🙎‍♀️🙎‍♀️ UMMAKATITI🙎‍♀️🙎‍♀️ (SHORT STORY) Na Aminatu Mansur Dikko (Meenart Wurma) *Sadaukarwa* Na sadaukar da littafin nan ga masoya na Hafsat (Aneesart Wurma) Da Hafsat(Nasreen) Da Ummukulthum(Ummitah) Ina roƙon Allah ya tsaremin ku aduk in da kuke, ya yi ma rayuwar ku albarka. PAID BOOK NAIRA 200 Payment via this account number 0017446862 jaiz bank Aminatu Mansur Dikko Or 7071524017 opay Aminatu Mansur Dikko Or Recharge card via this number 07071524017 A tura shedar biya ta numbar. https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💪✍️(J.W.A) Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✏️ **EPISODE ONE** *SHIMFIƊA* Suna na Ummukulthum Ibrahim amma an fi sanina da UMMAKATITI, Ni haifaffiyar garin Jaji ce dake tsakanin garin Zaria da Kaduna, Mu biyu Mahaifanmu suka haifa Ni da ƙanwata Hafsat ana ce ma ta MANGA. Daga mu Allah bai ƙara ba su haihuwa ba har Allah ya yi ma Mahaifinmu rasuwa. Ibrahim Musa shi ne asalin sunan Mahaifinmu tun ya na yaro Allah ya yi ma Mahaifinsa rasuwa, Mahaifiyarsa kuma sunan ta Ummukulthum bayan rasuwar Mahaifinsa ba ta koma garinsu ba saboda ba ta da kowa a yanzu, asalinta ƴar garin kankia ce dake jahar Katsina a wani hari da ƴan bindiga suka kai garin suka kashe duk wani dangi na ta. Hakan ya sa bayan rasuwar Mijinta ta zauna a nan Jaji ta ci gaba da kula da ɗanta har ya kai munzalin aure in da ta kawo ma sa ƴar Aminiyarta Laure me suna Hassatu ta ce ita zai aura, bai yi ma ta musu ba ya yadda suka daidai ta kansu ba wani ɓata lokaci aka sha biki. Sai dai kuma ba a nan gizo ke saƙa ba Kakarmu ganin har Hassatu ta yi shekara biyu a gidan Ibrahim ba ta taɓa ko ɓatan wata ba ya sa ta tashi hankalinta akan lallai-lallai sai Ibrahim ya ƙara aure. Bai yi ma ta musu ba dan dama faɗuwa ce ta zo daidai da zama tun da daman ya na da wacce yake so wato Mahaifiyarmu Maryam. Ita kuwa Kaka ba wani dogon bincike ta amince aka shiga shirye-shiryen biki. Ba ɓata lokaci aka sha biki in da aka kai Amarya gidanta anan cikin gidansu Ibrahim ɗin ga ɗakinta ga na abokiyar zamanta wato Hassatu. In da Allah ya taimaki Ibrahim da Mahaifiyarsa duka Matansa su na da ladabi da biyayya ga haƙuri don haka sai suka haɗa kansu suka zauna lafiya. Su na nan su na zamansu lafiya sai ga ciki ya bayyana a jikin Maryam, haƙiƙa sun yi murna mara misaltuwa kuma sun yi godiya ga Allah buwayi gagara misali. Hassatu ba ƙaramin ƙoƙari ta yi ba wurin danne abun dake cikin zuciyarta na ciwon rashin haihuwa , haka ta zage ta rinƙa kula da Maryam da abun da ke cikinta. Hakan kuwa ba ƙaramin ƙima da daraja ya ƙara ma ta ba a wurin Ibrahim da Mahaifiyarsa har ma da Maryam ɗin. Haka suka ci gaba da kula da cikin dake jikin Maryam da ma ita kanta har lokacin haihuwarsa ya yi in da ta haifi ɗiya mace, ranar suna yarinya ta ci sunan Mahaifiyar Babanta wato Ummukulthum mutanen gari su na ce ma ta UMMAKATITI. Bayan haihuwar UMMAKATITI da wata ukku sai ga ciki ya bayyana a jikin Hassatu ita ma, faɗin murnar da suka yi ɓata baki ne saboda abu ne da suka ri ga suka fidda rai da samun sa. Nan ita ma Maryam ta zage damtse wurin nuna ma Hassatu kulawa fiye da wacce ta ba ta lokacin da take da na ta cikin a cewar ta dole ta rama ma kura aniyarta. Haƙiƙa ita ma ta samu kulawa sosai har ta shiga watan Haihuwarta, In da suke zaune suna jiran Allah ya kawo ranar haihuwa tare da addu'a tuƙuru da fatan sauka lafiya. Dan tunda Hassatu ta shiga watan Haihuwarta idan su na fira da Maryam sai ta rinƙa ce ma ta"Dan Allah Maman Umma ki kula da abun da zan haifa kuma ki yi ma sa tarbiyya mai kyau, kar ki so shi da yawa har ki kasa ba sa tarbiyyar da ta dace, saboda ke ce Mahaifiyarsa wadda za ta kula da shi." Da ire-iren waɗannan