dasa kaya ba irin nakiba HODA BA WANKA . Yasin yanzun nan bakinki zeyi jini Binta nizaki cewa haka nifazanyi fada da duk wanda ya kirani da Wannan sunan kowaye hi cewar Abu Maida wukar nataba zuwa birni sau1 yanada kyau ginin su ba irin namuba kinga baze yu nabaki lbr ba saikin gani da idon ki cewar Binta Kai nima inaso naje zaki kaini dan Allah cewar Abu Inna inna ce matsala Abu damunje yasin cewar Binta Kinga bawata matsala ki kaini kawai inzaki kaini ya kika ganni zanyi kyau a birni ko cewar Abu Ehhh to ban saniba saikinje tukunna saboda gaskiya tsoro zaki basu kalle kifa tab cewar Binta Waike hikenan bakida magana sai kice na kalli kaina me zan gani kodai ciki baki kike min ne cewar Abu Ko daya KWALLIYAR takice abin tsoro ga kafarki Fari fat gaskiya bazan kaikiba saikin waye cewar Binta Abinda Binta tafada yabatawa Abu rai yasa tayi gaba ta barta a baya . Wani yarone yazo siyan gurjiya gun binta Binta zuba min gurjiya Karki zuba mai cewar Abu Tinda na ganka nadawo mekace min jiyama Meka ce mata Eh cewar Binta Shiru yayi yakasa cewa komai saida ya gano yayanshi yace ' *YAR KWALLIYA* nace Ohh me dadtin dankwali itace *'YAR KWALLIYA* cewar Binta Barshi dani yanzu nanuna masa kalata Yasin harni zaka tsokana ka gudu anhi kudin nahi Binta cewar Abu Binta ta ansa tace kuma bazan siyar maka da gurjiyan ba na karfine Gaya mihi binta waihi Wannan dame yake dakama ne naga saiwani jijjidakai yakeyi cewar Abu Kasa ta diba ta watsamai a ido Binta tasamai kafa ya fadi suka rufeshida duka abin mamaki kato a kasa mata na duka abinda mutane ke cewa kenan Yayan shina kara sowa ya daka musu tsawa Suka bar dukanshi suna Harar shi Lpy kaikuma meya kawo ka kasan muko suwaye cewar Abu Suwaye Ku inbanda kucakai marasa hankali dalla dubeki kafa furu furu komai be ganiba dubi kayan jikinki fuska saikace Aljana waike kinyi KWALLIYA Ap abanza yafi na tsohuwa kaga ka gaggauta barin gurin nan inba hakaba kuma hmmm cewar Binta Karkusake suce zaku yimin haukan da kuka saba danni bazan daukaba wlh Ko Binta mu gwadamai aiki dan nakula saimun koya mishi hankali cewar Abu Waige Binta tafara can ta gano dutsa tace haryanzu bakinka be mutuba ko tsaya ka gani Dutsen ta dauko da buga mishi a kai Banza a banza cewar Abu Jini ya fara zuba a kanshi Abu da Binta suka zuba a guje suka wuce gidansu Binta Umma ga gurjiyar ki yau an hana talla inji me gari cewar Binta Ke Binta waya fada miki cewar umma Umma Nifa ganauce ba jiyauba Gashi can ya baza yan *DOKA* A gari cewar Abu Kunga bana son shegan taka waca tsiyar kuma kukayi na sanku da kyau cewar umma Wani ne ya nemi tso kanar mu hine muka fasa mai kai cewar Binta Eh banjiba naji kamar kince fasa kai Allah na gode maka daka bani Binta nidai shikenan bakina baze zauna shiru ba saboda inada Binta cewar umma Kofar gidan su Binta aka siga duka da karfi Kufito mana dasu ko mushigo yara sun gagari kowa wlh yau zamu sharewa kowa hawaye kufito dasu cewar mutanan da suka zo Kuna jiko yara kunzama dan kuka mejawa uwarsa jifa Umma kinga jeki kiji dame suka zo idan da sulhune kusulhunta idan kuma akasin hakane kikira womu katkenan cewar Abu Kushiga ciki bari naji dasu . Wai baza a fito dasu bane Eh mumafa yan zama nine kofar suka bude suna kokarin shiga Haba dan samari gidan matan aure ne fa Nasani ina 'ya'yan Allah banin nan suke Binta da Abu Basa nan sun fita Karyama kenan ina ganin su suka shiga gidan nan dan haka ki fito dasu kawai mu baza mu hakuraba dan uwanmu suka fasawa kai gashinan sai zubar jini yakeyi yanzu haka yana Asibiti Allah yabaku hakuri kuje idan sun dawo nida kaina zan kawo muku su cewar umma Eh to na yarda dake saidai be kamata mu tafi haka ba bari mu bar miki sheda idan sunzo ki nuna musu Yadaga gora ze sauke mata dagudu tabar gurin ta shige gida tarufo kofa Yauni umma naga ikon Allah ina kuke Umma sun bar miki sheda banzaye sokaye sun yarda ba ma nan gamunan muna jinsu kuma cewar Binta da Abu Au kujin dadin kune a bar min sheda saboda kun amsa sunan Ku Binta da Abu ko Allah yate makeku suna nan suna jiranku kuna fita sai abinda hali ya yiwu cewar mama Basu isaba yanzuma ba barinsu zamuyiba narike muryar su zan ne mesu 1 bayan 1 cewar Abu Umma kawo mu kai miki dan dali cewar Binta Gashi nan kutafi amma dan Allah karku nemi tso kanar kowa kuma Ku canza hanya karsu ganku