An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAI DAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....1 Gaba ki d'aya falon ya d'auki wani irin shiru wanda ko Allura ta fad'i zaka iya jin sautin fad'uwarta, banda karar AC baka jin motsin komi saboda yadda maganar Hajja ta daki zukatan kowa a wajen,banda kai kawo babu abunda zukatan su keyi domin kuwa wannan magana tai matuk'ar shammatar su,wannan shine ake kira ga bikin zuwa babu zanin d'aurawa,sannan ana zaton wuta a mak'era sai gata a masak'a, kowa bakin sa yayi nauyi kamar an d'ora dala da gauron dutse, tsayin mintoci ba mai uhm balle uhm uhm. sai da Hajja ta gama nazartar kowa a wajen sannan ta nisa cikin dakiya irin tata da kuma jaddada maganarta da cewa "wannan shine dalili na,da kuma k'wakk'warar hujjata ta hana Auren *ROOHEE DA RAFEEQ* ,don haka na juyar da Auren ga *RAMADAN*.............innalillahi wa inna ilahir raju'un shikenan ni kuma tawa ta sameni,Hajja kiyi wa girman Allah da manzon sa ki sauya maganar nan, wane irin had'ine wannan ba kan gado ina Roohee ina Wani Ramadan fisabilillahi Hajja?" Umman mu take wannan maganar cikin kuka da nuna zallar bak'in cikin had'in da ake k'okarin yi da bai daidai da ra'ayinta ba, Cikin fushi sosai Abba na ya ce, "maijidda!, idan na kuma jin bakin ki anan ranki in yai dubu saina bisu d'aya bayan d'aya na b'ata su, Hajja kike maida ma magana haka cikin k'araji?" "Kyaleta Taheer,hukunci ne na riga na yanke sa kuma ko bayan raina ban lamunce maku canza wannan hukuncin ba,inhar ba d'ayan su ne ya mutu ba" umma tashi tai a mutukar fusace tabar falon,wanda yai dai-dai da tashina nima aguje cikin fita hayyaci da firgicin abunda ke neman samu na rana d'aya,nai dakin mu nida Rukee. Abba Habibu cikin son neman Sulhu yace, "Hajja had'in nan zai iya kawo rashin zaman lafiya agidan nan,sannan mu da muke tsaffi akansu ba ai mana auren dole ba balle su y'an zamani,aganina a kyale ROOHEE ta kawo wanda take so tunda ba gaggawa ake ba,........inji waye yace ba gaggawa nake ba?aini dama tuni na gaji da ganin su haka zube gabana,tunda kowa ya gama wannan la'anannen Bokon ba sai a aurar dasu ba hakanan" Shiru yayi saboda bashi da ta cewa, amma kam da za'aji tashi da an hakura da wannan had'in tunda har yarinya bata so, "Wallahi Hajja baki tab'a abunda ya jefani cikin k'unci da bakin ciki ba irin wannan, in bacin ganin girma da darajar Aure wallahi da bazan lamunci wannan............zanci mutuncin ki Safiya anan wajen, idan bakin ki ya sa ke ya furta wata mummunan kalma akan Hajja wallahi summa tallahi sai kin gane kuren ki,zoki bar nan wajen kafin na sassab'amiki" "Ai dole ka tada jijiyar wuya mana,tunda an maida aure ga d'an d'an shafaffe da mai" Ta juya tabar wajen cikin fusata da fushi,Hajja bakin ta sake haka ta raka ta da kallo harta b'ace, "Kiyi hakuri Hajja don Allah" "Aa ko d'aya Habibu kaine da hakuri,ai kowa yasan da kai take wannan maganar, ai saboda inyi maganin iskancin su yasa nai wannan abun, gashi suna ji suna gani abunda suke buri yafi karfin su,kuma in sha Allahu sai sunzo suna jin kunyarku kaida ZEENAH (MAMA KENAN)...........Karar fad'uwar da sukaji ya katse mata cigaba da maganar, kowa yai firgigi yana duban inda karar take, "Innalillahi wa inna ilahir raju'un RAFEEQ!!!" Abba Habibu Abba Taheer sukai kanshi saboda ya mik'e kenan jiri ya daukesa da mugun karfi ya yanke jiki ya fad'i a some,hankalin kowa ya tashi ainun har ita Hajja, wadda dan danan ta soma kuka wiwi ba wanda ya waiwayeta suka kin keme shi a guje akai mota dashi don zuwa asibiti, labarin hakan yaje ma Mami mahaifiyar sa, gyale a hannu ta fito cikin tashin hankali tabi bayansu ita da Anty sha'awa. Ban san meke faruwa ba a falon saboda tunda na shigo dakin a cikin wani yana yi nake ciki, na fad'a kan gadon mu ina fashewa da wani irin kuka wanda bazan iya tuna tsawon lokacin danai kuka irin sa ba,kuka sosai nake wanda yake fitowa daga kasan zuciyata, duk mai saurare zai gane irin yadda nake jin zallar bakin ciki a cikin raina,don har numfashina yi yake kamar zai d'auke gaba d'aya,dan danan kaina ya d'auki wani irin zafi da ciwo kan kace me jikina shima ya dauka, Wani irin zazzab'i ya rufeni wanda ya haddasa mun kerma har hakorana suna had'uwa,kamar an jeho ummi dakin ta iskeni cikin wannan yana yin, "kai!Yah Roohee,innalillahi kema d'in ba lafiya, na shiga uku Yah Roohee kina ma jina kuwa?na bani.........ta rud'e gaba d'aya saboda ganin yadda jikin nawa ya rikice bana majin abunda take fad'a sosai, a guje tatafi kiran umman mu. Atakaice ranar daga ni har Yah Rafeeq a gadon asibiti muka kwana,har gara ma ni da sauk'i shi kam ai abun ba kanta har yanzu bai dawo daga suman da yai ba, likitoci sun tabbatar da cewar ya shiga shock mai girman gaske wanda ya jefa shi shiga wannan halin,ni kam damuwa da tashin hankalin da nake ciki ne da kukan danai suka hadda sa mun azababben ciwon kai da zazzab'i, kaini har zuciyata kanta ciwo take nama kasa yadda da maganar Hajja,gani nake kawai don ta tsani alak'armu yasa ta shirga k'arya da girmanta,don abun da hankali bazai d'auka bane kwata-kwata, na tabbatar Yah Rafeeq ya tashi daga halin da yake ciki bazai yadda da wannan abun ba,duk ta rasa lokacin da zata zo da wannan maganar sai sadda suka shirya yin aure,sun shiryama juna rayuwa mai dad'i rayuwa mai cike da farin ciki da kaunar juna,sun riga sun yadda cewar d'aya baxai iya wata rayuwa mai dad'i ba in babu d'aya, shine zata saka almakashi ta datse musu farin ciki,lallai tazo da abunda bazai yuwu ba,don kuwa ko za'a maida kanta gabas a yanka bata da wani miji in ba Yah Rafeeq ba,wai Ramadan waye kuma Ramadan?kazamin,wanda nera biyar ke masa wahala?wanda daga shi har uwayensa da bazar Abba suke rawa,wanda degree d'aya ma dak'er ya ida saboda dak'ik'anci,abokan kirki ma baya dasu tsabar yana da girman kai magana ma sai ya kwana ya wuni bai iya ma kowa?inaaa da sakel anyi sadaka da karuwa.............duk ina wannan tunanin ne a sadda nake kwance ana kara mun ruwa,Rukee da ummi suna gefena kowa fuska ba dad'i cikin alhini,idona biyu inajin duk firar da Umman mu da Mami suke duk akan Hukuncin Hajja,tsabar yadda zuciyata ke cunkushe kuma take a tunzure ko allurar Baccin da aka saka cikin drip din ma banjin zatai aiki,don idona kamas nakejin sa tsabar rad'ad'in dake cikin raina. "Wallahi wannan karon zanyi fito na fito da kowa akan wannan Had'in,Haba Mami anyi mun adalci kenan ace a rasawa wanda Hajja xata had'a Aure da Roohee sai RAMADAN?..........Ummah kenan,nasha gaya maki Hajja bata kaunar mu ko kad'an,in bacin rashin k'auna miya kaita yin wannan abun?yara sun shirya kansu ana daf da aure ki bijiro da wannan magana,kuma in bacin zaalinci miyasa tun da suka fara alk'a tagane abunda ke tsakani bata ce komi ba sai da suka shirya aure.....,.wallahi Hajja muguwa ce zeena kad'ai take kauna zeena kadai ce ta gari mai mutunci a idonta" Mami ta k'arashe tana hawayen bakin ciki, umman mu tace "ki bar zubar da hawayenki Mami,inhar bata karyata maganar nan ba,to wallahi ni kuma Roohee ba zata Auri Ramadan ba,watau duk tattali da kulawa da tanadin da nai akan Roohee shikenan ita a Ramadan zata k'are,wannan kucakin k'azami dashi?Allah ya sawak'e wallahi sai dai idan Abban ya sallameni," Cikin kuka da bak'in ciki Mami ke cewa, "Tashin hankalina yadda Rafeeq zai dauki lamarin nan idan ya tashi,wallahi na k'ara tsanar Xeena sosai a raina saboda duk don ita Hajja tai wanan abun,bazan iya yafe musu ba inhar wani mummunan abu ya samu D'ana wallahi har kotun k'oli zan iya kaisu..........Mami ba abunda zai samu Yah Rafeeq,ki daina cewa wani abu zai samai pls,idan haka taa faru mutuwa zan wallahi bazan iya baaaaa" Ban San bakina ya bud'e ba ina fad'ar wannan maganar, saboda jinai wani rugugin tashin hankali ya rufto min idan da gaske wani abu yasamu Yaj Rafeeq,rayuwata had'e take da tashi bazan iya jure ganin sa cikin mummunan yana yi ba,na yanzu ma ni kadai nasan abunda nakeji cikin raina,kuka ya kwace mun sosai bayan na gama maganar,saurin dawowa wajena tayi tana dora kaina jikinta ta rungumeni cikin lallashi take cewa, "Ba fata muke ba Roohee,ba abunda zai same shi in sha Allahu zai tashi lafiya kuyi auren ku" Daker ta samu na daina kukan nai lamo akan cinyarta, tana shafa kaina har bacci mai nauyi da na hana ya daukan dazu ya sace ni a yanzu ban shirya ba. *TAU FA!,SHIN WAI MEKE FARUWA NE HAKA DA WANNAN FAMILY?SHIN KUNA SO KUJI?KAR KU DAMU KU BIYO NI ZAN WARWARE MUKU ZARE DA KUMA ABAWAR, TAKU CE HAR KULLUM MOM MUHSEEN MAI NISHAD'ANTAR DAKU DA KUMA FAD'AKAR DAKU A CIKIN DAD'AD'AN LABARANTA, MUJE ZUWA...........* MOM MUHSEEN&ASAAD🥰👌🏻 _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....2 Kwana na d'aya aka sallame ni,yayin da Yah Rafeeq sai da yai kwana uku cib, acikin wad'anan kwana kin daga ni har shi muna cikin yana yi marar misaltuwa, ni dai gani nan ne kurin don ruwa ma kanshi wuyar sha yake mun,kamar mai azumi duk na addabi kaina banda aiki daga kuka sai tunani,kuma har yanzu bamu zauna da Abba ba balle in saka ran zaiyi wani abu akai, Hajja kau ban sake zuwa na gaida ta ba don wani irin haushin ta nakeji ainun,to balle wani Abba Habibu da matarsa wanda ko sunan su bana so inji ankira,don kallon munafukai nake musu. bana ma fita inba dakin Mami zanje inga jikin Yah Rafeeq,shima har yanzu baya uhm balle uhm uhm abinci kanshi Mami ko umma na ke bashi abaki daker da lallashi da kalamai sannan zai d'anci,ko idan an saka mana tare haka zamu ringa tsakura bamai ma d'aya magana,ni kam inaci ina hawaye masu zafi, baya iya mun mgn saidai ya aje mun hanky gabana alamun lallashina kuma baya son kukan,zan dauka na share hawayen har mu gama ba zan sake ba,ba kuma don na daina yin kukan ba gobe ma zan dasa wani. Kwata kwata baya iya fita koda falo,tun Abban shi na fad'a yana cewa son jikine da lambo har lamarin ya fara damun su suduka,Yah rafeeq sai dai kallo kurin ba magana,lamarin daya sake gigitani ya sake jefamun tsanar Hajja da su MAMA,Kai kowa ma ni haushin sa nakeji duk na lalace bana ko baccin kirki. Wajen aikina da nake services sun kira ni yafi sau shurin mu saki ban ma iya dauka balle har inyi wata maganar kare kaina na rashin zuwa kwana biyu, sai da Hajja ta kira wani malami ya ringa yo ma Yah Rafeeq rubutu yana sha don samun daidaiton hankalin sa,don nema yake ya zauce gaba d'aya,ni kaina ina bukatar rubutun dan ganan saboda duk dare ni kadai nasan halin da nake tsintar kaina aciki,zuciyata wani irin ciwo take mun da bazan iya misalta irin yadda take mun ba,kowa gidan ba walwala da farin ciki saboda mud'in mun shafe jigon duk farin cikin gidan, mun kasance cikin yin raha da juna da zolaya da wasa da dariya,in har Yah Rafeeq na gida tabbas kowa bazai b'acin rai ba,daya daga cikin halayyarsa kenan da taja zuciyata ga kaunarsa. Hmmm ba zaku fahimci me bakeji ba sai na baku labarin yadda rayuwar mu take a baya,amma ku bani lokaci. Kasancewar dokace duk dare b'angaren Abba Habibu ake dinner kuma baka isa ka take wannan dokar ba inba da kwakkwaran dalili ba,Hajja kad'ai ce ke cin abincin ta bangarenta saboda bata da lafiyar k'afafun da zata iya zarya,babban dining ne mai dauke kujerar kowa na cikin gidan har wadanda sukai aure har yau wajensu na nan,duk yadda naso karna fito dinner Abba ya kirani a waya cikin b'acin rai, "Kina so inzo har na inci mutuncinki ne komi?kar ki sake ki kara minty biyu ban ganki anan ba" Bai bani damar furta kalma d'aya ba ya datse kiransa,Hawaye masu zafi suka kwararo mun na tausayin kaina,wannan kad'ai ya nuna mun Abba baya goyon bayan na,koda zan nuna bijirewa to tabbas shine zai mun cikas,kuma zai iya shafe dukkan soyayyata ya hukuntani,Rukee ta turo k'ofar dakin namu tana kamo hannuna don na tashi,ban musu ba na tashi na sauko daga bisa gadon na biyo bayanta, fuskata kamar jaan k'osai saboda kuka daya zamar mun jiki. On ready sun fara cin abincin su bakajin karar komi sai ta spoon da d'an uwansa plate,kujerar kusada Mami na nufa zan zauna maganar Abba ta dakatar dani ya nuna mun kujerar dake Kusa da YAH RAMADAN, "daga yau can ne mazaunin ki,ku fara sabawa kafin komi ya dai-daita.........wani b'acin rai mai girma ya turnik'eni kuka ya k'wace mun, "Abba please" kar ki sake cewa komi wuce ki zauna kafin ranki ya b'aci,kuma ki rufe mana baki" Dole na maida kukan cikin cikina,na ja kujerar inajin yadda tsanar sa ke huda zuciyata, abunda ban tab'a kawo wa ba a rayuwata ko amafarki, wai tsayuwa ta minty biyar nida Yah Ramadan matsayin makusanta masu niyyar Aure,sai gani zaune gefen sa na tsayin mintoci ko a wanni,. "Roohee y'ata" Abba Habibu ya Kira sunana kamar yadda yake kirana kodayaushe, murya ba amo na amsa mashi daker, Ya ce "Kiyi hakuri ki daina kuka,me za'a zuba miki kici" Ina shashshekar kukan na ce, "Abba bana jin yunwa,ba zan iya cin komi ba" "Aa Y'ata,karki biyewa zuciyarki ki ringa kwarar cikin ki,saboda shi ai baisan wani damuwa ba,shi kawai in lokacin zuba mashi yayi kawai a zuba mai, zakici sinasir na saka miki da kaina,na san y'ata tana son shi" Kai na d'aga mashi kurin don ba abunda zan iya sake cewa kuma,..........."Bari na zuba mata Abbansu," Mama ta fad'a tana tashi da kanta ta fara k'okarin zuba mun,haushinta ya isheni don nasan na munafurci ne ba komi ba, Ummanmu ta kasa rik'e takaicinta taja dogon tsaki wanda ba wanda zaice baiji ba a wajen, wani dak'ik'in kallo Abbana ya watsa mata ya kauda kai ya cigaba da cin abincin sa, kamar tasan ba zan iya wuce cin guda d'aya ba ta zuba mun da namomi a cikin miyar sannan ta zuba mun zob'o mai sanyi kamar dai yadda kowa ya sanni da son abu mai sanyi,har ruwa saida ta zuba mun sannan ta ce "kici a hankali kinji ko" Banza nai mata don bata san yadda nakejin haushin ta ba,da ba zatai kasadar kusanta kanta dani ba,haka na ringa tsakurar sa ina ya mutsa fuska tsabar yadda nake kyamar Yah Ramadan har cikin bakina nakejin warin jikinsa, ba kuma don yana warin ba tsabar sama rai ne kurin da tsanarsa da nake. "Idan kowa ya kammala cin abincin zamu sake tattaunawa a falon Hajja,fatan ba zaku b'ata mana lokaci ba" Inji Abba Habibu yana mik'ewa ya ce masu Abbanmu "sai kun k'araso zan jiraku acan" Shida Mama da Najiba suka tashi tare,bayan kamar minty biyar Yah kucaki yabi bayan su Yah Ramadan kenan shida Yah Fahad wanda yau ya sauka garin daga lagos wajen aikin sa,duk rikicin da akai baya nan. Abbana ya gama shida Abba Nura suma suka tashi,daga ni sai Rukee dake jirana mutafi sai ummi da ummana da Mami, "Kina ganin siyasa ko Mami?" Inji ummanmu tana kallon Mami tai maganar cikin takaici, "uhm na gani mana,neman gindin zama ne kurin,tunda tasan dai D'anta ko za ai me bazai tab'a samun mace kamar ROOHEE ba,ba dole take rawar k'afa ba" Ummanmu ta ce, "ki barta wallahi saita d'an d'ana k'ud'arta inhar wannan abun ya faru,daga ita har uban yaron harshi yaron,ke ni ko shekara nawa ROOHEE zatai tare dasu ya saketa bana jin ko d'ar,don nasan tafi karfinsa kuma zata samu miji na nuna ma sa'a..........har ma tunanin anyi auren kike kenan?haba dai Maijidda kima bar wannan maganar wallahi" Nidai bance musu uffan ba,na gama cakalar sinasir din na tashi muka tafi can falon nida Ummi da Rukee. Su ummanmu ne karshen shigowa falon,Hajja na kan kujera ta hakimce tana kallon kowa d'aya bayan d'ayan har saida kowa ya gama shigowa,Anty Rahma da Anty Sha'awa Anty Rafeea ne basa nan,Kowacce tana d'akin mijinta........"Habibu bud'e mana taron da Addua" Cewar Hajja cikin isa da nuna ita d'in walkice daidai k'ugun kowa,kuma kujera dole azauna akanta, cikin natsuwa irin tashi ya karanto addua ya kuma bukaci ai salatin annabi aka gama sannan Hajja tai gyaran murya tana cewa, "Ba komi bane akan dai maganar ROOHEE DA RAFEEQ NE, a ranar ban gama magana ba taron ya lalace, to yau ban buk'atar kowa ya tashi saina gama maganata, sannan ban bukatar jin bakin kowa inba ni na buk'ata ba,kar kuma wani marar kunya ya katse mun zance na,ato inba mutum so yake yai zawarci da shekarun girma akansa ba" Kowa yasan dasu Ummanmu take ba sai anje ko ina ba, nikam ko zaman kirki bana iyawa sosai na zame na kwanta jikin Rukee kurin,ina rufe idanuna don ko kallon wasu fuskokin bana so nayi,Yah Rafeeq na zaune facing dina shima idonsa rufe kamar mai bacci. "Aure tsakanin Roohee da Rafeeq dai an soke har abadan,in kuma kun shirya taka dokar Allah bismilla tunda bani na hana ba,sannan na biyu Kamar yadda na fad'a rannan Ni da nake matsayin kaka wadda ta isa da ubaninku na yanke hukuncin iyayenku maza su had'a Auren ROOHEE DA RAMADAN,SHI KUMA RAFEEQ GA NAJEEBA NAN,RUK'AYYA KUMA GA FAHAD NAN, WALLAHI KO BAYAN RAINA WANI YA CANZA WANNAN WASIYYAR BAN YAFE MASA BA DUNIYA DA LAHIRA, don naga alamar zumuncin neman lalacewa yake,ada vanyi niyyar matsama kowa akan auren wanda bai ra'ayi ba don yana da illa,amma duba da yadda iyayenku mata ke neman tarwatsa mun iyalai yasa na canza wannan shawarar,bazan zuba ido ina kallo ku maida Habibu da matarsa kamar ba kowa ba,bacin sune kominku kuma kune kuke rawa da bazarsu ba wai su ba,kai Nura da kai Taheer ai kune shaidar hakan don haka ku shaida ma matanku da iyalanku cewar HABIBU DA MATAR SA ZEENA ba abun wulakantawa bane ko rainawa ba,sud'in mutanan kirki ne masu daddataku da sanin darajar y'an uwantaka,wallahi koda wasa naji wani yai musu wani abu na rashin kima ko rashin kunya zai gane wacece Hajja,kuma na bada umurnin a tsayar da ranar aure nan da wata guda,wannan itace magana ta in akwai wanda yake da ja sai inji." Tsiit kakejin falon saboda cikin fusata da hargagi take maganar wanda ya bawa kowa tsoro,don Hajja nada iska insuka tashi to kowa ma ubanshi yake ci,kuma fusatar ta nadaga cikin abunda ke jawo tashin aljannun,tana iya kwana da kwanaki basu sauka ba suna gana mana azaba,shiyasa yanzu kowa ya shiga taitayinsa. Abba Habibu ne yai karfin halin cewa cikin kwantar da murya da k'ank'an da kanshi, "Hajja ba wanda ya isa ya taka umurnin ki,daga mu har iyalanmu dole mubi abunda kike so,amma alfarma nake nema masu yaran nan mai zai hana abarsu su huce daga yana yin da suke ciki,sannan aba sauran dama su fahimci juna kafin a fara maganar tsayar da ranar aure...........Kai Ramadan kana da jaa akan hukuncin dana yanke?" Hajja ta katse Abba Habibu da fad'ar hakan ga Yah Ramadan, dagowa yayi cikin yana yinsa na koyaushe watau silently ya ce cikin muryar sa mai sanyi "Aa Hajja banda jaa akai, kuma na karb'a hannu bibbiyu" "Shin miye baka sani ba akan Qanwarka Roohee?" "Babu Hajja" Ta juya ga sauran duk tai masu wannan tambayar,Yah Rafeeq ne yai mata banza tai maganar har ta gaji ta kyalesa, hawaye suka tsinke mun jinake kamar na bar duniyar kozan huta da wannan bakin cikin. "To Habibu kaji ai ta bakin su,don haka hukuncina na nan inhar ba anaso anuna mun iyakata ba" "Aa kiyi hkuri ba wanda ya isa,Taheer kaji kaima Nura kaji ko?" Suka amsa da cewar sunji kuma zasu zartar da dukkan abunda ta buk'ata, tace "na sallami kowa na gama magana" Mom muhseen&Asaad🥰 _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....3 Shigowar Mamar dakin nashi yasa yai firgigi daga dogon tunanin daya shiga ya tashi daga kwanciyar da yake tun wayewar garin yau d'in, ida sa shigowa tayi ta zauna a gefen sofer tana kallon sa cikin nazari sosai kafin cikin natsuwa ta ce dashi "Meke damun ka RAMADAN,?kar kace mun babu komi domin bazan yadda da bakomin ba" Jujjuya kai yake yana tunanin me zai gaya mata,shi bai cika son fadar damuwar sa ba balle ma ga mahaifiyarsa wadda yasan duk duniya tafi kowa shiga damuwa in yana ciki,to mizai gaya mata akan abunda yasan itama bata da wani abunyi......... "Aduk duniya babu wandaa zai karanci halinka sama dani RAMADAN,saboda nid'in mahaifiyarka ce wadda ke tsaye don y'ay'anta,kuma take iya bakin k'ok'arinta akan ku,ku hud'u Allah ya bani amma ba wanda ban san halin sa ba,don haka karka b'oye mun nasan duk akan Auren ka da ROOHEE NE,ko ba shi bane???" Ya kasa cewa komi don bai da abun cewar,ta riga ta sani no need ya sake tisa mata........."koda yaushe ina k'ok'arin ganin na magance maku damuwarku duk sadda kuke ciki,Amma a wannan karon RAMADAN kayi hakuri bazan iya yi maka maganin damuwar ba,don abun yafi karfina ta inda bana iya cewa k'ala akai,ga Najeeba can tana kuka saboda itama abun bai mata ba, tana da wanda suka dai-daita kaima shaida ne,amma na bata hakuri da yi mata adduar in Allah yayarda addua ta akanku ba zata fad'i k'asa banza ba,Abunda na gaya ma Najeeba Kaima shi zan gaya maka KAYI HAKURI RAMADAN,duk wanda yai biyayya gaa abunda iyayensa suka d'ora shi akai bazai tab'a tab'ewa ba,amma sai kayi hakuri hausawa sunce duk wanda yai hakuri baici ribar sa ba,to baiyyi da yawa ba,nasan abunda kake hangowa nima ina hango maka shi,amma duk in kukai hakuri watarana zaku bada labari,nasanka na san waye kai zaka jure duk fitinar ROOHEE DA MAHAIFIYARTA,zan cigaba da maku addua Allah ya baku nasara ya kara maku hakuri," Tunda abun yafaru bai samu natsuwar zuciya da kwanciyar hankali ba irin yanzu,tabbas in Allah ya azurtaka da iyaye na gari ya gama maka komi, "Na gode Mama,Allah ya taya mu hakurin" "Yawwa ko kaifa,haka nake so naji maza ka fito ka karya yau ba zaka lek'a wajen aikin naku ba?" Kanshi ya shafa yana duba agogo, "sai gobe yanzu na makara" "Allah ya kaimu lafiya,kafa fito ka karya" Ya juya tafita tana ja masa k'ofar, yaja ajiyar zuciya mai nauyi da numfashi sannan ya mik'e ya shiga wanka. ******* Daren jiya ba muyi bacci ba saboda firgitar da naitayi tsabar zazzabin daya rufeni,in kana kusa dani har hucin zakaji yana dukan ka tsabar fiver,tun Ummanmu na iya jurewa har ta kasa ta kama kuka sosai saboda in kaga yadda nake zabura ina firgita da kakkafewa zaka dauka raina ake zarewa, tun daga kan ummi da Rukee da umma har Abbana ranar bamu runtsa ba,Yah Fahad Abba ya kira muje asibiti sadda zai zo sai gasu tare da Yah Rafeeq,kowa yai mamakin ganin sa don tunda aka fara wannan kitimillin baya mgn karshr ma kamar zautacce haka ya zama amma yau gashi nan Alhamdulillah, "Rafeeq jeka kwanta ai kai ba lafiya gareka ba" "Abba zan iya bata taimako ne,I'm fine" Dole suka hkr ya dubani kasancewar medical doctor ne sosai, bai jima ma da fara aikin sa ba ba'a shekara ba, Yah fahad yaje ya nemo duk abunda ya rubuta masa cikin daren yai mun duk abunda ya kamata,allurai da drip dan danan na samu bacci. "Koda da safe bata tashi ba kar atashe ta sai tatashi da kanta, kafin sannan kila prasure dake kanta ta sauka,itace tai causing wannan fiver" Abba ya ce, "Allah ya bata lfy,kuje kowa ya kwanta" Duk suka fito amma shi ya kasa barin ta ya fito,kallon fuskarta kurin yake yana jin abunda ke zuciyarsa kamar zai kashe shi,saida Yah Fahad yazo yajashi sannan suka wuce dakin su, umma ta ce ma Rukee inhar akwai matsala karkiji komi ki kiramu kinji ko" Ta ce, "in sha umma Ba abunda zai faru ma" *Dakin su Abba na* "Maijidda,bari na gaya maki abu na karshe wanda daga shi ba zamu sake maganar Auren nan dake ba, LAYLA KO MUTUWA TAYI SAI AN DAURA AN KAITA GIDAN MIJINTA SANNAN A KAITA KUSHEWA,don haka daga rana mai kamar ta yau karki sake tun karata da maganar auren Roohee inhar ba abunda zai amfani auren bane, na gama magana" Ya juya yai kwanciyarsa ya bata baya,umma cike da bakin ciki da takaici haka wuce ta shiga toilet don yin wanka. Washe gari da safe duk yan cikin gida kowa yazo don duba jikina saboda jin halin dana kasance ciki a jiyan zuwa yau da safen,da sauk'i sosai don karfe goma da raabi na safe allurar ta sake ni,ina bud'e idona akan sa asuka sauka na rufe na sake bud'ewaa tunanin ko mafarkin daya aure ni ne nakeyi,amma still shine zaune gabana muna kallon juna......."How are u feeling now?" Abunda ya fara fad'a min kenan yana ci gabaa da kallona,dan danan idona yaia rau rau zan fara kuka cikin sauri ya ce, "please stop it,kiji tausayina mana kukan baya isarki haka,bana so kinji" Ga ummana ga mamin sa,ga Rukke da ummi har ma da Anti Rafeea da tayo sammako tazo gani na,ga Yah Fahad duk za gabansu yake maganar,kamar ma ba kowa gaban mu. Lumshe manyan idanuna nayi masha Allah,sannan na bud'esu ina kalon kowa dake wajen, "Roohee yajikin,?" Muryata ta sake koma wa yar firitt fiye ma da sadda nake kal'au, na ce "Da sauki Mami," Kowa yai mun sannu da jiki na amsa Anti Rafeea ta ce "mi kike son ci" Na kalle shi wanda har sannan ni yake ta kallo kamar tv, na girgiza kai "Bana son komi Anty..........ki had'a mata tea mai kauri da zafi ta fara dashi,sannan ki soya mata planten da wainar kwai,idan taci sai tasha magunguna" Abunda ya fad'a kenan,na turo bakina cikin shagwab'ar da na saba masa, "ni bana so" Ya harareni kad'an ya ce, "ni kuma ina so" Ummana da Mami suka fita, Yah Fahad ya ce "tunda kin dawo hayyacin ki ni bari na fita to" D'an murmushi nayi k'adan wanda rabona dashi kafin a fara wannan dambarwar, shima ya fita yabar mu nida Shi da Rukee ummi ma tabi bayan Anty Rafeea, Mukai shiru mu duka ba mai magana,Rukee dai toilet ta shige don had'a mun ruwan wanka,ita har yanzu banga wani reaction a tattare da ita ba akan batun auren ta da Yah Fahad,kodan bamuyi mgnr bane oho! "Kizo kiyi wanka kafin ta gama had'a miki break din" Kallon sa nayi shima idonsa cikin nawa,wani irin lumshe su yayi ya bud'e akaina yana jinjina mun kanshi alamun inje inyi d'in, na shagwab'e fuska kamar zan kuka "to karka tafi pls" "Ina nan har sai kin karya,kije kiyi" Hannuna na mik'a masa alamun ya tadani,ba musu ya mik'o mun nashi muka rik'e juna, wani sabon reaction ya shige ni kamar in dawwama ina rike da hannun nashi,dai dai shigowar Abba Habibu da Mama sai y'ay'an su, Oga kucaki da mabiyan sa, zame hannuna yayi yana mik'ewa cikin bada girma ga Abba Habibun ya ce masa "ina kwana Abba" "Lafiya lau Rafeeq ya karfin jikin naka?" "Da sauki Alhamdulillah" Koma wa nai na zauna ina had'e raina kamar ban tab'a dariya ba, mama tayi masa yajiki kafin Abban ya jiyo kaina yana cewa, "Y'ata ya jikin, ashe jiya bakiji dad'i ba ya karfin jikin" Murya ba amo na amsa, "Na samu sauki" "Allah yasa kaffara ne," Ya jiya yana cewa Yah Rafeeq "in anjima da yamma ina son ganin ka Rafeeq" Ya amsa cikin biyayya, "In sha Allah Abba zan zo" Mama ta iso kusada ni tana mun sannu da jiki,fuska a d'aure nake amsawa, ganin yadda nai kicin kicin da fuska itama sai ta mik'e tana mana sai anjima, naja tsaki kad'an duk da kuwa ganin y'ay'anta dake cikin d'akin........."wa kike wa tsakin?" Cewar Yah Najib dake gefen Yah Kucaki, kallon da Yayan nashi yai masa yasa bai sake cewa komi ba, na sake jan wani tsakin nai banza na kyalesu bance komi ba, Yah Rafeeq naji yai ma magana "Ya mai jikin" Shi kuma ya wani kalloni yana mun wani irin kallo, kafin ya ansa ba yabo ba fallasa "Alhamdulillah" "Allah ya Kara sauk'i" "Amin summa amin" Daga haka suka fice daga d'akin inajin Rukee na cewa "sai Anjima Yah Ramadan" Shigewata toilet nayi cike da jin dacin ganin su danai, a duniya yanzu ba abunda ke samun jin zafi a raina sama da ganin shi da ahalinsa. A cikin toilet d'in na shirya na saka doguwar rigata yar kanti,mai mad'auri na daure su a bayana shafaffen cikina ya fito,wanda yaba Boob's d'ina damar bayyana sosai,kasancewar ina dasu ba laifi kuma yana yin dirin jikina yasa suke a bayyane,irin wanda ake cewa sharp din coca cola (😂),daha k'asa kuma ina Hips suma dai-dai misali ajikina in banda Hips dina da Boob's dina babu wani abu mai kiba a jikina,yar silib ce ni banda nauyi da girman jiki. zama nai wajen stool d'in madubi ina dafe kaina yayin da nake kallon sa,shima ni d'in yake kallo yana yin idonsa ya sauya sosai,Rukee da Anti Rafeea suka shigo Rukeen ta aje tiren breakfast d'in gefen Yah Rafeeq, tana cewa " kaine alhakin sata ta cinye wannan abin da kasa aka had'a mata,don inba kai ba banajin akwai wani da zai sata taci" Kallon su kurin nake,Anti ta tsaya tana gyara mun gashina daya jik'e wajen wanka,nai shiru inajin su suna ta firar su hankali kwance,ni dashi ne kawai bama mgn har ta gama mun lotion na shafa a jikina sai d'an roll all,daga haka na koma kan gado na jingina, "Yah Rafeeq ka tabbatar kasata ta cinye fa" Murmushi kad'an yayi yana daukar cup d'in tea din yasha madara da sauran kayan shayi,sai k'amshi yake silently yace "Karki damu," Fita sukai suka barmu tare,mik'o min yayi yana kallona wanda ni kad'ai nake iya hango abunda yaketa kokowar hidden a cikin idon sa,ko da caj a cikin idonsa nake fahimtar yana yin da yake ciki,tun yana karyata ni da maida abun wasa har ya sare ya yarda, ganin na tsaresa da kallo sai ya janye nashi idon yana cewa, "take it" Ansa nayi na soma suffing kad'an kad'an,kamar kurame saidai kallon kallo,zukata suna suya suna ko kawa, yadda yake ta son kawar da abunda ke ransa yasa nima na ke kokarin danne nawa,amma abun yaci tura planten d'in da bake ci daker take wuce wa a makoshina,ba shiri wasu zafafan hawaye suka ringa zarya a kan kuncina, kafin na soma shashshekar kukan kirjina yana d'agawa.........."Ya salam! Rooh please stopped,kina son ki rikita ni ne?so kike na koma ruwa kenan?kin san irin ciwon dake cikin raina?gani na kurin ake Amman ni kadan nasan uk'ubar da nake ciki,pls ki daina" K'ok'arin had'iye kukan nake ya k'i had'iyuwa numfashina nake ja sama-sama,cikin jin ciwo sosai da shashshekar kuka na ke cewa, "Yah Rafeeq.......naka....nakasa yadda a raina.......a raina cewar nida kai shikenan mun......mun rabu".........waye yace miki mun rabu?ba zamu tab'a rabuwa ba,abu d'aya ne muka rabu a kanshi shine AURE,amma kina nan a raina matsayin favorite cousin d'ina,kuma special qanwata" "Ya zanyi da abunda bakeji akan ka?bazan iya kallon ko wane namiji sa sunan So ko aure ba Yah Rafeeq kai kad'ai nake ma wannan kallon" Rik'o hannuna yayi duk ya susuce daga yana yin sa kad'ai zaka gane hakan, hawayena suka sake yawa suna zuba akan hannuwan mu, muryar sa da rawa-rawa ta dishe sosai ya ke cewa, "Za a wayi gari kin nemi hakan a ranki babu,Kiyi hakuri da KADDARAR MU haka Allah yaso, daman ba zamu kasance k'ar k'ashin inuwar Aure ba........."Hajja ta zalince mu, ni dai bazan iya yafe mat.....karki ce haka Rooh," Cikin fushi nace, "saina fad'a d'in, duk itace azzalumar miyasa tun farko batai kokarin dakatar da alak'ar ba,sai da komi yai nisa sannan?wallahi......ni.....nidai bazan yafe......yafe mata cutar dani da tai ba" Zafin hawayen sa dake d'iga akan hannuna yasa na sassauta kukan da nake, sai ajiyar zuciya da nake kanshi ya sadda k'asa cikin wani mawuyacin hali,tsayin wasu lokuta ya mik'e kurin ya fice daga d'akin. Sai kurin na sake rushe wa da kuka mai tsuma rai ainun,bana jin zan iya cire sa a raina haka zalika bana jin zan iya yafewa Hajja,saboda ta cutar damu mafi munin cutarwa,koma wane irin dalili gareta mu miye laifin mu? Da har zatai hukuncin da alak'armu............ *Nasan kowa ya k'osa yajin mafarin duk wanan rikicin,karku damu ana d'aura Aure zamu fara da MAFARI* MOM MUHSEEN&ASAAD 😍 _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....4 Haka na kasance yinin ranar cikin k'unci da k'unan zuciya,idan naga su Rukee na ta firar su ita da Ummi da Anti Rafeea sai inji inama ina cikin su,inama komi bai faru ba da bakina yafi na kowa kaifi,kullin saka rai nake zan bud'e ido inga na farka daga nannauyan baccin daya d'aukeni inga ashe mafarki nake ba gaske bane duk wannan rikicin,amma har yanxu ban farkan ba alamu sun gama nuna zahiri ne idona biyu abubuwan ke faruwa. Gani nake shikenan nayi bankwana da farin ciki,nayi sallama da wata aba wai dariya,duk abubuwan da suka faru tsakanina dashi sun zaka tarihi,ji nake inama ace in samu losing memories yadda komi Zan wuce a kaina da zuciyata,hakan yafi mun sauk'i akan na zauna suna zo mun ga idanuna babi babi. Tun da abun ya faru yauce rana ta farko dana kai goshina k'asa nai addua akan haalin da nake ciki,da kau zan sallame ne na koma gado na cigaba da kuka,sai na samu sauk'i kad'an danai adduar inayi ina kuka sosai ina kaskantar da kaina wajen Allah don neman sauk'i da mafita, ina kuma sake neman tsari da auren RAMADAN. _"YA ALLAH KAFINI SANIN ZUCIYATA,BANA SON WANNAN BAWAN NAKA DA AKE KOKARIN HAD'ANI DASHI,YA ALLAH KA WARGAZA WANNAN HAD'IN,YA ALLAH KA KAWO SILAR DA ZAN MASA NISA,NISAN DA BAZAI IYA ISKONI BA,ALLAH KA SAMAN SAUK'I AKAN HALIN DA NAKE CIKI,BABU ALKAIRI TSAKANINA DA SHI"_ ban damu ba da adduar da nake,saboda inajin idan nayi Allah zai ansa kuma zai rabani da Auren da ake niyyar yi mun da wanda na tsana nake k'yama fiye da komi a rayuwata. Haka na wuni kwance sai dai azo alek'oni a tafi,a kuma tambayeni ko inada buk'atar wani abu zaan girgiza kai kurin. *RAFEEQ* Dakin shi ya wuce ya fad'a bisa gado dafe da kirjin sa cikin wani irin yana yi marar misaltuwa,tun yana murk'ususu har ya soma kiran sunan Allah da d"an karfi,ya mirgino k'asa yana jawo drower dake gefen gado ya dauko maganin sa, yana haki da nishi ya afa abakin sa ya rarrafa ya dauko ruwa a bisa mirror yasha maganin ya wuce, ya zube nan k'asan kafet yana sauke numfashi,bayan minty goma ya fara jin sassauci,idonsa a rufe yana ayyana dole zai nesa da Rooh inhar yana son ya zauna lafiya,hakan shine zaman lafiyarsu shida ita inba haka ba za'a wayi gari ya mutu ta dalilin kaunarta dake neman halakashi,har akai azahar yana nan wajen daker yai salla ya dawo ya kwanta,sadda Mami ta kawo masa abinci bacci yake,ta aje masa tatafi bai farka ba sai karfe biyar agurguje yai wanka yai alwalla ta fito yai sallar cikin dakin,ya ga abincin ya dauka ya soma ci ahankali ba dan yana masa dad'i ba,sai don gujema tashin ulcer...........Fahad ne ya shigo masa da Sallama ya amsa yana kallonsa har ya zauna, sannan ya ce "Bismillah fa" Murmushi Fahad d'in yayi ya ce, "karfe biyar har da rabi kake cin lunch?" Jinjina kai yayi silently ya ce, "ya zanyi,bacci yaci karfina,to ya ake ciki" "Abba Habibu keson ganin mu shine nazo kiran ka," Jinjina kai yayi yana aje plate d'in ya dauki ruwa yana cewa, "Abun da bai saba faruwa ba,Abba bai cika tara mu ba kai a ganin ka mekake tunani?" Ya jefa ma Fahad tambaya, shi kuma ya ce "bai wuce kan batun case dinku ba,........case d'inmu dai ai yanzu kuma kun shiga tunda kuma auren dolen za'ai maku" Yar dariya Fahad yayi "anya kuwa?nifa dama na jima ina son qanwata Rukee" Hararar da yaga Rafeeq d'in na auna masa yasa ya fashe da dariya, "da gaske fa Nawan," "Ka gaya ma wani wannan maganar banda Rafeeq" Ya aje robar ruwan yana mik'ewa daga inda yai sallar,links yake sawa na rigarsa Fahad d'in ya sake cewa, "Ga Shawara mana my man,mai zai hana ku kawo karshen gabar dake tsakaanin ku kaida YAH RAMADAN,kun sani abunda kuke ba dai dai bane,beside Shine babban mu bai kamata ace ana masa abunda bai dace irin haka ba,kuma naga duk fitinar mutum bazai ce ga ranar da YAH RAMADAN yai ma mutum kallon banza ba,saidai ko ta wani bangaren amma ba nan ba............please ya isa haka muje kiran Abban mayi wannan mgnr daga baya." Rafeeq ya katse masa hanxari,girgixa kai kurin yayi yana mik'ewa suka fice daga dakin. ******* *ABBA HABIBU* su duka zaratan samarin gidan ya kira don ya tattauna dasu a hangensa da tunanin sa za'a samu d'an dai-daito ko yaya tsakanin yaran dasu. Acikin compound d'in gidan can cikin rumfa inda ake parking motoci,shimfid'a akai isassa da darduma babba Abban na tsakiya su suna gewaye dashi, Rafeeq da Fahad sune karshen isowa on ready RAMADAN yana wajen zaune, da alama sun jima suna magana da Abban, Fahad yaba Yah Ramanda hannu sukai musabaha sannan ya zauna gefensa, amma Rafeeq yai mirsisi kamar bai san da akwai mutum a wajen ba, Abban suka gaisar sannan suka natsu don jin dalilin kiran, "RAMADAN bude mana taron da addua" Ba busu cikin daddad'an lafazee nashi da cikekken tajweed cikin karatun ya kammala tare da bukatar a karanta salatin Annabi aka shafa,sannan Abban ya fara da Rafeeq. "Rafeeq banga ka ba d'an uwanka hannu kun gaisa ba kamar yadda Fahad yayi" Sunkuyar da kai yayi kunya na kama shi ainun,Abban ya juya ga Yah Ramadan "Kai ma maimakon ka bashi hannun tunda shi bai hakan ba sai ka share shi, ashe abunda ake gaya mun akanku da gaske ne cewa gabar kuke?.........Abba ni bana gaba dashi wallhi" Yah Ramadan ya katse Abban da fad'ar haka.........Aa kar ku maida ni sakarai mana,ba gashi kun nuna a gabana ba,ashe ku da zaku ga yara k'annan ku naayi ku tsawaatar ku dai-daita su shine ku ke aikata hakan,to ku gaya mun yadda za ku iya sasanci ko gyara b'araka irin wannan cikin k'ananku?" Duk sukai shiru bamai magana saboda sun san basu da gaskiya,Abban bai saurari jin tsakanin su ba ta ci gaba da cewa, "kune manya ku zaku gyara zumuncin dake k'ok'arin lalacewa a cikin gidan nan,koma minene yasa bakwa ga maciji da juna bana son inji, abunda nake so shine daga raina irin ta yau inason naga canji a cikin mu'amalarku,inaso ku zama yan uwan da ake kwatance daku,inaso ku had'a kanku ku ukun nan ku yak'i rikicin dake cikin gidan nan,saboda watarana kune iyayen mu bama nan ta Allah ta kasance damu kasa ta rufe idonmu,idan har akace tun yanzu bakwaa shiri da juna ta yaya kenan saura zasu so yan uwansu,?" Kowa yai shiru yana nazarin maganarsa wanda kowa yasan haka maganar take,don ba shakka zumuncin gidan nan na neman tab'arb'arewa,......."Don haka yanzu ba sai anjima ba kuyi musabaha da juna, tare da niyyar kun yafi juna kuma komi idan ya taso zaku zauna ku tattauna a a Fahimci juna,Ban da Matsala da Ramadan nasan duk abunda na d'ora shi akai bazai tab'a bijirewa ba,to inaso kuyi koyi dashi,Bismilla kuba juna hannu tare da Sallama" Jikin su yai sanyi sosai karma ace Rafeeq daya dauki abun da zafi fiye da Ramadan d'in, cikin sanyin jiki Rafeeq yaba Ramadan Hannu yana masa sallama,shima ya bashi nashi suna gaisawa tare da amsa masa sallamar. Fahad yai murmushi yace, "That's my brothers i like" Abba ma yai murmushin suma duk sukai, Rafeeq yace "Abba kai masa fad'a akan rashin sake fuska,yana d'aya daga cikin abunda ke had'ani dashi" Fahad yai dariya Shidai Ramadan murmushin kurin yake, Abban ya ce "to kaji Yah Ramadan,ko yaya ne a ringa ma y'an k'annan nan naka fara'a" Shafa kanshi yake cikin muryarsa irin ta y'an gayu kuma silently calmly ya ce, "Shikenan,daga yau zan fara salan kuma ace tayi yawa" Duk sukai dariya abun da yai ma Abba dad'i kenan, sannan ya gyara zama ya ce "Alhamdulillah Allah ya kawar da shaid'an tsakanin ku,magana ta gaba itace akan AURENKU ne,nasan kowa baya jin son wacce aka had'a shi da ita,bama kamar kai Rafeeq duba da yadda lamarinku yazo shi ya sake damalmala komi,inaso na baku hakuri kuma na rok'eku alfarma ku ba marad'a kunya,don Allah Ramadan,RafeeqFahad ku zama masu nuna biyayya ga abunda muka d'oraku akai,wannan auren yana daga cikin babban abu da zai kawo lalacewar zumuncin gidan nan,haka kuma shine abu mafi girma da zai kawo cigaba da sake d'orewar zumuncin,don haka ina jan hankalin ku da cewar duk ruwa duk iska karkuyi sake da matanku,kar kuyi abunda zai kawo cikas da yan tsugunne tsugunne,bance mutum in yaga wata yana so nan gaba karya k'ara ba,amma ya zama banda wulakanci banda tozarci inhar aka samu d'aya to ni bazan bada goyon baya ba,don Allah ku nuna mun cewar ni d'in na isa daku" "In sha Allahu Abba ba zamu baka kunya ba,zamu yi bakin iyawar mu" Cewar fahad kenan,Rafeeq ya ce "zamu kiyaye in sha Allahu" Ramadan ma ya ce, "zamu yi duk yadda kace Abba in sha Allah" Abban ya ce, "Allah ya yarda,sannan Rafeeq inaso ka zaunar da qanwar ka Roohee kai mata nasiha matsayin yayanta,sannan ka nuna mata yadda kai ka hakura ka amshi Kyautar da akai maka itama tayi hkr ta amshi k'addarata da hannu biyu,kila ta d'an sauko daga yana yin da take ciki" Kanshi k'asa yace a sanyaye, "zanyi mata magana Abba In. sha Allah" Sun jima yana nusar dasu abubuwa da dama da kuma kara haska musu rayuwa,saida aka soma kiran sallar magriba sannan suka tafi masallaci tare, har cikin ran Abba yaji dad'i sosai. *Bayan kwana biyu* Yanayin jikina ya sauya sosai na samu sauk'i don ina yin sabgogina yadda na saba,na kuma koma wajen aikina da nake service bautar k'asa wadda bamu jima da farawa ba, anyi jajena sosai friends d'ina suna ta fad'ar ramata alamun nayi ciwo ban gaya ma kowa ba azo a aganni,yak'e kurin nake musu saboda dai bazan iya musawa ba,saidai na basu hakuri akan cewar zan gyara next time,abubuwa da dama na daina tun dana dawo natsuwata sune bana zuwa b'angaren Hajja kwata-kwata,sannan bana fira da kowa duk nacin mutum,inma ta kama maganata da Rukee kawai nakeyi,sai ummanmu suma d'in daga uhm sai Aa sai tayi wuyar gaske inyi sentence da bai gaza kalma goma ba,sannan na daina zuwa b'angaren Mami in ta shigo wajen Ummanmu zan gaidata,tayi k'orafin har ta gaji kuma sun san dalilina nayin hakan,ba komi bane face bana son koda hanya ta had'ani da Yaj Rafeeq,muddin ina ganin sa ciwon dake cikin raina ba zai tab'a warkewa ba,Abba kuwa yasha jinin jikinsa daga yadda na koma tsani na dashi,iya kata gaisuwa da safe in ya fito zai breakfast ya tafi wajen aiki,daga haka bana sake cewa dashi k'anzil,bana tambayarsa ko biyar bana wata huld'd'a dashi bayan wannan. Kowa dai yaga canji sosai tattare dani wanda ya kara ma gidan zama silent sosai da sosai,kowa baiji dad'in yana yin da nake ciki ba amma kuma ba su da wani abu da zasuyi mun da zan iya dawowa LAYLA ROOHEE ta ainahi, wani lokacin idan na tashi daga wajen aikin mu zan wuce gidan Anti Rafeea inyi zama na sai dare nake koma wa gidan,don da anga ma ban dawo da wuri ba to ansan inda naje, itace kad'ai bata gajiya da lallashina akan in saki raina,babu wani tsanani da Allah ke d'orama bawa don baya son shi,jarabawa ce yake maka don ya auna girman imanin ka,sannan a duk sadda Allah zai daukaka darajarka tofa sai kasha wahala kafin wannan daukakar tazo..........."Auren Yah Ramadan d'in shine d'aukaka Anti?" Abunda nake gaya mata kenan,saidai tayi murmushi tace "shin kin san abunda Allah ya b'oye a cikin Auren nashi?bana so kiyi abunda zaki ciji yatsa nan gaba Roohee,.............Anti idan kin san irin wad'anan maganganun zaki ringa mun zan yafe zuwa gidanki na har abada,taya zan zo don na ringa samun sassauci anan amma ki isheni da wadannan maganganun,bana so gaskiya ki daina" "Allah ya baki hakuri in Allah ya yarda ba zan sake miki magana akan Abunda ya shafi Yah Ramadan ba,in har bake kika mun ita ba" Dajin kalamin taji haushi ammaa bata nuna mun ba, nace "Allah ma ya tsareni da maganarsa,yo wannan Allah na tuba har abun ai magana akansa ne" Girgiza kai kurin tayi ta rabu dani,daga ranar bata sake yi mun mgnr auren bama gaba d'aya saidai shawarwari da suka shafi rayuwata. B'angare guda shirye shiryen Auren ake don an siyo kayan saka rana na kowane b'angare,ana jiran lokaci an sanar da dangi da abokan arxiki da zasu anshi kaya,duk da dai agida d'aya muke amma baza'a fasa al'ada ba,Goggo habi na tafe ita dasu Mufee abunda ya d'an sanya na saki raina amma ba dariya nake ba,don rabona da ita har na manta ma gaba d'aya koba komi zamu had'u da Mufee jinin mu yazo d'aya ainun,acikin sa'anin mu Najiba ce kad'a a ware kuma itama dalilin iyayen