[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: https://chat.whatsapp.com/G0Tst06uPc12T74oZhhCa2 💅 ' YAN ABUJA 💅        WRITTEN BY HAERMEEBRAERH *Assalamualaikum my beautiful mutanen kwarai, ga Editing ɗin littafi na na biyu da na farayi a duniya, a karanta da hankuri* *2018/2024* *Dan Allah da kun ga an fara posting ku ɗan dinga adanawa saboda ba sai na yi nisa ba ku tambaya a dawo baya, Na gode.* PAGE 1: Gidan malam Baballiya gidane mai girma na qasa a tsakiyar garin kano, wanda ya qunshi mata biyu, Goggo Sarai itace uwar gida, sai Mama Bilkisu itace amarya, malam Baballe yana da yara guda huɗu dika mata ne, se dai a kullum ya na roqon Allah da kuma burin Allah ya azurta shi da d'a namiji mai albarka, wanda ko bayan ba shi zai kula da wannan zuri'a tashi mai cike da rikici, domin tin yaran nashi mata na qanana gidan yake a cikin rikici, wanda Goggo ce sanadin komai wato Sarai, ita Mama Allah ya sa mata sanyin hali, amma kome za ai bata yarda a taba mata 'yar ta tilo ba wato Juwairiyyah, dan haka in dai aka ji rikicin ta to fa akan 'yarta ne, ko shi ma ba zata tsaya aita bala'i ba , za dai ta tabbatar ta karb'ar wa 'yar ta 'yanci sannan ta ja ta su bar wajen, a haka Allah ya raya masu yaran su guda hudu, Goggo Sarai nada Suwaiba mai shekara 19 ,se  Saudat me shekara 18, sannan Salma me shekara 16, Mama  Bilkisu kuma na da Juwairiyyah wadda take sa'a ce ga Salma kwana uku ne tsakanin su kawai,a yanzu ta na dauke da tsohon ciki gashi nan haihuwa ko yau ko gobe. Sai dai muyi fatan Allah ya amsa addu'ar Abba Baballiya wannan karon a samu biyan buqata wato ya samu d'a namiji,domin kullum fatan shi Allah ya dube shi ya bashi namiji, mutum ne shi mai sanyin hali saidai sanyin halin shi be hana shi yin iya qoqarin shi na ganin ya isa da gidan shi ba, badan ma qoqarin da yake ba da tabbas Goggo Sarai zata zama itace mijin a gidan. ***************************** Da misalin 11:45am Juwairiyyah ce ke ta aikace aikace a tsakar gida, inda Mama Balki ke d'aki ta na naquda ba tare da sanin kowa ba, azaba ta yi azaba ta ga abun ba zai yiwu ba kawai sai ta buɗe murya ta na neman taimakon Allah da na 'yar ta ta da ke taya ta aiki. "Wash Allah na, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Juwaira, taimaka ki kira min Abban ku a waje" Yarinyar da aka kira da sunan Juwairiyyah ce ta miqe tsaye da sauri ta dau mayafin ta da ke kan qofa ta yafa ta fita, a bakin kofar gidan ta tadda mahaifin nata zaune ya na sauraren rediyo, sai ta durqusa cikin ladabi sannan ta ce, "Abba Maman mu na kiran ka,ka yi sauri Abba bata da lfy kamar ma haihuwar ce ta zo dai ina jin" Ya na jin haka ya miqe tsaye da sauri ya shura takalman shi dan ya saka,gaba ya yi ya bar su a wajen dan kuwa takalmin ma yaqi qarasa shiga qafar tashi sai kawai ya afka cikin gidan direct ya wuce sashen Mama Balki,labulen d'akin ya buɗe ya shiga, ganin mawuyacin halin da take ciki ne ya sanya shi cewa, " Subhanallahi Gimbiya, haihuwar ce ta zo mana bagatatan haka? Sannu Gimbiya" ( Yana kiranta da Gimbiya ne don a ilimin shi na addini ya san cewa kiran sunan mata da suna mai daɗi sunna ne, inda yake kiran Goggo Sarai Sarauta) Cikin tsananin azabar da take ji ta na ratsa ta ta ce, " Malam taimaka min na samu na kai uwar d'aka bana son zama a nan na haihu a rumfa" Cikin sauri ya kamata ya riqe da kyau a jikin shi sannan ya ce, "To  Gimbiya, bismillahi,amma kuma mun shigo d'aka ko dai muje asibiti ne ?" Murmushi ta yi kawai dan sanin cewa qarfin hali ya yi dan ya kwantar mata da hankali ya fad'i hakan ta san bashi da kuɗin yin hakan, ko na mota basu da shi, shi kuma ba mai kwad'ayi ba ne da zasu samu a wajen Goggo Balki, dan 'ya'yan ta kyawawa ne dukan su su na kawo mata kuɗaɗen da bai san ta hanyar da ake samo su ba shi yasa baya ci,ita kuwa Goggo Sarai ta kan ce, ta gode wa Allah da ya bata 'ya'ya 'YAN ABUJA , dan haka ne auren su sai mai kudi, dalilin wannan ne yasa take samun kudi sosai, duk da fadan da Abba Baballiya keyi akan su daina biyewa samarin banza, amma se suka yi kunnen uwar shegu da gargad'in shi, da taga ya yi musu wuta2 kuma ya fara kullen su a gida , sai ta fito da dabara tunda shi mai son ilimi ne musamman na addini sai ta saka su Islamiyya,daga sun fita zasu bi gidan qawaye su canja kayan su, su qara gaba neman mazan da zasu aure su su kai su Abuja, gaba ɗaya basa hulda da qawyen su na unguwar, sai 'ya'yan masu kudi, saboda anan suke saka ran samun nasarar samun mazajen aure yan Abuja, kullum su na cikin zuwa biki da partyn qawaye na birthday. Kukan jariri ne ya dawo da Abba daga tinanin ina zai samo kuɗin kai ta asibiti ta haihu lfy? Da hanzari ya qarasa taimaka mata yaro ya fad'o har da mabiyya, nan take ya taimaka mata ya gyarata ya aje jaririn ya fita qofar gida da hanzari ya na hamdala, Mama kuwa cikin raunananniyar murya ta ce, "Juwaira ɗora min ruwan  zafi da ya tafasa ki sanar da ni , Allah ya sauke ni lafiya" "Alhamdulillahi... Alhamdulillahi to Mamana sannu" Cikin zumud'i da washe kyawawan haqoran ta farare masu dauke da hushirya a saman su ta nufi gaban murhun nasu dan cika umarnin mahaifiyar ta na ɗora ruwan zafi, se dai ta na zuwa ta ga ba icce, amma duk da haka bata karaya ba ,sai ta je ta dakko tukunya ta wanke ta zuba ruwan ta kawo wajen murhun ta ajiye, zata juya kenan ta ga mahaifin ta na shigowa da icce a hannun shi na dama, hannun shi na hagu kuma riqe yake da baqar leda qarama, da hanzari ta isa ta karbi iccen tana mai yi masa sannu da zuwa, komawa ta yi ta haɗa wutar ta ɗora ruwan shi kuma ya yi d'akin da mai jegon take. Kamar saukar aradu ta ji an yi tsaki a gefen ta, qin juyawa ta yi dan tasan ba zai wuce ɗaya daga cikin 'yan uwan ta ba koma Goggo da kan ta. "Aikin banza sai rawar qafa ake, duk dai abun mutum mace ya qara haifa balle ai mana wani rawar kan uwa ta haihu" "Hhmmm Allah ya kyauta ya kuma shiryar da ku dika idan ku na da rabon shiriya, to bari ki ji Salma 'yar baqin ciki, wannan karon namiji Mamana ta haifa, dan haka baqin ciki ya kashe duk wani dan hassda" Wani uban ashar Salma ta saki ta saki jikin ginin da ta riqe tai sashen su da hanzari,kafin ta isa cikin rashin sa'a bokitin gaban ta ya bige tukunyar da take girka masu farfesun naman kaza,ai ko tini komai ya zube a qasa, nama ne na kaza cike da tukunyar wanda da gani yafi qarfin kaza ɗaya, ko kulawa ba ta yi ba ta shiga d'akin su da gudu tana faɗin, "Goggo ! Goggo ! Wai ni kina ina ne wannan mummunan labari ya same mu?" Da saurin su suka fito dikkan su daga d'akin,ana can an qule a d'aka ana hasafin kuɗin da suka samo, suna bata labarin mazajen da ke son su turo ai zancen auren su da su, cikin d'aga murya Goggo ta ce, "Ke meye haka duk kin bi kin fadar min da gaba kamar an ce maki  matar uban ki Bilki ta haifi saurayi" "Hhmmmm ai kin ji ashe kece ke yi  mana mugun fata baki da tinani sai wannan, gashi nan to ya tabbata ai Mama Balki ta haifi yaro namiji" Damqo Salma Goggo Sarai ta yi da qarfi cikin zare ido take tambayar ta "Me kk nufi salma?" Cikin rashin kunya da murgud'a baki da idanu Salma ta ce, " Ina nufin Mama Balki ta haifi saurayin d'a namiji,tunda ke kullum kk mana mugun baki akai to gashi ta tabbata" Wani wurgi Goggo  ta yi da Salma gefe, ta kuwa qume kai da gini ji ka ke quuummm,Goggo da sauran yaran nata dika suka yi gaba zuwa dakin Mama Balki, Salma ma miqewa ta yi ta na lailaya goshi ta bi bayan su, babu ko sallama suka afka d'akin, daidai Abbah Baballiya ya dauki gasasshen naman rago ya sa wa Mama Balki a baki, Goggo ce ta dafe qirji saboda abinda idon ta ya gane mata ta buɗe baki ta ce, "Me nake ji ne da gani yau kuma ni saratu? " Suwaiba 'yar boko kuma 'YAR ABUJA ce ta karkata baki ta ce, "No i can't believe this, what is going on here, ina jaririn yake?" Suwaibah na da kwalin ta na NCE ,ita kuma Saudat kwalin secondary ne kawai a hannu wanda duk daya take da su Salma da Juwairiyyah ,sai dai Juwaira tana son ta ci gaba da karatu amma ba halin yin hakan saboda babu arziqi,wannan shine dalilin da yasa ta hakura, amma sakamakon ta yayi kyau sosai, both WAEC & NECO, ganin yanda suke wani cika su na batsewa ne ya sanya Abbah Baballiyaya ce, "Haba Sarauniya ta ya zaki shigo d'akin ma'aurata da yaran ki gaba ɗaya haka babu ko sallama? Kuma bama ki tambayi yaya ko ta haihu lfy ba? Aa tambaya kuke ina jaririn? Anya wannan rayuwar da ku ke yi ta dace kuwa?" Cikin yatsine baki da fari da ido kamar wata qaramar yarinya Goggo ta ce, "Eh ban ga zan iya sallamar ba ne shiyasa banyi ba, tambaya ɗaya kuwa da zan yi shine me aka haifa? Da gaske ne namiji aka samu?" "Eh na miji Allah ya bani, me za ki yi, me zai faru? Me ya sa ba zaki yi hakuri kema Allahn da ya bani ya baki naki ba ,ai ba wai ya manta ki bane kema in ki ka yi hakuri watarana samu za ki yi,dan haka ku fita min a d'aki tinda ba arziqin yi min sannu ne ya kawo ku ba" Gaba dayan su shewa su ka ɗauka sannan suka tafa kamar wasu 'yan daudu Goggo ta ce, "Hahaiiiiii Cassssss, eh lallai ne, kinyi d'a na miji na gani tabbas, shine ya sa zaki fara min kitifi ko Balki ? to bari na baki wani labari, a da kam na damu amma a yanzu wani tinani ya wanken damuwa ta tass, Shi Uban yaran me ya ke da shi, me ya tara da zan damu raina akan haihuwar d'a namiji da girma na haka? Bayan ga 'Ya'ya mata Allah ya bani na zuwa Abuja ?  Ki kalla da kyau duka Yarana kowanne namiji mai lafiya ya gansu sai ya yaba, dan haka bama zan bar labarin nan ya kwana ba" Bakin ta suwaibah ke son rufewa tare da faɗin " Goggo ki bari ba yau ba kin sanar da su in komai ya kankama, ko kin manta halin yan baqin cikin ne? Se a shiga malamai a hana lamarin faruwa ai" "A'a Suwaiba banni na fada masu su ji duk wani d'an baqin ciki se dai ya mutu, yarana guda biyunnan sun samu mazajen aure mazauna Abuja, dan haka sai ka bude kunnen ka kaji, zan basu izinin su turo magabatan su a zo ai komai nan kusa ba da jima wa ba" Abbah Baballiya ne ya ce "Hhmmmm Sarai kenan wato kece ma mijin yau ni ne matar ko? Umarni kk ban akan za su ce mazajen da za su aure su turo  ko? Ba bincike ba komai kawai su turo, to bari ki ji na fada maki zan ba 'ya'yan ki mijin da suke so amma komai yaje yazo ki kuka da kanki kina jina ko? Fitsararriya mara kunya mai raina mijin ta a gaban 'Ya'yan ta dan su koya suma" Ranshi a bace ya ke sanda ya yi maganar kawai se ya matsa kusa da Maman yana ci gaba da bata naman a baki Shewa Saudat tayi tace "Ikon Allah wai na kwance ya faɗi" Dariya Suwaiba ta yi ita da Salma suka tafa har da uwar tasu suka fice suna dariya, can qasan maqoshin Goggo balki kuwa kishi ne damfare, kada kai ta yi a ranta tace, 'Kun yi ku gama da 'ya'yana sun tafi ABUJA aure kashin ku ya bushe a gidannan' A kwana na bakwai da haihuwa aka yi suna yaro ya ci sunan Ammar kyakkyawa da shi sak mahaifin shi,ba wani taro aka yi ba da yawa saboda babu abin hasafin, ba qaramin so da gata yake samu ba a wajen iyayen shi da yayar shi Juwairiyyah ba, zaune suke a shimfidar tabarma a tsakar gidan inda ya sha shara ko ta ina yayi fes da shi ta na masa wasa kamar ya na jin ta, can cikin d'akin su kuwa qamshin turaren wuta na tsinke ne ke tashi, Sallama Abban su ya yi ya shigo jikin shi a mace, amma dik da haka sai da ya yi masu Juwairiyyah wasa ya sumbaci Ammar ya shafa kan Juwaira sannan ya shiga cikin d'akin Goggo Balki, kwalama Juwaira kira ya yi yace ta kira mishi Goggo Sarai......... [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼   YAN ABUJA   💅🏼   WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 2: Juwairiyyah bata b'ata lokaci ba wajen isar da saqon Abbahn nasu a wajen Goggo, da kyar ta amsa mata sannan Juwairiyyah ta koma bangaren su,da isa da qasaita Goggo Sarai ta shiga parlourn Mama,hakan ne ya sanya Abban murmusawa duk da cewa ranshi na matuqar quna  game da abubuwan da take yi mishi. "Sarauta kenan yi ki qaraso mu yi abinda zamu yi na fita sallah ko?" Qarasa shiga ta yi tana hura hanci ta zauna a gefen hannun shi na dama, inda Mama Bilki kuma ke zaune a gefen shi na hagu, cikin wani irin yanayi mara misaltuwa ya buɗe baki ya fara magana, "Da farko dai zan ma Allah godiya daya kawo min wannan rana da nake ta buri, duk da cewa ta zo min a bazata kuma ba a yanda na so zuwan ta ba, amma dai Alhamdulillah,a yau ne manema auren yaran nan su Suwaiba, Saudat da Salma suka zo, kuma mun karbe su a gidan Yaya Balarabe cikin aminci da mutunci, inda suka damqa mana dukiyar auren yaran, Suwaiba kudin sadakin ta da na gani ina so da kudin da zata hada lefe dika, an bamu million huɗu da dubu ɗari biyu, sai na Saudat Ita kuma Million biyu da dubu ɗari bakwai, a gaskiya na so na qi karba saboda kudin sunyi yawa, kamar wasu wanda zamu saida 'ya'yan?....... " A hargitse cikin damuwa da jimami Goggo Sarai ta ce, "Abban su ina fatan dai baka yi mana baqin ciki irin na iyayen zamani ka sa an rage kudin nan ba?" Cikin ɓacin rai Abbah ya kalle ta ya ce, " Amma dai na rasa me yasa baki da d'a'a Sarai? Ya ina magana ban qarasa ba zaki katse ni? Har kina ikirarin zan ma 'ya'yana baqin cikin iyayen zamani? Anya rayuwar da kk ɗora yaran nan akai za ta ɓulle da ku kuwa? Gaba ɗaya kin sa tarbiyyar yarana ta zamo a lalace? Kin raina ni baki ganina da qima da mutunci? Kedai harka in ba ta kudi ba baki san komai ba? Na gode Allah da yasa ina iyakar qoqarin riqe gidana ni  Baballiya da ke kam na san da karuwanci zaki saka 'ya'yana yi su na kawo maki kudi, haba, bai ishe ki misali ba akan Balki da 'yar ta guda ɗaya tilo? 'Yarta ɗaya amma ta tsaya wajen bata ilimin addini dana zamani daidai iyawar ta, ke kuwa in ba Salma ba da ta yi sauka yarannan biyu ba zasu iya bude qur'ani su yi karatu mai kyau ba, Salman ma gashi nan ne dai kawai, to ina mai maki nasiha da kiji tsoron Allah akan abinda kk yi, ina jiye maki ranar kuka, ranar dana sani, ranar ni 'yasu,........ " Da sauri ta d'aga masa hannu ta na yatsine ta ce, "A'a faaaa, bafa zaka sani a gaba ba kana min mugun fata da kuma maganganu na nuna baqin ciki qarara a wannan al'amari ba, 'Ya'ya dai nawa ne, nice na yi naqudar su na haifa abina, ba wanda ya taya ni lokacin da nake qafa ɗaya a lahira, d'aya a duniya ko akwai? Dan haka sai wanda naga damar su aura sannan zasu aura, nifa takura ce bana so tammm, yanzu ka bamu kuɗin lefen da na sadakin dan musulunci bai yarda kowa ya taba dukiyar auren yara ba sai su ehe" "Hmmmmm Sarai kenan, ke kaɗai  ai ki ka yi cikin su ki ka haife su ba da ni ba dole ki ce yaran ki ne ke kaɗai,to bari kiji iya kuɗin lefe zan baku, sauran kuwa sai sanda akai auren su zan baki su,wai da ke a taki qaramar kwakwalwar sai na dauki wannan maqudan kudin na baki dika? Haka kawai aje wani abu ya faru bana fata ba ai aure ba ku barni da biya da tashin hankali? To bazai yu ba" Bala'i ta miqe tana zazzagawa son ranta ita sai an bata kudin, tashi ya yi ya kad'e rigar shi ya fice dika a gidan, daidai lokacin da Mama Balki ke cewa, " Ubangiji ya sanya alkairi da albarka, Allah ya kare dukkan abinqi ya basu zaman lfy" "Hahaiiiiiiiii Cassssss, ni zaki wa bariki Balki? Zuciyar ki cike da baqin ciki amma wai kk addu'a mai daɗi irin haka,to dama dai ba daga bakin ki ta fito ba dana ce ameen" Sa kai ta yi ta fice ta shiga madafin su ta hau aikace2, tana yi tana masifa kamar wadda ta zautu, yaran ne suka dawo daga yawon tazubar din su da sunan Islamiyya suka tarar ta na masifa, tambayar ta Saudat ta yi da cewa, "Wai Goggo me ke faruwa ne gaba daya muryar ki har qofar gida ana jiyowa" "Ba ni da wannan sallamammen uban naku ba ne, an kawo kudin auren ku sun riqe shida Balarabe, to ni ba zasu nuna min isa da iko ba, sai sun kawo kudin nan dika" Cikin qasa da murya Suwaibah ta ce, "Goggo kwantar da hankalin ki tashi mu shiga ciki ki gani" D'aki suka shiga ta d'akko mata maqudan kudi a jakar ta ta zube mata su a saman gado, tsabar razana da ganin yawan su se da Goggo tai baya dafe da qirji ta na zaro ido, "Suwaibah waya baki wannan kudi haka me yawa?" Fari ta yi farrrr da idanun ta kafin ta ce, " Alhaji Salihu mai tumbin Nera  kk ji Goggo, cewa ya yi ga su ko zan qara wasu abubuwa a lefe yaso bayar wa a can wajen karbar sadakin se ya fuskanci za a iya cewa sun yi yawa, shi kuma yana ganin ko nawa ne zai iya kashewa ya samu yar zumar shi" ( Sunan da yakan kirata kenan lokacin watsewar su) dariya Saudat ta yi ta ce, "Aaaaa kice Adda Suwaiba Alhaji ya ji zuma yau" Dariya suka yi dika har uwar tasu suka tafa, baqin cikin ma da take ciki tuni ta manta da shi, ba sallah ba salati suna nan zaune ana maida yanda akai da yanda za ayi. ************************** Washegari Juwaiirah  ce zaune saman sallaya da goshin asuba ta na ta ibada, kamar wata babbar mata, Maman ta ta saba mata da tashin dare, dan ta sanar da ita cewar duk abinda bawa ke so ya roqi Allah da ikhlasi da yaqinin Allah zai biya masa buqatar shi to fa ba makawa Allah zai biya masa buqatar shi musamman in bawan nan ya yi addu'ar a lokutan karbar addu'a, wanda qarfe uku zuwa asuba ko huɗu zuwa asuba Allah na amsa addu'ar bayin shi dan lokaci ne mai mahimmanci ga bayin Allah, sannan ba a son mutum mumini ya zage ya dinga kwasar bacci daga farkon dare har zuwa qarshen dare ba tare da ya farka ya yi nafila ko da raka'a biyu bane,mu ke da buqata a wajen Allah Allah ba shi da buqatar mu, ya na daga cikin cikar imanin mutum ya dinga rokar Allah ya bashi ikon ganawa da shi a cikin dare ko da ya na jin kiwar yin hakan da kan kan shi ,to sai Allah ya bashi ikon tashi ɗin. Hannu ta daga sama cikin qasqantar da kan ta a gaban mahaliccin ta ta ce, " Ya Allah kai ne masanin abin da ke zuciya ta Allah ka biya min dikkan buqatu na na alkairi Ka sa Yaya Jabeer ya zama shine mafi alkairi a rayuwa ta duniya da lahira....." Wannan addu'ar ce tafi daukan hankali na, nace tooooo waye kuma Yaya Jabeer? Addu'ar ta ta ci gaba bayan ta gama ta yi wa iyayen ta da yan uwan ta da dikkan muslmi, bayan ta idar ne ta hau karanta Qur'ani da zazzaqar muryar ta, har aka kira sallah ta gabatar da sallar asuba ta dora da azkar da karatu har gari ya waye, a sannan ne ta samu ta dan koma bacci zuwa qarfe takwas ta tashi, ta fara taya Maman ta aiki, bayan ta gama gyara gidan dan ba su ke girki ba balle ta taya ta aikin girki, wanka ta shiga ta fito,haka nan taji tana son yin kwalliya yau dan ita ba ma'abociyar yin kwalliya bane  a koda yaushe,sai lokaci lokaci ta kan dan taɓa ,ta na gama  sheqa kwalliyar ta me kyau ta buɗe akwatin ta ta dakko wata rigar ta doguwa ta atampa ,rigar na da fadi ta qasa ta sama kuma an dan tsuke ta da dogon hannu ,jujjuya rigar ta yi ta kara ta a jikin ta kafin daga baya cikin murmushi ta saka rigar,yanda rigar ta zauna mata abin kallo ne domin Juwairah  akwai shape mai kyau, gyara gashin kanta ta yi da kyar dan yawan shi da tsahon shi ke wahal da ita wajen kula da shi, bayan ta gama ne ta kafa dauri me kyau, ta samu tiraren ta da Mama ta bata ta fesa, tana gamawa ta je wajen Maman ta ta na wani yanga ta na nuna mata yau fa Allah ya yarda 'yar ta ta yi kwalliya, ta duqa zata dau Ammar, cikin tsokana irin na tsakanin 'ya da uwar da suka shaqu da juna Mama ta ce, " A'a kaga Juwairere saraunuyar mata,Juwairere  diyar Mamanta gaye ne aka sha haka yau, to ko dai suruki na ne zai zo?" Cike da shagwaba da nuna jin kunyar Maman nata Juwairiyyah ta ce, "Haba Mama wanne irin suruki kuma,kawai dai na yi sha'awar na yi kwalliya ne yau, kuma ni mama na ce maki bana son Juwairere  Allah dariya qawayena suke min in suka zo sukaji kina fada musamman Nafeesa" Cikin 'yar dariya Mama ta ce, "To in banda abinki Nafi ai qanwar ki ce kin fa bata kwana bakwai masu kyau dan haka data tsokane ki sai ki yi murmushi irin na manyan yayu saboda yarinta ce ba wani abu ba" Dariya suka saka a tare, sosai suke dariya abun su gwanin sha'awa,Goggo Sarai ce ta ja dogon tsaki ta ci gaba da aikin ta,a tunanin ta Mama Balkin na tsokanar ta ne kawai su na yi ne dan su bata haushi , ba tare da sun ji sallama ba Juwairiyyah ta ji an kama hancin ta, muryar da ta ke tsakanin buri da muradin ji ce ta ce mata, "Wannan dariyar taku Mama ba zata bari kuji komai ba , musamman wannan Juwaireren da ta buɗe wannan qaramin bakin nata take cika wa mutane gida da qara da wata Muryar ta se kace ta kanari" Tsalle ta soma yi na murnar ganin Yayan nata sannan ta kama hannayen shi dika biyun a nata ta na kallon kyakkyawar fuskar shi da ta yi kewa ta ce, " Yayana, wayyo Yayana kaine da gaske? I missed u so much Yayana, yaushe ka dawo? " " Oh Juwaiiraah ko zama bai yi ba fa wannan zumud'i da tambayoyi a bari ya ɗan zauna ya huta mana" "Mama rabu da ita nima ba qaramin Missing din Juwairere na na yi ba, ban ga laifin ta ba dan ta nuna murnar ta na gani na" Murmushi Mama ta yi sannan ta fita d'ebo masa ɗan ruwa ya sha dan gidan haka suka tashi ko na karyawa ba a miqo masu ba, jawo ta ya yi kusa da shi sannan ya ce, " Amma da Juwairere kin san na hana kwalliya ko?what if wani ya zo ya gan min kwalliyar mata ta? Ko a aike ki a haka kowa ya kallen min ke? A gaskiya ni dai bana so, ba wannan ba ma dai yanzu ai ta qare tinda ga angon ki nan ya gani kuma ya yaba kwalliya ta yi dari bisa dari" Duqar da kan ta ta yi qasa wata iriyar  murna da farin ciki na ratsa ta tunda ta ji ya  kira kanshi angon ta, ga hannun ta da yake murzawa a hankali, karɓe hannun ta ta yi ta canja mazauni tana turo baki, ita a dole fushi ta fara,Mama ce ta shigo ɗauke da kofi a hannun ta ta aje masa a gaban shi ta samu wajen zama, " Mama kin ga wannan yar rigimar ta turo baki, lallai akwai magana a cikin shi" " A'a ni kam ba ruwana ina gefe ba a shiga tsakanin ku ai ku se mutum ya ji kunya" komawa ya yi kusa da ita ya d'ago kanta ya na kallon kyakkyawar fuskar ta da ya ke jin zai iya shekara ya na kallon ta ba tare da ya gaji ba, "Juwairere na me ya faru?" Cikin 'yar kwallar da ta daddage ta taro a idon ta da ya sha kwalli ta ce, "To ba ga shi nan ba wai Juwairere, ni Allah bana son sunan nan,gaba ɗaya kun sa Nafee na tsokana ta, Kullum ta ganni sai ta hau ce man Juwairere " Ta qarasa maganar 'yar kwallar ta na qarasa sauka a kuncin ta bakin nan a gaba, dariya ta bashi ba kadan ba wauta da shagwabar ta na burge shi sosai "Ki kwantar da hankalin ki princess ba zan qara faɗa ba inshaa Allah sai munyi aure" Hararar wasa ta masa tare da jin kunyar kalmar aure da ya ce, sai kawai ta miqe ta fita a dakin da gudu tai tsakar gid tana dariya, kad'a kai Mama ta yi sannan tace "Ni Allah dariya kuke bani yaran nan, kun iya wauta da yawa" Cikin wata iriyar murya jabeer ya ce, " Mama kenan ba wauta bane da gaske auren ta nake son yi, amma idan Baba zai ban ita, ko ita ɗin ma Abuja za a kai ta? Dan na ji an maida sunan gidan nan wai gidan 'YAN ABUJA saboda yaran gidan a Abuja suke son yin aure su kalar Abuja ne, ina jin haka hankali na ya tashi ina fatan Allah ya sa ba Juwairere na a cikin wannan haukan, dalilin zuwana kenan Mama wato na yad'a manufa ta na son auren Juwairiyyah, na ji a wajen Innar mu wai har an kawo kuɗin Auren wadan can marasa kunyar" "Hhmmm haka ne Jabeer amma kasan ni ba ruwana da wannan kalmar ta 'YAN ABUJA ko? Duk inda mijin Juwairiyyah yake ina fatan ya kasance miji na gari mai addini wanda zai riqe min ita da amana ,kuma wannan magana ta Abuja su da kan su yaran gidan nan duka qirqirar wa kan su ita wai su  YAN ABUJA NE ba zasu auri kowa ba sai ɗan can, in su suna faɗa kuma sun yarda zasu aure su ni ban faɗa ba, kuma ban ba 'yata izinin kiran kanta da 'YAR ABUJA ba , in da rabon can ne gidan auren ta yake Allah ya zab'a mafi alkairi in ba can bane ni ko ina albarka na ke nema mata kullum" " Haka ne Mama, Allah ya shige mana gaba" "Ameeén ya Allah Jabeer" Jabeer dan gidan Yaya Balarabe ne ya dawo daga bautar qasa inda aka tura shi illorin, ya kammala karatin shi bangaren kasuwanci, to a yanzu haka yana taɓa saida jakunkuna da takalma, ba wani arziqi ne da shi ba, yayun ta sun so matuqa ace me kuɗi ne da sun aure shi ko dan kyawun shi, amma inaaaa talauci a cewar su ya dakushe tauraruwar shi. A yan kwanakin nan kusan kullum sai ya zo gidan su Juwairiyyah ,ga saurayin Salma mai baqin naci shima kullum ya na tafe, shi ma d'an Abuja ne ya na sana'ar saida motoci, kullum in zai zo zance se ku ga ya baza uwar riga ya shigo mota mai tsada ya zo amma fa baya bata ko sisi, wataran ne ma zai dan samu ya siyo mata yar shawarma kamar mayya tana rawar kai saurayi ya siyo mata abu ta amshe ta shigo gida,itama tini ta bi sahun manyan ta amsar kudin maza da basu jiki ai tabe2 , Alhajin da ke son ta shima in yazo zancen haka yake gama lalube ta ya yi gaba abun shi......... [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼   YAN ABUJA.  💅🏼 WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH Page 3: An saka ranar auren su gaba ɗayan su nan da wata ɗaya, gori kam da baqaqen maganganu ba irin wanda Juwairah bata karb'a a ba wajen 'yan uwan ta, tin tana kuka har ta kai ta daina sai dai ta kauda kai su yi tayi ranta na quna, takan ji kamar ta ce Ya Jabeer ya fito ayi auren su tare amma ba za ta iya ba saboda kunya, kuma ko ba komai ai shi ne namiji shi ya kamata ya fara magana. Wata rana ta na zaune tana yanka alayyahu wa Maman ta sai Adda Suwaiba ta fito ita da Salma,a tare suka kalli Juwairah suka sheqe  da dariyar shaqiyanci sannan Salmah ta ce wa suwaibah, "Hhhhhhh Adda dan Allah ki ga yarinyar nan, a kyau dai duk gidanan albarka tafi kowa, amma wai ta tsaya ta mori kyawun na ta inaaa ba rabo, ta tsaya ta na yi wa kanta baqin ciki da mugunta , ban taba ganin irin wannan yarinya ba" Suwaibah ce ta yatsine fuska kafin ta ce, "Hhmmm ina ruwan ki uwar kinibibi taje ta auri wanda ta gadama ma ba Jabeer ba, danni bari ki ji, ba kyau ba, ba ilimi ba, in dai baka da farare bugun Abuja, sannan ba zaka aure ni ka kai ni Abuja ba kayi kyawun banza da kyawun halin wofi, dan ba su zan ci ba ah toh, ai ka auri me nera wanda za ka ci me kyau ka sha me kyau ka kwanta a qaton gida mai kyau shi ne magana" Tafawa suka sake yi su na dariya tare da riqe baki kamar wasu 'yan daudu su a dole sun ma ta rashin mutunci, girgiza kai Juwairiyyah ta yi tace " Adda Suwai kenan, ina kyautata zaton kun manta wa keyi, sannan kun manta dawa kuke jayayya, wanda duk zai wa wani gorin talauci to ya sani ba da wannan bawan yake ba da ubangijin bawan yake yi, bayan haka ba fa kusan sana'ar mazajen ku ba gaba ki dayan ku damuwar ku kawai a kai ku Abuja, ku kawai matan Abuja ne, matan manya, bana maku baqin ciki, zanfi murna ace kuna gidan hutu dan nima ina ma kaina fatan hutawa, amma zan baqin ciki ace baku da alkibla saita kudi da son abun duniya, Allah ya kyauta, ammmm for ur information, ni haka nake son Yah Jabeer ba dan dukiyar shi ba ba dan komai ba , Son shi ni kaina ba zan ce ga daga in da ya fito ba, na tsinci kaina ne da So da qaunar shi tun kafin na san menene so da qaunar kan su,dan haka wannan matsalar ku ce wai rashin kudin shi, tinda ya zama jinin jikina ba zan iya rayuwa ba shi ba kun ga ko ko a wanne hali yake zan iya zama da abu na mtwss" Tafi ta ji ana yi mai cike da shauqi idon Jabeer tap kwallar dad'i da murna da farin ciki, Mama na d'aka tana mamakin yanda 'yarta ta ta iya zaro magana haka, lallai yau an kaita maqura kenan, Juwairiyyah ce ta d'aga kai ta ga Jabeer yana qarasowa gaban ta, wata irin kunya ta ji ta lullub'e ta da ko guduwa daga wajen ma kasawa ta yi, dan tinda suke bata taba zayyane masa yanda take son shi ba se dai ya na ganin alamu, kafad'un ta ya riqe ya juya ya kalli su suwaiba, inda suka qame qam suna wurga idanu alamun rashin gaskiya dan kuwa ya musu zuwan bazata, shi kan shi be san zai zo ba ya na komawa gida ne ya yi tunanin ya gan ta shi ne ya biyo,murmushi ya yi ya ce, "Princess wad'annan kalaman naki sun qara dasa man zazzafar qaunar ki da son ki akan na da, ba zan iya rayuwa ba ke ba nima, dan haka nake roqon Abba da ya taimaka ya aura min ke nima a haɗa gaba ɗaya da na waɗannan fitsararrun marasa tarbiyyar, ba dan komai ba sai dan a kafa tarihi an yi auren ku tare kar muzo lissafi yana kwace mana Ko ba haka ba Suwai?" Murguda baki Suwai ta yi ta na qunquni ta wuce d'aki, tsugunnawa Jabeer ya yi a gaban Juwairiyyah ya ci gaba da taya ta aikin yanka alayyahun,ita dai kunya ta ishe ta a haka suka gama yiwa mama girki ko leqawa gaida maman bai ba ita ma Maman ta kasa fitowa dan komai akan kunnen ta aka yi, Abba ne ya shigo da sallama bayan sun amsa ne yace, " A'a Juwaira !Jabeer ! yau kune kuke mana abincin daren? " Ya faɗa cikin dariya, sosa qeya Jabeer ya yi ita kuma Juwairyyah ta rufe fuska ta je ta amshi ledar hannun Abban, ta yi d'akin Mamar ta da shi, ta na shiga ta ga dakin ya sha gyara har da qamshin tiraren wuta irin na tsinke, Maman ce ta zo ta wuce su da ruwa a bokiti kanta a qasa dan yau dai yaran sun bata kunya sosai, Jabeer ya na dariya yace, " Hajiya Maman mu yau kuma kunya ta kk ji ne? Shi yasa sai yanzu ki ke fitowa da kk ji Abba ko? Ai dana sani to tafiya na yi da muka gama hirar tamu" Soson hannun ta ta wurga masa ta ce, "Wannan d'anneman tsokannen dole se ya sa ni  magana duk kauda kaina da na ke yi wato dai sai ka nuna min kai ɗan zamani ne ko? Ai gashi kun ja min makara yin wanka sai da Abban nasu ya dawo" Dariya suka yi dikan su, Abban ne ke tambayar me ya faru ne, da hanzari  Juwaira tace, "Ba...ba..komai Abba hira kawai ake yi" Dariya Mama da Jabeer sukai Mama ta wuce su Jabeer ne ya ce, "Abba ka huta akwai magana a bakinnan nawa mai mahimmanci, ni dai in ke ba ki da abin cewa ni ina da shi yarinya," Roqon shi take da ido akan ya bari sai gobe yau kunyar zata mata yawa, amma se ya kanne ido ɗaya yana mata gwalo, shi fa ba ruwan shi sai ya faɗa a yau, tura baki ta yi ta wuce daki, bayan sun gama komai taa yi wanka sunci abinci, in da wajen cin abincin ma Jabeer rashin ta ido ya so yi ta qi bashi haɗin kai, wai shi da sai dai suci a kwano daya, da taqi sai ya zauna kusa da ita, in ya faki idon kowa sai ya zura hannu a nata ya d'iba ya kai bakin shi yana lumshe ido, can sai yace, " Ke ni fa ban yarda ba ya akai naki ya fi dad'i? " Cikin muryar shagwab'ar da ta zame mata jiki ta ce, "Kai Ya Jabeer da rigima kk, ni duk d'aya ne kai ne  dai ka ji haka" "To kawo mu yi canjen kwano in dai  ki na da gaskiya baki qara komai a naki ba" Miqa masa nata ta yi ya bata nashi suka ci gaba da cin abincin su, can ya qara zura hannu a wancan da ya bata, ya debo  ya ci har ya na wani lumshe idanun shi ya Kalle ta ya ce, " Tab in ba sai an qara canjawa ba me ki ke fakar idona ki ke sawa naki ne wai?" Cike da muryar da ke nuna alamun ta na so ta yi kuka ta ce, "Yahhhhh Jabeerrrr" Ta qarasa tana turo baki cike da shagwaba,Abbah ne ya Kalle su ya ce, "Wai ni da ka ke wannan maganar ta ya aka yi kasan nata yafi dadi?" Saurin tashi zata yi daga wajen ya sa hannun shi ya danne hannun ta dole ta koma ta zauna kan ta a qasa saboda kunya, " Abba loma d'ai-d'ai na yi a dikka kwanon na ji" "Abbah yafi loma ɗaya ya yi" " Hmmm Abban su dan Allah ka rabu da shirgin yaran nan mu ci abincin mu bana son kana wasa da cin abinci kar wani ciwon ya kama mana kai" Jabeer  ne ya kashe wa Juwairyyah ido tare da matsa wa kusa da ita,ya kai bakin shi daidai kunnen ta ya ce, " To kin ji yanda ake wa miji ko, sauran mu yi aure kina raba mana kwanon abinci irin haka" Dariya ta gimtse, kamar daga sama suka ji muryar Goggo Sarai na faɗin, "Hmmmmmm bariki kenan, watohar da 'Ya'yan ake zaune ake iskanci a tsakar gida, sannan in nawa yaran sun fita ace masu yan iska, to ai bahaushe yace, qazantar da baka gani ba tsafta ce" Cikin jimanta maganar ta Abbah ya ce, "Subhanallahi, me kk fada ne ke kuwa a gaban yara,kin wani tattaro su gaba ɗaya  kun taho, ina za ku je haka?" " Eh abinda ka ji na faɗa mana ko maimaici ka ke buqata na qara karanto maka?" "To bari kiji mara kunya, Jabeer ya tabbatar man da auren Juwaira yake son ya yi, yana son a haɗa dana sauran ayi baki daya kuma a rana ɗaya, dan haka wannan shiriritar taki da gore-goren taki ta tsaya haka,ya ishe ki haka, duk abinda ki ke a gidan nan ina sane da shi" "Aiko ba wanda ya isa ya haɗa mana aure da wadannan yan maulan" Kan suwaibah ta rufe baki ta ji duka fauuu an make bakin da qarfi, saida bakin ya yi jini, cikin masifa da bala'i Goggo ta ce, " Kan uban nan Jabeer me suwaiban ta yi maka da zaka mata wannan dukan, ko uwar ka Hansai ba zata yi ma 'yata hukun ci ba  a gaba na balle Uban ka Balarabe" Wani dukan ya sake  kai wa Saudat dake kusa da shi sosai mai qarfin da ya fi na Suwaibah dan kuwa sai da ta kifa ta yi taga taga za ta fadi Goggo ta taro ta, cikin ɓacin rai Jabeer ya nuna Goggo ya ce, "Duk rashin kunyar da ki ka yi ma Abba kan 'Ya'yan ki marasa tarbiyya zan fanshe" Salma cikin d'aga murya ta hayayyaqo wa Jabeer ta na faɗin, "Sannu uban mu, se ka kashe mu idan ka tashi" Aikuwa bata rufe baki ba ya cire  takalmin qafar shi ya murde hannun ta ya yi ta maka mata shi a duk inda ya samu, sai ihu take ta na neman taimako,  Abbah na gani be ce komai ba dan ya jima ya na so shima ya yi musu duka da kan shi amma bai samu dama ba, Jabeer kamar taimakon shi ya yi Goggo ce taje da niyyar kwace Salma a hannun Jabeer ya sakar mata wani kallo da ya sa hantar cikin ta ta kad'a ta yi baya da sauri tana faɗin, " Allah ya isan su baqin mugu kawai" Sakin ta ya yi ya sa takalmin shi ya yi waje ba tare da ya kula kowa ba, Abba, Mama da Juwairah da idon ta ya cika da hawaye suka shige daki suma suka rufe qofa suka bar su nan tsaye su na cika su na batsewa tare da zage zagen rashin mutunci....... *************************** Washe gari sai ga Baba Balarabe yazo batin auren Juwaira da Jabeer, sadaki dubu ashirin, a taqaice dai dubu Hamsin ya miqa masu kudin komai dan iya su ya ke da,  take ita ma aka shaida hada bikin su dana yan uwan ta, sunyi murna sosai, inda suka sha gorin cewar " dadin ta kudin auren ma kamar anje siyan yar tsana a gwanjo dan ko matsayin kasuwa ma ba a samu ba" suna yi suna dariyar rainin hankali, ba wanda ya kula su, sauran dubu darin da yake da ita kayan gado masu sauqin kudi yaje ya siyo mata da kujeru, irin na talakawannan, Jabeer ya yi qoqari sosai Abba na ta hana shi amma ya qi, karshe cewa Abbah ya yi ai dama a musulunci haqqin miji ne duk wadannan amma al'ada ta sauya abun, dan haka na bar ku da siyan yan kayayyakin kitchen, Allah ya hore mana mu samu aiki mai kyau Abba kasuwancin nawa ya bude, komai zai zama tarihi, addu'a sosai Abban ya masa tare da godiya. Daki aka gyara mata a main house din su ya kewaye mata guda biyu da dan wani qaramin waje a matsayin kitchen sai wani budadden bandaki mara rifi daga cikin kewayen nasu dai, ba laifi daidai talaka, yanzu jiran ranar biki sike nan da 'yan satika. ************************** A yau ne dimbin mutane manya masu manyan motoci da qanan mutane marasa abun hannun suka shaida daurin auren wadannan bayin Allah kamar haka, Suwaiba da Alhajin ta Salihu mai tumbin Nera, Saudat da Alhaji Kalla na Abuja, Sai Salma da Alhaji Mansur, sannan kuma qaramar su Juwaira da Jabeer din ta, surutu kala2 ke yawo a tsakanin mutane wasu na sanya alkairi, wadan da suke bin bashin magana kuma suna gulmammaki akan su Suwaiba sun dakko ruwan dafa kan su ne basu sani ba dan kuwa manyan attajirai ne mazan nasu ba na wasa ba, Juwairiyyah kuwa bata da wayo, duk kyaun ta ta buge da auren talaka? Kowa dai da abinda yake fada, a haka aka tashi daga daurin aure, inda mazajen su Suwaiba suka ce su fa basu yarda ai komai a kano ba Abuja za a wuce ai dinna babba mai qayatar wa da abokan su, sai matan abokan su, ko dangin su ba za a dauki ko ɗaya ba dan kuwa abin na manya ne, shi dai mijin Salma shima cewa ya yi a bashi matar shi ya wuce da ita Abuja domin shi ba abokin mijin su Suwaiba bane tafiyar shi daban,sai dai mazajen su Suwaiba sun roqe shi akan yaje ai komai tare yaqi, dan haka kawai kauda maganar ya yi yace zasu tafi ba damuwa dangin shi da abokai na jiran shi za ai dinner, Ita kuma Juwaira sun yi yar walima kafin dare aka gama, YAN ABUJA kuwa jiki na rawa da daren  aka shirya su Goggo na kuka suna kuka suka fita suka shiga manyan motoci aka kai su filin jirgi suka d'aga sai ABUJA. Bayan tafiyar su Suwaiba kuma Juwaira ce zaune a gaban Innar ta da tazo biki mai suna Inna Dije tana qara bata yan kayayyakin matan da ta haɗa da natural abubuwan mu na abinci,wanda ta hada madara da zuma da ta sha dakakken kayan qamshi cikin babban kofi tace ta shanye, dama ta yini da yunwa tini ta shanye tsaf, ta qara mata da dafaffiyar kaza da ta sha kayan qamshi itama ta ci iya itawar ta, ( ita ni'imar mace ana son ta da dumi yan uwa, ba a son ni'ima da sanyi, dalilin haka ne ake son muna yawai ta amfani da kayan qamshi su citta kaninfari masoro, da dai sauran su, suna saukar da dumi ga jikin mace, ko had'in su kankana da su cucumber, ko mai  mutum zai ci ko ya sha na garin ni'imar yana hadawa da kayan qamshi, suna qara mai daɗi da qamshi da amfani a jiki,) a haka aka sa ta gaba ta yi wanka me kyau da dan tiraren su na wanka dan d'uri, dan basu da arziqin siyan mai tsada, a cikin makewayin ta samu ruwan d'umi mai had'in ganyen magarya da kaninfari kadan da turaren almiski a ciki ta yi tsarki da shi sai qamshi ke tashi ko ta ina, tana fitowa Inna Dje ta bata misk mai kyau ta qara sawa a HQ ɗin ta,sannan ta miqa mata brush din ta ta wanke baki duk tana tsaye a kanta, ita ko kunya duk ta dame ta ga mutane ba a gama tafiya ba, ai ko tana gama wa ta sata ta yi alwala suka yi d'aki batansa ta shafa wani kwalliya mai nauyi ba, iyaka ta gyara ta ta samata qanan kaya daga ciki riga da skirt masu matuqar kyau, sannan ta sa mata laffaya a sama ta yi mata nadi me kyau, ga wani irin qamshi na tashi ko ta ina, kunshin nan ya zanu kannan ya dau gyara na musamman , yan daukar amarya ne suka zo a mota biyu, tana kuka tana komai aka fiddata, wata goggon Su ce mai suna Kareema tace, "Yanzu Bilki ba wata yar nasiha haka za a fidda ta zuwa gidan miji baku mata ba ke da yaya?" " Hmmm Kareema kenan, ai Juwaira bata buqatar wannan, Alhamdulillah na san wacece Juwairere na,yanzu nasiha ta ma ba zai mata amfani ba, ta je gidan mijin ta da sawar  albarkar mu a rayuwar su dika" A haka ta tafi daki ta zauna saboda yanda take jin zuciyar ta, ta na zama a bakin gadon ta kuwa sai hawayen rabuwa da 'yarta take abar son ta, an kai Juwaira lafiya d'akin ta, daga nan kuma kowa ya kama hanya ya dawo wasu suka wuce gidajen su,ita kuwa an barta daga ita sai halin ta tana ta zare ido dan hawayen sun qare mata tasss,ba abinda take ambata da ya wuce sunayen Allah ta na nan zaune tana tunanin gida tare da jiran ta ga ta inda angon nata zai bullo...... [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA    💅🏼     WRITTEN BY HAERMEEBRAEH *SANARWA ! SANARWA !* *Ina masu buqatar sanin yanda za su gyara jikin su ta ciki da waje? Ina nufin daga gashin  kan su zuwa yatsun qafar su da qarin ni'imar jikin su?* *Ina masu son koyon sana'o'i dan samun taro da sisi? To 'yar uwa matso kusa ba sai kin biya maqudan kuɗi ba dan ki koyi yanda Zaki yi sana'ar da zata sama maki kuɗi da #1k kacal za ki mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA* *Idan kuma ke ma'abociyar karanta littafan Hausa ce ki yi wa HAERMEEBRAEH ❤️magana kai tsaye ta wannan No 09031416423 kai tsaye, Zaki samu Littafin MAHREEN DA KYAKKYAWAR FAHIMTA a kan farashi #500 each* *Please share*❤️ Page 4: Tana cikin wannan yanayi na tinanin Maman ta da Ammar taji hayaniyar maza na shigowa, sauri ta yi ta fito daga uwar d'akin ta da aka ajiye ta ta dawo palour ta zauna dan bata yarda wasu maza su shiga mata har dakin baccin su ba da sunan rakiyar ango dakin Amaryar shi, zama ta yi da sauri ta nad'e qafafun ta a kujerar ta rufe kanta har zuwa fuskar ta, Sallama suka yi suka shiga,dama akwai wasu daga abokan shi da basu san ta ba dan ba garin a suke ba da zama suna so su ga matar da Jabeer ya aura duba da cewa shi baya biye wa 'yan mata duk da yanda suke kai kan su gare shi kuwa. Amsa sallamar su Juwairiyyah ta yi da muryar ta mai daɗin sauraro kanta na qasa, tana tsaka da murna tare da jin daɗin babu wutar lantarki ba lallai su gani ta  ba sai nepa suka maida wutar,nan take haske ya gauraye ko ina, ai ko da sauri ta qara duqunqunewa a cikin laffayar ta ta na jin kunyar su, cikin ran ta ta na zagin Nafee da ta tafi ta barta ita ɗaya tunda ita ba wasu qawaye gare ta ba sosai, qawar ta ɗaya bayan Nafee Ita ce Shamsiyya kuma ta yi aure har da haihuwa,dariya suka yi gaba daya abokan angon har da angon,babban abokin ango ne ya ce, "To amarya ki kwantar da hankalin ki mu ba zamu takura sai kin bude mana fuskar ki ba,mallakin ango ki ce,kuma  angon naki ne ki zai bude maki da kanshi in mun tafi, sai dai akwai wasu shawarwari da nake son baku ke da angon naki  wanda na san kin san da dama daga abubuwan zamantakewar aure duba da gidan tarbiyyar da ki ka fito,ni na san ke wacece Indai ta bangaren sanin ya kamata ne, abinda zan ɗan maku nasiha akai mata da mazan wannan zamanin su na wasa da shi kuma ya na rusa aure,abun nan ba wani abu bane face, mantawa da sauke haqqin juna ko kuma na ce dena sauke haqqin juna,ta bangaren namiji sai ki ga da an kwana biyu ya daina dokin amaryar shi, sai ya fara fito mata da halayen shi mara kyau na kwadayin son ya zamana ta fara taimakawa gidan dan ya samu sauqin dawainiya wanda Allah ne ya ɗora masa wannan nauyin amma yake so ya sauke. Ba a ce mace karta taimaka wa mijin ta ba a gudu tare a tsira tare, hakan abune mai kyau dan zai qara mata samun lada mai yawa, sannan zata samu soyayyar mijin ta da yawa, amma abinda ba a so miji ya sa son zuciya ya dinga expecting ɗin matar shi dole dai ta taimaka a gida financially,in bata yi ba a zo rai na baci, yana jin haushin ta, daga nan an samu matsala, ita kuma mace ta bangaren ta kwadayin abun da mijin ta baida halin yi ta ce dole sai ya yi mata, dan ta gani a maqota kama ko jikin qawaye,abun ya kama daga kan sutura, abinci, da abin hawa, sai ta fara nuna halaye na kwadayin abin duniya wataran har ya kai ga tana sabon Allah dan ta samu kudin wadannan abin da ya fi qarfin ta da mijin ta , kinga kenan ta biye wa son zuciya daga nan aure sai ya lalace azo ana samun matsaloli, zan barku anan saboda dare nayi kuma na san amarya ta gaji tana buqatar hutu ko ba haka ba?" Murmushi ta yi kawai mai sauti tace, "Mun gode Allah ya saka da alkairi" " Ameen" Suka amsa gaba daya, anan wani abokin su kuma ya amsa ya yi masu addu'a mai yawa wadda zata yi masu matuqar amfani a rayuwa in Allah ya amsa masu, a haka ne suka ce bari su tafi, ya tashi zai raka su, yana miqewa ya bige yar qara ya yi, Juwairiyyah ta yi sauri ta dago tana mai sannu, ido abokan shi suka zuba mata suna mamakin kyaun matar Jabeer ɗin, ganin haka ne yasanya kishin Jabeer motsa wa cikin haɗe fuska ya sauri ya yi gaba yana fad'in , "To kuzo mu tafi mana" fita suka yi suna zuwa soron gidan yace "To abokai na ni zan koma na gode Allah ya bar mana zumuncin mu da amana" " Ameen" suka amsa, wani ne a cikin su cikin tsokana ya ce, " kai dai ba sai ka kore mu ba muma sauri muke yi dare ya yi muna da mata kai da ma farin shiga ne a wannan lamari na aure,amma gaba ɗaya ka matsu ka koma ba zaka iya koda qara second ɗaya bane anan" Dariya suka yi gaba ɗayan su Jabeer kuwa ya yi wuf ya shige yana daga masu hannu, sai da ya rufe gidan sannan ya leqa sashen iyayen shi ya ji shiru da alama sun kwanta bacci, direct sashen su ya wuce,ko da ya shiga sai ya tadda Juwairiyyah Zaune ta haɗe kai da quiwar qafar ta, bayan ya yi sallama ta amsa ne ya qarasa shiga ciki, kusa da Ita Jabeer ya je  ya tsugunna ya na bin dukkan jikin ta da kallo a hankali ya sa hannun shi ya riqe nata ya na murza wa, yanda nunfashin shi ke sauka a kan hannayen ta daya riqe ne ya sa zuciyar ta sauri wajen bugawa, ga wani irin tsoro shi da take ji a lokaci d'aya kuma  wani feelings sabo da bata taɓa jin irin shi ba ya na shigar ta, " Princess kin ga yanda ki ka yi kyau kuwa? Ba dan kar na yi qarya ba da sai nace tinda nake a duniya ban taba ganin kyakkyawa irin ki ba" Cikin sarqewar murya ta furta , "Kai Yah Jabeer wannan kowa ya ji ya san daɗin baki ne kawai ka ke min" Matsawa ya qarayi sosai fuskokin su na daf da na junan su, sannan yace, " Hmmm ke ki ka ga hakan amma ni iya gaskiya ta na fada" Wani irin abu ta ji  a jikin ta wanda bata taba jin irin shi ba ya na mata yawo daga kanta zuwa qafafun ta, 'Dama wannan ne rayuwar auren da ake faɗa ana tsorata mutane?, da na zaci wata azabar ake sha kamar yanda shamsiyya da akai wa aure ta faɗa min ni da Nafee, Dafa ta Jabeer ya yi sannan ya ce mata, "Me ki ke tinani haka" Ya qarasa faɗa ya na ɗora labb'an shi Saman nata,da sauri ta miqe tsaye ta yi breaking kiss din da yaso ya yi mata, ta hau kame2 tama rasa ina zata shiga, d'aki zata ko waje zata yi ne? kamo kafadun ta ya yi dika biyun ya miqar da ita tsaye a jikin bangon da kusa da bed room din su. " calm down my princess, na ga kina tsoro na kamar wani dodo" Murmushi ta yi na yaqe sannan  tace, " Yah bacci nake ji jikina ciwo yake min" " Ok to muje ki yi alwala mu yi nafila sai ki samu ki rage kayan jikin ki mu kwanta zan maki tausa ma in ki na so" Baki na rawa cike da sauri  da in-ina tace, " Aaaa..... bama....bama sai .. ka min tausaaa ba " Dariya ya yi mata ganin yanda hankalin ta ya tashi kamar wadda ya yi wa wani abun, alwala suka yi sannan ya ja  su suka yi salla raka'a biyu bayan sun idar ne ya kama kanta, ya fara kwararo addu'o'in da suka zo a sunna ana yi wa amare,kamar haka, " Allahumma innee as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha a laihi wa a'udhu bika min sharri ha wa sharri ma jabaltaha alaihi" Bayan sun gama ne ya koma palour inda ya ga an jera mata plates a 'yar qaramar  kitchenware ɗin ta ya dakko sannan ya dauki ledar da abokan shi suka aje masa mai kaza a ciki ya shiga d'akin, zama ya yi a gefen ta ya juye masu kazar a plate wadda aka gasa  ta aka zuba soyayyan chips din da yasha hadin hanta da kayan kamshi, ga attaruhu da albasa sai tashin qamshi suke yi, kamshin ne duk ya karade d'akin har ya yi sanadiyyar motsa mata da yunwar da take tare da ita, madara mai sanyi ya zaro a Leda ya ajiye a gefe da jus ɗin exotic na kamfanin Dansa, niyyar ta ta qi ci, dan qawar ta Shamsiyya ta ce in an bata kar ta ci, in taci sai ta biya shi da jikin ta,amma ina Juwairiyyah ba zata iya jure kamshin fa ke dukan hanci ta ba har ya yi sanadiyyar farfaɗo mata da yunwar ba,cikin ran ta take ayyana, 'Yana bani zan amshe ba zan iya fulako  ba ina dalili? iyaka da ya ce na biya shi na fara kuka nasan zai hakura ya kyale ni tun da baya son ɓacin rai na' Kamar Jabeer ya ji huɗubar da ta ke yi wa kan ta ya yanki wata tsoka mai gwab'i ya miqa mata bakin ta, ta kuwa buɗe bakin ya saka mata ta hau tauna wa cike da jin kunya,a haka ya na bata yana ci suka gama cinye wa tasa suka sha madara da jus ɗin su, bayan sun gama ne ya fara qoqarin rage mata kayan jikin ta dan ta ji daɗin bacci a cewar shi. Dan kuwa da kan shi ya zaɓo mata rigar da zata sanya ya ajiye a gefen gadon ya na mata murmshi,wurga ido kawai Juwairiyyah  ke yi ko ta ina ta na mamakin lamarin da ke faruwa,a hankali idanun ta suka fara cikowa da ruwa, Jabeer na kula da haka ya sakar mata riga da ya kama zai taya ta cire wa, baƙin ta na rawa ta furta, "Yah Ka bar ni na cire da kai na," " Ok cire ki kwanta dare ya yi" Sai ya ja baya ya je ya fara cire nashi kayan ya saka na bacci a gaban ta, a lokacin da ya cire rigar da wandon shi a gaban ta ba ko kunya sai ta zaro ido waje ta na sake mamakin abubuwan da ta ga Jabeer na yi ba ya ko jin nauyin ta, hankalin ta ya yi mugun tashi dan ganin yanda jikin shi yake a murd'e kamar na masu ɗaukan qarfe,take jikin ta ya fara bari ta yi saurin kauda kai gefe, cike da tsokana kuwa Jabeer ya ce, " Ki na son abinda ki ka gani ne? " Da hanzari Juwairiyyah ta sake juya masa baya ta ce, " No i don't, in fact banga komai bama ni, ba kuma na so na ga ni" Muryar ta na rawa ta qarasa maganar,Jabeer kuwa cewa ya yi, "A gskiya Naseer ya kyauta min da ya mata min na yi wanka kan mu zo amma da ban san ya zan ba yanzu dan a matse nake zuwa wankannan batan lokaci za yi" Zaro ido ta qara yi kamar za su fado qasa, ta ce, " Yah to ka tashi ka je toilet mana tinda ka matsu?" Murmushi ya yi mai sauti sannan ya ce, " Hmmmm gama ki ga me nake nufi" Tare da kashe mata ido ɗaya ,take hankalin ta ya tashi dan ta gano me yake nufi yanzu, a hankali ta d'au kayan ta zata fita palour ta canjo ta dawo amma Jabeer ya hana ya ce anan a gaban shi zata sauya,ba yanda ta iya a dole haka ta sauya kayan ta a gaban shi, sai binta yake da kallo kamar wani maye,ta na gamawa ta zauna bakin gado ta yi addu'ar bacci ta shafa a jikina ta, ta kwanta a farkon gadon kamar a ce kyat ta zura da gudu,gashi basu baro gida an kawo ta d'akin miji ba sai da Inna Deeje ta sanya ta yi mata alqawarin bazata guji mijin ta ba , zata bashi duk abinda ya nema a wajen ta mudin bai sab'awa Allah ba, janyo ta ya yi jikin shi, yana shinshina qamshin ta, Cikin dasasshiyar murya Jabeer ya ce, " kaiii amma princess gaba ɗaya qamshin nan ya sa na qara qaguwa na kasance da ke" Shafa ta ya fara yi yana mata salon da ita kanta ba zata so ya daina ba, a wannan lokacin Yah Jabeer ya fara qoqarin cika aiki, sai ta ji ya fara addu'a ta saduwa da iyali, kamar haka, " Bismillahi Allahumma janibnash-shaidhana wa jannibash-shaidhana ma razaqtana" Kukan da take son yi ta mayar ta had'iye, bata qaunar yin abinda da zai b'ata ranshi ya fasa cimma burin shi,amma daga qarshe dai dole da kuka da roqo da aka tashi wasan, har cewa ta yi tama fasa son nashi, tinda haka ne abin baya tausayin ta, bayan komai ya dawo masu daidai ne ya mannata da qirjin shi yana mata addu'o'i da saka albarkan da ya faranta ranta matuqa, hakan da ya yi mata ya nuna mata mahimmancin kawo budurcin ta da ta yi lafiya gidan auren ta , da kuma  illar abinda da zai same ta da bata kawo ba din, kuka take ta yi qasa qasa, Jabeer sai ya tashi ya saka kayan shi ya fita ya haɗa mata ruwa mai dumi ya dawo ya ɗauke ta ya kai ta bayin su da ya kewaye masu su kaɗai ya sata cikin roba mai faɗi da ya zuba ruwan. Godiya Juwairiyyah ta yi masa dan kuwa ta ji daɗin ruwan sosai bayan sun gama suka yi wankan tsarki suka fito suna koma wa d'akin sai ta hau abin sallah ta tada sallah dan kuwa lokacin qarfe 3:30am ya yi, sallolin nafilar ta ta yi bayan ta idar ta kwanta ta na tasbihi bacci mai daɗi ya ɗauke ta a wajen,sai shi ya daga ta bayan ya idar da tashi nafilar suka yi baccin su tare da addu'ar Allah ya basu ikon tashi su samu sallar asuba akan lokacin ta...... Ɓangare'YAN ABUJA matan manya kuwa bayan sun sauka a filin jirgi  sai suka tarar da motoci na jiran su, nan aka kwashe su sai babban hotel ɗin da za a yi dinner mai suna Chelsea hotel................. [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA    💅🏼     WRITTEN BY HAERMEEBRAERH *SANARWA ! SANARWA !* *Ina masu buqatar sanin yanda za su gyara jikin su ta ciki da waje? Ina nufin daga gashin  kan su zuwa yatsun qafar su da qarin ni'imar jikin su?* *Ina masu son koyon sana'o'i dan samun taro da sisi? To 'yar uwa matso kusa ba sai kin biya maqudan kuɗi ba dan ki koyi yanda Zaki yi sana'ar da zata sama maki kuɗi da #1k kacal za ki mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA* *Idan kuma ke ma'abociyar karanta littafan Hausa ce ki yi wa HAERMEEBRAEH ❤️magana kai tsaye ta wannan No 09031416423 kai tsaye, Zaki samu Littafin MAHREEN DA KYAKKYAWAR FAHIMTA a kan farashi #500 each* *Please share*❤️ Page 5: Tinda suka je farfajiyar hotel ɗin bakunan su Suwaiba yaqi rufuwa, ganin irin manyan motocin da suke ta gani an parker sai kwadayin arziqi da samun dukiyar su ya ninka na da,basu taɓa ganin manyan motoci haka ba a zahiri sai a American movies, wasu ma basu taba ji ko ganin su ba duk Yawon su da kallace kallacen fina-finan nasu, ( abun ku da masu idon cin nera ga Yawon tsiya gidaje da bukukuwan masu kuɗi) hankalin su ya kai qololuwa wajen kwadayin son suga mahallin su ma'ana wajen da za a kai su ya zama shi ne gidan su. Sun shiga wajen da ake gabatar da dinner tare da angwayen su da abokan angon da suka masu rakiya, inda suka qarasa wajen hight table din da za su zauna, iyakar ganin idanuwan su iya ganin jajayen hulina  da fararen kaya da sirkin ja a jikin farin kayan ne, daga matan har mazan shigar kenan, sune kad'ai suka saka baqin lace da ratsin fari a jiki, mazan su ma farar shadda da jan aiki a jiki da jar hula ne akan su. Wani mutum babba suka gani a gefe mutane kowa ya shiga sai ya gaida shi, ya hakimce a wata qatuwar kujera, suma tashi suka yi suka kai masa gaisuwa sannan suka koma mazaunin su an fara gudanar da dinner lfy, inda daga baya aka umarci kowa yaje ya yi serving kan shi abin da zai ci a wajen, wajen maza daban wajen mata daban,a bangaren Mazan akwai wani irin nama na daban da aka zo dafawa aka masa dahuwar laushi sosai duk abin mutum ba zai gane na meye ba,  matan kuwa kaji ne da sauran tarkace abinci kala2 a wajen har da na qasashen waje, sun ci sun sha, daga baya akai ta rabawa mazan wani ruwa a wata kwalba mai duhun kala, jikin su har rawa yake dan murna, kowa ana bashi yake kafa kai tas zai shanye ya ajiye kwalbar ya na lasar baki. Bayan an yanka cake ne da sauran bidi'o'i aka tashi daga wajen dinner din,daga nan angwayen suka kama matan su suka shigar mota sannan suka ba su wani ruwa a cups masu kyau da sirkin wani magani a ciki, suna sha take bacci ya dauke su, madadin su yi gidajen su na aure da matan sai naga sun ɗauki wata hanya kamar za a bar garin basu tsaya ba sai a dokar daji, wani katafaren gida ne suka isa mai gate guda uku manya, katangar gidan duk maitar mutum na ya gudu ba zai samu dama ba saboda tsayin su, suna isa wasu qattai ne naga sun fito murdaddu sun sha baqaqen kaya da neck tie red, daukar su Suwaiba suka yi a hannu suka shiga da su gidan, a wani qaton parlour suka aje su kan kujeru suka juya suka fita,angwaye kuwa na tsaye su na jiran fitowar Ogan nasu su ji wanne umarni kuma zai basu, ji suka yi wata qatuwar murya ta yi magana, "A kai min ko wacce d'aki, a haɗa su a gado daya," Ko da na duba sai na ga wannan turmusheshen mutumin ne na wajen dinner ya fito ba riga daga shi sai gajeren wando, nan take tunanin inda aka samu telan da ya iya dinka masa wannan wargajejen wandon ya faɗo rai na, ba karamin qaton mutum bane shi ɗin ,gaba ɗaya ya haɗa komai na zama qato ga tsaho ga qiba, ga tumbi, da sanqo, ga gashin baki, gana hammata nan cunkus, ga idonnan jawur, kamar gauta, ba zan taba iya kwatanta girma da yanda yake ba abin sai wanda ya gani kawai, haka ya tako da fataken qafafun shi ya kalli mazajen sukuma sai suka duqa masa alamun gaisuwa, d'aga masu kai ya yi ya ce, " kuje sai nan da sati biyu ku dawo,dan ban taba ganin mata masu kyau irin wannan ba," ya qarasa yana lashe baki, d'aga masa kai suka yi suka amsa da, " Tah oga zaks," Suka furta a tare, fita suka yi kowa hankalin shi kwance dan sun san samun su zai rubanyu da yawa, Nicon hotel suka wuce su hole abun su, dan su dama sunyi auren ne dan gudun maganar mutane, amma ba dan sun damu da auren ba, tinda a cewar su mata na nan kamar jamfa a jos. Shigar Oga Zaks dakin keda wuya ya isa gaban gadon, yana lashe baki, kashe wutar ya yi ya kunna bed side lamp, cire masu kaya ya yi ya dakko wani magani ya shaqa masu, maganin bacci ne, wanda zai kai su kwana bakwai cif suna bacci ba tashi, ina ganin zai zame rugegen gajeren wandonnan nai gaba da gudu, ba dani za ai kallon tashin hankali ba. Oga Zaks ba shi ya fito daga dakin nan ba tin daren sai qarfe tara na safe hamma yake yana miqa ya wani bangare ya shiga wani daki, waya ya yi naji yana, " ku shigo, " Sannan ya aje wayar ya shiga wanka, wasu mata ne dattijai suka shigo, dakin da su Suwaiba suke nan suka shiga, suna gyara su suna tausaya masu, ɗaya daga cikin matan ne tace, "Hmmmm wama ya sani ko garin shegen son abun duniyar su ne suka haɗu da su, ai kinga ban ga laifin mazan da suka kawo su ba kwadayi mabudin wahala" Jikin ajiyar zuciya d'ayar ta furta, "Haka ne kuma Allah dai ya kyauta" Bayan sun gama shirya su ne suka tafi suka bar su suna ta shaqar bacci, a palour suka haɗu da Oga Zaks yana zaune, ya baza uban tumbi yana kwasar girki,cikin qatuwar muryar shi ya furta, " Daga yau duk wata shegiyar tsohuwa a cikin ku da ta qara gulma akan matan da suke shigowa gidannan sai na mai da ita matata kuma ta inda baku tsammata ba tanan zan na amfani da ita, munafukan banza da wofi ku bace min da gani," Jiki na rawa baki na kyarma suka hau bashi hakuri, korar su ya yi ya barke da wata mahaukaciyar dariya. ************************** Salma kuwa matar Alhaji me saida motoci,wani qaton gida ya kaita a wata unguwa a gwarinpa, gidan ya haɗu iyakar haɗuwa dan kuwa tun daga baƙin gate d'in gidan za ka san cewa nera ta zauna, bayan ya tsaida motar a bakin gate d'in ne ya fita da kan shi ya je ya bude gate sannan ya koma ya shigar da motar cikin harabar gidan,a tare suka fito daga motar sannan ya daga ya riqe ta a jikin shi, bayan sun shiga cikin gidan ne Salma ta hau zare ido dan ganin uwar  dukiyar dake gidan. Wani d'aki ya kaita mai kyau, suna shiga ba tare da aikata komai da ya kamata amarya da ango sun gabatar ba a daren su na farko ya ja ta gare shi ya fara aika mata saqonnin shi da ya jima ya na jiran irin wannan ranar ya isar da su gare ta, dan kuwa shi dama bai wani more ta ba sosai, kuma babu laifi Salma bata yi irin wayewar su Suwaiba ba ko ya je soyayyar tasu bata wuce kiss da shafe shafe bata taɓa bashi dama ya kusance ta ba,haka angon Salma ya fara qoqarin cika burin shi a kan ta babu sallah ba salati ba godiya ga Allah na daren farko na ma'aurata ba adduar komai haka ya maida ita cikakkiyar mace,ai kuwa yasha kuka da zagi a wajen Salma, dan ashar sai wanda ta manta, bayan sun kammala komai ne ya yi ta rarrashin ta,a qasan zuciyar shi yana ayyana, 'Zakici uban ki ne wannan zagin da dukan da kk mun duk sai na rama na fanshe abuna, yar me kwadayin tsiya' A zahiri kuwa wani irin lelen ta yake kamar kwai, a cikin sati dayan nan ya nuna mata gata sosai, wanda ta dinga hango gidan su tana ayyanawa a ranta 'Dama haka rayuwar Abuja take da daɗi, ga miji gangariya na samu, ga kayan alatu na ci na sha na kwanta miji namin hidima, tab amma an bar Juwairiyyah a baya ina tausaya ma rayuwar ta, dan kuwa haka zata qare ta cikin talauci da babu' Shafa gefen  fuskar ta Alhajin nata ya yi tare da fad'in, "Tinanin me kike yi haka ?" Cike da shagwab'a ta kwanta a jikin shi ta ce, "Ba komai, ina tinanin ka ne kawai" Ta qarasa  maganar ta tana wani karairaya tare da qarasa haye cinyar shi, " karki damu ai gani kome kk so naki ne, nema kawai zaki a baki baby" Dariya ta yi tana shafa jikin shi tana limshe ido, sannan ta kashe murya ta furta, "Da gaske Alhaji na?" Da gaske mana tambayi ki ga aiki da cikawa" "Hmmm ni dama dubu dari biyu kawai nake so zan je na dan siyo kayan sawa na gida, dan na ga ba a kawon kayana nan ba, kace a bari inna zo gidan ka akwai amma ka hana ni shiga dakuna ukun can, sannan kuma in da nake ba wasu kayan kirki na saka wa" ' Yarinya wannan lokacin nake jira da zaki nemi wani abu a wajena' A zahiri Kuma sai ya ce, "Sorry my love ki yi haƙuri,maza  shirya muje na kaiki ki siyo kayan da duk ki ke buqata, menene wani dubu ɗari biyu kuma? Ai ba abinda ba zan kashe maki ba in dai ina da shi" Da sauri ta sauka tana murna ta saka kaya ta dauki jakar da tazo da ita ta fito ta na jiran su tafi shopping,tsaf ta ganshi a tsaye Shima ya fito yana mata wani irin shegen murmushi,  fita suka yi suka dauki hanya, suna ta tafiya, sai ta ga suna barin gari suna ta wuce shaguna da super markets, kasa jurewa ta yi cikin kissa ta ce, "Ina zamu ne haka sweety?" Idanun sa na saman hanya ya furta, "Wani waje zan kai ki na musamman in kk ga wajen zaki ji daɗi sosai" "Wooow  Sweety u ar so romantic , i love u" "I love u more dear" kiss ya yi wa hannun ta, a haka yana tuqi ta yi bacci, bata bude ido ba sai a wani qauyen da bata san ina bane, wani gidan qasa ne mai girman gaske, ko ta ina mata da yara qauyawa ne a ciki sai wasu dattijai a gefen wata bishiya, sina cin wani tuwo baqi miyar koriya sharrr da ita, da sauri ta miqe ta fara murza ido, a zaton ta mafarki take yi,cikin tsananin razana ta furta, "Babe ina ne nan? Me muke yi anan? Ko mafarki nake yi ne?" " Hhhhhhhh ba mafarki ki ke yi ba Salame, nan shine ya dace da ke, kuma nan ne gidan ki, na asali, can gidan gidan oga na ne daya karban auren ki, anyway sun yi tafiya shine na kai ku mu ci amarcin mu, karki damu bangaren ki yafi na dika gidan kyau, da taimakon ogana, harda TV an sa maki, tin da ko gidan uwale da ubale ai babu su ko?" Ya faɗa yana wani shu'umin murmushi, ita ko ta dad'e da fara kuka harda majina, kuka take tana bashi hakuri ya maida ita wa Goggon ta ita ta fasa auren nashi in dai a nan zai ajiye ta, wanka mata mari ya yi mai lafiya sannan cikin fushi ya ce, " Dan uwar ki mai kwadayin nan an gaya maki wawa ne ni? Na kashe maki yan kudaden nawa kice na maida ki gida, ai ke da gida sai kin haifi biyar a qalla, sai dangin ki sun manta dake , ba dai Abuja kk so ba, to ai nan ma Abuja ce, dan haka baki da damuwa,inna fita ki tabbatar kin biyo ni in ba haka ba a gaban su zan fara ballaki, danni ba sabon abu bane wajena dukan mace" D'aga kai ta yi ta na kallon shi cike da tsoro da mamaki,dan yanzu wani irin tsoron shi take ji ba kadan ba, hankailin ta kuwa idan ya yi dubu to ya tafi yawo, musamman da ta shiga ta ga daki daya ne dakin nata da wata yar TV da kayan kallo, sai gado qarami da kujeru biyu, da yan kwanika da ledar tsakar d'aki, kai abun dai kamar wata mara gata, haka ta shiga tana kuka kamar ta suma take ji dan baqin cikin da ke ran ta, biyo ta ya yi yace ta biyo shi d'aki mai kallon nata, amsawa ta yi ta bishi kamar raquma, wani d'aki ta shiga mai cike da tarkace da tsohon gado, sai wata uwar datti da aka tara a gefe na kayan wanki, ga poo din kashin yaro ba a zubar ba qazanta dai ta qarshen qarni kawai, wasu yammata ne a gefe an ci mai an yi fari ta fuska an d'ashe har fuskar ta yi wani kampala kampala, ba kyaun gani, sun sha bra ta dame su anyi daurin qirji da yan wayoyi a hannun su, manyan 'ya'yan Alhaji Talle ne, a qauyen nasu duk da Talle aka san shi, ko kuma a ce masa Tallen marka wato matar shi uwar 'ya'yan shi manyan kenan. Markan ce ta fito daga kicin kamar wata baqar mahaukaciya, futu2 da ita tana goge hanci da bakin zanin ta, ido ya yi mata