[28/05 13:02] Mai Zafafa: *WANI ZAMAN* BY SADIYA ABDUKRAZAK Marubuciyar Sandar dukan uwargida Ranar kuka Miji goma Zuciyar mace Matar shige Iya ruwa Wani auren Da walakin Wutar ƙaiƙayi. FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS Labarin ya ƙunshi Kishi Kissa Makirci Cin amana PAGE 1 Kowane mata da miji a farkon aurensu ne suke gina yadda tsarin rayuwarsu zai kasance, wannan lokacin amarcin shi ne babbar damar mace, wanda idan ta sarrafa ta yadda ya dace bisa adalci babu son rai sai a kafa kyakkyawan tubalin da zai samar da rayuwa mai inganci a wannan gidan har abada, idan kuwa aka samu akasin haka tun daga nan sai mace ta rasa damarta, gida ya rushe ya ruɓe, namiji ya dinga yin yadda ya so da rayuwarta. Haka ce ta faru a gidan Usman, sun yi auren soyayya da matarsa Fatima, kuma ƴar'uwarsa ta jini, da farko suna zaune lafiya gwanin sha'awa, kafin komai ya caɓe musu dalilin rashin ginawa gidansu tubali mai inganci, yana son matarsa yana kyautata mata daidai gwargwado, ita ma tana kyautata masa shi da danginsa, amma hakan bai sa ya ɗauke idonsa daga kan matan waje ba, son mata da sha'awarsu a jininsa yake, kuma wannan shi ne babban rauninsa a rayuwa. A halittar Fatima tana da zafin kishi sosai, sannan Usman yana , tana mugun son shi, don haka ta ɗaura ɗamarar hana kowace mace raɓar shi, domin gani take ita a yanzu da Allah Ya yi mata gyaɗar dogo ta samu miji na nunawa sa'a kuma gwarzo, son kowa ƙin wanda ya rasa to fa Allah Ya mallaka mata shi ne domin ita kaɗai da ƴaƴanta, shi ne komai nata, kuma duniyarta sannan tsanin samun lahirarta, don haka dolenta ta yi iya yinta don ganin wata ba ta ƙwace mata shi ba. Usman ɗan gayu ne sosai, mai tsafta da ɗaukar wanka, yana da shiga rai sosai, ga shi matashin ɗan kasuwa wanda ake garawa da shi, ƴan canji suka zauna masa, yana kasuwancin kaya kala daban-daban, sannan yana siyar da motoci. Sai dai ita Fatima tana da rauni a ɓangaren tsafta, ba ta damu da gyara gidanta yadda ya kamata ba, komai a hargitse, sannan ba ta iya girkin fita kunya ba, tana da sakaci dai ta wannan fannin, haka dai suke gudanar da rayuwarsu har ta yi haihuwar farko, ta haifi ɗanta namiji, mai suna Ibrahim ana kiransa da Mu'azzaman. Tana zaune da Usman da zuciyarta ɗaya, ba ta taɓa zarginsa da aikata wani abin da bai dace ba, idan zai fita ya bar wayarsa a gida ko kallo ba ta ishe ta ba, saboda yadda ta yarda da shi, ashe dai idan ana cin ɓaure ba a tona cikinsa, akwai wata rana da ba za ta taɓa mantawa da ita ba, domin a ranar ne ta san wane ne mijinta, ta san wata ɓoyayyiyar ɗabi'arsa da ba ta san yana da ita ba a baya. A lokacin ba ta daɗe da yin arba'in ba bayan haihuwar Mu'azzam, akwai wata a maƙotansu, buduruwa ce, amma irin manyan ƴan'matan nan ne, ta daɗe a gida ba ta yi aure ba, don ta girmi Fatima sosai, sunanta Lami, kuma irin mutanen nan ne da ba ka san ma taƙamaiman addininsu ba, to su dai ba sa yin sallah kuma ba sa zuwa coci, suna mutunci sosai da iyayenta, kuma tana shigowa gidan su yi fira da Fatima. Watarana ta shigo da daddare suna cikin fira, sai ga baban Mu'azzam ya dawo gidan, suka gaisa, Lami ta tashi za ta tafi, yana murmushi ya ce"A'a ki yi zamanki, ko dai ba kya so na ji gulmar da kuke yi ne?" Duka suka yi dariya, sai kuwa ta zauna, can sai Mu'azzam da yake ɗaki yana bacci ya farka, hakan ya sa Fatima ta tafi ɗakin don ta lallaɓa shi ya koma bacci, abunka da jikin jego gajiyayye, ga shi an wuni ana kujiba-kujibar tsakar gida, don haka daga lallaɓa yaron bacci ya kwasheta, tun ƙarfe takwas ba ta farka ba sai wajen sha ɗaya, da fito falo ta tarar Lami ta tafi, ta koma ta kwanta. Tun daga ranar kullum sai Lami ta shigo da daddare, ta ce ta zo fira, shi kuma baban Mu'azzam sai ya tsiri dawowa da wuri, sannan kamar abun almara ita kuma Fatima kullum sai Mu'azzam ya farka, idan ta je ta lallaɓa shi sai bacci ya ɗauke ta, kasancewarta mai nauyin bacci. Fatima ta zauna ta yi karatun ta nutsu, ta fara tunanin me yasa Lami take zuwa kullum da daddare? Me yasa shi ma mijinta ya canza lokacin dawowa? Sannan ta fara zargin wannan baccin da take yi ba ta sanin lokacin da Lami take tafiya anya alkhairi ne kuwa? Anya ba ta yin wauta? Hakan ya sa yau ta ce dole za ta fake su ta ga idan da matsala ko babu. Yau ma kamar kullum Lami ta shigo, riga ce bes a jikinta duk hammata a waje da siket, tun da ba musulma ba ce ba ruwanta da hijjabi, ta zauna suka fara hira, babu jimawa baban Mu'azzam ya dawo, ya miƙo mata leda ya ce"Fati ga kaza". Ta ce"Bacci nake ji wallahi, sai da safen zan ci". Ta bar ledar akan senter table ta shiga ɗakinta, ta tsaya tana safa da marwa, ta bada tazarar mintuma goma sha biyar, sannan ta lallaɓo a hankali ta buɗe labule ta leƙo, ƙirjinta ya yi mummunar bugawa sakamakon baƙin ganin da ta yi, Lami ce zaune a kan cinyar baban Mu'azzam, hannunsa ɗaya yana cikin rigarta, ɗayan kuma yana bata kaza a baki, hankalinsu a kwance tamkar dai ma'aurata, Fatima ta daskare tana kallonsu ƙirjinta yana bugawa, sun shagala ba su taɓa tunanin tana kallonsu ba, idan ya ba ta kazar sai ya yi kissing ɗinta, can dai ta ga ya ɗage rigarta, ko bireziya babu a jikinta, yana ƙoƙarin kai bakinsa ƙirjinta, Fatima ta ji zuciya ta ciyo ta yi wani ihu ba, ta yi tsalle ta yi kansu, tana zuwa ta wanke shi da mari, Lami ta zabura ta miƙe tsaye, ai kuwa Fatima ta yi kukan kura ta hau ta da duka, tamkar sa'arta, tana ta zaginta tana"Matsiyaciya maci amana, mai warin Hamata".Lami ta fizge ta gudu Fatima tana ta zaginta. Zuciyar Fatima kamar za ta fashe saboda kishi, ta dawo kan Usman da duka, yana ta riƙe ta yana ba ta haƙuri, ta fizge ta shige ɗaki da gudu, ta saka sakata, duk bugun da yake yi ba ta buɗe ba, ta kwanta tana ta kuka, da tunanin wai dama haka mijinta yake? Ya girgiza zuciyarta sosai ya raunata ta, ya shammace ta, ashe dai da gaske ba a shaidar miji? Ta raba dare tana tunanin dalilinsa na ƙyalle ido a matan waje, duk hankalinta ya tashi, domin ta san duk namijin da zai zo gidan aurensa ya aikata wannan abu da maƙociyarsu to fa tabbas dama ya saba, ko fargabar za ta iya fitowa ba ya ji saboda idonsa ya rufe? Ta yi kuka mai isarta kafin bacci ya ɗauke ta mai cike da ƙunci. A ɓangaren baban Mu'azzam kuwa da ya lura ba za ta buɗe ƙofar ba sai ya haƙura ya tafi ɗakinsa ya kwanta, nadama duk ta kama shi, bai so a ce Nana ta san da wannan halin nasa ba, domin ya san dole zai rage ƙima a idonta, shi kansa wani lokacin yana takaicin halinsa, amma yana rasa yadda zai yi, saboda abun kusan ya zame masa jini, idan ya ga mace ƙafarsa har rawa take ɗauka, ya rasa saitinsa, amma tun da yanzu matarsa ta san halinsa dole ya yi taka-tsan-tsan. Ya ɗakko wayarsa ya kira Lami, tana ɗagawa ta ce"Ka ga abin da ka ja mini ko? Wannan ƙaramar yarinyar har ta samu damar dukana da zagi saboda kai ko?" Ya ce"Ki yi haƙuri..." "Ai dama ka so tozarta ni ne, ka ce na dinga zuwa ba za a samu matsala ba, yanzu ga shi nan ai za ta yaɗa ni a unguwa na yi ta jin kunya". Ya ce"Ba za ta yaɗa ki ba in sha Allah, kawai dai shikenan kar ki sake zuwa". Ta ce"Yanzu a ina za mu dinga haɗuwa kenan?" Ya ce"Don Allah mu bar shi haka, tun da ta sani shikenan za ta saka ido a kanmu, a haƙura kawai, ki turo min acconut number na sallame ki". Kamar za ta yi kuka ta ce"Don Allah Usman kar ka yi mini haka, wallahi ina sonka, ina son kasancewa da kai ko sau ɗaya ne". Ya ce"Babu wannan damar ki turo min kawai na sallame ki". Ta ce"Nu ba kuɗinka nake so ba ai kai nake so". Ya yi tsaki ya ce"Zan saka ki a blacklist ne fa, idan ba kya son kuɗin shikenan". Da jin haka ta katse wayar ta tura masa, ya saka mata dubu hamsin ya yi block ɗinta, haka ya yi bacci cike da tunanin yadda zai shawo kan matarsa. 08028966015 [28/05 13:02] Mai Zafafa: https://chat.whatsapp.com/IqwGrPcKXM47271YQuTB2R *WANI ZAMAN* BY SADIYA ABDULRAZAK Marubuciyar Sandar dukan uwargida Ranar kuka Miji goma Zuciyar mace Matar shige Iya ruwa Wani auren da sauransu FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS Labarin ya ƙunshi Kishi Kissa Makirci Cin amana PAGE 2 Washegari Fatima ta kasa fitowa daga ɗakinta, saboda ba ta so ma ta yi ido huɗu da mijinta, sam ba ta san ganin shi, saboda kallon shi ba zai haifar mata da komai ba sai ɓacin rai, shi kuma tun asuba da ya dawo daga masallaci yake zaune a falo, jira yake yi ta fito ya ba ta haƙuri su fahimci juna, duk kunya da nadamar abin da ya aikata sun ishe shi, ganin har bakwai takwas ba ta fito ba, sai ya tashi a sanyaye ya shiga ɗakin, ya tarar da ita kwance a gado amma ba bacci take yi ba, ƙarar buɗe ƙofar da ya yi ne ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, ta juya ta kalle shi, kawai sai zuciyarta ta hasko mata hoton da yake kafe a cikinta, wanda take ganin ba zai goge ba har abada, ta hango shi ɗauke da Lami a cinyarsa hannunsa a cikin rigarta, zuciyarta ta sake kumbura, ta rutse ido hawaye suka sakko, ji take har gara a ce kama ta ya yi ya lakaɗa mata duka akan wannan abin da ya yi mata, da muryar kuka ta ce"Don Allah ka fita, ba na son ganinka!". Ya ƙaraso ya zauna a bakin gadon, ya ce"Ki yi haƙuri, na san ban kyauta miki ba, amma wallahi ba halina ba ne, sharrin shaiɗan ne da ruɗin zuciya, da kaidin mace, yaudarata ta yi wallahi, kuma ita ta zo ta zauna min, sannan jiyan ne kawai abun ya taɓa faruwa". Fatima ta ce"Wallahi ba zan taɓa yarda da kai ba, tun da har ka gwada a cikin gida na tabbata ka saba yi a waje, idan ka cuce ni Allah Ya saka mini". Ya ce"Don Allah ki yi haƙuri, na karɓi laifina na yi nadama, kuma in sha Allahu na farko na ƙarshe". Ta juyat da kai gefe, ya matso yana shafa yatsun ƙafarta yake cewa"Kin haƙura? Don Allah ki yi haƙuri, wallahi na yi nadama". Ta ƙi cewa komai. Ya ce"Ki fito mana don Allah, kin ga yau sassafe na so na fita, amma na kasa saboda na san ranki a ɓace yake". Ta yi banza da shi. Ya tashi ya fita, sai ya samu kansa da shiga kitchen, ya haɗa musu abun karyawa, ya ɗakko ya kawo mata, har lokacin tana kwance, ya zauna a ɗakin ya ci nashi, ya sake ba ta haƙuri da nuna nadama sosai kafin ya ce"Yanzu me kike so? Mene ne babu a gidan? Me zan taho miki da shi?" Ta ce"Ba na buƙatar komai naka, ka je ka cigaba da bawa matan wajen". Ya ce"To na ji, amma dai don Allah ki yi haƙuri, idan kin sake kama ni sai ki yi mini komai ma". Ya ce"Ki ci abincin, ko za mu fita ki ci a gidan cin abinci?" Ta yi masa wani kallo mai kama da harara, don tana yawan roƙonsa kan su je gidan cin abincin musamman idan ranar tana jin ganda, ko kuma tana son yin fafar a ganta da mijinta ɗan gayu, amma sai ya ƙi ya ce bai ga amfanin haka ba, ga kayan abinci ya ajiye ba zai je ya siya a waje ba, shi ne yau da ya san ya cuce ta ya guma mata baƙinciki zai ce ta zo su je, ta ce"Don Allah ka tafi, wannan borin kunyar taka ya ishe ni haka". Ya ce"A dai yi haƙuri, kuma don Allah ba ruwanki da Lami, idan kika ce za ki kula ta kamar kin daɓawa kanki wuƙa ne, kin ga kanmu za ki tonawa asiri ko?" Ta yi kamar ba ta ji ba, ya fice daga gidan yana cewa"Sai na dawo". Yau ta kasa ce masa a dawo lafiya.Da zai ya dawo ya yo mata uwar siyayya, kayan ciye-ciye da na amfanin gida, ta ji daɗi amma ba ta nuna ba, sam ta ƙi sakar masa fuska, shi kuma duk ya takura, suka shafe kwana uku a haka, kullum da abubuwan da zai siyo mata, sannan kullum sai ya ba ta haƙuri da nuna nadamarsa, ya siyo mata babbar wayar da ta daɗe tana faɗa masa tana so, wannan ya sa ta huce gabaɗaya, ta saki jiki ta daina nuna masa komai, sai dai fa wannan abin da ya yi yana nan maƙale a ranta, don ba ta jin za ta manta da shi. Tun da ta haihu ta yi tsarki ba ta koma ɗakinsa da kwana ba, sai take tunanin ko har da wannan kewar tata a bada gudunmawa ya aikata wannan abun, don haka ta yanke za ta gyara jikinta sosai ta koma masa, tun tana amarya dama ba ta wasa da maganin mata, duk inda ta ji indai da kuɗi a hannunta za ta siya, sai ta sayi maganin mata ba ta sayi humra ba, don haka yanzun ma ta nemi kuɗi a wajensa, babu musu ya ba ta, dama can ba ya yi mata rowa, ballantana yanzu kuma da yake neman ta yarda da shi, ta shirya ta ta je gidan mai maganin da ta saba siya, ta haɗa mata magunguna masu kyau, kwananta uku tana sha, ita kanta ta ji sauyi sosai a jikinta, don haka ta shirya gobe za ta koma ɗakin baban Mu'azzam, da safe ta fito cikin shirinta,sun yi da shi tun jiya yau zai kai ta gidan gyaran jiki, dulka za a yi mata da kitso da ƙunshi, ta fito riƙe da ɗanta a kafaɗa da jakarata a hannu, ya kalle ta yana murmushi ya ce"To da me zan taimaka? Ɗan ko jakar?" Ita ma murmushin ta yi tana kallon yadda shaddar jikinsa ta haska shi ya yi kyau sosai, ta ce"Za ka zuba mini kuɗi a jakar ne?" Ya ce"To me zai hana?" Ta miƙa masa jakar, ya karɓa ya rataya a kafaɗa kamar mace, hakan ya sa ta tuntsire da dariya ta ce"Shi kenan ka zama mijin Hajiya mai riƙe mata jaka". Ya ce"Ba wata Hajiya, yanzu fa kika gama kafa sharaɗin zan zuba miki kuɗi a jaka, Hajiya ai ita take zubawa mijin kuɗi a aljihu ko account". Ta ce"Ai kuwa idan hakane ni ba hajiya ba ce, ka ga ba ni jakata". Ya ce"A'a mu je dai na riƙe miki, amma babu batun mijin hajiya ki soke shi". Suka shiga mota suka tafi, suna ta fira cikin raha da dariya, suka ƙarasa wajen, ya ce"To ya za a yi? Zan jira ki ne ko sai an gama ki kira ni na dawo na ɗauke ki?" Ta ce"Ai gara ka je ɗin, kar a zaunar da kai, duk da safiya ce ba lallai a samu layi ba". Ya ce"To shikenan mu je na raka ki sai na ji kuɗin". Suka shiga a tare har lokacin yana riƙe da jakarta, suka tarar da matar mai wajen da yaranda suna kintsa wajen, da alama ba su daɗe da buɗe shagon ba, tun da suka shiga idon Usman ya sauka akan wata yarinya, surarta ta tafi da imaninsa, nan take ya ji gabaɗaya kansa ya fara hayaƙi, yana ta kokowa da control ɗinsa, ya kafe ta da ido yayin da Fatima take yi wa matar bayanin abin da ya kawo ta, sanda ta juyo don ta yi masa magana har sai da ta yi mamakin ganin saɓ hankalinsa ba ya kansu yana kallon can gefe, ta bi wajen da kallo, ta ga yarinya ce buduruwa tana ta goge-goge, babu ko mayafi a jikinta sai riga t-shirt wacce ta bayyana halittar ƙirjinta da siket, gabanta ya faɗi, zuciyarta ta tsinke ta yi baƙi nan take, don ta gane ita yake kallo, da ɗan ƙarfi ta ce"Baban Mu'az!". Ya ɗan dirirece kafin ya ce"Na'am". Ta ce"Mun gama magana, ka je kawai, idan an gama zan kira ka a waya". Yana satar kallon yarinyar ya ce"Ai kawai zan zauna na jira ki ɗin, babu damuwa ma". Ta ce"To ka je daga mota ko?" Matar ta ce"A'a ga kujera nan ya zauna". Kafin ma ta rufe baki ya ja kujera ta zauna, yana sauke numfashi, idonsa kafe a kan yarinyar nan har suka gama saita komai ta zo ta fara yi wa Fatima ƙunshin. Shi kaɗai ya san halin da yake ciki, ji yake zai iya ba wa yarinyar nan ko nawa ne indai za ta yarda da shi ko na minti talatin ne, ya daɗe bai ga macen da ta ruɗa shi kamar wannan ba, sai kallonta yake yi, so yake su haɗa ido ya yi mata alama ko da ido ko da hannu, idan ya dace ƴar