kalamai su take yi ma ta duk lokacin da suka keɓe su na fira. Idan ta ce ma ta haka ita kuma Maryam sai ta ce ma ta" Dan Allah ki daina sa damuwa a ranki in Sha Allah za ki haihu lafiya kuma ke za ki kula da abun da kika haifa da kanki har ki yi ma sa tarbiyyar da ta dace da shi." Idan ta ce ma ta haka sai dai ta yi murmushi kawai tabar maganar. Ranar wata Alhamis tun asuba Hassatu ta tashi da naƙuda sai gumurzu take har dare haihuwa shiru sai uban ciwo kamar za ta haihu sai kuma ta lafa. Ganin haka da Ibrahim ya yi ya sa asuba na ketowa ya yi sauri ya fita dan ya samo mota akai ta asibiti tun da abun ya ƙiya. Bayan ya fita da ƙyar ya samo mota suka garzayo dan zuwa su nufi asibiti da ita sai dai kuma kana naka Allah ya na na sa kuma na sa shi ne gaskiya. Shigar sa gida kenan ya ji kuka na tashi nan da nan hankalinsa ya tashi kar dai abun da yake tunani ne ya faru. Aiko dai ya na shiga gidan ya ji wannan mummunan labari na rasuwar Hassatu tare da abun da ke cikinta. Sun yi kuka sun yi baƙin cikin rasa Salihar mace irin Hassatu da abun da ke cikinta amma ba yadda suka iya haka suka dangana suka ci gaba da bin su da addu'a. Bayan shekara ɗaya Maryam ta ƙara haihuwar ɗiya mace in da aka sa ma ta sunan Marigayiya Hassatu wato Hafsat su na ce ma ta MANGA. Daga nan kuma sai haihuwar ta tsaya ma Maryam cakk. Ganin haka ya sa Kaka ta ɗauki son duniya ta ɗaura mana Ni da ƙanwata MANGA, ba ta bari kwata-kwata a ɓata mana rai ko mu nemi wani abu mu rasa hakan ya sa muka tashi a sangarce. Dan ma Mahaifanmu su na matuƙar ƙoƙari wurin ganin sun ba mu tarbiyya mai kyau da nuna mana mahimmancin abubuwa da dama. Ba dan haka ba da sai mun fi haka sangarcewa. A haka muke ci gaba da rayuwarmu cikin farinciki da ƙaunar juna a tsakaninmu. Babanmu ya sa mu a makarantar je ka ka dawo ta primary Ni da ƙanwata duk da bana son makaranta amma haka nake zuwa badan raina ya na so ba. Saɓanin ƙanwata ita ta na son makaranta sosai amma a haka kuma na fi ta ƙoƙari. Lokuta da dama idan na nuna Ni ba za ni makaranta ba aka tirsasa Ni akan sai na je sai na gudu ɗakin Kakata wadda daman acan muke kwana na ɓoye. Sai ta yi ta faɗa akan cewa a barni ai makarantar ba dole ba ce na je ta muhammadiyya kawai ai ita ce ta tafiya lahira ba waccen ba. Da wannan Nake fakewa in yi zamana gida ko in tafi gidansu ƙawata Lubabatu muna ce ma ta Luba sai dai ƙanwata ta tafi makarantar ita kaɗai. Dan jin yadda rayuwar su UMMAKATITI zata kasance ku ci gaba da bibiyar ƴar mutan wurma ta kafafen sada zumunta ngd. Fallow me on Instagram: Meenart wurma.... Tiktok: meenartwurmah.... Facebook:oum ummeeytah.... Telegram: meenart wurma.... Snapchat: meenart wurma.... ....✍️ 🙎‍♀️🙎‍♀️ UMMAKATITI🙎‍♀️🙎‍♀️ (SHORT STORY) Na Aminatu Mansur Dikko (Meenart Wurma) *Sadaukarwa* Na sadaukar da littafin nan ga masoya na Hafsat (Aneesart Wurma) Da Hafsat(Nasreen) Da Ummukulthum(Ummitah) Ina roƙon Allah ya tsaremin ku aduk in da kuke, ya yi ma rayuwar ku albarka. PAID BOOK NAIRA 200 Payment via this account number 0017446862 jaiz bank Aminatu Mansur Dikko Or 7071524017 opay Aminatu Mansur Dikko Or Recharge card via this number 07071524017 A tura shedar biya ta numbar https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💪✍️(J.W.A) Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✏️ **EPISODE TWO** Ina da shekaru goma a duniya na gama primary school ɗina, Babanmu ya yi-ya yi in ci gaba da makarantar secondary Amma na ƙeƙashe idona na ce"Ni wallahi ba me sani In ci gaba da Wannan makarantar Ni aure nake so dan haka shi za'a ma ni." Da ya ji na ce haka shi maganar ma dariya ta ba shi dan shi a ganin sa duka nawa nake da har zance aure nake so, bayan ko a cikin ƙawayena