mu mata yasa muka wareta,duba da cewar ba a shiri da uwarta da uwayen mu mata,duk da mun san cewa ba dai-dai bane hakan amma mun kasa jawota cikin mu,itama kuma sai ta janye daga garemu inba dole ba bata shiga duk abunda zai shafi sabgarmu. Ana gobe ansar kayan saka ranar mu na tashi aiki na wuce gidan Anti Rafeea nai zama na, aiki ma na d'an taya ta mijinta zai bak'i da daddare zasuyi meeting shine akai masu meat pie da samosa da cake,sai kaji da aka soya tun rana ake aikin sai magrib muka kammala,mukai wanka ta bani wasu daga cikin kayanta na saka kasancewar jikin mu guda,saidai nafita Boob's don rigar ta kamani sosai,ina sallame sallar magariba kira ya shigi wayata,haske na gaani tana yi yasa na gane kirane don bana barin wayata da ringtone, wanda banyi tunanin kiransa ba ne ya kirani YAH RAFEEQ........wani irin fad'uwar gaba naji ras ras ras,har saida na rufe idona ban ankara ba ta tsinke ba jima wa kuma ta sake shigowa, ni kad'ai nasan irin bugun da zuciyata ke mun,kamar nayi gudun kilometer dari da hamsin tsabar yadda take bugawa, ban san hannuna ya d'aga kiran ba,ahankali kamar wacce hannunta baya aiki sosai na saka a kunnena nakasa cewa komi. "Kina gidan Rafeea ne?" Abun da ya fad'a mun kenan, kaina na d'aga masa nama mance ba ganina yake ba,daker na dai-daita kaina na iya fad'a "Eh,amma yanzu zan tafi gida" "OK,wait for me" Ya kashe wayar ya barni da zullumi har wata zufa nakejin tana karyo mun tsabar shiga zullumi,to mi zai kawoshi wajena?har cikin raina bana son ganin sa don kuwa ganin nashi maaiface a rayuwata, "Roohe lafiya kuwa?" Sai hawaye sharrrrr na rik'e hannunta muka zauna bakin gado ina hawayen na ke cewa, "Yah Rafeeq zai zo nan,ni kuma bana son na ganshi Anti,pls kice karya zo don Allah ga wayata ki kirashi kice komi zai fad'a mun ya fad'a miki saiki fad'a mun"............tausayi ya kama Rafeea cikin lallashi ta ce "ya isa haka minene na tashin hankali a ciki Roohee?Yah Rafeeq ne fa ba wani ba,babu abunda zai Faru kinji ko,shima nasan babban dalili ne zai sashi neman magana dake a keb'ance,ki kara daurewa komi zai wuce" Kasa magana nayi na dora kaina a cinyarta ina shashshekar kukan har na samu ya tsaya, "in sha Allahu Roohee wata rana zaki bada labarin wannan yana yin da kike ciki,zai wuce har sai kinyi mamakin wucewar sa" Nidai bance komi ba ta sake cewa, "bari naje na idasa shirya musu falon bayan sallar isha'i zasu zo" Na tashi daga bisa cinyarta na koma bisa filo na kwanta idona rufe ban san wane irin kalar tunani zan ba, Na shafe a kalla minty talatin a haka kafin Iklas babbar yar Antin ta shigo ta ce "Ammi Roohee Anna ta ce kizo uncle Rafeeq yazo yana karamin falonta" Kaina na d'aga mata kawai har ta fita na kasa tashi daga inda nake, saida Antin ta shigo ta ce "wai miye haka kike yi,haba Rooheen umma tashi kinji ko" Tashin nayi na dauk'i gyalena madaidaici na yafa ga kafad'ana guda kurin na dauki wayana na fito, ina tafiyar kamar iska zata kayar dani tsabar bana da wani nauyi da kuzari jikina,da siririyar sallama na shiga falon wanda har k'amshin sa ya isko ni wanda ke sake samun son kasancewa dashi a kullim, Ban yadda na ciro kaina na kallai ba na dai zauna cikin kujerar farko dana isko kaina k'asa na ce a sanyaye, "Ina yini Yah" Shiru na wani d'an lokaci banji ya amsa ba mafarin naa d'an ciro kaina na kalli inda yake kyakkyawan four eye's mukai da juna ya tsareni da kallo,idona yai k'wal-k'wal zan kuka na ce "shine zaka k'i ansawa" Sauke wani gauron numfashi yayi yana cewa, "naga ko kallonaa bakya son yi shiyasa,ammaa yanzu sake gaidani zan ansa" Ban san sadda idanuna suka maka masa harara ba na kawar da kaina, naji ya ce, "kai kai kai,ni kike harara ko?uhm kin kara ma kanki hukunci akan wanda ke jiranki," Na sake watsa masa wata na ce, "ni zan tafi" "Kin san fa bana son ana hararata,tau gara ma ki daina yarinya," Sai kurin na saka masa kukan dake ta kai kawo a cikin kirjina, kuka sosai wanda daman jiran abun da zanyi sa nakeyi,ai ko a rikice ya dawo kusada ni a k'asa yana magana cikin kid'ima,don a rayuwar sa babu abunda ke saurin nuna weakness d'insa irin kukana........"Rooh pls stopped,kin sani bana so don Allah ki daina, karki sa na kamu da rashin lafiya,in dan nine kiyi hkr ki fad'a mun me na miki amma pls stopped kinji" A rayuwata babu abunda da nake so sama da a lallasheni idan ina kuka, ya sani sarai shiyasa yanzu ma nad'an sauko na fara rage kukan ina cewa, "gashi nan hankalin ka a kwance shirin aure kake,ga dukkan alamu baka damu da halin da nake ciki ba,watau kama amunce da wacce aka baka kenan" Ina shashshekar kukana kasa-kasa,ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi ya ce "Rooh kece fa kike guduna,duk hanyar da zan ganki kinbi kin toshe ya kike so inyi, sannan koda na tashi hankali na kamar a farko Rooh ba abunda zai canza k'addarar mu,a riga ta faru babu yadda zamuyi da abunda Allah ya shirya a tsakanin mu,daman ba zan zama mijinki ba kema ba zaki zama matata ba,wanin junan zamu aura pls and pls Rooh ki cire komi ya fawwalama Allah kinji ko," Hawayen sunk'i tsayawa nake cewa, "taya zan iya cireka a raina da sunan wanda nake kauna nake burin Aure,taya zan canza wannan mafarkin nawa na sanya wani akai?wallahi bazan iya ba,koda anyi wannan auren sunan anyi ne amma bazan tab'a zama matar wannan k'azamin kuma kucakin ba har abada.............RAFEEQ KABAR PHONE NAKA ANA TA KIRA" maganar kurin mukaji ba tare da munji sallama ko motsin da zai aankarar damu shigowar sa ba, kallon wulakanci na watsa masa na kawar da kaina ina goge hawayena, ko a jikina ban damu dana yaji kalamin da na fad'a ba,sab'anin Yaj Rafeeq da yaketa jin kunya yake kame-kame, "Ayya na shafa'a ne, na barka kana ta jira to ka shigo ka zauna sai mu wuce,har ma kun gaisa da Wife d'in taka to be ko?..........Allah ma ya sawak.........zan sab'a miki idan na sake jin wata magana marar dad'in ji anan LAYLA" Yah Rafeeq ya fad'a cikin fushi sosai da na dad'e bangan shi a ciki ba,fuskar sa ta d'aure ta mau ainun kamar bai san dariya da murmushi ba, Yah Ramadan ya ce "sai ka fito ina jira" Ya fice ya barmu anan zan cigaba da kukana ya ce, "tun da baki san lallashi da banbaki ba zan tattaraki na fita harkar ki,rashin kunya da fitsara ba halinki bane karki sake ki aro su ki yafa ma kanki saboda kina k'insa, don nasan watarana zaki nadama,nasiha nazo inyi miki matsayina na yayanki kuma wanda kika fi shak'uwa dashi a duk cikin yayyenki maza,Aure babu fashi Rooh sannnan masifarki da rashin kunyarki da duk wani kalar wulakancin da kika tana da don shi bazai fasa komi ba,saima dai ke ki jefa kanki cikin wani hali,don nayi imanin RAMADAN ko sama da k'asa zata had'e bazai tab'a SAKIN ki ba,don kuwa shi d'in mai biyayya ne ga umurnin iyayensa,da duk wani na gaba dashi nai masa wanna shaidar,don haka shiyasa muka muka daura d'amarar koyi dashi nida Fahad,zamu zauna da matanmu cikin amana da kwanciyar hankali har Allah ya kawo ranar da zamuji muna son su,tunda zuciyoyin mu ba a hannun mu suke ba suna hannun Allah,a duk sadda yaso yana iya canza komi,don haka don Allah Rooh don girman Allah ki zauna bil amana da RAMADAN, wallahi summa tallahi zakiji dad'in zama dashi baida fitina,baida hayaniya baida mugun nufi akan ki akan kowa ma,in kikai hakan zanji dad'i kinji nasiha ta kuma kin girmama maganata, ina miki fatan alkairi Allah ya canza abunda yake zuciyarki" Sosai nake kuka wanda har bakajin muryata saboda yadda nakeyin sa cikin fidda zallar bakin cikina, Har ya juya zai tafi ya tsaya bai waigo ba saboda kukan yana tsananin ratsa shi,wani yana yi dake cinsa yana neman galaba akansa ya ce, cikin raunanniyar murya "bazan tab'a juya miki baya ba Rooh,duk sadda kike da matsala karki tun kari kowa kizo gareni,duk girman ta ina fatan Allah ya bani ikon warware miki ita, Bissalam" Mom muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....5 Saboda halin dana kasance a ciki yasa saidai a gidan Anti Rafeea na kwana,don kuwa kuka nasha na koshi wanda har sai da ya haddasa mun ciwon kai da zazzab'i, na kuma hana ta sanar da Ummanmu kowa ma hana ta nai ta gaya mashi, saboda bana son wannan taron dangin akaina. Raba dare mukai tana lallashina da bani hakuri tana nuna mun shi namiji ma ya hakura ya kauda komi saini ce zan nace inyita damun kaina da rashin zaman lafiya? Da nasiha da ban baki har dai na samu nai shiru, ta kawo mun meatpie naci da tea mai kauri nasha magani sannan nayi isha'i,na dora da shafa'q da wutri, na jima a sujjadata ina kuka saboda adduar da zanyi nauyi take mun, daker na iya ambatar "Allah ka samun sauk'i da salama a cikin zuciyata,ka sassauta mun zafin kishin yah rafeeq ka sassauta mun kaunarsa ya Allah" Da wannan na samu nai bacci wanda na jima banyi irin sa ba. ******** Tun daga wannan rana na koma yin rayuwata kada ran-kada han,ni bana cikin farin ciki haka zalika bana cikin k'unci,yadda nake da magana amma yanzu wuya take mun ainun,ummanmu duk juyin da zatai inyi fira da ita bana iya wa Abba kanshi duk ya damu da yadda na sauya masa,iya kata dashi ina wuni ko ina kwana,sannan in an had'u cin abincin dare nice farkon gama wa in tashi kuma in na saddar da kaina k'asa bana d'agowa har sai na gama,saboda kowa ma ni bana son had'a ido dashi. Bikin ba fashi an sanya shi wata hud'u anan gaba,don tuni har anfara shirye shirye, daga b'angaren iyayen mu duk yadda basa son bikin amma bai hana sun fara shiri ba baji ba gani, ni kam nuna wa nake kamar ban san me ake ciki ba,nafi zaman gidan Anti Rafeea don can ne kurin nake iya fira sosai,Rukee kanta tasan na canza amma ba yadda ta iya dani dole ta samun ido. Rannan ina kwance uwar dakar ummanmu naji suna wata magana ita da Mami akan aurena da YAH RAMADAN, wadda nan take shawarar bata shigan ba, Ummanmu ce ke cewa Mami, "Safiya wallahi auren Roohe da yaron can neman d'ora mun hawan jini yake, dana zauna ban da wani tunani sai na neman hanyar dazan lalata abun,wallahi ni rayuwata ma ban jin akwai abunda na tsana irin auren nan nasu,duk hanyar da nake tunanin zanbi sai maganar Abban su tai mun tsaye a rai,ban san ya zan ba" Mami ta ce, "Maijidda kenan, ke yanxu har sai hanyar raba wannan auren ta gagareki?ni nan jira kawai nake inji kince mun kin shirya kawai mun nntaya tare," Umma ta ce cikin rashin Fahinta, "Bangane ba?wace hanya ce wannan haka da ban san da ita ba,kimun yadda zan gane" Dariya mamin tayi tana cewa tare da rage murya, "hajiya Huda k'awar nan tawa take bani labarin wani malami wallahi ya kware da aikin sa, tun da taje wajen sa ta samu kan d'anta isah da matar ta rabata dashi, to shine tun da taji halin da muke ciki tace wallahi zata raka mu cikin kwana uku maganar auren zata lalace na Roohe da Rafeeq, don wallahi da ya auri d'iyar mak'iyyata gara ya dawwama babu aure" Umma tai jimmm kafin ta ce, "safiya nifa duk abunda za'a had'a da shirka bana son shi wallahi,malam man nan wasun su basa tsoron Allah bokaye ne wallahi" "Ko d'aya maijidda,wallahi shi ba haka yake ba in munje ai zaki ganema idonki,rubutu ne zai bada ba wani abu ba fa" Jin inda suke son kai kansu saboda k'iyayyar auren mu yasa na taso na fito daga d'akin na d'aga labule ina cewa, "Mami,ummah,inhar don farin cikin mu zakuyi don Allah karku fara kai kan ku halaka,inhar kun yadda dani ba sai kunje wajen wani boka marar tsoron Allah za'a samu mafita ba,ni da kaina zan kashe auren bayan an d'aura nai maku wannan alk'awarin, shi kuma yah rafeeq ku barsa da Najeeba don naga alamar shi ya mik'a wuya,don Allah kar kuje wajen wani boka pls" Mami ta ce, "shikenan Roohe Allah ya baki sa'a,don auren dole babbar masifa ce" Na juya na koma dakin cikin tunani mai tsawo,taya zan iya kashe auren bayan anyi?nan danan zuciya ta shiga sak'a mun abubuwa baji ba gani,hadda wanda ban sanma ya akai ta hasaso mun shi ba,kuma na yadda da kaina dari bisa d'ari inhar nice zan kashe auren in sha Allah,burin su ai a daura ko?to kuwa bayan na tare bazan yadda koda yatsana ya tab'a ba zan bud'e masa shafe shafi na bala'i da masifa, ko baya kaunat uwatai saiya sawwake mun. (Tofah🤔, bari dai mugani Roohe) ******** Bamu sake haduwa da yah rafeeq ba tun zuwan sa gidan anti,ban nemai ba shima haka inda nasan zan ganshi ma bana zuwa kwata-kwata,bangaren nasu ma nai mashi yajin aiki Rukee har ta gaji da mun korafi,duk ita dakin mu guda bacci ke kawota tafi wuni bangaren su. Rannan ranar wani weekend ina ta game a laptop d'ina Ummi ta shigo dakin mu tana cewa, "Yah Roohe Abba na kiran ki" Dagowa nai ina kallon ta bance komi ba,illa nasan da dalilin kiran tunda rabon daa muyi magana nidashi kamar yadda muka saba tun kafin batun auren nan,saukowa bai daga gadon ina sanye da riga da wando kanana rigar iya cinyata wandon pencil ne, sunbi jikina sosai suyi kyau hijab d'in sallata na zira na nufi falon sa. Da sallama na shiga dai-dai sadda ya d'ago manyan idanun sa tubarkalla mukai four eye's,ras ras naji gabana ya fad'i nai saurin kawar da kaina naja tsaki dai-dai yadda xaiji ba tare da Abba shi yaji ba,na wuce da na isa inda Abban yake na zauna k'asa ina gaida shi.........."Abba ina wuni?" "Bazan tab'a ansa gaisuwarki ba Roohe har sai kin gaida Ramadan," Cikin fishi da bacin rai yai maganar,kaina k'asa ban dubi inda yake ba na gaida shi ciki-ciki, "ina wuni" "Lafiya lau" Ya amsa a takaice muryar sa clearly ba wani abu a cikinta,ma'ana haushi ko farin ciki babu ko d'aya, duk mukai shiru na wani lokaci kafin Abban ya ce dani, "LAYLA nasiha zan miki matsayin mahaifin ki daya isa dake,tun da aka fara batun auren ki bance miki komi ba akai,na bari ne inga iya hankalin ki da kuma samun natsuwarki tun da baki da lafiya,a yau daya rage auren ku baifi sati shidda ba shiyasa na tara ku don nai muku nasiha da kwatanci,Aure dai da kuke ganin sa ba abun wasa bane ba abun rainawa bane,kar kuga cewar bakwa son juna akai auren kuje kuyita yin abunda kuka ga dama akai,kowannen ku yana da ilimin addini dai-dai gwargwado,kunsan abunda yake haramun da wanda yake halas ne,kunsan hakkokin miji akan matarsa,haka nan kunsan hakkokin mata akan mijinta,don haka kuji tsoron Allah kuje ku xauna da juna lafiya don Allah,kuyi mun wannan alfarmar bama kamar ke Roohe nafijin ki kece mai taurin kai,kece wadda kowa yasanki da fitina to inhar kikaje kika ringa fitina dashi wallahi zan manta dana haifeki,inhar kina so albarkata tabiki har lahira to kije kiyi biyayya kiyi hakuri a dakin ki,inaso ace sai mutuwa zata rabaki da gidan auren ki,nasan cewa Auren nan ku duka babu maiso amma ku sani bamu da ikon bijirewa umurnin Hajja,yi kata biyayya shine xai saka mushiga aljanna,haka nan kuma in kukai mana zaku ga haske a rayuwar ku,ahankali Allah xai kimsa maku soyayyar juna wadda baku tab'a tsammata ba,sauran yan uwanku duk nai masu fad'a kuma nasan zasuji maganata kamar yadda kuma nasan ba zaki bijirewa maganata ba,don haka ina muku addua Allah yai muku albarka,yasa aalkairi a zaman auren ku ya kuma sanya muku son junan,ya baku zuri'a mai albarka da zasuyi muku biyayya kuma,zan tsaya haka ina fatan kunji kuma zakuyi aiki da abunda nace" "In sha Allah Abba ba zaka a samu wata matsala daga gareni ba" Cewar Ramadan cikin biyayya da ladabi, kaina k'asa zuciyata bugawa kawai take,kalaman Abba sun daure ni matuk'a jikina yai nauyi haka ma bakina, saida naji ya ce "kefa Roohe" Kwalla ta silalo mun ban dago kaina ba nace, "nima haka Abba" "Ma sha Allah,ubangiji yai muku albarka bari na barku ku zanta" Ya tashi ya shige cikin bed room d'insa ya barmu nan xaune kamar wasu kurame kuma makafi,ba wanda ya iya dagowa ya kalli d'an uwan sa,kowa da kalar tunanin da yake yi a cikin ransa,munfi minty goma haka zaune ba mai uhm bare uhm uhm,kafin naji tashin sa da muryar sa yana ce mun, "sai da safe" D'ago kaina nayi ina kallon sa da mamaki,bai dube ni ba ya sa kai yai ficewar sa binsa nai da kallo har ya fice, jinjina kai nayi ina sake jinjina tsabar d'agawar sa da girman kansa,shiba wani shege ba sai fad'in rai,naja tsaki nima na tashi nai tafiyata dakin mu. Abba Nura ne zaune da iyalin sa duka da yaran da matar tashi mami, Rafeeq,Sha'awa da tazo daga gidan auren ta sai Rukee, saida ya gama masu nasiha sosai akan had'in auren da akai yajawo hankalin su da nuna masu muhimmancin yin hakan, da kuma biyayya da iyaye akan abunda baka so. "Wai Abban su kun sani sarai Auren dole haramun ne amma kuka bada goyon bayan yima yaran nan shi..........Safiya kimun shiru!" Ya fad'a cikin yar tsawa,ba shiri taja bakin ta ta tsuke gudun rikici gaban yaran su, ya cigaba da ce mata "idan har ba zaki taimaka mun wajen ganin sunje sun zauna lafiya a gidajen su ba,to Safiya karki kuskure ki bada goyon bayan hana su zaman lafiya da juna,wannan shine kashedi na karshe tsakanina dake,in kuma wani tsaitsayi yasa kikai abunda har yasa wani cikin su ya kashe auren sa wallahi tallahi kema naki zai mutu" Su duka yaran saida suka razana, wajen dagowa suna kallon shi, Rafeeq ya ce "Please Abba" "Ba batun Please bane Rafeeq, na fad'a agaban kune yadda inhar hakan tafaru ba zakuyi blaming dina ba" Sha'awa ta ce "kayi hakuri Abba, Mami ba zata aikata haka ba in sha Allahu" "Allah yasa," Ya fad'a,sannan ya cigaba da cewa "magana ta gaba akan Yayah Habibu ne da matar sa, inaso kusan wani abu guda da baku sani ba akan su, Yaya da matar sa sunyi mana abunda bamu iya biyan su har abada,dani da Abban ku Taheer labarin mai tsayine amma abunda zan iya sanar daku shine Yaya Habibu da matar su da bazar su muka kawo wannan lokacin,sune komin mu tun daga sadda maka taso har kawo yanxu,sunyi hidima damu da jikinsu da aljihun su tun duniya na kwance, shine karatun mu na boko da islamiya har muka zama abunda muka zama,wuyar da Yaya yasha akan mu shida matar sa baki ma bazai iya misaltawa ba,har takai zasu iya rasa abun da zasuci inhar mu zamu samu kuma zamuje makaranta, wannan dalilin yasa Hajja bata had'a kowa dasu ba, duk abun da zai taso bata yadda wani ya raina su ba to balle mu, don haka ina sanar daku da babbar murya inhar kuna so mu shirya daku mu daidaita to ku kyautata masu,yadda kuke zumunci da y'ay'an Taheer suma su ramadan da su Rahma kuyi dasu,hakan shi zai samun cewar eh lallai kun yadda nidin mahaifin kune,sab'anin hakan kuma zai nuna mun cewar ban isa daku ba alamun ban haife ku ba,wallahi rashin bin yaya da matar sa kamar kun tsake kan ku daga cikin zuri'ata ne,don haka yadda zakuyi mun biyayya ku kyautata mun suma haka zakuyi masu,fatan kun jini kuma kun fahimce ni" "In sha Allahu Abba zaka samemu masu yi maka biyayya akan hakan,Allah ya bamu ikon binsu bisa dai-dai" Cewar Rafeeq, Abban ya ce "madallah,Allah yai muku albarka kuna iya tashi na sallame ku" Mom muhseen&Asaad🥰 _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....6 *WAI WAYE...ADON TAFIYA* Hajja kakata ce itace ta haifi ubannin mu maza, su hudu rak gareta Allah ya bata su uku maza sai mace daya mai suna goggo Habi,kuma itace autar su tana aure a lagos tana jimawa ma bata zoba yaranta uku itama, babbar sa'ar muce mufida sai sauran maza kamis da jamil. Abba Habibu shine babba cikin su Babanmu,shida matarsa MAMA suna da yara hud'u Anty Rahma sai Yah RAMADAN sai Yah Najib sai Najiba auta, Abba Nura da matarsa umma Safiya suna da yara uku rak, Yah RAFEEQ Anty sha'awa sai Rukee Abba Tahir shine mahaifina da nakeji dashi duk duniyata,ina alfahari da Abba na ubana da babu kamar sa a wajena,soyayyarsa mai girma ce agareni,shida mahaiifiya ta mai suna Maijidda sun haifi yara hud'u Yah Fahad,Anty Rafia saini LAYLA da naci sunan mahaifiyar Abba watau Tsohuwa mai ran k'arfe HAJJA ake mun lak'abi da ROOHEE,sai auta ummi mai sunan mahaifiyar ummanmu. Tunda muka taso a cikin gidanmu mun ga ummanmu da Mami basa shiri da Mama mahaifiyar su Yah Ramadan,wata irin k'iyayya ce suke mata wanda ko ganinta basa so,kuma suka katange mu daga yin huld'a da ita da y'ay'anta,to kun sani a duk sadda uwa bata son wancen to lashakka y'ay'anta zasu bi bayanta ne ba tare da sanin miye dalili ba,su dai tunda bata son wancen to suma basa son sa, A haka muka taso muna nuna halin ko in kula da Mama,bama yi mata rashin kunya amma kwata-kwata babu ruwanmu da shiga sabgarta kai har shi Abba Habibun in ba hanya ce ta matse mana ba bamu zuwa takanas muce munzo gaidashi, hakan kuma bai dame mu ba mudai tunda basa shiri da uwayen mu muma hakance, koda akai bikin Anti Rahma babu wanda yai anko cikin mu, kuma bamu shiga cikin sabgar bikin ba kamar ma ba biki ake gidanmu ba, duk mun san ba dai-dai muke ba amma kuma bazamu iya gyarawa ba gudun fad'an uwayen mu mata, kuma duk Hajja ce tajawo wannan k'iyayyar a cewar Mami saboda tana nuna tsananin banbanci tsakanin Mama da su,duk abunda ya taso to Mama ce kan gaba kafin su, kuma tafi janta ajikinta fiye dasu hasalima da ita kawai take fira bandasu Mami,wannan abun ya kara taka rawa wajen sake jefa kiyayyar Mama da Ahalinta a zukatan su. Wannan kenan........ Yadda muke kusanci da mami da y'ay'anta abun ba'a cewa komi,don Rukee tamkar Ummanmu ta haifeta haka muke tare,ko ina zamu tare ko a school sit d'inmu guda haka ma islamiyya,Anti shaawa ma ita da Anti Rafeea kamar tip da taya suma haka suke, haka zalika Yah Rafeeq da Yah Fahad suma sosai suke abota da juna,komi ya shafi d'aya to ya shafi d'aya, ummi ce kawai bata da partner, hakan ba kadan yai ma uwayen mu dad'i ba yadda muka had'e kanmu muka ware su YAH RAMADAN,. Zan fara daga sadda muka shiga Ss3 don daga nan ne zakufi fahimtar komi. Tunda mukai wayau da sanin kanmu yar tsama ce ke tsakanina da Yah rafeeq,tun ban da wayau inhar yana waje to ban da sak'at haka zai tisani gaba da tsokana yana jana fad'a, duk da tarin shekarun daya bani hakan bai hana shi tsokana ta ba,don shida yah fahad xasu bamu shekara bakwai-bakwai nida Rukee,amma in kaga yadda yake mun zaka d'auka wata tsarar sa ce, ba irin tsakanin da Abba Nura bai mana ba amma ta inda ta shiga ta nan take fita, kowa yasan a da niba mai fad'a bace balle wata hayaniya, hasalima zaka iya jana inyi kamar ban gani ba,zaka jima kana mun abu ko kallon ka banayi,amma silar Yah Rafeeq na zama mafad'aciyar karfi da yaji,sannan na zama soda uwar magana,har ta kai ga indai babu ni a gidan kowa zai gane,a hankali abun ya soma. Kasancewar duk cikin yan matan gidanmu gaskiya babu wacce ta kawo ni a komi na dirin jikin y'a mace da kyau,don komi na Hajja na kwaso kuma Hajja farace sosai sol da ita kuma ko yanzu ka kalli jikinta kasan sadda tana da kuruciyarta tayi kyau na ban mamaki,to nima haka don shiyasa ma dokar saka Hijab in za'a fita ta zama wajibi garemu duka, duk da wani sa'ilin a sace nake saka gyale ajaka in mun fita mu saka nida Rukee,ban tab'a jin wanda ya kushe ni ba sai akan Yah rafeeq, komi na saka saiya kushe bama akan sitira ba har k'ok'arin da nake dashi a makaranta inhar na anso abun yabo shine nafarko da zai kushe yace satar ansa ce, abun yana mun ciwo inyita kuka idan na kasa maida masa,shi kuma daman haka yakeso yaita dariya yana cemun rab'o ashe haka nake ma qawaye kuka suma,irin haka dai tasha faruwa ba iyaka ko inyi kwaalliya zamuje wani waje yai dalilin da zai saka a hana fitar ko ya dizgani inji na tsani kaina, karshe bazan je ko ina ba. Muna falon Mami watau bangaren su Rukee assignment muke na physic,duk kaina yai zafi daman kuma nice karfin assignment d'in, to yawa ne dashi kuma ga kaina dake ciwo,Rukee daman in inayi take kallo don ta iya saboda ba subject din da bata ganewa irin sa,daker take sha a exam. Jinai kurin an fige book din ta baya na a zabure na d'ago don ganin waye, "Aikin banza, wai wannan abun ya gagare ku fiddawa ohh ni Rafeeq, ashe daman k'ok'arin a baka yake malaman da alama cin hanci ake basu don su baki overall,yo inba haka ba ta ina zaki iya kawai dai an cuci overall" Ya fad'a yana jifata da book d'in,tsare sa nai da idanuna da suka rage girma saboda ciwon kai, haushi da bakin ciki kamar suyi mun me? Kwalla ta taru cikin idona na ce, "koma dai ya ya ne bai shafe ka ba Yah Rafeeq, nidai ka daina shiga sabgata............ked'in banza Roohe,saina shiga sabgarki inyaso kiyi duk abunda zaki" Sai kawai na fara tattara kayana ina hawayen bakin ciki, "ai don kana ganina a bangarenku shiyasa kake mun duk abun da ka ga dama, ni kuma daga yau bani babu nan b'angar...........Miyai zafi Roohee karki yadda yai nasara akanki,daman ai haka yake so inajin sa yana cewa ganin ki bangaren nan ne baya so,ke kuma saiki biye sa" Mami ta katseni da fad'ar hakan, Uffan bance komi ba,kuma ban fasa tattara kayayyakina ba ina hawayen bak'in ciki,ganin da gaske tafiyar zan kuma ya sani sarai in na bar Abu na barsa kenan.......keeee doluwa wai tafiyar zaki?amma anyi shashasha,baki san wasa ba ke wai?wallahi ke kam hamago ce, d'an wasan nan na abokin wasa ma baki iya ba,tirr da halinki" Nai masa banza na nufi k'ofa Rukee da Mami ba wanda yace k'ala dariya suke ma abun su, "kin san waye d'aya?wallahi ba zaki fita anan ba salan kija mun masifa ga Abba ko?" Na watsa masa idanuna manya tubarkalla masha Allah, nace "Ehy d'in,kuma saina fita tun da ba anan aka haifan ba" Dariya yai tayi yana sake tare hanya, yana cewa "yawwa ko kefa, haka nake sonki ai,amma mutum kullin dunkum kamar dankali.......duk'ewar da nai ta kasan kafafun sa zan wuce yai wuff ya rik'oni ya zaunar cikin kujera, "kifa kiyayeni Roohe ba inda zaki saikin gama abunda kike, ni zolayarki nake" Fafur yak'i barina in tafi na fara kuka na gaske ina cewa, "kabar ni natafi kaina ke ciwo zan sha magani ko" Sauri yayi yaje ya dauki box d'in magungunan gidan yana ajewa gabana, "yawwa gashi nan, gaya mun ta ina kike ciwon kan in san kalar maganin da zan baki kisha," Na nuna gaban goshina inata hawaye sosai, "to share wad'anan hawayen tukun, stress ne ke damunki ki ringa hutawa alhuda huda" Ya bani paracitomal tare da ruwa na sha "Rukee ki rakata ta kwanta ta huta,in so samu ne kiyi bacci ma dakin tashi zakiji ya sauka" Nace cikin laushin jiki da sanyin muryata "ni banajin bacci,assignment d'ina zan ida...........wai ke wace irin jarababba ce ehy?assignment din banza da wofi dalla malama kije kiyi bacci zan ida miki" Ban sake cewa komi ba na mik'e Rukee ta kamani muka nufi dakinmu dake cikin part d'inmu, kwanciyar nayi nai lamo kamar mai baccin, Rukee tai tsaye kaina har saida na gaji nai magana idona a rufen, "Wai miye ne?" Murmushi Rukee tayi ta ce, "kawai wata extraordinary caring nagani daga Yah Rafeeq,kin san nafara lura da hakan kwana kin nan.........ya isa don Allah mi kike son cewa?" Na katse ta dafar hakan ina lullumshe idona, xama tayi bakin gadon tana cewa "kawai ina ga ya fara canza wa daga yar tsama,lamarin sa yayi kama daaa........kinga don Allah kyaleni da maganarsa bana so,kije kawai bacci zan" Shikenan ta kyaleni,shiyasa bama fad'a da Rukee duk abun da na nuna bana so tofa tabar yi mun shi ba kuma zata sake tada maganar ba. Shiyasa muka shak'u sosai da sosai nida ita muna kaffa kaffa da bacin ran juna, kamar wasa kuwa sai gashi nayi baccin ban tashi ba sai ana kiran sallar magariba, kuma naji dad'in baccin ainun na sauko na shiga nai alwalla naxo nai salla,na gama na fita zuwa wajen ummanmu anan falon ta na iske su Anti Rafeea da Yah Rafeeq dasu Yah fahad suna fira,hadda anti sha'awa da Rukee...........jikin umma na lafe ina gaida su cikin jam'i muna had'a ido dashi yaja tsaki yana ci gaba da maganarsa kamar bai sanni ba, nima sai na fita sabgarsa nace ma umma yunwa nakeji, "Rafeea samo ma Roohe abinci mana" Yah Rafeeq yace, "wai Wannan katuwar za'a sanya ma abinci?haba Umma ke kike lalata ta wallahi," Nai banza dashi,Anti Rafeea daman jira take don ta tsani a sata tai mun aiki, "yawwa Yah gaya mata,sai kace dai Roohe ke sama dani don Allah don' Annabi.......to kawai kice baki zuwa mana ba shikenan ba" Cewar umma,ni kam nai murmushi ina kallon ta tana banko mun harara lodi lodi, na b'ata rai "Umma kice ta daina hararata wallahi" "Kyaleta Ai bata k'ari," Haka tatafi tana jin haushin aikin da aka sata akaina, daman kuma kowa yasan nice yar gaban goshin umma ba ummi ba,don duk da take da sunan mahaifiyarta to tafi ji dani,kuma hakan bai dameta ba tunda itama ana bata kulawa daidai yadda ya kamata, sai gata ta dawo bata zubo abincin ba tana ta fara'a tace "Sak'o mak'ok'o daga Abba,yace kowa yafito aje b'angaren Abba Habibu ayi dinner kamar yadda aka saba" Haushi ya cika ni ganin yadda kowa ke mun dariya, alamun dai dole ai zan taka naje can naci sab'anin a biyoni dashi har daki. Babu yadda muka iya dole duk muka tashi kowa ya wuce ya tafi, nice k'arshen tafiya don nawa na tsayayi saboda ba abunda na tsana irinz zuwa bangaren Abba Habibu a rayuwata, ba kuma don komi ba sai don bana son ganin wanan k'azamin Yah ramadan d'in wanda shi rayuwar sa kullin a k'untace take,fuskar sa kwata kwata babu annuri babu farar'a ga uwa uba girman kai kamar d'an wani shege,bacin basu ajeba basu ba wani ajiya ba amma sai fad'in rai, naja tsaki saboda tuna wa da nayi kujerata tana kallon tashi inda yake zama, haka nan na wuce don rashin zuwan nawa matsala ne wajena in Abba ya kamani, kowa ya hallara har an fara cin abincin naja kujerata dake kusa da ta Anti sha'awa na zauna ciki-ciki nake gaida Abba Habibun da shida Mama,na gaida su Abba Nura na soma zuba yar shinkafa yar kad'an na zabga coleslaw na zuba nama son raina har na kai spoon bakina Abbanmu ya katseni cikin b'acin rai........Roohe ashe baki da wayau har yanzu?su sauran yayyun naki kinfi karfin ki gaidasu,ki kiyaye ni fa!zan sab'a miki akan wannan taurin kan naki." "Bita a hankali Mana Tahir,shi yaro ai d'an kwatanci ne da lallashi,nasiha ma inkai mata zata sa ta gyara,Roohe y'ata duk wanda yake sama dakai ya cancanci gaisuwa koda da shekara d'aya ne kuwa,kuma rashin gaisuwa ga babba rashin d'a'a ne,wanda bai cancanci ace daga gidan ne hakan ke faruwa ba" Duk Abba Habibu ne ke maganar kaina k'asa ina sauraren sa, saida ya gama sannan nace "ayi hkr zan gyara" "Allah yasa to,maza ci gaba da cin abincin ki" Hakan bai sa na bud'e baki na iya gaida wadan da suke son na gaida ba, su Anty Rahma da Yah Ramadan, nai mirsisi abuna kamar ba aimun mgnr ba,haka dai aka gama kowa yaje ya gaida Hajja yai mata saida safe sannan katafi bangarenku,nida Rukee nan muke raba dare fira da Hajja tana bamu labarin k'uruciyarta da sadda take tashen samari,musha dariya musha takaici sai Abba yazo ya kora mu yana fad'a mun hana ta taje ta twanta ta huta, to sannan zamuje mu kwanta. Washe gari duk masu shirin makaranta mun gama shirin mu,yan secondary daman dagani da Rukee sai ummi da Najeeba, Ada Yah Fahad ne ke kaimu to sai ya tafi makaranta sokoto udus acan yake degree d'insa,sai Abbanmu yace tunda Yah Ramadan baya zuwa ko ina ya daure ya ringa kaimu,wannan abun bai mana dad'i ba nida Rukee saboda kwata-kwata bama son kusanci dashi,haka nan muka tsangwamesa ba laifin tsaye babu na zaune,da mun ganshi ma sai mu kwashe da dariyar iskanci,uffan bai tab'a ce mana ba kallon mu ma bayayi balle ya nuna mana yasan munayi,gaisuwa kau inhar mun gaidashi to Abba na kusa ko Abbansu Rukee,shima a ginshire zamu gaidashi kuma zai amsa kamar bai damu ba,tun da ya soma kaimu muka tsiri iskanci kala-kala,kuma har zaman da ake yanzu bai tab'a tanka mana ba,sai infa Abbanmu na nan ko Abban su Rukee shine zai tsawatar mana kafin mu fito mu tafi. Anti Rahma babbar gidanmu yayarsu Yah Ramadan,ita yake bi mawa ita NCE kawai tayi har ta gama anyi aurenta har da y'ay'anta mace da namiji ta farkon kausar sunanta,sa'ar ummi ce namijin kuma fauzan shekara biyuce tsakanin su data farkon,daga nan har yanxu shiru haihuwar,don bamu da wayau sosai akai bikinta. Sai shi mr k'azamin gidanmu sunan da muke yawan ce masa kenan,tunda a ganin mu baya gayu irin wanda su Yah Rafeeq da Yah fahad keyi,ko guga bai damu da ita ba haka zalika nidai koda wasa banjin k'amshi na tashi jikinsa irin wanda su Yah fahad da Yah Rafeeq ke sawa,shiyasa kullin kallon mugun k'azami nake masa,to balle ga fuska koda yaushe kamar fuskar shanu,bana iya cewa ga ranar danaga dariya ko murmushi a fuskar sa, haba mi ake da wannan dunkum d'in mutumin, Anti Rafeea da Anti sha'awa sai Yah najib sune suke level 2 a jami'a sai dai kowane da kalar cause d'in da yake yi,shi Mr kazami one year kenan da gama degree d'in nashi har ya gama service kwanan nan,anso ya wuce masters abun bai yuwu ba kasancewar ba wani k'ok'ari ne dashi ba, akwai shekarar da saida ya maimaita ta a daddafe dai aka samu aka gama shi,duk da cewa ban tab'a zama dashi na minty d'aya ba amma a ganina inba rashin k'ok'ari ba mizai ja ace ka shekara biyar kana degree ka kasa idawa,a ganina kawai babu kwalwar ne kurin, Yah rafeeq duk gidan nan bayan ni babu mai k'ok'arin sa don zan iya cewa zamuzo tangal dashi,watau zamu zo d'aya shiyasa ma Abba Nura ya zab'armasa medicine,yanzu ma hutu ya samu na karshen shekara yana cikin shekara ta uku ne, don ya riga Yah Fahad fara karatun nashi wannan kenan. Sauran masu zuwa jami'a kuma kud'in taxi Abbanmu ke basu suhau,in kuma driver na nan saiya kai ka in ka shirya,haka tsarin ya taho. Tun seven thirty na gama shirina nai breakfast duk da bana cin komi da safen sai black tea kawai,a school ne in akai break wajen ten sai inci wani abu shima ba wani mai yawa ba,normally bana cin abinci sosai kuma ban damu da mai nauyi ba, Nida Rukee muna ta firar wani sabon uncle d'inmu da zai ringa mana civic education,muna ta dariyar yadda yake magana kamar wata mace ummi ta shigo cikin shirinta, fuska da fushi-fushi "Haba Yah Roohe,miyasa kullin sai kun makarar damu ne wai?in ku ba a muku tare mu kuma fa?kullin fa sai an mana warning haba don Allah" Rukee ta kallan muka kyalkyale da dariya hadda tafawa, ta saka kuka tana cewa "wallahi Abba ne xai rabani daku, na gaji da wanan abun yanzu haka Yah Ramadan nacan kun shanya shi yana jira wannan ba dai-dai bane" Ta juya fuuuuu tabar dakin, Rukee ta diro daga gadon tana cewa "wallahi bazan zauna Abba ya isko ni ba,ke dashi inya zo" Ta kwashi takalmin ta a hannu da bag d'inta,nima cikin sauri nabi bayan ta da kayana a hannu a falo mukai kicibis dashi ya biyo sahunmu,ga Yah Ramadan a gefe. Cikin fad'a Abba ke cewa "watau ba zaku canza halin ku ba ko?wane irin kunnen k'ashi ne daku?kodan hannuna bai kai jikin ku ba ko?to shikenan daga yau a k'afa zaku ringa tafiya,kila hakan ya zama darasi har ku gane kuren ku.........wayyo Allah mun tuba Abba,munbi Allah mun bika wallahi ba zamu sake ba,na rantse maka Abba ko bakin titin unguwar nan ba zamu iya kaiwa a k'afa ba,kai mana rai" Nida Rukee muka zube muna magiya cikin tashin hankali,don mun san halin Abba kafin yai fushi irin haka ana jima wa,inko har yayi to anshiga tara,janye k'afar sa yayi yana nufar hanyar bangarenmu yana cewa, "bani kuka ma laifi ba wanda kuka ma wa inya hakura to,in kuma bai hakura ba wallahi maganata babu canji,Ramadan ka wuce ka kai Ummi da Najeeba kar su makara" Bai tsaya sake sauraren magiyar da muke masa ba yai shigewar sa, tsaye mukai muna bin bayan su Ummi da kallo da suka bi Yah Ramadan don a sauke su, Rukee ta ce "wai Abba na nufin sai mun bashi hakuri?...........Tabd'ijam kice akwai matsala don wallahi ba zan iya ba" Na katse Rukee da fad'in haka cikin k'unci,muna nan tsaye mun rasa mafita gashi yau zamuyi submitting na assignment d'in physic,kuma rashin submit din matsala ne,don bazai anshi naka daga baya ba, wata zufa ta karyo mun dana tuna da hakan, Rukee ta buga ta gumi a zaune cikin one siter cikin tashin hankali nace "Rukee yau ne zamuyi submit na Assignment d'in uncle harun,idan muka muce mun rasa 20 Mark fa" Itama zabura tayi ta mik'e ta ce "na shiga ukuna,bayan rasa mark ma Roohe akwai punishment,innalillahi wa inna ilaihir raju'un ya zamuyi............sallalamin me kike anan kamar wani ya mutu" Yah Rafeeq ya katse mana maganar,duk muka juya kanshi cikin son samun taimako, tuni idona ya cika da kwalla duk duniya ba abunda na tsana afannin karatuna irin rasa mark ko harf ne kuwa,yana tada mun hankali kasa ce masa komi nayi don nasan ma iza wutar zai bazai wani kawo solution ba.........Yah Rafeeq ka taimake mu yadda Allah ya taimake ka"............ta zayyane masa komi daya faru babu munafurci ko ragi a ciki,mi zai ba dariya ba hadda zama k'asa kamar wani yaro,yana yi yana kallona yadda tashin hankali ya bayyana b'aro b'aro a fuskata ga hawaye suna layi layi, "Amma Abba ya burgeni wallahi, ba dai kun iya iyashege ba to Abba yafiku iyawa kuma ni nan ba abunda zan iya muku,gara ku gane kuren ku...........kuka na fashe dashi sosai ni kadai nasan bakin cikin da nakeji akan rasa mark din nan,ahankali falon ya fara tara mutane Mami ta fito saiga Anty Rafeea da ummanmu,da Anti sha'awa, "Subhanallahi!,Roohe miya faru?halan wannan babban kwabon ne ya saki kuka?kai kuwa kaji kunya wallahi Rafeeq,ina anfanin abunda kake yi" Mami ce ka fad'in haka tana k'arasowa wajena ta janyoni jikinta, har sannan dariya yake yana cewa "Aa karki dora mun laifi Mami,wallahi bani na kar zomon ba ratayar ma ban ansa ba" Ummanmu ta ce, "mike faruwa Rukee,ya akai baku tafi ba har yanzu?halan Driver nakune saiya bata muku lokaci" Rukee ta zauna dab'as cikin damuwa take labarta musu abun da ya faru, Anti Rafeea ma tabi bayan Yah Rafeeq wajen yin dariya ta ce, "ni kam dai na wuce umma saina dawo" Haushi kamar zai mun me,yadda suke dariyar nan kamar zan je na shak'esu nakeji, Mami Ta ce "Miyasa Abban ummi zai haka?har wani abu ne nan da zai saurin yanke musu hukunci,shin miye aikin sa da bazai jirasu ba koma karfe nawa zasu kai?inace har biyansa yake akan hakan?gaskiya bana jin dad'in wannan abun" "Uhm kema kin fad'a ai,ni na rasa wannan k'unata da yake yi da wad'ancan yaran(su Yah Ramadan) tunda sun nuna basa son shigowa cikin mu dole ne?ya barsu suyi sabgarsu muyi tamu mana,to gaskiyani ban yarda da wannan hukuncin ba,hakuri name zasu bashi sai kace sun zagi tsohon sa,wallahi ba zasu bashi wani hakuri ba saidai ya aje tukin...........dai-dai nan ya shigo da Sallama cikin muryar sa mai cike da mazantaka da kwarjini,naja dogon tsaki wanda nasan dole zaiji fuskar nan kamar kodayaushe ya gaida su Mamin,amma ba wacce ta amsa bai damu ba ya isa gaban umma ya aje key d'in motar yana cewa, "kiyi hakuri umma,indai akai wannan ne kibar b'acin rai nima Abba matsamin yayi,inbacin haka bazan anshi aikin daya bani ba,sannan ubana ne bazai sani abu ince bazanyi ba,amma tunda takai ga haka ki bashi mukullin motar sa kice yayi hkr daga yau bazan sake hawa ba balle rayuwaka su b'aci,har takai ga inda bai kamata ba" Yana gama fad'in haka ya juya zai tafi, Yah Rafeeq ya ce, "wai kai nan zuciya kayi?ai wanda ke zuciya da abu wanda ya mallakin abun amma ba kai..........enough Rafeeq!!!" Abunda bai tab'a faruwa ba kenan wai kaji Yah Ramadan ya d'aga murya da sunan fad'a ko b'acin rai,kowa yasan wannan.......... "Kar ka soma,ka tsaya iya matsayin ka zai fiye maka alkairi,kuma ni koda ban da abun to nafi karfin a wulakanta ni saboda shi,wannan shine" Ya wuce kamar zai tashi sama,duk shiru mukai muka kasa magana,yah rafeeq ransa ya b'aci sosai duk da kuwa shine baida gaskiya, yace mun "ke kuma dalla can ki mana shiru da wannan kukan banzai,duk don zaki rasa mark dinki ne kike wannan kukan zanje nai muku submit,idan Abban ya dawo zanje na bashi hkr ya huce" Har raina naji dad'in maganar, sai na tsaya da kukan, ya dalla mun harara ya wuce yabar falon,Mami tace "lallai yaron can wuyan sa ya isa yanka,shi nan har wata zuciya ce dashi...........yo ta banza da wofi inhar da gaske akwai zuciyar ya tattara tsaffinsa subar mana gida shine kawai" Nan muka barsu suna tattauna maganar,muka koma d'aki muna cire kayanmu cikin sanyin jiki,duk da kuwa muna murnar dole Abba zai samar mana driver tunda burinmu ya cika. Mom Muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....7 Kwana kin da suka biyo baya Yah rafeeq ke kai mu makaranta,Abba yayi tafiya kwatsam shiyasa ba asake maganar ba Abba Nura kuma ba kasafai ya cika lura da abubuwa ba,kawai dai matsalar fad'an mu da Yah Rafeeq har muje sch muna fad'a dashi,in ya kaini bango inyita kuka dana fara kukan zai fashe da dariya,alamun yayi nasara. Rannan har Rukee tace "ke kam dai to,har yau kin kasa Fahimtar Yah Rafeeq kukan ki fa shine alamun nasarar shi, da zaki burgeni ki ringa shanye komi zai miki,ni na rasa gane wannan kyara da tsokana tashi akanki,miyasa bai ma kowa ba sai ke?" Alokacin ina cikin fushi ban bata ansa ba, amma nima abun yana mintsini na a rai miyasa bai tsokanar kowa saini?miyasa baya fad'a da kowa saini?rashin sanin dalilin yasa dole na bar a bun a raina. Tunda wanan abun ya faru bamu sake ganin Najiba ba, daman kuma ko a sch ba had'uwa muke ba, ita tana B class mu kuma muna A kuma akwai tazara, daman kuma ba magana muke da ita ba itama kuma bata yi damu,don zan iya cewa tama fi yayanta iya b'agarar da mutum,ko iskar data kwasomu bata kallo balle ta tanka mana,inhar ta iske mu waje sallama kurin take bata kama sunan ko d'aya acikin mu,abun yana kara mana jin zafinta ainun,Rukee tace "kyale banza jin zafi ne kurin da Hassada" To nasan akan Abunda ya faru ne yasa ta daina binmu,bamu san wanda ke kaita ba kila kuma taxi take hawa,. Muna bangaren Hajja nida Rukee muna taya ta kwalemar bangaren Yah Rafeeq ya shigo cikin shigar sa ta gayu kamar ko yaushe, yai masifar kyau har fiye da kullin, brown shadda ce d'inkin zamani na matasa anyi masa harf jamfer ta d'an kamashi kad'an,ya saka hula milk da brown sai sawu ciki suma brown,kamshi kam kamar kamfanin turare ne a wajen,duk yadda nake zillewa kallon sa saida ya gane kallon sa nake, Hajja ta ce "kai Rafequ,wannan turare kamar na yan bori sai hawan kai yake,kaaji tsoron Allah ka rage sashi da yawa haka,ai saika dauki alhakina" Me zamuyi ba dariya ba shima ya murmusa yace, "Hajja kawai dai kice nayi kyau ne baki iyawa, saiki b'ige da la'antar turarena" "Haba dai,miye abun kyau anan Allah yajikan kakanku Alh matawalle in yayi gayu saboda kyan da yake har idon mutum disashewa yake,kaga kuwa ai baka kamo shi a komi ba,...........muka tintsire da dariya ganin yadda yake yamutsa fuska, na ce "gaya masa dai Hajja," Ya dalla mun wani banzan kallo, "ki fita idona kafin nai k'asa k'asa dake anan wajen,waya sanya dake iye" Haushin ankushe masa gayun sa yake,dariya ta kamani Rukee dai tai gefe ta kame baki,don jibga takesha in ta shigar mun in muna abun mu, na ce "yo Yaj Rafeeq sai in k'i magana,ai gaskiya Hajja ta fad'a mu dai nan ba muga wani gayu na azo a gani ba wallahi.......a fusace yayo kaina na ruga bayan Hajja ina ihu. "Kar ka kuskura Rafequ,akan me zaka daketa don ta fad' gaskiya komi?" Huci kurin yake yace "wallahi Saina b'ata miki fuska,tun da na shigo na kasa dake?wajenki na zo,Hajjaa ki fita tsakanin mu kawai" Dariya kawai nake masa Na ce "ashe babu dad'i kushen da kake ma wani,aiko wallahi daga yau na soma rama wa kodan kaji yadda nakeji nima........ban aune ba naji kauuuuu ga bakina,wani zogi ya ziyarce ni cikin azaba na fasa