[4/21, 4:32 PM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SADAUKARWA GA YAN UWANA NA MUSAMMAN: Seemerh & Shaheedah, love u so much angels, u mean the whole world to me. SHAFI NA ‘‘‘‘‘1&2’’’’’ NIGERIA BAUCHI STATE SHIRA LOCAL GOVERNMENT GALLARA VILLAGE Gudu take falfawa tamkar zata furga sama yayin da duk wani wuri da tazo wucewa suke kaucewa su bata hanya kamar wata motar da babu brake. Bayan ta shafe fiye da 30minutes tana gudun ne ta iso dai-dai wani gida ba shiri taci burki kamar tayar da ta samu friction. Gidan ta nufa kai tsaye tana tsalle-tsalle kamar wata kwaɗo, bata tsaya yin sallama ba saboda sallamar kanta bata daga cikin jerin abubuwan da ta saka gaba balle su zame mata jiki. Tana tafe tana tsalle har ta gama tsallake zanar da aka kewaye gidan, tana isa kuwa ta shige wata ƴar bukka wacce ba sai na tambaya ba da gani mallakin ta ne. Ashe tun lokacin da na hango ta tana shera gudun nan Bala Mai kifi na biye da ita. Fitowa ta yayi dai-dai da isowar sa gidan, sallama ya shiga rafkawa kamar wanda aka ci bashin sa ba'a biya ba. “Salamu Alekum, Salamu Alekum!!!” Jin babu wanda ya amsa masa sallamar yasa ya ɗan ƙara matsawa dai-dai lungun gida. “Salamu Alekum!” “Wa Alaikumus Salam” Daga bayan shi aka amsa sallamar nan take ya juyo don ganin waye, ba kowa bane face Mallam Umaru Gallara. Murmushi Mallam ya sakarwa Bala Mai kifi yana faɗin “Mu ƙarasa ciki mana” Saboda tsananin kunyar Mallam da Bala ke ji yasa ya bi shi ba don ya so ba,damah shi ƙara ya kawo amma babu yadda ya iya dole bi shi. Sallama malam yayi yana nufan wani ɗaki wanda suke jere guda biyu, bai daɗe ba ya fito da taburma ya shimfiɗa musu. Gaisuwa irin ta mutunci suka yi bayan sun gaisa Mallam ya maida kallon sa ga Bala Mai kifi. “Mallam Bala fatan dai lafiya koh” Cike da jin kunya Bala yace “Lafiya Allah shi gafarta Mallam kawai na zo mu gaisa ne” ya ƙarasa yana sosa kai da kunne. Murmushi mai sauti Mallam yayi kafin yace “Nayi farin ciki sosai Mallam Bala, Allah ya bar zumunci” Bala ya amsa da “Amin Allah gafarta Mallam Ni zan wuce, na gode” “mallam yace Amin ” Daga nan ya rako Bala har bakin ƙofa. Babu yadda Bala ya iya ammah ya ɗauki alwashin yiwa Ƴar iya tsiya in ya kama ta. KO ME TA MISHI? THIRTY FIVE MINUTES BACK (Flash back) Tana dawowa daga yawon da ta saba ne sakamakon yunwar da ta takura ta, ƴan hanjin ta sai juyawa suke alamun suna buƙatar kaya. Da sauri ta karyo corner yayin da ƙamshin kifin da Bala ke soyawa ya bugi hancin ta, nan da nan hankalin ta ya tashi saboda haka da gudu ta ƙarasa zuwa teburin kifin. Tana isa shi kuma lokacin ya kwaso kifin da ya tsame cikin matsamin sa na ƙarfe ya zuba su kan teburin. Wani Shegen yawu Ƴar Iya ta haɗiye sai wani lumshe idanuwa da tanɗe baki da take yi kamar tsohuwar mayya. Gaban Bala ne ya faɗi saboda ya sha jin labarin Ƴar Iya wurin samarin da ke ƙauyen tare da irin rashin mutuncin ta da tsiyar da take shukawa. Dakewa yayi saboda shi babu abun da ya taɓa haɗa ta da shi. Ganin ya ƙi ƙunsa mata kifin a leda kamar yadda duk inda taje ina ana sayar da abu kafin tayi magana suke ƙalla mata salin alin ta tafi abun ta yasa ta ƙara zaro dara-daran idanuwan ta tana duban shi kafin tace “Kai kifin nake jira ka bani dai” Ta faɗa cike da ƙosawa tana hararar Bala mai kifi. Shi kuma irin ya gwada mata shi bai san ta ba yasa yace “Na nawa za'a baki?” Mamaki ne ya kama Ƴar Iya jin batun raini da Bala ya kawo mata, gashi ita duk ta ƙosa ya bata don zuwa jimawa in bai bata ba zata iya mutuwa. “Duk na kan teburin nake so ka juye min” Tana faɗan haka taga ya juya zuwa wajen abun suyar shi yasa ta janyo leda ta fara kwashe kifin. Leda uku ta cika fal sannan ta juya zata tafi. A lokacin ne Bala ya dawo gaban teburin shi ganin wayam babu kifi babu mai siyan kifi yasa shi bin bayan ta da gudu. Ai kuwa kamar tasan zai iya biyo ta yasa tana matsawa gefe ta fara tura kifin a bakin ta ba tare da ta damu da cire ƙayar ba. Within 2Minutes har ta kammala da leda biyu, (Ni kaina Bhatool sai da na zaro idanuwa tsananin mamaki). Ta janyo ledar ƙarshe zata fara ci ta hango Bala na tahowa ai kuwa babu shiri ta arta a na kare. Tana gudu tana cusa kifi har ta cinye ta wulla ledar ta ƙara wa jikin ta mai, tuni tayi wa Bala nisa. Duk da haka bai daina bin ta ba har ta iso wurin wasu mutane da suka taru, ai babu shiri ganin Ƴar Iya yasa suka matsa don sun san abu mai sauƙi ne duk ta bangaje su ta wuce. Duk irin nisan da ta yi wa Bala bai hana shi bin ta ba har ta iso gidan su....... WANNAN KENAN! BACK TO STORY. A lokacin da Bala ya koma wurin suyar kifin shi yayi mamaki sosai, kifin da ya zuba tasss ya ƙone babu yadda za'a yi ya sayar da shi. Nan da nan wani ɓacin rai ya ziyarci zuciyar shi, gashi bashi da wani kuɗin a hannu ballantana ya ƙara zuwa kogi ya saro wurin masinta.... Ganin ba shi da wata makama yasa yasa ya sauƙe mayin da ya rage ya shigar da shi cikin shagon ajiyar shi. Yana fitowa yazo ya rafka uban tagumu ga wasu hawayen baƙin ciki da suke gangarowa daga idanun shi. Yana cikin yanayin nan ne ya ji an dafa shi, abokin sa ne Tanimu wanda ya ƙure shi da ido ganin hawaye a idon shi. Tanimu ya tambayi Bala cike da kulawa “Aboki na ya naga hawaye a idon ka, ko dai baka jin daɗi ne” Cike da takaici ya goge hawayen nasa ya ce: “Kai dai ka bari kawai, wannan ai gwanda ace jinya na nake yi da abun da ya faru” Tanimu ya maida hankalin sa kan abokin sa yace “Ina sauraron ka” Gyara zaman shi yayi yace “Ina yarinyar nan da kuke bani labarin rashin mutuncin ta ɗin nan?” Tanimu yace “Wai Ƴar Iya kake nufi” “Eh ita dai in ma Ƴar Baba ce” Cike da zaƙuwa Tanimu yace “Baka faɗa min me tayi maka ba ai” Bala yayi tsaki yace “Hmmm aboki na yarinyar nan na soya kifi na na kwashe zan zuba wani tazo, bayan tace na bata sai naje duba wanda na zuba” Ɗan dakatawa yayi saboda yadda zuciyar sa ke ƙuna. Shi kuwa Tanimu duk ya ƙosa yaji artabun Bala da kuma Ƴar Iya. “Ina jin ka” “Kawai kafin na dawo duk ta kwashe kifin ta tafi, ina bin ta kan hanya naga har ta kusa cinyewa” Dariya Tanimu ya kwashe da ita kamar mahaukaci hakan yasa Bala tunzura ya miƙe. Da ƙyar Tanimu ya tsayar da Bala tare da riƙe hannun shi yana mai tsagaita dariyar. “Haba aboki na, ai baka gama bani labarin ba” “Shikenan ai tunda ma dariya zaka yi min kana gani dai sana'a ta kenan kuma kasan ita ce jari na, saboda ita na baro ƙauyen mu na dawo nan” “kayi haƙuri aboki na, yanzu dai ƙarasa min sai mu nemi mafita” Shiru Bala yayi can ya ci gaba “Bayan na sha wahala na bi yarinyar nan har ta isa gidan su ina doka sallama sai Mallam Umaru na gani kenan shine baban ta?” Kallon baka da wayo Tanimu yayi masa yace “Lallai kuwa, Baffan ta ne ɗan uwan uban ta, kuma wai kai da ka bita ɗin uban ne zaka yi mata?” Ya tambaye shi in a serious tone “Wallahi Babu abun da zai hana na ɓalla ta da na kamata” ya faɗa cikin zafin rai. Kallon wawa Tanimu ke aika masa daga nan yace “Lallai yau na tabbatar baka da hankali, ai kuwa in baka ɓalla ta ba Kai ka dawo da ɓallallen hannu ka rasa na suyar kifin” Zaro ido Bala yayi yace “Habadai....yanzu maganar da nake maka kaga can wanda na zuba cikin mai da na dawo duk ya ƙone” ya faɗa yana nuna masa kaskon suyar da ya mayar cikin shagon. “Lallai aboki na, baka san wace ce Ƴar Iya ba shiyasa ka sha wahalar bin ta, ammah shawarar da zan baka ka fita sabgar ta in ta zo tace ka bata kifi to salin alin ka bata ta tafi” Daga haka suka koma taɗin su na rayuwa.. ƳAR IYA Tunda taji dawowar Baffa Umaru ta lallaɓa ta fice daga gidan tana tafe tana raira waƙar ta. “Dan maliyo maliyo, *Maliyo* Ɗan maliyo nawa, *Maliyo* Yaje ina ne?, *Maliyo* Ya tafi Illorin, *Maliyo*” Haka ta ci gaba da tafiyar ta tana daga garin kamar marar aikin yi, tana cikin tafiya tayo hanyar fada, yanke shawarar zuwa can taci abinci tayi saboda haka kai tsaye ta wuce. Dakaru biyu da suke gadin fadar na ganin ta suka bata waje sun sani tsaf duka hana ta zata kwaɗe su ne ta shige abun ta. Tana shiga kai tsaye ciki ta wuce can sashen mahaifiyar Arɗo Innani. Ai kuwa taji daɗi ganin tukunya akan wuta nan da nan ta washe haƙwaren ta masu kama da na mage, gashi duk datti ya danƙare haƙwaren babu daɗin gani. Fara ƙwalla ƙiran Innani tayi “Ke Uwar Arɗo! Fito manah yau a nan zan ci abinci” Innani na jin Muryar Ƴar iya ta dogara ta fito da sauri tana yin yaƙe don ita a gaskiya in ba don fin ƙarfi irin na iblishiyar yarinyar nan ba da ta surfa mata ruwan Bala'i ammah babu yadda ta iya tunda yarinyar ta Addabi kowa cikin garin. Ganin irin dariyar yaƙe da Innani keyi yasa ta haɗe rai tamau tace “Ki ma daina yaƙe ɗin nan don yau ko mutuwa zaki yi sai naci, shegiyar tsohuwa sai shegen rowa ni ban ma san ya aka yi kika zama uwar sarki ba bayan baki cancanta ba” Ta ƙarasa tana hararar Innani. Innani da ran ta in yayi dubu toh ya ɓaci ta juya zata koma ɗaki caraf ta ji Muryar Ƴar Iya na cewa “In ma mutuwa zaki yi Aradu sai naci, don ko ɗan ki da ya siya bai isa hana ni ci ba, da kwalmaɗaɗɗiyar ƙafar ki a nan kamar agwagwa” Innani da ta shige ɗaki ta rasa abun da ke mata daɗi, wannan yarinya duk ta addabi rayuwar su, a da can ita ke da iko da gidan saboda baki da masifa irin nata amma yanzu sam yarinyar nan ƴar da tayi jika da ita sai mulkar ta take. Ƴar Iya na kai ƙarshen maganar ta ta nufi tukunya, tana buɗewa tayi ido huɗu da sulalen kajin da ke ciki, tuni ta fara haɗiye yawu tana farin ciki. “Shegiyar tsohuwa ƴar baƙin ciki, yanzu Ni zata yi wa buƙulun cin kajin nan, kwarangwatsa in naga dama guduwa zan yi da shi gaba ɗaya” Bata tsaya wata wata ba ta bi shawar zuciyar ta ai kuwa ta cire kwalin da ta ɗaure kan ta da shi tuni mummunan gashin ta da ya danƙare wuri guda kamar gonar mahaukaciya ya bayyana ga wani uban bugu da ke tashi daga gashin. Ɗaure kwalin tayi a kunkumin ta yayi da ta sa hannu ta rungume tukunyar a jikin ta. A haka ta sanya gudu sai waje......... [4/26, 8:44 PM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘‘3&4’’’’’ A haka ta falfala da gudu sai waje, duk irin tiririn da ke tashi daga cikin tukunyar hakan bai sa Ƴar Iya ajiye ta ba sai ma ƙara rungumar ta da tayi. Basu yi aune ba suka ji su duk a ƙasa, ɗagowar da zasu yi suka yi arba da Ƴar Iya mai hannun ɓarna wacce yanzu har tayi nisa don kuwa shegen gudu gare ta kamar barewa. Tana bangaje su bata tsaya bi ta kan su ba sai gida, tana shiga ta tarar da iya na tankaɗe garin dawar da zata yi tuwa. Bata yi sallama ba ta dire tukunyar gaban wani faifayin sannan ta hau kan faifayin. Tana zama Iya da ta kasa haƙuri tace “Ƴar Iya daga ina kuma kika samo wannan tukunya kuma miye a ciki? Kar dai ɓarnar da kika saba yiwa mutane kika je kika yo” Gurmuɗa ɗan ƙaramin bakin ta tayi tana buɗe tukunyar sulalen da ta ɗauko daga gidan sarki sannan tace “Ke iya dana wallahi kin fiye takura da sa ido...Ni har wata ɓarna nake yi ne in ban da sharri irin na mutane” Ta ƙarasa tana tura baki gaba. Iya da ta fahimci ɗiyar tata ta hau kuma bata son fishin ta saboda tsab zata musu aika-aika tace “Yi haƙuri shalelen Iya, ni kaina na san ƴan baƙin ciki ne suke son shigga tsakanina da ke, yo ƴan baƙin ciki manah, Aradu su ne sai su zo su ce kinyi kaza kinyi kaza, rabu da su duk ranar da kika je birni ba zaki yi musu tsaraba ba.” Lallashin da iya tayi mata yasa ta ɗan sauƙo ammah da tayi niyyar gurza wa Iya rashin mutunci. Ɗaya bayan ɗaya Ƴar iya ta fara ɗauki dunƙula dunƙulan sassan kajin da aka fara sulalawa basu ma dahu ba. Sai da ta ciro kusan dunƙule goma ta ajiye kan murfin tace “Iya ga kaza nan kizo ki soya mana sannan ki jira na dawo sai na raba kinji?” Bata jira amsar Iya ba ta wuce waje a guje.... Kaɗe jikin su dogaran dake a bakin gidan sarki suka yi. Ɗaya daga cikin yace “Lamara kai na ɗauka fa dokin ranka shi daɗe ne ya ƙwace har ya take mu” Wanda aka ƙira da Lamara yace “Toh Aradu ai gwanda ma ace dokin ne ya buge mu da wannan shaiɗaniyar yarinyar...."" Rufe masa baki yayi saboda hango Ƴar Iya na dawowa da yayi sai dai kash bakin alƙalami ya bushe tun daga can ta jiyo me dogaran ya faɗa. Fara zazzare ido yayi yana tunanin shi kam yau kashin sa ya bushe.....A gadarance ta ƙaraso wajen da suke tsaye ta fara bin su da kallon tuhuma. “Dallah can meyeh kuka bi kuka tsira min ido ko naci na uwar ku ban biya ba?” “A...a....h kiyi haƙuri ƴar iya ba zamu ƙara ba” Lamara ya faɗa yana maida kallon shi ƙasa yayin da ɗaya dogarin kuma jikin sa in in banda rawa babu abun da yake yi. Kamar wadda ta tuna wani abu kawai ta miƙe zata shiga gidan tana faɗin “Kun ci sa'ah yau ina farin ciki na ci kifi ga kuma nama na jirani Aradu yau da na karya ƙafafuwan ku musamman wannan me gemu irin na tauren nan. Ƴar Iya na shiga gidan bata wuce ko ina ba sai ƙofar matan sarki, don ko hauka take ba zata shiga ƙofar tsohuwar can ba sai ta kawo mata tukunyar ta. “Gafara dai gafara dai matan sarki” Ƴar Iya ta faɗa yayin da ta sauya tafiya sai wani lanƙwashewa take kamar hawainiya, farfara idon da take yi ne ya ƙara bawa Saratu Matar sarki ta tsakiya dariya. Babu tsammani kawai suka ji Muryar Saratu na sheƙa dariya. “Kan babar uban can, ke ni kike wa dariya?” Saratu da ta kasance Ƴar duniya gaba ɗaya ta takurawa uwargidan sarki Salamatu da iyalen ta ga kuma shegiyar rashin kunyar da take fama da ita. Salamatu tun ba yau ba ta san Ƴar Iya shiyasa tayi miƙit da bakin ta, ita kuma Saratu dama daga Kahin (ƙauyen da ke kusa da su) aka auro ta. Kuma Ƴar Iya bata fiye biyo ƙofar sarki ba iyakarta ƙoƙarin waccar tsohuwar. Saratu kuwa dariya ta ke sheƙawa kamar wanda aka sheƙawa laughing gas. Can ta tsagaita ta kalli Ƴar Iya irin kallon da uban wa kika zo tace. “Lallai kuwa yau naga iya shege, Salamatu kina ji wai ni yarinyar nan take kwatamawa rashin kunya, Aradu yau Sai ubanki ma yaci uban sa, dogarai zan sa su ɗauko tsumangun zane Dawaki su ci ubanki" Ta faɗa tana kama fuska wai ita babba, miƙewa tayi da niyyar fita don ƙiran dogari ai kuwa a lokacin Ƴar Iya da ta hasala ta ja ƙafar Saratu ji kake tiiiiiiiiim! Kamar faɗuwar buhun kaya. Bata yi wata wata ba ta samu saitin bakin Salamatu ta buga mata naushi tuni jini ya fara zuba kamar famfo....hango wani kashin shanu da ke can gefe tayi ai kuwa kafin ƙifta ido ta ciko hannun ta da shi ta dawo. Bakin Saratu da ke jini gashi sai ƙwala ihu take tana son tashi ma ta kasa. Buɗe bakin tayi ta fara cusa mata kashin shanun nan tana faɗin “Shegiya haɗiye ko naci ubanki, haɗiye maza, yauwah maza dai haɗiye” sai da ta cinye kashin nan tas har abun tausayi tukun ta ƙyale ta tana sakin dariyar mugunta, su Saratu kuwa anji jiki baki ya mutu, hawaye ne kawai ke zubowa. (Nace maganin maras kunya kenan, dama an ce kin ishe su ai, yanzu kin haɗu da gamon ki). Miƙewa tayi ba tare da ta damu ba ta bar gefen Saratu, Salamatu kuwa kame kanta tayi tana maida kan ta ƙasa. “Ke kuma sai kace wata munafika dallah ɗago kanki, wato mata dai sun iya tsula tsiya da munafurci, dubi kan ta kamar asusun boka, ja wannan lafcecen jikin naki ki bani wuri ko na dawo kan ki” Ai da gudu Salamatu tayi ɗakin ta. Maida kallon ta ga Saratu tayi tana yamutsa fuska tace “Ke kuma gobe in na zo ki ƙara min rashin kunya ki gani, bari na ƙira dogari ɗaya ya sanar da sarki matar sa ta karye” ta faɗa tana kashewa da dariya sannan ta fita. A bakin ƙafa ta sanar da dogarin cewa Saratu matar sarki na neman sa daga nan ta cika bujen ta da iska. Bata tsaya ko ina ba sai gidan su A'i Aminiyar ta wacce take take mata bayar kamar bafadiya. A'i ma ba baya ba a rashin ji shiyasa duk ƙauyen babu wacce Ƴar Iya ta zaɓa matsayin abokiyar ta irin A'i, tare suke tsula tsiyar su, su tsokali wannan su zagi wannan in sun ganshi su duka wannan aikin su kenan cikin gari ini suke suna yawo kamar ƙudaje daga nan sai can. Tun daga baƙin soron gidan su A'i Ƴar Iya ke ƙwala ƙiran ta. “A'i A'ilo kan kaza Amadu ya siyo mata kaza taci” wannan shine kirarin da Ƴar kewa Aminiyar ta tuni zaki ga ta fito da yake ita ma duk ta ishi gidan su har Allah Allah suke ta fita. Yau da bata fita ba tsiyar da ta tsula musu ba'a magana. A'i na fitowa daga gida ta dubi ƙawar ta tace “Kutt Ƴar Iya dama kina cikin Gallara yau ko kallon ki banyi ba, ko dai kin samu kaso ne shiyasa” “Dallah ni ba magana nace ki min ba ki zo muje gida yau na samo babban rabo” Nan ta bata labarin kifin Bala da ta kwaso da kuma Naman Iya Uwa Maman sarki. Suka yi ta dariya suna shaƙiyyancin su. Har sun kama hanyar gidan su Ƴar Iya A'i tace ”ah Ƴar Iya wallahi mu bi ta dandali ta wurin Bayero mai balangu nasan zamu dara. Tafa hannu suka yi suna dariya Ƴar Iya tace “Ke A'i yau kam dai sai cikin mu ya cire don ciwo mu dai wuce. Tafiya suke suna taɗe-taɗen su har suka iso dandali, duk da cewa dare bai yi ba lokacin ne ma ake kiran sallar Ishã ammah yara da manya, ƴan mata da samari sun cika maƙil ga kuma ɓangaren Bayero da yake sayar da balangu sai kai kawo ake a wurin. Ganin kowa hidimar shi yake yasa Ƴar Iya ƙwallah ihu ita da A'i Suna faɗin, “Wallahi Sakse ya biyo ta hanyar nan, kowa ya gudu ya tsira da kansa don kuwa har da wuƙa a hannun sa” Nan wasu suka fara gudu yayin da Ƴar Iya da A'i suka ci gaba da ihun “Wallahi dagaske ga nan Sakse....mun shiga ukuuuu” Waɗanda suka ɗan ja gefe tuni sun fara neman wurin ɓuya, Bayero kuwa da Mai Salisu mai shayi duk sun watse sun shige kiosk ɗin Baaba Mai trader, tuni wurin yayi tsit babu almaun motsi kowa yayi shiru don tsira da ransa shi, hakan yasa Ƴar Iya da A'i nausawa kai tsaye tsaye wurin bakangun Bayero. Tas suka kwashe shi cikin ledodin da ke ajiye bisa teburin balangun, har sun lallaɓo zasu tafi Ƴar Iya ta hango wasu ɓula-ɓulan breads kan teburin Salisu, tuni ta wuwuro biyu ta riƙe. Juyawar su da niyyar tafiya suka ji motsi a bayan su, waye kuwa in ba Sakse ba ai tuni suka arta a na kare Sakse na biye da su. Dama bread ɗin a hannun Ƴar Iya suke , sai da suka ja Sakse ta lungun ƙarashi kukan ka Ƴar Iya ta faki ido ta damƙo ƙasa ta watso masa sai ciki idon sa, ta ƙara damƙa ta watsa sai da ta tabbatar ƙasar ta masa illa ba zai iya gani ba ta tsokalo karen Baushe....tuni suka yi siɗaf-siɗaf suka gudu suka bar Sakse da kare ga kuma ido car ƙasa. Gudu suka ƙara har sai da suka iso gidan Iya tukun suka tsaya suna haki suna mayar da numfashi. Tun daga lungun da zai sada ka da cikin gidan suka jiyo Muryar Baffi...Ɓata fuska Ƴar Iya tayi saboda ta san halin ɗan tsohon sam baya ɗaga mata kuma duk iya shegen ta bata isa tayi masa musu ba in yace abu. Da yake su Ƴan duniya ne sai suka haɗa plan, Ƴar Iya ta shiga da gudu zuwa Bukkar ta kamar an biyo ta sai A'i ta biyo bayan matsayin wacce ta tsokalo. Hakan kuwa suka yi tuni Ƴar Iya ta arta A'i na biye da ita basu ko kalli Iya da Baffi basuka shige, dariya suka ƙyalƙyala suna tafa hannaye. Baffi da ya lura da su kuma ya gane shiri ne irin nasu bai bi ta kan su ba kawai yayi musu addu'a ya miƙe zuwa tashi bukkar. Har Iya zata bi bayan shi ta tsinki Muryar Ƴar Iya ”Ina kuma zaki je Iya baki bani aikin da nayi miki ba?” ta tambaya tana wani yamutsa fuska. Iya da dam tuntuni take jiran dawowar jikar tata saboda ta bata ita ma ko ta maida ƴaƴan yasa tayi murmushi ta nufi ɗakin ajiya ta ɗauko naman kajin da ta soya, ba tare da ta ɗauki ko ƙafa ba ta miƙa mata. “Gashi nan Ƴar Iyan ta” Cinya da fuka-,fukai ta zaro da miƙa wa Iya tuni ta amshe kamar sabuwar mayya sai wani wage Baki take ita ala dole zata ci nama. Wani abun mamaki tas suka cinye kajin da zasu kai huɗu kuma ba ƙanana ba sannan suka ƙara da balangun Bayero na yi tunanin zasu bar bread ɗin zuwa safiya ai kuwa sai Ƴar Iya taja ɗaya ta buɗe A'i taja ɗaya ta buɗe tuni suka lamushe su tasss.... Suna gama cinye wa suka ƙara fita waje ammah wannan fitar ta satar mangwaro ne kuma bishiya zasu hau. (Nace sai kun je aljanu sun wurɗo ku ai😀 ehmana) Gonar da ke kusa da gida suka nufa. Bayan sun tsinko mangwaro suka dawo. Duk da cewa dare ya tsala hakan bai hana su yawata cikin ƙauyen ba don farauto wani abun su ƙara a cikin su kafin kowa ta wuce gida don huce gajiya. *WACE CE ƳAR IYA*? Mu haɗu gobe don jin wacece ƴar iya, tabbas akwai ɓoyayyen al'amari a tattare da ita....ku ci gaba da bibiyar alƙalami na don jin ya zata kaya. COMMENT PLEASE!!! [4/26, 8:45 PM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘‘5&6’’’’’ *WACECE ƳAR IYA?* Malam Umaru Gallara haifaffen ƙauyen Gallara ne da ke cikin ƙaramar hukumar Shira da ke jahar Bauchi. Mahaifiyar sa AISHATU wacce aka fi sani da Iya sunyi auren zumunci ne da Baban sa Mallam Musa wanda ake ƙira da Baffi. Tunda suka yi auren nan Allah bai basu haihuwa ba har suka share shekaru goma sha biyu cikakku, hakan ne ya tada hankalin Iya saboda dangi sun yi caaa akanta suna faɗin juya ce, Musa ya ƙara aure. Wannan tashin hankali yayi wa Iya illa sosai, don kuwa haukacewa ne kawai bata yi ba, ana cikin wannan yanayin ne wani al'amari ya faru wanda shine mafarin komai cikin rayuwar wannan ahali na Malam Musa. Wata guda da fara wannan hatsaniya Iya ta samu ciki, kada ku so ku ga murna wurin Baffi don kuwa a ranar sai da ya raba buhun gero fiye da ashirin saboda farin ciki. Dangi murna kowa yake yi da wannan cikin yayin da kowa ya ƙwallafa ranshi akan yaron da masu so da kuma marasa so. Haka Iya ta raini cikin nan tare da taimakon Baffi da kuma Mahaifiyar sa Baba Maunde. Baffi da Baba Maunde sun matuƙar bawa cikin Iya kulawa ta musamman har ta kai watanni tara ta haifi ɗan ta namiji, kyakkyawa son kowa. Bayan sati guda da haihuwar yaro Baffi yayi masa laƙabi da Umaru. A ranar Iya ta samu goma sha tara na arziƙi daga kowanne fanni, dangin ta da kuma dangin Baffi. Haka dai yaro ya ci gaba da girma har ya kai shekarun fara zuwa ɗaukar karatu, da yake Allah yayi mishi baiwa ta musamman yana da shekaru goma sha shida ya kammala haddar sa ta Alqur'ani. Bayan ya dawo Baffi yasa aka shiryawa Umaru Ƴar wata ƙwarya-kwarya yadda aka ci aka ƙoshi. Tun bayan dawowarsa Baffi ya ke zuwa da shi gona har ya kai shekarun Aure. A lokacin ne kuma fitina ta ɓarke, Iya ta kawo zaɓi Baffi ya kawo zaɓi. Da ƙyar aka samu Baffi ya janye nashi zaɓin akan sharaɗin bayan shekara da auren Umaru zai auri Zaliha ɗiyar Abokin sa wacce ita tace tana son Umaru. Sannu sannu babu wuya inji hausawa, haka aka sanya ranar auren Umaru da Barira ƴar yar Iya. Barira mutum ce ba mai ƙaunar tashin hankali ba hakan yasa suka yi zaman su lafiya da mijin ta Umaru wanda shima lokaci guda yaji ba zai iya ƙara auren wata matar ba bayan Barira. Shekara guda da auren Allah ya albarkace su da samun ƙaruwar ƴa mace sai dai yarinyar tazo da salo na musamman. Ranar suna yarinya taci suna Aishatu...an yiwa Iya takwara kenan. Tun daga wannan lokaci Zaliha ta fara ƙoƙarin shiga gidan Mallam Umaru tare da ƙudurruka masu ɗumbin yawan gaske, da farko ta fara ne da salon ta na ƴa mace ganin ba zata ci riba yasa ta fara biye-biyen ƴan duba wanda suka tabbatar mata da cewa in dai Barira na raye to gidan Umaru bata da matsuguni. Wannan abu shi ya ƙara tunzura Zaliha saboda haka ta nemi Aminiyar ta Larai suka nufi gurin boka don cimma manufar su ko ta yaya ne. Abu mafi muni bayan boka ya maimaita mata irin abun da ƴan duba suka faɗa mata sannan yace matsawar tana son auren nan to sai an kashe Barira, Ba tare da ta damu ba kuwa ta sanar da BOKA shawarar da ta yanke. Bayan Boka ya sallame su suka nufi gida zuciyar su cike da ɗumbin farin ciki. Sati guda da faruwar wannan al'amari kwatsam Barira ta fara jinya, lokaci ƙanƙani jinya tayi tsanani bata iya gane komai sai dai a tayar a kwantar, ana cikin wannan yanayi kuma Mallam Umaru yazo da al'amarin son auren Zaliha. Kowa abun ya bashi mamaki sai dai babu yadda suka iya saboda haka kowa ya kawar da kanshi ya zubawa sarautar Ubangiji ido. Iya tayi matuƙar baƙin ciki da hakan, saboda irin halin ko in kula da Mallam Umaru ke nunawa akan jinyar Barira yasa Iya ɗauke ta ita da ɗiyar ta ta kawo su gaban ta tana jinyarta. Rayuwa kenan, kullu nafsin za'iƙatul maut...wata rana Allah ya karɓi ran Barira. Iya tayi kuka kamar ba gobe haka dangi sun ji mutuwar ta kasancewar ta mace mai sanyin hali da ƙaunar jama'a. Sati guda cif da rasuwar Barira Mallam Umaru ya auro Zahiha wacce yake jin ta kamar sarauniya a birnin zuciyarsa. Daga nan komai ya fara sauyawa. Ɓangaren Aishatu ɗiyar Barira Allah ya raya ta sai dai tun lokacin da ta fara zama ta soma addabar iya da ɓarna. Idan zanin shimfiɗa aka shimfiɗa a gado to in Sha Allah sai ta yaga shi fata-fata da hannun ta. Basu ɗauki abun da muhimmanci ba kawai sun ɗauke shi ne matsayin ƙiriniya, ana haka yarinya ta fara rarrafe sai abu yaci gaba, idan girki aka ɗaura to zata je ta tunkuɗar da shi ba tare da jin wahalar hakan ba, babban abun mamaki kuwa shine yadda wuta bata kama yarinyar duk irin wasan da zata yi da ita. A wasu lokuta kuwa ta kan rarrafa jikin buhuhunan hatsi da aka tanada don ci ta ɓula ƙasan su ba jimawa buhun zai yoye haka sai anyi sabo. Wannan abu ba ƙaramin mamaki yake bawa Baffi da Iya ba saboda ɓarnar ta wuce hankali da tunani amma basu taɓa sanar da wani na waje ba. Kwanci tashi babu wuya a wurin Allah, Aishatu ta fara tafiya, tunda ta fara takawa kuma zaman gida ya zama ba nata ba, ɓangaren ɓarna kuwa sai abun da yayi gaba ammah tafi so ta fita gidan maƙota sam bata son zaman gida. Hakan kuma na da alaƙa da Baffi saboda bata iya yi mishi musu in yace abu. Idan Aishatu ta fita maƙwabta babu abun da take sai ɓarna, tun suna shiru har abun ya fara isar su suka fara kai ƙarar ta. Iya da a lokacin ke daure mata gindi sai tace sharri akayi wa ɗiyar ta , hakan ne yasa jama'ar gari suka kafa ƙahon zuƙa kan Ƴar Iya bayan tattarawar sirri da suka yi. Sun riga sun yanke hukuncin hukunta Ƴar Iya a duk lokacin da ta musu ba dai-dai ba sai dai abun da basu sani ba tafi ƙarfin su baki ɗaya. Wata rana lokacin Ƴar Iya bata wuce shekaru shida ba a haife, ta fita yawon ta da ta saba ne kwatsam ta bi ta layin wani marowacin mutumi. Dai-dai zuwan ta ƙofar gidan mutumin ya fito da langar sa cike da waina. Tunda taga wainar nan kuwa hankalin ta ya tashi, hakan yasa tabi bayan mutumin ko ɗaya ya bata. Bayan ya zauna a shimfiɗar tabarma irin ta kaba ɗin nan ta iso, ido ta zuba mishi amma abun ka da marowaci bai gane ba. Ganin bashi da niyyar bata yasa ta faki idon sa ta jawo langar ai kuwa ta arta a na kare yayin da take cin Masar shi kuma mutumin bai daina bin ta ba. Sai da ta cinye tsaf ta daina wanda mutumin gashi abun tausayi ya jigata, ganin hakan yasa ta wulla masa langar ai kuwa rasss sai a kanshi. Tuni ya fashe jini sai zuba yake. Da ƙyar aka tsayar da jinin a chemist tukunna ya dawo. Wannan dalilin ne yasa mutumin harzuƙa har ya yanke hukuncin kai ƙara fadar Arɗo. Bayan ya faɗawa Arɗo abun da ya faru ne sai Arɗo ya aika a ƙira masa Baffi. Kamar ta sani kuwa lokacin suna zaune a tabarma ta tasa tukunyar ɗumamen safe a gaba sai ci take kamar jaka, ana sallama kuwa ta fita akace tace ana sallama da mai gidan a fada.... Tana isarwa Baffi saƙo ta shiga bukkar Iya, bata jima ba ta fito still hannun ta kwaɓe da ɓakar miyar kuka da ta shafe ko ina na jikin hannun. Baffi na fita bai tsaya ko ina ba sai a fada, mutanen da ya gani maƙil a fadar ne yasa ya shiga tashin hankali na wani lokaci, lokaci guda da ya tuna da jikar sa Ƴar Iya nan ya gano hala ta aikata wani laifin ne. Bayan gaisuwa irin ta mutunci da suka yi da Mai martaba kamar kullum. Mai martaba yayi gyaran murya yace: “Toh Mallam Musa tunda Allah yayi ka iso da wuri kai tsaye zamu fara abun da ya tara mu” Cikin sanyin jiki Baffi ya kaɗa kai. “Toh Malam Musa, kamar yadda kaga na aika a ƙira ka ba wani abu bane ya faru sai wannan abun da JIKAR ka ta wajen Iya ta aikata” Yana kai nan ya tsaya tare da yiwa dogarai alamar su shigo da mutumin nan. Baki buɗe Baffi ke kallon sa don kuwa abokin sa ne Ishiyaku. Ganin kansa ɗaure da bandage da kuma plaster yasa Baffi maida hankali don jin me Arɗo zai ce. “Toh Mallam Musa, kamar yadda kaga Mallam Ishiyaku kansa naɗe da kayan ciwo, ba komai ne ya faru da shi ba sai karon da suka yi da jikar ka wacce ta kusa hallaka shi bayan sace masa waina a daro da tayi” Kasa magana ma Baffi yayi yayinda kunya tabi ta lulluɓe shi, tuni ya sunkuyar da kan sa ƙasa. Mai martaba ya ƙara gyaran murya yace “Mallam Musa muna sauraron ka, kayi shiru” Cikin ƙarfin hali da takaici Baffi yace “Don Allah Mai martaba ayi wa Ƴar Iya haƙuri in Sha Allah in na koma gida Zan hukunta ta, yaran yanzu ne ka haifa baka haifi halin su ba, don Allah ayi mata afuwa. Tuni mutanen wurin suka kaure da hayaniya wani yana faɗin “Wallahi ba zata saɓu ba, ko dai a ɗauko yarinyar nan a hukunta ta ko kuma wallahi mu bi har gida mu nakasa ta.” yayin da wasu ke ganin hakan ba dai-dai bane. Wani Matashi ɗan azagwai ne ya miƙe yace: “Wallahi ko yanzu a zo a hukunta ta ko mu mu hukunta ta, yarinya ƙarama duk ta addabi jama'a, Aradu Arɗo in ba'a hukunta taba toh mu zamu bi mu hukunta ta” Tsawa Arɗo ya buga nan da nan aka yi shiru ana sauraron sa. “Toh mun ji ƙorafi daga wurin mahaifin mai laifi, Mallam Ishiyaku ya kake ganin za'a yi? Ka haƙura ko kuma sai an ɗauko yarinyar?” Na gefen shi ne ya zuga shi hakan yasa yace sai dai a ƙira yarinyar. Arɗo yace “Shikenan ammah miye hukuncin yarinyar?” Hayaniya ta kacame wasu na faɗin a biya kuɗin raunin da tayi kuma a bata aikin noma da yiwa matan Arɗo aike sannan kullum ayi mata bulala uku da safe. Wasu masu tausayin kuma cewa suke ayi mata haƙuri yarinya ce...cikin zafafan mutanen ne wani ya kalli mai cewa ayi haƙuri yarinya ce yace “Kutumar uba, toh wallahi yarinyar nan tafi mahaukacin kare haɗari” Ganin ba zasu yi shiru ba kuma sun tayar da rigima ne Arɗo ya daka tsawa kafin yai gyaran murya. “Ya isa haka” ya faɗa yana mayar da kallon sa kan Baffi. “Toh Mallam Musa, kai yanzu me kake ganin za'a yi?” Bai kai ga bada amsa ba suka ji Muryar yarinya ƙarama wacce bakin ta ma bai gama fita ba tace “Toh ai ba shi yayi laifin ba nice” Shiru ne ya wanzu yayin da kowa kallon sa ya koma kan Ƴar Iya da ta tsaya a gaban su ƙyam ko tsoro babu a tattare da ita, nan da nan wasu suka sha jinin jikin su yayin da wasu kuma suke miƙewa tare da yunƙurin kamo ta.... Mu haɗu gobe don jin cigaban yarintar Ƴar Iya! Ko kuna tunanin zata bari su hukunta ta kamar yadda suke ikirarin hakan? Duk AMSOSHIN ku na jiran ku, sai mun haɗu. Ku yi sharing sannan kuyi comments.🥰 *DIAMOND BHATOOL ce!* [4/27, 5:57 PM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘‘7&8’’’’’ Shiru ne ya wanzu yayin da kowa kallon sa ya koma kan Ƴar Iya da ta tsaya a gaban su ƙyam ko tsoro babu a tattare da ita, nan da nan wasu suka sha jinin jikin su yayin da wasu kuma suke miƙewa tare da yunƙurin kamo ta.... Kan uba, yadda zaratan matasa da magidanta ke yunƙurin kawo ma ƙaramar yarinya hari ammah ko gizau bata yi ba yasa masu hankali daga cikin su faɗawa duniyar mamaki.. Sai da taga rabin su sun yo kanta ta zaro silifas ɗin ta guda biyu ta fara buga musu ɗaya bayan ɗaya. Duk wanda aka bugawa sai kaga ya ja baya ya koma gefe yana shafa kansa, ganin suna watsewa yasa ta gyara tsayuwar ta tana kallon yadda jini ke ɓulɓulowa daga kawunan su wanda hakan ba ƙaramin burge ta yayi ba. “Hhhhhhh....dama na faɗa muku ai, shegu manyan banja kawai ku a dole jaku ci jalin yalinya kalama ko?, Toh in kun faca” ta ƙarasa tana sakin dariyar mugunta. Ba tare da ɓata lokaci ba suka fara zamewa ɗaya bayan ɗaya suna wucewa gida saboda jinin da yake zubowa. Shi kanshi Arɗo ya tsorata da lamarin wannan yarinya, an daɗe ana kawo ƙarar ta yakan ce suyi haƙuri yarinya ce ammah yau ta riga ta goge masa hadda. Idanuwan Ƴar Iya dake yawo kan Arɗo da Baffi da su kaɗai suka rage don tuni dogarai ma suka cika bujen su da iska. “Baffi ka tashi mu tafi Iya na can tana jiran ka, kai ma Alɗo kana biye wa makalyatan mutanen nan sai na maka naka” ta faɗa tana kallon Baffi. Da ido Arɗo yayi wa Baffi izinin tafiya don ya sare da al'amarin wannan aljanar yarinya. Bayan sun yi ƴar tafiya Baffi ya ɗan dakata yana Kallo Jikar tashi. Ganin ya tsaya yasa ta juyo tana kallon shi. “Baffi mu tafi manah” “A'ah Ƴar Iyan ta sai kin faɗa min me kika yiwa Shayibu kuma da me kika jiwa mutane ciwo” Dariyar da ta ɗaurewa Baffi kai Ƴar Iya tayi sannan ta maida kallon ta kanshi. Nan ta bashi labarin abun da ya haɗa ta da Ishiyaku, nan Baffi yayi mata faɗa sanann yace. “Toh da me kika ji musu ciwo kuma” A hankali ta ciro silifas ɗin ta daga ƙafar ta ta nuna mishi ƙasan su. Wasu Allurai ne a cake sun fi hamsin a cikin kowanne. Abun ya ɗaurewa Baffi kai ganin irin waɗannan allurai a ƙasan takalmin kuma abun mamaki takalmin na ƙafarta ammah ita basu cake ta ba in fact ko leƙowa basu yi ba. A haka suka wuce gida zuciyar Baffi babu daɗi ga kuma abun da ya ajiye a ranshi na gano dalilin wanann ɗabi'u na Jikar tashi. Bayan sun je gida bai faɗawa Iya komai ba ammah ya ƙuduri aniyar bincike akan jikar ta sa, haka ranar dai sukuku Baffi yayi ta har dare. Nan tunani ya hana shi sukuni ƙarshe ya fice daga bukkar. Wuri ya samu yana tunanin mafita ga Ƴar Iya daga ƙarshe ya yanke shawar fara ɗaura mata karatun Alqur'ani tunda shi Qur'ani haske ne kuma waraka ga kowacce jinya. Washegari kuwa Baffi yayi ɗamarar koyar da Ƴar Iya. Bayan gari ya waye ya ƙwalla kiran ta daga bukkar shi jin shiru yasa ya ƙwalla kiran Iya. A nan take sanar da shi Ƴar Iya ta fice sassafe. Cike da takaici ya koma ya kwanta, sai wajajen Azahar Ƴar Iya ta dawo saboda yunwar da ta koro ta, abincin da yarinyar ke ci kuwa ko samari masu aikin noma biyu iyaka. Bayan taci abinci Baffi ya tsayar ta ya fara mata karatu sai dai abun haushi ko bismillah ta kasa haddacewa. Haka Baffi yayi ta ɗawainiya da ita don ganin ta koyi karatu ammah ina ƙwaƙwalwar bata ja, babu abun da ta iya sai neman tsokala. Kullum cikin addabar mutane take, yau itace wannnan gobe wannan, yau ta illata wannan gobe ta illata wannan gashi babu damar hukunta ta don kuwa duk ƙauyen Gallara da kewaye babu wanda baya shayin Ƴar Iya. Hakan ne ya bata damar tsula tsiyar ta son ranta ita da shaƙiƙiyar ta A'i wacce gidan su ke ɗan gaba da gidan su Ƴar Iya. A'i ma dai ba baya ba wajen rashin ji shiyasa Ƴar Iya ta zaɓe ta don ta kasance ƙawa gare ta, tare suke fita ko ina da A'i, idan tsokala ne tare idan damfara da ƙwace ne ma dai tare suke yi. Iyayen A'i kan su shakkar waɗannan ƴan barandar ƴaƴan nasu suke yi kullum fatan su bai wuce Allah ya shirye su ba. Tunda ya fahimci akwai ɓoyayyen al'amari dangane da Ƴar Iya ya ɗan samu sauƙi, addu'ar sa kullum Allah ya shirye ta. Ana cikin haka lokacin Ƴar Iya ta ƙara girma, shekarun ta sun kai Tara lokacin. Wata rana wani mai magani ya zo ƙauyen Gallara, bayan ya samu karɓuwa wurin Arɗo aka bashi wurin zama nan ya kafa amsa ƙuwwar sa (Loudspeaker) ya fara talla r maganin sa. Inna Zaliha ne ta jiyo bayanin da Mai maganin yake yi ai kuwa ta saka Malam Umaru gaba kan ya kai Ƴar Iya tunda su ma bata ƙyale ba in ƴan ɓarnar ta suka motsa takan je ta yanka masa kaji ko agwagi ko kuma zabin da yake kiwo, wasu lokutan har akuya takan ja ta gudu da ita zuwa mahauta.....😀 Babu yadda suka iya dole su yanka ta kai Iyar ta ta soya ko ta musu farfesu wanda kaso tamanin na naman Ƴar Iya ke cinyewa. Shawarar Inna Zaliha ya ɗauka ai kuwa Yaje har gidan Iya ya kamo hannun Ƴar Iya tare da mata wayon zata raka shi birni ne. Bayan sun isa mai magani ya fara ƴan dube-duben shi irin na ƴan tsibbu, can ya fuskanci Malam Umaru yana faɗin “Lallai wannan yarinyar taka ba mutum nace, hannun ta bana mutane bane kuma bazata taɓa bari a zauna lafiya a wuri ba matsawar tana nan.” Bayan Mallam Umaru ya buƙaci maslaha ga batun Ƴar Iya mai maganin yace. “Maslaha ɗaya ita ce ku ɗauke ta ku mayar da ita wurin Ƴan uwanta aljanu ko kuma ku kawo ta gobe a yanke hannun ta” Ba tare da yayi shawara da Iya ba washegari ya ɗauko ƴar Iya da niyyar a maida ta can wurin ƴan uwan ta sheɗanu idan hakan bai yi aiki ba sai ya kawo ta a cire hannun kowa ya huta. (Nace ku jiye mun mutumin nan wai kowa ya huta, sai kace ya damu da rayuwar yarinyar ko yana hidimta mata). Bayan sun je Mai magani yayi surkullen shi sannan ya ɗauko wani makeken ganye wanda ya kai girman bargo duniyar kule guda biyu, wata garin magani ya watsawa Ƴar Iya ai kuwa lokaci ɗaya ta faɗi yashe kamar gawa. Duk wannan Shagalin da ake yi Iya da Baffi basu da masaniya haka mutanen gari basu sani ba ai da tuni sun fara haɗa ƴar ƙwar-ƙwaryan shagali na rabuwa da annoba. Bayan wani lokacin Mai maganin ya ɗauko wannan ganye ya ware shi sannan ya ɗaga Ƴar Iya ya jefa ciki ya naɗe abun kamar ƙuƙulen cabbage. Bayan ya gama wannan aiki ya ɗauko wani ruwa ya watsa mata daga nan ya umarci Malam Umaru da ya wuce da ita kai tsaye bakin kogi. Bai Musa ba kuwa ya ɗauki wannan ƙulƙule raf ya tafi da shi kogin da yake kusa da su kaɗan wanda yake cikin garin Zubo. A bakin ruwan ya ajiye ƙulƙulen abun ya juyo gida hankalin sa kwance don ya gamawa gimbiyar sa aikin ta. (Nace zaka sani idan aikin bai daidaitu ba ta dawo gida don nasan ba zata ƙyale ka ba). Bayan ya koma ya sanar da Inna Zaliha duk abinda ya faru da kuma maida Ƴar Iya ga ƴan uwanta shaiɗanu da yayi. Tuni farin ciki ya kewaye birnin zuciyar ta. Bayan ya fita bata tsaya wata-wata ba ta nemo Larai saboda ta sanar da ita abun da ke faruwa. Nan suka fara murna saboda su kaɗai suka san dalilin da yasa suke son ɗauke Ƴar Iya a kusa da su bayan jawabin da bokan su yayi musu. Can cikin gari kuwa shiru basu ga giftawar halittar da suke wa take da annobar su ba kusan ko ina ka wuce in dai daba ce walau ta maza ko mata zaka ji suna jajen Ƴar Iya yau basu ga wulgawar ta ba. Akace ko yaya wata alaƙa ta gifta tsakanin wasu zukata walau so ko ƙi toh duk ranar da wani sashi ya samu matsala ɗayan sashin dole ya ji abun a zuciyar shi.. Irin haka ce ta faru da mutanen garin Gallara, ta ko ina ka wulga zancen kawai ake yi, wasu har sun yanke shawarar zuwa dubo Ƴar Iya ko lafiya. Ɓangaren Iya ma da tun ficewar Ƴar shalelen ta bata ƙara ganin ta shigo gidan ba bayan kuma ta saba da in sun kewaya sun kewaya toh sai sun leƙo gidan Iya ko don cin abinci ma ammah yau shiru har Yamma tayi. Wannan dalilin ne yasa Iya zaro zanin yafawar ta ta fito cikin gari don neman shalelen ta. Yawo sosai tayi amma bata ga ko alamar ta ba, gidan su A'i ma da taje A'i cewa tayi yau Ƴar Iya bata zo ba da yake dama mafi yawancin lokaci ita ke bi takan A'i sai su wuce gantalin su. Nan da nan hankalin Iya ya tashi ta fara bin kowacce daba tana tambaya sai dai amsa ɗaya suke bata “Muma yau jajen ta muke bata leƙo mana ba”. Tun Iya na ɗaurewa har ta fara sheƙa kuka abun tausayi, Baffi da ƙyar ya shawo kanta ta haƙura yana ce mata “Ai zata dawo in dai shalelen ki ce, kin santa da rigima da shegen yawo wataƙila tana nan ƙauyukan maƙwabta kuma zata dawo ai ko dan saboda ke” Da haka dai Iya tayi shiru ba don ta yadda da jawabin Baffi ba. ★★★★★★★★★★★ Ɓangaren Ƴar Iya tunda Mai magani ya fara karanta wannan dalasimai shikenan taji an ɗauke ta gaba ɗaya, bayan Baffi ya kai ta bakin ruwa ya koma abun sa can bayan sallar Ishã wata tsohuwa ta biyo ta wajen don ta ciri alayyahu a lambun dake kusa da ruwan. Tunda ta hango abun ai kuwa ta isa don ganin menene wannan a bakin ruwa. Sai da ta duba sosai ta gano ganyen da ake naɗe ƴaƴan shaiɗanu ne idan za'a mayar da su. Toh idan hakaneh me yasa har yanzu basu ɗauke ta ba?, Lallai wannan mutum ce, saboda haka ta je ta buɗe ta bata tsaya ko ina da ita ba sai gidan ta. A nan ta jiƙa jiƙe-jiƙen ta ta ɗurawa Ƴar Iya ba jimawa kuwa ta dawo hayyacin ta. Duk yadda tsohuwa taso Ƴar Iya ta zauna taƙi a daren kuwa ta koma sai gidan Iya, bata kula kowa ba ta wuce bukkar ta washegari kuwa ta shiga gari don ci gaba da halin. Bayan kwanaki biyu da faruwar hakan Mallam Umaru ya ganta cikin gari, bai yi ƙasa a guiwa ba ya sanar da Inna Zaliha nan tasa shi gaba wai ya faɗawa mai maganin. Bayan ya faɗa masa yace gobe ga zo da ita a yanke hannun sai kowa ya huta. Washegari kuwa hakan ta faru da ƙyar Ƴar Iya ta bi shi ba tare da ta masa jayayya ba hakan kuma yana alaƙa ne da surkullen da mai maganin yayi mata daga nan inda yake. Tunda suka nufi hanyar ƴar Iya ke turjewa alamun bata so ammah saboda Inna Zaliha ce ta bashi aikin ai dole ya kai ta. Bayan sun isa mai magani ya fara haɗa kayan aiki. Wata sharɓeɓiyar wuƙa da yayi wa laƙabi da wuƙar shaiɗanu na gefen sa. Zaunar da Ƴar Iya aka yi a tsakiyar wata shimfiɗa daga nan ya fara karanta wasu dalasimai wanda nake kyautata zaton na tsafi ne. Cike da rashin imani Mai magani ya dubi wuƙar sannan ya karanta wani abu, da kanta wuƙar ta taso ta taho sai hannun sa. Bayan wuƙar ta dawo hannun Mai magani ya karkato ta yana mai riƙe hannun Ƴar Iya na dama. Ya ɗaga kenan zai buga mata....... TOH FAH, ANA WATA GA WATA! ƳAR IYA FANS KUNJI ME BABAN ƳAR IYA YA AIKATA MATA? GASHI KUMA ZA'A YANKE HANNUN ƁARNA! KO HAKAN ZAI FARU? ITA KUMA INNA ZALIHA KO MEYEH ƘUDIRIN TA? *Just follow Diamond Lady's pen and find out* COMMENT &SHARE FISABILILLAH. MU HAƊU GOBE DA SAFE, AMMA SAI NAGA YAWAN COMMENTS, INA NUFIN SHARHI FAH! IN BA HAKA BA KUWA SAI JIBI TUNDA YAU UPDATE UKU NAYI MUKU. NA GODE FANS NA INA MATUKAR SON KU DA YAWA ƊIN NAN!!! [4/27, 6:03 PM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘‘9&10’’’’’ Bayan wuƙar ta dawo hannun Mai magani ya karkato ta yana mai riƙe hannun Ƴar Iya na dama. Ya ɗaga kenan zai sara mata wani mahaukacin ƙarfi ya zo wa Ƴar Iya, a lokacin kuwa tayi wa wannan wuƙar wata irin wawura, cikin ƙanƙanin lokaci tayi nasarar amshe wuƙar daga hannun shi. Kamar mayunwacin zaki haka Ƴar Iya tayi kan Mai Maganin, duk iya ƙoƙarin shi na ƙwacewa abun yaci tura, ƙarshe cike da rashin tsoro Ƴar Iya ta datse hannun Mai Maganin, bata bar shi haka ba ta fara shata masa fuskar shi da wuƙar...wasu dogayen Bille marasa kan gado ta shata daga nan ta juyo tuni Mallam Umaru ya sa ta tunda yaga ta amshe wuƙar. Wannan zance kuwa tuni ya bazu cikin Gallara da kewaye, Ƴar Iya ta yanke wa wannan Mai Maganin hannu har da guzurin bille ai kuwa girma da tsoron Ƴar Iya ya hauhawa a idon mutane, kowa kaffa-kaffa yake da ita. Tun daga ranar Ƴar Iya ta samu salama daga wurin Mallam Umaru, shegantaka irin tata kuwa sai abun da ya ƙaru, idan nama take son ci sai ta wuce can gidan tsohon ta ta yanko zabi biyu ko uku...... *_CI GABAN LABARI_* *(BACK TO STORY)* Ƴar Iya ne da A'i ke tafiya cikin gari suna ƴan waƙe-waƙen su na yara. Suna cikin tafiya suka hango wani mai rake. “Mai rakeeee” Ƴar Iya ta ƙwala mishi ƙira, jin Muryar ta yasa ya fara tura kurar taken sa da sauri saboda ya tsere mata. Ba tare da sun ƙara mishi magana ba suka ɗora bayan shi da gudu. Bayan sun isa Ƴar Iya ta tare gaban kurar tana bin shi da mugun kallon, shi kuwa mai take ya sunkuyar da kan shi ƙasa zuciyar sa na bugawa. “Kai uban wa ka fi da Ƴar Iya ke ƙwala maka ƙira shine zaka gudu” A'i ta faɗa tana bangaje shi. Idanuwan mai rake tuni suka raina fata saboda irin kallon da Ƴar Iya ke aika mishi, tsoron sa ma bai san wacce irin mugunta zata ƙunduma mishi ba. “Hhhhhh...” dariya ta kwashe da ita sannan ta maida kallon ta ga mai rake da ya gagara ko da bada haƙuri ne. “Baka ji me ƙawa ta tace bane?” ta aika mishi da tambaya. Cikin ƙiƙina mai raken yace: “Ranki....shi... daɗe kiyi.....haƙuri....ban..ban san ke bace ai da...zan..tsaya” Dariya suka kwashe da ita a tare ita da A'i lokaci ɗaya kuma ta ɓata ran ta. “Ƴar Iya bata yafiya kuma bata haƙuri, saboda haka yanzu ba anjima ba sai ka shanye raken nan tasss” Ƙwalalo idanuwan shi yayi yana tunanin ta ina zai iya shanye kura guda na rake ai kuwa taji muryar A'i na faɗin: “Wallahi yanzu zaka shanye Bismillah, shege marowaci tunda rowa ne yanzu shanye abunka” Babu yadda mai raken ya iya haka ya fara gaftarar raken yana sha har cikin sa ya cika ya ɗan dakata. Ganin ya tsaya yasa Ƴar Iya daka mishi tsawa “Aradu yau sai ka shanye wannan raken tunda ka min rowa a kan shi” Babu yadda ya iya tun yana sha a matsayin ƙari har ya fara kuka yana roƙon su da suyi haƙuri bazai ƙara ba ammah inaaaah sai da suka tabbatar ya jigata kuma sun san raken yayi mishi yawa tukunna suka sallame shi. Basu tsaya ko ina ba suka yi cikin kasuwa. Ba tare da sun kula kowa ba suke tafiyar su suna haɗawa da ƴar waƙar su. Ganin yunwa ta fara addabar su yasa Ƴar Iya yanke hukuncin nema musu abun da zasu rage zafi da shi. ★★★★★★★★★★★★ Convoy na motocin sojojin da zasu kai goma ne suka shararo titin yayin da wata expensive white mota ƙirar Zenvo ST1 ta kasance tsakiyar su. Dai-dai Murtala Mohammed International Airport dake Lagos State suka ja can gefe suka yi parking. Ganin har lokacin Flight ɗin da Shugaban nasu ya biyo bai yi landing ba yasa wasu daga cikin sojojin fitowa daga cikin nasu motocin. At exactly 11:00am flight ɗin yayi landing . Few minutes bayan sauƙar jirgin sojojin nan suka dawo kusa-kusa so that their master will recognize their presence. Ƙafarsa da ke sanye da Black luxury covershoe ya fara zirowa bisa steps ɗin. A hankali yake takowa yayin da idanuwan mutane duk ya koma kan shi. (Nimah Bhatool nace bari na ɗaukowa fans ɗina report). Sanye yake cikin wasu expensive brand na Armani. White T-SHIRT ce wacce tsabar farin ta har wani ɗaukar ido take yi, sai Black three-quarter jeans da ya bayyana daga guiwar sa zuwa idanuwan sawun shi. Bai cika tsayi sosai ba sai dai yana da ƙira mai kyau wacce ke nuna zallar mazantaka da kuma jarumta...irin wannan physique nashi ake kira da *athletes* Fari ne tass kamar madara, da ganin skin nashi zaka san hutu da jin daɗi ya zauna jiki, uwa uba yadda fatar tashi ke wani glowing tamkar wani tauraro. Yana da idanuwa manya manya wanda suke farare tas sai kuma ƙwayar idon shi da ta kasance brown. Colour na ƙwayar idon ne ya sa idon nashi ke ruɗan mata ga kuma eyebrows nashi masu yalwatuwar baƙin gashi. Yana da siririn hanci da bai fiye faɗi ba sai kuma ɗan madaidaicin baki mai ɗauke da thick pinkish lips. Sajen da ya kewaye fuskar shi kamar wadda aka zana shi ba ƙaramin ƙarawa fuskar shi kyau da kamala yayi ba. Kan sa bai fiye girma ba ga kuma wata Black shiny suma da ta cika kan wanda ta sha wani haɗaɗɗen hairstyle da yasa na kusa sumewa. (“Masha Allah, Tabarakallahu Ahsanul Khaliqiin”, abunda na iya furta wa kenan). Ganin yana shirin sauƙowa yasa wasu daga cikin sojojin matsowa kusa da shi suna sara mishi yayin da ya ƙara haɗe fuskar shi tamau ya fara tahowa. Amsar Briefcase dake hannun shi ɗaya daga cikin sojojin yayi wasu kuma suka take mishi baya har zuwa cikin wannan white Zenvo ST1 ɗin. Shigar shi kuma yayi dai-dai da sanya trolley nashi a Boot da ɗaya daga cikin sojojin yayi. Basu tsaya ɓata lokaci ba suka tayar da motocin yayin da jiniya kaɗai ke tashi kan titin. Sun yi tafiya sosai kafin su iso wani katafaren unguwa wacce naga an mata alama da “BANANA ISLAND... Billionaires' paradise”. *LAGOS STATE* *BANANA ISLAND* Banana Island da ake wa take da billionaires 'paradise yanki ne cikin Lagos, yankin da in ka shiga zaka iya manta cewa bauta Ubangiji ya turo ka nan duniya, yankin da ba kowanne mahaluki ke iya samun matsuguni a ciki ba. Yankin da ya tara manya-manyan masu kuɗi dake a faɗin Nigeria. Sun yi tafiya mai ɗan nisa kafin suyi horn a dai-dai wani big and luxurious mansion, tuni gateman ya buɗe zirrrrrrr convoy ɗin ya wuce ciki. Dai-dai parking space suka yi parking, sojan da ke tare da wannan kyakkyawan guy ɗin ya buɗe mishi ƙofar matar, bayan ya fito wasu daga cikin sojojin wanda nake kyautata zaton sune Guards nashi suka biyo bayan shi. Dai-dai ƙofar da zata sada ka da cikin mansion ɗin ya ɗaga musu hannu, tuni suka juya suka bar ɗaya wanda ke riƙe da Briefcase nashi da kuma trolley. Da hannu yayi mishi alamar ya miƙa Briefcase ɗin sannan ya nuna trolley ɗin, babu ɓata lokaci shima ya koma wajen sauran sojojin yayin da motoci biyu suka fice sauran kuma suka fito, wasu na tsaye bakin gate wasu kuma suka kama wurare daban-daban suka ƙame. Riƙe da Briefcase a hannun shi na dama wanda ke sanye da wristwatch ƙirar Amelia Erhats sai left hand ɗin shi da ke janye da trolley ɗin. Tsam ya aje trolleyn ya danna password na entrance door na mansion ɗin. Janye da trolleyn ya shiga ciki (nimah na bishi don ɗauko wa fans na report). Masha Allah! Wani makeken haɗaɗɗen parlour da nayi arba da shi sai da zuciya ta ta yanke, babu abun da ke tashi a parlourn sai wani sassanyar ƙamshi mai kwantar da zuciyar mai shaƙar sa, haɗaɗɗun kujerun dake ciki wanda aka yi L-Shape arrangement da su white color ne, kallo ɗaya zaka musu ka fahimci Naira tayi kuka, da yake ɗakin akwai duhu sai da ya janyo remote na light ɗin tare da switching nashi on, nan da nan haske ya gauraye, sai a yanzu na fahimci ashe komai na parlourn white colour ne kama daga kujerun, Centre table, curtains har zuwa paint na parlourn. Tsaf-tsaf Kamar dai akwai mai rayuwa a ciki haka parlourn yake haka makeken plasma dake manne jikin wall na ɗakin babu ko alamar ƙura ajiki. Jikin wall na ɗakin kuwa frames ne masu ɗauke da pictures iri-iri. By the side kuma wani keɓaɓɓen waje ne da nake kyautata zaton dining area ne. Ban bi wurin ba ganin ya wuce ta wani corridor Wanda zai sada ka da staircaae na gida, a nutse yake takawa kamar ba zai wuce ba har ya iso saman, wani irin tsari da wurin ke da shi ba'a magana, ta wurin da muka bi dai 2bedrooms ne yayin da guy ɗin ya shiga first one. A nan na ƙara tabbatar da cewa favourite colour nashi is white duba da yadda komai na ciki yake fari tas including the furnitures. Bisa makeken bed ɗin dake shimfiɗe da white bedsheet ga kuma white blanket jikin pillow ɗin da ke sanye da white colored pillow cases ya ajiye Briefcase nashi yayin da yaja trolleyn kusa da white closet dake gefe. Bai tsaya ba yayi undressing kayan da ke jikin shi, ya bar iya wani Black boxers sannan ya nufi wata ƙofa da nake kyautata zaton toilet ne. Sai da ya shafe fiye da mintuna 35 kafin ya fito ɗaure da white towel a ƙugun shi yayin da yake drying sumar shi da ta jiƙe da ruwa ta samu damar kwanciya lufff. A gaban dressing mirror dake ɗauke da creams, perfumes, jail, and others jere ya zauna, sai da yayi drying sumar shi da hand dryer kafin ya fara shafa mayukan wurin ɗaya bayan ɗaya. (Haba dole skin nashi yayi glowing irin wanga provision duk na fata haka😂). Yana gama shafa mayukan ya miƙe ya nufi closet ɗin shi, wata white jallabiya ya janyo daga jikin hanger sannan ya sanya ta daga nan ya fara fesa perfumes dake jere gaban dressing mirror ɗin, nan da nan wani sassanyar ƙamshi mai tsuma zuciya ya gauraye ɗakin. (Ni kuwa nace waɗannan perfumes Bamu da su a nan Nigeria wataƙila daga wani wajen ya zo da su). Bayan ya gama kimtsawa tukun ya samu damar zama a bedside tare da janyo Briefcase nashi, phones biyu naga ya ciro daga ciki, ɗaya ƙirar Samsung Galaxy S24 ultra sai kuma wata Nokia brand phone. Zaro da laptop ɗin shi ƙirar Luvaglio wacce tunda nake ban taɓa ganin irinta ba. Briefcase ɗin ya ajiye a sidedrawer dake ɗakin sannan ya haye makeken bed ɗin shi. Nokia phone ɗin ya ɗauko tare da dialling wata number, ana picking call ɗin yace: “Assalamu Alaikum” cikin wata murya da na gagara gane larabci ne ko turanci ko dai wani Yaren na daban sai dai cikin zuciya ta yaba wanna murya mai daɗin sauraro nake. Banji meh aka ce a ɗaya ɓangaren ba can yayi murmushi wanda ya ƙara ƙawata kyakkyawar fuskar shi. “Barka da rana Mom” “Eh ban jima da isowa ba, yea, I'll be there tomorrow morning in Sha Allah.... can't wait to see u Mom.... alright don't forget to prepare my favorite please....ohk bye Mom I love u” ya ƙarasa yana sakin kiss 😘 ta wayar sannan yayi hanging call ɗin. (Ni Bhatool mamaki ya hana ni magana jin harshen Hausa a bakin wannan haɗaɗɗen guy Wanda Sam bai yi kama da Nigerians ba) Phone nashi ƙirar Samsung ya janyo bayan ya latsa ta na tsawon five minutes ya ajiye ta kusa da Nokia ɗin tare da janyo Laptop ɗin shi. GODIYA TA MUSAMMAN GARE KU ƳAN UWA NA ABABEN ƘAUNA TA DA KUKE ƘARFAFA MIN GUIWA A KOWANE LOKACI.....Seemah and Shaheeda! ALLAH YA ƘARAWA RAYUWAR KU ALBARKA. FANS ƊINA NA LITTAFIN ƳAR IYA KUMA GODIYA TA MUSAMMAN A GARE KU MUSAMMAN MASU BIBIYA TA DA KUMA ZABGA MIN COMMENTS HAR DA MASU TAYA NI SHARING....ALLAH YA BAR ƘAUNA.... KU CI GABA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY (GARKUWAR NAZARI WRITERS). PLEASE COMMENT & SHARE. [4/28, 8:18 AM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘‘11&12’’’’' Danne-danne ya fara almost 24minutes kafin ya aje laptop ɗin tare da phones ɗin shi. Ƙaramar wayar shi da tayi ringing yayi picking tare da kara ta a kunnen shi. Ban san me aka ce ba a ɗaya ɓangaren can guy ɗin yace “Alright, I'll be there now" Daga haka yayi hanging call ɗin. A hankali ya ziro kyawawan ƙafafun shi ƙasa tare da sanya takalmin dake bedside ɗin. Sauƙa downstairs yayi tare da buɗe door. Wani soja ne ya miƙo mishi manya-manyan leathers ɗin da alamau yayi order ne and it seems like abinci ne. Kallon sojan yayi tare da faɗin “Let me have one, the remaining is yours” Kamar yadda ya umarta haka ya miƙa mishi tare da faɗin “Thank You sir” ba tare da nuna alamun ya ji shi ba ya koma yana rufo ƙofar. A dai-dai dining area ya ajiye leather tare da wuce upstairs, ganin lokacin sallah ma yayi yasa ya shiga toilet, watsa ruwa yayi tare da ɗauro Alwala. Yana fitowa ya shimfiɗa praying mat tare da tada sallah. Captain Alee Muhammad Naira Kenan, kyakkyawan matashi son kowa ƙin wanda ya rasa. Ɗa na biyu wurin Gen. Muhammad Naira da kuma Dr. Rohmoh Isiaq. Su uku Allah ya bawa iyayen su, Yaya Saleem shine babba, sai shi daga nan kuma Autar su Fauzah. Daddyn shi Haifaffen jihar Adamawa ne bafulatani Usul wanda da ka gan shi zaka fahimci haka, Mom ɗin shi kuma daga India Daddy ya auro ta Lokacin sun je wani muhimmin taro ta maƙale masa ita ala dole sai ya aure ta. Irin kyau na Mom da kuma goyon bayan iyayen ta da ta samu kan batun yasa ya amince suka yi aure. Alee Matashi ne mai jini a jika, shekarun sa bazasu wuce 26years ba sai da yana da ƙirar jikin wani ɗan 30's ɗin. kyakkyawane ajin ƙarshe ga kuma uwa uba iya ɗaukar wanka. Duk da kasancewar shi youngest captain a Nigeria sai dai yanayin kwarjinin da yake da yasa colleagues nashi bashi wani girma na musamman, baya shiga abinda bai shafe shi ba haka shi ba ma'abocin yawan magana bane....miskili number 1 toh Yaya Alee ne shiyasa duk jarabar mata hardly kaga sun samu ko da kalma ɗaya ne daga bakin shi. Main house nasu a can Adamawa yake, Uncle Suraj da Uncle Bello da kuma Daddyn shi duk a family house nasu suke. Rayuwar su rayuwa ce irin ta ƴan gayu kuma ƴan boko duk da kasancewar su Fulani ne, Granny kaɗai ke ƙaƙabewa al'adun su na Fulani. Cikin familyn su kuwa babu wanda baya shakkar Hamma Alee....laƙabin da suka manna masa kan bayyanar da hakan “Zaki”. Shi sam a rayuwarsa baya son hayaniya komai ƙanƙantar ta...in kaga yana dariya kuwa to tare da Areef ne son ɗin Yaya Saleem. *Wannan kenan* ★★★★★★★★★ *ƳAR IYA POV* Tunda suka ɗunguma cikin kasuwar ta fara tunanin me zata ci ne mah, dai-dai wata rumfa da Iliyasu ke saro bread yayin da sauran ƴan gari ke sara a wurin shi suka biyo. Yana ganin su ya cillo wani tsumma da yake goge daron bread da shi kan bread ɗin, All this saboda kada su Ƴar Iya su gani ne sai dai abu ya riga ya faru. Kai tsaye rumfar suka nufa tare da faɗin “Iliyasu akwai burodi ne?” Cikin inda-inda yace “A...aa..eh..akwai guda.. shida da suka rage” Ba tare da ta ce uffan ba ta nufi wurin tsumman nan ta yaye shi ai kuwa A'i ta saki baki tana salallami. “Innalillahi wai dama akwai burodin shine kace ƙwara shida suka rage, lallai ka cika ƙatoto kuma zungureren maƙaryaci” Ƴar Iya kuwa tuni ranta ya soma ɓaci da halin ƴan ƙauyen nasu, kowa sai shegiyar rawar tsiya. Tsaki ta ja sannan tace “Ni na kasa gane halin ku ƴan garin nan gaba ɗaya kun addabi jama'a da rowa, to kowa baƙin cikin ciyar da kai yake...Ni Autar Iya ina ganin jalala, to Aradu burodin nan duk ka juye man shi cikin buhu yanzu ka miƙo man” ta faɗa tana banka mishi harara. Ba tare da ya musa mata ba ya juye bread ɗin baki ɗaya coz shine kwanciyar hankalin shi. Bayan sun ɗauki bread ɗin su suka wuce abun su sai gida Iya....babban buhu guda na bread suka sanya gaba sai da suka ga bayan shi tasss...ƙwara ɗaya suka bawa Iya wanda shima da ba don Iyar ta ɗauke shi ba da tuni sun gama da shi. Da yammaci ne Baffi yayi baƙo, amininsa ne wanda suka yi karatun Allo da shi a tsangaya ɗaya sai dai shi Haifaffen garin Galdimari ne ammah a can Sakwa yake da zama. Sun yi taɗi sosai da Baffi daga bisani ya tafi. Bayan tafiyar shi Baffi ya tunkaro Iya da batun da suka tattauna da abokin sa duk da cewa gabaɗaya kusan a kan Ƴar Iya aka yi shi. “Iyar Shalele dama wata magana nake so muyi da ke” “Toh ina sauraron ka, Allah dai yasa lafiya” “Lafiya ƙalau....damah ɗazu Amini na Shehu ai baki dai manta shi ba?” kai ta ɗaga shi kuma yaci gaba. “Toh shine muke tattaunawa akan matsalar Yarinyar nan mai sunan ki, toh ya bani shawara wacce ina kyautata zaton in mun bi ta zamu samu nasara da Izinin Allah kuma la'alla yarinyar ta daina wasu daga cikin halayen ta” Ganin Iya ta tsura mishi ido tasa ya ɗan dakata yana kallon ta. “Ammah baka tunanin haka Allah ya halicci yarinyar ne?, Ba ma wannan ba wace shawara ne kuka yanke kai da shi Malam Shehu ɗin?” Sai da Baffi ya gyara murya sannan ya ce “Malam Shehu ya bani shawara kan kai takwarar ki makarantar kwana, idan har bata ganin na kusa to za'a samu sauyi, kuma a can zata ƙara sanin rayuwa tunda mutane ne iri iri idan muka ci Sa'a sai tayi koyi da wani daga ciki” Jimm Iya tayi ta rasa abun faɗi can tace “Ammah baka tunanin in taje can ma tayi musu halin ne?” Murmushi irin nasu na manya yayi sannan yace “A'ah bana fatan hakan, fata na ta samu sauyi cikin rayuwar ta, itama tayi rayuwa kamar yadda kowa yake yi, ina da tabbacin ba haka ainihin yarinyar nan take ba saboda na sha yin mafarkai iri-iri game da ita ba a irin wannan yanayi ba” Hawayen da ya zubo masa ya goge, tuni zuciyar Iya ta karye don zata iya ƙirga sau nawa taga hawayen mijin nata saboda ba ƙaramin abu ne zai taɓa zuciyar gwarzon mijin ta ba. “Shikenan Ni kam duk hukuncin da ka yanke zanyi maraba da shi, fatan mu bai wuce samar wa jikar mu ɗaya tilo salama a rayuwar ta ba. Saboda haka sai a fara shirye-shiryen tafiyar ammah ina ne za' kai ta?” Iya ta jefawa Baffi Tambayar. “Can wani gari ne wai Sakwa, akwai makarantar kwana to can za'a kai ta” Cikin sanyin guiwa Iya da Baffi suka gama hirar su daga ƙarshe suka tsaya kan kaiwa Ƴar Iya makaranta. A daren Iya ta siyo sabulun wanka da kuma alimun har da soda da kanwa...ta haɗo da dutsin kaushi. Bayan ta siyo bata wuce gida ba sai da ta nemo Ƴar Iya cikin ƙauyen suka dawo. Kallon tuhuma Ƴar Iya ke bin Iya da shi tana ƙara wari idanuwan ta waje. “Lafiya Iya kika ɗauko ni ko dai wani abu ya samu ne” Murmushi Iya tayi tace “Jika ta kuma Shalele na birni nake so kije, shiyasa na bi kasuwa na siyo kayan gyara ko baki son zuwa birnin?” Caraf tace “Tab ɗijam, Aradu ina son birni Iya, baki ganin irin kayan da suke sakawa ga ginin su masu kyau ba irin bukkokin mu ba” Ta faɗa tare da nuna bukkokin su da yatsa tana yamutsa fuska. Cikin zumuɗi Iya tace “Toh ke a ina kika san birni ke da iyakar ki ƙauyukan kusa da mu ne” Kallon baki da wayo ta jefi iya da shi tana banka mata harara tace “Kiji Iyar nan, toh bari kiji in gaya miki a gidan kallo ne a can Zubo, idan naje sai na laɓe ina kalla...Aradu Iya kin ga wasu kyawawan samari kuwa?” Murmushi Iya tayi ganin ba zasu samu matsala da shalelen ta ba tace “Toh ai kema zaki zama irinsu musamman in Kika je kika yi karatun boko” “Miye kuma boka Iya, Ni ba zan yi tsafi ba” ƴar dariya iya tayi tace “Bokoooo nace ba boka ba” Ganin Iya na mata dariya yasa ta ɓata fuska tare da miƙewa zata fice, kamota iya tayi tana faɗin “Yi haƙuri shalelen Iya, boko shine karatun Ƴan birnin, kuma tunda suna burge ki ai zaki yi shi ko?” Kai ta gyaɗa tunda ita yau ta fara jin kalmar boko a rayuwar ta. Daga nan Iya ta sata gaba kanta ta gyara mata jikin ta tun yanzu kada in taje su raina ta. Babu musu suka shiga bayi, daga baki Iya ta fara, dama ta riga ta daka gawayin ta da gishiri haka ta gurza mata, irin gudajin datti da aka cire ba'a magana, sai dai har lokacin akwai su danƙare kamar gona. Daga nan iya ta fara wanke mata sumar kanta wacce in ka ga irin dattin dake fita sai kayi amai. Abun mamaki ana jiƙa sumar gashin ganta ya ware, Masha Allah sumar tana da tsayi ashe sai ɗan banzan datti. Fatan jikin ta ma ta sha wanka tuni ta ɗan ƙara haske. Babu laifi Ƴar Iya fa kyakkyawa ce 1st class sai dai rayuwar ƙauye da kuma ƙazanta yasa muke ganin ta kamar kashi. Bayan an gyara jikin ta, suka fita kasuwa tare da Iya ta ɗan zaɓa mata wasu kayayyakin amfani, har powder irin _buɗa ni jaka_ ɗin nan, jan baki ne da kwalli da dai sauransu. Daga nan suka dawo. Kwana biyu saboda ɗaukin zuwa birni Ƴar Iya bata fiye fita yawo ba, ko da A'i tazo su fita Ƴar Iya ta bata labarin ita fa birni zata je kuma Baffi yace zata yi karatun Ƴan birnin shiyasa ma ta daina fita. A'i tayi mamaki sosai daga ƙarshe har da kukan ta Aminiyar ta zata bar ta ita kaɗai. “Ko dai baƙin ciki kike da ni ne?” “A'ah Ƙawa ta, kawai zanyi kewar ki ne kuma kinga da kin tafi la'alla Inna ta tace aure zata min tunda kinga su Dijen Iyayye duk an bada su” “Kar ki wani damu, ba daɗewa zanyi ba musamman naji garin babu daɗi dawowa zanyi” Daga haka A'i ta wuce gida saboda yadda zuciyar ta ke mata. Shirye-shiryen tafiya kuwa tuni an gama ranar Lahadi za'a wuce da ita zuwa makarantar kwana dake Sakwa. Ranar Asabat Baffi yace zasu je suyi wa Baban ta sallama, ba don ta so ba sai kawai don Baffi yace in Bata je ba to za'a fasa tafiyar. Tunda suka isa gidan Inna Zaliha ke kallon Ƴar Iya ta ƙasan Ido yayin da zuciyar ta tayi wani irin bugawa. Ba tare da ta bari sun fahimci komai ba ta kawo ruwa a kofin silver bayan sun sha Baffi ya buƙaci tayi wa Baban Ƴar Iya magana, a nan Baffi ya sanar da shi zasu wuce. Cike da farin ciki ya amince haka Inna Zaliha har da bata kyautar kuɗi wai ta sha ruwa a hanya. Daga haka suka fito basu tsaya ko ina ba sai gida, Nan aka ƙara haɗa kayan Ƴar Iya wanda mafi yawanci sabi ne aka yi mata sai kuma ƙanzo da mai da yaji da Iya ta haɗo mata guzurin shi. Cikin gari tuni anji labarin tafiyar Ƴar Iya birni, kowa farin ciki kamar anyi mishi albashir da gidan Aljanna, wasu har kyautar abubuwa suke kawowa saboda zasu rabu da Annobar su, maƙwabta da aka ɓata da su suma sun shigo suna taya Ƴar Iya murna. Da daddare Ƴar Iya ta niƙi hanya sai gidan Arɗo. Ta samu tarba ta musamman saboda duk su ma murnar tafiyar ta suke, Innani ma ba'a bar ta a baya ba har da kyautar kuɗaɗe ga Ƴar Iya, Saratu Matar Arɗo ma ta bata ɗan kunne da jan baki. Arɗo kuwa kuɗi ya bata tare da sanar da ita goben in zata tafi ta biyo zai sa a gasa mata zabi, daga nan ta wuce ba tare da tayi wa kowa godiya ba. TOH ƳAR IYA FANS MASOYIYAR KU FA ZA'A TAFI BIRNI! MEH KUKE TUNANIN ZAI FARU?, ƳAR IYA ZATA SAUYA KAMAR YADDA SUKE FATA? YA KUKE TUNANIN RAYUWAR TA A MAKARANTAR KWANA? IN KUNYI COMMENTS ZAN ƘARA MUKU LUNCH, KUMA ZAKU SAMU DINNER. COMMENT& SHARE FISABILILLAH [4/29, 7:48 AM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘‘13&14’’’’’ *ALEE POV* Bayan yayi lunch nashi ne ya samu ya ɗan kwanta saboda irin gajiyar da yake ji. Bai tashi ba sai around 4:00pm, ganin time na Asr prayer na shirin wucewa yasa ya yi saurin nufar Toilet. A waje na jira shi ina ƙarema wani frame da ke ɗakin wanda ya tafi da imani na. Ƙarar buɗe ƙofar Toilet da naji yasa na ja gefe ina lafewa kada Yaya Zaki ya gan Ni. Cikin nutsuwa ya gabatar da sallar shi. Bayan ya idar ma ya jika bisa praying mat ɗin kafin ya miƙe tsaye yana nufar parlourn. Ruwa masu sanyi ya ɗauko a fridge ɗin da ke dining area daga nan ya dawo. Yana dawowa ya sanya bathrobe sannan ya nufi toilet. Sai da ya shafe 40minutes wannan karan tukun ya fito hannun shi riƙe da ƙaramin white towel da yake ta famar goge sumar shi da shi. Bayan ya shafa mayukan sa ya buɗe closet tare da ciro wasu kaya. Few minutes ya kammala sanya White Armani T-SHIRT nashi mai ɗauke da rubutu ta gaban _STRUGGLE_ sai kuma wani Navy blue jeans da ya saka wanda yayi matuƙar amsar jikin shi, tuni kyakkyawar surar shi ta ƙara bayyana yayin da ya fara feshi jikin shi da wasu turaruka nan da nan ƙamshi ya cike ɗakin kamar kogin turare. Wani expensive wristwatch ɗin shi ƙirar _Magsonic Sonnerie_ ya sanya tare da ɗauko phones ɗin shi yana ficewa daga bedroom ɗin. Cikin takun shi irin na cikakkun maza masu izza da kuma jarumta ya fito, suna ganin fitowar shi suka matso kusa da shi suna sara mishi. Bai bi ta kan su ba ya fito yana zaga gidan. Yayi tafiya kaɗan can ya iso garden ɗin dake ta ɗan gefen apartment ɗin nashi. Wuri ne wanda yaji shuke-shuke masu ɗaukar ido kama daga flowers izuwa green grass carpet da ya malale garden ɗin. Dai-dai wani ɗan cool down dake wurin ya nufa tare da zama ɗauke da ambaton Allah a bakin shi. Phone nashi da yayi ringing har ya kusa katsewa yayi picking da sauri ganin sunan *DADDY* make kan screen ɗin wayar. A kunnen shi ya kara ta tare da sakin nauyayyiyar ajiyar zuciya at the same time fuskar shi ta sake kamar ba shi ba. “Assalamu Alaikum sweet daddy” Murmushi Mai sauti Daddy ya sake jin Muryar gudan jinin sa kuma abun alfaharin shi Shareef. “Son, kana lafiya” “Lafiya Lou Daddy nake, ya su Mom da su granny?” “Lafiya ƙalau suke son, ɗazu muna magana da Mom ɗin ka take sanar da Ni ka dawo irin shigowa haka babu sallama” Murmushi Hamma Zaki yayi yana ƙara sauƙe Muryar shi wacce ke fita kamar an saka shi dole. “Ayya Daddy I just wanna make u surprise, gobe zan ƙaraso In Sha Allah” Daddy yace “Toh son sai ka dawo, i love u” “I love U too sweetheart” Daga haka kiran ya katse. Wayar tashi ya ajiye tare da kwantar da kanshi jikin kujerar da yake kai yayin da ya lumshe idanuwan shi, iskar da ke kaɗawa ne ke kaɗa sumar shi ta baya, hakan ba ƙaramin ƙara mishi kyau yayi ba. Ya jima a zaune kafin ya miƙe yana komawa apartment ɗin shi. ★★★★★★★★★ *ƳAR IYA POV* Tun kafin Asubahi ta tashi tana zagaya gida zuciyar ta fal murna yau zata koma birni. Bayan Baffi ya dawo daga masallaci ya je har ƙofar gidan Malam Salihu ya sanar da ɗan sa Shayibu wanda shi kaɗai ne ya mallaki babur cikin ƙauyen. Misalin ƙarfe 5:50am Ƴar Iya ta nufi gidan Arɗo ai kuwa zabin da yayi mata alƙawari an riga an gasa mata, tana amsa ta wuce. A tare da Baffi suka hau mashin ɗin, bayan ta hau Baffi ya hau sannan aka haɗa musu kayan a gaban Shayibu, Iya kuwa kuka take kamar ranta zai fita saboda za'a rabata da shalelen ta. Da ƙyar ta koma bayan tada babur ɗin da Shayibu yayi ɗiiiiiiiiiii.... (Ni DIAMOND LADY nace safe trip Ƴar Iya Allah ya bada abun da aka je nema....Team Ƴar Iya ma duk sun yi mata fatan alkhairi, su Ummu Basmat, Maman Usman, Ayeesh, Ameran Mama, Hindatu Hassan, Faty Shareef, har da su Maman Hakeem da sauran Fans na ƳAR IYA READER'S HUB duk suka bi bayan babur ɗin suna murna yau zasu birni😀). Bayan sun isa dai-dai bakin hanya wata mota irin Tanker ɗin nan tazo wucewa...saura kaɗan Ƴar Iya ta hantsilar da mashin ɗin don wani tsalle ta buga kamar biri sai da Baffi ya riƙe ƙafafuwan ta. “Ƙundun Jakar uban can.... Baffi wallahi ƙarfe me ciki ke tafiya kaga hala ya kusa haihuwa Aradu Baffi ka sauƙar da Ni na bi shi” Haka tayi ta musu ƙauyanci tun Shayibu na ɗan jin haushi har ya fara dariya. (Ni dai ban ga laifin ta ba saboda wannan ita ce first tafiyar ta). Tafiya suka yi mai tsayi a babur ɗin yayin da Ƴar Iya ke zuba ƙauyanci son ranta. Ganin yadda suke wuce bishiyoyi yasa ta calla ihun murna tana faɗin. “Baffi Aradu suma tafiya suke yi....kai jakar uba Baffi su ma raka Ni suke yi....woooohuhuuuu Ni Jikar Iya ina da masoya” Haka tayi ta zubar ta har suka iso Azare. Wani babban gida ta gani upstairs can kuma ta hango kamar mutum daga gidan Ai anan ne kallo ya koma sama don Ƴar Iya sabuwar rigima ta ɓarke da shi. “Baffi ka dakatar da shi don Allah Ina son hawa kan wancan abun...wayyoh Baffi Allah zan dirƙa in Baku tsaya ba” Baffi da ya rasa me yake masa daɗi da wannan hali na Jikar tasa ya fara lallashin ta . “Yi haƙuri shalelen Iyan ta, ke da zaki zauna a nan kuma ai ba sai kin hau yanzu ba, kullum in kina so kawai zuwa zaki yi ki hau” Da haka ta haƙura suka ci gaba da tafiya. Suna isowa cikin garin Sakwa suka ce karo da wani mai amalanke zai fita, tsayar da mashin ɗin Baffi yayi ya fara mishi magana cikin harshen fulatanci “Don Allah ina ne hanyar makarantar kwana?” Kwatanta wa Shayibu yayi saboda haka suka miƙe sai Gov'nt Girls College Sakwa. Tun daga bakin gate Ƴar Iya ta fara sakin murmushi, gani yara Sa'annin ta da check na pink yard wasu na tuƙa ruwa wasu kuma sun tsugunna gaban wata mai Blue Check hakan ya bata dariya tace. “Kutumar Uba....Aradu akwai kallo” Baffi ne yaja hannun ta zuwa wajen wasu matasa da suke zaune kan wasu kujeru bakin bishiya. Gaishe su Baffi yayi Ƴar Iya kuwa ko a jikin ta. Bayan Baffi ya faɗa musu cewa Ƴar shi ya kawo makarantar suka nuna mishi hanyar ofishin Principal. Sun miƙe zasu wuce ne wani Ƙatoton malami mai ƙaton ciki, gashi gunt, baƙi ƙirin yake ga kuma kanshi ɗan ƙarami kamar an san mishi. Ai kuwa da gudu Ƴar Iya ta fizge hannun ta tana nufar inda yake. Sai da tazo dai-dai da shi ta ƙara rage tsayi tana mishi kallon ƙwaƙwaf... Bai ma lura da ita ba sai da yaji ta kwashe da dariya “Hhh.....hhhhhhh..hhhhhhh wayyoh ciki na, A'i na baro ki da nace kizo kiga mai kama da Bijimin Baffi hhhhhhh....Kutumar Uba Aradu banbanci shi da Bijimin Baffi ƙaho ne sai jela” Haka ta ƙara kashewa da wata mahaukaciyar dariyar. A lokacin ne malamin yayi noticing nata ya kuma ji abun da ta faɗa, kunya da ɓacin rai suka sauƙa mishi lokaci ɗaya. Gashi yarinyar da yake so Sahiba Bashir sun zo wucewa ita da abokan ta kuma ya tabbatar taji. Tuni yayi kan Ƴar Iya yana ayyana ko ƴar uban waye yau sai taci uban ta. (Nace lallai baka san Ƴar Iya ba ne) Wata irin damƙa yayi mata kafin ta farga ai kuwa tuni tayi wani juyi tare da murɗe hannun da ya janyo ta da shi. Abun ka da ƙato dama muscles sun mishi yawa tuni jikin yayi tsami gashi ta ƙi sakin shi. Mamaki ne ya kama shi ganin iri ƙarfi da yarinyar ke da shi gashi ya kasa ƙwacewa. Yanke shawarar ihu yayi ko za'a samu masu taimaka mishi. “Wayyo Allah jama'a ku kawo ɗauki, innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir....” Bai kai ga ƙarasa ihun ba Ƴar Iya ta buge bakin shi nan da nan jini ya fara zubowa. Malaman da ke gindin bishiyar nan ne suka ji ihun ai kuwa suka taho don ganin MEH ya faru. Arba da yarinya ƙarama na riƙe da Mr. Small duk iri girman shi yasa suka shiga ɗimuwa. Faɗa wasu suka fara mata kan ta sake shi ammah shiru....wanda yayi dai-dai da fitowar Baffi da office ɗin Principal nasu don ya ƙira ta ayi mata interview. Ɗauke da mamaki a fuskar shi ya daka mata tsawa tuni tayi wulli da hannun Mr. Small Wanda yayi dai-dai da faɗuwar shi ƙasa. Tana sake shi ta nufi wurin Baffi su kuma malaman suka je don bawa ɗan uwan su agaji. Bayan sun shiga Principal ya fara mata interview ammah sai ya fahimci bata san komai ba....ABC common Bata sani ba tunawa da bayanin Baban ta yasa ya yanke shawarar kai ta aji ɗaya don kuwa ya san halin yarinyar tunda Baban nata yayi masa bayani. Babu ɓata lokaci Principal ya ƙira wata Senior tare da nuna mata Ƴar Iya yace ta tafi da ita hostel a Bata room da gado. Ba musu ta miƙawa Ƴar Iya hannu a kan su tafi. Ganin Baffi zai tafi yasa ta arta da gudu wurin babur ɗin. “Baffi ina zaka je?” “Zan tafi manah, ba kince kina son birni ba?, toh ki zauna gobe ma zan zo kinji” Kai ta gyaɗa kamar ta fahimta tare da komawa wurin kayan ta. Ganin babu kayan ta babu alama yasa ta kwarma ihu tare da sakin ashar. “Kutumar Buhun uban jakin nan, uban waye ya sace min kaya na?” Rasa mai bata amsa aka yi da ƙyar Principal yace “An kai miki shi makwancin ki” Senior ɗin da ta kai kayan ne ta dawo saboda haka ta lallaɓa ta suka wuce room ɗin da aka bata. _YAR IYA'S FIRST DAY AT SCHOOL_ Ganin makarantar cike da bishiyoyi yasa ta ɗan ji sauƙi a ranta shiyasa ta fito tana kewaya ko ina, kun san Sunday babu karatu mostly students sukan wanke uniform nasu ne suyi wanka. Ƴar Iya na cikin tafiya zata hau bishiyar mangwaro da ke ɗan nesa da hostel ɗin nasu taji an dakatar da ita. “Keeee! dan Bura Ubanki zo nan, uban me kike yi a wajen?” Senior ɗin ta faɗa cike da bada umarni da taƙama. Cike da ɗumbin mamaki Ƴar Iya ta waiwayo ta kalle ta, cikin ranta tana ayyana wace tsagerar ce ta tare ta yau zata san ta zage ta. Juyawa yayi ta ɗale bishiyar abun ta, yadda take tsalle kuwa kai kace biri ne. Senior da ta ƙulu da rashin kunyar da sabuwar ɗalibar ta ƙunsa mata wuri ta nema ta zauna tana jiran sauƙowar ta tare da tunani iri-iri akan uƙubar da zata bugawa yarinyar. Shiru shiru babu Yarinya ba labarin ta nan fa Senior ta tsorata Allah yasa dai ba ifiritan da ke makarantar bane. Ta juya zata tafi kawai taji sauƙar abu a bayan ta daga sama, wata irin ƙara ta sake....... IN ANYI COMMENTS ZAN ƘARA MUKU UPDATE ZUWA JIMAWA INA GODIYA GARE KU MASOYAN LITTAFIN ƳAR IYA, MASU COMMENTS ƊIN NAN DA MASU TAYA NI INA MATUƘAR ALFAHARI DA KU, ALLAH YA BAR ƘAUNA. much Love my esteem fans. DIAMOND LADY 💎 CE! SHARE FISABILILLAH. [4/29, 2:48 PM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘‘15&16’’’’’ Shiru shiru babu Yarinya ba labarin ta nan fa Senior ta tsorata Allah yasa dai ba ifiritan da ke makarantar bane. Ta juya zata tafi kawai taji sauƙar abu a bayan ta daga sama, wata irin ƙara ta sake yayin da ta kife a ƙasa kamar kwaɗo. Ba komai bane ya faɗo bayan senior sai Ƴar Iya wacce sai da ta saita bayan nata ta diro a kai. Ganin tayi wa Senior ɗin illa yasa ta cika bujen ta da iska, bata tsaya ko ina ba sai ɗakin da aka bata. Lokacin kuwa har an fara kiraye-kirayen sallar Azahar. Bata kula kowa ba ganin babu wanda ya kula ta, in fact kowa ma hidimar gaban sa yake sai dai abun da ta fahimta shine fita waje suke yi gabaɗayan su. Wata senior da taji ana kira da Ajaram taso saitin Ƴar Iya tace “Ke ba zaki je dining bane ko baki ga lokacin cin abinci yayi ba” Da yake babu kowa a room ɗin yasa ta fahimci da ita take saboda haka ta zubo mata ƙwala-ƙwalan idanuwan ta alamun bata fahimta ba. Da yake Ajiram na da sauƙin kai kuma bata cin zalin yara yasa ta ƙara maimaita mata. Ƴar Iya tace “Meye kuma Dayin?, Ba dai wanda ake lalle ba, to ai ni bana yi Aradu ko a ƙauyen mu” Mamaki ne ya cika Ajiram lokaci guda kuma ta fahimci yarinyar ƴar ƙauye ce saboda haka ta saki murmushi tace. “Dining gurin da ake bamu abinci ne a nan, ki tashi muje kada ya ƙare baki samu ba” Huhuhu! Su Ƴar Iya manya, wani zungureren mamaki ne ya maƙale ta, yau itace wani ke lallaɓa tazo taci abinci, ita da bata da aiki sai ƙwacen na wasu taci shine ake nunawa tausayi. Lokaci ɗaya taji tana ƙaunar matar. Da niyyar ta shine ta ɗauko zabin ta na wurin Arɗo taci kawai sai taji bari ta ɗauko su ci da wannan matar. A hankali ta ɓaro buhun kayan ta ta janyo ledar zabin. Duk abun da take Ajiram na jiran ta don bata tafi ba, tunanin ta ko dai zata ɗauko wani abun ne. Ledar ta ɗauko tare da buɗe ta, janyo zabuwa ɗaya tayi ta miƙawa Ajiram, mamaki ne ya cika ta lokaci ɗaya ganin gasasshiyar kaza.... “Gashi muci wannan sai muje Dayin ɗin” Murmushi Ajiram tayi tana tsintar kanta da zama kusan Ƴar Iya, tare suka cinye ta farkon ita dai ta ƙoshi ammah mutuniyar ta saba saboda haka ta janyo ɗayar. Tasss ta cinye ɗayar, ita kuwa Ajiram mamaki duk ya cika ta. Bayan ta cinye tace wa Ajiram ɗin ta raka ta Dayin suje suci wancan, a lokacin kuwa har ya kusa ƙarewa saboda haka aka ɗan zuba musu kaɗan kaɗan. Bata wani damu ba tacinye sannan ta fara waigen inda zata ga wannan baiwar Allah ta ɗazu, tana hango ta ta wuce wurin ta guduuuuuu.... Tare suka dawo da yake room ɗaya suke Ajiram na jan Ƴar Iya da hira ita kuwa ta zage sai bata labari take. Lokacin kwanciya yayi Ajiram ta taya Mutuniyar hawa nata gadon sannan tayi musu addu'a tare da shafawa Ƴar Iya a jikin ta. Nan da nan bacci ya kwashe su. Washegari da safe da yake ba kullum ake wanka ba a school ɗin ɗalibai suka fara shiryawa cikin uniform ɗin su, Ajiram ita ta taya Ƴar Iya saka nata tana mitar kayan meyeh wannan. Bayan sun shirya aka tafi classroom. Assembly aka yi daga nan kowa aka ce ya wuce aji. JSS one shine ajin da aka kai Ƴar Iya, tana shiga ta fara baza ido, ganin kowa yana neman waje ya zauna yasa ita ma ta nemi waje ta zauna kamar mutuniyar kirki. Malamin su na English ya shigo, kowa ya miƙe ya gaida shi banda Ƴar Iya wacce gabaɗaya hankalin ta na kan jakar da Ajiram ta kawo mata wai Principal yace a bata, cikin zuciyar ta tace ke kika san miye Principal ɗin ma ai. Mr. Bello kenan, mugun gaske ne kuma baya sake ma ɗalibai fuska, in ya bada assignment baka yi ba to kashin ka zai bushe ne. Ba tare da ya kalle ta ba ya fara magana cikin harshen turanci. “Ke wannan da baki tashi ba jira kike na gaishe ki?” Tuni idanuwan Ƴan aji suka dawo kanta ita kuwa da ake maganar akan ta bata ma san me ake ba, yoh ita da Hausan ma ya aka ƙare bare Yaren da tunda Innar ta haife ta bata taɓa ji ba. Idanuwan da suka zubo mata ne yasa ranta fara ɓaci ta fara hararar su. Mr. Bello kuma duk tunanin shi shi take harara saboda haka ya hasala ya tunzura daga nan yayi waje. (Ko meh zai yi ohoo) Ganin Baturen nan ya fita yasa ta miƙe tsaye tana bin Ƴan ajin da mugun kallo. “Ku kuma masu idanuwan mayi uban me naci muku zaku zubo min ido, duk ku juya ko naci Bura Ubanku” Wasu da suka sha jinin jikin su duk suka juya yayin da tsagerun da ke ganin suna dai-dai da ita suke Binta da kallon raini don daga gani wannan baƙauyiya ce. Ganin sun ƙi daina kallon ta ga kuma wani irin kallo da suke mata yasa ta ƙara harzuƙa....kan mai uwa jawabi tayi duk wanda ta yo kanshi in ta buga mishi duka sai tayi gaba, haka take taka saman desk ɗin kamar biri tana ta tsalle tare da bugun jama'a. Tuni wasu suka fara gudawa waje suna ƙwalla ihu don kuwa bugun da take musu ba na wasa bane. Su kuwa tsagerun nan basu bar ajin ba ai kuwa ita ma bata daina bugun Ƴan Iska ba don kuwa duk yawan su haka take gabzar su. Ana cikin gumurzun yaƙin ne sai ga Mr. Bello ya dawo hannun shi riƙe da wata sharɓeɓiyar bulala. Ba tare da yace komai ba duk da yaga wasu students a waje bai ko tambaye su dalili ba tunda ranshi a ɓace yake ga hankalin shi da ya tafi ga hukunta wanan yarinyar da ta ƙi gaida shi. Ganin yadda yarinyar ke tsalle tana bugun mutane yasa ranshi ƙara ɓaci babu ɓata lokaci kuwa yayi kanta ta bulalar. Murna ce ta kama su ganin Mr. Bello yayi kanta, ita kuma Ƴar Iya bata san da shigowar shi ba sai jin bulala tayi a gadon bayan ta nan da nan ƴan aji suka saka shewa. Bata kai ga waiwayo ba ta ƙara jin bulala a bayan ta wanda taji matuƙar zafin ta. Wani kukan kura Ƴar Iya tayi tana juyawa saman desk ɗin ta ƙara sakin wani tsallen tare da hayewa saman malamin, a dai-dai kafaɗar shi tayi masauƙi yayin da ta naɗe ƙafafuwan ta a wuyan sa. Ƙoƙarin wurgo ta yake tana hanawa har sai da ta tabbatar wannan fah ɗan banza ne. Bulalar hannun shi ta fuzge duk da haka bata bar kan kafaɗun sa ba, nan da nan ta fara zabga masa bulalar babu ƙaƙƙautawa. Mamaki ne ya cika shi jin irin zafin bulalar gashi ya kasa ƙwatar kan shi, ƴan aji kuwa jiki yayi sanyi ganin yadda newcomer ɗin ke bugun Mr. Bello. Tun Mr Bello na ƙoƙarin ƙwace kan sa har dai ƙarfin shi ya soma ƙarewa, ita kuwa duka kawai take kai mishi tana sakin wani irin huci. Class monitor ce tayi tunanin zuwa staff room ta sanar da su cewa ana yaƙi a class ɗin su. (Kaji ta fa wai yaƙi😂). Babu ɓata lokaci staffs suka taho Jss one, ganin students ɗin a waje ga kuma gurnanin da suke ji yasa cikin hanzari suka nausa don ganin me ke faruwa haka. Arba suka yi da Mr. Bello, mutumin da ko su staffs baya yi musu da sauƙi saboda irin yadda ya tsani raini. Gashi yashe a ƙasa sai kuma Newcomer ɗin jiya wacce ta azabtar da Mr. Small tana jibgar sa. Ƙoƙarin janye ta suke ai kuwa ta dawo kan su ta fara jibga, ihun malaman ne ya jawo hankalin students da sauran teachers dake sauran classes, tuni aka fito ana tambayar JSS one students dake a waje nan suka fara bada labari. Wannan abu da yake faruwa Principal dai na office ɗin shi, Ajiram lokacin da ta riski labarin sai ta tsinci kanta da kutsawa cikin ajin duk da riƙe ta da ake yi haka ta shige, nan fa tana shiga tace mata “Zo mu tafi sister” Abun mamaki babu musu suka ga Newcomer ta ajiye bulala a gefe ta nufi wurin Ajiram tana rungume ta. Cikin lallami Ajiram ta ja ta suka wuce hostel ai kamar jira ake ta tafi kuwa masu aljanu suka fara zubewa, ihu kawai ke tashi cikin makarantar, wannan in ta yanki jeji da gudu sai kiga an bita, cikin waɗanda suka bita suma sai kiji wata ta sake ihu tana kama tata hanyar. Lokaci ɗaya students duk suka ɓararrake, wanda basu da aljanu kuwa sai zare idanuwa suke ko ajajjaɓin abun basa yi. Bayan jibgar da staffs ɗin nan suka sha a haka suka ɗaga Mr. Bello suka nufi da shi clinic, nan aka ce kawai su wuce Hospital, da ƙyar aka amshi Mr. Bello don kuwa doctors ɗin cewa suka yi sai an zo da police. kuka wasu daga cikin malama suke yi ganin haka yasa doctor ɗin amsar shi nan aka fara bashi agajin gaggawa. Ɓangaren Ƴar Iya kuwa kuka kawai take zabgawa yayi da Ajiram ke aikin rarrashin ta. A haka suka isa hostel ta cire mata uniform ɗin tare da sanya mata check ɗin su na zaman hostel. Da ƙyar Ƴar Iya ta daina kukan saboda yadda Ajiram ke ta rarrashin ta. Bayan kukan ya tsagaita basu koma class ba har lokacin lunch, dining Ajiram ta Kama hannun Ƴar Iya suka tafi kafin su dawo ta gama wartsakewa. Abun da baku sani ba duk wannan alaƙa da ta ƙullu tsakanin Ƴar Iya da Ajiram babu wanda yasan sunan ɗan uwan shi. Sai da suka dawo Ajiram ke tambayar Ƴar Iya sunan ta ɗauke da murmushi a fuskar ta. “Kinga Ni ko sunan ki ban sani ba, yaya sunan ki” Sai da ta ɗaga kanta sama tukun ta tuna sunan tace. “Aishatu Umar Gallara” Murmushi Ajiram tayi tana faɗin “Sunan ki yana da daɗi sosai Ni kuma zaki iya ƙira na da Aunty Ajiram” Ƴar Iya ta maimaita “Antijiram” Dariya Ajiram tayi tace “A'ah kice Aunty” “Aunty” “Ajiram” “Ajiram” “Toh kice Aunty Ajiram" “Aunty Jiram” Ganin dai ba zata iya faɗa ba yasa ta ƙyale ta tace ta ƙira ta yadda take so. Haka Ƴar Iya ta saki jiki suna hira da Ajiram har ta fara bata labarin ƙauyen su, haka suka yi ta hirar su kamar ba Ƴar Iya tamu ba (There must be reason behind this fah). Bayan farfaɗowar Mr. Bello Babu abinda yake faɗi sai “Kiyi haƙuri, nace ba mutum ba mutum bace ke wallahi ki ƙyale Ni haka, ah wash” Jin irin sunbatun da Mr. Bello yake yi yasa suka sanar da likita, injection ɗin da aka mishi ne ya sa bacci ƙara ɗaukar sa. Sai lokacin malaman suka samu damar zuwa duba student ɗin da jiya da daddare aka ji ihun ta wajen bishiyar mangwaro, ita ma dai sunbatun kawai take yi. Lokacin da labari ya kai ga kunnen Principal ranshi ya ɓaci sosai, duk da cewa su ma malaman suna da laifi ammah ita wannan yarinyar gaskiya ba zai iya barin ta a school ɗin nan ba, dole baban ta yazo ya ɗauke ta in ba haka ba akwai matsala. Da yake Baffi a ranar ya siya waya saboda yasan dole za'a samu matsala da shalelen Iya. Yana zaune kan taburmar shi sai wayar shi ta hau ruri....da sauri ya ɗaga tare da sallama. Ko amsawa ba'a yi ba ya fara jin Muryar Malamin makarantar su Shalele nan ya maida hankalinsa don ji me yake faruwa.............. TOH FAH... AKWAI ƘURA FAH. KO PC ZAI BAR ƳAR IYA TA CI GABA DA ZAMA A MAKARANTAR KWANA BAYAN TSIYAR DA TA TSULA?????? MU HAƊU A DINNER IN KUNYI COMMENTS....MUCH LOVE MY ESTEEM FANS. SHARE & COMMENTS FISABILILLAH! [4/29, 7:57 PM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA ‘‘‘‘‘17&18’’’’’ Early morning ya tashi coz Flight ɗin 8:00am yayi booking. Sai da ya gama aikace-aikacen da ya saba cikin Laptop ɗin shi daga nan ya fara tattare kayayyakin sa, trolleyn da ya shigo da ita tun zuwan shi ya buɗe, ba tare da ya ɗauki komai ba ya zuge ya mayar. Sai da ya gyara mata zama tukun ya buɗe closet nashi tare da ɗauko wata Black Briefcase, a ciki ya jefa Laptop ɗin daga nan ya ajiye ta a bedside drawer. Bathrobe ya Sanya daga nan ya nufi toilet, bai wani daɗe sosai ba ya fito yana goge sumar kan shi da ƙaramin towel dake hannun shi. Cike da karsashi yayi drying lallausar sumar shi wacce lokacin ɗaya ya gyara hairstyle nashi. Mayuka irin iri ya shafa daga bisani ya buɗe closet nashi. Cikin mintuna ƙalilan ya kammala shirin nashi, so masha Allah, ƙaryar mace ta gan shi tace zata kauda ido, kyau kam ba'a magana ga kuma wani fayau da skin nashi yayi. Turaruka ya fesa masu yawan gaske nan da nan ƙamshi ya buɗe ɗakin kamar kogin turare, har ya juya zai fita ya dawo ya buɗe closet nashi tare da ɗauko wani ɗan ƙaramin kwali. Ya salaaam! Turaren nan mai suna _Majesté impériale_ wanda ni gaskiya ban taɓa arba da wani mai amfani da shi ba saboda tsananin tsadar shi, ko a ƙasashen Turai da wuya ka samu masu amfani da shi sai waɗanda suka jiƙe da ruwan Kuɗi. Yana fitar da turaren wani mayetaccen ƙamshi ya bayyana wanda yayi sanadiyyar disashe ƙamshin turarukan da ya shafa. Kaɗan ya fesa daga nan ya jawo trolleyn shi ya jefa turaren. Briefcase nashi ya ɗauka tare da trolleyn shi janye a ɗayan hannun ya sauƙa downstairs. A nutse yake takawa har ya fito daga parlour. Kamar jira suke ya fito kuwa suka amshe both trolleyn da kuma Briefcase nashi suna sara mishi saying “Good morning” in chorus. Bai ko kalle su ba ya nufi motar da take tsakiyar convoy da suka shirya kamar dai yadda yazo, yana shiga suka figi motocin sai airport. Suna isa aka fitar da trolleyn nashi, sojan nan da ya ɗauki Briefcase ranar zuwan shi still yanzu ma a hannun shi yake, hakan ya tabbatar min da cewa shi ɗin amintacce ne gare shi. Sunayen da aka fara kira ne yasa ya nufi steps na Flight ɗin tare da shigewa, sojan ya bi bayan shi. Without much time wastage Flight ɗin ya ɗaga yayi landing a jahar Adamawa, Yola. *ADAMAWA STATE* *YOLA* *SHAGARI ESTATE* Tunda suka nufo cikin ESTATE ɗin kowa ya tabbatar da cewa yaron General ne ya iso saboda yadda ƙarar jiniya ke tashi. Dai-dai wani ƙerarre kuma babban gida motocin suka yi horn, Babu arziƙi gate man ya wangale gate ɗin. Dai-dai parking lot ɗin su da ke ɗauke da wasu zuƙa-zuƙan motoci suka yi parking, bai bi ta kan kowa ba ya fice don ko Briefcase nashi bai samu ta amsa ba. Part na farko ya nufa, bai sha wahalar danna doorbell ba tunda ƙofar a buɗe take, kamar wani na bin shi haka ya shiga da sauri. Kai jama'a, anya kuwa wasu na tunanin mutuwa?, Makeken parlourn da na shiga ɗauko report ne yasa na tuna da hakan. Masha Allah kawai baki na ya furta, tsayawa bayani da kuma siffanta tsaruwar parlourn ma ɓata lokaci ne ku dai kwatanta shi cikin zukatan ku. Wani babban frame da naga wanda ke ɗauke da picture na wata kyakkyawar mata cikin shigar indiyawa ya bani tabbacin Mom ce tare da Daddy. Sai wani frame ɗin mai ɗauke da hoton wasu kyawawan samari da kuma iyayen su, tashi ɗaya na gano gwarzon maza kuma soja marmari daga nesa wato _Hamma Zaki_ sai kuma ɗan uwan shi wato Hamma Saleem. Ɗaya frame ɗin kuma dukkan su ne har da wata kyakkyawar yarinya wacce ta buɗe baki tana dariya sai kuma Mom, Daddy, Hamma Saleem sai kuma Hamma Zaki da auta Fauzah. “Mom, Mom, First love” (nace dama wannan yana magana haka ne?). Jin shiru bata amsa ba ya kwaɓe fuska kamar zai yi kuka, cike da mamaki nace anya wannan kuwa HAMMA Zaki ne?. Hanyar kitchen yayi yana ƙara ƙwala ƙiran “First love, where are u?” Kamar daga sama taji Muryar gudan jinin ta kuma mafi soyuwa cikin zuciyar ta. Ajiye cake ɗin da take baking tayi tana yiwa Laraba alamar ta ƙarasa, daga nan ta fice da sauri. Arba suka yi a dai-dai dining area ai kuwa da sauri ta ƙarasa tayi hugging nashi ta baya. “Oyoyo My Son, so you wanna surprise us shiyasa ka shiga da wuri, Daddyn ka yace zuwa yamma zaka shigo” Murmushi yayi yana juyowa tare da facing Mom dake ta zuba murmushi kamar an mata kyautar Aljanna. Peck ya manna mata a cheek nata sannan yace “Common first love, ai gashi na baku mamakin” Maƙale da juna suka dawo parlourn ta zaunar da shi kan sofa tana kallon shi tana murmurshi. He can not afford to reject this saboda haka shima ya buɗe baki sai murmushi yake. Sun shafe more than 5minutes kafin Mom tace “Oya lemme get u some refreshments now” har ta fara tafiya ta juyo. “Do You know what?” Kai ya gyaɗa tare da zaro ido. “Na yi baking favourite naka” Ɗauke da tray ta fito, sai da ta tsiyaya mishi drink ɗin ta miƙa mishi, sai zuba take cikin Hausar ta da kana ji zaka ɗan ba cikakkiyar bahaushiya bace. Yana gama sha ya miƙe saying “Mom, lemme fresh up please” Duk irin gayu na Mom tana mamakin son nata, duk uban ƙamshin da yake yi wai let him fresh up, mutum sai kace kifi. Ta faɗa a ranta. Steps ɗin ya ɗale, yana isa bedroom nashi ya shiga. Kai jama'a wannan guy fah he's addicted to white color, everything there is white ga kuma wani makeken frame Mai ɗauke da photon shi shi kaɗai cikin wasu jahilan English wears daga gani a wani beach yayi.. kyawun fuskar shi ba'a magana a picture ɗin. Irin wannan shi ake kira da *NAMIJIN NOVEL* (Littafi na na gaba kenan) Da sauri yayi wanka ya sanya jallabiya tare da feshe jikin shi da turarukan shi masu daɗi. Yana fitowa ya nufi ƙofa, part ɗin Uncle Suraj ya shiga, bayan sun gaisa da Nenne matar uncle take sanar da shi uncle Suraj baya nan. Daga nan ya wuce part ɗin Uncle Bello, sun gaisa cike da girmamawa ya taho zai fita yaji Muryar Salma cikin shagwaɓa kamar wata ƙaramar yarinya “Mommah don Allah yau kam ki barni naje shopping ɗin nan kinga su Rumah da su Ayra duk yau zasu je ko so....” Bata kai ga ƙarasawa ba taci karo da Hamma Zaki da ya juyo ya zuba mata ido. Haɗiye maganar tayi ta fara rarraba idanuwa tana ƙarasawa kusan shi. Cikin cracking voice tace “Good morning Hamma Zaki” Ba tare da ya amsa mata ba ya watsa mata tambayar “Meh ya hana ki zuwa school?” Cikin Muryar inda-inda tace “Uhm...eh..aaaa...damah ba...bani..da...lafiya ne” Da ƙyar ta kai ƙarshe saboda irin kallon da yake jifan ta da shi kuma sarai ta san ya gano ƙarya take. “Shine kike tambayar fita shopping ko?” “Eh...ah... I'm sorry Hamma Zaki....i” “Shut ur mouth up” Ya daka mata tsawa “In na ƙara ganin baki je school ba ranki sai ya ɓaci, stupid girl” Nan da nan jikin Salma ya fara rawa ganin hakan yasa ya wuce abun shi. Mommah kuwa dariya tayi tana faɗin “Alhamdulillahi, naji daɗin hakan, tunda dodon ku yazo ai zamu samu salama yanzu kam” Bai zame ko ina ba sai part ɗin tsohuwa mai ran ƙarfe wato granny. Tun daga bakin ƙofa ya fara jiyo ɓaɓatun ta tana faɗin. “Yo ni AISHATU ina ganin ikon Allah, bari anjima Salamatu ta zo ta saka min ƙiran wayar nan dai” Sallamar shi ce ta dakatar da ita daga maganar. “Ah soja marmari daga nesa, soja mazan fama an baro ƙasar nasara kenan?” Dariya yayi sai a lokacin na ƙara gane cewa shi ƙarshe ne a kyau. “Tsohuwa mai ran ƙarfe, nayi zaton ai in nazo zan tarar kin bunga ne” Zaro ido Granny tayi tace “Bakin ka ya sari guntun kashi ɗan baƙin ciki kawai, yo Ina dalili ni anya kai jinin Muhammadu ne ma?. Kai to bari kaji in gaya maka in ma mutuwa ne ubanka da uwar ka ne zasu fara mutuwa kafin ni, ja'iri kawai” Dariyar sa yake babu ƙaƙƙautawa can yayi shiru “Haba Uwar gidan Alee mazan fama kuma uwar Muhammadu, ai ba zaki mutu yanzu ba ko bakya son ganin matar jikan naki ne”. Goron da ta gutsira ta cire tana murmurshi sannan tace “Ba shakka kuwa ammah kai anya ma akwai wacce zata aure ka, abu kamar kututturen ice ga kuma fuska babu fara'a, wallahi duk wacce ta aure ka ma jaraba ta aura” Hamma zaki yace “Lallai ma tsohuwar nan, ni ne kututturen icen ko? To sai anjima” Ya faɗa yana miƙewa zai wuce. “A'ah haba Maigida duk kishi ne dai irin nawa kasan bana so kayi min kishiya ai” Murmushi mai sauti Hamma Zaki yayi yana ficewa. “Daga baya kenan, zan dawo Granny”. Around 12:00pm wata babbar mota ta danno hanci cikin gidan, bayan tayi packing wasu ƴan yara suka fito su shida. Fauzah da kuma Yesmeen kan su ɗaya, Najma da Ra'eesa kan su ɗaya sai Rumah da Ayrah suma kan su ɗaya. Fauzah part ɗin su ta shige, Yesmeen da kuma Najma suka wuce nasu haka Ra'eesa da Ayra suma suka wuce nasu part ɗin. Ɓangaren Baffi yana ɗaga wayar yayi sallama sai dai ko amsa sallamar Principal bai yi ba ya fara masa bayani. “Baba gaskiya kazo ka ɗauki ɗiyar ka don ba zamu ci gaba da zama da ita a nan ba, hak kawai a yau ta illata fiye da mutane bakwai” Baffi yace “Ka dubi darajar Allah Misbahu, duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi, kada laifin ta yasa aikin ladan da kayi niyyar yi ya wargaje” Da ƙyar dai Baffi ya shawo kan Principal ya amince Ƴar Iya ta ci gaba da karatun a makarantar. ★★★★★★★★★ *ƳAR IYA POV* Cikin ƙanƙanin lokaci Ƴar Iya ta yi sabo da Ajiram, ƴan room ɗin su kuwa mamaki suke yadda Boss ɗin nan ke taɗi da Ajiram. Lokacin Sallah nayi Ajiram ta saka Ƴar Iya gaba kan su je suyi sallah. “Hamrah, tashi muje muyi salla” Da kallon mamaki Ƴar Iya ke kallon Ajiram tana tuna wai ma meyeh sallar ne. Ƙara maimaita mata tayi “Ki tashi muje muyi sallah” “Bana yi” abinda ta tsinci Ƴar Iya na faɗa. Zaro ido Ajiram tayi, na ta saka ta gaba ala dole sai sun je sun yi. Yadda take threatening Ƴar Iya yasa ta miƙe ta bita. Da ido ta bita gani tana alwala, ita fa bata taɓa yin salla ba tunda Innar ta haifeta. Haka dai ta jiƙa fuskar ta da hannun ta matsayin Alwala. Bayan sunyi suka wuce mosque don yin sallah. Ƙememe Ƴar Iya tayi ita wallahi bata iya ba kuma bazata yi ba. Da Ajiram ta takura mata sai ta fashe da kuka..... JAMA'AH KUN JI MUTUNIYAR YAU HAR DA KUKA?? TO AKWAI ƘURA FA! MENENE SILAR FARA SAUYUWAR ƳAR IYA? A TUNANIN KU SAUYI NE YA FARA SAMUWA? ANYA ƳAR IYA ZATA IYA KARATUN NAN??? MUJE ZUWA ƳAN AMANA KU CI GABA DA ZUBO COMMENTS INA ZUBA MUKU UPDATE! Oum Zainab ce😍💋💫 Garkuwar Nazari Writers. [5/1, 1:14 PM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘‘19&20’’’’’ Da Ajiram ta takura mata sai ta fashe da kuka. Ganin hakan yasa ta ƙyale ta tare da ɗumbin tambayoyi a ƙasan ranta. Yinin ranar haka ya Ƴar Iya ta shafe shi tare da sabuwar ƴar uwarta Aunty Ajiram ba tare da ta ƙara shiga sabgar kowa ba. ★★★★★★★★★★★ *ALEE POV* A nutse ya koma part ɗin su ganin Sarah a parlourn duk sai yaji gidan ya fita a ranshi. Sarah ɗiyar uncle ɗin shi ne haka kawai yarinyar bata burge shi musamman saboda rashin kamun kai irin nata. Har ya juya zai koma part ɗin Nenne tunda can akwai extra room da aka ware don shi kasancewar shi ɗan ɗakin ta. Step ɗaya yayi ya jiyo Muryar Daddy da a lokacin ya fito daga bedroom ɗin Mom. “My son Ina kuma zaka je?” Babu yadda ya iya haka ya juyo yana sakin murmushin yaƙe don sam baya son ganin Sarah. “Sweet Daddy zanje mu gaisa da Granny ne, I don't even know u're back” Ya faɗa tare da shigewa parlourn. Side hug yayi wa Daddy tare da manna mishi peck a kumatu. Ita dai Sarah idon ta ƙyam akan Yaya Zaki ganin irin wani kyau da ya ƙara ga kuma girma da ya ƙara yi a zuciyar ta take faɗin har ya so ya fi yayan nashi ma girma. Ganin yayi wa Daddyn shi peck yasa ta saki wani murmushi, kiss is normal to her tunda su gaisuwa da kowa in zasu yi haka suke a India to ammah wannan ɗin yafi burge ta musamman da taga Daddyn nashi Nigerian ne amma kuma wayayye. Ji take kawai ina ma ita ta samu wannan dama Yaya zaki ya sumbace ta. “Baka ga Sarah bane, jiya tunda taji labarin ka dawo Nigeria ta bi ta dame su sai da suka barta ta taho nan, she'll stay with us sai ka tashi tafiya ita ma ta koma” Ran shi ne ya ɓaci a lokacin, don meyasa zata zo saboda shi, shifa ya tsani mutum maras kamun kai more especially mace. “Good morning brother” faɗin Sarah tana wani smiling as if tana tare da boo nata ne. Banza yayi mata sai ma ƙara haɗe fuska da yayi. “Kayi shiru son, ain't u happy to see her here?” Sai a Lokacin yayi murmushin gefen baki wanda ba lallai ka fahimci yayi shi. “I am” kawai yace tare da miƙewa. “Son....wait where are u heading to?” Narkar da face nashi yayi kamar wani ƙaramin yaro saying “Zan je na gaisa da Granny kafin tace na zo banje ba” ya ƙarashe cike da ƙosawa. Coz shi bai son yin magana a gaban yara musamman wannan good for nothing cousin sister ɗin tashi. “Alright son, we'll have time da dare coz I'll be attending Quranic Memorization walimah of a friend's daughter, and gobe da safe ina son zuwa Bauchi. Murmushi Yaya zaki yayi tare da kissing Daddy a cheek daga nan ya fice ya bar Sarah Baki a wangale. Directly part ɗin Nenne ya wuce bai tarar da ita a parlour ba kawai ya wuce kai tsaye izuwa bedroom nashi na part ɗin. Wayar shi dake aljihun jallabiyar ce tayi ƙara, da sauri ya fito da ita yana kwantawa bisa makeken bed ɗin shi. Picking call ɗin yayi ya kars a kunnen shi. Daga ɗaya ɓangaren aka yi sallama kafin ya amsa “Buddy ba kada kirki ko kaɗan, yanzu har ka shigo Nigeria bazaka sanar da Ni ba ehh?, Ka kyauta” A hankali cikin Muryar sa ta jaruman maza yace “Sorry Man, ɗazu isowa ta gida and na so kiran ka sai na manta” Kamar an sa shi dole haka yayi maganar. “Alright zan shigo zuwa yamma” “Ohk” daga haka bai jira me za'a ce ba ya katse ƙiran. Yusuf da ke office nashi a asibiti ya janye wayar daga kunnen shi yana ƙare mata kallo cike da mamaki ya furta “He'll never change, zan so naga lokacin da zaka faɗa soyayya, u'll suffer” ya faɗa yana cije leɓe. Yusuf kenan, aminin Hamma zaki ne, Abbien Yusuf abokin Daddy ne ƙut da ƙut haka Amma maman shi suna shiri da Mom sosai. Unlike Hamma Zaki Yusuf mutum ne mai fara'ar gaske ga kuma kirki uwa uba barkwanci irin nasa. Ta yadda halayen su ya banbanta kenan sai dai duk da haka suna matuƙar ƙsunar junansu. Bacci ne ya ɗauke Hamma Zaki ba shi ya tashi ba sai around 11:30am. Toilet ya faɗa ya wanko fuskar shi ya dawo. Wayar shi ƙirar Samsung Galaxy S24 ya ciro wacce tunda ya diro Naija ban ga yayi amfani da ita ba. WhatsApp ya shiga don ganin messages ɗin da ya tara. Yana kunna data kuwa suka fara zubowa kamar babu gobe, ganin sunyi yawa yasa ya ajiye wayar. Kusan 10 minutes messages na shigowa tukun ya ɗauki wayar don fara reply. Daga can ƙasa Hamma Saleem me yayi mishi magana, “Hi brother, please when you're going home text me so that I can book flight to spend the holiday with u” Emojij surprise ya tura sannan yayi typing “Sorry Dear, I'm already home, banga ni da wuri ba”. Haka yayi ta replying messages ɗin da yaga suna da muhimmanci saurann kuma yayi ignoring coz mostly Ƴan mata ne ke mishi safe journey sun ƙira wayar shi bata tafiya, wasu kuma neman soyayyar shi suke yi. Shi har mamaki yake yadda mace zata zubar da mutuncinta ta tunkari namiji wai tana son shi abun haushin ma wasun kamar Mayu...duk da baya buɗewa bare ya gani amma yakan ga subject ɗin. Tsaki yayi shi kaɗai jin hayaniya kamar ana faɗa. Rashin son hayaniyar yasa ya fito saboda ya koma part ɗin su. Karo da Najma yayi tana bugun Yesmeen wai tayi mata rashin kunya, ita kuma duk dukan da tayi mata sai tayi Allah ya Isa. Duk tsiyar da suke shukawa basu san ya dawo gida ba sai da suka ji mayetaccen ƙamshin sa. Kamar a mafarki da haɗin baki su duka biyun suka juyo. Ganin shi tsaye bakin ƙofar bedroom nashi yasa suka fara Ƴan kame-kame. Najma da ke son kuɓutar da kanta ko gaida shi bata yi ba ta fara “Eh...am...eee....damah Haa...ha...mma...za...ki Yesmeen....ce..ke...ja...min Allah ya isa wai don sunyi faɗa ita da Fauzah a mota na duka su.” Itama Yesmeen don son kuɓutar da kanta daga wahalar Hamma Zaki ta buɗe baki tana sakin hawaye. “Aaah Hamma Zaki ƙarya Adda Najma take ban zage ta ba.” Sai da ya samu waje ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun dake parlourn ya ɗago yana kallon su. Irin kallon da yake aika musu yasa Yesmeen risinawa ta gaishe shi. “Good afternoon Hamma zaki” Da sauri Najma ma tace “Good afternoon Hamma” Kamar ba zai yi magana ba coz ko gaisuwar bai amsa ba yace “Be on your kneels” Ba shiri suka zube, nan da nan su duka suka fara hawaye don sun saddaƙar yau sai kashin su ya bushe wurin Hamma Zaki. Maimakon ya hukunta su ma wayar shi ya ciro yana dialling number Hamma Saleem. “Assalamu Alykum” Fuskar nan tamke haka yayi wayar har ya gama suna zube a kan guiwowin su. Gashi sun matuƙar gaji ga yunwa uwa uba kuma zuwa Islamiyya su ƙara tarar da dukan Ustaz Umar. Nenne ce ta fito daga kitchen ɗauke da warmers ta fara jerawa a dining, kamar daga nesa ta hango shi da sauri ta fito, ganin Najma da Yesmeen durƙushe yasa ta juya ko ba komai yanzu zata samu salama tunda dodon su ya dawo, rashin kirkin su dole zasu daina. Sai da ta gama jera komai ta dawo parlourn, bata ko kalli inda suke ba ta wuce sama ɗon ta samu tayi wanka. Har ta fito suna nan yadda ta barsu shi kuwa Hammma Zaki wayar shi ma yake dannawa. Murmushi Nenne tayi tare da ƙarasawa gefen shi, “Damah kana nan ne yaushe ka shigo ko tun zuwan ɗazu baka fita ba” “A'ah” kawai yace daga nan yayi shiru. Ita ma Nenne bata sa a ranta zata ji wani amsan ba bayan wannan. “Son, food is ready” Daga haka ta juya zuwa dining. Kallon su Hamma Zaki yayi yace “Ku je kuyi LUNCH in kun dawo daga Islamiyya ina neman ku” daga haka ya wuce dining ba tare da ya ƙara bi ta kan su ba. Da ƙyar suka miƙe hawaye da majina shaɓe-shaɓe a fuskar su har abun tausayi,suna ɗingisawa suka ƙarasa bedroom ɗin su, sai da suka yi wanka suka sanya uniform ɗin islamiyya suka taho dining ɗin. A lokacin Nenne ma ta wuce bedroom haka Hamma Zaki ya fice. Yana fita gym room nashi ya wuce coz yana da tabbacin yanzu suke dinner a part ɗin su and he don't wanna see that creature. Ta ƙofar baya ya shiga bai fito ba sai bayan 1hour, yana fitowa jikin shi duk gumi ya wuce part ɗin shi. Wanka yayi ya shafa mai sannan ya sanya wasu light T-shirt da Trouser sannan ya fesa turare daga nan yayi sallah ya kwanta. Ɓangaren Najma da Yesmeen a duddurƙushe suka ci abincin don ba ƙaramin jin jiki suke ba gashi ita ma Nenne ko ci kanki bata ce musu ba. Bayan sun ci abinci suka fito wanda yayi dai-dai da fitowar sauran but wannan karon har da Ayra. A cikin motar kuwa duk sun yi wani iri da su, damuwar su basu san wani irin hukunci zasu karɓa daga Yaya Zaki ba. Fauzah ce ta kalli Yesmeen tare da ƙare mata kallo. “Yesmeen ya naga kin yi wani iri, ɗazu mun rabu ƙalau ko baki iya haddar Ustaz Umar ba ne?” Cike da jimamin abunda ya faru da su ta kalli Fauzah tana kwaɓe fuska ga wani hawaye da ya zo mata. Dukkan su hankalin su suka mayar kanta banda Najma da ta san MEH ya faru. Duk jira suke suji me ya samu talkative Yesmeen ɗin su. “Kun san cewa Hamma Zaki ya zo?” Abun da ta fara faɗa masu kenan. Idanuwan su suka fara zarewa take fuskar su ta bayyanar da ainihin tsoron da ke tattare da su. Ganin basu sani ba yasa ta fara basu labarin abun da ya faru da su. “Yanzu ma yace in mun dawo daga Islamiyya muje...Ni....baaaaan san wani hukunci Hamma Zaki zai ƙara bamu ba, kin san tun dukan da Adda Najma tayi mana ɗazu shi ya jawo? ” Ta ƙarasa wani hawayen na zirarowa daga idanuwan ta, tausayi ta Basu coz duk sun san waye Yaya Zaki, sun san irin punishment ɗin shi. Haka suka ƙarasa islamiyya kowa bai jin daɗin ranshi...su ma da basu da appointment da shi sun maida hankali saboda tsaro. Mom da tun ɗazu take jiran shi ya dawo suyi dinner shiru shiyasa tace ma Sarah tazo tayi nata. Ƙarar wayar shi ne yasa ya fara juyi alamun baccin bai ishe shi ba. Laluɓo wayar yayi yana picking ido rufe tare da kara ta a kunnen shi. “Hello Buddy, muna kan hanya ni da Sameer da Faruq.” Cikin Muryar bacci Yaya Zaki yace “Alright sai kun zo” Jin alamun bacci yake yasa Yaya Yusuf ƙara cewa “Buddy, Are u asleep” “Uhm kawai Hamma Zaki ya iya furtawa” “Please wake up now, ka ma yi sallah ne?”. Cikin baccin da ya fara sakin shi yace a'a I'm about to” “Oyah tashi manah, it's almost past four” Sallama suka yi Hamma Zaki yayi hanging call ɗin. Wanka yayi daga nan yayi sallah, yana idarwa ko gama kimtsawa bai yi ba wayar shi ta fara ringing. “Buddy, we're here...ka zo ka shigar da mu” “Idan gidan baƙon ka ne ka zauna a yadda kake bayan ka nuna wa sauran hanya.” daga haka yayi hanging call ɗin yana tsaki. Sun jima tare da su Yaya Yusuf, Barr. Sameer, da kuma Dr. Faruq. Sai wajajen maghrib suka fice tare zuwa masjid daga can suka wuce. [5/1, 1:16 PM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘‘21&22’’’’’ Sai bayan ya dawo daga masallaci su Fauzah suka zo yi mishi Barka da dawowa tare da sauran yaran gidan. A lokacin yana zaune a sofa dake parlourn, ɗauke da sallama a bakin su suka shigo. Ƙasa-ƙasa ya amsa sallamar tasu ba tare da ya ɗago ya kalle su ba sai ma hankalin sa da ya mayar ga system ɗin dake gaban shi. Ƙasan lallausan carpet ɗin dake shimfiɗe a parlourn suka tsuguna yayin da Hamma Zaki bai ma nuna ya sa su ba neh. Fauzah ce tayi ƙarfin halin faɗin. “Ina yini Yaya ka iso lafiya?” Banza yayi da ita ammah hakan bai sa sauran buɗe baki su maimaita abun da ta faɗa ɗin ba saboda sarai sun san halinsa, tsab in suka yi shiru suna jiran amsar yace zai hukunta su. Dukkan su miƙewa suka yi a sukwane zasu wuce suka ji gyaran Muryar shi. Nan suka dawo suka zube kamar bayi a gaban sarki. “Wa ya baki izinin tafiya?” Rarraba idanu suka fara wannan ta kalli wannan sai su sunkuyar da kai ƙasa. “Kayi haƙuri Yaya Zaki” Ayrah ta faɗa a tsorace. Wani irin kallo da yake bin su da shi yasa suka ƙara shiga taitayin su. “Yaya ko?, Haven't I warned u several times ku daina ce min Yaya?, Idan bazaku kira Ni da yadda yare yace a faɗa ba U better keep ur dirty mouths shut, ohk?” Duk wannan jawabin yana yin sa ne cikin harshen fulatanci, nan da nan na ƙara jin ya fi burge Ni fiye da da. Kawunan su suka ɗaga tare da faɗin “Toh Hammah Zaki” Banza yayi da su can yace “Better”. Sun share fiye da mintuna 30 a zaune ba tare da yace su tafi ba su kuma suna tsoron tafiya ya hukunta su. Duk zaman nasu gashi ya takura shi can ya ɗago yana musu alama da hannu da su tafi. Tsam suka miƙe suka wuce banda Najma da Yesmeen da suke durƙushe still. Lokacin su da suka ga yana ƙurewa yada Najma yin ta maza tace “Hamma Zaki ɗazu ka ce mu zo mu same ka Ni da Yesmeen” Har sai da ta cire ran tankawar shi taji yace. “Kuna ji na koh? Ke Yesmeen bana son rashin kunya kina ji?” Kai ta ɗaga sannan can ya ci gaba “Idan kika ƙara yi wa wanda ya fiki Allah ya isa to ranar Ni da ke a gidan nan.” Kamar wanda aka sa dole ya ɗanyi shiru na wasu mintuna dan ba ƙaramar jarumta yayi ba, har kan shi ya fara sarawa. “Ke kuma Najma banda cin zali kina ji na?, Idan anyi miki abu ki kai ƙara ba ki ɗau hukunci a hannun ki ba, ohk?” Kai suka kaɗa suna faɗin “Eh” Daga haka ya musu alama da su wuce. Ya jima zaune a parlourn yana aiki a nutse cikin system nashi, har lokacin da Sarah ta leƙo ta gan shi. Komawa tayi tare da sheƙa wanka ta sanya wasu nighties masu bayyana jiki, sai da ta fesa turare mai uban yawa ta fito. Tray ɗin abinci ta haɗa masa tayi sama sai ɗakin shi. Lokacin da ta shiga ya fito daga wanka daga shi sai bathrobe sai kuma towel ɗin da yake goge sumar shi. Kallon da ya aika mata yasa tana ajiye tray ɗin ta fita da sauri. Shi kuwa Hamma Zaki duk ranshi ya gama ɓaci, shin wai duk mata haka suke ne?, Basu da kamun kai gabaɗaya?, If yes to su sani shi babu budget ɗin aure ma a rayuwar shi. Bai taɓa ko da hasashen kan shi a matsayin wanda zai yi aure ba. (Nace ayi dai mu gani, in tusa zata hura wuta). Ko bayan dawowar Daddy da bai tarar da shi a parlour tare da Mom ɗin shi ba yasa yayi tunanin ko bacci yayi tunda ba wani hutawa yayi ba. ★★★★★★★★★★★ *ƳAR IYA POV* Wasa wasa sati guda kenan Ƴar Iya bata shiga sabgar kowa ba haka babu mai shiga tata saboda tsoro. Aunty Ajiram kaɗai ke samun magantuwa da ita cikin sauƙi kuma Alhamdulillah su Ƴar Iya cikin satin nan an iya ABCD zuwa Z wanda duk ƙwarin guiwar ta same ta ne daga Aunty Ajiram. Wasu lokutan takan ƙarfafa mata guiwa da rayuwar birni tuni Ƴar Iya an fara dagewa da karatu. Malaman ma sukan yi mata uzuri duk iya shegen da zata yi basa tanka mata, idan kuma aka samu matsala sai su nemo Aunty Ajiram. Dawowar su daga classroom kenan zasu je dining, Ƴar Iya babu abinda ke damun ta irin rashin cin abinci isasshe, sai a wani zuba mata abincin da ko baki baya wuce mata bare ya ƙarasa wuya har ya shiga ciki. (A faɗar ta kenan). Bayan an zuba musu sun cinye taji bata ƙoshi ba ai kuwa ta ɗauki bowl nata ta koma wurin matar da ke serving nasu. Ba tare da tace komai ba ta miƙa bowl ɗin da nufin a ƙara mata. Abun ya ɗaurewa mai raba abincin kai don ita a tsawon aikin ta a nan almost 12-13years Bata taɓa zuba abinci wani ya dawo da sunan ƙari ba. Kallon mamaki take bin Ƴaƴan Iya da shi ko ina dalili gashi da gani sabuwar ɗaliba ce don bata san ta ba. Students da basu bar dining ba tsayawa suka yi suna ganin ikon Allah, don kuwa so suke suga wannan drama ta Mama Jebu da Angel 👼 (Sunan da suka bata kenan don wannan basa mata kallon mutum cikakkiya). Basu san ya aka yi ba kawai suka jiyo Muryar ta tana faɗin “Kinga bigi-bigi bombom ki ƙara min bai ishe Ni ba” Dariya students ɗin suka yi jin sunan da Angel ta ƙira Mama Jebu da shi, ai kuwa sunan ya dace da ita. Mama Jebu irin matan nan ne manya manya masu ƙirar maza, gata da ƙaton ɗuwawu don kuwa da ƙyar take tafiya kawai ƙarfin hali ne da neman halal ya danne ta har take iya wannan aikin na raba abinci wa ƴan makaranta. Kallon banza Mama Jebu ta aiko mata tana faɗin “Ke amma sabuwar ɗaliba ce naga sai wani karambani kike yi?” Ƴar Iya bata kula ta ba saboda Aunty Ajiram na gwaɓar ta kan ta koyi haƙuri thatz why ta ƙara miƙa bowl ɗin ta gaban Mama Jebu. “Jiran ki nake bigi-bigi bombom” Ai kuwa sai a lokacin Mama Jebu taji sunan da sabuwar ɗalibar ta ƙira ta da shi. A hasale ta zagayo daga gaban tukunyar tayi kan Ƴar Iya. Ƴar Iya da bata yi tsammani ba kawai taji dundu a bayan ta. Babu shiri ta janyo robar yaji da ta gani a gefen tukunyar, bata tsaya ɓata lokaci ba ta ɗiba ta watso wa Mama Jebu a ido. Ihu Mama Jebu ta saka “Wayyo Allah na na shiga uku, jama'a ku kawo ɗauki wayyoh wayyoh na shiga uku wayyoh ido na shikenan don Allah jama'a a taimaka min” Ja da baya Ƴar Iya ta yi ganin Mama Jebu na ihu tana sowa, ga kuma lalume-lalume da take yi ganin ta taɓo wani. Dariya sauran students suka fara wasu na madallah musamman foodies irin Ƴar Iya yayin da wasu ke jin tausayin ta amma babu damar taimaka mata, su je garin taimako Ƴar Iya ta dawo kan su?, A'a babu ruwan su. Ana cikin haka wata student ta lallaɓa ta tafi clinic don samowa Mama Jebu ɗauki. Ƴar Iya kuwa kujera ta samu tana babbaka dariyar ta. Bata yi aune ba taji Muryar Aunty Ajiram na doka mata ƙira. “A'ishatu A'isha” Bata amsa ba sai ta lallaɓa bayan Mama Jebu da ke rausa ihu jikin ta sharƙaf da gumi da hawaye har da majina. ta ɓuya, ƙara damƙo wani yajin tayi a hannun ta, a hankali ta fara ware zanin Mama Jebu ta watsa mata tare da arta a na kare. Bayan clinician ɗin yazo da ƙyar aka samu manya manyan students dake senior class suka tallafawa Mama Jebu aka wuce da ita clinic. Taimakon gaggawa aka bata amma ina ta kasa buɗe idanuwan ta. Duk wannan tsiya da Ƴar Iya ta tsula babu wanda yayi gigin kai ƙarar ta saboda tsoron abun da zai je ya dawo. Washegari da yamma dai da ƙyar idon Mama Jebu ya buɗe, duk ta bi ta faɗa har abun tausayi. Bayan ta ji sauƙi clinician ɗin ya tambaye ta meh ya faru da idon nata, garin yaya ta zuba yaji haka a ciki. Bayanin abinda ya faru tsakanin ta da sabuwar ɗaliba ta bashi tare da roƙon shi don Allah ya taya ta neman fada wurin Principal a samu a koru ɗalibar nan in ba haka ba zata iya kashe mutum wallahi. A yau ne kuma da yamma aka sallamo uncle Bello daga asibiti, babu laifi jikin sa yayi ƙwari kuma fuzge-fuzge da kuma surutai da yake yi duk ya daina sai dai ma wani tsoron Ƴar Iya da ya ɗarsu a kogon zuciyar shi. Bayan Ƴar Iya ta koma hostel Bata samu Aunty Ajiram ba hakan yasa tayi murna don ta san idan taji labarin abun da ya faru sai tayi mata faɗa. (Nace, aaah an fa samu ci gaba, su ƴar iya har da gudun magana...eh..lallai kam). Ganin bata samu AISHATU ba yasa ta yanke hukuncin dawo hostel. A kwance ta same ta tana sheƙa baccin ta hankali kwance, ƙarar gwartin ta ne kawai ke tashi. “Aishstu Aishatu”, Aunty Ajiram ta faɗa tana tapping bayan ta “Tashi mana Aishstu” Miƙa tayi ta tashi nan Aunty Ajiram ta tisa ta gaba akan abun da tayi wa Mama Jebu. Kuka ta saka ita wallahi sharri akayi mata ita da yau ko dining Bata je ba ma akan bishiyar mangwaro take. “Kuma tun ɗazu da na sauƙo daga bishiyar nan nan dawo na kwanta bacci, Aradu duk mai min sharri sai na hukunta shi” “Shikenan ya isa na yadda dake, sharri aka yi miki, is ohk stop crying” ta faɗa tana tapping bayan ta cikin sigar rarrashi. Sai dare aka ƙira Principal aka sanar da shi abun da ke faruwa, duk irin yadda yake tausayin Ƴar Iya da kuma jarrabawar da take ciki sai da ranshi ya ɓaci yana ayyana wa a ranshi wannan ai har da sakaci ba iya Aljanu ke saka ta yin hakan ba. Principal yayi alƙawarin zai ɗau mataki a kanta, saboda yana jin tausayin Baban ta shiyasa ya barta da wannan karan babu mai hana shi koran ta a school ɗin. Washegari da safe sai ga jiniya wiwiwi....wiwiwi.... Tun daga cikin hostel ɗin su ake jin ƙarar jiniyar, lokacin da yawa suke saka uniform don tafiya classroom. Bayan motar tayi packing dai-dai office na Principal, wasu daga cikin Ƴan sandan suka shiga. Bayan sun gaida Principal suka sanar da shi aiko su da ogan su yayi. Bai ɓata lokaci ba yace “Hostel zaku je kuce waye Angel, in ta zo sai kuce tazo zaku kaita wurin Baffin ta da Iya. Kai tsaye ku wuce police station da ita, ku kaita ɗaki mai duhu sannan ku hukunta ta sosai sai taji jiki tukun ku ƙyale ta sai ku dawo min da ita nan” “Alright ur wish is our command sir” Daga haka suka fito da Principal's office, Basu tsaya ko ina ba sai hostel, a lokacin Ƴar Iya tare da Aunty Ajiram da ke riƙe da hannun ta suka fito daga hostel ɗin zasu wuce classroom. Alama police ɗaya yayiwa Aunty Ajiram da tazo Saboda gargaɗin Principal Akan yarinyar na da hatsari gaske. Bayan Aunty Ajiram da Ƴar Iya sun ƙaraso yace “Please sisters ku shiga hostel ɗin ku kuce Angel ta zo” Shaye da mamaki suke kallon police ɗin............... TOH INA TEAM ƳAR IYA, YAU FA ZAKU HAƊU DA GABAN KU! KO ME ZAI FARU? ZA'A TAFI DA ƳAR IYA POLICE STATION, KO A CAN NE ZATA YI HANKALI?? DUK AMSOSHIN KU SUNA A TARE DA ALƘALAMIN DIAMOND LADY 💎. COMMENT &SHARE PLEASE! [5/1, 8:11 PM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘‘23&24’’’’' [Ƴan uwa na masu albarka ina muku nasiha da ku yawaita yin sadaƙa. Ko kun san irin alkhairin da ke tattare da sadaƙa musamman gare mu mata?. TOH bari kuji wani hadisi. Daga Abi Sa'eed Alkudriyyu yace: Annabi tsira da aminci su ƙara tabbata a gare shi ya fita ranar sallar idi ƙarama ko babba zuwa wurin sallah, sai ya biyo ta wurin wasu mata daga wurin sai ya tsaya yace: «Ya ku taron mata, ku yawaita sadaƙa, domin mafi yawancin ku kun kasance ƴan wuta» Bukhari ya rawaito. Mai buƙatar ƙarin bayani game da wannan hadisi tana iya yi min magana kai tsaye a nan WhatsApp +2347061707238]. Shaye da mamaki suke kallon police ɗin da ya basu wannan saƙo. Shiru suka yi su biyun, ganin sun yi shiru yasa police ɗin faɗin “Kinga sister ki ƙira mana ita ba komai zai faru ba wurin Baffin ta za'a kai ta” Jin an ambaci Baffi yasa Ƴar Iya faɗin “Toh ai gani a gaban ku, Aradu da na fita kilasmum da wuri da bazan ga Baffi na ba, Allah sarki banda Iya zan gani?” Ta tambaya tare da marairaice fuska. Murmushi police ɗin yayi yace “Har da Iya duk suna jiran ki, maza shigo Mu tafi.” Ya faɗa yana nuna mata wurin da suke ajiye masu laifi in zasu tafi. Aunty Ajiram haka nan taji babu daɗi daga nan tayi wa Ƴar Iya sallama. “Ki gaida min Baffi da Iya kinji A'ishah?” Kai ta gyaɗa tare da zagayawa don shiga wurin da aka nuna mata. Ganin polisawa da yawa kusan biyar zaune suna pointing mata wani ɗan wuri a tsakiya yasa ta Banka musu harara. “Kutumelesi, Aradu ni ba Ƴar Iska bace da zan shiga tsakiyar ku, sai dai ku koma can ku cakuɗu in ba haka ba na faɗawa ogan ku” Ƙasa magana suka yi saboda tsantsar mamaki ganin yarinya ƙarama na tsula musu tsiya son ranta, ko mutuncin uniform ɗin su bata gani. A harzuƙe ɗaya daga cikin su ya buga mata tsawa “Oya get in or else I'll shoot u to death” Ya faɗa yana saita ta da wata pistol ɗin roba. Ba shiri ganin bindiga ta shige ciki. Cikin ranta duk tsoro ya cika ta har ta fara tunanin satar bindiga. “Wannan fah irin bindigar nan ne da ake kashe mutane da ita a TV, kutt, Aradu don wurin Baffi zasu Kaini amma sai na sace ɗaya saboda ƴan banzan mutane. ★★★★★★★★★ Zaune suke a katafaren dining area na gida, Daddy, Mom, Sarah sai kuma Fauzah. Babu abun da ke tashi sai ƙarar cokali yayin da na jiyo sautin taku daga staircase na gidan. Sanye yake cikin wata haɗaɗɗiyar Black suit da farin shirt a ciki sai farin necktie. Sumar Kan shi ta sha gyara sai wani ƙyalli take kamar wanda ta fito daga rijiyar mai, Black shoe ne a ƙafan shi sai kuma wani uban ƙamshi da yake yi na turaren _majesté impériale_ wanda tuni ya sanar da mutanen dake dining ɗin isowar shi. Mom da tunda ta fara jiyo ƙamshin sa ta daina cin abincin sai sakin murmushi take haka Daddy yayin da Fauzah taji kamar ta tashita bar wurin. Idon Sarah ƙyam a kan shi yayin da shi kuma babu abinda yake kallo sai frame ɗin dake kallon shi, fuskar nan a tamke kamar kullum ammah hakan bai hana kyawun shi fitowa ba. Yana ƙarasawa dining area kusan Mom ya fara zuwa yayi mata side hug tare da peck a cheek nata “Good morning Mom” Murmushi tayi tana faɗin “Morning first love, how's your night?” “Absolutely fine one” “Alhamdulillah” Daga nan ya ƙarasa zuwa wurin Daddy, kamar yadda yayi wa Mom haka suka gaisa da Daddy tukun ya samu kujerar shi ya zauna. Mom da kanta tayi serving nashi cips and fried egg sai Hot coffee. A hankali Fauzah tace “Good morning Hamma Zaki” Ba tare da ya ɗago ba yace “Morning” Sarah ma ta gaida shi ya amsa kamar baya so. Fauzah ce ta fara barin dining ɗin ta ɗauko school bag nata tayi waje, Sarah ma ta miƙe zuwa bedroom ɗin ta. Ya rage saura Mom da Daddy. Daddy ya kalli Hamma Zaki ɗauke da murmushi a kan fuskar shi “Daddy's love jiya na dawo da dare, I was thinking of meeting you a parlour sai na tarar kayi bacci ma” Shima murmushin yayi yace “I'm sorry Daddy, I'll squeeze and have time with u” Daga haka ya miƙe yana waving hands “Bye, Mom and Daddy” Yana fita Joseph ya zo ya amshi Briefcase nashi zuwa mota, daga nan driver ya ja motar sai Barrack. Bai dawo ba sai wajen yamma saboda ayyukan da ke gaban shi. A wahalce ya dawo, yayi wanka sannan ya wuce bedroom ɗin Mom. Saman sallaya ya same ta alamar sallah tayi. Sallama yayi ya shige daga nan ya samu gefen sallayar ya ɗan kwanta yana ɗora kanshi akan cinyar ta. Murmushi Mom tayi tace “Welcome back Son” “Thanks Mom” “Ya aikin dai, da alamu ka gaji da yawa, muje kaci abinci” Kan shi ya jijjiga saying “No Mom, Ina cake ɗin da kika yi baking?, Shi nake so sai Hot coffee” “Ohk ɗaga Ni na haɗo maka” Kwaɓe face yayi yace “Nifah Mom ban gaji da cinyar ba, baki ganin ina jimawa ban hau ba...da na hau kuma sai ki tashe ni” Murmushi tayi tana jan kumatun shi “Toh shikenan sai ka zauna da yunwa haka kake so?” “Auchh..sakar min kunnen mana ko so kike ya cire saboda yafi naki kyau?” “No yi haƙuri Son Bari na haɗo maka.” Dining ya wuce ya jira Mom sai gata ɗauke da cakes cikin bowl sai kuma hot coffee a kan tray. Da kanta tayi feeding sakaltaccen yaron ta daga nan ta kawo mishi batun Sarah coz sun taɓa magana da Mommyn Sarah ɗin wai tana so su haɗa yaran aure. Mom ɗin Sarah cousin ɗin Mom ce. “Son Kun gaisa da Sarah kuwa?, Ta zo ne saboda kai Please ka ke sakar mata fuska” Fuskar shi ya ɓata yana tura baki “Wai Ni Mom meyasa kuke son cusa mutane cikin rayuwa ta, bana buƙatar kowa bayan ku don Allah Mom ku daina zubo mutane rayuwar classic yaron ku” Dariya Mom tayi coz Bata son duk wani abu da favourite ɗin ta baya so. “Is ok Son, na daina but ko ba komai Sarah is your sister” “I know, all I hate from her shine rashin kamun kanta, but if she'll change me too I'll change” Bayan ya gama ci ya ce ma Mom zai je garden zuwa maghrib. ★★★★★★★★★★★ *POLICE STATION* Suna isa duk suka dire haka Ƴar Iya ma tayi ganin yadda suka yi. Kallon su tayi tace “Ina Baffi?” Banza suka yi mata yayin da biyu daga ciki suka fizgo hannun ta, tana turjewa suna ja har suka isa ciki. Da yake an riga an musu bayanin me zasu yi tuni suka shigar da ita Cell. Fitowa suka yi don su nemo abun da zasu hukunta ta da shi bayan sun sakawa ƙofar kwaɗo da key. Few minutes suka dawo ɗauke da Koboko (Dorina) irin wacce ake jibgar Dawaki da ita, suka haɗo da bucket cike da ruwan sanyi har wani tururi yake yana fitar da raɓa. Ƴar Iya da ke cikin Cell hankalin ta baya kan su duk tunanin ta Baffi zasu ƙira mata. Har suka buɗe ƙofar bata sani ba, babu zato babu tsammani police ɗaya ya janye Hijabin check ɗin ta, tuni ta fito daga duniyar tunani ta fuskanci duniyar asali. Tana juyowa kuwa ɗayan ya fizge rigar ta da sauri yayin da ɗayan ya zame wandon. Tsabar mamaki da ya cika ta rasa me zata yi ma tayi. “Kutumar Uba, me nayi muku zaku cire min kaya na?, Dama ba gun Baffi zaku Kaini ba ku Ƴan Iska ne?” Bata aune ba taji ruwan sanyi a jikin ta...tuni ta fara rawar sanyi, yo ita wankan ma yaushe tayi shi ballantana ma da ruwa irin wannan. Har abun tausayi yadda take rawar sanyin ammah su basu ji ba, wani bucket ɗin suka ƙara janyowa suka ƙara tsula mata shi tas. (Toh fah Ƴar Iya yau kin gamu da gamon ki). Sai da suka tabbatar sanyin ya ratsa ta suka ciro dorinonin su suka fara sharɓa mata, irin yanayin da take ci ba zata iya ƙwatar kanta ba saboda zazzaɓin da ya rufe ta lokacin ɗaya. Dukan ta suke yi su biyu da dorinonin su tun tana ihu har Muryar ta ta dishe ta daina fita da kai. Duk da haka maimakon su sarara mata saboda ƙarancin shekaru irin nata sai suka ci gaba da dukan ta har sai da ta daina motsi. (ALLAH SARKI, ƳAR IYA AN MUTU) A haka suka fice suka barta. Ta share kusan awa biyu zuwa uku a suke kafin ta farfaɗo, lokacin kuma zazzaɓin da take ji ya sake ta tana buɗe idon ta ya sauƙa a kan baƙin ɗakin da take, nan ta fara tariyo abun da ya faru da ita. Babu shiri ta fara miƙewa, a hankali ta janyo wandon ta da har ya bushe da kuma rigar ta ta ƙwama, bata ƙara bi takan hijabin ba ta fara ƙoƙarin buɗe ƙofar sai dai ƙyam ƙofa taƙi buɗuwa alamun akwai padlock jiki. Ba tare da ta damu ba ta fara jan ƙofar da iyakar ƙarfin ta. Kyawawan ja guda uku tayi lock ɗin jikin ƙofar ya ɓalle, wangalewa tayi ta fito. A reception ta fara tarar da wasu polisawa saboda haka tayi kansu ba tare da ɓaga lokaci ba. Wani katako ta gani a gefe ai kuwa ta wawuro shi tayi kan su. Tsabar mamaki da jin kai irin na polisawa suka ƙame suna jiran ganin ƙarshen iskancin yarinyar. Gani suke yi kamar ƙaramar mahaukaciya ce shiyasa kowa yayi ƙyam. Ba tare da wani tunani ba Ƴar Iya ta sa hannu cikin aljihun ta da ta cika shi da yashi ta watsa a fuskar su. Nan fa suka farga zasu fara guduwa, ƙara ciko hannun ta tayi ta watsa musu. Sai da ta tabbatar idanuwan su sun raunana ta janyo na baki-baki tare da buga mishi katakon a ƙafar hagu, ta juyar da shi dama ta ƙara buga mishi nan da nan ya cilla ƙara tare da faɗuwa yana sowa. “Wayyo ƙafa ta na shiga uku wayyoh Allah wayyoh shikenan ta karya Ni wayyo” Jin ihun da ɗan uwan su ke yi yasa suka far lalume zasu buɗe office ɗin da ke kusa sai dai ina ta riga ta far musu da shiri. Haka ta ringa bugun ƙafafuwan su da katako tana yasar da su, polisawan da ke bakin Gate ne suka jiyo ihu nan da nan suka shigo ciki don ganin me yake faruwa. Kafin shigowar su kuwa ta gano fuskar mugayen da suka buge ta ai kuwa tayi kan na farko. Hannun sa na dama ta samu ta buga mishi katakon da ƙarfi sannan na hagu daga nan ta buge masa ƙafafuwa kamar yadda ta bugawa sauran. Haka ta jawo ɗayan shima ta fara bugun shi kamar yadda tayi wa ɗayan sannan ta bar shi ƙasa ta dawo gefe tana maida numfashi. Ganin aika-aikar da yarinyar tayi yasa duk suka fara jin shakkun ta. Kallon su tayi tace. “In ba zaku kai ni gun Baffi na ba to ku mayar da ni sukul ni wurin Iya ta zan koma Aradu birni duk mungaye ne” Kuka ta raushe da shi kamar ba ita ce wacce ta nakasa waɗannan tarin ƴan sanda da sun kai takwas ba. A gaggauce suka fara kwasar ƴan sandan suna jera su cikin mota ba tare da sun bi ta kan Ƴar Iya ba. Kai tsaye asibiti suka wuce a nan aka tabbatar musu da cewa duk sun samu karaya a ƙafafuwan su biyu biyu sai waɗannan biyun da suka karye a hannayen su. Ƙiran DPO suka yi suka sanar da shi, nan da nan shima ya tsorata da al'amarin yarinyar yace su mayar da ita makarantar su kafin ya zo asibitin zasu yi magana da shugaban makarantar su. Ba musu da suka koma police station suka nemo Ƴar Iya suka saka ta a mota sai school................. Ina godiya sosai da addu'oin ku masoya na, masu ƙira da masu tura saƙo duk na gode Allah ya bar ƙauna. Babu daɗin yadda kuka damu da Ni, ina matuƙar son ku da yawa da yawa. MU HAƊU GOBE DON JIN YADDA ZATA KAYA. KUN JI ƘUDURIN ƳAR IYA NA KOMAWA GUN IYAR TA DA BAFFI BAYAN TA KWASHI KASHI GURIN POLISAWA. TOH FAH, GA KUMA DAI AN FARA SAMUN SAUYI TA ƁULLO DA TSIYA. KU CI GAVA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY 💎 DON NISHAƊANTUWA DA KUMA WA'AZANTUWA. DIAMOND LADY 💎 CE TOH ƳAR IYA NACE ALLAH YA TAIMAKA. COMMENT AND SHARE FISABILILLAH! [5/2, 9:03 PM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘‘25&26’’’’’ [Annabi tsira da aminci su ƙara tabbata gare shi yace: «Akwai wasu kalmomi guda biyu masu soyuwa wurin Ubangiji, masu sauƙi akan harshe, masu nauyi akan mizani, sune _subhanallahi wabihamdihi subhanallahil azeem». Bukhari da Muslim suka ruwaito. Ya ke Ƴar uwa mai albarka ki lazimci furta waɗannan kalmomi da basu da nauyi da wahala wurin faɗi domin mizanin ki ya nauyaya ranar sakamako] Ba musu suna komawa police station suka Iya suka saka ta a mota sai school. Kafin Isar su DPO ya ƙira Principal, ranshi a ɓace bayan Principal yayi picking call ɗin ya fara magana “Haba Misbahu, fisabilillahi wa rasulihi me ka aikata haka?” Kwantar da murya Principal yayi yace “I'm sorry sir, wallahi an samu matsala ne” “Matsala kake cewa eh, matsala koh?, To bari kaji in faɗi maka Yarinyar nan ba full mutum bace” “Ban gane ba full mutum bace, kaga kofato ne a ƙafarta” Principal ya faɗa yana rarraba idanuwa. Jin batun Principal yasa ran DPO ƙara ɓaci yace “Eh kofato kake magana Misbahu?, Ana maka magana ta aika-aikar da yarinyar tayi kana batun kofato?” “I'm sorry sir, kayi haƙuri ka faɗa min me tayi don Allah” Principal ya faɗa yana kwantar da murya. “Toh bari kaji na faɗa maka yanzu polisawa takwas ne a karye, shida ƙafafuwan su biyu kuma hannu da ƙafa” ya faɗa cike da ƙosawa da jin zancen. Principal da yabi ya ɗimauce, rasa abun faɗa yayi sai kawai yayi shiru. “Ohk ba zaka ce komai ba Misbahu, lemme hang off the call” ya faɗa cikin hasala. “Aaah ehma sir mamaki kawai nake yi wallahi, how can that small creature defeat nearly 8police officers?, Da farko ina tunanin dabara ce da ita ammah yanzu na gano tabbas ba mutum ɗin bace.” Nan Principal ya bawa DPO dabarin Ƴar Iya Tun ranar zuwan ta zuwa wannan lokaci. Cike da fargaban abun da zai ƙara faruwa DPO ya bawa Principal shawara kan ya mayar da ita gida lallai-lallai in ba haka ba duk matsalar da ya shiga shi ya jawo ma kan shi. Yana katse ƙiran ya ƙira Baffi kan cewa ana neman shi da gaggawa. Duk da cewa yammaci ne hakan bai hana shi amsawa da Toh ba. Nan da nan ya ƙira Shayibu don ya kai shi makarantar. ★★★★★★★★★ *ƳAR IYA POV* Tun kafin motar ta gama daidaita tsayuwa Ƴar Iya dire tana wani muzurai. Da gudu ta arta sai hostel ɗin su, tana shiga ta faɗa kan Aunty Ajiram dake zaune alamun karatu ta gama. Kukan da take yi kuwa har abun tausayi nan fa kowa ya zubowa Angel Ido ganin. Yadda take kuka bilhaƙƙi, wasu na tunanin taci wahala ne wurin polisawa wasu kuma suna tunanin ta cutar da polisawan. Kowa dai jira yake yaji me ya faru haka. “Aishatu?” Aunty Ajiram ta ƙira ta cikin sanyin murya. Kukan da take yi ta ɗan tsagaita tana sauƙe ajiyar zuciya. “Aishatu me ya same ki kike kuka haka?” Shiru tayi in banda ajihae zuciya babu abinda take sauƙewa. Sai da ta koma dai-dai ta fara ƙoƙarin cire rigar ta babu ko ɓata lokaci, tana cirewa zanen dorinar da ta sha wurin polisawa ya bayyana. Ƙwalalo idanuwan su mutanen da ke room ɗin suka yi. Aunty Ajiram da ta rikice ganin irin shafin bulalar yasa hawaye fara zubo mata. Cikin raunatacciyar murya tace “Aishatu dukan ki suka yi?” Sai a lokacin Ƴar Iya ta samu bakin magana. “Ni wurin Iya na zan koma Aradu, duk Ƴan birni mugaye ne saboda haka na haƙura yanzu da ABCD ɗin in na ƙara girma a can ƙauyen mu sai na dawo.” “Yi haƙuri A'ishah kiyi zamanki, babu wanda ya isa ya ƙara taɓa ki har ji gama. In Kika koma wurin Iya yi ba zaki zama Ƴar Gayu ba” “Ni na fasa zama Aradu, in kuwa. Ba'a kai Ni wurin Iya ta ba Aradu kashe mutane zan far...” Rufe mata baki Aunty Ajiram tayi saying “Is ok za'a kai ki wurin Iya tunda baki son zama kusa da Aunty Ajiram” ta ƙarasa tana juya mata baya. “Halan kin ci wani abun a can koh?” Sai a lokacin cikin ta ya fara ƙugin yunwa, tuni ta jawo Bagco nata ta ciro wani ƙunshin ƙanzo,bata tsaya jiƙa shi ba kuwa ta cinye shi tas. Tana gama ci kuma ta tayar da rigima ita fa yanzu zata tafi, da ƙyar Aunty Ajiram ta lallaɓa ta ta Zauna kafin Baffi yazo su tafi. , ★★★★★★★ *ALEE POV* Tunda ya dawo ya zama busy, gaba ɗaya ayyukan da yake son kammalawa sun yi mishi yawa. Batun wani attack da aka bar case ɗin a hannun shi yasa ya zama kamar mahaukaci sai dai ba zaka taɓa fahimtar wani aiki yayi mishi yawa saboda irin yadda koyaushe fuskar shi take a kame. Motar shi ce ta danno hanci zuwa mansion nasu. Ko jiran Joseph bai yi ba ya fice abun shi. A parlour ya tarar da Sarah taci ado, ba laifi Sarah kyakkyawa ce kamar Mommyn ta. Sanye take cikin traditional kayan su na blue sari, hannun ta fari tas sai jan lallen da ya ƙara haska su. Kallo ɗaya yayi mata ya kau da kan shi tare da wucewa bedroom ɗin Mom. Ganin tana toilet yasa ya fito ya wuce bedroom ɗin shi. Wanka yayi ya sanya light kaya tare da fesa turare. Ya zo zai fito har ya murɗa handle na ƙofar wayar shi tayi ringing. Ganin number Major Kabir Joda yasa yayi picking da sauri. “Hello, Is Captain Alee on the line” “Yes sir, anything wrong?” Cikin muryar tashin hankali yace “Waɗannan mutanen sun ƙara attacking ƙauyen nan yanzu nayi recieving call daga sojojin da muka tura, sun ce abun babu kyau” “On my way, yanzu zamu shirya tafiya mu far musu” Daga haka yayi hanging call ɗin. Komawa bedroom ɗin shi yayi ya sauya dressing nashi zuwa uniform ɗin su na sojoji. Bai wani ɓata lokaci ba ya rataya bindigar sa ya fice. Mom da ta bi ta damu tun ɗazu take zaman jiran dawowar shi ammah shiru yasa ta fito. A parlour ta tarar da Sarah zaune kan sofa. Murmushi Mom tayi mata, cikin harshen Hindu tace, “Sarah, brothern ki bai shigo bane” “Ya shigo har bedroom naki sai ya fito ya wuce sama. Bai ma daɗe ba ya fito inaga wanka yayi sai kuma ya sanya uniform ya fita cikin tashin hankali” Hankalin Mom in yayi dubu to ya tashi, fara jera mishi calls tayi ammah baya picking daga ƙarahe ma wayar ta daina shiga. Tuni zancen ya bazu. Duk irin tashin hankalin da suke ciki haka granny ta sanya su gaba tana kuka duk ta ƙara ɗaga musu hankali. “Hande enbone, Ni Shatu yau shikenan ɗan jikan nawa aka rasa, wayyo ni ƴar nan, wallahi Muhammadu, Suraja har da kai Bello ku nemo min jika. In ba haka ba wallahi kar ku dawo min gida” Haka tayi ta surutai tana ƙara ɗaga musu hankali. Lokaci ɗaya gidan ya koma tamkar maƙabarta, Yaya Saleem ma a ranar ya diro hankali tashe. Har dare shiru number Hamma Zaki baya tafiya, su Fauzah da ƙyar aka lallashe su suka yi shiru coz duk irin yadda yake haɗe musu da tsare musu suna matuƙar ji da su saboda yadda yake hidimta musu. Ɓangaren Hamma Zaki yana zuwa can Barrack a nan ya haɗa tawagar sojoji sannan ya haɗa musu kayan aiki. Kai tsaye wucewa suka yi zuwa ƙauyen da tun kafin su shiga suke jin ihun yara ga kuma ƙarar bindigu dake tashi. Suna cikin tafiya basu kai ga ƙarasawa ƙauyen ba suka ji tsit kamar ba daga nan hayaniya da ƙarar ke tashi ba ɗazu. Hamma Zaki da shine commander a wannan gwagwarmaya, tsayar da shigar su ƙauyen yayi, wasu har suna a shiga ya dakatar da su saying “Suna da matuƙar wayo Ƴan ta'addan nan saboda haka ba zamu shiga yanzu ba, idan muka shiga yanzu ba ma samun su zamu yi ba saboda sun gama na yau. So we'll stay here kamar bamu zo ba, hakan zai sa su ƙara samun kwanciyar hankali gobe ma su kai hari, ammah yanzu...” ya faɗa pointing to motar farko da a ciki akwai likitici sannan yaci gaba “Ku zaku shiga ku fara treating waɗanda suka raunata, mu zamu jira a nan. And kuyi taka tsan-tsan kada su fahimci mun zo da ku” Basu yi musu ba suka shiga suka fara treating waɗanda suka raunata. A nan suka tabbatar da cewa waɗannan ƴan ta'adda ba ƙananan mugaye bane, sun kashe mutane da yawa wanda yawancin su maza ne sai kuma waɗanda aka raunata suma kuma da yawa. Gaskiyar Hamma Zaki ƴan ta'addar na da basira don kuwa babu wanda ya ƙara taɓa kowa cikin ƙauyen sai ma samun maɓoya da suka yi. Dr. Faruq yana ta saka musu ido ba tare da sun sani ba bare su fahimta coz yana shiga ya cire labcoat da wndon shi ya sanya riga ƴar shara da wando da ya ara a wani gida bayan sanar da su shi ɗin likitane. Haka ya yawata cikin ƙauyen yana ganin maɓoyar ƴan ta'addar ba tare da sun gane ba. Sai yamma ya dawo zuwa gidan da aka basu don kula da majinyatan. Da yamma su Hamma Zaki ma suka samu shigowa ƙauyen su ma ammah basu shigo da mtar su ba sai bindigun su da suka shigo da su. Wani ɗan gidan kara suka samu suka maƙale a ciki har lokacin sallar maghrib, a nan kuwa suka yi sallah sannan suka yada zango. Su kan su jama'ar ƙauyen basu san da shigowar su ba bare kuma ƴan ta'addar su fahimta. Irin daidai lokacin da suka tada tsiyar au jiya irin shi suka fara yau. Sun fara sake bindigu suna kashe mazajen ƙauyen ai kuwa sojojin nan suma suka afka musu. Nan da nan fili ya kacame, waɗannan na kaiwa wannan farmaki har dai suka daina farmakar ƴan ƙauyen. An shafe fiye da Hour uku ana wannan faɗa yayin da Hamma Zaki ya nuna ainihin jarumtar sa, yadda yake harbi a dabarance kaɗai zai sa ka fahimci shi ɗin ƙwararre ne ga kuma yadda yake sa ƙarfin shi wani lokacin. Duk irin raunin da ya samu bai sa ya sare ba sai ma ƙara ƙaimi da yayi, tuni suka ƙarar da ƴan ta'addan tass. Sai a lokacin suka lura da Commander nasu, nan aka fara treating raunukan shi daga nan suka kwashi hanya har inda motocin su suke ba tare da an rasa rayuwar soja ko ɗaya ba. (Ya ubangiji ka ƙarawa sojojin mu lafiya tare da imani ka kuma kare su daga sharrin waɗanda Basu Son kawo cigaba, Amin). ★★★★★★★★★★ *ƳAR IYA POV* Rikicin da ta tayar ne yasa Aunty Ajiram ɗaukar da suka wuce office ɗin Principal. Jin batun Ƴar Iya yasa ranshi yin wasai ko ba komai yasar da wannan ƙwallon mangwaro zai zo da sauƙi. Baffi bai iso ba sai wuraren yammacin ranar basu wani ɓata lokaci ba saboda yadda Ƴar Iya da kan ta ta nuna tana son tafiya. Aunty Ajiram kuwa kamar ta tsala ihu haka ta je ta kwaso Bagco na Ƴar Iya bisa umarnin Principal. Bayan ta kawo ta ja hannun Ƴar Iya gefe ta sanya mata wani zobe mai kyan gaske sannan ta riƙe hannun ta. Idanuwa Ƴar Iya ta zuba mata yayin da zuciyar ta ke mata wani iri ammah kewar Iya yasa dole zata bar Aunty Ajiram. Hawayen fuskar ta ta goge sannan ta fara magana cikin sanyin murna “Aishatu, ga wannan zoben na baki kyautar sa kasancewar bani da wani abun da zan baki yanzu, kimin alƙawarin kasancewa da zoben har zuwa ranar da Allah zai ƙara haɗa fuskokin mu. Ki gaishe da Iya” Tana kaiwa nan ta goge hawayen da ya ƙara zubo mata sannan ta saki hannun Ƴar Iya ta juya. Daga nan babur ɗin su Ƴar Iya yayi horn, juyawa tayi ta ɗale kamar yadda suka yi a zuwa daga nan mashin ya tashi sai Gallara......... *WANNAN SHI AKE ƘIRA KOMA BAYA, BAHAUSHE YA CE WAI GA CI GA KWANAN YUNWA, TOH ƳAR IYA, SADUWAR ALKHAIRI, IN DA RABO KUMA WATA RANA KI ƘARA HAƊUWA DA AUNTY AJIRAM ƊIN KI.* *MU HAƊU GOBE DON JIN YA RAYUWAR ƳAR IYA ZATA ƘARE A GALLARA, SAUYIN DA TA FARA SAMU KO ZAI TAFI OHO...* *INA INNA ZALIHA NE?* *DUK AMSOSHIN KU NA TARE DA ALƘALAMIN DIAMOND LADY 💎* *KUCI GABA DA BIBIYAR ALƘALAMI NA* *COMMENT AND SHARE FISABILILLAHI!* [5/3, 7:23 PM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘‘27&28’’'’’ *[Gare ki ƴar uwa, ko kin san cewa na ɗaya daga cikin dalilin da yasa mata suka yi rinjaye cikin wuta butulcewa kyautatawar da mijin ki ke masu?* *Matso kiji ƴar uwa, butulcewa kyautatawar miji kamar dai yadda mata yanzu muka ɗauki abun kamar hali ..kowa tana da shi.* *Mijin ki zai jima yana ɗawainiya dake yana ƙoƙarin kyautata miki ammah da an samu matsala na rana ɗaya sai ki butulce kina faɗin _me ka taɓa yi min a rayuwa?_* *Wannan abu yanzu mata sun ɗauke shi sun yafa har wani tinƙaho suke yi...TOH maza ƴar uwa tun kina da sauran lokaci maza ko yada wannan ɗabi'ar domin kasancewa cikin ahlul jannah* *Allah Ubangijin yasa muna da rabo baki ɗaya*. Daga nan babur ɗin su Ƴar Iya yayi horn, juyawa tayi ta ɗale kamar yadda suka yi a zuwa daga nan mashin ya tashi sai Gallara. Tunda suka ɗauki hanya take famar zare ido tare da juya zoben da Aunty Ajiram ta bata yayin da wani ɓangare na zuciyar ta ke jin babu daɗi. Har ƙofar gida Shayibu ya kai su, daga suka dire. Ƴar Iya bata samu damar shiga da Bagco nata ba tayi ciki da gudu. A zaune ta tarar da iya bisa kujerar tsakar gida, da gudu ta faɗa kanta tana sakin kuka. “Iya ta bakiyi kewa ta ba neh?” ta faɗa bayan ta tsagaita da kukan da take yi. “Haba shalelen Iya ni ɗin ne kuwa nayi kewar ki, kullum sai nayi hawaye ina tunanin shalele na” Murmushi tayi tare da sakin Iya “Iya birni babu daɗi, akwai mugaye a sukul ɗin mu” Zare ido yayi tayi tace “Miye sukul kuma shalelen iya?” Dariya da shewa Iya ta saki lokaci guda. “Ayyiriri nanaye....lallai Iya na manta ashe fa ke ƴar ƙauye ce” ta dakata tana wani fari da ido kamar wacce ke gaban saurayin ta. Iya kam dariya tayi tana faɗin “Yo Ni kam ai nan ne iyaka ta sai ƙauyukan kewaye, ban taɓa zuwa birni ba shiyasa naso ke ki tashi a can kinga wata rana sai ki kai ni” Ta ƙarasa sounding serious. Dariya Ƴar Iya tayi tace “Iya kenan, to Aradu ƴan birnin nan mugaye ne barin ma masu baƙin kayan na, hegu kingan su ƙataye da su ammah sai da na basu kashi” Ta ƙarasa tare da kaɗa yatsa. Cike da ƙosawa iya tace “Yanzu faɗa min suku ne Kika ce ko sumul?” “Hhhh..... Kiji Iya wai suku😒😂, to ai ba haka ake faɗa ba, in Kika faɗa a gaban ƴan birni to dariya zasu yi miki” ta faɗa tana wani kaɗa kai ita ala dole ƴar birni. “Toh ai sai ki gyara min yadda nima in na shiga maƙwabta zanyi musu su san Shalele na taje birni” Murmushi Ƴar Iya tayi tace “Ai kuwa, to Iya ai sukul ake cewa ba suku ba” “Ayya sukwal” “Hahhhh. Iya ba sukwal ba sukul” “Ai to sukul” “Yauwa Iya ta yanzu dai-dai kika faɗa” Dariyar farin ciki iya tayi tace “Toh shi sukul ɗin me yake nufi?” Ta tambaya cike da ƙaguwa. Sai da ta juya kai kafin tace “Makaranta shine sukul ɗin” Haka suka yi ta shirmen su yayin da cikin gari ya ɗauka ai Ƴar Iya ta dawo. Wasu na farin ciki musamman A'i wasu kuma har sun fara kuka da kansu. ★★★★★★★★★ *ALEE POV* Bayan sun isa wurin da suka bar motocin su, kai tsaye suka shige tare da wucewa. Bayan sun isa waɗanda suka samu rauni aka miƙa su asibitin dake can for effective treatment yayin da Hamma Zaki yaƙi tsayawa. Bai samu kunna wayar shi ba ko da bayan sun dawo, saboda haka ya kunna tare da ƙiran Joseph, cikin mintuna kaɗan Joseph ya ƙaraso yayi driving Hamma Zaki gida. Tun kafin motar ta gama packing gaba ɗaya mutanen gidan suka iso wurin,p Mom da fuskar ta ke ɗauke da tsantsan damuwa da sauri ta shige gaba ganin Joseph ya buɗe mishi motar, cikin zafin nama taje tayi hugging nashi tana sakin wani irin kuka. Zuciyar shi ce ta karye ganin yadda Mom ɗin shi ke kuka. Granny ma ba a bar ta baya ba, “Ku bani waje nagan shi don Allah, lafiya ƙalau yake ai koh?” ta faɗa tana Matsowa kusa da shi. Ganin raunin da ya samu yasa jikin kowa yin sanyi. Nan take Mom tace su wuce Hospital, bai iya yi mata musu ba haka suka ɗunguma zuwa Hospital. Bayan an yi treating raunukan likita ya buƙaci su koma don yana buƙatar hutawa. ★★★★★★★★★ Yammacin ranar kuwa Ƴar Iya tayi wanka har da wanke baki da gawayi da kuma alimun, aka saka kaya masu kyau ita ala dole an je birni. Ko sallama bata yiwa Iya ba ta fito abun ta tana taku tana yauƙi kamar wata kuɓaiwa. Kai tsaye gidan su Aminiyar ta A'i ta wuce, kafin isar ta kuwa duk wurin da ta gifta sai anyi gulmar ta wai Ƴar Iya taje birni baku ga har sauya tafiya tayi Baneh irin ta ƴan birni?. Sai da suka sha hirar yaushe gamo da kuma labarin bayan rabuwa a nan A'i ke faɗa mata tsiyar da ƴan garin suke mata bayan tafiyar ta. “Hmm ƙawata dai tunda kika sa ƙafa kika bar Gallara shikenan ƴan gari suka tsaneni,” “Ban gane ba” “Ina faɗi miki Aradu har duka na wasu suke yi wai zasu huce tsiyar da muka tsula duka a kaina” Mamaki ne ya kama Ƴar Iya jin abun da ƴan garin suka yi wa Aminiyar ta kuma ta ɗaukar mata alƙawarin ɗaukar mata fansa. Daga haka suka fice don yawata gari. Gulma ko ina Ƴar Iya annoba, Ƴar Iya mai hannun ɓarna ta dawo, wasu wurin kuma gulmar su bata wuce yadda Ƴar Iya ta sauya tafiya ba ga kuma kaya masu kyau da suka gani a jikin ta saɓanin da da sai tayi wata da kaya a jikin ta. (Nace ah toh, don ma makaranta taje da ace wani gidan ƴan gayun taje da tafi haka). A dai-dai wata corner suka ga wani yaro ɗauke da kaji a hannun shi alamun sayar da su zai yi. Ƴar Iya kuwa murmushin mugunta tayi sannan ta dakatar da shi. “Dauda ina ne zaka je haka a yammacin nan da kaji?” Dauda da duk ya tsorata ya duburburce saboda ya san karon sun da Ƴar Iya mai hannun ɓarna ya fara magana cikin ƙiƙina. “da...da...dama...innnn...innna ta...ce...ta..ta...ce..na..je ka...ka..kasuwa na..sa..sa..yar da...kajin...sai...na.auno...geron tuwa”. Murmushi kawai tayi tace shikenan jeka abun ka ammah kace kada a ƙara aiken ka da kaji kaji ko?” Kai ya gyaɗa daga nan suka bar shi ya wuce. Nausawa cikin kasuwar suka yi still Ƴar Iya na kwalmaɗewa kamar wata kara tana ƙara gyara tafiya. Dai-dai wurin Bala Mai kifi suka tsaya ganin lokacin yake soya kifin. Fari Ƴar Iya tayi da ido sannan ta gaida Bala wanda take zuciyar sa ta fara wani irin bugu. “Ina wuni mai kifi” Cikin ƙarfin hali Bala ya amsa yace “Ina wuni Ƴar Iya ya gida?, Kin dawo ashe” “Eh wallahi mun dawo jiya da Yamma, akwai kifin ne?” Ta faɗa tana ƙara leƙa kifin dake zube kan teburin. Bala ya amsa mata da “Eh akwai” Ai da tunda suka zo bata ce uffan ba ta ce “Mai zafi zaka saka muna” Da “Toh ” ya amsa sannan ya jawo leda ya cika ta da kifi daga nan ya miƙa musu. Godiya suka yi mishi sannan suka ja ƙafafuwan su sai gidan Iya. Bayan sallar maghrib A'i ta yi sallah a ɗakin Iya, don ita duk tsiyar ta tana yi ne idan mai tare mata tana nan kuma ba laifi tana bubbuga sallar ta duk da cewa ba yadda ake yi ba abun ku da mutanen ƙauye. Kai tsaye gidan wata Halima suka shiga. Duk da cewa basu taɓa shiga gidan ba ammah haka Ƴar Iya ta jagoranci A'i zuwan cikin gidan saboda ta jiyo ƙamshin dahuwar da ke tashi ta jikin zana. Ƴar Iya ce ta fara kwaɗa Salama “Salamu Alekum, Salamu Alekum ga baƙin maghriba” Halima da bata san waye ba ta amsa tana gyara murya da alamar a makewayi take. Shigowa suka yi suka zauna kamar mutanen kirki a kan taburmar da ta shimfiɗa kusa da murhun. Halima mace ce mai son gayu, fara ce kakkaura kuma ba ƴar cikin Gallara bane, daga Azare aka auro ta. Da yake tayi zama cikin birni kuma irin matan nan ne masu kutsawa cikin manya babu wahala ta san abubuwa da dama. Sana'ar ta a nan Gallara shine sayar da maganin mata iri iri kuma babu laifi ana siya saboda kowa so take ta zama gwana wurin mijin ta. Hakan yasa Halima ta saba da ƴan garin cikin ƙanƙanin lokaci, da wuya kazo gidan ta baka tarar da baƙi ba wasu sun zo ayi musu irin dahuwar nan ne wasu kuma siyan maganin mata suke yi. Ɗaure da zani a ƙirjin ta ta fito daga makewayi tana kallon su Ƴar Iya da suka make a kan taburma tana aika musu kallon tambaya. “Sannun ku da zuwa Ƴan mata” “Yauwah sannu” Ƴar Iya ta amsa tana ƙara kame kanta wuri guda kamar ta ƙwarai. “Bari na sako kaya sai nazo” Bayan mintuna 30 sai ga Halima ta fito cikin wata koɗaɗɗiyar atamfa sai dai tas-tas take babu alamun datti. Tayi kwalliyar ta ta kuma shafa janbaki har da eyeshadow. KO ƙifta ido Ƴar Iya bata yi ganin irin adon da matar ta caɓa. Haka nan taji matar ta burge ta kuma tana son su ƙulla zumunci. “Kuyi haƙuri ƴan mata na ɗan ɓata muku lokaci, wacce ce amaryar a ciki?” ta faɗa tana yin wani murmushi tare da zama kusa da su bisa taburmar. Kallon mamaki Ƴar Iya ke bin ta da shi jin wai wacece amarya?. A'i da yake an riga an sanya bikin ta bayan tafiyar Ƴar Iya birni saboda dama tun kwanaki aka fara auren sa'annin su. Sunkuyar da kai ƙasa tayi tace “Nice, Ina wuni” Murmushi Halima tayi tace “Lafiya ƙalau ai na ɗauka wannan ce amaryar” Ta faɗa tana nuna Ƴar Iya da yatsa. Kamar ta Allah Ƴar Iya bata ce komai ba sai murmushi kawai take saki nace anya kuwa wannan murmushi babu biyu a ƙasa kuwa?. Bayan sun gaisa tace “Bari na sauƙe dahuwar nan don Allah, kema ya kamata ki fara shirin auren nan fa, in kin je gida ki cewa Innar ki ta fara shirya ki kuma ki ce mata ina gyara sosai da kuma bada magungunan mata masu kyau” Caraf Ƴar Iya tace “Gyara kuma na me?” Halima da yake irin matan nan ne marasa kunya kuma babu ruwan su da yaro ko babba tace “Bari na sauƙe na dawo” Sauƙe tukunyar tayi tare da ɗaura wata tukunyar da alamar abincin dare zata girka. Wurin su ta dawo ta zauna sannan ta maida kallon ta ga Ƴar Iya. “Yauwah Ƙawar amarya kike tambaya kan batun gyara koh?” kai Ƴar Iya ta gyaɗa tare da maida hankalin ta ga Halima. “Toh kafin nan dai ya kamata na san sunan amarya da ƙawar ta ko?” A'i tace “Ni suna na A'i wannan kuma Aminiya ta ce Ƴar Iya, halan zaki ji ana labarin ta ko da yake mu ma kan mu bamu san ki ba a ƙauyen duk irin yawon mu” Murmushi Halima tayi tace “Yoh ai dole na san Ƴar Iya mai hannun ɓarna, ai naji ance ma taje birni, halan yaushe kika dawo?” Duk irin tsiyar Ƴar Iya da yake nema take bata ce komai ba sai ma murmushi da tayi tace “Jiya na iso, ammah nima na kusa yin auren ai tunda ƙawa ta zata yi, sai dai ina son ki min bayani akan gyaran da kuma maganin mata da kike magana a kai” Halima ta gyara zama tace “Babu damuwa zan miki bayani kamar yadda kika buƙata sai dai bari na kammala girka mana abinci muci, idan muka yi sallah sai mu fara bayanin don zamu kai zuwa gobe bamu gama ba. Tunda mai gidan baya nan ai zaku jima koh?” Gyaɗa kai Ƴar Iya tayi haka nan A'i ma. Halima ta tashi ta gyara wuta ganin ruwan ya riga da ya tafasa yasa ta wuce ɗaki ta ɗauko taliyar murji mai ɗan yawan gaske, zubawa tayi a tafasasshen ruwan daga nan ta gauraya da muciya. Har taliyar ta dahu cikin su babu wadda yayi magana, da kan ta ta kwashe taliyar cikin matacin ta na ƙarfe. Sai da ta soya manja ta ɗauko yaji sannan ta fito. A tray ɗin silver ta juye duka taliyar sannan ta saka musu manja da yaji, nan aka hau taliya aka cinye ta tsaf..... (Masoya littafin Ƴar Iya ina matuƙar godiya da irin haɗin kai da kuke bani ta hanyar suburbuɗo comments don ƙarfafa min guiwa. Ina godiya sosai ƙawayen Ƴar Iya, su AMEERAN MAMA, HINDATU HASSAN, da sauran da ban ambace ku ba, ina fatan samun haɗin kan ku har abada, Allah ya bar ƙauna. ME KUKE TUNANI GAME DA ALAƘAR HALIMA DA ƳAR IYA? MENENE DALILIN TAMBAYAR ƳAR IYA GA HALIMA? SHIN WANE IRIN SALO NE ƳAR IYA TA DAWO DA SHI GALLARA? MU HAƊU DA SAFE IN SHA ALLAH DON JIN CIGABAN LABARIN. DUK AMSOSHIN KU NA TARE DA ALƘALAMIN DIAMOND LADY 💎, KU CI GABA DA BIBIYAR ALƘALAMI NA DON YANZU NE ZA'A FARA WASAN! TAKU HAR KULLUM, DIAMOND LADY 💎 [5/5, 7:13 PM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘‘29&30’’’’’ *ALEE POV* Ana kaishi asibiti kuwa aka fara bashi kulawa, kwanan su ɗaya suka koma can gida da shi saboda yadda Ƴan jarida suke sintiri a bakin asibitin, ga kuma mutane kamar tururuwa safe, rana yamma, dare basu bar asibitin ba. Kulawar da ya samu yasa cikin two days ya warke sumul da yake dama ciwon a iya jiki ne zuciyar na nan ƙalau. Kowa nan da nan yake da shi kamar wani ƙwai, duk irin yadda yake takurawa ƙannen sa hakan bai sa sun gajiya wurin yi mishi addu'a ba. Musamman waɗanda suke jin kaunar shi daban cikin zukatan su. Ɓangaren kulawar nan ba'a bar kowa baya ba, Granny, ƴaƴan ta, jikokin ta da sirikan ta musamman Nenne ga kuma Sarah da itama take iyawar iyawar ta, Allah these ko Allah zai sa Hamma Zaki ya so ta ne. Ƙira kuwa ta ko ina, wasu na ƙiran Mom wasu kuma Daddy yayin da wasu ke ƙiran wani daga cikin ahalin suna tambayar jikin sa don tuni labari ya karaɗe Nigeria ta ko ina zancen ake. In ka hau facebook, IG har da Tiktok kowa abun da yake wallafawa a shafin sa kenan. Dr. Faruq ne yayi Video ɗin a lokacin da suke kan aiki. Ai kuwa a ranar da suka dawo ya wallafa Video ɗin a shafin sa na Facebook, Instagram, Twitter, YouTube, da sauran su. Kafin kace me kowa sai tofa albarkacin bakin sa yake. Kowa na yabawa wannan zarton matashi da yake aikin sa babu ƙakkautawa. Comments ɗin wasu kuma bai wuce kan yanayin shi ba, wasu na faɗin wannan ai baindiye ne irin waɗanda ake nuna su a indian film ɗin nan. Ashe dai da gaske akwai masu irin ƙarfin nan. Kowa dai da abun da yake faɗa, ƴan uwa mata kuwa santi ne kawai ke jansu. Videon nan fah tun da mata suka gani suka rikice, su ba jarumtar shi ce ta burge su ba kaɗai siffar shi kawai ita taja hankalin su. Daga nan batun zai fara, Ƴan mata a ko ina a faɗin ƙasar mu Nigeria burin su yanzu bai wuce su mallaki wannan Lion ɗin ba. Ga kyau ga kuma jarumta. Tuni ƴaƴan mommy da Daddy (Ina nufin ƴan gayu, shagwaɓaɓɓu ƴaƴan manya) suka fara yiwa iyayen su daru su fa ga wanda suke so, sun ji sun gani in Babu shi ba zasu rayu ba. Ana wannan drama ne kuma hukumar sojoji ta ƙasa ta shirya gagarumin bikin cin nasara da suka samu bisa jajircewar Commander da ya jagoranci aikin wato Hamma Zaki. Flyer na taron ma kar ku so kuga yanda yake trending a yanar gizo. Ai kuwa mata fa sunyi shiri tsaf don halartar wannan taro kowa da irin tata aniyar don jawo hankalin samɓalen saurayin nan. (Wannan kenan, nimah gaskiya na haɗa sabbin kaya na don ina so nimah nasamu matsuguni a zuciyar Hamma Zaki na). *ƳAR IYA POV* Bayan sun samu cinye taliya da manja kowa tasha ruwa aka wanke hannu. Halima tace “Toh sabbin abokai na, da farko zan fara amsawa Ƴar Iya tambayar ta.” tayi shiru tana maida duban ta ga Ƴar Iya. “Tabbas akwai gyara na musamman da ake yiwa amarya idan zata yi aure. Wannan gyara kuma ana yin sa ne dai-dai al'adun kowa. Gyaran nan na da matuƙar muhimmanci musamman saboda shi kanshi ango ya son amarya tayi, yana don ya ji ta daban. Ana gyaran jiki, tun daga fuska zuwa ƙafa, gyaran gashi da kuma sauran gyararraki. Kin gane, misali da zan baki yanzu saboda baki kai ɗaukar bayanan ba shine, kamar ke yanzu in Zaki yi aure, ni da kai na zan gyara ki fes, kinga fatar nan taki da gani Allah ya zuba mata kyau da haske datti ne kawai ya ɓata ta, To zan gyara ta ta koma fes da ita irin ta ƴan gayu ko ba komai ango ya gani zai yi mamakin hakan. Sannan wannan bakin naki ma da kike gani in Zaki yi aure tas zai koma in yasha gyara ....” Haka Halima ta fayyace musu gyaran jiki da ake yi. “Sai kuma batun maganin mata, ku da yake ƙananan yara ne ba zaku fahimta ba amma dai zan faɗi muku abu kaɗan” Halima ta faɗa musu batun sex idan anyi aure tare da muhimmancin da ayyukan waɗannan magungunan matan. Daga haka suka koma normal hirar su. Ƴar Iya tace “Oh Ni Halima kika ce za'a iya gyara baki na?, To da me za'a ke gyara shi?” “Ƙwarai Ƴar Iya Tun yanzu ma ki fara,idan kika samu gawayi, ko don ashe ku da kara kuke girki, to in kun tashi tafiya ga gawayi a nan sai ki tafi da shi. Ki daka gawayin nan da gishiri da kuma lalle, sai ki daka kanunfari da kuma alimun ki haɗe da wannan dakakken gawayin, kullum sai durje bakin ki, ina tabbatar miki bazaki jima ba zai koma fes kamar farin wata” Sai da dare ya fara duka suka yiwa Halima sallama tare da alƙawarin zasu ke shigo mata. Ɓangaren Angel Ƴar Iya kam ba'a magana, haka kawai taji tana son yin sana'a cikin ƙauyen, tou yanzu tunda an mata bayani kan maganin mata shi ta yanke zata fara siyarwa ba tare da ta san menene da menene constituents na maganin matan ba. Sassafiya kamar kullum Ƴar Iya ta tashi, bata, tana miƙewa ta fito daga bukkar ta, bata tsaya ko ina ba sai wurin kiwon Baffi, kashin shanu ta tsinta akan faifayin busa, ta hau kan turmi ta ɗaura shi bisa bukka. Tana ɗaurawa ta diro tare da ɗaukar langa ta fice abun ta. A dai-dai gonar wani mutumi da yake kiwon tumaki da awaki ta tsaya. Ciki ta tsallaka saboda an riga an kewaye wurin da fence. Sai da Ƴar Iya ta kusa cika langar nan da kashin tumaki da awakin nan ta fito abun ta. Gida taje shima ta ɗaura shi a sama daga nan ta ƙara fitowa, wannan karan ciyawa taje ta tsigo a buhu, ta sanya ta kamar yadda tayi wa sauran abubuwan. Gidan su A'i ta wuce suka fita yawon su. Suna fitowa Ƴar Iya tace wa A'i “Ke A'i yau kwaɗayin mangwaro da kashu nake yi, muje lambun Baba Haro mu ciro” Bata Musa ba su ka ɗebi ƙafafuwan su suka wuce lambun Baba Haro. Sun ci Sa'a kuwa kamar baya nan har da murnar su don sun riga sun san Bala'in wannan tsoho, don duk maitar ka ko zata fito tayi rawa ba zai bayar ba. Sai da suka kewaye ko ina suka tabbatar Baba Haro baya nan suka ɗale bishiyar kashu tare, suna tsinkowa suna ɗaurewa cikin kwalayen su. Da yawa suka tsinka sannan suka sauƙo suka ajiye ƙullin a gefe. Basu tsaya ɓata lokaci ba suka hau bishiyar mangwaro. Tun akai suke Sha in sun sha sai su wullo ƙasa. Suna cikin haka ko tarawa basu yi ba Baba Haro ya shigo lambun. A dai-dai lokacin ne kuma Ƴar Iya ta wullo ƙwallon mangwaron da ta lashe shi har ya zama fari sol. Bai yi aune ba kawai yaji ƙwallon mangwaro akan sa. Duk tunanin shi irin wanda jemagu suka sha ne shi yasa bai samu ya duba ƙwallon ba. Ba zato babu tsammani yaji wasu ƙwallayen har biyu da suka iso kan sa lokaci ɗaya. “Ashh" ya furta tare da sunkuyawa ƙasa. Arba da lasassun ƙwallayen yayi ai kuwa ya ɗaga kai sama. Mutane biyu ya gani kan bishiyar mangwaron. Nan ya fara musu magana kan su sauƙo. “Ku sauƙo yanzu ko na hawo na ci ubanku” Dariya suka kwashe da ita Ƴar Iya tace “Kaji tsoho da wani zance, har ya bani dariya...hhhhhhh..to ka hau ɗin mu gani ina zaka iya” Haushi ne ya cika Baba Haro Jin Muryar yarinya tana masa baɗala a bishiyar da ke cikin lambun sa. “Wallahi in na hau duk sai kun raina kan ku, ƴan iskan yara marasa tarbiyya” Daga sama Ƴar Iya ta ƙara jefo wani ƙwallon mangwaron tana faɗin. “Shegu tsofin nan sai shegen son girman tsiya kamar gyambo, Toh ina ka isa ka hau” Baba Haro yace “Ammah dai kukan Allah yayi matasa albarka, tsofait-sofai da ni kuke wa ɗiban albarka, Toh yau kuwa baku isa barin lambun na nlafiya ba. A'i tayi dariya cike da raini da gatsali tace “In mun zo fita lafiya ka zare lafiyar tamu. Kaji tsoho da ɗan banzan mugun baki” Ƴar Iya tayi caraf tace “Ni shi yasa bana sararawa tsofin nan, da lanƙwasassun ƙafafuwan su kamar agwagi” Duk wannan tsiyar da suke wa Baba Haro kawai ya ƙyale su ne, rigar sa ya ɗage tare da naɗe ƙafar wando sai kan bishiya. Ganin yana hawa bai sa sun ji tsoro ba saboda sun san salon su zai ƙayatar. Sai da Baba Haro ya fara nisa a hawan bishiyar su kuwa dariya kawai suke yi ganin yadda yake wani kama bishiya kamar ba namiji ba. Daf da reshen da suke ya bi hakan yasa suka fara niyyar barin reshen, duk inda suka yi sai yace sai ya bisu. A haka suka yi ta kewaya wa da Baba Haro ɗan ƙarfin hali har sai da suka tabbatar ya wahala ba kuma zai iya cigaba ba. A'i ce ta fara sauƙa ta can wani bangare ita kuma Ƴar Iya tabi wani tsililin reshe. Baba Haro ganin babu nisa tsakanin shi da wannan hatsabibiyar yarinya yasa yayi azamar bin ta. Tsam ta dire ƙasa abun ta tana kaɗe ƙasar da ta buɗe jikin ta sannan ta tsaya dakon faɗowar rigimammen tsohon. Tiiiiiiiiim kake ji sai ga Baba Haro a ƙasa. “Wayyo Allah na, na shiga uku Ni Haro, shikenan wayyoh Allah na” Dariya mugunta Ƴar Iya ta sheƙe da ita tana yima Baba Haro gwalo. “Shegen tsoho ai sai muga ƙarshen abun naka, yanzu sai ka bi mu ai. Babu ko kunya kana bin Ƴaƴan cikin ka don sun hau mangwaro.” ta ƙarasa tana wulla masa harara tare da ke cewa da wata dariyar. A'i kuwa dariya ta hanata faɗin komai sai iya nuna Baba Haro take d yatsa tana dariya. “Tashi mana ɗan tsoho rigimamme” Ƴar iya ta faɗa cikin shaƙiyyanci. Baba Haro kuwa danasanin biye su yake yi, ya haɗa uban zufa kamar wanda yayi gudun ceton rai, fuskar nan shaɓe-shaɓe da hawaye da majina. A gaban sa suka koma kan bishiyar tunda ya kasa ko da tashi ne yana ma tunanin ya karye. Tun daga bishiyar suke wullo ɓula ɓukan mangwaro ƙasa kuma sai sun saita kan Baba Haro su wullo. Baba Haro dai yau yaga ta kanshi, sai da suka wullo fiye da mangwaro hamsin tukun suka sauƙo daga bishiyar. Tsam ko ɗaya basu bar mangwaron ba suke kwashe abun su cikin wani daro dake cikin lambun. Bayan sun kwashe suka ɗauko ƙullin kashu ɗin su suka yi hanyar fita, har zasu wuce Ƴar Iya ta juyo tare da zaro mangwaro ɗaya daga daron dake kan Ai. A gaban Baba Haro ta tsugunna haɗi da miƙa masa mangwaron sannan ta ce: “Allah ya sauwaƙe Baba Mai mangwaro, sai mun zo ciran na gobe. In an tambaye ka waye yayi maka haka kace Ƴar Iya mai hannun ɓarna ce.” Daga haka suka fice daga lambun suka ɗauki hanyar gidan Halima. (Nace wannan ƙawance haka, daga haɗuwa ɗaya har anyi wa Iya hijira?” TOH FAH! ƳAR IYA ANYI ƘAWA FA DA GASKE. GA KUMA SU HAMMA ZAKI FARIN CIKIN ƳAN MATA. YANZU FA WASAN ZAI FARA KU CI GABA DA KASANCEWA DA ALƘALAMIN DIAMOND LADY SHARE & COMMENT PLEASE! [5/9, 7:59 PM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘‘31&32’’’’’ [*Gare ki ƴar uwa mai albarka, ki riƙe ibadar ki yadda ya kamata a gidan auren ki*. *ko da wasa kada kiyi abota da mutanen banza, ko kin san illar alaƙar mace mai aure da mutanen banza?* *To kaɗe kunnuwan ki kiji alaƙa da mutanen banza tsaf zai sa ki rasa ƙimar ki a wurin mai gida saboda ko yaushe zasu kasance cikin baki gurɓatacciyar shawara ne wanda in baki yi hankali kin lura da wuri ba kan sa ki rasa mijin gabaɗaya* *Saboda haka a kula da ƙawayen da za'a yi mu'amala da su a gidan aure, da zarar kin fahimci ƙawar nan ba ta ƙwarai bace to tun wuri ki sallame ta kafin tayi galabar koya miki miyagun halaye.* *A ko da yaushe, ki riƙe wannan ƙawar da in kin samu saɓani da mai gida bayan kin sanar da ita zata yi ta baki haƙuri tare da nusar dake laifin ki cikin zaman auren ki*.] Daga haka suka fice daga lambun suka ɗauki hanyar gidan Halima. “Salamu Alekum, masu gidan suna nan?” A'i ta faɗa tare da shigewa gidan Ƴar Iya na bin bayan ta. Daga cikin ɗaki Halima ta fito tane washe baki “Wa alaikumussalamu, masu gidan suna nan...maraba da baƙi ku iso ciki manah” Ƴar Iya da suke tsaye bakin bishiyar yandi dake tsakar gidan suka fara ajiye shirgin su, A'i ta sauƙe daron mangwaro Ƴar Iya ta jiye ƙullin kashu ɗin su a ƙasa. Halima ce ta ƙaraso yadda suke ɗauke da taburma a hannun ta. “Maraba da Ƴar Iya mai hannun ɓarna” dariyar shaƙiyyanci Ƴar Iya tayi yayin da take ƙoƙarin zama kan taburmar da Halima ta shimfiɗa musu. Sai da suka zauna ɗamas sannan suka fara janyo mangwaro da kashu ɗin. Murmushi Halima tayi tace “Mangwaro haka daga ina?” Ƴar Iya ta amsa da faɗin “Cirowa muka yi a lambun Baba Haro” A'i ta ƙyalƙyale da dariya tace “Yana can mun bar shi ma a ɓalle” Zare ido Halima tayi tana ƙara kallon su alamar tana buƙatar ƙarin bayani. A'i tace “Munje cira inji in gaya miki tsohon ya hana mu, shine muka masa kwaskwarima muka cira daga nan muka yo nan” “Hmm” Halima tace “Ku dai kam bakwa gajiya da tsokala, ko da yake akwai mai hannun ɓarna cikin ku.” ta ɗan dakata ganin irin kallon da Ƴar Iya ke bin ta da shi, cikin wayincewa taci gaba “Duk da haka gaba ta kaimu Ni da sabbin ƙawaye na, To yanzu dai bari na wanke mana uku uku sai mu sha” Tashi Halima tayi ta wanke mangwaro goma ta jawo su suka fara sha suna hira. Daga ƙarshe dai tas suka shanye wannan mangwaro haka kashu, daga nan suka yi mata sallama Ƴar Iya na faɗin zata tafi neman halal ɗin ta ita ma. Daga haka A'i tayi gidan su Ƴar Iya ta nufi gidan Iyar ta. ★★★★★★★★ *SHAREEF POV* Shirye-shirye ake cikin gidan General Muhammad Naira. Ta kowanne ɓangare shiri ake yi babu kama ƙafar yaro. Kowa ka gani cikin farin ciki yake yayin da Hamma Zaki yaƙi fitowa gabaɗaya. Zaune yake a bedside kamar kullum cikin white pyjamas, ƙafarsa ɗaya na kan ɗaya yayin da fuskar shi ke a ɗaure. Hakan ya bani damar fahimtar ba don hidimar yake ba duba da yadda ahalin sa ke ɗauki akai. Wayar shi da yake latsawa ce tayi ringing bai yi niyyar picking ba saboda sam yau baya son a dame shi. Can ganin mai ƙiran nashi da niyyar dainawa yasa ya zaro wayar da niyyar kashe ta gabaɗaya, sunan Dude da ya gani yasa yaja tsaki tare da picking. Can ƙasan maƙoshi ya amsa sallamar Dr. Faruq ɗin “Wa alykumussalam” Dr faruq kuwa murmushi Mai sauti yayi tare da faɗin “Buddy duk cikin magagin rashi don taron ne har nayi kira uku baka yi picking ba? “Mtss” Hamma Zaki yayi tsaki kamar wanda aka yiwa dole yace “Idan abun da ka ƙira ka faɗa ne, lemme hang the call.” Cak Dr. Faruq ya tsaya da dariyar da yake yi coz ya san halin mutumin nashi. Cikin son danne dariyar tashi yace “Yau Buddy shiru naji daga ɓangaren ka, Hamma Saleem ɗazu ya ƙira yana tambaya ta ko ya batun shirye-shiryen namu, I told him baka ce komai ba sai yanzu dai yace nayi maka magana” “Ok” kawai Hamma Zaki yace. Cikin takaici Dr. Faruq yace “Alright tunda ok kaɗai zaka ce, sai mutum ya dage yayi maka magana ka wani ce ok. Shikenan nimah zan cewa Hamma Saleem ɗin kace ok kawai” Cike da ƙosawa da maganar ɗin tuni kan shi ya fara sarawa yace “Sorry Buddy, ban hana ku shirya komai ba, kawai ni ɗin ne bana buƙatar shiri dole ta sa zan yi attending ma” “Na fahimce ka Buddy, worry less please zan kula da komai and ka daure ka fara sabawa da jama'a da kuma hayaniya ko don saboda gaba.” “Ok” Hamma zaki ya faɗa tare da katse ƙiran yana jan tsaki. Sauƙa yayi tare da sanya bathrobe ya nufi toilet. Yana fitowa yayi drying jikin shi tare da shafa creams nashi. Cikin closet ya ɗauko wata white jallabiya ya sanya, ko turare be samu damar fesawa ba ya nufi sidedrawer tare da ɗauko pcm tablet, fridge ya nufa ya ɗauko warm bottle water tare da Shan pcm ɗin yana yamutsa fuska. Yana gama sha ya haye bed Don ya huta. Vibration na wayar shi ya tayar da shi Major Kabir Joda ne hakan yasa yayi picking tare da kara wayar a kunnen sa. “Assalamu Alykum” aka ce daga ɓangaren can. Sai a lokacin Hamma Zaki ya fara motsa baki tare da yamutsa fuska. “Wa alykumussalam” ya amsa can ƙasa-ƙasa. “Captain?, Ain't u preparing anything there?” “Nothing sir!” ya bashi amsa a taƙaice. “Toh akwai sabbin uniform da zaka sanya a wurin taron, Please ka aiko a amsa maka” “Ok sir!” Sanin Halin Captain yasa Major Kabir hanging call ɗin. Lokaci ya duba ganin 12:22pm yasa shi nufar Toilet, bayan ya watsa ruwa ya ɗauro Alwala. Masjid da ke cikin estate ɗin ya wuce. Bayan sun idar ya dawo. Tun daga bakin entrance door na part ɗin yake jin ƙamshin girki, sai a lokacin ya tuna ko breakfast bai yi ba coz lokacin da Mom ta aika Sarah Koro ta yayi da girkin. A hankali ya shiga ciki, lokacin dukan su suna zaune a dining ɗin, Daddy, Mom, Fauzah, sai kuma Sarah. Ɗan yamutsa fuska yayi tare da ƙarasawa wurin cikin takun shi na zaratan maza. Tun kafin ya ƙarasa Mom da Daddy ke sake mishi murmushi yayin da Fauzah ta sunkuyar da kanta ƙasa. Sarah Kam ko ƙifta idon ta batayi coz gani take kamar za'a iya cire wani abu daga jikin shi a lokacin da ta ƙifta ɗin. Kyau sosai yayi mata sai dai hararar da ta gani ya aiko mata yasa babu shiri ta janye kanta. Ita ma babu laifi tayi kyau, sanye take cikin yellow Sari yayin da ta zubo da kwantacciyar baƙar sumar ta har gadon baya. Yana isa ya gaida Mom da Daddy a tare coz he's eager to start eating yadda cikin shi ke wani irin ƙara. “Good afternoon Daddy and Mom” Cikin sakin fuska suka amsa mishi yayin da Mom ta miƙe tayi serving nashi, white rice ne with stew, sai cips da ta soya saboda shi. Hot coffee ta zuba mishi a cikin mug ɗin dake gefe kafin ta zauna. Fauzah da kanta je ƙasa tace “Good afternoon Hamma Zaki” Itama Sarah bakin Fauzah tabi “Good afternoon Brother” Harara ya banka wa su biyun ba tare da ya amsa gaisuwar ba, babu shiri Fauzah ta miƙe zata bar dining ɗin ai kuwa suna haɗa ido ya ɗaga mata hannu. Mom da Daddy ma miƙewa suka yi don cigaba da shirye-shiryen su. Hanjin cikin Fauzah sai da ya kaɗa yadda su Mom suka tashi suka barsu da Hamma zaki, babu abinda take cikin ranta sai addu'a Allah yasa ba wani laifin tayi ba. Sai da ya gama tas sannan yayi wiping bakin shi tare da ɗauko hot coffee nashi yana sipping a nutse kamar wani mace. Sauƙewa yayi tare da kallon Sarah da Fauzah wanda kawunan su ke ƙasa. Cikin sassanyar murya yace “Ku baku san lokacin gaisuwa bane sai mutum ya fara cin abinci?” Kasa magana suka yi musamman Fauzah dake wasa da yatsun ta. Ɗago fararen idanuwan sa yayi tare da kallon su ɗaya bayan ɗaya sannan ya maida hankalinsa ga Coffee ɗin da yake sha. “Alright since You don't know how to talk kada yarinya ta ƙara gaishe ni idan ina cin abinci” ya faɗa cikin Muryar da ke tsantsar nuna umarni, bai jira amsar su ba ya wuce bedroom nashi. Har ya shiga ya tuna da wayar su da Major hakan yasa ya ƙira Dr. Faruq ya sanar da shi. “Please Dude, in zaka shigo ka biya ta barrack ka amsa min saƙo wurin major Kabir” cikin ƙosawa da maganar ya tsaya haka. Dr. Faruq yayi murmushi mai sauti yace “In zaka zo ka amshi abun ka to in kuma baka zuwa shikenan, ni ba ɗan aiken ka bane” Jin amsar aminin nasa yasa ya katse ƙiran without pleading...Sam shi bai san wani abu rarrashi ba in fact bai ma iya ba. Ɓangaren Dr faruq murmushi yayi coz ya san halin aminin nasa sarai kuma abun da yayi expecting kenan. Ƙasa ƙasa yace “Watarana dai zamu ga ƙarshen wannan izza taka da zarar mace ta samu muhalli cikin ƙalbin ka” Daga haka yaja motar shi zuwa barrack da yake basu da nisa. Yana karɓowa ya taho gidan su Hamma Zaki. A parlour ya haɗu da Mom, bayan sun gaisa ya wuce sama. Knocking door ɗin yayi wanda kawai tsokala ta saka shi haka. Tsaki yaja daga ciki yace “Yes come in”. Maimakon ya shiga sai ya cigaba da Knocking ɗin. Cikin hasala ya miƙe daga bakin gadon tare da nufar ƙofar da niyyar hukunta koma waye wannan. Dr. Faruq jin ana ƙoƙarin murɗa handle ɗin yasa yayi baya, ai kuwa kamar ya san meh zai faru Hamma Zaki yayi niyyar cafke kowaye ya hukunta shi shi yasa yaja baya yana dariya. “Kai Buddy, irin wannan cafka ai sai ka kashe mutum in ka samu nasara.” ya ƙarasa yana dariya. Tsaki yaja ya koma ciki abun sa, duk haushi ya cika shi bayan ma yace bazai amso masa saƙon ba shine zai wani zo ya dame shi. Ƙarasawa cikin ɗakin Dr. Faruq yayi hannun sa ɗauke da babbar army bag. Bakin gadon a gefen Hamma Zaki ya zauna tare da ƙura masa ido. Ganin yadda ya wani haɗe rai kamar wanda zai mutu yasa ya kece da dariya. Tsaki yaja tare da shirin miƙewa Dr. Faruq ya maida shi mazaunin sa. “Haba Buddy, me kake yi haka ne kam?” Harara kawai ya aika masa tare da ƙara miƙewa. “Since baka amsomin saƙon ai ban kuma ce ka zo ba” Cikin sigar rarrashi Dr faruq yace “Haba Buddy yi haƙuri mana, ai na riga na amso” ya faɗa tare da miƙa mishi babbar army bag ɗin. “Thanks” kawai yace haɗe da ajiye ta gefen sa. Sanin hali yasa Dr faruq bai ji haushin sa ba sai ma murmushin da yayi tare da cewa “Ba za'a buɗe mu gani bane?” Banza Hamma Zaki yayi mishi. Miƙewa yayi zai ɗauka ai kuwa Hamma Zaki ya riƙe hannun sa. “Auch! To sake min hannun in ba so kake ka nakasa Ni ba, nimah na haƙura” Ganin ya saduda yasa ya sake mishi hannun. Haka suka zauna har wuraren 2:30pm daga haka Dr. Faruq ya wuce don samu ya shirya on time. COMMENT & SHARE PLEASE [5/10, 10:03 AM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘‘33&34’’''’ [ *Gare ku mata masu sanya turare idan zasu fita waje, haramun ne sanya turare a lokacin da zaki fita waje domin baki san wa da waye zasu ji ƙamshin ba AMMAH babu laifi ki sanya yadda iya ke zaki ji ƙamshin abun ki.* *Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ya ce, duk matar da ta sanya turare a lokacin da zata fita, bayan ta fita kuma wani da ba muharramin ta ba yaji ƙamshin har ya yaba, toh za'a rubuta mata zunubi kamar wacce tayi zina a ka'aba.* *SABODA haka ƴar uwa idan zaki fita unguwa ki kiyaye, addini bai hana ki tsafta ba amma bai ce ki bayyana adon ki ga waɗanda ba muharraman ki ba. Babu laifi kiyi wankan ki a gida ki saka turare cikin trailer ma idan kina so matsawar ba zaki fita ba* *Allah yasa mu gane*] *3:03pm* Wasu kyawawan motoci kusan guda bakwai suka Kunno Kai cikin tamfatsetsen gidan nasu, dai-dai parking lot suka yi parking. Samari ne da suka kai su goma suka fito daga cikin motocin, cikin waɗannan samari kuwa har da masu jajayen kunnuwa. Dr. Faruq shine jagoran su kuma shi yayi musu iso zuwa main parlour na gidan. A nutse suka kutsa kawunan su cikin parlourn da ya sha gyara ƙamshi kawai ke tashi. Bayan sun zauna da kanshi ya wuce ɓangaren masu aiki ya sanar da su su kawo refreshments Mai ɗan yawa daga haka ya wuce sama. Directly bedroom ɗin Hamma zaki ya nufa wanda yayi dai-dai da fitowar shi daga toilet, Sanye yake cikin bathrobe kamar ko yaushe yana drying sumar shi da ta jiƙe da wani pink towel yayin da jikin shi ke fitar da daddaɗan ƙamshi na shower gel ɗin sa. Cike da mamaki yake kallon Dr. Faruq da ke sanye cikin Black expensive jeans da kuma suite ɗin shi white colour da necktie black, ya kuma ɗaura newly white labcoat da ta ƙara haskaka shi. Ba tare da yace mishi komai ba kai tsaye ya nufi gaban mirror ɗin shi. “To Sarkin miskilanci a taimaka a shirya da wuri friends namu na can parlour suna jiran ka....saura ka ɓata lokaci kasan masu jajayen kunnuwan nan basu san african time ehe” Ba tare da ya jira amsar shi ba ya wuce zuwa wurin friends ɗin su dake parlourn, hirar su suka ci gaba suna raha bayan ya sanar da su Shareef ɗin na zuwa. Sai da yayi drying sumar nan tas daga nan ya fara gyara ta haɗe da zuba mata mayuka iri iri. A nutse ya koma kan body creams da lotions dake jere gaban mirror ɗin, cikin ƙwarewa da gayancewa ya gama shafa mayukan tukun ya nufi closet nashi, bag ɗin da Dr. Faruq ya amso wurin major Kabir ya ɗauko. A daidai gaban mirror ɗin ya ajiye tare da zuge ta a hankali. Kayan sojoji ne a ciki sabbi, tundaga boxer, singlet, riga, wando, wristwatch, handkerchief, da kuma cap. A hankali ya sanya kayan tas. Yana gama saka kayan Dr. Faruq yayi Knocking tare da shigowa, ganin ya shirya ma yasa ya juya coz dama ƙiran shi yazo yi coz lokaci ya kusa. Turaruka ya fesa lastly ya fesa favourite nashi wato _Majesté impériale_ tuni daddaɗan ƙamshi ya buɗe ko ina. A hankali ya faro tako ƙafarsa da ke sanye cikin takalmin sojojin yayin da ainihin izza da kuma ƙasaita tashi irin ta zaratan maza da bayyana. Tunda ya murɗa handle na ƙofar ya jawo ta suka jiyo ƙamshin sa. Tun kafin ya ƙaraso yadda suke suka fara sakar mishi murmushi, shima murmushin kawai yake aika musu har ya isa wurin da suke. A tsattsaye suka gaisa ga in lokaci ya kusa cikawa, hakan yasa duka suka ɗunguma zuwa wurin da za'a yi taron. Makeken hall ne mai ɗan karen girma, aƙalla hall ɗin zai ɗauki mutane dubu biyu. Ta ko ina ya tsaru don ba ƙananan masu decoration ne suka ƙayata hall ɗin ba. Gwanin ban sha'awa multi colored lights ɗin ke ƙara haskaka ɗakin taron. Maimakon hayaniya wurin tsit ko da yake abun na zarata ne wato sojoji, ɓangare ɗaya Governor ne da kanshi tare da wasu commissioners , manya manyan sojoji ne dake faɗin ƙasar, manya manyan masu kuɗi da sauran su. Ɓangare guda kuma mata ne waɗanda keda muƙami cikin gwamnati tare da sanannun mata waɗanda ke da burin Kawo sauyi. Akwai ɓangaren da kuma samari ne matasa sai kuma ɓangare ƴan mata wanda kowacce tayi wanka na kece raini. Shigowar wanda aka shirya taron domin sa wato Captain Shareef Muhammad Naira yasa aka ƙara nutsuwa kowa na bawa idon sa abinci. Cikin takunsa na zaratan maza yake tafiya har ya kai zuwa wurin da aka tanada domin sa. Nan da nan MC ya fara magana tare da welcoming manyan mutane da suka halarci wurin. Bayan ya gama da su ya dawo kan mai gayya mai taro. Cikin harshen turanci yace: “Hausawa suka ce barewa ba zata yi gudu kuma ɗanta yayi rarrafe ba...dole dai shima gudun nan zai, kamar dai haka, ɗa ga General Muhammad Naira Shugaban sojojin wannan ƙasa ta Nigeria yake take sawun mahaifin sa, tabbas mahaifin sa mutum ne jarumi wanda kowa yasan shi tun kafin ya kai wannan mataki yake hidimtawa ƙasa da ƙarfin sa da kuma dukiyar sa....ga kuma ɗan sa nan Captain Alee Muhammad Naira Wanda ya gado halin mahaifin shi” Nan fa aka sake tafi taf taf taf. MC yaci gaba “Ba tare da ɓata lokaci ba zan miƙa abun magana ga mai gayya shugaban sojojin ƙasar wato General Muhammad Naira.” Taf taf taf taf Bayan General yayi jawabin sa ne aka bawa mai girma gwamna abun magana, a nan ya yabawa ƙoƙari da ƙwazo irin na wannan soja tare da jan hankalin sauran sojoji da suyi koyi da sadaukarwa irin ta wannan soja. Duk wannan hidima da ake yi babu wanda zai ce yaga ko da murmushin Hamma Zaki ne bare kuma azo gandin sanin kalar haƙorin sa, fuskar nan tamau amma hakan bai hana sihirtaccen kyau da kwarjini irin nasa bayyana ba. Nan MC yace za'a bada damar ci da sha daga nan kuma akwai speech da Hamma Zaki zai yi sai kyaututtuka na musamman da za'a bayarwa wanɗanda suka halarci dagar da aka yi cikin ƙauyen nan. Bayan an kammala jawabai daga wurare daban-daban ne aka fara ciye-ciye da shaye-shaye. Bayan an gama ci da kuma sha MC ya gabatar da abu na gaba a matsayin speech Wanda Captain Shareef Zai gabatar. Ran shi bai so ba haka ya miƙe daga wurin zaman shi nan fa ƴan mata aka ƙara ruɗewa musamman waɗanda Basu ga shigowar sa ba. Ƙarasawa yayi karɓi abun magana tare da riƙe shi. Mintuna 5mins ya share ba tare da yace komai ba, fuskar nan kuwa a haɗe kamar me. Can ya buɗe baki a hankali ya fara magana. “Good day to u all” nan fa hall ya ƙara ɗaukan shiru jin yadda amo da sautin Muryar shi ke karaɗe wurin. Minti 1min yayi yana magana daga nan ya miƙa abun taro. Kowa mamakin rashin magana irin na haɗaɗɗen guy ɗin yake musamman irin yadda mutane ke matuƙar ƙaunar sa. Bayan ya gana nan aka fara basu kyaututtukan su, su Dr. Faruq duk sun karɓi nasu kyaututtukan da ban girma har aka zo kanshi. Ko da zai karɓa masu hotuna ƙyas ƙyas ƙyas ɗin camera kawai ke tashi. Alhamdulillah! Cikin ikon Allah aka yi taro lafiya har aka kammala, daga nan baƙin Hamma Zaki suka lallame shi akan ya tsaya suyi pictures. Babu yadda ya iya aka fara yi musu pictures. Daga family ma suka fito aka fara. Hamma Zaki an sha hoto don kuwa sai da suka yi da kowa, kada kuso kuga yadda suka yi mugun match da Sarah wacce ta sanya army green sari, suna cikin snapping pictures ɗin wata farar matashiyar budurwa ta tunkaro su. Fara ce, kyakkyawa babu laifi, ta saka fitted English gown Wanda suka bayyana ainihin suffar jikin ta, bata cika tsayi sosai ba kuma bata da jiki, haka take zuit kamar alifun, fuskar nan kuwa shaɓe-shaɓe da make up Kamar aljanar roba. Ga wani high hill shoe da ta saka, attachment ɗin da tayi kitso da shi bai samu arziƙin rufuwa ba. Tafiya take tana kwalmaɗewa kamar macijiya har ta iso wurin nasu, lokacin Sarah na gefen Hamma Zaki ta hagu sai Fauzah ta ɓangaren dama. Tana isowa ta ƙaraso tare da miƙa hannun ta tana riƙo hannun Hamma Zaki. Babu zato babu tsammani yaji an riƙo hannun sa, hakan yasa ya ɗago yana duba waye ne don shi tunanin sa ma Dr. Faruq ne. Ido cikin ido ta wani ɗaga mishi gira saying “Hi handsome” tare da kissing hannun nashi. Fuzge hannun sa yayi tare da watsa mata wani dirty look haɗi da tsirta yawu yana yamutsa fuska, a lokacin ne Sarah ta lura da yarinyar ai kuwa ta kifa mata mari ji kake tasss. Hamma Zaki kuwa daga wurin ya wuce zuwa motar da yazo cikin ta. Babu ɓata lokaci ya fuzgi motar sai waje. Ɗagowa tayi da niyyar ganin habibyn nata ne ya mareta ai kuwa taci karo da Sarah da ke watsa mata wani banzan kallo. Ba shiri budurwar tayo kanta wanda yayi dai-dai da zuwan Captain Sulaiman, yana ɗaya daga cikin abokan Hamma Zaki da suka yi aiki da shi Lokacin yana Jigawa State. Captain Sulaiman kuwa tunda yaga Sarah ya faɗa mata. “Keee! How dare You zaki ɗauki wani koɗaɗen hannun ki ki mare ni? Wallahi yau sai naga wanda ya tsaya miki a ƙasar nan har kika samu damar mari na” Captain Sulaiman yaja hannun Sarah da ta juya a fusace tana faɗin “Ubanki ne ya tsaya min nace” ta faɗa cikin Hausar ta da kana ji kasan ba Yaren ta bane. Budurwar ta hasala tare da bin bayan su, jawo gashin Sarah tayi nan Sarah ta saki wata irin ƙara. Cike da ɓacin rai Captain Sulaiman ya juya ya ƙara wanke budurwar da mari. Duk da uniform ɗin dake jikin shi hakan bai sa tayi shiru ba sai ma hawayen da ta goge “Wallahi duk ku biyun sai naga uban da ya tsaya muku cikin ƙasar nan, har Ni wasu zasu saka hannu su mara?, Wallahi sai kun san kun taɓa shalelen Dad.” Ta faɗa tare da ɗauko wayar ta ƙirar iPhone 14 promax, snapping ɗin su tayi sannan ta ja gefe tana haki. Ƙawayen ta ne suka kewaye ta tare da ɗago ta “Pretty ya haka?, Kin dace kuwa” Ɗagowa tayi tana kallon su, ganin shatin yatsu a fuskar ta yada duk suka zaro ido “Kutmelesi....this guy do u shege abi?, Dama irin kyawawan samarin nan basu san ƙimar mutum ba” Ɗaga musu hannu tayi alamar ya isa “Ba Sweetheart bane ya mare ni, wata baindiya ce da ban san uban me ya kawo ta ba ta mare ni, ban Kai ga hukunta taba wani soja yaja hannun ta....bayan na bisu na ja gashin ta kawai shima ya mare ni” Tayi shiru tana haki “Wallahi duk sai sun san wa suka mara, ko Dad bai taɓa ɗaukar hannu ya taɓa Ni ba, talk less of Mommy ammah yau wasu shegu sun saka hannayen su a fuska ta, wallahi sai na koya wa rayuwar su darasi” Ɗaya daga cikin ƴan matan da suka shigar tasu duk irin tata ce tace “Gaskiya ya kamata ki ɗauki matakin da ya dace....ke da kike taka uban kowa ya za'a yi yau wasu banzayen su taɓa ki, wallahi ina bayani ptty ki hukunta su yadda ta dace” “Ke dai Ishy ki bari, wai yau wasu shegu sun mari pretty da alama dai basu san wacece ba” daya budurwar ta faɗa. Ishy ta karɓe zancen da faɗin “Lallai kam ai ko mu bazamu bari ba Wallahi, sai da nace mata mu bi bayan ta kada matsala ta faru tace a'a” Murmushin mugunta Pretty tayi tare da faɗin “Ki rabu da ni wallahi duk sai sun yabawa aya zaƙin ta, ku tashi mu wuce wurin da muka sauƙa, bazan bar Adamawa ba har sai na sace zuciyar mutumin nan” Daga haka su Pretty suka shiga motar da suka zo da ita tare da figar ta zuwa hotel ɗin da suka sauƙa. TOH FAH, WAI JAMA'AH INA ƳAR IYA NE? HAMMA ZAKI AN NUNA HALI KO WANNAN PRETTY A TUNANIN KU ZATA YI NASARAR SACE QALB ƊIN HAMMA ZAKI KUWA? WACECE MA TUKUNNA PRETTY? DUK AMSOSHIN NA A TARE DA DIAMOND LADY, KU CI FABA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY. ZAMU HAƊU GOBE IN SHA ALLAH COMMENT & SHARE PLEASE! [5/18, 10:45 AM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘‘35&36’’’’’ Ɓangaren Hamma Zaki a hasale yaja motar tare da barin wurin. Yana cikin tafiya babu abunda yake sai huci farar fuskar nan tashi ta koma ja, haka fararen idanuwan shi duk sun sauya kala tsabar ɓacin rai. “Why all this!” Ya faɗa tare da buga steering wheel na motar. Da taimakon Allah da kuma dai Addu'a ya samu isa gida lafiya, yana shiga yayi wanka ko zai rage jin ɓacin ran da yake ji. Yana fitowa bai shafa komai ba ya zura jallabiya tare da ficewa garden. Mom kuwa tun fitar da yayi suma suka biyo bayan sa da yake lokacin da yana ƙarami in an ɓata masa rai toh duk abun da ya gani a kusan shi sai ya hallaka shi. Ganin motar tasa lafiya lafiya yasa Mom shigewa ciki tare da shiga bedroom nashi sai dai bata ga ko alamarsa ba, ta duba Toilet nan ma dai shiru, hakan yasa ta fita hankali tashe tare da sanar da sauran ahalin gidan da suka yi tsaye babu mai cewa uffan. ★★★★★★★ *ƳAR IYA POV* Tunda ta fito bata kula kowa ba har ta iso gidan Iya, shigewa tayi abunta tare da janyo daron da ta zuba kashin shanun haka nan na awakin da tumakin ma. Ganin ciyawarta ma ta bushe yasa ta haɗa su cikin babban daro tare da ficewa daga gidan. Kai tsaye gidan Arɗo ta wuce, daga baƙin ƙofa Babu wanda ya kulata haka itama bata kula kowa ba. Tana shiga ta wuce ɓangaren Saratu amaryar Arɗo tare da janyo turmi. Saratu da ke ɓangaren madafan ta jiyo alamun ana taɓa turmi. Daga wurin da take ta ƙwala ihu “Waye a nan?” Ƴar Iya ta amsa da “Ubanki ne!, Daka zanyi”. Saratu na jin Muryar Ƴar Iya ta lallaɓa ta wuce can ɓangaren Innani ba tare da ta kuma cewa komai ba. Tass ta daga ciyawar nan har ta zama gari, daga nan ta juye ta zuba kashin shanun.....shima dai kamar ciyawa sai da ya koma gari, haka ta zuba kashin awakin nan da nan shima ya zama gari. Kai ta ɗan jijjiga alamar ne zata yi next, can kuwa tayi murmushi na samo solution. Haɗe abubuwan da ta daka tayi cikin turmin tare da gauraya. Cikin ikon Allah ta kammala nan kuwa dakan nan ya bada colour mai kyau kamar dai ba kashi ne da ciyawa ba. Kaɗan ta lakuto a hannun ta tare kaiwa hanci tana shinshina kamar mayya. Zaro ido tayi Jin warin still na nan. “Kutumelesin uban can” ta faɗa tare da ƙara dandalowa tana ƙara kai hanci “Aradu warin sa har yanzu na nan, to uban me zan saka ya daina warin” Lokaci ɗaya ta saki murmushi.... Juye abunda ta daka tayi tare da ficewa daga gidan Arɗo don neman abun da zai kashe warin. Gonar Baba Haro ta wuce tare da. Tsinto ganyen mangwaro, ganyen kashu busassu ta koma gidan Arɗo. Suma sai da ta daka su sannan ta haɗe su baki ɗaya. Kamar yadda tayi ɗazu Yanzu ma Sai da ta shinshina haɗin nata, jin warin ya ragu sosai yanzu sai ma ƙamshi ƙamshin ganye yake yasa tayi dariya. Har ta saka hannu Zata kwashe tace “A'ah, akwai ciyawar lemon tsami a bayan ɗakin Arɗo bari na ƙara sai ƙamshin yayi yawa” Tsam taje tare da ciro ɗanyar lemon grass da ƙamshin ta ke fita lokaci guda. Da yake a jiƙe take tuni ta fara haɗe garin maganin waje ɗaya, sai da ta tabbatar ya daku da kyau ta janyo ludayi tare da ɓanɓaro haɗin kayan sana'ar ta. Ba tare da tayiwa kowa magana ba ta wuce tana ƴar waƙarta har gidan Iya. A kan rumfar yayi da kara da aka yi don rufe madafa ta ajiye. Tana ajiyewa ta juyo, bata kai ga fara tafiya ba ta kama baki tare da faɗin: “Na fan gulmar Iya, tana gani sai ta tambaya, mtss” ta ƙarasa da sakin wani dogon tsaki tare da janyo daron ta ta wuce da shi bukkar ta. Wani baccin wahala ne yayi gaba da Ƴar Iya ko dan guje-gujen da tayi a lambun Baba Haro, ga yawon neman kayan haɗin ta. Ba ita ta tashi ba sai da yamma, miƙa tayi tana hamma, ba tare da ta rufe baki ba ta miƙe ta zagaya baya don kama ruwa. Ko tsarki bata samu damar yi ba ta fice da guduuuuuu. Kasuwa ta shiga yayin da wasu ke miƙa gaisuwar su saboda tsoron kada ta ci zalin kayayyakin su. Ganin mutumin Salisu mai burodi tuni ta saki murmushi. Har da wani sunkunyar da kai kafin ta shige rumfar. “Ah Salisu kana nan abun ka!” Murmushin da bai kai zuciya ba yayi yace “Eh wallahi, aka ce mana kin je birni ke kam, yaushe kika dawo rai” Ƴar Iya tace “Ai nayi kwana biyu da dawowa nan ɗin ne ban fiye shigowa ba” “Ayya sannu da dawowa” ya faɗa tare da miƙa mata burodi biyu cikin leda. Murmushi tayi ta ce “Nagode Salisu, kamar ka san yunwa ce ta kawo ni” Mamaki duk ya cika Salisu jin mutuniyar tashi da godiya, abun da tunda suke bai taɓa jin tayi ba. Maganar ta ne ta dawo dashi hankalin sa “To Salisu na tafi, sai na kewayo” Ta faɗa tana wucewa “To toh toh” shima ya faɗa a ɗan firgice. Tana barin wurin Salisu ta ƙara kutsa kai cikin kasuwar. Can da ta gaji da kewaya wa ta fito tare da komawa gida. Gwaten shinkafa da wake Iya tayi musu, daron da ake saka mata ta janyo ba tare da wanke hannu ba ta fara ci hannu baka hannu ƙwarya kamar wacce bata taɓa ci ba, few minutes ta haɗa cinyewa tare da janyo burodin ta, tas ta cinye tana yin gatsa . Shaf ta manta fa ashe bata da abun ƙulla kayan neman halal ɗin ta. Ai kuwa a zabure ta miƙe ta fice a guje, tana isa kasuwa ta shiga shagon Baban Balki. Ganin yana salla kuma ga ledodi nan a baje fara da baƙa kan teburin shagon ai kuwa ta wawusa tare da cikawa bujen ta iska. Tana komawa gida ta fara ƙulla abun da nimah kaina ban san me take nufi da shi ba. Tana murmurshi har ta kammala ƙullawa. Lokacin har an fara ƙiraye-ƙirayen Ishã saboda haka ta adana abun ta. Daga nan ta fice dandali ba tare da bi takan A'i ba. Ba ita ta dawo ba sai da taga dare ta ɗan yi nisa, a hanyar ta ta dawowa ta tsinci wuƙa. Kar kuso kuga murna a gun Ƴar Iya kamar wacce ta samu abun arziƙi. Rungume wuƙar tayi a ƙirjin ta sannan tace “Kai yau dai da shegiyar Sa'a na tashi Aradu, wuƙa sabuwa haka” ta faɗa tana ƙarema wuƙar kallo “Kai daga gani wuƙar nan zata yi kaifi aradu” dariya mai sauti tayi sannan tace “Da gaske mutanen ƙauyen nan so suke na fara samun halaliya ta!!! Toh ai shikenan nikam bani da wata matsala zan yi sana'a da ita” daga haka ta caka wuƙar a kunkumin ta tana tafiya tana ƙwambo irin dai yadda masu yawo da. Wuƙar nan suke yi cike da taƙama. Cike da farin ciki ta wuce abunta har ta isa gida. Tana shiga ta ƙara jawo daron ta ta buɗe tare da irgawa don kada taje fitar ta Iya ta sace Mata. Tas ta lissafa tare da yankewa kayan sana'ar ta kuɗi. Daga nan ta ɗale gadon ta mai ɗauke da katifar yayi Nan ta faɗa duniyar bacci. Babu jimawa sautin gwartin ta ya karaɗe ɗakin. (Nace Allah hokku sa'a Ƴar Iya”) Ba ita ta tashi ba sai wuraren ƙarfe goma na agogo. Hankali kwance tayi miƙa tare da tashi, yawun baccin da ya bushe a fuskar tata ta ɗan ɗebi guntun ruwan dake ƙasan buta ta goge sannan ta cika bujen ta da iska. Ba ita ta dawo ba sai wuraren sha ɗaya na rana, ɗumamen da iya tayi taci sannan taci caccanga da miya da iya tayi da rana. Sai da tayi hani'an ta miƙe tayi wanka. Tana fitowa ta ɗauko murtar da Iya ke ajiye Vaseline nata, shafawa tayi abunta duk da cewa wani wurin yayi yawa wani wurin kuwa bai san wani zance ake ciki ba don babu alamar maiƙo a tattare da shi. Tana shafawa ta ɗauko kwandon kwalliyar ta ɗauko ledar powder irin mai ƙasar nan tare da ɗauko madubi tana kallon fuskar ta. Murmushi tayi kafin ta fara shafa powder ɗin tace “Nimah dai kyakkyawa ce, idan nayi ado ai sai naci gasar kyau ta duniya” dariyar da tayi kumatun ta suka lotsa, abun da ban taɓa tunanin akwai shi fuskar ta ba. Ganin in ta tsaya kallon madubin zata ɓata lokaci yasa ta fara shafa powder ɗin. Yadda take laftawa kai kasan za'a kwashi kyau a wurin. Kamar dai yadda shafin manta ya kasance haka shafin powder ɗin ma, duk tayi damɓare damɓare ga powder Allah ya zuba mata ja kamar masifa. Tuni fuskar nan ta sauya kama daga ta mutum zuwa ta aljana Ƴar Iya. Murmushi tayi tana ci gaba da kallon madubin ta “Ni ƴar nan da yanzu na zama ƴar gayu fah a birni” tayi murmushi lokacin ɗaya kuma ta kwaɓe fuska “Toh ƴan birnin mugaye ne shi yasa amma ina son sukul ɗin” kamar zata yi kuka ta ƙara cewa “Zan koma watarana lokacin na ɗan ƙara wayo....ko dan sai nayi aure tukun” haka ƴar Iya ta saka madubin a gaba tana ƴan zantukan ta. Jambaki ta ɗauko tare da murɗa shi har sai da ya kai ƙarshe, ai kuwa a lokacin ya karye. Tsaki tayi tana kwaɓe fuska “Mtss kaima ai sai kayi, don ubanka yau duk sai ka ƙare” ta ƙarasa tare da damƙo jambakin da ya ɓalle daga stand nashi ya faɗo. Ba iya baki bane ya samu janbaki har kusan hancin ta ta sama ta ƙasa kuwa har haɓar ta. Ganin akwai saura yasa ta shafa akan cikakkiyar girar ta tare da shafa wani a saman fatar idon ta. Har zata miƙe ta ƙara kallon madubin. Murmushi ta sake tace “Aradu zan ci kuɗin samari, dubi kyau kamar Ni nayi kai na!” Ta faɗa tana miƙewa. Bagco nata ta ƙarasa tare da ɗauko atamfar ta leda mai kalar ja, blue, green, yellow sai orange. Blue gyalen ta ta ɗauko ta yafa tare da janyo daron kayan sana'ar ta. Har ta ɗaura a kanta ta tuno da wuƙar ta, saurin ɗaga katifar ta tayi ta janyo ta sannan ta soka ta a kunkumin ta. Daga nan ta ɗaura daron kayan sana'a ta fice tana waƙar ta _kai ku kama sana'a mata_ _kai ku kama sana'a mata_ _macen da bata sana'a aura ce_ Haka tayi ta waƙen ta wasun dai-dai wasun kuwa ta kwaɓa abinda taga dama. Gidan Arɗo ta fara shiga. “Salamu Alekum, gafaran ku dai iyayen ƙauye, gafaran ku dai matan sarki, ga baƙuwa mai neman halaliyar ta nan” Ta ƙarasa tare da shigewa cikin gidan. Ƙofar Saratu ta shiga tana tafka sallama kamar wacce ta kawo abun arziƙi. Daga ɗaka Saratu ta fito jin Muryar Ƴar Iya tana amsa mata sallamar. “Wa Alekumussalamu, maraba da Ƴar Iya shugabar kowa cikin ƙauyen Gallara, maraba da Ƴar Iya tamu mai hannun ɓarna” Jin kirarin da Saratu ke zabga mata yasa tayi murmushi tare da ƙara sawa wajen ta. Sauƙe daron tayi “Wayyoh” Saratu tace “Sannu da zuwa ga taburma nan” ta faɗa tana nuna mata taburmar roba da ta ɗauko daga ɗakin ta. Zama suka yi tare a taburmar Saratu ta gaishe da Ƴar Iya ita kuma ta amsa. Daga nan ta miƙa hannu ta jawo daron kayan sana'ar ta........ COMMENT & SHARE PLEASE! [5/18, 10:47 AM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA ‘‘‘‘“36&37””” Zama suka yi tare a taburmar Saratu ta gaishe da Ƴar Iya ita kuma ta amsa. Daga nan ta miƙa hannu ta jawo daron kayan sana'ar ta. Da mamaki Saratu ke kallon Ƴar Iya ganin dai dagaske take. Murmusawa Ƴar Iya tayi tace “To Saratu Amaryar Arɗo...ga ƴar iya tazo neman halalin ta, kuyi mata ciniki.” Riƙe haɓa Saratu tayi tace “Toh Hajiya Ƴar Iya ai dole ayi maki ciniki, meyeh wannan ɗin?” ta tambaya tare da ɗaukar ƙulli ɗaya tana ƙarewa abun kallo, ganin bata gane meyeh ba yasa ta kaiwa hanci. Hannun ta Ƴar Iya ta buge tare da wafce ƙullin tana aika mata harara. “Ungo wannan” ta miƙa mata ƙullin “Maganin mata ne sadidan da kike gani, Aljanu ne suka bani sirrin wannan maganin da nace musu ina son fara samun halal ɗinah” Tsurewa Saratu tayi jin an ce Aljanu tare da damƙe ƙullin a hannun ta. Ganin yanayin da Saratu ta shiga yasa Ƴar Iya kwantar da murya ƙasa sannan tace: “Kina ji na ko Amaryar Arɗo?” gyaɗa kai saratu tayi “Kinga wannan ƙullin ba wa kowa zan sayarwa ba saboda tsadar sa, kinga ke na zaɓo har gida na aiko miki, saboda haka ki gwada amfanin sa kiga in baiyi ba a biya ki kuɗin ki. Ba tare da ta fahimci me Ƴar Iya ke cewa ba saboda tsananin mamakin taya ma za'a ce yarinyar nan har tasan wani abu aure, balle kuma gyaran shi....toh zai iya yiyuwa tunda Aljanu gareta ammah abun akwai ɗaure head ace yarinyar da yanzu ne ma ta fara fitar da ƙirgen dangi. “Baki tambaya nawa ake saidawa ba kuma kin riƙe a hannun ki” “Yi haƙuri duk farin ciki ya mantar da ni” Ƴar Iya cikin ranta tace “Ke kika sani ai nidai kuɗi kawai nike so” a fili kuma tace “Babu tsada ₦500 ce. Gwalo ido Saratu tayi tace “Ɗaribiyar fa kika ce Ƴar Iya?” “Eh haka nace in baki siya ne ai sai ki faɗa bana son rainin wayo” ta faɗa a ɗan hasale . Marairaice fuska Saratu tayi sannan tace “Kinga kuɗin ne ba'a samu sosai ina ma laifin jaka ɗaya?” Kallon baki da wayo Ƴar Iya tayi wa Saratu kafin tace “Bani abu na in Baki siya a haka, ƴar rainin wayo naga idan maganin yayi amfani ko million Kika tambayi Arɗo ba haka ki zai yi ba” Ɗan tunani kaɗan Saratu tayi ta gyaɗa kanta “Shikenan yanzu yaushe ne ranar biya?” Ƴar Iya tace “Da an kawo sabon kaya ko gobe ne to zaki bani kuɗi na” “Shikenan” Daga haka Ƴar Iya ta miƙe tare da ɗaura daron ta aka ta fice. Ɓangaren Salamatu ta shige tana roɗa sallama “Salamu Alekum, ina mutan gidan ne kam?” Salamatu dake madafa ta kammala kwashe tuwo cikin ƙwarya ta amsa sallamar tana washe baki. “Wa Alekumussalamu, maraba da Ƴar Iya tamu, yau ke ce a gidan nan” “Eh nice amma neman halal ya kawoni, kinga miƙo min taburma In Zauna” Taburmar kaba salamatu ta shimfiɗa wa Ƴar Iya ita ma ta zauna. Hakan ya sa Ƴar Iya sauƙe daron ta tare da zama gefen salamatu. “To salamatu tallan maganin mata na kawo wanda na gaji sirrin daga wurin Aljanun soyayya, sabila da haka ban san ko zaki saya ba” “Toh maganin mata kuma Ƴar Iya, meyeh shi?” ta faɗa tana zare idanuwa. Harara ta wullo mata tana aika mata kallon baki da wayo “Wallahi sai kin siya salamatu na riga na faɗa miki, sarai kin sani Ni zaki yiwa tsiya?, To bari kiji nimah nan na san kina buƙatar maganin, kaji shegiya burgujejiya kamar shanuwa.” ta ƙarasa tana aika mata kallon raini. Cikin kiɗima Salamatu tace “Yi haƙuti Ƴar Iya ai ban ce ba zan saya ba, dole na siya kam.” “Ah to karma ki siya nikam bani da hurobulom ai, kece zaki neme Ni da kaina tunda kishiyar ki ma ta saya, idan Arɗo ya koraki gida nan zaki zo har bukka ta a gidan iya” “Shikenan dai Ƴar Iya, nawa ce kuɗin?” “₦500 ce babu yawa!” “Ɗari biyar!” “Eh a haka kishiyar ki ma ta siya ai, in baki siya ba ma kece a ruwa, a to” “Na ma siya ai, bari na ɗauko kuɗin ko cikin na abincin gobe ne” Murmushi Ƴar Iya tayi kafin tace “To yi sauri ina son shiga cikin garin ne” Fitowa tayi riƙe da ₦500 sannan ta miƙawa Ƴar Iya, daga nan ta ja daron ta ta fice. Gida uku ta ƙara shiga ganin sun bata kuɗi a hannu yasa ta dawo gida abun ta tana murna ita ma yanzu zata yi kuɗi daga nan kuma zata koma birni. ★★★★★★★★★★★ *SHAREEF POV* Bisa grass carpet dake a garden ɗin ya zauna saboda ɓacin rai. Da ya rufe ido babu abunda yake gani sai wannan ƙazamar halittar da ta taɓa hannun sa. Tuno da koɗaɗdiyar fuskar ta mai ibi da a Aljanu yayi, ga kuma wani attachment da tayi kitso tuni zuciyar shi ta fara tashi amai ya taso mishi, da ƙyar Hamma Zaki ya miƙe ya wuce sink ɗin dake cikin garden ɗin, amai yayi sosai kafin ya wanke bakin sa ya fito saboda lokacin sallah yayi. Daga cikin abinda ya tsana yaga mace ta sanya bai wuce attachment ba, ya tsani abun gabaɗaya ma shi ƙyama abun ke bashi. A daddafe ya miƙe ya ƙarasa ciki, part ɗin Nenne ya wuce ba tare da kowa ya san yana can ɗin ba saboda duk suna can part ɗin Mom ana ajajjaɓin ko ina Hamma Zakin ya shiga. Da ƙyar yayi sallar a zaune ma saboda yadda kanshi ke ƙara juyawa. Yana idarwa ya samu gado ya kwanta tare da lumshe idanuwan shi. Yanayin gabaɗaya is not stable for him. He just wanna forget that devil creature and yayi alƙawarin wulaƙanta ta idan ya warware daga takaicin da ta ƙunzuga mishi a gaban ƙannen shi. (Bata da ma hankali, bata san waye Hamma Zaki ba, mutumin da kyawawan mata waɗanda ba na ƙasar ba wasu ma ƴaƴan sarakuna suke nuna zalamar su kan shi baya damuwa da su, ko kallon arziƙi baya bari su amsa daga wurin shi. Ballantana ita...toh ai ko Sarah da take baindiya bai bawa fuska bare kuma nunar rana. Afwan Aunty pretty gaskiya mike faɗa miki) Allah sarki Mom da ƙyar aka lallashe ta ta haƙura ta zauna. Gaba ɗaya hankalin ta duk ya fice daga jikin ta jin ance ya dawo ammah kuma gashi su sun rasa shi, tsoron ta ma kada ace ya illata kansa. Hajiya Granny ma sai Nenne ke aikin rarrashin ta saboda kuka take bilhaƙƙi. “Shikenan uban me rai suka yiwa ɗan jikan nawa, yo Ni dama can Shagalin bai kwanta a raina ba gashi wata tsinanniyar ta wargaza wa jika na farin ciki. Wallahi ko ɗiyar waye sai muyi Shari'a da ubanta akan jika na” Cikin kwantar da kai Nenne tace “Kiyi haƙuri Granny, Ina da tabbacin duk inda Shareef yake yana cikin aminci, kin san Allah bazai cutar da wanda baya cutar kowa ba saboda haka kiyi haƙuri nasan zai dawo” Cikin shessheƙan kuka Granny tace “Toh Allah yasa” A nan part ɗin Mom dukkan su suka yi sallar maghrib daga iyaye mata zuwa ƴaƴayen, iyaye mazan kuma sun fice don neman mafita. Wani matsiyacin bacci ne ya ɗauke shi a kan gadon cikin wannan yanayi. Ƙiran sallar Ishã ya sa ya farka, miƙa yayi ɗauke da addu'ar bacci a bakin sa. Ganin duhu ya tabbatar masa da Ishã tayi. Tuna cewa babu wanda yasan yana nan yasa ya yi yunƙurin miƙewa don yasan iyayen shi na cikin tashin hankali. Miƙewa yayi ya fara takawa a hankali, da ya fito parlourn yaga babu kowa ciki ya tabbatar ma kanshi suna can ana neman shi, da sauri ya fice daga part ɗin Nenne zuwa part ɗin Mom. Kamar ance su juyo dukan su duka waiwayo ai kuwa ganin shi ɗin ke shigowa ya sa duk suka miƙe tare da nufar sa. Kukan Mom keyi tace “Son where have u been?, Duk nan ka sa mun shiga tashin hankali” Murmushin yaƙe yayi yace “Calm down everyone Ina can garden ne” daga haka kowa ya koma tare da miƙewa da niyyar yin sallar Ishã in sunyi sai suyi dinner daga nan kowa ya wuce part ɗin su. Mom kuwa sai da ta ƙira su Daddy ta sanar da su cewa an samu son ɗin nasu tukun tayi sallah. Bayan sunyi sallah duka suka hallara a dining area, a nutse aka fara ci yayin da baka jin sautin komai sai ƙarar cokala. Ana gama dinner kowa ya watse zuwa nashi ɓangaren. Hajiya Sarah na gama cin abincin ta ta wuce bedroom nata tare da ɗauko wayar ta. Instagram ta fara hawa tare da posting pictures ɗin da suka yi ita da sauran family wurin taron, few seconds aka fara liking, COMMENTS kuwa ba'a magana. Wasu na tambayar mijin ta ne ko dai?. Wasu kuma har sun ajiye zancen mijin ta ne, hala shi yasa ma baya kula kowacce mace tunda ya samu wannan indian girl ɗin. Cikin daren kuwa babu abinda ya kai pictures masu trending a Media, Instagram, Facebook, Twitter, YouTube, duk ta ko'ina zancen ake. Wasu na can suna publishing sati faɗin su kan Sarah da kuma Hamma Zaki, yayin da wasu ke ƙara santin haɗa jini da wannan kyawawan family masu nagarta. Around 10:00pm wayar Sarah tayi ringing, picking tayi tana murmurshi tare da kara wayar a kunnen ta. “Hello” aka faɗa daga ɗaya ɓangaren “Hi” ta faɗa cikin sanyi murya. “Princess how're u doing?, Kin koma gida lafiya?” “Alhamdulillah” “Masha Allah, kiyi saving digits na, we'll talk tomorrow” “Ok bye” Murmushi Mai sauti yayi sannan yace “Ok good night and sweet dreams” Daga haka suka katse kiran. Haka kawai Sarah ta tsinci kanta cikin tsananin farin ciki bayan kammala wayar da Captain Sulaiman wanda shima ɓangaren sa wani irin farin ciki ya shiga, burin sa ya kusa cika, ya samu choice nashi, ga kyau ga wayewa ga kuma ilimi. Uwa uba nasabar ta da abokin su wanda suke ji da shi. Ɓangaren Hamma Zaki bayan sun ci abinci kiran Hamma Saleem ya shigo, sanin wane irin hali ɗan uwan shi zai shiga bayan jin bayanin abinda ya faru a wurin taro yasa yake ta banko masa ƙira tun lokacin sai dai shikam yana can garden ma, ko da ya dawo cikin gidan ma bai samu sukunin taɓa wayar ba. Lallamin sa shima Hamma Saleem ɗin yayi nan da nan ya sauƙo har da ƴar dariyar shi, daga haka suka yi sallama yana ce masa zai shigo in Sha Allah. Bayan sun kammala wayar ne kawai yaji sha'awar hawa online. A nan yaci karo da abubuwan dake trending, cike da mamaki ya shiga pictures ɗin yana dubawa wasu yayi tsaki wasu kuma yayi murmushi, kan picture nashi wanda aka yi musu da duka sisters ɗin shi ya tsaya. Ya jima yana dubawa yana murmushi. Ƙaunar su ce kawai ke yawo cikin zuciyar shi yayin da yake jin zai iya sadaukar da komai nadhi saboda su. Daga nan comment section ya shiga, nan fa yayi ta jera tsaki ganin haukar mutane. Ya jima yana dubawa wani wurin kuma ya yi murmushi. Haka ya leƙa all media handles nashi daga nan ya kashe phone ɗin tare da ajiyewa. Wanka yayi tare da ɗauro alwala ya saka Armani pyjamas tare da fesa turare, daga kashe light ya bar iya bedside dim light, nan ya haye bed ɗin sa tare da janyo blanket, addu'oin baccin sa yayi tare da kwanciya. _Annabi tsira da aminci su ƙara tabbata gare shi yace, duk wanda yayi alwala kafin yayi bacci, ya kaɗe shimfiɗar sa sannan ya kwanta ɓangaren dama tare da karanto addu'oin bacci, Ubangiji zai sanya Mala'iku su zama dakarun da zasu yi gadin sa har zuwa lokacin da zai tashi._ Hadisin ingantacce ne. _Addu'oin bacci_ ★Ayatul kursiyy ★Amanarrasul ★Suratul-ilhlas (qul huwallahu ahad) ★Suratul falaq (qul authu birabbil falaq) ★Suratul-Nas (qul authu birabbil nas) ★Bismikallahumma Amutu wa ahya. COMMENT & SHARE FISABILILLAHI! [5/18, 10:50 AM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA “““39&40””” Sanyin asuba da ke busawa yayin da alfijir ya keto, Babu abunda ke tashi sai kiraye-kirayen sallah wanda ake jin sa daga can nesa. Miƙa yayi ɗauke da addu'a a bakin sa. (الحمد لله الذي أحيانا بعد ما أماتنا و إليه النشور). Sai da ya shafe wasu sakanni kafin ya ziro sawayen shi ƙasa. Toilet ya nufa tare da alwala sannan ya gabatar da sallar sa. Yana idarwa ya yi azkar ɗin sa na safiya tare da karanta wasu ayoyi daga cikin Alqur'ani. Ba shi ya tashi daga praying mat ɗin ba sai around 6:00am. Bayan ya naɗe ta ya haye gado tare da komawa baccin sa saboda har yanzu bai gama cinye hutun da aka bashi ba. (*Ko kun san cewa miƙewa tsaye immediately bayan tashi daga bacci ne ahaifar da matsaloli da dama?, Idan baki sani ba toh daga hau in kin farka daga bacci ki tabbatar kin cigaba da kasancewa a kwance na wani lokaci kafin ki miƙe domin kiyaye lafiyar ki*) *PRETTY POV* Directly Cikin tuƙin ganganci suka fizgi motar sai hotel ɗin ransu a matuƙar ɓace. Bakin kowa tsit banda sautin waƙar _Rush_ babu abinda ke tashi cikin motar. Bayan sun isa Pretty ta buɗe musu ɗakin tare da shigewa. Pretty dake wani hura hanci ga fuskar nan tayi ja jawur kamar an watsa mata ruwan zafi (nace ai kusan hakan, ga marin Sarah ga na Capt Sulaiman). Kayan dake jikin ta ta fara cirewa. Tas sai da ta cire komai tukun ta ɗaura towel ɗin dake lanƙaye jikin hanger. Toilet ta shiga ta sakarwa kanta ruwa ko zata ji sauƙin raɗaɗin da ke damun ta. Ishy, Fauzy, da kuma sumy suma a lokacin suka tuɓe suna jiran fitowar ta, sai da ta ɗan ɓata lokaci kafin ta fito, Ishy da Fauzy suka shige abun su a tare yayi da sumy ta tsaya taya Pretty shiryawa tana lallashin ta. Su biyun tare suka fito sannan sumy ma ta samu ta shiga. Cikin wasu tsinannun kaya suka shirya waɗanda ko a zaman gida wanda ba kai ɗaya ba bai dace ka sanya su ba. Bayan sun shirya Pretty ta ƙira aka aiko musu da abinci. Sai da suka yi hani'an suka yi brush, batun sallah kuwa babu shi, turare suka fesa tare da miƙewa suka yi waje. Motar su suka nufa but this time around Sumy ke driving, duk irin yadda kiɗa ke tashi a motar basu daina hirar da suka fara ba. Pretty da kanta ke lafe jikin kujerar motar tace “Guys yau ban san ya zanyi ba, yet zuciya na bai daina zafi ba” “Sorry Pretty, yanzu zuciyar ki zata sauƙa for a while, ance Adamawa akwai sweetboys wadanda suka san harƙa, just relax kiyi mankas muyi rawa abun mu, all this sadness will fade away.” Sumy ta faɗa tana juyo gefen ta da Pretty ke zaune. “Uhmm” Pretty ta faɗa tana sakin wani killer smile “Ban jin zan iya mantawa da wulaƙancin nan da wuri fah” “Ke dai ki bari” inji Ishy dake sit na baya ita da Fauzy. Fauzy tace “Just relax babe, ko baki mance ba in mun dawo we'll make u forget it” “Toh Allah yasa” Suna isa suka samu wani ɓangare tare da parking motar su. Tun daga fitowar su suka ci karo da wasu gang ɗin samari suna busa shisha. “Payo....ɗago kaga wasu hot babes a nan” ya faɗa yana tsaida kallon sa kan su Pretty dake sanye cikin wasu tsinannun transparent gowns da basu da maraba da babu. “Bura uba” payo ya faɗa yana muƙewa tsaye “Alquran yau akwai shagali Subato” ya faɗa tare da miƙa wa subato hannu. Miƙewa suka yi tare da nufan su Ishy da suke daf da isowa yadda suke. Kallon banza su Pretty suka aikawa su subato tare da raɓawa ta gefen su suka shige ciki. Sauran gang members ɗin kuwa dariya suka saka suna musu gwalo. Directly hall ɗin suka nufa, a daidai entrance door ɗin suka ci karo da wata budurwa samanta wani ƙato sai haƙarta yake yi (Authubillah ko kunyar ido babu). Raɓa su suka yi sannan suka shige cikin hall ɗin. Suna zama waitress ɗin ta miƙa musu alcohol Wanda brand ɗin ta ana hana mutane ta'ammali da ita. Sai da suka yi mankas daga nan kowacce ta manta yadda take, sautin waƙar dake tashi sai a lokacin yake ɗibar su, Pretty da Ishy suka nufi stage ɗin suna tangal-tangal. Rawar da sukeyi kaɗai ya isa ta bawa mutum haushi, su gasu kamar macizai saboda lanƙwashewa amma haka suka yi tayi. Payo da ya shigo yaga mutanen nasu sunyi mankas yasa ya janyo hannun Pretty suka shige room ɗin da ya kama. Suna shiga ya fuzge mata rigar da da ita Gara babu nan ya cafki boobs ɗin ta ya fara sucking, tuni salo ya canza aka wuce zuwa wata duniyar. Ishy kuwa tare da subato suma suka baje tasu hajar. Fauzy da Sumy kuwa dama sun fi ƙwarewa a fannin lesbian hakan yasa da suka samu partner suma suka shige nasu room ɗin tare da ci gaba da masha'ar su. (Innalillahi wa inna ilayhi rajiuun, wannan itace rayuwar da matasan wannan zamani suka ɗauka a matsayin wayewa, zina ta zama ruwan dare, maɗigo (lesbian) da kuma luwaɗi (homosex) sun zama jiki a wurin matasan mu. Subhanallah, ayyukan da suke samarda fushin Allah su bayi suke aikatawa hankalin su kwance?, Ina zamu je ne?, Ina zamu saka rayuwar mu ne?, Shin mun manta akwai mutuwa ne?, Lallai ya kamata mu farka mu san ne muke yi, ba fa komai ce wayewa ba! Mu tuna zamu mutu, ya muke tunani idan mutuwa ta riske mu a irin wannan hali?, Me zamu faɗawa Ubangijin mu?. Ƴan uwa ya kamata mu san cewa aikata waɗannan abubuwan baya daga cikin wayewa sam sai dai ma taɓewa, kuma masu aikata waɗannan ayyuka in Basu tuba ba kafin mutuwar su toh Ubangiji ya tanada musu azaba mai raɗaɗi tun daga mutuwa har zuwa hisabi da kuma miƙa kowa gidansa na har abada. Allah yasa mu dace). Su Pretty basu bar club ɗin nan ba sai around 2:00am, lokacin alcohol ɗin ya saki sumy da yake ita ba wani da yawa ta sha ba, hannun Fauzy ta kama tare da miƙa ta cikin motar su sannan tabi rooms ɗin da Ishy da kuma Pretty suke, suma ta ɗsuko su ba tare da ta mayar musu da kayan jikin nasu ba ta miƙa su motar. A haka ta fuzgi motar sai hotel ɗin su, da ƙyar ta taya su suka shigo ciki saboda har yanzu suna kan network. Nan duk suka baje wasu ƙasa wasu suka haye bed. Sai around 10:00am suka tashi, bayan sunyi wanka suke tambayar taya suka dawo. Dariya sumy tayi tace “Dole kuce haka babes, irin wannan dare da gani U guys enjoy it” Su duka suka kwashe da dariya, Pretty tace “Tuni na manta da maganar Sweetheart, sai yanzu na tuna, hope zaku ƙara raka ni tunda sai gobe mu wuce ko?” Ishy tace “Shegiya Pretty dole ki manta da shi mana, kinje kin buɗe xender ya tura Miki bahubali!” ta faɗa tana sakin dariyar shaƙiyyanci. Fauzy da har yanzu ke dariya tace “Babes baku da dama gaskiya, kiji wai xender!” ta faɗa tana miƙa wa Sumy hannu wacce itama dariyar take tsulawa. “Ke dai ki bari sumy, ai gwanda xender wai kinji bahubali!” itama ta faɗa suna cigaba da dariya. Bayan sunyi breakfast kuma suka ja motar su neman pretty's Sweetheart. ★★★★★★★★★★ *ƳAR IYA POV* Yau tunda ta tashi daga bacci tayi wanka tare da sheƙa kwalliyar ta irin ta Aljanu. Janbaki kamar zai yi magana haka powder kamar wata dodanniya. Neman halal ɗin ta ta fita, yau ma dai bata biya ta gidan su A'i ba saboda ita ta a can tana shirye-shiryen bikinta ne. Tana fita ta fara zagayawa daga gidan dake maƙwabta da su. Da sallama ta shiga kamar dai ba Ƴar Iya ba. “Salamu Alekum, ina mutan gidan ko sun fita ne” Goggo hari dake cin ɗumamen tuwon dawa tace, “A'ah yau kuma mu aka tuna shalelen Iya?, Maraba lale iso muci ɗumame” Zama Ƴar Iya tayi kan taburmar tana sinne kai. “Iy Aradu inna Hari yau ke na tuna, talla na kawowa sirikan ki, bari na shiga ciki” “Tallen me kuma shalelen Iya?” Goggo hari ta jefa mata tambaya. “Maganin mata ne, ku fa tsofin nan kun fiye tambaya, haka iya ma ta sani gaba da tambaya to Sarkin Aljanu da kansa ya koya min, kuma duk wanda bai siya ba Aradu mijin ta sai ya sake ta” Ta faɗa tana miƙewa tsaye. Goggo Hari jin ambaton Aljanu da Ƴar Iya tayi yasa ba shiri ta bata hanya. “Allah ya kawo kasuwa” Gaba Ƴar Iya tayi abunta ba tare da amsawa ba. Lirwanu ɗan Goggo Hari na farko ya fito zai fita suka ci karo da Ƴar Iya. Dakatar da shi tayi ta hanyar faɗin “Mallam ka bawa matarka kuɗin siyan magani” “A'a shalelen Iya ce?, Ya Iya ɗin tana lafiya” Katse shi tayi da cewa “Ba shi na tambaye ka ba in ka damu da Iyar ka je ka gaishe ta ai, mtsss ka bawa matar ka jaka biyu da rabi kaji” “Toh toh babu damuwa” ya faɗa tare da bin bayan Ƴar Iya har suka isa, su Ƴar Iya ashe akwai hankali a bakin ƙofa ta tsaya jira, bayan ya fito ta tambaye shi ko ya bayar, da ya bata amsa ta barshi ya wuce ita kuma ta kutsa cikin ɗakin. Ala dole haka tabi sirikan Goggo Hari duk suka siya tukun ta fito daga gidan. Tunani ta fara ina zata kuma nufa? “Gidan Baba na!” ta faɗa tana murmurshi. Bata tsaya ko ina ba sai gidansu. A lokacin Inna Zaliha na zaune a kan kujerar zaman gida tana wanke-wanke tana rera ƴan waƙen ta. Ko sallama Ƴar Iya bata yi ba ta kutsa cikin gidan sai wani hura hanci take tana ɗaga shi sama, bakin nan yayi gaba kamar bututu. Inna Zaliha da fuskar ta ke nuna tsantsan mamaki ta kalli Ƴar Iya tana yatsina fuska “Ke kuma rasa kunya daga ina?” Ƴar Iya bata amsa mata ba sai ma ƙoƙarin sauƙe kayan tallar ta da take. “Wai ba magana nike maki ba?, Me Kika zo yi gidana?” Duk rashin hankali irin na Ƴar Iya sai da ta tsaya ta maimaita me kike yi a gidana cikin ƙwaƙwalwar ta. Can ta kalle Inna Zaliha tace “Gidan ubanki ne ko nawa?” Baki buɗe Inna Zaliha ke kallon Ƴar Iya tace “Eh ba shakka gidan ubanki ne kam..eh babu shakka haka ne” Ƴar Iya ta harare ta tace “In baki sa na dawo gidan da zama ba, shegiya mai shegen baƙin hali da baƙar zuciya” Inna Zaliha tuni ta tsure da zancen Ƴar Iya tunawa da sharaɗin da Bokan ta ya bata....hakan yasa tayi murmushi tana sunkuyar da kai. “Wa ya isa ya hana shalelen Iya guda?, Yanzu dai me ya kawo ki maza ki faɗamin” Ta faɗa cike da ƙosawa coz zaman ta a tare da su akwai matsala. Sai da ta gama shan ƙamshin ta tace “Maganim mata na kawo miki ki saya, ai nasan kina amfani dashi” “Maganin mata kuma Ƴar Iya?” ta watsa mata tambayar. “Eh shi dai, ko kin fi so nayi ta maimaita magana kamar jaka?” “Aah ba sai kin maimaita ba, wane iri ne” “Irin wadda kike amfani da shi ki mallake min tsoho na har kika raba mu da shi gaba ɗaya, Aljanu da kansu suka bani wannan maganin bari kiji, Kuma in Kika karɓa bakiyi amfani da shi ba Aradu sai kin mutu, shegiya mai raba ɗa da uwa” Cikin sanyin murya Inna Zaliha tace “Nawa ne?” Ƴar Iya tace “Naira dubu biyu ne babu yawa, kuma zan dawo don kullum sai kin siya Aradu” Zaro ido Inna Zaliha tayi tana kallon Ƴar Iya “Dubu biyu fa kika ce shalelen Iya?” “Eh haka nace!” ta bata amsa a fusace, “Kina amsar fiye da haka ma daga wurin Baba na ki hallaka a wurin ƙato ai” “Shikenan yi haƙuri, bari na ɗauko miki kuɗi” ta faɗa tana miƙewa don ta ƙosa Ƴar Iya ta bar gidan zata shiga ɗakin taji Muryar Ƴar Iya “Ki taho min da dubu ɗaya zan biya na siya burodi” Kamar inna Zaliha zata yi kuka haka ta amsa da to tare da shigewa ɗaki. LIKE PLEASE [5/18, 10:52 AM] 💎Diamond Bhatool💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA “““41&42””” Dubu uku cas Inna Zaliha ta ɗauko tare da damƙawa Ƴar Iya tana zuba godiya. A yatsine Ƴar Iya ta amshi kuɗin sannan tace “Idan Baba na ya dawo kice masa inji ni ya bani wasu kuɗaɗe za'a yi bikin ƙawata daga nan kuma nima za'a yi nawa ba daɗewa. “to to zan faɗa masa, sai anjima” Harara Ƴar Iya ta Banka mata tare da ɗago daron ta ta aza shi bisa kayin ta, nan ta fice abun ta tana murna. Ganin tayi ciniki yasa ta yanke shawarar komawa gida ta adana kuɗin ta. ★★★★★★★★★★★★★★★★ *PRETTY POV* Yammacin yau Laraba Pretty ta shirya kaima Sweetheart nata ziyara bayan ta binciko bayanai game da shi. Sanye take ciki wasu expensive English wears, Wanda suka ɗame ta sosai, surar jikin ta ana gani kamar dai babu. Kitson attachment da tazo da shi ta sa aka sauya duk da ta kashe kuɗi mai yawa kafin ayi mata, ƙwaƙuyayyen kan nata ta ɗaurawa wata cap na gashin doki tare da gyara ta tsam, nan sai ka rantse gashin ta ne. Fauzy ce ta mata makeup wacce ta mayar da ita mutum-mutumi, in ka ganta babu abinda zai hana ka guduwa, hankali kwance ta fesa uban turare tare da yiwa ƙawayen nata alama da suzo su wuce, suma da shigar tasu babu gwanda, sai dai ita sumy Abaya ta saka tare da rolling veil. Cikin motar kuwa Pretty farin ciki ya hana ta sukuni, zata ga Sweetheart ɗin ta, babu abunda ke tashi sai sautin waƙar India tuni ta manta duniyar da take. Dai-dai Gate ɗin gidan General Muhammad Naira suka yi horn, gateman ya buɗe, sai da suka kai dai-dai parking space suka yi parking motar. Ba tare da sun fito ba suka tsaya ƙarewa motocin dake wurin kallo, ga kuma tsarin gidan da tuni ya tafi da su. Pretty da ta tuna mai ya kawo ta ta ce “Babes wanne part ɗaya zamu shiga ne?” Fauzy tace “Mu shiga na farkon idan ma ba nan bane ai za'a tura mu wani” “ƙwarai yadda Fauzy ta faɗa haka za'a yi” Sumy ta amsa mata. A gadarance cike da yauƙi suka fito daga motar tare da nufar entrance na part ɗin. Ganin door ɗin a buɗe yasa suka kutsa kayuwan su ciki. Ƙamshin da ya daki hancin su kaɗai yasa su lumshe ido, bisa latsa-latsan kujerun suka yiwa kansu masauƙi. Ganin babu wadda ya ko gifta yasa Ishy faɗin “Pretty wai zaman me muke yi ne?, Letz just get in mun tsaya a nan babu mai fitowa fa” Sumy kam da kallo ta busu don tuni gidan ya matuƙar burge ta, sai taji inama ace tana da wata alaƙa da gidan. Su Fauzy ma dai zuciyar nan a cunkushe ana bawa ido abinci. “Assalamu Alykum” sallamar Fauzah da ta doki kunnuwan su yasa su waiwayowa don ganin waye” Mutuwar tsaye taso yi ganin baƙi a parlourn Mom, baƙin ma Christian, sai da ta hango Sumy tukun taga ita kamar musulma ce. A hankali ta ƙara sa tare da faɗin “Ina yinin ku” Murmushi duka suka yi mata tare da faɗin “lafiya ƙalau a tare” “Bari na sanar da Mom tayi baƙi to” Daga haka bata jira amsar su ba ta wuce bedroom ɗin Mom. “Good evening Mom.... I'm back oh sorry u've visitor outside” Cike da mamaki tace “Visitors kuma Fauzah, su waye” “I don't know them but it seems like Christians ne, suna jiran ki” ta ƙarashe tare da nufar hanya zata fice. “Wait Fauzah, ask Laraba to bring something for them, Ina fitowa” “Ok Mom” Kamar yadda Mom ta umarce ta haka ta wuce ɓangaren su Laraba ta sanar da ita saƙon Mom kafin ta wuce bedroom nata ta cire uniform tare da yin wanka. Sai da Mom ta ƙara kusan five minutes ta fito sanye cikin kayan al'adar su, sari ce blue wacce tayi matuƙar ƙara bayyanar da kyau da kuma izza irin ta Mom ga kuma kyakkyawar kwantacciyar baƙar sumar ta da ta zubo da ita ta baya. Jin takun takalmi yasa duka suka waiwayo..... idanuwan su suka zaro tare da sakin baki kowa na ayyana abun da ke zuciyar sa. Cike da mamaki ganin duk ciki babu wanda ta sani yasa ta ƙara ƙure su da ido ko zata tuna su. Su kuwa kallon da Mom ke jifan su dashi ya sauƙar musu da shakkar ta na lokacin. Tana ƙarasowa ta zauna tare dayin murmushi. Ganin kamar ba kansu ɗaya ba yasa Mom fara gaida su. “Ƴan mata ina yinin ku?” Cikin ƙiƙina suka amsa babu kunya da “Lafiya Mom,” Mom! Mom ta ƙara nanata sunan cikin zuciyar ta, “Ikon Allah, wai mom ko wace Mom ɗin rai?” ta faɗa a ranta a fili kuma tayi murmushi tare da faɗin “Sannun ku da zuwa, sai dai ban gane ku ba fah” Sumy ce tayi ƙarfin halin faɗin “Laa Mom yaranki ne ai” Ishy ta cafke da faɗin “Mun zo wurin Captain ne Mom” Mom kam sun ɗaure ta da abun mamaki, ita dai iya sanin ta Son nata baya ma kula mata bare yayi mu'amala da waɗannan masu kama da Ashawos ɗin nan, murmushi kawai tayi tace “Ku ƙira shi kuce kuna jiran shi parlourn” Jin hakan yasa fitsararriya Pretty faɗin “Ji rainin wayo...” bakin ta Ishy tayi saurin rufewa da hannun ta tare da fatan Allah yasa Mom Bata ji ba, sai dai aikin gama ya gama. Fauzy ce tayi ƙarfin halin faɗin “Ki bar zancen ku da Sulaiman ya wuce mana Pretty, na san shine har yanzu a ranki” daga haka ta kalli Mom dake mamakin Pretty tace “Kiyi haƙuri Mom kada kiyi tunanin dake take, tana da rashin lafiyar maimaita abu idan ya faru da ita, ga bata iya mantuwa” Murmushi Mom tayi tace “babu komai” Ganin shiru babu wacce ta ɗago waya ta ƙira Hamma Zaki yasa Mom tace “Ku ƙira shi manah, ni zan wuce ciki” Cike da duniyanci Ishy ta kaɗa yatsar ta “Wayyo Mom, Kinga saboda saurin da muke na har mun mace wayoyin mu a gida” “Shikenan bari na wuce, zan ƙira shi”. Bedroom ɗin ta ta koma tana mai juya maganganun baƙin Hamma Zaki. Bayan ta sanar da shi ta hanyar kiran shi a waya ta faɗa tunanin su waye waɗannan, ko suwaye da gani babu alkhairi a tattare da su, yara sam babu ɗaa bare girmama babba..... “Hmm to Allah ya kyauta, amma tabbas tana son sanin abu game da su. Kwance yake yana latsa wayar sa kasancewar bai jima da dawowa daga wurin aikin shi ba. Ya miƙa wayar zai ajiye gefe yaji ringing na wayar. Kamar ba zai yi picking ba ya na tsani tare da ɗagowa, ganin Mom yasa ga zare idanuwa tare da picking. “Sweetheart...” ba tare da ta barshi ya faɗi me zai ce ba ta katse shi da faɗin “Kana da baƙi a waje, suna jiran ka a parlour” “Parlour?” ya faɗa cikin sigar tambaya coz Basu yi da Dr. Faruq zai shigo ba ko wani friend nashi. “Who Are they Mom?” “Get down and see” daga haka ta katse ƙiran. Kamar baya so ya buɗe ƙofa tare da fitowa, shi ba mutum bane mai son gulma ba hakan yasa bai dubo daga can ba. Black jallabiya be jikin shi, kamar koyaushe ƙamshin daddaɗan turaren shi ke tashi. Sam ko kaɗan bai sa a ranshi matan nan ne baƙin shi ba hakan yasa ya miƙe zai je Bedroom ɗin Mom. Cak ya tsaya jin an riƙe hannun shi. A hanzarce ya waiwayo don ganin waye wannan. Dum! Ƙirjin shi ya buga, shi bai yi magana ba sai wani kallo da yake aika mata cikin ranshi kuma yana faɗin (This girl again?”. Ganin hankalin shi na kanta yasa ta marairaice fuska “Please Sweetheart, no sau ɗaya ka bani damar nan, wallahi ina son ka shi yasa na baro Abuja takanas saboda kai, Please ko sau ɗaya ka bani lokaci”. Ba tare da yace mata komai ba ya janye hannunsa ya wuce zuwa bedroom ɗin Mom wondering why yarinyar nan ta ƙara dawowa gare shi. Tun shigowar shi Mom ta tare shi “Kun gaisa da baƙin ne?” Kai ya gyaɗa yace “Mom, why are they here, ban san su ba” Mom tace “Ban gane ba, baka sansu ba fa kace?” Cike da ƙosawa yace “Is ok” Daga haka ya fito, fitowar shi yayi dai-dai da shigowar Sarah daga bedroom ɗin ta. “Good Evening bro” “Evening” daga haka ya wuce zai haye stairs ɗin. Ganin zai wuce yasa Pretty miƙewa da sassarfa tabi bayan shi, babu tsammani taji an riƙe ƙugunta ta baya. Juyawa tayi don ganin waye ke shirin yi mata shamaki da abun son ta. Cikin sanyin murya Sarah tace “You again?, What brought u here?” ta faɗa tana pointing Pretty. Cikin son danne fushin ta don ita kanta ta fara tabbatar wa cewa Sarah matar Sweetheart ɗin ta ne ko da ganin mahaifiyar Sweetheart ɗin nata tace “Rabu da Ni ba rigima nazo yi ba” “Then me ya kawo ki?” jin tayi shiru yasa tace “Idan ma saboda shi ne ki sani baki kai ya soki ba, mata masu daraja kaɗai ke samun matsuguni a zuciyar shi, hope I'm clear!” Cikin jin haushi Pretty ta janye jikin tare da nufi bedroom ɗin da taga Mom ta shiga ɗazu, babu sallama tace “Mom!” mamaki ya hana Mom ko da amsawa ne sai jin Muryar Pretty tayi tana faɗin “Mom na zo ne don furta soyayya ta ga ɗan ki Captain, da farko i thought zai yi sauƙi kamar ke but ashe kawai hasashe ne iri nawa, don Allah Mom let him Know that Ina son shi. Gobe zan wuce gida Abuja, amma zan ƙara dawowa” Daga haka ta fice tare da yiwa su Ishy da ke cikin mamaki da ɗimuwa alamar su fito. Babu shiri suka miƙe suna makawa Sarah harara tare da ficewa. ★★★★★★★★★ *ƳAR IYA POV* Sana'a Ƴar iya ke yi babu kama hannun yaro, ciniki kuwa sosai baa magana, da zarar kayan sana'ar ya ƙare zata ɗebo ta ƙara busarwa taje gidan Arɗo ta daka abun ta. Samun da take yi bai hanata yin halin da ta saba ba, gashi bikin A'i sati mai zuwa ne, hakan yasa Ƴar Iya bada himma wurin sana'ar ta, kullum tayi ciniki zata kawowa Halima ta ajiye mata. Safiyar yau tunda Ƴar Iya ta tashi take jin shiga hancin mutane, hakan yasa ko karyawa batayi ba ta fice sai gidan Inna Zaliha. Inna Zaliha da aka ce wai ciki gare ta abun yayi wa Ƴar Iya daɗi don yadda ta san wannan kwaɗayayyiyar to dole zata ji daɗi musamman da ta tuna duk zuwa gidan da zata yi sai ta tarar da abun daɗi. Tana isa lokacin Inna Zaliha ta shiga bayi ga kuma tukunya bisa murhu ƙamshi na tashi. A hankali cikin sanɗa ta ƙarasa wajen murhun tana lashe baki. “Wayyo Ni Ƴar nan, yau akwai burauba, bari na samu na fice kafin mayyar nan ta fito.” A haka ta ɗaga tukunyar daga kan murhun tare da lallaɓawa ta fice abun ta. Tana kaiwa hanyar waje ta ajiye don ganin menene a ciki. Ido ta zaro tana faɗin “Shegu ai yau kam mun haɗu, Aradu kun daina ci ku kaɗai”. Dahuwa ce ta kaza wacce daddawa taji a ciki, ga romon jajir da shi kamar me. Bata tsaya ɓata lokaci ba ta arta a guje sai gidan Iyar ta. COMMENT PLEASE 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* __Fictional story of life with full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __ SHAFI NA “““43&44””” _ina Taya ki murna sosai Ameeran Mama (amarya), Allah Ubangiji ya bada zaman lafiya ya sa gidan ki Kenan. Ina godiya da ƙaunar ki sannan ina ƙaunar ki da yawa_ _Shafin nan na baki shi ke kaɗai duk da cewa littafin na Nazari Writers ne amma Ni da kaina nayi kyautar shi😀😏 Inna Zaliha na fitowa daga bayi ta ƙyalla idon ta ga murhun da ta ɗaura dahuwar ta. Ƙwalalo idanuwa waje tayi tare da rufe bakinta da hannu. “Subhanallahi” ta furta tana juya wa tare da fara ƴan dube dube. Ta shafe kusan mintuna 30 tana dube-duben da take yi gashi fitowarta daga wanka kenan. Zuciyar ta na wani irin bugu ta shiga bukkar ta tare da ajiye soson buhu da kuma garin omo da tayi wanka da shi. Zanin ta iya ƙirji ta fito tana mai ci gaba da dube-duben nata sai dai babu tukunya babu kuma alamar ta. Hakan ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba musamman da bata ji ko ganin alamar shigowar wani ko wata ba. Ganin dube-duben ba zai fisshe ta ba yasa ta koma bukkar ta tare da zama a bakin gadon karan ta tana jajantawa kanta. Bata kawo cewa Ƴar masu gidan ce ta ɗauke ba duk tunanin ta Almajirai ne, bayan dawowar Baba da ta sanar masa ya lallashe ta tare da bata haƙuri. *ƳAR IYA POV* Tana Isa gida iya ta shige da gudu, bayan ta ajiye tukunyar ta fara ƙwallawa Iyar ƙira kamar wuyan ta zai faɗo “Iya! Iya!” Jin shiru yasa ta shiga bukkar ta. Kwance ta sameta tana sharara bacci har abun haushi, ga wani yawun baccin ta a wurin. Tsinke ta zara daga tsintsiyar kwakwa dake gurin, sai da ta saita cinyar iya ta caka mata tsinken tana cije baki. “Inna lillahi” iya ta faɗa tana miƙewa a zabure, “Na shiga uku meyeh wannan ɗin” Ƴar dariya Ƴar Iya ta sake tare da faɗin “Aiki na kawo miki, kizo ki ƙarasa dafa mana muci daɗi” Bayan ta Iya ta bi suka fita, a dai-dai wurin tukunyar ta tsaya tare da nuna mata “Ki juye ki bani na mayar musu” “Toh” iya ta faɗa tana juyewa cikin wata tukunyar. Bayan ta juye Ƴar Iya ta ɗauki tukunyar tare da wucewa gidan Inna Zaliha, tana shiga kamar dai ɗazu haka ta lallaɓa ta ajiye tukunyar. Ta juya zata fice murfin tukunyar ya karkace tare da bata sautin ƙarr...ƙurrr. Da gudu Inna Zaliha ta fito daga cikin bukkar ta don ganin ko an maido mata da dahuwar ta ne. Bata ga kowa ba sai wulgawar mutum, hakan yasa ta ƙaraso da gudu tana buɗe tukunyar sai dai ga mamakin ta babu komai a ciki. Ihu ta tsala tana faɗin “Na shiga uku ni Zaliha ƴar dahuwar tawa aka sace min!” Ta share mintuna tana kukan ganin dai babu sarki sai Ubangiji yasa ta janyo tukunyar ta wulla ta wurin wanke-wanke. *ƳAR IYA POV* Wankan ta tayi tare da sheƙa kwalliya abun ta, atamfar ta ɗinkin riga da zani ta sanya tare da wani yanƙwanannen mayafin ta irin na ƴan ƙauye ta saka. Bayan tayi wa Iya sallama kai tsaye ta wuce gidan su A'i. Matsayin ta na Aminiyar amarya yasa tana shiga suka wuce dandali coz dama ita suke jira ta iso. Wasanni iri-iri aka yi a dandali ciki kuwa har da wani wasa da ya ƙayatar. Amarya da angon na zaune a kan benci ne dama tare da ƙawayen su dake kewaye da su. Ƴar Iya da kanta ta iso gaban su ɗauke da faranti a hannun ta, haka shima Sama'ila abokin Basiru shima da nasa. Cikin farantin Ƴar Iya jar hoda ce, turare ɗan feshi sai kuma hula, ledar dake hannun ta kuma tsire ne ciki. Farantin Sama'ila kuma turare ne ɗan feshi da kuma kwalin kayan dake jikin amarya A'i sai kuma leda dake hannun shi. Ƴar Iya a gaban ango ta tsugunna shi kuma Sama'ila gaban amarya. Sai da aka tabbatar kowa ya shirya tukun aka fara. Ƴar Iya tace: yanzu ango zai nuna mana yadda zai tafiyar da matar sa, zamu ga ko zai iya kula da ita ko a'a”. Sauran ƴan mata da samar suka saka shewa. Basiru ne ya ɗauki hodar dake kan farantin Ƴar Iya, ya buɗe tare da zazzaga hodar jikin soson hoda. Bai tsaya ɓata lokaci ba ya kamo fuskar A'i tare da fara shafa mata hodar. Nan fili ya kacame da ihun ƴan mata da samari, kowa sai dariya yake don wasan ya burge su. Sai da ya gama shafa mata hodar ya janyo kwali ya ɗaura mata tare da ɗaukar turaren yana feshe ta da shi. Bayan nan Sama'ila ma yayi gyaran murya yace “Yanzu zagayen na ango ne, Saboda haka zamu so muga yadda amarya zata shirya shi. A hankali A'i ta jawo hula tare da sanya masa ita daga nan ta fara feshe shi da turaren. Nan da nan ƙamshi ya cike ko ina. Bayan an yi shiru kuma aka juye tsiren dake cikin leda bisa farantin. Ango ya bawa amarya a baki haka amarya ma ta bawa ango. Daga nan aka watse kowa ya wuce gida abun sa. Rana bata ƙarya in ji malam bahaushe yace sai dai uwar ɗiya taji kunya. Kamar haka ne yau Lahadi aka ɗaura auren A'i da mijin ta Basiru mai gyaɗa. Murna da farin ciki sosai su Ƴar Iya suke musamman yadda suka yi haske abun su saboda gyaran da Halima ke musu. A daren ranar ne kuma aka miƙa A'i gidan mijinta. Ginin jar ƙasa ce wanda aka laikaye shi da jar ƙasar, ɗakuna biyu gareta sai kuma madafar abinci sai bayi. Ko ina zancen A'i ake yi ai yarinya tayi goshi, yarinya tayi goshi. Bayan an kai amarya Ƴar Iya ta dawo gida tare da adana kuɗaɗen ta da ta samu. Washegari da sassafe Ƴar Iya ta daka kayan sana'ar ta ta fita talla, sai da ta sayar da shi tas sannan ta wuce gidan A'i. A can taci abincin rana da aka aiko daga gidan su Basiru sannan ta wuce zuwa gidan Iyar ta. *ALEE POV* Mom ba ƙaramin mamaki tayi ba jin batun su Pretty. Ganin zama bai kama ta ba yasa ta fice don dubo yaron nata. Kwance yake bisa faffaɗan gadonshi dake laikaye da white bedsheet, idanuwan shi lumshe yayin da fuskar shi ke kallon sama. Zuciyar shi ke mishi ɗaci da zafi. “Why this girl?, Me yasa suke son shiga rayuwar shi ne kam?” Ganin babu mai bashi amsar yasa shi miƙewa tare da nufar Toilet ya watsa ruwa. Ƙarar ruwan da Mom taji yasa ta fahimci yana Toilet me but duk da haka da buƙatar ta jira taga a wani hali yake. Ganin shiru bai fito ba ne yasa Mom sauƙa ƙasa ta jira shi. Fuskar shi a ɗaure ya sauƙo, ganin babu kowa yasa ya fice tare da nufar motar shi, Joseph da ya zo hannu kawai Hamma Zaki ya ɗaga masa alamun bai buƙatar tafiya da shi, Wani pack dake kusa da su yaje ko zuciyar shi zata daina ƙuna da kuma zafi. Sai around 11:00pm ya dawo, lokacin Daddy ma ya dawo. Mom da ta sanar da Daddy abun da ke faruwa yasa yake jiran dawowar Hamma Zakin. Daddy ne ya miƙe tare da tunkaro Hamma Zaki dake shigowa, cike da sakin fuska ya iso dai-dai Hamma Zakin yana hugging nashi. Duk irin yadda yake ji sai yaji zuciyar shi tayi wasai. “Good Evening Dad” “Evening sweetheart, Ina ta jiran dawowar ka” Daddy ya faɗa yana sakin murmushi. Shima Hamma Zakin murmushi yayi yana faɗin “Thatz my Dad, I'm back” Ya faɗa tare da zaunar da Daddy a kan kujera sannan ya zauna kusa da shi. Shafo sajen sa Daddy yayi yana murmushi kafin yace “Sweetheart me yake damun ka?, It seems like you are not happy today” marairaice face Daddy yayi yace “Tell your Dad what's wrong with u?” Cike da kulawa Hamma Zaki yace “Nothing Daddy, I'm ok” Kallon ka raina min wayo Daddy yayi masa sannan yace “Ok what about that young lady?, I mean wacce tazo ɗazu” Ɓata fuska Hamma Zaki yayi yana yamutsa ta “Oh Dad, please don't like her at all” Murmushi Mai ɗauke da ma'anoni daddy yayi sannan yace “Alright tunda baka so, brothern ka ya kira ka and baka picking call ɗin, ya ce a faɗa maka he's coming back tare da Waheeda da kuma baby Fauzan.” daga haka Daddy ya fara shirin miƙewa, murmushi Hamma Zaki yayi yace “Ill call him in na shiga, good night sweetheart” Waving hand ✋ Daddy yayi tare da wucewa. Shima Hamma Zaki ya wuce bedroom ɗin shi. Nasan readers sun Matsu su san wacece pretty!. *Wacece pretty?* Alhaji Saminu Hambali shine cikakken sunan mahaifin ta, matar shi ɗaya rak wato Hajiya Salima. Sunyi aure ne irin na soyayya sai dai sun shafe shekaru basu samu haihuwa ba sai akan Nabila (Pretty), Hajiya Salima (Mami) mace ce mai shegen biye-biyen malaman tsibbu da kuma bokaye, ko kaɗan bata ƙaunar wata ta shigo gidan mijinta da sunan mata, hakan yasa ta mallake Alhaji Saminu (Dad). Dad a ɗaya ɓangaren Hamshaƙin ɗan siyasa ne wanda a yanzu haka yake riƙe da matsayin ministan walwala. Pretty ta tashi cikin gata da sangarci, hakan yasa ta tashi da buɗaɗen ido tunda ita kanta mahaifiyar Tata bata samu isasshiyar tarbiyya ba talkless of ta bawa wani. Sam ko kaɗan Pretty Bata shakkar kowa, ko uban waye yayi mata bata ƙyale shi. Bayan ta kammala secondary school ta fara karatun ta a Nile University dake birnin tarayya, a nan tarbiyyar ta ta ƙara taɓarɓarewa don kuwa maza ne ƙawayen ta, biye-biyen hotels da clubs baa magana, a nan suka haɗu da Ishy wacce ita ma mahaifin ta babu laifi yana da kuɗi. Sanadiyyar Ishy da ta kasance ƙawar Fauzy. Fauzy ma ta gagari iyayen ta duk da irin gatar da suke mata amma haka ta zaɓi rayuwar banzanci ta bar su, takan shafe watanni ba tare da ta ziyarce su ba. Sai kuma Sumy wacce itace baya bata a harƙar shaiɗanci, iyayen ta ba wasu masu hali bane compared to Iyayen sauran, sanadiyar Fauzy ta fara harƙar lesbian hakan kuma na da nasaba da yadda Fauzyn ke kashe mata kuɗi. Waɗannan ƙawaye ka nemi tsarin Allah daga sheɗan sannan ka nema kan su, don sun san salon bariki da iskanci, Pretty kuwa in ta saka rai akan abu to babu makawa sai ta samu, hakan yasa bata damu ba ko da Hamma Zaki ya nuna baya yin ta, coz ta san da Mamin ta tasan batun shikenan zai shigo hannu. Wannan kenan! Kun jini shiru masoya Littafin Ƴar Iya?, To na dawo da zafi zafi na fatan ba zaku bari na huce ba😒😂 ah toh, in na huce sai kun neme ni. Mu haɗu gobe don jin yadda zata kaya, yanzu ne Littafin Ƴar Iya zai fara daɗi, wai hausawa suka ce wasa farin girki😄 to haka a nan ma fah, ku dai kuci gaba da bibiyar Littafin, Ga Ƴar Iya, ga Hamma Zaki, ga Pretty kuma? To ko yaya haɗuwar su duka zata kasance?. Ku ci gaba da bibiyar Alƙalamin DIAMOND LADY💎, Ina matuƙar ƙaunar ku. Yanayin comments ɗinku yanayin tsayin page da yawan post. Love U all. [6/12, 11:40 AM] Diamond Bhatool💎🩷✍️: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA “““46&47””” Tunda Pretty suka isa Abuja, ko dropping ƙawayen nata bata yi ba su ma basu buƙaci hakan ba coz da gani tana cikin tsantsar damuwa, ta kuma yi alwashin auren Hamma Zaki ko ta halin yaya. Mamin ta na zaune a parlourn ta ƙaraso janye da trolleyn ta, da gudu ta saki trolleyn tare da nufar ta. “Mami na oyoyo” Murmushi matar tayi wacce fuskar ta ke zubi da ta prettyn. “Oyoyo shalelen Daddyn ta, kin dawo kenan?” Yamutsa fuska Pretty tayi tace “Eh na dawo Mami” Ƙura mata ido Mamin tayi ganin damuwa a fuskar ta. “Lafiya mutanen Adamawa an dace dai?” Kwaɓe fuska Pretty tayi kafin tace “Mami wannan sai kin taimaka, wallahi mami kamar gunki yake, ko saurara ta baiyi ba” Zaro ido Mamin tayi tace “Ban gane ba” Pretty ta ce “Mami nidai kisan yadda zaki yi na auri Captain Alee in ba haka ba mutuwa zanyi” Cikin sigar rarrashi Mamin tace “Is ok Shalele, Yau ba sai gobe ba zamu wuce wurin na kan dutse, shi ɗin wa da zai ƙi saurarar ki?, In kina so ma cikin one month za'a yi auren” Cike da farin ciki tayi hugging Mami tare da kissing goshin ta. “Thank u Mami na, bari na shiga ciki” Kai Mami ta gyaɗa hakan yasa Pretty Jan trolleyn ta ta wuce ciki Mami kuma ta tsunduma duniyar tunani. Cije leɓe yayi tare da faɗin “Fansar mu ce wannan lokacin!” Daga haka ta miƙe. *ƳAR IYA POV* Tun bayan bikin A'i Ƴar Iya ta rasa abokiya amma duk da haka bata bar halin ba. Yau ma kamar kullum tafe take tana waƙar ta sai ga wasu yara sun zo wucewa kowannen su da kaji biyu a hannu. Ƴar wuƙar ta da banyi tunanin daga ina ta same ta ba ta zaro tare da nufar yaran. Dariyar mugunta tayi haɗi da kallon su sannan tayi shiru, jikin yaran in banda karkarwa babu abinda yake yi kowa sai addu'a yake cikin ransa. Kamar ba ita ta gama murmushi da dariyar nan ba ta haɗe rai. Kallon ɗaya su tayi tace “A! Ɗan Manunu ina zaku je haka da kaji” Cikin rawar murya yaron da ta ƙira sa Ɗan Manunu yace: “Ƴar Iya aikan mu aka yi mu siyar, don Allah kar ki mana komai” Hararar Ɗan Manunu Ƴar Iya tayi tace “Don ubanka nace zan ma wani abu ne?” Jin ta ɗau zafi yasa Ɗan Manunu sunkuyar da kai ƙasa tare da faɗin “Kiyi haƙuri don Allah”. Dariya take abunta kamar ba wacce ta tsare gida yanzu ba, can kuma tayi shiru tana bin yaran da harara, Allah sarki su kuwa kawunan su ƙasa kamar bayi a gaban sarki. “Kuzo nan ɗaya bayan ɗaya,saura ku gudu Aradu duk na san gidan iyayen ku, kuma Aradu wanda ya gudu har uwar sa sai na yanka” Ƴar Iya ta faɗa tana fitar da ƴar wuƙar ta waje. Ɗaya bayan ɗaya kowa yake zuwa, haka zata karɓi kazar a gaban idon su ta yanka , in ta yanka sai ta bayar sannan tace “Wuce gida don ubanka, ai ana buƙatar naman a gida maza a je a ci” Haka Ƴar Iya ta kammala yanka kajin nan tas sannan ta wanke jinin da ruwan rijiyar dake gefen su sannan ta wuce gaba hankali kwance. Ba Ƴar Iya ce ta koma gida ba sai wajajen Ishã don kuwa sai da ta biya gidan A'i taci abinci duk da cewa bata ƙoshi ba tukun ta dawo. Dawowarta kuwa yayi dai-dai da dawowar Baffi daga masallaci. Jijjiga kansa yayi cikin ransa yana roƙawar Jikar tasa shiriya a wurin Ubangiji. A zahiri kuma murmushi yayi tare da faɗin “Shalelen Iya an dawo kenan?” Murmushin ta maida masa, ko ba komai in taga Baffi tana jin wata irin nutsuwa “Eh wallahi Baffi, sannu halan daga. Masallaci kake” “Eh daga can nake” Baffi ya amsa mata. “Sannu to, mu shiga mana” Bin bayan ta Baffi yayi suka shiga tare. Bayan sun shiga Iya ta kawowa Baffi langar tuwon sa da ta miya sannan ta ɗebo masa ruwa a kofin silver. Bayan ta gama da Baffi ta haɗawa shalelen ta ma nata abincin. A nan suka ci abinci dare can suka baje hira a wajen. Ana cikin hirar Baffi ya ɗan yi shiru can kuma ya maida kallon sa ga Ƴar Iya. Baffi yace “Shalelen Iya Ni kuwa kina zuwa gidan ƙawar ki A'i?” Cike da basarwa ta ce “Eh Baffi ɗazu ma naje, wani abun ne halan?” Girgiza kai Baffi yayi yace “Aah babu komai”. Daga haka yayi shiru yanayin fuskar shi na sauyawa. Jin shirun da Baffi yayi yasa Ƴar Iya ɗagowa ta kalle shi dai-dai lokacin da ta tura langar tuwon ta da ƙafa. Ƙwalalo ido waje tayi saboda yanayin hasken farin wata yayi dau, kana iya ganin komai ba tare da ka haska ba. Tafi minti biyar tana kallon Baffi, iya kam dama bacci ya ɗauke ta bata ma san me ake yi ba. Hawayen dake zirarowa daga idon Baffi babu ƙaƙautawa shine yaja hankalin Ƴar Iya ya kuma sanya ta faɗawa duniyar tunani a karo na farko cikin rayuwar ta. Ko me ya samu Baffin ta yake kuka? Nan da nan ita ma yanayin fuskar ta ya sauya izuwa mai nuna tsantar damuwa. Wannan shine karo na farko da ta taɓa shiga irin wannan yanayin! Karo na farko da taji kukan wani mahaluki ya taɓa zuciyar ta har take jin rauni cikin ta! Karo na farko da taji zuciyar ta na bugawa ko me yasa? Ba komai ne ya sanya Ƴar Iya shiga wannan yanayi ba sai jin ana mata magana cikin kunnuwan ta. Ba zata iya tantance Muryar waye ba ammah tanajin koma waye mai irin Muryar nan yana kashe mata jiki. Wannan ba shine karo na farko da taga damuwa a fuskar Baffi ba amma wannan ya tsaya mata. Cikin kunnen ta na dama taji ana faɗin “Ke Ƴar Iya baki ganin yadda Baffin ki yake hawaye ne?” Cikin kunnen ta hagu kuma taji ance “Yo ke Menene naki a ciki? Kin taɓa shi ne?” Caraf a kunnen ta na dama aka ce mata “Ƙwarai kina da haɗi da shi, kin manta matsayin uba yake gare ki?” “Amma ai ba uban bane” Muryar ta doke ta cikin kunnen ta na hagu. “In kin faɗi haka baki kyauta ba, shi uban naki ya damu da ke ne?” Toshe kunnuwan ta tayi tare da sakin wata irin ƙara sannan ta miƙe. Dai-dai wurin da Baffi yake “Baffi na me yake damun ka” Goge hawayen fuskar shi Baffi yayi yace “Babu komai shalelen Iya, yau ba zaki fita dandali bane?” ya ƙarasa tare da sakin murmushi. “A'ah Baffi, sai ka faɗa min me yake damun ka” Murmushi yayi tare da faɗin “Babu komai shalelen Iya” Haɗe fuska tayi tana faɗin “Allah Baffi duk cikin ƙauyen nan kowaye ya taɓa ka bana ƙyakewa Aradu rama maka zanyi” Baffi yaji daɗin maganar hakan yasa ya ƙara yin murmushi. “Ina roƙon Allah ya nuna min auren shalelen Iya ko ba komai akwai shagali” “Hhhhh kaji Baffi” Ta faɗa tana sakin wata mahaukaciyar dariya “Baffi ai Ni ba zan yi aure ba” Fuskar Baffi ta sauya ganin hakan yasa ta ce “Kai ɗin so kake nayi aure?” “Ehmana shalelen Iya kinga na kusa mutuwa” “Aah Baffi na, to ai zanyi kafin ka mutu ɗin” Murmushi Baffi yayi yace “To Allah yasa!” Ba tare da ta amsa ba ta cika bujen ta da iska daga bakin zauren tace “Na fita zaga gari” Washegari da safe bayan ta farka kamar kullum, ko fuska bata wanke ba ta jawo ɗumamen ta da Iya ta gama rabawa. Tana gama cinyewa ta cika bujen ta da iska. Tayi yawo sosai sai da Azahar ta wuce gidan A'i, guntun abinci taci bata wani daɗe ba tace zata tafi. Da yammaci Ƴar Iya ta nufi fada, a can ta zauna gaban Arɗo. Cike da tsoro Arɗo ya gaida ta. “Ƴar Iya ina wunin mu” Babu kunya ta amsa da “Lafiya ƙalau” Nazartar ta yayi na wani lokaci kafin yace “Lafiya dai ko wani abun kike so halan” An zo wajen, dariya tayi don ranta kafin tace “Arɗo akwai fahimta Aradu, ƙwarai abu nake so” Gyara zaman shi yayi yace “To ina jinki Ƴar Iya, menene kike so haka?” Itama sai da ta gyara zaman ta sannan tace “Ina so zanyi aure ne” Arɗo bai yi mamakin jin hakan ba saboda dama ita bata ga kunya ba duk da kasancewar ta jinin Fulani. Dariya yayi tare da faɗin “Masha Allahu, abu yayi kyau, ai haka ake so, shekaru sha uku ai kin ɗana ya kamata ki huta” Murmushi tayi sannan ta fara magana “To Arɗo ai ba iya maganar da ta kawo Ni ba, ba kuma ka tambayi waye mijin ba” Ta ƙarasa tana fari da idanun ta. “O oo ai dai kam, to wanene angon?” Dariya tayi sannan tace “Nima ban sani ba, sai dai yau ina so ka sanar bayan sallar magrib duk wani saurayi dake cikin Gallara ya iso fada ana neman sa, daga nan sai in zaɓa” Cikin farin ciki arɗo yace “To to to ai shikenan yanzu za'a sanar, wannan ai abun farin ciki ne” Cikin ranshi yace “Zaa rabu da Bala'i da yardar Allah ” Tun daga wannan lokaci Ƴar Iya ta baro fada bata tsaya ko ina ba sai gidan Iya. Hajiya Iya lokacin tana kwashe tuwo taji shigowar shalelen nata. Kallon ta Iya tayi ganin farin ciki kwance a fuskar ta yasa itama tayi murmushi tare da faɗin “A! Shalelen Iya har kin dawo yau ɗin” “E Iya na dawo, yau kam farin ciki nake kuma zaku shiga in kun san dalili” Cike da mamaki Iya tace “Affafai! Halan kuɗi kika samo?” “Yo Iya in kuɗi ne ai da sauƙi, to na kisa komawa birni saboda aure zanyi” Farin cikin ya hana iya magana can dai tace “Naji daɗi sosai, Shalele aure fa kika ce?” “Eh mana Iya aure nace! Ko baki so ne?” “A'ah Shalele na, Ni kuwa nake so kiyi aure baki ga duk sa'annin ki ma sunyi auren ba, basu har da ɗa ko ƴa” Iya ta faɗa tana murmusawa. Ɓangaren Ƴar Iya ma haka kawai take jin wannan auren a ranta, zata yi ko dan Iya sa Baffi su ji daɗi. COMMENT, LIKE and SHARE FISABILILLAHI! Ina matuƙar alfahari da ku masoya na, wannan shine wasa farin girki 😄 kuci gaba da kasancewa sa alƙalamin DIAMOND LADY 💎 don jin ci gaban labarin _Ƴar Iya_ Kuyi sharhi da yawa ɗin nan thanks alot. [6/13, 7:21 AM] Diamond Bhatool💎🩷✍️: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA “““47&48”””" Washegari da sassafe Mami ta shirya musu tafiya. Ta haɗa komai tun daga kan abinci har zuwa abun sha kasancewar tafiyar zata yi tsawo zasu kwashe kwana guda da yini kafin su isa. Zuciyar Pretty tayi wasai, farin ciki kawai take Sweetheart zai so ta kuma zata mallake shi. Duk wannan shirin da suke Daddy bai sani ba, sai dai tun ranar da Pretty ta tayar mishi da gyambon dake zuciyarshi ya kasa sukuni, wutar ɗaukar fansa ce ko yaushe take ruruwa cikin ranshi. Misalin ƙarfe goma na safe suka ɗauki hanya sai wajen Natoli aiki yanzu magani yanzu. Mami da kanta take driving nasu har suka yi tafiya mai nisa. Wuraren Azahar suka yada zango tare da cin abinci daga nan suka yi gaba babu batun sallah a ransu. Har maghrib basu ƙara tsayawa ba sai da suka ga sun shigo wani ɗan ƙauye, hakan yasa suka yada zango ba tare da sun fice daga motar ba, a nan suka ƙara cin abinci suka sha abun sha. Mami da ta riga ta gaji ta koma seat ɗin mai zaman banza tare da kwantar da kanta, nan bacci ya kwashe ta. Ba su suka bar ƙauyen nan ba sai da Asubahi sannan suka ƙara yankar hanya, sunyi tafiya sosai kafin suka kai ga wata hanya da ta rabe biyu, ɗaya abushe take ƙaraf yayin da ɗayar kuma alamun damshi da ni'ima suka bayyana tattare da ƙasar. Hanyar da ta bushe Mami ta umarci Pretty da ta ɗauka, babu musu ta yanki hanya. Tafiya suke amma babu ko alamar ƙuda da ke rayuwa cikin wannan sahara, har sai da yamma tayi tukun suka fara hango hayaƙi na tashi, nan Mami tayi murmushi ta kalli Pretty dake tuƙi cike da gajiya sannan tace “Kuka ya ƙare, Captain Alee zai so ɗiyata” Ɗaga ido Pretty tayi tare da maida hankalin ta kan tuƙin da take yi tace “Wayyoh! Can't wait”. Daga wurin sukayi packing sannan suka fito tare da ɗaukar jakar kuɗaɗen sa suka zo dashi suna tunkarar wurin da hayaƙin yake tashi. Sunci uwar tafiya kafin su kai ga wani ƙatoton dutse wanda ke ɗauke da wani wankamemen kogo, nan da nan jikin Pretty ya fara rawa. “Mami nikam mu koma” Harara mami ta Banka mata “Baki da hankali ma” ta faɗa tare da jan hannun Pretty suna tunkarar kogon. Tun daga baƙin ƙofa suke jin wani sauti, shi ba kuka ba sannan shi ba dariya ba, a haka dai suka daure tare da kutsawa ciki. Wata mahaukaciyar tsawa mai razanarwa aka yi ana faɗin “Ba'a shiga da ƙafar dama” Da ƙyar suka shiga aikin yadda suka kiɗime. Suna shiga wata guguwa ta tashi yayin da wani duhu ya mamaye wurin. Can bayan waɗansu daƙiƙu haske ya dawo, guguwar nan ma ta ɓace nan da nan!. Basu tsinci kansu ko ina ba sai a wani ɗaki wanda ke ɗauke da fatotin naman daji, kura ne, zaki ne, damisa ne! Da makamantansu. Tun daga nan bakin su ya mutu. Can daga wata kusurwa ya fito, baƙi, jibgege mummunan gaske wanda fuskar shi ke ibi da ta shanu.....Natolu kenan! Suka ce sha yanzu magani yanzu. Cikin dariyar su irin ta rikaƙƙun bokaye ya zuba musu ido tare da zama gaban kayan aikin sa. “Maraba da zuwa Hajiya Salima uwar ɗakin Ɗan Hambali” Bokan ya faɗa yana murmushi Sunkuyar da kai tayi don ta san dokar shi ba'a haɗa ido da shi. “Kinzo ne batun ɗiyar ki ko, ba sai kin min bayani ba na ga zuwan ku tun jiya cikin madubi na, sai dai wannan aiki zai yi matuƙar wahala amma in kin sake kuɗi zai tafi dai-dai” Shiru mami tayi boka yaci gaba da bayani “Zai so ta, zai aure ta ammah kuma akwai wani abu da baya nunawa wanda da gani matsala ce, akwai abun da zai bayyana cikin rayuwar shi wanda zai zama katanga ga wannan aiki, har yanzu ban samu fahimtar menene ba ammah dai aure tsakanin ɗiyarki da yaron ba fashi” Haka dai boka ya zance su su kuwa tsabagen farin ciki suka zuba masa kuɗin tare da fecewa abun su. _(Ina ƙira gareku Ƴan uwa mata ku tuna cewa zuwa wurin boka haramun ne a musulunci, ku tuna duk wanda ya aikata hakan kuma toh ya aikata mafi girman laifi wurin Ubangiji kamar yadda Annabi Sallallahu Alyhi wa Sallam ya faɗa. Duk wanda ya halarci wurin boka to haƙiƙa ya kafurcewa abinda aka sauƙarwa Annabi Muhammad)_ _(Har ila yau iyaye mata ya kamata musan cewa ƴaƴan mu amana ce da Ubangiji ya bamu, ya zama dole mu kula da su mu kuma basu tarbiyya mai kyau kamar yadda yazo cikin Alqur'ani, haka nan annabi ma ya ƙara nanatawa Muminai a kan irin girman da amanar yaro take da shi a wurin iyayen shi!)_ _(Kada ki kasance cikin iyayen da zasu banzatar da yaran su, iyayen da basu damu da tarbiyyar yaransu ba! Kada ki kasance cikin su don kuwa ki sani Ubangiji zai tsayar da ke ranar alƙiyama ya tambaye ki a kan kiwon nan tun daga haihuwa, girman su zuwa mutuwar su? Wace rawa kika taka cikin rayuwar su?, Shin kin basu tarbiyya ko akasin haka)_ _Allah ya shiryar da mu sannan ya bamu ikon kiyaye amanar da ya bamu na yaran mu_ Tunda suka dawo tayi wanka ta huta washegari tabi Flight ɗin da zai kaita Adamawa. Tana isa ta wuce army barrack na su Hamma Zaki, tana isa ta tambayi office nashi aka nuna mata. Dai-dai corridor na office ta tsaya tare da fitar da wata kwalba mai ɗauke da wani jan abu a ciki. Murmushi tayi tare da buɗe ta ta juye ta kaf a jikin ta, nan take wani irin mahaukacin ƙamshi ya tashi a wurin. Sai da Pretty ta daidaita kanta sannan ta yi knocking, “Yes come in” ya faɗa cikin kamammiyar Muryar shi. Shiga ciki tayi tana wani rangwaɗa shi kuwa hankalin shi na kan wata takarda da yake karantawa. Ƙamshin da ya bugi hancinsa ne ya dawo dashi daga duniyar tunani. Murmushi ta aika masa tare da faɗin “Hi Sweetheart!, Na dawo gare ka Please wannan lokacin kada kace a'a in ba haka ba zan iya rasa rai na” Lokaci ɗaya ya ɗago da niyyar balbaleta sai dai ƙamshin da ya ƙara ziyartan hancinsa ya dakatar da shi. “Say something sweetheart ko na koma?” Samun kanshi yayi da jijjiga mata kai, murmushi tayi tace “Alright bari na zauna” Wuri Pretty ta samu ta zauna tare da kafe shi da Mayun idanuwan ta. Cikin ranta kuwa murna ce fal haka tayi ta masa zuba shi kuma ya kasa hanata sai ido kawai yake Binta da shi. Lokaci azahar ya shiga toilet tare da ɗauro alwala yayi sallah Pretty kuma lokacin ta fice, abinci tayi musu order tare da dawowa. A nan suka ci har Yamma. Lokacin tashinsa ma da yayi tare suka wuce a motar shi kowa sai mamaki yake ganin Captain Alee da mace. Wanda hakan ɗin duk shirin ta ne da kuma roƙon shi da tayi ya barta ta sauƙa gidansu. Bayan sun koma gida Mom ta jima tana mamakin dawowar Hamma Zaki da mace! Haka dai sauran mutanen gidan. Ita dai Sarah Bata kula ta ba haka ta ishi mutane da iyayi da feleƙen tsiya. Washegari ma tare suka fita coz tace mishi zata koma gida washegari ne ammah tana so ya tura iyayen shi a sanya ranar auren su. Kamar wani gaula kuwa ya sanar da Daddy da Mom, duk irin yadda Daddy ke son Hamma Zaki yayi aure kawai taji abun ya fita mishi a rai saboda yarinyar amma babu yadda zai yi tunda shi yake so. Ita kuwa Mom a matsayin ta na baindiya tasan sihiri iri-iri coz duk wasu shu'uman sihirhiru daga India yawanci suka samo tushe, a lokacin ta tabbatar ɗan ta yana cikin kogin asiri ne sai dai ta ɗauki alwashin ɓata aikin nan gaba saboda wani dalili. Bayan Pretty ta wuce gida haka tayi ta damun Hamma Zaki da ƙira, dare, raba, safiya kamar jaraba, babu laifi kuma tana ɗagawa duk da cewa baya jin komai game da yarinyar kawai dai shima ya ji ya amince da buƙatar tata ce. Su Dr Faruq sunyi mamaki sosai haka su Nenne, Mommah, granny Kai duk iyalen Muhammad Naira sunji a jikin su. Bayan sati ya zagayo uncle Suraj da Uncle Bello suka je nema wa Hamma Zaki auren Pretty babu Musu aka basu don kuwa shi kanshi uban Pretty akwai wata ajiyar tsakanin shi da wannan ahali. Wata guda aka sanya ranar bikin, tun daga nan Pretty aka fara shirye-shiryen bikin. Babu wanda ya nunawa Hamma Zaki rashin son auren nasa sai dai granny kullum sai tayi magana in yazo part ɗin ta, in kuma ya zauna har kuka sai tayi wai yaje ya nemo Ƴar mutunci ba wannan da ta haɗa rigima kwanaki ba. Sarah kuwa babu ruwan ta coz yanzu ta riga da ta cire son Hamma Zaki cikin ranta, yanzu mutum ɗaya ne yake yawo cikin jinin jikin ta wato Captain Sulaiman wanda tuni ya isa gida har an fara shirin yin bikin al'ada irin na indiyawa. Tunda ya diro ƙasar shi da Aunty Waheeda suka sauƙa a ɓangaren su dake cikin family house ɗin nasu. Labarin auren Hamma Zaki ya dirar musu a kunne su ma dai basu ji daɗi musamman da suka ji babu wanda ke son auren. Fatan Alkhairi tare da addu'oi kawai suka yi musu. ★★★★★★★★★★★★★ *ƳAR IYA POV* Kamar yadda ta buƙata haka arɗo ya sanar da saƙon ta sai dai bai ce Ƴar Iya ke son ganin su ba. Kafin kace me fada ta cika da samarin garin gaba ɗayan su. Cikin nuna isa da taƙama tazo ta kama wuri ta zauna sannan tace da arɗo ya sanar da su dalilin taruwar su. Gyaran murya yayi sannan yace “To kamar dai yadda kuka gani an haɗa wannan taro na matasa ne ba don kowa ba sai Ƴar Iya, kuma dalili shine zata zaɓi miji cikin matasan ƙauyen nan” daga haka ya dakata yana maida kallon shi ga Ƴar Iya wacce take famar sake murmushi. “To Ƴar Iya bismillah, ga su nan ki zaɓi duk wanda yayi miki a cikin su” Sai da ta farfara ido kafin ta fara binsu ɗaya bayan ɗaya tana dubawa, ta shinshini wannan ta yatsina fuska tayi kallon banza daga ƙarshe dai duk ciki babu wanda yayi mata. Dawowa tayi ta zauna tare da yamutsa fuska tace “Basu yi ba” Arɗo yace “Shikenan kada ki damu zan gayyato samarin ƙauyukan dake kusa da mu zuwa gobe kinji? Ki kwantar da hankalin ki maza” Jijjiga kai Ƴar Iya tayi tace “Aah Arɗo ka barshi ai naga wanda yayi min ma ba sai an gayyato wasu ba” Jin furucin ta yasa kowa fara zare ido yana sunkuyar da kanshi ƙasa. Cikin zukatan su kuma addu'a suke Allah yasa dai kada ta zaɓe su. Don kuwa babu wanda zai so ya auri Bala'i, a faɗar su ai Ƴar Iya saidai aljani. Can Ƴar Iya tayi murmushi tace “Ba kowa ne wanda na fitar a matsayin miji na ba sai kai Arɗo, kai ne zan aura” Ta faɗa tana pointing nashi da yatsar ta. (Toh fah, kunji pretty dai ta samu Hamma Zaki na zai aure ta.! I'm jelous fah☹️😥. Su Ƴar Iya kuma ta yadda aka ɓullo kenan! Toh zadai.muji yadda zata kaya!) COMMENT, LIKE and SHARE FISABILILLAHI! Mu haɗu gobe don jin yadda zata kaya, comments ɗinku kawai nake buƙata don shine ƙwarin guiwa ta. [6/22, 12:47 PM] Diamond Bhatool💎🩷✍️: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* Eid Mubarak to you all! Barkan ku da sallah, muna roƙon Allah ya maimaita mana Amin. Gaisuwa gareku Ƴar Iya READERs Faty Sharif~ Ameeran Mama~ Oum Basmat~ Ummi Hafsat~ ~And the rest.....Allah ya bar ƙauna. SHAFI NA “““49&50””” Arɗo da ya rasa tunaninshi na wucin gadi baki kawai ya sake yana ganin ikon Allah yayin da sauran matasa suka shiga wani irin yanayi mai kama da tsoro, tsoron su Allah tsoron su kada iskanci irin na Ƴar Iya ya ƙaru sakamakon auren arɗon gari. Bayan wasu mintuna ta ƙara murmushi tare da kallon Arɗon wanda har lokacin bai gama dawowa daidai ba tace. “Arɗo baka ce komai ba har yanzu” Cikin wani irin yanayi arɗo yace “Haba Ƴar Iya ai nayi miki tsufa, ki dube Ni kice ni Zaki aura, Ina laifin Matashi mai jini a jika?” Haɗe rai tayi tace “Na gama magana Arɗo, Ni kai ɗin dai nike so” Irin yadda tayi da fuskar tata yasa Arɗo tsorata cikin karyayyiyar Muryar sa yace “Shikenan Ƴar Iya babu komai Allah ya kai mu lokacin” Sai a lokacin Ƴar Iya ta saki fuska tare da faɗin “Yauwa Arɗo sai a fara shiri, wani satin ne bikin” Daga haka taro ya baje, kowa mamaki kawai yake wai Arɗo zai auri Ƴar Iya. Abun ka da ƙaramin gari tuni zancen ya bazu, babu shiri Inna Zaliha ta ƙudurta ziyartar Bulebule washegari. Gidan Arɗo ma an rasa zaman lafiya don kuwa Saratu ihu tayi ta kurmawa jin batun auren Arɗo da Ƴar Iya. Daren ranar dai babu bacci don kuwa Innani ma abun bai mata daɗi ba sai dai babu yadda suka iya dole su bi umarnin Sarauniya Ƴar Iya. Saratu kuwa mancewa da waye Ƴar Iya tayi, washegari sassafe tayi niyyar wucew kahin ta kwaso Ƴan daba azo aci uban Ƴar Iya. (😂😂😂, Zamu ga yadda za'a yi dai. Su Ƴar Iya masu bikin manya, an zaɓi miji kuma an saka rana. Hooohohooo). Inna Zaliha da safe ta wuce wurin Bulebule. Taso a dakatar da auren a cewar ta mahaukaciyar nan bata dace da auren Arɗo ba sai dai Bulebule ya tabbatar mata da cewa auren nan dole za'a yi shi sai dai ba zai yi ƙargo ba. Wannan yasa ta ɗan samu salama cikin ranta ai ko ba komai zata fito daga gidan. Bulebule ya tambaye ta yanzu me take so ayi. Nan ta wangale baki tace tana so Ƴar Iya tayi nesa da gida. Babu ɓata lokaci Bulebule ya haɗa mata magungunan da yadda zata yi amfani da shi daga nan ta baro wurin zuwa gida. ★★★★★★★★★ *ALEE POV* Soyayyar Hamma Zaki da kuma Pretty ta kankama don kuwa yanzu babu laifi shima yana jin wani abu game da ita, shi kan shi yanzu ya ƙosa suyi auren nan. Mom da kuma sauran Familyn Alhaji Naira sun dukufa wurin yiwa Hamma Zakin addu'a don sun tabbatar ba haka kawai future wife din shi ta barshi ba musamman yadda suka san ɗabi'un shi na rashin son mata, matan ma marasa kamun kai sai gashi rana tsaka yace sai ita. Burin su Allah ya maida mummunan nufin Pretty kanta saboda Hamma Zaki bai cutar da kowa suma basu fatan Ubangiji ya bawa wani izinin cutar da shi. Ana saura two week bikin Hamma Zaki da kanshi ya wuce Canada ya haɗo lefen gimbiyar shi Pretty. A cikin satin su Nenne suka kai gidan su amarya. Tuni lefen ya karaɗe duniyar sada zumunta don irin yadda ya kashe kuɗi wurin haɗa shi. *ƳAR IYA POV* Bayan ta koma gida wurin Iya bata yi ƙoƙarin ɓoye mata ba, tas ta kwashe batun auren ta sanar da ita. Iya tayi farin ciki sosai ko ba komai ƴar ta zata huta tunda a gidan arɗo zata yi auren. Nan fa Iya ma aka fara shirye-shiryen biki, a cewar ta zata yiwa shalelen ta bikin Ƴar gata, irin wadda ba'a taɓa yiwa wata ɗiya Mace ba a cikin garin Gallara da kewaye ba. Ɓangaren Saratu kamar yadda ta ƙudurta sassafe ta fice daga fada, babu ɓsta lokaci ta nufi hanyar kahin. Da isarta kuwa bata ɓata lokaci ba ta nufi wurin su Balamo da su Hodiyo waɗanda suka kasance gagararru cikin kahin. Da ƙyar suka amince da ƙudurin ta daga nan suka ɗaura bayan ta sai Gallara. Saratu ce ta nuna musu gidan su Ƴar Iya sannan ta tsaya a ƙofar gidan, wani yaro da yazo wucewa ta ƙira akan ya ƙira mata Ƴar Iya amma kul yace inji ta ne, yace ƙawarta ke neman ta. Cikin gidan yaron ya rantaɓa sallama tare da isar da aikan matar sarki, daga nan yace da su “Tana zuwa” ya wuce abunsa. Saratu na cije baki tace “Don Allah in ta fito ku nakasa ta, ku daki banza ku daki wofi... Ta rasa ubanwa zata aura sai miji na, yar bura......” Bata kai ga ƙarasawa ba taci karo da Ƴar Iya na fitowa, alama tayi wa su Balamo, ai kuwa tana ida fitowa suka fara ɗaga bulalun da sunan bugunta. A nan kuwa suka ga burauba don dukan Kawo wuƙa tayi musu da ƙyar suka samu hanyar fecewa. Kan Saratu tayi ta bugi banza daga nan ta barta ƙofar gidan. Da rarrafe Saratu ta koma gida ta yi jinyar kanta. Ranar Laraba aka kawo lefen Ƴar Iya, babu laifi kaya sunyi a matsayin ta na sarauniya to be. Washegari aka saka Ƴar Iya a lalle. Ranar juma'a da misalin karfe biyu na rana aka ɗaura Auren A'isha Umar Gallara da kuma angon ta Alhaji Arɗo Usmanu Jauro. Ɗaurin auren da ya samu halartar mutane masu ɗan karen yawa. Cikin gidan Iya kuwa cike yake maƙil da jama'a, ƴan uwa da abokan arziƙi kowa sAi shige da fice yake. Shinkafa kuwa an daga sama da kwano ashirin don kuwa zuwa ake ana tafiya. Wasu daga cikin dangin amarya ne suka ce su zasu yi mata rakiya, ai kuwa babu tsammani suka ji tace “Ni zan kai kaina ban yadda wata tabini gida na ba” Miƙit suka yi saboda sun san halin ko zancen basu ƙara tadawa ba. Sai da aka yi sallah Halima tace Ƴar Iya tazo ayi mata ado, babu musu da yake ƙawarta ce ta amince, kwalliya aka sheƙawa Ƴar Iya ta kuzo mugani. Duk da cewa ba wata hamshaƙiya bace tayi mata amma tayi kyau sosai kamar ba ita ba musamman yadda ainihin kyau da Ubangiji yayi mata ya ƙara bayyana. Ana gama mata kwalliya ta yi sallama da iya wacce ke riskar kuka kamar ba gobe sannan tayi gaba abun ta. Gidan Arɗo wato mijin ta kenan ta nufa kai tsaye. Bata ga kowa ba hakan yasa ta nufi ƙorarta wacce aka yi mata ginin bildin (block) inji su da faɗa. A hankali ta tura ƙofar tare da shigewa ciki. Baki ta buɗe sosai tana kallon irin kayan arziƙin da Iyarta tayi mata. Bayan ta gama ƙauyancin ta ta haye gadon ta mai rumfa tare da sheƙarewa nan bacci ya ɗauke ta. (To amarya Ƴar Iya mai abun mamaki Allah ya bada zaman lafiya, ayi amarci lafiya) *ALEE POV* Mom CE ta hana yin duk wasu shagulgula a bikin, da ƙyar ta amince mishi da dinner da gidan su amarya suka shirya. Irin rawar kan da Hamma Zaki yake kaɗai zai ƙara tabbatar maka ba lafiya musamman ga wanda ya sanshi before wannan abu ya auko mishi. Gidan shi da yake Banana Island ya Sha gyara don kuwa dai ƙarfi da yaji Pretty tasa kuka wai ita ba zata zauna a Adamawa ba. Hakan yasa ya zaɓar musu zama a Lagos ɗin tare da ɗaukar transfer zuwa can ɗin. Ba'a daɗe ba kuwa Mom ta gano take_taken shi, babu shiri kuwa ta dakatar dashi kan cewa su zauna a Abuja tunda bata son Adamawa, dalilin mom na hana hakan shine ba zata bar yarinyar nan tayi rayuwa a Lagos ba yanzu ma ya aka kaya balle ta koma Lagos. (Ni kuwa nace ita da take yawo duk yadda taga dama halan ta yi zaman Lagos ɗin ma Mom). Dalili na biyu kuma irin yadda Mom taci alwashin ƙarawa Hamma Zaki aure koda cikin cousin sisters ɗin shi ne. A lokacin da Hamma Zaki ya sanar da Pretty cewa a Abuja zasu zauna not lagos ji tayi kamar ta shaƙe Mom ɗin nan nashi don taga alama matar babu sauƙi a tattare da ita kuma zata saita ta ne, bari dai shi mai kankat ɗin. Ranar Laraba a ɓangaren Pretty sunyi kamu, wanda dai ango dama yace shi baya zuwa, ranar Alhamis suka yi Ladies' party. Cikin duk waɗannan events AMARYA tasha kwalliya abunta kamar mai zuwa gasar kyau, sai dai akace mai hali baya fasawa kayan da ta saka sam basu dace ba. Nan social media ta ɗauka wasu na zaginta wasu kuma na zagin mijin, a cewar su ai laifin shi ne da ya barta ta sanya su. A daren ne kuma taje wurin party da friends nata suka shirya mata wai farewell party. (Ni kaina Bhatool ban so zuwa wurin ba coz Babu alkhairi a ciki). Duk da cewa Mamin ta tayi mata faɗa kan ta guji maza na wani lokacin in ba haka ba duk gyara da aikin da aka yi mata zai ɓaci amma tayi kunnen uwar shegu da ita don kuwa a nan ta kwana tare da su, wannan yayi ya bawa wannan wannan ma yayi ya bawa wannan a cewar su ai farewell ne. Sai da safe ta koma gida ba tare da wani ya fahimta ba ta nemi wuri ta baje sai bacci...... Washegari juma'a, wadda ta kasance ranar da za'a ɗaura aure. Da misalin karfe 10:00am na safiya aka ɗaura Auren Captain Aliyu Muhammad Naira da kuma amaryar shi Nabila Saminu Hambali akan sadaki ₦100,000 cif a Central Mosque dake birnin tarayya wato Abuja. Ɗaurin auren da yasamu halartar manyan mutane a faɗin Nigeria kasancewar bikin na ƴaƴan manyan ne. Bayan an ɗaura aure Hamma Zaki ya ƙira Pretty yake sanar da ita. Wani ihu daga saki saida ta tsoratar da soja marmari daga nesa. Daga baya take sanar da shi ihun murna ne, daga nan suka taɓa Ƴar hirar su. Can Naira family ma babu yabo babu fallasa haka suka gudanar da hidimar bikin sai dai zukatan dukkannin su cike fal da alhonin auren suke. Granny kuwa tunda aka saka bikin nan ta rikice musu, yau kukq gobe kuka don ma Aunty Waheeda na nan takan kwantar mata da hankali don babu laifi akwai sabo da alaƙa mai kyau tsakanin ta da granny. Sisters ɗin shi ma dai basu so auren ba musamman su Najma da suka so a cikin su aka aura mishi sai dai sunyi alƙawarin taimaka mishi a karya wannan sihirin. Nenne da Mommah duk basu so hakan ba suna sai dai babu yadda zasu yi Hamma Zaki na son Auren amma zasu yi maganin wannan mushrika dake shirin kutsowa cikin Naira family. Ina Sarah kuwa?, Ko a jikin ta tunda itama tayi nata masoyin ga kuma irin yadda Captain Sulaiman ya ke nuna mata kula, soyayya uwa uba yadda ya shagwaɓa ta sai dai tana jin wani iri ko ba komai Hamma Zaki ɗan uwanta ne kuma ba zata so abinda zai cutar da shi ba komai ƙanƙantar sa. Tun da suka gama wayar da Pretty abokan shi suka fara yi mishi tsiya wai tun ba'a kai masa ba ya fara zakwaɗi irin na angwaye. Hamma Yusuf ne kan gaba shi da Dr. Faruq duk da cewar suma suna baƙin ciki da wanga aure ɗin duk da cewa abokin nasu yana cikin farin ciki shi ɗin. (Akwai aiki a gaba fa, Naira family sun yi shirin tarwatsa Pretty sai dai ita ma fa shirin take yi. Allah ya bawa mai rabo Sa'a, happy married life Hamma Zaki na, gaskiya nikam ina jin kishin wanga aure. Ƴar Iya kema Allah bada zaman lafiya). # Sarauniya Ƴar Iya # Pretty # Hamma Zaki Kowa tayi indicating a wanne team take. COMMENT & SHARE PLEASE Diamond Bhatool ce!!!! [6/22, 12:48 PM] Diamond Bhatool💎🩷✍️: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* Bazan manta da ku ba: _Baby Unah_ _Murjanatouh_ _Zeely_ Haƙiƙa kuɗin ƙawaye na gari ne, Allah ya kula min da ku. SHAFI NA “““51&52””” Ranar Asabat Pretty da kuma Hamma Zaki suka biyo Flight ɗin 9am zuwa Adamawa. Direct Naira family house aka nufa da su. Tun daga entrance door pretty take sheƙa iskancin ta shi kuma ya kasa hana ta. A nan aka yi musu tarba ta musamman, bayan sunyi lunch taja hannun Hamma Zaki suka wuce bedroom nashi upstairs. Flight ɗin 4pm suka bi suka koma gidan su dake Maitama a can birnin tarayya. Daren ranar angon ya shigo bayan rakiyar da yasamu daga wurin abokan shi. A lokacin Pretty na Sanya wani tablet cikin coke, ɗauko coke ɗin tayi tana fitowa daga kitchen ɗin zuwa bedroom, kiciɓus ɗin da suka yi da Hamma Zaki wanda ya fito duba ina zai ganta don bata cikin bedroom ɗin. Da sauri Pretty ta ɓoye coke ɗin a bayan ta tana addu'ar Allah yasa yace ta bashi. A zahiri kuma ta marairaice fuska tace “Sweetheart ka shigo kenan, na shiga kitchen ne na nemo abun da zan sha. Murmushin sa mai sanyaya zuciya ya saki tare da kamo hannun ta suka wuce bedroom ɗin. Kazar hannun shi ya ajiye tare da komawa kitchen ya ɗauko plate da cups sannan ya dawo, lokacin Pretty har ta cire kayan jikin ta ta shiga toilet ta watso ruwa. Murmushi kawai yayi cikin ranshi yana jaddada rashin kunya irin na Pretty. “Nabees” ya ƙira sunan ta can ƙasan maƙoshi. “bari na shirya Sweetheart” Sai da ta sanya night wear ɗin tukun ta ƙaraso zuwa yadda yake. Gefen shi ta zauna tare da janyo kazar ta saka kan plate ɗin, ganin harda yoghurt yasa tayi saurin janyo coke ɗin ta. Saurin riƙe hannun ta Hamma Zaki yayi tuni taji wani irin yanayi na ziyartar ta. Cike da shagwaɓa tace “Ni shi nake soooo” Hamma Zaki yace “Sorrie Nabees, ki haɗa da yoghurt not coke please” “Kenan asarar coke ɗin za'a yi” ta faɗa tana marairaice fuska. Cike da ƙosawa da maganar yace “I'll use it” Farin ciki ya mamaye Pretty don irin yadda ta ƙagu su keɓance sai taji daɗi sosai. Sai da suka ci kazar sannan ta ɗauki yoghurt ɗin ta sha, shi kuma yasha coke ɗin. Suna gamawa tace dashi yayi wanka, babu musu ya shiga toilet ɗin tare da watsa ruwa sannan ya ɗauro alwala. Ko da ya fito duk baya jin jikin shi dai-dai, wani irin feeling ne ya taso mishi haka yasa yace da Pretty ta shiga tayo alwala. Murna sosai tayi ta ɗauro alwala tare da sanya babban hijabin da ta gani a gefe. Nan Hamma Zaki ya jasu suka yi raka'a biyu kamar yadda Manzon tsira ya koyar da mu, bayan sun idar ya ɗauki tattausan hannun shi ya kama gishin amaryar shi Pretty ya karanto addu'ar da Manzon Allah ya koyar da duk wani sabon ango da ya karantawa matar shi, sai da ya kammala ya fara mata tambayoyi game da addinin ta. Abun mamaki babu abunda ta sani, hakan ya matuƙar bashi mamaki ace mace wayayyiya irin Pretty Bata san komai game da addinin ta ba. Jin shirun da tayi yasa ta zare hijab ɗin tare da kwantawa jikin Hamma Zaki, irin yadda yake jin kanshi ɗinnan tuni ya fara aika mata da saƙonni, nan ta bashi haɗin kai kamar ba amarya ba. Ganin abun ba na ƙare bane ya ɗauke ta cak sai kan katafaren bed ɗin su. Kun san dai babu kyau sanin sirrin wasu shi yasa nima na basu waje tare da ja musu ƙofa sai dai ina jin sunbatun Pretty haka nan angon ma..... Shi ya fara farkawa lokacin sallar asuba, cikin ƙwaƙwalwar shi ya fara tunanin daren su, “Tabbas ban taɓa kusantar wata mace ba sai daren nan, to amma a yadda ake faɗi ba haka abun ya kasance ba, anyways zan san komai ne” daga haka ya miƙe zuwa Toilet. Can ya fito ganin har lokacin Pretty bacci take yasa ya ɗan taɓa ta “Nabees!” Juyi tayi sannan yace “Ki tashi lokacin salla yayi” daga haka ya fice ganin time har ya kusa wucewa. Ba shi ya dawo ba sai 6:00am, har lokacin Pretty bacci take, ciki ɓaacin rai ya ƙarasa tare da ɗan ɗaka mata duka. A zabure ta miƙe tana sakin kukan shagwaɓa. “Tashi ki gyara jikin ki kiyi sallah” “Uhm Ni ban iyawa, ka taya ni” Babu yadda ya iya haka ya taimaka mata ko dan tunawa da yayi bata iya ko da wankan tsarkin ba. Cikin ransa yayi tsaki tare da kwatanta mata yadda zata yi, nan ya baro ta tayi wanka da alwala. Bayan tayi salla ta miƙe tare da niyyar komawa gado. Shi kuwa mamaki yake ganin ko gaisuwar sace da alamar bata iya ba. Cikin kane fuska ya ƙira sunan ta “Nabees” waiwayowa tayi tana shagwaɓe fuska. “Baki iya gaisuwa bane?” Turo bakin ta gaba tayi can dai tace “Good morning”. Ba tare da ya amsa ba ya fice tsabagen takaicin halin amaryar tashi. Ita kuwa baccin ta ta koma. Garden ɗin dake baya ya wuce kai tsaye. Zama yayi kan ɗaya daga cikin kujerun da aka kafa a wurin tare da ajiye phones nashi a kan table ɗin dake gaban shi. Kamar wadda aka tsakala ya ɗauki phone nashi tare da dialling numbern Mom. Early morning taga ƙiran son ɗin ta da cikin kwana ɗaya har ta fara kewar shi. “Assalamu Alaikum” ya furta kamar yadda ya saba, ta ɗaya ɓangaren Mom ta amsa sallamar “Mom....good morning” “Morning Son, how's your night?, Ya kwanan baƙunci” “Fine Mom, and you?” ya faɗa cikin gajarce zancen. “Fine son, ya AMARYA?” Yamutsa fuska yayi kamar yana gaban ta yace “She's ok First love” Nan dai Mom tayi mishi ƴar nasiha tare da jaddada masa kiyaye haƙƙoƙin matar shi dake rataye a kanshi. Cikin sanyin jiki ya katse ƙiran. Har zai ajiye wayar ya fasa tare da dialling numbern Hamma Yusuf. Lokacin yana gym yana motsa jiki ƙiran ya shigo. Cikin sigar zolaya yace “Ango ango, ango ka sha ƙamshi, Allah yasa dai baka haƙewa ƴar mutane ba” “Dalla man bana son iya shege, how're you?” Hamma Yusuf yace “Toooooo kaji wani sabon zance, kai da ya kamata ace yanzu kana nan kana lallaɓar amarya shine zaka dami masu iyali sassafe” Cikin sigar son kawar da zancen yace “Look man, don na kira ka shine zaka faɗa min magana?, Well-done bye” Daga haka yayi hanging call ɗin yana sakin siririn tsaki. Ɓangaren Hamma Yusuf dariya yayi tare da faɗin “Can maka dai, ka san yadda zaka yi da ita ai”. Dr faruq ya ƙira bayan sun gaisa yace “Ehm Dude Ina son tambayar ka ne!” Dr faruq yace “Alright Allah yasa na sani” Cikin nauyin maganar yace Please dama ina son sanin taya ake gane cewa mace budurwa ce idan an kusance ta” Ɗaya ɓangaren Dr faruq yace “Dama na san za'a rina ai, wannan fetsararriyar matar da ka ɗauko” A zahiri yace “Ai ba sai nayi maka wani dogon bayani ba, shi dai budurci kamar yadda Hausawa ke faɗa wani membrane ne da ya kasance marar ƙarfi sosai. Akwai shi jikin kowacce mace a genital area nata specifically a vaginal orifice nata, idan har wannan membrane bai ruguje ba, first time da akayi sex da mace yakan yage saboda yadda aka takura mishi. But in har mace ta taɓa yin sex before, Babu wani wahala zaka shigeta ne.” Gyaɗa kai Hamma Zaki yayi sannan yace “Toh ya ake gane yagewar shi kenan?” “kamar yadda na faɗa maka idan yana nan sai ka sa ƙarfi tukun ka samu damar shiga, wanda raɗaɗin yagewar wannan membrane yakan sanya mata jin zafi sosai. Idan kuma ya riga ya yage before to zata shiga easily without any obstruction.” Kamar wadda aka sake tsigala yace “Kace kowacce mace has that membrane, ko akwai waɗanda Basu da shi, and then miye da miye ke kawo yagewar shi?” “Eh halitta ce da Ubangiji yayi, sai dai wasu matan sukan rasa nasu ne ta hanyar ɗaukar abubuwa masu nauyi, tsalle tsalle, yawan wasa da al'aura ko kuma dai sun taɓa yin sex acan baya” Bayan sauraran bayanin Dr faruq yayi shiru can yace,“ thank you, bye” Daga haka ya gimtse kiran. Ya jima a wurin Yana tunane-tunane can dai ya tashi tare da komawa cikin gidan. Har lokacin Pretty bacci take hakan yasa yayi ordern abinci kawai. Gaba ɗaya baya jin daɗin yanayin shi, a yadda yaji ana faɗa kowanne ango yakan kasance cikin farin ciki idanyayi aure, amma nashi ɓangaren kam wani iri ruɗani ya shiga gashi babu halin yin magana. Abincin sa ya ɗiba yaci tare da hayewa sama zuwa bedroom ɗin shi, wanka yayi sannan ya sanya wasu Mayun English wears sai wani irin kyau ya ƙara bayyana a tattare da shi. Turare ya shafa daganan ya sauƙo ƙasa. Bedroom ɗin ta ya shiga sai dai ga mamakin sa baccin take har lokacin. Tsaki yayi sannan ta fice. Daidai fitar shi gateman na shirin rufe gate ɗin motar su ta doso gidan, yana ganin su ya gano fuskokin su cikin ranshi ya ƙudurta dole matar shi ta rabu da irin ƴan iskan ƙawayen nan. Daga haka ya figi motar sa sai hotel ɗin da friends ɗin shi suka sauƙa. ★★★★★★★ “Najma! Najma!, Wai ina kike ne kina ji ina ƙwala miki kira?” Muryar granny na jiyo tana magana. Daga can nesa Najma ta amsa da “gani nan zuwa dai” Daga haka ta nufi part ɗin granny. “Gani granny” “yauwa ɗiyar albarka maza taimaka min ki ƙira min mai gida na tun safe nake son ƙiran shi” ta faɗa tana washe baki. Da kallo Najma tabi granny sannan tace “Haba granny, shi fa ango ne ta yaya zaki kira shi, ki bari in dai Hamma Zaki ne zai neme ki da kanshi” Sakin baki granny tayi tana kallon Najma kafin tace “Ji min jaira, in ba Zaki ƙira min shi ba ki faɗa min mana ba sai kin min salon manyance da iya shege ba” Babu yadda ta iya haka ta dubo numbern shi tare da dialling daga haka ta miƙe ta fice zuwa part ɗin su zuciyar ta na ƙuna ganin wata bulhuwa taƙwace mutumin da ta jima tana ƙauna tun bata san kanta ba. Part ɗin su ta koma lokacin uncle Suraj da Nenne na zaune a parlourn, gaishe su kawai tayi ta wuce abun ta zuwa bedroom ɗin su. Tana yin wanka ta fito zuwa part din su Salma. Bayan ta gaisa da Mommah ta shige bedroom ɗin su Salma. Ƙare mata kallo Salma tayi gani yadda ɓacin rai da damuwa ta bayyana a fuskar ta. Sai da ta ƙaraso ta dafa kafaɗar ta sannan tace “Najma bakya jin daɗi ne?” Hawayen da take riƙewa ne suka zilalo saman kuncin ta. “Lafiya ta ƙalau Salma, kawai dai ina tausayin kaina ne kamar nayi yaya.” “Subhanallah! Me yake faruwa” ta faɗa tana share mata hawayen. “Babu komai Salma” “A'a Najma, nifa Ƴar uwar ki ce bai dace ji ɓoye min wani abu game da ke ba, Please ki faɗa min damuwar ki, la'alla na taya ki samun solution”. Irin kulawar da ta samu yasa ta saki jiki tace “Salma Hamma Zaki” Nan da nan ƙirjin salma ya buga jin ta ambaci sunan Hamma Zaki. COMMENT & SHARE FISABILILLAHI! [6/22, 12:49 PM] Diamond Bhatool💎🩷✍️: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA “““51&52””” “Me ya faru da Hamma Zakin?” Goge hawayen ta tayi sannan tace “Salma tun ina yarinya nake son Hamma Zaki, tun ban san meye so ba nake ƙaunar shi gashi yanzu lokaci ɗaya yayi breaking heart ɗi na yayi aure abun shi, Salma Yaya zanyi ne don Allah?” Itama salmar Hawaye ne ke zuba daga idanuwan ta da ƙyar ta goge tace “Najma, Ni Ƴar uwarki ce ta jini, kuma Hamma Zaki shima ɗan uwan mu ne na jini, Najma irin son da nake mishi baa magana, amma shawarar da zan bamu itace mu haƙura da shi kuma muyi ƙoƙarin yakice shi daga zukatan mu. Hamma Zaki yayi mana nisa musamman irin yadda auren shi ya kasance....kin san komai Najma, Ni na taushi zuciya ta kuma na haƙura da shi don na san ba samu zanyi ba! Kema ina so kiyi hakan” Ta ƙarashe tana rungume Najma a jikin ta tare da sakin wani irin kuka. Nan suka sha kukan su su biyu sannan suka godewa Allah tare da ƙudurta haƙura da soyayyar shi cikin ruhikan su. *ƳAR IYA POV* Arɗo da ya shiga ɗakin Saratu ta hana shi yin komai da ita, a cewar ta ba zata ƙara haɗa shimfiɗa da shi ba gashi kuma a wannan daren yana jin buƙatar kasancewa da iyalin shi. Tausar zuciyar shi tayi ya nufi wurin Uwar gida salamatu, nan ma babu sauƙi cemishi tayi ya tafi wurin amarya don wannan ranar tata ce ba ta kowa ba. Babu yadda ya iya cikin tsoro da bugawar zuciya ya shiga ɗakin. A lokacin Ƴar Iya kuwa ta wuce Gallara a baccin ta. A nutse ya shiga tare da cire babbar rigar shi sannan ya ajiye ledar hannun shi. A hankali ya ƙarasa jikin gadon da yake ko hasken ubasanjo da yake kunne a ɗakin baa kashe ba. Kyakkyawar fuskar ta ya zubawa ido cikin ranshi kuma yana ayyana wasu abubuwa. Rigar da ke jikin ta yayi ƙoƙarin cire mata, kamar amafarki taji ana shirin cire mata riga ai kuwa babu shiri ta miƙe, shi kuwa Arɗo lokacin ya haye gadon. Ido cikin ido take duban shi “Me kake yi a gado na Arɗo?” ta faɗa cikin Muryar bacci. “Babu komai zaki ci kazar taki ko na cinye?” Kwaɓe fuska tayi tace “Sai ma yanzu zaka kawo min kazar ko?” “Yi haƙuri amarya na tsaya ne afada shiyasa” “Shikenan amma ance min da wuri ake jawo kazar kuma in mutum yaci sai ya biya” “Ƙwarai kuwa” “Ni dai bani da komai, ka miƙo min naci bacci nake ji” Babu musu ya sauƙa ya miƙa mata kazar! Tas ta cinye ta tana shirin komawa yace “To amarya ki biyani kaza ta” Zaro ido tayi tace “Ba na faɗa maka bani da komai ba?” Murmushi Arɗo yayi yace “Kina da shi mana bari ki gani” Ya faɗa yana janye mata rigar da tun ɗazu ya fara cire mata. Zaro ido Ƴar Iya tayi ta ma gagara magana sai bin arɗo da ido kawai take. Tas ya cire mata rigar sannan zanin ma ya ware shi, duk wannan shagali Ƴar Iya babu baki hakan ya ƙara wa arɗo himma. Hannun sa ya kai kan ƙananun breasts ɗin ta da suka fara fitowa yana shafawa. Babu shiri wani ƙarfi yazo mata ta fizge jikin ta tare da jan rigar ta ta shimfiɗa ta jikin ta. Arɗo kam ya fara shiga wani yanayi jin ta fizge jikin ta yasa ya ɗago ya dube ta. “Haba AMARYA ki bari na ɗana mana, naga kin riga kin ci kaza ta!” “A'a Ni dai wannan fa iskanci ne arɗo, ta yaya zaka zo kana taɓa min jiki, har da nono na fa kake shafa min, Aradu Ni dai ka bari”. “Ki bari mana, ba wani iskanci ai an ɗaura mana aure” Ya faɗa yana ƙara jawo ta jikin sa tare da cigaba da shafa twins ɗin. “Ka bari Aradu arɗo kai ma ɗan iska ne Ni ka bari zan biya ka kazar ka da safe” “Kiyi haƙuri amarya, iya haka zanyi in ba haka ba zan iya mutuwa”. Kamar ba Ƴar Iya ba haka ta barshi, can dai bacci ya ƙara ɗauke ta. Sassafiya kamar kullum ta farka tana buɗe idanuwan ta a kan rufin Aluminum na ɗakin, ƙasa tayi da kan zuwa ginin block ɗin daga nan kuma ta juyar da kallon ta zuwa gefen ta, ganin arɗo kwance dagashi sai gajeren wando a gefen ta yasa tayi saurin miƙewa ta zauna. Tun da ta tuna abun da ya faru da dare ranta ya ɓaci, don me Arɗo zai yi iskanci da ita. Duka ta ɗaka masa ya tashi a zabure daga haka ya zuba mata idanuwa. “Kai arɗo dama ashe kai ƙaton ɗan iska ne?, Ka dube Ni ƴar ƙarama da Ni amma kayi iskanci da Ni, to Aradu bazan yadda ba” Cikin sigar lallashi yace “Haba amarya, kiyi a hankali kada su Saratu da salamatu su jiyo sirrin mu” “Kutumar uba!, Wannan ai ba sirri bane, iskanci fa kayi arɗo, kana shugaba a garin amma kayi iskanci, babu ruwana sai na faɗawa kowa” “Ai kuwa kina faɗa zaki mutu, wannan sirrin mata da miji ne, duk wacce ta faɗi nata mutuwa zata yi” Jin batun mutuwa yasa ta ɗan risina tace “Shikenan bazan faɗa ba, amma kai ma ka daina ai ka san babu kyau namiji yake taɓa mace” Arɗo yace “To ai ke mata ta ce” Ƴar Iya tace “Duk da haka kayi alƙawarin ka daina” Kallon ta yayi ido cikin ido sannan yace “Bari kiji babu abunda ma muka yi, kuma kullum sai anyi” Zaro ido tayi tace “Ai kuwa Aradu bazan zauna ba, sai ka sake Ni na koma gidan Iya ta!” Shima idon ya zaro yace “Saki kuma amarya, ai babu wannan zance” “Aradu sai ka sake ni, haka kurin zan zama Ƴar Iska?” Ta faɗa a zafafe. Ganin yanayin ta ya sauya yasa ya fara Binta a hankali. “Kiyi haƙuri bazan iya sakin ki daga aure ba,. Ki bari muyi rayuwar mu har ki haifa min yara” “Bura ubaaaa” ta faɗa da ƙarfi “Aradu yanzu zaka sake ni ko na kashe ka anan!” Sanin hali yasa Arɗo cewa “Shikenan Zan sake ki ba sai kin kashe Ni ba, na sake ki saki ɗaya” Dariya tayi sannan tace “Yauwah ka kyauta, na bar maka kayan ɗakin, Ni barin garin ma zanyi Aradu. Amma kafin nan ka samo min irin kazar jiya ina ci zan bar garin” Babu yadda ya iya ya fice ɗon neman kazar. Ita kuma tafito cikin gidan. Ƙamshin wainar da ake soyawa a ƙofar Innani ta jiyo, tuni ta wuce can tana wani taku ita ala dole amarya. “Sannun ku dai” “Sannu da fitowa amarya, an tashi lafiya” Salamatu ta faɗa tana kallon Ƴar Iya. “Lafiya ƙalau, waina ce ake soyawa?” “Eh wallahi,” “To a zubo min na taɓa mana” A wata kanga salamatu ta zuba mata daga haka ta wuce ƙofar ta. Tas ta cinye wainar ta zauna jiran arɗo, sai can gashi ya shigo. “Yauwa arɗo, na gode Ni zan wuce sai watarana kuma SADUWAR alkairi” Ta faɗa tana amsar ledar. Wani iri yaji yace “Ina zaki je ne haka?” Kai tsaye ta bashi amsar “Birni zan koma gurin Aunty jiram ɗina” “To ga wannan sai wata rana” Hannu tasa ta amshi kuɗin tana faɗin “Nagode arɗo, sai watarana. *Masu tambayar littafin Ƴar Iya daga farko kuyi following channel ɗina zaku samu.* [6/23, 10:49 AM] Diamond Bhatool💎🩷✍️: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA “““55&56””” Tana amsa ta fice daga fada. Bata tsaya ko ina ba sai gidan Iyar ta. A lokacin kuma ƴan taron biki basu gama tafiya ba, cikin su ne wata taga amarya....nan mamaki ya cika ta amma bata ce komai ba saboda ta san in tayi magana zata kwaɗu ne. Ƙira ta fara ƙwalawa Iya yayin da Iya ke makewayi “Iya! Ina kike ne Iya ta?” Ba shiri Iya ta fito tana gyara zaman zanin ta tana faɗin “A'ah shalele na a gida?, Har kin fara yawo Shalele?, To muje ciki” Iyan ce ta fara shiga ɗakin, sai da Ƴar Iya ta tabbatar da cewa Iya ta shige ta dubi matan dake zaune a kan taburmar kaba suna hira, yamutsa fuska tayi tace “Ba a gama bikin bane?” Ɗaya daga cikin su ta ce “An gama” Harara Ƴar Iya ta cilla musu tana faɗin “To uban me kuke yi baku tafi ba?” Jikin su ne ya fara rawa suka kasa magana. Ƙasa da murya Ƴar Iya tayi tace “Ku haɗa kayan ku ku ɓace a gidan nan” Daga haka ta shige bukkar Iya. Su kuwa Tuni suka fara haɗa shirgin su don su wuce. Tun kafin ta zauna Iya ke Binta da kallon tuhuma, murmushi ta aika mata tare da zama a baki gadon bunun dake ɗakin. “Shalele lafiya na ganki a nan?” ta tambaye ta cikin Muryar dake nuna tsantsar damuwa. “Iya ai birni zan tafi nikam, tuni Arɗo ya sake ni” Cikin ƙwalalo ido waje Iya tace “Ya sakeki kuma? Jiya fa kika tare?” Cikin sigar kwantar da hankali tace “Eh Iya ni na saka shi, birni nake son tafiya, nima ina so na zama Ƴar gayu, na zama abun alfahari gare ku.” Duban ta Iya tayi kafin tace “Duk da haka ban ji daɗin kashe auren ki da kika yi ba” Hawaye ne suka zilalo daga idanuwan yayin da suke sauƙa akan kyakkyawan kumatun ta. Duban Iyar tayi cikin ido tace “Iya na gaji, tunda nake kullum jefa ku cikin damuwa nake saboda wannan” Ta faɗa tana nuna hannun ta “Hannu na shine dalilin komai, Iya zan koma birni nima na gina rayuwa ta kamar yadda Aunty Jiram ke faɗa min” Cikin karyewar zuciya Iya ta dubi shalelen tata sannan ta saki murmushi “Duk da haka muna buƙatar ki Shalele, ƙaddarar ki ce haka, mu bamu gaji da ke ba kuma bazamu gaji da ke ba koda kuwa kece zakiyi silar ajalin mu” Murmushi itama tayi tace “Iya ta kenan, banajin zan cigaba da zama da ku, Ni ɗin annoba ce ƙwarai, amma duk dare kwanan nan sai an ƙira Ni zuwa birni....dole naje birni iya a can ne zan zama mutum kamar kowa...gaskiya ne Ni ba cikakkiyar mutum baceeeeeeeee” Ta ƙarasa cikin murya mai fidda wani razanannen amo. Jikin Iya har rawa yake ta rasa ya zata yi, bayan wasu daƙiƙu kuma ta koma kamar ba ita tayi ihun ba. Duban Iya tayi tace “Ki amince da tafiya ta saboda hankali na duk ya tafi can, zan dawo gare ki a matsayin cikakkiyar mutum Iya ta, ina ƙaunar ki. Sannan idan Baffi ya dawo ki sanar da shi, duk wanda ya tambayi ina nake kuce na tafi birni....zanyi kewar ku Iya” Iya ta goge hawayen ta tace “Shikenan Shalele na amince ki je birni, kije birni Shalele na! Ina so ki zama abar alfahari a gare ni, zan so kiyi rayuwa mai kyau” Murmushi tayi tare da rungume Iyar kamar zata mayar da ita ciki, sun ɗau tsawon mintuna kafin ta saki iyar tana miƙewa tsaye. Daga haka ta nufi bukkar ta....duk kuɗaɗen ta da ta tara na maganin mata ta ƙwaƙulo su tare da fara jera su. Sai da ta jera sannan ta Ƙirga taga dubu 20 cif, haɗa su tayi da kuɗin da Arɗo ya bata ₦2000 sannan ta ƙulle su cikin wani tsumma, daga haka ta miƙe tare da komawa ɗakin Iya. Jakar Ghana Must go da aka saka kayan auren ta ciki ta janyo tare da saka kuɗin ciki, iya kuma duban ta kawai take cikin karyayyiyar zuciya da kuma tausayi. “Tabbas ta cancanci rayuwa mai kyau, tun daga kan iyayen ta take fuskantar hukunci, hukunci maras daɗi, an mayar da yarinya rabi mutum, ya Ubangiji!” a zahiri kuma tace “Ka kula da Shalele na” Bayan ta tabbatar ta haɗa komai nata ta ajiye gaban ta, hawaye na tsiyayowa daga idanuwan ta ta ƙarasa tana rungumar Iya “Zsn wuce Iya, Baba na ma ki sanar da shi in ya buƙaci hakan, zanyi kewar kuuuuu” Daga haka ta saki jikin iya tana ɗaukar Bagco nata ta ɗaura a ka. A haka ta fice daga gida ta nufi hanyar bayan gari, duk da cewa bata san ina zata je ba haka take tafiya ba tare da waiwayowa ba. (Safe trip Ƴar Iya.... Allah sada mu da alkairin shi) *ALEE POV* Bai wani jima ba ya dawo gidan, ko alokacin su Ishy basu bar gidan ba. Cikin takun shi na zaratan maza ya fito daga motar tare da nufar apartment ɗin su, fuskar nan tamau kamar dai Hamma Zaki yaron Mom 😒. Ciki-ciki yayi sallamar yana sanya ƙafar shi ciki, ganin basa parlourn yasa ya haye sama zuwa bedroom nashi. Wanka yayi sannan ya kwanta kan lallausan gadon nashi. Bacci yayi niyyar yi amma kuma ya kasa, ya rufe idon amma ina, ganin baccin ba mai yiyuwa bane yasa ya janyo wayar shi ya fara latsawa don tunanin da yake addabar shi baya so ya samu matsuguni. WhatsApp ya shiga Yana replying messages Wanda yawanci wishes ne ake masa, ɗaya ɓayan ɗaya yayi replying duka wishes ɗin sayin “Thanks”, “Thank You”, “I appreciated” “Thanks alot” amsoshin kenan. Sai kuma messages ɗin Hamma Yusuf da su Dr. faruq wanda duk zolaya ce. Ba tare da yayi musu reply ba ya fice ya koma status, duk da cewa shi ba ma'abocin ganin status bane haka nan ya tsinci kanshi da sha'awar haka. _Sarah_ ne farko, gaban shi ne ya faɗi ganin numbern ta a wayar, haka kawai ya tsinci hannunsa da shiga. Pictures nata ne da gani a bikin Hamma Zakin tayi. Sanye take cikin blue and pink sari wacce ta fidda ainihin kyau irin nata, doguwar sumar ta da ta jiƙa da gyara ga kuma wani mahaukacin hairstyle da akayi sai abun ya ƙara ƙayatarwa, pink 🎀 ribbon aka ɗan maƙala ta baya....nace Masha Allah. Sai da yayi zooming gashin yana ƙara dubawa tare da lumshe idanuwan shi. Tunawa da kan Pretty da yayi wanda ya kasance kamar hamatar ɗan iska sai uban attachment da ta maka yasa yaja tsaki “Mtsss”. Bai tsaya ba yaci gaba da kallon Sara, fuskar Mom ɗin shi ne ta faɗo a ranshi nan ya ƙara tabbatar da cewa Sarah kyakkyawa ce. Da ƙyar ya bar picture ɗin yayin da wani yayi appearing, wannan kuma ita da Captain Sulaiman ne, haka kawai yaji ranshi ya ɓaci daga nan ya fice yana viewing sauran statuses ɗin. Sauƙa yayi daga WhatsApp ɗin ya koma Instagram nan ma dai karo yaci da pictures da kuma videos na dinner ɗin su, tsaki yaja tare da ajiye wayar gabaɗaya yana runtse idon shi tunawa da Pretty da yayi, ya kamata ya duba ta. Wata zuciyar tace “Waɗannan bullshits ƙawayen nata na nan” “To kai ina ruwan ka?” wata zuciyar ta faɗa mishi. Miƙewa yayi yana nufar bedroom nata dake downstairs. Kamar kar ya Ƙarasa kawai yayi ƙarfin hali tare da danna kanshi zuwa hanyar, sai da yayi knocking jikin ƙofar sannan ya shiga. Su Ishy kuwa najin knocking suka wuce Toilet abunsu. Da gudu tazo tayi hugging nashi tana sakin kukan shagwaɓa. “Sweetheart ina ka shiga haka tun asuba ban ƙara ganin ka ba....” “Sorry Nabees” abunda ya iya furtawa kenan sakamakon yanayin da ya tsinci ruhin shi da gangar jikin shi. Kissing nashi tayi sannan tace “Ok shikenan kaga ko abinci fa ban ci ba” “Baki ga abinci a dining bane?” “uhm uhm Ni ban gani ba, ai baka ce min akwai ba” “Sorie” Hannun ta ta ɗaura a kafaɗar shi sannan tace “To muje ka raka Ni naci” Kasa musa mata yayi sai ya bi bayan ta. Nan ma dai kukan shagwaɓa ta saka wai ita sai dai yayi feeding nata. Haka ya zauna yana bata har ta ƙoshi daga haka tace yazo su gaisa da friends ɗin ta. Kamar ba shi ba ya haɗe fuska yace baya zuwa daga nan ya wuce sama ya barta a wuri tana kallon shi galala. Sai da ya wuce tayi ƙwafa tace “Zaka gane baka da wayo ne, bari nayi sati zamu koma sai ka dawo kamar bawa na Captain....sai na wahalar da kai kwatankwacin yadda ka wahalar da Ni, mami da Daddy ma ba zasu Barka ba” Ganin babu amfanin tsayuwar yasa ta koma wurin su Ishy waɗanda suke ƙunshe a Toilet har lokacin. Tunda suka fito suka ci gaba da budurin su hankali kwance. Hamma Zaki tunda ya koma Bedroom ɗin shi yake jin shi wani iri, why yake ma pretty abun da take so? Me yasa? Ganin tunani na shirin saka mishi ciwon kai yasa ya diro tare da nufar Toilet, Alwala ya ɗauro yazo ya gabatar da sallar walaha tare da yin addu'oi, nan yaji ƙirjin shi ya yi sauƙi kamar an cire mishi wani nauyi. Daga nan ya yi musu order na Lunch sannan ya kwanta. *SALATUL-DHUHA (Sallar walaha* _Ya inganta ayi sallar dhuha raka'ah biyu da kuma raka'ah hudu sannan qna yinta dai-dai rana ta daukako lokacin da take da zafi._ _Akwai hadisi masu yawa wa danda suka zo da bayaninta da kuma falalar ta, daga ciki akwai:_ *1. Hadisi daga Abu Dharrin Al-ghifariy (ra) daga manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallama):* _yana wayar Gari cewa akwai Sadaƙah bisa kowacce Gaba dake Jikin kowanne mutum guda cikinsu:_ _kowanne tasbeehi Sadaƙah ne kuma kowanne tahmeedi Sadaƙah ne kuma kowacce hailala ma Sadaƙah ce kuma kowacce kabbara ma Sadaƙah ce._ _yin Umurni da akin Alkhairy ma Sadaƙah ne kuma yin hani Daga mummunan aiki shima Sadaƙah ne_ _kuma raka o'i guda biyu wadanda daya daga cikin ku zai sallata to Da walaha sunyi dai dai da wannan imamu Ahmad da muslim da Abu dawud ne suka ruwaitoshi_.__ _Wato wannan hadisin yana faɗakar damu cewar ladan sallar walaha yana daidai da ladan yin Sadaƙah sau dari uku da sittin kenan domin gaɓoɓi ɗari uku da sittin ne ajikin dan adam. *2. Ga wani hadisin wanda yake Ƙara fitowa fili da bayanin da nayi yanzu shine hadisin da Imamu Ahmad da Abu Dawud suka ruwaito daga sayyiduna Abu buraudah (Radhiyallahu anhu) cewa manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallama) yace.* _Ajikim Dan adam akwai Gabobi guda dari uku da sittin lallai ne gareshi ya rika sadaqah bisa kowacce gaba_ _FALALARTA_ _Sallar walaha dai-dai take da sadaka 360. Sahihu,Abu dawud(5242)_ _Sallar walaha tana ɗaga darajar mutum har ta kaishi zuwa darajar auwabina. Sahihun muslim(748)_ _Duk wanda yayi sallar walaha toh yana cikin kariyar Allah a duk yininsa. Sahihun Abu dawud(1289)_ _Sallar walaha dai-dai take da ladar umrah. Hasanun Abu dawud(558)_ _Sallar walaha wasiyyar manzon Allah ce ga al'ummar sa. Buhari(1178) muslim(721)_ _Sallar walahs aikine kaɗan amma lada mai yawa. Hasanun Abu ya'alah(6424) _Ƴan uwa masu albarka muyi ƙoƙarin kasancewa cikin masu sallatar dhuha ko dan saboda ɗumbun daraja da falalar da take da shi. Allah ya bamu iko._ COMMENT & SHARE FISABILILLAHI! [8/17, 6:12 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: 🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA “““57&58””” *ƳAR IYA POV* Tunda ta fito ta miƙi hanyar da zata sada ta da bakin titi bata ƙara waiwayowa ba. Yayi tafiya sosai kafin ta iso bakin titin. A wata ƴar rumfa ta yada zango har wani lokaci babu alamun abun hawa balle har ta tafi. Tun tana jiran tsammani har dai taga abun na shirin fon ƙarfin ta ga wata shegiyar yunwa da take ji kamar tayi yaya. Ganin dai zaman bashi da amfani yasa ta fara tafiya akan titin yayin da bagco na kayanta ke bisa kanta. Tayi tafiya sosai kafin ta hango wata mota na tahowa, murmushi tayi har sai da kumatun ta ya lotsa yayin da farin ciki ya mamaye zuciyar ta. Tsayawa tayi tun kafin motar ta iso tana ta kallon ta. “Wai yau ni shalelen Iya zan shiga wannan abun, kai Aradu birni akwai daɗi, wayyo birni” Ta faɗa a zahiri ta kallon motar da ta tsaya gaban ta, cikin harshen Hausa drivern ya sauƙe glass ɗin tare da leƙowa yace “Hajiya ina zaki je?” Shiru tayi tana tunanin ina zata ce, ita dai a rayuwar ta bata san wani gari ba in ka cire Gallara da kuma ƙauyukan da ke kewaye gashi ko sunan garin da tayi sukul bata sani ba. Katse mata tunanin yayi da faɗin “Hajiya ko baki ji ne? Ina zaki je” Can ƙasan maƙoshi tace “Birni zanje” Daga cikin motar wani mutum yace “Wannan fa da gani bata da hankali, driver mu wuce tana ɓata mana lokaci” Caraf maganar shi ta faɗa kunnen ta hakan yasa ta ɗago a zafafe tace “Aradu nonon uwarka nasha shi yasa ban tashi da hankali ba” Ƙoƙarin buɗe motar yake wai ta zage shi, driver ya katse shi da faɗin “Haba malam kai ne fa ka fara zagin ta kuma yanzu kace zaka hukunta ta don ta rama” Haka sauran ƴan motar suka yi mishi caaa wannan tace kaza wannan yace kaza. Ganin dai babu mai bin bayan shi yasa yayi shiru. Driver ya ƙara kallon Ƴar Iya yace “Mu nan Bauchi muka nufa, Hajiya zamu wuce in Baki san yadda zaki ba” Cikin rashin sanin madafar ta yasa tace “Nima can zanje” Daga haka driver yasa aka samar mata space ta shigo. Nan motar su ta miƙe sai Bauchi. Awanni uku da abubuwa suka shafe suna tafiya kafin motar su tayi packing a Tasha, nan aka fara sauƙewa kowa kayan shi. Bayan Ƴar Iya ta sauƙa daga motar ta fara tunanin ina ɗaya zata nufa!. Can ta hango wata mota a tashar ana ƙara ɗiban mutane, a hanzarce ta ƙarasa wurin. Ji tayi ana “Gombe, Adamawa” Caraf tace “Gombo zani” Dariya wani na gefen ta yayi yace “Gombe ake cewa” bata kula shi ba saboda kayanta da aka karɓa aka saka a Boot, ba'a daɗe ba motar ta cika bayan kowa ya biya kuɗin shi ta tashi sai Gombe. Dai-dai roundabout ɗin dake ɗauke da signboard na Welcome to Gombe State ne wata gingimemiyar mota trailer da tayo loading shanu ta bugi motar su Ƴar Iya. Ƙiiiiiiii kake ji sai kuma na cikin motar suka fara ihu, wayyo Allah, mun shiga uku shikenan!. Ba tare da trailer ɗin ta tsaya ba ta ƙara ɓangare motar tasu nan da nan ta kifa itama trailer matuƙin ta da ya tsorata ya saki staring ɗin shi tuni tayi wani irin juyi. Mutane na ihu shanu na ihu har dai motocin suka tsaya lokaci guda kamar haɗin baki. A lokacin ambulance ta iso tare da motar ƴan sanda. Da sauri suka nufi motar su Ƴar Iya tare da ɓanɓare ƙofar da ƙyar, innalillahi wa inna ilayhi rajiuun!!!! Mutanen ciki babu wanda ke motsi sai wani hijab baƙi dake tsakiyar su dake ɗan motsawa da gani kuma neman agaji yake. Da sauri aka fitar da su ɗaya bayan ɗaya har aka gama sannan aka yi asibiti da su. Cikin ikon Allah ashe mutane uku ne kaɗai suka rasa ransu, sauran dai sun ji ciwo wasu da karaya wasun kuma gocewar ƙashi. Abun mamaki yarinyar dake ciki babu abunda ya same ta sai dai ta tsorata har ta shiga shock. Mintuna kaɗan da faruwar hatsarin aka fara nunawa a gidajen talabijin da kuma rediyo. Ciki har da Ƴar Iya da ake magana akan abun mamaki babu abunda ya sami matashiyar dake cikin motar. Inspector Suraj da kanshi yayi handling issue ɗin, and alhamdulillah duk an ɗaura waɗanda suka karye, masu gojewar ƙashi suma an daidaita kuma kowa Ƴan uwan shi sun zo. Abun mamaki yarinyar dake cikin shin kuma babu wani nata da ya bayyana. Shi kuma inspector Suraj Yana son wucdwa Adamawa ne sai dai babu hali saboda wannan yarinyar. Ƙarshe dai shawara ya yanke bayan ya cike waɗansu takardu ya wuce da yarinyar Adamawa kan in ta dawo hankalin ta sai aji ina ne gidan su sannan a miƙa ta. Jiya iyau dai matashiyar yarinyar bata farka ba hakan yasa yaci gaba da jinyar ta da yake a asibitin dake cikin estate ɗin da yake rayuwa take. Tana samun kulawa ta musamman kuma kullum sai familyn shi sun zo dubata....tsawon sati shiru yarinya taƙi farkawa Gashi dai numfashin ta dai-dai yake tafiya, zuciyar ta ma na bugawa dai-dai haka bp nata ma bai yi ƙasa ko sama ba amma abun mamaki shiru. *CAPTAIN ALEE POV* Tun daga bakin ƙofar da zata sada ka da ɓangaren zaka san cewa gidan ya sauya. Ƙura ce a parlourn ga kuma wani irin smell dake fita daga ciki, in ka tsura idanuwan ka a ƙasan zaka ga datti kamar dai abinci ne ya bushe. Wai a cikin gidan nan kuwa Hamma Zakin mu yake rayuwa?, Mutumin da ya tsani ƙazanta, datti komai ƙanƙantar sa baya so amma gidan shi ne wannan 🤔. Tsawon sati guda kenan Hamma Zaki ana cin amarci, sai dai wani abun mamaki kullum ƙara ramewa yake yi kamar dai ba wannan giant Hamma Zakin ba, miskilanci kuwa ƙaruwa yayi don yanzu gabaɗaya baya sakarwa kowa, ita kanta amaryar ya mugun sauya mata cikin satin ga kuma wani rashin mutunci da ya ƙago na hana ƙawayenta shigo masa gida. Haushin shi sosai Pretty ke ji hakan yasa ta shirya zuwa gida don tayi maganin shi. Ranar juma'a da safe, misalin ƙarfe bakwai kamar kullum Hamma Zaki ya sauƙo daga bedroom ɗin shi cikin shigar kakin sojoji wanda suka yi mugun amsar shi. Babu laifi yayi Fayau amma da ka ganshi in har ka sanshi zaka gano ramar da yayi, fuskar nan kamar an aiko mishi da saƙon mutuwa har ya ida sauƙowa, ganin irin dattin dake kacame a parlourn yasa yaja tsaki tare da nufar bedroom ɗin ta. Cikin baccin ta ta jiyo ƙamshin turaren shi hakan yasa tayi juyi alamun ko sallar asuba bata yi ba. Tsaki yayi yana mamakin irin hali na Pretty, mace kamar ba mace ba ace common gyaran gida da girki ba zata iya ba. Tabbatar wa da tayi shine yasa ta miƙe zaune tana hamma. “ahhhhhh lafiya Sweetheart” Cike da mamaki yake kallon ta, don shi kullum sai ta ƙunsa mishi abun mamaki hakan ko shine tata gaisuwar?. Banza yayi mata ganin dai zata ɓata mishi lokaci yasa yace “Please Nabees a gyara gidan nan duk yayi datti babu daɗin gani” Daga haka ya fice abun shi. Da harara Pretty ta bishi tace “Sai kayi kuma, mutum da shegen tsafta sai kace shine tsaftar kanta....mtsss zanyi maganin ka ne”. Sai da ta tabbatar Hamma Zaki ya fice itama tashiga toilet tayi wanka, kwalliya ta cancara kamar mai zuwa gasar kyau kafin ta ɗauko wasu English fitted gown ta saka tare da fesa turare sai ta fito sak dadar roba lol😂. Wani siririn mayafin ta kamar net ta ɗauko ta yafa sannan ta fito. Tsaki taja da ta iso parlourn ganin dagaske yayi dattin sannan tace “Ka nemo ƴar aiki in ka gaji ai” daga nan tayi waje. Tana fitowa tayi dialling wata number Bayan anyi picking tace “Yea, na shirya, Please don't waste time”daga haka ta yada zango a ƙayatattun kujerun dake compound ɗin. Baa fo mintuna biyar ba wayar ta tayi ƙara, ba tare da tayi picking ba ta fice kai tsaye, gateman na sakin gaisuwa amma ko kallo bai samu ba sai ma tsarabar tsakin da ta bishi da shi. Motar da pake a ƙofar gidan ta nufa, directly seat ɗin gaba ta buɗe ta shiga. Wani matashin saurayi ne da bai wuce 34years ba a ciki, baƙi ne mai ƙaton kai, bai cika kyau ba ga kuma sanƙo da yake da shi. Kallon shi Pretty tayi tana murmurshi tace “Sugarplum nayi kewar ka tsawon week ɗin nan ban ganka ba” Ɓata rai yayi yana maida hankalin shi ga tuƙin sa kafin yace “Ba wani nan, kinyi aure kin ma manta da Ni, kin barni da tsantar kewa da buƙatar ki, Please ki sama mana time don gaskiya Ni bazan iya ba” Shu'umar dariya Pretty tayi sannan tace “Baka da damuwa sugarplum, in dai wannan batun ne ka saka ranka a inuwa akwai wani shiri da nake mana” Murmushi guy ɗin yayi yace “Yauwa hotbabe na!” Daidai wani katafaren gida yayi horn, bayan gateman ya buɗe mishi ya tura hancin motar zuwa ciki, parking yayi sannan ya fito ya zagayo ya buɗewa Pretty motar itama ta fito. Tun kafin su shiga gidan suka fara kissing junan su kamar wasu Mayu. A parlourn suka yada zango nan suka cigaba da sheƙe ayar su daga haka nace bari na basu wuri. (Sun shafe kusan hour guda tukun naji maganar su hakan yasa na shige domin ɗauko muku report). Hannun su saƙale da na juna suka wuce bedroom ɗin tare da nufar Toilet,bayan sunyi wanka sun fito suka kimtsa sannan suka fito suna hirar su. “Gaskiya hotbabe ki nema mana mafita, yanzu ma kawai na haƙura ne saboda kince kina da abun yi kuma baki so ya dawo yasan kin fita, but ki sama mana mafita” “Nevermind sugarplum, yanzu me zan samu?” Murmushi yayi irin nasu na ƴan duniya tare da ciro wayar shi yayi mata transfer na ₦500k daga nan yaja motar zuwa gidan Mami kamar yadda Pretty tayi mishi umarni. Bayan sun isa tayi kissing nashi sannan ta fita, daga nan yaja motar shi ita kuma tayi ciki. “Oyoyo Mami na” ta faɗa tana rungume mami dake zaune a kan kujera. “Auta ta kinzo kenan” Kwaɓe fuska tayi kamar zata yi kuka tace “Ai Mami tun washegari naso zuwa ban samu dama ba” Ido ta tsurawa ƴar tata tace “Lallai Kam, hankalin ki kwance saboda burin ki ya cika kin manta da mami ko?” Zaro ido tayi tace “Habadai mami kullum kina raina, yanzu dai ba ma wannan ba akwai matsala!” “Too matsalar me kenan?” mami ta tambaya “Mami ina ga za'a ƙara yiwa guy ɗin nan aiki, wallahi ya cika tsauri da yawa, ni yanzu damuwa ta ma kawai ya ɗauko ƴan aiki yanzu ma na baro gidan duk datti, Ni kuwa ba iya gyarawa zanyi ba” “Gaskiya kam kiyi masa magana ya nemo miki ƴan aiki tunda ko a gidan ku ba yi kike yi ba” Kai ta jinjina tace “Kallai Mami, captain Alee ya wuce tunanin ki, kinga yadda yake wani bani umarni kamar Daddy” ta ƙarasa tana yamutsa fuska. Mami tace, “Kar ki damu auta, zanje gun bokan nan na ƙara samo miki magani ta yadda sai abunda kika ce” murmushi tayi tace “Yauwah Mami na shiyasa nake sonki, bari na wuce kafin ya dawo ya tarar bana nan” [8/17, 6:12 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: 🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA “““59&60””” Cikin hanzari suka rabu, yaja motar shi ita kuma ta shige ciki da sauri, taji daɗi sosai ganin Hamma Zaki bai dawo ba and dama bata yi expecting dawowar shi ba. Salim Umar Baloli shine matashin da ya ɗauki Pretty, ɗa ne ga wani mai kuɗi a ESTATE ɗin su, kuɗin da yake ɓarar mata yasa ta amince da shi har suka ƙulla alaƙa. Bayan ta cire kayan jikin ta ta saka wasu, sai ta tuna da cewa mami tace ta lallaɓa shi ya kawo mata ƴar aiki. Ɗan yamutsa fuska tayi sannan ta fara tattare parlourn, sama sama ta ɗan share and babu laifi dattin ya ragu. Sai wajen 4:00pm Hamma Zaki ya dawo gidan, ba tare da ya duba ta ba kamar yadda ya fara a farkon aurensu ya ajiye abincin da ya dawo da shi kan dining daga nan ya wuce zuwa bedroom nashi. Wanka yayi sannan ya sauya kaya ya fito. Sai a lokacin ya tuna ashe fa yana da mata, cikin rashin son zuwa ya nufi bedroom ɗin ta. Chat take a wayar ta sai dai ƙamshin turaren shi ne ya sanar da ita shigowar shi. Da gudu ta miƙe tayi hugging nashi. “Oyoyo Sweetheart, ka dawo” Bai ce komai ba sai ma zame ta da yayi daga jikinsa. “Ga can abinci a dining” Kuka ta saka mishi wai don me iya abinci zai nuna mata bayan ta riga da tayi missing nashi. Kukan mace da baya so a rayuwar shi yasa ya ɗan riƙe ta. Cikin nuna kulawa yace “Alright nayi laifi yanzu dai kici abinci sai muyi magana” Bayan sun ci abinci tace “Sweetheart ina buƙatar Ƴar aiki to keep the house clean, yanzu ma kana complain akan datti Allah da ƙyar na gyara parlourn nan” Cike da mamaki yake kallon ta wai ta gyara parlourn, parlourn da ko alamar gyara bai gani ba, lallai ma ƴar nan ta raina shi, amma zai saita ta ne. “Shikenan yanzu me kike so ayi?, Ni bana cin girkin Ƴar aiki ko a gida Mom ke dafa abincin da nake ci” “Ni dai gaskiya ka nemo, in yasa kai sai ka cigaba da shigowa da naka” Maganartata ta matuƙar bashi mamaki, irin wannan halin ko in kula da take nuna mishi yasa kawai yayi shiru. “Kayi shiru Sweetheart” “Ok ki nemo” Rungume shi tayi tace “Thank You my love, I love you”. *ƳAR IYA POV* A hankali ta fara buɗe idanuwan ta da suka yi mata nauyi har ta buɗe su gabaɗaya suka sauƙa a kan fuskar Nenne dake zaune a kujerar dake side ɗin gadon. Ganin ta buɗe idon yasa Nenne farin ciki, da sauri ta miƙe tayo kanta. “Kin farka?, Sannu sannu bari a ƙira likita” Ita dai Ƴar Iya da kallon mamaki kawai take bin Nenne har ta fice daga ɗakin. Tunanin ta ne ya dawo, ta tuna ta shiga Mota daga nan kuma motar tayi ta buguwa. Tunanintaa ne ya katse Saboda shigowar doctor sai Nenne dake biye da shi. Cikin sakin fuska Doctor ɗin ya ƙaraso bakin bed ɗin tare da taɓa wuyan ta da goshin ta, jin babu zafi yasa ya fara mata magana cikin kulawa. “Ya jikin naki?, Me kike ji yanzu?” Kai kawai ta girgiza masa saboda wani irin farin ciki da ya lulluɓe ta lokaci guda. Cikin ranta tace “Shikenan na zo birni yanzu kam, wayyo daɗi” ta faɗa tana sakin murmushi yayin da Nenne ke murmushin itama. Bayan Doctor ya tabbatar tana cikin hayyacin ta kuma babu wani abu dake damun ta a wannan hali yasa ya fice. Nurse on duty ta shigo ta gyara mata shimfiɗa sannan ta tallafa mata ta shiga toilet, toilet bath tayi mata, tare da oral care, bayan nan ta tallafa mata suka fito daga bayin, daga nan kuma tace a bata abinci. Nenne da kanta tayi feeding Ƴar Iya sai dai ta sha mamaki kamar ba maras lafiya ba, tas duk girman warmer ɗin ta cinye abincin cikinta. Bayan ta ƙoshi aka bata Nutri-milk ta kora da shi. Ciki ya ɗauka sai Ƴar Iya ta fara murmushi. Yarinyar ta burge ta, gata kyakkyawa ce sai dai daga gani daga ƙauye ta fito ko gidan masu ƙaramin ƙarfi. Tunanin Nenne ya katse ne sakamakon ihun da Ƴar Iya ta fara “Wayyo Allah na, ina jaka ta da kuɗaɗe na, wayyo shikenan nikam” Da sauri Nenne ta ƙarasa wurin ta tana riƙe ta tare da tallafa bayan ta tana tapping bayan. “Ki shiru maza, kinga baki da lafiya” Samun kanta tayi da gyaɗa kai tace “Toh jaka ta ban ganta ba, kuma akwai kuɗaɗe na da yawa har da wanda Arɗo ya bani da zan taho” Arɗo da Ƴar Iya ta ƙira yasa Nenne faɗin kenan bafulatana ce cikin ranta. A zahiri tace “Kar ki damu Ni inada kuɗaɗen da suka fi naki yawa, ki nutsu zan baki in Zaki tafi” “To kawai Ƴar Iya tace. Nenne tace “Yaya sunanki?” “Suna na A'isha amma Ƴar Iya shine sunan da ake kirana da shi”. “Ashe takwarar Granny CE, Masha Allah. A wane gari kike kuma?” Cikin burus tace “A Gallara nake, amma na baro can ɗin ne gabaɗaya saboda ina son birni, ina so nake saka kaya irin nakin nan, nake kwalliya kuma na zama mai matsayi” ta ƙarasa yayin da ƙwalla ke zubo mata. Cike da tausayawa Nenne tace mata “Kina son zama da Ni?, Zaki zauna a tare da Ni?” Kai ta gyaɗa tace “Eh zan zauna” “Shikenan zaki ke iya ƙira na da Nenne, ina da yara da kuma ƴan uwa sosai. Zamu koma can da zama, amma kimin alƙawarin zaki zauna lafiya da kowa” “Eh Nenne” Murmushi Nenne tayi daga nan ta bata labarin hatsarin da suka yi da yadda ya faru. Cikin ƙanƙanin lokaci alaƙa ta ƙullu tsakanin Ƴar Iya da kuma Nenne, Ƴar Iya najin cewa wannan matar ta cancanci zama uwa gare ta tunda yanzu babu Iya. Ba'a jima ba Doctor yayi discharging nasu. Uncle Suraj Nenne ta ƙira ta sanar dashi, yace su wuce gida kawai. Babu musu suka wuce cikin motar da Nenne tazo da ita. Tun a bakin Gate Ƴar Iya ta saki baki da hanci tana kallon gidan, cikin ranta tana faɗin “Aradu na huta, na kusa zama ƴar gayu nima”. Bayan sunyi parking Nenne ta fita, sannan ta buɗe side ɗin da Ƴar Iya take tare da janyo hannun ta suka fito. Part ɗin ta ta wuce da ita, lokacin babu kowa su Najma duk suna Islamiyya. Bayan sun shiga Nenne taja hannun Ƴar Iya tace “Muje ki gyara jikin ki, ranar Saturday sai muje a gyara muku jiki tare da su Najma” ba tare da ta Musa ba tabi Nenne. Toilet ɗin su Najma ta kaita, tare da nuna mata yadda zata yi wankan, ta nuna mata brush da MacLean ta nuna mata yadda zata yi daga nan ta fice. Ita dai mamaki duk ya cika ta wai nan ne bayi?, “To a can ai babu komai kawai kewaye wurin aka yi da zana sai ramin shadda” Mintuna 30 ta kwashe tana zuba ƙaiyancin ta, thank God ma ita kaɗai ce, Nenne dake zaman jiran fitowar ta taji shiru. Daidai door ɗin ta saka kanta tace “Baki gama wankan bane?” Sai lokacin ta tuna wanka fa aka ce tayi, cikin wata irin murya tace “Nenne bana iya amfani da abubuwan” “Bari na zo na koya miki” Nenne da kanta tayi wa Ƴar Iya brush, duk irin damɓare damɓaren dattin da ya fita bai sa haƙwaren fita tas ba, ƙara wanke nata tayi sosai, lokaci guda suka fita kamar ba dai Ƴar Iya ba, har da su mouthfresh aka fesawa Ƴar Iya, ita dai ikon Allah kawai take kallo. Bayan nan Nenne ta sunce towel ɗin da ta ɗaura mata tare da ajiye shi, tas ta wanke Ƴar Iya tana mamakin irin dattin dake jikin ta, gashin kanta kuwa kasa gyara shi tayi tace sai sunje wurin wankin kai. Bayan sun gama Nenne ta ɗaura nata towel ɗin tare da jan hannun ta zuwa bedroom ɗin ta, tas ta shirya ta, mayuka daban-daban ta shafa mata, powder sannan ta shafa mata wetlips a pinkish leɓen ta. _Ƴar Iya Fans in kun ganta ba zaku gane ta ba_ Wata doguwar riga Nenne ta saka mata sannan ta saka mata hula. Masha Allah kawai nace tayi kyau kamar ba ita ba. ★★★★★★★★ Motar ce tayi packing a dai-dai parking space. Bayan ta tsaya gabaɗayan su suka fito kowa suka nufi sashen su. A parlour Fauzah ta tarar da Mom tana aikin nata da ta tsiro na tunani. Ɗauke da sallama ta shiga sai dai Mom ko sallamar bata ji ba. A gefenta ta zauna sa'annan ta ɗaura hannun ta a kafaɗar Mom ɗin. Sai a lokacin Mom ta dawo daga duniyar da ta faɗa. “Mom wai tunanin me kike yi ne haka?, Har fa na shigo baki san na shigo ba” ta faɗa cike da shagwaɓa. Murmushin da bai kai zuci ba Mom ta sake tare da hugging nata “Sorry Daughter Ina tunanin Hamman ku ne, gabaɗaya yanzu ya fara mancewa da mu, 2days kenan bai neme Ni ba” ta ƙarasa cikin sigar da ke nuna tsantsar damuwa. “Kiyi haƙuri Mom kina yiwa Hamma Zaki addu'a, tunanin bashi da amfani.” Sanyi Mom taji a ranta saboda ƴar maganar da suka yi da Fauzah. “Oya fresh up muje wurin Granny ko?” “Toh Mom” Bayan Fauzah tayi wanka ta biyo bayan Mom, tare suka jera har suka isa part ɗin granny. A can suka tarar da Mommah da Ƴaƴanta ammah Nenne bata nan. Sai wajajen maghrib suka watse kowa ya wuce, Fauzah ta cewa Mom bari taje wurin Yesmeen ne. Daga nan Mom ta wuce zuwa part ɗin ta. A nan suka yi salla, bayan sunyi suka kafa dandalin hirar su wanda duk sun kafa ta ne a kan Shagalin da zasu yi a JSSCE nasu. Har aka yi Ishã suna can sai da suka yi Najmah ta ƙira su suzo suyi dinner. Idon su ne ya sauƙa kan Ƴar Iya da ta make a ƙasa tana harba lomar dambun couscous da ke gaban ta yayin da idon Nenne ke akanta tana sakin murmushi. Mamaki da kuma tsoro ne suka dira cikin zukatan su lokaci guda su basu ƙaraso ba kuma basu koma ba, ita kuwa wacce suke abun a kanta bata ma san da su ba. Har ta gama cinyewa Allah bai basu ikon koda kuwa motsawa ba. Tana cinyewa ta ɗago da kanta, sai a lokacin idonta ya sauƙa kan kyawawan Ƴanmatan da ke tsaye suna kallon ta, lokaci ɗaya ta fahimci kallon tsoro suke mata. Murmushi ta sake sai da dimple nata ya bayyana. Kallon ta ta mayar kan Nenne da ke aiko mata da murmushi. “Nenne na cinye,” Nenne tace “Ti kice alhamdulillah” Ɓata fuskar tayi ƙasa-ƙasa tace “Alhamdudillah” Dariyar su Najma ne ta sa ta dawo da duban ta gare su, sai kuma ta marairaice fuska tana kallon Nenne. Harara Nenne ta aika musu tana faɗin “Kar ku saka min yarinya a gaba, ku bani waje in ba zaku ci abincin ba” Wani iri suka ji hakan yasa suka ƙarasa a sukwane zuwa dining ɗin suka zuba abinci suka fara ci. Ƴar Iya ta dubi Nenne tace “Nenne ku dukan ku masu kyau ne, waɗannan Ƴan gayun su ma ƴaƴan ki ne?” Murmushi Nenne tayi tace “Bari su gama ci sai na faɗa miki su waye ne” Kai kawai ta gyaɗa taci gaba da kallon ƙauyen ta a parlourn. TO FAH, ƳAR IYA A NAIRA FAMILY, KO YA KUKE TUNANIN WASAN ZAI KAYA? KUCI GABA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND BHATOOL DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA. MUCH LOVE MY ESTEEM FANS COMMENT & SHARE FISABILILLAH! [8/17, 6:17 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: 🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA “““61&62””” _Afwan masoya bayan wani dogon zango In Sha Allah yau na ɗaura alƙalami na kuma bana jin zan sauƙe sai na kammala muku wannan littafi, COMMENTS ɗin ku kawai nake so, ku taya ni SHARING kowanne update ta haka zan ƙara tabbatar da ƙaunar ku gare ni, Ina son ku irin loadi-loadin nan_💃🤩❤️ Bayan Najmah sun kammala cin abincin su, duka suka kwaso jiki suka dawo parlour, bisa lallausan carpet ďin dake shifide a parlourn suka zube tare da maida hankulan su kan Yar Iya da kuma Nenne. Cikin karfin hali Najmah tace “Nenne ina kika samo wannan?” Harara Nenne ta jefa mata kafin tace “To uwar tambaye-tambaye ban sani ba” Marairaice fuska tayi tana faɗin “I'm sorry Nenne an, kawai ta bani dariya ne, kiga fa yadda take cin abinci” ta faɗa cikin sigar zolaya. Ayrah da bata ce komai ba tunda suka dawo parlourn ta kece da wata irin dariya “Kai Adda Najma, itama fa mutum ce” Ran Nenne ne ya fara ɓaci da tsiyar da suke tsulawa hakan yasa ta daka musu tsawa “Is ok, bana son sakarcin banza, ku baku iya mutunta ɗan Adam bane?” ta jefa musu tambayar da ta saka lokaci ɗaya jikin su yayi sanyi. Cigaba da magana Nenne tayi “Ahalinku sun san ƙimar mutane saboda haka bana son na ƙara gani ko jin makamancin abinda kuka yi yanzu not only to her but to anyone, ok?” Gyaɗa Kai su duka suka yi yayin da Najma tace “Kiyi haƙuri Nennen mu ba zamu ƙara ba”. Murmushi tayi musu sannan ta ɗora da “Ban san ko a nan A'isha zata zauna ba, idan zamanta a nan ɗin ya tabbata ku shirya ɗaukar ta matsayin ƴar uwar ku. Kun gane” “Eh Nenne” suka bata amsa. Daga haka bata ƙara ce da su uffan ba ta mayar da duban ta zuwa ga A'isha. Bata ga alamun rashin jin daɗin abinda suka yi mata a fuskar ta ba amma sai da ta bata haƙuri a kan hakan. Cike da mamaki nake duba A'isha da tayi murmushi tace “Babu komai Nenne, nima Iya ta da kuma Baffi na suna yawan cewa na koyi haƙuri saboda bani da shi kuma ban sanshi ba, amma yau sai naji na fara shi” Dariya kaɗan Nenne tayi tace “Ai kuwa Iya sun kyauta, haƙuri yana da kyau sosai cikin rayuwa” kai ta gyaɗa alamar gamsuwa yayin da Nenne ke ƙara nazartar A'isha. Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ta sauƙe jin takun mai gidan uncle Suraj na shigowa. Bata yi ƙoƙarin sauƙe A'isha da kanta ke bisa cinyarta ba, sai ma ƙoƙarin gyara ma kanta zama da tayi. Cikin fara'a ya ƙaraso ganin A'isha a tare da Nenne duk da dama ya tsammaci hakan, coz Nenne akwai son jama'a. Sallamar ta amsa mishi tare da sannu da zuwa, ba tare da ya damu ba shima ya wuce ya watsa ruwa. Lokacin Nenne ta raka A'isha bedroom ɗin Hamma Zaki na ƙofar in yaso in taji matsayar zamanta sai ta maida ta ɗakin su Ayrah. Bayan uncle Suraj ya dawo ya tarar da Nenne a parlour, sabuwar gaisuwa suka yi. Abinci ta tambaye shi yace a'a baya buƙata. Hirar su suka ci gaba can Nenne ta sako zance A'isha. “Abbi Najma inaga ya kamata a san matsayin yarinyar nan, ta nuna min ita dai bata son komawa can ma, in babu damuwa sai ka barta a nan tare da su Yesmeen” Murmushi Uncle Suraj yayi yace “Kamar kin san me ke raina kuwa, yarinyar akwai ayoyin tambaya a tattare da ita, zata cigaba da kasancewa da mu har zuwa lokacin da zan gano ɓoyayyen Al'amarin dake cikin rayuwar ta” Haka suka gama hirar su. Washegari da safe kamar kullum suka tashi, bayan sunyi sallah itama ta tashi, sai dai ita bata yi sallar ba ta cigaba da zamanta a kyakkyawan ɗakin da aka bata ta kwana. Nenne da kanta ta shigo don tayar da A'isha sai dai da ta ganta kwance idi biyu sai ta tambaye ta “A'isha kinyi sallah kuwa?” Ido ta ƙwalalo waje tana duban Nenne. Sake maimaita tambayar Nenne tayi “Kinyi sallah ne A'isha?” Duru-duru ta fara hakan yasa Nenne fahimtar ta. “Oya tashi ki shiga bayi kiyo alwala ki kuma tabbatar kinyi sallah kinji?” Kai ta gyaɗa sannan ta miƙe tana nufar bayin, fuska da hannun ta ta wanke sannan ta wanke ƙafa, bayan ta fito ta fara kife kife ala doke tana sallah ne. Yunwar da ta dame ta ne yasa ta fito parlourn ko angama abinci, karo taci da Yesmeen da Adda Najmah cikin shirin su na makaranta. Lokaci ɗaya taji sha'awar komawa _sukul_ kamar yadda take faɗa, a dai-dai lokacin ta tuna da Aunty Jiram ɗin ta. Murmushi kawai take yayin da hankalin ta ya gushe. Fitowar Nenne daga kitchen tana jera abinci a dining yasa Yesmeen da Adda Najma ƙarasawa dining area ɗin. Sai a lokacin ta dawo hayyacin ta, Nenne na kula da ita sarai sai dai ba tace da ita uffan ba. Sai da ta gama jera breakfast ɗin ta juyo tana kallon A'isha. Fuskar ta ɗauke da murmushi tace “Aisha babu gaisuwa ne” cikin inda_inda tace “Ina wuni” Da “lafiya” Nenne ta amsa mata sannan tace, ki wuce dining ina zuwa” ba tare da sanin meye dining ɗin ba kawai ta tunkari wurin don iyakar ƙoƙari tayi shi, ji take kamar ƴaƴan hanjin tazasu tsinke saboda babu. Cikin mintuna da baza su wuce biyar ba sai ga Nenne da Uncle Suraj sun fito cikin shirin sa na kayan police 👮, Aisha na hango shi ta tsura mishi ido kamar zata cinye shi, lokaci guda kuma rana tuna shegun da suka tafi da ita suka mata dukan tsiya. “Allah yaso naci ubansu kafin na dawo ai” abunda ta furta kenan tana cije leɓen ta. Da kallon mamaki Adda Najma ke binta kawai haka nan Yesmeen, isowar Uncle Suraj ne da Nenne tayi gyaran murya. Kujera taja mishi tare da faɗin “Good morning Abbi Najma” Cike da murmushi ya amsa da “Morning” Nan Najma da Yesmeen suka gaida shi banda A'isha dake bin shi da kallo. Nenne ce ta katse ta da faɗin “Baki gaishe da Abbin ku ba A'isha” Cike da basarwa tace “Ina wuni” Cikin sakin fuska Uncle Suraj ya amsa da “Lafiya ƙalau A'isha”. Nenne ce tayi serving kowa, daga nan baka ƙara jin bakin kowa ba sai cak cak da spoons ke bayarwa idan sun haɗu da plate. Cinyewa da tayi yasa ta zubawa plate ɗin gaban Nenne ido. Ƙaraf suka haɗa ido sai ta kawar da nata, Nenne kuma ta yi murmushi tare da jawo plate ɗin ta ƙara mata sannan ta tura shi gabanta. Babu kunya A'isha tasa hannu taci gaba da ci har ta kammala, lokacin su Najma duk sun shige ciki don su yo brush sannan su ɗauko schoolbags nasu. ★★★★★★★ Bayan fitar su Najmah uncle Suraj suka fito shi da Nenne wacce hannun ta ke riƙe da A'isha, part ɗin granny suka nufa a tare. A parlour suka tarar da ita tana kallon Africa TV3. Bayan ta amsa sallamar su suka shiga tare da samun matsuguni. Gaishe ta suka yi ta amsa sannan ta bisu da kallo alamar tana buƙatar ƙarin bayani game da yarinyar da suka zo tare. Cikin dakewa uncle Suraj yayi mata bayanin komai game da A'isha tun daga haɗuwar su da zaman da tayi tare da su. Cikin farin ciki granny ta miƙe tare da kamo hannun A'isha, babu musu ta bi ta har zuwa gefenta da ta zaunar da ita tana famar murmushi. “Kai amma naji daɗi sosai, wannan yarinya kamar ɗiyar Ramatu” (Mom)😂 da yake bata iya faɗin Rohmoh ɗin. Shafa fuskar ta tayi tace “Yarinya kyakkyawa da ita, to babu komai amma ina neman wata alfarma daga gare ku” Ba tare da sunce komai ba granny taci gaba. “Ina so ku bar yarinyar a tare da ni don Allah, nasan zata ɗebe min kewa” Cikin murmushin yaƙe Nenne tace “Babu komai ta zauna ai duk ɗaya ne,zamu wuce Inna” Murmushi granny tayi tace “Na gode muku ƙwarai da gaske, Allah yayi muku albarka” Da “Ameen” suka amsa sannan suka miƙe a tare. A'isha dake gefen Granny tayi luƙus don ji take yi kamar tare da Iya take. Hannu kawai Nenne ta ɗaga mata daga haka suka fice. Sai da granny ta tabbatar sun tafi ta juyo da A'isha tana duban ta. Murmushin dake kan fuskar granny yaƙi ɓacewa saboda tsantsar farin cikin da take ciki. “Ƴan mata yaya sunan ki?” A'isha tace “Suna na A'isha amma ana cemin Ƴar Iya” Granny ta wangale baki “aaaaa kice takwara ta ce ke ɗin, amma wane suna kika fi so ana ƙiran ki dashi anan?” Ɗaga kai tayi alamun tana tunani can tace “Aisha nafi so” “Tooo too shikenan Amma za'a sauya miki suna saboda sauran ƴan gidan basa iya kiran suna na” Kai ta gyaɗa ba tare da ta fahimci me Granny ɗin tace ba. “Tashi muje na nuna miki ɓangare na” Ko ina sai da granny ta nuna mata daga ƙarshe ta nuna mata wani ɗaki “Wannan ɗakin na baki shi ke kaɗai, amma fa in kina son kwana a ɗaki na ma bazan hana ki ba”. Farin ciki kamar ya kashe A'isha saboda yanzu ji take har ta zama Ƴar gayu. Granny kuwa sai nan da nan take da A'isha wai tayi ƴa. Cikin ƙanƙanin lokaci A'isha ta sake da granny Kamar dai Iyar ta. Hakan yayi wa granny daɗi sosai. Da yamma bayan su Yesmeen sun dawo daga islamiyya suka taho ita da Fauzah da kuma Ayrah zuwa part ɗin granny bayan sanar da su fauzan da Yesmeen tayi game da A'isha. Sun kuwa ci Sa'a A'isha na zaune a ɗaya daga kujerun parlourn. Cikin sakin fuska suka nufe ta gabaɗayansu. Ayrah tace “Sannun ki, ke kyakkyawa ce” murmushi A'isha tayi tace “Aradu ku kun fini kyau, duk gidan nan Aradu babu maras kyau kamar aljanu” Dariya suka shaƙe da ita kafin Fauzah ta dakatar dasu da faɗin “Ni suna na Fauzah, wannan Ayrah, wannan kuma Yesmeen, ki ɗauke mu a matsayin ƴan uwanki” Dariya A'isha tayi tace “Babu komai, sunayen ku na ƴan birni ne Aradu, ko dan kuma ƴan birnin ne” ta ɗan dakata sannan tace “Ni suna na Ƴar Iya, Amma fa Nenne wacce nake ɗakinta jiya tace daga yau ba haka sunana ba” Dariya su duka suka yi, Ayrah tace “To meye asalin sunan ki?” “A'isha sunana fa, don sunan Iya gare ni, amma acan Gallara Ƴar Iya mai hannun ɓarna ake cemin, Aradu kowa ya Sanni a can, hhhh” ta ƙarasa tana sakin dariya. Kallon mamaki duka suka bita da shi, can Fauzah tace “Ba zamu ƙira ki da wannan sunan a nan ba, sunan ki kuma sunan granny ne, za mu tambayi Mom ɗina sunan da ya dace da ke” “Waye kuma Mom?” Aisha ta tambaya Murmushi Ayrah tayi kafin tace “Ke maman ta ce, Ƴar Indiya ce, baki ga Fauza ma na kama da su ba?” Ba tare da ta fahimta bata gyaɗa mata kai. Nan suka yi ta hira abun su har lokacin maghrib, kowa yayi sallah banda Ƴar Iya wacce ta make akan kujera sai hura hanci take wai ita Ƴar Birni. Granny da kanta ta tsaya kan Ƴar Iya har saida ta buga sallar tata. A nan ɓangaren granny suka yi ta hirar su har bayan Ishã, bayan sunyi dinner suka yi wa Ƴar Iya sallama daga nan kowa ta wuce part ɗin su. Babu laifi sunyi sabo sosai cikin ƙanƙanin lokaci, Fauzah ta sanar da Mom batun Ƴar Iya tace mata gobe su rako ta wajen ta. [8/18, 10:03 AM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA””” “““63&64 A daren ne Granny ta aikawa surikanta da kuma ƴaƴan ta tana son tattaunawa da su. Washegari kuwa duka gidan suka ɗunguma part ɗin Granny. Bayan sun gaisa cike da girmamawa take yi musu bayani akan Ƴar Iya, wacce a lokacin aka sauya mata suna da _Ummul-khairy_ domin sunan granny gare ta. Daga ƙarshe Granny ta rufe taron da faɗin “Wannan yarinya ina so kowa ya nuna mata ƙauna tamkar yadda zai nunawa ɗiyansa, ku ja ta a jikin ku domin akwai wani al'amari a tattare da wannan yarinya, ku so ta don Allah” Gaba ɗaya suka amsa da “In sha Allah Hajiya zamu kula da ita” Nan taron ya watse. Ɓangaren Khairy kuwa bacci take kwasa a lokacin ma, sai bayan wucewar su Granny ta tayar da ita. Daga jiya zuwa yau granny ta fihimci abubuwa da dama game da yarinyar shiyasa bata wani takura mata ba. “Tashi Khairy kiyi sallah” Ba musu ta miƙe tsaye tana miƙa kamar wacce zata cinye na gefenta, hakan ya bawa granny dariya sai da ta dara. “Ja'ira wuce kiyi sallah” Bayi ta nufa ta wanke fuskarta da hannayenta, daga ƙarshe ta wanke ƙafa ta fito. Sallaya ta shimfiɗa ta gabatar da sallar ta. ★★★★★★★★ Rayuwa kenan, yau kaine gobe kuma ba kai bane, haka Ƴar Iya wacce a yanzu ta koma Khairy ta cika sati guda cikin Naira family, abubuwa sun faru cikin satin, a ciki akwai ganawarta da Mom, wacce lokaci guda taji ƙaunar yarinyar cikin ranta, sai kuma hutun makaranta da sauran yara suka samu. Duk tsawon wannan lokaci, Hamma Zaki bai antayo gida ba, wayar da yake yi musu ma yanzu ba sosai ba. Mom ta shiga matsanancin tashin hankali game da hakan, amma kullum addu'a kawai take yiwa yaron nata kan Allah ya kuɓutar da shi daga sharrin wannan matar tashi. Yau juma'a, Mom da kanta ta saka yaran su shirya zasu je shopping, basu wani ɓata lokaci ba kowa ya shirya, fuskar kowa ɗauke da farin ciki da annashuwa banda Adda Salma, wacce haka kawai taji ta tsani Khairy, ba don komai sai tsananin kishin yadda kowa yake nan da nan da ita yayin da ita Khairy bata ma san tana yi ba. Mall suka fara nufa, Mom tace kowa ya ɗauki abun da yake buƙata, ta saka Adda Najmah zaɓarwa Khairy kayayyakin buƙata. Kayan da aka loada mata kamar wata ƴar gata (ko dan, yanzu kam ƴar gatan ce ai). Bayan sun gama aka wuce da su wurin gyaran jiki, kowacce ta ƙara kyau kamar ba gobe, tabbas familyn Naira babu na yarwa. Ban tsinke da mamaki ba sai da na hango Khairy wacce duk ta zarce kyawawan ahalin kusan kowanne fanni. Fuskar nan tata ta ƙara haske, ga wani ƙyalli da take yi, ban gama dawowa hankali na ba na cilla ido na kan gashin da aka gyara sai ƙyalli yake. In da badan da ido na na kalli gashin nan ba da sai nace ba na Khairy bane, wannan danƙararren gashin nata ya koma wani miƙaƙƙen gashi. Ayrah ce ta kalli Khairy tace “Khairy kin ganki kuwa?” Wani murmushi ta sake, take wasu fararen haƙware jere ras da su suka bayyana, yayinda kuncin ta ya lotsa. Cikin Muryar ta mai daɗi tace “Aradu kuma kunyi kyau” Mom dake kallon su cike da sha'awa ta cilla wa Khairy harara, ba shiri tace “Yi haƙuri Mom, na manta!” Sake fuska mom ɗin tayi tana rungumo Khairyn “Is ok daughter, kiyi ƙoƙarin gyara maganar ki, yanzu in wani yaji kina cewa Aradu to ko kallon ki ba zai kuma ba duk irin kyan da kika yi” Zaro ido tayi tace “Zan ma gyara ai” ta ƙarasa a yangance har sai da ƴan uwanta suka dara. Daga nan suka fito suka wuce gida. Cikin hutun su Fauzah Khairy ta ƙara wayewa, Mom na janta a jiki, haka Mommah yayin da duk kulawar da suke bata Nenne ta kere su a wannan fanni. Daf da zasu koma ne Granny ta shawarci uncle Suraj game da karatun Khairyn. “Eh Hajiya nima Ina son tuntuɓar ki Kan hakan amma ina laifin a fara nema mata mai Lesson daga baya sai ta shiga makarantar?” Granny tace “Babu laifi, dama kawai saboda yadda naga itama ta fara sha'awar karatun ne” “To Hajiya zanyi wa Nennen yara magana, ta nema mata Malama mace in yasa ko na 1month tayi mata sai a Kaita makarantar”. “Toh madalla, Allah amfana”. Daga nan suka shiga hirar su ta Duniya. Nenne da kanta ta zaɓawa Khairy ɗaliba, ranar da Madam Ajimola ta fara zuwa tayi iyakar iyawarta ganin Khairy ta fahimci darasin, babu laifi ta gane sosai. Malama Ruƙayya ma tazo tayi mata karatun Alkur'ani sai dai babu wani cigaba, hakan yasa ta nemi ganawa da Nenne kan batun. ★★★★★★★★ *ALEE POV* Kwance yake akan makeken gadon sa ya rasa me yake masa daɗi a duniyar, a hankali ya miƙe tare da ziraro kyakkyawar ƙafarsa ƙasa, parlourn ya fito ya duba ko ina Pretty ta shiga. Cike da ƙyanƙyami yake takawa duk da akwai takalmi a ƙafar tashi, fuska ya yamutsa a hankali ya furta “bullshit” Ƙarar fitar motar ta da yaji yasa ya maida dubansa ga window, ganin tabbas motar ta ce ta fita yasa yaja tsaki tare da dafe kanshi. Cike da takaicin Hali iri na pretty ya koma bedroom ɗinsa. Da kanshi ya tattare ya gyara bed ɗin sannan ya share, ya fesa room freshener, nan da Nan ɗakin ya gauraye da ƙamshi, Yana yi Yana tsaki. Cikin ranshi kuwa Allah wadaran aure irin nashi yake yi, to me ma Wai yakai shi Auren pretty ne?” Kanshi da ya Sara ne yasa ya bar tunanin ya nufi toilet, cikin ranshi Yana ayyana dalilin da yasa idan zai yi dogon nazari Akan pretty sai kanshi ya Sara. A daddafe ya fito ya shirya cikin khakin sojoji Wanda ke matuƙar amsarshi, fuskar nan tamau Kamar a filin yaƙi. Yurare ya buɗa sannan ya fito. Direct parking lot ya nufa, daidai farar motarshi ya ysaya Yana ɗan yamutsa fuska, ko ta Kan gateman dake gaisuwa bai bi ba ya figi motarshi sai barrack. Captain Stanley wanda ya zamo sabon aboki gare shi ya fahimci Hamma Zaki na cikin damuwa. “Dude, watz wrong, you look so worn out, why?” Har sai da ya cire ran zai amsa mishi can yaji muryarsa na faɗin “I want to go home friend” ya faɗa cikin tsantsar nuna damuwa. Captain Stanley kuwa mamaki ya cika shi, tunani yake wai dama Captain Alee na da relations a Nigeria?, If Yana da why baya ziyarar su. Murmushi yayi Yana kamo hannun sa “C'mon friend tare Zamu je ai, naga Kamar baka da lafiya ma” Shiru Hamma Zaki yayi Yana bin Captain Stanley da Ido. A ranar yayi musu booking flight, sannan ya koma gida, har lokacin pretty Bata dawo ba. Tsaki yayi ya wuce Zuwa bedroom ɗin shi sannan ya haɗa kayansa cikin trolley. Ko tsaraba bai yi musu ba ya nemi wajen baccin sa. Washegari da safe suka wuce airport, sai Adamawa, Dr. Faruq ne yazo ya miƙa su gida. Lokacin Mom na haɗa snacks a kitchen Kamar daga sama ta jiyo ƙamshin turaren da ko giya ta Sha in taji tasan na waye. Cikin sauri ta juyo Dan ganewa idon ta abun da take tsammani. Ai kuwa shi din ne, Bata yi aune ba Hawaye suka fara zubo mata, Shima hawayen ne yake zubowa daga idanuwan sa, idan yace bai yi missing mom din NASA ba to yayi ƙarya. Hamma Zaki ne yayi ƙarfin halin share hawayen dake ambaliya daga idanuwan Mom ɗin. “Is ok Mom, I miss u, ” Ya faɗa Yana hugging Mom ɗin, Murmushi Mai haɗe da Hawaye ta sake itama tana hugging nashi tightly Kamar zaa ƙwace mata shi. A parlour suka yada zango, ganin yadda ya rame yasa Mom ƙara tausaya mishi, ko Bata sani ba tasan yana Jin jiki. Trolleyn shi yaja zuwa bedroom ɗin shi, daidai frame ɗin dake ɗakin ya tsaya Kamar wani dolo ƴana nazari. Wayar shi da tayi ƙara yasa ya zabura Yana sakin tsaki. Ganin Mai ƙiran yasa yayi picking. Ba tare da yace komai ba yaji muryarta na dukan dodon kunnen sa. “Haba Aliyu, yanzu FISABILILLAHI don zaka je wurin iyayenka kawai sai ka tafi babu wani notification, ba za ka ma iya jura na ba kenan....?, Naji ka rasa wa zaka barwa saƙon ma sai maigadi, to lallai lallai Sati ɗaya na baka ka tabbatar ka dawo kaji ko?” Kamar tana gaban sa ya gyaɗa kai Yana hanging call ɗin. “Kai Fauzah, kin san Allah a duniyar nan ni babu abunda nike tsoro, ina daidai da komai da kika ganni” Ayrah ta sheƙe da dariya tace “gaskiya Khairy baki da dama, to wallahi duk iya shegen ki da zaki ga Hamma Zaki wollah sai kin jijjiga” Itama dariyar tayi tana miƙewa tsaye “Inma Hamma Namun daji ne ba zaki ba wollah bai kai naji tsoronsa ba, ni naga Alama koma waye shi tsoronshi kuke, hala malamin kune?” Janyo ta Yesmeen tayi ta zauna tace “Ke Khairy wallahi ki godewa Allah Hamma Zaki baya nan yanzu, kina cewa malamin mu ne shine fa na jikin picture ɗin parlourn Mom, ƴaƴan Fauzah ne” Dumm gabanta ya faɗin cikin ranta tace “Wannan mai siffar aljanun tsabagen kyau?” zahiri kuma ta cillawa Yesmeen harara “Ke kar ki wani dame ni, ina ruwa na da shi, nidai abunda na sani shine ko shi waye bazan ji tsoronsa ba”. “hmm” Fauzah ta faɗa “Zanso naga ƙarshen iyashegen ki Khairy, wollah zan so naga karon ki da Hamma Zaki” “Mtss sai kiyi kuma, don baki san wacece Ƴar Iya ba shiyasa kike tunanin zanji tsoron wani mahaluki, ni nan da kike gani duk ƙauyen mu kowa tsoro na yake, b don komai ba wasu kam sai saboda hannu na” Ta faɗa tana pointing hannun nata. Cike da son kawar da zancen Ayrah tace “Allah sarki Hamma Zaki, wallahi Ni yanzu fa tausayi yake bani” ta ƙarasa kamar zata yi kuka. Fauzah tace “Wallahi kullum sai nayi mafarkin ɗan uwa na, kin san Mom fa kullum sai tayi kuka” Yesmeen tace “Ai dole tayi, ni kan wannan matar tasa mai siffar aljanun dama daga ganin ta ai shaiɗaniya ce” “Ke dai kibari Yesmeen, wallahi da Hamma Zaki zai barmu gidan shi zamu koma muci uban shegiya ko kuma a haɗa shi aure kawai da Adda Salma tunda tana son shi” “Toh ƴan Manzon manyance, ku tashi ku bani wuri munafikan yara, ƙanana da ku kun iya gulma” Muryar granny ce ta katse su. “Kai don Allah granny, ke matsalar mu dake kenan wollah, don kawai mun jajanta abun dake damun mu” Ayrah ta faɗa tana tura baki. Baki Granny ta kama da hannunta ɗaya, ɗayan kuma ta riƙe kunkumi tana bin Ayrah da kallo “Toh rasa kunya ɓeran tanka, kin Isa ƙwarai, to ko ubanki Bello bai isa na faɗa ya faɗa ba, shashasha kawai, shi Mazan ne damuwar ku?” Fauzah tace “Yi haƙuri ƴar tsohuwar mu me ran ƙarfe, nasan kema dai kina kewar Wannan jikan naki da mace ta ƙwace shi ta hana shi zuwa kallon ki” Ai jin batun Fauzah sai granny ta ɓare baki tana kuka “Ƴar nan fauziyya ai dole, wannan shaiɗaniyar matar tasa kullum sai na tofa mata yasin ƙafa goma don ta cuce mu, shegiya mai fuskar aljanu” ta faɗa tana fyace majina da gefen zanin ta. Khairy da bata fahimtar komai gashi granny da kuma ƴan uwan ta sai ƙwalla suke zubarwa yasa ta ƙarasa tana rungume granny “Ki shiru haka nan granny, Ni nan nayi miki alƙawarin dawo miki da Maza (kamar yadda taji granny ta faɗa) garemu, ƴan uwa na kuyi haƙuri kunji?” *Hamma zaki da Khairy* _Ya kuke tunanin za'a kaya, kuyi comment an jima nayi update, Ina son mu kammala littafin nan kwanan nan ne_ COMMENT & SHARE PLEASE [8/18, 5:46 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA””” “““65&66 Granny tace “Shikenan ɗiyar kirki, na yarda dake sosai, Allah yayi muku albarka” “Ameen dukan su suka amsa mata” daga nan suka ɗunguma sai part ɗin Mommah. Lokacin Madam Ajimola tazo, dole Khairy ta tsaya yin karatu wanda suke yi a parlourn Granny. Tafe yake cikin takunshi mai nuna tsantsar haiba da kamala irin tashi. Can ƙasan maƙoshi sallamar tasa ta fita, Madam Ajimola dake ƙoƙarin koyawa Khairy karatu ta ɗago, kasa haɗa ido dashi tayi hakan yasa ta sunkuyar da kai. “Good Morning sir” Kai kawai ya ɗaga alamar iya amsar da zai iya bata kenan. Ganin yarinya zaune amma bata yi ko gigin gaisar da shi ba yasa ranshi ɓaci. Cikin ranshi yace “Koma wacece, I'll teach her a lesson” daga haka ya wuce Bedroom ɗin granny. Lokacin da ya shiga granny na sallar walaha saboda haka ya fito da niyyar komawa anjima. Sauran parts ɗin gidan yabi ya gaida su kamar yadda ya saba kafin ya koma bedroom ɗin shi yana mamakin wannan ƴar yarinya mai zarra da har zai shiga ta gagara gaida shi sai dai malamar ta. “silly girl” ya faɗa yana juyawa zuwa ɗaya ɓangaren. Madam Ajimola na gama yi mata Lesson ta wuce abunta. Granny da ta idar da salla ta fito tana faɗin “Maza ina ka shiga ne” Da kallon mamaki Khairy ke binta, ko ina taga mazan?. “Ke Khairy ina maza?” “granny wani maza kuma?” “Ke bana son shiririta, yanzu ya shigo ina sallah ko ya fita ne?” “Eh ya fita amma ina ga zai dawo” Bata rufe baki ba taji irin ƙamshin da ya bugi hancinta ɗazu, babu shakka wannan shine mazan granny Kuma Hamma Zakin ƴan uwanta. A hankali ta ɗago da idonta don kallon mamallakin wannan ƙamshi. Ganin granny ajikinshi tana share ƙwalla yasa ta nufi Bedroom ɗinta. “Maza sai yau ake ganin idon ka?, Yau wata nawa da auren ka sai yau ka tuna da mu?” “kiyi haƙuri granny, nasan Ni me laifi ne a wajen ku, Wallahi ban san me yasha kaina ba ne”. Ya faɗa yana yamutsa fuska alamar maganar da yayi tayi tsayi. “Ai dama na san wannan matar taka mai kama da tsatson bokaye ita ta raba mu, shikenan na haƙura, ina ita matar taka?” “Gida can abuja” “Hohoho dole ma ta dawo nan Adamawa da zama, don bazata raba mu da kai ba ita kuma tana tare da nata iyayen ba” Cike da ƙosawa da zancen granny yace “wacece wannan yarinyar?” Washe Baki granny tayi jin an ambaci Khairyn ta. “Ayyo, ƴar wajena wai?, Ummul Khairy ce sabuwar ƙanwar ka” Cikin ransa yace “Wannan fitsararriyar?, Ai sai na koya mata hankali”. “Amma dai tana da taɓin ƙwaƙwalwa?” “haba maza ya za'ayi kana cin mutuncin yarinya, to bata da taɓin hankali ko kaɗan, ragas take Kamar kai” Cikin ransa yace “In kuwa ragas take tabbas zan koya mata hankali”. Cike da jin haushin yadda granny ta nuna son fitsararriyar yarinyar da ko kallo bata isheshi ba yasa yayi mata sallama ya koma ransa babu daɗi yana tunanin ta yadda zai yi maganin ta. Da yamma sunje part ɗin su Ayrah Adda Salma ta tsokalo Khairy. Suna zaune a parlour suna hirar su wacce rabi da quater akan Hamma Zaki ne, ita dai bata cewa uffan saboda har yanzu bata taɓa ganin fuskarsa ido da ido ba, iyaka dai bata taɓa ganin mutum mai girman jiki kuma mai ɗaukar hankali ba irinsa. “Kai dallah ku rufawa mutane baki, idiots. Kun wani saka wannan gidahumar baƙauyiyar kuna mata zancen Hamma Zaki, oya ku tashi ku bar parlourn nan” Adda Salma ta faɗa tana cilla musu harara, cike da kallon da ke nuna ƙyama. Tunda Khairy take baa taɓa ci mata fuska irin na yau ba, kuma yau ne karo na farko a rayuwarta da wani ya taɓa nuna ƙyamarta. Har ta juya zata fita ta juyo ta kalli Adda Salma tace “Kada ki ƙara ƙira na da bagidajiya, ƙauye kuma tushen kowane” daga haka ta saka kai zata fita, babu tsammani taji hannun Adda Salma ya damƙi wuyanta. Duk abinda suke Mommah na kallon su, ita kanta ta gaji da mugun hali irin na Salma, shiyasa ko da yarinyar tayi mata rashin kunya bata ce komai ba. A hasale Khairy ta juya tana taskawa Adda Salma Mari, Marin da tunda Mommah tahaife ta bata taɓa jin irin sa ba coz sai da tayi loosing sight ɗin ta na wani lokacin. Da yatsa take nuna ta tace “Wannan shine karo na farko da kika saka na karyar alƙawarin da na ɗaukar wa Iya ta, kin sa haƙuri na ya ƙare, to Wallahi ki fita sabga ta” Daga haka ta arta a wani irin speed kamar wata iska, bata tsaya ko ina ba sai Bedroom ɗin ta, tana isa ta kulle ta faɗa kan bed sai wani irin numfashi take fitarwa. Gabaɗayan su basu bi ta kan Adda Salma dake zaune a ƙasa ba dirshan, sai ma bin bayan Khairy da suka yi. Hankalin su yayi mummunan tashi, gurnanin da ke tashi daga rufaffen ɗakin ya matuƙar razana su. Granny kuwa kuka take tana faɗin “Kuje ku ƙira maza yazo, nashiga uku ni Aishatu, ke Najma karɓi waya ta ki ƙira min Daddyn ku” Da ƙyar ta laluɓo number Daddy, cikin tashin hankali ya shigo gidan, ko parking bai daidaita ba ya fito ya nufi part ɗin granny. Tun daga bakin part ɗin yake jin gurnanin kamar an sake mayunwacin zaki. Ƙarasawa yayi, bai gama shiga tashin hankali ba sai da ya ga Hajiyarsu na kuka. “Maza ɗan nan a fito mun da yarinya, in ba haka ba zan bar gidan nan nima” Cikin ɗimuwa ya tambayi Fauzah dake kuka shabe-shabe coz tunda take bata taɓa jin irin wannan kukan ba. Bayani tayi masa, cikin ɓacin rai yace “Shikenan yanzu ya za'a yi ta fito?” Granny tace “Ka ƙira min maza nasan shi kaɗai ne zai fito da ita, wallahi yarinyar nan ta illata sai na saɓa muku” Daddy wayarsa ya ɗauko ya ƙira Hamma Zaki, thank God Yana ma gidan ashe. Kasancewarsa maras son hayaniya yasa gurnanin nata ya fara sauƙar mishi da ciwon kai, a haka ya daure ya ƙaraso zuwa ƙiran Daddy. Nan yayi masa bayani kamar yadda Fauzah tayi masa. Takaici ne ya kama Hamma Zaki amma ya dake yace “Daddy to a ƙira Sheikh Imam mana” Murmushi Daddyn yayi don shi har ga Allah kansa ya kulle. Number ya Sheikh ya danna amma bata shiga, hakan yasa ya ƙarasa bakin ƙofar yana ƙiran sunan ta “Khairy, Khairy” Babu alamun za'a amsa kuma gurnanin bai daina fita ba. Cikin ransa ya ɗauki aniyar hada ta da Sheikh Imam ko ma meyeh in sha Allah ba zai gagare shi ba. Har lokacin azahar ya kusa wucewa shiru, hakan yasa Nenne lallaɓa su suje suyi sallah. Bayan tafiyar su kowa zuciyar sa babu daɗi Nenne ta ƙaraso jikin ƙofar ta kafa kanta ta fara magana “Yarinya ta kiyi haƙuri ki buɗe kinji, Kinga ni da grannyn ku ga ƴan uwanki duk muna cikin damuwa, ki taimaka ki buɗe” Cikin wata razananniyar murya da amon ta ya zaga ko ina na gidan tace “Meyesa Nenne, ki tafi kema, ba ita bace, ku tafi in mun gaji zata buɗe” Jikin Nenne karkarwa kawai yake, cikin ƙarfin hali tace “Toh kada ku cutar da ita don Allah” Tsawa aka daka mata wanda sai da kowacce kusurwa ta gidan ta jijjiga. “keeee, ki tashi ki tafi muka ce, wannan ba damuwar ki bane, tun tana ciki muke tare da ita, da munyi niyyar cutar da ita da munyi” Ai tun kafin maganar ta kai karshe Nenne ta fice da gudu, duk gidan a ɗimauce suke, musamman yadda Muryar ke tashi ga kuma tsawar da ta jijjiga ginin gidan. Allah Sarki granny kuka take, ta kasa cin abincin ma, gwanda yaran an saka su dole sun ci. Adda Salma ana can ana zaryar shiga toilet, don tunda ta fara jin wannan sautin cikinta ya juya, ga kuma wani surutu da ake yi mata a cikin kunne, gashi kowa ya gudu ya barta ita kaɗai, kuka take kamar zata mutu amma babu mai rarrashi. Tayi da-na-sanin tsanar yarinyar da bata ji ba bata gani ba. Gashi yanzu ta jawowa kanta, Mommah sai ta hukunta ta, gashi kuma sai ta shiga uku da bareɗeɗen granny. Da haka tayi sallah tana roƙon Allah ya kawo abun da sauƙi. Sai wajajen maghrib gurnanin ya lufa, sannu A hankali kuma ya disashe kamar ba a gidan ba. Can kuma sai suka ji ƙarar ƙofa ƙiiiii, Khairy ce idon ta a kumbure, fuskar nan tayi jawur da ita. Dukkan su kanta suka yi suna rungume ta. Granny ta janye ta gefenta tace “Haba ɗiyar nan, kiyi haƙuri faɗa min wadda ya taɓa ki” Nenne tace “Ysnzu dai ba wannan ba Hajiya, tayi sallah taci abinci” Babu musu tayi sallarta kamar yadda ta saba. Granny da kanta tayi feeding ɗin ta, ƴan uwanta kuwa na kewaye da ita don har ga Allah su suna jinta a jikin su. Ɓangaren Hamma Zaki abun ya ɗaure masa kai cikin ransa yake faɗin “Dama nasan yarinyar nan ba lafiya take ba granny ta kafe har take kwatanta lafiya ta da tata” yamutsa fuska yayi yace “So disgusting”. Ƙiran pretty ne ya dawo da shi daga duniyar da ya dulmiya, tsaki yayi ya ɗaga. “Aliyu shine ko kira na bazaka yi ba saboda kana tare da ahalin ka?” A hankali yace “Kinga Nabila meyasa kike hakane, ke da ko nuna kulawarki gare Ni bakya yi don yanzu ina samun kulawa sai ki ɗaga hankalinki” Cikin ɗaga murya tace “Dakata Aliyu, iyayenka sun fini ai?, Gaskiya ka dawo ma in zaka dawo don ba zaka shiga hakki naba” tsaki yaja Yana hanging call ɗin. Cikin ranshi yana tunanin meyasa yarinyar ta raina shi, tabbas sai ya saita ta. Da daddare Daddy ya ƙara gwada numbern Sheikh Imam, and luckily ya same shi, bayan sun gaisa cike da mutuntawa yake sanar da shi game da Khairy, da irin yadda tayi yinin yau. Sheikh Imam yace “Tabbas akwai abun dubawa a game da yarinyar, sai dai bana Nigeria yanzu haka, kuma zan kai wani satin kafin na dawo,amma da na dawo in Sha Allah zan taimaka da taimakon Ubangiji mu ceto yarinyar nan.” “Yauwah ya Sheikh, Allah ya dawo da kai lafiya, na gode sosai” “Babu godiya tsakanin mu, sai na dawo, kafin nan ake yawan karanta Alqur'ani a wurin da take, kuma a guji duk wani abu da zai tada hankalin ta na wannan lokaci” “In sha Allah za'a kiyaye” Daga nan suka yi sallama. Nan yake sanar da Mom akan yadda suka yi da Sheikh Imam, da kuma shawarar da yanke idan Sheikh Imam ɗin ya dawo a haɗa shi da Alee, don Yana da tabbacin akwai sihiri a tattare da shi. Mom taji daɗin hakan kuma ta shawarci Daddy a kan Hamma Zakin ya dawo Adamawa da aikin gabaɗaya don hakan ne kaɗai kwanciyar hankalin su. _Toh Fans, ya kuke tunanin wasan zai kaya?, mom da Daddy suna yunƙurin lalata shirinta, ko kuna tunanin zata yadda kuwa?, Ya kuke tunanin haɗuwar Hamma Zaki da Pretty?, Kuci gaba da bibiyar alƙalamin diamond bhatool ta hanya yimin comments da share_ [8/21, 11:00 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: 🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA “““67&68””” Sheikh Imam yasha wahala ƙwarai dagaske kafin ɗaya daga cikin shaiɗanun suka amince da batun shi. Gyaran murya yayi ya fara magana kamar haka: “Mu ma ba yin kanmu bane, mun kasance muna aiki da wani bil'adama wanda yake aikin bokanci a can Gallara. Hatsabibin boka ne wanda ba abinda baya iyawa da taimakon shaiɗanu.” “Wata rana, shekaru goma sha biyar da suka gabata, wata mata mai suna Zaliha taje ga bokan don yayi mata aiki. Tana son a raba auren Wani mutum mai suna Umaru da matarsa Barira, wanda hakan ba abu ne da zai yiwu ba. Bayan sanar da ita da hakan da boka yayi, bata sare ba tace da shi yayi yadda yake ganin zai yi don ita so take ya aure ta. Boka yace ba zai yiwu ba saboda tauraron matar na da matuƙar ƙarfi, kashe ta ba abu mai sauƙi bane. Ammah akwai mafita, dole zata sadaukar da jinin yarinya wacce zasu sarrafa, sannan kuma zata sadaukar da mahaifarta ga baƙin aljani. Duk da haka matar bata sare ba ta amince da hakan. Boka yayi mata alƙawarin zai kashe matar kuma zai haɗa aurenta da Umaru”. “Bayan wani lokaci taji shiru sai ta dawo wurin bokan, take masa ƙorafin ya taji shiru?, A lokacin ne kuma boka yake sanar da ita ai Barira na da ciki, amma kuma da zarar ta rabu da cikin kashe ta zai zama abu mai sauƙi. Zaliha tayi murna sosai saboda haka bata yi ƙasa a guiwa ba duk bayan sati sai ta ziyarci boka yayi mu'amala da ita. Bayan an haife yarinyar, wacce boka ya musanya hannun ta da hannun ɗan guigui, sai ya bawa Zaliha mutunmutumi wanda da shi zata hallaka Barira. Kamar yadda ya bata haka tayi amfani da shi, ta soka allura a jiki, nan Barira ta fara jinya, ta soka na biyu, jinya tayi tsamari, tana soka na ukun Barira tace ga garinku nan, a ranar kuma boka ya zuba tsantar soyayyar Zaliha cikin ran Umaru, tun a ranar ya fara samun uwarsa cewa shi aure zai yi, sati da mutuwar Barira kuwa ya auro ” Zaliha wacce ta mallake shi, bashi da ikon yin abu sai da izinin ta”. “A lokacin da Barira ta fara jinya, sanin cewa Umaru mutum ne wanda zai iya wargaza aikin, yasa boka ya tura masa shaiɗanu ciki har da Mantau, gaba ɗaya ya manta da ita, har tayi jinya ta rasu kai har yanzu da nake maka magana Umaru bai san mutuwar Barira ba. Ranar da Barira ta mutu ranar boka ya amshi mahaifar Zaliha kamar yadda suka yi alƙawari. Nan kuma boka ya binciko wannan yarinya ta Barira tana da matuƙar tasiri, kuma ita zata kawo ƙarshen taaddancin Zaliha, saboda haka ya zaɓo mu cikin ma'aikatan sa ya sa mu kasance tare a ita, kada mu barta ta samu sukuni, muke saka ta aikata munanan abubuwa da taimakon hannun ɗanguigui da aka musanya mata. Tun daga ranar muke tare da yarinyar, ba ma barinta tayi wani abu mai kyau tun tana yarinya, mugunta, ta'adi sune abinda tasa gaba, kakanta da kuma kakarta da suka raine ta duk sunyi iyakar iyawarsu don ganin sun kawar da mu sai dai munfi ƙarfin su. Bayan ta kai girman ta ne muka juya ƙwaƙwalwar ta saboda muna tsoron ta sauya daga turbar da muka ɗaura ta. Bata duk wani abu da ya shafi addini, babu abunda ta tsana sama da sallah, karatun Alqur'ani kuma mun riga mun juya ƙwaƙwalwar ta ko sau million za'a yi bazata taɓa haddata ba. Mun fara samun tsaiko ne ta hanyar wasu fararen shaiɗanu da suka shafe ta, da yake mun fi ƙarfin su yasa tasirin su baiyi ƙaimi a tattare da ita ba.” “Yanzu haka ba mu bane muka zo ba, waɗannan fararen shaiɗanun ne da suka fara tasiri a tattare da ita saboda irin kyautatawar da mutanen da suke rainon ta ke nuna mata, har ta fara sanyi kuma ta daina ɓarna kamar yadda ta saba, hannun ɗanguigui ma yayi sanyi. Ko a lokacin da suka samu hatsari, mun so hallaka ta a lokacin saboda mu huta da wannan aiki mai dogon zango sai dai fararen shaiɗanun sunyi galaba a kan mu, duk da mu muka haɗa hatsarin ko ƙwarzane bata samu a jikin ta ba” “Yanzu maganar da nake maka muna kan aikin mu, indai muka ce zamu rabu da goɗiyar nan boka zai mummunan hukunta mu, saboda haka babu yadda zamu je” Sheikh Imam ya share hawayen dake fita da idanuwan sa yace “Lallai kun cika azzalumai, kuma Ubangiji ba zai barku ba, ita Zaliha kuma tun a nan duniya zata ga sakamakon ta. Barin yarinya kuma dolen ku ne”. Cike da hasala shaiɗanun suka tada wata baƙar guguwa wacce ta zo da girgizar ƙasar gidan, tuni gidan ya fara rawa kamar zai rushe, duk da haka Sheikh Imam bai tsorata ba yaci gaba da karanta Alqur'ani, can guguwar ta lafa suka fara ihu suna faɗin ya dakata, zasu fita amma har sai an since ƙullin da aka yi a lokacin aikin, wnada yanzu haka yana tare da Inna Zaliha a bayan gidan ta. Dole aje a ɗauko wannan ƙullin a since, daga nan zasu bar yarinyar”. Murmushi Sheikh Imam yayi yace “Shikenan zamu je a since ƙullin amma kafin nan ina so kuyi imani da Allah ku tuba daga irin waɗannan ayyukan da kuke yi, don kuwa Allah baya zulunci kuma baya goyon bayan zalunci”. Nan Christins na ciki suka musulunta , musulman mah suka yi alkawarin sauya sheƙa daga miyagu zuwa nagari. Sheikh Imam yayi matukar farin ciki. Daga nan jikin Khairy ya sake. Wani ruwan magani ya watsa mata daga nan ya wuce zuwa ɓangaren baccinsa ya kwanta. Washegari kuwa sai ga Daddy sassafe tare da Hamma Zaki, har lokacin Khairy na kwance bata tashi ba. Bayan Sheikh Imam sun gaisa da Daddy nan ya sanar da shi komai kamar yadda ya wakana daren jiya. Daddy sai da ya zubar da ƙwalla, Hamma Zaki ma ya tausaya wa yarinyar cikin ranshi yace “Ashe ba banza ba”. Daddy ya umarci Hamma Zaki ya basu wuri za suyi magana da Sheikh Imam. Bayan fitarsa Daddyn ya sanar da Sheikh Imam game da Hamma Zakin. Murmushi irin na manya wanda yanzu na fahimci ɗabi'ar Sheikh Imam ɗin ne yayi. Ya fuskanci Daddy yace “Tabbas tun jiya da kuka zo na fuskanci hakan, alamomin wanda sihiri ya kama sun bayyana a tattare da shi. Amma babu komai zan bashi wani magani, da izinin Allah zai samu waraka. Akwai wasu addu'oi ma da zai lazimci karanta su, bi'idhnillah zai samu kariya daga wurin Ubangiji, Allah ya kiyaye gaba”. Hirar su suka ci gaba da yi can Daddy ya tambayi ina Khairyn?, Sai a lokacin Sheikh Imam ya sanar da shi cewa “Ba lallai ta farka a yau ba, saboda shaiɗanun manya ne kuma baƙaƙe, amma akwai maganin da zan baku, ruwan addu'a da kuma wasu addu'oi da za'a ke karanta mata. Idan ta farka za'a iya samun sauyin yanayi game da ita saboda rayuwar da tayi a da duk bata da hankali, don Allah a kula da maganin nan. In ta ware zamu je can garin nasu tunda sun faɗa, sai a tono bisnen a ware shi, daga nan baƙaƙen aljanun zasu bar jikin ta.” Da “Toh Daddy ya amsa yana ajajjaɓin abun cikin ransa,”. Sai wajajen Zuhr Daddy ya nemi Hamma Zaki, bayan sunyi sallah a masallacin dake jikin gidan Sheikh Imam ɗin Daddy yasa Hamma Zaki ya ɗauki Khairy ya kaita mota. Da ya dawo Sheikh Imam ya bashi magungunan da kuma addu'oin kamar yadda ya faɗa, ya bawa Daddy ma na Khairy sannan yayi wa Hamma Zaki tunatar wa akan kula da ambaton Allah musamman zikirorin safiya da maraice. Nan suka yi sallama suka dawo gida. Allah Sarki granny tunda aka tafi da Khairy hankalin ta bai kwanta ba, haka Nenne da sauran mutanen gidan. Horn ɗin motar da suka ji yasa duka suka fito waje suka yi tsaye. Hamma zaki har ya miƙe zai shige part ɗin su Daddy ya dakatar da shi “Waye kuma zai shiga da ita?” Ba tare da sanin yadda zai kaita ba ya ɗauko ta sai part ɗin granny, sauran mutanen gidan ma duk suka biyo bayansa cike da alhinin Allah yasa Khairy ba mutuwa tayi ba. Granny, Nenne, Mommah da kuma Mom duk saida suka zubar da hawaye, Adda Najma uwar tausayi Kam kuka take shaɓe-shaɓe. Su Ayrah dama sun wuce islamiyya. Har yau Adda Salma a suƙure take, a cewarta itace silar komai, Mommah ma bata sake mata kuma tace duk abinda ya samu yarinyar ta kuka da kanta. A kan gadon granny ya fire ta daga nan ya fito, magungunan sa ya ɗauka ya wuce part ɗin su. Granny dake ta famar sharar ƙwalla tana fyace hanci sai haƙuri suke bata. “Dole nayi kuka mana, yarinyar nan jinta nake kamar yadda nake jin maza, wallahi wani abu ya same ta bazan yafewa kaina ba. Allah Sarki Ummul Khairy” Daddy ne yayi gyaran murya yace “Yanzu dai ba wannan ba Hajiya, kiyi haƙuri Allah zai bata lafiya. Sannan waɗannan magungunan ta ne,” Nan ya faɗa mata yadda za'a yi mata amfani da shi. Mom tace “Sai naga kamar Hajiya zata takura, ko za'a kaita waje na na kula da ita” Da sauri granny tayi caraf tace “Aah Ramatu, barni nayi jinyar Ummul Khairy da kaina, babu wani takurawa” Kowa sai da ya murmusa don dama da biyu mom tayi maganar. Nan Daddy yayi musu sharhin yadda abun ya wakana, dagar da aka sha kafin kai ga wannan mataki, kuka dukkan su suke yi, granny tace “Allah sarki shiyasa nake jin tausayin yarinyar ashe, amma wannan mata in munje can Mai Hana ni muƙe ta da ice ma sai naji dalili” Fyace hanci tayi tace “Allah sarki ɗaya ta ” Jikin su Nenne duk yayi sanyi. Nan Daddy ya ɗaura da yi musu nasiha akan suji tsoron Allah su kuma guji shirka, domin mafi munin zunubi itace shirka. Daga nan suka watse granny aka fara jinyar Khairy. Ɓangaren Hamma Zaki kamar yadda Sheikh Imam yayi masa bayani haka ya fara amfani da maganin, addu'oin ma ya karanta su, tunda ya fara yake ji kamar ana sauƙe masa wani nauyi daga kansa, mugun ɓacin rai da baƙin rai da yake fuskanta tun bikin sa tuni ya fara jin sassauci. Tunani kuma ya fara kama shi tun bayan yin addu'oin da kuma shafa magani da ruwan addu'ar. Ba abinda ya fara faɗo masa a rai sai batun auren sa, taya ma aka yi ya fara son yarinyar da ta so nuna masa raini ranar bikin girmamawa da akayi masa, wai anya shi yace yana son Auren kuwa shida ko kaɗan baya son tashin hankali?” Ganin kansa ya fara sarawa yasa ya shiga Toilet ya watsa ruwa tare da ɗauro alwala, daga nan bacci ya ɗauke shi. _Toh, ko ya zata kaya tsakanin Hamma zaki da Pretty?, Zai ci gaba da zama da ita?, In baku manta ba akwai fansar da iyayen Pretty ke son ɗauka, ko meye dalili?, Khairy fa? Wane irin sauyi kuke tunanin rayuwar ta zata samu?, Su inna Zaliha fa?, Duk cikin littafin ƴar Iya ne, ku ci gaba da bibiyar alƙalamin diamond bhatool_ _In har ba'a comments zan ƙara rage yawan post gaskiya, kuyi comments ni kuma nayi ta Baku update_ Comment & Share Please. [8/21, 10:36 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: 🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA “““69&70””” Sai wajajen ƙarfe goma na dare Khairy ta fara mutauniyar tashi, granny da idonta ke kanta tayi maza ta ƙara matsawa kusa da ita. Shafa bayanta ta fara tana faɗin “Ummul Khairy kin tashi?” shiru babu amsa hakan yasa granny kunna bulb na ɗakin. Idanuwanta sun sauƙa ne akan fuskar Khairy da tayi Fayau da ita sai yamutsa fuskar take. “Khairy” granny ta ƙara ƙiran sunanta a karo na biyu. Ganin ba zata amsa ba yasa granny yin shiru tana zubawa sarautar Allah ido tare da jin ɗumbun tausayin Khairyn na yawo cikin jininta. Tabbas ko maƙiyinta ne yaga irin yanayin da take ciki zai tausaya mata. Ɓangaren Hamma Zaki sai da yayi amfani da maganin kafin ya kwanta bisa katafaren gadonsa, addu'oin bacci ya karanta sai dai baccin sam yaƙi zuwa masa in banda tunani babu abunda yake yi, wanda kaso 40 ya tafi ne akan sauyin da ya samu a cikin rayuwarsa. This sudden change yasa shi shiga cikin wani yanayi. “Ya Allah” ya furta yana ƙara juyawa akan faffaɗan gadon nashi. Ganin tunanin yana shirin sanya shi shiga cikin wani mugun yanayi yasa ya fara tunanin maslaha ga rayuwarsa. Tabbas akwai baƙon al'amarin da ya ziyarce shi kwanakin baya, in ba haka ba me yasa zai yi aure so sudden haka?, Bashi da mai bashi amsar yasa yayi tsaki “And the worst part of it mahaukaciya ce matar tawa” ya faɗa cikin ɗacin rai. “Allah sarki yarinyar nan! Ko ta farka kuwa?, I pity the little creature”. Miƙewa yayi yana sauƙa a kan gadon, direct part ɗin granny ya nufa. Da sallama a bakinshi ya shiga. Granny ta amsa amsa masa cikin sakin fuska lokaci ɗaya kuma fuskar damuwa ta bayyana tattare da ita “Maza kaga yarinyar nan Khairy har yanzu bata tashi ba, anya ba mutuwa ma tayi ba?, Ɗan duba min” sai da ya murmusa kafin ya dube ta yace “Granny ba dai anyi miki bayanin abinda ke damunta ba?” gyaɗa kai tayi sannan yace “To tana da rai, addu'r ki kawai take buƙata a yanzun sannan Sheikh Imam yace ake kunna karatun Alqur'ani a wurin da take” Da sauri granny ta miƙe ta nufi wayarta ƙirar tecno mai madannai. Ƙira'ar babban ƙari'in nan Sheikh Muhammad Ayyubi ta kunna wanda tuni sautin ya karaɗe ɗakin. Murmushi yayi cikin ransa yace “She too much care about the little creature” Mintuna biyar suka shafe babu mai magana, mutsu-mutsunta ne ya dawo da hankalinsu gare ta. “Ash, kaina!, Iya ta kaina zai cire” da sauri granny ta matsa kusa da ita tana faɗin “Kin tashi, sannu maza bari na kawo miki abinci” Da ido Hamma Zaki ya nunawa granny ruwan addu'a ai kuwa tayi sauri ta ɗebo ta shafa mata a goahinta sannan ta shafe mata a sauran jikinta sai famar sannu take jera mata. “Wollah yunwa nake ji, wai haka zan zauna” murmushi yayi yana miƙewa cikin ransa yana ayyana “Wannan da gani dama foodie ce” Granny ce tayi feeding ɗin ta daga nan ta koma baccin ta. Washegari Hamma Zaki yayi shirinsa na zuwa Abuja don samarwa kanshi transfer bisa umarnin iyayensa. Bayan ya isa kamar koyaushe ya tarar da gidan cikin datti kamar ba sabon gida ba. Tsaki yayi ya nufi ɗakinta don babu shakka bacci take sai kace kasa. Ai kuwa zatonsa ya tabbata. Cikin ɓacin rai ya ɗaka mata duka “Tashi kiyi sallah” Kamar daga sama ta jiyo muryarsa ai kuwa zubur ta miƙe, wallahi har cikin ranta tana ƙaunar Captain Alee. Hugging nashi tayi zata kai masa peck ya ja gefe “See You, ko salla baki yi ba kina shirin taɓa ni, oya go and pray, ki Kuma same ni a bedroom ɗina” ya faɗa cike da taƙama tare da yamutsa fuska. Baki Pretty ta sake tana ganin ikon Allah. Tsawon aurensu bai taɓa yi mata magana da irin wannan sigar ba duk da cewa tasan a jininsa ne, kai ta karkatar tana faɗin Allah yasa ba aiki na bane ya ɓaci ba” Daga haka ta nufi toilet ta ɗauro wanka da alwala. Ko sallar bata yi bata sheƙa kwalliya kamar mai zuwa gasar kyau. Kitchen ta nufa ta buɗe fridge tare da ɗauko sauran abincin da tayi order jiya, warming tayi sannan ta ɗauka ta wuce Bedroom ɗinsa. Kwance ta tarar da shi yana lallatsa wayarsa ga kuma wani irin kwarjini da yayi mata. Sai ta tsinci kanta da faɗin “Good morning sweetheart” idan da wayar da yake dannawa tayi magana la'alla ta amsa mata. Kusa da shi ta zauna tana ajiye abincin bisa side drawer. Ba tare da ya tanka mata ba yaci gaba da uzurinsa. Ganin ma ba kulata zai yi ba yasa ta miƙe jiki a saɓule zata fita. Muryarsa ce ta daki dodon kunnenta “Wa ya baki izinin fita?” Cike da takaicin sauyin halin nasa ta juyo rai babu daɗi. Cikin ranta tana ayyana “Ba zai saɓu ba, dole ne ka dawo ƙarƙashina Captain. You're mine alone”. Ba tare da ya juyo ya kalle ta ba yace “Ki haɗa kayan da zaki buƙata, in a day time zamu wuce Adamawa” Baki sake take kallonsa ta ma kasa furta komai. “Me mutumin nan yake nufi?”. Cikin ƙarfin hali tace “Sweetheart kwana nawa zamu yi?” Har ta cire ran samun amsar sa taji yace “Can zamu koma da zama” “Kutumar uba!, Wallahi ba zata saɓu ba” Ta faɗa tana riƙe kunkumi tare da jijjiga jiki irin ta tsumu da bala'in nan.. Bai kalle ta bare tayi tunanin yasan me take, saboda haka ta fice a fusace cikin ranta tana tabbatarwa kanta aikinsu ya ɓaci. “Dole kuwa nasan yadda zanyi” Mami ta ƙira take sanar da ita komai. Wani Ashar da ta kututtumo kamar bamagujiya. “Amma wannan Allah yayi ƴan abu ta kazar uba, karki damu Daughter, yanzu ki nuna masa babu komai ki lallaɓa shi tunda ya dawo hankalinsa, ko bayan tafiyarki zan koma wurin bokan yayi masa babban aiki ke harda iyayen nasa ma” Da haka ta fara haɗa trolleyn ta, komai na buƙata ta saka, ga yanzu damuwarta ma ɗaya itace ta cikin dake jikinta. Tana ayyana dole Captain ya amshi cikin ko kuma tayi aborting nasa. Da haka ta haɗa komai ta zauna cike da zulumin komawarta Adamawa. Washegari da safe ma sai da ya tashe ta tukun ta tashi, daga nan ya fita yana jin takaicin wannan aure nasa, sai da ya kammala komai tukun ya wuce yayi musu booking flight. Abinci ya biya ya siya daga nan ya ƙarasa gidan. Bai bi ta kanta ba har washegari. Ƙarfe bakwai dai-dai yaje ya tasheta saboda Flight ɗin 8 zasu bi, shi kam already ya gama shirinsa cike da haɗuwa da burgewa. A daddafe ta kammala shirin saboda zazzaɓi zazzaɓin da ya sauƙa mata. Tare suka wuce zuwa airport ɗin ba tare da wani ya cewa ɗan uwansa ƙala ba. Ɓangaren Khairy kwana biyun nan bata san me ake yi ba, kowa tausayin halin da take ciki yake, Adda Salma Kam ta taro part ɗin granny tare da ita ake kula da Khairyn. Flight ɗinsu na landing suka ƙarasa zuwa motar Hamma Salim da yazo ɗaukarsu. Kallo ɗaya yayi mata ya gano tana ɗauke da juna biyu, cike da barkwanci yace “Ke amarya zuwan farko da tsaraba” Cike da duburburcewa tace “Ehm ah ehm yayan mu..” Bata Kai ga ƙarasawa ba ya katseta yana dariya “Kinga ba wani abu bane, baki ga basaraken mijin naki ma bai ce komai ba” In banda ƙyaƙƙyafta ido babu abunda pretty keyi har suka iso. Shi dai Hamma Zaki ko kallo basu ishe shi ba. Bayan sun isa a part ɗin Mom suka sauƙa, babu yabo babu Mom ta tarebe su, Laraba aka sa ta kai trolleyn su Bedroom ɗin Hamma Zaki dake upstairs.Dawowar su Fauzah daga school yasa Mom ta umarce ta taje su raka ta ta gaida sauran mutanen gidan. Sai dai suka je kowanne sashi sai dai gaisuwar mutunci basu samu daga wurin Pretty ba, daga ƙarshe sashen granny suka wuce. A lokacin granny na gaban Khairy wacce ta farka, abinci take bata sai gocewa take ita kuma granny sai famar sannu take aika mata. Isowarsu ko sallama babu, ita kanta granny Bata san da shigowarsu ba har sai da Fauzah tace Granny Khairyn ta tashi?” Juyowa granny tayi yayin da idonta ya kai kan Pretty da ta hakimce tana wani hura hanci. A faɗace granny ta dubi Pretty tace “Ke Kuma fa Malama? Daga ina?” Fauzah ce ta rufe bakinta da hannu cikin ranta tace “Shikenan granny ta ɓata” a zahiri kuma tace “Granny Aunty Nabila CE fa matar Hamma Zaki” Baki granny ta kama tace “Ah ai dole, ashe dai kece, zakiyi fiye da haka, to rasa kunya tashi ki bani waje tunda ba'a koya miki ɗaa a gidanku ba” Daga haka ta juya tana maida dubanta ga Khairy tana ƙara jera mata sannu. Sai da ta saisaita kanta kafin tace “Yi haƙuri Hajiya naga kina bawa yarinya abinci ne shiyasa, ina wuni mun same ku lafiya?” Ɗan sanyi granny taji ta juyo babu yabo babu fallasa tace “Shikenan lafiya ƙalau” sannan ta maida dubanta ga Fauzah “Ke fauziyya raka ta ina kula da yarinyar nan, sa dawo ita da mijin nata ai”. Pretty Kam danne fushinta tayi ta wuce ta koma part ɗin granny tana tunanin yaya zamanta zai kasance a wannan gidan? Dole ne tayiwa tufkar hanci don ba zata juri iskancin wannan ahalin nasu ba. Tunawa da wannan yarinyar da tsohuwar ke wani tarairaya kamar jaririya tayi “Tsaki taja tana shigewa cikin Bedroom ɗin da aka ajiyeta. “Wow!” ta furta, “Kai komai nasa daban ne, ina sonka Captain, ina sonka sosai Captain!” Haka tayi ta bin frames ɗin dake ɗakin da kallo sai yaba irin kyan da mijinnata yayi, “Tabbas nayi sa'ar samun Captain matsayin mijina, tabbas zan tsaya da anyi sabon aikin nan na kula don cikin cousins ɗin nan nasa masu kama da aljanu zai iya ƙyasa wa”, fuska ta ɓata tana wucewa Toilet ɗin shi. Bayan ta fito main parlourn ta dawo, da yake babu kowa duk sai taji zaman ya ishe ta saboda haka ta fara chat abunta. Tun fitar Pretty granny ke sauƙe bala'i kamar tana gabanta.“Ho ni Shatu, wannan wace irin mata ce?, Yo ai nayi mamaki ma, in Banda iya shege tazo ɗaki na kuma tana buɗe min hanci kamar wando,mtsss marar tarbiyya ko ina ya shiga sai ya nuna. Ai dole na nemawa maza mata don baya zama da wannan mai zubin shaiɗanun” Kamar daga sama taji Khairy na faɗin “Granny ruwa zan sha” “Yi haƙuri ɗiyar arziƙi wannan shashar duk ta ɓata min rai, karɓi ki sha abunki” _To ga Pretty a Adamawan Yola fa, Mami Kuma tace za'a sabunta aiki, ga kuma ƙudurin granny ma, uwa uba ya kuke tunanin tashin Khairy?, Kasance da alƙalamina don jin yadda zata kaya._ _Comment and share please_ [8/24, 9:35 AM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IWQW3ytbVc611XLon2sn66 🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA “““71&72””” Kwana biyu suka shafe a gidan, Pretty dai damuwa tayi mata yawa sosai, gabaɗaya bata samun kan mijinnata, saboda haka yasa ta fara tunanin aborting cikin don babu yadda za'a yi ma ta fara cewa cikin nasa ne saboda kwatakwata ma sau nawa ne suka tara?. Dole ta samawa kanta mafita don ba zatai sakacin rasa kyakkyawan mijinta ba. Khairy ma dai har yanzu babu wani kyakkyawan cigaba da za'a yi magana sai dai takan bi duk wanda yazo dubata ne da ido, babu wanda aka bari a baya wurin bata kulawa. Yau Litinin, a kuma safiyar nan ne Pretty ta shirya zuwa asibiti don aborting cikin da wanda ake tunanin nasane bai sani ba. Sassafe ta tashi ko jira ya tashe ta bata yi ba ta nufi toilet. Wanka tayi ta shirya cikin wasu English wears sannan ta feshe jikinta da turare tana jiran zuwansa don tashinta kamar kullum. Around 5:58am ya shigo ɗakin da niyyar tashinta, ganinta zaune yasa yayi yunƙurin juyawa sai dai da sauri ta isa gare shi, cikin wata yaudararriyar murya tace “Good morning sweetheart” Bata yi zaton zai amsa mata ba yasa ta buɗe baki don sanar da shi zata hospital sai taji yace “Morning” hakan ma ya faɗa ne cike da mugun jin haushinta. “Sweetheart dama ina son zuwa hospital ne bana jin daɗi” Sai da ya kusa fita ya juyo yace “I'll call the family doctor, zai zo ya duba ki”. Cike da jin haushinsa tace “Wallahi sai naje, sai dai ka kashe ni, shegen baƙin rai, mami zata yi mana maganinka ne” Ko da suna breakfast da yake tare da su Mom ne, da wuri ya miƙe saboda kallon da take aika masa. Fitowarsa cikin uniform ɗin da suka matuƙar dace da shi yasa Pretty jin daɗi. Sai da ya fita bayan Daddy ma ya miƙe, Fauzah ma ta fita ɗauko school bag nata ta kalli Mom cikin ladabin ƙarya tace “Mom, dama ina son zuwa shopping ne don siyo abunda bani da shi a nan” Kawar da mamakinta Mom tayi tace “Kin sanar da shi mijin naki?” “Eh ah dama na faɗa masa sai yace wai driver zai kaini” Mom tace “Shikenan, zuwa 10:00am sai ya miƙa ki” Bata iya ɓoye farin cikinta ba har godiya tayiwa Mom wadda ya matuƙar ɗaure kanta. Alhamdulillah, yau tun safiya Khairy ta tashi kuma Alhamdulillah da warginta ta tashi. Murna wurin granny kamar tayi rawa. Darun da ta tasa wai zata je school yasa granny yin fushi, bata so hakan ba saboda haka tace ta haƙura. Ko da Pretty taga motar da za'a kaita sai da ta saki baki, cikin ranta tace “Bazanyi sakaci na bar wannan daular ba, dole ka dawo nawa Captain” umarni ta bawa drivern ya kaita wani private hospital Mai kyau. Bayan sun isa ta shiga, card ta yanka daga nan ta zauna a reception tana jiran layi yazo kanta. Ba'a jima ba kuwa aka kira sunanta “Nabila Ali Naira” da sauri ta shiga don ganin likitan. Bayani tayi masa a kan abinda take so, da farko cewa yayi it's illegal Kuma basu yi a nan, daga baya ya amince tare da tambayar ta cikin wata nawa ne?, “3months” tace masa, Magungunan yayi prescribing daga nan ta fita pharmacy ta siya. Tana kammalawa tace ya kaita shopping mall. Pads ta kwasa sai wasu abubuwan saboda rufe baki da cewa shopping taje. Can gida Hamma Zaki ya kira family Dr nasu in person of Dr. Faruq abokinshi. Ko da yazo suka gaisa da Mom ya sanar da ita yazo duba matar Captain ne tayi mamaki. Bata iya ɓoyewa ba tace “Bata jin daɗi ne?” “Eh Mom haka ya faɗa min yace Please I should come and see her” Haɓa ta riƙe tace “Ai kuwa ta fita shopping ma, ikon Allah” “Kar ki damu Mom, inaga taji sauƙi ne” Daga haka ya wuce abunsa, ko da Hamma Zaki ya tambaye shi yaje ce masa yayi Madam ta ɗan fita shopping amma zai koma in ta dawo. Cikin sanɗa take taka steps ɗin yayin da takalmanta ke riƙe a hannunta. Tana isa last step kuwa tayi wuff ta shige ɗakinta ta zauna tana mayar da numfashi. Ba tare da bata lokaci ba tasha drugs ɗin kamar yadda Dr ya faɗa mata sannan ta haɗa da pain relief. Few minutes ta fara jin mild ciwon ciki, a hankali kuma ya fara tsananta. Tun tana jurewa har ta fara fita daga hayyacin ta. Daga nan bata ƙara sanin yadda take ba sai wuraren ƙarfe 5:00 na yamma. Ganinta a ɗakin asibiti yasa ta fara maimaita innalillahi wa inna ilayhi rajiuun cikin ranta. Ganin mom ce yasa ta ɗan ji sanyi a ranta. “Kin farka, sannu tashi maza kici abinci” Mom da kanta tayi feeding ɗinta, bayan ta gwma Dr ya shigo ya ƙara duba ta, daga nan ya buƙaci ganin mijinta, an ci Sa'a kuwa lokacin Hamma zaki ya shigo room ɗin. Bayan Dr yabi yadda yayi masa bayani kan cewa “Eh Yallaɓai matarka tasha maganin zubar da ciki ne and munyi ƙoƙarin ceto cikin sai dai ya riga ya zube. Yanzu tana buƙatar kulawa sosai, za'a yi discharging ɗinta sai aci gaba da kulawa da ita a gida” Ba zaka iya banbance irin yanayin da yake ciki ba, Bayan anyi discharging nasu suka koma gida kai tsaye. Bai ce da kowa komai ba ya fice daga motar bayan daidaita parking da yayi. Yana shiga Bedroom ɗinsa ya zube bisa faffaɗan gadonsa, shi kaɗai yasan azabar ciwon da kansa yake yi. Bawan Allah jiniyoyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu ga wani ɓacin rai da yake ji kamar yayi hauka. How comes ace matarsa nada ciki and unknowingly to him har tayi aborting cikin?, Nazari ya fara tare da lissafa zaman su, 8-9months kenan amma yana iya tuna last tarawar da suka yi about 6-7months back. To wane irin ciki ne wannan da drugs ya zubar da shi, tabbas baa daɗe da samun wannan ciki ba kenan, then how?. Da ƙarfi ya furta “Noooooo!, That's impossible” barazanar da zuciyarsa ke masa yasa ya runtse idonsa yana maimaita Innalillahi wa inna ilayhi rajiuun. Khairy ce zaune a parlourn tana shan yankakken fruits da granny tasa a kawo mata. Shigowar sisters ɗin ta yasa ya miƙe da gudu tana hugging ɗin su. “Khairy, sannu ya jikin?” Suka haɗa baki suna tambayarta. “Da sauƙi gobe ma zanje makaranta saboda na warke. Bana son a wuce ni” Fauzah tace “Shikenan Allah ya ƙara miki sauƙi” Ayrah ta dubi Khairy tace “Khairy Kinga Hamma Zaki da muke faɗa miki kuwa?” Yamutsa fuska tayi tace “A'ah tukunna dai, kuka ce baya zuwa ina?” Yesmeen tace “Ya fa zo, yanzu kam ya dawo nan da zama tare da muguwar matar tasa” “Muguwa kuma Yesmeen?” Khairy ta tambaya. “ke dai ki bari, ” nan suka kwashe labarin yada aka yi bikin suka faɗa mata fuskarsu ɗauke da damuwa. Cikin halin ko in kula Khairy tace “Amma dai zanso naga matar nan! Ni nan zanyi maganinta, kinsan nifa bani da mutunci?” Dariya suka yi gabaɗayansu tace “Bari na baku labarin ni ɗin wacece” Nan ta fara basu labarin rayuwarta ta ƙauye tare da Ai ƙawarta amma bata faɗa musu batun auren Arɗo da tayi ba. Sun ci dariya sosai kamar zasu yi kuka har sai da granny tazo tayi musu magana. ★★★★★★ *A GURGUJE* Haka rayuwar Khairy ta cigaba da gudana cikin wannan ahali wanda suka zame mata komai na rayuwa. Kulawa da soyayya tana samu daga wurin kowa ina ka cire Boss ɗin gidan da matarsa. Wani abun mamaki da ya faru shine Khairy taci gaba da zuwa makaranta saboda Sheikh Imam ya samu ƙiran gaggawa kafin suje ƙauye, saboda haka ta bada himma kan karatunta, a term ɗinta na farko tayi ƙoƙari don hukumar makarantarsu da kanta tayi promoting ɗin ta zuwa JSS 3 instead of jss two. Khairy ta ƙara kyau da kuma shiga ran mutane cikin sauƙi, tayi sabbin ƙawaye a school kuma babu laifi yanzu turanci kam ba'a magana. Tana kwatantawa don kuwa ko magana zata yi zaka ji ta jefa turanci a ciki. Ɓangaren karatun Alkur'ani ne dai babu cigaba sosai, amma karatun sallah kam ta koya kuma tana ƙoƙarin kiyaye sallah. Wani sauyin kuma shine na halittar jikinta, Da yake tana cin mai kyau tasha mai kyau in ka ganta sai kace ta kai shekaru goma sha takwas amma shekarunsu 15 ne gabaɗaya. A wannan lokacin ne kuma aka saka bikin Adda Salma da Adda Najmah. Adda Salma zata auri Dr Faruq ita kuma Adda Najma wani Captain ne abokin Hamma Zaki. Shirye-shirye ake yi babu kama hannun yaro. Kowa murna yake yi. Su Khairy sai shiri ake yi. Yau Litinin suka je su kai ankon su ɗinki. A _Gorgeous tailoring service_ suka miƙa. Tunda suka shiga tailors ɗin dake wajen suka fara binsu da ido suna faɗin Masha Allah. Khalifa shine Wanda yafi kowa iya ɗinki cikin wajen, so da suka isa Yesmeen ta tambaya “waye yafi iya ɗinki cikinku?” Khalifa dake famar aikinsa ba tare da ya kalle su ba aka nuna. Cike da takunsu irin na yara masu tasowa suka ƙarasa. Khairy ce ta fara isa tana mai sallama cikin sassanyar muryarta. Da sauri Khalifa ya ɗago yana kai dubansa gare su, cikin ransa yana faɗin “Tabarakallahu ahsanul kaliƙin”. Ɗauke da murmushi ya amsa Musa yana ajiye ɗinkin da yake yi. “Ina yini” suka faɗa a tare. Washe baki Khalifa yayi yace “lafiya lou” Khairy tace “Don Allah kaine Khalifa?” “Eh” ya faɗa yana murmushi. Yesmeen tace “Dama ɗinki muka kawo amma muna buƙatar shi ne da wuri, Allah yasa zamu samu” “Ah babu komai zaku samu, kala nawa ne?” “kala Uku uku ne, ya kama 12 kenan” Ayrah ta bashi amsa. Zaro ido yayi yace “12?” “Eh ba zamu samu bane?” Khairy ta jefa masa tambaya. Murmushi yayi yace “A'a zaku samu, mu gani” Fitowa da kayan Yesmeen wacce ke riƙe da su tayi “Gasu nan, ka faɗa mana kuɗin, sai ka bamu account numbern ka da mun koma a tura maka” Murmushi yayi yace “Ku uku, da ke da ke” yana pointing Yesmeen, Ayrah da Fauzah “kuɗin naku 20K each, ita kuma wannan” ya nuna Khairy “Ba sai an biya ba”. Ƙwalalo ido suka yi suna faɗin “Me?” “Babu komai fa, dama haka nake aiki na, idan na mutane da yawa ne ina yiwa customers ɗina ragin na mutum ɗaya saboda su ƙara zuwa nan gaba” Murmushi suka yi suna mishi godiya, sannan suka amshi account numbern shi suka wuce. Tun a mota suke ta famar zolaya Khairy wai tayi goshi. Ayrah tace “Amma fa babu laifi yana da kyau fa Khairy, mun samu wurin kai ɗinki yanzu kam” harara Khairy ta Banka mata caraf Yesmeen tace “Daina harararta mana Khairy ai gaskiya ne, Ni dai Allah yasa kar yayi mana rashin mutunci yayi naki yafi namu kyau” tafawa suka yi ita da Fauzah. Fauzah tace “Ai kuwa yayi haka ba zamu bashi ita ba” Haka suka yi ta shirmen su har suka dawo. _Comment and share Please_ [8/24, 9:35 AM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IWQW3ytbVc611XLon2sn66 🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA “““73&74””” A parlourn Granny suka yada zango sai mita suke yi. Granny na jinsu suna z ancen amma bata tanka musu ba. @@@@@@@@@@@@@@@@@@@ Ina Hamma zaki ne da Pretty?, Sati guda suka yi Daddy ya basu umarnin su koma gidanshi su bar family house ɗin. Pretty tayi murna sosai ko ba komai zata samu damar yin yadda take so don yanzu yana ɗan sake mata kuma yana ƙoƙarin sauƙe mata haƙƙinta da ya rataya a wuyansa. ★★★★★★ Mom da kanta ta tura kuɗin ɗinkinnasu tana murmurshi saboda yadda suke ta zolayar Khairy. Kamar yadda yayi musu alƙawari kuwa ranar driver ya kaisu shagon su Khalifa. Tunda suka shiga yake ta kallon su, but kallon duk na Khairy ne. Bayan sun gaisa ya basu ɗinkin Ayrah har da cewa a buɗe a gani idan yayi na Khairy yafi kyau sai dai su ma ya sake yi musu. Ai kuwa su uku nasu yayi shige sai santi suke yi. Tunda suka ga na Khairy suka tada mishi rigima wai dan me zai banbanta su?. Shi dai Khalifa yaga ta kanshi ita kuwa Uwar gayya tayi musu banza kamar bata san suna yi ba. Ganin zasu ɓata musu lokaci gashi sai sunje saloon da sauran abubuwa yasa Khairy haɗe rai tace “Ku zo mu tafi Please” Da ƙyar suka fito suna faɗin “Don naki yafi kyau shine kike wani kafsewa to wollah sai munyi magana”. Murmushi tayi musu daga nan suka wuce. Biki yayi biki inji Sarkin waƙa, tabbas duk wanda yaga bikin nan yasan anyi biki. Masha Allah an Kai kowacce gidanta wanda ya gaji da haɗuwa, ƴan rakiya suka dawo tare da barin kowacce da halinta. Ranar Sunday Sheikh Imam ya ƙira Daddy Kan su shirya Monday suje garin su wannan yarinya don ɗazu ya dawo. Daddy bai yi ƙasa a guiwa ba ya sanar da granny. Murna wurin Khairy kamar ba gobe musamman da aka ce tare da su Ayrah za'a je. Ta kasa zama sai haɗa wannan take da wannan duk saboda za'a ga iya. Washegari da sassafe suka shirya, motoci biyu ne, ɗaya yaran ne da driver sai kuma ɗayar Daddy ke driving sai granny da kuma Sheikh Imam dake gidan gaba. Nan motoci suka lila sai Bauchin Yakubu. Wass-wasa tafiya ake yi amma taƙi ƙarewa, duk tunaninsu ba wani nisa daga nan zuwa can saboda sun saba flight suke be koyaushe. Isarsu Bauchi suka yada zango a wani restaurant, bayan sun ci abinci suka siya tsaraba a wani wuri Mafi kusa daga nan suka nausa bisa titi. Tafiyar awanni uku suka yi suka isa Azare, basu ƙara 1hour ba suka iso Shira, hanyar kam babu daɗi saboda ramukan gashi duk jikinsu yaji. Ai tunda suka miƙi hanyar Gallara Khairy fa hankali ya tashi, sai uban zuba take musu tana basu labarin tana zuwa wurin nan ita da ƙawarta A'i. Hango gidajen zana da kuma shanu da suka gani suna kiwo yasa suka fahimci an iso, saboda haka suka yi parking motarsu a dai-dai bakin kasuwa. Mutane sai kallonsu suke yi suna mamaki, yara kuwa sai ihu suke suna faɗin “Yeye yaye wallahi wannan sunanta mota, in kaje birni zaka gansu, ahayye mota a Gallara”. Su dai murmushi kawai suke yi yayinda Khairy ke musu jagora sai dai duk wajen wanda suka wuce cikin ƴan kasuwar sai tayi musu magana yayinda basa gane ta har sai ta bar wurin. Ai kafin isarsu gidan iya tuni zance ya isa mata cewa Ƴar Iya tazo wallahi ita ce ta zama ƴar birni. Dai-dai ƙofar gidan Iya taja birki yayinda take tunawa da asalinta, a zahiri kuma kallonsu Sheikh Imam take yi. Granny tace “Ummul-khairy nan ne?” “Eh granny nan ne” Granny tace “Wallahi har na tuna lokacin da muke kiwo, mu shiga yaran nan”. Da sallama a bakinsu suka shiga, Lale maraba, sannunku da zuwa, baƙi daga birni”. Ta ƙarasa tana shimfiɗa musu sabuwar bujukurar tabarma. “Maraba ku zauna” abun mamaki ko kallon Khairy bata yi ba. Da gudu Khairy taje ta rungume Iyar tana faɗin “Haba Iya ta kina gani na shine ko ki ɗan rungume ni?” Sai a lokacin Iya ta gane cewa shalelenta ce ai tuni ta fara sharar ƙwalla tana faɗin “Shalelen Iya kece?” lokaci ɗaya kuma ta sake ta tana ja da baya tare da ƙare mata kallo. Kamar wadda aka tsikara ta ƙara rungume Khairyn tana sakin kuka. “Yau Allah yayi Shalele na ta waiwaye ni, Allah na gode maka ni Shatu”. Tunawa tayi da tare dasu granny suke ta saki Iyan tace “Iya ga baƙi nan baku ko gaisa ba” “Ai, wallahi duk na Shafa'a tunda na ganki, kuyi haƙuri, sannunku da zuwa maraba lale” Granny tace “Yauwa sannu” “Ina wuni ina gajiya, ya hanya kuma” “Alhamdulillahi” inji granny “Tare muke da baƙi muma” “Kuma kuka barsu a waje, ke Shalelen Iya shigo da su mana” Bayan sun shigo ne aka sake buɗe babin gaisuwa. Nan Khairy ta sanar da Iya waɗannan sune Sabbin iyayenta, ” abun har abun dariya sai da aka ƙara gaisawa sai godiya iya ke zuba musu. Gyaran murya Sheikh Imam yayi yace “To dama dai akwai abunda ya kawo mu, amma kafin nan idan mai gidan yana kusa to da shi sai muyi muku bayani” “Ah ai Mallam kam baya nan, sai dai ke Shalele kuje ku ƙira shi mana” Tare da su Ayrah suka fita sai zuba take musu tana nuna musu wurare tare da tuna memories ɗin ta a wurin. Dariya su dai suke yi tare da tabbatar da labarin da ta basu a baya. Duk inda suka wuce kallonsu ake manya da yara kowa sai gaida Ƴar Iya ake ana mata maraba da zuwa. Mutauniyar kuwa sai wani shan ƙamshi take ita ƴar birni. Bayan sun dawo daga ƙiran Baffi ne kuma suka tarar da Damammiyar fura da nono ƙwarya-ƙwarya wanda suma a nan suka baje suna sha ana ta zance kamar an daɗe da sanin juna. Ita dai Khairy mamaki take yada suke shan furar hankalinsu kwance ba tare da nuna ƙyamarsu ba. Nan ƙima da darajarsu ta ƙaru a idonta. Bayan Baffi yazo ne aka sake gaisawa, nan yake ta sauƙe musu damin godiya da irin sauyin da jikartasa ta samu. Daga gaishe-gaishe Daddy yace '“Khairy ki ja ƴan uwanki kuje ku yawata gari ko?” Ai tunkan ya gama tace “To Daddy sai anjima, kai ku tashi muje cikin gari”. Nan suka nausa cikin Gallara sai kewayawa suke. Dai-dai wajen Bala mai kifi ta tsaya tace “Ku zo mu gaisa da Bala ” Suna ƙarasawa suka yi sallama, bala sai kallonsu yake yana ƙarawa ganin zuƙa-zuƙan ƴan mata kamar daga aljanna ya washe baki. Gaisawa suka yi yayinda hakima ke zaune akan benci. Cike da yatsina tace “Bala baka gane Ni bane?” “A'ah Hajiya ku da ba ƴan gari ba kuma taya zan sanku?” Dariya ta sheƙe da ita su kuma suka zuba mata ido don iya zamansu da Khairy basu taɓa ganin tayi irin wannan dariya ba. Tsagaitawa tayi tace “Bala ka manta Ni kake nufi, idan na kwashe kifin naka zaka gane Ƴar Iya ce kenan” ta ƙarasa tana kai dubanta ga kifin dake tashi da ƙamshi. Ƙwalalo ido Bala yayi yace “Ai ban ganeki bane Ƴar Iya, ina ni ina mantawa dake?, Yaushe a garin” Murmushi tayi tace “Bamu daɗe da isowa ba, waɗannan ƴan uwa na ne” “To sannu da gajiyar hanya, bari a saka muku kifin” Ayra tace “A'ah ka bar abunka in mun koma zamu fito da kuɗi sai mu siya” Hararar ta Khairy tayi tace “Kaga Bala zuba mana” jiki na rawa kuwa ya zuba musu ya miƙa musu ledar. Khairy ce ta amsa daganan suka yi masa sallama suka yi gaba. Ganin gidan Halima yasa tace “kuzo mu shiga gidan ƙawa ta Halima mu gaisa sai mu koma gida ko?” Halima tayi mamaki ganin ƴan gayu a gidanta don ita bata ma gane Ƴar Iya ba sai da tace mata “Ƴar Iyace” salallami Halima ta fara tana faɗin “Ikon Allah, Ƴar Iya ke kika zama haka” Murmushi tayi mata tace “Ƙwarai kuwa Halima, nice dai wannan rigimammiyar” Dariya suka kwashe da ita Halima tace “Gaskiya kin canza sosai don ban gane ku ba, wallahi kamar wata ɗiyar Indiyawa kin ganki kuwa? Sauran kuma su waye halan” “Waɗannan sune ƴan uwa na na can birni, Ayrah, yesmeen sai kuma Fauzah” Halima tace “Sannunku da zuwa, bari na dafa muku taliya nasan dai da kina son ƴar murji” “Ai kuwa har yanzu ina so, ammah zamu koma gida yanzu, ma dawo wataƙila kafin mu tafi” Halima tace “Haba ƴar iya, to zan aiko muku can gidan Iyar” Daga nan suka koma gida. Can gida kuma bayan fitar su ne Daddy yayi wa Baffi bayanin dalilin zuwan su, ammah kafin nan ance waƙa a bakin mai ita tafi daɗi, saboda haka Sheikh Imam yayi masa bayanin komai da komai. Baffi har da hawayensa yace “Kai amma Allah ya saka muku da alkhairi, wallahi yau naji daɗin da rabona da jinsa tun haihuwar shi uban yarinyar! Mun gode sosai, yanzu dai bari naje na sanar da Arɗo zuwanku sai a buɗe masauƙin ku tunda sai zuwa gobe ko jibi zaku wuce.” Bayan Baffi ya sanar da Arɗo, tuni aka buɗe musu gidan bakin wanda yake ɗauke da ɗakuna biyar ginin block. Sai da aka gyara tsaf tukun suka wuce Fada, sai wajen takwas na dare mazajen suka wuce. Abinci kuwa daga gidan Arɗo aka kawo musu, kuma sunci suna ta yaba karamci iri. Na mutanen ƙauyen. Washegari da sassafe aka aiko da abinci daga gidan Arɗo, Shinkafa ce da miya sai kuma gasassun kaji da kuma Damammiyar fura da nono. Bayan sun karya suka yi wanka daga nan akace su Ayrah su tafi can gidan Iya su kaiwa Khairy abinci, daga nan kuma su sanar da Baffi cewa suna jiransu a gidan. Yaron da suka gani a waje suka tambaya ya raka su gidansu Ƴar Iya yace “Tab, ku kuwa me zai kai ku gidan nan bayan Ƴar Iya ta dawo, to Aradu nidai duk abunda ta muku kada kuce Sa'idu ne ya raka ku” Dariya suka yi kamar ba gobe, suka ce masa “Eh ya raka su mana babu damuwa ai ba zasu ce shi ya raka su ba. Nan Sa'idu ya raka su yana ta basu labarin ƴar Iya har da labarin ranar da ta ganshi da kaji zai je ya sayar ta ƙwace ta yanka da ta yanka kuma sai ta bashi wai yaje gida a dafa, ta san duk su ma na gidan kwanɗayin naman suke yi. Yace “Ai kuwa ranar naci duka duk da ba laifi na bane, kawai da dare sai ga ƴar Iya wai a bata rabonta, daga nan aka ce babu nan masifa ta tashi wai ya za'a yi tayi musu sanadin dadi kuma suci su kaɗai?, Sai da Baffan mu ya bata kaza ɗaya ta tafi” Me su Fauzah zasu yi in banda dariya. Da suka iso ne suka ce masa ai tare suka zo da Ƴar Iya, daga nan suka shiga. Bayan sun gaisa da iya suka miƙa mata abincin don sun san ba lallai Khairy ta tashi ba. Fauzah tace “Iya ina ne ɗakinta, don na san ba lallai ta tashi ba” “Ina kuwa zan tashi tunda Fauzah bata zo ta tashe ni ba” ta faɗa tana cillawa Fauzah harara. Dariya suka kwashe da ita suna faɗin “Kinga abinci muka kawo miki ba komai ba, in Baki ci sai mu koma da shi” Da sauri tace “Yi haƙuri Ƴar uwata mai hanjin lagwani, bani abincin” Iya ce ta miƙa mata tana murmurshi, sun matuƙar burge ta ba kaɗan ba. Ayrah ce tace “Au Iya, wai a sanar da Baffi su haɗu dasu Daddy tare da Ƴar Iya” Harara ta banka mata tace “In zaki ƙira Ni da Khairy na to, kar ki ƙara ce min Ƴar Iya” Dariya suka yi ita dai iya cewa tayi “Ke Shalele ai ba'a manta da, maza kici ku wuce Kinga baffin ki ya riga da ya shirya tun ɗazu” Da “To ta amsa tana cin abincin, tas ta cinye daga nan kuma tayiwa Baffi magana cewa ta shirya. _Naga alama Fans so kuke na rage post, ko dai labarin ya daina burge ku ne😔😣, gaskiya da sakel, in bazaku ke yin comments ba zan ajiye alƙalami na._ _Na gode_ _Ku biyo ni don jin ya za'a kaya a gidan Inna Zaliha tare da Sheikh Imam_ _Comment and share Please_ _Diamond Bhatool ce_ [8/25, 10:15 AM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: https://whatsapp.com/channel/0029VamEf2Y4dTnFmjl4Dv1Z 🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA “““75&76””” A can suka haɗu tare da su Daddy, bayan ta gaidasu ne suka nufi can gidan mahaifin khairy wato Mallam Umaru Gallara. Suna tafe suna hira yayin da Khairy tayi tsam bata cewa uffan har suka iso. Baffi yace “Shalelen Iya ki shiga ki mana iso ko” “To” tace tana gyaɗa kai. Daga nan ta kutsa kanta cikin gidan da akewa laƙabi da na mahaifinta bayan ko kwana ɗaya bata taɓa ɓatawa cikin gidanba. Da sallama a bakinta ta shiga yayinda ta tarar da Inna Zaliha tana wanke kwanukan da suka ci tuwo. Inna Zaliha da taga kyakkyawar yarinya ƴar birni yasa ta ajiye wanke-wanken tana washe baki “Lale maraba da zuwa ƴan mata, bari a shimfiɗa miki tabarma” bata dakatar da ita ba sai ma makewa da tayi tana jiranta. Inna Zaliha ta fito da sabuwar tambarmarta tana shimfiɗawa “Sannu da zuwa sannu sannu” Sai da ta zauna kafin ta dubi Inna Zalihar a wulaƙance tace, da baƙi muke a waje idan mai gidan yana nan ki masa magana” Washe baki tayi tace “Babu komai bari nayi masa magana” Can ta fito daga ɗakin nata tana murmurshi tace “Gaahi nan zuwa ki sanar musu” Miƙewa tayi ta sanar da su Baffi, don a cikin shirin ya Sheikh babu barin inna Zaliha tasan me yake faruwa shi yasa suka jira a waje. Ta juya zata koma suka ci karo da Baba yana fitowa, kanta ta kawar saboda irin kallon da yake mata tace “Ina wuni” “Lafiya ƙalau” Daga haka ya shige waje ita kuma tayi ciki. Ƙara ajiye wanke-wanken nata tayi tana dawowa kan tabarmar sai surutu take zuba mata, ita dai Khairy ji take kamar ta kamata da duka don tun da ta tsani wannan matar. A can waje kuma bayan sun gaisa ne cike da girmamawa Baffi yace “Waɗannan baƙi ne daga birni, kuma Arɗo ne yace a rako su saboda akwai wani abu da suka harbo daga can birni kuma nan ya faɗo a dai-dai bayin gidan, saboda haka sun zo tonewa ne su tafi” “To Baba ai ba komai sai su iso ko?, Ku shigo mana, muje bari na ɗauko magirbi”. Sallama suka yi suna kutsawa gidan yayinda Inna Zaliha ta gansu sai da gabanta ya faɗi amma ta dake tare da bin bayan Baba wajen kayan nomarsa. “Mallam su waye waɗannan ɗin” Bayani yayi muta kamar yadda suka yi mata. Cike da firgici tace “Allah yasa ba abun mutuwa suka Wullo mana ba” cikin ranta kuma tana tuna ajiyarta da tayi a wurin, tsoronta ɗaya kar a tono wannan abun don in bata manta sharaɗin boka ba cewa yayi idan har aikin nan ya ware to itama zata yi mutuwar wulaƙanci ne kamar yadda Barira ta mutu ammah ita sai ta tozarta. Tsoro da firgici ne lokaci ɗaya suka yanyameta, daga ƙarshe dai ganin zaman nan ba zai fisshe ta ba yasa ta fito tare da ƙarasa wanke-wankenta. Tana gamawa wata dattijuwar mata ta shigo wacce da gani kasan uwar manya ce. Granny kenan. Bayan sun gaisa ta koma gefen baƙuwar da bata san wacece ba, ita dai nata ido ne don yau kam ita kaɗai tasan me take ji ga kuma zuciyarta dake bugu kamar wanda ake harzuƙa ta. Ɓangaren su Sheikh Imam, Baba ƙin barinsu yayi suyi tono a cewarsa ba zasu iya ba ga kuma baƙi ne da mahaifinsa yayi musu iso. Nan ya fara tono yana tono sai dai basu ga komai ba. Har wajajen sha ɗaya basu tarar da komai ba. A lokacin ne kuma ya iso kan wani makeken dutse baƙi ƙirin, haka ƙasar wurin itama kamar gawayi. Basu tsinke da mamaki ba sai da ya kafa magirbinsa kan wannan dutse, nan wurin ya fara jijjiga ga kuma wani gurnani da yake fita. Ba kowa bane sai Khairy da ta baje akan tabarmar da take zaune ita da Granny. Kuzo kuga idon Inna Zaliha Tuni ya Raina fata nan jikinta ya fara ɓari da jin gurnanin da ke fita daga bakin baƙuwar tata. Da sauri Sheikh Imam ya juyo daga bakin bayin da yake dama shi bai shiga ba iya Baffi ne, Daddy sai kuma Baba. Yana zuwa yayiwa granny Alana da ta fito da jakar da suka bar mata ta taho da ita. Wata bottle ɗin ya buɗe yana kallon da ruwan tare da ɓare zamzam yana zubawa a ciki. Gaurayawa yayi daga nan ya watsa mata ruwan. Wani mahaukacin ihu ta saka wanda a daidai lokacin ne Baba dake tono ya kammala sare baƙin dutsen nan. Baki buɗe yake kallon abunda ke ciki. Da sauri Baffi ya ƙaraso yana kai dubansa ga ramin, shima Daddy ƙarasowa yayi ganin duk sun kasa magana. Mamaki ne ya kama gabaɗayansu yayin da Baffi yayi bismillah cikin ransa sannan ya sa hannunsa zuwa ga ramin. Da ƙyar da taimakon Daddy suka ciro da baƙin ƙullin da ya kai kaya kala 20. Basu bata lokaci ba suka fito waje tare da nufar wurin da Sheikh Imam yake. Ina innna Zaliha?, A dai-dai lokacin da Baba ya fara sare dutsen bugun zuciyarta ya ƙaru, yayinda numfashinta ke fita da sauri da sauri. Gagara tsayawa tayi akan yarinyar da akewa karatu hakan yasa ta jingina da bangon ɗakin nata tana kallonsu. Fitowar su daga bayin akan idonta ne, ai ganin abinda ke hannunsu, abunda ta ajiyeshi tsawon shekaru goma sha shida ba tare da sanin kowa ba yau an haƙo shi yasa ta miƙe tana nufarsu da gudu. “Yau naga ta kaina ni zalihatu, me nake gani haka, wacce irin rana ce wannan?” ta faɗa tana zubewa ƙasa a gabansu tana kuka. “Kuyiwa Allah da ma'aiki ku bani ajiyata” Da mamaki Baba ke kallonta yayinda furucinta ya matukar bashi mamaki cikin ransa yana nanata “Ajiyarta”. Daddy kuwa amshe ƙullin yayi yana zamewa gefe tare da nufar Sheikh Imam gani matar tana son kawo musu wargi. Ai da hanzari ta miƙe zata bishi Baba ya riƙe ta “Ina zaki je haka ne Zaliha?” Cikin fitar hayyaci tace “Kaima kana gani zai tafi da ajiyata, rabu da ni naje na amso abuna” Bai sake ta ba yaja ta zuwa ɗakinsu sai lallaminta yake don shi gabaɗaya hankalinsa bai kai ga Sheikh Imam da yake ta rera karatu a yarinyar ba. Bayan shafe wasu awanni yana karatunne suka fara magana. Sallama yayi musu don in bai manta ba sun karɓi shahada a wancan karen . A tare suka amsa kamar haɗin baki. Shi dai Sheikh Imam kamar ko yaushe fuskarsa ɗauke take da murmushi. “To ƴan uwa na yau gamu mun ƙara haɗuwa, ina muku fatan alkhairi, Annabi tsira da aminci yace “Almuslimuna ala shuruɗihim, saboda haka yau zamu kammala sadaukarwar da kuka yi alƙawarin zaku yi, gamu ga ƙarshen aikin amma kafinnan bari a ƙirawo mahaifin yaron”. Baffi ne ya leƙa yana ƙwalla ƙiransa, tare da Innna Zaliha suka fito idonta ya raina fata kamar wacce ta shekara ɗari tana jinya jikinta kuwa sai ɓari yake. Sai da suka zauna tukun Sheikh Imam ya umarce Aljanun da suyi bayani kamar yadda suka mishi a kwanakin baya. Baki buɗe suka fara bayani tamkar dai yadda suka yi a wancan lokacin. Murmushi Sheikh Imam yayi yana duban su gabaɗaya sannan yace “To yanzu dai Mallam Umaru kaga abinda ya kawo mu, duk da cewa kaima a yanzu ba dai-dai kake ba muna so muji ta bakinka”. Inna Zaliha kuwa ta ma kasa magana jin asirinta yau ya gama tonuwa, idonta sauƙe a ƙasa hawaye ne kawai ke zubo mata. Kasa magana shima yayi hakan yasa Sheikh Imam yace “Malama Zaliha, muna so muji ta bakinki” Cikin Muryar kuka ta fara magana “Tabbas ban taɓa nadama akan abinda na aikata ba sai yau ko don ina tunanin asiri na ba zai taɓa tonuwa bane” taja hanci sannan taci gaba “Bazance kada a since wannan asiri ba saboda nima na ɗana rayuwar, a yanzu bana fargabar mutuwar saboda nayi nadama akan abinda na aikata, na sa an kashe rai da bata ji ba bata gani ba saboda son zuciya irin nawa da neman cikar buri, na sa an juyar da tunanin yarinyar da bata ji ba bata gani ba, na raba ɗa da iyayensa ba tare da wani ƙwaƙkwaran daliliba” jan hancin ta ƙara yi tace “Na cancanci duk wani hukunci, Mallam a since wannan asiri nima na girbi abinda na shuka”. Ina granny? Granny sarauniyar tausayi kuka kawai take yi, haka Daddy Shima hawaye yake sharewa, Baffi ne ma kawai za'a ce idanunsa ne kaɗai suka sauya launi sai kuma Baba da shima yake sharan ƙwalla. Sheikh Imam yayi gyaran murya sannan yace “To, komai da zai faru da bawa a rubuce yake, Zaliha ki ji tsoron Allah ki tuba tuba Mai kyau duk da cewa mutuwa boka yace zaki yi bazamu yi imani mu yadda ba saboda ba shi ya baki ran ba, naji daɗi da kika gano kuskuren ki kuma kika amsa hannu bibbiyu, ki sani ramin ƙarya ƙurarre ne, kuma hausawa suka ce rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya, kamar haka ne ta faru, kin jima kina morar abinda kika yi yau ɗaya kuma waɗanda kika jima kina zalunta zasu fara more tasu rayuwar. Ubangiji Allah ya shirye mu” “Amin” dukkaninsu suka amsa. Ba tare da ɓata lokaci ba ya fara since ƙullin yana karanta ayoyin karya sihiri. A hankali ya kammala buɗe komai dake cikin ƙullin wanda ba komai bane sai wasu mutunmutumi guda uku, sai kuma gashi, da kuma tsumman atamfa da yadi” _Tabbas addinin musulunci haske ne kuma ni'ima ne, wane addini ne cikin addinai ke da irin wannan ni'ima?, Babu. Alqur'ani da kuke gani ƴan uwa abincin ruhinmu ne, wallahil adhim duk wanda ya riƙe Alqur'ani babu wata musiba da zata same shi sai dai abunda Allah ya riga ya rubuta zai same shi._ _Azkar, wato ambaton Ubangiji shima makami ne na mumini, Allah maɗaukakin sarki ya nuna mana muhimmanci ambatonsa a cikin Alqur'ani a wurare daban daban, haka hadisai ingantattu sun zo akan muhimmancin ambaton Allah_ _Akwai zikirorin safiya da maraice waɗanda suke da matuƙar muhimmanci. Imam Annawawi Allah yayi masa rahama yace “Madallah da masu ambaton Allah musamman zikirorin safiya da maraice, ida mutum bai yi su duka ba to ya daure da safe ya karanta ɗaya haka da yamma”. Saboda haka ƴan uwana, mu riƙe azkar ɗin nan da kyau wallahi zamu ga faidar hakan, babu wani da ya isa ya cutar da mu sai dai abunda Ubangiji ya riga ya rubuta zai same mu_ _Ƴan uwana mata ina ƙira gare mu da muji tsoron Allah kuma mu sani shirka itace mafi muni daga cikin kaba'ir. Idan muka dubi ayoyin da suka zo cikin Alqur'ani zamu tabbatar da hakan, mu tuna lokacin da Luƙmanul Hakeem yake yiwa dansa wasiyya, shirka itace abinda ya fara tsawar masa akai, ayar tana suratul luƙman. Akwai makamantan ayoyi da suka zo, saboda haka mu kiyaye, kada mu bari shaidan yayi galaba akanmu har ya kaimu ga halaka._ _Wasu matan suna cewa shirka sai ka je wajen boka, sai su fake da ai wane malami ne, duk wani malami da zai yi duba, bugun ƙasa shima boka ne, saboda haramun ne hakan, akwai hadisin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama, inda yake cewa “Duk wanda yaje wurin boka ko ɗan duba, to haƙiƙa ya kafurcewa abinda muka sauƙarwa Manzon Allah”. Mata muji tsoron Allah, duk wata buƙata ko buri da kike son cimmawa to ki roƙi Ubangiji, babu abinda yafi ƙarfinsa in kika ga ya Hana ki ko bai biya miki ba to ki saka a ranki ba alkhairi bane abun kamar yadda yazo cikin suratul baƙara, Allah maɗaukakin sarki yace “Zaka ga kana ƙin abu yayinda abun ya kasance alkhairi a gare ka, zaka ga kana ƙaunar abu yayinda abun ya kasance sharri gareka, Allah shine mafi sanin abinda ku baku sani ba”. Don Allah ƴan uwa na mu guji zuwa wurin irin malaman nan ko ince yan duba, in Zaki yi addu'a kiyi da kanki ba sai wani yayi miki ba, babu wani hijabi ko shamaki tsakanin ki da mahaliccinki, so ki roƙe shi duk abinda kike so kina mai ƙaskantar da kai, sai kiga addu'ar ki ta karɓu wurinsa, idan shawara ne ma kiyi istikhara zaki ga kin dace_ _Mu haɗu gobe don jin yadda zata kaya_ _Taku Diamond Bhatool ta gargajiya, ina ƙaunarku fans ɗina_ [8/26, 8:15 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: Follow the DIAMOND BHATOOL'S LIBRARY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VamEf2Y4dTnFmjl4Dv1Z https://chat.whatsapp.com/IWQW3ytbVc611XLon2sn66 🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA “““77&78 ””” Idanuwa ta ƙwalalo kamar zata yi kuka yayinda su Fauzah ke kwasar dariyarsu. “Haba ƙawa ta duk kin sauya kamar ɗiyar Indiyawa taya zan gane ki?, Matso kusa da ni don Allah, yaushe gamo?” Kusa da juna suka zauna nan Khairy tace “Fauzah, Ayrah, Yesmeen, ku haɗu da ƙawata ta yarinta abokiyar ƙiriniyata kuma mai suna na A'i” ta faɗa tana nuna A'i da yatsa fuskarta ɗauke da murmushi. Ta juya kuma ta kama kafaɗar A'i “Ƙawata A'i ki haɗu da ƴan uwana kuma ƙawayena wannan Fauzah,wannan Ayrah wannan kuma Yesmeen”. Nan kowa yaji daɗin haɗuwa da ƴan uwansa don Ai ma ba baya ba wurin sabo, tsiyarsu ta da dai ta bari amma akwai barkwanci ta shega. Nan suka fara hirar yaushe gamo. Ƙiran sallar Ishã yasa Ai faɗin “Gashi ban girka komai ba saboda nauyin jiki, bari ya shigo sai ya nemo muku shayi da bredi don ba iya cin girkinmu zaku yi ba” Harararta Khairy tayi tace “Ba sai kin faɗa mana kina da ciki ba ai mun gani, kin faɗa kin maimaita” “To ke ina ruwanki don ke baki da shi kuwa baki isa hana Ni faɗa ba" nan dai suka yi ta jan magana Khairy team ɗin ta ita kaɗai su suma duk suna bayan A'i. Shigowar Iliya mijin A'i ta sanar da shi game da baƙinta, ai bai manta lokacin bikinsu ba tuni ya fita ya nemo musu bread bisa umarnin uwar gida. Tare da ita suka tasa tsire da bread ɗin a gaba suna ci suna hira har suka kammala. Bayan sun kammala ne Fauzah tace “Ƙawarmu ki taya ƴar uwarmu murna, ta samu lafiya” nan suka kwashe komai suka faɗa mata dom a cewarsu ciwon su ne duka, A'i tayi kuka kam sai tsinewa Inna Zaliha take, daga baya kuma ta dawo lafta mata godiya da albarka tunda yanzu tayi sanadin wayewar ƙawar mu ga kuma wani mahaukacin kyau da kika yi”. Sai da suka yi sallah tukun suka miƙe suka ce sai watarana zasu kara zuwa, nan suka rabu suna sharar ƙwalla. Har sun kama hanyar gida Khairy tace “Zamuje dandali? Don nasan gobe za'a wuce” “Eh muje mu gani” Ba su suka koma gida ba sai wajajen goma na dare. Suna komawa kuwa suka yashe sai bacci. Bayan tafiyarsu granny ta so abar Khairy tayi ko sati ɗaya ne sai dai saboda makaranta yasa tace in anyi hutu zata zo ko sati ne tayi. Suma su Baffi da iya tare da Baba duk basu ji haushi ba, sunji daɗi da zancen ma saboda Khairy ce mutum ta farko da ta fara yin karatun boko. Washegari bayan sun karya dukkansu harda iya suka ɗunguma sai gidan Arɗo, nan suka yi masa sallama ya haɗa su da tsaraba irinta ƙauye. Sunyi matuƙar farin ciki tare da yaba halacci da karamci irin na ƴan ƙauyen. Iya da Baba harda kukan su kafin su rabu, daga nan motar su ta tashi sai Adamawa. Wuraren la'asar suka isa kowa jikinsa yayi tsami, sai da Daddy ya ajiye Sheikh Imam kafin su zarce gida baki ɗayansu. Babu wanda yasan da dawowarsu sai dai horn ɗin motar da suka ji ya tabbatar musu da cewa sune. Tuni kowa ya fito ana musu sannu da hanya. Kafin maghrib an cika dining ɗin granny da abinciccika. A nan aka yi dinner gabaɗaya ranar. Bayan an kammala Daddy yayi addu'a tare da fara musu bayanin abinda ya faru a can, bai ɓoye musu ba don yanzu an riga an zama ɗaya. Bayan ya kammala wasu harda kukansu, kowa yaji kabarin ajikinshi. Kamar wancan lokacin Daddy ya ƙara jan hankalinsu akan rayuwa daga nan kowa ya koma bangarensa. _______________________________________________ Hamma Zaki ya shigo gaida granny Amma bai sameta ba, da ya tambayi mom.ta faɗa masa ai sun tafi garinsu Khairy don kammala aikin da Sheikh Imam ya fara. Haka kawai ya tsinci kansa a damuwa yana ta fatan Allah yasa a dace. Zuwansa uku bai semeta ba, gashi numbers ɗin su duka basa tafiya. Bayan sunyi waya da Mom me ya tambaye ta ko granny ta dawo? Tace masa eh, bai san MEH yasa duk ya damu da yarinyar ba, “Ko dan ta cancanci a tausaya mata ne” ya bawa kashi amsa. Wanka yayi ya shirya cikin Farar jallabiya tas tare da feshe jikinsa da turarensa da har yau bai daina amfani da irinsa ba wato _Imperior majéste._ Ganin irin wankan da yasha yasa Pretty tsayawa tana binsa da kallon mamaki. “Sweetheaft ina zuwa haka?” Ko kallonta bai yi ba ya ɗauko key ɗin motarsa ya fito, bayansa ta biyo tana faɗin “In dai hira kaje da kai da ita duk Allah yana ganin ku ” ta faɗa tana komawa. Shi fa har yau mamakin irin ɗabi'unta yake, ace mijinka zai fita ba zaka yi masa addu'a ba sai ma mita da rashin ɗa'a. Jan motar yayi zuwa gidansu. Bayan sun gaisa da mom ya bi ko ina suka gaisa kamar yadda ya saba. Party ɗin granny shine ƙarshen zuwa. Yana shiga ya tarar da granny zaune bisa lallausan carpet ɗin dake parlourn sai Khairy da kanta ke cinyar grannyn. Sallamar da yayi dama ba ji suka yi ba sai da ya doso cikin ɗakin ƙamshinsa ya karaɗe ƙofofin hancinsu. Zama yayi kan kujera yana faɗin “Granny sallamar ma ba zaki amsa bane?” “I haƙuri maza, wallahi duk na gaji ne, jiki na ma ciwo yake, ina irin maganin zafin nan da ka taɓa bani, da zan samu ma shi nake so”. Haka kawai ta kasa ɗaga ido taga fuskar da ta saba gani jikin photo a zahiri. Kanta ƙasa tace “Ina yini” kamar bazai amsa ba yace “Lafiya, ya jikin ki?” Tayi mamaki sosai jin ya tambaya ta, don a yadda su Fauzah ke bata labarinsa ba ya son wargi ko kaɗan” Murya a sanyaye ta amsa da “Alhamdulillahi, naji sauƙi” Daga haka ta fara ƙoƙarin miƙewa don tafiya ɗakinta, har ga Allah ba zata iya zama wuri ɗaya da shi ba. Zata fara tafiya taji yace “Ina zakije, ni tafiya ma zanyi, Allah ya sauuwaƙe” Kunya ce ta lulluɓeta tace “Ameen na gode” ba tare da ta kalleshi ba yayin da shima hankalinsa yake kan wayarsa. Daga haka ta koma ta kwanta akan cinyar grannyn. Miƙewa yayi yana faɗin “To granny mu tashi lafiya, man zafin zan bayar a shigo miki da shi” Amsa masa tayi da faɗin “To maza, mu tashi lafiya, ka gaishe da ifritiyar matarka” Murmushi yayi yace “Granny dai”. Daga haka ya wuce ba tare da ya amsa mata ba. Sun sha hirar su sosai duk da sun gaji kafin su kwanta, ɓangaren sauran ma daren ranar kowa sun sha hirar da mahaifiyarta, wanda duk a _________________________________________________ *A GURGUJE* Haka rayuwa taci gaba da kasancewa, Khairy ma ta shiga islamiyya kuma karatun nan abun mamaki shiga yake yi har sai da tazo ta wuce su Fauzah, a bangaren boko ma ba a barta a baya ba, don in kaje kana fadan sunanta kowa ya santa ba dan komai ba sai don ƙwazonta da kuma shiga rai da take da shi uwa uba iya mu'amala da mutane, abun mamaki kuma idan mutum ya nuna mata wargi sai ta cire rigar mutumci tayi masa tas tamkar dai *ƳAR IYA* *TWO YEARS LATER (Bayan shekara biyu* Wasu kyawawan Ƴan mata ne da suka gaji da haɗuwa da kyau su huɗu tsaye a bakin gate ɗin Islamiyya, kowaccen su sanye take da hijabi babba brown colour sai kuma wando coffee brown yayinda ba'a iya ganin colour na rigar don yadda hijabin ya sauƙo Duk cikinsu babu baƙa, farare ne tas wanda in kayi musu kallo ɗaya bazaka so dainawa ba sai ka kai wani duban garesu. Ta biyunsu a ɓangaren dama ne tace “Ya Ilahi, wollah yau ɗin nan I'm exhausted sisters, gashi drivern ma yaƙi zuwa da wuri, don Allah ku samar mun wurin zama in ba haka ba anjima zan faɗi muku” Ta farkon tace “Sorry Khairy Ai dole ki gaji, rabonki da runtsawa tun jiya, and all this is bcuz of so called competition ɗin da zaku ce, ga kuma musabaƙar da kika makalawa kanki” ta ukunsu ce tace “Ni wallahi Fauzah na rasa Khairy wace irin mata ce, in tasa abu gaba ko abinci bata ci, Allah dai ya shirya ki” Tare suka ce “Amin” ta ƙarshen ne bata ce uffan ba dai-dai da zuwa driver Yana parking gabansu tace “Oyah! Letz go babes” Ai kuwa nan suka shige motar sai gida, suna parking dukkansu suka wuce part ɗin granny, bayan sunyi wanka kowaccen su ta ɗauko Alqur'ani tare da shimfiɗa sallaya. Baka iya jin muryoyinsu har lokacin sallar maghrib suna karatun. Alwala suka ɗauro tare da tayar da sallah. Har zuwa lokacin babu wanda ya ƙara yiwa ɗan uwansa magana, bayan sun idar da sallah Khairy ta kwaso mordern biology textbook, new school chemistry textbook, new general mathematics da kuma okeke's Physics. Nan ta baje tana karanta su tare da warware matsalolin da dama, ni Bhatool ido kawai na bita da shi don abun ya bani mamaki musamman yadda take ragargaza equations, tana solving mathematics ba tare da amfani da calculator ba. (Allahu akbar). Sauran ƴan matan a ɗaya ɓangaren suna karanta Alqur'ani ne cikin ransu ba tare da mai karatu yana iya jiyo muryoyinsu ba. Ƙiran sallar Ishã ya tayar da su suka gabatar, bayan sunyi sallah kuma suka ɓarke da hira tare da komawa parlourn. Granny dai sai mita take wai sun shige jikin jikarta yanzu bata samun kusanci da ita. Ƙyalƙaylewa da dariya yesmeem tayi tace “Kai granny ba dai kishi ba, na so an haife ni lokacin da kike matashiya da naga salon love ɗin ki” duka grannyn ta kai mata ita kuma tana zamewa, sauran dariya kawai suke yi. Granny tace “Wannan yarinya ba dai iskanci ba, kuyi dai ku gama makarantar nan duk aure za'a yi muku, yara sai shege faɗin lob kamar akansu aka fara” ta ƙarasa tana sakin tsaki. Dining gabaɗayansu suka nufa, bayan sunyi dinner kowa tayiwa granny sallama tare da wucewa ɓangarensu. Washegari weekend ne, da safe suka shirya don yau Mom ta tasa su gaba sai sunje gidan Hamma Zaki coz Basu taɓa zuwa ba tsawon lokacin nan, a cewarsu kar suje Aunty Nabila tayi dambunsu. Cikin Expensive abayas da suka gaji da haɗuwa ƴan matan suka shirya, sunyi kyau kam kamar ka sace ka gudu, ba zaka san da irin kyan da suka yi ba sai kun kai dubanku ga tauraruwarsu wacce kamanninta suka juye tamkar wata ɗiyar larabawa, i doubt not Fulani ba ba baya ba a kyau. Handbag ɗin hannunta ta gyarawa zama tare da gyara veil ɗin da tayi rolling. Cikin muryarta mai daɗin sauraro tace “hey Babes...mu wuce ko,” Murmushi suka yi kamar haɗin baki suka ce “wow! Khairy kin gaji da haɗuwa fa” Hararar wasa ta jefa musu tace “Babes ai kuma kun gama haɗewa, Ni inaga ma zan daina yawo da ku don zaku sa kasuwata ta yi sanyi” ta ƙarasa tana kanne ido ɗaya tana dariya” Yesmeem ce ta kawo mata dukan wasa tana faɗin “Wallahy Khairy ke kike kashe mana kasuwa, kin tuna wannan Khalifa mai ɗinkin?” Duka ta kaiwa Yesmeen ɗin, Fauzah tace “Muje Babes, Kuna ɓata mana lokaci, Allah dai yasa mu dawo lafiya” Kyaɓe baki dukkansu suka yi suna faɗin “Ameen”. _Toh jama'a me kuke tunanin zai faru a gidan Pretty?, Ku dai ku ci gaba da bibiyar alƙalamin Diamond Bhatool, loads of love_ [28/08, 9:07 PM] 💎Diamond_Bhatool💎: 🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA “““79&80 ””” Mota suka shige daga nan driver yaja motar, bakin wani tafkeken gate yayi horn, babu bata lokaci aka bude musa, “Masha Allah” dukansu suka furta, sai da driver ya daidaita parking suka fito. Entrance door din suka nufa suna zazzare idanuwa kamar wasu barayi. Doorbell suka danna amma tsawon wani lokaci babu alamar zaa bude har sai da suka kosa da tsayuwa. Khairy tayi tsaki tace “Nifah babes na gaji wollah, tunda nazo da wayar granny kawai mu kira Hamma Zakin ko bata nan. Amma kafin nan muyi ta danna doorbell in ta gaji da ji hala ta bude ” Duk sunyi na'am da shawarar Khairyn suka fara danna doorbell din ba kakkautawa. Tsawon mintuna bakwai amma babu wani yunkurin budewar, in banda tsaki babu abunda suke saki. A hankali taja gefe tare da shiga contacts na wayar, _Maza_ ta fara dubawa don tunaninta ga hakan ya tsaya, abun mamaki numbernsa wanda special ne ya bayyana. (Bari dai na bawa readers numbern Hamma Zaki in da mai sonsa to.....0707777....). Dialling tayi tare da karawa a kunnenta, a lokacin kuma sauran suma suka iso gareta. Ajiyar zuciya khairu ta sauke jin numbern ya shiga, sai dai yana fara ringing akayi rejecting, bata kai ga kara kira ba kuma kiransa ya shigo wayar. Picking tayi tare da saka wayar a handsfree. Cikin mutyarta mai dadin sauraro tayo sallama, shima amsawa yayi sai dai ya shiga wani yanayi jin wata daddadar mutya wacce take dauke da wani sinadari da bai aan na menene ba. A gefe daya kuma yana tunanin lafiya? Numbern granny kuma wata ta daga don shi har ya manta akwai wata khairy a gidan. Tsawon lokacin da suka shafe babu mai magana a ciki alamun dukkansu sun shiga wani yanayi ne, don ita khairy a nata bangaren zuciyarta ne ke wani irin bugu, Fauzah ce ta tabo ya nan ta dawo hankakinta, cike da inda-inda tace “Ehm eh dama su Fauzah ne, mom tace muzo kuma muna ta jira a bude mana kamar babu kowa a gidan” “Shikenan ku tsaya yanzu zaa bude kunji” daga haka yayi rejecting kiran. Numbern Pretty ya lalubo tana picking ta furta “Hello sweetheart...” katseta yayi yana fadin “Ki wuce ki bude kofa tun dazu kina nufin baki ji karar doorbell ba?” bai jira amsarta ba ya katse kiran yana sakin tsaki. Lokaci daya kuma ya tuna da wannan daddadar murya, “Fauzah” ya furta, “Noo that should not be Fauzah, then who?” ganin zai bata wa kansa lokaci yasa ya mike tsaye. A bangaren su khairy ko 3minutes basu kara ba suka ji karar bude kofa, waiwoyawa dukkansu suka yi suna duban kofar. Pretty ce tsaye cikin wasu tsinannnun kaya, ganin wadannan cousins din Hamma Zakin yasa ta saki tsaki tsaki tana jifansu da wani matsiyacin kallo, tayu yunkurin konawa idonta ya sauka kan Wata kyakkyawar yarinyar da bata santa cikin familyn ba, dumm zuciyarta ta buga amma ta kafse tare da shigewa abunta tana juyi kamat wata macijiya. Dariya khairy ta kwashe da ita tana fadin “Babes don Allah baku ga muciya bane, hhhhh kinga yanda take wani juyi don Allah” Dukkansu dariyar suka yi kamar zasu yi kuka, daga hakan khairy tace musu “Mu shige ciki mana babes” ta karasa tana kanne musu ido daya. Dukkansu suka dunguma zuwa parlourn, cak suka tsaya saboda kurar da parloun yayi, ta can gefe kuma ga datti alamun dai matar gidan ba girki take yi ba order take. Cikin ransu duk Allah wadai suke da hali irin na in-law din tasu wacce babu wani kyakkyawan hali daga gareta da ya isa garesu, tabbas jarrabawar Hamma Zakin ne amma ina mutum mai nagarta itinsa da mace irin Aunty nabila?. Ganin babu inda zasu yi gashi kuma Mom tace yini zasu yi wallahi da ba zasu zauna a wannan kazamin parloun ba. Khairy ce tayi tsaki tace “Babes mu nemo kayan aiki mu tsaftace parloun don wollah ni bana iya zama a cikin kazantar nan” Yamutsa fuska Ayrah tayi tana fadin “Ai dolenmu, amma wai dagaske Hamma Zaki kuwa yana iya rayuwa a hakan?” Fauzah tace “Nima abun ya tsaya a raina, mutumin da tsabagen tsafta wani lokacin har mamaki muke yi” Yesmeen ta cafke da fadin “Kin manta kullum cikin kiranmu da kazamai yake yi bayan babu wani abun kazanta da muka yi” Fayzah tace “Ai wollah dole mom taji, haba no wonder Hamma ke ramewa, ku tuna lokacin da Hamma Salim yayi aure yanda kullum kara kyau suke duk da akwai yaro ma, amma ki ga Hamma Zaki, miskilamcinsa ma kullum karywa yake” ta karasa hawaye na silalowa daga idanuwanta. Khairy ce ta goge mata hawayen cike da kulawa tace “I'm sorry sister, Allah yana tare da my haka Hamma Zaki ma, addu'a kawai zamu ke yi masa ok?” kaibta gyada khairy tace “Now babes to work, mu gyara parloun nan irin wanda baa taba yimasa ba” “Yea” suka hada baki tare da fara tattare parloun. Mintuna ashirin suka bata kafin su kammala gyara parloun, “wato tsafta tayi a rayuwa” Yesmeen ta fada tana mika. “Gaskiya da sakyal babes, mu huta please”. Har zuwa lokacin pretty bata fito ba bare suyi tsammanin gaisawa da ita, wannam dai matsiyacin kallon da kuma tsakin tana nufin sune tarbarsu. To Allah ya kyauta. Kallo suka kunna suna dan tadinsu, idan aka yi wani abu da ya burgesu sai sun tsaya sun magantu. A bangaren pretty tun juyawarta ta haye upstairs tana sakin tsaki. Zama tayi bakin bed tana fadin “Allah na gode maka, nayi zaton ma iyayensa ne ashe wadannan masu siffar aljanun ne” tsaki tayi tana fadin “Amma wacece wannan matashiyar?” ta tambayi kanta tana mai daga kai sama alamun tunani. Can kamar wacce aka tsikara tace “Oh!!! Wannan wannan yarinyar da na taba zuwa na samu kakarsu na nan da nan da ita ne!, to wacece?” ganin babu mai bata amsa yasa ta jawo wayarta tana fadon “I'll ask sweetheart in ya dawo” daga nan taci gaba da tadinta ba tare da tuna cewa tayi baki ba talkless of ayi musu girki. Kallonsu suke hankali kwance har wajajen Karfe biyu, yunwa ce ta fara dawainiya da khairy, kalkon yan uwanta tayi tana fadin “Babes i'm hungry!, wollah ba alamar zamu samu wani abu a gidan nan muje kawai mu samarwa kanmu abun tabawa”. Su ma duk yunwar ta ishesu dama shiyasa suka mike suka nufi kitchen. Mamaki ne ya kama su ganin kamar baa taba amfani da kitchen din ba, komai kura ga uban plates zube a sink. Basu fara girkin ba sai da suka tabbatar sun gyara ko ina, plates ma tsaf suka tsaftace su tukun suka hau kan girki. Hadaddiyar fried rice suka hada wacce kamshinta kadai mai karatu ya samu a matsayin rabo to ya gode Allah, sai chicken pepper, Sai kuma Tigernut drink da kana gani zaka fara hadiyar miyau. Cikin tsadaddun food flask suka zuba fried rice din sannan suka saka shima chicken pepper din, daga nan suka zuba tigernut drink din duka nufi dining, isarsu kenan suka zaro idanuwa. Khairy tace “Tab! Sunan wani abu wai shi badakala” babu yadda suka iya dining din ma sai da yasha dusting. Sauran suka debo suma suka ci, kiraye kirayen sallar asr yasa suka yi alwala, a parloun suka yi sallah. Ita dai khairy hamshakiyar take jira ta fito tasan dole zata nemi abin tabawa. Ai kamar ta sani ashr tunda suka fara girkin kamshi ya cika mata hanci, tunani take ko daga ina?, tunawa da kannen mijin nata da ta manta da zuwansu ma yasa tace laalla sune, tana lashe baki ta fito daga dakin, sallar ma bata samu damar yi ba. Downstairs ta nufa ai tana fara taka steps din bata san me ta taka ba taji ta a kasa yarrrrrr. Wani mahaukacin ihu ta saje tana fadin “Na shiga uku shikenan nikam na karye, wayyo sweetheart ” cike da jin haushinta suka saka dariya kamar zasu yi kuka yayinda ita kuma take famar ihu tana ta shiga uku. Sai da suka yi mai isarsu tukun suka je gareta, bs tare da sunce komai ba suka ja ta zuwa sama har zuwa dakinta, khairy ce tayiwa Ayra alama da ido ita kuma suka daura pretty kan gado daga nan suka dawo parloun ba tare da sunce mata uffan ba. Suna zaune a parloun yayi sallama, kamar koyaushe cikin uniform da suka mugun karbi jikinsa. Cikin takunsa na kasaita ya shigo. Sunkuyar da kai suka yi suna gaida shi a tare. “Ina yini Hamma Zaki ” Can kasan makoshi yace “Lafiya” yana bin parloun da kallo, cikin ransa kuma tunani yake “Waye ya gyara parloun? ” yasan dai ba pretty bace, “then who?” ganin yana tsaye yasa Fauzah yin gyaran murya tace “Hamma ga Abinci a dining. Bai ce uffan ba itama bata yi tsammanin zai fadi ba, cike da takama ya fara takawa zuwa sama. Wanka ya fara yi ya sanya wasu ligjt blue pyjamas sannan ya fito. Ba tare da ya kallesu ba ya nufi dining din don dama yunwa yake ji rabonsa da abinci tun daren jiya da yaje gida. Sanin ko a gida mom ke serving dinsa yasa fara mikewa taje ta zuba masa komai daga nan ta dawo wurin zamansu. Bayan yaci na plate din sai da ya kara kadan tukun ya goge bakinsa da tissue, tigernut drink din ma ya sha sai dai ba zaka iya gane yanayin fuskarsa ba. Sama ya kara komawa ba tare da ya kara kallonsu ba, bedroom din pretty ya shiga da niyyar nuna mata kuskurenta na wulakanta danginsa don ranar da Hamma Salim da matarsa Aunty Waheeda suka zo haka ta musu. Fuska daure ya shiga, ganinta kwance yasa ya karasa wurinta. Cike da shagwaba ta fara magana “Oh sweetheart sai yanzu ka dawo, wallahi yunwa nake ji kamar naci babu, kaga naji kamshin girki inaga yan uwanka ne suka yi sai da naje ci nayi missing step na fadi, sweetheart duba kaga har ya kumbura” fuska daure ya duba ganin bai ga komai ba yasa yace “Nabila!, Nabila! Nabila! ” dagowa tayi tana kallonsa tasan babu wasa “Sau nawa na kira sunanki?” a shagwabe tace “Uku sweetheart ” “Gargadi a karo na karshe ki daina wulakanta yan uwana idan sun zo in ba haka ba kuma zan baki mamaki” daga haka ya fice ya barta. Downstairs yq sauko yana nufi wurinsu. Cikin dakakkiyar murya yace “Yaushe zaku koma”. Khairy da ta gama kosawa da gidan tace “Yanzu muke son komawa”. Minti biyu tukun yace “Ku bari kuyi sallah sai mu wuce tare” babu yadda zasu yi haka suka zauna suna jiran in anyi sallar sa wuce amma sun kosa. Ita dai khairy haushi yau dinnan ya bata duk da cewa ba don shi suka yi hakan ba amma atleast ya kamata yayi appreciating effort dinsu, cikin ranta tace “Har da zama ya kwaahi girkin bayan ko nuna yaji dadi bai yi ba” (Nidai ina gefe nace khairy so kike Hamma Zakin yayi ta washe miki baki yana fadin ya gode???). *COMMENT & SHARE PLEASE* [29/08, 2:36 PM] 💎Diamond_Bhatool💎: 🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 *ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)* 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀 _NA_ *Fadimatu Adamu Hassan* *Diamond Lady 💎* SHAFI NA “““81&82””” Bayan sunyi sallah Hamma Zaki ya shigo alamun daga maajid yake, da ido yayi musu alamun su tashi, thank God kowa yayi sallah hakan yasa suka fito dukkansu. Shiga suka yi cikin sauri kamar wani zai riga su, Fauzah, Ayrah da Yesmeen suka shige gidan baya, isowar khairy kamar zata yi kuka ta shiga gaba amma ta shirya yi musu rashin mutunci idan suka isa gida. Maimakon ya nufi gida Shopping Mall ya mika su, suna isa yace musu “10 minutes na baku ku fito, take this” ya mikawa khairy ATM card dinshi. Basu kai 10minutes din ba suka fito daga nan suka wuce gida zuciyoyinsu wasai don tuni sun mance da iya shegen da aka tsula musu a can. Bayan ya daidaita parking suka fita suna masa godiya. Da gudu khairy tayi part din granny. “Ina kike ne granny ta” Cikin sakin fuska granny tace “yar albarka sai yanzu, aah wannan kuma fa?” granny ta tambaya tana mai kai dubanta ga ledar dake hannun khairy. Murmushi tayi tace “Granny Hamma Zaki ne ya kaimu muka yi shopping, kema na siyo miki naki. Nan ta fito da turaren daki da na jiki da ta siyowa grannyn. Murmushi granny tayi tana fadin “Allah yayi albarka, madalla madalla ummul khairy ”. Daga nan ta kwashe sauran ta kai bedroom dinta. Bata san lokacin da ya shigo ba coz bacci ne ma ya dauke ta. Hamma Zaki tunda ya koma gida bai kuma leka bangaren pretty ba don mugun haushinta ma yake ji. Ko da yayi wanka ya kwanta baccin ma kin zuwa masa yayi, banda tunanin wannan muryar babu abunda yake, ya kasa tantance wacece cikin yaran nan ta kira shi. Lokaci daya kuma zuciyarsa tace “Khairy! Ita kadai granny zata iya bawa wayarta, Amma gaskiya muryarta akwai sanyi ga nutsuwa” ajiyar zuciya yayi yace “Su suka gyara parloun sannan suka girka abinci mai dadin nan, kai gaskiya yau kam na kara yabawa tarbiyyar gida, see how kananan yara suka gyara waje amma wannan katuwar sai ci da chat, mtss” Wata zuciyar kuma tace “Tabbas Dr. Farouk yayi gaskiya, zan kara aure amma fa bazan auri wacce ta gama wayewa ba, naga ishara” daya zuciyar tace “To wa zaka aura kai da baka san soyayya ba bare ka taba yinta” amsa dayar ta bayar da fadin “Ai ba sai anyi soyayya ba kawai dai in tana sona fine” wata zuciyar tace “To wacece?” amsa dayar ta bashi da “I dont know” Ganin tunani zai haukata shi yasa ya kunna wayarsa yana duba messages nashi. Washegari duka yan matan suka taho part din granny kamar yadda suka saba a yanzu. Tare da granny suka baje dandalin hirarsu. Fauzah kuwa tas abunda ya faru gidan Hamma Zaki sai da ta fadawa granny, nan fa hau fada da masifa sai da ta gaji tayi shiru don kanta, abunda suka so kenan dama. Bayan ta tafi khairy ta kalli Ayrah tace “Mutuniyar basu san fa me muka yi ba!” tafawa suka yi Ayrah tace “Me kika yi dai, ni ai taimaka miki nayi” dariya khairy taui tace “Ai duk da haka kinyi participating a ciki dai” ta karasa tana daga mata gira. Cike da kaguwa Yesmeen tace “Kunga kun samu a duhu fa, ku fada mana me ya faru” “Ai kam” Fauzah ta fada. Dariya suka kara yi suna tafawa. Khairy tace “Kai babes kunsan nace sai mun rama duk tsiyar da aka yi mana idan muka je, do u know what?” kai suka jijjiga “Bayan mun gama gyaran gida munyi girki nasan kamshin ya isa hancin wannan fifgaggiyar Aunty Nabilar, sai da na fakaici idonku na watsa morning fresh a staircase shine fa da ta fito ta wuntsilo” dariya dukkansu suak saka can suak tsagaita. Fauzah tace “Wallahi kin kyauta kuwa, wannan shegiyar maganinta ke ce, ashe har yanzu yar iya kike” ta fada tana dariya. Khairy ma dariyar tayi tace “Ai abun a jini ne, wollah da ace gida daya muke da ita da taga tsiya”. Idanuwa suka hada su uku sannan suka kwashe da dariya. Kallon mamaki khairy ke binsu da shi tana fadin “Meye kuma ” Kamar hadin baki suka ce “In tayi tsami zata fito kiji” Nan suka yi son ransu daga bisani duk suka wuce bangaren su. khairy dai littafanta ta fitar tana biyawa har lokacin lunch. Ranar monday ne su khairy aka je competition din da ta wahalar da kanta a kai. Alhamdulillahi kuma an samu nasara dob har award school nasu ya samu. An karrama ta ranar a gaban assembly, sosai taji dadin yadda bata bawa malamanta kunya ba, haka a musabaka ma da aka yi na daya tazo a hizb 50, su ma su Ayra daga na biyu sai na uku. Sun yi farin ciki sosai da wannan nasarar, kowa sai son barka. yanzu gabadaya hankalinsu ya koma ga shirye-shiryen WAEC da NECO suke a daya bangaren kuma shirin saukarsu suke yi. Cikin nasara kuwa suka kammala WAEC & NECO sai kuma jira result, meanwhile, abubuwa sun faru ciki harda haihuwar Adda Najma da Adda Salma, anyi shagalin suna lafiya kuma Babes fa sun sha kyau a ranakun sunan da suka kasance mabanbanta. A nan ne kuma Fauzah da Ayrah suka yi catch, da farko basu biye su ba sai da su Yesmeen suka saka su gaba tukun suka yarda, Khalil wanda brothern mijin Adda Salma ne kuma ya kammala karatunsa aiki ma yake yi a Dubai, da kyar ya samu amincewar Fauzah, sai kuma Ishaq btothern Mijin Adda Salma ne, shi kuma a nan yola yake aiki a katafaren companyn mahaifinsa. Su da suke ki sai gashi yanzu sunfi kowa so, Allah Allah suke daddy ya saya musu waya su huta da satar wayar granny suna waya da masoyansu. Su dai Yesmeen da Khairy nasu ido ne. A cikin hutun nan ne kuma khairy ta je Gallara, a nan ta riski labarin mutuwar Inna Zaliha wacce sai da ta sha jinya a gidansu don tuni Baba ya sallame ta, satinta biyu ta dawo. Dawowarta ne kuma abun farin ciki ya samu, pretty ta samu juna biyu, ganda ta karu, ga shegen fi'ilin tsiya da ta samo. A yau Laraba suna zaune suna hirarsu kamar koyaushe Hamma Zaki ya shigo, duk irin yadda zuciyarsu shi da Khairy ke bugawa sai suka meze, gaidashi suka yi ya amsa daga nan Granny ta fito. Sun dadr suna hira kafin yayi mata sallama ta koma bedroom dinta. Har lokacin su khairy na nan suna hirarsu. Can kasan makoshi yace “Kai kuzo” Yesmeen kadai taji yayi magana sai ta rada musu. Addu'a auke Allah yasa ba laifi suka yi masa ba. A gabansa suka durkusa suna fadin “Gamu” kamsu kuma na kallon kasa. Sai da ya share 3minutes kafin ya janyo ledar dake gefensa. A hankali ya zaro wayoyin kirar Iphone 14 guda hudu, Daya bayan daya ya bawa kowaccensu. Karba suka yi cikin ransu kamar su tashi su taka amma ba hali. Kamar baya son magana yace “Ba an baku waya ba kuma, bana son rawar kai, banda tara numbers din samari kunji ko?” A tare suka ce “Munji Hamma, Allah ya saka da alkhairi ya kara bude” Cikin ransa ya amsa daga nan ya mike yana nufar waje, har ya kai bakin kofa ya dawo yace, “Ke!” ganin ita daya ce a wurin su sun koma wurin zamamsu yasa ta dago kyawawan idanuwanta tana kallonsa yayinda zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri. Mikewa tayi ta nufi wurinsa tace “Gani” “Idan granny ta tashi kice ta fada miki sakona” daga haka ya tasa keyarsa gaba. Kafin Zuhr kuwa sun saita wayoyinsu komai zam, duk social media handles kowa sai da ta bude account, don a cewarsu ba zaa yi babu su ba. Bayan granny ta tashi ne take sanar da ita wai zata koma gidan Hamma Zaki tana taimakawa matarsa da aiki saboda cikin dake gareta. Babu yadda ta iya amma ranta bai so ba saboda zaa raba ta da ababen kaunarta wato babes. Kamar yadda granny ta fada mata tare dasu Fauzah suka hada kayan Khairyn cikin trolley, da daddare kuwa sai gashi yazo. Da zai koma auka wuce da Khairy. Tun a parloun ta fara tsinewa kazanta irin ta matar gidan Cikin ranta, in banda karni babu abunda yake tashi. Shima ba iya zaman zai yi ba yasa ya nuna mata daki. Itama bata ce komai ba ta nufi daki, karkadewa tayi sannan ta wanke toilet daga nan kuma ta janyo wayarta. Ba ita tayi bacci ba sai wajajen 1pm bayan gama latsa wayar da tayi cike da annashuwa da farin ciki. Washegari ko da tayi sallar asuba bata koma ba don aikin dake gabanta yana da yawa, ta kudiri cewa zata yi aiki kam amma wallahi sai ta saita matar gidan. Parloun kasan ta gyara fess kamar ba shi ba, duk kurar nan babu ita, ta feshe parloun da room freshner daga nan kuma ta wuce kitchen. Ba ita ta gama gyaran kitchen din ba sai wajajen 9am, har lokacin kuna masu gidan babu wanda ya fito. Ko da ta gama gyarawa sai ta daura breakfast daidai yadfa zai ishi dukkansu. Tana gamawa ta jera a dining daga nan ta koma bedroom dinta ta shiga wanka, wata Black atamfa mai flower green da ja, dinkin doguwar riga fitted ta sanya wanda tuni ya amshi jikinta, cikakkiar surarta ta bayyana kamar ka sace ka gudu. Powder da wet lipa kawai ta shafa daga nan ta fito don zuwa ta tayar da majiya dadin. A hankali take taka steps din har ta iso jerin dakunan da bata san wannene nasa da matar tasa ba, har ta kai hannu zata yi knocking sai ta fasa ta wuce na gaba, knocking tayi daga ciki ta jiyo muryarta tana fadin “Yes come in” A hankali ta murda handle din ta shiga, wani irin karni ya ziyarci hancinta tuni ta fara yamutsa fuska, dakewa tayi ta karasa gaban bed din tace “Madam, breakfast is ready” sai a lokacin pretty tasan wanda ya shigo don duk tunaninta sweetheart dinta ne. “Kan uba!” ta furta tana tsirawa Khairy ido, ganin irin kyan da yarinyar ke da yasa taji ta tsaneta. Har khairy ta kai bakin kofa taji muryar pretty na fadin “Uban waye ya kawo ki gidana?” Murmushin da ya karawa fuskarta kyau har sai da dimples dinta suka lotsa tayi sannan tace “Dan uwana mai gidan shi zaki je ki tambaya, mtss” Daga haka ta fice, a harzuke pretty ta mike tana nufo Khairyn wacce ta riga ta fice ma daga dakin. Matar da bata iya komai sai gashi ta biyo wata fa gudu. Khairy kuwa bata damu ba ta cigaba da tafiyarta cikin takunta mai daukar hankali. Pretty kuwa bata hakura ba saboda ganin takun da yarinyar ke yi kamar da gayya yasa ta bi bayanta har ta sauko daga steps din ta shige dakinta tana rufe kofar, wani banzan murmushi tayi tace “Wallahi sai nayi maganinki Auntu Nabila”. Isowar pretty kuwa ganin parloun a tsaftace kamar na shi ba yasa ta furta “Wow!, ko dai munyi mai aiki ne?” kamshin girkin da ya nugi hancinta yasa ta leka dining area, ganin abinci a jere yasa ta yunkura zata nufi wurin. Ji tayi an dakatar da ita ta hanyar rike hannunta ana juyo da ita. _COMMENT & SHARE PLEASE_