ba wacce aka yi ma aure ballantana na ce wata na gani an mawa nima nake so. Dan haka sai ya share zancen nawa ya ci gaba da cuku-cukun nema min makarantar gaba da primary. Ban tashi raina kaina ba sai da ya kawo min kayan makaranta da littattafai sannan, aiko nan na tada bori akan ni fa har yanzu ina akan bakana na aure nake so. Jin haka da Kaka ta yi ya sa ta ce" to ai shi ke nan sai a ƙyale ni tun da na ce bani so." Allah Sarki Babana ba yadda ya iya haka ya haƙura ya bar Ni da maganar karatun, amma kusan kullum sai ya min nasiha mai ratsa jiki. Ranar da bazan taɓa mantawa da ita ba ranar wata juma'a da asuba muna kwance a ɗakin Kaka, Mama ta zo ɗakin ta na tada mu ta na cewa "mu zo Babanmu ba lafiya." haka mu ka tashi hankali a tashe mu ka nufi ɗakinta dan acen yake. Muna zuwa ya kamo hannuna jikinsa na ƙyarma bakinsa na ɓari ya ce min"Ummana dan Allah ke ce Babba ko bayan ba raina ki kula da Mamata da Mahaifiyarku da ƙanwarki kar ki bari su yi maraicin rashi na, kuma dan Allah ku kula da mutuncinku kar ku bari wani abun duniya ya ruɗe ku har ku zubda mutuncinku, ku kula da ibada da bin dokokin Allah, na yafe ma ku duniya da lahira Allah ya yi ma ku albarka ya zaɓa ma ku mazaje nagari." Ya na gama faɗar haka ya fara wani jijjiga ga shi ya na so ya yi magana amma ba hali. Ganin haka ya sa su Mama suka fara biya ma sa kalmar shahada har Allah ya sa ya maimaita daga nan rai ya yi halinsa. Faɗin irin tashin hankalin da muka shiga ɓata baki ne haƙiƙa mun yi rashin Mahaifi mai son mu da gaskiya wanda a kullum yake nuna mana bin Allah shi ne gaba akan komai na rayuwar duniya. Nan Kaka ta rushe da kuka ta na faɗin "shi ke nan Ibrahim kai ma ka tafi ka barni yanzu ba Ni da kowa innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, amma ba komai na yafe ma ka Ibrahim duniya da lahira Allah ya ƙarbi bakuncinka." Kafin ka ce me gidanmu ya cika da jama'a ana ta ba mu haƙuri, muna ji muna gani aka yi ma sa sutura aka kai sa gidansa na gaskiya. Bayan sadakar arba'in Mahaifin Mamanmu ya ce ta dawo gida ta ida takabarta, anan ta ce za ta tafi da mu Kaka ta so ta ƙi amincewa amma haka ta haƙura muka bi Mahaifiyarmu gidansu. A haka ma kusan kullum mu na gidan Kaka domin mu ma mun ri ga mun saba da ita, kuma mun fi jin daɗin zaman wurinta saboda ba kwaɓa ba ƙyara. Mahaifiyarmu ta gama takabarta da wata ukku Allah ya fiddo ma ta Miji farko ta ce ita ba za ta yi wani aure ba amma Mahaifinta ya ce ba ta isa ba dole ta yi aure tun da ba wuce yin sa ta yi ba. Haka ta haƙura za ta yi auren wani mai garin ƙauye ne dake kusa da garinmu za ta aura, Matarsa ce ita ma ta rasu shi ne zai yi aure, ya na da yara ukku shi ma duka mata, biyu ya aurar da su ɗaya ce kaɗai ta rage zata zauna wurin Mama, kusan sa'anni muke da ita hakan ya sa ya ce ya amince ta tafo da mu. Amma kaka na jin haka ta yi tsalle ta dire ta ce "wallahi ba mai tafin ma ta da Jikoki agolanci dan haka a maido mu wurinta, dama ba da son ranta ta bada mu ba." Haka kuwa a ka yi ba yadda Mama ta iya ta tattara mu muka koma hannun Kaka da zama, ita kuma ta yi aurenta a wani gari dake kusa da mu. A lokacin ina da shekaru goma sha biyu a duniya ita kuma MANGA shekaru Goma daidai muka koma hannun Kaka da zama. Komawarmu hannun Kaka da zama ya sa duk muka manta da nasihohin da Mahaifanmu suka rinƙa yi ma na, saboda sabon shafin tattali da kulawa da so ta ɓude ta na nuna mana, a cewar ta ba ta da wasu da suka wuce mu a duniyar nan. A cikin ƙanƙanin lokaci muka ƙara sangarcewa saboda ba abun da muka nema muka rasa kuma ba wanda ya isa ya taɓa mu ya zauna lafiya. Ina mugun son ƙanwata MANGA fiye da yadda nake son kaina, zan iya yin komai domin ta. WANNAN KENAN KAƊAN DAGA CIKIN TARIHIN RAYUWARMU NI DA ƘANWATA, YANZU ZA MU SHIGA LABARIN KAI TSAYE. Fallow me on Instagram: Meenart wurma.... Tiktok: meenartwurmah.... Facebook:oum ummeeytah.... Telegram: meenart wurma.... Snapchat: meenart wurma.... ....