jawur, da dukkan alamu girki take yi dan kuwa jikin ta sai qauri hayaqi da warin hammata ke tashi, cikin d'aga murya Talle ya ce, "Dalla malama ki yi sauri yau zan koma ni" Shiga d'akin ta yi tana bin salma da wani irin mugun kallo,cikin neman qarin bayani ta ce wa Talle, "Wannan fa Talle?" "Qanwar ki ce, dama na zo ne na kawo ta zan koma, ki kula da ita in ta bar gidannan kashe ku zan da ke da asararrun yaran ki, kun dai san hali na ai" Ya na gama maganar shi ya liqe ya sa kai zai fita, Marka ta kama qugu cikin masifa ta ce, "To ina zaka rabon ka fa da nan wata uku kenan, sannan yau kazo ko kwana ba zaka yi ba zaka wuce"  "Jarababbiya muje na maki ko sau daya ne ba dai jarabar ki in ta motsa har a gaban 'ya'yan ki sai kin nema ba" Cikin rashin kunya ta furta, "Eh ɗin na ji muje" A gaba ta sa shi suka koma d'akin yaran na dariya suna tafawa, ita ko salma qafafun ta ta ja ta yi d'akin da yake nata a yanzu,gado ta faɗa tana kuka mai ban tausayi, ga mijin da take so can da wata qazama yana mu'amalar aure da ita duk suna jiyo wa, ga talaucin da ta hango tsabar shi a gidannan, yau ina zata saka kant ? Kuka take sosai ta ji an banko qofar d'akin nata da ta saya , cikin masifa ta ga wata matashiyar yarinya ta tsaya a kan ta tana fad'in, " Malama ki je ki qarasa mana abincin tin da baba ya qule daka da marka, yunwa muke ji , dan yanzu kan su fito sai an gan su" sShewa yaran suka yi suka tafa tare da fad'in , "Hahaiiiiiiiiiiii casssssssss " Miqewa Salma ta yi ido ya yi mata jawur saboda kuka tace, "Ni na saka uwar taku shigewa d'aki da uban naku da zaku nuna min ku fitsarraru ne?" "Ni ki ke mayar wa da magana? Yau zamu daga maki qafa ko dan darajar Baba na gari, amma ki kiyaye mu, mu nan da ki ka ganmu zane matan baba muke yi, ki tambaya kiji, sakarai kawai, kema ba zai wuce tarkon baba kika faɗa ba ai kwadayi mabudin wahala ne dama ai," Dariya suka saka suka sake tafawa, wata ce a cikin su da bazata wuce shekara 14 ba ta shigo ɗauke da bokiti akan ta na markaden koko, kallon su ta yi ta kauda kai , " ke jummala je ki qarasa abinci marka  bata kusa," " ku me kuke yi tin dazu baku je ba? Ba in da zani sakarkaru kawai" wucewa zata yi Huwaila ta janyo ta ta kwada mata mari, kuka ta saka tana fad'in, " Allah ba zan ba mugaye kawai sai dai ku kashe ni, baku da aiki sai dai kuci ku yi wanka in su yaya Baban gida sun zo su yi ta lalibe ku da sunan wasan abokan wasa kuke yi, ko ji kuke ban sani ba ne?" Shiru suka yi suka sake ta suka kama hanyar shiga madafin nasu, kuka taci gaba da yi, daga baya kuma a hankali ta yi shiru ta daga kai tana kallon Salma, cikin washe baki ta ce, " laaaaa kece amaryar Baba da za a kawo dama?" Daga mata kai Salma ta yi ta shige d'akin ta, shigar ta ke da wuya Talle ya fito daga dakin Marka............. [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼     ' YAN ABUJA  💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAEH Page 6: Talle ne ya qarasa fitowa Yana gyara wandon shi, rigar shi kuwa na yafe a kafadar shi, d'aurin qirjin gado ne a jikin Marka lokacin da ta fito daga d'akin nata ta na wata miqa , bakinnan na ta na ta fidda wani wari kamar an bude shaddar gidan haya, hammatar ta har wani kore2 brown2 take, qafar nan fururu da ita kan ya danqare, ba a qanin tsagar kitson ma, kuma gashi ita mace ce mai cika da tsahon gashi amma ba gyara ,yawu ne cike a bakin Talle na kyankyamin Marka ya je ya zubar yana masifa. " ke ba a binda ki ka iya sai aukin son a kwanta da ke, in ba ai maki yanda ki ke so ba ki tara wa mutane jama'a ba ki kunyar Idon kowa,a dai biya maki buqata kawai,gaki nan ne kawai baki san ya ake gyara ba sannan in na nema a wani wajen ki fi kowa kishi da nuna jin zafi, to bari ki ji ba zai yu ba, ko ki canja hali ko wannan karon inna tafi sai na yi wata shida ban dawo ba" " ka yi hakuri Talle amma dai kasan ba laifi na bane ko, kana ganin baka bar mana komai ka ke tsallake mu ka yi tafiyar ka, ni ke wa kai na komai a gidannan ba mai taimaka mana,a hakan dai nake samun abinda nake yi wa nawa yaran da na haifa da ciki na,sannan ga wadannan shegun 'ya'yan da iyayen su ba sa nan, duk a kaina, yaushe nake da lokacin gyara? Kawai hakuri za kai, in ka gyara kaga gyara, in baka gyara ba ka ga dan gundun uban qazanta a gidan ka ah toh,ko 'yan iskan da ka ke bi ai kai ka ke kahye musu kuɗi suke yin gyaran ko kuma wasu 'yan iskan su kahye musu kuɗi su gyara ka tsinci dami akala" Ta qarasa maganar ta tare da murguda baki ta wuce tana kada manyan duwaiwakan ta, tsaki Tallen ya yi sannan ya ce, " Ga mace dai a nan har mace da mutum zai huta amma an kashe waje da qazanta Allah wadaran naka ya lalace jakin dawa ya ga na gida" Zubda yawu ya qara yi har zai fita ya tina da salma, leqawa ya yi yaga tana kwance har lokacin sai kuka take, dakin ta ya tura qofa ya shiga sannan ya hau gadon ya sa hannu ya d'ago ta, saka ta ya yi a cinyar shi da niyyar ya lallashe ta, nan take wani irin wari ya kai wa hancin ta ziyara, yunqurin  amai ne ya taso mata, da gudu ta fita waje ta hau kakarin amai amma kuma ta kasa aman ga wahala duk ta ishe ta saboda yunquri, kuka ta fashe da shi na takaici, cikin ɓacin rai Talle ya biyo ta ya tsaya a kan ta babu ko digon tausayawa a tattare da shi ya ce, " Ke dan uwar ku mai shegen kwadayin tsiya ni zaki wa iskanci? Ni zaki fito kina toshewa hanci kina qoqarin haras wa? Yau zaki ci uban ki kan na tafi kuwa" Janta ya yi da qarfi ya yi d'akin nata da ita yaran nashi manyan suna labe suna jiyo kukan ta, ya wurga ta gado ya cire kaya ya hau kusantar ta da dattin jikin shi da warin da najasar da ya gama saduwa da Marka,Salma kuwa da ta ji azaba kuka take tana kakarin amai amma saboda yunwa ba komai a cikin ta sai aman ya qi fitowa banda wahala babu abinda take kwasa, cikin kuka da nunfashin wahala ta ke fad'in, "Ni ka daga ni kaje kai wanka kasan ba zan qi ka ba, wannan warin zai kashe ni in baka tashi ba,nimfashina kamar zai dauke haka nake ji " Mari ya sakar mata ya ci gaba yana cewa, " kema sai kin shaqa dan uwar ki niba a haka aka sani na yi har sau biyu ba ban tsinci komai ba? Dan haka dole na sauke akanki dan inna tafi ban san randa zaku ganni ba" A haka ya gama abinda zai ya tashi gajiya fal jikin shi, ba wankan tsarki balle na daud'ar daya kwasa haka ya fice ya sa kai ya yi cikin garin Abuja,inda ya tafi ya Salma a nan kamar matacciya, ita kuma Marka ana can gabam murhu anyi goho ana hura wuta, Itan ma ko wanka bata damu da ta je ta yi ba, gaba daya murna ce fal cikin ta, yau Talle ya biya ta bashin da take bin shi, hankalin ta kwance take ayyukan ta dan kuwa ta sani talle ba qaramin gwarzon maza bane, ya qi tsayawa ne kawai ya kula da ita da iyalin shi dika, ga girma na kama su, dan shi zai yi shekara 47, ita kuma zata yi 38,  lokaci ne da ya kamata su zauna su mori rayuwar su kafin tsufa ya rufe su,amma inaaa kowa da nashi matsalar, tin asali ita ta bazama shi neman mata saboda muguwar qazantar ta da rashin sanin ya kamatan ta, shine sanadin kwadayin matan waje da yake yi a Koda yaushe musamman in ya gansu fes da su a cikin gari, daya shigo dan ya sauke buqatar shi sai ya ganta duqun2n kamar jakka, ai kuwa nan take haushi zai kama shi ya ji kamar ya rufe ta da duka, a hankali ya fara da marin ta in ta cika masa ciki, sai duka ya biyo baya, a haka har halayen shi suka munana, lokacin da take son ya gyara lokacin shi kuma idon shi ya buɗe da matan waje, still ita kuma bata gyara ba, ita ba ma ta ganin wai laifin daga gare ta ne balle ma ta ɗauki matakin gyarawar,ga yaran su da suka lalace duk a sanadin muguwar tarbiyyar iyayen na su, tinda in suka tashi kusantar juna ba ruwan su da yaran za su ji ko baza su ji su ba,kawai zasu yi abun su kamar dabbobi su fito suna zagin juna ko yabon juna a gabam yaran, ta haka Huwaila babbar yar su ta fara miqawa Baban gida cousin din su jikin ta yana lalubewa, domin so take itama ta ji me Marka kewa ihu tana nuna jin daɗin ta akai, ana haka Badamasi shima ya ke jan Jummala su yi nasu, kafin kace me yara idon su ya buɗe, Haule ce kawai Allah ya sawa nutsuwa a yaran Talle kaf, dan ita har makaranta take zuwa, kuma mamar ta daban a gidan,bata san ta ba, shi kanshi bayace ga uwar ta bama, tinda ya saki uwar ta da za ta tafi ta ajiye masa Haulen ba ta sake juyowa ba, dan gani suke gidan shi ba abin son haɗa zuria bane ba sam qaddara da tsautsayi ne ya sa auren su ya qullu shi yasa ta yafe masa 'yar ta cire ta a ran ta ta qara gaba. Kullum haka rayuwar gidan Talle take, gidan babban gida ne na gado tare yake da yayun da wato  iyayen su Badamasi da Baban gida, iyayen su sun rasu,  suma Su Badamasin Mahaifiyar su bata da rai sai mahaifin su, watan ta shida da rasuwa, sun rasu ita da jaririn ta da tazo haihuwa, dan haka daga su sai uban su da yaqi aure sai bin 'Ya'yan jama'a sa'annin su Jummala, gidan su Talle gida ne na marasa da'a da tarbiyya, ko kadan ba mai kwab'a a gidan balle ya tsawatar akan abinda ake aikata wa mara kyau. Lokuta da dama Marka na leqawa dakin Yayan mijin ta su watse tare ba tare da kowa ya sani ba,sakamakon nesa da mijin na ta ke yi da su,idan ya tafi ya na jimawa bai waiwayi gida ba dan kuwa watarana idan ya sa kai ya yi gaba sai ya yi watanni shida zuwa bakwai bai dawo ba yana can cikin garin Abuja, wannan ta'asar da ake ta tafkawa a gidan gaba ɗaya yaran da manyan gidan duk basu sani ba,domin a fili nunawa suke yi su ko gaisuwa ma basa yi da junan su sun tsani juna, amma da dare yayi in wani na buqatar wani zasu qwanqwasa qofa a bude su shige su gama su fice ba wanda ya sani, wannan shine Gidan Tallesious. ************************** A bangaren amarya Juwairere kuwa, suna shaqar amarcin su cikin jin daɗi so da amince wa juna tare da girmama junan su, rayuwar ta na yi mata daɗi matuqa dan kuwa ba ta da damuwa ko kaɗan ko kewar gida ta yi Jabeer na kore mata damuwa a gefe d'aya Kuma ga qawar ta kuma 'yar uwar ta Nafeesa itama ta na debe mata kewa sosai, tare  da taya ta aiki in Yah Jabeer ya fita kasuwa wajen saida jakunkunan shi. A haka rayuwar su ke ci gaba yau da gobe ana cin daɗi saboda garar da aka kai ta da shi, amma bahaushe ya ce zara bata barin dami, sai ibtila'in talauci ya ziyarce su,kasuwa ta kulle sai ya fita Watarana ya gama wunin sa be fi a sai takalmi ɗaya ba ko ya dawo ma Watarana ba a sai komai ba, Juwaira kuwa bata taɓa nuna masa wani sauyi ba sai ma qara masa qwarin gwuiwa da take yi a kullum. A cikin wannan yanayin da ake ciki ta fara fuskantar canji daga wajen Surukar ta wato Hansai wadda suke kira innarmu, bata nuna mata a fili sai dai a qasan qasa ta yanda ba mai sanin halin gallazawar da take yi wa Juwairiyyah, ga shegen habaici kamar wadda ke tare da kishiyar ta,ta na so ta fito fili ta nuna wa Juwairiyyah qiyayyar da take yi mata amma ta kasa saboda ba qaramin kwarjini Juwaira ke mata ba. Ba komai ke jawo wa bawa kwarjini ba kaga yana da maqiya amma su rasa ya zasu yi da shi face tasbihi,zikiri , da yawaita hailala da istigfari, komai maqiyin ka zai yi maka sai dai ta bayan Idon ka ba dai ta gaban ka ba domin kuwa Allah zai kare ka ko abun ya same ka ka sani yana daga cikin jarabawar rayuwar ka shiyasa u can not escape it, iya hakurin ka iya lada da daukakar ka,sannan yana sa maqiyan ka su dinga shakkar ka, ga soyayyar Allah da mala'iku da bayin Allah managarta, mu riqe ambaton Allah a koda yaushe, kina tuqa tuwo ne, kina shara ne, kina tafiya ne, kina ma megida wanki ne ko guga, kina ma yara wanka ne, ko zaki sauke tukunya ne, ki yi bismillah, komai zaki ki sa ambaton Allah a ciki rayuwar ki zata zama abin so wajen kowa, sannan Allah zai so ki ya ambace ki a tsakanin mala'ikun shi. Wannan dalilin ne yasa ta fito da dabarar yi mata zagon qasa wajen Yah Jabeer tunda ta kasa musguna mata gaba da gaba. Wata rana Juwairiyyah ta fito daga d'akin ta dan ta yi abinci sai ta fara da share madafin ta ta gyara shi tsaf,sannan ta qara dauraye tukunyar ta , ta haɗa wutar murhu ta dora ruwan zafi,sai ta deb'o waken ta ta fara gyarawa, ta gama gyara waken kenan ta wanke ta zuba sai ta yanka albasa a ciki dan ya yi laushi da qamshi, dama tasan ba su da kayan miya man da za ta yi miyar  kan shi manage za ta yi da shi bashi da yawa, kuma da dikkan alamu in suka ci wannan na dare sai dai ai hakuri, ta kammala dafa waken kenan sai nufi d'akin ta dan dakko shinkafa ta rege sai shinkafa tace ɗauke ni a inda ki ka ajiye,duban duniya Juwairiyyah ta yi amma haka ta nemi shinkafa ta rasa. Hankalin ta ya tashi sakamakon duba lokaci da ta yi ta ga lokacin dawowar Yah Jabeer da ya kusa, cikin tsananin damuwa ta zauna ta zabga tagumi tare da fad'in, " Oh ni Juwairah yanzu in ya dawo me zan bashi, ya wuni kasuwa bai ci komai ba, sannan ya bada kuɗin cefane daidai gwargwadon ikon sa a masa girki, kawai sai ya dawo ince shinkafar ta b'ata?"  Tana tsaka da tunani da damuwa ne ta ji muryar Nafee na fad'in, " kin kusa gama abincin ne ? Dan na fara jin yunwa , Innarmu ma na can tana neman abinci yunwa take ji sosai" "Na shiga uku ni juwairah, kin ga Nafee anan na aje shinkafar daga kewayawa bayi kan na fito na rege na saka ban ganta ba, na neme ta sama ko wasa na rasa " Cikin mamaki Nafeesah ta kalli Juwairiyyah ta ce, "Baki ganta ba fa ki ka ce, to Ina zata ke ita ba qafa ba?" kuka Juwairah ta fara ta koma daki ta yi tagumi ta rasa abin yi,ta na nan zaune dabara ta faɗo mata, tashi ta yi ta samu wannan waken ta rage masa ruwa sosai, ta samu dan man daya rage masu, da dan wani magi da take da guda uku, sai gishiri ta zuba a ciki ta qara albasa sosai, inda suke shuka alayyahu ta je ta yanko mai yawan gaske ta zauna ta cinke ta gyara ta wanke sosai ta zuba, nan da nan abinci ya haɗu murna ta dinga yi tana godewa Allah da wannan dabarar da ta yi, duk da qarancin shekaru irin nata amma hakan be sa ta tsaida tunanin ta waje ɗaya ba, sai ta faɗad'a tunanin ta ta yanda har sai da ta sama wa kan ta mafita, bayan ta gama ta zubawa kowa ta kai masu, ko da ta shiga d'akin Innarmu bata gan ta ba sai ta yi zaton ko ta na makewayi ne,kawai sai ta ajiye ta yi wa Nafee magana ta wuce sashen ta, kan ta fita daga sashe su Nafeen ne ta ji Innarmu da wani yaro tana ce masa, "ka siyar shamusu nawa ya baka me shagon?" Kasa kunne Juwairiyyah ta yi amma bta jin me yaron yace,sai ta sake jin muryar Innamu na fad'in, " Amma dai bai kyauta ba gaskiya, a fa wajen shi Juwairah ta sai shinkafar amma shine ya rage har nera saba'in ɗan nema mai kan buta kawai sallamamme shi yasa shagon ya qi ci gaba gashi nan jiya iyau" Kafin ta dawo Juwairiyyah ta bar wajen cike da mamakin da ya  cika mata ciki, dama Innamu ce ta dauke shinkafar? Me hakan yake nufi?dama Innarmu bata qaunar ta? Bata son zaman lafiyar da suke yi da Yah Jabeer?shin me yake faruwa ne? [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAEH Page 7: Juwairiyyah na nan tsaye cike da tarin tambayoyi da mamaki ta ji Innarmu na fad'in, "Shegiyar yarinya, daga zuwa komai na mu ya fara tabarbarewa, gaba ɗaya Jabeeru ya tare a qasan ta, ko shigowa gida ya yi da mun gaisa wuf ya tashi ya tafi wajen ta, ya dan zauna ma mu yi hira yanda muka saba sam ai yake yi,to an janye mai hankali, to ni ba zaki mulkar min d'a kamar yanda uwar ki ta yiwa uban ki ba in dai ina raye, haka kawai, ke na haifarwa dan? To mu zuba shege ka fasa tsakanin ni da ke" Kuka ne ya kusa kwace ma Juwairah jin kalaman surikar ta, wannan wace irin rayuwace kuma? " Ya Allah ka taimake ni na ci wannan jarabawar" Abinda ta iya furtawa kenan ta share hawayen ta ta koma ban garen ta, qarasa gyara wajen ta yi tai wanka, ta yi brush sai ta koma daki ta tsaya cikin madubi ta gyara gashin ta da ta wanke ta shafa wa mai sannan ta taje shi ta daure a bayan ta, buɗe wardrobe ɗin ta tayi ta tsaya kallon kayan ta ta na nazarin wanda zata saka, kafin daga qarshe ta yanke shawarar dakko wasu riga da wando rigar pink wandon baqi siriri Wanda ake kira da pencil, Inna Deejee ce ta siyo mata su a 'yan gwanjo,tin su dai basu da halin siyan sabbi,kayan sun amshi jikin ta ba kadan ba, fita ta yi ta debo garwashi ta saka tiraren wuta, sannan ta feshe jikin ta da tirare ta qara da humra, kyautar Goggon ta Kareema kenan wato kayan qamshi, kafin kace me sai ga Juwairiyyah ta fito chass da ita,da ka kalle ta zaka dauka yar wani hamshaqin me kudin ce, ko matar wani attajirin, Nafeesa ce ta shigo tana murmushi ta ce, "Dad'i na da ke matar Yaya ba dai tsafta da qamshi ba,kina burgeni fa ba kaɗan ba,ko ta wacce gab'a aka latsa ki kina nan kyam, a shekarun mu kina da kaifin hankalin da wani babban ma bai da shi, duba kiga yanda ki ka yi mana dabara d'azu, Innar mu da ta koma d'aki da ta ga abincin da ki ka kai mana ban san me ya razana ta ba, dan na ji harda ashar ta baza mana a dakin dazun" Nafee ta qarasa maganar ta cikin dariya, Juwairiyyah ma dariya ta yi ta ce, " kai sisto irin wannan fasa kai haka, in kk fashe man kan nawa yayan ki ya dawo kin masa bayani ai" Sallamar shi suka ji da sauri Nafeesa ta fito zata bar wajen, tsayawa ta yi ta gaida shi sannan ta wuce, tana jin Nafee ta fita ta taso cikin yauqi da tafiya mai daukan hankalin masoyi,tare da wani lumshe ido kamar mai jin bacci ta isa wajen shi, ledar hannun shi ta Karb'a, sannan ta jawo hannun shi zuwa d'akin su, suna shiga kamar jira yake yi ya d'aga ta sama ya manna ta da jikin bango,dariya take mai sanyin sauti, ta zagaye wuyan shi da hannayen ta , dora fuskar ta ta yi a kan tashi, tare da hade bakin su waje ɗaya, sai da tayi masa kiss mai tsayawa a rai, sannan ta kai bakin ta wajen kunnen shi tana mai sannu da zuwa, " Jarimin maza ina maka barka da dawowa, ina fatan yau kasuwa da mutanen cikin ta basu wahal min da kai ba ko? Dan in haka ta faru akwai hukunci mai tsanani akan su daga wajena" Hura masa iskar bakin ta ta yi a kunnen tare da yin kiss a ciki ba shiri ya nemi wajen zama da ita a hannun shi suka zauna ya na sauke ajiyar zuciya,cikin kasalalliyar murya Jabeer ya furta, " Agaskiya samun mace kamar ki Juwairiyyana akwai wahalake ɗaya ce tamkar ba iyaka, samun kamar ki a cikin mata million zai wahala, in zance zan tsaya fad'an wacece ke bakina zai rasa kalaman magana,so kawai ke kadai ce ba ta biyun ki , kuma ke ɗaya Yah Jabeer din ki ya ke so har abada ba na jin zan so wata kamar yanda nake son ki" Wani irin daɗi ne ya lullube Juwairiyyah, kamar yanda kullum take son faranta mashi rai shima qoqarin shi kenan ya ga ya faranta mata rai, basu da arziqi, ba su da abubuwan more rayuwa, amma suna da junan su, tashi zata yi daga cinyar shi amma sai da ta goga mazaunan ta a jikin shi sannan ta miqe, gwalo ta masa ta tafi da sauri zata yi d'aki, binta ya yi a baya yana fad'in, " Ai baki isa ba ki tsokanen ki gudu yarinya, tsayawa zaki ki qarasa ladan ki kawai" Dariya take tana bashi hakuri,dan ta san tabbas ya na jin yunwa, " Dan Allah Babe ka bari kaci abinci ka yi wanka, sai namaka tausa kamar kullum, in yaso in ka samu qarfin jiki yau sai abinda ka ce shi za a yi" Tana kaiwa nan ta rufe fuska tana dariya ta zagaye shi ta fita da sauri, zuwa ta yi ta haɗa masa ruwan wanka,kafin ta dawo shi kuma ya shirya wanka, shiga suka yi bandakin a tare bayan ta je ta rufe qofar bangaren su, wanka ta masa da kyau ta sa masa toothpast a brush din shi ta bashi dan ya wanke bakin shi. Mata da yawa suna cewa wai mijin su yana warin baki baya son yin brush da sauran su, shawara gare ki sister mai wannan matsala shine, ba a ce ma na miji je kai brush ko wani abu makamancin haka, dik da akwai mijin da in shaquwar ku ta kai qololuwa kina iya sanar da shi kuma ba zai damu ba dan yasan duk amfanin ku ne ke da shi, so in ba irin mijin nan gare ki ba dabara zaki yi, ki haɗa maku ruwan wanka tare kafin wankan ki tabbatar kin gama gigita shi yanda ba zai maki musu a ba, daga nan sai ku yi wankan tare, in ba ku yi tare ba ma saboda maybe yanayin gidan naku, sai ki saka masa ruwan ki kai masa da kayan wanka, sannan ki saka mai toothpast a brush ki aje mai a kusa, ba yanda za ai ya qi musamman yaga kin saka maku tare, kinga ba zai zargi kina jin wari bane daga wajen shi, har ya yi feeling bad kuzo kuna samun sabani. A d'aki ma Juwairiyyah Bata bar jabeer ba sai da ta gyara mai jiki tare da feshe shi da tirare, palour ta dawo da shi yana biye da ita kamar raqumi da akala, abinci ta zaunar da shi ta bashi, yana ta santi " kaiiiii amma ba qaramin birge ni ki kai ba, kin san rabona da faten wake har na manta kuwa?" "Alhamdulillah na ji dad'i da yabawar ka Hubby" kusa da ita ya matsa sannan ya ce, "Ai dole in yaba saboda ke din ta daban ce, komai naki daban ne,Allah ya barmu tare har a aljannah" Murmushi suka yi dikan su suka ci gaba da cin abincin su, kiran sallar magrib ne ya katse su suka tsaya suka saurara sannan suka bi kiran sallahr suma, bayan an idar ne suka yi addu'ar da ake yi ba yan idar da kiran sallah,wato " Allahumma rabba hadhihidda'awatittammah, wassalatil qa'ima, a ti muhammadal wasilata wal fadeela waddarajatirrafee'a wab'athhu maqamam mahmudan lladhi wa adtah." Sannan suka dora da salatin annabi ingantacce, addu'a suka d'aga hannayen su sama suka yi a tare ita da shi, suna idarwa suka tashi suka yi alwala, shi ya tafi masjid ita ta yi sallar ta a gida, bayan ta idar ne tayi azkar din bayan kowacce sallah ne, sai ta samu ta yi kuma azkar din yamma, tana idar wa ta miqe ta je d'akko dan ragowar abincin nasu ta juyo masu ta kawo ta had'o da ruwa da komai da ya dace ta ajiye a gefe, d'aki ta shiga ta saka rigar baccin ta mai matuqar kyau da daukan hankali, sai ta ɗora zani akai da hijab tana jiran sallar isha'i bayan tayi sallar ne da minti 15 Jabeer ya shigo,abinda ya tsayar da shi kuwa sai da ya biya wajen Innar mu ya gaida su, baban shi na ta sa mai albarka, ita ko ta cinkishe fuska tana hura hanci, daya tambaye ta ne ke damun ta sai ta yi qaryar kanta ke yi mata ciwo, dan yau wuni tai da yunwa bata ci abinci ba, can kuma sai ta saki fuska ta ce, " kasan da yake bana son faten wake, kuma bana son bawa yar albarkar nan aiki shiyasa, amma da shinkafa zan bata ko gwangwani dayar nan ne ta dafa min, tinda Nafee ita har yau bata iya tsantseni irin na Juwairah ba" " Ba komai Inmar mu kawo na kai mata za ta yi maki ai, ba zai yu ku kwan da yunwa ba" Dan haka da sallama ya isa sashen su riqe da ledar shinkafar a hannun sa,daidai Juwairah ta fito daga d'akin ta ta cire zanin ta da hijab din ta, tana qarasa shafa mai a cinyar ta, ko da ya higo tini ta sauya salon shafawar, sake baki ya yi kamar dolo yana kallon ta, qarasa shigowa ya yi ya aje ledar shinkafar a qasa still idon shi na kan Juwairiyyah, juyawa ta yi ta koma d'aki tana tafe tana juya bayan ta tana waigowa tana masa wani mayen kallo da murmushi, ni dai tin da ya shiga suka ja qofar ban qara ganin me suke aikatawa ba sai dai kunnuwa na sun jiyo man Jabeer na sambatu da bana gane yaren da yake yi, sayyarar qafa ta na ja na yi waje, ji nake kamar na kai wa Innarmu gulmar me ke faruwa. Qarfe hudu na asuba suka fito suka yi wanka tare da alwala mai kyau suka koma dakin su, bayan sun shirya ne suka fara gabatar da nawafeel, kowa ya fara addu'ar shi, Jabeer ne ke hango baqi, a gefen shi dan ba wuta sai ta wayar shi suka kunna, miqa hannu ya yi dan yaga meye a wajen, dagawar nan da zai yi sai ya ga shinkafar da Innarmu ta bashi ce jiya a dafa mata, cikin damuwa da tashin hankali ya ce, " Ya salam ! Tab lallai da safe na shiga magana wajen innarmu, aiko ni ta yi fa jiya na kawo ki dafa mata wai yunwa take ji, tin safe bata ci komai ba, bata cin faten wake, shine gaba ɗaya na manta" "Haba Yah Jabeer bai kamata ka manta da wannan mahimmin abu ba kuwa, domin yunwa ba ta da mahadi ai bayan haka Innarmu ce fa ta baka umarnin a yi abu be kamata ka shagala ba gaskiya ban ji daɗin abinda ka yi ba," A qasan ranta kuwa jinjina wa Innar mu take wajen iya hada makirci, matar da taci ta tande kwano, har ta aiko wai a dad'a mata in akwai, tace babu shine take cewa ba ta ci, ikon Allah, lallai Allah mai jin qan bawan sa ne mai tinawa da shi a kowanne hali yake musamman idan bawan na yawan neman taimakon Allah a dikkan lamuran shi, da bata zama mai neman taimakon Allah a komai ba da bai taimaka mata jiya ba,gashi bata san me aka qulla mata ba Allahn ta ya kare ta, kiran sallar asuba ne ya katse su daga mayar da magana akan abinda ya faru jiyan Jabeer ya tashi ya fita masjid ana yin sallah ya dawo, ita kuma tayi tata a gida tayi azkar da karatun asuba da take yi kullum ba fashi komai aikin da ke gaban ta sai tayi ko rabin shafi ne kan ta tashi, tana rufe qur'ani ya shigo, lokacin gari ya dan waye, daki suka shige suka ɗan miqe dan su maida bacci,tund Nafeesa ke abin karyawa a gidan, in ba arziqin abin karyawan ma da dama koko kawai zasu dama su sha a ci gaba da rayuwa, har bacci mai nauyi ya fara ɗaukan su suka jiyo sallama daga bakin kofa......... [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA.  💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 8: Nafeesa ce ta tsaya tun daga bakin kofar shiga sashen su Juwairiyyah ta kwankwasa tare da yin sallama,bayan an bata izinin shiga ne ta qarasa shiga ciki,gaishe da Jabeer da Juwairiyyah ta yi sannan ta kalli Jabeer ta ce, " Yah Jabeer Innarmu tace wai ka bada shinkafar na kai mata tin da ta yi wuyar dahuwa" "Inna lillahi,  kin gammu yanzu haka zancen shinkafar muke yi ni gaba daya mantawa na yi shaf dana shigo, dan Allah ki bata hakuri kice yanzu za a dafa mata a kawo" Dariya Nafee ta yi sannan ta ce, "Tace idan ka faɗi haka na ce ka bata ta fasa wataran an dafa mata" "Oh my God yau ya zan yi na iya zuwa gaida Innar mu? Dan Allah Nafee ya kika ga fuskar ta ta yi fushi sosai ko?" Cikin jimamta lamarin Nafee ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Hmmmm ba kadan ba kuwa Yah Jabeer, amma tace kar na fada maka ta yi fushi" Juwairah a ranta kuwa sai tace 'Ina fa zata so ya sani tinda tana son nakasani ta qarqashin qasa' Ba yanda ya iya haka Jabeer ya ya miqa mata shinkafar yace ta bata hakuri sosai kan ya shigo, fita ta yi da ita tana masa dariyar zaka amsa ne in ka shigo kai da Innarmu ka san halin ta ba ta da sauqi. Sai da su Juwairiyyah suka taɓa baccin su sannan suka tashi suka yi wanka tare da brush, d'aki suka shiga su ka shirya cikin shiga mai kyau da burge junan su ta qananan kaya, hijab Juwairiyyah ta ɗora akan kayan ta matsattsu da ta yi ma mijin ta kwalliya da su kafin ya fita kasuwa, a tare suka shiga bangaren na su Innar mu lokacin ta gama raba abin karyawa tace akai masu sai ga su sun shiga, duqawa Juwairah ta yi har qasa suka gaisa, " Ya jikin naki Juwairah,ai Nafeesa ta ce min ba ki ji daɗi bane shi yasa ya ajiye shinkafar bai baki kin dafa min ba duk da tsananin yunwar da nake ji jiyan" Zare ido Juwairiyyah ta yi cikin duqar da kai da sauri ta furta, "Da sauqi Innarmu na ji dama sosai alhamdulillah" " To Allah ya qara lfy, yasa amarya za ai min ko ango, danni na gaji da lafiya sa banga qaho ba aure wata na biyar kenan shiru ba magana?" Innarmu ta fada a matsayin wasa take yi, amma duk wanda ya kula ya san magana take faɗa mata, murmushi Juwairiyyah ta yi sosai sannan tace, " Innar mu karki damu komai lokaci ne amare za a samo maki masu yawa da masu kawo cefane har sai kince sun isa haka" Tana fadar haka ta miqe ta yi wajen Baba Balarabe ta gaida shi, sake baki Innar mu ta yi ta na bin Juwairiyyah da kallon mamaki, shiko gogan be gane magana suka sakar wa juna ba, daɗi ma yake ji a ganin shi Innar shi da matar shi sun fahimci juna sosai akwai shaquwa ta musamman a tsakanin su, tun da har suke irin wannan maganar ga junan su, matsawa ya yi kusa da Innarmu ya ce, "Akwai abinda zan taya ki ne Innata?" Murmushin qarfin hali ta yi sannan ta furta, "Eh toh ba a rasa ba ai, A qoqarin ta na hana shi ya koma wajen da matar shi take, Can bangaren kuma Juwairiyyah da Baba Balarabe ne ke gaisawa cikin sakewa da mutuntawa, " Babana ina kwana?" "Lafiya qalaou d'iyar albarka, kina lafiya dai ko?" " lafiya qalaou nake babana" "To madallah, Juwairah ina son ki yi ta hakuri da wannan Innar taku, wani hali ta d'akko  na daban wanda har ni kaina ta canja min kwata2 ba kamar yanda na santa ba, dan haka kema sai kinyi hakuri, abotakar ta da Goggon ku ba abu ne mai kyau ba, na yi nayi na raba su amma abun yaqi yuwuwa, da dukkan alamu daga can ta samo wadannan sabbin halayen dan kawai kar a zauna lafiya" " Babu komai Baba , ai ita ɗin uwa ce a wajena ko da ace ba matar ka bace ba mahaifiyar Yah Jabeer ai uwa ta ce, tinda ita ta haife shi kuma shi din mijina ne, in ban so mahaifiyar shi a tawa ba ni kaina ba zan samu kwanciyar hankalin gidan aure ba, rikicin yawa zai yi min, dama kuma ko da asalin mahaifiyar mutum ma ai ana samun sab'ani dan haka ita ma uwa ta ce,watarana ba zata yi ba" " Allah ya miki albarka , halayyar mahaifin ki da mahaifiyar ki sak ki ka dakko ba wanda ki ka baro" Murmushi suka yi dikan su ita da Baba Balaraben, bayan Jabeer da Juwairiyyah sun gama gaishe2n su sai suka koma sashen su suka karya, suna gamawa ya sauya kayan da zai fita kasuwa da su sannan ya ɗauki makullin shagon shi da duk abinda yake da buqata ya fito hannun sa riqe da hular shi ya na gyara karin ta, ya na gamawa ya kafa ta akan shi ya kalli Juwairiyyah ya ce mata, "To ni fa na fito zan wuce sai na dawo, ki kular min da kanki, kar ki wahal da kanki da yawa Allah ya yi miki albarka " Tashi tsaye ta yi ta isa gaban shi cikin yanga da kashe ido da murya sannan  ta zagaye hannayen ta a wuyan shi ,shi kuma ya zagaye qugun ta, sannan  ta ce, "Allah ya kiyaye hanya, zan yi kewar ka da yawa a cikin waɗannan awannin da za mu yi ba ma tare" Cike da shagwab'a da tura bakin ta kaɗan gaba take maganar,Jabeer na ganin haka kuwa ya qarasa da fuskar shi jikin ta ta suka hau sumbatar junan su, da kyar Juwairiyyah ta kwace kanta a hannun Jabeer, sai wani shinshina ta yake ya na jin kamar kar ya fita,cike da shagwab'a ta furta, " Yah zaka makara fa, ka tafi cikin kariya da amincin Allah, Allah ya bada kasuwa mai yawa mai albarka, ya kare ka daga haramun komai qanqantar ta, Allah ya haɗa ka da halal komai qanqantar ta, ka kular min da kan ka, ka tsaida sallah akan lokacin ta, in kaji yunwa ka taimake ni kaci abinci, kaga yanzu ba da bane, ba abubuwan da zan iya ci gaba da dafa maka kana tafiya da shi, karka barmin kan ka da yunwa kaji Yayana?" " Karki damu,duk abinda ki ka ce an ma gama shi kawai ur higness" Yanda ya duqar da kai a gaban ta da girmamawa ne ya bata dariya, ai kuwa sai suka fashe da dariya a tare, ta sanya hannun ta cikin nashi ta raka shi har waje,bata dawo ba sai da ta ga tafiyar shi sannan ta dawo d'aki ta hau gyara wajen da suka ci abinci. **************************** A can gidan Baba Baballiya kuwa Goggo ce ta fito daga d'akin ta ta na qarasa d'aura dankwalin kan ta, cikin masifa ta duqa ta d'aga wani food flask Mai kyau sannan ta ce, " kai jama'a wai dan tsabar baqin ciki na aje flask din nan a can amma  na zo na tarar an d'aga an kai min shi nan, ko uban wa ya ce a taba min kaya oho, shikenan mutum idan yana jin haushin talaucin da ya yi masa katutu sai ya dinga taba kayan da ba nashi ba yana canja masu waje? Oh ni sarai na ga abin da ya ishe ni yau" kamar Mama ba zata amsa ta ba amma sai taga dacewar ta bata amsar, dan haka ita ma sai ta ce, " Hmmmm Allah nawa in ji bamaguje, to ai dai har yau wata kusan biyar ban ga ɗaya daga YAN ABUJAN sun yi koda waya bane balle nace ko an yi maki wani aike na azo a gani, ana nan dai yanda ake jiya iyau, ba wani hura hancin da za ai mana kuma, flask ne fa tun wanda aka samu a gudummawar biki ba wata tsiyar ba, sannan ban taɓa sanin gyara kayan ka zai zama sauke mu raba ba da ban kawar maki da shi ba na bar awaki sun tattake" kamar dama Goggo jira take Maman  ta tanka mata, sai kuwa ta hau masifa da bala'i kala kala har ta na jin kamar ta ari baki dan tsabar masifar da ke cin ta,nan da nan ta taso wa Maman a lokaci daya ta dinga zage zage da kira mata alkaba'i kala kala, har da su gori ta dinga yi ta na fad'in ai abinci ma wataran ita ke taimakawa da shi a gidan ba dan haka ba sai dai yunwa ta kashe su, 'yan Abujan da aka sanya wa ido su ne suka bata kud'in da take ci da su sai dai baqin ciki ya kashe Mama, Mama tace daga yau in Goggo ta haifu cikin Mahaifiyar ta karta qara taimakawar ta ga in bazata rayu ba ita da danta. Ammar ne ya kama hannun maman shi yana kuka dan kuwa su na tsorata shi da hayaniyar da suke yi baya son hayaniya shi sam, ɗaukar shi Mama ta yi suka yi daki abun su suka bar Goggo na kumfar baki ita kaɗai. ************************* Oga Zaks ne da mazajen su Suwaiba tafe sun fito daga wani d'aki mai tsananin duhu sosai, Alhj Kalla dauke da Saudat a hannun shi sai kallon fuskar ta yake yi abokin shi kuma aminin shi Alh Salihu na dauke da Suwaiba, suna fitowa daga dakin, Oga Zaks ne ya furta, " To ku maida masu sabbin kayan da kuka zo da su kuyi gida,nan da awa uku zasu farka, kuma ku kwanta gefen su da sun farka su yi tozali da ku, domin wannan magungunan da suka yi ta sha zasu sa masu kasala da ciwon jiki, na kammala duk wani aiki da za ai akan su na wannan watan, za ku yi kuɗi na ban mamaki, domin kuwa kuɗi kuma sai kun ce sun ishe ku, dan mahaifar su na da kyau sosai, Dodo yayi farincikin samun ta, ba a taba kawo masa irin wannan ba, nima kuma shaida ne, hahhahaahhha" Cikin farin ciki su Alhj Ƙalla suka haɗa baki wajen fad'in, "Godiya muke Oga Zaks" Sannan suka ajiye su suka canja masu kaya suka yi mota da su sai cikin garin Abuja, suna isa cikin gari kowa ya ɗauki hanyar gidan shi, fad'ar kyau da tsaruwar gidajen nasu ma b'ata baki ne kawai, gidaje ne irin ginin qasashen turai wanda ko a turan ma sai masu kuɗi ke da irin wannan gidan, ko ta ina ka gilma masu hidima ka ke gani sun gyara sun tsaftace gidan sai sheqi da kyalli tare da ɗaukan ido yake yi ga qamshi kamar a qasar Arab. Bayan gaisawa da masu aikin gidan ne kowannen su ya shige da matar shi d'aki ya ajiye ta a gado sannan suka kwanta a gefen su suka hau baccin asara ba sallah  ba salati,basu suka farka ba sai wajen la'asar, miqa Suwaiba ta yi ta na hamma, tana kallon d'akin nata, yanda ta zaci za ta zo Abuja ta zauna a gida mai kyau sai ta ga gidan ya wuce zaton ta da tunanin ta,ko ta ina d'akin ya gama rud'a ta da kyau da qayatuwar shi, shiru ta yi ta na son ta tuna abubuwan da suka faru tun da aka gama dinner bikin su ta kasa, lokaci take kallo ta na tunani anya time na tafiya daidai kuwa? Qoqarin kawar da wannan tunanin ta yi ta miqe ta hau takawa kamar mai koyon tafiya ta na so ta ga ya wannan gidan na ta mai dimbin kyau yake, taku ɗaya biyu ta yi a na uku ne ta ji wani irin ciwo a cikin ta  mai tsanani da sauri ta komawa ta zauna, tana fad'in , "Wasssshhhhhh Allah na ciki na, me ya samen a ciki kuma nake ji na haka? Gashi ina jin duk jikina ya na min ciwo" Kusan a tare suka farka su ke yin wannan maganar ita da 'yar uwar ta Saudat, Saudat da tafi Suwaiba raki ma harda kukan ta, a rude mazajen nasu suka tashi kamar ba abinda ya faru suka hau tambayar su da me ya faruwa, Suwaiba ce ta langwab'e jikin mijin ta ta na wani karya wuya sannan ta ce masa, "Ciki na na min ciwo" Tashi ya yi ya duqa gaban ta ya d'aga rigar ta ya leqa cikin tare da shafawa a hankali, sannan ya ce, " Ayya kiyi hakuri zai warke ne a hankali hatsari muka samu a hanyar mu ta dawowa gida daga wajen dinner  sai muka kai ku asibiti ke da 'yar uwar ki, kwalbar glass ce ta yayyanke ku shine muka wuce da ku asibiti aka yi maku dinki a wajen, so a hankali zamu jira ya warke mu ci gaba da shan amarcin mu ko?" Ya qarasa maganar shi tare da jawo ta jikin shi yana shafa ta, kwantar da kanta ta yi a jikin shi, ta na tunani ya akai shi babu ciwo ko ɗaya a jikin shi? Da sauri ta kawar da wannan tunanin sakamakon tashi da ya yi ya fita dan ya hado mata abinci, tana daga kwance a gadon ya dawo ɗauke da wani ɗan qaramin teburin cin abinci Saman shi an aje plate ɗin abinci da cup ɗin juice sai mug ɗin tea,gefe kuma ga wani plate nan an yanka fruits a Kai sai ya ajiye mata a saman cinyar ta,sannan  ya zauna yana bata a baki, wani daɗi ne ya lullub'e Suwaiba yau mafarkin ta ya zama gaske ta samu fiye da abinda ma take kwadayin samu a auren d'an Abuja. Tana gama wa ta dauki wayar ta da ke kashe ta kunna ta kira Goggo,wayar na shiga Goggo ta ɗauka kamar wadda ke gadin wayar ta na jira a kira, cikin kuka Goggo ta ce, "Haba 'yar nan yau wata biyar kenan da kwana uku, kun tafi shiru ba waya ba aike meke faruwa ne Suwaiba?" Cike da Mamaki Suwaiba ta furta, "wata biyar da kwana uku kuma Goggo?????............ [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 9: Tunani suwaiba ta zauna ta na yi bayan ta katse Kiran da ta yi wa Goggo, so take ta tuna abubuwan da suka faru amma kanta ya kulle sai ma wani irin bugawa da ciwo da ta ji ya na mata, komawa ta yi ta kwanta a hankali,ajiyar zuciya ta sauke a qoqarin ta na dena tinanin, " Babe what is wrong, na ga gaba ɗaya mood ɗin ki ya sauya" A hankali ta furta, "kai na ke min ciwo sosai, so nake yi na tina abubuwan da suka faru a tsakanin wannan watannin da akai auren mu amma gaba ɗaya na kasa" Cikin sigar lallashi ya kama hannun ta ya ce, "ki dena yawan tinani likita ya hana, saboda zai jawo maki ciwon kai mai tsanani, ki kwantar da hankalin ki kin ji, aikin da akai maku ne yasa kuka kai wadannan watannin ba tare da sanin inda kan ku yake ba, ni dinnan da kk ganni sai da nai sati uku a asibiti ban san ina kai na yake ba, abokina kuma wata daya da sati biyu, kafin mu ka ji sauqi ai ba karamin abu ne ya faru ba a ranar" Tausayin kansu ne ya kamata, lallai ashe hatsarin babba ne? A haka bacci ya ɗauke ta shi kuma ya yi palour yana murmushin samun nasara, waya suka yi da Alhj Kalla, cikin nishad'i suka fara hira, "Aboki ya ka qare da 'yar rigimar ka?" "Ba wata damuwa Komai ya tafi as planed, ban samu matsala ba, wannan shegiyar uwar tasu ce taso sawa mata ta tinani,amma na kawar da shi, yanzu haka bacci take yi" Sariya suka saka a tare sannan Alhj Ƙalla ya ce, "Ai ni tashi ta yi tana min shagwaba sai na ji kamar na manta da ciwon na dan more ta kadan, dan sai ta min kyau sosai, gaskiya mun iya zaɓe aboki na, kyawawa na gidan talakawa a b'oye talauci duk ya rub'ar da wasun su, su zo a fantama da su a samu kuɗi amma sai ka ga sun ki wai su na Allah, yanzu su wadannan da suka fito ba gashi sun haɗu da mu ba za mu shagwab'a su da nera? Ga kyau ka kuɗi Alaji" Dariya Alhaji Salihu ya yi sannan ya ce, " shegen sama, ana halin neman yanda za ai a rufawa kai asiri kana neman biyan buqatar ka, to amma fa mutumi na suna da gaskiyar su,mu ɗin ba rud'in shaid'an muke bi ba, ai tsoron Allah ne ya hana su fitowa gwanda su je lahira su shiga aljannah, mu ma dai kafin mu mutu mun tuba," (Kamar an sanar da su ranar mutuwar su) Dariya suka yi ta yi kamar abinda suke faɗa ɗin ba wani abun damuwa bane,Alhaji Ƙalla n e ya ce, " Anyway gate can dai na yi mata dabaru irin namu na manya ta bar zance fatan ta Allah ya bata lafiya, kasan har yanzu maganin bai gama sakin su ba, bacci take ta yi" "Haka ne, to sai dare in mun hade a gidan Oga, yau akwai meeting fa ka san" "Eh haka ne fa,to ba damuwa sai daren ma haɗe a can ɗin" kashe wayar suka yi kowa na jin daɗin samun nasarar da suka yi akan su suwaiba mutanen ABJ, yanzu tinanin su bai wuce yanda zasu na samun jini da aka ce suna kawo wa duk wata ba daga matan nasu, dan su ba sa son suna satar 'ya'yan mutane ana tsafi da su shi yasa suka yanke shawarar auren matan da za a dinga amfani da jikin su da kuma jinin su ana tsafin,dan satar yara a wajen su babban aiki ne da kuma wahalar wa,sannan su na tsoron kar watarana a kama su, dabara ce ta fado mai na yanda zasu na samun jinin daga wajen su, murmushi ya yi sosai,sannan ya ce, "Dan ta rashin haihuwa me sauqi ne, tunda ba ni aka cirewa mahaifa ba bare na damu, 'ya'ya dama takura ne a rayuwa ta, sanda na so haihuwa na nemo matar da zan haihu da ita na aura," Dariya ya dinga yi kamar mahaukaci sabon kamu ni ko nace hmmmmm kwadayi mabudin wahala. ***************************** A gidan Salman Talle kuwa, ko in ce Tallen Salma, ko kuma Tallen Marka, ana can ana badaqala uwa ba hantara uba baya nan sai ya ga dama ya leqo ya koma. Huwaila ce ke duqe gaban murhu ta na hura wuta, can ta d'ago ta yi wurgi da maficin hannun ta ta na buga qafa a qasa ta ce, " Ni dai Marka gaskiya na gaji da yin abinci kusan kullum a gidan nan habaa ai ni ba baiwa bace,kullum ni nake abinci talla sannan na yi na gida ?" "Nima haka gaskiya, wannan yar rainin ajawalin na zaune a d'aki kullum sai dai mu dafa mu bata, ga Baban ma baya nan sai sanda ya ga dama yake zuwa" "Tab ai ko yau ita zata yi tuwon dare ko ta ji a jikin ta, ni hutu ya samen, dan ba zai yu na nemo na tuqawa ba kuma na dafa na ba ku ku ci ba inaaaa, dole Itama ta fito ta girka ai gidan mijin ta ne itama" Ihu 'yammatan suka sanya suna fad'in, "Sai Markaaaa, uwar gidan Talle, an buga an barki" Dariya da shewa suka sake sanya wa kamar wasu 'yan daudu, ita kuma marka ta wani d'age qafa tana zaune a qasa ta turo dankwali gaba, tana kada qafarta da ta yi fururu kamar tunda aka haife ta bata san menene nan shafi ba, " Je ki kiran ita Huwaila yanzun nan" Da hanzari Huwaila ta miqe kuwa tana gyara daurin qirjin ta, tana tafe tana banqaro qirji, qugun kamar an daurawa tabarya zani, ta na Isa qofar d'akin Salma sai ta tsaya a bakin kofa ta daga labule ta cake tare da kama qugu ta ce, " Amarya ki zo Marka na son magana da ke yanzun nan" Salma na kwance ta ji Huwaila na mata magana cikin raini sai ta ji kamar ba zata amsa ba dan kuwa duk tana jin su, sai dai kuma wani irin mugun tsoron su take ji yanzu, dan duk wani rashin mutunci da yake faruwa a gidan ya na shiga kunnen ta, yau da gobe duk tana jin su, fitowa ta yi dan ta tsira da jikin ta, dan yanda suke ikirarin dukan ta kullum tasan za su aikata,ga uban su baya nan, ko yana nan bata jin a tarbiyyar gidan Talle zai ɗauki mataki sun dake ta sun daki banza a banza ne kawai, "Auuu kinzo shine ba zaki yi magana ba ma ki ka tsaya qiqam akan mutane haka?" Cikin tura baki gaba ta ce, "Gani" Saida Marka ta kalle ta asheqe sannan ta ce, "Salma ki ke ko wa? Ni kin San ba sabgar ki nake shiga ba balle na riqe Sunan ki,ki bude kunne da kyau ki ji, daga yanzu ke zaki dinga girkin gidan nan na safe da rana da dare, su yaran sun ji da na siyarwa, ba zai yu na yi ta wahala ba a gidannan, ke kina nad'e a gado, sai dai na dafa na miqa maki, ki cinye ki gyara d'aki ki yi wanka ki koma ki kwanta, ai ba abinda ya kawo ki gidan miji kenan ba, bautar aure kika zo yi, dan haka kula da yaran tsakar gidannan ma yana ciki, tsarkin kashin su da yi masu wanki, duk naki ne yanzu, in dai hutun amarci ne sati ɗaya budurwa, bazawara kwana uku, ke ko ban san ame zan saki ba, tsabar adalci irin nawa wata biyar da kwana hudu na baki kika huta, dan haka daga yanzunnan ba sai anjima ba ki dau aikin ki" " Wooo ke wooo ke markan Talle" Yaran suka dauka suna ta mata kirari tana kad'a qafa tana hura hanci su kuma suna dariya, kallon Salma da ke tsaye ta na kukan zuci ta yi ta ce, "Ban ji kin amsa ni ba fa" Cikin rawar murya Salma ta ce, " To" Ta juya zata tafi ta ji wani daga yaran na fad'in, " Naaa gaaamaaa" Kukan da take ta yi a zuci ne ya taso mata da karfi,nan take ta tuna da tinda take bata taba ɗaukan Ammar ba ma balle ta kai ta ga yi masa tsarkin kashi, gashi yau za ta yi wa ɗan wasu tsarki, kuma an maida hakan aikin ta. Cikin Isa Marka tace, "Ba ki ji bane ana sanar da ke an gama kashi ki je ki wanke sai kin gama qamar da dan mutane?" Sim sim sim Salma ta wuce zata je wanke masa kashin,Haule ta taso tace wa Salma, " Aunty bar shi na wanke masa" Marka ta sauke qafar ta da ta ɗora a d'ayar ta kalli Haule ta ce, "Ke uwar kitifi uwar kinibibi, ina ruwan ki da hukuncin dana yanke? To a hir din ki kar kina min haka ranki zai mummunan baci, ita na ga dama ita zata wanke" Salma ce ta kalli Haule da murmushin yaqe ta ce, "Na gode Haule zan masa kije kawai ba komai" Wanke wa yaron kashin ta yi zuciyar ta na matuqar tashi, tana fitowa daga band'akin wajen zubar da na poo ɗin yara suka kwashe da dariya har da uwar tasu suka tafa, murhu Salma ta nufa ba tare da ta tanka su ba to me ma ta isa ta ce? Ta na Isa ta duqa ta ci gaba da hura wuta ta dora ruwan tuwo, ranar dai a taqaice ba ita ta kwanta ba sai goman dare, jikin ta ba inda baya yi mata ciwo dan aikin wahalar da ta tiqa, tuwo ta tuqa da ya kai yawan kwano ɗaya da rabi har na dumame, dan haka tana kwanciya ta hau bacci kamar wata matacciya. ************************** " Dan Allah Juwairah ki yi sauri mana, duk wannan wankan naki na qa'ida sai ya sa ba mu fita da wuri ba" Nafeesa ke jiran Juwairah da ta gama girkin rana wajejen qarfe sha daya na safe,ta kammala gyaran gidan tsaf tana son yau ta je ganin Maman ta , Nafee tace zata yi mata rakiya, dan haka ita har ta shirya amma Juwairah na can na wanka, can bayan kamar minti takwas ta bude ta fito daga bayin ta na fad'in, " kin san Allah, ba dan kina jirana ba sai na qara five minutes, ya zan na yi wanka jikina bai fita ba, kowanne bangare a jikin mace fa ana son amasa wanki mai kyau, musamman lunguna da saqon jikin mace ke har kunne da cikin kunne sai na wanke, haka kurum Yah yazo min soyayya a kunne ya ji d'acin datti" Cike da tsokana Nafee ta ce, "Inyyee iyayen love, aiko ba zan gangancin wanke kunne na ba ruwa ya shige min a banza a barni da zuwa asibiti da jin azaba" "Hhhhhh dad'ina dake komai baki iya ba, in zaki yi ai dabara zaki yanda ruwa ba zai shiga ba, tinda kinga yawan goge kunnen nan likitoci na ta hanawa bai da kyau, to sai ki samu ki karkata kunnen ki gefe d'aya, ki wanke ta baki bakin da lungu da saqon shi, in kk gama kik d'auraye sai ki saka towel ko zani ki tsane ruwan tas, in kika gama da b'ari ɗaya sai ki wa bari ɗayan ma haka, kinga ba ruwan da zai shiga kuma kin wanke shi fesss" " kaiii Juwairah wayon ki da sanin yakamatan ki na ban mamaki, dan na kula wataran Mama Bilki ma mamakin ki take sosai akan halayyar ki" "Hmmm tashi to mu wuce na gama shirya wa" Tashi suka yi suka tafi bayan sun leqa sun yi wa Su Innarmu sallama ita da Baba Balarabe, qara masu kud'in mota ya yi yace su gaida mutan gidan in sun je, kar su yi magariba a can su dawo gida amsawa suka yi suka yi godiya suka tafi. Da sallama suka shiga gidan, cikin zumudi ta fada dakin nasu, Mama Bilki ce ta fito dauke da fara' a sakamakon gane mai sallamar da ta yi, a hanya suka haɗe suka rungume juna suna ta murna, Ammar ne a gefen maman, da sauri ta dauke shi tana masa kisses ko ta ina,cikin farin ciki ta ce, " I missed u so much my baby brother, how ar u doing my love?" Dariya yake ta yi kamar ya gane ta yana ta surutai irin na yara masu son yin magana, dariya ta yi ta aje shi a cinyar ta suka hau gaisawa, Nafee ma gaida Mama ta yi, tana mai jin daɗin yanda taga soyayyar 'ya da uwa a tsakanin Juwairiyyah da Mama Balki, Goggo ce ta fito ta na shewa ta na dariyar shaqiyanci ta ce, " A'a mutanen kano ta dabo ci gari jalla babbar hausa, ne a gidan namu yau kuma?" Goggon ta qarasa tana dariya, Nafee da ta san irin zaman doya da manjan da ke tsakanin Goggo da su Mama Balki sai ta karɓe maganar ta ce, " Kano ko da me kazo an fika ba, in mutum ya faɗi alkairi yanzu mu bashi amsa dan gidan ya tarar amma in ya kuskure nan ma sai muje maqota mu yi aron rashin mutunci mu bashi amsa da kalar yaren shi" Nafee ce ta qarasa maganar ta ta na murgud'a baki da fari da idanun ta, Mama ce ta kalli Nafee ta ce, "Kul Nafeesa, ai uwa ce Goggo a wajen ku, kome zata yi kar ku tanka ta, ku barni da ita nice daidai ita" Goggo Sarai ce ta buga cinya ta tafa hannu sannan ta ce, "Hahaiiiiiiiiii Casssssss a hakan? A hakan ne kike daidai da ni? Daga shekaran jiya da yarana suka min waya zuwa yanzu kudin da suka shigo mun ta akawun ( account) ba qanana bane, ke kuma fa? Me ta kawo maki, tuwon dusa miyar lalle?" Dariya ta kwashe da shi sosai harda riqe ciki,Baba Baballiya ne ya shigo ya ji abinda ke faruwa cikin ɓacin rai ya ce wa Goggo, " ke dai anyi sallamammiyar mace saratu, yanzu me kike yi kenan? Kin tsaya kina rashin mutunci gaban yara, ke da baki da kamun kai, baki son a zauna a gidannan lafiya, kullum sai kin nemi tijarar da ki ka qirqira aka yi a gidan nan kar ki zaci ban sani ba ina sane da duk abinda ki ke yi, ashe yauma ba zaki sawa kanki salama ba?" Juwairiyyah ce ta tashi da sauri dan ta kauda maganar da Baban nasu ke yi ta ce, "Oyoyo Baba na da gudu ta je wajen shi ta rungume shi, shima rungume ta ya yi ya kama hannun ta suka zauna, qasa ta duqa ta gaishe shi, Nafee ma haka amsawa ya yi cikin nishadi" Ganin haka sai ran Goggo ya sisi, ta kalle su ta ce, "Ehhhhh lallai ne yau 'yar so ta zo, ka balbale ni da bala'i a gaban su mana, yarana tunda suka tafi baka neme su ba, amma wannan nunar ranar kullum sai ka tambaye ta, yau kuma ji yanda kk rungumar yar cikin ka kamar a gidan qabila" " Ke malama in baki da abin faɗa mai kyau fita ki ban waje, Jahila kawai wadda bata san me ake kira da musulunci ba balle ta san abin cikin shi" Magana Goggo ta buɗe baki za ta yi,Baba ya daka mata tsawa, ba yanda ta iya dolen ta ta fita tana qunquni, ci gaba da gaisawa sukai yi sosai ya zauna suka yi ta hira da 'yar tashi,haka dai har lokacin tafiyar su yayi, Mama ta tashi ta hau dan harhad'a mata wasu abubuwan iya qarfin ta dai, sallama suka yi tana kuka suna lallashin ta suka rabu. Su kuma su Juwairiyyah suka koma gida,ko da suka isa gidan sun zaci za su tarar Innarmu ta dora girkin dare sai suka ga sab'anin haka, murmushi Juwairah ta yi ta shiga ta canja kaya, sannan ta fito ta hura wuta ta dora taliya a cikin kayan da mama ta basu, ta hada da ganyen alayyahu da albasa, ta daka yar daddawa kaɗan dan ba isasshen maggi to daddawar zata taimaka abincin ya yi daɗi , nan da nan ta kammala ta fada wanka abunta kamar ma ba ta yi ba. Hikimar gyara daki kenan a wajen mace kafin ta fita unguwa, in kika gyara gidan ki tsaf in da hali ma ki yi girki kan ku fita har na dare tunda baki sani ba ko ku jima musamman idan da mutane a gidan, da kin dawo to wanka zaki yi kawai ki zauna ki huta abinki, ba ruwan ki da zama cikin qazanta, da kuma taraddadin aiki a gaban ki,in dai da ran ki da lafiyar ki to ki qoqarta ki na tsafta. Juwairiyyah na fitowa daga wanka Jabeer ya dawo, fita ta yi ta amshi ledar hannun shi ta ajiye suka yi barka da dawo war su yanda suka saba, sannan ta ja shi bayi, sabon wanka ta sake domin cewa ya yi bata fita ba sai ya sake yi mata, tana dariyar gano wayon shi da ta yi tace, "To shikenan ka gama nima sai na maka naka muje muci abinci dan na gaji yau da wuri zan kwanta" "Tab yarinya ki daina zancen bacci da wuri ma in zaki bari" Yana maganar yana matsa cinyoyin ta da yake wankewa, yar qara ta yi ta shagwaba ta faɗa jikin shi, tana goga cinyar ta ta a jikin shi,ta ce, " Yah Jabeer akwai zafi fa" Yanda ta yi maganar a saitin kunnen shi ne ya sanya shi jin wani ya tsarga masa har tsakiyar kanshi , janye ta ya yi a jikin shi ya jiqa mata soson ya bata ya ce, " Yi sauri ki wanke ni nima ba zan iya jira ba baccin nake ji" Dariya ta yi ta amsa tana masa wankan cikin wani salon da ya amshe soson ya aje gefe ina ganin haka na ari qafafu wajen masoyan Juwaireren Mama na qara gaba a guje........ [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼     'YAN ABUJA    💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 10 Dare ne yanzu a cikin garin Abuja,manyan Alhazawa ne masu ji da nera a wajen shaqatawa na wani babban hotel da ke cikin garin su na hutawa da 'yammata da samari, sai kai komo manyan 'yan mata masu ji da kan su suke yi a gaban Alhazawan saboda suma a dama da su wajen cin kud'in da aka samu na yaki halal yaki haram. Alhj Salihu da Alhaji Kalla ma ba a bar su a baya ba, dan kuwa su ma suna tare da 'yan matan su da bazan iya tantancewa arna ne ko musulmai ba saboda shigar banzan da ke jikin su,watace a cikin 'yammatan da na ji an kira da 'yar Gwal na kalla da kyau,daga nan na gane hausawa ne ma ashe ba arna ba,amsawa ta yi ta juya ta na kallo 'yar uwar tata da ta kira Sunan ta, nuni ta yi mata da ido, bin inda aka nuna mata ta yi da ido suna murmushi, "Mene ne na ga kuna wani dariya kamar wasu wadan da suka tsinci damin kudi a qasa?" Inji Alhj Kallah kenan da ya ga sanda suka yi murmushin, 'Yar gwal ce ta hau cinyar Alhj Salihu tana wani karairaya tana shafa shi sannan ta ce, " Alhaji na kuɗi muke so ne shi yasa, gaba ɗaya qawayen mu sun wuce mu a komai na more rayuwar duniya bayan duk tare muke wannan harkar kuma muna tare da manyan mutane kamar ku,gaskiya zai zama abin kunya ace ko motar hawa bamu da ita su da suke bin qananan kwari su na jan mota mu kuwa kullum sai dai mu yi waya ku aika a d'akko mu ko mu hau taxi, gaskiya yawa ne Alhaj" Tana magana tana kai bakin ta jikin nashi ta na masa wani salo mai ɗaukar hankali,wani irin nunfashi Alhj ya fitar da bai san yana ruqe da shi ba,a hankali ya ce, "Haba 'Yar gwal yanzu dan wannan qaddamar buqatar shine kuke wani abu kamar baqi, ai in kuna son abu kamar umarni zaku bamu kawai, dan haka,....." kafin ya qarasa maganar shi 'Yar Gwale da qawar ta suka tashi tsaye suka kama hannun Alhazan nasu dan kai su d'akunan da suka saba sheqe ayar su tinda sun ji buqatar su za ta biya, kuma Alhazan ba su yin alqawarin karya. Tin a hanya suka fara romancing din su, ina ganin haka na yi baya na koma gidan Suwaiba naga wainar da take toyawa. Hango suwaiba na yi tana zaune ta baza kaji a gaba da fresh milk tana darje baki, hankalin ta kwance ba ta da wata damuwa da ta wuce ta faranta ran ta da dukiyar da mijin ta ya ke da ita,hannun ta ɗaya riqe da waya tana dannawa, bayan ta gama cin naman ta ne ta shiga band'aki ta yi wanka ta yi brush, ta saka kayan bacci dan ta yi bacci, amma sam bacci ya qi ɗaukar ta,komawa ta yi palour ta kunna kallo, ta na kallo tana duba lokaci, wannan rayuwa anya za ta yuwu a haka kuwa? ace miji ba zai dawo da wuri ba sai dare ya raba? Tashi ta yi ta dakko fruit salad data hada ta saka a fridge, ta zauna tana kallo tana shan abunta, bayan ya qare ne, ta ajiye bowl din a gefe, sai hamma take tana miqa, duk ta gaji da zaman shirun, wayar ta ta ji tana ringing, miqa hannu ta yi ta dauka, Sunan Saudat ta gani na yawo a screen ɗin wayar ta ta, "Saudat love" Shine sunan da ta yi saving No Saudat da shi. " Hey sis" "Hi" "Ya ki ke, da yayan nawa?" " Muna lafiya, Ya Alhjn ki?" "Muna lafiya" "Dama kiran ki na yi na ji ko Baby na gidan ku, tsoro nake ji, gidannan ya min girma ni kaɗai masu aiki na bangaren su, duk dare sai na dinga ji kamar kirana ake," Ta faɗa cike da tsoro,shiru Suwaiba ta yi kafin daga baya ta ce, " Sis kiyi hakuri baya nan, nima zaman jiran mine nake yi yanzu haka, duk yanda akai suna tare, ki kwantar da hankalin ki ki mori abinda ya kawo ki, tin kan lokaci ya qure maki" Saudat amsawa tai da "To" Sallama suka yi suka kashe wayar Suwaiba ta tashi ta yi d'aki, bata jima da kwanciya ba, lokacin qarfe 2:45am ya shigo bakin shi duk warin giya, tsabar kwarewa da suka yi dan shan barasa ko layi na marisa  ba sa yi,sai dai a gane ta idanun su da ke yin jawur, da kuma saurin fushin su,Suwaiba ce ta miqe ta nufe shi a zafafe ta ce, "Wai wannan wanne irin wulaqanci ne Sweethert, tinda nazo gidan nan i can't remember the last time we had xxx, amma da na yi maka magana sai kace lokacin ban da lafiya a bari na wanke to yanzu da na ji sauqi ka kasa sauke nauyin dake kan ka, amma kai da dikkan alamu har yanzu kayi auren ma wasu kake bi a waje baka dena ba,ga wani sabon hali da na ga kana yi na shaye shaye wai ashe  har da giya ka ke sha wadda ni ban san kai din dan giya bane kuma d'an maye,wannan ai iskanci ne da wulaqanci" Suwaiba ta qarasa maganar cikin d'aga murya da masifa, a karkace Alhaj Salihu ya kalle ta ya ce, " Ni ki ke kira dan iska,ni ki ke kira dan iska ko, ba dai ni ki ka cewa dan iska ba suwaiba ? Yau Zaki ga iskanci ganin idon ki Suwaiba" Miqewa ya yi ya janyo ta ya hau duka kamar an aiko shi, a haka ya cire mata kayan jikin ta ya wurgar duk ya yaga su saboda kiciniya da dambe, wurgara gado ya yi ya ta kanta, Suwaiba kuwa ba abinda take da ya wuce kuka da neman taimakon tare da ban haƙuri, "Dan Allah Mine ka yi hakuri nice yar iskar ba kai ba, ba zan qara ba , ka taimaka min, ka duba auren soyayyar da muka yi da kai ka yi hakuri" kwad'e bakin ta ya yi ya ci gaba da abinda yake yi sannan ya ce, "Auren soyayya ki kai da wa? ko dai auren kwad'ayi auren kudi? Karki zaci ban san ke da uwar ki da qanwar ki kwad'ayayyu bane,  Ina sane da komai, ni ba qaramin mutum bane, kamar yanda ku ka yi auren kuɗi mu ma mun aure ku ne dan kyan ku da biyan buqatar kammu,kowa kin ga ya samu abinda yake so ko Suwaiba 'Yar Abuja? Ko ba haka qawayen ki suke Kiran ki ba?" Qara wurgata gadon ya yi da take qoqarin guduwa ya kwanta a jikin ta, kamar wani wanda aka yi wa allurar bacci nan da nan bacci ya dauke shi, kuka ci gaba da yi sosai jikin ta na yi mata ciwo, haka ta tashi ta ja jiki da kyar, ta tafi toilet, ruwan zafi ta haɗa mai zafi sosai ta shiga, tana shiga ta yi wata muguwar qara saboda azaba, a haka ta gasa jikin ta sai da ta ji ta daina jin ciwon wajen sannan ta saki jiki ta kwanta a ruwan da ta sake sanya wa nan da nan bacci ya fara diban ta a zaune a ruwan, buɗe ido ta yi ta fita ta je ta saka wasu kayan ta koma ɗaya dakin ta kwanta, ta rufa, nan da nan baccin wuya ya yi awon gaba da ita. Da asubar fari Saudat ta kira ta a waya tana kuka, ta sanar da ita irin cin mutuncin da Alhj Kalla ya mata itama, sata ya yi ta yi ta masa tausa, har wayewar gari shi kuma ya na shaqar bacci, data fara gyangyadi ya zabga mata mari dole ta farka ta ɗora daga inda ta tsaya, kuka suka yi ta yi a tare ba mai lallashin wani, itama Suwaiba labarin nata bala'in da ta qunsa tayi sannan suka ce gobe zasu haɗu in mazajen sun fita. Shigowa dakin suwaiba ta ji za a yi cikin sauri  ta danne wayar ta kwanta ta yi lamo kamar me yin bacci, qarasa shiga Alhj Salihu ya yi ya zauna kusa da ita ya ce, " Haba my Suwai hakuri zaki yi, ke ma kin san in rai na ya ɓaci bana son a cika tambaya ta musamman maganganu na rainin wayo, auren kuɗi ki ka yi kuma ga kud'in nan, to meye na damuna sai na maki wani abun?" Kuka take a zuci hawaye na zuba ta gefen idon ta bata ce masa komai ba, janta ya yi jikin shi yana shafata, take ta fara sauke ajiyar zuciya tana hamma, don bacci take ji sosai, kiss ya mata ya maida ta ya kwantar yace shi zai fita, d'aga masa kai kawai ta yi ta koma ta lumshe ido, bayan ya fita ne ta yi baccin awa uku ta tashi ta yi wanka , ta haɗa abin karyawa mai rai da motsi da tea mai kauri ta ma manta jibgar da ta sha, taci tai nak abinta, Wayar ta ce ta yi ringing ta amsa da , " ku barta ta shigo qanwa ta ce" Sannan ta kashe, Wajen kamar minti 5 Saudat ta shiga cikin gidan cikin shiga ta alfarma, ga wata arniyar mota da ta zo da ita driver na tuqata, ta ci gold ko ta ina hannu da qafa da kunne, dan harda sarqar qafa suke daurawa saboda wadata ba dan wani abu na,har parlourn sama mai aikin Suwaiba ta yi mata jagora ta na  isa ta zauna kusa da sister din ta akan dinning table ta ja plate ta zuba chips da kwai da farfesun naman kan rago, sai tea da ta haɗa itama mai kauri ta hau sha, ba wadda ta ce wa 'yar uwar ta sannu,sai da ta gama sannan ta yada kai baya ta zame kaɗan daga kujerar tace, " Sis ina cikin tashin hankali wanda da dikkan alama kema hakan take a wajen ki, dan ga jikin ki nan ya nuna, dubi fuskata nima ki gani" Ta fada tana mai nunawa Suwaiba fuskar ta da ta yi jawur ta kumbura, sai rufewa ta yi da mayafi da ta shigo gidan kar a gani, sannan ta ci gaba da magana, "Ga kuma zaman yunwa da na yi dan jiya kwata2 kasa cin komai na yi har safiyar nan, sai da na ga wannan abincin ne na ji yunwa ta motsa min" Suwaiba ce ta yi murmushin takaici sannan ta ce, "'Yar uwa bari ki ji, ki cire komai a ranki shawarar da zan bamu shine mu cire rai a son sai sun zama mutanen kirki, tin da dai ba halin su bane, mu zauna mu mori dukiyar da muka zo Abuja domin ta, mu zama manyan hajiyoyi,mu bawa maqiyan mu kunya, dan ni kam kin ganni nan, in ba jiya dana sha jibga ba, bana wasa da abin ci ko wani nau'i na jin daɗi, sannan kuma da kk ganni nan haqqina na aure in daga yau ya ce ya daina ban ba zan damu ba ba zan sake tambayar shi ba, domin kuwa akwai hanyoyi da dama da zan iya maganin matsala ta, wanda na san kema kin san su ba sai na tsaya bayani ba, i hope ba zasu yi gangancin turamu wannan stage din ba, zasu na daure wa ko once in a while ne suna biya mana buqatun mu, to kinga ba mu da matsala da bin matan su ko kuma wani abu mai kama da shan giya, sun dad'e ba suyi ba, dan ba zan qara yarda a taba lafiya ta ba, an gama daga jiya" " kaiiiii yar uwa wannan shawara tayi sosai" Tafawa suka yi suka koma palour suka debo dambun nama da juice suka zauna tare da kunna kallo, sunayi suna hira qarshe waya suka dauka, suka hau kiran Goggo Sarai, suna waya,  a lokacin suna tsakar gida dikkan su, Mama Bilki, Abban su Juwairah da ta kai masu ziyara sai Ammar dake zaune a cinyar Juwairiyyah, da ita kanta Goggon, wanki Mama Bilki keyi na kayan Abban su da na Ammar, ita kuma Goggon su na duba girkin ta wanda ta dad'e da dena cin abincin gidan sai dai ta yi nata, su kuma suci nasu, hakan da ta yi yaba Abban damar su samu sauqi daga dawainiya, shiyasa ma wataran suke samun abinda suke aikawa Juwairah dan Mama ta kula da rayuwar da take ciki a zuwan da ta yi sau ɗaya, amma da ta tambaye ta ya zaman nata yake a gidan ta sai ta qeqasa qasa tace ita lafiya lau komai yake tafiya masu, ganin ba zata buɗe baki ta yi bayani bane ya sa Mama yi masu addu'a kawai ta kyale ta, amma tabbas tasan akwai wata a qasa, cikin firgici ta daga kai daga tinanin ta sakamakon wata qara da Goggo Sarai ta saki......[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼      'YAN ABUJA   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH *SANARWA ! SANARWA !* *Ina masu buqatar sanin yanda za su gyara jikin su ta ciki da waje? Ina nufin daga gashin  kan su zuwa yatsun qafar su da qarin ni'imar jikin su?