kara ina dafe wajen,dan danan har jini ya fito a lips dina Hajja ta ce "kai kai kai!Amma dai Rafequ anyi mugun mutun Ashe baka da mutunci ban sani ba,daga yarinya ta fad'i gaskiya shine kake son zubar mata da hakora saboda kana bakin ciki da kyawun da Allah yai mata?" "Allah ya kyauta nayi bakin ciki da wannan yarinyar Hajja, ni kawai bana son rai ni ne kawai ba komi ba,kinga daga yau ba zata sake tsoma mun bakinta ba" Ya juya ya fice ya barni inata kukana, Rukee keta ban hkr Abba Nura ne ya shigo ya nemi ba'asin kukana Hajja ta soma zayyane masa komi,hadda k'ari saboda itama abun ya bata haushi,cikin fushi ya sa waya ya kirasa "komi kake kazo nan wajen Hajja ka sameni" Lallashina ya ringa yi yana ban hakuri tare da cin alwashin saiya sab'a ma shi,har sadda ya iso inata shashshekar kukana don ba kad'an ba bakin yake mun zogi ba,tun kafin ma ya zauna Hajja ta soma surfa masa masifa, "watau kai mai karfin duk duniyar nan shine zaka saki k'wanjin ka ka nausar mata baki,to wallahi ba zan lamunta ba ko ubanka ya rama mata ko ni in rama mata," Kanshi k'asa jijiyoyi sun fito sosai abunka ga farin fata,idon nan yai jaa sosai alamun bacin rai tsantsa tatare dashi, "watau ba zaka iya bud'e baki ka bata hakuri ba kenan,duk fad'an da zatai taje tai tayi bai dame ka ba ko Rafeeq?" "Kuyi hakuri kuskure ne............karyar banza da wofi ba wani kuskure ai har shiga tsakanin ku nayi amma hakan bai saka ka fasa abunda kai niyya ba,yo Allah na tuba in bacin tsufa wallahi huncewa zan mu daku nida kai,bazan lamunci abunda zai takura mun takwarata ba eheee".........duk yadda naki cikin kunci saida nai dariya amma na duk'e ban yadda ta Gani ba,Rukee ce saida ta dara Abba kanshi murmushi ya saki,gogan ne kurin kamar ba ai komi ba fuskar nan murtik,nida aka zalinta ma ban kaishi fushi ba...........kalleni nan Rafeeq" Ya d'ago yana kallon Abban, "sau nawa xan shata maka layi da Roohe?sau nawa xan maka magana akan tsokanarta da kake,watau ni ban isa in baka doka kabita ba ko?.........kayi hakuri" Rafeeq ya fad'a kanshi k'asa yana kokowa da bacin ranshi, "yo to daman in ba hakurin ba me xaka bada,?ai ka riga ka cuceta kawai saidai Allah yai kata sakayya" Hajja ta fad'a tana banka masa harara,Abban ya cigaba da cewa "wanan shine karo na karshe dazan ja maka kunne game da Roohe,inhar ka sake take dokata wallahi ni kadai nasan kalar hukuncin da zan maka, tashi ka bani waje" Haka ya tashi a mutukar fusace,amma sai wanda ya sanshi sosai ciki da bai zai gane yana yin da yake ciki, Hajja taja tsaki bata ce komi ba illa dai nasan hukuncin bai mata ba, yajiyo kaina yana cewa "ki yi nesa dashi,bance kuyi gaba ba amma wannan tsokane tsokanen bana son shi,inkin san kina masa ki daina shi zai kawo rikici tsakanin ku,inkun had'u ki gaidashi da girmamawa yadda kike ma sauran yayunki,kinajina?" "Naji Abba Zan kiyaye" "Allah yasa,ku bani waje zan magana da Hajja" Tashi mukai muka fito saida muka isa Dakin mu sannan rukee ta zube tana ta dariya kamar ba gobe, tun bata ban haushi ha har ta bani cikin fusata na ce, "wai miye ne?" Tana rik'e cikinta take cewa cikin dariyar, "wai kina nufin Hajja bata baki dariya ba,wai in bacin tsufa huncewa zatai su daku..........murmushi na saki sosai ina cewa, "uhm Hajja ce fa,fiye da haka ma zata aika" Ta zauna tana nishin dariyar ta, ta ce "kin san miya hasala mutuminki?" "Aa saikin fad'a" "Uhm kushe shin da kikai ne fa?baki san bai son ka kushe shi ba koda wasa?ba abunda ke saurin hasala shi irin kushe" Jinjina kai nayi ina Cewa, "ohhh ashe ba dad'i,ai ke gabanki ake komi wace rana ce bai kushe ni?ni abunda yake mun ma ai bana masa irin sa,sai yau daga na d'ana?kuma fa cikin wasa nai maganar" Rukee ta ce "uhmm har yau baki gane waye Yah Rafeeq ba,toshi cikin wasan ma yafijin haushin maganarka,ke dai kawai yanzu kiyi nesa dashi don wallahi a tunzure yake,kuma abu kad'an zai saka ya karya dokar Abba,zuciya ce dashi kamar ta mutanan farko,amma kuma abu k'alilan na iya sawa ya huce nan take ya mance" "Hum shidai ya sani" Daga wannan ranar tsakanina da Yah Rafeeq ya kara tsananta, idan ya ganni kamar yaga kashi iskar data kaso ni baya kallo balle ya tanka mun,ni kuam ba nuna masa ban san ma yana yi ba,abu guda ke had'amu shine gaisuwa amma baya ansawa,ni kuma ban fasa gaidashi ban damu da rashin ansawar ba saboda Abba yace kar muyi gaba,kuma inaso sallata ta ansu to akan me Zan yi gaba dashi. Muna cikin wannan yana yin Abbanmu ya dawo daga Uk,watan sa guda da sati biyu da tafiya,daddare aka had'u babban falon dake bangaren Abba Habibu,bayan anyi dinner aka taru anan ana fira hadda Hajja kuwa,anata raha dasu Abban damu amma bamai sanya MAMa da Ahalinta,inaba su Abban ba da Hajja,itace ma keta janta da fira sai ta saki jiki suna yi tare,amma Mami da Ummanmu bamai ce mata ci kanki,Haka Najeeba da Yah Ramadan ba mai magana dasu inba Su Abban ba,yah Najeeb yana makatanta boadin yake a kano BUK, Abba ya dauko tsarabar kowa ya bashi da hannun sa murna kamar muyi me?saboda abunda mukace muna so ya siyo mana,sabbin abayas ne new design masu kyau hadda jikuna,ba wanda bai ba tsarabar ba su Umma ba yadda suka iya don hadda su MAMA ya yo mawa,don ta Abba Habibu tafi ta kowa yawa. Ya ce"baka gajiya da d'awainiya Taheer,kaida kaje aiki kuma ka b'ige da kashe kud'ad'e har haka" Abbanmu ya ce,"Haba Yaya!ina abun yake anan,kuma ai kunfi karfin komi a wajena don nai maku wannan hidimar wallahi ba komi bace, ba zan iya biyanka abunda kai mana ba nida Yah Nura (Abban su Rukee kenan)" "Shikenan Allah yakara bud'i da arziki,ya kuma kara lafiya" Kowa ya ansa da amin,Abban su Rukee ya ce "yawwa gara da Allah yasa na tuna,saida na ganku gaba d'aya sannan abun ya fad'o mun arai,kai Rafeeq rannan da zaka kai su Roohe makaranta nace yo ina Ramadan d'in mikace mun a lokacin?" Wani mugun fad'uwar gaba ta same ni,muka had'a ido da Rukee kowa cikin zullumi,shi kam ko ajikin sa ya hau bashi Ansa, "Abba ce maka nayi ya aje aiki bai yi,key d'in ma umma yaje yaba wai aba Abba Taheer Hakuri ya aje motar" Tsit kakejin Falon kowa da kalar tunanin sa,kafin Hajja ta katse shirun da cewa, "kar ka soma lafta masa sharri Rafeequ,na san ka nasan waye kai da shegiyar k'arya,waye bai san halin Ramadan ba,ai haka kawai bazai kawo mukulli yace bazai sake tuk'a motar ba,sai inda dalili" Jinjina kai Abbanmu yake alamun maganar Hajja ta shigeshi,Abban su Rukee ya ce "haka maganarki take Hajja,dole ma akwai dalilin ai haka kurin Ramadan bazai wannan abun ba" "Aa ku daina goyon bayan shi Nura,ku barshi yai magana ba lallai yana da gaskiya ba,kila rashin hakuri ya gwada ko?" Kamar jira kuwa ummanmu keyi ai wannan maganar ta anshe da cewa, "gara da ka fad'a da kanka cewa rashin hakurin sa ya nuna,tunda ranar har so yai yamun rashin kunya daga na ce bazai yuwu ace sai su Roohe sun bashi hakuri ba,tunda ba zaginsa sukai ba" D'ago kai yayi yana kallon ta da idanun sa masu kamar an zuba oil a ciki,kallon tuhuma da nuna baki da gaskiya tunda tasa ba haka ta fad'a ba.........."Ramadan" Abba Nura ya Kira sunan sa, ya dago cikin natsuwa yana kalonsa sannan ya amsa, "Gaya mun miya faru?..........watau baka yadda da maganata ba kenan Abban Rukee" Umma ta katse sa fad'ar hakan, cikin tsawa Abbanmu ya ce "maijidda idan kika sake magana anan ba tare da an sanyo ki ba ranki zai mummunan b'aci wallahi" Ranta ya b'aci ainun,ta hau huci kamar kasa magana na cinta ta kasa furta wa,don duk abunta tana tsoron fushin sa, Hajja tayi k'uta tana cewa, "duk iskancin mutum dai akwai na sama dashi,kuma wallahi ka k'i yin abunda akeso kaga karyar iya shege" Mami ta tab'e baki bata ce komi ba,su dukan kowa ta ciki na ciki ne kawai,Abba Nura ya sake tambayar Yah Ramadan yadda abun ya faru, Kanshi k'asa cikin wannan munafukar muryar tashi yake cewa, "ya riga ya wuce Abba,abar duk wani tone-tone daman Abba Taheer ne ya yanke Hukuncin cewa bazan sake kaisu Ruk'ayya school ba saboda sunyi laifi yace har sai sun bada hkr,to shine dai kamar abun baima Umma dad'i ba ta wasu maganganu da raina ya sosu har na gaza hakuri na aje mata key d'in nace taba Abba hkr ga key d'in motarsa nan" Abba Habibu ya ce "kaji ko?kaji dai ai nagaya maku rashin hakuri ya nuna,miye anan to har da zaka aje mukulli?koma miye ta fad'a ai tana sama da kai...........yi hakuri Yaya na katse ka,amma Ramadan bai laifi ba anan duk da bai fad'i maganganun da tayi har ya hasala shi ba,nasan wallahi ba kananun maganganu bane zasu sa ya hasala,ai duk mai zuciya ba zai juri a wulakanta shi ba,kuma ni ya mun dai-dai wallahi sannan hallau hukuncina akan su Roohe yana nan daram,wallahi muddin basu bashi hkr ya ya hakura ba,daga nan har su kammala secondary d'insu a k'afa za suje,in ba zasuje a k'afa ba kuma saidai su fasa zuwa makarantar" "Kash!ban so kai rantse ba, Taheer kullin ina gaya maka su Roohe yara ne,kwatanci da nasiha suke buk'ata ba zafin rai ba,kuma Ramadan yayansu ne da baka shiga cikin maganar nan ba,nasan ma shi bai k'ullace su ba kaine ka zafafa abun.........ai da yake kaine zai yadda,in wani ne ya isa ya furta cewa laifin bai kai laifi ba" Mami ta furta cikin fushi sosai,wani kallo da Abba Nura ya auna mata saida tayi dana sanin maganar da tayi, a kausashe fiye da yadda Abbanmu yayi yake ce mata, "waya sanyo ki anan?Safiya ki fita idona wallahi na kusa sallamarki saboda wannan d'abi'ar" "Yanzu Abban Rukee ni zaka ce zaka sallama akan..........idan kika sa ke kika sake wata magana anan na rantse da Allah saikin je gidanku" Ya sake fad'a cikin tsananin fushi wanda muka jima bamuga irin sa tattare dashi ba, Abba Habibu ya ce "Auzubillahi minna shaid'anir rajim,Nura miye haka?miyai zafi karka soma karka sake furta mummunan kalami irin wannan,agaban yaran zaka ringa wannan maganar" Ransa sosai ya b'aci har Huci yake yake cewa, "saboda raini da iskanci zata sanya baki kana magana yaya?wane irin abune suke son yi haka?kullin basa son a zauna lafiya Maijidda da Safiya,wallahi yaya duk wacce zata raina ka ta nemi wulakanta ka ba dai agidan nan ba,don haka in ana son zaman lafiya a girmamaka akuma mutuntaka,wannan shine" Jinjina kai kurin Abbanmu keyi,alamun hakaan yai masa dai-dai,Hajja ta ce "Allah yai maku albarka,ashe dai kun cika y'an halak wad'anda basa mance alkairi,ina goyon bayanku akan wannan hukuncin duk wacce ta nemi raina HABIBU ta wulakanta shi babu girmamawa wallahi saitabar gidan nan,don da bazar Habibun kuke taka rawa,in bacin Habibun bana jin d'ayan ku zata iya kallon Nura ko Taheer tace tana so zata aureshi,don haka duk wacce bata kiyaye ba k'ofa abud'e take" Hankulan mu sunyi tashin gauron zabi,don irin haka bata cika faruwa ba mudai bamu saba gani ba,yawan cinmu kuka muke Rukee ta rarrafa gaban Yah Ramadan tana cewa "Don girman Allah Yah Ramadan ka ya kuri,ba zamu sake ba in sha Allahu" Tana ta kuka take maganar, kamar bazai magana ba ya ce "ya wuce Ruk'ayya na yafe miki" Wani abune ya k'ulle mun ga mak'oshi,kenan ni ma saina bashi hkr wata tsanarsa ta dirar mun a zuciyata,saboda duk shine ummul aba isin komi har ake kirarin za'a kora uwayen mu gidajen su saboda su,naji duk duniya ba wad'anda na tsana sama dasu Abba Habibu da iyalin sa.......kallon da Abba ke mun yasa na tashi naje daga kusa dashi muryata da kuka na ce, "I'm sorry" A ginshire ya ansa da cewa, "it's ok" Sallamarmu akai su iyayen suka zauna tattaunawa,har iyayen mata muka fito tare dasu,muna fitowa umma ta fashe da kuka gabanmu wanda ya tada mana hankali, ta ce mana "wallahi duk wanda yai huld'd'a da iyalin Habibu ban yafe masa ba nono na daya sha" Ta shige dakinta Mami kam ta kasa magana,sai hawa numfashin ta yake Anti sha'awa ta jata suka wuce bangaren su,haka muka kwana nida Rukee kowa rai babu dad'i saboda abunda ya faru. Mom Muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....8 Duk yadda Abba yai mana nasiha da kashe di akan su Yah Ramadan mun kasa masa biyayya muyi abunda yake so saboda furucin Umma,kuma muna kishin ta sosai don a ganin mu saboda su duk Abba ke mata abun da yake mata. Yah Ramadan ya koma kai mu school kamar baya,amma ko hak'orin mu baya gani gaisuwar ma mun daina sadda zai fito saidai ya same mu cikin mota,Haka zamu isa baka jin ko tarin mu wanda shi banga alamar hakan yana damun sa ba,daman kuma ko da can hakan muke dashi,ummi ke zaka gaba Nida Rukee da Najeeba a baya wadda Ban san ya akai ta dawo tana binmu ba,kila Abba ne yai mata fad'a. Wannan ya wuce ba kuma don an samu dai-daito ba anyi shiru ne saboda kashedin su Abbanmu,amma badan mun yadda zamu bisu Mama da ahalinta ba,kuma bamu da gamsashiyar hujja da zamu bada da zamu ce ba zamuyi zumunci dasu ba,kawai dai munbi ne tunda ra'a'ayin uwayenmu ne. Hutun yah Rafeeq yazo ya k'ara ya soma shirin koma wa,har sannan babu wata alak'a mai dad'i tsakanin mu,ko zamu bi ta k'ofar allura baya tanka mun,nice dai har yau ban fasa gaidashi ba rannan dana kaishi bango ya hayyak'o mun kamar zai cinyeni d'aya, a falon mami ne muna kallo shi kuma ya dawo daga ball ya shiga yai wanka ya fito ya zauna yana cema Rukee ta kawo masa black tea, tatashi kenan daga ni sai shi na ce "Yah Rafeeq ina wuni?" Zaka rantse ma baisan sani a wajen ba,banyi fushi ba na sake cewa "Yah Rafeeq ina fa maka magana" Wani k'azamin kallo ya watsa min dayai mun ciwo, raina ya sosu na ce "in bacin Abba yace kar nayi gaba dakai wallah.............Roohe kike ko ubanwa?wallahi tallahi kika sake mun magana saina b'allaki,saidai Abban ya kashe ni,ke wace irin mayya ce ne iye?bana son gaisuwar dole ne?" Sai kwallah sharrrrrr suka zubo mun, bakin ciki ya cika ni zan fara kuka kenan yaja dogon tsaki, "sakarai kawai banda kuka ba ubanda kika iya,tashi kiban wajen kafin nayi ball dake.............bazan tashi ba,nace bazan tashin ba!Yah Rafeeq ka isheni ka fitineni, ai ba kai ka kawoni nan ba,kuma wallahi in baka b'allani ba baka haihu ba,kai d'in mi?mi akai akayi ka,don kawai kaga ina yin shiru ina kyaleka zaka ringa cimun fuska,to daga yau na daina kyaleka in kace mun kulle sai na ce maka chass,ai ba tsoron ka nake ba fa, ba kuma bala'in ne ban iya ba" Mami ta fito da sauri Rukee ma haka sukai tsaye cirko cirko,suna kallona da mamakin yau nice nake masifa haka, shi kanshi daska rewa yayi daga inda yake zaune,sannan maganganuna sun sake fusata shi ainun,don ga fuskar nan tayi jajir da idonsa tashi yayi yana nuna kanshi da yatsa manuniya, "ni kike cewa ban haifu ba?kuma in nace kulle sai kince chass?" Numfashina har wani d'agawa yake saboda masifar dake cikina, na ce "ehy haka na fad'a,inhar kaji haushi ka daina abunda kake...........kauuuuuu kakeji ba zato ya dauke ni da wani ba hagon mari saida na zube k'asa saboda azaba da rud'ani, "Rafeeq!!!" Mami ta daka masa tsawa sosai,tana nufo ni da sauri saboda wani rikitaccen kuka dana saka daya kid'ima su,kuka nake sosai da sosai wanda ba zan iya cewa tsayin rayuwaa ta ba nayi sa ko aa, zallar bakin ciki ne da tsanar sa araina suka kara zugani a kukan, Rukee na lallashina Mami nayi kaina cikin cinyoyina ina ta kukan,har sannan tsaye yake don ban daina jin k'amshin sa a inda nake ba,saida na fara gajiya wa da kukan na tashi zan tafi bangaren mu,Mami ta rik'o ni. Ta ce "zo Roohe,babu inda zakije sai kin rama,a yau duk wani girma da yake dashi zai tashi abanza, tunda kai ba mutumin kirki bane Rafeeq, ashe duk irin tausayin ka na banza ne,ka bud'e wannan katakon hannun ka sauke akan fuskar yarinyar mace kamar Roohe,kaje kai mata illa ta kasa auruwa?kai ne zaka aureta ko yaya?ashe baka da imani ban saniba.............kamar almara muka ga ya zube gaban mami yana cewa, "kiyi hakuri don girman Allah Mami kiyi shiru kar aji,na rantse da Allah bana cikin hayyacina,sadda Hannuna ya kai ga fuskarta ban sani ba,raina ne ya hangula" "Dalla tashi ban waje,b'acin rai Hauka ne?to tunda har baka ga idona ba,baka ga kimar maganar ubanka ba,zanje na shaida masa inyaso sai yasan irin yadda zai dakai........." Aguje ya rufe k'ofar yana durk'ushe kan guiwar sa,daka kallin fuskar sa zaka ga zallar tashin hankali,gefe guda kuma kukan da ta ke yana sake tafarfasa mashi zuciya,da jefashi cikin mummunan tashin hankali. "Rukee zoki dauko mun wayata,in kirashi tunda ya tare k'ofar" Aiko ta ruga dakin mamin saboda itama yau yayansu ya kaita kwano,kafin Rukee ta kawo wayar ya kama k'afar mamin cikin magiya da rikicewa, "Kiyi man rai Mami,karki gaya mashi don girman Allah wallahi zan bata hakuri,ba kuma zan sake ba pls mami nine Rafeeq naki" Bata saurare sa ba Rukee ta kawo waya kenan tana ba Mamin,yai saurin anshewa yana sawa aljihu,jikinsa har rawa yake "ashe baki k'auna ta Rukee?shine kika je kika d'auko wayar?kenan ko korata Abba zai bai dameki ba" Fuskar ta a dame ta ce "yah Rafeeq Roohe fa ka mara,mari irin wanda k'ato namiji ya can canta ba mace irinta ba,,,,,"zan bata g Hakuri wallahi,ki yadda dani ban sane kalaman ta ne suka dimautani" Danne dariyar ta mami tayi tana cewa, "zoki kira min shi Rukee" A guje tazo zata tsalla ke shi ya damk'ota yana huci,muryar sa ta roma rawa kamar ba namiji ba duk ya susuce lokaci guda, "Rukee bakiji ba nace zan bata hakuri,Mami wallahi zan bata hakuri har sai ta hakura,karku sanar da Abba zai mun abunda zai jefani cikin masifa" Mamin ta ce "saketa to" Duk ya diririce,ya saki Rukeen yana ta sauke numfashi amma bai bar k'ofar ba, ta ce "ka bata hakuri har sai ta furta da bakinta cewa ta hakura kuma ta yafe ma,da kunnena nake son naji wannan,sannan koda wasa tsonaka ta sake had'a ka da ita ko bakar magana wallahi Rafeeq sai na gurfanar dakai wajen Abban ku,don haka gaka ga Roohe nan ka bata hakuri" Duk drama da ake inajin su ina kallon su,wani abun in bacin ina cikin wannan halin dole sai nayi dariya, to bana cikin mood d'in da zan dara, ina k'asa zaune ina ta sharar hawaye da suka kasa tsayawa, naci alwashin nida masa magana har abadan,inda yake ma bazan sake zuwa ba balle in ganshi. Mamin taja can gefe ta zauna cikin kushin,tana danna wayarta data ansa hannun sa,Rukee ma ta zauna tana kallon mu,jikinsa yai sanyi sosai ya dawo gabana yai zaman cin tuwo ya rasa ta ina zai fara,zaman sa kusa dani ya sake jefani cikin kunci kukana ya k'aru,matsowa yai sosai kusadani ya rik'o hannuwana duka yana saka Hankchif yana k'ok'arin goge mun hawayena, na kaudar da kaina ina k'ok'arin anshe hannuwana, "please" Ya fad'a da muryar da tunda nake ban sanshi da ita ba,ban yadda na kallai ba balle yasa ran zan saurareshi, yana rik'e da hannuna ya saki d'ayan, sark'esu yai waje guda yana cewa "I'm very sorry,I don't mean to hurt u..........cikin kukan na ce "bana son hkr" Matse hannun na wa ya sake yi,kamar zai fashe mun da kuka ya sake cewa, "please Roohe na fa ce bazan sake ba,wallahi daga yau mun zama favorite cousins,ba wanda zai kai mu kusanci da juna" Na daddage na b'alla masa hararar da bansan ma na iya ba,sakin hannun na wa yayi yana had'e nashi waje guda da sigar rok'o da magiya, "Don Allah,dan kaunar da kike ma Abbanki,inci darajar Abbanmu Roohe" Nai shiru wasu hawayen na silalo mun,yai saurin saka hannun sa ya tare su, "in sha Allah wad'anan hawayen sune na karshe da zaki zubar a dalilina, I promise u" Ban tanka masa ba,duk mukai shiru nida shi idonsa kawai ya zuba mun yana mun wani irin kallo,wanda ya fara shigata a hankali-a hankali,na k'i yadda na kalle shi amma kuma yana huda mun fatar jikina sosai, so nake na tashi na gudu amma banga hanyar tashin ba, "Roohe" Ya kirani da wata la'ananiyar muryar saa data jani ga kallon tsakar idonsa, zuciyata saida ta doka sau uku saboda abunda na ke gani cikin idonsa,mai makon na dauke idona sai na samu kaina da cigaba da kallon idonsa,wani abu na ratsa ni nan take,yana shiga jikina da zuciyataa da duk inda banyi tunani ba ma,muryar sa ta sake zama so cool ya ce "forgive me,I will never do it again please" Wani irin abu naji da bazaan iya misalta shi da komi ba, na dai sauke idona k'asa kurin kuma hawayen tuni sun tsaya,sake rik'e hannuna yayi sosai ya matsa kad'an, runtse idona nayi na bud'e kafin na kwace hannun na boye shi,ya sauke numfashi a hanakali ya sake cewa "bazan tashi anan ba har sai kince kiyi hkr kin yafe mun" Inaso nayi magana na kasa,wani abune ya danne mun halsheni,muryata ma bata fita sosai ko naxo maganar kasawa nake, "Roohe" Ahankali na dago na kallai,wani irin lumshe idonsa yayi yana sake sassauta murya, "I'm sorry plsssssss," Bansan na d'aga masa kaina ba da sauri,cikin jin dad'i ya waiga yana cewa, "Mami tayi hkr.........baiga mami ba baiga Rukee ba. Ya juyo yana kallona da wani irin murmushi a fuskar sa,dayai masifar fito da zahirin kyan sa, saurin maida kaina k'asa nayi inajin wani abu mai kama da kunyar sa, to miyasa suka tafi?kuma ban san tashin su ba ya akai haka? "Su mami sun tafi sun barmu" Kasa ansa shi nayi,illa sai jan yatsuna nake dana samu ya cika mun hannuna, Duk'owa yayi yana lek'o fuskata "zaki gaya ma mami kin yafe mun,kuma mun zaka favorite cousins?" Kai na d'aga masa da sauri don ya kyaleni na tafi, "to muje mu gaya mata a dakinta" Girgiza kai nayi ina fizgo maganar, "Aa,anjima ni zan gaya mata ba sai munje tare ba" "Why,tace fa in kaiki ki fad'a" Girgiza kai nayi "Aa nidai ba yanzu ba" Murmushi ya saki yana cewa, "ohk bani yatsan ki mu k'ulla kyakkyawar alak'a wadda ba wanda ya isa ya rusa mana ita," Kallon saa nayi ya d'aga mun girar sa,nai saurin kaudar dakaina ina ta luliyar yatsuna na kasa bashi, "Ayya Roohe pls mana" Ban San na turo baki na gaba ba,sai dai naji ya ce "wow u look so cute" Boye fuskata nayi cikin hannuna ina murmushin da ban shirya mashi ba,naji yana dariya kunya sosai ta kama ni,na mamesa na tashi na ruga bangarenmu na barshi anan,kan gado na fad'a inajin zuciyata na bugawa har yanzu tun sadda ta buga sau ukun nan,bata sake tsaya mun dai-dai ba. Ranar har Rukee nauyin ta na ringaji,duk son da tayi tamun maganar na hana ta damar, nai zama na a daki ko dinner da akacena fito cewa nai kaina ke ciwo,dan danan Abba yazo dakin yana tambayata miya jawo mun ciwon kan,na rasa karyar da zan nace masa ban sani ba, aiko ya kira Yah Rafeeq wai yazo ya dubani tunda yana shirin zama likita, kamar na fashe da kuka,saboda daman ai shi nake ma guje gujen,sai gashi Abba ya jajubo min shi. Ummanmu na gefena ta had'a mun coca oat mai zafi da madara,shi kuma ya shigo runtse idona nayi gam kamshin sa na ratsa hancina zuciyata ta sake dokawa, ya gaida ummanmu ta ce "ina tunanin ma ko fever ne,amma jikinta bazafi" Ya ce "kila stress ne umma karki damu,only paracitomal ma zai iya sata ta warware,amma van sani ba ko bayan ciwon kan akwai abunda ke damunta" "To gata nan tambayarta muji" Zama yayi gefen kafafuna yana kiran sunana, amsa wa nayi ban bud'e idona ba "sai mi bayan headache d'in" "Aa ba komi" Murmushi ya danne saboda ganin umma, ya ce "ok tashi kisha oat dinki saiki sha magani,zan ba rukke sai ta kawo miki" Kai na d'aga mishi,ya tashi yai ma umma saida safe, na sauke ajiyar zuciya na tashi na ansa oat din na fara sha,saida taga nasha maganin sannan tatashi tatafi,su Anti Rafeea suka shigo da Anti sha'awa suna mun sannu,sai ga Mami ita ma da Rukee jinai kamar zan tsere don kunya, daker nake ansa mata maganar har tatafi. Daga wannan ranar komi ya soma.! Mom Muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....9 A cikin kwana kin da sukai mashi saura ya koma makaranta wata irin kulawa yake bani,gashi inhar yana cikin sabon feeling to fa kowa gane mashi yake,don haka yanzun ma gidan ba wanda bai san sabuwar alak'ar mu ta kirki ba,kowa sai da yai mamaki ainun da ganin yadda Yah Rafeeq yake mun,yini yake agida duk abokan sa dake sintirin neman sa,daya fita bai jima wa yake dawowa,har na soma rikicewa ta fannin karatun mu,gashi mun kusa fara weac. a wajena abun bak'one don na kasa sakin jiki dashi, zai ta mun magana yana jana da fira daker nake bashi ansa,duk inda zanje yana biye damu har na gaji da magiyar ya daina binmu,makaranta ma in bacin baiga fuska ba shi zai kaimu,to wanda ke kaimun baiga fuskar tun karar sa da wata magana ba,amma kullin safiya saiya rakoni har bakin mota ba zai tafi ba har sai yaga tafiyar mu sannan. Rannan Rukee ta ce "da alamun fa kin susuta mun yayana,irin wannan rawar k'afa haka?" Murmushi kawai nayi don ban san me zan ce mata ba,ummi da Najeeba dai ba wanda yace k'ala balle kuma uban yan fad'in ran duniya. Mun soma weac da kwana d'aya yah rafeeq ya tafi,ban san cewa na soma kamu wa da irin halin daya ke ciki ba sai wannan ranar, duk yadda nake basarwa abun ya ci tura,nashige toilet d'in dakin mu na kama kukan da ban sa dame xan kira shi ba,na dauka ya tafi na fito kenan sai gashi ya shigo. "Shine Kika b'oye don kawai kar ki rakani" Idonsa yai rau rau kamar zai kukan shima,na gama gane akaina Yah Rafeeq baida wata jarumta irinta namiji, ban yadda na kallai ba na ce "Aa ba haka bane" Jingina yayi da kofa yana crossing legs dinsa yana kallona,jinai wasu hawayen sun sake tahowa nai saurin juya baya ina gogewa, nama rasa abun da zanyi, jinai yace "kibar goge hawayen ki a b'oye,ki jiyo ki fuskan ceni nine ya dace na share miki su" Makale kafad'a na nayi inajin kukan zai k'wace mun, ya tako zuwa bayana ya riko hannuna cikin wata irin murya marar amo, "zo muje kimun rakiya airport,mu sake yin bankwanan sosai" (Na manta ban Sanar daku inda yake karatun ba, yana india wata scholarship Abbanmu ya samar mashi) Kasa mashi musu nayi,na dauki hijab d'ina muka fito,anan main falon gidan gaba d'aya kowa na nan har su Abbanmu,kasancewar weekend ne ba aiki ba school, Mami tana ganin mu tayi murmushi don zan iya cewa tafi kowa shiga farin cikin alakarmu dashi, Abba Nura ya ce "saida ka fiddo ta kenan," Kaina k'asa shi kuma ya sosa kai ya ce "Abba ai bazan tafi bamuyi bankwana ba" Murmushi kawai yayi Anti Rafeea ta ce "duk bankwanan da akai dazun da sauran kwanaki bai yi ba kenan" Harara ya sakar mata,yana cewa "kewai miye naki aciki?" Anti sha'awa ta ce, "ai kai baka son gaskiya,ni wai mike tsakanin ku ne farat d'aya ka zama haka..........."mami ki shiga tsakanin mu da wannan yarinyar,nidai ai ba sa'anta bane da zata ringa gaya mun haka" Dariya duk aka kama yi mashi,saboda angane dai borin kunya yake bai son a gane miyake boyewa, "Bari muje muyi ma Hajja sallama" Yajani muka tafi nidai na kasa cewa uffan,jikina duk amace yake ainun,bamu jima sosai ba wajen Hajja muka fito Abbanmu ya ce muje bangaren Abba Habibu yai masu bankwana,Yah Ramadan xai kaishi Airport d'in. Nida shi duk bamuji dad'in maganar ba,amma bamu isa muce aa ba,koda muka je bangaren nasu Fuska ba annuri yake musu sallama,su kam basu damu ba saima nuna jin dad'in su suke yazo musu sallama, Mama tatashi ta shiga ciki ta fito da wata leda tana cewa, "ga wannan Rafeeq,kila yai maka amfani Rahma ta sani nayi mata shi zasu zo jibi", donuts ne sutu-sutu mai wata madara-madara a ciki,sai dambun kifi mai yawa. Hakan bai sa ya saki ransa ba ya ansa yana cewa, "Angode" Bata damu da yadda ya ansa ba karsashi da nuna jin dad'i ba,ta rakomu har wajen mota inda sauran yan gidan ke tsaye,Abba Habibu yana ta mishi nasiha ya kula da kanshi ya rik'e ibada ya kuma tsaya yayi karatun sa hankali kwance, "karatun ka na son natsuwa da kwanciyar hankali,Allah ya taimakeka kaji yarona" "Amin" kawai yace ni har na soma jin kunya ma,don ba dad'i irin abunda yake musu. Daga ni sai shi sai Yah Ramadan,duk baya muka zauna shi kuma yana tuk'i,muka dauki hanya sai Airport,tunda muka tafi munyi shiru yak'i sakin hannuna kamar zan b'ace mashi, saida mukai nisa da gida sannan cikin sanyin murya ya ke cewa kamar mai baya son aji, "Wane irin alk'awari zaki mun kafin in dawo?" Kaina k'asa na kasa cewa komi,ya sake matsoni yana cewa "kinji Rooh" Har raina sunan daya kira ni dashi ya mun dad'i, daker na iya cewa cikin siririyar muryata "ni ban san wane irin alk'awari kake nufi ba" Iska ya busar yana cewa, "badan tafiyar nan ta zamar mun dole ba,wallahi Rooh ba inda zani inbarki,ji nake kamar zam bar duka rayuwata anan" Saurin kallon sa nayi yajin jina mun kai, "sosai ma" Na rausayar da kaina cikin rashin abun cewa, ya katseni da fad'in "in so ki kasance tare dani a zuciyarki har inje in dawo,sannan inaso ki nisanci ko wane namiji don duk duniya ba wanda zan iya barma ke,nasan kin gane mi nake nufi please Rooh,kimun wannan alfamar zan jima ban dawo ba amma saboda ke zan ringa zuwa duk bayan shekara daya da rabi in ganki in koma,karki ba wani dama akanki koda kun gama weac kima Abba magana kina son nursing,kinga ni dr ke kuma nurse ko had'in bai miki ba?" Murmushin na saki ina kaudar da fuskata,watau duk kewaye kewayen sa dai so yake yace sona yake kuma duniyar nan baida burin auren kowa saini, "yes ban da wani buri a rayuwata illa na mallake ki,ban san taya zan sanar dake ba amma cikin raina kece kawai muradina,duk wani abu da nake miki a baya ba har raina bake yi ba,kawai inayi ne donki maido hankalinki kaina,ganin zan tafka kuskuren da har Abada bazan iya gyarawa ba yasa na dawo hanya, ina fatan babu wani abu da zai mun katanga da cikar burina kinji my Rooh" B'oye fuskata nayi saboda wata irin kunyar sa nakeji matsananciya, ga wata irin kewa da nakejin tana ratsani ko ya zan kasance babu shi a cikin gidan?har muka iso airport ban iya ce masa komi ba,shine yake ta kokarin ganin ya fayyace mun abunda ke cikin ransa,koda yai parking saiya ki fita ya dai bud'e kofar inda yake zaune ya fidda kafarsa guda yana danna wayarsa. Dogon tsaki Yah Rafeeq yaja ganin abunda Yah Ramadan d'in yayi,ya ce mun "kar ki dauka bana nan,ki dauka always ina gida kuma zaki ganni,zan ma Mami magana a siya miki waya I promise u zamu ringa video call at least twice par day, yayi miki hakan?" Na d'aga kaina kurin saboda jinake zan kuka, har na kasa controlling hawayen suka ringa silalowa, muryar na rawa na ce "ka ce zaka ringa zuwa after one year" Murmushi ya saki mai cike da tsananin bege da soyayya, ya rik'e hannuna sosai ya ce "in sha Allah,kodan farin cikin ki zan takura Abba har sai nazo" Ya shiga goge mun hawayen da Hanky d'insa, yana cewa "oya inhar ba kina so na tafi cikin damuwa ba give me smile" Ban san sadda na sakar mashi murmushin ba,yaja iska yana cewa "u are very beautiful Rooh,ban tab'a fad'a miki ba yau na fad'a,kina da kyau mai rud'a duk wani namiji,saidai wanda yasan daman bazai same ki ba,ki kula mun da kanki kinji ko" Daker muka rabu saida yaji ana sanarwar neman su sannan ya bud'e motar ya fita yana d'aga mun hannu,kuka ya kwace mun don alokacin ji nake duk wani jin dad'i na ya kare tunda bai nan,haka muka kamo hanya nida shi kamar sabbin kurame,har gara ni inata shashshekar kukana,shi kam banda tuk'i ba abunda yake kamar daman tukin aka halliceshi yazo duniya yayi,ni ban tab'a ganin mutum irin sa ba kwata-kwata rayuwar sa babu armashi,ba walwala babu farin ciki sai fad'in rai da girman kan tsiya, da tsabar k'azanta wannan dalilin ke sake samun jin tsanar sa araina,bana son namiji babu gayu babu kula dakai,.........ban san sadda naja wani dogon tsaki ba,ai ban idasa jaan shi ba naji wani uban burki ya taka,har kaina na bugar kujerar gaba,a mutuk'ar fusace naga ya bud'e bayan motar inda nake cikin zafin nama ya finciko ni, muryar sa ta wani irin disashe cike da b'acin rai matsananci ya ce "uban wa kike ma tsaki?" Jinai zan saki fitsari a inda nake,tunda nake rayuwata a gidan magana tafatar baki bata tab'a had'amu ba in banda gaisuwa sai yau,cikin tsananin tashin hankalin dana ganshi a ciki yasa na rud'e don ban tab'a jin tsawar data gigita tunanina ba irin yau,idon sa har tsoro ya bani kamar yai shaye-shaye ya bugu,sun wani rikid'e sun juye ban san ina cewa "Aa....Aa ni.....ni banyi tsaki.....banyi maka tsaki b...........mahaukaci kika d'aukan komi?ashe zaki kwana nan" Muryata kerma kurin take na soma girgiza kai, cikin tashin hankali "ka yarda dani ba dakai nake ba,ban san nayi ba don girman Allah ka maidani gida,wallahi bazan sake maka tsaki ba,kuma ba dakai nake ba kubce mun yayi na rantse da Allah Yah Ramadan" Babu sassauci ko k'adan a fuskar sa,ban tab'a ganin tashin hankali irin wannan ba,inhar ya barni a dajin nan shikenan bani ba sauran wata rayuwar jin dad'i,yadda ake kidnapping d'inan ana kashe mutane,aini tawa ta k'are. Cikin kakkausar murya ya ce, "shiga muje, wallahi na kuma jin tarin ki saina tsaya na zubar dake anan ba abunda ya daman" Aguje na fad'a motar ina kerma, ya ce "fito dalla shiga Gaba uban waye driver ki anan?" Jikina tsuma kurin yake na zaga na shiga,sannan yaja motar muka cigaba da tafiya,mai makon gudun da yake yi da farko sai ya koma yin tafiyar kamar wanda ba shi da lfy,sikiyarin ma daker yake sarrafa shi,ni dai kamar ruwa ya cini nama kasa kallon fuskar sa,mugun tsoron sa ya dirar min tare da tsanar sa mai yawan gaske. Abun kamar wasa tafiyar ta nemi gagararsa,wani irin burki yaja yana dafe kirjinsa,da fari na dauka ko na d'an lokaci ne amma naga mutum ya bud'e murfin mota ya zube k'asa ba numfashi,wata razananniyar k'ara na fasa na fito jikina kerma kurin nake,wace irin masifa ce wanan na shiga ukuna. Jijjigashi nake ina kiran sunan sa ba alamun zai tashi,ko ina rawa yake jikina sosai kuka kurin nake,don gani nake ya mutu kawai kuma ban san wane irin bayani zan yima yan gida ba,banda waya ban ma fito da ko hanky ba ga hanyar ko kare babu,gashi rana tatafi zata fad'i la'asar tataho duk da ban duba time ba,tsabar tashin hankali fitsari naji yai mugun matsata, na fara lalubar aljihun sa naji wayar sa yar karama nai saurin daukota na saka no. Din Abbanmu,bugun farko ya dauka "ke Roohe ina kuka tsaya haka,inata neman ku ban samu lafiya kuwa.........kuka na rushe dashi sosai "Abba ya mutu,gashi nan ya zube a titi ban San Miya samai ba,kawai......kawai naga ya fad'i" "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un,bar kuka kuna ina maza gaya mun" Na soma waige waigen inda muke,na samu wata alama na gaya mashi wajen,yace gasunan zuwa yanzu na zauna gefen sa ina kukan,, "ni banga abun da ya faru ba,ko dama baka lafiya?na shiga uku ban tab'a ganin an mutu gabana ba,Allah kasa ba mutuwa yai ba. Mom Muhseen &Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....10 Cikin d'an k'ank'anin lokaci su Abba suka iso shida Abba Habibun,sai naji hankalina ya sake tashi ainun ganin yadda aka kin keme shi kamar gawa aka sa amota,su duka hankalin su a tashe yake jinake kamar zan zauce tunda nake ban tab'a ganin an mutu gabana ba,hawaye kurin nake don ba batun wani abuba ina cikin kid'ima da tashin hankali. Driver akai ma waya yazo ya dauki motar ya maida ta gida, dani suka wuce asibitin da ake kwantar damu in wani bai da lafiya anan gida,gefe guda na tsayaa inata hawaye su Abba ne keta shege da fice har aka anshe shi aka shiga dashi emergency,su ka dawo inda nake suka tsaya Abba Habibu yai shiru kanshi k'asa,duk sai naji ya ban tausayi don kuwa kowa yasan duk cikin zuriar sa ba wanda yake so kamar yah Ramadan,amma yana kokarin dannewa bai nuna ba. "Miya faru a hanyar taku har haka ta kasance?" Abbanmu ya jefeni da tambayar ina cikin wannan halin,kan in bada ansa Abba Habibu Yace "haba Taheer,tana cikin kid'ima har tuhumar ta zakai?taya zata san wani abu?" "Tare fa suke Yaya,kaga kau ai dole tana da masaniyar wani abu" Sai yai shiru bai sake cewa komi ba,Abbanmu ya sake kallona da son karin bayani,hawayena suka k'aru na soma cewa "wallahi ban san komi ba,lafiya lau muka isa airport ya sauke Yah Rafeeq,muka kamo hanya muka taho,to.....to....to......shine sai kawai naji ya taka burki,ya dafe kirji da cikinsa,sai......sai.....kurin naga ya bud'e k'ofa ya fad'i k'asa,wallahi Abba iyakar abunda ya faru kenan" Ina ta sharb'en majina,shiru bai ce mun komi ba zuwa can, sai ga Abba Nura ya iso shima cikin tashin hankalin, "Mike faruwa ne Yaya? Taheer lafiya?Hajja ta kirani tana kuka wai Ramadan yai hatsari,meeting muke dole na dauki excuse nataho" Ajiyar zuciya Abbanmu ya sauke, Abba Habibu yace "ka kwantar da hankalin ka insha Allah ba matsala" "Allah yasa" Ya fad'a yana zama bisa kujerun dake wajen, Abbanmu yake gaya mun bayanin da nai masa,inaji suna tattauna maganar da tunanin ko yana da wani ciwo ba wanda ya sani,shine ya tashi farat d'aya haka. An dauki tsawon lokaci likitan dake kanshi da nurse basu fito ba,har na gaji da tsayuwa na zauna inata masa addua bakin iyawata har raina banaa son ya mutu,koba komi d'an uwana ne na jini akwai kauna ta jini tsakanin mu,duk da ba jituwa muke ba. Cikin taimakon Allah sai gasu sun fito su Abba suka tare shi da neman ba'asin jikin nashi, yace su isa office hadda ni aka bishi don son jin meke damunsa da ya sashi wannan halin, "Karku tashi hankalin ku ya samu,yana bacci ne a halin yanzu amma ulcer yai mishi mugun kamu sosai,don gaskiya sai ankula da abincin sa yana zama da yunwa,kuma itace babbar illa ga mai irin wannan ciwon,in aka kiyaye komi zai zama lfiya lau,in sha Allah zuwa gobe kila na sallameshi in naga yana yin jikin nashi," Hankalina ya kwanta na dawo hayyacina,duk da banga gamsuwa ba afuskar iyayen nawa,bama kamar Abba Habibun duk da bai furta ba amma ga damuwa nan sosai akan fuskar sa, shiga mukai inda yake muka duba shi yana ta bacci ga drip na shiga jikinsa,lokaci d'aya har ya rame a fuska. Nan muka bar Abbanmu nida Abba Habibu da Abba muka koma gida,da ace da kara da zumunci Ummanmu ko mami wani xai zo ya zauna dashi,ba dole sai Mama ba to babu kod'aya shiyasa dubiyar ma saida su Abba sukai masu jan ido sannan suka zo,shima a ginshire sukai masa yajiki,da yake shima gwanine uffan bai tofa musu ba. Inaji maman na mishi magana, "Ramadan ana maka sannu baka ansawa?" Saima ya rufe idanun sa kamar baiji ba,aiko suka kama surfa masifa da muka dawo gida,nidai uffan bance ba tunda bai mutu ba ai da sauk'i, na cigaba da hidimata. Ammin kausar sun sauka Abuja kwatsam,watau Anti Rahma wadda Yah Ramadan ke bima wa,duk halin ko inkular da muke da ita bai hana tayo mana tsaraba ba,mu duka yan matan har su Anti Rafeeq da Anti Sha'awa,sannan tabi uwayen mu har d'akunan su ta gaidasu,bata damu da shan murr da ko inkular da suke da ita ba,mace ce mai kirki duk abuna dole na fad'i gaskiya,ta biyo halin uwarta duk abunda zakai mata na sharri bata tab'a maida maka da sharrin nan,saidai Alkairi,kuma indai zata zo to hidima take yoma su Abbanmu sosai,dankalin turawa ne doyace manja ne da su fruits,jibgi guda haka take kawowa. Indai tazo to kowa sai ya gane,mace ce mai alkairi ga kowa don a wajena tafiye mun Yah Ramadan da sauran yan uwansa,su kam ai yan iska ne miskilan banza da wofi. Ita dasu kausar d'in suka zo kasancewar sun samu hutu acan kebbi inda take aure,ba laifi mijin nata yana samu d'an kasuwa ne ita kuma tana aiki da wata makaranta secondary dake cikin garin kebbin,Ammin kausar duk gidanmu ba mace mai kirkinta,duk hassadarka dole zaka yaba mata da irin son zumuncinta,don zan iya cewa halin su Abbanmu ta dauko na son zumunci da yan uwa,duk safiya in har tazo to har falon Abba zataje su gaisa susha fira duk yadda umma ke had'e rai tana shan kunu bai dame ta ba,haka Mami ma duk shak'a shak'enta bai damu Ammin kausar ba,su gama firar su tatashi abunta. Saidai bata daukar raini ko kad'an,zata sake maka sosai amma bata yadda da raini ba ko iskanci,tsaf zata ci ubanka a zauna lafiya,shiyasa muke shayinta ainun bata daukar wargi,har gara Yah Ramadan zai nuna baisan kana yi ba,amma ita kam nan take zata gurjeka. Wannan kenan.......... An sallami Yah Ramadan daga Asibiti wanda saida ya kwana uku sab'anin dayan da Dr yace zaiyyi,ya warware kamar bai ba haka nan nima na share komi ya wuce kamar ba ayin ba,ba ruwan sa da sabgar kowa haka muma ba ruwan mu da sabgarsa da ta yan uwansa,in baa Abba Nura daya sanya doka ba don dole kowa yaje sashen Abba Habibu ya gaida su mama in gari ya waye,to inba hakan ba babu mai shiga huld'arsu,sai fa Kausar da ummi da suka jone kamar wasu k'awaye,duk fad'an ummanmu da zage-zagen ta ta saka musu ido,saboda ummin taki bata hadin kai hadda kukanta cewa zata gaya ma Abba,umma ranta ya b'aci sosai ta ce "watau har wuyanki yayi gwab'in hakan ko ummi?saboda wad'ancan matsiyatan zakice zaki had'ani da ubanki?to Allah ya baki sa'a" Daga nan bata sake mata magana ko hanata huld'a da Kausar ba,nida Anty Rafeea dai kadaran kadahan,har gara ma ita don ni gaskiya bazan b'oye ba bana yinsu haushin su nakeji,yadda sun hana ummanmu da Abba zaman lafiya inhar suka samu sab'ani to akan su Mama da Abba Habibu ne taya zanji ina son su? Bangarena da Yah Rafeeq kuwa ba a magana don kamar yadda yace in dauka yana gida hakan ce take faruwa,always muna tare a waya wadda Abba ya siya mana nida Rukee,tare da kwakkwaran warning,ranar ban iya bacci ba kusan raba dare mukai muna magana dashi,jina nake cikin wata sabuwar duniya wadda ban tab'a shigarta ba,wata irin Soyayya ce mai ratsa dukkan zuciya da gangar jiki muke ma juna,son juna muke kamar Allah don juna ya halicce mu,kulawa muke da juna ainun walwalata tak'aru sosai hakaa fara'ata da maganata,ya zamana inhar ina gida to bakin kowa ma bazai huta ba,wani irin farin ciki nake samu dagaa Yah Rafeeq a yadda muke ji da juna ko k'uda bama so ya shiga tsakanin mu,a hankali a hankali gida aka fara fahimtar halin da muke ciki,wanda wannan abun ba wanda yakai su Ummanmu da Mami jin dad'in shi,har Rannan Anti Rafeea ta ce ma ummanmu. "Umma na dauka fad'a zaki ma Roohe akan turb'ar da take son d'ora kanta tun yanzu,ko ni da nake cikin shekara ta biyu a jami'a Abba bai bani damar yin saurayi ba balle Roohe da ke zana weac,a ganina ki dakatar da ita kafin abun ya shafeki in Abba yaji" Ina gefe ina karatun neco da muka kusa gama wa,time to time ina chat da Yah Rafeeq, raina ya sosu sosai da maganarta ina jiran Umma tace wani abu kafin ni ince, "Ai Rafeeq d'an cikin gida ne Rafeea,sannan d'an uwanta na jini yadda ba za aima Roohe Aure yanzu ba shima babu mai yi masa Aure sai ya kammala karatun sa ya samu aikin yi,kinga kenan zasu iya jiran juna har sadda ya dace suyi auren,sannan dukan su idonmu akaan su sab'anin wani na waje da ba ganin sa zamu ba musan abunda ke faruwa,ki kyalesu su so junan su ni abun yayi mun,daman kullin burin mu kenan nida Safiya Allah ya had'a kansu to gashi kuma,don haka kiyi musu Addua" Bata ji dad'in maganar ba Amma bata isa sake cewa komi ba akai,jin hakan da umma ta fada sai bance komi ba,na tashi na bar falon na wuce dakin mu sai eleven na gama karatun,muka dasa video call dashi har Rukee ta shigo. "Allah dai ya sassauta muku wannan k'unatar junan,haba ko gajiya bakwayi" Harara na wurga mata na ce masa, cikin shagwab'a "Yah kayi ma qanwarka magana,nidai yanxu ba tsarar ta bace ato" Daga inda Rukeen take ta hangame baki tana kallon,shi kuma ya ce mata "Ruk'ayya zamu yi mummunan sab'awa dake,ki fita idona Allah ko baki saj Antyn ki bace yanzu"? Nai mata gwalo ina fari da idona, ta ce "Sorry Yah" "Sorry for your self" Ficewa tayi don naga ranta ya b'aci,ni kuma ba dan haka nayi ba nasan zamu shirya,na cigaba da video