cewar umma To sai mun dawo suka fada gaba dayansu suka fita . Suna fita umma taji wani hadeden wari Umma taja dogon nun fashi Wannan wani sabon yayi ne kuma Abu irin Wannan bugawa haka nida Allah yasa kar Binta tadau Wannan halin na rashin Wanka Suna tafiya suna waka suna ciye ciye suna neman tso kana Abu ta gano bishiya tace Binta ajiye gorjiyar nan muhau bishiya kinga yanzu basu fara zuwaba zuwa anjima sai muje dan dali To muje suka tarar da yara a jikin bishiya suna wasa Kubar gurin nan Abu da Binta sunzo ko sokuke jiki yayi tsami cewar Binta Tinkan Binta ta karasa magana yaran suka bar gurin dan sunsan halin Abu da Binta Suka cire takalmi suka haye bishiya suna wasa kamar yara Wasu yan mata suka zo wucewa suka gano Binta da Abu suka kwashe da dariya Abu na ganin su ta sauko Binta ma sauko wa tayi Wakuke wa dariya Eh daku nake magana Abu ta fada tana dungure musu kai Karki sake dun guremin kai kinsan kowaye babana kuwa A garin nan . koma waye hi beda meniba abinda yasa kika kallemu shine yanzu ze Ja miki dukan tsiyama kuwa cewar Binta Jiki ko kayama baki iya sawaba ji hodar fukarki janbakin ma tsohon yayi ne amatse ciki asai sabo cewar Abu Kaji wai harkurace zata ce da kare maye jiki kalli kafarki kalli fuskarki ji wani wari mara dadi da kikeyi gaskiya kinci sunan ki HODA BA WANKA Nanfa Abu tayi kukan kura ta rufesu da duka Binta nadukan daya Abu ma na dukan 1 . Duka sukai musu bana wasa ba harda yaga riga Cikin muryar kuka yarinyar tace saina nuna miki bakida wayo Saikin ga gatana Abu tace Jeki turo duk wanda kika gadama ni Abu ina jiran hi banza qazama Eh nice qazama idan ni kazamace ke kuma fa fada min cewar yarin yar Bakinki be mutuba ko Abu saimun zubar mata da hakwara tukun na cewar Binta Kuyi duk abinda kuke so lokacin kune yanzu nima lokacina nanan zuwa cewar yarin yar . Tana gama fada ta mike ta debi takal manta a hannu ta kalli kawarta da suke tafe tare Tace 'YAR KWALLIYA suka zuba da gudu Matsoratan banza kawai harni zakibawa tsoro da baban ki Wannan kalmarta zakiga me rama min yazama tamkar tatsoniya a gurina ni Abu naci dubu sai ceto Sukayi dariya Kinga dauki tallar mu karasa dandali yanzu kowa yazo zamusha kallo kai ni harnaji ma bana son zuwa cewar Abu Binta tace meyasa Tiraren jikina Akoda yaushe shine matsala ta dana je dandali daga kallo sai tohe hanci a gurin sama ri cewar Abu Binta tace dagaske kike Abu warin najan hankalin samari Abu tace bana son wula kanci binta wayace miki warine kanhidai nibama nason irin kallon da sama rin suke min nasani nafi matan dandali kyau da kanhin tirare sosai ma nice kadai nasan sirrin Nanfa Binta ta tafi tuna ni Ke tina ninme kikeyi Abu gaskiya nima zan fara fashin Wanka konima turaren jikina zefito kwana nawa zanyi banyi wankaba Abu tace yauwa yar gari kinga bake ba Wanka indai kinaso tiraren yazauna tareda ke duk inda kika higa ansan kin higo Binta tace To hi kenan nagode kawata Tadauko farantin gurjiya tace debi kici iya San ranki aikin bani sirri babba Abu tace Bakomai yiwa Kaine Binta amma ya zakiyi da umman ki idan tagane kin dena kwanka Kibari kawai nikaina bansan abinyi ba mutafiko kinga yamma tayi kar a fara bugawasa bama nan Abu tace ga aiki zan saki indan mun higa dan dali ki ki zuba ido kiga abin mama ki gurin sama rida yan mata To hikenan muje Abu Suka je dandali hakan kuwa akayi Abu nazuwa masu toshe hanci nayi masu dariya nayi Abu harda sake tafiya Kawata Abu gaskiya nima na rike sirrin nan hannu 2 Sukayi dariya suka tafa Suka sha kallo sukayi tsokana iya son ransu suka koma gida Daga ina kike Waye Wannan Abu tace tana daga kai taga Nura Daga dandali nake Yariko hannunta yawuce da ita ciki ya watsar da ita kamar kayan wanki Nura ya fara shin shine shin shine Yace Inna bana tunaninda Abu ta shigawanka tayi Inna tace Ko hmm zata aikata nasani Wannan nan gaba kadan nizan fara yimata Wanka da kaina . Abu tace Waaa niii tab bawanda ya isa dan bakin ciki turaren nawama rabani dahi za a yi Nura ya Wanka mata mari tafashe da kuka Inna abinda ya dace kenan kifara yi mata da kanki tinda ita bata yi Nifa bawanda zemin wanka Nifa yaya anyi walkiya na ganka bakin ciki kawai ka keyi dani dakaji kanhin tirarena saika dinga yamutse fuska saboda bakin ciki Tirare ko wari kinga kidena shiga cikin mutane kina kiran waikin fesa tirare