* *Ina masu son koyon sana'o'i dan samun taro da sisi? To 'yar uwa matso kusa ba sai kin biya maqudan kuɗi ba dan ki koyi yanda Zaki yi sana'ar da zata sama maki kuɗi da #1k kacal za ki mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA* *Idan kuma ke ma'abociyar karanta littafan Hausa ce ki yi wa HAERMEEBRAEH ❤️magana kai tsaye ta wannan No 09031416423 kai tsaye, Zaki samu Littafin MAHREEN DA KYAKKYAWAR FAHIMTA a kan farashi #500 each* *Please share*❤️ Page 11:   Mama na juya wa sai ta ga wai ashe Goggo Sarai dariya take a hakan dan kawai ta ja hankulan su Mama Balki su ji ta na waya da 'Yan Abujan yaran ta da take alfaharin sun haye a rayuwar zaman duniya dai ba ta qiyama ba. "Hahhhhaaaaaiiiiii kaiiii amma na ji daɗin haduwar ku gaba ɗaya waje guda, ikon Allah ana can ana cin amarci sai yau aka samu haɗuwa kenan, to ya masu gidan? Ya rayuwar hutu da jin daɗi kuma?" Suwaiba ce ta ce, "Lafiya qalaou Goggo, ina Baba?" " Hmmmm ga shi can wajen waccan sallamammiyar matar tashi da ta shanye shi" " Bashi mu gaisa kar yace bamu neme shi ba" " Aiko bada wayata ba ehe ku kira shi a yar rakani kashin shi kawai" Tana fada tana hura hanci tana turo dankwali gaba irin na fitsararrun matan nan? Kad'a kai kawai Baba Baballiya ya yi sannan yace, " Allah ya kyauta" Murgud'a baki Goggo Sarai tayi kamar wata qaramar yarinya, irin na rashin kunyar nan da raini ita a dole sai ta nuna ta fi ƙarfin mijin ta kuma ba ta jin maganar shi balle girmama shi. Makaranta kunsan fa shi murguda bakin ma kala2 ne, akwai sexy murguda baki mai daukan hankalin oga, ya ji dole sai ya kai nashi bakin a naki sabida yanayin yanda ki ka yi shi da salon jan hankali, sannan akwai na rashin kunya kamar na Goggo sarai kenan. Ganin yanda take masa rashin kunya gaban matar shi da yara shi ne ya sanya shi tashi dan ya je waje ya sha iska sai wayar shi ta hau ringing, d'agawa ya yi da sallama muryar su Suwaiba ya ji a tare su na gaida shi kamar ba sa son gaishe shi,ya kula sarai amma sai ya danne ya amsa tare da tambayar su gidajen su tare da Mazan sannan ya qara da fad'in, "Ku na nan dai lafiya ba wata matsala ko?" Cike da rashin kunya suka buga shewa tare da fad'in 'Hhhhh Baba do u really have to ask ? To muna lafiya qalou alhamdulillah, komai normal kamar dai yanda ka sani Baba mazajen mu masu kuɗi ne, so ina ganin ai bamu da wata matsala mu a rayuwa, sannan gida da mazajen namu duk suna lafiya da Fatan mun amsa tambayar ka" Cikin qunar rai Baba ke magana, " Suwaiba ni mahaifin ku ne dan haka ba zan gaji da yi maku nasiha akan ku bi duniya a sannu ba, yau in kaine gobe ba kai bane, dukiya da abinda ke cikin duniyar nan ba komai bane face rudin shaid'an ga wanda ya mai da su abin bauta, kuji tsoron Allah a lamarin ku, Hello ! Hello..... " Shiru ya ji ashe sun dad'e ma da kashe wayar tin da ya fara wa'azi suna ta fad'in yanzu zai takura masu, mamaki ne cike da zuciyar shi Baba ya ce, " Yaran nan ni suka kashewa waya?" " Baban su ka yi hakuri komai zai daidai ta da qarfin addu'ar da zaka dinga wa iyalan ka, Allah zai shirya maka su inshaa Allahu, adduar iyaye amsasshiya ce a wajen Allah, Allah ya shirya mana zuria" "Hmmmmm Ameen Gimbiya ta Allah ya albarkace ki da zuriar mu duka" Daɗi ne ya kama Mama mara musaltuwa kwatankwacin daɗin da take ji a duk sanda ya yi mata irin wannan adduar, " Ameen a bin sona" Murmushi suka yi wa junan su wanda ya sanya shi ya ji baqin cikin shi ya tafi gaba ɗaya ,ruwan wankan da ta saka masa ya ɗauka ya tafi ya shiga wanka abin shi ya fito tsaf,ita kuma Mama sai ta fara qoqarin dora masu abincin dare. Magidan ta ku dinga qoqarin yi wa matan ku godiya da addu'a  musamman ta nema masu albarka a wajen Allah, in albarkar nan ta samu a garesu zata shafe ku kuma da zuri'ar ku kenan,ku kuma mata ku dinga yawan yin abinda ku ka san zai faranta wa Mazajen ku rai su yi maku addu'a, soyayya bata tsufa sai dai masoyan su tsufa. Juwairiyyah bata bar gidan nasu ba sai yamma liss cike da tunanin halin da rayuwar gidan su take ciki. **************************** Bayan kwana biyar da zuwan Juwairiyyah gidan iyayen ta suna hira da Nafee da safe suka shirya yanda suke so Watarana su kai wa Shamsiyyah qawar su ziyara,nan take Nafee ta ce me zai hana su kai mata ziyarar a yau? Juwairiyyah sai ta nisa sannan ta ce, "To bari mu gani Allah ya sa aiki be sha min kai ba lokacin" Cikin ran ta kuwa ta na tunanin yawan fitar da take yi a 'yan kwanakin gashi ita ɗin ba ma'abociyar yawan fita bace. Da yamma kuwa sai ga Nafeesa ta shirya tsaf cikin riga da skirt na atampa, tayi kyau sosai ta taho bangaren su Juwairah, ganin Juwairiyyah ta yi na harkokin gaban ta ba ma ta da niyyar fita,cikin jimamta lamarin ta ce, "Matar Yayah ya na ga baki shirya ba kin saka dan guntun wando da vest an faka gashi gefe?" " Nafeesa kenan da dikkan alama kin manta yau Yaya da wuri zai dawo gida ko? sannan yau ranar dana ware ce domin gyaran lambu na ko duk kin manta qafar yawo? Sannan ga girki da zan yi da wasu aikace2n, kuma sanin kan ki ne ni fa yawon shiga nan shiga can dinnan ba son shi nake yi ba, shike kawo mace ta daina kula da iyalan ta da gida tana qarewa a titi" Cikin mutuwar jiki Nafee ta ce, "Hakane kuma gaskiya ki ka faɗa,amma gaskiya ni dai zan tafi gidan Shamsiyya na gaida ta dan na riga na yi niyya kuma na yi mata alkawarin zani yau din, na zaci zamu tare ne tinda na ga ke kin dad'e baki je ba, sai na dawo to" " To ki dawo lafiya, ina gaida ta da yaran" Fita Nafee ta yi ta tafi gidan Shamsiyya, ko da ta isa gidan Shamsiyya sai ta tarar da ita a gida tare da yaran ta biyu mace da namiji, Farha da farhan, goyo take yi na 'ya macen , gaba daya gidannan sai a hankali, komai da kan shi yake zaune a inda bai kamata ba,cike da kyankyamin halin da ta samu gidan qawar tasu ta shiga parlour ta zauna a kujera ta na qarewa parlourn kallo,da sauri ta miqe tana duba skirt din ta daya jiqe, hannu ta sa ya tab'o skirt ɗin sannan ta kai hancin ta,wani irin  mugun zarnin fitsari ta shaqa, da sauri ta kauda kanta ta fita tsakar gidan ta ɗauki buta ta sa ta ruwa ta wanke hannnun ta sannan ta saka a skirt d'in ta tana masifa ba tare da ta amsa lale maraban da Shamsiyya ke yi mata ba, "Ni gaskiya shiyasa bana son zuwa wajen ku shamsiyya, ga gida har gida Allah ya hore maki amma sai uwar qazanta, duba dan Allah daga zuwa na na zauna akan fitsari , ko da Juwairah bata haihu ba na san abin da ba za a taba samun ta da shi ba kenan a duk lokacin da ta haihun, yanzu haka saboda gyaran gidan ta da kula da haqqin mijin ta yasa taqi biyo ni, Juwairah na da lokutan yin komai na kula da iyalin ta da gidan ta, tinda ba za a hadu ace kullum zaka haɗa kowanne aiki kayi ba zaka gajiya watarana, sai wanda suka zama aikin yau da gobe, dan Allah ki gyara, dan yana ɗaya daga abinda yasa Baban Farhan yake neman aure duk.da ya faɗa maki amma kin qi gyarawa haba Shamsiyya" "kaiiii Hajiya bala'i daga zuwa.sai wannan dogon karatu? To dan Allah ya kuke so nayi? Ga aikin gida gana miji gana 'ya'ya, ni dai gaskiya abun ya min yawa ya kuke so na yi ne wai" Kawai sai ta fara hawaye wai ita a dole komai ya mata yawa, kama hannun ta Nafeesa ta yi suka koma palour ta zaunar da ita a kujera, sai da ta laluba wata kujerar ta ji ba jiqa sannan ta zauna ta fiskanci Shamsiyya ta ce, "Qawata ki yi haƙuri ki daina kuka ni ba wai ina maki faɗa dan ranki ya baci bane" " To dan meye? Saboda kowa ya tsane ni sai a dinga ce min qazama ? Kalmar qazama fa na da ciwo tsakani da Allah" Majina ta sharb'a tana goge hancin ta da zanin ta,Nafee na ganin haka ta ji kamar ta kwad'a wa Shamsiyyah mari,cikin karkace kai ta ce, " To yanzu kin ga hakan da ki ka yi ni da nake budurwa Banda miji ba zan yi shi ba, da na goge majina da zani na gwara na je na wanke hancin gaba ɗaya, ai in kk ji ance qazama akwai kalmar tsafta kuma ko? To ni so nake ki cire kalmar da kowa ke kiran ki da shi na qazanta ki mai da shi mai tsafta, yanzu ki fa duba kiga  Mama Bilki, kullum kika shiga wajen  ta feeesss za ki gan shi,  kin ga dai ta girma ko tunda Babar aminiyar ki ce ba yarinya bace, saboda tsabar qamshi da tsafta ba zaki so barin d'akin ta ba, come to think of it ba fa ta da kuɗi ma a hakan da wadata kamar yanda ki ke da shi? Dan Allah kema ki gyara ki rage son jiki,son kallo da karancr2n nan na zamani har sai kin gama komai sannan ki ɗauka ki ta yi,ina fatan wannan ya zama na qarshe da wani zai baki shawara ko za a zage ki akan tsafta, in baki gyara ba Abban Farhan yace maki zai qara aure kuma ya fara nema in kika gyara nasan bari zai dan matsalar shi dake kenan ba wani abu ba" " Na gode qawata, ba wanda ya taɓa zaunar da ni ya min bayanin ya shige ni kamar yanda ki ka yi min yanzu" "Ba godiya a tsakanin mu, Allah ya baki ikon gyarawa" Murmushi suka yi wa juna shamsiyya ta miqe ta fara tattara kayan wajen data loda a kujera, nan da nan Nafeesa ta taya ta suka gyara gidan ya dau haske da qamshi, girki suka yi mai rai da lafiya kala2, wajejen la'asar Nafeesa ta bar gidan cike da tsaraba daga wajen shamsiyya, a ranar ta sha wanka da gaye, Abban Farhan daya dawo ya sha mamaki amma bai nuna ba, sai ya nuna mata matuqar jin daɗin shi, dakuma yabawar shi tashi ya yi ya je dakin shi yace, "Ina zuwa" wata sarqace ta gold mai kyau d'akko a cikin wani madaidaicin box kalar maroon,ya na fitowa ya zagaya ta bayan ta ya d'aura mata a wuyan ta ya na shafa sarqar da wuyan nata, a hankali ya kai duban shi inda yaran shi ke kwance har sun yi bacci ta saka masu pampas da kayan baccin su wanda tun da su na da shi amma baqar qiwa ta hana ana saka masu,Nafee ce ta koya mata yanda zata na qoqarin sanya yaran baccin da wuri kafin baban su ya dawo, watarana kuma ta bar su ido biyu dan su masa sannu da zuwa su yi wasa ya gan su su gan shi suma, godiya ta yi ta masa shima yana godiya da sabon sauyin da ya gani a tattare da ita, a daren ranar saboda kulawar da ya samu a wajen ta ya yi mata alqawarin zancen aure ya rushe sai dai idan ta koma yar gidan jiya ne, cikin salon lallashi ya ce, " Baby ki kwantar da hankalin ki dan ni ba mai ra a yin mata biyu bane ko sama da haka tun tini, tsaftar ki da rashin tsaftar ki in ni me ra ayi ne ba zata hana min yin aure ba, na faɗa maki ne dama dan ki gyara mu more rayuwar auren mu yan da ya kamata, tun da ko shekara biyar ba mu yi ba har yanzu amma duk kin dena kulawa da ni da gida da yaran ki,masu shekara arba'in su na can su na more rayuwar aure su" Ta ji daɗi sosai da wannan albishirin da aka yi mata,iya kuwa ta qudurta ma ranta zama mace mai tsafta ta bugawa a jarida kuwa dan ganin ta faranta wa mijin ta, yanda kowa ya yi mata tambarin qazanta sai an buga mata na tsafta in Allah ya yarda. Ni ko na ce to Allah ya yarda ya shirye mu mu gane tsafta na da kaso mafi tsoka a rayuwar aure. Bayan Juwairah ta gama komai ta yi wanka ta kwanta tana hutawa ne bakin ta na ta yin tasbihi ga Allah bacci mai daɗi ya dauke ta,Jabeer ne ya shigo ya ga yanda ta kwanta ta na bacci ba qaramin kyau ta yi masa ba,zama ya yi a gefen ta ya sa hannu ya na yi mata tafiyar tsutsa a qafar ta,a hankali ta farka amma idon ta na qara lumshewa saboda baccin da ke damu ta, juyi ta yi ta cusa kanta a cinyar shi ta ci gaba da baccin ta, a hankali ya janye ta ya gyara mata kwanciyar ta dan ya kula a gajiye take, da kan shi ya tafi d'aki ya cire kayan shi ya ajiye inda take aje masu kayan wanki bayan ya ninke su, ya na yi ya na tuna da idanun ta biyu ba zata bar shi ya yi duk haka da kan shi ba, maida shi take kamar wani sarki a wata Babbar masarauta, murmushi ya yi sannan ya tafi wanka dan har da ruwan wanka Juwairiyyah ta aje masa kan ta kwanta. Bayan ya fito daga wanka ya gama shirya wa ne ya ga  kamar bata ci abinci ba, sai ya  ya shirya abincin ya zo ya qara tashin ta amma still bata farka ba sai ma magagin bacci da take yi masa,da alama dai bacci ne a  idon ta sosai, a haka ya daga ta ya zubo abincin yana bata yana ci duk abinnan da ake idon ta rufe yake sai ta fara taunawa sai bacci ya fizge ta ya tada ta ta ci gaba da taunawa, cikin gigin baccin ta furta, " Yah Jabeer ka dawo?" " Eh na dawo princess" " Sannu da zuwa" "yawwa, meke damun ki ne yau?" "Bacci nake ji na gaji ne sosai, ga jiri danake ji, tin shekaran jiya kuma sai naji cikina na ciwo ciwo, kamar ana min motsi a cikin shi" Har ta gama maganar ta idanun ta a kulle suke, cikin damuwa Jabeer ya hau shafa cikin nata ya na fad'in, " Subhanallahi, gobe zamu asibiti mu ga likita, shiyasa kika ji kwanaki ina ce maki sai naga kamar baki da lafiya, abinda ke kwantar min da hankali kawai ganin yanda jikin ki ba wani damuwa sai kyau da kike qarawa ma, nan din ki har wani kyalli suke" Hannun shi ya kai saman rigar ta yana shafawa, a hankali ta janye hannun shi ta juya baya ta ci gaba da baccin ta, wani yawu ya hadiya, ganin yanda hips din ta suma suka ciko sosai kamar su yi magana, tashi ya ui ya maida plate din ya wanke bakin shi da hannu ya rufe ko ina ya dawo ya ce, " princess ko dai fushi kikai ban dawo da wuri ba yanda na saba? Shi ne kike share ni kik eson yin bacci?" Shiru yaji ta yi babu amsa,matsawa ya yi jikin ta ya janyo ta, bacci yaga tana yi sosai abunta  hankali kwance,bai so hakan ba sam, gaba ɗaya shigar ta ta rikita shi, amma haka ya hakura dan yasan ba halin ta bane kyale shi koda tana cikin fushi ne, ja masu abin rufa ya u yi tare da yi masu addua ya shafa masu, suka kwanta bacci........ [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH *SANARWA ! SANARWA !* *Ina masu buqatar sanin yanda za su gyara jikin su ta ciki da waje? Ina nufin daga gashin  kan su zuwa yatsun qafar su da qarin ni'imar jikin su?* *Ina masu son koyon sana'o'i dan samun taro da sisi? To 'yar uwa matso kusa ba sai kin biya maqudan kuɗi ba dan ki koyi yanda Zaki yi sana'ar da zata sama maki kuɗi da #1k kacal za ki mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA* *Idan kuma ke ma'abociyar karanta littafan Hausa ce ki yi wa HAERMEEBRAEH ❤️magana kai tsaye ta wannan No 09031416423 kai tsaye, Zaki samu Littafin MAHREEN DA KYAKKYAWAR FAHIMTA a kan farashi #500 each* *Please share*❤️ Page 12:    Da asuba da Juwairiyyah ta tashi ta duba sai ta ga har ya fita masjid, addu'ar tashi daga bacci ta yi "Alhamdu lilLAAHi alladhi ahyani ba'ada maa amatani wa ilaikannushour" Sannan ta sakko daga gadon ta je ta yi alwala ta dawo ta gabatar da raka'atanil fajr ta yi sallar subh tare da  azkar din safiya, tana gama wa wanka taje ta yi ta sake yin brush, gaban madubi ta zo ta warware kitson da ta yi da yamma kafin ta yi bacci guda biyu akan ta sakamakon ba ta son kitso sosai kuma shima Yah Jabeer din nata yafi son tana masa adon gashin haka ba tare da ta kitse ba. Idan mijin ki mai irin ra'ayin Jabeer ne to ya na da kyau mace ta iya yin kitso biyu irin na indiawan nan da muke gani ana raba kai biyu a kwantar gefe da gefe a dame shi a kitse sai ya yi matuqar kyau in ke mai santsin gashi ce ma zakiga har sheqi yake da dare ake wannan kitson bayan kin gama wa oga kwalliya, ma'anar yin wannan kitson na farko dai zaki yi bacci ba tare da kanki ya yi irin buyaya ɗin nan ba ki yi muni,da safe zaki tashi kan ki tsaf da shi bai barbaje ba, sannan kuma in ma kun samu kusantar juna da me gida kin yi wanka kanki ba zai na lalacewa ba nan da nan ki ji mata suna cewa kai yasha ruwa gashi ya na zubewa, akwai fa'ida sosai akan yin hakan wanda sai kin fara zaki gano su da kan ki. Da sauri take yin komai ba tare da son jiki ba,dan ba ta son sai ya dawo ne zata yi wadannan abubuwan, ya na dawo wa daga masjid ya tsaya wajen Innar mu su gaisa, kamar kullum riqe shi ta yi da surutai na ba gaira ba dalili, daga baya ne ta fara tura masa saqon dake ranta cikin dabara irin ta masu son qulla sharri, " Allah sarki Juwairah yarinyar nan akwai hakuri, kaga fa yanzu wata na wajen shida kenan da auren ku amma ba wani labari,gashi duk qawayen ta sun haihu ma su,ita ko da b'atan wata bata taɓa yi ba ka ga sam bata damu ba, ko dake dama yaran zamani ai ku ba ruwan ku, mu ne dake son yan jikoki mu za mu damu, waya sani ma ko maganin hana haihuwa take sha" Wani irin faduwar gaba ne ya samu Jabeer ido ya zaro waje yace, " Haba Innar mu Juwairan nawa take d zata yi wannan tinanin? Kuma har ta aikata hakan ma? Inaaaa sam ba zata yi haka ba kima daina wannan tinanin dan Allah, kuma da kk zancen sa'o'in ta Innar mu Nafeesa ma fa sa'ar ta ce ita kinga ai har yanzu ma bata yi aure ba, in da zaki gane komai nufi ne na Allah kenan" Da jin wadannan kalaman daga bakin Jabeer sai Innarmu ta ji kamar ya watsa mata wuta, bala'i ta fara yi kamar ta ari baki,cikin masifa ta ce, " Inyeeeee lallai ne Jabeeru ka nuna min mata tafi 'yar uwar ka ko? Har qanwar ka zaka duba ka yi wa gorin aure? To bari na faɗa maka abin da nake boye maka, nifa na fara gajiya da wannan yarinyar, tin da ka aureta ka daina bamu lokacin ka, ka daina zama ai hira kamar ta da da kai, sannan gaba ɗaya soyayyar ka da kulawar ka ta koma wajen ta, akan me?" " Akan shi ne mijin ta, kuma hakan da yake shine yake nuna ya haifu ɗan sunna daga iyayen shi,yanzu dan Allah ba ki ji kunya ba? Kike haɗa kan ki da surukar ki?sannan 'Yar ki ta wani bangaren? Habaaaa Hansai, wace irin rayuwa kk daukar wa kan ki yanzu, abinda ba halayyar ki ba kina neman shaid'an ya maki huɗuba ki fara yi, to bari na faɗa maki abinda mata kan ku yake toshewa akai, kowacce mace dangin miji ce, kuma uwar miji ce wataran in ranta ya kai, dan haka in ki kai wa matar dan ki adalci, kema sai wata ta yi wa taki 'yar adalci, in kk kyautata wa matar wanki ko matar qanin ki, kema naki qannen mijin da matan yayun sa zasu tausaya maki su miki adalci, in kuma duk kin kiyaye amma ana maki abinda bai dace ba, to ki sani kowanne dan Adam akwai jarabawar shi, wataqila taki anan take, sai ku hakuri ki yi qoqari kuma ki cinye jarabawar taki, dan haka in kk kula, tin da Jabeeru ya yi aure kulawar da na ke ba ki ta qaru, ba dan komai ba sai dan kula da na yi kin kai idon ki gidan matar dan ki, ki gyara hali ko kin samu rabauta a lahira, baki tafi da haqqin kowa ba, haihuwa ta Allah ce, ko bata haihuwa haka yaga zai zauna da ita ke baki isa ki ce dan me ba" Baba Balarabe kenan ya ke yi wa Innarmu faɗa akan abinda take yi mara kyau, wanda ya dad'e a tsaye yana jin maganganun Innar mu, wata irin nadama da kunya ce ta kama ta nan take cikin jin nauyi ta furta, " Malam ka yi hakuri, Jabeeru ka yafe min sharrin zuciya da shaid'an ne, baqin ciki na da tin da ta zo komai namu ya ja baya, ga shi kana nuna mata tsantsar so, idona ya rufe akan hakan na manta nima nawa mijin yana iya qoqarin shi akaina, ku yafen ba zan qara ba" Nan ta zayyano yan sace2n da tai ta yi wa Juwairah dan ta haɗa su faɗa da Jabeer amma sai ta ji shiru, sakamakon iya zaman duniya da Juwairah ke da shi da ta kula hakan ta faru zata san dabarar da ta yi ta bashi hakuri, da jikin ta da kalaman ta, " Babu komai Innarmu ya wuce ke uwa ce a wajen ta, da bata ɗauke ki a uwa ba uwar miji ta ɗauke ki da ita kanta zaman sai ya mata wuya amma tasan ko da uwa da uba ana sab'awa fiye da haka ma a kuma ci gaba da zama, dan haka na san ba ta qullace ki ba, jiya kwana ta yi ma ba lafiya, asibiti zamu je  yanzu ma ni take jira na san" " Subhanallahi" Suka hada baki dika ukun har da Nafeesa suka fada,Innar mu ce ta furta, "Meke damun ta?" " Da ciwon jiki ta kwana ga zazzabi da ciwon kai, ciwon mara da yawan kasala, dan jiya wani irin bacci ma ta dinga yi" Murmushi Innar mu ta yi sosai sannan ta ce, " Ikon Allah ai ya kamata a kaita ta ga likita bokan turai a fada mana wata nawa ne, na fara tanadin kayan kwalliya dan da alama bana zan yi ango nima, in kishiya ce na samu na gyaran daki,kar ta zo ta fini a Wajen Malam" "Innar mu me kk nufi da hakan?" Nafeesah ta yi tambayar cikin mamaki, Jabeer kuma a ranshi cewa yake yi, 'Allahumma ameen Allah ka amsa ka sa hasashen Innarmu ya zama gaskiya' A zahiri Kuma ya ce " Innar mu bari na wuce naga ko ta shirya mu tafi kar mu makara" " To Allah ya qara afuwa" Tashi ya yi baki a washe kamar gonar audiga ya isa sashen nasu, qamshin da ya ji ne ya qara kwantar masa da hankali da nutsuwa tare da qaunar matar tashi da yake matuqar so, sallama ya yi ta amsa cikin muryar da ke tafiya da hankalin shi,durqusawa ta yi ta gaida shi, ya amsa tare da jawo ta jikin shi, d'aga kanta ya yi yana kallo, wata riga ta saka shara2 ko ina ana hangowa a jikin ta, sai wando guntu rigar bata gama rufe mata cibiya ba , ta yi parking gashin ta a tsakiyar kan ta, fuskar ta ta yi fayau kyaunta ya qara fitowa, the more yana kallon ta the more yana qara ganin kyaunta, bata cikawa fuskar ta makeup ba, iyakar ta powder da lipstick, sai tirare da ta fesa ta shafa mai, zame rigar ya yi daga kafad'ar ta yana shinshina wuyan ta, maida ita ya yi baya ya tsaida ita ya na kallon ta,cikin shagwab'a Juwairiyyah ta ce, " Babe ni dai bana son wannan kallon da kk man ya yi yawa, tin da ka shigo kk ta kallona" Ta wani sake narkewa a jikin shi tana wani dan zame wa shi kuma da sauri ya janyo ta, gaba daya ta gama rikita shi, daukar ta ya yi cak suka yi daki, ban qara sanin me ake ba sai da naje na wajen Innarmu na sha kokon safe na dawo a gadon na hango su suna manne da juna, Jabeer ne ya ce, " My princess , jiya kin manta yau munyi zan kai ki asibiti ne? Gaba daya naga yanda jikin ki yake jiya da yamma yau kin tashi garau da ke" Eh My dear, kaga in banda da asuba dana tashi na ji kaina na ɗan ciwo kadan, sai da na zo brush warin toothpast din ya sani amai, tin da na yi aman nan na ji daɗi daga nan ban sake jin komai ba, ni fa Ina jin ma na warke ba sai mun je ba ma" " A'a ba haka za ai ba, ya kamata mu je asibiti muji me ke saka motsin da kk ji ko ya daina" "Ah ah ya na yi har yanzu" Jabeer ne ya shafa cikin nata da tausayawa, nan da nan idon ta ya ciko da kwalla ta ce, " Ɗazu ma fa sai da ya min, ga tsoro da yake ban in ya motsa din, sai naji kamar wani abu ne a ciki" Ta qarasa tana mai sakin kuka " Yi shiru my princess bari kuka,ba komai inshaa Allahu sai alkairi, u don't have to worry ur self babe, koma meye zamu samu maganin shi tashi muje mu yi wanka mu shirya muje" Tashi ya fara yi sannan ya miqa mata hannu ta kama, a hankali ta miqe tsaye sai yanzu ya qara ganin qirman da qirjin ta yayi, ga cikin ta ya dan tasa ta qasa, ta yi wani fari sosai, kamata ya yi ya  zura mata doguwar riga da dan hijab din da take zuwa wanka, tinda gidan akwai suruka duk da ba sashen su ɗaya ba dai amma Juwairiyyah na gudun kar watarana a yi kicibus,sai shima ya zura tashi riyar sannan ya fara fita waje ya rufe qofar su,daga nan suka shiga wankan a tare bayan sun gama ne suka dawo suka shirya za su tafi asibitin ,kafin su fita saida ta biya wajen Innar mu ta gaida su sannan ta tashi zasu wuce,ta ji Innarmu na fad'in, " Juwaireren Mama ki yafe wa Innar ki laifukan da ta yi miki domin Allah, sharrin shaid'an ne ya shige ni da son zuciya, amma in Allah ya yarda ya wuce ba zan sake yi maki duk abinda na yi a baya ba" kwallar farin ciki ce ta fito wa Juwairiyyah ta godewa Allah da ya kawo mata komai da sauqi kuma cikin gaggawa,cikin murmushi ta cewa Innarmu, " Haba Innar mu ai ba komai, ni fa 'yar ki ce, ke uwa ta ce, ban dauki hakan a komai ba face ma gani nake nice bana kyautata maki yanda ya kamata, nima ki yafe min, Baba balarabe na d'aki yana jin dadin kasancewar Juwairah a matsayin surukar shi, yarinyar dan uwan shi na da hankali da tarbiyya mai kyau,ta samu tarbiyyar a wajen  iyaye na gari. Sun isa asibiti suka tarar mutane sun zo an cika suma dole suka bi  layi kamar kowa,sanda likita ya kira ta sai aka bata gwajin jini sannan aka yi mata scanning dan ta matasa ta ce abu na motsi dole a duba mata, a  gwajin farko aka gano tana dauke da cikin wata hudu da sati biyu, zaro idanu take kamar mara gaskiy, ga wata iriyar da farin  ciki da suka kama ta, kunyar jabeer da tunanin ya iyayen ta da surukan ta za su ɗauki wannan labarin duk sun ishe ta ta rasa ya zata yi, janyo hijab din ta ta yi ta sunne kan ta a ciki tana dariya qasa qasa, Jabeer ta gani ya tashi ya yi sujjadar godewa Allah yana kwallar murna, itama a cikin ranta take maimaita ' Alhamdu lilLAAHi ala kulli halin, hamdan katherran ya rahman,' Murna take yi sosai ta ji hannun jabeer a jikin  ta ya  ja ta jikin shi, hada fuskar su ya yi waje daya suna shaqar nunfashi junan su,cikin murya mai ɗauke da amon farin ciki Jabeer ya ce, " Juwaireren mama kin ga ikon Allah akan mu ko,Allah ya yi mana kyauta mai daɗi da sanya farin ciki ba zato babu tsammani" D'aga masa kai kawai take tana murmushi, Dr. ne ya ce, "To  Lovey-Dovey sai a tsaya a saurare ni kuma in an je gida an qarasa murnar a can, ina da wasu masu jira na a waje" Shi kan shi likitan cikin fara'a da jin sun burge shi yake maganar, shawarwarin da zasu taimaka masu wajen kula da cikin da lafiyar ta ya basu, sannan ya rubuta magani inda yace su je su nuna takardar kawai za a basu kyauta ne,godiya suka yi masa mai tarin yawa sika fita, Jabeer ne ya sarqafe hannayen su waje ɗaya ya na jin son Juwairiyyah na qara shiga zuciyar shi, dan ji yake kamar ya dauke ta karta wahala da tafiya, kula da hakan da ya yi ne yasa ta tsaida su a wani wajen da ba mutane sosai tace, " Babe Dan Allah zan iya roqon ka wata alfarma?" Cikin zumud'i Jabeer ya ce, " Anything for u my love,just say it, inshaa Allahu in baifi qarfina ba i will do it for u" Murmushi ta yi ta sunkuyar da kai qasa sannan ta ce, " Yah pls don't tell anyone that i am pregnant plssss" Ta faɗa tare da qara damqe hannayen su waje ɗaya, " But why, abun murna ne fa ya same mu da ahalin mu baki ɗaya? Don't u want them to be happy for us, and must importantly to pray for us, and our baby" Ya qarasa maganar shi cikin rad'a, " Eh Ina so mana sosai amma ka fahimce ni, kawai ni kunya nake ji,  yanzu fa kowa sai ya san me na yi na samu cikin nan har fa Babana" Kiran Baban ta da ta yi sai ya sa ta sake jin wata kunya ta qara kamata kamar yama ji labarin ta na da cikin, dariya Jabeer yake yi sosai yana riqe ciki,cikin dariyar ya ce, "Amma dai gaskiya baki da wayo na kula, to bari kiji tin kan a kawo ki aka san in an maki aure zamu yi abin da zaki samu cikin,me yasa ake hana 'yammata biye wa samari kafin aure? Ai saboda gudun kar su samu zunubi sannan kuma kar su samu ciki kafin aure su haifi dan shege, come on wuce ni mu tafi gida rana na dukar min ke" Maqale kafad'a ta yi tana turo baki, "Yanzu menene kuma?" " Yah Yunwa nake ji sosaiii" "Amma dai naga bamu jima da cin abinci ba muka fito ko?" "Eh na sani, ni dai ina jin yunwaaa" Yatsina fuska take kamar in bata ci ba wani abu zai same ta ne, "Ok to yanzu me kk so?" " Yah ga me agwaluma can ita nake so, kuma ina son waccan zogalen dafaffe" "Ikon Allah, ashe kwadayin da kk ta min kwanaki babyn mu ne ke saka ki" "Yah ni dai agwaluma kuma dan Allah Yah ka taho mun da gyad'a mai gishiri, ka had'o min da rake, yauwa ka siyo agwalumar mai yawa fa", Gani ta yi ya saki baki ya na kallo ikon Allah, daga baya ya fashe da dariya,kawai sai ta saka masa  kukan shagwaba,da sauri ya yi maza ya kama bakin shi alamar yayi shiru, sannan ya ce, " Yi hakuri ba zan sake ba kin ga a titi muke duk da katangar nan ta kare mu kinga masu agwalumar zasu iya maki dariya" Narke fuska ta yi sannan ta ce, " Oh ni Juwairah yau naa ga tsokana da ranar Allah dan Allah ka yi sauri" "Auuuuu kin fi son a tsokane ki da dare dama? Ohhh to kar ki damu wannan ma ba a barmu a baya ba ai bari mu koma gida" Da sauri ya yi wajen masu agwaluma yana dariya dan ganin yanda take banka masa harara ,zura hannun ta ta yi a riga tana shafa cikin ta dayake a lafe kamar ba komai sai ɗan tudu da ya yi ta qasan marar ta, amma a haka tana jin motsawar shi kadan kadan, " Ikon Rahman Ar-raheem kenan,wato wai ni Juwairah ke dauke da ciki ban sani ba, Allah na gode maka, kasa duk abin da zan haifa ya zama musulmi mumini salihi, Allah ka sani na bi dukkan yanda Annabin ka ya tsara mana don samun 'ya'ya na gari, tin kafin aure na har yanzu da ka ban wannan arziqi, Allah ka sa su zama wadan da muslunci da musulmai zasu yi alfahari da amfanuwa da haihuwar su, Allah na gode maka ka ba wadan da basu da shi, ka sauqaqa min wajen haihuwa" Hannun shi yasaka a gaban fuskar ta ya ce, " Shin me Juwaireren mama take tunani haka? Gani na dawo ina tsaye baki ji ina maki magana ba, wato har zaki fara manta ni ko saboda kin samu baby" Ya fada yana shagwabe baki kamar yanda take yi, " Ba komai muje gida na yi na sha abunnan yunwa ta qaruwa take yi" Dariya ya yi suka kama hanyar fita suka samu abin hawa sai gida, lokacin da yake fadawa innarmu Juwairiyyah na da cikin gudu ta saka ta yi bangaren su tana dariya, kowa murna yake a gidan kamar me, labari nan danan ya bazu a dangi Juwairah na dauke da cikin wata hudu da sati biyu, kowa na murna da saka albarka, jin wannan labarin da Goggo Sarai ta yi ya daga mata hankali, domin tunanin ta ya tafi akan dama yaran ta ne suka sama mata jika, ko dan samun wani kaso na dukiyoyin surukan nata,nan take tinanin Salma ya faɗo mata a rai, wayar ta ta d'akko ta yi ta zabga kira ana mata turanci, hankalin ta ya tashi sosai musamman da ba gane ne ake faɗa take yi ba,mayafi ta yafa ta leqa ta kira Baban su, ta bashi ya ji me ake faɗa, ce mata ya yi "Wai an ce layin baya aiki yanzu," "Wai ni wa kake kira ne malam Salma fa na ce ka kira min" "Ita dai ki ka kawo waya na kira kuma aka ce No  ta ta daina aiki," "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una me yake faruwa ne? Malam wannan Yarinyar Salma so take ta kashe ni da tashin hankali da damuwa, ka na gani dai duk 'Yan uwan ta sun yi waya gida an ji daga wajen su amma ita shiru yau wata kusan bakwai, ga wannan mummunan labarin da ya iske ni na samun cikin wannan kodadiyar"   "Mummunan labari kuma, a wajen wa kenan? A wajen ki dai amma ko? Hmmmm Sarauta kenan a gabana ki ke son ki ciwa 'yata fuska wai kodaddiyar 'ya na gode, Allah zai raba su lafiya, ita kuma Salma Allah ya sa ki same ta a wayar, in kun yi magana kin sanar da ni" Ya na gama maganar shi  ya yi shigewar shi cikin gidan, wayar suwaiba ta kira ,tana dauka itama tambayar ta ta yi tace bata ji daga wajen Salma ba ko ta kira iya Goggon sun gaisa? Nan dai Goggo Sarai ke sanar da Suwaiba abinda ke faruwa. Saudat ma da ta kira ta amsa ɗaya ta bata da ta suwaiba,daga qarshe dai suka haɗu suka kwantar mata da hankali akan cewa ta yu ma sun fita qasar waje ne da mijin ta honeymoon shiyasa ba a samu ta,wani farin ciki ne ya maye damuwar ta suka ci gaba da hirar su wadda rabi da kwatan ta ta yanda suke cikin rayuwar jin daɗi da hutu ne a Abujan ita kuma ta na sukar su Mama Balki da Juwaireren ta. ************************** Salma kuwa wadda yaran Talle suka mayar mata da suna Salame ana can qauye jikin ta qaura ya yi la'asar, ba kowa ne da yasan ta a da ba zai iya gane ta ba a yanzu, duk ta kode ta jeme ta rame, wahala daga ta gama wannan ta faɗa wannan,har kuma wannan lokacin Talle bai sake waiwayar su ba. **************************** Watan karb'ar jini a wajen su Suwaiba ya zagayo,Oga Zaks ya buqaci ko a kai su, ya qara sa musu albarka irin tashi ko kuma akai jinin su kamar yanda qungiya ta bukata zaɓi ya rage ya na su Alhaji Salihu...... [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼     'YAN ABUJA    💅🏼      WRITTEN BY HAERMEEBRAERH *Dan Allah masu tambaya daga farko ko wasu pages da ba su karanta ba ku yi haƙuri a gama dika a had'a document sai ku karanta, zan yi qoqari na yi saurin gama editing ɗin kamar yanda na yi na sauran,na gode* page 13: Alhj Salihu da Alhj Kalla Mazajen su suwaiba da Saudat ne ke zaune a wani wajen shan iska da suka tanada na musamman dan tattaunawar sirri,bayan doguwar shawara da neman mafita ne suka  samu nasarar tsayar da  hanya ɗaya da za su samu jinin su suwaiban da qungiyar asirin su ke da buqata a duk ƙarshen wata cikin sauqi,bayan samun mafita da nasara antattaunawar da suka yi sai suka bushe da dariy a tare suka tafa tare da furta kalmar " 'YAN ABUJA"  Tashi suka yi suka shige motocin su masu gadin wajen shaqatawar nasu suka buɗe gate su ka hau daga masu hannu tare da yi masu addu'a da fatan alkhairi, direct clube suka wuce kamar kullum,sai dai yau basu wani dad'e ba dan kuwa sha ɗayan dare suka dawo gida. Cikin kwalliya ta alfarma kowannen su  ya tadda iyalin shi, an sha kayan ado masu tsada, fatar nan har wani sheqi take sabida jin daɗi da hutu. Kowaccen su kamar abin had'in baki tashi ta yi ta nufi mijin ta domin yi masa barka da dawowa, dan kuwa qorafi ba nasu bane yanzu tsoro suke ji kar su sha jibga a banza. Bayan sun gama kulawa da Mazan nasu an ci an sha an yi wanka sun zauna su na hutawa a parlour suwaiba ta hau wata karairaya ta zauna a gefen Alhaj Salihu kamar za ta shiga cikin shi, cike da shagwab'a ta fara gabatar da uzurin ta a kunnen shi kamar yanda Goggo sarai ta koya mata, " Mine " "Na'am" Sake mannewa ta yi a jiki shi sannan ta ce, " Dama cewa na yi ko zamu je asibiti a duba mu ne ni da kai saboda a ga ko lafiyar mu qalaou kuwa har yanzu shiru ba ciki ba komai, dan ni fa har period na dena yia zatona ma ciki ne amma kuma gaskiya ban ga wata alama ba ni dai ina jin tsoro dan Allah za ka kai ni asibiti mu ga likitan? Ko ka san yanzu haka qanwar mu Juwairiyyah da aka yi bikin mu tare ta na da ciki,hakan zai zame mana abin gori mu da mahaifiyar mu ace mu uku babu mai ciki har yanzu" Wani wawan mari ya antaya mata, ya hankada ta qasa sai da ta kifa,cikin ɓacin rai ya kalle ta ya na nuna ta da yatsa ya ce " Dan uwarki ni zaki mayar qaramin mutum qaramin yaro? Wanda bai san me yake yi ba? Ohh wato ki haihu na samu magaji ko? Ko kuma ki kashe ni ki karɓe dukiya ta ko? To bari kiji wani abu, wannan dukiyar daga karuwai sai masu saida giya su zasu more ta in dai ba Zaki kwantar da hankali ki ci arziqi ki barshi a mazaunin shi ba,ni babu tsarin yara a rayuwar nan tawa, ban sani ba ko a gaba, amma a yanzu kam ban da wannan burin da kwadayin yaran da ke zaki sani neman haihuwa kamar ni an faɗa maki Banda ra'ayin kai na sai naki," Cikin kuka suwaiba ta rarrafa ta kama hannun shi ta ce, " Dan Allah ka saurare ni ka kuma fahimce ni" kafin ta qara magana kwakkwara ya rufe ta da mugun duka ko ta ina tare da fad'in , " Ke kin zama jaka ko? Baki yarda ki daina sa in sa da ni ba ko, ina faɗa kina faɗa kamar ki na magana da sa'an ki, yau kuwa Zaki ji a jikin ki sai soyayyar yara ta fita a zuciyar ki har abada", Wayar charging phone ɗin shi ya ciro ya dinga zabga mata, tin tana kuka ta na bashi haƙuri karshe ma sai faɗuwa ta yi ta rufe idon ta a wajen ta daina motsawa, a haka ya samu damar ida qudirin shi na yi mata allurar bacci, ya debi jinin ta dan mugunta har leda uku, yana gamawa ya yi ma mijin Saudat magana ta waya dan sanin halin da suke ciki, mijin saudat tambayar shi ya yi ko lafiya ya ji ya na haki, nan take ya bashi amsa da cewar, "Sai da jakar taci duka tukunna, wai ni zata yi wa zancen haihuwa" " Ale  Salihu ka dinga rabuwa da ita ba laifin su bane laifin wannan shegiyar uwar tasu na tabbata ita ce zata zugo su dan kuwa in baka manta ba ba kalar labarin son kud'in uwar su da Basu bamu ba , na samu na deb'o Leda hudu ai dai ta gina jikin ta da kayan kud'in da ake samowa ko?" Dariya Alhj Salihu ya yi sosai sannan ya ce, "Ni kuma hudu da diba" "Shgeb sama, to shi kenan sai mun haɗu yanzu zan fito,tsallake ta ya yi ya fice dakin shi ya saka jinin a inda aka basu su saka, wata jakar fata ce da akai mata ado da ja kamar an qara riƙa ta sai rubutun Arabic a jiki wanda ko mutum ya karanta ba zai bashi wata ma'ana ba, rataya wa ya yi a jikin shi dan kuwa ba a son su aje ta a qasa ko da da mistake ne sai sun ba da wani wannan ya tashi aiki kenan idan jakar  ta taɓa qasa,ko kuma idan ba haka ba sai an kaiwa Oga Zaks matan dan ya diba da kan shi,domin ko kusantar su ya yi jinin nasu diban shi ake yi. Sun isa wajen Oga zaks da misalin ƙarfe ɗaya na dare, suna isa suka miqa masa jinin wata dariya ya barke da ita kamar ana yaga zani, ba ko daɗin saurara daga baya kuma ya haɗe fuska kamar bai taɓa dariya ba ya ce, "Aikin ku ya na kyau, shiyasa kuka fi sauran abokan harka shanawa, bakuda tsoro sam ,sannan bakwa jinkiri, ku gaggauta maza muje a bawa Dodon tsafi jinin kyawawa ya sha" Ta shi suka yi suka shiga wani daki, dan tsoro ina leqawa nai baya a 360 ba zan iya dakko maku rahoton komai ba anan, gidan Saudat na je, tana kwance rabin jikin ta na kujera, rabi na qasa, fuskar ta ta kumbura ta yi sintim, dan tafi ta kwanaki hayewa ashe Itan ma jibga ta sha amma yake wa abokin shi magana akan ya dena biye wa suwaiba ya na jibgar ta, nan take na ayyana a rai na wato shi Alhj  kalla hukuncin shi Kalla mari ne kawai, mari kam iya mari ta shashi da dikkan alamu, dan ina jin shi ya sata suma ma, ruwa na yayyafa mata na labe, a firgice ta miqe tana fad'in, "Ni bana son Yaran ma har abada, kayi hakuri ka daina kallan mari" Tana fadin hakan tana kuka fuska dagaje2 da hawaye ga majina da yawun azaba duk suna ta tarara,dube2 ta hau yi taga ba kowa a gidan sai ita kaɗai ,ta na miqewa ta ji wani irin jiri ya na ' dibar ta tare da tsananin ciwon kai, komawa ta yi ta kwanta, tana maida nunfashi, suwaiba ko bata farka ba sai da suka koma gida wajen qarfe hudun asuba. Yana isa d'aga ta ya yi ya kai ta toilet ya hada ruwan zafi ya saka ta, ihu ta saka na azabar da ta ziyarci jikin ta, dan kuwa jikin ta duk ya farfashe,kuka ta fashe da shi ta na ja da Baya a cikin kwamin wankan ta na fadin, " kayi hakuri mai sunan Annabawa na tuba, ba zan qara maka zancen yara ba har mu mutu, ka yafeni sharrin shedan ne d'azun ma Allah ya ƙara nesanta mu da sharrin la'ananne jefaffen Allah" Rufe mata baki ya yi yana hawayen munafurci yana bata hakuri shima, harda in ya sake ko taba hannun ta da sunan duka ne duk hukuncin da ta ga za ta masa ta masa, runtse idon ta ta yi tana jin yanda zafi ke shigar ta, nan take zuwa Abujan ma ya sire mata a rai, wannan wace irin azaba ce, in kaci daɗi na wata ɗaya sai an zai zaye maka shi a kwana daya? Yanzu yanda take jin ta kamar wadda akaiwa yasar wani abu, bata da qarfi ga ciwon kai da take ji kamar kan ya fice, barin ta ya yi ya tafi kitchen ya samu fruits ya markade ya tace ya kawo mata ya sa mata abaki yace ki sha zaki samu qarfi sosai a jikin ki, bangaren da masu aikin su suke yaje,ya tashi mai girke2 dan ya mata farfesu, ko na naman meye ma a samu ta samu kwarin jiki, ai ko ba komai ta maida mugun yawu, sannan abinda ya kawo ta kenan, in ji shi, farfesun naman rago ya yi mata da yaji kayan haɗi, irin farfesunnan ne wanda mutum zai zaci gashi ne, yasha kayan lambu a ciki, qamshi da maiqo sai tashi yake, fresh milk ya zubo mata, ya koma toilet din bata shanye jus din da ya mata ba dika, dakko ta ya yi a hannu daure da towel ya dawo da ita gado ya cire towel din ya samo riga iya guiwa mai dan fadi ya zura mata, kanta ta jingina da frame din gadon idon ta lumshe, zuwa ya yi ya d'akko wannan had'in ya shigo da shi, ai tana jin wani qamshi mai daɗi sai ga idon Suwai a buɗe, wani yawu ta hadiya na kwad'ayi, Alhj Salihu ya ayyana, 'Shegiya dangin maita, ji fa uban dukan da taci amma ta ga nama har ta miqe' Isa ya yi gaban ta ya aje mata ya fara bata a hankali,ita kuwa sai taga baya sauri, d'aga masa hannu ta yi ta saka nata dayan hannu ko ta kan spoon din bata bi ba ta hau ci kamar tsohuwar mayya, ci take ba ko tsayawa sai da ta yi nak, ta kora da fresh milk, ta zame ta kwanta, lokacin Subh payer ta yi amma ko a jikin su daga shi har itan, haka suka kwanta bacci, manne da junan su,abin ku da wadda ta dad'e miji na gabza in ta nemi haqqin auren ta, yau ta samu a bagas dik da zafin da take ji haka ta miqa mai kanta, ranar ta yi murna da farin ciki ba iyaka, tini ta nemi zafin ciwon ra rasa, kusan abinda ya faru kenan a gidan Saudat,sai dai akwai wani plan da Suwaiba ta haɗa a qasan ranta na ganin me yasa ba su son su haihu,dole sai ta binciko dalilin da ya sa ba su son haihuwa. **************************** A gidan Talle kuwa cikin dare Salma ta ji kamar buga qofa ake yi,dan haka a hankali ta miqe ba tare da ta yi wanai kwakkwaran motsi ba, dan tare suke kwana da Haule yanzu, leqawa tayi ta qaramar bular jikin qofar d'akin nata,ta bular ta hango Yayan mijin nasu na waige2 yana kwankwasa qofar Marka, mamaki ne fall cikin ta na me ya kawo shi d'akin Marka da tsohon daren nan, dan kuwa duk yan kwanakin nan marka ke zuwa wajen shi, yau fushi take yi da shi shi yasa ya biyo sahu, saboda  daren jiya ya hana ta dari da hamsin da ta roqa yace bai da su, shine tace yau ba za ta ba, shi kuma gashi a mugun matse yake,jikin shi har wata rawa yake  sanda yake kwankwasa qofar, budewa ta yi tana magana qasa2 ta ce, " Dalla can sai ka tada yaran ma sun gan ka, ni shigo kayi ka gama ka tafi jarababbe kawai" Jan shi ciki ta yi su ka rufe qofar, aiko akan idon salma, kame baki salma ta yi tana fadin, "Tab ashe wannan matar munafuka ce? Ba ta da maqiyi da rana da ya wuce Baban Bangis,amma kuma ashe  da dare bata da masoyin da ya wuce Baban bangis, lallai ran da Su Badamasin suka sani akwai case a gidan nan ko kuma idan Talle ya ji labari" Tana cikin wannan tinanin ta fara jiyo qarar dan qaramin gadon na Marka irin na qarfen nan, sannan ga sambatun ta nan da bata iya shiru ita sai ta tona masu asiri, yaran akwai nauyin baccin tsiya shi yasa ma basu san wainar da ake toya wa ba, to an wuni shiririta kuma anyi bacci  late dole in sun kwanta su zama kamar gawwaki Marka a wayon ta hade yaran take dika daki daya saboda irin haka, kafin Salma ta zo ne d'akin tan yake na Yammatan, amma kawo ta yasa aka haɗe su waje ɗaya maza da matan,motsin qofa Salma ta ji Baban Bangis zai fito sai da ya fito Marka ta biyo shi tana miqa masa hannu ta na wani gantsaro girji, shi kuma yana qara shafawa, ya ce, " kamar na koma mu yi ta yi sai asuba na tafi" "Lallai ma Yaya kaima a gaida ka, duk wannan aikin da garar da ka diba bai ishe ka ba, in kana son ka koma ciki qaron nera dari kacal" Murmushi ya yi haqoran shi jajaye suka bayyana ya ce, " Aaaa dari tab na gama baki dari ukun yau, ni dai gaskiya ban da su"  "To kuwa kama gaban ka ka wuce ya ishe ka haka a barwa gobe" Yana qarasa fitowa gaba daya Salma ta fito da buta a hannu ita ma , hankalin su ne ya tashi gaba ɗaya da ganin ta tsaye ta na murmushi ta na bin su da wani shu'umin kallo,jiki na rawa baki na karkarwa su Marka suka zube a Saman guiwowin su suna roqon Salma, " Salame dan Allah ki rufa mana asiri, kar kowa yaji labarin nan" Cikin Isa da gadara Salma ta ce, " Anawa zan yi shirun ko ko haka nan zan rufe bakin nawa kuke nufin baku ban ko sisi ba tunda ke na ji ɗari uku ma aka baki" Jiki na rawa Baban Bangis ya sa hannu a aljihun shi ya dakko dari biyar guda biyu ya miqa wa Salma , "Ke ma ina naki  kud'in?" Da sauri Marka ta shiga d'akin ta ta d'akko dari biyar ta haɗa dana hanun ta ta bawa Salma, " Kallon su ta yi ta na juya kud'in ta ce wa Marka, "Marka ina son ki sani Talle ya kusan dawo wa dan jiya baki nan kina yawon ta zubar Badamasi ya faɗa sun yi waya ya ce zai dawo nan ba da jimawa ba, in ya dawo kika kuskura na ganku tare har kika haɗa  wannan qazamin jikin baki da shi warin ki ya mannu a jikin shi saina faɗa masa, dan ba zaki sa yanda ni na tsare aure na ba ina juran ya dawo mu raya sunna ki ja min amai kuma ba biyan buqata, kinji ni ko baki ji ba?" Wani yawu Marka ta had'iya na yau ta shiga uku an raba ta da gwarzon maza Talle, sannan a hankali tace, "Na gane kiyi wa Allah ki rufa mana asiri" " Baku da matsala in ma komawa zaku yi sai asuba din zan iya yi maku gadi" Da sauri suka furta, "Aaaaa tafiya zai yi/zan yi" Fakam fakam Yayan Talle ya bar sashen nasu, ita kuma salma  ta koma d'akin ta ta  bar Marka da cizon yatsan an amshe yan kudaden ta kuma gashi ba wai ta wani samu biyan buqatar ta bane, yau ta yi biyu babu, tura qofar ta ta yi ta koma dakin ta. Salma na shiga d'aki ta datse qofar ta zauna ta dinga babbaka dariya, a ranta ta na ayyana, 'Shikenan yanzu sun dawo hannun na sai yanda na yi da su' Shikenan yanzu da ta ji tana son kuɗi zata neme su kuma dole su bayar ko ta tona masu asiri, cikin murna ta dale gadon ta ta miqe. **************************** Yau garin na Kano an tashi da ni'ima sakamakon sanyi da ya ɗan fara shiga, garin ya yi daɗi ya yi kyau gwanin sha'awa,rana ta yi sanyi babu kuma zafi. Shamsiyya qawar su Juwairah da Nafee ce ta kawo ma Juwairah ziyara ta musamman dan tana son ta qara bata wasu shawarwarin game da yanda zata gyara nonon ta da suka lamushe kamar an yi gobara ta ciki an yashe komai sai fata, sannan ga kanta dake yawan karyewa gashin ta na zuba, bangare ɗaya kuma abu mafi mahimmanci da zai kaita ta taya su murna dan Nafeesa ta bata labarin samun cinkin da ta yi, murna take yi sosai itama da jin hakan. Shiryawa ta yi bayan ta gyara gidan ta tsaf kamar ba ita ba ta fito ta hau abin hawa ya kai ta har gidan su Juwairah da Nafeesa bayan ta sauka ta sallami mai adaidaita sahun ne ta shiga ciki, bangaren innar mu ta fara shiga ta gaishe ta, bayan sun gaisa ne ta mata murnar abun alkhairin da ya same su sannan ta shiga ciki wajen Juwairah, a can ta hango Nafeesa tana alwalar la'asar, Juwairah na d'aka tana gabatar da tata sallahr......... [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA    💅🏼         WRITTEN BY HAERMEEBRAERH page 15: Ranar litinin da safe ne su Suwaiba da Saudat suka shirya tsaf dan zuwa asibiti su ga meke faruwa har yanzu ba su samu ciki ba balle a kai ga sa ran haihuwa, shiga suka yi ta alfarma sai walwali suke da ka gan su ka ga matan manya. Qarya suka yi wa mazajen nasu suka sanar da su zasu tafi shoping ne, Dunes Supermarket suka nufa cikin isa da qasaita irin ta isassu kuma hamshaqan mata, Alhj Salihu ne ya biyo su a b'oye dan ya tabbatar da ina zasu je, ganin sun isa super market ne da gasken ya sa hankalin shi kwanciya sai ya kira ya Alhj Kalla ya sanar da shi cewar da gaske shoping suka tafi, Suwaiba ta kula da binna ta da yake yi duk kuwa da qoqarin boyewar da ya yi ta yi kar ta gan shi,wannan shine dalilin da ya sa ta ce ma driver ya kai ta can super market ɗin a hanya ta yi wa Saudat message akan su tafi can din daga baya sun san shawarar da za su yanke. Bayan sun isa ne suka fito a motocin su suka shiga super market su a dole siyayya za su yi,suna shiga suka hau waige Saida suka tabbatar ba direbobin su ba su gani su cikin sauri suka fita ta wata qofar suka samu taxi suka ce ta kai su asibiti mafi kusa,nan take kuwa aka kai su wani private hospital dake kusa,bayan gwaje gwaje da aka yi masu a tashin farko likitar ta gane ai ba ma mahaifa a tattare da su an cire ta. Sanda ta sanar da su suwaiba hauka ne kawai ba su yi ba saboda tsananin  damuwa da shiga tashin hankali, kuka suka saka sosai kamar an masu duka, jikin Saudat sai rawa yake dan ta fi Suwaiba son yara,ita Suwaiba dama ita ba wai ta wani damu da su ba ne, amma kasancewar yanzu ta ji bata da mahaifa kwata2 hankalin ta ya dagu sosai, tashi sukai bayan sun gama biyan komai suka dawo supermarket din suka debi wasu daga abubuwan da suke buqata musamman na gyaran jiki, Suwaiba kuwa acici kayan kwalam da maqulashe ta jida sannan suka je suka biya kud'in aka zuba masu kayan su a leda,jerawa suka yi su na tafe suna magana,suwaiba ce ta ja hancin ta sannan ta ce wa Saudat, " Da mu zauna ba mahaifa ba kayan more rayuwa ai gwanda mu kwashi rabon mu muci tin da bamu da magada" Fadin hakan ke da wuya sai Saudat ta saka kuka har ta na shassheqar kuka, cikin faɗa Suwaiba ta ce, " Malama kar ki taran jama'a, meye na kukan kuma a cikin mutane, daga cewa mu more rayuwar mu,an fa tabbatar mana da ba za mu haihu ba,to in dai haka ne me zan haihu ba zamu more rayuwar mu ba? Ki fa duba ki gani ba mahaifa ba haihuwa ba kuɗi,to haka ki ke so mu zauna cikin wahala? Sanin kan ki ne ma mazajen mu suka san bama haihuwa mun shiga uku, in gaba suka so qara auren su za su yi, ba gwanda mu ware ba mu saki ran mu mu tatsi abinda muka tatsa, tin da mun taba zaman Abujan mun ji abinda ke cikin ta, kinga sai mu canja sheqa da uwar kud'in mu wa ya isa ya taka mu?" Gyada kai Saudat take ta yi kamar wata qadangaruwa, ta fahimci suwaiba Sarai,kawai ta na wani tunani ne na wannan zancen rashin mahaifar tasu abu kamar na had'in baki ace basu da mahaifa iya da yar uwar ta ? Anya babu wata a qasa kuwa? Lallai ba zata huta ba kuwa sai ta binciko ta san mene dalilin da ya sa suka rasa mahaifa a lokaci d'aya da yayar ta bayan ta san ko a da da suka yi yawon su ba su taɓa yunqurin zubar da ciki bama balle cire mahaifa, suna gama tattauna wa a tsaye nesa da drivers ɗin su suka yi sallama da juna suka koma gidajen su. ************************* Yau fa gidan Talle shar da shi domin ta shi kawai suka i suka ga Salma na bada umar ni ko ta ina kuma Marka bata ce komai ba,ta ɗauki ido ta zuba mata ba ta uhuummm ba kuma ta ah ah. Tun da ta ga yara sun tashi daga bacci ta sa masu hankalin a gaba sai da suka gyara d'akunan baccin su ta na yi ta na masifa kamar yanda ta ga Markar na yi,daga nan ta ware manyan ta sanya su shara nan suka haɗu suka share gidan tsaf,daga nan ta sa aka deb'o toka a murhu aka cika a shaddar gidan aka kwab'a wata da omo aka wanke bayin nasu tasss. Kiran kowa ta dinga yi da Sunan shi ta na bada umarni kowa ya d'akko wankin shi,nan fa suka fara fito da wanki tsibi tsibi kamar a gidan wankau,ta na zaune a qofar d'akin ta tana kallon yanda 'yan matan ke kallon Marka suna jiran su ji ta tsawatar amma shiru, ga wani uban kwarjini da Salma ta yi masu ko rashin kunyar ma sun kasa yi mata,da kudin da ta Karb'a a wajen su Marka a daren jiyan da shi aka siyo sabulun wankin, bayan sun gama wanki ne Salma ta sa su a gaba Saida kowaccen su ta yi wanka. Abun nasu sai ya zama gwanin sha'awa gidan ya yi fes da shi yaran ma sun yi acan acan,sai da Salma ta tabbatar kowa ya yi fesss sannan Itama ta shiga ta fesa wannan ta ta fito ta shirya tsaff cikin kwalliya,ganin haka ne ya sanya Marka leqa Salma da ta ke dakin ta ta na huce gajiya, dan kuwa ta bada kuɗi a siyo kayan miya a yi girki,Saida Marka ta tabbata ba za ta fito da wuri ba ta deb'i ruwa a bokiti Itama ta je ta yi wanka,ita da kan ta sai ta ji iska na ratsa ta. ko da ta gama shirya wa Itama sai ta bi lafiyar gado dan ta dan matse ido kafin a yi girki,kwanciyar ta ke da wuya  Huwaila da Jummala suka shiga dakin mamar su ta da ya sha gyara suka hau tambayar ta wai me ke faruwa ne yau a gidan ko dai asiri salame ta yi mata ne? Marka ce ta kalli hanyar kofar d'akin ta ta gyad'a kai tare da fad'in, " Um Um Um Um Um" Wannan kalmar kawai take ta maimaitawa tana kama bakin ta, alamar su yi shiru maganar babbace , kame bakin nasu ko suka yi ba su qara tambaya ba dan sun san wacece Marka duk abinda zai ta tashiga hankalin ta haka ba qarami bane,Marka ko cikin zuciyar ta cewa take, 'Yarinya ni ce fa uwar shed'anu, ki gama wannan mulkin naki na yan kwanaki, kiga abinda zai faru dake nan gaba kaɗan, dani kk zancen' Da yamma sakaliya suka ji qarar motar Talle,yaran fita suka yi da gudu dan tarbon Baban nasu, Huwaila na can Ita da Baban gida a wani lungu na gidan suna sana'ar tasu, su ka ji qarar motar Tallen, a firgice suka saki juna suka yi hanyar fita daga lungun kowa na zare Idonu. Talle kenan mai gayya mai aiki shine ya dawo gidan nashi bayan tsahon lokaci, Salma na jin haka ta miqe tana rangwada ta je ta taro shi, dawowa suka yi cikin  yaran yaran nata gaida shi yana amsawa. D'akin Marka ya leqa ya ganta ta yi wanka dakinnan fes kamar ba shi ba, wata uwar dariya Talle ya saki sannan ya ce, " Hajiya Marka, Markar Talle ,Marka Ikon Allah, wato ganin Kyakkyawar amarya ta ne ya nutsar dake har ki ke wanke da gyara gida, yo ni dana san haka ne ai dana dawo da jimawa, da ban tsaya wajen qadangarun bariki suna amshen 'yan kud'ad'e na ba," Qafar sa ɗaya ya d'aga zai shiga d'akin na Marka Salma ta koma ta tsaya a bayan shi tana kallon Marka da wani irin mugun kallon ya na shiga zan tona maki asiri, da sauri Marka ta miqe ta ja baya ta na fad'in, " Aa Talle in ka zauna d'akin nan ba ai wa yarinyar can adalci ba kuma, wancan karon ai a wajena ka fara zama ina ganin wannan karon wajen ta zaka fara zuwa" Tsantsar mamakin Marka ne ya kama Talle har ya sa shi sake baki ya na kallon ta, qarasa ya yi wajen ta ya taɓa wuyan ta dan ya ji anya lafiyar ta qalaou kuwa? Jin ta ya yi daidai ba alamun zafin jiki ko wata lalura,girgiza kai ya yi ya na tsananin mamakin sauyawar da Marka ta yi kad'a kai Talle ya yi sannan ya juya ya nufi d'akin Salma dan tana ma Marka kallon nan ta juya ta bar wajen,hira ya dinga yi mata da ba wani ganewa ta ke yi ba, dan gaba ɗayan shi tsami yake yi kamar wanda ya yi aikin qarfi kafin ya dawo. Dabara ce ta fad'o mata tashi ta yi ta na yanga ta fita, shi kuwa Talle wata shashashar dariya ya sake ya na bin mazaunan ta da kallo, ta na fita ta ɗauki bokiti ta zuba ruwa a bokiti babba, ta koma d'akin ta dakko brush guda biyu ta saka toothpast a jiki ta je kusa da shi zuciyar ta na tashi amma ta jure ta zauna a cinyar shi tana shafa shi ta ce, " Babe taso mu je mu yi wanka magariba na yi, kaga in munyi sai mu yi sallah ka zo na yi maka tausa dan da alama ka gaji sosai" Gyada kai ya dinga yi kamar qadangare ya daga ta yana son ya dauke ta, da sauri ta sauka dan in ya sata a kafadar nan tashi sai ta yi aman hanji ta tasss saboda tsamin zufar da yake yi,cikin kirsa ta ke masa nuni  da yara, kawai ya je ya fara shiga zata biyo shi ta masa wankan daga baya, tafiya ya yi yana washe baki, rabon da a masa irin haka tin tana amarya a cikin garin Abuja. Ai kuwa da Salma ta samu dama ta kora yara Mazan su tafi masallaci,matan kuma a shiga a yi sallah  sai tayi wuff ta faɗa band'akin,wanka ta masa sosai, ta bashi brush ya wanke bakinnan fes,sai ga Talle an yi shar, shima kar ba ya yi ya mata wankan ta wanke bakin ta, ta fara leqawa taga ba yaran maza 'yan matan na d'aki suna hira da Marka sai ta fito, daga baya shima ya biyo ta dakin, shirya shi ta yi tace ya yi alwala ya je masjid, amma sai Talle ya buɗe baki cikin b'ata fuska ya ce, "Ka ji min yarinya da ke kike sani na yi sallar? To banga dama ba haɗawa zan da isha'i in na gama abinda zan yi" Cikin kwantar da kai Salma ta ce wa Talle,   " Ah ah ba ni nake saka ka ba Allah ya baka hakuri, ni so nake dama kayi da wuri saboda in na zo maka tausar nan bana son abinda zai sa na tsaya ne ka ga idan baka yi sallahr ba dole ana tsaka da tausa ka ce na tsaya ka je ka yi sallahr shi yasa na ke baka shawarar ka yi yinsa wuri amma tinda baka so kwanta na yi maka tausa" Cikin yauqi da kwarkwasa ta qarasa maganar ta,tini Talle ya washe baki kamar dolo, miqewa ya yi zai tafi masjid, yajiyo maganar ta tana fad'in, " Babe in ka je ka jira ayi isha'i kawai ka ga in ka shigo sai asuba zamu sarara ko ya kace" Ta qarasa ta na kashe masa ido ɗaya, wata dariya Talle ya saki kamar wawa ya ce, " Maganar ki dutse sweety na se na dawo" Koda ya isa masallacin har an yi magariba makararru ya samu aka ja su jam'i suka yi sallar,lokacin isha'i na yi aka kira sallah aka tada sallah,ana idarwa kuwa Talle ya miqe ya koma gida,tafe yake cikin sauri fakam fakam ya qarasa tsakiyar gidan nashi,Marka ya yi wa sallama ya faɗa dakin Salma wadda ya tadda ta sha gayu sosai da yan kayan da take da su, ta dan fesa turaren ta da ya kusa qarewa dan kale ma take yi, yana shiga d'aga sama Talle ya yi yana juyi da ita,ita ko sai dariya take yi, sumbatar ta ya fara aika mata da shi tana mayat mashi da martani, suna tsaka da wasannin su ya katse ta ya ce, "Ni fa yunwa nake ji, mu fara cin abinci kannan yarannan sun yi bacci sai mu dora daga inda muka tsaya, dan yau kam sai yanda hali ya yi," Cikin jin daɗi Salma ta saki dariyar murna,a haka ta tafi ta dakko masu abinci suna ci suna hira Salma cikin shagwab'a ta ce, " Babe me yasa ka amshen waya ta ne, tinda nazo yanzu kusan wata bakwai da wasu kwanaki ban ji muryar kowa nawa ba" Wani mugun kallo Talle ya buga mata daya sa cikin ta kad'awa, dan dai Tallen Tallen ne fa kar ta ga ya na biye mata ta kawo masa raini, sunkuyar da kan ta ta yi qasa cikin kwantar da kai tace, " Ka yi hakuri ba zan sake zancen ba dama na yi kewar Goggo da Baba ne" Wasu hawaye ne masu zafi suka sauka a fuskar ta, hannu tasa ta share su kamar ba ita ta yi kuka ba, ta dakko cokalin abincin ta kai bakin shi, amsa ya yi ya dan sake rai kadan, a haka har suka gama, Huwaila da Jummala kamar yanda suka saba sun fita zance amma zancen da su Badamasi ne, ana can ana latse2 da tabe2  da tsotse2, ita kuma Marka sun gama shirya duk abinda ya kamata cikin duhun nan ita da Yayan Talle, da zata wuce ne ya daki mazaunan ta ta baya, juyo wa ta yi ta hau masifa, " kaifa yayan nan jarababbe ne, kwana dayan nan da mukai ba a tare ba duk ka zama kamar ka dauke ni mu gudu, to ina sanar da kai ka iya takun ka, kasan Talle ya fika wayo ko dan ba soko bane kamar ka, zai iya gane wa" kad'a mata kai ya yi alamar zai kiyaye, shigewa tai d'akin ta,Salma amarya ana can ana soyewa ita da me gida, Sun yi nisa ba sa jin kira, komai ya kankama, suna cikin raya daren nasu cike da kewar juna ne su ka ji motsi ana sand'a, gaba daya Talle ya cika wajen na su da gurnanin shi, Marka kamar ta mutu dan kishi da baqin cikin da ke cin ranta, sai kaiwa da komowa take a d'akin, tana jin motsin Itama tace, " Alhamdu lilLAAHi ƙarshen tika tiki tak"   Da sauri ta manna kan ta a jikin qofa dan ta ji ya za a kaya, " Salame bude qofar mana na iso, me kike yi ne baki riga kin buɗe ba sai na zo ina bugawa sun ji kamar rannan, so kike wannan shegiyar kishiyar taki mai baqin tsiya ta ji ta leqo irin na rannan, Salame ya dai na ji ki shiru, dan Allah ki yi sauri mana ki buɗe muyi mu gama na tafi a matse na zo yau" Talle da ya gama jin komai wani shaqa ya yi ma Salma da idon ta ya firfito waje tsabar mamakin abinda kunnuwan ta ke jiyo mata,da sauri ya sake ta ya sauka ,ya saka wando shi jin da ya yi ba a daina taba qofar ba,kuma ba a daina kiran Salma ba, ai ko mai maganar da ya leqa ta bular da yake hango su yaga yana tahowa da gudu ya kwasa ya yi waje, yana fitowa da hanzari yaga an gilma da gudun tsiya komawa ya yi d'akin, dan ya san laifin ta ne koma wanene ya zo da ace bata bada qofa ba babu mai zuwar masa kwartanci. Kafin ya koma d'akin Salma ta zura rigar ta tana ta kukan wannan masifa da ake neman jefa ta a ciki,nan take ta furta kalmar " Marka" Dafe kan ta ta yi, da ta sani da bata tsuye ta ba ta bar su da halin su, gashi yanzu ta jawa kanta masifa da bala'i,Talle na isa gaban Salma ya hau dukan ta ko ta ina,it a kuwa sai ihu take tana fad'in ya tsaya yaji me ya faru ita ba ta da laifi, inaaa dukan ta yake tin tana kuka tana bashi hakuri sai da ta koma ajiyar zuciya, sai da ya tabbatar ta kasa motsa ko da ya tsan ta ne sannan ya fita zuwa d'akin Marka, tana bude qofar ta Talle ya talle fuskar ta da wani azababben mari sannan ya ce, " Dan uban ki kin san hakan na faruwa ashe kika munafurce ni baki gaya min ba ko da ta wayar yarannan ne su Bangis ? Ga shi kwarton na ta ya ce kin gansu da Idon ki" kuma ta fara yi sosai dan kuwa marin ya yi matuqar shigar ta,cikin shassheqar kuka ta ce, " Inna faɗa maka ba yarda za ka yi ba cewa zaka yi kishi ne ke damu na shi yasa nace Allah ya nuna maka da kan ka wataran ka gani ba gashi yanzu ka gani ba" Kwafa ya yi yace , "Ai kuwa zata ci uban ta na san maganin ta ai," komawa ya yi ya kwanta a dakin markan, nan take kuwa Marka ta manne masa ba ko kunya da nadamar sharrin da ta qullawa salma,matsawa ta yi da zummar kwanciya gefen shi, da dabara ta kwanta a bayan shi wata ajiyar zuciya ya sake da sauri ya ja ta jikin shi, nan take Marka ta sanya murmushin samun nasara,ina ganin haka na fita kofar dakin na ja kujera 'yar tsuguno na zauna dan na jira masoyan biyu. Ina nan zaune bacci ya fara ɗauka ta na jiyo kukan Marka ta na ba wa Talle haƙuri akan ya kyale ta ta gaji, karshe dai Saida Marka ta gwammace ba tayi wa Salma mugunta ba a ranar, Talle kuwa ce mata ya yi, " Dake da iya duk sai kunci uban ku, zan maganin kowa a cikin ku, ki min shiru ko na farfasa maki baki" Tare da kaiwa bakin nata duka, dip tai bata qara kokawa ba kuwa sai kukan zuci, da sassafe ya shirya ya daukar wa Salma kayan ta suka wuce cikin garin Abuja, Marka kamar ta mutu dan haushi da baqin ciki, ita da ta so a barta ta zauna da su dan ta rama abinda ta yi mata kawai ai a d'auke ta a Kai ta cikin birni? kai wannan abin haushi da yawa yake. Sun isa Cikin garin Abuja lafiya  da rana wajejen 12pm, gidan Alhjn shi ya kaita, wannan karon ma sun qara yin tafiya, amma wannan karon d'akin shi na gidan na mai gadi nan ya kaita ya ajiye ta ya yi ficewar shi yawon shi, miqewa ta yi fuska ta kumbure mata ta yi sintim da kyar take gani,a haka ta jingina da gini ta rungume guiwowin ta tana kuka mai ban tausayi A rana irin ta yau Salma ta yi nadamar zuwan ta ABUJA, wato in baka iya kama barawo ba shi ya kama ka, wannan shine ya faru tsakanin ta da su Marka. *************************** A can garin Kano kuwa jabeer ne ya yi sallama ya shiga gidan su fuskar shi cike da fara'a kamar wanda ya yi tsintuwar dimond......... *Too Yan Jabeerun Innarmu da Juwaireren mama minana kakawa murna hakan ga?" [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼   ' YAN ABUJA   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 14: Itama sallahr ta samu waje ta tada, domin dama da ta yi wanka kafin ta fito daga band'akin ta yi alwala ta saboda idan lokacin sallah ya kamata a ko Ina ne za ta yi sallar ta, cike da murna Juwairiyyah ke kallon Babyn Shamsiyya da ke goye a bayan ta ta na sallahr. Bayan sun idar da sallar ne suka hau gaishe gaishe, Juwairah ta karɓi Farha ta na mata wasa tare da tsokanar Shamsiyya ta na fad'in Farha fa ta isa yaye,cikin sauke ajiyar zuciya Shamsiyyah ta ce, "Hmmm ke dai bari sis ai maganar yayen ma na daga cikin abinda na ke son ki bani shawara akai sis, ya zanyi na gyara jiki na musamman kirji na dan kuwa  nan da sati uku nake son yaye ta, nono gaba daya ya koma slipas ba kyaun gani duk ya zube ya barni da fata, gashi duk nankarwa ta b'ata shi, hatta da ciki na ma nankarwar ce tun ta haihuwar farhan haihuwa, dan ma Allah ya sa Abban su mutum ne mai kawaici baya son ya b'ata raina amma ba namijin da zai so hakan, dan kafin su zube su yamushe ɗin nan na kula yana matuqar son wajen,"   "Sister kin ko kawo kuka wajen maganin ki"  Inji Nafeesah da ke sauraron hirar tasu. Dariya suka saka gaba dayan su Juwairah tace, " Nafee kina ban matsayin da bai kai nawa ba fa" " Ba haka bane dear a gaskiya kina burge ni wajen hangen nesa  na san ba komai bane ya jawo haka sai mai da hankali da ki ka yi kika koya wajen Mama Biliki a fa  gani muke kamar wahala take baki duk da kasancewar ki a matsayin 'yarta, komai a gidan fa da ke ki