hannu ce sai su san dabarar da za su yi su yi musayar lamba, amma hankalinta yana kan ƙunshin da take yi, yana ta chart a wayarsa yana kallonsu har aka gama, wata tana yiwa Fatima kitso, ganin wasu sun zo ya sa shi fita waje ya koma ƙofar wajen ya zauna, zuciyarsa tana ta azalzalarsa, ji yake idan bai samu ya taɓa yarinyar nan ba kamar yau ba zai iya bacci ba, ya saƙa wannan ya kunce ya ƙulla wancen shikaɗai, ana dab da gama mata ya koma cikin shagon, Fatima da ta gama lura da kallon da yake yi wa yarinyar nan duk kishi ya kama ta, ta ce"Ai an gama ma, ka he wajen ka jira". Ya ce"To kawo Mu'az ɗin, sai kuka yake". Ba a cire mata lallen ba, don haka ita wannan yarinya da ta soki rayuwarsa da kibiya, ita ce ta ɗauki ɗan ta tafi miƙa masa, idon Fatima yana kansu, ganin yadda ya narke ido yana kallon yarinyar kamar tsohon gwarto har wani lashe baki yake yi, dama ta san wannan halayyarsa ce, ko ita ce ya matsu da ita haka yake lasar bakin nan, don haka ta gama fahimtar inda ya doda game da yarinyar, ita kuwa yarinyar da zuciyarta ɗata take miƙa masa yaron, Usman ya ga wannan damar idan ta wuce shi ba, don haka ya kai hannunsa kan ƙirjinta kai tsaye, ya taro yaron da ɗayan hannu, saukar hannunsa tarr a cikin idon Fatima, wacce ta ji zuciyarta ta yi dokawar da ba ta taɓa yin irinta ba, sai da ta ji kamar numfashinta zai ɗauke. Ita kuwa yarinyar da sauri ta matsa bata tare da ƙunduma ashar, hakan ya jawo hankalin duka mutanen wajen, suka fara kallonsu, ta ce"Ni za ka taɓa? Saboda ka cika ɗan iska a gaban mutane za ka saka hannu a jikina?" Usman ya ruɗe ya fara rawar murya ya ce"By...by mistake, wallahi ban sani ba, na zama zanin jikin yaron na danƙo". A fusace ta ce"Wallahi ka taɓa Allah Ya isa, ɗan iska, asararre babban banza, ɗan wahala, kwaro, daƙiƙi!". Kowa a wajen ya yi tsit, shi kuma ya juya ya fice ɗauke da ɗansa, Fatima ta ji ina ma ƙasa ta tsage ta shige, ko ta huta da wannan kunyar da ta mamaye ta, haka ta miƙe tsaye da ƙunshin ba ta cire ba, ta zuge jakarta ta biya kuɗin, ta fito daga wajen takalmi a hannu, tana tafiya kamar za ta faɗi saboda yadda santsin ledar ƙunshin yake kwasarta, ta shiga motar ta rufo, ta tarar da shi ya sunkuyar da kai, ta rasa me ma za ta ce masa, ya ce"Ki yi haƙuri don Allah Nana, mutane ne ba su da fahimta, ban da ta yi niyyar yi min sharri daga karɓar yaro?" A fusace ta ce"Dalla rufe mini baki...!" "Ni kike yi wa tsawa? Fatima?" Ta ce"Na yi ɗin, ai ka cancanci fiye da hakan ma, ashe kai abun naka ya wuce zatona? Usman a titi a idon mutane, a gabana ka kai hannu ka taɓa mace?Ashe har ka shahara haka? Waye kai? Da wa nake zaune ne?" Ta sake fashewa da kuka. Ta ce"To wallahi ban yafe maka ba, kuma na gama zama da kai, daga nan ka kai ni gidanmu!". Ta yi maganar cikin fitar hayyaci, domin ta san ba ta da wani gidan da ya fi na mijinta, tun da mahaifiyarta ba ta raye, kuma ta fuskanci ƙalubalen rayuwa tsakanin rasuwarta da kafin aurenta da Usman ɗin, kusan ma a ce mahaifiyar Usman ɗin ita ce gatanta, duk da tana da sauran dangin uwa da na uba, amma karamcin matar a gare ta ya sa take ganin ta fi wasu danginta sau dubu. "Kin ga ki yi haƙuri" Ya faɗa a daƙile, don ransa ya ɓaci da wannan tsawar da ta yi masa. Ta cigaba da yi masa kalaman cin mutunci, shi kuma ya ja motar suka tafi, ya zama kamar kurma ya kasa ce mata komai, saboda ya san ba shi da gaskiya, a ransa kuwa rayawa yake yi anya ba zai dawo su sasanta da yarinyar nan ba? Yana ajiye ta ya bar gidan, don ya gaji da wannan tijarar tata, Fatima ta ci kuka ta gode Allah, tun daga ranar kuma ta gama sanin da wa take zaman aure, tana son Usman, ba ta ma hasashen rabuwa da shi saboda wannan halin nasa, don haka ta shiga tunanin wace hanya za ta bi ta canza masa tunani, ya dawo gareta ya kafe a kanta ita kaɗai? Ya daina ganin kowace mace sai ita? Tunaninta bai tsaya a ko'ina ba sai a kan maganin mata, gani take kawai ita ta gaza ne, ba ta da ni'imar da za ta gamsar da shi, shiyasa yake neman na waje, don haka ta yanke dole a yau ba sai gobe ba za ta samawa kanta mafita. Da yamma ta saka hijjabi ta shiga gidan maƙociyarta wacce ta kasance ƙawarta, Salima irin matan nan ne waɗanda suka ɗauki maganin mata a matsayin makaminsu na zaman aure, suka gaisa ta ce mata so take ta samo mata maganin da zai saka mijinta ya kau da ido daga ganin kowace mace sai ita kaɗai, Salima ta ce mata ai kuwa akwai wani magani da ta gwada ta ga aikinsa sosai, don haka za ta yi mata hanya ta siya, nan take ta kira mai maganin a waya, ta ce mata gobe za ta kawo mata har gida, Fatima ta yi wa Salima sallama ta tafi gida tana jin sanyi a ranta, saboda rashin sanin matsalar da za ta shiga silar wannan maganin, inda ta sani da ba ta kai kanta ba. 08028966015 [28/05 13:02] Mai Zafafa: https://chat.whatsapp.com/KHaNhtgfrBoAKxQ6GGKFyq *WANI ZAMAN* BY SADIYA ABDULRAZAK Marubuciyar Sandar dukan uwargida Ranar kuka Miji goma Zuciyar mace Matar shige Iya ruwa Wani auren da sauransu FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS Labarin ya ƙunshi Kishi Kissa Makirci Cin amana PAGE 3 Fatima ta koma gida tana jin rabin damuwarta ya yaye, ko da Usman ya dawo ba ta tada masa zancen abin da ya yi ba, shi ma sai ya yi shiru, sai dai yana ta kaffa-kaffa da ita, ko da ya neme ta a daren ba ta hana shi ba, saboda ta san fushi ba zai zama maslaha ba. Washegari kafin ya fita ta tambaye shi kuɗi, babu musu ya ba ta, wajen ƙarfe goma mai maganin ta zo ta kawo mata, wani abu ne ta ba ta ce saka shi a za ta yi a gabanta sai bayan kwana biyu za ta ciro shi, sannan ta ba ta wani mai kama da zuma ta ce a sati sau ɗaya za ta dinga shan cokali ɗaya, Fatima ta biya ta kuɗinta, nan take ta fara amfani da maganin, a ranar ta yi wankan dare ta ci kwalliya ta tafi ɗakinsa, ai kuwa ta ga kyaun maganin nan sosai, har tunani ta fara yi anya ba sa haɗawa da Malaimai kuwa? Washegari baban Mu'az wani kallo na musamman yake yi mata, cikin sati biyu ta bi ƙa'idar maganin nan, Usman ya ninka kyautatawarsa a gare ta, ya rage yin dare a waje, ana yin sallar isha'i zai dawo gida, ya rage bawa wayarsa muhimmanci, babu wani kiraye-kirayen ƴan'mata, sai nan-nan yake yi da ita, tare da kyautar bazata, hakan ya sa ta ƙara ƙaimi wajen shan maganin, a maimakon duk satin da aka ce ta sha cokali ɗaya, sai take shan cokali ɗaya kullum, saboda aikinsa ya linka fiye da yadda yake yi, maganin da ya kamata ya ƙare a wata uku sai ya ƙare a sati uku, ta shirya ta tafi gidan mai magani, bayan ta yaba mata kyaunsa ta faɗa mata ya ƙare za ta sayi wani. Mai maganin ta dafe ƙirji ta ce"Ya ƙare!? Ta ta zai ƙare tun yanzu bayan na wata uku na ba ki? Anya kin bi ƙa'ida kuwa?" Fatima ta ce"Ni fa daga baya kullum cokali ɗaya nake sha". Mai magani ta dinga salati ta ce"To Allah Ya tsare ki kuwa, amma wallahi ko miliyan za ki ba ni ba zan sake siyar miki da maganin nan ba, sai dai ku sayi wani kalar". Fatima ta ce"A haba don Allah ki taimaka mini, ban taɓa amfani da magani mai kyaunsa ba wallahi". Duk yadda ta kaɗa mai maganin nan ta ƙi siyar mata, ta haƙura ta koma gida tana mamaki, don ita ba ta ga wata illarsa ba. Duk da maganin ya ƙare amma ba ta daina ganin aikinsa ba, a wannan lokacin sun samu zaman lafiya sosai da mijinta, ya rage abubuwan da yake yi. Wata rana da safe tana zaune tana chart hankali kwance, kawai ta fara ciwon mara, ciwo mai tsanani sak na naƙuda, kamar wacce za ta yi ɓari. Tun tana daurewa har ta kasa, ta kwanta tana ta juyi, ga shi ranar Usman ba ya garin, ta aika aka siyo mata maganin ciwon mara, ta sha a banza, ciwo sai gaba yake yi, ta gama saddaƙarwa ciki ta samu zai zube, don haka ba ta kawo tunanin wannan maganin ne ya yi mata illa ba, haka ta wuni cikin mawuyacin hali, dab da magriba ta kira shi a waya ta faɗa masa, ya ce ta tafi asibiti shi ma yana hanya. Ta shiga maƙota ta ba da ajiyar ɗanta, don kar ta jefar da shi a hanya saboda azabar ciwo, ta je wani asibitin kuɗi da yake kusa da su, ta yi wa likita bayanin abin da yake damunta, ya yi mata scanning, ya tsaya da mamaki a fuskarsa ya ce mata"Amma dai kina yawan amfani da magungunan mata ko?" Gabanta ya faɗi, ta san faɗan likitoci don haka ta girgiza kai ta ce"A'a, ban yi amfani da komai ba". Ya ce"To amma dai da mamaki, wani datti ne ya taru a mararki, kuma yawanci silar shaye-shayen magunguna barkatai ne yake haifarwa, dole sai an yi miki tiyata an cire shi, idan ba haka ba rayuwarki tana cikin garari". Fatima ta fara kuka, duk ta rikice da jin zancen tiyata, likitan ya ce"Yanzu ki je gida ki shirya, sai ki taho tare da mijinki ko iyayenki, a yi miki aiki a cire wannan dattin, idan ba haka ba komai zai iya faruwa". Fatima ta ce"To na gode". Ta fita daga asibitin tana share hawaye, ga azabar ciwo ga ta tashin hankali, sai ta kasa komawa gidan, ta zarce wani asibitin, don rana ganin kamar wannan likitan ƙarya ya faɗa mata. Shi ma nan ɗin kamar yadda asibitin farko suka yi mata bayani, haka ya faɗa mata datti ne a mararta, sai dai shi ya ce zai iya rubuta mata magunguna ta sha, ƙila dattin ya fito, idan bai fita ba sai a yi aikin. Ya rubuta mata magungunan ta fita, ba ta zarce ko'ina ba sai babban kemis, ta sayi magungunan ta dawo gida, ko zama ba ta yi ba ta sha maganin, sannan ta karɓo ɗanta. Ana kiran sallar isha'i ta ji ciwon ya ƙaru, ya taso gadan-gadan, nan fa ta fara nishi mai ƙarfi tamkar dai mai naƙuda, kamar ɗa zai fito ta gabanta, hakan ya sa ta tafi banɗaki ta tsukunna, sai kuwa wasu irin abubuwa suka fara fitowa, baƙi da shi kamar chocolate, idan ta yi nishi mai ƙarfi sai ya fito curi guda, idan ciwon ya lafa ta yi tsarki ta koma ɗaki, idan ya taso ta koma banɗakin, cikin ƙanƙanin lokaci ta jigata. Wajen ƙarfe tara Usman ya dawo, ya tarar da ita a galabaice, ya ce su koma asibitin, ta ce ai ta ji sauƙi ma, saboda ba ta son ya gane maganin mata ne ya ja mata matsala, ya siyo mata abinci ta ci, a ranar a ɗakinta ta kwana, saboda kar ya ga tana yawan shiga banɗaki, kwana ta yi tana zubar da wannan abun, sannan ta samu sauƙin ciwon marar. Washegari da safe ta koma asibitin, aka sake yi mata scanning, aka tabbatar mata da ya fita babu komai yanzu, sannan aka yi mata faɗan ta kiyaye abubuwan da za ta dinga sha ko amfani da su, ta koma gida tana yi wa kanta barka. Tun daga nan sai ta tsorata da duka maganin mata, ta jingine shi a gefe guda, babu jimawa kuma mijinta ya koma gidan jiya, tare ɓa da sabon salon da ba ya yi mata, yanzu haka kawai saa ya tsiri yi mata faɗa, musamman akan rashin tsaftarta da rashin iya girki, abun yana damun shi sosai, zai yo cefane haɗaɗɗe amma a kwaɓa masa abinci kamar a gidan yari, wanke-wanke sai a samu na kwana uku a gidan, kitchen har tsami yake yi saboda lalataccen abinci, ga shi sam ba ta damuwa da kwalliya, idan ka ganta fess to fita za ta yi. Haka suka cigaba da zama har ta sake wata haihuwar, zuwa yanzu ta saba da halinsa, domin neman matansa a bayyane yake, ta sha yi masa laɓe a ɗakinsa sai ta ji yana waya da mace, tun tana daurewa har ta fito suka hau sama suka faɗo akan wannan wayar, ta cw kar ya sake yi mata waya da mata a gida, rai dai ya ɓaci amma sam bai fasa ba, tana yawan jin labaran an gan shi da wata, hatta ƴan'matan unguwarsu bai ƙyale ba. Maganin matan dama shi ta riƙa a matsayin makaminta, to kuma yanzu ta daina don ta tsira da lafiyarta. Sosai take damuwa da wannan halin nasa, yanzu ya ma rage zama da ita sosai, ya koyi wani tsare gida da ƙananun wulaƙanci, idan ka ga dariyarsa to waya yake yi. Wataran ta same shi har da hawayenta tana tambayarsa me take yi masa wanda ya sa duk ya canza mata? Ya yi banza da ita yana danna waya, cikin kuka ta ce"Don Allah baban Mu'az me nake yi maka? Gabaɗata ka tsane ni ka jingine ni a gefe, yau na ji an ganka da wannan gobe an ganka da waccen, ni ba mace ba ce ba wai? Me matan wajen suka fi ni ne?" Ya ce"To me nake yi miki ne wai? Ci nake hana ki ko sutura?" Ta ce"Ba ka hana ni su ba, amma ai ka san ba iya su kaɗai nake buƙata ba, har da kulawarka, ba macen da za ta so a ce mijinta yana neman wasu a waje, kana ta zubar mini da ƙima, yara ƙanana suna ganina a banza a hoto, a wacce ba ta gamsar da mijinta". Ta sassauta murya ta ce"Don Allah mu tattauna mu gyara, zan daina duk wasu abubuwa da ba ka so wallahi, me nake yi maka ne?" Ta ba shi tausayi, ba wai son ta ne ba ya yi ba, kawai dai shi wannan son matan ƙaddararsa ne, yana jin Fatima ta yi masa kaɗan ita kaɗai, don haka yakr haɗawa da na wajen, duk da ya san wannan ba hujja ba ce, yana da niyyar ƙara aure, amma ba yanzu ba, sai ya gama lissafin da yake yi. A tsanake ya ce"Ni fa ba wani abu kike yi mini ba, kawai wannan ƙazantar taki ce ba na so, ke kenan ba za ki gyara jikinki ba? Gidana duk kin dafar mini da shi, komai ya fita daga hayyacinsa? A ce falo ma ba kullum za ki share ba, banɗaki zarni, sai dai na wanke nawa, wannan wace irin rayuwa ce? Sannan batun girkin nan, zan siyo komai na ajiye amma ke ba za ki sarrafa yadda ya dace ba, sai ki yi abinci babu fasali, wataran kamar cikina zai yi ciwo, na rasa ya ma kike ki yi wanj kaɗon, ki kwakkwaɓa abinci tun daga ido babu kyaun gani, ballantana kuma an kai baki, yanzu wannan jollop ɗin wake da shinkafar da kika yi yau tsakaninki da Allah a ido ba za a ce fate-fate ba ne? Kina yin adalci kenan? Wallahi ina son gayyatar abokaina cin abincin gidana, amma saboda gudun jin kunya sai na haƙura na share, idan na je gidan abokai na ga giriki kamar ba a ƙasar nan ba, kuma wallahi ba fi na yin cefane suka yi ba, kawai dai iyawa ce". Ta ce"Duk na ji, kuma na karɓi laifina, amma mene ne zai haɗa waɗan nan abubuwan da neman matanka?" Ya ce"To ban ganki fes ba kullum ke ga ki nan kamar dusa me zai hana na ga wata a waje na yi sha'awa? Ni fa zan fara gina wannan babban filin nawa, ina kallamawa aure zan yi in sha Allah!". Fatima ta ji kamar ya caka mata kibiya, ta fara share hawaye kafin ta ce"Don Allah ka daina wannan maganar, wallahi zan gyara indai iya wannan ne matsalata na yi alƙawarin zan gyara". Ya ce"To Allah Ya sa, idan kin gyara ni kuma na yi alƙawarin zan daina yin komai". Sai kuma ya yi murmushi ya ce"Kenan saboda kin ji batun kishiya ne za ki gyara ko?" Ta ce"A'a". Ya ce"To sau nawa ina faɗa akan wannan abubuwan, amma kullum babu canji?" Ta ce"Ni dai tun da na ce zan gyara shikenan, a bar maganar kawai". Ya ce"Allah Ya ba mu ikon gyarawa". Tun daga washegari ta fara ƙoƙarin gyarawa, ta cire ganda ta gyara gidanta tsaf, sannan ta cire girman kai ta kira yayarta a waya ta yi mata zancen rashin iya girkinta, ta ba ta shawararwarin da za su amfane ta, kamar na daidaita ruwan sanwar da kuma kula da magi, da rage yawan juya abinci, sannan ta ce mata duk abin da za ta dafa ta dinga faɗa mata da kuma adadin yawan ita kuma za ta dinga koya mata yadda za ta yi. Cikin ƙanƙanin lokaci hannunta ya fara faɗawa a girki, kuma tana kula da gidan da jikinta, don haka zaman nasu da Usman ya fara saituwa, shi ma ya ce mata ya daina kula mata, kuma ta yarda har zuciyarta, saboda ya canza takunsa, amma a zahiri bai daina komai ba. 08028966015 [28/05 13:02] Mai Zafafa: https://chat.whatsapp.com/KHaNhtgfrBoAKxQ6GGKFyq *WANI ZAMAN* BY SADIYA ABDULRAZAK Marubuciyar Sandar dukan uwargida Ranar kuka Miji goma Zuciyar mace Matar shige Iya ruwa Wani auren da sauransu FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS Labarin ya ƙunshi Kishi Kissa Makirci Cin amana PAGE 4 Da farko da ta yarda cewar ya daina sun samu fahimtar juna, hankalinta ya kwanta sosai, suna zaman lafiya, kuma ɓangaren tsafta tana ta ƙoƙarinta. Da yake da kuɗi da kuma niyyar ƙara aure a ransa, babu jimawa ya kammala ginin sabon gidansa babba mai kyau, tun ranar da Fatima ta ga gidan nan hankalinta ya tashi, sam ba ta yi farinciki ba, saboda ganin ya yi gini mai ɓangare uku, wanda ko bai faɗa ba ya nuna dole yana da ra'ayin ƙara aure nan gaba, wanda take ganin ba zai taɓa yiwuwa ta yarda ta zauna da kishiya ba, a yadda ta tsani kishiya take kuma jin kishin mijinta ta saka a ranta ko za ta yi yawo tsirara sai ta hana shi ƙara aure, ko da kuwa za ta kauce hanya ne. Usman jikinsa ya yi sanyi ganin yadda ta nuna ba ta yi farinciki da ganin sabon gidansa ba, ya ce"Amma Nana sai na ga kamar ba kya murna, ko gidan bai yi miki ba ne?" Ta ce"Ya yi mana, kawai dai ban ganewa tsarin ginin ba ne". Ya ce"Kamar ya?" Ta ce"Daga ni sai kai da yaranmu me yasa za ka yi gini mai ɓangare uku?" Ya yi murmushi ya ce"Nana kenan, kin san dai ina da ra'ayin zama da mata biyu ko? Wannan na farkon ɓangarena ne, babban falo ne wanda nakr fatan ya zama general, nan gaba idan na ƙara aure shi ne wajan zaman fira dukanku don a samu shaƙuwa da haɗin kai tsakaninku da yara bakiɗaya, ga ɗakin gadona a ciki, ga kuma banɗaki, sauran kuma kowanne babban falo ne da ɗakuna biyu da banɗaki, sai kitchen kin gansa a waje yake, ga store can a kusa da kitchen, ina fatan komai ya yi". Zuciyar Fatima ta kumbura, ba ta san lokacin da hawaye ya sakko mata ba, ta ce"Au wai dama da gaske dole sai ka ƙara auren? Don Allah me nake yi maka? Na zata tun da mun sasanta tsakaninmu na daina abubuwan da ba ka so shikenan". Ya ce"Haba Nana, ai ban ce yanzu kina yin wani abun ba, shi auren ra'ayina ne, zan yi ne ba don kin gaza ba, don haka ki kwantar da hankalinki, kina ɓangarenki tana nata, shiyasa na bari sai da na gina wadataccen gida". Ta ce"Wai yaushe za ka gane ba zan taɓa iya zama da kishiya ba? Ni fa ba zan juri ganinka da wata ba, ka ga duk abin da kake buƙata wanda ya sa za ka ƙara auren ka faɗa mini, ni zan san yadda zan yi na gyara, na dinga yin yadda kake so". Ya ce"Nana kenan, za ki iya zama mace biyu? Ina nufin za ki rabu gida biyu? Kuma kowacce kalarta da ban, surarta da ban? Ni biyun kawai nake so ba ɗaya ba". Ta ce"Shikenan Allah Ya ba ka iko". Ta gama ganin gidan rai duk babu daɗi, suka tsayar da ranar tariya sati biyu, saboda a yi shirye-shiye cikin nutsuwa. Tun da ta ji ra'ayinsa akan auren nan shikenan ta shiga damuwa, amma tana ta dannewa, ba ta som nuna masa zaƙewarsa akan ƙara aurensa, ta yadda zai gane tana da wani shiri a kai ya ɗauki mataki, ba ta manta abin da ya faru da wata ƙawarta ba, da ta dage ta hana mijin ƙara aure, ƙarshe sai ya yi mata lamfo ya yi kamar ya fasa, sai da ta kwantar da hankalinta ta yi zaton ya janye, rana ɗaya kawai ta ji labarin an ɗaura aurensa, kuma ya ɗakko wacce ta fi ta gogewa, haka ta zauna da kishiyar don dole, don haka take tsoron ita ma hakan ya faru da ita. A cikin tsakanin nan ta linka kulawar da take ba shi sosai, wai ko hakan zai sa ya fasa, sannan tana yawan jansa da firar ƴan matan nasa ko za ta ji a inda batun auren ya kwana da kuma kalar wacce zai aura, amma ba ya babta fuskar da za su yi firar, a haka har sati ukun da suka tsara za ta koma sabon gida ta yi, duka ya canza mata kayan ɗaki, ya siya mata wanda suka fi nata tsada da kyau, sannan ya ba ta kuɗi ta ƙara wasu kayan kitchen ɗin, ta tare a sabon gida tana farinciki sama-sama, ƴan'uwa kowa ya ga yanayin ginin sai ya ce mata ta shirya zuwan ƙanwa, wato kishiya, sosai hakan yake sake hasala ta, amma tana da daurewa tana nuna ba komai ba ne a shirye take. Kullum daidan ta kalli part ɗin da amarya za ta zauna sai ta ji kamar ta rushe ginin, saboda yadda zuciyarta take yi mata ƙuna, amma abun da sauƙi tun da dai ta ga bau sake tada zancen auren ba. Komawarta sabon gidan nan ya zama wani cigaba a rayuwarta, saboda unguwa ce ta masu kuɗi, kuma akwai yaran mata masu irin shekaratunta, wayayyu ƴan gayu, hakan ya sa ta shiga cikinsu tana ta samun ilimin zama da miji, da kuma sirrikan girki da na gyaran jiki, nan da nan ita ma ta waye sosai ta zama gogaggiya, yanzu Fatima babu batun ƙazanta tana gyara kanta da gidanta sosai, tun tana yi don kar ƙawayenta su rainata har ta fara yi don kanta, saboda ta saba, kuma sosai hakan yake yi wa Usman daɗi, don yana son tsafta da gayu, amma sam hakan bai sa ya ji wai zai fasa ƙara aure aure ba, don wannan ra'ayinsa ne. Akwai wani gida da ta fi sabawa da su, matar gidan za ta haife ta, don tana da manyan yara, ta fi zuwa gidan, su yi fira kuma dayake ta shiga islamiyyar ta magriba, can take kai yaranta Mu'az da Khalil, sai su zauna har ta dawo daga makaranta, don sun saba da gidan. Sai da ta sakankance ya bar zancen auren, rama ɗaya kawai ya zo ya zaunar da ita, yake cewa"Nana kamar yadda a baya na sanar da ke ina da niyyar ƙara aure, to yanzu maganar ta tashi, ina son yin aure, amma don Allah ina so ki kwantar da hankalinki, na faɗa miki wannan auren kawai ra'ayina ne, ɓangarenki da ban, nata da ban, don haka ban ga abin da zai haɗa ku faɗa ba". Fatima ta jinjina masa kai alamar gamsuwa. Ya ce"Ba ma ƴar garin nan ba ce yarinyar, wallahi a status ɗin abokina na ganta, ƙanwarsa ce, rabo dai kawai na ji ta yi mini, zuwana zance biyu sai ta waya muke gaisawa, to jiya an ce na tura iyayena, nan da kwana huɗu in sha Allah zan tura, za a tafi da kuɗin auren a saka rana kawai, tun da na shirya ba wani tsayawa ɓata lokaci". Fatima ta ce"Hakane Allah Ya sanya alkhairi". Ya ce"Amin, na ji daɗi da kika fahimce ni". Ta yi murmushi ta ce"To ai ya zama dole na fahimce ka, tun da ba ka yi mini rufa-rufa ba". A ranar bacci rabi da rabi ta yi, ta gama yanke hukuncin da za ta ɗauka tun kafin zuwan ranar nan, akwai ƙawarta maƙociyarta wacce tasu ta zo ɗaya sosai, ita ce ta ba ta shawarar da za ta bi, ta faɗa mata ita Malaminta ne ya hana mijinta ƙara aure, aikinsa kamar yankan wuƙa yake, duk auren da ya ɗakko tana zuwa wajen malamin nan cikin kwana biyu magana take lalacewa, a haka har ya gaji ya daina neman, don haka ita ma ta yanke hakan za ta yi, domin a ganinta ba ta da sauran dabarar da ta wuce wannan ɗin, saboda alƙawari ta yi ba za ta zauna da kishiya ba. Washegari da safe yana fita, ta shiga gidan ƙawarta, har da kukanta ta zayyana mata komai, Zulaiha ta fashe da dariya ta ce"Kuma ke maman Mu'az mene ne abun kuka? Ko dai ba ki shirya zuwa wajen Malamina ba ne?" Fatima ta ce"Wallahi tun kafin na ji Malaminki ni ma ina da niyya dama, don na zauna da kishiya gara a ce na kauce hanya, ai Allah gafurur-rahim ne". Zulaiha ta ce"Ƙwarai kuwa, da zarar kin yi istigfari shikenan, don haka ki ɗaura belt, yaushe za mu je?" Fatima ta ce"Ai ni ko yau ma na shirya wallahi, ba na so ma a kai ga kai kuɗin auren, gara a fasa tun kafin manya su shiga ciki ya ji kunya". Zulaiha ta ce"Da fatan dai kina da kuɗi ko?" Fatima ta ce"Ina da shi, mu je kawai". Nan suka tashi suka kama hanya, cikinsu babu wacce ta tambayi mijinta. Babu wani nisa tsakanin gidan malamin da unguwarsu, kuma gidana ne gidan aurensa da matansa biyu, ɗakin da yake aikinsa kuma yana farkon gidan cikin zaure, suka shiga da sallama, yana ciki a zaune cikin shigarsa ta alfarma mai tsafta, ɗakin ma komai tsaf babu kayan haukan nan na manyan bokaye, sai farantin ƙasa a gabansa, wannan ne karo na farko da Fatima ta je wajen Malami da sunan neman taimako, kuma ta san a bayyane yake shirka ce za ta aikata, don haka ta shiga fargaba da faɗuwar gaba, amma fa babu nadama a zuciyarta, domin ita biyan buƙatarta kawai take nema. Suka gaisa da malamin a mutunce, Zulaiha ta gabatar masa da Fatima, ta yi masa bayanin matsalarta, Fatima ta ɗora da faɗin"Malam don Allah ka taimake ni, ni kawai ba na so ya yi auren ne, na fi so ya daina son kowa ya zauna da ni ni kaɗai". Malam ya ce"An gama, taimako ne za a ba ki da yardar Allah maganar auren nan za ta ruguje, ko aure dubu zai nema sai magana ta lalace, da haka har ya gaji ya daina". Ya buga ƙasa ya yi zane-zanensa, ya yi murmushi ya ce"Na gani a ƙaddarar mijinki akwai ƙara aure". Rasss! Ƙirjinta ya yi mummunar bugawa, ta ce"Kenan dole sai ya yi?" Ya ce"Wane mutum inji mutuwa? Mu za mu iya canza komai, ai tun da kika zo nan to kukanki da wata fargaba ya ƙare". Ya tambayi sunan shi ta faɗa masa, ya tambayi sunan buduruwar ta ce ba ta sani ba, ya ce"To babu damuwa, zan ba ki maganin da za ki zuba masa a cikin abinci, indai ya ci sau uku shikenan magana ta ƙare, ko tashin zancen ba za ki sake ji ba". Fatima ta yi godiya, ya ba ta maganin ya ce kuɗinsa dubu hamsin ne, ya ba ta account ta yi masa transfer, suka koma gida ranta fess. A abincin dare ta barbaɗa masa maganin, zuciyarta tana bugawa saboda rashin sabo, Usman ya dawo ya ci abinci hankali kwance, kuma ko a ranar sai da ya yi mata zancen auren nasa, a ranta ta ce"Sai dai ka yi a lahira". Kwana uku a jere tana saka masa maganin, kullum cikin jiran sakamako take, a ranar da ya kama za su je kai kuɗin auren, a ranar maganin ya yi tasiri a kan shi, domin haka kawai ya ji ya fasa auren, gabaɗaya yarinyar ta fita daga ransa, da sassafe waliyinsa ya kira shi don jinsa shiru, saboda sun yi da shi sassafe zai zo da mota ya ɗauke su su tafi, shiyasa ya tuntuɓe shi don tabbatar da tafiyar, Fatima ta shigo ɗakin don ta wanke banɗakinsa ta ji yana waya a kasalance yana cewa"Baba ina ganin fa babu tafiyar nan, auren ma kawai na fasa". Wani farinciki ya lulluɓe ta, har murmushi ya kufce mata, ta shige banɗakin shi kuma ya cigaba da wayar, yana bayanin shi ma bai san dalili ba, kawai dai ya ji ya fasa auren ne. Tun daga nan Usman bai sake tada zancen ƙara aure ba, hakan ya farantawa Fatima rai sosai, suka cigaba da zaman lafiya, babu jimawa kuma ta tsiro masa da zancen ya siya mata gwal, saboda ƙawayenta na cikin unguwa mutum uku duk suna da shi, ita har kunya take ji sabga ta zo ta je da normal sarƙa, amma Usman ya nuna ba shi da wannan kuɗin, duk da ta san yana da shi, ba ta sare ba dai tana ta bin kansa don ya siya mata ko ƙarama ce. 08028966015 [28/05 13:02] Mai Zafafa: https://chat.whatsapp.com/KHaNhtgfrBoAKxQ6GGKFyq *WANI ZAMAN* BY SADIYA ABDULRAZAK Marubuciyar Sandar dukan uwargida Ranar kuka Miji goma Zuciyar mace Matar shige Iya ruwa Wani auren da sauransu FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS Labarin ya ƙunshi Kishi Kissa Makirci Cin amana PAGE 5 Wata biyar da fasa aurensa, suna zaune lafiya, sai dai ta koyi halin roƙo, duk da yana ba ta kuɗi haka kawai ma, amma ta koyi roƙonsa yanzu, ta yi ta ƙaryar za ta yi abu kaza, wanda ajiye kuɗin kawai take yi, burinta ta tara kuɗin da za ta sayi gwal ɗin nan, don ra fita kunya wajen ƙawayenta ƴan gayu. Duk a zatonta ta kashe bakin tsanya, babu sauran batun ƙara aure a lamarinsa, kwatsam sai ya sake zuwa mata da batun wata bazawara, sai a ranar da aka kai kuɗin auren ma ya faɗa mata, da daddare sun gama cin abinci yake ce mata"Nana yau fa na yi miki laifi, laifin da yake halal amma" Ya yi maganar yana dariya. Ta ce"Laifi kuma na halal? Ban gane ba". Ya ce"An kai kuɗin aurena yau, an saka rana wata uku in sha Allah". Damm! Ta ji ƙirjinta ya doka da ƙarfi, ta ce"Wata uku!?" Ya ce"E in sha Allah, dayake ita ma yarinyar iyayenta a shirye suke, kin ga ni ma na shirya, don kuɗin haɗa lefen ma yana nan a ajiye a gefe guda, lokaci kawai ake jira, shiyasa na ce ya kamata a saka kaɗan ɗin". Takaici ya kama ta sosai, har ƙwalla ta kawo idonta, ta ce"Yanzu baban Mu'az kana da kuɗin haɗa kefe a gefe amma ba ka da na siya mini gwal ko?" Ya yi guntun tsaki ya ce"Wai ni kam Nana mene ne muhimmancin wannan gwal ɗin da kika ƙwallafawa rai ne? Idan kadara kike son ajiyewa ai gara ma ki sayi fili ko ginannen gida, kin ga kya saka ƴan haya, amma ke komai gwal, sai ka ce dai wani abu mai muhimmanci ga rayuwarki?" Ta yi shiru tana jin zafin kalamansa. Ya ce"Aure fa zan yi, ƴar wasu zan aura, kin ga na taimaja musu sun aurar da ƴarsu, sannan ita ma na taimaka mata ta zama matar aure, kuma ta zama uwar wasu a nan gaba, za a haifi zuri'ar da za su taru su zama abun alfahari in sha Allah, kuma bazawara ce da ɗanta ɗaya, na ce ma zan riƙe mata ɗan, kin ga nan ma an taimaki yaron zai rayu a gaban mahaifiyarsa cikin aminci, yanzu wannan bai fi siyan gwal muhimmanci ba? Ki duba girman gidan nan, a ce ki rayu ke kaɗa? Abokiyar zama ai tana da daɗi, ko motsinta kika ji zai rage miki wata kewar". Fatima ta ce"Hakane, Allah Ya tabbatar muku da alkhairi". Ya ce"Ya tabbatar mana dai. Fatima ki kwantar da hankalinki don Allah, ni ba nufina munana miki ba". Ta ce"Ni hankalina a kwance yake, Allah Ya kai mu wata ukun". Ya ce"Amin". Duk da ta ga yadda aikin Malam ya ci da wuri a wancen yunƙurin ƙara auren nasa, amma sai da ta sake shiga fargaba, washegari ta nemi rakiyar ƙawarta kamar lokacin farko, suka tafi, a hanya Zulaiha take cewa"Indai bai gaji na ke ma ba za ki gaji ba, maza sai jarabar masifa, me matan wajen suka fi mu? Wallahi kafin ya bar batun auren nan gabaɗaya ke ba ki ga yadda na rame ba, saboda ko abinci rage ci na yi, ba na bacci, da ya ɗakko magana na rushe ta sai ya sake nemo wata, kamar wanda aka yi wa baki ko gorin auren, sai da na tashi tsaye gyam sannan na cire masa son abun, yanzu ba ga shi nan ba komai ya zama labari? Ke ma kar ki gaji, yanzu ma aka fara wasan, dole da mu kaɗai za su zauna wallahi, kalle ki fa me kika rasa da yake neman wata? Da kyaunki da komai". Fatima ta ce"Namiji kenan! Ni wallahi fargabata ɗaya kar ta shigo ta raba ni da shi, son mijina nake kamar na haɗiye shi na huta wallahi, kuma shi ne gatana". Zulaiha ta ce"In sha Allahu ƙwalelensu, mazajenmu namu ne, can su je su nemi samari daidai su". Haka suka yi ta fira har suka ƙarasa gidan malamin. Yau ma dai ta zayyana masa abin da ya kawo ta, tare da yaba masa akan wancen aikin farkon da ya yi mata, Malam ya yi murmushi ya ce"Idan zai yi yunƙuri sau dubu, mu za mu dankwafar da shi sai dubu, wannan ƙaramin aiki ne". Ya ba ta irin maganin da ya ba ta a lokacin farko ya ce ta saka masa a abinci, sannan ta yi masa ƙorafin kuma ba ya sakar mata kuɗi yadda ya kamata, sai ya ba ta wani abu ɗan ƙarami a leda ya ce ta yi matsi da shi, ta tabbata ya kusance ta a ranar, wannan matsalar za ta kau, ta sallame shi suka tafi, a cikin kuɗin da take tarawa na siyan gwal ta bada kuɗin, sam ba ta damu ba tun da