call d'ina sai d'ayan dare muka rabu,asuba nayi mukai waya dashi sai six muka rabu saboda shirin makaranta da zanyi,shi kuma yana da aji karfe bakwai zai test. Sallama nayi cikin main falon na Abba Habibu,babu kowa tsit kakeji sai k'amshin turaren wuta dake tashi a boner,cikin shirina makaranta uniform ne jikina sun sha guga sosai, don kullin sai munyi wanki da guga saboda karma a raina mu,falon Mama nayi ma tsinke don nasan duk suna can,ba ka cika samun su a babban falon ba inba dare bane,har na d'ora hannuna akan k'ofar naji maganganun su,Mama ke cewa "nidai inhar na isa dake Rahma kar ki sake ki fara tunkarar wani da wannan maganar,ba ruwanki naki ido ne ance abunda ba ruwanka yafi dad'in kallo,inma kinje kin tofa wata magana takice zatai zafi,ni duk abunda zai kawi cecekuce bana so tunda dai ga yadda mutanan nan suka dauke mu" "Yawwa Mama gara hakan,Allah ko Ammi ki fita maganar nan inba ke bama wallahi mudai nan babu mai zuwa yayi ta,har kuwa Yah Ramadan" Cewar Najeeba da alama breakfast take a sadda take maganar, Anti Rahma ta ce "Mama ni bana son irin wannan wallahi,ai na dauka mu da muke manya mun isa mu fad'a aji?taya za'a zuba ido yarinya kamar Roohe ace tana soyayya mai zafi irin wannan,kuma ma ba aure aka tashi yi mata ba,sannan shi kanshi yaron ba aure ne ke gabansa ba karatune saiya gama ya samu aabunyi kafin nan,ai su Rafeea ne ya dace ace suna wannan soyayyar suma da sunan aure za'ai next" "Nidai na haneki,tunda dai iyayen maza ba wanda ya sani kifita maganar nan,inma sun sani su zasu yanke hukunci bake ba" "Shikenan Mama nayi shiru tunda bakyaso nai maganar" Jinjina kai kurin nayi watau duk akaina ake wannan muk'abalar,uhmm walahi ko sama da k'asa zata had'e bazan rabu da Yah Rafeeq ba,naja tsaki na tura k'ofar a hankali tare da sallama, Duk suka ansa ni kuma fuska babu walwala a cinkushe na gaida Mamar, "lafiya lau Roohe har an shirya kenan?" "Ehy" "Ammi ina kwana,daman Abba yace yazo mutafi time yana wuce wa" Yadda nai maganar zaka d'auka wanda akace yazo d'in baya wajen,amma ban kalli inda yake ba balle na tanka masa,Ammin ce ta ce "lafiya lau Roohee y'an mata,amma ai naga bani ce zan kai kun ba ko?sannan kila kin san sunan sa don haka kije ki nemo shi inda yake saiki isar da sak'on naki" Tayi maganar ne cikin sakin fuska,amma kuma cikin maganar akwai bacin rai aciki,kamar zan ja tsaki sai na fasa nai shiru bance komi ba,kuma ban tafi ba na kuma kasa yin abunda ta ce,tunda nufinta inyi masa magana da bakina..........."Kinga jeki abunki gaya nan zuwa" "Aa MAMA karki shiga maganar nan don Allah,ki kyale ni da ita kawai" Sai naji kwalla ta cika idona saboda bacin rai,mamar bata sake magana ba ta kyale mu wani k'ullutu yazo mun wuya bakina na rawa na ce, "Kazo ka kaimu inji Abba time na wuce wa" Da rawar murya nayi maganar wadda kiris nake jira na fashe da kuka,kamar ma baya wajen nayi maganar mama ta sake cewa "Ramadan kanaji ai" Uffan baice ba Ammin ce ta sake cewa, "kila ba a rad'a masa suna ba,kila duk gidan nan shine wanda baida suna............"Rahma!" "Aa Mama ki bari kawai" Ta sake katse mamar da fadin hakan,hawaye suka ringa silalo mun na bakin ciki labbana na rawa na ce "Yah Ramadan Abba yana........sai kuka ya kwace mun na fita aguje ina kukan sosai don bakin ciki kamar zai kasheni. "Miyasa kike haka Mama?bayan ni duk gidan nan sama yake dasu,akan ke ba zasu bashi girma ba?sai ki bada goyon bayan a raina shi?kaima hadda kai daka zuba ido kana kyale duk ubanda yai maka iskanci,har nawa Roohee take da zata kasa risina ma Ramadan,?sanyin halinka yai yawa wallahi ni bazan dauki wannan abun ba" Ya gama kalacin sa ya mik'e ya ce, "Na tafi Mama,daga can zan wuce wurin Abulkhair kila yau zan fara aikin nan" Mamar ta ce, "Ma sha Allah,ubangiji yasa albarka ya kuma tsare ka ya bada sa'a sai a rik'e amana duk da bana jin ka RAMADAN saidai inyi maka tuni" Ammin Kausar ta ce "wane aiki ne haka Ramadan?" D'an murmushi yayi wanda yana jima wa baiyi ba,sai ya kara masa wani irin kyau sosai yace "mama tai miki bayani,Najee muje ko" Yai gaba ita kuma ta ruga ta sanyo hijab d'in kayanta Uniform iyakar guiwar hannu take tsaya musu,saboda rigunan har guiwa suke,bayan tafiyar Ramadan Ammin kausar Ta ce "Wane irin aiki ne haka mama,ni da ina can nida Baban yara muna kokarin bud'e masa boutique yafara dashi,don har ya tura kudin kayan shi dubai" "Nidai Addua nake masa kullin,duk inda arzikin sa yake Allah ya kaishi can,ya kuma zab'a masa mafi alkairi saboda zaman sa haka yana damuna,shiba ga koma wa makaranta ba shiba ga wani aiki ba,kina gani karatun ma daker aka gama Rahma,ki barsa yaje nan d'in in munga ana samun wani abu ba sai yatafi kebbin ba,in kuma sama-sama ne sai ya tafi Allah ya kiyaye" Tana maganar ne duk rauni da damuwa sun bayyana tattare da ita, Ammin kanta duk damuwa ta nuna a fuskarta, taja ajiyar zuciya cikin sanyin jiki ta ce "Abun nan yana bani mamaki Mama,duk cikin gidannan bana jin ko Roohee da Rafeeq zasu nuna ma Ramadan kwalwa da basira,kina gani duk abunda ya shigema Abban yara duhu kan kasuwancin sa shine yake bude masa komi,kina gani duk semester baida c.o ba a tab'a kama shi da wani abu na rashin kokari ba,amma kuma akai ta maida shi baya,kullin abun nan yana raina" "Bakomi Rahma,jarabawa ce kowa da kalar tashi in sha Allah komi zai wuce" "Allah yasa,Allah ya nuna mana lokacin lafiya" "Amin" ********* Da Abba mukai karo na fito da gudu ina wannan kukan bakin cikin,suna tare da umma hankalin su ya tashi ya rik'oni yana tambayata ko lafiya, "Minene Roohee?lafiyarki kalau,daga ina kike haka?kiyi shiru kimun bayani mana,ina shashsheka da jan numfashi daker nake maganar,umma ta rungumeni tana shafa kaina. Falo muka zauna tare dasu nan main falon mu,umma ke cewa "nasha gaya maka mutanan nan ba kaunar mu suke ba,karma ace Roohee kamar su kunna wuta su jefata ciki saboda ganin yadda Allah ya kyautata halittarta,bayan haka kuma kafi sonta kafi yimata hidima fiye da kowa,shiyasa suka kafa mata k'ahon zuk'a to gaskiya ni nagaji idan ba zaka sama mana wani gidan mu koma ba ni zan tashi nida y'ata..........y'arki kika ce?ashe da ita kika zo gidan ban sani ba?" Tai shiru bata tanka ba,nidai ina kwance kan cinyarta nai lamo,har sannan ban daina hawayen ba zuwa can ya ce mun, "Roohee" Na tashi ina ansawa murya a shak'e, "tashi kije ki kira Rukee ku wuce mota kafin ya fito,ban son koke-koke kiyi shiru ya wuce hakanan,anshi nan kud'in break dinku yau na kara muku ma" Ya zaro kudi ya kirga yana bani, "kiba Najeeba budu biyar,Rukee ma haka saiki dauki goma ke" Sai naji sanyi yadda yaketa lallashina saina sauko daga fushin,nai masa godiya na tafi sannan ya koma ga ummar,fuska ba annuri ya ce "idan kika sake furta irin wadannan maganganun gaban yarinyar nan wallahi maijidda ranki zai b'aci,ashe bakida hankali ban sani ba,wace irin dauka kike so tai musu?kina so ki dakile zumunci tsakaninta dasu?nai imanin cewa izgilanci da iya shege tai musu wanda na tabbata Rahma ba zata dauki hakan ba shiyasa tai mata haka,don haka ki kiyaye kalamin ki,kuma gida ba zan nemo ba inanan tare da yan uwana har mutuwa ta rabamu,inkinji zaki zauna bismilla in kinji baki iya zama k'ofa abud'e take kije duk inda kike so,saidai bada y'ata ba wallahi" Daidai nan muka fito ni da Rukee,tai masa godiya sannan muka wuce wajen motar,umma ranta ya b'aci sosai ta ce "ni zaka wulakanta akan yan uwanka Taheer?duk irin karamci da mutuncin da nai maka a rayuwa...........duk abunda kike k'ok'arin cewa kinyi mun baiyi rabin rabin abunda Yaya Habibu yai mana ba shida Matarsa, don haka zan iya zabarsu akanki............alamun shigowa yasa yai shiru har sadda mai shigowar yai sallama, "Ah Ramadan ne?" Inji Abban yana sakin fuskar shi sosai, Ramadan d'in calmly ya na shafa kanshi ya risina ya gaida shi,sannan ya ce "umma ina kwana" Tsaki taja tatashi fuuuu tabar wajen kamar kububuwa, binta sukai da kallo harta bace, Abban cikin jin kunya da takaici ya ce "kayi hak.......haba Abba miye na bani hakuri anan,bakomi ai ansaba" Abban yaja iska ya fesar ya ce, "Allah ya kyauta" Ramadan ya amsa da "Amin,daman yau ne zan fara zaman shagon da mukai magana dakai rannan" Abba yad'an dafe kanshi cikin damuwa, kafin ya nisa ya ce "Kayi hakuri Ramadan,Allah shine shaida ta ina bakin kokarina akan neman aikin ka,ban tab'a neman abu mai wahala irin aikin ka ba Ramadan,damar tak'i zuwa" Murmushi yai yana cewa,"bakomi Abba,ai komi lokaci gareshi" "Haka ne,Allah ya kawo mana wannan lokacin to" "Amin Abba,bari na wuce kar su makara........Ramadan!" Abban yakira shi,ya jiyo yana sauraren shi "ka kara hakuri da k'annan ka don Allah" Yana murmushi ya ce "to Abba" A haka suka rabu yazo yaja mu muka tafi,tunda muka dauki hanya banda tsaki ba abunda nake,Har muka so yin Fad'a da Najeeba abunda banmu tab'a yi va kenan,duk abunda zanyi bata saka baki kallo ma ban isheta ba,yau kila abun ne ya cika ta. Da farko Rukee ta ce "wai miye ne kika dame mu da tsoki kina bakar magana" "Kyale don Allah,ai kin san dai ba dake nake ba,ni har an isa ai gulmata uhm duk gulmar mutum kanshi zata k'are bai isa akomi ba wallahi,yana ji yana gani za'ai komi abarshi" Naita maganata ina jan tsaki can Najee ta fusata ta ce, "ke dakata kiji,na gane bada kowa kike ba sai nida Yah Ramadan,to duk iskancin da zaki kiyi da sa'anki inba haka ba wallahi zaki rasa halshen ki,don Yah ba abokin yayanki bane balle ke banza karan kad'a miya.........nan fad'a ya kaure tsakanin mu na cacarbaki,na soma masu gori kala-kala har dai Rukee saida taji ba dad'i,Najeeba ta kama kuka saboda maganganun sunyi zafi,nake ce mata. "Aikin banza da wofi,da bazar wa kuke rawar zance ci da sha da sutura da wajen kwana duk nauyin Abbanmu ne,banda kashi da tusa babu abunda kuka iya yi,har kina da bakin magana ke a wa?ai in ma ana maganar tunk'aho kidaina yi da Abbanku don kuwa babu abunda zai iya tsinana muk.............nan ne naji ya taka wani mahaukacin burki,zaka dauka hatsari zamuyi, yana yin dana ganshi radda muka raka Yah Rafeeq airport yanzu yafi lokacin, fuskar ka kamar wani dodo saboda rikicin bacin rai, yana bud'e motar ya dauke ni da wani mahaukacin mari saida naga wata wuta ta gilma mun,kafin ya sake dauke ni da wani marin duhu ya mamaye idona na wucin gadi,azabar danaji tunda nazo duniya ban tab'ajin irinta ba. Mom Muhseen &Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....11 "Duk abunda zaki kiyi mai isarki amma akul d'inki kika zagi iyayenmu,wallahi xan iya sabautaaki akan wannan!kiyi mun zan dauka kiyima kowa ma amma kashedenki da iyayenmu ba tsararrakin ki bane, shashasha ballagaza akuya" Ya salam,kwatanta irin d'acin dake cikin mak'oshina babban abune, ni kadai nasan irin ciwon da zagin sa yai mun,don marin ma bai mun ciwo irin wannan zagin ba,wani irin rikitaccen kuka yazo mun ban iya tare sa ba dole na sake shi ya fito,don idan na rik'eshi zai iya sumar dani..........anshi nan jeki hau napep ki wuce makaranta" Yaba Najee kudi ita kadai tana hawaye tace, "Aa ina dasu Ammi ta bani" "Karb'i nan ban son musu" Ta ansa ta nufi inda zata samu abun hawa, shi kuma ya jiyo kanmu Rukee tayi hucking inda take, cikin kakkausar murya da ban tab'ajin sa da ita ba ya ce "ku fito" Sosai nake kuka mai tsuma rai,ko a kwalar rigarsa don yadda yakeji ma tsaf zai iya jibgata ya huce haushin sa dabai ida hucewa ba, "I said get out!!" Aguje muka fito daga motar,ya zaga ya shiga mazaunin driver ya bata wuta yai tafiyarsa yabar mu tsakar hanya,kukana ya k'aru sosai nafi minty goma ina kuka sanan Rukee ta soma bani hakuri,kasa hakuri nayi saida na gaji don kaina nayi shirun,murya ta shak'e sosai ta dishe ido yai jajir kamar jini zai fito haka ma fuskar. Daker muka samu adaidaita muka tafi makaranta,sadda muka isa har an soma raba booklet daker aka barmu muka isa sit d'inmu,kowa ya ganni sai ya tambayi dalilin kunburar fuskata,don ga dukkan alamu marin da yai mun ya sabauta kumatuna,don inajin alamun sunyi fushi sosai,Rukee ce ke iya bada ansa cewar banda lafiya,muna gamawa ko tsayawa bamuyi ba muka taho gida. Wannan al'amarin ya sake dagula zumuncin cikin gidan nan,don saboda rikici har Abba Nura saida ya tura Mami gidansu,Umma kam saida Abba ya sauke mata tafinsa a kuncin ta, rigima akai sosai wadda ta sale dagula lissafin gidan,kwatsam Ya Rafeeq ya diro garin babu wanda yasan da zuwan sa, nidai nasan na gaya mashi abunda ya faru na kuma dauki picture na fuskata na tura mashi,ko alokacin muryar sa kadai zaka ji kasan cewa ransa yakai k'ololuwa wajen b'aci,ashe yana tafe bamu sani ba,Ai ko ranar Abba Nura yace bazai kwana gidan ba saiya juya. Sanda ya iso direct bangaren Abba Habibu ya nufa,akai sa'a Yah Ramadan d'in nanan kowa ma na nan har Yah Najib daya dawo hutu,Ammi bata tafi ba tana nan itama,kamar daga sama suka ganshi duk suna falo bayan sallar magariba ne lokacin, mama ce tai karambanin cewa, "Aa aha Rafeeq kaine da daren nan?saukar yaushe haka.........ke munafuka ba wajenki nazo ba,kibar wani rawar bakin karya nasan bai kai ciki ba,kinga wajen wanda nazo nan..........ya isa cikin fusata ya cakumi wuyar Yah Ramadan yana jijjigashi yana cewa, "har ka isa ka sabauta mun mata,kai waye?talaka kawai d'an talaka........cika mun riga!" Ramadan ya fad'a cikin wani irin fushi mai tsanani,ba wanda yace musu komi saboda kalaman Rafeeq sun daskarar dasu a wajen, cikin karaji yace "bazan cika ba,inka isa ka kwace da kanka mana" yaja da karfi har ya keta masa rigar, wata shak'a Ramadan ya kai masa ya buga shi da bango idonsa jajur ya kasa magana,tuni Rafeeq ya fara kakari idonsa suna tafiya luuuu kamar zai suma,Mama sa Ammin kausar sukai kansu suna kokowar rabasu ammaa sun kasa,hayaniyar su ta janyo hankalin Abba Habibun dake can falon shi,ya fito yana ganin abunda ke faruwa yai saurin isowa yana daka ma Ramadan tsawa,amma ko gexau bai ba kiran duniya da tsawa Abba yai masa bai jiyo ba balle yaji,kwata-kwata kamar ma baya cikin hayyacinsa ga rafeeq yana ta kakarin mutuwa idonsa sunyi luiuuu sosai zasu rufe,saida Abba ya dauke sa da zazzafan mari sannan ya dawo hayyacinsa. "Ashe baka da hankali?kai wane irin mutum ne marar hakiri,komi yai makaa ai ba ka shak'esa kai niyyar kashe shi ba............Hawayen da suka gani akan fuskar Ramadan sunyi masifar sanyayar da guiwar su,jikinsu yai sanyi ainun wanda tunda suke dashi vasu tab'a ganin hawayen sa ba,Ramadan jarumi ne mai hakuri ne kuma mai dakakkar zuciya,wannan hawayen yana nufin komi ma a tattare dashi. Shiru Abba yai bai sake magana ba,Rafeeq ya kama suka fita xuwa bangaren su sai lokacin aka san da dawowarsa,Abba Nura bai tausaya masa halin k'ak'anikayen da yake ciki ba yaita surfa mashi masifa. "Daka tako k'afarka kazo ubanka zakai?nace ubanka zakayi?ka fita cikin idona Rafeeq kafin nai mummunan kalami akan ka,uwarku ta koya muku rashin kunya da iyaa shege ko,to bazan dauka ba wallahi bazan dauka ba duk ubanda ya hanani zaman lafiya da yan uwana a cikin gidan nan wallahi zan sallamashi............"Abba ka daina masa fad'a,kana gani baida lafiya duba kaga halin da yake ciki,don Allah Abba kai shiru" Kuka nake ina maganar,ga ruwa hannuna ina bashi a baki saboda tarin da yaketa faman yi, Abbaanmu ya banka mun harara yace "tashi kibar nan kafin na tattakaki" Aguje na tafi daki ina kuka sosai saboda ganin halin da yake ciki,sannan ga masifar su Abba shin taya zamu so su Abba Habibu?bacin koda yaushe sune suke hana mana zaman lafiya da iyayen mu. Acan falon kuma. "Nura wannan fad'an ya isa haka,ka kyalesa yaji da kanshi fad'a sukai da Ramadan na iske ya shak'esa mafarin yaketa wannan tarin kenan,tashi muje mu kaishi asibiti" Abba Nura ransa Bace yace "kayi hakuri Yaya ba wata asibiti da zan kaishi,ai shiya jawo koma miye na tabbata Ramadan bashi yajashi da fad'a ba,sanin kowa ne Ramadan baida hayaniya,shine zaije yai masa abunda zai jawo ransa ya hangula yai masa duk abunda yayi masan,ya tashi yaban waje ba abunda zan mashi,kuma ka tabbata gobe kaje kabi wani jirgin ka koma inda ka fito,kuma wallahi kwandala ba zatai ciwon kai ba,sannan daga rana mai kamar tayau idan na ganka gidana ba tare da ka kammala karatunka ba,wallahi tallahi ka manta na haifeka" "Subhanallahi,Nura wace irin magana ce wannan ka shiga hankalin ka mana" Abba Habibu ya fada cikin fad'a-fad'a, Sai lokacin Abba Taheer ya ce "kayi hakuri Yaya,yaran ne idan ba haka ake masu ba basu shiga taitayin su,kana gani saida mukai hannun riga da Fahad kafin yake yadda da hukuncina yabi abunda nakeso,don haka kabarshi yai masa hukuncin da ko da wasa bazai kuma abunda yakeyi ba" "Ai ba ta haka ake hukunta yaro yayi abunda akeso ba,kuyi masu nasiha mana kuyi masu addua kujawo su ajiki,kuna masu kwatanci ahankali zasu gane ba dai-dai sukeyi ba,tashi Rafeeq muje ni na kaika asibitin a dubaka" Daker ya bud'e baki ya ce "Ba sai anje ba,zan je na shafa magani in nagasa wajen da ruwan zafi" "To shikenan Allah ya kyauta gaba,kuringajin magana don Allah ku kiyaye bacin ran iyaye masifa ce babba,ka bashi hakuri kayi masa laifi" Muryar sa tai wani iri gwanin ban tausayi ya ce, "ka yi hakuri Abba in sha Allah bazan sake abunda nayi ba,kaima Abba Habibu kayi hakiri natuba" Kwallace ke zarya afuskar sa duk jikinsu yai sanyi, Abba Habibun yace "ya wuce Allah ya yafe mana,ka kiyaye gaba kaji ko tashi maza kaje ka gasa wajen" Ya tashi daker yana tafiya, Abba Taheer yace, "zan maka bucking wani flight d'in ta online,zuwa jibi saika tafi" "Nagode Abba" ******** Kwana biyu gidan ba dad'i,mudai mun gama jarabawa muna zaune gida zaman banza,sai fa islamiyya da muke fita duk juma'a da asabar da lahadi,mami bata nan har yanzu shiyasa duk bama jin dadin gidan,kowa tsoron Abba Nura yake yanzu balle har ka iya bashi wani hakuri akan yaje ya dawo da ita,cikin kwana biyun kuwa ba abunda ya sauya daga tattali da kulawar da muke dajuna nida Yah Rafeeq,saima abun da yai gaba nice hidimar abincin sa da komi da komi har zuwa daren da zai tafi don tashin dare zasuyi karfe takwas da rabi jirgin zai tashi, muna zaune dashi bayan sallar magariba falon Umman mu daga ni sai shi yake ce mun, "Rooh inaso kiyi mun wani alk'awari guda please" Yana yin sa ya sauya sosai,nima duk cikin rashin sukuni na ce "miye shi?zan maka shi yah Rafeeq koda bai dai-dai da son raina ba" Lumshe idonsa yayi ya bud'e su akaina,zuba ma juna ido mukai kamar ba zamu sake ganin juna ba,saida nai karfin halin sadda kaina k'asa inajin ilahirin jikina yana tsuma da soyayyarsa.........."inaso daga yau magana ta fatar baki karta sake had'aki da RAMADAN,In hanya ta matse maki dashi kinji kina iya gaidashi ki gaidashi ki wuce,in kinji baki iyawa ki wucewarki,bana son wani abu kamancin kusanci ya sake had'aki dashi balle har kazamin hannunsa yakai jikinki,idan haka ta sake faruwa wallahi zan iya kashe shi zan iya masa abunda iyayenmu maza ba zasu yafe mun ba,ki janye daga garesu kam yan bangaren su,Abba kurin na lamunce mawa ki gaidashi ki sakar masa fuska,please Rooh kimun wannan alfarmar" Jinjina kaina nayi kafin na ce,"koda bakace na Yah Rafeeq magana nida shi har Abadan inba dole ba,amma don ka yadda dani nayi maka wannan alkawarin" "Thank you my love," Nai masa murmushin da yakeso har dimples dina suka bayyana, Sai sannan naga walwalar sa yana murmusawa shima, kafin ya d'ora da cewa "Abu na gaba shine Abba yayi rantsuwa bazan sake dawowa hutu ba har saina kammala karatuna,wannan shine abu mafi d'aga hankalina daya gindaya mun,Rooh ina cikin damuwa sosai tsoro nakeji inacan ke kina nan wani yazo ya rabaki da Soyayyata,karshe ma inji kawai anyi miki aure please ya zanyi i need more advice from u,ga rashin Mami agida yana tada mun hankali" Hawaye suka cika idona nai kokarin hanasu karsu zuba,saboda iya tashin hankali na shiga jin cewar baxai sake zuwa gida ba har sai ya kammala, idan nace kuka zanyi zan karya masa guiwa zan rabashi da d'an karfin zuciyarsa,shiyasa na danne iyakar dannewa sannan na ce masa, "Tabbas na Zan shiga rud'u da kewa mai yawa yah Rafeeq,bazan iya kwatanta yawan kewar da zanyi ba taka amma in mukai hakuri mu duka komi zai zama labari,shekara kamar kwana ce in sha Allahu lafiya zaka gama ka dawo ka iskeni ba abunda zai faru,ka sama ranka zaka jure duk son zuwa gida da kakeji kai namijine kafini juriya sosai,abun zai zo maka da sauki inhar ka yadda kayi biyayya ga maganar Abba,tunda na yadda rashin biyayyar shike jefa mu cikin masifa,kayi masa yadda yake so Yah Rafeeq ba zamu tab'e ba,kuma in sha Allah nidai ban da wani miji sai kai a duniyar nan,sannan alkawarin da zan maka mai dad'i shine zan kulle xuciyata,idanuna daga kula kowane namiji da sunan soyayya I promise to u,Mami kuma ka kwantar da hankalin ka zata dawo nasan bacin rai ne daya wuce shikenan" Shiru yayi na wani lokaci kafin ya d'ago yana kallona irin kallon kewa da soyayya,ya ce "ban da wani buri a rayuwata da nake so illa na mallakeki,akan ki ban da wata jarunta Rooh,komi inhar ya had'a dake bana iya mallakar kaina,amma wannan alkawarin naki shikad'ai ya isa ya rik'e ni har ba gama karatuna na dawo gida,har raina na yadda dake kuma shawarar ki ta ansu 100%, inaso na sake jaddada miki wani abu guda" Na dago idona da sukai cika da hawaye ina sauraren shi, "in hawayenki suka zubo Rooh zaki karya mun kwarin guiwata,please ki kara jurewa kinji" Jinjina kai nai saboda idan nayi magana kuka zanyi, "inaso na fad'a miki *_INA SONKI,INA KAUNAR KI,KUMA BURINA A KULLUM NA MALLAKE KI,KECE NATSUWA TA DA KWANCIYAR HANKALINA,KECE KAWAI KIKE BURGENI A CIKIN MATA KOMI KIKAI YANA DAUKAR HANKALINA,KI KASANCE DANI A RANKI,INA NAN KO BANA NAN ROOH"_* Juriyata ta kare zafafan hawaye suka silalo mun sharrrr ba tare dana shirya ma hakan ba,na sadda kaina jikin hannun kujera ina shashshekar kuka ahankali mai ratsa zuciyar mai saurare,na rasa yadda zanyi da raina da irin abunda nakeji akan tafiyar tashi,muryar sa tai wani irin rauni kamar yana kukan shima yake cewa, "sorry,I'm so sorry Rooh,stopped kukan ki yana kassarani in kika cigaba dayi bazan iya tafiya a yau ba,ina mai tabbatar miki zan kamu da rashin lafiya mai tsanani" Don dole na sassauta na soma hakura da kukan,ya bani hanky dinsa na share fuskata,munyi shiru kamar ba kowa har lokaci ya k'ure,Anti Rafeea ta shigo ta ce "Abba na jiranka a mota Yah rafeeq," Kallon ta yayi cikin yana yi marar dad'i ya ce, "ki kula mun da k'aunata Rafeea,kece takwarar sunana nasan zaki tayani yak'i akan soyayyata,karki bari wani yazo daga waje yace zai shiga inda ba hurumin sa ba" Dariya tayi ta ce, "angama Yah Rafeeq,baka da matsala indai nan ne" Ya jiyo kaina ya mun wani sassanyan kallo, "zaki rakani airport?" Girgiza kai nayi da sauri cikin salo na ce "Aa,zan iya rasa jarumtata,kaje kawai Allah ya tsare ya bada sa'a akan dukkan abunda ka sanya a gaba" Lumshe idonsa yayi "naji dadin adduar nan,kici gaba da yi mun ita akodayaushe" Ko bakin mota ban rakashi ba anan mukai sallama ya wuce yaima Umma bankwana sannan ya tafi,sai lokacin nai kuka kamar ba gobe shekarun da zai dauka banganshi a zahiri ba kawai nake hangowa,kuma acikin wannan shekarun Allah kadai yasan mizai faru? ******** Tunda suka dauki hanya shida Abban shi ba mai magana kowa da irin tunanin sa a ransa,saida tafiyar tayi nisa Abban yai gyaran murya ya ce "Rafeeq" D'ago kanshi yai ya ansa murya ashak'e, Abban ya cigaba da cewa "kana ganin kamar bana kaunar ka saboda wasu abubuwa da nake muku ko?kuna ganin nine nake ba dai-dai ba kune kuke kan dai-dai ko?shiyasa kuka juya mun baya kuka had'e kanku dana mahaifiyarku kuna yak'i da abunda nakeso kuyiko?" A sanyaye ya ce, "Ba haka bane Abba.........haka ne mana Rafeeq,inda ba haka bane ba zaku k'i abunda ni mahaifinku nake so ba,ba zaku ringa take umurnina ba kuyi nata,shin ni banda hakki akanku komi?" "Kana dashi Abba" "Ban cancanci ai mun biyayya ba kenan?" Ya ce da sauri, "wallahi ka cancanta sosai ma" "To miyasa bakwa yi mun biyayya akan Yaya Habibu da iyalin sa?miyasa kuka d'ora masa tsana da iyalin sa bacin bai muku komi ba sai alkairi," Jikin Rafeeq yai sanyi sosai ya ce, "wallahi zamu gyara Abba,munyi magana da su Sha'awa za a gyara Abba kayi hakuri" "Idan banyi hakuri daku ba ya zanyi muku?ko nayi hukunci ai ba bin abunda nake so kuke ba,kunga kenan hukuncin ma baida amfani,don haka wallahi ko kaje kayi karatun nan ko kuma inga wanda zai aura maka Roohee,ai nasan duk wannan tada jijiyar wuyar saboda ita kake yi don an daketa shine ka baro uwa duniya kazo ka rama mata ko?" Soke kai yayi baice komi ba,kunya na kama shi don bai dauka yasan da abunda ke tsakanin su ba, "zan kiyaye Abba" "Allah yasa" Saida suka isa airport d'in sannan Rafeeq ya ce, "Abba ba dan halinta ba kaje ka dawo da ita,gidan baya masu dad'i yan matan can in babu ita,kayi hakuri ka dawo da ita" Dafa kafad'arsa yayi yana cewa, "karka damu lokaci nayi zata dawo da kanta" Da haka suka rabu saida yaga tashin jirgin su sannan ya dawo gida,cike da tunani kala kala. Mom Muhseen &Assad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....12 Bayan kwana biyu Mami ta dawo munyi murna sosai,Amma ummanmu tafi mu murna saboda har kwallah tayi data rungumeta tana murnan dawowar ta,ba abunda ya canza daga dawowar Mami saima kara k'ullatar su Abba Habibu da sukai ita da Ummanmu,ko ince mukai don muma mun sake ja baya dasu sosai,har Ammin kausar d'in mun ja baya da ita,in zata shigo sau ba iyaka kauda kanmu ma muke gaisuwar ma mun daina,haka zuwa gaida Abba Habibun ma mun daina lamarin ya sake dagulewa sosai a cikin gidan,rannan Hajja ta tara meeting ranta b'ace hadda kuka saboda yadda abubuwan suke tada mata hankali,kowa ya hallara sai wanda bai nan ne babu a wajen, Ta so ma magana cike da damuwa ainun, "kowa yasan akan me zanyi magana,ba saina bata bakina nace ga dalilin tara ku ba,kun sani akan zumuncin da kuka dauka ba abakin komi bane, na soma gajiya da abubuwan dake faruwa a gidan nan,wace irin masifa ce kuke son hadda sawa a cikin gidan nan,uwa daya uba d'aya amma kuna son raba mun kan y'ay'a na da jikokina,wallahi abun nan ya isheni haka nan inba so kuke in dauki mummunan mataki akan ku ba,kuma ba kowa ke had'a wannan husumar ba sai SAFIYA DA MAIJIDDA, wallahi in bakuyi wasa ba ungulu zata koma gidanta na tsamiya,na gaji hakanan ku biyu kun addabi iyalina kun hanasu zaman lafiya,ina da rai kenan to randa Na koma ga Allah kuma fa.........sai ta fara kuka haik'an wanda bamu tab'a ji ko ganin tayi irinsa ba, jikin mu yai sanyi sosai kowa yai shiru sai Abba Habibu daketa bata hakuri,....."ka daina bani wani Hakuri Habibu,kai za'a ba hakuri saboda kai ne kake kwankwad'ar bakin cikin da yafi nawa,ban san me kai masu na sharri ba suka kafa maka k'ahon zuk'a irin haka........... "Kiyi hakuri Hajja,wallahi Yaya babu abunda yai masu sai alkairi,tunda in bacin shi kila da yanxu ba wannan mgnr ake ba,kiyi hakuri don Allah kibar kuka wannan kukan naki masifa ce a garemu,zamu dauki mataki yadda ya kamata in sha Allahu,kiyi hakuri kaima Yaya ka kara abisa wanda kake yi,jarabawar mu kenan wadannan matan Allah yasa mu cinye" Abba Nura ne yake fadar haka,Abban mu kau saboda tsananin b'acin ran dake cinsa ya kasa magana,haka dai taron ya tashi da tsaurarrun matakai da Abba Nura da Hajja suka kafa da Abbanmu,wanda take d'aya daga cikin wad'anan sharud'd'an na nufin hukunci akan ka mai tsananin gaske. Rayuwa ta cigaba da tafiya a cikin gidan kadaran kada han,ba wannan zumuncin sosai haka babu wannan gabar mai tsanani,saidai kuma har yau su Ummanmu basa hulda da mama itama kuma daman bata shiga tasu Huld'ar,tana dai sauke hakkinsu dake kanta ta kuma ja girman ta ba ruwanta dasu,haka aketa tafiya gidan kullin in muka zauna fira falon Abbanmu nasiha ce da jan hankali tsakanin mu dasu Abba Habibu,ya daina fad'anan sosai saidai janmu ajiki da nuna mana hanyar data dace,har muka saki da tsanar da muka kwallafa musu,amma ta Yah Ramadan na nan daram a sak'e a gefe,don bana jin shi zan daina tsanarsa saboda abunda yai mun. Shikenan muka koma sama-sama dasu Najeeba,Ammi dama ta koma tun tuni ita dasu kausar d'in,yah najeeb ya dawo hutu shi muna gaisawa duk sadda aka had'u,daga ba gaisuwar ba babu wani abu dake sake had'amu,to wannan abun ya kawo farin ciki sosai a fuskokin Abbanninmu,sai suka zage wajen hidinta mana komi muke so duk tsadar sa Abba da Abba Nura zasuyi mana,don daman komi namu sukeyi tunda Abba Habibu bai aiki tun fil azal bamu tashi munga yana wani aiki ba,komi daya shafi iyalinsa da hidimarsu Abbanmu keyi shida Abba Nura,don ma dai Abbanmu yafi Abba Nura samu sosai don shi Abba Nura Babban lauya ne da akeji dashi cikin garin abujar,shi kau Abban mu NNPC yake aiki kuma yana da babban muk'ami sosai,bayan haka suna kasuwanci shida Abba Nuran sai suka sanya Abba Habibu ciki,duk wata alwuns suna shigar ma kowa ta bankin sa,to inba wannan ba Abba Habibu bai komi gaskiya tunda bai karatu ba,primary kawai yayi. Wannan kenan! Tsakanina da Yah Rafeeq kuwa sai dai ince Aure ne kawai ba a daura mana ba,amma soyayya tayi nisa wanda zaka dauka an saka mana rana,amma muna kokarin kiyaye duk abunda bai kamata ba,duk kuwa shaid'an yana d'an samu nasara wani lokaci,amma muna baki iyawar mu wajen ganin bamuyi abunda zai jefamu ga dana sani ba,a wannan lokacin bana jin komi sai nishad'i da annashuwa,don Yah Rafeeq yana samar mun da natsuwa fiye da kima,wata irin kauna da soyayya yake mun mai ratsa dukkan jiki da b'argo,idan ina waya dashi bana son koda k'uda ya gifta tsakanin mu,wata natsuwa nake kamar ina daukar wata muhimmiyar lecture,har an gane mun ma in ina waya dashi ba mai mun mgn,don ba ji zan ba shiyasa na rage zaman fira,ina daki abuna muna soyewa salo-salo na daukar hankali ban san na iyaba sai da nafad'a tarkon sa,nida shi bazan iya gane wanda yafi son wani ba,ko fad'a bama yi sai muyi wata bamuyi fad'a ba shiyasa shak'uwar mu tai k'arfi sosai,muna tsananin ji da juna kamar rai sannan muna kishin juna kamar hauka,inhar yaji zan fita zuwa wani waje hankalin sa tashe hake,haka zaita damuna da kira yana bani umurni ga yadda zanyi,kar in sake inyi murmushi har in dawo,sannan dole na ringa saka nik'af da doguwar abaya,doka kala-kala da yake son sa nake bana iya sab'a ko daya daga cikin dokarsa,Rukee har mamaki nake bata tasha ce mun, "ke kam yar wahala ce,yanzu shida ba ganinki zai ba bainan yana can wata uwa duniya shine kike biyesa kike duk wannan abun,lallai ba ayi namijin ba walllahi" Murmushi kawai nake mata in ce, "ba zaki gane miye so ba sai ranar daya sark'e ki,a sannan zan gane shin Rukee tana da wani ra'ayi ko saina habibinta" Sai dai ta girgiza kai kurin ta rabu dani,to shima kuma inhar naji muryar wata a kusa dashi ranar bamu wanye wa lafiya, rigima muke sosai saboda zafin kishin sa da nakeji,gani nake kawai k'wace mun shi za'ai balle can akwai yan mata masu sunan yan mata da suka dameni a komi,india fa!ai karshen kyau kenan. To da muka gane cewar ko wannen mu nada kishi sosai kan d'an uwansa sai muke kiyaye abunda zai motsa mana shi,muke zaman mu lafiya har Allah yasa muka shiga jami'a muma. Wata private university dake nan cikin Abuja wai ita *BAZE UNIVERSITY* Abbanmu yai mana komi da komi na zuwa makaranta,hadda sabbin d'inku na mukayi Abba Nura yabamu kudi muka shiga kasuwa muka siyo kayan duk da muke buk'ata,jakunkuna da takalmomi,da sauran tarkace na yan mata masu ji da kansu,shigata jami'a ya jawo mun farin jinin samari sosai ma duk da na kasance mai killace surata,bana yadda na bayyana zahirin kyauna kodan kar wani yace yana sona ina kiyaye ma Yah Rafeeq wannan bangaren,Rukee har ta gaji da mamakina yadda na maida kaina wata matar aure wajen kula da rufe duk inda zai bayyana kyawun ta,amma duk da haka ban tsira ba daga samarin cikin makaranta,yanzu driver na musamman Abba ya samar mana yace saboda Yah Ramadan bai da lokacin da zai ringa kaimu da dauko mu,saboda yana zuwa wajen aikin furniture's ranar da naji wannan labarin munyi dariya sosai nida Ruky,lokacin munje yima Abba Nura sannu da dawowa yayi wata tafiya muka same su suna maganar,wai ana biyan sa a sati dubu goma,wanan yasa bamu san sadda dariyar ta kwace mana ba,sosai mukai tayin dariyar aiko ran Abba ya b'aci sosai da sosai saida muka gwammace bamuyi ba,don wayar charger ya dauko ya dunga tsula mana,rabon kau da adake mu har mun manta har kwalla mukai ya kuma ce mu bashi hakuri. A rayuwata abunda yake kunsa mun bakin ciki kenan,ace in bashi hakuri ina hawaye da shashshekar bakin ciki na ce, "I'm sorry" Uffan bai ce mana ba har Abba ya kora mu yace ko kudin break ba zai bamu ba yau,ya kuma sanar da Abbanmu abunda mukai,shima yace sai munyi kwana uku ba abami kudin break ba,aiko munji jiki kuma mun sakejin tsanar Yah Ramadan,saboda duk don saboda shi akai mana haka saidai ummanmu ko Mami wani ya bamu,duk da ba zasu kai yawan wanda su Abba ke bamu ba,don mu a rana ma muna iya had'a 30k ba wani abu bane wajen mu,shiyasa ai mukai dariya jin wai har sai anyi kwana bakwai sannan zai samu 10k abun da dariya wallahi,shi karatun ma bai mashi rana ba tunda almost 2years bai ci moriyar sa ba,daman kuma daker aka sha wajen karatun. *********** "Gafara dai masu wuri,ai mana iznin shigowa da iznin zama," Wata mahaukaciyar dariya ce ta karad'e dajin har cikin dodon kunnenta,duk da cewar ba yau ta fara xuwa ba,amma kuma ta kasa sabawa da jin wannan dariya mai sata jin kamar zatai fitsari a wando,zuwa wani lokaci kuma dariyar ta lafa sanna taji sautin maganar bokan daga can saman wata gingimemiyar kuka bama a ganinsa,saboda duhun dajin da kukar. "Sai yau kika wai waye mu kenan?hajiya kina wasa fa naga kin Fara tsorata da lamarin,karki sake kija baya inba haka ba komi zai lalace,zakisha mamaki nan gaba inhar kika ja baya damu" Jikinta na rawa take cewa, "wallahi rashin kud'i sukai mun tsaye kwana kin nan,shiyasa kajini shiru,kai kuma ba a zuwa maka saida kud'i shiyasa saida na tara iya tarawa sannan nazo ayi min aikin gafara" Wani sautin gurnani mai karfi ya karad'e wajen,saida ta dod'e kunnenta sannan ya ce "ga mutumin nan ya bayyana kiyi masa bayanin komi,yau dai kandala bata kusa na aiketa wani tsibiri inkin dawo wani lokacin sai ku gana,amma kin san kafin kiyi bayanin sai kin aje kud'i ko?" "Na sani nakan tudu,shiyasa ban fito ba saida na shirya" Ta zage jikkarta ta aje damen kudi sunkai miliyan biyu,sannan wannan dariyar ta sake karad'e dajin na wani lokaci sannan ta tsaya, "kiyi bayanin ki dan duwala yana saurare" Ta gyara zama tana cewa, "godiya nazo na karayi maka d'an duwala aiki yana tafiya yadda ya kamata,wannan yaro dai har yau ba batun wani aiki sai kame-kame da yake,to haka nake so rayuwar sa tai ta tafiyar har abadan babu wani cigaba kamar dai yadda aka hana shi yayi karatun kirki wanda yayi ma don shine rabon sa,a hana shi duk wani abu da zai kawo masa cigaban rayuwa,sannan a sake cusa ma mazajenmu tsanar taimakon sa duk da kace zai wuya,to nidai a dage kota halin yaya ne a hana su taimakon shi,sannan bamu son yaranmu su sosu a damalmala tsakanin su,in bacin wannan ni banda wata damuwa sai ta uwar mijinmu dake son hanamu zaman lafiya,itama ai mana magninta karta sake uzzirawa mazanmu balle har su takura mana,sai kuma batun mijina asake kama mun shi sosai yadda duk sadda na nemi kud'i ba sai yaja ba zai bani,wannan shine kawai buk'atata" Dajin ya sake daukar wannan dariyar fiye data farkon,kusan minty biyar har tafara kerma sannan ta tsagaita,amma tana yi kasa-kasa jitai na kan tudu ya ce, "buk'atar ki ta biya hajjaju,saidai d'an duwala yace kin tabbata babu wata matsala a had'in auren da kuke sonyi da y'ay'anku?" Tayi shiru na wani lokaci kafin tace, "banda matsala da yar uwata,nasan hakan kuma suma yaran basu sa wata matsala,son junan su suke bilhakki da gaskiya ba za'a samu wata matsala ba" "Ki je ki sake tunani,ki kuma saka ido ga yar uwar taki tunda kin yarda da ita sosai,kiga ba wata muna-muna da take kokarin yi? Sannan wannan yaro da kike ta kokarin a hana rayuwar sa tayi kyau,aikin sa babban aiki ne don nasha gaya miki daga shi har mazajen naku basu zaune haka nan,suna rik'o da azkhar sosai bama kamar shi yaron munsha wuyar aikin sa wancen karon sadda yana karatu,yana daya daga cikin nasarar gama karatun sa wannan azkhar din da yakeyi,gaskiya ki karo kud'i don na gaya miki taurarin sa sunsha banban da duk wani d'a dake cikin gidan nan,ke har mazajen naku taurarin yaron sun fi nasu kyau nesa ba kusa ba,in akai wasa arzikin da zai saiya kusan haukataki.........dakata nakan tudu bana son jin irin wad'anan maganganun,nidai ko nawa ne zan biya kar hakan ta faru,kai ni inba y'ay'ana ba kar wani yai arxikin da zai fisu,indai kudine zan kawo nawa kake bukata" Wata mahaukaciyar dariya ya saki ya ce, "shegiya marar imani,to kamar wannan zaki karo daga haka komi kike so ki dauka anyi angama" Ta Saki murmushi, "yawwa yanzu naji bayani,zuwa jibi zan dawo ma dasu" Tatafi da baya-baya har ta bar wajen, saida tayi tafiya mai nisan gaske kafin ta shigo cikin wani kauye ta samu d'an mashin ya kawota cikin garin abujar. *TAUFA! 🤔,A GANIN KU WACECE DA WANAN AIKI? UMMA KO MAMI?