ke yi, to yanzu gashi yana maki amfani"  "Haka ne kam, dan ko ni a da wataran sai na ji na gaji bana son taimaka mata, data fahimci haka bata mun faɗa amsa take tayi takan ce jiki da jini,Allah dai ya karawa iyayen mu lafiya da imani..... to tanzu dai kin san me zaki yi yar uwa? Da farko ki nemo wadannan alkama,Fatar shinkafa,dankalin Hausa,(a wanke a fere a yanka a shanya ya bushe a inuwa) aya, gyad'a mai bargo,kantu/rid'i, plantain ki busar da ita,jar dawa,hulba,dabino ki same su gaba daya ki gyara ki kai a niqa maki ki dinga damawa da kunu ki na saka madara ki na sha, sannan za ki iya haɗawa ki sha ko ba madara, idan kuma mai haɗe haɗen magunguna ki ke so,to ki nemo wadannan magungunan a wajen masu maganin mata ko maganin Hausa sai ki haɗa da wadancan abinciccikan da na lissafa maki,ga abubuwan kamar haka, NONON KURCIYA, GANYEN BAFULATANA, GADALIN NONO,  su ne abubuwan da Zaki nema, sai kuna na gaba,mai sauqi kuma yana yi sosai shima, wanda zaki samu farar shinkafa ki wanke ki jiqa ta akai markade ta zama kamu, sai ki daka bagaruwa da ake tsarki da ita idan ta yi laushi sai ki ajiye idan Zaki dama kunun shinkafar sai ki tafasa cokali ɗaya a ruwan da Zaki dama kunun da ita ki sha da madara bayan jin gama damawar,ya na da kyau ki kiyaye ki na yi kullum ki na sha dan ba a son qiwa kiyi yau kiqi yi gobe, sannann ana son ayi kamar na wata ɗaya ne, zuwa yanda ki ke son qirjin naki ya tashi ya gyaru,sai kuma ki siyo man kwakwa Mai kyau ki haɗa da man hulba ki na shafawa a wajen ki yi massaging ma'ana ki ta murzawa har sai kin ji man ya shiga Fatar jiki ki sosai. Ta bangaren nankarwa kuma ki samu man kad'e(wanda ake shafawa faso ko kaushi) sai kina shafawa a jikin ki da duk inda ta fito musamman ma a cikin naki da duk inda nankarwar ta fito maki, kinji wadannan a sauqaqe kenan" " kaiiiii amma yar uwa na gode sosai, Allah ya saka miki da alkairi, Allah ya sauke ki lafiya, ya bamu bby mai albarka," Sunkuyar da kai ta yi a ranta ta amsa, " Dalla in zaki amsa ki amsa ba ma son gulma karshe dai gaki nan ciki ne da ke dai" " Sannu Nafeesa sarkin rashin kunya na gode dani kike wannan maganar tin da ni nayi abuna" Cikin kad'uwa da tsoro Nafee ta hau zare ido ta na kallon ta inda maganar ta fito, gaba ɗaya ta tsorata ta kasa magana,su kuma dariya da kunya ce ta kama su musamman ma Juwairah ashe Yayan ta ya dawo su na ta surutu ba su ji ba gashi duk ya ji su. Tashi ta yi ta ja labulen ta fita wajen shi kan ta a qasa ta ce, " Sannu da zuwa mine" "Yawwa princess, ya ki ke jin jikin naki yanzu?" "To alhamdulillahi da sauqi gaskiya sosai,amma fa kaina yanajuyawa wani lokacin kuma cikina na motsawa sai na yi ta jin tsoro kuma abin na min daban haka" "Ki yi ta hakuri kin ji princess u will be fine inshaa Allah, kawai hakurin nan naki dana san ki dashi zaki ci gaba zamu iya komai a tare Allah ya shige mana gaba" Murmushi kawai ta yi dan kuwa ta amsa a ran ta shima murmuahin ya yi tare da  sumbatar  gefen kunnen ta a hankali,cikin sauri da kuma shagwab'a ta ce, "Yayaaaahh" Murmuahin ya sake yi mata sannan ya ce, "Yanzu tinda shamsiyya ta zo bari na je wajen Innar mu na yi hirata nima" Gaishe shi shamsiyya ta yi ya amsa tare da yi ma Farha wasa ya tafi, Nafeesa ta aika da abincin shi da komai da zai buqata can wajen Innarmu da kyar ta karba dan kunya da tsoron Yayan nata take ji ya kamata ta na surutu akan shi, dariya suka yi ta mata,bayan ta dawo ne ta ce, "Laaa Matar Yayah na haɗa mana kwad'on zogalen da rama?" Cikin tsinkewar yawu Juwairiyyah ta ce, "Kaiii Nafee amma Allah ya yi miki albarka, dan Allah haɗa mana" Ta shi ta yi suka fita tsakar gidan a tare Nafee na hadawa suna hira ta saka komai zata yanka albasa kenan, Juwairah ta dakatar da ita da sauri ta ce, " Nafeesa kar ki sa mana albasa sai dai a naki dan mu muna da masu shinshinar bakunan mu kar su ji warin albasa na tashi,baki san ba a son in yamma ta yi mace ta ci albasa ba? Dan haka ki kiyaye ko dan gaba idan kin yi aure musamman idan miji na gida ki hakura da albasa kawai ,in ko kinci ki tabbatar kin wanke bakin ki tass yanda ba yanda za ai ya ji warin ta kuma ki qara da abinda zai qamsasa bakin naki" Cikin farin ciki suka haɗa baki wajen gode mata,dan kuwa duk wanda ya zuba da ita sai ya qaru shamsiyya tace, " Lallai zan yawaita zuwa gidannan don na samu sirrin da yasa baki taba faɗa da mijin ki ba kuma kk iya controlling din shi haka"   "Hhhh haba shamsiyya ai mace bata controlling miji sai dai ya zamar mata bawa a lokacin da itama ta zamar masa baiwa,shi kan shi na miji ba ya sanin ya zama maki bawa sai dai yaji mutane na cewa ya zama mijin hajiya, ko mijin kan tace, da sauran su, babban abinda ke jawo ma mace hakan kuwa shine, neman soyayyar Allah makadaici, in mace ta nemi soyayyar Allah, ta kuma samu, to tabbas zata samu soyayyar mijin ta cikin sauqi, wanda hakan ya yi qaranci a cikin mu mata, daga wajen boka sai dora rai akan maganin mata shi kaɗai ne maganin matsalar auren mu,bayan ba su kadai ne ke riqe zaman aure ba, wallahi in Allah ya so mace ta gama samun dacewar duniya da lahira, dan haka ni sirrina na zaman gidan aure shine son Allah da neman Allah  ya so ni, saka soyayyar namiji a saman ta Allah shi ke saka mata fadawa halaka, daga zuwa wajen boka, zuwa zinace2, da dikkan abin da ya kauce hanya dan haka ina horon ku da neman soyayyar Allah kafin ta mazajen ku, sannan ba wai ba ma faɗa da junan mu bane, mu na yi, mun dai zaɓi soyayyar junan mu akan fushin mu ne shi yasa da mun yi fad'an muke shirya kammu ba wanda ya ji ko ya gani balle ya raba mu," Wani irin daɗi ne ke ratsa su dikkan su, musamman Jabeer da ya kawo kwanuka da niyyar yin alwala ya tafi masjid, godiya ya dinga yi wa Allah a zuciyar shi sosai da samun mace kamar Juwairah buta  ya ɗauka ya fita ba tare da sun san ya shiga ba. Suma sallahr la'asar suka yi, suka raka  Shamsiyya ta hau abin hawa ta tafi, tana cike da farin cikin samun qawa kamar Juwairiyya....... [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA    💅🏼     WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 16: Hannayen shi biyu boye a bayan shi ya qarasa sashen na su da ke share kwal, yashin wajen har wani zanen tsintsiyar kwakwa ya yi gwanin sha'awa, duk da cikin da Juwairiyyah ke da shi bai sa ta zama qazama ba, sanda ba ta da lafiya ba za ta iya aiki ba sai ta zauna ta huta,da Jabeer ya kula shi kuma zai taya ta, lokacin da take da lafiya kuwa zata haɗe gidan dika ta yi masa gyara na musamman. Juwairiyyah kuwa ta sowa ta yi da niyyar mishi sannu da zuwa yanda suka saba, sai taga ya maqale a jikin gini yana mata dariya, daga girar ta ɗaya ta yi tare da lumshe su cikin wani salon daukar hankali ta ce, "Yayana me kake boyewa baka son na ganiiii" Kwaikwayon yanda ta yi masa ya yi sannan ya ce mata, "Matso kusa ki gani manaaa" Matsawa ta yi, kusa da shi sosai  idan ta matsa sai yace ta qara matsawa kusa kaɗan, haka ya dinga yi mata har sai da jikin ta ya zama gaba daya a nashi sannan ya fidda hanneyen shi ta bayan ta ya rungume ta ya sumbaci kuncin ta da goshin ta, sannan ya kama ta suka zauna, miqa mata leda ya yi ya tallabe fuskar shi yana kallon ta da murmushi, bude ledar ta yi itama tana murmushi tana kallon shi tana kuma kallon ledar, tana budewa taga wayar da zata kai ta dubu sha biyar a ledar, buɗe baki ta yi cikin murna da tsalle, ta dane shi tana ma sumbatar shi ko ta ina, kama ta yai ya riqe kafadun ta sannan ya ce, " My princess ki nutsu kina girgiza mana baby, so kike ku ji ciwo?" " Kaiiii amma mine na gode, na gode , na gode, Allah ya saka maka da alkairi, Allah ya sama dukiyar ka albarka da rayuwar ka gaba ɗaya, Allah ya jiqan iyayen ka ya sa su cika da imani" Hannu ya sanya a Saman labb'an ta ya ce, " Shhhhhhh wai wannan godiya haka kamar na sai maki mota?" "Hmmmm kai ka ga bai kai na yi wannan godiyar ba amma ni na san ya wuce haka ma, kai ma kasan ina da son waya, a matsayina na wacce ba ta taba riqewa ba yau na samu ai sai godiya ko, bayan haka ma macen kwarai dole ne ko tsinke mijin ta ya kawo ya bata ta nuna masa godiya da murnar ta akan abinda ya bata, in ba haka ba ta yiwa kanta baqin ciki dan gaba ba zai ji qwarin guiwar kawo mata komai ba" " wannan haka yake macen kwarai, macen da zata zamo daga cikin matan aljanna in shaa Allah, Juwairah in dai ta dalilin miji ake shiga aljanna na maki alqawarin na yarje maki ina fatan Allah ya karb'i roqo na ya sanya min ke a aljannah" Wasu irin hawaye ne masu dumi ke bin fuskar ta, wanda duk ya kalle ta a wannan lokacin ya san ta na cikin tsantsar farin ciki da nishadi, ga wani sabon son Jabeer ɗin da ke ratsa ta,a hankali ta furta, " Yah Jabeer, na gode sosai Allah ya bar mu tare , mu je aljannar tare, domin kaima ka shiga cikin alqawarin Allah duk mai kyautata wa iyalin shi zai shiga aljanna, kana ɗaya daga cikin mazan da suke koyi da halayen Annabin rahama da sahabban shi na tabbata nima Allah zai amsa addu'a ta mu shiga aljannah a tare" Haka suka yi ta yi ma junan su dad'ad'an kalamai wanda suka tabbatar da har abada ba za su taɓa manta wannan ran mai cike da farin ciki ba. Kusan abinda aka rasa kenan a wannan zamanin,sai ka ga  saurayi zai je zance ko ta waya ya yi ta yi wa budurwar shi dad'ad'an zance kafin a yi aure, amma da anyi auren aka yi kwanaki ko watanni ko shekara ɗaya zuwa biyu ya daina kenan, itama kuma haka sai a dawo kowa na dana sanin auren dan uwan shi, auren duk da muke ganin yana dad'ewa wallahi ba sa dai na yabon junan su kamar ranar suka fara haɗuwa, kowa a kullum yana son ya fidda sabon salon da zai faran ta ran ɗan uwan shi ne, dan haka mu ci gaba da nemawa juna farin ciki sai auren mu ya yi qarko, idan ki na yi wa mijin ki ko ka na yi wa matar ka abubuwan alkhairi da soyayya bata kulawa to da wato da hikima da dabara ake nuna masu sai suma su koya, duk taurin namiji ko mace kyautatawa na karkato da hankalin su ga junan su,haka su juwairiyya suka kwana suka hantse cike da farin ciki bata huta ba sai da ta dinga kiraye kirayen waya bayan ta nuna wa Innarmu ta sanya mata albarka. **************************** Bayan kwana biyu da sanin cewa basu da mahaifa,Suwaiba da Saudat sun fara sabawa da wannan mummunan labarin da suka juyo wa kansu, Saudat ta fara neman dalilin da zai sa ta san me ne ne silar rashin haihuwar su, watarana Alhj Kalla  zasu tafi meeting gidan Oga Zaks shi da abokin cin mushen shi,already har an kusan fara tattaunawar da za a yi mutane duk an hallara, a cikin waɗannan kwanakin Sudat ta fahimci ko su Alhj Ƙalla su waye kuma ne suke boye masu,sai dai ta qi gayawa Suwaiba dan ita akwai wauta, da ta sani zata fasa kowa ya san sun sani, idan haka ta faru ta tabbata za ta jawo masu masifa ne kawai, sai da ta gama jin gaba ɗaya hirar tasu ta sabon member da suka samu da zai shiga qungiyar tasu amma bai san location ba, take Alhj Kalla ya fara bashi address, Saudat kuwa na boye tana kwafewa, ta gama kenan zata tura a riga Alhj Kalla ya fito, gaban ta ne ya yi mummunar  faduwa amma sai ta yi qoqari ta dake, ta ci gaba da jan rigar ta kamar tana gyaran rigar ne tun farko,kallon ta ya yi ya na murmushi ya ce mata, " Ohhh mata kenan, daga kwalliya sai saka kayan ado, sai gyare2 kawai kar dai aga munin ku" Dariya suka yi gaba dayan su,kafe ta ya yi da ido sannan a hankali ya furta, "D'azu ina ta kiran ki ina palour ban ji kin amsa ba min ba" Take ta gane wayo yake son yi mata,dan haka sai ta ce, " Ayya ka yi haƙuri ban jiba bane Alhj na, ni da nake nan kana can,wataqila ma da ka daga murya dana jiyo ka, tinda kai ba zaka yi amfani da waya kana kirana ba , sai ka yi ta kira in ban ji ba kace na yi laifi" Murmushi ya yi a ranshi ya tabbatar bata ji komai ba na daga hirar su, "Ok shikenan je ki dakko min ruwa na sha anjima kaɗan zan fita"  Tashi ta yi tana kad'a jiki tana yauqi ta fita, tana isa kitchen ta qarasa da hanzari ta ciro takardar ta wulla a bayan fridge din dan ya fi kusa da ita, motsin shi ta ji ya biyo ta Shima kitchen ɗin, bude fridge ta yi kan ya qaraso ta dakko ruwan da cup, yana isowa tace masa, "Hmmmm Alhj na kana sona da yawa na kula 'yan kwanakin nan kamar ka maidani rigar sawa ko ina zaka sai dani" Murmushi ya yi yace, " Ai ke kk koma haka shiyasa na koma hakan nima" Sannan ya karbi cup din ya haɗe da hannun ta ya matse saida ta yi qara, ya zaro mata idon shi jajaye yace, "Ki kiyayi bincike domin yana kai maiyin shi ga halaka" " Bannnn......ban ganee...baaa? Me ka ke nufi?" "Dalla malama rufe min baki, ji kike ban san kina bin waya ta ba? Ko bibiyar inda na fita? Ina nake zuwa me nake yi a can ɗin? Me kike son sani yau na sanar dake? Dan ba tsoron ku muke ji ba? Auren kwad'ayi auren kuɗi ku ka yi da mu, kuma kuna samun kud'in ko ba ku samu? Basu ishe ku bane? to meye na sai kin ji kwakwaf?" Jikin Saudat sai rawa yake wani ruwa2 tabji na tsattsafo mata ta qafart ta bata ii aune ba ta ji ya kwada mata mari sannan ya ce, " Dan uban ki fitsari kika yi a tsaye? Ji yanda kika bata min takalmi ni da zan fita,Me kika sani game da mu?" " Alhj ban san komai ba, sai dai zargi da nake yi" Aje cup ɗin ya yi ya zaunar da ita a kujerar dinning dake kitchen din ya ce, "Ehen ina jin ki zargin me kike yi?" "Dama ina zarkin ko ku yan damfara ne, kai da Alhj Salihu" " Kin tabbata zargin da kike yi kenan?" "Allah shine" " To bari ki ji, zargin ki ya tabbata, amma idan na ji wannan maganar ko a wajen waccan doluwar yayar taki da ba abinda ta sani sai b'arin zance, da son kuɗi ranar za ki mutu, kinji ko baki ji ba" cikin tsawa ya qarasa zancen nashi, baki na rawa Saudat ta ce, "Nnnnaaajii..." " Da kyau,ni na fita miqon takardar da kk boye kan na karya ki" Tashi ta yi ta dakko ta miqa masa ficewa ya yi ya barta a wajen,ya na fita ta durqushe tana ta kuka, lallai yau data gaya masa abin da ta gano game da shi da fa shikenan kashe ta zasu yi, yanzu ta gudu ma nan ma har gidan su zashi wataqila ma ta jawa uwar su a haɗa da ita a kashe, ta zauna ta yi shiru su yi ta cin kud'in haram kudin jini, "kaiiiiii wannan Abuja ba ta yi ba, inaaaa" Ni dama na sani a Damaturu na yi aure na huta" Ta fada tana share majina. ************************ A cikin garin Abuja kuwa bayan Talle ya dawo da salma gidan da yake aiki ya ajiye ta a dakin shi na masu aiki sai ya fice ya bar gidan , tun da ya fita take zaune a wajen take faman aikin kuka,idanun ta duk sun kumbure,a nan inda take zaune baccin wahala ya ɗauke ta,Talle kuwa ba shi ya dawo ba sai wajen la'asar hannun shi riqe da koko da qosai irin ɗan yamman nan da ake yi, sai wata leda mai kaya a ciki kala uku da takalmi kala biyu sai jaka daya, da yan kayan kwalliya da ba a rasa ba, miqa mata ya yi, ba musu ta tashi ta isa gaban shi ta Karb'a, leqawa ta yi ta yamutsa fuska,Talle na ganin abinda ta yi ran shi sai ya ɓaci, cikin haɗe fuska ya kalle ta ya ce, "Baki daku ba kenan ko, har da zan baki abun da ban sai wa Marka ba na tsahon shekaru ke kin samu amma ki ke kyabe baki ko" A tsorace tace, "Na gode" Ta Karb'a ta ajiye sannan ta shiga dan bandakin dake maqale a dakin ta yi wanka ta canja kayan ta fito, koko da qosan ta ɗauka ta ci ta sha, sannan ta koma ta zauna, kallon ta ya yi a wulaqance ya ce mata, " kin iya cewa wani ya yi sallah amma ke bata dame ki ba, ji kike ban gane ki ba, wa'azi a baki amma ke baki aiki da shi munafuka, irin kune kuna da yara kuna sa su sallah su qi yi, to basu ga kuna yi ba" Miqewa ta yi kamar munafuka da tsaho kamar raquma ta tafi,zalo zalo taje ta yi alwala ta Yi sallar ta koma ta zauna,kallon ta ya yi ya kama kunnen sa alamar zai yi mata gargad'i, " zuwa gobe ogana zai dawo shi kaɗai yake zama anan, matan shi suna maiduguri, aiki ke kawo shi nan,  dan haka in ya dawo da yamma ki shirya muje mu gaida shi, in muka dawo na gan ki a waje ko kusa da wajen dakinnan kin mutu ranar, dan na san ki idon ki idon kuɗi, kice zaki maqale ma bawan Allahn da bai san neman mata ba, na kula akan kuɗi komai yi zaki yi, tinda an iya bin qattin qauye masu bada dari da hamsin" Hawaye take zubar wa sosai saboda tausayin kanta a ganin ta ba abinda yafi sharrin zina da sata baqin ciki a duniya, haushin ta bai wuce yanda yama qi ya saurare ta ba sam, ya tsaya ta masa baya ni yaqi, kawai sai ta maida kanta ta kwanta, bata qara furta komai ba har ya shirya ya fice, kuka take mai ban tausayi,cikin kuka ta ce, " Oh ni Salma na saiwa kaina wahala daga 'yar shawarma da motar dana gani duk na rud'e yi yau ga inda na kawo kaina, Abuja ko wahala?" A can qauyen su Talle kuwa da kyar Marka ta miqe ta je ta hada wuta ta shiga ruwan dumi ta gasa jikin ta,bayan ta gama ta zubar da ruwan ta yi daki, komawa ta yi ta ci gaba da kwanciya, wani qaramin yaro ne shafi'u daya d'aga cikin yaran tsofaffin matan Talle ne ya shiga d'akin ,yaron zai kai shekara goma, baya jurar yunwa shi, dan ko da su Huwaila na baccin gajiyar iskancin su da suke sheqewa da dare, ita Marka takan tashi ta yi abin kari da wuri, to yau sun ji shiru kowa dif a gidan, tura kai ya yi dakin ba sallama, to ba a Koya masu ba,Marka na kwance ta ware qafafu tana ta firfita da mafici,bata ji motsin yaron ba sai maganar shi ya na fad'in, " Marka yunwa muke ji" Da sauri ta sake zanin ta ta juyo kan shi,ta qanqance ido sannan ta ce, "Me kace?" Cikin dauriya yaron ya ce, " cewa na yi yunwa muke ji" Kiran shi ta yi tace ya je ya karba, yana isa data damqe shi ta hau duka, tare da fad'in, " Yau sai na fanshe duka na da  uban ka ya min a jikin ka ,baka da labarin ta'annutin da uban ka ya min shine har abinci ka zo ka na tambaya? Ga shi yanzu na san tinda ya dauke waccan jaja amaren sai na gan shi kuma, to kuwa yau zaka ci abinci har ka qoshi," D'im d'im d'im kawai ka ke ji na tashi a d'akin Marka ta na ta dukan dan mutane, " Marka lafiya me ya yi miki haka ki ke dukan shi kamar kin samu jaki?" Cewar wadda ta shiga d'akin ta na qoqarin kar bar yaron a hannun Marka da ta haukace da b'acin rai,ganin da gaske yarinyar take yi zata karɓe yaron a hannun ta gashi bata ji ta huce ba, kawai sai ta sakar wa Haulen wani mari itama a kuncin ta mai shiga ƙwaƙwalwa. Makaranta na taqaice maku labari a ranar nan duk wanda ya yi gangancin shiga d'akin nan nema wa su Haule taimako sai ya karɓi nashi ɗaukan,idan ta na dukan wannan wani ya shiga sai ta saki na hannun ta ta kama sabo ta daka, haka ta dinga yi kamar wata mahaukaciya, sai da ta gaji jikin ta ya yi laushi sannan ta kwanta tana kukan baqin ciki kamar wani ne ya aike ta qulla wa kishiya sharri,cikin kukan ta ne ta ke fad'in, "Wayyoo ni Allah na Marka yau na shiga uku na qulla sharri gashi ya zame mini bala'i,na yi abinda zai jawo wa kishiya baqin jini a wajen miji ni kuma sun tattara sun wuce binni sun barni a qauyen"............ [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼   ' YAN ABUJA  💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 17: Tun da Jabeer ya sai wa Juwairiyyah waya ba su samu suka haɗu da Nafee ba sai da aka kwana biyu,domin kuwa a washegarin ranar Nafee ta tafi gidan wata qanwar Innarmu ta yi masu kwana biyu, dawowar ta da yammar ranar ke da wuya Juwairiyyah ke nuna mata wayar cike da zumud'i da murna,cikin fara'a ta amsa sallamar Nafeen sannan ta qara da, "Wa'alaikumussalam shigo shigo yar uwa kiga me yayana ya sai min da bakya nan" Da sauri Nafeesah  ta qarasa shiga itama cike da d'okin ganin me za a nuna mata, sanda ta gani itama 'yar qaramar qarar murna ta yi ta haye kujerar da Juwairah take tare da fad'in , kaiiiii amma Allah ya saka ma Yah Jabeer da alkairi, ya sai mana waya mun daina leqen ta qawaye" "To malama ba wai an sai mana waya ba na dinga neman ta ina rasawa" "Hhhhhh Allah baki hakuri ai wannan wayar inna ɗauke ta kema  kin San zan ririta ta, yanda kk san jariri haka zan kula da iya sai kin neme ta sannan zan miqo maki, ko kuma idan tana buqatar a sa mata kudi" Dariya suka yi a tare sosai, sannan Nafee ta ce wa Juwairiyyah, " Yauwa wai ni ruwan meye wancan a butar qarfe na ga kin saka a garwashi? Tunda na shigo nake jin kamshin na tashi ko shayi za mu sha ne na musamman" Dan dafe kirji Juwairiyyah ta yi sannan ta ce, " Oh ashe ban cire ba dama? Dan je ki sauken dan Allah ki dawo na fada maki hajiya tambai" " Ah tohhh dole ki min bayani dalla dalla dan kin san in baki fad'an ba baki da zaman lfy yau" Fita ta yi ta sauke mata butar ta dora ruwan wankan ta , ta koma dakin, zama ta yi tare da tanqwashe qafa agaban Juwairah tace, " To malama a bamu darasi, dan zama dake akwai diban ilimi" " ke ko, ke ko, hmmm kina raina sanin da Allah ya baki ne amma kin fini ilimi ai, kefa duba ki gani yanzu ci gaba da karatun ki kike yi ni fa ina zaune a gida kullum ba wani ci gaba da karatun da na ke" " kema zaki ci gaba ne watarana komai lokaci ne sis kar ki damu,oya ina jin ki meye wancan a butar qarfe?" Dariya Juwairah ta yi sosai sannan tace, " ke dai ba ki mantuwa to magani ne, maganin infection musamman na masu ciki, Mama Bilki naga ta yi lokacin cikin Ammar shine nayi, Oh har naji ina son ganin yaron nan " "To na ji magani ne amma ai baki fad'an ya ake haɗa shi ba ko" "Haka ne, kinga dai da fari zaki samu ganyen garahuni, da 'ya'yan hulba ki tafasa su sosai sai ki bari ya sha iska sai kina tsarki da shi, da yawan masu ciki suna fama da infection sosai, mai fidda ruwa kala2, amma da zasuna amfani da wannan zai masu magani duk da ba wai yana ɗauke shi dika bane kwata2 amma yana ragewa sosai, in aka hada da wasu magungunan na sanyin ana sha, kin ga na ciki na mutuwaaa na waje ma ana kashe shi, amma idan mace bata da ciki zata iya neman sassaqen sanya,bagaruwar mata,lemon tsami, d'anyar citta,kaninfari,masoro,kimba,danyen kurkur, ganyen magarya,sai ta haɗa su waje ɗaya ta dafa ta dinga shan ruwan, ta yi na sati biyu ita da mijin ta da kishiyar ta idan mai kishiya ce saboda su yi maganin abin a lokaci d'aya, in shaa Allahu Zaki ga an samu sauqi gefe d'aya ana tsarki da wancan ruwan garahunin,sannan wannan had'in ga masu neman haihuwa in dai matsalar ta danganci infection to da yardar Allah zai wanke mahaifa a samu ciki, sai dai kuma idan matsalar ba wannan bace sai a nemi maganin matsalar," "Yauwa 'yar albarkan Yah Jabeer ko ke fa, ba ga shi kin qara min ilimi ba ni ina ma na san wannan abun in ba yanzu ba, yauwa rannan ma na ji kina faɗa ma shamsiyya wani abu lokacin na fita ban ji me kuke cewa ba game da warin gaba dan Allah ki yi min bayani akwai wata a department din mu ba zaki so zama kusa da ita ba sam saboda wari" " Ohh wannan ai ta na tare ko da babbar matsala gaskiya,in ki na so ki yi maganin matsalar warin gaba dole sai kin san kala kalar shi,na farko dai akwai na lalura, akwai wanda mace da kanta take jawo wa kanta" "Hhhhhh ka ji Matar yaya wai mace ta jawo wa kanta to kamar yaya? Kana sane kabar jiki ya yi ta tsami" Dariya suka yi a tare sosai suka tafa, sannan Juwairiyyah ta ce, " Allah da gaske nake yi, yanzu misali Nafee, ke ce kin tashi a rana kin wuni da pant ɗaya a jikin ki, kin je fitsari kin yi fitsari baki wanke wajen sosai ba kin maka pant kin mayar, kin yi bayan gida kin maka kin mayar, sannan da jiqar da komai ki ke mayar wa, ki fadan min shi pant din d'an uwan ku ne da zai qi yin wari?"  Wata iriyar dariya Nafee take yi, cikin dariya ta ce, " Whhhhhh alqur'an dole yayi wari, amma dai misalin nan dama ba dani aka buga shi ba a canja gaskiya a saka Salma" " wulaqanci Yayar tawa, Allah sarki mutan Abuja ana can ana shan daɗi an manta da dangi" " Hmmm ke dai bari buri ya cika, Allah muma ya sada mu da mafi alkairi" " Ameen dai" " To yanzu fad'an ya za ai ayi maganin wannan warin dan Allah dan akwai yar makarantar mu na faɗa maki, da kin zauna kusa da ita sai kin ji wannan warin,ni ba zan ji kunyar faɗa mata duk bayanin da Zaki yi min ba, da azo ana ta gulmar ta ko ana gudun ta ta na jin haushi ai gwanda a faɗa mata matsalar ta da maganin matsalar ta gyara ko? Wataqila bata samu iyayen da ke koya mata ba kin san wasu iyayen ba su koya wa yara su komai kin dai gane me nake nufi" Ta faɗa tana nuna hanyar sashen Innarmu,qunshe dariya suka yi sannan Juwairiyyah ta ce " Allah sarki, aiko gwanda ki sanar da ita, dan aboki na gari ke wayar da kan abokin shi idan ya ga irin haka na faruwa da shi,to kina ji ba,na son a rana a baki canja pant ba ki canja sau biyu, ya zama na kina da tsimma ko towel qarami a toilet din ki wanda in ki ka yi fitsari ko bayan gida zaki tsane wannan ruwan bayan kin yi tsarki tunda yanzu yawanci banɗakunan na masu da shi ne tsarin ginin za ka iya ajiye qaramin towel,sannan in kin zo tsarki ki fara da gaba ko da baki yi komai ba, sannan baya ya zama na qarshe, karki hade wajen a lokacin wankewa, in kika gama ki goge wajen sai ki maida pant din ki, in rana tayi kika yi wanka sai ki canja,in da hali da dare ma kan ki kwanta ki caja, ba yanda za yi a same ki da wari ko da baki shafa misk ba, balle a same ki kina wanke wajen da ruwa mai dumi da ki ka zuba musk, ko ki saka ruwan d'umi kaɗan bayan kin gama wanka ki tsiyaya zuma asalin mai kyau ki wanke gaban ki da shi,yana daga taskar magunguna da ya kamata  muna amfani da shi, bake ba warin gaba in dai kina wanke wa da ruwan zuma kina saka misk, kina tsanewa in kinyi bayan gida, ina fatan na amsa tambayoyin ki gaba ɗayan su yanzu Hajiya tambai" "Hhhh kwarai da gaske Juwaireren Mama da Yah Jabeer kin biya ni kin amsa har da wanda ban ma zata ba ke dai Allah ya barki da yaya, ya sauke ki lafiya" Cikin jin daɗin addu'ar Nafee ta hau shafa cikin ta sannan ta amsa, tashi ta yi ta shiga bayi dauke da butar ta a hannu, bayan ta fito ne take ce ma nafee, " Nafee na ga kina zare ido, kar fa ki je ki yi fitsari ko ba haya ki hau tsarki da ruwan almiski kin dai san ba ya tsarki , ana tsarki ne da ruwa mai tsarki kuma mai tsarkakewa,ah toh gwanda na yi maki bayani dalla dalla kamar yanda ki ka ce, yauwaa kin San fa gobe ne ranar gyaran jikina ina zan samu dankalin turawa pls na wa ya qare,dan Allah in an samu ki zo ki taya ni kin dai ga yanda na koma ba zan iya yi ba ni kaɗai" "Haka ne bayanan ki, maganar dankali kuma kar ki damu zan samo maki kan goben in shaa Allah,in ba ke ba ma wa yake ta wani gyaran jiki a wannan yanayin,ji cikin ki fa ya girma amma kk maganar gyaran jiki, ki bari ki haihu mana" " Tab a'a ni dai ki samo min, in babu ma ina da zuma da sugar sai na yi amfani da su kawai lemon zaqi ko ɗaya ne ko biyu Zaki samo min" "To Allah ya kaimu da rai da lafiya bari na yi wanka na fita makaranta" "To Allah ya bada sa'a, bari na dan huta nima". ***************************** A Abuja garin shugaban qasa kuwa Talle ne ya sanya manya kaya har da hula shiga dai ta kamala ya yi ranar ya sanya Salma yin shigar kamala Itama suka shiga sashen uban gidan shi dan ya gabatar da Salma a matsayin iyalin shi, cikin wata murya mai cike da ladabi Talle ya ce, " Alhj wannan itace mata ta da kuka Karb'a min auren ta a garin kano, dama na dawo da ita nan ne dan na dinga samun kulawa, zama ni ɗayan ba daɗi" Talle ya fada yana sosa qeya, murmushi uban gidan na shi ya yi sannan yace, " Allah sarki ai ba damuwa, hakan da ka yi kayi tinani mai kyau,sannan kuma ka kyauta, ina maku fatan alkairi, Allah ya bada zuri'a dayyiba" " Ameen" Gaishe shi salma ta yi kanta a qasa tana wasa da gyalen ta,shi kuma ya amsa ba tare da ya kalli in da take ba, kuɗi ya qirgo dubu goma ya bata, yace gashi ta sai wasu abubuwan da take buqata, amsa ta yi hannu na rawa,dan kuwa rabon ta data riqe kuɗi haka ai ta manta, tashi suka yi suka fito, suna isa daki ya miqa mata hannu fuskar nan ba walwala, ita ma ta d'aure tata fuskar ta ce, "Me zan maka kuma" Ta karasa maganar ta cikin tsiwa, " Kee! ni za ki tambaya me zaki min, to in baki san me zaki min ba bari na fada maki, kawo su nan" Alamun da ta gani na ba wasa yasa ta miqa masa kud'in tana hawayen baqin cikin ganin samu ga rashi a lokaci d'aya, murmushi ya fara yi saboda jin dumus ɗin kuɗi da ya yi, " Ko ke fa salameme na, yanzu ai kin ga ko dari biyar na baki ai yafi na qattin qauye masu baki dari da hamsin ko" Juyo wa ta yi cike da bala'i tana kallon shi kuma sai ta fasa yin maganar da ke bakin ta ,wani irin tsoron shi ne kamata saboda yanda yake kallon ta,gani ta yi yana cire kayan shi ya na nufar ta, hankalin ta ne ya tashi dan ko bata shirya ba masa ba har a wannan lokacin ciwon jikin da take fama da shi bai tafi dika ba, gashi shi in ya fara abu bai san ya bari a huta ba, sai ya gajiyar da mutum, kuka ta fara tana fad'in, "Ni na bar maka ɗari biyar ɗin dan Allah ka bari sai nan da kwana uku, na gaji banda lafiya fa ka sani" Dariya Talle ya yi sosai ya maida kayan shi, ya kalle ta ya ce, " Da kyau matar manya matar Ɗan Abuja, ku baku da buqatar kuɗi ai, ni na fita to ga wannan ki leqa waje akwai shago ki siyo kwaki da sugar ki sha, ina jin har canjin gyada zaki samu ma a ciki" Nera ɗari biyu ya wurga mata ya fice yana wata tafiyar yan duniya a shagide, kuka Salma ta durqusa a wajen tana yi tare da fadin, "Wai ni ina yan uwana ne, suna can suna jin daɗin su sun manta da rayuwa ta, basu san a halin da nake ciki ba,Oh Allah ka kawo min ɗauki, Allah na tuba, Juwairah kin huta, da baki bi zabin aure irin nawa ba, gani ina cin ubana a garin da na taso da kwadayin yin auren a cikin shi, na manta da neman zaɓin alkhairin Allah a lamura na,wataqila da na nemi zaɓin Allah da ko mummunar jarabawa Allah ba zai haɗa ni da ita ba a Abuja,sai na biye wa son zuciya gashi ina ganin b'acin zuciyar har da gangar jiki na, wayyooo Allah na na shiga uku ni Salma ina zan saka kai na?" kuka take ta yi mai ban tausayi, yunwar dake cin ta ce ta dawo da ita cikin hayyacin, tashi ta yi ta wanke fuskar ta, ta saka mayafi ta je ta siyo garin ta da sugar da gyada, haɗawa ta yi tana sha tana kuka,ganin duk talaucin su a can gidan iyayen ta ba su shan gari, amma yau gata da gari ba isasshe  sugar , share hawayen ta ta yi, ta jingina da katifar su, a haka baccin wuya ya dauke ta. **************************** Parlour ne na alfarma da ya sha kayan more rayuwa kala da kala, matan biyu masu ji da kyau da nera na zaune su na shan kayan marmari da lemo irin na manyan kwalaben nan mai tsada, saudat ta kalli yayar ta ta da tsabar kwanciyar hankalin da take ciki ya sa ta dan yi qiba kaɗan irin mai ban sha'awar nan ta murje fata sai sheqi take, alamun bata da wata matsala a rayuwar ta, dan gyara zama Saudat ta sake yi a karo na ba adadi sannan ta ce, "Ni kam Adda Suwaiba ki na tunanin kai ziyara gida kuwa? Ina gani fa ya kamata mu je ganin gida yanzu haka, haba tinda muka zo yau watan mu na takwas kenan fa muna cikin na tara amma bamu taba zuwa gida ba sannan ba a taɓa zuwa mana ba, ga labarin Salma shiru, har yanzu ko waya bamu yi mun ji daga gare ta ba" Iska Suwaiba ta furzar sannan ta kora jusi ta ajiye glass cup ɗin ta ce, "Hakane kam ya kamata muje muga ya su Goggo suke, batun Salma ki daina damun kanki tana can suna cin amarcin su a qasar waje da dikkan alama, kin san mijin ta ma ba laifi akwai kudi, wataqila ma basa qasar nan fa" "Haka ne kuma Allah dai ya jiyar da mu alkairi, amma nikam na tambaye ki mana," "Uhumm Ina jin ki" "Dan Allah baki taɓa zargin komai game da mazan nan namu ba kuwa?" Ɗan yatsina fuska Suwaiba ta yi sannan ta ce, "Kamar ya fa?" Tina wa da ta yi in ta sake Suwaiba ta san me ake ciki kashin su ya bushe, dan haka sai ta yi saurin kauda zancen ta basar tace, "Ba komai yanzu dai mu tambaye su, yaishe zamu je gida" " Ba rana balle wata" Amsar da suka ji kenan ana basu bayan an bude qofa an shigo,cikin haɗe fuska Alhj Ƙalla ya kalli Saudat ya ce, " Ke tashi mu tafi gida, ai an sada zumuncin haka, ku da kuke son Abuja kamar ran ku in ban manta ba, Saudat kan mu yi aure cewa fa ki kai, in Allah ya baki miji kuka tare a Abuja sai kin shekara biyar baki je ganin gida ba, ko ba ai haka yi ba?" Cikin qunar rai da kwallar da ta maqale mata tace, " Anyi haka, amma a da ai ban da isasshen sanin ya Abujan take kuma gani nake zan iya amma ni yanzu gaskiya gidan mu nake son zuwa naga uwata" Wani hatsabibin kallo ya watsa mata wanda ya sa ba ta san sanda ta durgusa ta dauki jakar ta ba ta yi hanyar fita, sallama ya yi wa abokin shi wanda daga jin warin da suke yi zai sa mutum ya san sai da suka biya suka yi mankasss sannan suka dawo gida. Nikam nace Saude Allah shi kyauta karki daku yauma.......😂 [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼     'YAN ABUJA   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 18: Tabbas gaskiyar mutane ne da suke cewa wani talakan bai iya samun waje ba, da ya samu waje sai ya dinga wulaqanta mutanen da bai kamata ya wulaqanta ba. Goggo Sarai na daga cikin irin wadannan mutane masu wulaqanta duk wanda suka ga sun fi qumbar susa,rashin iya cin arziqi da baqin ciki ne ya sanya ta bada umarni a gyara iya sashen ta har da ƙara d'aki ɗaya wanda na yi zaton Baba Baballiya ta sa a yi wa shi, amma ga mamaki na sai na ga ta cika shi da kayan alatu ta ce na 'ya'yan ta ne a duk sanda suka sauka a gidan, dan kuwa a yanzu sun girmi zama a d'aki ɗaya da ita suna gogar kafad'un junan su. Haka ta yi ta gama wulaqancin ta babu wanda ya kula ta a gidan, amma ita gani take gaba ɗaya an saka mata ido a matsayin ta na uwar masu kuɗi. A yanzu mijin Salma kawai take jira su dawo daga qasar waje a yo mata kabakin arziqi irin na qasar waje. Ammar ne ke ta wasan shi a tsakar gida ya na tafiya abun shi dugui2, dan ba wai tafiyar ta gama wani kwari bane,tafe yake har ya samu nasarar zuwa wajen randar ruwan Mama Bilki, da dikkan alamu qishirwa yake ji, Mama Bilki kuwa na d'aka tana baccin tsakanin azahar da la'asar. (Bacci ne da in bawa yayi shi yake samun lada daga wajen Allah) Ita ko hakima Goggo Sarai ana zaune a ɗaya daga cikin sabbin kujerun da aka sanya mata a d'akin ta ta na kora jus da meatpie, ga mafici a hannun ta irin wanda ake zuge shi dinnan ta kwama uban baqin glass a ido irin na ba mutunci dinnan, Baba Baballiya yau a d'akin ta yake, amma gudun wulaqanci sai dare yake shigowa shi duk ranar girkin ta,kafin tace ita ke ci da gidan ko makamancin haka gwanda ya je ya nemi na kan shi idan ya dawo ya bata duk abinda ya samo sai ya koma qofar gida ya zauna sai dare. Ammar ne ya dakko cup ya yi ta buqawa a jikin randar a qoqarin sa na son d'iban ruwan ciki ya sha, cikin Fushi Goggo ta sauke qafar ta da ta ɗora ɗaya kan ɗaya ta cire baqin gilashin idanun ta ta qanqance Idon cike da masifa sai ta ga ashe ba randar ta ake bugawa ba ta Mama Balki ce, dariyar qeta ta saki sannan ta ce, " Yauwa yaro fasa wa uwar taka dan arziqin da ya rage mata ka huta gadon mugun abu kawai" Bata gama rufe baki ba ya saki fitsari a wajen da yake tsaye fitsari kuwa ya sauka qasan qafafun shi ya gangara yatafi har  qofar ta da aka lailaye da tiles,nan da nan ta hasalo kamar wadda aka watsa wa ruwan zafi, ta miqe ta fita kafin ta isa wajen shi kamar ya san wajen shi za ta je ya fara qoqarin tafiya yana kuka, da alama ba iya fitsarin zai yi ba ma, daidai nan ne Mama Balki ta fito daga d'akin ta ta na miqa tare da salatin Annabi,Sallama Baba Baballiya ya yi ya na Kiran Sunan Ammar da ya gani ya na tafe ya na koke koken yaran da ke buqatar wani abin. Kafin kowa ya ankara ko ya ce wani abun Goggo ta saka hannun ta ta wanke Ammar da wani lafiyayyen marin da ko Mama Balki akai wa sai jikin ta ya gaya mata, "Bar ganin wannan kinibabbun iyayen naka masu son abun duniya da har suke ganin D'a namiji ya fi 'Ya mace daraja ba zai hanani cin uban ka ba, in banda baqin ciki da aka koyawa yaro qarami tin yana ciki, duba fa ku ga yanda ya tsanyaran mini fitsari a qofata ya yi gaba, to ba zan lamunta ba,haka kawai ina zaune 'Ya'Yana mata da aka tsana Allah ya ɗaukaka su sun zama wani abu a rayuwa har sun gyara wa uwar su wajen zama a zo kuma a koya wa yaro qarami mugunta ya lalata min waje," Tsabar Ammar ya gigice sai ya kasa kukan ma sai neman inda zai je yake garin haka har kashin da yake ji ya biyo bayan fitsarin da ya yi,zuciyar Mama Bilki tafasa kawai take da b'acin rai,tin da Baba Baballiya yake da ita bai taɓa ganin irin wannan bacin ran nata ba, ita kanta Goggo Sarai ta tsorata da ganin fuskar Mama Balki, wandon Ammar Mama Bilki ta cire ta wurga a jikin qofar da aka canja wa Goggo Sarai, qofa ce irin ta qarfen nan mai kauri milk color,sannan ta aje Ammar din ta isa jikin qofar ta samu wandon ta goga sosai har labulayen, sannan ta dawo ta d'aga hannu zata wanka mata mari, sai ta tsaya bata maretan ba , ta kafe ta da wani irin kallon da ke huda gabobin jiki da tsoka ta na nuna ta da yatsan ta manuni alamar gargad'i. Ko me ta tuna ta tsaya bata mare ta ba oho, sai kawai ta duba ta dauki Ammar da ke ta kuka yaqi yin shiru ta je ta fara gyara shi ta bashi ruwa da abincin shi ya sha ya yi bacci,sai da ta gama kula da yaron ta tsaff sannan taje ta dauke wandon nashi ta wanke ta shanya ta hau kiciniyar ɗora girki,wata irin wuta aka ɗauke a gidan gaba daya, kaff cikin gidan har Baba Baballiya ba mai iya cewa komai, Goggo Sarai na tsoron tace kanzil yanda Mama Bilki ta b'ata rai bata san me zai je ya zo ba, ita kuma Mama Bilki ta fasa marin ta ne ganin datajar Baba Baballiya dake bayan ta, shi kuma ya fuskanci hakan, sannan ya yi shiru ne saboda kar ya bata damar magana ya san kuka zata yi dan zuciyar ta cike take da baqin ciki, sai da ya tabbatar ta fara sauka tinda gashi ta ci gaba da 'yan aikace2n tsakar gida sannan ya samu waje a tsakar gidan ya zauna ya cewa Goggo Sarai, "Yau kin ban mamaki Sarai ba kaɗan ba, ki duba ki ga abinda kika aikata, yanzu marin da kika yi wa yaron nan ko ni ki kaiwa ai sai na ji shi a jikina ba shi ba ma, dubi yanda yatsunki suka kwanta a kan fuskar shi kamar qunar wuta, haba dan Allah, kin kyauta kenan, baki taɓa ganin fushin Bilkisu a kaf rayuwar ku ba irin haka ko kin taɓa gani? to ina mai tabbatar maki ki kiyayi sakata a irin fushin nan bana kusa, dan duk abinda ta aiwatar akan ki ke kika jawo wa kan ki da kan ki tunda baki iya riqe girman da Allah ya baki ba,a iya yau dai ai kin ga misalin abinda zata iya aikata wa ko?" Sai a sannan ne Goggo Sarai ta samu bakin magana, " Eh tinda kun haifi ɗan gwal, dole mana ku fifita shi akan komai, to da dan da uwar na san meye matsalar ku ba komai ke damun ku ba face baqin ciki, kuma nan gani nan bari dumamen mayya in dai nice ni da 'Ya'yana yan albarka mun fi ƙarfin ku" Cikin Fushi ta juya ta tafi fuuuu ta hau cire labulayen dika d'akin ta watso su tsakar gida ta dauki ɗaya a ciki ta goge qofar dakin da ya ɓaci da kashin Ammar da shi, ta saka ruwa ta wanke, ta qara gogewa da labulayen masu kyau din,duk kyau da tsadar labulayen haka ta saka hijab din ta ta fita waje ta watsar ta dawo, tana wani isa da taqama taje ta canja wasu,ta buga shewa da gud'a ta ce, " Ahayyyeeeeee ayyuuuuririiiiii, to bari ku ji sau goma wannan shegen tsinannen yaron zai b'atan qofa sau go......." Goggo sarai bata samu damar ida fad'in me take so ba ta ji qummmmmm a bakin ta, Mama Balki ce da ta hasala dan jin ana tsinewa ɗan ta ta saita bakin Goggo Sarai da ludayin da take juya miya ji ka ke kwalll ya daki fuskar ta, ihu Goggo Sarai ta saka ta na zagin Mama Balki, ita kuwa kamar ba ita ta aikata hakan ba ta je ta durqusa ta dauki ludayin ta ta juya ta ci gaba da aikin ta. Mai Baba Baballiya zai yi da ya wuce, cikin dariya ya ce, " Kai amma Gimbiya yau kam sai dai ace na zama munafukin mata, amma kin burgeni, ke kuma ɗan da kk kira shege, duniya ta san ni ne uban shi, sannan, tsinanne da kika kira min d'a ba za ki ga tsinewa a 'ya'yana ba inshaa Allah ina mai musu addu'a komai abinki Allah zai karen su, sai dai kiga tsinewar a kan kan ki dan ba yau na fara jin kin kira min D'a da wannann sunan ba, ke yanzu ba abin kunya bane ace ki na faɗa akan qaramin yaro har irin haka na shiga tsakanin ku ke da abokiyar zaman ki? To ina qara gargadin ki ki kiyayi randa bana gida ki taba wannan baiwar Allah ina tausaya maki " Ya qarasa maganar cikin dariya ya fita qofar gida, duk abinnan da ake Mama bata ce uppan ba aikin ta take kawai, nan da nan kuwa bakin Goggo Sarai ya haye sama,to abinka da farar mace fatar wajen kanta ta yi jawur, d'aki ta shiga ta d'au waya ta danna Numbern su Suwaiba, dannawa ta yi tayi tana kira amma ana mata turanci, gashi yau harda Malam din aka yi fad'an ba mai duba mata yaji me ake fada, kama kan ta ta yi da taji yana ciwo ta hau kuka, zama ta yi a gefen tamfatsetsen gadon ta da ta sake mai matuqar kyau da girma, kukan ta sake fashewa da shi, sai da ta yi kuka ma'ishi sannan ta miqe ta kwanta, yau ita Bilki ke bigewa baki da luddai? 'Oh duniya, da kudin ka da komai ba za a ji tsoron ka ba yanda naga ana yi wa masu kudi, to kwarjini ne bani da shi ko me,' Miqewa ta yi ta je gaban madubi ta kalli kanta daga sama har qasa, ga atampa nan mai tsada ta saka ta haɗa da sarqar gwal da zobuna komai ya ji, dubawa ta yi ta ga ashe fa har yanzu ko umara bata taba zuwa ba balle Hajji? Murmushi ta yi tace, " Gaskiya mana, to ai ko kashin ku ya bushe dan kuwa dole ne wannan shekarar a sauke farali da  ni naga ta raini" komawa ta yi ta kwanta baccin wuya ya dauke ta cike da mafarkai kala2 na ban tsoro, ta dad'e tana irin mafarkan nan,a mafarkin sai ta ga 'Ya'yan ta na cikin matsala, amma sai ta dangan ta shi da sharrin maqiya masu yi masu hassada, in suka zo ganin gida za ta saka su a gaba su je neman taimako. ***************************** Yau ce ranar da Juwairiyyah ta fi yin gyaran jikin ta kasancewar ta ranar jabeer na gida ba ya fita kasuwa,ta yi sa'a kuwa Yah Jabeer ɗin ta na gida bai fita ba,tun kafin ciki ma duk in da hannun ta ba zai iya kaiwa ba shi yake taimaka mata ya yi mata,kamar dai yanzu ma ba dika take iya wanke bayan ta ba,gashi kuma wannan abin gyaran jikin da zata yi yana buqatar a taimaka mata. Zaune suke a tsakar gida sun fara haɗa kayan gyaran jiki, Lemon zaqi 2,lemon tsami 1, sugar cokali 2 , Zuma cokali 1,gishiri qaramin tea spoon,dika waɗannan abubuwan ta matse ta zuba a mazubi ɗaya ta juya har Saida komai ya narke sannan ta d'akko soson wanka, ta miqa masa ta juya baya, Jabeer ne zaune a kujera 'yar tsuguno daga shi sai gajeren wando, dan kuwa ya shirya wa aikin Shima, ya na jin daɗin irin wadannan ayyukan saboda su na saka wa ya ji shi ma wani basaraken ne tun da dan shi ake gyarawa. Gyara zama ya sake yi a Saman kujera 'yar tsuguno ya nad'e soson zai tsoma a wannan haɗin Juwairiyyah ta yi saurin riqe hannun sa ta ce, " Yah Dan Allah sammin zan sha ya ban sha'awa" Ta na magana tana turo baki cike da shagwab'a, " ke fa kika ce kin ware kwanon nan ne dan gyaran jiki ko abu za a debo a ciki kin dinga kyankyami kenan shine yau zaki sha abun cikin shi?" Cike da mamaki yake kallon ikon Allah,Sake kwab'e fuska ta yi irin na yara masu son yin kuka ta ce, " Ni dai zan sha a haka Yayahhh" Ɗiba ya yi a spoon din da ta gama juyawa ya bata, aiko ido a lumshe ta shanye kusan sai da ta shanye rabin haɗin, Jabeer na ganin haka yace, "Tsaya,shin za mu yi abunnan ne ko na dawo ta gaba na qarasa baki ki shanye?" Kad'a kai ta yi alamar A'a su ci gaba da gyaran jikin, sai sud'e baki take kamar ta ci wani kayan daɗi, fara wanke mata fuskar ta ya yi zuwa wuyan ta har  bayan ta da wannan haɗin da soson,sai ya d'aga hannun ta ya wanke mata hammatar ta, sai ya dawo ta gaba ya wanke mata tsakanin cinyoyin ta zuwa cinyoyin da guiwar ta a haka saida ya hade kaf jikin ta ya wanke mata shi da wannan haɗin da soso, bayan sun gama ne ta yi masa godiya, tare da furta masa kalmar da ta zama masu al'ada wato, " Ina son ka" Maimaita mata shima ya yi ya d'aga ta, cikin nishi ya ce, "Wai wai waiiii Babyna gaba ɗaya kin yi nauyi yanzu, da kyar fa na d'ago ki" Turo baki ta yi kamar zata yi kuka, dama yasan za ai haka tsokana ce kawai da ta masa yawa ya sanya shi tanka qibar ta,dariya ya fara yana kame bakin shi, tura hannun shi ta yi daga kafadar ta zata fara tafiya, cike da tsokana Jabeer ya furta, " Mai ciki ihmmm ganinan tafe, me ciki, wallahi bani son sunan nan," Juyo wa ta yi ta biyo shi suka fara zagaye bangaren na su tana kukan shagwaba, tare da fad'in, "Inna kama ka yau a gidannan sai ka yi tsallen kwado," Sai huci take yi tsabar ta gaji kuma da gaske ta ɗan qara qibar, dariya Jabeer yake tayi mata harda riqe ciki dayaga ta gaji ta nemi waje ta zauna kuwa sai ya je ya duqa tare da kama kunnen sa kamar na masu tsallen kwado, cikin marairaice murya yace, " Haba Babyn Yaya, kiyi hakuri, in dai nine na yi alqawari ba zan sake tsokanar ki ba na tuba a yafe min" Ya qarasa maganar tare da karkata kai gefe alamun yayi nadama,murmushi ta yi sannan ta ce masa, "Na hakura amma ka jawa kan ka kai zaka kaini toilet a hannun ka ka dawo da ni, dama na kula tinda cikin nan ya yi girma sai dai ka tallebe ni ta gefe baka daukata, bazan lamunci hakan ba ehe" "An gama ranki ya dad'e da imani" Murmushi suka yi wa junan su a tare suka furta, " Ina son ka/ki" Wucewa ya yi ya je ya haɗa mata ruwa wanka mai d'umi ba mai zafi ba,sannn ya je ya ɗauke ta kan su tafi band'akin ne tace masa "Ina zuwa zan dau wayata," A haka ta na hannun shi ya kaita d'aki ta miqa hannu ta dauki wayar ta, " Kashhhh ashe ma Nafee bata da waya, bari inna fito na leqa na karbo dankalin in ta gama hada min din" kai ta band'akin ya yi ya dauraye mata wannan danqon, sai ga jikin ta yana wani laushi da haske, kamar wata matar masu kuɗi irin wanda fatar su ta ji hutu ɗin nan, sun fito kenan yana dauke da ita a hannu ya bada baya za su shiga parlour Nafee ta yi sallama, dakata wa ta yi, sai da aka bata izini sannan ta shiga,baje ta tadda Juwaira a kujera a zaune cike da tsokana ta ce, "Me ciki ! Auuu Yi haƙuri na manta,ga dankalin na mai da shi ya yi laushi kamar yanda kika ce na saka lalle da k'wai amma ba dika k'wan na juye ba farin ruwan kawai na saka, bayan na haɗa na zuba gishiri da kuma manjan kamar dai yanda ki ka ce,ai d'azu da ki na nan da sai kin ci dariyar Innarmu , wai fa cewa take wani abun daɗin za a haɗa, wai Nafee, irin abun rannan zaku mana mai kwai?" Dariya suka saka harda jabeer, sai da suka yi mai isar su sannan ya b'ata rai ya ce, "Ya ishe ku haka Innata ce fa" Dariya suka qara tintsirewa da ita harda shi din,sannan Jabeer ya ce " Feena taso ayi wannan dake, kuma kiyi a hankali kar ki ji ma mata ta ciwo" " Hummmm Masu mata" Nafeen ta furta a hankali Jabeer kuwa ya ji ta amma sai ya ce, "Me kk ce?" Cikin sauri Nafee ta ce, " Niiiii me na isa cewa, ba abinda na ce ko nake shirin faɗa ma" Dariya suka bawa Juwairah ta yi ta yi kuwa, daga baya suka samu wannan haɗin suka yi ta murza mata a jiki kamar dilka, kafin kace me juwairah ta yi kamar wata amarya, suna cikin yi Nafee ta miqe ta dakko ayaba daya, da k'wai, sai zuma da markadadden dankalin hausan da ta markade ya yi laushi, haɗe su ta yi har ayabar suka yi laushi sosai ta koma ta saman kan Juwairiyyah tana tsaga gashin kan ta tana shafawa a can qasan gashi,shi kuma Jabeer yana yi mata dilka, bayan ta kusa gamawa ne Juwairah tace, " Amma dai Nafee baki saka albasa a hadin yau ba ko? Dan na ji ba warin ta" "Eh ban saka ba na san ba zaki so ba maybe ya saka ki amai shine na bi ɗaya hanyar da ki ka taɓa faɗa min na yi wannan ɗin" " kaiiii amma ko na gode yar uwa Allah ya kawo miji na gari mumini salihi wanda zai so ki ya qaunace ki fiye da yanda Yah Jabeer ke yi min, ko dake anya za a samu kamar Yah Jabeer d'ina a wannan zamanin kuwa?" Ta karasa maganar ta cike da tsokanar Nafeen da ta kasa amsa addu'ar saboda kunyar Yayan nasu. Wannan haɗin na dankalin turawa da lalle da kwai da manja kaɗan da gishiri ko baqar mace ce take yi zai sanya ta yi haske mai ɗaukan hankali,dan kuwa ya na fitar da kalar mutum ta asali ya sa kalar ta yi kyau, ga laushin jiki da santsi da yake sanyawa. Shi kuma haɗin dankalin hausa yana qara tsahon gashi ne da hana shi karyewa,sannan ana yin zallahn na albasa madadin dankalin ko dankalin a madadin albasa, kowanne yana fidda gashi sosai kuma ya hana shi karyewa, ya yi laushi da santsi, sai dai na albasa na da wari, dan haka in uwargida ta gama ana son ta samu abun wanke kai mai qamshi sosai ta wanke kuma in an saka ana son a yi massaging scalf din sosai ya shiga ko ina. Ba su suka gama ba sai wajejen azahar, Juwairiyyah tayi bacci kafin su gama, tashi Jabeer ya yi yana miqa ya ce, "Wai gayu da daɗi da wuya" "Hhhhh Yah to ai kai zaka mora gwanda ka taɓa ka ji ya take ji da da take yi ita daya" "Waya faɗa maki da din ban taya ta wasu qana nan abubuwan? Ban dai taba irin wannan me hawalar bane, ashe haka take shan wuya duk dan ta burgeni baiwar Allah" Ya fada yana shafa gefen fuskar ta, bude idon ta ta yi ta ce, " Ku kuma ne kuke faɗa?" Nan da nan ta tsargu ta zaci suna magana ne akan qibar da ta yi, haɗe fuska ta yi kamar bata taɓa dariya ba, Nafee kuwa da ta gane dariya ce taso kwace mata, amma tace bari nasan me zan yi masu na gudu na bar shi da aikin lallashi, " Ni dai daya faɗa cewa na yi ba ruwana in kika ji, dan haka ba ruwana yanzun ma ni tafiya zan yi innarmu na kirana, Yah ka fada mata" kama baki ya yi yana mamakin sharrin da yarinyar ke son haɗa masa, kan ya yi yunqurin wani abu yaji ta janyo hannun shi gaba daya ya zube agefen kujerar da take zaune hawaye ta fara ta dora kanta a qafar shi ta rushe da kuka, "Shikenan yanzu dan na yi qiba sai a dinga tsokana ta, ai ba muni na yi ba, kuma da na haihu zan dawo daidai" Tana magana tana shan majina irin na masu kuka, rasa me zai yi ya wanke kan shi ya yi,dan yasan sharri kam Nafee ta gama haɗa masa shi ta yi gaba bai da hanyar fita, kamo ta ya yi ya hau massaging kafadun ta sannan ya ce, " kiyi hakuri princess, dama gani na yi cikin ya yi girma sosai shine nace ko yan biyu zaki haifa?" Cikin zumud'i tashi zaune ta na goge hawayen ta ta kalle shi tace "Allah yasa yayana" " Ameen to tashi muje mu yi wanka an kusa kiran sallah" miqewa ta yi da kyar, a ranshi yace, 'Waiii Allah ya taimake ni, Nafee Allah na son ki da ta burkicen yau sai kin wahala kema' Wanka suka yi ya gyara mata kan ta ya saka mata riga doguwa har qasa mai bud'ad'd'en qugu, ba qaranin kyau ta yi ba, kallon ta yake kamar kar ya daina, ita ko murmushi take ta danga wa dan ganin kyau da laushin da fatar ta tayi sai fidda wani annuri take yi, bayan sunyi sallah ne Innarmu ta aika masu da abincin su suka ci, tin da ya saka mata ruwa ta sha ta bingire a zaunen ta hau bacci, daga ta ya yi da kyar ya na nishi ya kwantar da ita a Saman gado shima ya kwanta a gefen ta dan sha baccin su tare. Yah Jabeer kam ya dad'e kan ya samu wannann bacci ya ɗauke shi, dan kuwa haƙuri kawai ya yi ba qaramin kyau Juwairiyyah ta yi masa ba, ga princess din shi a kusa da shi,yawan bacci irin na me ciki ya hana shi more gayun da ta sha domin shi,ni ko nace sai kun tashi asha bacci laaaafiyaaa masoya...... [21/07, 7:46 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 20: Alhj Kallah, Alhj Salihu, Oga Zaks, su kad'ai ne mutanen da na iya ganewa a qaton table din da yake cikin wani makekeken waje a zazzaune, taron wajen ya haɗa da wasu manyan Alhazawa masu ji da kuɗi, izza, taqama da qarfin iko, wanda adadin su zai iya haura mutum ashirin. Gaba ɗayan su sanye suke da  shigar tasu da suka saba yi wato shigar farin kaya da ratsin ja, kowa ka gani a wajen muzurai yake kamar su na jiran wani abu mai mahimmanci,haka zalika kowa ji yake da kan shi tare da ganin Shima ya kai wani jan wuya a wajen. Oga Zaks ne ya yi gyaran murya, sannan ya fara magana kamar haka, " A'a Salihu, wannan qorafin naku bai karb'u ba, kun san qa'idar qungiya, an baku damarmakin da ba kowa aka bawa irin su ba, ba dan komai ba sai dan babbar gudummawar da kuke bawa qungiya,ku kadai nake bawa damar da ban ba kowa ba a wajen nan,dan haka a wannan karon zan faɗa maku gaskiya kun bani kunya, kun karya dokar qungiya wanda ban yi zaton haka daga wajen ku ba, dan haka dole ne ku biya abinda ku ka yi,a matsayi na na shugaban wannan qungiya ina baku umarni ba shawara ba, ku je gida ku kawo matan ku nan wajen,dole ne a yanki abinda ake buqata daga wajen su, ba dan komai ba kuwa sai dan cika sharuddan Dodo, dan haka na baku nan da kwana uku, kuje ku gama sallama da su ku kawo su" Miqewa ya yi cikin izza da fushin b'acin ran da su Alhaji Kallah suka sanya masa ya nufi hanyar waje, tafe yake dif dif dif ya na uban nishi tsabar qiba masu tsaron lafiyar shi na take masa baya,Alhj Salihu ne ya kife kan shi a Saman table ɗin gaban shi, dan a qashin gaskiya ya fara son Suwaiba duk da wautar ta da gab'untar ta,Alhj Kalla na kula da shi ya gano abinda ke cikin zuciyar abokin nashi tun ba yau ba dama ya jima ya na jin tsoron faruwar hakan dan shi Alhaji Salihu zuciyar shi bata kai ta Alhaji Kalla bushewa ba wasu lokutan ya na tausayi ko kuma ya ji ya na son mutum, wanda hakan ya sha kawo masu cikas wajen gudanar da ayyukan su, a wannan karon ba zai bari abokin nashi ya rusa masu ɗaukakar da suka jima su na ginawa ba dole ne ya taimaka masa ya kawar masa da duk wani so da qaunar Suwaiba da ya fara yi. Taɓa abokin nashi ya yi, ya masa nuni da kofar fita daga babban hall ɗin alamar su tafi kenan, miqewa ya yi da kyar jikin shi a mace suka fice, tun kafin su bar wajen kuwa mutanen wajen ke ta 'yan gulmace gulmace , ko ina ba a raba mutane da gulma,bayan sun isa gidan Saudat ne, suka shiga inda suke tattauna matsala irin haka in ta taso musu suka zauna, Alhj Kalla ne ya fara magana, dan ya kula in bai yi ba Alhj Salihu ba zai ce uppan ba, " Salihu ni ban ga abin d'aga hankali a maganar nan ba fa, duk da ni kaina a yanzu haka na fara son yarinyar can,koba komai duk matan da muke huld'a da su yaran nan na kula suna da na su sirrin daban a jikin su, ga yarin ta ga kyau, amma kasan bijirewa Oga Zaks na nufin qarewar arziqin mu, niko dana talauce gwanda na aikata abinda yake so, mu kaisu kawai,a yanke abinda za a yanke a jikin  nasu kawai, naga dai ana ciwon cancer ma a yankewa wasu nan ɗin kuma su ci gaba da rayuwa" "Ba zaka gane ba abokina, in ba wajen a ina mutum zai na hutawa? Kai ni fa bari kaji ba zan iya bane kawai, duk sokoncin yarinyar nan ina son ta, dan in tare kake da ita ta b'aro maka wani haukan sai ka ji kamar ka yi ta zane shegiya, amma kuma yarinyar tayi ta na da wani sirri na daban wanda ba kowacce mace ake samu da shi ba, banjin zan iya rabuwa da ita, yanzu ni dai shawarata shine su je gida kawai su ga gida na kwana ɗaya ko biyu in suka dawo munga ya za ayi, tinda kaga bai kamata har in ma mutuwa za su yi tsohon su bai gan su ba, dan ta uwar su ita ta jiyo banda case da ita ni" "Haka ne kayi gaskiya, to bari na faɗa masu kawai gobe su shirya zasu gida ko ya kace, dan da kaina ma zan haɗa mata kayan ta dan ta tabbatar da gaske nake tunda a ganin ta ni ne bana so su je ganin gida dama,ahmmmm ai sai ka tashi ka tafi ko?  dan kuwa ina so na yi sallama da iyali na, bamu san ya abubuwam zasu kaya ba" Dariya suka yi suka tafa,Alhaji Salihu ya ce, "Shegen sama nima ba ri na hanzarta na koma gida na taya ta haɗa kaya kuma mu yi sallama" Yanda suka tsara hakan suka gudanar, washe gari da asussuba su suwaiba suka ɗauki hanyar kano kowa da drivern ta dan wadata, ga wata mota nan shaqe da kayan arziqi na bin su a baya, haka suka isa garin Kano direct gidan su Suwaiba suka isa, Goggo Sarai duk ta baza wa dangi da 'yan unguwa zuwan su Suwaiba dan haka gidan a cike yake da jama'a kowa ka gani ya na cikin doki da murnar ganin dawowar 'YAN ABUJAn,sanda motocin suka parker a qofar gidan nasu basu fita ba sai da drivers suka fita da sauri suka buɗe musu motar sannan kowaccen su ta fito hannun ta riqe da manyan wayoyi da jakunkuna masu tsada da kyau,a hankali suke takawa tare da d'aga wa mutane hannu suna sakin murmushi kamar wasu matan gwamnoni,da Salma suka fara yin tozali kanta a bisa cinyar Mama Bilki tana mata kitso a kwance kamar wata jaririyar ta, salati Suwaiba ta yi ta kalli Saudat sannan ta ce, " Sudat me nake gani haka ni Suwaiba? Yaushe gidan ya koma haka? Da jin muryar ta Salma ta miqe da gudun ta ta yi kansu tana ihun murna ta na fad'in, " Goggo ! Goggo fito ga su Adda sun zo, Mama kinga su Adda sun zo, ina Baba? Baba fito ka ga ikon Allah su Addana ne a gidan yau" Shanye mamakin ganin yanayin Salma suka yi aka ci gaba da murna ana gaisawa da jama'a amma cikin ransu akwai tambayoyi masu tarin yawa dangane da rayuwar qanwar tasu Allah Allah suke mutane su tafi su zauna su ji me ke faruwa, shi yasa da sun gaisa da mutum sai su bashi dubu d'aya ko biyu, su kuma mutane ana basu kuɗi sai su yi godiya su bar gidan dama su suka kawo su,dakin su da Goggo Sarai ta sake gyara masu suka shige su na shiga ciki suka tadda  Goggo Sarai da ta danne murnar ganin yaran nata bata bazama ta taro su ba, ta yi hakan ne dan ta nuna wa mutane ita fa mai aji ce uwar matan manya,su na shiga kuwa Goggo ta fashe da kukan daɗi, bakin ta kuwa ya qi rufuwa saboda murna, su kan su su Suwaiba sai da suka zubar da kwallar farin cikin ganin mahaifan nasu basu san sun yi kewar su sosai ba sai yanzu da suka gan su, nan fa aka hau gaishe gaishe ana tambayar juna bayan rabuwa,wata shewa Goggo Sarai ta sanya ta daki cinya sannan ta ce, " Ayyyuririri ! kai yau ni saratu na ji dad'i na,shiyasa nake son Allah dan kuwa akwai shi da biyan buqatar bawa Jama'a ku dubi yarana , san kowa baqin cikin marashi, ga kuɗi ga kyau, ga hutu, na ji daɗin zuwan ku yarannan, ya mazajen naku? Su na can an baro su a Abuja , waiwaiwaiiii Allah sarki garin daɗi na nesa" Cikin murmushi da d'agun kai irin na mutanen da aka gama yi wa kirari suke jin kan su ya kumbura suke amsawa a cikin taqama, "Suna lafiya suna gaida ku, ga abubuwan kayan abinci nan da kud'ad'e da suka aiko a baku ke da Baba" Cikin murna kamar zata kifa ta dafe kudin dika har na Baban nasu, ta jibge su a gefen ta ta na ci gaba da washe baki ta na surutu,shi kuwa Baba ko wajen kud'in bai kalla ba, ya yi masu godiya, Mama Bilki ce ta shigo ɗauke da ruwan Pure water a plate ta doro masu sanyi ta kawo masu, ajewa ta yi ta zauna dan a  gaisa,Goggo Sarai ce ta haɗe fuska ta ce, "Wai ni shin gaisuwar nan dole ce ne, a bar yara su huta dan Allah, na ga dai duk baqin sun tafi dan a bar su su huta to a bar su su huta mana haba,kuma in banda abin talaka ma duba fa wa zai sha wannan ruwan, dan Allah ki je an yafe Allah ya bada lada" Goggo Sarai na gama maganar ta suka haɗa baki da yaran cikin shewa suka furta, " Hahaiiiiii Casssss sai Goggo, ashe ana nan ana ci gaba da gashi, Allah dai ya sassaka Goggon mu" Dariya ta yi cikin isa tana wani d'aga hanci ita a dole uwar masu kuɗi ,Mama Bilki ce ta tashi ta ja hannun Ammar da ke son shigowa suka yi gaba, Salma ma tashi ta yi rai b'ace ta fita,cike da mamaki suka bi su da kallo dikan su, Saudat ta ce, "Wai ni Goggo me ke faruwa ne me nake gani haka tun da muka zo?  Salma da waccan matar a tare? Me kenan?" Baba ne ya basu labarin duk abinda ya faru da salma nan da nan suka hau jin tsananin tausayin 'yar uwar su akan wahalar da ta sha, sannan ya qara masu da labari akan irin hukuncin da ta yanke na zama wajen Mama Balki, anan ne ransu ya baci sosai, suka k'wala mata kira, bayan ta shigo ne suka balbale ta da faɗa kowa da abinda yake faɗa, sai da ta tabbatar sun gama ta miqe ta yi waje ba ta tanka ma kowa ba a cikin su, da bala'i Suwaiba zata bita ta dake ta amma Goggo ta hana ta ta ce, "Ai ni yanzu na cire ta a Yarana nima, taje can ta qarata, ina da ku kun ishen rayuwar zaman duniya har ma da qiyama, kuma yanda ku ka yi jan nan da alamar kuma kuna ɗauke da ciki, dan haka jika ne nake matuqar kwad'ayi yanzu a duniya fiye da komai, ta je ta yi ta fama, ita ta sani naku sun ishen zaman duniya dai ba na qiyama ba" kallon kallo suka hau yi wa junan su,nan take Saudat ta faɗa jikin Goggo tana kuka, Suwaiba ma idon ta ya cika da kwalla sosai,cikin kuka Saudat ta ce, "Adda Suwaiba akwai abinda nake so dama in faɗa maki tun da jimawa amma na qi sanar da ke dan nasan halin ki tona mana asiri kawai za ki yi ki jawo su kashe mu a banza" Cikin zaro ido Goggo tace wa Saudat, " Suwa..... suwaye zasu kashen ku?" Kuka saudat ta ci gaba da yi ta ce, "Mazajen mu Goggo yan qungiyar shan jini ne,na gano hakan da jimawa, yanzu haka bamu da mahaifa da ni da Adda Suwaiba kuma ina zargin su ne sanadi" Wani irin mari ta ji guda biyu sun sauka a fuskar ta suna neman dasa mata toshewar majiya,da ido ta ke bin inda marukan suka fito ɗaya daga Hajiya suwaiba ɗaya daga hannun Hajiya Goggo Sarai ne (uffararan ashe basu sauke faralin ba),cikin matsanancin Fushi Goggo ta fara magana, "Dan ubanki sharri kuma zaki yi masu, mutanen da suke kasuwanci a qasashe ko ta ina, arziqi ya wadata ya bunqasa shine zaki ce haka, so kike kema ki dawo ki zauna ki jamin asara, na haifi yarinya zankad'ed'iya kamar ki da zan samu dukiya amma sai ki dankwafe kan ki ki hana arziqi rab'ar ki? To ki bude kunnen ki da kyau ki ji, ko ya ake ciki gobe zaku koma ai an ga juna ba zan lamunci asara ba shashasha kawai, ina ganin ki kamar mai hankali ashe ba ki da hankali" Cikin kuka ta rarrafa wajen Baban su ta ce, " Baba ka yarda da ni,na rantse gaskiya na faɗa, ba sharri nake yi musu ba 'yan shan jini ne, na ji da kunne na Alhaji na magana akan qungiyar su ta asiri" "Na yarda dake 'ya ta, dan baki taba fad'an hakan ba kuma da dikkan alamu akwai gaskiya a zancen ki, wannan kud'in nasu yayi yawa" "Baba ya zaka yarda da wannan maqaryaciyar ? Qarya ne fa kawai dan sun taɓa dukan mu sau biyu, shine fa ta qullaci abun take son ta gudu, to in ke ba zaki koma ba ni zan koma d'akina, ina son miji na ya na so na da kyar ma ya hakura ya bari na zo saboda baya so ina yin nesa da shi, dan haka ke ki zauna duk abinda na tsakuro na sammaki tunda haka ki ka zab'awa rayuwar ki ta qare a wahale" Cikin washe baki da jin Suwaiba ta share mata hawayen baqin cikin da Saudat ke so ta saka mata Goggo Sarai ta ce, "Yauwa 'yar albarka, ai nasan in kowa zai juya min baya ke kin haifu cikin Saratu ba za ki juya min baya ba" Duk yanda Baba ya so ya nusar da suwaiba da goggo kin ganewa suka yi dan haka haka aka tashi  kowa zuciya ba daɗi, Saudat ta kafe bazata koma ba, inda Suwaiba tace ita zata koma, Salma da Mama Bilki kuma suna jiyo duk abinda ke faruwa,hankalin Salma ya tashi amma tasan bata da abinda za ta ce su saurare ta a wannan lamarin,Mama Bilkince ta shawarce ta akan ta musu addu'a kawai, hakan aka yi kuwa ta kwantar da hankalin ta suka hau yankan farce bayan sun gama kitson. " Babyna wai ni yaushe zaki je gaida su Mama ne ga cikin nan ya yi girma kar a Kai minzalin da  baza ki iya fita unguwa ba kuma, tinda ita tana abunnan na mutanen da har yanzu taqi zuwa ta ga dakin ki," "Hmmmm kaidai bari abunnan na min zafi ace wai uwa ba zata je taga d'akin 'yar ta ba? Ba komai zan je ko gobe ne na ji dazu Nafee tace su Adda sun zo, kuma Salma ta dad'e a gida ma zan so zuwa duk mu gaisa da su," " Eh haka ne, randa na je gaida su ma na ganta ai, Allah ya kaimu goben sai na samu na kai ki da kai na ko?..........