✍️ 🙎‍♀️🙎‍♀️ UMMAKATITI🙎‍♀️🙎‍♀️ (SHORT STORY) Na Aminatu Mansur Dikko (Meenart Wurma) Sadaukarwa Na sadaukar da littafin nan ga masoya na Hafsat (Aneesart Wurma) Da Hafsat (Nasreen) Da Ummukulthum (Ummitah) Ina roƙon Allah ya tsaremin ku aduk in da kuke, ya yi ma rayuwar ku albarka. PAID BOOK NAIRA 200 Payment via this account number 0017446862 jaiz bank Aminatu Mansur Dikko Or 7071524017 opay Aminatu Mansur Dikko Or Recharge card via this number 07071524017 A tura shedar biya ta numbar. *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ **EPISODE THREE** "Na rantse da Allah yau sai naga abun da ya ture wa buzu naɗi a cikin garinnan, yara marayu za'a bi duk a takura masu saboda anga ba uwarsu a gari ubansu kuma ba ya raye to bada ni za'ayi wannan iskancin ba wallahi." Kaka ta haƙiƙance ta na masifa, yayin da suke tattaunawa ita da Aminiyarta Laure. "Ai maganar gaskiya kar ki wani yadda, danni da Ni ce ke wallahi wurin hukuma zan kai zancen nan dan a shiga tsanin jikokina da wasu daga cikin mutanan garin nan." Iya Laure ta ƙarashe zancan da son ƙara kunno ƙawarta dan su ɗauki mummunan mataki. "To ai Laure ko yanzu ba haƙura na yi ba saboda abun ya yi yawa wallahi dan haka bari wani ɗan kutumar uba ya ƙara zuwa min da maganar yaran nan ya ga yadda zamu ƙare wallahi." Nan suka zauna sun kai awa biyu su na ta bambamin masifa akan abun da bai kai ya kawo ba. Duk wannan masifar da suke yi fa akan wata makwabciyarsu mai suna Hinde ce da ta zo har gida ta samu Kaka bayan sun gaisa a mutunce ta ce mata" Kaka dan Allah daman abun da ya sa na zo wurin ki akan abun da UMMAKATITI take yi a cikin garinnan ne, ace kamar UMMAKATITI duka shekararta sha ukku fa amma ta hana yaran mutane saƙat a cikin garin nan, ba ka isa ka aiki Yaro ba in dai ta haɗu da shi ko dai ta duke sa ko ta lalata abun aiken." Ta numfasa ta ci gaba da cewa"shi ya sa na zo dan In faɗa maki dan Allah ki ja mata kunne akan ta daina abun da take yi kar wata rana ta jawo wanda ya fi ƙarfinta a samu matsala." Ta na kaiwa nan ta ɗaga kai ta kalli Kaka jin tun da ta fara magana ba ta ce komai ba, aiko ta ga Kaka ta hangame baki ta na ta zabga mata harara sai huci take. "To sannu Sarkin munafikan duk duniya wa'azi kika zo ki min ko kuwa kina so ki nuna jikokina ba su da tarbiyya iyye! Nace iyye!!." Tuni Hinde ta shiga taitayinta ganin Kaka ta miƙe tsaye ta na nunnunata da hannu kamar zata mare ta, Hakan ya sa ita ma ta miƙe ta ce" A'a Kaka wallahi ba haka nake nufi ba kawai na faɗa maki dan a gyara ne." "To na ji kuma ki fita a harkar jikokina, na san ba kowa ma kike magana a kanta ba sai takwarata UMMAKATITI tun da naga duk mutanan garin nan ita kaɗai ku ka sa ma idanu." "Kuma da kike cewa kar ta jawo wanda ya fi ta to ko ta jawo ina ruwanki nace ina ruwanki." Nan Kaka ta rufe ta da masifa kamar zata hauta da duka. Hinde na ganin haka ta tashi ta ƙwamishi ɗan silifas ɗinta da duk ya siɗe ta yi gaba. Ko bayan fitarta Kaka ba ta yi shiru ba ta ci gaba da mita har Aminiyarta ta shigo ta isketa a haka take tambayar ta mi ya faru ta kora mata zancen shi ne suka ci gaba da mitar a tare. Har wurin shidda na yamma sannan Laure ta ce "kin ga Umma bari na tashi na tafi yanzu Malam zai neme Ni don basa ruwan alwalla ga magriba ta ƙarato." " To shi ke nan Laure sai gobe in nayi shawara da UMMAKATITI kin ji yadda muka ƙare." Nan suka tafi zaure su na bitar zancen, kusan mintinan su goma a zauren sannan ta tafi. Ta na tafiya