* muje zuwa mu karasa lbrin. Mom muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....13 Kwanci tashi ba wuya wajen Ubangiji sai gashi har min shiga aji biyu cikin nasarori,don kuwa daga zuwan mu har munyi suna sosai karma ace ni,don kokarina yasa duk malamanmu sun sanni sosai har ma da masu nuna suna sona ina ta kaucewa da guje-guje,ban yadda ma in nuna maka nasan abunda kake nufi to balle student masu nacin tsiya,ahaka dai aketa rarrakawa zuwa sannan su Anty sha'awa da Anty Rafea duk sun gama degree dinsu suna services haka ma yah najeeb shiyama rigasu gama wa,kowa yanxu cikin su services yake har an fara maganar bikin su,don tuni sun samu mazajen aure,tun kafin a saka rana mun fara shiri da tanaji,shi kuwa yah Rafeeq yana can shekara biyu xuwa uku ta rage masa,yayi nacin zuwa gida har yagaji karshe na murje idona na roki Abba Nura ya barshi yazo,aiko nasha fad'a na gwammace ban rokesa ba,don dole muka hakura ni dashi amma muna cikin tsananin kwadayin son ganin juna,duk da ba ranar da bamu video call amma a zahiri muke son ganin junan mu. Anty sha'awa wani babban Dr ne zata aura yana da asibitin kanshi katuwa tayi suna a cikin garin abuja,sannan kuma yana aiki da babbar asibitin kwalwa dake cikin Garin abujar,da Mami taso ta bada matsala,cikin ikon Allah kuma abun yazo da sauki,ta hakura ta sauko. Anty Rafeea kuma mijinta mint and print waje buga kudi kenan yake aiki,yana daya daga cikin manyan masu muk'ami a wajen,ita kuma ba wani son shi take ba akwai wani lecturan su a makaranta da suke soyayya kamar su cinye juna,to yana da mata itace matsalar data hana auren su,saboda matar har gida tazo tai rashin mutunci akan zai auri Anty Rafea,da alkawarin mummunan hukunci da tayi zatai mata,wannan ya tsorata Umma sosai daman gwanar tsoro ce indai batun kishiya ne,mafarin tasa Abba ya raba wannan kaunar,sai d'an abokin Abba yazo gidan wajen Abba anan suka had'u ya nace mata,ba wani so take ba kawai dai don su Abba sun nuna suna so ne ta amunce,a haka aka azo sanya rana goggo Habi suka sauka da ita da ahalinta Mufee da kamis da jamil,on ready daman mufeey age mate dinmu ce,sosai muke friending da ita ba kamar Najeeba ba,zuwan su yai bala'in yi mana dad'i gashi daman mun samu hutun mid-semister break,inda kawai muke samun matsala da Mufeey akan Yah Ramadan ne, ba tun yanzu ba indai suka zo to duk inda zaya tana manne dashi,ita kad'ai nake ganin yana sake ma fuska,wai ita Tausayin sa takeji sosai kuma bai mata komi ba akan ke zata ringa misbehave d'insa,don dole muka sa mata ido. Muna jin dirar motar su a compound kamar wasu yara muka baza aguja nida Rukee,Goggo da Mufeey muka kaima cafka saida muka kusa kai su k'asa,muna ta dariyar farin ciki don ana iya kashe shekara uku zuwa hudu ba a hadu ba, "Na shiga uku da yara zasu ida gawar da batasu ba,haka kuka zaka wasu broler's.........muka sake fashewa da Dariya Mufeey tace "Mamma ya kike so kiga sister's dina to,ai fiye da haka ma zaki gansu yan gatan Abba Taheer ne fa" Muna ta farin ciki muka kwashi kayan su mukai ciki,Khamis sai tura baki yake wai bamu yi masa oyoyo ba,nai masa gwalo muka shige aiko ya riga kukan iya shege daya saba,don yaji ana ce masa auta bai ganin ya girma. Ranar aka anshi kayan saka ranar su Anty,gidan ya cika ba laifi kowa danginsa na bangaren uwa sun zo sunyi hidimar da ya dace, in ana hidima gidan mu abun dad'i yake mun inason inga antaro ana ta shiga da fita, "Ke nifa banga Favorite d'ina ba tun da muka iso,gashi har anyi sallar isha'i dazu da na gaido Mama na kasa tambayarta na manta" Cewar mufeey muna dakin mu muna cin danmun naman kaza da lemu,kallon juna mukai da Rukee muka saka dariya bamu ce komi ba, tabi mu da kallo kafin ta ce, "Wai har yanzu baku canza alak'ar dake tsakanin ku dasu ba,ku kam dai na kusa ince kunyi asara..........haba dai bari mana malama,wace irin asara kamar wani ubanmu ne shi,kinga bama so gaskiya" Na katseta da fadar haka cikin murguda baki, ta girgiza kai tana cewa "ina jiye maku ranar nadama,abun da kuke ku kanku kunsan ba dai-dai bane ba abunda zance sai Allah ya shirya ku,saboda dai abunda yai Abba Nura da Mamma da Abba Taheer shiyai Abba Habibu,don haka ku cigaba daga inda kuka tsaya" Ta tashi tabar dakin cikin fushi,tab'e baki nayi ina cewa Rukee "anya waccen yarinyar ba son wancen kazamin take ba" Rukee ta ce tana dariya "Wallahi har kin ban dariya,Allah natu ba duk mazan duniya ta rasa abunso sai shi.........saboda shi ba mutum bane komi?wallahi Rukee ku kiyayi kanku,kuji tsoron duniya uhmm wataran akeji,ashe gulmata kuka dasa dana fita" Mufeey ta shigo tana fadin haka,ta haye gado tana danna waya, Na kurbi lemuna nace "au da gaske dai son shin kike?" "Inason shi mana,bakiji ma sunan da nake ce masa ba ina son shi kamar yadda nake sonku,ba wai da sunan soyayya ba" Mukai dariya nida Rukee muna kashewa, Rukee ta ce "Ashe kema kyamar auren sa kike,to ina ga ta waje da bata had'a komi dashi ba" Mufeey idonta har ya canza saboda bacin rai,ta damu dashi sosai fiye da tunanin kowa, "wallahi tallahi bana kyamar auren YAH RAMADAN, da ace zanji ina masa so na soyayya kuma shima yaji hakan a zuciyarsa wallahi ko sama da kasa zata hade saina auresa,ba ruwana da halin rashi da yake ciki,ba ruwana da rashin gayunsa saboda don Allah zan soshi ba don wani abu da yake dashi ba," Tatashi ta shige toilet ta rufe k'ofar,kallon juna mukai nida Rukee saboda ganin hawaye a idonta sadda tana maganar,ba mamaki shigewar da tayi kuka take, "Sis mubar mgnr Yah Ramadan da Mufeey,inba haka ba zamu samu matsala sosai tunda bata so" Rukee ta fad'a cikin nuna damuwar halin da ta shiga yanxu, na daga kafad'a "hakan zaifi,fatana kar Allah yasa ta fada son shi don wannan tausayin is too much wlh" Daga lokacin bamu sake magana irin wannan akanshi da ita ba,za muyi firar mu muyi nishad'i da taga lokacin dawowar sa yayi zamuga ta fita kawai,bangaren su take tafiyarta bata dawowa sai can dare,sadda zata dawo wayarmu muke nida Yah Rafeeq, saidai suyi fira da Rukee. Goggo Habi sunfi d'a sawa sa Mama don haka can take sauka,hakan yana ma su umma ciwo sosai amma basu isa su nuna ta koda da baki ba,bayan idonta dai sunyi yan maganganun su gabanta kuma su sake mata fuska,khamis da jamil kuwa bangaren Hajja suke kwana abun su,zuwan su Goggo Habi ya d'an kara zumuncin gidan, tare ake breakfast da dinner,aita fira duk da ba acika sanyo mama ciki ba ita da goggo suke maganarsu,Su Abba kuwa abun yana musu dad'i,rannan ana Breakfast da safe ya kama weekend,kowa ya hallara hadda Yah Fahad daya zo gida don daya gama degree dinsa yai joining masters dinsa,shiyasa yana jima wa baizo gida ba. Daman mufeey ce keyin sarving kowa a wajen,amma duk iyayenmu dake wurin favorite dinta take fara zuba mawa,yau ya zo a makare kamar ma sauri yake ya ce mata cikin sanyin muryar sa, "only tea mufeeyda" Ta shagwab'e fuska,"Allah Yah ba zaka sha tea kadai ba,kaje ka wuni zungur a wajen aiki baci ba sha Abba kace masa yaci abinci da yawa" Kowa ya saba da halinta tunda suka zo,Abbanmu da taima maganar yace masa "kai ko miye acikin tea Ramadan,ka kara da ferfesu mana tana ta ji dakai tunda suka zo" Abba Nura ya ce, "Ai da yake ma itace kwanan nan baka ga yana yawaita murmushi ba" Duk akai dariya banda su umma,nima d'in dai banyi wata dariya ba wayata nake dannawa ina duba sabbin pictures din Yah Rafeeq da sukai masifar kyau,inka ganshi zaka rantse ma d'an india ne, kamar ance in dago kaina mukai kyakkyawan four eyes dashi kamar an rik'e idona sadda naga yana sakin wani mashahurin murmushi wanda tunda nazo duniya ban tab'a ganin yayi irin sa ba,kai zaka d'auka ba daga fuskar sa yake ba,da mugun sauri na kawar da kaina don in nace bai masa kyau ba na zabga muguwar karya,magana suke da Mufeey ban maji me suke cewa ba,na gadai ta buga tsalle tana cewa thank you favorite. Bansan miya toshe kunnena daga jin wace firar ake ba,fuskar sa dai cike da walwala yau ba kamar kullin ba,saida na dawo daki ne naji Rukee na cewa "ni yaushe rabona da buga basket ball gidan nan,ai harna manta" Ina kokarin saka headphone na ce, "kina missing dinta kenan," "Sosai ma shiyasa banja ba da Mufeey ta shirya mana ita yau" Aje headphone din nayi na ce, "ta shirya mana ita kamar ya?" "Wai duk drama da akai bakiji ba ina hankalin ki yake" Shiru nayi kafin nace, "inajin pictures din Yah suka dauke mun hankali sadda ya turo mun su,sunyi kyau sosai wlh kamar dan india na gaske" "Uhm,to saiki shirya karfe biyar na yamma za'a fara,team d'in mu nida yah fahad da anty sha'awa ,sai ummi da jamil din. Naku kuma Yah Ramadan da yah najeeb,da ke sai anty Rafeea da Mufeey" Naja d'an tsaki, "da Yah Rafeeq na nan wasan sai yafi dad'i,kuma a rasa team din da za'a sani sai nashi" "Uhmm kedai kika sani anriga an raba team dole kiyi hkr anan,bari nai wanka ki fiddo mana jessi d'inmu a wanke don sunyi k'ura" Tun muna yara aka taso da wadannan wasannin a cikin gidan,mune volleyball,mune table Tanis mune basket ball wasanni kala-kala muna yi,da muka girma ne duk aka watsar,gidan babban gidane sosai ma duk muna da filayin yin su,Abbanmu da Abba Nura sun yi kokari sosai wajen k'awata gidanmu,karyar mai karya ya shigo yace bai burge sa ba. *5:00PM* A wajen filin wasan an zagaye sa da kujerun roba dasu Abba zasu zazzauna sune yan kallo,kowa na gidan ya fito ba wanda ya fita har su mama da Hajja duk sun fito kallo,yan team kuwa kowa ya shirya ya fito,kasancewar Family d'in kowa kyakkyawane sai jessin sukai masu kyau sosai,ni da Rukee kawai akejira tun a daki dana kalli kaina cikin dark pink dan blue Jessy din na Kara gode ma Allah,domin ya kyautata halitta ta sosai,kayan sunyi matukar yimun kyau rigar am less ce ta fiddo Boob's d'in sosai ma sha Allah,daman gasu a ciki ta fitar da shafaffen cikina,sai three quarter wando daya bi cinyoyina ya lafe,na daure dogo cikekken gashina mai sulbin gaske cikin pink ribbon a tsakiyar kaina sai na saka ban dana blue mai rubutun angel, "na rantse da Allah ban tab'a ganin kinyi kyau irin na yau ba, da ace qalbinki na nan wannan wasan ba zai iya buga shi ba saboda susucewa zai........dariya na kama yi nace "wallahi saina fad'a masa,ke dashi ne" Tare muka fito muna ta dariya muna zaga yowa na hangi Mufeey ita da mutuminta sun sha nasu jessy din suma sunyi kyau sosai, duk kushen ka da hassadar ka dole ka fad'a,Rukee ta ce "ke mutumin can mugun yai kyau ko baki gani ba,shi gara ma yaita saka jessy din anfi ganin kyan sa" Ban bata ansa ba saboda wani kallo dana hangi yana bina dashi,duk iya hasashena bazan iya gane ma'anar sa ba ya iya kallon munafurci wanda karyar ka ka fahimci manufarsa a kallon, tsaki kawai naja ina kaudar da kaina gefe,wajen su Anty Rafeea muka je kowa sai yaba shigata yake har su Umma da Mami,kar ma ace mami don wani iri ji take dani tunda muka soma dating da d'an gaban goshinta. Abbanmu yace azo a fara don fita zai baison ruwa ya sauko baije inda zaije ba,don garin hadari keta had'uwa har ya fara baki hadarin, na ce ma Rukee "ina ma ruwan nan ya sauko ana cikin wasan nan,wallahi dana ji dadi ina son wasa cikin ruwa" "Kedai Bari,amma kuma kinji ajikin ki inya dakeki ba" "Ai magani zan sha,amma kam bazan wuce shan dad'in ruwan saman nan ba indai ya sauka yanzu" Cikin kan kanen lokaci aka fara buga wasan,team d'inmu yawan ci duk aka tara k'wararrun amma duk da haka kusan minty shabiyar ba ajefa kwallon ba,karo na biyu ina isa ga inda zan jefa kwallon da jikina da nashi ya gogu zan saketa kawai inja baya raina b'ace,duk yadda na kai ga son jefawa da mun kusanto juna sakinta nake,karshe ta koma hannun su Rukee,tana koma wa zai ansota cikin hikima da wayon sa,haka aketa fafatawa karon farko ya jefata cikin raga,aiko su Umma da su Abba suka hau tafi da shewa,sai kuma naji kishin hakan haushi duk ya isheni,Abbanmu cewa yake "ai daman nasan Ramadan zai fara jefata a raga,keep it up Babban yaya" Ya saki wani killer smile yana shafa sumar sa kamar ta india ya ce, "thank you Abba" Kowa dai yaita yaba mishi,su Rukee kuwa suka hangula aka sake koma wa karo na biyu,nan fa su Yah Fahad suka dage baji ba gani muma muka zage,tuni na manta da banson had'a jikina dashi gogayya muke sosai ana son a cimma nasara,Mufeey tai wata irin fad'uwa Allah yaso ta yana baya ya tareta dalilin da yaja kenan muka fad'i, Yah Fahad ya jefa kwallo a raga,sai ihu da shewa aka hauyi na murnar anzo one-one, raina ya b'aci saboda duk iskan cin Mufeey ne shikuma sauna ya biye mata na ce mata "banza ai duk ke kikaja mana,ko ince kukaja mana daga duzgud'ewa zaki wani lauye,mtss sakarci kawai" "Allah yasa bada favorite kike fadar sakarcin ba,waike miye damuwarki ne iye?" Na sake hangula da maganarta, "naje nafad'a kiyi maganin abun,koma da wa nake ki dauki mataki........Roohee shot up karna sake jin wata magana anan,kafin na sab'a muku kuduka" Abba Nura yai maganar,dole mukai shiru da yake rab'oce har ta fara hawaye,ta juya zata fita daga cikin filin ya riko hannun ta ya ce, "miye haka?oya come in" Dole ta dawo ta tsaya position dinta,tana goge hawaye aka tillo ball muka cigaba daga inda aka tsaya,wasa ya dau zafi ta ko ina kowa so yake yacimma nasara,mun shafe mintoci sosai ana gwabzawa tari ya sark'e anty Sha'awa dole ta fita taje shan ruwa,fitar ba jima wa na anshe ball nai ciki da ita na buga tsalle na jefata a raga,sadda zan dawo na fad'a jikinsa ban ankare ba muka fad'i warwas a tare,can kuma sunata ihun murnar cin da mukai,kunya ce takaici ne haushi ne bazan iya gane me nakeji ba,saboda yadda na hayesa abun inka gani dole zakasan naji wani abu a raina,na saurin tashi cikin rawar jiki haushi ya tirnik'eni na juya kawai ina kakkabe jikina duk da kuwa babu k'ura a wajen,duk na diririce ne ban san dalili ba fita nai daga filin wasan naje na sha ruwa, su Abba suna ta yaba mun don nima nasan nayi kokari sosai,aka huta sannan aka koma round d'in karshe wanda sukai nasara Abba ya dauki nauyin gift mai tsoka a team din,saidai ana koma wa wasan aka soma yayyafi Abba yace shidai ya tafi komi kenan inya dawo yaji labari,ai kan kace me duk yan kallo sun watse saboda ruwan daya soma yawa,zuwa can Anty Rafeeq ta fece itama kafin Anty Sha'awa ta bi bayanta a takaice dai ko wane team ya rage mutum uku,can nasu Rukee daga ita sai jamil da ummi,namu kuma nida shi da Mufeey,a haka mukai ta bugata ruwa na sauka kanmu wani irin nishadi na ratsani,abunda na lura suma suna jin dad'in wasan da ruwan,jik'ewar da nayi yasa gashina ya bi bayana ya kwanta am less din jikina ta lafe sosai inka ganni kamar wata flawer don tsananin kyau,muna cikin wasan muka sake wani irin karo dashi gaba-da gaba kirjina ya dau zafi sosai, bansan nace "wayyo Allah na" Yai saurin cewa, "I'm sorry" A tarihin rayuwar mu wannan ce kalma mai taushi tsakanina dashi,sai na juya kurin bance komi ba,Mufeey ta ce "sannu" Kai na d'aga mata kurin,aka cigaba da wasa danaga zamu sake gamewa zanyi saurin ja baya,kafin su Rukee su sake ankarewa mun sake cinsu,tsalle da ihun dana buga sadda ya jefa kwallon a raga shine dalilin da sulb'in wajen ya dauk'eni ya nanani da k'asa nai wata irin gurd'ewa na fad'i, wata razananniyar kara na fasa mai tada hankali,saboda azabar danaji ga k'uguna da k'afata wajen guiwa,aguje sukayo kaina shine farkon zuwa ba zaka kalleshi kace ya razana ba,amma idonsa kawai zai nuna maka a kid'ime yake,ruwa sosai akeyi kafar ya kama zai murza na fasa kara,rukee ta kamani da mufeey in tashi na kasa,wata irin azaba nakeji ga k'uguna kuka nake ina kiran"nashiga uku K'uguna ya kare,Rukee na bani wayyo umma Abba ka taimakeni na kare k'ugu" Mufeey sai kuka da yake gwanace a kuka,Rukee ma hawaye take tunanin ta dagasken karewar nayi,ganin halin da nake ciki yasa ya nufoni ina zaune dirshen k'asa ya sak'o hannunsa ta kugun ya saka d'ayan karshin kafafuna sai jinai kurin d'afff ya daukeni yai cikin gida dani,azabar da nake ciki bata hanani mamaki da al'ajabin abun ba,rungume nake jikinsa sosai don zan iyajin bugun zuciyarsa,ruwa nata dukanmu bamu damu ba su Rukee suna bayanmu,wata kwarankwatsi da aka saki bansan na k'wak'ume shi ba na saka kaina tsakanin wuyansa da kirjinsa,Ya salam musallim wani abu naji ya ratsa hancina da kwalwata, *K'AMSHIN TURARE* azabar da k'uguna keyi bai hanani dagowa ina kallon fuskar ba cikin mamaki,kamar bai san me nake ba koda wasa bai kalli fuskata ba,har sadda muka shigo cikin main falo ya wuce dani har dakinmu bisa gado yad'orani,bai kallan ba ni kam kamar na samu tv wajen zare hannun sa daga k'uguna ne na zabura nace "wayyo Allah na" Ya mik'e yana ce mun, "Allah ya sawake" Dai-dai Su Rukee sun shigo,shi kuma ya fice sai na saka kuka kurin ina cema Rukke ta kira umma akaini asibiti,mutuwa zanyi duk sun damu sosai Rukee tatafi kiran umma,Mufeey sai sannu take mun. "Laifina ne Roohee nina jawo wasan nan,da ba ayi ba bazaki samu matsala ba ki yafe mun" Kukana kurin nake sosai hadda hawaye,don k'ugun yafi mun ciwo sosai, cikin kankanin lokaci na tara mutan gidan,hadda goggo Habi anata mun sannu ita takira Abba Nura aka kaini asibiti,sun duba babu wani mugun rauni buguwace kurin,aka bani magani na shafawa in angasa,su Mama da najeeba duk sunzo dubani har Abba Habibu kowa yazo amma ban ganshi ba,Abbanmu washe gari yace in ina iyawa zai tura ma YAH RAMADAN KUD'I muje shopping mu siyo duk abunda mukeso yan team d'inmu,jin ance shopping nace zan iya duk da kuwa d'angyashi nake sosai. Na fito wanka ina shafa mai daga ni sai Rukee nace mata, "wani abu yaban mamaki jiya Rukee,ashe guy d'in nan yana saka turare,turaren ma mai aji mai tsada Abbanmu kad'ai nasani da irin sa wallahi Rukee" Mamaki itama take kafin tace, "ya akai kikaji to" Shiru nayi kawai bance komi ba,kamar banji ke tace ba dariya naji tana yi na dago ina kallon ta, "miye ne to?" "Aa mefa,hangoki nai dare-dare a jikinsa,shine nace kunyi kyau..........na jefeta sa robar man da nake shafawa, "Allah ya isa tsakanina dake,ashe kina nan kinyi mun tanaji,dadin abun bance ya daukan ba da ina cikin hayyacina hakan ba zata tab'a faruwa ba" Dariya kurin take tana cewa,"aa ni kam me zaki cemun kuma" Aiko na k'ule-k'ule na hayeta naita jibga har sannan bata daina dariyar ba,saida naji ina fama ciwona na sauka daga cikinta, raina a b'ace haka na gama shirin,Mufeey na can b'angaren mama indai yana gida to ita kam tana nanik'e dashi. _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....14 Mun tafi yin shopping daga ni sai shi da mufeey,suna gaba sai fira take masa bata damu da rashin ansa ta da bayayi ba,sai an dad'e kafin yai sentence da bai wuce three letters ba (😂 miskili kafi mahaukaci ban haushi),duk haushin su ya kamani sosai a haka dai mukaje mukai uwar siyayya don nikam jidar kaya naitayi ban damu da insan ko adadin nawa Abban ya bashi ba,saida Mufeey ta ce "ke kam dai Allah wadaran halinki,duk ina zaki da wad'anan kayan to in kudin basu isa ba fa" Na harareta nai gaba abuna,na bar musu kayan na koma mota nai zamana,yah Rafeeq ya kirani daman yinin ranar van same shi ba,sai nahau mishi kuka ba gaira babu dalili "Ya salam Rooh minene?waya tab'amun ke don Allah kiyi shiru karki dagula mun lissafina" Cikin kukan na ce, "to ni daka dagula nawa fa?kana can kana tare da yan matanka ka manta dani,through out yau ka hanani jin muryar ka,gashi ban da lafiya ko" Shagwab'a zalla naita zuba mishi ina kukan,bilhakki da gaskiya wanda ban san ya akai nake yin sa ba, cikin laushin murya da yake anfani da ita wajen lallashina ya ce, "Roheena pls stop crying kinji babyna,I don't mean to hurt u na fada miki muna da wani practical kuma zaici lokaci,shine ya hanani kiranki kuma in dakin kira zakiji wayana switch off,uhm Rooh kin san ke d'aya nake da a duniyata matsayin masoyiya ta kuma matata,ki daina tada hankalin ki kinji ko" Ahankali na rage sautin kukan ina cewa, "nidai ko yaya ne ka ringa kirana hankalina zaifi kwanciya" "Ayya zanyi hakan inhar zai faranta miki,yanxu gaya mun miye yake damun masoyiya" Bansan na saki murmushi mai sauti ba na ce, "ba jiya bane mukai basketball,shine fa na gurd'e na bug'e k'uguna" Cikin nuna damuwa ya ce, "wayyo Allah na Bbyna I'm sorry kinji,ki daina yin duk abunda zai wahalar mun dake,ko ya shafi lafiyarki inajin abun har raina,ki kula mun da jikinki yana daya daga cikin abun da ya shafi farin cikina" Na lumshe idona ina murmushi,hankalina yana can ga waya ban san sun shigo motar ba,saida na ce masa "uhm ohk love zan kula yanzu munzo shopping in na Isa gida muyi video call kaji" "Baki da matsala Allah ya tsare" Na sauke wayar ina satar kallon su,jira nake inji ya tada motar amma shiru "Wai motar bata tafiya ne mufeey?" Ta jiyo tana kallona ta ce, "kayan ki na can kin baro shiyasa muka jira ki gama kije ki ida biyan kudin sai mutafi" Idona duk a warwaje na ce, "me?kayana na can?wace irin magana ce wannan shine zaku baro mun kaya acan mufeey!in kowa bai tausayina ke ai kina yi shine saiki biye" Kamar zan kuka nake maganar saboda bakin ciki, "kiyi hakuri sister wallahi hanani yai in dauko,wai kudin kayan sunfi karfin abunda Abba ya turo an biya rabi rabin ne suna can" Wasu kwalla su cika idona na ce, "Allah ka raba bawa da talauci,nayi imanin da Yah Rafeeq na nan bazan wulakanta ba,Amma bkomi wannan ma k'addarace..........Haba Rohee miye haka kike yi ne?kudin da Abba ya tura fa duk kayan sun lashe su,shifa ko hanky bai siya ba kayanki sun hana,ni kaina banda set din dove da inears da turare ban sai komi ba,amma shine kike fadar wannan bakar maganar?" Cewar Mufeey,har idonta ya cika da kwallah,ita dai haka Allah yayita mugun tausayi gareta sosai. Tsaki naja dogo nafita a motar daker,saboda k'uguna har yanzu ciwo yake, "Yah RAMADAN don Allah kaya hkur......shiiiit,bana so pls minene zaki ta b'ata ranki akai" Idonta da hawaye ta ce, "bana jin dadi ne in tana maka haka" Murmushi ya saki mai d'an karen kyau,idanun sa sun d'an canza kad'an yace "don't mind her,watarana zai zama lbri ohk?" Ta jinjina kai kurin ya bata hankyn sa dake cikin aljihu ta ansa tana share fuskarta da ta b'aci da hawaye, da karfin hali na isa wajen biyan kudin na kira Yah Fahad na gaya masa abunda ya faru,nan take ya tura musu sauran kudin su sannan na saka aka kaso mun kayan na fito,har mukaje gida bance komi ba raina bace sosai. Koda Rukee taga kayan dana jido ta rik'e baki ta ce, "Roohee kema kin san kinyi k'wara dubi uwar siyayyar da kikai kamar dai kece CBN,haba mana" Ina shirya kayayyakin a ma ajiyar su nace, "ina sane wallahi nayi haka,ban son ya mori koda k'wandala ne a cikin kudin" Rukee tace, "magana ta gaskiya zamuyi Rohee,kin san gaskiya nima na sani mu sassauta hakanan,k'iyayya bata da dad'i fa annabi yayi hani da zurfafa k'iyayya haka soyayyar ma ba ace ka zurfafa ta ba,shiri ne dai ba muyi dasu amma mu daina wannan halin" Rik'e baki nai ina kallon ta, na ce "sannu mu'allima Rukayya yaushe kika iya wa'azi ne haka?" Murmushi tayi ta ce "uhm nasan halin ki ai,inhar ba maganar Yah Rafeeq bace bamai fad'a miki kiji, kiyi yadda kikeso LAYLA" tunda naji ta kira ainahin sunana nasan taji ba dad'i,sai na kyaleta nasan ta inda zan b'ullo mata. Kwana biyu bayan nan mukaji wai YAH RAMADAN kwanan sa biyu asibiti kwance, duk abun nan bamu sani ba,munga dai bamu ganin mufeey kwata-kwata ashe tana can wajen sa ita da Yah najeeb,in dare yai zata dawo gida shi ya kwana dashi, Abba yace ashirya aje a duba shi. Munje mun samu jikin da sauki ba laifi,yana ma shan watermelon lokacin fuskar sa ta d'an fad'a alamun yaji jiki sosai, su Umma ko minty biyar basu ba a dakin suka fito suka koma mota,daman daga nida Rukee sai su Anti Rafeea da Anti sha'awa on ready sunzo su. Yadda Rukee ta saki jiki tana masa magana yaban mmki, hadda dauko masa ruwa daya buk'ata,wani kallo nake mata ban dai ce komi ba tunda nazo,inaso nai masa magana sai inji bakina yai nauyi sosai,ya dubi fuskar kowa ban dani ko kusa da inda nake tsaye bai waigo ba balle ya kalli fuskata,hakan ya sake ban haushi ban san naja wani dogon tsaki ba na juya zan fice, "Keee!da uban wa kike?" Muryar Yah Najib ta katseni daga fitar da zanyi, na jiyo fuska ta aturb'une goggo Habi na gefe tana kallonmu, na bata fuska na ce "ni na ce da wani nake ne?........wallahi zaki fita da ballalallar k'afa a nan don ubanki,ki cigaba kar ki daina" Kamar in sake jan wani tsaki tsoro ya hanani,don Yah Najeeb ba dai mugunta ba. Na murgud'a bakina na juya aiko yayo kaina a fusace, goggo ta tare shi "yi hakuri Najibullahi kai babba ne kyaleta,ke kuma Allah ya shirya ki wannan halin ba halin kwarai bane saboda gidan wani zaki,ki gyara in kina gyarawa" Duk abunda ake bai ce komi ba kamar baya dakin,Haka mufeey da Rukee wadanda suka ban haushi yadda naga duk sunyi mu bayi'a akan shi,fita nai daga dakin don haushi zai iya sumar dani a wajen, ni kam ai banga abunda zai saka na canza daga tsanar da nake ma ahalin Abba Habibu ba,to akan me ma Zan canza?wanda duk wani fitina da tashin hankali suke kirkiro mana su,sun hana uwayen mu mata zaman lafiya da mazajen su,suda ake ka alfarma to kan wane dalili zan jasu jikina. Karshe nabi su Umma Da Mami muka dawo gida,sukuma sai dare suka dawo, Kamar jira nake su shigo daki Rukee da Mufeey na hausu da masifa, "Wallahi kunyi a sara,ko ince dai Rukee kinyi asara ke kam ai na sallamaki indai akan wancen gallafirin ne,ana cimun mutunci gabanki ko ajikin ki Rukee?yaushe kika sallama haka?wai kin mance duk abubuwan da suke k'ulla mana?kin mance irin wulakanci da iskancin da wannan dan isk...........ban san miyasa nai shiru ba,gani nai duk sun zuba mun ido sai kawai naja dogon tsaki na shige toilet,tun daga ranar Rukee bata sake bani hadin kai wajen yima Yah Ramadan wulakanci ko iya shege ba,dana fara zata tashi tabarni ko kuma tabar wajen,har Mami na gaya mawa aiko ranar kamar zata mareta don fad'a, take cewa "Ashe baki kishina Rukayya?ashe duk abunda Ahalin Habibu suke mana ke baki gani,anya kece kuwa Rukayya" Anti sha'awa ta ce "Mami ba rashin kishin ki ne batayi ba,tana so tayi ma Abba biyayya kamar yadda tayi miki,kuma hakan dai-dai ne tunda dai abayyane ba wani abu suke mana ba da zamu k'isu,hasali ma duk gidan nan ba wanda ya kai yaran Abba Habibu sanyin hali in kacire Najeb..........au ashe ba Rukee kad'ai ta sallama ba hadda ke Sha'awanatu?innalillahi wa inna ilaihir raju'un,minake shirin gani haka?" Sai suka tashi suka barta dagani sai ita,na bata hakuri tare da cewa duk rintsi ina tare da ita,ni a cikin tsanar da nake musu bana jin ko da dakwayar zarra zai ragu,da haka na shawo kanta. Wannan dalilin yasa Nida Rukee muka samu matsala,inajin haushinta sosai akan sabon halin data tsiro dashi,bata iya bina akan ra'ayina haka nima ban iya binta akan nata,sai dan danan kowa ya gane mana a gidan bama shiri,har su Mufeey suka tafi bamu shiri da Rukee. Ranar da zasu tafi naga abun mamaki wajen Mufeey,weekend ne ba sch karfe goma suka gama duk shirin su,daman tunda muka tashi ba walwala tare da ita,kadan-kadan ta share hawaye koda tai wanka bata saka komi a fuskar ba,ni dariya ma abun ya bani da yake daga ita har Rukee ba wanda muke wata magana sosai dashi sai ta kama. Inata karatu na a computer da yake mun fara test a sch,ina lura da ita jikin window tana share hawaye,dariya ta kamani nai ta abuna kafin naja tsaki nace, "to kice baki koma wa mana,kiyi zamanki wallahi sai kawai a daura muku aure ba shikenan ba" Daga ita har Rukee ba wanda yace ci kanki,Rukee ta gama gugar kayanta ta shirya su a wadrope inda dane tare take mana,yanzu ko kowa sabgarsa yake ba ruwan kowa da abun kowa,Ummi ta shigo dakin tana cewa "Yaya Mufeda ance ku fito goggo sun fito compound tun dazu" Rukee ta daukar mata wata jikka ita kuma taja akwatin ta,har suka fice ban da niyyar tashi,sai nakejin ba dad'i sosai a raina bamu tab'a irin wannan rabuwar da Mufeey ba,duk sadda tazo mana hutu da kuka muke rabuwa,farkon zuwanta kuwa kodayaushe cikin raha da wasa muke mu ukun nan,amma wannan zuwan yazo da sabbin abubuwa,sai naji can kasan raina babu dad'i kwarai,inata dannewa kar raunina ya bayyana in bada kaina har dai na kasa,na mik'e na isa ga tagar ina lek'ensu amma ban hangota ba,wayata Abba ya kira na dauka ya ce mun "me kike baki fito rakiyar su goggo ba,maza ki fito ki rakasu kibiya Bangaren Yaya kice da Ramadan su ake jira" Bai saurari abunda zan ce ba ya kashe wayarsa,nai tsaye sororo da wayar a hannu har saida ya sake kirana,na dauka nace gashinan na fito,har na iso kofar bangaren nasu inata tunani wanda ban san ma wane kalar tunani bane,Mama ce kawai falon na gaidata sama-sama ta ansa itama kadaran-kadahan, "Daman Abba ya ce ace masa yafito lokaci na k'urewa" Hanyar bangaren su shida Yah najeb ta nuna mun,ta cigaba da abunda take na gama tsayuwata na wuce can,cikin raina ina mamakin yadda itama ta canxa ai da ba haka take mun ba,naja tsaki kurin ina tura k'ofar falon su...........kyakkyawan gani nai musu Mufeey ce rungume dashi ajikinsa,ta zagaya da hannuwanta bayansa,shi kuma yana tallabe da kanta dashi mukai four eye's saboda ita tabada baya,wani mugun fad'uwar gaba naji wadda ban tab'ajin irin ta ba a rayuwata,kallon-kallo muke ma juna nama rasa me zanyi kawai mamaki ne,?al'ajabine ko ko minene ban sani ba,kawai dai ganin su a haka ya dakeni sosai,kuka take tayi masa shi kuma yana lallashin ta,dauke idon sa yai daga barin kallona yana d'ago kanta yana goge mata hawayen,sai kawai na juya da sauri na fice daga dakin,koda na iso farfajiyar gidan duk su Abba na nan sai Mama data fito da Rukee da ummi,sai su Anti Rafeea sai ni har na tsaya gefe guda ban fita daga cikin shock din ganinsu haka ba,Abba ya ce mun "ina suke ne wai?" Nama kasa cewa komi,sai na nuna hanya da hannuna bance komi ba,goggo ta ce "miya sameki ne?" Girgixa kai na nayi kurin kamar wata sakarai,dai-dai nan suka fito suke rik'e da hannun Juna,kallon su nai tayi ban san miyasa al'amarin su yaban mamaki ba,gashi ba magana muke da Rukee ba balle in labarta mata,kai ko muna magana ba bana iya fadar wannan abun,ban kuma san dalilina ba. Ban kwana aka shigayi dasu goggo ta rungume mama tana cewa, "sai Allah ya sadamu kuma Mama,mungode da karamci Allah yabar zumunci" "Haba ba komi Habi,ai anzama d'aya komi mukai muku ai kanmu mukai mawa,sai Biki kuma in Allah ya kaimu da rai da lafiya" Tai ma su Abba sallama on ready sun sallameta da duk abunda zasu bata,ta shiga bayan motar da Yah Ramadan zai tuk'a Rukee ma ta shiga,Mufeey ta shiga baya ana d'aga musu hannu Abbanmu ya ce "Rohee bazaki ma Yar uwar taki rakiya ba,ba haka kuka saba rabuwa ba ko kunyi fad'a" Na sadda kaina k'asa bance komi ba,goggon ta taga tace mun "bud'e kishigo kinji ko,karku biye ma shaid'an ya raba kanku" Ina dago kaina muka hada ido dashi,wani kallo da ban san ma'anar sa ba ya jefan dashi,na kauda kaina gefe Mufeeyn ta ce cikin muryar datasha kuka "please Rohee" Sai na bud'e inda Rukee ke zauna na shiga,Abbanmu ya ce "in kun dawo keda Rukayya ina son ganin ku" Kai muka daga sannan yaja motar muka tafi,tunda aka fara tafiya goggo keta mana nasiha mai shiga jiki,tana nuna mana muhimmancin zumunci da nuna ma d'an uwanka kulawa da soyayya,ta bamu takaitaccen tarihin su ita dasu Abbanmu da Abba Habibu,da dalilin da yasa suke jin duk duniya basu da kamar Abba Habibu bayan Hajja,yai d'awainiya dasu da aljihun sa da karfinsa,sadda suna kananu babansu ya rasu,har kaskare da jan ruwa a baro ya siyar yayi don suci abunci,shine baci shine walda shine gini shine duk wata sana'a mafi kask'anci ga mutum yayi don ya samu suci suyi karatu,shiyasa suke tsaye akan duk wanda yace zai raina shi to sai ida karfinsu ya k'are,"don haka kuyi hakuri da juna kar ku biye ma zuciyar ku ta kaiku ga kogin dana sani,inkuka rik'e zumunci kun tsira a duniyar nan baku da kamar juna,don Allah Rohee akula a gyara wasu d'abi'un kunji Rukayya?" Rukeen ta ce, "in sha Allahu Goggo zamu gyara muna kan gyarawar" "Allah yasa ya baku ikon hakan" Har muka iso tashar jirgin k'asan bamai cewa komi,muka fito shi kuma yaje yai musu duk abunda zai ya fiddo musu kayan su aka kaisu inda ake killacewa,ya dawo inda muke muka zauna don lokacin ya idasa, suna zaune kusa da juna kuma rik'e da hannun juna bamai cewa komi,ni kam idona a sace yana kansu,dana ga zamu had'a ido dashi zan maza in canza direction din fuskata,har aka soma neman su mutane suka fara shiga,mukai ma Goggon sallama ta shiga Mufeey tana ta hawaye sukai sallama da Rukeen,sai ta iso inda nake ta rungumeni tsam tana kukan, "ki yafeni sister in akwai abunda nai kika k'ullaceni,sai watarana" Wasu kwalla masu zafi suka zubo mun nai saurin rungumeta nima muryata tai sanyin sosai na ce, "baki mun komi ba sister na yafe miki,nima ki yafeni karki kullaceni please I'm very sorry" Daker muka rabu da ita ta koma gareshi ta rungumeshi tana kuka shiya kaita har sit d'inta,sannan ya fito muka shiga mota mukai gida,har muka iso kamar masu ciwon hakori ba mai uhm balle uhm uhm,yana yin parking muka fito tuni Rukee kamar walkiya har ta shige gida,banga alamun sassauci a fuskar ta ba dangane dani,sai na tuna inhar tai fushi to saukowar ta abune mai wahala,nima na nufi hanyar part din mu nasan ma Abbanmu ya fita saidai zuwa dare..........."Ba kiji ba" Cak na tsaya saboda dai nasan dani yake duk wajen ba kowa sai ni dashi, "Bakiji ba....?na nanata maganar,to bai san sunana ba kome?juyowa nayi ina kallon sa shima ni yake kallo da idanun sa masu wata irin kala ni banma tab'a lura da yana yin kwayar idonsa ba sai yau,saurin kawar da kaina nayi daga barin kallon cikin idonsa, isowa yai gabana ya sa hannu aljihun wandon jeans din sa ya ciro wani chan din dan hannu,waro idona nai saboda nasan nau ne kuma ko dana tashi a yau yana sanye a hannuna,na kalli hannuna na sake kallon wanda ke hannun sa,mamaki ya kamani na sake kallon fuskar sa har sannan kallona yake,inaso ince ina ka samai?ya akai yazo hannun ka?bakina yai nauyi,sai ya mik'o mun "wajen kallonmu d'axun kika yar" Ya mutsa fuska nayi, "Ban gane ba?" Juyawa yayi yana tafiyar sa ta isa da yakeyi ya ce, "Ai bazaki tab'a ganewar ba" Ya barni nan kamar sakarai, taya d'an hannu na d'aure damtsen hannuna kuma ya zare ban sani ba?tafiya nake zuwa cikin gida ina duba chan d'in,dana lura sosai ya tsinke ba kuncewa yai ba,sai na tuna sadda na juya zan fita lokacin danaje kiran sa dakinsu,naji kamar abu ya rik'eni na fizge hannun nai gaba,to why? *"Ai ba zaki tab'a ganewa ba"* Maganar ta sake dawo mun,tab'e baki nayi na wuce dakin Ummanmu, _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....15 Bamu je ga Abbanmu ba sai washe gari monday zamu je sch,munje gaidashi kamar yadda muka saba ya bamu kudin breakfast sannan yace damu, "Kafin kubar nan inaso inji miya had'aku?ban son jin bakomi kun sani ban son musu ko gardama don haka ina sauraren ku" Mukai shiru na wani lokaci,kafin zuwa can Rukee ta fara magana, "Abba ka gafarcemu,shaid'an ne yaso dagula komi kuma muka biye masa,duk da ni akan gaskiyata nake itace take son nabita akan rashin gaskiya" Ta zayyane masa komi ba rage ba k'ari game da abunda ya hada mu,kaina na soke k'asa don tun kafin yace komi naji kunya ta kamani, saida ta gama naji ya ce mata "Allah yai miki albarka Rukayya,Allah ya baki miji nagari kinji ko,tashi kije karki makara" Ta sadda kai tana ansawa kasa-kasa,sannan tatashi tai ficewar ta bata tanka mun ba,shima sai ya tashi zai barni anan hankalina naji yai mugun tashi,nai saurin rik'o k'afarsa cikin nadama na ce, "Abba na tuba,nabi Allah nabika karkai fushi dani don Allah,fushin ka masifa ce a gareni wallahi zan gyara Abbanmu" Cikin rawar murya nake maganar,saboda inhar ya tafi yana wannan fushi dani na shiga uku,bazai sake shiga sabgata ba balle ma akan wanda yafi dauka da muhimmanci ne,ahalin Abba Habibu yana son su fiye da son da yake ma nashi ahalin. Tsaya wa yayi bai jiyo ya kallan ba,hakan ya sake bani damar rik'esa gam na fara hawaye,don ba abunda ke saurin karyar masa da zuciya irin ganin hawayena,......"Abba ka yadda dani zan gyara wallahi zan gyara nayi alkawarin irin haka ba zata sake faruwa ba,zan yi duk abunda kake so Abba ka yafe mun don Allah" Sai lokacin ya jiyo yana fuskanta ta, fuskar sa da damuwa sosai ya ce, "zan iya yafeki a cikin ahalina LAYLA saboda iyalin Yaya Habibu dashi kanshi,ina masa kallon mahaifina ba yayana ba,idan akwai wani da zai tsine mun bayan Hajja da Alhaji ta binito Yaya ne,don haka zan iya komi akan sa in kina son zaman lafiya dani to karki kuskura a hada baki dake wajen muzguna musu,ina sonki sosai amma son bazai hanani yi miki hukunci mai tsanani ba Rohee" Hawaye nake tayi jikina yai mugun sanyi, na ce "ka yafe mun Abba,zan kiyaye zan gyara zanyi duk abunda kake so" Yai shiru na wani lokaci kafin ya dago yana kallona inata sharbar majina,ya sa hannu ya dagoni ya zaunar dani gefensa,ya shiga yimun nasiha cikin kwantar da hankali da kulawa,jikina yai la'asar ya kare da cewa, "ki tayani mu idasa wannan zumuncin,uwarku ta kasa kuma tana kokarin ta hanaku kubini,karki yadda ki shiga cikin jerin wadanda zan hukunta su" "Bazan shigaba Abba in sha Allah,alfarma daya nake nema wajenka itace, karka tilastani dole mu zama cloth da YAH RAMADAN Abba bamu jituwa,muna yawan fad'a amma zanyi kokari in ringa gaidashi in bashi girman sa,ba sai na zama cloth dasu ba" Murmushi yayi mun yace, "shikenan,na yarda na san watarana shi zai zama favorite d'inki........Aa Abba ai Mufeey ke ce masa haka,nidai mu tsaya a gaisawar ma yayi suje can suyi ta favorite dinsu" Yar dariya yayi ta manya ya ce, "naji,tashi kije kinga har ten tayi.......da sauri na suri jakata ina cewa, "Abba test gareni ten thirty saina dawo ai mun addua pls" Girgiza kai kurin yayi yana adduar Allah ya kara shirya masa zuria,tare da fatan wani buri nasa ya tabbata ba tare da saka hannun sa ba,Allah yake fatan yai masa jagora acikin burin nashi. (Tofa Abba wane burine wannan🤔) ******** Rayuwar ta cigaba da tafiya abubuwa suna caccanzawa yau fari gobe bak'i,mun shirya da Rukee kamar ba abunda ya faru saidai kuma ko yaka junan mu bama firar Yah Ramadan balle yan uwansa, iyakar mu dashi mu gaidashi in hanya ta matse mana,ko wata magana wadda ta zama dole sai munyi dashi,ba shiri amma babu gaba ko kad'an,sabgar gabansa yake muma ita mukeyi,yana yawan kwanciya asibiti lokaci zuwa lokaci wanda hakan ya fara damun su Abbanmu,har ya shirya masa tafiya zuwa india a duba lafiyar tashi sosai tunda nan sun ce ulcer ce ke yawan kwantar dashi,su kuma su Abba sun kasa yadda da hakan shiyasa yafara masa shirin tafiya can,amma kiri-kiri yace bazaije ba shi yana jin sauki jikin sa sosai ba sai anje har india ba,dole aka kyalesa aka sa masa ido. Kwanci tashi ba wuya wajen ubangiji sai gashi biki yazo,zuwa lokacin munyi hutun session zamu koma aji uku,murnar da nake saura shekara d'aya Yah Rafeeq d'ina ya dawo,nida shi kullin ba lissafin da muke inba na dawowar sa ba,ban san waye yake cikin tsananin d'oki da son zuwan wannan lokacin ba,kowa ji yake yafi dan uwan sa son zuwan wannan ranar,yadda nakeji a raina inama yana nan za'ai wannan bikin da abun sai yafi armashi,duk events din da za'ai sai yafi burgewa in muna tare,amma duk da haka bamu fasa shiri ba,tunda muka taso ba ai biki da wayan mu ba sai wannan karon,kuma gagarumin biki na y'ay'a biyu. Kudi Abbanmu yake saki kamar bai san darajarsu ba,su dukan su sune yai musu kayan d'aki na burgewa duk kushen mai kushe bai isa ya kushe kayam nan ba,shi kuma Abba Nura ya dauki dawainiyar duk wani nau'i na abinci da za'aci tun daga satin biki har a wanye,Abba Habibu kuma shine ya dauki nauyin duk wani nau'in lemo da ruwa da za'a sha a bikin,ba laifi yayi k'ok'ori don tunda aka soma hidimar kullin mota guda ke sauke lemuka da ruwa tatafi,kuma shine da wannan aikin. Rannan naje kan batun kudin d'inkunan mu na anko wajen Abbanmu,na ji yana ce masa Haba Yaya don Allah kabari ba abunda zai gagara ahidimar nan,mu so muke ka huta kwandalar ka bamu son tayi ciwon kai,kayi mana a baya yanzu ne lokacin da ya kama ta kaji dad'i,don Allah karka ce zaka dauki nauyin wani abu." Naji yace, "sai Ace ana bikin y'ay'ana Taheer kace kar nayi komi?na zuba ido kurin kuyi saboda kuna dashi,sai dai idan kun raina arzik'ina.........Subhanallahi!miya kawo wannan mgnr Yaya fisabilillahi" Cewar Abba Nura, Abba Habibun Ya ce, "to Nura ba dole ince haka ba,tunda kun kawo karfi yanzu ai dole kuce ku zakuyi komi" Duk jikin su yai sanyi, "kayi Hakuri Yaya ba nufin mu haka ba,wallahi da zuciya d'a mukai maganar nan nan" Murmushi yayi ya ce"na sani ai,don haka kubarni nayi abunda nayi niyya,ba donku zanyi ba y'ay'ana ne zan aurar" "Shikenan Yaya Allah ya saka da alkairi ya k'ara girma ya kuma ja da rai" Sai na koma kurin don kar suce ina musu lab'e, ina mamakin irin kaunar da suke ma junan su irin haka,kullin kara son juna suke bam tab'ajin koda da wasa sunyi musayar yawu ba,ko ja in ja basa yi,sunfi amfani da ra'ayin wanda yake babba karami sai yayi hakuri,hakika zumuncin su yana burgeni in bacin halin mu na mata ko ince in basu su Umma ai da bakaramin jin dadin wanan hadin kan za'ai ba,da ba wani fada ko tashin hankali. Ankuna kala hudu akai ni kam nida Rukee da Mufeey dinkuna kala bakwai mukayi,zamu fara saka wa tun daga monday d'in biki,don baifi saura kwana goma ba bikin shiri kawai ake ta faman yi,wani abu da naji yaso ya tsaya mun a rai naje Bangaren Mami neman Rukee ina daf da shiga bedroom din Mamin naji suna magana ita da wata kanwar ta, Mamin Ke cewa "shiyasa tun farko banso ta dashi ba mutumin nan sailuba,saboda banga wani abu da zai iya tsinana mana ba,ki duba kiga babban mutumin da Rafeea zata aura,wallahi tunda aka fara hidimar nan yake sakin kudi kamar hauka,ko jiya a bakin uwar nakejin yai ma amaryar alert din five hundred thousand kudin kama hall din da zasu kamu kawai,to nasan yau ma ya turo wasu kudin da zasu kwalliya,kina tunanin kafin a gama bikin basu tara dukiya ba,amma sha'awa ta bijire mun saboda tana son aga gazawar mu,ga Abbansu ya makale bakin aljihu ni kam ai na shiga tara wallahi,Allah ya sani inajin kishin mijin Rafeea sosai...........sai nai kwana na koma don ban san me zan sake jiyoma kunnena ba kuma,na jima abun yana damuna to miye matsalarta da kudin mijin Anti Rafeea,ba dole bane Allah ya baka abunda yaba wancen, in ta dauro wanda ya bakan shine alkairi a wajenka da wanda duk yake tare dakai,haka dai na share ban yi maganar da kowa ba muka shiga sabgogin mu. Yau ya kama alhamis saura tara biki,zamuje ansar d'inkunan mu cikin gari gashi Abba baya nan,inata kiran sa baya picking nasan kila abune mai muhimmanci ya hana ya d'auka,gashi dole sai da kudin zamu tafi duk munyi jigum jigum kowa da tunanin inda kudin zasu fito muke,daman Abbanmu yai alkawarin bamu to bainan,don kud'aden da dama gaskiya,ko na mutum d'aya kad'ai zasu kai 35k,naje ga Umma ta koroni wai in rabu da ita itama jiransa take ya cika mata zasu siyo wasu abubuwan,Abba Nura ma bai nan kuma ko hauka muke ba muzuwa ga Abba Habibu,duk damun san zai bamu in har mukaje. "Ga shawara mana" Cewar Mufeey,duk muka zuba mata ido nida Rukee, ta cigaba da cewa "favorite na nan mai zai hana muce ya kaimu,tunda daman taxi zamu shiga,kunga in mukaje sai daya ya shiga shagon yafito irin cikin damuwa kun gane,nasan zai tambaya sai muce sun hana kayan dole saida kud'i,kila ya bamu wani abun koda ba duka ba................ban san sadda dariya ta k'wace mun ba har ina fadowa daga gado,Rukee kan ta saida tayi murmushi mufeey ta soma k'ulewa ta ce,"bana son wannan abun kin sani,miye na dariya shawarar ce ba tai ba komi?" Daker na tsagaita na ce, "ke wai tunanin ki ko 30k yana da ita a account ne?to wallahi har gara ni ma inada 25k shi kau daker ne,ni banji shawara anan ba wallahi" Rukee tace, "ba batun raini bane Mufeey,wallahi Yah Ramadan baida wannan kud'in,in kuma kina ganin kamar mun son wulakanta shine muje kiyi masa magana ya kaimu,sai abi shawarar taki bamu san mizai faru ba koko Rohee?" Inta dariyar kasa-kasa na ce "sosai ma,ba asan inda rana zata fad'i ba" Tatashi ta fita duk jikinta yai sanyi,Rukee ta ce "bata san bai wani aiki babba ba,kila kallon k'udi take masa" Ina kyaran muryata data shak'e nace,"yau zata sani ai,inbam da kankanba sai kawai muce ya biya mana kudin dinki,uhmm bada Rohee ba nan gaba ai maka gori shiyasa Abba kawai nake rok'o kudi ko yai mun gorin banjin komi" Muna nan zaune ta shigo ta ce, "ku shirya shaf-shaf ni dai a shirye nake ina jiranku a mota........ai ke kam indai tafiya ce da shi to baki bata lokaci" Murmushi tayi tafice,doguwar rigace jikina ta Atamfa dinkin rafa tai bala'in yi mun kyau,ko ina ta hau jikina ba kamar daga kasa data bud'e kuguna yai daidai da rigar,haka daga sama ma ma sha Allah,d'an gyalena baki nai rolling kawai na d'an saka turare kadan na saka lipstick fari mai dank'o na zizara kwalli,amma a hakan inka kallan saika ce ma sha Allah. Rukee abaya ta saka bak'a tayi rolling gyalenta ni na daukar mana handbag muka fito,motar dai da yake fita da ita ce kamar kullin,don kamar ta zama tashi ma tunda duk inda zaya da ita yake fita,Abba yabar mishi key hannun sa. Baya muka zauna nida Rukee ita gwanar tana gaba sai d'umi take masa, saida muka fita cikin gidan sannan Rukee ta ce "Yah Ramadan ina wuni duk yau van ganka ba" D'an smile yayi ya ce cikin lallausan lafazin sa mai dad'i, "Ruk'ayya wallahi nima dawowa ta kenan" "Ayya kuma mun tado ka baka huta ba" "No,karki damu mufeeda tafi karfin na tsallake bukatar ta" Inajin su nidai bance komi ba hankalina na kan wayata,duk ina jinsu dai saida sukai shiru sannan na d'an ciro kaina in gaida shi silently na ce, "good evening" ta center mirror muka had'a ido mai makon inji ya ansa mun,sai ya lumshe idonsa kawai bai sake kallona ba,su kuma da basu san miyai ba sai mufeey tace, "Favorite ana gaidaka Roheen Abba na gaida ka" Yana karkata kan motar wajen shiga wata hanyar yace, "ohhh mufeeda na ansa fa" Ta ce, "Allah baka ansa ba,Rukee kinji sadda ya ansa ne?" "Aa gaskiya Yah baka ansa ba" Gajeren murmushi yai yace, "to ku tambayeta mana" "Wai haka sister?"inji Mufeey ta waigo tana kallona,toni mizan ce musu cewa zan ya ansa mun da ido?to yaushe ya ansa da idon shida ke tuk'i,in nace musu ta mirror ya zasu dauki maganar?sai na zab'i cewa "kila ya ansa banji ba" "To kaji abunda ta ce,kodai ta kurame kayi Yah" Jinjina mata kai kurin yayi don magana wuya take masa,nayi mugun mamaki ma yau da yake fira haka ni ban tab'ajin maganar sa data wuce seconds ba,har muka iso shagon mufeey keta masa fira parking yayi sai Mufeey da Rukee suka fita zuwa shagon,jira nake inga karshen wannan game d'in. Suna fita kamar jira sai ga Yah Rafeeq ya kirani,duk yadda na kai ga jin d'okin dauka sai naji na kasa daukar,komi yasa oho saida yai kira biyu a na ukun dole na dauka saboda zai damu, murya k'asa-k'asa na ce "Hello love" "Rooh na ykk" "I'm fine,saida kuma I'm so much missing u love" Murmushi yai mai sanyi ya ce, "me too,naki na fila ne Rooh ko yau na kira Abba na rokesa yabarni ko bikin ayi dani in dawo ko ranar monday ne,amma yaki ya Rooh ina nan saboda damuwa har zazzabi naji ya sauko mun,shiyasa na kiraki kozan samu saukin halin da nake ciki," Tausayin sa ya kamani nama mance inda nake, na ce "kaya kuri love shekara guda kamar gobe ne in sha Allah,inda ina da yadda zanyi wallahi da nayi,saboda ni ji nake nafika son in ganka,Amma tunda Abba ya hana kayakuri kaji ko karka saka damuwa ni ma tana iya shafata,saboda duk abunda da ya dameka to lallai ya dameni............karar buga k'ofar motar yasa nai saurin dubawa,sai sannan na fahimci da wa nake tare,kuma shine ya fita ya bango murfin mota kamar ana yak'i,hango su Mufeey da nai sun fito sai nace masa, "sorry love munzo ansar dinki in na koma gida muyi waya pls" "Ohk karki manta dani,inaso yau inta jin muryarki zai karfafa mun zuciyata" Nai masa murmushin da yakeso nace, "dont mind love" Mom muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....16 Fitowa nayi daga cikin motar dai-dai sun iso inda muke jikin motar,shidai wayarsa yake dannawa Mufeey ta shagwab'e Fuska, "favorite" D'ago kai yayi yana kallon ta, kafin ya ce "kun gama?" Ta sake narkewa, "Aa," Idanun sa suna lullumshewa ya ce, "why?" "Ba cewa yai bazai bada ba saboda bamu kawo kudi ba,kuma fa sun san ba guduwa zamuyi ba" Rukee ta ce, "duk Abba ne yaja mana,da yana nan duk haka ba zata faru ba..........aljihu yasa hannun sa ya ciro ATM yaba mufeey, "su cire naki dana Ruk'ayya ku anso mu tafi akwai inda zani" Wani tsalle ta daka da yar k'ara, "thank you so much favorite I really appreciate it" Har ta ruga zata koma sai ta dawo,nidai kallon su kurin nake ta tsaya gaban sa bayan ta dubeni fuska ba walwala yanzu, tace "Yah Rohee fa?" Bud'e motar yai ya shige yana cewa, "ban da ita" Duk sai sukai hucking suna kallona,ni kaina abun ya dakeni na