❤ [21/07, 7:46 pm] asiyahabibu93: 💅🏼     'YAN ABUJA   💅🏼   WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Sis Ramlat Baba larens Aunty Ummu sokoto Cute one *Waɗannan sunayen na sama na kasa goge su a cikin sunaye kusan guda goma da na yi wa dedicating page ɗin nan, da can da ana yawan yi wa mutane dedication sai mutum ya jera Sunan mutane da yawa wanda a zaton shi masoyan shi ne na gaskiya na haqiqa😂 ashe inaaa kowa da abinda ya kawo shi rayuwar ka,dama bahaushe yace ba a San maci tuwo ba sai miya ta qare, tabbas rayuwa cike take da qalubale kala kala, wanda ya baka dariya watarana zai saka kuka, wanda ya sa ka kuka watarana zai saka dariya,Ya Allah ka ci gaba da yi mana zaɓi na alkhairi ka haɗa mu da mutanen kirki ka nesanta mu da na banza, Allah ka sa mu zamanto mutanen kirki a wajen mutane ka tsare mu cin amanar wanda suka yarda damu Ameeen...* Page 19: Yau Salma tun asuba ta tashi da matsanancin ciwon kai da mara, in da Talle hankalin shi ya tashi ba kadan ba,tsoron shi bai wuce a ce yau 'Yar mutane ta mutu a hannun shi ba,shi dai tun farko dama ba wani son ta yake ba kyan ta da dirin tane ya rud'e shi,ko ba komai ya more ta yanda ya kamata,yanzu haka ya k'yalla ido ya hango wata shi yasa ya fara tara 'yan kud'ad'en da zai yaudaro ta, ba zai yu kuwa ya kashe kud'in sa a jinyar Salma ba, tun da dama wa'adi ya debar mata lokaci na cika zai auna ta tai gaba,zaune yake a kujerar shi ta aiki a farfajiyar gidan ya lula duniyar tunani a hankali ya fara magana ya na fad'in, "Anya zan iya jiran lokacin da na ɗebar mata ya cika kuwa ? kawai bari Alhj ya fita nan dai da Kano na auna ta gida, nace sai nazo ba shikenan ba ta zauna ta jira ni idan auren da nake nema be samu ba na d'akko ta kan nan ta ji sauqi, idan kuma auren ya yuwu na aika mata takardar ta kowa ya huta, ko kuma yanzu in na shiga na sallame ta a rabu gaba ɗaya," Ya na nan zaune ya na magana da kan shi ya ji Alhjn na kiran shi, da gudu ya fita, ya je ya durqusa ya gaida Alhaji sannan ya ce "Gani Alhaji," Alhaji ya ce, " To ga wannan a kula da gida, ni zan tafi wannan karon zan ɗan kwana biyu gaskiya a gida ban dawo ba, dan kasan na faɗa maka amarya ta ta samu qaruwar d'iya mace, so ina ganin zan ɗan jima kaɗan fiye da yanda aka saba, a kula da gida, kar na dawo na ji shigen labaran dana saba ji, ba zamu kwashe da kyau ba Talle" Gyada kai yake kamar qadangare alamun ya ji gargad'in uban gidan nashi,can qasan zuciyar shi kuwa Allah Allah kawai yake yi ya tafi shi kuma ya ɗauki mota ya kai Salma tasha ya dawo, kar ta mutu a hannun shi. " Allah ya kiyaye Oga ba zaka taɓa samun wani labari mara daɗi ba" D'aga kafad'a Alhj ya yi sannan ya ce, "Ruwan ka Talle kowa ya yi da kyau zai ga da kyau ai" Alhaji na fita Talle ya rufe gate ya koma d'akin da gudu,samu ya yi Salma ta dan samu dama ba kamar yanda ya barta ba, ta fito daga toilet da alama amai ta yi,cikin hanzari da d'aure fuska ya ce mata, " Ke haɗa kayan ki yau zaki je ganin gida" Cikin kad'uwa tare da murna, a gefe d'aya kuma kunya da tashin hankalin da wanne ido zata kalli su Juwairah da Mama Bilki ne suka mamaye ta, Uwa uba kuma Goggon ta, tace mata waye mijin ta idan ta je gida driver ne ko mai gadi? Zubewa ta yi a katifa cike da wani irin had'ad'd'un yanayi mabanbanta da suka cud'e mata, a hankali ta furta, " Nikam Sweet na fasa ba yanzu ba ka bari na murmure, sannan mu dan samu kuɗi, ko a haka zan tafi ganin gida, ai sai a zage ka a ce baka kula da ni"  "Ah ah a zage ki dai yo ni meye nawa a ciki? in zaki miqe ki miqe ki kwashi dan abinda zaki iya dan kin ga ni daga yanzu ma barin gidanan nan zan ko kin dawo ba ganina zaki yi ba nima na bar aiki anan daga yau, dan na kwashi rabona wajen Alhj, qauye zan koma, na ji da iyalina, kuma dai ba sanin Sunan qauyen mu ki kai ba, ba kuma ki san hanyar bama, dan haka in kin tafi ki manta da wani mai suna Talle, ko in ce Alhj Mansur da kika taba aura, ki manta kin sanni, sai dai in kin tashi tuna ni ki min godiya a ranki na sama maki hanyar zuwa ABUJA, harda qauyen ta ma, dan haka ga wannan" Takarda da kuɗi dubu goma cass ya miqa mata, a zaunen ta daskare, bata gaskata me yake faɗa mata ba sai da ta ji tsawar shi yana maimaita mata da kuma bata umarnin ta tashi su gudu dan kuwa tana b'ata masa lokaci zai fita ya gudu nashi waje shima, wanda qarya Talle yake mata ba inda zai gudu kawai sanin bata ko san sunan inda suke ba shi ya sa shi fad'in haka, baya son ta yi tinanin dawowa rayuwar shi kwata kwata. Miqewa ta yi da taimakon shi saboda wani irin jiri da tashin hankali da ta ji ya mamaye jin ta da ganin ta,nan take ciwon kan ta ya dawo sabo dal,da kyar ta samu natsuwa ta ɗan shige ta ta fara haɗa kayan ta a haka ta gama komai, ta kasa tambayar shi dalilin yi mata wannan wulaqancin, ta kasa cewa uffan saboda kalamai sun qauracewa bakin ta. Duddubawa ya yi duk abinda bata ɗauka ba ya ɗaukar mata yana bata a hannun ta ita kuma tana riqewa, idon ta a tsaye suke kuma hawaye na zuba, haka ya gama ya sata gaba ya kulle qofar ya dauki wata jaka dan tsabar ya raina mata wayo ta zaci tare zasu bar gidan, mota suka ɗauka ya saka ta suka bar gidan kifa kanya ta yi a cinyar ta ta yi ta kuka. Su na isa ta tasha ya yi parking a bakin tashar ya sauke ta ya yi gaba ko waiwaye bai yi ba balle ya ga a halin da ya bar ta,a haka ta samu ta isa cikin tashar bata ko ganin gaban ta da kyau tsabar hawayen da ke zuba a idanun ta, in da ta ji ana kiran Kano ! Kano ! nan ta isa ta shiga wata mota sauran mutum biyu ta cika ma,tana shiga wata arniya ta shiga itama, sunayen su aka basu su rubuta, amma ita ta yi shiru ta kasa rubutawa, kuɗi suka buqata ta miqa masu dika kud'in hannun ta ba tare da tace komai ba,ko da ya qirgi iya kud'in shi sai ya miqa mata sauran ta nade a hannun ta,ta jingina kan ta da jikin gilashin motar ta dinga raira kuka mai sauti ba tare da ta damu da kallo da qusqus ɗin da mutane ke ta yi akan ta ba, a haka har mota ta cika. Har suka isa kano Salma bata daina zubda hawaye ba, adaidaita sahu ta ɗauka ya kaita har gida ta miqa masa kuɗi ta yi gaba shi kuma ya na neman canjin da zai bata,har ta yi gaba ya bita ya miqa mata a hannun ta, ya tafi yana fad'in, " Allah ya kyauta" Shiga gidan su ta yi babu ko sallama, Goggo Sarai tana zaune a kujerar da ke kallon duk wani mai shiga da fita a gidan tana kad'a qafa akan kujera, hango Salma a wani mawuyacin hali da ta yi sai da Goggon ta kusa tintsirawa qasa tsabar tashin hankali,da gudun ta zani na warwarewa tana gyarawa ta taro ta ta na fad'in, " Lafiya Salma,Me nake gani haka? Ina mijin naki? Daga wace qasar kuka dawo haka? Fashi aka yi muku a hanyar ku ta shigowa Nigeria? " Haka Goggo Sarai ta dinga jerawa Salma tambayoyin nan amma bata samu amsa ko ɗaya ba, d'aki ta ja ta suka shiga sai waige waige take da fatan babu wanda ya gan su, har Mama Bilki zata fita dan jin Goggo Sarai ta kira Sunan Salma amma Baba ya riqe ta, ya ce, "Gimbiya bassu ni na je,yanzu da kin je sai abun ya koma tashin hankali kuma da. cewa za ta yi gulmace ta kai ki ba komai ba" " To Baban su Allah ya jiyar da mu alkairi" " Ameen" Fita ya yi ya isa dakin, zaune Salma take a gefen gado idon ta na kallon waje ɗaya kawai ko qiftawa bata yi, kukan kuma ya tsaya cak kamar wadda aka cire wa batiri, tambayar duniya Goggo ta yi mata amma taqi magana, Goggo banda kuka ba abinda take yi a haka Baba ya shiga ya tadda su, cikin damuwa da jimanta lamarin Baba ya ce, "Subhanallahi, me ke faruwa ne haka sarauta ki ka tasa yarinya a gaba kina ta kuka, Ke Salma ki yi mana bayani me akayi miki, ina mijin naki kuma? Daga ina kika fito a haka?" Da jin murya da kalaman Baba Baballiya sai Salma ta saki wani kuka mai cin rai, nan take ta dakko takardar da Talle ya bata ta miqawa Abban nata, dan yanzu haushin Goggo take ji sosai, ta dalilin ta ta shiga wannan halin quncin da qananan shekarun ta tinda ai duk ita ce bata basu tarbiyya mai kyau ba, uban su kuma na son ya basu ta musu hudubar shed'an ta hana su saurara, wannan wace irin rayuwa ce haka, Salati suka ji Baba ya sake ya aje takardar ya zauna tare da dafe kan shi,cikin kuka Goggo Sarai ta ce, " Malam me ya faru? Ku sanar dani ko hankalina ya kwanta dan Allah" Cikin dakiya Baba ya kafe Goggo Sarai da idanun sa da suka yi jajawur saboda b'acin rai sannan ya ce mata, "Mijin nata ne na can garin ABUJAN YA SAKE TA SAKI UKU" Ɗora hannu a ka Goggo Sarai ta yi ta kurma uban ihu kamar wata qaura,sannan ta miqe a harzuqe ta hau jibgar Salma tana fad'in, " Shegiyar yarinya me kika masa ya sakon ke, yanzu gashi kin yi mana asara, mutumin da ya fitar dake qasar waje Kuke shaqatawar ku cikin jin daɗin rayuwa, ki zalunce ni ki zalunci kan ki Salma ki sa ya sako ki, da dukkan alamu ma ciki ne da ke, amma shine tsabar baqin ciki ba zaki bar ɗan ki ya taso cikin jin daɗi ba sai da ki ka yi abinda ya maki sakin kare dangi" kalmar ciki ne da ita da Goggo ta yi ba qaramin razana Salma ya yi ba,nan take ta sake tabbatar da Talle ya yi mata illa ba kaɗan ba,dan ko giyar wake ta sha a yanda ta san waye Talle ba ma zata yi gigin ta haihu ta kai dan ta qauyen su ba wanda shi yake ganin bata san Sunan qauyen ba amma a iya watannin da ta yi har qauyukan kusa da su ta san Sunan su, ai kamar yanda yace sun rabu ta manta da shi hakan za ta yi,ture hannun Goggo ta yi a jikin ta ta je gaban Baban ta ta durqusa ta ce, " Babana ka yafe min, ka ji tausayi na ba dan halayyata mummuna da na yi a baya ba, ka duba girman Allah da soyayyar ɗa da iyayen shi ka yafe min duk abinda na aikata mara kyau a baya, ka tausaya ma abinda ke ciki na in ya tabbata ina dauke da cikin kenan, kar ka yi fushi da mu, ka bamu wajen zama a gidannan karka kori abinda zan samu, zan yi wahala ta hanyar halal na kula da abinda Allah zai bani, amma kar ka ce za a sake d'aga zancen uban d'an nan na gama da shafin shi, sabon shafi nake son budewa Baba" Kuka ne ya ci qarfin ta sosai, wanda ya sanya Babansu hawayen tausayawa diyar tashi, yarinya fara mai kyau duk 'ya'yan shi Juwairah ce kawai ta fisu komai, amma Salma na bayan ta, dubi yanda ta koma ta jeme ta d'ashe kamar mara isashhen jini a jikin ta, har yau Salma bata rufe shekara ashirin ba, d'aga ta ya yi tsaye ya rungume ta,aiko kamar jira take yi,tunda abubuwa marasa daɗi sukai ta faruwa da ita take neman kafad'ar da zata jingina kanta ta koka baƙin cikin ta amma ta rasa, sai yanzu ta samu strong and loving arms ɗin da suka yi huging ɗin ta,hakan ne ya bata k'warin guiwar fitar da duk wani b'acin ran ta, haka Baba ya bar ta a kafad'ar shi ta yi kukan ta ma'ishi,da kan ta ta hakura ta samu waje ta zauna a gefen shi ta na sauke ajiyar zuciya. Cikin murya mai rauni Baba ya ce yace, "Ina zuwa Salma bari na dawo" Mama Bilki ya kira bayan ya faɗa mata duk abinda ya faru, a tare suka shiga d'akin Goggo Sarai wadda har a wannan lokacin kuka take tare da tambayar Salma me ta yi wa Alhaji Mansur ya sake ta,Salma kuwa ko qala ta qi ce mata,Mama Balki na qarasa shiga sai ta isa wajen Salma ta zauna tare da dafa kafad'ar ta, Salma na ganin Mama Balki sai ta rungume da sauri , tana neman gafarar ta, Mama Bilki kuwa nan take ta ce, "Salma na yafe maki Allah ya yafe mana laifukan mu, faɗa mana me ya faru" Mama Balki na gama rufe baki Goggo Sarai ta isa gaban Salma a guje ta damqe mata baki ta na zaro ido ta ce, "Yi shirun ki wannan sirrin mu ne kar ki yi magana a gaban maqiya" Wani irin kallo dukkan su suka watsa mata, Salma kuwa kwace kanta ta yi a hannun Goggo Sarai ta fara magana,nan take ta sanar da su komai da ya faru tin daga tafiyar ta har dawowar ta a yau din, kuka sosai Baba ke yi duk jarumtar shi sai da ya tausaya wa 'yar shi har ya zubar mata da hawayen tausayawa,Mama Bilki ma ta yi matuqar tausayawa Salma,ita kanta Goggo Sarai abun ya dake ta kwarai,ga tausayin Salma ga kuma kunyar mutanen da ke zaune a gaban ta, ita kanta kuka take kamar an mata duka, Salma ce ta juya ta kalle ta ta na murmushin takaici ta ce, " Yanzu Goggo a wanne hali su Adda Suwaiba suke, suna Kiran ki a waya ? kin je kin ga muhallin su ko kuma baki sani ba, kawai suna aiko maki da kuɗi ne kina ajewa ki na kashe na kashewa? Goggo baki san ina ne Abuja ba, amma tin tasowar mu kika kimsa mana son ta, yanda kika saka mana son abun duniya da hutu, da haka kika saka mana son ku kaɗai da yi muku biyayya da duk inda mu ka je aure ko min talauci da za mu zauna mu samawa kammu farin ciki,amma baki yi wannnan ba, Bama a maganar ki yi qoqarin dasa mana tsoron Allah da son Allah da yi wa Annabin rahama biyayya akan saqon da ya zo mana da shi na gaskiya, Goggo kin ci amanar kiwon da Allah ya baki, Baba na iyakar qoqarin shi akan mu kina rusawa, ni yanzu ba zan zauna anan d'akin ba, Mama Bilki ina riqon arziqin komawa wajen ki na zauna, dan tabbas nima ina zargin ciki gareni a yanzu duba da rashin ganin al'ada ta da ban yi ba,ga yawan ciwon kai da mara sai zazzaɓi da nake yawan yi, Mama Balki dan Allah ki koyan dukkan irin tarbiyyar da ya kamata nima inna haifi nawa na basu,ba irin wannan tarbiyyar mara kyau da ma'ana ba" Goggo Sarai ce ta kwad'e mata baki da qarfi har sai da jini ya fita daga bakin Salma sannan ta ce, "Dan uban ki to da haka ki ce ita ce ta haife ki ma mana? Ku tashi ku fice man a d'aki gaba ɗayan ku bana buqatar kowa, yaran da suka san daraja ta da qimata za su zo su kula dani, dama ke tinda aka yi auren ki me ki ka tsinana min? A wajen neman mijin me yasa baki tsaya kin nemi kamar na yan uwan naki ba ? Banda wahala me ki ka samo wa kan ki? Sai ku tattara ku je can ku qarata,jikoki kuma ko awajen yarannan biyu ba zan rasa su ba, dan ba zaman banza na aika su yi ba a gidan Mazan nasu" Ganin cewar ita fa Goggo Sarai bama ta yi nadama ba sai suka miqe za su fita daga d'akin, Mama na yi mata addu'ar shiriya a ranta, dakin ta ta kai Salma sannan ta fita tsakar gida ta dakkowa Salman abinci ta bata, kamar mayya haka ta hau shi da ci kuwa tana hawaye, tana gama ci ta sha ruwa nan take kuwa bacci mai daɗi ya kawo mata ziyara. Mama Bilki ce ta gyara mata kwanciya tana tsananin tausayin ta, Abba sai godiya yake mata da sanya albarka. ***************************** Bangaren su suwaiba 'yan Abuja kuwa suna can Abuja su na cin duniyar su da tsinke hanakali kwance, su kuwa su Alhaji Kalla na can na shirya wani babban lamari akan su ba tare da sun sani ba.........[21/07, 7:46 pm] asiyahabibu93: 💅🏼   ' YAN ABUJA.  💅🏼       WRITTEN BY HAERMEEBRAERH *SANARWA* *Makaranta ku yi min afuwa shekaran jiya na tura page 20 amma suka maqale basu tafi ba shi yasa kuka ji shiru na san na tura na zaci matsalar network ne za su iso daga baya,shiru basu zo ba kuma wayata kwana biyu ta na bani ciwon kai shi yasa,amma a yi hakuri za a ci gaba daga inda aka tsaya...masu nema daga farko ku yi haƙuri a gama editing a mayar document..kar ku manta wannan ba sabon rubutu bane tsoho ne na yi shi tun 2017 editing nake yi za a gama da wuri da yardar Allah...na gode* Page 22: Zaune suke gaba ɗaya 'yammatan Markan a d'akin ta ta sa su a gaba ta zabga uban tagumi hankalin ta a matuqar tashe,Huwaila na kwance da gwangwanin madara da suke yin alalen gwangwani ta zuba masa qasa sai zuba yawu take yi a ciki, wani wawan tsaki Marka ta zabga ta kauda kan ta ta na kallon Jummala da ke yatsuna fuska,kan ta kai ga tambayar bahasin yatsinar suka ga Jummala ta fita da gudu tsakar gida ta na kelaya amai, kukan da Marka ke ta riqewa ne ya kufce mata, Jummala ce ta dawo riqe da cikin ta ta zube a qasan simintin d'akin daidai inda ledar d'akin ta yage ta na bin sanyin wajen,a haukace Marka ta yi kan su da duka ta na fad'in "Ina zaune da qananan 'yan iska ashe ni Marka ban sani ba,da uban wa ku ke lalata har dika ku biyu ace wai ciki ne da ku, yau in mahaifin ku ya ji wannan mugun labarin ni Marka ya zanyi da raina, wannan abun kunyar ina zan kai shi a garin nan?" Kuka take tana share kwalla, shirun da suka yi mata ne ya qara b'ata mata rai matuqa, watakan sun ma mai da ta yar iska kenan ko,dukan ne da alama bai shiga jikin su ba, a haukace ta fita madafin su ta dakko zankad'ed'en maburgin  miyar ta ta yi d'akin ta rufe qofa ta rufe su da mahaukacin duka, ita dai Huwaila ba k'warin guduwa sai baki, nan take ta ko fara magana cikin kuka ta ce, " Allah marka ki kyale mu ai iskanci ba kan mu farau ba, kuma naga iyayen yaran na gida ne ba bare ba su bangis ne fa, Baban su na gidannan shima yana zuwa lalubar ki duk daren duniya baku ko gajiya ko d'aga wa juna qafa ko ji kike bamu sani ba? Na san komai duk mun san ki na da hannu a qullawa Salame sharri ke da Baban Bangis dan asirin ku ya rufu  ku ci gaba da watsewa idan Baba baya gari,dan haka mu ki daina dukan mu kema ai duk ɗaya muke da ke gwanda ma mu bamu da aure, kuma shikenan dan naki bai fito ba namu ya fito ba za ki kashe mu a banza ba, kika qara dukan mu sai na faɗa ma Baban mu in ya dawo kuna kub'ewa keda yayan shi" Da sauri Marka ta sa labccen hannun ta ta damqewa Huwaila da ke tona masu asiri baki,ta na ta zaro ido da waige waige tare da fatan Allah ya sa ba wanda ya ji wannan mummunan sirrin da suke b'oyewa, ashe dama yaran kallon su kawai suke yi sun san komai? Ji suka yi an banko qofar da mugun qarfi, wani tsoro ne ya kama ta ba ta san sanda wata muguwar tusa ta kwace mata ba, zama ta yi kusa da yaran ta na jiran taga wanda ya ke son shigowa d'akin kamar aradu,yaran kuwa sai toshe hanci suke tsabar azabar warin tusar da ta sakar musu. Talle ne ya bayyana a gaban su idon shi ya kada ya yi jawur akan wanda yake da shi, idan aka ce Talle zai iya kisa a wannan yanayin ba mai yin musu,nan take ya damqo wuyan Marka ya mata mummunar shaqa, ya ja ta suka fita har tsakar gida yaran su na biye da su cike da tsoro, qananan sai kuka suke yi,'Yan matasan kamar su Haule kuwa sai bin su suke suna mamakin abinda ke faruwa yau a gidan nasu , har qofar sashen yayan nashi ya je ya wurga Marka a jikin shi,shi kuma a daidai wannan lokacin ya fito da tabarma a hannun shi na dama  ɗaya hannun nashi na hagu riqe da buta za shi zaman qofar gida na safe da suke yi, janye jikin shi ya yi yana wani ja baya tare da fad'in , " Subhanallah,meye haka zaka rab'an matar ka a jikina, bayan kasan ba muharrama ta bace ba" Wani gigitaccen mari Talle ya bankawa yayan nashi, buɗe baki ya yi zai yi magana Talle ya qara make shi Saida ya tintsira ya faɗi qasa tabarmar hannun shi da buta tini sun yi nasu waje,shiru ya yi ya damqe bakin sa saboda tsoron kada wata kalma ta fito a sake banka masa mari ya tabbata asirin su ne ya tonu dan shine kaɗai zai bawa Talle yi masa wannan rashin mutuncin,nan ya samu waje ya yi zaman 'yan bori a wajen ya hau kuka, Marka kuka Yaya kuka saboda nadama da kunyar abinda suka dinga aikatawa, wani haushi ne ya kama Talle kukan uban me suke yi kuma yanzu, kuka ai shi ya kama, miqewa ya yi a haukace ya bisu da duka, duk wanda ya samu ya maka har yayan nashi,wata iriyar tsanar su ke huda zuciyar shi, sai da ya yi masu lilis sannan ya fice ya bar gidan,jiki duk tsami baki kamar an liqa masu super glue haka suka kad'e jiki kowa ya yi d'aki dan kuwa yanda Talle ya jibge su ba tare da ya tona asirin abinda suka aikata masa ba suma haka za su yi gum da bakin su, to in ba su yi shiru baaa me za su ce wa yaran da ke ta koke koke saboda ganin yanda Talle ke jibgar su? Hannun Yayan Talle ne ya kumbura ta wajen tsintsiyar hannun haka ya karasa shigewa d'akin shi ya na numfarfashin wahala dan ya san tabbas sai ya ga mai dori a ja masa hannun. ****************************** Allurar bacci Alhaji Salihu ya yi wa Suwaiba da ya dawo ya tarar ta fara bacci,sai kawai ya tsaya akan ta yana qarewa qirjin ta kallo,duk kyan wajen nan yanzu haka za a je a yanke su ba ko d'igon imani? Alfarma ɗaya Oga zakas ya yarda zai yi masa, alfarmar kuwa itace tinda yana son matar shi to a yanke mata irin yankan da bazata mutu ba wajen yin shi, in an gama gudanar da tsafin za a yi mata operation yanda daga baya zata ji sauqi a hankali su ci gaba da rayuwar su, hawayen tausayin ta ne ya zubo masa, wanda hakan sabon abu ne a wajen Alhaji Salihu,bai taɓa zuwa gabatar da wani aiki ya ji tausayin da ya sanya shi zubar hawaye ba,hawa gadon ya yi ya rungumo ta ya ɗora kan shi a qirjin ta,hawaye ya dinga zubarwa tare da ɗora hannun shi a Saman qirjin ta cike da jimanta lamarin, ya jima a haka ya na zaune da kyar ya hakura ya dauke ta ya yi mota da ita,dajin da suke gudanar da tsafin su ya nufa ma'ana gidan Oga Zaks. Hankalin Alhj Kalla a tashe yake ganin rashin dawowar Saudat,ta ina ma zai fara tunkarar shugaban qungiya ya ce matar shi bata dawo ba bayan ya san an yi masu duk wata alfarma da za a iya yi masu? Ta ina zai fara samo wadda za su yi aikin akan ta a wannan qurarren lokacin? Anya ma zai iya kyale Saudat haka kuwa ba tare da ya lahanta rayuwar ta ba? Yanzu idan yace zai yi mata wani abu kuma asirin su ne zai tonu akan na da,dan tabbas tunda Saudat ta qi dawowa zargin shi ya tabbata ta san komai game da su kuma ba za ta kasa sanar da dangin ta ba. Ya na nan ya lula duniyar tunani da damuwa tare da neman yanda zai ya shawo kan matsalar da yake ciki  Alhj Salihu ya yi masa waya yace shifa ya ɗauki hanyar zuwa wajen Oga zaks amma ya ji shiru bai ji daga gare shi ba, "Ka na nufin Suwaiba ta dawo ita?" "Kwarai da gaske,me yasa ka tambaye ni bayan a gaban ka muka yi waya da ita ta ce min suna hanyar dawowa? Ko dai Saudat bata dawo bane?" "Ina fa ta dawo aboki na, ka je gani nan nima ina nan tafe yanzu nan" Ya na kashe wayar shi ya lalubo lambar 'Yar Gwal,kamar ba zata ɗauka ba sai da ta kusan katsewa ta d'aga ta na wani yauqi da yanga, Alhaji Ƙalla kuwa a ran shi ya yi murmushi ya ce, 'Duk wanda yaci ladan kuturu dole ne ya yi masa aski' Ita kuwa 'yar Gwal ta ɓangaren ta murna take dan ta san Alhajin akwai kashe kuɗi,a bai bata kuɗi masu yawa ba yana bata dubu ɗari biyar sai kuma abinda ya yi sama,cikin yauqi da yanga ta ce, "Hello Alhajina yau ka tuna da ni kenan" "Kwarai kuwa, kin san har yau madam bata dawo ba ina gayyatar ki wajen shaqatawa ta nan da rabin awa kar ki b'atan lokaci zan kirawo zinariya idan ki ka wuce lokacin da na qayyade maki" "Baka da matsala Alhajina" Da hanzari ta tashi ta hau shirye-shiryen fita, qawayen ta ne suka fara tambayar ta ina zuwa da safennan, bayan qa'idar su fitar dare ne? Sanar da su ta yi inda zata je ta yi,shewa suka ɗauka saboda sun san kuɗi sun zo kenan,wasu a cikin su kuma suka tab'e baki saboda baqin ciki suke yi kar ta samu kuɗi sama da yanda suke samu. Ko wanka bata tsaya yi ba ta shirya a gaggauce ta tafi, a qofar gidan ta same shi ya na jiran ta sai zuba qamshi yake ya haɗe cikin manyan kaya farare tasss sai jar  hular su ta zuwa gidan Oga Zaks, motar shi ya nufa ta mara masa baya ta na taku cike da yanga buɗe wa suka yi suka shiga, Alhaji Kalla ya kalli 'Yar Gwal ya na kashe ido da murya ya ce, "Ya kamata yau na kai ki wajen shaqatawa na musamman mu yi aqalla sati a can muna more rayuwar mu ba mai takura mana ko ya neme mu" Wani juyi ta yi da mazaunan ta a kan cinyar shi da tunda suka shiga motar ta haye sai ta sakko ta zauna a gefen shi amma rabin jikin ta na nashi,cike da kissa da  murmushi ta sumbace shi a kuncin shi, ba tare da sun sake magana ba Alhaji Kalla ya kunna mota suka bar gidan suka ɗauki hanyar dajin Oga Zaks. Sun jima suna tafiya kafin su isa, suna isa wajen taga wajen cike da motoci kala kala, ga maza da mata nan ko ta ina sanye da kaya iri ɗaya kamar ankon biki, wani abu ta ga su na yi a matsayin gaisuwa, sannan suka shige cikin qaton gidan gaba ɗayan su kamar dama su ake jira. Ko da suka shiga gidan sai ta ga sun zagaya bayan asalin ginin gidan inda wani qaton waje yake ga wani sassaqen icce nan kamar gunkin mace lullub'e da jan kyalle iya rabin jikin ta an zuba wani jan abu a qasan qafafun ta mai kama da jini,sai wuta da ke ci a cikin wasu tanderu na qasa kai da ka ga wajen ka san waje ne na tsafi ko bautar gunki, kafin su isa taga dukkan Alhazawan nan da suka zo da mata sun d'akko wani jan yadi a aljihunan su sun nuna masu suna kalla har ita sai suka zube a qasa, ita dama Oganniya Suwaiba ta dad'e a sume, ɗaukar su suka yi suka aje a wani gadaje da aka tanadar masu na musamman sai ƙwarya a kowanne gado wadda aka yi wa fenti da jar kala, Oga zaks ne da sauran mutanen wajen kowa ya cire kayan shi, haka suka tsaya zigidir babu kaya a jikin su,kowannen su hannun su ɗauke da wuqa kowa ya kama wadda ya kawo da niyyar aiwatar da ayyukan da ke gaban su, muryar su ta karad'e wajen da Kiran Sunan gunkin da suke yi wa tsafi. Alhj Salihu ne ya zo gaban Suwaiba da wuqar hannun sa ya na yi wa gunkin tsafin nasu kirari zuciyar shi a cunkushe da baƙin ciki, ji yake kamar ya bijire ma Dodon nasu,amma tinawa da azabar da zai shiga indai bai yi wannan abun ba,sai kawai ya saka ma nonon Suwaiba wuqa ya yanke shi ya tara jinin a kwaryar gaban shi jinin suwaiba na zuba a ƙwarya hawayen shi na zuba a Saman fuskar ta,haka sauran ma suka yanke wa matan da suka kawo nonon su dukkan su suka tari jinin a irin ƙwaryar da Alhaji Salihu ya yi amfani. Kuka Alhj Salihu ya fashe da shi wanda ya yi sanadiyyar  jan hankulan mutanen wajen, kowa daya kalle shi ya ga yanda yake kuka ga uban ciki a gaba ba tufafi a jikin shi, ga uban baqi da ya yi yana zufa yana maiqo, sai dariya ta kama shi haka suka dinga yi masa dariya, saida Oga Zaks ya daka masu tsawa suka nutsu, cikin haɗe fuska Oga Zaks ya ce, " Me yasa ka kuka kai Salihu?" Cikin kuka Alhaji Salihu ya bashi amsa da Cewar, "Ina son mata ta Oga a san ya za ai a mata aiki a shafe wajen kar ta mutu , ka taimaka min Oga kumin alfarmar nan oga ka yi alqawari ba zaka bari mata ta ta mutu ba Oga" Dariya sosai Oga Zaks ya yi sannan yace, "Kar ka damu Salihu zan cika maka alqawarin da na ɗauka, ni nace maka zamu san ya zamu yi matar ka ba zata mutu ba, ita waccan guduwa ta yi ne na ga an kawo wata a madadin ta ko ka na nufin ba zan gane ba ne Kalla?" Ya maida tambayar shi kan Kalla wanda ya zaci ba za a gane ya yi sauyi ba, " Eh Oga ba ta biyo 'yar uwar sun dawo tare ba da suka tafi ganin gida sai ita ta qi dawowa, a min afuwa Oga  sanin mahimmancin wannan rana a gare mu ne ya sa na gaggauta samo madadin ta" "Babu damuwa yanzu ɗauke ta kai salihu ka kai ta d'akin duba marasa lafiya a duba ta" Da gudu Alhaji Salihu ya ɗauke ta ya yi d'akin duba marasa lafiya na cikin gidan ya shimfide ta a gado Doctors biyu ne suka hau kula da ita shi kuma ya koma wajen tsafin nasu dan su ci gaba da gudanar da tsafin da suka zo domin shi, layi suka bi suka dinga zuba wannan jinin a qafar dodon tsafin nasu sai su d'aga kwaryar a gaban ta sai su shanye ,haka suka dinga bin layi layi suna yi har kowa ya gama,bayan sun kammala komai ne wasu qarti suka shigo filin wajen suka tattare matan suka kai su wani d'aki mai duhu. Bayan an gama yi wa suwaiba dinkin da ya dace da duk wata kulawa sai suka bashi matar shi ya sanya kayan shi ya kaita mota, Alhaji Kalla na biye da shi a motar shi hankalin shi kwance, horn ya yi ta wa abokin nashi yanda suka saba in zasu rabu amma bai mayar masa ba tsabar damuwar da ke cikin ran shi, kad'a kai Alhaji Kalla ya yi ya wuce abun  shi, sai ya ga ai ba ma amfanin ya koma gida ba mata kawai ya yi kwana ya tafi club. Alhaji salihu kuwa yana isa gida ya d'akko Suwaiba a hannu kamar yanda ya fita da ita a hannu ya shiga d'akin shi da ita, kan gado ya ajiye ta, ya zuba mata ido ya na kallo yanda a cikin qanqanin lokaci ta d'ashe ta yi fari alamar ba jini sosai a jikin ta, kwanta wa ya yi kusa da ita ya rungume ta, a haka Shima ya yi bacci. Bashi ya farka ba sai sha ɗaya na safiya wanda ta sanadin motsin Suwaiban ne ya sa shi tashi, hannayen ta biyu ta miqar dan ta yi miqa an tashi daga bacci sai ta yi saurin sauke su saboda wani azababben ciwo da ta ji ya soki qirjin ta , komawa ta yi ta kwanta cikin zubda kwallah ta ke son sanya hannu ta tab'o qirjin nata, da sauri ta sauke hannayen nata saboda jin zafi da ta yi sannan ta ji wayam alamun ba komai a wajen,mamaki take yi ina kayan wajen suka tafi dan kuwa ta sani Allah ya azurta ta da su manya ma kuwa amma  me yasa ta ji wayam sannan take jin wajen kamar an yanke ta??? Ni kuwa 'yar kawo maku rahoto na ce ba kama bane Suwai matar manya da alama dai kin zama Nonoless .............. [21/07, 7:46 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    ' YAN ABUJA   💅🏼     WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 21: Yau Juwairiyyah ta tashi da aikace aikace da yawa amma dik da haka ta sa a ran ta a yau take son ta je gida dan su gaisawa da 'yan uwanta dan bata san ranar komawarsu ba, da farko Jabeer yaso hana ta ta bari sai jibi tace sam zata iya ba wani gajiyar da zata yi, haka ya hakura ya barta, tana idar da sallahr asuba ta ninke hijab da abun sallah ta ajiye ta fara da gyaran d'akin ta ta na yi ta na azkar,a haka ta gama da d'aki da parlour sannan ta nufi kitchen dan yi ma Jabeer  abinda zai samu ya tafi da shi Abuja wajen interview da aka kira su na wani aiki da ya nema a NNPC, dubawa ta yi taga basu da wasu kayan abinci sosai kamar kullum, ragowar Flour da ba zata wuce gwangwani biyar ba ta dakko da ɗan kifin da ta siyo a jiyan na naira dari biyu da attaruhu da albasa ta gyara su ta ajiye, sai ta samu guntun cabbage da take da shi ya riga ma ya kusan qarewa sauran irin qasan nan sai ta yanka shi da albasa mai ganye ta wanke ta tsane su,sai ta koma ta daka attaruhun ta haɗa da ɗan kifin nan, ta soya sama2 ta zuba wannan cabbage ɗin da ganyen albasa. Ta na kammalawa da wannan sai ta ajiye dan ya sha iska tunda ta masa irin suyar nan ne da ruwan jiki ya qafe tass, kwab'in meat pie ta yi wa flour . (Mata a dinga faɗad'a tunani saboda a samu mafita mai girma) Tana kammala meat pie ta ɗora ruwan kunu bayan ya tafaso ta dama masu koko da d'umamen tuwo ta kai masa dan ya karya, a shirye ta gan shi tsaff ya na sake duba jakar shi da k ta hada masa tun cikin dare. Cikin wata roba fara ta zuba masa meat pie sannan ta zuba masa zob'on da ta haɗa tun jiya da yamma mai daɗi a gora ta d'aure bakin ta da kyau ta saka a leda har biyu dan kar ya b'ata masa takardu ta zuba duk a jakar ta zuge,kallon ragowar meat pie din ta yi ta ga ba laifi da yawa za a samu wanda za a baiwa surukan su idan sun zo da rana dan neman auren Nafee, ɗan girki kawai zata qara yi shikenan sannan an fita kunya tunda sun san gidan da za su zo neman auren ba na masu da shi bane, d'aki ta shiga ta ga ya kammala komai ita yake jira su yi sallama,ta na qarasa shiga d'akin ya ja ta jikin shi ya na bin fuskar ta da kallo ya ce, " My princess ba abinda zan ce maki sai dai na yi maki fatan shiga aljanna, tin da ance sai miji ya yarda da matar shi sannan za ta shiga aljanna, My Juwairiyyah na yarda da ke ina rokon Allah da ya sanya min ke a aljannah madaukakiya, ke macen kwarai ce Juwaireren mama, matar da kowanne namiji zai yi fatan samu,macen da zan iya nunawa duk duniya ta gani ba tare dana kunyata ba, Allah ya sauke ki lafiya, ya shiryar min dake , Allah ya qara miki imani, kinga ga riqe wannan ba yawa kwana biyu zan yi kamar yanda na sanar dake, ki yi ta tayani da addu'a inna samu aikin nan zamu samu hutu sosai, zan jiyar da ke daɗin da baki taɓa zato mace zata iya samu wajen mijin ta ba, Juwaireren Mama ina son ki, Allah ya yi maki albarka" Tun da ya fara magana Juwairiyyah ke murmushi sai dai ya na  cewa Juwaireren mama ta turo baki tana buga qafa,sannan ta ce masa, " Ni dai Yah Jabeer bana so, taso ka tafi kar ka makara, Allah ya karen kai mijina kaje lafiya ka dawo lafiya, Allah ya bada sa'a a abinda aka tafi nema, inshaa Allahu kai me nasara ne akan komai na alkairi da ka sa a gaba, dan haka kar ka ji wata damuwa ko ka sa shakka a lamarin,zaka iya miji na saboda kai din na daban ne a cikin mazaje,karka manta da karanta lahaula wala quwwata illa billahi, da hasbunallahu wa ni'imal wakeel,sai kuma hasbunallahu sa'yu'utinallahu min fadhlihi inna ilallahi raghiboon,Allah zai zama jagoran ka, zai taimaka maka ya kare ka, ina son ka Yah Jabeerun Baba" Ta karasa maganar ta tare da miqewa da sauri tana dariya bin ta ya yi ya cafko ta ya haɗe ta da gini ya na dariya Shima ya ce, "Maimaita me kika ce in ba tsoro ba" Turo baki ta yi cike da shagwab'a tace, "Yo ni me nace, dan dai kawai an ga yau mijina zai yi tafiya shine za a yi min yar qure a ci zalina, Yah Jabeer irin wannan kallon da kake yi min ji nake kamar na dawwama da kai a haka a tsaye ba tare da duniyar ta juya ba" Ta karasa maganar ta cikin yin qasa da muryar ta, wani irin farin ciki ke ziyartar zuqatan su a wannan lokacin suna jin kamar kar su rabu da junan su, a cikin ran su kowa na yaba kyau irin na dan uwan shi, sumbatar ta ya yi da salon bankwana wanda Juwairiyyah ta biye masa dan faranta ran mijin nata, Nafeesa ce ta yi sallama ta shiga dayake Juwairah tace ta zo su yi komai da wuri zata je gida a yau d'in, janye jikin shi ya yi a kasalance ya riqe hannun ta ita kuma ta kwantar da kanta a jikin shi, fita suka yi tare idon ta taf hawaye, yau ce ranar farko da zai yi tafiya mai nisa tin bayan auren su, saurin maida kwallar ta tayi kar ya gani hankalin shi ya tashi, sai dai inaa ta makaro dan kuwa ya gani,cikin muryar lallashi ya ce, " Haba my Queen, ki kwantar da hankalin ki mana, inshaa Allah jibi da yamma kina maqale a jikin mijin ki kamar haka,daga wannan tafiyar ba zan sake yin wata tafiya ba ke ba ko ina zan je to fa qafa ta qafar ki kin ji" Kamar wadda ya ce wa ta yi kuka haka Juwairiyyah ta b'are baki irin na yaran nan masu rikici ta fara kuka, rungume ta ya yi a jikin shi ta yi kukan ta son ran ta da kan ta ta yi shiru ta sake yi masa addu'a, suka fita tare har Nafee suka raka shi wajen Innarmu Itama ta masa addu'a daga qarshe ta hau tsokanar Juwairiyyah, "Tooo kukan rabuwa da masoyi aka shaaaaa ?? Hoh yan zamani ba ko kunya to d'akko mayafi ki bishi kawai 'yannema sai kace cinye ki za mu yi kafin ya dawo" Juwairiyyah na jin haka ta saki hannun Jabeer ta taka da gudu ta bar wajen tana dariya, suma dariyar suka yi mata, sai da taje baqin qofar shiga wajen su ta juya, dan tsuke bakin shi taga yayi alamar kiss, ta waro ido ta kalli su Baba Balarabe dake gefe zasu raka shi qofar gida, rufe baki ta yi da hannun ta ta fada wajen nasu tana dariya, " Allah sarki mijina,kaje lafiya ka dawo lafiya cikin sa'a da nasara, tare da kariyar Allah" Nafee ce da ta biyo bayan ta tace " Ameen masoyan asali" Murmushi suka yi wa junan su sannan suka shiga kitchen dan fara aikin da ke gaban su, leqa parlour Juwairiyyah ta yi ta duba lokaci ta ga har takwas da rabi ta wuce,cikin sauri ta ɗauki kwaryar da ke ɗauke da masarar da aka barza ta duba ta ga tabbas za ta isa su yi dambun masara, nan da nan suka je suka tsinko zogalen da Juwairah ce ta shuka da hannun ta da alayyahu, sai albasar su mai lawashi, gyarawa suka yi suka dake gyad'a, da kayan qamshi attaruhu da maggi da gishiri suka saka yanda zai isa ya yi daɗi suka zuba wa wankakken tsakin su suka dora a wuta. Cikin qanqanin lokaci dambun masara mai daɗi ya haɗu, man gyad'a Juwairah ta soya da ya ji albasa, suna kammalawa Juwairiyyah ta d'akko mazubi masu kyau ta zuba komai a inda ya dace har zob'on da meat pie sai da aka zuba su a waje mai kyau da tsafta.   Nafeesa ta ji daɗi sosai dan haka duk inda Juwairiyyah ta sa kafa Nafeen na biye ta na godiya da addu'a har saida ta ba Juwairah haushi,dan kuwa godiyar ta yi yawa a cewar ta, ajewa suka yi a gefe Juwairah ta sa Nafee deb'o wani alayyahun da albasar mai ganye, ta sa ta gyara su ta daka kayan miya wannan karon harda tumatiri, jelop rice mai daɗi ta dafa wadda ta yayyanka ɗan naman a ciki qanana ,kasancewar nama bashi da yawa yasa Juwairah tace bari su yanka qanana sai a soya sama2 su saka a abincin, har da dan carrot ɗin su, nan da nan sai ga girkin da su suke ganin anyi a talauce ya koma a yalwace, dan kuwa wata macen ma ko an kawo mata kayayyakin girkin da ya fi wannan ba lallai ta tada abinci mai kyau da daɗi kamar wannan ba. Wanka ta tafi ta yi ta sa Nafee taya ta gyara gidan, dan bata son fita ta bar gida da datti in ta dawo ranta baya yi mata daɗi, sannan kuma ta san idan bata gyara ba zata dawo da gajiya sai dai a bar gidan ya kwana da datti kenan Wasu matan taqamar fita za su yi unguwa sai su bar gidan kamar bola su tsallake su tafi abun su,idan baki gyara ba ki ka tafi ki ka dawo ki na iya yin baqin kunya su tadda gidan ki g kaca-kaca, ko kuma ki dawo a gajiye ga shi maybe miji ya kusa dawowa, shima ya dawo yaga yanda ya fita haka ya tarar wataqila harda qarin datti ma, amma in kika gyara gidan ki fes in da hali ma har girki ki yi ki ajiye, da kun dawo wanka zaki yi kawai ki faɗa gado ki huta,maybe sai bacci ma tinda baki da aikin da za ki yi. Sai da ta gama shirya wa tsaf sannan ta zauna ta ci abinci a gaggauce ta rufe sashen ta ta sanya mayafin ta ta riqe jakar ta a hannu mai ɗauke da waya da ɗan kud'in abun hawan ta ta wuce bangaren Innarmu ta yi mata sallama ta dau hanyar gida cike da zumud'i da d'okin ganin iyaye da 'yan uwa ta. Mai adaidaita sahu na ajiye ta ta sallame shi ta shiga cikin gidan su bakin ta ɗauke da sallama,ba wanda ya ji ta ma ballantana a amsa mata saboda ta isko ana ta daru akan komawa Abuja ,ita Saudat tace bazata koma ba, Suwaiba kuma ta shirya tsaf da shirin tafiya ta na tursasa Saudat akan sai sun koma tare Goggo ma ta sa ta a gaba da magiyar ta daure ta koma, ba zai qara dukan ta ba, Shima kuma Baba ya kafe Saudat ba zata koma ba tinda bata so mijin nata ya biyo ta da takardar sakin ta idan a son shi ne ma ita kanta Suwaiban ba za ta koma ba,ganin abun ya qi ci ya qi cinye wa ne ya sanya Mama Bilki cewa, " Ayya Goggon su tinda ta ce bazata koma ba a barta mana in aka kwan biyu kin taushe ta sai a maida ta dakin ta" " Ba laifi yau ɗaya kin yi magana mai ma'ana,Allah ya kaimu ta huce an maida ta ɗin, dan kuwa 'ya ta ba zubin zaman Kano bace zubin rayuwar Abuja ce ah toh" Cike da rashin kunya Saudat ta kalli Mama Balki ta ce, " Ka ji Maman nan ina ruwan ki da sa mana baki a maganar 'yan d'akin mu? To bazan koma ba ɗin har abada, sai dai ya biyo ni da takarda ta, ke kuma Allah ya bada sa'a zaki ce na fada maki, dama saboda irin wannan halin naki na ki yarda na sanar da ke tun a can da na sanar da ke da kin sa an kashe mu a banza" Da jin kalaman Saudat sai Mama Balki ta bar wajen ta wuce d'akin ta,Juwairah kuwa sai ta qarasa cikin sake yin sallama,ta dan duqa ta gaida Suwaiba da ke qoqarin qota ta ta wuce, cikin b'ata fuska suwaiba tace wa Juwairiyyah, " Malama bani waje driver na na jirana ina da wajen zuwa mai nisa, ko dake ke ya za a yi ki san nisan da ke tsakanin Kano zuwa Abuja tinda kin qunshe kan ki daga Kano sai kano?" Ta na gama magana ta saka hannu a jaka ta d'akko kudi mai ɗan yawa ta watsa wa Juwairiyyah a jikin ta tace, "Ga shi nan dama na san gaisuwar kenan, shine ya sa ki zuwa da wuri kar mu tafi ba a baki rabon ki ba" Ta sa kai za ta bar gidan cike da takun kasaita ita a dole ga mai arziqi, cikin qunci da haushi tare da fushi irin na masu ciki in an tab'o su Juwairiyyah ta bi bayan ta ta jawo hannun yayar ta ta, kamar yanda ta wurga mata kudin a jiki itama ta wurga mata a fuska ta ce, "Ashe har yanzu baku canja hali ba? Ban zo dan wannan banzan kud'in naku ba, nazo dan na ga 'yan uwana dana dad'e ban gani ba da kuma iyaye na, na zo domin zumuncin Allah ne, dan haka u keep ur filthy money with u,it will help u some day" Ta juya tare da  shigewar ta cikin d'akin Mama Balki ta bar kowa na binta da kallo baki sake, tab'e baki Suwaiba ta yi daga baya ta dauke kud'in ta ta shiga mota tana d'aga ma Baban ta da Goggo hannu, suka juya birnin tarayya ABUJA. Komawa ciki suka yi in da Baba ya shiga bangaren Mama ya isko Juwairah da Salma, Salma tana ba Juwairah hakuri akan komai da ya faru a baya, Juwairiyyah na ganin baban nasu ya shiga sai ta miqe da kyar dan ta durqusa ta gaishe shi, shi kuwa sai fad'in tayi zaman ta yake yi amma saida ta isa gare shi,ta durqusa ya dafa kafad'ar ta ta gaida shi tare da fad'in, " Babana na yi kewar ka ba adadi ina ta so na zo na gan ku tunda Mama har yau bata je d'aki na ba ta sanya min albarka" " Juwaireren Mama nima na yi kewar  ki sosai, da fa jibi muke saka rana zani ni da Salma mu gan ki, ki rabu da maman nan taki da alama sai na fara Kiran ta tsohuwa tunda ta na yi mana halin tsoffi" Turo baki ta yi alamar shagwab'a ta ce, "Babaaaa" Dan ta riga ta gano faɗa kawai Shima ya yi ba zuwan da zai yi, shi ɗin ma kamar Mama Balki yake tun da aka yi mata aure ya daina zuwa gaida yayan shi a gida sai dai ya tadda shi a masallaci su gaisa  ya koma gida,dariya suka yi dikan su Mama Balki ta ce, " Oh mai hali baya fasa halin shi an girma amma shagwab'a na nan" Haka suka dinga hira cikin nishad'i da annashuwa, nan da nan Salma da  Juwairah suka qara shaquwa, hira suka shiga yi Salma ta ba ta labarin abinda ya dawo da ita gida, Juwairah akwai tausayi da saurin kuka dama,tausayin yar uwarta ne ya cika ta tai ta kuka kamar wadda aka daka, sai da ta gama ta rungume ta tace, "kar ki damu yar uwa, da kin haihu zaki samu miji na gari inshaa Allah mai kud'in dai da kike so da yardar Allah" " A'a Juwaireren Mama banni da talakan ma zan zauna ni ai yanzu talauci baya bani tsoro tunda na ga na gidan Talle" " Kaiii Salma harda ke a Kiran wannan Sunan ko" " A'a nima yau tab'awa na yi ai, ai baki taba jin na fada ba ko? To qara'i nai na da da ban tsokane ki ba" " To shikenan ke kaɗai na yarda ki ce man Juwaireren Mama, ke ma iya na sati ɗaya kacal" Ta faɗi hakan cike da nuna ita ɗin yar farin maman ta ce, dariya suka yi harda iyayen su dika, anan Ammar ya tashi daga bacci saboda shewar da suke ta yi, da sauri Juwairah ta isa ta d'akko shi, sai kallon ta yake yi, wasa take masa ta ji yana qoqarin yin magana, " Mamma" Shine abin da ya furta, daɗi ne ya kamata ta ce, " laaaa mama yana magana dama?" " A'a ya dai iya barna wannan" Dariya suka yi suna kallon Ammar da ke taya su dariyar Shima,haka Juwairah ta gama yinin ta cijin jin daɗi,dan kuwa a tare suka yi girkin rana ita da Salma,ganin suna girki tare ne ya sanya saudat fitowa ta na ta auna masu rashin mutunci kala kala,amma ba wanda ya kula ta,dan kanta ta gaji ta koma daki, kyaliyar Mama Balki suka koya irin abun nan na mugun bata wa duk wanda yake maka masifa rai. Ta bangaren Suwaiba mutanen ABUJA kuwa sun isa Abuja lafiya a matuqar gajiye kamar ita ta yi tuqin, tana isa ta tarar da masu aikin ta sun gyara gida ko ina fesss sai tashin kamshin turaren wuta yake yi,ga girke girke nan an yi na tarbon ta,ta na gama buɗe wa ta shaqi qamahin girkin sai kawai ta saki murmushi tare da fadin, "Amma gaskiya Saudat shashasha ce, ni yanzu ina zan bar wannan gara ta wuce ni akan zargin banza da wofi? Hummmm bari ma na je na yi wanka na zo na ci na sha na yi hani'an gidan uba babu an dawo gidan miji ai sai a shoshale" D'akin ta ta wuce direct wanka ta faɗa, bayan ta gama ne ta shirya cikin qananan kaya ta feshe jikin  ta da turare ta kwanta a gado ta na latsa wayar ta ta ce, " Wawuya, yaushe zan bar wannan daula ta wuce ni, ana ki dawo kina wani ke gida yafi gidan miji, ai ni da barin Abuja sai da ziyarar ganin dangi" A haka ko abincin bata samu ta koma ci ba bacci ya dauke ta, cikin baccin ta ji wani zafi kadan kamar an soke ta da wani abu mai tsini ta so buɗe ido ta ga menene amma ko bude ido bata sake iyawa ba ta lula duniyar duhu.......... [22/07, 8:44 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 23: Gobe ne ranar da Jabeer zai dawo gida daga wajen interview da ya je yi a Abuja, waya suke yi da Juwaireren shi wadda ke kwance a gadon ta da ya sha gyara kamar Jabeer na gida dan,bata daga cikin matan da ke qin gyara d'akin su saboda taqamar miji ya yi tafiya,hira suke sha ta soyayya gaba ɗaya Juwairiyyah ta shagwab'e masa ta susuta masa lissafi, ji yake yi kamar ya dawo a daren ko da fuskar ta ne ya kalla, ya san zai ji nishadi,  kwantar masa da hankali ta yi da cewar gobe suna tare da junan su da yardar Allah dan haka kar ya damu ya qara haƙuri,dole jabeer ya hakura ya daina yi mata shagwab'ar da ya ke sanya ta nishad'i da dariya, Itama ta na jin ta kai wata a wajen miji tinda duk girman shi ya yarda ya amince ya bayyana mata yarintar shi. Suna gama hirar su ta soyayya ta tuna masa kar ya manta fa ya yi addu'ar bacci kafin ya kwanta,sai  su ka yi addu'ar tare suka kashe waya, bayan cika juna da "I love u", haka suka yi bacci cike da matsananciyar kewar junan su. Da sassafe bayan tayi sallahr asuba tayi abubuwan da suka zama na al'adar ta da safe kamar yanda kuka san Juwaireren Mama, taso yau ta bar gyaran lambun ta da ta yi a cikin gidan saboda sauqaqa masu wahalar rayuwa sai ta ga dacewar ta gyara ɗin in yaso daga baya ta gyara gidan ta da girke girken tarbon mijin nata. Da misalin 9:28am Juwairiyyah ce sanye da doguwar riga mara nauyi mai hannun shimi, ta dauki kayan gyara lambun ta ta fara gyara abubuwan da suke da buqatar gyaran, da ke ta na da saurin aiki cikin qanqanin lokaci ta gama cire ciyayi da bawa shukokin nata ruwa sannan ta ajiye komai inda ya dace ta wuce d'akin ta ta gyara shi ta hanyar sauya wankakken zanin gado da sauya wankakkun labulaye. Tattare zanin gado da labulayen da ta sauya ta yi zata fitar Nafeesa ta yi sallama, cikin ɗan haɗe fuska Nafeesa ta ce, " Haba matar Yayah ai sai ki kirani, da wannan tsohon cikin haihuwa ko yau ko gobe Zaki zauna ki na aiki mai wahala haka? Salon kawai ki ja mana wani aikin, habaa gaskiya ban ji daɗi ba" Ta qarasa maganar ta ta na karb'ar kayan hannun Juwairiyyah, murmushi Juwairah ta yi ta dafa kafadar Nafeesa da ke kumbura baki ita a dole Fushi take yi sannan ta ce, "Kar ki yi fushi da ni 'Yar qanwata,na jima ina so in sanar da ke ina matuqar jin daɗin yanda ki ke bani girma a gidannan ba dan na girme ki da shekara ba sai dan sanin darajar ɗan uwan ki da kuma mutunta shi da ki ke yi har ta dalilin haka nima ki ke daraja ni,na jima ina mamakin yanda ki ka ajiye duk wata quruciya da yarinta da muka ci ki ke kasa Kiran suna na kai tsaye sai idan kin so tsokana ta, sannan tunda muke baki taɓa yi min abu cikin gadara da isa ba dan ganin ke qanwar miji na ce ki na da 'yanci da iKon yin duk abin da ki ka ga dama a gidan yayan ki,a gaskiya Nafee samuna irin ki sai an tona Allah ya barki da masoyin ki kema ya nuna mana ranar auren ku,Allah ya sa ki samu kwanciyar hankalin da tafi tawa a dangin mijin ki,Allah kuma ya qara mana zumunci ina son ki 'yar uwa ta,maza taho to ki taya ni aikin ki dena Fushi da ni,abinda ya sa ma ban kira ki ba na dauka kina taya Innarmu aiki ne shiyasa ban kira ki ba, tayata aiki ai yafi nawa ko? And dan Allah ki dena fad'ar min da gaba dika dika fa yanzu cikin ya shiga wata takwas" Murmushi suka yi wa junan su Nafeesa ta ji daɗin maganganun Juwairiyya sai kawai ta nufi inda Juwairiyyah ke yin wanki ta ajiye kayan ta koma ta tattaro sauran 'yan kayan da ba su da wani yawa ta fara wankewa,ranar dai kusan a tare suka ci gaba da aikin su, sallah ce kawai da cin abinci ke tsaida su,Saida ya rage sauran wanke band'aki kawai Juwairiyyah ta deb'i ruwa a bokiti ta ɗauki omo da tokar murhun da ta zuba wa gishiri kaɗan ta matsa lemon tsami ta zuba ruwa akai ta nufi hanyar band'akin. Nafee na ganin haka ta bi bayan ta ta amshe wankin toilet ɗin, bayan ta kammala ta fito da komai ta ajiye inda ya dace ta kalli Juwairiyyah ta ce, "Wai nikam me zaki dafa wa Yah Jabeer ne naga baki fara batun girki ba ga shi yamma ta yi" "Abinda ya fi so zan dafa masa, da kud'in da ya bani kafin ya tafi, jiya na yi aike kasuwa aka siyo min k'wai, nama dankalin turawa, da cabage sai carrot da green beans kin san bani da su a lambu na dama zan iya noma su har su zan saka tinda Yah Jabeer na so a yi girki da su, sai flour ina da mai dama, an siyon yan kayan qamshi da maggi, ɗan wake zan yi mishi mai ajiiiii Hajiyata kin san shi a duniya na kula yana son abunnan" "Waiiii sosai ma kuwa, baki gan shi bane yana satar danwake a tukunyar Innarmu da sai kin sha dariya, Innarmu in ta kama shi sad'af sad'af take tafiya ta damqe hannun shi ta matse da ludayin tsamar danwaken, shi kuma ya yi ta ihu dan azaba ita kuwa ta qi saki sai ya wahala ta sake shi ta na bin shi da zagin ya na mata satar ɗan wake a tukunya ni da baba mu yi ta musu dariya" Dariya suka yi tayi sosai dan kuwa Juwairiyya bata taɓa jin labarin ba sai yau, miqewa suka yi suka fara gyara dankalin, suka yanka veges harda na lambun nata da zai tafi da kalar  girkin da zata yi,musamman alayyahu da albasa mai ganye, sai da suka yanka komai ta wanke tsaf ruwan jikin su ya tsane sannan ta shiga soya dankalin turawan da ta yi wa yanka a tsaye,sannan ta dakko dafaffen naman ta da ta yanka qanana-qanana ta soya sama-sama ta aje gefe, sannan ta rage man suyar ta dakko jajjagaggen kayan miyar ta, da ta sanya tumatur guda biyu jal ta zuba, ya na tsaka da soyuwa ta zuba kayan qamshi da na dandano,bayan miyar ta soyu ne ta dakko wannan veges din ta zuba, ta bari ya dahu har sai da ruwan jiki ya qame tass sannan ta zuba dankalin ta soyayye da dafaffen k'wai a ciki ta juya ya haɗe jikin shi da kyau. A gaban Nafeesah ta d'akko flour da wani gari ta zuba kuka ta juya sosai sannan ta fara kwab'a wa da ruwan kanwa, cike da mamaki Nafeen ke bin ta da kallo, cikin tuhuma ta tambayi Juwairiyyah ta ce, "Wai nikam Matar yayah wannan garin meye ne naga kin zuba a cikin flour ɗin kuma?" "To Hajiya tambaya an fara tambayar ko, to garin wake ne na niqa da yar dawa kadan sai alabo shine na haɗa da flour din, ɗan wake yafi dad'i sosai idan aka saka su" " Auuuuhooooo, to ai sai ana yi ana tambaya ko kinga laifina ba gashi yanzu na qaru ba?" " Ban ga laifin ki ba Hausawa sun ce matambayi baya bata ai" Hira suka ci gaba da yi ita kuma ta na kwab'in danwaken ta,bata bar kwab'a wa ba har sai da ta ji ya yi laushi sosai sannan ta buɗe tukunya ta ga ruwan ya fara alamun tafasa sai ta fara jefawa qanana, dan yafi son a jefa d'an wake qanana, rufewa  ta yi sai da ya tafaso ya yi kamar zai zube ta buɗe marfin ta bari ya ɗan qara dahuwa sai ta kwashe a ruwa Mai kyau daga nan kuma ta tsame shi a mazubin ta mai riqe zafi, ta zuba wa su Innarmu ta bawa Nafeesa. Nafeesa ta barwa wajen dan ta gyara ita kuma ta dakko nunannen tumatur  ta wanke ta raba shi biyu tare da baɗe shi da sugar a tsakiyar shi ta hau goge fuskar ta da shi, nan da nan fuskar ta ta dau kyalli kyan  ta ya qara fitowa. Lalle Juwairiyyah ta deb'o ta zuba masa man kwakwa ta kwab'a shi da ɗan ruwa kaɗan ta dinga bin ko ina na jikin ta ta na murjewa,gaba ɗaya lamarin ta ya gama bawa Nafee mamaki,kasa shiru ta yi sai da ta yi magana, "Tab a gaskiyar magana Yayah na shan daɗi aradun Allah, yau fa ba ranar gyaran jikin ki bane kamar yanda ki ke tsara abubuwan ki, bama fa ki wani dad'e da yi ba amma ji yanda ki ke faman dirzar fata kin koma kamar wata tauraruwa mai haske da kyau" " Nafee kenan, ai ita mace ana son in mijin ta ya yi tafiya ko na kwana ɗaya ne ya dawo yaga ta canja kawai ko da sauyin ba yawa, balle kuma Nafee muna magana ne fa akan Yah Jabeer d'ina, My love, my  everything" Dariya suka fashe da ita tare da tafawa,Nafee nata tsokanar ta ta gama ta shiga wanka abun ta ba tare da ta biye wa tsokanar Nafeesan ba. Ta na fitowa ta tsane jikin ta tare da shafa mayukan ta masu kyau da ta haɗa da kan ta dan gyaran fatar ta sannan ta yi shigar da yake matuqar so, doguwar rigar material ne aka mata irin na masu ciki ma'ana mai faɗi ta yanda ba za ta takura ba,an d'aure hannayen rigar dika ta wuya daga qirjin ta ɗan kama ta kaɗan, cikin nan ta bi ta shafe shi da mai sai kyalli yake gwanin sha'awa,kwalli da powder kawai ta shafa sai man leb'e, wani irin sassanyan qamshi mai ratsa zuciya take fitarwa saboda bata amfani da turare mai karfi. ( kwalli na da matuqar tasiri a idon mace, macen da ta saka kwalli ta kuma iya sarrafa idanun ta ta daban ce) Dogon hijab ta saka akan kayan ta tada sallar magrib bayan ta idar ne ta zauna ta na azkar a hankali ta fara karanta qur'ani, ana kiran sallar isha'i ta kabbara zata yi sallah kenan Sallamar Jabeer ta daki kunnuwan ta dake buɗe suna jiran su ji muryar shi da ta yi kewa. Jin shiru bata je tarbon shi bane ya sanya Jabeer leqawa parlour ganin tana sallah ne ya sanya shi ajiye kayan shi a cikin palourn ya tafi ya d'aura alwala shima ya tafi masallaci. Ta jima ta na gode wa Allah da ya dawo mata da mijin ta lafiya qalou kafin ta yi tahiya ta Sallame sallar ta, ninke hijabin ta take yi bakin ta na tasbihi ga Allah ta shiga d'aki ta dan sake shafa humra da powder sannan ta hau kallon kanta a madubi, murmushi ta yi wa kan ta kafin ta koma parlour, ɗauke kayan da ya dawo da su ta yi ta hau dubawa nan take ta hau ware komai ta na ajiye wa a mahallin da ya dace da shi,hatta da kayan wankin da ya dawo da su sai da ta yi masu mazauni sannan ta dawo ta ɗauke wata leda da bata buɗe ta ga meye a ciki ba ta kai ta ajiye. Ruwan wanka ta haɗa masa mai d'umi, fitowar ta kenan ta shiga parlour kafin ta kai ga zama Jabeer ya sallama ya kulle sashen nasu, kafin ya gama karanta ayatul kursiyyun a qofar gidan ta tashi da sauri ta na dariya qasa qasa ta b'oye a bayan qofa. Shigowa jabeer ya yi bakin shi ɗauke da sallama fuskar shi cike da annuri saboda ganin gidan qal fiye da yanda ya saba ganin shi,cikin murmushi ya hau dube -dube alamun neman ta yake, gajiya ya yi da tsayuwar ya kama qugun shi ya ce, " Juwaireren Mama ko ki fito ko na zauna a qasa na yi ta maki kukan wahal da idanu da ruhi na da ki ke yi, dan na kula da alama baki son gani na ni kaɗai ne na yi kewar ki" Ta bayan shi ta lallab'o ta fito ta yi masa wata iriyar runguma wadda tasanya shi sauke ƙanƙk'arfar ajiyar zuciya, juyawa ya yi gaba ɗaya ya d'aga ta sama, suna ta dariya, sumbatar ta ya dinga yi ya na nuna tsantsar yanda ya yi kewar ta,daga baya ya tafi suka samu waje suka zauna a kujera,inda Jabeer bai bar Juwairiyyah ba sai da ya zaunar da ita a Saman cinyar shi, yana shafa cikin ta tare da yi wa cikin nata hira kamar wanda yake hira da mutum babba, dariya kawai take yi ita kam, daga baya ta rage sautin dariyar ta tace da shi, "Sannu da zuwa fitilar da ke haske cikin gida na, a gaskiya dole na dinga godewa Allah da ya ban kai a matsayin miji, Yah Jabeer tafiyar nan ta kwana biyu da ka yi ya sa na tabbatar wa kai na ba zan iya rayuwa mai ma'ana ba idan babu kai, i missed u so very much" Ta qarasa maganar ta tare da qanqame shi tana hawayen farin cikin dawowarsa lafiya kamar wani wanda ya shekara baya gari, d'ago ta ya yi yana jin wani sabon qaunar ta na ratsa shi, dan kuwa kalaman ta sun ratsa zuciyar shi sun samu wajen zama ya kuma tabbatar da iyakar gaskiyar ta ta faɗa masa, "Yi shirun ki my princess, ki daina kuka, Yah Jabeer na Juwaireren Mama ne ita kaɗai har abada, bana fatan na wayi gari na ga baki kusa dani,ke ce farin ciki na Juwairiyyah ke ce komai na, dan haka kar ki taɓa jin tsoron rasa ni saboda ni naki ne har abada,na mallaka maki gangar jiki na, ruhi na da zuciya ta ki yi yanda ki ke so da su dika " Wata sabuwar runguma ta qara yi mashi da ta saka shi jin daɗi sosai, d'aga shi ta yi ta ja hannun shi zuwa wanka ta taya shi ya yi wankan ya yi brush suka fito, sannan ta taya shi shiryawa. Bayan sun gama ne  suka nufi kan shimfid'ar da suke cin abinci suka zauna, duk abinda take yi masa ba qaramin daɗi yake ji ba, qima daraja da mutuncin ta na qaruwa a idanun shi,ita mace ce mai yawan kyautatawa,shi kuma namiji ne mai son a kyautata masa kuma mai yaba kyautatawar da ake yi masa,dan haka binta kawai yake kamar raqumi da akala. Ta na buɗe mazubi na farko idon shi ya sauka a kan d'an wake murmushi ya saki mai sauti sama ya kalla cikin ran shi ya na godewa Allah tare da tunanin shin me ya aikata mai kyau a rayuwar shi Allah ya bashi Juwairiyyah a matsayin mata ya ninka wannan aikin alkhairin dan Allah ya bar masa ita su yi ta rayuwa tare har abada? Hadiyar yawu ya yi dan ganin ɗan waken da har wani kyalli yake dan santsi sannan ta zuba mai wannann hadin da ta yi na dankali, zobon da ta dafa da abarba, cittta kaninfari, cucumber, goruba da sugar ta zuba masa, kafin ta gama dubawa Jabeer ya fara ci yana lumshe ido kawai tsabar yanda abincin ya yi masa daɗi, sai wani sautin santi  yake fitar wa dan kuwa bata gane abinda yake faɗa, Juwairiyyah kuwa dariyar jin daɗi ta dinga yi. Kowacce mace ta na so idan ta yi abun kwarai a Yaba mata, dan haka yabon Jabeer a wajen ta ba karamin abu bane, hannu ya miqar ya ɗauki zobon da aka saka a randar sanyi ya yi sanyi dan kuwa Juwairiyyah bata da fridge ya kai bakin sa ya kurba, saurin buɗe idon shi ya yi sannan ya mayar ya kulle, ya ci gaba da santin  da yake yi, a hankali Juwairiyya ta ce, " Yah Jabeer menene, yayi d'aci ne ko wani abu ka ji da be yi maka ba a ciki na ga ka buɗe ido da sauri?" Ta yi maganar tana zaro ido waje dan a tinanin ta ko ba yi masa bane,da hannu ya yafice ta ya ce, "Matso kiji me ya yi" Yana ɗan yatsina fuska saboda ya ja wasan da kyau,nan take ta ɗan ji zuciyar ta ba daɗi, saboda gani take ta b'ata zob'on garin iyayin yi  masa had'e-had'e, dan ba ta san dama ana saka cocumber ba qirqira ta yi, matsawa ta yi kanta a qasa, Jabeer ya ce, "To ai sai kin rufe idon ki sannan zaki iya jin me na ji nima ba ido rufe ki ka ga na sha ba ? matso sosai na baki da kai na ki ji ya ya yi" Matsawa ta sake yi ta rufe idon nata, ji ta yi ya hau sumbatar ta har sai da ta ga wasu taurari na gilmawa a idanun ta ta kasa motsawa, a hankali Jabeer ya ce mata, "To buɗe idon naki mana Princess wannan tukuicin kyautatawar ki a gare ni na baki duk da na san ba zan taɓa iya biyan ki ba,ni ba mai kuɗi bane bare na maki kyautar kuɗi gida ko mota, albarka kawai zan yi ta sanya maki tare da fatan alkhairi,sannan zan yi qoqarin sanya ki farin ciki har qarshen rayuwar mu" A tare suka kammala cin abincin su ya na ta santi tare da yaba mata, anan ne Juwairiyyah ta gane lallai mace ta yi sa'ar mijin da idan ta kyautata masa ya yaba mata ma ba qaramin abu bane, duk wahalar da za ta yi dan taga ta kyautata masa ba zata tashi a banza ba. (Abinda ya yi qaranci kenan yanzu ya na wahala maza su yaba wa matan su, mace sai ta jima ta na wahala dan faranta ran namiji amma kallo ma bata ishe shi ba balle ya yaba mata,amma idan ya ga wata a waje wadda ba muharramar shi ba ya dinga yaba mata ta na gwale shi, kuma haka zai ci gaba da yabawar wataqila ma har da tukuici kamar wani mara zuciya, ya bar halal ya tafi yabon haram) Sad'af sad'af na miqe zan bisu amma 'yar nan ta banko qohwa ta ruhe wai kar na bi su sai gobe mun haɗu............. [22/07, 8:44 am] asiyahabibu93: 💅🏼    ' YAN ABUJA   💅🏼     WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 24: Saudat ce zaune a tsakar gida bata jima da aiken yaro ya siyo mata gasasshen kifi mai haɗe da chips da ake gasawa ba a wani suya spot a farkon shigowa layin nasu da ta saba ci tun lokacin 'yammatancin su, Goggo Sarai kawai ta iya bawa ta sa saura a gaba ta na ci ta na kora maltina mai sanyi, Salma mai ɗauke da ciki ce ta haɗiyi yawu saboda ranta ba qaramin biyawa ya yi ba,amma haka ta danne kwad'ayin ta dan ta san ba bata Saudat za ta yi ba,sai da ta ga ta kammala ci ta wanke hannu ta koma ta zauna a kujera ta na latsa waya sannan ta isa wajen ta ta gaishe ta, a daqile ta amsa ta na karkad'a qafar ta ɗaya da ta ɗora Saman d'ayar,cikin wani maqasqancin kallo ta ce da Salma, "Meye ki ka zo ki ka tsaya min a ka,idan gaisuwa ne ai mun gaisa ko sai a yi gaba tunda an sauya uwa,idan kuma wani abu ki ke da buqata ki yi gaggawar sanar da ni dan bana so a tsaya min aka" Murmushin takaici Salma ta yi,nan take ta hau tuna baya yanda yayun nata ke ji da ita suke ɗora ta a hanyar karb'ar kud'in maza, ba su jin kunyar nuna mata yanda za ta yi wa namiji kwarkwasa da taɓa bikin shi san ya bata kuɗi shi ne yanzu dan ta zaɓi hanya mai kyau suke gudun ta, cikin magana mai cike da ladabi ta ce wa Saudat ɗin, " Adda Saudat dan Allah zuwa na yi ki ɗan bani koda dubu d'aya ce ina son in ɗan ja jari ne ko Saida gishi da omo ɗan qulli ne in fara yi a cikin gida, saboda zaman haka baya min daɗi ba kud'in kashewa,ke ma kuma ina mai baki shawara da ki nemi abun yi da kud'in da ya rage maki tun kafin su qare saboda yanzu kin ga kin saba da kudi, randa kike da buqatar su kika rasa ba qaramin damuwa zaki shiga ba" Tunani Saudat ta shiga yi mai zurfi, can ta nisa tace, "Gaskiya kin ce wani abu kema, zan baki dubu biyar ki ja jarin, ni kuma zan fara kasuwanci ta waya da naga qawaye na da na yi a whatsapp da facebook suna yi, ana samu sosai in ka riqe amanar mutane, sai kaga ka samu riba mai yawa kana daga zaune" "Yauwa Addana na gode sosai, sai wata magana kuma mai mahimmanci da nake so mu yi ni da ke, ina son ki gane Mama Bilki mace ce mai kirki tana matuqar son mu, sai dai tabbas tana kishi da Goggo, wanda wannan dole ne a zaman kishiyoyi dama,shiga wannan kuma ba hurumin mu bane mu kau da kai akan wannan mu bar su su yi kishin su after all miji ɗaya suka haɗa,abinda kawai za mu yi shine mu yi masu biyayya dikkan su a matsayin su na iyayen mu," Shiru Saudat ta yi domin maganar qanwar ta ta yau tana shigar ta dan gaba ɗaya ba qarya a ciki amma akwai nau'i na girman kai da taya Goggon su kishi a zuciyar ta,dan haka sai ta yatsuna fuska ta ce, "Hmmmm zan duba maganganun ki na gani" Sannan ta miqe ta d'akko mata kud'in da ta alqawarta zata bata ta bata, duk abinda ya faru akan idon Goggo Sarai ya faru, sai dai bata ji kalaman da suke yi ba ta dai ga an bawa Salma kuɗi,magana take cikin b'acin rai, "Habaaaa Salma ai innice ke yanda na canja uwa, yan uwan ma canja su zan yi, auhoooo ba zaki iya canja yan uwa ba saboda su masu arziqi ne Zaki yi roqo za a baki , amma ita uwar ki tinda talaka ce shi yasa ki ka sauya ta" " Ni fa Gogga ba haka bane, ya kamata ki buɗe idon ki ki gane inda gaskiya ta dosa, ki daina rufe idon ki ki na yin abinda bai kamata ba" "Rufen baki sallamammiya kawai, an yi asiri da tuggu kala2 an raba ni dake, to ki je nima na huta da dawainiya da ɗan wani" Juyawa ta yi tabar wajen Salma kuwa cikin qunan rai da baqin cikin halayya ta uwar ta ta shige d'akin Mama Bilki, wadda ta ji komai da ya faru, fad'awa kan cinyar ta  Salma ta yi tana kukan takaicin hali irin na uwar tasu, shafa kanta kawai Mama Bilki take, bata furta mata komai ba,cikin kuka Salma ta ce, " Mama ni fa ba kwad'ayi ne ya sa na tambayi Adda Saudat kudi ba, na tambaye ta ne kawai saboda ki na ganin ko tirare bani da shi, ga shi yanzu sai da alimun ko lemon tsami nake amfani a hammata ta a madadin tiraren,da ace ina sana'a yaushe zan zauna haka? Tunanin da na yi na ina sana'a kudin zasu taimakan wajen kula da abinda ke ciki na da ni kai na shine ya sa na tambayi Addah Saudat kuma ta bani dubu biyar na ja jari, shine Goggo take fad'an maganganu marasa daɗi akai na da abinda ke ciki na" " Hakuri zaki yi Salma uwa ba abin wasa bace, dole mu yi mata biyayya matsawar ba sab'on Allah a duk abinda ta sanya mu,dan haka ki yi hakuri, to tin da kin samu jarin yanzu me zaki na yi na siyarwa?" Tashi zaune Salma ta yi ta share hawayen ta sannan ta ce, " Mama Bilki ni da ina son na fara saida gishiri da omo da ɗan qulle qulle na gida, amma yanzu da na samu wannan kud'in mai yawa sai na ji ina son in fara Saida Meatpie, naga kina da injin yin taliya, kuma na kula kayan flour ana cinikin su, in ba su ba ban san me zan iya yin sana'a akai ba kuma" Murmushi Mama Balki ta yi sannan ta ce, " Hakan ma shawara ce mai kyau, Allah ya sanya albarka a ciki" " Ameen mamana" Kwantar da kanta ta sake yi a jikin ta ita kuma tana shafa gashin kan Salman a hankali. ****************************** Yau kusan sati ɗaya da kwana uku kenan Suwaiba na kwance tana jinyar qirjin ta da aka fafe wa albarkatun wajen, Alhj Salihu dayaga zata farka sai ya danna mata allurar bacci ta koma, ko ya shaqa mata wata powder ta koma baccin, a haka ta yi wadannan kwanakin,shine yake yi mata wanka ya canja mata kaya,sannan ya saka mata ruwa da allurai na kashe zafin ciwo da anti biotics,ya zama babban likita kawai a cikin gidan shi dan ya kula da Suwaiba, a haka sai da ya kula wajen ya warke tas sannan ya kyale ta da allurai na bacci da yake mata. Ranar da ya bar ta kuwa bai yi mata allurar baccin ba da ta farka sai ta ji kan ta kamar an ɗora mata abu mai nauyi, da kyar ta tashi daga gadon ta ta isa gaban madubi a hankali ta d'aga rigar ta ta na kallon qirjin ta, nan take wasu hawaye masu azabar zafi suka hau zuba a kuncin ta, ina dukiyar Fulanin ta suke ne, me ya same ta? Duk abinda take yi akan idanun Alhaji Salihu take aikata su, cikin rashin k'warin jiki ta koma ta kwanta a Saman gadon nata tare da nitsar da kan ta cikin pillow kuka take yi sosai mai taɓa zuciya, zama ya yi a gefen ta ya kama hannun ta ya na lallashin ta, a hankali ta d'aga kan ta ta na kallon shi,da kyar ta buɗe baki ta ce masa, " Sweet wai me ya same ni ne, wanne mummunar qaddarar ce ta hau kirji na ni suwaiba ?" " Shiiiiiiii kar ki na yin magana sosai, hatsari muka samu a gidan, yan fashi  ne suka suka shigo a ranar da ki ka dawo kina bacci suka yanke maki nono, ni kuma dana dawo na ganki kin suma shine na kai ki asibiti aka maki aiki daga nan na dawo da ke gida nake ta kula da ke" A firgice ta miqe daga kwanciyar da take ta ce, " Dama abinda ya faru kenan? Yanzu tsabar rashin imani su rasa me za su cire min sai wannan waje mai daraja?" Ta fada tare da zaro idanun ta da ke ta zubar da zazzafan hawaye, cikin kukan nata ta ce, "Na shiga uku ni Suwaiba,ya zan rayu ba mahaifa ba nono,yanzu nan gaba me zan rasa kuma, Alhj na fa san kai ne sanadin rasa nono na  ba wani 'yan fashi,Saudat ta fad'an min ban ji ba ban yarda ba, saboda ina son ka, ko da ina son kudin ka na yarda cewa a yanzu ina son ka so na gaskiya,zan iya rayuwa da kai ko ba mahaifa shine hakan  be ishe ka ba sai da ka qara da wata kadarar tawa yanzu ta ya zan rayu ba nono ba mahaifa" Rushewa ta yi da wani irin kuka mai ban tausayi, cikin tausaya mata Alhj ya fara magana" "ki yi hakuri Baby yau zan........" katse shi ta yi cike da bala'i ta ce, " Kar ka sake kira na da wata baby again, i hate u Alhaji, na tsane ka, na tsane ka da dikkan rayuwa ta" Kukan ta ci gaba da yi mai ratsa zuciyar mai tausayi kai har da mara tausayin ma,matsawa ya yi ya kamo ta jikin shi, da sauri ta zame ta ci gaba da cewa, " Kar ka taɓa ni azzalumi kawai,ka kuskura ka sake taɓa ni ni ma sai na yanke maka inda ba zaka taɓa amfanuwa ba a jikin ka" Cike da matsanancin fushin da bai taɓa sanin suwaiban da yake wa kallon doluwa na da shi ba ta yi maganar,nan take wani irin shakkar ta ta shige shi, miqewa ta yi cike da jiri zata fita, cikin sassanyar murya Alhaji ya ce mata, "Ina zaki je kuma" "Gidan mu zani, na gama auren ka, na kuma gama aure a ABUJA har abada daga yau,daga rana mai kamar ta yau bani ba Abuja" " Lallai ma Suwaiba, abinda baki sani ba shine, ba inda zaki qara fita ko nan da can ne kuwa sai da sani na, dan kuwa ni a yanzu ba zan iya rayuwa ba ke ba, kin ga kuwa sai ki shirya zama da masoyin ki na gaskiya, na amince ni zan jure rashin albarkatun qirjin naki tunda ni ne sanadi" "Za kuwa ka mutu dan ba abinda zai hana ni barin gidannan, ko kana so ko baka so sai na bar gidan nan, in ka barni na tafi lafiya ba hukumar da zan haɗaka da ita, amma in ka hanani ba abinda zai hana ni haɗaka da hukuma zaɓi ya rage ya naka" Wani shu'umin murmushin rainin hankali ya mata ya ce, "To ai baki san wani abu ba, qungiyata babbar qungiya ce suwaiban,ni ɗin ba wai qaramin mutum bane ko baki gani bane?manyan gwamnati da yan kasuwa ba wanda babu a cikin qungiyar mu, ba yanda za ai ki had'a ni da hukuma kuma a samu hukunta ni din, mata kalar  ki da wanda suka fiki komai sun fi dubi kuma mun masu wannan aikin balle ke, dan haka hakuri zaki yi kawai mu qarasa rayuwa dake a haka, in kin tafi wa zai na baki abun daɗin da nake baki? wa zaina debe maki kewa? wa zai zauna dake babu nono? Hakura zaki yi kawai mu zauna a haka tun da kuɗi ki ke so ni kuma zan ci gaba da jiyar dake daɗi da dukiya ta" Tallabo wuyan ta ya yi ya na kallon fuskar ta,iya kuwa gaba ɗaya ta qame ta dauke kan ta daga ganin shi hawaye kawai ke zuba mata, ga wani irin tsoron shi da ke kwance a qasan zuciyar ta, yau ya zata yi ta kub'uta daga hannun wannan azzalumin? Kuka ne ya kwace mata sosai, key din motar shi ya ɗauka ya fice ya bar mata gidan, anan inda take tsaye ta durqushe tana kuka mai ban tausayi. ***************************** Talle kam ya saka marka a tsaka mai wuya ita da yayan shi, dan baya son maganar ta fita waje shi yasa bai ce masu qala ba,sai kawai ya fito da wata mugunta, gonar shi ta daji mai shegen nisa ya ke sa su zuwa gyaran ta, duba da cewar damuna ta kusan zuwa, a cewar shi ya na da majiya qarfin zuciyar cim amana irin su ba abinda zai sanya shi biyan kud'in gyaran gona,in sun ga dama in sun shiga dajin ma su ci amanar shi ya yafe masu amma tabbas sai sun gyara masa gona kafin damina ta sauka. kullum can suke tafiya ba abinci ba ruwa, amma shi zai je a machine din shi da abincin shi da ruwan shi ya yi shawagi ya sa ido ya ga ya aikin yake tafiya,su kuma su Baban gida gonar shi ta can wani qauyen dake kusa da su ya tura su, saboda ya yi yarjejeniya da su akan hakan, in ba haka ba ya kaisu birni ga hukuma a huhunta su akan yi wa 'ya'yan shi ciki da suka yi,da jin haka suka amince suka yi biyayya suma. Kan kuce me Marka ta fita hayyacin ta, 'yan mazaunan nan da ake kad'awa ana jan hankali da su duk sun zube, duk ta dame qashi ya fito mata ko ta ina,mutanen gari kuwa sai gulmammaki suke yi akan abinda ke faruwa a gidan Talle, kowa da ruwayar shi akan abinda ke faruwa amma ba wanda ya san gaskiyar lamari. Kowa ya rasa gane dalilin Talle na aikata haka, da damar mutane sai suka alaqanta hakan da tsantsar rashin mutuncin shi, su Huwaila kuwa kullum sai sun yi surfen abinda za ai tuwo da shi sun dake da hannun su sun mayar dashi gari, sannan su yi tuwon da za a ci a gidan, ga aikin qannen su da ya ɗora masu, walaka ta yi masu yawa kamar zata kashe su,ga qaramin ciki suna fama da shi. Jummala ce ta fito daga d'akin su da rarrafe saboda azabar ciwon cikin da ya sako ta gaba sai  murqususu take yi, cikin tsawa Talle da ke zaune ya na sauraron rediyo ya na aswaki zaune Saman tabarma ya d'aga kai ya kalli Jummala ya ce, "Ke meye hakan zaki zo kina ma mutane kuka, kin gama aikin da na saka ki ne?" Cikin kuka da tashin hankalin da take ji a jikin ta ta buɗe baki zata yi magana sai maganar ta maqale ta kasa fita,wani abu ta ji ya taho da gudu zai fita ta qasan ta, jini ne ya tsinke mata, nan da nan ta faɗi a wajen tasuma tsabar azaba, a gigice Marka ta yi kan ta,shi kanshi uban gayyar ya tsorata da ganin jinin da ke zuba a jikin Jummalar,daukar ta ya yi a hannu ya ɗora ta a kan machin ɗin shi, marka ma ta hau ta riqe ta, asibitin qauyen suka kai ta, bayan bincike da gwaje gwaje likita ya tabbatar masu da b'ari ta yi, sakamakon ta sha wani magani na zubda ciki, ga kuma jini yaqi daina zuba a jikin ta, suna buqatar a sai mata jini a qara mata zasu yi iya qoqarin su su tsaida jinin, Talle ne ya kalli matar shi ya ce, " Sai ki fito da kud'ad'en da kike ajewa na tarin auren su ai mata magani ko" Ya qarasa maganar cikin haɗe fuska, kallon shi ta yi ta sunkuyar da kai da sauri, duk wanda ya hanta a wannan yanayin bai san halin ta ba zai ce zalintar ta mijin ta ke yi, a sanyaye ta ce, "To bari na koma gida na d'akko" Dan rashin mutuncin Talle ko duba halin da Jummala ke ciki bai yi ba haka ya na gani Marka ta taka a qafa ta d'ebi hanyan jiki duk ya mace mata ba wannan cikar da take yi da izzar nan. Kafin ta isa gidan ne ma likitan ta fito, take sanar da Talle Jummala dai babu ita, sakamakon shan maganin zubda ciki da ta yi ba bisa qa'ida ba shi ne ya yi sanadin zub da jini mai tarin yawa a jikin ta, kuma sun kasa tsaida jinin har rayuwar ta ta qare, dafe kai Talle ya yi, nan take nadamar rayuwar shi ta baya ta baibaye shi, kuka yake kamar qaramin yaro, nan suka samu wani mai machine d'in ya taimaka masa ya nemo mai motar da zasu kai ta gida, mai machine d'in kuwa tasha yaje ya samo masa motar, Tallen ya biya shi kud'in ya masa godiya, a motar aka maida su gida shi da gawar Jummala, Marka na shirin fotowa ta koma asibiti taga an fito da gawar Jummala, zubewa ta yi a qasa ta hau kuka da bori tare da kururuwa....... 💅🏼    ' YAN ABUJA   💅🏼     WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 24: Saudat ce zaune a tsakar gida bata jima da aiken yaro ya siyo mata gasasshen kifi mai haɗe da chips da ake gasawa ba a wani suya spot a farkon shigowa layin nasu da ta saba ci tun lokacin 'yammatancin su, Goggo Sarai kawai ta iya bawa ta sa saura a gaba ta na ci ta na kora maltina mai sanyi, Salma mai ɗauke da ciki ce ta haɗiyi yawu saboda ranta ba qaramin biyawa ya yi ba,amma haka ta danne kwad'ayin ta dan ta san ba bata Saudat za ta yi ba,sai da ta ga ta kammala ci ta wanke hannu ta koma ta zauna a kujera ta na latsa waya sannan ta isa wajen ta ta gaishe ta, a daqile ta amsa ta na karkad'a qafar ta ɗaya da ta ɗora Saman d'ayar,cikin wani maqasqancin kallo ta ce da Salma, "Meye ki ka zo ki ka tsaya min a ka,idan gaisuwa ne ai mun gaisa ko sai a yi gaba tunda an sauya uwa,idan kuma wani abu ki ke da buqata ki yi gaggawar sanar da ni dan bana so a tsaya min aka" Murmushin takaici Salma ta yi,nan take ta hau tuna baya yanda yayun nata ke ji da ita suke ɗora ta a hanyar karb'ar kud'in maza, ba su jin kunyar nuna mata yanda za ta yi wa namiji kwarkwasa da taɓa bikin shi san ya bata kuɗi shi ne yanzu dan ta zaɓi hanya mai kyau suke gudun ta, cikin magana mai cike da ladabi ta ce wa Saudat ɗin, " Adda Saudat dan Allah zuwa na yi ki ɗan bani koda dubu d'aya ce ina son in ɗan ja jari ne ko Saida gishi da omo ɗan qulli ne in fara yi a cikin gida, saboda zaman haka baya min daɗi ba kud'in kashewa,ke ma kuma ina mai baki shawara da ki nemi abun yi da kud'in da ya rage maki tun kafin su qare saboda yanzu kin ga kin saba da kudi, randa kike da buqatar su kika rasa ba qaramin damuwa zaki shiga ba" Tunani Saudat ta shiga yi mai zurfi, can ta nisa tace, "Gaskiya kin ce wani abu kema, zan baki dubu biyar ki ja jarin, ni kuma zan fara kasuwanci ta waya da naga qawaye na da na yi a whatsapp da facebook suna yi, ana samu sosai in ka riqe amanar mutane, sai kaga ka samu riba mai yawa kana daga zaune" "Yauwa Addana na gode sosai, sai wata magana kuma mai mahimmanci da nake so mu yi ni da ke, ina son ki gane Mama Bilki mace ce mai kirki tana matuqar son mu, sai dai tabbas tana kishi da Goggo, wanda wannan dole ne a zaman kishiyoyi dama,shiga wannan kuma ba hurumin mu bane mu kau da kai akan wannan mu bar su su yi kishin su after all miji ɗaya suka haɗa,abinda kawai za mu yi shine mu yi masu biyayya dikkan su a matsayin su na iyayen mu," Shiru Saudat ta yi domin maganar qanwar ta ta yau tana shigar ta dan gaba ɗaya ba qarya a ciki amma akwai nau'i na girman kai da taya Goggon su kishi a zuciyar ta,dan haka sai ta yatsuna fuska ta ce, "Hmmmm zan duba maganganun ki na gani" Sannan ta miqe ta d'akko mata kud'in da ta alqawarta zata bata ta bata, duk abinda ya faru akan idon Goggo Sarai ya faru, sai dai bata ji kalaman da suke yi ba ta dai ga an bawa Salma kuɗi,magana take cikin b'acin rai, "Habaaaa Salma ai innice ke yanda na canja uwa, yan uwan ma canja su zan yi, auhoooo ba zaki iya canja yan uwa ba saboda su masu arziqi ne Zaki yi roqo za a baki , amma ita uwar ki tinda talaka ce shi yasa ki ka sauya ta" " Ni fa Gogga ba haka bane, ya kamata ki buɗe idon ki ki gane inda gaskiya ta dosa, ki daina rufe idon ki ki na yin abinda bai kamata ba" "Rufen baki sallamammiya kawai, an yi asiri da tuggu kala2 an raba ni dake, to ki je nima na huta da dawainiya da ɗan wani" Juyawa ta yi tabar wajen Salma kuwa cikin qunan rai da baqin cikin halayya ta uwar ta ta shige d'akin Mama Bilki, wadda ta ji komai da ya faru, fad'awa kan cinyar ta  Salma ta yi tana kukan takaicin hali irin na uwar tasu, shafa kanta kawai Mama Bilki take, bata furta mata komai ba,cikin kuka Salma ta ce, " Mama ni fa ba kwad'ayi ne ya sa na tambayi Adda Saudat kudi ba, na tambaye ta ne kawai saboda ki na ganin ko tirare bani da shi, ga shi yanzu sai da alimun ko lemon tsami nake amfani a hammata ta a madadin tiraren,da ace ina sana'a yaushe zan zauna haka? Tunanin da na yi na ina sana'a kudin zasu taimakan wajen kula da abinda ke ciki na da ni kai na shine ya sa na tambayi Addah Saudat kuma ta bani dubu biyar na ja jari, shine Goggo take fad'an maganganu marasa daɗi akai na da abinda ke ciki na" " Hakuri zaki yi Salma uwa ba abin wasa bace, dole mu yi mata biyayya matsawar ba sab'on Allah a duk abinda ta sanya mu,dan haka ki yi hakuri, to tin da kin samu jarin yanzu me zaki na yi na siyarwa?" Tashi zaune Salma ta yi ta share hawayen ta sannan ta ce, " Mama Bilki ni da ina son na fara saida gishiri da omo da ɗan qulle qulle na gida, amma yanzu da na samu wannan kud'in mai yawa sai na ji ina son in fara Saida Meatpie, naga kina da injin yin taliya, kuma na kula kayan flour ana cinikin su, in ba su ba ban san me zan iya yin sana'a akai ba kuma" Murmushi Mama Balki ta yi sannan ta ce, " Hakan ma shawara ce mai kyau, Allah ya sanya albarka a ciki" " Ameen mamana" Kwantar da kanta ta sake yi a jikin ta ita kuma tana shafa gashin kan Salman a hankali. ****************************** Yau kusan sati ɗaya da kwana uku kenan Suwaiba na kwance tana jinyar qirjin ta da aka fafe wa albarkatun wajen, Alhj Salihu dayaga zata farka sai ya danna mata allurar bacci ta koma, ko ya shaqa mata wata powder ta koma baccin, a haka ta yi wadannan kwanakin,shine yake yi mata wanka ya canja mata kaya,sannan ya saka mata ruwa da allurai na kashe zafin ciwo da anti biotics,ya zama babban likita kawai a cikin gidan shi dan ya kula da Suwaiba, a haka sai da ya kula wajen ya warke tas sannan ya kyale ta da allurai na bacci da yake mata. Ranar da ya bar ta kuwa bai yi mata allurar baccin ba da ta farka sai ta ji kan ta kamar an ɗora mata abu mai nauyi, da kyar ta tashi daga gadon ta ta isa gaban madubi a hankali ta d'aga rigar ta ta na kallon qirjin ta, nan take wasu hawaye masu azabar zafi suka hau zuba a kuncin ta, ina dukiyar Fulanin ta suke ne, me ya same ta? Duk abinda take yi akan idanun Alhaji Salihu take aikata su, cikin rashin k'warin jiki ta koma ta kwanta a Saman gadon nata tare da nitsar da kan ta cikin pillow kuka take yi sosai mai taɓa zuciya, zama ya yi a gefen ta ya kama hannun ta ya na lallashin ta, a hankali ta d'aga kan ta ta na kallon shi,da kyar ta buɗe baki ta ce masa, " Sweet wai me ya same ni ne, wanne mummunar qaddarar ce ta hau kirji na ni suwaiba ?" " Shiiiiiiii kar ki na yin magana sosai, hatsari muka samu a gidan, yan fashi  ne suka suka shigo a ranar da ki ka dawo kina bacci suka yanke maki nono, ni kuma dana dawo na ganki kin suma shine na kai ki asibiti aka maki aiki daga nan na dawo da ke gida nake ta kula da ke" A firgice ta miqe daga kwanciyar da take ta ce, " Dama abinda ya faru kenan? Yanzu tsabar rashin imani su rasa me za su cire min sai wannan waje mai daraja?" Ta fada tare da zaro idanun ta da ke ta zubar da zazzafan hawaye, cikin kukan nata ta ce, "Na shiga uku ni Suwaiba,ya zan rayu ba mahaifa ba nono,yanzu nan gaba me zan rasa kuma, Alhj na fa san kai ne sanadin rasa nono na  ba wani 'yan fashi,Saudat ta fad'an min ban ji ba ban yarda ba, saboda ina son ka, ko da ina son kudin ka na yarda cewa a yanzu ina son ka so na gaskiya,zan iya rayuwa da kai ko ba mahaifa shine hakan  be ishe ka ba sai da ka qara da wata kadarar tawa yanzu ta ya zan rayu ba nono ba mahaifa" Rushewa ta yi da wani irin kuka mai ban tausayi, cikin tausaya mata Alhj ya fara magana" "ki yi hakuri Baby yau zan........" katse shi ta yi cike da bala'i ta ce, " Kar ka sake kira na da wata baby again, i hate u Alhaji, na tsane ka, na tsane ka da dikkan rayuwa ta" Kukan ta ci gaba da yi mai ratsa zuciyar mai tausayi kai har da mara tausayin ma,matsawa ya yi ya kamo ta jikin shi, da sauri ta zame ta ci gaba da cewa, " Kar ka taɓa ni azzalumi kawai,ka kuskura ka sake taɓa ni ni ma sai na yanke maka inda ba zaka taɓa amfanuwa ba a jikin ka" Cike da matsanancin fushin da bai taɓa sanin suwaiban da yake wa kallon doluwa na da shi ba ta yi maganar,nan take wani irin shakkar ta ta shige shi, miqewa ta yi cike da jiri zata fita, cikin sassanyar murya Alhaji ya ce mata, "Ina zaki je kuma" "Gidan mu zani, na gama auren ka, na kuma gama aure a ABUJA har abada daga yau,daga rana mai kamar ta yau bani ba Abuja" " Lallai ma Suwaiba, abinda baki sani ba shine, ba inda zaki qara fita ko nan da can ne kuwa sai da sani na, dan kuwa ni a yanzu ba zan iya rayuwa ba ke ba, kin ga kuwa sai ki shirya zama da masoyin ki na gaskiya, na amince ni zan jure rashin albarkatun qirjin naki tunda ni ne sanadi" "Za kuwa ka mutu dan ba abinda zai hana ni barin gidannan, ko kana so ko baka so sai na bar gidan nan, in ka barni na tafi lafiya ba hukumar da zan haɗaka da ita, amma in ka hanani ba abinda zai hana ni haɗaka da hukuma zaɓi ya rage ya naka" Wani shu'umin murmushin rainin hankali ya mata ya ce, "To ai baki san wani abu ba, qungiyata babbar qungiya ce suwaiban,ni ɗin ba wai qaramin mutum bane ko baki gani bane?manyan gwamnati da yan kasuwa ba wanda babu a cikin qungiyar mu, ba yanda za ai ki had'a ni da hukuma kuma a samu hukunta ni din, mata kalar  ki da wanda suka fiki komai sun fi dubi kuma mun masu wannan aikin balle ke, dan haka hakuri zaki yi kawai mu qarasa rayuwa dake a haka, in kin tafi wa zai na baki abun daɗin da nake baki? wa zaina debe maki kewa? wa zai zauna dake babu nono? Hakura zaki yi kawai mu zauna a haka tun da kuɗi ki ke so ni kuma zan ci gaba da jiyar dake daɗi da dukiya ta" Tallabo wuyan ta ya yi ya na kallon fuskar ta,iya kuwa gaba ɗaya ta qame ta dauke kan ta daga ganin shi hawaye kawai ke zuba mata, ga wani irin tsoron shi da ke kwance a qasan zuciyar ta, yau ya zata yi ta kub'uta daga hannun wannan azzalumin? Kuka ne ya kwace mata sosai, key din motar shi ya ɗauka ya fice ya bar mata gidan, anan inda take tsaye ta durqushe tana kuka mai ban tausayi. ***************************** Talle kam ya saka marka a tsaka mai wuya ita da yayan shi, dan baya son maganar ta fita waje shi yasa bai ce masu qala ba,sai kawai ya fito da wata mugunta, gonar shi ta daji mai shegen nisa ya ke sa su zuwa gyaran ta, duba da cewar damuna ta kusan zuwa, a cewar shi ya na da majiya qarfin zuciyar cim amana irin su ba abinda zai sanya shi biyan kud'in gyaran gona,in sun ga dama in sun shiga dajin ma su ci amanar shi ya yafe masu amma tabbas sai sun gyara masa gona kafin damina ta sauka. kullum can suke tafiya ba abinci ba ruwa, amma shi zai je a machine din shi da abincin shi da ruwan shi ya yi shawagi ya sa ido ya ga ya aikin yake tafiya,su kuma su Baban gida gonar shi ta can wani qauyen dake kusa da su ya tura su, saboda ya yi yarjejeniya da su akan hakan, in ba haka ba ya kaisu birni ga hukuma a huhunta su akan yi wa 'ya'yan shi ciki da suka yi,da jin haka suka amince suka yi biyayya suma. Kan kuce me Marka ta fita hayyacin ta, 'yan mazaunan nan da ake kad'awa ana jan hankali da su duk sun zube, duk ta dame qashi ya fito mata ko ta ina,mutanen gari kuwa sai gulmammaki suke yi akan abinda ke faruwa a gidan Talle, kowa da ruwayar shi akan abinda ke faruwa amma ba wanda ya san gaskiyar lamari. Kowa ya rasa gane dalilin Talle na aikata haka, da damar mutane sai suka alaqanta hakan da tsantsar rashin mutuncin shi, su Huwaila kuwa kullum sai sun yi surfen abinda za ai tuwo da shi sun dake da hannun su sun mayar dashi gari, sannan su yi tuwon da za a ci a gidan, ga aikin qannen su da ya ɗora masu, walaka ta yi masu yawa kamar zata kashe su,ga qaramin ciki suna fama da shi. Jummala ce ta fito daga d'akin su da rarrafe saboda azabar ciwon cikin da ya sako ta gaba sai  murqususu take yi, cikin tsawa Talle da ke zaune ya na sauraron rediyo ya na aswaki zaune Saman tabarma ya d'aga kai ya kalli Jummala ya ce, "Ke meye hakan zaki zo kina ma mutane kuka, kin gama aikin da na saka ki ne?" Cikin kuka da tashin hankalin da take ji a jikin ta ta buɗe baki zata yi magana sai maganar ta maqale ta kasa fita,wani abu ta ji ya taho da gudu zai fita ta qasan ta, jini ne ya tsinke mata, nan da nan ta faɗi a wajen tasuma tsabar azaba, a gigice Marka ta yi kan ta,shi kanshi uban gayyar ya tsorata da ganin jinin da ke zuba a jikin Jummalar,daukar ta ya yi a hannu ya ɗora ta a kan machin ɗin shi, marka ma ta hau ta riqe ta, asibitin qauyen suka kai ta, bayan bincike da gwaje gwaje likita ya tabbatar masu da b'ari ta yi, sakamakon ta sha wani magani na zubda ciki, ga kuma jini yaqi daina zuba a jikin ta, suna buqatar a sai mata jini a qara mata zasu yi iya qoqarin su su tsaida jinin, Talle ne ya kalli matar shi ya ce, " Sai ki fito da kud'ad'en da kike ajewa na tarin auren su ai mata magani ko" Ya qarasa maganar cikin haɗe fuska, kallon shi ta yi ta sunkuyar da kai da sauri, duk wanda ya hanta a wannan yanayin bai san halin ta ba zai ce zalintar ta mijin ta ke yi, a sanyaye ta ce, "To bari na koma gida na d'akko" Dan rashin mutuncin Talle ko duba halin da Jummala ke ciki bai yi ba haka ya na gani Marka ta taka a qafa ta d'ebi hanyan jiki duk ya mace mata ba wannan cikar da take yi da izzar nan. Kafin ta isa gidan ne ma likitan ta fito, take sanar da Talle Jummala dai babu ita, sakamakon shan maganin zubda ciki da ta yi ba bisa qa'ida ba shi ne ya yi sanadin zub da jini mai tarin yawa a jikin ta, kuma sun kasa tsaida jinin har rayuwar ta ta qare, dafe kai Talle ya yi, nan take nadamar rayuwar shi ta baya ta baibaye shi, kuka yake kamar qaramin yaro, nan suka samu wani mai machine d'in ya taimaka masa ya nemo mai motar da zasu kai ta gida, mai machine d'in kuwa tasha yaje ya samo masa motar, Tallen ya biya shi kud'in ya masa godiya, a motar aka maida su gida shi da gawar Jummala, Marka na shirin fotowa ta koma asibiti taga an fito da gawar Jummala, zubewa ta yi a qasa ta hau kuka da bori tare da kururuwa....... [04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA    💅🏼      WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 25: Tun fitar Alhaji Salihu da safe suwaiba ke zaune tana ta saqa da warwarar neman mafitar yanda za ta kubuta a gidan amma shiru bata samu mafita ba,ta yaya aka yi ta rasa albarkatun qirjin ta? Ko dai da gaske 'yan fashin ne suka yi mata wannan ta'asar, anya kuwa ba maganar Saudat bace gaskiya Alhaji ɗan qungiyar asiri ne masu tsafi da sassan jikin bil'adama? Waɗannan tambayoyin da ma wasu tunane tunanen ne suka haɗu suka yi wa suwaiba yawa ta yanda ko sallah bata tashi yi ba balle ta nemi abinda za ta ci duk tsawon lokacin nan. Shi kuwa Alhaji Salihu yana can ana sa toka sa katsi tsakanin shi da Oga Zaks akan wata yarjejeniya da suka kulla wadda ko Alhj Kalla bai san da ita ba,kafin Oga zaks ya amince za su bar suwaiba a raye ba za su kai ta d'akin duhu ba dodon tsafi Itama ya zuqe Jinin ta bayan an yanke nonon ta, sai da Alhaji Salihu ya ɗauki alqawarin idan ta warke an kwana biyu zai kai wa Oga Zaks ta yi sati biyu wajen shi, wannan yarjejeniya ce ta d'aga masa hankali har ya je wajen Ogan nasu dan a bincika idan akwai wani abu sassauqa a sassauta masa ya aikata,dan kuwa a wannan karon ba zai iya bada matar shi a Kai wa wani qaton ya na kwana da ita ba ko da na kwana ɗaya ne balle har tsawon sati biyu,ya kamata a kyale ta haka ta wahala kuma shi fa yana son matar shi yanzu. Duk bayanin da Alhaji Salihu ya yi wa Oga Zaks sam ya qi aminta da shi,yace shi fa bai san zance ba, nan da sati ɗaya zai buqaci a Kai Masa ita in dai ya na so dukiyar shi ta dore ba tare da ya samu matsala ba, dan kuwa idan har bai kai masa ita ba duk abinda ya same shi shi ya sani ya kuka da kan shi kar ya ɗora laifin akan kowa, hankalin Alhaji Salihu a tashe ya koma gida. Zaune ya tadda ita ta fada dogon tinani ba ta ma san shigar shi parlourn ba, qarasa wa ya yi ya zauna kusa da ita a doguwar kujera, a hankali ya zame ya ɗora kan shi a cinyar ta ya rufe idon shi, cikin kulawa da tsoro ta fara shafa kanshi sannan ta ce, " Alhjna me ya faru? Me ke damun ka haka? Dan Allah ka barni na koma gida na amince zan rufa maka asiri ko dan darajar son da nake yi maka, ba wanda zan sanar da halin da ake ciki ni dai ina so rayuwa ta ta tsira" Bai bata amsa ba sai ma hawaye da ta gani ta gefen idon shi suna sauka, hawaye ne na nadamar shigar shi wannan qungiya da ya yi tun farko a rayuwar sa, dan yanzu soyayyar Suwaiba ta yi masa yawan da ta sanya shi farkawa daga baccin son abin duniya da yake yi,duk  da ya san ita har yau tana nan akan bakan ta na son cin daula,matsala ɗaya wannan babban rashin kadarar qirjin ta da ta yi ya sani da zata samu wata damar da zata zauna da shi ko dan kud'in shi, a hankali ya ce, " Baby ki kwantar da hankalin ki akwai maganar da zamu yi dake yanzu, wadda na san kin sani an kuma sanar dake gaskiya tun kan ku dawo son abun duniya ne ya rufe maki ido ki ka sake dawowa," Tashi zaune ya yi da kyau suna fuskantar junan su ya riqe hannayen ta ya fuskance ta suna shaqar nunfashin junan su, kanta har juyawa yake saboda tsoro, tana matuqar jin tsoron ya tabbatar mata da abinda Saudat ta faɗa duk da ta ga manyan alamu a yanzu,tun da gashi ya yi nasarar maida ita Nonoless and mahaifaless,tinanin ta ya katse ne a daidai lokacin da kalmar da take matuqar jin tsoron tabbatuwar ta ta daki dodon kunnen ta, " Ni Alhaji Salihu ɗan qungiyar shan jini ne, domin samun kuɗi ɗaukaka da qarfin iko" Wani irin ihu suwaiba ta kurma ta dafe qirjin ta da yake a shafe kamar na matashin saurayi,miqewa ta yi jiki na rawa kamar mazari dan ta nesanta kan ta da shi amma jiri da duhun da take gani sun sanya ta komawa ta zauna ,lallai maganar Saudat ta gama tabbata a yau, maganar zargi da waiwai ta qare,hannun ta ta kai jikin fuskar shi dan ta taɓa shi ta tabbatar shi ɗin ne kuwa ko dai wani ne ke tsokanar ta dan kawai a hana ta cin daular da Alhajin ya tara? shi kuwa ya na jin hannun ta a fuskar shi sai kawai ya dora hannun shi saman nata, saurin zame nata hannun ta yi tare da rushewa da kuka sosai, cikin kukan tace,. "Me yasa ka ke sanar dani wannan mugun labari yanzu? Me yasa tun kafin aure baka sanar da ni ba na nemi wani mai kud'in na halal na aura na ci dukiyar shi da gaske ko da kuwa kullum safiya duka na yake yi? Ka sanar da ni ne yanzu saboda sun ce ka kai ni yanzu a yanken qafa ta ne ko hannu, Ko kuma kaina suke so a yanke yanzu kai kuma ba zaka iya kai ni ba? Me yasa ka zaɓi shan jinin mutane ka yi kuɗi? Ina da son kuɗi da son abun duniya sosai na sani, amma ba zan iya kashe mutum domin samun su ba, son kuɗi da abin duniya tane ya sa Saudat tana sanar dani na rufe ido ƙwaƙwalwa ta ta toshe zuciya ta ta rufe na qi yarda, mene ne hukuncin da ka yanke yanzu akaina har ka ke sanar dani wannan mummunan maganar?" Shi kan shi Alhaji Salihu hawaye ne ke zuba daga idanun shi,tabbas so ba karya bane ba, yanzu ya gane ya na son  suwaiba so mai tsanani, cikin muryar lallashi ya ce, "Babe Dan Allah kwantar da hankalin ki" "In kwantar da hankali na, ta yaya kenan? Bayan wannan mummunan labarin da ka sanar da ni ka ke tsammanin kwanciyar hankali daga gare ni? Ta ya ka ke tsammanin in sake yarda da kai da duk wani abu da zai fito daga bakin ka?" Ta qarasa maganar ta cikin matsanancin kuka mai cin rai, a idon ta kuwa ba wanda take hangowa sai Goggo Sarai, ta yi dana sanin kasancewar ta uwa a gare su a yau, da ace ta basu tarbiyyar mai kyau irin wadda ta dace da basu zama masu son abun duniya ba, da idon su bai rufe da son  kuɗi ba har su nemo mazaje masu yin kuɗi da sassan jikin mutane su aura har a dinga bata alamu sannan afito fili a sanar da ita abinda suke aikatawa duk da haka ta yarda ta sake dawowa saboda tsabar son abun duniya. Yanzu gata a cikin babbar matsalar da bata san ta yanda za ta yi ta kub'utar da kan ta ba. "Wayyoo Allah na rayuwa ta, yanzu ya zanyi na ci gaba da rayuwa kun riga da kun nakasa min rayuwa? ka fad'a min yanzu a wanne matsaya ake dan na tabbata wani abun aka sake buqata a jiki na za a yanke shi yasa ka damu ka ke sanar da ni gaskiya, ka faɗa min menene kuke buqata kuma a waje na yanzu !" Da sauri ya share hawayen da ke kwaranya a idanun shi sannan yace, " Ogan mu ne da muka yi yarjejeniya da shi akan in ba a kashe ki ba zan kai masa ke har na tsawon sati biyu ,shine yake da buqatar ki ko ya dauki fansa akaina, farkon zuwan ku ma sai da muka kai masa ku kuka zauna a wajen shi na tsawon sati biyu ya  huta da ku, a cewar shi Kuna da wani sirri na musamman wanda ba ya da misali, wannan shine dalilin da ya sa ya ce na kai masa ke a madadin alfarmar rashin kashe ki da ba ai ba " Wani ihun kuka Suwaiba ta sake sanya wa sannan ta miqe  ta hau kan Alhj salihu ta na duka tun qarfin ta, qarshe da taga ko gezau bai ba sai ta kife a wajen tana ta rusar kuka ta na fad'in, "Kaico na ni Suwaiba, kaico na, na shiga uku,yau ina zan saka kaina, ga abinda son abin duniya nan ya jawo min, a yau duniyar ta juya min baya, bata riqe ni a matsayin masoyiya ba kamar yanda na so ta, yanzu ni aka kaiwa dan shan jini har tsahon kwanaki goma sha huɗu bai biya sadaki na ba, sannan yanzu da aure na za a sake Kai masa ni na tsawon wasu kwanaki goma sha huɗun,lallai ni suwaiba yau na ga yanda rayuwa a Abuja take," Qanqame ta Alhj ya yi yana shafa bayan ta da sigar lallashi, fizgewa ta yi cikin son jin qarashen labarin nasa ta ce, "Uhumm ina jin ka? Kana nufin kai masa ni ɗin za ka yi shiya sa ka zo kana sanar da ni wannan mugun labarin ko me?" Da sauri Alhaji Salihu ya ce, "Ko ɗaya suwaiba ba inda zan kai ki, da ina so na kai ki ai ba zaki sani ba ma zan kai ki, da da muke diban jinin ku dik wata sani ku ka yi?" Zaro ido ta yi kamar su fad'o qasa dan firgita da tsoron shi, baya ta fara ja ta durqusa a guiwowin ta ta na kuka ta ce, "Dan son ka da annabin rahama kai yi min rai kar ka qarasa ni,dan kuwa yanzu ni da mamaciya bamu da maraba, banda mahaifa, banda nono, jini na duk wata ake kwasa kamar a teku, an kaiwa wani qato ni ya gama kwana da ni kamar wani miji na, yanzu kana shirin maida ni sai ta Allah kuma, ina ga sa'i na ne ya zo,Allah ka ji qai na ni suwaiba" Matsawa ya yi zai riqe ta ta ko falla da mugun gudu ta yi d'aki ta na ihu, kan ya isa ta fara qoqarin rufe qofar,ya yi saurin saka qafa ya tokare, ihu ta zunduma tana bashi hakurin ya yi mata rai ta tuba, ya maida ma baban ta ita, dan yanzu ta tsani Goggo Sarai shi yasa ko tunanin ta bata yi ba, ya taimaka kar ya tsotse mata sauran jinin nata da ya rage, tura wa ya yi da qarfi ya janyo ta jikin shi cikin ɓacin rai ya ce, " Ke! Ki nutsu dalla malama kar ki taran mutane ni, in da zan kai ki da tini  ban kai ki ba ko kuwa sauran duk sanin an je ki ka yi? ba sai yanzu dana sanar dake bane ki ka sani? Na faɗa maki ne saboda ina son na maida ki gidan ku da kaina, in yaso duk abinda zai min ya min, na sadaukar da rayuwa ta domin taki ta tsira, Suwaiba wannan shine iya adadin soyayyar da nake maki, ina son ki suwaiba zan iya sadaukar da rayuwa ta saboda taki ta tsira" Ya qarasa maganar shi a hankali wanda ya sa jikin ta yin sanyi, qanqame shi ta yi tana kuka sosai,Itama ta ce, "Ba na son na rasa ka Alhajina, nima ina son ka sosai, ban san sanda na fara son ka ba nima, a da kam tabbas kud'in ka nake so, amma yanzu kai nake so, bana son abinda zai raba mu" Jin kalaman ta ne ya sanya Alhj Salihu kuka kamar wani yaro,haka so yake,shi  SO ba ruwan shi da girman ka ko qanqantar ka in ya shige ka yana saka aikata abinda ba hurumin ka bane aikatawa, haka suka yi ta kuka ba mai lallashin wani, ba su ankara ba sai kiran sallan farko suka ji na asuba, kasancewar dama bai dawo gidan da wuri ba tun safe da ya fita. Suwaiba tashi ta yi daga jikin Alhajin nata jiki duk ba k'wari,yau ce rana ta farko a rayuwar ta da ta yi alwala dan wani abu na damun ta take son ta roqi Allah akai dan ya yaye mata damuwar ta. Shima Alhaji daya ga haka alwalar ya yo, ya kabbara salla ta na bayan shi suka yi nafila,suka hau addu'a akan Allah ya yafe masu, ya gafarta masu zunuban su, ya kubutar da su daga wannan al'amari da suka tsinci kansu a ciki, bayan sun idar da addu'ar ne suka yi sallar subh  suka tashi suka hau gado, bacci mai nauyi ne ya dauke Alhj amma ita kuwa inaaaa yaushe taga na barci ana shirin kaiwa matsafi ita, lallabawa ta yi ta buɗe wajen da take aje kud'ad'en da yake bata ta d'iba, ta dakko akwatin ta ta loda kayan ta a ciki, ta fita ta dauki makullin mota babbar ciki a motocin shi,Saida ta loda kayan ta a ciki sannan ta hau ta nufi gate mai gadi ya buɗe mata ta fice ta bar gidan a guje. Hanyar kano ta ɗauka duk da cewar bata gama gane hanyar ba ta tabbata zata iya kai kan ta gida,haka suwaiba ta dinga bin rubutun Sunayen garuruwan da ke kan hanya tana shara gudu a Saman titi har ta isa cikin garin Kano Haka ta isa gida a firgice, Alhj kuwa bai farka ba sai azahar, miqa hannu ya yi dan ya tab'o Suwaiba yaji wayam, bai kawo komai ba a ran shi dan ya zaci ta shiga toilet ne, komar da kan shi ya yi ya lumshe ido,tunani yake ya kamata ya haɗa mata kaya ta tafi gida in yaso duk yanda suka yi da Oga Zaks daga baya ya dawo da matar shi, miqewa ya yi zai shiga toilet din in ma wanka take suyi tare ya na shiga yaga wayam ba kowa a ciki, fita ya yi palour nan ma bata nan, leqa kitchen da sauran dakunan ya yi yaji shiru bata nan, a hargitse ya fita waje wajen gate man ya ce, "kai Audi ina Hajiya?" " Alhj ta fita da kaya da motar ka babbar tun da sassafe" Cike da damuwa ya hau shafa kanshi, komawa ciki ya yi zuciyar shi cunkushe da tunani kala kala,shin ya take a yanzu, ta samu nasarar isa Kano lafiya ? Tinda iya sanin sa bata gama kware a tuqi ba, gashi a yanzu tana cikin halin tsoro da firgici, kar wani abu ya je ya same ta a hanya. Ɗaya bangaren na zuciyar shi ya ji haushin yanda ta iya guduwa ta bar shi ba tare da sun yi koda sallama bane,ta san ya na son ta ba zai bari wani abun cutarwa ya sake rabar ta ba, kuma Itama  ya ga soyayyar shi a tare da ita. Wayar  shi ya dakko ya hau kiran ta dan ya ji ina take idan kanon ma ta gudu ya ji shin ta isa lafiya ko ta na hanya ne bata isa ba,wayar na ta ringing bata d'aga ba, hakura ya yi da Kiran ta ya je ya yi wanka ya yi sallahr da ya jima da dena yi sannan ya fita ya bar gidan. Qarfe uku na rana a qofar gidan su ta yi mata, hankali tashe ta kashe motar  ta buɗe ta fada gidan tana kuka, da sauri Salma da Saudat dake tsakar gidan suna murza meatpie din da Salma ke sana'ar shi a yanzu suka je za su taro ta, sai dai ganin ta shiga da uban gudu ne ya sa suma suka so kwasa da gudu amma suka yi ta maza suka tsaya, tsayawa suka yi suga me ya koro ta shiru ba wanda ya biyo ta,ta na qarasa shiga ta fada jikin Salma tana kuka tare da fad'in , "Na shiga uku Salma na halaka kai na da kai na, Saudat kinyi gaskiya Alhj da kanshi jiya ya tabbatar min shi ɗan qungiyar asiri ne masu shan jinin mutane da tsafi da sassan Jikin su, duba ku gani yanda aka maida ni mata maza" D'aga masu rigar ta ta yi suka ga yanda qirjin ta ya koma babu komai fayau kamar filin ball,a daidai nan Goggo Sarai ta fito cike da tashin hankali sakamakon jin abinda Suwaiban ke fada............ [04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 ' YAN ABUJA 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 26: Kamar yanda mata da dama ke kokarin kyautata wa mazajen su ta fannin kula da gida, kula da kawunan su ta bangaren tsaftar Jikin su, mahallin su da ta Yaran su, ya na da kyau su ma maza a same su da kula da tsaftace Jikin su da duk abinda ya kamata su yi dan faranta wa matan su rai da tabbatar da cewar matan su sun dawwama cikin son su da qaunar su tare da burge su,ba ya daga cikin adalcin zamantakewar aure ace koda yaushe mace itace za ya yi ta kokarin faranta wa mijin ta rai tare da neman mallake shi shi kuma miji ya zauna ba ya wani yunqurin burge abokiyar rayuwar shi. Wannan dalilin ne ya sanya Jabeer zuwa aski aka wanke masa qafar shi tass, duk da a baya kafin Juwairiyya ta samu ciki ita ke wanke masa qafafun da har sai sun yi karr da su kamar na jinjiri saboda ta na amfani da kayyakin da muke da su na yau da gobe wajen gyara qafa, kamar su lemon tsami,baking soda,gishiri kaɗan, toothpaste na kamfanin Colgate sai zuma, ta na haɗe su waje ɗaya ne ta juya ta shafe musu qafafun su da shi idan ya kai minti 15 sai ta wanke masu da soson wanka da ruwa mai d'umi ta tsane masu qafafun su idan sun tsane ta shafe su da man kad'anya da ta haɗa da man kwakwa da man zaitun. Hannun shi riqe da qaramar ledar da ya siyo mata shaving stick da sweets ya shiga gidan,duba wa ya yi bai ganta a parlour ba,direct d'aki ya shiga dan ya san dole ta na can idan bata zaune a parlour ko tsakar gida ko kuma wajen Innarmu,ya na shiga kuwa ya gan ta a d'akin,cike da mamaki ya kalle ta ya ce, "Yanzu baby idan ki ka yanke fa? Na ce ki jira a yi sallah na je aski na dawo zan taya ki tunda yanzu ba ki iya yi da kan ki amma kin kasa jira na, kuma kin san reza sai dai ta ji maki ciwo amma still ki ke yi da kan ki,ni ban san me yasa yanzu ki ke kin jin magana ta ba,bani nan" Kwalla ce ta taru a Idon ta ta miqa masa rezar hannun ta ya Karb'a ya ajiye a gefe sannan ya rufe qofar dole na koma parlour na zauna zaman jiran masoyan. Bayan mintinan da baza su wuce biyar ba Juwairiyyah da Jabeer suka fito sai tura baki take ita a dole fushi take yi an yi mata faɗa, ba tare da Jabeer ya kula ta ba ya wuce wajen murhu inda ta ɗora ruwan da ta ke haɗawa na tsarki shi ya ɗauka ya juye a babbar buta ya surka mata daidai yanda zai ɗauke ta ba tare da ta ji zafi ba ya miqa mata. (Abinda ake tafasawar sune kaninfari ,ganyen magarya, lalle kaɗan da ɗan gishiri sai ganyen garahuni) Jabeer gani ya yi ta karɓi butar kanta na kallon wani waje ta na tura ciki gaba da baki murmushi ya yi dan kuwa ya san ba halin ta bane, ta fara yi masa irin haka ne tun sanda suka gano ta na ɗauke da ciki, abu kaɗan za a yi mata ta yi Fushi,dan haka cikin sigar lallashi ya ce, " Haba Juwaireren Mama Juwaireren Yah Jabeer, me kuma ya faru, me kk so na yi maki? Ni ne na yi maki faɗa? To yi hakuri kin San fa ni gaba ɗaya bana jin daɗin rasa murmushin nan naki mai kwantar min da hankali,ni fa da ki hana ni murmushin ki gwanda ki hana ni ruwan randar sanyin nan idan na dawo daga kasuwa a gajiye" Murmushi ta saki ta na qunshe dariyar ta ta shige band'aki ta yi wanka ta gyara Jikin ta yanda ya kamata sannan ta fito, gani ta yi ya gama kashe wutar da ta hura ya deb'i garwashi a kasko ya sanya masu turaren wuta sannan ya fito ya kama hannun ta ta sauka daga tudun band'akin, alwala ta yi sannan suka wuce d'aki tare ba tare da ta ce masa komai ba, sai dai wannan karon fuskar ta sake take babu wani b'acin rai a tattare da Ita. Sai da Juwairiyyah ta shirya cikin kayan bacci sannan ta ɗora after dress d'in ta ta sanya hijabi ta tada sallahr ta, ta na idarwa ko azkar bata yi ba ta kalli Jabeer da ke zaune a gefen gado ya na latsa waya ta tashi da kyar ta kwanta a gefen shi ta hau kukan shagwab'a ta na fad'in, " Baby ni agwaluma nake son sha fa, ka samo min agwaluma" Cike da kasala Jabeer ya zuba mata idanun sa yana kallon ta, dan kuwa a gajiye yake amma ba yanda zai yi dole ya yi mata abinda take so ya san ba yin kanta bane,ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce mata, "Kin tabbata ita kike so yanzu?" Ya qarasa maganar shi yana shafa cikin ta, saurin kauda kai ta yi gefe,dan kuwa kallon nashi na ratsa ta da yawa,bata so ma ya bata tausayi tace ta fasa dan kuwa muguwar sha'awar agwalumar take yi, d'aga kai kawai ta yi alamar Eh agwalumar take so, murmushi ya yi ya miqe tare da ajiye mata wayar shi a gefen ta ya tashi ya ja rigar shi ya sanya ya na fad'in, "Bari na je na kawo maki kada sai sun tashi ki sa min kuka ki ce baki hakura ba sai na nemo ta" Murmushi ta yi na jin daɗi, Jabeer ya sunkuya ya sumbaci goshin ta sannan ya bar gidan dan zuwa nema mata abinda ranta yake so tun da akwai inda za a samu ɗin a unguwar tasu, jabeer na daga cikin irin mazan nan da ke bawa matan su mahimmanci sama da danna wayar su ko wani abu a rayuwar su. Jabeer bai dawo ba sai da ya samo wa Juwairiyyah agwalumar kalar wadda take so mai zaqi,zama ta yi ta sha ta qoshi,shima ya ɗauki ɗaya ya sha ya na ta yamutsa fuska kamar an mare shi, kafin daga baya ya miqa mata duka ya ce, "Gashi nan ki yi ta fama," Dariya ta yi ta karɓi abunta ta yi masa godiya,gidan ya je ya rufe tare da tofe ko ina da addu'a sannan ya dawo ya rufe qofar palourn su, ya na zama ta tashi ta nufi d'akin baccin su Jabeer Shima ya kashe fitila ya bi bayan ta. ****************************** Fad'uwar Goggo Sarai ce ta ja hankalin su Suwaiba suka yi kanta gaba ɗayan su da gudu,kwance take magashiyan a qasa ta na bin su suwaiba da kallo kamar waɗanda suka sake sabuwar halitta a Jikin su, (ai ba qarya Hajiya Goggo suwaiba kam ta sauya halitta lols) idonta a buɗe hawaye na zuba ya wanke mata fuskar ta take qoqarin yin magana amma ta kasa,da karfi ta sa hannun ta ta toshe bakin ta ta sake fashewa da sabon kuka sai kace wadda aka aiko wa da rasuwar iyayen ta a qauye. Ganin halin da take ciki ne ya sanya Mama Balki daure wa ta isa wajen ta da sauri, dan ta kula gaba ɗaya yaran nata kallon ta kawai suke ba wanda ya yi yunqurin d'aga ta daga qasa, d'aga ta ta yi da kyar ta kai ta kan kujerar dake daf da bakin qofar shiga d'akin ta ta zaunar da ita,sannan ta tafi cikin hanzari ta ta deb'o ruwa a randar sanyin ta ta miqa mata a cup, kasa shan ruwan ta yi tana ta kallon Suwaiba da ta haɗe girar sama da qasa, qarshe ma sai ta yi hanyar d'akin Mama Bilki. Kuka ne ya k'wace wa Goggo Sarai da ta ga gaba ɗaya yaran ta duk sun bar wajen ma sun yi dakin kishiyar ta da ta dasa musu tsanar ta a ransu tun suna 'yan qanana,sai gashi tun ba a je ko ina ba yau ita suke nuna wa soyayyar su, wani gululun baqin ciki ta hadiya ta kalli Mama Bilki da ita ɗaya ce a kanta ta kauda kai taci gaba da zubda hawaye har wannan lokacin ta kasa magana. Baba ne ya yi sallama ya shiga gidan,Mama Balki ke da girki ranar dan haka can ya nufa zai shiga,sai dai kukan da ya ji ana yi a d'akin Goggo Sarai ne ya tsaida shi, sai da ya tabbatar da gaske kuka yake jiyo wa kuma da alama na Goggo ne sai ya wuce d'akin nata dan ya ji me ke faruwa. Ko da ya shiga sai ya tadda su Mama Balki a d'akin,ba kalar magana da lallashin da bai yi wa Goggo ba dan ya ji me ya sanya ta kuka amma ta ƙi magana,iyakar abinda Mama Balki ta sani ta sanar da shi sai kawai ya fita ya koma d'akin Mama Balkin dan ya tabbatar da maganar ta na cewar suwaiba ta dawo. Ya na shiga ya tarar da suwaiba na kuka da sauran 'yan uwan ta, " Suwaiba ke nake gani a gidan? Meke faruwa ne wai na ga kuna kuka? ku sanar dani damuwar ku yarana, duk da banda arziqin da zan maku maganin ta amma Allah ya hore min bakin yi maku addu'a akan ko meye matsalar ku" Suwaiba ce ta je gareshi da gudun ta ta rungume shi, shima rungume ta ya yi a Jikin shi, nan da nan lokacin yarintar ta da tashin ta kafin ta girma ya dawo zuciyar mahaifin nasu,suwaiba kuka take mai ban tausayi,Baba ya kyale ta bai d'ago ta ba sai da ta yi kukan ta ya ishe ta sannan ya zame ta a Jikin shi ta zauna a qasa a gefen qafar shi,a hankali Baba ya ce, "Sanar da ni damuwar ki d'iyata,ku zo duk ku fad'an damuwar ku na ji ko zan iya yi maku maganin ta" Cikin shassheqar kuka suwaiba ta ce, "Baba.... Baba ka yafe min, Baba ka yi hakuri akan qin jin maganar ka da na yi abaya,Baba nadama ta same ni a qurarren lokaci...." Da sauri Baban su ya dakatar da Ita cikin tausayawa ya ce mata, " Ah ah Suwaiba karki ce haka, lokaci bai qure maki ba 'yata" Da sauri Itama ta katse shi ta hanyar d'aga rigar ta ta ce, "Baba duba ka gani" Cikin kukan da take yi ta juya wajen Saudat tace, " Saudat nuna masa cikin ki kema ya gani" Saudat ma nuna masa cikin ta ta yi dai-dai inda aka yi masu aiki aka cire masu mahaifa,. "Me ke faruwa ne ku buɗe baki ku yi min bayani" Baba ya faɗa cikin tashin hankali saboda ganin da ya yi Suwaiban su ta zama Nonoless, "Baba mazajen da muka aura ta dalilin mugun son kud'i da abin duniyar tare da zuga da muka samu daga Goggo ashe 'yan qungiyar shan jini ne, Baba matsafa ne masu yin kuɗi da sassan jikin mutane" Suwaiba ta qarashe maganar ta cikin qunar rai da d'acin da take ji a wuyan ta, a tsorace Baban su yace, "Suwaiba ! Ki ka ce me? Shan jini fa Suwaiba, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Ya Allahu ya rahmanu wannan wace iriyar rayuwa muke ciki mai cike da rud'ani da tashin hankali? Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Zama ya yi ya dafe kan shi da yake jin ya yi masa nauyi sosai,ya jima a haka kafin daga baya ya ce, " Sanar dani me ya sami qirjin ki da kuma gefen cikin ku gaba dayan ku ke da yar uwar ki?" Kwashe duk abinda ya faru ta yi ta faɗa masa, cikin kid'ime wa da tashin hankali ya miqe ranshi ya gama ɓaci da jin abinda ya samu yaran shi, duk ta dalilin matar shi da ta kasa taimaka masa wajen ba yaran shi tarbiyya, ficewa ya yi a d'akin ya nufi d'akin Goggo cikin sauri kamar zai faɗi tsabar damuwa da tashin hankalin da yake ciki, da wata iriyar murya Baba ke wa Goggo Sarai magana ya ce, "Shikenan yanzu hankalin ki ya kwanta, Saratu hankalin ki ya kwanta nace an maida min Yara marasa haihuwa, ba zan taba ganin jikokina ba ta bangaren su kenan,saratu bana manta wa ke da kan ki ki ka yi kutun-kutun ɗin da ya sa ki ka tsaida haihuwa, wai yaran sun ishe ki, wace irin mace ce ke? Da baki yi haka ba da na tabbata zuri'a ta tafi haka yawa a yanzu,Ki duba kiga Suwaiba an yanke mata nono gaba daya, banda jinin yaran nan da ake diba duk wata, tsahon wata takwas, ina zaki kai alhakin su saratu? Ga mahaifa an cire masu babu su babu haihuwa fa kenan" kuka ne ya k'wace wa Baba bai san sanda hawaye suka fara zuba a idanun shi ba ya na kallon Goggo da kallon tsana da danasanin zaɓen ta a matsayin uwar Yaran shi,babu wanda baya kuka a gidan hatta Mama Bilki hawayen tausayin yanda rayuwar gidan na su cikin qanqanin lokaci ta koma take yi. Goggo ta kasa cewa komai, bakin ta rawa kawai yake yi saboda kuka, sai zata yi magana sai ta ji bazata iya cewa komai ba sai ta sake rushe wa da kuka, Suwaiba ce ta katse su da cewar, " Baba ina neman izini a wajen ka ka barni na yi mana d'aki a ta can wajen, dan ba zan iya ci gaba da zama da Goggo a d'aki daya ba ko kusa da d'akin ta" Wani irin murmushin takaici Baban su ya yi yace, " kin ji ko ? Kin ji dai da kunnen ki yau 'Yar ki ba zata iya zama dake ba a d'aki ɗaya ba saratu ? Kar ki damu Suwaiba, wannan kud'in bai kamata ki yi amfani da su ba, kamata ya yi a bada sadakar su, ina da qasa da ciment da komai dama ina da aniyar yin d'aki saboda ku idan kun kawo mana ziyara tinda na kula rayuwar ku ta sauya nima dole na sauya maku d'aki ko da bai kai na masu aikin ku a can ba,sai kawai muka tashi babu neman izini na na fita na dawo na ga ta riga ni,har tana yi mana taqama da fankama tare da gore-gore akan Yaran ta su 'YAN ABUJA ne matan masu kuɗi,dan haka yanzu da kaina zan gina maku d'akin naku" Juyawa ya yi ya fita dan ba zai iya zama a gidan ba ya na gani Goggo Sarai b'acin rai na sake lullub'e shi,kamar abun wasa bayan kwana uku da yin maganar sai ga Baban su ya fara haɗa qasa da kan shi dan gina wa Yaran nashi d'aki tinda dama aikin shi ne,nan da nan Suwaiba da yan uwanta suka haɗu suna taimakawa mahaifin nasu da duk abinda za su iya,suna tsaka da aikin Ammar ya taka dugui-dugui ya isa wajen su ya deb'o qasar a hannun shi ya miqawa Baban su, dariya suka yi gaba ɗayan su, a haka Ammar ya zama shi ne ke saka su nishad'i har yamma ta gabato sannan suka tashi suka bar wajen dan wanke Jikin su da yin alwalar sallar magariba. Mama Bilki ko tana can tana masu girki har ta kammala,Hajiya Goggo mai jiran gadon tafiya Makka kuwa ba wanda yake kula da yin ta yanzu a gidan tun bayan dawowar suwaiban,babu mai kula da kukan ta balle a lallashe ta. Gaba ɗaya sun maida hankali akan gina d'akin da zasu nesanta kan su da ita, dan kuwa har sun ɗora foundation, gaba ɗayan su tattare wa suka yi suka zauna bangaren Mama Bilki, wadda yau kusan kwana uku da dawowar suwaiba duk yanda za ta yi ta nuna masu rashin dacewar abinda suke yi ta yi amma sun qi jin maganar ta. Yauma a babban faranti Mama ta zuba masu abinci kamar kullum, kowa ya saka hannu har Baban su suka fara ci, Mama Bilki ce ta miqe Baba ya kalle ta ya ce, " Ina zaki kuma Gimbiya?" " Baban su zan je na kira Yaya ne, mu ci abincin dika" Gaba ɗayan su yaran sai suka zare hannayen su a abincin suna kallon ta tare da turo baki alamar basu yarda ta kirawo Goggo Sarai ba, "Ai sai ki zauna ko? Tun da dai kin samu amsar ki a wajen Yaran dan haka zauna mu ci bincin mu" Koma wa ta yi ta zauna jiki duk ba kwari,haka suka gama ci suka wanke hannayen su suka sha ruwa, wanke farantin Saudat ta yi ta ajiye a kwandon wanke-wanke ta dawo suka zauna suna ta hira, suna wasa da Ammar, " Mama Ammar ya girma ya yi wayo sosai" In ji suwaiba da ke kallon shi cike da soyayyar da bata taɓa zatan haka ake ji akan 'yan uwa wanda aka fito ba daga ciki ɗaya ba, a zaton ta 'yan d'akin su ne kaɗai 'yan uwan ta da zata so bayan su ba wata soyayyar d'an uba, Goggo ce ta yi murmushi ta ce, " Aiko dai kinga dik sa'annin shi ya fisu girma da wayo, har yaron maqotan nan namu da ya bashi wata biyu Ammar ya fi shi wayo" "Lallai kam ga alama nan na gani" Mama Balki ce ta nisa kafin ta ce, " Suwaiba, Saudat, Salma ina so ku bani hankulan ku nan dikan ku" D'aga kai suka yi a tare suka kalle ta jin yanda ta ambaci sunayen su alamar babu wasa, amsawa suka yi gaba dayan su suka zuba mata ido,cikin kwantacciyar murya Mama ta ce, " Ina son na baku shawara a matsayina na uwa, sannan ina son ku duba abinda zan faɗa maku da da kyau da kuma Kyakkyawar zuciya kuma ku qoqarta ku yi amfani da shi, kun ga da farko dai uwa ba kamar ta a rayuwar duniya, Allah ya ce abi shi sannan abi iyaye, Annabin rahama ya jaddada bin uwa sau uku kafin ya kira sunan uba, dan haka ni ina son ku yafe ma mahaifiyar ku abinda ta yi maku, tabbas bata kasance uwa ta gari ba wadda take bawa yaranta tarbiyyar da musulunci ya tanadar, amma ta baku so, ta nuna maku qauna, na uwa da yaranta, in kun kula ita a tinanin ta tayi abinda ya dace daku da rayuwar ku ne, amma koma dai menene ina son ku sani, wanda bai yafe ma wani ba, shima ya ji tsoron kar Allah ya qi yafe masa nashi laifukan, dan haka nake mai baku hakuri a madadin ta, ku taimaka ku yafe mata, kar ku ja wani ciwon ya kama ta dan Allah na roqe ku" Cikin kuka sosai suka matsa kusa da ita suka rungume ta, Suwaiba ce ta yi magana a cikin su ta ce, " Mama Bilki ke alkhairi ce a rayuwar mu, ki yafe mana abubuwan da muka yi maki a baya, tabbas mun cutar da ke da kalaman mu, da ayyukan mu, bamu zama yara masu biyayya ba, ki yi hakuri ki yafe mana" "Indai nice na yafe maku, sai dai har yanzu baku ce min komai game da Yaya ba?" Salma ce ta amsa masu dan Suwaiba da Saudat har yanzu akwai d'aci da wata irin qiyayya da suke ji game da mahaifiyar tasu, amma sun sani dole su yafe mata, su yi hakuri da abinda ta yi musu, "Mun yafe mata Mama Allah ya yafe mana mu ma" "To ya kamata yanzu ku je ku sanar da ita kar ta kwana cikin damuwa, na kula ko bacci bata iyawa tun ranar da ki ka dawo gidannan suwaiba" Suwaiba ce ta yi saurin miqewa ta ce, "Ni dai Mama ba zan iya zuwa yau ba, dan Allah kar ki tirsasa ni yin abinda ban jin zan iya yin shi a yanzu" Ta qarasa maganar ta cikin kuka,baba ne ya ce, "Bilkisu Allah ya miki albarka, amma ki bar su haka, zuqatan su cike yake da qunci akan abinda ta yi musu, daga baya a hankali komai zai warware masu" "To Baban su Allah ya kaimu lokacin, Allah kuma ya sanyaya zuqatan ku ku yafe mata gaba daya har kai ɗin ma" Amsawa suka yi dika da, " Ameen" Hankalin Goggo kam ya kai qololuwa wajen tashi da jin hirar Yaran nata da kishiyar ta da ta tsana nan take ta fara ganin wani irin duhu ya na lullub'e mata ganin ta,qoqari take yi ta buɗe ido da kyau ko ta yi magana amma ta kasa a hankali ta ji kan ta na juyawa har duhun da take gani ya mamaye ganin ta baki ɗaya ...... [04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼   'YAN ABUJA  💅🏼 WRITTEN BY HERMEEBRAERH Page 27: Kuka kawai talle yake ya kasa tsaida hawayen shi tsabar yanda mutuwar Jummala ta dake shi, wannan rayuwar da iyalin shi suka yi a baya ko kuma suke yi ya tabbata ba wanda ya ja ma su ita face shi, mugayen halayen shi ne da yi ma yaran mutane sakin wulaqanci da zinace-zinacen shi ne ya dawo masa ta haka. Yau gashi an wayi gari tsabar lalacewa Yayan shi uwa ɗaya uba ɗaya ke neman matar shi ta sunna, Yaran yayan shi na neman na shi yaran, kaiii jama'a wannan wace irin musiba ce ta sauko mana a wannan zamani, Marka kam irin kukan qabilun nan ta dinga yi, ta yi girgiza ta yi girgiza sai ta kwarara ihu sai kuma caaan ta yi dif ta cigaba da gyad'a kai,itama abun ya shige ta sosai ba kadan ba, jummala ta mutu sakamakon yunqurin zubda ciki, ga Hawaila tana kallo a gaban ta da ciki dan kuyat ya fito a gaba,nata farkan kuwa na can gefe ya na jinyar dukan da ya sha, wace irin rayuwa suka jefa kansu a ciki ne ita da mijin ta da Yaran ta dika? Maqota kowa ya zo ya yi gaisuwa sai ya tafi babu mai zama wai da sunan zaman makoki, ko sun shigo yada magana ne yake kawo su, wasu daga ciki ma cewa suke yi, " Tohhhh abinda ya faru kenan hmmmm Allah dai ya jiqan ta amma zunubi kam an kwasa" Ire-iren kalaman nan ne ke fitowa daga bakunan mutane suna yi suna kyab'e baki, wasu kuma bayan sun yi gaisuwar sai sun dora da cewa, "Laaa ikon Allah kamar ciki nake gani a jikin Huwaila, ni dai bani da labarin auren ta, sannan mun san ba a shan ciki a ruwa, hmmmm Allah ya kyauta,gidan Talle kenan gidan ban mamaki, uwa ba kwab'a uba babu hantara" Kusan kowa ya zo da abinda zai furta kafin ya tafi,baqin ciki kamar ya kashe Haule saboda ji da ganin munanan abubuwan da ke faruwa,wai yanzu nan ne gidan uban ta, gidan da babu tarbiyya ba kwab'a, banda Allah ya kare ta Itama da duk haka zata taso a lalace tinda duk abinda ke faruwa a gidan kenan,yanzu gashi wannan mummunan baƙin fentin ya shafeta, ai kuwa da an gama arba'in guduwa zata yi qauyen da ta ji wata qawar Marka da ta zo da jimawa ta faɗa acan mahaifiyar ta ke aure, qauyen baida wani nisa yana nan kusa da su ne,dan da alama idan ta ci gaba da zama a gidannan ko mashinshini rasawa za ta yi balle manemin aure, in ko ta koma can ko sunqi karb'ar ta ba zata dawo nan ba dole su sanya za su yi da ita. kwalla ta share ta ja hanci, tana kallon su cike da tsanar halayen su, tashi ta yi daga wajen da su Marka ke zaune ta yi shigewar ta d'aki,addu'a take ta yi ma 'Yar uwar ta a ranta na Allah ya yafe mata, Yayan Talle kuwa bayan jinya da zaman d'aki ya jawo masa har da gudun abun kunyar da ya tafka gani yake mutanen waje sun sani, wanda bai sani ba ba wanda ya san ya na neman Marka a waje maganar iya cikin gida ta tsaya dan babu mai zamar yin kirari ya dab'a wa cikin shi wuqa a cikin su . Duk maza da ke zama a majalisar qofar gidan su Talle sun sauya wajen zama,tabarmin da aka shimfid'a domin zaman makoki ba mutane akai da an gaishe su ake wucewa daga Baban gida da Badamasi sai Talle a wajen, Talle kuwa mugun haushin Yaran yake ji sai kallon su yake ya na jin kamar ya je ya shaqe su, amma haka ya dinga haɗiyar yawun baƙin ciki dan kuwa a irin iskancin da ya aikata a duniya ko kwata basu yi ba ya san sakayya ce yake Karb'a da hannun hagu tun a duniya. Basu tashi a wajen ba sai bayan la'asar,Talle tashi ya yi ya hau nade tabarmar da yake kai sannan ya shiga gida fakam-fakam ya tsaya a kan Huwaila, kwalama su Baban gida kira ya yi, a tare suka isa tare da jingine tabarmar da suka zauna akai kan su a qasa kamar munafukai, cikin b'ata fuska Talle ya ce, "A cikin ku waye me cikin Huwaila?" Badamasi  ne ya nuna Bangis da sauri, shi kuma Bangis sai ya qara duqar da kai qasa,kallon su Talle ya hau yi daga sama har qasa cikin qunar rai ya ce, " Yanzu yarannan wai har kunyi girman yi wa wata ciki? Ko dake maganar wai kun yi girma ma bata taso ba tinda ga misali kun bayar, kun yi sanadin mutuwar ɗaya ga ɗaya nan da tambarin abin kunyar da zai bi zuri'ar mu har abada, dan haka sai ka bari ta haihu a maku aure kun reni ɗan shegen cikin gidan da kuka samar tare," Ita dai Marka bata cewa umm bare A'a, ta yi dif sai hawayen nadamar rayuwar su ke fita daga idanun ta, a cikin zuciyar ta tana ayyana wannan lamari ba laifin kowa bane face na shi, daya tsaya ya tsare mata sha'awar ta da buqatun ta da bata yi zina da auren ta ba. Ni kuwa na ce wannan ba hujja bace ga matan da suke ganin dan mijin su baya sauke haqqin shi akan su bari su bazama neman mazan waje, ko su fara aikata wani abun da ya kauce hanya, su sani Allah zai masu hukunci dai-dai da abinda suka aikata ne shima mijin Allah zai masa hukuncin abinda ya aikata,dan haka ni a ganina ba dabara bace aikata Zina da aure, wadda ke da matsala da mijin ta ta bangaren auratayya ta gaggauta neman mafita ta hanyar shari'a ko sulhu ita da mijin su rabu ta nemi wani, ko ya bi duk wata hanya ta halal da ya san zai katange ta daga fad'awa haram,bai halatta ta faɗa halaka ba da sunan rashin kulawar miji mu kiyaye. Miqewa marka ta yi zata shiga d'akin ta, Talle ya dakatar da ita,cikin muryar da Marka bata taɓa zato ba ta ji Talle na fad'in, " Marka ina neman yafiyar ki akan dikkan abubuwan da suka faru tabbas laifi nane, da na tsaya na zama namijin kirki da duk haka bata faru ba, ki yafe min mu dawo mu gyara rayuwar auren mu," kauda kan ta ta yi saboda kukan da yake neman cin qarfin ta ga wani haushin shi da take ji na jefa su wahala da ya yi, Yayan shi ne ya fito daga ɗan qaramin d'akin shi ya zube akan guiwowin shi ya na hawaye ya ce, " Talle qanina ka yafeni na biye wa son zuciya, da rudin shed'an na aikata mummunan abun da ko mutuwa muka yi sai yabi zuri'ar mu domin kuwa shi mugun labari kamar tusa ne a wajen bodari ba ya riquwa watarana sai ta fita, ka taimaka ba dan ni ba domin Allah da zumunci ka yafe min" kuka ya kifa hannayen shi a fuskar shi yana yi hakan kuwa ba qaramin bawa kowa tausayi ya yi ba har ta kai da Talle ya daga shi sannan ya ɗan daki kafadar shi dan shima kukan yake ji, kauda kai ya yi zai shige d'aki yaji maganar Yayan nashi na fad'in, "A gaskiya sai mun haɗu mun gyara rayuwar gidannan namu kan komai ya tafi mana dai-dai yanda ya kamata cikin tsari da tarbiyya irin ta islama, na farko sai Marka kin gyara yanayin shigar ki a tsakar gidan, dan kuwa yanayin yanda iyalin ka take yawo a tsakar gidannan ne ya jawo min matsananciyar sha'awar kasancewa da ita,haka za ka ga tana yawo ba isasshen kayan da ya rufe dikkan jikin ta, tana tafe tana juya dikkan jikin ta, sannan ga maganganun ta da na ke jiyo wa wanda yawancin su akwai sakin layi, ma'ana akwai batsa da watsewa a cikin su, wajen kallon ta da maganar ta bata kiyayewa, wadannan abubuwan sun ja ra'ayina matuqa ainin, dan haka in muna son mu samu kwanciyar hankali da kiyayewar zinace-zinace a tsakanin mu sai mun kiyaye,sannan sakewa yarannan da muka yi shima ya jawo wannan bala'i da muka shiga har ya yi sanadin mutumar Jummai, Yaran nan kan su ba su yin shigar arziki ga mazan da ba muharraman su ba a cikin gida,mu na ji za su dinga mugun wasa a tsakanin su ba ma hana wa a haka muna ganin ai 'yan uwan juna ne,to wannan sakacin namu duk shi ya jawo mana komai,Su ma kuma yaran mata kamata ya yi idan maza suka kawo maku hari irin wannan ku na sanar da iyayen ku da wuri gudun kar abun ya ci gaba har a samu matsala yarinya ta lalace a gaban iyayen ta,iyaye kuma idan yara sun kawo masu magana makamanciyar wannan su wayar wa da yaran su kai akan yanda za su kare kan su da kuma karb'ar maganar su dau mataki akai kar su hantari yaro dan gudun zubewar mutuncin mutumin da ke neman cin zarafin yaran nasu ko gujewa tonuwar asirin yaran su, a dinga ɗaukan mataki saboda rage faruwar haka a cikin al'umma" Talle ne ya amshe maganar da sauri ta hanyar gaskata yayan nashi,sannan ya basu tabbacin dawowar shi qauye da zama, don ya gama zaman birni kenan har abada, murna a wajen Marka kuwa da jin wannan labari mai daɗi ba a magana,sai dai ta bar wa ranta ba ta ce komai ba har wannan lokacin,a haka suka watse kowa ya kama inda zai yi cike da alhinin mutuwar Jummala. ****************************** A cikin sati uku Baba da 