kuwa sai ga su UMMAKATITI sun dawo daga makarantar allo. Wanda UMMAKATITI badan komai take zuwa ba sai dan saida ɗan tamatsitsin da take tare da daɗi biyu(kwalbebe). "Yawwa ƴan albarka kun dawo ko?." "Ey Kaka mun dawo sannu da gida." In ji MANGA cikin ladabi take maganar. Ita kuwa gogar tamu wato UMMAKATITI tuni ta baje saman tabarma ta fara ƙirga kuɗin cinikin da ta yi na kayan sana'arta a makaranta. Kaka na magana da MANGA amma hankalinta ya na a kan Ƴar lelenta dan haka ta ce mata" Ƴar lele an dawo daga makarantar ne?." UMMAKATITI ko ɗaga ido ta kalli in da Kaka take ba ta yi ba saboda gabaɗaya hankalinta na akan ƴan canjinta da yau ta yi ciniki sosai. Sai da ta gama ƙirga kuɗinta chass ta ga sun cika Sannan ta ɗago ta kalli Kaka ta ce "Kaka ya gida? ya gari? Ni wallahi yunwa nake ji, ina abincina." Ta na magana ta na shafa ciki alamun cikin dai sai kukan yunwa yake yi. "Bari na ɗauko maki abincin, ai abun da kike so ne na dafa wato shinkafa da miya hada nama na sa a ciki." "Yawwa Kakus kai gaskiya ina mugun yin ki dan haka duk ranar da na yi kuɗi za ki ji daɗi aradun Allah." Ta faɗa ta na washe baki alamun ta ji banza ta samu. Ƙasa-ƙasa MANGA ta ce"tabɗi ke ɗin ce za'a ci kuɗinki wai sai dai wata ba dai ke ba wallahi." "Ke MANGA mi kike cewa na ji kamar kina gunguni." " A'a Yaya Umma ni ba abun da nake cewa wallahi." "Ke wai dan uwarki bana ce ki daina cemin Yaya ɗin nan ba kamar wata Babba, duka nawa nike shekarata sha ukku fa da har za ki wani rinƙa cemin wata Yaya." UMMAKATITI ta faɗa ta na dungure ma MANGA kai. Daidai nan Kaka ta iso da kular abinci ta sako ta saman plate da cokali guda ukku. Ta ce "ke MANGA Wallahi kin cika jan faɗa, shin tunda ta ce ba ta son kina ce mata Yayar nan ba sai ki bari ba, ko ana dole ne?." "Kaka Malaminmu ne fa ya ce idan mutum ya girme ka ba'a faɗin sunansa kai tsaye, shi ya sa nake ce mata Yaya." "To wallahi kika ƙara cemin Yaya sai na ci kutumar ubanku ke da Malamin dan mi nace dan mi ko ana dole ne?." Ta na ida faɗa ta jawo plate ta fara zuba farar shinkafa ta na siɗe baki tun kafin ta ga miyar ballantana ta fara cin abincin. (Dan UMMAKATITI ba ta wasa da cikinta ga kwaɗayin tsiya). "Ki yi haƙuri bazan ƙara ba In Sha Allah." "Da dai ya fi maki wallahi Ni kawai ki rinƙa cemin UMMAKATITI na nafi jin daɗin sunan wallahi." Kaka na kawo miyar suka fara cin abincin a tsanake kamar basu bane suka gama cecekuce yanzu ba. Kaka da MANGA da cokali suke ci ita kuwa mai capacity ɗin tamu hannu ta duma a cewar ta" cin abinci da hannu yafi albarka." Su na gama cin abincin suka yi alwalla suka gabatar da sallar magriba suka baje nan tsakar gida suka fara fira kamar yadda ya kasance masu al'ada dan kullum magriba na yi zasu shimfiɗa tabarma ƙatuwa su na yin Sallah zasu zauna fira isha'i na yi su tashi su yi su dasa wata firar daga nan har lokacin kwanciya bacci ya yi. Idan lokacin sanyi ne shi ne zasu shige ɗaki ,idan kuma lokacin zafi ne shimfiɗa suke yi su yi kwanciyar su anan waje har asuba ta yi. Su na cikin firar ne Kaka ta sako ma UMMAKATITI zancen ɗazu tun daga zuwan Hinde har shawarar da suka yi fa Aminiyarta sai da ta rattaba mata labarin Sannan ta ƙare da ce mata ita mi ye shawarar ta. Nan UMMAKATITI ta lailayo wani ashar ta ɗurka ma Hinde akan abun da ta ce a kan ta. Follow me on Instagram: Meenart Wurma.... Tiktok: meenartwurmah.... Facebook:oum ummeeytah.... Telegram: Meenart Wurma.... Snapchat: Meenart Wurma.... ....✍️ 🙎‍♀️🙎‍♀️ UMMAKATITI🙎‍♀️🙎‍♀️ (SHORT STORY) Na Aminatu Mansur Dikko (Meenart Wurma) Sadaukarwa Na sadaukar da littafin nan ga masoya na Hafsat (Aneesart Wurma) Da Hafsat (Nasreen) Da Ummukulthum (Ummitah) Ina roƙon Allah ya tsaremin ku aduk in da kuke, ya yi ma rayuwar ku albarka. PAID BOOK NAIRA 200 Payment via this account number 0017446862 jaiz bank Aminatu Mansur Dikko Or 7071524017 opay Aminatu Mansur Dikko Or Recharge card via this number 07071524017 A tura shedar biya ta numbar. *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ **EPISODE FOUR** Nan UMMAKATITI ta lailayo wani ashar ta ɗurka ma Hinde akan abun da ta ce a kan ta sannan ta ce" yo Kaka wallahi na rantse da Allah Hinde ta bani da Ni cikin garin nan, munahika ashe ta na nan ta na samun idanu da wata shegiyar ƙafarta kamar mariƙin lema." " Haba Yaya...." "In kika ƙarasa na rantse da Allah sai na baje ki ƴal bura'uba kawai, ke wallahi kamar ma na lura dake ba ki ƙaunata Yarinyar nan kamar yadda nake son ki." "Wallahi Yaya ba haka bane kin san duk duniya bani da wacce nake so sama dake saboda irin mugun son da kike min kema, Ni abun da nake so ɗaya ne dan Allah ki daina zage-zagen nan da neman rigima kawai." Ta na magana ta na ƙara marairaicewa dan UMMAKATITI ta ɗauki maganar da gaskiya. Abun da MANGA ba ta sani ba shi ne tun lokacin da ta ce ma UMMAKATITI Yaya zance ya lalace dan tuni ta shiga tunanin abun da za ta yi ma MANGA dan ta huce takaicin Yayar nan da take ce mata. Dan ba ta ƙaunar sunan ko kaɗan kuma ta yi-ta yi MANGA ta daina ce mata haka amma ta ƙi ta bari. Duk lokacin da ta yunƙuro dan ta ɗauki mataki a kan MANGA sai ta kasa saboda mugun son da take mata. Jin UMMAKATITI ta yi shiru ba ta ce komai ba ya sa MANGA ƙara cewa"Yaya wai ban ji kin ce komai ba......." Take ta zuƙe maganar da ta ɗebo lokacin da ta ɗago kai ta kalli UMMAKATITI jin shirun ya yi yawa, aiko ta yi arba da wata munafukar harara da UMMAKATITI ke ta aika mata da ita ba tare da ta sani ba. Hakan ya sa ta tuno ɓaranɓaramar da ta yi na cewa Yaya, ai ba shiri ta miƙe tsaye daga zaunan da take tare da kama kunnenta sannan ta ce"Dan Allah ki yi haƙuri wallahi na kasa daina kiranki da Yaya." Ta na ƙara marairaicewa hada ɗan matso wasu guntattakin hawaye duk dan ta haƙura. Aiko plane ɗinta ya yi aiki dan UMMAKATITI duk duniya ba abun da ta fi ƙi irin ta ga hawayen MANGARTA, duk laifin da ta yi mata sai ta haƙura, In ko wani ne ya sa ta kuka to ya kuka da kansa, dan ba makawa sai ta sa shi mafiyin sa. Sai a lokacin kaka ta buɗi baki da duk ta cika da goro ta ce"nikam MANGA ban san wane kalar kunnen ƙashi ke gare ki ba, ache kullum magana ɗaya ake dake, tunda ta ce ba ta son kina ce mata Yayar nan ba sai ki bari ba." "Haba Kaka mai makon ki ba ta haƙuri a'a kuma sai ki ƙara zugata." "Yo to MANGA ai abun naki ne da ban haushi wallahi." Ta na magana ta na gantsarar goronta ta na ci. "Hmmmn Kaka ki barni da wannan yarinyar dai, wallahi duk ranar da kika kai ni ƙarshe sai na maki mugun duka cikin gidan nan in ga wanda zai kwace ki wallahi." Ta faɗa ta na ƙwafa alamun dai za ta gane kuranta idan ta danƙeta. "A'a a'a wallahi in dai Ni ce ba zan wani kwace ta ba ,tun da ita kunnen ƙashi ke gare ta." Nan dai suka ci gaba da cecekuce har suka manta da zancen Hinde. Sai kusan ɗaya da rabi sannan suka wuce ɗaki suka kwanta. Asuba na yi UMMAKATITI ita ce farkon tashi a gidan, sannan ta tashi MANGA sai da suka gyara gidan tass sannan suka tashi Kaka dan ta yi sallah lokaci ya yi. Bayan sun gama gabatar da sallar asuba suka yi wanka suka yi shirin tafiya school, dan bayan rasuwar Mahaifinsu Mamarsu da ƙyar ta samu UMMAKATITI ta koma makaranta, shi ma sai da ta yi mata alƙawarin da ta yi junior weac za ta yi mata aure sannan ta haƙura ta koma (dan duk duniya babu abun da UMMAKATITI take so yanzu wanda ya wuce a yi mata aure) dan ta na ƙaunar ta ji an ce wannan gidan UMMAKATITI ne, kuma ta na son ta ga ta haihu dan ta na da son yara sosai. Sun gama shiryawa ta kwashi kayan sana'arta dan ba ta wasa da harkar kuɗi sannan suka yi gaba. Su na hanyar tafiya Makaranta suka haɗu da ɗan Hinde shi ma zai tafi Makaranta, sai a lokacin ta tuno da munafurcin da ta yi mata. Aiko ta kama Yaron ta yi ma sa dukan tsiya da ƙyar MANGA ta amshe sa, ita kuma ta na cewa"ka ce ma Uwarka ta fita harkata in ba haka ba wannan somin taɓi ne na yi maka, dan na rantse da Allah sai na sata asara da yawa, tun da ta ce Ni tsararta ce." Ta yi ƙwafa sannan ta yi gaba abun ta, ta bar MANGA da lallashin Yaron. Ko da suka je Makaranta UMMAKATITI ba ta bar Yara wanda tafi aji ba da sa'anninta har ma da wanda suka fita aji, kowa shakkar ta yake ji dan ba ƙaramar masifaffiya ba ce ba, ga ta da ƙarfin bala'i. Malamai ma ba ta bar su haka nan ba, dan duk wanda ya yi gigin taɓa ta sai ta rama ta hanyoyi da dama, Amma duk da haka Malamansu su na son ta, saboda ƙoƙarinta dan ta sha ciwo masu gasa wadda suke yi da Maƙwabtan ƙauyikansu. Yanzu haka UMMAKATITI ta na js2 MANGA kuma ta na js1, saboda jinkirin shekara ɗaya da UMMAKATITI ta yi ba ta yi joining secondary School ɗinta ba ya sa tafi MANGA da aji ɗaya. Sun dawo Makaranta UMMAKATITI take ba ma Kaka labarin dukan da ta yi ma Lawali ɗan gidan Hinde. Nan Kaka ta ce"Ai kin yi daidai ƴar Albarka, gwara da kika gwada mata ke jininace ba wai ba." Haka suka yi ta tattauna zancen, ita dai MANGA ta na gefe ta na jin su dan ta na iya da ta yi Magana su yi mata cha, shi ya sa ta yi shiru ta na sauraransu. Yau ta kama juma'a ana tasowa daga Masallaci ƴan ta'adda suka yi ma garinsu UMMAKATITI dirar bazata. Haƙiƙa sun yi ɓanna sosai dan har sun kashe Mai Garin garin da wasu mutane daga cikin Al'ummar garin, sun raunata wasu daga ciki sosai. Cikin waɗanda aka kashe hada Mijin Laure Aminiyar Kaka, shi ya sa su UMMAKATITI suke cikin tashin hankali su ma. Kowa ka kalla a cikin garin ya na cikin tashin hankali akan abun da ya faru da su. In da suka ɗan samu kwanciyar hankali har suka gudanar da Jana'izar wanda suka rasu washe gari Asabar shi ne turo masu sojoji da aka yi daga headquarter ta sojoji. Hakan shi ne ya ɗan ba su ƙwarin guiwa da har su ma waɗanda suka raunata aka kwashe su aka miƙa hospital..... Follow me on Instagram: Meenart Wurma.... Tiktok: meenartwurmah.... Facebook:oum ummeeytah.... Telegram: Meenart Wurma.... Snapchat: Meenart Wurma.... ....✍️ 🙎‍♀️🙎‍♀️ UMMAKATITI🙎‍♀️🙎‍♀️ (SHORT STORY) Na Aminatu Mansur Dikko (Meenart Wurma) Sadaukarwa Na sadaukar da littafin nan ga masoya na Hafsat (Aneesart Wurma) Da Hafsat (Nasreen) Da Ummukulthum (Ummitah) Ina roƙon Allah ya tsaremin ku aduk in da kuke, ya yi ma rayuwar ku albarka. PAID BOOK NAIRA 200 Payment via this account number 0017446862 jaiz bank Aminatu Mansur Dikko Or 7071524017 opay Aminatu Mansur Dikko Or Recharge card via this number 07071524017 A tura shedar biya ta numbar. *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ **EPISODE FIVE** **AIRFORCE BASE OF JAJI** "Hey Soldiers never ace Terrorist su zo har cikin garin da muke a zaune su yi ta'addancin da suka ga dama, kuma mu naɗe hannu mu kwanta ba tare da mun ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki a kai ba." Wani Marshal na Sojojin Airforce dake tsaye gaban Hall yake magana cikin ɓacin rai cikin meeting room ɗin da suke meeting a kan abun ya faru a cikin garin Jaji. Can wani daga cikinsu ya yi magana ya na ƙoƙarin kwantar wa da Ogansu hankali ya ce" Sorry Sir In Sha Allah za mu yi ƙoƙari mu kuma Jajirce wurin ganin hakan bai ƙara faruwa ba." Ai sai maganar ma ta ƙara ɓata ma Ogan rai cikin tsawa ya ce" ok za ku yi ƙoƙari wurin ganin hakan bai sake faruwa ba kenan, Amma shi wanda ya faru fa haka za ku zuba idanu kenan sun ci banza?." Ya ƙarashe maganar da buga table ɗin dake gabansa nuni da alamun ransa ya ƙara ɓaci kenan. Wani ɗan Matashin Soja dake zaune kusa da chair ɗin Marshal ɗin wanda tun zamansu fara meeting ɗin bai ɗago kai ba ballantana ya ce wani abu ba Marshal ya kalla ya ce" Hey!! Chief are you ohk?." Sai a lokacin ya ɗago kai cikin husky voice ɗinsa ya ce" Sir I'm ohk." Kamar ba ya son yin maganar, ya na faɗar haka ya yi shiru sannan ya bi kowa da sexy eyes ɗinsa da kallo. **WAYE SHI** AIR CHIEF MARSHAL NURUDDEEN AMINULLAH HABIBULLAH kenan wato CHIEF DEEN Matashin saurayi ne wanda ya taka Babban matsayi a hukumar Sojoji ta AIRFORCE wato Sojojin sama da ƙananun shekaru, Saurayi ne ɗan kimanin 27years a duniya,Fari ne sol kamar ka taɓa jini ya fito,dogo ne mai ɗan jiki wato GIANT MAN , fuskarsa ta na ɗauke da dogon hanci ga daradaran idanuwa masu kalar sexy eyes,ga wani ƙayataccen kwantaccen saje da ya kwanta ya yi luff saman fuskar, ya sha gyara wanda ka na gani kasan ba ƙaramin kuɗi ake kashewa wurin gyara shi ba, gashin kansa ya kwanto luff ya haɗe da sajensa gwanin sha'awa, wanda ka na gani kasan tabbas ya haɗa jini da Fulani ko yaya ne. Ya na sanye da kayan Sojoji a jikinsa wanda a gaban rigarsa a wurin sa Suna a kasa CHIEF DEEN , in da yake da matsayin AIR CHIEF MARSHAL a kakin Sojojin sama. DEEN Miskili ne na bugawa a Magazine, ga shi ba ya ɗaukar raini ko kaɗan, kuma ba ya shiga harkar da ba ta sa ba, Hakan ya sa wurin aikinsu kowa yake son sa, saboda kawaici irin nasa da rashin shiga abun da ba'a saka sa a ciki ba. Ɗan asalin garin Kaduna ne Mahaifinsa ALHAJI AMINULLAH HABIBULLAH shahararren mai kuɗi ne kuma ɗan kasuwa dake zaune a cikin Unguwar Ƴan Majalissu, Matarsa ɗaya Aminatu wato Mahaifiyarsa, su biyu kaɗai Mahaifansu suka haifa shi da Ƙaninsa ZAHRADDEEN wanda a yanzu haka shi ma Soja ne amma NAVY ne shi, shekararsa 23 a duniya, DEEN ya ba ma DEEN 4YEARS kenan **OHK COME BACK TO STORY** "Ohk mi ye shawarar ka akan hakan." Marshal ya ƙara yi ma sa magana ganin in ba haka ya yi ba bawai ƙara kula su zai yi ba, saboda ya san halin ƴan kayansa. "Marshal ina ganin kawai abar min aikin nan zan ji da shi In Sha Allah." Ya faɗa da comfidense na sanin zai iya ji da aikin. Marshal sanin cewa zai iya aikin da ya fi wannan kuma ya yi nasara a kansa, saboda ya sha yin aikace-aikace masu haɗari kuma ya yi winning ya sa shi faɗin"that's good! CHIFF na san za ka iya ban da haufi a kanka, dan haka I wish you all the best." Nan kowa ya rinƙa ma sa fatan alkhairi da fatan samun nasara amma ban da mutum ɗaya daga cikin wanda suke cikin Hall ɗin. UMMAKATITI POV "Kaka dan Allah ki sha maganin nan kin ga zawon nan ya ƙi ya tsaya, idan kika sha na san zai tsaya In Sha Allah." MANGA ce take magana duk ta yi wank suku-suku. Kaka tun da abun nan wa faru ta ruɗe take ta zawo abu ya ƙi ci ya ƙi cinye wa, shi ne MANGA ta samo mata flagyl dan ta sha ko zawon zai tsaya. UMMAKATITI tun da abun ya faru ta yi sanyi na kwana biyu daga baya kuma ta ci gaba da in da ta tsaya. Yanzu haka ta tafi yawon ta gidansu Ƙawarta Luba, Abokiyar shiƙiyancinta da ita suke tsula tsiyarsu a cikin gari..... SHIN YA RAYUWARSU SU UMMAKATITI ZA TA CI GABA DA GUDANA? CHIEF DEEN YA ZA SU ƘARE IDAN YA SHIGO ƘAUYENSU UMMAKATITI DAN GUDANAR DA AIKI? YA HAƊUWAR CHIEF DEEN DA UMMAKATITI ZA TA KASANCE?. DAN JIN YADDA LABARIN SU UMMAKATITI ZAI KASANCE, SAI KOWA YA YI ƘOƘARI YA BIYA KUƊINSA DAN CI GABA DA SAMUN NEW UPDATE NA BOOK ƊIN UMMAKATITI. Follow me on Instagram: Meenart Wurma.... Tiktok: meenartwurmah.... Facebook:oum ummeeytah.... Telegram: Meenart Wurma.... Snapchat: Meenart Wurma.... ....✍️