dariya zasu miki Wannan warine warinma mara dadi qazama cewar Nura hi kenan Inna kina jinhi ko ni ya kira qazama tafara timami akasa Nura yace Inna kice mata ta tashi kokuma yanzu jikinta ya fada mata Bashiri ta mike tana gunguni harya fito fili tace nagaba yayi gaba kanshi kuma nayi bawanda ya isa yakwace Ehhhe Waye ze kwace inbanda Wanka Inna duk sanda kika tashi wankar *'YAR KWALLIYA* kitanaji kwalin sabulu saboda tsoro Inna saida safe Yana fada yayi fice warsa Allah yakaimu Inna kinji shi ko Yasin yaya kajawa budur warka Allah ya hadani da ita Kinga Abu bana son neman tsokana karki sake kitaba musu 'ya kisamu wanda yamiki badai itaba ki kwanta saida safe To Inna Allah ya kaimu WASHE GARI DA SAFE Abu ta fito tana hamma . Inna Allah dai yasa kin gama abinci dan yau yunwa nakwaso abaccin Bagai suwa ba komai sai Neman abinci baza kiciba saikin goge baki kinyi sallah tukunna cewar Nura Tamatso kusa dashi tace yaya a gidan nan kaine kwai matsalata yanda sauran suka tafi suka barini kaima zaka tafi ko ince kagaji kabarni Yatoshe hanci tinda tafara magana harta gama Nura yace Wai Wannan bakin naki Abu ai sai ya kashe me rai yaushe rabonki da goge baki AF anzo wajan nikaina na manta gawayin da gihirin na ban wuya Yasin hiyasa na dena wankewa yawan goge baki na kahe hakori Nura Yana nesa da ita yanda bazeji warin bakin ba Injiwa Yau saikin goge baki yaushe rabonki da sallah dan Inna tace rabonda taga kin kalli gabas harta manta cewar Nura Eh hakane yaya hadasu nakeyi hiyasa bata ganina Hadasu kamarya Abu Nasati1 nakeyi a rana1 sauran ranakun kuma ina hutu tafada tana dariya Nura yace Abin ma dariya yabaki ko Abu amma kin dena zuwa isilamiya ko Tab tsohon zance tin yauhe nadena zuwa bari kaji laifi nayi yace ze dakeni nikuma nace be isaba shine yasa yara suyimin waka waini *HODA BA WANKA* hine na sace mai tayar keke hine fa yake ne mana ruwa a jallo . Tana fada tana Sosa kai da jikin ta Inna haka lamarin Abu ya kara lala cewa cewar Nura Inna tace kaji da kunnan ka kakuma gani da idonka yazu kuma abin zekara finnada tinda ta hadu da Binta Ido yazare yace Binta gagare Ita dai yanzu kawartace sosai duk inda Abu take zakaga binta Cewar inna Dole nakara samiki ido Abu jeki kwanke baki kiyi Alwala kizo kiyi sallah a gabana kuma ma inbanda rashin hankali irin na Abu a i na akace miki hada sallah a keyi kowacce ana yinta akan lokacin ta kina jiko cewar nura Abu tace Yashiga tanan ya fita tanan bayan kai ba malami bane me zaka fada min nayarda bayan sanin ma nafika Na yarda jekiyi alwalar kizo Taje tayi ta zo gabanshi tace yaya na hutar dakai dama yau nake hadesu guri guda barima nayi ka gani Nura yace Ke bana son hauka fa sallar Asuba raka'a nawane Lallaima yayan nan nawane inbanda 2 Sallama Alaikum Nura yajiyo sallama daga kofar gida girgiza kai kwai yayi yatashi yatafi Nura ya Inna taku Lpy kalau cewar nura To Alhamdulillah megarine yace kuzo dakai da inna dakuma Abu Allah daiyasa lpy cewar nura Ehhhhhto lpy ba lpy ba saidai koma meye idan kazo fada kaji To gamu nan zuwa yace yakoma ciki Inna yarinyadai tasake ballo ruwa megarine yake Neman mu To Bakomai bari ta idar da sallah saimu tafi cewar Inna Abu tace Inna Nifa ba inda zani idan banci abinci ba Ehhhhe Waiba sallah kike yiba Abu cewar Inna Abu tace Inna kwantarda hankalinki na idar bani na bawa cikina tukunna Inna ta bata ta ansa tana hannu baka hannu kwarya harta gama Tasha ruwa Tace Inna saura kwalliya idan banyiba bazan iya sa kafata wajeba Nura yace kin isa waye ze zauna jiranki Inna tace kai kanka kasan hakan baze yiyuba kabarta tayi mutafi Abuta baje kayan KWALLIYA tayi kamar yanda ta saba fukarnan kamar Aljana Inna mutafi naga ma Warin bakinta yadoki hancin Nura Kaiiiiiii Abu baki wanke bakiba ko Eh ban wankeba bakina ko naka . Tayi gaba abinta sukuma suna binta a baya harsuka karasa fada kowa na gaida megari amma banda Abu Megari yace Ke Abu me yarin yata tai miki kika daketa jiya tareda bakuwar gidana Tawatsawa yarin yar harara tace kuma na dake ta nadaki banza ba uwar dayasa tace min HODA ba Wanka Ke Abu baban nawa kike fadawa haka cewar yar megari Anfada mihi ubanki ubanane cewar Abu Kaji yarinya mara kunya me garin kike fadawa haka Ayi hakuri yarin yace cewar Inna Abu tace Inna saboda ni karki fara karya niba yarinya bace hekarata goma shabiyar Inna nayimata alama tarufe baki amma ina zance kwai Abu take saki.. Writing By Jabeer Rabiu Idris.. Whatsap Number.. 