'yan taya aikin shi ko na ce 'yan taya hirar shi suka kammala ginin babban d'akin su suwaiban, da yake filin dama ya na da ɗan girma,sai dai kuma ba filasta ba fenti, sai ledar d'akin da suka fara shimfida qaton buhu a qasa sannan suka saka ta, katifa biyu suka yada, babba da qarama, sai kayan sawar su da suka kwaso suka zuba a ciki, d'aki yayi ba laifi, kullum dare Suwaiba sai ta yi kukan rashin mijin ta da kuma yanda ta koma mara amfani a cewar ta, yanzu wa zai aure ta a haka? Yaushe Salihu zai aiko mata da takardar sakin ta ko kuma ya zo ta gan shi? haka za ta yi ta saqe-saqe har bacci b'arawo ya ɗauke ta. Hajiya Goggo kuwa mai niyyar hawa jirgi a je Makka bata samu hawa jirba ta samu mummunan hawan jini, sakamakon sanya tinani da damuwa da ta yi a ran ta,ta riga da ta saba a Koda yaushe Yaran ta na manne da ita suna shan hira,amma yanzu tsakanin su gaisuwa ne kawai,Shima dan ta san Mama Balki ta matsa masu ne da ba za su gaida ta ba,in suka gaida tan suka tafi sai dai ta jiyo hayaniyar su da Mama Bilki tana koya masu abubuwa masu amfani a rayuwar su ta duniya da lahira, wanda ita ya dace a ce ta koyar da su tun farko,gefe d'aya kuma haka za ta ji suna wasa da Ammar kamar ciki ɗaya suka fito da shi, abun ba qaramin d'aga mata hankali yake yi ba,uwa uba Baba ya juya mata baya, baya kula ta, baya cin abincin ta ballantana kwana a dakin ta,Goggo ta je asibiti a kwanakin nan yafi sau uku, dan kuwa wata rana sai kawai tana zaune ta ji wani jiri da duhu ya mamaye ganin ta har sai ta suma, haka za su kaita a bata magani  su yi qoqarin da zasu yi akan ta, da ta farfad'o su sallame ta Baba ya maido ta gida, a kullum takan ce a cikin ranta, 'Oh ni Sarai naga duniya,  Yarana da nake taqama da su a idon duniya su suka juyan baya yanzu, Allah gani gare ka ka dawo da hankalin su kai na' Yau Goggo ta tashi da matsanancin ciwon kai, in da ta dinga kiran Suwaiba ta na zaune tana jin ta amma ta yi shiru, Mama Bilki ce ta leqo ranta a b'ace tace wa suwaibar, " Suwaiba kina son shiga aljanna kuwa? Mahaifiyar ki na kiran ki kina ji amma ki yi shiru? ki kiyayi Allah, ki kiyayi fushin uwa akan ɗan ta suwaiba, meyasa kk da ruqo ne, shi wancan mijin naki mai qaton ciki ba dan d'an kyaun da yake da shi ba meye abin so a wajen shi, duk da wahalar da suka jefa ku ciki kina nan kina faman son shi, kina begen shi sai uwar da ta haife ki ce Zaki kasa yafe mata? To na qara jin tana kiran ki kina ji ki zauna kiga ya zamu qare da ke a gidannan shashasha kawai,kin miqe ko saina kwad'o maki wannan murfin kwanon a ka?" A hanzarce ta miqe tana kallon hannun Mama Bilki mai riqe da kwano, shigewa dakin Goggon ta yi tana zumbura baki ta ce, " Gani" Ta ja ta tsaya a kan ta,a hankali Goggo ta buɗe baki ta ce, " Suwaiba nice fa Goggon ki abar son ki, Suwaiba ba dan Adam ɗin daya wuce kuskure a rayuwar shi na san na yi kuskure,amma yanzu na yi nadama ku yafe ni ke da yan uwan ki, na san ban zama uwa ta gari ba a gare ku,ko wannan ciwon da nake fama da shi ya ishen azaba suwaiba, kullum da ciwon kai nake kwana ba qaqqautawa, na rasa ya zan kuma duk na san sanadin juyan baya da kuka yi ne, a tinani na a da rayuwa mai kyau nake baku ashe ban sani ba ina tura ku ga halaka ne, dan Allah suwaiba ku yafe wa Goggon ku kun ji?" Kuka Suwaiba take yi sosai harda majina, kusa da goggon ta ta je ta zauna ta dora kanta a kan cinyar goggon ita kuma ta hau shafawa hankali, ba wanda ya qara cewa komai a cikin su, nan take Goggo sarai ta ji kamar ana zare mata ciwon kanta,damuwar ta na raguwa. **************************** Jabeer ne ya sauka a saman machine cike da matsanancin farin ciki, bakin shi washe ya kasa rufe shi kamar gonar audiga ya shiga gidan, qoqarin shi bai wuce ya ganshi a gaban mahaifan shi ba da matar shi. Cikin murna ya qarasa shiga bangaren Innarmu ya na kwala mata kira, sai dai abinda ya bashi mamaki be wuce ganin sashen nata wayam da ya yi ba an karo qofar sashen, bangaren su ya yi cike da doki da zumud'in ganin Juwairiyyah, durqushe ya ganta gaban ta robar da ta haɗa zuma da ruwan zam-zam ne da ta yi wa fatiha qafa bakwai, falaqi bakwai,nasi bakwai, da suratul ikhlas bakwai, sai Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla wa anta taja'alal hazna idhashi'ita sahla qafa bakwai tana sha tinda cikin ta ya yi wata takwas dan samun sauqin haihuwa, ta shan ye ya kai rabin robar tsabar azabar da take ji a Jikin ta, zufa kuwa sai karyo mata take ko ta ina, sai addua take tana qarawa, " Allahu Allahu Allahu rabbi la ushrika bihi shai'an wa huwassami'ul aleem" Shine abinda take faɗa tana maimaitawa, da sauri ya isa gare ta, ita kuwa ruwa ya fashe mata tana wani irin nishi na son ta sillub'o koma meye a tattare da ita, sauri ya yi ya juya ta daga durquson da ta yi sabida kar ta haihu a haka ta samu mummunan tsaga, zaunar da ita ya yi ta gaba ya koma bayan ta yana qoqarin taimaka mata, dan a yanda ya ganta da yanda suke karantawa shi da ita a wani littafi mai suna EVERY WOMAN ya san haihuwa ce ta zo, ba yanda zai ya fita da ita asibiti haka zata iya haihuwar a hanya. Suna haka suka ji sallamar Innarmu ta zo da kwad'on rama zata bawa Juwairah, "Ki na ina? Fito na samo maki ramar da ki ke so har na ma sa mata kuli na kwad'anta ta, ai ina zuwa gidan Iya mai rama na yi sa'a har zata fita talle na samu na samo maki" Jin nishin Juwairiyyah da maganar jabeer ne ya sanya Innarmu saurin shiga parlour ganin gwagwarmayar da ake yi ne ya sanya itama ta duqa ta hau taimaka masu, nan take Juwairiyyah ta fara yin nishi mai qarfin gaske........... [04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼   ' YAN ABUJA  💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 28: Duk qarfin ta ta tattara ta damqe hannayen Jabeer ta ci gaba da nishi, har babyn da ke cikin ta ta samu damar sako kai cikin duniyar tamu,cike da murna da farin ciki jabeer ya qanqame Juwairiyyah a Jikin shi ya na jera mata sannu ba iyaka, sai share mata zufar goshin ta yake yi,a hankali ya sumbaci kuncin ta,Innarmu na ganin haka ta haɗe fuska ta na ɗaukar yarinyar ta kauda kai irin na mutanen da masu kunyar nan ta ce, " Oh yarannan ba ku jin kunya ta sam, Jabeeru kalli yanda ka yi jagab da hawaye duk dan tausayin matar ka,ita kanta mai haihuwar ma ta yi jarumta ko kuka ba ta yi ba sai kai" Cikin dakewa da son boye halin da ya shiga na farin ciki bayan kukan tausayin matar shi ya ce wa Innarmu, " A gaskiya Innarmu ba abinda zan ce dake sai dai na ce kawai ubangiji ya miki rahama, ya sanya min ke a aljanna madaukakiya, ke kuma Juwairah Allah ya maki albarka, ya biya maki dukkan buqatun ki, ni Jabeer yau na qara alqawarin riqe amanar ki har qarshen rayuwata" kallon Innarmu ya sake yi ya ce, " Innarmu da ace mazaje suna shiga d'akin haihuwa da matan su su na ganin yanda mata ke k'ok'ari wajen fito da wata sabuwar rayuwar zuwa duniya tabbas da an rage mace-macen aure da wulaqanta mata, da maza sun daraja mata fiye da qima, Innarmu duba fa kiga irin wahalar da yarinyar nan ta sha, dan Allah Innarmu idan na taɓa aikata maki wani laifi ko na b'ata maki rai ba tare da na sani ba ko kuma na yi da ganganci ki yafe min, na yi alqawari daga yau zan zamo daga cikin yara masu biyayya," Nan take jikin Innarmu ya yi sanyi, dan kuwa tabbas ta san iyaye mata suna qoqari,bamu da abinda za mu yi musu da ya wuce muyi ta masu addu'a da qoqarin yi masu biyayya,a hankali Innarmu ta ce, " Jabeeru duk abinda ka fada gaskiya ne,kai d'a ne mai biyayya da kyautata wa ga iyayen shi da ma duk wanda Allah ya haɗa ka zama da shi, ba abinda ka yi min a rayuwa mara kyau da zan iya tunawa balle har na riqe a raina,kyautatawa ce kullum a tsakanin mu da kai Jabeeru, Allah ya yi muku albarka ya raya jinjirar nan cikin imani,ka ga yanzu yarinyar nan tana ta bushe wa, tashi ka je sashe na ka saka ganyen magaryar nan a ruwan zafin da na saka dan na yi wanka su tafasa tare saboda ya fidda dattin jikin yarinyar sosai,oh ni Hansai Jabeeru kazo ka dauki 'yar ma mana ka riqe matar ka kamar wani zai ɗauke ta magana nake yi amma hankalin ka na wajen matar ka" Dariya ya yi yana sosa qeya ya gyarama Juwairah zama sosai yanda zata ji daɗi sannan ya isa gaban Innarmu, kallon yarinyar yake da tsantsar soyayya irin ta uba zuwa ga 'yar shi, wani irin kyau ya ga Allah ya yi mata na musamman, wannan kyaun daga ina ta samo shi? juyawa ya yi ya samo amsar tambayar shi wajen juwairah, murmushi ya mata sannan yace, "Tabbas na samu amsar tambaya a fuskar ki, kyaun yarinyar nan duk naki ne Honey" Innarmu ce ta yatsuna fuska cikin rashin gane ne ya ce ta ce, "Meye wata Hamee ni ta shi ka dora ruwan ka dawo ko kuma ka gyara ruqon ta naje na kwaso na bangare na dana zuba d'azu dan na yi wanka,riqe ta na je na dawo" Gyara wa babyn zaman kanta ta yi dake a lankwashe a hannun Jabeer da bai iya ɗaukan jinjiraye ba sannan ta fice tana fad'in , "Yara ido ya bushe ba kunya, zamani duk ya canja iko sai lillahi ji yanda yaron nan ke abu kamar a fim din hindiya" Zuwa ta yi sashen ta ta zuba ganyen magaryar a ruwan ya ci gaba da tafasa sannan ta kwashe ta qara wani,ta taho da shi sashen Juwairiyyah,yarinyar ta Karb'a a hannun Juwairiyyah da Jabeer yake wa tsiya ta fara wanke wa, mamaki ne ya ishe ta ganin Jabeer na gyara Juwairah kamar ya san ya ake kula  da mai jego, "Sai wani tsokanar ta ka ke yi ta ji zuwa na ta na so ta ajiye yarinya, ba gwanda ita ba da sauran kunyar ta a Jikin ta,kai ni fa sai na bar maku wajen ku ku qarata, wannan rashin kunya har ina, wa ya koya maka yanda ake ma mai jego ni Hansai" Cikin dariya Jabeer yace, " Innarmu na koya ne a wani littafin anti-natal ɗin ta da na ke karanta wa lokaci zuwa lokaci, littafai ne da suka qunshi yanda ake renon ciki da haihuwa da kuma yaran kansu, da irin taimakon da uba zai ba uwa in ta haihu, ina fatan kin fahimta, baya daga cikin kyautatawa namiji ya bar mace ta yi ta wahala ita ɗaya bayan tare suka samar da abinda aka haifa ko za a haifa ɗin, yana daga cikin karamci da kyautatawa tare da soyayya namiji ya shiga dumu-dumu a yi komai da shi, hakan na qara ma ma'aurata fahimtar juna da so da tausayi, sai kiga aure ya dad'e ba fad'a ba yaji bare kai qarar miji gida" Innarmu gyada kai kawai take yi dan kuwa gaskiya Jabeer ya faɗa ,  amma fa gaskiya ita kunya suke bata, shiru ta yi kawai bata ce komai ba, Jabeer ne ya kammala gyara wajen ya tallabe Juwairah suka fita tsakar gida, kujera ya bata ta zauna ya fita wajen Innar mu ya deb'o ruwan zafi, ya shigo da shi cikin babban bokiti, ya raba biyu, ɗaya a babbar roba ɗaya na wanka, kai mata ya yi ya koma d'aki ya dakko ruwan kal fari ya zuba kamar murfi uku a ruwan da zata zauna din, ya je ya fara tayata wankan,cike da shagwab'a Juwairiyyah ta ce, " Yah Jabeer dan Allah ka bari zan iya yi da kai na,Innarmu fa na nan, ta yi shiru ta kyale mu ne  amma na san ba zata so ganin hakan ba,na san akwai fahimta a tsakanin mu da ita amma wani lokacin yawan zaqewar ka zai iya jawo min qiyayya wadda bana fata, ka je zan iya da kai na na gode, ina son ka da yawa" " ke ba abinda zata gani kar mu b'ata lokaci, maza bari na gama maki kan ta gama da Babyn mu ki ka sani watarana ba a gaban su Zaki haihu ba za mu yi rayuwa a inda daga ni sai ke kawai kin ga dole ai ni zan yi maki ko?, ya kamata ma muje asibiti a duba ki duk da na ji Innarmu ta ce ba ki samu wata matsala ba" A haka Jabeer ya kashe bakin ta da zance ya mata wanka ta zauna a ruwan ta ji daɗi sosai, ya koma ya qaro wani ya saka ta a ciki, ya qara ruwan kal din a ciki. ( ma'ul kal, wato ruwan kal yana wanke datti shima sosai, ya fidda qarni da warin HQ sannan yana matse mace, ya gyara ta, sai dai ba a so in ba kamar yanzu da aka haihu ba a cika amfani da shi, da shi da bagaruwa, baya-baya ake son amfani da su, dan kar su yi illa ma wajen, kuma ana son in ana amfani da su a yawaita cin fruits da veges da kuma shan zuma mai kyau da zam-zam, dan su zama sun saukar da ni'ima) Bayan sun gama wankan ne Jabeer ya fito daga band'akin sai ga Nafee ta dawo daga makaranta, shigowa ta yi da gudun ta, sakamakon kukan baby da ta jiyo, ai suna ido huɗu da Juwairah ta kwasa da gudu ta isa wajen ta ta rungume tana murna ta ce, "Sannu matar Yayah Allah ya qara maki lafiya ya raya mana abinda muka samu" "Ameen Nafee sannu da dawowa" Jabeer ne cikin salon wasa ya ce wa Nafee, "To malama sake ta haka ta ji da kanta" Sakin ta ta yi ta na dariya, bakin ya qi rufuwa kamar gonar audiga, d'aki Jabeer ya wuce ya bar su tsaye Juwairiyyah na takawa a hankali suna hira da Nafee za su shiga d'aki,su na nan tsaye Jabeer ya fito hannun shi riqe da zanin haihuwar ya aje mahaifar a cikin leda zai wanke zanin,Nafee ce ta yi sauri ta yarda jakar  ta a qasa ta ajiye mayafin ta a igiyar shanya tai wajen Jabeer zata karbe wankin, "Yah Jabeer barmun na wanke ni ban yi komai ba ai" " A'a sis basshi yanzu kika dawo daga school bana son ki wahal da kanki, kayan jini ne ke kuma baki son su suna sa ki jiri dan haka ki bari zanyi, bayan haka kin san Innarmu ta tsani wanki a kaf aikace-aikace ni me nake yi da ba zan wanke ba? Yanzu dai ita  Juwaireren Mama ta yi me wuyar da ta haifo mana queen of beauties, shiga ki ga inda ake kyau yarinya barakallah Masha Allahu" Ta na jin haka ta bar su a wajen ta yi d'aki dan kuwa sai ta ji ta qara kwadaita da ta ga yarinyar, tana isa ta zube gwaraf gaban Innarmu,Innarmu kuwa ta gyara yarinyar ta sha kwalli rambad'ad'au, ta yi matuqar kyau, idon ta bude fes kamar haihuwar sati, cikin zumud'i ta amshe ta tana yi mata addu'a Juwairah ce ta shigo da sallama d'aki,Idon ta na sauka akan jinjirar Itama ta hau tasbihi ga Allah tana matuqar godiya daya sauke ta lafiya ya bata Kyakkyawar yarinya kamar wannan, Mama Bilki ta sha addu'a yau a bakin Juwairah, kallon gefen ido take yi wa yarinyar saboda kunya,a ranta take ayyana; 'Ikon Allah ke nan yanzu da wanne ido zani gida na kalli Mama da Baba tinda dama dai su sun qi zuwa gidan nan saboda kunya, wai yau ni Juwairiyya ce na haihu" Shafa cikin ta tayi da ya yi mata babba kamar bata haihu ba ga nankarwa da ta ji yayi rad'o-rad'o, murmushi ta yi ta qara gode Allah, nan da nan ta hau shiri ta d'akko man kad'en ta ta shafe cikin da shi sosai ta mulke shi da man har sai da ta ji ta daina jin maiqon shi sosai a hannun ta, murmushi ta yi dan tunawa da yanda cikin nata ya sha gashi wajen Yah Jabeer don jinin ya samu fita ita kan ta mamakin yanda duk ya iya abubuwan nan take yi duk da ta san yana karanta littafan ta na rainon ciki amma bata zaci ya riqe komai akan shi haka ba, bayan ta gama murje cikin ne ta kwalama Nafee kira dan ta zo ta d'aure mata cikin, zuwa ta yi ko ta tamke mata shi tsam, kayan ta ta saka atamfa riga da zani ya mata kyau sosai, kalar atamfar ruwan kwai ce dika, sannan ta feshe jikin ta da turarika masu daɗin qashi ta fito parlour zata zauna,a dai-dai wannan lokacin Jabeer ya gama komai ya yi wanka shima ya shigo, sannu ta yi masa da addu'ar Allah ya saka masa da alkairi, ya yi murmushi yace, " Is my duty love, so ki daina damun kan ki da yi min godiya, amma fa bacci ya kamata ki yi bayan kin ci abinci yanzu" Murmushi ta yi masa wanda  tasan yana biyan komai a wajen Yayan nata, kad'a kai ya yi alamar zamu haɗu ne, ya wuce d'aki dan ya shirya. Ya na gamawa ya fita palour ya tadda su dika a zaune Juwairiyyah ta gama shan kunu da tuwon da ya sha man shanu, gyaran murya ya yi ya kalli Abban su ya gaida shi, dan kuwa yana shiryawa ya shigo shima a yi murnar zuwan jikar tasu da shi,Abbah ya yi ma yarinya addu'a, Nafee na ta masu tsiya shi da Innarmu akan tsufa ya qara kama su sun zama kakanni,miqa wa Jabeer babyn Abban su ya yi shima ya yi mata addu'a, sannan ya faɗi sunan da za a ana kiran ta da shi, wato Hafsat sunan Innarmu kenan, Innar mu har kukan daɗi sai da ta yi dan jin hakan, sannan yace ma Juwairah, "To ai sai ku nema mata sunan ku na yan gayu da na san dole sai kun saka mata," Nafee ce ta kalli Juwairah tace, "Matar yaya sai ki bamu suna ko?" Juwairah murmushi ta yi sannan ta shiga tunani,daga baya tace, " Na saka mata Abrar, wato mai tsoron Allah" " Oh ni Hansai yanzu ina ni ina iya fad'an wata Abras fisabillahi" Dariya suka kwashe da ita har  Abbah, Abban ne yace, "Haba Innarsu, yanzu Abrah ɗin ne zai gagare ki?" Haba me zasu yi in ba dariya ba dan shima kan shi Abbah ya kwafsa, gyaran murya Jabeer ya yi ya fara magana cikin tsantsar farin ciki da annashuwa tare da son sanar da su abin farin cikin  da ya same su yace, " Abba, Innarmu,Juwaireren Mama, and my little sis Nafeesa, ina mai farin cikin sanar daku ci gaban da ya same mu, a yau kuma a d'azu dana dawo na zo da labari me dad'i na samun aikin da na yi a NNPC na can Abuja in da suka ban gida dake kusa da gidan man da zan yi aikin, a unguwar Jabi har ma da mota, sun dauke ni a matsayin Manager na wajen gaba ɗaya, sanan kuma ɓangaren kasuwanci na yau na biya ta kasuwa, Saifullahi dana kan bari ya min jiran wajen in bana nan ya d'akko min kud'ad'e masu tarin yawa, da kuma wasu jakunkunan da na saro ba su iso ba daga malaysia , to a yau suka iso, har wasu yan kasuwan sun yi sari ma, shine ya bani kud'in da suka kai dubu dari biyu da talatin cif a hannuna, nan take na bashi talatin ɗin nayo gida da sauran gasu" Juye-juye ya fara yi yaga ina ya wurga ledar da yazo da ita, dubawa ya yi ya hango ta can hanyar shigowa inda ya yar ya iso wajen matar shi mai naquda, kasa kudin ya yi kashi biyu, sannan ya qara kasa kashi daya biyu, miqawa Abban shi ya yi kashi ɗaya, sai kuma ya ɗauki dubu goma ya bawa Nafeesa sauran dubu arba'in ya bawa Innarmu, yace gashi su sa mai albarka,Abbah ne ya ce, " Lallai wannan yarinya ta zama mabudin alkairi a gidannan, muna ma Allah godiya, nayi murna da farin ciki sosai na jin wannan abun alkairin daya same mu, Allah ya taya ka ruqo da gaskiya da amana, Allah ya qaro maka arziqi mai yawa mai albarka," Amsawa suka yi gaba ɗaya da, " Ameen" Innarmu kuwa kukan daɗi take ta yi tin da aka fara maganar, dan bata taba tunanin riqe kuɗi rabin wannan bama a lokaci d'aya dan tasan ba ta dasu, bata bawa kowa ajiya  ba,yau gashi an mallaka mata su,shi ya sanya take kukan farin ciki, ta ma kasa magana sai kukan murna take na ɗaukakar da Allah ya yi wa d'an ta a lokaci d'aya,Nafeesan ce ta ce, " Innarmu ki bar yin kuka, addu'a da sanya albarkar ki Yah Jabeer ya roqa a wajen ki" Juwairah ma sai murmushi take zabgawa a lokacin da ta sake kurbar shayin da Nafee ta hada mata mai kauri da d'umi, innarmu kuwa share hawayen ta ta yi tace, " Jabeeru ba abinda zance sai dai nace Allah ya qara maka albarka ninkin ba ninkin akan wadda ya maka, ina alfahari da kai a matsayin ka na d'a na, Allah ya kare min kai daga sharrin maqiya" Amsawa suka yi dikka, Nafeema ba a barta a baya ba wajen taya murna da godiya balle mai jego Juwairiyyah,kiran sallah ne ya karad'e wajen tare da duhun da ya bayyana hakan ya nuna masu cewar magrib ta yi, miqewa suka yi bayan sun gabatar da addu'a, suka yi alwala mazan suka tafi sallah matan suka yi a gida Juwairiyyah kuwa d'aki ta je ta kwanta, ana cewa ana bacci bayan an haihun ita dai gata nan ido biyu, bata sani ba ko dan ta na cikin matsanancin farin cikin samun aikin da Yah Jabeer ya yi ne ya sa ta kasa bacci? bayan ya dawo ne ya d'akko kaza a akurkin su, ya yanka guda biyu ya kaiwa Innarmu ya ce a dafa wa Juwairiyya,Nafeesa ce tace ita za ta yi dan ta san yanda take son ta. D'auka ta yi ta koma ɓangaren Juwairah ta d'akko ridin da suka daka tare , da madarar shanun dake aje a randar sanyi,sannan ta dakko kayan qamshin da suka niqo harda minannas a ciki ta gyara kayan miya ta soya sama sama ta tsaida ruwan dahuwar kazar kasancewar ta ta Hausa to fa dole sai an qara ruwa kafin ta dahu da kyau. Zuba wannan kayayyakin kamshin ta yi ta zuba kazar da ta gyara ta wanke ta yayyanka a ciki, amma banda madarar ta ajiye ta sai naman ya dahu sannan zata zuba, sai da farfesun ya dahu sosai sannan ta zuba madarar shanun, tana tafasa ɗaya biyu ta sauke ta juye  a mazubi Mai kyau ta kaima Juwairah mai jego. Godiya ta yi mata Jabeer na shigowa ya zauna zai saka hannu, Nafee ta riqe ta ce, " A'a Yah ga tamu can wajen Innar mu wannan nata ne, ita fa ta haihu ba kai ba, sannan na zuba mata maganin basir a wannan ka jira tamu" Dariya ya yi sosai har yana kama ciki ya ce, " Yarinya ni za ki yi wa qaryar? zaki yi bayani ne kice kawai Nafeesa na hada maki kayan da zaki warke da wuri to da kyau Allah ya baki lafiya,ke kuma me maganin basir ki dena qaryar,banqi ba in an hanani ci saboda ita ta haihu ta yi wahala ya kamata taci ta yi qat, amma batun ace wani maganin basir ne ma bai taso ba, in haka ne ai na fita basir ɗin nifa namiji ne zaman kasuwa waje ɗaya wasa ne?" Dariya suka dinga yi dikan su, Wajen jaririyar ya je ya ɗauke ta yana kallon ta yana mata wasa kamar gane wa take, wani farin ciki yake ji a ran shi, nan take ya hau yi mata hotuna, yana gamawa ya danna kiran Baban su Suwaiba dan  tun da aka yi haihuwar ya kira sau biyu bata shiga ba, sai ya sa a ran shi ko ba wuta an kai caji ne, shi yasa ya sake gwadawa. Su kuwa a can gidan Baba Baballiya duk suna zaune a tsakar gida gaba ɗayan su har da Goggo Sarai, duk da ba wani sake mata kowa ya yi ba sosai amma sun rage gudun ta, sallama ya yi ya sanar da shi haihuwar, cike da murna kowa ke amsar wayar suna gaisawa, Juwairah kuwa sam taqi karb'ar wayar wai kunya take ji, dariya suke ta mata Suwaiba tace sai gobe zasu zo, dik da mamakin da ke a zuqatan Jabeer da Juwairah har ma da Nafee Hakan bai hana su suma sakewa da ita ba suka yi ta hira. Bayan sun gana ne Juwairah ta ɗauki pillow da aka kawo mata dan ta zauna ta jefawa Jabeer, tana buga qafa cike da shagwab'a ta ce, "Ni baka fad'an zaka kira su ba kawai sai dai naji kana waya da Baba, kuma wai Babana ka ke iya fad'awa na haihu, wayyo ni Allah da wanne idon yanzu zan kalle su?" "Da idon da ki ke kallo na yanzu mana" A haka Juwairiyyah ta miqe da Baby Abrar suka wuce d'aki dan ta kwanta ta shayar da ita Itama ta ɗan rintsa dan kuwa yanzu ne take jin bacci na ratsa idanun ta......... [04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA. 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 29: Alhaji Kalla gaba ɗaya ya tattare hankalin shi ya mayar kan Alhaji Salihu da ke yi masa wata maganar da yake jin ba mai yiwuwa bace a gare shi,cikin nuna kafiya akan ra'ayin shi ya ce wa Alhaji salihun, " kai nifa ba qungiyar da zan bari gaskiya, habaawaa yo me ma aka yi da maza? har yanzu fa da quriciyar mu Salihu ko hamsin bamu rufa ba, akwai sauran rayuwa a gaban mu na tuba, me zai sa kuma mu katse rayuwar mu tun kafin mu more ta?" "Hmmmm Kalla kenan, kai abokina ne wanda na ke matuqar so saboda tare mu ka taso da kai tun mu na yara,kar ka manta dika iyayen mu da wasu daga cikin 'yan uwan mu mun bada su ta wannan harka, kana ganin zunubin bai isa haka ba? Tin da ba yanda za ai mu dawo da su? Ka duba fa in bamu tuba ba yanzu kowanne lokaci mutuwa na iya zuwa, ita bata sallama bare qwanqwasa qofa in......" Cikin haɗe fuska da taurin kai irin na mutane marasa rabon shiriya Alhaji kallah ya d'aga wa Alhaji Salihu hannu tare da fad'in, "Malam dakata, yau kuma da abin da kazo kenan? i am very sorry to disappoint you my friend, cos i am not ganna buy this shit, akan me ina tsaka da jin daɗin rayuwa ta kace na koma rayuwar talauci, bayan kasan sharad'in fita daga qunyiya mai da duk abinda ka mallaka ne dai-dai da allura ba a yarda ka ajiye ba ballantana ba ma za su ajiyu ba wuta ce zata cinye su ko ka manta me ya samu sauran mutanen da suka bijire wa qungiya? Idan na bar qungiyar me na tanada wanda ba daga qungiya bane kuma ka ke ganin ba zai kare ba ballantana na yi rayuwa mai daɗi ko bayan babu ƙungiyar? Haka siddan mad'alaqan kasa na koma almajirin qarfi da yaji? kan kuma ka fita kar ka manta sai an yi asiran rufe maka tinanin ka na gidan Oga da qungiya gaba ɗaya wanda a kallah zai kai nan da sati ɗaya, kai ka san dan mun riga da an bamu ɗaukaka a qungiya ne yasa akai mana wannann alfarmar da qananan yan qungiya ne kashe ka za ai ko da tinanin nan ka yi, ni dai ina nan kai kuma Allah ya taimaka ka fita lafiya, amma ka sani sisina ba zan taimaka maka da shi ba in ka talauce,amma kuma abotar mu na nan har yauma ta nade" Baza babbar rigar shi ya yi ya fice ya bar Alhj Salihu da tinani, wata zuciyar na kwad'aita mai ci gaba da rayuwar hutu, ɗaya ban garen na nuna mai illar hakan, in ya ci gaba da zama ɗan qungiya ya kai soyayyar Suwaiba kuma inaa? da ace ya rasa abar son shi gwara ya hakura da qungiyar nan Allah zai kawo mai wata hanyar, miqewa ya yi dan shima ya bar wajen, yana tashi kuwa wayar shi ta hau ringing, dubawa ya yi yaga kiran Alhj Kallah, tsaki ya yi kamar ba zai ɗauka ba, dan abin da ya masa d'azu ya sosa ran shi sosai, amma sai ya lallashi zuciyar shi ya d'aga dan yaji ko ya canja ra'yi ne zasu fita tare, yana d'agawa ya ji wata muryar daban da bai san ta waye ba, cikin mamaki ya ce, "Waye kai ina mai wayar?" "Ranka ya dad'e mai wayar Allah ya masa cikawa,yanzunnan ya samu hatsari da wata babbar mota hakan ya yi sanadiyyar fashewar kan shi nan take sannann qafar shi ta dama ta karye" Komawa ya yi Saman kujerar da yake kai ya dafe kan shi tare da Kiran Sunan Allah cike da jin tsoron Allah na sake huda naman jiki da b'argon shi ya furta. "Innalillahi wa inna ilaihirra ji'un" Itace kalmar da yake maimaitawa a bakin shi,qarar message ne ya maida shi cikin natsuwar shi,cikin tashin hanakali ya duba sai ya ga address ɗin inda Kalla ya yi hatsari aka turo masa, kamar wanda aka ma allurar bacci haka ya miqe ya na jin wani jiri ya na d'iban shi,tafe yake yana fad'in, " Allah na tuba ka yafeni, Allah ka gafarta min ni Salihu daga yau na yi alqawarin tuba daga zunubaina na daina harkar nan ko zan rasa raina ne" kuka yake yi sosai kamar zai shid'e a haka ya kai zuwa inda motar shi take ya tada ita ya yi inda aka kwatanta masa, wayar shi ce ta qara ringing ya miqa hannu ya ɗauka,Sunan da ya ga ya na yawo a Saman screen ɗin wayar shi ne ya bashi mamaki ko dai har maganar rasuwar Alhaji kallah ta riske shi ne? " Oga Zaks" Shine Sunan da ya karanta a Saman wayar tashi,tsaki ya yi ya d'aga cikin dakiya ya kara a kunnen sa, kafin ya yi magana Oga Zaks ya riga shi, " Salihu kaji abinda wani ya kira ni yake faɗa min? Kana ina yanzu haka,shin da gaske ne Kalla ya mutu?" " Ni ma ban sani ba sai na isa wajen na gani, ka kashe wayar na kusa isa ga mutane can dai an taru a wajen sosai" kashe wayar ya yi ya qarasa,halin da ya ga abokin nashi a ciki ya gigita ƙwaƙwalwa da tunanin shi dan haka nan take ya yanke jiki ya fadi, wasu ne a gefe suka taimaka suka watsa masa ruwa ya farfad'o,da rarrafe ya yi wajen abokin nashi yana kuka, riqe shi mutanen wajen suka yi suna bashi hakuri, umarni ya basu akan su taimaka mai su d'aga gawar akai masallaci mafi kusa a yi masa wanka da sallah a binne shi kawai,dan kuwa basu da kowa balle a ce sai an kai shi gida wajen dangin shi,haka ko aka yi, nan take mutane suka taimaka aka d'aga gawar Alhaji Kalla aka kai wani masallaci da ke kusa,waya ya zaro ya sanar da Oga zaks, jikin Oga zaks ya yi sanyi amma dake zuciyar ta dake ko kuka bai yi ba, sai dai ma kawai ya masa ta'aziyya kawai yace in an kai shi yaje yana son ganin shi, kashe wayar shi ya yi yace, "Ba dole ma na fita daga wannan muguwar ƙungiyar ba, ai ko ba komai Kalla ya yi wa qungiya hidima ya cancanci azo kan gawar shi a mai addu'a amma wai in an kai shi na je, ko baka ce ba zaka ganni kuwa" Share hawayen shi ya yi shima yabi bayan yan tsiratun mutanen da suka gama rife Kalla a makwancin shi na gaskiya,mota ya fada ya yi gidan shi, tattaro duk wata dukiya tashi ya yi, yaje ya dakko ATM cards din shi, da makullan motocin shi, da takaddun filaye da gidajen shi da kamfani da komai ya zuba a akwati ya wurga cikin motar shi, ya sa kai dan zuwa gidan Oga zaks, Haka ya shiga motar shi ya tuqa bai zame a ko ina ba sai qofar gidan Oga Zaks, yana isa a tsaye a ka ya tsaya ma Oga Zaks , cikin bacin rai Oga Zaks ya ce, "Ya haka Salihu zaka zo ka tsaya min akai kamar wani sanda" Duk wata dukiya da Alhaji Salihu ya tattaro ya zube ta gaban Oga Zaks cikin haɗe fuska ya ce, " Oga ina son barin qungiya ba dan komai ba sai dan ina son na koma tsaftatacciyar rayuwa na tsira daga azabar da Allah zai yi min,sannan abinda ya faru yau da Kalla ya qara min son barin wannan qungiyar" Nan take ya kwarorowa Oga Zaks duk abinda ya faru da Kalla da shi kafin hatsarin da ya yi, nan danan jikin Oga Zaks ya ɗauki rawa, qaton cikin nan kamar ana buga ganga haka yake qara da karkarwa, maganganun sun shige shi sosai sun bashi tsoro,cikin rawar murya Oga Zaks da ya zama shi ne ya qirqirar masu wannan ƙungiya ta shaid'an ya ce, " To salihu ba za ai haka ba ka fita kai ɗaya? Ni kai na na wa'azantu da wannan abinda ya farun,yau kuma a yanzu zan tara mutanen mu na sanar da su abinda yake faruwa kuma ni da kai mun shirya barin wannan ƙungiya ko da za mu rasa ran mu kuwa, zaɓi ya rage wa sauran,wanda yaga zai fita ya biyo mu, wanda yaga zai zauna ga waje nan, amma zan so ace yanda ni ne na assasa wannan qungiya na rusa ta da kai na, dan ko na tafi zunubin zai ci gaba da bina" Wani irin farin ciki ne ya lillibe Alhaji Salihu dan bai taɓa zaton hakan ba, ya zaci zai sha wahala kafin ya amince mai, waya yasa ya kira mutanen su baki ɗaya,kusan awa biyu suka ɗauka kafin kowa ya hallara, fuskar Alhaji Salihu da ta sha kuka ya ba wa kowa mamaki, nan take kuwa Oga Zaks ya fara zayyana masu komai, cikin qanqanin lokaci wasu da dama suka aje makaman yaqin su, wasu kuwa suna ganin ai su akwai sauran lokacin tuba,tsawar da Oga Zaks ya daka masu ce ta dawo dasu daga cece kucen da suke ta yi, cikin bada umarni ya ce, " Na yanke hukunci wannan qungiya rushe ta zan yi da hannu na kamar yanda na kafa ta, wanda ya sake kafata shi ya sani, amma ni kam na gama , dan haka daga gobe zan rushe ta, tsakanina da dodo ko kashe ni ya yi babu komai fata na shine na kubuta daga cutarwar shi da ikon Allah,ina neman gafarar Allah ya yi min afuwa, ya ba wa wadan da na zalinta ikon yafe min a filin qiyama" Nan da nan sai ga Oga Zaks na yin kukan nadama,tabbas Allah shi ne mai shiryar da duk wanda ya so a lokacin da ya so, basu rufe baki ba suka ji gidan na wani irin qara mai firgitarwa,da jin haka kuwa mazajen nan suka hau gudun ceton rai, Alhaji Salihu ne ya ke ta qoqarin taimaka wa Oga zaks su gudu ya kasa saboda tsabar qiba da nauyin shi,sai ya kamo shi su tashi sai ya koma shab'ar ya zauna,daga ƙarshe dai dole ya dakatar da shi ya ce, " Salihu kai ta kan ka kawai, ni nasan tawa ta qare, da wannan uban tumbin nawa kake tsammanin samun gudu a gareni? Ka dube ni fa ka gani na ninka ka sau bakwai, ka barni kawai, abin da na aikata zan girba, a shirye nake dan na sadaukar da rayuwa ta na fanshi taku, saboda ni ne na fara komai, i think it has to end with me, just go now ! Ka gudu ! Kar ka juyo kar ka dawo baya, kar ka manta da ni ka dinga nema min gafarar Allah idan ka yi tsawon rayuwa," Tura Salihu ya yi da qarfi a dai-dai lokacin da wani qaton baqin zaki ya fito daga wani baqin d'akin da suke ajiye mutanen da suke tsafi da su yayo kansu, Salihu ɗiba ya yi da gudu ya bar wajen, Oga Zaks salati kawai yake ya na Kiran Sunan Allah tare da neman gafara a wajen Allah,tsabar tsoro da shiga tashin hankali har ya cika wandon shi da fitsari shataf bai sani ba, nan take ya hau tunanin ashe haka waɗanda suke bawa dodon tsafin nasu suke ji kafin su mutu, nan take ya ji qirjin shi na wata iriyar muguwar bugawa,cafka zakin nan ya kaiwa wuyan shi ya hau cinye shi,shure-shure ya hau yi na azabar fitar rai kafin daga qarshe ya yi shiru alamar ya mutu,Oga Zaks kam an tafi inda Kalla ya tafi, Salihu kuwa gudu yake kamar zai tashi sama , mota ya gani da makulli a jiki me ita wataqila tsabar tsorata ne ya hana shi ci gaba da tada ita ya gudu, dan harda takalmi qafa daya a cikin ta a ajiye, ruwa duk ya jiqe mazaunin driver maybe fitsarin shima ya sake kafin ya gudu,take Salihu ya tada motar ya debi hanyanyar kano dan bai ga ta zama a garin Abuja ba. ****************************** Tinda suka tashi daga bacci suka yi sallah suka hau gyaran gidan nasu tare da yin abincin safe zuwa rana, bayan sun gama ne suka yi wanka suka hau shirin zuwa ganin babyn tasu. Suwaiba aiki kawai take yi amma Jikin ta duk babu kwari,sannan ga wata iriyar fad'uwar gaba da take ji,Saudat ma in banda sharar d'akin su ba abinda ta tsinana, Salma da Suwaiba ne suka fi yin aikin gidan, ta rasa dalilin da ya sa take jin wani yanayi a tare da ita,ko da ta sanar da Mama Balki sai ta koyar da ita wasu addu'o'i, nan take ta yi ta maimaita addu'o'in a bakin ta, bayan sun gama shiryawa ne suka yi wa su Goggo Sarai Sallama su ka ɗauki hanyar gidan Juwairah me jego, sun isa dai-dai Jabeer ya fito riqe da towel din da yake gasa mata jiki da shi sai suka tsaya kallon shi,daga bayan shi kuma Juwairah ce ta fito tana fad'in, " Ni dai gaskiya a canja min me yi min wanka a gidan nan kai gaba ɗaya mugunta ka ke yi min, ni ban ma taɓa jin inda aka ce namiji ke yi wa mace wankan jego ba dan h.......... " Maganar ta ce ta maqale dan ganin yayun nata na shigowa, niyyar ta ta koma bandakin dan juyawa ta yi tare da damqe bakin ta zata shige bayin, cikin dariya Saudat ta yi sauri ta isa ta ruqo ta, " Me Yah Jabeer din ya ke maki? In kina son a canja maki mai wanka sai na dinga yi maki, amma ni sai ruwan ya tafasa sau uku sannan zan yi amfani da shi" Zaro ido waje Juwairiyyah ta yi sannan tace, " A'a Adda Saudat a barmin Yah Jabeer ɗin mu lallaba a hakan" Dariya suka kwashe da shi, Jabeer yace, " ku ji yarinyar nan fa, wai zata lallab'a a haka sai kace wani muguntar nake yi mata" Nafee ce ta amshe da cewa, " Hmmmm Yah ayi shiru kawai da wannan maganar amma ko d'azu na jiyo qarar ta" Hararar ta ya yi yace, " Suwaiba ku shiga ciki mana kuka tsaya a waje" shiga suka yi har me jegon, Nafee ce ta bar d'akin sakamakon kiran ta da Innarmu ke yi, zuwa ta yi ta bata wani kwanika biyu ɗauke da abinci ta kawo wa juwairah, amsa ta yi ta tafi bangaren juwairah, sallama ta yi musu kafin ta shiga suna ta hira kowa na yaba kyaun jaririyar da sunan ta, "Wannan suna na :yan gayu anya kowa zai iya fada kuwa kar a je a b'ata mata suna kin san halin mutanen mu" Cewar Salma, dariya Nafee ta yi da ta qarasa aje kwanon gaban Juwairah dake shafa man kad'e a cikin ta ta ce, "Ai jiya sai kun sha dariya dan daga Innarmu har Abban mu basu iya fada ba, Innarmu Abaras take cewa Abbah kuma Abra" "Ai ko wannan suna zan so jin shi a bakin Goggo" Cewar suwaiba da ta tuna da Goggo Sarai, dariya suka bushe da ita dikkan su sun san a kwai case din fad'an Abrar a bakin Goggo sarai, Juwairah ce ta gama shiryawa Suwaiba ta d'aure mata cikin ta, sannan Jabeer ya shigo ɗauke da plate da Spoon da cup sai tea spoon, gaishe shi suka yi dikan su ya amsa su cikin sakewa, nan dai suka yi masa barka da samun wannan qaruwar da aka yi mai albarka, godiya ya yi ya isa gun kwanukan ya buɗe, farfesu ne na naman qaramar dabba, yasha kayan qamshi irin na jiya harda rid'i a ciki, gefe kuma kabewa ce innar mu ta dafe ta ta yi laushi ta dame ta ta yi kamar kunu, sannan ta zuba masa madarar shanu mai matuqar yawa sai zuma, zuba mata ya yi a cup din ya zuba mata naman a plate ya haɗe fuska alamar ba wasa ya ce, " Gashi maza taso ki ci ki shanye, dan bana son kina zama da yunwa" Turo baki ta yi gaba ta ce, "Ni fa na qoshi Yah Jabeer,dazu da asussuba na qarasa cinye naman jiya saboda yunwar dana tashi da ita, yarinyar nan ci gare ta kamar Innar ta Salma" Dariya suka sanya dikkan su, Jabeer ne ya ce, " Ai kuwa baki isa qoshi ba da dan ragowar naman nan, in baki matso kin fara ci ba zan maki d'ura a gaban su," zaro ido ta yi waje sai gata a qasa ta saka pilo ta haɗe qafafun ta waje ɗaya ta miqe su tare da danna hannun ta a plate ɗin naman. ( haka ake so mai haihuwa tana zama, kai ko ba haihuwa ba ma, ba a son zaman nan na ware qafa da wasu matan ke yi, kabewa kuma da madarar shanu da zuma duk wadda ta haɗa ta sha zata bada labari bazan ce komai akai ba) Kaiwa baki ta yi ta fara ci, wani daɗin da ya ziyarce ta ne ya sa bata san sanda ta cinye ba ta shanye kabewar dika,murmushi Jabeer ya yi da suke ta hira da qannen na shi ya ce, "Da kyau yarinyar kirki" Sumbatar Saman kan ta ya yi sannan ya dauke kwanukan zai fitar Salma ta yi saurin Karb'a dan ta fitar da su cikin jin nauyin shi ta ce, "Haba yayah muna nan ai sai ka bar mana aikin in mun tafi ka ci gaba" Murmushi ya yi ya sakar mata yace tare da cewa, "Ni bari naje na shirya zan wuce Abuja yau dan zuwa qarasa shirye-shiryen komawar mu bayan suna" Anan ne ya sanar da su komai game da aikin da ya samu a Abujan, murna suka taya shi , da fatan alkairi suwaiba da saudat har ma da Salma suna jinjina iko na Allah, ko da suka auri mazajen da ke son su kuma masu kuɗi ba wadda ta taɓa samun irin kulawar da Juwairiyyah ke samu, gashi kuma yanzu Allah ya nufa ashe ita ce asalin 'YAR ABUJAN gasken,wanka ya shiga ya yi, ya dawo d'aki ya wuce su dan ya shirya,Juwairah ce ta tashi taje wajen shi ta zauna a gefen gado yana shiryawa suna hira tana haɗa masa kaya a jaka, duk da hana tan da yayi sai da ta haɗa masa, bayan ya gama ne ya dauki Abrar ya mata addu'a tare da sumbatar fuskar ta, sannan ya haɗe babyn da maman ya rungume, a bakin kofar fita daga d'akin su zuwa parlour suka gama Sallamar su ya yi wa su suwaiba sallama ya fita, bai jima da fita ba ya yi mantuwa dole ya dawo dan daukar mantuwar da ya yi, " Af nayi mantuwa" " Me ka manta honey?" Matsawa ya yi kusa da ita ya janyo ta jikin shi yana mata kallo qasa-qasa cikin sauri da gane mantuwar da ya yi Juwairiyyah ta hau ja da baya ta na son kwace kan ta a hannun shi ta ce, "Yah Jabeer ka bariiii su Addah Suwaiba na nan fa, ni dai dan Allah ka daina bani kunya a gaban mutane," Ta qarasa faɗa tana 'yar kwallar ta dan ya kyale ta, lakece mata hanci ya yi yace, "Ina baki kunya fa ki ka ce? Ai shikenan mun kusa komawa gidan mu mu uku, mu yi abinda muke so ba tsoron zan kunyata ki a gaban mutane ko?" Dariya ta yi na samun nasara akan shi ya hakura da yin abinda ya fake da mantuwa ya dawo domin sa, Juwairiyyah ta yi masa addu'a ta rako shi suna zuwa palour ta yi fuska ta zauna kamar ba tare suke ba, kunya ce da ita kamar me shi kuma duk abinda zai yi matsawar bai saɓa wa shari'a ba babu ruwan shi kowa ma ya gani, meye abin jin tsoron kar wani ya ga ya na kyautata wa matar shi? dariya suke yi mata Salma tace, " kin ji da shi ciwon ajali a ɗan yatsa, mu zaki layancewa?" Dukan wasa ta kai wa salman tace, " Adda Suwaiba kin ganta kooo" Dariya suka yi, suwaiba ta ce, "Juwaireren Mama ya kamata ki rage shagwab'a yanzu kin haihu," Nafee ce ta fashe da dariya,ita kuwa Juwairiyyah sai ta murguda mata baki sannan ta kauda kai, ranar a gidan Juwairiyyah su suwaiba suka wuni da yamma Suwaibah ta yi wa Juwairiyyah wanka, nan take Juwairiyya ta ce wankan ta ya fi na Jabeer daɗi ta dinga yi mata ko da ya dawo. ******************************* Ahj Salihu ya iso kano lafiya, da kyar ya gane gidan su suwaiba saboda ko a da ba su zuwa zance gidan su sai dai su su suwaiban su je hotel su same su a can,a qofar gidan su ya tsaya....... [04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 30: Jingine yake a Jikin motar da ya je da ita saboda rasa ɗan aike da ya yi,bayan haka Alhaji Salihu yana matuqar jin nauyi, kunya, da tsoron wacce Karb'a za a yi masa a gidan su suwaiban,juyawa ya yi ya kife kan shi a Jikin motar ya na fidda wani irin numfashi wanda ke nuni da halin damuwar da yake ciki. Mai adaidaita sahu ya na ajiye su ta gane mijin nata,domin kuwa da shi take kwana da shi take tashi a ran ta, Alhaji Salihu kuwa na nan tsaye wasu siraran hawayen nadamar rayuwar shi ta baya na bin kuncin shi, ga rashin babban aboki kuma ɗan uwan shi da ya yi, a gaban shi zakin nan ya kaiwa Oga Zaks cafka a wuya, da sauri ya d'aga kan shi cike da damuwa ya ke tunanin yanzu me zai faru idan Shima zakin ya biyo shi har nan dan ya hallaka shi? Anya hakan ba zai jawo wa Suwaiba da iyayen ta da 'yan uwan ta matsala ba? maybe this is a bad idea for him to risk there life for his mistake,juyawa ya yi dan ya bar wajen cikin gaggawa kafin wani ya gan shi, cikin wata iriyar murya mai cike da shauqi da kewa ta kirawo Sunan da take Kiran shi da shi, " Baby ! kai ne a qofar gidan mu da gaske? Me ka ke yi a nan?" Qarasawa ta yi da gudu ta faɗa qirjin shi tana kukan kewar shi da ta yi, shima rungume ta ya yi kamar wani zai k'wace masa ita, gyaran murya Salma ta yi masu ta ce, " Adda a waje kuke fa kin san halin mutanen mu, ba za a yi tunanin mijin ki bane za a fara qananan maganganu mu shiga daga ciki " Janyewa suka yi daga yanda suke ta ja hannun shi zuwa cikin gidan su ta tsaida shi a soro, Saudat kam ta qame qam a wajen, dan zuciyar ta bugawa kawai take yi, ina nata mijin yake? Ya aka yi suka rabu yau bata gansu a tare ba bayan ta san ba sa rabuwa? Wannan tambayoyin Salihu ne kawai zai amsa mata su bayan ya samu nutsuwa, dan ta kula shima ba a nitse yake ba, Salma da ta yi gaba ne ta dawo baya ta ja hannun yayar ta ta suka yi cikin gida, ta kula da cewar Saudat na cikin damuwa tin safe yanzu kuma data ga Salihu shi ɗaya ba nata mijin damuwar ta ta qaru akan ta da, ko ba komai tana son mijin ta kawai halayen shi ne yasa ta gudowa ta qi komawa gare shi dan ba zata zauna a kashe ta a banza ba. Sun riga da sunyi Sallahr la'asar a gidan Juwairah dan haka bayan sun shiga sanar da Baban su suka yi zuwan Alhaji Salihu ga kuma a yanayin da suka gan shi a ciki, da fari Baba ya hasala ganin rashin kunyar Alhaji Salihu na zuwa gidan shi bayan abinda suka yi wa yaran shi,da suka samu ma bai kai ƙarar su ba shi ne har zai zo to ya ce musu me? amma da Mama Bilki ta taushe shi sai fushin nashi ya sauka, ta shawarce shi da ya tafi cikin nutsuwa ya buɗe ma Salihu zuciyar shi ya ji me ke tafe dashi, in yazo da rainin hankali gidan su yazo duk abinda Baba ke so zai iya yi masa ya huce haushin shi, ta bashi goyon baya ya yi masa duk abin da yaso, kad'a kai ya yi cikin qunan rai ya fita amma sai ya danne bacin ran nashi, kamar yanda matar tashi ta bashi shawara. Sallama ya yi masa ya miqa masa hannu dan su gaisa,amma sai Alhaji Salihu ya noqe ya qi miqa nashi hannun ya durqusa qasa yana mai sakin kuka mai ban tausayi tsakanin kukan shi ya fara magana, "Baba ni mai laifi ne babba a wajen Allah da kuma ku, babban mai zunubi ne ni Baba,na taso ban san menene ilimin addini ba, duniya kawai na saka a gaba, bani da ilimin addini daya ratsa zuciya ta da zai hana ni aikata dukkan abubuwan dana aikata a baya, dan son ka da Allah da Annabin shi ka yafen abinda na yi wa Suwaiba, ka yafewa abokina d'iban jini da cire wa Saudat mahaifa da ya yi domin ya mutu a yau, a dazun nan ta hanyar hatsarin mota" Wani qara kunnuwan saudat suka ɗauka shuuuuuu, tabarmar da ta d'akko dan ta kawo wa Alhaji salihu da ruwa a jug ne suka zube a qasa, kafin ta qara d'aga qafar ta ta isa wajen su Baba ta yanki jiki ta faɗi, da gudu Baban su ya yi kanta, ya d'aga ta ya yi ya shige ciki da ita, ruwa suka yayyafa mata ta sauke ajiyar zuciya mai karfi daga nan kuma a hankali ta fara buɗe idanun ta,a kan Alhaji Salihu idanun ta suka zuba wanda ya shiga gidan ba tare da izini ba dan ganin halin da matar abokin nashi ta shiga, kuka ta saka ta kai masa wani wawan naushi a baki tare da fad'in , "Mugaye azzalimai kawai, wato kashe shi kuka yi ko? Dan na san yanda Kalla ke sona zai biyo bayana ko bajima ko ba dad'e, shine kuka kashe shi saboda ba ku son ya bar azzalumar ƙungiyar ku ya zo gare ni," " Saudat ya kamata ki natsu,abinda ki ke zargi ba shi bane ya faru,ni da ki ka ganni ni na shawarce shi akan mu fita daga qungiya dan son da muke maku, da kuma tsoron Allah daya shige ni a wannan lokacin, amma Kalla ya qi ya mun bayanin shi akwai sauran lokacin tuba ba zai fita ba, na masa nasiha da in mutuwa ta riske mu kan tuban fa, yace akwai lokaci, yana fita ya yi hatsari mummuna, kan shi ya fashe qafarshi ta......." " Stop it ! Stop ! Ba na son ji..bana so..bana son ji" Fashewa da kuka ta yi mai ban tausayi, a nan dai Alhaji Salihu ya qarasa labarta masu komai daya faru har da shugaban qungiyar tasu wato Oga Zaks. Goggo Sarai ta fito dan ta yi wa Alhaji salihu masifa akan rufe su da suka yi da zaluncin da suka yi wa yaran ta ta ji abinda ke faruwa,nan da nan sai jikin ta ya yi sanyi,sai kawai ta koma kwallar tausayin yaran ta,tabbas wannan ba laifin kowa bane illa laifin ta, ba su taɓa sanin Saudat na son mijin ta haka ba sai yanzu, a zaton su tun da ta taho ta bar wata soyayya da duk wata rayuwa da ta yi a baya jira kawai take ya zo dan kan shi ya sake ta ta sake sabuwar rayuwa, taimaka mata Mama Balki ta yi ta kai ta d'akin su ta kwantar da ita, kuka kawai take yi ta na jin kamar a gaban ta komai ya faru da mijin nata,cikin tausayawa Mama Bilki ta ce; " Saudat ki yi hakuri , na san rashin masoyi akwai zafi, amma soyayyar da zaki nuna wa kalla a matsayin shi na mijin ki shine addu'a, tinda bai sake ki ba ke ki ka qi komawa, dan haka daga yau zaki fara takaba, har tsawon jini huɗu da kwana goma,dan haka har abada mijin ki na buqatar addu'ar ki, baya buqatar kukan ki, kin ji" Ta qarasa tare da shafa kan ta cike da tausayawa, cikin sakewar jiki ta dora kan ta a kan cinyar Mama Bilki hawaye masu zafi na fitowa daga idon ta, nan take ta hau kwarorowa mijin nata addu'a, mama Bilki na amsawa,a haka har ta samu sauqin zuciyar ta itama, Salma na maqale tana tina nata tsohon mijin tana hawaye, ga tausayin Addar ta ta da ya dame ta. Alhaji salihu kuwa bayan ya yi alwala ya yi sallah ne ya zauna cin abinci Abba ya ce idan ya gama su je gidan Yayan shi za a zauna a yi magana wato gidan su Jabeer,a cikin motar Alhaji Salihu suka tafi,bayan sun isa ne suka samu Yaya Balarabe na gida, tabarma suka sa a waje suka zauna,Baba ya yiwa Yaya Balarabe bayanin komai,bayan jimanta wannan mummunan lamari tare da yi wa Alhaji Kalla addu'ar samun rahamar Allah sai ya amince da mijin Suwaiba zai zauna a shagon gidan har Allah yasa su Jabeer su koma Abuja sai su kuma su zauna a bangaren su Jabeer ɗin,Baba godiya ya yi wa yayan nashi, ya koma gida ya bar Alhaji Salihi a nan,Alhaji salihu ya musu godiya sosai musamman da Yaya Balarabe yace zai fara koya masa ilimi na addini dan ya kula yana da qarancin shi, godiya ya yi sosai kamar zai kwanta a wajen dan kuwa ba karamar alfarma da karramawa suka yi masa ba. Nafee Baban su Jabeer ya kira ta gyara shagon, aka shimfida masa wata yaloluwar katifa da wankakken zanin gado da pillow, sai sallaya da buta da ruwa mai kyau a bokiti rufaffe saboda ko zai buqata, Abban su yace in yana buqatar zagawa zai iya shigowa cikin gidan, godiya ya yi ta musu kamar zai kwanta, zuciyar shi cike da tausayin rayuwar da zai koma, sannan qasan ta kuma cike da murnar ganar da shi gaskiya da Allah yayi. ************** Yau kwana tara kenan da haihuwar Juwairah har an yi suna an gama lafiya kuma bikin suna ya qayatar, dan kuwa Jabeer ya yi qoqari sosai, ga akwati nan biyu da ya yi ma mai jego da jaririya, ɗaya babba ɗaya qarami, gobe suke son komawa Abuja, dan wajen aikin na buqatar Jabeer ɗin da gaggawa, sun gama kwasar duk wani abu da zasu dauka mai amfani sun gama, kayan d'akin ta kuma zata barwa Addan nata da mijin ta tun da ba su da shi, a haka taje gida ta yi wa Saudat ta'aziyya ta kuma yi wa iyayen ta sallama, Juwairiyyah ta sha kuka kamar wadda za ai wa auren dole,da kyar suka lallashe ta sai da taga Jabeer ran shi ya fara ɓaci da kukan ta sannan ta hakura, sun dawo gida bayan Isha'i,Nafee ma kan ta ta sha kuka har sai da idon ta ya kumbura saboda kukan rabuwa da bestyn ta kuma yar uwar ta, sannan matar yayan ta da ke son ta,Innarmu ma ba a barta a baya ba wajen matse kwalla,tana qara bawa Juwairah hakurin zaman da suka yi a baya tare da fad'in, "Ashe ma ita duniyar ba matabbata bace, ba abinda ke tabbata sai iKon Allah, gashi dai mutuwa bata raba mu ba amma zaman a tare ya kare, Allah ya sa ku koma sabon wajen a sa'a,Allah ya yi maku albarka" Baba Balarabe ma jikin shi duk ya yi sanyin saboda rabuwa da Jabeer da Juwairah,musamman Juwairiyya dan kuwa itan yarinya ce mai shiga rai matuqa,gashi ta na da kyawawan halaye da kuma iya zama da mutane, a haka aka kwana gidan kowa da abinda ke ran shi. Washegari da sassafe Jabeer da Juwairah ɗauke da Abrar suka fito suka shiga sabuwar motar Jabeer zasu tafi Abuja, Nafee ta riqe hannun Juwairah tana matsar kwalla, Jabeer ne yace, " My little sis ki yi hakuri,kwana nawa ne zamu qara dawowa, ranar fa da Saudat zata fita takaba ranar za a fara bikin ki ko kin manta ne? dan haka ki kwantar da hankalin ki, sannan wataqila ma Salma ta haihu kafin nan zamu zo, ki yi hakuri kin ji," Hawayen ta ta share, ta yi masu addu'ar tafiya lafiya da samun sa'a da nasara a rayuwar su baki ɗaya,Innarmu da Abbah Balarabe ma haka, sai mijin Adda Suwaiba dake gefe shima yana masu fatan alkairi, motar ya tayar suka yi gaba cike da kewar juna. Salihu kuwa gaba ɗaya ya canja,fatar shi ta qara duhu saboda dama shi baƙi ne, irin baƙin nan mai haske kaɗan, Alhaji Salihu na da kyan shi dai-dai misali,tumbin nan na shi ya ragu,hakan ya ba wa kyan shi damar sake fitowa, ganin yanda ya faɗa ne ya bawa Baba Balarabe tausayi,a qasan ran shi kuma yana ayyana ko zasu fara zuwa kasuwa tare ne wajen gwanjon su da shi ne? Bayan su Innarmu sun shiga gida ne ya same shi ya masa wannan tayin, cikin jin daɗi ya amsa da zai yi ko meye in dai halal ne ba damuwa, qasa ya yi da murya da kan shi sannan ya ce, "To Baba ai ban da jari kuma" " kar ka ji komai akwai jari a wajena ,ko da dubu biyar zaka iya farawa mu gani" Godiya ya yi ta zubawa sosai har Baba Balarabe yaga dai ba zata qare ba, dariya ya yi ya shige cikin gidan ya bar shi a nan, rayuwa kenan Alhaji Salihu da ko masu aikin gidan shi albashin su daga dubu ashirin ne zuwa sama yau shi ne zai kafa jari da dubu biyar. Ba jimawa Suwaiba da mijin ta suka tare a sashen su Juwairiyyah,kuma kasuwanci ba laifi wataran a samu ya siyar da kayan dika har ma a samu ribar da ta kan kai dubu uku zuwa huɗu, wataran kuma ribar ba ta kaiwa haka, a haka ɗin shi da ya fara da jarin dubu biyar yanzu ya kai dubu goma,duk abinda aka samu na Saman ya yi wa iyalin sa hidima da su watarana ma har da su Innarmu. Salma da Huwaila kuwa kusan a tare suka haihu, Salma ta haifi Yaran ta biyu mata masu matuqar kama da iya kyawawa, ita kuma Huwaila ta haifi yaro namiji mai kama da Bangis sak, kwana tara ne a tsakanin su ,dan kuwa yaran Salma sun girmi na Huwaila. Ranar suna kuwa Salma sai da ta yi taron suna dangi suka zo suka taya ta murna da sanya albarka har ta samu kyauttuka,dan kuwa da dama an zata haihuwa ta dawo yi gida,ba wanda ya san mijin ta ya sake ta sai daga baya magana ta yaɗu a dangi, wasu suka yi mata fatan samun wanda ya fi Talle wasu kuma na Allah ya ƙara ai ga auren miji ɗan ABUJA inda ya Kaita ta zama bazawara da qananan shekarun ta. Bangaren Huwaila kuwa komai qayau-qayau su ka yi shi, ga habaici da suke sha wajen 'yan gulmar da ke zuwar masu barka da kuma wanda suka je sunan, yaron Huwaila ya ci suna Bilal,haka rayuwa ta yi ta juyawa wadannan bayin Allah da daɗi ba daɗi. Ta bangaren gidan Baba Balarabe kuwa al'amuran gidan su ya bunqasa da arziqi dan Salihu ya shiga gwanjo a sa'a, yanzu har dila biyu yake iya bud'ewa wata rana ma har uku,haka gidan Yah Jabeer ɗin Juwairere suma arziqi ya wadatu a gidan su dai-dai misali abun dai sai godiya ga Allah, gidan su da suka koma a Abuja mai kyau da shi d'aki uku ne da dinning area sai babban parlour mai ɗauke da manyan kujeru da kayan kallo, yarinyar ta sai wayo take yi cikin koshin lafiya. **************************** Shirye-shiryen bikin Nafeesa ne ya kankama gadan-gadan,wanda ya kama sauran kwana uku saudat ta fita daga takaba, a yau din ne su Juwairah da Jabeer tare da diyar su Abrar za su zo baza su koma ba har sai an gama bikin Nafeesa, Jabeer ba qaramin qoqari ya yi ba a yan watanni huɗun nan, shi ya yi wa Nafee kayan d'aki Abbah Balarabe ya bada kuɗi su Suwaibah suka siyo mata kayan kitchen da wasu abubuwan buqatar. Jabeer ya kashe kuɗi sosai dan ita Juwairah ma ba ta sani wasu abubuwan da yake yi ba, tinani take yi in sun je ina zasu sauka? Tunda bangaren su yanzu Adda Suwaiba ne a ciki da mijin ta,bata da masaniyar d'aki daya da bandaki da palour madaidaicin da Jabeer ya masu a filin dake gefen gidan su wanda yake kamar kango ne a da, sai yar tsakar gida madaidaiciya, ba laifi ginin ya yi kyau,sai wajen azahar suka iso, ta ce wa Jabeer ya fara kai ta ta gaida su Innarmu idan yaso sai ya maida ta gidan su ta kwana,shiru ya mata ya na murmushi har suka isa gidan nasu,wajen Innarmu ta shiga cike da kewar ta, Nafee da gudu ta je ta rungume ta suka hau murnar yaushe gamo..... *Juwaireren mama na gayyatar dukkan fans din novel din 'YAN ABUJA zuwa wajen bikin Nafeesa, Allah ya bada ikon zuwa ameen😂*[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 31: Hankalin Talle yanzu ya koma kan Salma, dan kuwa ya san a yanzu ta haife abinda ke cikin ta,ya na sane da cewar ciki gare ta shi ne dalilin da ya sa tai ta wannan ciwon kafin su rabu, fatan shi yanzu ta yafe masa tunda ya san babu wata maganar kome a tsakanin su duba da cewa saki uku ya yi mata a lokaci d'aya,bayan haka ma wannan rayuwar da yake ciki ba irin ta Salma ke da buri ba sam ko a baya ta aure shi ne saboda kwad'ayi da tunanin shi wani ne, addu'a Talle ya d'aga kan shi ya na yi; " Ya Allah ka bata ikon yafe min a duk sanda na bayyana a gaban ta ina mai neman yafiyar ta ko ban samu zuwa ba mutuwa ta riske ni Allah ka wakilci ce ni a zuciyar Salma ta yafe min abinda na yi mata" " Haba Talle, sai yaushe zaka daina zubda hawaye ne? Na baka shawara mu kama akuya ɗaya mu siyar ka samu na mota dana guzuri ka je wajen yarinyar nan ka nemi yafiyar ta, amma ka kafe kace a'a to ta yaya kud'in zasu samu idan baka samar wa kan ka su ba? In aka siyar nima ba sai na samu na kafa wani jarin ba ai ya fi zaman nan da muke yi da ni da kai ba abin yi ko? Koda nera ɗari biyu zuwa ɗari uku yau muke samu a rana a matsayin riba ai zamu toshe wata kafar, balle nasan zamu samu ma yafi haka,ni yanzu babban tashin hankali na be wuce b'atan Haule ba, duk da ina kyautata zaton gajiya ta yi da halayen mu ta gudu wajen mahaifiyar ta, amma abun na matuqar damuna" " Dan ta zancen Haule kwantar da hankalin ki ta na wajen mahaifiyar ta mantawa na yi ban sanar da ke ba,da ta je ma da kyar suka amshe ta, amma yanzu baki ga gatan da take sha ba in ji abokina da ya min hanyar auren babar ta, yana ta mun godiyar kyautawa da na yi na barta tazo ta ga mahaifiyar ta" " Allah sarki, a gaskiya mun tafka babban kuskure a rayuwar mu Allah ya bamu ikon gyarawa, me zai hana ka samu a islamiyyar malam Sallau kaga ana karatu kyauta, awa biyu zamu bayar a kwana uku kawai, dan akwai jahilci mai tarin yawa a rayuwar mu sai mun kawar da shi ibadar tamu ma za ta karb'u,ka ga kai kuma sai ka na zuwa ta bayan isha'i kai da Yaya" "Gaskiya kin kawo shawara mai kyau dan abubuwan da muka tafka da da ilimi a tattare damu musamman na addini da bamu yi ba, Allah ya yafe mana" " Ameen" "Ni wai ina yarinyar nan Hawaila? Ki taran su har Baban gidan zuwa anjima za ai maganar auren ta, gobe juma'a, suna da d'aki a bangaren su da katifa dan haka ban ga dalilin da zai sa ta ci gaba da zama a gaban mu ba a zo ana maimaita 'yar gidan jiya,ko ba gaskiya ba, kin ga a hankali muka samu sai mu yi mata kayan d'aki kamar kowacce 'ya" " Wannan ma shawara ce mai kyau, ai duk yanda za a rufa wa juna asiri yi za a yi, tin da ga yaron su nan Umar Allah ya bayar gwanda ai auren gobe komai ya wuce,Allah ya sanya mana albarka dikkan mu, ya yafe mana" " Ameen na gode maki da ki ka canja halaye daga munana zuwa kyawawa, yanzu kyaun ki ma ya fitowa matata, nima ina fatan kin ji daɗin canjawa ta?" Talle ya fada yana mai matsawa kusa da ita, ita kuma tana wani sissine kai, wai kunya take ji. "Na ji daɗi sosai mana Talle na, nan gaba ma swatyn nima zan dinga kiran ka irin yanda kk cewa Salame, ko mata kawai ake kira da haka?" Dariya Talle ya kwashe da ita da ya gane inda ta dosa ( Sweety) shine abinda take son cewa. "Ana Kiran mace da namiji Sweety, ina godiya ni kuma daga yau sai na koma ce miki honey" ******************************* Duk wani gyaran jiki da ya kamata a yi wa amarya Juwairiyya ta gama da wannan fannin,da yamma za a tafi dinner kowa ya sha gayu an yi kyau gwanin ban sha'awa, ba a cika wa Nafee irin kwalliyar nan ta yanzu da ake yi ba har a kasa gane asalin fuskar mutum, sai aka yi mata sassauqa saboda ta riga da ta sha kyaran jikin da ya fito da kyaun ta, ( aikin Juwaireren mama kenan) ba qaramin kyau ta yi ba, sun so kwarai a aske mata gira a yi shaping ɗin ta amma Juwaireren mama ta hana, domin kuwa hakan haramun ne, tinda akwai abinda ake yi a danyi dabara kamar an yi shaping ɗin ba zata bari a aikata sab'on Allah ba da Sunan kwalliya, aiko nan take Adda Suwai nonoless ta qara gyara Nafeen ta na gasgata Juwairiyyah tare da shigar mata faɗan da qawayen Nafeen ke yi akan ai yanzu haka ake ya yi ya kamata Itama ranar auren ta ta tafi da zamani, bayan Suwaibah ta gama gyara mata kwalliyar ta ne kowa ya tabbatar da lallai ado da kwalliya ba sai an sab'i Allah ba yake kyau,mutum zai iya kula da Fatar shi da asalin halittar da Allah ya yi masa kuma ya yi kyau ba sai ya yi bleaching ba ko saka gashin doki ko aske gira da qara farce ba. Nafeesan ta yi matuqar yin kyau, haka ma Saudat da Salma maman yan biyu ba a bar su a baya ba wajen cakarewa su da yaran su, ga wani irin qamshi mai daɗi da sanyi dake tashi a jikin Yara mai ni'ima kowa son ɗaukan su yake yi, Shamsiyya, Innarmu, Goggo Sarai Mama Bilki da sauran dangi sun sha kwalliya suma irin ta zamani,sai dai fa angwaye sun yi sanarwar ba za a je da iyaye ba, nan fa ran Goggo Sarai ya ɓaci ta tashi fidda hali, "Ni dai gaskiya ko su Bilki ba zasu ba ni a tafi dani, dan nasan irin wajejen nan akwai k'walama ba zai yu na ci kwalliya haka ba na zauna a gida" Wani kallo Suwaiba ta yi mata sannan ta ce mata, " Haba Goggo har zuwa yaushe zaki daina wannan halayen ne dan Allah?" Yashe baki Goggo Sarai ta yi cike da jin kunya ta ce, " 'Yannan wasa dama nake ina ni ina zuwa wajen matasa, ai irin wannan hidima sai ku" Can qasan ranta kuwa ba qaramin son zuwa dinner take yi ba,haka ta hakura ta danne ta tashi ta fita wajen masu soyawa amarya ka ji da za a tafi kai ta gidan miji da shi,saboda hanyar akwai nisa sosai, kuma a cikin garar ta Jabeer yace a saka harda kajin shine dalilin da ya sa ake soya su da yawa,ta na isa wajen ta danna hannu a kan wanda aka soya ta ɗauki yanka ɗaya ta yaga cikin tsinkewar yawu tace; "Wannan biki ana abin arziqi da yawa, in ban ci a wajen dinner din ba na ci anan ai," Kad'a kai kawai Salma ta yi da ta ji me take faɗa, mai hali baya fasa hali sai dai ya lafa kawai,in dai abun nashi ya motsa sai ya yi yake jin daɗi. Wajen dinner ya qayatu da ado, angon Nafeesa Shima na da kyan shi dai-dai shi, sai suka fito kamar wasu wata da zara dan kyau,tun da su Salma suka isa wajen dinner mazaje ke ta binta da kallo, wasu ma har magana suke yi mata saboda yanda ta ɗauki hankulan su,yaran ta kuwa su na wajen Suwaiba nonoless, Salman sai ta fito kamar wata budurwa ba mai jego ba, Saudat ma ta yi kyau mai ban sha'awa, abokan ango da suke zaune kusa da ango ne wasu daga cikin su suka qura ma su Salma ido kamar su sace su su gudu da su, ana tsaka da rawa da shagalin biki ne samarin suka taso wanda da gani babu tambaya alamu sun nuna gidan su ɗaya,saboda tsananin kamannin da suke da shi, Sallama suka yi wa su Salma da ke manne da juna su na rawa a gefe dai-dai hanyar fita daga hall ɗin,juyawa suka yi a tare suka amsa da karfi suma saboda samarin su ji muryar su da kyau. Nuni suka yi wa su Saudat da wajen zama mai ɗaukan mutum shida amma ba mutane akai saboda duk ana wajen rawa,ba musu Salma ta yi gaba saurayi ɗaya ya bi bayan ta suka zauna,a gefe kuwa Addah Suwaibah ce da Juwaireren Mama suna hango abinda ke faruwa, Saudat kuwa jikin ta rawa ya kama yi a zuciyar ta ta na tinowa da Kalla, ɗayan ne yace mata, " Haba sarauniyar kyawawan duniya ina zaki je kuma bayan ga sarkin ki ya iso domin ya ɗauke ki ya kai ki masarautar masoya?" Murmushin da bata shirya wa zuwan shi bane ya k'wace mata,amma can qasan zuciyar ta tunanin tsohon mijin ta ne danqare da zuciyar ta, ji take kamar ta zura da gudu. Jiki a sanyaye ta bi bayan shi suka zauna suma a kujerun da ke wajen tana ta wasa da hanun ta, ɗayan ne yace ma Salma, " Angel da farko ni suna na Ibrahim aboki ne ga ango, wannan kuma yaya na ne farouq, tin da kuka zauna anan muka sa idon mu ana ku mu ka ji ba zamu iya barin ku ku tafi ba ba tare da mun isar da manufar mu ba a gare ku, dan da dikkan alamu ku yan uwan amarya ne duba da kamannin da kuke da ita," Cikin nuna kulawa Salma ta kalle shi dan itama sai ta ji ya yi mata ta ce, " Eh mu yayun ta ne, amma bayin Allah ba ku sammu ba, baku san ya rayuwar mu take ba, kawai sai ku fara isar da manufar ku a gare mu? Gashi wajen ma duk hayaniya da kid'a ya yi yawa, to da farko dai ku duba kuga waɗan can yaran na hannun yayata ku kalle su da kyau sai mu ci gaba da maganar da za a yi" Duba Yaran suka yi suka ga kyawawan yara, sannan suka dawo da kallon su suka ce, "Masha Allah ga yara kuwa kyawawa qannen ku ne?" Murmushi Salma da Saudat suka yi a tare sannan Salma ta ci gaba da magana dan bata son abinda zai karya masu zuciya gaba ɗayan su, tunda har suka kasa haƙuri su samu wajen da ya fi wannan natsuwa su bayyana soyayyar su to fa ba za su bari abu ya yi nisa ba suma,gwanda a yi maganar gaskiya da gaskiya ,Salma ta kula dikkan su samari ne basu taɓa yin aure ba ma,cikin nuna masu gaskiyar da ke zuciyar ta ta ce, " Waɗancan 'yan biyun nawa ne ni na haife su ba qannen mu bane, sai dai ni aure na ya mutu, ita kuma wannan yayar tawa mijin ta Allah ya yi masa rasuwa ne har ma ta fita a takaba," Cike da mamaki da tausaya wa a gare su suke kallon su,amma dai duk yanda aka yi mijin daya saki Salma na da tab'in hankali ko kuma shafar aljanu, hauka ne kawai zai sa kana da mace kamar wannan ka sake ta, nan take suka yi wa Saudat ta'aziyya sannan farouq yace, " A gaskiya ni har yanzu ina ciki kai fa ɗan uwa? Dan ba zan taba barin wannan