*WASU MAZAN* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMSY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. PAGE 1 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Cikin tashin hankali take tafiyar tana duba lokaci a wayarta. Duk wanda ya kalleta ya san cewa tana cikin tsananin damuwa! Damuwar da ta sanya canza yanayin fuskarta. Musaddik ta ƙara gyara goyon da ta yi masa daidai lokacin da wayarta ta fara ringing alamun ana kira. "Na shiga uku! Har ya dawo ban iso gidan ba." Ta furta tare da dage ƙirjinta hawaye na bin ƙuncinta. "Hello Abban Raihan, wallahi gani nan na shigo cikin unguwarmu, ka bani mintina ƙalilan zan shigo gidan." Daga can ɓangaren aka tsaki wani wawan tsaki." Ni dai ba ki ɗauke ni a matsayin mijin ba ko Nasreen? Tun da karatun ki yafi girkin sai na ga uban abin da za ki ci a gidan, domin kin ji na rantse miki yau ke da abinci sai ƙarfe sha ɗaya inna daw..." "Don Allah ka yi hakuri ko don yaranmu. Ka san horan yunwa ba shi da amfani. Kuma kana ganin ragowar taliyar da muka ci jiya da daddare, shi na sawa Raihan ta tafi makaranta da shi." Ta katse shi cikin rawar murya tana faɗin haka. "Kin damu da ita ne? In har kin damu da ita tun lokacin da na kira ki, ya kamata ace kin bar duk abin da kike yi kin dawo, tun da na ga karatun bokon ba lahira za ki tafi da shi ba." "Ka yi hakuri lecturer ɗin ne san ba shi da hakuri ko na ɗauki excuse ba zai lamunta ba." "Tun da ubanki ne ba." Ya ce tare da jan tsuka ya kashe wayar. Hawaye ne suka ci gaba da bin ƙuncinta. A yanayin da take ba za ta iya biya wa ta ɗauko Raihan ba, musamman da ya ke jiranta. Da sauri ta ƙarasa shiga cikin gidan bayan ta buɗe ƙofar get ɗin gidan. A harabar gidan ta same shi yana ƙoƙarin shiga motarsa. Da sauri ta ƙara da gurinsa dai-dai lokacin da ya shiga cikin motar ya rufe ƙofar. Ganin ya ta da motar ya sa ya ta ruga ta buɗe masa get. Sai da ya zo bakin get ɗin ya kalleta ya ce,"Tun da kin fi jin maganar Malaminku sai ki je ya ba ki abinci." Hawaye shar! Suka zo mata. Yayin da cikinta ya yi wani irin ƙugi na yunwa. Ganin ya fice daga gidan ya sa taka ƙafa zuwa inda Musaddik yake ta ɗauke shi. Falon ta shiga ta zauna jabar tana jin yadda zuciyarta ke tuƙuƙin baƙinciki. Cikin rashin dubara ta miƙa zuwa kicin da sauri. A tunaninta ko ya kawo mata cefane, amma babu komai. Ƙofar ɗakinsa ta ja a kulle Komawa ta yi ta zauna tana jin yadda zuciyarta ke bugawa tamkar za ta fito waje. Saboda takaici ta kasa fita sai kiran Maman Muwadda maƙociyarta ta yi, ta roƙeta ta turo mata Raihan. Tana zaune a gurin tana karanta wasiƙar jaki suka shigo. Da gudu ta rugo ta faɗa kanta." Umma, kin dawo?" "Eh Raihan, ya makaranta?" "Lafiya lau kuma an mana karatu sosai. Sai dai abincin da kika bani lalacewa ya yi tunkafin na ci, haka na yi ta wuni da yunwa har sai da na dawo Maman Muwadda ta zuba mini." "Allah Sarki! Ki yi hakuri ina can ina tunanin zai iya lalacewa saboda akwai wake." "To,"Ta ce tare da ɗaukar wayarta ta zauna a gefenta. Tun tana saka ran zai ji tausayinsa ya dawo, har ta cire tun da ba shi ne farau ba. Bayan ta isar da sallar Isha ta yi shafa'i. Wuri kuma ta barshi da ninyar in ta tashi da daddare za ta yi." Ɗaukar Musaddik ta yi ta shinfiɗar da shi kan gadon bayan ta yi masa shinfida. Sannan ta kama hannun Raihan suka shiga ciki. "Ummu, har yanzu Abba bai dawo ba, kuma bacci na ke ji ga shi ina jin yunwa." "Bari na ɗauki miki ruwa kisha ki kwanta in ya dawo na girka zan tashe ki, kin ga Musaddik shi ma ya yi bacci." "To," Ta ce bayan ta hau gadon. "Addu'ar bacci fa?" Ta ce mata wanda ya sanya ta ƙaranto sannan ta rufe idanunta. Ita ma cire kayan jikinta ta yi sannan ta kwanta tana karanta addu'ar bacci ta shafa musu. Tana kwance sai juyi take yi kamar wata maciya. Hawaye ke kwaranya a ƙuncinta yana jiƙa matashin da take kwance. Cikin dare ta kasa bacci janyo Musadik da yake kukan ta ba shi mama. Duk da cewar babu komai a ruwan nono, amma ihu kukan da yake mata wanda zai iya tada maƙota ya sanya ta saka mishi fatar a baki, wanda ya shiga ja yana ajiyar zuciya. Tausayin yaron ya cika mata zuciya dai da suka yi nasarar zubar ƙwallar dake idanunta. "Ka yi hakuri ka daina jan fatar nan babu abin da za ka samu." Ta ce masa da tare da ƙoƙarin janye fatar nonon a bakinsa, wanda ya sanya shi canyara ƙara. Cikin sauri ta mayar masa ina jijjiga shi. Ganin ya ja babu komai a fatar ya sanya shi saki yana faɗin,"Umma, ci ci." Cikin gwaranci yake daɗi yana dukanta da hannunsa. Miƙewa ta yi na nufi kicin da sauri tana jijjiga shi duk da ta san cewa babu komai. Ka yi hakuri ka kwanta?" Ta yi masa maganar tamkar ba ƙaramin yaro ba, tana nuna masa kular da babu komai. Ganin ta miƙa masa kular abincin ya sanya shi turewa yana kuka. Turus! Ta tsaya ina kallon yaron da bai wuce shakara ɗaya da rabi ba cikin tausayawa Kukan da yaron yake yi ya sanya ta kasa komawa baccin wahalar da ya ibe ta. Wannan dalilin ya sanya ta kasa yaye shi don na samu rangwame da ga tsotson da yake mata. Cikinta ne ya yi wani irin ƙara tare da bada sauti. Da sauri ta dafe cikin tana jin yadda kayan cikinsa suke juyawa, tamkar za ta yi aman da ta san kummalo kawai zai fito. Kanta ta ɗaga tana duba agogon bangon dake cikin ɗakin. Ta san cewa ba ya dawowa da daddare, amma na yau ya fi dadewa. Wani irin juya yake rufe mata idanuna har ba na iya ganin komai na cikin ɗakin. Ba ta san lokacin da ta fashe da kuka ba tuna halin da ta ke ciki. Zaman aurenta; da ba shi da maraba da zaman gidan yarin! Mijinta Farouk bai san darajarta ba. Ko na ce bai ɗauke ta a wata aba wacce Allah ya yi wa daraja ba. Irin rayuwar da suke gudanarwa ta gwammace gara mutuwata. Sai dai, ba ta da gatan da ya fi nan. Tunaninta ya katse daidai lokacin da na ji alamun buɗe get tare da shigowar motarsa. Da sauri ta mike jikinta na rawa ta fito ta isa ƙofa ta buɗe masa, tare da fita don ta ɗauko kayan da ya zo da shi. "Saboda iskanci kin ji na dawo tuntuni ba ki fito ba? Uban wa kike kira ya zo ya kwashi kayan?" "Ka yi hakuri sankatan ne ya ƙi budewa da wur.." "Ke tsaya!" Ya daka mata tsawa yana faɗin haka, wanda ya sa ta ja ta tsaya ba tare da ta ɗauki kayan da ta buɗe gaban motarsa don ta ɗauka ba. "Wallahi kin ji na yi miki rantsuwar ɗan musulmi matukar kika ɓata mini ƙofa sai dai ubanki ya gyara mini " Da sauri ta ɗago kanta tana kallonsa, yayin da hawayen da take ƙoƙarin maida su, suka shiga turereniya a kyakkyawar fuskarta. "Eh, kin ji ai ubanki na ce har wani daraja ya ke da shi da ba za a dage shi ba? Mutumin da ya kasa ci daku ballantana ya ba ku ingantacciyar rayuwa?" "Ka ji tsoron Allah Faruk, ka daina zagin iyayena. Ban san me na yi maka ba, ka auro ki ka kawo ni cikin gida ka, kana gasa mini aya a hannu, sannan ka matar da ni kamar baiwar ka. Rayuwar aure ba kangin bauta ba..." "A hakan ma ai gata na yi miki, da yanxu kina can kina fama da ƙanzon tuwo da garin kwaki in an samu." Ya ce yana watsa mata mugun kallo. Ranta ne ya ƙara ɓaci jin tozarci da yake mata ta rintse idanunta tana faɗin,"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Alllahumma ajirni fi musibati!" "Zagina za ki yi ko ƙarya na yi?" Ya furta yana ƙoƙarin matso ta da shirin zare bell din dake wandonsa. Matsawa ta shiga yi domin in har ba ta yi watsa ba, sai ya ɗumama mata jiki kafin ya kwanta. "Ka yi hakuri." Ta furta tare da saurin iban kayan da ya siyo "No, da ki tsaya ki yi mini rashin kunya tun da ba ki da tarbiyya. Yanzu ki kwana a gidanku da ko gurin kwana ba ku da shi mai kyau. Stupid girl. Har wani baki kike da shi na magana. In mata ne ga su nan birjik a duniya sun yi kwantai ba irin ki ba, kin yi da ƙugu kamar an daurawa taɓarya zani. Wata jemammiya dake." Ya ƙarashe maganar daidai lokacin da ta shige cikin falon. Kuka ne sosai ya kubce mata har sai da ta duƙa. "Jiran ki na ke yi ki zo ki kwashe kayan fa." Ya daka mata tsawa yana faɗin haka wanda ya sanya ta fito da sauri ta ɗauki sauran kayan. Tsaki mai ƙarfi ya ja tare da rufe mirgina motar har ya kusa haɗawa da hannunta. Sannan ya bita cikin gidan yana takun isa. Wayarsa a hannunsa kamar yadda ya saba duk lokacin da ya dawo ita ce take zama abokiyar hirarsa. Da ya shiga cikin falon sai ya zauna a kan kujerar ya hakimce yana latsa waya, yayin da take gefensa cikin damuwa tana kallonsa. Murmushi ya ke yi har da buga ƙafa. Murmushi da yake yi zai tabbatar maka da mata yake chatting ɗin, duk da cewar ba sabon abu bane a gareta, amma sai da ta ji wani irin ƙunci ya mamaye ta, yayin da wutar kishinsa da ƙaunarsa suka yi matu rubdugu. "Kina gidan uban wa na yi ta kiran ki ba ki ɗaya ba?" Tambayar da ya yi mata ya dawo da ita cikin hayyacinta. "Wallahi babu inda na je, bayan na dawo makaranta, sai dai in wayar ta mutu ka san ɗauke wa take yi." "It didn't concern me.'" Ya ce tare da make kafaɗa sai kuma ya ɗora dacewa,"Shegen son gasa da goga kafaɗa da 'ya'yan masu hannu da shuni. Kina 'yar gidan Malam Shehu ko uban me ya sanya kika na ce sai kin yi makaranta? Na gaya miki ɓacin Mommy wallahi da ke da makarantar nan har abada!" Shiru ta yi ta yi tare da mayar da kanta ƙasa ba tare da ta tanka ba, don ta saba. Neman hanyar da zai gabata abinci ya ke yi. "Ma za ki tashi ki dafa mana abinci." Ya ce ba tare da ya kalleta ba. Kallonsa ta yi da sauri tana hawaye, amma ganin baya kallonta ya sa ta miƙa cikin galabaita tana haɗa hanya. Binta da idanu ya yi tare da sakin wani wasan tsaki. Ƙazamiya ji shigar da kika yi da daddare kina zaune da wata banzar doguwar riga. Ni na ƙara auran mata Bahaushiya an yi an gama yare zan ɗauki don sun fi ku sanin darajar mijinta iya tattalinsa, saboda na san da ace ita ne, yanzu ta yi shigar da zai ɗauki hankalina. Ko da yake ina abin da za a nuna ƙirji kamar silifas?" Ya faɗa hankalinsa na kan wayarsa. Idan da sabo ta riga ta saba da cin mutuncin da yake mata, ko da a gaban kowa ne, amma duk lokacin da ya gaya mata, sai ta ji kamar ta kashe kanta don baƙinciki. Da ta shiga kicin ɗin, sai da ta yi kuka mai idan ta sannan ta kunna gawayi da ƙurar tana kallon gas ɗin ta da ya daina repelling tun da suka gama amarcinsu. Da ƙyar ta samu gawayin ya kama kasancewar jiƙakke ne. Bayan ta hura wutan sannan ta zuba ruwa ta koma don ta gyara waken ganin akwai gyara. Tana girki tana hawaye har ruwan ya tafasa ta sanya waken. "Ke! ma za ki zo ki ɗauki wannan ɗan banzan yaron na ki ya tashi zai hana ni kallo." Ya ƙwala mata kira yana faɗin haka. "Abba Hairan, kai fa uba ne a gurinsu bai kamata ace kana kiransu da munanan kalamai ba." "Ƙarya na yi? Yabon ne kuke yi mini ke da shi a cikin gidan nan in ban da kuci ku yi kashi?" Shiru ta yi ta kasa ce masa komai sai zuciyarta da take mata rukunin ɓaci rai. "Wuce ki bani guri tun kafin ƙi ƙara ɓata mini rai na sanya ki kashe girkin nan." Da sauri ta shige kicin ɗin domin ta san cewa ba ƙaramin aikinsa bane. Goya shi ta yi da yake kuka yana ƙunnai ta cigaba da girkin da shi. Ganin ta ɗora girkin ya san mya shi daina kuka yana kiran ta gama. Tausayin yaron ya cika mata zuciya har sai da ta ji kamar ta yi kuka. Tana kicin ɗin ba ta gama girkin ba har sha biyu ta buga. Sannan ta ga shinkafar ta tsotse sannan ta zuba masa fulas ta kai mishi bayan ta sanya wa Musadik. Kallon wulakanci ya yi mata tare da bude fulas ɗin fuskarsa a yatsine kamar ya ga kashi. "Na gaya miki ki daina sanya mini spicy da yawa ko?" "Wallahi curry powder da ganyen na'ana'a na sa." Ta ce mishi a tsorace. Ba tare da ya kalleta ba ya ɗauki cokalin ya fara cakala yana ci wanda zuwa can ya ture abincin. Cikin wahala take cusa abincin sakamakon ƙirjinsa da ya riƙe mata. Sam ba ta jin ɗandanonsa saboda yunwar da ta ƙwaƙwuleta. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 2 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Cikin wahala take cusa abincin, sakamakon ƙirjinsa da ya riƙe mata. Sam ba ta jin ɗanɗanonsa, saboda yunwar da ta ƙwaƙwuleta. Da ƙyar ta samu ta yi loma biyar, sannan ta mayar ta rufe, don ta san ƙila wannan abincin har gobe shine abincin da za su ci. Ɗaukar Musadik ta yi, da ya gama cin abinci ta yi ta wanke masa hannu, sannan ta kai shi ɗaki ta kwantar. Gyara yaron ta yi, tare da ɓingirewa sai bacci. Da kyar da siɗin goshi ta samu ta tashi Hairan, kasancewar ta mai nauyin bacci. Littafan karatunta ta ɗauka, ta shiga ɗakin cikin murna ganin jefa sun kawo wuta, za ta yi karatun test ɗin da za su yi gobe. Yana zaune a gurin yana chatting da 'yan matansa, har agogo ya buga daya daidai, sannan ya miƙe ya kashe kayan kallon ya shiga ɗakinsa. Wanka ya yi ya fito zuwa ɗakinta . A lokacin ta dakata da karatunta ba don ta so ba, sai dai bacci ɓarawo da ya yi nasarar sace ta. "Ke Nasreen," Ya ce yana dukan bayanta wanda ya sanya ta farka da sauri tana zare ido. Harararta ya yi bayan ya kwanta." Ba na gargaɗiki da ki daina sa yaron nan a gadon nan ba?" Ya ce mata cikin ɓacin rai. "Abban Hairan, akwai sanyi ka tausaya musu." Banza da ita ya yi tare da jan Musadik can gefe da karfi. Shiru ta yi ba ta da bakin magana. Ta san cewa in aka kawo agola a gidansa, tsaf zai iya kashewa, tun da ɗan cikinsa ma bai tausaya masa ba. Babu kunya ya kwanta tare da rungume ta yana sauke ajiyar numfashi a fuskanta. Hawaye ne ke zuba a ƙuncinta wanda take gogewa ba tare da ta bari ya gane ba. "Ni shikenan ba ni da daraja da ƙima, sai in dare ya yi nake mace a gurinsa, amma da safe baiwa?" Jin ya yi shiru ya sa ya ta yi laƙwas, a jikinta saboda tana so shi ya kai sunan da za a kira shi namiji, amma kwata-kwata ba shi da hali, munanan halinsa da suke sanya tana jin kamar ba ta yi dace miji ba. Ture ta da ƙarfi ya yi har ta bugu da gado. Ta rintse idanunta tana shafa gurin daidai lokacin da ta ji ya ce,"Kin wani shiga jikinta kamar mage? Nufin ki ni zan yi aikin? Ke ma kin san yau ba ni a wannan mood. Yanzu na hakan taimaka miki zan yi don kar ki je kina kwaɗayin mazan jami'a, saboda ba wani tarbiyyar ƙwarai kika samu ba?" Gabanta ne ya yi mummunar faɗi jin abin da ya ce. Hankalinta ya tashi sanin cewar sam babu kyau miji ya rinƙa zargin matarsa. "Zargina kake Abba Hairan? Duk tsawon shekarun da mun ayi ban yi zina ba sai yanxu?" "Ko wa na iya canzawa lokaci guda. Yadda rayuwa ta canza, babu wa da zan iya yadda da shi a wannan duniyar, kuma yadda kike cuɗanya da waɗannan mazan jami'an masu kama da buntsura, ai ba zan yi shedar ki ba. Na yi karatun na san yadda mazan jami'a suke." Ya ce cikin zafi. "Na shiga uku kaicona! Sai na yi tur da rayuwa matuƙar mijina bai yarda da ni yi ba." Ta ƙarashe maganar tare da sakin razanannen kuka sai kuma ta ɗora da cewa," Sau nawa kake chatting da 'yan mata, a kan gadona kuma magana ta batsa? Wane namiji ka ga na taɓa yin waya da shi ko na kawo shi gidanka?" "Ke kina ke jina? In ga za ki yi aiki kiyi in kuma ba ki so, sai na ce huta rororo." Ya faɗa tare da jan filo ya rungume. Kuka sosai ya kubce mata har da sheshsheka. "Ke wallahi in kika tayar da maƙota sai na yi mugun saɓa miki, domin duk wanda ya tsare ni yana tambayata jikin ki zai gaya miki."Ya faɗa tare da zama a kan gadon wanda ya sa ta yi tsit sai na zuci da take yi. Kwanciya ta yi nesa da shi tana hawaye. Ganin haka ya ja bargo yana faɗin,"Aikin banza, tura agwagwa a ruwa. Ki riƙe jikinki uban me zan ji." Banza da shi ta yi ta kwanta tana jan majina. Kasa haƙura ya yi don ya san ba za ta kawo kanta ba. A hankali ya ja jikinsa ya shiga jikinta tare da rungumota. Da sauri ta mike zaune, tana kallonsa duk da babu wadataccen haske a cikin ɗakin. "Na sha gaya maka ka daina irin wannan domin ba ɗabi'a nace na musulmi. Annabi ya horar da mu kafin aikata sunna mijinta gabatar da abin taɓi. Ko ba ka gabatar ba ya kamata ka tashe ni. Faruk, kuma ni ma mutum ce ina buƙatar mu gabatar da soyayya ba wai ka yi gaba gaɗi ba." "Saboda ba ki da abin da zan shafa a jikinki ne. Ki zauna kina nan za ki ga na auro mace yar duma-duma wacce zan more sadakina." "Ni ma ba haka ka auro ni ba. Ta zo wane dare ne jemage bai gani ba. Matuƙar za ka yi mata irin rayuwar da kake mini wallahi yadda za ta koma sai ya fi nawa. Kai fa ma'aikacin gwamnati ne, amma sai an yo cefane a gidanka. Hatta man shafewa watarana sai na roƙo. Duk sana'ar da na fara sai ta karye saboda ci da gida. Ba ka da mu da karatun yaranka ba. Ni nake ɗawainiya da su. Wallahi Abban Raihan, ina tausayawa rayuwarka, saboda haƙkin iyalinka da kake ɗauka." "Fitowa fili za ki yi kice ni ɗan wuta ne, domin na lura abin da kike son ki faɗi kenan. Banza shashasha, kin san yadda na yi karatu? An gaya miki ni wawa ne, da zan saki kuɗina da na samu a wahalar ki wulaƙantar? To wallahi ki cire wannan bazan tunanin na ki, saboda na san darajar kuɗi. A lokacin da na yi rayuwar wahala babu uban da ya taimaka mini, sai yanzu za ki rinƙa tsara mini yadda zan yi rayuwa. In kin raina abin da na ke miki ki nemo in kin ɗauka neman kuɗin a banza ne." "Wannan dalilin ya sanya nake son na kammala digirina, na samu aiki ko da koyarwa ce a private." "A tunani ki kuma sai na bar ki ko?" "Haba Abban Raihan sam ba ka yi wa rayuwata adalci ba, matukar ba ka bar ba, ai ba za ka hana ni nema ba. Kana ganin iyayena basu da shi mahaifiyata tana fama da jinya." "Ni na ɗora mata? Tun da bani bane sai ki shafa mini lafiya. Ko da yake cigaba da karatun ma yana ƙila wa ƙala, tun da ɗan iya da ya sa ya ki shi ma ya kasa biya." Gabanta ne ya faɗi tuna haka wanda hakan hawaye ya wanke mata fuska. "Allah zai taimaka mini ba zai barni ba, tun da ya ga ina son karatun." "Aci gaba in iska na hura wuta." Ya ce sai kuma ya kalleta ya ce,"Nasreen, za ki bani hakkinsa ko na je titi na nema? Tun da ga mata nan masu kyau waɗanda suka fiki." "Ka je ba zan bayar ba wannan kai da Allah." "Ke kuma wutarki daban ce, don in har Ina sama kina can ƙasa-ƙasa. Kina sane da Allah da Mala'iku suna tsine miki. Ki rinƙa buɗe murya kina karatun qur'ani ke a dole malama. Ƙiri-kiri ko bancin kirki ba kya bari na yi, amma in har na kawo buƙata ta sai ki koma kamar ba musulma ba." Kallonsa ta yi cikin tsananin mamaki jina bin da yake faɗi."Dama ai ba ka nuna ilmin ka sai anan gurin, ni kuma ka ji na rantse in har ba za ka rinƙa yin soyayya ba, wallahi ba zan lamunta ba." "Kin amince na kunna miki mu kalla sannan mu yi soyayyar? Domin ni sha'awarki kwata-kwata ba na ji." "Allah ya kyauta! Ubangiji ya tsare ni da kallon surar wasu kai ma ina maka addu'ar ka daina domin babu kyau. "Ashe jiki zai yi tsami." Ya ce tare da sanya hannunsa ya haɗata da jikinsa da ƙarfi. Hannu ta sanya ta ture shi ta sanya kuka. "Nasreen zan ci ubanki wallahi zan miki dukan tsiya a dakin nan!" "Don Allah Abba, karka dake ta." Ya ji muryar Hairan tana faɗin haka. Tsaki ya ja yana kallonta cikin takaici. "Kina ganin abin da kike mini ko? Ba gaya miki za ki rinƙa kwana a ɗakina, amma wallahi ba da yarannan ba. In kin amince ki tashi mu je." "Ni kuma ba zan bar yarana ba ƙanana saboda kai. Yarannan fa 'ya'yanka ne ba agola na taho da su ba." "Ina ruwana ko daga jiki a suka fito. Ni wallahi yarannan suna ɗaya daga cikin abin da yasa na ƙara tsanarki. Duka shekararmu huɗu da aure, amma kin tara mini 'ya'ya biyu. Kin ji na rantse miki wallahi na ganki da ciki sai dai ki haifa a gidanku, tun da kin ƙi yin tsarin iyali." "Ni ba zan kashe kaina ba, ai akwai na maza ka je ka yi mana. Sai ni? Da ba ni da gata, kuma 'ya'ya rahama ne wani na nema da kuɗin da bai samu ba." "Ki je ki basu duk na yafe musu, ba ni buƙata saboda ina cikin tashen ƙuruciyata, ba za ki tara mini 'ya'ya ba ki tsigar da ni." "Ka ji tsoron Allah kai ka ganni kana so ba tushe aka yi maka ni ba." "Na yi dana sani saboda ba ki dace da ni ba. Sam da na san haka kike da ƙafiya da taurin kai babu abin da zai sanya na siyo ciwon kai na kawo gidana, kuma wallahi in har ba ki canza ba, kina gab da shiga cikin layin zawarawa don ba zan ɗauki iskanci ba." Gabanta ne jin abin da ya ce, sai ta yi shiru can kuma cikin muryar kuka ta ce,"Allah shi ne gatana." "Ni kuma ki ce sheɗan ne gatana in kin so." Ya ce tare da ɗaukar ta can ya yi ɗakinsa. Tana kuka tana dukan ƙirjin shi, amma bai kula ba sai da ya biya buƙatar ta kamar yadda ya saba, sannan ya koma ya kwanta yana sauke numfashi. "Allah ya saka mini ni da 'ya'yana." "Ki fito kai tsaye ki zage ni." Ya ce tare da rufe idanunsa sai bacci. Ita kuwa ta kasa yin bacci tana jin yadda Musaddik ya ke kuka yana faɗin,"Umma, fo." Wanda hankalinta ya ƙara tashi amma babu yadda za ta yi.Hankalinta ya kwanta jin Hairan ta sanya shi a fon.Miƙewa ta yi ta, shiga bayi ta yi wanka tare da ɗauro alwala ta daura tawul ɗin da ta fito. Ganin ya yi bacci yana jan rago ya sanya ta lallaɓa ta ɗaya kansa ta ɗauki key ɗin ɗakin.Buɗewa ta yi ta fice tana takaicin rayuwarsa, don ta san da kyar ya yi wankan sai gobe in zai fita aiki ya yi. Daki ta koma ta gyara musu kwanciya, ta mike tare da sanya rigar sallarsa ta shinfiɗa dadduma. Sallah ta fara yi. Raka'a biyu ta yi bayan ta isar sai ta mayar da kanta ta rinƙa fadin,"La'ilaha illa anya subuhanaka.inni kuntu minaz zzalimin." Har sau arba'in da ɗaya, sannan ta yi wa Allah kirari tana kuka, da ya shirya mata mijinta ya zaunar da su lafiya. Haƙiƙa Ummar Faruk miji ne na nuna wa tsara. Yana da kyau daidai shi. Dogo ne amma ba shi da haske sosai. Sannan yana da jiki na maza hali ne kawai ba shi da shi. Sai shegen son 'yan mata duk da cewar yana da maƙo, amma yana sakin ma 'yan matansa. Ba ta tashi daga daddumar ba, sai da ta aka kira sallar asuba, sannan ta miƙe ta yi Raka'atul fijr ta sallame tare da yin sallar asuba. "Umma na tashi." Hairan ta ce tana miƙa da salati. "Good girl, then go and brush your teeth." "Ok, Umma." Ta ce tare da wucewa cikin bayin. Bayan ta yi brush ta yi alwala, sannan ta fito ta shinfiɗa karamar daddumarta ta yi sallah. "Ummu, good morning?" "Morning baby how are you?" Ta ce mata tare da rungume ta. "Am fine Umma." "Good, mu koma bacci kafin gari ya waye ina da lecture zuwa ten, kuma test za mu yi, ina shirya na kaiku school sai na dawo na gyara gidan na tafi ko?" "To umma, I wish you all the best." "Thanks babyna. Allah ya yi wa rayuwarmu albarka." Ta ce tana shafa ka kansu tare da tofa musu addu'a. Yaran sune duniyarta, a dalilin su take rayuwa a gidan ubansa, domin ta san matuƙar ta rabu da mahaifinsu rayuwarsu da na ta sun shiga garari. Wannan dalilin ya sanya ta ke jure duk ɗaci da uƙubar zaman gidan ubansa don ta tallafi rayuwarsu. Tana ƙoƙarin ba su tarbiyya ta gari, a yadda take son su yi karatun boko ko Hausa ba ta cika yi musu ba. Sannan tana kula da karatun Muhammadiya ta su. Da kyar da taimakon Allah ta sanya mahaifiyar Faruk, ta tilasta shi ya sa ya su a makarantar boko mai tsada da islamiya da hadda. Ga shi yarinyar kwanyarta na ja, don tana da wayo wani lokacin maganar da take yi ya girmi shekarunta. Kuma duka shekararta uku. "Umma, zan je na gaida Abba." Ta ji yarinyar tana faɗi tare da ƙoƙarin sauka daga gadon. "Karki damu ya yi sallah, ya kwanta kin san in ya yi sallah sai tara yake tashi." Ta yi mata ƙaryata hakan tare da mayar da ita ta kwanta. "Mu yi bacci in muka tashi sai ki gaishe shi." "Ok,".Ta ce tare da kwanciya. Ƙarfe baccin awa ɗaya ta yi, ta tashi dama akwai wuta ta sanya ruwa a kettle. Ɗaukar ruwan ta yi ta yi musu wanka sannan ta shirya su. Ragowar abincin ta ɗumama ta saka mata a kula sannan ta zuba mata ta ci. "Umma, don Allah ki daina sa mini ɗumame lalacewa ya ke yi kafin na ci. Kuma 'yan ajinmu bobo da biskit suke zuwa da shi." "Ba na gaya miki ki daina sa ido kan abin da suka zo da shi ba?" "Sorry Umma." "Good girl. Na ce miki ina gama makaranta na samu aiki zan rinƙa siya miki duk abin da kike so." "To, Umma Allah ya taimaka ya sa ki gana kuma ki samu aikin." "Amin." Ta ce tana kallonta tana murmushi. "Bari na rinƙa sa miki abincin a roba kar ya lalace, sannan kuma mu je shagon Dauda na siya miki biskit guda ɗaya." Ɗaya mata kanta ta yi sannan ta ci gaba da cin abincin. Kallonta take yi cikin tausaya wa, ganin mahaifinta na da halin da zai siya nata duk abin da take so, amma tsabar maƙonsa da son abin duniya, tare da rashin girmama yaran ya sanya shi ƙin siya mata. Kasancewar babu wani tafiya tsakanin gidansu, da makarantar ba ta jima ba suka isa. Miƙa mata biskit ta yi tare da kama hannunta." Ga shi ko kawo jakarki na sanya miki. Ki ci kin ji sam kar ki roki kowa, in kuma kika yi haka aljanuna za su faɗa mini." "To ba zan riƙa ba ai na daina tun da kika ce babu kyau." "Yauwa, Allah ya yi miki albarka ya ba ki ilmi mai amfani." Ta karashe maganar tana ɗaga mata hannu ganin ta shige cikin makarantar. Bayan ta dawo a gauguace ta gyara gidan ta shiga wanka. Ba ta jima ba ta fito ta sanya doguwar rigarta tare da rolling ɗin ɗankwalin abayar ta dauki jakarta da littafanta. Ɗakinsa ta tura ta shiga yana zaune kan sallaya da waya a hannunsa da alama lokacin ya yi sallah, don ko tashi daga gurin bai yi ba. Zuciyarta ta ɓaci ganin tsadadden murmushi da yake yi a fuskarsa, amma sallamar da ta yi ya canza fuskar daga farinciki zuwa ɓaci rai. "Abban Hairan, ina kwana?" Ta furta cikin sanyi ta tare da danna kishinta. Harara ya watsa mata sannan ya ci gaba da danna wayarsa tuna abin da ya faru juya. "Da ban kwana ba za ki ganni?" Dariya ce ta suɓuce mata, ta san dama yana da shegen riƙo shi zai ɓata maka, kuma ya riƙe mutum sai su yi sati yana jin haushinta. "Zan wuce school." "Na riƙe ki ne?" Ya ba ta amsa tare da ije wayarta. "WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 3 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Zan wuce school." "Na riƙe ki ne?" Ya ba ta amsa tare da ije wayarta. "A'a, Allah ya ba ka haƙuri." Ta furta tana ƙoƙarin juyawa. Tsaki ya yi tare da gyaran murya."Umma ta gaida ashsha. Kin san dai ƙwandalata ba za ta yi ciwo ba, don ban aike ki ba. Shegen baƙinciki da son gogayya da ni, ya sanya kika nace karatun. In kika gama digirin sai ki ɗaura da masters sannan Phd kin ga mun zama ɗaya." Ba ta ce masa komai ba ta miƙe za ta tafi. "Nufin ki ba za ki haɗa mini breakfast ba za ki tafi? Kin san dai ba zan ci wannan ɗan iskan abincin, da kika cika gishiri da barkono ba." "Sai mu da ba mu da gata." Ta ce a ranta amma a fili narai-narai ta yi da fuska. "Haba Abban Hairan na yi matuƙar latti fa. Kuma in ban da tsatsuba yaushe rabon da ka yi breakfast a gidan nan?" "Saboda ban da ra'ayi yau kuma yunwa nake ji, saboda jiya don mugunta abincin da na ci duk kin ƙwaƙule ni." Harararsa ta yi jin abin da ya ce sai ta kalli agogo. "Don Allah ka yi haƙuri ka je ka ci a inda ka saba ci, na riga na yi latti, kuma test na ke da shi." "Allah ya sanya exam za ki zana wallahi sai kin dafa mini abinci. Ki ma godewa Allah indomie ne, kar kuma ki ja na ce taliya ko shinkafa." Shiru kawai ta yi ta tsaya tana kallonsa don ta san zai iya. "Ga shi." Ya ɗauki guda uku ya miƙa mata. "Ki hanzarta ni ma zan yi latti." Banza ta yi da shi ta juya tana ƙunkunai."Wallahi kika zage ni saina naɗa miki na jaki kuma babu inda za ki. Dama kwana biyu ban more fata ba." Ya ce tare da komawa ya zauna wannan karon da ya ɗauki wayar kiranta ya yi suna bidiyo call. Cikin sauri ta kunna wutar, sannan ta zuba ruwan zafi Allah ya so ta tana da shi a fulas. Da sauri ta jajjaga sauran kayan miyan da ta rage jiya. Burinta ta gama kafin lokacin ya ƙure. Bayan ta gama, ta rage kaɗan ta zuba masa sauran don ta san in ta iba da yawa, zai iya mata tijara. "Ga shi." Ta ce tana ƙoƙarin fita. "Ina za ki?" Ya yi mata tambayar tare da miƙewa, ya ƙaraso inda ta ije abincin ba tare da ya kashe wayar ba. Ranta ya ɓaci hawaye suka zubo mata a fuskarta. Kauda kanta ta yi, daidai lokacin da ya kalli wacce suke wayar ya ce mata. "Baby, zan kira ki I love yo..." Maganar ta katse sakamakon ganinta da ya yi ta nufi gurin wayar cikin huci. "Na gaji Faruk! Na gaji da tozarci da wulaƙanta ni da kake yi, domin na kasa gane mata ko baiwa ka ɗauke ni. Ba ni da 'yanci da ƙimar da za ka bari ka rinƙa waya da sheɗanun 'yan matanka?" "Matar da zan aura kike kira sheɗaniya?" "Wallahi in da abin da yafi sheɗaniya zan kirata. A cikin gidana kake waya da ita ki kunya ta ba ka ji. Ban isa na ga dariyar ka ba, sai in kana waya da wasu matan. Ni ma fa ina da haƙƙi a kanka kamar yadda kake iƙirarin kana da shi a kaina." "Ke dai na lura wallahi baƙicikin zan yi ajalinki. Saboda kin ganta yar duma-duma kalar madara shi ne kake tada hankalinki. To ni dama mai zan janyo mini na je na ƙara ɗauki irinki? Ina ciyar dake ana zargina ina barin ki da yunwa. Kalle ki fa Nasreen kullum sai ƙara tsukewa kike kina komawa wata tsohuwa, saboda fitinar da kika sanya a kanki. Ki kula karki jawo abin da zai sanya na tura ki gidanku, kin ga wannan ya'yan na ki da yake tada jijiyan wuya ina barin ki da yunwa, sai na barki in gani in zai iya cida ke. Saboda baƙin ciki kamar jaka haka kike." Wasu irin zafafan hawaye suka wanke mata fuska. Ji ta yi kamar ta mutu."Ni kake kira haka?" "Ƙarya na yi in aka dafa taliya ɗaya tana kwana ta wuni?" "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Allah ka jarabace ni da mijin da bai san darajar mace ba." "Ni zan roƙa Allah ya kawo mini ɗauki da ya haɗa ni da mace bagidajiya mara wayewa. Sai aikin ɗaukar jaka da sunan an tafi makaranta. Haka kika ga matan jami'a suna yi? Ko irin shigar da kike yi suke yi? Ba kya ganin mata masu kyau da zubi da tsarin da suke sace zuciyar maza?" "Kana siyen mini kayan ne Faruk? Tun da na shigo cikin gidanka yaushe ka siya mini sutura? Ko haihuwa na yi a gidanka turmi ɗaya ke haɗani da kai. Su kuwa maza na yi musu hidima. Ko fa gida ba ka iya siya mini ka ji tsoron Allah da ranar da Ubangiji zai tsayar da mu don yin hisabi." "Ke ma ki ji tsoron Allah ranar da Allah zai tuhume ki bisa kasa ɗauke mini ido da kika kasa yi ga matan waje. Kullum sai dai na yi ta raba idanuna kallon abubuwa a gurin matan waje, amma matata ba ta da maraba da tsinke." "Wayyo Allahna!" Ta ce tare da zubewa a ƙasa tana kuka. "Ki mutu gaskiya ce ɗaci gareta kuma ba zan dai na gaya miki. Sai dai ta kashe ki." Ya furta yana saka lomar abinci a bakinsa. Kallonta kawai ta yi sai ta miƙa tsam ta saba jakarta ganin ta yi latti. Ɗaukar Musaddik ta yi za ta fita ba tare da ta yi masa magana, daidai lokacin da ya saki tsaki. "Kuma wallahi kika daɗe ba ki dawo ba har inda kike zan biyo ki na tozarta ki. In aka ci amanar Allah ya isa ban yafe ba." Da sauri ta juyo yayin da hawayen ta suka ci gaba da zuba, sai kuma ta fice ba tare da ta ce komai ba. Gurin famfo ta je ta buɗe ta wanke fuskarta da wasu hawayen suke zuba. "Umma, kuka?" Musaddik ya ce yana goge mata hawayen da ya haɗe da ruwan fuska. Sai da ta kai bakin get ɗin gidan ta tsaya ta ciro wayarta da duk ta ragwargwaje. Da kyar ta samu ta numbata domin kashe kanta take yi. Ɓacin assignment da take yi da ita, da tuni ta yi jifa da ita tun kafin ta yi ajalinta. Numbar Ahmad ta laluba ta yi masa peep wanda ko minti ɗaya ba a yi ba, ya kira ta. "Ya Ahmad!" Sai kawai ta fashe da kuka. Daga can ɓangaren ya ja ajiyar zuciya, cikin damuwa yana jin yadda kukan yake damunsa. "Nasreen!" "Na'am." Ta amsa cikin sheshsheƙar kuka. "Kina ji na ko? Kiyi haƙuri har yau ita ce kalmar da zan rinƙa baki. Na san halin da kike ciki, amma wallahi kin ji na rantse miki zaman gidanki yafi miki kwanciyar hankali. Ki karbi jarrabawar aurenki. Ubangiji yana sane dake. Ni kaina ina cikin damuwa. Jiya wallahi ba mu yi bacci ba, saboda ciwon Mama ya tashi. Yanzu haka na sanya Zainab ta gyara ta zamu wuce asibiti, kuma Baba ko ƙwandala bai bamu ba, tun da ya shigo ya yi mata sannu ya fice daga gidan." Damuwarta ta ƙara yawa har ta ji dama ba ta kira shi ba. "Yaya, Faruk baiwa ya ɗauke ni ba mata ba. Ina cikin damuw.." "Hakurin da kike yi ki ƙara, yanxu zan sanya miki dubu ɗaya na san za ta ɗan yi miki kuɗin mota da ko gurasa ki ci a makaranta. Za mu wuce da Mama asibitin in an kwantar damu zan kira ki, sai ki taho in kuma dawowa mu ka yi duk zan gaya miki." "Don Allah ka bani ita na gaishe da ita." "Ba za ta iya ɗaga waya ba. Ki je makarantar Allah ya tsare." "To Yaya Ahmad, ina dawo zan biyo, kuma ka bar kuɗin ina da sauran ɗari biyar, da ka bani ranar Monday na yi amfani da sauran na ije. Ka je ka kula da ita, zan tafi a mashin tun da na yi latti ina dawo sai na tako." "Karki damu juya na yi aikii na samu kudi, saboda don ciwon Mama ya tashi dubu biyar zan tura miki." Tausayinsa ya kamata ganin yadda yake ɗawainiya da ita." Na gode Allah ya ƙara budi ya biya maka buƙatunka." "Amin ƙanwata." Fatana ki ci gaba da fito da sakamako mai kyau ki samu aiki ki tallabi rayuwarki." "Da kuma na bukatun da na Mama da sauran ƙannina." "Ina sha Allahu." Ya ce mata yana murmushi tare da kashe wayar. Maganar da ta yi da shi, ya sa ya ta ji ɗan dama sama-sama, har ta iya taran acaɓa ta hau zuwa bakin get ɗin makarantar. Wani ƙaton tangamemen falo ne wanda yake ɗauke da kaya na alfarma. Tabbas falon ya cancanci waɗannan kaya da aka shake falon dashi duba ga yadda ya tsare an kashe dukiya tamkar aljannar duniya. Wata farar mace siriya take zaune da 'yarta ɗaya wacce take kan cinyarsa tana bacci. Kyakkyawar matar waya ce a hannunta tana chatting, yayin da fuskarta ke bayyanar da wani irin tsantsan annuri, wanda zai tabbatar maka da wanda take chatting ɗin da shi mutum ne mai daraja da ƙima a gurinta. Darajarsa da ta wuce darajar gwal da Dirhami. Murmushi ta yi, tare da amsa kiran da ya yi mata domin iya chatting ɗin ba zai gamsar da zuciyoyinsu ba. Sun dade suna waya tamkar ba za su rabo ba, sannan daga bisani suka yi sallama bayan ta yi masa kiss din da iya ƙwaƙwata ba zan iya lissafawa ba. Kashe wayar ta yi sannan ta shiga cikin galary ta yi ta kallon hotunansa, duk da cewar akwai wani mai kyau wanda ya ɗauka da kayan saurauta a fuskar wayarta, amma bai ishe ta ba. Hankalinta ta mayar kan tanƙamemen tibin bangon, da take kallo a cikinsa kafin ya kira wayar. "Mommy, yaushe Daddy zai dawo?" Yar kyakkyawan yarinyar mai suna Marwana ta furta tana murza idanunta da bacci ba su gama sakin su ba. "Daddy will come back tomorrow. Ok?" "Yes, kuma ya siyo mini teddy ɗina?" "Sure." "Mommy how many?" "Ten." Ta ba ta amsa wanda ya sa ta daki dariya tana tsalle murna. "Mommy call daddy I will give him a peck." "Ok,"Ta ce tare da ɗaukar wayar tana ƙoƙarin kira. "Hello, babies." Ta ji muryarta cikin bazata ya buɗe ƙofar falon yana faɗin haka tare da ware hannunsa. Tsananin mamaki ya kamata, duk da cewar ya saba yi mata bazata, duk tafiyar da zai yi baya gaya mata lokacin da zai dawo. Wani lokacin in ta rage kwanakin sai ya ƙara in kuma ta ƙara sai ya rage, wannan dalilin ya sa sam ba ta shiri in zai dawo, duk da cewar da ma ko da yaushe cikin gayu da ƙwalisa take mace ce wacce take kula da kanta, saboda sanin mijinta kamar Bature yake. Akwai son classical things musamman ga matarsa. Everything na sa it is extraordinary and rare. Da gudu suka ruga har da ita da take ɗauke da ƙaramin ciki wata huɗu." "Oh no, baby easy." Ya furta tare da ƙarasowa ya haɗe su duka ya rungume yana kissing. "I really missed you my babies like crazy!" Dukan ƙirjinsa ta yi cikin wasa tana harararsa." Yanzu shikenan an tauye mini wannan yaƙin?" "Subuhanallahi! Baby don't say that. Hakkinsa wajibi ne da ya kamata na sauke ke. Faɗa mini waya, mota jari ko abroad kike son zuwa? Ko kuma gidan ne kike son canzawa. In ma nine na fara miki tsufa sai na yi kwaskwarima You know." Ya faɗa yana kashe mata ido da cige lebbensa. Dariya ta saki tana kashe masa ido sai kuma ta ɓata fuska. "Haƙƙina da ake tauye mini, na rashin gaya mini lokacin da za a dawo don na gyara kaina, ta yadda zan sace zuciyarka na zama ni kaɗai." "Aike kadai ce babu wata fa? Kin ga nan ɗina?" Ya nuna mata ƙirjinsa. Dariya ta yi tare da ɗaya mata kai ta sumbaci goshinsa. "Ke ce dai ke ba wata sai ke. A jirgi haka wata haɗaɗɗiyar bab ta rinƙa kallonta tana kashe mini ido. Ina gani na yi maza na ɗauke kyalle na rufe fuskanta har muka iso Nigeria." "Oh my goodness baby, you are so funny." Ta ce masa cikin dariya wanda shi ma ya taya ta. "Amma duk da haka I have to know." "Do not worry ke fa zazzafa ce kullum a hot kike." "Let's go and do shower then eating." "No, shower then sleeping am very tire. Bacci ne kawai zai dawo dani daidai." Hannunsa ta kama duka haye sama yana rungume da ita. Ji yake kamar ya kasheta don so. Tun da yake bai taba son abu kamar ta ba sai ƙanwarsa Marwana. Hakika yana matuƙar don waɗannan halittu guda biyu kafin kuma ya haifa masa babu girl ya sanya mata, little Marwana da babu na biyu ta a duniyar sa. Bayan ya yi wankan, ba ta barshi ya kwanta ba sai da ta ba shi tea mai zafi yana kauda fuska tana rarrashinsa. Sannan ya subbaci Marwana da ta yi bacci ya ɗauke ta. "Bari na kaiwa Baba Azumi ita na dawo ki bani labarin baby na kuma tabbatar da lafiyarta, saboda shi zai watstsake mini gajiyata." Dariya ta yi ba tare da ta ce komai ba sai raka shi da idanu da ta yi cikin so da ƙauna. "Gaya mini duk abin da ya faru da bana nan?" "Babu sai kewarka da kwana rungume da filo tun da babu kai." "Karki damu jaririyata. Yau za ki yi filo dani har ki gaji." Ya ƙarshe maganar yana tusa kansa a cikin yar yaloluea rigarta. "Kin je check up?" Ya yi mata tambayar bayan ya ɗago kansa tare da mayar da hankalinsa gareta. "Na je Muhsin Hajiya ta Turo ta ya kaini. Likitan ya ƙara tabbatar mini aiki dole za a yi mini. Kamar na Marwana." "Kar ki damu,ni kaina na fi so ayi miki aikin. Kin ga ba ki da wata isashshiyar lafiya ga condition ɗin ki. I think aikin will be saved." "Ok," Ta ce tare da share hawayen da ya zubo mata. "Please kar mu yi haka dake. Na gaya miki duk wuya duk rintsi muna tare ba zan taba rabuwa dake ba. Kuma in sha Allahu za mu yi tsawon rayuwar da zamu tsufa tare." WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 4 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Please kar mu yi haka dake. Na gaya miki duk wuya duk rintsi, muna tare ba zan taba rabuwa dake ba, kuma in sha Allahu za mu yi tsawon rayuwar da zamu tsufa tare." "Ina fatan haka ina fatan na kasance da kai har abada mijina. Ka ci gaba da bani kulawar da kake bani, wanda na san ko akwai matan da suke samun kamarka ƙalilan ne. Ina sonka mijina yadda kake nuna mini tsantsan so da ƙauna. Zan yi kishin ka duk ranar da ka nuna kana son wata 'ya mace." "Ke kadai kin ishe ni Batula, na gaya miki bani da ra'ayin ƙara mace. Kin ji kuma na rantse miki ba zan taba miki kishiya ba."Ya karashe maganar yana haɗe bakinsu. An sha soyayya tare da biyan bashin kwanakin da ba su a tare. Bayan sun yi wanka suka rungume junansu bacci mai dadi ya tafi dasu. Ba su tashi ba har ƙarfe huɗu saura. Shi ma bugun ƙofar Marwana ya tashe su. "Daddy and Mommy, wake up." Suka ji tana fadi tare da buga ƙofar tana rungume da teddynta da sauri tana kiran su. "Innalillahi! See time ban gaya wa Baba Azumi ba abin da za ta girka ba." Ta faɗa tana dan dukan filon da yake ya tashi. Juyi ya yi tare da kai hannunsa zai rungume ta." Ban gaji da baccin ba, kar ki damu da abinci. Please mu kwanta." "Subuhanallahi! Ashe har an yi la'asar." Zubbur ya mike yana zare ido tare da ɗaukan agogo ya duba." Kai ina da an kira dole na tashi." Dariya ta saki tare da sauka daga gadon." Ga shi nan na tashe ka." Shi ma dariya ya yi yana shafa sunan kansa."Kin san lafiya ai." Buɗe dakin ta yi Marwana ta nufa da sauri ta faɗa jikinsa. "Baby, bari na sanar da Baba, Azumi abin da za ta girka." "Kar ki damu ki gaya mata ta huta mu je na hada mana lunch." "Don Allah ka gaji ka bari sai gobe." Karki damu just give me two minutes lemme go to resting room. Ba tare da ya ji mai za ta ce ba ya shige bayin, ita kuma ta fita daga dakin bayan ta kama hannun Marwana. "Baba, Azumi kin ga na sha bacci ko?" "Eh, ai na so na taso ki, sai kuma na ga tun da mai gida yana nan bari na kyale ku. Na yi mana girki ni da masu aiki. Kuma Marwana ma ta ci, amma saboda ban san me kuke so ba sai barshi, don na san wataƙila mai gida zai yi da kansa." Murmushi ta yi tana kallonta."Aiko Gara da ba ki yi ba don ya ce ki huta." "Sanin hali, ai yafi sanin kama. Allah dai ya barku tare." Ta ce tare da komawa ta zauna, amma ganin ya shigo kicin din sai ta miƙe. "Baby ina afron?" Ya yi mata tambayar yana amsa gaisuwar da azumi ke masa. Dauko masa ta yi tare da ɗaukar masa sannan ta tsaya tana kallonsa. Tana mishi hira tare da taimaka masa suka haɗa lafiyyayen abinci sannan suka dawo dining. Shi ya rinƙa ba ta abincin, har ta ci ta ƙoshi sannan ya ci. Bayan ya ci suka koma falo suka zauna. "Kin san rigimammiyar nan wai ni zan dauko ta a school, tun da na kira Hajiya, na gaya mata na dawo ta sanya rigima sai na zo, dama motarta ta samu matsala ba ta je da ita ba." Dariya ta yi."Rigimarta ne kawai ya tashi, amma ko jiya a motarta muka je gidan Anty Ƴahanasu. Watakila canza mata take son ayi." "Zan je na duba motar in tana bukatar canxawar ai sai ayi." 'Gaskiya ya kamata." Ta ce. "Bari na shirya Little Marwana sai mu je tare." "Ok, ka dawo lafiya." Ta furta tare da jan remote don ta canza tasha. Shiga ya yi ta alfarma cikin suit masu kyau baƙaƙe. Wayarsa da key ɗin motarsa ya ɗauka. Ganin kyau da ya yi Batula ta sauya wayarta za ta yi mishi hoto. "Kai ka yi kyau matuƙa gaskiya Allah na gode maka da ka bani wannan gayen." Ta ce tare da jan kumatunsa. Dariya ya yi ya ce," Ke ma kina da kyau ai." Ya ƙarshe maganar yana sumbatar ƙuncinta . Har bakin mota ta raka su. "Bye Mommy I will buy you chocolate." "Ok baby, promise?" Ta ce mata tana daga mata hannu. Juyawa ta yi cikin farinciki ta koma ciki. Nasreen kuwa, a lokacin da mai mashin ya sauke ta da sauri ta saɓa Musaddik ta fara tafiya. Tana tafiya ta tana kallon agogo ganin lokaci ya wuce har da minti goma. Ta san Malamin yana da tsananin zafi Allah ya sa ya barta. Cikin sa'a ta shige ciki lokacin hankalinsa na kan ɗalibai da yake raba musu gurin zama. Da sauri ta ji an kama hannunta ana faɗin," Ummu Hairan, zo mu zauna a nan." Ta ce mata tare da jan hannunta suka zauna. Lecturer na kallonta ba tare da ya ce komai ba. "Kin yi matuƙar latti, har na fara tunanin ko ba za ki zo ba? Ina ta waige-waige na kuma tambayi wannan matar auren da kuke zuwa tare, sai ta ce mini wai ta kira numbarki ba ya shiga. Wannan dalilin ya sa ya na ban karɓi numbarki ba." Yaƙe ta yi mata jin abin da ta ce, tana mamakin maganar da ta yi mata, domin za ta iya irga maganar da suka yi. Shi ma gaisuwa ne in sun haɗu a masallaci sai kuma in tana son assignment ta tambaye ta. "Kin san am manna mana result?" Ta yi mata tamabayar cikin murna. "A'a." Ta ce mata tana kallonta tare da kallon kayan alfarmar dake jikinta. "Wallahi an manna. Ai tun jiya muke sa rai. Yau kuwa tun asuba na sanya Ya Muhsin ya kawo ni, na duba daga ke sai ni." "Alhamdulillah!" Ta ce mata. "Gaskiya kina da ilmi sosai kamata ya yi da result da kike beating gwamnati ta ɗauki nauyin karatunki, but you know how situation we are in Nigeria." "Haka ne Allah ya rufa mana asiri." Ta ce tare da kama bakinta, ganin yadda yan ajin suke kallonta don Marwana ba ta cika kula kowa ba harkar gabanta take yi. "Mu fara test ɗin." Ta ce bayan an rubuta a allo. Ajin ya yi shiru, kowa na ƙoƙarin nuna ilmin da yake da shi, yi sai kuma masu ƙuskus 'yan satan amsa. Marwana tana rubutu tana satan kallonta, dama so take ta ga satan amsa take yi, ko ƙoƙarin ta yake ba ta result ɗin, saboda so take ta ga babu wanda yake gabanta a result ta yadda Ƴaƴanta zai kaita abroad ta yi masters. Ta cika mamakin ganin yadda ta cika paper. Ta yaba da ƙoƙarin ta domin tun da ta fuskar da kanta ba ta ɗago ba. Ganin gulma zai sanya ta ɓata lokacin ta ya sa ta fara rubutawa. Bayan sun gama sun fito." Zo mu je mu ci abu yunwa na ke ji." "No karki damu bana jin yunwa." "To don Allah ki raka ni." Ta ce tare da karbar Musaddik da ta ije shi a gurin wata yar ajinsu kafin ita su shiga. Murmushi yaƙe ta sake yi ganin yadda idanun ke kallonta. Lura da hakan Marwana ta yi, sai ta kamo hannunta, suka fara tafiya har suka isa cafateria. Abincin da ta yi oder ya yi matuƙar razana ta. "No sis ba zan ci ba, na ci abinci daga gida." Bata rai ta yi tana kallonta." Sheɗan ne kawai yake maida hannun kyauta baya."Ta ce tare da yin raurau alamun za ta yi kuka. Dariya ta ɓata tana mamaki shagwaɓa irin na 'ya'yan masu da shi. "Na ƙoshi ne fa so kike na yi amai?" "Ok, ba damuwa bari na sa ayi miki a sanya mini a leda. Sai ki bawa kyakkyawan yaron ki ya ci. " Murmushi ta yi ba ta ce komai ba. Mamakinta ta yi ganin yadda take ci tana bawa Musaddik a baki ba tare da ƙyamar sa ba. "Kin ga kishin ki na ke yi fa." Jin abin da ta ce ya sa ta ɗago tana kallonta da sauri. "Kishi kuma ni? Mai na ke da shi har da kyakkyawar mace kamar ki, wacce take da kyau kamar an kyankyaso ki aka yi za ta yi kishi da ni?" "Ilmin ki mana. Wallahi tun muna hundred level na ke jin haushi ke ce kike zuwa a gabana, domin da ni ce top a ajinmu yanzu ina abroad, kuma kin ga irin wannan kishin ai ya halasta ko addini sai na dage na wuce ki." "To shi ne na ba ki da matsala. Wannan semester zan yi yadda za ki wuce ni sai ki cika burinki." "Wow, sis you are so kind." Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba. Wayarta ya yi ƙara sai kuma ta mike."Yauwa Yaya Damir ya iso. Zo mu je ku gaisa." "No, kar ki damu kawo shi kawai." Ta ce mata bayan ta miƙe. Ita sam ba ta son shiga harkar masu da shi. Gara ta tsaya a matsayinta. Za ta riƙe ta sai ta ga ta canza fuska. "Bari na je kawai tun da ba kya son zuwa, amma zan je da Musaddik." "Ok, ki gaishe shi." Ta furta tare da wucewa. "Oyoyo Yayana." Ta ce tare da rungume shi. "Marwana, yaushe kika fara ɗaukar yara?" Ya yi mata tambayar yana kallon babyn. Dariya ta yi ita ma shi take kallo." Ka ganshi kyakkyawa ko?" Ta furta tare da miƙa masa shi. Hannu ya sa ya amsa yana fadin,"Eh, Allah ya sanya Mommy Little Marwana ta haifa mini kalarsa." Hannunsa ta kama suka shiga cikin makarantar tana faɗin,"Mu je ka ga result ɗin mu." Babu musu suka shiga ya tsaya yana dubawa."Gaskiya ƙanwata kanki na ja, amma wace ce wacce ta sha miki gaba?. Ni kuwa zan so na ganta." "Maman yaron nan ne, kuma abin mamaki daga shigarta ba matar mai kuɗi bane" Ta nuna Musaddik dake hannunsa, bari na kira ta.". "Ai shi Allah ba ruwan shi da duba wannan ya ba ka ilmi. Ki dage ki wuce ta kin ji." "To bari na kira ta." "No matar aure ce ba zai kin kira ba, amma kuwa zan yi mata kyauta ta musamman, domin kamata ya yi gwamnati ta ɗauki nauyinta." "Gaskiya Yaya." "Gobe sai ki shirya mune ki zaɓi duk motar da kike so, in kuma na Muhsin da kika na ce sai ya bar miki dama motar mata ya je ya siya." "No bana sonta, ba ka ga ya je ya ƙuje ta ba?" "Ok, tom sai ki shirya goben." " Na gode Allah ya ƙara budi." Tace masa cikin tsananin murna. "Ina little Marwana?" "Tun da muka shiga gidan Hajiya, ta ga za ta fita sai ta manne mata, kin santa da son yawo da Hajiya." "Hajiya da ita ai sai Allah." "Yanzu kin gama ne?" "Eh bari na kai mata yaron." "Ok," Ya ce tare da sanya hannu a aljihunsa ya ciro kuɗi 'yan dubu-dubu har 20k. "Ga shi a siya masa chocolate." "Thanks Yaya." Da sauri ta shiga cikin abin tana nemansa. Ganin ta can a gefe ta ciro jigattaciyar wayarta taba ƙoƙarin kiran Ya Ahmad. Ba tare da ta ji zuwa ta ba sai dai kawai ta ji maganarta. "Ga shi zan wuce gida." Da sauri ta shiga tare da ɓoye wayar a jaka. "Sannu ya wahalar da ke ko?" Ta yi tambayar tana ƙoƙarin ɗaukar shi. "Kai haba wane wahala." Ta ce mata tare da miƙa mata kuɗin. "Ya Damir ya ba wa Musaddik." Zare idanunta ta yi tana kallon kuɗin tare da haɗiye miyau da ƙyar. "Kai haba duka wannan uban kuɗin ai sun yi yawa." "Kar ki damu Yaya zai iya ba shi fiye da haka." "Gaskiya ba zan karɓa ba." "Saboda me?" "Saboda sun yi yawa, kuma daga haɗuwa da ke yau, sai ki yi mini kyautar wannan kuɗin." "Musaddik ya yi ma kyautar, don haka ya zama dole ki karba, kuma kin san wane ne Ya Damir da kuɗin da yake da shi? Ban ba ki san shi bane." Ta ƙarashe maganar, tare da cusa mata kuɗin a jaka, sannan ta juya ta fara tafiya tana faɗin. "Sai gobe zan wuce." A ranta ji ta yi kamar za ta sume ganin kuɗin, domin rabin ta da ta samu irin wannan kuɗin har ta manta." Miƙewa ta yi ta goya Musaddik sannan ta ɗauki jakarta ta tafi. A hanya ta ciro wayarta ta kira numbar Faruk da yake zaune a ofis ɗinsa yana waya. Yana ganin kiran na shigowa, amma bai damu ba ya ci gaba da wayarsa, har lokacin da ya gama, sannan ya kashe tare da sakin wawan tsaki. "Ko uban me za ta ce mini oho? Ana magana da mata ba ke kamar sandar rake ba ki addabe da..." Maganar ta katse sakamakon kiran da ya ƙara shigowa. "Wai mene kin addabe ni, ko ke makauniya ce? Tun da kin ga ina waya ba sai ki yi haƙuri ba." "Ka yi haƙuri kiran ne da mahimmanci zan gaya maka ina son na je na duba Mama jikinta ya tsananta." "Wannan ne kira mai mahimmanci?" Ya yi mata tambayar cikin tsawa wanda ya sanya ta yi sororo sai kuma ta ce," Mahaifiyata ce fa ba lafiya?" "To ni ina ruwana in kin so kar ki dawo ba ta shafe ni ba. Kin ga sai na huta da ci da ke." Yana faɗin haka ya kashe wayar tare da ƙara jan tsuka mai ƙarfi ya kashe wayar. Ranta ne ya ƙara ɓaci, ta kalli wayar hawaye na son zubowa a fuskarta, amma sai ta daure ganin yau rana ce ta musamman, domin ko babu komai za ta taimaka a ciwon Mama. Tsayawa ta yi, ta sayi lemo da ayaba na dubu ɗaya, sannan ta siya mata gashashshen nama da dubu. A ƙofar gida ta kusa cin karo da Zainab. "Ina za ki je kike sauri haka har za ki buge ni?" Ta ce mata daidai lokacin da suka ci karo. "Oyoyo Anti Nasreen." Ta furta tare da rungume ta tana shafa kan Musaddik. "Zan siyo ruwan gishiri Mama ce za ta sha. Ta ce jikinta babu ƙarfi." "Sai kin dawo to." "Anty kawo shi." Ta ce tana miƙa hannu ta Kwanto mata shi. "A'a, ki yi sauri ki dawo." "To," Ta ce tare da shafa kanshi ta ruga da sauri. Da sallama ta shiga cikin tsakar gidan, da Mama Dije take zaune tana ƙoƙarin hura wuta. "Yau 'yan boko ne a gidan? Ko da yake dole ki zo tun da tsohuwa babu lafiya." Ta faɗa tana yatsina bakinta. "Ina wuni?" Kawai ta ce mata ba tare da ta ji abin da za ta faɗa ba ta shige. Rakata ta yi da kallo ba ta amsa gaisuwar ba. Ɗakin ta buɗe ta shiga, tare da saurin ƙarasawa, kan lamushashiyar katifar da Mama take kwance. "Sannu Mama, ya jikin ki?" Ta yi mata tambayar tana daga goshinta da ya ɗauki zafi kamar tukubar mai tsire. "Yauwa ya gidan?" WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 5 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Sannu Mama, ya jikin ki?" Ta yi mata tambayar tana daga goshinta da ya ɗauki zafi kamar tukubar mai tsire. "Yauwa ya gidan?" Ta amsa cikin rawar murya. "Allah ya ƙara sauki." "Yaya Ahmad mai ke damunta?" Bayan ta yi mata fatan samun sauƙi, ta juya tana kallonsa tare da tambayarsa hakan. "Ciwon nan dai nata. Yanzu likitanma ya ce gaba take da zuciyarta ta buga, matuƙar ba za ta cire damuwarta ba." Ya ba ta amsa yana share hawaye. "Haba Mama! Sanya damuwa a cikin ranki ba shi zai kawo karshen matsalar nan ba. Mama, iya tsawon shekarun da kika yi da Baba ya kamata ki yi hakuri ki rungumi ƙaddararki." "Ya zan yi Nasreen? A halin da na ke ciki na fi buƙatar mutuwa fiye da rayuwata, domin ban zaɓawa rayuwata da na yarana bango mai kyau ba. Ina dana sanin auren mahaifinku, kamar yadda na tabbata ke ma dana sanin da za ki yi kenan. Na cuci rayuwata wanda a dalilin haka na sanya ki da yaranki cikin halin ƙaƙa na iya." "Mama, babu wanda ya isa ya tsayawa kansa rayuwa. Kowa da kika ganshi rayuwa yake yi ba tare da ya tsara wa kansa ba. Allah ya ƙaddara shi ne mijinki, kamar yadda babu makawa sai na auri Faruk. Ki kauda damuwa mu rungumi ƙaddara da Allah ya ɗora mana." Kuka ta fashe da shi ganin Nasreen na hawaye. "Ina tausaya wa makomar rayuwar ki da 'ya'yanki kamar yadda na ke tausaya wa kaina." "Mu roki Allah kuma mu mai da lamuranmu ga Ubangiji." Ta ce tare da buɗe jakarta ta cire lemu da ayaba da kuma ƙunshi nama. "Ina kika samu kuɗi? Ke da ake taimaka miki?" Murmushi ta yi jin abin da ta ce, tana kallon Ahmad da ya kashe ta da ido. "Ai yau na haɗu da gamdatakar!" Ta ce tare da fito da dubu goma sha takwas ta ɗora a gado. Zare idanunsu suka yi. Mama cikin ƙarfin zuciya ta miƙa wanda ganin haka ya sanya ta jingina mata filo a bayanta. Take ta kwashe kaf abin da ya faru ta gaya musu. "Kin san bana son leƙen rayuwar wasu? Ki tsaya a matsugunin da Allah ya ije ki, domin yawancin masu kuɗi wulakantattu ne." "Wallahi Mama sai da na ce mata ba zan amsa ba. Kin ga ko abincin da ta siya mana ƙin ci na yi, amma ta kafe na kaiwa yarana gida." Ta ƙarashe maganar tana miƙa mata take away ɗin abincin "Ga shi ƙila ki samu kici." Ta ce bayan ta ije mata. "An ya wani abu zai iya shiga cikin nan?" "Ki daure rayuwa dole sai da abinci." Gyara. Nasreen ta ɗauki cokali sannan ta iba tare da kai mata bakinta. Buɗe bakinta ta yi a hankali ta karɓa."Yauwa Mama, ko ke fa. Allah ya ba ki lafiya." "Amin," Nasreen ta amsa tare da miƙewa bayan ta karɓi ruwan gishiri ta ta miƙe don ta ɗauki kofi ta jiƙa mata. "Yadda za a yi da kuɗinnan, Ya Ahmad ka karɓe su duka ka ci gaba da nema mata magani, Allah ya ba da lada kana matuƙar ƙoƙari." "Haka ya kamata ko wane ɗan mai son ya gama da iyayen sa lafiya ya kasance Nasreen. Mama ita ce fatanmu a duniya. Kina ganin Baba bai damu da rayuwarmu ba, kasan kawai ya sani. Sam bai san haƙƙin 'ya'yan da ya haifa ba. In har bamu nema mata lafiya ba wa zai nema mata?" "Haka ne, Allah ya shirya iyaye masu halinsa ya sanya su gane cewa. Aure da 'ya'ya duk a ranar lahira sai Ubangiji ya tambayeka yadda ka kula da su, kuma Ubangiji ya ce dukkanninku makiyaya ne ranar gobe kiyama zai tambayi kiwon da aka baku. Amma abin takaici da alhini har da zaman makoki WASU MAZAN sun ɗauki rayuwar aure don biyan buƙatunsu sa ba wai ibada ba. Sun mata cewa aure bauta ce ta Ubangiji ne, haka kula da yara duk Allah ya azurtata ya kuma ka ce ka kula da su." "Haka ne Ya Ahmad, da yawa WASU MAZAN yanxu don buƙatar kansu suke aure ba don bauta ba." "Allah ya sa su gane, su ɗauki auren a matsayin bauta sai a taru a gudu tare kuma a tsira tare." "Amin," Ta furta. "Wallahi tallahi a gidan nan daidai na ke da uban kowa. 'Yan iskan yara matsiyata mara sa mutunci." Suka ji muryar Baba yana faɗin haka daidai lokacin da ya iso ƙofar ɗakin. Da sauri suka haɗa idanu Nasreen ta kai hannu za ta ɓoye kuɗin da abincin, amma sai dai ba ta yi nasarar ɓoye kuɗin, ban da abincin da fruit ɗin, ya riga ya banko ɗakin babu sallama yana mazurai. "Haba Baban Ahmad, ya kamata ka daina zagin yaran nan ka san babu kyau haka?" "Ban yi magana dake ba don haka ki ji da ciwon ki, tun kafin na yi miki tijara. Ba dole na yi magana ba. Ɗan bazan yaron Aminu, na gani ya dawo daga kasuwa ya samu kuɗi, na tare shi ya bani naira dubu na sha shayi, amma ya rantse mini ba zai bayar ba, wai zai biya kuɗin islamiya." "Haba Baban Ahmad, kai ya kamata ka kula da karatunsa, ba ka biya ba, ya samu kuma zai biya sai ya zama tsiya?" Harara ya zabga mata jin abin da ta ce,"Ai to laifina za ki gani ko? Ai dama kullum ni mai lafi ne a gurin ki. Yanzu ma na tabbata kun haɗu ne ke da yaranki kuna zagina. Wallahi kin bani mamaki ƙwarai, domin ban san lokacin da kika canza ba. Ace wai da yaran da na haifa za ki zauna kina gulmata?" "Gaskiya ce ba ka so, amma ba gulman ka muke yi ba. Haƙƙinka da ka kasa saukewa a matsayinka na uba muke magana a kai." "Ba ni da shi zan yi ma kaina dole ne? Ko sata kike so na je na yi? Ai na riga na gaya muku koya ya yi ta kansa, domin wallahi Allah bai yi ni mai arziki ba, ba zan je na kashe kaina ba." "Amma ka san ba ka da shi Baba ka rinƙa aure-aure kana tara yara? Duk da yadda rayuwarsu suka zama Allah sai ya tambaye ka." "To fitsarrare mara kunya! Ai ni na yi mamakin tun da ka na shigo maka yi mini fitsara ba. Ɗan banza wanda ya fitsare ƙafarsa. Sunnar ma'aikin da na ɗanbaƙa, shi ne kake ɓakincikin da ladar da zan samu. Manzon tsira ya ce,"mu yi aure mu hayayyafa ranar gobe kiyama ya yi alfahari da mu." "Baba, ba irin yaran da kake haifa ba. Kana ganin halin da kake sanya yaranka, saboda ba ka tsaya ka inganta rayuwar mu ba. Jiya fa haka Ashiru ya dawo gidan na yana tangaɗi. Ga Na'ima kwana biyu ba ta kwana a gida ba, kuma ko ajinka hankalinka kwance." "Au to so kake na mutu? Ai duniya ce duk wanda ya ce lalacewa zai yi ya je duniya ce, ta ishi bagaruwa jima." "Amma dai kai ka haife su kana da haƙkin ka kula da su." Cewar Nasreen cikin damuwa tana kallonsa. "Nasreen! Au ke ma fitsarar za ki yi mini? Wai tsaya yaushe kika zo ma cikin gidan nan? Allah ya sa mijinki ya sani, don wallahi ya zo ya yi mini tijara sai na yi mugun saɓa miki, in kuma kika kuskura ya sako ki sai dai ki nemi wani gidan uban. Kin san dai ba za ki yi mini zawarci a gidana ba, domin na gaya muku dama alla-alla na ke na aurar da ku, tun da kuma na samu waɗanda suka ɗibe ku, babu shegiyar da za ta dawo mini gida. Ballantana ta zo mini da 'ya'ya." Shiru ta yi ta matsa cewa komai, sai hawaye shar suka wanke mata fuska. "Da ma na san ba ni da gatan da ya fi zaman aurena." Ta furta tana share hawaye. Ganin babu wanda ya tanka masa, ya ci gaba da kallon da yake yi ma abincin da ayabar. "Tuni na san cewa ni a gidan nan. Babu mai ƙaunata. Duk ɗan da zai shigo gidan nan sai dai ya kawo wa uwarsa abu, amma ni ba ku da mu da na ci ba ko na mutu oho!" "Kai ya kamata ka basu, in ba ka basu ba, dole mu nemo ko a wuta mu basu, don kar mu rasa su." "Ni kuma inna mutu ba ku da damuwa." Ya ce ba tare da ya kalle su ba ya ɗauki ayabar ya ɓare tare da jefawa a baki. Zama ya yi a gefen gadon yana zare idanu."Wannan abincin na cikin farar robar nan. Tak away ake ce mata ko take way?" Ya ɗauki abincin tare da ɗauke cinyar kazar. "Ikon Allah masu kuɗi na sha'aninsu." Ya ce tare da kai loma. "Ke Nasreen, ba dai ke kika kawo wannan abincin ba, domin na san wannan ɗan iskar maƙoƙon mijin na ki ba zai iya ba ki wannan abincin ba. Mara mutunci shekaranjiya na kira shi ya bani bashin dubu goma, amma ƙememe ya ce ba shi da kuɗi. Wallahi bacin bana son ki yi zawarci da saina raba ki da shi na aura mai kuɗi irin mijin Nadiya, saboda shi ina ce ya bani za ki ga ya miƙa mini." "Ta ya ya zan yi daraja a guri sa Baba, kana zubar mini da mutunci kana cin bashi a gurinsu? Bana haƙuri kawai na ke yi a zaman aure a, amma wallahi zaman gidan yari yafi mini zama da Faruk." "Kuma ba ki da zaɓin da ya wuce zama da shi." Ya furta tare da kai lomar abincin. Cikin takaici suke kallonsa tamkar za su rufe shi da duka suke ji. Haƙiƙa ba su yi dacen uba na gari ba." Tsananin mamaki da ya kama su, ganin yana shirin cinye abincin nan, ya na zuba surutu mara ma'ana. "Baba, abincin nan na Mama ne domin shi za ta ci ta sha magani." "Ni ma bani da lafiyar ai. Jiya da na je gurin yaran nan Tukur mai kyamis ya ce yunwa takama ni. In kuma so kuke na mutu shikenan dama na san baku da asara." Ya furta ba tare da ya ƙara magana ba, sai da ya cinye abincin nan tas! Ya tsaki wata mahaukaciyar gatsa yana shafa tunbinsa. "Yauwa, ku yi wa mahaifiyarmu magana ta cire wannan damuwar banzar da ta sanya ma kaina, saboda ita kanta ta san cewa da ace zan canza halina da tuni na canza, don haka ban ga abin da zai sanya ta sawa kanta hawan jini ba." Ba tare da sun ce masa uffan ba suka ci gaba da kallonsa. Har zai fita sai ya dawo ya kalli Ahmad." Ɗan bani naira ɗari biyar na sha ruwan bunu." "Bani da shi saboda na kashe duk kuɗin a asibiti. Yanzu haka ma akwai maganin da ban siya ba." "Ai sai ka ba da himma." Ya ce yana harararsa. "Ke dai na san ba samu zan yi ba, don haka ba zan ɓata bakina ba." Ya ce mata tare da ficewa daga ɗakin. "Kai halin Baba sai shi. Allah ya shirya mana mahaifinmu." "Rashin ilimi da sanin darajar aure yake damunsa." Cewar Mama tana hawaye. Sun kasa rarrashinta su kansu hawaye suke yi. Tun da suka taso suke cikin wannan rayuwar har zuwa girmansa ba ta sake zabi ba. "Yanzu kin ga yadda za a yi da kuɗin nan. Ki bawa mama, dubu goma ta ije a gurinta, ta rinƙa siyan abinci tana ci. Sannan dubu biyar ki ɗauka ke ma kina buƙatar kuɗin. Dubu uku kuma a bawa Zainab ta je ta biya kuɗin islamiya da hadda." "To Yaya Ahmad, kai kuma fa? Kana bukatar kuɗi?" "Kar ki damu da ni. Namiji na ke zan kula da kaina." "Amma ko dubu biyu ka karɓa." Murmushi ya yi yana girgiza mata kai, wanda ta tabbatar ba zai karɓa ba tun da ya ce. "Yaya Ahmad, Allah ya buɗe maka saboda kula da mu da kake yi." "Amin," Shi da Mama suka amsa har da Zainab. Miƙewa ta yi da sauri kamar an tsikareta ta ce,"Bari na tafi gida Raihan na can zan biya na ɗauke ta, kuma ban yi abinci ba." "Har yanzu dai yana nan yana ba ki abinci tazarce ko?" Mama ta tambaya cikin ƙunar rai. "Ai Mama, yadda yake mini ya wuce tazarce. Girki ɗaya zan yi sai kuma gobe. Ga shi ba ya isanmu sai dai na haƙura." "Allah ya kawo mafita ki kammala karatun ki. Ko koyarwa kika samu a makarantar gashin kai, za ki samu sauƙin rayuwa." "Amin Allah kuma ya sa ya yarda." "Inda uban kuturu ya yi kaɗan kenan." Cewar Ahmad da sauri. "To, mai za ka yi masa? Matarsa ce fa. Kai dai Allah ya sanya ya amince ɗin dai." "Hmmmmh! Aiko da wuya, gurguwa da auren nesa." "Ashe ko za a kwashi 'yan kallo ni da shi. Don yadda na ke kashe kuɗi a karatunta dole ta amfani da shi." "Allah ya sa." Mama ta ce tana nishi da ƙyar. "Mama, na tafi zan dawo in sha Ubangiji ya ƙara sauki." "A gaida gida na gode, kuma ki gaishe mini da kishiyata." "Za ta ji." Ta ce tana ƙoƙarin goya Musaddik tare da kallon Ahmad da ya miƙe. "Bari na taka miki har ki samu mashin." "Yauwa ɗan'uwa rabin jiki." Ta ce tana dariya. Fitowa suka yi a tare suka jera duk da cewar ba magana suke yi ba. Sai da suka fita daga gidan sannan ta kalle shi ta ce,"Ina son na je gidan Yaya Sha'awa na ƙara duba mijinta." "Ni ma ina so na ƙara zuwa ciwon Mama ya sanya ban je ba, saboda ya kamata na kai mata wani abu." "Allah dai ya biya ka ƙoƙarin da kake yi." "Amin," "Bari na ɗan yi cefane dubu uku sai na ije dubu biyu." "Ok, ki sayi abu a shagon Habu." Ya ce mata tare da yin shagon. Biskit ta siyasa Raihan na ɗari biyar, sai ta sayi indomie na dubu da ɗari biyar. Dubu ɗaya ta tsinci ashana, suga da gishiri. Sai ƙaramin makilin da ta saya musu don na su ya ƙare. Bayan sun fito da ga shagon, ya tsayar mata da adaidaita ta shiga tana ɗaya masa hannu. Da ta isa daidai unguwarsu ta sauka sannan ta biya kudin. Gidan Maman Muwadda ta nufa don ta ɗauki Raihan. Da sallama ta shiga cikin gidan, ganin babu kowa a tsakar gidan sai ƙarar tibi, da kuma surutun da take ji a falon ya sa ta tura ta shiga. "Yar Halas! Da ma yanzu Raihan take mini ƙorafin yau Ummanta ta daɗe a makaranta." Ta ƙarashe maganar daidai lokacin da Raihan ta miƙe, tare da rugawa ta isa gareta tana faɗin,"Oyoyo Umma." Rungume ta yi ta ce,"Ke dai bari kawai. Ciwon Mama ya tashi na biya na dubata." "Allah Sarki ya jikin?" "Da sauƙi." Zama ta yi gefen kujerar da Maman Muwadda take tana kallonta. "Bari na kawo miki abinci dama yanzu na sauke." "Da kin barshi Rainah ta ci kuma sai na ci?" Ta ce mata tana murmushi. "Haba dai! Kin fi ƙarfin abinci a gidan nan, domin mun zama 'yan'uwa. "Allah dai ya saka miki da abin da kike mini, domin shi kawai zai iya biyanki." Murmushi ta yi, ba tare da ta ce komai ba, sai ta miƙe ta shiga kicin ta ɗauki kula ta zuba mata abincin. "Yau rigimar oga ta tashi. Sai da rana ta yi ya aiko mini da kayan ciki wai waina da miya zan yi mishi. Kin ga yadda na ji haushi kuwa? Don ma Allah ya so ni, lokacin tashin Baba Talatu bai yi ba." Dariya ta yi cikin tsananin sha'awarta. Duk da cewar Faruk ya fishi matsayi a gurin aiki, amma yana matuƙar ƙoƙarin kula da iyalinsa, don ko kayan da suke sakawa sun bambanta da nasu. Ga shi mutum ne mai tsananin kula da abincin da iyalinsa za su ci. Sam ba ya muguwar cima, wannan ya sa ya kullum kicin ɗinta, shaƙe da kayan abinci. Tana matuƙar sha'awar rayuwarsu, musamman yadda yake mata magana cikin taushi da soyayya. Ko ita da take maƙociyarta da mutunci yake kallonta. Saɓanin Faruk da rashin mutunci da ba ya tashi sai in ya ga ta yi baki. "Bari na wuce dare ya fara yi." "To shi ke nan Allah ya kaimu gobe. Ya kamata in za ki koma duba Mama na biki." "Ai da kin barshi duka yaushe kika je?" "Haba kar ki damu. Allah ya ba ta lafiya." Amsawa ta yi sannan ta fita daga gidan. "Umma kin yi mini tsaraba?" "Eh, na yi miki kuma Mama ta ba da ayabar da lemu na kawo miki." "Yauwa Ummata." Ta ce tana tsallen murna. Addu'ar shiga gida suka yi, sannan ta buɗe musu get suka shiga ciki. Hutawa ta yi, ta ɗan ƙara gyara gidan, ganin kafin ya fita sai da ya ƙara ɓata gidan. Tana wanke filet ɗin da ya ci abinci aka kira sallah. Gama wanke wa ta yi, sannan ta shiga bayi, ta ɗauro alwala bayan ta taimaka ma Raihan ta yi. Da suka idar da sallar, suka zauna a falo, suka ci abincin da Maman Muwadda ta ba su. "Na ga kamar an kawo wuta a maƙota, amma babu a gidan nan. Raihan, zo ki haska mini na duba mita ko ya ƙare." WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43 GE 6 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 6 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Miƙewa ta yi, tare da karɓar wayar ta nufi inda take zuwa don ta haska mata. "Ikon Allah ɗage wutan ya yi kenan?" Ta tambayi kanta cikin tsanani mamaki. Ba ta kunna wutar ba, don ta san mai zai haifar. Komawa ta yi ta zauna tana mamakin mugun halinsa. Kasancewar sun ci sun ƙoshi, sai ba ta jira shi ba. Suka yi isha'i ta yi kwanciyarta tana karatu har bacci ya kwashe ta. Ba ta san lokacin da ya dawo ba. Cikin bacci ta ji an ɗauka mata duka mai ƙarfi. Da sauri ta tashi tana salati tare da sosai wurin. "Mai na yi maka za ka duke ni ina baccina?" Cikin muryar kuka ta yi masa tambayar. "Ok, tambayata kike ko? To bari na yi miki wanda ya fishi sai ki yi tambayar mai dalili." Ya ce tare da ƙara kai hannunsa wanda ya sa ta miƙe da sauri. "Uban wa ya ce ki ƙi tashi kina jin ina ta hon?" "Bacci ne mai ƙarfi ya kwashe ni, saboda na gaji sosai." Ta ba shi amsa cikin muryar kuka. "Sai aka ce miki hakan ya dame ni, ko ni na ce dole ki nace sai kin yi boko? Kamata ya yi ki zauna a cikin gidanki, ki nemi lada ki zama full house wife, kamar yadda kowa ce mace ƙwarai take yi." Ba ta ce masa komai ba ta tsaya tana mazurai. "Oya, ma za wuce ki buɗe mini get don ban shigo da mota ta ba, a waje na ije ta, don ga ki ba zan wahalar da kaina ba." Miƙewa ta yi, jin abin da ya ce ta sanya hijabi bayan ta ɗaura zani. Get ɗin ta buɗe masa, bayan ya shigo ya kashe motar, ta buɗe bayan motar ta kwashi kayan da ya shigo da shi. Wucewa ya yi gurin motar ya kunna wutar sannan ya shigo cikin falon. "Abban Raihan, saboda me ka kashe wutar?" "Akwai uban da ke biya mini ne?" "A'a, mamaki dai na yi da ka kashe, saboda matarka da yaranka za su ga haske. Raihan tana ta damuna na kunna mata kallo." "Shi ma kallon daga yau na daina bari kuyi, domin matuƙar ba za ki zama mace mai tarbiyya ba, ni kuma ƙwandalata ba za ta yi ciwo ba." "Mai na ke maka Abban Raihan? Iya kokari ina yi na ga cewar ban shiga haƙƙinka ba, amma kullum maganarka ni ba mace ƙwarai ba ce." "Ok, da ma kina yaudarar kanki kenan? To bari ki ji matuƙar ni zan ɗaga ƙafarsa ki shiga aljanna, babu ke babu samunta, domin ba ki da kirki sam ba kya jin maganata Nasreen." Ranta ne ya ɓace, ba tare da ta ce masa komai ba, ta juya za ta koma ɗakinta. "Nasreen!" Ya kira sunata da ƙarfi yana huci. "Har kin isa ina magana ki tafi?" "Bacci zan yi na gaji yau." "Bacci?"Ya maimaita yana mata kallon ƙaskanci. "Bacci saboda kina hauka ba ki yi girki ba?" "Na gaji ba zan iya girki ba." "Ki dai gaya mini kin yi rokon da kika saba, don na san a gidanku babu abincin da za ki samu. In ma kin samu ba ci za ki iya ba." "Saboda ba a gidan na girma na rayu ba? Wallahi babu rayuwar da ba zan iya fuskanta a cikin gidan ba." "Bana tunanin za ki iya, saboda shi kanshi maigidan da ya aje ku, ya kasa ci daku, ba iya haƙura yake yi ba. Na tabbata ƙila ya tambaye ki ko kin kai masa kuɗin da ya tambaye ni?" Ba ta ce komai ba, sai ta fara hawaye tana baƙincinkin halinsa da yake ja mata tozarci. "Ki gaya masa ba zan iya ci da mutane biyu ba. Ke kaɗai na aura, kuma ina da abin yi da kuɗina. Kar ya ƙara tambayata bashi." "Ka gaya masa da bakinka tun da shi ya roƙa ba ni ba." "Amma saboda ina aurenki ne ko? Ai tushiya mafarkin dawa." Sosai ta fashe da kuka ta kasa cewa komai sai kallon sa take yi. Tsaki ya ja tare da zama a kan kujera."in kin gama kukan kike ki ɗora mini girki, kuma yau tuwo da miya na ke jin ci." Zare idanunta ta yi tana kallonsa tare da barin kukan."Tuwo da miya fa kace a wannan daren. Yau ma fa ba ka dawo da wuri ba, dubi lokaci sha biyu saura?" "Ai kin san makaho ne ni. Kuma ai ba a dare a girki. Shi na ke jin ci, kwana biyu ba ci ba." "Na gaji ni ba zan iya ba." Ta furta masa. A ranta kuwa cewa ta yi." Bana jin yunwa babu wanda ya isa ya sanya ni dole. Da ace ina jin yunwa ne dole na yi don cikina da 'ya'yana." "Ke!" Ya daka mata tsawan da ya sanya ta tsaya cak. "Wuce ki ɗora mini tuwo." Ya ce tare da nuna kicin yana zare mata ido. Zumɓura baki ta yi, ta tsaya ba tare da ta ce masa komai ba. Ganin haka ya shiga ƙoƙarin neman abun duka. Da sauri ta shige tana hawaye. Ruwa ta sanya a kettle sannan ta fara jajjage. Kafin ta gama ya tausa ta yi tankaɗe ta yi dame, tare da ɗora ruwan miyan a dayan murhun. Tana girkin tana gyangyaɗi, har ta kamalla tuwon da taimakon Allah ta kawo masa. "Allah ya sa ba ɗanye kira yi mini ba." Ya duba agogo ganin ɗaya ta yi. Ba tare da ta tanka masa ba ta juya ta shige ciki. Bayan ya gama cin abinci ya zauna yana kallo har ƙarfe biyu da rabi. Kashe kayan kallon ya yi, sannan ya shiga ɗakinsa ya kulle ƙofa. Da asuba da ta tashi ta yi sallar asuba, don har ta so ta makara saboda girkin da ta yi. Tana ji yana wanka. Takaici da kishin sa ya kamata don ta san waya ya kwana yi da 'yan mata sa ya sanya shi wanka. Tana ta sauraren ko zai fito sallah, amma har ta cire tsammani, ta ɗauki qur'aninta ta haye kan gadon yana karatu har lokacin tashi ta yi aiki ya yi. Kicin ta nufa ta yi ɗumamen tuwon da ta yi, sannan ta ɗora ruwan indomie ta dafa wa Raihan ta sanya mata a kula.Wanka ta yi ta shirya ta tafi makaranta. Marwana da Damir suna kan hanya zai kai ta makaranta. Hira take masa. Yawancin jiran kan karatunta ne, shi kuma yana ta dariya. "Yauwa Yayana." Ta ce tare da kamo hannu sa ta riƙe wanda ba ya tuki. "Akwai magana kenan" Ya yi mata maganar yana murmushi tare da kallonta sai kuma ya mayar kan hanya. "Eh," "Ina jin ki ƙanwata." "Ba ka ce za ka yi wa wannan matar kyauta ba?" "Wacce?" Ya tambaya don shi ya manta da maganar da suka yi. "Wannan 'yar makarantarmu." "Ok, na gane ta." Ya ba ta masa tare da shiga get ɗin gidansu. "Waya nake son na ka saya mata." Da sauri ya kalle ta jin abin da ta ce."Waya kuma? Ita ta ce miki tana buƙatar haka ?" "A'a." Ta ba shi amsa tana girgiza kai. "Saboda me ya sa kika buƙata?" "Dacewar hakan na gane Yaya, saboda ba ka wayar da take amfani da shi ba. Ko almajirin gidanmu ba zai rike ta ba." Dariya sosai ya yi musamman yadda take yatsina fuska." Marwana rigima! Duk a gurin ki little Marwana, ta gaji nata rigimar. Ke in ban da abin ki. Allah bai halicce mu duka ɗaya ba. A haka da take da wannan wayar kar ki yi mamakin irin rayuwar farincikin da take yi, saboda Allah ya halicci mutane daban-daban, kuma rayuwarsu daban-daban." "Na sani Ya Damir, amma ita tana da bukatar wayar. Tun da ka ga karatu take yi, in za ta yi assignment da karatu tana shan wahala." "Duk da hakan ba ta wayar kamar shishshigi ne a rayuwarta." "Ni dai Please Ya Damir, sai dai kuma in ba ka yi ninya ba." "Na isa? Zan siya mata system da waya hakan ya yi miki?" "Really?" "Sure, for you sis." Ya ba ta amsa tare da ɗaga mata kai yana dariya. "Na gode Ya Damir, Allah ya ƙara buɗi ya sanya ka fi haka." "Amin sis," Ya ce mata. Da ya sauke ta, gidan Hajiya ya wuce ya kai mata magani ta da ya siyan mata, sannan ya wuce gida don za su je check up yau. Da ya isa ƙofar get ɗin gidan, ya yi hon mai gadi ya taso ya buɗe masa. Shiga da motar ya yi, sannan ya yi parking. Kai tsaye falo ya shiga yana faɗin," Honey." "Na'am." Ta amsa tare da rungume shi ta ba shi hot kiss. "Ka dawo?" "Eh, da fatan kin shirya." "Am ready, we can go." Ta ba shi amsa tare da ɗaukar jakarta. "Karɓar jakar ya yi, sannan ya ɗauki makullin motarsa, ya kama hannunta suka fita suna sakarwa junasu murmushi. A asibitin teaching hospital na Ahmadu Bello University Zariya. Suna zaune kan kujeru, hankalinsu ya ɗauki ga siririn likitan da yake ta yi musu bayani cikin harshen Nasara. Jikin Damir ya yi sanyi, yana kallon abar ƙaunarsa da take kallon likita. Hannunta ya kama sannan ya ce,"Ina da burin matata ta haifa mini yara, amma saboda lafiyarta Doctor in ta haihu a juya mata mahaifar." Ya ƙarashe maganar cikin sanyi. "Yanzu shi ke nan ya'ya biyu kawai zan haifa maka Baby? Tun kafin mu yi aure ka sanar mini kana son ka cika family ɗinku da 'ya'ya tun da ba ku da yawa. Kenan aure za ka ƙara?" "Kece mace ta farko da na so kuma ta ƙarshe. Kin ji na yi miki alƙawarin ba zan taba auren wata 'ya mace ba." Duk da abin da ya ce hankalinta bai kwanta ba. Ƙara janke hannunta ya yi cikin wani yanayi. "Doc ka gaya mini yadda zan ƙara kula da lafiyarta saboda na rayu da ita har abada." "Ba ka da matsala, saboda kana kula da duk wani abu da mai cutar sikila zai kula." "Shi ke nan na gode. In Sha Allah, da zarar watan haihuwarsa ya tsaya zan kawo ta a cire babyn." "Allah ya kaimu." Ya ba shi amsa tare da miƙewa ganin sun mike. Jikinta a mace har suka isa gurin motarsu. Ya buɗe mata ta shiga. Zama ta yi bayan ya shigo ta rungume shi tare da fashewa da kuka. "Ina sonka mijina, sai dai ina ji a jikinsa kamar ciwonka ba zai barni mu yi tsawon rayuwa ba. Ga shi kuma alamu sun fara nuna wa, tun da ba zan iya haifa maka yara ba. Dole ka yi wani auren, ka samu matar da za ta haifa maka yara" Ta ƙarashe maganar tana kara ƙanƙame shi. "In har kika gaya mini haka sai na ji zuciyata ta sare. Ina jin za mu yi rayu dake har abada. Jikinsa yana bani kece mace ta farko kuma ta ƙarshe a gareni." "Ina fatan hakan mijina. Ina son na rayu da kai har abada." "Ni ma haka matata, in Sha Allahu zamu rayu tare." Ya furta yana shafa bayanta cikin tsigar rarrashi. FARUK Tun da daddaren da ya ci tuwon bai ƙara ci ba, don ko da safe da ta kai masa ɗumame, watsa mata mugun kallo ya yi. "Ba zan ci ba saboda ɗanye kika yi mini. Shi zu ku ci har kwana biyu." "Kwana biyu muna cin tuwo an ya da adalci kuwa?" "Babu ai dama ba ki ganin adalcina." Ya ce mata cikin ɓaci rai. "Gani na yi ko kai ba za ka iya cin tuwo har kwana biyu ba, don ba zai kai ba lalacewa zai yi." "Kisa a firjin dama ai amfaninsa kenan." "Tun da gas ɗin ya ƙare ka sanya ne?" "Ni fa na gaji komai ki ce ni zan yi a gidan nan. Mene ne amfanin ki?" "Lokaci ya kusa da zan taimaka." Ɗaukar brief case ɗin da ya yi zai fice ba tare da ya ce mata komai ba. "Allah ya dawo da kai lafiya." Ta ce tana kallon bayansa.Ba tare da ya amsa ba ya fice. Tun da ta karya da tuwon ta kasa ci. Fita ta yi ta siyo musu awara da yaji suka ci da rana. Da daddaren daurewa ta yi, ta ɗunduma tuwon suka ci. Cikin magagin bacci ta ji dirin motarsa. Da sauri ta sauko ta kunna fitilarsa, saboda babu wuta. Fita waje ta yi ta bude masa get ɗin gida. "Ba ki yi bacci ba?" Tambayar ta yi mata bambarakwai! Wai namiji da suna Hajara. "Na ɗauka kin yi bacci har zan buɗe get ɗin da kaina." Ya ce tare da rigata ɗaukar kayan da ya siyo. Sororo ta yi tana kallonsa cikin alamun bacci. "Mu shiga ciki." Ya ce mata cikin taushi murya yana mata kallon ƙasa-ƙasa, wanda ya sa ya ta ji wani iri. Da suka shiga falo zama ya yi a two seater sannan ya ɗaga idanunsa yana kallonta da ta yi tsaye kamar soja."To ki zauna mana." Ya ce yana nuna mata gefensa. Zama ta yi, tare da ƙasa da kanta tana mamakin canzawarsa. "Kin ci abinci?" WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 7 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Kin ci abinci?"Tambayar da ya yi mata, ya sanya ta kasa amsa masa. "Na san kema ba ki ci tuwon ba, tun da babu daɗi." Ya ƙarshe maganar tare da kama hannunta yana mata wani irin kallo ƙasa-kasa."Ga shi na siyo miki." Ya miƙa mata ledar da ta kasa amsa sai dai ya ɗora mata a jiki. Ganin ta kasa ɗaukar ledar, tana mamakin sabon salon da ya fito da shi, wanda za ta iya cewar tun farkon amarcinsu. Aka yi yunwa halin kowa ya fito, ya dai na siya mata. "Ki buɗe ladar mana, sai ki ije wa su Raihan na su." Ya ce mata wanda ya sanya ta yi namijin ƙoƙarin buɗewa.. "Ikon Allah! Tabbas akwai abin da ya shirya." Ta ce a ranta, amma kuma ta san dai cewa ba don haƙƙin kwanciya zai yi mata wannan tattashin ba, saboda zai iya sanya ƙarfinsa. Gabanta ne ya faɗi da zuciyarta ta ayyana mata ko aure zai yi. "Kai ina ba aure bane, domin bani da ƙimar da don zai shigo da wata sai ya tattashe ni. To mene? Allah kaɗai masani da shi da ya shirya." Ta ba wa kanta amsa. Ba ta ƙara shiga cikin tsananin mamaki ba, sai da ta buɗe ledar. Wasu irin haɗaɗɗun kaji guda biyu da Rufaida yogot. "Na yanka maka ne?" "A'a, na ki ne ke da yara ku ci." Ya ce yana murmushi tare da shafa bayanta. Cikin tsoro da fargaba ta ci kazar da yogot ɗin, domin zuciyarta cike da fargabar abin da za ta biya da shi, don ta san in har ta kasa biya, sam ba zai yi mata sausauci ba. Sai da ta ci ta kammala ta kora da ruwa, sannan ya kalle ta ya ce,"Ga shi daga yau za ki fara sha." Ya ce mata tare da ɓarewa ya miƙa mata sannan ya tura mata ledar ƙullin magani. Cikin tsanannin mamaki ta kalli ƙullin maganin"Na sha magani, ba ni da lafiya ne?" Ta yi masa tambayar cikin zallar mamaki tare da juya ƙwayar maganin a hannunta. "Ban sani ba, jahila ce ke da ba za ki duba ki ƙaranta ba?" Ya ce mata da ɗan ɗaga murya duk da yadda ya so ya danne zuciyarsa. "Supplements na gyara jiki Abban Raihan ka siyo mini? Ce maka aka yi ina muzanta da yanayin surata?" "A'a, saboda ina buƙatar na ganki kin zama 'yar duma-duma komai yana rawa a jikinki." "You must be jorking Abban Raihan, don wallahi ba zan sha abu da zai cutar da ni ba." "In da kuma kika yi kaɗan kenan, don ko ɗure zan yi miki sai na yi. Su sauran matan da suke sha mutuwa suka yi?" "Akwai yiwuwar sun mutun, domin mata nawa na ji labarin shan supplements, na ƙara girman halitta ko canza fata ya sanya sun kamu da cutar kansa? Ni ba zan sha abin da zai cutar da ni ba, saboda ban taɓa jin na raina halittar da Allah ya yi mini ba. A haka ka ganni ka aure ni, in da ka san mace mai ƙiba kake so da ba ka aure ni ba." "Sai kuma na yi laifi don na taimaka miki? Saboda na tabbata da ban aure ki ba, kina can kin yi kwantai. Ni ɗin ma tsautsayi da ƙaddara ya ja mini, in bacin haka ba zan sa ya kuɗina na auri mace kamar ki ba. Ke babu biyayya bare iya kissa da kwantar mini da hankali, sannan ɗan jikin ma ba za ki yi ba." "Ni fa duk abin da za ka ce ba zan sha ba." "Ki sha maganin nan tun kafin raina ya bace."Ya furta cikin ɓacin rai yana kallon ta. "Ba zan sha ba ko kashe ni za ka yi." Ta ba shi amsa za ta wuce. Fusata ya yi, tare da zare mata idanu ko mai ya tuna oho ya sausauta murya ya riƙe mata hannu. "Babu wani illa da yake sawa fa. Abokina ga ya siya wa matarsa, shi ne ni ma na ce zan siya miki. Da ma na sha tambayarsa yadda matarsa komai ya ji, ashe wannan maganin yake siya mata. Za ki sha safe da rana." "Ka san yadda na tsani magani shi ne kake cewa na sha. Ni ba zan zama 'yar kwaya ba." "Karɓa kisha tun muna mu biyu." Tsaki ta ja za ta wuce. Kau ya kaureta da mari. "Ina wasa dake zan miki umurni ki musa, sannan kuma ki yi mini tsaki?" Kuka ta fashe da shi tare da dafe ƙuncinta."Wallahi ko kashe ni za ka yi ba zan sha ba." Ganin ya nufe ta da sauri ta ruga da gudu ta shige ɗaki ta kulle ƙofa. Dukan ƙofar ya shiga yi, cikin tsananin fushi yana faɗin," Ki buɗe ƙofar na kafin na ƙaryata na canza miki halitta. Kin san nawa na sanya na siyo miki?" "Ba zaka iya bani abinci masu gina jiki ba na yi kyau, sai dai maganin da zai cutar da lafiyata to ba zan sha ba." Ta ce mishi tare da kwanciyarta. Tana jin yadda ya rinƙa buga ƙofar, amma ta yi banza da shi har ya gaji ya je ya kwanta. Da safe komai a cikin ɗakinta ta yi, kasancewar asabar ce ta yi zamanta a cikin ɗaki har ya fita, sannan ta fito ta girka ragowar indomie guda ɗaya ta bar musu. Kamar yadda ba ta yi tunanin zai bar mata abin da ya siyo mata ba, haka ta zo ta ga ko ƙashi babu. Wasan 'yar ɓuya suka fara har sai da suka yi kwana biyu. Ita ce ta fara gajiya da ɓuyan don kuɗin hannunta ya ƙare, sai garin kwaki da awara take ci. Ga shi Monday aka shiga dole ta nemi abin da za ta rinka bawa Raihan. Ranar Monday duk yadda ta so ya kulata ya ki. Har duƙawa ta yi ta bashi hakuri, amma bai kulata ba ya sa kansa ya fice. "Cikinku zai gaya miki." Ya faɗa yana murmushin mugunta. Idanunta ya raina fata. Ahmad ta kira ya tura mata da dubu ɗaya, ta siya wa Raihan abin da za ta ci a makaranta sannan ta wuce school. Marwana Kamar yadda ya yi mata alkawarin ya siyasa, Nasreen laptop mai kyau da waya tsaddadiya Rungume shi ta yi cikin farinciki. Dariya kawai ya yi mata ganin yadda take murna sosai. Bayan sun tashi daga makarantar. Nasreen na ƙoƙarin fita daga ajin ta ƙara so gurinta. "Ummu Raihan hanyarmu ɗaya, amma ba ki taɓa cewa na rage miki ba." Murmushin yaƙe ta yi, don tana tunanin abin da za ta ci in ta koma. "Ba haka bane. Na ga ke da ƙawayenki kuke tafiya." "To daga yau babu wanda zai ƙara shiga mini mota, daga ke sai Musaddik." Zare idanunta ta yi, jin abin da ta ce."Ayi haka? Mu dai shiga tare in ba zan takura ba?" "No, daga ni sai ke za mu rinka komawa gida." Daɗi ta ji sosai domin duka ɗari biyu ta rage mata ba zai isheta ba. "Bari na shiga, amma kar ki hana su." Ba tare da ta ce komai ba, ta buɗe mata gaba ta shiga sannan ta zagaya ta shiga ta tada motar. Sun yi nisa babu wanda ya ce uffan. Marwana ta waiwayayo ta kalleta tare da mayar da hankalinta kan tuƙi. "Hala tunani exam kike yi da aka sanya time table?" "A'a, mai kika gani?" Ta ce mata tana kallonta. "Babu." Suka yi shiru na 'yan daƙika. Marwana tana mamakin yawan shirin da take yi. "Kalli wayar nan da laptop ɗin na sun yi kyau?" "Wow, sun yi kyau sosai wallahi." "To na ki ne." Tsananin mamaki ya sanya ta kalleta da sauri. "Ni kuma?" "Eh, Yayana ya siya miki." Ranta ne ya ɓaci sosai." Saboda kin ga wayata shi ya sa kika sa ya siya mini? Bana buƙatar su domin wayar nan da kika gani tana mini komai." Hankalinta ya tashi jin abin da ta ce."Wallahi ba haka bane. Ya ce zai ba ki presents saboda ƙoƙarin ki. Shi ne na bashi shawarar ya sai mai waya da laptop don kin fi buƙatar su." "Bana so ki mayar masa ina jin daɗin rayuwata a haka." Ta ce mata amma a ranta ta ji dadi sosai mamakin siya mata abubuwa masu tsada ta yi. Ga mamaki ta sai ta ga ta gangara gefen titi ta yi parking."Don Allah kar ki yi mini mummunar fahimta. Wallahi bani da nufin tozarta ki. Yayana he is generous and kind, amma in zai ɓata miki rai zan mayar masa." Ta ƙarashe maganar sai hawaye shar a fuskarta. "Ikon Allah! Wannan Mommy's pet zan ce ko daddy's?" Murmushin ta yi tare da share hawaye."Brother's pet. Yayana shi ne gatanmu. Mu uku mahaifiyarmu ta haifa. Shi ne ya ɗauki duk wani ragamar rayuwarmu." "Allah Sarki kamar Yayana dai Ahmad. Shi ne na uku a ɗakinmu, amma shi ne namiji, kuma yake ɗaukar duk dawainiyarmu. Shi ya sanya ni a makaranta yake biyan kudin." "Ba kina da aure ba?" "Eh," Ta ba ta amsa sai alokacin ta tuna ɓaranɓaramar da ta yi. "Allah ya ɗaukashi kamar Ya Damir." "Amin." "Yanzu za ki karɓi kyautar?" "Na gode ki yi masa godiya sosai. Allah ya ƙara ɗaukaka shi." Amsawa ta yi sai kuma ta sanya hannu a jakarta ta zato dubu biyar."Ki sa kati." Ta kasa karɓar kallonta kawai ta ke yi." Kar ki ce a'a wallahi Allah ya sanya mini ƙaunarki tamkar 'yar'uwata na jini. Watakila kuma don bani da 'yar'uwa mace ce." "Zan karɓi wayar da laptop ɗin amma ban da ku..."Maganar ta katse ganin ta ɗauke jakarta ta sanya mata. Murmushin ta yi cikin farin ciki ta ce,"Na gode Allah ya bar ƙauna." "Daga yanzu babu godiya a tsakaninmu fatana na yi ƙoƙari lamari. Ya Damir ya tura ni waje na yi masters a can." "Za ki yi ƙoƙarin fiye da ni in sha Allahu." Duk yadda ta so ta kaita gida, amma taƙi sai ta kafe ta ije ta a unguwarsu. Unguwar ta bi da kallon mamaki ganin yawancin gidajen duk na masu kudi ne, saboda za ta iya rantse wa babu gidan talaka a gurin. "To shi ke nan, Ummu Raihan my regards to her." Ta amsa mata sannan ta juya ta wuce ita kuma ta kunna motar ta wuce. Tsayawa ta yi tana duba wayar da laptop ɗin."Ikon Allah! Wayar nan da laptop ɗin nan masu tsada ne, kuma wai sun ba ni kyauta?" Gabanta ne ya fadi da ta tuna ko mai Faruk zai ce game da kyautar. Shago ta wuce ta siya indomie, har da ƙwai da madara, sannan ta sayi kati na duba ɗaya ta wuce gida. Da ta isa gidan sauke Musaddik da yake bacci ta yi. Kwanciya ta yi kan kujera tana hutun gajiya. Bayan ta huta sannan ta shiga kicin ɗin ta girka indomie ta ibarwa Raihan, kafin su dawo islamiya a kawo ta. Tana zaune a falo har aka kira sallah magariba, daidai lokacin da Raihan ta shigo. Alwala suka yi sannan suka yi sallah. Ɗaki ta ja su suka koma. Bayan ta kulle ƙofar ta ɗauko laptop ɗin da wayarta. Da ma ta sanya katin da ta siyo Tana ta danna wayar ta kasa bacci har dare ya yi. Ko da ta ji dawowarsa ba ta damu ba, tun da ta san cewa ɗakinta a kulle yake. Faruk kuwa tun da ranar da ya siyo mata maganin ta ƙi sha yake jin haushinta. A ranar da ya sanya matuƙar ba za ta sha ba, shi kuma ba zai ba ta abincin ba. Mamakin inda take samun abinci ya kama shi matukar gaske. Duk da ya san ba ya wuce wannan ɗan'iskan Ƴaƴanta Ahmad. A yau dole sai ya ganta, don haka ya je ya nemo makullin ɗakin ya sanya a aljihunsa. Sai da ya shigo ya ci abinci da ya ƙoshi sannan ya buɗe ɗakin. Jin kiciniyar buɗe ɗakin, ya sa ya ta yi maza ta mike za ta ɓoye wayar, domin har yanzu ba ta san mai za ta ce masa, don ta san ba lailai bane ya yarda. Sai dai, duk ƙoƙarin ta na son yin hakan, kafin ta ɓoye har ya buɗe ƙofar ya shigo. "Saboda kin mayar da ni ɗan'iska, ba ni da matsayi a gurin ki. Shi ya sa kike kull..." Maganar ta maƙale masa sakamakon wayar da laptop ɗin da ya gani. "Ai iyye!" Ya faɗa cikin tsananin mamaki yana kallonta. "Ke! Gidan uban wa kika samu waɗannan?" Ya yi mata tambayar tare da ɗauka yana kallonta. Haɗa wayar ya yi da tasa yana kallo, duk da cewa ya san tafi ta sa tsada. "Nasreen?" Ya kira sunanta cikin tsanani mamaki. "Na..am,"Ta furta cikin tsananin tashin hankali tana kallonsa tana matsawa. "Gidan uban wa kika samu waya?" "En..uhm..e." Ta ce mishi tana zare ido. "Ta tabbata mazan jami'a kike bi. Shi ya sa kika raina ni, sam ba ki ɗauke ni a bakin komai ba. Ni da matsiyaci a gurin ki duk ɗaya." Zare idanunta ta yi cikin tashin hankali tare da matsawa ganin yana dumfarota. "Tsaya ka ji Abban Raihan, wallahi ban taɓa bin wani ɗa namiji ba. Don Allah karka buge n.." Ta yi shiru tare da ƙwala ƙara ganin ya kai hannu ya mangareta. "To in ba maza kike bi ba uban wa ya baki?" Ya faɗa tare da kai mata wani bugun. Faruk lafiyarka kuwa? 'Ya mace ba abin duka bane. Tsakanin mata da miji ya kamata akwai kyakkyawar fahimtar da kowanne zai san abin da ɗan'uwansa zai yi. To mu je dai zuwa mu ji yadda za ta kama Ba kwa comments lafiya?🙄🙄 In har ana son posting safe da yamma na ga ruwan comments. WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 8 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Kyauta yar aji.." Sai kuma ta canza maganar tana cewa,"Ya Ahmad ne ya siya mini." Ganin yadda ya zare mata ido yana son jin abin da za ta furta, sai ta canza shawara ta ce,"Ahmad? Ƙarya ne domin aikin kanikancin da yake yi, da ci da mahaifiyar da nema mata lafiya, ba zai bari ya siyaiki ba." "Na rantse da gaske ne ka kira shi ka ji." Ta faɗa cikin muryar kuka. "Na kira shi na ji uban me? Maza kike bi da aurena kike kula maza? Wannan dalilin ya sa ya har kwana biyar ban baki abinci ba, kuma ba ki damu ba." Ya faɗa tare da cire bell ɗin da ya shiga fuskanta tana ihu. Ganin yana shirin illantata, ya santa ta yi maza ta faɗa bayi ta rufe ƙofa. "Ki buɗe ƙofar nan, kafin na buɗe da kaina na yi maganinki." "Don Allah ka yarda da ni, wallahi ba zan taɓa cin amanar ka ba." Yaran sun yi tsuru-tsuru, suna kallonsa don Raihan kuka take yi sosai. Duk da cewar sun saba ganin yana dukanta, amma na yau ya ƙazanta. "Abba, don Allah ka daina dukan Umma." Cewar Raihan tare da kama hannunsa. Ba tare da ya kalli Raihan da take kuka ba ya ce, "Allah ya kaimu safiya, da asuba zan kaiki gidan na tsare Ahmad, na ji ko shi ya siyan miki." Ya faɗa tare da yarda bulalar. Saboda tsoron karya dawo a ranar kusan a bayi ta kwana. Ta yi kuka har ta bawa uku lada. Gabakiɗaya jikinta ciwo suke mata. Kwata-kwata ba ta yi tunanin zai ɗauki zafi sosai haka ba, in ya ga ta da su. Matuƙar nadama da dana sani suka cika ta. Tun da ya ce za su je gurin Ahmad, take ta kiran wayarsa ta sanar masa maganar, amma cikin rashin sama wayar ta sa a kashe Ga shi dama shi kadai yake da wayar a gidan. Kiran sallar asuba ya tashi ya rinƙa buga mata ƙofar ta buɗe. Tsananin mamaki da ya kamata, domin in dai da asuba ne sam baya tashi da wuri. "Ki buɗe ƙofar nan, muje na tambayesa in kika ƙara sakan biyar wallahi a igiyoyin aurenki..." Bai gama maganar ba ta fito, da hijabinta da ta yi sallah jin abin da ya ce."Da ki zauna kar ki fito, sai na ga gidan uban da za ki in na sake ki." Tsaki ya yi ya juya ya fice, ganin haka ta ƙarashe goya Musaddik tana hawaye ta bi bayansa. Yana isa ƙofar gidan ya fara sakin hon babu ƙaƙƙautawa. Jin hon ɗin ya farkar da Baba, da yake ta sharan bacci, ya ƙi tashi ya yi sallah, duk da nacin tashin da Mama take mishi. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Yau kuma mai Nasreen ta yi wa wannan tsinannen mijin nata?" Ya yi tambayar tare da miƙewa yana zare ido. Mama ita kanta jin hon ɗin na sa hankalinta ya yi matuƙar tashi. Fita ya yi tare da ɗaukar rigarta yana da sanyawa. "Yau wallahi yadda ba ni da ƙo ƙwandala, ya ce zai yi mini rashin kunya sai na ci ubansa." Ya faɗa tare da fita wajen. "To isasshe ɗan ƙaruna. Ka kashe motar ma ka fito ba za ka iya ba, sai dai ka damu mutane da hon, kamar wanda ya zo da jirgin sama." "A gurinku ai kamar tafi jirgin tun da ko keke ba ka da shi." Ya bashi amsa fuska a tamke, tamkar ba da surukinsa yake magana ba. "Ka san ba mutunci ne da ni ba ko Faruk? Wallahi yanzu zan maka rashin mutunci. Da ma ba ka san haushinsa na ke ji ba. Ƙiri-kiri na nemi aro dubu goma ka hana. Sai kace dubu ɗari na nema." "A kan me zan ba ka kuɗin bayan 'yarka da ka aura mini tana gasa mini gasa a hannu? Tambayeta rabon da ta bani haƙƙina kwana biyar kenan, saboda ta samu mazan jami'a, tana iskanci da su suna biya mata bukatunka." Kallon mamaki ya yi mata jin abin da ya ce. "Baba, wallahi ba haka ba ne, Baba bana kula ko wane ɗa namiji." Ta faɗa cikin muryar kuka tana gyara goyon Musaddik. "Ƙarya zan yi miki kenan?" Ya ce tare da kai mata duka ta kauce. "Faruk! Ko mutuwa tana jin kunyar mahaifi a gabana za ka duketa?" "Ƙarya ta zan iya yi, domin zuciyata gaba take da ta bani shawarar na yi ajalinta. Matuƙar ba za ta gaya mini, wanda ya siya mata waɗannan ba." Ya ce tare da nuna masa. Zare idanunsa ya yi, yana kallon wayar da laptop ɗin sai kuma ya juya yana kallonta. "Zina take yi suka siya mata." "Wallahi Baba ba zina na yi ba." Ta ƙara cewa." Baba kuwa mamaki sosai ya kama shi, sai ya shiga tunanin wa ya siya mata, don ya san Ahmad ba shi da kudin da zai iya siyan mata. "Nasreen, wa ya siya miki?" "Na'am eh Ya Ahmad ne." Ta ba su amsa cikin kuka. "Ahmad?" Ya yi tambayar yana kallonta. Kafin ya ce wani abu Ahmad da ya dawo daga Masallaci, rike da karbi yana ja a hannunsa, ya ƙaraso da sauri ganin motarsa. Harara suka ba ka ma junansu, domin tamkar mage da ɓera suke. Faruk yana ɗan shakkar Ahmad, saboda ba sa gama maciji, kuma ya san shi kamar zawayi yake. Sai ya ɗan rage hargowar da yake yi. Ba tare da ya kalli Faruk ko Baba, ba ya karasa gurinta da ganinsa, ya sa ta fashe da kuka tare da kama hannunsa. "Nasreen, mene ne?" "Mazan jami'a take bi suka saya mata waya da laptop mai tsada." Maganar ta buge shi, musamman da ya nuna masa wayar da laptop ɗin Shi kansa ya razana da ganin wayar. "Ya Ahmad ka san halin ba zan taɓa bin wani ɗa namijin da aurenka ba. Na gaya mishi kai ka siya mini, amma ya ƙi yarda." Jin abin da ta fada, ya sa shi ƙoƙarin shanye mamakin inda ta samo su. "Ƙarya ne ba shi da kuɗin da zai iya siya miki." Faruk ya ce yana kaɗai makullin motarsa. "Saboda ka mayar dani matsiyaci ko, sannan ka manta dare ɗaya Allah kan yi Bature? To ni na siya mata tun da kai ka kasa. Adashi na kwasa na siya mata, tun da kai ka kasa." Kallon mamaki suka yi masa har da Baba. "Yanzu dama Amadu, kana da kudin siyen waɗannan na yi da kai, jiya ka bani naira dubu shegiya ka hana?" Ba tare da ya amsa masa ba, ya juya gurin Faruk."Na gaya maka ka daina dukanta, domin ita ba jaka bace." "Dole na duketa, tun da ko addini ya bamu damar in mata mu suka ɓata mana mu duke su." "Wannan fatawar na ka ya sanya na gane kai babban jahili ne. Ilmin boko kawai kake takama da shi." "Na gode ma Allah tun da na yi bokon, kai kuma da ubanka ya kasa ba ka duka f.." Kafin ya ƙarashe ya ɗaya hannunsa zai kai masa mari, amma sai ya doje. "Wallahi in har ka yi kuskuren marina, sai na kashe ƙanwarka da duka kuma ka yi zaman burtsuna." "Kai Amadu wai mai ke damunka ne?In ka tunzura shi ya saketa, wallahi kai da ita sai dai ku bar mini gidana." "Baba, Allah zai kama ka a kan haƙƙin Nasreen. Ka ba shi dama yana cutar da rayuwarta." "Ka fita idona ɗan iska kawai! Uban me ka sani game da aure. In ta rabu da shi kasan mijin da za ta ƙara aure?" "Ba..." "Kar na ƙara jin muryarka. Wulaƙantaccen yaro kawai." Ya daka masa tsawa yana faɗin haka. Ransa ne ya ɓaci hannunta ya ja za su shiga ciki. "Kai Amadu! Gidan uban wa za ka kai ta?" Ya yi masa tambayar cikin ɓaci rai. "Ka barshi ya shiga da ita ciki, ta zauna har illa ma sha'a. Ki an gaya masa amfani take mini? Ci da ita kawai zai zamar masa aiki." Ya ce yana ƙoƙarin shiga cikin motarsa. "Ke Nasreen dawo ki tsaya kai kuma wuce." Ya ce mishi cikin tsawa. Idanunsa suka kawo ruwa, ya kalle ta da take ta kuka, ganin har mutane sun fara tsayawa ana kallonsu. Tausayinta ya sanya hawayensa zuba. Girgiza kansa ya yi, tare da wucewa ba tare da ya ƙara cewa komai ba. "In kin san ba shi ya saya miki ba ki bawa mijinki hakuri, sannan ki kawo ni zan san yadda zan yi dasu." Ya faɗa tare da fatan Allah ya sa ta bashi ya siyar. "Shi ne Baba." "To ka ji ka yi hakuri kamata ya yi ya gaya maka." Kallonsa ya yi don har yanzu bai yarda ba. Ba tare da ya ce komai ba ya fara ƙoƙarin shiga motarsa. "Za ki shiga ki bi mijinki shashasha kawai! Kuma wallahi kika ƙara barin ya kawo ƙarni sai na saɓa miki." Da sauri ta shiga tana kuka. Ganin ya shiga motar har ya tada ya sanya shi duƙawa. "Faruk, tafiya za ka yi? Maganar kuɗin nan fa. Har gida zan zo na ja mata kunni." "Ni fa kana isata 'yar ka babu tarbiya, amma kullum buƙatar da kake kawo mini daban. Wallahi na yi dana-sanin auren zuriyarka." "Ka yi hakuri ba za ta ƙara ba." Hannu ya sanya a aljihunsa, ya ciro kudi da yawa kamar zai bashi sai kuma ya fara irga dubu biyar. "Iya wannan zan ba ka, kuma na rantse in ba ka dawo mini da su ba. Karka ƙara tunanin zan baka rance, tun da ba biya kake ba." Ya ce tare da kunna motarsu ya fara tafiya. "Raba mugu da makami, ibada. Kuma wallahi ko kafi maye maita ba zan bayar ba. Ni zan yi dana sani da na ɗauka gidan da zan rinƙa zuwa maula na aurar da ita. Ashe ɗan Iskan ƙalƙo na aura mawa." Ya faɗa yana aika ma motar mugun kallo. "Kai Allah na gode maka. Na tashi bani da ko fincika, amma na samu kudin da zan kashe har kwana uku.Na yarda da cewar dare ɗaya Allah kan yi Bature." Suna hanya yana gudu sosai ya juyo ya kalleta."Kina ganin halin ubanki? Kina kallon duk abin da yake faruwa? Kin san baki da gatan da ya wuce gidana, amma ba za ki yi mini biyayya ba mu zauna lafiya. Wallahi in har kika ce saba mini za ki rinƙa yi sai na lahira yafi ki jin dadi." Shiru ta yi ba tare da ta ce masa komai ba. Kuka take yi sosai har idanunta sun kubbura. Dana sanin zuwa ta duniya da tunanin makomar rayuwarta sun addabi zuciyarta, domin matuƙar mahaifinta zai cigaba da haka. Ba ta da kima da daraja a idanunsa. Da suka isa gida, duk kukan da take yi haka ta taso ta buɗe masa ƙofa. Fita ya yi daga motar, ba tare da ya kulle ba ya kalle ta ya ce," Ki wanke mini mota, tun da ba ki da amfani a matsayin matata, ba kya iya ɗauke mini damuwata, don haka komai ke za ki rinƙa mini." "To," Ta furta tana share hawaye don wanke motar ba shi ne na farko ba Har ya tafi ya dawo ya karbi wayar da laptop ɗin ya shige. "Na shiga uku! Da na sani da ban ƙarfi kyautar nan ba. Dama ance dana sani ƙeya ce." Ta furta tana share hawaye. "Umma, ki bar kuka ina girma sai na sanya 'yan sanda sun kama Abba." Raihan ta faɗa tana share mata hawaye. Da ta gama wankin motar. Ƙullin kayansa ya ji ga mata ta wanke. "Kuma ki goge kafin na dawo." Ya ce mata tare da ficewa daga gidan. Tun da ya fita take kuka. In ta tuna toxarcin da ya yi mata sai hawaye. Saboda fitan da suka yi Nasreen ba ta je makaranta ba. Ita kuma ba su da lecture sai ƙwara ɗaya kuma presentation suke yi group ɗin su sun yi. Tana kwance bayan ta gama wankin tana jiran su bushe ta yi gugar. Maman Muwadda ta yi sallama ta shigo. Gani ta ya karyar mata da zuciya ta fashe da kuka tare da rungume ta. "Lafiya mai kuma ya ƙara faruwa?" Kuka sosai take yi har ta jin zuciyarta na yi mata zafi tamkar za ta fito waje. "Ni dai ban yi sa'ar zuwan duniya ba, domin na kasance daga cikin wadanda suke karɓan ruwan mara daɗi a cikinta. Zaman aurena ba shi da maraba da bauta. Mijina bai bai ɗauke ni da wata daraja ba. Zuciyata zafi take yi tamkar za ta fito waje." "Ki yi shiru ka yi mini bayani." Sai da tasha kuka son ranta sannan ta kwashe lamarin ta gaya mata. "Allah Sarki! Ita kuwa wannan wace ce ta shigo rayuwarki? Haƙiƙa na yi miki farincikin. Allah ya sanya ta zama sanadin da za ta kawo haske a cikin rayuwarki." Ta furta cikin tsananin farin ciki. "Zan matar mata ba zan iya jurar toxarcin da nake fuskanta ba." "Saboda me za ki mayar masa? Wallahi ina gaya miki matuƙar ba ki tashi kin nuna wa Faruk, ko babu shi za ki iya rayuwa ba. To rayuwarki na cikin siradi rayuwa. Nasreen, kina da kyan ki da ilmin ki. Sannan kuma da kyawawan halaye. Ko da ace mahaifinkk ya kore ki ba za ki rasa inda za ki zauna ba, har ki samu miji ki yi aure. Faruk ba mijin da mace za ta zauna da shi bane, domin so yake ya tsotse ƙwallon mangaron ya huta da ƙuda. Ki tashi ki nuna masa kema mace ce kina da gata. Talauci da 'ya'ya ba hauka bane da za ki kashe kanki saboda su. In har kika nuna masa ko babu shi za ki iya rayuwa, zai rage abin da yake yi, domin yana sonki. Faruk! Rayuwar aure na ƙargin bauta bane da za ka mayar da mace tamkar jaka. Masu hali irin na Bana haƙiƙa suna kawa 'ya'yansu gori da tozarci. Makaranta innsha Allahu yau zan yi posting safe da yamma a cigaba da surbubuɗo comments ❤️❤️❤️❤️💃💃💃💃 WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 9 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Saboda me za ki mayar masa? Wallahi ina gaya miki matuƙar ba ki tashi kin nuna wa Faruk, ko babu shi za ki iya rayuwa ba. To rayuwarki na cikin siradin rayuwa. Nasreen, kina da kyan ki da ilmin ki. Sannan kuma da kyawawan halaye. Ko da ace mahaifinki ya kore ki ba za ki rasa inda za ki zauna ba, har ki samu miji ki yi aure. Faruk ba mijin da mace za ta zauna da shi bane, domin so yake ya tsotse ƙwallon mangaron ya huta da ƙuda. Ki tashi ki nuna masa kema mace ce kina da gata. Talauci da 'ya'ya ba hauka bane da za ki kashe kanki saboda su. In har kika nuna masa ko babu shi za ki iya rayuwa, zai rage abin da yake yi, domin yana sonki. Tsabar jahilci da rashin sanin darajar mace da kuma ɗaukar aure a matsayin ibada ba, ya sanya yake wulaƙanta rayuwarki." Kamata ta yi ta rungume tana shafa bayan ta sannan ta ɗora da cewa,"Guda nawa kike da har za ki fuskanci wulaƙancin ɗa na miji?" Kuka take yi sosai har ta gaji ta yi shiru sai ajiyar zuciya. Ba ta baki ta shiga yi har ta samu sauki a cikin zuciyarta. Wayarta ta ɗaya ta kira babbar 'yarta ta kawo musu abinci. Ta daɗe tana gidan tana kwantar mata da hankali, sai da aka kusa kiran magariba sannan ta yi mata sallama ta tafi. Bayan tafiyarsa ta gama gugan ta yi alwala ta yi sallah. Sannan ta ɗauki qur'ani tana karantawa har kusan a kira isha'i. Ƙwankwasa get ɗin gidan da ake yi da dutse ya sa ta tashi ta je ta bude da tunanin waye cikin daren nan "Wane ne?" Ta furta daidai lokacin da ta isa bakin get ɗin. "Ahmad ne." Ya ba ta amsa tare da jefar da dutsen Tana buɗe get ɗin gidan ta saka mishi kuka tare da faɗawa jikin shi. "Mai ya sa kika aikata haka? Kin san za ku zo ai da kin kira ni." "Na yi ta kira ka wayar a kashe." Ta ce masa cikin muryar kuka. Kama hannunta ya yi suka shiga ciki. Zaunar da ita ya yi, sannan ya zauna a gefenta. "Faɗa mini wa ya ba ki waya da laptop masu tsada haka?" "Ka yarda da ni Yaya Ah.." "Da ma na zarge ki ne? Na san wace ce ke. Ko Baba ya rantse ba za ki taɓa kauce hanya ba. So kawai na ke na san inda kika samo su." Cikin kuka ta sanar masa wanda ya cika da mamakin kyautar. "Da kin sani da ni kika kawo mawa, sai na kawo masa na ce na saya miki, amma dama ko wane namiji ya ga matarsa, da abu mai tsada haka dole ya tambaye ta ba'asi." "Na yi kuskure Yaya." Ta furta tana share hawaye. Kwantar mata da hankali ya shiga yi har ta samu ta saki. Ledar awara ya miƙa mata yana faɗin," Ga shi ki samu ki ci na san wataƙila ba ki ci komai ba." "Maƙociyarta ta kawo mini." "Allah ya saka mata da alkhairi." "Amin," Ta furta tare da miƙewa ganin ya miƙe. Ko da suka zo bakin get nasiha ya yi ta mata, sannan ya kawo Naira ɗari biyar ya ba ta. Koma ɗauki ta yi ta kwanta yayin da hannunta ɗauke da carbi tana lazimi. Faruk kuwa tun da ya fita ya rasa sukuni. Kallon wayar yake yi cikin tsananin mamaki, saboda wayar mai tsada ce. A yadda Ahmad ya ɗan nuna alamun rashin gaskiya, ya sa ya shi kokwanto kan siya mata da ya ce ya yi. Sannan ko da bai nuna ko kokwanto ba. Sam ba zai yarda ba don ba, shi da arzikin da zai iya sigar ko da wayarce. A hanya yanke shawarar dole ya sa ya ta ta yi rantsuwa da qur'ani shi ya siya mata. Saboda jaraba yana dawowa ɗakinta ya shiga, wacce ta yi nisa a duniyar tunani ba ta ji hon ɗin motarsa ba. Ballantana shigowarsa. Ganinsa ya sa ta tsorata tare da miƙewa tamkar za ta ruga. "Ka yi hakuri ban san ka..." "Rufe mini baki banziya kawai! Da ma kina jin maganata ne? Ai kin raina ni duka kuwa kin saba kamar jaka!" "Kawo qur'anin." Ya ce mata. Mika masa da sauri ta yi tana ƙare kanta da hannu a tunaninta dukanta zai yi. "Ka yi haƙuri don Allah." "Ungo." Ya ce mata. Da sauri ta karɓa a ranta tana mamakin dalilin da ya sanya ya karɓar da ya yi. "So na ke ki rantse da qur'anin nan Ahmad ya siya miki." Zare idanu ta yi har ta saki qur'anin zai faɗi, ta yi maza ta riƙe da sauri jikinta na mazari. Ganin yadda ta firgita, ta shiga cikin tsananin tashin hankali, tare da hawaye ya sanya masa shakku a ransa. "Ma za rantse na ce, saboda shi zai sanya na yarda dake. Na san yadda kike daraja qur'ani da kuma wanda ya yi, sam ba za ki iya rantse wa kan ƙarya ba. In har kika rantse yanzu zan ba ki na yi miki fatan alkhairi." Ta yi shiru tana zare ido, a ranta ta fara tunanin ta gaya masa gaskiya ko ba zai yarda ba, domin ko da suka zai sanya mata a maƙoshi ba za ta rantse ba. Tana tsane da ko a kan gaskiya mutum ya rantse Allah zai iya hukunta shi, domin Alqur'ani ba abin wasa bane. "Ki rantse na ce." Ya daka mata tsawar da ya ƙara firgita ta. Ije wa ta yi tare da ƙara sakin kuka."Zan gaya maka gaskiya." Ta ce tana ɗaya yatsunta, kamar wata ƙaramar yarinya. "Ina jin ki." Ya furta cikin mamaki yana kallonta. "Wallahi wata 'yar ajinmu ta bani. Kuma in har ba ka yarda ba. Mu je makarantar na ma mayar mata." "Ta ya ya zan yarda, in kun haɗa baki ne ita ke ɗora ki a hanya fa? Yar iska da aurena za ki ci amanata." Ya kai mata mari yana faɗin haka. "Wallahi ban taɓa cin amanar ka ba. Ba zan iya rantse wa kan wayar ba, amma zan rantse da qur'anin tun da na aurenka ban taɓa kallon wani ɗa namiji da sunan sha'awa ba. Kai ne namijin da na fara sani, kuma har yau ban taɓa kula wani ba. Ka yarda da..." Ta kasa ƙarasa maganar sakamakon hamɓarin da ya kai mata a ciki. Duƙawa ta yi tana jin yadda kayan cikinta ke juyawa. Jiri ya ibe ta. Da sauri ta dafe cikin tana faɗin,"Wayyo Allah! cikina za ka kashe ni." "Eh gara na kashe ki don babu amfanin ki a duniya. Matar da take cin amanar mijinta, mutuwa ya fi a gareta. Kin ga ko banza na yi maganin irinku." Kuka take yi sosai yana dukanta yana haurinta. Tun maƙota na jin kukan suka daurewa har suka gaza. Cikin kuka Maman Muwadda ta kalli mijinta. "Kuna jin zai kashe ta? Saboda tsoron sa da masifarsa. Shi Allah ne? Wallahi zan fita na ɗauki icce na ragije shi." Ta furta cikin tsananin kuka. "Me kike so na yi? Yaron nan mahaukaci ne. Kin san ba zai bar kowa ya shiga cikin gidan ba, kulle gidan yake yi. Kina sane da tozartar da ya yi mana da Alhaji Munir, saboda mun yi mishi nasiha. Ba zan shiga cikin rayuwar iyalin sa ba. Shi mahaifin na ta wane irin dabba ne?" "Nasreen, ba da gata sai Allah. Ubangiji shi ne kawai gatanta, domin tana cikin wani mawuyacin hali. Wallahi in har ba ku taimaka wa rayuwarta ba sai Allah ya hukunta ku." Miƙewa ya yi tare da ɗaukar wayarsa ya fice daga gidan. Buga ƙofar da ya ji an dame shi ya sa ya daina dukanta, wacce ta yi lamo kukan ya gagareta sai nishi take yi. "Gobe zan ɗauke ki muje cikin makarantar na tabbatar. Kuma wallahi in har ƙarya kike yi, sai na lahira yafi ki jin daɗi." "Na yarda zan mayar mata, in haka zai sanya ka haƙura." Ta ce tana share hawaye a wahalce. A daren ranar ta yi kuka har ta ji babu dadi. A gurin da ya gama dukanta ta samu da ƙyar baccin wahala ya ɗauke ta. Baccin mai kama suma ta yi, sai da sanyin asuba ya fara sannan ta farfaɗo. Cikin ƙarfin hali ta mike ta dafa ruwan zafi sosai ta gaza jikinta. Kallon fuskarta ta yi, da yake mata wani irin zugi sai ta ga ashe ya fasa mata gefen idanunta. Bayan ta yi wanka, ta shirya ta yi sallah tana kuka. Komawa ta yi ta kwanta har gari ya waye. Ƙarfe tara na yi, ya sanya a cikin mota suka nufi makarantar. Saboda yadda ya fasa mata jiki. Niƙabi ta sanya ta rufe fuskarta. Cikin sa'a yana parking da motarsa, sai ga Marwana ta shigo gurin parking ɗin. "Ga wacce ta bani can." Ta furta tana nuna ta da yatsa Da ya ga motar da take hawa sai da gabanshi ya faɗi. Bai gama firgita ba sai da ya ga wata tsuleliya kyakkyawar gaske, fara mai kyawun diri da shiga ta alfarma ta fito Idanunsa ya zare tare da kallonta, sosai bayan ya cire gilashin da ya sanya. Jikinsa ya kama rawa yana kallonta." Irin wannan baby ɗin ne take kulata? Kai ina ni ya kamata na ta kula, amma ita ba."Ya ce yana ƙare mata kallo kamar maye. "Ma za ki je ki bata." "To," Ta amsa cikin sanyi tare da buɗe ƙofar ta fita. Tun da ta fito Marwana ta bi ta da kallo, saboda tafiyarta ya yi mata kama da na Nasreen, amma kasancewar ba ta taɓa ganinta da niƙabi ba, sai ta ɗauka tafiyar ta su ce ta yi kama. Ta fara tunanin ita ce ganin goyo a bayanta kuma tana dumfaro inda take. Ƙwayar idanunta ta kalla daidai lokacin da ta yi mata sallama. "Subuhanallahi! Mai ya samu idanunki?" Ta yi mata tambayar, ba tare da ta amsa sallamar ba tana ƙoƙarin cire mata niƙabin "Ga shi na dawo miki da kyautar ki. Da na san abin da zai faru a dalilin kyautar da ban karba ba. Mijina ya yi fushi kuma ya ce na mayar miki. Ki gaya wa yayanki na gode, zan ci gaba da karatuna ba tare da ina da su ba." "Nasreen, wai me ya faru? Da ma kyauta yana zamo abin faɗa ne? Shi mijin na ki bai yarda dake bane?" Ta yi mata tarin tambayoyin tare da buɗe fuskarta. Ja ta yi ta matsa cikin tashin hankali."Nasreen? Mai ya faru da ke?" Kawai sai kuka ta kai hannu za ta kamata. "Ki fita daga rayuwata na ce!" Ta daka mata tsawa tana faɗin haka, sannan kuma ta ɗora da cewa,"Kin san abin da ya faru a dalilin kyautar nan? Ya ce ina cin amanar sa, kuma ya duke ni ya tozarta mahaifina. Na yi dana sanin karbar kyautar nan." Tsananin tashin hankali ya bayyana a Kyakkyawar fuskarta. Kuka sosai ta rushe da shi ga in yadda halittun ta suka canza. "Kina rayuwa da mijin da bai yarda da ke ba and you call this marriage Nasreen? What the hell kike yi har kika yarda namiji ya raina ki kamar haka? Dubi yadda ya canza kyakkyawar fuskarki. Kin san yadda fuskan ɗan adam take da daraja? Ko kin san darajar da Allah ya bawa 'ya'ya mata?" "Ba na son jin komai daga gare ki, zan bi umurnin mijina saboda shi ne kawai gatan da na ke da shi. "Namijin da zai duke ki shi ne kike kira miji?" "Eh, saboda bani da wanda ya fishi. Ina rokonki da ki fita daga rayuwata. Na gode da taimakon ki." Ta ce tare da juyawa. Ba tare da kula da ije mata da ta yi ba ta bi bayanta. "Nasreen!" Ta furta daidai lokacin da ta ƙaraso motar. Tsayawa ta yi ganin har ya tashi motar ya bar harabar makarantar. Matuƙar mamaki ya kamata ganin mijinta na da mota. Sam ba ta taɓa tunanin mijinta yana da mota ba Kuma mota mai tsadar gaske. Sannan shigarsa da yanayin sa ya tabbatar mata da yana da kyau da hutu, sannan ya yi karatun boko. Kanta ya ɗauke wuta, har ta ji yana shirin sara mata. Zama a gurin ta yi cikin tsananin tashin hankali tana tunanin fuskarta. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Wannan aure take yi ko bauta? Ace mijin ka bai yarda da kai ba?" Sosai hawaye yake zuba a ƙuncinta matuƙar tausayinta ya kamata. A maimakon ta fita daga rayuwata kamar yadda ta ce, sai ta ji wani irin mugun sonta da ƙaunarta, ya shiga cikin ranta har tana ji ta san rayuwar ta kuma ta san asalinta. "Ta ce shi ne kawai gatanta marainiya ce?" Ta yi wa kanta tambayar hakan. "A'a, ita ba marainiya nace, saboda na ji ta ce a dalilin kyautar ya wulaƙanta iyayenta." Ta bawa kanta amsa. "To mai yasa take zaman aure a gidansa na ƙangin bauta?" Ta kasa gane dalilin haka. Dama ta shigo ta je Library ta yi karatu ne. Faruwar abin ya sanya ta juya ta koma gida cikin tashin hankali. A hanya kuka take yi, tana tausayinta da mamakin rashin imaninsa da ya yi mata haka. Tana isa cikin gidan ta yi parking sannan ta fito ta wuce ciki. Mamaki sosai suka yi ganin ta dawo. "Marwana, mantuwa kika yi?" Hajiya ta tambayeta cikin mamaki. "A'a." Ta ba ta amsa tana zama a kan kujerar da take zaune, tare da ture Little Marwana da ta haye cinyarta tana faɗin, " Anty." Makaranta innsha Allahu yau zan yi posting safe da yamma a cigaba da surbubuɗo comments ❤️❤️❤️❤️💃💃💃💃 WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 10 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Marwana, mantuwa kika yi?" Hajiya ta tambayeta cikin mamaki. "A'a." Ta ba ta amsa tana zama a kan kujerar da take zaune, tare da ture Little Marwana da ta haye cinyarta tana faɗin," Anty." "Sis, lafiya?" Cewar Damir da yake zaune gefen Hajiya. Sai kawai ta fashe musu da kuka sosai. Gabakiɗaya suka yi kanta. "Mai ya faru? Suka yi mata tambayar cikin mamaki." "Wallahi na fasa auren Ya Ashman in har haka auren yake." Ta ce tana share hawaye. "Mai ya faru, wani abu ya yi miki?" "Ya duketa ya fasa ya fasa mata kai, har yana cewa tana cin amanar sa, sannan ya tozarta iyayenta." "Wa ke nan, ko ya yi aure ne bamu sa ni ba." Hajiya ta yi mata tambayar cikin mamakin kalamanta. "Mijin Nasreen." Ta furta cikin muryar kuka. "Nasreen?" Suka yi mata tambayar har da Damir, saboda shi ya manta da ya bawa wata kyauta. "Nasreen ɗin da ta ke top a ajinmu wacce ka siya mata waya da laptop." "Ohh," Ya ce tare da tunawa. "Waye ita Damir?" Hajiya ta ce. "Wata yarinya ce a ajinsu tana da ƙoƙari shi ne na ce zan yi mata kyauta. Ta ce na siya mata waya da laptop ta samu na karatu. Da na siya mata ta kai mata. Ina ga shi ne mijinta ya zargi wani abu." Ya ce cikin basar da zancen. "Kuna da hankali kuwa? Dama dole ai ya nuna tashin hankalinsa, saboda yanzu duniya Babu tsoron Allah. Yin zanace-zinace ya yawaita ba 'yan mata ba, ba kuma zawarawa ba har matan aure marasa tsoron Allah suna aikatawa." "Amma Hajiya kin ga dukan da ya yi mata? Ya fasa mata fuska, ko ina jikinta shafin duka ne." "Bai kyauta ba saboda bai kamata ya duke ta ba." Cewar Hajiya. "Kuma in ban da shi mahaukaci ne, iya zaman da suka yi ai ya kamata akwai yarda da amana a tsakaninsu. Ko da ace an gaya masa cewar matarsa na cin amanar sa bai kamata ya yarda ba." "Abin da nake tunani kenan. In har babu yarda da ita ba. Ban ga dalilin da zai sanya ta zauna da shi ba. Yaran su biyu." "Haka WASU MAZAN suke sun ɗauki mace kamar baiwa." Cewar Hajiya. "Kuma abin mamaki she is young. Ba za ta wuce sanata ba, don zan iya girme mata." Ta faɗa tana kallon Damir da ransa ya ɓaci. "Saboda wannan zai sa ya ki fasa auren Ashman? Ina ba zai taba aikata haka ba, kuma duk ranar da sheɗan ya sanya shi ya aikata. To nine ajalinsa. Ki kwantar da hankalinki matukar ina raye, babu wanda ya isa ya yi miki tsawa ballantana ya ɗora hannu a kanku." "Na gode Yaya Damir, kuma ina godiya ga Allah da ya ba ni kai a matsayin Yaya. Allah ita ma ya bata Yaya kamar kai." "Amin," Ya ce yana murmushi. Ɗakinta ta shiga ta kulle ƙofa tare da zama kan gadon. Ɗan kwalinta ta cire cikin damuwa. "Anya yana da imani kuwa?" Ta furta cikin takaici yayin da take ji kamar ta je ta rama mata. A mota kuwa hankalinsa ya tashi matuƙar gaske! Ganin Marwana. Ya tabbata duk inda ta fito ta iyayenta ko mijinta suna da kuɗi. Harararta ta gefen idanu yake yi cikin jin haushinta. "Wallahi kin ji na gaya miki matuƙar kika ƙara kula yarinyar nan, sai na yi mugun saɓa miki, saboda daga ganin yarinyar nan, irin matan da suka gagari iyayensu ne." Shiru ta yi ba ta tanka masa ba hawaye suke zuba a ƙuncinta. "Wa ya sani ko 'yar lesbian ce, saboda irin wannan kyautar da ta yi miki in dai ba wani abu take buƙata daga gareni ba, to babu abin da zai sanya ta yi miki shi." Nan ma ba ta ce masa kanzil ba, domin ba ta da abin da za ta ce. Da suka koma gida wanka ya yi sannan ya fice daga gidan. Tun da ya fita take kuka kamar za ta haɗiye ranta. Ta yi kukan har ta ji babu daɗi. Dana sani kuwa ya fi cikin kwanon masaki. Ganin kukan ba shi ne mafita ba, ya sanya ta share hawayenta ta ɗauki qur'ani tana karantawa. Sallamar Maman Muwadda ya katse mata karatun da take yi. "So kike ki kashe kanku Nasreen? Dukan da yake miki bana hankali bane. Wallahi da na zauna da kalan mijinki gara na shiga duniya." "Ba ni da zaɓi ne, zaman aure a shi ya fi mini kwanciyar hankali." Ta furta tana kuk,a wanda ya sanya ta yi fushi ta bar mata gidan. Cikin dare Marwana ta kasa bacci. Da ta rintse ido sai ta ga fuskar Nasreen tana kuka. Miƙewa ta yi ta zauna a tsakiyar gadon. Tun bayan da ta dawo gida take ta neman layin ta amma a kulle. Na damu da na ji halin da kike ciki Nasreen. Don Allah ki buɗe wayarki. Ta tura mata tsaƙo kamar haka sannan ta koma ta kwanta. Washegari da safe ta shirya don ta je makaranta. Nasreen kamar ba za ta je makarantar ba, amma saboda gidan da ya yi mata ƙunci ya sanya ta shirya ta tafi. Bayan ta ka Raihan makaranta ta wuce school. Ganin ta ya sanya taso da sauri har tana tuntuɓe. "Wallahi juya sai dai bacci ɓarawo ya sace ni. Nasreen, ban yi miki kyauta don ki samu matsala da mijinki ba. Na so ki bani da ma na yi masa bayani, watakila da ya fahimci nufina." "Ba zai fahimce ki ba, ina son ki yi hakuri mu yanke alaƙarmu, saboda ya yi mini kashedi mai girma, daga ciki har da yanke igiyar aurenmu" Zare idanunta ta yi sai hawaye shar suka wanke mata fuska. "Har cikin raina na ke jin ki kamar 'yar'uwata, amma matuƙar zan zamo sanadin mutuwar auren ki zan yi nesa dake har abada, amma ki sani ya kamata ki gyara zaman auren ki da mijin, saboda mijinki bai yarda da ke ba, matukar da ace akwai yarda a tsakanin ku ba zai yi miki wannan dukan ba. Ina jiye miki gaba matuƙar ba ki gyara zaman aurenki ba, za ki yi dana sani a lokacin da ruwa ya ƙare wa ɗankada. Ina miki fatan alkhairi da zama mai ɗaurewa a rayuwar aurenki." Ta juya za ta tafi sai kawai ta fashe da kuka. Mamakin kukan da take yi ya kamata ƙwarai. Ita kanta kukan take so ta yi. Ji take kamar ta ɗora hannu aka ta yi ta ihu, tana fadawa mutane abin da ke damunta, watakila ta samu rangwame na raɗaɗin da zuciyarta take yi." Dama mai shirin kuka ne, aka jefe shi da kashin awaki, sai kawai ta fashe da kuka tare da rungume tana kuka. "Ina cikin wani hali na fi buƙatar na mutu da rayuwar da nake yi. Duniya ba ta maraba da ni, kullum cikin kurɓar ruwan baƙinciki nake a cikinta. Zaman aurena ya zaman mini tamkar zaman gidan yari ko ƙangin bauta. Mijina bai damu da ni ba." Ya duke ni ya zagi iyayena, sannan babu yarda a tsakanin mu abincin da xanci baƙinciki yake ya bani." "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Kuma kike zaune da shi Nasreen? Da kyanki da ilmin ki kika zauna baƙincikin ɗa namiji zai kashe ki? Dubi yadda kika rame kika koma duk adalilin ɗa namiji. Wallahi na tabbata kina ɗauke da ciwon depression." "Ya zan yi? Zaman aure a shi ne kawai gatana da 'ya'yana." "Ba ki da iyaye ne?" Murmushin mai ciwo take tana kallonta."Wannan shine dalilin da na gaya miki zaman aure a shi ne kawai gatana. Mahaifina da shi da babu a cikin rayuwata duk ɗaya." Zare idanunta ta yi tana mamakin abin da ta faɗa. A iya saninta iyaye sune ginshikin da kuma jigo ga 'ya'yansu. Matuƙar za ta furta haka kenan bai kasance bango abin jingina ba? "Na san za ki yi mamakin dalilin da ya sa ya na ce miki haka. Mahaifina shi ne dalilin da rayuwata ta koma haka. Sam bai damu da rayuwarmu ba. "Ina buƙatar na ji rayuwarki. Please mu je wani guri ki bani tarihin rayuwarki." Kama hannun ta ta yi suka shiga mota. "A halin da na ke ciki ba zan iya ba ki labarina ba, amma na yi alkawarin zan sanar da ke wani lokacin." Kallonta ta yi cikin tausaya jin abin da ta ce. Jakarta tana kallon Musaddik da yake son ya yi kuka. Hannu ta sanya ta ɗauke shi tana masa wasa. "Shi kenan, zan jira ki duk lokacin da kika shirya. In sha Allahu zan samu Faruk na yi masa bayani..." "Ba zai saurare ki ba." "Zan jaraba saboda ya kamata na fiddaki cikin zargin da yake miki." Ba tare da ta ce mata komai ba suka fara tafiya. A maimakon su tafi makaranta su tafi gida ta biya da ita shopping mall ta yi musu soyayya sosai. Mamaki ya kamata ganin yadda ba ta jin ƙyashin kashe mata kuɗi. Kamar yadda ta yi mata alkawari suka samu lokacinta ba ta labarinta. Mamaki sosai Marwana ta yi. Kallonta take cikin tsananin mamaki. "Nasreen rabuwa da Faruk shi ne alkhari, saboda dole watarana za ku rabu." "Bana sonsa na aure shi, amma ba ni da zaɓi saboda yarana. Bana son su samu tarbiyar wata. Uwa ita ce ginshiƙi ga rayuwar 'ya'yanta." "To saboda yara za ki kashe kanki? Kina da tabbacin in kin ƙi rabuwa da shi zai zauna da ke? Nasreen Allah ba ya ɗorawa bawansa abin da ba zai iya ba, dai sai mu ɗorawa kanmu. Akwai buƙatar ki natsu ki yi tunanin makomar rayuwarki da Faruk. Ki rabu da shi zan ɗauki nauyin karatunki, sannan in kin gama zan sanya Ya Damir ya ba ki aiki a campaninsa. Rayuwarki za ta yi kyau za ki taimaki iyayenki, amma a haka wallahi matuƙar ba ki samar da kanki mafita ba za ki yi dana sani." Sosai take kallonta yayin da maganganun ta duke yin tasiri a zuciyarta, amma kuma da ta suna a magantarta, dai ta ga zama da Faruk ya fi kan ta ɗora musu ɗawainiiyarta babu dangin iya ba na Baba." "Na gode da ƙaunar da kike mini. In Sha Allahu zan ci gaba da addu'a, domin duk wanda ya roƙi Allah zai kawo masa mafita. Zan ci gaba da zama da Faruk saboda yarana." "To shikenan tun da haka kika ce. Allah ya kaimu mu kammala karatun mu zan saya Yayana.ya ba ki aiki." Kama hannunta ta yi ta riƙe jin abin da ta ce."Haƙiƙa kin wuce matsayin ƙawa a gare ni sai dai 'yar'uwa. Ina fatan Ubangiji ya bar mu tare." "I will do anything for you Nasreen. Soyayyar ki Allah ya saka mini, saboda yadda na ke jin ki tamkar Hajiya ta haife ki." Daga nan gida suka wuce sai da ta kai ta har unguwarsu, sannan ta yi parking don ta sauka."Zan yi masa magana domin ba zan iya jure ganin yana dukanki ba, zan gwada watakila ya daina." Fita ta yi daga motar sanna ta leƙo ta windon motar tana kallonta ta ce,"To shikenan, tun da kin na ce sai na yi miki fatan alkhairi Allah ya sa ya daina, saboda Ni kaina zan so na samu 'yanci a gidan aurena." "Zan gwada kuma zai daina in sha Allahu." "Ina fatan haka sahibata." Ta ce tare da ɗaga mata hannu. Makaranta innsha Allahu yau zan yi posting safe da yamma a cigaba da surbubuɗo comments ❤️❤️❤️❤️💃💃💃💃 WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 11 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Kamar yadda ta yi mata alkawarin cewar za ta same shi. Har ofis ɗin shi ta je. Farouk zaune da waya a hannunsa yana chatting da amaryarsa to be. Tsaddaden murmshi yake saki fuskarsa ɗauke da annuri. Cikin nishaɗi yake sakin murmushi yana jujjuyawa kan kujerar da irin mai juyawa nan. Da ya ga chatting ɗin ba zai gamsar da shi ba, kiran wayar ya yi. Daga ɓangaren da ya kira, aka saki wani lallausar murmushi bayan ta yi sallama. Shi ma murmushin ya sakin mata, yana jin kamar ya zaro ta cikin wayar. "Ni fa gani na ke kamar da wasa sanya ranar da aka yi mana. Wallahi na zaƙu na shigo gidanka a matsayin mata, na nuna maka tsantsar kula, domin uwargidanka sai ta raina kanta. In ban da shashanci ace ta samu miji kamar ka, kuma ta kasa kula da kai?" "Hmmmmh! Ni kaɗai na san halin da na ke ciki, saboda matata shashasha ce. Wallahi halin da na ke ciki, da zan gaya miki sai kin tausaya mini. Sam ba ta iya gyara kanta ba, kuma ba ta san yadda ake tattashin miji ba." "Ba ka da matsala Hubbyna, domin ni zan share maka hawayen da matarka ta kasa share maka." "In har kika ɗauke mini damuwata, ni kuma zan zamo miki miji abin alfahari, saboda Nasreen sai ta raina kanta. Zan barta da yara ta yi ta fama da ɗawainiyarsu. Ni kuma na kula da ke sarauniyar zuciyata." "Duk abin da kake so ka samu babyna. Za ta sha kallo, don babu kalar soyayyar da ba zan yi maka ba, ita kuwa sai ta yi ta zama da gidadancinta." "Kar ki damu masoyiyata, zamu ci duniyar rayuwar aurenmu da tsinke." Wayar suka ci gaba da yi da musayar kalamai. Kalaman da ya kamata da wanda bai kamata ba, suka rinƙa faɗa wa junansu. Daga bisani suka yi sallama, bayan ta yi masa alkawarin turo masa da zafafan hotunan da ta ce masa ta ɗauka. Suna gama wayar ta tura masa da hotunan. Kallon hotunan yake yi yana murna da ya samu mace wayayyiya, ba irin matarsa da ba ta san komai ba sai gidandanci. Yana cikin kallon hotunan, Marwana ta ƙwanƙwasa ƙofar cikin fargaba, don ba ta san yadda za su kwashe ba. Da sauri ya amsa tare da ba da umurnin shigowa. Cikin siriyar sallama ta shigo cikin ofishin. Farouk ya miƙe bayan ya amsa sallamar da sauri yana kallonsa. Miyau ya haɗiya da ƙyar yana mata kallon ƙurulla. Idanu ya zuba mata kamar zai lasheta. A zuciyarsa tunani yake yi kamar ya taɓa ganinta. "Ba ka gane ni ba ko?" "Eh, wallahi amma kamar na taɓa ganinki." Ya ce mata cikin tashin murya yana mata wani kallo ƙasa-kasa. "Da ma na yi tunanin ba za ka gane ni ba, saboda sau ɗaya ka taba ganina." "Eh, gaskiya ba lailai na gane ki ba. Daga ina baiwar Allah? Saboda da kika shigo na ɗauka 'yan matan hurul ain ce ta faɗo duniya. Haushi da takaicin abin da ya faɗa suka sanya ta murmushin dole." To ba ita ba ce, domin ni mutum ce kamarka." Ta furta a gajarce tana gyara zamanta. "To ai dole mutum ya yi tunanin haka, saboda kyawu ki da zubin jikin ki." "Ƙawar matarka Nasreen ce." Ta furta masa tana kallon sa jin abin da ya ce. Lokaci guda fara'ar fuskarsa ta kau. Ƙara ɗauke fuska ya yi."Ok, mai ya kawo ki ofis ɗina?" Yadda ya yi maganar, ya sanya zuciyarta harzuƙa don sam ba ta da hakuri. Faruk kuwa, ji ya yi ransa ya ɓaci matuƙa, domin ya ɗauka tarkonsa ya kama kurciya. Ganin ya yi shiru, ya sa ya ta ƙara gyara zama ta ce,"Na zo kan kyautar da na yi wa matarka Nasreen?" "Ke dakata! Ya katse ta yana faɗin haka sannan ya ɗora da cewa,""Nasreen matata ce kuma ina da ikon na zaɓa rayuwar da na ke son ta yi..." "Ka yi haƙuri ba ni da nufin na yi kutse a cikin rayuwar ku, amma don Allah. Ka ji tsoron Allah, ka san cewa Allah yana ganin rayuwar da kuke yi kai da ita, kuma zaman aure ba zaman bauta ba ne. Wallahi ni na yi mata wannan kyautar, ba tare da ta roƙe ni ba, kuma a tunaninta farinciki za ka yi, saboda maƙiyinka ba zai taba..." "Ke! Fitar mini da ga ofis." Ya furta cikin tsananin fushi yana nuna mata hanya."Kin san Allah? In har kika ƙara gigin tako mini har ofis, sai ka wulaƙanta rayuwarki." "Ba ka isa ga wulaƙanta rayuwata ba, saboda bacin darajar da Ubangiji ya yi mini. Ba ka kuma san ni waye ba? In har Kasan Damir Hussain Gamawa ba za ka yi gigin nuna mini ɗan yatsa ba." Idanunsa ya zare lokaci guda ya ji zufa na keto masa. Tsananin mamaki ya kama shi tare da tunanin yadda aka yi Nasreen har ta ƙulla abota da ita. Haƙiƙa sanin ita ko wace ce, ya yi matuƙar razana shi sosai. "Wane ne a duniya bai san Damir ba yaro matashin mai tashen nera. In har kuwa ƙanwarsa ce za ta iya mata kyautar da ya fi haka. "Ina dole na raba ta da ita, domin shigowa wannan zuriyar a rayuwar Nasreen tamkar arziki ne ya shigo a cikin rayuwar su Nasreen gabakiɗaya." Ya furta yana share zufan da ya tsatso a goshinsa. "Ba na zo na yi maka barazana da arzikin Yayana bane, don ka daina wulaƙanta matarka. Na zo na gaya maka zaman aure ba wasa bane, ko shirin Film da za ka rinƙa tozarta matarka, kuma duk zaman da kuke yi a ranar gobe kiyama, sai Ubangiji ya tambaye duk wanda ya cuci wani a cikinku, saboda iyayen Nasreen talakawa ne hakan bai zama hujjar da za ka rinƙa wulakanta rayuwarta ba. Ina rokon ka da Allah ka ji tausayinta ka daina cutar da rayuwarta."Ta ƙarashe maganar tare da ficewa daga ofishin. Jaɓar ya zauna yana share zufan da take kwararo masa. Idanunsa ya zaro yana kallonta da ta rufe ƙofar da ƙarfi, har sai da ya rintse idanunsa zuciyarsa na bugu. Wani irin kishi da baƙin ciki, sosai ya ji na ganin mutanen da Allah ya haɗata da su. Miƙewa ya yi, da sauri ya fice daga ofishin zuciyarsa na bugu, saboda magungunta sai kuwwa suke masa a kansa. Nasreen na kwance a falo, tana kallon Raihan da take ta tsalle-tsalle a falon tana murmushi. Jin hon ɗin motarsa, ya sa ta tashi da sauri don ta buɗe masa get, tare da mamakin abin da ya dawo da shi da wuri. Bayan ta buɗe masa get, ya shigo ta kalle shi ganin yadda ya shigo babu fara'a. Gabanta ne ya buga sosai, saboda ta san hushin a kanta zai sauke. "Sannu da zuwa Abban Raihan." Ta ce masa tare da matsawa gaban motan, tana jiran ya fito don ta ɗauki kayan da ya siyo. Kallonta ya yi tare da jan tsuka ya shiga cikin falon. Sororo ta tsaya tana kalonsa har ya shige cikin gidan. Idanunta suka kawo ruwa, ganin ita da miji babu maganata arziki kullum cikin faɗa da hushi. Yana zaune ta yi sallama ta shigo hannu ta riƙe da leda. Ƙarasawa gabansa ta yi, ta ije tare da juyawa za ta shiga cikin ɗakinta. Farouk ya bita da idanunsa cikin damuwa. Tsoro da fargaban abin da zai faru, da rayuwar ta in har ta ji gaba da hurɗa da Marwana suke damunsa. "Ina ba zan bari ta ci gaba da hurɗa da waɗannan family ba, dole na raba su." Ya ce yana girgiza kansa. "Nasreen," Ya kira sunanta daidai lokacin da za ta shiga cikin ɗakinta. "Na'am," Ta amsa tare da dawowa gabansa ta tsaya. Mugun kallo ya watsa mata, sai kuma ya gyara zama ya ce,"Na raba ki da wannan yarinyar, amma saboda ba ni da daraja da ƙima a gurinki, sai kika je kika sanar mata da ina cutar ki ta zo ta ƙwayar miki 'yanci, tun da ga ta human right ko?" Hankalinta ya tashi matuƙa gaya, jin abin da ya faɗa."Idanunta suka suka yi raurau za ta yi kuka. Sam ba ta ji dadin maganar da ta yi masa ba, saboda ta san cewa da ma babu abin da maganar zai jawo mata, sai wata damuwar. "Wallahi ban aike ta ba kuma.." Ta kasa ƙarashe maganar tana in'ina. "Ok, ita ce ta ga ya dace ta zo ta yi mini fitsara da rashin kunya ko? Saboda kin ba ta labarin rayuwar aurenmu ko?" "Ka yi hakuri ni ban gaya mata..." "Dallah! Rufe mini ba ki shashashar banza." Ya ce mata tare da miƙewa cikin ɓacin rai yana kallonta. Ganin yana matsawa, ta fara ja da baya cikin tsanannin tsoro. "Abban Raihan, don Allah ka yi hakuri karka buge ni." Ta ce masa cikin raunin murya, tare da sa hannu ta kare fuskarta, don ta san zai iya wanka mata mari. Kunnenta ya kama ya riƙe da ƙarfi." Wallahi Nasreen, kin ji na rantse miki. In har ba ki rabu da wannan yarinyar ba, Allah sai na wulakanta rayuwarki. Bana son hurɗa da ita, in har kika ce za ki ci gaba da hurɗa ita zan yi mummunar saɓa miki, don haka ki sanar da ita kar ta ƙara zuwa mini ofis. Saboda iskanci. Ita tana yawo ta kasa samun mijin aure, ke Allah ya raba da yawo a titi ya baki miji sai ta hure miki kunni." "Ka yi hakuri zan gaya mata." Ta furta tare da zubowar wasu hawaye a ƙuncinta. Tsaki ya ja tare da ture ta, ya wuce yana bambami. Nasreen kunninta take murzawa, saboda ba ƙaramin riƙo ya yi musu ba. Maganganun da sun firgita ta, amma sai dai ba ta tunanin za ta iya sanar mata da kashedinsa, kuma ba za ta iya daina hurɗa da ita kamar yadda ya buƙata ba. Tsananin mamakin rashin tsoron Marwana ya kamata, da har ta iya zuwa har ofis ɗinsa ta yi masa kashedi. Ko da suka haɗu a makaranta washegari, ba ta yi mata magana ba. Bayan sun tashi daga lecture suna hanyar dawowa gida. Hira suke yi sosai Marwana tana gaya mata yadda ƴaƴanta yake matuƙar sonta. Da irin darun da take yi masa. Sosai take dariya tana kallonta cikin matsanancin farinciki. Tuni ta fahimci Marwana irin mutanen nan masu sanya mutum cikin farin ciki ko da ba su shirya ba, saboda rabon da ta yi irin dariyar nan ba za ta iya tuna ranar ba. Marwana dariya take yi sosai tana tuki, tana kallonta yadda take dariya cikin farinciki. Ƙara kallonta ta yi, sannan ta ci gaba da tuƙa motarta cikin kwanciyar hankali. A lokacin da suka isa inda za ta ije ta. Marwana ta kalleta ta ɗauko. "Ga shi ki je kici gaba da aiki da shi, domin a yadda na ga Faruk ya razana ba zai hana ki ba." "Haka kike tunani? Faruk sam ba shi da tsoro." "In har kina jin tsoronsa ba za ki taɓa ƙwatar 'yancinki ba. Rayuwar aure ba ƙangin bauta bane, domin ya kamata Faruk ya mutuntaki a matsayinki na matarsa kuma uwar 'ya'yansa." "Ba na son abin da zai kawo mini saɓani tsakanina da shi..." "Kar ki damu ki karɓa, kuma in sha Allahu, babu abin da zai faru." "Na gode da ƙaunar da kike mini Allah ya barku tare." "Tsakaninmu babu godiya domin kin zama 'yan uwa." Fita ta yi daga cikin motar, tana ɗaya mata hannu har ta ɓace daga gurin. "Haka Ubangiji yake ikonsa, sai ya haɗa ka da mutanen ƙwarai." Ta furta tana kallon hanyar da ta wuce. Faruk yana ta shirin aure ba tare da ya sanar da Nasrin ba. Har ana saura sati uku ba ta da labari. Ta fara zargin ko aure zai yi ganin yadda yake ta gyaran gidan. Hankalinta ya tashi matuƙar gaske. Tana don ta yi masa maganar, amma tana tsoron abin da zai gaya mata. Wata zuciyar ta shawarce ta da ta yi shiru ta zuba masa na mujiya, don ya fi mata alkhairi kan abin da zai gaya mata. Faruk kuwa har ya kai kuɗin sadaki, da yake bazawarace ba a wani sanya ranar da tsayi ba. Sosai suke shirye-shirye a tsakaninsu. Har ana saura kwana biyar bai sanar mata da maganar aurenta ba. Maman Muwaddat ce ta ji zancen bikinsa, wanda ya tayar mata da hankali. Sosai tausayinta ya kamata, duba ga halin da take ciki na zaman aurensa, ina ga kuma ya ƙaro mata kishiya. Ita ba auren ne ma ya fi tayar mata da hankali ba, wacce zai aura. Rashida bayerabiya ce amma ta zauna a cikin Hausawa. Mace ce jarabbiya sam ba ta da hakuri. Ko shi kansa bai san ruwan dafa kan zai ɗauko ba. Sannan ga shi ta girme wa Nasreen don ba sa'arta bace. Ko da ace Faruk zai ba ta shekarun bai wuce ɗaya ko su zo tsara ba. Idanunta a buɗe suke saboda mace ce wayyaya, wacce take cuɗanya da maza, don har sai da abinci a bakin titi ta yi. Daga baya ne da ta auri mijinta, sai da ta mayar da shi matsiyaci, sannan tsuka rabu. Bayan sun rabu ta kafa zawarci. Maza sosai take tatsa, don ko Faruk da fari ba ta yi ninyar auren sa ba. A cewar ta maza mugayen ne mayaudara masu daɗin baki. Mahaifiyarta tasha wuya sosai a gurin mahaifinsu, kafin Allah ya ɗauki kwananta. Su kansu ba su samu kyakkyawar tarbiyya da kula a gurinsu ba. Wannan dalilin ya sa ta ɗauki aniyar tsakaninta da su babu sausauci. Da fari ta yi ninyar shanye ƙwallon mangaro ta huta da ƙuda, amma kuma sai ta ga Faruk ya yi mata. Yana da zubin halitta mai kyau, sannan ga shi ɗan gayu, mai tashe da nera da ƙuruciya. Abin da ya ƙara jan hankalinta yadda yake kushe matarsa da cewar ba ta ba shi kula. Wannan dalilin ya sanya take son aurensa don ta more ƙuruciyarsa, domin har zuwa gurin malaminta ta yi don a karkato mata da hankalinsa. Abu ɗaya ta fara fuskanta game da shi wato maƙo. Duk yadda yake iƙirarin yana sonta, amma ba ya sakin mata kuɗi sosai. A ganinta hidimar da yake yi na bikinsu ya yi mata kaɗan, amma sai ta share ba tare da ta nuna masa komai ba, burinta kawai ta shigo cikin gidansa, yadda za ta samu damar juya shi, ya zamo mata janitalau. A na saura kwana biyu, Maman Muwadda ta shirya sanar mata da bikin, ganin ranar da ta shiga cikin gidan ba ta yi mata maganar ba. A ranar da ta je, sai ta tsokane ta don ji ko ta san da maganar, amma sai ta yi murmushin yaƙe ta ce,"Wallahi sai gyaran gida yake yi. Wataƙila aure zai yi, don ya sha gaya mini ba zai zauna da ni kaɗai ba." Jin hakan ya sanya, a wancan ranar ta kama bakinta ta tsuke, don ba za a ji mutuwar Sarki a bakinta ba, amma daga baya sai ta ga in har ta bari aka yi bikin, kamar ta cuce ta ne. Bayan ta shiga cikin gidan ta zauna. Nasreen da take zaune a falon tana yi wa Raihan tsifa. Ganin ta ya sanya ta miƙe tana murmushi. "Ban ji ƙwankwasa ƙofar ki ba?" "A buɗe na ga gidan har na yi mamaki." "Ikon Allah! Kuma ban san abuɗe yake ba, watakila da na fita siyo ashana na manta na kulle. Kin ga da Abban Rainah ya dawo dai ya zamar mini abin faɗa." "To ki rinƙa kula." Ta ce mata bayan ta zauna. "Raihan, tsifa ake yi?" Maman Muwadda ta yi mata tambayar tana shafa kanta. "Wallahi kuwa, kin san gobe Monday shi ne na ke son muje kitso." "Haka ne, ni ma can na barsu suna tsifa." Sun ɗan yi shiru, babu mai magana a tsakaninsu. Nasreen ta fahimci kamar akwai maganar da za ta gaya mata. Maman Muwadda ta gyara zama, ta buɗe baki kenan ta ji ƙarar motar Faruk yana hon. Da sauri ta mike jikinta na zikiri. Ganin haka ya sa ita ma ta miƙe."Dama magana na ke so mu yi kuma ga shi ya dawo." "Ok, in ya tafi zan shigo." "A'a ki aiko Raihan ta kira ni, don na fi son mu yi ta a nan, zamu fi samun natsuwa." Gabanta ne ya faɗi jin abin da ta ce."Lafiya Maman Muwaddat, ko laifi na yi miki?" "Lafiya lau, kuma babu laifin da kika yi mini. Ai tsakanin mu babu wannan, domin da ace kin yi mini laifi zan sanar miki, saboda kamar 'yar'uwa na ɗauke ki." Tunanin abin da za ta gaya mata yi, amma sai ta kasa fahimta."Ok, to shikenan, zan aiko ta gaya miki. Bari na je na buɗe kafin ya zama rigima." A tare suka fito. Maman Muwaddat ta fice ita kuma ta buɗe masa get. Kallo ya bi ta da shi har ta ɓule, sannan ya mai da idanunsa kan Nasreen da take tsaye tana jiran ya shigo. Harararta ya yi, sai kuma ya shigo da motar. "Sannu da zuwa." Ta ce masa bayan ta buɗe masa motar. "Nasreen, ba na hana ki shiga maƙota kuma suna na hana su shigowa ba, don kin san bana son gulma da munafunci?. "Ka yi hakuri Maman Muwaddat ce." "Ita ɗin fa tun da ba ciki ɗaya kuka fito ba." Ya ƙarashe maganar tare da fita. Gaban motar ta shiga, ta kwashi kayan da ya shigo da ita. Gabanta ne ya faɗi ganin sabbabin kaya masu tsananin kyau a bayan motarsa. Hannu ta ɗauko tana kallon kayan, duk da cewar ta san yana kashe wa kansa kuɗi, amma ɗinkin da ta ga ya yi sabbabi, sai da suka sanya kanta ya juya, saboda kayan sun yi kala bakwai. Jikinta babu ƙarfi ta shigo da su. Yana zaune a falo ta shigo da kayan. Ɗakinta ta kai ta dawo ta wuce da cefanen da ya yi musu. Ƙaramin tsuka ya ja ya shiga cikin ɗakin. Bayan ta kammmala girkin ta ɗauka ta kai masa. Tana ƙoƙarin shiga cikin ɗauki da ta ji muryarsa yana waya. Da sauri ta fasa murɗa ƙofar ta laɓe don ta tabbatar da zargin ta. Dariya mai sauti ta ji ya yi, sannan ya faɗi wata magana wacce sai da ta ji kishinsa, saboda batsa da ta ji yana yi a cikin wayar. Kalamansa na ƙarshe, ya sanya ta ji kamar za ta faɗi ta kuma fara tabbatar da zargin ta. "Sai ta shigo gidansa ya kwanta da ita zai tabbatar da ya auri mace? Faruk aure zai ƙara ba tare da ya sanar mini ba?" Ta yi wa kanta tambayar cikin tashin hankali, yayin da idanunta suka ciko. "Innalillahi na shiga uku!" Ta ce bayan ta ije tiren abincin kanta na juyawa. Da ƙyar ta samu ta daidaita kanta ta shiga ciki, tunawa da ta yi dama ya sha faɗan, sai ya ƙara aure kuma ga shi har sun ɗauki shekaru bai ƙara auren ba. Ta gaya wa zuciyarta hakan ne don kawai ta yaudareta ta samu kwanciyar hankali, amma cikin zuciyarta tana ƙarfafa mata aure zai ƙara. Yana wayar ta yi sallama ta shigo. Bai fasa wayar ba, sai ƙasa da murya da ya yi. Ganin haka ta ije masa abincin ta fice cikin tsananin damuwa. Satan kallonsa ta yi da zata fita. Tana matuƙar son mijinta domin ta ko' ina Faruk ya kai namijin da mace za ta damu da shi. Halinsa ne kawai bai yi ba, na rashin ɗaukar mace da daraja. Ko da yake ba za ta ce baya ɗaukar mace da daraja ba, ita ce kawai ba ya daraja ta, duba ga yadda yake waya da 'yan mata yana kashe murya.Ɗaki ta koma ta zauna sai kawai ta tsinci fashewa da kuka. Makaranta innsha Allahu yau zan yi posting safe da yamma a cigaba da surbubuɗo comments ❤️❤️❤️❤️💃💃💃💃 WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 12 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Sosai ta yi kuka tana baƙincikin rayuwar da suke yi da Faruk. Tunani take yi wane irin zama za su yi, da matar da zai auro don ta san ya riga ya gama zubar mata da ƙima a gurinta. Bayan fitarsa ta aiki Raihan ta kira Maman Muwaddat. Ba ta jima ba suka dawo da Raihan. A yadda ta ganta a firgice, ta ɗauka ya gaya mata. Kallonta ta yi cikin tausaya. "Ina jinki kin ce za mu yi wata magana, kuma na lura ke kanki ba kyau son faɗin maganar." Tausayi ta bata sosai tana mamakin mugun halin Faruk. Haba ai zalunci ne ace zaka yi wa mace kishiya ka ƙi sanar da ita. "Nasreen, hakuri zan ba ki a rayuwarki. Na san cewa kina cikin wani hali na zaman ki da mijinki, amma yanzu dole ƙi ƙara saboda..." "Saboda zai ƙara aure ko?" Ta furta tambayar hawaye yana shatata a fuskarta. Dafata ta yi ganin yadda ta rikice."Ya gaya miki ne?" "A'a bai gaya mini ba, ji na yi yana waya cewar yanzu zai san ya auri mace. Maman Muwaddat mai na yi wa Faruk, wanda ya zaɓi ya shigo cikin rayuwata ya cutar da ni? Don zai yi aure sai ya sanar da amaryarsa ba ni da ƙima a idanunsa. Da wane ido yake so ta kalle ni. Hakan da yake yi ya ba ta ƙofar da zata ɗauke ni mara daraja a idanunsa. In har ba zai yi mini kayan faɗar kishiya ba, na cancanta ya sanar da ni ko da ace ba zai rarrashe ni ba." Kuka take yi sosai tana ji tamkar zuciyarta za ta fito. "Ki yi hakuri Nasreen, haka WASU MAZAN suke yi. Ba ke kaɗai aka yi wa hakan ba, domin mata da yawa mazajensu na ƙara aure ba tare da sun gaya musu ba, kuma in suka yi haƙuri sai kiga komai ya wuce. Ki ɗauki kishiyar da zuciya ɗaya kuma ki riƙe Allah." Sosai take yin kuka tana jin bai yi mata adalci ba. Hawaye ta share tana kallonta."Na gode da sanar mini da kika yi, kuma na gode da shawarki. In sha Allahu zan haƙura na barwa Allah komai." "Yauwa dama na san za ki jure ki ci gaba da hakuri Allah yana tare dake." Ta ce mata cikin tausayawa. Ta daɗe a gidan tana ba ta baki har sai da ta ɗan ji dama, sannan ta yi mata sama ta tafi. Tana fita ta ƙara sakin kuka ta shige cikin ɗakinta. Ƙoƙari kawai ta yi ta daure ta nuna mata ta haƙura, amma Allah kaɗai ya san zafin da take ciki. Tayi kuka sosai har sai da ta ji hawayen sun daina zuba, sannan ta haƙura ta ɗauki maganin damuwar ta ta fara karantawa. Sai da ta ji ɗan dama ta shiga kicin ta ɗora abinci. Tana tsaye a kicin ɗin tun da ta ɗora ruwa ta kasa yin komai. Zuciyarta take tafasa da wani irin abu na kishin mai kama da ƙwallo ya taso mata kuma ya ƙi wucewa. Ita kanta ba ta san tana mugun sonsa ba sai yanzu. Tana tsaye har ruwan ya tafasa. "Umma ruwan yana tausa." Ta ji muryar Raihan da take tsaye tana rike da hannunta. A maimakon ta wanke shinkafar ta zuba, sai kawai ta ɗauki ruwan zafin ta zuba a cikin ɗanyar shinkafar, ta sanya hannu don ta wanke. Tsananin zafin da ta ji ya farga da ita abin da ta yi. Da sauri ta cire hannunta tare da sanya ƙara tana salati. Hannu ta da ya tashi ya yi ja take dubawa hawaye yana zuba a ƙuncinta. "Umma, kin ƙone ne?" Raihan ta ce mata tana kallon hannunta. Tsintar kanta ta yi da rungumeta tana kuka sosai da kuma ƙarfi. Tuna shinkafar za ta iya lalacewa ya sa ya ta yi saurin sakinta ta mayar da shinkafar da ruwan kan wuta. Bisa abin da ya faru kan dole ta tafasa sannan ta zubar da ruwan ta girka abinci. Hawaye kawai take sharewa. Cikin dare da ta kwanta ta kasa bacci. Har ya dawo idanunta biyu. Saboda haushinsa da take ji bayan ta buɗe masa get. Wucewa ɗakinta ta yi, ba tare da ta kalle shi ba, saboda mugun haushinsa take ji. Raka ta da idanu ya yi ganin yadda take. "Ko an gaya mata ne?" Ya yi wa kansa tambayar cikin rashin damuwa. Tsaki ya yi tare da ɗaga kafaɗunsa alamun bai shafe shi ba. Shiga cikin ɗakinsa ya yi, bayan ya yi wanka ta fito da naman da siyo, ya ci ya ƙoshi ya kira da lemunsa ya kwanta. Rintse idanunsa ya yi yana ta ayyana surar Rashida da fanshe kuɗinsa da zai yi. Har ana ɗaurin aure Faruk bai sanar mata ba. A ranar ta ga ya yi wanka ya ɗauki gayu ya fice daga gidan. Tana jin mutane suna kiransa a waya. Bayan ya fita ta fashe da kuka sosai. Tabbas ta tabbata yau za a ɗaura masa aure, don ko bai gaya mata ba, wankar da ya yi ya isa ta fahimci aure zai ƙara. Tana zaune a gurin tun da ya fita ta kasa motsawa. Kuka take yi sosai tana tausayin kanta, ganin tana rayuwa da mutumin da bai san darajar ta ba. Tunanin zaman da za su yi da amaryar take yi. Saboda bai sanar mata ba ya sanya babu wacce ta gayyata, don ko 'yan gidansu ba ta sanar musu ba. Kamar yadda bai gaya mata ba, duk wanda ya tambayeta sai ta ce ba ta da labari. Ita ma amarya kawai ta gani. Duk yadda take da Ya Ahmad ta kasa da ar masa, domin ta san babu abin da zai iya mata sai dai ta tayar masa da hankali. Bayan fitarsa babu jimawa aka ƙwanƙwasa get. Sai da ta wanke fuskarta, sannan ta je ta buɗe get ɗin. Ganin Yarsa Asiya ce ya sanya ta yi murmushin yaƙe."Sannu da zuwa." Ta ce mata ba tare da sun haɗa idanun ba. Turus ta yi ganin yadda idanunta suka kumbura."Nasreen lafiya? Ko kishin ne ya sanya kika koma haka?" Ta ce mata tana kallon harabar gidan ganin babu alamun ana taro. Kasa magana ta yi saboda zubowar hawaye. Matsawa ta yi ta ba ta hanya. Ganin haka ya sanya ta tura ƙofar ta shiga ciki. "Ke Nasreen, lafiya ban ga ana taro ba? Ko ba yau bane ɗaurin auren?" Tambayar da ta yi mata, ya sanya ya ji kamar ta kwasa mata mari. Ashe ta san da bikin ba ta gaya mata ba, in shi ya ƙi sanar da ita, yadda ta ɗauke ta 'yar'uwa ai ya kamata ta sanar mata. Dangin miji kenan. "Ni ma ban san zai ƙara aure ba, hasashen haka kawai na ke yi, don bai gaya mini ba." Ta ce tana hawaye. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Amma Faruk ya cika tantiri. Wannan wane irin rashin dalci ne? Wallahi tun da ya je mini da maganar ƙarin aure nan, na yi masa tatas da na ga ba zan iya hana shi ba, tun da addini ya ba shi dama. Sai na ja masa kunne kan ya yi adalci ya sanar miki kuma ya yi miki kayan faɗar kishiya." "Hmmmmh!" Kawai ta ce tana share hawaye. Ganin ba ta ce komai ba sai ta kalle ta ta ce,"Nufin shi haka zai ƙara auren ba tare da kin yi taro ba?" Ba ta ce mata komai ba don bata dan me za ta ce mata ba. "Bar ni dashi bari na kira sa ɗan ƙwal uba." Ta ce cikin takaici. Ciki suka shiga ta zauna, daidai lokacin da kiran wayar ya shiga. Kira har sau bakwai ta yi masa ba a ɗaya ba. Tana zaune cikin takaici tana jin kamar ta je ta duke shi, sai ga shi ya kira ta."Hello Anty Asiya, an ɗaura na zama mijin Rashida." Ya ce mata cikin tsananin farin ciki. Maganar da ya yi ta ji kamar ya soka mata allura."Innnali wa inna ilahir raju'un!" Ta furta sai hawaye shar! Da sauri ta share don karta gani, amma ta makara domin idanunta na kanta. Tausayi da kunyar abin da ya aikata, ya sa ta ta lailayo ashra ta yi masa."Ashe ba ka da kirki Faruk? Kan me za ka ƙara aure ba tare da ka sanar da uwargidanka ba?" "Haba Anty Asiya, saboda wannan kike so ki ɓata mini ranar farinciki? Ina gaya mata mai za ta yi? Na san dai iyayenta talakawa ne ba su da abin da za su yi mata. Ballantana na sa ran za a kawo mata wani abu. Zuwa kawai za su yi su ɓata mini gida su cinye abinci." Takaici da haushi da ya sanya ta ce,"Uwarka na ce Faruk! Wai mai yasa ba ka da mutunci ne?" Ta ce masa cikin tsananin kunyar abin da ya faɗa. "Kin ga Anty ina cikin taro zan kira ki." Ya ce yana ƙoƙarin kashe wayar. Kafin ta yi magana ya datse wayar. Dafa Nasreen ta yi da take kuka sosai, jin abin da ya ce."Ki yi haƙuri kin ji wallahi dole ya dawo, sai ya yi miki kayan faɗar kishiya kuma sai ya san bai kyauta ba." Ta ce tana mamakinsa. "Ki barshi kawai, fatana Allah yasa ya zaɓo wacce za mu zauna lafiya da ita." "In sha Allahu ina fatan haka nima, kuma ki ci gaba da haƙuri. Kin san dole in aka ƙara wa mace kishiya ta yi haƙuri." "To," Ta ce tana share hawaye. Zama ta yi tana ta bata baki har ta ji kishin ya ragu. Wayarta ta ɗauka ta kira mahaifiyarsa ta zayyane mata komai. Sosai ranta ya ɓace ta ce,"Ki bar ni da shi, wallahi dole ya ɗaya tarewar nan, har sai ya yi mata kayan faɗan kishiya, kuma ya ba ta abin da zata dafa ta tara mutane. Wannan wane irin rashin mutunci ne? Ga duka ga mari ga tsinka haka. Ko da cinya ya barta suka yi taro ai za ta ji daɗi." "Faruk ba ya kyautawa Mama." Ta ce mata jin abin da ta ce. "Ki ƙyale shi zan kira shi. Mika mata wayar." Ba musu ta miƙa mata ita kuma ta karɓa. Sosai ta ba ta baki sannan ta yi mata alkawarin ta sa ya shi dole ya yi. Bayan an gama ɗaurin auren aka je dinner. Daga dinner a mota sai da ya ji kamar zai karɓi haƙkinsa, saboda yadda ta rinƙa masa. Shi kan yasan ya zu ya yi aure, tun kafin ta shigo cikin gidansa. Da ƙyar suka rabu bayan ya fara more sadakinsa. A hanya Mama ta kira shi. Da ya ɗaga ya gaishe ta. Tatas ta yi masa sannan ta kafa masa cewar dole a ɗaga tarewar har sai ya yi mata. Ransa ya ɓaci sosai jin abin da tace. A ransa ya sanya hakan ba zai faru ba, wai gurguwa da auren nesa. Yadda ya ƙosa a kawo ta ya more sadakinsa. Don shi kadai ya san zumuɗin da yake yi. Sauri yake yi ya koma don sun ce za su kawo kaya. Cikin ɓacin rai ya shiga cikin gidan. Bai samu ya yi mata rashin mutunci ba, saboda masu kawo kaya da suka iso. Nasreen na ganin kayan ta tabbatar da auren na sa. Ɗaki ta koma har suka gama jera kayan a ɗayan ɗakin da ya gyara. Da yake gidan four bedrooms ne. Nata sai na yara da kuma na sa. Ɗaya tun da ya fara burin aure ya rufe shi. Ya zama za su rinƙa sharing falo da kicin. Bayan an gama jera kayan ya shigo cikin ɗakin. Tana zaune da carbi a hannunta tana ja. Ɗayan hannun kuma tsaƙon da Marwana ta tura mata na assignment da ta yi take dubawa, duk da cewar hankalinta ba shi sosai a kan wayar. Ganin ya shigo ya sanya ta miƙe."Saboda na aure ki ba zan yi aure ba, ko kuma ke kike aure na da dole sai na gaya miki zan ƙara aure?" Ya yi mata tambayar yana zare idanunsa. Miƙewa ta yi cikin tsoro tana kallonsa sai kuma hawaye."Abban Raihan, ni fa matarka ce ina da haƙƙi a kanka, ya kamata ka gaya mini." "Ashe da sauƙi tun da matata kike ikona. Na ɗauka uwata za ki ce?" Ya yi mata tambayar yana zare mata idanu. Jin abin da ya ce ya sanya ta share hawayenta tare da zubowar wasu."Look Nasreen, kin san yanzu ba ɗaya bane da da, saboda ina da wata matar, ba zan jure rashin mutunci ba, don ban ga amfanin ki a gidannan ba, sai dai ki ci ki yi kashi ki tara mini yara?" Jin bin da ya ce ta kalle shi,"To mene auren Faruk? Ai samun zuriya shi ne albarkar aure." "Ni ba wannan bane albarkar aure. Na huta da matata ta yi mini biyayya, kuma ta so duk abin da nake so." Kallonsa kawai ta yi cikin rashin hayyaci ba tare da ta ce masa komai. Ganin haka ya sa shi harararta. "Kin san Allah ba zan ba ki ko ƙwandala ki tara mini gayyar talauci ba, kin hana na tare da amarya saboda baƙin kishinki. Hotel za mu je don yau babu abin da zai hana ban more sadakina ba, kuma kika ƙara sanar wa Mama waje za ki yi sai ki je ki yi zawarci, na ga uban da zai ƙara aurenki, a yadda kika yangwaɗe babu mamora a jikin ki, dubi fa yadda kika dawo komai ya shafe, gabakiɗaya kin haɗe da ko'ina, kuma kike kishin kar na auri wata? "Kallonsa ta yi cikin tsananin mamakin abin da ya furta."A haka ka aure ni Faruk? Lokacin da ka aure ni a haka na ke? Kai da kanka ka sha yabon surata, ita ma kanta wacce za ka auri za ta dawo haka matuƙar za ta yi ciki ta haihu, kuma ka kasa ba ta kulawar da ya kama." Kallonta yake yi kamar wata mahaukaciya."Sai aka ce miki mahaukaci ne ni da zan barta ta haihu? To ki jira ki zuba idanu ki ga yadda za mu more rayuwa, saboda ban aure ta ba don ta haihu." "In har tana da hankali ba za ta yarda da hakan ba, saboda babu macen da za ta yarda da wannan. So kake ta kare rayuwar ta ba tare da ta haihu ba? Akwai sufa da yanayin rayuwar da mutum yake shiga, dole yaranka kawai za su taimaka maka." "Ki bar ni in na shiga lokacin sai ki zo ki gaya mini haka. Ina da kuɗi da kyau sam ba zan tagayyara ba." "Ba komai kuɗi suke yi ba kuka dukkaninsu masu wucewa ne." Ta ce masa tana kallon sa. Tsaki ya ja yana harararta."Na dai gaya miki sai ki san yadda za ki zauna a cikin gidan nan. Don wallahi in har kika yi gigin da na sake ki, ba za ki taɓa samun miji irin na." Kuka kawai take yi ta kasa furta kalami. Ganin haka ya saki tsaki ya fice tare da buga ƙofar. Rintse idanunta ta yi cikin tsananin bakin ciki. Ta ɗauka wasa yake mata, amma sai ta ga ya kwashi tarkacen da zai kwana da shi ya fice. Kuka take yi tun tana yi har ta ji idanunta sun ƙafe. Ita kanta ba ta san tana da kishi haka ba. Bayan kiran sallar Isha sai ga kiran Ahmad. Tana ganin kiran ta ki wasu zafafan hawaye sun wanke mata fuska. Da ƙyar ta samu ta tsayar da hawayen ta yi sallama "Hello Nasreen, da gaske Faruk ya ƙara aure?" Tambayar da ya yi mata ya sanya ta fashe da kuka. Jin kukan ya sanya shi yarda da jita-jitar da ya ji. "Haba Nasreen amma kika kasa sanar damu? Wata ƙawar Mama ta sanar mata, don ta san matar da ya aura." "Ni ma bai gaya mini ba." Ta ce masa cikin muryar kuka. Jin abin da ya ce sai tausayinta ta ƙamashi. Daga ji ya san tasha kuka. Ƙoƙarin kwantar mata da hankali ya shiga yi. Sai da ya ji ta ɗan saki sannan ya ce,"Wayata babu caji bari na kai shagon Ado mai caji, zan kira ki in na karɓo." "To Yaya, ka gaida su Mama." "In Sha Allahu." Ya ce tare da kashe wayar yana mamakinsa. Mama da ke gefensa tana jin abin da take faɗi. Ganin ya kashe wayar ya sanya ta saki salati. "Kai amma Faruk, ba shi da kirki. Ace za ka ƙara wa mace kishiya, amma ka kasa sanar mata. Haba wannan zaluncin ya yi yawa. Ko taro ta yi ai ta rage raɗaɗi." Ina zai gaya mata tun da ya raina ƙuranmu? Ya san bamu da abin da za mu kawo mata, da ya san za a kawo mata abin duniya zai gaya mata." Ya karashe maganar cikin ɓacin rai yana tausayin ta. "Wallahi Baba ya cuci Nasreen." Ya ƙara cewa. Mama dai shiru ta yi ɗin maganar ma babu amfani sai ɓacin rai. Tana kwance tana juyi tamkar kasa. Wani irin tsananin kishinsa take ji. Miƙewa ta yi don ta ɗauro alwala ta yi sallah. Don in ba haka ta yi ba wataƙila kafin wayewar gari zuciyarta ta buga. "Ashe haka mata suke ji in aka ƙara musu kishiya?" Ta ce a ranta tana share hawaye. A bayi wanka ta yi saboda yadda take jin zafi yana keto mata. Tana ƙoƙarin alwala sai ta ji kamar zubowar abu a ƙasanta. Tsoro ta ji din dama tana tunanin ciki ne da ita. Kusan wata uku ba ta ga al'adarta ba. Duk da cewar tun haihuwar Musaddik sai ta yi wata huɗu ba ta gani ba. Wannan dalilin ya sanya ta shiga kokwanto ko ciki ne da ita. Ganin jini ne gabanta ya faɗi. Ta rintse idanunta daidai lokacin da cikinta ya yi wani irin murɗawa. "Wayyo Allah!" Ta ce cikin tsananin ruɗani. Jin yadda mararta ta ƙulle. Fasa alwalar ta yi ta koma ta kwanta, amma sai bacci ya gagara. Tana kwance tana juyi tana kiran sunan Allah. Ko jirgawa ta ɗauki wayarta ta kasa. Salatin ta ya farkar da Raihan. "Umma, ba ki da lafiya ne?" Ya ce mata tana kallonta. "Eh Raihan, ɗauko mini wayata na kira Ya Ahmad, ya zo ya kai kai ni asibiti." "To," ta ce tare da miƙewa tana tangaɗi ta ɗauko mata wayar inda ta nuna mata. "Umma, in je in ta so Abba?" Ta ce mata ganin yadda take masoso. "Abba bai kwana gida ba." "To ki kira shi." "Raihan ba zai zo ba, yau ya samu wacce ta fini." Ta faɗi hakan tana hawaye. Ba ta fahimci komai ba sai ta yi shiru tana kallonta. Yau pages ɗin masu kishiya ne a fito masu kishiya a gaya mana abin da aka ji da mijinki zai ƙara aure. Akwai wacce mijinta ya ɓoye mata kamar Nasreen? In akwai wane mataki ta ɗauka? Ga Nasreen duk da ba ta zama da shi na daɗi, amma zafin kishi ya sanya ta yi ɓari. Tana ta kiran ango yana can gurin amarya ya ji sabon guri🙈🙈🙈💃💃 to ko zai zo ya taimaka mata ko kuma amarcinsa zai sha da amaryarsa Rashida? Faruk sau a sausauta don ma bazawara ce 😆😆 makar ta duk da na yi da tsayi in kuka tashi kaina zan iya antayo muku next page don mu ji yadda za ta kaya. Aci gaba da comments ina murmushi ina shan ganta ina karantawa. Na gode muku sosai Allah ya bar ƙauna. WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 13 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Raihan ba zai zo ba, yau ya samu wacce ta fini." Ta faɗi hakan tana hawaye. Ba ta fahimci komai ba sai ta yi shiru tana kallonta. Da ta kira wayar sai ta ji a kashe. Tunawa da ta yi ya ce ba shi da caji, ya sanya ta yi tunanin ƙila bai karɓa ba. "Wa zan kira?" Ta yi wa kanta tambayar cikin tsananin tashin hankali, domin har ta fara fita hayyacinta. Maman Muwaddat ta faɗo mata. Da sauri ta nemi layinta, amma cikin rashin sa'a wayar a kashe. Juyi take tana salati. Ƙoƙarin miƙewa ta yi don ta je ta ƙwankwansa musu, amma da sauri ta kwanta jin ba za ta iya tafiya ba. Kwanciya ta yi kan gadon ta ce,"Wash Allah zan mutu!" Kuka take yi sosai ta sadaƙar mutuwa za ta yi. Wayar ta ƙara janyowa ta nemi layinsa don ganin za ta mutu. A lokacin yana kwance ya rungume amarya Rashida da take ji kamar za ta mayar da shi ciki, musamman ganin kalar soyayyar da yake nuna mata. Kiran ya shigo daidai lokacin da ya ƙara rungumota ya haɗa bakinsu. Jin su suke a wata duniyar. Haƙiƙa ji yake yau ya samu matar da yake so, wacce za ta yi masa duk abin da yake muradi a makwanci. Ganin yadda ta cire kunya take nuna masa kalar basirar ta, wacce ya yi farincikin da samun mace mai irin basirar. Sun yi nisa su shiga wata duniyar. Ana ta durzar amarci ba tare da ya kula da kiran Nasreen da yake ta shigowa ba. Ko da hankalinsu ya dawo jikinsu, Rashida ba ta barshi ya rintsa ba domin so take ta nuna masa ya samu kalar macen da take fata, don a daren cinye shi ne kawai ba ta yi ba. Jin sa yake cikin aminci ya rinƙa takaicin kansa da ya zauna ya auri mace Bahaushiya, wacce ba ta san komai ba, sai ta ci ta tara masa yara. Ai matan yare sune ka aure su zaka more aure, babu kunya a baka kalar rayuwar da kake so. Ganin ba zai ɗauka ba, ya sanya ta daina kiran tare da takaicin kiransa. Kishi da tunanin halin da suke ciki yanzu ya ƙara rikita jikinta. Ganin za ta mutu ya sanya ta nemi layin Marwana. Marwana dake zaune a falon Damir tana kallo. Little Marwana kwance a cinyarsa tana shafa kanta. Tun da cikin ya girma sai Hajiya ta sanya ta dawo gidan. Sosai cikin ya girma ga kumbura da take yi. Likita ya sanar da su ba za ta iya haihuwa ba, dole sai dai a cire cikin. Ɗin haka ya shawarci Damir da zarar cikin ya shiga wata tara za a yi mata C.A. A yanzu haka shirye-shirye tafiya suke yi zuwa waje, don har ya yi musu viser lokaci kawai yake jira. Wayarta a hannunta bayan sun gama waya da masoyinta. Har ta ije sai kuma ta ɗauka tana kallon hotunan da ya turo mata. Ganin kiran Nasreen ya tsorata. Kallon agogo ta yi tana mamakin dalilin da ya sanya ta kira ta. Tunawa da ta kirata da rana, amma ba ta ɗaga ba, ya sanya ta danna kiran tana dariya. "Hello Sahibata.."Maganar ta tsaya sakamakon ji da ta yi tana numfashi da ƙarfi ta ce,"Wash Allah! Marwana zan mutu cikina, don Allah ki sa ya direbana gidanku ya zo ya kaini asibiti. Na kira wayar ya Ahmad a kashe. Ɓari na yi." Ta ƙarshe maganar tare da sakin gigitaccen ƙarar da ya tayar da hankalinta. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Nasreen ɓari ina Faruk?" "Ki taimaka mini Faruk ba ya nan." Ta ce tare da kashe wayar. Ruɗewa ta yi ta rasa yadda za ta yi. Har ta fita don ta sanar da direba ya fito su je, amma kuma sai ta fasa ta koma ciki. Ɗakin Damir ta shiga ƙwankwansawa cikin tashin hankali tana kiransa. Damir da yake kwace rungume da matarsa yana tunanin halin da take ciki. Fatansa Ubangiji ya sauke ta lafiya, don ba zai iya rayuwa babu ita ba. Tun lokacin da ya haɗu da ita yake jin matuƙar ƙaunarta, ko lokacin da ya san cewar ita sikila ce, bai ji sonta ya ragu ba, sai dai tausayi. Soyayyarta daga Allah ne. Fatansa ta yi tsawon rayuwa, domin ba zai iya auren wata mace ba in har babu ita, ji yake da ta mutu gara ace shi ya rigata. Kullum tunani yake ina ma da za a ba shi damar ya zaɓi ciwon ya dawo jikinsa. Kai bakinsa ya yi ya sumbaci goshinta yana shafa kanta. Ƙwankwasa ƙofa da kiran da Marwana take masa, ya sanya hankalinsa tashi matuƙar gaske! Shi a tunaninsa wani ne ya mutu. Da sauri ya miƙe tare da sanya rigar da ya fito." Lafiya Marwana?" Ya ce mata tare da riƙeta ganin yadda ta ruɗe. "Ya Damir, ƙawata Nasreen ba ta da lafiya za ta mutu, don Allah mu je mu kaita asibiti." "Ke Marwana ki natsu ki yi mini bayani." Jin bin da ya ce yana girgiza ta ya sanya ta fashe masa da kuka."Nasreen ƙawata 'yar ajinmu ta kira ni tana kuka za ta mutu ta yi ɓari jini yana ta zuba." "Ɓari? " Ya yi mata tambayar cikin tsananin tashin hankali, sabida yana tausayin mata a wannan condition na ciki da haihuwa. Ya san cewa a wannan lokacin suna cikin tsakanin mutuwa da siraɗi. "Ɓari ta yi Ya Damir." Ta ce masa tana share hawaye "Ina mijinta?" "Baya nan." Ta ba shi amsa. "Kalli lokaci dare ya yi, kuma bai kamata mu fita ba, ina ga ba ri na kira Doctor Sadik ya je da ambulance a kai..." "Please, Yaya ba zan iya kwana ba, ba tare da na san halin da take ciki ba. Babu nisa sosai kuma duka yanzu ten ta yi, don Allah ka taimaka mata kar ta mutu. Mijinta bai damu da ita ba, kuma wallahi in don ta shi zai iya barin ta mutu." Ta ƙarashe maganar tare da kama hannunsa. Shuri ya yi yana jinjina lamari."Amma kin san abin da ya faru ko? Bana son matsala in kuma kin nace sai ku je da Idi direba." "Please, Ya Damir don Allah mu je da kai, za ka fi gudu a mota, kuma ko asibiti muka je za a fi kula ta." "Haba Marwa..." "I insist Yaya Damir, please." Ta ce tare da haɗa hannunsa. "Ba zan iya fita na bar ta ita kaɗai ba." "Don Allah ka taimaka yanzu za mu dawo, kuma Baba tana nan." Babu yadda zai yi, kan dole ya shiga ciki ya canza kayansa. A hankali ya ja mata ƙofar suka fice. Duk gudun da yake yi gani take ba ya gudu. "Don Allah ka yi sauri kar ta mutu." Da sauri ya kalleta yana mamakin abin da ta ce, tare da mamakin yadda take sonta. Shi a iya saninsa Marwana ba ta tara ƙawaye, sai ga shi ta yi ƙawa mace mai aure. "Duk iya gudun da na ke yi kin raina? So kike na je na watsar damu? In kin raina sai ki karɓi tuƙin." Jin ya yi magana cikin fushi ya sa ta ce,"Am sorry." Da suka shiga cikin unguwar a lokacin goma har da minti goma. Kallonta ya yi, daidai lokacin da ya yi parking ba ta jira ya gama ba ta fice daga motar. A lokacin Nasreen ta yi nasarar fitowa ta buɗe get ɗin gidan. A hanyar falo ta kusan tuntunɓe da ita. Har ta tsorata sai ta duƙa ta kama hannunta fahimtar ita ce a gurin. "Nasreen ya jikin ki?' ta kama hannunta ta yi mata tambayar cikin tashin hankali ganin yadda ta koma. "Marwana zan mutu ki taimake ni." Ta furta tana nishi da ƙyar. "Ba za ki mutu ba." Ta ce tare da kama hannunta. Bayan shigarta gidan Damir ya bi get ɗin gidan da kallo cikin mamaki. Shi kansa bai taɓa tunanin gidan mai kyau take ba, jin yadda take na shi labarin tana wahala. Sai ya jinjina kansa cikin mamaki yana mamakin WASU MAZAN da suke ƙuntatawa matansu alhalin suna da shi. Yana wannan tunanin ya hange su, sun fita kusan a jikin Marwana take. Da ƙyar Marwana take janta Wani irin bugawa zuciyarsa ta yi, har sai da ya dafe gurin, yana jin yadda take masa zillo tamkar za ta fito waje. Hango ta ya yi a cikin duhun, amma sai ya ji ya tasa sukuninsa. Wani yana yi ya tsinci kansa wanda ya rasa wani irin yanayi ne. "Please Ya Damir, ka buɗe bayan motar." Muryar Marwana ta katse shi tana faɗin haka. Cikin hayyacinsa ya dawo, da sauri ya zagaya ya buɗe mata motar ta sanya ta a ciki. "Marwana yarana suna ciki kuma babu kowa a gidan." Ta ce mata tana cige bakinta. Jin abin da ta faɗa da sauri ta koma ciki. Yaran ta ɗauko ta sanya su cikin mota. Shiga cikin motar ya yi, sannan ya tada tamkar wanda yake jin bacci. Ganin halin da take ciki domin a wannan lokacin ta fita hayyacinta. Kai tsaye asibiti su ya kaita. Suna isa likitoci suka karɓe ta tare da gungurata a kan gado sun yi ciki da ita. Ganin yadda Marwana ta tayar da hankalinta kamar za ta yi hauka. Ya sanya shi jawo ta ya rungume daidai lokacin da ta yi kamar za ta shiga ciki "Take easy za ta samu sauƙi. Kina sonta da yawa." "Yaya Nasreen ba ta da gata sai Allah. Kai kanka in har ka ji rayuwarta za ka tausaya mata." "Allah ya kawo mata ɗauki, amma ina mijinta yake a wannan lokacin? Ya san matarsa na da ciki ya tafi ya barta." "Ban sani ba ta ce ya yi tafiya." Jinjina kansa ya yi, ba tare da ya ƙara cewa komai ba. Sun daɗe a gurin sannan likitan ya fito yana share zufa. Da sauri suka yi burinsa. "Doctor how is she?" Damir ya riga ta tambayar ganin yadda ta damu da ita. "She is getting better. Mun yi ƙoƙarin mun tsayar da jinin, yanzu so muke ta ɗan huta ayi mata wankin ciki." Tausayinta ya sanya ta ja numfashi."Ok please do." Damir ya ce yana cusa hannunsa a aljihunsa. "We will." Likitan ya amsa tare da ba shi hannu ya koma ciki. "Marwana I think I will take my leave. Kin ga halin da Mommy Little Marwana take, bai kamata na barta a ita kaɗai ba." "Ok Yaya, amma kwana zan yi saboda ba zan iya barin ta ba." "Ƙarki damu zan dawo na kawo muku breakfast. Sai ki sanar da iyayenta, ki dawo gida." "To Yaya, Please drive safe." Ta ce masa tana kallon sa. Har ya kai baƙin ƙofa, sai ya dawo da ya tuna yaran suna cikin mota."Ina ga zan wuce da yaranta, tun da bai kamata su kwana a kwana asibiti ba." "Haka ne Yaya, ka wuce da su da safe sai ka kawo mini su." Kaɗa kansa ya yi, ba tare da ya ce komai ba, ya fice daga asibitin. A lokacin da ya isa gida sai ya kashe motar, bayan ya yi parking. Yaran ya ɗauka ya shiga ciki da su. A lokacin da ya shigo cikin ɗakin, da ta farka ta shafa inda yake kwance ta ji babu shi. Tana tunanin yana bayi ne, don haka ta koma ta kwanta tana jiran ya fito. Jin shiru sai ta fara shiga damuwa. A hankali ta miƙe ta shiga cikin bayin amma ba ya nan. Falo ta duba nan ma ba ya nan. Wayarta ta ɗauko tana ƙoƙarin kira, ganin sha biyu saura sai ta ji ƙarar motarsa. Daidai fitowar ta falon ta gan shi ya shigo da sallama rungume da yara. Gabanta ya yi mugun faɗi, ta ƙara da burinsa daidai lokacin da ya kwantar da su. Kallon yaran ta yi ganin su kyawawa sosai kuma farare. "Baby, ina ka samu yara?" Ta yi masa tambayar tana kallon sa, da yayin da zuciyarta ke kimtsa mata mugun tunani. Yana ƙoƙarin amsawa sai ta katse shi da cewa,"Wai ina ka je da daddaren nan? Hankalina ya tashi ina ta nemanka." Kallon yaran ya yi, yana mamakin kyawun yaran, domin suna da kyau sosai, musamman Raihan da har wani tsanwa take yi, kuma da ma Musaddik ya taɓa ganinsa. Tunani yake haka uwarsu take, amma mijin ta yake wulaƙanta su. "Yaran ƙawar Marwana ne. Ina bacci ta tashe ni ta yi ɓari, kuma mijinta ba ya nan ya yi tafiya. Shi ne na ce su je da direba, amma kin san halin ta da rigima, kan dole ta sa ta muka je. Wallahi da muka je na tausaya mata sosai. Kai gaskiya wa WASU MAZAN ba sa yi wa matansu adalci. Jin ta yi ba ya ce, sai ba ta ce komai ba, tana kallon yaran da ya kasa ɗauke idanunsa. Ta ja numfashi ta fesar sai kuma ta daure."Ikon Allah." Ta ce sai kuma ta kalle shi ta ce,"Shi ne ta rasa wacce za ta kira sai ƙawa? Ita ba ta da kowa ne?" Tambayar da ta yi masa ya sanya ransa ya ɗan ɓaci, duk da cewar shi ma ya yi tunanin haka. "Please dare ya yi bacci na ke son na yi. Ina ga wannan tambayar inta dawo sai ki yi mata. Yaran nan bari na kai su ɗakin little Marwana." Ba tare da ta ce masa komai ba, ta juya ta shiga cikin ɗakinta. Zama ta yi tana jin yadda zuciyarta ke suya. Duk da cewar matar aure ce, amma ta ji babu daɗi, saboda ba ta son mijinta ya yi hurɗa da kowa ce ya mace." Raka ta da idanu ya yi, ganin yadda fuskarta ya canca."Mata.." Ya ce tare da girgiza kansa. Har ɗauki ya kai su ya kwantar, sannan ya ja musu ƙofa, bayan ya yi musu addu'ar bacci. Da ya tura ɗakin ya shiga, sai ya same ta a zaune ta zabga damuwa.Da sauri ya ƙarasa ya janye mata tagumi."Kin san yanayin da kike ciki za ki sanya wa kanki damuwa?" Hawaye ya gani suna zubowa a fuskarta." Yarannan da ka shigo da su ya sanya na ji kamar watarana za ka shigo da su a matsayin 'ya'yanka, waɗanda wata macen ta haifa maka. Wallahi ba zan iya jurar ranar ba, fatana gara ace na mutu za ka ƙara aure. " Ta ƙarashe maganar tare da rungume shi ta saka kuka. Jin abin da ta ce hankalinsa ya tashi matuƙa gaske! Ƙara matseta ya yi ajalinsa yana saukar da numfashi. "Mai ya sa kike tunanin zan iya ƙara aure? Wallahi kin ji na rantse miki. Ko babu ke a cikin duniyar nan ba zan iya kallon wata 'ya mace da sunan aure ba. Ina sonki ban taɓa kallon wata 'ya mace da sunan soyayya ba. Ke ce mace ɗaya wacce zuciyata take bugawa saboda da ita. Tun lokacin da ba haɗu dake tausayinki da ƙaunarki suka cika raina. Ina sonki kuka zan yi miki alƙawarin da zai sanya ki yadda da soyayyarsa. Ni Damir ba zan taɓa kallon wata 'ya mace da sunan ina sonta ba, ko da ace bakya raye. Zan rayu ni kaɗai har lokacin da Allah zai ɗauki raina, na je gare ki sai mu ci gaba da rayuwarmu a Aljanna." Jin abin da ya ce sai ta share hawaye."Karka ga laifina da son kaina. Kishinka da sonka suka sanya nake jin haka, saboda lalurata kuma na ke jin kamar ba zan yi tsawon rai ba." "Shiri!!!" Ya ce da sauri bayan ya sanya hannunsa a bakinta yana mata wani irin kallo wanda yake sanya ta ji ta ƙara zurmawa a sonsa. "Mai ya sa kike yawan tunanin mutuwa za ta raba mu? Ki daina tunanin haka saboda duk lokacin da kika faɗa mini, sai na ji kamar ki ma wa'adina ya cika. Kina tunanin zan rayu a duniya in babu ke?" "Dole za mu mutu babyna." "Amma ba yanzu ba, sai mun ga jikokinmu har da tattaɓa kunni." Yadda ya yi maganar, yansa ta saki murmushi, tare da rungume shi tana haɗa hancinsa guri ɗaya suna jin saukar numfashinsu. Ƙara haɗata da jikinsa ya yi yana shaƙar ƙamshinta ya ce,"To ki kwantar da hankalinki. Mijin ki na ki ke ke kaɗai, kuma za ki yi tsawon rayuwar da za mu tsufa tare. Bayan ya tafi ta zauna a bakin ƙofar tana tunanin halin da take ciki.Ta kasa bacci tunani kawai take yi. Har zuwa asuba sannan ta samu ta kwanta bayan ta yi sallah. Da gari ya waye ta miƙs daidai lokacin da wayarta ta yi ƙara. Rungumeta ya yi ya kwantar da kanta a ƙirjinsa yana shafa bayanta, kamar wata jaririyar da yake son ta yi bacci. Tana kwance a kan ƙirjinsa hawaye ya bin ƙuncinta. Ji take yi kamar za ta mutu wata ta samu tsadadden mijinta. Tana sonsa da mugun kishinsa, sai dai a jikinta ba ta jin za su yi tsawon rayuwa. Bayan ta yi bacci ya kwantar da ita ya miƙe. Bayi ya shiga ya ɗauro alwala, sannan ya shiga cikin ɗakin yaran. A lokacin Musaddik ya farka yana kwance a kan gadon "Umma," Ya ke kira da muryar gwarancinsa. Da sauri ya ƙarasa kan gadon ya ɗauki yaron ya rungume. "Ka tashi baby boy?" Ya yi masa tambayar yana tunanin sunan shi da Marwana ta gaya masa. Kallonsa ya yi kuma yana kallon ɗakin. Da sauri ya ɗauke shi. Ganin bai san shi ba sai ya saka kuka. Da ƙyar ya samu ya yi shiru. Kicin ya nufa yana ƙoƙarin haɗa masa tea, Baba ta shigo tana goge idanunta. "Sannu Alhaji." Ta ce masa ganinsa ɗauke da yaro yana jijjiga shi. "Yauwa Baba, don Allah ki kula da shi." "To Alhaji, baƙin yara muka samu ne?" Ta yi masa tambaya tana kallon yaron. "Eh, ki ba shi abinci, da alama nono yake son sha, kuma mahaifiyarsa na asibiti babu lafiya." "Ashsha! Allah ya kawo sauƙi." Ta ce bayan ta karɓi yaron. "Amin," Ya amsa sannan ya koma cikin ɗakin ya fara sallah. Sai da ya kai kusan ukun dare, sannan ya miƙe ya kwanta. Bai ta shi ba sai da aka kira sallar farko. Bayi ya shiga ya yi alwala, sannan ya zauna yana jiran a kira sallah. Bayan gari ya waye wayarsa ya ɗauki ya danna layin Marwana. Ganin Damir ne ya sanya ta saki murmushi."Hello Yaya," Ta ce bayan ta ɗauki wayar. "Marwana kun kwana lafiya? Ya mai jikin?" "Da sauƙi har yanzu ban ganta ba. Cikin dare suka yi mata wankin cikin kuma sun ba ta rest bed. "Okay, Allah ya ƙara sauƙi, bari na sa ya Baba ta haɗa muku breakfast sai na kawo muku." "To, Yaya don Allah da kayan da zan canza da kuma ita." "Ok zan kawo miki." Ya ce tare da kashe wayar. Bayan ya kashe wayar, miƙewa ya yi ya ƙarasa gurin ta da take zaune a kan kafet tana azkar, hannunta ɗauke da Hisnul Muslim. Hijabinta ya cire tare da kai hannunsa kan cikinta."Da fatan tauraruwar mata gimbiya ta shi lafiya?" Murmushi ta yi masa tana kallon sa. Bakinta ta kai saman goshinsa ta sumbata. Ya rintse idanunsa yana jin kiss ɗin har zuciyarsa. WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 14 Wancan group ɗin ya cika an buɗe wannan, masu son shiga sai su bi link. BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Bayan ya kashe wayar, miƙewa ya yi ya ƙarasa gurin ta da take zaune a kan kafet tana azkar, hannunta ɗauke da Hisnul Muslim. Hijabinta ya cire tare da kai hannunsa kan cikinta."Da fatan tauraruwar mata gimbiya ta shi lafiya?" Murmushi ta yi masa tana kallon sa. Bakinta ta kai saman goshinsa ta sumbata. Ya rintse idanunsa yana jin kiss ɗin har zuciyarsa. "Ina lafiya lau my Nurii.""Daddy, yana son ya ji ɗumin babbynsa?" Yadda ya yi maganar ya ba ta kunya ta kalle shi."Baby ya ce kar daddy ya wahalar da mommynsa." Jin abin da ta ce sai ya yi murmushi ya miƙe yana faɗin,"Kar Baby ya damu, Daddy zai ƙara masa ƙarfi ne." Cak ya ɗauke ta duk ƙaton cikinta, ya ɗora a gadon tare da yin mata rumfa. Bayan ya kasheta da kalar soyayyarsa ya miƙe ya shiga bayi. Wanka suka yi, a tare sannan suka shirya suka fito don su karya. "A dining suka zauna ganin Baba Azumi ta shirya musu abin kari." Ƙwala mata kira ya yi. Ta fito da sauri ta ce,"Alhaji gani." "Yauwa don Allah ki haɗa abinci a kai wa su Marwana, sannan yaran nan ki shirya su, kuma sun ci abinci.?" "Eh, na sanya musu kayan Marwana. Na mijin ne dai na duba a cikin kayanta na jarintaka, na sanya masa su." "Ok, ba matsala bari na gama karyarwa na kai su gurin mahaifiyarsu." "To Alhaji." Ta ce tare da juyawa. Cikin so da ƙauna suka ciyar da junansu. Da ya kammala aka kawo mishi su Raihan. Kallo su ya yi yana sha'awa yaran. Kallon su suke yi cikin rashin sabo. Raihan ta kalle shi ta ce,"Daddy good morning?" Mamaki da sha'awar yarinyar ya kama shi. Hannunta ya kama yana shafa kanta."Morning How are you?" "Fine, ina Ummata?" Ta yi masa tambayar tana kallon sa. "Ummarki ba ta da lafiya, yanzu zai kai ku gurinta." Ɓata fuska ta yi jin ba ta da lafiya."Allah ya ba ta lafiya." Ta ce tare da zama kan kujerar. Kallonta ya rinƙa yi cikin sha'awa, yana ji ina ma ace duka yaronsa ne. Ita ma kallo ɗaya ta yi musu ta ɗauke kanta. Ba ta ce komai ba, har ya yi mata sallama ya fice. A gidan gaba ya sanya su duka, har da Little Marwana da ta na ce da ita za a je. A hanya sai da ya tsaya ya yi musu soyayya sosai, sannan suka tafi asibitin. Marwana bayan ta gama waya da shi likita ya kira ta. Binsa a baya ta yi cikin murna dama burinta ta ganta. Tana kwance kamar gawa. Idanunta kawai ke motsi. Tsananin mamaki ta ke yi yaushe har ta samu ciki ya girma ba tare da ta sani ba?Addu'a ta yi wa Allah da ya fita, domin ta san tsaf Faruk zai iya cewa ba cikinsa bane, ganin ko ita ba ta san da shi ba. "Marwana!" Ta furta cikin rawar murya sai kuma kuka. Ƙarasawa ta yi kan gadon ta zaunar da ita."Jiya kin tsorata ni! Na ɗauka mutuwa za ki yi." Ta ƙarashe maganar cikin hawaye tana rike da hannunta. "Ni na na ɗauka mutuwa zan yi Marwana, ina su Raihan?" "A gidan Yaya Damir suka kwana yana hanya zai kawo su." Kuka ta fashe da shi."Na gode da kika taimake ki. Haƙiƙa kin zamo mini 'yar'uwa. Bacin ke jiya da na mutu. Faruk zai kashe ni sam baya ƙaunata. A jiya aka ɗaura masa aure ba tare da ya gaya mini ba.Yana can da amaryarsa a hotel suna amarci, saboda mahaifiyarsa ta rantse sai ya yi mini kayan faɗar kishiya, kuma na yi taro. Na kira wayar da ya fi a ƙirga, amma bai ɗaya ba. Amarci ya fi masa lafiyata, ya san ko na mutu ba shi da asara." "Aure?" Ta yi mata tambayar cikin tsananin mamaki. "Aure ya ƙara ya gaya mini ba ni da ƙima da matsayi a zuciyarsa. In na ga dama na zauna da shi, in kuma bana buƙata yanzu ya san ya yi aure." Jin abin da ta ce sai ta kama hannunta "Please ki haƙura da Faruk ki canza sabuwar rayuwa." " Ina son mijina ina fatan na rayuwa da yarana. In har na rabu da shi ba zai bar mini su ba. Kuma ba ni da fatan da zan riƙe su a gidanmu. Bayan haka ina son shi jiya tsananin kishinsa ya sanya na yi ɓari.". Jin abin da ta ce ya sa ta ji haushinta matukar gaske!"To zama za ki yi ya yi ta wulaƙanta ta ki? Nasreen ina son ki ƙwaci yancin kanki tun da ƙuruciyarki, kar sai kin tsufa ya tsotse kallon mangwaro ya huta da ƙuda." "Ba za ki gane halin da na ke ciki ba. Rayuwata tana cikin gaba kura, baya siyaki. Zaman gidanmu shi ma ba mafita bace, sannan ina tausayawa rayuwar su Raihan bana son su ta so a hannun matar uba. mahaifiyata ta sha wahala sosai a hannun matar babanta." Shiru kawai ta yi ta kasa cewa koma. Ta buɗe baki za ta yi magana, daidai lokacin da aka ƙwankwansa ƙofa. Sanin Damir ne ya sanya ta ce,"Yes come in." Bayan ta sanya mata hijabinta. Cikin natsuwa ya yi sallama ya shigo. Yana rungume da Musaddik da ya fara bacci a kafaɗarsa. Idanunsa a kan Marwana, domin haka nan ya ji sam ba ya son ya kalle ta. Haka zuciyarsa ta kitsa masa kuma ya bi, don samun maslaha. "Ya Damir, welcome." Ta ce tare da ƙarasawa ta kai hannu za ta karɓi Musaddik. Idanu ta zuba masa da nufin ta yi masa kallo ɗaya, amma sai ta kasa ɗauke idanunta. Wani irin abu mai ƙwarjini ta gani a cikin idanunnasa. Zuciyarta ya fara bugu fiye da wanda take yi. Rintse idanunta ta yi tana son kauda idanunta gare shi, amma ta kasa kallon sa take cikin tsananin sha'awar ina ma ace shi ne mijinta, mahaifin 'ya'yanta. Ganin yadda ya rungume shi cikin tsananin so da ƙauna. Namiji Kyakkyawan gaske ingarma da shi ga shi dogo sosai, mai faffaɗar ƙirji. Shigarsa da kamarsa suka sanya ya ke ɗauke da wata irin charisma dake sanya masa ƙima da daraja ga duk wanda ya kalle shi.Wani irin ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi, tare da ta'awizi a zuciyarta, domin ta san sheɗan yake ƙoƙarin ƙitsa mata surarsa a zuciyarta. "Haƙiƙa matarka tafi ko wace mace sa'a, duniya samun miji kamarsa ba ƙaramin tagomashin bane. "Ta furta a cikin zuciyarta. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta saki tare da rintse idanunta. Da sauri suka kalle ta har da shi da bai yi ninya ba. Gabansa ya yi matuƙar faɗi. Ganinta mace kyakkyawar gaske! Mai manya idanu masu tsananin ƙwarjini. Ƙara kallonta ya yi, duk da ba ta da lafiya, amma hakan bai hana bayyana kyawunta ba. Jikinsa ya yi sanyi, sanyin da ya hana shi jirgawa. Ganin hakan ya sanya Marwana ta ƙarasa gabansa ta karɓi Musaddik ta kwantar da shi. Yana tsaye a gurin kamar gunki yana kallonta da ta fuskar da kanta ƙasa, tana wasa da yatsun hannunta. "Ya Damir, ga ƙawata wacce na ɗauke kamar 'yar'uwata Nasreen. Nasreen, ga Yana Damir, wanda ba ni da kamarsa. " Ta ce ganin ko wannensu ya kasa motsi. Ɗago idanunsa ya yi, ya ƙara kallonta daidai lokacin da, ita ma ta yi nasarar kallonsa. Zuciyarsu ta buga a tare. "Sannu ya jikin ki?" Ta ji muryarsa mai kama da sarewa yana faɗin haka. "Da sauƙi," Ta ce cikin sanyin murya, don bai ji abin da ta faɗa ba, don kawai yana kallon bakinta ne. "Ya jikinta mai likitan ya ce?" Ya yi wa Marwana tambayar haka yana mai da idanunsa gareta. "Jikin da sauki, amma kuma ya ce sai an ƙara mata jini." "Ok, ba matsala bane, amma kin kira mijinta?" "A'a, tun jiya dai." "Sai ki kira shi, ya san halin da matarsa take ciki, duk inda ya je ai dole ya dawo." Kallonsa ta yi sai hawaye shar. Marwana hannunsa ta kama suka fita."What? Kina nufin mijinta aure ya ƙara ya tafi ya barta a cikin wannan halin?" Ya yi mata tambayar cikin damuwa. "Eh, yana hotel yana cin amarcinsa." "Kai wannan mutumin ba abinda imani. Matarka na cikin wani hali a kira ka, amma ka kasa amsawa saboda kana amarci? Akwai abin da ya fi iyalinsa mahimmanci?" "Yaya sai ka yi mamaki wallahi auren bai gaya mata ba." "Ikon Allah! Amma WASU MAZAN suna matuƙar ba ni mamaki." Shiru suka yi kowa da abin da yake tsaƙawa a ransa. Can ya sauke numfashi ɗauko wayarta ki kira shi. Ba musu ta juya ta ɗauko wayar. Ta yi masa kiran duniya, amma bai ɗaya ba. A lokacin sun ta shi daga bacci kenan. Saboda gajiyar da suka yi, babu wanda ya iya motsawa har aka kira sallah aka idar. Sai gurin tara saura suka ta shi. Ganin bai yi sallah ba, hakan bai dame ta, domin ita ma ba ta damu da sallar ba. Bayan sun yi wanka sannan suka yi sallah. Matsawa kusa da shi ta yi tare da janyo shi ta haɗa bakinsu, tana masa wani irin salo. Janye jikinsa ya yi tare da ture ta."Please, baby ki bari na huta, kuma yunwa na ke ji." Jin abin da ya ce ta ɓata fuska ta matsa can ta zauna. Ganin ta ɓata rai ya janyota. Babu yadda zai yi, haka nan ya biye mata, amma shi kansa ya san yana buƙatar hutu. Kamar yadda lamarin ya faru cikin daren juya haka suka gudanar. Sam babu tsari na addini suka rinƙa ihu. Ita ta fara dama haka yake sosai ya biye mata. Ya sha fama da Nasreen kan hakan, amma ta ƙi tare da yi masa nasihar hakan ba koyarwa bace ta addinin Musulunci, sai dai Yahudu da suka kawo wannan salon, ɗin su ɓata tarbiyarmu da tsarin Islama. Da ƙara ya iya ɗaukar wayarsa ya sanya aka kawo musu abinci. A nan ya ga tarin kira sau babu adadi. Tsuka ya ja tare da jifa da wayar. "Shashashar banza! Ba ina gaya miki da ma akwai lokacin da za ki yi sani sani ba? Wato tun jiya idanunki sun raina fata? Ai dama za ki gani. Baƙincikin kishinta sanya kin kasa bacci sai kirana kike yi. Ai kin riga kin makaro, tun da na samu macen da za ta yi mini duk abin da na ke so. In har ba ki takatsantsan ba, walllahi saf zan yarda ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda." Shi kaɗai yake ta maganar. Rashida ta kalle shi."Babya magana kake?" Ta yi masa tambayar tana masa wani irin kallo tare da hura masa kiss. "Ni da wancan shashashar ce. Kira yafi sau ɗari." Dariya ta yi ba ce komai ba tana kallon sa. Ya buɗe baki zai yi magana sai kiranta ya shigo. Kin ɗagawa ya yi har aka kira sau bakwai. Ganin ta na ce sai ya kai hannu ya ce,"Bari na ɗaga na ji uban me za ta ce mini." Carab ta riƙe hannun sa."Ni baby, kishi ne kawai yake damunta. Ba ta son mu ci amarci. Ka shareta, don ni na fi son mu yi amarcinmu anan. Ka san matan Hausawa suna da kishin tsiya." "Ok, babyna yadda kika ce haka za a yi. Ai ni in har za ki iya sarrafa ni a gado kin riga kin samu kaina har da ƙafafuwana. Ita shashashar sai dai ta kwanta kamar gunki. Kai matan Hausawa sam ba su yi ba." Dariya ta yi jin abin da ya ce, tana masa salon da take son ya bambanta ta da matan Hausawa. "Ikon Allah! Har yanzu ba ya amsa Calls din." Marwana ta ce cikin takaici. "Ungo wayata kira shi da nawa." Ya ce mata yana miƙa mata wayar. Karɓa ta yi tare da cire password ɗin. Ta danna numbobinsa a wayar. Cikin mamaki ta ga ya ɗaga wayar da sallama. Kallon junansu suka yi cikin mamakin rashin ba ta daraja. Ta san zai iya tuna muryarta sai ta miƙa masa wayar. Ƙin karɓa ya yi."Ki yi magana kin san ba shi da mutunci, zai iya mini wata fassarar, kuma bai kamata na yi masa magana." Babu musu ta yi masa sallama.Cikin izza ya amsa don ya ɗauki muryar. "Lafiya?" Ya ce mata a gimtse yana mamakin kiran Daurewa ta yi ta kawar da muguwar shawarar da zuciyarta take ba ta tana zugata kan ta danna masa ashar, a maimakon hakan sallama ta yi masa, wanda ya amsa kamar mai ciwon baki. "Na san ka gane ni matarka ce ba lafiya tana asibiti." "Ya za a yi na kasa gane ki uwar shishshigi." Ya ce mata yana girgiza ƙafafunsa. Ranta ya ɓace amma sai ta daure za ta yi magana ya riga ta."Ba ta da lafiya sai ta kasa kiran kowa, sai ke dangin dagiro?" "Faruk, don't provoke me. Nasreen tana cikin halin rashin lafiya ɓari ta..." "Ɓari me? A gidan uban wa ta yi cikin?" Tambayar ya yi matuƙar ba su mamaki da haushi, har bai san lokacin da zuciya ta cika shi ba ya gushe wayar ya ce,"Kai wane irin mara mutunci ne? Kana rayuwa da matarka kake tambayar ina ta samu ciki?" Jin muryarsa ya yi ta doki kunnensa "To ɗan iya! Kai kuma a dangin wa? Kuma ba zan tambaye ta ba, tun da ban san da cikin ba?" Ya yi dauriyar faɗin haka duk da cewar muryarsa ta firgita shi. "Kana tsoron Allah kuwa?Anya ka ɗauki aure a matsayin bauta, kana da sanin cewar Allah zai tambaye ka yadda ka riƙeta a ranar alkiyama" "A'a ba na tsoron Allah sai na ka. Kuma da kake mini tambayoyin nan kai a zuwa? Ban san matata na da ciki ba, laifi ne na tambaya?" "Ban yi mamaki ba saboda ba ka da hankali, har za ka iya sanya ƙwanka ba tare da ka sani ba." Zuciyarsa ta tunzura jin bin da ya ce. Zaginsa ya fara yi, amma sai ya dakatar da shi ta hanyar cewa,"Ni ba jahili bane kamar ka. Matarka tana kwance a asibiti kuma jini ake so, don haka sai ka yi sauri ka zo ka bada jinin, saboda an nema babu kalar nata." "Kutumar uba! " Ya ji ya danna ashar. Yana mamakin abin da ya ce, sai kuma ya ɗora da cewa,"Wallahi ko mutuwa za ta yi ba zan bayar ba. Ina tsaka da cin amarci sai a iban mini jini?Wallahi uban kuturu ya yi kaɗan." Ƙit ya kashe wayar yana zagi. Kallon wayar suka yi cikin mamaki. "Marwana irin mijin da take aure kuma take zama da shi kenan?" "Ya za ta yi? Rayuwarta rana zafi inuwa ƙuna. Mahaifinta shi ma rayuwar sa babu dama. Ƴaƴanta daya shine kawai haskenta." "Kira shi ki sanar masa." Ya ce cikin ɓacin rai yana jin kamar ya zama hukuma ya hukunta shi. Cikin sanyin jiki ta danna kira. Ringing biyu ya ɗauka."Hello, ƙanwata, yanzu na karɓo cajin na ke shirin kiran ki." Gyaran murya ta yi ta ce,"Ba ita ba ce ƙawarta ce. Muna asibiti ta yi ɓari." Salati ya sanya jin abin da ta ce,"Don Allah wane asibitin?" Kwatance ta yi masa ya kashe wayar. "Ƴaƴanta yana so ta shi ne gatanta." Shiru kawai ya yi ba tare da ya tanka ba. Bai ɗauki tsawon lokaci ba ya ƙara so. Hankalinsa a tashe ya shigo cikin asibitin. Mamakin kyaunsa asibitin ya kama shi, domin ya dai san asibitin, amma bai taɓa shiga ba. Kallonsu ya yi yana mamakin kyawunsu da haɗuwarsu. A ransa yake godiya ga Allah da ya haɗa ta dasu. "Tun jiya take asibitin nan ta kira wayarka a kashe, sai ta kira ni. Ta yi ɓari jini ake so kuma ba su da jini. Shi ne suke son a samu wanda za a ɗiba. Ta gaya mini Faruk kalar jininsu ɗaya." Kansa ya ɗage domin kalar jininsu ba ɗaya ba."Yanzu mai Faruk ɗin ya ce?" Ya yi mata tambayar duk da ya san ba zai yarda ba. Cikin takaici ta ware hannunta ta ce,"Ya ce ba zai bayar ba, ko mutuwa za ta yi." "Hhmmmm!" Ya ce dama ya san za a rina, an saci zanin mahaukaciya. Ɗakin da take ya shiga. Ganin haka suke bishi har da Damir. Damir ya shiga don ya ɗauki Little Marwana su koma gida. Don in bai bar asibitin ya yi baz zuciyarsa za ta iya harzuƙa ya sanya a ɗaure sa. Yana ƙarasawa kan gadon ya hau ya kama hannun ta."Ƙanwata ashe ba ki da lafiya." Kuka ta saka tare da kama hannunsa."Yanzu ina za a samu jinin?" Jin bin da Marwana ta ce sai ta kalle ta. "Faruk ya ce ba zai bayar ba ko?" Shurin da ta yi ya tabbatar mata da hakan. Kuka take yi sosai. Damir ya ɗauki Marwana zai fita saboda kukan damunsa yake yi. A rayuwar sa ya tsani kukan mace, wannan dalilin ya sanya Batula ta gane lagonshi take masa kuka a duk lokacin da take son ya amince da wata buƙata da take da shi. Hannunsa Marwana ta kamo tana kallonsa. Juyowa ya yi yana kallonta ba tare da ya ce mata komai ba. "Jininku iri ɗaya ne, don Allah ka taimaka a ibi naka.." "What?" Ya ce yana zare idanunsa yana kallonta, sai kuma ya ɗora idanunsa kan nata da ta yi ƙasa jin abin da ta ce. Fita kawai ya yi yana girgiza kansa, ba tare da ya ce komai ba. Shi kansa ya rasa gane dalilin da ya sanya shi ƙin amincewa. "Zan je na nemo jinin ko kuma wanda yake da kalar jinin. Mun gode da ƙaunarku gareta." Ahmad ya ce tare da miƙewa. Wai readers kun san me? Labarin WASU MAZAN kamar yanzu aka fara it is just beyond predictable. This part that we are is just like the introduction part. Ku ci gaba da bibiyarsa kuna rikirkitani da zafafan comments akwai ƙura a cikin labarin. WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 Follow the 𝑊𝐴𝑆𝑈 𝑀𝐴𝑍𝐴𝑁 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xqsd72WTrg772JU2P *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 Na buɗe wani group wancan ya cika mai son shiga ya bi link ɗin nan👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg PAGE 15 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "What?" Ya ce yana zare idanunsa yana kallonta, sai kuma ya ɗora idanunsa kan nata da ta yi ƙasa jin abin da ta ce. Fita kawai ya yi yana girgiza kansa, ba tare da ya ce komai ba. Shi kansa ya rasa gane dalilin da ya sanya shi ƙin amincewa. "Zan je na nemo jinin ko kuma wanda yake da kalar jinin. Mun gode da ƙaunarku gareta." Ya ce tare da miƙewa. Damir da ya shiga cikin mota sai ya kasa tuƙawa. Rintse idanunsa ya yi. Yana jin wani iri saboda hana jinin da ya yi, amma ya zai yi ya ba da jininsa a sanya wa matar wani? Bayan shi mijin da yake morarta ya ƙi ba da na sa? Sakarcin Marwana ya gani da ta yi masa tambayar. Ta san yadda yake matuƙar shan wahala in har aka ibi jininsa. Baya manta wahalar da ya sha a lokacin da aka sanya wa mahaifinsa jininsa. Sai da ya suma har sau uku. Yana da wadataccen jinin, amma duk lokacin da aka ina ba ya sha ta daɗi. Kunna motar ya yi, yana jin ba zai iya wannan taimakon ba, amma kuma sai ya ji ya kasa fara tuƙa motar. Cak ya tsaya yana tunani. Tsintar kansa ya yi, da buɗe motar ya koma cikin asibiti. Saura kaɗan su ci karo da Ahmad da ya fito cikin tashin hankali. Yana tunanin inda zai samu jini. Naira dubu biyu ya tashi da ita, kuma ya ba su Mama su yi girki da shi. Matsawa ya yi yana kallonsa. Marwana ganin ya dawo sai ta ƙarasa gurinsa."Na yarda a ibi jinin." Ya ce mata cikin murya mai sanyi. Faɗawa jikinsa ta yi cikin farin ciki. "Mun gode Yaya Allah ya biya ka." Ba tare da ya amsa ba ya nufi inda ake iban jinin. Ita da Ahmad sun kasa magana, sai kallonsu suke yi cikin mamaki. A lokacin da aka sanya masa allura aka caka masa inda jinin zai rinka zuba. Rintse idanunsa ya yi. Yana jin yadda zafin ke shiga ƙwaƙwalwarsa. "I will do everything for you little sis." Ya ce tare da rintse idanunsa. Ba tare da ya motsa ba har aka gama iban jinin. Yana kwance sai da ya tabbatar da ya huta ya miƙe. Sai bayan an kammala iban jinin, sai tsoro ya kamata ganin yadda ya koma. Tunawa ta yi da yadda yake komawa in ka gama. Tsoro da firgice ya sanya ta kusa hauka. Sam ta manta, son ƙawarta da tausayi sun sanya ta manta halin da ɗan'uwanta zai shiga." Ganin yadda idanunsa suka birkice sai ta kalle shi, tare da kama shi da sauri cikin rawar murya ta buɗe baki ta ce,"Ya Da..." Hannunsa ya ɗaga nata yana jin yadda kansa ke juyawa, abubuwa na rabuwa nasa gida biyu."Kar ki damu son ƙawarki ya sanya kika manta da halin da yayanki zai kasance and I will do anything for you." Kallonsa ta yi, yana murmushi daidai lokacin da ya shiga ciki. Abin da ya ce mata kamar magana ya daɓa mata. "Ya Damir, wallahi na manta ba ka sha ta daɗi, in har aka ibi jinin ka." Murmushi kawai ya y, yana jin yadda kan shi ke juyawa, komai na rabuwar masa gida biyu. "Don Allah ka bari na kai ka." Idanunsa ya buɗe ya ɗora kanta sai ya ga kamar uku-uku yake ganinta, amma saboda ƙarfin hali ya ce,"Don't Bother ki kula da ita." Shiru ta yi tana fargabar Allah ya sanya kar wani abu ya faru da shi, domin Allah kawai zai raba ta da Hajiya lafiya. Tana kallon yadda yake tuƙin cikin mutuwar jiki. Ta san abinda lafiya, in har ya ce zai yi, to dole sai ya yi. Wannan dalilin sa ya ba ta ja da tsawo ba. Ganin ya fita daga harabar asibitin, sai ta shiga ciki don ta yi mata sallama, kuma ta yi mata transfer na kuɗi, ko za a bukata kafin ta dawo. A lokacin da ta shiga tana kwance a cikin zuciyarsa, tana girmama karamci irin na su. Tana kwance idanunta rufe hawaye yana ganganrowa Ahmad yake mata wa'azi yana kwantar mata da hankali. "Zan je gida na dawo. Na yi miki tranfer na kuɗi a wayarki, ko ana son wani abu kafin na dawo." Kallonta suke yi sun kasa magana."Mun gode Allah ya ƙara buɗi." Ahmad ya ce mata. Ita kuwa sai hawaye tana kallonta. Ƙarasawo ta yi kan gadon ta shafa kanta."Ki kula da kanki kuma ki ci abinci. Zan je gida na yi wanka na dawo." "Na gode Allah ya saka da alkhairi." "Don't mention." Ta ce tare da juyawa ta fara tafiya. Kallo suka bita da shi har ta fita. A hanya yana tuƙi yana haɗa hanya. Da ƙyar ya samu ya isa gida. Ko parking bai gama ba, ya samu ya ja hannun Little Marwana suka shiga cikin gidan. Batula ta taso ta tare shi tana faɗin,"Ka daɗe fiye da yadda na yi tsammani." Ajiyar zuciya ya ja ya kalle ta cikin rashin hayyaci. Tsoro ya ba ta ganin yadda idanunsa suka dawo. "Lafiya mai ya faru da kai?" Sharab ya zauna kan kujera yana saukar da numfashi. "Ba komai." Ya ce mata yana kallonta. Tsoro sosai ya ba ta ganin yadda ya koma."No, akwai abin da ya faru." "Na ce miki ba komai..." Ya fara maganar cikin fushi zai mike, amma sai jiri ya kwashe shi ya fadi ƙasa. Ganin haka ta sa ya ihu, tana girgiza shi tana kiran sunanshi, amma ina idanunsa sun ƙafe. Jin ihu ta ya sanya Baba Azumi ta sheƙo don ta ɗauka haihuwar ce ta taso. Ganinsa kwance babu numfashi tana girgiza shi sai ta ruga waje ta kira maigadi. Da ƙyar suka sanya shi a cikin mota. Wayarta ta ɗauka ta kira Hajiya ta sanar mata suna asibitin. Hankalinta ya tashi matuƙar gaske! Ta shiga tambayarta. "Lafiya mai ya faru? Na kira shi ya ce mini yana asibiti, zai zo gidana in ya dawo. Dama ba shi da lafiya ne? Saboda da na kira shi kamar ya ce mini dubiya za shi." Jin tambaye da take mata cikin ruɗani ya sanya ta ce,"Ni ma ban sani ba, ya dawo mini kamar ba shi da lafiya sai kawai ya faɗi." Ta karashe maganar cikin kuka. "Ina Marwana?" "Tana asibiti ƙawarta ce babu lafiya shi ne suka kaita tun jiya da daddare." "Ƙawarta?" Ta yi mata tambayar cikin tsananin mamaki, tana tunanin wace ƙawar ce. "Eh, ita da shi suka kaita asibiti don ta yi ɓari tana zubar jini." Kanta ya kawo wuta ta tuna da Nasreen. "Ok, ma za ku kaishi asibitin gani nan sai na ji abin da ya faru." "To Hajiya sai kin zo." Ta ce tare da kashe wayar tana kallonsa. Kuka take yi sosai tana girgiza shi. Sun shiga cikin asibitin ta buɗe ido sai kuma ya fara jijjiga ya ƙara sumewa. Tsananin tashin hankali ya ƙara kamata. Dafe cikinta ta yi da yake juyawa. Marwana tana tuƙi zuciyarta na bugawa na halin da yake ciki. Dana sanin iban jinin ya fi kwando masaki. Ta san yau Allah kawai zai raba ta da Hajiya, domin ko mai za ta ce mata ba za ta fita ba, daga ƙarshe ƙalubantatarta za ta yi cewar ƙawa tafi shi matsayi, da har zai sanya halin da take ciki ya sa ya ta manta halin da zai shiga. Tana ƙoƙarin karya kwanar gidansa kiran Hajiya ya shigo. Saboda tsananin tsoro har parking ta yi kafin ta ɗaga wayar. "Marwana?" "Na'am," Ta masa cikin rawar murya jin yadda ta kirata. "Mai ya samu yayanki ya sume kuma wace ƙawarki kuka kai asibiti?" Tambayar da ta yi mata ya tsinkar da zuciyarta."Ya sume?" Ta yi mata tambayar cikin tsananin tashin hankali. "Ya ina tambayarki kina tambayata? Kina ina ne?" "Um, eh, ina kwanar shiga gidansa." Ta ba ta amsa cikin rawar murya. "To ma za ki dawo asibiti don yana can sai ki yi mini bayani." Ta ce tare da kashe wayar. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Na shiga uku!" Ta furta bayan ta yi jifa da wayar ta yi reverse ta nufi asibitin. A lokacin da suƙa karasa da shi aka kai shi asibitin. "Innalillahi ba yanzu muka ibi jininsa ba?" "Jini?" Batula ta tambaya tana zare ido. Duk da cewar, ba ta san cewa yana shiga cikin yanayin ba in har aka iba, amma ta yi mamakin abin da ya sanya aka iba. Tana ƙoƙarin tambayarsa daidai lokacin da Hajiya ta karaso. "Ina Damir ɗin mai ya faru da shi?" "Ban sani ba yana ciki likitan dai ta ce mini jininsa aka..." "Ji mene ?" Ta yi mata tambayar tamkar zata zauce. Ganin ta firgita ya santa ta ce,"Eh, jininsa aka iba haka suka gaya mini." "Saboda me aka ina mai aka yi da shi?" Ta yi tambayar daidai lokacin da Marwana ta shigo, jin tambayar da take yi wa likitocin ta santa ta tsaya tana zare ido. "Wata petien da suka kawo da daddare wacce ta yi ɓari aka sanyawa jinin Damir?" Mamaki ya cika Hajiya ta juyo tana kallon Marwana da ta gama tsurewa."Petien? Wai mai yake faruwa Marwana? Ko kun fara yin abu ba tare da na sani ba?" Daurewa ta yi cikin rawar murya ta ce," Ƙawata ce Nasreen wacce na gaya miki tana samun matsala.da mijinta. Ta yi ɓari kuma ya yi sabon auren ya tafi ba tare da ya kula ta ba. Shine ta kira ni ta gaya mini. A daren muka je muka ɗauko ta. Yau likita ya gaya mana sai an ƙara mata jini. Mun kira mijinta ya ƙi zuwa shi ne na roƙi Yaya ya ba da jininsa, tun da kalar jininsa take da shi." Kau ta ji ta wanke mata fuska da mari."Ashe shashasha ce ke? ba ki da hankali. Saboda wata sai ki nemi kashe ɗan'uwanki?" Kuka take yi sosai cikin muryar kuka ta ce,"Hajiya ki gafarce ni wallahi na manta cewar yana shiga cikin wannan yanayin." "Saboda me za ki tuna, tun da wata banza can ta fi shi matsayi." Ta yi mata maganar tana hararar ta Matsawa ta yi zata kara marinta, daidai lokacin da likitan ya ce su shiga ɗakin da yake. Batula da ba ta a cikin hayyacinta jin an ƙarawa wata mace jinin mijinta. Idanun ta suka rine da kishi. Ranta ya ɓaci laifinsu ta gani, domin in har da bai amince ba, babu yadda za a yi a iba. Tuna waya da laptop ɗin da ya siya mata wanda sai Marwana ta gaya mata da suna hira, amma bai taɓa gaya mata ba, duk da cewar sun yi alkawarin ba za su rinƙa ɓoyewa junansu komai ba. "Son matar aure yake yi?Ta yi wa kanta tambayar cikin tsananin tashin hankali! Sai kuma ta ƙara tambayar kanta da cewa," Wannan dalilin ya sanya har ya ɗauki yaranta suka kwana a gidansa, kuma ya kasa bacci ya rinƙa kula da su. Why mijina? Mai ya sa za ka yi ƙoƙarin sanya na daina yadda da kai" Ta ji zuciyarta ya yi mata tambayar da har sai da gabanta ya faɗi. Rintse idanunta ta yi, tare da fita cikin ɗakin zuwa inda ta ji an ce an kwantar da ita. Nasreen tana kwance har yanzu hawaye yake bin ƙuncinta. Kamar yadda ta ga 'ya'yanta dama ba ta yi tunanin mummuna ba ce. Tana kwance tana rintse idanunta har ta gana kallonta ba tare da ta san ta shigo ba. Fita ta yi zuwa cikin ɗakin da yake kwance. Kansa ya dafe yana kallonta sai kuma ya ƙara suma. "Wallahi Marwana in har kika yi sanadin da na rasa Damir sai kin gwammce kin bi shi lahira." Kuka take yi tana girgiza shi tana kira sunasa"Yaya ka tashi don Allah Karka mutu." Hajiya fita ta yi da sauri, zuwa ɗakin da Nasreen take kwance. Ganin haka ya sa ya Marwana ta bita."Don Allah Hajiya kar ki tozarta su, wallahi ba su da laifi kan lamarin laifine. Don Allah kar ki yanke ƙawancen da muke fatar mutuwa kawai za ta raba shi." "Ko mahaifiyarki ce sai na wulaƙanta ta." Da sauri Nasreen ta buɗe ida ita jin abin da matar take cewa.Ahmad shi ma miƙewa ya yi yana zare ido. "Ke ce aka ibi jinin ɗana aka sanya miki ko? Wallahi in har ya mutu sai na ɗauke ki daga ke har dangin ki har sai igiya ta yi rara." Jin abin da ta ce hankalinsu ya tashi. Suna kallon Marwana da take kuka cikin dana sani. Ta yi ninyar alkhairi sai ga shi ya koma ya zama tsiya. Ba ta ƙara shiga tashin hankali ba sai da ta ji Hajiya tana musu zagin fitar arziki. Ta rintse idanunsa cikin kuka ta kama hannunta. "Ki hukunta ni wallahi bata da laifi." Kau ta ƙara kaureta da mari."Ina nan zuwa gunki dama ba kyale ki zan yi ba." Batula ce ta shigo cikin ɗakin tana haɗa hanya, Saboda kishi da ya rufe mata idanu ba ta gani. Kan gadon da take kwance ta ƙara da tana kallonta cikin tsanannin tsana Tun da take a rayuwarta, ko 'yan mata ba ta taɓa ganin Damir ya kula su ba, sai matar aure wacce take talaka? Kai ina akwai lauje cikin naɗi! Anya ba asiri suka yi wa mijina ba, saboda ta samu ta kashe aure ya sake ta?" Ire-iren waɗannan tambayoyin suka cika mata zuciya, tare da makantar da ita, har ta kasa tuna waye mijinta da abin da zai aikata. "Banza jaka da aurenki kike bibiyar mijin wata, har a rasa jin da za a sa ya miki sai na mijina, wato ga ki mai iya asiri kin yi masa asiri ya zama miki bita zaizai don ki shiga cikin ɗaula ko?" Tsananin mamakin abin da ta furta, ya sanya ta ji tamkar an ɗora mata dutsen dala. Wasu irin zafafan tagwayen hawaye suka sauka a ƙuncinta. Zare idanunta ta yi tana kallon Batula jin abin da ta ce. Hakan ya tabbatar mata da ita ce matarsa. Kalaman ta suka tayar da hankalin Marwana matuƙa gaya! Da sauri ta ƙarasa gabanta ta ce,"No Anty Batula, don girman Allah ƙarki wulaƙanta ta wallahi ba ta da laifi." Ta ƙarashe maganar cikin kuka ta haɗa hannunta tana roƙonta. Tureta ta yi cikin tsananin zafin kishi."Wallahi jinin nan ba zai ƙarasa shiga cikin jikin ki ba, domin ba zan bari jinin mijina ya yi yawo a jikin wata ba." Ta kai hannu za ta fisge sauran ragowar jinin da ya kusa karewa. Damir bayan ya farfaɗo, cikin dauriya ya fito daga cikin ɗakin da aka kwantar da shi, ya nufi inda aka kwantar da Nasreen hankalinsa a tashe. Ya san cewa yadda ran Hajiya ya ɓaci, sam ba za ta yi musu da daɗi ba. Sannan yana kallon irin kallon, da Batula take masa a lokacin da ta ji an ibi jininsa. Yana daidai ƙofar ɗakin ya ji mugayen kalaman da take faɗi. Kansa ya sara, da sauri ya dafa bango jin abin da take fadi."Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Ya Allah taimako na yi sam zuciyata babu mugun nufi." Ya furta tare da shiga cikin ɗakin, daidai lokacin da ta yi nasarar fisgo allurar dake soke a hannunta. Wani irin ƙara ta saki tare da rintse idanunta, tana jin tsananin azaba, yadda yake shiga cikin ƙwaƙwalwarta. Da sauri Marwana da Faruk suka yi kan gadon, ganin za ta cutar da ita. Hankalinta ya gusar da tunaninta, burinta kawai ta hana jinin mijinta shiga. Ji ta yi an riƙe hannunta da sauri ta juyo.Ganinsa tsaye yana nishin wahala ya sanya ta fashe da kuka. "Jininka fa ka yarda aka sanya mata zai rinƙa yawo a jikinta?Ni da bana fatar ka kula wata mace, amma sai ka yarda ka bada jinin ka aka sanya mata. Matar auren kake so?" "Kau ya kaureta da mari jin abin da ta ce?" Kina da hankali? Ransa ya ɓaci! Idanusa suka firfito. Gabakiɗaya jijiyoyin jikinsa suka tashi."Kin san abin da kike faɗa? Taimako na zama sharri ne?" Riƙe gurin ta yi tana hawaye jin abin da ya ce. "Marina ka yi, da tsohon cikinka a jikina?" Ta faɗa tana dage ƙaton cikinta da yake barazanar fitowa a kodayaushe. "Kin cancanci fiye da haka Batula in har iya tsawon rayuwar da muka yi babu yadda a tsakaninmu." Dukansa ta shiga yi a ƙirji tana faɗin,"Ka gaya mini ta yaya zan yarda da kai, bayan ka aikata abin da ko a duniyar mafarki ba zan yarda ba?" Jikinsa ya yi sanyi duk da cewar bai ga lamarin da zafi ba, domin saboda Marwana ya yi, kuka ta san a rayuwar sa zai iya komai anything for her." Jikinsa ya ƙara yin sanyi sosai, domin zai iya cewa wannan shine karo na farko, da ya taɓa kai hannu a cikinta. Hankalinsa ya tashi har yana jin ba zai yafewa kansa ba, ga tsohon ciki a jikinta."Kiyi haƙuri bai kamata ki yi mini wannan zargin ba, saboda kin fi kowa kusanci da ni. Ka da ki bari kishi ya rufe miki ido. Wallahi ban taɓa ganinta ba, kuma na taimake ta saboda Marwana." Ya ƙarashe maganar yana ƙoƙarin kamota ganin yadda take cige baki. "Karka taɓa ni! Na tsane ka bana sonka mayaudari kawai." Ta ce masa sai kuka ta dafe cikinta tana nishi da ƙyar. "Please kar kishi ya sa ya ki illata mini kanki da baby. Wallahi na rantse miki ban taɓa son wata ya mace ba, bayan ke ballantana matar aure." "Anty Batula ki yarda da shi kar ji jawowa kanki wata cutar. Kin san a cikin satin nan za ki..." Hajiya ce ta ƙara sauke mata mari."Rufe mini baki shashasha kawai, duk abin da ya faru ba ke kika kawo ba, saboda ba ki da hankali da tunan.." Maganar ta tsaya sakamakon Batula da ta dace cikinta ta ce,"Wayyo Allah!" "Bayana, cikina, marata." Ta furta cikin gigitaccen ƙara. "Please Batula, kar mu yi haka dake. Kar ki yi ƙoƙarin haihuwa kin san C.A sa a yi miki." Ya faɗa yana dakatar da ita da hannu, amma ina ya makaro, domin kafin wani lokacinta fita hayyacinta. Hannu ya kai zai kamata sai ta ture hannun, ba tare da ya kula ba, cikin tsananin tashin hankali ya sungume ta zuwa cikin ofishin likita. Ganin halin da take ciki ya ruɗe yana kallonsa."Ka na sane da aiki za a yi mata, mai ya sa ka bari ta fara naƙuda da kanta?" "Please we don't have time. Intentionally ya faru, don Allah ka duba ta." Ya faɗa tare ɗa ƙara matsawa gurinta daidai lokacin da ta kira sunansa ta ƙara ƙankame. hannunsa. "Wayyo na shiga uku! Mutuwa zan yi!" Ta furta cikin tsananin tashin hankali tana nishin wahala. Jikinta zufa ya jiƙata sosai har ɗiga take. Kafin wani lokaci ta fita hayyacinta. Naƙuda ta taso mata gadan-gadan. "No ba za ki mutu ba, don Allah kar ki haihu ki bari ayi miki aiki." Ya furta yana ƙara riƙe hannunta. Tofa Batula wannan kishi haka?🙄🙄🙄 Wai Allah lamari fa ya rikice har na kasa cewa komai, saboda mai haihuwa akwai tausayi. Allah kawai ya san wahalar da iyayenmu suka sha. Allah ya ba su lafiya. Wannan page ɗin na duk wata uwa ce. Batula Allah ya sauke ki lafiya. WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 16 Duƙawa kan gadon da aka kwantar da ita ya yi. Cikin wani irin yanayi yake kallonta, ganin yadda ta fita hayyacinta."Saboda kishi sa ki yi mini asarar rayuwarki." "Ka taimake ni, su cire mini cikin nan mutuwa zan yi, ka taimake ni ka sanya su cire mini cikin." "No, ba za ki mutu ba, saboda inhar kika mutu, ni ma mutuwa zan yi." Ya furta yana tofa mata addu'a. Ganin cikin ƙanƙanin lokaci ta fita hayyacinta. Hakan ya tayar da hankalin likitocin da su Damir. Tun sun ganin lamarin da sauƙi har ya tsananta. A lokacin da Doctor ɗin ya fito yana share zufa. Da sauri ya ƙarasa gunsa."Kana ganin za ku iya ko na yi mata viser?" Dafa kafaɗunsa ya yi,"A halin da take ciki ba za ka iya fita da ita ba. Ka yi mata addu'a domin matarka tana cikin wani yanayi." Jin abin da ya faɗa ya sanya shi daga kansa yana salati. Kansa ya zarga da kuma yarda da ya yi aka ibi jininsa, domin da duk haka ba ta faru ba. Ina ma ace lokacin da ta buƙaci ya zo ya kaita asibiti bai zo ba. "Ku shiga ciki tana son ganin ku." Tsoro ya sanya shi kasa jirgawa har sai da Hajiya ta ja hannunsa suka shiga. "Wayyo Allah!" Ta ce tare da miƙa masa hannunta. Kama hannun ya yi ya ƙarasa kusa da ita."So kike kiyi mini asarar kanki? Wallahi babu abin da ya haɗa ni da ita. Ƙawar Marwana ce, kuma kin san zan iya komai a kanta. Wannan dalilin ya sanya har na ba ta jinina, don na faranta mata." "Ka yafe mini mutuwa zan yi, sannan ka kula mini da Little Marwana. Ka tuna da alƙawarin da ka yi mini cewar ko na mutu ba za ka ƙara aure ba. Ina mugun sonka, don Allah kar ka auri ko wace 'ya mace. Ka jira mu yi rayuwarmu a Aljanna." "Ki bar wannan maganar ba za ki mutu ba. Za ki haifa mini yarona kuma ki raine shi da hannunki." "Lokaci ya ƙure ka yafe mini." Ta ce tana kallonsa sai kuma ta fara jijjiga. Kallon lamarin suke kamar wasa, amma sai suka fahimci ya wuce lamarin wasa. Ya ruɗe iya ruɗewa ganin da gaske yana shirin rasata. Yana tsaye a gurin kamar gunki aka canza mata kaya. Miƙa masa takkadda aka yi ya sanya hannu. Idanunsa suka kaɗa suka yi jajir, hankalinsa ya tashi matuƙar gaske! Ya kama hannunta ya riƙe, daidai lokacin da aka gungurata zuwa cikin ɗakin. Tsayawa a gurin ya yi hawaye yana bin ƙuncinsa. Sun yi jugum-jugum har da Marwana, da take jin kamar ta rufe idanunta ta zama lamarin da wasa. Kusan awa ɗaya suke tsaye ba tare da kowa ya fito ba. Ganin haka hankalinsa ya tashe, domin a wancan aikin da aka yi mata, uwar haka tuni an fito da ita. An nuna masa Marwana har ya yi mata huɗuba. Tsoro fargaba da damuwa suka cika masa zuciya. Suna tsaye a gurin har lokacin da likitan ya fito. Ganin yadda ya yi kace-kace da jini gabansa ya faɗi. "Doctor, ya take?" Suka yi masa tambayar cikin tsananin tashin hankali. "Please, ku shiga tana son ku yi bankwana, saboda we tried our best, but unfortunately we couldn't, saboda kafin mu yi mata aikin ta haihu." "No," Ya ce yana matsawa sai kuma ya riga ya shiga ciki, daidai lokacin da su Mommy suka shiga. "Batula," Ya kira sunanta tare da riƙeta ba tare da ya damu da jinin da yake zuba ya ɓata jikinta ba. "Kaga maganar da nake maka na cewar ba za mu rayu tare ba ya tabbata? Mutuwa zan yi! Jikinsa ya ba ni ba zan rayu ba, don Allah ka ɗora mini abin da na haifa a jikina, ka nuna mini shi." Idanunsa ya kai kan jajirin da yake ta kuka yana neman nono. Hannu Mommy ta sanya ta ɗauko.mata, ta ɗora mata shi a saman ƙirjinta. "Kin haifi ɗa namiji." Murmushi ta yi tana kallon yaron."Allah ya yi maka albarka. Za ka rayu cikin maraicin uwa, amma na san mahaifinka zai kula da kai." Ta ce tana nuna alamun a ɗauke shi daga jikinta. "Ina little Marwana? Don Allah ku kawo ta mu yi bankwana." Ta ce tana kallonsa. Matsawa ya yi kawai yana kallon ikon Allah. Tunawa da ya yi mahaifinsa da zai mutu, haka ya rinƙa ba shi wasiyya. Tun yana ganin wasa yake yi, amma tafiyar da ya yi kenan, wanda har yau bai ƙara ganin sa ba. Mommy ta fita cikin kuka tana kuka. Kallon da ta yi mata ya tabbatar mata da sai wani ikon Allah. Little Marwana ta ɗauko ta zo ta ɗora ta kan jikinta. Hannunta ta kama tana murmushi."Allah ya yi miki albarka." Ta ce tana kallonta hawaye yana zuba a ƙuncinta. "Don Allah ku ɗauke sa, ƙirjina zai fashe." Da sauri ya janye ta ganin tana tari. Jini yana ta zuba. Iya ruɗewa sun ruɗe. Kuka suke yi sosai hankalinsu ya tashi matuƙa. Duk yadda suke ɗaukar lamarin ya wuce wasa. Damir da ya ga numfashi yana ƙoƙarin bankwana da gangar jikinta. Ƙara ya saki cikin tashin hankali. Da sauri likitoci suka yi kan kanta. "Da gaske mutuwa za ki yi? Don Allah kar ki mutu ki bar ni." Ya ce yana miƙa hannunta. Da ƙyar likitocin suka yi nasarar fita da shi suka rufe ƙofa. Tari ta fara tana faɗin,"Ruwa ku ba ni ruwa zan sha." Na take jikinta ya rikice. Bayan fitarsu Nasreen ta shiga cikin tsananin tashin hankali. Ahmad shi ma tsaye ya yi yana mamakin lamarin. "Ya Ahmad, anya ina da sa'a a rayuwa? Dubi yadda suka shiga cikin damuwa saboda sun taimaka mini?" Ta yi masa tambayar tana zare idanunta kamar taɓaɓɓiya. "Ki yi shiru in sha Allahu, komai zai wuce." Ya ce cikin damuwa yana kallonta. "Wayyo Allah na! Da na sani da ban kira ta ba, wallahi na yi ta kiranka, amma wayarka a kashe. Don Allah ka je ka basu haƙuri su daina faɗa" Kama hannunta ya yi ya riƙe yana rarrashi ganin yadda take ta kuka. Kwanciya ta yi tana ta kuka, tana ganin duk abin da ya faru laifin Faruk ne. Da ace ya kula da ita babu wacce za ta kira. Tausayin Marwana ya kamata tana tunanin halin da take ciki. Duk iya ƙoƙarin su, na son dawo da numfashinta da ya ɗauke sun gaza. Doctor Fadil ya janye mata oxygen da aka sanya mata bayan ya sanya farin ƙyalle ya rufe mata fuska. Kallonsa ya yi kamar zautacce yana faɗin,"No! No doctor, ka da ka furta mini matata ta mutu? Don Allah kar ka ce ta mutu ta bar ni?" Ya yi masa tambayar yana jijjiga shi. "Am so sorry to say, matarka Allah ya yi mata ras..." "I said no! Batula ba za ta mutu ta bar ni ba." Ya furta tare da ƙwala ƙara. Ƙarar da ya ƙwala sai da asibitin ya ɗauka. Nasreen hankalinta ya tashi matuƙa. Zabura ta yi za ta fita."Ba za ki iya fita ba, sam ba ki da ƙarfi." "Don Allah ka bar ni na je, Allah ya sa matarsa ba ta mutu ba, a dalilina." Ta ce masa tana kuka. Kamata ya yi ya kwantar yana rarrashinta. Kuka take sosai kamar ranta zai fita. Tunani take innhar matarsa ta mutu zai yafe mata kuwa? Jin ihunsa ya sanya suka sheƙo da gudu zuwa ciki. Ganinsa zube a ƙasa ya sanya suka fahimci ta mutu. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! 😭 Batula Allah ya jikan ki." Ta furta tare da ƙarasawa gurin ta tana kallonta. Jin abin da ta ce wani irin zabura Marwana ta yi. Hankalinta ya tashi matukar gaske. Gani take yi lamarin kamar a mafarki. Ƙarasawa ta yi inda take kwance babu numfashi."Anty Batula," Ta ce tare da ɗaya ƙyallen da aka rufe mata fuska. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Ta furta sai ga ta a ƙasa babu numfashi. Gabakiɗaya sun rufe sun shiga cikin tsananin tashin hankali. Kuka suke yi sosai suna gani kamar za ta farfaɗo. A lokacin da ya farfaɗo ya karasa kan gadon. Tsayawa ya yi yana kallon ta tamkar ya zauce."Yanzu tafiya kika yi kika bar ni? Dama da gaske ne kike gaya mini ba za mu rayu har abada ba? Batula don Allah ki tashi ni da Little Marwana muna buƙatar ki." Ya faɗa yana girgiza ta. Ganin ta ƙi tashi sai kuma ya je ya ɗauko jaririn ya ƙara mata jikinta. "Kin ga yana kuka ko? Ki tashi ki ba shi nono." Kuka suke yi sosai suna kallonta. Lailai rai ba a bakin kowa yake ba. Duniya kenan kana ciki yau babu kai. Ga Batula ta tafi ta bar su a cikin wani yanayi. Jin kukan ya yi yawa ya sanya Ahmad fitowa. Tsananin ruɗani da tashin hankali ya shige shi. Duk da ba a mamaki da mutuwa, amma sai da mutuwarta ta buge shi. Ɗaki ya dawo ya samu Nasreen tana ƙoƙarin miƙewa."Ki koma ki kwanta sai haƙuri. Allah ya yi wa matarsa...." "No, Ya Ahmad!" Ta furta tana toshe kunninta. "Don Allah don Annabi, kar ka ce mini na zama sanadin da matarsa ta mutu? Kaicona! Ba ni da amfani a duniya. Da ma ni na mutu ba ita ba." Kuka take yi sosai ta kasa daina surutu, sai sumbatu take yi. Ahmad tun yana rarrashinta har ya ga ji ya zuba mata idanu, yana mamakin faruwar lamarin. "Ya kamata Ku ɗauke ta don kuke ku yi mata sutura." Likitan ya furta yana kallonsu cikin tausayawa. Cikin mota aka sanya gawar. Har suka isa gida Damir yana jin lamarin kamar a mafarki. Tamkar mutum-mutumi ya dawo. Babu um babu a'a sai kallo. Ita kanta Marwana ji take kamar ta mutu, ganin lamarin duk ita ta zamo silar faruwarsa. Kuka kuwa tun tana yi har idanunta suka ƙafe. Kafin kace me mutuwarta ta zaga duniya. Yan'uwa da abokan arziki suka fara zuwa cikin tsananin tashin hankali. Masu kuka na yi masu salati na yi. Damir zama ya yi ya tasa gawar da ido yana kallo. Shi har yanzu ji yake kamar ba ta mutu ba. Ya tuna a darenjiya da ta shayar da shi madarar ƙaunarta, da safe ma haka suka kasance cikin farinciki. In ya tun haka sai ya rintse idanunsa yana jin tsanar Nasreen. Ba ita ba hatta mai sunan da ya fara da harafin sunanta, ba ya kaunar ya gani. Ya yi kuka har ya gaji duk dauriyarsa. Bai ƙara shiga cikin tashin hankali ba, sai da aka ce ya shiga ya yi bankwana da ita. Anan ya mike yana mazurai."Na rantse babu wanda ya isa ya fitar mini da matata, saboda ba ta mutu ba, tana numfashi ku lura ku gani." Ya ce yana ƙoƙarin janye likafanin. "Ka yi haƙuri ka ɗauki ƙaddara, amma ta riga mu gidan gaskiya." "Babu wanda ya isa ya ɗaukar mini mata, duk wanda ya ɗauke ta sai na kashe shi." Ya karashe maganar yana kallon abokinsa da ya furta maganar. Kama hannunsa ya yi suka ƙarasa inda take kwance."Ka yi mata addu'a dole a kaita makwancinta." "Nazir, kai ma ka yadda Batula ta mutu?" "Ka yi haƙuri lokacinta ya yi." Ya ce tare da kama hannunsa ya kai shi har gurin. Durƙusawa ya yi ya fashe da kuka."Batula, kin ga ana son a raba mu? Don Allah ki tashi ki gaya masa ba ki mutu ba." Ganin shiru babu magana ya sanya shi sakin kuka." Da gaske kin mutu? Ba za mu rayu tare ba?" Da ƙyar ya miƙar da shi, sannan aka samu aka ɗaga makarar da su fice. Ganin haka Little Marwana ta riƙe tana kuka tana faɗin,"Mommy, ina za ki je? Daddy za su fita da Mommy." Jin abin da take faɗi ya ƙara tayar da hankalinsa. Ya ƙaraso da gudu ya riƙe makarar. Da ƙara aka samu aka raba shi da gawarta, sannan aka fita da shi. Ganin sun fita ya ƙara zubewa haka Marwana. Rayuwa kenan mai canzawa. Suna cikin farin ciki 'yan awannin da suka wuce, amma yanzu komai ya canza musu. Daga farar takadda zuwa baƙa mara daɗin karantawa. Faruk Tun da suka gama wayar ya kashe wayar yana huci. Rashida ta so daga inda take, ta sanya hannunta ta jawo sa jikinsa. "Don Allah ka share su, kar maganar da suka gaya maka ya ɓata mood ɗin ka." "Ki ƙyale ni da su marasa mutunci. Ni na rasa dalilin da ya sanya suke shiga cikin rayuwar iyalina." Shiru ta yi ba ta ce masa komai ba. Ganin haka ya kwanta akan gadon yana mamakin Nasreen na da ciki, amma ba ta gaya masa ba."Kenan ɓoyewa ta yi sai dai ya ganta da shi kenan?" Ya tambayi kansa cikin tsananin mamaki. Kwanciyarsa ya yi suka yi bacci da ba suka ci bashin sa. Sai kusan sha biyu sannan ya tashi ya yi wanka. Kallon Rashida ya yi, wacce ta fito daga bayin tana share ruwan kanta."Baby, bari na je na duba Nasreen, sannan zan yi wa Anty Asiya maganar tarewar mu." "Ai da ka ƙyale su mu yi zamansu anan." Wani banzan kallo ya yi mata jin abin da ta ce."An gaya miki yayo kuɗin na ke yi, da zan yi rayuwar aurena a hotel?" Fita ya yi bayan ya yi mata sallama. Kwanciya ta yi tana tunanin hanyar da za ta ci kudinsa. Jin abin da ya ce sai ta kalle shi kawai, dama ta san shi da shegen maƙo, don da bikin duk abin da ta ce za a yi sai ya rage kuɗin. Tsananin mamaki ya kamata da bai yi mata kyautar kuɗi ba, saboda maganin da Malam ya ba ta ya tabbatar mata da ingancinsa. Ko da ace bai tabbatar mata ba, yadda ta sha wahala a darenjiya ta san cewa yana da kyau. Tsanannin mamakin maƙonsa ya ƙara kama ta, amma a ranta ta sanya za ta yi maganinsa, duk hanyar da za ta fito, saboda ba zata iya rayuwa babu kuɗi ba, watakila kuma don bai san inkiyar sunanta Rashida lashe money ake kira ta ba. Tsakaninta da kuɗi akwai amana domin in har kana dasu sam baka da damuwa. Kudi kenan abokan harka. In har yana tarawa ba ya kashewa. Ita za ta koya masa yadda zai kashe. Wayarta ta ɗauko tana son kiran Malam. Sam zuwa gurin Nasreen da ya ce zai yi, bai dame ta ba, tun da ba ta a gabansa. Asalima ba ta jin kishinta, musamman yadda yake kusheta. Kamar yadda yake gaya mata ƙaddara ya sanya ya aureta, ta yarda da hakan, saboda kamarsa ɗan gayu babu yadda za a yi ya zauna da irinta a yadda yake fasaltata da kalmomi irin kucaka ƙazamiya wacce ba ta iya tarairayar namiji ba. Faruk hon ya rinƙa yi a ƙofar gidan domin a tunaninsa ta dawo. Ganin ba a buɗe ba, ya sanya shi fitowa ya sanya ɗan makullinsa ya shiga. Tsananin mamaki ya kama shi ganin bushashshen jini a ɗakinta. Fita ya yi zuwa falo ya zauna. Wayarsa ya zaro ya kira numbarta. A wannan lokacin tana cikin halin gaba kura baya siyaki. Tun da ta ji Batula ta rasu, sai da ta yi suma.ya fi a ƙirga. Ahmad hankalinsa ya tashi. Shi kansa mutuwar ya gigita shi. Yana rungumeta da ita wacce ta fita hayyacinta. "Yanzu da gaske ta mutu? Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Kaicona sun yi mini alkhairi na saka musu da tsiya." Ta ƙarashe maganar da sakin razanannen kuka. "Nasreen, don Allah ki natsu wani bai isa ya kashe wani ba. Lokacinta ne ya yi. Ki duba halin da kike ciki." Ganin duk rarrashinta da yake yi, amma ta ƙi kwantar da hankalinsa ya sanya shi kiran gida. Mama da Zainab suka zo cikin tashin hankali. Fita ya yi daga asibitin cikin tashin hankali. Lamarin ya ruɗa shi. Ofishin likitan ya shiga don ya bukaci ya ba su sallama, domin fitar da ita daga asibitin kawai zai sanya ta kwantar da hankalinta. WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 17 Fita ya yi daga asibitin cikin tashin hankali. Lamarin ya ruɗa shi. Ofishin likitan ya shiga, don ya bukaci ya ba su sallama, domin fitar da ita daga asibitin kawai zai sanya ta kwantar da hankalinta. Bayan fitarsa Faruk ya kira wayarta. Mama ta sanya Zainab ta ɗaga wayar.Tambayar da ta ji ya yi mata, ya sanya ta kalleta daidai lokacin da ta gaya masa."Dama wannan mara mutuncin bai zo asibitin ba?" Ta yi mata tambayar tamkar tana asibitin. "Ban sani ba mama, ya dai tambaye ni kuma na gaya masa." "Mai ya sa kika gaya masa?" Ahmad ya faɗa daidai lokacin da ya shigo ya ji abin da take faɗi. Tsuru-tsuru ganin haka ya kalli Mama ya zauna gefenta ya ce,"Wallahi ban ga amfanin zama da Faruk da Nasreen take yi ba. Ya sake ta mana rabuwarsu ya fi kawai. Tun da ya yi aure Allah ya ba ta wanda ya fi shi. Da ace ya kula da ita da duk abin da yaru bai faru ba." "Kai innalillahi! Wallahi lamarin bai yi daɗi ba. Kuma da gaske matarsa ta mutu?" "Eh, dama tsohon ciki ne da ita, kuma likitocinsun gargaɗe ta, kar ta sake ta haihu a gida. Da zarar cikin ya shiga watannin haihuwa za a cire mata. Dalilin mijinta ya bawa Nasreen jini kishi ya sanya naƙuda ta tashi. Kamar wasa ta haihu ta rasu." "Kai mutuwar kenan? Rai ba a bakin komai yake ba." Mama ta ce cikin kaɗuwa. "Ki bari kawai Mama yau na shiga cikin tsananin tashin hankali. "Allah ya yi mata rahma, amma babu abin da za mu yi suga farincikimu, kuma ya kamata mu je musu ta'aziya?" "Ai ya zama dole."Ya furta cikin damuwa. Ya buɗe baki zai yi magana, sallamar Faruk ya katse shi. Da sauri ya miƙe ya ƙarasa ƙofar ya dakatar da shi. "Uban me ka zo yi?" "Ban gane ba? Matata na zo gani." Ya ce masa yana harararsa. "Ka san Allah ba za ka shiga cikin ɗakin nan ba, kuma a yau sai ka rubuta saki ka bata." Jin abin da ya ce ya ɗaga murya ya ce,"To sai na ga uban da zai sanya na saki matata. Banza wawa kawai don na taimaka ina zaune da ita. Karka manta amarya na yi jiya, in har na sake ta ita ce da wahala. Yarana kawai na ke tausayawa, amma kai ka san babu abin da zai sanya na ci gaba da rayuwa da bagidajiyar ƙanwarka." Jin a bin yake faɗi sai kawai zuciya ta kai shi ya shake shi. Dabbe suka fara kicikici. Dama Ahmad jiran ranar yake, don haka ya fara aika masa da nushi. Ganin suna shirin illanta juna Mama ta wanka wa Ahmad mari."In har ka ƙara kai masa nushi ban yafe maka ba Ahmad." Ta faɗa cikin Muryar kuka. Cak ya tsaya yana huci, ganin haka Faruk galla masa harara, yana mai da numfashi. Nasreen da ta lallaɓo ta zo gurin da suke faɗan. Rushewa da kuka ta yi tana kallonsa."Laifin me na yi maka Faruk? Ka zaɓi ka cutar da zuciyata? Ka san a rashin ƙular da ka kasa bani halin ƙuncin da na jefa kaina kuma na sanya wadanda suka taimake ni? Saboda me ba za ka iya ba ni jininka ba? Alhalin akwai wani can wanda babu dangantaka zai iya. Yayan Marwana ya ba ni jininsa wanda hakan ya sanya matarsa ta mutu. Mai na yi maka da ba ka sona? Don Allah ka sake ni Faruk. Na gwammce na fuskanci ko wace irin rayuwa, da na zauna da kai ba ka san daraja ta ba." Kallonta ya yi cikin tsananin kishi jin wani ya ba ta jininsa. Hannunsa ya sanya ya shaƙeta ba tare da ya kula da halin da take ciki ba."Kika bari aka sanya miki jinin maƙiyina? Na gaya miki na tsani family ɗin su, a dalilin ƙanwarsu da take son ta ɓata miki tarbiya. Tun ranar da kika hadu da ita na rasa gane kanki. Wallahi kin ji na rantse miki sai na je na ji dalilin da ya sanya ya ba ki jininsa, kuma sai na sanya hukuma ta hukunta shi. Daga yau zan sanya ayi miki tsakani da su, domin na lura in har kina tare da su. Kwaɗayinki ba zai bari mu zauna lafiya ba." Mamaki, takaici, da haushi suka kama su jin abin da ya ce. Ahmad ya kalle shi ya ce,"Kai dabban ina ne ne? Taimakon da suka yi mata sai ka ɗauke shi da mummunar manufa. Idan ka kasa kula da matarka ka ba ta jini, sai aka gaya maka kowa zuciyarsa mara imani ne kamar kai?" "Wallahi ban yarda ba, ai dama tuntini na fahimci tana kula wasu mazan, saboda innba kuka shi take yi ba, babu yadda za a ya rinƙa ba ta kyauta." "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Na shiga uku Faruk ka san babu kyau zargi a aure ko?" "Ke zan gaya ma haka don ki san darajar aurenki." Ya ce mata yana zare mata ido. "Faruk ka sake ni na gaji da zama da kai. Wallahi ka ji na rantse maka ko kai ne autan maza na gama zama da kai. Am done in this hell that you call marriage." Wata 'yar iskar dariya ya saki."Ok, na sake ki don ki je ki auri ɗan iskan nan ko? To da na yi ninyar sakin ki, amma kin ji na rantse miki ba zan sake ki ba, sai na tabbatar da babu abin mora a jikinki. Sai na wulanƙa ta rayuwarki, ta yadda babu namijin da zai iya kallon ki har ya yi sha'awarki..." "Wallahi ba ka isa ba sai ka sake ta yau." Ahmad ya ce yana gyara hannun rigarsa. "To uban da yake iko dani sai ya yi mini dole. In har kuma son na sake ta, sai ku biya ni tas bashin mahaifinku da yake karɓa sannan kuma ku biya ni duk abin da na kashe, domin tun da na aure ta ban mori komai ba, sai uban yara da ta tara mini." Tsananin mamaki ya kama su, ganin tozarcin da yake musu ya sanya suka kasa ce masa komai, har ya fice yana takun taƙama. "Ya Allah ka ɗauki raina don rayuwata babu amfani." "Kar ki ce haka Nasreen ki yi addu'a." Mama ta ce mata Ahmad kuwa ya kasa cewa komai zama ya yi cikin tashin hankali. Jikin Mama ta faɗa ta rinƙa kuka tana jin kamar zuciyarta za ta fito waje. Ƙirjinta wani irin zafi take mata sam ba ta da amfani a cikin duniyar. Faruk na fita kai tsaye ya fara neman gidan su Damir. Saboda tsananin kishi ƙirjinsa har tafasa take masa. Ya san cewa yana sonta tun da ya ganta soyayyarta ta hana shi sukuni, amma mugun halinta da ta kasa bin duk abin da yake so, ya sanya shi wulaƙanta rayuwarta. Kasancewar gidan na su ba ɓoyayye bane, sam bai sha wahala ba. Ɗaya daga cikin ɗan sandar da ya ɗauko ya kalle shi cikin tsananin razana. "Dama wannan gidan ka ce mu zo mu kama mai gidan?" "Eh matata yake bibiya ku kama mini shi, sannan ku yi masa warning na yi alkawarin biyan ku ko nawa ne." Shiru ya yi yana tunani amma jin ya ce zai biya su, sai ya ɗan samu ƙarfin gwiya. Parking suka yi a ƙofar gidan. Ganin taron mutane sai jikinsu ya yi sanyi. Kamar rasuwa aka yi a gidan?" "Ban damu ba ko uwarsa ce ta mutu. Don ayi rasuwa sai ku kasa kama mai laifi? In ɗan kidnapping ne uwarsa ta mutu ba za ku kama shi ba?" Ya yi musu tambayar a fusace yana zare idanu. "No ba haka na ke nufi ba." Ya furta cikin sanyin murya yana kallon da. "To kamar haka ne ka san dai hukuncin wanda yake bin mace da aure?" Ɗaga masa kansa ya yi ba tare da ya ce komai ba, suka nufi ƙofar gidan jikinsu a sanyaye. Damir da yake ƙofar gida yana karɓar gaisuwa. Tun lokacin da aka yi rasuwar ya zama kamar mutum-mutumi. Kallon mutane kawai yake yi ya kasa ce musu komai. Idanunsa sun canza sun yi jajur. Ganin motar 'yan sandar gabansa ya faɗi. Kasancewar bai taɓa ganin Faruk ba. Wannan dalilin ya sanya shi tunanin dalilin da ya kawo su. Da fari ya ɗauka gaisuwa suka zo, amma bayan sun yi masa gaisuwar sai suka kalle shi." Don Allah nuna son yin magana da kai, saboda wancan ya turo mu don ka zo ayi maka tsaka Ni da matarsa Nasreen. Ya ce yana zarginka da bibiyar matar..." "What!" Ya ce yana zare idanu."Am sorry ba wani babbar magana ba ce. Cewa ya yi so yake kawai a ja maka kunni kar ka ƙara shiga lamarin matarsa." Ransa ya ɓaci idanunsa suka firfito. Hawaye kawai yake yi yana mamakin da ga taimako ya sa ya rayuwarsa cikin tashin hankali. Matarsa ta rasu ranta a dalilin haka, kuka yanzu mijin ta yana zargin sa da bibiyar matarsa. Jiri ne ya ibe shi ya dafe mota da sauri yana karanto duk addu'ar da ta fito bakinsa. Ganin yadda ya birkice. "Please Yaya Damir, take easy bari na je na yi musu magana." Ƙaninsa Fadil ya ce yana ƙoƙarin kama shi. "No, kar ka damu." Ya ce masa tare da ture hannunsa ya nufi inda Faruk yake yana aika masa da mugun kallo. Kallo kallon suka yi wa juna. Kowa tsana ce ƙarara a fuskarsa. Kallo ɗaya suka yi suka tsani juna. Ji suke yi da za a basu takubba don kare kai, ko wane zai iya kaiwa abokin gabarsa farmaka da ninyar kai sa kushewa. Faruk ya bi shi da kallon tsana. Mamaki yake yi har ya kula Nasreen kuma ya ba ta kyautar jininsa. Wani irin kishi ya lulluɓe shi. Sai ya bi shi da wuƙa yana jin tamkar ya sassare shi da wuƙa. Damir kuwa mamaki ya kama shi ganinsa wayayye. Saboda halin da yake ciki sai kawai ya kalle shi tare da ɗauke kansa. "Ba zan iya zuwa ofis ba ina karɓar gaisuwar matata." Ya furta cikin karayar zuciya. "Eh, ku yi masa tsakani da matata." Faruk ya ce yana zare idanu da kumfar baki. "Shi kenan in sha Allahu ba zai ƙara ganina ba, kuma matarsa ba zan ƙara shiga lamarinta ba." Ya ce tare da juyawa. Harara Faruk ya bi shi da shi har ya shige cikin gidan. Damir yana shiga cikin ɗaki kai tsaye ɗakinsa ya wuce. Gilas ya ɗauka ya yi jifa da shi. "Mai ya sa kika shigo rayuwata don ki tarwatsa mini farincikina? Ashe taimakon ki zai zame mini rashin alkhairi? Haƙiƙa kin cancanci a kira ki tauraruwa mai wutsiya. Na tsane ki Nasreen ko a mafarki bana fatan Allah ya haɗani dake." Sai ya fashe da kuka cikin tsananin tashin hankali. Mommy ta kama shi ta riƙe ganin ya ji wa kansa ciwo."Haba Damir ka zama mai imani da hakuri." "Mommy taimako yana zama laifi? Mijin ta ya kawo 'yan sanda ayi mana tsakaninsa ita, wai ina bibiyar matarsa!" "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Wannan wane irin musiba ce? Yarinyar nan wallahi in har Marwana ta ƙara hurɗa da ita sai dai ta nemi wata uwar. Yarinya ta zamar mana baƙar daga tauraruwa mai baƙar wutsiya!" Marwana da take bakin ƙafa tana jin abin da Mommy nta ce, sai ta fashe da kuka. Kuka take yi sosai tana tunanin halin da take ciki. Mommy da ƙyar ta rarrashe shi sannan ta fito. Marwana ta gani a tsaye a bakin ƙofar tana ta kuka. Wucewa ta yi ba tare da ta ce mata komai ba. Zama ta yi ta ɗauki Little Marwana da ta samu bacci ya ɗauke ta. Nasreen da aka ba ta sallama Ahmad gida ya wuce da ita. Kuka sosai take yi har suka isa gida. Da suka isa gida ɗaki ta shige ta kwanta. Kanta ke ciwo ga cikinta da har yanzu yana mata ciwo. "Rayuwata ba ta da amfani Allah ka ɗauki rayuwata na huta." Ta ce tana share hawaye. Kafin wani lokaci kanta ya ɗauki zafi sosai, tamkar tukubar mai tsire. "Nasreen, ki sha magani ki samu ki ji sauki, gobe mu je mu yi musu gaisuwa." "Mama, ku je kawai ba zan iya ƙara ƙara hada idanu da su ba. Sun yi mini alkhairi na zamar musu tauraruwa mai baƙar wutsiya." "Duk abin da kika ga ya faru haka. Allah ya ƙaddara. Duk abin da za su ce, ai ya zama dole mu je mu yi musu ta'aziya." "Kai innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Ta ce tana rintde idanunta. Da daddare sun kasa bacci sai tunanin lamarin suke yi, musamman ita da take ganin duk abin da ta faru a sanadinta ne. Ahmad kuwa tunanin hayar da zai ɓullo wa Faruk ya sake ta yake yi. Ya san cewar baƙaramin daru za a yi ba, kafin Baba ya amince ta zauna a gidan, amma a wannan karon duk abin da zai faru sai dai ya faru. Ya shirya don ya shanye duk wani wulaƙanci. Ko da ace Faruk zai nace sai ya biya shi, zai je ya samu ko bashi ne ya biya shi, don ya saketa. Da safe Baba ya shigo ɗakin. Tun daren Faruk ya kira shi ya sanar masa da duk abin da ke faruwa. Ya kuma yi masa barazana da ya biya shi kuɗinsa kaf. Hankalinsa ya tashi tunawa da ko wata ba a yi ba, da ya aro naira dubu talatin, kafin ya bashi kuɗin ba kalar tozarta da bai yi masa ba, amma ya haɗiye. Ya je ofis ɗin da ya fi a ƙirga kafin ya ba shi kuɗin. Babu babu irin tozarta da bai yi masa ba, amma ya jure har sai da ya ba shi. A yanzu cikin kuɗin ba ya tunanin ko dubu uku za a iya samu. Barazanar da ya yi masa kan ya dawo da kudin ya tayar da hankalinsa. Fuskarsa babu rahma ya shigo. Mama tana zaune tana ba Musaddik koko da ta gama damawa. "Mai Nasreen take yi a gidan nan?" Ya furta cikin ɗauke fuska ba tare da ya amsa gaisuwar da ta yi masa ba. WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 18 "Mai Nasreen take yi a gidan nan?" Ya furta cikin ɗauke fuska, ba tare da ya amsa gaisuwar da ta yi masa ba. "Maganar mai tsawo ne zama ya kamata ka yi." Ta ce masa cikin tashin murya. "Na zauna saboda me? Abu ɗaya na sani kishi ya sanya ta dawo, kuma wallahi kin ji na rantse, ba za ta zauna a gidan nan ba. Ai na gaya miki duk yarinyar da na aurar, babu ita babu zawarci a gidana. Ke kishiya nawa aka yi miki? Amma kin mutu ne? Saboda baƙin kishi har ta ɓarar da cikinta." Ba ta yi mamakin abin da yake faɗi ba, don ta san Faruk ya gaya masa ƙarya da gaskiya. "Lamarin nan da kake gani ya wuce wasa. Inda ka san abin da ya haifar da sai ka yi mamaki." "Ta ya ya zan sani tun da ba kwa shawara da ni? Kin mayar da ni mara amfani, saboda ba na ciyar daku." Shiru kawai ta yi, tana girgiza kanta don ba ta san inda za ta fara ba, amma kuma sai ta daure ta ce,"Faruk ba ya kyautawa, a sanadin rashin ƙular da yake ma ta ya janyo matsalo..." "Kin ga ko kai mai za ki ce babu ruwana, abu ɗaya na sani ba za ta zauna mini a gida ba." "Baba, wallahi ka ji na rantse Nasreen ba za ta koma gidan Faruk ba, a wannan karon na fito na shirya zan ja da koma waye, don ya ba ta takaddarta. Ko da ace ba shi zan ciyo sai na biya shi sadakinsa." "Au iyye lailai wuyanka ya isa yanka. Fito na fito za ka yi da ubanka, anya Ahmadu kai ɗan kirki ne?" Ya yi masa tambayar cikin tsanannin mamaki yana kallonsa. "Ka yi hakuri da abin da zai faru, amma bana tunanin akwai abin da zai sanya na janye ƙudirina." "Haka kace? To shikenan mu zuba shege ka fasa." Ya faɗa tare da zabga tsaki ya juya ya fita. Cikin takaici ya ƙaraso gurinta da take kuka kamar ranta zai fita."Ki yi shiru ki daina zubar hawayenki. Da yanzu in sha Allahu in har ina raye, na yi miki alƙawarin babu wanda zai ƙara sanya ki zubar hawaye." Ya ce mata tare da kama gefen hijabinta yana share mata hawaye. "Yaya, dole na koma saboda Faruk, ba zai sake ki ba sai an yi masa hulɗi, kuma ka ga bamu da kuɗi." "Kar ki damu da wannan duk inda kuɗi yake zan nemo. Akwai aikin da oganmu yake sanya ran samu a kudi. In sha Allahu zan bi shi don na samo kuɗin." Kallonsa ta cikin tsananin ƙauna."Na gode Ya Ahmad, Ubangiji ne kawai zai biya ka." Murmushi ya yi jin abin da ta ce."Ki samu kisha ruwan koko, sai ki shirya mu je musu gaisuwa." Girgiza kanta ta shiga yi cikin zubar hawaye."Ba zan iya ƙara haɗa idanun da wadannan mutanen ba, domin sun yi mini alkhairi na saka musu da tsiya. Ku je kawai zan kasance ina yi wa matarsa addu'a har tsawon rayuwata." "Nasreen, ki taɓa ganin wanda ya kashe wani ba tare da lokacinsa ya yi ba? Allah kawai yake da ikon ɗaukan ran bayinsa, domin shi ne ya halicce su. Lokacin mutuwar bawa Ubangiji ya riga ya tsara ta tun kafin zuwan mu cikin duniya. Ko wace mutuwa da sanadinta a rayuwa." "Na sani Yaya, amma sam ba za su fahimta hakan ba. Ni ce na yi sanadin mutuwar matarsa. Na san cewa a yanzu ba shi da abin da ya tsana sama da ni. Na zama baƙar daga na sanya rayuwarsu cikin damuwa. Marwana kullum burinta ta sanya ni farinciki, sai ga shi na sanya su a cikin ƙuncin da za su dauwama a cikinsa." Ta ƙarashe maganar tana kuka sosai. Miƙewa ya yi, yana kallon ta ganin rarrashinsa bambaki ba za su yi mata ba."Ko mai za ki ce dole mu je musu gaisuwa, don haka ki gama karyarwa ki shirya bari na yi wanka." Idanun ta bi shi da shi, ta kasa cewa komai har ya fita. Tun da ya gaya mata zuwa gaisuwar gabanta yake faɗi. Kunya sosai take yi, tana tunanin tarbar da za su musu. A ranta ta yi dana sanin haduwa da Marwana ya fi kwando masaki. Cikin mutuwar jiki ta gama shiryawa. Tana cikin uwar ɗakar Mama ta yi zugum hawaye yana bin ƙuncinta. Ahmad ya je ya samu tashar napep suka hau. Tun da suka shiga suka yi shiru. Babu wanda ya yi ko tari, kowa da abin da yake saƙawa a cikin ransa. A lokacin da suka isa ƙofar gidan wani irin faɗuwar gaba ta ji, har sai da ta kama hannun Ahmad ta riƙe. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! 😭 Ta tabbata matarsa ta mutu saboda ni." Ta furta tana kallon get ɗin gidan da ya cika da motoci da mutane. Ganin ta kasa fita daga cikin napep.Ahmad ya sa ya hannu ya kamo ta. Da ƙyar ta ƙoƙarta ta fara taku tamkar 'yar koyo. A haka suka rasa ƙofar gidan cikin tsananin damuwa. Tun daga ƙofar gidan Nasreen ta tsinke da dukiyar da suke da shi. Tsananin mamakin ƙawance su take yi, domin ta san ruwa ba a san kwando bane. Duk da cewar jikin Marwana, kawai mutum zai kalla ya tabbatar da hutu da jin daɗi, amma ko kaɗan ba ta taɓa tunanin suna da kuɗi haka ba. Saboda babu wanda suka sani a gidan, sai suka tsaya a harabar gidan suna raba idanu. Marwana da ta fito, za ta raka ƙawayenta da suka zo mata gaisuwa. Cak ta tsaya tana kallon Nasreen da take tsaye kamar gunki. A hankali ta ƙarasa gunta. "Nasreen," Ta furta cikin sanyin murya. Da sauri ta juyo ta kalle ta. A tunaninta kamar yadda danginta, suke kallon ita ta yi sanadin Batula haka za ta yi, amma sai ta ga ta share hawaye ta rungume ta. "Ya jikin ki?" Tambayar da ta yi mata ya sanya ta fashe da kuka. "Marwana ashe za ki ƙara mini magana? Na ɗauka ke ma kina kallona a matsayin ni na...." "Shit! Kar ki faɗi haka." Ta katse ta tana faɗin haka. Ganin ta yi shiru sai hawaye suke ga zuba daga ƙuncinta ya sanya ta ɗora da cewa,"Kin taɓa ganin wanda ya kashe wani? Anty Batula, lokacin ta ya yi, kuma dama can ba lafiyayya bace, tun kafin ta auri Ya Damir Allah ya ƙaddara sanadin haka za ta mutu. Family ɗina sun yi fushi. Zafin rashinta ya sanya sun ɗauki laifin mutuwarta sun ɗora miki." "Wannan dalilin, yansa ya na ce ba zan zo gaisuwa ba. Ina jin tsoron haɗuwa da Yayanki. Na san cewa ya tsane ni babu wacce ya tsana kamar ni." "Haka ne Nasreen, musamman da Faruk ya zo har gida da 'yan sanda ayi masa kashedin ya daina kula matarsa, amma zuwan ya fi rashin zuwan." Jin abin da ta ce ya sanya ta zare idanunta."Anya Faruk na da imani kuwa? Duk da abin da ya faru kan rashin kula da ni ne?" Ta yi mata tambayar cikin muryar kuka. "To ya za mu yi? Lamarin ya riga ya faru." Shiru ta yi tana kallonta ta kasa cewa komai. Yadda Marwana ta dawo kawai zai tabbatar maka da tashin hankalin da suke ciki. Ganin ta kasa cewa komai sai ta kama hannunta. "Ku zo mu shiga ciki ku yi musu gaisuwa." Tamkar waɗanda aka zare musu lakka haka suka shiga ciki. Damir yana zaune da hoton Batula ya riƙe yana hawaye. Hannunsa ɗaya kuma Little Marwana da take ta yi masa kuka tana kiran Mommy. Hawaye yake yi sosai. Ya kasa cewa komai, domin shi kansa da ace akwai wanda zai kwanta a jikinsa ya yi ta kuka yana rarrashinsa hakan zai yi, don ya samu sauƙin zafin da zuciyarsa ta ke yi. Ya san cewa lokacinsa shi ma ya yi, domin ba zai iya rayuwa babu Batula ba. Yarinyar da ya so kamar ransa. Tun tana ƙaramar Allah ya sanya masa tausayinta saboda wahalar da take sha na ciwo. Daga baya ta riƙe ta koma soyayya. Yau ga shi ta yi masa nisa. A sanadin taimakon wata can ya rasa masoyiyarsa. In ya tuna hakan sai ya ji ba zai taɓa yafewa kansa ba. Ya yi kuka har ya ji babu daɗi, in ya tuna cewar da shi da Little Marwana sun zama marayu, sai ya ji duniya da abin da ke cikinta sun gimshe shi. Haka nan rayuwar sa za ta ƙare, domin ya yi mata alkawarin ba zai taɓa aure ba. Zai yi ta zama haka har Allah ya ɗauki rayuwarsa ya koma ga Allah. Jin sallama ya sa shi da Mommy suka ɗago kansu. Zubbur ya miƙe yana nuna ta da hannu. "Mai ya kawo ki gidan nan? Ki kin zo ki kashe ni ne?" Jin abin da ya ce yana nuna ta ya sanya ta tsaya cak, tare da ɓoyewa a bayan Marwana. "Ya Dam...." "Please shut up!" Ya daka mata tsawa yana faɗin haka sannan ya ɗora da cewa,"Kina tunanin akwai malaman da zai sa ya na ƙara kallonta da tausayi? Marwana a sanadinta na rasa matata wacce na ke so fiye da komai. Mai kike so ki gaya mini?" Shiru ta yi tana hawaye ganin yadda yake magana cikin tsawa tana zare idanu. "Fita da ita kuma ki gaya mata kar ta ƙara shigowa gidan nan, don ko a lahira bana fatar Allah ya haɗa fuskokinmu." Duƙawa ta yi cikin kuka ta ce,"Ka yafe mini na san ce...." "Kar ki ce mini komai! Bana son jin muryarki na tsane ki kar ƙi ƙara fatan ki haɗu da ni, domin kin ji na rantse miki haɗuwarmu ba za ta yi kyau ba." Jin abin da ya ce ta fisge hannunta cikin na Marwana ta juya za ta fita. Mama ta gyara murya ta ce,"Mun san cewa haƙuri da malamai ba za su taɓa goge abin da ya faru ba, amma don Allah mu zama musulmai masu yarda da ƙaddara, Allah ya riga ya ƙudurta a za ta mutu, kuma babu makawa sai ya faru." "Don Allah ku fita daga gidan nan don bamu buƙatar ganinku. Marwana ta haɗa zumunci kuma na yi mata gargaɗi in har ta ƙara zuwa inda take sai na yi mata baki." "Subuhanallahi! Haka ba zai faru ba. In sha Allahu Nasreen za ta yi nesa da ku. Mun gode da abin..." Maganarta ta katse sakamakon jifa da ƙaton gilas ɗin ɗakin da Damir ya yi. Kallonsa suka yi cikin damuwa. Kukan da Little take masa ya isa ya mai da shi ƙaramin mahaukaci. Ga kuma jaririn da ta bar masa yana ta tsotsan hannu. "Mommy ki ce musu su fita daga gidannan, in ba haka ba zan iya aikata abin da zai zama dana sani. Zuciyata zafi take yi mini in na ganta. Bana son ganinta na tsane ta."Ya furta hakan yana dage ƙirjinsa, sai kuma ya ruga da gudu kamar zautacce ya ƙara sa gurunta da dake tsaye tana kuka tamkar ranta zai fita. "I hate you whatever you name. Ki fice daga gidan nan, tun kafin na yi ajalinki. I hate you kar ƙi ƙara fatan ki zo inda na ke, domin duk ranar da kika bari muka hadu sai na yi ajalinki." Cikin tsawa yake maganar yana zare idanu, wanda a dalilin haka ya sanya duk idanu suka koma kansu. Ganin haka Ahmad da sauri ya kama hannunta suka fita zuciyarsa na zafi. Faɗawa jikinsa ta yi tana kuka. So take yi ta yi magana, amma ta kasa sai kallonsa take yi, tana haki tamkar ranta zai fita. Shiga cikin napep suka yi ya kwantar da ita a abaya. Ganin yadda ta jiƙe da zufa sai ya cire mata hijabi. "Don Allah ja napep ɗin mu bar ƙofar gidan nan." Ya ce masa cikin dana sanin zuwa. Da ya sani da ya ji maganar ta, amma ga shi zuwan ya haifar da wata damuwar. Sai da suka yi nisa sannan ya umurce sa da ya tsaya. Ruwa mai sanyi ya siya ya ba ta. Babu musu ta karba sai da tasha leda biyu. Da suka koma gida sun yi jugum-jugum suna kallonta da ta kwanta. Idanunta rufe amma ba bacci take yi ba. A ranar ta ita kawai ta san zafin da zuciyarta take yi. Ta yi fatan ace ita mutuwa ta ɗauka ba Batula ba, domin mijinta yana so ta haka dangin mijinta. Sannan duniya ta yi maraba da zuwanta, har ta sanya take kurɓar ruwan daɗi a cikinta, amma ita fa sam babu wanda yake kaunarta. Bayan Yaya Ahmad shi ne ya damu da ita sai mahaifiyarta. Tana kwance cikin damuwa. Ta yi kuka har ta ji babu daɗi. In ta tuna rashin mutuncin da Faruk yake mata, sai ta ji tamkar ta haɗiye kanta ta huta. Tana kwance ta ji sanyi na ratsa jikinta. Ganin ta fara kyarmar sanyi Ahmad ya lulluɓeta. Idanunsa sun ciko da hawaye. A ransa ya ƙudiri ko nawa zai nemo sai ya yi wa Faruk hulɗi ya sake ta. Faruk Ango kasha kanshi kenan. Tun lokacin da ya je gidan su Damir ya yi musu kashedi. Ya wuce hotel kai tsaye. Amarya tana kwance kamar ruwa tana shan baccin gajiya. Da ya shiga ɗakin ya zauna ya kalleta da take jan rago. A hankali ya zauna a gefenta. Bubbuga filon ya yi kamar wanda zai ta shi jariri."Baby na dawo." Ya ce mata yana kashe mata idanu. "Oh darling sannu da zuwa." Ta ce masa tare da miƙa masa hannunta da nufin ya zo su kwanta. Amaimakon ya kwanta sai ya kalleta ya ce,"Ki tashi mu tafi gidanmu." Miƙewa ta yi ta zauna tana kallonsa."Ba ka ce Mahaifiyaarka ta ce sai ka yi mata kayan faɗan kishiya ba?" "Ai ba ta gidan tana gidansu. Bakin shi ya sa ya ta zubar da cikin da take da shi. Ni wallahi murna sosai na yi da cikin ya fita, don ban san tana da shi ba." Jin abin da tace sai ta kalle shi kawai. A ranta mamakin halinsa take yi. Duk yadda take tunaninsa ya wuce haka. Haɗa kayanta ta yi sannan suka bar hotel ɗin. Da suka isa gidan kallon gidan take yi sosai tana ƙara kallonsa. Ta gaya mata Nasreen ƙazamiya ce, amma sam ba ta ga ƙazanta a cikin gidan ba, duk da ya yi gyara. Da ace ƙazamiya ce a gidan dole a ga zahiri. Komai tsaf-tsaf hatta kayan kicin ɗin ta sai da ta yi mamakin tsaftarsu. Abinci ta shirya musu lafiyayyen suka ci cikin farin ciki. Ganin jikin Nasreen ya yi zafi Ahmad ya kaita kyamis. Ƙarin ruwa ya zo ya sanya mata har gida. Ƙarin ruwan da aka yi mata ya samya ta samu sauƙin ciwon da kanta yake yi. Tana zaune bayan an cire drip ɗin tasha magani. Ruwan koko Mama ta dama mata ta samu ta sha. Raihan take ta kallonta cikin tausaawa. Ja yota ta yi ta rungume tana hawaye. "Umma, ki bar kuka za ki samu sauki." Jin abin da ta ce sai ta yi ƙoƙarin tsaida ruwan hawaye dake zuba kamar famfo. Duk bala'in da Baba yake yi, Ahmad ya tsaya kan kaifi ɗaya ba za ta koma gidan Faruk ba. Mamaki ya ke ba shi. Ganin ba ta da lafiya, amma ko sau daya bai leƙo ya gaishe ta ba. Yana mamakin mugun halinsa da ya haife su ya kasa sanin darajar su. Damir Rayuwarsa ta zama abin tausayi domin ya canza kamar ba shi ba. Abin da ya ƙara rikitar da shi. Jaririn da Batula ta bari, cikin dare ya fara zazzaɓi mai zafi bai ɗauki wani tsawon lokaci ba ya koma ga mahallicinsa. Hakan ya ƙara rikitar da shi gabakiɗaya. Ya kasa yarda an yi masa rashina lokaci guda. Har yau ya kasa yarda cewa Batula ta tafi ta bar shi. In ya kalli Little Marwana sai ya ji kamar zai fasa ihu, saboda tausayinta. Yana mugun tausayinta sosai, ganin har yau ta kasa yarda cewar ta tafi ta barta. Kullum kuka take yi masa kan ya kaita gurin Mommy. Ya yi kuka har idanunsa sun ƙafe. Baya bacci sai sallama dare yana roƙon mata yafiya. Ya rame ya susuce ya fita hayyacinsa. Ya tara ƙasumba kamar sabon mahaukaci. Ya daina shiga cikin mutane yana cikin ɗakinta rungume da hotonta yana zubar hawaye. Ganin yadda yake son ya takura kansa in ya kalli little Marwana, ya sanya mommy ta dawo gidan kullum taba sashinta. Gabakiɗayan rayuwarsa ta canza. Damir da aka sanshi da haƙuri da tausayi da girmama mutane, sai ya zama mutum mafaɗaci. Sam ba ya uzuri ga kowa. Ko Marwana da ba ya iya mata tsawa bayan rasuwar rasuwar mari biyu ya yi mata. Ganin yadda ya tashi hankalinsa Mommy ta sanya aka kwashe hotunanta. Hatta wayarsa sai da ta sanya aka goge, amma a banza domin ya adana hotunanta a inda ko da an goge zai gansu. Ganin yana shirin kashe kansa Mommy ta sanya shi a gaba cikin kuka. Lamarin ƙara girma yake yi, domin da ya rintse idanunsa sai ya ga batula tana masa gizo. Ganin haka hankalin Mommy ya tashi kan dole suka koma gidanta. "Damir, ba a mutuwa mahaifinka ya mutu? Allah ya halicci Batula kuma ya ɗauke abinsa. Ka tuna kai ma watarana tafiya za ka yi. Rashin yadda da kaddarar da ba ka yi ba, tamkar kana ja da ikon Allah ne.". Rungume ta ya yi jin abin da ta ce,"Ya zan yi Mommy? Na kasa yarda cewar Batula ta tafi ta birni. Ta yi mini nisa da ba zan ƙara ganinta ba." "Ya za ka yi? Haka Allah ya ƙaddara sai ka yarda da ƙaddarar Ubangiji. Ka yi mata addu'a." WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 19 Rungume ta ya yi jin abin da ta ce,"Ya zan yi Mommy? Na kasa yarda cewar Batula ta tafi ta bar ni. Ta yi mini nisa da ba zan ƙara ganinta ba." "Ya za ka yi? Haka Allah ya ƙaddara sai ka yarda da ƙaddarar Ubangiji. Ka yi mata addu'a." Durƙushe wa ya yi, ya saka kuka kamar ƙaramin yaro."Ki yafe mini Batula, saboda son zuciyata. Na taimaki wata can na bar matata ta mutu! Na san cewa abin da na yi ban kyauta ba, amma ki gafarce ni. Na karashe rayuwa ta ba tare da ƙara aure ba, shi zai sanya ki gafarta mini. Mu yi rayuwarmu a Aljanna. Ni Damir ina ƙara miki alƙawarin, ba zan..." Da sauri Mommy ta sa ya hannu ta toshe bakinsa."Kar ka yi alkawarin da ba za ka ci ba, domin rayuwarmu tana hannun Ubangiji. In Allah ya tsara za ka yi aure, babu makawa sai ka ƙara. Sannan dole ka yi aure ka haifa mini wasu yara. Dubi tarin dukiyar da Allah ya ba ka? Nufin ka ba za ka samu ɗa namiji wanda zai gaje ka ba. Dole ka yi kaffara don ba zaka ƙarashe rayuwarka babu aure ba." "Ba zan iya ba, ba zan iya karya alƙawarin da na yi mata ba. Kuma bayan iya ba zan iya auren ko wace mace ba." "Zan nema maka aure dole ka yi aure! Ka manta alƙawarin da ka yi mini na cika family ɗin mu da zuriya?" "I can't mommy ba zan iya ba." "Ka shirya gobe ka je Companyka ka ci gaba da kula da Company. Duniya babu amana mutane cuta ya yi musu yawa." "Ban damu da na rasa komai ba tun da na rasa Batula. "Ya ce tare da shigewa cikin ɗakinsa. "No dole za ka ci gaba da harkokinka haka rayuwa take, duk yadda muke son wani Allah ya karɓe shi. Kuka da alhini muke yi, sannan mu ci gaba da rayuwa. You have to move on, and start a fresh life." Girgiza kansa kawai yake yi, domin ya san da wuya ya manta Batula, har ya yi farin ciki a rayuwarsa. Kan dole washegari ya shirya cikin riga da wando na shadda sky blue, ya tafi aiki. Duk wanda ya Ganshi sai ya yi mamakin yadda ya koma. Sanin cewa shi ɗan gayu ne wanda ya iya ɗaukar wanka. Ƙasumbar da ya tara shi yafi bawa kowa mamaki. Da isa cikin Company Muhsin ya tuka shi. Yana zaune a baya ya haɗa kai da gwiya. Hawaye yake yi sosai yana jin matsananciyar kewarta. Cikin rashin sa'a suka yi hon a get ɗin babu masu gadin gurin. Damir da zuciya ta tuƙoshi, da sauri ya fice daga motar ya shiga ciki. Daidai lokacin da ɗaya daga cikin masu gadin gurin ya ƙara so. Ba tare da wani dogon nazari ba, ya ƙara sa inda yake ya wanka masa mari, ji kake kau da ƙarfinsa. "Ashe wawaye na ɗauka ban sani ba? Ina biyan ku kudi, amma kin kasa yin aikin ku?" Ya yi masa tambayar yana huci cikin tsananin bacin rai. Da sauri Baba Bala ya kalle shi cikin tsananin mamaki. Ya san wane ne Damir da yadda yake jin daɗin kirkinsa. Matsawa ya yi, tare da dage ƙuncinsa yana mamakin marin da ya yi masa. Yadda ya koma da gashin da ya tara, yansa ya shi matsawa yana tsoro ko rasuwar matarsa ya haukatar da shi. "Ka yi hakuri Yallaɓai." "Ka je na sallame ku duka masu gadin gurin." Ya ce tare da fara tafiya daidai lokacin da Muhsin ya kama hannunsa suka shiga cikin campanin. "Ka yi hakuri Yaya Damir." "Ka tabbatar da ka sallame su." Ya ce masa tare da shiga cikin ofishin nasa. A ranar kowa ya san ba shi cikin hayyacinsa. Duk wanda ya kawo masa aiki zai yi musu fata-fata, duk da cewar daidai suka yi, amma sai ya kafe ba su yi aikin daidai ba. Mari kuwa shi kansa ba zai san mutanen da ya mara ba. Kallon tsoro ya yi ya yi masa a lokacin da ya fatattaki P.A ɗin da yana faɗin,"Nonsense, ka je na sallame ka tun da ba ka iya aikin ba." Kwashe takaddar ya yi cikin tausayi yana kallon sa. Ya san wane ne Damir. Da irin kyautatawar da yake masa. Saboda tausayinsa bai san lokacin da hawaye suka wanke masa fuska ba. Yana fita Damir ya watsa littafin da suke kan teburin."Na tsani kowa da duniyar da na ke ciki. Na fi buƙata na mutu na je na tarar da Batula." Ya ce cikin ƙaranci yana buga kansa da gini. "Ka yi hakuri Ya Damir."Ya ce tare da kama shi."Mu koma gida kawai." Ya ce masa bayan ya kama hannunsa suka fita, domin in har bai koma gida ba, kafin ya tafi zai iya ƙona kampany. Bayan sun koma Mommy hankalinsa ya tashi jin abin da ya ce."Haka rayuwa za ta tafi Damir?" Ta ce masa cikin kuka. Rungume Little Marwana ya yi yana hawaye . Ganin ya ƙi cewa komai Mommynta ce,"Ku shirya mu fita Ƙasar wajen wataƙila ya manta da komai." Shiru ya yi yana kallon ya ji dadin abin da ta ce, saboda yana son ya yi nesa in da hali karya ƙara dawowa. Ya bar ƙasar ya daina tunanin wacce ta kashe masa mata tana nan a duniya tana numfashi. Cikin ƙanƙanin lokaci suka fara shirye-shiryen tafiya. Marwana babu yadda za ta yi dole ta je makaranta don ta yi differing. Jikin Nasreen ya yi sauƙi domin ba karamin kula Ahmad ya ke ba ta ba. Duk abin da take so shi take ci. Hatta yaranta yana kula da su. Ta samu sauki ta warke sosai. Tana jin daɗin zaman gidan, duk da cewar samuwar halin da ta sanya halin Marwana yana damunta. Rikici sosai suke yi da Baba da Ahmad, amma ya rantse ba zata koma ba. Shi kansa Faruk ɗin ko aikinsa don yana can yana cin amarcinsa. Rashin zuwa ya ƙara ƙular da Ahmad, ganin bai damu da ita ba. Yana nan yana shirin tafiyar da za su yi. Ya sanya ran da dawo zai maka shi kotu ya yi masa hulɗi ya sake ta. Ganin ta samu sauƙi ta shirya ta je makaranta. Haushinta ɗaya Faruk ya ƙi yarda a kwaso mata kayanta. Tun da ta doshi get ɗin makarantar zuciyarta ke bugu. Sam ba ta son ta ƙara ganin Marwana, domin har yanzu tana jin ba ta saka mata da alkhairi ba, amma ya za ta yi? Ya zamar mata dole ta ƙara da karatunta musamman da ta kusa gamawa. Da ta shiga cikin makarantar idanunta na ƙasa har ta ƙarasa kan kujerar ta zauna. A gida ta bar Musaddik don Mama ta ce ta barwa Zainab. Tana zaune tana sauraren darasin har lecturer ya gama suka fita, kafin wani darasin. Zama ta yi a cikin gerden. Marwana ta ƙara so, cikin sanyi ta zauna a gefenta bayan ta yi mata sallama. Da sauri ta ɗaga kanta tana kallonta jin muryarta. Hawaye share suka zubo mata. Miƙewa ta yi za ta bar gurin cikin jin kunya. Hannunta ta kamo ta tsaya tana kallonta. Sai kawai ta fashe da kuka. Idan akwai wanda take jin kunya a duniya, bai wuce ita da ƴaƴanta ba. "Ki yafe mini na ruguza miki farincikin ahalinki. A lokacin idona ya rufe. Tsananin azaba ya sanya na kira ki. Na kira Ya Ahmad..." "Is ok, ban zo nan don na ji uzurin ki ba. Komai za ki gaya mini ba zai canza komai. Anty Batula ta rasu addu'a kawai za ki yi mata." "Allah ya jiƙanta kuma zan kasance har ƙarshen rayuwata ina mata addu'a." Ta ce tana share hawaye. "Na zo na yi miki sallama za mu bar ƙasar. Akwai yiwuwar dawowarmu da wuri ko akasin haka. Tun bayan rasuwar Anty Batula ya canza ya zama tamkar mahaukaci kuma masifaffe. Sam ba ya shiga cikin mutane. Gabakiɗaya rayuwarsa ta susuce."Tsayawa ta yi ko za ta ce wani abu, amma sai ta ga ta share hawaye kawai ta gyara zama. Ganin haka ya sa ta ja numfashi ta ɗora da cewa,"Wannan dalilin ya sanya Mommy ta ce mu bar ƙasar na wani lokaci. Na zo na dakatar da karatuna inna dawo to, in kuma na ci gaba a can shikenan. Ina ta tunanin yadda zan yi miki sallama, cikin ikon Allah sai ga shi mun haɗu." "Eh, yau na fara zuwa. Ya Faruk ya hana ni komawa. So yake ya yi tafiya ya tara kuɗi akai shi kotu, ayi masa hulɗi." "Da kyau Ya Ahmad ya cike gurbinsa na Yaya har masa na mahaifinki. Sam bai kamata ki ci gaba da zama da Faruk ba, domin in har kika ci gaba rayuwarki za ta tagayyara. Faruk ba ya ƙaunarki. " Kanta ta ɗaga ba tare da ta ce komai ba. Hannu ta sanya a jakarta ta ciro maƙudan kuɗi."Ga shi ki kula da kanka. Za ki iya kai shi kotu da waɗannan kuɗin." Girgiza kanta ta yi cikin hawaye."Ki yi hakuri ba zan karɓa ba, na yi wa kaina alƙawarin ba zan ƙara amsar taimako da ga gare ki ba." "Haba Nasreen, wallahi ko kaɗan ban zarge ki kan abin da ya faru ba." "Haka ne na sani amma ki yi hakuri. Ina muku fatan kyakkyawa ra rayuwa, kuma ina neman alfarmarki. Don Allah ki yi ta rokon mini yayanki ya yafe mini. Ki gaya masa akwai wata gangar jiki da jininsa yake yawo a cikinta. Ita gagar jikin ta ba shi wani matsayi mai girma, duk da tsanar da ya yi mata." "Zan gaya gaya mishi don Allah ki karɓi kuɗin nan." Girgiza kanta ta yi sai ta juya da gudu ta shige ciki. Marwana ta daɗe, a tsaye tana kallon ta cikin tausayawa. Har ga Allah ta yi kunyar ta taimaka mata. Burunta su gama karatu ta sanya Ya Damir, ya ba ta aiki, amma ƙaddara ta canza komai. Bayan sun gama lecture ta koma gida. Tana kwance a ɗaki suna hira cikin nishaɗi. Ahmad ne ya kalle su ya ce,"In sha Allahu, ina ga cikin sati nan za mu wuce Inugu. Ogana ya ce na kasance cikin shiri a kodayaushe zai iya kirana mu wuce." "Allah ya kaimu kuma ya kaika lafiya ya tsare mana kai." Cewar Mama tana kallonsa. "Amin." Ya amsa tare da ɓallar raken da yake sha. Nasreen ta ƙura masa ido ya cikin tsananin so. Ta san cewa abin da yake mata Allah ne kawai sai biya shi. Inda ace babu shi a rayuwarta, Allah kaɗai ya san halin da za ta shiga. "Ubangiji ya kai ka lafiya ya dawo mana da kai lafiya." Ta ce tana kallonsa. A maimakon su tafi kamar yadda ya ce, sai ba su tafi ba har suka ƙara sati biyu. A lokacin. Nasreen ta kwantar da hankalinta, ba kamar da ba tana ta zuwa makaranta. A daren da za su wuce Nasreen da ka ta ta yi masa wanki. Bayan ta gama ta shanya, da suka bushe ta goge masa, sannan ta shirya masa a jaka. Duk wani abin da ya kamata ya ɗauka ita ta shirya masa. Da ya zo zai yi musu sallama. Ta tsaya yana kallonsu cikin tsananin ƙauna."Mama, Nasreen zan wuce ku yi mini fatan sauka lafiya. Ga wannan kuɗin ku rinƙa amfani da shi kuma cin abinci. Ni ma ba a bani kuɗi sosai ba, in sha Allahu da zarar na fara aiki zan turi muku." "Ubangiji ya kai ka lafiya ya dawo mana da kai lafiya." Ta ce tana share hawaye sai kuma ta kalle shi ta fashe da kuka."Ka yafe mini na ɗora maka nauyin da ba naka ba." Murmushi ya yi jin abin da Mama ta ce."In sha Allahu Mama zan kula da rayuwarki da ƙannina sai baba ya yi nadamar rashin bamu kulawa da bai yi ba." "Allah ya ba ka iko." Cewar Mama. Nasreen kuwa ƙarasawa kusa da shi ta yi ta riƙe hannunsa."Ya Ahmad amma ba za mu daɗe ba ko?" "Eh wata ɗaya kawai za mu yi. Duk abin da Bana zai yi miki kar ki koma gidansa. Da zarar na dawo in sha Allahu zan biyasa duk abin da ya kashe ba." "Faruk ba zai zo gare ni ba, saboda ya samu wacce ta fini. Ina sha Allahu ba zan koma ba." Ta ƙarshe maganar maganarta tana kama hannunsa tana ji kamar karya tafi. "To in zauna mu je mu zauna mu ci ƙasa kenan?" Ya yi mata tambayar cikin tsokana yana harararta cikin wasa. "A'a, Ubangiji ya dawo kai lafiya." "Amin," Ya amsa bayan ya karɓi Musaddik ya riƙe hannun Raihan. Har ƙofar gida suka raka shi. Har ya hau mashin ta ƙwala masa kira."Ya Ahmad, sai ka dawo Allah ya tsare." Ta furta tana ɗaga masa hannu. Shi ma hannu yake ɗaga musu har ya ɓule. Da suka dawo cikin gida. Zama suka yi suna ta hirarsa har aka kira sallar azahar, sannan suka tashi suka yi sallah. A ranar da ya tafi Nasreen cikin dare kasa bacci ta yi. Tana ta tausayinsa yadda ya zaɓi ya wahala don ta kula da ita. Addu'a ta yi masa sannan ta kwanta. Cikin dare ta yi wani mugun mafarki. Mafarkin da ya sa ta tun da ta farka ba ta koma ba. Ta yi karatun Alkur'ani sannan ta yi ta tasbihi tana roƙon Allah ya musanya mata mafarkin ya zama alkhairi. Duk da cewar ba za ta gane abin da yake cikin sa ba, amma tun da ta yi ta nemi natsuwarta ta rasa. A haka ta wuni sukuku da ita, don ko makaranta cewa ta yi ba za ta ce ba. Tana kwance Mama ta shigo, Da shinkafa da mai da ya ji ta da girka."Nasreen, lafiyarki yau kuwa?" WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 20 Tana kwance Mama ta shigo, da shinkafa da mai da ya ji ta da girka."Nasreen, lafiyarki lau kuwa?" "Mai kika gani Mama?" Ta yi mata tambayar, tare da miƙewa tana gyara Musaddik da yake shan nono. "Gani na yi kin tashi sukuku da ke,kuma kin ƙi zuwa makaranta. Ko kina so ki koma gidanki ne?" Jin tambayar da ta yi mata ya ɓata ranta."Haba Mama, yanzu har za ki iya mini wannan tambayar? Na koma gidansa ai sai ya yi bandana." "To na sani? Kin san ance tsakanin mata da miji sai Allah, ko kin ga wahalar da muke ciki ba za ki iya zama ba." "Kar ki manta a cikinta na tashi, sannan babu abin da na manta. Ko da sonsa zai kashe ni na haƙura da shi. Ballantana Faruk ba shi a gabana. Mafarki na yi mara daɗi, kuma na kasa gane komai." "Ban da abin ki mafarki ba gaskiya bane, in har ki yi addu'a babu bin da zai faru sai alkhairi." "Na yi Mama." "Shikenan Ubangiji ya kare mu." "Amin," ta ce tana kallonta. Har ta ɗaga labulen za ta fita sai kuma ta kalle ta."Yayanki ya ce zai kira amma shiru. Ɗazu kin kira shi wayar a kashe." "Eh, wallahi sai gwadawa na ke yi, ma bari na ƙara kira." Ta ce tana kallon wayar. "Yauwa wayar ta shiga." Ta ce cikin murna, amma har ta gaji da jira ba a ɗaga ba. "Ki bari an jima mu gwada wataƙila ya sanya wayar a caji." "To," Ta amsa. Har ta miƙa zata fita aka kira wayar. Gabanta ya tsinke a maimakon ta yi farincikin ganin kiransa. "Assalamu alaikum Yaya." Ta ɗauki wayar cikin mutuwar jiki tana faɗin haka. Amsa sallamar aka yi jin murya da ba nasa ba, gabanta ya yanke ya faɗi." "Ina mai wayar?" Ta yi maganar cikin ruɗu. "Wace ce take kira?" Tambayar ya sanya ta zauna cikin tsananin tashin hankali. "Nasreen ce ƙanwar mai wayar, don Allah yana ina?" Ta ƙarashe tambayar cikin ruɗani. "Ya za ki kira ni kuma ki tsaya kina tambayata? Ya ƙarashe maganar cikin tsawa. Sororo ta yi jin tsawar da ta yi mata, sai kuma ta furta."Innalillahi wa inna ilahir raju'un! A cikin zuciyarta. "Yayane yake da wannan layin, ya tafi neman kuɗi ne zuwa kudu. Don Allah ka haɗani da shi, in yana kusa in kuma yar da wayar ya yi ka gaya mini." Tsaki ya yi yana faɗin,"Wayata ce wannan kuma layina ne, kar ki ƙara kira na." Jin abin da ya faɗa hankalinta ya tashi."Mai ya faru da Ya Ahmad, ya aka yi layinsa ya zo gurin wannan mutumin?" Irin tarin tambayoyin da suka cika kwanyarta kenan, har ta kasa aiki bisa ƙa'ida. "Mama," Ta kira sunanta cikin rashin hayyaci tana jin kanta yana juyawa, tamkar ana murza sitiyarin kan motar da aka ƙure mata maneji. Ƙarar ya sanya Mama shigowa, da sauri tana tofar da lomar shinkafar da ta kai baki."Lafiya Nasreen, Faruk ne ya sake ki?" Kallonta ta yi kamar wacce ta taɓu."Mama wayar Yaya Ahmad na kira, wani ya ɗauka yake gaya mini wai wayarsa ce." Ta furta cikin tashin hankali. "Kai anya ki kira numbarsa wani ya ɗauka. Ina ga dai ki sake dubawa, wataƙila ba numbarsa kika kira ba." Jin abin da Mama ta ce sai ta yarda. Da sauri ta ɗauko wayar cikin ruɗani, domin ta tabbata layinsa ta kira."Wallahi numbar sa ce Mama. Haba ya za a yi na kasa gane numbarsa Yayana, da na haddace a kaina." Ganin yadda ta rikice sai Mama ta kamata ta zaunar. "Natsu ki ƙara kiransa insha Allahu zai ɗauka Ahmad yana nan lafiya, jikina yana ba ni haka." Ta ce cikin ƙarfafawa duk da cewar zuciyarta na bugu. "To Mama," Ta ce tare da fara danna wayar hannunta na rawa. Kallonta ta yi cikin damuwa ta ce,"Na ƙara kira ya kashe wayar." "Nasreen don Allah ki natsu Ahmad yana lafiya, duk ina yake zai kira. Addu'ar da na ke masa, Allah zai kare shi." Ɗaga mata kanta ta yi ba tare da ta furta kalami ba. Mafarkin da ta yi ya dawo mata. Tunani take yi in ba shi ya za ta yi. Duk da Mama ta ce ta bari zuwa an jima ta kira, amma haka ta rinƙa kiran waya ba ta shiga. Ganin dare ya yi sai hankalinsu ya tashi. Da ƙyar bacci ɓarawo ya kwashe su. Da asuba kiran farko ta tashi ta ƙara kira, amma har lokacin wayar a kashe. Tun suna jiran kiransu har suka fara shiga damuwa. Ganin an kwana biyu sai Mama ta shirya ta je gidan ogansa. Yadda ta tarar da matarsa cikin damuwa ya tayar da hankalnta ƙwarai. "Wallahi sai dai mu yi addu'a, saboda ni ma ina ta kiran numbar Baban Intisar a kashe " "Ikon Allah! Ko mai ya faru?" Ta ce cikin damuwa. "Bamu sani ba sai dai mu yi addu'a." "Addu'a ya zama dole. Allah ya jishe mu alkhairi." "Amin,"Ta ce tare da sauke tagumi. Nasreen da take tsaye tana zubar hawaye. Ta kasa cewa komai. Tunani take inda yake. Wane hali yake ciki? Da kuma tunanin dalilin da ya sanya layinsa yake hanun wani. "Don Allah ga numbata in kin ji wani labari ki kira ni." Ta ce mata cikin damuwa. "To in sha Allahu kuma mu ci gaba da kiran ƙila kuma rashin caji ne." "Allah shi ya barwa kansa sani da su." Sallama suka yi mata suka dawo gida. A ranta sun kasa bacci sallah suke yi suna roƙon Allah. Nasreen kuka take yi tana addu'ar Allah ya bayyana shi. Ganin an kwana uku babu labarin da ya sanya ta tari Baba da maganar cikin damuwa. Kallonta ya yi jin abin da ta ce."To Amaduu yaro ne da za ki tashi hankalinki? Yana nan watakila bai samu damar kiranki bane." "Ni dai na damu da halin da yake ciki." "To mu jira iya wata ɗaya suka ce za su yi mana." "To shikenan Allah ya bayyana mana su." Fita ya yi daga gidan ita kuma ta tashi ta shiga ɗakinta. Ganinta zaune a ƙasa tana shatatan hawaye ta yi tagumi ya sanya ta ƙaras kusa da ita."Don Allah ki bar sa wa kanki damuwa, mu yi addu'a kawai. In sha Allahu lokacin da suka ina za su dawo." "To Mama Yaya Ahmad shi ne na ke gani nake jin daɗi, in har babu shi rayuwa ta zata munanta." "Akwai Allah ki yi addu'a." Ta ce mata cikin tsigar rarrashi. Haɗiye kulan da yake son kumbce mata ta yi. "Bari na yi wanke-wanke." "To maza ki yi ki ɗora abinci." Tun daga ranar suka cigaba da addu'a, kuma kullum sai sun kira layinsa, amma wannan mutumin ne, daga baya sai ya yi blocking ɗin su. Kafin wata ɗayan sun yi shi cikin tsoro, firgice da ruɗani. A ranta da wata ɗaya ta yi, sun shiga cikin fargabar ko zai dawo, amma shiru har aka ƙara kwana uku babu Ahmad babu ogansa. Lamarin sai ya firgita shi. Shi kansa Baba hankalinsa ya tashi matuƙar gaske. Cikin tashin hankali aka sanya cigiyarsu, amma shiru babu labarin su tamkar malam ya ci shurwa. Iya tashin hankali wannan ahali sun shige. Kuka Nasreen take yi cikin damuwa ta ce,"Ya Ahmad shi ne gatanta yau kuma ya nace babu shi babu labarin sa. Na shiga uku Allah ka bayyana mini Yayana. Kuka take tana sumbatu taba faɗin kalaman da basu kamata ta faɗin ba Ganin haka Anty Binta ta kamata ta zaunar da ita. "Nasreen ki bar kuka ki yi hakuri kar ki yi saɓo, in sha Allahu Ahmad zai bayyana." "Saboda me za ki hana ni kuka? Bayan kin san daga yau na rinƙa yi har ƙarshen rayuwata. Ya Ahmad shi ne gatanta kuma ya tafi ya bar ni." Sai ta ƙara fashewa da gigitaccen kuka. "In sha Allahu za a gan shi mu cigaba da addu'a da sadaka." Mama ta ce zuciyarta na ƙarfafa mata yana raye. Da ƙyar suka samu ta yi shiru tana faɗin."Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Domin ta yi kukan har idanunta sun bushe. Babu hawaye sai zafi da ƙunci da zuciyarta yake. Ga dai Ahmad ya ɓace ya barsu da jimamamin rashinsa. Shi kansa Baba ɓacewarsa ta buge shi, saboda sai da ya ɗauki lokaci kafin ya dawo natsuwarsa. Da fari har sallah yana kiyaye a kan lokaci, musamman in ya tuna yadda Ahmad yake zubar hawaye a duk lokacin da ake kiran sallah yana zaune. Da ga baya kuma sai ya watsar ya koma ruwa. Dama ita sallah ginuwa take a jiki, haƙiƙa duk wanda ya yi sakaci da ita sai wani ikon Allah. Ganin kukan ba shi da amfani, ya sanya suka maida lamuransu ga Allah. Kusan kwana uku take sauka tana fatan Allah ya bayyana shi.. Kullum gani take kamar zai yi sallama. kamar zai dawo daga tafiyar da ya yi. Kullum hotonsa take ɗauka tana kallo hawaye na zubar mata. Haka Damir ya ji a lokacin da matarsa ta mutu?" Ta yi wa kanta tambayar cikin damuwa, saboda ga shi ita tana tunanin zai dawo, amma Allah kaɗai ya san halin da zuciyarta take ciki."Idan kuwa haka ne, haƙiƙa dole ya tsane ni ya yi fatan kar ya ƙara fatan ganin mai sunanta. Damuwar yadda rayuwarta zai cigaba take tunani. Ta san cewa rayuwarta ta shiga cikin gararin, amma duk abin da zai faru ba za ta koma gidan Faruk ba, musamman da ya ɓace ko zuwa bai yi ba. Tun ɓacewarsa na ɗanye a lokacin da tai wata biyu. Yau ga shi ya zama wata huɗu rayuwa ta yi musu ƙunci. Kullum sai sun yi kukan rashinsa, musamman gurin kula da abin da za su ci. Wayar da Marwana ta ba ta har ta sayar da ita. Ya rage laptop ɗin. Ita ma ganin halin tsotsan tsamiya da suke yi, ya sanya ta siyar, sanin babu wanda zai biya mata kuɗin makaranta ta cire kuɗin ta ije. A lokacin da aka gaya mata kuɗin da za a siya ta yi mamaki ƙwarai. Ashe ba ƙaramin kuɗi ya kashe gurin siya mata ba. Bayan ta cire kuɗin suka fara sana'ar cikin gida. Da cinikin take samu ta je makaranta ta kuma ɗan yi wasu abubuwan na makaranta. Damir zaune kan farar kujerar a bakin ruwa idanunsa lumshe. Zuciyarsa ɗauke da tunani barkatai. Tun ranar da suka baro Nigeriya, har yau ka kasa sakin jiki kamar yadda Mommy take so. Kullum ya kwanta bacci sai ta yi mafarkin ya, domin har yanzu zuciyarsa ta kasa daina zargin cewar shi ne ya yi ajalinta. Duk lokacin da ya tuna hakan sai ya ji tamkar zai haɗiye zuciya ya mutu. Ya yi dana sani tafi cikin kwando dubu. A hankali ya buɗe manyan idanunsa ya ɗora su kan Little Marwana, da ke gudu a bakin ruwa tana dariya, Marwana na biye da ita. Kallonta yake yi cikin tsananin tausayawa. Hawaye suka taru a gefen idanunsa."Anya za ta yafe mini kuwa?" Ya tambayi kansa cikin tsananin damuwa. Miƙewa ya yi, yana kallon ruwan da ya kusa mamaye gurin. Hannunsa ya ji little Marawana ta kama ta riƙe tana faɗin,"Daddy, ka zo mu yi wasan gudu da kai a bakin ruwa, kuma Anty Marwana ta ce in Mommy ta dawo daga tafiyar da ta yi za mu zo tare." Hawaye suka cika masa idanunsa. Har yau ta kasa fahimtar Batula ta yi musu nisa."Mommy ba za ta dawo ba, domin ta tafi inda ba a dawo wa." Ya ɗauke ta tare da shafa fsskarta yana faɗin haka. Kallon da ta yi kamar mai tunani,"Daddy, to za ka siyo mini wata Mommy?" Tambayar da ta yi masa, ya sanya tashin hankali a zuciyarsa."Ba zan siyio miki wata ba, amma na yi miki alƙawarin zan ba ki ƙular da kowace uwa za ta bawa 'yarta." "No, daddy na fi so ka siyo mini wata." hankalinsa ya ƙara tashi jin abin da ta ce. Ije ta ya yi zai tafi ba tare da ya ce komai. Hannunsa Marwana ta riƙe cikin hawaye."Ka yafe mini Yaya, har yau ina tuna ni na yi sanadin gushewar farincikinka, ina shiga cikin tsananin tashin hankali. Don Allah ka yafe mini Yayana." Kukan da take masa ya ƙara ninka masa damuwa. "Sis, ki bar kuka komai ya wuce." "Karka faɗi haka domin ka canza ka koma kamar ba kai ba, duk lokacin da na ganka a wannan yanayin ina jin kamar na kashe kaina." "Kar ki damu ki manta komai lokacin ta ne ya yi, sannan bamu da ikon dakatar da mutuwarta." "Ka yi mini alƙawarin za ka daina sanya damuwa a cikin ranka. Za ka dawo kamar da, yayana wanda na sani yake sani dariya da farinciki?" Shiru ya yi yana tunani sai kuma ya ƙwace hannunta ya fara tafiya. Sosai take kuka tana kallonsa har ya yi nisa ya zauna a can gefe. Duk da cewar sun je gurin domin su sanya shi farunciki, amma haka suka dawo jiki a saɓule. A lokacin da suka dawo Mommy tana zaune da qur'ani a hannunta tana karantawa. Shigowarsa ya sanya ta dakata, bayan ta kai ƙarshen ayar. Kallon sa ta yi har ya shige cikin ɗakinsa. Marwana ta zauna kusa da ita tana hawaye."Ya Damir zai koma kamar da?" "Ni ma na fara tunanin haka, ina ga za mu koma gida kawai, saboda zuwanmu bai yi amfani ba, kullum cikin damuwa, sannan ga campani babu mai kula da shi." "Haka ne amma Mommy ya kamata mu ƙara lokaci kafin mu koma." Shiru ta yi ba tare da ta ce mata komai ba. Ganin wata biyar da ɓacewar Ahmad ba tare da Faruk ya zo ba, ya sanya Baba ya shirya ya je gidansa. A lokacin yana falo yana kallo shi da gumbiyarsa da take kwance kan cinyarsa. Wasu irin arnan kaya ta sanya, wanda da su gwanda babu. Hakan ba ƙaramin yi masa daɗi ya yi ba, musamman da take da cikar jiki ko ina duk tsoka. Ya tasa ta ya yi ta kallo. Tuni suka fahimci juna game da tsarin iyali. Duk abin da yake so shi take masa, wannan dalilin ya sanya hankalinsa ya kwanta har wani ɗan tumbi ya yi. "Baby, kamar ana knoking get?" Ta ce masa tare da ɗaga kanta tana kallonsa. "Ni ma haka na ji." Ya ce sannan ya miƙe ya sanya doguwar riga ya fice. Ganin Baba ya ɗaure fuska yana kallonsa a wulaƙance."Lafiya?" Ya ce masa yana kallonsa. "Lafiya lau, ba ka gane ni bane Farukuu?" "Na gane ka mana ba uban Nasreen ba ne?" Jin tambayar da ya yi masa, ya sa ya jikinsa ya yi sanyi. "Eh ni ne..." "Allah ya sa dai lafiya? Kuma ina fata ba tambayata kuɗi ka zo yi ba?" "A'a Faruk yaron kirki, ba ka san Ahmad ya ɓace bane?" Ɗan jim kamar bai sani ba sai kuma ya kalle shi."Na ji wataƙila kunya ta sanya shi ɓoye kansa ya ga ba shi da kuɗin da zai iya biyana." "Allah dai shi ya barwa kansa sani fatanmu ya bayyana shi." Ba tare da ya amsa ba sai motsi da bakinsa da ya yi. Ganin bai tanka ba, sai ya gyara tsayuwa ya rasa abin da zai ce, amma dai ya daure cikin rashin ƙwarin gwiya ya fara magana da cewa," Da ma na zo kan maganar matarka..." "Ba kun ce za ku kai ni kotu ba? Ina jiran a yi mini sammaci sai na je na amshe kuɗaɗena kashe." "Ka bar wannan maganar ai wanda ya tsaya mata ya ɓace. Ni kuma ka san dai ba zan goyi bayanta ba, dole gidan ka za ta dawo. Don ba za ta yi mini zawarci da yara ba." "Na san ya ɓace, ina jiran na ga inda za su samu wanda zai tsaya musu ne. Tun da an gaya mini wanda yake hure mata kunnin ya bar ƙasar" "Duk haka ba ta ta so ba. Ka san dai Nasreen da auren ka ba za ta kula wani namijin ba?" "Ok, ka yarda da ita kenan? Tarbiya ka bata da har za ka shede ta?" Shiru ya yi jin abin da ya ce sai kuma ya nisa,"Faruk duk wannan maganar ba ta taso ba, ka yi hakuri ka zo ka ɗauki matarka..." "Na zo fa ka ce?" Ya katse shi yana faɗin haka, sai kuma ya girgiza kansa ya ɗora da cewa,"In har ba za ta dawo ba, sai ta yi ta zama har Mahadi ya bayyana. Ai ni wallahi rage mini aiki ta yi, don yanzu hankalina kwance na samu mace mai ladabi da biyayya." "Yanzu dai duk zancen tone-tone bai ta shi ba, kai da Nasreen kin riga kun zama ɗaya. Ka yi haƙuri ko don tausayin yaranka." "Tun da ba ta tausaya wa kanta ba sai ta ci gaba da zama ba. Na san dai rayuwarta a garari zai ƙare, wanda yake yi mata ƙaryar zai tsaya mata kunya ta sanya ya gudu." "Ni zan wuce in sha Allahu za ta dawo yau." "A'a ban shirya ta dawo yau ba." Ya ce yana kallonsa saboda ya yanke shawarar ya je ya gasa mata maganganu. "Ka bari zan zo sai mun yi magana da ita na gaya mata dokokin gidana." Jin abin da ya ce ya yi shiru ya kalle shi zai tafi. Faruk ya raka shi da idanu ya ɓule, ya san kallon da yake masa ya ba shi kuɗi."Wallahi ai daga yau ka daina cin sisina. Yar ka ce yanzu na samu wacce ta fita, don inta ga dama ta zauna in ba ta buƙata ga hanya nan." Ya furta yana nuna hanya. Da ya shiga cikin gidan har lokacin tana zaune. Ganin ransa a ɓaci ya sanya ya dawo kusa da shi."Hala 'yan maula ne?" Ta yi masa tambayar haka, don ta san a tambaye shi kuɗi ne ya fi ɓata ransa. "Baban wannan mara mutuncin Nasreen ne ya zo, wai na je na ɗaukota. Ni kuma na gaya masa ai ba ni na kaita ba." Jin abin da ya faɗa ya sanya gabanta ya faɗi, don ba ta ƙi su zauna daga ita sai shi ba.Ɓata rai ta yi tana kallonsa cikin kissa."Yanzu baby, dawowa da ita za ka yi mu rinƙa sharing ɗinka." Kallonta ya yi tare da jawota jikinsa."Ƙarki damu dawowarta ba zai hana mu jin daɗin rayuwarmu ba. Don ban damu da ita ba, in ta ga dama ta zauna, in ta ce za ta ɓata miki rai jikinta zai gaya mata, don yanzu kin fi mini kowa a duniyar nan." Murmushinta saki tana kallonsa."Lallai aikin Malam yana ci, na samu kansa sosai, sai kuma ayi mini maganin maƙonsa." Ta furta hakan a cikin ranta. "Shikenan ta dawo ka ga dama ni kaɗai nake aikin gidan nan." "Ƙarki damu babyna, da zarar ta dawo ita za ta rinƙa aikin gidan, tun da ita ce take da yara."Daɗi sosai ta ji jin abin da yace. Baba da ya koma gida ya sameta tana zaune a ɗaki ta zabga tagumi.Ganinsa ya sanya ta janye tagumin. "Sannu da shigowa Baba." "Yauwa,"Ya amsa tare da zama kan kujerar. "Gurinki na zo." Jin abin da ya ce gabanta ya faɗi, har ta kasa amsa masa sai kallonsa da ta yi. Zama ya yi yana kallon ta. "Nasreen, ki daina yaudarar kanki ki koma gidan aurenki, domin kin san dai wanɗanda suka ɗaure miki gindi duk sun gudu sun barki?" "Ya Ahmad ba guduwa ya yi ba, Ya Ahmad ba zai taba guduwa ya bar ni da gangan ba." "Ko ma dai mene ne ke kike tunanin haka. Don haka ya zama dole ki koma gidanki tun da babu shi." "To don babu su dai na kasa ƙwatar 'yancina, wallahi na gwammce na fuskanci ko wace irin rayuwa da na zauna a gidansa, domin Faruk azzalumi ne macuci, a dalilin ayi masa hulɗi Ya Ahmad ya ƙarfafa tafiyarsa. Na tsane sa bana ƙaunarsa, kuma ba zan koma gidansa ba." "Wallahi ba ki isa ba, in har ni na haife ki sai kin koma." Ya ce cikin tsawa yana kallonta. Kasa amsa masa ta yi tana kallonsa cikin zubar hawaye, ganin haka ya ɗora da cewa,"Yadda Faruk, ya watsar da ke ya ishi ya nuna miki zai iya rayuwa babu ke, saboda kina nan kina shan wahala, amma shi yana morewa da amaryarsa. So na ke na wa 'ya'yanki da ke kanki gata, saboda wallahi in har ba ki hakura kin koma ba, sai kin zama abin tausayi. Kina gani dai yadda abinci yake nema ya gagareki, don haka na je na ba shi haƙuri, sai ki tattara ki koma gidanku." Ta kasa magana sai kawai ta fashe da kuka."Yanzu Baba, duk wulaƙancin da Faruk ya yi mini, amma har ka iya zuwa gidansa ka ba shi haƙuri?" "Taimakon ki na yi, kuma da kike wannan maganar mata nawa suke zaman ƙunci a rayuwar aurensu kuma suke haƙuri? Wasu matan babu abinci babu sutura, amma hakanan suke zama a gidajensu." "Ka yi haƙuri Baba, ba zan iya komawa gidansa ba." "Ni kuma wallahi ba za ki zauna mini a gida ba, sai dai ki nemi wani gidan uban, sannan in har kika faɗi haka yarannan a yau za ki mayar masa da 'ya'yansa." Sharhi game da Ahmad. Jiya da na saki post na ji ƙorafinmu mutane da dama cewar kar na kashe Ahmad masu biyo ni pc da kuma masu comments a group. Duk na fahimce ku kuma na gane abin da kuke nufi. Ku kwantar da hankalinki Ahmad ba zai mutu ba, amma ku sani dole na kauda Ahmad na wani lokaci, saboda Nasreen ta zama jaruma ta ƙwaci yancin kanta. Ahmad so yake a yi wa Faruk hulɗi, kuna ganin hakan mafita ne a gareta? In har aka yi masa hulɗi suka rabu Nasreen ta yi experiencing rayuwa kuwa? Karfa ku manta wanda za ta kuma haɗu da shi wato Damir a dalilin ta matarsa ta mutu har ya tsane ta. Kuna ganin a haka har za ta iya fuskartar ƙalubalen da zai faru, kafin soyayyarsu ta ƙullu? Dole tana buƙatar ta tsaya ta zama jaruma don ta iya fuskantar ko wace irin rayuwa ta tsinci kanta a ciki. Na gode da yadda ku ke kuke bibiyar WASU MAZAN haƙiƙa comments ɗinku yana sanya ni cikin duniyar nishaɗi. Fatana na faranta muku ta hanyar tsara muku labarin domin farincikinku.❤️❤️❤️❤️❤️💃💃💃💃💃💃💃💃👏👏👏👏 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 21 "Taimakon ki na yi, kuma da kike wannan maganar mata nawa suke zaman ƙunci a rayuwar aurensu kuma suke haƙuri? Wasu matan babu abinci babu sutura, amma hakanan suke zama a gidajensu." "Ka yi haƙuri Baba, ba zan iya komawa gidansa ba." "Ni kuma wallahi ba za ki zauna mini a gida ba, sai dai ki nemi wani gidan uban, sannan in har kika faɗi haka, yarannan a yau za ki mayar masa da 'ya'yansa." Sosai take kuka jin abin da ya ce. Kallon yaran ta yi tana jin duk wuya, duk rintsi ba za ta rabu da su ba. Ahmad ya faɗo mata a rai, ta san cewar da yana nan, Baba bai isa ya yi mata dole ba." "Nasreen ba za ta koma gidan Faruk ba, sai dai duk abin da za ka yi ka yi." Ya ji muryar Mama tana faɗin haka. "Au ke kike ɗauke mata gindi ko?" "Haba ka tausaya mata mana. Yaron nan ya nuna baya ƙaunarsa, kan dole sai ta yi rayuwa da shi?" "Ke mai ya sa ba ki rabu da ni ba? Tun da kullum gaya mini kike ba kya son halina? Sai ita ki sanya ta kashe aurenta. Kina ganin yadda maza suka yi wahala.To wallahi gara tun wuri ki farka da ga barin da kike yi. Kar ki yadda ta ɗora ki a kan keken ɓera." "Sai dai in ka sake ni, amma Nasreen ba za ta koma gida sa ba." "Mene ne abin tada jijiyar wuya? In har kin shirya biyansa kuɗi sai ki kai shi kotu." Ya ce yana ɗaya kafaɗarsa alamun bai da mu ba. Gabanta ne ya faɗi tunawa da hakan. Hawaye ta share tare da kama hannunta ta miƙar da ita, wacce take kuka kamar ranta zai fita."Ta shi ki daina kuka ba za ki koma ba." "Mama, na san cewa ba ji da gata, tun da Yaya Ahmad ya ɓata. Baba so yake ya raba ni da yarana, ba zan iya kai su gidan ubansa ba, saboda na san Faruk ba zai iya riƙe su ba. In har zai sanya dole na mayar da su, zan koma gidansa ne don kawai bamu da kuɗin da zamu biya sa, amma ba don na ci gaba da biyayar aure ba. Ba zan iya jure rashin mutuncin sa, idan ma yana ganin ba zan iya rayuwa babu yarana ba, zan haƙura da su na yi musu addu'a. Ya Ahmad ya ɓata zan tsaya tsayin daka na ƙwaci 'yancina da yake mafarkin samar mini" "Allah yana tare dake ki yi addu'a, in sha Allah ba za ki rabu da yaranki ba." Mama ta furta mata cikin rashin ƙarin gwiya. "Au komawa za ki yi don ki gurza masa rashin mutunci?" Dariya ya saki jin abin da ta ce, sai ya ɗora da cewa,"Da yake ta yaro kyau take ba ta ƙarko. Kina sane da halin sa, saboda ban taɓa ganin tijararren irin sa ba, duk jarabata wallahi ya fini. Ɗan banza mara tarbiyya, amma a haka yake kiran 'yata ba ta da tarbiyya." Kallonsa Mama ta yi cikin takaici jin abin da ya ce."Saboda ba ka riƙe mutuncin ka bane, duk wannan wulaƙancin da yake mata, ai kai ka janyo mata shi, saboda da ace ka riƙe talaucinka ba ka roƙonsa, wallahi babu yadda za a yi ya rinƙa maka rashin mutunci, amma saboda mutuwar zuciya wai suruki kake gaya ma ya taimaka maka, ba ka ci abinci ba. Ai dole ya wulaƙanta ta, tun da ya san uban da ya ubanta, shi ma rokonsa yake abincin da zai ci." "Au tijara kike son yi mini kenan?" Ya tambaye ta cikin borin kunya yana kumfar baki. "Gaskiya nake gaya maka wallahi in har ba za ka canza ba, za ka yi nadama saboda abin da kake yi babu kyau." Banza da ita ya yi domin gaskiya ta faɗa, ba shi da abin da zai ce. Kallon Nasreen ya yi ya ce,"Oho, yanzu dai shawara ta rage wa mai shiga rijiya. Da na ban yi mata dole ba, zaɓi na ba ta." Ya ƙarashe maganar tare da ficewa da ga ɗakin. Kuka take yi sosai, ta san cewa ba ta da zaɓi da ya wuce ta koma gidansa. Ba ta da kuɗin da za ta biya shi, da kanshi dole ya saketa, saboda a halin yanzu babu wanda ta tsana fiye da shi." Miƙewa ta yi, bayan ta share hawaye ta zauna tana tunanin rayuwarta. Da dadddare tana zaune ta ranka tagumi ta yi nisa a cikin duniyar tunani. Ƙarar motar Faruk ya dawo da ita hayyacinta. Gabanta ya faɗi sosai har sai da ta dafe gurin. Idanunta suka fito, don ta san zuwansa ba alkhairi zai gaya mata ba. Kafin ta yi wani yunƙuri ya shiga sakin hon ba ƙaukautawa. Da sauri Baba ya fito daga cikin ɗaki yana ƙoƙarin saka takalmi."Ga wancan tijararren ya iso, bari na yi sauri kafin ya kurmantar da mutanen unguwa." Ya ce tare da ficewa. Raka shi da idanun cikin tsananin takaici ta yi. Ta san cewa da ace Faruk yana da sakin hannu, sujjada ce kawai ba zai yi masa ba, amma yadda yake da mugun son abin duniya, babu abin da ba zai yi masa ba. Da sauri ya ƙarasa gurin motar nasa. Yana cikin motar ya ƙure waƙa yana ji."Ashe ka zo? Sannu da zuwa bari a kira ta." "Ita ba ta san ƙarar motana ba, sai na kira ta? Ko rashin tarbiyar za ta nuna mini?" "Bacci take yi." Ya yi masa ƙaryata hakan yana kallon sa. Tsaki ya yi, ba tare da ya ce komai ba ya ci gaba da shan waƙarsa. Ganin haka ya juya ciki a lokacin da ya isa cikin ɗakin Mama. Tana zaune a falo tana kuka. Mama ke gefenta tana ba ta baki. Tsaki ya yi sannan ya sannan ya kalle su," Ke Nasreen mijin ki na waje ya zo biko, kuma wallahi kika yi masa rashin mutunci sai kin sani." "Baba, don Allah ka sanya Faruk ya sake ni wallahi na tsani zama da shi." Ta ƙarashe maganar cikin kuka. "Hmmmmh!Kina dai ganin turjiyar da Ahmad ya nuna kan zai raba aurenki, amma daga karshe kin ga an neme shi an rasa. Ko wannan bai isa ya nuna miki aurenki da Faruk, mutu ka raba ba?" "Shikenan, cikin ƙunci zan ƙarashe rayuwata? Ban sha ta daɗi ba, a lokcin da na ke ni kaɗai a gurinsu, ballantana yanzu da yake da wata matar?" "Sai ki je ki yi hakuri, kuma Nasreen in an bi ta ɓarawo, abu ta ma bi sahu, don shegen kafiya ce da ke, wataƙila ɗiban albarka kike masa." Takaici ya sanya ba ta amsa masa ba, sai kuka tana share hawaye."Ki je yana jiran ki, kuma wallahi kika yi masa rashin kunya, kin san shi ma ba kanwar lasa bane." Ya ƙarashe maganar tare da juyawa ya fice. Kallon Mama ta yi sai ta fashe da kuka, tare da faɗawa jikinta."Mama, ki yi mini addu'a, kar na koma gidansa na kwaso zunubi duk bana jin akwai sausauci a tsakanina da shi. A dalilin a biya shi kudinsa, Ya Ahmad ya ƙarfafa tafiyar nan, duk lokacin da na tuna ji nake kamar na shaƙe sa ya mutu." Kuka take yi sosai tana tausayinta."Ki yi hakuri ki ci gaba da addu'a, kin ga yanzu ina kafe dole ya sake ki, ba mu da kuɗin da za mu yi masa hulɗi. Allah yana tare da ke, tun da ya halicce. Ko ci gaba da kai masa kuka, watarana zai ji kukan ki, domin baya zalinci kuma ba ya barin ayi." "To,"Ta ce ba don ta haƙura ba, sai dai ba yadda za ta yi. Ta san cewa tun da Ahmad ya ɓata, ba ta da sauran gata, sai dai zuciyarta na ƙarfafa mata ita ce kawai gatanta a duniya. Ita za ta tashi ta ƙwaci 'yancinta, tun da Baba bai damu da rayuwar ta ba. Wanke fuskarta ta yi sannan ta sanya hijabi ta fita. A lokacin har ya tada mota zai bar gurin. Ganinta bai sanya ya fasa ba, har sai da ya fara tafiya. Ko mai ya tuna oho ya ja ya tsaya. Ganin shiru bai tafi ba sai ta ƙarasa gurin motar. Tamkar wani baƙo a gurinta ta tsaya ba tare da ta ƙarasa ba. Zuciyarta bugu take mata tare da wani irin tsanarsa. da haushinsa suka haɗu suka sanya zuciyarta tafasa. Don kawai ta san Faruk ba zai taɓa sace Ahmad ɗin ya ci gaba da zama da ita ba, saboda ta san ba ya sonta, kawai yana zama da ita ne don ya wulakanta rayuwarta, amma za ta iya zargin shi ya sace shi. "Ke an gaya miki zan cigaba da jure wulaƙancin ki ne?" Ya furta daidai lokacin da ya buɗe ƙofar yana mata kallo tamkar ya ga kashi. Ganin ta yi shiru ba ta ce komai ba, sai kallonsa take yadda ya ƙara kyau har tumbi ya ɗan yi. Tsaki ya saka yana kallonta."Dubi yadda kika lalace kika koma wata tsohuwa dake. Ɗan watannin da kika yi, ya sa ya kika koma haka? Wannan in da za ki yi shekara sai an tausaya miki, kuma a haka kike mini wulaƙanci har kike wani banza gardi can da aurenki ya ba ki jininsa? Kin san ba ki da gatan da ya wuce zaman gidana. Ita wacce take zuga ki tana ina? Ta bar ƙasar bayan ta lalata miki rayuwar auren ki." Ya numfasa yana watsa mata mugun kallo ko za ta ce wani abu. Raihan ce ta fito daga cikin gidan da sauri ta ƙara so."Abba," Ta ce tare da kama hannunsa. Da sauri ya fisge yana kallonta kamar zai yi amai."Kina gani ko Nasreen, kina ganin irin rayuwar talauci da ƙaskancin da kika zaɓi yarana su kasance. Dubi jikin Raihan kamar wacce ta shekara ba ta yi wanka ba? A haka kike son ki wulaƙanta rayuwarsu. Su taso cikin talauci da dauɗa kamar yadda kai taso." Hawaye share suke ƙoƙarin zubo mata jin tozarcin da yake mata yana ɗaya murya. Juyawa ta yi za ta shige ciki ba tare da ya ce komai ba. Da sauri ya fito ya sha gabanta."Zaman wahala da kika yi a gidanku, har yanzu ba ki zama mai biyayya ba, saboda iskanci ina magana za ki wuce." "Ba ni da abin da zan ce maka Faruk, duk abin da kake yi mini Ubangiji yana kallonka kuma ya san halin da na ke ciki. Kana amfani da rashin iyayena kana wulaƙanta rayuwata, saboda ƙofar da mahaifina ya ba ka. Na san cewa watarana za ka yi dana sani mara amfani, domin aikin alkhairi kawai mutum zai aikata ba tare da ya yi nadama ba, amma watarana za ka yi nadama a lokacin da ruwa ya ƙare wa ɗankada, kuma tusa ta ƙarewa bodari. Wata mahaukaciyar dariya ya saki tare da buga bayan motar sa."Matuƙar kika ce haka kin yaudari kanki. Abu biyu zai sanya ki gane ba zan taɓa nadama, yadda ɓacewar Ahmad ta zo miki bazata, wadanda suke miki ingiza mai kantu suka gudu." "Akwai wanda ba ya bacci kuma ba ya barin mai zalinci, da Ni kaina Faruk. In har sun kauce a rayuwata. Ubangiji yana nan domin shi ya yi wa masu hakuri da cewa su ci gaba da hakuri, sannan ya yi musu busharar samun sauƙi a rayuwa. Akwai wanda zai iya sanya maka soyayya ta a lokacin da na yi maka nisa, a lokacin da wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa. Allah zai iya jarrabar ka da mutuwar sona.." "Ƙarya kike yi matuƙar ina da kuɗi zan iya auren matan da suka fi ki kyau da ƙuruciya, kamar yadda na auri Rashida wacce take bin duk abin da na ke so, kuma take cike mini gurbin da duk macen ƙwarai ta kama ta." "Kuɗi ba sa maganin komai Faruk, yadda kake wulaƙanta rayuwata ina kaiwa Allah kukana. Ina ji a jikina za ka yi nadama mara amfani. Watarana zai zo ka durƙusa a gaban kana roƙona a lokacin da ba zan saurari kukanka ba" "Na lura ɓacewar Ahmad ya zautar da ƙwaƙwalwarki. Ya kamata kafin na mayar da ke gidana, aje a duba ki kar ki zo ki cutar da matata." . Jin abin da ya ce hawayen suka wanke mata fuska."Ni kuma zan tuna maka da wannan ranar karka manta da kalaman da ka gaya mini, saboda zan tuna maka da su, watakila a nan ko a wani guri." "Ba za ki tuna mini ba, don na yi wa kaina alƙawarin wulaƙanta rayuwarki, sai na canza miki kamanni ta yarda babu wanda zai iya kallonki da sunan yana sonki. Sai na mayar da rayuwarmu abar tausayi na ɓata ki a idanun kowa, sannan zan yarda ƙwallon mangaro na huta da ƙuta. Murmushi mai ciwo ta yi tana faɗin,"Wannan shi ne soyayyar da kake mini kafin ka aure ni? Dama soyayya yana zama ƙiyyaya Faruk?Mai na yi maka ka zaɓi ka wulaƙanta rayuwata?" Ta yi masa tambayar tare da durƙushewa a gurin. "Wannan shi ne sakamakon macen da ba za ta bi umurnin mijinta ba, har za ta iya yarda a sanya mata jinin wani ƙarto, bayan ta gana cin ama...." "Faruk, kar ka zarge ni da mutumin da na yi maka rantsuwar ɗan musulmi ban taɓa ganinsa ba sai a ranar. Kar ka zarge ni da mutumin da halin yanzu ba shi da maƙiya kamata. Ya yi mini rana na saka masa da dare, ta hanyar yin sanadin matarsa, wacce yake so fiye da komai. Mutumin da na sanya ƙasarsa ta yi masa baƙi har ya yi hijira duk adalilina da na zamo masa butulu, ya yi ninyar mini alkhairi sai na saka masa da sharri na zaman masa tauraruwa mai wutsiya. Kar ka zamo WASU MAZAN da babu yarda da amana a tsakaninsu da matansu. Kar ka zamo WASU MAZAN da suke wulaƙanta iyalansu.. Hannun ya sanya ya ture ta yana faɗin,"Ba zan yi sausauci a gareki ba, sannan ina gargaɗinki da ki zama mai ladabi da biyayya ga matata, in kuka ba haka ba, sai ki fara irga kanki a cikin zawarawa, don ina sonta ba zan lamunci ki wulaƙanta mini ita ba. "Akwai Allah yana kallon ka shi zai kawo mini mafita. Zan koma gidanka saboda tursasa ni da Baba ya yi, amma ka sani wallahi ba zan ɗauki wulakanci da gurinka ba, da matarka saboda a yanzu na shirya don na ƙwaci 'yancina. Ina da daraja da ƙima 'ya mace na ke sam ba zan wulaƙanta kaina. A yanzu zan tsaya da kaina na ƙwatar wa kaina 'yanci "Ashe kuwa kin dawo ne don na ƙarasa yanke igiyar dake tsakaninmu, saboda kin san a lokacin da kike ke kaɗai ban ɗauki raini ba, ballantana yanzu da nake da wacce take share mini hawaye. Wallahi kin mini rashin kunya sakin ki xan yi ki je can gidanku ki yi zawarci." "Murmushi mai ciwo ta yi tana girgiza kanta ta ce,"Ashirye na ke Faruk! A yanzu a shirye na ke na yi rayuwata ni kaɗai matuƙar zan samu farin ciki. A yanzu na ƙuna bana jiran wake. Tursasar mahaifina kawai zan sanya na koma gidanka. Zawarci kaina farau? Mata nawa suke zawarcin kuma suke samu ingantacciyar rayuwa, sannan suka samu ci gaba? Sannan suke cikin farin ciki ba na tsoron zawarci in har Allah ya ƙaddara mini. In don talaucin iyayenta ne a ciki ka ganni. Yanzu da na koma gida mutuwa na yi? Da zaman aure irin na gidan ka Gara na mutu babu aure." Wani kallon wulaƙanci ya yi mata yana dariyar rainin wayo." Nasreen marabinki da gawa rai ne kawai, amma dubi yadda kika koma tamkar mai ƙanjamau?" Jin abin da ya ce ya yi masa kallon wulaƙanci ta juya kawai ta shiga cikin zauren gidan su. Kuka ta fashe shi, duk da cewar ta yi alƙawarin ta daina yi masa kika, amma maganar da ya gaya mata yi mata ciwo. Yana goranta mata talauci kamar ita ta ke ba da arziki.. Muryarta ya shaƙe yi kamar ta ta sha guba ta mutu. Ji take yi rayuwa ba ta mata adalci. Anya za ta kurɓi ruwan daɗi a cikinta, yaushe za ta yi farincikin da mata suke yi a gidan mazajensu.? Yaushe za ta zamo ɗaya daga cikin matan da WASU MAZAN suke nuna wa ƙauna, suke shayar da su madarar ƙauna da tafi zuma daɗi. Anya hakan zai faru? Tarin tambayoyin da suka cika ƙwaƙwalwarta kenan har suka sanya ba ta ganin abin da ke gabanta. Da gudu ta shige cikin gida tana kuka. Tsaki ya ja tare da shiga cikin motar da ya tafi. Mama ta yi turus! Cikin damuwa tana kallonta."Na ɗauka ya zo tafiya da ke ne? Amma sai kuka na ga kina kuka." Hawaye ta share tana kallonta."Mama Faruk ba zai canza halinsa ba, a yanzu rayuwata sai ta fi muni a gidansa, domin ya gaya mini cewar ko na zauna ko ya sake ni. Zaɓi ya ba ni, saboda ya ce yanzu ya samu kalar macen da yake so." "Haƙuri za ki yi, kina gaya wa Allah kukan ki, saboda yanzu kamar yadda ya ce ba ke kaɗai ba ne, kuma sai kin yi hakuri saboda yawa WASU MAZAN in suka yi sabon aure suna juya wa matansu baya." "Faruk, bai ƙara aure ba yana wulaƙanta ni, ina ga ya samu matar da yake so. Na san cewa rayuwar da zan yi a gidansa, Ubangiji ne kawai gatana, amma ki sani Mama a wannan karon ba zan yi masa biyayya ba, saboda na gaji da cin kashin da yake mini. Ni ma fa mutum ce mai daraja. A rayuwar aure sai a yi ta cewa mace ta yi haƙuri, bayan an san miji yana cutar ta. Shi ya sa asibiti muka yi yawa mama. Ciwon depression ya yi yawa a cikin mata. Mata suna wani irin rayuwa sai kaga mace tana tafiya tana magana kamar zarrariya. Namiji ya ƙunsa mata baƙin ciki in ta zo gida iyayenta ba za su ƙwato mata haƙƙinta ba, sai a ce ta yi haƙuri. A aure mata kawai ya kamata su rinƙa haƙuri? Mama ba zan yarda ciwon depression ya kamanni ba, na haukace a banza su Raihan suna bukata. ." "Ki mai da lamuranki ga Allah, duk wanda ya yi haƙuri ba zai taɓe ba." Kuka ta fashe da shi,"Allah Sarki Ya Ahmad! Ubangiji ya bayyana ka haƙiƙa na yi rashin jigo, amma na yi maka alƙawarin ba zan ƙara zama Faruk ya wulaƙanta rayuwata ba, zan ƙwaci 'yancina, domin tun da na rasa ka bana tunanin a yanzu, akwai abin da ba zan iya rabuwa da shi ba. A yadda nake ji ko ni kaɗai ne a cikin duniya, zan rayu kuma na sanyawa kaina farinciki. " "To ya za mu yi? Ubangijin kawai ya san yana raye ko ya mutu, fatanmu Allah ya bayyana shi." Cewar Mama tana share hawaye. A daren ranar ta gama shirye-shirye ta. Kasa bacci ta yi sai juye-juye take yi. Tana tunanin yadda zamansu zai kasance, don ba zata yarda ta ƙara wulakanta ba. Sallah ta yi ta roƙi Allah ya ba ta haƙurin jure duk abin da za ta gani, sannan ya ƙara cire mata tsoron Faruk ta ƙwaci 'yancinta. Washegari da safe duk yadda Mama ta yi da ita don ta yi kitso da lalli, amma ta ƙi don ba da ninyar zaman auren za ta koma ba, ballanatana ta yi abin da zai burge shi. Kallon kanta ta yi yadda ta rame, duk da cewar ta ciki ba kamar lokacin da ɓacewar Ahmad take sabo ba. Da dadddare Baba ya tsareta sai da ta shirya. Shi da kansa ya kaita har ƙofar gida, sannan ya buga ƙofar."In kin ga dama ki yi hakuri ki zauna da mijin ki, in kuma kin sanya kishi ya sake ki, wallahi kin ji na rantse miki sai dai ki samu wani uban, domin kin san Faruk ba zai karɓi 'ya'yansa ba, ni kuma ba zan riƙe ɗan uban kowa ba, musamman shi da ba shi da ta ido. Kina dai ganin zawaran layinmu sun yi yawa, saboda yanzu maza sun yi ƙaranci. 'Yan matan ma, da yaya suke samun maza, ballanatana zawarawa, kuma in..." Maganar ta maƙale masa sakamakon jin ya buɗe get ɗin. Ganinsu ya sanya shi canza fuska, ya tokare get ɗin yana kallonsu. Dariya Baba ya yi."Ga shi na dawo da ita a rinƙa haƙuri, na ɗauka da ka zo tafiya da ita za ka yi?" "Saboda ni na kaita ko? Sharuɗɗa na kafa mata, don wallahi yanzu ba zan ɗauki rashin mutunci ba, ina da matar kirki da take faranta mini tana mini duk abin da na ke so." Ɗago idanunta ta yi cikin tsana tana kallonsa."Eh ki ji da kyau ɗin haka ki san zaman da za ki yi." Ya ce mata ganin shi take kallonta. "Ayi dai haƙuri komai ya wuce. Ke Nasreen shiga ciki." Ya ce mata. Jin hakan ya sa ta fara tafiya za ta shiga. Ganin haka ya matsa ya ba ta hanya yana harararta. Da ta dumfari gidan gabanta ya fara wani irin sauti. Tana zaune a falo mace ƙatuwar mai jiki sosai. A yadda fuskarta ta nuna ta girmi Nasreen sosai. Tana da ƙiba da kuma ƙirji, sannan ko ina na ta a cike yake. Fuskarta fara ce sosai, domin an dade ana mai. Sanye take cikin wando skin tie ya matse ta dosai, domin kusan yana bayyana surarta, sai riga iya cibi. Kanta babu ɗankwali sai uban attach da aka yi mata kitso ƙanana da su. Tana riƙe da remote a hannunta tana kallon Nigeria film.Tsoro firgici da tashin hankali ya kama ta har sai da ta ji kamar za ta yi hauka. Wani juwa ya kamata har ba ta gani abin da ke gabanta, sai kuma ta dake don ta sanya a ranta daga yanzu ba lokacin da wani a duniya zai tsorata ta bane, ballanatana wata jibgegiyar matarsa ta tsorata ta. Ta riga ta kama yankewa ko zai kasheta ba za ta yi zaman wahala a gidansa ba, don a yanzu ko a mutu ko a yi rai. Za ta nemi farinciki a duk inda take. Ba za ta ƙara yarda wani ɗa namiji ya sanya ta kuka ba. Ita ma mace ce, kuma mace mutum ce da take da daraja. Tana wannan tunani, Faruk ya ƙaraso cikin falon yana ƙoƙarin cire jallabiyar da ya zura. Da ya cire sai ya rage da ga shi sai gajeren wando. Zama ya yi kusa da ita yana watsa wa Nasreen mugun kallo. Peck ya ba ta gashi tare da sakin mata murmushi, ita kuma ta kamo hannunsa. Zan iya hakuri na zauna kuwa?" Ta furta hakan cikin tsanannin tashin hankali tana ƙaranto duk addu'ar da ta fito bakinta. Basarwa ta yi kamar ba ta gani ba. Rashida ta mike zuɓbur tana kallonta. Lokaci ɗaya suka ƙara kallon juna. Tun kafin ya aure ta ta so ya nuna mata hoton Nasreen, amma ya yi mata rantsuwar babu hotonta a wayarsa. Da fari ba ta yarda ba, amma da ta karɓi wayar sai ta yarda da maganarsa cewar ba zai sa ya hotonta ba, abokansa su ga ni su yi masa dariyar matarsa mai kama da taɓarya, amma duk da cewar ba ta da ƙiba kyakkyawar gaske ce na nunawa tsara. Tana da haske amma ba irin sosai ɗin nan ba, doguwa ba sosai ba, sannan jikinta mai kyau, irin wanda yake nunawa in ta samu hutu za ta yi hibs. Idanunta dara-dara, sannan fuskarta doguwa ce da hancinta mai tsawo sosai. Tsananin kyawunta ya ruɗar da ita, musamman ƙuruciyarta, domin ita a tunaninta matarsa babba ce. Ta yadda ta ga ta ta san za ta girme mata sosai. Hankalinta ya tashi, amma kuka da ta tuna duk kyawunta ba ta a idanunsa sai hankalinta ya kwanta. Kallo-kallon juna suka yi, wa junansu kowacce da abin da take tsaƙawa a cikin ranta. Hanyar ƙofar ɗakinta ta yi, zuciyarta a dake ba tare da tanka musu ba za ta shiga. Wata uwar tsawa ya daka mata mai ƙarfi. Tsawar da in ya yi mata a da, sai ta ji hatta hantar cikinta ya kaɗa jikinta ya kama rawa, hawaye ya fara zuba a ƙuncinta, amma a yanzu sai kawai ta juya tana masa wani kallo kamar kashi. Idanunta ta ware sosai ta ɗora a cikin nasa fuskarta babu alamun tsoro. Kallon banza ta watsa masa da shi da Rashida, ta take cikin jikinsa kamar za ta shiga cikin jikinsa, tana shafa sajensa. Ta kama hannun Raihan za ta shiga. Faruk sai ya tsaya sororo, yana kallon ta cikin tsananin mamaki. Goge idanunsa ya yi yana kallon ta da take taku cikin isa za ta shiga ciki. Ya kalli Rashida ta take kallonsa cikin tuhuma. Ya gaya mata cewar ko muryarsa ta ji, sai ta rikice in ya sanya kara ba ta iya tsallake wa, amma sai ta yi mamakin kallon wulaƙanci da rainin da ta ke masa. Ganin ganin haka ya kira sunanta da ƙarfi. "Nasreen!" Ba tare da ta amsa ba, ballantana ya yi tunanin za ta juyi, sai ya ji ta saki tsuka mai ƙarfi ta ci gaba da tafiya. "Kutumar uba!" Faruk ya furta tare da dumfarota tamkar kububuwa. Sai dai, ya cika da mamakin ba ta gudu ba, kuma ba ta jirga daga inda take ba. A zuciyarta ta riga ta rantse ba za ta ƙara yarda ya taɓa jikinta ba, in kuwa ya yi sai ta yi masa abin da ba zai ƙara gigin dukanta ba. Za ta ƙwatarwa kanta 'yanci ba za ta yarda su wulaƙanta ta ba. Lokaci ya yi da za ta zama mace mai 'yanci kuma ta samu walwala a gidan cikin rayuwarta. A shirye take da duk wani hukunci da zai ɗauka. Lokaci ya yi da zai daina dukanta kamar jaka a gaban yaranta. Ni kaina yadda ya dumfarota sai da na tsorata na yarda sahara, amma sai na ga ba ta razana ba. To fa Nasreen anya capacity Faruk zai ɗauka kuwa? Kin ga san halinsa. To ban dai san yadda kika ɗauki alwashin ƙwatowa kanki 'yanci ba, amma bari mu ci gaba da bibiyarki. Laifin daɗi ƙarewa😁😁😁😁 Anan na kammala littafin WASU MAZAN book one sai mun hadu a book two wanda yake na kuɗi ne 500 in aka gama 800. Allah Sarki Nasreen baiwar Allah. Ubangiji ya na sane da halin da kike ciki kuma ba ya bacci. Ki ci gaba da addu'a kina kai masa kukan. Watarana zai ɗube ki kuma ya kawo miki sauki. Masu karatu ya rayuwar Nasreen za ta cigaba da kasancewa a gidan Faruk?😭😭😭😭 Shin za su yi zaman lafiya da Rashida? Wane irin zaman kishi za a yi🙄🙄 Nasreen za ta ci gaba da hakuri ko za ta mike ta ƙwaci yancin ta? Kuna ganin faruk zai ɗauki abin da za ta yi masa? Garin zai yi adalci kuwa tun da ya samu kalar madara zubin ajebota ko ina a cike?😆😆😆 Allah Sarki Damir bawon Allah zai dawo Nigeria kuwa? In har ya dawo wane irin rayuwa zai yi? Ya labarin Ya Ahmad?😭😭😭😭😭 Marwana da take addu'ar Faruk ya rabu da Nasreen har take tunani Innhar ya saketa sai ta yi duk abin da za ta yi ta haɗa soyayya a tsakaninsu har ya aure ta🙄🙄🙄🙄 s. Shin kuna tunanin haka zai yiwu? Damir zai iya kallon Nasreen har ya aure ta su zauna lafiya, bayan babu wacce ya tsana samaa da ita? Ƙarku manta har yanzu ba mu ji Asalinsa ba, sannan ya aka yi rayuwarsu ta rikiɗe ta koma haka. Duk za su samu amsar tambayoyinku a cikin littafin WaSU MAZAN book two wanda paid book ne kan naira 500 zai zo muku, in kuma aka gama 800. Posting safe da yamma babu fashi, domin an riga an gama book ɗin. Ga masu son shiga don su karanta sai a tura kuɗin ta wannan account ɗin. 8144072423 Jamila Lawal opay A turo shedar biya ta wannan numbar 07072971093 Kar ku sake a baku labari ku kasa sannan ku tare har ku karanta. Wannan dai maribuciyar taku ce, mai son faranta muku da kuma.sin ganin farincikin ku. Jamila Lawal Zango Jamsy. Ta shirya ta wasa ƙwaƙwalwaarta don ta sanya ku nishaɗi. Labarin yanzu aka fara don ba a je ko ina ba. Akwai wata irin soyayya mai kama da ƙiyaya, sannan akwai gaba mai ƙarfi da take haddasuwa a tsakanin abokan hamayya biyu.