farko har yaushe yake da wannan kud'in da zai iya biyan har na mutum biyu?kafin wannan mamakin sai na maganar sa ta karshe ya sake kama ni,Rukee ta ce "ko kin masa wani abunne bayan shigarmu ciki" Wani abune yazo mun wuyana ya tsaya mun,saboda bak'in ciki nama rasa mi zance don ina bud'e baki hawaye zasu zubo mun, na juyar da kaina kurin ban tanka ba, mufeey ta ce "karki kuka please..........Allah ya kyauta kukan me zan?shi har yana da kud'in da xai iya mun abu aduniyar nan ne?karki sake cemun haka" Duk yadda naso sarrafa b'acin raina abun ya faskara,iyakar k'ulewa nayi watau dole saiya nuna cewar nid'in ba komi bace a wajen sa,Rukee ta rik'o hannuna "come down pls,kiyi hkr danne bacin ranki" Fizge wa nai daga rik'on da tai mun,na shiga motar ji nake kamar zan banka mata wuta,su kuma suka koma shagon don kwaso kayan,kuma da gaske suka hana nawan saboda teloli basu da kirki,nai alkawarin nida sake kai musu dinki har abadan,bayan sun shigo motar ne shi kuma ya tada ta zamu tafi, naja wani dak'ik'in tsaki ni kadai nasan yadda zuciyata take tafasa,maganganun dake kai kawo a kirjina suna da zafi,saidai nasan fad'insu zai jawo mun matsalar da ban san karshen ta ba..........fitowa yai daga motar saidai kawai naji ya bude inda nake zaune, idanun sa jajir daker yake budesu muryar sa ta sake zama cool ya ce, "fito" Da idanuna da suka tun batsa da bacin rai sun firfito waje nake kallon sa, kirjina har wani d'agawa yake don b'acin rai na ce da rawar murya kuka na son kwace mun, "mizan yi?" "Idan kin fito saiki san ke zaki" Fitowar nayi ina jiran ganin ikon Allah,sai kawai naga ya rufe kofar ya juya zai koma motar, hawayen da bake rik'ewa suka silalo mun ban shirya ba muryata da kuka na ce, "Kana nufin anan zaka barni?" Wani kallo ya jefa mun ya bude murfin motar ya shiga, "duk abunda kakeji dashi inaji nima,saidai ka sani baka isa ka tsayar da numfashina ba,kuma yadda kakejin tsanata a ranka ni wadda bakeji akanka da zaka ganta saika tsorata" Ya jima bai tada motar ba,kansa a bisa sikiyarin motar tsawon lokaci yana a haka,zuwa can ya dago ya tada motar suka tafi,kuka na durkushe a wajen inayi mai cin rai,saboda irin yadda bakejin haushi da bakin cikin abunda ya faru,ban san iyakar lokacin dana bata ba naji dai ankira magriba, na tari taxi nahau na taho gida. Ranar kwana nayi cikin k'unci da bakin ciki,nama kad'aice ni kadai a daki na juyama kofa baya,duk iyakar hikimar su Rukee da Mufeey sun kasa shawo kaina,ko wayata kasheta nayi don ko ya kira bazai sameni yadda yake so ba,wajen eleven thirty na dare Mufeey ta dawo daga firar ta ita da Rukee ni kuma sannan nai sallar isha'i ta na gama ina linke sallayar Rukee ta jawo ledar data shigo da ita ta ce, "ga kayanki" Kallon ledar nayi na kalleta na ce, "kaya na?na ina?" "Ankon ki mana" Nai mata wani kallo kafin na ce, "waya biya kudin?" "Abba Habibu ya biya,mufeey tai masa magana" Bance komi ba na haye gadon nai kwanciyata,inajin su suna shirin fara gogesu nidai daga haka bacci ya dauke ni. ******* An shiga hidimar biki ka'in da na'in amare sunsha kyau kamar basu ba,mai gyara ta musamman aka dauko tai aikin kwana goma aka biyata,ita dai Anti sha'awa saidai Anty Rafeea ta biya kudin gyaranta angon bai bada ba,hakan ya sosa ran Mami sosai taita fad'a cikin jama'a daker Umma ta shawo kanta tai shiru. Ko hidimar event ba wasu kudi ya bata ba duk su Anty Rafeea ne keyin komi da kudin da Angota ya bayar,shi kam ai kamar ana masa ruwan su haka yake barar dasu,abu kadan da tai masa magana zai turo dubu dari kaza,mu kam ai gaba ta kaimu muna jikinta muna kwasar rabon bu,ranar alhamis za'ai kamu juma'a ayi Arabian sai asabar dinner za'ai,duk mun shirya tsaf sauran tsararrakin mu yan uwa na bangaren uwa duk muna tare dasu kodayaushe,mufeey ce zamu nema mu rasa tana can wajen wannan mutumin,don sunan da na koma ce masa kenan,inhar zan fadi sunan sa wani kullutun bakin ciki ne yake cika mun zuciyata. Duk inda zan shiga wayata nake da Yah rafeeq ina bashi labarin komi dake wakana a bikin,Bluetooth nasa ga kunnena sai anji ina magana ake gane waya nake. Alhamis tazo aka tafi kamu wani rantstsetsen hall da yagaji da had'uwa,an shirya shi yadda ya kama ta,an kuma tsara komi bisa ka'ida yadda zai tafi ba matsala,in zaka shiga saida get pass in babu KO waye kai saidai kaja baya. Irin wankan da mukai dole ma kace munyi kyau,namiji duk taurin kan sa sai munja hankalin sa akanmu,saboda duk inda muka wuce saidai ace Masha Allah tubarakallah,ankonmu mu uku iri d'aya ne less ne mai sunan less d'an kasar chana haka Abba yabiya kud'in oder sa nida Rukee da Mufeey kudi masu tsadar gaske,baida nauyi shawal yake kamar material red ne da golden sai ratsin light purple a jikinsa,gashi mai d'inkin ya zuba fasahar sa anan wajen,dukan mu gown ce akai mana an ratsa wani abun kwalliyar d'inki tun daga kafadar dama ya ratso ta tsakiya har k'asa,gaskiya munyi kyau sosai kamar wasu triple😂 Saida duk aka tafi ina can ina video call da Yah Rafeeq,na lalace wajen sa sai santin kwalliyata yake duk ya susuce ya hanani tafiya,ni kuma na biye masa muna ta shan kaunar mu,tun Rukee na magiyar in fito mutafi har ta gaji tatafi ita da Mufeey,daker muka rabu da niyyar dana dawo kamu zamu dasa. Sadda na fito naga gidan duk ba yawa,hankalina ya tashi za ayi babu ni na fito compound ba kowa ba alamar ma wata mota,wajen umma na koma "Umma ki kira Yah Fahad yazo ya daukan pls" "To ke miya tsayar dake har kamar yanzu,ai da hakuri kikai tunda ankusa tashi" Kwalla ta cika idona ina diddira kafafu, "please Umma ki kirashi inaso inje in aka tashi banje ba wallahi bakin ciki kamani zai" Dariya take ita da wata yayarta,tace "kin san halin Fahad dai ko?" "Ki jaraba Umma kila adace ya dauka" Nan ta soma kiransa har five missed call bai dauka ba,har na soma hawaye na fito na dawo compound din gidan, ba kowa kamar anyi shara na jingina da bango hawaye na silalo mun kan make up din da aka kashe kudi kanta, can saiga Abba Habibu ya dawo Sallar isha,na kauda kai na dauka wani ne cikin samarin da suka zo biki, "Rohee lafiyarki kike nan tsaye?ba kije partyn ba" Sai hawaye sharrrr suka zubo mun, na ce "Abba duk tafiya sukai suka barni,na rasa mai kaini kowa bai nan" "To daina kukan karki b'ata kwalliyar ki,ai zakije ko?" Nai saurin d'aga kai ya ciro wayarsa ya ce, "Ramadan na gidan nan baije ko ina ba,bari yazo ya kaiki motar tana waje" Wani sanyi ya ratsani,duk da haushin sa bar barni ha har yau amma indai zai kaini banjin komi, wallahi na ce "to Abba nagode" Ya shiga kiran sa a waya bugun farko ya dauka naji yana cewa, "fito ina nan farfajiyar gida ina neman ka" Ya sauke wayar yana cewa, "kwantar da hankalin ki yanzu zaki ganki kunje" Minty biyar sai gashi ya fito,wallahi ban dauka shi bane saboda tunda bake ban tab'a ganin sa cikin shiga mai kyau irin wannan ba,shadda ce mai mutukar tsada a jikinsa kalar golden dinkin zamani rigar iyakar guiwar sa take hannun mai links,tasha aikin computer ya zauna d'as jikin rigar kanshi ba hula sai lallausan gashin sa irin na Yah Rafeeq,ya sha gyara sai daukar ido yake kafarsa cikin cover bakake,.........."gani Abba" Bai tsaya bashi wata damar zillewa ba ya ce, "Anshi key din motar tun dazu na dawo masallaci na shiga, kaje ka sauke Rohee wajen partyn nan..........daskarewa yai dajin batun Abban,amma sai bai ce komi ba ya ansa key din shi Ku ma Abban ya wuce ciki, dagowa nai na kallai yayin da shima ni yake kallo,fuskar na ba fara'a kamar kullin..........."ni drivern ki ne?" Na ya mutsa fuska bance komi ba,don burina nidai ya kaini bazan rigima dashi ba yau duk tsiyarsa, ya waiga yaga Abba ya shige,sannan ya tako kad'an gabana "ki nemi wanda zai kaiki" Cikin sauri na d'ago manyan idanuna ma sha Allah na zuba mashi su,nai narai-narai zan kuka na d'aga murya zan kwala kiran Abba, na ce "Abba.........cikin yan seconds naji hannun sa bakina,da muryar da tunda nazo duniya ban san shi da ita ba yake cewa, "shut up,are u mad?" Ganin yadda na zuba mai ido yasa yai saurin dauke hannun sa ya matsa daga inda yake, yaja tsaki yai hanyar wajen mafarin na sauke ajiyar zuciya nabi bayan sa, mamaki nata kamani ashe ya iya gayu amma yake zama da k'azanta,yanzu inkaji yadda yake k'amshi sai kai mamaki kuma k'amshin mai dad'i mai shiga rai, na tab'e baki a fili na ce "duk da haka bai kama k'afar Yah Rafeeq ba," Sadda na isa har ya shiga motar kamar munafuka na bude gaban na zauna,ina ta duba wayata lokaci nata tafiya yak'i tada motar, har hakurina ya kare na ce "kaji lokacin nata tafiya" Kamar da dutsi nake magana,yai banza dani na danne fushina ban sake tanka masa ba,sai da ya mula ya mulmule sannan ya kunna motar muka dauki hanya, kin yin gudu yai sai ya ringa nawa kamar baida lafiya,a lalace yake sarrafa sikiyarin motar had'iyar bakin cikin kawai nake,har Allah ya kawo mu Hall d'in,saidai muna tsayawa na tuna gate pass d'ina........."innalillahi na shiga uku,don Allah ka maidani na dauko gate pass dina,wallahi ba za a barni na shiga ba in babu shi" Wani lalataccen kallo ya watsa mun,ya kashe motar ya kwantar da sit yai kwanciyar sa,tun ina iya sarrafa kaina har na kasa na soma hasala,amma na danne zafin raina ina rok'onsa.........."karen gidan ku kika maidani?karki cika mun kunne pls" Abunda yace dani kenan,nai shiru ina kai kawon numfashi sai na ja k'ofar in fita ko zan samu nasarar shiga da rok'onsu,sai me?.........ya gark'ameta na jiyo ina kallon sa idona ya cika da hawaye,ba kasafai nake kuka ba sai abu ya kai kololuwar bata mun rai,..........."wai miyasa baka kaunar farin ciki na,yanzu miye na rufe kofar" Kamar bazai tanka ba har na juyar dakaina gefe naji ya ce, "miye amfanin fitar tunda baki da gate pass din" Ban sake tanka masa ba nai shiru inata share hawayena akai-akai,bakin ciki kam ai ina shan shi akan wannan mutumin,baifi saura yan mintoci ba a tashi naji ya fita amotar,can wajen masu gadi yaje bansan meyaje yai ba zuwa can ya dawo ya ce "kije kishiga" Kallon sa nai kurin kullin abubuwan sa mamaki suke ban,bai dubeni ba ya ce "kifita nace,ni ina da wajen zuwa" "Ka mai dani gida" Na fad'a cikin dacin rai wani k'ullutun bakin ciki na mamayata a zuciyata, had'iyar kuka kurin nake ban cika son nayi kuka gabansa ba,rainin zai yawa wanda zai mun...........saboda kin daukan d'an iska,kin sanya an tadoni ina hutawa ta,na kawo ki wuri sanan kice baki shiga in maidaki,watau ga drivern ki ko?" Nai shiru saboda ina bud'e bakina kuka zan saki,kirjina ke kai kawo kurin..........."darajar ubana kikaci in bacin haka" yaja k'uta kawai bai sake magana ba bai tada motar ba saida yaga an fara fitowa daga cikin Hall d'in taron,sannan ya gyara kujerar sa ya ja muka bar wurin,kamar jira kukana yake mubar wajen ya kubce mun mai rikirkita zuciya,zallar bakin ciki ne kurin cikin sa har jijjiga nake saboda yadda kukan ya taho mun,tafukan hannuna na saka fuskata aciki ina kukan,tun yana yin kamar baiji har kukan ya ishe shi yaja burki gefen titi,wanda ba mota ko d'aya dake wucewa kuma akwai duhu,hasken fitilar kotar kad'ai ne sai wanda ya kunna na cikin motar,jiyowa yai yana kallonta yajingina bayan sa da allon kujerar, yai shiru kurin. Ban fasa kukan ba saima cigaba da nayi don ji nake inba kukan nayi bazan huce haushin dake dankare a cikin kirjina ba,Naji dai motar ta tsaya amma ban ciro kaina daga cikin tafukan hannuna ba,..........*"LAYLA PLEASE"* sautin ya ratsa kunnena sosai har ya sanya mun wani irin duka a kirjina,diff naji kukan ya tsaya mun don tsananin mamaki da rud'anin abunda naji,tunda nake rayuwata ban tab'ajin bakin sa ya ambaci sunana ba,sannan bacin sunan yadda ya ambace shi shine ya kid'imani,har hakan ya tilasta mun d'ago fuskata da tayi jaga-jaga da hawaye idanuna sun canza launin su saboda kuka na zuba mashi su,ido cikin ido muka tsare juna da kallo,gabana wani irin mugun fad'uwa naji yana yi,nai saurin kawar da kaina na rasa abunyi,na juyar da fuskata wajen window sai lokacin na ga inda muke. Shiru ya ratsa motar kamar babu bil adama aciki,natsuwa ta fara shigata na duba wayata naga network ya dauke d'af,kuma lokaci yaja sosai na had'iye wani miyau na ce, cikin sanyin "it's almost eleven thirty yanzu,.........zaki iya jan motar?" Saurin kallon sa nayi da mamaki,ba dan ban iya na kawai dai miyasa zaice mun haka?kuma Abba ya hanani tuki tunda na tab'a buge wani mai adaidaita, "Aa bazan iya ba" Na sake juyar da kaina kurin,Inajin mugun son barin wajen bama wajen ba motar nake so inga bana ciki,......."ki gyara kujerar ki kwanta don ban san ranar barin mu nan ba" A zabure na jiyo ina kallon sa, ko kadan na tsani mu had'a ido idanuwan sa wasu irin idanuwa ne, sai na dauke idona daga cikin nashi kamar zan sake kecewa da kukan na ce, "don Allah mu tafi gida,inma horani zakai da haka don Allah kayakuri nidai mutafi" Shiru yai kuma inajin kallona yake ta faman yi,kafin ya ce "to ai bazan iya tuk'in bane kizo kija..........idona ya tara kwalla na ce "Abba ya hanani driving" Ya rausayar dakai yana lullumshe idonsa da sukai jaa,kamar bai da lafiyar dagaske kuma sannan ya ce cikin gajiyawa da magana, "ai yau ne kawai,kuma bazan fad'a masa ba.........Don Allah *YAH RAMDAN*" Wani irin kallo yajiyo yana mun,mai kama da na mamaki da al'ajabi,nai saurin maida kaina k'asa ina jin nadamar fad'in sunan sa,nasan shi yake ma mamakin jinake nai mugun takura da wannan zaman,haushi ya isan kamar nayi fiffike na ganni gida,nasan bacin daukewar network da yanzu an kirani yakai sau ba iyaka.........."mika ce?" Naji ya katseni da fad'ar haka,har sannan kallona yake ban dube sa ba na ce "ba komi" "Ohh na dauka magana kikai sai mu tafi.........cewa nai don Allah ka tada motar" "In Kika maimaita abunda kika ce zan tada mu tafi" Ya juyar da fuskar sa can side d'in,na rasa yadda zanyi na goge guntun kwallata ina wasa da zoben dake sanye ga ya tsana, kirjina na kai kawo na ce, "Don Allah YAH RAMDAN" Jiyo da fuskar sa yayi yana zuba mun mayun idanun sa,na juyar da kaina wurin taga kurin don na tsani mu hada ido,ni na ma rasa abunda ke damun sa a yau d'in nan............"mu tafi?" Na d'aga kai na ban dubesa ba,wani numfashi ya sauke kamar wanda yasha kuka ya k'oshi,sannan ya tada motar muka cigaba da tafiyar shiru-shiru har muka k'araso gida. Mom Muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....17 Gaba d'aya main falon gidan kowa na nan harda yan biki anyi jigun jigun,Abbanmu da Abba Habibu da Abba Nura duk tsaye Ummanmu kau sai share hawaye take,Mami ce ke ta lallashi da ban baki. Rukee da Mufeey suma sai kuka suke,cak muka tsaya nida shi bakin k'ofar entrance d'in.........."Laaaa Abba gasu nan wallahi" Cewar mufeey da muka fara had'a ido da ita, sai kowa ya mimmik'e tsaye ana ta kace na ce na tambayar mu,mun ma kasa ansawa kowa saida aka natsu Abba Habibu ya ce "Ramadan lafiya kau?ina kuka shiga har karfe shabiyu?kun san irin tashin hankalin da kuka samu ciki?" Kallon juna mukai nidai na wuce wajen Ummanmu na kwanta cinyarta, kafin naji ya lafta k'arya karon farko da naji yai karya tunda nake agidan nan........"Abba wallahi motar ce ta tsaya mana a titi,gashi ba kowa wajen daker na isa na samo wasu suka tura mun ita inda ake gyara,kuma muna ta gwada kiran ku network ya d'auke kuyi hakuri mun saku cikin tashin hankali" Yadda nake kallon sa galala haka naga Abban yana masa,sai ya sadda kai kurin bai sake magana ba,anan dai aka wawwatse shima ya mik'e yai hanyar bangaren su,har ya kulle ina kallon sa. ******** Washe gari Friday da yamma ranar ne xa'ai Arabian night,ana ta shige da fice ni dai ina d'aki abuna mun gama video call da Yah Rafeeq Rukee ta shigo ta ce, "ni kam tun jiya nake so muyi magana banga fuska ba,gaya mun gaskiya miya faru jiyan nan da daddare?" Tsaki naja kurin na diro na shiga toilet na fito,sannan ne nake cewa "wallahi duk duniya ban ga d'an rainin hankali irin wancen guy d'in ba,ke ni ban ma san yana magana ba sai jiya ashe iskan cine daman sai yai zuru kamar wani kurma hmmmm kigan shi kawai wannan mutumin..........Dariya Rukee tayi ta ce "to ai ni har yanzu banji abunda ya faru ba sai bayani kike mun" Na zauna bakin gado ina bata lbarin abunda ya faru, ta ce "uhmmm anya kuwa?" Na kalleta cikin rashin Fahimta, "ban gane ba?" "Aa mubar maganar yanzu ba zaki gane ba ai" Tatashi tana cewa bari naje wajen Mami indawo,ta fice ta barni da binta da kallo ina nanata maganarta har nagaji na mik'e na fita nima. Karfe bakwai na dare aka Fara tafiya wannan karon ban yadda an barni baya ba,xan iya cewa nice farkon shiryawa abaya ce bak'a sabuwa dal zata kai 45k haka muka siyo su rannan kuma duk Abba ne da wannan aikin,duk cikin namu mu uku tawa tafi ta kowa kyau fad'ar yadda ta hau jikina ma bata bakine,na sagala gyalenta ga kai na jefa jelar gelen hagu da dama,na saka agogo fara ga hannuna yar siririya,sai yar bag d'ina itama fara takalmana ne kurin bakake cover ne masu stones ajiki sai daukar ido suke,nai hotuna na tura ma love nai saurin kashe wayar don zai iya tsai dani yace sai munyi video. Duk mun gama shiri muka fito zuwa farfajiyar gida inda sauran abokan amarya da yan uwa suke anata dauka zuwa hall din partyn,abokan anguna ne suketa turo da motoci anata dauka,da yake bikin biyune saiya tara al'ummar sosai abokan arziki da yan uwa duk anzo, "Kuzo muje ga motar abokin Yah fuad can mijin Anty Rafeea saiya kaimu kafin wasu su shiga" Muna isa muka ga sun fito shida wani........mamaki ya kama mu ganin shi da Yah Ramadan,kallon mu suke muma kallon su muke,kyakkyawan four eyes mukai nida shi,nai saurin juya wa ko gaida abokin mijin Antin banyi ba,zuciyata naji ta doka sosai naji Abokin ya ce "ina zuwa Rohee?kuzo muje mana" Na waigo ina yak'e tare da in ina ina cewa "ai......ai da....sai dan anjima zamu tafi" Koda nake maganar bai fasa kallona ba,saima ya jingina da kofar motar yana crossing legs dinsa ya cigaba da kallona, mufeey ke gefensa tana magana amma ba ita yake kallo ba, ya ce "to jiran me kuke yi ne Rukayya?" Rukee na murmushi ta ce, "aa ba komi ban sani ba ko ita akwai abunda zatai ciki,mudai mun gama komi" Na dalla mata harara murmushi yayi yana cewa, "RAMADAN muje ko sai mu kaisu" Ya tilla masa key d'in motar,Rukeey da mufeey suka fara kokarin shiga,dole nima nabi su na shiga suka sani tsakiya duk haushi ya isan, wallahi wallahi duk abunda zai had'ani dashi bana son shi,kwata kwata ni ko a hanya ma bana so ina ganin sa,balle daga jiya zuwa yau wani irin mutum ya zama,bazan ma iya misalta yadda yake abubuwan sa ba,babu ma mai fahimtar ga abunda ke faruwa inba ni ba, to miyasa??? Na tambayi kaina wanda vanda ansar hakan. Duk jallabiyoyi ne jikin su ta abokin angon ash ce tai masa kyau,shi kuma tashi fara ce sol sabuwa ma kau fadar yayi kyau b'ata bakine,don ya wuce kima sai miskilancin sa ya k'ara masa kyau,motar ta dauki sanyin Ac da wani irin k'amshi na turaruka da suka had'u,ga nasu najikinsu gana motar sai namu dayake da sanyin k'amshi,wani yana yi ya shigeni inama ace Yah Rafeeq na nan,wayyo Allah da anyi kauna iya kauna wannan bikin,amma kashh hakan bata samu ba,tunda muka fara tafiya firar su kawai suke da juna su dukan,amma ni nama kasa ciro kaina daga k'asa saboda gudun abu daya, shine mu had'a ido dashi duk da vanda tabbas din hakan,tunda tuki yake tun ina iya jure wa har kaina yasoma rik'ewa dole na d'agoshi,kamar wasa kau idona cikin nashi ta center mirror wani kallo na samu,ban san ma'anarsa ba yau fuskar sa da wata irin walwala da ban saba ganin sa da ita ba,sai annuri yake samun kaina nayi da danna masa harara na juyar da idona,jinai kurin motar tatafi dakarfi kuuuuu duk saida muka tsorata,daker ya taka burki yaya deeni ya ce "lafiyarka kuwa?kamar wani sabon driver haka abokina" Kanshi ya shafa daga keya zuwa gaban kanshi yana cewa calmly "I'm sorry wallahi kaina ke ciwo shiyasa" Rukee da mufeey sukai masa sannu,ya ansa yaya deeni ya anshi tukin shi kuma ya koma inda yaya deenin ya tashi,sannan muka cigaba da tafiya yaya Deenin ya ce "ko mu tsaya ka siya magani kar muje karar kid'a ya kara maka ciwo" Lamo yai cikin kujerar yace, "No it's normal zai sauka ba sosai yake yi ba" Tab'e baki nayi nasan karya ce kawai,tunda kwana biyu ya zama shugaban makaryata har muka iso wajen taron bai sake mgn ba,ni daman uffan bance ba,wow,wow wallahi wajen yasha decoration sosai da gani an kashe kud'i over,Rukee har ta soma tsuma saboda kid'an wajen da aka sanya,Mufeey ma haka ni dai rawa bata daban ba,kunya ma nakeji gaskiya. Babban wajene aka kama sai aka fito daga farfajiyar wurin aka shirya shi sosai yai kyau,can ciki akwai wurin hutawa har toilet akwai da dakuna,da gani kasan an kashe kudad'e mukai parking inda ake aje motoci muka fito daman saida mukai sallar magariba muka fito,duhu yayi sosai sai hasken fitilu ta ko ina,akwai tables da aka sanya kowane table kujera hud'u uku ce a wajen,an dora flowers akai da plate's an zuna snack's a ciki da tsire da pies din kaza uku sai friut drink,sai plax d'in shayi kowane mutum da nashi a gabansa,abun yai tsari sosai mufeey da Rukee wajen kida suka tafi suna rawa,ni kuma na zauna kan kujera yaya Deeni suna tsaye gefena suna magana,amarya basu iso ba sai anjima kad'an. Na rasa abunda ke mun dad'i duk d'okina na zuwa wajen ya fita kaina,wani iri nakeji duk damuwa ta isan na ciro wayata ina kunnawa na samu sak'on love yana cewa, _"uhm Rooh wannan kyan naki yana bani tsoro,ina wata duniya ke kina wata yadda Allah yyiki dole duk wani namiji yaji kin shiga ransa,please take care for ur self,koda wasa karki ba wani damata kinji Rooh d'ina,i love u so much"_ Murmushi ya kubce mun naji sanyi a raina na maida masa da nawa kalaman masu dadi da kwantar da hankali,baya online nasan daya d'ebe mun kewar da nake ciki,plax d'in black tea din da aka aje na dauka na zuna a cup na saka sugar cube d'aya don bana son zak'i sosai,na zo kaiwa bakina kenan naji ya b'aromin a jikina duk rabinsa ya zube, wani irin haushi ya kamani na aje cup d'in na mik'e. "Ina zuwa Rohee?" Cewar Yaya deeni,kamar zan kuka na ce cikin sanyin murya "tea ne ya zubar mun zanje na wanke ne" "Kinsan toilets d'inne?" Na girgiza kai kurin,suna tsaye tare dashi nidai banko kalle sa ba,Yaya Deenin ya soma mun kwatance sannan na ce "nagode" Na tafi inajin ido yana bina kamar zan kifa. "Baka da kuzari Abokina,anya ciwon kai kad'ai ne ke damunka?" Cewar Deenin yana kallon RAMADAN din,lumshe kyawawan idanun sa yayi yana magana gently, "Aa bakomi kasan wani lokaci zakaji bakajin dadi" "Hakane Allah ya kyauta,ka zauna anan bari nayi waya a mota please amaryata keta kirana tun dazu banso ta damu ko ta dauka ina tare da yan mata" murmushi yai masa kurin sannan ya juya ya koma inda sukai parking. Daker na gano toilet d'in na shiga na kunna famfo na wanke inda ya b'ata ni a rigata,inata tsaki ji nake ma kamar na koma gida kwata-kwata babu wani annashuwa a raina,na gama wanke war na fito zan koma can kawai naji na bugi mutum,wata irin k'ara na fasa yai saurin rufe mun bakina, zuciyata kau kamar zata fito waje don tashin hankali,don wajen lungu yake kuma ba kowa,dole nake tsorata yanzu dana gane waye sai na sake shiga tashin hankali,nai baya ina ture hannun sa daga bakina na aro jarumtata duk da yadda gabana ke fad'uwa, muryata na rawa na ce "miye haka?akan me zaka biyoni har nan,kasan hukuncin ba mutum tsoro a addini?" Dafa bangon dana ke jingine yayi da hannunsa,yana tsura mun idanun sa yake cewa "Aa ban sani ba sai kin gaya mun" Na juyar da kaina gefe inason nagudu amma ya tare hanyar, "zunubi ne babba" "Ita kuma Harara miye hukuncin mai yinta?" Na jiyo da fuskata muna fuskantar juna,idona cikin nashi ya tsare ni da su nagaza dauke kaina, jinai ya ce "bakiji ba?" Nai saurin dauke kaina ina cewa, "oho ni bansan ba" "Amma ai kinsan na mai ba mutum tsoro ko?" Na masa shiru,ya sauke hannun sa daya tare hanyar aiko nai zuruf zan fece jinai kawai ya cafke hannuna,cak na tsaya ina runtse idona dawo dani baya yai ya tare duk hanyar da zan ruga yana tsaye gabana hannuwan sa cikin aljihun jallabiyar sa,nak'i kallon sa balle ma ingane yana yi..........."ki mai-maita?" Saida na nanata maganar a raina kafin na jiyo ina kallonsa, na ce "ban fahimta ba" Taku guda ya kara tsakaninmu ya tsaya yana cigaba da kallona,ni kuma na juyar da fuskata "Hararar da kikai mun na kusa accident" Idanuna duka a warwaje girar sa d'aya ya d'age na b'ata rai, "ashe ma,to ni banma san da kai ba" "Really?" Naci daci naki bashi ansa,takunsa zuwa inda nake naji na jiyo da sauri ina ja baya, bai fasa bina ba nima ban fasa ja baya ba,saina na dan gane da k'ofar toilet d'in,hankalina ya tashi sosai dan danan idona ya raina fata zan kuka har ya tara ruwa "ba....bana son wannan a....abun" "Mai maita Hararar da kikai?" "Ni.....ni....ban hararek,hannunsa ya saka ya dafe kofar kusancinmu yakaru sosai,nimfashina nake ja ina hawaye,......."Don Al......don Allah ka matsa anan" "Zaki Mai maita ko aa?" Na fara shashshekar kuka,"please kayakuri" Na fad'a cikin rawar murya cike da tashin hankali, "Aa bazan yi ba gaskiya,ai kince ke bakisan dani ba ai.......Aa na sani kayakuri" "In Kika sake zanyi hakurin" Ya Dora gudan hannun jikin k'ofar,ya sani tsakiya tsakanina da kirjinsa kamar tsayin biro ne,hawayena suka k'aru cikin rawar murya mai cike da tsiro,ina shashshekar na ce "kayakuri" *"Aa LAYLA"* Ya fad'a da wani irin sauti,silalewa k'asa nayi na saka kaina cikin guiwata ina rera kukan bilhakki da gaskiya, na rasa inda zan saka kaina bana son abunda yake mun ko kadan, dirkushin sa naji gabana muryar sa ba kamar sadda ya fara mun magana da farko ba, calmly ya ce "zaki kara Hararata koda wasa?" "Don Allah YAH RAMDAN kayakuri" Hannunsa yasa yana shafar gashin kanshi yasaki iska kad'an sannan ya ce can k'asa, "it's ohk,tashi" "Kaje Zan taho.......Aa tare zamu fita" Ya katseni da fadar hakan,na ciro kaina daga cikin guiwar ina mik'ewa tsaye don ma wajen tayils ne yasha guga babu datti da sai kayana sun b'aci, bud'e mun k'ofar yai na shiga na wanke fuskata, ya mik'o mun hanky sa na ansa ina tsane fuskar,na mik'a masa muka fito. Wajen ya sake cika mak'il,ga duhum dare yayi muna ciki bamu sani ba,har amare sun hallara anguna anata gudanar da partyn yadda ya kamata,komi inka kalla very nice cikin tsari da wayewa,kasa tsaya wa wajen nayi na wuce can wani wuri na ke'b'e kaina,amma ina iya hango komi da yake faruwa,shi kuma ya wuce wajen motar yaya Deeni ya hau sama daga wajen but ya zauna. Saida aka fara picture's sannan naje akai ta mana dasu,ina iya hangoshi daga wurin baida niyyar zuwa ayi picture's din dashi,to daman ni haka nake so muka sha hotuna kala-kala,sai daga karshe naga Mufeey ta ruga ta jawo shi yazo akai masu shida ita,tana ta wani shige masa ko kallo basu isan ba,akai masu da amaren inajin tana rokon karya tafi amma saida yabar wajen,duk wanda yazo saida ya koma da jikka mai dauke da sunan angowayen da amaren,masu kyau haka aka rarraba ma kowa. Ba a tashi ba sai wurin karfe shad'aya sannan kowa yai haramar gida,yawanci duk abokan angon suka mammaida mutane gida,wasu kuma suka tafi da kansu. Ina tare da Anty Rafeea naki binsu Rukee a motar Yaya Deeni,suna can suna jirana ni kuma nak'i tafiya, saiga Yah Deenin da kanshi ya iso wajen, "Roohee ke muke jira" Na b'ata fuska ina kallon Anty Rafeea na ce, "zan taho dasu Anty nidai" Murmushi yayi yana mun rad'a kar Anty taji, "ke kau waye yake shiga motar ango da amarya,ki kyale su kizo mutafi please" Kallon mu Anty keyi cikin rashin fahimta ta ce, "Deeni yadai?ko kana ciki da yar qanwata?" Dariya yayi "Aa haba kod'aya ki rufa asiri kar kija mun bore a gida " Tayi dariya kurin,sannan tace mun "miye ne wai kike ta cin d'aci keda wa?" Na kalli Yah Deeni sannan nace mata "bakomi" Na bisa muka tafi,wannan karon shine kejan motar Yah Ramadan na gaba,motar shiru Rukee har da bacci Mufeey ce kawai keta chat d'inta,har muka iso gida bamai mgn,kamar jira nake motar ta tsaya nai saurin ficewa cikin gida,Mufeey ta tada Rukee suka wuce ciki suma. "Aboki na da magana abakina fa" Sai sannan Ramadan ya bud'e idonsa yana kallon sa na yan second sannan ya maida idonsa ya rude ya ce calmly, "talk" Deeni na murmushi ya ce, "anya ba akwai wani abu tsakanin ka da yarinyar can ba,na kasa ganewa fa" Wani d'an iskan kallo Ramadan yai masa kafin ya ce, "wake nan?" Dariya Deeni yayi ya ce, "Aa karka mun halinka mana Abokina,wace yarinya fa inba Rohee ba" Dogon tsaki yaja yana bud'e gaban motar ya fito,shima ya bud'e ya biyo sa ya ce "ya zaka wani fito muna mgn" Ya dube sa sosai sannan cikin sassanyar muryar sa mai dad'in saurare, "kar ka sake mun wannan mgnr please" "Miyasa?bacin ga gaskiya nan b'aro b'aro............DEENI!," Ya kirasa da d'an karfi sannan ya ce, "LAYLA qanwata ce,babu wani abu mai kama da abunda kake tunani tsakanina da ita, beside ma Rafeeq ne suke dating da ita,akan me zaka ringa wannan mgnr pls banaso" "Sorry Abokina na daina" "Zan wuce ciki sai da safe" Deeni na murmushi sukai musabaha kowa ya kama gabansa. Mom Muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....18 Daga wannan ranar zan iya cewa van sake saka fuskar sa ga idona ba,har aka kammala biki lafiya dangi duk suka watse kowa ya koma gidansa, su Mufeey ne kawai basu kai ga tafiya ba,mu kuma muka koma sch saboda mun shiga sabon session. Mufeey basu tafi ba sai bayan biki da sati uku,ji mukai kamar kar tatafi wata irin shak'uwa ta sake shiga tsakanin mu,balle yanzu bama fad'a sosai muyita shiriritar mu tare muje islamiyya tare duk wani abu da zai d'ebe mana kewa tare mukeyin sa, shiyasa har kuka mukai da zasu tafi ranar,Yah Ramadan ya kaisu tashar jirgin k'asa,da nayi niyyar rakasu inajin shine drivern na fasa,nace karatun test nake munyi bankwana suka tafi abun su. Soyayyata da Yah rafeeq uhmm ba acew wa komi,yanzu ba abunda muke sai lissafin dawowar sa,don yace a Nigeria zaiyi house menship d'insa,shiyasa walwata ta k'aro ainun kullin cikin lissafi nake,har Rukee ta gaji dajin labarin ranar dawowar sa,irin tarbar da zan masa da irin abunda zan shirya masa da kaina,musamman na shiga class na snacks a online cikin sati guda na iya abubuwa guda bakwai,duk da na kashe kud'i sosai amma bukatata ta tabiya. ********** Akwana a tashi baby wuya wajen ubangiji sai gashi mun shiga shekarar karshe a sch,wanda yai dai-dai da haihuwar Anty Rafeea don wata rata cib tayi ta haifo mana ummanmu, muna kiranta da Iklas anty Sha'awa dai cikin bai isa haihuwa ba,ansha suna sosai anyi bajinta kwarai da gaske wajen wannan suna,uban yarinyar ya zubar da naira sosai kowa yazo sai yatai da su a bakin sa saboda irin bajintar da akai.............still naji Mami na cewa wata qawarta "kinga irin abunda nai ma Sha'awa fata nan hajiya rabi,amma ita da ubanta suka watsa mun kasa ga ido,ki duba kiga yadda ake facaka da kaji da namomi,kiga abinci kala har goma akai dubi irin jikkunan da aka rarraba cike da snacks da kaji,don bakiga jibga jibgan ragunan dake can baya ba da aka yanka,haba wallahi sha'awa ta cucemu" "Ai duk laifinki ne Safiya,halinki ne yaja miki yo in nice wallahi y'ata ce cikin wannan daular...........Mubar maganar nan dai kawai Hajiya Rabi,haka Allah ya k'addara". Ban sani ba ko ganina yasa suka bar mgnr,oho nidai tashi nai na basu waje daga cikin falon,ina mamakin Ammi akan son dukiyarta duk irin kudin da Abba Nura yake kashe mata bata gani,ban wani maida abun babba na cigaba da hidimata ban kuma yi mgnr dakowa ba,aka gama suna kowa ya watse raguna uku tik'a tik'a aka yanka,munsha aikin soye washe gari. Anyi sunan Anty da sati uku Yah Rafeeq yake sanar dani albishir din tahowar sa cikin satin,wayyo Allah na karka so kaga murna wajena a lokacin ne Hajja ta fara ankarewa da halin da aka ciki,Ana gobe dawowar sa ne ta kirani bangarenta in mata aiki,daman kuma mune masu mata gyaran komatsanta intatashi nidai Rukee, Bayan na fara aikin inayi ina janta da tsokana muna wasa da dariya,har ta sako maganar da take son yi mun, "wai ni kam takwarata Kodai da yayanki za'ai abun nana ne?" Dariya ta kamani na boye kaina cikin filo nak'i magana, ta ce "ja'ira ehy din ce ke wahalar fadi shine zaki mun irin abun y'an da,shakiyya ai ni naga alama ai ubangiji yasa ayi damu to" Daga haka bata sake cewa komi ba,mukai ta aikin har na gama mata taita samun albarka,daga ranar kuma bata sake tashin maganar ba,ni a tunani na bata da wata matsala da alakarmu,tunda yan uwan junane kuma ba wani aibu tattare da hakan,karewa ma zumunci ne za'a kara karfafawa, Ashe akwai k'ura baya bamu sani ba. Ranar da Yah Rafeeq ya dawo tana daga cikin ranakun da bana mantawa, saboda na tsinci kaina cikin farin ciki marar misaltuwa,kowa saida ya gane ina cikin farin cikin dawowar sa,gidan kanshi kanshin girke-girke na yake tunda gari ya waye nake abu guda har bayan sallar magariba,don saukar Dare zasuyi ina gama komi na ruga nai wanka,Rukee ta tayani zab'en kaya sanyawa wasu sabbi ne dana d'inka musamman don dawowar sa kala hudu,na zab'i wani material mai dan karen taushi da sulb'i yai mugun kyau ainun,sannan telanmu ya zuba fasahar sa wajen tsara mun gown d'ita don yace gown tafi yimun kyau,banyi make-up ba yace mun yafi son yai tozali dani fuskana fresh,daman kuma nasha gyaran jiki kamar wata amarya,amma aboye nayi Anty Rafeea da Rukee kawai suka sani,fatana tai wani irin lukui sai daukar ido take har umma saida ta tanka mun rannan, take cewa "Rohee kin fara shafa whitening cream ne?" Nace"Aa Umma wallahi bana shafa shi,kila zafin nan ne kin san cikin zafi haka skin d'ina yake yi" Sai ta yadda kuma,amma ni nasan karya nake kayan gyaran Anty Rafeea naita amfani dasu,bani kadai ba duk yan gida jiran isowar sa ake,karfe takwas jirgin zai sauka na gama shirina sai kamshi ke tashi kamar wadda aka daura ma aure,no kadai nasan yadda nakejin zuciyata akan Yah Rafeeq,ji nake in ban auresa ba zan iya rasa raina. Abbanmu ne ya ce, Yah Ramadan zai je dauko shi,a ranar banji inajin haushin sa ba kuma bance bazan je ba, saboda farin cikin da nake ciki ban damu ba nace ma Abbanmu, "Abba to don Allah kace yaje dani" Kanshi sadde lokacin a falon Abbanmu,Abban ya ce "ai gaki gashi nan saiki rok'esa" Cikin shagwab'a nake ce masa, "Kaji YAH RAMDAN, kaje dani don Allah" D'an ciro kanshi yayi ya mun kallo daya sannan yace, "ohk" Nadaka tsalle na ruga don dauko gyalena,sadda na fito har yaje wajen mota na bud'e gaban na zauna na rufe ya sanya Ac saboda zafi, ya na yinsa kamar wanda yake rashin lafiya,tukin ma kamar baya so bance masa komi ba nidai sai faduwar gaba danaji inaji ban sani ba ko haduwar face to face zamuyi da Yah Rafeeq ce, inata zuba masa kalamai a waya yanzu kau ai nasan karya nake in kalli donsa in masa su, har muka iso nida shi kamar kurame karfe bakwai da rabi muka iso dole mujira na minty talatin. Har nakai wajen da aka tanada don jiran baki banji Alamar ya biyoni ba, koda na juya na waiga yana can cikin mota abun sa,dage kafada nayi na samu waje nai zamana ina duba time lokaci zuwa lokaci,banzo da wata shaida da zata sa ya iya ganoni cikin sauki ba,don haka idona akan hanya yake har sadda lokacin ya cika,munajin dirar jirgin dan danan naji zuciyata ta soma bugawa nai nadamar tahowa ni kadai inama Ruky ta biyoni kila da nasamu courage,ahankali mutane suka fara bayyana kowa yana zuwa don tarbo wanda yazo domin sa,zuciyata nata bugawa inata zuba ido amma banga mai kama dashi ba,har na sare da tsayuwa zan koma na zauna kawai naji anyi mun d'ass da yatsa a fuskana, a firgice na jiyo don na tsorata...........caraf mukai kyakkyawan four eyes dashi,mugun daskarewa nayi a inda nake saboda kwata-kwata ya rik'ide mun ya canza muguwar canza wa, wani irin had'ad'd'an murmushi ne yake saki mai dan karen kyau a fuskar sa, yayin da kamshin sa ya cika mun cikina tab tsabar dad'insa, kafin na dawo hayyacina naji dadda'ar muryar nan tashi ta ratsa kunnena yana fad'ar, "Easy mana Rooh,karki cinye ni tun anan bamuje gida ba" Muguwar kunya ta ratsani na boye fuskata cikin tafin hannuna,Ina murmushin farin ciki da annashuwa wani irin kaunar sa na sake samun waje a zuciyata, cikin shagwaba na ce masa "nifa bangane ka bane,halan ma an canza mun yayana" Yar dariya yayi mai kyayatarwa,ya dan matso kusadani yana kallon fuskata kamar me rad'a ya ce "Nima Love d'ina kamar an canza mun ita,u look so cute and more beautiful" Wani iri naji sosai na sadda kaina kasa murmushi sosai, na kasa cewa komi ganin duk kunya ta isheni yasa ya ce, "ke da wa kuka zo?" Na nuna masa hanya Ina cewa, "muje ka gani da idonka ma na" Yana jaye da trolling dinsa ni kuma na daukar masa bag d'in muna tafiya zuwa parking space din motoci,sai tsokana ta yake daman ba kuma gwanine wajen tsokanar mutane,munzo wajen motar kenan suka had'a ido da shi,kallon juna na seconds sukai ma junan su ba wanda yace ci kanka, Yah Rafeeq ya zaga ya bud'e But da kansa ya saka akwatin jikkar kuma ya saka ta a gaban motar,ya bud'e mun baya na shiga sannan shima ya shigo yana rufewa, fira ya fara mun Ina biye masa muna dariya, jira muke muji motar tatashi amma shiru har saida na ce, "lafiya kuwa?" Kafadar sa ya dage sama alamun bai sani ba,kuma ga Yah Ramadan din nan zaune wayarsa yake dannawa, na hadiye miyau na daure na ce "Yah lafiya bamu tafi ba?" Kusan minty uku baice komi ba,saida ya mulmule sannan ya ce "waye drivern ku?" Sai na gane cewar zaman mu duka a bayan ya jawo rashin tafiyar,duk da raina ya sosu sai na danne na ce , "ayya to bari na dawo gaban.......rik'e mun hannu Yah Rafeeq yai dan danan har ransa ya baci gashinan a fuskar sa ma, "ba inda zaki,in bazai ja ba ya fita yatai" Bazan so ai wanan rigimar ba daga isowar sa KO ruwa bai sha ba,na ce "miye aciki Yah Rafeeq just 40minutes ne fa sun kaimu gida kayakuri kaji" Dole ya kyaleni na koma bayan,amma sai tsaki yake da karfi nidai kagare nake mu isa gida saboda a rabu lafiya, na rasa wace irin rashin jituwa ce tsakanin su,duk nima ba wani shiri muke ba amma takun sakar yafi karfi tsakanin su,duk yadda naso jansa da fira muje gida kiyawa yayi,dole naja bakina nai shiru abun yai mun ciwo sosai,kamar sabbin kurame haka muka iso gida. A fusace ya buga kofar motar ya fice,ko waigena baiba abun ya sake bata mun rai watau kaina zai huce aiko wallahi zai gane kurensa,ko jikkar tasa van dauka ba nabi ta hanyar bangaren Abba Habibu na wuce dakinmu, ban samu Rukee ba nasan tana can falo ana jiran shigowar mu,gyalena ya yakice na jefar na kwanta rubda ciki bisa gadon kurin, raina inyai dubu ya baci toni miye nawa aciki?don kawai na bi hanyar da zata hana rigima da tashin hankali tsakanin su? Ban san iya lokacin dana dauka a haka ba,sai ga Rukee ta shigo "Aaha,ke kuma nan kika yo ana ta cigiyarki?lafiyarki kalau kuwa?" Sai kurin na sakar mata kuka saboda iyakar k'ulewa na k'ule da abunda yai min, mamaki ya kama Rukee tai saurin zama gefena tana cewa, "kece ke kuka yah Roohe?abun yai zafi haka?" Ni kaina nayi mamaki yadda kuka ke min wahala amma yanzu abu kadan kuka, "wallahi saiya biya wannan bacin ran,duk irin kokarin da nake akansa shine zai saka mun da haka.............daidai sadda mukaji shigowar mutum,dago kan da zanyi nagansa tsaye hannuwan sa cikin aljihun jeans dinsa, saurin kawar da Kai nayi Rukee kuka tatashi ta fita, kamar daman jiran fitar ta yake yai saurin isowa bakin gadon ya zauna saman bedside, nai saurin tashi zan matsa don a hangule nake, amma sai ya rik'eni gammm yak'i sakin hannun, sai na sanya kuka mai karya zuciyar duk wani lafiyayyan namiji, dan danan ya fara rawar jiki "Rooh sorry pls I'm very sorry,I don't mean to hurt u naji ba dadi ne yadda kika biye masa akan ra'ayinsa, amma banyi don bacin ranki ba,nayi laifi kimin afuwa wallahi kukan ki yana kassarani,zan iya kamuwa da rashin lafiya please Love pls pardon me" Shashshekar Kukana kurin nake lallashin da yake min yasa nafara sabkowa,ba abunda nake so idan Ina kuka sama da lallashi da tattausan lafaxi, haka yaita gaya min dad'ad'en kalamai har naji nad'an huce, na daina kukan sai jan majina nake, "ki yafe mun na sanya kin zubar da kwallarki akaina," Kaina na jinjina kurin bance komi ba, "muje ki zuba mun abunda kika hadamun,bazan iya cin komi ba in bakya gefena" Makale kafad'ana nayi ya sassauta muryasa sosai ya ce, "Ayya my love I'm feeling hungry" Harara na masa na dauke kaina,sai ya saki wani kafirin murmushi mai kid'imani, "naji komi zaki mun zan dauka nidai zaki tashi muje,bazan iya asarar wannan delicious d'in naki ba pls Rooh dina" Da wadannan kalaman ya siye mun zuciya,daman kuma ban iya dogon fushi dashi ba,soyayyarsa bata barina nayi hakan. Ana ganin mun fito tare aka saki baki don sunyi zaton tunda nayi fushi to fa bazan fito ba, dariya aka kama yi mana wai duk wanda yashiga fadanmu zaiji kunya, sai gashi inata murmushi yana mun fira yana zolayata sai santin duk abunda na zuba mishi yake, saida kowa ya watse yabar mu anan, fira mukai tayi ko ince kauna don kamar mu kad'aine a duniyar haka muka ringajin kanmu, naita narkewa kamar wata kankara,saida Allah ya jeho Abba Nura ya ce "firar ta isa duk kutashi kuje ku kwanta" Lokacin daya da rabi tama wuce sosai,badan rai ya soba saida ya biyoni zuwa hanyar dakin mu Abba ya ce, "kai! Ina zaka?" Sosa Kai yayi yana cewa, "raka ta zanyi Abba" Dak'uwa yai masa yana nuna masa hanyar dakin sa, "ban son sakarci kajiko" Dole ya kyaleni amma har yakusa kullewa yana waigo ni, ranar Ina bacci amma murmushi nake ina jinjina irin kauna da soyayyar dake cikin zukatan mu,Ina tunanin to in har Auren mu bai yuwu bafa?cikin sauri nake kauda wannan tunanin don lokaci guda zanji hankalina yai kololuwar tashi,daker nai addua na kwanta. Mom muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....19 Washe gari dana tashi kamar wacce mijinta yai tafi tsayin lokaci ya dawo,haka na kasance nice shirya wannan gyara wannan haka nai tayi na hada masa lafiyayyan breakfast da kaina,wanda ko yai mamakin ganina a kitchen tunda ba sana'a ta bace,na gama naje nai wanka na d'an d'asa kwalliya kamar zanje biki,Rukee dai har ta daina mamakina ma saidai tayi murmushi kawai ta kauda kai,yanzu ma abunda tayi kenan na jiyo ina ce mata, "Na miki uziri baki san gard'in soyayya ba,dakin sani ba zaki ga laifin abunda nake ba amma muje zuwa akwai ranar da zaki zo kina neman shawarata akan kin afaka rijiyar kaunar wani..........dariya ce ta kwace mata ta ce "Allah ya kyauta mun,bana fatan shiga soyayya irin wannan, don cutuwar ta tafi dad'inta yawa,ni hasalima kin ganni nan bana son duk abunda zai hanani sukuni a zuciyata, bance miki bazan yi soyayya ba,tabbas zanyi watarana tunda dole muyi aure amma irin wannan da kike ma Yah Rafeeq uhhh aa gaskiya tayi yawa,ace baka iya ganin laifin mutum inyai maka?kuma baka iya dogon fushi dashi?sannan bakajin kunyar kowa indai akanshi ne?uhhh Aa ba irin wannan ba sai sa sai sa dai mastad'aa" Dariya ma na kama yi mata nace, "we shall see" Na gama kwalliyata na fita zuwa bangaren su Mami,amma saida na biya na gaida Abba na