tsaleliyar ta wuce ni ba na yi asara, domin da dikkan alamu akwai tarbiyya awajen ku" A sannan ne Saudat ta yi magana ta ce, " Yanzu dai yanda za a yi ku yi hakuri zuwa har a gama biki da komai da komai sai kuje can gida ku samu mahaifin mu ku gabatar da kan ku,duk abinda mahaifin mu ya ce maku shikenan da shi za mu yi amfani dikan mu" Godiya suka yi sosai kuma suka qara tabbatar da tarbiyyar su, karbar No wayar su suka yi tare da yi masu sallama suka tafi. Adda Suwaiba ce ta dawo kusa da su ta zauna ita da Juwairah, suna zama Salma ta labarta masu duk abinda ya faru, suna cikin addu'ar neman zabin Allah Hussainar Salma ta hau kuka, kuka take sosai har Salma ta rude kamar za ta yi kukan itama,miqo masu hannu suka ga anyi ta sama; "Hey baby how are you?" Ibrahim ne ya karɓe ta ya na kallon kyan yarinyar ta yi kama sak da maman ta,jijjiga ta ya yi ya tafi wajen yayan shi suna ta hira da sauran abokai ko damuwa da yanda take zuba masa yawu a jiki bai yi ba,haka abokan ango suka dinga ɗaukan ta, daga wannan ya karbe ta sai wannan ya karbe ta, daga qarshe Ibrahim ya karɓe ta ya sanya ta a kafad'ar shi har ta yi bacci,cike da yabawa abinda ya yi Salma da yan uwan ta ke kallon shi. An gama dinner za a tafi gida ne ya iso ya miqa wa Salma ita, godiya ta yi ta masa har sai da yace, "Ya kike man godiya ne haka? A gani na dan uba ya kula da yar shi ai ba wani abu bane ba ko?" Murmushin jin daɗi ta yi idon ta cike da kwalla ta gyad'a kai ta yi gaba, bayan sun fita ne suka fuskanci basu da abin hawa ga dare ya yi dama a adaidaita sahu suka zo, su Farouq ne suka zo a motocin su suka parker a gaban su salma,sun so matuqa Juwairiyyah ta bi su su sauke ta a gida amma ta qi ta ce Yah Jabeer na nan tafe ɗaukar ta. Tafiyar su da wasu 'yan mintinan da ba za su wuce biyar ba kuwa ya iso ya ɗauke ta, a hanyar su ta komawa gida ne take sanar da shi labari mai daɗi game da samarin da suka nuna suna son su Salma. Murmushi ya yi tare da fatan alkairi ya ce, "Allah dai ya kaimu gida lafiya baki ji yanda na gaji ba sai kace ni ne angon wanka nake so na yi da ruwa mai dumi ko na warware" Murmushin Itama ta mayar masa sannan tace, "Hmmm Abu Abrar kenan na gane in da ka dosa, to yau kam dole a min hakuri dan kuwa ni kaina a mugun gajiye nake" Dariya Jabeer ya yi yace, "To za mu gani dai Allah ya kaimu gidan lafiya, ni da na san halin ki ai sai dai na ba wa wani labari ki 'yar mama" Jabeer ya kashe mata ido ɗaya ya ci gaba da murmushi ya na tuqin shi, kauda kai ta yi tana murmushin itama a ran ta ta na fatan Allah ya kai su gida lafiya dan kuwa ita ɗin ma ta yi kewar shi....... [04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 33: Washe gari angwaye zasu zo dan tafiya da amaren su da kan su tsabar zumud'i, dan kuwa ji suke yi kamar sun auri sabbin 'yan mata duba da yanayin kyan jiki da su Salma ke da shi babu mai cewa sun taɓa yin aure idan ba an sanar da mutum ba, su Goggo Karima ana nan sune yan rakiya zuwa Abuja. Da wuri suka shirya dan su shiga kasuwa Juwairiyyah ce ta dage sai sun je sun yi siyayyar lefen su saudat ɗin da mazan su suka damqa masu kud'ad'en a hannun su anan garin kano,sannan su sai wasu abubuwan amfanin gida dan kuwa a ɗan zaman da ta yi a Abuja har yanzu bata gano inda ake Saida wasu abubuwan da take buqata ba,akwatuna masu kyau da sha'awa suka siya suka cika da kayayyaki masu kyau da tsada, Suwaibah ce ta haɗa su da manyan shagunan 'yan kasuwan da ke haɗa wa mutum lefe idan ya na da buqata a farashi mai sauqi saboda yanzu sana'ar da take yi kenan kuma ta na samun riba sosai. Cikin abinda bai fi awanni huɗu ba suka kammala da bangaren lefe suka shiga kasuwar kurmi suka sayi kayan qamshi na girki sannan aka yi masu haɗi na musamman da za su niqa su dinga sanya wa a cikin madara da zuma su na sha dan qarin ni'ima da d'umin jiki. Juwairah bata manta da Yah Jabeer ɗin ta ba dan kuwa ta lodar wa mijin ta kayayyaki dangin qanan kaya irin su vest, boxers, turaruka, takalma, da huluna guda biyu masu kyau sosai, mamaki ne ya kama yayun nata sai suka kasa jurewa sai da Saudat tace mata, "Ke kuma ya naga kina ta siyan kayan maza baki saiwa kanki komai ba sai tirare da kayan bacci," " Adda Saudat Yah Jabeer na d'ebarwa ai, ba dan komai ba sai dan yanda shima yake kyautata min yake min dukkan wata hidima da ta taso min da jikin shi da aljihun shi, na sani komai zan masa ba zan yi kamar yanda yake yi min ba, sannan wannan abun da na siya already yana da su, amma kyautata wa juna na qara danqon soyayya, kyauta tsakanin miji da mata musamman irin wannan ta tiraren da miji ya fi so, tana da matuqar tasiri a zuciyar namiji, shiyasa naga ya dace tinda ya wadata ni da kuɗi shima na sai mashi" "Lallai Juwairere ke kin ma fi Mama Bilki iya tattalin miji, na rasa waya koya maki duk wadannan dabarun da ki ke da su, ko kayan baccin ki da tiraren ki da ki ka siya duk shi za su amfana ai" Dariya sukayi, Juwairiyyah ta ce, " Salma ai gaba kin ga in ya tashi bani zai bani wanda yafi wannan tinda yasan ko me zan siya duk inda aka je aka dawo zai amfana shima ta kowanne fanni" Tafiya suke suna jinjina wayo irin na qanwar tasu,cikin jin daɗin had'in kan da ta samu da yayun nata ta ce masu, "Adda Saudat ku daina mamaki na, kowacce mace tana da kaifin hankali da basirar zaman gidan miji, bambancin mu shine wata tana shiga kwakwalwa da zuciyar ta ta yi tinani ta sama wa kan ta mafita a kan duk wata matsala da ta tunkare ta ta na tsayawa ta yi abinda zata amafana da baiwar ta wasu ma su amfana, wata kuma dunkufe kanta take yi bata son yin dogon tinani sam, bama ta son tana zurfafa tinanin ta akan komai, da matsala ta same ta sai tace sai ta nemi shawarar qawa, wani lokacin a yi sa'a ta samu shawar qwarai wani lokacin kuma ayi rashin sa'a ta samu muguwar qawa ta bata gurguwar shawara, amma in da zamuna bude zuqatan mu da maza sun ji daɗin zama damu, aure kuma daya rage mutuwa, da hakuri da sanin ya kamata ya wanzu a gidan auren mu, Adda muna a garin da ba mu da iyaye acan mu ne iyayen junan mu mu zamu taimaki kan mu, dole sai mun zama masu irin wannan tinanin gudun shiga matsala kan dayan mu ya kai mana agaji" Wani kallon so da qaunar qanwar tasu ke yawo a idanu zuwa zuqatan su, a haka suka samu abin hawa bayan an masu niqan kayan qamshin suka wuce gida a gajiye da kaya masu mugun yawa, alwala suka yi sukai sallah azahar da la'asar da basu samu damar yi ba suka bar Goggonayen su da su Mama Balki suna kallon kayan lefen daga qarshe ma maqota aka aikawa duk suka shigo suka ga kayan alkhairi,su kuwa ganin ana ta cika ne ya sa suka yi wanka suka ci abinci, sai baccin gajiya ya ɗauke su. Tin da sassafe angwaye suka jera mota guda huɗu saboda ɗaukan amaren su da wasu kayan nasu,Jabeer ma ya dakko hanya shima amma bai iso ba Innarmu ta zo gidan da sassafe dan a yi komai gaban ta, amare na ta dan koke koken rabuwa da gida na al'ada, Saudat kuwa tsoro ne fal cikin ta na komawa Abuja, ji take yi kamar ta fasa auren amma ta dake, tana son ta yi wa mijin ta kyakkyawan zato, Adda Suwaiba anyi anyi ta yi rakiya tace ita da Abuja ko a film ba ta so taga Ali Nuhu a can balle ita ta sa qafarta a Abuja, haka aka hakura aka barta wataran zata je ne da kan ta, Jabeer ne ya iso nan ya tsaya Shima aka yi sallama da Amare daga nan ya ɗauki matar shi suka wuce gidan iyayen shi dan ya huta gajiyar aiki da ta tuqi. Bayan tafiyar su ne Hajiya Goggo Sarai mai niyyar zuwa Makka ta na tsaye tana zabga masu addu'a da fatan alkairi,haka ma Baba Baballiya da Mama Bilki ba a bar su a baya ba wajen amsawa da Ameen tare da ɗora tasu addu'ar akan ta ta,kwalla Goggo Sarai ta share na tsoro da tausaya wa yaran nata dan bata san wannan karon me zai faru da su ba, gaba ɗaya son Abuja ya bar ran ta a cewar ta koda Makka za a biya mata ta na rokon kar a ce jirgin su zai tashi ko ya sauka ta Abuja dan akan ya bi ta Abuja sai ta fasa zuwa Makka,Mama Balki ce ta ga yanda take cikin damuwa a hankali ta dafa kafad'ar Goggo Sarai ta ce mata, " Addu'ar fatan alkairi zaki ci gaba da binsu da ita kamar yanda ki ka fara ,ki daina zurfafa tunani, ki yi masu kyakkyawan zato Yaya," " To Bilki Allah ya kai su lafiya, Allah ya zaunar da su lafiya da alkairai maras yankewa" Amsawa dukkan su suka yi da " Ameen" suka koma cikin gida. ***************************** A gidan su Jabeer kuwa ya na can bai samu hutun da ya so ya samu ba ba dan komai ba sai dan tafiya da su Ammar da Abrar da suka yi, dan ma yaran sun shaqu sosai da Suwaibah musamman Abrar, amma ganin Jabeer sai ya sa Abrar maqale masa ta na yi masa rikici, daga qarshe da ya gaji ya tattara su ya kai wa Suwaibah su dan ya huta. Ko da aka kai wa Suwaibah su nan da nan ta karɓe su Ammar ɗin ta hau yi masu wasa, Ammar ya damu sosai da rashin Adda Calman shi, fitowa Suwaibah ta yi zata deb'o masa dambun naman da ya ragu a kitchen wanda akaiwa amare, tana tashi Abrar ta dinga tsaga kuka kamar ana zare mata rai ita ala dole Suwaibah ba zata tafi ta bar ta ba sai dai su tafi tare, Jabeer da Juwairiyyah na kwance a parlour sun d'aga labulayen d'akin su dan su sha iska su na hango duk abinda ke faruwa, mamaki ne ya kama Jabeer dan ganin yanda Abrar ke matuqar son Suwaibah, Juwairiyyah ce ta yi murmushi ta ce "Haka suke fa, in dai Addah Suwaiba na kusa to fa ni na huta,sai mu yini ko nono bata nema ba, sai dai ta yi ta bata kunun ta, idan kuwa na gama bata nono ban mayar da ita wajen Addah Suwaibah ba kuka zata dinga yi min kamar na sato ta" " Ikon Allah lallai akwai soyayya mai qarfi a tsakanin su," Lokacin bacci na yi Suwaibah ta d'akko Abrar dan ta dawo da ita wajen iyayen ta,Ammar kuma zai kwana wajen ta kafin gobe a maida shi gida Shima,tunani ta hau yi, 'Yanzu shikenan idan su Abrar suka koma gida na maida Ammar zan dawo na ci gaba da zama babu d'a babu jika, dama bahaushe ya ce son zuciya ,b'acin ta' Bayan ta yi sallama Juwairiyyah da ke kwance a jikin Jabeer suna kallo ta miqe ta buɗe qofar ta yi wa Yayar tata izinin shiga ciki, miqa mata Abrar ta yi ta na murmushi sannan ta ce, "Ga Iya rigima nan ta yi bacci sai da safen ku," Murmushi Juwairiyyah ta yi ta ce, "Iya rigimar gaske, ai wannan kyanta kawai a yaye ta ma dan ba wani shan nono take yi ba da dare" Da sauri yarinyar ta sake qanqame Suwaibah ta na so ta yi kuka, Jabeer ne ya tashi ya yi dabarar karb'ar ta a hankali sannan suka yi sallama da Suwaibah ta juya dan komawa sashen ta, ta na juyawa hawayen da suka taru a idanun ta suka zuba da qarfi a kuncin ta, zafin su ne ya sanya ta saurin sanya hannu ta share su sannan ta sa hannun ta na dama ta shafa marar ta, hawaye na ci gaba da fita a Idon ta. Ta na shiga sashen su ta tadda Alhaji Salihu zaune ya miqe qafa ya na jiran dawowar ta,ya na hango ta cikin wannan halin ya tashi cikin hanzari ya isa gareta, rungume ta ya yi dan ya fahimci halin da take ciki, kuka ta saki mai ban tausayi ta ce, " Yanzu Mine shikenan ba zan haihu ba, d'a ko 'ya ba zasu taba samun mazauni a wannan marar ba? Ya zanyi da son yara dake addabar zuciya ta Mine?" Kuka shima yake sosai, sai da suka yi ma'ishi sukai shiru dan kan su, sannan Alhaji Salihu ya ce, " kiyi hakuri ni na jawo maki wannan nakasar, ki gafarta min, nima ina cikin quncin rashin haihuwa,musamman inna kalli yanda Abrar ke son ki take matuqar qaunar ki,ba dan zaluncin da mu ka yi maku ba da na san zaki haifamin yara kyawawa kamar ta, amma na yi mana mugunta ba zamu ga k'wan mu ba a duniya Allah wadaran rayuwata bata da amfani" Da sauri Suwaibah ta sa hannu ta rufe masa baki ta ce, "Dan Allah kar ka sake cewa haka Mine, Allah ya albarkaci rayuwar ka Mine, ka ci gaba da gyara kurakuren ka na baya, ka duba ka ga ni fa yanda Allah ya maka albarka a kasuwancin nan, har fili ka siya, nan gaba kadan gida zamu yi na kammu mu koma, mu ci gaba da jin daɗin rayuwar mu, to meye na d'aga hankali har ka na wa kan ka mummunan kalami? Allah ke bada haihuwa fa, kuma ya na bawa duk wanda yaso ne,mu ba zamu yi kuka da Allah akan bai bamu ita ba,saboda mu da kan mu muka yi wa kammu mugunta dan haka hakuri zamu ci gaba da yi," Juwairah ce ta koma sashen ta da gudu tana kuka, sai da Suwaibah ta koma sashen ta ta tuna da turaren da ta siya masu da garin kayan qamshin da bata bata nata ba saboda ba su samu zama ba, shi ne dalilin da ya sa ta biyo sahun ta dan ta kawo mata nata sai kuma ta ji duk abinda ke faruwa a tsakanin ma'auratan, kuka take sosai har tana shessheka, wani irin tausayin su ne cike a zuciyar ta, Jabeer gaba daya ya rud'e ya rikice sai ya kama tambayar Juwairiyyah ya na fad'in, " Babe me ya faru ? Me aka yi maki ki ke kuka haka?.... Ya Allah Sanar dani abinda ke damun ki ko zan iya sama maki kwanciyar hankali, ki sanar dani kome ki ke so na yi miki , kukan ki na d'aga hankalina" Da sauri ya maida k'wallar Idon shi dake barazanar fitowa saboda rashin son ganin Juwairiyyah a cikin damuwa, cikin shessheqar kuka Juwairiyyah ta ce, "Sweet one ka taimake ni ka bawa su Adda Suwaibah Abrar" Maganar ta ta yi matuqar dukan shi,anya ba gamo matar tashi ta yi ba kuwa? Kyautar fa gudan Jinin shi k'walli ɗaya jalli jal take so ya yi? to ta yaya ma zai iya yin kyautar ɗan mutum balle Abrar ɗin shi farin cikin shi? Duba da yanayin damuwa da tashin hankalin da take ciki ne ya sanya shi rungumar ta ya na lallashin ta dan ta dawo hayyacin ta da wuri ta bashi labarin abinda ke faruwa. Sai da ta nutsu ta daina kukan ne Jabeer ya umarce ta da ta sanar da shi akan wane dalilin zai ba da yarinyar shi guda ɗaya tilo,babu bata lokaci kuwa Juwairiyyah ta yi masa bayanin duk abinda ta ji Suwaibah da mijin ta suna tattaunawa akai cikin kuka batare da ta rage komai ba, shi kanshi Jabeer labarin ya taɓa zuciyar shi sosai, " Tabbas sun cancanci wannan kyautar daga gare mu,nima Allah ne ya ban ita ai ba ni naba wa kaina ba,dan haka na basu ita halak malak, ko bayan raina Abrar wato Hafsat 'yar su Suwaiba da Salihu ce" Sai Jabeer ya wani kashe murya dan ya sake sanya ta farin ciki ya ce, "kinga da mun koma gida sai mu samu qanwa ko qanin Abrar ko? Idan mace ce a sanya mata Sunan Mama Balki idan kuma namiji ne mai rabo ya ɗauka tsakanin Abbah da Baba ko?," Yana maganar yana shafa cikin ta yana murmushi,cike da narkewa a jiki shi Juwairiyyah ta ce, "Ni dai Yah Jabeer anan nake so, sai mu haɗa da addu'a Allah ya sa a dace, ka ga daga gobe ma zaka iya fara kira na da Maman Abbah" Dariya ta sanya ta kai masa dukan wasa saboda ta bawa kanta da kanta kunya, shi kuwa sai ya goce ta daki iska ya shiga d'aki da gudu ta bishi suka kashe fitila, abinku da makauniya ido sai da gilashi sai na fito na basu waje. Da misalin ƙarfe goma na safe su Juwairiyyah ne suka gama shirin tafiya Abuja sun shirya kayan Abrar da komai da take da buqata a wani akwati,Sallama suka je yi ma su Innarmu tare da qudirin sanar da su hukuncin da suka yanke suna zama su suwaiba da Salihu suka shiga,cike da fara'a suka gaggaisa, Abrar na ganin Suwaiba ta hau yunqarin zuwa wajen ta, cikin shauqi da kewar yau zata rabu da Abrar ɗin ta ta ɗauke ta ta rungume tana kissing din ta, ita kuma sai dariya take yi ta zaci wasa ake yi mata, k'walla Juwairah ta share ta tsananin son 'yar ta ta amma haka zata bawa Addan nata ita dan kuwa gaba ɗayan su sun san matsalar da take ɗauke da shi na rashin haihuwa,cikin murmushi Juwairiyyah ta miqa wa Addah Suwaibah akwatin yarinyar tace, " Addana daga yau kin zama Ummu Abrar, dan Yah Jabeer ya miki kyautar ta gaba ɗayan ta, kin cancanci zama uwa a gareta, dan haka ga ta nan dama ita ba wai ta damu da nono bane, kunun nan da kike bata shi yakamata ki ci gaba da bata, Allah ya raya maku ita da imani mu zamu wuce muna yi maku fatan alkhairi" Ta ja baya Suwaibah da Salihu tare da Innarmu da kuma Abbah Balarabe sai suka shiga wani irin yanayi na tsakanin mamaki da ta'ajibi, Abbah ne ya iya magana ya ce, "A gaskiya Juwairah ke alkairi ce ga rayuwar zuri'ar mu baki ɗaya daga birni har qauye, tabbas Qanina da Bilkisu sunyi matuqar qoqari wajen baki tarbiyya managarciya, baki nufin kowa da sharri a rayuwar ki kullum alkhairi ne a tsakanin ki da kowa,wannan shine dalilin ne ya sa kika zamo mai samun nasara da ɗaukaka a rayuwar ki, Allah ya yi muku albarka, kai ma Jabeer na ji daɗin wannan kyauta da ka yi, duk da nasan ita zata saka ka yi, amma da baka aminta ba da hakan bai samu ba," Sai a wannan lokacin ne su Suwaibah suka fita daga yanayi na mamaki suka hau godiya ba qaqqautawa, Innarmu ce tace, " Suwaiba Allah ya taya ku riqo, ya sa ki qoqarta bata tarbiyya mai kyau yanda zata tashi abar so ga kowa" Cikin kukan farin ciki Suwaibah da mijin ta ke gyad'a kai alamar za su yi duk abinda ya dace dan baiwa Abrar rayuwa mai inganci,daga qarshe Suwaibah zuwa ta yi ta rungume qanwar tata tare da durqusawa a gaban Jabeer ta na kuka, d'ago ta ya yi ya na buga bayan ta da sigar lallashi, yana kada mata kai alamar ta dena kuka,Salihu ne ya je ya miqa mai hannu daga baya ya rungume shi ya saki kukan murna Shima dan kuwa sun yi masu kyautar ba zata, " Na gode ! na gode ! Ban taɓa ganin mutanen kirki irin ku ba,baku yi la'akari da rayuwata ta baya ba kuka mana wannan kyauta Allah ya faranta maku, ya baku yara masu albarka,Allah ya bamu iKon kula da ita fiye da yanda za ku yi mata," "Ameen" kowa ya amsa sannan su Juwairiyyah suka ja akwatin su suka tafi zuwa mota,suna barin qofar gidan nasu Juwairah ta saka kukan rabuwa da 'yar ta, hannun ta Jabeer ya kama shima yana jin wannan kewar na damun zuciyar shi, amma ba yanda zasu yi dole su yi haƙuri na ɗan lokaci ne, Allah ya basu ladan abinda suka yi a hankali Juwairiyyah ta warware suka hau hira har daga baya bacci mai daɗi ya ɗauke ta........ [04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA    💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 32: Ba a tafi kai amarya Nafee d'akin ta ba sai da misalin 10am saboda kukan da suka tsaya yi ita da Innarmu da Juwairiyyah sai kace idan an rabu ba za a sake haɗuwa ba, kuka suka dinga zuba wa har sai da suka ba wa mutane tausayi shaquwar da ke tsakanin Innarmu da Nafee ba karama bace domin kuwa ko hutu Nafee ba ta zuwa gidan kowa kullum ta na tare da Innarmu su yi faɗa su yi daɗi,sai gashi yanzu aure zai raba su zai kai ta can nesa garin da ba ta da kowa, nasiha aka dinga yi masu tare da nuna masu ai rabuwa ba mutuwa bace wata rana za su gana,har a cikin mota Nafee bata daina kuka ba a haka suka kama hanyar garin Kebbi dan kuwa anan ne za ta tare. Mama Balki da Saudat na daga cikin 'yan kai amarya gidan ta dan kuwa kowa ya san halin Goggo Sarai idan aka ce ta je zuwa za ta yi ta zubar wa da Nafee mutunci a gidan surukan ta musamman da yake su na da rufin asiri,har yanzu halin ta na son abin duniya na nan sai dai kwad'ayin ace yaranta ne ke da dukiyar ya ragu gudun kar a koma 'yar gidan jiya, ga wani irin  jiji da kai da take yi, ta ji zafin rashin tafiya da ba a yi da ita ba amma haka ta jure ta danne saboda kar ta yi magana a yi mata caaa dan ta kula dangin mijin nasu haushin ta suke ji tun da suka samu labarin abinda ya samu su Saudat. Juwairah ta so matuqa ta je amma Abrar ta sha gajiyar biki bata da lafiya dan haka Jabeer yace ba inda zata kar su je gajiyar hanya ta sake sanya 'yar shi rashin lafiya,ai kuwa haka ta zauna ta dinga kuka har dai daga qarshe ta ba wa kan ta da kanta hakuri. Cikin masu kai amarya har da qannen Abbah Balaraben su  Goggo Karima da Goggo Mero,sai ta bangaren Innarmu ma mutum biyu aka zab'a Inna Fateema da Inna Aishe, sai kuma wata aminiyar Innarmu wato Baba Maryam,lokacin da suka isa Birnin Kebbi dare ya yi sosai gaba dayan su jikin ta qaura ya yi la'asar, a unguwar Alieru Quaters motoci guda ukun da suka d'akko amarya suka tsaya,tun daga yanda gate ɗin gidan yake zaka gane fasalin gidan nasu gidan ya bambanta da na sauran mutanen unguwar,kana kallon gate ɗin zaka san gidan masu akwai ne, yan uwan ta sai san barka suke su na yi mata addu'ar Allah ya zaunar da ita lafiya ya sa gidan zaman ta ne na mutu ka raba, kwanan su biyu suka fara shirin komawa Kano,Saudat kuka tasa data tuno nisan hanyar da suka kwaso, sai lallashin ta ake abokin angon daya tuqo su yana ta mata dariya ya ce, " A gaskiya zan faɗa ma Umar farouq ya shirya matar shi raguwa ce" Ta na jin haka ta miqe ta goge hawayen ta tare da zabga masa harara ta ce, "Inji waye ya ce maka ni raguwa ce? Ni kar ka wani fada masa komai mu tafi" Dariya aka saka a wajen banda Nafee da take rab'e a gefen mijin ta ta yi kalar tausayi, ai ko suna barin qofar gidan nasu ta fashe da nata kukan,'yan kai amarya na hanya suna tausayin Nafeen, ganin yanda take zubar da hawaye ne ya sanya angon ta ɗaukar ta cak a hannun shi ya yi ciki da ita yana lallashi, mijin Nafee ya na son ta sosaiii ya na da kirki gashi da kulawa da tattali gefe d'aya kuma ya na tausayin matar shi duba da garin da ya kawo ta bata da kowa sai shi. Bayan dawowar su Saudat Kano lafiya ne aka kai kowa gidan ta aka aje ta, abokin angon daya kawo su Mama Bilki ne ya tsaida Saudat, cikin kashe murya ya ce, "Ba daban Farouq ya rigani ba yana da kirki da nagarta tabbas dana kawo kaina nima,zuciya ta ta kasa haƙuri ta ce kar na tafi ban sanar dake sirrin dake raina ba,Saudat na kamu da son ki a kwanakin nan da muka yi tare, ina maki fatan alkairi, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a mumina saliha" Saudat ta ji daɗin yanda ya ke da fahimta da addu'o'in da ya musu,ta kula shi ɗin mutum ne mai natsuwa da hankali, murmushi ta yi sannan ta ce, "Na gode sosai da soyayyar ka a gare ni, ina ma ka fatan alkairi, Allah ya baka wadda ta fini, tabbas abotar ku akwai amana kuna da halin manya," Murmushi suka yi sannan daga baya ya mata sallama ya ja ya tafi. Kwana biyar tsakanin bikin Nafee masoyan huɗu suka hau musayar saqwanni da jaddada manufar su ta son auren su Saudat ɗin, dan haka su kuma suka ce su zo su sami Baban su a San da zaman su. Babu b'ata lokaci kuwa wata ranar lahadi da yamma wasu dattijai suka zo gidan Baba Baballe dan nemawa Farouq da Ibraheem auren su Saudat ɗin,a wasu manya-manyan motoci suka zo wanda yasa baba jin tsoron kar a maimaita 'yar gidan jiya fa,daga ƙarshe dai Baba  ya kirawo yayan shi wanda ya jima da fara bincike akan zuri'ar gidan su Farouq ɗin tun da Jabeer ya sanar da shi labarin da Juwairiyyah ta faɗa masa game da yaran, ya na zuwa ya tabbatar wa da Baba Baballiya ai mutanen kirki ne a nan take suka roqi arziqin a d'aura auren in babu wata damuwa, saboda ba a kusa suke ba kowa da garin da yake aiki, shi Abban su Farouq mazaunin Abuja ne sai qanin shi dake lagos, dayan kuma a kebbi yake, Baba Baballe sawa ya yi a kira wani kawun su daya rage masu da abokin shi babba ga kuma Yayan shi aka haɗu aka daura auren su Saudat da Farouq, Salma da Ibraheem akan sadaki naira dubu hamsin hamsin, tare da alqawarin Ibraheem zai riqe yaran Salma kamar nashi in sun masu izinin hakan, su Abbah sun yarda amma sun qara da cewa in babu takurawa sun masa izini,su kuwa iyayen su Farouq suka jaddada masu cewa shi Ibraheem da kan shi ya sanar masu ba Salma kawai yake so ba, har da Yaran ta ya gani ya kamu da qaunar su dika,Baban su Suwaiba ya ji daɗin hakan sosai, a haka taron ya tashi cikin farin ciki da yarjejeniyar sanda duk Amaren da angwayen suka shirya a tsakanin su sun tare. Bayan wannan daddad'an labarin ya iske dangi kowa ya yi murna Juwairah ta roqi Jabeer akan ya barta har a gama hidimar tarewar Yan uwan nata kan ta koma, ya amince mata ta zauna amma shi da yamma zai koma Abuja sabida aikin shi, sun bari akan in ta kammala ta sanar da shi sai ya zo ya ɗauke ta, kuɗi ya bar mata mai yawa a hannun ta kan ya tafi saboda hidimar yau da gobe. Haka Jabeer ya tafi suna jin kewar junan su dan kuwa  basu son abin da zai raba su sai dole,gashi bata san ma ranar tarewar amaren ba ta yi azarb'ab'in cewa a bar ta,haka Juwairiyyah ta dawo daga raka shi jiki ba kwari. Ta na zama ta ji wayar ta na ringing a gefen ta, dauka ta yi taga Nafee ce cikin murna ta amsa suka yi wa junan su sallama tare da gaisuwa,cike da jin nauyi Nafee tace, " Matar yaya kunyi min mantuwa fa, kun manta tsimi na ba a sako da shi ba" " Subhanaka ya raheem, ai ko kinga har yanzu ba wanda ya kula, babu damuwa ai kinga yanda na haɗa maki wancan ko? ki haɗa wani kawai,idan yaso wannan na bawa su Adda Saudat, keee ! Ban faɗa maki ba, an daura auren su ma jiya, tarewa kuma ance ba yanzu ba sai sun shirya magana da mazajen su, iyayen sunce basu buqatar komai sai matan yaran su za a kai masu kawai kin ga kuwa Ina kyautata zaton ba za a ɗauki wani lokaci mai yawa ba za su tare" Cikin murna Nafee ke addu'ar Allah ya basu zaman lafiya, bayan gama murnar ne tace, "Ni fa matar Yaya na manta wasu abubuwan ɗan sake faɗan mana pls" " kai Nafee ko dai angon ya kwashe har da basirar ki ne?" Dariya suka yi Nafee tace cikin shauqin son mijin nata, " Matar yaya wato My love daya ne tamkar da ba iyaka acikin mazajen wannan zamanin" " Oh ni Juwarah yarinya ta fitsare bari nayi na gama faɗa maki na kashe wayata, ina nan ina tausayin ki ashe ke kin gama zama yar hannu ma abin ki," Dariya suka yi tayi kafin Juwairah ta ce; "kanin fari Zaki sa a siyo maki kadan zaki saka ba mai yawa ba, saboda masu magungunan gargajiya da na asibiti na ji sun tabbatar da cewa shan shi da yawa na kawo ciwon hanta, dan haka ki saka kaɗan sai citta mai dan yawa,da minannas, sai ki matse ruwan rake mai yawa, ba a qara wani ruwan da wannan ruwan raken Zaki yi amfani, Zaki samu rake ne iya adadin yawan da ki ke so yawan tsimin ki ya kasance, sai ki samo zuma mai kyau sosai ki saka sai ki dake kayan qamshin nan ki saka a ciki, sai kin ga ya yi kauri kadan ma'ana bai yi irin ruwa tsululu ba, zumar ce zata saka ya yi kaurin, ki dinga sha da yamma,amma pls wajen nemo zumar ku tabbatar me kyau ce kin san yanzu an b'ata zuma sugar wasu ke saka wa,idan taso na baiwa su Adda saudat wannan nakin nima na dan sha kafin na koma nawa gidan" "Na gode matar yaya sai an jima ki shafan min kan bbyna, ina gaida yaya" " Ni ma ina gaida angon ki" . Washe gari sallama ta yiwa Innarmu ta tafi gidan su ba zata dawo ba sai an gama tarewar yayun ta, ta kaiwa Yayun nata wannan tsumin, sannan tun da suka faɗa mata mazan su sun ce ai nan da kwana biyar za su tare, Juwairiyyah ta shiga hidimar taya su gyaran jikin su,sai ga su  Saudat sun fito fess da su fata na sheqi da kyalli , itama kanta uwar gyaran jiki sai da ta gyara dan a cewar ta itan ma amarya ce, tin da ta je gidan take ma su kwad'on zogalen daya sha timatir da cucumber,haka take wa zogalen tafasa ɗaya ta kwashe shi da ruwa-ruwa a babban mazubi,ta yanka manyan timatir masu yawan gaske sannan ta zuba masu qulin da ya ji kayan qamshi. (Wannan haɗin ba k'aramin ƙara ni'ima yake yi ba sosai) Duk daren duniya kuwa ta na samun kabewa ta yi ta haɗa masu da madara da zuma suna sha,( wannan haɗin yana gyara skin da qarin ni'ima) Suna cikin lokaci na mangwaro ne, dan haka Juwairiyyah sai ta sa a siyo masu mangwaro mai yawa su zauna suna sha suna zuba hira abun su gwanin ban sha'awa. Idan aka zo maganar tsarki da had'in ta na musamma da bata gajiya da haɗawa sai Salma ta yi ta jin kunya kar a gan su ace su na rawar kai,haka za su haɗu a d'akin su su yi ta mata faɗa musamman tunda ita ta haihu ta fi saudat bukatar wannan gyaran. Goggo Sarai gaba ɗaya jikin ta ya yi sanyi qalou da lamuran gidan ganin yanda Mama Balki da 'yarta ke k'ok'arin ganin nata yaran sun je gidan Mazajen su da martaba da k'ima, tabbas Allah shine mai azurtawa ba mutum ba, duba da cewar gashi dai duk bala'in son kuɗin ta ta kai yaran Abujar kuma sun wahala babbar 'yarta ma har da nakasa, finally gashi yanzu Allah ya basu inda za su huta ɗin cikin sauqi ba tare da sun wahala ba sannan mazan nasu ' YAN ABUJAn ne dai ba wani garin na daban ba, hawayen da take qoqarin mayar wa ne wani ya gangaro,Mama Balki ta kalle ta ta ce, " Yaya ki daina kuka, in yaran nan suka gani zaki d'aga masu hankali" " Hmmm Bilki dole abun ya dame ni, ban zamo uwa ta gari ba sam sam a gare su, na tsani rayuwa da turbar dana ɗora yarana akai a baya" "Hakane Yaya kinyi kuskure babba a baya, amma yanzu ai ya wuce ya zama tarihi,kuma in shaa Allah hutun da kike nema masu a rayuwa zasu same shi, kai sun ma same shi da iKon Allah" Cikin gyad'a kai da yarda da maganar ta ta ɗauki kwanon abinci ta isa d'akin su ta miqa masu ta fice.......... [04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 34: Labarin kyautar Abrar zuwa ga Suwaibah da mijin ta babu inda bai shiga ba a dangin nasu baki ɗaya har ma da mutanen unguwa, inda kowa yake farin ciki da irin wannan kyautar da Juwairiyyah ta yi wanda ba kowa ke iya yin irin ta ba, banda sanya albarka da fatan alkhairi ba ka jin komai a wajen mutane, sai kuma addu'ar Allah ya ba wa su Suwaibah iKon kula da tarbiyyar yarinyar. Ya ku masu yi wa wanda Allah bai ba wa haihuwa ba gori ku ji tsoron Allah ku bari dan kuwa shi ke bayarwa ba mutum ne zai ba wa kan shi ba, da mutum ne yake ba wa kan shi da wata ba zata haifi yaro mai kalar baqi ba fari zata ba wa kan ta, da mutum ke ba wa kan shi da wata ba zata haifi fari ba baqi za ta baiwa kan ta, kun ga kenan Allah shi ne yake bawa wanda ya so ya hana wanda ya so ba dan baya son shi ba. A yanzu wai mutane idan baka haihu ba ka zama mutum mara daraja a idanun su har kalmar juya za su dinga Kiran ka da shi, wannan matsala tafi fitowa daga dangin miji, musamman idan aka yi rashin sa'a basu da ilimin addini da wayewar ilimin zamani, jahilci ya musu yawa to daga ranar ka shiga uku in baka haihu ba, ba sa tinanin cewar ma ko laifin daga ɗan su ne? Ko kuma jinkiri daga Allah ne, ko wata rashin lafiyar da za a nemi maganin da ya dace da an samu haihuwar,su na mantawa komai himmar ma'aurata ba za su samu haihuwa ba sai da izinin Allah,mata masu gorin haihuwa mu sani kowacce mace dangin miji ce, ki kyautata kema sai a kyautata maki. Da yawan gorin ma idan ki na da yaran wata bata da su ne zai hana ki zama kamar Juwairah? Ba zaki iya ba ko? To kar ki sake shiga hurumin Allah,idan kuma ba haka ba ki sa a ran ki ba da wadda bata haihun ba ki ke yi da Ubangijin ku da ya baki ita kuma bai bata ba da shi ki ke yi, sai ki jira amsawar shi domin kin tab'o shi. Satin su Juwairiyyah uku da komawa Abuja har ta fara sabawa da rashin Abrar a tare da ita,ta bi duk wani process na yaye dan ta samu jikin ta ya zauna da kyan shi,ta yi had'in Sabaya wanda ta qara masa da dankalin hausan da ta busar aka niqa mata da sauran kayan had'in, sannan idan ta tashi sha ta na zuba madara sosai ta shanu,da yamma kuma ta markad'e ayaba da gyad'a ta zuba madara ta shanye,gefe ga man kaɗanyar ta da ta kwaba shi da man hulba da na Habbatussauda ta na shafawa a qirjin nata,cikin qanqanin lokaci ta yi wani irin kyau ta yi fresh ga cikakkiyar ni'ima da had'in ya qara mata,Jabeer ba ya gajiya da hidimta mata da ya ji ta ce Yah Jabeer siyo min kaza a guje yake siyowa dan ya san karshe shi zai amfana da hakan. ( Dan Allah maza ku sauya hali ku gyara matan ku na gida sai ku jima kuna morar su,ko da za ku ƙara aure ba zaku wulakanta na gida ba saboda duk abinda wadda Zaku kawo gidan Itama ta gida ta na da shi,duk abinda zaku yi wa matan na kyautata wa wallahi ba ku faɗi ba riba ce a wajen ku duniya da lahira, kai kuma saurayi da ka ke shirin yin aure ka dai ji yanda Jabeerun Innarmu ke kula da matar shi,ke kuwa uwar gida ko amarya kin ga yanda Juwairiyyah ke qoqarin gyaran jiki, tsafta, shagwab'a,iya girki,kula da miji a azaroom da duk wani abu da ya dace, dan Allah kowa ya gyara saboda rayuwar aure ta yi kyau ta yi qarko) Yamma ce sakaliya, gari ya yi luf luf gwanin sha'awa kasancewar lokaci ne na damina hadari ne ya ke son haɗuwa iska sai kad'awa take mai sanyi,a daidai wannan lokacin kuwa Juwairiyyah ta gama duk wani abu da ya kamata ace macen kirki ta aikata shi kafin dawowar mijin ta daga aiki,irin su girki, gyaran gida, wanka, da kuma tsaftace ko ina na jiki da muhallin ta tana zaune tana jiran Haerbeebeen ta ya dawo,ko me ta tuna sai kawai ta miqe ta shiga kitchen ta sanya hannun ta ta d'akko wata roba da ta cika ta da niqaqqen garin rid'i, a hankali ta fara jin wata iriyar kasala na shigar ta ta na jin jikin ta ba kwari tin kwana biyu da suka wuce ta fara jin hakan, cup din da ke hannun ta ta matsar jikin robar domin ɗiban rid'in,tana bud'ewa qamshin kantun da take so ya daki hancin ta ta ji gaba ɗaya ya hau kan ta,a haka ta daure ta saka spoon ta d'iba sannan ta buɗe robar kayan kamshin da ta niqa na had'in kaninfari minannas da citta ta deb'o kadan ta zuba, zuwa ta yi tukunyar da ta dafa madarar shanu wadda Jabeer ke nemo mata a cikin wani qauye anan Abujan ta d'ebi yanda zai ishe ta ta zuba, zuma asalin mai kyau mara haɗi ta d'iba ta zuba a cup ɗin ta hau juyawa, a haka ta isa parlour ta samu waje a ɗaya daga cikin kujerun da suka yiwa palourn qawanya ta zauna, bayan ta yi bismillah ta riqe cup din da hannun ta na dama ta kai bakin ta da sauri ta sauke shi saboda wani irin amai da ya taso mata, da gudu ta miqe zata yi hanyar dakin su dan ta je toilet,ta ci karo da Jabeer wanda shigar shi kenan gidan,kafin ta yi yunqurin kauce masa amai ya taho da gudu nan take ta wanke masa jiki da amai, jikin ta har rawa yake yi kamar mai jin sanyi, wani irin zazzaɓi ta ji ya rufe ta a lokaci d'aya, ajiye jakar shi ya yi hankalin shi a tashe, ya kama ta ta duqa tana ta ci gaba da kwarara amai, sai da ya zamana bata iya fitar da komai sai yunqurin azaba sannan ya ja ta zuwa toilet ɗin da ke a cikin parlourn su, sai a sannan ne ta tuna da samuwar shi,tun Juwairiyyah na iya amsa sannun Yah Jabeer har sai da ta dawo gyad'a masa kai kawai ko ta lumshe masa ido. Idan hasashen shi ya zama gaskiya to fa wannan karon Juwaireren shi ta haɗu da ciki mai laulayi da wahalar wa, dan ya kula kwana biyu kenan tana fama da wannan zazzaɓin da kasala da kuma yawan amai,a lissafin shi ya kamata ace tun sanda suka dawo daga Kano ta yi al'adar ta amma ya ji shiru wanda ita ta ma manta gaba ɗaya. Bayan ya taya ta wanke bakin ta ne sai ya fara cire masu kayan jikin su ya saka a washing machine sannan ya tara ruwa a kwamin wanka mai d'umi kamar yanda yake so dan kuwa Jabeer na son wanka da ruwan zafi baya son ruwan sanyi a cewar shi ruwan sanyi na sanya shi kasala da zazzaɓi shi ne dalilin da ya sa ko da zafi ne sai ta kashe masa sanyin ruwa ya iya wanka da shi,wanka ya musu tas suka fito a tare, bayan ya shirya ta ne ya kwantar da ita a a gado ya je ya gyara parlourn sannan ya shirya shima,zuwa ya yi kusa da ita ya kwanta ta bayan ta ya riqe ta tsam a jikin shi, a hankali ta furta, " Honey ka je kaci abinci na ajiye maka komai a inda ya kamata idan kuma ka na buqatar wani abu ka kira ni, na gode da kulawar ka a gare ni Allah ya yi maka albarka" "Ameeen tare da ke,na san kin gama komai 'yar aljannah ta da yardar Allah,bana jin zan iya cin wani abu bayan ki na cikin wannan halin,yanzu menene ke yi maki ciwo, me kike son ci? dan daga ganin ki da kuma aman da kika yi na gane baki ci komai ba in ba wainar flour ɗin da ki ka yi mai manja ba da safe," Turo baki ta yi daga baya ta kwab'e shi irin na shagwab'abun nan, shi kuma yana jin yanayin saukar nunfashin ta ya san kuka take yi, saurin juyar da ita ya yi suna fuskantar juna ya ce, "Ki sanar da ni duk abinda ki ke so zan yi k'ok'arin sama maki shi in shaa Allah" kukan da take son yi ne na shagwab'a ta fara sauke masa shi, rungume ta ya yi yana sumbatar goshin ta a hankali yana shafa bayan ta,sai da ta yi kukan da ita kan ta take mamakin dalilin yin shi sannan ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya, a hankali ta fara yin magana, " Yah Jabeer bani da lafiya, kwana biyu jikina ciwo yake yi min sosai, ga zazzaɓi da amai da nake fama da shi, abubuwan da nake so a da yanzu sai na ji bana son su," Sai kawai ta sake b'arkewa da sabon kuka cikin murmushi Jabeer ya ce, "Shhhhhhhh ! ya isa haka to, yi shiru Babyn Yah Jabeer,ki daina kuka kin ji? ko zaki yi gwajin ciki a gida ne na d'akko maki PT strip ɗin ki?" Jimm ta ɗan yi kafin daga baya ta wuntsila daga gadon cikin d'oki da zumud'i, binta ya yi a baya yana mata dariya, dan ya kula bata kawo hakan ba sam a kan ta tun fari sai yanzu, zuwa ta yi tai gwajin ta fito ta na murmushi cike da jin kunya ta nuna masa layuka guda biyu da ke jikin tsinken, kwab'e fuska ta yi cikin shagwab'ar da ta san ta na birkita Yayan nata tace, "Ni dai ban gane komai ba," "To ko asibiti zamu je kawai a tabbatar?" Hakan take so dan kar ta ba wa kan ta false hope akan abinda ta gani a jikin tsinken gwajin, dan haka cikin zaquwa ta ce, "Ehhhh Yah mu je dan Allah,ina zuwa na shirya" Barin toilet ɗin ta yi da hanzari taje ta sauya kayan jikin ta zuwa doguwar riga da babban mayafin da zai rufe har mazaunan ta, Jabeer ma tuni ya shirya cikin doguwar Jallabiyyar shi kalar blue mai farin aiki,ya ɗauki makullin mota suka jera a tare suka fita zuwa asibiti A wani private hospital suka tsaya wadda yake a unguwar Jabi, suna zuwa suka yi duk abinda ya dace dan ganin likita, daga nan ma'aikatan wajen suka shiga yi mata gwaje-gwaje bayan an d'ebi Jinin ta da kyar sai kuka take saboda bata son allura sam,bayan kammala komai ne lab suka bata result su kuma suka kai wa likita, likitan ya tabbatar masu da tana dauke da ciki na sati uku, wata irin murna ce ta kama su gaba ɗayan su, Jabeer ba ko kunya ya daga ta sama ya hau juyi da ita, ita ko sai dariya take yi su asibitin ganin hakan ba sabon abu bane a wajen su, dan kuwa shi kan shi likitan sai yaba wa yanda ya ga suna son juna da kulawa da junan su yake yi,sumbatar labb'an ta ya yi sau ɗaya sannan ya ajiye ta,hamdala ya dinga yi ga Allah sannan ya hau godiya ma Dr. da bakin shi ya qi rufuwa, bayanan yanda zasu kula da cikin ya yi musu, wanda sun riga da sun sani tunda wannan ba shi ne na farko ba,amma sai suka koma kamar ba su taba ma sanin ya ciki yake ba tsabar murna, bayan sun gama ne suka fito Jabeer na wani lallaba ta kamar k'wai ita kuwa abin nema ya samu sai wani narkewa take yi kamar cikin ya yi watanni a jikin ta,cike da kulawa Jabeer ya ce, " Babe me kike so ki ci kinga kar kina barin kan ki da abinda zaki haifa mana da yunwa" kad'a kai ta yi a hankali sannan tace, "Ni ba komai kawai ina son wainar flour ne irin ta dazu," Babu b'ata lokaci ya saka ta a mota suka yi gida, suna zuwa ya shiga kitchen da kan shi ya hau yi mata wainar, cup ɗin da ta yi haɗe haɗen ta ya gani a fridge sai ya tuna sanda ya na gyara parlour ya gan shi ya dawo da shi fridge dan kar ya ɓaci,dakkowa ya yi ya na murmushi, ya juye wainar da ya gama ta qarshe ya kai mata da yaji mai daɗi da ya ji garlic da busasshen soyayyan nama a ciki, tana cin wainar ta yana shan had'in, cikin santi ya ce, "Lallai babyn nan da qoqarin shi ya zo,da alama baya so ki na shan irin wadannan abubuwan" Dariya suka saka dikkan su Juwairiyyah ta ce, "Idan ban sha ba ai kai gaka nan ka na sha ko?" Qara fashewa da dariya suka yi a tare, Hadin kantu da madarar shanu ko ta ruwa ta gwangwani ko da nonon Raqumi,had'i ne tested and trusted dake saukar da ni'ima sannan ya yi maganin wasu cututtukan jiki in baka da nonon Raqumi sai kai da madarar shanu. ***************************** Wata iriyar shaquwa ce mai tsafta tare da so da qauna da tausayi ke wanzuwa a tsakanin Saudat da Farouq ɗin ta,wanda a kullum ganin ta ya ke yi kamar sabuwar budurwa, lallab'a ta yake yi kamar k'wai baya son duk abinda zai taɓa masa ita tsakanin su akwai tazarar shekaru bakwai, shi yasa take zuba shagwab'ar ta yanda take so musamman dan har mantawa take yi da ta taɓa aure sai wani dalili ya faru da zai tuna mata da hakan. Wasannin su suke ta yi a palourn su kamar wasu ƙananan yara, irin wannan rayuwar Umar da Saudat ke buri a rayuwar su sai gashi sun samu abokan cika burin nasu,qafar saudat ce ta tafi gaba sai ta yi kamar za ta faɗi, da sauri Farouq ya isa gaban ta ya riqe ta ya na tambayar ta lafiya take dai bata ji ciwo ba ko ? Ganin yanda ya rikice ne ya sanya saudat murmusa wa ta kama fuskar shi a tafukan hannayen ta ta na kallon k'waryar idanun shi daga baya ta lumshe Idon ta a hankali ta sumbace shi. Lumshe nashi idanun ya yi kafin daga baya ta janye cikin murya mai taushi ta ce, "Me ma ka ke tambaya ta d'azu?" Murmushi ya yi ya sauke idanun sa qasa sannan ya sake kallon ta cikin sarqewar magana ya ce, "Amm...nace...ammm.." Dariya suka sanya baki ɗayan su kafin Umar ya ce, "Ina son ki mata ta" "Ni ma ina son ka miji na fiye da yanda ka ke so na" Nan da nan ya shagwab'e mata ya na buga ƙafa irin yanda take yi masa ya ce, "Ah ahhhh ni dai na fi son ki" Itama ta shagwab'e fuska ta ce, "Ban yarda ba ni ce na fi son ka" Dariya suka saka sosai har tana riqe ciki, d'aga ta ya yi ta bayan ta suka samu wajen zama a kujerun nasu, bayan ya kwantar da ita a kujerar ne ya kwanta ta bayan ta Shima ya rungumo ta ta ciki ta,suna ci gaba da hirar su, a hankali suka yi shiru yana mata wasa da gashin ta ta ce, " Babe me yasa baka damuwa da batun rashin haihuwar da kasan ba zan yi ba, bayan kasan babu mahaifa a jiki na? Kuma kai baka taɓa yin aure ba, ko dai ka na da qudirin qara aure ne a nan gaba?" Murmushi ya yi mai sauti ya sake rungume ta a jikin shi cikin kulawa da tausayawa ya ce, " My dear ina so ki san cewa da auren da haihuwar duk nufin Allah ne, tayu a baki da mahaifan mu haihu saboda Allah shi ya san yanda yake yi ya azurta bawan sa mu namu hasashe ne da k'ayyade sai muna da kaza sannan kaza zai iya faruwa,sannan ta yu ba za mu haihun ba, to ina son ki sani, haihuwa is a blessing that everyone will love to have, amma ni bana daga cikin waɗanda suke ganin in mace bata haihuwa bata da amfani a wajen su,to ina soyayyar da ake yi mata? Dama dan Yara kawai aka aure ta? Ita ce take bawa kan ta? Idan zan maki kishiya saboda baki haihuwa tabbas na zama daga cikin azzalumai, na kuma zama daga cikin masu butulci ga Allah, domin ya min kyaututtuka mara iyaka da ba zan iya qirga su ba, to me zai sa dan akan abu ɗaya dana ke so ban samu ba na yi mai butulci? Ba zai yu ba, daga ranar da kika ji na qara aure ki tabbata na qara ne kawai dan ra'ayin kai na ko kuma ina son matar ne ya sa na aure ta Saudat, ba zan qara aure wai dan baki haihuwa,dan haka ki kwantar da hankalin ki ni ba mai ra'ayin tara mata bane bama, bana son hayaniya, ban son takura, mata da yawa na saka ni damuwa dan bana son raba fada kullum," Maganganun shi ba k'aramin kwanciyar hankali suka saukar wa da Saudat ba,har sai da hawayen farin ciki suka dinga fita daga idanun ta, tabbas Allah ya azurta ta da namiji ɗan gaske, Allah ya qara masa hakuri da juriya akan hakan ta ayyana a ranta. Ci gaba da shafa wuyan ta zuwa bayan ta ya yi da sigar lallashi,a haka bacci mai daɗi ya ɗauke su. ***************************** "Ki taho da fidar yaran nan da tissue love" Salma amsawa ta yi shi kuma Ibraheem ya zauna yana masu wasa, bayan ta iso ne ta zauna kusa da su ta miqa masa abinda ya ce ta kai, cikin tura baki irin na shagwab'ar nan Salma ta ce, " Ni dai gaskiya ban yarda ba nima sai an min wajen zama a nan, dan wayo kullum ni a qasa ko gefe zan zauna su kuma a cinyar ka?" Driya ce ta kama Ibraheem, sai ya dauki Hassana ya ɗora a wuya, sannan ya d'ago Salman ya saka a cinyar shi ta na facing ɗin Hussaina,murna ta hau yi tare da sumbatar kuncin shi ta ce, " Na goooode na zaci ai ce min za a yi na yi hakuri yaran su zauna na yi girma kamar yanda ka saba,da kuwa yau ba zan yarda ba sai dai a maida su d'aki ni na hau" Ta ƙarasa maganar ta tana sauka daga cinyar tashi, dariya yake sosai dan ya kula da Salma ta na kishi da yanda yake share ta idan ya na tare da yaran, gani take yi gaba ɗaya ya kwashe soyayyar ta ya basu dika, lokacin shi gaba ɗaya nasu ne in yana gida, amma a qasan ranta ba qaramin daɗi take ji ba saboda yanda yake son yaran kamar nashi, hankalin ta a kwance yake dan bata tsammaci hakan a wajen saurayi da bai taɓa aure ba kuma gidan su babu qananan yara balle ta ce ya iya reno. A cikin kujerar basu abinci ya saka su,ya ɗorawa kowa nata abincin a gaban ta, sannan ya damqa masu cokulan su a hannun su na dama,da kyar suke riqewa saboda rashin iya hakan, yana tsaye a kan su in ya ga zasu karkace ya gyra masu, ta baya ta ziro hannun ta ta tsugunna itama ta kwantar da kanta a bayan shi ta furta, "I love u" Shima waiwayar da kan shi ya yi suka hada ido yace mata, " I love u more my wife" Tare da sumbatar goshin ta ya juya ga yaran su suma ya yi musu,Salma ta tura baki ta ce, "Na hakura ni dai na saddaqar an fi son su akai na, ba za a taɓa yi min abu ba sai an yi musu suma" Dariya ya yi kawai dan ya san idan zai biye mata haka za su kwana ta na masa qorafi. Jama'a ina so mu gane cewa shi d'a na kowa ne, baka san wa zai more shi ba,shi yasa bahaushe ke cewa da d'a da dukiya ba a yi masu mugunta, in ka lalata su wataqila kai ka lalata wa goben ka da al'umma, idan kuma ka kyautata musu wataqila su amfane ka a gaba ko su amfani al'umma, wani sai ya gama tarbiyyar yaron ya girma saura qiris ya fara morar shi sai ya rasu ya bar wa duniya ta mora,wani kuma sai ya lalata tarbiyyar sai ya mutu ya bar wa duniya mugun iri ko rayuwar shi ta yi tsaho ai ta shan wahalar da shi,wanda ya kyautata ya na da lada mai yawa a wajen Allah, wanda kuma ya munana shi ma ya na da zunubi a wajen Allah . ***************************** Talle ne ya shirya tsaf da yar jaka a hannun shi wadda ta qunshi kayan yara mace da namiji dan bai san me Salma ta haifa ba, ko ma dai me ta haifa zai kai mata kayan ya fi ya je hannun shi na dukan cinyar shi,sallama suke yi da Marka wadda can cikin qasan ranta kishi ne danqare,sai ta danne kishin nata saboda yanzu ta waye ba duhun qauyanci da mummunan jahilci a tattare da ita, miqa masa leda ta yi wadda ta daka kuka,daddawa, da kub'ewa, tace ya kai wa Salame, godiya ya yi mata,Huwaila ma shiga sashen nasu da qullin ledar gyada soyayyiya itama ta bashi, dan sana'ar ta kenan a yanzu, tace ya gaida su ya nema masu gafar ta, amsa ya yi ya fita bakin shi ɗauke da addu'ar fita daga gida........ *To masu karatu Talle fa ya yi shirin zuwa Ta dabo,kun dai ga ya koma islamiyya har da addu'ar fita daga gida...* [04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏻 'YAN ABUJA 💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAEH PAGE : 35 https://chat.whatsapp.com/I8ImAD44ZKU2x8N4dbCpDr https://Wa.me/+2348036802447 *INA AMARYA INA UWAR GIDA HARDA MAI JOGO DA KE MAI SHIRIN ZAMA AMARYA MUNYI MAKU TANADIN KAYAN DA ZASU GYARA KU TSAB TSAB KIFITO DAGWAS DAKE KAMAR KE KIKA KERA KAN KI SANNAN KADA KU MANTA MUNA HADA JEGO PACKAGE BRADAL PACKAGE & SLIMMING PACKAGE WEIGGHT GAIN PACKAGE GA KUMA ANTI AGAIN PACKAGE SUPER WHITENING CAMBO BREAS AND HIPS PACKAGE GLOWING SET SKIN REPAIR ND REJUVENATIG PACKAGE BEAUTY START FRM WITHIN TAKE CARE OF THE*💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 35: Ammar ne zaune a tsakar gida ya na wasa irin na yara, ƙasa ce yake kwab'a wa da ruwa a buta,tare da rero karatun da Mama Balki ke koya masa,daga ya yi na qur'ani sai ya saki ya kama na boko,ya na nan zaune ya ji ana buga kofa tare da yin sallama,tashi ya yi ya nufi k'ofar gidan da gudu tare da yin wurgi da karan hannun shi da yake juya tuwon qasar shi,ya na zuwa ya d'aga kan shi sama ya na kallon mai yi masu sallama. Murmushi Talle ya yi da ya ga yaron nan take ya hango kamannin da ke tsakanin Salame da yaron, a hankali ya durqusa dai-dai tsahon Ammar ɗin sannan ya ce, " Yaro ina malam," " Faya nan" ( Baya nan), Talle ne yaga yaron ya kalli gaban shi yana dariya daga baya kuma ya fita da gudu yana fad'in " Babana Oyoyo" Wajen da Ammar ya nufa Talle ya bi da kallo,idanun shi ya sauka cikin na Baban su Salame,da saurin shi ya isa gaban Baba ya durqusa, gane wanene a gaban shi ne ya sanya Baba ya sauya fuska daga fara'a zuwa bacin rai, a hasale ya ce wa Talle, "Me ya kawo ka k'ofar gida na a yau?" Cikin sunkuyar da kai cike da tarin nadama Talle ya ce, "Baba dan Allah da son Annabin rahama ka yi hakuri ka saurare ni,Baba na san na tafka babban kuskure a rayuwa ta wanda zan mutu ina nadamar aikata shi dan Allah Baba ka yafe min, tabbas na kasance daga cikin jahilai, marasa sanin Allah a baya, sakamakon jahilcin da ya mamayi zuciyata, kuma naqi na nemi sanin Allah da dokokin shi, ina jin girman kai da ganin na wuce na nemi ilmin addini na yi girma da hakan, shiyasa na aikata munanan abubuwa a rayuwata kala-kala waɗanda naga isharar su tun kan aje ko ina, babbar isharar da na fara gani shine mutuwar 'ya ta,sannan na kama dan uwana Yayana da mata ta suna zina, ɗaya 'yar tawa ga ta can da ɗan gaba da fatiha, babbar isharar da ke d'aga min hankali itace rabuwa da Salame da na yi, ta tafi da cikina na rabu da ita rabuwa da ban nuna tausayi da imani a ciki ba,a yanzu nayi nadama, na koma islamiyya ni da iyalina dika, ka yafe min ba dan halaye na ba sai domin Allah" kalaman shi sun saka jikin baba ya yi sanyi amma sai ya wuce cikin gida kamar bai ji shi ba, yana shiga Mama Bilki ta sauke shi da ruwa da abinci, ga kuma ruwan wanka ta kai mashi bayi,zufa ta hau goge masa tare da jera mishi sannu da zuwa cikin tattausan lafazi, umartar ta ya yi da ta kira yayar tata,miqewa ta yi ta tafi Kiran Goggo, ta na shiga ta tarar da Goggo Sarai ta yi zurfi a cikin tinani har bata san shigar ta d'akin ba ma, yanzu da hankali ke qara shigar ta ba qaramin kunyar Mama Bilki take ji ba akan abubuwan da ta yi mata a baya, saqon Baba Mama Balki ta isar mata ta fita ta fara yin gaba,itama tasowa ta yi kamar wadda kwai ya fashe ma a ciki, ta bi bayan ta ta na shiga ta gansu zaune ita kaɗai ake jira ta samu waje ta zauna ta ce, " Ga ni baban su" D'agawa ya yi ya kalle su cikin sha'awar yanda suka koma a nitse ba hayaniya ko mummunan kishi, Ammar ne yaje wajen Goggo Sarai ya zauna a cinyar ta, shafa kanshi ta yi tana mai murmushi, cike da natsuwa Baba ya labar ta masu zuwan Talle da abinda ya sanar da shi, sannan ya tabbatar masu da cewar yanzu haka Tallen na qofar gida, haquri ya bawa Goggo Sarai da ya ga ranta ya baci, ya na juyawa yaga fuskar Mama Bilki ma a b'ace, mijin Salma ko da ba matsafi bane ya cutar da ita a zamantakewar su shima ba qaramin azzalumi bane, kwantar masu da hankali ya yi da dad'ad'an kalamai a hankali suka sauke fushin su, aika Ammar waje ya yi yace yaje ya shigo da baqon nan, cikin tsalle-tsallen yara ya tafi ya sanar da Talle Baba na Kiran shi. Talle ne ya shiga kai a duqe qafa duk ta sage masa saboda tsaiwa, waje baba ya nuna masa a kan tabarma, tsakiya ga abinci nan da ruwan sha, Goggo Sarai ce ta qaro ruwan sha da ɗan abin motsa baki dangin su cincin ta ajiye musu, ci suka yi suka qoshi, sannan Baba ya kira su baki ɗaya suka zo suka samu kujeru na tsugunne suka zauna kowaccen su sanye cikin hijabi,bayan sun gaisa da Talle ne Baba ya ce, " To da farko dai zan fara cewa alhamdulillah,dikkan godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai,sannan in sanar da kai dukkanin mu nan iyayen Salma mun yafe maka abinda ka aikata a baya, kuma muna saka ran itama ta yafe maka, tabbas ka cutar mana da yarinya, ka zalunce ta, amma duba da cewar muma masu zunubi ne a wajen Allah kuma mu roqe shi ya yafe mana banga dalilin qin yafe maka da muka yi ba, daga qarshe ina mai sanar maka yanzu haka Salma na Abuja gidan kuɗi gidan hutun dai da take fata da buri a rayuwa ita da yaran ka, dan kuwa biyu ta haifa dika mata,kuma ta samu miji saurayi ya dauki yaran kamar shi ya haife su, ni ba zan sanar da kai ina Salma take ba a yanzu dan ta fara samun farin......." " Ban katsi nunfashin ka ba baba, amma tabbas nima ba zan so abinda zai hana ta farin ciki ba a dai-dai wannan lokacin, tabbas na amince su ci gaba da rainon yara na a tare ba dan ina gudun d'awainiya ba, lokaci zuwa lokaci zan dinga zuwa nan ɗin dan mu gaisa,ga address d'ina saboda wataran ko za a buqaci hakan," Takardar da ya rubuto adireshin sa tun a gida ya zaro ya miqa ma baba, idon shi ya kad'a ya yi jawurr, tabbas har yanzu akwai son Salma a ran shi, wanda a da ya ɗauka sha'awa ce kawai sai yanzu da hankalin shi ya dawo jikin shi ya gane ba hakan bane,miqawa baba ledar hannun shi ya yi ya masu sallama dan komai dare gida yake son ya kwana zaman Kano ba nashi bane, Mama Balki ce ta d'akko hotunan yaran guda uku ta bashi ya riqe ya na kallo hawaye na zuba a idanun shi. Kaff haife haifen da sauran matan shi suka yi ba wadda ta haifi 'yan biyu, sannan babu mai kyaun wadannan da ya kora tun kafin su zo duniyar, tashi ya yi bayan ya sake yi masu sallama da godiya ya isar da saqon su Huwaila da Marka,godiya suma suka yi masu tare da bada saqon gaisuwa a Kai masu, ya kama hanya ya tafi sai qauyen su. *BAYAN SHEKARA UKU* Yau ta kama ranar Asabar ce kowanne ma'aikacin gwamnati ya na gida ya na hutawa da iyalin shi, bangaren 'Ya'yan Alhaji Baballiya kuwa su na can sun tare a Abuja gaba ɗayan su, Suwaibah da Abrar ne suka kai masu zira wanda da kyarrr aka samu Suwaibah ta yarda ta sanya qafafun ta a garin Abuja dan kuwa har a wannan lokacin ba ta jin so da qaunar Abuja a ran ta, Alhaji Salihu kuwa shi ya biya kud'in jirgi suka tafi ya ce idan an gan shi a Abuja to gawar shi ce amma ba dai ya koma mata ba da rayuwar shi da kuma qafafun shi. A gidan Juwairiyyah duk suka taru, duba da cewa Jabeer shi ne babba sai ta ci wannan girman ake yawan taruwa a gidan ta, hira suke ta sha tare da tuna yarintar su suna dariya ma junan su,wayar saudat ce ta yi qara alamar shigar saqo ta na dubawa ta ga mijin ta ne, murmushi ta yi ta samu wata kujera ta zauna ta na ci gaba da hira jefi-jefi sannan ta na chatting da mijin ta da ke can k'aramin parlour shi da Jabeer da Ibraheem. Abrar ce ta shiga da mashacin gashi da kibiya ta zauna a jikin Suwaibah ta ce, "Mom dan Allah ki yi min kalba guda huɗu irin na 'yan biyu ya bani sha'awa" "Ah toh dai,a ce wai mutum baya son kitso sam a rayuwar shi gashi Allah ya hore masa gashi?" "Ni dai dan Allah Mom kar ki yi faɗa zan yi kuka" Gum Suwaibah ta yi da bakin ta ta karɓi kayan kitson ta raba mata kanta huɗu ta fara kitse mata, suna ci gaba da hira. 'Yan biyu ne suka shiga da gudu su na wasa yara sun girma sosai, dika-dika ba za su wuce shekara uku ba, amma iyayin su da maganar su sai mutum ya rantse sun kai shekara huɗu ko biyar,wasa suka hau yi suma Salma na yi masu faɗa akan yanda suke ta rikici,sam ba su zama waje ɗaya ba su yi faɗa ba, sannan kuma ba su iya zama ba tare da junan su ba,Ibraheem ne ya yi sallama ya shiga,bayan sun amsa ne yaran suka nufe shi da gudu suna fad'in, "Daddy !" "Na'am yaran Daddy,wa zai je play ground?" "Niiii, ni daddyna zan je" In ji Hassana da ta maqale masa wuya tun qarfin ta, Hussaina ce ta janye hannun Hassana a wuyan shi ta ce, "Dalla sake masa wuya malama kuma Daddy na ne ba naki ba, ke ba ga Mommy can ba ita ce Mommyn ki?" "Ah ahhh daddy na ne, ko Daddy? Ai dai kai nawa ne ko?" Yaron da Juwairiyyah ta haifa takwara ga Abbah Balarabe ne ya isa gaban su ya ce, "Dattyna ne" Dariya suka sanya a wajen gaba dayan su,har saudat mai latsa waya,Salma ce ta miqe ɗauke da yarinyar ta a hannu ta dungure kan Hassana da ke kukan banza ta ce, "Na ji kar a so nin, nima ga Faihah nan Allah ya bani in ta girma za ta ce ni Maman ta ce sai me" Saudat ce ta sauke wayar ta qasa ta ce wa Salma, "Why are you like zis Maamaa? Are you jealous?" Dariya suka sake sanyawa, Abrar ta miqe da sauri ta sumbaci kuncin Suwaibah tare da furta mata, "I love you Mommy sai mun dawo" "I love you too baby a dawo lafiya" "Mommy zan siyo maki kayan daɗi " "Ina nan ina jira my love, kar ku manta a yi addu'a kafin a fita daga gida,ki kuma d'akko hijab ɗin ki ko d'ankwali a rufe kai" "Toh Mommy bye" A haka Ibraheem ya kwashe yaran dika suka bar gidan, dan shi ba mai yawan surutu bane, da ya zauna ya na hira da mutane ya gwammace ya yi ta hira da yara,shi yasa Farouq da Jabeer suka fi shaquwa dan kuwa idan suka haɗu suka fara hira kamar ba za su daina ba. Bayan fitar su ne Juwairiyyah ta miqe ta ce, "Sisters a shirya tunda yaran sun fita kuma bayin Allah'n can na hira a parlour ku zo mu tafi shopping akwai wasu sabbin abubuwa da nake so mu siyo" Cike da murna da ihu Saudat ta ajiye wayar ta ta na fad'in, "Yeeeehhh shopping" Salma ce ta kalle ta ta ce, "Kaiii Addah Saudat ke dai ba kya girma you are very childish" "Yess I am, saboda har yanzu ni kaɗai ce babyn miji na dole na yi abinda na ga dama,wata kuwa an fi son yara akan ta woooo" Dariya suka sanya Salma ta ɗauki pillow ta wurga wa Saudat ta na cewa, "Addah Suwaibah kin gan ta ko?" Murmushi kawai Suwaibah ta yi hankali ya game jikin ta a yanzu bata cika hayaniya ba sam. Jabeer ne ya yi sallama shi da Farouq da sauri Saudat ta miqe ta na wani yanga, Jabeer na shiga ya sauke idanun shi akan Juwairiyyah da ta riga shi kafe shi da nata idanun tin shigar shi parlourn, "Ni ma ina baby na take? " Cike da jin daɗi Juwairiyyah ta isa gare shi ya rungume ta sannan ta ce masa, "Gani nan yayana, ya na ga kun ɗauko car keys sai ina?" "Wai da fita muke dan so mu yi da ku tinda wancan baban yaran ya deb'i yaran shi sun fita suma" Kallon juna matan suka yi dan kuwa sun so su tafi shopping ɗin su su kaɗai su sai abinda suke so, dariya suka sanya a tare Jabeer ya bi su da kallo ya ce, "Lafiya?" Da sauri Juwairiyyah da Salma suka ce, "Babu komai," Sun yi haka ne dan hana Saudat faɗan abinda suke shirin yi, yanzu ita ce ta ɗauke halin Suwaibah na surutu, Farouq ne ya ce, "To Babban Yaya a saki madam ta d'akko hijabi mu wuce ko?" Dariya suka yi suka tafa, sannan Juwairiyyah ta wuce d'aki ta yi shigar ta ta Ninja in ji cewar Saudat, dan kuwa hijabi dogo take sanyawa da niqabi ba ruwan su da wai sun yi kuɗi yanzu bari a saka matsattsen kaya sannan a yafa siririn gyale, ko zata saka mayafin to fa kayan ta na da wadataccen ɗinki ba a matse yake ba. Suna gama shiri Juwairiyyah ta kira mai aikin ta Huda ta ce ta dafa mata doya irin yanda take dafawa kafin su dawo ta na da miyar taushen ta a fridge dumamawa kawai za ta yi ta yi masu sakwara da sun dawo. Motar Jabeer Suwaibah ta shiga suka nufi ShopRite, wanda da kyar Suwaibah ta saki jikin ta saboda tunawa da baya da ta yi yanda suka dinga kashe kud'in haram a ire-iren wuraren nan. Bayan sun kammala siyayyar su ne suka tafi shan ice-cream,anan suka kirawo Ibraheem ya zo da yaran, su na gama sha kowa ya yi wa dan uwan sa sallama ya kwashi iyalin shi suka koma gida. Haka rayuwar su Suwaibah, Saudat, Salma, da Juwairiyyah ta ci gaba da tafiya cikin farin ciki da tarin nasarori tare da albarkar rayuwa, Juwairiyyah da Jabeer basu taɓa nuna wa Suwaibah Abrar 'yar su bace ko su nuna suna son su karɓe ta, lokuta da dama ma Suwaibah ke haɗa Jabeer da ita idan ya je gaida su Innarmu aka yi sa'a ana masu hutu sai ya tafi da ita da an gama hutu ya dawo da ita gida,ita kan ta yarinyar ta na jin daɗin samun iyaye har guda huɗu dan kuwa har gori take yi wa wasu yara,ta san Juwairiyyah ce ta haife ta amma kuma Suwaibah ita ce Mommyn ta, rayuwa suke yi cike da fahimtar juna da soyayyar 'yan uwantaka, gaba ɗayan su sun kama sana'a duk da Jabeer ya ce tun da haihuwa ta yi jinkiri ma Juwairiyyah zai maida ita ta ci gaba da karatun ta, da jin haka Farouq da Ibraheem suka ce suma za su maida matan su karatu, karatu ba ya hana sana'a da kula da iyali, Alhaji Salihu kuwa ya ce kasuwanci kawai Suwaibah za ta dinga yi dan kuwa da kan ta ta ce bata son yawan shiga mutane saboda gudun kar watarana garin surutun ta ta bada labari rayuwar ta ta baya. Tarbiyya da sanin ya kamata sun wadatu a gidan Talle sakamakon sauke girman kai da suka yi suka koma islamiyya baki ɗayan su, dan kuwa yanzu Talle ya zama babban mutum har ya na yi wa wasu wa'azi musamman ta hanyar basu misali da rayuwar shi. Saudat da mijin ta, sun fawwala ma Allah dukkan lamuran su game da rashin haihuwa suna ta baza soyayyar su kamar sabbin aure. Alhamdulillahi anan na kawo ƙarshen labarin mu mai suna 'YAN ABUJA,kuskuren da na rubuta a cikin shi Allah ya gafarta min ya shafe shi a rubutu na da zuqatan duk wanda suka karanta,Allah ya sa wannan rubutu ya zame min sadaqatul jariya ko bayan babu raina, Allah ya yi wa dikkan masoya na masoya littafai na gafara da rahama da albarka. Thank you so much my beautiful mutanen kwarai masu albarka. Allah ya albarkaci rayuwar mu baki daya *DAGA TASKAR HAERMEEBRAEH*❤️ 1- WATA UWAR 2- 'YAN ABUJA 3- 'YAR RAWA 4- KALAN DANGI 5- DA SANIN SU 6- KAI NE JARUMI 7- MIJIN YA TA KO MIJI NA 8-  KUN MAKARO 9- MAHWISH 10- MAHREEN 11- BIYAYYAH 12 - A GARIN MU 13- DAGA TUSHE 14- MUGUN MIJI 15- MUGUN HALI 16- KYAKKYAWAR FAHIMTA 17- MAZAUNA GIDA 18- ALBASA BATAI HALIN RUWA BA 19- TAUBASHI 20 - ALMAJIRI NA 21-  AURI SAKI 22- SANADIN FYAD'E 23- RIKICIN KISHI 24-  AND NOW............ SHARHIN ASIYA HABIBU Duk littafan nan na karantasu,kuma babu na Bari a cikin su wlh,saboda ko wanne Yana dauke d darrusa da ilimin daya shafi rayuwar duniya data lahira da kuma zamantakewa Yan Abuja ya nuna mana illar kwadayi daga bangaren su suwaiba,ya nuna mana illar sakawa Yara dogon buri a rayuwarsu daga bangaren goggo Ya nuna mana bangarori na zamantakewar aure tun daga gidan mama bilki har izuwa gidansu juwairere mun ilmantu da abubuwan gyaran jiki fannin iya tattali da kuma mace tazama me hikima Taubashi y nuna mana illar barin sakewa sosai tsakanin cousin saboda komai na iya faruwa a tsakani (na dauki wannan ilimin kwarai d gaske) Biyayya ya nuna mana muhimmancin yiwa iyaye biyayya akan abunda suka bamu umarni akai,domin duk dadewa zamuci ribar hakan Kaine JARUMI ya nuna mana illar hassada sannan kuma y nusar damu muhimmancin zumunci Mugun miji ya nuna mana halin wasu mazan mugaye irinsu abashe🙄🙄mazan da basa kishin matan su kuma basu dauki Mata wasu abun darajawa BA a rayuwarsu,daga karshe kuma suzo suna nadamar hakan MAHREEN bantaba karanta littafin da komai na cikinsa y kasa barin zuciyata BA kamarsa wlh,na Jima kuma ina jinjina abubuwan d suka faru a cikin SA, Hakuri Juriya Jajircewa Addua Kawaici Zamantakewa Komai de ya hada Hakuri da duk Abinda Allah y jarrabeka dashi,d kuma hakuri d duk Abinda y sameka Yarda d qaddara da karbar ta adik yanda tazo maka Addua mahreen bata taba karaya BA wajan kaiwa Allah kukanta akan duk halin da ta tsinci kanta ta kasance me neman taimakon Allah akan duk halin data tsinci kanta Takasance jajirtacciya kuma me tsayuwa akan raayinta me kuma bayyana gskyr ta ko a gaban waye bata taba kasa fadar gskyr Abinda yake ranta ba❤️.