07034488635... 'YAR KWALLIYA Page 6-10 . Can saiga Binta ga gare sarkin kwadayi da umman ta suna ta howa Yauwa Allah na gode maka ga binta cewar Abu Dan rainin wayo da sassafen nan a aiko gidan mutane ace suzo ko uwar me za a mana cewar Binta Abu tace Kema dai kya fada gamunan ana surfo mana zancan banza Eh waye yake zancan banza ke kuma Binta ba a koya miki gaisu waba bakya ganin manyane a gurin nan cewar liman dake zaune a gefen me gari Binta da umma suka samu guri suka zauna Abu tace Wanda yatsargu dahi nake Babba bangan shiba saidai naga me gari tinda ba a barni naci abinci ba nazo nan to kowa yayi hakuri da abinda zeji koya gani cewar binta Liman yace kaji yara da rashin kunya Barsu dani liman cewar megari Umma ta gaida me gari binta kuwa aikin gun guni kawai takeyi Sauran mutanen gurin hanci a to she sun kasa cewa komai daga liman sai megarine kawai suke magana Binta kinji wai dan mun daki wa yancan 'yaran hine aka kawo mu nan gasu 'ya'yan kuli da mai cewar Abu Binta tace Kan uba Yasin bazan zauna ba akan su aka hanani cin abinci tafiya zanyi Yasin karki yarda binta kanki tafi kizo ki daki rabon ki zan taya ki cewar Abu Sukayi kansu zasu daka liman da megari mutuwar zaune sukayi wato kanhin jikin Abu dana binta da itama tafara hawa layi sukaji sukayi lup kamar basa gurin Megari yace Karku sake Ku tabasu kuna jiko wai warin me nake ji haka ina kuke kusa baki mana meye aikin ku liman Caraf Abu tayi da cewa nice nan kanhin tirarena babu inda baya zuwa megari ka gode Allah tinda kaji kanhin tirarena Megari yace Tirare kuma tab Wannan uban warin shine tirare . liman ba lbr yakasa cewa komai sai kallo da ido sauran ma sunyi shiru Megari cikin bacin rai yace waime nake gani haka kun dena magana ne kuma banson sha shanci kunwani zuba min ido me kuke nufi Me gari sai hakuri binta Abu kuzauna cewar inna da umma Binta hannu a dun kule tana shirin kai naushi take cewa Inna kubar mu dasu yanzu mu koya musu hankali Nura cikin muryar tsawa yake cewa kuzauna karku bari na kara magana Ganin fuskarshi ba alamar wasa yasa suka zauna Megari yace gaskiya yaran nan abin naku azimun ne kuma da laifinku wajan bata yaran nan kuduba fa Ku gani baruwansu da babba koyaro duk wanda ya musu yi mishi zasuyi Me gari ayi hakuri zamu gyara insha Allah cewar umma Me gari yace To shi kenan gaskiya kudau mataki inba haka ba ni da kaina zandau mataki Wani yaro ya fito daga gidan me gari hannun shi rikeda samira Tinkafin ya karaso Binta sarkin kwadayi tafara hadiyar yawu wayanda suke kusa da ita saida sukaji karar Yaron ya gaidasu ya ajiye kwanon a gaban liman Binta idonta na kan kwanon ko kiftawa bata yi ta janyo kwanon kusada ita Kanshin abinci yadawo da liman daga dogon suman da yayi Liman yace Ke me kike nufi yajanyo kwanon gaban shi Binta ko magana ta kasa hankalinta nakan kwanon Liman Allah ya yanka maka binta taga abinci ranta ya biya dan haka ka bata taci cewar Abu Liman yace In naki fa dawani bakinki dayake zuba wari anya kina wanke shi kuwa Abu tace Yasin wanke baki kahe hakori yake hiyasa bana yi liman kaida kanka kace hi bakin me azumi kanhin Almuski yakeyi hiyasa nima na dena wanke baki saboda Almiskin yazauna a bakina nafita daban daku nawa basai ina azumiba ta fada tana Dariya Liman baki yasaki yana kallon Abu Megari yace ke Abu anya kina da kai kuwa Abu tamika mishi kanta tace shafa kaji Inna ta rufe bakinta tana kallon Abu Megari ina fada maka saika dauki babban mataki akan Abu da binta cewar liman Bakomai kubani lokaci zansan abinyi kuna iya tafiya amma kubar binta da Abu liman ze musu fada cewar megari Waaaanii gaskiya babu abinda zan iya fadawa wayan nan yaran banshirya takun saka da suba sunyi nisa basa jinkira cewar liman Yi shiru liman nagama magana cewar megari Inna,umma da Nura suka tafi Binta batama San tafiyar suba itadai burinta taji abinda ke cikin kwanon a cikinta Liman kabata abincin nan taci yasin tanada cutar duka idan aka hanata abinda takeso hine suke tahi cewar Abu Liman Ya kalli binta dake zaune hannu a dunkule ido akan kwano tana sude baki Liman yace Me gari Abuya tabbata duka zatayi kalli kaga . Liman karka zama soko mana kayi musu fada sutashi su tafi ita