iske Hajja tazo wurin sa suna magana, duk kallona suke kamar wata sabuwar Halitta. Abban ya ce "Ina zuwa mamana?" Na sunkuyar dakai Ina murmushi "Ba ko Ina Abba,gaidaka nazo inyi kawai?" Murmushi yayi ya ce, "Aa gaya mun gaskiya dai?" Na soke kai Ina dariya,Hajja ta ce "zai wuce wajen Rafeeq zataje" Abban ya ce "wai haka?" Na d'aga kai alamar ehy,murmushi yayi sannan ya ce "to a rage rawar k'afar nan kinji ko?kuma a rage shigema juna" Na jinjina kai na kasa magana saboda naji kunya sosai, "jeki abunki,kice da Abbanku Nura Hajja na jiransa anan" Sadda na isa bangaren Mami na iske falo tana shirya dining na gaidata,Ina ansar kayan na soma shirya mata, na ce "Mami Abbanmu yace agaya ma Abba Hajja na jiransa" Ta amsa da cewar bari taje ta sanar dashi,tana tafiya nai wuff na wuce dakin sa,kwance yake yanata bacci na fizge bargon daya rufa aiko yai firgigi ya tashi, aiko na kama masa dariya yai k'urii yana kallona da idanun sa cike da Bacci,sai suka kara kasa kyau sosai naji wani abu ya tsarga mun,na hade hannuwa na alamun ban hakuri "afuwan Yah,ka koma ka cigaba da baccin ka bazan sake tashinka ba" "Ai wallahi karya kike yarinya, ni zaki tada kuma kice na noma nacigaba da baccin,bacin kinfi kowa sanin in natashi bana iya koma wa,bayani zaki.......ya diro daga bisa gadon yana niyyar biyo ni,aguje na yo hanyar waje Ina tsuwwa caraf ya cafke hanuna daidai budewar k'ofar, mukai ido hud'u da Yah Ramadan,kallon mu yake muna kallon sa kafin Yah Rafeeq yaja wani dogon tsaki yana yin kamar bai ganshi na,,ni kuma sai kokarin anshe hannuna nake yaki sakina, "waye yace ki tadani,don haka koki biyani baccina ko kuma bake ba fita dakin nan,anan zamu yini baci ba sha.............Kazo Abba yana kiranka" Abunda Ya fad'a kenan ya juya yai gaba,shi kuma kamar anyi mgn da dutsi bai ma nuna dashi ake mgr ba,magiya naita masa ina cewa "wallahi ba da niyya nayi ba,zuwa nai na ce maka kazo nayi maka breakfast mai dad'i sai muci tare" Kokarin had'e ni yake da jikinsa,nikuma inata ja baya gabana na fad'uwa,duk karfina saida yai nasarar sani cikin kirjinsa,wata nannauyar ajiyar zuciya muka sauke muduka,sai kuma mukai shiruuu,zukata nata biting sosai ahankali na zare jikina gabana na fad'uwa na fice daga dakin, Breakfast din saidai yazo ya dauka da kanshi,kasa sakewa nayi bare muyi tare,kunyar sa ta cika mun ciki shikau ko ajikinsa yakeji, ranar lectures din yamma garemu nida Rukee shine kuma ya kaimu ranar,karfe bakwai na dare muke tashi ya koma ya dauko mu,ya biya damu shopping muka siyo kayan zak'i sannan muka tsaya wani bakery muka siyo cake ice cream da sauran su,ya kashe mana kudi sosai muka dawo gida. Daga wannan rana shi ya zama yana kaimu sch inda baya komi, sannan yaje ya dawo damu hidima yake mun kamar dai anriga an bashi ni, bayajin komi abu duk tsadarsa ya siya mun,kayan kwalliya dana gayu baya gajiya da siya mun,haka kayan shafa masu masifar gyara fata don zan iya cewa shiya lalatani da bana iya amfani da wasu maya-mayai inba dove da Nevia ba,ko wane set dinsa yake siya mun banda su shampoo na wankin gashi turarukan jiki dana kaya,Dana gashi kai yah Rafeeq har turarukan Hq da sabulan tsarki siya mun yake,tun Ina nuna haushi dakunya har na daina,don fara House man ship dinsa abun yakaru,don duk wata yanajin alert na dubu dari biyu asibitin da yake aiki, baya komi dasu sai hidimata da tashi sai Rukee. Yaje gidajen su Anti Rafeea da Anti sha'awa ya kai musu abun arziki,kuma duk tare muke zuwa inka ganmu zaka dauka sabbin amare ne tsabar yadda jikinmu yake glowing yana wani fresh tsabar jin dad'i da kuma kud'i da ake kashe ma jikin,sannan sitira yinsu yake kamar me duk sati saiya je boutique donshi yana son kananun kaya, nima kuma zaisiyo mun duk abunda ya siya ma kanshi. Idan bamu zuwa ko Ina to tabbas muna lambu ko farfajiyar gida muna fira,ko wasanni volleyball ko basketball irin wannan lokutan muka fi haduwa da Yah Ramadan,kallo bamu isheshi ba nice ma nakan iya cemasa Ina wuni,zai ce lafiya kawai ya wuce. Yah Rafeeq ya ce, "ke banga kwakwar dakike ta gaida mutumin da bai damu dake ba,nifa gaskiya vana so ma inga ko kallonsa kinayi" "Arzikin Abbanmu yakeci kai ma kasan ai bai daman ba,akwai alkawarin da Abba yasani na dauka shiyasa,amma badan wai na huce daga jin haushin Saba" Ire iren wadannan maganganun muke yawan yi inmun ganshi,tun Ina gaidashin har na daina saboda hudubar Yah Rafeeq d'in,rayuwar gwanin dad'i yanzu nakan mance da wani b'acin rai ko damuwa,kuka kam tun ranar da Yah Rafeeq ya dawo ban sake yinsa ba,baya bari na nuna damuwata sosai. Akwai abunda yake daure mun kai,sau uku hakan na faruwa ban dai sanar da kowa ba,watarana munyo saloon nida Rukee to tarigani tahowa sabo kiran da Mami tai mata na gaggawa,sai nayo dare ban iso gida ba sai bayan sallar isha'i Yah Rafeeq na wajen aikin sa balle ya dauko ni,muna daf da isowa naga napep ya tsaya wata mata ta fito da dogon hijab jikinta da nik'abi a fuska,ta shiga gidanmu. Amma koda nashiga banga alamun wata bakuwa agidan ba,ba bangaren da ban shiga ba don ganin ko bakuwar ce, amma babu alamun ta har shabiyun dare Ina falo amma banga wata tafito ba,haka naje na kwanta ina kokwanto a raina. Na biyu kuma let evening ne gab magriba,mun rabu da Yah Rafeeq zai je masallaci na zagayo daga baya wajen lambu zan shigo ta kofar entrance d'inmu,na hangi again matar tana ta sauri kamar zata kifa ta shige cikin gida,aiko na ruga da gudu don inaso inga yau wacece ke shigo mana cikin b'adda kama haka,saidai duk shige da ficena na rasa ta sama ko k'asa, zuciyata ta soma tsorata anya ba aljannu keson budemun ido ba,na rasa dawa zan mgnr kar ace na samu tab'in hankali,haka dai nabar abun a raina badan ya daina bani tsoro ba, Na karshen wanda ya kid'imani,karfe d'ayan dare na fito zuwa main kitchen d'in babban falo insha ruwa,na manta ban shiga dashi ba ranar Ina cikin kitchen naji wani kauri haka ga hanci na,nai saurin juyawa naga wulgin mutum ya shige corridor na hanyar bangaren Mami,duk yadda zuciyata take bugawa da tsoro hakan bai hanani bin hanyar ba cikin tashin hankali,don jinake kozan yi miye saina ga wacece wannan? _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....20 Jikina wani irin tsuma yake ainun,saboda dai Ina cikin tsoro matsanan ci saboda al'amarin yana matuk'ar bani tsoro da mamaki,jiki na rawa nabi hanyar da tabi duk da wannan warin yana bugar hancina yana sani jin jiri kamar juwa na neman kadani,kamar walkiya banga kowa ba saidai k'ofar shiga bangaren Mami abud'e zuciyata keta bugawa,na kasa shiga zuwa can naji duhu ya mamaye idona daga haka ban sake sanin Inda kaina yake ba, Sai farka wa nayi da sanyin asuba na ganni bisa gadonmu,mamaki da al'ajabin abun yai mugun kamani dan danan abubuwan da suka faru a daren jiyan suka soma dawo mun tiryan tiryan, nai saurin tashi zaune cikin wani irin firgici har saida Rukee tatashi tana tambayata lfy "Rohee?" Jikina kamar an zuba mun ruwa,saboda zufar data kwaranyo mun, na kasa bata ansa kaina ya kulle. tashi tayi taje ta d'ebo mun ruwa ta kawo mun, "kisha ruwa, ko mafarki kikayi na tsoro?" Kallon ta nai kamar yau na fara ganinta daker nasha ruwan,na jingina da allon gado ina kallon ko ina nad'akina,kafin na iya bud'e bakina nace mata, "Waya kawoni nan Rukee?, jiya da daddare na farka naji kishirwa,nafita insha ruwa........ Sai na kasa bata labarin abunda ya farun, nai shiru dai. "Sai miya faru? Tsoro aka baki ne?" Ajiyar zuciya naja mai karfi kafin ince mata,"Ehy, to nidai nasan dana fita ban dawo nan ba,yanzu kuma na farka na ganni anan" "Kodai mafarki kikai kin tashi kin fita,inba haka ba ya za'ai haka ta faru, to waya dawo dake nan d'in?" Idona cike da kwallar tashin hankali nace mata"wallahi ban sani ba,kuma ni cikin hankalina nake ba mafarki nayi ba" Cikin son ta kwantar mun da hankali tace"Ki natsu ba fa wani abu bane,irin haka na faruwa sosai koni nasha yin irin wanan mafarkin sai kaga kamar gaske,karki damu kanki kinji ko ki dauka mafarkin kikai, kuma Rohee kina wasa da adduar bacci tunda yah Rafeeq ya dawo, ba dole ki ringa munanan mafarkai ba. " Shiru kurin nayi ina jinta ban sake cewa komi ba,nidai nasan ba wani mafarki danai abunda ya faru zahirin gaskiya ne bakomi ba,abunda ke rikitani shine waye ya maidoni dakin? Wannan ya wuce. ******** Bayan kwana biyu nayi kokarin ganin abun bai dameni ba,duk da idan na zauna ni daya abun yana dawo mun tsoro matsananci ya cika zuciyata,hakan saiya haifar mun da zazzabi mai zafi shiyasa nai iyakar k'ok'arina wajen ganin na cire ma raina abun,na zama Busy a makaranta indai ina ni kad'ai to zaka sameni ina karatu ko research,a d'an tsukin na rage kara kaina sosai,duk na zama sukuku dani Yah Rafeeq Yafi kowa damuwa da hakan,sbd na kasa sake wa kamar yadda muke,ya gaji da min tsogumi har ya gaji,Ummanmu kanta ta damu matuk'a rannan ta zaunar dani take tambayata, "Rohee mike damunki?,kusan sati biyu duk kin rage walwala,abinci ma bakyaci sosai kin faye zaman daki sai a yini ba ajiyo muryarki ba,ni mahaifiyarki ce sanar dani kinji ko" Shiru nayi kwalla suka cika idona kafin nai aune sun silalo kan kuncina, cikin sanyin murya na ce, "Umma kwana biyu mafarkai nake marasa dad'i,abun yana damuna shiyasa.........daidai lokacin Mami ta shigo falon ta zauna,ganin ina kuka take tambayar mike faruwa, umman cikin jimami ta ce " wai mafarkai take na ban tsoro shiyasa duk kwana biyun nan gatanan sukuku" Mamin ta kalleni cikin rashin jin dad'i ta ce "Shiyasa Rafeeq ya dameni akan Rohee kamar bata lfy kwana biyu,kuma nima naga alamar rashin sakewa tattare da ita,Y'ata zonan inji" Na matsa jikinta na dora kaina bisa cinyarta, ta dafa kaina cikin kulawa take mun mgn, "kin rage Azhkar ko?na sani kin rage don haka ki cigaba karki daina,shi daman shaid'an ai inda ake wasa da ibada yake zuwa,ki ringa alwalla in zaki kwanta kinji" Kaina kurin na iya D'aga mata,sai suka cigaba da firar su ita da Umman,har bacci ya daukeni kan cinyar Mamin. ******* A hankali a hankali sai na fara da ya yewa daga yana yin dana ke ciki na rud'u da damuwa,na dawo kamar komi bai faru ba,ban sake ganin matar ba balle wani abu makamancin irin na ranar ya faru, muka cigaba da soyayyar mu da Yah Rafeeq,kamar ma yanzu ne muka farata saboda shauk'in juna, kuma har zuwa wannan lokacin alak'armu dasu Mama su Yah Ramdan bata canza daga yadda take ba,saima abunda yai gaba. Duk yadda iyayen mu maza basa jin dadin wannan wariyar da muke musu amma mun kasa gyarawa,saboda ganin cewar iyayen mu Mata basa son hakan muma muke tayasu k'in abun,mun fara project dinmu tun farkon semester mu ta shekarar karshe, nida Ruky duk Yah Rafeeq ne yake tai maka mana wajen yin sa,lokacin har ya gama horsemanship dinsa yana Hutu kafin ya koma kuma ya cigaba da aiki da asibitin,don kuwa ya samu upper bayan gama horsemanship din shida Yah Fahad lokaci guda suka samu aiki,hakan yai ma su Ummanmu dad'i ba kad'an ba,saboda dai komin su na y'ay'an su yake tafiya tare ba wata tangard'a. Yah Ramadan da Yaj Najib kau jiya iyau rayuwar tasu, an dai gama karatu amma aikin yi yai wahalar gaske,har gara-gara ma Yah Najib ya samu wata privet sch anan cikin Abuja yana koyarwa ana biyasan da d'an auki,sab'anin Yah Ramadan da aikin ma da yake zuwa wani satin ba a biyansa,yana iya kashe sati biyu ko sisi baida,sai in Abban mu ya bashi ko Abba Nura, zuciyar dai a mace ba wani katab'us sai bakin rai da huzunu kamar wani ya d'ora masa. Kwanci tashi asarar mai rai sai gamu an wayi gari mun kammala jami'a da dad'i ba dad'i dai an samu an kammala, zuwa lokacin duk wani nau'i na cikar budurwa maiji da kanta jikina ya gama kammala,wani irin jiki Allah yayi mun mai cikar halitta ga fata ta wani irin daukar ido take kamar ana sani cikin inji a wanke kullin,saboda kalar kulawar da nake bata da taimakon Yah Rafeeq,don kuwa duk rabin albashin sa akaina yake qarewa, zuwa sannan ba inda soyayyar mu bata zagaya ba cikin gidan nan da kuma sauran yan uwa na kusa,har friends dinmu sun san cewar nid'in mallakin yah Rafeeq ce,don wannan mgnr kamar fariha ce a sallar farilla abakina kowa ya sani,hakan yasa na haramtawa kowane saurayi kaina, har malaman mu ba irin naci da k'wak'war da basuyi akaina ba, amma Ansar daya ce nake basu cewar nidin matar aure ce akwai saka rana da sadakin wani akaina, dole suke shafa mun fatiha. Mun gama da makaranta yanzu result kawai akejira da kuma mgnr Bautar kasa,don haka zaman gida muke yanzu sai Kuma zuwa islamiyya, a Wannan zaman namu bama komi ya sake haddasa wasu abubuwan tsakanina da Yah Ramadan,lokacin Yah Rafeeq yaje wani course na sati biyu a Lagos. Anti sha,awa ce ta haihu bayan tsawon shekaru uku da auren su sai lokacin Allah ya nufa,don wancen cikin barin sa tayi yana wata hudu,munyi Murna sosai da sosai saboda dai mun san taso haihuwa kamar hauka,zuwa lokacin ikee din Anti Rafeea shekararta uku an kusa yi mata kane ko qanwa don cikine da ita sannan,murnar da mukai tayi nida Rukee bata wuce ta yawon da zamuyi tayi ba har ayi suna,don yanzu an hanamu wannan gantalin da muke yi sadda muna school, gashi Yah Rafeeq bai nan daman shine yake daure mana gindin yawon, to tunda ya tafi ba wani waje da muke zuwa inba islamiyya ba itama din sau uku a sati ne,anyi haihuwar kamar yau washe gari saiga Goggo Habi da Mufeey sun sauka, wayyo dad'i murna kan murna haka mukai tayi don mun shekara wajen uku rabon da mu hadu,kowa yasan muna cikin farin ciki saboda gidan saida ya dauka da hayaniya. Washe gari karfe tara muka shirya don tafiya gidan jegon,jiya raba dare mukai muna fira itama ta kammala karatun ta kamar mu zaman fara bautar kasa take agida,cikin yan mazan gidan ba wani available dazai kaimu, Yah Najib tun seven thirty yake fita Yah fahad yana sokoto acan yake aiki sai karshen wata yake zuwa gida,Yah Ramadan ne kurin baya fita da wuri sai ten,munje muka gaida Hajja sannan muka wuce don gaida Abbanmu shidai Abba Nura ya riga ya fita, Yana ta aiki akan computer da glasses a idonsa,yana ganin mu ya cire ya bamu hankalinsa,gaidashi duk mukayi ya ansa cikin fara,a da nuna jin dad'in ganin mu yana cewa "an samu hanyar yawo hankali ya kwanta ko Rukee?" Dariya duk mukai muna sake kai k'asa da kanmu, Na ce "Abba Gashi gidan ba wanda zai kaimu mai zai hana ka barni na ringa kaimu tunda yanzu nayi hankali Abba" Murmushi yayi ya ce "indai akwai namiji agida bazan sake gangancin barinki kija mota ba,in kikai aure can tsakaninku keda mijin" Na sunburi baki ina shagwab'e fuska,su mufeey na mun dariya shi kuma ya dauko wayarsa yana cewa, "Ramadan baya fita sa wuri bari na kirasa ki ruk'esa ya ringa sauke ku," Ni sai lokacin ma na tuna dashi don nafi karfin wata van sashi idona ba,tun Yah Rafeeq na nan har raina nama mance ya yake,muna nan zaune ya kirasa ko minty uku ba Acika ba sai gashi sanyi cikin wani sassauk'an yadi marar tsada,ba guga kuma ba suquizing ba kamshi kuma ba wari, kallon sa nai na jima ban sashi idona ba sai naga fuskar sa ta sake haske da shalk'i,sai matashin gemunsa daya had'e da gashin bakinsa sun sake wani irin baki da daukar ido,alamun su yana basu kulawa. Saboda tafiya dogon kallon da nai yasa banji ma sadda Abba ke magana ba,saida Ya ce mun "Rohee gashinan ku rok'i alfarmar ya ringa sauke ku in zai fita," Nidai bance komi ba Mufeey da Rukee ne sukai magana, ya amsa musu cikin wata cool voice da najima banji sa da ita ba, "Ba damuwa Abba,saidai ni karfe goma nake fita ban sani ba ko zasu iya jirana sannan" Caraf Mufeey ta ce "zamu jiraka mana,ban bancin awa daya ne kuma nasan kafin mu isa Anti Rafeea ta isa zata fara rage ayyuka" Rukee ma tace"kuma tana da mai aiki duk abun bazai wahala ba" "To ba damuwa bari na gama abunda nake a ciki kafin nan time yayi sai mu wuce." Mom Muhseen & Asad🥰 _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....21 Ban garen su Rukee muka koma muka zauna jiran sa,raina duk a duk'unk'une sudai basu ce min komi ba saboda sun san suna tofawa zamu iya samun matsala,sai suka kyaleni kawae. Bai fito ba sai karfe goma da rabi,ya kira layin mufeey yace mu fito sannan muka tashi muka tafi,itace gaba muka zaga baya muka shiga kananun kaya ne jikinsa black din wando sai sky blue din shirt,banga wata karin guga ba akayan haka zalika ba wani cukuikuyewa tare da su,sannan banji wani fitanannen kamshi na tashi ba,Ina mamakinsa namiji kamar sa ace baya saka turare imagine,na tab'e baki kawae na zauna saitin kujerar driver na saka air pies kunnena na cigaba da danna wayata,duk da ban kunna komi ba haka nan nai sha'awar sawa,amma kuma all ears dina akan firar mufeey dashi ne,Rukee na taya su nidai kam uffan ban ce ba amma duka hankalina yana kansu,zuwa caan naji tace "favorite please ga inibi inaso" Bai musa ba kurin yaja ya tsaya dai-dai inda mai inibin yake,ya ciro kudi aljihunsa ya bata kurin ba tare daya tanka ba, sai Rukee da ta ce "kayakuri yah Ramadan mun tsayar dakai" Atakaice ya ansa mata da cewar "Don't mind" Ni dai k'ala bance ba tare suka fita da Rukee suka siyo ina nan zaune,kowa da nashi a leda saida muka cigaba da tafiya mufeey ta miko min wata leda guda tana cewa, "Sister ga naki" Girgiza kai kawai nayi nace, "I'm ohk" Su duka ita da Rukee suka had'a baki wajen fad'ar, "are u ohk?inibin?" Saboda sunyi mamaki matuk'a don cikin kayan fruits ba abunda yafi soyuwa agareni kamar sa, banza nai musu kawae sai basu sake tanka mun ba har Allah ya iso damu gidan Anty Sha'awa. "Favorite karfe nawa zamu jiraka to?" D'an jimm yayi kafin ya ansa cikin sanyin sa yana kallonta, "Indai kun tashi tafiya ki kirani kawae" Cikin murna da jin dad'i tace "ohk Allah ya tsare ya bada sa'a ya kuma dawo dakai lafiya" Kamar wasa ya saki wani kafirin murmushi yana lumshe mata idanun sa ya amsa can ciki "Amin thanks" Bata biyo bayanmu ba saida taga tafiyarsa,na rasa gane miyasa mufeey ta damu dashi har haka,ni bata san haushinta nakeji ba in tana wani nu ta damu dashi,tsaki naja nai gaba cikin gidan, Duk da kasancewar mijin Anti sha'awa baida kudin mijin Anti Rafeea,amma gidanta babban gidane upstairs ke akwai kuma sama da k'asa dakuna ne sai wanda ka zab'a zaka zauna, falukanta hud'u sai bed rooms uku, sai single room uku kuma kowane ba wanda babu furnitures acikinsa, ga Ac ta ko ina dole ma kaji dadin gidan kuma ta ko ina tayils ne har bango,a bangaren gida kam zasu zo daya da Anti Rafeea,saidae kawae samayyar miji da hidimar da yake mata ne ba d'aya ba,don Mijinta mak'one dashi duk da baida halin sosae amma wani abun yana da halin yi mata mak'one kurin irin nasa,sab'anin na Anti Rafeea ba abunda zatace tana so baiyi mata ba,saidai idan bata ce d'in ba. Munsha Aiki sosae saboda Anti Rafeea cikinta baya son wahala,aikin da bai gaza ba shine takeyi a zauna sauran hidimar cikin gidan kau duk mu mukayita,ga dangin mijin nata zaryar zuwa gida fa masha Allah anata zuwa barka,saboda ganin an dad'e ba asamu ba kowa yana musu murna. Sanwa damun sauke zamu d'ora wata don ma Allah yasa mufeey akwai son aiki ita da Rukee aida na bani,Allah ya sani ban son moriya aikin cikin gida wahala yake ban,don ma Allah yasa umma duk ta hutar dani abubuwa shiyasa nake dan hutawa,ummi ce gandun aiki bata ko gajiya aiko Hajja taita Fad'a akan mi za a samun ido bana yin aiki,gidan mijina wani ne zaije yai min. Ni kam daman ai munyi da Yah Rafeeq cewar duk abunda bazan iya yi ba zai daukar min masu aiki,girki ne kurin zamu ringayi da kanmu ko muringa fita cin abinci. (Uhm banji hanya mai bullewa ba anan) Bamu samu kanmu ba sai karfe shidda da rabi na yamma,jikina kamar an bubbugeni su Rukee sai dariya suke min,suna tsokanta wai azo kallona gidan mijina saboda dole zan sha wuya,jinsu kawae nake nidai saida nayi baccin gajiya ina tashi muka hau waya da Yah Rafeeq yana bani lbrin aikinsa,yace in yai sa'a ma bazai wuce kwana goma ba zai dawo,naita murna ina ce masa "gidan duk babu dad'i da baka nan,nasan da ace kana nan akai haihuwar nan kullin tare zamu fita mu dawo," yai saurin cewa "waye yake kaiku?" "Wannan ne mana,ai kasan dae in yana nan Abba baya sanya kowa akan wata hidima saishi kamar yafi kowa" "Rooh" Yai mgnr cikin wani yana yi marar misaltuwa,jikina yai sanyi jinsa kamar cikin damuwa sosai na amsa masa tare da tambayar ko lafiya? "Naji ka so cool,akwai wani abunne?" "Wallahi da ina da hanyar da zan hanaki zama duk inda yake da nayi,kwata-kwata bana kaunar ganinki tare dashi koda hanya ce kau,.........."yah Rafeeq ni kam inaso yau ka gaya min dalilin ka na yawan fadar hakan" na katsesa da fadin haka cikin damuwa,sabda ni nagaji daji tunda yasan dai nid'in tashice ba wani d'a namiji da zan iya ma kallon rahma sama dashi indai akan mgnr soyayya ne da aure..........."Rooh wannan da kike ganin sa munafukine,ni kad'ai nasan irin kallon da yake miki,ke ba zaki gane ba da zai samu dama wallahi zai iya cewa".........."karka karasa Yah Rafeeq!!!" Numfashina har wani sama da k'asa yake saboda yadda naji bugun zuciyata ya karu sosai,kwata-kwata ban tab'a kawo wannan tunanin a raina ba saboda ma duk abunda zai tada min hankali game day aurena Dashi bana kaunarsa......."come down Rooh,Ina so na nuna miki ne yadda zaki nesa dashi,.......Yah Rafeeq ko maza sun kare walahi gara min na dawwama babu aure,Dana auresa gara na mutu wallahi.....sai kawae na sanya kuka sosai sbd yadda hankalina yai kololuwar tashi,kuka sosai nai tayi da yake dakin ni kadai ce yana ta kiran sunana da niyyar lallashi hankalin sa ya tashi sai kawae na kashe wayata. Naci kuka sosae wanda na dad'e banyi ma irinsa ba,bansan dalilin da yasa nakejij tashin hankalin mgnr ba, ni koda wasa bana kawo ma irin haka a zuciyata,sabda nasan nafi karfinsa nesa ba kusa ba,kuma a ganina ko ga kafa aka daura masa ni dagudu zai kunce saboda yasan wutsiyar rak'umi tayi nesa da k'asa,sadda su Mufeey suka shigo da fara shirin tafiya gida suka sameni cikin wannan yana yin,Anti Rafeea ta kalleni ta ce "miya sameki?kinga fuskarki kamar jan kosai?" Mufeey ta ce "Haba Anti,maimakon lallashi saiki ce mata haka?,yakuri sister miyafaru?" Bance komi ba nidai ina kwance abuna har sannan zuciyata bana jinta dai-dai, Rukee tace "bai wuce ita da Yah Rafeeq ba,kila shine ya sata kukan" "To miya shafeki ne idan shine?,sunfi kusa ai inma shiga kikai kunya zasu baki" Cewar Anti Rafeea mufeey na cewa, "yanzu dai abar mgnr,sister ki tashi ga Favorite can yazo ganin baby daga nan mu wuce gida" Kai kurin na d'aga mata bance komi ba,suna ta firar su nidai kallo ne nawa,har suka gama komi sannan na sauki na shiga toilet,gyara jikina nayi na wanke fuskana na tsane da towel na maida kayana danazo dasu na fesa turare na daura veil dina,kana kallon idona da fuskar zaka san nayi kuka ainun,lipstick na saka ma bakina na dauki phone dina nabiyo su,duk suna babban falon Anti sha'awa,mu kadai ne ba wasu yan barka,anata fira shi kuma rik'e da Babyn mufeey na kusa dashi cikin two siter,Ina saukowa daga stairs naji kawae na soma hard'ewa gabana ya fad'i sosae ban d'ago kaina ba har sauko na zauna gefen maijegon........"Roheen Abba lafiya kuwa?kinga fuskarki,ku fararen nan matsalar da kunyi kuka sai angane maku" Uffan bance ba ban kuma tanka ma kowa ba sai suka kyaleni,har sannan inajin alamun ana kallona naki duban ma inda raina ke ban nan ake kallon nawa,.........idona rufe naji Antin tana cewa "Yah Ramadan hadda wata hidima kuma?to Angode Allah yasaka da alkairi" Bud'e idona nayi naga wata leda ce babba da kayan jarirai na tab'e bakina,na maida idona na rufe saida ya fita sannan Muka tashi mukai musu saida safe,Anti Rafeea mijin take jira yazo ita muka baro da mai jegon........ ********* Tunda muka taho a hanya bakin mufeey baiyi shiru ba,ita dai bata gajiya da magana ko kad'an sai in bacci take amma inhar ido biyune tofa bata hutawa, tunda na zauna mazaunina ban d'ago kaina ba saboda bana kaunar koda wasa idona ya shiga cikin nashi,caan naji anja uban burki duk saida muka tsorata ba shiri na ciro kaina da sauri,hakan yai dai-dai da haduwar idanun mu cikin madubin center mirror, jinai zuciyata ta tsinke gabana ya fad'i rasssss da karfi, da sauri na kauda kaina Ban ma tsaya kallon kiya faru ba nasan iskanci ne kawae,ya tada motar muka iso gida muna tsayawa nice farkon shigewa saboda a k'agare nake na ganni a dakinmu. Mom Muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....22 Mun cigaba da zuwa gidan zaman jegon Anti sha'awa har kwana hudu,duk wata hidima mukeyin ta anyi sa'a Ammi tazo ita da kausar mun samu saukin hidimar duk dasu ake tayi,wata ranar Najeeba zata zo ayi da ita duk da bama sake mata itama kuma batamu take ba,Ammi Rahma kuwa bama ruwanta da wani kin sakewar da muke da ita, sabgar gabanta kurin take zata samu aiki dole muyi tunda gaba damu take sosae,in maganarta tazo kanmu zata tanka mana dole mu bata ansa,tun muna kakkauce mata ala dole saimun nuna bama yi da yan bangarensu,dole muka sake da ita anata hidima. Don itace tayi uwa tayi makarb'iya a hidimar sunan,kuma hakan yai mana dad'i har ita maijegon,saboda babu wani babba sosai dazai shige gaba a hidimar,Su ummanmu Abba yace subar mana mune ya dace muyi,to tunda suka zo barka basu sake zuwa ba. Daren suna aiki ya kacame Ammi ta kirani ta bani list d'in abubuwan da za'a siyo kasuwa,su Rukee da Mufeey na can sunata aiki nice na gudu na b'oye ashe rabon ni zanje kasuwar, idona yai narai-narai zan hawaye na ce "wallahi Ammi ban san kasuwar da zanje ba,kuma Abba ya hana shiga taxi ba kamar in yamma tayi sosae" Ni duk dan in zillema aiken,sai kawae naga ta dauko wayarta tana kira,zu wacan naji tace "yanzu nake son ganin ka pls,magariba nayi bana so ace tayi ba asiyo kayan ba,ohk ina jiranka" Na sauke ajiyar zuciya nasan na tsira, sai naji ta ce dani "kijara RAMADAN farfajiyar gida zaizo kuje tare," Ta juya kurin ta kyaleni nan tsaye nabita da ido,na ma rasa mi zanyi inama na ansa mata kurin naje da kaina?inama banyi musu da ita ba balle ta had'ani tafiya dashi,wallahi ba abunda nake gujema wa irin haduwa wuri daya dashi,bana so har raina bana so.........."mikike baki tafi kinjira sa ba,Roohe wallahi ki kiyayeni"........."yanzu zan tafi" na wuce dakin da muka aje kayanmu na dauko veil d'ina,doguwar rigace rafa jikina ta atamfa ta kamani daga sama boobs dina sun fito ma sha Allah,daga k'asa tabi k'uguna ta baje sosai tayi masifar fidda shape dina,yane kaina nayi da veil din inata jan tsaki kurin na fesa turarena da duk inda zani da kayana,da lipstick dina. Ina bud'e kofar mukai kicib'is da ita, "wallahi dana cinmaki baki niyyar fitowa ba dakin sha tafi,ki wuce yana waje yana jiranki,sai hadarin ya taso ruwa ya sauka kuyi mana salalar tsiya" Ina tafiya inajin zuciyata kamar ta fito don bakin ciki,raina b'ace haka na tafi farfajiyar gidan yana tsaye bakin motar yana danna wayarsa keypad,naja tsaki Ina cewa a raina "KO uwar meye acikin keypad din da zaka samesa kodayaushe yana dannawa?............tsaye nayi daga nesa kad'an dashi nace cikin shan murr, "gani nazo" Saida ya gama shan k'amshin sa bai dubi inda nake ba ya zaga ya shiga motar, na ja wani tsakin kurin,na mance ba abunda ya tsana sama da tsaki ni ina ruwana........na bud'e motar na shiga yaja muka tafi KO radio bai kunna ba balle ta dauke mana shirun,inda saboda ma ai mun saba tafiya ba mai cema d'ayan sa ci kanka,ba muyi nisa ba iskan tasowar hadari ya soma kad'awa gwanin dad'i ga sanyi ga k'amshin ruwa,har lumshe idona nayi. Haka mukaita tafiya zuwa can aka kirasa a waya, ya ciro ya saka speaker ya aje daga saman motar naji muryar Mufeey, "Favorite don Allah Ina son kwa-kwa in ka gani kaji" Yadda take maganar cikin wata shagwab'a da salo yaban mamaki,anya mufeey ba son wannan mutumin take ba kuwa?........."ohk Mufeeda,bayan ita bakya son komi" Ta sake narke murya cikin salon daukar hankali, "Ina son dabino to favorite," Ya sake ce mata yana murmushi wanda ya daskarar dani inda nake,Ina satar kallon sa ta gefen ido. Ya sake cewa "To mufeeda bayan shi sai mi kike so?" Dariya tayi mai kyau tana lauya murya "Aa Fa favorite shikenan,bayan wadannan abu d'aya nakeso" Juyo da kaina nai na kallesa sau d'aya shima akai sa'a ya jiyo muka had'a ido,bazan iya fassara kallon sa ba nima bansan miyasa na kallesa ba, ansa yake ba Mufeey amma idonsa ni yake kallo, "miye kikeso fad'a min" Saurin juyar da kaina nayi ga taga kawae,Ina kallon yadda aka d'an soma yayyafi jefi-jefi........"inaso ka dawo lafiya,ka kuma kula da titi" "Ohk angama sai na dawo" "Ohk bye" Ya kashe wayar yasa aljihunsa, ban san sadda wani dogon tsaki ya kubce min ba,saboda haushin mufeey intana wannan zazzak'ewar akanshi wallahi bata min rai take sosae,munzo dai dai bakin get din kasuwar yaci burki,na sake jan wani tsakin na bud'e na fito ina buga k'ofar motar,ashe rigata ta datse sadda naja zan tafi naji rigar ta mak'ale daker na fizgota,saboda naja murfin naji kamar yasa lock ta ciki,Ina d'aga k'afata kenan naji an fizgoni da karfin gaske an had'a ni da jikin motar,wani rasssss kirjina ya ansa saukina wajen ba kowa saika shiga cikin get din zaka ga mutane,idon sa cikin nawa dana fiddosu waje saboda tsorata,nashi idon jajawur da bacin rai nima raina ya b'acin,yadda ya damke min hannu da karfi yasa na fizga da karfi Ina cewa "Dalla malan sakeni..........takalmina mai tsini ya tusgud'e na tafi zan kifa a k'asa,yai saurin saka hannunsa ta wajen k'uguna ya taroni,kamar jira ruwan sama keyi aiko jikake shaaaaaaaaa ya balle da d'an karfi,dagani har shi kamar wad'anda aka d'aure mun daskare a wajen,sai ya zama kamar yana rungume dani ne,hannunsa ya zagayo dashi ta bayana saman k'uguna ya rik'eni,nima hannuwana suna bisan wuyansa na rik'esa gam sadda nazo fad'uwa,tun ina kalon idonsa da suka washe daga jaan bacin rai,har ruwan yasa dola na sauke idona k'asa na runtse su,cikin sand'o na sauke hannuwana dake bisa wuyansa,jikina yana yar rawa saboda abune da bai tab'a faruwa ba sai saudaya radda na fad'i a basketball,amma wannan karon kusancin yafi yawa sosai nake jikinsa har inajin sautin bugun zuciyarsa a kirjina da muka manne,sannan hancina yana shak'o wani sassanyen kamshi daddad'an kamshi mai ratsa hanci da kwalwa daga jikinsa,ruwan nan ya mana shar kaff har d'iga muke kayanmu amma motsin kirki ba wanda ya iyayi acikin mu,zuciyata nima kamar zata fashe saboda yadda take bugawa sosae,bazan iya gane tsawon lokacin da muka d'auka a hakan ba,har ruwan ya rage karfe sosae. Sai lokacin naji ya d'an saki jikina kamar jira nake nai sauri ida fita daga jikinsa,santsin kasar wajen ya kwasheni na tafi zanci k'asa da sauri ya sake rik'oni again muka sake had'ewa waje guda,fuskata cikin kirjinsa Ina sauke numfashi,gaba d'aya na rikice ma hankalina ya tashi natsuwa na neman gagarata,muna a hakan ya bud'e motar ya zaunar dani sannan ya rufe jikina sharkaf har pant dina kanshi a jik'e yake,dunkulewa nai waje guda Ina kermar sanyi nama rasa wane kalar tunani zanyi,haushin kaina zanji komi? "Ina list d'in abun da za'a siyo" Naji sassanyar muryar sa yana tambayata,ai bazan ma iya gane ina na sake shi ba,girgiza kaina nayi kawae bance komi ba,sai ya zagayo inda nake ya bud'e k'ofar yana dubawa,kaina na cikin guiwata shi kuma ya duk'o ya dauko takaddar dake wajen k'afata,jin sa a wurin nai saurin ciro kaina dai-dai shima ya sawo kai a wurin,fuskokin mu suka had'u har hancin mu yana haduwa dana juna........YA SALAM!!! Abunda ya bak'uncin ilahirin jikina tunda nazo duniya ban tab'a jinsa ba,a zabure naja baya da kaina shi kuma cikin sanyin jiki ya dauki takaddar ya fita, bansan ya akai ba nadai ga ya shigo ya kwantar da kujerar sa ya dora hannunsa bisa fuskarsa,ban san hawaye sun balle mun ba na rashin abunyi,nidai nasan harga Allah bada niyyar kaina hakan ke faruwa ba, shima kuma nayi imanin baida wata manufa akaina,to miyasa hakan ke faruwa?ban sani ba,ban San ansar ba shashshekar kukana ta fito fili har yaji da kamar bazai tanka ba,sai zuwa can naji ya ce mun "Sanyi kikeji ne?" Ba tare daya cire hannun sa daga fuskar ba,banza nayi masa tunda banda abun cewa,daga inda yake ya sanya hannu ya kunna heater yadda zamuji gumi don sosai nakejin sanyin. Bayan wani lokaci akai knocking ta glass ya tashi ya bud'e glasse din wani mutum ne yake ce masa, "an had'a komi yallab'ai" Jinjina Kai yayi yace "bud'e kaya ka sanya" Ya bude bayan motar yana loda kayan,sannan ya ce an gama ya biya kudin sannan yace "please kawo mun kwa-kwa da dabino" "To yallab'ai" Har mutumin ya juya sai ya tsayar dashi,yana jiyowa kaina yace "ba kyason komi?" Mamaki ma tambayar ta bani,ce masa nai inason wani abun? Amma banyi magana ba na girgiza kai alamar aa, sai yace dashi "ka had'o da inibi please" sannan mutumin ya tafi,haushi duk ya isan nama rasa abunyi nace, ciki-ciki "Ni bana shan inibi ai" Ya koma ya kwanta yana ce mun, "na sani ai,daman kuma ba naki bane mufeeda na siya mawa" Yadda naji haushin mgnr ban San sadda naja wani tsakin ba mai tsawo tsuuuuuuu,a zabure ya taso kamar wani kubuwa "keeeee!" Na jiyo gabana na fad'uwa,Idona cikin nashi yai mun kuriiii nima ina kallon sa, "idan Kika sake mun tsaki wallahi sai kin gane baki da wayau" Na juyar dakaina Ina murgud'a baki kawae,.........yai k'uta yana cewa, "sai karyar iskanci" Ina gunguni nace, ciki-ciki "wallahi ni ba yar iska bace.........mikika ce?zagina kike?" Ya taso da sauri yana kawo hannu kamar zai buge mun baki,nai saurin ja baya ina turo baki, "Wlh ni ban zageka ba,cewa nai niba yar iska bace........idanunsa a warwaje yake kallona ni kuma na makale jikin k'ofar kamar zan shige cikinta, kanshi ya nuna yana wani kala da idonsa "nine d'an iskan kenan.........Aa wallahi ba haka nake nufi ba nidae" ya sake yin k'uta yana koma wa ya kwanta, har sannan ruwa ake sosae ya dawo kan dazun daya dan rage,munyi shiruu bakajin komi sai karar ruwa zuciyata ansawa kawae take,Allah yasa ma na baro wayata gida da kiran da yah Rafeeq zai mun yawane dashi,kiran salla da akai yasa na jiyo ina kallon sa shima a takuren yake alamun sanyin yakeji,don ma heater daya kunna aida mun gane kurenmu......."ba zamu tafi gida ba?" "Anan zamu dawwama,har saikin gaya mun waye d'an iskan naki" "Ya salam,wallahi ba da kai nake ba, ka yarda wallahi bance ma haka ba" Banza yai ya kyaleni har sannan ruwa ake daman ankwana biyu ba ayi ba zafi ya addabemu, "Wallahi sanyin kayan nan y daman,inaso na canza ka tada motar mutafi.........."kizo kija to,ni kam yanzu bazan iya tuki ba ana ruwan nan" "Ni zanyi," Ya jiyo yana kallona cikin hasken kwan cikin motar,duk na marairaice na ce "ehy zan ja motar wlh na matsu naje na canjaa" Kamar bazai daina kallona ba,ya wani lumshe idonsa ya d'age kafadar sa yace "bismillah bude ki zagayo" "Ruwan dukana zai sakeyi fa" Wani kalar kallo yai mun yana cewa "ohk,lemme exchange" Ya mik'o mun hannunsa in kama in taso daga inda nake zuwa mazauninsa, (uhmmm wadannan sun raina mutane😂🫣)kasa musu nayi da dai in fita ruwan ya sake dukana, rike hannunsa gam nayi na sanyo kafata daya inda tashi take,na dafa kujerar da d'ayan hannun nawa sai ya zamana kamar nai masa rumfa,wajen in ida sanya dayar kafar ne kawae naji na fad'a masa a rashin sani,daman kujerar kwance take sai kawae naji mun tafi gaba d'aya na fada bisa kirjinsa shi kuma bayan sa ya bugu da kujerar har saida yace "Ausshhh" Mom muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....23 Fuskata na bisan dokin wuyansa,wanda naji zafi kamar alamun baida lafiya,wata irin kunya da ban tab'aji ba ta lullun'eni,motsin kirki na kasayi kamar yadda shima ya kasa motsawa daga yadda yake,Hannuwansa duka biyun suna bisa bayana,ban san ma ta yadda zan sauka ajikinsa ba,ban san iyakar lokacin da muka dauka a haka ba,saidai naji mgnrsa a kunnena cikin sanyin muryarsa da ta kara zama cool, "*LAYLA please a d'agani haka nan ko*" Wani iri naji kamar in b'ace daga inda nake sai kawae na sanya kukan rashin abunyi,da borin kunya don wallahi sosai naji kunya dubeni duk irin k'iyayyar da nake masa,da k'yank'yamin da nake ji akansa amma gani d'are-d'are ajikinsa kamar zan shiga cikinsa,kasa motsi nai duk haushi ya kamani. Ganin na kasa motsin kirki sai ya d'ago kujerar daga kwantar da itan da yai dazun,d'aff ya cironi ya maida ni mazauni na,zuwa sannan yayyafi ne akeyi ruwan ya rage sosai,tada motar yayi cikin sanyin jiki ya fara sarrafa sikiyarin har muka bar wajen,muka sake zama kurame sosae ko motsin kirki banyi ba,na dunkule kamar curin tunkuza ga wani zazzabi naji ya sauko mun,sannan ba abunda nakeji illa wannan sassanyan kamshin nasa har cikin bakina,ilahirin jikina shine nakeji,zuciyata kamar zata fad'o k'asa so nake na bud'e ido na ganni gidama gaba d'aya ba gidan Anty sha'awa ba,hon din da naji yayi anbud'e get yasa na d'ago kaina har mun iso gidan Antin,magadi yazo zai bud'e ya kirasa yazo Yace"don Allah ka shirgar musu da kayan nan,kace ina sauri na wuce zan sauke wannan yarinyar gida bata lfy" Mamaki ya kasheni ya akai yasan banda lfyr?kamar ya shiga raina ya gano cewar banda lafiyar, daker na ciro kaina nace ma maigadin "don Allah ka ce Rukee ta baka wayata ta kawo mun" cikin girmamawa ya ansa da "to hajiya" Ya kwashe kayan yai cikin gidan dasu,yana shigewa yaja motar yabar kofar gidan,jiyowa nai ina cewa "wayata fa?" Uffan baice mun ba sai na kama kaina nima,in miskilanci ne gidan ka tarar mun kusa isa gida aka kirasa, yai picking yana sa wayar speaker, yanzun ma Mufeey ce take cewa "Favorite lafiya baku iso ba?" Muryar sa ta d'an dishe kad'an yace "Bakiga anyi ruwa ba,shine ya tsayar dani sakon ki na nan cikin kayayyakin kiduba" Cikin murna ta ce "thank you very much Favorite,to ina sister ka barota?" Kai tsaye ya ansa da cewar "gida" "Ohk sai munyi mgn bye" Ya kashe wayar yasa aljihunsa,yana yinsa ya nuna shima baida lafiyar kamar ma yafini jinjiki mgnr daker yake yinta,mun iso gida cikin yardar Allah na bude na fito wani sanyi ya ratsani tsikar jikina tatashi,daker da daker nake tafiya har na shige k'ofar entrance d'in. Falon mu ba kowa haka main falon gidan,alamun dai duk suna cikin dakunan su. ******** "Ramadan Ina kashiga haka?kar dai duk ruwan nan kanka ya k'are subhanallahi" Cewar Mama bayan shigowar sa bangaren su ya zube cikin kujera yana rawar sanyi har bai jin abunda take fad'a sosae, daker yai mgn "Mmn kausar ta aikeni kasuwa nida waccen yarinyar to a can ruwan ya iske mu" "Wace yarinyar?kaifa wuyarka kenan kayi mgnr da mutum zai gane ma ka kasa...........Mama inajin Rohee yake nufi ba kowa ba" Cewar Najeeba dake zaune tana masa sannu, Maman tace "tashi ka isa daki ka cire kayan,bari naje na had'a ma ruwan d'umi kayi wanka,Najee had'o masa tea mai zafi ki dauko masa paracitomal sai yaji saukin jikin" Maman ta kamashi suka tafi dakin sa,ta kwantar dashi sannan ta hada mai ruwan wanka mai gumi sadda ta fito ya daura towel,tace"kayi wankan sai kaji sauk'i Allah ya sawak'e, kuma zanyi mamakin yadda zaku tsaya ruwa yai muku wannan dukan kamar wasu yara kananu" tafice tabarsa yana shiga bayin,kwamin wankan ya shige ciki yai lub idonsa a rufe Allah kad'ai dashi suka san abunda ke damunsa har ya haifar masa da wannan fitinannen zazzabin,ya jima cikin ruwan nan saida yaji dad'in jikin sannan ya wanke jikin da sabulun wankan yafito,ya iske tea da maganin ya tsane jikinsa ya shafa mai ya saka kayan baccin sa,sannan ya dauki tea d'in da maganin yasha. Shiru yai na wani lokaci kafin ya duba agogo time yaja sosae tashi yai sallolin sa magriba da isha'i dasuka wucesa, yai shafa'q da wutri yai adduo'in sa ya shafa sannan ya jingina da gado yana kulle idonsa,ya kasa baccin kwata-kwata ya sake duba agogo yaga karfe biyu saura,kawae ya tashi ya fito. Ai ban san inajin sanyi ba saida na iso dakin mu, Ac nata aikinta karma kawae nake daker na cire kayan jikina hakorana har gamuwa suke,mai makon nayi wanka da ruwan zafi sai na kasa sabda ba karfi jikin,zazzabi sosae ya rufeni na jawo bargo kawae na shige dagani sai towel jikina canza kayan ma na kasa,ga ba waya hannuna balle na kira umma,tunda ummi nacan gidan jegon Ina cikin tasku,sai kawae na kama kuka saboda a halin da nake ciki Ina bukatar agajin wani,Ina cikin wannan halin na ciwo da tsoro don ban saba kwana nid'aya ba gashi yau wani irin tsoro nakeji,har jinake kamar ana kiran sunana ana dariya,abunda ya sake gigitani kenan dai-dai wannan lokacin naji an bud'e kofar dakin nawa,dunkulewa nayi Ina karanto duk adduar da tazo bakina hawaye kamar an kunna famfo,shirun da naji bayan bud'e kofar yasa na ciro kaina cikin bargo a hankali, wazan gani tsaye?? Sai kurin ya kunna glub din dakin haske ya karad'e KO Ina,saurin maida kaina cikin bargo nayi zuciyata kamar zata kece don bugawa, miya kawoshi dakina?banda wannan ansar zuwa can naji ya bud'e toilet d'inmu ya shiga na fiddo kaina ina sake tsorata dashi bai ce mun komi ba dai,ya gama ya fito ya tsaya gaban gadon mu yana kallona, "ki shiga kiyi wanka" Kamar sakarai nake kallon sa,wani sabon mutum ya koma mun yau wai anya shine kau?Miya canza shi to? "Ko bikiji ba?" Duk da bargon na sauko kafafuna na rawa haka ma jikina,na shiga bayin Ina shiga ruwan saida nai ajiyar zuciya,nai shiruu kirjina kurin ke ansawa sosae na dad'e cikin ruwan d'umin gwanin dad'i sai naji d'an relief,na manta shaff wa na baro cikin dakin na dauro towel din na fito,yana zaune kan bedside drawer da cup din tea hannun sa yana motsawa a hankali,koda yaji alamun fitowa bai ciro kanshi ya kallan ba,saima ya tashi yana aje cup din bisa drawer silently yace "ga tea nan, sannan ga magni nan kisha,zakiji sauki saiki sallolinki saida safe" Kamar walkiya ya ficewar sa,ban san iyakar lokacin dana dauka tsaye ba ina kallon hanyar daya fita, ban san ya akai naji maganar a bakina ba nadai ji labbana suna mgnr "daman yana da kirki?ko yau ne ya zama haka?" Ahankali na isa ga tea d'in sai kamshin coffee yake yasha madara,nai suffing naji ba sugar sosae yadda nakeson sa,nasha rabi sannan na balli maganin ina runtse ido na had'iya,dan danan zufa ta karyo mun don sadda na fito wanka ya kashe Ac din,kayan bacci nasa KO mai ban shafa ba na zauna akan sallaya,nayi sallolina na kasa daina mamakin sa sosae a raina,karshe anan wani baccin ya sace ni,sanyin asubar fari ya maidoni kan gado bayan nayi sallar asubar. Nice ban tashi ba sai karfe shad'ayan safe,na shiga nai wankan na shirya cikin wata maroon abaya mai adon duwatsu masu kalar pink da blue,fuskata fresh farar powder na saka kurin da kwalli sai lipstick fari mai dank'o,bangaren Abba naje na iske sa kulle da alama ma bai kwana gida ba,na dawo wajen Ummanmu itama bata nan ga dukkan alamu tatafi gidan sunan tunda safe,Mami kuwa nasan tana can da mutanan ta bama zan nufi can ba,sai nace bari na gaido Abba Habibu kodan Darajar Abbanmu, jinai kurin nai karo da mutum nai saurin jaa baya Ina dago kaina idona cikin nashi,k'urii mukai ma juna kamar yau ne haduwar farko wajenmu,hannunsa yasa bisa goshina kawae labbansa na kalla na iya gane miyake fad'a, "yajikin?" Juyar da kan nayi gefe guda nace nima kasa-kasa, "I'm fine" "Ina zaki?" "Abba zan gaido" "Baya nan ai" "Ohk" Na juya da niyyar koma wa d'akinmu naji ya ce, "keeee" Saurin jiyowa nai da idona warwaje don na tsani ace mun keee, "Sunana Rohee" Ya wani kalar dage girar sa cikin salon iskanci ya ce, "dagaske?" Na juyar dakai bance komi ba,har na cigaba da tafiya zuwa dakin mu najisa yana cewa, "tace ba zata zo ba,don haka ki kyaleni na huta Mufeeda" Wai gowa nayi Ina kallonsa cikin ido shima kuma hakan,ga waya kunnen sa takowa yai yazo ya samu wayar ga kunne naji tace, "Hello sister" Har sannan idona a kanshi nace "Naam" "Wai dagaske ba zakizo yinin sunan ba?" Sai nace mata kawae "ehy" "Haba dae miyasa?ko jikin ne favorite yace baki lafiya sannu kinji,to in yamma tayi kidaure kizo zai kawo ki aimana pictures" "Ohk tohm" Na janye kunne na daga jikin wayar nai gaba na barsa nan,na shige dakinmu duk raina ba dad'i nakeji hadda kari da wayata bata kusa,ga kewar Yah Rafeeq nasan yakira har ya gaji ransa zai masa ba dad'i,naji kwalla kurin ta silalo mun sannan maganarmu ta rannan a waya har mukai fad'a ta dawo mun,sai na cigaba da kukana kawae wallahi a raina ba wanda nakejin haushin sa irin RAMADAN, bana kaunar had'a hanya dashi amma yana shige mun,yanzu da Yah Rafeeq na nan hakan ba zata faru ba nasani,saboda duk inda nasa kafa yana biye dani bazai samu damar da zai iya koda rik'e hannuna ba,amma miya faru jiya?jikina duka ba inda bai shafi nashi ba miya kai wannan van haushi da takaici,na tsanesa wallahi na tsane sa duk da yana mun kirki wani lokacin,amma ban haushin sa yafi kirkin sa yawa,na gaji da kukan nayi shiru dole na fita neman abinci wajen Mami,ita bata san ma ina nan ba nace mata ai nan na kwana banjin dadine shiyasa, naci fankasu na koshi da naman kai na dawo na sake shiryawa cikin sabbin dinkin sunan sa mukai mu uku, less ne marar nauyi sawai yake amma akwai kyau da tsada, golden da White ne ajikin sa ya had'u akai mana riga da siket,na saka golden gyale da takalmina sai white bag dina ko sauraren jiransa banyi ba na wuce na shiga taxi na tafi. Mom muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....24 Anyi suna lafiya an watse lafiya an samu Mustafa inkiya farhan,sbd sunan baban mijin aka saka mashi,an yanka raguna biyu manya ba laifi gaskiya a d'anyi hidima yadda ya kama ta anci ansha,sannan aka rarraba robobi na ayyukan gida,Amman duk da haka Mami k'orafi take wai ya gaza yak'i sakin kudi ayi hidimar yadda ya kamata,inaji tana waya tana ta sababi ita wallahi auren Anti sha'awa bai amfana mata komi ba sai tsiya, don duk yawanci ita aka tatike akan wasu abubuwan,don cewa yake shi bazai kaza ba kaza zai iyayi,akodayaushe mamakin Mami nake idan naji tana fadar wasu abubuwan,to mitake son samu a mijin y'arta?nidae banga aibu a tattare da mijin Anti sha'awa ba,iyakar gwargwado yana hidimar da yaji yana iyawa,kawae dai shi bamai facakar kudi bane kamar mijin Anti Rafeea,kuma kusan halinsu d'aya da Abba Nura don shima d'in baya b'arin kudi in wani abun ya taso,wannan saidai Abbanmu shine bayajin zafin fitar kud'i bayarwa kawae yake ba ruwansa. Daga ranar sunan Anti magana ta fatar baki bata sake had'ani da Yah Ramadan ba,ganin sa ma yai mun wahala saboda ba zuwa sashen su nake ba sai a kwana uku ma banje na gaido Abba Habibun ba,duk Nacin mufeey akan muje can muyi firar dare bana zuwa,har gara Rukee takan d'an leka suje tare bata jimawa take dawowa,to shiyasa haduwar mu tai wahala balle tunda ba wani waje muke zuwa ba islamiya ce anyi hutun azumi daya gabato bai wuce sati biyu ba haka. Mufeey wannan zuwan gaba d'aya bata wuni ma cikin bangaren mu,indai akace yana gida bai fita ba to ba shakka tana wajensa,abun yana ban mamaki kwarae da gaske hidima take dashi kamar dae yadda nake ma Yah rafeeq in har yana gida, rannan ina ta danna computer falon ummanmu Rukee nama ummi kalaba ita kuma tana kwance kasan capet tana danna wayarta, ummi ke cewa "wallahi Yaya Rukee kin rage sauri yanzu fa awar mu daya da rabi da fara kalabar nan amma har yanzu bamu gama ba" Na ce "wai kardae kice mun anyi azhar muna nan zaune?"