ta ji zai sakar mata bakin aljihu. Ta dawo gida da farinciki, yau ma haka ta yi girki ta saka masa magani, sai da ma ta dafa masa abincin da ya fi so, ya dawo tana ta tarairayar shi, Mu'az ya zo ya zauna zai ci abincin, Fatima ta ce"Kai ba ka ci abincinka ba?Tashi dalla". Usman ya ce"To mene ne idan ya ƙara a nawan? Ya ɗakko cokali ɗaya zai kai masa bakinsa". Da sauri ta janye yaron tana cewa"Wannan ai ba tarbiyya ba ce ba, idan bai ƙoshi ba ne sai na ƙaro masa wani". Abun ya bawa Usman mamaki sosai, saboda ya ga ba yau suka fara cin abinci da yaron ba, kuma ba ta taɓa magana ba sai yau ɗin". Ya ce"Haba Nana, mene ne idan uba ya ci abinci tare da ɗansa? Kamar yau muka fara ci?" Ta ce"Ni dai kawai ba zai ci ba, naka ne kai kaɗai, idan zai ci na zuba masa nashi". Usman ya ce"Ai kuwa ba ki isa ki hana shi ba, dole tare za mu ci". Fatima ta ce"Wallahi ba zau ci ba" Ta ɗauki ɗan ta mayar da shi gefe. Usman ya kalli abincin ya kalle ta, ya yi mamakin yadda ta haƙiƙance, duk da ba ya zarginta amma sai da ya ji ɗar a kan abincin, ya ce"To wai mene dalilinki na hana shi ci? Tun a baya ba ki hana ba sai yanzu?" Ta ce"A islamiyya ne fa aka yi gargaɗi akan hakan, an ce wannan ba tarbiyya ba ce, saboda idan aka bar yaro yana cin abinci da babansa nan gaba sai a yi baƙo ya zo ya saka masa hannu, ka ga kuma ai za a ji kunya". Ya ce"To ke ai sai ki sakko mu ci ko? Idan ka ci da matarka dai ai babu laifi ko?" Ta ce"Ni ai na ci na ƙoshi kuma". Ya ce"Lallai wannan islamiyyar ashe dai ba na biyan kuɗin wata da na littafai a banza, amma idan aka ci aka ragewa yaro fa?" Ta ce"Wannan ai babu damuwa, kuma wallahi ya ma ƙoshi". Usman ya ce"Ai shikenan" Ya ja abincin ya ci ya ƙoshi, ya rage ɗan kaɗan ya ba wa yaron. Yana cewa"To ga shi na rage maka". Fatima ta ɗauke kwanon ta ce"Allah ba zai ci ba, sai dai na zubo masa wani". Ya ce"Ke za ki ci wannan ɗin?" Ta ce"Ni ai na ƙoshi". Ya ce"Ai kuwa ko ki ci ko ya ci, don ba za a yi asararsa ba, ya yaro yana son abu za ki hana shi ci?" Ta ce"Kawai ni dai ba zai ci ba, saboda idan ya cika cikinsa sosai kashib dare yake yi mini" Usman ya ce"Idan ya yi ki tashe ni zan wanke masa, amma Allah sai ya ci abincin nan". Ya zo ɗaukar abincin Fatima ta ɗauke kular, ya tsaya yana kallonta na ƴan sakanni kafin ya ce"To Nana ko dai wani abun kika zuba min a abincin wanda ba kya so ɗanki ya ci ya cutu? Maganin mutuwa ne ko na mallaka?" Gabanta ya faɗi, ta ce"Wallahi tallahi babu ɗaya". Sai kuma ta fara kuka ta ce"Kenan ma zargina kake yi ko? Ni za ka zargi zan zuba maka mugun abu a abinci? Me ka yi mini da zan kashe ka? Akan me zan mallake ka?" Ta rushe da kuka. Ya ce"To idan ba haka ba ne ba ba ni kular nan". Ya miƙo hannu zai karɓa ta noƙe ta, ya ce"Nana zargina ya tabbata kenan ko?" Ta ce"Wallahi ban zuba maka komai ba". Ya ce"To ke ki ci na gani". Ta ce"Na ƙoshi". Ya ce"Ko kin ƙoshi na tabbata akwai wajen da cokalu ɗaya zai zauna, don haka dole ki ci". Ta ce"Wallahi na ƙoshi, kamar zan yi amai ma". Usman gabansa ya fara faɗuwa, ya ce"To shikenan, bari na sanarwa mahaifiyata tun yanzu, don idan na mutu a samu sauƙin bincike". Da jin haka sai ta ajiyr masa kular a gabansa tana sosa kai ta ce"Ni fa dama...". Ya ce"Dama me?" Ta ce"Dama maganin maza ne na saka maka, ka ga idan Mu'az ya ci sai a samu matsala". Ya yi tsaki ya ce"Allah Ya kyauta, maganin maza kuma? Yanzu ni duk wannan yanayin nawa da nake ma ganin kin yi mini kaɗan ashe ke kallon lusari kike yi mini? Ba na kiranki yadda ya kamata ne?" Ta ce"A'a kana kirana". Ya ce"To akan mr za ki ƙara mini ƙarfi?" Ta ce"Na ga aure za ka ƙara shiyasa na ce bari na fara tsuma ka, ka ga masu mata biyu ba sa iya bawa kowacce hakkinta yadda ya kamata, ni kuma ka sabar mini da jarabarka". Har ransa ya yarda, don haka ya yi ƴar dariya ya ce"Ki ce dai kawai tsuma ni kika fara yi, ai kuwa indai na ga kyaunsa sai na ba ki tukuici". Ya ɗauki sauran abincin ya ce"Irin wannan ai bayani ake yi, sai na cinye duka na siɗe kwanon, mu ai a nan muka fi kauri". Ta yi dariya, ya cinye abinci duka, ta fesa wanka ta yi matsi da wannan maganin ta bi shi ɗakinsa. Bayan kwana biyu tana ta zuba ido ta ga ya zo ya faɗa mata ya fasa auren, amma ta ji shiru, sannan ta sake tada masa da zancen siyan gwal ɗin nan ya ce ba shi da kuɗi, shiyasa duk hankalinta ya tashi, ta fara tunanin wannan aikin dai bai yi ba, sati ɗaya da yin haka ta koma wajen malamin nan, ta faɗa masa aiki fa bai ci ba. Malam ya ce"Aiki ya ci, ki jira lokacin ki gani, idan an yi auren nan to sai dai a lahira, amma a gidan duniya dai wannan magana ta mutu miɗis". Duk da haka hankalinta bai kwanta ba, suna zaune da shi wataran take cewa"Ni baban Mu'az aurenka saura wata biyu ko?" Ya yi shiru kamar bai ji ta ba. Ta ce"Magana fa nake yi". Ya yi guntun tsaki ya ce"Auren nan fa na fasa shi tun tuni". Wani farinciki ya lulleɓe ta, amma ba ta nuna ba, da alamaun mamaki a fuskarta ta ce"Amma me yasa?" Ya ce"Wallahi kawai, ji na yi yarinyar ta fita daga raina gabaɗaya, kawai dai Allah Ya yi ba matata ba ce". Fatima ta ce"Ikon Allah, amma abun da mamaki, to kuma ka karɓo kuɗin auren da aka kai?" Ya ce"A'a na bar musu, tun da dai kin ga ni ne na ce na fasa, kar abun ya yi musu yawa". Fatima ta ce"Hmm kai dai kawai kuɗin ya yi maka yawa ne, ka yi niyyar yi mata kyauta, amma ban da haka ni ina zaune ba ka ba ni ba, za ka je ka ce ka barwa wata kuɗin aure? Ka ga kenan ka nuna min ta fi ni daraja da ƙima a idonka". Ya ce"Za ki ji alert anjima, don Allah zancen nan ya mutu". Ta fi murmushi ta ce"Yawwa, sai yanzu ka so ya mutu ai". Daga haka wannan zancen auren nasa ya sha ruwa, to bai sake neman wani auren ba, sai ya ƙara ƙaimi wajen neman matansa, dama ba wai dainawa ya yi ba, ragewa kawai ya yi. 08028966015 [28/05 13:02] Mai Zafafa: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt WANI ZAMAN* BY SADIYA ABDULRAZAK Marubuciyar Sandar dukan uwargida Ranar kuka Miji goma Zuciyar mace Matar shige Iya ruwa Wani auren da sauransu FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS Labarin ya ƙunshi Kishi Kissa Makirci Cin amana PAGE 6 IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account a Instagram @imzeed _venture. Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Sadiya Abdulrazak tuni na antaya🏃 Wannan maƙotan nasu da ta fi shiga har take kai ajiyar ƴaƴanta, tana kiran matar gidan da Umma kamar yadda yaranta suke faɗa, ba ta ɓoyewa Umma komai na damuwarta, don har zancen Usman ya ƙi siya mata gwal sai da ta yi mata, ta ce ita fa ba ta da wani burin da ya wuce ya siya mata gwal ɗin nan, Umma ta ba ta haƙuri ta ce ai wataran sai labari zai siya mata ɗin. Irin yadda Fatima take zama ta yi ta faɗar abubuwan da mijinta yake yi mata, da kuma nuna ba ta nemi komai ta rasa ba, shi ne ya ɗauki hankalin Zahra wati ƴar Umma, bazawara ce mai ƴaƴa biyu, auren ya daɗe da mutuwa tana gida a zaune babu miji, ta bakin Fatima take sanin halayen Usman, wanda suka sa ya shiga ranta sosai, har take jin dole sai ta shiga gidan nan ta kowane hali, ko kyautar kuɗi Usman ya yi wa Fatima sai ta zo ta bawa Umma kasonta, ta ce yau Usman ya ba ta dubu kaza, haka idan sutura ya siya mata ita da yara sai ta ɗakko kayan nan ta nunawa Umma don a taya ta murna kuma a yabawa mijinta, kullum da kwanon abincin Umma a gidan nan, duk da su ma suna da rufin asirinsu. Zahra ta yi ta dakon son Usman a ranta, indai ta gansa sai ta ji kamar ta je ta faɗa masa, amma tana kasawa saboda ba ta san halinsa na son mata ba, don tun da suka dawo sabuwar unguwar nan an samu sauƙi, bai fiya kula yaran layin ba, har ta fara jin kishin Fatima, sannu a hankali tsanarta ta dira a zuciyarta, ko son ganinta ba ta yi, idan ta shigo gidan ta yi ta ɓata rai kenan, magana kaɗan Fatima za ta yi sai ta gwale ta, ko kuma idan Fatiman ta so su yi fira da Zahran sai Zahran ta manna mata hauka, tun Fatima ba ta gane ba har ta fahimta, duk da ta girmi Fatima, amma a ganin Fatiman ai tun da ita ma babba ce da aurenta da ƴaƴanta bai kamata Zahra ta dinga raina ta ba, hatta Umma ta fahimci baƙon halin na Zahra, duk da ta yi mata faɗa amma babu canji, sai suka zuba mata ido Fatima ba ta daina shiga gidan ba, amma dai ta janye jikinta ga Zahran. Akwai wata rana, Usman ya zo ya zauna a ƙofar gida yana shan iska yana wasa da yaransa, Zahra ta zo wucewa, ta kalle shi tun daga nesa ta fara murmushi, da ta ƙaraso ta duƙa har ƙasa tana narke murya ta gaishe shi, ya amsa yana murmushin shi ma, ta fara yiwa yaran wasa, zuciyarta kuma tana bugawa, ba kasafai Usman ɗin ya fiya irin wannan zaman a layi ba, don haka take ganin wannan ranar sa'a ce a rayuwarta don haka ba za ta bari dama ta wuce ta ba, tana ɗan kare fuska da alamun kunya ta ce"Baban Mu'az dama alfarma nake nema". Ya ce"To Allah Ya ba ni iko, mene ne?" Ta sake sunne kai ƙasa ta ce"Dama ina ta neman lambarka ne". Ya ce"Lambata kuma? Allah Ya sa lafiya". Ta ce"Lafiya lau, gaisawa nake so mu dinga yi dama, amma idan babu damuwa". Ya ce"Wannan ai babu damuwa, ba komai ba ne, kawo wayar na saka miki". Ta miƙa masa wayarta, ya saka mata lambarsa ta karɓa tana rangwaɗa ta ce"Na gode sosai". Ya yi mata wani shu'umin murmushi ya ce"Ni ma na gode". Ya bi bayanta da kallo yana murmushi. Tunaninsa ya fi ba shi yarinyar son shi take yi, ƴan matan gidansu suna burge shi dama, kawai dai ya kau da kai ne saboda ganin yadda Fatima ta ɗaukake su take yi da su, kar ya je ya ce yana so ya sa ta ji kunya, ko ya raba musu zumunci, amma tun da yanzu ita ta kawo kanta indai ta ce tana son shi babu abin da zai hana shi karɓar tayinta. Can bayan azhar ta kira shi a waya, lokacin yana gida don haka yana ɗagawa da ya ji ita ce ya tashi ya kkma ɓangarensa, har da murɗa key, suka gaisa suka taɓa firar duniya kafin ta sanar masa maƙasudin karɓar lambarsa, ta ce"Dama alfarma nake nema a wajenka, duk da dai na san ni ban kai ba, duba da ganin ka wuce ajina, amma karambanin zuciyata ya hana ni sakat, shiyasa na ce bari dai na gwada". Usman ya yi murmushi ya ce"Haba, ai namiji ba ya wuce ajin mace, sai dai ita ta wuce ajinsa, ki faɗi maganarki kai tsaye, kuma ki faɗawa zuciyarki na ce ta daina kamba ni da yawa har haka, don ban kai inda take zato ba". Zahra ta ce"Wallahi baban Mu'az na daɗe ina sonka, kana burge ni sosai, abun ya fi ƙarfina na garara dannewa, har ta kai na fara jin kishin matarka, na san dai ka fu ƙarfina amma don Allah ka taimaka min". Wani daɗi ya kashe Mu'az, a zahirin gaskiya shi sam Zahra ba ta cikin jerin matan da zai iya aure, zai iya sonta amma ba da aure ba, sai dai idan za ta dinga ba shi kanta yana biyanta, amma idan ya wuce haka sai dai ta ƙara gaba. Zahra ta ce"Ka yi shiru". Ya ce"Na ji batunki Zahra, sai dai fa akwai matsala". Ta ce"Mene ne matsalar?" Ya ce"Kin ga dai Fatima kamar ƴar gida take a wajenku, ba zai yiwu na fara zuwa wajenki ba, saboda tana da kishi, sai dai mu dinga soyayya a ɓoye". A sanyaye ta ce"Amma ɓoye soyayya zai kai mu ga aure kuwa?" Ya ce"Sosai ma, ai a hankali za mu dinga bayyanawa, sai mun gama shaƙuwa da juna mun fahimci juna sai kuma a fito a bayyanawa ƴan gidanku, idan suka amince aka saka rana, dab da auren sai Fatima ta sani, a lokacin aikin gama ya gama, ba ta da yadda za ta yi da mu". A sanyaye ta ce"Hakane". Ya ce"To yanzu a ina za mu dinga haɗuwa kenan?" Ta ce"Ko a bayan layinmu ma" Ya ce"Lallai ashe ba ki san yadda Fatima ta saka matakan tsaro saboda yadda take kishina ba, ai ni ban ga inda za mu dinga haɗuwa a layin nan ba, har gaba da layin nan ma, kuma kin ga soyayya ba za ta yiwu a ce ba a ganin idanun juna ba". Ta ce"To yanzu ya kenan?" Ya ce"Ai maslaha ɗaya ce, kawai mu dinga haɗuwa a cikin gidana". Ta ce"A cikin gida? A layi ma kana ganin ba mu tsira ba ballantana kuma a cikin gida?" Ya ce"Ai tana zuwa makarantar magriba, a wannan tsakanin daga magriba zuwa isha'i ya ishe mu fira". Ta ce"Amma idan ƴan unguwa suka ga ina shiga fa?" Ya ce"Ai kowa ya san yadda Fatima take da ƴan gidanku, to babu wanda zai kawo tunani mara kyau, za a yi zaton ba ta je makarantar ba tana gida". Ta ce"Kai, gaskiya sai na yi tunani". Ya ce"Ok, ina jiran amsarki". Suka shiga wata firar kamar ba wanda suka fara waya yau ba, kiran sallar la'asar ne ya katse musu wayar. Tun daga ranar suka jone a waya, gabaɗaya ta saki jiki ta yarda Usman sonta yake kuma da gaske aurenta zai yi, yanzu ta kai idan ya dawo da daddare sai ya yi mata waya su haɗu a farkon layi ya ba ta ledar tsaraba, duk abin da zai shiga da shi gida na ci, sai ya ƙunso mata nata rabon, don haka ta sake yarda da son da yake yi mata, ta kuma sake tsanar Fatima da jin kishinta. A hankali suka samu shaƙuwa sosai, ta yadda ita ma kanta wannan soyayyar ɓoyen ta ishe ta, don haka ta yarda da tayin da Usman yake ta yi mata na cewar su dinga haɗuwa a gidansa, ranar da ta fara zuwa da magriba ne Fatima ta tafi makaranta, a ɗakinsa suka zauna a nan falo suka yi firarsu mai tsafta, ana fara kiran sallar isha'i ta tafi, tun daga nan sai Usman yake dawowa da wuri, idan ya dawo saa ya laɓe a unguwar sai ya tabbata Fatima ta tafi makaranta sannan ya yi wa Zahra waya ta zo gidan, tun suna firar arziƙi har Usman ya yi nasarar yaudararta da kalaman ƙarya da nuna mata ai ita bazawara ce don ta ba shi kanta ba wani abu ba ne, kuma ma ai shi ne zai aure ta, ta yarda saboda son da take yi masa, da kuma yawan kyautar da yake yi mata musamman ta kuɗi, suka ɗinke suke ta sheƙe ayarsu, suna gamsar da juna sosai, domin Zahra har maganin mata masu mugun kyau take siya kamar wata matar aure, kawai don ta farantawa Usman, don haka komai ta ce tana buƙata babu musu yake bata shi, amma sam babu niyyar aurenta a ransa. Ko da wasa Fatima ba ta taɓa hasashen akwai matsala a gidanta ba, rana ɗaiɗai ne ba ta shiga gidan su Zahra, ko ba ta shiga ba ƴaƴanta za su shiga, wataran suna fira da Umma zancen gwal ɗin nan ya tashi, silar wata da ta gani a tiktok ta sha gwala-gwalai tana rawa da ƙawa, ta yi ƙwafa ta ce"Hmm! Allah kai damo ga harawa". Ta ƙara da faɗin"Wai ban da lalacewar zamani a ce mutum yana da kuɗi ba zai biyawa matarsa dukkanin buƙatunta ba?Wallahi Umma Usman yana da kuɗin da zai siya min gwal ɗin nan na miliyoyi ma, amma na ce masa ko ƙaramin ne ina so, duk da haka ya kafe, idan bai siya mini ba wa zai siyawa?" Umma ta ce"Gaskiga dai, amma ki bi shi a hankali da kyautatawa sai ya siya miki ko ba yanzu ba". Suna ta tattauna zancen, Zahra tana jin haushin Fatima, kuma ta saka a ranta za ta gwada roƙonsa gwal ɗin ta gani, tun da ya sha faɗa mata ta fi Fatima daraja a wajensa, idan kuwa ya siya mata ɗin gaskiyarsa ta tabbata. Kamar wasa ta faɗa masa tana son ya siya mata gwal ko ƙarami ne, ya ce babu damuwa, ba ta taɓa zaton da gaske yake ba, sai ga shi bayan sati ɗaya ya kawo mata ɗankunne da zobe na gwal ɗin, a ranar ta ji ta ƙara son shi sosai, farinciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, ta kuma sake raina Fatima don ta gama yarda hoto ce kawai a wajensa, kuma ta sake sakin jiki ta yarda da gaske aurenta zai yi. Sati ɗaya da siyan gwal ɗin nan Fatima ta samu labarin wannan alaƙa tasu, domin bakin Zahra bai iya shiru ba, sai da ta faɗawa ƙawarta wata buduruwa a layin mijin maman Mu'az ya siya mata gwal, har ma ta nuna mata shi, ita kuma abun ya ba ta mamaki ta san da alaƙarsu, ta sana haɗuwa a gidan Fatiman suna yin harkarsu, amma wannan siyan gwal ɗin ya sa ta ji tana yiwa Zahra hassada, a ce ita tana buduruwa bai ce yana sonta ba sai bazawara? Ta yi niyyar tona mata asiri, don haka ta samu mahaifiyarta ta sanar mata, babar Shamsiyya da farko ƙaryatawa ta yi, sai da ta dinga yi mata rantsuwa sannan ta yarda, ai kuwa a ranar ta saka hijjabinta ta shiga gidan Fatima, duk da ba ta shiga gidan amma ta ji dole ta shiga ta sanar da ita halin da take ciki. Suka gaisa da Fatima, ta kwashe komai ta faɗa mata a tsanake, sosai hankalinta ya tashi ta fara kuka, don tabbas ta san mijinta zai aikata, kuma ta yi mamakin cin amanar da Zahra ta yi mata, da ma duka ƴan gidan bakiɗaya, don ba za ta taɓa yarda da cewar babu sanin Umma ba, tun da har abu ya kai ga siyan gwal, ita fa siya mata gwal ɗin nan har ya fi kawo ta cikin gidan da yake yi zafi a wajenta. Kasa ɗaukar shawar maman Shamsiyya ta yi na cewar ta fake su ta kama su da hujja, kawai ta yanke a yau za a yi ta, ta ƙare. 08028966015 [28/05 13:02] Mai Zafafa: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt WANI ZAMAN* BY SADIYA ABDULRAZAK Marubuciyar Sandar dukan uwargida Ranar kuka Miji goma Zuciyar mace Matar shige Iya ruwa Wani auren da sauransu FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS Labarin ya ƙunshi Kishi Kissa Makirci Cin amana PAGE 7 IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account a Instagram @imzeed _venture. Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Sadiya Abdulrazak tuni na antaya🏃 Fatima ta cika ta yi fam tana jiran dawowarsa, bayan ta gama cin kukanta, har ɗakin nasa ta shiga ta tsaya kawai take kallo da tunanin wai da gaske yana kawo mace ɗakin nan? Ta hau kan gadon da ita ma take hawa? Ashe dole Zahra ta dinga yi mata wani gani-gani, Zahra ta ba ta mamaki sosai, ba ta taɓa zaton za ta iya yin haka ba, kuma da mijin maƙociya, abun ya ma wuce a haɗu a wani wajen wai har cikin gidan aurensa saboda rainin hankali, ita kam me baban Mu'az ya ɗauke ta ne? Usman ya dawo gida ana idar da sallar magriba, hankalinsa kwance, har da tsarabar gasassun kaji, wanda ya siyo su da sunan Zahra, domin sun yi da ita yau za ta shigo, da ya tarar da ita Fatima a tsaye a falon sai da ransa ya ɓaci, ya ce"Nana me ya hana ki zuwa makaranta yau?" Ta zabga masa harara ta ce"Ok ka so ka zo ka ga ba na nan ko? Ka so ka kawo wacce ka saba kawowa ku aikata masha'arku ko? To ai a gabana ɓa za ku iya yi, tun da har ka iya kawo mace cikin gidan aurenmu ai kuwa saura ƙiris ka fara yin iskancinka a gabana, to yanzun ma me ya rage?" Tun da ta fara magana gabansa yake faɗuwa, kuma sam bai yi mamaki ba tun da dama ya san wannan harƙalla da suke yi tsakaninsa da Zahra riski ce, komai zai iya faruwa, musamman da abun ya yi nisa sosai a tsakaninsu, amma ya dake ya aro suffar mamaki ya shimfiɗa a fuskarsa har da haɗe gira ya ce"Ke me kike cewa ne? Me kike nufi? Zargina m kike yi?" A hasale ta ce"Ai ya wuce zargi, ashe Zahra kake kawowa gidan nan kuna cin amanata? Wai abun ya kai har ma ta samu darajar da ka siya mata gwal?" Ya ce"Anya yau ba ki sha wiwi ba kuwa? Ni ne nake kula wata har nake kawo ta gidan nan? Wace ce kuma Zainab?" Ta ce"Zahra na ce! Kar ka raina mini hankali mana, wallahi ba za a yi maka ƙarya ba, yau da a ce neman mata ba halinka ba ne da zan yarda, to amma na riga na san halinka ko me aka ce ka yi akan mata ba zan musa ba wallahi, don haka ka aikata!". Sai ta fashe da kuka ta ce"Amma baban Mu'az har cikin gida? A gadon da muke raya sunna? Abun naka har ya kai haka? Ka cuce ni ka zubar mini da ƙima a idon duk wanda ya sani, dama kai ba ka da sauran mutunci..." Ya ce"Ke dalla dakata a nan haka, ban gane ba fa, ke anya ba ki da aljanu kuwa? Uban waye ya ce na taɓa kawo mace gidan nan? Wace ce Zahra? To ki wuce mu je wajen munafukar da ta faɗa miki wannan ƙaryar, wallahi sai na yi shari'a da ita!". Ta ce"Wannan borin kunya kake yi wallahi, na saa halinka don haka kp maƙiyina ne ya kawo min labarin nan zan gasgata shi, kawai ka aikata, kuma ban yafe maka ba, har da siya mata gwal wai? Ni ta gida ina ta naci ka ƙi siya mini sai ta waje ko? Yau ka sake tabbatar mini da ba ni da sauran daraja a idonka!". Sai ta zauna ta kifa kanta a kujera ta rushe da kuka. Jikinsa ya fara yin sanyi, ya san dai dole ta sani, amma haka ya kafe ya ƙi karɓar laifinsa, sai dai ya daina kumfar bakin, ya sanyaya murya ya ce"Nana ki ɗago mu yi magana". Kamar ba ta ji ba, amma ta tsagaita da kukan. Ya ce"Wallahi ƙarya ne, duk wacce ta faɗa miki wannan kawai ta yi ne don ta haɗa mu, na san ina da son mata, amma abun nawa bai kai na kawo mace har cikin gida ba, kuma yanzu ma Allah Ya taƙaita mini fa na daina". Ta ɗago ta ce"Wallahi duk da ban gani ba na yarda, don na san za ka aikata, wai don Allah mene ne ba na yi maka? Kullum ina zuwa ɗakinka fa, ko ba na gamsar da kai ne? Ai sai ka faɗa mini na gyara". Ya ce"Ni ban ce ba, ban ce ba kya gamsar da ni ba, kin san kowane bawa da kalar ƙaddararsa a rayuwa, ni wannan shi ne ƙaddarata, kuma hakkinki ne ki taya ni da addu'a Allah Ya yaye mini, amma batun Zahra wallahi ni ba ni da wata alaƙa da ita, kuma ban taɓa kawo mace gidan nan ba". Ta ce"Wallahi ko za ka kwana kana musawa ba zan yarda da kai ba". Ya ce"To ai shikenan, sai ki ɗauki matakin da kika ga ya dace, amma ba zan ɗauki shirme ba. Ya fice daga ɗakin Ɗakinsa ya shiga ya zauna, ya kira wayar Zahran, ko gaisawa ba su yi ba ya ce"Ke dama kin zo kin yaudare ni ne don ki haɗa ni da matata?" Gabanta ya faɗi ta ce"Me ya faru my love?" Ya ce"Kar ki sake kirana da wannan sunan, domin na rufe babin soyayyarmu daga yau, ta ya aka yi matata ta san na siya miki gwal? Alhalin kin ce ko ƴan gidanku ba za ki sanarwa ba?" Ta ce"Wallahi ban faɗawa kowa ba, sai dai..." A tsawace ya katse ta da faɗin"Sai dai me? So kike ki sa mutuncina ya zube a idon duniya da ƴan unguwa ko?" Kamar za ta yi kuka ta ce"Ka yi haƙuri". Ya ce"Ke kin ga, haƙuri ke ya kama ba ni ba, kuma daga yau kar ma ki sake nuna kin san ni, kawai mun rabu har abada!". Ta ce"A'a don Allah, ba mu yi haka da kai na fa, mun yi alƙawari..." Ya ce"Ke da alƙawarin kun ci ubanku! Wallahi idan kika sake nuna kin san ni sai na tona miki asiri, sai na hana ki aure a garin nan". Daga haka ya katse wayar, ya saka ta a black list, ya kuma yi alƙawarin ya bar ta har abada, ai babu laifi ya more ta sosai kamar matarsa, a tsakanin nan ta taimake shi sosai, ba ya kula kowace mace sai ita, don haka yanzu sai dai ya canza sheka ita dai ya gama da ita. Washegari sai ya wuni jiki a mace, saboda ya ga Fatima ta ƙi sakin jiki da shi, sai ɓata rai take yi, duk da ba ta sake tada masa da zancen ba amma abun ya dame shi, don haka da daddare ya ɗakko kuɗi dubu ɗari biyu ya ba ta, ta kalli kuɗin tana cewa"Wannan kuma fa?" Ya ce"Kawai ba ki na yi ko za ki sayi wani abun". Ta ce"Ok kenan na toshiyar baki ne ko? Tun da na san ka siyawa kwartuwarka gwal". Ya ce"Haba Nana, ke me yasa kike haka ne? Da ba na ba ki kuɗi?" Ta ce"Kana ba ni amma ba mai yawa haka ba". Ya ce"Kuma kenan ba kya so na fara ba ki". Ta ce"Ni dai ka ji tsoron Allah". Ya ce"To in sha Allah, amma fa wallahi wannan sharri aka yi mini". Ta ce"Ni dai a bar zancen kawai, raina ƙara ɓaci yake". Ta ɗauki kuɗinta ta je ta adana. Tun daga lokacin magana ta mutu, Fatima ba ta sake zuwa gidan Umma ba, ta ɗauke ƙafa cak ta daina kai yaranta, tun Umma tana yi mata aiken ko lafiya? Har ta fara zuwa da kanta, sai Fatima ta yi ta sha mata ƙamshi, ko kuma da ta shigo saa ta ce mata fita unguwa za ta yi, hakan ya sa Umma ta rabu da ita, suka yanke alaƙa gabaɗaya, ita Fatima gani take ƙarya ne a ce Umma ba ta sani ba, haɗa baki suka yi kawai suka yaudare ta, ita kuma Umma tana ganin ba ta yi mata komai ba akan me za ta canza mata fuska? A haka suka rabu. Babu laifi hankalin Fatima ya kwanta, tun da bai sake tada zancen aure ba, sannan ya rage yin waya da mata a gabanta da firarsu, sai ta yi zaton shikenan ma duka ya rabu da su, suka cigaba da zama cikin zaman lafiya, suna farantawa juna, a haka har ta samu wani cikin ta haifi ɗanta na uku, shi ma namiji ta haifa. Tun da cikinta ya tsufa take gudun Usman, ta rage ba shi hakkinsa, haka zai ta bin kanta yana kiranta tana ƙin zuwa, har dai ya jingine ta a gefe ya daina kiranta, ya koma harkarsa ta neman mata, dama ba dinawa ya yi ba, ya dai rage ne kawai saboda yana so ya daina ɗin, sai dai idan ya ji marmarin wata sai a ɗan taɓa, amma tun da ta fara gudunsa sai ya koma ruwa tsundum. Ranar suna aka yi taro aka gama lafiya, kowa ya watse sai ƙanwarsa, yayarta da ƙanwar babarta da suka zauna za su kwana a gidan, don suyar naman suna washegari. A ranar ne kuma Usman ya haɗu da wata yarinya, wacce abokinsa ya yi masa hanya, har ya biya kuɗi za ta zi gidansa su kwana tare, don ita a ƙa'idarta ba ta zuwa hotel sai gida, tun a waya yarinyar ta gama ruɗa shi, duk ya susuce ya matsu dare ya yi ya ɗakki ta, hankalinsa a kwance yake, saboda ya san babu mai shigo masa ɗaki, tun da dai Fatima ta daina shiga tun kafin ta haihu. Ana idar da sallar isha'i ya dawo gidan, yarinyar tana bayan motarsa, haka ya ajiye motar ya fito, sai dai ransa ya ɓaci ganin mutane a tsakr gidan, don ba a ɗora naman kai da wuri ba, ba a gama dafa shi ba. Ya shiga ɗakin Fatima yana cewa"Ni Fatima me ake dafawa haka da tsohon daren nan?" Ta ce"Naman kai ne, ba a babbako shi da wuri ba". Ya ce"Amma babu gas ne da za a zo a tisa murhu da daren nan kamar wasu aljanu?" Ta ce"Akwaa gas, kawai dai ganin ga icen nan, ga kuma murhun da aka yi girki ɗazu shiyasa aka ɗora a nan ɗin". Ya ce"Gaskiya ni ba na son haka, a ɗauke shi a mayar gas kawai ko a haƙura sai gobe a ƙarasa". Ta ce"Ya kusa dahuwa fa". Ya ce"To amma zaman me suke yi a bakin murhun? Su dawo ɗaki mana". Cikin ƙosawa ta ce"To idan sun zauna mene ne? Iska suke sha". Ya ce"Ya ga Ac a ɗaki ki ce mini wai suna shan iska?" Ta ce"To ka je ka faɗa musu su bar maka tsakar gidanka". Ya ce"Ni dai ba da wata manufar na faɗa ba, kawai gani na yi a ce mata kun wuni aiki kun gaji kuma dare ya yi ba za ku kwanta ku huta ba?". Ta ce"Sai kuma ka yi". Ya koma motar ya shiga ya rufe, yarinyar ta ce"Ni fa na gaji da zaman mota, wai ya ake ciki ne?" Ya ce"Yi haƙuri kin ga ba su bar tsakar gidan ba ne, amma sun kusa gamawa". Ya fito ya shiga ɗakinsa, yana leƙe ta windo, yana ganin sun shiga ɗakin ya fito ya shiga ɗakin, suka sake gaisawa yana cewa"Sannunku, kun gama aikin ko? Kun sha aiki, akwai lemo a firjin nan kuwa? Bari na ɗakko muku ba falona ya fi sanyi". Ya juya ya tafi ɗakinsa ya kwaso musu lemo ya kawo, ya ce"Ai kun gama da tsakar gidan nan duka ko? Ku dai rufe ƙofar ɗakin nan don Allah a saka sakata, Allah Ya tashe mu lafiya". Suka amsa da amin, ya sake shiga ɗakin Fatima ya ce"Ga lemo can mai sanyi na kwaso muku daga firjina, ba kya buƙatar komai dai ko? Ki kwanta ki huta na san duk kin gaji". Fatima ta ce"To". Sai dai tana mamakin wannan kulawar da yake nuna mata, a iya saninta haushinta ma yake ji, saboda gudunsa da take yi, har jiya ba ya sakar mata fuska, amma ta ga yau komai ya canza. Ta fito falon inda suke kasa naman, kamar an ce ta leƙa ta windo, ta hango shi yana ta hange-hange kamar mai neman wani abu, sai kuma ta koma ɗaki, kawai sai ta ji ba ta yarda da shi ba, don lokacin har ya shigar da yarinyar ɗakin, yana son ta babbatar da babu wanda ya ganta ne. Aka zuba naman Usman ta ɗauka ta haɗa da abincinsa za ta kai masa, lokacin yana wanka, bai fiya rufe ƙofa da wuri ba, amma yau da ta tura ta ji ta a rufe, ta ƙwanƙwasa ta ji shiru gabanta ya fara faɗuwa don kai tsaye ta fara zarginsa, ta dinga bugawa babu ƙaƙƙautawa, bai ma gama wankan ba ya fito, gabansa yana faɗuwa ya ja hannun yarinyar ya kai ta ɗakin gado ya janyo ƙofar, sannan ya je ya buɗewa Fatima, yana cewa"Lafiya? Me kike yi ba ki yi bacci ba?" Ta ce"Abincinka na kawo maka". Ya ce"Ni wallahi a ƙoshe ma nake, na tsaya a gidanmu na ci fa". Ta ce"Ka dai ƙara". Ya karɓa don kar a ja maganar, ya koma ciki ya rufe ɗakin tana ji ya saka sakata, hakan ya ƙara ƙarfafa mata zarginsa, saboda idan ta kai masa abinci ba ya karɓa sai dai ta shiga ciki ta ajiye, kuma yana so ma ta shiga ɗakin nasa ta zauna yana ci suna fira, sannan sai dare ya yi sosai yake rufe ƙofa. Ta koma ɗaki ta kasa nutsuwa, can anjima ta kira ƙanwarsa gefe, da yake suna da kyakkyawar alaƙa ta su ta zo ɗaya, kuma sun saba firat neman matansa da ita, sai ta faɗa mata ita fa tana zargin da wata a gidan nan, Hasana ta ce"Tabɗijan! Da mace a gidan nan? Kuma har kika iya tsayawa kina ba da labari ba ki ɗauki mataki ba?" Fatima ta ce"Ai na kira ki ne don ki taya ni ɗauka, amma za ki laɓe daga nan, idan kika ji na yi kabbara to zargi ya tabbata sai ki shigo mu ƙaddamar musu". Hasana ta ce"Bari na ɗakko taɓarya, ke kuma sai ki riƙe muciya". Fatima ta ce"A'a ba kashe ta za mu yi ba, rufa min asiri, ki ɗakko muciyar dai ni kuma ki ciro mini wayar jikin TV". Hasana ta je ta ɗakko, sannan Fatima ta nufi ɗakin nasa, ta ƙwanƙwasa, lokacin yarinyar tana zaune tana cin abincin da aka kawo masa, shi kam ba shi da nutsuwar ci, burinsa ta gama ci su hau aiki kawai. Ya ce da yarinyar"Shige cikin ɗaki, ƙila matata ce" Yarinyar ta yi tsaki ta ce"Amma dai wannan matar taka an yi ƴar wahala wallahi". Tana tsaki ta ɗauki kwanon naman ta shiga ɗakin gadon ta zauna ta cigaba da ci hankali kwance. Shi kuma ya je ya ce"Wace ce?" Ta ce"Ni ce mana". Ya ce"To mene ne?" Ta ce"Lemo za ka ba ni". Ya ce"Wane kala?" Ta ce"Zaɓa zan yi, ka buɗe mana". Ya buɗe yana haɗe rai, yana juya baya don koma cikin ɗakin ta hankaɗa shi ta shige ita ma, kai tsaye ɗakin gadon ta nufa, hankalinsa ya tashi ya ce"Ke! Ke Fatima! Ina za ki je, mene ne haka?" Inaa har ta antaya cikin ɗakin, ai kuwa ta ci karo da yarinyar zaune a bakin gado, ta ɗaga murya ta yi kabbara kuwa, sai ga Hasana dake laɓe ta taho a guje, dama haushin yayan nata take ji saboda wannan halin nasa, don haka ranta fess yau. 08028966015 [28/05 16:35] Mai Zafafa: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt *WANI ZAMAN* BY SADIYA ABDULRAZAK Marubuciyar Sandar dukan uwargida Ranar kuka Miji goma Zuciyar mace Matar shige Iya ruwa Wani auren da sauransu FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS Labarin ya ƙunshi Kishi Kissa Makirci Cin amana PAGE 8 IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account a Instagram @imzeed _venture. Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Sadiya Abdulrazak tuni na antaya🏃 Hasana ta shiga da gudu ta miƙawa Fatima wayar, Usman mamaki ya kashe shi, ga shi jikinsa duk ya yi sanyi, ya ce"Wai Fatima me kuke shirin..." Kafin ya ƙarasa Fatima ta fara zabga mata wayar nan tana cewa"Don ubanki me ya kawo ki gidana? Kwartancin naku ya wuce titi ya kai gidana? Ai kuwa ƙabarinki kika shigo". Hasana ta ma shiga rafka mata muciyar, tuni yarinyar ta ruɗe ta fara yi mata magiya tana cewa"Ki yi haƙuri don Allah, Usman kana kallo wai?" Ya matso yana cewa"Ke Hasana kin ci ubanki! Ficr daga ɗakin nan, Nana". Fatima ta ce"Wallahi kana taɓa ni sai na shauɗa maka, ai kai ne ma abun duka dama ba ita ba, macuta kawai ƴan iska!". Ta sake zabga mata, Usman ya ce"Hasana wai ba magana nake yi miki ba? Wallahi zan tattaka ki fa". Hasana ko kallonsa ba ta yi ba, tana ta muƙa mata muciyar ta ce"Yaya sai dai fa ka yi haƙuri ni jahadi nake yi". Ya ƙarasa da niyyar riƙe Fatima ta zabga masa wayar, ya wanka mata mari za ta rama ya murɗe hannunta, yana ta ƙoƙarin ƙwace wayar, saboda sun fara jigata yarinyar, Fatima ta hana wayar, ganin haka sai Hasana ta figi kwartuwar ta yi falo da ita, ta cigaba da muƙa mata muciya a duk inda ta samu, Fatima ta sakar masa wayar ta fita a guje, kafin ya fito ta ja yarinyar ta fizgo wayar jikin kayan kallonsa ta cigaba da zabga mata. Usman ya ruɗe ganin yarinyar tun tana kuka ta kasa yi, sai wani tari da take yi kamar za ta mutu, ya ce"Hasana, Nana kar ku yi kisa fa, ku rufa min asiri, ba laifinta ba ne, ni na gayyace ta wallahi, ni za ku daka ba ita ba". Hasana dai ta rabu da ita, sai Fatima ta ɗauki muciyar ta cigaba, da ƙyar Usman ya riƙe ta ram ya ce da yari yar ta tafi, ko mayafi ba ta tsaya ɗauka, ga shi siket ɗinta mai tsaga ne a baya, ya yage har sama ana ganin fant ɗinta, sun yi mata jina-jina sun yi mata raga-raga, da jan ɗuwawu ta bar gidan tana ta wani nishi, saboda yadda ta jigata, Fatima tana ta zaginta tana fizge-fizge, amma ya ƙi sakinta, sai da ya tabbatar yarinyar ta bar gidan, sannan ya sake ta, ya tafi da gudu ya rufe gidan da key, kafin ya dawo Hasana dai ta tsere, ita kuma Fatima zama ta yi ta kifa kanta, sai yanzu ta samu damar sakin gursheƙen kuka. Ya dawo jiki a mace, bai kula ta ba ya nemi waje ya zauna, ta gama kukan ta tashi za ta tafi, ya ce"Yanzu Nana abin da kika yi kin kyauta kenan? Da kun kashe ta fa?" Ta ce"Haka ma za ka ce? To da na kashe ta na kashe banza, don an rage iri ne, irin gayyar tsiya". Ya ce"Kuma amma don wulaƙanci ba za mu kashe mu rufe mu biyu ba, sai kin kira ƙanwata kin tona mini asiri a gabanta, salon ta raina ni?" Ta ce"To kana jin kunyar ƙanwar taka me yasa ka aikata? Ai kai abun kunya gaba ka ba shi ba baya ba, wallahi ka yi asara! Kuma bari ka ji na faɗa maka, babu ni babu kai, ba zan sake haɗa jiki da kai ba, ba za ka kwaso mini cuta a jikin gantalallun mata ka shafa mini ba, dama kar na sake ganin ƙazamar ƙafarka a ɗakina, ka yi rayuwarka a nan kai kaɗai!". Ya ce"Ni dai ki yi haƙuri da baƙi a gidan nan, idan suka ji ke ma za ki ji kunya ai, ƙila ma sun ji". Ta ce"Babu kunyar da zan ji, kai ne ka yi abun kunya don haka kai jinta ya kama, ai gara ma kowa ya san halin naka". Za ta fita ya ruƙo ta, ta fizge ta ce"Kar ka sake taɓa ni! Kar ka sake hannunka ya ƙara taɓa jikina, ka taɓa ƙazama ko wanka ba ka yi ba kama ta taɓa ni, ni da shigowa ɗakinka har abada". Ta fice yana kiranta ta ƙi dawowa. Hasana ba ta faɗawa sauran ƴan cikin gidan ba, ɗakin Fatiman kawai ta shiga ta zauna tana jiran shigowarta, ga jaririn sai kuka yake yi tana ta jijjiga shi, su mutanen falo da ba su san me ya faru ba suna ta cewa ta kai shi amma ta ƙi. Fatima tana shigowa ƙanwar babarta ta fara yi mata faɗan ta tafi wajen miji ra bar yaro yana kuka, ba ta ce komai ba ta wuce ɗakin nata, Hasana ta miƙa mata yaron tana cewa"Ya ce na je ko?" Fatima ta ce"A'a". Ta zauna ta fara ba shi nono. Hasana ta ce"Don Allah ki yi haƙuri maman Mu'az". Fatima ta fara kuka ta ce"Mutumin nan ba shi da adalci! Yana cutata, ba fa wannan ne karo na farko ba". Ta ce"Gaskiya ya cuce ki, amma ki yi haƙuri, in sha Allah watarana sai labari". Ta ce"Amma fa mun jibge ta, ni kar ma ta mutu a hanya". Fatima ta ce"Da kuwa ko Allah Ya ji ƙanta ba zan ce ba". Hasana ta ce"Har shi fa kika dinga duka, wallahi ni ma na so na samu damar muƙa masa muciyar nan a ƙugunsa". Fatima ta ce"Hmm, ai wannan na farko ne, ya sake wata ya gani, Allah tsaf zan ƙone su gabaɗaya". Hasana ta ce"Hmm! Dama gobe asuba tana yi zan bar gidan nan, don na san idona idonsa sai ya karya ni". Fatima ta ce"Babu abin da zai yi miki, ai ya san za a tambayi dalili, kin ga kuwa ba zai so asirinsa ya tonu ba". Hasana ta ce"Allah Ya shirye shi to". Haka suka kwana rai babu daɗi, ita Fatima ta yi alƙawarin kawai ta jingine shi a gefe, ta fita harkarsa, shi kuma nadama duk ta dame shi, ya yi alƙawarin ba zai sake gwada kawo mace gidan shi ba, amma gaskiya zai ƙara aure, don yana da buƙatar hakan. Washegari yana tafiya masallaci Hasana ta bar gidan, don ba ta yarda ba zai yi mata komai ba. Aka yi soyar nama aka gama, sai yayarta ta zauna don taya ta wasu ayyukan, sati biyu ta yi kafin ta tafi, a cikin sati biyun nan Usman ya ga ikon Allah, Fatima ba ta sake shiga ɗakinsa ba, idan ya shiga ɗakinta sai ta fara yi masa masifa tana cewa ya fita, kuma a gaban yayarta, sai ya fita sum-sum don kar zancen ya yi tsayi yayar tata ta ji, idan an gama girki ma Mu'az take aika ya kai masa ɗakinsa, ko gaisuwa ba ta haɗa su, ba kullum ma yake ganinta ba, yayarta ta yi mamaki kuma ta yi mata faɗa sosai, duk da ta ƙi faɗa mata dalili. Bayan yayarta ta tafi, sai Usman ya ga dole fa ya zo su samu sasanci, don haka yau yana dawowa ya shigo ɗakin ya zauna, ta yi banza da shi tana danna waya, ya ce"Nana sannu da gida". Ta yi kamar ba ta ji shi ba. Ya tashi ya ɗakko kofi ya buɗe firji ya zuba ruwa ya sha, yana ajiyewa Mu'az ya ɗauka zai ƙarasa sha, ta daka masa tsawa ta ce"Ajiye shi! Maza ka kai shi bola ka yar, mu zunubi ba zai shafe mu ba, an gama ƙazanta an zo ana taɓa mini kofi? Kularka ma ware maka taka na yi, wallahi komai ka taɓa na daina amfani da shi, dattin zina ba zai ja mini masifa ba!". Ransa ya ɓaci sosai, ya ce"Ni kike faɗawa haka? Kuma a gaban yara?" Ta ce"To ƙarya na yi? Ai ka san da yaran dai ka aikata ko?" Ya jinjina kai ya tashi zai fita, a gabansa ta janyo zanin goyon ɗanta ta fara goge wajen da ya tashi ɗin tana cewa"Ni gaskiya a daina shigo mini ɗaki ehe!". Haka suka sake kwashe sati biyu suna wannan zaman, ta sha zuba kofuna a bola sabofa ya taɓa, idan ya zauna a waje ya tashi sai ta goge kujerar da ruwa ta fesa turare, har kyautar kuɗi ya ba ta wai ko za ta huce, ta ƙi karɓa ta ce ya je ya kai wa matan waje kamar yadda ya saba. Abun duk ya dame shi, yana neman sasanci, ga buƙatuwa ta sako shi a gaba, tun bayan abun sau biyu kawai ya keɓe da wata a hotel, don haka yau ya zaunar da Fatima ya ce"Kin ga Nana magana za mu yi ta fahimta, kin yi arba'in har kin wuce amma kin ƙi dawowa ɗakina, me kike nufi? Kuma wannan wulaƙancin da kike yi mini a gaban yara ya ishe ni haka". Ta ce"Ai kai ne ka ja, kuma tun da ya ishe ka me zai hana ka ɗauki mataki?" Ya ce"Ni fa ba fitina nake nema ba, ai na san na yi laifi, kuma na yi nadama, shiyasa nake neman sulhu, don Allah ki yi haƙuri, na gaji da wannan zaman". Ta ce"Kanka ake ji, ni dai ba zan sake haɗa jiki da kai ba, tun da ni ban ishe ka ba, ka je waɗanda suke isarka su baka". Duk yadda ya so su yi sulhu ta ƙi, ta botsare masa, don haka kawai ya kira yayarta a waya, suka gaisa ya faɗa mata shi fa ya yi wa Fatima laifi kuma ta ƙi ta haƙura ta ƙaurace masa, yayarta ta kira ta tana ta yi mata faɗa, kuma shi da itan duk sun ƙi faɗa mata laifin da ya yi, ta yi mata faɗa da nasiha sosai. Fatima ta yarda sun zauna zaman sulhu, amma ta faɗa masa ba za ta sake zama a kan kujerar da karuwa ta zauna ba ballantana kuma kan gado, a takaice dai ba za ta sake shiga ɗakinsa ba, ta ce sai dai ya canza kayan ɗakin, haka kuwa aka yi duka gadon da kujerun ya canza, hatta zannuwan gado sai da ya bayar da su duka ya sayi wasu, kuma ta ce ya ba ta dubu ɗari biyu za ta yi gyaran jiki, ya ba ta, daga nan aka samu maslaha, ta sayi magunguna masu kyau da inganci, kuma ta bi ƙa'idar amfani da su, zamansu ya gyaru suka koma kamar da. Sai dai tafiya ba ta yi nisa ba Usman ya zo mata da zancen zai ƙara aure, da raunin murya yake cewa"Kin ga ni mabuƙaci ne, idan na ce da ke kaɗai zan rayu sai na ga kamar zan dinga cutar da ke, kuma ko ba haka ba ma ina da ra'ayin ƙara auren ne, ga ginin mata biyu na yi". Ta ce"Ka saka ƴan haya mana". Ya ce"Auren dai zan yi in sha Allah, akwai wacce muka daidaita". Ta ce"Allah Ya ba da sa'a". Ya ce"Amin, bazawara ce ma, don haka ba da yawa za a saka ba". Ta ce"Allah Ya kaimu". Wannan karon ba ta wani damu ba, tun da tana da tsayayyen malamin da zai ruguje maganar, hmm Fatima ta manta da maganar nan da aka ce 'Idan jurinka sammako wani a tafe ya kwana'. 08028966015 [29/05 18:31] Mai Zafafa: https://chat.whatsapp.com/DqC9XDRW7ee7y5JtVxNqGr *Zoki mallaki kayan kitchen cikin saukii,Adashen kitchen(weekly)🤭👌* *Duk kayan kitchen dakikeso zaa siya maki da kudin adashenki…Kikwashi kayanki tamkar kyauta🤭💃💃* *Gold kitchen Adashe dinmu ba wasa aciki! 100% aminci, 100% sauki !* *WANI ZAMAN* BY SADIYA ABDULRAZAK Marubuciyar Sandar dukan uwargida Ranar kuka Miji goma Zuciyar mace Matar shige Iya ruwa Wani auren da sauransu FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS Labarin ya ƙunshi Kishi Kissa Makirci Cin amana PAGE 9 Ta yi masa shiru tana jiran ya gama shiryawa ya tsayar da zancen auren, sannan ta ziyarci malam. Bayan sati biyu da maganar sai ga shi ya zo mata da zancen auren, abun ya taso gadan-gadan, ya ce mata gobe za a kai kuɗin aure, kuma sati shida za a saka, sao farinciki yake yi yana ba ta labari, da alama dai yana zumuɗin auren nan, don haka ta shiga damuwa, washegari ta shirya ta tafi wajen Malaminta, a wannan karon ita kaɗai ma ta je, ta zayyana masa komai, ya buga ƙasa ya baje ya sake bugawa ya baje ta, ya ɗago ya kalle ta, ya ce"Wannan yarinyar da zai aura ita ma ba a zaune take ba, kuma na ga cewar wannan auren tabbatacce ne, sai an yi shi". Fatima ta ji tashin hankali ya dirar mata, ta ce"Na shiga uku! Sai an yi kuma? Yanzu babu wata mafitar? Wallahi ba zan iya haɗa miji da wata ba". Ya ce"Haka dai ƙasa ta nuna, amma mu muna iya canza komai ai, don haka zan yi iya yina don ganin komai ya wargaje, sai dai fa aiki ne da yake buƙatar kuɗi da kuma kula wajen gudanar da shi". Fatima ta ce"Zan ba da ko nawa ne, ni dai don Allah ka taimake ni". Ya ce"Za mu yi yanka don a bawa aljani jinin, shi ne zai yi aikin tarwatsa taurarinsu, sannan ya saka masa wasi-wasi akan ita yarinyar da ma auren gabaɗaya, sannan kuma zan ba ki maganin da za ki saka masa a abinci wanda zai sa ya dinga bin umarninki, idan kika ce ya fasa auren zai daina" Fatima ta ce"Duka nawa kenan?" Ya ce"Dubu ɗari biyu za ki ba da, tun da an zama ɗaya". Nan take ta yi masa transfer ta account ɗinsa, ya tabbatar mata da za a yi yankan, sannan ya ba ta wanda za ta saka a abinci, ya faɗa mata amma yana da ɗaci, kuma duka za ta juye a lokaci ɗaya, don haka ya ba ta shawarar ta yi miyar shuwaka. Ai kuwa daga nan kasuwa ta zarce, ta yi cefanen miyar shuwaka, ba ta taɓa yi ba ma don ba ta sonta saboda ɗacinta, haka ta yi tuwo da miyar, iya cikinsa ta yi ta zuba masa a kula, dayake ba ya garin ma, amma dai zai dawo komai dare, ita ta yi girkinta suka ci da yara. Wajen goma na dare ya dawo lokacin har ta gaji da jiransa, ya dawo da gasassun kaji, ya zauna tana yi masa sannu, yana amsawa, ta kawo masa abinci ya ce"Ai kuwa a ƙoshe nake, don mun ci abinci da magriba, ga kuma kaza nan". Ta marairaice ta ce"Amma dai ai ka san da na gidanka ko? A kan me za ka je ka cika cikinka a waje?" Ya ce"To kuma abin da ba yau na fara ba?" Ta ce"Ai yau girki na musamman na yi maka, ni dai sai ka ci". Ya ce"To me kika dafa? Kawo na yi ko cokali biyu ne". Fatima da bugar ciki ta ce"Ko dai wajen amaryar ka tsaya ka ci?" Ya yi murmushi ya ce"A'a wallahi, na dai tsaya na ba ta tata kazar". Fatima ta ce"Ka kyauta kuwa, ya sunanta ne?" Ya ce"Zainab ce, wannan karon Zee baby na ɗakko". Fatima ta je ta ɗakko abincin ta ajiye masa tana cewa"Allah Ya sa dai ita ba yaudararta za ka yi ba". Ya ce"Yaudara kuma?" Ta ce"To ai na ga idan ka ɗakko mahanar auren haka kawai sai ka zo ka ce ka fasa". Ya ce"Hmm ni kaina abun yana damuna wallahi, haka kawai sai na ji na fasa ba na son yin auren, amma dai wannan jikina yana ba ni abun ya zo ƙarshe". Ta ce"Allah Ya sa". A ranta kuwa cewa ta yi'Nan da kwana uku sai dai ka yi wata maganar ba wannan ba'. Ta zuba masa tuwon ta miƙa masa, ya ce'Kuma tuwo kika yi? Yadda nake a ƙoshen na na sake ɗora tuwo?" Ta ce"Kai dai ka ci idan kana son yi mini adalci". Ya kai lomar tuwon ba tare da bisimillah ba sai cewa da yake yi"Wannan miyar alayyahu ce?" Yana ci ya yamutse fuska ya ce"Ya ɗaci haka?" Ta ce"Miyar shuwaka ce". Ya ce"To mene ne amfanin yinta? Ni ba na son sabgar miya mai ɗaci". Ta ce"To ai magani ce, ka daure dai ka ci tun da ka fara ci, idan ya kwana sai a yi asararsa, ni na ci har ya min yawa". Haka ya daure ya ci tabin tuwon ba don ya yi masa daɗi ba, duk tadda ta so ya cinye ya ƙi, ya ce ya ƙoshi. Bayan kwana uku ta zuba ido tana jiran ta inda zai fara ce mata aure ya fasu, amma ta ji shiru, bayan sati ɗaya sai ta tambaye shi don ta ji halin da ake ciki, lokacin bayan sallar isha'i ne, ya yi wanka zai fita taa ce"Amma dai wannan wankan na amarya ne ko?" Ya washe baki ya ce"Hasashenki ya tafi daidai, don kuwa can zan je". Fatima ta haɗiyi wani yawu ta ce"A dawo lafiya, a gaishe ta". Ya ce"Za ta ji". Ya fice daga gidan. Tun daga ranar abun duniya ya fara damun Fatima, domin ta ji zancen fasawa shiru, sotari Amaryar da ya kira da Zainab ɗin tana yawan kiransa a gaban Fatima, sai ya tashi ya fita waje ya gama wayarsa ya dawo. Auren ya rage sati uku ya zo mata da zancen kayan faɗar kishiya, ya ce"To kin ga dai duk da bazawara ce lefe zan yi mata, ke kuma ki zaɓa lefen zan yi miko ko kuɗin kayan zan ba ki?" Wani baƙinciki ya kamata sosai, amma dai ta dake ta ce"Kuɗin dai, saboda na zaɓi kalar da nake so". Don a ganinta idan ma ta karɓi kayan na banza ne, tun da auren dai fasuwa zai yi, ba yi za a yi ba. Ya ce"To shikenan zan tura miki kuɗinki". Suka yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce"Gida ya kusa cika dai, na gaji da ganin ɓangaren can babu kowa". Fatima ta ce"To ai ga shi saura ƙiris". Ya ce"In sha Allah". Da fargaba ta kwana a ranta, don ta ga alamar wannan karon aikin malamin nan bai ci ba, don haka washegari da safe yana fita ta tafi gidan Malam, ta gurfana kamar mai neman gafara tana kuka take cewa"Malam wannan karon fa aikin nan bai ci ba, wallahi yana nan akan bakansa, bai fasa ba, aure saura sati uku". Malam ya ce"Kuma kin juye masa duka wannan maganin ya cinye a abinci?" Ta ce"Wallahi ya cinye". Ya ce"To zan ba ki wani da za ki yi matsi da shi, idan kin yi ki tabbata kun keɓe a ranar, idan za ki yi matsin ki dangwalo maganin a ɗan yatsanki, ki kira sunan shi sau bakwai, ki tofa a jiki, sannnan ki rufe idonki kina ambatar sunan shi kina cewa ya fasa auren nan har sau bakwai, sannan ki yi amfani da maganin, idan kuka gama kawai ki kalle shi kai tsaye ki yi masa umarni da fasa auren, duk taurin kansa ba zai yi miki musu ba". Ya ba ta maganin a wata ƙaramar kwalba, ya ce mata dubu hamsin ne, ta yi masa transfer, ta yi godiya ta tafi, tana ta jimamin yadda take ɓarnatar da kuɗinta, wanda tana tarawa ne don siyan gwal, amma ta wani fannin ta san dabara ta yi, don idan ba ta yi yadda ta yi an fasa auren ba, ko ta sayi gwal ɗin na banza ne, don ita a nata ganin a ce kana da kishiya shi ne babbar gazawarka a rayuwa, don haka ko za ta yi yawo tsirara sai ta hana auren nan. Ƙarfe goma na dare ta gama komai, ta fesa wanka, ta ɗakko maganin nan ta dangwalo shi, ta kira sunan Usman sai bakwai, sannnn ta rufe ido ta ce"Usman ka fasa auren nan, Usman ka fasa auren nan". Haka ta maimaita har sau bakwai, sannan ta yi amfani da shi, ta haye gadonsa ta kwanta tana jiran dawowarsa. Sanda ya dawo ya gama abin da zai yi ya kwanta, ya matso kusa da ita har wata ajiyar zuciya ta sauke, saboda ta gama yarda yau burinta zai cika, tun da har zuciyarta ta yarda da maganin nan, bayan sun gama mu'alar ita ce ta fara yin wanka, kafin ya fito daga nashi wankan, ta zauna a gefen gadon tana ta kintsa kanta, da auna maganar da za ta yi masa ɗin, tare da taraddadin karɓuwarta ko akasin haka. Ya fito ya shirya zai kwanta, ta kalle shi ta ce"Ina da magana". Ya ce"To ina jinki". Ta saka idonta a cikin nasa gabanta yana faɗuwa ta ce"Usman ka fasa auren nan". Shi ma ji ya yi gabansa ya faɗi, mamakinta ya kama shi, sai ya ji kamar ma kunnuwansa ne ba su ji daidai ba, don tabbatarwa sai ya ce"Me kika ce Nana?" Ta ce"Usman ka fasa auren nan". Ya ce"Ikon Allah! Na fasa aure kuma? Me yasa?" Zuciyarta ta tsinke, don ta san wannan karon ma aikin bai yi ba kenan, ta ce"Saboda ba na so, ni Fatima ina yi maka umarnin ka fasa auren nan". Ya fara yi mata wani kallon ba ki da hankali, kafin ya ce"Ke Fatima uwata da kika haife ni, ko ke Fatima da kika auro ni kike ci da ni?" Zuwa yanzu kam ta sare, kawai ta saddaƙar aikin bai yi ba, don haka ta fara hawaye ta ce"Ba haka ba ne, amma wallahi zuciyata zafi take yi, ba zan juri ganinka da wata ba, don Allah ka janye auren nan, ka faɗa mini matsalata, na yi alƙawarin zan gyara". Usman ya nemi waje ya zauna, ya tausasa murya ya ce"Haba masoyiyar matata, wai me yasa kika kasa fahimtata ne? Na faɗa miki fa zan yi auren nan ne ba wai don kin gaza ba, na faɗa miki dalilina ina da ra'ayi ne, kuma mun gama magana da Zainab sai na dawo na ce ba haka ba? Ki kwantar da hankalinki za ku zauna lafiya, zan yi wa kowa adalci". Gyaɗa kai kawai ta yi, ta fita a guje ta koma ɗakinta, yana ta kiranta ba ta dawo ba, ta saka sakata ta kwanta a falo ta saki kuka sosai, kuka biyu take yi, da na baƙincikin aiki bai yi ba, da na takaicin asarar kuɗinta, ta yanke ta bar wannan malamin za ta nemi wani kawai. Washegari ta shiga gidan maƙociyar nan tata, hankali tashe take faɗa mata aikin nan fa bai yi ba, ta yi asarar kuɗinta, Zulaiha ta ce"Daɗina dake gajen haƙuri". Fatima ta ce"Kin ga babu wani gajen haƙuri, abin da ya ce nan take zai yi aiki, ai ya kamata na ga aikinsa a lokacin idan mai kyau ne, ni dai idan akwai wani malamin ki haɗa ni da shi kawai". Zulaiha ta ce"Akwai su, akwai mutum biyu da yayata take aiki da su, sai na haɗa ki da ita ƙila a dace". Fatima ta karɓi lambar yayarta, nan take ta kira ta, suka yi mata bayani, suka yanke gobe Fatima za ta je gidanta sai ta raka ta. Washegari ta tambaye shi za ta je gidan yayarta, dayake gidan da nisa shiyasa a wannan karon ta nemi izininsa, don kar su kai dare, ya ce yana da uzuri da ya kaita, ya ba ta kuɗin mota ta tafi. Kafin su je ta shirya Fatima kawai take jira, suka gaisa, suka tafi, a hanya tana ta ba ta labarin aikin malamin nan yadda yake da kyau kamar yankan wuƙa, Fatima ta ji hankalinta ya kwanta sosai. Bayan sun je wajen ta yi bayanin so take a fasa auren, shi ma ya yi dube-dubensa ya ce zai iya, ya ba ta wani magani kala biyar ya ce za ta samo zuciyar rago ta dafa ta da wannan maganin ta cinye ta shanye romon, gabanta ya faɗi ta ce"Zuciya kuma Malam?" Ya ce"Ƙwarai kuwa, amfanin hakan shi ne kamar kin cinye zuciyarsa ne, ke kaɗai zai ji yana so har abada, kuma da ke kaɗai zai iya rayuwar aure, sannan zai ƙara son ki, zai dinga bin umarninki sau da ƙafa, zai manta ko hanyar gidan su yarinyar nan ma". Fatima ta ce"Amma Malam ban san wanda zan sa ya siyo mini zuciyar ba". Ya ce"Idan kika ba da kuɗin babu damuwa, ni zan saka matata ta dafa miki". Fatima ta biya kuɗin, ta yi godiya suka fita daga gidan yayar Zulaiha tana ƙarfafa mata gwiwa. Washegari aka dafa zuciyar rago, aka kai gidan Zulaiha, ita kuma ta aikawa Fatima, tana buɗe kwanon ta ji ƙyanƙyami ya kama ta, ba komai take iya ci a nama ba, amma yau saboda gudun kishiya sai ga shi ta zauna za ta ci zuciyar rago. "Zuciyar Usman zan ci, bayan na ci zan mallake shi, zai dinga bin umarnina, zai daina son kowace mace sai ni, da ni kaɗai zai yi rayuwar aure". Ta faɗa kamar yadda aka ce ta faɗa kafin ta fara ci. Tama ci tana runtse ido, haka ta daure ta cinye ta, ta shanye romon duk ɗacinsa, tana fatan ƙarshen wahalarta kenan. Bayan sati ɗaya ta ji shiru Usman sai ma shirye-shiryen bikinsa kawai yake yi, yanzu ya ma rage zama da ita su yi fira, hankalinta bai tashi ba sai da ta ji an kai kayan lefensa, kuma wai bikin saura sati ɗaya, a maimakon sati biyu, don rage sati ɗaya aka yi, a ranar ji ta yi kamar za ta haukace, ko tambayarsa ba ta yi ba ta je gidan malamin nan, ta yi masa bayani, ya buga ƙasa ya ce mata aikin ya wuce zatonta, babba ne, idan za ta iya ba da dubu ɗari biyu zai yi mata abin da za a fasa cikin kwana biyu. Gabaɗaya dubu tamanin ne a account ɗinta, don haka ta ce masa za ta dawo. A ranar da daddare ta tuntuɓi Usman da zancen kuɗin kayan lefenta, nan take ya saka mata dubu ɗari biyar ya ce ita da yara, ai kuwa washegari ta je ta kaiwa malamin nan ɗari biyu, ya ce ta je gida za ta ga aiki nan da kwana biyu. Kwana biyu ta yi, babu wani canji, aure saura kwana biyar, hankalinta ya tashi sosai, ta je tana yi wa malamin nan kuka, ya ce mata zai sake ƙaimi wajen aikin, amma zai shiga wata halwa, kar ta dawo sai bayan kwana uku. Cikin kuka ta ce"Ai lokacin saura kwana biyu auren". Ya ce"Kar ki damu, ko saura minti biyu ne mu za mu canza komai". Ta bar gidan jiki duk a mace, sam ba ta yarda da cewar aikin nan zai yi ba, ta biya ta gidan wata ƙawarta wacce suka yi makaranta tare, suka gaisa take tambayarta ya ta ganta a cikin damuwa? Fatima ta faɗa mata halin da take ciki, na kishiya da za a yi mata. Ƙawar tata ta ce"Ai kuwa kin ga mijin Saddiƙa Habibu malami ne, yana ba da taimako, da kin gwada zuwa wajen nashi". Fatima ta ce"Me zai hana? Don Allah ba ni lambarta". Ta ba ta lambar, ta kira ta a waya suka gaisa ta ce mata za ta zo gidanta, ta yi mata kwatance, duk da ta ji da nisa amma sai ta ji dole ta je a yau ɗin, don haka ko gida ba ta koma ba ta wuce gidan ƙawar tata. Shi ma gida ne mata baje a wani ƙaton ɗaki masu bin layi, shi kuma yana wani ɗakin a zaune, ta shiga ɗakin ƙawar tata a ranta tana mamakin ita kuwa Saddiƙa me ya kai ta auren boka? Sai da ta yi awa uku a gidan, a hakan ma tsallaken layi aka yi ta ga Malamin, saboda Saddiƙa ta roƙa mata alfarma. Fatima ta zayyana mata buƙatarta, ya buga ƙasa ya share, ya ɗago ya kalle ta ya ce"Hajiya ke ƙawar matata ce, kin san ko ina cuta ke ba zan cuce ki ba saboda albarkacin matata ko?" Ta ce"Haka ne, kuma na gode sosai". Ya ce"To a gaskiya sau ɗaya nake buga ƙasa na ga sakamako, na buga kuma abin da ta nuna mini babu daɗi". Zuciyarta ta buga da ƙarfi, kamar za ta yi kuka ta ce"Me ka gani?" Ya ce"Na ga cewar wannan auren tabbatacce ne, babu makawa sai an yi shi, domin har hango ta na yi a cikin gidanki a zaune da ƴaƴanta". Fatima ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Na shiga uku, yanzu babu wani abun yi?" Ya ce"A wajena dai babu, kuma bari na faɗa miki gaskiya, duk wajen wanda za ki je ya faɗa miki zai iya wani abu to kuɗinki zai ci, ina ba ji shawarar ki ajiye komai ki haƙura, idan an yi auren za a iya nakasa ta ta wani fannin, amma aure dai sai an yi shi". Ta share hawaye ta ce"To na gode". Ta ciro kuɗi a jakarta ba ta ma san nawa ba ne ta ajiye masa, yana ta yi mata magana ta zo ta ɗauka ba ta juyo na ma, ko sallama ba ta yi wa Saddiƙa ba ta fice daga gidan, tana kuka kamar an yi mata mutuwa. Sai a lokacin ma hankalinta ya dawo jikinta, har an idar da sallar magriba, ba ta cewa kowa a maƙota ga ajiyar yaranta da za su dawo daga makaranta ba, ƙaramin dai yana goye a bayanta. LITTAFIN NAN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 500 KACAL, ZA KU IYA TURA KUƊIN KARATUNKU TA NAN 8028966015 Sadiya Abdulrazak opay Shaidar buya ta nan 08028966015 [30/05 17:50] Mai Zafafa: https://chat.whatsapp.com/DqC9XDRW7ee7y5JtVxNqGr *Zoki mallaki kayan kitchen cikin saukii,Adashen kitchen(weekly)🤭👌* *Duk kayan kitchen dakikeso zaa siya maki da kudin adashenki…Kikwashi kayanki tamkar kyauta🤭💃💃* *Gold kitchen Adashe dinmu ba wasa aciki! 100% aminci, 100% sauki !* *WANI ZAMAN* BY SADIYA ABDULRAZAK Marubuciyar Sandar dukan uwargida Ranar kuka Miji goma Zuciyar mace Matar shige Iya ruwa Wani auren da sauransu FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS Labarin ya ƙunshi Kishi Kissa Makirci Cin amana PAGE 10 Ta buɗe gidanta ta shiga, tana ganin motar da ya fita da ita a gidan ta san ya dawo gidan, ta shiga da sallama a sanyaye, ta gan shi zaune da yaran, don da ya dawo da su ya fara cin karo a layin suna wasa da yaran unguwa, ga kuma unifom a jikinsu, kuma lokacin bayan la'asar ne, ya haɗa kan yaran ya buɗe gidan yana tambayarsu ina babarsu? Suka ce sun dawo daga makaranta sun ga ba ta nan, ya shiga ya ga ba ta nan ɗin, suka zauna ya ce"Kenan ko abincin ba ku ci ba ko?" Suka ce sun ci a gidan maman Sadik, ya yi musu wanka ya canza musu kaya, suka fita tare ya siyo abinci ya dawo suka ci, ya yi zaman jiranta, dawowarsu daga masallaci kenan sai ga ta ta shigo, yana kallon yanayinta ya ga babh nutsuwa a tare da ita, ta zo ta wuce ta gabansa tana cewa"Sannu da gida". Bai amsa ba, murya a dake ya ce"Daga ina kike?" Ta ce"Gidan Mama Binta". Mama Binta ƴar'uwarsu ce, wacce take uwa a wajensu, ya ce"Da izinin wa?" Ta yi shiru. Ya ce"Me kika je yi da za ki tafi babu neman izini? Ki bar yara a titi suna gantali, ana sammu su abinci a maƙota, me kika je yi?" Ta ce"Kawai ji na yi ina son zuwa, kuma ban san zan daɗe ba". Ya ce"Kar ki sake yi mini haka daga yau, don za mu samu matsala!". Ba ta ce komai ba ta shige ɗakinta, wanka ta yi ta, ta yi sallah ta fito za ta shiga kitchen, ya ce"Ki dafa iya cikinki, don mu mun ci na siyarwa". Sai ta fasa shiga kitchen ɗin, ta koma ɗaki ta zauna, hawaye suka fara bin kuncinta, idan gaskiya mijin Saddiƙa ya faɗa mata cewar auren nan tabbatacce ne, tabbas tana cikin masifa, ta ya za ta iya raba mijinta da wata? A ranar bacci rabi da rabi ta yi, washegari kuma Usman ya ce mata yau masu jere za su zo, sannan idan za ta yi biki ta yi masa list ɗin abubuwan da take buƙata, ta ce masa ba za ta yi ba, sannan ta tambaye shi za ta fita unguwa duba ƙawarta ba ta da lafiya, ya ce"Kamar ba yanzu na faɗa miki za a zo jere ba? Sai a zo ba kya nan?" Ta ce"Ka ba su mukullin gidan mana, idan sun zo ɗin ina nan me zan yi musu? Ni da ba a kaina za su yi jerensu ba?" Ya ce"Ko ma dai mene ne ki zauna, kar ki fita ko'ina, Hasana ma ta ce za ta zo yau ɗin". Daga haka ya fice daga gidan. Ta gama shirinta tsaf ta zauna, wajen ƙarfe goma Hasanar ta zo, tana zuwa ta bar mata ajiyar gidan da yaran, ta saka hijjabinta ta fice, gidan Zulaiha ta shiga ta zayyana mata duk abin da yake faruwa. Zulaiha ta ce"To tun da kika ga haka ita ma amaryar ƙila ba a zaune take ba, don haka ina ga kawai ki haƙura, ko kuma a nakasa ta ɗin bayan auren". Fatima ta ce"Na haƙura a yi mini kishiya? Wallahi ba zan yarda ba". Zulaiha ta ce"To sai ki cigaba, akwai wata ƙawata da take zuwa wajen wani, amma fa shi boka ne, don da nisa sosai ma wajen nasa, tana ganin kyau aikinsa sosai". Fatima ta ce"Yanzu ya za a yi? Za ta raka ni?" Zulaiha ta ce"Bari na tambaye ta". Ta ɗakko waya ta kira ta ba ta shiga ba, sai ta yi mata magana ta whatsApp, an kusa minti talatin har Fatima tana shirin tafiya, sai ta duba saƙon, Zulaiha ta yi mata bayani, ta ce ai kuwa ba ta ƙasar, sai nan da sati biyu idan ta dawo sai ta raka ta". Fatima ta ce"Ai kafin nan kuma an yi an gama". Ta ce ta yi mata kwatance, ta ce musu da nisa sosai, kuma ba lallai ta gane ba, amma akwai ƙawarta da take zuwa, za ta tambaye ta idan za ta je nan kusa sai su je tare, suka yi sa'a kuwa ta ce mata gobe za ta je, amma fa tana ta jadda mata ta shirya, don sassafe ake tafiya, kuma sai dare ake dawowa saboda nisan wajen, sannan ta saka kuɗi a jakarta, don ba a yi masa transfer, Fatima ta ce ta ji ta gani. A ranar ta ciro dubu ɗari biyu ta saka a jakarta, ta koma gida, sam ba ta ɓoyewa Hasana komai, duk da ƙanwarsa ce uwa ɗaya uba ɗaya, amma haka ta ba ta labarin zaryar wajen malaman da ta yi, da kuma inda za ta je gobe, Hasana jikinta ya yi sanyi ta ce"Amma maman Mu'az kina ganin hakan daidai ne? Kin san fa shirka ce wannan, kuma kin san hukuncin, akan kishiya bai kamata ki kai kanki ga halaka ba, kina fa sane yanzu duk sallar da kike yo ba karɓa ake ba, to me za ki ce da Allah idan kika mutu a kan haka? Duk abin da Allah Ya tsara ba wanda ya isa ya rushe shi fa, ya kamata ki zubar da makamanki, ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddara". Fatima ta ce"Ai Allah mai yafiya ne, kuma komai na ɗan lokaci ne, ba wai zan dawwama ina yi ba, a gaba zan tuba". Hasana ta ce"Ke ce da gaban? Wa ya san gobe? Dukanmu gawa ne a tafe, yanzu idan kika kwanta kika mutu a yau fa?" Fatima ta ɓata rai ta ce"Kin ga ya isa, a bar maganar haka". Hasana ta ce"Dama ai gaskiya tana da ɗaci". Fatima ta tashi ta bar mata falon. Ana gobe ɗaurin aure ya kama za su je wajen bokan nan, duk da ta ce ba za ta yi biki ba, amma a gidan nata dai za a yi taron, haka ƴan'uwa suka tsara, don haka tun yau za su zo a fara shirin hidimar goben, sannan kuma yau za a yi dinner. Ƙarfe shida Fatima ta shirya tafiya, don a yadda suka yi da wacce za su tafin ma ce mata ta yi ana idar da sallar asuba ta fito, ba ta fito ba sai shidan, ko ƙaramin ɗanta ba za ta tafi da shi ba, ta yi wa Hasana sallama tare da roƙonta don Allah kar ta faɗawa kowa inda ta tafi, kawai ta ce ita ma tashi ta yi ba ta ganta ba, idan ta dawo ita za ta ji da kowa har Usman ɗin, Hasana ta ce a dawo lafiya. A motar matar suka tafi, suka yi tafiya mai nisa, bayab azhar suka zo wata ƴar ƙaramar kasuwa, a nan suka tsaya suka ci abinci, don ita Fatima ko karyawa ba ta yi ba, bayan sun gama cin abinci suka yi sallah a nan, sannan ta bawa wani ajiyar motarta, da alama dai ta san shi sosai, suka hau babura suka fara tafiya, tun suna ganin garuruwa har suka shiga daji, ana ta zura tafiya, har abun ya bawa Fatima tsoro, tafiyar awa ɗaya suka yi a babur, ya ajiye su, matar ta roƙi masu baburan su jira su, za su ba su dubu ashirin, suka yarda, su Fatima aka fara tafiyar ƙafa, aka nausa cikin daji ana ta yi. Fatima ta gode Allah da ba ta taho da ɗanta ba, ganin tafiya ta ƙi ƙarewa, ta gaji liss, ta kalli matar ta ce"Ni Hajiya me yasa muka sauka ba mu ƙarasa a babur ɗin ba?" Ta ce"Ai wancen bishiyar da kika ga mun tsaya mun sauka madakata ce, babur ko mota a nan zai tsaya muddin wajen bokan nan mutum zai je, saboda yanzu mun riga mun shiga masarautarsa, yanzu haka a ciki muke tafiya, yana kallonmu yana jinmu, kuma kafin mu ƙarasa zai gama ganin buƙatunmu, ya gama tsayar mana da mafita, da mun je babu wani bayani sai dai ya zartar da hukunci kawai mu sallame shi mu juya". Fatima ta jinjina kai, suka cigaba da tafiya suna sauri kamar za su tashi sama. Suna ƙarasawa kallo ɗaya ta yi masa ta ji gabanta ya fara faɗuwa, don wannan hamshaƙin boka ne irin wanda take gani a TV, "Ke ɓatacciya! Ki cire takalminki!" Ya dakawa Fatima tsawar da duka dajin sai da ya amsa, saura kaɗan Fatima ta faɗi saboda yadda ta rikice, sai a lokacin ta lura ita Hajiyar ashe ta cire nata, ta cire da sauri ta tsugunna jikinta yana karkarwa, Hajiyar ta ce"Tuba take ranka ya daɗe mai girma Duhu, laifina ne ban faɗa mata ba, tuba muke". Fatima da rawar baki ta ce"Tuba nake". Ya wurga hannuwansa biyu sama yana wasu abubuwa masu kama da gurnani, da wani yare, ledoji biyu suka bayyana a hannuwan, ya wurgawa kowaccensu guda ɗaya, ya kalli Fatima wacce ta cafe ledar ta ƙanƙame, ya ce"Mun ga komai, burinki mijinki ya fasa auren da zai yi gobe, to wannan auren tabbatacce ne, za a ɗaura shi gobe da misalin ƙarfe goma da minti ashirin da biyu da sakan biyar, amma kina da mafita, idan an ɗaura auren zai iya sakinta a ranar, indai kin bi ƙa'idar wannan maganin da na ba ki, akwai itace a ciki, idan kin koma yanzu ki jiƙa shi a babban bokiti ya kwana, gobe da daddare idan an kawo amaryar kafin ya ganta ki yi wanka da wannan ruwan, sannan akwai kwalli, ki saka shi, sai ki kalle shi ido cikin ido, ki yi masa umarnin ya sake ta, nan take buƙata za ta biya! Kuɗin aikinki naira dubu ɗari da hanmsin ne". Ya ajiye mata wata baƙar ƙwarya a gabanta, ta saka kuɗin hannunta na rawa, don a firgice take. Ya kalli abokiyat tafiyar tata ya ce"Akan maganar surukarki kika dawo ko? Burikinki ta mutu kawai yanzu ba wai ki rufe bakinta ba, to ki je gida, yau cikin dare za ta mutu a kan gadonta! Kuɗinki dubu ɗari biyu da hamsin". Ita ma ta ciro kuɗin ta saka a cikin ƙwaryar, suka yi godiya suka tashi suka tafi. Duk irin gudun da Hajiya take zurawa a mota, ba su suka isa gida ba sai ƙarfe sha biyu na dare, a lokacin hankalin Fatima ya gama tashi, ta ci kuka ta gode Allah, saboda ta san asirinta sai ya tonu, ana can ana nemanta, ina za ta ce ta je ta kar sha biyu na dare? Ga shi ta bar yaro mai shan nono a gida, ba ta tafi da wayarta ba kuma, ita kuwa Hajiya ranta fes, don mijinta ba ya gari, yaranta kuma ta kai su gidan kakarsu, inda za a yi rasuwar kenan yau. Ƙarshe dai Fatima a gidan wannan matar ta kwana, ta ma kasa bacci saboda damuwa. A can gida kuwa, tun safe da Usman zai fita ya tambayi ina Fatima Hasana ta ce ta fita, kuma ba ta faɗa mata inda za ta je ba, ya kira wayarta ya ji tana gida, sai kawai ya fita, da la'asar ya dawo gidan ya ga ba ta dawo ba, zuwa lokacin gida ya cika da baƙi ana ta jajanta ina ta tafi ba ta sanar ba? Kuma ta bar ƙaramin yaro, don ma ba shi da rigima, ana ta hada-hadar girkin abincin gobe, wasu suna gulmar kishi ne ya hana ta zaman gidan. Sai da aka idar da sallar isha'i ba ta dawo ba, sannan aka fara shiga damuwa, aka dinga kiraye-kirayen waya ko'ina sai a ji ba ta je ba, zuwa ƙarfe ɗaya na dare hankali ya gama tashi, har da masu kuka, Usman ne yake ta kwantar musu da hankali, yana cewa ba ɓata ta yi ba, tun da dama ba ta faɗawa kowa inda za ta je ba, tana sane ta yi hakan, shi sam bai damu ba, gani yake haukan kishi ne kawai ya sa ta yi haka, don haka shi tsaf ma ya je wajen dinner suka sha paty da amaryarsa. Haka aka kwana kowa babu nutsuwa. Washegari da sassafe ta tafi gidan yayarta wacce suke uwa ɗaya uba ɗaya, Sumayya tana ganinta ta ce"Fatima! Daga ina kike? Me ya same ki? A ina kika kwana?" Fatima ta fara share hawaye ta shige ɗakin, bayan sun zauna ta ce"Don Allah Yaya ki rufa mini asiri ki ce a gidanki na kwana". Sumayya ta ce"Ke kuwa ina kika je? Kuma ta ya zan ce a gidana kika kwana, bayan da ni aka yi ta jajenki jiyan?" Ta ce"Sai ki ce ni na ce kar ki faɗa, don Allah ki taimaka mini" . Sumayya ta ce"To ina kika je?" Fatima ta ce"Wallahi na kasa jurewa ne, da garin zan bari, na je na wuni a tasha na rasa ina zan nufa, tun da idan na je gidan ƴan'uwa ma na san za a tona min asiri, ina tasha har isha'i, sai na yi gidan ƙawata na kwana a can, kawai ji na yi kamar kar na koma gidan nawa wallahi, zuciyata zafi take yi". Sumayya ta ce"Assha! Haba Fatima, ke kuma ta haka za ki nuna naki kishin? Wannan dai ba hali bane gaskiya kar ki sake yin haka, yanzu abu na taro kowa ya ji ba ki kwana a gida ba, yanzu idan na ce kina gidana a nan kikw kwana ba kowa ne zai yarda ba wallahi". Fatima ta ce"Ba komai ki ce haka ɗin dai". Ta ɗauki waya ta kira Usman ɗin, suka gaisa, ta ce masa Fatima fa tana gidanta a nan ta kwana, ta ƙi faɗa ne kawai saboda Fatiman ta roƙe ta akan ta ƙyale ta a nan ɗin, gidan ya yi mata zafi. Ran Usman ya ɓaci ya dinga faɗa yana cewa shi me ya yi mata na jin zafi da za ta zaɓi barin gidan ta bar ƴaƴanta? Sumayya ta ce ya zo gidan dai su sasanta. Kafin ya zo Fatima ta yi wanka ta saka kayan yayarta, ya zo gidan yana ta haɗe rai, ya ce"Fatima me na yi miki? Tun da na faa zancen auren an na zage ki ko na ci zarafinki?" Ta girgiza kai alamar a'a, ya ƙaraci faɗansa ba ta ce komai ba, tun da ta san tana da maganin iskancinsa a hannunta, komai zai yi kafin anjima ne, sanda za ta yi masa umarnin ya saki amaryar da yake ta rawar kai akanta, kuma dole ya sake ta ɗin. Tare suka koma gidan, a motar babu wanda ya tankawa wanh har suka ƙarasa, ƴan'uwa ana ta yi mata nasiha da faɗa, ta ɗauki ɗanta ta shige ɗaki. WACE CE ZAINAB AMARYAR USMAN? Zainab irin kangararrun yaran nan ne da suka taso da rashin ji, sannan ba ta samu isasshiyar tarbiyya ba, shekararta biyar a duniya mahaifinta ya rasu, tana da yayyu mata guda biyu, ragamar kula da su duka akan mahaifiyarsu take, ita ce cinsu da shansu, komai nasu ita ce, tun sanda mahaifinsu na da rai take tsaye akansa, ta mallake shi ta hana shi sakat, ta hana shi ƙara aure, domin ta shahara ta bunƙasa ta fannin bin bokaye, har kwanan kan bishiya ta yi don neman biyan buƙata, ta zura hannu a kabari ya fi mini talatin, ta yanka hannunta ta tari jinin ta kwaɓa magani da shi, za ta iya yin komai saboda buƙatarta ta biya, bayan rasuwar mijinta ta auri maza har biyar, kowacce auren ba ya cin Talata ballantana Laraba, saboda tijararta da rashin haƙuri, ba ta taɓa yin aure ta bi miji gidansa ba, nan dai gidan ƴaƴanta da marigayi ya bar musu gado a ciki mijin yake zuwa ya iske ta, har yanzu da shekaru suka ja Hanne ƴar gayu ce, dama kyakkyawa ce, kana kallonta ka ga ƴar bariki, a yanzu haka tana da wani wanda ba a san ma me za a kira shi ba, mijinta ne ko kwarto? Matashi ne ta girme masa, ya aure ta suka tare a gidanta, yau faɗa gobe daɗi, a haka har aka yi saki biyu, ashe matarsa ba ta taɓa sanin ya yi auren ba, a ranar da ta sani ta zo har gidan ta saka shi a gaba ta ce sai ya sake ta, nan take ya cike saki na ukun, Hanne tana son Baba ƙarami don haka ta shiga ta fita ta ɗaure shi ram, ya zama babu auren amma ba su rabu ba, kwana ne kawai ba ya yi a gidan, zai zo ya wuni, suna shiga ɗaki su kwashe awanni su biyu, sannan kullum sai ya ba ta kuɗin cefane, idan faɗa ya tashi haka za su yi a gidan, suna maganganu da zage-zage irin na ƴan bariki, kuma tana da wasu samarin da suke zuwa zance, haka za su shiba ɗaki su ƙule, ko kuma ta ci kwalliya ta ce ta tafi neman na kanta, haka za ta wuni bin office-office ɗin zawarawanta, sai dare ta dawo niƙi-niƙi da kaya, da uwar kuɗinta a jaka, babu ruwanta da kunyar buduruwar ƴarta Zainab dake gidan, sauran sun yi aure, kuma dayake tariyya ta Allah ce cikin yaran Zainab ce kawai ta kafe halayen Hanne, su sauran kafin aurensu har nasiha suke yi mata. Zainab tun tana shekara sha huɗu mazan layi marasa tarbiyya suka fara buɗe mata ido da kuɗi, ake ɗan taɓata ana ba ta kuɗi, bayan ta gama secondary kuma abun nata ya shahara, take bawa maza kanta ana biyanta, har wani saurayinta ya yi mata ciki, daga nan ya ɗauke ƙafa, Hanne ta zubar da cikin, don wannan ba baƙon abu ba ne a wajenta, ita kanta kafin ta yi aure sau biyu tana zubar da ciki, sannan bayan rasuwar mijinta ma ta zubar da ciki, ta kai sunan saurayin wajen boka aka kafe shi tsaf, sai da ya aure ta, wata biyu da auren Zainab ta ce ta gaji da auren, saboda yawan faɗan da suke yi, sannan ji ta yi auren ma duk takura ne kawai, ta matsa masa da rashin mutunci, na safe da ban, na dare da ban sai da ya sake ta. Tana gama idda ta samu wani mai kuɗi a nan maƙotansu, bai daɗe da tarewa ba, don ba ƴan gari ba ne, aiki ne ya kawo shi garin, ya zo da matarsa ya kama hayar babban gida, tun da Zainab ta ƙyalla ido ta gan shi ta ji tana son shi, kuma kai tsaye ta tunkare shi da maganar so, amma ya nuna ba ya sonta, tama faɗawa mahaifiyarta damuwarta, ta tashi tsaye ta yi iya yinta, sai ga wannan mutumin ya zo da kan shi ya ce yana son Zainab, duk ya gigice, auren ma sati huɗu aka saka, kuma shi ya yi mata komai na kayan ɗaki, duk abin da ta ba shi umarni ba ya tsallakewa jiki na rawa zai yi mata, matarsa ta shiga tsanani da ƙunci sosai tun da ya fara shirin auren nan. A ranar da Zainab ta tare a gidan, washegari ta ce masa ita fa ba za ta iya zama da kishiya ba, ko dai ya sake ta ko kuma ya saki matarsa. Duk da bai daina son matarsa ba, amma haka ya ji da ya rasa Zainab gara ya saki uwargidansa, uwar ƴaƴansa, don haka a ranar ya sake ta, ya ba ta kuɗin mota ta koma garinsu. Zainab ta dinga murza kambunta, tana gara kan bawan Allah, kafin danginsa su duƙufa addu'a da neman taimako, da ƙyar suka janyo shi ya zo gida, lokacin wata uku da auren, ba su bar shi ya tafi ba suka dinga yi masa maganin karya sihiri har sai da ya dawo hayyacinsa, ƙarshe ta waya ya saki Zainab tun kafin ya koma garin, amma fa a wannan watannin har filaye biyu ta siya da kuɗinsa. Mutuwar aure sam ba ta damun Zainab, tana gama idda ta samu wani mai mata ta aura, shi ma sati ɗaya da auren ya saki uwargidan, iyayensa suka tilasta masa sai da ya mayar da ita, wata biyu da auren, wataran Zainab ta yi masa barbaɗe a cikin abinci, tana cikin barbaɗawa ta ji muryarsa zai shigi falon, don haka da sauri ta juye maganin ba ta tsaya juyawa ba ta shige ɗakinta. Ranar girkin kishiyarta ne, ita ta gama jera abincin ta tafi wanka, Zainab ta samu wannan damar, mai gida ya watsa ruwa ya zo ya zauna zai ci abinci, uwargidan tana buɗewa gabanta ya faɗi, ganin koren abu kamar kuka an barbaɗa akan jollop ɗin shinkafar, ta kalle shi, shi ma ita yake kallo, a raunace ta ce"Mene ne kuma wannan?" Ya yi mata kafirin kallo ya ce"Ni kike tambaya? Me kika zuba mini a abinci? Kashe ni za ki yi ko mallake ni za ki yi?" Ta ce"Wallahi ban zuba maka komai ba, ƙalau na ajiye abincin nan, sai dai ko Zainab ce ta fito ta saka". Ya ɗaga murya ya kira Zainab ɗin, ta fito gabanta yana faɗuwa, amma sam ba ta nuna a fuska ba, ta ƙaraso tana karairaya ta ce"Alhajina ashe ka shigo, sannu da zuwa". Fuska a haɗe ya ce"Me kika zuba mini a cikin abinci?" Ta ce"Kamar ya?" Ya ce"Ga ki, ga ta, ga abincin nan, wallahi idan ba ku fitar da wacce ta zuba mini maganin nan ba kowaccenku a gidansu za ta kwana". Zainab ko ɗar ba ta ji ba, saboda ita dama bayan auren ma duk ta ji ya fice a ranta, ita kuwa uwargidan sai rantse-rantse take yi, da Alhaji ya ga da gaske babu wacce za ta amsa ita ce, sai ya shiga ɗakinsa, ya fito da takardu biyu a hannunsa, ya bawa kowaccensu ɗaya, duk ya yi musu saki ɗai-ɗai. Zainab sam ba ta yi sha'awar komawa gidansa ba, ita kuma uwargidan ƙarshe babarsa ta sa ya mayar da ita, ta ce ai amaryar ce ta zuba, tun da duk tsayin zamansu da matarsa haka bai taɓa faruwa ba sai yanzu da ya yi wannan auren, don haka ya mayar da matarsa suka cigaba da zama. Daga nan sai ta dakata da auren, kawai take barikinta, har ta haɗu da wani abokin Usman, suke sheƙe ayarsu, shi kuma ya yi wa Usman hanya shi ma suka ɗinke da ita suke aikata masha'arsu, da ya fara gajiyada ita ya so zame mata sai ta nuna masa ita fa da aure take son shi, za ta shiryu indai zai aure ta, Usman ya nuna bai san zance ba, sai dai bai san ya riga ya shiga tarko ba, suka tashi tsaye suka dinga banka masa asiri har suka karkato hankalinsa ya amince zai aure ta. Wannan ita ce Zainab, matar da za a ɗaura musu aure da Usman a yau, shin Fatima za ta iya kishi da ita kuwa? Za ta iya fitar da ita daga gidan? Bayan dai bin bokaye da take yi, ita ɗin rainon uwa ƴar bariki ce. Daidai yadda bokan nan ya faɗa mata za a ɗaura auren nan ko mistake ɗin sakan ba a ƙara ba aka ɗaura, Fatima tana ta yaƙe a cikin mutane, sai bayan an ɗaura auren ta tuna ba ta jiƙa maganin ba, ta tashi ta jiƙa ta saka a banɗakinta ta ɓoye ta rufe da mukulli, tana ta fargabar aikin zai ci ya saki amarya ko a'a? Da magriba aka kawo amarya ɗakinta, kowa ya watse sai ƙawayenta masu siyan baki, wanda Fatima take rayawa a ranta tare za su koma gida da amaryarsu, ita ma a ƴan'uwanta babu wanda ya zauna, sai ƙanwarsa Hasana da ta ce za ta kwana biyu. Ana yin sallar isha'i ta yi wanka da wannan maganin, ta zo falo ta zauna, tana jin shigowar motarsa ta ɗakko kwallin ta rambaɗa har ya zazzago ƙasan idonta, ta fito harabar gidan ta kame, shi da abokansa ne biyu, hango ta da ya yi ta riƙe ƙugu ya sa shi ƙarasawa wajenta, ya ce"Nana, akwai wani abu ne?" Ta kalle shi, shi ma ita yake kallo, ido cikin ido suka kalli juna, ta ce"Usman ina yi maka umarni da ka saki amaryar nan taka yanzu-yanzu". Usman ya ji gabansa ya faɗi, zuciyarsa ta buga da ƙarfi, ya tsaya yana kallonta. LAST FREE PAGES! A nan za mu dakata da free pages, akwai tirka-tirka kala-kala a gaba, za ku ji dalilin sakawa labarin ban wani zaman, sannan za ku ji yadda za a kwashe tsakanin Fatima da Amaryarta, shin wace ce mai nasara? Kowacce dai kar ta san kar! Littafin na kuɗi ne akan naira 500, domin jin yadda za ta kaya ki saka kuɗin karatunki ta nan 8028966015 Sadiya Abdulrazak opay Shaidar biya ta nan 08028966015