kuma binta ka bata taci cewar megari Kwanon ya miki mata ta ansa tabude tana ci kamar kura yaga nama Binta ta gama ci tasa kafa ta ture kwanon ta kalli 'yar me gari tace jeki kawo min ruwa Niii kalle ni sama da kasa nayi kama da 'yar aikin gidan Ku cewar yar me gari Zancen banza meye dan kin debo min ruwa yan matan garin nan kaf yan aikina ne saboda na fisu haduwa cewar Abu Ya isa kunutsu kuyiwa kanku fada kungirma aure zakuyi gidan wani zaku kuyiwa Allah kudena abinda kukeyi Dariya suka yi suka tafa kinji wai aure cewar Abu Binta tace kaika sanshi nidai tinda ba a bani ruwaba bangode ba taso mu tafi To tace suka tashi zasu tafi Binta tarike ciki tace washiii cikina ya motsa Binta tayi nishi saiga tusa ya biyo baya Megari yatoshe hanci yace liman Sa a kamo min yarin yarnan Binta da Abu najin haka suka sa gudu **** *WACECE BINTA DA ABU* ABU 'yace ga munzali malam munzali fatauci ne sana arsa shikadai yake tafiya inya tafi saiya jima kafin ya dawo sai matarsa Suwaiba yaranta na kiranta da Inna yaransu 4 Ramatu itace ta farko tana aure a garin da suke me suna *DARAUDAU* sai zulai itama tayi aure sai Nura da Zainabu Abu itace auta ABU yarin yace mara tsoro duk girman mutum inya mata saita mai farace tas amma qazanta ya maida ta baka dan qazanta kokitso intayi saiya dankare layin ya bace kafin inna tai mata ta karfi ta tsefe Binta 'yace ga murtala Malam murtala mahaucine Allah ya masa rasuwa tin Binta tana karama a hannun ma hai fiyarta ta tashi sunan ta Baraka binta kadai ta haifa BINTA yarin yace mara nutsuwa ga kwadayin tsiya idan taga abinci jikinta har rawa yakeyi itama bata barin ta kwana dan haka tasu tazo 1da Abu gasuda taurinkai ***** Binta da Abu na cikin gudu wata yarinya kanta dauke da buhu ta tsaya a gaban su ta shaki wuyan Abu Ke meye haka a ina nasanki cewar Abu Tace idan maye ya manta uwar diya bazata mantaba nice wadda kika daka kika cimin gyada kika kuma zubarda sauran Abu tace Kinsan abin da yawa yanzu me kike nufi da kika shaki wuyana Dukanki zanyi na kwashi saura nakai gidanku cewar yarin yar Banga Alamaba ance da kuturu a gama lpy ni Abu banga wanda ya isa yamin abinda kika fada ba ba a hai fehiba Binta tace ke ware inba haka ba hmm jiki zeyi tsami Ke waya sa dake ni din nan da kike jida gani ban tinkare kuba saida na samo makarin ki ke binta dan nakula kema matsalace ta daban cewar yarin yar Makarina kuma ni binta banganshiba anan gurin yau banga abinda zesa na bar kiba batareda na sosakida bulala ba Ko to shikenan nida ke za a ga me gaskiya yarin yar ta Bude buhun taciro goriba,kurna,magarya da gyada Tinda ta Ciro Binta ta hadiyi yawu kamar yanda ta saba tabi hannun yarin yar da kallo Abu tace Ke karki sake ta rudeki da abin hannunta Binta nizan siya miki fiye dahi Ko jinta binta bata yiba Tamika hannu alamar ta bata harya rinyar ta miko mata saita janye Binta tace meye haka kuma bana son irin Wannan Kina zaton kai tsaye zan baki batareda na kafa miki doka ba Meye dokar cewar Binta Yarin yar tace zakiyi Alkawarin cewa bazaki sa hannu a fadana da Abu ba inkikasa hannu zan kwace abina Binta ta kalli Abu ta kuma kalli ledar hannu yarinyar da irin abinda ke ciki Nan tashiga raba idanu . Jikin Binta sai rawa yake Na amince bani Yarin yar tace in na baki ki tafi ko juyowa karkiyi Binta tace to bani dai Tana ba binta tawuce ta tafi Yarinyar tace yanzu daga ni seke Abu tace hakane kuma zam miki dukan tsiya kamar mu2 muka miki Yarin yar ta kama Abu da duka Abu na ramawa Abu ta Bude baki ta sakar mata cizo a hannu Waiyoo kika cizeni Yasin bazan yarda ba koni koke a gurin nan cewar yarin yar Saukar duka yarin yar taji bazata koda ta juyo Binta ta gani zatai magana binta ta dauketa da mari binta da Abu sukayi mata taron dangi saiga yarin yar a kasa wanwar tana kuka Abu ta bude buhu ta leka taga garin tuwo tayi dariya Binta ta daga ta juyewa yarin yar a jiki Inkinje gida saikiyiwa tsohuwa bayani yanda Akai da garin tuwo cewar Abu Suka tsalla keta suka wuce Binta tace Abu kina jin abinda liman yayi mana dan yaga me gari waimun girma aure zamuyi Rabu dashi nasan abinda za muyi mihi damu yake magana ba a taba mubama munyi fada bare ka ta bamu zomuje cewar Abu Ina zamu cewar binta Zaki gani cewar Abu Koda suka tafi basu tsaya ko ina ba sai gidan liman Abu tace Sallama Alaikum goggo me tuwo Goggo me tuwo ta amsa da Wa'alaikumus salam Abu Binta yaukune agin namu Eh wlh cewar Binta Goggo me tuwo tace Gashi kuma ban gama tuwonba yanzuma na dora Bakomai mu abindaya kawo muma daban ne bansan ta yanda zanfara fada mikiba goggo cewar Abu Kar kuji komai kufada min idan baku fada minba wazaku fadawa bayan nasan Ku tin kuna yara nan kuke zuwa cintuwo cewar goggo Binta tace Hakane munsan da wannan goggo hine dalilin da yasa mukejin nauyin abinda zamu fada miki Binta Abu kufada min bakomai komai girmanshi zansan abinyi Abu tafashe da kukan karya taceTo hikenan goggo kiyi hakuri da abinda zakiji sai Abu takara sautin kun da takeyi Binta ma kukan karya takeyi tace yi hakuri Abu bakomai sakai yar daze mata kenan Nanfa hankalin goggo ya tashi tace kunga kufada min duk kunbi kun daga min hankali Abu tace goggo dagir manki da komai liman ze miki kishiya Gogo ta mike tsaye tarike kirji tana huci . Ni liman zewa haka zezo ya sameni bemin kishayaba tin ina yarinyata saiyanzu dana tsufa Goggo abinda ze kara daga miki hankali hine irin kalaman da yake mata idan yaje zance cewar binta tafada tana kuka Dan rahin mutunci hine ta aiko mu da kala man soyayya muzo mu fada mihi Takuma ce karya manta yau yazo zance ita kadai tasan abinda ta tana dar mihi cewar Abu Kafar goggo ya haurawa taji juwa na ibanta tajin gina da bango ta ciji lebe a nan gidan ze kwana daiko badamuwa ina jiranka cewar goggo Binta takara sautin kuka tace babban abin hine mahaifin yarin yar yace liman yaturo anbahi ita Suna fada goggo ta zube kasa ba nunfashi Munhiga 3 Abu munyi kisa cewar binta Abu tace ke bata mutuba tsabar kihine kawo ruwa kigani Binta takawo ruwa Abuta watsa mata taja dogon nunfashi tabude ido tana Cewa ina yake kumiko min shi Abu tace goggo aibaya nan bari zahigo saiku yita takare Goggo tace bakomai zaka dawo kasa meni liman nida kaine yau agidan Goggo mu zamu tafi Nagode muku binta da Abu Allah ya muku Albarka Goggo me tuwo macace me kishi akan kishi zata iya yin komai sanin hakane yasa Abu da binta sukazo gurinta sunsan ita zata hukun ta musu liman yanda suke so Ameeen goggo aiyiwa kaine suka ce suka nufi hanyar fita harsun sa kafa zasu fita Abu ta gano liman yana ta howa da alama gidan zezo da sauri ta riko binta suka boye cikin wani duhuwa dake zauren gidan liman Liman yayi sallama ya fada gida kai tsaye ya nufi bandaki Goggo na jinshi binta da Abu Suka dauke sawun takalmi suka matso tayanda zasuji kuma suga Abinda ke faruwa Liman yafito yashiga daki yasa sababbin kaya yafesa tirare Nanfa kishi ya turnike goggo me tuwo tashiga waigen Abinda zata samu tarike ta hukun tashi dashi Me gari ya fito yana gyara hula yace in na kike na fito zan tafi Goggo tafito tana huci tace nasani kagai sheta wato danka raina min hankali nika ajiyeni a gida kaikuma ka fita kana neman aureko har ance katuro Yace ni liman a ina kikaji zan cen nan wlh bana ne man aure a ko ina ni liman ke kadai kin ishe ni Tace karyar banza ba abinda zaka fada min na yarda bayan nasan komai yanzu kayan nan dakasa kafesa tirare ina zaka Abuda binta na labe suna ji kuma suna ganinsu suna dariya Yace daliban malam rabi'u ne zasuyi sauka yau shine aka gai yace ni na shirya yanzu zan tafi Bata gamsu da abinda yace ba yasa tafara buga kafa tana tsaki . Tace malam malam ni goggo ni zakai wa kishiya Tana juyawa taga murhuna cida wuta ta Ciro icen dayafi ci tasa mai ababban Riga wuta yafara ci liman na ihon temako yana kokarin cire baban riga dakyai ya samu ya cire abin beyiwa gogoba ta dauko tukunyarda ta gama hada kayan hadin miya ta kwaramai a fara ren kayan shi Binta da Abu dariya harda faduwa Ta rarimo bokiti tana jifan shi dashi ganin abin nata bana Kare bane yasa liman ya mike ya zuba da gudu Binta da Abu suka Tsaya a gaban shi Abu tace liman mun girma aure zamuyi ko toga auren mun gwada maka tafada tana dariya Binta tace waiyoo cikina liman mezan gani haka yazaka gudu kaida yadace kai mata fada kamar yanda kayi mana dazu Amma dai yaran nan kwai shedanu kune kuka hadani da matata bakomai dani kuke magana Abu tace gogo me tuwo gashinan Liman yasa gudu binta da Abu na dariya Raina fesa cewar binta Duk wanda yace ze higa harkarmu to yadebowa kanhi kwarkwasa cewar Abu Sukayi dariya suka tafa Suka nufi gidan su Abu Liman be tsaya ko inaba sai fada gurin me gari wayanda suke tareda megari ganin liman yashigo da gudu suma suka mike zasu gudu Megari yace kudawo Ku zauna liman mezan gani haka da girmanka da komai Allah yabaka yawan rai ai duk abinda ya sameni kaine sila saida nace ba fadan da zanwa Binta da Abu kace kaisam saina musu gashi abin daya jamin dagir mana da komai na yanko ta cikin unguwa da gudu kowa na kallona Yanzu binta da Abune sukai maka haka a garin nan cewar me gari Liman yace hmmm ni nasan su sarai shiyasa tin farko naki kadage kace sainayi yanzu gurin saukarma ba halin zuwa ta kona babban rigar sukuma wayan nan kaga dai yanda tai musu harda manja a jiki kamar za a Kada miya gashi badamar na koma gida yanda ranta yake a bace Kai kutashi kuje Ku ne mo min su A'a kudawo Ku zauna Allah ya baka yawan rai nayafe Abarsu kawai nidai goggo me tuwo itace kadai damuwata ita taimin hakafa . Nan yakwashe duk abinda ya faru yafada wa megari Shine zakace a barsu gwara mu koya musu hankali cewar megari Eh Bakomai a barsu cewar liman To shi kenan zansa a kiramin gogo me tuwo zan mata bayani karka samu damuwa To shikenan godiya nake Allah ya baka yawan rai Kai tsaye suka shiga gidan ba sallama Yaushe zaku girma abin naku kara lala cewa yakeyi ko Abu da Binta cewar Inna Saida suka samu guri suka zauna sannan sukace salama Alaikum Inna tace Allah nagode maka binta da Abu Nura yatafi maka rantar boko Yinme inna cewar Binta Inna tace Yaje saku a maka rantar boko daga nan yamai daku isilamiya dan harda rashin ilimi a abinda kukeyi Abu tace Boko tab ba inda zani Inna bokoko awuta kike nunfin zamu toko su yan bokokon Awuta tsoron bokon sukeyi ba inda zani saidai ko binta gata nan Waaaaniii tab namutu Allah yasani awuta ba bokon da zani cewar Binta . Wlh baku isaba haka kuke so mu zauna daku a jahirce cewar Inna Yasin bazani ba wuta tsilim cikin sauki bokoko Awuta bada niba cewar Abu Binta ta tashi daga inda take ta koma kusa da Inna Tace Inna kisa baki akahe maganar nan dan baze taba yiyuba Yasin haka kawai ze Kaimu lahira da kanhi Kanshi kanshi inna taji yana tashi A jikin Binta Tato she hanci tace Binta warin me nake ji haka kardai kema kinhau layin rashin yinwanka Dariya Abu tayi tace Inna nice nan nadorata alayi tam bayeta kiji ita kanta tafijin dadin jikinta yanzu fiye da da Rufemin baki sakarai qazama nayi dake *'YAR KWALLIYA* Binta kiyiwa Allah karki bari Abu ta koya miki rashin Wanka da Wannan maya taccen KWALLIYAR nata Inna saidai kar a kuma dankuwa karatu yamin qanhi yabi jiki bakiga irin kallon da megari yake minba nikadai nagane meyake nufi cewar Binta Abu tace Nagani rabu dahi binta ze fado hannu banda hima ya tema kawa kanhi besa bakiba aida tuni munkoya mihi hankali kamar yanda muka koyawa liman Oohni Inna ina zansa kaina nan nasamu lbr anga liman yana zuba gudu a gari har ana zaton ya Hauka ce ashe ba Hauka cewa yayiba gamo yayi da 'ya'yan Aljanu binta da Abu babban gamo yai cewar Inna Abu kwaso kayan KWALLIYAR muyi muje gidan Amaryar da aka kawo nan bayan layin ku cewar Binta Abu tace Hakane fa banjeba kuwa Tashiga ta dauko ta ajiya a gaban binta Inna tace shiyasa tin farko banso qawan cen kuba wlh nasani sarai cewa abinda kuke da NA yanzu saiya fishi kuma gashi na gani Suka kafe inna da idanu Inna tace bance komai ba ni badaku nakeba Allah yabaku hakuri Suka juya suka cigaba da KWALLIYA Salama Alaikum inna nadawo Wa'alaikumus salam gonda da Allah ya kawo ka Yi shiru Inna nasamu lbr komai inaji nasan sune zasu aika tawa liman haka komai yazo karshe na sasu amaka rantar boko hakama isilamiya ga kayan maka rantar nasu Alhamdulillah shikenan kurinkus kandan bera boko Saikun je kokuna so ko ba kwaso cewar Inna Abu tace Boko Boko dai hikenan naji duk abinda ake fada akan boko ance yan wutane hine mu za a kaimu saboda ba a sonmu Ba a San naku gobe zaku fara zuwa daga nan idan kuntaso saiku wuce isilamiyar malam rabi'u Binta ta tashi ta daka tsalle tace rabi'u Yasin ba inda zani Wannan bakin mugun baki da Wannan kan nahi dayake kyalli kamar an cirohi A tandun mai Malamin naku kinga binta nasan irin takun sakar da kukeyi da malam rabi'u idan kika bari yakawo min karar ki kikuka da kanki irin dokan dazan miki baze faduba harda ke Abu cewar Nura Abu tace hikenan dai zamu leka wutar bakomai amma idan mukaji da zafi bazamu sake koma waba Tsaki Nura yayi yatafi ya basu guri Sukaci uwar KWALLIYA suka fice basu cewa Inna komai ba . WASHE GARI Abu tana tashi tasa kayan maka ranta ta janyo kayan KWALLIYA zata yi Nura yace karki sake kiyi KWALLIYA makaranta zaki ba dandaliba Abu tace Tab yaya Nura gaskiya bazan iya fita banyi KWALLIYA ba ga kanhin tirare i nayi Amma ba KWALLIYA a fuska ta Nura yace Eh ba a KWALLIYA idan za aje makaranta Abu dole kidena wasu abubuwan yanzu tinda kinfara zuwa makaranta Binta ta shigo ba sallama agaban kayan KWALLIYA ta zauna zatayi KWALLIYA Nura yace ke Binta ba sallama Bakomai kiwani zo gaban kayan KWALLIYA Binta tace yaya Nura tinda nafito banyi magana da kowaba Gahi yanzu kasa nayi magana Almiskin bakina yafita Hanci yatoshe yace naji Almiskin kice kema kinbi layin qazantar Abu ko makaranta zaku zakuje kuga yanda Ake safta Binta tace *'YAR KWALLIYA* mezan gani haka meyasa bakiyi KWALLIYA ba Abu tace Binta kibarni kibarni kwai ni Abu *'YAR KWALLIYA* ni za a hana yin KWALLIYA badole kiga haka ba Binta tace shine kike daga hanka linki ina Inna Abu tace tana ciki Binta tace yaya I na bayanka gwanda daka hanata bani kayan KWALLIYAR NA shiga dasu au baza kibaniba bari na dauka da kaina Binta na shiga ta juye kayan KWALLIYAR a Jakarta tafito Binta tace bata cikifa Abu tace hakane yanzu ta fita zomuci Abinci bayan sun gama cin Abinci Nura ya kaisu maka ranta Duk wanda yaga fuskar Abu ba KWALLIYA sai yayi mamaki dan bata taba fita ba KWALLIYA ba Suka shiga Aji Binta tace Abu Albishirin ki Abu rai a hade tace goro Binta ta bude Jakarta tace kalli Abu cikin mamaki tafasa kara ta rungume binta ta tsalle a aji Hankalin daliban ya koma Kansu Abu tace muna fukai me kuke kallo da sannu duk zanyi maga ninku . Daliban Suka dena kallon su Suka baje kayan KWALLIYA sunayi malami ya shigo aji akatashi ana gaisuwa banda Abu da Binta KWALLIYA kawai suke yi Malamin ya karaso gurin su yace Ku meye haka kwalliya a cikin aji me kukeyi a nan aji bantaba ganin kuba Abu tana shafa Jan baki tace baza kasan muba hime maka rantar be sanar dakai komu suwaye bako hege wato ya cinye kudin ko to hikenan Yace bagane me kuke nufiba fa Binta tace kaga waimu sa babbin dali baine kuma nanne ajin mu kana jiko jeka to Yace kee Nifa malamin kune kibani girma bakowana magana zaki dinga fada minba Abu tace inji kaba girma idan karike girmanka mutayaka rikewa idankuma kaki rikewa mubi takai mu wuce Malamin yayi murmushin keta yace kugoge fuskarku sannan kubani kayan KWALLIYAN Abu tace tab ba abinda zamu baka kuma ni Abu bazan goge KWALLIYA ta ba Binta tace nimadai bazan gege ba malam kabar daliban naka a tsaye fa Yace kuzauna yayi murmushin yaje gaban Allo yafara koyar dasu kamar yanda ya saba Abu tace gaskiya nagaji baza a yi wani abin bane bayan Wannan kazo ka I hemu da surutu Binta tace a he kekina jin hi tinda yafara har I yanzu banji komai ba ni yunwa ma nakeji Yace Anya karatu kuka zoyi kuwa Abu tace waya sani Abu a duhu Nifa karatun higa wutan nan beda meniba dahi da bahi duk1ne bokoko Awuta Binta tace gaya mihi kadai koyarda su dan naga kamar suna gane wa Yace anya Ku muta Nene kuwa ke dawani fuskarki kamar aljana waya gaya miki karatun shiga wuta nake koyawa Binta tace baka jiba bokoko a wuta hine zakace bakaratun higa wuta bane Yace kutashi Ku fita daga ajin nan kufita kuyi shir menku a waje Abu tace seme danka koremu kahiga wutar kaika dai kacike gurin karkabari asa wani Yace keni zaki fadawa haka Tamurguda baki Yadauko bulala ya zuba mata Tasaki kara . Binta tace meyasa ka daketa kai ko a qauyen mu mune muke yiwa maza duka hmmm Yace me kike nufi nima dukana zakuyi kenan Abu tace meze hana tinda ka dakeni saina rama Yace waya gaya miki idan malami yadaki daliba tana ramawa Binta taja hannun abu Tace Abu rabu dahi zomu fita ze fito ya same mu damu yake maga mekoya karatun higawuta dole mukoya mihi hankali Suka fita Abu kinga ya aika a siyomai abinci Abu tace waye ya aika asiyo mihi abinci mekoya karatun higa wuta Binta tace Eh hine zomuje Yaron ya siyo abincin zekai wa malam binta da Abu suka tsare shi Abu tace Kai bamu abinci kaje kadebo min ruwa zansha kagani ba quwace Yace malam ya aikeni bari nakai mishi nadawo saina debo miki Binta tace harna hadiyi yawu banga abin dake cikiba amma nasan zeyi dadi tafada tana dariya.....