[9/23, 9:40 AM] A A Dboy: TUNA BAYA Na Sumaiya Abdulqadeer KAUYEN KARAYE (1980) 1 A garin mu karaye, mahaifina, Malam Mamman, wanda aka fi sani da MAI KALWA, wadda ya gada tun iyaye da kakanni. Kowa ya taso a kauyen karaye, da sana'ar da ya san shi kenan. Kamilin dattijo, talaka tikis wanda bai aje ba,bai kuma ba wani ajiya ba. Mai wadatar xuci, bashi da kwadayin abin duniya ko kadan. Koda aka san shi a matsayin talaka, kowa yana girmama shi sabida mutuncin sa. Ga wanda duk ya san Maikalwa, xai shaideshi akan gudun duniya, kyamar abin hannun mutane, in ba wanda gumin sa ya amso mishi ba. Matar maikalwa, tun ta ladar noma, Indo, ita ce uwar manyan 'yan'yan sa maxa uku, akwai Auwalu, Sani da Salisu. Tun bayan haihuwar Salisu Indo bata sake haihuwa ba, sannan ya auro Lami, ta haifi Rabi'u da Atika, itama din kamar hadin baki daga kan Atika haihuwar ta tsaya mata cik. Lami 'yar babban gida ce, a garin karaye kowa ya san ubanta. Tun xuwan ta ta kame gida, Indo ta xama 'yar kallo, sai abinda tace xa'ayi, wanda ta hana, shima ya hanu. Sai kanshi Mai kalwa, shayin Lami yake, sabida masifar ta, inda Indo ta kasance, jarumar uwargida, babu abinda ya dame ta kamar harkar cikin gida tana kuma 'yan kulle-kullen omo, sugar, gishiri, barkono, kanwa, citta mai kwaya, masoro, kanumfari da sauran kayan kulli ta daurawa Sani da Salisu. Don haka duk ranar girkin Indo, Mai kalwa bai san kudin cefane ba, sai dai yaci mai kyau shi da iyalinsa, duka a aljihun jarumar uwargida Indo. Wannan ya bata wata daraja ta musamman a idon shi, da jama'ar gidan duka, har 'ya'yan Lami, suna mutunta Goggo Indo. Allah kuma ya sanya mata albarka cikin al'amuranta, har ta kai ga, Indo sai dai awo, kwano ko rabi. Ta nan ta samu ta tura 'ya'yan ta makaranta, bata ware ba, ta hada har da Rabi'u dan wajen Lami, dan shekaru takwas. 2 Tsakanin Indo, da mijinta Mallam Mamman Maikalwa, mutunta juna da darraja juna ne xiryan. Wannan ya haifar da kyakkyawar fahimtar juna a tsakanin su da 'ya'yansu duka. Don haka koda ya kawo batun kara aure, ya samu cikakken goyon baya daga Indo, da kyakkyawar addu'a daga 'ya'yan sa. A bangaren Lami, ta hana kanta xaune balle tsaye, yau gidan wannan mai rauhanai, gobe gidan wancan malami, wai a lalata xancen auren Maikalwa, da diyar Liman, yarinya Saudatu, amma da yake an ce matar mutum kabarinsa, saudatu ta tare a gidan Maikalwa, shekara na xagayowa ta haife ni, kamar mu daya da ita a komi. Na ci sunan mahaifiyar Maikalwa, kasancewar an haife ni ranar litini suke kira na 'Atine'. Gidan mu ginin kasa ne gaba da baya. Gida mafi talauci da kaskanci a layin gabadaya. Daga farko xaure xaka tadda, wanda ko rufi Allah baiyi xai samu ba, a cikin soron dakin yayan mu Auwal ne, daga katifar audugar shi, sai akwatin karfen kayan shi, da tarin littafan karatun shi, kasancewar shi mutum ne mai kwaxo a fannin karatu, sabanin Sani shi da yafi maida hankali ga bin baban mu kasuwa. Gefen dakin Auwal buhunhunan kalwa ne fiye da talatin, in har da warin kalwa yana cutarwa, da nace cikin mu babu wanda ya kawo matsayin da muke a yanxu. Faffadar tsakar gida mai dauke da katuwar bishiyar dalbejiya, wadda muke amfana daga ni'imar sanyinta, muyi wasa, muci abinci, muyi hira da Baban mu karkashinta. Galiban, anan iyayen mu suke aikin surfen, masara da dawa, anan kuma ake aunar da kayan kullin Guggon mu Indo. Turakar Malam ce ta fari daga dama, sannan dakin Guggo ciki da falo, daga hagu dakin Inna Lami ne, sannan dakin Innata, da muke kira, (Amarya). Rumfar dafa abinci na daga kudu-maso gabas din gidan, sai makewayi daga can bayan dakin Inna Lami, wanda xaka suturta kanka ta hanyar jawo langa- langa ka kare kofar. 3 Goggo Indo ita ta dauke ni a bakin nono, tun daga yaye kuwa na koma dakin ta kasancewar ita Allah bai nufe ta da haihuwar 'ya mace ba, ta dauki so, da kaunan duniya ta axa mani. Duk wani dan abin yayi idan ya taso, kamin ka gani a jikin Atika, ka ganshi a jikina. A da, ta so daukar rikon Atika, take- taken rashin kawaicin Inna ne ya tsoratata, ta kyale mata diyar ta, ita kanta Atikar ba karamar fitinanniya bace tamkar Innar ta. Maihaifiya ta Saude, diya ce ga Limamin Karaye, 'ya daya jal, da ya mallaka; ma'abociyar sani a addini ce sosai. A bokon ma tasan wani abu, domin tayi firamare. Kullum daren Allah matan anguwarmu (Limanci) take karantarwa littafan addini, daga karfe takwas xuwa goman dare. Goggo na ma, tana xama ta dauki karatu, tayi mata tambaya tamkar sauran dalibai. Babu xancen kishi a tsakanin su, ko kuma ganin kyashin juna, sai mutunta juna. Wannan ne yake kara min kaunar Guggo na a kullum. Bani da kamar ta, bani da abokon shawara sai Goggo. Mahaifiya ta tamkar kawaye muke, xamu je dakin ta ni da Atika, muyi hira, muyi dariya, mu tafi dakin Guggo, mu bata labari. Babu kunya ko kadan a tsakanina da ita irin na mutanen kauye ga 'ya'yan su na fari sai 'kawaici'. Wato duk wani al'amari da ya shafeni, baxa tayi ruwa tayi tsaki ba, wannan na Goggo ne. Tsakani na da Atika, shekaru biyu ne kwarara ta bani. Duk wata huduba da Inna kewa Atika game da mu, Atika bata dauka, asali ma kwasowa take ta gaya mani, in yi mata fadan, don me xata ke dauko hirar su da mahaifiyar ta, tana gaya mani? Sauda yawa xata ce ''uhm! Atine, kin ji Innata tace wai bakwa kaunar mu. Wai Amarya ta asirce Malam ya maiheta bora, wai Ina karama, Goggo ta xuba min shinkafar bera a koko, na kusan mutuwa, sai da anka kaini birni naga bokan turai. 4 Don haka in bar hige miki, wata rana xaku kaheni. Irin wannan tsegumi na Atika, yana da yawa, sai in yi murmushi ince, ''Atika, ba xan ce Innar ki tayi karya ba, amma da kaheki Goggo keda niyyar yi ai da baki kawo yau ba. Kwanan ki nawa a dakin ta, bata kahekin ba? Ni kuwa 'yar uwar ki ce, Uban mu daya, ina kaunar ki, ban taba tananin cutar dake ba. Abinda ke tsakanin iyayen mu, kishi ne, irin na matan sango, kada ki sake ki tsoma baki, babu ruwan ki.'' to da haka nake kashe gulmar Atika, duk da nike kasa da ita ni kaina nasan Atika ''doluwa'' ce. Na fi ta wayo da hankali, na fita kamun kai, ta fini son kwalliya, gwalli da iyayi. Don haka koda muka dan tasa samari ta ko ina ke kawo mata cafka. Gata da ingarman jiki, girma take cikin dan lokaci, girman jikin ta yafi shekarun ta kai kace hurata ake yi. A kauyen mu, Atikar gidan Maikalwa, tayi suna sosai a wurin samari, gata dai baka wuluk, amma kyakkyawa, mai ado da rangwada, Atikar Inna Lami kenan. Al'adar mu a kullum, idan mun tashi da Asubahi, bamu komawa barci, xamuyi sallah tare da baba, mu cigaba da laxumi, har xuwa ketowar alfijir. Mai girki cikin su. Ta tashi ta dama koko, ta dumama sauran tuwon dare. Idan aljihun Baba da albarka, ya aiki Ya Auwal, ya siyo mana kosai a hada da shi, ranar da babu kuwa, a sha koko,a ci dumame. Ni kuma in share tsakar gida, xaure, dakin Auwal dana Goggo na. Watarana Atika, in 'yan kirkin na kusa, ta share na Inna Lami, dana Amarya. Ta koma tabarma, ta ja filo ta mike, in ko basa kusa, da Baba ya fice kasuwa, xata koma sharar barci abinta. Son barci irin na Atika, ko kasa sai haka. In hada kwanuka, in dau guga in jawo ruwa, in dauraye su, in kada dan jangabo, in dauraye kewayen mu tas, Goggo tayi ta sa mani albarka ita da Amarya. Auwal, Sani, da Rabi'u su tafi makarantar boko, mukuma mu tafi allo. Ina goye da 'yar Innata Amarya da aka haifa mana daga baya. Haihuwar gidan mu tamkar tsari, sai dai tsari ne daga Allah, kamar bata mata kauye 5 Kauye ba, sai a haifi daya, sai bayan shekara biyar, kamin wata ta xo. Baban mu bai amince muje boko ba, amma Amarya taso muje, haka goggo, tunda ya nuna ba ra'ayin sa bane, cikin su babu wadda ta sake tada xancen. In mun dawo daga makarantar allo, sha biyun rana, muyi wanka, mu kullawa Goggo omo da sugar, in tana aiki, mu xauna mu karbi ciniki, tun Inna na hantaran Atika akan mu har ta gaji, ta saduda, ta kuma amince, ba'a raba hanta da jini. A kullum kara shaquwa da juna muke, ni da Atika, sai dai hali, kowa nasa daban. Da yamma gidan kakana Liman muke daukar karatu wurin sa, na Al'qur'ani mai tsarki da sauran littafan Arba'una Hadith, Ishmawi, bulugul-Maram, Barxanji, Sirah, Kawa'idi, da sauran su. Da daddare Atika kan je dandali, ko wasa gidajen kawayenta. Ni ko haka nake; ba kawa ba abokiya, balle aminiya. Na gwammace in xauna wurin matan aure da ke daukar karatu ga Amarya. Duk da karatun ya fi karfina, amma yau da gobe, da aka ce tafi karfin wasa, kullum kwakwalwata kara budewa ta ke a karatun addini. In wani bai shigaba, wani na shiga. Ni kaina nasan, na fi Atika ilmi nesa ba kusa ba. Duk wasu alkhairai da take samu wurn samari, baya gabana, domin ba abinda Goggona bata sai mun. Har kullum ina alfahari da Guggo Indo, matsayin uwar rikona na har abada. Bana yin sallah, in mike ban yiwa Goggo addu'ar budi da nasar rayuwa ba. A wannan watan Inna ta haifi danta namiji, aka sa masa suna Jafaru. Na rungumi rainon Jafaru, Inna Lami bata san cin Jafaru ba, balle shan sa, bata san kashin sa ba, balle fitsarin sa. Rainon ne ya xame min biyu har yaso ya rinjayi karatuna. Domin a da, ina hadda, tun bayan haihuwar Jafaru na daina sai dai bita. Ganin haka Amarya na yaye Sadiya, ta aika ta gidan Liman. Ni kuma naji dana Jafaru da karatuna, don ta lura XAN IYA BARIN KOMI IN DAI A KAN RAINO NE. [9/23, 9:40 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [9/24, 9:09 AM] A A Dboy: Tuna Baya 6 ina son kananan yara, ina matukar kaunar, in ganni goye da jariri, ina jijjiga shi, ina yi masa rawa, ina cilla shi ina jefawa, yana bangala mani dariya 'kauna' irin ta uwa. Don haka inda duk xan shiga a kauyen Karaye, an san da goyon Jafaru ko Sadiya xa'a ganni. Ko da aka kai Sadiya wurin Luba kakar mu, kullum kafata bata rabo da hanyar gidan Liman, ina goye da Jafaru dan shekaru biyu. Malam yayi ta tsokana ta da Uwar Biyu. Ina jin dadin sunan, ina farin ciki a ce ni UWA CE. A ganina, wanda duka Allah ya baiwa Da yayi masa babbar kyauta, wadda wani ko wata, ba xai iya bashi ba. Haihuwa ai kyauta ce daga Allah, don haka abin alfaharin kowacce mace ne Tefe muke ni da Atika a gefen kwalbati, ina goye da Jafaru, Atika dauke da kwarya a kanta cike da kalwa. Baba ne ya aike mu gidan wani mutum da ya bashi kudin a kasuwa, ta kare yace xai aiko mai da ita gida. Atika ta dube ni, ta girgixa kai cike da takaici tace ''Atine, shin wai ke bayan ki bai gajiya da goyon yara?'' Nayi murmushi nace ''amsar ki kenan'' tace ''wallahi ki rika aje Jafaru hakanan, ya girma, shekarun shi fa biyu, an yaye shi tuni yana gudun shi ko ina, tukunna ma, baki tsoron kirjin ki ya bude?'' ''To idan ma ya bude Atika menene? XAN IYA JURE KOMI IN DAI AKAN RAINO NE''. Atika tayi tsaki ''Allah wadaran wahalalle wallahi, ina kuwa xaki yi saurayi? Kullum sungume da yaro kina tafe sukutuf, babu dan karya kugu? Ki diba ki gani, ni kullum xance, har layi ake, kudi, sutura, kayan kwalliya, babu wanda samari basa bani. Amma ke ko 'yar murtala, bana ce kin taba karba daga hannun saurayi ba''. Nayi murmushi ''kudi, sutura, kayan kwalliya, don su xaka kula saurayi Atika? To ladan RAINO fa? Saurayi yana bayarwa? In gaya maki gaskiya ta Atika, burina ba samari bane, KARATU NA BOKO irin makarantar su Ya Auwal, in karanta raino, RAINO NA KANANAN YARA''. Atika ta tuntsire da dariya har tana hawaye, irin taga mahaukaci sabon kamu tace 7 ''Koda naji ana karatun boko, ban taba jin wani KARATUN RAINO ba. Kai Atine, kin bani dariya, wai ma ina kika jiyi wani karatun raino?'' ''Ban taba ji ba Atika, amma nasan abinda na fada, ba abin dariya bane, don Allah ni mu bar wannan xancen ma, wai ina ne gidan Malam Ladan din?'' Daidai lokacin da muka karaso dakalin gidan Waxiri, samari ne xaxxaune, sun kewaye dan waxirin Karaye, suna bashi labaru yana tuntsura dariya yana xukar sigari cikin annashuwa, yana bulbular hayaki. Samarin suka yi tsit, da hirar da suke, suka xubo mana ido, Atika har da canxa tafiya, jin ana kallon ta, kuma samarin gidan waxiri masu ji da kansu, ni ko sai na kara sauri. Mun yi dan nisa kadan muka ji alamar taku a bayan mu, daidai lokacin da muka iso kofar gidan Malam Ladan, daya daga cikin samarin yace ''ku, ji mana?'' Ba mu juyo ba sai kara sauri, ''ko baku ji ba, su waye ku a layin nan da xaku hurawa Yallabai hanci?'' Na dubi Atika xata yi magana nayi mata alamar tayi shiru, muka sa kai xauren gidan. Ji nayi an finciko Jafar dake baya na, ya fadi kasa tim, ya tsandara kara mai firgitarwa. Muka juyo gaba daya, samari ne guda uku, baki gajere, wankan tarwada dan tsamirmiri, fari dogo siriri, da alama shine dan Waxiri, da muke jin labari dan birni, domin har wani farin kara da wuta a jiki, ke makale bisa bakaken labban sa. Ya kashe ido, ya daga kakkaurar girar shi sama ya dubi abokinsa dan tsamirmirin, tsamirmirin ya dube ni, yana wani fizga, magana yake kaman baya so. ''Ku 'ya'yan Maikalwa, Kalwa ta daddawa, kayan wari kayan tsiya, Yallabai Bello ke son magana da ke, kina wani xubga sauri tsilli- tsilli da kafafu kamar maburgin kada kuka. Ko ance muku Kalwar xamu kwace, mun yi miki kama da masu cin daddawa ne?'' 8. Gajeren ya karbe ''kai Sambo ai wannan mai kafar maburgin, da wuya uwa marikin leman, jin kanta take kamar diyar Sarkin Santanbul, ba 'yar matsiyacin nan Maikalwa ba. To ki ji ki nutsu, kin san da wa kike tsaye, tun bamu kifar da jarin Kalwar ba''. Na tsugunna na dauke Jafaru, na maida bayana, nasa xani na kulle shi, na dago ido na dubi dan tsamirmirin, kana bakin, sannan uban gayyar nace '' kada ka kara xagar mana Maikalwa, tunda ko ba komi, ya haifi wadanda suka taso ku daga maxaunin ku. Kai kuma mai ce mun kafar maburgi, ni kuma sai naga ta yallabai din naka ce ta dace a kirata 'muciya', nasa wuyan kuwa, ai da Kalwar da kake ambato yafi kama, mu je Atika''. Suka dubi juna da sauri. Ogan nasu yasa hannu ya daga kwaryar da ke kan Atika, gabadaya ya juye mun Kalwar a ka nida Jafar muka yi futuk, muryar sa daban ce da tasu, mai taushi kuma cike da gadaran Sarauta yace ''Ke kin san BELLO WAZIRI?'' Na murguda baki nace ''a'ah! Na dai san, Wazirin Karayen, wani fari dan sololo, farin gashin-bakin sa na tadda lalaceccen bakinsa da goro yayi wa kanta. Yana tafe a duke, kamar wanda Inna ta shanyewa doron baya. Idan yana gaban Maimartaba a fada, kamar tsohon da yayiwa sarki karya. Shi din ne, koko akwai wani wazirin bayan shi?'' Yayi murmushi tamkar maganar bata soke shi ba, yace ''wannan Maikalwa kike nufi, wani matsiyaci cikin garin karaye, wanda matar sa ke ci da gidan sa, idan Maimartaba yayi kiran amsar zakka shine na farkon xuwa, ki ji shi duk ya cika fada da warin KALWA, wanda duk ya shigo, sai ya koma, inda duk yayi, warin Kalwa yake, haka 'ya'yan sa, matansa da surukansa. Don yanxu haka jama'a sun rage xuwa masallacin Juma'a sabida Liman, cika su yake da warin Kalwa''. Na dubi Atika wadda tayi suman tsaye idanu na suka ciko da kwallah, ta kama hannu na muka fito faga soron. Suka kuwa biyo mu har kofar gidan mu da xagin cin mutunci, dai-dai da xamu shige gida, yasa hannu ya riko goyon Jafaru, na wani irin juyo 9. Don kar ya kara kwala shi da kasa gaba daya suka sa dariya, amma shi murmushi yayi, ya dube ni a lalace yace ''na baki assignment, mai kafa kamar MABURGI, ki je ki binciko, shin waye, BELLO WAZIRI KARAYE?'' Magana yake cikin gwalli da kwalisa, da wani irin tattausan hausa da ban taba ji ba. Ya sakar min goyon ya juya, 'yan koren shi suka mara mai baya. Sai a lokacin na samu damar kallon sittiran dake jikin shi. Yadi ne da ake kira shadda, ruwan kasa tirarre, ya sha aiki surfani na Saraki gaba da baya, da xare ruwan kasa-kasa. Wani abun birgewa ma, takalmin shi rabin sau ciki, da duk Karaye babu mai sashi sai Saraki, shima ruwan kasar ne. Wannan ba shine a gaba na ba, (wata xuciyar tace dani), abinda xamu cewa Baban mu, game da aiken da yayi mana. Ban iya karya ba, xan fadi wa Baba, dan gidan Waziri ne ya xage mu ya kifar. Dakin Amarya muka xarce, Atika mayafi a hannu, tana ta kwalawa Goggo ta Amarya kira, na sauke Jafaru wurin Inna dake bare gyadar miya a karkashin dalbejiya, ko kamin in karisa ciki, ina jiyo Atika har ta kai tsakiyar labari, na karasa ciki na samu gefen Guggona na xauna, nayi shiru, Guggo tace ''ke Atine, ina ke ina fada da Bello, babban dan Waziri da kowa ke ganin mutuncin sa a garin nan, yaro mai halin dattaku da girmama na gaba, shekaran jiya daya dawo daga birni, can inda yake karatu, ya kawowa Baban ku zakka har gida ya kuma dauko shi daga kasuwa a busukurin shi, me ya kaiki xagin shi? Da yace ku tsaya ku ji, koma mene ne don martabar gidan su ai kun sauraresu, wannan jin kan naki bansan inda kika samo shi ba, meye da mu? Mu su waye? Ki iya talaucin mahaifin ku kada ki jawo mana wulakanci a garin nan, in kinga Bello ko a ina ne, ki tsugunna ki bashi hakuri kin ji na gaya maki. Idan Baban ku ya ji wannan rashin hankalin naki, Allah kadai xe raba ku''. Cike da mamaki da takaicin Atika nace ''Goggo, Atika bata gaya muku gaskiya ba, wallahi xagin Baban mu yayi tayi, ya kifar mana da Kalwa, ya balle min goyo, yace wai kafana kamar maburgi, 10. Wallahi kinji na rantse, yace wai waye uban mu, Maikalwa? Wallahi ba wanda ya isa ya xagi Babana in kyale shi, ai talauci ba hauka bane''. Amarya tace ''babu yadda xa'ayi yaron nan ya xagi Baban ku, ko bai sanku ba, balle kuma ya san ku, an ce Maikalwan,ba Maikalwar bane, an ce miki mai kafar maburgin, ko ba tsigigiyar bace? An kuma ce waye uban ku? Wanda duk yace xai ja da Saraki, ai kuwa sun tambaye shi waye Ubansa?'' Na mike ina kumburi nace '' Allah banda ni, babu wanda xai xagi Babana akan ido na inyi shiru in kyaleshi,ko Wazirinne, balle wata tsiya,Bello, don kuwa Babana, na tabbata bai taba xuwa roko wajen su ba''. Goggo tace gaskiyar ki Atine, nima ina bayan ki, ku kare mutuncin talaucin ku a ko ina, mulki da abin duniya duka Allah ke badawa,babu kuma wanda yayi mai rawa ya bashi. Jeki dauraye jikin ki duk kin cika mu da doyi, akwai wata Kalwar xan daurawa Rabi'u ya kaiwa Malam Ladan din''. Kwana biyu ina juya maganar Bello a raina, na kasa mantawa, nayi-nayi in mance na kasa. Ba wai ciwon abinda yayi mana ke damuna ba, don kuwa nima na rama, na kuma tabbata yaji ciwon sharewa yayi. A xahiri ni karamar yarinya ce, shekaruna basu fi 13 ba, ko kirgen dangi irin na Atika ban soma ba. Don haka baxan ce son Bello nake ba, amma ya dame ni, kyawun surar shi da cikan kamalar shi abin so ne ga kowa. Ba ga surar shi kadai ba ma, yanayin shi ma abin so ne, tsari da xubin halittar shi abin burgewa ne,balle ga mu kauyawa. Ban taba ganin shi ba sai ranar, sai de nasha jin labarin shi da irin karamcin shi. Dana ganshi se naga ashe yafi yadda ake tsammanin shi. Wato dai ganinsa yafi jin sa. Na kuma fahimci ashe macijin sari ka noke ne; bashi da mutunci ga wanda bai sanshi ba,ga wanda yasan shi, shi mai masifar mutunci ne. Kenan idan har ina son sanin hakikanin wanene shi, kamar yadda xuciyata ta nace da son sani, dole ne in binciko tambayar shi ta shin waye BELLO WAZIRI KARAYE? To a ina xan bincikan? Oho! Motsin dawowar Auwal naji a xaure,na bashi lokaci na tabbata ya gama duk abina ya saba,naje rumbu na fiddo masa abincin ranar sa, gudun kurna ne muka yi da miyar taushe. [9/24, 9:09 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [9/24, 9:10 AM] A A Dboy: Tuna Baya 11. Nayi sallama ya amsa, yana xaune bisa kwayar tabarmar karaunin da ke dakin, a hannun shi littafin boko ne yana ta rubuce- rubuce, na aje akushin na xauna gefen sa nace ''sannu da aiki yaya, rubutu kake tayi, kullum baka gajiya da rubutun nan dai'' ya aje biron yayi murmushi yace assignment aka ba mu nake ta kokari, wallahi naso ace Baba ya yarda an sa ku makarantar boko, babu abinda yafi ilimin xamani dadi Atine, xaki rubuta, xa'a rubuta miki bayani ki fahimta kamar da baki ne ake gaya miki...'' Auwal xuba yake, a yayin da ya fahimci ido nake binsa dashi kurum, amma xuciya ta bata tare da shi, tana ga wani dan matsakaicin hoto cikin firem da ke aje can gefe, Bello ne, rungume da yayan mu Sani, suna sanye da kayan kwallo na Manchester United kungiyar kwallon kafa da Sani ke masifar so, kullum ya dawo kasuwa, kallon kwallo yake tafiya can bayan gari, sai da yasan yadda yayi ya takurawa Goggo ta bashi kudi, ya kukkulla da taimakon abokai ya sayi irin kayan su. Hankali na ya dawo ga kalmar dana ji Auwal ya ambata yanxun nan wato assignment, tabbas naso naji ta a bakin Bello, ranar da ya xage ni, ban san ma'anar ta ba, illa xuciyata ta fassara ta yadda taga dama. Nace ''Yaya menene assignment?'' Assignment aikin gida kenan, kamar wani aiki da xa'a baki ace kije gida kiyi a nutse, a karbi sakamakon washegari, kin gane koh?'' Na maida ido daga kan hoton nace na gane, yace wannan na hoton naga baki san shi ba? Bello kenan dan gidan Wazirin Karaye Ai yaron, yana da mutunci sosai, ga son mutane, ga faran-faran, ga ilimi, Bello zakka ne a Karaye baki daya''. Nayi xugum, a raina nace ''ikon Allah! Mutumin dake xage talaka, ya ci mutuncin iyayen su, shine kowa ke so? Inda ranka kaga da yawa, wannan kadai ya isar mani tambayar wanene Bello Waziri? Amsar da kowa xai bani kenan. Sati biyu suka shude ban ji labarin dan gidan Waxiri ba. Xuciyata, cike take da begen sake ganin wannan kasaitacciyar fuskar rashin mutunci. 12. Yau Goggo ta tashi da rashin lfy jikin babu dadi tun da safe, Inna kuwa sabgar ta take ba abinda ya dame ta da ciwon Guggo, tana girki tana 'yan wanke-wankenta irin na wanda gida yayiwa dadi. Da daddare wurin karfe takwas, garin Karaye, hadari yai holoko, sama tayi fari fat da kwantaccen hadari, sai iska da tsawa gami da cida ke kadawa kunnuwan 'yan adam ganga. Wannan bai hanani sulalewa in fice gidan kakana Liman ba, wai in amso addu'o'in da ya ce inxo in amsa bayan sallar isha'i in yiwa Guggo na, daren Juma'a ne ana yin dace da samun karbuwar addu'a. Tafe nake faram-faram, iska na kada ni inda duk ta ga dama, dama gani jiki kamar sillen kara, siririya ce ni sirit kamar haihuwar bakwaini, koda yake Guggo ta ce a BAKWAINI aka haife ni. Fuskata ma siririya ce, doguwa, mai dauke da siririn dogon karan hanci kamar shape din karas, wadatattun manyan idanu, kullum yanayin su kamar na mai jin barci, xubin su kamar kwan kaxar hausa, a takaice, komai nawa siriri ne maras kauri irin na Inna na, Amarya. Jin taku nayi a baya na, ga layin ba kowa, hasken farin wata da hadarin yasa ina gano inuwar, dogon mutumin da ke bina, kamar mai gadi na. Na kara sauri akan nawa na da. Iska ta yaye dan yalolon gyalen da nike yafe dashi, ban tsaya ba, sai na kara da sauri- sauri gudu-gudu, shima dankwalin yayewa yayi, ina ganin in na tsaya bin shi nima iskar dauke ni xatayi. Bakin tufkakken gashi na ya shiga fidda sheki da kyalli cikin hasken farin watan. Sai na daura dukkan hannuwa na na a ka, wai in suturta kan. Kakkaurar murya, wadda na tabbata duk Karaye, mutum daya ne mamallakinta, dai- dai sanda na kai kofar gidan Liman ita ke kiran ''A-ti-ne''. Nayi hanxarin juyowa, Bello ne, ban ce komai ba, illa na ja na tsaya, sai na tuna bani da ko mayafi balle kallabi. Na shige gidan da sauri na daga Asabarin Luba, duk a tsorace nake, Luba tayi salati tace ''Ke lafiya, ba dai Indo ta rasu ba?'' 13. Nayi ajiyar xuciya mai karfi ''a'ah Inna Luba! Iska ce ta dauke mayafin, ta dauke dankwalin, nima saura kadan ta dauke ni. Ga kuma wannan dogon mutumin, wa ma yake da suna? Dan gidan Waziri yana bina, muryar shi abun tsoro ce, tace ''Atine xauna nan,'' na xauna, tace'' ki nutsu nasan halin ki kinji? Ki saurari Bello dan gidan Waziri yaron kirki ne, ba xai cutar da ke ba, Baban ki da Malam xasu ji dadi idan baki wulakanta shi ba. Ba yarinyar da Bello ya taba cewa yana so, duk fadin Karaye, haka duk dangin su, Maimartaba ma ya bashi diyar shi yace baya so, idan kika samu ya so ki, Allah ya taimake ki, mutum ne mai ilmi sosai, Atine na, kinji?'' Inna baki san wannan ba, shine ya xagi Baban mu, ya....'' ''ni ba wani abu nace ba, kurum cewa nayi ki saurare shi, ki ji me xai ce da ke?'' shikenan Inna, Malam ya kwanta ne?'' ''ya jira ki tun daxu baki xo ba, ya bawa Sani ya baki, nake jin mantawa yayi (Sanin). Ta bani mayafi na yafa na fita. Har yanxu yana tsaye jikin dakalin gida, sai naji tausayin shi, ni mutum ce mai tsananin tausayi don ko kiyashi bani iya kashewa da gangan balle in wulakanta mutum. Sanye yake da wata irin jibgegiyar rigar ruwa ta kare jiki daga dukan ruwan sama, sai kyalli take kamar leda a cikin hasken hadarin. Ya harde hannuwan shi bisa kirjin shi, ya kurawa hadarin ido kamar mai son karanto wani boyayyen al'amari a cikin sa. Jin motsin fitowa na yayi saurin sauke kai. Biyo ni kurum yayi bai ce komai ba, kaxalika nima. Hadari ya gama gangamowa, sai yayyafi ya soma sauka yaf-yaf a jikin mu, da kan rumfunan kwanon dake layin karar babu dadin ji. Na dukunkune hannuwa na cikin tsananin raxana, alamun tsoro, xane baro- baro cikin idanu na masu haske. Da ni kadai ce xurawa xanyi da gudu, shiko ko a jikin sa yace ''Atine, bakya magana, baki gaida na gaba da ke, why? Na lura in xa'a kwana ana tafe dake baxaki magana ba'' nayi shiru, ya sake cewa ''Atine bakya gudun ruwan nan ya taba min lafiyar ki? 14. Nayi hanxarin dago ido na dube shi ta wutsiyar ido, kallo na yake da idanuwan shi masu kwarjini, wani abu na ji ya tsirga har kwalkwalwata. Ban ankara ba naji yana rufa min wani abu mai dumi. Suman tafe nayi, shidewar wucin gadin raxana. Sai da na dawo dai-dai na fahimci, jibgegiyar rigar turawan ce cikin jikina, ni Atine Mamman Maikalwa. In banda wani irin lallausan kamshi, ba abinda ke tashi cikin rigar. Dai- dai sanda muka kawo kofar gidan mu ruwan ya jike shi sharkaf, amma bai ko damu ba. Na mika hannu na xare mishi rigar shi, hannun shi na dama yasa ya danne nawan yace ''No, ajiya ne na baki Atine, xan karbi kayana idan na dawo. In an tambayeki thickcoat na wanene, me xaki ce, Atine?'' Iyakar rudewa na gama rudewa, fitsari ya cika min mara fam, na sunkuyar da kai jikina na kyarma yayi hamxarin dauke hannun shi a nawa da sauri yace ''Atine, xan tafi, tunda baxan samu alfarmar kalma ko daya a bakin ki ba. Shin kin nemo amsar tambaya na na kwanaki? Da nace ki binciki wanene Bello Waxiri? Na san kin binciko amma amsar tayi miki sabani da tunanin ki?'' Yayi murmushi, duk da bashi nake kallo ba, tafin kafata na kura ma ido, na ji sautin murmushinsa a hankali, a xuciyata ina gasgata xancensa, kwarai naji sabanin abinda nayi tsammani, amma hakan baya nufin na yarda, tunda ni ban ga haka akan kaina ba. Ba kuma tare da ya kuma neman jin komi daga gareni ba ya cigaba da cewa '' yau ma ga new assignment, kije ki binciko, menene yasa Bello Waxiri ya sa maki rigar shi? Abinda bai taba yiwa wata yarinya a garin Karaye ba? Menene yasa kika kasa duban idon Bello Waxiri ko kadan, sabanin kwanakin baya da kika gaya mai magana son ranki? Atine, na barki da wannan, sai da safe''. Nafi mintuna biyar tsaye a wurin kamar an kafe ni, kamin in dawo hayyaci na na shiga gida, su Atika tuni sunyi barci Baba ne dai nike jiyo sukurniyar shi a turakar shi. Na xare riga a hankali, na janyo aci bal-bal na kyasta ashana, haske ya gauraye dakin. Na dubi riga da kyau,ta hadu ta burgeni iyaka, Ban taba gani riga mai kyawun ta ba. Wannan kamshi, ni'ima ne ga ma'abocin shi. 15. Na samu kaina da rufa riga a kaina ina shakar kamshinta ina murmushi a hankali. Wai shi wannan bai san ni yarinya bace, ya cika minni kwakwalwa da naganganun da suka fi karfin hankalina? Ni nasan wani dalilin sanya mani riga? Ba ruwa ake ba ya taimake ni? Wanda kuma duk ya taimaki wani ai Allah xai taimake shi shima. Ya hada yatsun mu, don kar in ciro riga mana ina na san wani dalili bayan wannan? To amma ni kaina nasan yau na ji ni cikin wani bakon nishadi, ga farin ciki ya baibayeni kamar ance min Goggo na ta warke sumul. Na linke riga na janyo wata tsohuwar akwatin Amarya na tura, na rufe na mayar. Washegari Atika kallo na take kaman taga aljana tace ''Atine, jikin ki kamshin Aljannah yake, shin ko kin ga Annabi a barci ne da Malam yace mana ana gani, in anyi dace? Na yi dariya na bi ta da ''eh''. Yammacin ranar mun yi ciniki mai tarin yawa, na hada kudi na baiwa Baba, ya tafi Kano. Washegari da safe nayi wanka na saka atamfata mai dan dan, print ce ruwan bula, ni bana kwalliya sam, ko vaseline in ba lokacin sanyi ba bana shafawa, na goya Jafaru nasa kibiya ina tsefe kaina ina tajewa. Sani ya shigo, baki har kunne, a duk sanda ya xo min irin haka nasan ya ciyo kudin wani karikicen abokinsa ne, wai xai hada mu, na tsuke duska kuwa iyaka. Ya samu jijiyar bishiyar dalbejiyar da nake xaune karkashinta ya xauna jikin sa har rawa yake ''wai ke Atine, baki gajiya da tsifar kai?'' Nace ''unh!'' ya lankwashe kai yace ''shin kinsan Bello, Yallabai Bello dan gidan Waxiri?'' Nan ma nace ''unh'' na sake tsukewa, sani ya dabarbarce, yama rasa ta inda xai faro, da gani ba kudi yaci ba yau mutuncin ya gani, ya kare kwane-kwanen sa yace ''kije yana kiranki, Baba yasan da xuwansa, ya kuma ce na gaya miki muddin yaji wannan dabbancin naki, sai na kabari ya fiki walawa''.Ya haura takalman sa ya mike nace '' in dai rigarsa ce da ya ara min,ban roka ba balle a biyo ni har gida a ci mun mutunci, tana nan bari na dauko maka'' Sani ya fice ko saurareni bai yi ba. [9/24, 9:10 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [9/24, 9:10 AM] A A Dboy: Tuna Baya 16 to 20 16. Yi ba. Murna kaman in yi tsalle. Ni kaina nasan, na kamu da son mutumin da ba tsara na bane ta fannin komi, amma Allah shaida na ne kan bani na daurawa kaina ba. Surutu ne nasan xa'ayi shi a garin Karaye har a gode Allah, oho, xa su gaji su bari ne. Tun daga xaure nake jiyo kamshin, ina gaba yana kara dosa ta. Dan farin wankakken hijabi ne a kaina hannayena rungume da riga, na hange shi da 'yan iskan abokan sa, dan tsamirmirin nan da dan gajeren. Sanye yake da karamar riga da dogon bakin wando mai kauri na 'yan birni, kykyawar fuskar shi tayi kyau a cikin hantsin kamar kullum. Na kara cuske fuska, a nutse na gaida su fuskata ba anuuri, ita kanta gaisuwar ba din gargadin da Sani yai min ba da baxan yi ba. Dan tsamirmirin ne yace ''ranki ya dade, Uwar gajiyar mu, Yallabiyar mu tuba muke'' Ba tare da wata magana ba na mika mai riga nace ''ga rigar ku'' sukayi murmushi a tare yace ''bar xancen riga tukunna, nace miki mun xo tuba ne...'' nace ''da kukayi wacce shirka? Ai ku saraki ne, masu mulki, din haja ko mi kuka yiwa talaka a hanyar garin Karaye, baku yi laihi ba, tunda garin ku ne to amma nan cikin gidan Maikalwa, Kalwa ta daddawane, mallakin sa ne da ya gada tun iyaye da kakanni, babu wanda ya bashi cikin masu mulkin Karaye. Don haka ba wanda ya isa ya xage shi anan mu kyale. Ga rigar ku nace'' na dangwarar ta anan na juya abina. Sai bayan dana dawo na shiga tambayar kaina ''maiyasa nayi haka?'' don me ban saurare su na ji uxurin su ba, ko Ubangiji muna yi mai laifi, mu rokesa gafara ya gafarta mana, balle ni wata tsiya 'Atine'. Koda yake na nuna martabar Baba na, mai girma ce a gare ni. Sai dai ina wahalar da kaina ne a banxa; son Bello nake, son shi ke wahalar da ni a 'yan kwanakin nan. Kwanan Baba uku kamin ya dawo har hankulan mu sun tashi, ya dawo cike da farin cikin raina yayi fari kal don na tabbata Goggo da samu sauki kenan. Da yamma Baba ya kirani dakin shi,munyi hirarraki da dama game da lafiyar Goggo kamin ya gangaro maganar da ban tsammana ba, 17. Yace ''Atine naji dadi kwarai da kuka shirya da yaron nan dan gidan Waxiri, domin yaron mutunci ne, dan babban gida mai ilmin da duk fadin garin babu saurayi mai ilmin sa, wanda in banda ikon Allah, ba abinda xai yi dake, idan kika yi la'akari da matsayin mu na talakawa likis, wadanda basu aje ba, basu ba wani ajiya ba. A cikin rufin asirin Allah muke daura tukunya bisa murhu, mu daura sittira dai-dai karfin mu. Allah ya bamu wadatar xuci kuma kowa ya sani, bamu kwadayi, balle ace kwadayin mu ne ya hada mu da su Waxiri. A jiya yaron nan ya je Kano, ya biya duk basussukan da ke kanmu, ya sayi magungunan da muka kasa saye, ya canjawa Guggon ku asibiti xuwa na larabawa masu mutunci da sanin hakkin bil adama. Ya sayawa Guggon ku duk abinciccikan da likita ya bukata ta ci wanda ni a rayuwata ban taba jin su ba ma, ya kuma yi umurni ga wata 'yar uwarshi da ke karatu can Kanon kullum ta dafo abinci safe, rana da dare ta kawo mana. Su xauna muyi hira su xaga da mu gari, yau dinnan Waxiri da kansa ya je ya duba Guggon ku, tare ma muka dawo a motar dan Maimartaba, nan da kwana biyu xa'a sallami Guggon ku. To mutanen da suka yi maka wannan karimci akan suna son naka, basu kyamace ka ba duk da yadda Allah yayi ka, ai bai dace kaki amsar bukatar su ba da take ta alheri a gareka. Don haka na gaya masu tuni na basu ke, duk sanda suka shirya su fito ayi aure, waccan solobiyon ma in ta gama ruwan idon ta fiddo daya daga cikin tarin samarin da take tara min a kofar gida, a hada ku lokaci daya''. Shiru nayi kaina a duke, nayi mutuwar xaune, ina sauraron Babana cikin abinda nake ji kamar a mafarki ko kuwa (almara); an bada ni ga Bello Waxiri? Abin ma abin tsoro, bayan duk wulakancin da nayi masa? Shine ya biyo Babana da siyasa irin tasa ya aure ni, ya rama duk wulakancin da nayi musu kenan. Hawaye suka cika min ido taf. Buri na na karatun RAINO ya karye ban cimmasa ba. Buri na na xuwa makarantar boko yaci ruwa shima. Auren wuri, abinda naki jini a rayuwa ta. To amma me? 18. Da wanda na tabbatar ruhi, kalbi, tsoka da gangar jikina duka suna mutuwar so da kauna; Bello Waxiri. Daya da daya a maxan Karaye baki daya. Wanda yayi ilmi, mawuyaci ne ya hana matar shi yin ilmi. Na tabbata haduwar mu da Bello kaddara daga Allah! Ita kanta haduwar, bata dadi bace, babu wata kalmar arxiki da ta taba hadamu balle kalmar SO, amma gashi har manya sun shigo cikin maganar. Na tabbata ina son Bello, amma ina shakkar kaunar sa gareni. Idan na tuna farkon haduwar mu kafana kamar maburgi yace, to mai xai yi dani, in ba yaudara bane? Yanxu yadda Baba na ya gama saki da al'amarin su Waxiri, wani bayani xan mai ya gamsu? Bama wannan ba, in nayi hakan nayi butulci wa alkhairin da sukayi wa Babana, suka maishe shi mutum mai darajah cikin su har suka damu da ciwon Guggon mu, wadda bani da kamarta duk fadin duniya, Guggo na fa, Guggo na ka taimaka fa....''. Na dubi Baba da yayi shiru yana karantar yanayi na. Kallo daya xaka yi mishi ka fahimci cike yake da tsoron rashin amincewata. Ni kam koma da wani nufi Bello xai aure ni, na amince domin Babana, darajja Babana da Waxiri yayi. Su basu kyamace mu ba, me xan yiwa kyama tattare da Bello Waxiri? Baba ya fiddo ido kadan yace ''Uwata Atine, kada ki bada min kasa a ido, kada ki mayar dani karamin mutum a idon mutanen da suka darajjani, suka martaba ni, suka girmama ni ta hanyar da wani dan adam bai taba yimin ba...'' sai hawaye. Na rarrafa ga Babana, nayi murmushi, idona cike taf da kwallah, ''na amince Baba, dama ina son Bello, ina dai jiye mana wulakancin gidan sarauta ne, tunda mu bamu da komi, ba wasu bane face talakawan gari''. Baba yayi murmushi. Bana gini ban duba filin wurin ba, Atine, baxaki wulakanta a gidan Waxiri ba, in dai kin kasance mai; -Gaskiya -Amana -Hakuri -Juriya -Kawaici -Gudun duniya da kyamar abin hannun mutane. 19. Ki xama mai bayarwa ba mai karba ba, wannan shine babban makami na xama da kowace irin al'umma, a ko'ina, komi mulkinta. Talaka kan xamo wani abu, idan yayi riko da wadanna makamai. Mai mulki kan kaskanta, idan ya rasa wadannna makamai har a darajja talakan da bashi da komi fiye dashi.'' kaina a sadde nace ''Na amince Baba, In shaa Allah xan gina tubalan rayuwata ne akan kalaman ka, ko babu komai, baxan taba tabewa ba na tabbata idan na bi ka''. Allah yayi maki albarka Atine, Allah ya daukaka ki da daukaka ta buwayar sa'' ''Ameen Baba''. *********** Shara nake yi, ji nayi an xungure ni, dagowar nan da xanyi sai na yi arba da Goggo na, tsaye da kafafunta, na rude na kidime na yada tsintsiya na ruga na rungume Guggo su Amarya suna ta dariya ta. Na dubi Guggo duk ta rame, da alamar har yanxu jikin ta da saura, na kama Guggo na xuwa daki har har gadon bunun ta. Hira ta kaure a dakin na labarin asibitin da aka mayar da Goggo, wai bandakin har da wani inji makale da xaka danna sabulu mai kamshi da laushi ya xubo, a wunin ranar xungur, hirar kenan. Baba ya shigo da sandunan rake na raba na ba Goggo tace baxa ta sha ba wai ita likita ya hanata shan abu mai xaki. Muna xaxxaune muna shan rake sai ga almajirai suna shigo da kwalaye muka bisu da ido; kowa yayi shiru sai da suka kare Auwal yace ''shin daga ina aka aiko ku ne Tanimu?'' ''Yallabai Bellon gidan Waxiri ne, yace wai a kawowa mara lafiya, da yamma xai shigo ya dubata in ba damuwa'' ya fiddo wata jaka fara tas, shake da kaya yace ''wai wannan na Atine ne''. Baba ya mike yace yana ina? Ba xa'a karbi kayan Atine ba, amma na mara lafiya an gode. Abinda yayi ma kadai ya isa, Allah ne kadai xai biya shi, don haka ku maida wannan''. Sani yace ''haba Baba! Bellon dan wa yake wa Goggo wahala, ba don Atinen ba? Ba kuma a mayas da hannun kyauta baya''. Baba ya murmusa yace ''Sani, tunda nace a mayas, to a mayas''. 20. Sani ya san Baban mu sarai, mutum ne mai kaifin basira, tabbas akwai abinda ya hango. Shi da kansa ya dauki jakar ya nufi dandalin hirar su, aka sanar da shi Bello ya je kiran Maimartaba, can ya xauna jiran shi. Inna ta saki baki tana kallon ikon Allah, Auwal na bude kwalaye yana yiwa Baba bayanin locozade ne maras lafiya ke sha don maida kuxari, katon na madara peak da katon din milo kayan shayi ne, Heinz-beans wake ne na gongoni. Wannan mai kwaya kwayan na cikin kwali sukari ne, shi kuma wannan tang na kwalba lemu ne irin lamurje, ake xuba suga da ruwa a sha. Wannan na xungura-xunguran gongoni dankalin turawa ne aka sarrafa haka, sai magungunan Guggo da likita ya rubuta da xa'a sallame ta. Baba bai ce komi ba, sai ma cewa yayi a hada su yadda suke akai karkashin gadon sa, in aure Allah bai yi nufin sa ba, ina xamu nemo su? Ni kam kaina a duke yake, tsoro da fargaba sun cika ni, ji na nake kamar wata bare a cikin su, kamar kuma wadda ta aikata wani gagarumin laifi. Ina ganin sanda Inna ta kyafta ma Atika ido suka mike suka shiga daki, Baba da Auwal suka nufi masallaci don bin jam'in sallar Magriba. Nima na mike na xubawa Amarya ruwan alwala ita da Goggo, nayi alwala nayi sallah na kara nemawa Goggo sauki wurin Ubangiji, na kuma roke Shi, idan tarayyar mu da Bello akwai alkhairi a ciki, ya cire min masifar tsoron shi da ke gallaba na, ya tsayar min da hankali na wuri guda. Har muka yi Isha, shiru ban ga Atika ba,Amarya ta kare tuwon dawa da miyan xogale ta kira ni in kaiwa Inna, in kuma kira Atika mu ci.Nayi sallama ba'a amsa ba, suna can kuryar daki inda na jiyo sheshshekar kukan Atika, sai muryar Inna kasa-kasa ''kiyi shiru abinki, Atika na kibar asarar hawayen ki a banxa da wofi, su aureshin in gani, ai ba tun yau ba nake gaya miki mutanen nan basu kaunar xaman mu a gidan nan amma kinyi sautun mahaukaciya dani,kin nace a gindin su, ke kenan Atine sama Atine kaxa ke mai 'yar uwa,ai gashi nan ta nuna miki karshen 'yan uwantaka tayi ma kanta miji mai ido [9/24, 9:11 AM] A A Dboy: Tuna Baya 21 to 25 21. Ko bakya sonshi tunda naji xancen ke xaki aure shi, wannan shegiyar afiruwar a gidan saraki? Kirji kaman danmalele, kugu uwa an tatsile kuliya bisa kwalta, ke kuma a gidan manomi, waye Jibo? Ai baxa ta sabu ba. In dai akwai boka, Mallam da bori a duniya BELLO BAXAI AURI ATINE BA, sai ke, ko kuma duk ku rasa''. Muryar Atika ''wallahi Inna ni in baki sa ya soni ba, sai dai in mutu ba aure, wallahi shikadai nake so Inna, duk cikin samari na babu kamarsa, mai kyau ne dan birni kuma mai ilmin bokon nan irin na radiyo, ke baki ganshi ba fa...''nace naji ya isa, Atika, ASIRI FA GASKIYA NE, wallahi kin ji na rantse miki daga Atine har Amarya sai sun bar mana gidan nan, sai sun... Na gyara murya na kwarara sallama sukayi tsit, ya tsumma cikin mai, Atika ta leko jikin ta a sanyaye idanun ta sun yi ja tace ''au, ke ce, baki shigowa? Tun yaushe kike tsaye?'' Nayi murmushi ''abincin Inna ne na kawo, ke kuma in kin gama kukan kixo muci namu''. Na kwanta rigingine ina tunanin maganar su Inna, wata xuciyar tace dani in fadiwa Goggo da Amarya. Nasan Inna bata da imani ko miskala xarratin duk abinda ta furta xata yi, to sai tayi shi hankalin ta ke kwanciya, amma sai nayi wani xuxxurfan tunani sanda Liman ke ce mani. ''A kowane hali kika tsinci kanki, ki rike Allah, ki sanyawa ranki cewa yana tare dake a duk inda kike''. Akwai kuma sanda yake yi mani nasihar munanan aiyuka masu kai mutum wuta, yace ''ku guji munafinci. Cikin kaba'irai shima babba ne, wanda Allah (SWT) yayi wa ma'abotan sa tanadin wutar jahannama, inda yake cewa ''Innal munafiqina fid- darkil asfali minan nar'' ya kuma ce ''fa bash-shir hum bi adhabin azeem''. Atika tace dashi a lokacin wai ''MEYE MUNAFUNCI?'' Yace ''shine; - Yi da mutane(cin naman mutane) -Hada husuma tsakanin mutane -Daukar xancen wani ka kaiwa wani -Zunde, yafice da kifce duka munafinci ne -Xama da mutum da xuciya biyu. Saboda haka sai naja bakina nayi shiru. 22 Da dare Bello dan gidan waziri yazo duba Goggo na shi da abokinsa, sun shigo har cikin gida shi da abokin mai suna Muhammad ya gaishe da mutanan gida sannan aka raka shi dakin Goggo ya duba ta, ya cika su da alkhairi tana ta godiya, daga nan dakin Inna ta suka shiga nan ma tayi ta masa godiya ya ajiye mata kudi mai yawa, ta ce an gode Mamman Allah ya saka da alkhairi, sai kuma tayi sauri Tace ashe abokin na ka ne Mamman ko?'' sukayi dariya ''Mama ai nima Mamman din ne, a can Jos, Muhammad nike, ainihin sunan Muhammad Bello'' ta jinjina girman sunan tasa musu albarka tace ''Ka dinga hakuri da Atine, sai a hankali xaku saba, tace tsoron ka take, kuma dama dai halin ta wani iri ne sai Goggonta'' kai ya dukar cike da kunya Muh'd din ne ya amsa ''to Mama''. Suna fita tana kwallan kira tace in dau kudinnan in mayar mai baxata amsa ba, ba kuma ta sigar rashin da'a ba. A dan filin da ya xama xauren mu, jingine suke jikin buhunan kalwa, basu ko damu da warin kalwar ba, na russuna na gaida abokin da alama mai barkwanci ne yace ''naki in amsa Atine, ya xaki gaida Muh'd Jos, baki fara gaida Muh'd. Karaye ba? Bayan a dalilin shi kika ganni?'' Nayi shiru, kaina sadde ina dan murmushi ''Atine, kuma sai aka dawo da ajiya mai ita bai ce akawo ba, kin kyauta kenan?'' da kyar cikin 'yar siririyar muryana nace ''wane ajiya ne?'' ''Rigar sanyin Dan Karaye mana''. ''Wane dan Karaye?'' ''Au, baki san shi ba?'' ''Da na san shi baxam tambaye ka ba'' ''to dago dubar ni, in nuna maki Dan Karaye''. Kamar wata doluwa, wai sai na dubeshi har ga Allah, ni da xuciya ta daya nake magana. Ashe tuni har ya canxa wuri sai muka hada ido hudu da Bellon da ke rikita ni. Idanuwan shi lumsassu ne, kuma manya tamkar nawa, bakin xanen idon shi har wani kyalli yake na musamman cikin hikimomin Ubangijin halitta. Wani irin kallo ne da shi mai jan hankali da ban sha'awa, ban iya na dauke kwayar idanuna ba kaxalika shi din. Dan Karaye, kokari yayi ya sarke kwayan idanun mu sarkewa mai ban mamaki. Ke da gani kinsan ya saba yiwa mata, ba ni ce ta farkon ba. Kallon da ko kin ki Allah, dole ki fada a tafkin kaunar shi... 23. Ni naga Bello mai kyau ne, amma ba wannan ne ya raxana ni ba; tsabar kwarjini da cikar xati, Ingarman namiji ne tako'ina, Bello Waxiri bai da makusa. Dogo ne hakika, mai ginannen kakkarfan jiki, ga wani lafiyayyen saje da ya aje tun daga gefen kunnuwansa har xagayen lafiyayyen bakin shi, lebba gare shi masu sulbi da sheki bakake sidik. Shi ba fari ba shi ba bakii ba gashi nan dai ruwan kasa mai daukar ido. Sanye yake da Jabba (kayan sarauta) kufta da wando na wani rantsatstsen yadi ruwan madara, wani irin budadden takalmi ne a kofar sa, wanda ya tona asirin lafiyayyun yatsun shi da sullubebiyar kafar shi tamkar bai taka kasa, gashin kansa baki wuluk sai sheki yake kaxalika bakar daran dake kanshi, gassun ta na reto a wuyan sa. Ta ko'ina nasan Bello ba tsarana bane. Koda yake nima wai ina da kyau inji Goggona? Oho. Tafin Muh'd., har tsakar kan mu, gabadaya muka juyo muka dubeshi, idanuwan mu jaxur; so kenan, ke aiki a tsakanin mu. Dan Jos yace ''a'ah Atine! Daga cewa ki dube ni, in nuna miki Dan Karaye, sai ki dulmiya gabadaya? Ya dace in kauce hakannan, don naga Dan Karaye bai son fadin son a gabana. To an ce dai kallo in ya wuce daya, biyu haramun ne na barku hakannan''. Bello bin shi yake da ido kamar ya ga mahaukaci sabon kamu yace ''Atine na aiko miki da sako kika ce a maido mun kayana? Don sunyi kadan, ko don har yanxu kina jin tsorona?'' na harare shi kasa-kasa ''na ji ne daga bakin da ba xai mun karya ba'' ''ni wallahi bana tsoron ka, da ina tsoron ka ashe da ban rama xagin Ubana da akai ba''. Yayi murmushi a karo na biyu ''to tunda baki tsoro na, kuma ki na son in yarda baki tsoron, shin yaya sunana?'' '' Dan Karaye mana''. ''Ai kin ji tsoron kenan, wannan ba suna bane don ko ke 'yar Karaye ce, amman ai Atine ce, don haka ya sunana?'' ''Na manta'' ya sake murmusawa ya kashe xancen ta hanyar russunawa ya tura min jakar daxu gabana ''Atine, ba'a maida kyautar miji, don haka kada in kara baki abu ki maido manni, kina ji na?'' Ya dan fiddo ido na kara tsorata don haka ya saki, ya koma xolaya. 24 ''Kyauta yana kara dankon kauna, bana yiwa kowa kyauta sai wanda yake (so special) a gare ni, sai dai sadaka. Na fahimci baki iya karatu ba, don haka kiba Auwal ya karanta miki abinda na rubuta, doguwar wasika ce. Akwai hotunana a ciki don ki karen kallo, ko akwai wani abu wanda yake wani nakasu a tattare dani, don na gane har yanxu ana so, ana cillawa kasuwa ne. Xan koma Jos, baxan dawo ba sai da kayan auren mu. Amma Atine, baxan samu kosa gaisuwa ta mutunci, daga matan da nike so da aure ba, daga Atinen da ta sani aure bam shirya ba?'' wani tattausan murmushi ne ya subuce min, wai na sashi aure bai shirya ba. Meye shirin, bayan suna da kudi, suna da muhalli mai tsabta? Oho! ''Me xan ce maka to?'' ''Ina son ka Muhd. Bello'' nayi hamxarin kai tafukana na rufe fuskana cike da matsananciyar kunya, ina girgixa kai alamun ''a'ah banda wannan'' ji nayi ya matso gabana na kara rudewa, daddadan kamshin shi, kwarjinin shi, jinin mulkin shi da cikar xatin shi sun mani mayafi na runtse ido da karfi, tattausan yatsun shi yasa ya dago habana ya dubeni sosai da murmushi ''kada ki tsorata, child, ke 'yar shilla na ce, Atine, ba abinda xan maki illa RAINO, raninon ki xanyi har sai kin xama kaxa, sannan...'' ko me ya tuna? Yayi saurin toshe bakin shi ya maida hannuwan shi aljihu, ba xai wuce tunanin Atinen yarinya ce karama kuma 'yar kauyen su ba, da kyar in ba kara tsoron shi xata ji ba. A duk sanda yake tare da yarinyar, mance shekarun ta yake, rayuwar barikin Jos, ba daya take data kauyen Karaye ba. ''I am sorry, Atine yi hakuri na tsorata ki wasa nake maki, kai dan Jos!'' Muhammad ya shigo ''mu je ko?'' ''Ina fatan an sayi bakin, Atine me xaki bani in kai tsaraba Bukuru wa Inna na?'' Na dube shi a sanyaye ''bani da komi Muhd. sai daddawa da muke yi da KALWAR Baban mu, sai kuma citta, masoro, kanumfari,cittamai kwaya, barkono da xogale.Ban sani ba ko Innar ka xata so?'' ''Sosai kuwa, don Innata bata girki sai da kayan kamshinnan da kika ambata, 25 Hakanan ma'abociyar cin xogale ce da yin miyar sa, wallahi kin ji na rantse, ko dan Karaye? Yayi tsaki ya soma tafiya yana cewa ''kai dai surutun ka Muhd., is too much, talkative soldier, try to remember always Atine is too young!'' Na juya ina kunkuni na shiga dakin Amarya ''kai ni Amarya yau Allah ya hada ni da mai kwadayin tsiya, wai lallai sai na bashi tsaraba, gashi gallele ko mai xai yi da 'yan shirgin kauyen mu oho, yanxu haka ma xubdawa xaiyi a lambatu'' tace ke kuma marowaciya ba, da mai rowa ai gwara mai kwadayi, da kyar ma in akwai masoron ke dai hada ki bashi, son ki suke, mai son ka kuwa ai ya gama maka komi. Ko ya dauka ko ya xubar, ruwan sa.'' Ina jin tashin motar su na kinkimo jaka na nufi dakin Guggo, Goggo tayi murmushi, ''har an soma cafko toshi'' nayi dariya ''ni ban ma iya budewa ba, bari Sani ya shigo'' dan halak din ban rufe bakina ba naji gyaran muryar shi yana surutun su ma 'yan bal, ya shigo yace ''eye, Afiruwar yarinyar nan da farin goshi take, a'ah su Afiruwa yau an aje tarihi'' Goggo ta kwada mai maficinta yana dariya yayi kici-kicin kauyancin sa shima da kyar ya bude, har wani karfen da ake turawa gareta, ga tayoyo kanana sai kace wata mota, (trolley), turamen atamfofi ne Ingila sunan ta inji Guggo, har turame uku, sai wasu irin dogayen riguna masu kyau baka, ruwan hanta da ruwan hoda da akayi su da wani irin yadi mai santsi, daya hula ce makale ragowar biyun mayafai ne da su, sai wasu lesussuka masu taushi da daga ganin su xaka kimanta tsadarsu, kore kalar lemun tsami da aka yiwa yarfen fararen fulawoyo da ja mai ratsin baki, takalma kafa biyu marassa dunduniya hade suke da jakunkunan su masu firgitarwa ban san abinda yake rubuce jiki ba, na xare wasikar da wani sukunbiyan abu kamar littafi wanda na fahimci hotuna ne aciki. Ban bari Sani ya bude su gaban Goggo ba don kunyar ta nake ji. A yau har da takardun kudi, bamu kirga ba,nace baxan taba komi a ciki ba, tunda Baba ya hana,bamu san abinda yake hangowa ba,sai hotunan sai takardar. [9/24, 9:12 AM] A A Dboy: Tuna Baya 26 to 30 26. Can uwar dakin Amarya na shige, duk suna tsakar gida suna hira. Tun jiya na lura Atika bata gidan, Inna tace wai ta tafi gidan kanwarta Tani data haihu, haihuwar fari, sai bayan arba'in xata dawo. Ni kan daga ji nasan karya ne, me Atika xata yiwa mai haihuwar fari? Oho su suka sani. Na bude abin nan mai kama da littafi (album) ba komi bane ciki sai hotuna, da alama babu wanda aka dauka cikin Karaye sai ko can wajen karshe tare da Muhammad a fadar Maimartaba sarkin Karaye. Ya tura xungureriyar wasikar a can kasan hotunan, komi ya fito hannun Bello kamshi daya yake, na rasa dalili. Na fiddo takardar na rika jujjuyata a hannuna cike da matukar son sanin abinda ta kunsa. A yau ne nayi dakacen ina ma naje makarantar boko, dafa wai na karanta kyawawan rubutun da ke cikin takardar nan na fahimta, shine yace in ba Auwal ya karanta mani? Ba xan bashin ba, illa in bi Auwal din ya koya min har na iya kana in karanta da kaina. Na farke wasikar, doguwar takarda ce da aka yarfawa rubutun gwanaye a fannin boko. Na cigaba da juya ta a hannu na gabanta da bayanta. Shin me ya hana Baba sanya mu a makarantar nan ne don Allah? Ido na ya ciko taf da kwalla. Na tattara na boye, na koma dakin Goggo na kwanta lamo, a bayan ta, naji jikin ta xafi rau. Nace ''Goggo jikin ki xafi'' ''to ya xanyi Atine? Jiki da jini ai dole ne''. Tayi shiru xuwa can tace ''Atine nayi ma Allah godiya ina kan yi masa ma, da ya hada ki da miji irin wanda nake miki addu'ar samu tun xuwanki duniya. Wato miji na gari mai kaunar ki tsakani da Allah, babu yadda xa'ayi Bello ya xo gareki. Sai dai tun daren da na fara samun sauki, nayi maki istikhara ta kwarai, abinda na gani wai mijn ki yana nesa, gashi kuma naga Bello da gaske yake, Allah shine masanin gaibu, don xancen nan da nike maki yanxu Waxiri na shirin turawa Maimartaba xancen aure, duk da nauyin shi da yake ji na kin amincewar Bello auren Fatima diyar Maimartaba 27. Abinda nake so da ke, Atine kada ki bari wata baraka ta bullo daga gareki, domin yanxu mahassada sun saki gaba. Dama auren irin su Belli sai mai gagarumar sa'a, kuma jaruma. Ki xama jaruma Atine ki jure rayuwar duk da kika tsinci kanki a gaba, mai dadi ko akasi. Ina ji a jikina, rayuwar ki Atine mai wahala ce daga farko, mai dadi daga karshe. Atine cikin ko wane irin hali kada ki butulcewa ATIKA, kada ki guje ta, kuma kada ki cuceta Atine rayuwar talaka gabadaya cikin wahala take. Cikin ko wace irin daukaka da kika samu kanki a duniya kada ki boye baban ki MAI-KALWA NE. Da arxikin kalwar kika ci, kika rayu har kika kawo matsayin da duk kike. Kada ki taba barin abinda xaki iya yau kice sai gobe, hakan shi ke kawo rabon wani. Yau naki ne gobe na wanin ki ne. A duk abinda xaki yi Atine, ki xama mai karfi kuma mai gaskiya. Gaskiya da karfi, sune kyawawan sutturar TALAKA. Kada ki karbi alfarma, sai dai taimako a inda ya dace. Ki guji duk wani abu da xai saki jin kunyar mutane, gara ki mutu da ki bar ABIN KUNYA. Ki xama mace ta gari a gidan aure, wadda xata taimakawa mijin ta da karfin ta, lafiyar ta da aljihun ta koda yana dashi. Siirin 'ya mace a gidan aure sune girki, kyakkyawan raino, tsafta da kama kai. Atine ki kula da kanki. Kwanta kiyi barci, Allah ya bamu alkhairi''. To amma na kasa barcin, illa kara mannewa jikinta. Maganganun ta ke yawo da juyi a kwanyata sai tsakar dare kan in samu barci yayi awon gaba da ni. Na farka ana kiran sallar Asubahi na tashi Goggo ta mike, muka xaga mukayi alwalah muka dadda jam'i a dakin Baba. Tun dai raka'ar farko Goggo bata dago ba, na kaddara hakan da addu'a take yi doguwa. Har muka sallame ba wanda ya kula,domin dai ta saba nisan kiwo a sujjada.Gari ya soma wayewa alfijir ya keto Goggo na duke cikin sujjadar ta. Amarya ce ta sha jinin jikinta,ba lafiya ba domin Guggo raka'a daya tayi,yaya xa'ai ta katse jam'i haka kawai?Sai ta kai hannu ta dafo Goggo, kamar jira take wani abu ya shafeta, sai ta kwanto sharaf, tsakiyar dakin. 28. Kwanaki uku muna amsar ta'axiyyar Guggo, a kullum ka'ida ne sai an kawo abinci lafiyayye a cikin fanteku safe, rana da dare daga gidan Waxiri. Tun ranar rasuwar a ka yiwa Goggo sallah. Waziri, Matanshi da 'ya'yan shi duka masu aure da marasa aure kwansu da kwarkwatarsu sun xo mana ta'axiyya dukkansu sukan ce, Bello yace a isar da sakon ta'axiyyar shi, yana xana jarabawar karshe ne daya kare xai xo. Bayan share makoki da kwana biyar muka ga Inna na sauke kwallayen ta da bamba, almajirai na fita mata da su, duk matan gidan ita kadai ce mai jere. Tace da Baba wai bikin diyar aminiyar ta Jummai ne ya tashi xata yi mata gudunmawa, Inna sarkin rowa, da ko auren kanwarta da suke ciki daya, Tani, bata bada ko sisi ba ita ce mai sauke kwallaye domin auren 'yar aminiya, shikan Baba mun lura kwanan nan wani 'yar tsoro ne tsakanin shi da Inna, komi ta fadi, jiki na rawa xai amsa. Wani abin mamaki har akayi rasuwar nan aka share makoki babu Atika, ba labarin ta amma ban ji Baba yace komi ba. Kwanaki biyu bayan haka ta kulle dakinta ta tafi, bata ko ce mana ga ranar da take sa ran dawowa ba. Auwal ya shiga shekarar shi ta karshe a sakandire, shi kuma Sani dama tuni ya daina, Rabi'u ya shiga babbar sakandire aji daya. Auwal ya xo yana gayawa Baba an ce duk mai son shiga jami'a, dole sai ya sayi wani form wai shi (Jamb) ya cike naira dubu da dari biyar. Hankalin Baba ya tashi ainun, ko jarin kalwar gabadaya xa'a hada bai fi naira dubu biyu ba, gashi yana son Auwal da karatun nan kwarai da gaske, don ba karamar amfana muke da shi ba, ko wasika aka kawowa dayan mu shi ne mai karantawa, shine mai fadin tsarin shan magani yadda likita ya fadi. Rashin lafiyar Guggo da kaita asibitin birni, Auwal ne yayi wa likita bayanin abinda ke damun Guggo kasancewar shi Bayarabe. Haka a asibitin larabawan da Bello ya maida su duka Auwal ke fadawa sisters (malaman asibiti) abinda Goggo ke cewa. Na kawo shawarar a fidda sauran kayan kullin Goggo kasuwa a saida tunda,.. 29. Tun bayan rasuwar ta babu wanda ya kara xuwa siya, Baba ya yarda da shawarata can kuma yayi tunani yace kaya na magada ne, rabawa xa'ayi a basu, Allah ne gatan mu, ya kuma dogara gareshi yasan baxai bar shi ya tabe ba. A satin su Inna suka dawo a tare, kai da ganin su kasan cike suke da farin cikin wani abu, Atika ta daina kulamu kwata-kwata abinda xamu ci wannan kansa nema yake ya gagaremu domin kasuwar kalwa ta kara wulakanta a dai-dai wannan lokacin da kan jama'ar karkara ke kara wayewa da sana'o'i masu gwabi. Amma duk da haka Baba bai taba cewa a taba kayan Bello ba, ko mai yasa? Wallahi oho! Ina tsaye ina surfen 'yar ragowar dawar data rage mana xamu yi tuwon dare. Sallamar Haj. Talatu muka ji, ni na amsa ta, na santa baiwar gidan Maimartaba ce mai ji da kanta amma tasu taxo daya da Amarya, takan dan xago lokaci-lokaci su gaisa, tace ''Saude na ciki ko Lami?'' Nace ''duk suna nan''. Ban san me ya kawota ba, bayan tafiyar ta Amarya ta je ta gayawa Baba, kira mu duka ya dubi Inna da Atika yace, ''tunda Atika ta kasa fidda wani cikin manemanta, kafin Allah ya fiddo wani, xataje yin wanke-wanke gidan dan Maimartaba da yake aiki a Habuja, xa'a biya mu kudi naira na gugan naira har naira dubu goma a kowane wata. Ko na wata daya muka karba ai mun warke, ga auren Atine da ke tafe, wanke-wanken nan shine rufin asirin mu. Ni dama nasan nayi rashin mata kuma matallafiya, Indo Aisha. Don haka ku tallafa mani, Lami ki bar Atika ta je wanke-wanken nan ko na wata daya ne. Inna ta shiga keta wata irin dariya mai ban haushi tace ''WANKE-WANKE! WANKE-WANKE!! WANKE-WANKE!!! Allah ya sauwake Atika ta je muku bara, kuna xaune, tayi aiki da karfin ta da lafiyar ta don amfanin kan ki. Baka tura Sani kwadago koko makarantar Auwalu dole ce? Kai da baka yi karatun ba me ya same ka a rayuwa, ga ka nan da ranka da lafiyar ka daram ina ce? 30. Atine 'yar gata, mai aure gida Waxirawa, me kuwa xai hana a yi wanke-wanke domin hidimar aurenta, tana xaune; kura da shan bugu, gardi da amshe kudi. To Atika, tashi maxa mu tafi taron nan ba namu bane''. Suka tsallake mu suka wauce. Baba ya sunkuyar da kai sabida kunyar abinda Inna tayi mishi a gaban mu shiko Auwal tsananin bacin rai sai yace ''Baba ni xani je kodagon, ko kodagon laifi ne ko talauci abin kunya ne?'' Baba yace ''a'ah Auwalu, ka kyale ni in yi tunani, mutuncin auren kanwarku xaka diba, bai kamata ace yayyun ta manya da xa'a karbi auren ta a hannun su kodago suke a tasha ba, karshen tsiya kenan. Abinda ya daure min kai maganganun Lami, ina Atikar tayi miji har ta xartar da hukunci kan gaban kanta, bada yawuna ba?'' Sallamar yaro a xaure yace wai Yallabai Bello ya xowa Baba gaisuwa. Baba ya mike tsaye yace Sani ya je ya gaya mishi idan ya xo ya daina aike, ya shigo kansa tsaye, nan gidan su ne. Ni da Amarya muka nufi daki, ko tatafasa Amarya bata tofa a xancen nan ba. Ina jiyo kamshin raina yayi fari, duk wani bacin rai da ke damuna naji ya yaye. Daga dakin Amarya, na hango Inna da Atika sun fito a hanxarce rike da koko, tabi kofar dakin Baba ta yayyafa tabi har soro ta yayyafa, ita kuma Atika garwashi ta debo a murhu ta xuba wani turare mara dadin kamshi tamkar na bori, ga bala'in hawa kai, ita kanta Amarya na lura hankalin ta na kansu, ina gani tana marmasa addu'a a bakin ta, ta mike ta dawo jikina, ta kama yatsun hannuna na dama da hagu tace ''rufe idon ki'' ban san me take tofa min ba, naji duk jikina yayi kwari gadagar tamkar na sha 'Daga'. Tayi shigewar ta daki. Na hango fitowar Bello, ya kara girma ya kara kyau da ilhama. Sanya kafar shi ke da wuya a tsakar gidan ya shiga atishawa ba kakkautawa. Baba na mishi 'Yarhamakallah'amma bai iya ya amsa ba sabida yadda atishawar tafi karfin shi. Da kyar ta tsaya ya kama kanshi da ke juyawa ya fice daga gidan da sauri tare da Sani. [9/24, 9:12 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [9/24, 9:12 AM] A A Dboy: Tuna Baya 31 to 35 31. Can xauren fita Sani yace ''bari in kira ma Atinen, na dauka xaka shiga ku gaisa da su Inna?'' Yace ''No, kyale ta kawai bana jin dadi, kaina kaman ana tsaga shi guda biyu. Xan je clinic in sha magani, gobe in naji sauki na bullo''. Sani jikin shi ya mace murus, ya soma xargin nan gidan Bello ya dau ciwo, shi kanshi ya ji kamshin mai hawa kai da bai san daga inda yake ba, bai kuma san ko na mene ne ba, ya dauka makotane, wala'Allah Bello bai son kamshin? Allah masani kwana daya, biyu, uku, hudu, biyar, ba Bello babu labarin su. A na shiddan ne labari ya iske mu yana kwance a can wani asibiti a Jos. Na rude, na rikice na rasa inda xan tsoma raina inji sanyi. Nayi kuka har na ba uku lada. Ina naga hanyar xuwa Jos, wa xai kaimu? Idan muka je gidan Waxiri, muka ce a kaimu Jos, ai munyi karambani da xakewa da yawa. Sati biyu bayana nan Muhammad ya aiko sallama da ni, ba karamin jin dadin xuwan sa nayi ba, don nasan hanyar gano abin kauna ne yaxo, na dan gyaggyara na fita. Kallo daya yayi min yayi dariya yace ''shin tsakanin ki da Dan Karaye, waye ke kwance ne? Kin ga yadda kikai koxai-koxai dake Atine?'' Ba wannan ne a gabana ba, a ganina Muhammad bai damu da ciwon Bello ba sam, barkwancin shi kurum ya sanya a gaba, hawaye xurrrrr... Suka bilbilo min nace ''Muhammad ya Dan Karaye?'' ''Sai kin fadi sunan yau, in har da gaske kina son sanin halin da angon naki ke ciki''. Tamkar in mangare shi, wannan mugun aboki ne, bai damu da Bello ba sam, yadda yake kiranshi amini. Ya ga dai bani da niyyar magana ya xama kintsatstse yace ''ki kwantar da hankalin ki Atine, Muhammad ya samu sauki, yanxu haka yana gida tun jiya muka dawo...'' ''amma shine ko ku neme ni a jiyan? Dan Jos, baka kyauta mani ba'' ''Kin san Allah daya ne Atine, ba laifi na bane, ba yadda banyi dashi ba muxo, ya ki, yanxuma bai san na taho ba da ya hanani. 32. Yace wai baki damu dashi ba shine kadai yake haukansa, satin shi guda a kwance baki nemi da kije ba bayan in har kina nuna xaki, akwai masu xuwa kullum ba xa su ki tafiya da ke ba...'' ''Kaga ni don Allah ya ishe ni, idan naje gidan Waxiri duba shi, nayi laifi?'' Muhammad yayi shiru, ''tukunna kamin wannan, so nake na tambaye ki wani abu, amma don Allah kada hankalin ki ya tashi, ko kiyi tunanin wani abu daban'' nace ''to..'' (jikina ya soma sanyi). ''A ranar da muka kare jarrabawa, kayan da Muhammad ya aikewa Yayan shi dan wurin Maimartaba ya hado mishi daga Washington D.C suka iso, muka taho Karaye, cike yake da begen ganin ki, kada ki so kiga irin tsarabe-tsaraben da ya yo miki. Duk wani dan abin ado ya gani a jikin matan barikin Jos, sai ya ce su sayo mishi ya bawa matar da xai aura, har su ci riba da shi. Muna sauka, ko ruwa bai tsaya sha ba, karewama abinci nace ya tsaya in ci, ya ki, yace na same shi a gaba, ko Yallabai bai ganshi ba ya kamo hanya ya taho. Ya kima dawo mana ba a hayyacin sa ba ke kamar wanda yai gamo. Sannan ya ishe ni da xancen wai wata ATIKA shin wacece ATIKA ko kin santa?'' kafafuwa na sun sage, yawun baki na ya kafe, gangar jikina ya saki, kuxarin jikina ya kare nace ''Na san Atika mana, Atika yayata ce Uban mu daya, ba Mamaki Muhammad ko kadan ban yi mamaki ba, mu bar wannan xancen don Allah don ba shine a gabana ba. Kayi mani jagora kawai in dibo jikin Bello, shine ya dame ni. Don nasan ko ma menene ciwon shi, gidan mu ya kwasa, bai kuma kyautu in ki xuwa ba'' yace ''in kina ganin ba komi, muje?'' na koma na gaya wa Amarya xani dibo jikin Bello, tace ''haka xaki tafi ba kintsi, ba gyara Atine yaushe xaki girma ne? Kuma me xaki kai mishi?'' ''Me muke dashi, shima ai ya sani Amarya bamu da abinda xamu bashi, KALWA KO DADDAWA?'' Idanun Amarya ya ciko da kwallah, ta dauko min sabon xanin atamfar ta da bata da kamarta, kwadebuwa ce, ruwan anta, Liman ya aiko mata da ita tun haihuwar Sadiya, tun sawar da, 33 ..tayi mata ranar suna bata kara sawa ba. A gurguje nayi wanka na murxa man kuli-kuli a sawayena da yatsuna kada a gansu furu-furu, fuskar kuwa sai tayi fayau, na murxa kwalli don boye rama. Na kawo sabon gyalena mai-barewa na yafa, ban daura dankwalin atamfar ba don haka na nannade mayafin a fuskata, sai na fito ya bakuwar balarabiya. Karo na farko a rayuwata da nayi tunanin shafa turare a jikina. Na dubi turaren wuridin Amarya wai shi (Dan-Daula) na bulbula. Muhammad na gaba ina bin shi a baya har kofar gida Waxiri. Ya tambayi samarin wurin da ke kofar gida, ko Yallabai yana ciki? Suka ce yanxu yayi baki 'yan dubiya daga gidan Maimartaba sun wuce gidan sa na bayan gari..... Muhammad ya dubeni, ''kina ganin muje, Baba ba xai yi fada ba?'' ''Ba xai yi ba, dubiya ne fa, na mutumin da yake matukar kauna, fiye da mu, Baba ya amincewa Yallabai fa Muhammad''. Muna tafe muna hira, har muka kawo gidan yana gaya min asalin gidan Yayan Bello, dan wurin Maimartaba, shi ya gina shi domin sauka idan ya xo da iyalin shi, daga baya kuma ya mallakawa Bello halak-malak shi kuma ya dora wani sabon gini a jikin katangar wannan din. Ya nuna min shi da hannun sa. Gidan karami ne hawa daya tsarin ginin turawa, shuke- shuke sun kawata harabar gidan sosai, motoci har biyu tabbacin da baki, na lura Muhammad ya rude, tafiya yake tamkar bai so. A babbar kofar gilashi ya tsaya, ya danna wata 'yar danja kamar abin kunna fitillar lantarki, muryar mace ta amsa ''Yes, Muhammad, shigo''. Yace ko xaki tsaya in kirashi waje? Kannen shi mata ne suke falon'' ''muje kawai ba komi'', cike da xargi na fada. Bello kishingide jikin abin tada kan saraki (tuntu) daga shi sai jallabiya ruwan toka-toka ya xubawa allon talbijin ido, daga gefen shi dai-dai kan shi wata kyakkyawar farar budurwa ce mi dan jiki take sanya mai wani irin abu da akayi da fulawa da ban sani ba a baki, ta kuma sanya mai gongonin lemu ya kurba. Ya dubi Muhammad sannan ni, yace ''Kai ina ka shiga ne tun daxu ina neman ka?'' 34. Muhammad bai amsa sai da ya nunan wurin xama, na xauna a darare sannan yace ''naje wurin Atine ne, Atine ku gaisa mana'' Na dan xamo daga cikin kujera na russuna nace ''ya jiki?'' ''jiki alhamdulillah, ina kika baro min Atika?'' Tana gida, tace a gaida ka da kyau'' Ya maida dubansa ga 'yanmatan, ''ku, baku gaida baki? Kanwar yarinyar da xan aura ce, Atika'' suka kyabe baki gabadaya, mai bashi abincin tace ''na dauka itace Atikar, da nace ai tayi kankanta da aure, me xaka aura anan, abu uwa KYANDIR!'' Suka kwashe da dariya shima dariyar yayi yace ''me xa'a kawo miki; lemu ko ruwa ko ko coffee?'' Wallahi Bello, kaman bai taba gani na ba, sai ranar. Babu wannan kallon so da kaunar da yake mani. Na mike jiri na kwasa na, na samu na dafa bango na isa kofa ''ki ce Fatima na gaida Atika, tunda tayi min fashin miji, to tayi mashi kyakkyawan riko kamin in iso, xan amso abina koda a ta biyu ne'' suka kyalkyale da dariya. Muhammad ya biyo ni ''me na gaya maki Atine? Bello baya cikin hayyacin sa wallahi tun a Jos, ya koma min haka..'' sai hawaye, yasa hankici ya share fuskarsa ya fyace hancin sa yace ''Atine, kiyi hakuri ki saurare ni, koda rabuwar ce bai dace mu rabu da haka ba. Xa'ayi wa Muhammad addu'a xai warke, wallahi xai komo dai-dai''. Hawaye ne masu xafi suke fita min tarara, amman ban fasa tafiya ba shi kuma bai fasa bina ba ''da yake shine autan maxa, ai dole ayi masa addu'a mana, mutum lafiyar sa lau na gani da ido na kace wani a yi masa addu'a, to dama BAN TABA FURTA INA SON BELLO BA, koko na taba? Ka je ka tambaye shi''. Atine, ki fahimceni mana, nasan kina fa da hankali, Muhammad ba yin kansa bane... 35. ''yin kafafunsa ne, tunda ba yin kansa bane. Kaga wallahi ka rabu dani tun ban xage ka ba. Ina ganin mutuncin ka Muhammad, kada kayi sanadiyyar da sauran matuncin xai xube, tunda nace ka rabu da ni, ka daina bina, to ka rabu da ni. Baxan mance kaunar da ka nuna min ba, amma maganar aure ni da Bello BABU ITA HAR ABADA; WA XAI AURI MAI KAFA KAMAR MABURGI? KYANDIR? Ai wallahi ko ni na miji ce baxan aura ba''. Muhammad yace ''duk naji, amma Atine, komai akayi shi cikin fushi, sai anyi dana sanin aikata shi''. Dai-dai lokacin da muka kawo kofar gidan mu, na dube shi duba na karshe ''ni ba cikin fushi nake ba. 'Yar uwata fa jinina Bello ya koma yana so? Kuma sai inyi fushi, don ni mahaukaciya ce tamkar shi? Kaga tafiyata, kada ka sake kayo aike kace inxo ko Babana, xaka ga kaskanci, na gaya maka, na kara gaya maka wannan!''. [9/24, 9:12 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [9/24, 9:13 AM] A A Dboy: Tuna Baya 36 to 40 36. Na juya na bar shi anan tsaye, na isa ga dakin mahaifiyata, na kamata na rungume na shiga rusa kuka mai matukar tsanani. Digar hawayen Amarya cikin kunnuwa na ya tabbatar mani, taji yadda mu kai da Muhammad. Ni nasan Allah ne ya hutar da Goggo ganin abin bakin ciki. Maganar ta ta fado min a ranar da xata tafi ga sarki Allah ''Yau nake ne, gobe na wanin ki ne''. Kenan ba abin damuwa bane don Bello ya nuna min so jiya, gobe ya koma wani na; Atika? Yayata da muke Uba daya? To amma ya xanyi da son BELLO WAXIRI? Da ya riga ya kanannade ni ba tare da sani na ba. To wai ance in so cutane, to hakuri ma maganine, xan hadiyi hakurin in gani? Ko xai mini maganin? Na dago na dubi Amarya nayi murmushin karfin hali ''To meye abin damuwa Amarya? Bello ba shi ne autan maxa ba. Ni wallahi gare ni ba komai. Amarya bata ce komi ba, na share fuskana nace mata na tafi gidan Liman in ga Sadiya. Kakata Luba na daka, nayi sallama na shiga, Sadiya ta sheko da gudu ta rungume ni, Luba ta aje tabaryar ta dube ni sosai ''wani mummunan labari xan ji, Atine meya faru, can gidan ku ko ko gidan Waxri?'' Na tube silifana na ja kujera 'yar tsugunne na xauna ''eh to, Bellon ki ya canxa Luba, kamar bai sanni ba kamar bai taba gani na ba....'' hawaye suka xubo min sharrrr! Luba da alama xancen bai ko dadata da kasa ba. 37. ''Idan kika sake kuka akan Bello, ke ba jikar Liman bace. Labari ya xo min, Lami ta sa duk kadarorin ta a kasuwa, bata a birni bata a kauye ta raba ki da Bello ya dawowa Atika, tun lokacin mun dukufa addu'a a kanki, asiri bai ci ki ba, domin jikin ki shiryayye ne. To idan Lami a sammako take, ni a can na kwana. Kakan ki a tsaye yake kwana, da asirin ta mai ci ne, da Saude bata kai yanxu a gidan Maikalwa ba''. ''Don Allah Luba, kada ku wahalar da kanku, ni Bello ya fice min a rai, auren ma baxan yi ba, ko na rasa mijin aure na barwa Atika, Bello, dama ban taba furta masa ina son shi ba''. Na mike xan tafi, Luba tace ''yaro dai yaro ne, an ce kashe makiyin ka kafin ya kashe ka. Idan ke baki san ciwon kanki ba, baki san muhimmancin auren irinsu Bello ba, ni na sani. Jeki ku karata da saunar uwarki da rashin baki ke cutarta''. ''Ni dai nace na yafe dole ne?'' Tuni har na kai xaure, ta dandalin gidan Waxiri na wuce, gaba kadan da gidan Waxiri jingine suke jikin motar Muhammad. Bello na bulbular hayakin taba kamar mai hada gajimare, Muhammad kuma na magana suka dubeni gabadaya. Akuyar data debe su ma bata ishe ni duba ba. Baban mu ya dawo yana xaune yana harhada cinikin sa na yau wanda sulallan biyu da sisi, kwandalaye, sisi da 'yan ficikoki sun fi naira biyar yawa. Na xauna na taya shi, duk iya kokarinsa a satin, naira dari biyar ya hadawa Auwal, da kyar da sudin ludayi. 38. Washegari ina wanka, hargowar mata cikin gude- guden gidan sarautar Karaye, na ji cikin gidan mu. Sai kuma sauke akwatuna da kuma maraba- maraban da Kandala aminiyar Inna ke yi musu, cikin dan lokaci na ji gidan ya cika taf da matan makota, 'yan gulma, ganin kwaf da 'yan bani na iya. Ban fito ba sai da na ji ficewar su kaf, akwatuna ne masu taya tun daga ta daya har xuwa ta uku, ga wata 'yar mitsitsiyar (kit), fanteku da kwallaye shake da kayan kunshi, tsibe a kofar dakin Inna su Kandala na kwasa suna shigewa daki da su, (a wannan lokacin ba kowa ake kawowa lefe cikin akwati ba sai wane da wane). Na wuce dakin mu. Amarya tayi xugum can uwar dakin ta. Na dubeta nayi murmushi duk da raina suya yake, wai in dan faranta mata, nasan iyaye sun fi dan su jin ciwon abinda ya same shi, tace ''Atika, Bello yace a kawowa lehe, daman ya santa ne? Na san dai ganin su da ita sau daya ne, ranar da muka fara haduwa kuma ko magana bai mata ba''. Amarya tace ''wannan abin mamaki da yawa yake, wannan duniyar cike take da rudani, tattare take da ababen mamaki. Mutanen cikinta, sun shagalta da kyale- kyalen ta basa ko tunanin karshen su. Atine, ki xama mai tawakkali cikin kowane hali, ba duk abinda kake so xaka samu ba. 39. Ni nasan kina son yaron nan ko baki furta ba amma don Allah, kisa masu ido, munafurci dodo ne, mai shi yake ci. IDAN BELLO SHI YA SAURA DA NAMIJI A DUNIYA KIN BAR SHI HAR ABADA in har ina raye abinda mutum ya shuka, shi xai girba. Kin ganni nan, ban iya shige da ficen gidan Malamai ba. Takobi na da kowa addu'a. Kada ki nunawa Baban ki damuwar ki, bai san me akayi ba''. ''Ni Amarya na yanke shawara, ki gayawa Baba, xani WANKE-WANKEN da Atika taki xuwa, xanyi wanke-wanke domin ku wadata, Auwal yayi karatu, ku ci abinci mai kyau. Xan kare rayuwata gaba daya a wanke-wanke, bana ko son xaman Karaye, na tsani Karaye, na tsani mutanen da ke cikin ta banda Uwata, Ubana da Liman. Allah ya taimaki Goggo na da bata nan, nasan da anyi tashin hankali wanda bakya so Amarya, da an bata min ranta a banxa, da ta hanani tafiya wanke-wanke''. ''Allah yayi maki albarka Atine, Allah kuma ya baki miji wanda yafi Bello komi da komi''. Sai nayi murmushi kawai na kama harkar gabana, cike da fin karfin xuciya. Amma can a karkashin xuciyata nasan nayi rashi, babba kuwa. Wanda na tabbata cike shi sai dai wani babban ikon Allah (Tuna baya Shine Roko). 40 Atika, sun fa kawo lehe mallam, bari kaga abin arxiki. Baba ya xubawa kaya ido kaman mai ganin abin tsoro da kyama ''ina Atikar ta samo wannan mijin, dan yankan kai, ko dan birni?'' Inna ta kyalkyale da dariya cikin jin dadi ''dan Waxirin Karaye ne, Muhammad Bello sunan sa, ai Atika tayi farin goshi''. ''Bello? Bello wane? Wanda na baiwa Atine?'' Ya jero tambayoyin da bashi da yakinin samun amsar ko daya, ''to dai ina jin bashi bane, don wannan Bellon Atika yake so ka kuma je ka tambayo shi, wa ya aiko wa da lefe?'' ''Wai wane irin xancen banxa ne kike haka Lami? Da alamu baki da cikakken hankali, ya xa'ayi ana neman kanwa kice yar ce? Ko an ce miki Atika ta rasa miji?'' Inna ta hasala ''ko dai wane irin xancen banxa kake? Sai ka je ka shafo labarin daga can sama inda ya sauko'' Ta shiga maida kaya yanda suke. Ya tsallaketa, nitsatstsen dattijon, a nitse ya tadda Amarya, ''Saude meke faruwa ne? Ku fiddo ni duhu, ku yaye min duhun da kuka sanya ni''. ''Ka ganni nan Malam, tun safe ina nan xaune, ban san me ake a tsakar gida ba'' Mallam yace ''xurfin cikin ki bana son shi Saude, xaki gaya min ne ko a'ah?'' ''To xan gaya ma gaibu ne, abinda bani da masaniya akai? Daga inda labarin ya faro can xaka neme shi, ni ina daki, na san me ake a gidan Waxiri ne?'' Ya tabbatar ba xai ji kalma ko daya daga bakin ta ba, kasancewar ta mai KAWAICI da KAU DA KAI akan duk wani abu da ya shafi ATINE. Ya juya ya fita ya nufi neman bello. To xance dai ya bayyana ga Baba, Bello Atika yake son aure yana kuma son a sanya ranar auren kurkusa domin xai tafi karo karatu Kasar Sanyi da ita. Baba a rikice ya dawo, karo na farko daya xargi Lami da asirin da ake cewa tana yi tun bayan auren su sama da shekaru sha biyar. Bai ce komi ba. ************** Nayi sallama dauke da koko, mai cike da ruwan farau-farau. Na durkusa na gaida Baba, ya amsa ta hanyar daga kai kawai, na mika mai koko ya amsa ya kafa kai ya shanye tas, ya ajiye kokon. [9/24, 9:13 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [9/24, 9:14 AM] A A Dboy: Tuna Baya 40-45 41. Ya dube ni da idon rahmah ''Atine kar ki damu, albarka na tare da ke, albarkar Uwa da Uba, ba xaki taba tabewa ba!'' Murmushi nayi, ''Baba ka aurawa Bello Atika, kada ka ji nauyi na, da ni da Atika duk daya ne, ba banbanci. Na xo ne in gaya maka ni xani WANKE- WANKEN da Atika ta ki xuwa, ko a sami dan abinda xa'a kai mata daki, ko a samu a biya kudin makarantar Ya Auwal, xan kare rayuwata duka a wanke-wanke domin taimaka maka Baba na''. Baba ya sa habar taguwar sa ya share ido yace ''Atine ke da Uwar ki tausayi kuke bani, baku dauki rayuwa a bakin komi ba. Don haka har kullum nake addu'ar Allah YA YI MAKU ALBARKA. Duk wani abu da xai taimake ni shi kuke yi. Ku kyale Lami da diyar ta da mai kowa mai komi, ''kowa yace gonar wani baxa tayi albarka ba, tashin ce baxa tayi ba''. Kuma da muguwar rawa, gwamma kin tashi. Tashi jeki, xan nemi Talatu ta kai ki gidan aikin, dama sun matsa mani''. *********** Na hade kayana tsaf, cikin kullin dan kwali. Duk wasu shirgin Bello na tattara su cikin jakar shi har kuwa da takardar da nike ta kwakwar ajiyar ta na ba Salisu (mai bin Sani) nace ya je ya ba Bello, idan baya gidan su ko gidan Maimartaba yana gidan sa na bayan gari. Talatu tayi sallama muka amsa, suka gaisa da Baba da Amarya. Ta lalo kudi 'yan dari-dari da muke jin labarin su an buga, ta bawa Baba, na naira dubu goma, kudin da ko a mafarki, bamu taba gani ba a rayuwar mu. Kai ni ban ma taba jin inda aka fara bada kudin aiki ba'a fara aikin ba sai wadannan. A cewarta wai don sun matsu da 'yar aikin ne domin matar gidam tsohon ciki gareta bata da mai yi mata hidima. Baba yace ''Talatu na ba Allah, na baki amanar yarinyar nan, Atine yarinya ce karama, dole ce ta sami turata wanke-wanken nan. Domin duk halin matsin da kake ciki, gara Dan ka ya tashi a gabanka, duk wani wulakanci xa'a raga masa kana nan. 42 Nasan ni talaka ne futuk, amma ban taba xuwa wajen wani mai mulki neman alfarma ko bashi ba, don haka in aka wulakanta Atine, bafa xan kyale ba, xan iya jure duk wani halin talauci in dai akan MUTUNCIN 'YA'YA NA NE''. Hajiya Talatu tace ''Maikalwa kada ka damu, gidan Yallabai Magajin Gari, babu wulakanci a cikin sa domin 'ya'yan Maimartaba mulki suka tsotsa ba dukiya ba. Share- share ne kawai da goge-goge xata yiwa matar Yallabai kullum, sai dauraye kwanukan da aka ci abinci, bayan wannan ba abinda xatayi. Atine xata ci mai kyau, xata sha mai kyau, xa kuma ta xaga duniya ta ganta domin yanxu daga nan, Abuja, babban birinin tarayyah muka nufa cam gidan matar Yallabai take. Duk shekara xan je in kawo ta ganin gida In shaa Allah.'' ''Wannan duk bai dame ni ba, idan Atine na cikin wulakanci, xan karbi 'ya ta ne kawai a hannun ki. Maganar xuwa gida bayan shekara a barta, bi ban ce ba, sabida ina gudun surutun mutanen Kauyen mu. Illa idan lokacin da nake gani ya dace in mata aure yayi, xan yi maki magana ki dawo min da ita''. Hajiya Talatu tayi dariya tace ''shikenan, ke fa Amarya me xaki ce?'' '' Me kuwa xan ce, banda kada wanke-wanke ya hana Atine sallah, da sauran ibadodin da suka hau kanta?'' Hawaye suka xubo min sharrrr! Na tausayin iyaye na, na san dole ce xata sa su TURANI WANKE- WANKE. Idanuwan su sun fada, bakunan su sun fada; neman halalin su ne. Ni kuwa wulakanci da xan fuskanta, wanda Baba ke fadi xan jure, don cigaban samun halalin sa. ''Na bar gida, cike da kewa da kaunar ki, Inna ta Amarya. Na bar gida, xuciyata cike da bakin cikin ki, kishiyar Inna ta Lami. Na bar gida, xuciyata cike da kaunar wanda bargo, ruhi, ba xai taba daina kaunar sa ba; MUHAMMAD BELLO WAXIRI KARAYE''. Haka na rubuta da Ajami, saman dakin Ya Auwal, da gawayi, a lokacin da Talatu ke sallama da su Baba. TUNA BAYA SHI NE ROKO FARKON LABARIN KENAN! 43. Tafiya muke, tamkar baxa a daina ba. Nayi barci, nayi kalle-kallen gefen hanya har na gaji. Wajajen Isha'i muka shiga garin Abuja. Na bude ido na mutstsike su na dirki kallo son raina, ga fitulu kala- kala sun haske ko'ina kamar rana. Ji nake kamar wata duniya ta daban ba wannan tamun wadda muke ciki ba. Ga wani irin sanyi da nike ji yana ratsa kasusuwa da bargon jiki na, tamkar a Aljannah na ji ni. Direban ya dauke kan motar ya shiga wata kebantacciyar anguwa ta daban, wadda ko a Abujan nasan wannan daban ce (Ministers Hill Colarado Close). Da alama sun san direban don mu ba'a wani bincike mu ba aka daga mana kafa muka wuce. Ya shiga keta gine-gine masu ban tsoro a gareni, kafin ya tsaya a wani gida mai katuwar kofa kamar bangon duniya, wata irin wayar lantarki ta xagaye katangar gidan gabadaya. Sojoji ne ke gadin gidan, da alama sun san Hajiya Talatu don har daga mata hannu daya daga cikin su yayi. Muka doshi wata tangamemiyar kofar gilashi dake fuskantar mu amma ba'a iya hango abinda ke cikinta sabida duhun gilassan. Kofar ta bude da kanta (automatically). Sanya kafata ke da wuya, naji na nitse cikin wani abu mai laushi kamar katifa, ga wani irin kamshi mai dadi, na koma baya da sauri ina haki. Haj. Talatu tace ''Atine, ki saki jikinki don Allah, kada ki nuna mamakin komi kika gani a gidan nan, ki nuna ke kamar ba 'yar kauye bace. Domin kin fito daga tushen mai gidan, KARAYE. Matar gidan bata da mutunci, in kikayi wani abu da bai mata ba tana iya cewa a koma da ke''. Jikina yayi sanyi ''kinsan bata da mutunci kika kawoni baki gayawa iyaye na ba?'' Haka na fadi a xuciya ta. Tsallake wannan sashe, tsallake wannan falo har muka dangana da kuryar gidan wato ainihin sassan matar gidan 44. Hajiya Talatu ta danna wani abu a jikin kofar, sannan ne kofar shiga sassan ta bude muka shiga. Wata murya ce ke fitowa daga cikin wata farar akwatu mai hoto, da tafi min kama da akwatin talbijin, tana fadin wani abu cikin harshen turanci (computer). Hajiya Talatu tace ''tana wanka wai mu jira ta''. Nace ''to ke turancin kike ki? Koko talbijin din ce ta fada maki?'' Harara daya tayi mun na ja bakina na bame da mukulli. Xaune muke tsayin awa daya, biyu har uku, ta fito bata fito ba, a raina nace wannnan wanka ko daye fata? Amsa ga tambaya ta, sai muka ji motsin bude kofar ta, tana tafe da wani xungureren ciki irin na haihuwa yau ko gobe. Na dauka xan ga wata kasaitacciyar Hajiya wadda taba arba'in baya, sai ganin mace nayi tamkar budurwa. Baka, 'yar gajeriya, hancin ta da fuskan ta duka gajerun ne, idanta mitsimitsi kamar 'yar chinese sai dai 'yar lafiyayyar fatar ta mai tsananin taushi da sheki kadai, ta isheta yiwa ko wani irin hadadden namiji yanga; musamman a wannan xamanin da muke ciki da kyawun fata shine kyau, ba kyawun halitta ba. Tana sanye da dogon siket din Jeans wanda ya kama jikinta sosai da 'yar riga mai xanen tutar Amurka (ja,fari da shudi). Gashin kanta cure cikin wani xagayayyen abu da alama doki ne ya sammata, (ba nata bane). Ke da ganin ta kin ga cikakkar bahaushiya, amma 'yar duniya, idanunta a tsaitsaye kuma a soye kamar na soyayyar gyadar Kano (marau-marau). Tayi 'yar hamma tayi mikar data turo xungureren cikin ta gaba tace ''wash, Talatu sai yau?'' A dai-dai lokacin da ta kai dan duwawunta uwa tafin hannu cikin luntsuma-luntsuman kujera. Muka xube a kasa muna kwasar gaisuwa, tana amsawa a yatsine kamar dole aka yi mata, muryar ta kamar an shaketa, ta dube ni sosai tace ''mike tsaye'' tare da kai hannu ta toshe hancin ta. Ta kare min kallo tas, daga sama har kasa, tayi tsaki tace ''ina wannan 'yar siririyar yarinyar xata ita mun irin gyaran da nike so a dakunana? 45. Da wanne kaxamin hannu xatayi mun wanke- wanke mai tsabta da maigidan nan xai iya cin abinci da shi?'' Talatu ta sauke kai irin yadda bayi ke yiwa iyayen gidan su cikin ladabi ''ranki ya dade, Fulani ce tace a daukota, domin 'yan gidan su nada tarbiyya, hakannan girman kauye ne sun saba da aikin wahala. Ki bar ganin ta haka lange-lange, babu irin aikin da baxa ta iya yi miki ba, wanda su maxa, karti, masu aikin ki suke yi miki. Amma idan kika ga kwana biyu baxata ta iya ba, sai a maidata a dauko miki katuwa'' tayi tsaki sabida haushin da Talatu ta bata, tana toshe hancin ta dai tace ''shikenan, xan gwada ta kwana biyun in gani, kuje falon waje xan turo Tom ya nuna mata dakin kwana, ke kuma ki kwana a dakin baki, gobe da safe xan ganku''. Bayan Talatu ta shiga dakin da xata kwana, wani saurayi ga dukkan alamu kabila ne, ya shigo ya dube ni ''Oya yaro muje in nuna maka daki in ji Madam'' na bishi a baya rungume da 'yan kullin kayana, ya bude wani daki da baya da nisa da sassanta, ya bani mukullin a hannu na ''ga dakin ka nan, ka kwanta ka mige, ka futa gajiya ko?'' Da alama shi mai kirki ne, nayi dan murmushi ''to''. Ya sake kallo na ''yaro kayi hakuri da Madam, she is bad (bata da kyau), muma duka muna hakuri da halin ta ne, ka kula duk abinda tace da kai, in kayi kuskure daya, ranka xaya baci.'' Na gyada mishi kai cikin sanyin jiki '' ya sunan ka?'' Ya tambaye ni ''Atine sunana, kai kuma fa?'' Ni sunana Tom. Atine, xan ke ce maka TINE, xaka amsa?'' ''Ba komi Tom, ka kira ni duk yadda ka so'' to sai gobe, ka kwana lafiya, Allah futa gajiya''. Na dubi daki matsakaici, an shimfide shi da jar darduma, amma bata kai taushin wadanda na gani a baya ba, haka labulayen dakin jajaye ne, masu kyau, ga wani bakin tebur (t.v stand) an daura wata 'yar akwatu akai (talbijin), a samanta ma wani dan akwatin ne (receiver). Akwai kofofi guda biyu a cikin dakin, daya a dama daya a hagu, na bude ta hagun; bandaki ne fari sol da shi, kamar tuwon ka ya fadi, [9/24, 9:14 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [9/24, 9:14 AM] A A Dboy: Tuna Baya 46-50 46 Ka tsugunna ka dauka ka ci, komi dake cikin bandakin fari ne sol. Na bude ta daman. Ni Atine mai xan gani? Gado ne na gogaggen katako, lullube da lallausar bargo, da xanin gado mai taushi, ga filallika har guda biyu, mudubin dogon yaro da abin xaman sa (stool), ga sundukai masu taya irin na lefen Atika, babu komi cikin su, wanda ke nufin, in xuba 'yan tsummokarana a ciki. Na kuwa bude na jefa su ciki, uwar dakin ba darduma, sai wani irin falle-falle a jere irin na bandakin, wanda na lura duk gidan ma shine har jikin bango (tiles), wadanda in bakayi da gaske ba, sai su kayar da kai don santsi, don haka nake taka su a hankali ina kuma hadawa da kama bango. Ban kwanta ba, na shiga bayan gidan don in dauro alwala, in sauke sallolin da ke kaina, na Maghriba da Isha'i da suka riskemu a hanya. Banga wani famfo ba sai na jikin kwamin, mai kama d kwale- kwale, na tsaya daga gefe, ban yarda na shiga daga ciki ba kada inje in xame, na kunna famfon na tara hannuwana biyu, ba sai naji ruwan xafi tafasashshe ba? Na kwalla kara iyakar karfi na, ina yarfe hannu, na ji shigowar mutane a guje, Hajiya Talatu ta daga murya tace ''kina ina?'' Nace ''gani nan a bandaki'' tace ''to fito mana''. Na fito ina haki, ita da Tom suka hada baki suka ce ''lafiya?'' ''Ina fa lafiya Talatu, na kunna ruwa in yi Alwala na ji tafasashshe, don ma Allah yaso bai salube mun hannu ba'' na fashe da kuka. Talatu da Tom suka dubi juna, ya tambaye ta ko me nake cewa, domin hausar tashi bata yi kwari ba, tayi dariya sosai ta gaya mishi da turanci, shima yayi dariya, muka dunguma gaba daya cikin bandakin. Ya kashe fanfon dana kunna yana ta xuba yace ''baka gani famfo har guda uku me? Wadannan guda biyu, dake kwami, na wanka ne, na jikin 'sink' dinnan, shine na amfanin da ba wanka ba. In xa'ayi wanka, in ana bukatar ruwan dumi, shine ake kunna wannan, a kuma kunna wancan na kusa da shi ya sirka shi, bayan an toshe rariyan da wannan abun. A shiga ciki ayi wanka sai a bude ruwan ya fita. 47. Wannan da yake rufe, xama akeyi ayi bayan gida, a murda wannan, tayi floshing dinsa, wannna na kusa da shi kuma sai a hau, a murda wannan sai yayi ma tsarki, ba sai ka sa hannun ka ba, O.K?'' Na gyada kai, ''gobe xan xo in koya ma kunna t.v da a/c, right?'' na sake gyada kai, suka fita na rufe kofar. Na idar da sallolin da ke kaina, na rufe da nafilfili na musamman. Na daga hannu nace ''Ya Ubangiji, ni baiwarka ce, mai yawan sabon ka, dare da rana, safe da yamma, fili da boye. Ya Allah kai ka halicce ni, ka raineni, ka bani ikon shigowa wannan gida, domin neman halak dina. Ya Allah kaine mai kowa mai komi, ya wanda Al'arshin sa yake sama, wanda Rahmarsa ke Aljannah, axabarshi da ukubar shi ke wuta. Ya masanin siirn da ke rufe, ya Ubangijin lamarina. Don sirrin dake cikin Suratul Rahman, Yasin da Waqi'ah, wanda in ance LA'ILAHA ILLALLAHU,, yake cewa MUHAMMADUR-RASU LULLAH. Wanda ikon ka, mulkin ka da buwayar ka ya xarta duk tunanin mai tunani. Ubangijin sammai da kassai, buwaya gagara misali. Lallai dukkanni na, xunubi ne. Kuma kaine mai rangwame, mai gafara. Na roke ka, ka sadar da ni alkhairin da ke cikin xama na a wannan gida, ka nesanta ni da dukkan sharri da abin kin da ke cikin sa. Ka bani hakuri, juriya da karfin xuciyar xama da iyayen gida na da duk wanda nake tare da shi cikin gidan nan lafiya''. Na kwanta a gadon da ko a mafarki, ban taba gani ba. Na ja bargon da ko a tunani ban taba tunanin irinsa ba. Na tuno karaunin mu, na tuno ginin gidan mu; katangar ta tsage, rabin ginin ya rufta. Dukkannin mu in damuna ta xo bama jin dadin kwanciya sabida yoyo. Na tuno sauron da ke kumbura mana fata, ba yadda xa muyi da shi, sai dai mu bishi da duka da hannun mu, in bamuyi sa'ar samun sa ba, ya dawo kunnuwan mu yana mana eho, ya sha jinin mu, muxo dukan shi mu doki kan mu 48. Idan Allah ya raya ni, xanyi amfani da karfi da lafiyar da Allah ya bani, duk da kasancewa na diya mace, in ga na fitar da Baba daga rayuwar saida KALWA, in kai Sadiya da Jafar makaranta, in fiddo Amarya daga hawa salga mai tsutsotsi, itama ta hau tangaren. In kai Ya Auwal abinda yafi so a rayuwar shi (karatun Jami'a). Na runtse idona a hankali, hawayen tausayin ahalina, shi ke xuba min, mai xafi da daci a xuci. Yanxu dama akwai wanda Allah yayi wa baiwar rayuwa irin haka cikin kasar mu? Basa ko tunawa da 'talaka' wanda ke wuni yana digar gumi, don kurum ya samarwa iyalin shi abinda xasu ci balle su taimake shi? Meye amfanin shuwagabannin mu, me suke yi na taimakon 'yan kasa, musamman talakawa? Bamu ganshi ba. Sai dai su kai 'ya'yansu yin karatun shedanci a kasar waje, su sayawa matan su motoci na garari, su tamfatsa ginunnuka tamkar baxa amutu ba aikin kenan. Ni ko in nice da kudi, a ganina na talaka wanda ke bisa hanya ne, rana tana dukan su, suna neman abinda xasu sa a bakin salatin su. Kaico! ************* Washegari tunda na tashi da asuba ban koma ba, tunda kuwa na riga na saba da hakan. Na tuna su Baba nayi murmushi, nasan yau xasu samu karin kumallo mai kyau, tunda sun samu 'yan kudin wanke-wanke. Sai da gari ya waye Tom ya shigo da 'tray' yace ''Tine, ba dai har ka tashi ba'' nayi murmushi ''na tashi mana, tun asuba, ni bana dogon barci''. Na fito falon na tsugunna na gaida shi, na lura ya ji dadin girman da na bashi yace ''kaima sai ka xauna shiru, maimakon ka kunna t.v, ana programme mai kyau a B4u Movie''. Ko me yace, oho! Ya jona waya talbijin ya kama, ya dauko wani abu baki yaxo gaba na ''wannan shine 'remote', in abinda kake kallo bai maka ba, sai ka yi ta danna nan xai yi ta canxawa, har sai kaxo wanda yayi maka. Ta nan ake kunna t.v'' ya dauki wani irin sa amma fari ''da kin danna nan, A/C xai kama, nan kuma xai mutu, nan xai kari, nan xai ragu....'' 49 ..haka yai ta nuna min, sai da na tabbatar mishi na gane yace ''ka gane? To kunna min A/C yanxu'' na kwa danna ta kama shuuuuu!. Yace ''in xa'ayi wanka, a wannan bandaki, ya xa'ayi?'' ''Xa'a toshe rariyar kwamin ne, a kunna famfo wanda ake so (mai xafi ko mai sanyi), sai a shiga a cuda da soso da sabulu''. Ya tintsire da dariya yai mun tafi guda uku ''da alama xamu shirya da kai, Tine, domin kai yaro ne mai saurin fahimta, ga karin kumallon ka nan, ni xani makaranta, sai sha biyu da rabi xan dawo, din ba ni xan daura lunch ba (abincin rana) Ejiro ne'' 50. Ya juya xai fita, sai kuma ya juyo, ''af, Madam tace a gaya maka, in ka kintsa kaje can falon jiya, yau xaki fara dutyn ki''. Na bude farantan gilashin da ya aje mani, kodayake tun kamin in bude naga abinda ke ciki, kasancewar sa garai-garai. Farantin farko kwai ne aka soya mai kauri da ayaba da dankalin turawa, dayan farfesun koda da hanta ne, sai wani abu a kwalba mai kama da ganda (Jam), sai da na diba hoton dake jiki, na fahimci a biredi ake shafawa, sai wani irin dogon biredi mai kyau da laushi, a gefe filas din ruwan xafi ne da dan karami dai-dai cikina, da sauran gwangwanaye da kwalaben da na fahimci duka a shayin ake xubawa. Na ci iya ci na, kunnena kamar xai tsinke don dadi, sai girgidi yake. Santi kam nayi shi har na gaji, sai dai a bakina abincin ba dandano na rashin sabo. Nayi wanka nasa 'yar atamfar da tafi kowacce kwari cikin kayana. Ko mai ban tsaya shafawaba na bi hanyar jiya, xuwa kayataccen falon. Na taddata tsaye tsakiyar dakin tana magana cikin wani abu, mai kama da abinda naji Tom ya kira 'remote' (a wancan lokacin mutane dai-dai ke da wayar hannu a Nijeriya), sanye take da siket iya gwiwarta, rigar jikin ta iya cibinta, wanda hakan ya baiwa tirtsetsen cikin damar watayawarsa yadda yake so, abin babu ko kyawun gani. Ban taba ganin cikin mace haka muraran a sarari ba kamar randa, sai yau. Yau ma kamar jiya, kan ba hankali. Ke da ganin yadda take maganar, tana karkashe 'yan kananun idanun ta, kinsan da Maigidan da ake masifar so a ke. Abinda ma na tsinkaya xance na ne, don naji tana cewa ''wallahi baka ganta ba fa, baka kirin, 'yar siririya kamar kaxar mayu, kafafunta kamar na shanshani, idanunta ribda-ribda ga tsummokara a jikin ta babu kyawun gani, hakoran ta yalaye sharr, ni kam tsoronta ma nake, don bata yi mun kama da mutane ba. [9/24, 9:14 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/5, 7:50 AM] A A Dboy: Tuna Baya 51-55 51. Tunda taxo gidan 'atmosphere' na gidan bakidaya ya canxa, gaskiya tabi Talatu su koma, in ya so a nemo wata'' ban san me ya gaya mata ba, naga ta tsuke fuska, can kuma ta ja tsaki tsuuuu! Tayi wurgi da abin maganar, dai-dai lokacin da Talatu ta shigo, ga dukkan alamu, tayi shirin komawa KARAYE ne. Hankalina ya tashi ainun, tsoron matar ya kara kamani, gashi kuma itama tace ni nake bata tsoro. Ni kaina nasan sirinta na yayi yawa, amma ban san wani aibu a halitta na ba bayan wannan. Ta dubi Talatu ''nayi magana da direban da xai maida ke, ga wannan inji TAHEER ki sha ruwa a hanya''. Ta fiddo rafar kudi sababbi, ta xari goma ciki, ke da gani kinsan kwangen kudin tayi, duka aka ce ta bayar. Talatu tasa hannu biyu ta karba ta fadi tana godiya. Tace ''kamin ki tafi, ga wannan 'dettol' ne da 'anticeptic soaps', ki hada ruwa mai xafi ki xuba su a ciki, suyi kaman awa guda, kisa yayrinyar nan ciki ki cudeta, musamman hannuwa, kafafu da kasan hammatarta, ki tabbatar sun fita fes, kiyi ta canxa ruwan kamar sau goma. Sannan ga wannan 'brush' da 'maclean' ki dirje yalayen hakoran nan nata ban son ganin su, xuciyata tashi take. Direba xai kaiku saloon ayi mata wankin kai, duk wata kwarkwata da birbishin amosari, xanyi masu waya, su dirje shi. Sannan wadannan tsummokaran na jikin ta, da wadanda aka shigar dasu daki, kije ki tube maxa- maxa a fidda mun su a gida tun basu jawo mun sauro ba. Daga saloon xai kaiku boutique, ki xabo mata kayan sawa, wanda ba'a dinkawa. Idan naga xani a ciki, Ubanta xan ci. Ku tashi ku fice mun a falo, sauran in ga an saba umarni na daya''. 52. Sum-sum muka tashi muka fito, kamar an rarrade mana gwowoyin mu da murfin kwano. Talatu na cuccudani a baho tana hawayen tausayin tafiya ta barni da wannan mai halin yahudawa, gata dai cikakkiyar bahaushiya kuma musulma gaba da baya, amma kwata-kwata babu tausayi da kyautatawa cikin al'amarinta. Tace ''Oh ni Talatu ya xan yi da amana? Ban san rashin mutuncin matar nan ya kai haka ba, ina jin labarin ta wurin bayin gidan Maimartaba da 'ya'yanshi duka, ban xaci ya kai haka ba, me xan ce da Maikalwa? Ni kam ko a jikina. Babana fa xa'a baiwa naira dubu goma a wata, abinda ko ma'aikacin gwamnati mai digiri, ba'a basu a ranar su ta farkon fara aiki. Baba da Innata ne fa xasu ci jan miya, su daina dumame. Yayana ne fa xai yi karatun da watakila watarana, ya hanani wanke-wanken; ya rungume mu cikin inuwar iliminsa. To me xai sa inji ciwo? A karkashinta nake, a karkashin inuwarta ne xamu ji sanyi ni da iyaye na! Wulakanci yana tofo ko yana taimakon dan adam? Ban xo don ta yabi halittana ba, sai don samun halalina! ''Hajiya Talatu na gama ki da Allah, kada kice da su komi game da halin Uwargijiyata. Ni nace naji na gani, ko me xatai min, xan iya jure xama da ita''. Ta share fuska ''shikenan Atine, nayi miki alkawari baxan bari Maikalwa yaji ba''. Wani irin inji ake tura min kai, na dauka fille shi xai yi, sai naji ashe wai cuda sumar kaina yake, aka wanke tas, yasha sahfe-shafe da mulke-mulken mayuka masu kyau in banda kamshi mai dadi ba abinda yake tashi. Mamakin da nake, wai gashi ma yayi matsayin da xa'a bude mishi irin wannna kasaitaccen waje domin sa? Ni kam jikina yayi dadi, kaina yayi sayau, kaman an dauke min nannauyan kaya aka, iska na shiga ta ko'ina. Kayan da Talatu ke xaba, rigunane da su dogayen ruguna da pakistan masu dan karen tsada don tace mata baxan sa wando ba. Bamu dawo ba sai bayan axahar, direba ya juya da Hajiya Talati Karaye, ni kuma na rungumi jakar kayana na nufi dakina cike da kewar ta. 53 Tom ya kawo min abinici yana tamin bahaguwar hausar shi ina dariya, wai kwana daya kawai yaga nayi kyau, ga gashi mai kyalli yaga ya leko. A hankali sai ya mantar dani kewar Talatu. Ya kunna mun talbijin nace ''ni dama ka kashe ba jin abinda suke fadi nake ba, sai dai cikani da sur-sur-sur'' yayi dariya sosai ''idan kayi alkawarin koya min Hausa, ni kuma xan koya ma turanci, har da rubutu da karatu''. ''Xan koya maka mana. Hausa ba wuya, ko yanxu ka iya hausa, matsalarka daya kana ba mace sunan namiji, shikima namiji ka bashi sunan mace'' ''haka english abu ne mai sauki, Tine, in har kasa kanka xaka iya''. Ya koma, jim kadan ya dawo da farar takarda da alkalami ''wannan shine pencil da dan boko ke amfani dashi yayin koyon rubutu'' ya rubuta wasu haruffa daban-daban, kira su a nitse A, B, C, D. Yana fadi ina fadi har ya tabbatar na rike su a bakina. Yace in dubesu sosai in gane yadda ake rubuta kowannen su, na kuwa daddage na rubuta mai nan da nan. Cikin dan lokaci, kirista Tom, ya fahimci Atine yarinyace mai saurin fahimta, da xata ke makaranta, da anka kwaruwar yarinya. A daren kadai ta haddace A-Z sai dai rubuta su ke wahalar da ita. Washegari kamin ya fita sai da ya jaddada min in haddace rubutun su kafin ya dawo, in har ina son sabon darasi. ********** Nayi wanka kamar yadda Talatu da koyar da ni, wato sai xuba abubuwan roba a ruwan wankan (turaren wanka, dettol da sauran abubuwan kashe kwayoyin cuta), sai naji fatata har wani tsantsi take, wani danko-danko da wani maiko-maiko da naxo dashi na kauye, duk ba ko kadan, haskena ya fara fitowa, na taje dogon siririn gashina na kallabe shi kalba daya, ta sauko har dokin wuyana na nufi sassan Uwargijiyata, sanye da farar karamar riga da ruwan bular siket mai fadi, yau ma waya take, amma kwance a cikin kujera... ''wallahi na sa Tom ya dinga bata abinci sau uku a rana... Me? In yi hira da ita? In ji ko tana da matsala? Tab, kaima kasan impossible (ba xai yiwu ba... ban bata aikin ba tukunna, sai na..... gama tsaftace ta... Kayi hakuri nace ko? (Ta sassauta murya) ai yau xan bata dama, ni kaina dattin ya ishe ni, dakina har yana ta soma taruwa...'' tayi tsaki ta yi cilli da abin maganar ''stupid kawai''. 54 Nayi mata sallama ta juyo, na xube a kasa na gaisheta, ta amsa kamar tayi bal da ni cikin kufula da daga murya tace ''sai yanxu kika ga damar tashi? To nan ba hutu kikaxo ba, kinji mai kafar shanshani? Ba a banxa xaki ci kudin aiki ba da lafiyar mu, lokacin mu da ilmin mu, mu hana idanuwan mu barci mu tafi mu tafi nema. Ki bar ganin komi baja-baja kamar na banxa, a kididdige yake cikin gidan nan. Na fiki sanin muhimmancin 'naira daya' sabida ni aiki nake tun safe har dare, yanxu haka da kika ganni a gida, hutun haihiwa na ke. Don haka in xaki yi aiki, ki mike kiyi axama. In banda Fulani ta kawo ki, ke dinnan baki isa kiyi mun aiki ba, ke duk 'yan garin ku ma wallahi baki isa ba. To ba yadda xanyi, tunda na auri Dan da Uwarsa ke juya al'amuran shi. Daga yau karfe bakwai xaki dinga tashi masamman in na koma aiki, kixo ki gyara mun daki da sassana gabadaya, ki wanke min toilet ki canxa min xanin gado kullum. Peter xai xo ya nuna miki yadda ake komi. Iya kacin aikin ki sassana ne kawai ba ruwanki da sauran bangarorin ko apartment na maigida na, duka aikin Peter ne. A sanda muka ci abinci sannan ake wanke kayan ba sai an barsu sun bushe ba, kina jina?'' Na gyada kai da sauri. ''Yaya sunan ki?'' ''Atine shine sunana'' ''meye kuma Atine? Atini ciwon kashin yara da naji ana fadi?'' ''A'ah sunan rana ne'' ''to meye na daren?'' ''Nima ban sani ba sai iyaye na, tunda na taso, Atine suke ce mini'' ''to na ji, ni a wuri na baxan iya fada ba, domin yana tuna mini da kashin yara. Daga yau sunan ki a gidan nan 'BLACK'. Sai ka'idodin xaman gida na. Da farko dai bama rasa abinci, duk abinda kike so Tom xai dafa ya baki. Iyakacin yawon ki daga nan sassan da xaki dinga gyarawa sai can dakin girki wajen Tom inda xaki dinga yin wanke-eanke. Babu 'yar aiki mace cikin gidan nan balle ki sami kawa, su Tom kiristoci ne da Inyamurai, don haka ki maida hankali kan aikin ki kadai, ko tsinke bana son gani cikin sassana. 55 Xakiyi wanka sau uku a rana, safe, rana da dare don karki canxa min atmosphere na daki kamar farkon xuwan ki. ''Ba yawo, ba kawa ba kaxanta''. Sune ka'ododi na. Idan miji na yana gari, kada ki sake in ganki a hanyar sassannan, domin in ya ganki, amai xai yi. Ko xaki xo kwasar kwanukan abinci, sai kin tabbatr ya tashi. Duk ranar da tsautsayi yasa ya tambayeki, ko ina kyautata miki? Kikace ba haka ba, wannan dogon jelar gashin da ke reto a wuyan ki xan cinnawa gas da ashana, kinji abubuwan da na gaya maki?'' Na gyada kai ''to Hajiya''. ''Uwarki ta kauye yaushe ta je Makkah da har kika sa mata Hajiya? Suna na, MUBINA, amma 'yan aiki na suna ce min ''Madam'', amma ke tunda 'yar wanke-wanke ce xaki ce mun Aunty''. Na gyada kai don tabbatar mata na ji abinda tace, na kuma dauka. Ta xaro ido tace ''ya sunana?'' ''Aunty Mubina'' ''ke kuma fa?'' ''Atine 'yar gidan Maikalwa'', ta mike ''nace miki 'BLACK' kin ce ATINE', sunan da na tsana a rayuwata. Har da bayanin gidan ku ko daddawa ce gidan ku na tambaye ki? Bari in baki maganin mantuwa, shige mu je''. Na bita a sanyaye, duk jikina ya mace. Tafiya muke lngu-lungu har muka xo kayataccen dakin da xuciyata ta gaya mib kichin ne, ba don nasan amfanin kayayyakin dake wurin ba, illa don ganin tukunyar girki da na yi. Ta bude wani farin abu kato mai fadi, iri biyu ne da dogo da gajere, ko ince dana tsaye dana kwance mai fadi, to mai fadin ta bude wai in shiga, bayan ta fidda lemukan dake ciki. Tsoro ya kamani, jikina ya soma kyarma, ta daka mun tawar data firgita ni, nayi kundumbala na fada, ta rufe kif, duhu ya mamayi ganina, wani irin sandarewa naji tsokar jikina nayi, in shaki numfashi, inji kamar ana tura min kankara a hanci. Nayi kara ba murya, sai can ta bude ni na fito, duk na sandare ji nake tsokata kamar ba tawa ba, da kyar gudun jini ma bai daskare a jikina ba ''gobe in kara cewa sunan ki ''Black'' ki ce ''Atine'', in kara gaya maki abu ki manta, shige ki tafi''. [10/5, 7:50 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/5, 7:52 AM] A A Dboy: Tuna Baya 56-60 56. Jikina sai bari yake da karkarwa, na kunna tafasashshen ruwan nan na surka kadan na shiga ciki na kwanta na soma kuka, jikina yayi min dadi naji ana kwankwasa kofa, na maida kayana na fito. Tom ne ya shigo yace ''maxa-maxa'' inje in yi wanke-wanke, ta gama karin kumallo, idan kuda ya hau mata kwano, komi tsadar shi a shara take sakawa''. Tun bai rufe baki ba, ai ni tuni har nayi nisa da gudu na, dariya ce sosai ta kamashi, ya tabbatar ba karamin tsorata nayi da Aunty Mubina ba. Na kwaso kwanukan na fara wankewa. Cikin wata guda kacal na fahimci Aunty Mubina kakaf. Irin mutayen 'yan gayun nan ne da har gayun ya so ya shafi ingancin addinin su. Tana son duniya, kuma ta same ta a yadda take so, tana cin karenta ba babbaka, cikin katafaren gidan ta kuma babu wulakantacce kuma kaskantacce a gareta kamar dan aikinta. A wurin ta dan aikin ta dabba ne kurum, da idan taga dama, xata ce ya kwanta ta taka shi ta wuce. Gogaggiyar mace ce 'yar duniya kuma 'yar boko, 'yar gata kuma wadda ta dauki auren ta da suna kawai. Abin nufi, komi da ke gabanta yafi auren muhummanci, haka rayuwar auren su da mijin ta, irin rayuwar auren nan ce ta kayi gabas inyi yamma, kowa yaje ya nemo nasa, ba mai jiran dan uwansa yaxo ya bashi. Duk da bansan hakikanin aikin ta ba na fahimci ba karamar ma'aikaciya bace, sabida irin jama'ar da take mu'amala da su, da irin motocin da take hawa na kece raini. Babban abinda yake bani mamaki da Uwargijiyata shine duk gayunta, ballagaxa ce, bata da kintsi ko kadan. Hatta panties din ta da bra in ta tube nan tsakar dakin take cillarwa, ni xan dauka in wanke in adana mata. In kuwa xata shirya, sai ta hautsina bakidaya dakin ta rikirkito da dukkan sitturun da take cikin sif. Komi ta dauka, haka xata cillar dashi komi tsadar shi, sai ni in bi in gyara, haka ko kayanta masu datti, bata san ta fitar ba a'ah, ni xanyi tunanin ai tasa wadannan jiya, in xauna kullum in ware mata masu dattin. 57 sannan duk iya kokarina kullum aikina baya gamsheta, bayan sau dubu xan gyara, sau dubu xata bata, barin ma in bakin ta sun xo sunyi ciye-ciyen su, ni kuma a ranar ba dai hakarkarina yaga katifa ba. Xagi kuwa da aibantani da take a cikin su, har ya xame min jiki. Rannan ina ji tana ce da aminiyar ta Mansina ita dai Allah ya isa tsakanin ta da mijin ta da ya hana Peter gyara mata daki, don bata ga abinda nake tsinana mata ba. Rannan kuma naji tana koka mata bakin cikinta akan wannan cikin da take dauke dashi, don bata son tayi (losing shape) dinta, kuma ko ta haihu baxata shayar da jaririn ba, kada mamanta su rankwafa. Nanny xata dauko daga turai. Mansina tace ''wace Uwa kika taba gani ta haihu lafiya, nonon ta lafiya bata shayar da jaririn ba?'' Ni dai nayi gaba ina mamakin hali irin na Aunty Mubina, domin yahudawa ta dora rayuwar ta akai, ita kuwa cikakkiyar bahaushiya ce gaba da baya kamar yadda Tom ya gaya mani. A ganina girman kanta yayi yawa, domin bata aje kanta anan kusa ba, daga Inyamurai sai Nupe, da ake debowa daga Jihar Neja, rayuwar ta mai tsada ce fiye da ta su Mansina. Ranar wata lahadi ina canxa mata xanin gado lokacin ta shiga wanka, na jiyo ta tana nishi da wani irin wahalallen numfashi, na saki xanin da gudu na je na kwankwasa kofar nace ''Anti ki bude'' da kyar tace in murda kofar a bude take. Na murda na shiga sai na ganta kwance male-male cikin ruwa da karnin dana tabbatar na haihuwa ne, domin a irin yanayin naga Amarya lokacin da xata haifi Sadiya, na karisa da gudu na kama ta nace ''Aunty haihuwa xaki yi'' duk da halin da take ciki sai da ta dalla min harara cikin karaji tace ''kirawo min Peter'' nace cikin mamaki ''Aunty to gyara xanin ki'' wani kofin wanka ta wawuro ta maka min a goshi, ba shiri na fito a guje neman Peter, mukayi karo da Tom yana jera mata karin kumallo, cikin kaduwa na gaya mishi Aunty nakuda take yi tace a kira mata Peter, bai kira shin ba ya dauki waya ana falon ya kira likitar da ke xuwa yi mata awo..gida cikin mintuna goma sai gata ta iso, wata nurse biye da ita ta riko mata kayan aiki, da saurin su suka shiga toilet din da Aunty take 58 Shiru-shiru, in kai gwauro in kai mari a tsakiyar kayataccen falon. Allah ya gani, ina matukar tausayawa iyayen mu mata a yayin haihuwa. Duk da ban taba yi ba, nasan ba karamin hikimar Allah ce cikin ta ba. Don haka na daga hannu ina nemawa Aunty Mubina sauki cikin nakudar ta, ban san sanda hawayen tausayi suka xubo min ba, duk gayu irin na Aunty, in ka ga yadda ta koma lokaci daya sabida axaba, dole ka tausaya mata. Ihun da take kurmawa, da xagin da take narkawa mijin ta abun babu dadin ji, data lailayo wani ashariya ta yarfa mishi sai da gidan baki daya ya amshi kuwwar, fadi take ai sai da ta gaya mishi bata shirya haihuwa ba ya sace mata pills dinta, ya hada ta da jangwam, ya tsallake ya barta, amma anyi na farko anyi na karshe ita da shi sai a lahira, tunda ya fuskanci watan haihuwar ta ya kama ya gudu yana hutawar shi a turai ya barta da bala'in da ya kunsa mata. Babu kiran sunan Allah babu na Annabi ita dai ya jawo mata ya gudu ya barta, tsakanin ta dashi Allah ya isa. Tom yayi tsaki ya juya ya fita bayan yasa yatsun shi biyu ya toshe kunnuwan sa yana cewa, baxai iya jurar toxarcin da akewa Ubangidan sa ba. Sai kace a kanta aka fara haihuwa. Sai karfe hudu na yamma su Aunty aka sami kai da kyar. Jariri ya canyara kuka da xaxxakar muryar shi kamar gyare, yana gaya mana ya iso gidan Ubansa. Jaririn da ya juya rayuwata da ma rayuwar gidan bakidaya. Tunda Aunty ta haihu bamu xauna ba, hidima muke da karfin mu da lafiyar mu kamar babu tsokar nama a jikkunan mu. Baki ne ke ta barkowa daga ko'ina cikin Abuja duka ta bangaren Aunty, amma ko kuda na lura babu daga masarautar Karaye, wato dangin maigidan. 59. A kullum Tom ya daura tukunya ya sauke sau goma. Ni kuwa shara, wanke-wanke da goge-goge kamar inji don ma yawanci komae da inji ake yin shi. Akwai wata kanwar Aunty mai suna Mimi har fargabar xuwanta nakeyi domin in ta soma ''ke Black, dauko min kaxa, karbo min kaxa, miko min kaxa har sai kafafuna sun sare. Ana i gobe suna kuwa kafafun ta tasa a ruwa wai in goge mata kaushi, taje wajen wankin kaushin sun tashi gashi gobe xasuyi luncheon din suna. Cikin mamaki na dube ta, ba tare da ko dar ba nace ''wannan ba aiki na bane. An dauko ni shara da wanke-wanken Aunty, amma ba'ace da Ubana xan dinga yin gugar kaushi ba''. Daga hannun nan da xatayi sai fuuuu! Ta dauke ni da mari tace bari inje in ji idan ita maijegon ne tace ki dinga yi mun rashin kunya. Ai dama da ganin idanun nan naki kwala-kwala nasan yarinyar nan ke nan gaba abin tsoro ce. Ina daki ina ta kuka Aunty ta fado dakin ta soma surfa min xagi, tace daga yau Mimi ta sake sani aiki nayi mata musu, a bakin aikina. Bayan sunan da akayi shi da sati biyu ga yadda na fahimta maigidan ya dawo, aka sake wata walimar a rockview, wadda Tom ya kawo mana jarida mai dauke da hoton Aunty da Babyn da fuskarshi ke kushe cikin farin showel matar shugaban kasa na mika mata kyauta, nade cikin wata leda mai kyalkyali, cikin mamaki nace ''yaya Baban Babyn bai shigo hoton ba?'' Yayi murmushi mai nuna matukar girmamawa ga wanda na ambata yace ''Ogan mu, ba daya yake da sauran mutane da kika sani ba''. Tunda aka haifi Dan nan bamu san kalar shi ba, sabida yadda ake kulawa da shi ko kwai sai haka, sai dai mu hangoshi daga nesa a hannun baki masu xuwa, wadanda kallo daya xakayi masu kasan sune jama'ar Aunty Mubina, wato daga matan ministoci sai na manyan ma'aikatan Banki abokan huldar ta, da basu san me ake kira talauci ba. 60. A wata asabar ce Aunty da Mimi sun baje kyaututtukan da Babe ya samu suna hira, ni kuma ina durkushe gaban t.v ina gogewa, Mimi ta dube ni tayi tsaki tace ''wallahi Aunty ko kadan yarinyar nan bata dace da aikin ki ba kwata-kwata ba ajinki bace, wai baki san ko 'yan aiki yanxu ba kowane irin kwashi kwaraf ake dauka a Abuja ba? Kin dauko yarinya sai tsayi xankankan da manyan ido kaman ta cinye mutane, ni wallahi duk sanda naga dubeta sai naji gabana ya fadi, sabida tsoron da idanun ta suke bani'' Aunty ta yarfar da hannu, tace ''oho! Fulanin Sariki ta aiko da ita kema kin san ban isa in maida ta ba, dama kadan ake jira a aibata ni, don ita ke xuge shi wai bai dace Peter ya dinga shiga uwar daki na ba...'' Mansina ta jirkito daga cikin kujerar da take kwance, ta dubesu daya bayan daya tace cikin mamaki. ''Wadanne idanuwa ne suke baku tsoro, kodai suke saku kishi? Ki dubi idanuwa sparkle (masu walkiya) kuce suna baku tsoro?'' Ni dai jikina na rawa nayi hamxarin fita na barsu batare da naji amsar da Auntyn ta bata ba, bam san yadda suka kare ba. Sai dai daga ranar na fahimci Aunty ta kara daure mini sosai haka duk wata kafa ta hutu, ta toshe mini ita a gidan. Baby nada wata daya, watarana ina wanke-wanke kwanukan da aka ci abincin rana, Tom yana tsaye daga can baryar sa yana can kiciniyar daura tukwanen dare. Wata murya muka jiyo daga can kofar shigowa tana kiciniyar shigo da akwati tare da neman ixinin shigowa falo. Ba muryar matar ne ya samu fitowa dukkan mu ba illa yaren da take magana dashi. Ni dai nasan wannan ba hausa bane kuma ba yarbanci ba haka ba fulatanci ba. Wata yamusashshiyar baturiya ce, da alama ko cikin turwan wannan babu wata wadata a jikinta, tana tura akwatuna masu taya guda biyu (trolley), gashin kanta ja ne irin turawan nan masu jan gashi da ake kira blonde, xatayi shekaru arba'in, Tom ne ya amsa mata yayinda ni kuma na saki baki ina kallonta, shi yayi mata jagora xuwa falon Aunty..., [10/5, 7:52 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/7, 7:07 PM] A A Dboy: Tuna Baya 61-65 61. Can anjima Aunty ta rika kwala min kira na je na tsugunna a gabanta, tace ''kwashe shirgin ki daga dakin ki, ki maida su dakin da ke kusa da shi, wannan falle dayan, Tom xai kwashe injinan sharar da ke ciki, na bayar a sayo maki katifa'' nace ''to'' murya ta abin tausayi. Ina kwashe kayan ina hawaye don ba karamin sabawa da dakina nayi ba, duk da cewa shima wancan dakin cikin bangaren Auntyn yake, amma babu toilet, don haka nakoma na tambayeta ko da wane toilet xan dinga amfani? Ta kunduma min ashar tace ai talaka wai iya samun wuri ba, a gidan Ubanki ba a filin Allah kike kashin ba? Kamar ince da ita ai in ma a filin Allahn ne, akwai kasar da xamu haka mu bixne, nan kuwa fa? Da tangareren shine abin takawar ku? Sai da taga dama tace in dinga shiga dakin muna amfani dashi mu biyu. Daga baya Tom yake gaya mani mai raino ce baturiya Aunty ta dauko bada sanin Oga ba, sabida a gobe ne xata koma aiki, tuni ta so ta dauko ta tun Babyn yana sati biyu sabida hutun da aka deba mata ya cika. Yace Oga yayi-yayi ta aje aikin nan ta kula da yaron taki, nonon ma da take bashi, wanda ba kullum ba, ba karamar badakala a ka kwasa da ita ba kafin ta yarda ta dinga ba shi sau uku a rana, sai da yayi karar ta gun Baban ta tukunna. Don tana tsoron Baban ne yasa take bashi amma ita tana ganin rainon yara bai dace da ita ba wannan lokacin da take kan gabar kuruciyar ta, haihuwar ma Allah ne ya kaddari yaron mai numfashi ne a doron kasa, amma bata shirya mata ba, ba kuma kokarin da bata yi ba don xubar da cikin abin ya ci tura, karshe dole ta hakura, don har kasar waje ta je a fitar mata sun tabbatar mata ko dai ita a rasata ko mahaifar gabadaya, sabida cikin ya girma sosai a lokacin shiyasa ta hakura. Nace ''amma da aka haife shi ai gashi nan tana son shi, ko kuda bata bari ya taba mata shi''. Yace ''wannan ne kuma bani da tabbas a kai (tana son shi ko bata son shi?)'', Tun xuwan Elizabeth bama jin dadin xama da ita, kwata-kwata ta maida mu 'yan aikin ta sai kace itama ba 'yar aikin bace. Ita aikin Baby kawai take wanda nake ganin kullum ta sa shi cikin wani keke ta tura mai fankon fida a baki (kan fida kawai babu fidar da turawa ke sarrafawa don hana yaro kuka) ko ta dau keken goyon jarirai ta hada da bayanta ta kulle, bayan ta sanya shi a ciki, tana harkokin ta ko kallo bamu isheta ba. Wani xubin kuma sai ta sashi cikin wani irin lilo mai kamar gado tana cillawa a hankali, hatta madarar da take bashi a kididdige take, sai ta auna, ko kusa ko da wasa bata bari wani cikin mu ya je ko kusa da shi. 62. Duk abinda Tom ya dafa sai tace bai yi mata ba, ya sake dafo mata wani. Wata rana kuma taje kasuwar Wuse (Wuse-Market) ta sayo kaguwa da dodon kodi taxo ta soya, yawancin abincin ta kwari ne, in ta so kuma ta aiki Peter manyan gidajen cin abinci dake cikin Abuja ya sayo mata abincin kasarsu, wanda duk rabin su tsutsotsi ne da ganyayyaki. Ranar da na fara ganin ta tana loma da tsutsotsin nan, wuni nayi ina kwarara amai sabida kyankyami, daga ranar kuwa ko plate ta taba bana kara cin abinci da shi, ita kanta ma tsantsamin ta nakeyi. Gata da kaxanta a toilet, sai ta cire auduga (pad) batacciya ta ajiye a kan bahon wanka, sai dai ni da abin ke daga min hankali in dauke mata. Ko ta jika kaya taki wanke su sai sunyi tsami haka tun xuwanta bandakin mu yake wani irin xarni. Ni dai na ji an ce turawa suna da tsafta, amma wannan ko a cikin kaxaman turawan ma ta daban ce. Ko brush tayi bata san tasa ruwa ta wanke kumfar daga cikin sink ba haka xata barta ta bushe, ko kuma ni in wanke mata. Gata da fadan tsiya, Tom boyi-boyin ta, Peter dan aiken ta, ni kuwa 'yar aikin ta, Ejiro da baya sakar mata fuskar har da xata raina shi, shi ta mayar makiyin ta, kullum cikin bata shi take a wajen Aunty, don dai Auntyn tana son aikin sa ne kawai da tuni tasa an sallame shi. Tsaye muke ni da Tom a kicin kowa na aikin sa, yayi kwafa yace ''nifa xaman matar nan ya ishe ni Tine'' nayi dariya nace ''da yake kai ka ajiye ta ba?'' yace Allah ba xancen wasa ba, kiga kullum sai na gama abinci taxo tace bai mata ba, in sake, an gaya mata aikin ta nake, Allah ko Oga na ban taba yi mai girki yace bai mishi ba, sai wannan matar, who the hell she thinks she is, tana 'yar raino ina kuku, matsayin me ta fini?'' Nayi murmushi da ya kara kular da shi don ni kadai nasan hakurin da nake da Elizabeth, shi nashi shafar mai ne ''kome yake yi daurin gindi ta samu daga Uwargijiyar ta, amma da baxa ta yi ba''. Tom ya kuta yace ''ban ga dama ba ne, na rantse da tuni da bar gidannan..., 63 ...don Oga bai san da xaman ta ba, a tunanin shi Aunty na tafiya da Babyn wajen aiki ne'' nace ''akan me xaka fada mishi? Ina ruwan ka da sha'anin su, kai dai kayi aikin ka na kuku, a biyaka ba shikenan ba? Ni ka ganni abinda Allah bai daura mun ba kenan, shiga abinda babu ruwa na. Idan ba so kake Aunty tayi sanadiyyar lalata hanyar abincin ka ba''. Bai yi magana ba, amma yanayin fuskar shi ta nuna maganata tayi tasiri a tare da shi. Rannan Aunty ta tafi aiki, Elizabeth na wanka ta bar Babyn yana kyankyara kuka, ba tun yau ba ina kallon ta idan har ba Auntyn na gida ba bata wani mai da hankali kan yaron, sai ta bar shi yayi ta kuka har Allah ya gajishshe shi. Naji baxan iya jure kukan da yaron ke yi ba, domin kuka yake har cikin kwakwalwata. Na lallaba na leke dakinta naga bata fito ba, na shiga da sauri na sungumi Babe nasa a bayana, na dau towel din da aka nade shi da shi ina jijjiga shi. Wannan shine babban buri na a rayuwa; in ganni goye da jariri, ina jijjigashi, ina yi masa rawa ina cilla shi ina cafewa. Rabona da goyon jariri tun ina rainon Jafaru. Don haka yau na jini cikin wani sabon nishadi. Shi kuma jaririn da na tabbata ba'a taba goya shi ba, tunda uwar sa ta haife sa, sai yayi tsit daga kukan da yake, yana ajiyar xuciya. Sai naji tausayin yaron ya kama ni. Tausayin sa nake, ba don bashi da gata ba, yana da gatan komi, amma ya rasa gatan da yafi komi amfani da muhimmanci a gareshi, watau dumin jikin Uwa, a dai-dai lokacin da yake tsananin bukatar shi. Na tabbata ba kukan komi yake ba tunda babu yunwa a tare dashi, illa kukan jin sa shi kadai ba tare da kowa ba, balle Uwar da xai laluba ya rungume har ya samu damar tsotson abinda yafi komi dadi a gare shi, wato nonon Uwa. Ban san sanda Elizabeth ta fito ba sai jin ihunta nayi a kaina tana tafi tana kakabin a kawo mata agaji ''Help! Help!! Help!!! The baby will die'' wato Dan xai mutu. Nayi saurin sauke mata shi saboda yadda ihunta ya kidimani ya gigitani. 64. Wai ashe duk wannan ihun da take na goya shin da nayi ne, da gudu ta xo tana tattaba kafafun shi ta gani ko na karya shi? A sukwane Ejiro ya shigo ta shiga gwada mishi tale-talen da nayi wa Baby har tana daukar filo tasa a bayan ta da xani, yayi tsaki ya fice nima na fice yana yi min korafin ni me ya kaini shiga shirhinta. Ashe bata bar xancen ba domin Aunty na dawowa da gudu ta kai mata dan ta tana kuka wai baxa ta iya ba tana gani in kashe shi a daura mata laifi, ta gwada mata yadda nayi mishi. Auntyn ta kira ni tasa ni a gaba, yau ma firji ta sani, wai karambani na yayi yawa, gobe in kara goya mata Da. Don haka washegari na tashi da matsanancin xaxxabi ko gani bana yi sosai, musamman da yake a watan Fabrairu muke, sanyi yayi tsanani ainun. Aka kuma sani a firinji, na kwana hancina na yoyo, kuma a cushe ta yadda hatta numfashi ta baki nake iya futar dashi. S haka na rarrafa na shiga dakin Aunty don ka'ida ne kafin ta fito naa gama da falo, da xarar ta fito sai in shiga cikin dakunan barcin in gyara mata. In banda rawar dari ba abinda nakeyi duk da riga (sweater) mai kauri da ke jikina, ina yi ina hutawa in na jiyo motsi in yi saurin mikewa, in cigaba. Sama-sama na jiyo muryar Aunty da ke 'dinning' wato kwararon da aka xagaye da farin labule da makeken tebur, domin cin abincinsu wanda ke gefe guda na cikin falon, tana lissafo kudin aikin ma'aikata na wannan watan, da alama da Maigidan ta take magana. Yana magana ne a hankali don haka bana jin me yake cewa, sabanin ita da take da karfi, don daga baya ma fada-fada ta koma magana wai babu inda Elizabeth xata, waye xai dinga kula mata da Babyn sai dai in shi xai dinga goya yaron yana tafiya nashi office din, amma ita baxa ta bar aikin ta ba, sabida wani yaro can (unwanted Babe) da yaxo mata ba'a sanda ta shirya haihuwarsa ba. A fusace kuma cikin fada yace ''ina yarinyar da ke maki aiki da Fulani ta aiko daga KARAYE? A bata Babyn ta dinga kula da shi, amma wannan matar yau xata tafi..., 65. Baxan biya wadannan makudan kudaden ba, sabida ba daga kasa nake tono kudin ba. Idan kuma ganin hakan bai maki ba, to xan dauke shi in kai shi gaban Fulani, tunda ke kika haife shi, kin fi kowa sanin ciwon sa, baxa ki xauna ki kula dashi ba. Kina kiran shi (unwanted Baby) Mubina, a gareni yaron nan yafi min komai a duniyar nan da abinda ke cikin ta. Don idan xaki ajiye aikin ki ki bashi kulawar Uwa da ta dace, to, in kuma baxa ki iya ba, to cikin biyun da na baki dole ki xabi daya''. Ga yadda tayi shiru bata kuma magana ba,maganar nasa ba karamin kada ta su kai ba, jin an ture kujera baya na taho falo nace kafa! me naci ban baki ba, kada suce ina labe, bayan kuma ba haka bane, aiki na ne ya kawo ni. Allah bani da wannan halin. Kafin axahar ba sai muka ga Elizabeth ta turo akwati ba tana xumbura baki, Ejiro aka danka wa nemo visa yana tsaye rike da passport dinta a hannu, yace ta bar yafiyar sai jibi wajen visa xasu je. Ni da Tom har tsalle a muka yi, a daki don murnar tafiyar Elizabeth, Aunty kuwa ta cika fafam, kiris take jira ta fashe don haka muma muka shiga taitayin mu ba wanda ya nuna yasan abinda suke ciki. Na shiga aiki washegari, da misalin karfe bakwai na tadda Aunty tayi shirin tafiya aiki, tana xaune a luntsumemiyar kujerar falon ta, tana cika tana batsewa wannan sabida tsabar son aikin ko ince sabida son kudin, ma'aikacin banki takwas take masa a office amma ita Aunty tsabar xafin nama bakwai da rabi a bankin su take mata shi kuwa miji ko oho, don shi kan sa Oga tana riga shi fita. Tom ne ya gaya min cewa Aunty Manajar Banki ce guda don haka nayi mamaki, tace ''ajiye tsintsiyar kixo nan'' da sauri naje na russuna a gabanta ''kina da masaniyar gobe ne Elizabeth xata tafi?'' ''Ban sani ba Aunty'' ''to in baki sani ba gashi na fada maki, don haka xaki dinga kula da JAWAD kamin in dawo don bana son Baban shi ya maida shi Karaye, kina jina?'' Na gyada kai da sauri. [10/7, 7:07 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/7, 7:08 PM] A A Dboy: Tuna Baya 66-70 66. ''Daga yau karfe bakwai da rabi nake fita aiki, don haka xaki xo ki dau Jawad kiyi mai wanka, ki shirya shi yadda nurse xata xo ta koya maki, duk kayan shi dakin ki xasu koma bana son rainon Baby. A rana sau uku xan ganshi, in bashi nono sau uku; da safe kafin in tafi, da yamma idan na dawo da kuma da daddare kafin ya kwanta barci. Idan kuma na yaye shi, a wurin ki xai dinga kwana. Ki cigaba da wanka sau uku a rana, kamar yadda na gaya maki farkon xuwanki domin karki shafawa dana datti. Ayyukan da kike a da, gabadaya an dauke miki Peter xai cigaba da yi, dama shi yake yi. Dakin barci na kuwa tunda ya hana shi shiga, na dinga gyarawa da kaina koda a karshen sati ne in na samu lokaci. Don haka ki maida hankali bisa aikin ki na yanxu kadai, KULA DA JAWAD. Ba'a goya min da, kada a karya masa kafa domin siriri ne. Akwai gadon shi, akwai abin shan iskar shi duk xa'a kawo su wurin ki. A rana xaki canxa mai pampers sau shidda. Ki kwaso kayan ki ki koma dakin ki nada idan Elizabeth ta tafi gobe''. Nayi godiya na mike na fito duk jikina babu kuxari. Daga wanke-wanke kuma na koma 'Nanny' babu yadda rayuwa bata yi da dan Adam. Ta wani fanni kuma ni dama RAINO NA FI SO A RAYUWATA. Dana gayawa Tom yadda mu kai da Aunty, bude baki yayi cikin mamaki, ya kuma fi mintina biyu bai rufe ba ''Tine, ka lissafa kanka cikin masu sa'a a duniya. Uwar goyon Babe Jawad? Xaka ji dadi wurin Oga in har ka ba Jawad kulawa mai kyau. Yana son Jawad, fiye da komi a rayuwar shi.'' Ina wanka da safe naji ana kwankwasa kofa, na sanya wasu sabbin riga da siket jajaye cikin irin kayan da Talatu ta hada min ne. Na bude kofar ba tare da na tambayi ko wanene ba, wata macece mai dan jiki gajeriya, tana sanye da fararan kayan asibiti, da alama mai kirki ce tayi min murmushi tace ''kece mai rainon Jawad yanxu ko?'' ''Eh'' ''ni sunana Sister Sadiya Danladi, (nurse) ce, an turo ni musamman domin in koyar da ke yadda ake yiwa yaro wanka, da yadda ake bashi abinci bisa..., 67. ..ka'ida da sauransu don haka xauna ki saurare ni''. Tayi min bayani tiryan-tiryan har na gamsu nayi mata godiya ta tafi. Washegari da asuba na tashi, karfe bakwai na kimtsa shiri tsaf, irin wanda take so. Na je falo na jira ta har ta fito cikin shirin fita. Na gaishe ta bata amsa ba ta miko min jaririn. Na sa hannu biyu na amshe shi cike da dukkan kulawa. ''Sai karfe biyar nake dawowa, ba'a soma bashi ruwa ba tukunna, sai yayi wata shidda, yau watannin shi hudu, xaki fara shayar dashi madara yadda sister Sadiya ta gaya miki, an kai miki kayan tun jiya sai na dawo''. Na xauna bakin gadona na sanya Babe Jawad cikin ni'imtaccen gadon sa, na kura mishi ido kurrr! Allah gwani tsatstsarka, da ya nufi mummunar mace kamar Aunty Mubina da haifar kyakkyawan yaro irin Jawad. Fari ne sol, sumar kanshi mai yawa baki wuluk, hancin sa dogo xirit, labban sa jaxur 'yan kaurara, kanana, yana da cleft da kyawawan yatsun kafa da hannu. Ban taba yi masa wani kyakkyawan kallo ba sai yau. Kaunar yaron ta tsirga mani tun daga tsakar kaina, xuciyata, bargona, kasusuwa har yatsar kafata. Na fiddo shi daga cikin gadon na rungume shi tsantsan a kirji na, tamkar na tsaga kirji na sanya shi, in haifo shi ya xan mallakina. A haka barci ya sure mu, motsin shi na ji cikin barcin yana shafa ni yana neman nono kenan. Na tashi na farke katon din da ke ajiye gefe, na fidda wata irin madarar yara, wannan ta musamman ce. Hoton kyakkyawan Babie ne a jiki, amma sai naga bai fi Jawad dina kyau ba. Na debi adadin da Sister Sadiya ta ce min, na duba iya lambar da ta nuna mini a jikin feeder na tsiyayi ruwan dumi da ke cikin flask na hada na jijjiga sosai, ya bar shi ya dan shan iska, na xaunar da shi a cinya ta, nasa mai kan fidar a baki, ya ko kama da karfin sa, kadan yaki shanyewa. A raina nace kawai a ce baxan ba dan Adam ruwa ba, sai yayi wata shidda? Don bani da imani ko don me? 68. Yaran gidan mu ana basu ruwa tun a ranar da aka haifesu, kuma sun rayu lafiya, don haka sai na ba Jawad ruwa. In Tom xai kawon abinci, yakan hado da wani ruwa da naji yana cewa FORMOSA table water, naje kithcen na dauko mara sanyi, na xuba a murfin fidar kadan, na daura mai a baki, yaro ya kwalkwale ruwa da sauri, na kara cika murfi, ya shanye, na kara mai, ya rage rabi, yana dubana da kyawawan idanun sa ya shiga bangala mani dariya, nima sai naji dariyar ta kamani. Na sashi a bayana da tawul din sa na goye shi cike da matsananciyar kauna. Ko Uban wa yace mata goyo na karya kafar siririn yaro? Ni har bakwaini na goya, na kuma sauke shi lafiya. Daga goya shi sai barci ya dauke shi, na kwanta rub da ciki da shi a bayana. A haka Tom ya cimmana, hannun sa rike da bakar leda, bai san sanda ya saki bakar ledar a kasa ba ''lalala! Ga goya dan kwan gidannan? Babu goyo, babu goyo, Aunty xata xage ka Tine'' ''Tom mu Hausawa da goyo muka rayu, itama Uwarta ta goya ta, akan me xata ce baxa ta goya nata ba? Akan wani dalili mara tushe da asali? Kayi hakuri baxan bari ta gani ba'' ya kyabe baki, daga bisani yayi dariya, nasan mamakin karfin hali da karambani na yake ''is not my own business'' ''me kenan kace?'' ''Nace (babu abinda ya shafe ni), i brought you something special (na kawo miki wani abu na musamman) wanda nasan xaki yi murna dashi''. Ban ji me yace daga farkon ba, illa naga ya xaro wasu littafai iri-iri daga ledar da ya shigo da ita, duka na koyon karatun turanci da rubutu, irin na 'A for Apple' da sauran abubuwa da sunan su ya fara da A, haka ya tafi har Z, kowanne da hoton abin radau a cikin kala, muka shiga karatu, ko abinci bamu ci ba. Karfe hudu ya tashi ya kawo min farfesun gudar kaxar gidan gona, da biredi wai inyi maneji kamin ya gama girkin dare. Nayi sallar la'asar sannan na sauke Jawad, sai ya bude ido, na sake dama mai madara, wannan karon harda nutrient din da tace kar in bashi wai ya wuce sha..., 69. ...shan shi, abinda local yara ke sha ne, na kuma bashi ruwa, na kaishi cikin robar wankan shi na fidda mai pampers, wadda bai yi komai cikin ta ba sai gumi. Nayi mai wanka da wani irin tsadaddan sabulun Babies dana gani cikin kayansa, bayan na xuba duk wani abu da sister tace in xuba. Ina sanya mai kayan sanyi Tom ya shigo dauke da tray, nace ''da ka koma dashi, wannan ya ishe ni sai ko 'dinner' naji kana cewa ko?'' Yayi min tafi ''Yauwa, haka nake so Tine, ka dinga rike duk abinda na fadi cikin turanci, da haka xaka saba. Daga sati masu xuwa, ka daina magana 'in Hausa'. Sati na xagayowa, na soma yara turanci da Tom, ya dinga kunna min labarun BBC, labarun kasa da sauran su, suna yi da babban turanci yana bani bayani cikin sassaukan turanci, rubutu kuwa na iya rubuta su Ant, Ball, Cup. A satinne ta kara tura ni saloon, da wurin gyaran akaifa, don wai taga alaman yakushi a wuyan danta, bayan shi ya yakushi kan sa. Wannan karon da Tom ta tura ni. Wani yammaci bayan ta fita, na gama dirkawa Jawad abinci na goya shi, na tadda Tom da Ejiro a kitchen, suna ta kiciniyar kwabin coconut-sandwitch da beef burger, abin ya burgeni, ya kuma bani sha'awa, ganin komi da inji suke yi, ba wahalar komi sai ta tsayuwa. Nan na xauna kallon su har suka kare. Na tabbatar abin ya xauna a kaina, ko yanxu akace inyi yadda sukayi, xan iya. Daga ranar duk sanda suke girki, in dai Maman Jawad bata nan, sai in goya shi inje in xauna inyi ta kallon su, muna hira ana kara min bayanin komi. Watarana nace da Tom don Allah ya samo min waken suya (soya-bean), ya tambaye ni abinda xan yi dashi nace wani kamu ne muke sha a kauye. Kullum sai inyi kamun waken suya mai tsabta, in shige da shi dakina in kulle, inyi ta durawa Jawad, shiko komi na bashi ya shanye shi tas. Bama bari yayi awanni biyu ban bashi abinci ba da ruwa, ba ruwana da wani kididdige, shiyasa yake yawan fitsari da kashi, in fidda in wanke shi tas, in canxa masa. 70. Cikin watanni biyu kacal da dawowar shi hannu na yaro ya shiga wata irin kiba da wayo mai ban mamaki. Wani marece Tom yake ce da ni ''Tine ka iya raino mai kyau, hannu ka mai albarka ne. Dubi yadda Babe ya koma daga xuwan shi hannun kam yaro dan siriri ya koma Bouncing Baby''. Washegari ranar naga sun fiddi na'urorin gidan, dukkan ma'aikatan sun kasa xaune, sun kasa tsaye aiki suke cikin kuxari da xafin nama tamkar anayi masu allurar kuxari. Ga wani nishadi na babu gaira babu dalili, tattare da kowannen su. Maman Jawad ta iske ni har daki na tana daga shi da kyar, don wai bata iya daukar shi yanxu kada ya sata ciwon kirji. ''Yau Abban Jawad xai dawo daga tafiyar da yayi Kasar Canada, idan ya nemi Dan sa, ki je ki kai masa, ki tabbatar kin gyara shi sosai, in ya nemeni ki ce ina gidan kwamishina Mansina ce ke fama da mura, amma xan neme shi a waya''. Na amsa da ''to''. Ina sallah, nayi sujjadar karshe ina sadar da bukatu na ga Lillahi, Tom ya shigo, ya xauna ya xauna har ya gaji ya tafi, can kuma ya dawo ''Tine pieous (wato mai Ibadah), ni xani (lecture) sai biyar xan dawo. Mun gama shiryawa Oga Spanish-Lunch, idan xai ga Jawad xai neme ki da kansa, ba ruwan shi da matsantawa irin na Aunty''. Na rungume Jawad a kafaduna da ya soma kokarin tashi daga barci nace ''yauwa! Dama tuntuni ina so na tambaye ka Tom, tun da nake, ban san dan aiki yana da 'yancin xuwa makaranta ba, har ya fita sanda yake so, ya dawo sanda ya ga dama? Imagine!'' Ya kyalkyale da dariya sosai yace ''Ogan mu, mutum ne da baya dannewa dan Adam hakkin sa ko kadan. Mutum ne mai masifaffen ilmin boko. Ba kowadanne iyayen gida bane irin Ogana ba. Bai xama da wanda bai ilmi, shi ba maxauni bane haka matar shi da muke xamanta bata faya xama ba. Mu biyar ne duk maxa, ita ta kawo mu ba shi ba, amma yace lallai tunda munyi sakandire, mu tafi makaranta. Xama a karkashinsa baya nufin bamu da 'yancin sauran abubuwa masu muhimmanci a rayuwar bil adam musamman ilmi. [10/7, 7:08 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/8, 5:11 PM] A A Dboy: Tuna Baya 71-75 71 Ni da Ejiro, muke kuku, don haka muke karantar catering, Peter da Joseph da ke kula da gida, tattalin gida suke karanta, Samson da ke kula da shukoki yana karantar ilmin tsirrai (Botany) a Jami'ar Abuja. In daya nada darasi, daya baya dashi, xai yi aikin gida kamin daya ya dawo koda ba aikin sa bane, wanda yawanci, mu ke cinye abinda muka dafa domin ita bata cin abinda ya hau wuta, sai na gongoni. Shi kuma Oga, asalin shi kauye, bai son wanna tsarin, in yana nan xai bamu odan muyi masa tuwon semovita miyan danyen kubewa da busashshen kifi, yace kunun aya yace kunu xaki. Wallahi idan kinga abinda yake ci, sai ki raina mishi. Matsayin shi; Minister of Foreign Affairs, (Ministan huldar Nijeriya da kasashen waje). Sun yi artabu da Aunty akan xuwan ki, domin a da, Peter ne yake mata dukkan ayyukan da kike yi, Oga yace bai lamunta ba, katon na miji ya dinga mata hidima, ya gayawa mahaifiyar shi cewa a sama mata 'yar aiki mace, kuma karamar yarinyam haka sunyi artabu akan cewa da yayi ke ki dinga kula da Jawad, tunda ta dage baxata bar aikin ta kan rainon yaro ba, domin Aunty ta dauko raino daga Brussel can cikin kasar Belgium (Elizabeth) da xai rika biyan ta tsabar kudin Amurka dubu dari da hamsin a kowanne wata, shi kuma ya dage, wanda ba dan AREWA ba, ba kuma dan masarautar sa KARAYE 72. KARAYE ba, baxai rainon mashi dan jinjirin shi a duniya ba. Ita tana ganin Bahaushe kaxami ne, sai kace ita ba bahaushiyar bane. ('Yar asalin garin Xaria ce). Ki saki jikin ki da Oga mutum ne mai saukin kai, xaki ji dadin xama dashi fiye da Aunty, domin suna tare ne amma halin su daban-daban. Sai dai kada kiyi mata abinda bata so ko kadan, xata ci miki mutunci daga ke har shi, don bata darajashi sam. Talaka da dabba a wurin Aunty basu da maraba balle kuma dan aikin ta. In kinga yadda shi kuma yake jan mu a jiki, yana jin damuwar mu, kamar kannen shi da suka fito ciki daya, wadanda ta haramta masu xuwa gidannan sam, kiyi taka tsan-tsan da Aunty, ''bata da mutunci''. Ya fada ya kara maimaitawa har sau uku, domin kara tsoratar dani ga kowace ce Uwargijiyata (Aunty Mubina). Bayan tafiyar Tom, na dade ina sake-sake, gami da jinjina abinda na ji a raina, ba a jima ba naji dirin ribda-ribdan motoci, na dau Jawad cikin nustuwa nayi mai wanka na fiddo sabbin kayan shi da ban taba sa mishi ba na kakin sojoji, na saka mashi, na xura mai sabon takalmin shi, rufaffe sak dana sojoji mahadin kayan, na taje yalwatacciyar sumar shi na mulke ta da mai mai kamshi, sai kyalli take ta kwanta lub a dokin wuyan shi. Na dauko turarukan shi Dune da Caleutta na feshe shi sosai. Na dura mai kamu na goge mai baki, na bashi ruwa yasha ya koshi yayi gyatsa, ga yadda yake mun rigima nasan so yake in goya shi yadda na sabar mashi bayan cin abinci. To amma ta yaya xan goya shin? Uwarsa ta hana balle Uban sa? Na sashi a kafaduna nayi ta jijjiga shi amma yaki yin shiru, kuka harda digon hawaye. Ejiro ya shigo ''A'ah Jawad kuka kake, why? Papa ya dawo'' ya karbe shi ''Nanny Tine, Oga wanna see his son, gashi yana kuka'' nace ''goyon da nake mai yake so, gashi bana son su san ina goya shi, kai dai kai shi hakan, watakila in ya ga Uban yayi shiru''. (An dan jima Ejiro ya dawo) ''kixo ki goya shi yace''. Gabana ya fadi dam! Xuciyata ta tsinke, na fiddo 'yan idanuwana hantar cikina na murdawa, muryata abun tausayi nace ''Haba Ejiro? Meyasa kace ina goya shi? Idan ya gayawa Aunty fa?'' Ejiro ya kyalkkyale da dariya, yayi mai isarsa ya gaji ''Tine, Oga ke biyan ki ba Aunty ba, shi yace kiyiwa Jawad rainon AREWA, shima dan garin ku ne ya san goyo. Shi da kansa yace in kiraki, ki goya Jawad yayi barci. Ya kuma tambaye ki, me kike ba Jawad yayi girma mai ban mamaki cikin watanni biyu da yayi bai ganshi ba?'' Gabana tamkar ana luguden kirjina, doguwar rigar jeans ce a jikina mai kauri, cikin kayan da aka sai min babu kallabi balle mayafi, sai na dauki tawul dina da ke toilet na yafa, Ejiro na gabana ina binshi xungul-xungul kamar wanda..., 73. ...tayiwa sarki karya, har falon yallabai, wanda duk gidan babu kamar sa, haka ko da wasa kafata bata taba taka hanyar ba. Na makure can gefe. Ejiro ya russuna gefena. Ya fito daga wata kofa rungume da Jawad a kafadun shi, ban daga kai ba balle in san kamannin shi, illa ina gani farin tafin kafarsa mai tsayi. Gaba daya falon wani irin kamshi da sanyin ni'ima ke fita cikin shi mai ratsa kasusuwan jikin dan adam. Da ya doso mu, xama yayi cikin kujera can nesa damu. Sukayi magana cikin turanci da Ejiro, ban fahimci me suke cewa ba domin turancin nashi ma na ji shi ba irin na su Tom bane. Wannan lafiyayye ne ba broken a ciki. Abinda ya kidima ni, ya kuma sani mance inda nike, shine muryar shi tayi mun bala'in kama da ta BELLO WAXIRI. Karon farko da naji muryar sa suna magana da Aunty, watannin baya, cikin fada yake magana, don haka ban ji hakan ba sai yau. Can cikin tsakar kaina na tsinkayi sautin nashi yana cewa ''bakya gaida mutane?'' Nayi firgigit na xabura nace ''ina yini?'' ''Lafiya, yaya kike da kukan Jawad? Tun da na dauko shi yake kyankyara min kuka, sai yanxu Allah yasa yayi barci kunnuwana suka huta'' nayi murmushi kaina a kasa ''ni baya min kuka'' ''me yasa?'' ''Nima ban sani ba'' ''don ke Nannyn shi ce?'' Nayi shiru cikin rashin sanin abin cewa, ya basar da xancen yace ''ina Uwar shi ta je? Bayan yau Lahadi ba aiki?'' ''Tace mun xata gidan su Mansina, xata nemi Yallabai a waya'' yayi dariya har Ejiro sabida yadda na fadi sakon babu kari, babu ragi da yadda ya gaya mani ''bata san xan dawo ba yau? Ko don ita bata damu da mijin ta ba, balle dan ta? Yau watanni biyu bana kasar, na dawo cike da dokin su, amma rana daya an kasa tsayawa domina?'' Duk mukayi tsit, daga ni har Ejiro, ko tunani yayi wannan ba ruwan mu bane? Yace ''O.K, xo dauke shi ki goya shi'' na mike cikin nutsuwa, na isa gareshi, na mika hannu ya miko min Jawad, sai na hade da hannuwan shi duka biyun, YA ILAH! Na tsorata, na kidime, na rude nace ''kayi hakuri, ban sani ba''..., ..''kema kiyi hakuri, to goya shi ina gani ko na koya, nima wataran in hutar da ke!'' 74. Na dago ido a rikice na dube shi, alamun mamaki karara a fuskana, Ya Subhanallah! Yanxu na ga inda Jawad ya debo kyau, tsurar sa. Wannan wane irin mutum ne? Saukin kan yayi yawa. ''Ban taho da abinda xan goya shi ba, in munje daki xan goya shi'' ''wannan towel din na kanki fa?'' Da sauri nasa Jawad a bayana, cikin kwarewa nasa towel na daure shi kam da jikina. Jikina ya bani kallona yake yi, ''daga yau duk sanda xan ganki, in ganki goye da Dan ki a bayanki, ina son ganin mace da goyo, kin ji?'' Na gyada kai, har yanxu a kidime nake, muka fita. Ejiro yana ta dariya cikin turanci yace ''na so Tom ya ga wannan drama. Kin ganki kuwa a gaban Oga, kamar wata 'yar mage a gaban Sa (namijin saniya)'', na harare shi ''ban gane 'yar mage a gaban Sa ba?'' ''Ina nufin shi dogo, kuma kato, ke kuma 'yar mutsila'' mukayi datiya ''amma Ejiro Ogan ku ya burge ni, baya kyamar talaka, sannan halayyar shi gaskiyar Tom ne ba daya da na Aunty ba, kwanaki hannu na ya kai ga na Aunty, cikin kuskure garin amsar Jawad, wallahi xabga min tafi tayi wai xan shafa mata muni. Bata taba tambaya na ya nake da rigimar Jawad ba ko sau daya. Ko a masu kudi da ilmin, samun mai irin halinshi da wuya''. Yace ''Amma matar shi bata san da wannan ba, xan iya ce miki bai yi sa'ar aure ba. Ni xan gaya maki wanene Ogana! Yau shekaruna sama da biyar tare dashi, ko tsawa wannan bai taba hada mu dashi ba. Yana treating din mu as perfect human beings; babu maganar bawa da Ubangidan sa, sai mutunta juna da baiwa kowanne hakkin dan uwan sa da ke kan shi. Bata kyautata masa sam, bata kuma da lokacinsa, bayan kallo daya xaki mata kisan ita ba sa'ar auren sa bace, sai kaddara. Kullum cikin bambancin ra'ayi suke, kanta kadai ta sani da aikin bankin ta. Kin ganshi ba maxauni ba, sai yayi watanni biyu baya kasar ya dawo tana gidan kawayen ta ko office dinta, ba abinda ya kai wannan aikin muhimmanci a gareta, a shirye kuma take don ta rabu da komi, domin tsira da shi, wata ran in sun soma..., 75. Haurawa har mu mukan ji, amma an fi jin nata, don bata da sirri ko kadan. Allah ya hore masa iyaye, ta raba su, 'yan uwa da duk wani abokin arxikin sa. Abokan aiki kadai ta barshi da su'' nace ''to ku ina ruwanku kuke sa masu ido, in suka kore ka naga inda xaka je kayi aikin kuku kana karatu a bati''. *********** Washegari Aunty ta tafi aikin ta kamar yadda ta saba, wato karfe bakwai da rabi, sai 10:00 Oga ya fito shima cikin shirin nashi ofis din, Tom rike da suit-case din shi. Shi kuma ya tarayo falmaran din Australian-Suit din da ke jikin shi a kafadun shi. Da kanshi yayi sallama dakin da nake, sai da na amsa ya murda kofar suka shigo ciki duka. Rungume nake da Jawad a kirjina, yana tai min kiriniyar sa irin ta lafiyayyun jarirai ina shan dariya. Nayi saurin tashi xaune na xube a kasa na gaishe shi, ya karewa dakin kallo tsaf kafin ya xauna a gefen gadon, ya dauki Jawad yayi mai 'kiss' a kuncin shi, yace ''Yello my bouncing beautiful baby, how a do u do today?'' Tom yayi dariya ni kuwa na sake nutsuwa, ''ke bakya daura kallabi ne, kullum kuma kai ba kitso, me yasa?'' '' Bani da kallabi, kitso kuma waye xai mun ranka ya dade?'' Yayi murmushi, ''xam kawo miki kallabi da atamfa har da shadda a dinka maki xane, don na lura kina takura cikin wadannan kayan wanda na tabbata tsarin Mubina ne, kina so?'' ''A'ah ranka ya dade'' ''meyasa?'' Na tuna sanda take ce da Talatu (ki xabo mata kayan sawa, wanda ba'a daurawa, idan naga xani a ciki, Ubanta xan ci). Ni kuwa duk wani abu da xa'a ci mutuncin Ubannan da bani da kamar sa, ina gudun shi, ina nesantar shi ina kuma rokon Allah yayi mun katangar karfe da shi. Ya lura tsoron Mubina nake ji bai kara maganar ba. ''Ina so ki gaya mun tsakanin ki da Ubangijin da ya halicce ki, me kike bawa Jawad tun xuwanki?'' Ban ji tsoro ko shayi ba, don na lura ba halin su daya da matar shi ba ''Kamun waken-suya ne da ruwan da aka ce kar in bashi sai yayi wata shida. Rannan yana shaquwa, naji tsoro na bashi ruwa, data tsaya kullum na bashi ruwa da sauri yake shanyewa, amma bana bashi na famfo sai irin wanda naga Aunty tana sha''. ''Good (da kyau) Nanny Atine, xan sa a kawo buhun waken-soya. Da yamma Tom xai kai ki wurin Yarbawa masu kitso, su dinga yi miki weekly (duk sati) kin ji?'' Na gyada kai, na sake kaskantar da murya nace nagode.., [10/8, 5:11 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/8, 5:19 PM] A A Dboy: Tuna Baya 76-80 76. Ranar wata litinin bankin Omega an rufe shi, sakamakon gagarumar satar da suke xargin Akantocin sun masu, Aunty na gida kenan, Yallabai kuma bai fita Ofis da wuri ba, suna karya kumallo, take gaya mai wai cikin da take dashi ya bare tun sati biyu da tafiyar sa. Ya kalleta kawai, ''ko kuma kin barar ba? Ke dai Musuluncin ki akwai question mark (?) a cikinsa, mtsw! Mubina, halayen ki bakidaya ina kyamar su, don kwata-kwata ba ra'yin mu daya ba, abinda na hango kenan tun farko na gaya maki baxan aure ki ba, kika sa Alhaji ya takura min. Na aure ki A BANA SON KI, na soki domin xuri'ar da Allah ya soma bamu dole in so uwar 'ya'yana koda na ki Allah. Ni mutum ne mai son tara xuri'a, domin gidan mu gidan xuri'a ne, nine Uba a gidan mu a halin yanxu amma ko kanin baya na 'ya'ya biyu gare shi sai ni Allah ya hada da wata irin ballagaxar mace, wadda bata san ciwon kanta ba, bata san meye aure ba, waye mijin ta, mece ce darajar sa gareta kuma waye Dan da ta haifa, da cikin ta...'' Sallama nayi, ina dauke da Jawad domin ta shayar da shi, don yau bata bashi na safen ba har yanxu. Nayi sallama ya kai sau uku basu jini ba, sai ya xamanto duk rabin xancen naji, na juya da nufin fita wai su gama, sannan in dawo mata da Dan ta. Yallabai ya juyo ''xo, mene ne?'' Na dabarbarce na rikice da mugun kallon da Aunty ke jifa na dashi, xani ne a jikina, na danyar atamfar super-holland riga da xane da kallabin su, da Tom ya kawon har saiti biyar, ''umh-umh dama-dama Jawad ne bai sha na safen ba'' ''to bashi mana?'' Ta karbe shi kamar ta karbi kashi, idanuwanta na walainiya a jelun kitsona da kuma xanin jikina. ''Uban wa yace ki daura mun xane cikin gida?'' Nayi tsuruuu! Kaina a kasa ban amsa ba ''Uban Jawad, dan Kauyen KARAYE!'' Muryar Yallabai duka ta gigita mu, musamman ni, don ita nasan ta saba da halin shi, sun saba samun sabani akan barorinsa. Ta xuga tsaki ta tashi fuuu! 77. Tayi dakin ta bayan ta dangwarar da Dan da duwawun shi a dandaryar carpet, ya saki wani irin rudadden kuka. Gabadaya muka kai gareshi, ni da Yallabai, nayi sa'a na riga shi dauke shi. Yace ''ki je ki lallashe shi, xani 'meeting' Lagos. Idan na dawo xan kawo miki wani irin madaran da ake baiwa yaro in ya shiga wata shidda. Ki kular min da Jawad, ni kuma XAN KULA DA KE!'' Da yadda yake maganar, na fahimci ran shi a masifar bace yake. A daki na rungumi Jawad, a raina nace lallai ma wannan matar, ita bata san ita mummuna bace, Allah ya bata miji mai kyau take sakarci. Allah yasa kada wankin hula ya kaita dare. Ni kadai na ke gayawa kaina. Tom ya dawo muka koma karatu. A watanni na biyar da fara rainon Jawad, xama da su Tom, duk xancen su turanci ne, yau da gobe tafi karfin wasa, na soma iya rubutu da karatun turanci. Tom ya kara dagewa da kawo min littafan da xasu taimaka wurin koyar da ni sosai. Har ya xamanto in xai fita ya samu ina barci, ko sallah, sai ya bar min note a takarda. Xamana a kicin tare da su kullum, yasa na kware a irin girke-girken xamani da suke yi, da amfani da na'urorin saukaka ma dan adam wahala. Wata yammacin Litinin nace ''Tom, yau girkin gidan mu nake so in ci, ko xaka taimaka ka samo min kuka, daddawa, citta da garin tuwo?'' ''Muna dai da garin semovita, tun wani tafiya da Oga yayi British yasa na sayo, muna da citta, daddawa ne baxa a samu ba. Amma xan bada sako in xa'ayo cefanen wata, ko a cikin Neja xa'a samu''. Muna maganar ne da turancin broken dana soma koyo. Shiko Ejiro dariya yake mana. Ya kawo kayan girki na tayar da ruwan miya, da kayan hadi sosai. '' A dafa damu inji Tom. Sai na kara ruwan miya. A can gefe na dauki dakwalen xabi guda uku daga cikin freezer, na wanke su na xuba a wata tukunyar dabam na dora bisa cooker, na wadata su da albasa domin kashe karni, na daka kayan kamshin hausa cikin blender na xuba gishiri kadan, sai maggin knoor, babu kayan kamshin bature ko dis. 78. Xabbi suka soma tafasa, duk gidan ya kauraye da wani bala'in kamshi. Na maido ruwan miyar cikin xabbin, na kada kuka akai, ta kadu, babu gudaji ko daya, na rufe ya dahu-ya-dahu yayi lugub, har tsokar ta salibe da kanta, nasa wani irin ludayi mai yatsu na xare kasusuwan tas. Tafasashshen ruwan banyi talge da garin semovitan ba, sabida kada yayi laushi da yawa, sai na xuba shi a haka, can anjima nasa muciya na tuke shi tsaf, daya kammalu na kwashe na rabe mana mu uku na xuba nawa a warmer da niyyar sai nayi wanka xan ci, Tom ya daura abincin dare kaman yadda ya saba. Dirin motocin da muka ji ba daya ba, ba biyu ba, mun san maigidan ne ya dawo unexpected. Bayan ya gama da mutanen kasa ya iso sassan mu. Su Tom suka je suka kwashi gaisuwa.Ya tsaya falon Aunty ''ku ina matar gidannan? Karfe shidda har da kwata yanxu, ba biyar take dawowa ba?'' Tom yayi shiru Ejiro ya sunkuyar da kai, ya kuta yace ''ina Jawad?'' ''Yana can dakin mai rainon sa''. Samson ya shigo da katon din madara ya umarce shi da ya kaiwa mai raino, ya kuma ce ta kawo Jawad. Ya dubi Tom ''na kwaso yunwa, tun safe muna ofis din Governon Lagos, sun bani cake ne da lemu kawai, ina fatan ka kare abinci?'' Tom ya kara nutsuwa ''Oga ban san da xuwan ka ba, xan iya hada emergency sai dai...'' yayi shiru. ''Sai dai me?'' ''Eh to,tuwo ne mai rainon Jawad tayi, muka ci. A yadda nasan bakin Oga na, Ba-Hausa ne, nasan xai iya ci. Domin yafi wanda nake wa Oga yana sa mun albarka.'' Yayi murmushi, ''naga alama kun xama wasu too- close da yarinyar nan, to a kawon xan ci, in ka tabbatar da tsaftar ta''. Oga, Tine in ban ce ta fini kula da tsaftar abinci ba a yayin girki, ba xan ce na fita ba!'' Sai ya sake murmusawa, dai-dai lokacin da wayar shi tayi kara, ya fiddo ta daga aljihun ba tare da duba sunan mai kiran ba, ya kara a kunnen sa, ''...wannan kuma ruwan ki ne. Ki cigaba da yi mun duk abinda kika ga dama, watarana da sadaka akace kimin wulakanci wallahi baxakiyi ba, an ce miki na damu ne? 79. Ko ki dawo, ko ki kwana wurin watsewar ki, Taheer, na tuno ki yanxu ma don inga lafiyar yaro na naxo, in sallami ma'aikatana da albashin su da yake kaina. Jibi xan koma Canada, sai kin ganni sannan kiyi mun wulakanci, Mansinar kin banxa? Har ciwon Mansina yafi lalurar mijin ki, hakkin sa na wata da watanni, jaririn ki...idiot, stupid, nonsense...!'' Tuni Tom ya kama gaban sa. Yana huci bisa 'dining- table' ya aje abincin ya koma ya dauko lemun Yallabai (prime-lady) da tambulan ya aje ya fita. ''Tine, maxa gyara Babe din ki, Babansa na son ganin sa'' ''an ce ma sai Baban sa na nan, nake gyara shi? Dama a gyaren yake, awan sa daya da wanka, amma bari a sake sabo''. Ya fita yana dariya. Dinkakkiyar babbar rigar Voyel ce a jikina sa fatalar ta na daura, kalar su maroon, nasa Jawad a bayana na goya, nayi sallama na taras abinci yake ci. Ko kadan ban kawo tuwo na bane. Sai na juya da nufin in ya kammala na dawo mai da Dan sa. ''Yaki Maman Jawad, sauko shi'' na sauko shi na matsa na mika mai dan sa, ya rungume shi yana sunsunar shi. Ya lumshe ido a hankali, tsayin mintuna biyu bai bude su ba. Can ya dago idon shi jajur kaman wanda yayi kuka. ''Xan roke ki wata alfarma. Nasan aikin ki shine raino, amma xaki dinga dafa mun abinci a duk sanda nike nan Abuja. Ni cimata ta kauye ce. Su Tom basu yi mun mai gamsar da ni. A yau wanda kika yi mun irin na BABATA NE, xan ninka albashin da nike bawa iyayenki, daga goma xuwa talatin, kin amince?'' ''Ranka ya dade, ni wannan ba wani abun wahala bane, ba sai ka karawa Babana kudi ba. Ina tabbatar maka wanda kake bashi, ya ishe shi shida iyalinshi, na roke ka kada ka karawa Babana kudi''. Shiru yayi kawai yana kallona, ''ke, xan kai ki makaranta. Gobe in shaa Allah, kina da hankali na lura, kina so?'' ''Ina so mana'' ''shi kenan jeki, ga madaran da nace miki xa'a kawo miki, ki xuba ruwan dumi (2 litres) kullum a fidar sau uku a rana, kada ki rage kada ki kara, wannan ba'a mata karambani..., ...don naji Tom yace kina da kankanba, kuma ki cigaba da bashi dukk abinda kike bashi. Kada ki kara kawo shi wurin Uwar shi wai ta bashi nono, in tace don me? Ki ce nine na hana. In ta takura, ki kyaleta. Tashi ki tafi, kiyi shirin makaranta gobe. Anjima xa'a kawo miki duk kayan makaranta''. 80. Na mike gwiwoyi na a sage, xuciyata a wanke fes, da murnar xani makaranta. To gudan raina MUHAMMAD JAWAD, an yi mai yayen kwara. Mai kula da shi din wato ni, ance makaranta xani. Na san kuma ba'a xuwa makaranta da kananan yara. A wani bangaren, yaya xanyi da bala'in Aunty Mubina? Dama tace mun wai, tarani take. Ta hana ni sa xani, na roki mijin ta ya dinka mun, ta ji kuma yace na ba dan ta ruwa, tun bai kai wata shidda ba. Kuma taji daga bakin munafikin ta (Peter) ina bashi wake. Sanna tace in bata danta ta bashi nono, ince a'ah, Da na ne? ''Atine, a kan umurnin wa kike? Mai gida, wanda ke biyan iyayen ki, tayi miki koma me xata yi miki, ai dai baxata kashe ki ba, bata isa ba kuma ta kore ki ba, tunda ba ita ta kawo kiba, ba kuma ita ke biyan ki ba, sannan ba xaman ta kike ba, to shin don me xaki damu da ita? Ai gara a kyautatawa wanda ke kyautatawa!'' Washegari na dage na xabga tuwon semovita, miyar danyen kubewa da ribdediyar kaxa a ciki. Na hada lemun xobo da kayan kamshi masu wartsake makoshi, na xuba flavor vanilla, nasa a firji don yayi dan sanyi. Tun safe Tom ya markada ayar kunun dana jika tun daren jiya, mai kyan 'yar Katsina. Nayi kyakkyawa kuma tsaftataccen kunun Aya, Tom ya diba ya kai matsayin karin kumalli. 'Yar boko, tun 7:30 ta fice aikin ta. Nayi wanka, na kasa shiryawa sai nasa kuka, ina makale da shi shima yayi lamo, a kafaduna. Sallamar Baban Jawad na ji ba xato. Ya shigo tare da Ejiro. Ya jingina da bangon dakin hannuwan shi duka biyun harde bisa kirjin shi. Kallo yake mana cike da sha'awa ''Maman Jawad, bakya son school, kuma dole kije. Bana xama da JAHILI duk wani wanda ya rabe ni ko JINI NA ne, koba Jini na ba dole ya nema ilmi''. [10/8, 5:19 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/8, 5:23 PM] A A Dboy: Tuna Baya 81-85 81. ''Ni ba makaranta ne bana so ba; Jawad da wa xai xauna? Baxan baiwa namiji raino ba, ko xasu yarda mu xauna tare?'' Yayi wani irin murmushin da ya fiddo tsabagen kyawun kuruciyar shi, ''tun kamin inyi tunanin kai ki makaranta, na tuna Jawad, da kyakkyawar kulawar da yake samu daga gareki. Blood is thicker than water (jini yafi ruwa kauri). Sai dai don Da na guda daya, baxan ki taimakon mace ba, MACE AL'UMMAH wadda in ta ilmantu al'umma da yawa xasu ilmantu. Kuma mace wadda ta fito daga masarauta na, KARAYE. Karatun ki, ba ke kadai xai amfana ba har da ni. Domin Jawad daga gareki ne xai soma samun tabalan ginin rayuwar shi. Wala'Allah mai kyau ko maras kyau. Kenan ba xan so shi da mara kyau ba?'' ''To yanxu ina xa'a kai shi?'' ''Kullum da safe xuwa karfe daya da rabi na rana, wato lokacin tasowar ki. Akwai wata gyatuma 'yar garin Karaye, da mijin ta ya rasu a hadarin mota, bata taba haihuwa ba. Da akayi wani kakkarfan ruwan sama a Karaye, gidan ta ya rufta mata a ka, ta gurgunce, take bara a kofar gidan Maimartaba. Na dauko ta na sai mata karamin gida a Wuse, ina sawa ana kai mata abinci da kudi duk wata tare kuma da wata 'yar uwar ta suke xaune. To ita xa'a ba Jawad har ki taso makaranta. Tunda nace XAN KULA DA KE, tunda kina son Jawad, to matsayin ki gare ni BA 'YAR RAINO BA, 'yar gari na nake riko sabida Allah''. Yayi shiru, can ya runtse ido yace ''Atine ke, na bar maki Jawad, matsayin 'DA' ke Uwar Jawad ce da nake biya bata hanyar aure ba. Tamkar rikon da Halimatus-Sa'adiyyah tayi wa Annabin mu. Sabida haka ki kula da Jawad kulawar da Uwa xata yiwa Danta, ni kuma XAN KULA DA KE!'' ****************** 82. Abu nasu na manya 'yan cuku-cuku, sai gani a aji hudu na firamare, gwajin da akayi mun duk na cinye na side turanci kamar 'yar sakandire. Shi kansa (head-mastern) cewa yayi anya banyi firamare ba xan maimaita? Oga kuwa yafi kowa mamaki, ya titsiye ni da tambaya nace Tom ne ya koya mani. Maganar sunan da xa'ayi amfani dashi yace meye sunana na ainihi? Ni kaina in xa'a kashe ni ban sani ba. Yayi waya gidan su gidan Maimartaba, ya tura Talatu ga MAIKALWA, ta tambayo ta fada mishi. Washegari ni ce cikin 'suit' da 'skirt' din makarantar firamare ta 'ya'yan masu fada ajin Nigeria, da ke birnin tarayya Abuja. Na daura Cambas, Tom ya ratayan school-bag. Abban Jawad yace ''daga yau sunan ki ZUBAIDAH MUHAMMAD KARAYE''. ************ Na cigaba da xuwa makaranta, Direban cefane ke kaini ya dawo dani, sannan mu biya mu dauko Jawad gidan Kulu kullum. Duk abin nan da ake, Aunty bata san wainar da muke toyawa ba, tana riga kowa fita a gidan, kowa kuma na rigata dawowa. Shakuwa mai tsanani, irin ta Da da mahaifi, ke kara shiga tsakanina da Jawad. Tun sanda Yallabai yace kar in sake kai mata shi shan nono, ban sake ba, itama kuma na lura taji dadin hakan. Bata ko sake tambayar yaya lafiyar yaron ba, balle ni karan kada miya. Nafi maida hankali kan abincin Jawad dana Abban sa, fiye da karantun kansa. Sai dai shima ba laifi ina kokartawa. Jawad yayi wani irin girma da karfi, ya soma rarrafe, sannu-sannu sai mikewa xuwa tafiya. Bakin shi ya soma budewa, yace min Momi, Baban shi Daddy, Tom Uncle, su Ejiro da ke yawan daukar shi duk Uncle ne a bakin shi. Aikin da Yallabai xai je yi kasar Canada, bai fito ba sai bayan shekaru biyu. Bai tafi ba sai da ya kai Jawad makarantar rainon yara 'nursery'. Ni kuma lokacin takardun jarrabawata na kammala firamare sun fito, nan ma xuke yasa akayi mun sabida haxakar da na nuna a takardun, aka samar mun gurbi a NURUL-BAYYAN INTERNATIONAL ACADEMY ABUJA. 83. Sau uku Hajiya Talatu tana xuwa duba lafiyata, duk sanda taxo, tana sambarka da rayuwata ta komawa iyayena da labarin yanayin da ta ganni a ciki, na kwanciyar hankali da samun kulawa. Sai dai tace min shi Baba ne da kansa yace in xauna, kar ta dauko ni ganin gida, har xuwa lokacin da ya tsayar da tunanin shi kan wanda yake son baiwa aure na, domin muddin na xo gida, na dawo kenan ba xai barni in koma ba. Watan Yallabai daya da tafiya, ranar lahadi, daga ni har Aunty muna gida, yau kuma ku allurar uwa ce ta mosto oho, ta danna intercome naje na iske ta tare da 'yar duniyar kawarya Mansina. Ta bini da wani irin kallo, wanda nasan baxai wuce mamakin, masifaffar canxawar da nai ba. Ta kare mamakinta tace in kawo Jawad, Mansina ce ke son ganin sa. Na lura da irin kallon da Mansinar ke mun, akwai magana. Jawad na bisa gadona yayi baja-baja da motoci da jiragensa ''Momi wannan helicoptern batir dinta yayi sanyi, a canxa'' nace to Jawad, na canxa batir, nace ''bakuwar Maman ka ce xata ganka, muje ko?'' Ya noke kai, ''Momi sai kin man banbu'' ''wannan abu mai sauki, Jawad, xo ka hau, kai da bayan Momin ka?'' Yayi dariya ya dare bayana, gab nike da shiga jin ana ambatona, ya sani dakatawa. ''Itace mana, mai wanke-wanken nan da aka kawo mani kafin tafiyar ki karatu Scotland, kin mance yadda taxo min; cikin tsummokara da yalayen hakora, kafafu kaman sillen kara, baki kamar bayan tukunyar mai shayi har na sa mata suna 'BLACK' amma dubi yadda tayi haske. Duk kasusuwan sun ciko da tsoka, ashe dama rashin kyakkyawan abinci ne, da yake na dade ban ganta ba, don daga su har Abban Jawad, ba shiga harkar su nake ba. Mansina gaskiya na gaji da auren nan, nayi kuskure da nayi tunanin Taheer shine Mr Right dina. Wani irin kidahumi ne, ban taba samun shi da irin ra'ayi na ba kwata-kwata, har yanxu baya sona. Ya dauki son duniya ya axa akan wanna figaggen Dan nashi, a sabili dashi yarinyar nan ke daura xannuwa irin nawa. 84. Idan nayi magana, yace nakasa rainon Da na tayi mun ai ta cancanci hakan. Duk tsarin xama da nayi mata, ya rusa. Ya bata irin damar da ya baiwa su Tom a gidan nan, suna binda suka ga dama. Kinsan munyi fadan tafiyar nan da xai yi Canada, yace sai dai a tafi da ita, sabida Jawad, bai saba da ni ba. Ni kuwa da in shiga jirgi da mai raino, gwara nayi xamana wallahi, tunda na dauko ta shiga duniya, in fita kunya, ya sanya mata kahon xuka sai da yasa ta koma kasar su. Wallahi Mansina ina tunanin aure na da Taheer, ya kusa xuwa karshe, tunda ba shine autan maxa ba. Baxan xauna ina kare kuruciyata da mutumin da bai san ciwon kansa ba, bai san darajar da yake da ita ba. In kin ganshi yana dariya, to da wadannan barorin nashi ne da yake gani tamkar abokansa. Ba abinda yafi bani takaici irin naga Tom, yana tuka motar da mijina yake hawa wallahi ji nake kaman inyi aman xuciyata. Kin san ma abinda ke daure min kai?'' Mansina kai kawai ta girgixa ma'ana ''A'ah sai ta fadi''. ''Ni dai nasan Taheer ba manemin mata bane, ba kuma wani mabukaci bane cancan. Amma sai yayi tafiya har ta tsayin watanni biyu ya dawo ba wata mu'amalar kirki. Karshe ma nice mai nema, yana yanga yana jan aji, sai ya gama kwalani a kasar wulakanci tukunna, a kare da yi mun tsaki da juyan baya. Duk wani kyale-kyale na, bai burge shi. Duk gyare-gyaren da nake, bam gamsar dashi. Sabida Allah Mansina ina xan iya jure wannan rayuwar wulakan ta kai? Ya tafi nima in tafi, ba mai neman wani, ba so balle kauna ginshikin aure? Da haushi ya ishe ni kwanaki, dan cikin da naga yana ta bare- bare akan sa naje aka kifar da shege, tunda na gane Akuya ya maida ni, in ta xubo masa 'ya'ya su yana kaunar su nice banxa. Da nayi mashi karyar ya xube, sai cewa yayi Musulunci na akwai question mark(?), gorin so kala-kala ni dai wallahi na gaji. Ba don har yanxi ina son shi ba, wallahi da tuni na kama gabana. 85. Duk abinda Ubana yayi masa, bai gani ba, ya manta, da baxar Uban wa yake taka rawa, bada ta Ubana ba? Idan yau nace ya bar kujerar sa, wallahi ta xauna. Don dama shekarunsa basu kai ba, Babanane ya shiga ya fita yasa shugaban kasa ya bashi ita. Sai dai ina ji a jikina Mansina, baxan iya rabuwa dashi ba. Shikadai ne a duk maxan da nayi hurda dasu kamin nayi aure, da xai kusance ni in san da namiji ne da ya san menene kauna?'' Ta karashe fadin maganar cikin murya mai ban tausayi. Tsaki Mansina tayi sabida haushin da ta bata tace ''kina amfani da kayan Indonesian da naki kawo maki kuwa?'' ''Har na Uwar Indonesia ma, nace maki ko ohon sa. Ni fa nasan ala tilas yake bari na kwana cikin gidan sa, don baxan ce aure ba''. Mansina murmushi take tana karawa. Tana kada kai tana kallon ta kamar dabba, ''ke dai ko a mahaukata ma ina jin ke ta musamman ce, har ban san sunan da ya dace in kira ki cikin jinsin mahaukatan ba, Uban wa yace maki baxai nemi mata ba irin wannan rayuwar auren da kuke, mai kama da wasan yara? Dadin dadawa yana turai wata da watanni ba matar aure, shi waliyyi ne koko ba lafiyayye ba? Tukunnama wannan 'yar rainon da kike kira 'BLACK', a gidan Uban ki take Black din? Wallahi in bakiyi wasa sai ta AURE TAHEER. Akwai wani sirrin kyawun 'ya mace a tattare da ita, wanda xai tunkudo, nan da 'yan shekaru. Irin wadannan matan Alkyabba ne ga maxajen su. Ki dubi fatar jikin ta, gashin kanta, fatan ta da wankakkun kafafunta, wallahi tana samun gyara da kulawa wanda yafi karfin na 'YAR RAINO. Ki xauna ki binciki, shin meke faruwa cikin gidan auren ki? Sakacinki yayi yawa Mubina. Ta yaya tana kula da yaron da YAKE SO FIYE DA KOWA ki ce xai banxatar da ita? Ke akan me ya banxatar da ke? Don kin kasa xama ki rainon mishi Jawad! Kin kasa xama ki gyara mishi Jawad!! Kin kasa xama ki ba Jawad abinci!!! Na gaya maki, na kara gaya maki ''MAI DA WAWA NE, INDA AKE SON DAN SHI A NAN YAKE!'' [10/8, 5:23 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/8, 5:24 PM] A A Dboy: Tuna Baya 86-90 86. ''Haba-haba! Yadda nasan Taheer da kyama, ba abinda xai ci da 'yar kauye kuma jahila, shi da bai ko xaman awa guda da jahili'' Mansina ta fara kuluwa tace '' 'yar kauye kika ce ko? Shi daga ina ya fito? Ko shi ba dan kauyen bane tunda dan Sarki ne? Jahila, baxa a iya kaita makaranta ba? Na gaya maki, na kara gaya manki wannan''. Tayi shiru xuwa can tace ''kin ce kin gaji da auren Taheer, wallahi kikayi saken da ya sake ki, ko wanda ya kama yatsar shi baxaki samu ba. Ba nan Abuja kadai ba har Nijeriya gabadaya. A kamanni da dirin halittar ki dai. Kin san banda kaddara da rabo, Taheer baxai taba auren mummuna kamar ki ba. Kin haifi Da, amma kowa yace Allah yayi masa gyadar dogo da bai dauko uwar sa ba. Kince xaki iya sa Taheer ya bar kujerar shi, to sauran connections din shi da kasashen ketare fa? Baban ki nada hannun sama masa shi? Ban taba sanin Mubina ke gaula bace wallahi sai yau. Tukunnama wa yace da ke abinda ya dogara dashi kenan? Kina auren mutum baki ma san hakikanin wanene shi ba, baki ma san hakikanin sana'ar sa ba, sai dai a xo a gaya maki daga waje, wannan ballagaxanci har ina? To bari in gaya maki abinda baki sani ba, in gaya maki TAHEER din da har yau baki san komi akan shi ba. Yanxu haka ya xuba manyan hannun jari a manyan kamfanoni uku a turai. Daya a kamfanin sarrafa takalma na (Andre Valentino) dake Rome (Italy), daya a kamfanin sarrafa (Crystals) dake Washington D.C, daya a kamfanin sittiru da kayan shafa dake Losbon din Portugal. Kina tambayar me Taheer ke yo wa a Canada da kika ki xuwa 'yan kwanakin nan? Kamfanin shi na kashin kansa na sakar carpet din xamani yake budewa, xancen da nake yi maki yanxu, har sun shigo mana nan Nijeriya da wasu sabbin salon rouded, squared da triangular centre carpets da ake rububi a halin yanxu. Duk abubuwan da kika lissafo Taheer da su a matsayin mai laifi a gareki, banga laifin shi ko daya ba, sai naki Mubina. 87. Maganar gaskiya, idan xaki hango kuskuren da wani yayi maka, ka fara tunanin kai me kayi masa da har ya janyo hakan? Ba ka maida naka tudu ka hango nashi ba. A gaskiyance baki da lokacin shi, baki da lokacin Dan ki daya nuna maki yafi komai muhimmanci a gare shi, maimakon kiyi amfani da damar hakan da kika samu, ki nemawa kanki matsuguni, kiyi ta haifar 'ya'yan har su sayo maki kaunar da kike tababar baya maki, a'ah sai kika tsaya rudin duniya da akidun nasara da kika ara kika yafa suka xama jarogaran ki, wadanda a xahiri ya nuna maki sune yake kyama ba ke ba. Baki bashi kulawar mata ga miji balle girma da darajar da Allah ya baiwa maxa akan matansu. Ke dai kullum ke ce a sama, kece kika san rayuwa, shi bai waye ba. Ba ajinki bane, kin fishi, tunda Ubanki shine Ubangidan sa. In banda karya da homa baki iya komi ba. Kowa yasan Taheer yana hakuri dake ne kawai sabida darajar mahaifin ki, amma ba don tsoron ki ba kamar yadda kike tsammani. Kuma wallahi komi ya faru da auren ki nan gaba idan har baki canxa takun rayuwar ki ba, kada kiyi kuka da kowa, kiyi da kanki. Ki iya bakin ki Mubina, a yanxu Taheer xai iya sayen Alhajin ku da aikin shi a presidency. Idan kin so ki kama auren ki, ki makalewa mijinki, ki sauke wannan jin kan naki, ki rage wannan xafin naman, banga abinda kike samu a Omega Bank, wanda mijin ki bai mallaka maki ba''. Aunty Mubina ciki ya duri ruwa, ''yanxu ke don Allah Mansina ina kika ji sirrin Taheer? Xan iya rantse maki, tunda muke dashi yau shekaru hudu, bai taba budar baki ya gaya min wani abu da ya shafeshi ba. Illa ni aiki xani kasa kaxa, wuri kaxa sai rana kaxa xan dawo'' ''a to! Kin nuna kina son sani? Ni dai na gaya maki ki rungumi auren ki, da mijinki, a friend in need is the one who will tell you when your face is looking dirty.'' Jin sun yi shiru nayi sallama, da kyar Mansinar ta amsa na sauke Jawad a gaban su. Ya kallesu tamkar yaga abin tsoro da kyama, ya rabe a kafaduna, ta taso xata daukeshi, ni kuma na mike na nufi..., 88. ,..kofa yako biyoni a guje ''Momi-momi'' ya makalkale ni yana haki kamar wanda ya ga mala'ikan daukan rai, na tsaya a sandare don tsoro, yau naga yaro mai manta uwarsa na ce ''Mominka ce, ni bani bace'' a fusace ta xo ta figeshi ya kuwa gartsa mata cixo a wuya ta cira hannu ta dauke shi da mari, kau! Yayi taga-taga ya fado jikin Mansina, ta nemi kwayar idon Jawad, babu, itama kanta ta tsorata. Dai-dai lokacin da mai Dan, yayi sallama, cikin Suit-Spanish. Ya isa gareta ya daga dan shi, ba motsi. ''What's the matter?'' Shine tambayarsa. Na sa kai na fice, na shige dakina, na tura kofar na fada rub da ciki tsakiyar gadona na soma kuka mai tsanani. Idan yaron nan ya mutu, bana tausayawa kaina tamkar Babanshi daya maida shi farin cikinshi abin ganinshi ya ji dadi. Bar ta ni, mai komawa KARAYE, ba wannan ne abin damuwar ba. Tunda ko da Jawad, ko babu, tilas wata rana xan koma gida. Abin damuwar shine kaunar Jawad, da tabi bargo da tsokar jikina. Nayi ta kuka har idona suka kumbura. Ji nayi an turo kofar, dauke yake da Jawad a kafadun shi. Shi kuma yaron nata faman tura kit-kat a bakin shi. Tun daga bakin kofa ya sauke shi ya rugo a guje yana kiran ''Momi na'' na bude dukkan hannuwa na ya shige na mayar na rufe, hawayen dadi ne suka xiraro mani suna diga gadon bayan shi. ''Sahad (na Abuja) muka je, kin gani Daddy na ya sai min kit-kat, ke kuma ya sayo miki 'ribbon'. Ya xaro tafkeken hair-bound cikin aljihun wandon shi, kalarshi 'brown'. Shi yana son kala 'brown' yawanci komi da xai saiwa Jawad, brown ne, nima hakan. Na amsa cike da murmushi ''to kaje kace ma Daddy, na gode''. Ya ruga ya rike shi ''Momina tace thank you Daddy''. Ban san me ya rada mai ba, sai ya dawo ya dare ni, ya karbi ribbon din a hannuna, ya xare kallabina, ya hada jelunan siraren kitso (Jennifer Lopez) dake kaina, ya xurasu cikin ribbon din, ya maida min dankwali na. Ya rada mani cikin kunnuwana, ''Daddy ya ce xa'a baki 'thank u daddy'. 89. Na kyalkyale da dariya ''menene kuma thank u Daddy?'' ''Ba ke kika fada ba daxun?'' Ya maida duba ga Uban a shagwabe ''Dad! Amma baxa a bawa wannan matar ta can dakin ba ko? Bana sonta! Daxu baka nan ta dalla min mari, wai don kawai naki ta daukeni, ko Momi na ai kina gani ko?'' Na sunkuyar da kai ban ce komi ba ''ki amsa masa ZUBAIDAH, anything it's, yaro baya son yayi tambaya ba'a amsa ba''. Sai na dago a hankali na dubi Jawad da dukkan idanu, cikin murya mai nuna kashedi da tsananin tsoratarwa ga yaro karami. ''A'ah, xa'a bata, itama Momin ka ce ita ta haife ka ni na raine ka ni 'second Mominka' ce. Jawad, kai ne ka cije ta kayi rashin kunya, ba'a cixon babba. Daddyn ka yace ''idan kayi wa babba rashin kunya, baxai kaika 'Military School' ba (baxai kai ka soja ba)''. Sai ya kwanto a kirji na, yana wasa da sarkar wuya na. Bai ce komi ba. Abban shi yayi mana sai da safe ya fita, ya ja mana kofar. ************* Aisha Ibrahim Hardo, tun xuwana Nurul-Bayan ta ke kaunata, seat dinta na bayan nawa. Kasancewa ta kwararriya a darasin turanci ni ce wakiliyar ajin mu. Aisha 'yar wani kusa ce a Abuja, suna xaune a Wuse Zone 6, Aisha bata son ace mata Aisha wai sai 'Ashsha', don tsabar son burgewa. Ni kuwa Allah ya daura mata kaunata kamar me. Tayi ta shishshige min niko taka-tsan-tsan nike dasu, don sanin ni ba 'yar kowan-kowa bace a Abuja. Har kullum maganar Goggo na tana nan tana min yawo a kwanya ''duk wata daukaka da kika samu a duniya kada ki boye Babanki Mai-Kalwa ne'' don haka da shishshigin Ashsha ya yi yawa, nace mata ''Goggo na, nifa ba tsararki bace, ni ba 'yar kowan-kowa bace, RAINO ne ya iso dani NURUL- BAYAN, mu 'yan Kauyene a can wata Karamar Hukuma a Kano, Karaye. Yallabai da kike xaton Yayana ne, UBANGIDA na ne''. 90. ''Zubaidah, kina bani dariya, to waye ba asalinshi Kauye ba? Mu ma asalinmu Kauyen Jama'are can cikin Jihar Bauchi, rugar Kakana Hardon Fulani a can yake, sai dai kawai don ban isa bane? Don nasan bani da kyawun da xan jere, a matsayin kawarki''. Baki na bude hangangan cikin mamaki, ''kiyi hakuri Ashsha ba haka nake nufi ba, kuma tunda kin ce haka shikenan''. Daga ranar muka xama wasu irin aminai, duk inda Ashsha Hardo take, kaga Zubaidah Karaye. Malaman mu da abokan karatun mu, duka sun san mu tare. Rannan Ashsha tace wai xata xo gidanmu su gaisa da Jawad Babe, nace mata Jawad bai son baki, amma bata yarda ba tace wai bana son ta je ne. Da yamma lis, wurin karfe shidda, Aunty Mubina tayi parking Volswagen-Bettle dinta, Ashsha ma tayi parking (Volswagen) amma ba (Bettle) ba. Bata ko gaida Aunty ba domin ita yarinya ce mai jin kanta; Ubanta (Commisionern kudi, uwarta Ministan Mata), kanta tsaye ta tura kai cikin gidan. Tom da Ejiro sukayi mata kyakkyawar tarba, Jawad da nake shayi, shima yayi mata murmushi yace (I've been hearing alot about u) Aunty Ashsha, naji dadin ganinki''. Ashsha taji dadi, ta fito sayayyar da tayi mashi kayan ciye-ciye da lashe-lashe masu bala'in tsada. A daki na muka sha hira, ta tambayi Yallabai na sanar da ita yana Canada. Tace Uwar Jawad fa? Nace lokacin tasowar ta yayi, da kyar ma in bata shigo ba. Ta xaro ido ''ba dai wannan mai nanannen hancin da mirimirin idanu da gajarta uwa an kife kwarya ba? Data gani a shigen motarta?'' Na ce ''ki rufa min asiri, ki ceci mutunci na, ta ganki?'' ''Ta gan ni mana! Ko kulata na yi? Ni na dauka bakuwarta ce''. Gabana ya fadi, ni kuma na san yau sai yadda Allah yayi da ni ''ba yawo, ba kawa, ba kaxanta sune ka'idodina''. Ita kanta Ashsha ta lura tayi min ba dai-dai ba. Ta yi shirin tafiya tace in yi hakuri, daga yau baxa ta sake xuwa ba. [10/8, 5:24 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/8, 5:25 PM] A A Dboy: Tuna Baya 91-95 91. Na lura ranta ya baci, na kamo hannun ta na xaunar da ita, nayi mata bayanin yadda muke da Aunty Mubina dalla-dalla, Bata san ina xuwa makaranta ba kuma ba'a son ta sani, don haka xata yi tunanin ina na samo Kawa? Ni da a tsammanin, ko makota bana xuwa? Ashsha ta fahimceni sosai, tace xata fiddani in nuna mata sassanta. Ban san me ta gaya mata ba, sai gani nayi wai har ta rakota kofar sassanta. Bayan tafiyarta Aunty ta kirawoni, wai wannan bakuwar 'yar garin su Tom ce, taxo ganinshi daga America take, tana son sayen share a Bankin su Omega ta hanyar ta, xata kawo wasu takardu in ajiye mata. Mun hadu da Ashsha, washegari a class, nayi dariya har cikina ya kulle itama hakan. Ta rubuta 'short note' tace in bata. ''Aunty, kiyi hakuri don Allah, munyi magana da Babana, yace Omega bai mishi ba, mun saya da Allied Bank, don haka baxan dawo ba. Ashsha Hardo. Da na ba Aunty, ta buga tsaki, ta runduma mata ashar, nima duran xagi tayi, ba girma ba arxiki na kama gabana. Wata rana muna hira da Ashsha a dai-dai (Biology Practical Room) ta ce ''wai Zubaidah mai yasa bakya kwalliya ne?'' ''Kwalliya fa kika ce Ashsha, me yayi ruwan 'YAR RAINO DA KWALLIYA? Kin gan ni, daga wanka, man shafawa mai tsada da Abban Jawad ya aje mani katon daga Lisbon sai farar 'powder' ko kwalli ban sawa''. 92. ''Zubaidah don kina 'yar raino, wannan baxai hana ki yin kwalliya ba. Ke kyakkyawace, kin cika mace a fannin komi, ki dibeni ba abinda xan nuna miki ta fannin kyawun halitta, amma sau nawa xam yi samari ke baki da ko daya? Ba kuma komi bane illa rashin gyara irin wanda maxan yanxu ke so a jikin mace. Ki daina wulakanta kanki. Ki dinga jin kanki 'YA MAI 'YANCI tamkar yadda Ubangidan ku ke so kuyi. Ki dubi Tom, motocin da yake shiga, baya nuna cewa shi kuku ne, sai ke? Wallhi ki yi kwalliya ki gyara jikinki, ki ga abin mamaki cikin Abuja''. ''An ce maki ina da ra'ayin soyayyah? Samari basu dame ni ba Ashsha, na taba yin soyayya can baya wadda ta wargaxa min farin cikin rayuwa. Ban kara marmarin soyayyah ba har yau! Ba kuma na fatan xan yi ta nan gaba. Ko xanyi aure sai don cika sunnar Ma'aiki, amma namiji daya ne, na taba so, na so da dukkan ruhina. Ba kuma xan iya kara son wani tamkar shi ba. Don kada ki ce na ki shawar ki, daga yau xan dinga kwalliya!'' a karshen hutunmu, wanda daga shi in mun dawo, xamu xana 'final papers'. Wata rana Ashsha ta fiddo wasu irin cleansers 'yan Humburgh, wai cikin tsarabar 'Fiance' dinta Alphat daya dawo New- Orleans in da yake karatu. Sai kuma wani da ta ce min a nan ta saya mai tsadar gaske, wai in dinga amfani dasu safe, rana da dare bayan wanka, xasu bada wata irin kala ga bakar mace. A raina nace ''oh, ashe abinda kike yi kenan kalarki kamar matan Morocco, na cigaba, yadda ta koya mani, hakanan duk dinkin da akayi mata a gida, irin shi xata kawo mani dinkin, kalar har komai. Daukana ta yi bayan mun tashi makaranta, ta kaini wani katafaren shago nasu na 'ya'yan gata ('N' park shopping complex). Kayan kwalliya na 'ya'yan hutu, ba wanda Ashsha bata sai min ba, turaruka, jambaki da mayukan gyaran gashi harda 'hand- dryer' ta ce ''ke kanki xaki ji dadi a jikin ki, ki ga kinyi kyau, kina kamshi mai dadi''. 93. Ashsha na masifan son Alphat, dan wani kusa ne aminin Babanta, dake karatu Jami'ar Grosslow ta New Orleans. Duk cikin masoyanta ba wanda tafi yi min xancenshi kaman Alphat Rumah. 'Yan asalin garin Rumah ta Juhar Katsina. Ni ma ina son in ganshi, in ga wanda ya haye kan Jewel in the Savannah tamkar, Ashsha Hardo. To yau da albishir din xuwan sa yi mata week-end ta xo mani, kuma wai lallai in bita mu je can gidan su mu gaisa koda Uniform ne shi ba ruwansa, sai ta maido ni kamin karfe hudu, gidan su Ashsha ba abinda ya dauki hankali na kamar yadda nayi xato don bai kai gidan Yallabai komi ba, sai (swimming- pool) da babu gidan Yallabai. Sai karfe uku ya xo, ni ban ga abin son ba wallahi ban da dai ance shan koko daukan rai. Irin sakarkarun 'ya'yan masu hannu da shunin nan ne kawai, shi kansa bai kama kansa ba, balle ya kama aure, tare da wani abokin sa, da alama abokin yafi nutsuwa, muka gaisa, sabanin Rumah din da tashi gaisuwar ga masoyiyar sa ta nuna min babu tarbiyya cikin al'amarinsa, ko da yake a wurin su wannan ba komi bane, wayewar ce. A gurguje mukayi hirar don hankali na yayi kan Jawad da dawowar Aunty, har kofar gida suka kawo ni bayan sun cikani da tsarabar sittiru cikin wanda suka kawowa Ashsha, da faya-fayan music wanda ni sam ba harka ta bace. Na tarar Jawad yayi kuka ya gaji, su Tom sai aikin rarrashi suke yana dukansu da kafa da kutufo, nayi kiranshi cikin kakkausar murya ''Jawad! Uncle kake bugu, sai na gayawa Daddy, wato in yana nan ne kake dan kirki, in ya tafi mai rashin kunya ko? Ka tuna yace ''Idan kayiwa babba rashin kunya, baxai kai ka Military School ba, (ba xai kaika Soja ba)''. 94. Ya taho a guje ya rungume ni, yayi wani irin ajiyar xuciya, hawaye sun hade da majina, na ja 'tissue' ina share mashi ''Momi na, ina kika tafi kika barni? Suna ta tsokana na wai sai dare xaki dawo, shine nake dukan su, don Allah kada ki fada mishi, ba xan sake ba Momi''. Nayi gaggawar daga shi na rungume a jikina, fuskar Tom ba annuri yace ''daga ina, sai yanxu Tine? Kin samu fargaba. Oga yayi waya Jawad ya fada masa yau kin dade baki dawo ba. Ya yi fada sosai, yace ki rabu da Aishah, ya jaddada ya kara jaddadawa, kuma ki jirayi wayar shi 9:00pm''. Jikina yayi sanyi. Na isa daki na kunna A/C, na fara yiwa Jawad wanka, sannan ni, shirt ce baka nasa maishi da farin wando. Tom (cous-cous) yayi da miyar macen Tolo-Tolo, naci nayi nak, nayi-nayi Jawad yaci ya kiya, wai shi dole sai kamun waken suya, gashi kwata-kwata babu waken suya a gidan ko kwara daya. Na gayawa Peter yace xai nemo. Da kyar na samu na lallabeshi, sai da yaga Peter ya dau mota ya fita sannan ya daina kukan, ya dawo ba'a samo ba, nayi masa inkiyar kada ya fada masa, nasan ya manta. Da daddare mun yi shirin kwanciya, na canxa mai kayan barci nima haka, na kulle kofa muka kwanta, Jawad baya barci idan har bai rabu da jikina ba, na manta shaf Oga xai yo waya. Can tsakar kaina naji bugun kofa, na mike na daura xani da mayafin sallata ''ki fito, Tine Oga a waya''. Tunda naji ance Tinen, nasan Tom ne, shi yace bai son Zubaidah ya riga ya saba. Na ce masa ''ka fara gayawa Aunty Oga yayo waya kamin ni?'' To sarkin tsoron Aunty, da yace in kirawo ta, xan kira kin ne? Ko in xai kirata, bata GSM xai kirata ba?'' ya fadi cikin turanci 95. Na dauki wayar Abban Jawad a falon su Tom, gudun fitowar Aunty. Na lume cikin kujera. Mun gaisa kamar yadda muka saba wato cikin mutunta juna 'Zubaidah, wa cece Aisha Ibrahim Hardo, wanene Alphat Ruma, wanene Yusuf Dabo? Wanda ya baki 'American-Wears' cikin akwati? Wanda ya kawo ki kofar (gate) a motar Camry?'' Mamaki ya kama ni iyaka. Oga ya koma tsibbu? Babu raini tsakanin mu, bana yi mishi musu, bana yi mishi karya, wadannan sune halaye na dake BURGESHI. ''Aisha Hardo, class-mate dina ce, nace muyi kawance har taxo gidan nan kwanaki ta yiwa Jawad dina hidimar data sani sakin jikina da ita. A yau ta ce lallai inje inga wanda xata aura wanda shine 'Alphat Ruma', dayan daka ambata, ni ban ma taba jin sunansa ba. Amma ina jin wanda na gansu tare da Alphat ne. Baki, mai matsakaicin tsawo, shi ya bani kayan daka ambata. A matsayin tsarabar New Orleans, kasacewa ta aminiyar Aishar su''. Ina jin sanda yayi dariya ''dadi na dake; fadar gaskiya a duk inda take, bakya karya, bakya ha'inci. Ina Dan ki, me yake yi a daren yau?'' ''Jawad yayi rigimar shan kamun waken-suya, ya yiwa su Tom rigimar rashina. Lallai ne a kawo waken-suya gobe, in ba haka ba dukkannin mu ba mai barci''. Ya dau lokaci, bai yi magana ba, xuwa can ya ce ''yaya karatu ina fatan kina bita sosai?'' ''Ana yi'' ''ba ku bukatar komi nan Canada? Xan xo unexpected as usual, amma xan gaya maki ina gab da xuwa, don in samu delicious tuwonki, xan samu Zubaidah? A nan ina matukar kewar abincin ki. Zubaidah, 'KE KADAI CE XAKI YI GIRKI IN JI NA CI BAN YI TSAKI BA, BAN TURE KWANUKAN DA RAGOWA BA'. Na lumshe ido a hankali, taushin muryar shi ya ratsa har cikin kwakwalwana, da kyar na iya na ce ''xa'a samu Yallabai, har abin da yafi tuwo, wanda nasan Ba-Hausan bakinka xai soshi. Wai da gaske ka ce in rabu da Aishah?' ''Idan har xata sanyaki turbar samarin ta ba? If not, ki gaida ASHSHA IBRAHEEM HARDO'' [10/8, 5:25 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/8, 5:27 PM] A A Dboy: Tuna Baya 96-100 96. Kalamin Oga, sun bani mamaki, ta yaya xai ce ba xanyi samari ba? Alhalin ya ce muna da 'yancin yin komi gidansa tamkar 'ya'yan da ke gaban iyayen su? Na yi murmushi ''In shaa Allah, xan kiyaye, but please do for me one favour (wato kayi mani alfarma daya) ka gaya min wanda duk yayi maka bayanan da kayi min yanxu, game da su Aisha, I am extremely intrigued!'' Dariya yayi, cikin matsanancin nishadi. ''Xubaidah, kin manta na ce ''XAN KULA DA KE!'' Don haka a ko'ina nake cikin duniya, ina ji, kuma ina ganin duk wani takun sakarki a rayuwa. Kada ki tsaurara bincike, Zubaidah, ki shafa min gudan raina JAWAD''. Har na kwanta barci, ina juya kalamin Ogana, mutum ne da wuya ka fahimci inda xancensa ya dosa. Idan ya murda wata maganar, bana iya warwareta. Ko ma dai me ke akwai, xan kula, baxan taba yin abinda baya so ba! ''Aishah, Abban Jawad na gaisheki'' ''Ke ma Alphat da Yusuf suna gaishe ki, sai dai wani muhimmin sako daga YUSUF DABO, wanda nike fatan ki amsa da hannu bibbiyu'' ta xaro wani dan karamin (complementary carde da akayi dan rubutu a baya, da farko kamar in ki amsa, sai kuma na amsa din. (Zubaidah! Luv, so easy 2 say, so easy 2 spell, but we've ever given luv a chance 2 spell itself 2 u) Yusuf . Na dubeta, cikin tsananin rashin fahimta ''me kenan?'' ''Ma'ana yana SON KI. Wallahi Zubaidah Yusuf dan manya ne, mai sanin ya kamata.'' Duk sai ta bani dariya. ''Goggo na kada ko kara yiwa kanki karambani irin wannan a kaina. Ki na so Oga ya kore no ko?'' Why, don me?'' ''Ra'ayin shi ne, ban kuma tambaye shi ba''. ''Shikenan xan wa Yusuf bayani''. *********** 98. Mansina, ta dawo Indonesia ranar lahadi wurin karfe 9:00pm, bata xame ko ina ba sai gidan aminiyarta. Mubina xaune bisa 'carpet' din falonta, ta barbaxa takardu da 'yar karamar 'computer laptop' a gabanta, kai da gani kasan lissafin Bankinne da baya karewa. Mubina ta tare ta da murna, amma da ganin fuskarta, ta san labarin ba mai dadin ji bane. ''Me kike yi?'' Abinda Mansina tace da ita kenan tun kamin ta samawa kanta maxauni a falon. ''Wallahi sabon Manajan mu ne ya hada ni da aikin lissafa abinda muke bin wani 'foreign trader' amma nake jin na kammala''. ''Game da taryar mijinki fa?'' ''Wai mara mutuncin nan (Baban Jawad), cewa yayi xai dawo? Yaushe?'' Tayi xugum tana dubanta kamar ta makure ta don haushi, ''wato Mubina duk abinda na gaya maki, kinyi watsi dashi. Don ke naje Indonesia da kaina. Don in gyara ki, mijin ki ya soki, amma kina nan kina bobbotsaren taki. Jiya a labaran BBC naji sun taso daga Canada, me kika tanada?'' ''Yo in ma nayi kwalliyar yabawa yake? Inna yi shegen shaye-shayen ya san an yi? Kin ganni nan, gobe idan na bar gida sai goma na dare. Akwai aikin lissafin da xan yi... ''Na ji-na ji, Banki uwar ajiyar kudi, kina da labarin 'yar rainon ki, na shekararta ta karshe a makarantar su kanwata Aisha? Aisha na koya mata karuwancin kwacen miji? Mubina ki kama kanki, ki fidda 'yar rainon nan daga gidannan. Ga magungunan gyara na hado maki kiyi amfani da kowannen su a yau, (kuji sai kace wata uwar ta, Takori), ba Taheer ba, ko Sarkin Karaye kika danawa wannan tarkon, sai dai uwar shi ta haifi wani, amma ba shi ba kara kallon wata diya mace da sha'awar aure. Sauran dubarun na bar maki, kiyi amfani da hikimar ki ta diya mace, ki lallameshi cikin hila da kissa ya sallameta, ki karbeshi da murnar ki, ko kin samu ya taya, in ma bai taya ba, kada ki kyaleshi, ai hakkinki ne''. Da haka sukai sallama, xuciyar Mubinah tamkar tafasashshen ruwa. ''Black, a Nurul-Bayan?'' 98. To me xata yi mata ta huce? A doke dai, yanxu sai dai su kirbi juna. A xage, sai dai tayi ta kare, ba xata daga ido ta dibeta ba balle ta tanka mata ba. Abu mafi a'ala ta Mansinar ce da tace ta lallame shi, ya sallameta hakannan. Washegari, bakwai na safe a Omega tayi mata. Wai tayi ta kammala abinda xatayi xuwa shidda na yamma ta dawo. Tun karfe goma na safe, ina ji a radio saukar shigaban kasa da ministocin sa da sukayi mai rakiya xuwa kasar Canada, domin kulla cinikayyar man fetur tsakanin kasashen biyu. Shi kuwa Yallabai dama ya je da biyu ne, rakiyar shugaban kasa da karbar ragamar kamfanin su na carpet wanda a da yake mallakin su su hudu, wanda a yanxu ya xama nashi shi daya bayan wasu kudade masu yawa da ya biya sauran share-holders mamallaka kamfanin. Sun sauka ne a filin jirgin saman Abuja, karfe biyu na rana. Na rubuta komi, na baiwa Tom, ya nemo mu yiwa Oga abinda xamu burge. Sai gashi harda garin masara da tsaki daga wurin Kulu da Gasara mai kyau. Jawad na gefe a kicin din yana ta fama da bindigar roba, na tankade gari tas, na ware tsakin nayi kyakkyawan tuwon masara miyar xogale, da aka wadata da toxon Saniya. Sannan dambun tsakin masara da dambun shinkafa, wanda yaji kayan hadin su green beans, cabbage, carrot da sauransu. Maimakon nama, da yankakkun kananun hanta nayi amfani. Tuwon shinkafa mai sulbi da miyan taushe, wadda ta ingantu da kayan hadi cikin tsokar kaxar gona. Na hada kunun xaki da gasarar yaji kayan yaji da kayan kamshi. Lemu da na hada kayan marmari kala-kala har kala biyar wato abarba, lemun xaki,Inab, tuffa da strawberry, shi ne na karshe. Na adana kowanne a flask dinshi daban. Na kama Jawad yana ihun in barshi yayi wasan sa, nayi mai wanka, na shirya shi cikin wani irin 'suit' kalar 'brown' da fari ta ko ina kamshi yake. Yayi dariya a yayin da nike fesa mashi Dune ''Momi na, kullum Daddy yaji ina kamshi, sai yace Allah ya sakawa Momin ka alkhairi'' na ce ''na ji''. 99. Tun haduwan mu da Ashsha nayi sittiru ba kadan ba, kowanne bana banxa ba. Dama kuma Abban Jawad bai rageni da komi ba ta fannin tsadaddun sitturu. Kuma nafi son in sa nashi in yana nan, bakin shi baya shiru da yaba mani, ya kan ce wai ni bana raina abinda aka bani. Wannan ya tabbatar mani duk kyautar da yayiwa matarsa, baya burgeta. Nayi wankan rana na kamar yadda na saba. Atamfa Super-Holland kalar ta orange da blue, duk cikin kayana, itace tsohuwa, domin akalla ta doshi shekaru uku, itace a jikina. Dinkin mai kama jiki, dan caras iya cibi, xaninne ke karawa har kasa. Banyi daurin kai ba, don ba damu na yayi ba. Xagayo da dankwalin na yi wuya na sai shacin fuskata kawai xaka iya gani, wadda na san haduwarmu da Ashsha, gabadaya ta canxan, tsari da fasalin halitta na ya koma irin nata. Tace wai turare in ka fesa shi yana sawa kaji ranka da dadi, don haka na dau daya cikin turarukanta ''GUCCI'' na feshe ilahirin jikina dashi. Na kuma ji dadin. Jawad yayi dariya ya sakalo hannayen shi xuwa wuyana ta baya ''Momi na, kinyi kyau. Idan Daddy na yaxo xan ce ya baki turare, yau kin fesa turare'' ''ni kuma in ka fada, in fada masa kutufo da ka rinka yiwa Uncle Tom rannan''. Ya kyalkyale da dariya ''ai bai ji xafi ba, bari ma in tambaye shi Uncle Tom!'' ya shiga jerawa Tom kira, sai gashi a sukwane, hannuwan shi dama da hagu rike da tumatir da tattasai ''lafiya? Irin wannan kira haka Master?'' ''Nothing actually. Dama tambayar ka xan yi, wannan kutufon da nayi maka kaji xafi?'' Tom yayi tsaki ya juya ya fice, sai kuma ya dawo ''Tine, danki bashi da dama''. Momi na baki tambaye ni ba, karatun da kika biya min jiya da daddare, na rike'' ''To na tambaye ka yanxu, yi in ji?'' ''Sai mun kwanta akan carpet'' ''ni kuma bana son kwanciya, sai barci ya daukeni'' ''To Momi ki xauna akasa, in kwanta a cinyarki, sai kifi jin in ina karatun sosai''. 100. Na sauka kasa daga kan kujera, ya kwanta duka a jikina, ya soma karanto ''Suratul A'ala'' ina shafar kanshi, in yayi kuskure, in gyara mashi. Ya dade yana kallon mu, admiringly, baya son katse mu, baya son daina kallon wadannan fuskokin guda biyu. Wadanda ke faranta masa, su wanke duk wani bacin rai da ke tare dashi, wadanda da ganin su kasan ba abinda ya dame su a rayuwa, face kauna da kulawa da junan su. Sabanin shi da xuciyar shi ke cike da kuncin rayuwa, duk a dalilin rashin dace da samun mata ta gari, thoughtful and caring tamkar mai rainon Jawad. SHIN MAI XAI HANA SHI AUREN ZUBAIDAH MUHAMMAD KARAYE? Wadda ke kula da gidan sa, gudan jinin sa, cikinsa da mutuncinsa baki daya? Wadda xuciyar sa ta dade tana kawata masa tsararren jikinta da ko a turai, bai ga kwatankwacinsa ba! Wadda ya dade yana kimanta dan kyakkyawan bakin ta a yayin kissing! ''Kada kayi haka Oga ne fa'', xuciyar shi ke tunatarwa 'to Oga, bai san mai kula dashi ba? Bai san mai mutunta shi ba? Bai san abinda xuciyar shi ke so ba? Bai san mai kula da cikin sa ba? Sai kawai ya juya, ya maida musu kofa ya rufe. Munji maida kofar dukkan mu. Muka dubi kofar, ba kowa. Amma kamshin da ya turare dakin na Yallabai ne. Jawad ya mike a guje ''Daddy na, ya dawo Momi ki tashi muje mu bashi abinci''. A'ah Jawad, jeka kai kadai. Uncle Tom xai kaiwa Daddy abinci'' ya shagwargwabe fuska ''Momi na, kullum nace muje dakin Daddy na, sai kice baxaki ba, amma shi yana xuwa dakin ki, kuma waccen matar tana xuwa kullum''. Me xancewa yaron nan? Tambayarshi ta bani mamaki, ba kuma nason ko kadan yayi tambaya in ki amsa mishi ko in mishi karya. Ya tsatstsare ni da fararen idanunsa, na sunkuyar da kaina. ''Jawad ita matarshi ce, ni ko mai rainonka ce kawai, kaga ya dace yaron gida ya dinga shiga dakin Ubangidansa, ba'a kirawo shi ba?'' Ya girgixa kai, da alama ya gamsu. ''TO ME YASA BAXA KI AURE SHI BA KEMA?''.Wannan yaron da kure mutum yake, kaifin basirar shi yana bani tsoro, to me xan ce masa kuma? [10/8, 5:27 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/8, 5:35 PM] A A Dboy: Tuna Baya 101-105 101. Sai na wayance ''kai na daura xuwan xafi a Gas, maxa jeka yiwa Daddy welcome''. Na mike, shima ya kama hanyar kofa yana kunkuni. ''tunda baxa ki gaya min bam xan je in tambaye shi ai shi xai gaya mini''. Xuwa can ya dawo ''Daddy yace, kixo ki xuba mashi abinci, yaji ciwo a hannu'' ''kai don me baxa ka xuba masa ba?'' ''Ni baxan taba tuwo ba, bana son shi''. Nayi dariya ya dare bayana, muka tafi sassan Yallabai. Sanye yake cikin kafta da wandon farin danyen voyel, yana kwance cikin kujerer alfarmar main falinshi, rike da waya ana ta xabga turanci, ya rufe wayar a cikin kallona ''Xubaidah Jawad ya wuce goyo, bakya tsoron ya bude maki kirji ne? l' ''Ai shi din ne, ya riga ya saba'' ''ki sauken abincin kasa, yau bana son hawa table din''. Nayi murmushi, Na yi murmushi, a raina nace ''gargajiyar ta motsa kenan''. Na koma na dauko katuwar ledar cin abinci, na shimfida a gabansa na sauke komai, Jawad na kalmashe cikin jikin shi, ''wanne xa'a fara ci?'' ''Wanda duk kika ga ya dace'' ''ai kowanne ya dace'' ''to a bani kowannen''. Ina xubawa yana kallona, wanda hakan ya haifar min da rudewa, rawar hannu da rikicewa duka. Ya sauka a kujera ''kin tsugunna kamar ace ar, ki danna a guje, xama xaki sosai. Yau tare xamu ci abincin'', YA ILAHI, na dubi Yallabai ya xame min wani karamin yaro, magana yake min kamar Babyn dake gaban Mamarshi. ''Ni da Axumi nake'' ''axumin menene?'' ''Na tadauwi'i mana'' ''A'a na ramumuwa ne, in kuma kince baka ba, ki rantse; wallahi axumin tadauwa'i nake. Sai nayi kus, na xauna can gefe a darare. Al'amuranshi masu ban mamaki ne, komi nake yi ya sani. Tunda ya fara cin abincin bai kara magana ba. Sannnu-sannu, daga gyan-gyadi barci mai nauyi ya dauke Jawad. Duk abinda ke wajen nan Yallabai ya ci kowanne, ko ba'a fadi ba. Shiru ga mai cin abinci santi ne. Da gani ya bala'in yunwatu, don ma dai yana da jure yunwa. A turai yafi son yayi Axumi, duk bayan kwana daya, don bai son abincin su bai burgeshi. 102. Na yi murmushi, a raina nace ''gargajiyar ta motsa kenan''. Na koma na dauko katuwar ledar cin abinci, na shimfida a gabansa na sauke komai, Jawad na kalmashe cikin jikin shi, ''wanne xa'a fara ci?'' ''Wanda duk kika ga ya dace'' ''ai kowanne ya dace'' ''to a bani kowannen''. Ina xubawa yana kallona, wanda hakan ya haifar min da rudewa, rawar hannu da rikicewa duka. Ya sauka a kujera ''kin tsugunna kamar ace ar, ki danna a guje, xama xaki sosai. Yau tare xamu ci abincin'', YA ILAHI, na dubi Yallabai ya xame min wani karamin yaro, magana yake min kamar Babyn dake gaban Mamarshi. ''Ni da Axumi nake'' ''axumin menene?'' ''Na tadauwi'i mana'' ''A'a na ramumuwa ne, in kuma kince baka ba, ki rantse; wallahi axumin tadauwa'i nake. Sai nayi kus, na xauna can gefe a darare. Al'amuranshi masu ban mamaki ne, komi nake yi ya sani. Tunda ya fara cin abincin bai kara magana ba. Sannnu-sannu, daga gyan-gyadi barci mai nauyi ya dauke Jawad. Duk abinda ke wajen nan Yallabai ya ci kowanne, ko ba'a fadi ba. Shiru ga mai cin abinci santi ne. Da gani ya bala'in yunwatu, don ma dai yana da jure yunwa. A turai yafi son yayi Axumi, duk bayan kwana daya, don bai son abincin su bai burgeshi. 103. Ya kammala, na tsiyaya mishi ruwan lemun SANA ya fara sha, sannan wadanda nayi ''Zubaidah, kada ki kara yi min haka, ya baki fara bani wanda nake so ba, xaki bani farin ruwan banxa?'' ''Na tuba Yallabai'' ''baki tambayeni ciwon da naji ba, ko Jawad bai gaya miki bane?'' ''Ai ban ganshi bane shiyasa, amma ya gaya mani'' ''kin ganshi, ai a ido ne''. A karo na biyu, tamkar wata doluwa, sai na kai idona ga idanun Yallabai. Wai me yasa maxa suke shammata na irin haka? Su dulmiyar dani a tafkin kaunar su? Babu ko tantama nasan irin wannan kallon cikin idanun BELLO WAXIRI. Babu komi cikin kwayar idon Baban Jawad, face fitinannen so. Sun juye, sun rikide xuwa 'luv colour'. Wani abu ne ya tsirga min tun daga kirjina har xuwa yatsar kafata, na ji wani irin yarrrr! Nayi saurin sauke idona. ''Kina da maganin wannan? Zubaidah! Xaki bani?'' ''Ni... ni.. ni.. bana da maganin komi''. ''To tashi je ki, tunda bakya badawa, ki binciko mani komi kankantarsa''. Har na kai bakin kofa yace ''xo ki fice min da Dan ki'' na dawo da sauri kafafuna se karo suke da juna, shin yaya xanyi in dauki Jawad, alhalin gabadaya cikin kirjinsa yake? Ganin na tsaya cak, na kasa koda motsi, ya san tunani na. Ya fidda yaron daga jikinshi, ya kwantar dashi a kujera, na matsa na russuna na kai hannuwana ga Jawad ''iye, ashe gaskiyar Jawad kin sa turare mai dadi, to nima gobe xanxo a sammi ni''. Ai Zubaidah, baki ya mutu murus, na dauki Da na na yi waje, na gayawa Tom yaje ya kwashe kayan abinci. A wannan daren mai cike da rudani a gareni, na kasa barci. Wani abu ne na ji yana yanyameni, a gabadayan sassan jikina, game da Abban Jawad! Ba dai SO ba? Bana fatta, kuma bana addu'ar, in kara son wani namiji a rayuwata! Tun daga kan Bello, na rufe shafin soyayyah, balle da Ubangida na da nake gani da mutunci tamkar Babana!!! 104. Idan nayi haka, ai nayi abin kunya, 'YAR WANKE- WANKE TA AURE MAI GIDA? Na tuna da maganar marigayiya Goggo na Indo. ''Ki guji duk wani abu da xai sa kiji kunyar mutane. Gara ki mutu da ki aikata ABIN KUNYA!'' Xan yi kokari in bar gidan nan haka, tun kamin abin kunya ya tabbata. In ba xolaya ba, xuciyata taki amincewa. Cewa take ''Zubaidah, baxa ki iya barin Jawad da Abban Jawad ba!'' Mutumin da ya mutunta ki, a yayin da aka wulakanta ki, mutumin da bai kyamace ki ba, a yayin da ake ce dake mai yalayen hakora, mutumin da ya suturta ki, a yayin da aka so kiyi yawo cikin tsiraici, mutumin da ya fidda ki daga matakin JAHILA xuwa DALIBA mai 'yanci. Mutum da ya dauki Dan shi sukutum, yace ya mallaka maki... Ya maida KYANDIR mutum. Ya maida MUBURGI muciya. Ya maida BLACK LIGHT, ya maida ATINE MAMMAN MAI KALWA ZUBAIDAH MUHAMMAD KARAYE... (these and many more), ai ya cancanci a so shi koda baya da abinda xa'a so shin, balle yana dashi, yana da komi tunda yana da halaye na kwarai, wanda mace baxa ta taba dana sanin auren shi ba. Mutum wanda ya san mutuncin dan adam, ya ke kiyaye martabar kauyen shi, kasar shi da al'adun shi na AREWA. Ban taba ganin mutum mai daukaka kasar shi da kare martabar al'adun shi a duniya irin Baban Jawad ba (Ethnocentrism). Mutum wanda yake karrama 'yan mahaifar shi TALAKAWA, wanda bai taba xagin MAI-KALWA ba mai xai hana ki aure shi Atine koda BA KYA SON SHI! Ki jiyar dashi dadin aure wanda bai samu ba a rayuwar shi, ki mutunta shi, mutuncin da bai samu daga Uwar Dan shi ba. Ki nuna mishi TALAKA BAI MANTA ALKHAIRI, ki mallaka mishi jikin da ya raina daga 'YAR SHILLA XUWA KAXA bai taba nuna yana kwadayi ba. Auren shi shine hanyar da gudan xuciyar ki JAWAD, rayuwa ta har abada! Shine sakamakon da ya dace da shi. In kika bijirewa soyayyar shi kin yi butulci balle ma kina so, kina son miji irin ''TAHEER'' wanda bai dauki rayuwa a bakin komi ba. 105. Arxikin shi bai sanya shi ya maida duniya gidan kashe-ahi-ba. Kuma tabbas, xai darajja MAIKALWA xai mutunta AMARYA! Shin me kike nema a rayuwa da ya wuce wannan? Wasu irin hawayen dadi suka xubo mani, na mirgina na rungume Jawad, cike da tunanin wani magani xan bincikowa ciwon idon Abban Jawad?????? A bangaren 'yar boko, bata shigo gidan ba sai karfe 6:00pm. Sun shigo tare da wasu kabila 'yan office dinsu maxa guda biyu, inda ta sauke su har main falon ta. Abokan aikin ta ne, ita a dole ta nuna musu eh, ya ne! Mijin ta Minister ne. Don haka ne taki saukar su a falon baki, don bai kai haduwar nata ba ko kadan. Wasu takardu ne suka xo amsa da ya shafi aikinsu, ta xarce daki don ta binciko. Daga can sassan Yallabai, 'yar karamar na'ura mai kama da karamar talbijin, mai nuna masa wanda duk ya shigo ko ya fita cikin gidansa, haka in baya nan, xata dauka in ya dawo yayi rewinding ya gani. Ya hasko mishi Peter na jerawa bakin Aunty lemuka da kayan tande-tande, bai taa xaton xagewar Mubina har ta kai ta shigo mishi da abokan cinikin ta gidan auren sunnarsa ba. Inda duk ranshi yake, in yayi dubu ya baci, dama wai mai hakuri, bai iya fushi ba. Mubina ta fito daki da takardu a hannu, sai ganin falo tayi wayam. Ta leka ta taga, sojoji ta gani na ball dasu, har suka fidda su kofar godan ta. Ta san ba yin kansu bane, suna a bisa umarnin Ubangidan su ne. Ta ji haushi, amma ai fushin fari ba nata bane. Ta tuno rayuwar su da Taheer yawon amarci birnin Toronto. Da yaga wani abokinta sun gaisa ya sambace ta. Ita da abokin ya hada ya dinga tamaula dasu a harabar hotel din, kadan ya rage auren sati biyun ya tungule, sai da Alhajinta yayi masa kuka. To wannan taci sa'a kenan da ba'a hada da ita ba. Ita wannan ba shine damuwar ta ba, abinda ya dameta kawai, yadda xa'a dinga nunata a Bankin su ana mijin ta da take takama 'kidahumi ne'. [10/8, 5:35 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/15, 9:14 AM] A A Dboy: Tuna Baya 106-110 106. Hakannan wannan tamkar baraxana ne ga shirin su da Mansina, sai dai tasan Taheer sarai mutum ne mai tsananin tausayin mace, musamman in yaga tana kaskantar da kanta. Da wannan ta samu kwarin gwiwar xama ta fece kwalliya, ta cika cikinta da tsatsibe-tsatsiben kayan da'arsu 'yan duniya. Kwalliya ce da take ganin ko xaben Miss Nigeris ta shigo da ita ba abinda xai hanata lashe xaben. Wata riga ce da ko a turai ba'a ko'ina ake samunta ba, sai a wani boutique dake cikin birnin Beijing din China, da ta ba Yayanta Yahai dake karatu can sautu. Wuyanta ya rufe har saman wuyan mutum ruf. Hannun kuma an wani irin ketashi tun daga sama har xuwa 'armpits' din mace. Tsayinta iya cibi ne kawai, laushi gareta tamkar kirar (Romania) tasa wando ya taho a matse daga sama ya bude kadan daga gwiwar har xuwa kasa. Ya sha ce mata bai son kwalliyar ixgar dokin da take mishi don najasa ne, don haka ta hade shi cikin wani tafkeken ribbon mai ciki, kunnenta da wuyanta ta kawata shi da fashion na garari, wato majoricca-pearl, ta kawo turarukan ta duka sexies ta bulbula. Ana taku tamkar ana tausayin kasa, aka nufi sassan Daddyn Jawad. Shi har yayi shirin kwanciya, ya yi nafilolin shi ya kare, yana daure igiyar pyjamas dinshi, ta danna kararrawa, ba tare da jiran ya amsa ba, ta dannan kai, abinda ya tsana kenan ''wai ke bakya sallama ne? Annabi (SAW) ya ce; mafi rowarku shine wanda baya yiwa jama'ar musulmi sallama. Kullum ki danno min kai ba sallama, ance maki ni kafiri ne xaki ishe ni da kararrawa. 107. Ta langwabar da kai ta rausayar da 'yan idanunta ''kayi hakuri Taheer, baxan sake ba''. Tun daga nan ya gane take-taken ta, tunda har ta bashi hakuri, tana wannan lallankwashewar shegiyar tata ta kawota. Ko dai shi ake so, ko kuma wani dalili nata na daban. Xa ko tasha mamaki, don shima yanxu kan mage ya waye, ya daina tolerating iskancin banxa. Ya bar ta nan tsaye, yayi light-up yabi lafiyar ni'imtaccen gadonshi, ya dauki remote ya karo karfin room heater. Kasancewar sanyi yayi nisa kwarai da gaske, farkon watan April. Barci mai dadi ke dibarsa, xuciyarshi cike da tunanin hanyar da xai bullowa 'yar yarinya Zubaidah, mai tsananin kunya da kawaici. Ruhinshi ke hasko mishi ranar da xai mallaki Zubaidah Uwar Jawad, a wannan katafaren gadon da ya narkarda dalolonshi amma bai taba samun nutsuwa a kanshi ba. Cikin shekarun shi masu tsayi, da aure sai shirme, sai fitsara, sai rashin kamun kai. Shi dai yana da yaqinin Zubaidah xata xam mai nutsuwa agare shi. Ya tuna a yau, taki yadda ta dauki Jawad a jikin shi gudun haduwar fatar jikinsu. Shi ko tashi matar tun kamin a yi auren take nuna mai kulaficinta a fili. Ba don ya kasance mutum wanda yafi karfin xuciyarshi ba, da Jawad yanxu Dan titi ne. Yayi Allah wadai da tarbiyar da Mr. Dango, yawa su Mubina dasu Mimi. In ba don kaddara ba! Me ya kai shi hada xuri'a da Balarabe Dango? Ji yayi ta rungume shi ta baya, ta soma magana cikin muryarta mai kama da an shaqeta. ''Taheer, ina ganin lokaci yayi da ya kamata mu MAI DA BLACK KARAYE. 108. Iyayenta suyi mata aure, tunda Jawad ya girma xan iya kula dashi yanxu, tunda kaga ba xancen kashi da fitsari, ba xancen goyo da bada madara. Ajiye baligar yarinya kamar wannan a garemu bai dace ba. Ka duba fa ka gani ko su Tom na iya lalatata! Mu xo muna jin kunya, ai gara ayi abi lokacin da ya dace. Sai muyi mata kyauta ta musamman, ko 'yar mota ce da 'yan kudi, a bawa kauyawan iyayenta, kuma ita ma kanta na lura, ta matsu ta ga iyayenta, ko ya ka gani?'' Ta fada tana kara shige-mishi. ''Kai wannan yarinya, ba dai rainin hankali ba''. Ya fadi maganar a xuci ne, bai san har ta subuce, ta fito ta shiga kunnen ta ba. ''Dama nasan abinda ya kawo ki kenan?'' Ta kara narke mishi ''bayan wannan, wata da watanni, ina xaman jiran mijina ya dawo, ai dole in nemi hakkina na aure ko?''. Yayi murmushi, ya mike gabadaya ya sauka bakin gadon, ko kadan tarkonta bai kamashi ba. Lallai ne da aka ce bacin rai ke danne komi. Ya girgixa kai cikin matsanancin takaici ''Taso-taso nan Mubina''. Jikinta a bala'in sanyaye, ta xaro kafafunta ta xauna gefen gadon, kusa da shi. ''Hakkin aure kika ce ko? To a gaskiya, in gaya maki aurennan, aurennan namu da gyara a cikinsa, a addinance da al'adance. Shin ina kika taba ganin masu rayuwar aure irin namu? 109 Addinin Musulunci ya sanar damu cewa idan ma'aurata suka doshi akalla watanni ukku, basu kusanci junansu ba, haka kawai, ba wani dalili, to sai an gyara auren, domin kamar ba aure ne tsakaninsu. A bar wannan xancen, don ni bai dameni ba, ba shine a gaba na ba. Maganar da kika yi, na wadda kika kira, Black! Wadda ainihin sunan da Ubanta ya rada mata , ZUBAIDAH! Kin yi gaskiya, akwai abin dubawa a ciki. Dama na dade ina tunanin abin, don haka ne gwanda da kika tunasar da ni. Zubaidah ta isa aure kwarai, shekaranjiya dana lissafa ya kama nan da wata uku xata cika shekaru ashirin da daya. Ta xo mana nan shekarunta goma sha uku, na kai ta Primary tayi shekaru biyu ta xarce babbar makaranta daga aji biyu (JSS 2), a yanxu tana shekarta na karshe. Bai fi wata uku ba xata xana (Secondary School Certificate) din ta. Allah ya bata mijin aure tuni, da ta kammala xan shirya masu birthday a can KARAYE, ita shekara 21 Jawad 'seven'. Idan xaki muna maraba da ke. Harma kawar ki, data fi mijinki muhimmanci a gareki, MANSEENAH IBRAHEEM HARDO. Xancen su Tom, kada su lalatata! Allah ya kare, wannan yarinya mai sanin darajar kanta, addininta, iyayenta, mutuncin ta na talaka, wanda bai aje ba bai ba kowa ajiya ba. 110. Ta yarda ta saida mutuncinta ga KIRISTOCI, tayi shiru bata gaya min ba. Kuma in gaya maki gaskiya, yaran nan baxa su taba cin amanata ba... Suna kaunata, kaunar dake bakya mini, suna kula dani, kulawar da ke bakya mani, suna kyautata mani, kyautatawar da ban samu daga gareki ba. Suna kaunar Da na, da bani da kamarsa a duniya. Don haka nima bani da kamarsu, baxan taba xargin su da abinda xuciyarki ke tunani ba. Ba don kudina suke xaune dani ba, sai don na nuna masu suma suna da 'YANCIN KANSU, talaka nada 'yanci a gidan mai kudi, 'yancin da xaiyi abinda yaga dama, daga cin abinda yake so xuwa amfani da motocin sa, kwana a gidansa shiga dakinsa, ba tare da wani kyama ba. Na nuna masu everybody have right to education. Ba sai dan wane ba, ba sai wanda Uban sa yake wane a Abuja ba. Don haka baxa su taba xalintata ba. Baki san wani abu bane, wani kiristan yafi wani musulmin tsoron Allah. Yafi wani musulmin rikon amana. Tom, tamkar Uba yake ga Zubaidah. [10/15, 9:14 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/15, 9:15 AM] A A Dboy: Tuna Baya 111-115 111. Shi ya koyar da ita A,B,C,D, ya koya mata yadda xatayi rayuwa cikin masu kudi, yadda xatayi magana cikin turanci tamkarsu, yaya xa'ayi ya nemeta? Yaya xa'ayi ya bari wani cikinsu ya bata ta, bai gaya min ba kada ki karayin wannan tunanin game da bayin Allahn nan, domin kin masu KAXAFI. Dole Zubaidah ranar da ta kammala makaranta, ranar xan sadata ga iyayenta, tare da mijin aurenta amma yanxu tunda kince kin lura tana son gaini iyayenta, karshen satinnan xan kaita ta gansu, ta dawo ta kammala jarrabawar sai ta koma ga iyayenta suyi mata aure. To amma Mubina? YAYA XAMU YI DA JAWAD? XAMU BARWA MIJINTA NE, KOKO XAMU KYALESHI, KEWARTA TA KASHE SHI, KO RASHINTA YA SANYA MISHI CUTAR DA BAMU DA MAGANI? IN GAYA MAKI GASKIYA BAXAI IYA RAYUWA BA TARE DA ITA BA! Itace wacce; - Ta rungume shi, a yayin da Uwar shi ta dangwarar da shi a dandaryar kasa, ta rungume shi a kirjin ta mai ni'ima. - Ta bashi madara, a yayin da Uwar sa ta hana shi nono. - Ta xauna dashi, a yayin da Uwar shi ke gantali. - Ta bashi ruwa, a yayin da Uwar shi tace wai kada a bashi ruwa. - Ta goya shi ta rarrashe, a yayin da Uwar shi ke ganin GOYO XUBEWAR AJI NE. - Ta wanke mishi kashi da fitsari da tumbudi, a yayin da Uwar shi ke ganin KAXANTA NE. - Ta bashi dumin jikinta na Uwa, wanda yafi komi dadi da muhummanci ga yaro, a yayin da Uwar shi bata da lokacin wannan. - Tayi mai murmushin Uwa, amsa tambayoyin yarinta, ba gaxawa ba hantara. Shin ya xa'ayi ba xai so kasancewa da ita har abada ba? - She is some1 who knows all his needs, his hopes, his dreams and desires. - With a genuine interest in all that he do, some1 who guides him and inspires. - Her smile to him is loving and tendered. By her maternal understanding and gentleness too, makes his life more rich and complete. - She is full of true wisdom and strength to loveliness, insight and grace. - She is some1 whose love he will cherish forever! 112. Amma ta yaya wai xaki ce yanxu xaki kula dashi? Kuma ya yarda da ke, bayan ya sha gaya mana BAYA SON KI! Waccan matar yake ce miki. Yarinyar nan, na kokarin ta wurin fahimtar dashi ke ce Uwarsa! Ita 'yar Raino ce. Bata taba boye masa ba dai-dai da rana daya. Don haka? Wanda yayi wa jininka wannan abu? Akan wasu 'yan kudi kalilan, da bai ma taba karba da hannunsa ba, bai tabbatar ba, ana bashi ko ba'a bashi? Me kike ganin Uban yaron nan xai mishi, ya biya shi, yayi mishi karimci fiye da wanda yayi mishi? Motar banxa! Mubina na barki da wannan, barci xanyi, kada ki sake ki rabe ni bana so!''. Ya juya, yayi kwanciyarsa. Ta dade a xaune tana jera kuka mai tsuma xuciyar miji. Amma mijin ko gexau. Ta mike ta kunna fitilar dakin, dakin ya gauraye da haske. Ta dafa kirjinta da hannunta na dama, idanuwanta cike taf da hawaye, ta soma magana; Taheer dan Usman, dan Sarkin Karaye! Akan mai yalayen hakora, mai kafa kamar ta shanshani, dadiron ka mai rainon ka, ka wulakanta ni, ka manta alkhairin da Ubana yayi maka. 113. Daga dan Kauye ya kai ka makaranta, ya maida ka dan birni. Daga Dan Sarkin Kauye ka koma shugaba a Ministry of Foreign Affairs, amma sakamakon ka; wulakanta da toxarta 'yar da baya da kamarta. Ba sai ka tsaya kwana-kwana ba, kwana-kwana ai na kananan maxaje ne, wadanda matansu suka fi karfin su, kai ko nasan namiji ne, dan Sarki jikan Sarki, mai ji da kansa da ilminsa, amma ka tsaya rabe-rabe? Ai kawai kace xaka auri 'YAR RAINO, tir! GIRMA YA FADI! (sunan littafin Takori mai xuwa), koda yake dama tuntuni ya fadin, don daga ganin yarinyar nan tana shining tana haske tana cika, nasan an saba holewa. To ni Mubina, 'yar Balarabe Dango! Idan har na haifu cikin Uwata da Ubana... Baxa ka auri yarinyar nan ba. Koda hakan na nufin xamu koma yawo cikin bante da dako ni da iyayena, baxa ka aureta ba! Sai na salwanta rayuwar ta, na kakkarya kafafun shegiya, na munana fuskar tsinanniya, na maida ta NAMIJI. Namiji sai ya auri namiji kenan''. Yallabai ya mike, tana gab da kaiwa bakin kofa, ya fincikota ta fado tsakiyar dakin ''ai gara a baki garanbawul din tafiya mayar da ita namijin, idan ke kika halicce ta''. Ya figo belt, tafkeke cike da karafa, ya soma shimfida mata tana ihu tana kara maimaitawa sai ta maida 'Black' NAMIJI. Ya yada 'belt', bayan ya tabbatar yayi mata ligi-ligi, bakin ya kumbura suntum, jiki yayi birda-birda da karfe. ''Bari in baki guarantee na tafiya Xangon-Kataf, kije na sakeki saki daya. Saboda mutuncin rainon Jawad, wata tara da nakudar haifeshi. Da kuma karamcin Balarabe Dango. 114. Gobe inji an sallameni daga kujerata, karewa kenan dama baso nake ba, asiri akai min to Dango kije ku cigaba. 'Yar raino kuma da kike ambato KAMAR NA AURETA NA GAMA. Kin san kakan holewa? To har shege mun haife mun kai KARAYE. Ranar duk da kika xo kofar gidana, sai nasa an yanke maki wadannan kafafun masu kama da tabarya! Ranar duk da naji wani abu ya samu 'yar mutane, sai kin kwanta a kiri-kiri... '' Yana fadi yana ball da ita, har iyakan falonshi. Kwana uku suka shude, ba mu sa Yallabai a idonmu ba, hankulan mu sun tashi ainun. A na hudunne ya nemi Tom, a waya ya sanar dashi yana nan lafiya. Yana hotel din Sharaton, yana samun hutu, sabida baki masu xuwa suna damunshi. Ejiro ke kyankyasa mana, wai yana tsammanin Oga ya saki Aunty, bayan ya dankara mata dan banxan duka. Domin jiya General Balarabe Dango, yaxo neman shi a rude, shi Ejiron ya samu inda shi kuma ya bayyana mishi basu san inda Oga ya tafi ba, kwana biyu. Kuma ya ga kannenta su Mami da Yayan ta Yahai sun xo daukar wasu akwatunan ta. Hankali na ya tashi ainun, na shige daki nayi ta kuka. Bawai tausayin Jawad nake ba. Na san a kowanne hali Ubanshi xai kula dashi. Amma ni na xamo annoba kenan? Ni ma tabbas ya gano wadda ta fini son Jawad din, ya dankara min duka ya sakeni. Allah yaso dama ban amsaba. Na shiga hada kayana tsaf, xaman me xanyi? Gida ba mace? Ba mai gidan? Dama cikin hutu nake. Nayiwa Jawad wayo na turashi kitchen wajen Ejiro, na hada kan kudadena masu yawa, wadanda yawanci irin wadanda Yallabai ke bamu ne, in xaiyi tafiya. Bana sayen komi, tunda bamu rasa komin ba. Dama ance ajiya maganin watarana. Sun tasamma naira dubu tamanin (N80,000), akwatuna biyu kawai na diba. Na kai su waje da dai-dai da kyar. Nace direban da ke kaimu makaranta ya kaini gidan Kwamishina Ibraheem Hardo. 115. A kofar gidan su Ashsha, tsaye suke jikin farar Camry din Alphat. Gabadaya suka iso ga motr, Alphat ya bude min kofar. ''Ya, kawar mu lafiya dai kike wani a birkice?'' ''Ba komai, kaina ke sarawa''. Ashsha bata ce komi ba, ganina ina sauke akwatuna kamar wata wadda tai gudun hijiri, illah ta lallaba Alphat ya tafi. A dakinta take sanar dani Mamanta taje taron matan Women-Affairs jihar Calabar. Na nade kafa na warwarewa Ashsha komi, na kuma roketa da ta rakani Karaye. Na kare xaman gidan Yallabai. Ashsha ta dade tana kallona ''Kin taba gaya mani wani sentimental da Marigayiyar Goggonki ta gaya maki, ''Zubaidah! Gaskiya da karfi, sune kyawawan sutturar talaka''. To baki da karfi ne, ko baki da gaskiya? Mara gaskiya shi ke gudu, shi ke ja da baya. Ba duka da saki ba, kome Yallabai yayi wa Aunty Mubina, dai-dai da shine. Aminiyarta Mansina yayata ce Ubanmu daya, tana yawan korafin aminiyarta bata jin kyawawan shawarwarin da take bata. A ganina Baban Jawad, bai cancanci wannan butulcin daga gareki ba. Ke da bakinki kinsha gaya mani abinda yake maki ko Ubanki sai haka, baxaki iya biyan shi ba, kina tausaya mishi rashin dace da macen kwarai. Yanxu ne lokacinda ya dace ki biya wannan alkhairin da ingantacciyar kauna, kulawa da soyayyah, wadda bai samu daga matar da bata mutunta shi ba. Zubaidah! Baki dace da kowanne namiji a duniya irin Baban Jawad ba! Ki fidda tsoro, nasan kina so ba bakya so ba. Mubina ita ta yar, kika dauka, ba laifi bane, babu cin amana a ciki, tunda dama ita bata rike ki da AMANA BA! Ki xamo wise mana! Xuby na, ki maida martanin soyayya mai gardi, ki more miji mai tsada? Na dade ina maki sha'awar, hadadden Ogan nan naku. Maxa irinsu wuya suke 'never leave something you can do today, until tomorrow (kada ki bar abinda xaki iya yau kice sai gobe). Opportunity comes only once in life! Maxa tashi muje, in maida ke gidan aurenki, naga kinyi yaji harda su akwati, shame on you!!! [10/15, 9:15 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/15, 9:16 AM] A A Dboy: Tuna Baya 116-120 116 Muje oya, tun bai dawo baki nan ranshi ya sosu ba. Mu je my dear one; Jawad, jikina ya bani ya fara kuka. Haba 'yar Karaye?'' Da haka ta sani dariyar dole, ta shigo motar mu tana kiran Alphat a waya, wai yaxo ya maido ta daga gidansu 'yar Karaye. *********** Tom ya shigo inaiwa Jawad shafa ''Tine, Yallabai fa yana palour, ana bidar lemun ki mai sanyi''. Na mike kawai na hado kemu na bashi ''a'aha! Yau kuma mulki ake ji. Baxa ki kai ba? Nima baxan kai ba, in baxaki ba kada ya sha kenan''. Ni dai nasan bani tsoron Yallabai. Amma kunyarsa nake ji yanxu, kunya ba kadan ba. Na dake na gyara fuskana, na canxa kaya xuwa babban dinkin shadda Senegal. Dana na gaba ina biye, har falon Yallabai. Yana hada takardu Jawad ya ruga gareshi, ya kama shi ya rungume, wai sai ya gaya mishi inda yaje kwana biyu, bayan ba Canada bane? Ya ce ''naje Sheraton, na kwana na wuni ina hutawa, naso in tafi da kai, sai nayi tunanin Momin ka baxa taji dadin kwana ba kai ba'' ''to ba sai mu tafi da ita ba?'' ''Tambaye ta mana! Me yasa baxa mu tare ba? Bayan bamu da Momi yanxu sai ita? Ba ta tausaya mana? Ko mai yasa? Oho!''. Ya dawo gareni, da na takure a can gefensu ''Momina, kwanaki na ce don me bakya shiga dakin Daddyna? Kika ce ke ba matarshi bace. Na ce don me baxa ki aureshi ba? Kinyi shiru, to yanxu don me baxaki aure shi ba? Tunda waccan matar ta tafi?'' Nayi kus, tamkar ruwa ya ci ni, ina kallon fuskar Yallabai dake kan takardu yana murmushi kasa- kasa. Ya san yaron ya hada mani xafi ya kuma sani a kwana ''wai kai Jawad, komi sai ka ji ne? Ka fiya surutu'' na mike ina shirin tafiya ''sai yaji mana? Tunda ya shafi Babansa. Jawad, ka ji bata so na ko? Wai nayi mata tsufa, tunda na haife ka''. Ya yi wani iri da fuska kamar karamin yaro, yadda yaron xai ji ya damu sosai. Saura kadan, dariya ta kwace mani, Jawad, yayi shiru yana hararata, da kyawawan idanunsa. 117. Nace ''ni kake harara ko? To gaya min ni da Daddyn, wa ka fi so?'' ''Ni ba ruwana dake''. Ya koma jikin Babanshi ya kwanta. Naji ba dadi, na fita raina a jagule. Na kwanta, amma barci yaki xuwa. Tom ya shigo da akwatuna biyu, wai tsarabar Jawad ne inji Yallabai. Na tashi na duba kaya, kayane irinna yaran da iyayensu ke ji da su. Kayane na 'ya'yan daga wane sai wane, na kara sakankancewa da kaunarda Yallabai ke yiwa Jawad. Ina hada kayan naji sallamar Yallabai, Jawad a gaba kamar marayan da ya rasa Uwa. Tausayin su ne ya kamani duka. Lallai duk matsayin mutum a fagen soyayyah, yaro ne. Kujera daya suka hade shi da Dan shi, na sunkuyar da kai, na rasa me yake min dadi? ''Ba mu yi fushi ba, mun biyo Zubaidah da kokon barar mu, taji kanmu, gatan mu Allah, kuma Zubaidah. Mai nema shi ke kasa har kullum, don haka gamu a dakin Zubaidah. Muna rokonki shin are we accepted?'' Gyada kai kurum nayi ''dama tana xuwar wa mutum sau daya ne a rayuwa''. Na tuna maganar Ashsha Hardo, gashi nima so ke ci na. Yallabai ya lumshe ido, kenan farin cikin ya fi gaban kwatantawa. Ya kannewa Jawad ido, ya nunani da baki ''to yanxu da ruwana dake'' na harareshi nima. ''Jawad wai me Mominnan naka ke shafawa fatarta ne? Ta xama farar Morocco? Tayi kyau, tayi fata lafiyayyu?'' Kunya ta kama ni, nayi cikin daki na barsu ina ji Jawad yana fada masa wai Aunty Ashsha ce ta kawo mata kayan shafa. A kofar dakin ya tsaya, a yayinda na koma can gefe ina jan carbi, wanda in xa'a kasheni, bana ce ga ayar da nake ja ba ''wallahi sai naga abinda ake murxawa. Don baxan yarda da wanda xai cutar ba. Ko ya kace Jawad?'' Ya gyada kai yana dariya da jerarrun hakoransa farare kal ''Kwarai Dad, u're quite right! Ai ni nasan inda suke'' ya soma janyo drawers ya xaxxage tulin kayan shafe-shafe. 118. Oga yayi mamaki, ya kwashe duka a babbar leda. Ya daga ledar 'cleansers' din wurinsu Alphat ''clean&clear'' ya fadi a mamakance, ya kara fadi, ''ai bakin naki ne kilin-kiliyar''ya turasu duka a ledarsu ''sai da safenku, karshen wadannan dustbin baxa a sake shafasu ba. Bakin AREWA, nake son MOMIN JAWAD DA SHI''. Ni dai bance kanxil ba, ban kuma dube su ba, yana fita na dubi Jawad ''munafiki dan wuta ne inji Allah'' ''yanxu Momi munfunci nayi?'' ''Munafinci ne mana! Ina ruwanka da abinda nake shafawa?'' Ya kanainaye a jikina na ture shi, ''na tuba Mummy na. In ya xuba a dustbin, xansa Uncle Tom ya kaini in debo miki''. ''Ni ba ni xaka tubarwa ba, Allah da ya hana munafinci''. Yayi dagwalo kamar yayi kuka ''Allah na tuba'' na jawo shi na rungumeshi sosai ''shikenan ya karbi tubanka, Jawad. Domin shi yace mu gaggauta tuba''. ''Lah! Momona kin ga na manta, yace ga tsarabarki ta Canada, wai sai xamu kwanta xan baki'' ya xaro mani dan karamin kati daga aljihun wandon sa, cikin ire-ien mitsi-mitsin greeting cards din kasar Canada. Katin cike yake da xanar xuciya guda biyu. Ganinshi kadai xaki kimanta darajarshi, daban take da sauran cards. Dan gajeren rubutun ya sanyaya mani, ya faranta mani, ya fiye mani akwatin kaya daya saba yo mani. 'The truth..... I must confess! Since you arrived, you've touched and influenced my life dramatically 4 good. To the extent thay a day without a thought of you, is a dead day. You have in no little measure helped me to realized my life's dream. You've made my life rich in a wonderful way. Taheer. 119. Ji nayi idona ya wani lumshe a hankali, A! Wai na canxa mai tsarin rayuwa xuwa mai kyau, KO DAI YA CANXA MANI? Maganar Maikalwa, Babana ita ke min yawo a wannan lokacin. ''Kowa yace gonar wani ba xatayi albarka ba. To tashin ce baxa tayi ba!'' Ni kaina nasan gonata, tayi albarka, ta kowanne fanni. Ilmi masoyi na hakika wane BELLO WAZIRI KARAYE? ********* Jakunkuna ne da akwatuna Tom ke jera min, tun daga uwar dakina har falo. Yana dariya yana tafi ''Tine, ashe yau sai kwanan Karaye. Sai kwana gaban BABA da AMARYA. Xan ga Ya Auwal ashe?'' Sai naji maganar wata irin banbanrakwai. Lokaci guda, xuciyata ta soma harbawar farin ciki ''Oga yace ki diba kayansu Baba. Inda abinda xa'a kara in karo. Karfe 11:00am xamu dauki hanyar KARAYE''. Hawaye suka xubo min masu xafin gaske. Mafarkina na shekaru, me xan yiwa Abban Jawad dinnan in biyashi in ba kauna ba? Tamkar an tsikareni. Na fada wanka, a gurguje na kammala, Jawad tun safe da na shirya shi, yana can wurin Babanshi. Na kira Ashsha, ina cike da doki da murna ''Ashsha Karaye-xani-Karaye-xani, na rasa ina xan sa kaina ne don murna?'' ''Ki bari don Allah. A! Gaskiya nima baxa a barni a baya ba, xani inga Sadiya inga Ya Auwal. Above all, our beloved Amarya da Baba''. Allah Ashsha da gaske kike?'' ''Na taba yi miki wasa ne?'' ''Xaki iya kwanan kauyen mu? Da gidan mu da ko fanfo babu?'' ''In naje Tilde yaya nakeyi? Nima in mun dawo, xaki rakani Tilden, bikin wata cousin dinmu Joda'' ''kiyi sauri to don Allah ina jira'' ''kin fara yiwa me tafiyar bayani? Kinsan tsarinsa? Kika sani ko xai daukeni? Don naga alama Yallabai bai damu da kawancen mu ba''. ''Bari to inje in tambayo shi, haba! Xai yarda mana''. Na ruga a guje, sai kuma na dawo agujen, na daura xani bisa rigar wanka, na yafa babban gyale. A guje nake wallahi, nayi sallama bai amsaba. Na sake yi da alama baya kusa, Jawad yaxo ya bude. 120. Ya dareni ''wai Kauye xamu inji Daddy?'' ''Ina Daddyn?'' ''Wanka ya keyi''. Na xauna cikin kujera, ina kallom tashar CNN dake ta aiki. Yallabai ya fito, cikin jallabiya fara sol, da farin towel akansa yana tsane ruwa. In banda kamshin bathrobb dinshi na dunhill ba abinda ke tashi a falon. ''Ga ni meye ake nemana urgently, kamar naci bashi ban biya ba?'' Na kunyata, na muxanta da xaman jiran da nayi, meya hana in koma in dawo, da naji wanka yake? Wannan jallabiyyan, ya fidda xahirin kira da xatin Yallabai ne. Har wani lafewa take a lafiyayyar fatar jikinshi. Yadin 'xeena-gaxar' ne iyakacinta kauri, bakaken gassu ne masu yawa suka rufe kafarshi baki daya tamkar wani balarabe. Dogo kakkarfan namiji, mai tashen talatin da biyar. Wanda ya tara dukkannin halittar karfafan maxa. Barin ingarmar kirjinshi, shike burge Mubina a halittarshi bakidaya. ''Yallabai na... na...dawo..'' na samu harshe na da tangarda a yayin furta hakan ''a'ah ki fada mani, yanxu xamu tafi, nagode da breakfast, a yi min lamurje a cooler. Tuwon shinkafa, taushe da naman tolo-tolo shine guxiri na. Jirgi xai tashi sha daya da rabi, don haka ki hanxarta''. Na mike kaina a kasa, naki yarda in kara dubanshi. Har na kai bakin kofa, na tsinkayo sautin shi na cewa ''idan munje, da kudin aurena, xan fara tarar Baba. Mu dawo Abuja a karasa jarrabawa. A kammala birthday, in cafki amaryata, mai kunya. Amma ina jin, da ta isa Wellington ko Rio 'de Janeiro (Brazil) xata koma hatsabibiya...'' Ina! Na kai kofa na fice, Jawad ya biyoni, shekarunshi bai kai ya fahimci me ke cikin xancen Abban shi ba, illah dai yayi dariya. Ya san tsokana ce yake mani. Barin da yaji ance 'a cafke' sai ya kara tintsirewa da dariya. ''Aisha Hardo na, ke neman matsugunin xuwa Karaye. Sabida ingantacciyar kaunar da take mani''. Haka na rubutuwa Jawad, cikin tafin hannuwanshi. Nace ya je ya kaiwa Daddy. Ya dawo rike da wayarshi. ''Wai ki rike xai yi miki magana''. [10/15, 9:16 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/15, 9:17 AM] A A Dboy: Tuna Baya 121-125 121. ''Aisha Hardon, ta ci gidan su, nacinta da shishshigin ta yayi yawa. Kinsan mai yasa na tsaneta? Sabida taso ta kakaba maki Yusuf D. wani dan tsohon barawon Gwamnati''. Haka yace mani cikin wayar. Haushi ya kamani. Ya xanyi da kunyar Aisha? Dabara taxo mani, na kira ta nace mata Yallabai yace tayi hakuri ya turo mata da driver, domin yayi 'booking' kujeru ba ita. Allah sarki Ashshah! Tace min ba komi itama xata bi jirgin yawo. Mu hadu a Kano, filin jirgin saman Mal. Aminu Kano. Karfe 11:00 na kammala komi na xuba mishi cikin 'cooler' da 'flask' kaman yadda ya bukata. Tafiyar shi daban da tamu, sabida 'yan rakiyar shi. Hakanan Yallabai inda duk ya sauke kafarshi nan (escort) din shi xai mayar. A reception na hango Hardo, jingine jikin karfen bene. Sanye take cikin english-wears kaman yadda yake a al'adarta ta daura siririm kallabi a kanta. Hannunta na dama sakale da jakarta helena-ricci yayin da na hagun 'yar karamar waya ce Siemens. Muka hade da rabi-rabin runguma. Tuni direba daga gidan Maimartaba ya sha gaban mu, Jawad na gaba mu muna baya. Mun dauki hanyar Karaye, nake bayyana mata rashin jituwar su da Yallabai. Tayi dariya sosai tace xata neme shi a Karaye ta bashi hakuri. Ita dama tun sanda na gaya mata Oga ya hanani samari, ta san da kyar in ba kamu yake wa kansa ba. Da kyar in wanna Ubangidanci bai koma something special ba. Mun iso Karaye, kimanin 4:00pm. Na umurci direban ya saukemu dai-dai gidan kakana Liman. Bana son su Amarya su ji wani kugin mota. Sai dai kawai su ganni, kamar daga sama. Nayi mamakin yawan akwatunan da Ashshah tasa direba ya sauke, bayan na wurin Yallabai. Nayi mata magana tace Mamarta ce tasa ta hado su wai taba Amarya, da Atika da nake yawan bata labari. 122. Duk yawan sauye-sauyen da garin Karaye ya samu sakamakon sabon 'chairman' mai aiki tukuru, jan gwarxo Honourable Sunusi Atta A karaye. Wannan bai hanani gane hanyar gidanmu ba, gidan Maikalwa da Daddawa. Abinda ya dan sani faduwar gaba, rashin ganin almajiran Liman, wadanda ada kullum basu rabo da kofar gidan. Tuni wasu almajirai sun yanyame mu, sun kwashi akwatuna, nace musu su kai gidan Maikalwa. Suna tafe muna biye dasu, har kofar gidan mu. Wani abin mamaki rusashshiyar katangar an tadata da siminti, xauren da ba ruff, an rufeshi ruf da Axara. Kalwar dake tike dashi babu ko buhu daya. An malale tun daga dakalin gidan har ciki da malalen siminti. Auwal na soma hange tsaye, fes dashi, cikin makubar shaddah keda ganinshi kinga wankakken dan bokon Kauye. Yaga yara yuuu na bin wasu 'yan mata wadanda da alama ba daga Nigeria suke ba, kuma gidansu suke dosowa, ya daka masu tsawa suka watse, suna ihun yeee! Ga 'yan Agulla daga Wantsandan da baturen Dan su. Jawad ya rude ya rukunkume ni, nayi masa magana cikin sauri da turancin da yafi sabawa da shi, ina kallon Auwal, ina doka murmushi. Ya koma relaxed. Har yanxu Auwal ya kasa magana, sai da muka karaso, xamu shiga ''can i offer u any help?'' Ya tambaya da alamun bai son mu shigar musu gida ''Ya Auwal kenan. Ni ko mutuwa nayi na dawo, na ganka cikin kowanne hali, baxan kasa ganeka ba!'' Xuciyar shi ta soma xolayar shi, wai wannan kanwar shi ce, ATINE, da aka kai wanke-wanke a birni? Haba! Ina Atine ta iya turancin da ya ji tana xabgawa wannan karamin yaron? Ina Atine tayi kyawun haka? Ina ta samo wadannan turawan? Bayan ance matar gidan dan Maimartaba take yiwa wanke-wanke? To ko waccan ce dan matar dan Maimartaban? To amma ai, basu fice shekaru daya da Atinen ba kai ina! Ficiciyar kanwar shi Atine mai siraran kafafi, ta koma tamkar 'yar sarkin Masar? 123. Tuni suka baxama nemo Baba shiko Auwal neman pure-water ya tafi ya sawowa Aishah, da Dan da yake xaton kanin ta ne. Cikin dan lokaci gida ya cika fam da 'yan uwa da abokan arxiki kowanne yana shafata yana sunsunani, sun rude da yiwa Amarya murnar dawowa ta. Kakata Luba ta shigo xanin ta na kwancewa tana rikoshi, ta tsufa ainun. Na mike na tarota na rungume ''ashe Atine xan saki idona kamin tadda kushewa?'' Abinda take fadi kawai kenan, cikin xubda hawaye. Ashsha ta xama 'yar kallo, tausayin mu ya cikata. Ta tabbatarwa kanta ba karamin xaman kadaici nayi ba, yadda nake da iyaye da 'yan uwa masu kaunata haka. Sai ta shiga share hawaye. Shiko Jawad yayi wuri-wuri sai jefa ido yake waje-waje. A haka Maikalwa ya fado su Sani biye dashi, ''wai Uwata ce ta dawo?'' Ya ratso mutane ya iso ga wadda ake yanyamewa. Sanye cikin tsalelen Lesi ruwan kasa mai firgitarwa. Doguwar mace siririya sambal tamkar tarwada, mai tattare da duk wani sirrin kyawun da 'ya mace ke tinkaho da shi., daga yatsar kafarta har gashin kanta kyau ne xiryan, mai nuni da jikin da ya huta. Tabbas duka wurin babu kamarta. ''Atine na ce?'' Ya fada a yayin da hawaye suka wanke masa fuska. Na mike daga jikin Luba, na rungumo dattijon Babana, na xaunar da shi nima kukan dadin nake ''Babana, naji dadi da na sameka lafiya. Na tafi a MOTA na dawo a JIRGI, na tafi a wadda tayi rashin masoyi, na dawo da MIJIN AURE. Na tafi a JAHILA, na dawo a DALIBA mai 'yanci. Na tafi a KYANDIR na dawo a MUTUM, na tafi a MUBURGI na dawo a MUCIYA, na tafi a ATINE MAMMAN MAIKALWA na dawo a ZUBAIDAH MUHAMMAD KARAYE, to meye na kuka? Kuyi farin ciki, wanke-wanke alkhairi ne a gareni''. Baba yayi murmushi, tunda kika tafi Uwata bamu kara yin TALAUCI ba. Bamu kara saida KALWA ba. Bamu kara rasa kudin makarantar yara ba. Bamu kara saida KALWA ba. Bamu kara rasa abinci mai kyau ba. Wannan bawan Allah da kikewa aiki naira dubu hamsin yake bani a kowanne wata. Duk wata sai ya xo ya gaishe ni, ya gaya mun lafiyar ki kalau. 124. Don haka hankalin mu duka a kwance yake, ni kaina nasan rainon ki, RAINON ALKHAIRI ne a garemu. Gashi a yau a dalilin rainon, ki xama mace abin alfaharin kowanne Uba. Lallai kowa yace GONAR WANI BAXATA YI ALBARKA BA, TASHIN CE BAXATA YI BA!'' Inna dake xaune wai sai ta kama kuka. Tana rokon in yafe mata, in yafewa Atika ba laifin ta bane. Ni wallahi na ma mance da xancen kaf. Nace ''ni mai kikai min ne? Me Atikar tayi min?'' Sai a lokacin na tuno wai wani saurayi can dan gidan Waxiri shine take kuka? Na bita har dakin ta ina rarrashin ta, ina tambayar ta INAA ATIKA? Sai ta kara tsananta kukanta. Ganin haka na kyale ta na dawo ga bataliyar dangina. Ana ta labarin bayan rabo. Wacce 'yar gidan wane ta mutu, wane ya mutu, wane tayi aure. A nan na tsinkayi labarin mutuwar kakana Liman, bayan tafiyata da shekaru biyu. Bamu samu kebewa da iyaye na ba sai misalin karfe goma na dare. Amarya na can madafi tana kokarin hadawa Ashsha abinci. Jawad tun maghriba Kakarsa ta turo Talatu ta tafi dashi wai taga Maigidan ta. Ni kuma a barni in xanta da iyaye na. Baba ya ba Auwal yayo cefane na musamman, Amarya kuma ta aika Sadiya sayen lemun kwalba mai sanyi wajen wani mai shago can wajen gidan Maimartaba, duka sabida bakuwar su, Aishah. Xancen cigaban da Karaye ta samu, shi yafi daukar hankali na. Ga dai ruwan sha mai tsbata, ga kuma wutar lantarki ta haske ko'ina. Ashsha ta ji dadin hira da Baba da Amarya, ba don komi ba sai don su mutane ne masu saukin sha'ani. Amarya ta kare shinkafa fara da taliyar macaroni, ga farfesun kajin hausa yaji kayan kamshi. Auwal ledar pure-water ya dire mana, amma Ashsha bata nuna komi ba, ta dauka ta sha fuska a sake, duk da nasan ko spring water ba kowanne take sha ba, wannan yasa na kara jin kaunar ta, ba don komi ba sai don fahimtar da nayi ita mai kauna ta ce kurum sabida Allah ba don wani abu da na mallaka ba. 125. Babana ya rasa ina-yaka-saka-ina-yaka-aje da ni? Ya dubi Ashsha cike da murmushi ''Uwargida na, Indo, me xamu baki ki ci?'' Ashsha sai dariya take. Ta jero akwatuna dai-dai har bakwai, uku nata ne, hudu daga yallabai, ta farko ta Maikalwa ce, shadda, yadi, voyel bandir-bandir ga kudin dinkin su a kai har (N30,000), mai bi mata ta Amarya ce, tamkar kayan lefen budurwa, lesika, shaddojo, atamfofi (super-exclusive) da Aura. Aura ne kawai a ciki. Ta fidda turamen Hollan da Ingila guda bakwai tace wannan Baba yaba Innar Jafaru, na Atika ma wanda da kudin ta ta hada mata ta bude masu sun gani, tace sai hanu da hannu xata bata. Auwal, Sani, Salisu da Rabi'u kowanne ya samu kayan samari, na fito da tsarabar autar Amarya Sadiya da Jafaru duk ba wanda aka bari tamkar Yallabai ya binciki adadin mutanen da ke cikin gidan, koda yake nasan kadan daga aikin shi. Maikalwa sai kuka wanda baya mishi wuya yace ''shin meke tsakanin Atine da Yallabai Magajin-gari ne? Ni fa wannan abu ya soma bani tsoro''. Ashsha ta kalmashe kafafu tana murmushi tace ''koma menene Baba shi da kansa xai gaya maka. Amma in kyankyasa ma karambani, Yallabai auren Zubaidah ne ya kawoshi''. Baba yayi shiri da alama kanshi yayi xafi. Ya sunkuyar da kai ''In nace xan gaya maku abinda mutumin nan ke yi mani a shekarun nan, wallahi sai in yi karya in kuma mance wasu. Duk sanda yaxo Karaye, daga gidan Ubansa sai kofar gida na. Duk shaddar da ke jikin shi haka xai shimfide ta a kasa yace ''Baba ina wuni?'' Idan har akwai abinda xan mishi in biya shi bai wuce bashi auren Uwata ba!'' To a dakin Amarya ma xancen da suke yi kenan, ni ina uwar dakin Inna na barci mai dadi na dibana kadan-kadan sabida gajiya. Ashsha da Inna kusan kwanan xaune sukayi. Gabadaya rayuwata gidan Yallabai, makaranta da ya kaini, barmin rikon dan shi da yayi, rabuwar shi da uwar yaron, duk Ashsha bata boyewa Inna komi ba. To Inna ta nuna rashin gamsuwa da halayyar Yallabai tace da sanyin muryar ta ''kuma sai ya saki Uwargidan shi don xai auru YAR RAINO?.. [10/15, 9:17 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/15, 9:18 AM] A A Dboy: Tuna Baya 126-129 126. Haka akeyi? Waya ke son mutum mai saurin saki? Ashsha ciki ya duri ruwa, nayi nadamar surutun ta da har bai boye wani sirrin tayi hamxarin gyara xancen ta da cewa ''ita ce tace baxata xauna da mai wanke-wanke ba, shine ya sallame ta''. Ga dukkan alamu Inna bata gamsu ba. Washegari tun kamin in tashi barci, da sanyin asuba har Ashsha ta sa tsintsiya ta share tsakar gidan mu tas, ta sharewa Inna Amarya daki, tasa tsumma a ruwa ta goge ledar. Ta hada 'yan kayan Sadiya ta ninke ta kimtsa dakin tsaf. Ta sa guga a rijiya ta janyo ruwa, ta hada kwanukan da ke gindin rijiya ta wanke ta kife su a kwando, ta cika bokiti ta dauraye jikinta. Ina hana ta amma taki ji, cewa take ''wai baki san in naje Tilde, har tatsa nikewa Kakata Danejo ba?'' Ta shirya cikin siket da riga mai dogon hannu kamar kullum, ta nufi dakin Maikalwa suka gaisa Auwal ma yana nan suka shiga hira wadda duka ta Yallabai ce. Buhunan shinkafa, katon na taliya, katon na maggi, garwannin mai, kwandunan kayan miya, buhunan gishirin Dangote, katon na madara, katon na bournvita, buhunan suga da katon na lemun (five- alive). Katon na (tropical and squash juices) duk daga Yallabai a kawowa Baba. Bai shigo ba sai karfe goma na safe. Mallam Mamman, ya rasa ta inda xai sa surukin shi sai ya shimfida masa buxun sallar shi. A wurin shi karshen karramawa kenan da yake yiwa baki masu muhimmanci a gareshi. Shi Yallabai Baba burge shi yake, yadda bai rudewa duk sanda yaxo gaishe shi irinna sauran talakawan Karaye, komi na shi cikin nutsuwa. Ya cika su da kudi duka gidan, babba da yaro. Tom ma ya shigo ya gaida Baba, Inna da Amarya. Washegari yamma lis yaxo, wannan xuwan na gimbiyar ne kenan. A dakin Auwal akayi mai masauki. Tun safe da ya aiko xai xo Amarya bata barmu mun huta ba. An yiwa Yallabai funkason alkama da taushe cikin tantakwashi, ga gudun kurna, alkubus da miyar agushi cikin naman kajin hausa, wainar masar shinkafa da sinasir. A bangaren lemu kunun xaki ne da yaji kayan kamshi, 127. Lemun citta (ginger) da lamurje (xobo). Salisu ya samo kankara an sa yayi sanyi. Dakin Auwal bai bukatar gyara tunda degree na biyu yake hadawa a Bayero. Hutun karshen mako ke kawo shi Karaye. Duk da haka naje na xuba turaren wuta cikin garwashi mai dadin kamshi. Muna aiki Ashsha na tambayana wai me xata ce da Yallabai yayi hakuri? Sanye nake cikin karamar atamfa Cote D'voire dinkin 'yanmatan Abj ke yayi a lokacin, kalarta ruwan bula ne mai duhu, Ashsha na gaba ina bin ta a baya har dakin Ya Auwal. Yana rike da jug na kuma tambulan mai garai-garai. Yallabai magana yake a waya..'' (Yahai) ka faye damuwa, nace xanxo, yanxu ina Mubinar? A yanxu ina garin mu ne, amma yau xan taho, ka gaya mata Zubaidah da Jawad na gaishe ta in tana amsawa... ''Hardo ta dube ni mukayi murmushi, a raina nace har xa'a shirya kenan. Xa'a hada biko da neman sabon aure, manya kenan! Ya rufe wayar shi duk ya wani wayance, ya san munji yace ina Aunty? ''A'ah Ashsha ke da nace bana gayyatar ki, shine kika biyo mu gayyar sodi?'' ''Ranka ya dade ai don in wanke wancan laifin nawa ne, na baiwa Yusuf kanwata, naxo Karaye musamman don in wa Yallabai campaign ne'' ''tunda haka ne? You are highly welcome to our beloved town, Karaye. Muma in xaki Tilde? Xamu rakaki''. Ya juyo gareni da wani irin rikirkitaccen kallo cikin kwayan idanun sa ''Momin Jawad, jiya Fulani bata yi barci ba, Jawad, ke kiran Momin sa. Ranar da xan cafki Momin, ko yaya xa'ayi da Babyn?'' Sai gani yayi Hardo ta fita babu ko waiwaye. Shaf ya mance da ita a dakin xaune. Ya dinke fuska ''ke ni nace ki kawo kawarki?'' Na tintsire da dariya na dawo kasa ina xuba mai Alkubus, ''an dai yi abin dariya, MANYA sun kwafsa'' ''wannan kamshin da nike ji, tun kafin in kai bakina, nasan Alkubus dinnan xai hadu. In na rage, xaki juyan a flask in tafi dashi in ci a jirgi?'' Nayi dariya kadan ''haba-haba, Oga da flask din abinci, wannan abin kunya da me yayi kama? Kuma ya bude a ga Alkubus, cukusum, babu ko kyawun gani, haba Baban Jawad!'' 128. ''To an ce maki ni xan rike? Kin ga in kin hana ne ki fada, ba sai inje in sa matar Waxiri tayi min ba?'' Na durkusa gaban sa a hanxarce ''Na tuba Yallabai. Na tuba na bi Allah, na bi umarnin ka! Allah ya huci xuciyar Yallabai na, xa'a bada Alkubus da taushe, harda funkaso''. Dariya na bashi sosai, ya kwantar da kanshi a masangalin kujera yana nuna ni da dan makullayen hannunshi, a tausashe yace ''Zubaidahhhhh, Atine-Zubaidah ki na BURGE NI!'' Duk abinda ke wurin nan Yallabai yaci kuma ya yaba yace ya gode. Kuma in ba Hardo hakuri daga yau aminiya ce. Mun rabu akan sati mai xuwa xamu koma makaranta mu xana JAMB da SSCE. In mun kare sai bikin birthday da xai shirya mana. Gobe xa'a kawo kudin gaisuwa dana aure duka, don Baba tuni ya bashi aure. Muna dawowa xa'ayi daurin aure da biki da biki gabadaya. Lefen ma duk kafin mu dawo xa'a kawo. Ya kuma bani waya nokia don in muna da matsala ya ji? Sai kudi don bukatan mu a Karaye. Kwana biyu ana ta amsar baki 'yan taya murna a gidan mu, na kudin aure da aka kawo. Kudin aure na da aka kawowa Baba dana gaisuwa, kamar kullum yace sun yi yawa. Sai kace sai da 'yar xai yi? Duk rikon wahalar da yayi mata? Da kyar Waxiri ya lallabeshi yace Taheer don kar ya firgita shi ne ya bada (100,000) gaisuwa da kudin aure duka. Amma ko auren shi na fari, a sanda ma baiyi karfin haka ba, ninkin haka sau biyar suka kai akace sunyi kadan, 'yar ma da basu san asalin ta ba balle tushen Karaye? Gabadaya dangin Yallabai suna murna da wannan auren, domin cikin dangin Yallabai kaf, babu mai shiri da Aunty Mubina, ba don komi ba sai don hali irin nata da kowa ke kokamawa. Masu xuwa ganina, duka Ashsha karbar mutumnci take masu, gata da son mutane, cikin dan lokaci kowa ya saba da ita. Jawad na wajen mu tun tafiyar Yallabai, sai dai tambayoyi kam, nasha su a wurin sa game da nan ina ne? Su waye tsofaffin nan, na nan gidan, da na can gidan? Wancen yaron da majina a hancin sa, meyasa? Wannan yarinyar Momi an fara mata kitso, 129. Ba'a karasa ba. Kafar wannan tsohuwar, a tsatstsage Momi. Ni baxan sha ruwan rami ba (rijiya), ni baxa ai min wanka da ruwan rami ba. Ana I gobe xamu koma, na bar Ashsha da Jawad, xasu gidan wata kanwar Oga, na nufi gidan Kakana, Marigayi Liman. Inda nake tsammanin xan samu labarin 'yar uwata, ATIKA. Na tambayi Inna tace tayi aure kawai, shima Baban haka yace, 'ya'yan ta uku, sun ki suce a rakani gidan ta, haka shima Ya Auwal. Wai ina ruwana, sai naji kwakwaf? Ita Inna tun xuwan mu ta kasa sakewa a gidan, ta hana kanta sukuni, daga daki sai daki, to shin me ya faru ne? Don jin wannan Amsa sai mu hadu a littafi na 2 Alhamdulillah, nan muka kawo karshen littafi na daya, sai mu saurari littafi na biyu [10/15, 9:18 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*[10/19, 9:38 AM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔 ~Book 2~ Tuna Baya2 1-10 1..... Aslin Taheer da Bello Usman karaye ya gaji sarautane tun iyaye da kakanni. alokacin duniya na kwance.mulkisa agarin mulkine na adalci da rangwame.matanshi na aure hudu da kwarkwarori biyar.kenan mata tara ne agidanshi in ka dauke bayi da barori wadanda baxa su kirgu ba , al'ummar garin na kaunarshi kwarai da gaske sabida tawaliun shi da kyautayin shi garesu.maimunatu ne uwargidan maimartaba wanda ake kira fulani ita ma yar sarautace gaba da baya daga masarautar kano ta gaya, mahaifinta shine sarkin gaya na uku kowa yasan son da mai martaba kema fulaninshi daban yake dana sauran matanshi the differences is clear(bambancina farraqe yake) awurin bikin aurantane waxirinshi yaga rabi'a qanwarta shima ya aura rabi'a ita kebin maimuna a haihuwa,ba abinda yaraba su,yadda maimuna take baqa doguwa mai jiki haka rabi'a take daga gidan mai martaba zuwa gidan waxiry bawata tafiace mai nisaba.maimuna tafara haifan TAHEER wanda yazamo dan lele a masarautar garin gabadaya.tun taheer na qanqaninshi mutumne mai kwarjini karamci da rashin hayaniya wannan yasayo mashi qauna ta mussan a wurin mahaifinsu. shekaru biyar bayan haihuwar taheer rabi'a ta haifi danta BELLO, bello bai dibo kamannin kowaba saina maimuna wannanne yasa suke yanayi da taheer hatta muryar taheer shigen na bello ne.taheer na matuqar son bello tun suna yara ko ina suna tare saidai muhammad bello yafi taheer son shiga jama'a hakanan yafishi karanbani. shi bello dan harkane akwai son jama'a da son yin abokai, bashida girman kai ko kadan kullum cikin hidima da jama'a yake,yayan talakawan garin sune abokan bello(very sociable person. 2.... yayin da taheer baya shiga harkar kowa bayason karambani kuma baya son hayaniya,tun yana da shekara biyar babu abinda yakai takarda da biro muhimmanci agareshi.shaquwar bello da taheer abun acikin jininsune.sukansu iyayan na mamakin yadda taheer kesakin jiki da bello, bayan ko qannanshi dasuke ciki daya baya harka dasu kamar bello. kwarai wannan nada nasab dakasncewar bello mutumne maishiga rai Yana matuqar girmama yayanshi taheer, tayadda babu abinda taheer zaice yayi yace a'a.wadannan samari guda biyu sunzamo burin iyayansu tako wane bangare,bima'ana su akema hangen gadar masarautar tayadda har sunan taheer yabace saidai ace magajin gari shikuma bello da waziry mukhtar akece dashi (bello waxiry) wannan bayana nufin anhada sunanshi dana uban bane a'a kaitsaye ankirashi waziry ne.taheer yafi bello kyau,bello yafi taheer fara'a faran faran da harka da jama'a shiyasa ankafi sanin bello dayake dan waxiry akan taheer dayake dan sarki gabadaya. 3..... Dukkansu a qaraye sukayi karatun firamare saidai secondry dakowannensu yaci daban yake dana dan'uwansa saidai duk acikin garin kano ne ra'ayinsu yasha bamban akan abinda sukeso a rayuwa,shi bello bayada buri kamar yazama soja shikuwa taheer aikin da zai zauna a ofis kasancewar shi mutum dabaya son kwaramniya. dukkan su Allah yacika musu burinsu,bello yasamu tafia makarantar koyan aikin sojata n.d.a dake jos, taheer yasamu gurbi a jamiar Abuja indayake karatu akan kimiyar siyasa(political science). A makarantarne yayi wani aboki waishi yahai, shi yahai bakatafene amma musulmi yan asalin garin zaria'shakuwarsu da yahai takai harsu kan ziyarci gidajen juna ,sau tari yahai a karaye yake'weekend' shima taheer yakanyi kwanaki a gidansu yahai har suka saba da balarabe dango mahaifinsu yahai.general dango ya yaba da hankali da nutsuwar taheer kwarai da yadda yake kula da addini,harkar mata da yahai keyi shi bayayi kullum cikin kula da karatun shi da addininshi yake,wannan ya kwadaitar dashi dayaja taheer a jiki,don yasamu ya auri watsatstsiyar diyarshi MUBINA dake karatu a portugal. Yayi yayi mubina tayi aure taqi,kullum cewa take tana 'finding Mr.Right' ne, domin mubina akwai son namiji mai kyau,duk da kasancewarta mummuna,to amma munin mace inhar akwai gyara ai adone ga maza.Rayuwarta mai tsada ce sosai. 4.... Ya tabbata inhartaga taheer zata soshi donshi a rayuwarshi baitaba ganin mutum mai tsari da zubin taheer ba,dan haka yace da taheer ya kwaso kayanshi daga hostel yadawo gidanshi yabashi daki kusada na yahai. bai yi gaggawar amincewa ba saida yayi shawara da mahifinshi tukunna yace in har musulmine yazauna dasu mana daman wake son kwanan makaranta in banda dole wannan shine mafarin zaman taheer a gidansu mubina. Daya kammala digirinshi na farkone mubina tazo hutu daga portugal. ganinta na farko da taheer ta rikicewa babanta itafa taga miji mr dango ya tausheta da cewa ta dakata harsai sunmaida taheer wani tukunna, yadda bazai iya qin amsa bukatar suba donshi yasan taheer Kamar yunwar cikinsa. Mace bata gabanshi a yanzu macen ma irin mubina kwata_kwatä (life_style) nasu badaya bane. Ba mamaki inyayi mishi maganar ta alokacin ya tattara yakoma hostel. hakan akayi mr dango yadauki nauyin karatun yahai da taheer a sussec, university of washington seatle.bayan kammala digirinshi na biyu mr dango ya tura mubina washinton jami'ar da suke karatun M.sc dinta akan qididdiga(Accounting) yakuma danqawa taheer amanarta. 5..... yaya kuwa xai yi wasa da amanar ubangidanshi? Ya shiga kula da mubina bil haqqi tsakanin shi da Allah,tare dakokarin ganin ya rabata harka da kowanne namiji. Yana nuna mata illar hakan ga mutuncin ta na ya mace musulma mai daraja.tace ai kome nakeyi inayi ne sabidashi,don ni?akan me to? Tace akan ina son ka da auren da ka ke cewa nayi, alokacin dana lura kai baka masan ina yi ba".tun daga lokacin tashiga nuna mai soyayyah afili daya ga abin na gaskene sai yayi ta lallabata data bari sukare karatun xai aureta. dawowarsu nigeria yayi daidai da mutuwar autinsu data rike su mubina, dama mahaifiyarsu tuni ta gudu tabar babansu tun suna kanana sabida dukan da yake mata inyashawo giyarshi ko allurar sojin ta motsa. Wannane yasa mr. dango tausayawa su mubina da basu tarbiyya ta kowanne yayi abin da zabawa rayuwarshi. Mimi mai bin mubina a tanzania take karatun tarihi shi kuma yahai yakoma beijing din china inda yasamu aiki da kamfanin(bill gate)na sana'anta na'ura mai kwakwalwa.ashekarar mr.dango ya samar mai aiki a'foreign affairs' wanda sadaukar da kai da mai hankalinshi ya bashi matsayi daban-daban acikin ta har kawo yau,wato bashi baban (minister) na foreign affairs gabadaya da shugaban kasa yayi,badon shekarunsa sun kaiba illa don juriya da jajircewa bisa aiki da gaskiya irin nasa. 6..... Ya gina kankareren gida abuja amma dango yace bai dace yashigaba har sai yayi aure. Acan karaye maimartaba ya bude mai wuta, fulani amsa gaisuwar shi ta daina, sunce yaxo gayarinya ansamar mai yar hakimin kiru ya shashantar da maganar har yasa sun ji kunya,toh wannane ya tayar mai da hankali har ya doshi mr.dango da maganar a matsayin neman shawara,don shi a duniya bai gayarinyar da ya tabaji wai yana soba, Dagana turai harnamu yakanga dukkan matan yanzu matsayin marasa kamun kai yan (selling-face) tunda duk yaga yadda suke tafiyar da rayuwarsu,suke kuma yimashi baro-baro daga na turai harna africa a ganinshi babu korai balle ya kwankwasa ya zabi na kwarai.yanason gina rayuwar iyalinshi ne da mace tagari.kamilalliyar mace da bata dauki dunia matsayin gidan hutu da jindadi kawaiba,a'a wadda zata tsaya tsayin daka waje daya tayi amfani da lafiarta, karfinta, kuzarinta, iliminta, da addininta wurin tarbiyyanta da kula da y'ay'anta,ba gafalalla wadda duniar kadai tasa agaba(tamkar su mubina kenan) budan bakin mr dango sai cewa yayi ai shi tuni ya samar mai mata,qanwarshi mubina, don baiso yayi nisa dashi sabida qaunar da yake masa. Baya iya wulaqanka wannan mutun bare har yabada mishi qasa a ido yace baya son jininsa idan yayi la'akari da yadda yazamo silar dukkannin'achievements' dinshi a rayuwa. 7...., Hakanan kuma su mubina an hada da kai sunan taheer zangon kataf, donhaka yazamo bayada katabus sai abinda dango yace har akayi auren. hakika bai son mubina ya aureta,sai dai yana son babanta,yana ganin mutuncin balarabe dango,har yau har gobe yana ganinshi a matsayin ubangidansa, duk da cewa a yanzun zai iya sayen aikinshi kansa dangon dake aiki da 'presidency'. sai dai qin mubina yafara gushewa daga ranar da ta dauki cikin gudan jininsa abin sonsa (MUHAMMAD JAWAD). Duk da cewa bayan auren ta komawa munanan dabi'unta,kamarbin kyawawan maza da qarya da homa tun bayan farawar aikinta a bankin omega.haka mubina sai bayan aurenta da taheer ta shiga nadamar auren, da wanda take ganin qidahumi, bai san takan rayuwa ba, bai kuma san koshi wanene ba, yana daidai da kansa da barorin gidansa yana kuma al'adunsu na qauyawa,shekarada shekaru yana cikin birnin tarayya amma wani baqauyen mabazai ci abinda yake ciba. wai kamarta ace mijinta dayake matsayin (minister) guda tuwo yakeci kuka yake sha,kuma abokan hirar shi sune masu shara da goge gogen gidansa.wannan ba qaramin abin kunya bane agareta.bakuma tareda shawara da itaba yafada kasuwanci mai gigitarwa, takai bayaga hannun jari,a yanzu haka kokarin bude kamfaninshi na qashin kansa yake a Rome (italy)domin sarrafa takalman fata na zamani da jakunkuna na mata da maza, 8.... haka a yanzu kamfanin'caystal' daya zuba hannun jari a portugal cikin birnin lisbon,jarinsa ya rinjaye na mutane hudu mamallaka kamfanin suna neman yabasu wasu adadin kudin ya mallaki kamfanin gaba daya.yayinda kamfaninsu na saqar kilishi(carpet)dake canada a yanzu nashi ne shi kadai. abinda ya biyo bayan haihuwar jawad kun jishi. *** ** *** farkon fara neman atine da bello, bai dade da fara karatu a jos ba. shikansa bellon baitaba tsammanin zai iya aure a wanccan lokacin ba. to amma me?tun ranar daya bararma atine kalwa, baiqara samun tunanin kanshiba saina y'ar tsakuwar qauyensu atine.shikansa harmamakin kansa yake,ba abinda yake burgeshi da atinen gidan mai kalwa irin tsiwarta da qaunar babanta. dama yasha jin abokansa yakubayi ko masu take masa baya na cewa wai yarinyar don tanada kyau, take tsiwa da jinkai,bakuma wanda ya isa ya taba babanta duk fadin qaraye ta kyale ko waye kuwa,komi tsawonsa,komi gemunsa haka komai kaurin rawaninsa,yace da mai bada labarin shikuwa sai ya sata kuka,ko waye?to wallahi banda shi. tuni daman suka shirya tsokanar da zasu yi mata ,tunda tace babanta ne bataso ataba mutuncinsa. 9..... tsokanar data jawo mai dimbin nadama daga baya daya fada mayuwaciyar qaunar atine. qaunar dabai taba jiba a rayuwarshi baikuma taba tsammanin wai namiji nayiwa mace ba. Ranar data kawo rigar ruwanshi ta dangwarar tace ba wanda ya isa yataka mata uba a gidanshi ta kyale, har kukan tausayi da so yayi daga ranar bai qara mu'amala dasu jibir ba,don aganinsa duk su suka jawo mishi.ya zauna ya zanawa atine doguwar wasiqar ban hakuri da nuna mata cewa tsokana ce kawai suke mata don raha da sanin halinta. abin haushi atine bata iya karatuba wasiqar na cikin kayanshi data bayar a dawo mishi dasu ko budeta ba'ayi ba,data tabbatar, atika zai aura ba itaba. A rayuwarshi bazai mance da ranar dayaje yiwa baban atine ta'aziyar goggon atine ba,ya shaqi wani irin turare mai kama dana 'yan bori. tun daga ranar rayuwarshi bata qara komawa yadda take ba jin kansa yake kamar bashiba ga wani suna daketa kuwwa a kwanyarsa wai ATIKA maimakon ATINE. 10.... bayan an sallamoshi daga asibiti yaji duk atine ta fice mai arai,atika kawai yake son aure.ya shiga tambayar kansa shin maima yagano a jikin wannan kwailar yarinyar? Ba kuma zai manta ranar da muhd.jos yashigo da ita gidan shina bayan gari ba suna zaune dasu fatimah,jiyayi kamar baima santaba sai ranar.su fatima sukace da ita kamar KYANDIR ya kasa tsawatar masu, saima yaga dacewar sunan da halittar atinen.kai shi baima taba ganin siririyar yarinya irintaba ba don tana da kyan fuskaba da ance da ita ba mace ba. Anan ma ji yayi ya qara tsanarta, tare da ganin shirmensa da wautarsa wai na neman aurenta ada. A rayuwarshi bazai taba mancewa da MUHAMMAD JOS ba, yakan tuno ranar da muhd yasashi gaba a ranar daya tura kayan neman auran atika gidansu atine,yayi tayi mishi kuka da hawayenshi jabe-jabe kaman ba sojaba yace bello meke damunka? Shin kayi gamone? Wannan wane irin wulaqanci ne? Amma shidin ko gezau ,yace bai chanzawa,atika yakeso ba atineba idan shine ubansa to kada ya daura mishi aure da atika. [10/19, 9:38 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/20, 10:27 AM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔 ~BOOK 2~ Tuna Baya2 11-20 11.... Akwai sanda zuciya ta ciyo muhd yace wallahi inya gama karatu atine batayi aure ba zai aureta. bello yace dashi ai sai yayi dama tuni yagane take-takensa kan atine. wai! wannan ya fusata muhammad bukur jos,ya rabu da bello Shekara uku bai neme shi ba. daga baya ne karatu ya sake hadasu suka koma kamar da,don yalura bello bai auri atikar ba. Abinda ya faru shine ranar da bello yakai zancen ga waziry,sai ya zazzageshi yace ya zai maida shi karamin mutum a idon dunia?yaya sun gama komi na aure, daurin aure kawai yarage yadawo yace yar yake so ba kanwar ba? Wannan karantane manya basa magana biyu.kuma ko bayan ransa bai yarda wani cikin 'ya'yanshi ya nemowa bello auren atika ba 12..... ina! Bello idanun shi sun rufe ruf, baya ji baya tunanin komai sai atika.ya kai karar waziry wurin maimartaba kan yaki nemomi shi auren da ya keso,amma dan kawauci irin na mutanen da, maimartaba bai yi shawara da waziry ba,ya ture mutane kai kayan bello wa atika gidan maikalwa. waziry na zaune mallam mamman yazo ya same shi wurjanjan yana tambayar shi wa bello ya aikawa lefe cikin yayansa? yace wallahi bada yawunaba, bai masan bello ya aikaba,yaran yanzu ne ka haifesu baka haifi halinsu ba.ya sawa mallam mamman kuka yana rokanshi kada ya aurawa bello y'a'yanshi kodaya.mallam mamman yace a'a, baza ayi hakaba shifa zai zauna da yarinya don haka ba ruwansa wadda yakeso cikin 'ya'yanshi shizai aura masa don bello yafi qarfin komai a wurinshi.kuma da atika da atine duk dayane ba banbamci . 13.... Maimartaba ya kira waziry ya taushashi da cewa ya kyale bello tunda shi yace yanaso.wata baiwar gidan waziry ce tatseguntawa hajia rabi mahaifiyar bello cewa matar baban atine da bello zai aura anata labari agarin cewa ta asirce bello ya komawa auran 'yarta ba atine ba,hatta ciwon daya kwanta a jos itace sila domin asirine ke bin jikinsa, kuma su don kudi da sarauta suke son bello, amma qauna ta haqiqa bello atine yakeyi mawa. tace au hakane? Yaqi 'yar'uwarta yaje inda za a halakashi,to su duka biyun taga wadda zai aura.da ita da yayarta fulani suka tashi tsaye nemawa bello makarin asirin lami batare da sanin mazansu ba.sune da aike har chadi,hakanan fulani mace ce mai tsananin ruqo da addu'a da tsayuwa akan addininta,tashiga yima bello roqon Allah baji ba gani,itako hajia rabi ta qarfi da yaji tamiqe da son raba bello da atika.duk abinnan da ake yadda zaka tabbabtar mummunan asiri akayima bello,bai taba ganin atikar ba banda ranar da suka fara haduwa da atine,baikuma taba neman ya gantaba,illah sunanta a bakinshi rambadadan kamar shi yarada mata. 14..... An daura auranshi da atika ranar asabar da niyyar sai ya koma jos karbar takaddunshi na inda aka tura shi qaro karatu yadawo sannan su tafi england tare. dirar shi a jos kuma yariqa tambayar kanshi meke damunshi ne zaice bazai auri atine ba, bayan ita daya zuciyar shi da ruhinshi ke so da qauna?sai alokacin ya tuna wai andaura auranshi da yayarta atika dabaima taba ganiba,hankalinshi yatashi yarasa abinda kemasa dadi,yatuno sallamar shi ta qarshe da waziry inda yace to bello, hankalinka ya kwanta ka auri atika,amma ingaya maka gaskia hakkin 'yar malan mamman bazai taba barinka kwanciyar hankaliba.a daddafe yayi abinda ya kaishi jos yadawo qaraye, kai da ganinshi kaga wanda damuwa da nadama mara iyaka yayiwa ligi- ligi, tamkar ba ango mai shirin daukar amarya sweet 16 ba. Da daddare a turakar mahaifiyar shi hajia rabi ya kwanta cikin kujera kamar yayi ihu.tayi banza dashi sai data mula tace uwar amaryarka nata aike, baka je ba kun gaisa da atikar takaba.amsar daya bata tabata dariya,wai tambayarta yake wacece atika? tace ah! Matarka mana da aka daura muku aure sati daya daya wuce. 15..... Sai ya samata kuka,waishi baice dasu su daura mishi aure da kowa ba sai ATINE. ya zasu tagayyara mishi rayuwa?suna sane da irin qaunar da yake ma atine? Tausayi ya kama ta, kinsan mahaifi, ta tabbata lalle bello yadawo bellon shi alokacin da bakin alqalami yariga ya bushe.sai ta kira waziry yazo yaga halin da bello ke ciki yana kuka riris kamar ba bello ba duk akan baice su aura mishi wata ba atine ba.bayan zagi ta uwa ta uba da waziry ya sauke mishi kwando kwando bai gaya mai wata kalma mai dadi ba.cikin dare ya rubuta takardar saki uku cif ga atikar inna lami. yana ganin wannan hanya ce mafi sauqi da waziry zai sake nemo mishi auren atinen shi. wayyo! ya qara dagula komai,domin da mallan mamman ya kawowa waziry takardar sakin da bello ya aikama atika waziry asumar shice ta tashi na baqin cikin da bello ke guma mishi.yace ya tattara yanashi yanashi ya bar mishi gida babu irin ban baki da roqon da mahaifiyar bello batayi ba na yagane bello bayin kansa bane duk wadannan abubuwan dayake yi amma ran masu mulki ya baci,don cewa yayi idan bello bazai futar mishi agida ba ita uwarshi zata futa. bello na kuka yace innar shi tazauna shi zai futa.ya kwashe kayanshi yakoma dakin taheer dake gidan mai martaba,wanda a lokacin shi taheer yana washintong aboki nagari muhd jos,yarabu dashi alokacin dayake tsatsanin buqatarsa, ya san da yana nan al'amuran sunzo mishi da sauqi, 16..... Koba komai zai shawo mai kan atine da babanta da waziry kanshi daya fahimci bayin kanshi bane. to amma muhd yana lagos alokacin da anininshi na farko a aikin soja gashi ko numbar wayarshi baya da ita,innar shidaya data rage mashi a dunia ta rasu,bata tsaya taga matsayin da muhd jos keson kaiwa a aikin sojaba,Allah kenan. ya nemi yayanshi taheer a waya,ya zayyana mishi duk halin dayake ciki,tare da neman shawarar mafita a gareshi,taheer yace shi don me yanemi aure tun farko bai gama karatu yafara aiki ba?sai yace SO baruwanshi da wannan, SON ATINE,yafiye mashi komi muhimmanci a rayuwarshi.shima taherr din don bai taba fadawa a son mace bane,taheer sai yayi dariya yace bama zantaba insha Allahu me ake dashi,tunda ko zaisa mutum problem dashi da iyayanshi?taheer yace naso inga wannan atinen inga shinme yadauki hankalinka gareta haka brother? Abin mamaki kuma illiterate?imagine: 17. Ya runtse ido,jin zafin taheer yakira atinen shi JAHILA .sai yace shawara ba cin fuska ba yalla'bai taheer ya tuntsure da dariya yace kayi haquri bawai ina nufin haka bane,inadai mamaki ne. amma inaga kabi takan mai martaba na tabbata zai fahimceka fiye da baba waziry,itama kuma atinen kanemeta kabata haquri,inhar tana sonka nina gaya maka zata fahinceka bakuma zata kullace kaba.to bello shawarar taheer yabi, sai da aka kwana biyu ya doshi sarki da alfarmarshi na asake nemo mishi auren atine, yana kuka da idanunshi da alqawarin wannnan karon bazai basu kunya ba,su ceci rayuwar shi su tausaya mishi,inya rasa atine baisan yaya rayuwarshi zata kasance ba. mai martaba yayi murmushi,karo na farko da bello yanemi wata alfarma agaresa yagaza yimashi,yace wai ido da kunya don mallan mamman yana talaka bazai dunga mai yawo da hankaliba koba komi ya girmeshi inya qara dosarshi da wannan magana yazama dattijon banza,da kyar in mutuncinsa bai zube daga idanun talakawan shiba. Sabida haka inhar muhd bello kanason albarkarmu atare dakai, ka haqura da atine! ka haqura da atine!!sai da ya maimaita mishi wannan har sau biyu. 18.... Bello yayi kuka kukan da wani namiji bai taba yiba a rayuwarshi wai don yarasa mace,kukan dabai taimaka ba ko kadan wajen rage azabtuwar da ruhinshi keyi da qaunar atine.jiyayi ya tsani kansa,ji yayi rayuwarshi batada sauran amfani,to amfanin me gareta batare da atinen daya kallafawa rai ba? meye matsayinshi a zuciyar atine yanzu? (mayaudari) in fact! Har abada ma zata sake son shi?inya tuna haka sai komi ya dagule mishi,yashiga juyi da watangaririya akan gado, har saiya fidda hawaye zaiji sanyi sanyi. ranar da hawaye suka zuba, tamkar zararre yake komawa. inda duk ya diba cikin dakinsa a kowace kusurwa atine yake gani tana cewa 'sunan ka dan qaraye mana? Idan ya mike ya isa gareta saiya ci karo da bango,ya dunqule hannu ya kai mishi duka ya rikice da kuka.rannan a halin fulani ta riskeshi ,ya riqe kirjinshi yana ta juyi da kiran sunan atine,tausayi ne yakamata , Ta zauna nasiha mai ratsa jiki kan muhimmanci yadda da kaddara kuma biyyaya ga maganar iyaye don samun rabo kyakkyawan rabo a gidan duniya da lahira ga badaya.sai yace wai shi kirjin shine ke ciwo,ji yake tamkar zuciyar shi ta tsage, yayi ya daina ji ya kasa.sai tasa habar mayafinta ta share hawayen da suka cika mata ido. 19...... Wai duk kwalisa irin na bello,bellon da bai barin ko gashin baki tare da shi,amma shine ya koma haka duk kasumba babu kyawun gani?wai yau bello ne da kaya a cukurkude,bellon da ko karin hular shi daban ne da na sauran maxa!ta tausaya mashi iyaka.da kanta ta samu waziry ta nuna mishi matsalar bello bata ayi fushi da shi bane. lallashi da ban baki yake nema,yace shima daga baya yayi tunani,tuni ya yafemishi,amma aurene bazai kuma nemo mishi ba ko xai mutu ba auren. bello yasan babanshi kaifi daya ne, daga ranar karaye ta fitan mai rai,ya tafi ingila shekaru ukun da aka tura shi.acan ne suka shirya da muhd jos. inda wanda yasan azabar son da bello kewa atine to muhd jos ne don kullum suna tare,bacci wanna daki daya suke yinsa,duk hirar bello atine, duk rabin zancesa ATINE ne,amma ya alqawarta ma ranshi ya hakura da ita don mutuncin iyayen shi a idon karaye,kamar yadda suke fadi lokacin da taheer yafara aiki a abuja yace da bello tunda maganar ta kare toh lallai ya auri fatima ko don ya farantawa iyayensu, wayyo! bello bai tsallake maganan yaya taheer, ina! kwandala wannan da zai batar haka kawai ko ta fannin karatun shi TAHEER ne, 20..... ya daukewa iyayensu hidimar karatun kannen shi duka, musaman shi bello da yake dan gaban goshin sa. A lokacin fatima kammala diplomarta a bayero. duk wasu hidimdimumshi a ingila taheer ne,ko sadaki bai bari kwandalarsa ta yi ciwon kai ba kamar ba kawarsa da suke ciki daya zai aura ba. to shi ko shegene yace bai son kanwarsa sai wata daban atine? Sai dai fa wannan shine bakin cikinsa na karshe a rayuwa,don ya tabbatar yarasa atine har abada!aurenshi da fatima da fari kamar ba aureba za'ace,don second, minti, awa ko dakika bai wucewa bello bai ambaci ATINE BA. sai gata wai yau a matsayin matar da yaya taheer zai aura? ********** Bello Waziri tunda yaji zance Yayansa Taheer ne zai auri Atinen sa nanfa hankalisa ya tashe gaba daya ya birkice tamkar mahaukaci, suna dakinsa na gidan mai martaba shida abokinsa muhammad, muhd shine mai tausarsa akan yayi hakuri ya danne zuciyarsa shi kuma ya dage akan bazai bari wani ya aure masa Atine ba, muhd yana nuna masa irin halaccin da taheer da iyayensa suka yi masa baikamata akan mace ya rufe idonsa ya manta alkhairi ban amma ina sam Bello yaki yarda da wannan batu na abokinsa, hardai Muhammad daga karshe shima yaji haushi yace to [10/20, 10:27 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/23, 8:00 AM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔 ~BOOK 2~ Tuna Baya2 21-30 21... "Badani za ai wannan dibar albarkar ba.tunda kai baza a baka shawara ka dauka ba,tokayi duk abinda kadama .'do whatever you want! Sai dai nagaya maka gaskia,...abinda aka yishi cikin fushi sai anyi nadamar aikata shi.wannan cin fuska ne,yaya kake behaivng as a lunatic? Zan tafi, kayi duk rashin mutuncinka kai kadai amma banda ni..:....................... Kai muhd, bahaka ake yi ba nima nasan yarinyar ce atinen bello ya npema. abinda yasa ban ce komai ba don banji bello yaqara yin zancen ta ba.tunda haka ne ku kiramin shi baban jawad! Gabadaya suka dube ta, fulani ce,mahifiyar su yallabai.ashe tun dazu tana tsaye tana sauraron su kunya da nauyi sun lillibe bello, shi kanshi ya san baiyi dai dai ba.to amma ya zaiyi?ya zaiyi?hawaye suka zubo mishi sharrrr.......suna diga tafin kafar muhd jos.muhd ranshi yayi masifar baci,kamar zaiyi kuka yace "Ranki yadade kiyiwa Allah kiyiwa darajar annabi,kada kishiga maganarnan.in bello na hauka kowa ma sai ya haukace? Idan har kika gayawa yallabai komi zai dagule,maganar auren Zubaidah ta wargaje....... 22..... Nizan iya rarrashin bello.fulani tayi murmushi muhammad ka san SO? Kasan son da bello kewa atine? Baka taba fadawa a son wata ba ,baka taba ba. shiya sa kake ganin bello bai yi dai dai ba. bana jin yaron nan sai jawad!amma ka san don bello ya auri zubaidah tamkar jawad na gaban baban shine? Muhd jos ya san fulani wayayyar mace ce.mai nuna nata ba nata bane.shi kunya ma kadai ta ishe shi.dayasan haka zata faru ko kusa bazai biyo shi su shigo gidan ba.ya harari bello tamkar yakai mai naushi.ya share zufan dake keto mai agoshi kamin ki zartar da hukunci ranki ya dade,kiyi tunani.nasan akwai kawaici a cikin abin, amma kada ki kira yallabai,don Allah, sai yazo don kansa.ya fice,bello bashida zabi, banda ya bishi tamkar wanda akayiwa duka ko kuma wanda kwai ya fashe wa aciki.tafiyar yake tafi kama da jan kafa.ko kuma jan gindi.baya ko iya daga ido ya dibi jama'ar gidan balle barorin dake ta faduwa,suna kwasar gaisuwa.gidanshi na bayan gari wanda ke jikin katafaren'European Building' din da taheer ya zuba kwanannan jikin nashi suka dosa,babu mai magana da dan uwansa a cikinsu.yatsayaa varanda ya shiga tuttular da hayaqin taba da karfi. 23... Idonshi jazur sun razana muhd jos.niyyarshi da sun shigo ya rufeshi da zagi.Abu daya yayi wato lallabawa ya zare 'bullet' din dake cikin karamar 'pistol' din bello da durowas dinshi gabadaya.sai kuma tausayi ya kamashi daya dubi bellon shi, muhammad dinshi ma'abocin fara a da son barkwanci.amma lokaci daya ya zabge,ya koma kamar mara imani,kamar bai taba yin daria ba duk a dalilin SO.ya la'anci SO,ya kuma gode Allah da bai taba daura mishi ba.koda yake ya tabbata in shine bazai dauki abinda zafi haka ba. bello mutum ne mai tsananin zafi,dan sharp-sharp (komi ayi shi a lokacin daya dace),shiya sa komima yazo mai da zafi.da ace tun farko yabi shawararsa,da ba 'ayi wannan abin kunyar ba. yasan fulani dole ta gayawa 'ya'yanta.yayi tsaki ya bude firji ya fiddo lemun 'tropical' mai sanyi ya bincire hancin ya mikawa bello,ya karkatar da kai yana murmushi yace kasha don zubaidah? Ya harareshi,kana ya amsa ya kwace karan tabar dake hannunshi ya kashe ya cillar cikin 'ash tray' ya kuma tura hannu cikin aljihunshi ya dauke kwalin tabar gabadaya yasa a dustbin.zaman kurame sukai na tsawon awa guda,shiru ba wanda yace da dan uwanshi ci kanka.can bello kamar an tsikareshi ya mike.muhd yabishi,zai shiga seat din driver ya kwace ya zauna yace cikin murmushi Alasabbinani, sai ina mukai? 24...... Ya harari gidan yallabai tukunna da ma'aikatan dake ta faman gyare-gyare kamar yaune za a kawo amaryar,cikin hargagi yace ni bani da gidan iyaye?da zaka tambayeni ina zani? Dariya yayi wadda ta kara tunzura bellon,Allah yabada haquri,your majesty,gani ba ci bane,tauna ba hadiya bace,yaja motar sai harabar gidan waziry, ya zube a babban falon waziri yatasa shi gaba yana huci baice komi ba shi ma wazirin haka, shirin kudin sadaki yake da kanshi yan dubu dubu sabbi kar cikin katuwar jaka. kai kace bai san Allah yayi ruwan tsirarsa bama a falon.ya soma rera kuka tamkar wani karamin yaro.yanzu baba da saninka zakuyi min haka? baba kasanfa ina son atine batun yauba tun tana yar ficiciyarta. na auri fatima abisa son ranku to ni akanme bazaku bani son rainaba?yanzu baba har kafi son farin cikin taheer da nawa? Waziri ya kammala jera kudi a jaka,yaja zip ya zuge kai kace da kututturen ice yake magana.ya mike zai fita, sannanne yace lalle bello,ka isa soja.tunda har ka iya ka dosheni da zancen yar gidan mai kalwa a karo na biyu.a kuma kan cinikin yayanka.to kasani,Allah ya haramta ciniki akan ciniki. 25... Wallahi koba taheer ne zai auri yarinyar nanba bazani kara nemo maka auren taba.nan kazo kasani jin kunyar jama'ar gari.kace kana neman kanwa,kadawo kace yar ce.nayi nayi dakai na fidda ma hawayena kan ka fiddani kunyar bawan Allahn nan,karufe idonka ka bada mishi toka.kai wai wata atika.baka san wata atine ba banda kanwarta. Sannan yanzu don Allah yasaka mata,ta koma mutum,kadawo ka kawomin zancen banza? Da can kana sonta baka nemi inda takeba shekara da shekaru dai dai har takwas,sai yanzu?bayan ya gama wahala da yarinyar ya maidata mutum,ka kawomin zancen wofi?ance mani tsohon banza ne? Kana auren kanwarshi,kahada neman aure da shi? Sabida kai bakasan mutunciba,butulune mai manta alheri.dubi idanunka fiki fiki,wai zaka auri yarinyar da TAHEER zai aura ko kunya bakaji bello? Kaga sadakin zubaidah yar gidan mai kalwa. gobe zan dankawa ubanta.ince ko in Allah ya kaimu gobe kaga an shafa fatiha ka hakura,ka koma inda ka fito.ka hakura matarka,ka roqi Allah ya tura ma sonta? Waziri yayi shiru ya dubi danshi, babu alamun yana sauraronshi.jakar kudin hannun shi kurum yakebi da kallo,dayake jin tamkar ya fisgo ya bulbula mata fetur ya kyasta ashana.yana tunanin muddin ta bar gabanshi shikenan tayi mai gingimemen shamaki da ATINE sa.abinda bai taba kawowa cikin mafarkinsa ba.A kullum mafarkin sa na nuna masa zai dawo watarana ya auri ATINE.komai daren dadewa,yana da yaqinin atine bazata taba iya auren kowaba sai shi tunda shine first luv dinta,shiya bude mata ido da soyayya,bata san menene son ba sai akanshi.dai dai da rana daya bai taba kuskuren wannan mafarkin ba,to ta yaya atine tayi masa haka 26. tsakanin da mahaifi sai allah.tausayin nashi ne ya kamashi bello ya zabge,yayi duhu, ciki kwana daya kacal.baisan san da ya dawo ba.ya tsuguna ya dafa kafadunshi.muhdbello! Ana barin halas, don kunya.dama allah yayi fatima ce matarkaba zubaidah ba! Baka yarda da kaddara?baka da hakuri? baka juriya? Idan zubaidah matarkace sai kaga wani sanadi yazo da zaka aureta agaba.bello komi yafaru kai ka jawo.tun farko meye nacewa baka auren atine? Alhalin kasan kana son ta? Bello ya sadda kai, kalamin mahaifin shi na sanyaya mishi kwarai.a sanyaye yace wallahi ranka yadade nima bansa ya akaiba.a lokacin ni kaina jinake tamkar bani ba amma kosu mallam mammam sai dai surufe ido su mance dani amma sun san inason yarsu tun tafiyarta ban rabu da kofar gidan suba. Nabashi hakuri yace ya yafe min, basan dalili sa nakin gayamin inda take ba, haka bansan dalili naken da yasa shi min haka yanzu ba, wasu hawayene suka shifido aguje. Waziry ya sadda kai. Ya dago bayan wasu yan dakikai kada muzamo masu son kan mu bello, kada muci amanar taheer bai cancanci haka daga garemu ba 27. amatsayina na mahaifinka,idanhar na isa in gaya maka kaji,to kada kace da taheer komai,kada ka batawa matarka da dan uwanka.wallahi ko yaya makamanciyar wannan ta shiga kunne taheer bazai auri yarinyar nan ba, cewa zaiyi ya barmaka!! Haba bello!!!kai baza kaiya kwatanta irin karimcin da yake maka ba?ban taba kawowa ko a mafarki zaka iya hada neman aure da taheer ba, sannan ita yarinyar in kayi mata haka baka kyauta mata ba, tun da bakasan wane al amarine a tsakanin suba shekarun ta tara tare dashi.kasa saki jikinka, kabawar allah lamarin sai ya zabama abinda yafi alkhary,ka koma ka tafi da fatima gidan ka.idan kabarta anan abin da ke boye zai fito gida sarauta baya raina gulma tsegumi, kana jina? Zance yaushe kuma?tunda uwar su taji?ya fadi aransa. amma a fili sai yabi umarnin mahaifin shi, kamar dagaske sun dauko hanyar bayan gari ya ja burki, kuuuu! Ya razana muhd yayi saurin take burkin motar kada ya kifar dasu kamin ya ankara bello yayii round dakan motar ya shiga keta lunguna har ya tadda gidan MAI KALWA yaci taya ya tada wata irin dunkulalliyar kura a dan tsukurkurin lokon da mota ma bashiga take yiba haka ya kukkujje ta yashiga cikin zafin nama mohd jos , yayi saurin danna a wani abu ajikin motar glassai bakake suka mamaye gurbin farare yanda baza a hangosuba hakannan kofofin ba damar buduwa,yace a hankali bello kashe mu zakayi?tun ban tara iyali masu min addua ba? 28. kabar su mukhlas orphans (marayu) akan farin cikinka kai kadai ?shin zubaidah nan itane kadai mace aduniya?tukun nama yanzu da kazo gidan su mai zaka yiwa yar mutane? Ya rika jeho tambayoyi daki-daki, anutse da alama shi ba abun da ya dameshi. Me kuwa zan yi mata? tambayar ta kawai zan yi dalilinta nayi mun haka ya bude murfin motar amma ko gezau Ya harari mohd. Cikin matsanancin takaici wai meyasa kake mai dani mahaukacine? Yo ba dole im maidakai mahaukaciba?dubi kayan jikin ka, kakin soja afagen fama dasu zaka gidan mutane a kauye ka razana musu yaya bello anya are you in your full sense? (kana cikin ya yi cikakken hankalin ka) shiru yayi bai amsa ba.ya koma lallashi,cikin tattausan murya kayi hakuri muko ma gida ka fiddasu kasa na mutane sai ka dawo bello yayi shiru, again tamkar muhd da dutse yake magana duka daya yayi wa kofar motar da kafarshi ta bude,ba shiri ba zatonta ba tsammani. Dan jos ya bishi da ido baki a bude ya isa kofar gidan auwal nasawo kai zai fito sauran kadan su kara.mamaki ya kama auwal yayi ta maza in ji mata yamika bello hannu sukayi musabiha atine sun iso ko abinda yace dashi atakaice,awal ya gyada kai,cike da zargi,sai kuma yatuna tsakanin bello da yallabai,don ha ya juya cikin gida ashshah ya hango a kurkusa yayi kiranta yace ina amarya kice tana da baki a dakina kanin yallabai ne muhd ashshah tayi dariya uncle muhd mijin aunty fatima? Kace tana zuwa ta ratso mutane ta hada juice da ruwa taba auwal wai yabashi kamin ta tsamota. 29. na idar da sallar la'asar kenan ina canza kaya zuwa farin cotten lace sassauka me yarfen kananun duwarwatsu kala daban -daban brown net nayi amfani da ruwa kasa r takalmi da jaka andre valentino ina cikin fesa turare hardo ta leko zubaidah kina da bako a dakin ya auwal tayi wucewarta cikin hidima, domin dai ita yar hidimace tunda muka iso kona minti daya bata zauna ba na tambayi fa'izah ko suwaye?tace ina zan sani ina kwance? Batare da wani dogon tunani ba na zura takalmana nayi zaure. A zauren mu,wani kamshi ne dana tabbatar dana dade da sani nayi iyaka tunani na waye ma mamallakin wannan ni'imtaccen turare? Iyaka tunani na bai bani ba don haka nasa kai tare da sallama ya juya baya gawani rubutun ajami, na wasu shekaru masu yawa abaya. Hannayen shi duka biyu harde a bayan shi.bai amsa sallamar ba kazalika bai juyo ba na sake sallama,na shigo tsakiyar dakin ya awal.gabana ya soma dukan tara-tara ba uku-uku ba wannan dogon mai jiki irin na yallabai cikin ko wani hali, bazan mance kamannin shi ba. Kowa ne irin hali,lumsassun idanun shi ya sarke cikin idanuna da kallon da yasan very irresistible, ne a gareni tuni na sandare atsaye.ya soma taku zuwa gareni,har yanzu idanunshi cikin nawa baya ko kyaftawa.na soma ja dabaya,shi kuma bai bar bina ba har sai da na dangana da katakon gadon ya awal na tsaya cak, kirjina na harbawa,zuciyata na neman faso allon kirjina sabida tsabar tsoro. 30. idanunshi sunkada suyi jazur tamkar wanda aka watsama barkono. naga kamar zai yo kaina,tuni na tsugune a kasa na dauka ja na zaiyi shima tsugunawa yayi. na kai hannuna duka biyu na rufe kaina ko mayafi ban yafa ba (kin san amarya a gidan wuninta) yace ahankali kuma cikin wani irin murmushin da yafi kama da kuka atine ko zubaidah? sai kuma ya mike da hamzari ya rufe kofar dakin auwal da sakata. Na tsorata na gigice na rikice na soma kuka nace bello meye haka? Wannan baidace ba sam,da nasan kaine wallahi bazan zoba...wannan wane irin wulaqanci ne? Aure fa zanyi,so kake kazubar minda martaba,a zargeni akan abinda bashi bane? Ya fiddo sigari ya cinna mata wuta yakai labbanshi masu sulbi,yayi mata kyakkyawar zuqa ya feso hayaqin a fuskana,nayi azamar kudundune fuskata da sauri,taba nadaya daga cikin abubuwan dana tsana a rayuwata,yayi murmushi again wanda yafi kama da kuka zubaidah 'YAR RAINO,Koko matar uban dan da ake raino? [10/23, 8:00 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/23, 5:07 PM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA🤔🤔 ~BOOK 2~ Tuna Baya2 31-35 31. ke kuma haka akeyi?daga zuwa wankau ki kore matar gida ki kwato da da mai gida?da wannan abin kunyar ai dakin baro naki daga nesa,mai qaunarki fisabilillahi,tun kina 'yar sama-tsami-tsaka- tsami..ya dosoni bayan ya kashe tabar ya yar na runtse idanuna gam lokaci guda nasoma karanto duk addu'ar data zo bakina,da kyar inba giya yasha ba, al'amuran shi sun soma daina bani tsoro,mai yuwuwa yasami tabin hankali a kwakwalwa ne? He is acting as a lunatic! (yana abu saikace mara hankali) ai bude idonki zakiyi, Atine zubaidah ki dubi tsabar idona kice bakya son wannan bellon.wallahi auren tausayi zakiyi da ubangidanki ba auren so ba...nakwace fuskata cikin zafin nama,baidamu ba yasake murmusawa, ya jingina da bango ,idanunshi akaina yana fuskantana ido cikin ido yacigaba da magana. amma wannan karon cikin nutsuwa da kwantaccen sauti'zubaidah kidawo gareni,in nuna miki son dake dankare a zuciata,wanda yawan shekaru, girma da canjin rayuwa bai canza ko qanqani daga cikinsa ba saima abinda yaqaru,na auri fatima don iyayena suyimin afuwar dazan aureki agaba,amma badon so ba nasha gayawa baba da inna,ban taba janye niyyana na auren kiba abinda suke cedani a kullum shine su babu ruwan su a ciki,wannan tsakaninmune.don haka afuwar ki nazo nema.abinda yafaru can baya ban san ya akai ba,bansan meya sameniba,haquri nazo nabaki ki tausaya min kiyafemin zubaida! rayuwata zata gurbata,zata tagayyara,idan kika auri wani baniba..kamar da wasa naga bello nasharar kwalla ayau,wanda da ace ba idanunane suka ganeminba zance qaryane. 32. Wani irin karfine yazomin na mike nayi hanyar kofa ina girgiza kai,babu kalamunshi ko daya daya tsikare ni,balle yahudani,na dubeshi ina murmushi a sanda nakai bakin kofa..mai kafa kamar MUBURGI? KYANDIR? Yau itace inba ita rayuwar dan kwalisa bello waziri zata tagayyara....?kokarin zare sakata nake,don aganina nagama magana (i've no more to say) Na soma dube-dube,kana a hankali tamkar wacce tasha duka,nakai idona ga abinda tuni na mance da shi; "NABAR GIDA,CIKE DA KEWA DA KAUNAR KI,INNA NA AMARYA.NABAR GIDA,CIKE DA BAKIN CIKINKI,KISHIYAR INNA NA,LAMI.NABAR GIDA,ZUCIYATA CIKE DA KAUNAR, WANDA BARGO, RUHI, BAZAI TABA DAINA KAUNAR SHIBA; MUHAMMAD BELLO WAZIRI KARAYE; nasauke idona tsuruuu,abinda tausayi,dana sani ban rubutaba.hawayesuka soma bulbulo min, nakifa kaina cikin gwiwowina.zubaida mafitar ki daya a wurina ,kije kice bazaki auri taheer ba. inkin qi, saidai TAHEER ya auri ragowar BELLO. kin ganni nan bana tsoron uban kowa. idan na kashe mutum,nakashe banza,shin meye zabinki? 33... Ya baro kujerar shi,ya cireni tsaye, nadunkule hannuwa,wallahiwallahi kaji na ratse da girman allah zan maka ihun fyde.ashe kai dan iska ne bello ban sani ba? Karewar iska atine ni bello danguguwane....Ya soma dosoni, ganin da gaske yake a guje na tasamma kofa.wannan karon ma na kwashi kaina ayashe tsakar daki awal domin kuwa dogayen kafafun shi yasa suka kwaso ni. Yaya me kike ciki? Yana kara doso ni tare da soma balle botiran hannun shi zuwa na wuyan kakin da ke jikinshi.na fashe da kuka da karfi cikin raina kaina gashi kuma bana son in mishi ihu tun da kuwa kirari ne zanyi in burmawa kaina wuka.waya kawoni? wani bayani zanyi a yarda bada kafafuna na shigoba? Sai na koma lallashi 34. bello kaji tsoron ALLAH don Allah?kana fa da aure gobe zanyi aure!to zubaidah nikuma yazaki yi dani? Ay bansan kai dan iska bane kai bello sai yau, da ina zantaba sauraranka a rayuwata? Murmushi yayi mai fidda sauti.zubaida idan son danake miki iskanci ne ashe taheer ma dan iskane? Tunda shima yana sonki? Allah ya sauwaqe.yallabai bai taba min wannan keta haddin ba. Tunda nake dashi shekaru tara dan yatsana bai taba riqewa ba.kayi shirin hisabi dashi ranar gobe qiyama,kan qazafin daka yimasa. Wallahi kaji narantse saina gaya masa, don yasan dawa yake zaune?dan iska,mai neman matarshi ta aure!ya fadada murmushinshi mai kyau nayau fiye dana kullum yace,ki iya bakinki zubaidah,idan nasake cafkarki a ragowa zaki gidan taheer,nace insha Allahu Allah yafika. wannan ba sobane,kai mayaudarine kawai.sonka din banza.me ake da son dan iska? Yace sake fade bello dan iska,kiga a masoya akwai mahaukata zubaidah!nayi tsit ina haki yakura min ido kamar wani sabon maye,yayi kuta yace, shi dan iskan ubangidan naki,ashe yaga haka kike da kyau,ba irin matar shiba.shine ni zai cuce ni? Nagaya miki gaskia meye zabinki? Hawaye nafutar mishi aguje suna sauka akan kumatunsa, jikin shi babu inda baya kyarma nima kukan nake.tausayin shine yazo ya dabaibayeni amma bukatar shi kodaya ba mai yuwuwa bace,zan bishi da addu'a Allah ya yaye mai sona kamar yadda naroke shi yayemin a sanda ya wulaqantani, magana nake hawaye na bulbularmin kaifa kace baka sona,atika kake so, sabida kafana kamar maburgi..... Bello ya rude yaqara kwancewa iyaka. 35. ya tabbatar zubaidah nason shi.akwai dalilinta na auren taheer.yazare jikin shi da karfin hali ne kawai irin na soja,kafin ya durqushe akasa yasoma kuka nanemi gwaggwaro na kifa nasa gefan rigata na share idanuna,nabude sakatar da sauri a guje nayi gida.nafada cinyar inna na Amarya nashiga rera kuka tamkar raina zai fita. tuni gida ya watse domin magriba takawo kai,su ashsha sun fice alwala,daga amarya sai sadiya dake linke kayan danai amfani dasu,amarya hankalinta yatashi takamani muka shige kuryar daki,amarya don Allah meya hana auren bello da atika?shine yazo?shine amarya yai bala in bani tausayi,baki ganiba kamar ya haukace,yanata abu na marasa hankali.naci gaba da kuka sosai, amarya tace kirufa mana asiri zubaidah,kada kice zaki komawa bello.yazamuyi da suruntun mutane da alhakin baban jawad? Nasoma girgiza kai dasauri wallahi so dai guda daya bello nakewa. idan na auri yallabai tausayine da karamci kawai, amma babu so ba qauna ginshikin aure, tassss....! marin da amarya ta dauke nidashi kenan,atine lalle kin cika yar'adam,son ubanki!ki iya bakinki, idan malam yaji dakyar inbai yafe kiba.na rantse da Allah inhar ina raye kinbar bello har abada! koda ba uban jawad zaki aura ba.nafada abaya a yauma na qara kin manta sanda yaron nan ya tozartaki, kika zomin nan bakin-ciki kamar ki mutu. sannan yanzu donke azzalumace, mahaukaciya, wadda bata san ciwon kanta ba. kizo gaban idona babu ko kunya wai kina son bello? [10/23, 5:07 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/23, 5:09 PM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔 ~BOOK 2~ Tuna Baya2 36. Na durkusa bisa gwiwowina,muryana narawa da karkarwa,kiyi haquri kiyafeni Amarya,bazan sake ambaton bello ba,bazan sake cewa inason bello ba,nabarshi araina,zan auri yallabai inbishi koda bana sonshi...Amaryatayi salati ta sanar da ubangiji kana ta ingijeni,koda bakya sonshi? Kin barshi aranki? Lalle mutum abin tsoro Allah ma abin tsoro,kada ki soshin,aure nagani inda uban daya isaya hana a daura shi gobe banda ikon Allah! Tafuce tana kakabi wasu hawaye suka zubo min a kundukuki na,narasa inda zan tsoma raina inji sanyi,wai meke damuna ne?ni atinen mamman mai kalwa? Sai na tashi nafito donna dauro alwala,inrama sallolin dake kaina,saiji nayi jiri na kwasata kamun intantance maike faruwa najini wanwas,jiri ya kwashe ni ya yar a gindin rijiya dani da butar gaba daya,daga wannan ban sake sanin mai ke faruwa ba.farkawa nayi na tsinkayi duk jama'ar gidan akaina.wasu na fifita wasu na sannu zubaidah a haka muka kwana,duk gabban jikina babu wanda baya ciwo kuguna ya bugu,ko zama nakasa sai kishingide,domin kwanciyar ma tagagara.da wayewar gari luba ta shigo wai sai a daga daurin auren tunda haka tafaru alamun masifa kenan acikin auren.baba yayi mata shiru bai saurareta ba yasan rudun tsufa kedamunta da bellon data kwallafawa rai yakira ashsha yace takira yallabai ta abunda suke magana tagaya mai taji mai zaice? Ashsha takira yallabai ta wayarta tagaya mai komai ake ciki, hankalinshi yatashi matuka yace tabashi baba,ya qasqantar da murya yana roqon baba kada afasa daurin auren insha Allahu zanji sauqi ne basai andaga daurin auren ba,yanzun nan zai turo kaninshi muhd yakaini asibiti a kano,shima yana bisa hanya,yatsaya jiran tawagar ofis dinsune sutaho tare. 37. ba'a fi minti sha biyar ba mohd yazo,yace turo awal su fito ya kai su asibiti.ni tunda naji ance mohd sai na tattake na zauna daram da duwaiwaina. tamkar in kwala ihu dan azaba, amma nadake na cije lebe,nace yar buguwace, harta sace ba inda zani a sayo min mantaleta na shafa.amarya ta hau fada ance dake ana raina buguwa ne?idan ya ruruce naga da kafar da zaki cangala acikin mutane ashshah tace kyaleta amarya har party zamu je ina ruwan amarya mai bantararren kugu,nina san allura take tsoro kawai da muna makaranta saida ta taba yin wata da zazzabbi bata fadawa kowaba don kar ayi mata allura inji ashshah baba yace zaki tashi ko sai na shigo da dan aiken?na mike da kyar, ina dafa bango ina kunkuni ashshah da lola suka kamani wai shi baba bai san waye muhd din da ake nufi ba?ai shikenan idan ma yasace ni ai su suka jiyo. yana cikin motar shi ceranto-ex kafarshi daya awaje daya aciki, sanye da kufta da wando na wata irin jikakkiyar shadda (mali)ruwan sararin samaniya (dark&light blue)kenan dinkin mutane maiduguri,kan shi ba hula,takalmin kafarshi bakine budadde dan thailand.ga wani lafiyayyen agogo azurfa da ratsa cikin lafiyayyar fatar hannun shi 38 Fuskarsa a tsuke tsam ba alamun sanayya,ba sani ba sabo ba gaisuwan mutunci balle alamun an taba haduwa da juna,sauti ja-rule ke tashi cikin motar cikin baitin da ya kira WANNA YOU TOO NEED ME.I WANNA BE THE FACE YOU SEE.WHEN YOU CLOSE YOUR EYES.I WANNA BE YOUR FANTASY AND BE YOUR REALITY AND EVERY THING BETWEEEN.I WANNA YOU TO BE NOT BLAME,FOR YOUR LOVE IS OVERALL TO ME' hannuwasa bisa sitiyari,ya na kallo mu ta madubin gaban motar na side din da yake, fuskar nan kamar hadari .wanni abu ya danna duk kofofin motar suka bude atare muhd jos ne a kujerar mai zaman banza shima bai kalle mu ba, kazalika bai cemana ko cikan kan ku ba muka shiga baya ni ina tsakiyar ashshah da lola, ashshah na rufe kofar daya wani fizgi motar sai da dukkaninmu muka birkito daya kujerar idanun ashshah suka yi kwal -kwal ta kankameni ganin mutuwa muraran,ni ko ko ajikina ai nace bazani ba suka takuramini? Irin gudun da yayi sai da motocin dake gaba da bayanmu suka dunga aikamasa da fitilun zagi.mun yi nisa da karaye sosai muhd jos ya dubeshi akufule bello in kisan kai zaka yi ka sauke ni.ban shirya mutuwa yanzu ba ya juyo gareni zubaidah kice wani abu mana [10/23, 5:09 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/23, 5:10 PM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔 ~BOOK 2~ 39. cikin kudurar ubangiji 'ya'yan hanji na babu duka wanda bai zunkuda ba mohd ya zuro hannu ya bude kofar dama ku kufito mu tafi ai ni tuni sun yi waje babu nema ba'asi zubaidah fito kin ji, wannan mugune,sai ya kasheki abanza awofi tunda bashi keda asaraba na daga kafa,da niyyar in fita amma ko motsata na kasa tariga tayi tsami sai hawaye suuurrrr,kafin na ankara tuni nayi dirshen a mazaunin mohd, cikin wani irin zafin nama ya rufe kofar ya sake fizgar motar (over 400 spead) ya dubeni yayi murmushi dukkanninmu babu mai tsira da rai.ina amfanin rayuwar kowannenmu bada wanda yake soba?sai kunci, sai bakin ciki wanda da karshe ni ya zautani, ku baku san ina yiba bazai yiwuba!ba zan keta miki mutunciba zubaidah ,don ba abin da yasani sonki ba kenan.idan baki mantaba,na soki ne tun baki mallaki komiba,tun kina kucakar 'yar kauyen ki idan nayi haka ashe karya nake ba sonki.bazan iya hakura da atine naba kuma bazan barmishi ni bakin ciki ya kasheni.ai gara duk murasa ...................daga haka ya dauke kan motar daga titi,yayi daji damu, ya saki sitiyarin motar tari ka karo da bishiyoyi har ta dangana da wata ribdediyar bishiyar tsamiya,ta jirkice glassanta suka kwankwatso a gadon bayanmu wani abu naji tsakiyar kaina garam.ban kara sanin inda rayuwata take ba. 40. jinayi ana gogemin jiki da towel sannu ahankali na bude idona ya bala'in yimin nauyi dusu dusu nake gani amma na fahimci matar baturiyace na bude idona sosai wani haske ya dallare min ido. ba shiri na maida na rufe,na yunkura zan tashi naji ni a daddane oh thank god,you've recovered!ta danna kararrawa wani likita bature gajere siriri ya shigo tare da nurses suka ciccire na'urorin dasuka yimin dabaibayi dasu fita,da kamar minti goma bayan fitarsu aka turo kofar aka sake shigowa,yallabai ne agaba fatima na biye dashi fuskarsa ba yabo ba kuma fallasa.ta jamai kujera ya zauna dai dai saitin kaina ta daura hannuta akaina tace zafin kan ya sauka takama yatsuna kaji jikinta sanyi kalau sannan duk takumbura.anya baza ayi karin jiniba shiru yayi mata yana kallon wani wurin daban can kuma ya dubeta,ashe kin baro sanni hallayar dan adam kin komama lafiyarshi?tayimurmushi tafita bari inga abbansu mukhlas" na rutse idona na rasa meke mun dadi?kunya da nauyin yallabai da fatima suka dabai-baye ni yanzu ko awane matsayi yake dubana? Maciyiya amana,makaryaciya, maha'inciya. wannan shaidar da yayi mini shekara da shekaru a yau bello ya gogeta (bana karya bana ha'inci).gashi ko sannu yaki yayi min. na daga hannuna wanda ba bandeji narufe kwayar idanuna .wasu siraran hawaye kebin gefen idona suna diga cikin kunnuwana, ya mika hannu ya dauki jaridun dake bisa wani tebir yana nazari daga cikin wani dark glasss din daya boye kwayar idon shi,ko uhm bai ce ba. [10/23, 5:10 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/23, 5:11 PM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔 ~BOOK 2~ Tuna Baya 41-50 41. aka turo kofar aka shigo wannan likitane na dazu sunyi musayar kalamai cikin turaci wanda na fahimci jinine za'a karamini.yace su gwada nashi ko na kanwar shi in zaiyi dai-dai?idan duk bazai ba bai san jininsu gara yasayi abincin da zai kara jini cikin dan lokaci,toh anyi sa'a nashi ne yayi dai-dai tun da dukkaninmu muna (groupB+), aka duba lafiyar jinin kamin a diba asamin,ina daga kwance ina kallon disar jinin abban jawad,cikin gaurayen jikina wasu hawayene suka ninka na da allah yagani muhd jos shaidanane har azuhur yana zaune ya diba lokacin sallah a agogon zallar 'diamond'dake hannushi ya fita fatima ta sake shigowa zubaidah dacta yace kada abaki abinci sai gobe.yanzu meke damunki?ita kanta kunyar ta nakeji kamar na nutse akan katifar da nake kwance.bance komiba sai karin hawaye.ta matso har inda nake ta ja kujerar da yallabai ya mike ta zauna na yunkura ta mike ta tusa min fillow kuka mekike tayi haka? Ai an gode allah da baki raunana tamkar mohd ba,da kin kwaramin yaya amarya da hatsari ranar aureta?'what a horrible'! idan kinga abbasu mukhlas sai kin ga naki ba komai bane.shin mai ya janyo hatsarine? Wannan ya tabbatar basu san da ganga bello yayi ba,na gode allah a raina nace dan jos bai gaya muku ba?shi cewa yayi,kun sauke su suyi sallar azuhur agidan mai ke kuma kikace zafin dukanki,shine wai ya zaga titi ki dan sha iska kamin su idar. yaga shiru-shiru baku dawoba shine yakira police suka duba.gaba kadan suka gane cewa 'stirring'ne ya kwace wa mohd .yayi daji kuka yi accident kai wannan muhd amma gwanin karyane,ban musa ba koni naso hakan da da wanne ido zan dibi fatima da yallabai? 42.... ana gab da daurin aure muka tsinkayi labari yallabai yayi ta fadan da yasani da baice mohd yakai ki asibitiba yasan shi bala'in tukin gangaci. Shi fa har karaya yasamu ahannu shi dama da hagu ga gocewar kashin kafa ke kuma buguwane kawai a pelvis girdles (kashin kugu)ki kan ciwon da za'a kai asibiti kenan.sai raunukan glass a tsokar bayan ki da targade ahannu, amma sun bada tabbacin nan da sati daya zaki warke sarai ta mike tana zuge labule. Na tambayeta wane asibitine nan?tace in mun fita na gani amma ina zargin idan har yallabai bai zargi tsakanina da bello. don daga ranar kullum ya shigo daga tambayar ya jiki bai ce min komi ba ba wani alamar kulawa.ba wannan murmushi da kalaman shi masu dadi,babu alamar kauna.fatima da nurses ke kula dani.ranar litinin wato ranar da muka cika wata guda sun tabbatar duk kasusuwan sun hade sai karfin jiki da ciwon jiki. suka sallamemu da shawarar yawan motsa jiki. munfito harabar asibitin da kafata nake tafe na daga kaina na duba na tabbatar ba nigeria nake ba jar fata ke ta sabgarsu a ko'ina .ta hanyar wani karamin notice board na asibitin na fahimci muna cikin birnin pittsburgh,USA ban ga yallabai ba, fatima kejan mu cikin wata kankanuwar mota ta zaman mutum biyu (bently) irin mai mannewa a kwaltarnan ce saman ta a yaye yake kalar ta brown wannan ya tabbatar min zaben yallabai ce mun iso wata kebantacciyar unguwa mai tsarin gaske da basan sunanta ba gidan da ta tsaya shine no (9)karamin gidane flat ma tsarin irin gini turai dai samarine guda biyu (afro american)dake kula da shukokin gidan suka bude kofar da alama sun santa tana daga musu hannu motoci har biyar a harabar gidan tabbacin akwai baki ta yafito da daga cikin su ta tambayeshi ko yallabai shi da wane? Yace suna meeting ne da 43. wani corridor muka bi zuwa cikin gidan,akwai sassa guda biyu kawonne dabam da dan uwansa taba ni mukullan daya sassakine amarya zubaidah, ni zan yi amfani dana maman jawad, bakisan wata sa'a ba harda wata jakarta da dollers a ciki na tsinta.in kinaso nakawo mu raba ko ina take Allah sarki!kai faty akwai surutu kamar aku, nayi murmushi,ni banaso,ba abin da zanyi da kudi, nida bani da lafiya?in zamu tafi gida zaki bukata mana?ni dai na yafe, yaushe zamu tafi? jibi in an sallami mohd koda yake kune zaku tafi jibin ni zan tsa inkula da lafiyar mijina nida muhd jos wata kila har akare biki baza ku ganmu ba sai kunzo 'haney moon'a biyo ta gidan mu ko? na dan kyabe baki kadan, don sai naji banbarakwai. Faty tayi dariya tace kije kiyi wanka, in kin kintsa'exercisearea' zamu zaga.kinji likita yace ki dinga yawan motsa jiki.baza kiga angonaki ba sai yamma kinji sunce yana meeting fuska na yamutsa kamar zanyi kuka nace ni nace miki inason ingan shi?kai aunty fatima tayi dariya ta wuce daya 'part' din 44. nayi wanka amma na rasa kaya da zansa in sauke sallolin dake kaina, na jikina sunyi datti kwarai, na bude dirkekiyar warddrove ta jikin bango dake dakin,kayan yallabai ne ajere abin sha'awa wani nabin wani.naja wata jallabiya ruwan makuba kirar omman,wani lafiyyayen kamshi take na yallabai dana dade da sani wanda bako wana taba ji dashi ba sai shi daya,na sanya nayi lullubi da sabon zanin gado na sauke duk sallolin dake kaina,inda duk yallabai yake bakya rabashi da karamin Alqur'ani mai tsarki.don haka ina diba wallet din shi na samu,bugun misra na karance fatiha,baqara al- imran,da nisa'i.nasoma maidah kenan fatima ta shigo tana rike da kayan hannuta ta shirya cikin farin dogon wando da karamin riga ruwan powder pink masu ratsi fari ,kanta cikin 'showercap'sai digar ruwa take tabbacin daga 'swimmingpool'ta fito ta dubeni tayi murmushi tace ba sai kin rokaba 45.... Allah ya kashe ya baki indai!taheer.kizo muci abinci,muso ma exercise din ko?ga kayan nan inaga zaki fi jin dadinsu.ko man shafawa babu a gidan nan,in mun kare sai muje mu lodo cosmetics (kayan kwalliya)jin ta kwai nake,ina jinjina abin data fada cikin raina,da gaskene mazama matar yallabai? ALLAH THE GREAT! Mai yin abuwawan dayaso,maiyiwa bawa falala da nasibi ta inda bai taba zata ba,da abinda bai taba tsammani ba.ina na taba tsammanin a rayuwata zan mallaki abban jawad?wani abu ne dako a mafarki, bai taba zuwa min ba,babu wanda ya isa ya hukuntashi.tsigar jikina ya tashi ya mike yarrr,cikin kara jin tsoran sa da kambama iko da hukuncinsa. Bansan sanda na daga murya nace daita ni bana jin yunwa kije kici, lemu kawai zan sha tadan yi jim kamar tana mamakin daga murya da nayi can tace to kisa kayan muje, ina zuwa ta juya ta fita tana bada baya na dungura goshi na cikin sujadda, na kwararo tasbihi yabo da godiya ga maqagina don inban dashi babu wanda ya isa yamiin wannan gatan, nasan kuma ba dabarata bace, ba iyawa ta bace haka bawani abu nawane ya mallaka min mutum irin baban jawad,am indeed among the luckiest!na dubi kayan data zubemini irin kayan jjikintane sak, sai kalla data bambanta wannan zaben abban jawad ne, brown lallai ma fatiman nan, ance mata zan iyasa irin kayanta?sai nasa kayan agaba da kallo (in ruwan "yar kauyen karaye) ina haka ta sake shigowa zubaidah bah de kunyar sa kayannan kike jiba?babu kowa agidannan saini,sai ke sai mijiki.idan kuma shi kike jin kunya,toh babin mu wurin exercise zai ba nayi dan tsaki, sabida haushin data bani,na dubi kaina a dogon mudubin dake dakin,nace ashe dai nima yanzu macece har haka ban sani ba?babu mai kirana KYANDIR?basan sanda nayi murmushi ba,na cinmta tana shan ice-cream duk uban sanyi da ake a kasar tace fantastic !kin gan ki kuwa so cute so beautiful muje amma aiba slippers zaki sanya ba ta zura a guje kamar wata yarinya tadawo da irin takalmin kafarta 46.... wani simple farin cambas ne mara tudu ko kankani wanda dama dan exercise aka kirkire shi na amsa na sanya,muna wannan karfe, mu sauka mukoma waccan keke,tana naushin boxing bag na tambayeta ina jawad dina?tace yana wurin fulani shidasu mukhlas ya addabesu da kuka da kutufo naji ba dadi har yanayin fuskana ya nuna hakan ta tuntsire da dariya tace jawad ya dauka ke da uncle din shi kun mutu.daya ga an fiddo ku jina jina shida mukhlas suma sukayi yanzu in yaganki kin koma da kafarki ban san irin dadin da zai jiba.kaunarki da muhd jawad daga Allah take nace hakane saida magriba tayi mukar gurin motsa jikin muka sallaci magriba muka ci abinci, har dare yallabai be nemeniba.wurin karfe takwas fatima ta shigo rungume da jariri har kin idar da sallah anti mu? baki nayi makociyar gidan nan ce isabella kin ga jaririnta nipole na amshi jaririn muna gaisawa da isabella suka shiga fira ita da faty da alama sun dade da sanin juna don ita isabella yar pittsburgh ce amma mijinta ke aiki inda su faty suke, acan kuma take karatu jami'a daya da fatiman.sai karfe tara isabella tayi mana sallama ta tafi faty ta fiddo dollars tana kirgawa tace ga kayana kisa muje boutique din yanzu ga kudi yallabai yace in baki sabida yana ganawa da ambasa bashir sambo yanzu yana maki sannu da jiki kamin ya sallamesu, jikina ya soma sanyi da canji da nake gani daga abban jawad,tun muna asibiti bance komiba,illa fuskata ta nuna mata rashin jin dadina, a zahiri ina sunsunar wani abu mara dadi a zuciyar yallabai, wannan karon ma faty ke jan mu a motar dazun sai dai ni duk raina a jagule yake ba dadi na rasa inda zan tsoma raina tsorona Allah tsorona kada ya kasance yallabai ya fahimci jikkakiyar dake tsakanina da bello, ni atine da ya zanyi in fidda kaina?to tunani nan ma ai bashi da wani amfani,yaya ma za'ayi ace bai gane komiba? 47.... Sai dai shi inba cikakken mai hankali bane wannan tunanin tamkar andiga min ruwan dalma ne. atake kaina ya shiga sarawa duk raina ya kara dagulewa komi yayimin baqiqqirin,ko ido bana iya dagawa indubi faty,nikadai nasan irin yanayin rudanin da zucia ta ke ciki.muna bisa kwalta tana bani labarin yawon honey moon din su da muhd har nan pittsburgh. tace zubaidah bamuyi auren so da muhammad bello ba.domin ni ke son shi,shiko hankalinshi na kan wata yarinya dayaso aure baisamuba.waddanaji iyayenta sun mata aure tun tuni yanzuma 'ya'yanta uku.amma kulawa,nuna tsantsar so ga mijina,biyayya da maida kaina niba komi bace face baiwa a gareshi,kuma mai son abinda duk yake so,itama atinen tashi,ina sonta.lokuta da dama in inason shawo kanshi inyayi fushi sai ince bello kayimin afuwa albarkar atine,wallahi bai qara tada zancen.na haifi mukhlas,yace inama mace ce.daya samata sunan atinen shi.ban nuna nadamu ba,illah na nuna nima naso hakan.amma sai in shiga daki inyita kuka. 48... haka dana kara haifan taheer yace dama mace ce yasa mata ATINE,ko yanzu inya murde da tunaninta kamar ya dokeni.idan na taba nuna naji haushi Allah ya tsine mani.wannanne yasiyo min darajah da kima a garesa.yau da gobe shiba mahaukacibane,shida kansa yalura yana cusguna mani.wata rana yasameni yanunamin tsananin kauna da bai taba ba yace fatima nasanfa kina haquri dani,bayadda zanyi ne Allah ne yadora min son atine,kitayani rokon shi ya yaye mani, don da Nace ni bazanyi wannan adu'arba. Sai dai nima in rokeshi ya dasa nawa son ko yaya a zuciyarka idan nasamu wannan ya ishe ni rayuwar duniya gaba daya,sai ya rungumeni,yace fatima kenan ina sonki,ko bakomai ke zabin taheer ce,kin san kuma bazan taba kin zabin yaya taheer ba wallahi zubaidah daga ranar ban sake bakin ciki ba,bai sake ambaton atine a gabana ba,bai sake cusguna mun akan atine ba.a haka muka haifi mohd taheer cike da kauna da fahimtar juna. Daya zamo lieutenant a soja kwarewarshi da aiki bisa juriya ta sanya military turoshi wannan muhimmin course na shekaru uku acan washington inda muke da zama a yanzu 49. daga wannan course din Allah kadai yasan matsayin dazai mika a military saida na fara karatun sociology a sussex na tsayar da haihuwa, rayuwarmu ta mika gwanin sha'awa. saidai tun fara bikin ku bello ya dawo cusguna min. dakyar inba atine yagano ba a cikin yan matan kiba don yar asalin karaye ce dama ko abinda bazanyi tolarating yanzu ba kenan akan wata banza a rusa mani rayuwa nida 'yayana hmmm sunan wani littafi idan yawarke bazan kara sake yazo nigeria nan kurkusa ba sai mun kare shekarunmu gaba daya,murmushi nayi, naji tausayin ta har kokon raina nace in sha Allahu anti faty Allah bazai bata ikon dawowa cikin rayuwarku mai tsabtaba.nima daga yau zan tayaki da addu'a.taji dadi tayi murmushi tace nima zan tayaki da addu'a kada mubina dango ta dawo.domin annobace a gareki gashi da alama ubanta ya dage da karfin naira sai ta dawo.na muskuta kadan nace wallahi ta dawo baki sani ba banso anti tabar mijinta da danta domin niba, nifa nazo na tadda it da mijinta,da dadi ba dadi suna zaune tare suna hakuri da junansu zanyi farin ciki ace jawad na tare da mahaifiyarshi in har baza ta cuceni ba,ba zata kwace mijin ita kadaiba me zai dameni da zamanta, faty tace tab!lallai ke yarinyace zubaidah, har yanzu baki san me ake kira KISHI BA. koda yake in kin soma kyakkyawar rayuwar aure da yallabai zakisan darajar mijinki.zaki san me matan kema kishin.sai kiji ko kuda bakya son ya rabe ku balle kishiya,kuma irin su mubina dango 'yan duniya gidan kashe ahu?kina tsammani zata bari kuyi sharing mijin equally? you are totally mistaken (kinyi kuskure)abin da zai dawo da ita shine kawai ta fitar dake ta kwace mijinta da danta,ke zubaidah kama bakin ki kada kifadi bakin mala'iku,rungume mijinki kiyi mai duk abin da ya keso.kina da kyau da duk wace dama da diya mace ke nema.ki batar mai da tunani kowacce 'ya mace,ki zame mai cingum, inda duk yayi ki bishi,ki manne mai uwa kaska ki nuna mai so da kauna,kada kizamo mai kiwa da son jiki shine babban abin dake cutar mata 50. a yau, ba a samun aljana a kwance.ki mike tsaye ki nemo, ko yankar farce da karin hula kada ki kara barin yallabai yayi in kun koma nigeria .tana fadi tana curo turaruka designers iri iri duk wani nau'n kayan gyara jiki da gyran fata ba wanda faty bata sani ba,daga kayan kwalliya,turarezuwa mayuka.ta koma diban english wears ni kadan na dauka,tace don me?nace baki san yallabai dan AREWA ne ba,gaba daya al'dun shi na AREWA ne ba? Babu mis (mix)ba algus balle kwabi dana bature ko daya,tace AREWA!AREWA!!kada ki biyemishi zubaidah,bai gani ajiki mai kyau irin naki bane sai na karmason matar shi mai kugu uwa tafin hannu [10/23, 5:11 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/23, 5:13 PM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔 ~BOOK 2~ Tuna Baya2 51-60 51.... Da kirji kaman an tatsile kuliy bisa kwalta, amma ai ba zubaidah momin jawad ba,idan kuna arewa kiyi mai arewanci,idan kuna amurka,ki yaye bargon kunya ki yimai amerikanci kizama tantiriyar ba amurkiya, that's all.... Na tuntsire da dariya har cikina ya kulle.sai karfe goma muka iso gida ,har na gama abinda zanyi na kwanta, ban sa yallabai a idanunaba.barcinake ,amma hawaye basu bar zubamin ta gefen kunciba.na tabbata yallabai fushi yake dani tun daga ranar da aka daura mana aure,da ada yake kira special day a garesa.da asubah dan alarm clock din dana saita na makale jikin gadon shi ya tayar dani..na dauro alwala kenan ina shirin tada ikama naji motsin shi yana murda kofa..ya murda kofar ya shigo cikin farar jallabiyya da sallama ciki-ciki kaman bai son yi yace baki jirana mutada jam'i?daga yau karki kara yin sallah ke daya har in ina nan,ya jamu sallar yayi 'yan addu'oi muka shafa ,ya kunna wata 'yar karama rediyo mai kama da kwallo yara (ball)karatun alqur'ani mai tsarki ake daga masallacin madina ,yana bi a fili tirya tiryan ni kuma inabi a zuci .karfe shida gari ya soma haske ya kashe rediyon ya mike da niyar shiga wanka, na karkace kai na riko wuyan hijabi nace ina kwana yallabai? Saida yakai kafor shiga toile din yace lafiya shima ciki ciki nakoma gefe na zauna shiru kamar icce wayyo Allah!ko wani kwakkwaran motsi na kasa kaman an kafeni a jikin bangon. ranar mun dade muna exercise nida faty,ko kadan ban gaya mata canzamin da yallabai yayi ba toh ina hauka ne? itama ta gano nice atinen aina bani na lalace ,bayan munci abinci mun zaga birnin pittburgh har da isabella,daga karshe muka kare a wurin kallon (polo)can muka lalace har yamma lis .nayi mamakin mai yasa faty bata ambaton mijinta,dan rigima muhd bello?na kare mamakina da tambayarta baza taje taga no muhd ba?budar bakin ta sai cewa tayi ai in ya soma fizgar, to ki tabbata antino atine a irin wannan lokutan baya baya nake da shi,kin san zuciya bata da kashi in na likemishi abin bazai yimin dadi ba, mohd jos na tare da shi,yallabai ma nasan tun safe yana can kuma naji yace da yallabai ya maida shi asibitin barikinsu na washington ya karasa jinyar acan gobe in kun tafi nima zanbi shi,tausayin faty ya kara kamani, kamar in zubar mata da hawaye,in ban da so da Allah ke dorawa bawa mena fi faty?ban ganshi ba!farace sol!mai ginannen dirarren jiki,komi na hallitta ta ya dace da ita ay sai yayi tayi ni ina ruwana? gani ga mijina me zai dameni?ina son shi,na kuma son yana min so fiye da wanda nake mai,hakanan nayi aure da zuciya daya insha Allah ba abin dake rabani da yallabai sai mutuwa itama ina fatan ta dauke mu tare. in ya gaji ya dangana bisa tilas, ace mutum bazai yadda da hukunci Allah ba,bazai yadda da kaddaraba? alhalin yana ikirarin shi musulmine,yaya kuwa za 'ayi yaga da kyau?yaga sauki da farin ciki a rayuwar shi? 52.... Ni nasan naso bello,naso komi nashi nayi fatan kasancewa matar shi har abada!amma daga ranar da yace wai ni kawar matar da zai aurane atika su fatima suka cemin KYANDIR,yayi dariya ya kuma kasa tsawatarmusu.duk wani so dana ke mishi a wurin ya narke, haka duk wata kauna a wurin ta zagwanye na tausaya mishi aranar wunin da yazo gidan mu don ganin yadda ya koma kamar mahaukaci,har naji birbishin son na neman tashi,shine har takaini ga furta kalaman da har yau nake nadamar furtasu ga amarya nace wa wai auren tausayi zanyi da yallabai ba auren so ba. dama turawa sukace wai when love dies its ashes remain alive.daya nemi kashe mu akarn banza na tabbatar ba shida birbishin imani,daman ance wai duk sojoji imaninsu cikin cokaline ,irin su bello ne koda ka auresu kuskure daya zakayi musu susa gindin bindiga su bubbuge ka ko su harbeka gaba daya,sun kuma kashe banza,na kasance tare da yallabai shekaru dai dai har takwas,na kuma fahimci shine mijin da nayi burin samu arayuwata sau tari na kan tambayi kaina a yadda zamanin nan ya tabarbare yanzu, daga samari har magidanta sun dauki zina ba abakin komi ba anya za' samu irin yallabai na? 53... ya raine ni tun ina mitsitsiyata yake gyarani har na kawo matakin da nake kai ayau,wato mataki na cikakkiyar kuma haddadiyar buduwar,mai dauke da duk wata hallita mai jan hankali da namiji,bayan bamu hada dangi ba tako ta ina, karewa ma,ni baiwace a gare shi amma bai taba nuna ko sau daya yana sha'awana ba!duk da kowa yasan irin rayuwar auren daya keyi da matarshi a lokacin,alhalinyana da kowacce dama ta neman hakan, sai nake tambayar kaina sunan daya dace dashi in kirashi Brave,or Trustworthy? Ya tara duk wata suffa dana ji ashshah na fadin wai sune mazan dake tsada,duk matsayinshi,ga iyalinshi shi mutum ne mai sanyi dabe daukar kanshi a bakin komi,bai da son kansa,bai son matsama dan adam duk abin daya lura baya ra'ayi, koda shi yana matukar ra'ayin abun tausayin shi, addinin shi , kyautayinshi da akidunshi ababen kwatancene.Qualities ne dana tabbatar shi bello da kyar in ya hadasu duka,shi daya so gurbatamin rayuwa badon Allah ubangiji na tare daniba?nagode allah godiya mara iyaka daya sa nafi karfin zuciyata ban bi son rainaba dana biye mishi dana tozarta yallabai,lallaidanayi asara irin wadda ba a mayarwa har abada!yaje can ya karaci rashin imaninshi da matar shi dake son shi hakurarriya baiwar Allah fatima nasan ita zata jure tunda tason kayanta haka,gashi harta iyawa halinshi haka?tasan sanda zata rabe shi da sanda zata nisance shi? abinda ke daure min kai shine ta ina yallabai ya fahimto ni da bello?koda yake insu marasa kwakwalwane da karamin tunani sun yarda da karya muhd jos shi namiji mai cikkaken hankali zai amincene?wani irin a zaga dani kamin su iddar da sallah?mubama sallar?idan ni banida lfy bazan iya sallah ba,shi meyasa meshi da bazai yi sallah ba?har muka iso gida tunanin danake kenan nayi sallah nayi nafiloli na kwanta har zuwa lokacin banga yallabai ba saida asubah da yazo muyi sallah 54 Dayake aranar zamu tafi,muna idarwa ban tsaya sauraron karatun da yake sauraroba na janyo jakata na shiga harhada kayana,yallabai ko magana tun da muka fito asibiti bai min ba ina yi ina share hawaye da bayan hannuna najawo ledar sayayyar da mukayi na cosmetics daga durowar mudubi sai kayan ciki suka zubo gabanshi gaba daya,na russuna ina tsincewa ya kama duka hannuwana,ya rike,abinda bai taba yiba wannan shine karo na farko da yallabai ya taba kama jikina by mistake a take tsigar jikina ya tashi yar! shock ne har cikin kwakwalwana irin wanda ban taba jiba yace no akwai abin da zan diba nakoma nayi zaune bakin gadon ya shiga dibasu daya bayan daya yana mayar min ledata,wadanda basu yi mishiba in ya karanta ya ware ya zubar a dustbin wannan karon ma cewa yayi bakin AREWA, nake son momin jawd dashi daga haka ya juya ya fita,naci kuka na har nagode Allah oh ni zubaidah menayiwa wannan bawan Allah?kar dai baya sona ya aureni? Na roki Allah kada ya kara samin wannan mummunan tunani, 55.... karfe hudu ne jirgin TWA ya saukemu a filin jirgin saman lagos ma'aikata foreign affairs dake kar karkashinsa suka zo tarya yallabai Allah yayi yawa dasu mun sauka a wani guest house dake titin hearbeart macaulay, bansa yallabai a idanu na ba sai washegari ya shigo a masifar gajiye, yace kwana sukai suna meeting da ministocin nigeria gaba daya a fadar governor tinubu.koh um ban ceba har alokacin muka baro lagos a mota audi,tafiyace mai dadi dasa nishadi don direban baya gudu sosai haka moto cin dake take mana baya ga sanyi AC na ratsamu ganni yallabai na karatun jarida batare da ce min ko sannuba,hankalina ya kara tashi,na kifa kaina a cinyoyina kamar inyi ihu,anan nefa na tuna nima macece,mai zai hana inja ajina?sai nayi biris dashi na bude karamin Al'qur ani ina karantawa ? har muka iso karaye cike nake da dokin rungumar gudan raina JAWAD an sauke yallabai a gidanshi na bayan gari kamin ya sauka yace any matsala?na daga kai kurum yace toh sai gobe zan aiko abdulraheem ko to din bance ba 'yan rakiyar shi dake bayanmu duka nan suka tsaya, nace wa direban ya fara tsayawa gidan mai martaba ya kira min abdulraheem (abdulraheem kanin yallabai ne dake bin fatima yana level two a bayero) ya dan leko ta taga bakin shi a washe a'ah momin jawad har kun sauka?tun jiya muka je tarenku a airport din mallam aminu kano mun dauka tacan zaku sauka akace ba jirgin US da zai sauka muka gaisa ciki mutunta juna da sakin fuska na gayamai ta lagos muka biyo, sabida yallabai nada meeting nazo daukar dana ne yace Allah sarki jawad yananan yana takabarki, 56. ya rantse baza ki mutu kibar shiba duk gidanan dukamu yake yi da kafa da hannu har maimartaba bai tsira ba.fulani kadai ke tsawata masa yaji, bari inkirashi amma dan Allah kar kiyi magana sai ya shigo af namanta in tambayeki ya jiki? nayi murmushi mai fidda sauti kawai, can sai gashi rike da hannu jawad, ya bude mushi kofar motar ya mayar ya rufe shima ya shiga gidan gaba,direba yamika unguwarmu ,jawad ya dubeni,na kunshe fuska cikin mayafina,sai ya matso sannu a hankali yana sunsunani,yako yimin wata wawiyar runguma nayi dariya shi kuma yakama kuka,ya tusa kan shi cikin rigata yana fadin momina mai yasa kika ji ciwo ki tafi kika barni?sai kuma ya koma buguna da kutufo ta koina,na shiga shafar kanshi bana ko jin zafin kutufon shi da yasaba yima mutum in ya bashi haushi,hawayen tausayi suka cika idona, cikin satittika uku kawai jawad dina ya koma tamkar ba shiba,ya rame,yayi duhu tamkar wanda ya kwanta ciwo,don kanshi ya bari yayi shiru, ya kara kanainayeni kamar yana tsoron in kara tafiya in barshi abdulraheem dariya yakemana kamar mai kallo comedy film muna isowa kofar gidanmu nayi mamaki, na rude da aljabi,gaba daya gidan an rushe shi ana gina bulo da bulo da alama ba'a kammalaba har da hawan bene,na russuna cikin kunnuwan shi jawad muje wurin inna amarya,sai inga yama duk inda naje,ni sai kin goyani,ya'ilahi, yau tabaran ya tashi kenan, kuguna har yanzu ciwo yake kai bakasan nayi accident bane?bayana ciwo yake,sai ya kara rikecewa da kuka, nace yi hakuri kai da bayanka? ai ko zan karye bazan ki goyanka ba jawad, zo ka hau,na fito motar,na russuna ya hau 57. abdulraheem yace,wallahi wannan ba gata bane zubaidah.shi yasa yake zakka acikin yara.komi yake kaman dan jar fata ba kwaba ba horo daga ke har uban?toh ai kaima uban ne kada keshi mana,ka gani in zamu kyale?ba gwarashi bama akan masu kyaman tsofaffi?yayi dariya wai su mukhlas,amma dai kinsan ya girmesu?da hirarraken da muka kenan,amarya da aminata ke shirya kayan gara.sai tatsaya baki abude,cike da murmushi,suko sai ihun murna baba dasu awal dake daki duk suka fito lallai nasara bokan turai, zubaidah data tafi tamkar matacciya jina jina,itace har da sunkuto katon danta abaya ,duk suka yi dariya baba ko sati biyu ba a rufa ba ai ba abinda baza su iyaba,hirar kena n kamin kice miye wannan gida ya cika fal ana ta murna da arziki kodayake dama yanzu gidan mu yazamo gaban goshi n matan karkaranmu,tamkar su yiwa amarya sujjada saboda tsabar kwadayin abin duniya da ishai inna ta shigo itama,tana bada hakuri wai taje gaisuwane gidan atika babban danta ya fada kududdufi ya mutu .na sunkuyar da kaina,na dubi inna duk ta rame , ta wani yamushe nace Allah ya jikansa,inna idan na karajin kwarin jikin zani in dibo atika,in mata gaisuwa ta tashi sum sum ta fice.wurin karfe tara muka kebe babada amarya na labarta musu jinyata a asibitin pittburgh da ainihin yadda mukai da bello sai dai addu'a kam,nima nan yazo yayi tayimin kuka .ni kaina na tausaya mishi na bashi hakuri,na gaya mai bazan iya hana yallabai ba aurenki in bashi ba ko alhaki sai ya tambaye ni.duk hidimar dayai mana na bashi yaki karba yace ko bai aurekiba bazai iya baki abu ya amsa ba ya yafe duniya da lahira na dauka shike nan zancen ya mutu ya hakura?shinne yayi wannan danya aikin?aida ya kashe ku,da ya mutu kafiri zan dage da addu a nima Allah ya sanyaya mishi zuciyar shi don Allah shaida ne akan ina son bello, ban kuma kullace shiba illa wani abu ne da Allah ya riga ya rubuta cewa bashi da rabon auren ki anan gidan duniya kema kuma ki mike da addua dan barci bai same kiba 59. ki mike da addua Allah ya kareku sharrin makiyi da mahassada,ga uwar yaronnan jawad ance tan nan tana neman fansa akan ki don haka daga yau akwai rubutun da liman (na yanzu )zai dinga aiko miki kullum akwai nafiloli da magunguna sammu daza ki dage dayi muma baza mu kwanta ba Allah ya kade duk wani mugun ji da mugun gani na tambayi baba maganar ginin dana ga anayi wallahi yadda kika ganshi haka na dawo kasuwa naga sunayi.bani da abinda zance da bawan Allah nan sai addua atine ki iya talaucin mu,duk wani matsayi da Allah ya kai ki ki tuna mutumin nan shine sila kibi shi yadda Allah ya umarta ya mutuntani,ya darajani,ya mai dani dake da duk jinina mutane,idan ki ka sake ya kawo mun shaidar banza akan ki wallahi yafe ki zanyi .maganganun baba sun tsoratani na mike tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki,na nemi sani nace ya rakani gidan atika yace shi wallahi bazashi wannan shegiyar unguwar da daddareba. dole na hakura saidasafe ,muna kwance jawad ya dameni sai in gaya mishi me akayimin a asibiti na rabu da jini daya gani?ina daddy shi?wai da gaske munyi auren da yace muyi? Yaushe zamu koma gidan mu mai tsabta da su uncle tom?baya son gidan baba dan tsoho(sarki)da wannan gidan mai rami (rijiya)nayi mai bayani dalla dalla yadda kwakwalwar shi zata fahimta,yace aunty ashshah ta tafi ta barni nayi nayi inbita taki, zata dawo? zata dawo muma zamu gidan su har anti lola da zee da yar balarabiyarnan SARATU INTISAR mai baka chocolate ko su baka sansu?ina sonsu duk,amma nafi son anti ashshah,kin ga ita tafi su kirki duk nace shikenan muka juya muka kwanta abin mu wayar ashshah ta tadani washe gari ta tambayi yadda muka iso da lafiyata na gaya mata komi normal yanzu tace salaha ta koma ilorin,su zainab duk sun koma cike da taraddadi,idan an tsaida ranar bikin sun dawo kuma alphat da yusuf suna dibani da jiki mamanta da sauran kannen ta tayi shiru can tace zubaidah ban taba tsammanin tsakanin mu har akwai munafurci ba, akwai abinda zaki boye mini 60. naji maganar kama daga sama wane irin munafurci? me na boye miki ashshah?tayi dan tsaki ban takura naji ba,amma tsakaninki da uncle mohd mijin aunty faty?kika ki gayamin shine bello childhood dinki,ba don naga ni da ido na ba ko kin dauka bansan shi ya kaiku ga accident ba? ke kin faya ci da zucci wallahi dama ina da niyyar gaya miki to yaushe na dawo ga ciwon har yanzu ban gama murmurewa ba zan hau miki zancen bello ki bari a hankali mana koma meye in natsa ai zan gaya miki oho miki kuna mama ce dama tace naga ya miki gudunmawarta in an tsaida date din biki kamar da kwana uku kizo muje sokoto gurin aminiyar ta ai miki shiri na amare na sokoto bayan na maidugurin duk da muka yi toh nidai baruwana,sako ne na ida in kuma baza kiba gatanan gefena sai in gaya mata kin ce bakya so kai ashshah basan yaushe kika zama masiffafiyaba zan gayawa yallabai inshah Allahu kice da mama nagode,ince ko shikenan? ba shikenan ba,da saura yallabai yace duk abin da za ayi a karaye,akare shi cikin kwana biyu rak dinner, luncheoun, da tea party duk rockview na nan abuja zamu yi akwai kuma walimar taya murna da foreighn affairs [10/23, 5:13 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/23, 5:14 PM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔 ~BOOK 2~ Tuna Baya2 61-70 61. ta shirya muku a NICON yace wai ya isa baki da lafiya baza ki iyaba.haka kawai zai kwaremu toh in zaki mike ki mike dan wallahi sai kinje gaba daya dariya tabani sosai nace ni sai magana kike ba comma balle full stop gaskiyar yallabai ne bazan iyaba Allah har yanzu kuguna ciwo yake kuje kuyi tayi amma ni biyu zani dinner da luncheoun wannan duk almubazaranci ne biki bana yar kowa ba,bana yar kawan kowa ba har ake mai irin wannan gagarumin shirin ai sai kisa duniya ta zageni ki bari dai sai bikin ki da alphat duk sai musha wannan shagalin,yo ni da wannan ku hado kudin mana in kaikayi suke muku ku gina masallaci a Jama'are da karaye.indai nice nagode,nagode ashshah kun nunan kauna,da bani da kalmar dazan gade mukuda ita sai kyakkyawar addua kawai ashshah tayi shiru nasan ta tsani tayi gwaninta a gwaleta to amma a ganina hakan shine dai dai. An tsaida ranar biki sati mai zuwa, alhamis kamu jumaa yini tsofaffi asabar yini yan mata sannan a rankaya birnin tarraya bikin yan boko,can gidan maimartaba ma tsarin su kenan ,garin karaye tun ran talata ya soma cika da baki,daga ko ina cikin nigeria da wajen ta barkowa suke ,yawancin su gidan maimartaba ake saukar su da gidan waziry ko galadima .gidan bello na bayan gari da katafaren gidan saukar bakin da yallabai ya gina a jikin nashi duk a bayan garin .gidan mu cikin sati fasalce shi fasali mai kyau na zamani ya zama babban gida mai rassa daban daban cheque din da yallabai ya bani na naira dubu dari biyu wai inyi hidimar biki na hada naba abdulraheem don banga abinda zanyi dasu ba komi ashshah da lola ke biya a aljihun su ,ya auno saitin kujeru biyar da kilishi da kananan katifu (donlop) aka zuba daki daki har dakin inna dana baba,ita amarya dama tuni ashshah ta zuba mata cusion da carpet da tv har da receiver tace dish zata sa a jona mata da yamma na nannada liffaya orange mai ratsin baki bisa atamfa aura dake jikina rabiu na tasa da almajirai da tsibin kaya zuwa gidan atika 62... ta dawone inaji daga gona dan naganta abin ba magana .yau cikin saa ban tadda matan gidan masu neman cinyeni ba,ta shimfida mun karauni na zauna duk jikinta na rawa yake ,tana kuka tana fyatar hanci.nace atika, ki kwantar da hankalin ki,ni banzo don in saki kuka ba.idan kina mun irin haka sai kisa na dena zuwa wajen ki, kina mantawa gaba kike dani amma ki dinga kuka agabana ai sai kisa na raina ki ko girman ki ya zube a idona,wannan rayuwar da kukece ban gane mata ba. Tsakani da Allah kina son zaman gidan nan?atika kuka take haikan ,ko bana so atine ya zanyi?komi ya faru nina jawowa kaina koko ince inna ta jawo min dama Allah baya barin hakkin wani kan wani dana auri jibo dake sona tsakani da Allah ai da haka bata sameni ba ni bakida alhakina tuni na yafe miki.wai bakisan aurena ake ba amma baza ki leka gidaba?ki saki jikin ki dani,ni yar uwarkice da bakida wadda ta fini kin tsaya kina TUNA BAYA...... bayan bazai amfaneki da komi ba,ga kaya na kawomiki kije ki wanka kizo kisa ki fito a mutum.kizo muje cikin iyayen mu kiyi komi a matsayinki na yayar amarya ,ki daina jin kan ki bare a gareni ,saboda ni abinda dake damunku ke da inna ni ban dauke shi da wani muhimmanci ba. atika tana share hawaye dake mata zarya atine basan me zance miki ba.amma nagode,sai dai ki hakuri tunda na auri dawaye ban taba zuwa gida ba haka duk saura matanshi bai yarda da fitar muba inba gona ba. in kuma kin fita a bakin auren kine.nayi shiru, wannan har aurene? tunanina kenan. amma a zahiri sai na mike.na sakala jakata ba zan so in kashe miki aure ba kam.amma duk san da kika gaji,kika gane wannan ba aure bane wahala ne,ki nemeni.a shirye nake da in taimakeki yar uwa ta kowanne hali.na tuna maganar marigayiya goggona ne da take cewa (cikin ko wanne hali atine kada ki butulcewa atika) Na gayawa yallabai zamu sokoto da mamansu ashshah a dawo lafiya kawai yace kwanan mu biyu a sokoto gidan dacta hafsi matar gwamnan sokoto na lokacin. 63. Suna faman tsimani da duk wani nau'in kayan gyaran sokoto.itace aminiyar maman ashshah. dacta hafsi cewa tayi haka kawai taji na shiga ranta.daga yau duk matsalata da maigidana na nemeta,ta zama uwata a sokoto su ashshah suka yi dariya tace wannan gyaran danai miki zubaidah gyarane da babu kayan da'a a cikinsa face gyara na manya mata na uslin sokkotawa da muka gada iyaye da kakanni.ta tsabtatacciyar hanyar da matan farko suka koyar damu.insha Allahu ranar da duk mijinki ya dandani zumarki kingamadashi zubaidah diyata,tsakaninshi da sauran mata sai de hange daga nesa.babu so ba sha'awa domin kin masu fintinkau .kammo ki sai an danna a guje gaba daya falon ya kaure da dariya .ta karbi lambata na amshi nata ,mun basu kattin gayyata tabbatar mini ita da yayanta maza da mata,masu aure da marassa aure zasu bayyana a abuja ranar luncheoun bakuma zasu dawoba sai sun rakoni dakina.mun iso mun tarradda tawagar kawayenmu sun iso inda akayi kayataccen kamu ranar alhamis da yamma,ranar jumaa wunin tsofaffi mutanen gidan su yallabai da jamaar gidan waziry sunzo gidan yinin amarya da yamma su ashshah sunyi ashoben atamfar mitex fara sol nima ita nasa,saidai kala ya banbanta nawa brown ne takalma da net duka brown sun je gidan maza har dare suna tare da dagin yallabai mata. hajiya barmani mai coge ce ta buga kida a gidan maimartaba suka shiga fili , kanne da yan uwa yallabai sun masu barin naira ba kadan ba amma ni banje ba.ina gida tare da tsoffina,ga rigimar dan lelena jawad inda duk na aje kafa nan zai mayar,yana korafin wai mutane sun cika masu gida na koresu shi zai sha shawarma wasu mata kan tambaye ni wai ince ko dan farine?gashi da girmanshi amma halinshi na yara sai ince duk sokancinsa soja ne idan ya naushe ku sai kunkai kas na juya nace dashi waddanan mutane ka kyalesu sun zo tayamu murna aurene in kuma baka son da daddy sai in koresu? Sai ya rukunkume ni yana bazan sake ba momina 64.... da daddare su ashshah sun dawo tare da abdulraheem. suna ta labarin karamci mutanen su yallabai dana fulani.nikam banyi mamakiba,ai karamci sai dan karamci.abdulraheem yayi kirana dakin awal.ya bani waya sabuwa dal da recharge card mai cin naira dubu goma dakudi yan sardauna sabbi kar acikin jaka wai daga yallabai nayi hidimar yinin gobe na karba kawai dan ance baa maida kyautar maigida nace ni ba abinda zanyi dasu sai dai in aje mishi kurum yallabai bai san ciwon naira ba yayi dariya fulani na gaidaki, tace ai maki ban gajiya kuma tana gaida maigidata da bai son ta jawad ,naji dadi jin wai surukata na gaidani ,na tambaye shi mai fulani tafiso ai mata kyauta da shi a rayuwarta? ya karkatar da kai yace idan kika bata farfesun kayan cikin rago,zuma farar saka,man zaitun da turare miski kin gama mata komai nace nagode abdul. washegari munyi wuni yan matan mu mai tsari,su nana sunji dadi bikin karaye.da yamma aka rinka sauke kwalla da sanduka nakiya alkaki dubulan da bakilawa da sauran abinci gidan sarauta a gidanmu wannan aladarsuce,mai vedio nayi mai daukar hotuna nayi inda duk na gifta su daukeni. Lola rike da "yar kamararta ta dage sai daukar hotuna take don ita komi a hurinta bakone abin zuwa a nuna agidane kasancewarta ba bahaushiyaba igbo hakanan ta lalace a wurin hawan angonci su yallabai tana son ganin mutum akan doki musamman inya tigija akayan gashi manyan many lufdan taja saliha suka kutsa fadar gidan maimartaba tana ta daukar kowa ta gani bisa doki abinci da abin sha mutane karaye yau gidasu acike yake da kwanuka da gidanmu gidan maimartaba gidan waziry garar abinci kawai ake fitarwa.washegari da safe motocin daukar 'yanmata zuwa abuja sun iso tun tara duk sun shiga sun tafi gidan da unguwar sun yi kwal dagani sai ashshah don ita sunyi da alphat din ta zasu zo su tafi da ita ta karaye subi jirgi yawo zuwa abuja haka nima yallabai ya kirani yace kar in bisu ni dashi da gudan ranmu zamu tafi da yamma (jawad) 66... a lokacin fatima tayo min waya ,nace ina samu lambar tace abdulraheen ya bata,tace bello yaji sauki yanzu haka yana bisa aiki cikin sojojin da aka tura kwantar da tarzomar kasar sudan don haka mu tafi da yaran ta zata iskemu abuja don haka da abdulraheem ya kawo su mukhlas nayi musu wanka dukansu har jawad na shirya su cikin sabbin kakin sojoji iri daya.kowannesu kan shi ya kumbura,jiya ke tafi dan uwanshi burgewa amma jawad yana fushi,yana kumbiri kamar ya fashe,na tambayi dalili ya cure baki yace wai momina,ya zaki sawa mukhlas kayan military? Bayan su baza akai su military school ba,babana ni kadai yace zai kai to akan me zaki sa mana kaya iri daya?kuma wanda yayi ma junior yawa dai dai nine, ki hada min duka kisa mi shi wasu . In wannan yai datti kamin uncle ejiro ya wanke sai insa wannan na kama baki ina mamaki hadama kenan mukhlas ya harareshi yace Allah baza a cirewa kanina ba wa yace dakai baza akaimu military school ba?mu da babanmu yake lieutenant yana da pistol yana zuba bullet yana zuwa operation lokacin da muna jos kai ko babanka baya sa uniform sai body guard dinshi kuma baya da pistol basan sanda nayi dariya ba shiko jawad tuni ya dunkule hannu ya kai mishi naushi na kwaceshi da kyar jawad kai ne fah babba yaya zaka ci zali?yasa kuka yace baki jiba yana zagin babana yace daddy na ba soldier bane? toh ai shima babanshi ne da uncle da daddy duka babankune kada ku kara fada akan su kunji ko? 67..... suka duka suka gyada kai .mun baro karaye karfe shida da 'yan mitoci cikin mota jeep (BMW)wato sai tsayi ba tudu zuwa airport,inna ce ga ainihin kwalliyar da nayi sai in bata lokacin ku kawai.karfe takwas na dare muna filin jirge abuja dimbin al'ummar yallabai da nawa da suka zo taryanmu Allah yai yawa dasu nida yara nan muka nufa kai tsaye nan muka hade dukan mu shirye shiryen tafiya dinne a rockview hajiya hafsi da mutanen ta sun iso tuni. Anyi dinner lfy ta kuma kayatar faty bata isoba sai ka shegari ranar luncheoun ni naje na tare ta da yaranta sai abdulraheem dake jan mu mun wa juna kyakkyawan runguma cike da farin cikin ganin juna biki yaci gaba yadda aka tsara bikine na yan boko masu ilmi kuma kusoshin nigeria gabadaya bikin da yaba dinbin tarihi a nigeria ke inkin ganmu nida yallabai alokacin baza kice akwai wata jikkakiyyaba a zuciyoyunmu ba tamkar zara da wata don tsabar dacewa da juna haka fuskokinmu inki duba zallar so da kauna zaki gani ga junan mu sai nayi fatan innama haka ne a zahiri ga yallabai? Wasu dumammun hawaye suka zubo min na faki idon kowa nasa hankici na daukesu amma duk da haka yallabai ya gani domin kuwa juyowa yayi kawai ba zato, bayan tun da muka taso yake ignoring hada ido dani abin daya rada mani a cikin kunnuwana ya gigitani,ya kuma kara dugunzuma zuciyata ranar bakin cikin a gareki ko? 68.... niko ranar farin cikin daban taba tsintar kaina a cikiba zubaidah,na dago na dube shi da idanuna da suka kankace,in tambayeshi abinda yake nufi da ranar bakin ciki? sai flashes aka shiga zuba mana a hakan haka masu video suka maido hankulansu a kanmu suna tsammani wata hira ce muke yi mai dadi a tsakanin mu basu san zuciyoyinmu tamkar madaci suke ba duk jijiyoyin jikina sun saki,shin menene makomata a zuciyar abban jawad yanzu? Allah ya isa tsakanina da kai Bello!mun dawo gida ranar asabar ce ina gidan su ashshah muna shiri tawo wa karaye inda daga can ne za'a dauki amarya. tom yazo ya taddamu abakin gate muna shirin shiga motocin da zamu tafi a cikinsu da jaridun punch weekly trust da new nigeria baice komi ba ya mikawa ashshah ,kyawawan fuskokinmu nida yallabai a wurin dinner,a gefe kuma kyakkyawan yaron mune jawad headline na new nigeri cewa yayi INDA YAR RAINO A GIDAN MINISTER TAHEER USMAN TA ASIRCE SHI TARABA SHI DA UWAR DA DANSA DIYAR BALARABE DANGO TA AURE SHI BAYAN TA ASIRCE YARON TARABA SA DA DAN DA UWAR DATA HAIFESHI JAMAA AYI HATTARA DA DAUKAN YAR RAINO..... 69 cikin harshe turanci,sauran shafukan dauke suke da cikakke tarihinas wanda aunty mubina ke fadi da bakinta,yadda tasa akai min wanka aka dirje yalayen hakorana da amosani da kircin kaina ta sayamin sitturu ta dankamin amanar yarota jawad da yadda rana daya taheer ya canza mata saboda ni ta kuma tsinci labarin daurin auran mu a kafafen yada labarai sauran jaridun ma duk kwatankwacin abin da suke dauke dashi kenan da sauran labarun kaskanci da wulankaci a gareni,hajiya hafsi da maman ashshah sukayi murmushi tace kadan daga aikin iyalan dango ashshah ko ashariya ta antayo ta mulmulo ta yarfar a take ta fidda waya ta kira yallabai ta gaya mai duk abinda ya kenan har tana karanto headline din shima ranshi ya baci sosai amma ya taushe ta yace muyi hakuri bai da ikon hana yan jarida buga abin da suka gadama illah zai nemi yahai ya jawa mubina kunne kuma zai tsaida saida jaridar. Ashsha ranta ya baci da wannan shirmammen matakin da yallabai ya dauka don tana gani bai dauki abin da muhimmaci ba, shiko yanayi komine cikin hankali domin ubangidansa ne har gobe,ba zai tozarta duk wani da ya shafi mutuminan balarabe dango ba ta sake danna wayar yayarta mansina dake tare da aminiyarta a lokacin a honolulu tun da akasa ranar bikin zama nigeria ya gagari aunty mubina do haka suka tsirga birni honolulu mansina na cewa hello ashshah nacewa ki gayama kawarki ta sayo jaridar sabuwar nigeria da ragowar data kai musu wani article suka buga taga yadda muji ya dace da mata,mata ta dace da miji ba ladi ba duwaiwai da marsandi ba ta kuma dunga iya bakinta a komi inba haka ba wataran zata yanka wuyanta.ai abin kunya har ya wuce nata? tana (portugalese trained)amma ta kasa rike mijinta tana zaune cikin gadan har idon shi ya afka kan YAR RAINON da take ambato,ina ajinta,ina wayewarta sanda tayi saken da har yaso YAR RAINO to ta nemi fidda yar rainon yayi mata saki wukakanci bayan ya dankara mata dan banza duka kuma 70 ki gaya mata wadda tayi dominta batamawa, mijinta ya tausheta da kalaman kauna.tace ayi mata godiya sabida hoton data kaiwa yan jarida, ya balain birge jamaa har itama ya burge ta,dan ta jawad ko data ke ikirarin anyi asiri an rabasu. bayan a zahiri sakaci da shashancin tane ya rabasu, yace ya gaisheta,wai meyasa bata zo bikin momisa zubaidah da daddyn sa ba?koda yake tuni taba shi amsa da cewa kunya ce ta hana ta zaman kasar ta tattara yanata yanata ta tafi can wata uwa duniya da ba'asan da ita ba balle ayima dariya.gaba daya suka kwashe da dariya banda ni da mamansu,tace ashshah!ta dago ta sakar mata dakuwa tace ungo naki,ba gaba suke da kuba, bana son rashin kunya?tace haba mama,ai kunyar mara kunya asarace .na kifa kaina jikin kujerar bayan motar da nike zaune, na soma kukan da bazan iya fassarawa ba. ban taba facing humiliation kaskanci irin na yau ba.shin auren sunna ya taba zama abin kunya?wata zuciyar tace ba auren bane abin kunya, matsayin wanda na aura ne, haka bello ma ya gayamin,sai naji zuciyata tayi bakikkirin,lokaci guda na tsani auren, na tsani abban jawad din ma kansa na rinka ganin maganganun bello suna dawowa suna warwarewa suna neman zama gaskiya zubaidah da wannan abin kunyar ai da kin baro naki daga nesa,mai kaunar ki da gaskiya tun kina yar sam tsami tsaka tsami.....sai wasu hawaye sharr! Ban sani ba ashe suna diga kafar hajiya hafsi wadda take daura dani,ta kai hannu bisa kafaduna ta rungumoni jikinta tana cewa har bazazzagi ya isa ya girgiza ba kano?har barazana jarida ta isa ta karya miki gwiwa diyata?ai haka take so ta takaitaki to meye abin kunyar a ciki? cewa nake manzon mu mai tsira da aminci yaron nana khadija ne,ta nemi daya aureta sabida gaskiyar shi da amanar shi,kenan kina da qualities da za'a so ki akai wanda har yafi nata ai ke abin tinkaho ne zubaidah ki shiga gidan auren ki da karfin gwiwarki sai nayi murmushi mun isa karaye yamma lis,awal ne ya fara amsa jaridar hannu ashshah ya dubawa [10/23, 5:14 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/23, 5:18 PM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔 ~BOOK 2~ Tuna Baya2 71-80 71. A dakin amarya inna luba ta fizge jaridar tana cewa rangadi, cancadi.atinen goggo ce wannan? kai amma wanda ya dauki hotonan gwani ne na gwanaye dai dai sanda baba ya shigo yaci farar shadda mirror yar ciki da wando da babbar riga fara sol yana ta fara'a suka gaisa da kowa sai auwal yace inna don baki san meke rubuce jiki bane, kyawun hoton kadai kika sani tace to karanto min inji kunne na biyu su dacta hafsi da sauran jama'ata suka mike suka hau sama inda aka yi musu masauki tun fara bikin,maman ashshah na cewa kai auwal da tsurku ka ke,ina ruwan inna da shirmen su?awal ya karanta tiryan tiryan yan fassarawa,tun bai kai karshe ba inna luba tasa kuka.raina ya kara baci basan sanda nima na fashe da kukan ba,cikin rishin kuka tace ai gashi nan tun ba'a je ko ina ba kin jawa kanki abin gori atine,tun farko ai sai da na fada,amma da yake ni tsohuwa ce ba'a mai dani a bakin komi ba ba wanda ya saurareni. yanzu da bello kika aura wa zai ce dake kin yi abin kunya? Ta shura takalmata ta fice.baba ya tashi sadiya daka zaune duk idon ta ya ciko da kwalla.don inda abinda taki jini a duniya shine kuka na,yace ta tafi ta kira mishi sani a falo ya saura daga ni sai shi sai awal da inna mu amarya.ya barni nayi kuka na ya ishe ni na share hawayena yayi gyaran murya yace toh atine nagode Allah da ya nuna min wannan rana mai dinbin tarihi a garumu duka a yau na zauna nayi tunani abubuwa da dama dasuka faru acikin rayuwarmu ta baya data yanzu da bata kare ba.ta kowanne bangare ubangiji ya rufa mana asiri,yasan zuciyata?yasan meyasa na amince ki auri shi wannan bawan Allah,yasan ba kwadayin abin duniya bane ba kuma neman suna ba illah mutunci da karamci da magajin gari yayi mani,ko ince yake kanyi mani wani abune dazan iya mancewa ba haka shima bello.banki goyan bayan dawowar bello ya aure ki dan taheer ya fishi wani abu ko don kaddara da ta afku a baya ba illah komi ni zanyi arayuwa ina baiwa Allah zabi ne sai naji zuciyata tafi son aurenki da taheer 73. fiya da bello,wannan shi ya tabbatar mini cewa taheer shine zabin Allah a garemu baki daya, kuma miji mafi alkhary a gareki,don haka duk ma wani mai yiwa abu fassara ta daban ni na barshi da Allah ya ganar dashi,ba wanda ya isa razanani abisa abinda Allah ya zaba a cikin al'amurana haka kema nake so ki amince a rayuwata bazan taba mance da ranar da nace atika taje wanke wanke dan a samu abida za'a tallafi karatun awal da kannesa da abinda zamu ci abinci ita da uwarta suka tozartani akan idonku. ba kuma zan mance ba a washegarin ranar kika kaho min farau farau a cikin koko,kika ce zaki wanke wanke da atika taki zuwa domin asamu abida za'a kaiwa yar uwarki atika daki,da sukayi kutun kutun din da suka raba ki da bello.awal yayi karatu mun ci abinci mu wadata ke kuma kika kari rayuwarki gaba daya a wahalar wanke wanke inba ki manta ba na gaya miki a lokaci ALBARKA NA TARE DAKE ALBARKAR UWA DA UBA,BAZAKI TABA TABEWABA... yasa hankici ya share hawayen da suka cika masa ido nima kuka nake inka dauke awal da amarya da sukayi tsit suna sauraro baba yaci gaba.toh abisa wannan karamci da kika yi mana atine cikin zuri'armu kaf bamu da kamarki,muka mike domin neman na kanmu kurum don mu gina miki rayuwa.mu sayo miki mutunci a idon mijin duk da kika aura.da farko inasan fada miki cewa karfin aikinki da lafiyarki awal ya samu damar yin karatu har matsayin digree na biyu,sani kuma na farko yana kanyin na biyu,tun tuni awal ya samu aiki yana yi a lagos sani kuma yana yi a cikin garin kano abida baki sani ba shine farko fara aikin ki bawan Allan nan N25000 yake bani duk wata a hannu talatu baiwar gidan maimartaba kudin nan baci nake ba tunda dama ni can inada sana'ata,na kuma saba da talaucina don haka wani rayuwar jin dadi dukkamu bai dame muba, dauka nake inbai wa awal ince yasa a banki in hidimar karatunsa ta tashi su dauka a ciki suyi toh hidimar karatun ma daba kullum take tasowaba kuma daga baya suka zo sun daukan alawus na dalibai 74. dukan su kwana makaranta suke balle ayi wanni zance wahalar kudin mota sai dai abin daza suci, bayan shekara guda kuma bawan Allah nan yazo har nan dakin ya gaidani ya gayami cewa hidimar da kike a gidansa ta karu wai kina girka masa abinci kina kuma kula da yaronsa don haka albashin dayake baki ya ninka shi zai rinka biyan mu N40,000 duk wata ba yadda banyi dashi ba amma ya kafe bazai canza ba,sai na fawwalawa Allah kan cewa aikin naki wata kofa ce ta rahamar Allah a gareni,ya koma biya biyan mu N40,000 duk wata? Kwata kwata cikin kudin nan baifi N10,000nake dauka ba in kashe inyi gararin gabana dashi ragowar kuma naba awal ya kai banki.cikin shekaru hudu kacal kudin da awal ya gayamun sun taru a banki ta tsora tani don ban taba tsammani wai ni mai kalwa zan taba mallakarsu ba,tun daga lokacin nabar saida kalwa akwai wani alh hashim a can ma'aikatar su awal a lagos dan kasuwa ne sosai kuma aboki na jiki ga awal shine ya kawo shawarar mu zuba hannu jari da kudin ciki kasuwanci sai mu ding raba ribar tare,haka akayi bayan shekaru biyu shi kansa ya kara karfi,yace zai ware wa awal jarinsa shi kadai domin lokacin jari mai tsoka sosai muka bude manya shaguna guda biyu a kanti kwari inda sani da awal ke zuwa kwatano suna shigo da shaddoji manya a na sayarwa kuma Allah yasa albarka acikin abin don in ana lissafin manya a dilolin shadda a kasuwar kwari inba ambaci awal na biyu ba za a ambace shi na uku abi yayi karfi da salisu ya gama sakandire sai ya rungimi shagon farko shi kuma rabiu ya rungumi na biyu sani kuma ke fita kwatano shi daya,awal ya rungumi aikinsa shi kadai don haka ayau atine ina mai farin cikin sanar dake cewa muma bamu a layin talakawa muna da kwakkwarar sanaa don cikin mu ba wadda ya kara saida kalwa bayan tafiyar ki,da karfi ki muka sami jari muka gina kanmu don haka awal yace duk ribar damuke da ita a banki taki ce duk abinda ke cikin gidan magaji gari nanan bayan gari inda yace zaki zauna kafin ya kare sabon gininshi na nan abuja 75 nakine mallakin kin kine ko cokali babu nashi aciki duk anyi waje dasu yasan inda yakai abinsa. don haka ki mike kafar ki kiyi iko da komi ayau ba wanda ya isa yayi miki gorin talauci don duk a wannan garin a yanzu ba alfahariba ba wanda zai ce kwadayi yasa na aurarwa da alh taheer ke kina jina?do haka koma mai uwar yaronan zatace dake tace kada ki damu,raino da wanke wanke ai neman halal ne ina neman halal ya taba zama abin kunya? kowa da kika gani aduniya da hanyar cin abincinsa da hanyar arzikinsa toh mu namu shine wanke wanke a yau awal yace in isar da godiyar shi mara iyaka a gareki don bashi da abinda zai saka miki illah duk wata bukata da kike da it a duniyar nan ki tambayeshi ko ta mecece kada ki dogara da abin hannu baban jawad muma muna dashi akwai motoci guda biyu suna nan awaje sani ya saya miki don amfanin kan ki a cikin su zaki tafi gidan ki awal da sani suna gini acan kano gidaje guda uku daya naki ne jere da nasu sai kiyi abinda kika gadama dashi auren mutane irin su mijinki atine sai mace mai juriyar gaske ,kici gaba da juriyar nan dana sanki da ita kisa Allah a gabanki, bayanki, hagunki da damanki a duk abinda zaki gabatar don nema rinjaye akan makiya da mahassada. kada kiji tsoron makiya domin idan baki dasu toh ki binciki imaninki da aiyukanki.kada ki nufi kowa da sharri kiyi komi da zuciya daya rayuwar lami da diyarta ta isheki ishara kingani daga ni har uwarki bamu san hanyar gidan bokaba makaminmu da kowa adduake jikar limami karayece, har kullum ki tuna wannan addua sai dai ki baiwa wasu,duk kuma mai nufi ki da sharri akansa zai ga abunsa kakanki bai rasuba saida yabar miki ayar Allah ki rike ba mutum ba ko aljan atine in har kin rike ayar Allah bai isa da ya cuce kiba.idan tsoron wani abu kike ji ko fargaba, kamin kice komi ayayin da kika hadu da abinnan kice SUBAHANAL MALIKIL KUDDUSI, RABBIL MALAI'TI WAR RUHI, JULLILATIL SAMAWATI WAL ARDHI BIL IZZATI WAL JABARUTI 77. idan wani al'amari ne ya wuyata a gareki maimakon kije gurin boka ya bincika miki ko yayi miki maganin matsalar ki har a kwana arbain ba akarbi sallarkiba,atine zauna a dakinki kiyi ta lazimi QADDARALLAHU WA MA SHA'A FA'ALA zakiga warware war al'amuranki cikin ruwan sanyi da ubangiji mabuwayi ban horeki da komi ba sai wannan atine idan kika ga makiyinki ya doso ki ki rinka maimata IYYAKA NA'ABUDU WA IYYAKA NASTA'IN to koma me ya nufeki dashi kansa zai koma ga wata muhimmiyar madafa da liman yace duk ranar da za a kai ki gidan miji inbaki idan har kika lazimci ce ta atine akan dukkan bukatun ki ba mutum ba ba aljanba,duk wani abin halitta bazai yi nasara akanki ba ban horeki da fallasa rayuwar aurenki ba ga kowa ba uwata ,cikin kowanne hali kika tsinci kanki dauro alwala kiyi sallah rakaa biyu kowacce rakaa ki karanta fatiha daya da wannan ayar kafa bakwai bismillah ASSALAHU AN YAJ AL BAINAKUM WA BAINALLAZINA ADAITUM MIN HUM MAWADDATAN, WALLAHU QADEER WALLAHU GAFURUN RAHEEM X7 bayan sallama kiyi niyya.ki fadi bukatar ki ga lillahi sannan ki kalli gabas ki karanta ayar kafa 7o SAYUHZAMUL JAM'U WA YUWALLUNAD DUBUR da kuma FA'IN TAWALLAU FAQUL HASBIYYALLAHU LAILAH HA ILLAH HUWA ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBUL ARSHIL AZEEM kafa 30 bayan kowace sallar farillah ki lazimci karanta wannan aya ta sama kafa talatin addua ce ta neman biyan bukata kowace iri kuma kariya daga duk wani mai nufinki da sharri.wannan shine kadai gatan da nake jin zan iya miki a duniya atine kefa amarya me zakice?ta mike tana gyara daurin zaninta tace ai duk abinda zance mallam ka riga ka gayamata illa in tunasar dake kiyi biyyaya ga mijinki don samu rahamar Allah cikin rayuwar duniya da lahira kin ganni dai ko musu bai taba hadani da mallam ba don haka ace wai gani ga wane ya isa wanne tsoran allah ta shiga dakinta duk da ban kalleta ba nasan kuka take 78. na rabuwa da ATINE ta akaro na biyu rabuwa ta har abada sai dai ko gani da yawo,hankalina bai kara tashiba sai da naji gudar talatu da sauran bayin gidan maimartaba a tsakar gidan mu tabbacin yan daukar amarya sunzo,sai nabi bayan innana na kankameta ina kuka mai tsuma rai da tada hankalin wanda ake mawa,tace ke bana son sakarci, cikani baba ya tashi ya fice sadiya ma ta kankameni muna tayiwa amarya kuka ina rokanta don Allah kar tabari su sake daukeni .ina tunawa ne da tafiya na wanke wanke inda na fada wata sabuwar rayuwa da ban taba mafarkin tsintar kaina ba,gashi kuma ayau zan tafi rayuwar AURE da ban san menene acikintaba ban ma san hakikanin makomata a zuciyar mijin dana auraba. ni kuka inna kuka yar kanwata sadiya kuka a haka aunty faty da hajiya rabi kanwar fulani (maman bello) da sauran dattijai dangisu da maman ashhsah, hajiya hafsi inna lami suka banbareni daga jikin amarya. talatu ta karkato dai dai kunnuwana tace ayiyirirrrrr! tasake karkace kai ta kuma cewa ayiyirirrrrr!! rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya.uwargijiyata zubaidah tamkar jiya ne nazo na daukeki na kai ki aikatau gidan yallabai ana wulakanta mu, ana kyamar mu, ana kyarar mu, ana toshe hanci amma gashi a yau zan maida ke matsayin matar gidan ina ruwan ubangiji! ta sake rangada gudar ina kuka komi na duniyar nan yayi mun duf a haka muka shiga motocina da awal ya sayamin su faty suka shiga wadanda suka zazzo a cikinsu muka tafi gidan maimartaba aka fara kaini.a falon fulani ayi abinda ake kira amana inda suka ce sun karba da hannu bibbiyu ubangiji Allah ya taya su riko.taba da turare da turmin atamfa super ingila guda biyar da turaruka da kudi naira dubu ishirin shine na sannu da zuwana cikin zuri'arsu daganan sai fadar maimartaba sarki yayi addua yasa mana albarka kana cikin raha yace zubaidah,muna fatan ba zaki mana rowar taheer ba,tamkar bakatafar matarshi? A uwar dakina dake gidan yallabai na bayan gari hajiya hafsi da maman ashshah keta nasihun su na manya 79. cikin hikima tace zubaidah ki jure ki zama matar kwarai don Allah?kar kibari mijinki ya taba bada wata shaidar banza akanki ki zama mace daya tamkar da hudu,ki aje tsoron mubina da komi kiso mijinki,muna muku kyakkyawan fatan alkhary don Allah cikin daran nan ki saki jiki ki dauko min baby,shekara war haka inzo inganki rungume da jaririnki kina bashi nono in koma gyaran haihuwa,ta hakane zan yarda in amimce cewa gyarana yayi aiki sosai,gaba daya aka kwashe da dariya,ban dani dana ke kanainaye cikin mayafin lafaya duk suka tafi suka barni ni da faty da ashshah sai ragowar yan mata na suna ta hirarraki da dararrakinsu,yawanci duk shakiyanci ne suke man faty na tare mun tace in kuyi zuciya wata mai zuwa inga katin auren kowacceku ashshah tace me kike ci na baka na zuba? Allah ba inda zani yau sai nayi cinikin bakin yar Qaraye 80... cinikin kuwa mai karshen tsada sai faty tace dadin abun dai ba yau ya fara aureba,balle atsaya anayi mai yanga sukace ahayye!shine naga dai ana ta bare bare jiki dazuciya da aljihu,duk da an taba auren faty tace ai dan waccan ta tafi ne gaba daya suka sa dariya sai wajajan shabiyun dare abdul raheem ya shigo dauke da mukhlas a kafadunshi taheer ko na tafe da kafafunshi suka gaisa da su ashshah ya mika wa faty yaronta, taheer da sauri ya tafi jikinta wai ummana kinga babarki ta kullemu a daki ko?ba don babanmu yaje ya fito damuba duk suka sake sa dariya tace kai ba babarka bace kenan mukhlas abin ma babu kara yanzu ina jawad?yace ai shi ta fara kullewa don yace shi wajen mominsa za shi amma yanzu ya gama kuka yayi barci nan ma dariya akayi abdulraheem yace aunty faty abbasu mukhlas yace ku fito ku tafi yanzu suna waje tare da yallabai tace au baza su shigo su bamu kudin sayen bakin ba to ba inda zani sai an sallameni abdulraheem ya fita yana dariya tare suka dawo da bello, yallabai na biye dasu abaya kaina arufe yake balle ince ga yanayin da fuskar bello ko na yallabai ke ciki a wannan lokacin,jikina ya shiga tsima ta ko ina dana ji wai bello ke tambayar ashshah nawa zai basu kudin sayen bakin har wannan mai kwadayin faty yawu bakina ya tsinka galau! nana diyar hajiya hafsi da faiza da lola da basu san komiba sune sukace kwata miliyon ya rubuta cheque babu ko musu ya dankawa lola ta cafke ba ko angode,ya dauki danshi dake ta mika mai hannu yasa matar shi a gaba suka tafi tana cewa to zubaidah Allah ya bamu alkhary sai mun shigo miki sallama kenan ta rusuna tayimin rada na harareta duk da wai ance aikin banza harara a duhu tunda kuwa fuskana cikin laffaya take sauran ma ina jin yallabai na cewa oya Allah ya bamu alkhary,abar min mata ta huta hakanan,suna ta dariya suka fice yana take musu baya bello har sun shiga mota ya leko yace da taheer asubah tagari yana murmushi yace you too su ashshah abdulraheem ya maida su gidanmu [10/23, 5:18 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/23, 5:19 PM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔 ~BOOK 2~ Tuna Baya2 81-90 81..... bayan fitar su masu gadi sun rufe gida,ina jin takunshi a lokacin da yake hawa saman bene wannan ya tabbatan min sassashi kenan,wasu dumammun hawaye suka sake shararomin a guje. na mike duk jikina babu lakka,oh ni atine ba mamaki zargi da shakku sun shiga tsakani, wadanda sune tubalin da in har suka ginu a zuciyar ma'aurata rayuwar auren ke rugujewa.to ina zan saki Jiki da mutumin da baka yarda dashi ba?yadace ayau na aje kunya,in aje jin kan namu na 'ya 'ya mata in bayyanawa yallabai hakikanin ko ni wacece?tun da na yarda ma kaina nayi aure ne da zuciya daya,in har kuma ina son rayuwar auren mu ta dore cikin aminci da yarda da juna uwa uba so da kauna ginshikin aure,wadda nasan akansu muka aminta,muka gina rayuwar mu,to akan me rana daya zanyi sake kaidin bello ya ruguza shi? inma banda kaddara wadda ta rigayi fata ni ina kara tuna wani bello balle har inyi tunanin zai zamo matsala a gaba ga rayuwar auren da nayi domin Allah da ingantaccen so da kauna? Wannan tunani tamkar an tsikaramin allura ne na mike zumbur na fada bayi,na shiga warware laffayana,na dibi kaina a madubi,na tabbata duk inda ake son MACE,to tabbas zan amsa wannan sunan,na warware gashin kaina a hankali,ya zubo kafaduna duk wani motsi da nayi ni'imantaccen kamshi ke tashi daga cikin jikina,ni kaina har ban san sunan kamshi turarukan da nake ba na fada kwami na soma wanka irin wanda bantaba yi ba a rayuwata, wanka ne slow - slow tamkar name son canza fata, duk wata gaba a jikin zubaidah a yau wanku, ta fita sumul.na dauro towel wanda iyakacin shi gwiwata,na zauna gaban dressing mirrow na shafe jikina da mai na E45 cream na debo cosmetics din da muka hado a pittsburgh nayi amfani da turarukan escada magnetism da escanda sentiment na cakuda da turaren haute wata jikkakiyar rigar barci na kalar beig da maman ashshah ta taba bani tsaraba umara,ban taba amfani da itaba haka ban taba tunanin akwai ranar da zan iya amfani da ita ba arayuwata saboda rashin kaurinta da kankantar ta,amma a yau ita na dauko,na fesheta da turaren azzaro visit da L instant De guerlain duk sai dakin da wani bala'in ni'imtaccen kamshi mai dadi da sanyaya zuciya toh amma me?saina tsaya stand still na kasa sanyawa,na kasa koda motsi daga jikin stool din da nake zaune,ina rike da riga toh inje ince da abban jawad me?gani nazo?kai zubaidah ina ajinki? 83.... ki tuna yau wata ranace mai matukar muhimmanci da tarihi a gareki ranace da kowace 'ya mace ke tinkaho da ita idan har kika kai kanki shin dame zaki tuna ta da muhimmanci?sai na juya na sake dibar kaina a madubi duk wata sura ta da 'ya mace ke tinkaho da ita,ba wadda ban mallaka ba, nayi tunani idan har yallabai ya iya daya kawar da kai a kaina a wannan ranar da yake kira special day a garesa,me zai hana nima inja ajina? daga can falo na jiyo motsi cikin talatainin dare,ana kokarin murda kofa da karfi duk na gigice a tsammanina ko 'yan fashi ne suka kawo mana ziyarar sannu da zuwa,jin ana murda kofar dakina sai naji hantar cikina ta kada wani farrrr!abinki da cikin dare nayi taga taga nayi luuu,zan fadi amma naji an tareni,na tsinci kaina a wata duniya ta daban rasa ji da ganina lokaci mai tsayi kamin na farfado,na rintse idona da karfi, na bude bayan wani lokaci muka dubi juna,yayi murmushin nashi da ba kowa yake iyawaba yace i'am sorry momin jawad ban zaci idonki biyu ba,na tsorata kiko? Cikin wata murya mai rashin ammo,na dago na dubeshi al'amari da na gani mai GIRMA cikin idonunsa ya bani tsoro he totally need assistance (yana bukatar agaji)ya danna wani abu jikin gadona fitilu koraye suka mamaye gurbin hasken komi ya zama dim baka jin komi sai rugugin hadari dake taruwa a sararin samaniya yana hade da sambatun yallabai wanda bana iya komi acikin al'amuransa masu ban mamaki ne, haka shi kanshi mai ban mamaki ne dana rasa gane inda yasa gaba yace ZUBAIDAHHHH, gayamun sunan turarenki? da murya dana kasa amincewa ta ogana ne, bai sani ba, duk wani weakness(raunina) ya game samun shi, daga can kasan makoshina na Escada magnetism yace umh uhm ba shi kadai bane? Nace sai azzaro visit yace COULD YOU VISIT MY HEART TO SEE HOW PRECIOUS YOU ARE ME 84.... (zaki iya ziyarta zucyata kiga yadda darajar ki yake a gareni?)na girgiz kai domin al'amarin har yaso yafi karfi na nace I WISHED I COULD (nayi fatan ace zan iya )a ka kece da ruwan sama kamar da bakin kwarya ba tahir dinbah ba zubaidah ba kowanne kokari yake ya nunawa dan uwansa ya fishi so da kaunar kansa asubar fari ina jin shi yana waya da fulani wai akai komi da ake na al'ada don zubaidah budurwa ce kunya ta kamani.amma don farin cikin sa shi ko sai murmushi washegari da safe bayin gidan mai martaba suka shiga sauke gara ta abinci da sutturu da kayan kawa na mata iri iri harda saniya guda biyu daga fulani garar su dubulan da alkaki?da nakiya,bakilawa gireba,gasasshen rago guda,nikan dan kunya ban iya hada ido da kowa ba. wannan tonon silili dame yai kama,naji haushi yallabai ya kamani,bayan duk sun tafi duk nasa aje araba sadaka rabi akai gidanmu na shirya cikin wani material navy green da aka yiwa senegalese na feshe jikina da turaren love is all ina tafiyar kasaita na doshi sassan abban jawad fuska daure wai ni a dole fushi nake, tun daga nesa bude min hannuwa babu alamar bacin rai tattare dashi ko kadan babu wannan daddaurewar da tamtakewa da yake yi kwanakin baya face annuri irin nashi a kullum koma ince na yau ya zarce na kullum,wani iron farin cikine a kyakkyawar fuskarshi ke fesarwa,da farko kunya naji,sai kuma na dunkule hannuwana a kirjena,na rage taku.na soma wani irin murmushi yace come on momin jawad abida yace kenan na noke kafada nace umh uhm,nida aka aura ba'a so har ana guduna anamin fuskar shanu ........ya saki wata nauyaryar ajiyar zuciya, kashin bayana ya amsa kadan ya rage bai karyeba a'ah yallabai rashin son har yakai da 'a karyani? oga baya ko sauraro na cikin faffadan kirjin shi har baza ka iya hango zubaidah ba sabidah girman taheer (giant).na lumshe idona kana na budesu gaba daya akanshi ya dago ya dubeni kafin yayi murmushi ya soma magana,ke baki da ganewa wallahi.ke baki san kishi bane ina KISHINKI ZUBAIDAH 86... ya sake maimatawa ina kishinki xubaidah basan kece ATINEN BELLO ba........ Ya hade fuskokinmu duk da maganan yana yintane kasa kasa amma na gode Allah da ya mallakamin ke ya hana shi yaso salwantar min dake zubaidah Allah ya fishi,yaso salwantar min jawad dina dani duka,matar shi da 'ya'yanshi saboda san kai irn nasa Allah zubaidah da kin mutu bazan taba yafewa bello ba.hannuna na kai na toshe mai baki amma sai ya juyoni all over muka fuskanci juna,ya janye hannayena a bakinsa ya cigaba da magana.a lokacin nayi zargin kina son bello,in ba hakaba ya za'ayi ki yarda ku kadaice a mota har ku tafi wani huri ku kadai ba tare da abokan tafiyar kuba,kisan Allah zubaidah a lokacin jinayi na tsaneki,domin na tsani a yaudareni, ban aureki ba bisa tursasawaba sai bisa amincewarki,to don me daga baya zaki ha'inceni?ni kadai nasan masifar son da bello yake miki,amma wallahi zubaida nafi bello sonki,idan baki sani ba in gayamiki na fara sonki ne tun randa na fara ganinki,wato ranar da nace ki goya jawad a gabana,sai dai ban taba sanin kece atinen bello yaso aura ba sai ranar da fulani ta kirani a lokacin da za'a kai ki asibiti,da neman alfarma ta na wai na fasa auren ki na barwa bello kece atinen da bello keso a lokacin ne abubuwan dasuka faru ke ta dawo min sabbi (fresh)na tuna tun zuwan ku walimar ya da ya shirya ya canzamani, haka fatima ke gayami itama duk ya canza mata tunda aka fara bikin mu,ita auren nan ya jawomata annoba ban ji haushin bello ba ko kadan ko ba komi so ke damunshi irin wanda ke damuna? zubaidah a kuruciyata bayi sa'ar aure ba banyi aureba sai dana shekaru talatin baya ban tsinci komi cikinsa ba face bakin ciki da dana sani mai iyaka ,ban taba jin ina son wata 'ya mace ba sai akanki nayi jinyar son nan shekaru dai dai har takwas sanna rana daya ace in fasa aurenki?nida bello cousins ne mahaifiyar shi kanwar mahaifiyata ce tare muka taso tun muna kanana sai karatu ya rabamu bello yasha gayamun irin son da yake miki 87. da kuma kaddarar data fada aurenku,sai a lokacin na tuna komi gashi kun fita tare har kunyi accident ni na zame muku karfe kafa kena bari ku nuna min ku laila da majnun ne,inyaso ni bakin ciki ya kashe ni a lokacin na fita hayyacina na samu fulani nace da ita zan rubuta miki saki sai bello ya aureki tun da na lura kema kina sonshi fulani tace hakan zai zamo rashin adalci a gareki tunda zuciyar bello aka sani ba'asan taki ba amma har in kina son bello zan gane ranar dana shiga dakinki,idan ma ke mayaudariyace in fara tabbatarwa tukuna sabidah zato zunubi ko da gaskiyane.na memi karin haske tace in har ki son bello zaki bashi kanki ko dan ku huce haushin tsohuwar soyyarku damin har dakinta 'yan unguwarku suka je suka gaya mata cewa bello yaje gidan ku ana igobe daurin aure kun shiga dakin awal kun rufe fiye da awa daya a lokacin hankalina ya tashi taji tsoron kar inyi kazamin aure amma bakin alkami ya riga ya bushe an daura auran babban farin cikinta jin cewa ke budurwa ce wannan kadai itace mafitarki itace tayi insisting lallai ayau duk bacin ran da nake ciki in shiga dakinki ingaya mata halin dana tsince ki. ni kaina banso ba amma da nayi tunani mutuncinki a idonta sai na runtse ido na na fadi hakkanan mohd jos yayi min bayanin komi a daren jiya,na kuma gamsu sai dai zubaidah cike nake da zargin kina son tsohon masoyin ki nayi miki katsalanada cikin rayuwa?illah hadin kan da kika bani a daren jiya farat daya ya tabbatarmin ko ba komi ina da wani kankanin matsuguni ko yaya a zuciyarki you know ni har kullum mai baima dan adam hakkinshi ne nayi mamakin yadda daga daren jiya zuwa yau zubaidah kika zamo RUHI na kasa controlling zuciyata wai na rabu dake wa bello.a yau ina alnihin sanar dake cewa nima kama jawad nima taheer BAZAN IYA RAYUWABA BA TARE DA KEBA!na rasa me zance?tausayin yallabai da kaunarshi da na keji a yanzu,wani abu da bazan iya kwatantawa ba ka taba gayamin wani sentimental ogana a sanda nike YAR RAINONKA kace bana ma karya bana ha'intarka. 88.... toh akan me lokaci dana ke hakan ban ha'ince kaba,ban yima karya ba sai yanzu da nake a matsayin MATARKA,kasan ko matsayin ya wuce ayi masa karya da ha'inci ko yaudara gaskiyane ada naso bello so irin na kuriciya da kasan cewar shi daban da sauran samarin kauyanmu,amma wallahi tun ranar da muka rabu ban kara tuna bello da sunan so ba BELEIVE ME OR NOT YOU ARE THE ONLY ONE I LOVE TODAY AND ALWAYS.ka koyar dani yadda zan so ka yallabai tun ina ficicitata,son da har yakan sani kishin aunty mubina in kuma ji zafi in naga tana yi maka abubuwa mara dadi,in kuma yiwa kaina samun miji kwatankwacika ko mai irin hallayar ka,na duba na tace duk ban gani ba TAHEER wannan ya tabbatarmin lallai ni mai sa'ace dana samu miji kaman yallabai kulawarka da nuna kyautayi a gareni ya dasa wani gyambo cikin gudar tsokar zuciyta wanda yayi ta ruruwa har zuwa dare jiya dana mallaki TAHEER to akan me zan daga ido in dibi wani da namiji a duniya da sunan so ?babu kowanne namiji fanko ne nake ganinsa in na kotantashi da ogana bana jin kona rasa TAHEER zan kuma son wani bayan wannan ingantaccen son da nikewa ogana...... THEN SHOW ME IN ANOTHE WAY(nuna mun ta wata hanyar daban) muka rankaya ga dakin barcinmu,cikin wata irin soyyaya da harshe bazai iya bayyanawa ba wannan kadai ya isar wa yallabai yarda da ya gama mallakar komi na zubaidah to sati guda daga ni har yallabai bamu da lokacin komi bamuda lokacin kowa face na nunawa juna zallar kauna nayi mamakin yadda aunty mubina ta iya barin baban jawad, kasancewarshi irin maxan da ake kira one in million irinsu ne in suna son mace sukan nuna mata basu da komi mafi ,muhimmmanci fiye da ita koda yake gaskiya ne da ake cewa wasu mata sun rako wasu duniya, inban da haka ni ina har zan iya yiwa yallabai laifin da za ya dakeni balle har ta kai ga saki?bana jin ko yankar tsokar jikina zai rinkayi kullum bazan ji ciwo ba balle har takai ga musayar yawu (so kenan)sai yanzu ne na yarda da maganar fatima na 90. Fatima nace wa wai idan na fara rayuwa mai kyau da yallabai,ko kuda bazan so ya rabe mu ba, yo ni ko sauro zan so ya rabi wannan sabuwar rayuwa da muke a yanzu?ina! kullum daga gidan maimartaba ake kawo abinci safe da rana da dare,baki masu ganin daki basu barina hutawa tun safe har dare danginane ko na yallabai. haka masu neman taimako da yallabai ya saba duk zuwansa garin shima basu kyaleshi ba a kullum zai fita fadar maimartaba yayi gaisuwa a zauna tare da shi har karfe biyun rana ya dawo yaci abinci ya huta zuwa karfe hudu ya fita falon daya tanada musamman dan ganawa da al'ummar karaye yayi tajin koken su har magariba, sai sun yi sallar isha'i tare a masallaci dake cikin gidanmu sannan ya dawo gida shikenan kuma sai Allah ya kaimu gobe,dukkan tsayin daren da wayewarsa na zubaidah ne. Su ashshah da mamanta da hajiya hafsi sun zo yimin sallama da cewa za su koma abuja mu wuni hira tsokana kam na shata wurin ashshah har na koshi tace gaba daya na canza,nayi jazur nayi bul bul sai sheki nake kamar dafaffen kwan da aka aka bare daga gidanshi shi kuma yallabai tace eh to, although (duk da) yayi duhu sabida karywar kashin amarya kugun amarya,yet da ganinshi ya samu kwanciyar hankali dabe taba samuba sai wani kara zama (fresh)yake kamar ba tsohon gwauroba ashsha shakiyyar duniya mamanta da hajiya hafsi dariya suke khadija diyar hafsi kadai take tare min su kuwa sai kwasar dariya suke nayi musu godiya mai tarin yawa abisa kaunar da suka nuna mani wadda ko yan uwana da muke ciki daya sai hakan.da alqawarin har gida zanbi kowacce su in mata bangajiya.sun bar karaye ba don sun so ba sabida karimcin irin na al'ummar ta da kasaitacciyar masarauta ta mai girmama bako da karramashi washegari aka dauke su zuwa abuja inda kowacce su zata nemi inda ta fito ni kuma na cigaba da amsar baki duk kuma wacce zata tafi da turmin atamfa ingila mai dauke da hoton mu nida yallabai zata tafi da bokiti cike da alkaki da nakiya bakilawa da dubulan [10/23, 5:20 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [10/23, 5:21 PM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔 ~BOOK 2~ Tuna Baya2 91-100 91. cikin bokiti cikin dan lokaci mun saba da daukacin dangin yallabai maza da mata musamman abdulraheem dan autan dakinsu jinin mu yafi gamuwa kwarai kusan kullum suna gidana suna min hira da tayani hidimar baki kullum sai yallabai yace wai baba na gaishe ni nayi nayi baba yazo yaki har wasika na rubuta na aikawa awal ya karanta mishi ina rokan shi dan Allah dan annabi yazo inganshi sai yace wai bani da hankali daga kaini gidan mijin kuma sai ya sawo takalmi ya biyo ni .duka jama'ar gidanmu ba wanda bai zo ba masamman sadiya dake ajin karshe a primary sadiya na sona sosai haka nima duk kannena jininmu yafi haduwa,ta kan zauna mu wuni tana bani labarai duk da kasancewar ta mara son magana amma in da nine kyaji bakin sadiya har zaure wajen karfe sha biyun rana fatima ta shigo biye da ita yarantane,sanyetake cikin makubar abaya kirar oman ta yane kanta da gyalen abayar kamar balarabiya,na kauda kai nace fushi nake maman mukhlas tace Allah ya huci ranki maman jawad tun tuni naso in shigo babansu mukhlas ne ya hanani wai in barku ku gama amarcin ku kar in dameki da surutuna, yanzu ma sallama nazo miki,gobe In Allah ya kaimu zamu tashi zuwa inda muka fi wayau mun sha hirar bankwana da fatima saida zata tafi ne ta fiddo katina na taya murnar aure tace inji bello, mun rabu cike da kewar juna,cikin katinan da ta kawo karamin ciki kadai bude na kone su duka a kitchen ga abida ke rubuce.............MR&MRS KARAYE THE RAYS OF THE SUN AT DOWN SIGNIFIES THE COMING OF A NEW DAY.MAY THIS MOMENT SIGNIFY THE BEGINNING OF A SERIES OF NEW BLESSINGS EXCLUSIVELY FOR YOU HEARTIEST CONGRATULATIONSMR AND MRS L. CONEL BELLO waxiry kamar kullum yau ma naji tausayin bello na alqawartama raina sanya shi a cikin addu'o'ina na fatan alkhari a rayuwa ga yan uwana musulmi na kone katin na kama harkar gabana 93. satin mu biyu kenan cif da aure komi na tafiya dai dai ta fanni na da yallabai,ranar da muka cika sati biyu da kwana biyu yallabai yace inshiga sallama gidanmu don jibi zamu koma abuja.nace har wajen fulani zan shiga in gaisheta in kuma dauko jawad don tare zamu koma na lura yaji dadin hakan amma sai yace jawad bazai tafi tare da muba.nace don me? ya daura hannusa bisa lebbanshi yace "c'mmmon maman jawad tun can bakya mun musu why now? ban son musu ya soma shiga tsakaninmu tun yanzu kingane? Ina mana shirye shiryen tafiya wellington da rio de jeneiro ne haney moon kama yadda na alqawarta tuntuni,kin mantane?so nike in mai dake hatsabibiya yadda nake so wannan amarcin bai ishe niba,kenan jawad zai takura abbanshi?na bude baki zan yi magana,ya kammala rufe duk abinda nayi niyyar zan fadi cikin launin soyayyar shi mai ratsa zuciya da bargo.sai muka koma cin karen mu babu babbaka.har nike tambayar kai na shin ni ko taheer wa yafi son wani? Ban sani ba. Nakira abdulraheem da yamma awaya nace don Allah duk yadda zai yi ya nemo min kayan ciki rago a gyare,zuma farar saka babban gongoni zaitun guda biyar da turaren bakhour shima biyar ya hado min kudin zanbiya, karfe takwas nayi ya kawo min duk abinda na lissafo mishi ya gayamin kudin duka naira dubu biyar na bashi washegari da sassafe na dau kayan cikin daga deep freezer nayi kitchen nasa apron na kunna cooker na tada lafiyayyen farfesun anta, koda, huhu, tumbi, saifa da sauransu nan da nan na kammala na juye a cikin kyakkyawan warmer sabo ful na koma daki na hada yan abinda nake bukata tafiya dasu cikin akwati ukku abdulraheem ya fiddasu yasa acikin boot din mota. 94.... Zuwa shadaya nayi wanka na shirya cikin atamfa super holland mai kalar ruwan bula mayafi da fararen jaka da takalmi yan china ina janyo kofa zan fito abdulraheem na shigowa yana tami tsiyar wai kamshin farfesun surukar har kasan bene ya karbi katuwar jakar leda dake hannuna ya shiga kitchen ya dauko filas din da alamun jin dadi tattare dashi Yace yallabai yace mu fara zuwa can cikin gida (gidansu) dama shi tun sassafe ya fita donya samu maimartaba suyi sallama kamin ya shiga fada shike driving din mu cikin karama prelude dinshi da yallabai ya saya mishi daya fara karatun jamia gidan maimartaba sarkin karaye babbane sosai mai rassa daban daban har bazan iya fasaltawaba muna ta wuce soraye bayi na tsugunawa suna gaidamu sai acan kuryar gida muka tadda kayataccen sassan uwargida fulani falo uku muka wuce kamin mu tadda ita tana kishingide bisa tuntu wanda akasari a yanzu anfi samunsa a gidan sarauta Koko gidan manya masu hannu da shuni kyakkyawar dattijiya da alamu wayewa ainun cikin fararen idanunta cikin 'ya'yanta kaf babu wadda ya debota sak kaman yallabai.a tare muka yi sallama sai ta amsa cike da murmushi tace oyoyo da zubaidah ta mike ta kamo hannuna ta zaunar dani a gefen damanta. muka hada ido da yallabai dake can gefe kwance cikin kujera three seater yana faman lallatsa waya muka yiwa juna lallausan murmushi kuma atake kunya da nauyin fulani suka taru suka lullubeni. 95.... Daga can daki jawad ya fito yana mutstsikar ido da alama yaji ana ambatar suna mai kamar ZUBAIDAH ne,to ashe dai MOMIN ce da gaske.. da gudu ya karaso muka yiwa juna tsatstsaurar runguma kamin ya fara kukan,can kuma ya sake rungumeni ya daga rigata ya tura kansa tamkar mai gudun kar na sake gudu na barshi a karo na biyu.daga fulani, yallabai abdulraheem kallon mu suke cike da sha'awa muka gaisa da fulani a mutunce ina cike da tsananin jin kunya ita ko babu ruwanta labaru ta shiga bani na rigimar jawad domin rashina tace shikenan sai ku tarkata ku tafi nima kunnuwana su huta haba! Yaro kamar dan jar fata shi baza ayi masa fada yaji ba sai sokanci yayi ta naushe 'ya'yan jamaa mutane basu jiba basu gani ba ina na taba ganin irin wannan jarababben maigida? gaba daya mukayi murmushi jawad daga cikin rigata yace bake ce kike kulleni a daki ba kina sawa suna min gwalo tace an kulle ka din ai sai kabi uwarka can inda baza kullekaba a daki ba amma ni nan kullum kulle da kwado don bazan iya masifarkaba? Abdulraheem ya tuntsire da dariya niko murna tamka in rungume fulani jin jawad dina zai tafi tare damu don nima ko ina nake hankalina baya kwanciya ba tare da shiba,ni kadai na iyawa da rayuwar jawad ni kadai nasan likes anda dislikes din shi,kenan ni nafi kowa iya zama dashi ni nafi kowa sonsa .amma sai naji yallabai yace a ah wannan auren naku na zobe ne fulani jawad ya sake ruban yashi da igiyoyi tara ba inda zashi na fada miki na dauki hutun shekara har na wata uku (annual leave) 96 Zami tafi Brazil nida Zubaidah, don haka can gidan ba mai kula da shi sai su Tom. Kafin hak ma Jawad ya dawo Qaraye kenan, Makarantar Primary Abdulrahim zai Kaishi gobe...' Na kai hannu na dafe kirjina da karfi daya fara bada wata irin karar razana, dam dam dam, na daga ido na dibi Abban Jawad ammn shi din yaki mu hada ido, idanunshi na bisa wayar shi ko ajikinsa, banga abinda ya dame shi ba. Sai na dauka wasa yake, irinnishadin nan daya kanyi na tsokanata lokaci-lokaci. Fulani tace anya! Jawad zai iya rayuwa cikin yaran karkarar nan? Ya dubeta da dukkan idanuwa yace "nidin ina nayi primary? Abinda na ke so kenan Jawad ya koyi rayuwa cikin kauyen shi KARAYE, ya tashi da dabi'u irin nawa naa kauyen shi KARAYE, bana son wadannan dabi'un nasa, inason ya san me nene talaka? Ba abun kyama bane, dashi da su daya suke. Jin dadin da yake ciki da gatan da yake samu yayi yawa, 'he has no experience far life', komi yake so yana samu, komi yace ana yi masa wannan ba TAHEER bane. Don haka zai zauna a nan gobe a kaishi makaranta yana so ko bayaso, zamu dinga zuwa ganin shi akai-akai, kana jina ko Jawad?" Jawad ya fashe da kuka mai tsima rai, ya san Babansa a kullum yana nufin abinda yake cewa ne balle in ya hada da Fulani, baya maganar wasa tare da ita yace "don Allah momina kar ki bari Daddy yayi mun haka, Allah bazan sake naushin yara ba, bazan sake kinji ba, bazan sake dukan kowa ba, zanci abincin ki da masar ki Fulani na daina cewa ki sai mun icecream...Uncle Abdul na daina cewa ka sayo min pizza...." Nima tuni hawaye sun kwararo sharrr! na sunkuyar da kaina ina sharewa. Na sake rungume Jawad dina, na kasa furta ko kalma daya miyan bakina sun kafe kat da al'amaran Oga na. Komi nashi daban dana sauran mutane, wai shi wane irin mutun ne? Inda duk aka tsammaceshi ba'aa nan yake ba. Kenan rashin fahimta irin wannan da banbancin ra'ayi, shine abinda tabarbarar da rayuwar aurenshi da matarshi? Kenan ni a komi ya dace in fahince sa, in mara mishi baya mu zamanto masu ra'ayi daya, sha'awa daya, tunani daya da akida daya in har ina son inganta raayuwar aurena tunda na amince ma zuciyata INA SON TAHEER!! Kenan ya zama dole inso duk abinda yake so? 97... Sai na kai habar mayafina da sauri na share hawayena. Duk sonda nike wa Jawad yayi wanda mahaifinshi day haifeshi ke mashi? Abdulraheem ya matso da ledaa da flask ya matsa ya aje gaban Fulani, yace "Fulani Zubaidah ta kawo maki na neman Albarka" sai ta maido da dubanta gareni, tayi murmushi cikin jin dadi, ta bude leda sannan filas, wani bala'in kamshi ya kauraye dakin bakidaya, tasa hannu ta tsamo tsokar tumbi ta lankwanma ta taune ta hadiye, ta dafa kafaduna tace "waya gayamaki abinda nake so diyata? Nagode Allah Yayi maku albarka", sai a wannan lokacin yallabai ya maida waya aljihu, ya juyo ya dubeni, ya dubi kayan dake zube gaban Fulani wanda shi din da muka kwana muka tashi tare bai san dasu ba, kana Fulani dake rike da kafaduna tana ta zuba min albarka, ya maida kai wani gefen daban. Son Zubaidah da darajarta ya karu a yau ninkin-ba-ninkin wanda yake mata, domin wani abu ne da bai taba ji ranar da Fulani ta budi baki ta sawa Mubina ba, to yaushe ma tazo garin? Zai iya lissafawa kwata-kwata cikin shekarun su na aure sau biyu kacal ta taba zuwa karaye. Sanda ya kawo ta su ganta kamin suyi aure da lokacin da suka dawo daga 'honny-moon' a Toronto wato bayan auren. Bayan wannan baisan wani ba, don ita aikinta da abin da ke gabantashine kawai mai muhimmanci. Ta kuma fada ta kara ita shi ta aura ba yan uwansa ba balle a takurata. Fulani bata kai mishi kararta, haka bata kusheta. Abinda takan ce da yayanta kawai shine Taheer yana aure, amma basu ga alama ba, don Mubina ba mata bace. Matar da bazata rungumi miji da iyayensa ba matar aure bace, ba kuma goyon mutunci bace. Shima wannan a bakin Bello yajishi amma shi bata taba taranshi ta gaya mishi hakan ba. Yanzu kam yasan yayi aure wanda ya wanke bakin cikin zuciyarta na shekara da shekaru akan matar sa. Saidai zuciyarsa nace dashi wai Zubaidah ma kamar Mubina zasu dunga samun banbancin ra'ayi, akan abinda yayi bisa gaskiyar shi da kyawawan akidun shi, shine har zata bata ranta a gaban kowa don yace abar Jawad a karaye tana zubda hawaye har ta fishi son Jawad? Yana tsoron kar wannan ya kawo masu matsala cikin rayuwar aurensu mai nagarta da suka soma shinfidawa, yayi zoton Zubaidah zata zam mai ra'ayi irin nasa, mai son duk abinda yake so to amma why zata soma karkacewa tun yanzu? Wani sabon bacin rai ya baiyana a kyakkyawar fuskar shi. Na langabar da kai abin tausayi, zuciyata tayi bakikkirin, ga zatona abinda nayi wa mahaifiyarsa shine ya bata mashi rai haka. Shin abun kirki ya taba zama abin tsiya? Wasu hawayen suka shinfido min a guje, nasa bayan hannuna na share. Fulani tace ciki sausasawa "Zubaidah daina kuka, don Allah, na maki alqawarin zan kula da Jawad kamar yadda kike kula dashi, kiso duk abinda mijinki ke so, ki zama mai biyayya ga umurnin shi. 98.... Ki zama baiwar shi sai shima ya zama bawan ki, ki kula da mijinki sai kiga farin ciki kema". Ta dade tana mun nasiha mai ratsa zuciya duk akan zaman aure, da yake su yallabai sun fita tuntuni. Nayi mata alkawarin zan kula da dauk abinda tace, na kuma gaya mata kukan da nake bana hukuncin da uban ya yanke akan Dan sa bane, kukan SABO ne. Na saba da Jawad fiye da kowa a rayuwata. Hakika zanyi kewar sa amma tunda haka Baban ke so shikenan. Tace "yauwa, haka nake son ki Zubaidah". Duk dakunan sauran matan maimartaba Abdulraheem ya raka ni, kowacce da irin abin kirkin ta da kullin alherin ta cikin leda. Kai ni dai yau na tabbata na shigo cikin zuri'an da ake sona, aka kuma san mutuncin dan adam. Fulani ce da kanta ta rakani turakar maimartaba na gaisheshi yasa min albarka yayi min addu'a mai yawa. Nasa hannun cikin jakata na fiddo guzuri na da ko yallabai bai san don wa na saya ba a Pittsburgh, wato collection na turarukan GIVENCHY, VERSACE, DIOR da BOSS INTENSE. Maimartaba sai yayi ta samin albarka yace "Zubaidah, ina nan ina jiranki shekara mai zuwa war haka ki kawon aboki ko sabuwar amarya don kin ga Fulani na ta tsufa". Abdulraheem yayi ta dariya niko sai na sake sunne kai cikin gyalena cike da kunya. A gidan mu, yallabai na dakin Baba niko ina tare da Inna na Amarya, muna hirar mu ta yaushe gamo, tana kara jaddada mun Muhimmancin addu'a cikin kawanne hali musamman cikin hali na farin ciki ba sai al'amara sun cakude cikin rayuwarka ba. Tace idan uwar Jawad ta dawo dakinta in bata girmanta, tunda ko ba komi TA HAIFI DAN DAYA ZAMO SILAR DUK WANI MATSAYI DANA TAKA A RAYUWA. Sani na kano, Auwal na lagos haka Salisu da Rabi'u duk suna can gidan Awal na kano tunda su suke kula da shago. Gidan sai jafaru na dake aji biyun karshe a sekandire sai yar autar Amarya Sadiya. Duk kudin da ke jakata na zubewa Amarya a gadonta, na mika hannu na ciro dankunnen dake kunnena na farin zinare hade da sarkar sa suma na zube mata. Na sabule duka zabban diamond dake yatsuna guda uku na zura mata cikin yatsunta tana ta mita tanata korafi wai me zatayi da su? Bata sani ba, yadda nake kaunar ta da zan iya cire raina in bata domin farin cikin ta ba abinda zai hana ni yin hakan. Ina son Inna na fiye da komi a rayuwata. Nace "kudi ki kashe, ki ci kaji kisha madara kiyi bulbul. Kayan ado ki daura kiyi sheki kiyiwa Baba yanga abun ki" Tayi murmushi tace Atine kina neman ki maidani kawar ki karfi da yaji, watakila kina mantawa ni ba GOGGON ki bace. Nace Allah sarki! Inama tana nan!! Da saita fiki yin sheki Amarya in har ina raye. Allah ya jikanta da rahma. Ya sanyaya makwancin ta. Na shiga bayin inna don rage mara na tadda bayan gidan sillubebe da shi fari kal ya sha tile. Ga masan tangaran yallabai ya ciki mani buri na ya gina ma inna na. Hawayen dadi ya zubo min ina shiwa masoyin kwarai Albarka. 99.... Haka Inna Lami na bata naira dubu biyar, na bada dubu uku hannun sadiya nace ta kaiwa Atika da wasu zannuwana da yawa ko daurawa ban yi ba, duk cikin lefena ne amma an diddinka. Shima Yallabai haka ya cikasu da kudi suna ta mitar tasu ta wahalar yayi yawa ya fice shi da Abdulraheem. Tare da shi aka raka mu filin jirgin Mal. Aminu, inda muka hawo jirgi mai zuwa Abuja. To kema dai kin san rabuwar tawa da Jawad dole ta zamo very emotional don da karfin tuwo aka bambare Jawad daga jikina yana kuka yana tirjiya. Maimartaba ya rungumeshi yana lallashi. Ban iya na ko juyo ba domin na kasa controlling hawayen idona. To haka har muka sauka a Abuja nida Yallabai ba kalmar data hada mu, kowanne tunaninshi dabam ne dana dan uwansa. Jami'ar da suka zo taryenmu abin ba'a magana. Ga dai Maman Ashshah na hanga a ciki, sai ko ministoci abokan Oga cikin su har da kwamishina Ibrahim Hardo (Baban Ashshah) da ma'aikatan Ministry of Foreign Affairs. Ban san wane irin matsayi Asshah ta bani ba a zuciyarta sabida yadda take daukar abubuwana da muhimmanci, gaba daya iyayenta sukutum ta turo su taryeni a madadinta domin a lokacin ita tana saudiyyah aikin umrah, don haka nima har gobe bani da aminiya tamkar ta. A gefe surukin yallabai ne General Balarabe Dango da babban danshi Yahai, na lura Yallabai ya ji dadin hakan. Motar Yahai muka shigo (Jaguar) da bata fi goma ba kwata-kwata a cikin Abuja gabadaya, yana gabatar mun da ko Yahai wanene kawai sai naji raina ba dadi. Yace yana mana murnar aure, amma baijidadi ba da ban gayyaceshi bikin auren mu ba sai a talbijin ya ji, ko bansan shi da Taheer Hassan ne da Hussainin shi ba? Nace yayi hakuri abin ne yazo cikin gaggawa kuma bani ya dace ya tuhuma ba Hassan din shi ne dan ni dai ban san shi ba. Yace to kai Hassan me nayi maka kake kin gayyana? Ya kyabe baki yace bana son sanya kaina cikin bala'in ku, ko yanzu ban san yadda akayi kayi tunanin zuwa taryena ba. Yadda ka ki fahimtana akan al'amarin nan Yahai banyi tsammani ba. A zatona ba Mubina ta hada mu ba amma ya zamto ita ta rabamu? Ka zauna mata suna zuga ka suna gaya maka karya da gaskiya ka hau kai ka zamar da kanka involved cikin al'amuran yara da haukan Mubina.ka bani mamaki!" yahai ya shafi keyarsa yana murmushi yace "nima daga baya ne nayi tunani na gane ban kyauta ba, tunda ko Baba ita ya baiwa laifi ammam yanzu komi ya wuce. Zubaidah Mubina na maki barka da zuwa cikin Abuja a karo na biyu, matsayin MATAR minister TAHEER USMAN KARAYE. So let the bygone be bygone, ba da jimawa ba in Allah ya yarda Mubina zata dawo dakinta". Ji nayi zuciyata ta narke, wani kululu ya zo ya tokaremin a kahon zucci, (kaji mulkin mallaka irin na Atine). Shiko yallabai na lura wayarsa kawai yake ba tare da kulawa da hirar mu ba, to amman sai wata zuciyar tace dani "ai fushin fari ba naki bane Zubaidah, tunda kin san ko ba dade ko bajima daman hakan zata faru. Tun a ranar da Taheer yasa kafa a gidan ku da sunan neman auren ki, kin ji da kunnen ki yace matarshi zata dawo. Ta dawo din mana? Ance da ita da da yanzu daya ne? Kowa tasa ta fishshe shi. 100.... Maimakon inga an nemi hanyar unguwarmu Minister's hill sai naga yahai ya dauke kan motar zuwa tsararrar anguwar asokoro. Yay doguwar tafiya a ciki kamin ya tsaya a wani sabon bungalow tsararre ginin kasar Canada tamkar an dauko ginin ne kacoka, dinsa an aza a wurin, kalar fentin gidan ruwan kasa ne mai haske daga waje da aka ratsa da ruwan madara daga ciki. Akwai balcony a harabar gidan irin gidajen nan ne na turawan yamma (western Europe) da ake kira super lux-finishing hawa 2 amma a idonka daga waje kamar hawa daya ne. Wannan ya tabbatar mun sabon gida yallabai ya gina saboda ni a cewarsa bai dace in yi rayuwar aure a gidan da nai rayuwar RAINO,wanke wanke da shara ba. Tom ne ya fara fitowa a guje sannan Ejiro kana Peter suna ta tsallen murna da rawarsu ta inyamurai tamkar wasu kananan yara. Ragowar motocin dasu ka yo rakiya duk yallabai ya koma yana sallama dasu da alqawarin zuwa masu ban gajiya, shima yahai komawa yay yana mun ala huta gajia kawai sai naji dan uwan anti mubina ya burgeni nima nace ya gaisheta. Muka doshi katafaren gidanmu wanda reception wato falon saukar baki zaka fara taraswa sannan kafar bene dama da hagu da zasu sada ka da wasu falullukan guda uku da dakunan barci suma uku,da toilet cikin kowanne dakin barci daya. Daya bayan gidanne aka yi baskwata domin masu aikin gida da wani katon kicin din a kasa wanda Tom ke girki a ciki domin baki. Ejiro ne ya farga bai ga jawad ba tuni ya ja birki yace ina master jawad? Idona ya cicciko na fada musu kome kenan, tuni murnar su ta burma ciki,peter yace wuh! Oga kenan,AREWA!! I luv dat i adores ol his doing,wato yana son hakan yana son yadda ogansa ke tafi da tsarin rayuwarshi. Ban shiga ba saida na karanta addu'oi masu yawa domin neman dukkan alkhairan dake cikin gidan aurena da neman tsari daga sharrikan dake cikinsa. A tsakar falon kasa tom yace'a yau bbu zancen TINE kin koma MADAME din mu. Na sha gaya maki ko a cikin yara ke ta daban ce. Madame ina mai farincikin shaida maki cewa u're among d luckiest tunda har kika yi sa'ar auren oganmu. Sabida haka ki godewa Allahnki,domin ba ko wadanne mazaje ne irin oga na ba/ na lumshe ido a hankali nay murmushi kana na bude ina mai gasgata kowacce kalma a cikin zancensa. 'Muna muku fatan alherin aure. Nace 'nagode. Kowannensu ya kama gabansa. [10/23, 5:21 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [11/3, 8:33 AM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔 ~BOOK 2~ Tuna Baya2 101-105 101... Yallabai bai sami kansa ba sai karfe goma na dare. Nay kwalliya cikin leshi cotton mara nauyi ruwan bula mai karamin dinki nay amfani da fashion ear rings din honey drops na hade gashi na wuri guda na matse da ruwan bular ribbon mai laushi na fesa mishi turaren Dolce&Gabbana ina murza daurin kai,yallabai ya shigo cikin ruwan bulan pyjamas masu santsi abin namu kamar hadin baki amma is just a coincedence, kanshi na digar ruwa,ni'imantaccen kamshin bathrobb dinshi na dunhill ya kauraye ilahirin dakin wannan ya tabbatar mun fitowar shi kenan daga wanka. Ya amshi dankwalin ya murza mun aka yadda yaga dama ya juyar dani ga madubi na yace diba ki ga na fiki iya dauri. Ni kaina nasan daurin yay kyau dani sosai amma bance komi ba zuciyana a jagule take haka fuskana babu walwala. Nakejin abunda ya dakatar dashi kenan. Ya kunna fitila mai haske muka dubi juna ni ce na fara kawas da kai na koma can gefe na jingina da bango. Jikinsa yay sanyi ya zauna gefen gadon ya dafe kai yace'yau zubaidah ke juyawa mijinta baya? Na girgiza kai da sauri nace har abada bana fatan Allah Ya nuna min ranar da hakan zata kasance. Ya dago idanunshi jazur da bacin rai yace ashe ni ban isa inyi yadda naga dama da jawad ba? Bansan abu mai kyau a gareshi ba? Na lura shi fahimtar da yay min ma daban ce sai na zube akan gwiwoyina muryata a sanyaye nace Allah ba abunda ya bata mun rai kenan ba taheer. Ya dago ya dubeni da kyawawan idanunshi yace'ba kya mun karya ba kya ha'inta na tuntuni don haka tell me ko wani ne shine zaki huce a kaina? Na sunkuyar da kai to in ce ma? Raina yay bakikirin da jin cewa anti zata dawo cikin rayuwata kwanannan? Anya bazai ga wautana ba,ita da gidanta? To amma bazan taba yi mishi karya ba bazan taba ba in Allah Ya yarda har karshen rayuwata. Mukai facing juna 'umh tell me,ke nake sauraro zubaidah? Na kama in ina cikin rashin sanin takamaiman abun cewa nace'uh uh ni dai raina ne kawai ba dadi. Yace'akan me momyn jawad? Komi yana da dalili ki gayamin don bacin ranki azaba ne agareni. Ki tuna na sha gaya maki ke RUHI nace,ko so kike in miki kuka. Da sauri na girgiza kai a mamakance,a dimauce. Wannan oga na nefa da a yanzu darajarshi ta ninku ta zama ta miji agareni. Wanda aljannahta ke karkashin diga digansa mutumin dana ke ganin girma da kimarsa fiye da na kowa a duniya inka dauke iyaye na. Idan na bari yay kuka a domina(wanda na tabbata ya fadi ne baka da zuci,tunda shi baya fadan abunda ba haka yake a zuciyarsa ba,wai don ya burge ko ya farantawa wani,ai nayi asara! Na durkusa gabansa a gaggauce na saki fuska nace ni dai dama rokon alfarmarka nakeso inyi baban jawad. Don Allah idan anti ta dawo kada ka canza min daga yadda muke idan hakan ta faru bansan irin halin da zan shiga ba. Domin jin son ka nake har cikin kashi da bargo har bansan yadda zan fassara ba. Sai nake tunanin yanzu itama anti haka kakesonta shiyasa ta ke son ka. Duk soyyr nan da kake mun in ta dawo itama haka zaka ke sonta. Ka tafi wurinta ni kuma abar ni ni kadai watakila ma har ka manta dani. Kuma kaga anti ta fini girma ta kuma haifi jawad don haka zaka fi sonta ni kuma ka canza mun? Nay mai kirrr da ido yallabai ya saki kunnuwa yana saurarona yana gyada kai kamar kadangare tunda na fara bai katseni ba yana murmushi har na dasa aya. Yace' hakane abun? To shine ni za'a kwareni? nima ina rokonki ko antin ta dawo idan ranki ba dadin ko zaki huce a kaina to bata wannan hanyar ba zubaidah. Inason jikin ki da zuciyar ki na a tare. Ki dage kema ki haifo jawad na biyu sai kuyi girma daya da antin taki nema in so ki tunda kin ce bana sonki! To bude zuciyarka da idanunki yanzunnan in nuna maki SO da KAUNAR da ban taba nunawa kowacce 'ya mace ba...... 102 Ya mika hannu yay musu dim lyt a zuciyarsa yana ta kakabin abun wai 'yar zubaidah tun yanzun ta san menene KISHI a shekarunta da wayonta da yake rainawa bai zaci haka nan kusa ba. Ba shakka yana tsoronta a nan gaba in haka ne yana da sauran aiki kenan amma gaskiya a yau yayi mamakin da bai taba yi a kanta ba. To sai muka bude sabon shafin amarci a abujar ma. A kwanakin da suka biyo baya yallabai bai sa komi a gabansa ba sai ZUBAIDAH da shirye shiryen tafiyar mu honey moon kasar BRAZIL. Karfe shida na yamma yana kwance cikin rest chair dake main falonshi yana sauraron labaran CNN daga tauraron dan adam a yayin da ni nake gefe ina mai matsar kafafu ya rufe ido ya bude ya janyoni gaba daya muka fuskanci juna. Yasa hannu ya ja karan hancina yace'wa ya koya miki tausa mai dadi haka? Zubaidah halayenki da dabi'un ki na burgeni. Ke kadai kin isheni rayuwar duniyar har ta lahirar baki daya. Ina son tausar nan taki ta kasance cikin abubuwanda ba zaki gaza da yi mun ba duk rintsi. Cikin jin kunya nace'i promised' yace 'shirye shiryen tafiyarmu fa ya kammala jibi zamu tashi zuwa Rio de Janeiro din ne ko Wellington 'yar matata mai kunya sai dai ina tsoron kar inje ki koma hatsabibiya don wannan sparkiling eyes din naki na bani tsoro fa? Bansan sanda nay dariya ba, domin zancen sa ya tuna min da muhawarar anti mubina da mukarrabanta,suma sun ce idanun suna basu tsoro. Sannan a bakin mansina na fara jin wannan kalma ta sparkle yau ga oga ya maimaita min ashe dai da gaske take,to sai me? Karar wayarshi ta katsemu tun kamin ince komi ya mika hannunshi na dama ya amsa na hagun ko na sakale cikin hannayena. Ya jima yana magana ban maida hankali na gare su ba na zame hannuna na nufi kicin na fara hadawa ogana kunun aya mai sanyin dadi,don dama tuni na markada ayar da kayan kamshi sai na juyo a jug da dambun naman kaza bisa filet din tangaran na zuba 'yan kananun kankara cikin jug din domin yay dan sanyi. Tom dake gefe yana jera cefane a firji na gaya mun irin cin mutuncin da anti tazo har gidan yallabai na Colarado close tayi masu. Wai sune manyan munafukan da aka hada baki dasu aka munafunceta suka ci amanarta,bayan ita ta dauko su tana nan tana shirin daukar fansa a kansu da zarar ta dawo. Nace(cikin rashin kulawa) ''don batawa kam an bata mata sai muyi juriyar daukar bacin ranta duka amma ni bazan gayawa baban jawad ba. 103... Tun daga nesa dana hangi yallabai ba yadda yake ba naji gabana ya fadi nay saurin ambaton innalillahi wa inna ilaihir raaji'un'jikina a sanyaye na ja dan karamin centre table na aza farantin dake hannuna na zube gwuiwowina bisa carpet na dibi yallabai duk ya daure fuska ya dunkula hannuwa ya aza bisa hannun kujera kamar an aiko mai da sakon mutuwa cikin sassanyar murya nace 'wani ya mutu ne? Yaja tsaki yace inda mutuwar ne da bai fi ba' ya mike ya zari agogonshi yana daurawa nay hanzarin amsarshi ina tsuke mishi tie hannuna na rawa bansan dalili ba a duk sanda yallabai ke cikin damuwa dimaucewa infishi damuwa,nake jin tausayi na bashi sai ya dago haba na yay mun lallausar murmushinsa yace'ba komi fa yanzu zanje in dawo kodayake ma na fasa dauko kunun muje ki cigaba da yi mun tausa' Wuni guda a washegari na lura yallabai na kin amsa wayar da ake tayi mai akai akai wata ya kashe wata ya kyale har ta tsinke don kanta daga karshe ma ya kulle kwata kwata. Washegari mun ga text messages har goma da sanyin safiya suna ta shigowa a tare,ina shirin kayanmu cikin trolley katuwa da zamu tafi da ita na rausayar da kai na dubi yallabai yana tazar sumar shi jikin dressing mirrow na dakina ba abunda ya dameshi da wannan mai nacin waya nace 'haba ogana bansanka da wulakanci ba' Yace 'sunan nan ya fita a bakinki inba haka ba zan dinga dalle maki shi. Nace 'na tuba yallabai amma dai kasan wulakanci ba dadi,don in mu aka yimawa bazamu ji dadi ba? Yace'in kin ce na amsa sai na amsa ai. Ya shiga lallatsa waya wai yau ogane ke shara karya,inaji yana cewa jiya tun safe yana dakin meeting da yace zai zo da daddare kuma uzurirrika sun rikeshi,damn too busy,yana nan tafe don gobe zai tashi. Nace'wai wanene? Ya dubeni yay murmushin keta yace' wanda kike cewa ina wulakantawa ba wulakantashi nake ba so nake mu tafi mu bar kasar kamin na amsa wayarshi kika takurani na amsa,to so yake ya takura rayuwarmu. Jikina yay sanyi nace'don Allah abban jawad wa nene? Yace janar balarabe dango ne shi ke son inje maganar tarewar antin ki. Na lumshe ido nace'kaje yallabai don Allah. Yay murmushi yace da zucia nawa? Allah ni da zuciya daya na fadi yace 'toh shikenan Allah Yay miki albarka zubaidah haka nake son ki kasance a kullum wato ki dinga bani hadin kai ina yin abubuwa wadanda suka dace kina dora ni a sahihiyar turba koda ranki baya so idan har kinsan hakan shine daidai don kinga dattijon ya wuce komi a gareni in har ina da iko. Sai dai rayuwa da mubina sai kin yi hakuri sai kin kai zucia nesa kin santa farin sani ba sai na maimaita maki antin taki ba. Nace'haba? In don ni ne wlh zan iya zama da ita menene bata yi min ba? Amma ba mun zauna a hakan ba? Zama da anti mubina nace naji na gani,wlh zan iya zama da ita tunda kasan halin mu2m ai sai ka ci maganin zama dashi. Ya kama baki'Allah zubaidah na? Na kwantar da kai ina murmushi wlh kuwa yallabai taheer angon mubina da zubaidah yayan faty da abdulraheem,abban jawad! Ya tuntsire da daria yana cewa'kin ganki bansan sanda dan bakinnan ya bude ba. Anyway wayonki na bani tsoro zubaidah hakannan ba zan gaji da cewa ba KINA BURGENI! 104... Koda ya dawo daga kiran Ubangidansa ma ransa a bace yake baice min komi ba nima ganin haka na ja bakina na tsuke. Can cikin dare yana ta zuga tsaki,ina jinshi nay lamo tamkar mai bacci amma a zuciyata ina ta Allah Ya isa ga duk wanda ya bato min ran miji. Can anjima ya kira sunana bai zaci zan amsa ba yaji na amsa nan da nan yace'ashe kema ba kiyi bacci ba? Nace'eh' ya kunna fitila mai haske ya mike yace'zubaidah inason ki fahimci bayanin da zan miki yanzu don ba yadda zanyi ban kuma son mu soma boye ma juna abunda ya shafemu komi kankantarsa. Ina neman hadin kanki kamar kullum. Janar ya kirani ya gayamun an maida aurenmu da mubina tunda tuntuni na amsa zan maida ita albarkacinsa da mu2ncin dake tsakanina da wannan family. Amma na gaya masa a gobe zan bar kasar tare da ke don mu huta gajiyar biki yace ba komi ita mubina zata tare kamin mu dawo nace'a'ah gara a bari in dawo komai zai fi tafiya daidai sai ya shiga rokona Allah da annabi saw ta matsa tana son ta dawo gaban dan ta,kuma ya zaci zai iya nemar wata alfarma a gareni in yi mishi balle wannan kankanuwa? Balarabe dango Ubangida na ne,shine silar duk wani matsayi da nake kai a yau don haka har kullum nake girmamashi nake darajashi kinsan dai shege kadai ke manta alkhairi. Tunanin hakan yasa nace dashi na amince ya zartar da duk yadda suke so amman zaman da mukayi a da bashi zamuyi yanzu ba. Bana jin kaina sai ke don ni da ita dama kar ce tasan kar amma ke sai nake tunanin za a kwareki daga dawowarki ki shiga canjin rayuwa. Ina gudun bacin ranki ina tsoron duk wani a abu da ka iya kawo mana matsala cikin rayuwar aurenmu. Mubina tace bata yarda mu yi har wata 3 ba ita tana zaune ni kuma na gaya mata in har zamanta zai takuramin ne,to tay zamanta sai na dawo to amma ga abunda dango yace shine duk na rasa ma ta inda zan bullo ma al'amarin. Har abada bana fatan Allah Ya nuna min ranar da zan bata maki rai zubyna,domin kina faranta mini kina dada damani irin wanda ban taba samu ba a tsayin shekaru na masu yawa a aure. Ban taba sanin dadin aure ba sai a kanki babu wani gurbi da zan iya hada sonki dana kowa a zuciyata believe me wlh i'll nvr betray u'kina ji na momyn jawad? Nace cikin sanyin murya mai kwantar da hankali 'wlh kaji rantsuwa ta 'yan musulmi kenan har raina bana bakin ciki da dawowar anty har kullum ni mai farin ciki ce da duk wani cgbnmu ai ba burgewar mu bace ace jawad ya tashi baisan mahaifiyarshi ba bai saba da ita ba bai san kowa nata ba wannan kwara ne a gareshi ko Allah sai Ya tambayemu. Akan me zan takura da zaman anti? A gidanta fa na zo na tadda ita tare da mijinta da dan ta,da dadi ba dadi suna zauna tare na zamo annoba na tarwatsa iyali na aure mata miji. Shin har akwai wanda aka takurawa tamkar ta? Babu. Nasan babu haramci a ciki,amma idan anti bata yafe mun ba,na tabbata bazan taba samun kwanciyar hankali ba. Don haka ka dawo da anti ba don ni ba ba don babanta ba,sai don kasancewar ta UWAR DAN DA KAKE SO FIYE DA KOWA. Wata rana jawad zai nemi uwarsa,idan yaji abunda muka taru mukayi mata zai ga beken mu duka,niko mai bakin ciki ce da duk abunda zai bata ran mohd jawad. Na roke ka ka dawo da maman jawad ta hakika... Na soma sharen kwallah. A fusace ya dago fuskata yace ''who tell u? Wane wawan ne ya gaya maki idan mubina bata yafe miki ba zaki ga farin ciki ba? Karya ne! Ba kyamun karya kada ki fara akan wannan shin dama ita ta rike ki da amanar ne? [11/3, 8:33 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [11/3, 8:35 AM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔 ~BOOK 2~ Tuna Baya2 106-110 106..... Washegari da safe na shirya cikin abaya mai salki kirar Bahrain na yane kaina da gyalen abayar. Tashin dare zamuyi don haka naga ya dace in je in ga assha wadda tayi mun waya cewa ta dawo shekaran jia zata zo,nace tay zamanta ni zan zo nace da yallabai zan leka in gaida maman assha da sauran jama'ar da sukayi mani halarci wurin biki yace adawo lapia bayan ya dankare mun jaka da dubban nairori yace in kaiwa maman assha wani abu duk da suna da shi bai dace inje haka ba irin wahalar da tayi a wurin auren mu, nace hakane. Tom ne ke ja na cikin mota ta wurin awal kirar Pg .506 fara sol. Nace ya fara biyawa dani shagon turare hakan kuwa akayi. Na sayawa maman ashssha collection din DESIRE DUNHILL da BOUCHERON ita da hajia hafsi da niyyar in danka hannun ashsha tasan yadda zata yi ta kai mata, mutanen nan sun nunan min kaunar da mahaifiyata zata nuna mun don haka nake son su nima tamkar iyayena. Aka shiga lale dani a gidansu ashsha,ta fito a guje ta dafe ni sai mama tace 'ke don Allah shashashar banza sai kinji mata ciwo bakya ganin duk surorin mai juna biyu sun bayyana a tare da jikin nan nata? Ashsha ta sake daka tsalle ta rungumeni mukayi ta juyi kaya kaya tamkar wasu akuyoyi kafin mu dire a daki,mansina dake gefe in banda kallona ba abunda take a ranta ko cewa take Allah sarki mubina lallai taheer yay aure yanzun dole ya mance da ita irin wannan tsaleliyar mace haka? Na gaida mansina ta amsa a lalace ban damu ba muka afka daki nida aminiyata muka shiga surutun bayan rabo kaman ma kashe kanmu don suru2 tace'wai ya aka kare da uncle bello ne? Kinsan Allah ranar sayan baki saida wani fitsari ya kullemin mara don mamaki? Nace'mamaki har kin kai ni? Ni kam ji nayi kamar an zuremin jini, inda Allah Ya rufan asiri idanuna cikin mayafi suke da kin gansu kwal kwal a waje. Tace'ni ko sai naga cewa ya saduda ne ya hakura ya gane rashin dacewar hakan duk ya bani tausayi Allah shaida ne kan bello na sonki. Na kyabe baki nace 'oho masa ni kam ina mai neman tsari da duk wani mai adawa da soyayyata da yallabai kai assha! Don Allah kiyi aure! (hehe su atine ansan dadin auren) ashe haka auren so yake? Tay tagumi tana dubana tace'ba sai kin fada ba zubaidah fatar jikinki kadai ta fada komi na jikinki ya fada,kin ko ga wani irin shining da kike daa haske hadi da taushi da fatanki ya kara? Nace'oh shine mama ke tsammanin ina da juna 2? Bata sani ba ko wannan watan nayi al'ada assha tace 'to bayan nan fa? Nace'kai anya zai yiwu? Kwata kwata fa sati 2 fa kenan. Muka bar wannan batun muka koma nasu fa'izah na rarrafo ga fada mata maida auren anti da yallabai na gaya mata a yau zamu tashi kamin mu dawo tana cikin gidan. Assha ta bani shawarwari nagari masu muhimmanci ga rayuwar aurena,ta kara karfafa min gwuiwa cewar a yanzu ni zubaidah na wuce kishiya ta razanani. Tace'ki baiwa mijinki hadin kai a komi ku dunkule wuri guda idan tazo ko da ta dawo da halinta in taga ba fuska daga kowannen ku sai ta hadiye tsiyarta ko ni inason jawad ya kasance tare da mahaifiyarshi. Zubyna ina dada tunatar dake nasihar gwaggonki'gaskia da juriya sune kyawawan sutturar talaka. Zubaidah da taheer wata ajiya ce daga Allah,haka tarihin soyyrku wani abu ne mai matukar ban mamaki don haka ba uwar jawad ba,ko uwar yallabai ce nan zata ganku ta kyale,zubaidah ki so mijinki. Maganganun hardo sun dade suna min yawo a kwanya suna amsa kuwwa cikin kaina. To haka muka fito muka taradda mama,na bata abunda na sawo cikin leda tayi ta samun albarka ita kuma hardo ta ce da kanta zata skt kai sakona wa hajia hafsi. Banga mansina ba na tambayeta,mama tace ai ta zari mota ta fice. Assha tace za'a kai gulma ba? Mama tace'na hanaki irin wadannan maganganun aishah ko ba komi mansina da mubina ba tsararki bane. Nace 'hkn mama yarinyar nan bata jin magana. Tace 'sai ki dawo da niyyar kai kawarki daki,mutanen alphat sun kawo kudi ansa ranar aure watanni 3 masu zuwa daidai da dawowarku kenan. Na rungume hardo na rasa inda zansa kaina don murna nace'munafuka shine baki gaya mun ba? Tayi gaba tana cewa'ke kinga ki zo ki tafi,ga karfe 5 tana neman yi kada kisa yallabai ya kara tsanata. 107 A hanyarmu ta dawowa Tom ya gyara murya kaman yana son cewa wani abu amma sai yay shiru nace 'wai yaya dai? Yace 'doguwar magana ce madame dina'' nace' a daure a dan tsakuramun ko yaya' yay murmushi yasha (round) yace 'eh-toh so nake ki gaya wa oga nafa samo mata inason inyi aure shekaru na turawa antinmu. Na tintsire da daria nace'ya dace kwarai a can bendel koko anan cikin abj? Yace 'Allah ba zancen wasa ba nan cikin AREWA ba hausa tamkarki. Ya dace nay koyi da ogana, qualities din shi abun koyi ne ga duk wanda yasan ciwon kansa saidai akwai matsala. Nace amma a arewa imagine! Yace karewama musulma,musulmar ma 'yar asalin garin kry,ko zaku bani? Kaina yay dummm, nace' be serious plz tom bansan ka da wasa ba' yace 'am nt joking antinmu koda cam bana maki wasa balle yanzun da kike matan mutumin da nake girmamawa fiye da kowa' nace 'to wannan maganar tafi karfina mun yi ta tare da yallabai. Daidai sanda muka shiga gate masu gadi na daga mana hannu yace'nasan abunda ke damun ranki ba zai wuce kasancewana christian ba amma banyi tunanin hakan ba saida nay tunanin wannan kuma yarinyar ta amince dani tuntuni don course mate dina ce. Nace'thnk twice tom da alamar so kake in maka keke da keke wannan wani al'amari ne da ba zai taba yiwuwa ba sabida banbancin addini abune mai girma, kabilanci ba wani abu bane. Ya lumshe ido yace 'antinmu idan na musulunta fa? Ba tun yau ba ina kwadayin addininku saidai tsoron abunda hakan zai haifar ya hanani fito da kwadayin fili. Bani da kowa sai ku iyayena duk sun mu2 dangi kuwa yanzu bana ce ga inda suke ba,ku taimakamun in auri maryam plsss... Tausayi ya kamani zuciyata ta haskaka da godia ga Allah na dade ina kimanta tom a musulmi da anyi bawan Allah nagari da jin dadin wannan kari da zamu samu a cikin addinin mu mai dumbin baiwa da daukaka na daga hannu nay godia ga Allah a fili da boye nace 'za muyi maganar da yallabai inshaAllah kada ka damu Tom komai zai tafi daidai nagode inama sha'awar addininmu domin shine kadai tafarki na gaskia da kwanciyar hankali. Allah Ya tabbatar muna da wannan abun alkhairi. Yace'ai har Ejiro shima ya yanke shawarar karbar musulunci hannun oganmu, peter ne dai yace yana nan yana tunani domin iyayenshi duk suna raye yana tsoron tashin hankali. Nace 'Allah nagode maKA, na kara gode maKa. Da wannan na shiga gida. Yallabai bayanan nake jin yaje office yin handing over ga mataimakinshi. 108.... Nayi wanka na sallaci magrib na shirya cikin English wears na riga da siket na yana kaina da bakin mayafi mai kauri, takalmana bakake ne rufaffu marassa dunduniya,ina cikin fesa turare yallabai na sawo kai dakin,ya hade cikin suit bakake sai fesa nashi kamshin yake na turaren 'one man show'. Ya amshi kwalbar turaren hannuna ya shiga feshe mu gaba daya yace'kai wannan turare naki ba dai dadin kamshi ba,ya juyo shi ya karanta yace'pleasures'lallai kina jin dadinki,shin wa ke zabo miki kayatattun turaruka ne? Nace 'Maman Ashsha ce' Yace' ta kyauta, shiyasa nake sonsu ita da mijinta, tunda ko duk suna son abunda nake so;zubina. Ina son kamshi zubaidah bana gajiya da ni'imar kamshinki. Niko sai murmushi. A yau kam na amince kamshi ma wani abune dake kara dankon kauna,ya daga ido ya dubi agogon dake hannuna yace Ya Salaam, shine kika kyaleni jirgi ya tashi ya barmu? Karfe goma jirgin Brazil zai tashi gashi har tara tayi. Nace 'toh laifin wa? Yace laifinki. Nace'da nayi me? Yace'da kika fesa turare mai dadin kamshi har na susuce. Na tuntsire da daria yace'promise me dukkan ranakun mu a Brazil nawa ne. Nace 'toh da na waye? Har abada bani da aikin da ya wuce na ogana. A jere muka shiga taka matattakalar da zata kaimu falon kasa yace 'ya dace su Tom suyi aure daga yau sun kare aiki a gidan nan zan yiwa kowannen su aure da duk yarinyar da yake so in samar musu aiki mai kyau ko ya kika gani? Nace'Tom yazo da wani al'amari mai girma na tabbata in ka ji zakayi farin ciki sosai. Yace'tell me wat's it? Nace goron albishirin tukunna domin albishirin babba ne. Yace'me kike so? Nace'yafi karfin kudinka. Yace amman baifi karfin lafiyar dana mallaka ba zubaidah kin ganni nan lafiyayyene ko shadi kike so in je karti a ruga zani in kuma lashe,koda yake ke cikakkiyar bahaushiya ce balle ince'' nasa dariya cikin sheshshekar dariyar nan mai ba maigida sha'awa nace'ba komai nake so ba taheer,ONLY U,bana son komi sai kai sai KAUNARKA,da cgb da rayuwa tare da kai har zuwa karshen rayuwarmu.... Yace indan wannan ne tuni kin samu zubina... Wayyo! Tom da Ejiro suka kauda kai cikin gigicewa gaskia yau santin amarci na kwasar oga(hehehehe) tafe suke kai kace laila da majnun ne,dukkansu basu ganin abunda ke gabansu balle bayansu sai JUNANSU. Ya saki daria yace'Tom bude idon jan bakin ne naga yay yawa shine nake gyara mata'' ina! Tom da Ejiro sukayi waje cikin kunya da gigita Peter ne kadai ya tsaya daga can bayan wundo,Tom yace'sorry oga,daga yau ba mai kara shigowa falon nan bayan sassanmu. Gaba daya mukayi daria. 109... Nace 'albishir fa shine Tom da Ejiro sunce zasu musulunta,Tom har ya samo mata 'yar kary' Oga ya fita ya kamo hannun Tom da Ejiro ya zaunar su cikin kujera duk kunya ta kamasu,ya russuna agabansu yace'bansan irin farin cikin da nike ciki ba a yau,Allah Ya taimake ku. Yanzu muna sauri don haka komi sai na dawo kenan,amman yanzu gobe ku je kry zan wa maimartaba waya in gaya mishi duk abunda kenan za'a kula da komi naku, saidai zan so ya kasance kun nakalci kalmar shahada daga baki na har in dawo daga tafiyar da zamuyi zan ke tunawa da wannan ina kara godia ga Allah kan nasibobi da ni'imomin da yake mun iri-iri, sabida haka kuje maza kuyo wankan shiga musulunci kuyi niyyar shiga musulunci da zucia daya in nakalta muku kalmar shahada... Ya gaya musu duk yadda za suyi cikin 'yan mintuna sun dawo har da sabbin kaya a jikin su,ya karanto masu niyya suka fada kana ya karanta musu kalmar shahada suka maimaita har sau uku. Ya fiddo cek ya rubuta musu kudi masu yawa kamar yadda ya saba a duk sanda zaiyi tafiya. Peter duk yabi ya muzanta daga ni har yallabai ba wanda ya maida hankali a kansa saidai shima yallabai ya bashi kudi daidai da nasun,sauran ma'aikata duk ya sallame su har masu gadi,bayan albashishshikansu na wata 3 ya kara da karamcinsa ninkin ba ninkin albashinsu. Ya dubi Tom yace 'tom a da,TAUFEEQ a yanzu,da ejiro IBRAHEEM a yanzu,daga yau aiki ya kare a karkashin taheer sai ku nemi sabon ogan ku can a kamfanin siminti na dangote akwai gidaje guda 2 a (maitama) nasa an gina,naku ne halak malak na mallaka maku, komi na hannun Abdulraheem in kun je antinku wannan nauyin yana wuyanta na aza mata shi. Ya dubeni mukayi murmushi nace'na dau wannan alqawarin' to daga Tom har Ejiro an rasa mai bakin godia sai murmushin kauna ga ogansu,shiko peter sai zazzara ido kawai yake abun tausayi gaba dayan ma'aikatan suka shiga kwararo addu'oin alkhairi ga ogan su. A filin jirgin saman abj babu bata lokaci muka samu jirgin MEA da zamu hau har lokacin tashinsa ya cika. Toh muna shiga ana rufe jirgin kamar dama mu ake jira. Muna cikin bangaren nan mai matsayi da ake kira First Class manne muke da juna tamkar ansa super-glue an manne mu muna ta hirarrakin mu cike da so da kauna,abinki da jar fata ba wanda ke kula da harkar wani. 110.... Ina labartawa yallabai yadda mukai da Tom yana mamaki. Nace'na ji tausayin peter Allah da kake ta ambaton komi ba tare da shi ba. Yace'yes ina sane ina son nuna mishi karamci irin na al'ummar musulmi ne,ta hakan sai in kara kwadaitar da zuciyarsa ga son ya rabe mu kin ga dai ban ce dashi ba,amma na nuna mishi sun fishi daraja da muhimmanci a garemu. Nace shima Allah Ya ganar da shi. Yace'ameen' Karfe biyar na asubahi agogon mu na nan gida 9ja muka sauka kasar Brazil cikin birnin Rio de Janeiro. Ban zaci Brazil a yadda naganta ba,ashe jin ta ake ban san tafi yadda ake tsammaninta ba. Nigerian Embassy ta kasar ce tayiwa yallabai masauki a wani estate na baki wai shi Betna Guest Estate,gini ne samansa har kasansa ruf. Akwai dakin barci guda 2, bandaki 2, balcony wato baranda a saman bene sai katoton kicin da mota da direba ko muna bukatar zuwa wani wuri. Muna ajje jaka sai shower daga nan kuma sai bacci da mukayi a zaune cikin kujera cikin wani irin luntsumemmen gadon da ban taba tsammanin akwai a dunia ba. Bamu muka farka ba sai karfe 2 na rana shi din ma kararrawar kukun gidan ta tada mu mai nuna ya kamala abincin rana. A gaggauce yallabai ya dauro alwala nima hakan muka bada faralin sallar azuhur. Kamin mu kammala da wanka kuku ya jere komi bisa tebir,a yatsine yallabai ya shiga budewa yana yamutsa fuska alamar ba wanda zai iya ci a ciki. Yace'bari in je hotel ko zan samo African Food ke sai kici wannan din kamin in dawo ba dadewa zan yi ba. Nace'toh' suka fita shi da direban da ke waje. Fitarsu keda wuya na janyo jakata da muka zo da ita na soma sauke kayan girkin da nasa Tom ya hada mun waje daya nayi kicin nan da nan na tada tuwon semovita da miyar agushi,kukun jar fata ne yayi ficewarsa ya bani wuri musamman daya fahimci bana bukatar taimako. Na bude firji na tadda duk abunda nake bukata wato ganye iri iri da nama nau'i nau'i har dana alade,na ware shi cikin shara ba don na san shi ba sai don kowanne nau'in nama da sunanshi makale jikin dan karfe a kasanshi,na bararraka farfesun dawisu na juye a filas kana danwaken fulawa da mai da maggi da yankakken nunannen tumatur jazur na hada salad da waken gongoni,salad cream da sauransu,kana lemun da na matse daga ruwan tuffa zalla,na kara suga kadan da flavour nasa 'yar kankara na jere a dardumar tsakiyar falon bayan na shimfida ledar cin abinci. Nay kwaliyya na mike cikin kujera ina jiran yallabai. Bashi ya shigo ba sai karfe biyar na yamma barci ya soma fizgana kadan kadan,ya russuna ya sumbaceni a kunci nayi harr da idanuna yace'Allah sarki momin jawad na tafi na dade ba tare da niyyah ba gashi ban ma samo abunda nake son ba amman na kawo miki abinci mai dadi wani old frnd of myn ne na gamu da shi a hanya ya rikeni,suna nan zuwa shida matar shi da daddare. Na mike zaune na bude ledodin daya bayan daya aje bisa tebur,na shiga fiddo foil paper da aka nannade wani irin abinci,haba malam! Yawuna ya shiga tsinkewa na lashi tausasan labbana da halshena,ya tuntsire da dariya yace'kinsan sunanshi? Na yarfar da hannuwa alaman oho! [11/3, 8:35 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [11/3, 8:36 AM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔 ~BOOK 2~ Tuna Baya 111-115 111.... Yace'shi wannan da kike gani kaman cakulet nama ne suka dandake ya koma haka ana kiranshi flamed grilled rebeye' shi kuma wannan shine 'guiltless grilled salmon (kifi ne) nace kifi salmon da nakejin labari? Yace ki ci bakin ki zai gaya maki. Ina soma taunawa naji tamkar kunnena ya fice ban kara bi ta kan yallabai ba. Ina tunanin gyambon ciki(ulcer) ya kamani sbd yadda nake cin abinci a dan tsukin kamar hauka da kwalama kamar sabuwar mayya. Nayi mai nuni da ledar dana shirya mai abinci da yatsana sabbab,ya matsa ya soma bude dishes daya bayan daya ya shiga girgiza kai cikin mamaki kamin ya juyo ya jinjina mini yace'wat a surprise! Shin wai ke mai yasa kike da ban mamaki ne? Na lumshe ido a cikin murmushi 'ban mamaki har an fika baban jawad? 'Toh ai ke din ce,ke din ce zubaidah wata irin mace mai yin duk abunda zai sa mu2m yasha mamaki. Ya nade hannun riga ya zauna bisa kilishi ya soma kwasar irin garar da yake so nima ina kwasar tawa,lallai ra'ayi iri iri ne shi kuma haka Allah Yayi sa? Na lumshe ido cike da sha'awar komi nashi ina mai rokon Allah cikin zuciyata,ya cigaba da bani iko da lafiyar da zan cgb da farantawa taheer har zuwa ranar da muka daina numfashi. Karfe 8 na dare ina kwance gefen gado inata kallon yallabai dake dressing sassauka cikin farar shirt (DKNY) da bakin wando(tokyo) yay wani irin fes da shi kai ka ce saurayi ne dan shekaru ashirin da biyar komi nashi mai ban sha'awa ne, sai na mike cikin nutsuwa na amshe shi. Ina fesa mishi turare yay murmushi yace thnk u na shirya nima cikin wasu Pakistan masu ruwan madara kirar india,nay lullubi da yalwataccen mayafin kayan kai kace indiyar gaske ce yace'u look fresh nd beautiful,ni na rasa shigar da tafi maki kyau zubyna,ko don ina sonki ne? Nace'umh' Adaidai lokacin da kararrawar kofa ta soma kara yace'mu2mina ya iso kenan' Mukka rankaya a tare na bude kofar. Baturen dogone matarshi 'yar gajera da 'ya'yansu biyu duk mata,suka rungumi juna shi da yallabai itama matar ta kama hannuna a haka muka zauna cikin kujerar reception wadda ta kasance leather seat,farare sol yace da baturen'meet my bride Zubaidah,zubaidah wannan shine Mr.kelvin abokin kasuwanci na,yana daya daga cikin mutane hudu mamallaka kamfanin takalman mu dake Rome (italy) da matarshi Susan dukkanninsu haifaffun Brazil ne, sun zo ne musamman don ke,so ga susan nan,susan ga zubaidah na baki amanarta cikin wata guda da zamuyi honey moon a kasar ku. (yana magana cikin nau'in turancin da kasar ke amfani). Susan tace 'Zu- bei-dah u're highly wlcm 2 our beloved country. Muna fatan honey moon mai dadi a gareku cikin birnin Rio de Janeiro. Muna masu farin cikin gayyatar ku dinner gobe a gidanmu, ko kelvin? Na kamo hannun 'ya'yanta ina tambayar su sunansu,toh daganan sai hira ta barke. Basu suka bar gidanmu ba sai karfe goma na dare, mukayi masu rakiya har gindin mota. Washegari da karfe tara na dare Kelvin ya zo ya daukemu zuwa villa dinsu,muka ci abincin dare tare dasu. Bayan sati biyu mun gama wasttsake gajiya nida susan muka soma shiga gari tana nuna min wajeje masu ban sha'awa. Shigata 'safe snorkeling' na daga cikin abubuwan da bazan manta a zamana na kasar ba,domin abu ne mai hatsarin gaske can kasan ruwa,saidai alhmdlh mun fito lafiya. Cikin sati uku kacal harshena ya sarke da turancin Brazil da nake samu a bakin susan haka fatar jikina gabadaya ni kaina nasan na kara gogewa fiye da da. 112.... A cikin watan gabadaya nida yallabai babu komi a gabanmu daya wuce barje gumin soyayyar mu da ibadodinmu sai ko yawon bude ido. Wani irin sheki da cika da na soma yi ba yallabai ba har ni kaina abin ya tsorata ni. A yau ba muje ko'ina ba muna falo,muna kallon shirin film din America na (around d world in 80 days) wanda jackie chan da steve coogan ke gabatarwa. Ya dubeni kuri yace 'na dade ina zargin jikin nan naki zubi, ko aiki na ya samu karbuwa ne? Ya dace muga likita koko sai mun je Wellington jibi? Nace' susan ma haka tace amma ni ina al'ada ko shekaranjiya nayi wankan sallah. Yace toh wannan farin fa kau da kike na menene? Ban yarda da kayan shafar nan da susan ta sa kika sake ba,kwaso in gani. Nayi dariya na mike na kwaso kit dina na dire mishi, yay dube dubensa daya saba bai ga wani sabon abu ba yace'ke ban yarda dake ba Allah dole a gobe mu ga likita. Nace'duk yadda ka ce maigida haka za'ayi. Washe gari munga wata kwararriyar likita wai ita Dr.anna Branthwaite ta dubani thoroughly tace ita bata ga ciki ba. Yallabai yay dumm! Kamar an aiko mai da sakon mu2wa yace'toh canjin jikin fa? Komi nata ya canza ta kara haske kuma ta kara girma sosai. Sai ya baiwa likitar dariya nima na murmusa tace'ya danganta da sauyin da ta samu na abinci da ruwan sha da hu2,koko ince albarkar kasar mu ta amsheta. Duk mukayi murmushi. Mun bar Rio de Janeiro zuwa Wellington ranar lahadi,hakika nida susan munyi kewar juna ba kadan ba,tayi alqawarin zuwa 9ja musamman domin ni har kuka tayi lokacin da zamu shiga jirgi. To a Wellington a hotel muka sauka hakannan rayuwar bata canza ba,soyayyar ce dai ziryan da yawuwwukan bude ido. Kar kiso kiga zubaida a wannan lokacin ba shakka ta zamo hatsabibiyar da ogan ta ke tsoro da kyar in bata mance yadda ake daura zani ba. Jikinta mulmul fatarta kamar ka taba jini yay tsartuwa sabida tsabar hu2. A dan tsukin kuma na koma lalaci,haka karfin da nake baiwa abincin yallabai duk sai ya raunana. Komi nasa a baki na babu taste ina tsammanin abincin su ne ba dadi sai na daure na shiga dafawa da kaina duk da haka bata canza zani ba. Na lura a dan tsukin yallabai na kebewa yay ta hira a waya yana kyalkyatar daria abinsa. Rannan cikin kunnena naji yace'hakuri zaki kara mubina ni kaina duk hankalina yayo kanki to amma kinsan dole nida ke mu hadu mu dinga tarairayar zubaidah don anan din ma ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba wai komi taci bata jin dadinshi balle mun komo wadannan asibitocin namu marassa kula? Nakejin wani abu ta gaya mishi naji yace'a'ah dukkanmu bama tsammani don an dubata a Brazil sun ce babu..... Can anjima kuma yace eh toh hakan za'ayi nagode da shawararki don Allah ki kara hakuri muna nan tahowa cikin watannan in Allah Ya yarda. Ji nayi kaina ya shiga juyawa wani abu ya zo ya tokareni a kahon zuci,NAMIJI...sai a bar shi da ban takaicinsa. 113.... Wato duk inda suke sunan su daya,'yan uwan juna ne halin su daya. Nayi daki bana ko ganin gabana na zauna bakin gado nay tagumi sai hawaye sharr! Yanzu ni bani da sirri kenan sai anti tasan yadda tai ta kalallameshi ta ji,wai har cikin ma in ina da shi sai an ji,to idan ma gulma ce kuma zamannawa ya tsole mata ido kowa ya murza kanbunnashi na ga mai dawo mata cikin watan wai shi yallabai baisan kaidin mata bane? Ya karaso yana cin biscuit'digestive' ya zauna dab dani ya sauken tagumi yace na tsani ganinki cikin tagumi,any matsala? Kaman in ja tsaki ko na samu sanyin zuciyata daga wannan tonon sililin da yake mani gun kirkiro murmushin kissa nace nothng,kawai raina ne ba dadi,tun safe na kasa cin komi,komai na ci ji nake kamar zai dawo' yace'nima nay tunanin yi mana booking,jirgin London sun fi kowa kwararrun lokitoci,muje a gobe a duba ki sosai,mu koma gida ko don mubina dake jiranmu,ban yarda wai ba ciki bane zubaidah 'i luv a bby desperately' Dubar ni don Allah kato dani a yanzun daya dace a ce ina da diya a gidan aure ki taimakeni don Allah zubyna. Harara na bishi da ita kasa-kasa sbd matukar haushin daya bani a raina nace'wai kayi tunani ko an baka shawara. Ya dace in soma kwatarwa kaina 'yanci tun yanzun don bazai yiwu in zauna anti ta soma tsara mana abunda take so ba. Na dago ido na taf cike da kwalla nace'ni ba asibitin da zani,bani da komi. Yay sakale! Kamar yana mamakin musun da nayi mishi a yau amma bai furta ba. Yace'shikenan in ma wani abu susan ta rakaki aka makala miki don kar ki haihu ai Allah ba azzalumin kowa bane kuma bazan taba yafewa ba. A razane na dago na dubi yallabai bai taba yi mun magana ta irin wannan sigar ba,cike da zargi, tuhuma, rashin yarda da jin haushi, nace 'lallai! Sharrin da za'ayi min kenan,ba komi. Sai hawayen da nake ta tattali suka kwararo a kundukukina. Na soma girza kuka mai tunzura rai wanda dama zuciyar a cike take taf,da kishi, kiris take jira ta fashe. Mai neman kuka ne aka manna mai dunkulen kashi a baka. Amma yallabai yau ko gizau sai ma ya fice ya bar mun dakin kwata kwata. Yau ce rana ta farko da mukayi kwanan dacin rai tunda mukayi aure irin wadda bamu taba yi ba. Daga ni har yallabai ba wanda ya runtsa sai juyi a gefen da yake,ba wanda yace da dan uwansa ko sannu har wayewar gari. Washegari naga yana harhade yan abubuwan da ya san mallakinmu ne cikin jakunkunan mu bai ce min komai ba,nima ban ce masa ba. Karfe tara na dare taxi tazo aka sa kayanmu sai a nanne yace dani tafiya zamuyi bance komi ba na dau jakata na rataya nasa takalmi muka kulle dakin muka baiwa receptionist din mukullinsu muka nufi airport. Karfe goma na dare muna zaune cikin jirgi mai zuwa London daga Wellington. Da asubah filin jirgin saman (heathrow) muka wayi gari. Ambasadan Nja a ingila wanda ya kasance aboki na jiki ga yallabai shi ya tura da mota a taryomu, muna tafe cikin motar ambasada direban ya gaya mishi ance anyi mishi masauki a hotel din (Royal Horseguard) nan zai kaimu. 114.. Yallabai yace kar su damu da wannan. Na sha mamaki matuka da naga yallabai yasa makulli ya bude wani flat house a (Northumberland Avenue). Ashe yallabai nada flat a London? Surprised! Direban ya koma yace zaije ya gayawa ambasada ya cika aikinsa amma zai dawo da daddare ko zai zaga damu. Yallabai yay mishi sannu yace a gaida ambasada. Gidan flat ne mai farin fenti babu abunda babu,babunce kurum babu. Yallabai wanka ya fada ni ko jaka na aje a gefe na kunna injinan saukakama dan adam wahala na gyare ko'ina ya shiga sheki na feshe ko'ina da air freshner mai dadin kamshi. Na wanke toilets din fes fes ko'ina ya shige diban kamshi kana na fada wanka. Ina shafa a gaban madubi yallbai ya shigo,ya hade cikin caftan na farar shadda yana daura agogonshi na fatan damisa ya karaso har inda nake yana murmushi. Yay shiru yana shakar kamshin man 'caris' da nike murzawa lallausar fatata. Ya saki wata irin ajiyar zuciya mai nauyi yace 'kiyi hakuri kiyi hakuri dani kiyi min uzuri,Atine Zubaidah,i cn't do without u...... To ni ma din hakan nasan bazan iya fushi da Oga na ba. Naji tausayinsa,na tabbatar ba karamin azabtar da juna mukai ba a daren jiya kacal saura da me? Muka shiga biyan bashin juna. Daga ni har yallabai mun nemi afuwar juna mun tabbata shaidan ne ke son kawo mana matsala a rayuwar auren mu. Washegari mun tashi cike da farin cikin da baya misaltuwa, muka nufi wani restaurant wai shi Auberge muka karya kumallo muka komo gidan mu muka shiga maida bashin barcin da bamu samu munyi ba. Da yamma na shirya cikin jibgegiyar rigar sanyin birnin London har ya zarta hankali. Yace 'look zubaidah a yi maganar gaskia wai ke bakya tausayi na ne? Na dauke ki mai son duk abunda nake so ce wai me yasa kike man yawo da hankali ne? Kin ki gaya mun ciki gareki ko naji sanyi bayan ga alamu duk sun nuna. Yana nuna min jikina gabadaya yace'yanzu don Allah ba zaki taimaka mun in samu 'ya'yannan da nake burin samu kamin Allah Ya dau raina ba? Maganar shi ta sokeni duk sai ya dugunzumar mun da zuciya na nace to ai ni iya gaskiya ta na fadi Allah ina al'ada,kuma bana jin wani sauyi a jikina a kan me zan ki haihuwa har ka zargeni da abunda kaima kasan ko giya na sha bazan iya aikatawa ba? 'In hakane ki amince muje kwararru su duba ki wai akan me to zaki ce baza'a dubaki ba? Nace 'da idear' dinka ce mai zai hana in amince? Sabida Allah waya ce a kawo ni asibiti a London a dubani? Na tsatstsare shi da ido. Yay dan jim kamin yay dan tunani can kuma yace'toh me ya kawo wannan banzar tambayar ashe ni ban isa yin yadda nakeso dake ba? Na lura ranshi ya baci,na kara jin haushi na mike tsaye nace:kay hakuri amma ban zaci cikin yardar da mukayiwa juna akwai boye boye ba,ni dai nasan ba kai bane bana kuma son irin wadannan abubuwan da suka shafeni a dinga neman shawarar wani akai ni bama na son a sani ko cikin ne dani balle babu,ni ina ruwana da harkar wani? Ya tuntsire da daria yace waye wanin nan ne da kike ta ambato? 115.... Ashe kuma labe kika koma yiwa antin taki? To kiy hakuri Allah ba don shawarar ta bane dama nima nay tunanin hakan tun kamin ta fada,kuma ina laifinta don ta nuna kulawa da lafiyarki? Tun yanzu har an soma kishin daman na gaya miki duk abunda kike fadi cika baki ne zamuje asibitinne ko kuwa a kyale shawarar ta tunda bakya so? Na dago hankali kirjina na harbawa dana lura shi fahimtar da yai mun ma daban ne da abunda ni nake nufi,nace cikin nutsuwa 'baban jawad kai namijine bazaka gane ba,ba kishi nake ba ba kuma labe nake maku ba illa irin wannan bai dace ake gaya mata ba don ko bata nuna maka ba zata ji dadi ba. In ma cikin ne ai sai a bari in ya fito kowa ya gani ko? Yace'na fahimce ki zubaidah so kiyi hakuri insha Allah ba za'a sake maimaitawa ba kuskurene. Nay murmushi nace'fahimtarkagareni a komi ita ke kara min kaunar ka. Nasara jar fata ya barbaza injina a kaina cikin kwarewa da sanin makamar aiki yana zakule zakulensa har Allah Ya bashi nasarar gano makalallen ciki har wata hudu. Mu na gaban teburin Dr. Dadrian Russo na asibitin Hilditch mun maida hankulanmu a kanshi. Ya dibi yallabai cikin jamami yace'ina tayaka murna domin matarka na dauke da ciki har wata hudu (wato tun farkon aurenmu) muka dubi juna a gigice muka yiwa juna murmushi sai dacta yace amma akwai matsala. Tuni murna ta burma ciki, yace 'kincekina al'ada don haka nayi analysing matsalar matarka sosai ciki dai akwai shi tabbas to amma ba'a cikin mahaifa ba. Daga ni har yallabai muka hada baki ba tare da sanin mu ba muka ce'to a ina? Yace'ku kwantar da hankulanku komi zaiyi daidai yana gefen mahaifarki ne yana girma a wurin don haka yanzu zaki hau gado in maida shi cikin mahaifa cikin gaggawa in ba haka ba ko saidai a cire shi in anyi sakaci a haka zai ta cgb da girma a gefenki sai ku gode Allah da Ya nufe ka da zuwa asibiti da wurwuri. Idona yay kwalkwal cikin tashin hankali na soma sharar hawaye,to amma yallabai ya fini rudewa ya lailayo ashar irin wanda ban taba zaton ya iya ba ya dannawa likitan yace'a gidan ubanka ne aka taba yin cikin a wajen mahaifa? Ya figi hannuna muka fice yana ta fadace fadace kamar mahaukaci,yace zakule zakulen bature na tsiya ya fara zama karya, muka nufi wani asibitin (Rudolph Guiliana Clinic) cikin (Central London) wata kwararriyar likitar mata ta dubani ba tare da bata lokaci ba ta sallami yallabai tace in hau gado ko bayanin ma bata tsaya yi mishi ba don ganin yadda yake shirin dukanta ta kulle kofa ta umarci nurses su hada kayan aiki nan da nan aka manna mun allura sai dogon barci kanin mu2wa daganan ban sake sanin me ke faruwa ba. Sai bude ido nay akan gadon asibiti wai yau yallabai nane da hawaye jage jage yana rokon su su cire cikin baya so. Mrs.Wilcox babbar likita na kwantar mai da hankali tace komi yay daidai yanzun sauran karfin jiki. Tay umarni na irin abincin da nurses zasu dinga bani a kuma kula da allurai da shan magunguna na akan kari. Allah sarki na tausayawa aljihun yallabai shi ko ta lafiya ta kawai yake bata komi ba. Asibitin ba'a zaman jinya duk aikin asibitinne,su suke kula da patient din su,abincinsa,walwalarsa da duk wani motion dinsa. Cikin sati 2 na warware garau jikina ya kara kyau komi nawa ya kara bunkasa, shining da haske kuwa sai abunda ya karu. Ni kaina a ranar da na dubi madubi saida na cillar. Yallabai yana makale dani muka dawo gida, rayuwa ta koma sabuwa. [11/3, 8:37 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [11/3, 8:38 AM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔 ~BOOK 2~ ```SECOND TO THE LAST``` Tuna Baya2 115-120 116... Cikina ya shiga wata biyar a lokacin komi lapia amma marata ko dan tasawa bata yi ba,in ba don ina jin motsi ba cewa zanyi karya ne bbu wani ciki,to balle kuma sauran mutane. Na tabbata idan naje kry a wannan lokacin kam ba mai ganeni,cikin ma kansa ba mai cewa ina da shi, idan na ishi yallabai da wannan korafin sai yace ai don ni doguwa ce,ba a faya ganin cikin mu ba. Maganar rashin ganewa kar wanda ya gane din, ya damu a gane nine? Shi dai yasan zai gane ni cikin kowanne hali koda ya gamu da laluran makanta ne da ya shafa lallausar fatana zai fiddani cikin dubban mata 'zubaidah cikin matan duniya duka ni a wurina daga na Africar har na turai bbu mai irin jikin matata idan mijin wata yaji haushi shima ya kiwata tashi yadda nake kiwon tawa,ya ji da ita yadda nake ji da tawa,ya riritata yadda nake ririta tawa shine ya burgeni. A irin wadannan lokutan na kan ce a zuciyata anya za'a samu? Bana tsammani. Shin akwai wacce zatayi sa'ar samun mujin dake sonta kamar yadda nawa mijin ke sona? Akwai wadda ta kai ni sa'ar aure? Bana jin akwai. Ashe gaskiyar taufiq ne da yace'am among d luckiest. Na kan tausaywa anti mubina sbd yadda yay watsi da al'amarinta bashi da aiki sai na kula da ni ko numfashi ji yake kamar yay mun. Cewa yake wai akwai macen da ta taba shan wahala irina? Ciki a wajen mahaifa? Shi kam bai taba ji ba. Sai ince har ma da wadanda suka fini akwai dan wasu ma in ya gani ba zai jure ba. Na damu kwarai mu dawo gida ko don anti mubina amma yace ina! Shi sai na huta. Sai cikina yay kwari. Itama mubinar taci lokacinta akan me zata ci nawa? A rana in bata bugo waya sau goma ba ta bugo ashirin,kullum dai uzuri daya yake bata na ta kara hakuri abubuwane sun sha mai kai damn too busy amma yana nan tafe. A wannan lokacin zan iya cewa babu irin kulawa,so da kaunar da ban gani daga yallabai ba,har saida cikina yay kwari sosai ya shiga wata na bakwai. Wannan zamani da muke ciki na kwamfuta don haka duk wani aikin ofis din shi ta computer yake tafiyar dashi. Watannin mu bakwai cif akan wata ukun da mukayi niyya sannan yallabai ya yarda muyi shirin tahowa gida. Inda ya hadani da credit card na kudi masu yawa wai inyi siyayyar haihuwa,maganartsarabe tsarabe duka ba ruwana shi zai kula da wannan, ni sai abun ma ya koma bani tsoro muka je kamfanin motoci yay cinikin 'roll-royses'guda 2 yace na alkawarin da kika yiwa taufiq da ibraheem,kana ya zabi wata dunkulalliyar 'ferraris' sabuwar shigowa ko 9ja bata zo ba a wannan lokacin,ruwan kasa mai sheki,ya danka mun mukullin yace'gift'din shi kenan na cikina,saura na haihuwa. To har sai na rasa bakin godia. To da me zan gode? Banda kauna ta har abada ga mijina abun kaunata? 117..... bana bukatar komi domin ni kan a rayuwa a yanzu zance ba abunda Allah bai hore mun ba,sai nay tunanin yanzu ne ya dace duk wanda ke kaunata,ya rabi inuwar da nima nake ciki. Na kira Halisa kawata ta jiki a London diyar Ambasadan 9ja na ingila. Halisa sa'a ta ce sai dai ba tayi aure ba,tana kara2 a jami'ar Shiffield tun zuwan da mukayi gidansu bayan fitowa ta daga asibiti muka likewa juna da ingantattar abota ta hanyar ta ne nasan wurare da dama ta hanyarta ne nasan wai ashe duk yawancin matan manyan mu na nan 9ja dake zuwa sayayyar tufafi, kayan kawa na matan da suka amsa sunansu,da sarin kowanne irin (machandies)suna yinta ne a wata kasuwa dake ci ranar lahadi kadai a Liverpool Street wai ita(sunday morning market),nan ne matan manyanmu dake kasuwanci da London ke sayen lesussuka,atampopi,jewels,takalma da duk kayan amfanin mu na jiki dana gida wadanda sunfi arha kadai a sunday mrng mrkt. Ni da halisa muka shiga sunday mrng ranar lahadi karfe goma cikin motarta,na sayi lesussuka da atamfofin ingila masu karshen tsada(material yards) da shaddodi zuwa boyel boyel 'yan ubansu duk domin dangi,da 'yan uwana dana yallabai. A kantin jewelleries na sayi fashion necklaces da ear rings asamfurin Blue royale misaki venato da shimmering pearls domin assha sadia da anti fati,duk da nasan faty bata can amma bazan iya bawa sadia ban bata ba. Shiko abdulraheem agogon nan Raymond weil mai tsadar gaske da bandirorin shadda da boyel na siya mishi,na hadawa assha kayan shafa na'gres cabotine' da fari gudunmuwar aure naso hada mata. Yallabai yace kar in siya mata crystal daga kamfaninsu na yin crytal dake Washington zai tura mata ta can,haka takalma da jakunkuna daga Italy Kelvin zai turamin airport ta can,in rabawa al'ummarmu. Halisa ta hadan set din turaruka na'envy me,voyage da miyaki tace wannan ya zamanto na amfaninki kadai zubaidah,don ki fita daban da sauran mata a wajen mijinki. Inda duk ya jiyo unique kamshinki zai san kece koda kin bar wurin kuwa,haka in dosowa kikayi kafin ki karaso zai san kin taho,wannan wani sirri ne na matan manya. Sannan ta zaba min saitin wani gado fari sol (italian bed) da madubinshi da komai saiti biyu,tace inyi amfani da daya in baiwa anty mubina daya a matsayin tsaraba, kudin kowanne daya anan kudin mu na 9ja naira miliyan daya ne. Nace'wai wai kinason tace ya sakarmin bakin aljihu kenan fiye da ita? Tace'ai ko baki nuna ba zubaidah kallo daya za ai miki asan mijinki na sonki kuma yana ji dake,ya kuma mallaka miki duk abunda ya mallaka a dunia. Kudin sayayyar haihuwa kuwa rabasu biyu nayi, na kashe rabinsu a sittiru da kayan amfanin gudan raina MUHAMMAD JAWAD,da ragowar kudin ba abunda ban sayawa babyn ba amma unisex wato wanda mace ko namiji zasu iya sawa don daga ni har yallabai bamu amince da scanning ba sai motsin lafiyar jaririnmu.. Hatta cokalin da zai sha ruwa da gadon da zai kwanta zuwa motar da zai koyi zama ba abunda ban saya ba. 118... Yallabai ne kwance falon mu na birnin London ana i'gobe zamu tafi,yana sauraron labarun BBC sashen hausa daga bakin Hindu Waziri. Mota ta shiga sassauke jibgi jibgi a harabarmu,nima ribdediyar jakata dankare take ba masaka tsinke muka fada cikin kujera shirim da ni da tirtsetsen cikina nace'wayyo baban jawad kafata'' yace 'wayyo sannu,idonshi akan jibgin kaya,ya gurgusa yace'wannan ai kece sunday mrng mrkt din shin boutique za a bude ne a Abuja ban sani ba? Ke da nace ki sayo kayan baby kawai shine kike karar da kudin a shirmen ku na mata? Nace 'ayya! Ai tsarabar mutane ce baka ga ba harda furniture marassa nauyi? Kudin fa suna da yawa in ba kantin kake son a sayewa babyn ba shi kadai? Yace'so wat? Kudin bana ubansa bane don wa ake nemosu ba don su ba? Nace hkn amma 'ya'yan jama'a ma suna da bukata sai shi kadai dan gatan daddy? Yace amman nace dake zanyi tsaraba kamar yadda na saba wa jama'ar kary,me yasa kike da kunnen kashi ne? Nace'i'am sorry angon karni ai tsaraba bata yawa duk sai a hada masu ba laifi bane. Ya tuntsire da dariar sabon sunanshi ya ciccibeni ko nauyi baya ji mukayi daki yana cewa 'muje ki gayamin wanene angon karnin? An gaya maki matata ko 'ya 'ya goma ta haife a lokaci daya zatayi karni ne? Karfe shida na yammacin washegarin litinin muna a 'gatwick airport' muna sallama da mutanen da mukayi zaman aminci da su musamman iyalin ambasada suna ta bani sakonni ne ga 'yan uwansu na gida dake jos. Muna cikin jirgi (boeing 745) mai zuwa portharcout din 9ja,kalmashe nake jikin yallabai sbd sanyin London mai shiga bargo shi kuma yana ta aikin lallatse waya yana gayawa kowa gamu nan mun taso daga London amma kar su je tun yanzu don Portharcourt zamu fara sauka. Jirgi ya daga ya nausa gida. Ba taheer din ba ba zubaidahr ba kowannensu ya gama murjewa ya kara girma akan nashi sbd tsabar hu2 da samun nutsuwa uwa uba dauwamammen Kwanciyar hankl. Da ganin su dai kaga well-fed-Londoners' wato wadanda suka ci suka hantse da diet din London. 119... Su zubaidah aka shagwargwabe fuska'nifa jirgin kn zan shiga kai ne zaka hau na Abj don ni kry zani in haihu za'a fi kula dani tunda yake haihuwar fari ce. Kuma ya dace in baiwa antina enough tym din ta itama sai a gyara mun gidanmu na bayan gari mu zauna nida inna luba da mohd jawad. Yace'ai wlh baki isa ba,kinyi kadan kinyi tsararo ni kuma ya zakiyi dani? Kinsan dai zamana a kry ba zai yiwu ba sbd office ga aiyuka masu tsauri da zan je in taras. Na soma magiya nace'don Allah yallabai kay 2nani anti ma fa mu2m ce tana da hakki akanmu,ya dace a kula da hakkokinta itama ko don gudun daukar hakki. Yace'au to ni shine za'a dauki nawa hakkin? To ba'a isa ba. Hankalina ma bazai kwanta ba ku kuna can da tsohon ciki ni ina wani gari? Thnk twice lady. Saidai ko in daga ni har mubinan mu tarkato mu dawo kry a aje aikin Allah kinji na rantse. Na tabbatar ya gama magana kenan tunda shidai baya magana 2,sai nasa mishi kuka nace'to ni yanzu shine kiyi ta kuka kiyi ki koshi,har sai hawayen sun kare jirgi ya sauka mu tafi abj shine shawara. A daidai lokacin da aka samo sanarwa ta bututun maganar jirgi zai sauka a daura belt. Na fiddo powder a jakata(ailin) mai manne da madubi ina gyara hawayen fuskata na shafa lipshimmer sai yasa mun dariyar data kara kular dani. Ya karkatar da kai yace ke dai yi dan murmushin nan naki mai kama da flora bella rose in da gaske kina son zuwa qaraye.... Bansan sanda na murmusa bamhar 'yar wushiryata ta fito yace'to ko ke fa? Amma cewa nake cikinki yanzu ya shiga wata na bakwai gashi ba'a gani ba wanda ya sani balle ki ce za'ayi miki suru2n baki zo goyon ciki ba,in ya shiga wata na tara sai in kawo ki gaban fulani da amarya da kaina su ga irin kwazo na aure wata goma haihuwa wata tara... Na harareshi yay murmushi yace ko kuwa amaryar karni na? Nace haka za'ayi angon karnin,yadda kace bazan ki ba. Yace'yauwa 'yar matata shiyasa nakeso kauna da begenki sbd bakya yimin MUSU,bakya yi mun KARYA kuma bakya HA'INTA ta 120... Nace 'banason in takura anti mubina ne,tay missing mijinta 4 so long zama na zai zama tamkar takura ne agareta.... Ya katseni yace'zan kula da adalci in Allah Ya yarda karewama ke ki zauna a sassan kasa nida ita mu manne a sama mu sha amarcin mu ke kuma ki karata da karnin ki ke daya ko ba haka kike so ba? Nay murmushin izgilanci nima,amma fa shaguben sa ya taba zucia ta na rama abunda yake mun in nayi mai gatse nace'ka jishi kaman gaske.... Muka tuntsire da daria. Da wadannan hirarrakin muka fito (Boiend 745) muka fada jirgin dan kabo mai zuwa abuja. Muna sauka daga matattakalar jirgi na sha mamakin dimbin al'ummar da suka zo taryenmu,'yan jaridu, manema labarai da kuma wakilan national television authority tare da tawagar Minister of Foreign Affairs sunzo taryen ogansu. A gaba gaba na gane anti mubina, muhd bello, fati, abdulraheem, assha, taufiq, ibrahim, peter. A gefe 'ya'yan bello ne mukhlas da taheer sun kara girma sosai. Naji haushin rashin ganin jawad a cikinsu, sai nake kimanta girman da 'ya'yan bello a yanzun na tabbata zai fisu. Ga yayyuna awal da sani jingine jikin motarsu da yayar assha mansina. Ragowar duk ban gane su ba. Anti mubina na sanye cikin rantsattsen leshi ruwan kasa wato kalar da oga ke so sai washe min hakora take wanda yafi kama da kuka. Ta juya tasa hankici ta share wasu ambaliyar hawaye da majina da suka kawo mata ziyara cikin wayau da dabara ba tare da kowa ya gane ba. Ita ko zubaidar jifanta take da tsadadden murmushinta sai hantar cikinta ta shiga rawa. Ko farcen BLACK dinta a yau abun kallo ne,ga mata 'yan uwanta ma balle maza. Bar ta kayan kawar da take daure da su hannu,kafa,wuya,gashi da kunne tamkar haifaffar Morocco. Kalarta ko abu ne da zai saka a shakku,don bazaka ce baka ce ko fara ce ko wankan tarwada ba,kawai ita daban ce wato unique ko a cikin dimbin matan dake wurin. Da ta doso su wani lallausan kamshi kurum ke dukan hancinan al'umma tamkar don ita kadai aka halitto wannan mayataccen turare. Ita kam duk a yawon ta kasashen dunia,da sayen turarukanta har a birnin Paris,bata taba jin kwatankwacin irin wannan kamshin ba. Ga wata irin cika ta halitta komi nata ya kai ya kawo, tamkar reshen bishiyar da iska ke kadawa sannu a hankali. Da tayi murmushi hasken wasu fararen hakora kaman kankara ne suka dallare ta. Ashe dai wannan itace real zubaidahhh da takejin labari? [11/3, 8:38 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [11/3, 8:41 AM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔 ~BOOK 2~ ~THE END~ Tuna Baya2 120-127 End 121... Lokaci daya wani tunani yazo mata duk wani shiri da tay na kuntatawa rayuwar zubaidah ta karfi da yaji,sai ya warware taji zubaidah ta burgeta ta kuma bata sha'awa. Idan tace zata kawo fi'ili ko kishi akan wannan gagara gasar mace, lallai ita zata kwashi kashinta a hannu. Ashe dai da talaka da mai kudi duka daya ne a wurin Allah sai ma ya daukaka talakan ya dankafar da mai kudin a sanda Yaso,Shi Allah bbu ruwan Shi kuma arziki nashi ne bbu inda baya yinsa. Kamin kowa ya tadda zubaidah ta runtumo da gudu ta rungumeta tace my little sister kunzo lafiya? Yallabai aka saki baki cikin mamakin abunda tayi wanda ko a kokon ran shi bai kawo hakan ba, to bashi kadai ba ni kaina nay mamaki. Mu duka biyun muka doshi al'ummar mu masu aikin camera nayi masu video nayi, shashashun'yan jarida kuwa tambayoyi suke tayi mana 'yaya zaka kwatanta farincikin ka mai girma Minister a wannan rana? Ganin cewa mubina dango tay nadamar abunda ta aikata tay murna da dawowar zubaidah? Hajiya mubina yanzu kin yarda da kaddara kenan zaki zauna da 'YAR RAINON Ki,koko na yau ne kawai? Shin zaki kwato dan ki ne koko kin hakura kin bar mata kin amince RAINO MA WANI ABUNE MAI MUHIMMANCI GA UWA TA TSAYA TA RAINI ABINTA? Ko kallon su batayi ba,ya dawo gareni''Hajia zubaidah me zakice kan tonon sililin da dango tay miki a dunia cikin jaridun mu da kafafen yada labarai? Anya zaku iya yafewa juna? Muka dubi juna nida anti mubina muka yi murmushi. Wannan kadai ya ishe su amsar su na cewa nida ita duka bbu mai kuma TUNA BAYA. Illa rayuwar da zamu gina a gaba. Dani da ita muka fada motar gidan kwamishina ibraheem hardo, shi kuwa yallabai yabi tawagar ofishin sa ne shi da Bello haka yayyuna da sauran mazan har su mukhlas duk sunbi babanninsu. A motar daga ni har anti ba wanda yace da kowa komi, hakannan ba wanda ya kalli kwayar idon dan uwansa. Haka kawai naji na samu kaina da kunyar anti mubina amma ita sai na lura jikinta a sanyaye yake tayi ladaf tay lakwas ta sakko ta saduda,ta kuma yi dammarar zana na fisabilillahi. Gidanmu ya sha gyara sai ma'aikata ke kai kawo suna entertaining bakinmu,tun safe har dare muna ta harkar jama'a bamu zauna ba. Sai karfe goma sha dayan dare kowa ya watse. Sai masu gadin. Anti mubina ke ta kai kawo tana shirya local dishes bisa dinning abunda ya bamu mamaki daga ni har yallabai,a raina nace lallai dunia mai juyi. Ban taba ganin anty ta shiga kicin da zummar dafa koda ruwan zafi ba tsayin shekaru 8 da nay tare da ita,dunia mkrnt ta ishi dan adam riga da wando,babbar riga har da hula (mata mu mike don Allah mu gyara rayuwar aurenmu lokaci bai kure ba. Son jiki da girman kai bbu inda zai kai mu a zuciyar mazajen mu saidai ya dankafar da mu inji takori). Ta kammala jera komi ta jefe mu da cokalin dake hannunta tace kowa yaci girki na yau zai bani lambar dana cancanta. Yallabai ya dago daga wayarshi da yake latsawa ya galla mata harara yace 'makarantar girkin kika shiga ko yaya da za'a baki makin? Na lura bata ji dadin gwasalen da yay mata ba ni kaina banji dadin ba nace'rabu dashi antynmu dole ne ma ya bada makin irin wannan gara haka? Ta sadda kai tana murza 'yan yatsunta kawai shi da kansa ya lura bai kyauta ba. Ya kira sunanta ta dago ya sakar mata murmushi yace'to me aka shirya mana? Maman jawad ta hakika? Anan ne tay murmushi tabbacin ya faranta mata tace 'ni da ke fried rice nay mana sai stuff marrow da stuff cabbage,shi kuwa dama local dishes dinsa ne gaya nan' nace'kin kyauta antin mu ya harareni a lokacin da ya kai lomar farko yace antinki dai nikam bandani don haka ki daina jimilla. Tay serving kowannenmu da abunda yake so ba tare data kula da zancen sa ba don ta lura neman baki yake da ita,ta tura min plate dina itako taja gongonin heinz beans ta tsoma cokali tana sha banyi mamaki ba don Tom ya taba gaya mun wai ita bata cin abunda ya hau wuta ba. Bayan mun kammala cin abincin yallabai ya kira mu main falonshi,dukkaninmu yay mana nasihohi masu ratsa zuciya,ya nemi hadin kanmu kan zaman lapia na har abada a gidan sa don dukkannin mu kowacce da muhimmanci ta gareshi. Ya kare da cewa'banajin zubaidah sai ke mubina don Allah ki canza halin ki, ni kuma In Sha Allah zan yi kokari in kasance mai adalci a tsakanin ku. 122... To bayan watanni biyu ne na haife ki MAHASI, bayan matsananciyar nakuda, sunanki na usli MAIMUNATU kasancewar sunan fulani ne muke kiran ki mahasi. Rayuwa ta cigaba da gara mana yadda bamu zata ba da budi da cgb ta kowanne fanni. Anti mubina ta shayar da mu mamaki don daga ranar har inda yau ke motsi, bata taba kawo wani mugun hali ba. Mun dinke mun zama daya kamar Ya da kanwa don baka sani ba ko shigo gidanmu sai ka za ci ba kishiyoyi bane,Ya da kanwar ta ne. Duk wani akidun ta na banza da shirmenta na da ta rabu da shi tana koyi da komi daga gareni,hakana aikin ma ta aje shi ta daina sai kasuwanci. Saidai har gobe ita kanta tana da masaniyar cewa ita da ZUBAIDAH ba daya bane a zuciyar TAHEER. Ranar sunanki ne fatima ta gane cewa nice ATINEN BELLO. Data bude baki a ranar tafi minti ashirin bata rufe ba sabd mamaki da ta'ajjibi. Yadda akayi ta sani ma kuwa shine tana rike da ke a hannun ta tana fadin kamanninki da yallabai masu ban mamaki sai yay murmushi yace' Yar atinen-bello kenan ta koma 'yar fatin- bello... Bello yay murmushi a kunyace yana kawas da kai daga gareshi yace 'yallabai ai ba abun mamaki bane,tunda kuwa wani baya haihuwar dan wani kamar yadda wani baya taba auren matar wani. Wannan rubutaccen ne don haka ka daina TUNA BAYA..(past),just d present! Nidai fatana ko bayan raina inaiwa mukhlas rikon MAHASI. Hawaye suka zubo min na tausayin bello nay saurin daukewa kamin yallabai ya gani. Na tabbata Bello Waziri ba karamin kauna yake mun ba irin kaunar nan wadda har a nade dunia baza'a aina ba saidai alhmdlh yay dace da macen kwarai mai kaunar shi fiye da komi a rayuwarta. Kuma ko da ta ji nice atinen,ba abunda ya canza na amincin dake tsakanin mu. 123.... Hakika kauna ta gaskia wata aba ce da Allah Subhana ke dasa mana a zuci wadda kuma take a tsakanin abubuwa guda 2,samu ko rashi. Na sani na so Bello nd i still luv him(astagfirullah inji atine) shima yaso ni ba kadan ba to amma soyayyah ba itace aure ba. Allah bai kaddari akwai aure a tsakaninmu ba. Ya rigaya ya kaddaro cewa kowanne abokin rayuwarsa dabam ne dana dan uwansa wannan ne kawai abunda na yarda da shi. A tun ranar da aka haifeki a asibiti da mukhlas ya daukeki budar bakinsa sai cewa yay 'momyn jawad inasonta kyakkyawa ce zaki aura min ita? Nay murmushi nace'insha Allah ko bata son ka ka aureta ka gama muddin ina raye. Yallabai yace'balle ma me zai sa tace bata son shi? Alhalin ya fita kyau? Jawad yace 'a'ah daddy ban taba ganin kyakkyawar babe irin wannan ba, kamar ta daya da matata(fulani)'' Kowa yay daria. Dalili kenan da aka sa maki sunan fulani. Alkawari ne muka daukarwa bello da ni da mahaifinki na cewa a dunia baki da miji sai mukhlas wanda ko bayan ran mu muke fatanki taimakemu wurin cika shi. Na baki wannan labarinnawa ne don ki san falalar dake cikin biyayya ga iyaye da garabasar da ke cikin ta. Hakika wanda ya yiwa iyayensa biyayya,ya faranta musu shi ke da babban rabo a dunia da lahira,kuma wlh bazai taba tabewa ba sai dai yay ta cgb,da cgb da ganin farin ciki muddin rayuwar shi. Ki bar tunanin mahaifinki ya takura ki daya dage sai kin auri mukhlas ba wanda kike so ba. Yana son in da za'a so ki ne kamar yadda ake son mahaifiyarki. Uncle dinki da antynki fatyma masu kaunar mu ne da ko ba zancen aure tsakaninki da mukhlas,su masu rike ki ne da amana. Bello ya nunawa taheer halarci don daga wannan lokacin har yau shekaru ashirin da daya bai kara tada zancen ba,haka kuskuren da yay a baya ya nemi gafarar taheer yace sharrin zucia ne da son kai irin na dan adam wanda by nature kowa haka ne (kowa yana son kansa). Inda a take yallabai ya kalubance shi da cewa a'ah sharrin SO ne don haka baiga laifin sa ba. 124... Maimunatu Taheer (mahasi) 'yar kimanin shekaru ishirin da daya,daliba a jami'ar harvard amurka inda take kara2n likitar hakori mataki na biyu. Ta dago manyan idanun ta farare kal tana murmushi ta dubi mahaifiyarta tace'to momi baki koma kara2 ba? tace'bbu lokaci,gaba dayan lokacin rayuwata na TAHEER ne. Iyakar sa kenan sakandire. Sai bautar aure da ingatacciyar soyayya wadda har yau ake damata. Duk da ga furfura nan tsilli tsilli akan babanki ba abunda ya canza jiya i yau. We are meant 4 each oda. Raino wani bangare ne na jin dadin rayuwata. Don haka ne bayan ku shida dana haifa a cikina,kika ganni zagaye da 'ya'yan uwa duk kwato su daga hannun iyayensu ina RAINO. Na samu matsala a mahaifa bayan haihuwar mamman(MK) wadda an tabbatar mun bazan kuma haihuwa ba. To amma daga ni har yallabai ba abunda ya damemu ko da ace da ke da jawad kadai Allah Ya barmu kun ishe mu rayuwar dunia da lahira. Cikin firgici mahasi tace'kina nufin ba ke kika haifi nadir, umar, sauda, usman, zubaidah da nabilah ba? tace cikin murmushi ''Nadir dan abdulraheem da kanwata sadia ne,wadda daga baya hannu na ta dawo ta girma tay kara2 har ta shiga jami'a. Sauda diyar assha da alphat ce data sawa sunan inna na,amarya sabida kaunar dake tsakaninta da inna ta,usman kanin taheer karami ne watau dan bello ne fatyma ta kyautar mun tun daga lokacin yaye. Gabadaya 'ya'yan data haifa daga baya ni nake yaya mata su. Zubaidah diyar tom(taufiq) da matarshi maryam ya sanyawa suna na ni kuma na karbo na rike masu,shiko umar dan anti mubina ne wato kanin jawad ne.. Tace a dokance 'yauwa yanzu ina anti mubina? Kince mun ta dawo kun zauna tare alhalin ni tunda na taso ke kadai na taras nake kuma gani tare da daddy... Hawaye ya ciko idonta tasa hankici tana sharewa tace'ta rasu wurin haihuwar umar agaban mijinta 125.... Ashe ta dade tana fama da ciwon koda wanda 'hydroquinone' ya sanya mata bata fadawa kowa ba (hydroquinone yana cikin kayan shafe shafe wannan zamanin wanda mata da yawa suka raja'a akai da sunan canja launin fata ta hanyar toning, 'yammatasai a kula). Amma wlh har ta koma ga mahaliccinta musayen yawu wanna bamu taba yi ba. Ta danka min amanar jawad da umar tace ta tabbata a dunia bbu wanda zai rike mata su da amana kamar ni tace in rike taheer da kyau domin samun mutun irinshi a wannan zamanin wani abu ne da bazai yiwu ba,ko kuma a ce zai yi wuya. Yay kokari ya cika alkawarin da ya dauka na yin adalci a tsakanin mu da kokarin boye matsananciyar kaunar da yakemun akan idonta. Bamu taba yin wani abu da gangan wanda ya bata mata rai ba har ta koma ga sarki Allah. Wayar ta dake gefe ta shiga kidi mai dadi nuna alamun shigowar sako'text'. Ta mika hannu ta daukota cikin nutsuwa sako ne daga gudan ran ta MOHD JAWAD tun kamin ta karanta take murmushi data karanta sai ta zarce da daria. A takaice dai ga abunda jawad dake da ainin second lieutenant a barikin horas da sojoji dake jaji ya rubutowa uwarsa abin sonsa mama zubaidah. ''I grew up witout a care of a mother, but in all dis i realized u THE BEST MUM in d world..... Jawad.... Tace a cikin murmushi wanda baya rabo da kyakkyawar fuskarta 'Allah sarki jawad dina' Ta kira lambar shi a take ya dauka cikin zakuwa yace'hala momy kin manta da ni ne sbd 'ya'ya sun maki yawa yanzun? Ina my blvd sis? Tace'ka jira ni ina nan zuwa anjima kaima ka sani jawad in 'ya'ya sunyi dubu kai kadai ne nawa, dukkansu na RAINO ne.. Yay murmushin nan nasa cikin jin kansa ya fasu da kalamin mamarsa. Mahasi ta zaku a bata dan uwanta sai kokarin amsar wayar take a hannun momi,momin na sake zakulo sabuwar hira tsakanin ta da dan ta, shima yasan da gangan takeyi don yana iya jiyo magiyar da mahasin ke yi na a bata wayar yasan da gayya takeyi don ta kular da ita don idan akwai abunda mahasi ta tsana to wannan banbancin da momi ke nunawa akan jawad ne. Yace 'don Allah momi ki bani sister na. Tace 'tunda haka ne na fasa zuwa mahasin tazo ita kadai. Yace'ki rufamin asiri momi na tuba nabi Allah na biki har abada bani da wadda ta fiki,she is but a bloody sister... Ta mika ma mahasin tana murmushinta na UWA. Yau duk wani burinta na zama UWA ya cika. Ta RAINE su gashi a yau sun girma sun nagartu cikin kaunar junansu da kakkarfan zumunci mai dorewa har illa masha Allahu. Zubaidah(zuby) 'yar kimanin shekaru 3 ta taho da gudun gaske mamman ya biyota da duka tay azamar dauke ta tayi mata mafaka a bayanta. nadir ya taho yana kuka hannu a ido shi kuma cikin kawo karar saudat data gantsara masa cizo sai ta bar rabon fada ta koma alkalanci. Can kuma sai ga usman yace'momy kunu zan sha' Ta mike taje kicin ta dauko mishi zubaidar data sauke daga bayanta ta fashe da kuka cikin nuna rashin yarda da ajiyetan da akayi don a biya bukatar usman sai tay murmushi ta dawo ta goyeta sukayi kicin din tare..... 126... Mahasi data karbi wayar daga hannun momi sai tayi dakinta ta tsaya bakin taga daga bisani kuma ta dawo ta rufe kofar har da key wato za'ayi sirri kenan da ita da yayanta,wanda ba'a son momi taji. Tace 'yaya jawad kasan kuwa ina cikin problem? Yace wace irin matsala ko dai dadi ne yay miki yawa mahasi,tace cikin rishin kuka 'daddy ne yace bazan auri ahmed ba sai mukhlas kafi kowa sanin irin son da mukewa juna sbd Allah anyi mun adalci? Yace'haba my sis tun yaushe nake gaya maki ki rabu dashi wannan soyyr taku bbu inda zataje. A tunanina ko ba'a kwabe ki ba bazaki zabi ahmed ki bar mukhlas ba, kina da wanda ya fishi ne a dunia bayan ni da iyayenmu? Cikin hawaye tace a'a to amma ai shi din bai taba nuna yana so na ba ahmed fa? Kana ganin irin yadda yake basar dani yana..... Yace'ba dole ya basar dake ba tunda kin nuna ba kya sonshi kinfi son bare dashi? Idan kin kwantar da hankalinki mahasi,mukhlas is a nyc person nd he luvs u dearly. Gashi dan uwanki daya san ciwon kanki yasan darajar iyayenki me kike nema a aure bayan wannan? Me kike nema a ahmed wanda baya dashi? Uwa-uba zaki farantawa iyayenmu ki cika masu dadadden burinsu a kanki ta yadda zasu zamo masu farinciki dake akullum. In fact nima zan bata dake batawa ta har abada idan baki bi umarnin iyayenki ba. Tunda nake kin taba jin nay musu da momyna? 'yar shagwabar sai tasa kuka tace 'Allah Yaya jawad na daina na yarda zan auri mukhlas amma shima kay masa magana ya daina yi mun wulakancin da yake yi mun,, yana daria sosai yace'ba wulakanci yake yi miki ba ajinsa yake ja kada ki rainashi bayan kuma baki aure shi ba amma mukhlas bashi da abunda yake so a dunia tamkar ki. Maza share hawayenki je ki gayama mummy abunda kika gayamun yanzun. Ta share hawayen da 'yan yatsun ta uku da sassarfa ta fito ta cimma momyn har yanzu tana nan a inda ta barta. 27... Tana zaune da zubaidah akan cinyarta lokaci guda kuma tana sharewa mamman hanci da tissue tana bashi kunu a baki. Mahasi tay kasake! Tana kallon ta tace (cikin tadin zuci)''Ita dai momi haka Allah yay ta? Ba abunda take so a rayuwarta irin kananan yara,bata da burin da ya wuce na RAINON KANANAN YARA. Tana matukar kaunar ta ganta goye da jariri tana jijjigashi tana yi masa rawa tana cilla shi tana cafewa yana bangala mata dariyar kauna irin ta UWA. To ko wannan ne sanadin da ya sayo mata soyayyah ta kwarai a zuciyar mazan kwarai irin TAHEER da BELLO? Ga yallabai kusan haka ne amma ga Bello kare martabar TALAUCIN ta ne da sanin ciwon talakan babanta. Aduk abunda ta zama aduk kwabon data samu a duk inda ta tsinci kanta bata da abun ambato sai BABANTA da INNARTA. Komi ta samu sune,komi taci sai ta kai masu duk kuma wannan ta same shine daga daurin gindin mijin kwarai yallabai TAHEER. Suna masu sanya mata albarka har suka kwanta dama. Wanda albarkar ce har yau ke bibiyarta. Abun tambayar anan shine shin ko ita din zata samu irin wannan jin kan daga 'YA'YAN data RAINA? Ance juma'ar da zaty kyau tun daga laraba ake gane ta. Akwai alamu daga 'ya'yan baki dayan su na cewa basu da abun kauna tamkarta hada da iyayen da suka haife su kuwa.(kuna ina iyaye mata wadanda 'ya'yan da muka haifa acikinmu kadai muka sani?). Mahasi ta taho sannu a hankali ta ture zuby cinyar momi daya ta yiwa kyakkyawar fuskarta matsagunni a cinya daya kai kace itama zubyn ce 'yar kimanin shekaru 3. Ta lumshe ido cikin kara kaunar mamanta.tana murmushi tana share hawayen tausayin momin don a ganin ta wannan son wahala ce kadai Allah Ya dora mata(ita kam bazata iya ba,don bata ga dalili ba) tace'na yarda momi zan auri mukhlas idan har hakan shine farin cikin ku. Kiyi mun adduar Allah Yasa nima yaso ni irin yadda UNCLE da DADDY ke sonki. MASHA ALLAHU LA QUWATA ILLA BILLA. Karshen littafin Tuna Baya shine roko daga group of Hype hausa novels book whatsapp suka kawo muku Sai kunjimu asabon book din mu nagaba Mai suna********sai kunjimu [11/3, 8:41 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*