..........wata irin zabura Mufeey tayi tana cewa "na shiga uku azahar tayi kikace sister?" Duk kallon ta mukai da mamaki na irin abun da tayi,Rukee tace "kanki d'aya Mufeey?" "Yaya Mufeey ina zaki to?" Cewar ummy dake kalonta itama,ni ai kasa mgn nayi ma na cigaba da abunda nake, ta maida wayarta caji tana cewa "wlh cewa nake zuwa yanzu na gama shirya ma favorite lunch d'insa,har wanka nayi jiransa kawae zanyi muci kinga ko d'orawar banba bari na ruwa shaf shaf in had'a mana wani abun..........ta ruga bangaren Mama duk muka bita da kallo mamakinta na kashe mu,ummi tace "Yaya Rukee Any kuwa yaya mufeey kalau take" Dariya kurin tayi batace komi ba,don bamu cika magana sosae da tashafi waninmu da Ummy ba kanwar muce. Bayan sallar magriba ina kan gado mun gama waya da Yah Rafeeq cewar jibi yana hanya in hada masa something special, Rukee na chat take ce min "Wae bakiga wani abu ba game da Mufeey?" Na diro daga gadon zan shiga toilet ina cewa, "ni kau na gani,wahala ce ke neman samunta ba sh akka" Nayo alwallar sallar isha'i na fito Rukeen ke cewa, "Ban tunanin ta san ma halin da take ciki,ita a haukarta duk shak'uwa ce" Tsaki naja kawae ina shimfid'a sallaya na ce "zata gane Annabi isa ba d'an Allah bane,don wannan baida kwabon aurenta..........turo k'ofar da tayi ne yasa nai shiru,daga yadda take kallona nasan taji mi nafad'a sai kurin na tada sallar bance komi ba, zama tayi har na kare sallar na sallame na tada shafa'q da wutri suma nayi na gama duk tana zaune batace k'ala ba, inata tazbihi na naji tace min, "LAYLA miya shafeki da nuna damuwata akan Yah Ramadan?ko ince miya shafeku akan hakan?shin kamar yadda kuke bangarar dashi kuke nuna halin ko inkula dashi haka kuke so dole inyi?damuwar da nayi dashi shine yasa har kuke mgnr ban ma san halin dana ke ciki ba akansa ko?to duk abunda nake ina sane,kuma cikin hayyacina nake ba hauka nake ba,tabbas na damu dashi sosae fiye da tunani na ina sonshi son yan uwan taka koma fiye da haka,to miye damuwar ku?bari kuji rashin aikin sa bai daman ba,nasan komi lokaci garai. Haka zalika rashin gayunsa bai daman ba saboda yana da kyawawan halayen kirki,sannan yana da ilimin sa boko da islama,ba kazanta yake ba Aa gayun da baiyyi ne kamar saurayinki Rafeeq a yake baku haushi,to kowa da ra'ayinsa hakan ba aibu bane,idan ku wajenku don na nuna kulawa ta da kaunarta ta yan uwantaka garesa illa ce ni wajena abune mai kyau,kuma ba abunda zan fasa daman ba danku nake ba ra'ayin kaina ne,tunda shi da nake ma wa bai tab'a nuna min wani hali ba,to bazan damu ba ,sannan mgn ta karshe itace kudaina gulmata haka nan akan Favorite,koma mi nake ciki akansa bai dameku ba" Tatashi ta fice a fusace idonta cike da kwalla,nasan hali ai kukan zataje tayi kuma zuwa gobe zatai kamar komi bai faru ba,dogon tsaki naja kurin ina cewa "Sakarai da bata san inda ke mata ciwo ba" Rukee tace "tayi nisa bata jin kira ai" "Kar Allah yasa taji kiran bai daman ba." Washe gari nasha mamakin fushinta don irin haka bai tab'a faruwa ba mufeey bata dogon fushi, mutum ce mai saurin hucewa duk da bata da saurin fushi,Rukee kanta tayi mamakin yadda kwata-kwata bata shiga sabgarmu ba yinin ranar,saima fara shirya kayayyakinta tai dake dakinmu, bamu sha mamaki ba saida mukaga ta koma bangaren Mama dakin Najeeba,abun ya matukar bamu mamaki har su Ummanmu da akai gabansu, Mami ta kasa shiru ta ce "waccen kuma lafiya?Ina zata da kaya haka? Naga ai lokacin tafiyarsu bai ba" Ummanmu da daman kamar jira take wani abun ya faru tsakaninmu da Mufeeyn, don kwata-kwata bata son alakarmu da ita saboda goggo Habi intazo bangaren Abba Habibu take sauka, ta ce cikin ginshira "inajin uwata zata bi can bangaren, ai gara haka azo a takura mana yara suna zaman su suna walawa" Naji banji dad'in mgnr ba duk da cewa fad'a mukai da ita, Mamin ta ce "Au kuma fa,amma Rukayya miya had'aku kamar kunyi fada tsakaninku?" Duk shiru mukai ba wanda yai magana saboda dai bamu son suna aibata Mufeey da Goggo Habi, Ummanmu ta ce "Don ubanku zaku Mana bayani ko kuwa?" Turo baki nayi Ina kauda kai gefe alamun bazance komi ba, Mami ta ma Rukee tsawar da dole saida ta fad'a mata abunda ya had'amu............"To daga yau na yanke kusancin dake tsakanin ku,daman kuma ai kune bakwa jin mgnr mu inbacin haka miye na hudda da ita tunda bata cikin jam'iyyarmu ita da uwarta,don haka koma mi zatai masa shi Ramadan d'in ba ruwanku,na raba tsakaninku ni Allah yasa ma ta aure sa zasu ci ubansu in ta rasa lomar kaiwa bakin salati wataran," Duk mukai shiru muna saurarenta ita Ummanmu,don wani lokacin tafi Mami zafi da daukar abu babba koda baikai babban ba,d'ago kan da zamuyi mukai ido hud'u da Abbanmu bayan sa kuma Ramadan ne,wata irin fad'uwar gaba naji ta rufto mun,nai imanin suma sunji kalar abunda naji,da alamar kuma sunji komi tun d'azun. Tsitt kaji falon yayi su Ummanmu suka sadda kanun su k'asa sun kasa magana,Mami tatashi cike da borin kunya tai bangarenta mukam ai kasa motsawa mukai,baice mana komi ba ya wuce hanyar part d'insa nayi imanin ba kyalemu yayi ba,yanzu dai baida lokacin mune don tafiya yayi tun ranar sunan Anti Sha'awa sai yau Allah ya dawo dashi.........Bin bayan sa ummanmu tayi mu kuma mukai zuru,Rukee ta ce "shikenan zamu gaya masu wajen Abba,kin san wannan shine karo wajen na uku cas d'inmu wajensa akan Yah Ramadan" Kasa magana nayi saboda nasan halin Abba sarai,nice zanfi kowa hukuntuwa saboda dae nafi kaud'in baki,kuma duk nina jawo abun tunda ni nai maganar data hangula Mufeey d'in,har akai sallar magariba jikinmu a mace ko dinner bamu samu damar zuwa munyi ba,amma naga umma cikin tsananin damuwa tabbas ita ya juye mata kwandon masifar,kuma nasan Abba bazai mata ta sauki ba shi bai had'a yan uwansa da kowa ba,kuma bai kaunar wariyar da akeyi acikin gidan. Abba bai neme mu ba sai da safe an gama breakfast ranar mun kasa zuwa gaida shi,fitowa ma muyi hidimar mu mun kasa aiko saiga Ummi ta shigo, "Yaya Rohee keda Yaya Rukee Abbanmu na kira" Duk saida muka tsorata wallahi da zullumin hakan muka kwana,bamai yima d'an uwansa mgn kamar kurame, jiki a sanyaye muka fito zuwa kiran da yake mana.,, Mufeey muka fara cin karo da ita zaune k'asa,sai shi Abban suna gefe guda Da Yah Ramadan suna magana,kamar wani ake zai masa ko miye oho dae,zaman mukai duk a kasan muna jiran ya sallamesa mu gaida Abban,mu duka ba wanda yace da mufeey k'ala ita ma batace mana ba,saida suka gama sannan muka gai Yah Ramadan d'in,ya ansa atakaice sannan muka gaida Abbanmu,bai ansa ba yafara cewa "Ku rik'e gaisuwar Ku bana so Rukayya da Layla,ashe kun daukan sakarai wofi.........don girman Allah Abba ka daina cewa haka wallahi bamu dauke ka haka ba" Na fad'a inajin kwalla na son zubo mun, kallon banza ya watso mun ya ce "ke ai yau mai ansarki hannuna sai Allah,wallahi zanar ki zan kamar Allah ya aikoni,yau zaki san cewar baki gama girma ba don duk girmanki dukanki bazai gagareni ba,dawo nan bazan ji duk wata mgnr ki ba" Sai hawaye suka balle mun,abunda na guda kenan nasan halin kayana,kuma yadda ya fad'a babu fashi yau mai ansata sai Allah, ya kalli Mufeey ya ce "gaya mun miya had'aki da yan uwanki mufeeda" Kanta k'asa tana share hawaye take masa bayanin abunda taji muna fad'a akanta a daki, sannan ta d'ora da cewa "Abba ba wannan ne karon farko da suke hantara ta akan Favorite ba,duk don me zan ringa kulasa ina nuna damuwata akansa,so suke na ringa banzatar dashi irin yadda sukeyi ni kuma bazan iya ba Abba, jinina ya had'u da nashi sosae,hakuri kawae nake dasu saboda ina son su ina son mu'amalar mu saboda kasancewar sune tsararrakina banda yaya mace banda qanwa,su nake kallo matsayin yan uwana abun soyuwa agareni,amma sun kasa ganewa sun kasa daina abunda suke mun akan sa,sai naji na hakura da shige masu zanja baya dasu kawae Abba..........." Falon yai shiruu sai shashshekar kukanta akeji da jan majinar ta,Duk Ramadan din na nan baije ko ina ba Abban ya nisa cikin sigar lallashi yake cewa "Mufeeda kiyi hakuri kinji ko,shi zumunci daman haka yake kana son yinsa amma su yan uwan basu baka had'in kai,kiyi hkr karkice zaki janye daga garesu ai kece mai hankalin cikin su,kin fisu wayau da hankali da sanin ya kamata kuma kece karamar su,amma kin cinye girman a haka don haka ki yafe musu kibarni dasu zan dauki mataki zasu gyara kinajina" Tana goge fuskarta ta d'aga kai ta ce "shikenan Abba sunci darajar ka na yafe musu,suma ina mai basu hk.........Aa karki fara basu hakuri sune zasu baki,don haka Ku bata hkr yanzun nan" Rukee ta fara magana tana hawaye, "kiyi hkr Mufeey hakan ba zata sake faruwa ba" Ta ce "ya wuce Allah ya yafe mana gaba d'aya" Abba ya kalloni kallon banza da wulakanci,muryata na rawa abu ya tsaya mun a makoshina ba abunda na tsana irin a turkeni,kuma ace inba mutum hakuri bakina na rawar kuka nace "I'm sorry" Abban yai k'uta yana cewa, "tashi kije abunki kinji ko,ki kuma kwaso kayanki ki dawo dasu dakin ku" "Shikenan Abba zanyi yadda kace" "Allah yai miki albarka" Tashi kurin naga yayi ya zaro shafceciyar dorina kamar ta zanar dawaki saboda girmanta, kamar sabuwa ma don ban tab'a ganin sa da ita ba, kafin kowa ya ankara ciki hadda ni ya shammaceni ya zabga mun ita ga ilahirin jikin,ban san sadda na zabura ba ina fasa wata k'ara kamar ana zarar raina,tunda na girma nai wayau ban taba ganin Abba ya dakeni ba,ko dunguri bai taba mun ba lallashine tsakanin mu da nasiha sai gashi yau ya cire hannu da dorina yana dukana akan wad'ansu da basu kaini daraja a wajensa ba,wannan bakin cikin ya danne zafin bulalar da yake mun duk da yadda yake dukana cicin karfinsa, mufeey keta bashi hakuri da Rukee amma Ramadan ficewar sa yayi kamar baisan mike faruwa ba,ban sake motsawa daga inda nake ba saboda zallar bakin cikin wannan abun,saida Allah ya kawo Hajja ta shiga tsakanin mu,sannan ya hakura sai sauke numfashin bacin rai yake........."Attahir kana lafiya kuwa?ka saka babbar budurwa kamar Layla kana duka da dorina?" Ransa b'ace yace "karki tambayeni Hajja,kin san duk abunda zai jawo na daketa ba karami bane,kuma akan k'in bin umurnina wallahi yanzu na fara dukanki koda gidan aure kikaje kai ko singa da sabon gari kika haifa kuwa,Ku tashi kuban waje ke kuma Rukayya na baki last warning idan na sake kamaki da kamancin wannan kinga hukuncinki kema,mutanan banza da wofi." Mun fito mukai karo da Umma a fujajan tataho zuwa part din,bata tsaya wajena ba ta isa garesa tana huci muna iya jiyota daga inda muke, take cewa cikin karaji........."Wallahi Tallahi TAHIR idan ka sabauta mun yarinya kotuce zata rabani dakai,!akan me?akan wasu shashashu wofi dasu zaka dakar mun yarinya da wannan dorinar ta bugu jakkai..........MAIJIDDA!!!" Tsawar da Abban ya daka mata harmu ta tsorata,durkushewa nai na saki wani irin kuka na bakin ciki,inajin yadda yake maida mata cikin kakkausan halshe tare da cewa, "wallahi idan kika sake aibata yan uwana saikin tafi gidanku,don ki gane yan uwana sun fiye mun ke muhimmanci nesa ba kusa ba...........to in na tafi gidan mun sai me?ai daman acan kaje ka ganni ka auro,don girman Allah Tahir ka sawwake mun yanzu ba sai anjima ba,daman nagaji da kwankwad'ar bakin ciki agidan nan" Abun yayi k'amarin da Hajja ta kasa tsawatar musu suji,sai magana take sun kasa yin shiru kafin sadda Abba Habibu zai zo Abba ya cire hannu ya zabga ma Ummanmu mari,sannan yace tatafi gidansu ya sawwake mata igiyarsa guda. Tashin hankalin da nake ciki ma ba a magana saboda ko kusa bamuyi zaton abun yakai haka ba,ji nayi duk duniya ba wanda na tsana irin RAMADAN da Mufeey saboda duk ta dalilin su ne Abba yake neman rasa hankalin sa har ya mari umma ni kuma yai mun bugun kawo wuk'a, mizan dasu kuma ahalin yanzu...........tuni Umma har ta had'a kayanta tana kuka,kuka sosae irin wanda ban tab'a ganin tana yinsa ba a rayuwata,alamar yau turarta takai bango kenan Bamu San ya akai ba tun fitowar Abba Habibu zuwa wajen Abba sai ga Abbanmu ya fito fuskar sa murtik,bazan iya tuna iyakar lokacin da naganshi haka ba,Ina rik'e da umma nak'i sakinta nida Ummi muna ta kuka ya shigo bedroom d'in,ya tsaya kurin bakin k'ofa rungume da hannunsa,sakin umman mukai munata sharb'en majina,ta dauko akwatin ta nufo k'ofar zata fita sha gabanta duk da bai sake fuskar ba har sannan,........."Ki koma ki aje akwatin na maidaki......ban maidu ba!nace ban maiduba a yau gidan ubana zani,koda bashida rai haka uwata ma na gwammace naje na zauna a kango.....da......dai in......in sake zama dakai" Kuka ya kwace mata ta durkushe tana yi sosae,muma muna taya ta saboda muna son uwarmu duk abunsa zai sata kuka muna k'insa.........durkushin yayi gabanta cikin sassaucin fushin sa yasake cewa, "yanzu ma gaban yaran zaki daga mun murya Maijidda?........naje na d'aga ni ai a gabansu ka cire hannu ka maran,na d'aga muryar zan kuma sake d'aga maka,ka tashi gabana TAHEER!"...........gani mukai kurin ya d'agota ya rungume jikinsa,ai har rige-rigen ficewa muke nida ummi,muka baro bangaren nata gaba d'aya. Daga haka mukaga umma ta fasa tafiyar amma kuma babu walwala fuskarta kwata-kwata,gidanma gaba d'aya ya canza kowa rai babu dad'i,mufeey ta kasa dawowa dakinmu kuma bamu ma juna magana kwata-kwata,sai ma naga sun fara shirin tafiya gida. Ranar da zasu tafi ma sai nai tafiyata gidan Anti Rafeea don har raina haushinta nakeji,karma ace RAMADAN tsanar da nake masa ta linka sosai,wannan ne dalilin rabuwar mu da mufeey ko a waya balle gani da ido,bata sake zuwa Abuja ba sai da akace an saka bikin mu,shima kuma Ramadan d'in wannan na daga cikin dalilin da yasa na kara tsanarsa. Mom Muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....25 Ana cikin hakan Yah Rafeeq ya dawo daga course din da yaje,koda yaga yana yin yan gidan kowa ba karsashi yasan akwae dalili,bai tambaye ni ba sai bayan kwana biyu,Ina kuka nake bashi labarin komi hadda dukan da yai mun da sakin ummanmu, ranar naga zallar b'acin rai ainun tattare dashi idanun sa kamar wuta saboda jaan da sukai,lokacin ne yake ce mun "Rohee lokacin da yadace in rabaki da gidan nan yayi,daman ina da niyyar in nadawo nayi ma Abba Maganar auren mu,inba haka ba komi zai iya faruwa tsakanina da Wannan mutumin (RAMADAN),don haka inaso kiban dama da sahalewarki afara batun auren mu," Kaina k'asa muna cikin motarsa sabuwa daya siya kwanan nan,Ina jan majina yayin da zuciyata ta shiga bugu ba k'ak'k'autawa ban san dalili ba, shiru kamar bazan ce komi ba saida na gama tunanin da nake nace masa "banda haufi akan Auren ka Yah,kuma ko yaushe aka saka banda matsala kawae inaso mu fara service kafin hakan,banso sai munyi aure in raba hankalina biyu" "Service ba matsala bane,karki damu da hakan nidae insan cewar kin zama tawa zan iya iko dake akodayaushe shine kwanciyar hankalina,in yaso daga baya koma miye sai kiyi banda matsala indai kin zama halalina,to ya kike gani inyima Abban mgnr?" Na kasa kallon sa kaina still a k'asa na d'aga masa kai,cikin jin dad'i ya daki sikiyarin motar yana cewa "Ohhh yess" Murmushi kurin nayi Ina juyar da kaina wajen window kunya na kamani,kamar wani wanda aka yima babbar kyauta. Bamu sake mgnr dashi ba bayan hakan,mun dai cigaba da muamalar mu kamar kullin koma fiye da kullin,don duk safiya karajin kaunar juna muke kodan shine mutum na farko da zuciyata tafara so oho? D'an tsakanin ne Result d'inmu ya fito munyi farin ciki sosae ganin yadda yai kyau sosae,kowa yai mana murna Abba Nura yai mana gift na sabbin wayoyi latest phones da aka yayi yanzu,hakan ba kad'an yai mana dad'i ba don rayuwata Ina son waya sosai,Abbanmu kau ko hanky bai bamu ba har sannan bamu dawo dai-dai dashi ba,haka ummanmu itama banga alamun hucewa daga gareta ba abundai ya tab'amu sosae shiyasa mun kasa yafewa Su mama,don duk ma miye sune da alhakin hakan. List dinmu ya fito na tafiya bautar k'asa mukai sa'a an ajemu waje guda Rukee,ganin hakan ya kwantar mun da hankali don bana kaunar zuwa wajen da babu Rukee jinta nake kamar raina,ina son Rukee fiyema da son da nake ma Ummi da Anti Rafeea,shak'uwar mu takai kololuwar shak'uwar da duk inda d'aya yaje bazai ji wani dad'i ba in ba d'ayan,muka fara shirye-shiryen shiga camping 3weeks da zamuyo komi munyi sa tare da taimakon Yah Rafeeq duk wata siyayya shine yai mana da aljihun sa,ya hutar dasu Abbanmu hakan kuma yai masu dad'i sosae,Ana saura kwana biyu tafiyar mu aka kwantar da Yah Ramadan Asibiti wai ulcer shi tatashi,wallah ko ajikina ban tausaya masa ba don dai ciwone aida cewa zan Allah ya k'ara,har Ana gobe zamu shiga camp bamuje ganin sa ba duk da mun san Abba ido ya sanya mana akan rashin zuwan namu,kowa yaje Hadda umma amma bamuje ba. duk da mun san ita da Mami ba da son ransu sukaje d'in ba,muna falon Umma zaune muna kallo yai sallama ya shigo,duk muka sauko muka gaidashi ya ansa ba walwala,Umma tace masa "sannu" bata dago kanta ba ta cigaba da danna wayarta, ya dubeta ransa b'ace "kin gaya ma su Rohee suje sugano Ramadan?" Yanzun ma bata kallai ba ta bashi ansa, "Kai nike jira ka sanar dasu" Mu kanmu bamuji dad'in maganar ba muka sadda kanmu k'asa cikin jin rashin dad'i, "nagode Maijidda," Yajuya zai fita har yakai k'ofa ya jiyo yana kallona, "keda Ruk'ayya da ummi Ku sameni a mota" Kasa motsawa mukai bayan fitar sa saida ta ciro kanta daga wayar ta dalla mana harara sannan kowa ya tashi cikin azama muka suri hijabban sallar mu muka rufa masa baya,yau da kanshi yake tuk'in daka kalli fuskar sa kasan ransa ab'ace yake ainun,uffan baice mana ba har muka iso Asibitin wani babban asibiti ne aka kawo sa ba wanda ya saba kwanciya ba, yana gaba muna biye dashi a baya jinake wani bakin ciki yana cika raina,bana kaunar sake had'a wuri da Ramadan,tsanar ganin sa nake yanzu ma da damar dazan b'ace ma zuwa inda yake wallahi sai nayi, muna isowa bakin k'ofar dakin aka kirasa a waya yace mu isa ga dakin nan bari yaje yayi bak'o can wajen parking. Dad'i ya kama ni yana juyawa ya b'ace naja tunga bakin k'ofar nak'i shiga, Ummi da Rukee suka kalleni kafin ma suce komi na rigasu ta hanyar cewa cikin masifa, "wallahi da dai inje inganshi inyi masa sannu gara ace Abba ya kasheni,yadda na tsani wannan mutumin ko mutuwa banajin na tsana hakan,don haka kudai da kukaji zaku iya ga hanya" Ummi ta shige bata sake bi takaina ba don tasan inta tanka ubanta zanci,Rukee ta ce "Rohee baki daddara Hukuncin Abba ba ko?miyasa kin faye kafiya ne?shin idan kinje kin masa sannun lafiya zaki basa?sannu ai ta fatar bakice basai kinyi masa addua ba,nima ita zanje inyi masa sannun ai daga ita dai bawani uwar zamuyi masa ba ko?" Sai kuma naji maganarta gaskiya ce dole na shiga daga shi sai Najeeba d'akin,yana kwance drip na shiga jikinsa singlet ce fara sol da ita jikinsa sai dogon wando na pajamas,idonsa a rufe ruff zaka d'auka bacci yake amma kuma idonsa biyu. Kallon farko da nayi masa naga ya rame sosai da sosae,zuwa can Mama ta fito daga bayin dakin,ummi da Rukee suka gaidata ni kuma nai kamar banga kowa ba. Duk sukai masa sannu da jiki ya amsa a takaice,daga haka ba wanda yasake magana nidae daman tunda na shigo wayata nake dannawa ina kallon status d'in mutane wani yagama wani yashigo,videos hadda na wakoki kala kala ba abunda ya daman kamar ina cikin dakin mu........"malama kina damun marar Lafiya pls" Cewar Najeeba tana mun kallon wulakanci,na ciro na watsa mata nawa kallon na ce "Dagaske?" Na cigaba da abunda nake, silently gently da muryar irin ta marasa lfy naji ance mun, "idan ba zaki iya adjusting kunna wannan hayaniyar ba pls workout" Dago kaina nayi na dubi inda yake kwance kamar bashine yai mgnr ba,naja siririn tsaki kurin nai hanyar fita ina cewa, "daman bisa k'aya nake ai" Ba wanda baijini ba don na fada da sautin da zasuji,ban damu da idon Mama ba don itama d'in natsane ta tunda sune ummul'aba isin komi na fitinar cikin gidanmu. Ina fita suma Suka biyoni muka nufi wajen mota, Rukee ke cewa "ki daina irin abunda kike,koma mi kikeji a ranki game dashi ki ringa dannewa,Rohee baki yana yanka wuya kuma watarana baka san illar da maganar ka zatayi ma ba,in kikai shiru ma ya isa ansan an b'ata miki ba dole saikin yi rashin kunya da rashin kirki ba,Abunda kikai baki kyauta ba koba komi Mama na wajen........Rukee ya isan haka don Allah,na riga na gama gane kin daina kishin iyayen mu kin daina kishin kanki balle ni,wad'anan mutanan da suka hana iyayen mu mata zaman lafiya da mazajen su kikeso na risina mawa?kina gani saboda su da Mufeey tsakanina da Abba ya lalace ko gaisuwata sama-sama yake ansawa,aka mari uwata akansu aka saketa duk kina nufin na risina na nuna rashin damuwata kenan?" Iska naja inajin tsananin takaicin hakan, ta ce "ni ban daina kishin su umma da Mami ba,haka kema ban daina kishinki ba nima kuma haka,saidai duk Abunda zamuyi da zaija ran iyayenmu ya b'aci suyi fushi damu muyi kokarin kiyayewa,kina da tabbuna wajen Abba Rohee kiyi fatan kirabu lafiya dashi,kina sane da cewar irin illar sab'ama iyaye kin sani sarai amma kike take sanin kina yin son ranki,ni nasan wallahi hadda zugar Yah Rafeeq sannan ki sassauta k'iyayyarki ga Yah Ramadan saboda watarana" Jikina ya d'anyi sanyi bance mata komi ba mukai ta jiran Abban ya dawo daga cikin asibitin muka dawo gida,washe gari muka shiga camping cikin sa'a da nasara. ******** Akwana a tashi ba wuya wajen ubangiji har gashi mun shiga camping mun fito cikin yar dar Allah,wasu kwanaki muka soma zuwa wajen service dinmu nan cikin garin Abuja, har sannan dai ba wata rigima da ta sake tashi a gidan,amma kuma shirin dai da ake nema ayi babushi har hanxun,kawunan sunk'i haduwa waje guda jiya iyau saidai hkr kurin dasu Abba keyi da iyayen mu mata,don matsalar duk ta tare a wajensu,kwatsam wata ranar lahadi ba aiki da safe muna gyaran dakinmu nidai Rukee,ita tana gugar kayanmu ni ina sanitation na dakin,saiga Umma ta shigo dakin da sallama muka ansa mata, tayi tsaye tana kallona sai na aje tsintsiyar hannuna na ce "umma lafiya" D'an murmushi tayi tace "kizo Abbanku na kiranki" Gabana saida ya fad'i don yanzu kiran Abba tada mun hankali yake,tunda muka daina d'asawa dashi shikenan ya zamar mun dodo........"Ke dallah can ba laifi kikai ba" Naja ajiyar zuciya nabita muka tafi,Ina shiga Falon idanun su sukai mun caaa har naji na sake shiga rud'u,Abba habibu da Abba Nura sai shi Abbanmu da Yah Rafeeq,na samu waje can na zauna Ina gaidasu cikin jam'i Abba Habibu ne ya fara mun magana "Y'ata Rohee natsu kinji ba wani babban abu bane,mun kiraku ne don muji halin da kuke ciki keda d'an uwanki Rafeeq,saboda a halin yanzu wani malamin ku a makaranta yazo neman aurenki ga mahaifinki,to sanin cewar akwai d'an uwanki dake sonki yasan ya mukace ya d'an jira tukunna, idan mukaji ta bakin ku cewar har yanzu kuna kan bakan ku na son juna shikenan,sai a bashi hakuri ku kuma mu tsayar da lokacin da ya kamata,kafin kizo munji ta bakin Yayanki cewar yana sonki kuma shirye yake da Auren ki,yanzu ke muke jira?" Kunya ta lillib'eni,na sadda kaina k'asa y'an yatsuna kurin nake wasa dasu na rasa abun cewa,sunyi mun yawa kunyar ansa musu nake,ganin hakan sai Abban ya ce "wannan shirun naki yana nufin kin amunce da d'an uwanki kenan,to ai Alhamdulillah mu daman haka muke so *GIDA BATA K'OSHI BA AI BA ANKAI DAWA BA* Ku tashi kuje Allah yai muku albarka,zamuje ma Hajja da wannan labarin mai dad'i don daman munfi son muji ta bakin Ku kafin taji komi wajenmu,Allah ya tabbatar da alkairi ya kuma nuna mana lokacin auren da rai da lafiya" Mom muhseen&Assad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....26 LAST FREE PAGE.......👏🏻 *BAYAN KWANA BIYU* Daga Ranar da akai mana wannan kiran nida Yah Rafeeq wani irin farin ciki ya wanzu a cikin zukatanmu,domin kuwa kallon kanmu muke matsayin ango da amarya don munyi imanin cewar Hajja itace mutum ta farko da wannan had'in zaiyi ma dad'i nesa ba kusa ba,tunda a kullin ba abunda take buri illa auren zumunci tsakanin mu da y'an uwan mu maza,saboda a ganinta hakan zai taimaka wajen gyaruwar zumuncin dake neman b'alb'alcewa,nidashi mun saki jiki sosae kaunar mu muke sha kamar an riga an saka mana rana,Sau tari Rukee kan ce mun "Ki ringa sassauta soyayyar nan Rohee,ance in zakai so kayi shi sai-sa,sai sa haka nan in zakai k'i kayisa shima sama-sama,saboda baka san abunda Allah zai nan gaba ba,shiyasa zakiga ko akan Yah Ramadan Ina miki mgn ki sassauta,ba dan cewar nima baya bani haushin ba Aa ina dai dannema raina ne kurin,to shima Yah Rafeeq d'in ki sassauta hakanan..........kasa danne bacin raina nayi nace mata "inajin raina yana b'aci sosae idan kina nuna mun kamar wani abu marar kyau zai faru dani akan kaunar da nake ma d'an uwanki,miyasa bakya kyautata zato akodayaushe tsakanina dashi Rukee?miyasa bakin ki baya fadar kalmar da zanji dad'i tsakanina da Yah Rafeeq,?kamar ba d'an uwanki ciki guda ba?" Girgiza Kai tayi tana cewa, "wallahi kaunar da nake miki ce tasanya nake jiye miki gaba,namiji ko ya kake dashi anso ka ringa jan ajinka saboda watarana,amma kiyi hkr tunda mgnta tana b'ata miki rai,banyi da wata manufa ba kuma ko kusa bana k'inki dashi,hasalima Ina matuk'ar farin ciki da hakan kiyi hkr bazan sake miki mgnr ba" Nafi kowa sanin Rukee,kuma nafi kowa sanin cewar tana kaunata duk abunda zai cutar dani bata kaunarsa,kuma zatai bakin iyawarta ta shigar mun fad'an,hakan danai tunani sai jikina yai sanyi sosae,na iso inda take na rungumeta jikina sosae ina cewa cikin sanyin murya, "Kiyi hkr Rukee wlh son da nake ma Yah rafeeq yasa bana iya jurar a kushe soyayyar mu,ciwo abun kemun amma na fahimce ki kuma zanyi kokari in gyara" Shikenan muka dai-daita bamu yarda wani abu yajamu ga doguwar gaba muna kokarin kiyaye hakan. Bamu sake ji daga su Abba ba,muna dai saurarensu. Yah Ramadan saida yai kusan kwana biyar asibiti kafin aka sallamosa,mudai daga ranar bamu sake zuwa ba har ya dawo gida,Ko agidan ma bazuwa bangaren nasu muke ba inba abinci za'aci ba,saifa in munga Abba na gari muje mu gaida Abba Habibun shikenan,ko mamar bama zuwa mu gaida inba suna tare ba. *********** *💥TUSHEN K'ADDARATA*💥 Abba Habibu,Abba Nura,Abbanmu su duka sun zagaye Hajja a falon ta sunzo da niyyar bayanin Auren Rohee da Rafeeq bayan sun gama dukkan bayanin da suke son yi mata, ta gama nazartar su da fahimtar dukkan abunda sukazo domin sa,tayi shiruuu na wajen minty ashirin da d'oriya batai magana ba,su kuma sukai zuru suna kallonta yayin da dan danan suka ga wani yana yi akan fuskarta, su duka ba wanda ya iya tambayarta dalilin shiga wannan yana yin da take ciki,sai Abba Habibu ne yayi jarumtar yin magana cikin tausasa halshen sa,saboda yaga wani abu dayake neman rikirkita masa natsuwa a tattare da Hajja, "Hajja munzo da batu mai muhimmancin da muka d'auka cewar zaki fi kowa farin ciki da hakan,amma kuma daga yana yin fuskar ki ya nuna mana kamar bakiyi na'am da zancen ba,ko kina ganin akwai wata matsala da kika hango mu bamu hangeta ba,don Allah ki magantu ko zamu fita daga rud'un da muke ciki" Shirun ta sake wanzuwa acikin falon Hajja,sai karar Ac da k'yaftawar agogo kurin kakeji yana tashi a falon,har sun riga sun sare da yadda Hajja tayi shiru ta kasa magana,kuma fuskar ta babu wani alamar lamarin yai mata dad'i.........kwatsam suka tsinci maganarta tana cewa cikin kakkausan lafazi, *"AURE TSAKANIN RAFEEQ DA ROHEE BAZAI TAB'A YUWUWA BA"* kamar saukar aradu haka sukaji maganar ta ratsa kunnuwan su,cikin razani da mamaki da neman ba'asin wannan maganar mai matukar rikitarwa suke kallonta, ta jinjina kanta cikin sake basu tabbaci mai kyau, "Wannan maganar haka take,kuma babu abunda zai iya canza ta daga yanzu daga gobe daganan har abadan," Wata irin zuface ta keto masu su dukan su,saboda abun yai mugun zuwar musu a bazata wannan shine ANA WATA GA WATA, ana zaton wuta a mak'era gata a masak'a,duk suka sauko k'asa cikin nuna k'ask'antar da kansu da neman alfarma da magiya, Abba Nura ne ya fara magana cikin k'ask'antar da kanshi yake cewa, "Hajja kiyi ma Allah da manzon sa,ki fidda mu daga cikin wannan rud'anin kiyi mana bayanin da zamu iya fahimtar wannan dalilin naki,wallahi kin jefamu cikin wani irin tunani mai rikitarwa" Abba Taheer ya ansa da cewar "Wallahi mun san kinfi mu son Auren zumuncin nan ga yaran nan,saidai bamu tunanin jin haka daga gareki ba muna bukatar karin bayani dole kina da Hujjar ki domin baki yin abu haka nan" Abba Habibu ma yace, "Tun da har kika fad'i cewar Aure tsakanin su babu shi har Abada,wallahi Hajja cikin mu ba wanda ya isa ya bijirewa umurnin ki..........."wannan ba umurnina bane Habibu,umurnin Allah ne shine ya haramta ba ni Layla ba" Kallon junan su suke cikin sake kullewar kai,duk sadda tayi wata maganar sai tashin hankalin su da kullewar kansu ta k'aru,shin ko dai Hajja ta fara rikicin Tsufa ne?to Amma Hajja batai kama da tsohuwar da zatai irin wannan rikicin ba,ras take cikin hankalinta babu wani rikicewa tare da ita garau take............."Ku tashi kuje idan Allah ya kaimu safe Ku tara mun kaf iyalanku na kusa dana nesa zanyi magana gaban kowa,Amma tabbas wannan Auren babu shi har Abadan,na sallameku kuna iya tashi" Tatashi tayi cikin d'akinta tabarsu kamar masu zaman gaisuwa,kowa da tarin tunani cikin kanshi da zuciyarsa wanda yake kamar xai faso kirjinsu ya fito. ******** *RANAR DA BAZAN TAB'A MANTAWA DA ITA BA A RAYUWATA* Tun Daren jiya na kwana da wani irin firgici na tunani da rashin sanin mike damuna,yinin jiyan ban iya tab'uka komi ba kwance kurin nake,ko abinci saidai liquid abu nakesha niba rashin lafiya nake ba,haka dae gani nan bazan iya sanin taka mai-mai abunda ke damuna ba,Rukee duk ta damu bini-bini zata shigo ta dubani har ta kasa hkr ta gaya ma ummanmu,itama tazo tai ta tambayata mike damuna saidai ince ba komi,data matsa mun sai na sanya kuka kawae,saboda ban san mizance mata ba. Kuka nayi sosai ko zan samu saukin zuciyata,da hakan dae bacci ya sace ni sai bayan la'asar na tashi,koda yah Rafeeq ya kirani a waya shima irin wannan yana yin yake ciki don dai shi namijine yafini jarumta,yace mun ko zamu fita yawo musha iska nace Aa ya kyaleni kila zuwa gobe zan warware,dole ya kyaleni. Amma bayan wani lokaci zai sake kirana yana tambayata ya nakeji,kuma bana iya hkr saina dauka inhar yakira inka gammu dole zamu baka tausayi ainun,kamar mun san akwae wata mummunar k'addara dake jiranmu safiyar Asabar d'in. Ina dakin Ummanmu Ina breakfast Abbanmu ya shigo da sallama,daga yana yin sa zaka fahimci baida kuzari,baida wani natsuwa tattare dashi na d'ago ina gaida shi ya kalleni wani irin kallo da ban tab'a ganin Abba yayi mun shi ba sai yau,cikin lafazi mai taushi ya ansa mun da kulawa har yana tambayata, "Lafiya lau Rohee,mike damunki duk jiya ban ganki ba,kuma gashinan naga ni duk kinyi wani iri" Kwalla ta ciko idona nace cikin son yin kuka, "Abba ban San mike damuna ba,bana jin dad'in komi wallahi tun jiya nake haka har yanzu," Sadda kanshi k'asa yayi cikin kulawa ya data kaina, "I'm sorry,karki damu kanki da damuwa everything will be fine ohk?" Na jinjina kaina kurin sannan yasake cewa "kuma kin iya addua why not ba zaki ta lazimtar addua ba har kiji sauki a zuciyarki" Jinjina kaina nayi Ina cewa, "Ina yi Abba,zan kara kan wacce nake yi d'in" "Good girl,Allah ya sawak'e ki maza ki gama zamuyi meeting babban falon Hajja nan da karfe shad'aya na safe,Fahad ma na hanya tun asuba na kirasa na sanar dashi" Ya nufi cikin bedroom d'in Ummanmu,na shiga cikin wani irin matukar faduwar gaba,duk da ba yau akafara meeting ba irin wannan amma naji jikina ya bani kamar akwae wani abu dazai shafeni marar dad'i,haka dai naita cakalkalar cheeps din na sha rabin tea din dake gabana na tashi na nufi dakin mu, na iske Rukee na shafa tayi wanka na ce mata,"kinji wai meeting za'ai" "Nima yanzu Mami ta shigo tana gaya mun,wai kowa da kowa zaizo hadda su Anti sha'awa suna hanya suma,Ammi ce kurin ba zata zo ba saboda nisa kuma abun yazo suddenly" Jikina sanyaye na zauna inata loliyar wayata nama rasa wane irin tunani zanyi,yah Rafeeq ya kirani a waya.........cikin sauri na d'auka "Rooh" Wani irin lumshe idona nayi inajin kiran har cikin jikina,kamar ranar ya fara kiran sunana, naji kwalla ga idona nace masa "Love kana jin ko abunda nakeji?wallahi ji nake kamar za'a rabani da wani abu mai muhimmanci a rayuwata, wata irin kewa nakejin kaina ciki kamar ina rayuwa ni kad'ai..........sai kawae na kashe wayar na kama kuka mai tsuma zuciya, Rukee tayo kaina cikin damuwa "Rohee wai miye haka,kwana biyu duk kin firgice kin sanya mun cikin damuwa,don girman Allah kiyi hkr ki ringa ambatar hazbunallahu wani imalwakeel,ba abunda yafi karfin addua don Allah,na kasa daina kukan saida naji itama tana kukan sannan na hakura,muna nan zazzaune saiga Anti Rafeea ita da iklas da tsohon cikinta daker take tafiya ma,ba dad'ewa Yah Fahad ya iso shima Anty Sha'awa da Farhan suka iso,gida ya kammala muka tattaru duka a falon Hajja inda ake meeting............. Kowa ya gama Hallara a wannan falon Hajja na cikin kujerar ta ta hakince, fuskar ta babu wani annuri a gimtse take baka isa kawa wani wargi ba, daman kuwa kowa na shakkarta yana shayin fushinta, don yanzu aljannunta sun ci uban mutum basu da mutunci,don ma suna dad'ewa basu motsa ba. Tunda na shigo na samu waje na zauna jikina yake wata irin rawa-rawa,addua ce kurin bakina saboda zan iya kasa control din kaina,Addua aka umurci Yah Ramadan ya bude taron da ita,yana can gefe guda cikin natsuwar sa ta kodayaushe ya gyara zama sannan yace sallu ala Nabiyyul kareem,akai salati ga Annabi sannan ya karato addua marar tsayi muka shafa.......... Shiru ya d'an ratsa na wani lokaci kafin Hajja ta tashi daga jinginar datai da kujera tana fara magana cikin kakkausan lafazi, "Na sanya a tara mun ku ne saboda inaso nafad'a gaban kowa,kuma in k'ulla wani zumunci da nake fatan ya d'ore har bayan raina, nasan kowa dake cikin wanan gidan yasan da cewar ROHEE DA RAFEEQ SUNA SON JUNA,KUMA AURE SUKE NIYYAR YI KO?"aka ansa mata da cewar hakane ba wanda bai san da wannan mgnr ba. Ta jin jina kai tare da cigaba da cewa, "to babbar maganar da nakeso kusa sani itace AURE TSAKANIN SU BAZAI TAB'A YUWU WA BA HAR ABADAN...........Innalillahi wa inna ilahir raju'un!Hajja wace irin magana kike fad'a haka?" Mami ta rabka wannan innalillahi cikin karaji da kid'ima da ta shin hankali,Ummanmu ta anshe da cewa "Hajja wace irin magana ce wannan?ya kike so yaran suyi tsawon shekara da shekaru suna tare sai yanzu ki b'ullo da wannan matsalar?" Su dukan su hankalin su ya tashi matuk'a ba wanda ya iya tanka musu cikin su Abba,saboda sun san dolene maganar ta gigitasu ta kid'imasu kamar yadda tayi masu,a wannan lokacin bazan iya misalta halin da zuciyata take ciki ba,abunda na sani shine tana bugawa fiye da kima tana bugawa ne kamar tana neman hanyar fitowa,na daskare inda nake zaune yayin da falon ya dauki wata irin hayaniya da surutu tsakanin juna,Hajja ta zuba ma kowa ido tana kallon sa, yadda bakeji nasan Yah Rafeeq fiye da hakan yakeji na kasa kallon inda yake zuface keta keto min kamar an jik'ani da ruwa,Rukee ta rik'e hannuna sosai cikin son bani kwarin guiwa wanda ban dashi a halin yanzu,Ummanmu hawaye ta fara yi tana cewa "inhar bakida wani dalili na yanke wannan alakar kin cutar da y'ay'an nan,ba karamar cutar wa b.........MAIJIDDA!!" Abbanmu ya daka mata tsawar data gigita kowa a wajen,falon yai tsit bakaji motsin kowa sai kukan ummanmu tace "kayi mun fiye da haka Taheer,amma wlh inhar babu Hujja wannan auren sai anyishi wallahi," "Kyaleta Taheer,barta tayi mai isarta Aure ne dai Ya HARAMTA tsakanin y'ay'an da suka dora ma dogon buri,kuma ba kowane da wannan abun ba sai ni nan,Nice nayi komi duk don inyi maganin ku akan k'iyayyar da kuke nuna ma ZEENAH Allah ya bani wannan damar na aikata hakan agaresu daku,saboda akan kunnena kukai maganar ranar da aka haifi Rohee cewar zaku had'asu Aure ita da Rafeeq idan Allah ya rayaku nan gaba,kuna son kaunar y'ay'anku ta d'ore har abadan kamar yadda zumuncin ku keda Maijidda zai dore har abada ta hanyar had'a zuri'a,akan kunnena kukai wannan alkawarin,ni kuma naci alwashin sai idan ba raina hakan zata tabbata" "Wata rana ke maijidda kina goyon Rohee a lokacin ba zata gaza wata hud'u ba,na tusa ku gaba muka tafi kauyen mu dake can hanyar katsina,domin muje bikin d'an kanena saboda tunda aka aureku baku tab'a zuwa garinmu ba,saboda a cewar ku baku san zuwa kauye ku kwaso kirci,ita kuma Safiya tana goyon Rukee watan ta Shidda tunda wata biyune tsakanin su,na tafi da k'udirina a raina Ina adduar Allah ya bani damar cikawa,munje Rimi lafiya aka tarbemu cikin mutunci da mutuntawa aka bani d'aki d'aya daku muka sauke kayanmu anan,muka shiga hidimar biki kunata sabgoginku ni kuma duk kallon ku nake,Ina neman hanyar da zan aiwatar da kudirina har aka kwana daya aka kwana biyu ban samu damar hakan ba,sai wata dubara ta fad'o mun na aiki yaro ya siyo min maganin bacci mai karfin gaske,na zuba a cikin zobon biki na sake leda na daure na kawo muku bayan kunci abincin dare kuka d'ora dashi,dan danan bacci ya zo maku kowacce ta tafi shimfid'arta ta kwanta tare da yarta,ranar banyi bacci ba har saida na tabbatar burina ya cika. Bayan bacci ya sace ku yaran ku nata wasa idonsu biyu,na dauki Rohee daga jikin ki maijidda,naje na ajeta jikin Safiya bayan na dauke Rukee na goyeta,Bayan wani lokaci Rohee ta fara kukan nono na banza da ita, naga dagaske ba kujin kukan sai nai amfani da wannan damar na ciro nono na bata ajikin safiya,yarinya ta anshi tana sha kamar ba gobe,sosai take shan nonon don daman Rohee lokacin Allah yayita da tsotso,Saida tasha tayi tatul har bacci ya sace ta,ban dauketa ba saida asuba tayi da tasake sanya kukan tana son sake shan nonon,na sake kanga mata ta kama zuk'a,ita ko Rukee na tare dani data motsa akwai koko sai in danna mata tasha ta koma bacci,dana tabbatar burina ya cika Rohee tasha nonon Safiya yadda aure ba zai tab'a tabbata tsakanin ta da d'anta ba sai na maida ma kowa d'anshi gabanshi naje nayi alwallar asuba nayi salla nayi kwanciyata,koda kuka tashi ba wacce ta fahinci miya faru,ni kuma ba wanda na sanar ma wa sai Habi ta itace kawae tasan da wannan sirrin,shima saboda halin rayuwa koda ban kawo yanzu ba,kunji dalilin da yasa nace Aure tsakanin su ya Haramta............ _INA FTN MASOYANA ZASU FITO SU NUNA MUN IRIN KAUNAR DA SUKE MUN,TA HANYAR SIYEN WANNAN LBRIN NASAN BA ZAKU BANI KUNYA BA,INA MATUK'AR ALFAHARI DAKU AKODAYAUSHE NI TAKUCE KU NAWA NE,LOVE U FISABILILLAH_ Last free pages. Ga duk wanda ke buk'atar sa complete zai iya biyan 500 ya samu nashi. 3150952555 First Bank Aisha Abubakar My phone no. 09034722970 itace no. Dinda zaka turo kati in kati ne zaka turo,pls banda kira only chat inka turo kudinka ka min mgn ta WHATS APP saina saka grp. Ngd sosae masoyana Ina alfahari daku sai najiku. Mom muhseen&Asaad An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels