[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒐𝒏𝒆_ _Assalamu alaikum masoya. Fatan alkairi a gareku tare da barka da salla. Ya rabbi ka amshi ibadunmu ka yafe mana kurakuran mu. Ka gafartama iyayenmu. Kafin komai dole na fara da tarin godiya a gareku musamman wanda suka sayi kayan salla a wajena. ALLAH yabar zuminci. Nagode sosai da yanda kuka nuna ƙarfafawa a gareni akan wannan kasuwanci. Ina sake albishir a gareku da in sha ALLAHU wasu kayanmu na gab da sauka musamman abayoyi da handbags na yara dana manya. Sai kowa ya ƙara zuba kuɗi a asusu 😂. Gamu mun dawo filin daga. ALLAH ya bamu ikon sauke nauyin juna mu daku, ALLAH ya haneku cin hakkinmu, muma ALLAH ya hanemu tauye hakkinku 🙏. Godiya ta musamman gareku baki ɗaya 😘😘😘🙏_. .......Kuka nayi sosai a wajen. Dan har sai da kaina ya dinga sara min tamkar zai rabe gida biyu sannan na miƙe. Cikin layi irin na rashin ƙarfin jiki na koma ɗakin dana kwana. Handbag ɗina na ɗauka tare da hijjabin danai sallar asuba. Gudun haɗuwa da shegen karensa ya sakani bi ta kitchen duk da ban san takan gidan ba. Ta bayan na bi, hakan yasa har na zagayo inda gate yake banga karen ba. Zaram maigadi dake zaune yana jin waƙa ya miƙe. Bakinsa har rawa yake wajen gaidani. Ban amsa masa ba. Face cemasa “Buɗe min!” cikin kakkausar murya da tsawa.      Cikin daburcewa da wuru-wuru ya ce, “Amma Hajiya oga baice....”    “Wlhy idan baka buɗe min ba zan haɗa kai da ogan na danna muku zagi.” nai maganar ina fisgo sandarsa dake ajiye saman bench. “Zaka buɗe min ko sai na ɗora maka ita a saman kanka”.             “ALLAH ya huci zuciyarki Hajiya bara na buɗe”. Ya faɗa cikin rawar jiki yana nufar ƙaramar ƙofar. Key yasa ya buɗe, na watsa masa harara sannan na fice. Sai da na tabbatar na fita sannan na jefa masa sandarsa nai gaba. Dogon street ɗin nabi da kallo, mai ɗauke da lafiyayyen titi. Sam ban gane a wace anguwa bane ba. Dan haka hankalina ya tashi. Amma sam banji na sare ba na cigaba da tafiya sauri-sauri duk da rashin ƙarfin jiki da nake ji. Addu'a kawai nake ALLAH ya kawo mai napep. Kai koda mota ce zan nema taimako. Na ɗan yi nisa a tafiyar inayi ina waigen bayana dan ji nake kamar makirin zai iya biyoni. Jiri ne ke ɗibata sosai, dan kaina har yafara harmutsawa. Na ɗan tsaya ina mai dafe shi da ambaton sunan UBANGIJI. Dai-dai nan wata farar mota da har ta gittani ta dawo da baya.       “Baiwar ALLAH lafiya kuwa?”. Muryar matashiyar mace ta daki kunnuwana. Hannuna na janye daga saman kaina. Cikin kallonta dishi-dishi a wahalce na furta, “Bakomai hajiya.”         “A ya zakice ba komai. Gashi kinayi kamar ma zaki faɗi”. Tai maganar tana fitowa a motar. Riƙoni tai dan jirin ne ya ɗeban zai zubar. Muryarta da damuwa sosai ta ce, “Kinga bara na sakaki a mota. Sai ki faɗamin ina zaki na kaiki”.     Ganin mace ce, kuma dama abinda nake buƙata kenan sai banyi musu ba. Da taimakonta na shiga motar. Ina zama na lumshe idanuna kaina na ƙara ƙarfin sarawa matuƙa. Koda ta shigo ta zauna tana tambayata ina zata kaini kasa bata amsa nayi, hakan yasa tai shiru ta bani ɗan lokaci da take tunanin na samu nutsuwa sannan ta sake tambayata. Da ƙyar na iya furta mata. “Yakasai”.              “Okay ba damuwa. Amma ina ganin mu fara zuwa clinic sannan. Dan kina cikin halin buƙatar taimako. Ni likitace”.        “Karki damu ki kaini gida kawai na gode”. Na faɗa a matuƙar wahale.    “Bazai yiwu ba, kiyi haƙuri na taimakeki dan ALLAH”.     (Dan ALLAH) data ambata yasa ban iya sake cemata komai ba. Daga haka ma na sulale ban sake fahimtar komai ba.     ★     Hankali tashe maigadi ya nufi cikin gidan. A dai-dai ƙofar shiga falo ya samu Maash tsaye. Rikicewa yay, musamman da yay ma fuskarsa kallo ɗaya ya ganta a tsuke kamar hadarin gabas. Cike da tashin hankali ya zube ƙasa saman gwiyawunsa yana kwaso rantsuwa. “Wlhy tallahi ranka ya daɗe ba laifina bane ba. Tace idan ban buɗe mata ba zata fasamin kai ne.”      Shiru baice masa komai ba. Maigadi ya sake rikicewa yana jera rantsuwa da magiya duk a gurbi ɗaya. Sai da ya mula dan kansa a hankali ya furta, “Jeka kan aikinka”.    Duk da a sauƙaƙe yay furucin hankalin maigadi bai kwanta ba sam. Dan gani yake akwai abinda zai iya biyo baya. So yake ya cigaba da bada haƙuri har sai yasan ainahin gaskiyar abinda ke zuciyar mai-gidan nasa, sai dai kuma baiga muhallin yin hakan ba. Dan haka sum-sum ya juya bakin gate zuciyarsa na rawa matuƙa. Cikin taraddadi da ƙaulani ya koma, kusan mintuna goma da komawarsa yana zaune ya zabga tagumi akai horn. Firgigit ya tashi domin dubawa. Sai da ya buɗe ƙaramar ƙofa yaga mai horn ɗin sannan ya buɗe gate ɗin gaba ɗaya. Cikin girmamawa ya gaisar da Hayatu dake shigowa. Shi kuma ya ɗaga masa hannu yana ƙarasa shigewa cikin gidan. Yana fitowa a motar Laalah ya zaburo, inda yake yazo shi adole ya sanshi, hakan ya sakashi sakin murmushi da kai hannu ya shafa kansa yana faɗin, “Laalah how are you?”. Daga haka ya wuce zuwa cikin gidan.          Koda yay sallama a ƙofar sai da aka kwashe kusan minti ɗaya kafin a amsa masa, tare da bashi izinin shiga.  Sarakin na zaune tamkar babu abinda ke damunsa. Hasalima dukan hankalinsa naga wayar hannunsa ne. Koda Hayatun ya shigo ma bai ɗago ba. A haka ya amsa masa gaisuwar da yay masa. Sanin hali yasa Hayatu bai damu ba ya cigaba da maganarsa. “Sir Alhamdullah yanzu haka tana tare da ita. Sai dai tace akwai matsala. Dan tana shiga motar ta sume mata, a yanzu haka ma suna clinic, sun kuma tabbatar da jininta yayi matsanancin hawa da take buƙatar taimakon gaggawa saboda gudun samun matsala a zuciyarta. Amma nadai basu damar yimata dukan abinda ya dace”.        Karan farko ya ɗan ɗago ya kalla Hayatun, sai kuma ya maida kansa ga wayar batare da yace komai ba. Tsahon mintuna biyu kamar yama manta da shi sai kuma ya ajiye wayar a gefensa. Hannunsa ya ɗan matsa tare da ɗagowa ya zubama Hayatun idanunsa. Dole Hayatu yay ƙasa da nasa kan dan baya iya jure irin kallon nan na ogansa mai kama da na abokin yaƙi a filin daga..         Cikin silent voice ɗin nan nasa da janye idanunsa daga kansa ya furta, “A sanarma Hameed ya shirya zuwa 9 zamu wuce Abuja. Sai kai magana da Faisal zamu iso masa da mara lafiya ya taremu a airport”.     Sosai Hayatu ya zaro idanu waje. Duk yanda yaso haɗiye abinda ke masa kai kawo ya kasa hakan. Bai ma san sanda ya furta, “Amma Sir baka ganin tafiya da ita zai iya ɗarsama family ɗinta wani abu a rai kuwa? Jiya ne fa suka kawota nan a matsayin amarya. Kasan fa sunan arewa komai nasu na tafiya da addini da al'ada”.         Ko motsi Maash daya kwantar da kansa jikin kujera ya lumshe idanu baiyi ba balle Hayatu yay tunanin samun amsa. Ya kuma san shirun nasa na nufin bazai tanka ɗin ba, ya kuma gama zartar da hukunci kenan. Jiki a sanyaye Hayatu ya juya zai fita. Yayinda yake ta sake-saƙen mai fishshesa a zuciya. Dan dolene fa suyi wani abu da zai gamsar da family ɗin ta. In ba hakaba akwai babbar damuwa fa, kwaɓarsu zata iya yin ruwa batare da sun farga ba, shi komai ma sake ruɗar da shi yake. Dan yarasa dalilin ogan nasa na ƙulla igiyar aure tsakaninsa da ƴar bala'in yarinyar nan. Tunda yasan idan amsar video ɗin nan yay niyya da tuni ya amsa tako wace hanya ai, duk da dai ya fahimci itama yarinyar akwai taurin kai, sannan tana da power a cikin al'umma game da aikinta, maybe shiyyasa ogan nasa yaƙi yin komai kai tsaye a kanta ya biyo ta wannan sigar. Gashi bai sanar masa komai akan shirin nasa ba. Hasalima sai a jiya shima ya san da batun auren bayan sun baro Lagos a jirgi yake sanar masa. Ya shiga shock matuƙa, sai dai bashi da hurumin iya cewa komai tunda ya riga ya zartar da hukunci, amma ya yini ya kwana al'amarin nan na juya masa a rai. Dan duk duniya shine kaɗai kuma yasan Maash ɗin yayi wannan auren, ko su dangin yarinyar basu san shine ba, saboda baije musu a Maash ɗin ba. To koma dai miye, shi kam zaiga yaya wasan zai kaya, dan shi ɗin shaida ne, ogansa mutum ne mai tsananin taurin kai da aljananci na gaske. Ga hatsabibancin masifa da dagiya akan abu, ya tabbatar ba son yarinyar nan yake ba, dan inda hakane kai tsaye zaije yace yana sontan saboda shi bai iya ɓoye-boye ba tamkar bature yake komai nasa kai tsaye yake yinsa. Ko minene a ransa kai tsaye yake fiddashi koda bazai ma kowa daɗi ba shi babu ruwansa idan yayi dai-dai da ra'ayinsa kansa kawai yake kallo..      Kai tsaye anguwar su Samraah ya nufa, dan dolene yaje ya tsara abinda ya dace gudun samun akasi.. ★★★    A gidan Abba kam sai a safiyar yau ƙananun magana suka fito sosai. Dan kuwa Mom ta titsiye Abba taji komai daya faru a wajen ɗaurin aure dama kafin ɗaurin auren. Dan haka ta shiga bazama na kusa da ita su kuma suka ɗauki zance ƙus-ƙus. Tun anayin abin a gwargwaɗe har dai komai ya fito cewar bada Mansoor aka ɗaurama Samraah aure ba da wani ne daban. Dan mahaifiyarsa ta shata layi akan auren nasu, duk da dai shi Mansoor ɗin yaso bijirewa amma su Kawu Musa suka ce bazasu bashi ba saboda abinda mahaifiyar tasa tazo tayi a jiyan har gida batare da matan cikin gida sun sani ba sai su Gwaggo Gudidi kawai. Tun dai zance na iya cikin gida har maƙwafta suka fara shigowa jin gulma da kawo wadda suka jiyo a waje. Yanda Mom ta nuna farin cikinta a fili akan abinda ya farun ya ƙona zukatan su Gwaggo Gudidi da ƴan Gwarzo. Sai ga faɗa ya kaure tsakaninta da Aunty Jimmai babbar ɗiyar Kawu Musa. Kafin kace mi gida hargitse. Suka haɗu sukama Mom tatas, dan babu abinda suka manta basu faɗa mata ba har sai da tai kuka. Kuma Gwaggo Gudidi ta tabbatar mata indai tana raye sai Abba ya ƙara aure. Da ƙyar da ƙyar dai Musaddiq ya kwantar da wannan tarzoma. A kusan kuma dai-dai lokacin Hayatu ya iso gidan. Inda ma ALLAH ya taimaka Musaddiq da Abba da su Kawu Musa na ƙofar gida a lokacin da ya iso ɗin, dan haka ya samu tarba ta mutunci. Cikin ɗar-ɗar da addu'a a ƙasan ransa bayan sun gaisa ya sanar da su abinda ke tafe da shi kamar yanda ya tsara domin bama ogansa kariya. Hankalinsu ya tashi da jin Samraah babu lafiya. A take babu ɓata lokaci suka muƙe domin binsa asibiti dubata. Bai hanasu ba, dan bashi da wani zaɓi, sannan hakanne ma zai taimaka masa tsarin nasa ya tafi dai-dai yanda yake buƙata batare da Maash ya rufta ba ko shi dake ɗan kore ba.........✍️ Hummmm🥱 _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒐_ .......Hankalinsu ya tashi matuƙa da ganin yanayin Samraah a asibiti. Yayinda Dr Su'adah ta sake ruɗar da su da bayanin haɗarin da Samraah ke ciki. Tare da tabbatar musu idan ba'a sadata da ƙwararren likitansu dake birnin tarayya Abuja da zama ba za'a iya rasata, dan zuciyarta na gab da bugawa saboda yanda jininta yay tsananin hawa sama. Sam babu wanda yay musu akan yarda da hakan. Sai dai sun nema alfarmar Hayatu akan Musaddiq zai bisu zuwa Abuja ɗin. Rasa abincewa Hayatu yayi, dan ya tabbatar tafiya da Musaddiq bazai yiwu ba. Amma rashin mafita sai ya amsa musu da to su jira suji daga likitar yaya za'ai tafiyar. Sun gamsu da hakan, dan haka ya lallaɓa ya koma gefe ya sake samun Dr Su'adah akan ta taimakesa ya fita a tarkon mutanen nan, dan yana da dalilin da yasa baya so kowa ya bisu. Ita dai Dr Su'adah bata san ainahin mike faruwa ba, dan Hayatu ɗan uwanta ne na jini, abinda ya gaya mata kuma bashi ne ainahin alaƙar dake tsakanin Samraah da Maash ba. Dan haka babu musu ta taimaka masan. Ita ce ta tsara su Kawu Musa ta hanyar da dole suka gamsu akan za'a fara tafiya da Samraah ta jirgi ne, masu son bin bayanta sai suyi hakuri subi a baya ta mota nan da kwana biyu haka. Haka kawai sai hankalin Musaddiq ya kasa kwanciya, sai dai babu yanda zai yi tunda su Kawu Musa sun yarda. Haka dai yana ji yana gani aka shiga yima Samraah shirye-shirye dan wai za'a wuce da ita ne a jirgin ƙarfe takwas na dare...         ★✓★✓★✓★✓     *_ABUJA AIRPORT_*         Ƙarfe tara dai-dai jirgin daya taso daga Kano zuwa Abuja ya sauka a filin jirgin na birnin tarayya. Maash da tawagarsa na ɗaya daga cikin passinges ɗin wannan jirgi. Hakama Samraah da likitan da take tare da ita suna a jirgin. Sai dai a tsarin tafiyar sam babu abinda ya alaƙantasu da Maash. Hasalima shi yana a private section ne. Yayinda ita da likita suke a sashen kowa da kowa, koda yake ita bama ta a hayyacinta balle ta fahimta. Dan an shigo da ita ne a yanayin wadda take bisa umarnin likita da zataje gani a Anuja. Ko'a airport ɗin ma tuni Maash ya shige ɗaya daga cikin tawagar jerin motocin da suka zo ɗaukarsu. Yayinda ita kuma ambulance ta ɗauketa ta wani babban private asibiti da ake matuƙar ji da shi anan birnin Abuja ɗin.. *_KANO_*          Anan Kano an wuce da Samraah an bar danginta da jimamami. Musamman ma Musaddiq da sam zuciyarsa ta kasa zama waje ɗaya. Kai shi tunma jiya hankalinsa a tashe yake da wannan aure. Sai dai babu yanda ya iya tunda su Kawu Musa sun bama mijin da suka aura matan yarda ɗari bisa ɗari. An ƙarasa dai wannan dare cike da jajantama juna bisa ga halin da Samraah ɗin ke a ciki. Daga ƙarshe dai a washe gari kowa ya shirya ya kama gabansa saboda wayar da akai da mijin na Samraah akan jikin da sauƙi suka ganta ta hanyar video call. Taro dai ya tashi an bar Mom da mijinta sai auta da Musaddiq da Hafizzullah kawai a gidan dan su Baby basa nan. Sai a washe gari suka dawo gidan. Hafizzullah ma dai shirin komawa makaranta yayi, duk da yaso zuwa wajen Samraah Musaddiq ya lallashesa akan yayi haƙuri tunda an kusa musu hutu, yanzu zuwa Abuja dubata ba nashi bane, shima ɗin da akace zai je su Kawu since ya dakata kada mijin yaga kamar ana nuna ya gaza ne. Badan yaso ba ya shirya ya wuce zuciyarsa duk babu daɗi. Dan duk wani masoyin Samraah ɗin zuciyarsa a ƙuntace take da abinda ya faru akan wannan aure da kuma halin ciwo da take a ciki yanzu. Dan idan ta shine ma baza'a ɗaura mata aure da wani da bata sani ba tun farko. Amma dai su Kawu Musa sun bada goyon baya babu abinda su zasu iya musamman ma shi dake amsa sunan ƙani a wajenta. Amma zai cigaba da binta da addu'a kamar yanda Yaya Musaddiq yace yayi. Musaddiq ɗin ne ya kaisa har Katsina da kansa. Ya sake masa nasiha sosai sannan ya juyo gida.....           *_MANSOOR_*      Kowa ka kalla a ahalin gidan hankalinsa a tashe yake. Dan kusan duk manyan suna a sashen su Mansoor da aketa ƙoƙarin gaggaɓe ƙofar ɗakinsa. Yau kwanaki uku kenan yana a kulle a ciki yaƙi ya fito. Lallashin duniya da roƙo yay biris da kowa. Tun ana ɗaukar abin nasa a fushi na ɗan lokaci har abin ya wuce makaɗi da rawa, dan zuwa yau ko motsinsa an bar ji a ɗakin, dole fa aka nemo mai gyara domin gaggaɓe ƙofar. Kuka sosai Mamynsu keyi tun jiya, dan ita kanta har sai da hawan jininta ya motsa. A yanzu haka a nane take da ƙofar ji take mai aikin ma kamar baya sauri ne.         Ana ɓalle ƙofar mafi yawansu duk suka afka ciki, tsakanin Attahir da Mamy har turereniyar rige-rigen isa ake kan Mansoor dake kwance samɓal a ƙasa babu alamar rai a tare da shi. A tare suka ɗagosa, sai dai me yaraf ya koma alamar babu rai. Wani mahaukacin ƙara Mamy ta fasa mai firgitarwa, tamkar ƙiftawar ido sai gata ƙasa wanwar itama ta sume musu. Sake harmutsewa ɗakin yayi, dole aka kwashesu zuwa asibiti kamar yanda wasu suka bada shawara.....                 *_ABUJA_*     Kaifin hasken rana da nake ji mai ƙarfi a saman fatar idanuna ya sani motsasu a hankali. Sosai sun min nauyi, dan illahirin jijiyoyinsu a takure suke waje guda. Hannuna da nake ji kamar an ɗaure nai ƙoƙarin motsawa domin kaiwa saman idanun, sai naji an sake damƙesa da ƙyau, tare da jin saukar wata murya cikin kunnena. “Bi a hankali akwai abu a hannunki. Sannu kin farka bari nai kiran likita”.         Sosai naji gabana ta faɗi. A can ƙasan zuciyata na ayyana (likita) a fili kam babu abinda nake iya motsawa a jikina saboda illahirinsa yay min nauyi. Amma sai na shiga ƙoƙarin buɗe idanuna. Dishi-dishi nake gani, sai dai hakan bai hanasu sauka akan mutumin daya shigo bayansa da wasu mata guda biyu ba saboda yanda hayaniyar maganar da suke taja hankalina. Duk da ba ihu suke ba ko fidda sautin maganar tasu da ƙarfi. Ƙarasa buɗe idanun nayi da ƙyar sakamakon jin inuwar mutum a kaina. Wani irin faɗuwar gaba naji ta sake riskata, dan kuwa tabbas a asibiti nake, dan shigar wanda ke kaina tsaye kawai ta tabbatar min da shi ɗin likita ne. Sannu suka shiga jeramin, sai dai na gagara amsawa kowa a cikinsu, na dai zuba musu ido ne kawai ina binsu da kallon ƙurilla. Ko tambayoyin da likitan ke jeromin game da jikina na gagara amsa masa ko ɗaya. Fahimtar kamar a rikice nake da yanda nake bin ɗakin da kallo ya sakashi ƙyaleni shima. Sai cikin matan da ya shigo da su ne ke ƙoƙarin cire min allurar drip dake a hannuna. Kusan mintuna biyar muna a haka kafin ya sake juyowa ya fuskanceni. Cikin harshen turanci ya furta. “I understand that you are confused. This is a hospital, you are under the care of a doctor. Alhamdulillah, your body is very easy.”         A hankali na kai hannuna saman kaina da har yanzu nake jinsa da nauyi, kafin na sake ɗagowa na dubesu murya a karye na ce, “Who brought me? Which hospital is this? Since when have I been?”.     Da alama yanda na jera tambayoyin sun bashi mamaki, dan sai da ya ɗan waro idanunsa, sai kuma yay murmushi da faɗin, "Oh relax! You will all know. Now they will help you to fix your body, eat something and I will come back and answer your questions". Ya ƙare maganar yana nuna min Nurses ɗin. Fuska na ɗan ɓata, sai dai bance komai ba. Shi kuma ya juya ya fita da Nurse ɗaya ya barni da biyu. Da farko naso naƙi yarda, dan nafi son na fara sanin a ina nake. Sai dai yanda suka nuna damuwarsu da tabbatar min ƙin yardata zai iya taɓa aikinsu yasa na amince. Amma zuciyata taƙi gajiya da daina kai-kawon ganin ɗakin da naken matsayin wai asibiti. Saboda sam bai kama da asibiti ba fa, duk da gado da tarkacen ɗakin duk irin na asibitin ne, sai dai da gani na musamman ne su. Ga television ga freight, sannan toilet da suka kamani suka kaini a cikin ɗakin dai yake shima sam bai kama da asibi ba. Ciwon da jikina kemin ya sakani bin umarninsu nayi wanka da ruwan da suka tara min mai ɗumi. Nako ji daɗin wankan, na saka doguwar riga irin wadda na cire pitch color da alama ta asibitin ce. Bata sauka min har ƙasa can ba sosai, amma dai banyi tsirara ba. Gashi tana da faɗi babu wani takura. Alwala na ɗauro na daddafa bango na fito. Da sauri suka iso gareni suka taimaka min muka ƙarasa, a saman lallausar sofa ɗin ɗakin nace su zaunar dani, sannan na buƙaci hijjab na salla da sallaya. Sai dai da alama babu, sai ɗaya ce tace bari ta sanarma doctor a kawo min. Komai bance ba, na jingina kaina da kujerar na lumshe idanuna. Bata fi mintuna biyar ba sai gata ta dawo da sallaya da sabon hijjab a ledarsa. Ita ta ciromin shi, sannan ta shinfiɗa min sallayar. Har ƙasa hijjab ɗin ya sauka min sosai dan ko ƙafafuna ba'a gani, hakan yasa naji nutsuwa dan dama rigar bai gama sauka ba. Juyawa nai na tambayesa "What day is today?". A tare suka amsa min da, “Today is Monday”.       (Litinin) na maimaita a zuciyata. A zahiri kam sai na sake tambayarsu alƙibla. Ɗayarce mai kama da musulma duk da shigarta zata iya saka kace ba musulmar bace amma akwai ƙaton tabon salla a goshinta ta nuna min tare da bayani, bance komai ba na kabbara sallata. Tun inayi a tsaye har hakan ya nema gagara. Dan dole na koma a zaune kasancewar duk sallolin da nasan suna kaina sai da na ramasu na kwanaki biyun nan da bana a hayyacina.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ .......Tun ina sallan shigowar doctor biyu. Sai dai ganin ban idar ba yana komawa. A na ƙarshe suka shigo su biyu dai-dai na idar ina zaune kawai nayi tagumi cikin dogon nazari da son sanin a ina nake wai. Jin muryar da banyi zato ba kasancewar nasan na kuɓuta daga garesu yasa na ɗago da sauri. Shi ɗinne kuwa. Wato yaron mugun nan Maash. Ganin yanda ina ɗagowa ya duƙar da nasa kan ƙasa kamar wani munafuki ya sani cigaba da kallon nasa kawai. Doctor ne ya katseni da tambayar yaya nake jin jikina yanzu. Cikin janye idanuna na amsa masa da Alhamdullah. Ya nuna jin daɗinsa kafin yay min nuna da mutumin nan. “Now you will get all the answers to your questions from him. I will send a nurse with your medicine. If you eat, she will give you.” daga haka ya juya ya fita. Shiru ɗakin ya ɗauka kusan na minti ɗaya, kafin a ƙufule cikin dasashjiyar muryata mai nuni da banda lafiya na furta, “Ya akayi na dawo gareku? Ina ne nan kuka kawoni?”.         Sake duƙar da kai yayi kamar mai tsoron bani amsa, sai kuma a hankali ya furta, “Kiyi haƙuri nan asibiti ne. Yaya jiki?”.      Wani irin takaici ne ya ƙuleni, dan haka cikin sake zafafa harshe na amsa shi da, “Ba ruwanka da jikina. Kaje ka sanar ma wanda ya aikoka yasa likitan nan ya sallaman. Sannan ku fita a sabgata. Idan ba haka ba zan sakaku nadama da dana sanin sani na. In ba hakaba zan tabbatar muku TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE”. Daga haka na yunƙura a hankali na miƙe, ko inda yake ban sake kallo ba na koma saman gadon. Dai-dai nan Nurse ɗin nan ta dawo... *_KANO_*.   A matuƙar tashin hankali zuciyar Mamyn su Mansoor ta gama shiga. Dan suna isowa asibitin ta farfaɗo ita. Amma Mansoor kusan awani uku kenan likitoci na tare da shi ba kuma su musu bayanin komai ba. Sai dai faman kaiwa da komawa suke a tsakanin ɗakinsa zuwa ofisoshinsu. Tun tana hawaye har ma sun ƙafe ta koma na zuci. Nadama take ji na sake shigarta akan abinda ta aikata. Lallai tayi dana sanin biyema shawarar ƴar uwarta. Inama zata iya maida hannun agogo baya. Data goge komai da yake a yanzu da maida baya data shuɗe. Dan har ga ALLAH Mansoor shine ɗa mafi soyuwa a zuciyarta. Kodan tasha matuƙar wahala ne a yayin haihuwarsa, ko kuwa dan kamanin da yake da mahaifinsa. Sam bazata iya jure rasashi ba. Dan bazata taɓa yafema kanta ba.        “Mamy dan ALLAH ki zauna ki huta, in sha ALLAHU ɗan uwana zai tashi. Kinga kema fa ba lafiyar ne da ke ba”. Attahir ne mai maganar cikin tsantsar damuwa ganin yanda Mamyn tasu ke faman kai kawo ga hannunta dafe da kanta. Yasan komai zai iya faruwa da ita, dan bata gama dawowa dai-dai ba ta fito a ɗakin da aka kwantar da ita. Anyi-anyi kuma taƙi ta koma dole aka haƙura aka barta. Dan Dad ɗin su ma haushin dagiyar tata ya sashi komawa can gefe ya zauna kawai bai sake kulata ba.          “Attahiru bazaka gane ba. Nasan bazaka fahimta ba. Barni kawai kaji. Barni da abinda ya dameni. Ni da kaina na jefa rayuwar yarona a bala'i. Da nasan haka zata kasance da ban aikata ba. Da ban hanashi aurenta ba. Attahiru idan na rasa Mansoor nima zaku rasani ne wlhy”.      “Dan ALLAH Mamy ki daina faɗa. In sha ALLAHU bazamu rasaki ba. Ki kuma daina zargin kanki kowa baya wuce kuskure ai. Mansoor zai samu sauƙi. Ki masa addu'a”.      Kuka mai nauyi ta sakar masa tana ƙoƙarin dafe bango saboda jirin dake neman yaddata taji ya kwasheta. Da sauri yayi kanta ya riƙota. Da taimakonsa suka zauna yana jera mata sannu. Dai-dai nan shima Dad ɗin su ya taso, hakama ƙannensu da suka haɗe kai gefe suna kuka. A ruɗe duk suke tambayar miya faru, sai da ta ɗago ta ce musu ba komai sannan suka shiga sauke ajiyar zuciya. Hakan sai yay dai-dai da fitowar amintaccen likitansu Dr Gana. Kamar waɗanda aka zabura duk suka miƙe garesa har Mamy. Har rige-rigen tambayarsa yaya Mansoor suke yi. Shiko ya ɗan bisu da kallo cikin damuwa. Sai kuma a hankali ya furta, “Alhaji idan babu damuwa na ganka a office mana. Amma Hajiya tai zamanta Please”.        Tsantsar tashin hankali ne ya bayyana a fuskokinsu. Yayinda Mamy ta fashe da kuka sauran ƙanensu na tayata. Shi kansa Dad ji yay ƙafafunsa sun masa matuƙar nauyi. Haka shima Attahir ya gagara tashi har sai da doctor ya sake musu magana sannan. Attahir ne ya fara jarumtar miƙewa, sannan shima Abban ya tashi suka nufi office ɗin su biyu kowanne na jin zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri tamkar zata faso ƙirazansu ta fito waje.....        _Ni kaina Bilyn ku zuciyar tawa bugawa take. ALLAH yasa dai ba rasa Mansoor mukai ba😭😭🙆._ *_ABUJA_*        ★Sosai na birkicema likitan nan akan nifa sai nasan a inda nake. Hankalinsa ya tashi, dan ya tabbatar min in har ban kwantar da nawa hankalin ba aikinsu zai iya komawa baya. Ganin fa ba saurarensa zanyi ba ya sanar min in a Abuja ne cikin MAASH HOSPITAL.       “Abuja?!”.     Kansa ya jinjina min da sauri. “Yes, yes. You were brought from our branch in Kano. Once you have finished receiving the medicine, you will return. Please calm down”     Rasama mi zance masa nayi, sai kawai nayi shiru ina kallon PA da suka shigo kusan tare. Shi doctor ya zata na fahimcesa ne, dan haka ya sauke ajiyar zuciya da cigaba da kwantar min da hankali. Ko kulashi ban sake yi ba. Har ya gama ɓaɓatunsa ya fita. Ɗauke idanu nai da ga kan PA ina mai cije lips ɗina da ƙarfi. Na fahimci waɗan nan mutanen so suke sai mun kai matakin ƙarshe da su. So suke sai na bijire ma maganar Yaya Musaddiq da Mansoor. So suke sai na musu fallasar da zata ruguza dukkan tanadinsu. Kamar PA ya fahimci mi nake ayyanawa a raina. Takowa yay ya ƙaraso gaban gadon ya ajiye ledar hannunsa. Kafin ya ciro wayarsa a aljihu yay ƴan danne-danne batare da yace komai ba ya ajiye min saman table da akai crossing a tsakiyar gadon da magunguna a kai da dama sune Nurse zata bani na birkice musu. Harara na ɗago zan watsa masa sai idanuna suka sauka akan fuskar wayar. Tamkar waccan ranar yanzun ma tar-tar nake ganinsa. Yanda ya kafeni da shegun idanunsa kaifafa kalar na maguna ya sakani sake ɗaure fuska tare da ƙarasa antayawa PA ɗin nasa hararar da nayi niyya. Sai dai ashe shi harma ya fice ya barni da wayar. Wani irin takaici ne ya sake ruƙunƙumeni. Dan haka na rumtse idanuna da ƙarfi ina jin matuƙar zafi a raina. Kafin na buɗesu gaba ɗaya a fusace kan wayar. Shiko shiru yay kawai yana kallona da kaifafan idanunsa da nake jin tasiri su har a cikin jinina. Duk da yanda nake jin tasirinsu ban janye nawa dake masa kallon tsana da takaici ba. Cikin kaushin harshe da disashiyar muryata ta marasa lafiya na furta, “Kai ko akwai zuciya a ƙirjinka?”.         Shiru babu alamar zai tanka min, sai ma janye idanunsa da yay a wani kalar slowly ya maida kan laptop dake gabansa. Dan alamu ya nuna kamar a study table yake zaune. Cikin sake jin wani sabon baƙin cikin na kai hannu saman kaina dake sara min. Fahimtar bazai amsa min ba ya sani cigaba da faɗin, “Anya kai Musulmi ne?”.       Cak ya tsaya daga barin abinda yake yi, dan haka ya ɗago muna kallon juna cikin ido, idanunsa sun wani kaɗa blue ɗin gwaiduwar tsakkiya ta ɓace ta zama siririya like mage sak. Zamansa ya gyara na ƙasaita da isa da ke tabbatar da shi matsayin ingarman namiji, ga wani irin shegen kwarjini da nake ji ya mamaye ɗakin har kamar na matsu kai kace a gabana yake mayen. Ganin haka ya sakani cigaba da maganata batare da na damu da duk abubuwan dake tattare da shi ɗin ba.        “Idan har kai musulmi ne bana jin kasan HARAMCI da HALLACIN dake cikin dokokin addinin musulunci. Idan kuma har da zuciya a ƙirjinka tabbas bata masu IMANI bace. Ina mai baka shawara kada kai wasa da wuta a tafin hannunka, dan wutar da UBANGIJI zai ladabtar da ma'abota bijirewa ta ninka wadda ake girka maka shinkafa a duniya kaci sau dubu bisa dubu. Idan baka sani bane zan faɗa maka a yanzu ni ɗin MATAR WANI CE. igiyoyin AURE ne a kaina ba igiyoyin ɗaure dabba a turken turka ba. Kaji tausayin kanka, da gujema saɓama UBANGIJI ka maidani inda ka ɗakkoni gidan aurena hannun MIJINA da IYAYENA.”           “Idan nan ne GARIN AUREN ni ne MIJIN kuma fa?”. Ya faɗa cikin wata iriyar muryar dakiya da gizago mai tsarga zuciya. Dan yanda sautin amon muryar tasa da kaifinta ya tasirantar da furucin nasa a tsakkiyar kaina kaɗan ya rage zuciyata bata ɓullo ta bakina ta fito ba. Amma duk da hakan sai ga tari mai ƙarfi ya sarƙe min numfashi. Gaf-gaf jikina dake a cikin yanayin rashin ƙarfi ya fara rawa. Bamma san lokacin da bakina ba ya furta “MIJI?!”. Sai kuma kaina yay wani irin masifar sarawa da ban taɓa ji ko tsinkayen irinsa ba. Ga nauyi da idanuna sukamin har inajin jijiyarsu na ja kamar za'a fincike min su. In dai har wannan ake kira hawan jini to tabbas ya sameni kuwa a yanzun nan. Dan ƙirjina kansa yay wani irin nauyi. A karo na biyu hankalina ya sake neman barina. Nai yaƙin maidosa jikina tare da ɗagowa ina kallonsa domin son tabbatarwa. Amma a maimakon amsa ma da nake buƙata garesa hankalinsa kwance yake cigaba da aikin gabansa. Wani irin kallo nake masa mai kama da firgici, yayinda shima ya zuba min nasa cat eyes ɗin cikin yanayin i don't care tamkar zai cinyeni da su. Cike da salon izza da ƙasaita ya wani sake tsuke fuska da yamutseta sannan ya furta, “Har yanzu kina da sauran dama. Domin guri bai ƙure miki ba na komawa inda kika fito. Ki bama yarona video ko fadar inda yake a ɗakko gobe ki koma garinku. Saɓanin hakan cigaba da dawwama ƙarƙashin mulkin mallakar Maashhhh. Ke baki mori rayuwar taki ba. Ba kuma ki iya yin komai akan abinda kike tunanin iyawa ba”.........✍️ Yayanmu Barka da salla, ban sani ba ko a duniyarku kunyi azumin kuma🥱👩🏻‍🦯. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓_ .......Wani irin sake sarawa kaina yayi, dole na kai hannu na sake dafesa tare da saurin dafe ƙarfen gadon dan ji nake zan zube ƙasa, hasalima sam bana fahimtar maganganunsa a yanzu. Sai kalamansa ne na farko ke faman maimaita kansu a cikin kaina cikin matuƙar amsa kuwwar data zarce ƙarfin muryar daya sanar min su. (Idan nan ne GARIN AUREN ni ne MIJIN fa?) Kalamansa suka shiga min amsa kuwwa a cikin kunne tamkar wadda akema shelarsu. Gaba ɗaya ma brain ɗina ta toshe, sai nake jin kamar na kasa fahimta ko fassara su a bigiren daya dace. (Kai ina wannan gangan ne) wani gefe na zuciyata ya ambata. (Samraah dawo cikin hankalinki mana) sashen zuciyar tawa dai ya sake maimaitawa. Hannuna dake a saman kaina na sauke tare da kaisa saman kumatuna na ɗan bubbuga, dan nafi tunanin mafarkine kawai. (Kai amma wannn mummunan mafarki da muni yake) na sake faɗa ina bubbuga fuskar sosai da ƙarfin gaske kozan farka. Zafin daya ratsata ya sakani rumtse idanun da ƙarfi. A masifar jigace da ƙoƙarin haɗiye hawayena na ce, “Wai kai minene alaƙarka da ni ne? Mi kaje ka ƙulla? Miye matsalarka dani?”.        Idanunsa ya ɗauke da ga kaina gaba ɗaya. Sai kuma ya ɗan taɓe baki alamar yanzun ma bazai tanka min ba. Rainin wayonsa ya gama zuwa min ko ina. Dan haka na fisgi ɗan ƙarfen dake cikin tasar asibiti a gefena na ɗago ina kaisa saman cikina cikin soyewar ido data zuciya. “Dana zauna da kai a matsayin miji gara na kashe kaina na san ban mori komai a rayuwata ba.”        Idanunsa dake min wani kallon ƙasa-ƙasa ya sake ja luuu kamar zai rufesu gaba ɗaya. Sai kuma ya buɗesu warr cikin yanayin i don't care manners ya furta, “So! Ai ba hanaki zan ba. Abinda kawai nake buƙata kafin ki mutum ki bani video”.       Wani irin sakartaccen kallon tsana da takaici nake masa. Na cije lips ɗina da masifar ƙarfi. “Har abada kuwa buƙatar taka bazata biya ba. Dan wannan videon bazai taɓa zuwa hannunka ba har gaban abada.”      “Ashe kuwa ko kin mutu gawarki zata cigaba da zama a gareni. Ahalinki kuma zasu cigaba da amsar hukuncin laifinki”.           “Idan kuma kai na kashe fa?”. Na faɗa ina jefar da ƙarfen cike da tsantsar fusata da tafi ta ɗazun. Idanunsa ya ɗan zuba min, sai kuma cikin nuna rashin damuwa ya janyesu yana wani shegen annamimin murmushi daya ƙona min rai.       “Oh are you threatening me? Ai game dani ba wasan yara bane ba. Har yanzu bamu fara wasan ba, balle ki tunanin samun game over. Zan iya baki damar kwanaki domin shiryawa. Ba kince kinfi ƙarfin laɓewa bayan wani domin faɗan sunƙuru ba. To gana gaba-da-gaba nan kin samun bissmillah. Matsoraciya kawai. Kwana uku kacal har kin fara banbance tsakanin aya da tsakkuwa”.       Bamma san lokacin da wani irin ƙarfin zuciya yazo min ba. Cikin tsantsagwaron ɗaukar alwashi da tsawa na ce, “Har abada nafi ƙarfin yin laushi a hannun matsoraci irin ka. Dan ni har yanzu banga MAZANTAKA ba anan tunda sai da ka laɓe a bayan aure yanzun ma. Kasaka a ranka daga yau ni Samraah bint Abdul-wahab Gwarzo, sai na sakaka lissafin lissafa kwanakin rugujewarka daga yau har zuwa ranar dana ɗeba maka da zan kuma koma ga masoyina. Ni nan sai na sakaka gudu, gudu irin wanda babu wajen zuwa a tsakkiyar sahara mai tsananin zafi rana da ƙarancin ruwa. Wlhy sai kasan ka ɗakko KARA DA KIYASHI. zakuma kasan TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE”. Daga haka na ture wayar ƙasa batare da na jira jin abinda zaice ba. Sai ma wani irin izza da ƙarfin iko da naji yana ratsa gaɓɓaina, duk da sara min da kaina yake tamkar zai rabe biyu. Sai kuma hawaye sharr suka shiga kwaranyomin masu zafin gaske....        (🥱🥱tofa irin wannan alwashi haka Sam-G).          💦💞💦💞💦💞    “Magana ta gaskiya Alhaji yaronka Mansoor na cikin haɗari. Sai dai akwai mafitar da in na baku shawara kuka gamsu da ita ina fatan za'a dace......”       Cikin tarar numfashi da taune harshe Dad ya furta, “Ka faɗi ko minene mu masu baka goyon bayane Doctor. Bama son rasa Mansoor dan ALLAH ka taimaka mana”.     “Wannan duk na ALLAH ne Alhaji. Idan kuma muka cigaba da roƙonsa shi mai amsawa ne. Shawarar dama itace ai gaggawar barin ƙasar nan da shi zuwa India. Akwai ƙwararren likita dana sani game da ciwonsa. Kuma inada yaƙinin in sha ALLAHU zai basa dukan kulawar da muke buƙata koma fiye da ita. Sannan ku shirya yaƙi na gaskiya game da nisanta komansa da abinda ya sake jawo wannan matsalar tasa da mukai tunanin ta barsa tun a shekarun ƙuruciya. In ba hakaba akoda yaushe komai zai iya faruwa magana ta gaskiya”.        Sosai zukatansu suka ƙara raunana da zancen Doctor. Dan duk dakiyar Attahir sai gashi yana share hawaye. Basu wani yi ja'inja ba dan basa fatan rasashi, tun ma yana yaro sanda matsalar ke da zafinta basu nutsu ba balle yanzu. A take aka fara shirye-shiryen fita da Mansoor zuwa India. Abinka da masu hannu da maiƙo, cikin kwana ɗaya da yini komai ya gama kammala. A cikar kwana na biyar da ɗaura auren Samraah da Maash aka wuce da Mansoor. Da ga shi sai doctor da Attahir ne suka wuce. Su Dad kuwa sai nan da kwanaki biyar saboda tsaiko da aka ɗan samu game da visa ɗin Amal. Duk wani masoyinsu ya bisu da fatan alkairi. Yayinda tausayin Mansoor ya sake cika zukatan wasu. Wasu ko nama iyayen nasa ALLAH ya ƙara kasancewar koma a wane hali yake sune suka jaza masa. Dolene kuma sakayyar Samraah ya bisa. Dan gashi itama ance babu lafiya har an wuce da ita asibiti. Dan tun a randa aka wuce da ita Abuja labari ya shiga kunnuwan mutane sakamakon shegen surutun Mom da ita take faɗa cike da nuna jin daɗi. Dan itafa jinta take fes uwa ya zuciyar sabon jariri haihuwar yanzu. Har faɗama mutane take ai mijin Samraah ɗin dama irin kwatakwalin yaren nan ne shiyyasa ma ya wuce da ita Abuja ɗin dan ya kaita ga danginsa a bata jiƙe-jiƙensu amma babu wani asibiti duk joni ne dan kar ai mata dariya. Wasu dai sun hau sun zauna, yayinda wasu ke fassara al'amarin nata da hassada kawai. Duk da dai mutane ba ganin mijin Samraah ɗin sukayi ba. Kowa dai batun an ɗaura aure da sunan wanda aka ɗaura ɗin mai suna Muhammad Mu'azz kawai sukaji. Sai kuma waliyayyansa da kowa ya gani ƙuru-ƙuru da ido dan wasu ma harda video sun ɗauka domin yaɗawa a media kasancewar Sam-G ɗin cele ce, yanda auren nata ya canja akala cikin ƙanƙanin lokaci sun san zai jawo magana. Ya kuwa jawo ɗin, dan har a yau da yake cika kwana biyar cif da ɗaurawa ba'a daina yawo da hotunanta da ƙananun magana ba harma dana Mansoor. Sai dai duk bin ƙwaƙwƙwafin mutane na son ganin sabon ango da iyayenta sukai mata auren huce haushi da shi har yanzu babu wanda ya gani. Duk da anata editing hotonta da maza daban-daban matsayin ita da angon nata. Masu ƙarancin hange sun yarda, masana da hangen nesa sun ƙaryata. Daga baya ma dai abokan aikinta da yawa sun fito sun ƙaryata ba ita bace editing ne.. ★★★★ Gwaggo dan ALLAH ki daina kukan nan hakanan. Ni wlhy ba wai ba zanji shawararki bane ko maganar ki. Ba kuma ina tsoron Jalilah bane da har zan gagara ƙara aure. Kawai dai ni ra'ayina kenan zama da mace ɗaya.”       “Ra'ayinka ɗin banza da wofi Imamu. Har ni zaka gayama wani ra'ayinka can na yahudanci. Mika rasa ko wane sharaɗine baka cika ba na ajiye mace fiye da ɗaya? Kaje bazan sake magana ba. Amma ka sani wlhy in dai na haifu cikin Balkisu da Usama bazan sake shiga sabgar zuri'arka ba. Sannan ina so daga yau ka saɓe hannunka daga ƴaƴan ƴar uwarka. Dan ba sai gobe ba a yau ɗin nan Musaddiq zai dawo wajena da zama. Shima Hafizun yana gama makarantar nan zai dawo. Kaje ka cigaba da rayuwarka da naka ƴaƴan da matarka tunda dama haka take so kai ma kake so ku rayu daga ku sai ku batare da wani ya raɓeku ba saboda kada mu rage muku jin daɗin duniyarku..”         “Amma Gwaggo dan ALLAH k.....”    “Na gama magana ta Imamu, tashi kaban waje. Ka dai tabbatar min bani na haifeka ba kuma na amince da hakan. Sai dai Alhamdullah bakai kaɗai bane ɗa balle hakan ya dameni, gasu nan bila'adadin harda jikoki duk mun godema UBANGIJI”. Daga haka ta miƙe ta bar masa falon. Da kallo kawai Abba ya bita zuciyarsa na kai-kawo tamkar zata fito. Babu abinda ke dawo masa a rai sai furucin mahaifiyarsu a lokacin da take gargarar barin duniya dan jinya tayi mai tsanani, kuma Gwaggo Gudidi itace ta kula da ita har ta koma ga ALLAH. (Imamu kona bar duniya nayi imanin baku rasa uwa ba kai da ƴar uwarka. Dan haka in har kuka bijirema umarnin ƴar uwata ban yafe muku ba. Kuma in har ina da hakki a kanku a matsayina na mahaifiya nasan bazaku taɓa ganin dadai ba. Ku ƙyautata mata, ku bita tamkar yanda zaku bini in sha ALLAHU zaku ribantu da hakan ba kuma zakuyi kukan rashina ba). Sosai tsigar jikinsa yaji ta tashi da tuno wannan magana. Dan tamkar a yanzu ne mahaifiyarsu ke faɗa masa shi da ƴar uwarsa mahaifiyar su Musaddiq. Bayan rasuwar ta kuma Gwaggo Gudidi itace ta cigaba da riƙe su. Itace tai musu aure da ga shi har ƴar uwarsa. Bata taɓa kuma gazawa ba a ɗawainiyarsu data ƴaƴansu har zuwa yanzu da tsufa ya risketa. Anya kuwa idan ya butulcewa wannan baiwar zai ga dai-dai? Bakin mahaifiyarsu kuwa bazai kamashi ba? Dan yana ƙyautata zaton shine ma ya taɓashi a yanzu abubuwa ke masa gangal-tangal uwa ya motar tirela mai ɗauke da siminti akan gadar icce dake tsakkiyar teku, dan yasan wasu kaso na rashin mutuncin da Jalilah ta dinga ma Gwaggo nasa a baya. Sai dai baisan miyasa baya iya tsawatar mata ba duk da abin na masa matuƙar ciwo a zuciya. Sannan yana matuƙar ƙaunar Gwaggo Gudidi, yana kallon fuskar mahaifiyarsu ne akan tata fuskar saboda tsananin kamannin da sukeyi. ya rabba yana a cikin tsaka mai wuya, dan baya jin zai iya ma Jalilah kishiya, yana kuma tsananin tsoron bijirema Gwaggo Gudidi bakin mahaifiyarsu ya kamashi.........✍️       _🥱To Abba adai sake tunani._        _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒗𝒆_ ____________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 _____________ .......“Alhamdulillah, I am very happy today we will send you off. I am very happy with the way you calmed down and gave us your cooperation. May God give you good health and protect the future”.       Murmushi na saki kaɗan ina jinjina kaina. Kafin a hankali na furta. “Thanks you doctor”.       “Ni ya kamata nayi godiya”. Dariya yanda ya haɗa hausar  da yanayin fitar kalaman ya bani, amma sai banyi ba nai murmushi kawai. A ƙasan raina ina jinjina karamcinsa gareni duk da kasancewarsa ba ƙabilata ba, sai dai ya nuna min kusancin musulunci dake tsakaninmu yafi na ƙabilancin. A kusan tare muka miƙe ni da shi, a dai-dai nan akai knocking ƙofar ɗakin jiyyar tawa. Kai tsaye ya bada izinin shigowa. Cikin gurɓatacciyar hausa hamshaƙiyar mace fara tas ƴar duma-duma tayi sallama ta shigo. Kallon cikin ido mukaima juna. Sai kuma matar ta janye nata tana maidawa kan doctor tare da rissinawa tana gaisheshi irin dai girmamawar ƙabilu. Ya amsa mata da kulawa. Sai kuma ya nuna mata ni. Hankalinta ta sake maidowa gareni tana murmushi. Sai kuma cike da kulawa ta gaidani da jiki. Amsa mata nayi a ɗarare, dan haka kawai naji matar batai min ba. Sai dai me bayani naji doctor na mata akan ya gama komai daya dace sai ta wuce dani. Kallonsa nayi a firgice zanyi magana sai kuma zuciyata ta ƙwaɓeni dan na tuna aljananci da hatsabibancin mai asibitin. A take na canja yanayi kawai na fara masa godiya.            Nurse ɗin da suka kula da ni ne sukai min rakkiya har inda motar matar take. Babu abinda zuciyata take face luguden daka da saƙawa da kwancewa. Dole fa a wannan karon na kuɓutar da kaina dan wannan ce kawai dama ta ta ƙarshe ta ƙuɓuta a hannun mutumin nan. Saboda zuciyata ta gama tabbatar min shine ya turo matar nan, idan kuma bashi bane to tabbas zai iya min wani tarkon da ita kamar yanda akai min a Kano sanda na baro gidansa.       “Ya rabba aiko nayi mantuwa”. Na faɗa dai-dai ina ƙoƙarin shiga motar da Semi ta buɗe min. Su duka kallona sukai, amma sai na sake zabura cikin hanasu damar min tambaya ina faɗin su jirani zan ɗakko na dawo yanzun nan. Yanda naga babu wacce tai yunƙurin bina nasan sun fahimceni, daga haka nai gaba cikin ɗan sauri-sauri da sassarfa irin ta mai gaggawa. Ina tabbatar da na ɓacema ganinsu na canja hanya. Duk da a rikice nake hakan bai hanani nemawa kaina dakiya ba na fara tafiyar nutsuwa. Da ƙyar nake iya gane inda nake jefa ƙafa har ALLAH ya fito da ni wajen wasu fanfuna da igiyoyin shanya. Akwai mutane tsiraru a wajen suna wanki, da alama wajen an tanadesa ne domin haka. Caraf idona akan hijjab dake shaye a igiya, tuni na tuɓe na jikina na ja wancan na saka, ɗan kwalin abayar jikina na naɗa a fuska tamkar niƙab. Daga haka na fito a wajen. Tambaya na dingayi har ALLAH yasa na fito a cikin asibitin gaba ɗaya dan babu laifi babbane sosai. Ajiyar zuciya mai haɗe da hawaye ne ya kufce min ganina akan titi, sai dai babban tashin hankalin banda ko sisi a jikina banda kuma abin siyarwa sisi. Ba kuma zan yarda kowa yaban lift ba dan an koyan hankali a baya. Haka na shari titi ina addu'a, ganin nayi nisa sosai da Asibitin zuciyata ta tabbatar min da zafa su iya biyo bayana su ganni duk da na canja hijjab. Ai tuni na kauce a titi na shiga wani street da naga an rubuta a ƙaramin symbol dake farkon shiga. Ganin an rubuta street nasan komai nisa zan fita, dan haka na zage damtse sosai naita tafiya duk da rashin ƙarfin jiki ga kuma rana mai zafi dake dukana ban damuba.....          ★★★....   Tun su Semi na irga mintuna har suka kusan haɗa ashirin. Mamaki ne ya kamasu, dan haka ɗayar nurse ɗin tace Bara ta duba Samraah ko ta ɓata hanya ne. Mintuna uku da wasu sakanni ta dawo a hargitse tana sanar musu itafa bata ganta ba. Sannan mutanen dake ata wajen sun tabbatar da bata dawo ba. Su dukansu har matar da doctor da aka je aka sanar mawa rikicewa sukayi. A take kuma doctor yay kiran Hayatu a waya...         Tako ina an bincike asibiti babu Samraah. Har cctv footage aka bincika, sai dai ta iya gaba kawai aka ga shigarta wajen inda ake wanki, kasancewar ta wajen babu camaras ɗin sai ba'a fahimci komai ba. Saboda ta canja hijjab sannan ta fita, ta inda ta fitan ma camara na wajen yana da matsala. Matuƙa Hayatu ya tada musu da hankali, gashi yayi kiran Maash ya sanar masa amma sai yaƙi ce masa komai. Ya kuma san minene ma'anar shirun ogan nasa, dan haka ya sake birkicewa ya birkita likita da Nurses har ma da matar nan da tazo ɗaukar Samraah ɗin. Kai dama kowa na asibitin dan har securitys basu tsira ba da sauran ma'aikatan...         💦💞💦💞💦    Ƙuuuuu!! Razanannen taka birkin ya karaɗe illahirin titin tare da sautin ihu mai firgitarwa. Ba hamshaƙiyar matar dake cikin danƙarereiyar motar kawai ba, hatta da mutane dake kai kawo a street ɗin tuni sunyo caa. Sosai Samraah da aka kusa kaɗewar ta matuƙar razana, dan durƙushe tai ta cusa kanta a cikin ƙafafunta nuna alamar sadaƙarwa kawai. Haushi da takaici ya saka mutane yimata caa da faɗa, dan duk wanda al'amarin ya faru akan idanunsu sun tabbatar da laifin ta ne ba mai motar ba. Ganin yanda wasu ke ƙoƙarin kai mata duka ma adalilin yanda har yanzu taƙi motsi daga durkuson razanar da tai yasa matar dakatar da su da sauri ta hanyar riƙota ta miƙar. Rawa jikin Samraah ya cigaba da yi har hakan na rinjayarta tamkar zata faɗi. Duk wanda ya kalleta yasan a gigice take har yanzu, dan haka matar ta shiga bama mutanen daketa faman hargowar zagin Samraahn haƙuri tare da jan hannunta ta buɗe motar a gefen mai zaman banza ta sakata. Sai da ta rufe sannan ta sake fuskantar mutanen da har yanzu sun kasa barin wajen..        “Kowa yayi haƙuri dan ALLAH kuma mu mata uziri. A yanayin halin rayuwar da ake ciki yanzu muma zamu iya tsintar kammu a fiye da yanda yarinyar nan take ciki yanzu. Tun dai ma komai bai sameta ba ai Alhamdullahi ko, sai muyi fatan ALLAH ya kiyaye gaba”.      Da kalmar (Amin) suka shiga amsa mata cikin nuna gamsuwa da yabama ƙyaƙyƙyawar zuciyarta, dan ba kowa bane zai iya yin abinda tai ɗin. Daga haka kowa ya fara watsewa itama ta shiga motar dan ta tsarema mutane hanya har wajen ya fara tara mutane musamman masu gadi na cikin gidaje nata fitowa. Bayan rufe motar ta ɗan kalli Samraah ta sauke numfashi mai kauri, batare da tace komai ba taima motar key cike da ƙwarewa ta harbawa saman titi da ƙyau. Tafiyar da bata gaza mintuna uku ba ta samu waje ta gangare gefen titin, dan bata son tai nisa da anguwar ta zamto kuma anan yarinyar take duk da ta ganta da niƙaff a fuska. A yanzu ma dai yarinyar kanta ƙudundune yake a cikin ƙafafunta, yayinda sautin shashshekar kukanta ke fita kaɗan-kaɗan.       “Ɗiyata a ganina godema ALLAH ya kamata muyi, dan da abinda yaso faruwa ya faru da ga ni har ke da ba wannan matsayin muke ba ai. Kiyi haƙuri ga ruwan nan kisha ki samu nutsuwa ko”. Shiru kamar bazata motsa ba, kusan cikar minti ɗaya kuma sai ta ɗago, Samraah ƙyaƙyƙyawace sosai ta yanda hawayen da suka ma fuskarta kaca-kaca bai hana bayyanar hakan ba.       Idanu na tsira mata mai haɗe da sauke ajiyar zuciyar dawowa hayyaci, sai kuma na kauda kai na, a hankali na furta, “Ba kukan tsorata nake ba Hajiya, kukan baƙin cikin rashin tabbatuwar abinda nai fata ne ya sakani kukan nan. Inama ace kin kaɗeni na huta da wannan rayuwar da babu komai a cikinta face kayan ƙunci da baƙin ciki da ruɗani. Inama ace kin kaɗeni na mutu banko shuraba na tafi tafiya ta har abada da babu dawowa na iske su Abbana. Hajiya dan ALLAH ki fitar dani a motar nan na sake tarar gabanki ki bi takain.....”          Cikin sauri ta katseni da faɗin, “Haba haba ɗiyata wace magana kenan! Miyay zafi haka da irin waɗannan furuci masu tsauri. Ai duk da mun san zamu mutu bama fatan mutuwar a kayinmu sai dai dan babu makawa sai ta zo ne. Amma muna addu'ar a koda yaushe ALLAH ya jinkirta mana kodan tara ayyukan alkairi da neman gafarar UBANGIJI da ga na sharri da muka aikata. Minene matsalarki? Miyasa kike ma kanki fatan mutuwa a wannan ƙarancin shekarun naki da zamu iya kallo a matsayin yanzu ma kika fara rayuwar, ko kika fara buƙatar ta? Idan ban shiga abinda ba hurumina ba ki daure ki sanar min ko zan iya fahimtarki da taimakonki da wani abu....”             “Ba taimako nake buƙata ba Hajiya, sannan babu wani abin sha'awa ko birgewa da ƙawatarwa a labarina ko bayana. Ganni ki barni a yanda kika ganni yanzu kawai.” na ƙare maganar da yunƙurin ɓalle murfin motar zan fice. Da sauri Hajiyar ta riƙoni tana girgiza kai. “A'a ɗiyata yi haƙuri ki saurareni”. Juyowa nai na ɗan kalleta, sai dai bance komai ba........✍️ _Kuyi haƙuri da wannan Please. Zuwa anjima idan na samu damar yin wani zan ƙaro muku. Wlhy abubuwane suka min yawa amma ina fatan kammalawa na dawo muku da ƙarfina😘😘_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙_ ........A hankali ta ɗan sakar min murmushi da faɗin, “Ko zaki iya mun alfarma”.       Cikin ƙosawa nace, “Tami?”.    “Ta sanin inda zakije yanzu?”. “Ban san inda na nufa ba, sai dai ina fata da addu'ar koma ina ne ya kasance hanyar cimma ajalina”.       Ɗan jimm Hajiyar tai kamar mai nazari, sai kuma ta saki murmushi mai ban mamaki tana wani juya idanu cike da salo, “Bazan hanaki tafiya ba, amma zan so ki bani dama ta ƙarshe muje gidana, maybe zan iya nuna miki hanyar cimma nasararki ta barin duniyar kamar yanda kike fata”.       Idanu sosai na tsira mata tamkar mai son tankaɗe gaskiya da rairayeta akan fuskarta, kusan minti ɗaya na ɗan kauce zuciyata na ayyana min na bita na samu mafaka koda na wasu kwanaki ne, dan na tabbatar a yanzu na koma Kano makirin nan zai iya bina. Kuma Abba da su Kawu bashi ni zasuyi, amma yanzu idan na laɓe a bayanta zan iya kiran Yaya Musaddiq muyi shawara dan shiga Kano kai tsaye yanzu haɗari ne. Sai dai kuma ita kanta bawai ina jin na yarda da ita bane ba ma ai. Amma bari na gwada sa'ata mugani. fuskata na ɗago na ɗan kalleta da faɗin, “Kina so kiyi wasa da hankalina ne kawai Hajiya”.     Da sauri ta dakatar da in da faɗin, “Ko ɗaya ba haka bane ba. Mizaisa nai wasa da hankalinki ni kuwa, dama kawai nake buƙata daga gareki zaki tabbatar da abinda na faɗa ɗin in sha ALLAHU”.         Nan ma dai shiru nayi ina kallonta kawai, tai saurin faɗin, “Ki yarda dani koda na sati guda ne, idan kinga ba hakaba zaki iya ɗaukar mataki kowane iri”.      Shiru na sake yi na wasu ƴan sakanni kamar mai nazari, sai kuma batare da nace komai ba na dawo da jikinna cikin motar sosai tare da jawo ƙofar na rufe kamar yanda take. Sosai Hajiya ta sauke ajiyar numfashi da har ya bani mamaki, sannan ta ɗan kalleni, sai dai batace komai ba. Nima ban sake cewa komai ba ina dai addu'a a zuciyata ALLAH ya hanata nasarar cutamin, ALLAH kuma yasa ba daga ƙarƙashin makircin makirin nan Maash tazo gareni ba.           ★(✷✷✷‿✷✷✷)★      Tunda Hayatu yake bai taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba musanman a yanzu da yake waya da Maash yana mai sanar masa guduwar Samraah daga asibiti. Dan Maash ɗin yayi wata ƴar tafiya ne ta gaggawa, tunda ya fara harkar business duk inda zai je yana tare da Hayatu, amma a wannan gaɓar ya barsa saboda al'amarin Samraah da ya kasance da ga shi sai shi suka sani.        Har tsawon mintuna biyu babu alamar Maash zai amsa. Kuma yana online. Hankalin Hayatu ne ya sake tashi, muryarsa har harɗewa takeyi wajen sake faɗin. “Wlhy nayi duk yanda kace Sir, zaman jiran isowarsu gidan kawai nake ma amma tai kirana wai basuganta ba. Ba laifina bane, ba daga ɓangarena bane aka samu kurkure ka yarda dani. Ka kuma bani izinin sanarma ƴan sanda na tabbatar tana cikin garin Abuja bata isa fita ba”. Shiru nan ma Maash yaƙi ya tanka. Wayar Hayatu ya cire daga kunnensa ya duba, har yanzu yana online ɗin dai tankawar ce bazai yi ba. Yafi kowa sanin halin Maash yanzu, dan ko iyayensa bazasu faɗa masa hakan ba. Ko motsi da idanu ogan nasa yayi yakan fahimci yaren balle. Ya tabbatar shirunsa a yanzu na ɓacin rai ne, kuma bazai tanka masa ɗin ba har sai idan shine yaso hakan. Hakan kuwa akayi, bai tanka masan ba shi kuma ya kasa yanke kiran saboda shakka, haka ya haƙura akaita ɗibar masa kuɗi har tsahon fin awa sai da shi uban gayyar ya gaji dan kansa ya yanke kiran sannan hayatu ya kai zaune cikin kujera jagwab dan tun ɗazun ko zaman ya kasa yi. Kansa kawai ya dafe yay shiru zuciyarsa na gudu. Dole ma duk yanda zai yi yayi dan gano yarinyar nan kafin cikar awanni ashirin da huɗu. Idan ba hakaba yasan akwai matsala.....          💞💞💞💞    Wata shegiyar dariya Alhaji Sadisu mai agogo babban aminin Abba ya saki harda ƙyaƙyƙyewa. Cikin ƙuluwa da nuna jin haushi kuwa Abban ya zuba masa idanu. Sai kuma ya yunƙura zai tashi amma Alhaji Sadisun ya riƙosa yana faɗin. “Afuwan afuwan Imamu. Wlhy abin naka ne zabban dariya. In kana abu sai naga kamar wani ɗan yaro bai mai garjejen saurayin ɗa kamar Abbas ba. Yo banda abinka Gwaggo ai gata tamaka wlhy. Ka buɗe bakin aljihu kawai malam musha biki ai ba wuce auren kai ba. Dama dai kaine kaso maida kanka pastor zama da mace ɗaya shekara fin ashirin bayan ALLAH ya baka dukan rufin asiri. Yo ALLAH na tuba da ana yin fin huɗu da ba tuni nayi ba”.         “Amma dai ai na sanar maka matsalata ko Alhaji Sadisu. Kuma kaina shaida ne akan halin Jalilah tunda na gwada son ƙara auren a shekarun baya har sau biyu amma aka nema nakasa yaran mutane.”     “Yo dan ta samu nasara a baya sai akace yanzu ma ka karaya zata samu. Alhaji Imam zama namiji kaji, tun farko kai ne kake ɓata shirin dama da kake sanar mata da wuri. Kayi shirunka yanzu har sai ɗinyar makaho ta nuna a hannunsa sannan ka bada filin fara wasan jifa tunda tsoronta kake ji”.            “Humm bazaka gane ba kawai, amma zan iya yarda da shawararka akan ɓoye matan. In kuma hakan zata faru fa sai dai na nema auren a wajen kano.”     “Wannan duk mai sauƙine, kabar komai a hannuna kawai. Kai dai jeka ka fara shirin gyara inda amarya zata zauna nan da sati ɗaya zan maka jagora kai da kaina sai ka gode min saboda inda zan kaika wlhy”.     Murmushi Abba yay a karo na farko, dan haka kawai yake jin kuma batun ƙara auren na sake masa tasiri a zuciya....        🥱Hummm Abba cin amana ko. _________★        Gida ne mai ƙyawun gaske madaidaici muka isa a anguwar mai tama kamar yanda na gani a symbol, dan komai najin daɗin rayuwar gani da ido a kwaishi. Ƙamshi da tsarin gidan yafi komai ɗaukar hankalina, dan haka nake ta ɗan kalle-kalle a kaikaice. A karo na babu adadi Hajiya da tuni takai zaune cikin ɗaya daga kujerun falon ta dubeni ganin yanda nai tsaye a farkon shigowa. Cike da kulawa ta ce, “Ƙaraso ciki mana ɗiyata. Kar kiji wani shakku ko tsoro, wannan shine gidana anan Abuja, sai dai bana zaman daya wuce sati biyu a cikinsa a duk ƙarshen shekara. Sai kuwa idan wani uziri ne ya kawoni nakanzo nai kwana ɗaya biyu har ma zuwa uku wasu lokutan na koma. A yanzu haka ma kwana biyu ya rage na wuce”. A hankali na haɗiye yawu alamar son cewa wani abu, sai dai kafin nace ɗin Hajiya ta katseni ta hanyar ƙwala kiran sunan “Janny!”.       “Yes Ma'am”.   Wata murya ta amsa daga can gefen wata ƙofa da hanyarta aka shirya kujeru da tebiri. Kafin na gama nazarin tsarin da kujerun dining ɗin sukayi da zamansu a wajen wadda Hajiya ta kira da Janny ta fito. Budurwa ce itama sai dai zata girmeni sosai, da gani shigarta da uban gashin attachment dake saman kanta ya isa baka amsar ba musulma bace. Cike da girmamawa Janny ta sake gaida Hajiya tana ɗan satar kallonna. Nuna ni Hajiya tai da faɗin, “Kije da ita ciki, tai wanka a bata abinci”.     Murmushi Janny tayi a karo na farko, cike da girmamawa ta amsawa Hajiya tana nufoni. “Sannunka”. Abinda Janny ta faɗa kenan tana mai riƙo hannuna. Ban amsa mata ba, sai ma ƙoƙarin turjewa da nayi alamar bazanje ba. Hajiya dake kallonmu ta sake sakin murmushi. “Kinga ɗiyata nasan mike a ranki, karki damu shi komai na rayuwa mataki-mataki ne tamkar ajin makaranta. Ki kwantar da hankalinki zamuje gaɓar da kike buƙata. Bani nai miki alƙawari ba”.       “Amma Hajiya.....”   “Shiiii!! Kar kice komai bita kawai”. Hajiya ta faɗa cikin katseni tana tsuke fuska a karo na farko. Canjawar fuskar Hajiyar ya ɗan firgitani, dan haka nabi Janny kamar yanda aka bata umarni tun farko....      Cikin dauriya da danne duk abinda ke mun kai-kawo a cikin rai nayi wanka na fito fes dani cikin doguwar riga mara nauyi ƴar kanti da Hajiya ta bani na saka. Ga wani ƙamshi mai daɗi na tashi a jikina. Hatta da dunƙulallen gashina da zaman asibiti yasa baya samun gyara sai da na wanke na busar da hair dryer dana gani a toilet ɗin. Yanda na fito da shi ne a buɗe yasa Janny sakin baki tana kallona. Fuska na ɗan tsuke amma sai hakan bai sata yin shiru ba sai da tayi magana. Da ga ƙarshe ta laƙemin wai zata tayani gyarawa. Mai sosai Janny ta saka min masu daɗin ƙamshi da ma wasu abubuwan da suka sake miƙar da tsahon gashin nawa daya fara dankwafewa tsaff, sannan ta fake min shi a ribbons. Ni a karan kaina sai da naji daɗin kan nawa dama a kwanakin nan ya isheni da ƙaiƙayi. Shiru nayi kawai zaune ina ƙarema kaina kallo, a take naji tausayin kaina ya kamani. Wasu hawaye masu zafi da ɗaci suka shiga sakko min. Hannu nakai na sharesu da sauri, saboda tuna nayi alƙawarin bazan sake kuka ba akan halin da nake ciki. Plate ɗin da aka kawo min na abinci na ɗan tsurama ido, sai kuma na tureshi gefe dan bana buƙatarsa a yanzu duk da uban ƙamshin dake tashi mai tabbatar da abincin zaiyi daɗi koda banga minene ba. Zamewa nai kwance a saman lallausan carpet ɗin da shima ke ta tashin wani irin ƙamshi mai daɗi, gashi tsaf babu datti. Gajiya da wahalar dana sha ya sa barci yin awon gaba da ni cikin ƙanƙanin lokaci..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ ......“Madam bafa taci abincin nan ba, ko buɗe plate ɗin ma batai ba kuma tayi barci.” Janny ta faɗa cikin nuna damuwa.      Ƙaramar dariya Hajiya ta sauke tana wani lumshe idanu, sai kuma ta buɗesu akan Janny cike da salon irin na wayayyun mata da suka gogu da sanin duniya. “Barta yunwar ai ba ƴar  gidansu bace, dan kanta ma zata ɗauka taci”.       Dariya tayi itama Jannyn da jinjina kanta. “Hakane Madam. Amma yarinyar yana da ƙyau fa sosai, ina ka samo shi haka? Ko dashi zamuje Lagos ne?”.          “Tsintacciyar mage ce, dan haka ma na dawo da tafiyarmu gobe kafin ta canja shawara. Saboda na kula babbar kaddarace wannan, kwalliya da sutura kawai take buƙata”.       Sosai Janny ta washe haƙwara, dan duk hausar da Hajiya tai tsaff ta gane kasancewar taji hausa sosai. Hajiya ma murmushin taketa faman yi, dan ita kanta tasan zata ƙaru da yarinyar sosai...       ★Washe gari kamar yanda Hajiya ta faɗa suka tashi da shirin wucewa Lagos, harda Samraah nan dako sunanta basu sani ba har yanzu. Tunda suka tambayeta sau ɗaya tayi shiru basu sake tambayar ba. Tun jiyan kuma tana ɗaki kwance sai dai akai mata abinci a ɗakko kwano.. Janny ce mai ƙoƙarin kai-kawon, Hajiya dai nata bada umarni kawai, bakuma ta sake neman ganin Samraah ba tun shigowarsu gidan sai a yanzu da suka kwana suka yini dan tafiyar yamma zasuyi.      Ita dai Samraah bata san ina zasu je ba. Koda ta tambayi Hajiya kuma sai cewa tai ta jira zata gani. Badai tace ita ƴar Kano bace, zata bata mamaki ne. Al'amarin kamar asiri Samraah ta gagara cewa da Hajiya komai. Hasalima jinta take jikinta duk ya gama mutuwa ga bakinta ya mata nauyi. Sannan bata jin zata iya tsallake umarnin Hajiya sam koda cewa tai ta shiga wuta ta ƙone ko ruwan teku.        Tunda suka fito Janny taga Samraah na faman laɓe-laɓe a bayanta, Idanu Hajiya ta zuba musu kawai. Sosai ƙyawun yarinyar ya ɗauki hankalinta, sai taga tama ɗara yanda Jannyn keta kurantawa tun jiya. Baki ta buɗe zatai magana Samraah tai saurin faɗin, “Ina yini” cikin risinawa. Murmushi Hajiya ta ɗan yi tare da ɗauke kai, sai kuma ta sake maidawa ga Janny. “Wai nikam ashe amarya na kawo gidan nan ban sani ba. Irin wannan ɓoyo haka”.       Dariya Janny takeyi sosai itama idonta akan Samraah dake ta faman sinne kanta, da alama dai itama taji kunya, tunda koba komai ya kamata ta fito ta gaida Hajiyar da safe amma taƙi yin hakan. Duk sun fahimci taji kunyar ne suma, dan haka Hajiya ta kamo hanunta tana murmushi. “Daughter ai ko gaisuwa a fito muyi tunda dai naga baki son musan sunanki. Da alama dai yana da tsadar gaske, ko sai mun saya ne?”.          Karan farko na ɗago dara-daran idanuna masu shegen haske na sauke akan Hajiyar ina mai girgiza kaina da sauri, idanuna cike da ƙwalla alamar ina gab da shirin sakin kuka, dan haka kawai naji wani irin tsoro da shakkar matar ya shigeni mai tsananin gaske..    “A'a da alama dai ɗiyar tawa shagwaɓaɓɓiya ce, to mun haƙura tunda dai ba'a son mu sani. Mu sai mu saka miki namu sunan ai kawai kinga an huta canki canka ko”. Hajiya ta sake faɗa cike da salo tana murza hannuna a hankali.     Janny dai dariya take, yayinda ni kuma na duƙar da kai kawai, sai dai abinda Hajiyar ke min a hannu sam bana so, amma tsoron janye hannuna nakeyi.. “Baby zata shiga gaba koni Hajiya?”. Janny ta faɗa dai-dai muna isowa gaban hamshaƙiyar motar Hajiya data sha wanki take ta ƙyalli. Kallon Janny Hajiya tayi, yayinda ni kuma na ɗan ɓata fuska, a raina ina ayyana (baby kamar wata ƴar tsanar wasan yara) a fili kam sai na girgiza kaina a hankali na ce, “Sunana *_Samraah_*”.        A kusan tare Hajiya da Janny suka kalleni, Hajiya ta saki murmushi, Janny ta ce, “Woow nice name dear. Dole ki mana yanga irin wannan golden name haka”. Ta ƙare maganar tana ɗan rungumoni. Jikina na ɗan jaye daga nata batare dana sake cewa komai ba. Hakan yasa Hajiya ɗan harararta akaikaice alamar ta sakeni. Jayewa Janny tai tana faɗin, “I'm sorry maa”. Bata tanka mata ba ta kama hannuna muka shiga baya, dan tuni driver ya buɗe mana. Gaba Janny ta shiga, daga haka driver ya harba mota zuwa gate. Mun ɗan tsaya a bakin gate Hajiya tai magana da maigadinta, tare da bashi kuɗi masu yawa da suka bani mamaki. Shiko sai faman godiya yake bakinsa a washe har motar tai nisa da gate ɗin bai bar ɗaga mana hannu ba....       ★ A cikin tafiyar ƙanƙanin lokaci muka iso airport, hakan sai yay matuƙar bani mamaki. Dan na fahimci airport ne muka zo, sai dai na gagara iya cewa komai dan ji nake tamkar an ɗaureni ne da sarƙa, bakina kamar an saka masa padlock. Wani irin sarawa naji kaina namin da tunani barkatai akan inda zasu kaini, a wane rami kuma na sake jefa rayuwata ni Samraah, kamar fa batun Lagos naji mutanen nan nayi, sai kuma zancen Hajiya ya sake tabbatar min da hakan. Dan bayan fitarmu a motar take sanarma drivern ta yay ƙoƙarin wucewa Lagos da sassafe gobe, bata son ya kwana a hanya bai iso ba. Shiko yana tabbatar mata da in sha ALLAHU cikin girmamawa. Daga haka Janny ta gungura akwatinansu ita kuma Hajiya taja hannuna muka shige ciki. Mun ɗan yi zaman mintuna goma a wasu kujeru kafin mu miƙe lokacin da ake sanar da parssinges ɗin Lagos suyi himma. Cikin kasa haƙuri da suɓutar baki saboda sunayen ALLAH da naketa ambato a ƙasan zuciyata na ce, “Muma wai jirgin zamu hau Hajiya?”. Kusan lokaci guda Janny da Hajiya suka saki ƙaramar dariya, kafin Hajiya ta kamo hannuna cike da kulawa. “Eh Samraah muma jirgin zamu hau zuwa Lagos, dan yafi sauƙin tafiya sai kiga nanda wani ƙanƙanin lokaci mun isa. Idan kuma baƙya son zuwa ne bazamu takuraki ba, tunkan driver yay nisa sai na dakatar da shi ya koma da ke, amma fa ba can gidan zaki koma ba, dole garinku zaki faɗa ya maidaki gidanku”.         A take batare da nasan dalili ba na ruɗe, na shiga girgiza kai idanuna na cika da ƙwalla. Cikin rawar murya na ce, “Hajiya kiyimun rai. Wlhy dana koma gida gara ma ki kasheni kawai. Sannan kuma shima ya tabbatar min zai iya salwantar da dangi.....” sai kuma nai shiru tamkar wadda aka tsawatarwa har ina kai hannu saman bakina na dafe. Ganin kallon tuhumar da Hajiya ke bina da shi da Janny ya sani sakin hawayen suka zubo. “Na yarda Hajiya ki kaini koma inane, amma banda maidani gida, zaki sameni a mai yi miki biyayya ɗari bisa ɗari...”         “Miya samu dangin naki?”.     Hajiya ta katseni tana mai tsatstsareni da idanu. Ruɗewa nayi jikina ya fara rawa da lips ɗina. Saina fara ƙoƙarin jan jikinna baya daga kusa da su. Dai-dai nan aka sake shelanta neman passinges na flight Lagos. Hajiya ta ɗan ja numfashi ta fesar, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da kamo hannuna. “Ok ok kiyi haƙuri ba sai naji ba. Muje kawai kar jirgin ya wuce ya barmu”. Ƙoƙarin tirjewa nayi Hajiya ta sake damƙoni da ƙyau tana min magana a hankali mai nuna alamar lallashi, sai dai nauyinta ya wuce duk yanda mai karatu ke hasashe....         Sosai jikina ke maƙyarƙyata a cikin jirgi saboda zantukan Hajiya. Sai faman maƙurewa nake a waje ɗaya alamar dai a firgice nake. Hajiya kam na riƙe da hannuna katamau tamkar zan tsere mata ne. Janny dake daga can ɗayan gefenmu kam kallonmu kawai take tana danne dariya. Dan duk wanda ya kalleni zai ɗauka ƙauyanci ne cike taf a kaina ba wai tsoro ba. A haka dai jirgi ya lula sama  harda yunƙurin amai na amma na danne, bayan ya gama dai-daita dole sai da Hajiya ta rakani restroom nayi sa. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga zazzaɓi ya rufeni ruff abinka da wadda bata gama murmurewa ba dama. Koda muka sauka a Lagos kaina a juye yake ma gaba ɗaya. Dan bana iya gane komai yanda ya kamata har muka shiga mota zuwa anguwar da Hajiya take....           Babbar anguwace mara yawan cinkoson jama'a kamar ba'a cikin Lagos da nake jin ana faɗa ba. Duk da kuwa kafin mu iso cikinta mun shiga cinkoson matuƙa wani gurin ma da ƙyar muka fita, dan tafiyarmu daga filin jirgi zuwa gida yafi tafiyarmu daga Kano  zuwa Katsina nisa, duk da dai shi wancan gari da gari ne, wannan kuma cikin gari dole akwai banbanci. Iya ƙagara na ƙagu a zo gida, dan a yanzu ma amai ne keta faman taso min tunda muka shiga motar. Da alama Hajiya ta fahimci halin da nake ciki ne ya sata siya min lemon zaƙi a hanya tace na dinga shanshana ɓawon, sai goro da shi kuma na dinga ɗan ci kaɗan-kaɗan. Wannan ne ya riƙeni zuwa gidan Hajiya.        Anan ɗin ma dai maigadi ya buɗe mana gate, sai faman washe baki yake da jerama Hajiya sannu da zuwa. Da taimakonsa mai taxi ɗin daya ɗakkomu ya fidda mana akwatinansu biyu madaidaita. Janny ta tsaya biyan mai taxi ɗin, yayinda ita kuma Hajiya ta kama hannuna muka nufi wata ƙyaƙyƙywar ƙofa fara da adon golden. Wannan gidan yafi gidan Abuja girma, lokacin da muke shiga falon kuma ya sake tabbatar min da yafi wancan ɗin kayan alatun more rayuwa ma. Dan falon ƙato ne na gaske, ga wasu manya-manyan hotunan Hajiya da wani mutum a jiki tamkar zasuyi magana dan girma. Sai ƴammata biyu masu tsananin kama da juna sannan suna kama da mutumin. Fitowar wasu ƴammata biyu da dattijuwa ya katse min kalle-kallen hotunan da nakeyi. Nai tsai ina kallon dattijuwar da ƴammatan da suka zube gwiwa bibbiyu suna gaida Hajiya da jera mata sannu da zuwa. Itako amsawa take cike da nuna isa da gadara tamkar ba Hajiyar dana sani daga jiya zuwa yau ba. Dan bayan ta gama amsa su a taƙaice tai musu nuni da ni. “Kuje da ita sashenku kafin na nemeta, duk kuma wanda ya mata wata any magana sai na wulaƙantasa ta yanda sai yayi dana sanin sani na a gidan nan. Ina sauran suke?”.         Da sauri dattijuwar ta amsa mata da “Madam Oyinka ta ɗauki Surayya da Umayyah, dan tare sukazo da wata baƙuwa tun jiya da yamma kamar yanda na sanar miki a waya”.      Kaɗan Hajiya ta yamutse fuska tana kallon agogo, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa, dai-dai nan Janny ta shigo maigadi biye da ita jaye da akwatuna. Hannu kawai Hajiya ta ɗagama Dattijuwar alamar suje. Miƙewa duk sukayi suna min nuni da ƙofa.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ _______________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 ____________ ......Wani irin yamutsawa kaina ya shiga yi, dan gaba ɗaya suffar ƴammatan nan da dattijuwar batai kama data mutanen kirki ba, sai irin gogaggun matan barikin nan da idanunsu ya gama gogewa. Juyowa nai a karan farko na dubi Hajiya, itako ta ɗauke kanta gefe fuskarta babu alamar wasa a yanzu. Kamar ba itace keta faman min murmushi ba a Abuja da lallaɓani. Kallona na maida ga Janny da itama take kallon Hajiyar, a karo na farko na ce, “Dan ALLAH Hajiya ku barni a wajenku”.         Wata irin tsawar data gigitani Hajiya ta daka min. “Ka jimin shegiyar yarinya, su ɗin sama suka ce miki suna da gida bayan wannan da suke ciki?!! Zaki wuce ko sai na banbance miki tsakanin aya da tsakkuwa ku gammin yarinya da tsurku. Kin fini sanin abinda ya dace ne!”.             Rawa jikina ya cigaba dayi har ina neman kifewa ƙasa. Bamma san sanda nabi wanda akace nabin ba. Da harara Hajiya ta raka bayansu, sai dai suna ficewa taja tsaki da fincike gyalen abayar data naɗe kanta da shi. Tuni gashin dokin kanta ya bayyana, ta jefar da ɗan vail ɗin tana magana cikin yare, sai kuma ta miƙe ta fincike abayar ma. Anan ɗin ma wani wandon bomshot ne na jeans ya bayyana a jikinta da riga best....         “Hajiya ya haka?”.     Cewar Janny tana dariyar shaƙiyanci. Da sauri ta harari Jannyn da zagaya hannunta saman kai ta ce, “God for bed yoo, sunana Jannifer Can hajiyansu su ƙarata da shi bani ba Mtsowww!!. Yanzu ma zanyi shirin Church pastor yay min addu'a akan hakan. I beg, give me wine na ɗan sha ma ko zandawo hankalina da ƙyau”. Tai maganar tana komawa saman kujerar ta zube. Wucewa Janny tai hanyar kitchen, babu jimawa ta dawo da kwalban giya mai tsadar gaske da cups guda biyu. Ita ta ɓalle ta zuba musu tare da miƙamata itama ta ɗauki ɗaya, sai da suka ɗan haɗa kofunan alamar chess sannan kowa ya kai bakinsa yana murmushin samun nasara. Dan kuwa dai sun samo nasarar da suke buƙata a wannan tafiyar.       (Tofa abin mamaki, idan na fahimta dai wannan Hajiya ta bogi ce, hasalima ba musulma bace, ba kuma bahaushiya ba. Ko kuma dai bahaushiyar ce musulma ada tayi ridda? Tirƙashi, muje zuwa wai maƙwafcin mai akuya ya sai kura).. _______★         “Duk yanda na lissafa miki kayan nan haka zatai amfani da su Jalilah. Sannan wannan da za'a dafa abincin da shi ki tashi da kanki kiyi girkin bawai kiba wannan shegiyar mai aikin da kika kwaso ba. Ni wlhy haka kawai yarinyar sai bata min ba, dan kawai kinƙi jin shawara ne”.       “Wai Umma ya kike so nayi dan ALLAH. Mai aikin nan fa dolece. Sanin kanki ne da ga Baby har Bibaa babu abinda suka iya na aikin gida, ni kuma wlhy yanzu na riga na sangarce tunda shegiyar yarinyar can ke komai tun tana ƙanƙanuwarta. Da nasan haka abin zai ƙwaɓe min ALLAH da auren zan hanata gaba ɗaya a rayuwarta”.       Dariya Umman tata tayi da faɗin, “Daga baya kenan. Ni dai muyi abinda ke gabanmu nata kuma ya zama labari ai tunda kin ɗebi rabonki. Yanzu babban burina Bibalo da takwarata su auri mazan kere sa'a. Dan haka bana son wasa. Awakina na sayar har Niger naje amso kayan nan kema kin sani, dan haka kiyi yanda nace ni zan wuce bana son mijinki yazo ya sameni anan. Magana ta gaba kiyi duk yanda zakiyi waɗan nan samarin biyu ƴan uwan yarinyar nan suma su bar miki gida dan nafi son na cigaba da ganin daga ke sai ƴan ƴaƴanki a cikinsa.”       “Banƙi na naki ba Umma, sai dai fa yaron nan yanzu shine komai na gidan nan, ina mora a jikinsa wlhy bazan so yabar gidan ba. Shiko ƙaramin dama yana makaranta sai lokaci-lokaci yake zuwa. Mudai sake shawara yanzu ne lokacin cin amfaninsu su dama macen ce nauyi ai”.          “Eh to da kuma wannan dan wannan. To wai tsaya ma, idan yaron nan kinga yana samun wasu manyan kuɗi ne mizai hana mu haɗa shi aure da Bibaa”.      “Bibaa kuma Umma?”.   “Ƙwarai da gaske. Ga gida bai ƙoshi ba sai a kaima dawa. Ke dai ki nutsu ki sake tabbatar da nauyin aljihunsa. Dan ni dama hidimar da yay a bikin ƙanwar nan tasa da wadda yake a baya tana firgitani”.          “Amma Umma iyakar yaron nan fa Sakandire”.     “Ina ruwanmu da wani Sankandire ɗinsa ko digiri. Shi namiji ai aljihunsa adonsa. Yo ko besan (A) ba indai akwai babbar (N) a aljihunsa miya damemu. Kidai yi nazari nima zan sake tunani”.      Cikin jimamami Mom ta ce, “To shikenan Umma ALLAH yasa mu dace, sai na jiki ko kin jini.”       “To mu huta gajiya. Amma ki tabbatar sunzo sun gaisheni fa ita da shi idan ya iso”.      “Zasu zo Umma kar ki damu”. Tofa ban ganeba wai anyi gabas da kare🤔🥱 ★★★★ Gaba ɗaya a firgice nake da komai, dan wani irin juyewa ƙwaƙwalwar kaina ke neman yi. Musamman ma da naga inda ƴammatan nan suka nufa da ni. Tacan bayan gidanne alamar Bq. Sai dai an raba tsakaninsu da inda su Hajiyan suke da katanga harda ƙofa. Akwai ɗan filin tsakar gida, wanda ke da ƴan kayayyakin ajiya kamar su drum na ruwa guda uku, sai botikai da yan tarkace na aiki. Sai murhun gawayi guda biyu da wasu tukunya masu girma guda biyu. Duk da gidan a share yake tsaff ko kusa bai kama ƙafar ƙyawun inda muka baro ba. Lokacin da muke ƙoƙarin shiga ƙofar da nake ƙyautata zaton ɗaki ne na kusa cin tuntuɓe da tarin takalman dake a wajen, sai da ɗaya daga cikin ƴammatan ta taroni. Sannu tai min cike da nuna alamar tausayawa, na gyaɗa mata kai kawai ina mai haɗiye abinda ke min kaikawo a maƙoshi. Ƙaton falone sosai, sai dai babu komai a cikinsa sai carpet blue da aka malale ƙasa da shi. Sai ƙofofin ɗakuna a jajjere a kowanne bango akwai biyar. Shima falon dai babu datti, sai dai carpet ɗin yay masifar tsufa har a wasu wajajen ya yage wani gurin kuma ya gurje alamar yawan takawa, duk naga hakane saboda hasken wutar lantarki dake haske dako ina. A hankali nakai zaune kamar yanda suka umarceni, na takure jikina waje guda ina ɗan kalle-kalle. Kusan minti uku dattijuwar nan ta kawo min abinci a plate ɗin roba. Shinkafa ce da wake da mai da yaji. Sai ruwan ƙwara ɗaya.       “Bissmillah kici abinci ƴar nan. Sai kije kiyi wanka kizo ki kwanta”.      Kasa cema tsohuwar komai nai, sai binta da kallo kawai nake. Babu alamar ta damu da hakan itako tai gaba abinta ta sake fita. So nake na danne komai a raina karna sakama kaina wata damuwa ko tsoron inda na tsinta kaina. Dan haka na shiga turereniyar ture komai na fara cin abincin. Kaɗan naci abincin dan bakina sam babu daɗi har yanzu, hakama jikina babu ƙarfi sosai. Ruwanne na shanye gaba ɗaya, cikin sauke numfashi nai hamdala ga UBANGIJI. Ƙoƙarin miƙewa nake dattijuwar nan ta shigo, kallonna tai ni da plate ɗin abincin, da yanayin mamaki da gurɓatacciyar hausarta da zaman Lagos ya ɓata ta ce, “Ƴar nan badai har kin ƙoshi ba?”.             A hankali na gyaɗa mata kai alamar hakane. Mama tai ɗan jimm kamar mai tunani, sai kuma ta amshi plate ɗin ta ajiye tana faɗin, “Shikenan muje kiyi wankan sai ki kwanta ko?”.     Kai na girgiza mata, cikin yanayin dana tsinta kaina na sanyi da rashin ƙarfin zuciya kamar wadda aka jefa na ce, “Mama zan kwanta kawai basai nayi wankan ba, dan in har nayi zan iya samun matsala koda da ruwan zafi ne”.       Jimm mama tayi kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Cikin sauke ajiyar zuciya tai min nuni da hanyar ɗaya daga cikin ƙofofin dana gani. “Ba damuwa muje ciki to”. Ɗaki ne ƙarami sosai. Amma duk da haka akwai katifu ƙanana irin na ƴan makaranta har guda biyar jere reras. Kowace katifa akwai filo da bargo. “Nan shine zai zama ɗakin ki. Ba kuma ke ɗaya bace za'a iya sake kawo wasu kuna kwana a tare. Sai dai a yanzu babu kowa sai ke kaɗai dan ankwashe wanda suke ɗakin gaba ɗaya”.        “Mama saboda mi to?”.    Na faɗa cikin suɓucewar baki da jin wani irin ƙarfin zuciya a lokaci ɗaya. Komai mama batace da ni ba. Sai ma juyawa da tai abinta ta fita kawai tana faɗin “Sai da safe”. Sosai mamaki ya saka ni ƙurama ƙofar ido na tsawon lokaci. Sai kuma zuwa can na taɓe baki da ɗage kafaɗa alamar oho muku nai kwanciyarta. Amma a can ƙasan raina aikin jaridancin ne ke faman yinƙuromin, dan haka kawai nake ji a raina a wannan gidan akwai abinda ake ƙullawa. Abin mamaki na farko canjawar Hajiyar nan da mai aikinta a lokaci ɗaya, ita da suketa tattalinna tun daga jiya kamar wata ƙwai amma muna shigowa gidannan kamar basu ba. Na biyu wannan ƴammatan dana gani anan da kuma shi kansa wannan part ɗin da alamu suka nuna mutanene da yawa ke mu'amala da shi. Na uku ganin kusan ƴammatan duk hausawa ne musulmai haihuwar arewa. Lallai ina buƙatar nasan wani abu kam. Sai dai ta yaya? A wajen wa?. Wannan shine babban tsallen baɗaken....       Washe gari kiran sallar farko Maman nan ta tadamu, salla muka farayi, muna idarwa ta tattaramu zuwa ainhin cikin gidan. Babu motsin kowa alamar mutanen gidan basu tashi a barci ba. Aiki Mama ta rarraba mana, ta kuma tsaya a kanmu sai da kowa ya kama nashi yanda ya kamata. Kafin kace mi cikin abinda baifi awa ɗaya da rabi ba mun kammala ko ina ƙal, sai ƙamshin fresheners ke tashi da girkin da Mama keyi a kitchen. Can sashen nasu muka koma, yayinda muka bar mama na ƙarasa girkin, a can ɗin ma ba zaman mukai ba, gyara ko'ina muka shigayi, wasu kuma na haɗa wutar gawayi domin ɗora abincin kari. Ni dai duk abinda akace nayi yinsa nake yi, yayinda nake faman bin kowa da komai da idanu cike da nazari. Babu wanda ya tambayi sunana nima kuma ban tambayi sunan kowa ba, sannan ko'a junansu bana jin suna hira balle ambatar sunayen juna, kowa aikin gabansa kawai yake baki ruff. Kafin goma na safe mun kammala komai, masu shiga wanka nata ƙoƙarin yi duk da banɗaki biyune kacal a sashen na toilet dana wanka, amma haka suke bin layi kamar wasu ƴan makaranta. Kasancewar basu da yawa sosai basuja wani dogon lokaci ba suka kammala wanka. Zuwa sannan mama ta dawo, ita ta rarraba mana abincin kowa yazo ya ɗauki nasa yaja gefe yana ci, sai a sannan wasu ke ƴar hira ƙasa-ƙasa. Ni dai nama gagara cin abincin sai kallonsa kawai nake har sai da Mama tai min magana akan na maida hankali naci dan Madam na buƙatar ganinmu.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆_ .......Wanke-wankenta take hankali kwance, yayinda bakinta ke faman raira waƙar Ado gwanja ta Chass. Sosai zazzaƙar muryarta siririya ke faman ratsa zuciyar Abba dake falo zaune yana waya. Shi kaɗai ne a gidan sai ita. Dan tun ɗazun Mom da Baby da Bibaa suka fita kasuwa wai yi cefane Baby zata yi baƙo. Sai Auta dake ɗaki yana barci saboda zazzaɓi da yake yi kwana biyu. Abbas kam ma yanzu sai ya gadama yake kwana a gidan. Shiko Nabeel yana hostel ne. Ya Musaddiq ma ganinsa yayi wuya a gidan yanzu.        Halime kenan sabuwar mai aikin Mom da ta saka wata ƙawarta ta nemo mata tun bayan wucewar baƙi ƴan biki da kwana biyu. Dan kuwa daga ita har su Baby sun gagara gyaran gidan ga hargitsewar da yayi na hidimar biki. Da gaggawa ta buƙaci samun mai aikin dan haka ƙawar tata ta kawo mata Halime da itama ta samo wajen wata mata mai kawo ƴan aiki daga ƙauye. Da farko Mom taso ƙin amsar Halime, saboda ƙyaƙyƙyawar yarinya ce ga ƙirar jiki irin ta manyan mata ALLAH ya bata. Rashin gyara ne kawai da rashin suturar kirki ya ɓoye baiwar da ALLAH ya matan. Sai kuma ɗan shirme na rashin ilimi. Har tace ƙawar tata ta koma da ita a samo mata wata su Baby suka shiga roƙonta dan su kam aikin suke gudu, dole ta haƙura ta amshi Halime akan nan da wani lokaci za'a sake samo mata wata sai ta sallameta. Sai dai duk da haka ta kafama Halime dokoki sosai a gidan musamman akan Abba. Dan tunda tazo gidan ma kusan sati uku da wasu kwanaki kenan bai taɓa ganinta ba, itama bata taɓa ganinsa ba. Yau ma Abban har ya fita kasuwa mantuwa tasa ya dawo gidan, kiran wayarsa da akayi ya sakashi zama a falon yana amsawa. Gaba ɗaya wayar ta gundiri Abba, dan sosai muryar take sake tasiri a zuciyarsa. Sallama yay ya miƙe zuwa ɗakin barcinsa yana ƙwala ma Mom kira dan bai san basa gidan ba tunda ba gaya masa tayi zata fita ba. Cak Halime ta tsaya daga raira waƙar da take yi, tai ɗan jimmm alamar saurare. Jin da gaske dai muryar namiji take ji na kiran hajiyarta yasata ɗauraye hannunta a fanfo ta fito a kitchen ɗin. Dai-dai lokacin Abba na ƙoƙarin shigewa bedroom ɗin da cigaba da ƙwala kiran sunan Mom. Cike da rashin wayo da gaɓanci Halime ta ce, “Ikon ALLAH kai kuma waye haka kake kiran mafarauta sanƙamemen ƙato har ɗakin kwanan mutane?”.      A bazata furucin nata ya shiga kunnen Abba, dan shaf yama manta da wata batun mai aiki da Mom tace masa zata kawo, tunda shi dai bai taɓa ganinta na tunda tazo gidan, dan haka ya juyo gaba ɗayansa. Idanu sosai ya tsira mata, ganin yanda ta riƙe ƙugu tana hura siririn dogon hancinta da tura madaidaicin bakinta ya bashi dariya. Amma sai baiyi ba cikin suɓutar baki ya furta, “Aljani ne”.       “Na higa uku ni Halime aljani kuma? Ita dama Hajiya tasan da aljanu a gidanta ta kawoni nai mata aikatau”.      Murmushi Abba ya saki a karo na farko, yayinda a kaikaice yake sake ƙarema yarinyar kallo. A fuska dai bazata wuce sha bakwai zuwa kaɗan ba. Amma a jiki akwai ƙira ta manyan mata, dan tako ina a cike take. Ganin tana neman zurawa da gudu yay gyaran murya. “Kinga kwantar da hankalinki ba aljani bane. Mai gidan ne. Ina hajiyar taki?”.     Da mamaki Halime ta waro idanu waje sosai, sai kuma ta dafe baki tana juyawa ta kalla makeken hoton dake falon, wanda tunda tazo gidan Ita dai bata gajiya da kallonsa saboda ƙyawun da sukayi a jiki shi da Mom da su Baby. Su Samraah dai babu su daga ita har su Yaya Musaddiq. Tabbas mutumin dake zaune kusa da Hajiya ne. Amma duk da haka sai da ta sake juyowa ta kalla Abba. Kamar wadda aka tsikara ta zube ƙasa tana faɗin, “Na shiga uku wlhy kuwa kaine ɗin. Alhaji dan ALLAH ai min aikin gafara”.        Murmushi Abba ya sake yi, sai kuma a hankali ya furta, “Ba damuwa tashi abinki. Ina hajiyar taki?”.      Miƙewa Halime tayi, sai dai yanzu kanta a ƙasa alamar jin kunya. Cikin ƙanƙan da kai ta furta, “Sun fita da Aunty Baby da aunty Bibaa”.     Ɗan jimm yay yana kallonta. Sai kuma bai ce komai ba ya kaɗa kansa zai shige bedroom ɗin. Sai da ya juyo zai rufe ƙofar suka sake haɗa ido da Halime dake kallonsa itama. Da sauri ta juya masa baya har jikinta na kaɗawa. Numfashi ya ɗan furzar da cewa, “Je ki cigaba da aikin ki”. Bai ma kai ƙarshe ba ta zura da gudu hanyar kitchen. Kansa kawai ya girgiza yana murmushi shima ya ƙarasa shigewa ciki....        💦★💦★💦★💦   Washe garin da nake cika kwana biyu a gidan bayan kammala aikin dana fahimci wajibine a garemu a gidan muna dawowa wanka nayi na shige inda ke matsayin ɗakina batare dana shiga aikin namu sashen ba. Kwanciya nayi wasu hawaye masu zafi na sauka min batare dana sani ba. Gaba ɗaya na rasa mike damuna. Koda tunani nai ƙoƙarin yi akan kaina da zaman wannan gidan sai kaina ya fara ciwo. A yanzu haka har ya fara saramin. Dole na tattara komai na watsar na cigaba da kwanciya shiru a wajen har suka kammala aikinsu Mama tazo tai kirana dan a zatonta banda lafiya ne. Da ƙyar na iya faɗa mata na ƙoshi. Jimm tai tana kallona, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta juya ma ta fita. Kusan mintun talatin da fitar tata sai gata ta dawo. Wai na taso Hajiya na kiranmu. Babu musu na miƙe dan bama zan iya musun ba. Hasalima sai wani irin tsoron Hajiyar ne naji ya sake shigata har zuciyata na rawa. Haka dai muka fito duk a ɗarare.       Mun kai tsahon mintuna goma a tsaye bayan shigar Mama cikin falon kafin a bamu izinin shiga ciki. Hamshaƙan mata muka samu har guda uku zaune cikin shiga ta alfarma. Basai an faɗa ba, a kallo ɗaya da zakai musu zai baka tabbacin daloli sun zauna musu bama naira kawai ba. Hajiya na zaune itama cikin tata shigar alfarmar tamkar mai shirin fita ma. Gefenta Janny ce ke tausa mata ƙafafu a hankali. Gaishesu mukai a tare, duk suka bimu da kallon ƙurulla batare da sun amsa ba.      “K fita anan banda ke”. Furucin Hajiya ya samu ɗagowa gaba ɗaya dan bamu san dawa ake ba a cikinmu. Sai dai ganin kai tsaye ni ta nuna yasa sauran maida kawunansu ƙasa. Cikin dokawar ƙirji na yunƙura zan fita a cikinsu kamar yanda ta umarceni. Amma sai ɗaya a cikin matan ta katseni da faɗin, “Kamar ya banda ita? Ai ni gaba ɗaya ma hankalina a kanta yake Madam”.     Kai Hajiya ta girgiza mata. “No Alajah ita wannan sabuwa ce. Babu abinda ma ta koya balle nai cinikinta. Sannan ba aikatau ne aikinta ba”.         “Babu wani damuwa a hakan ni tamun. Dan dama irinsu nake so sunfi daɗin sha'ani ya zama komai kaine ka koya musu. Nima zayi gift da itane kar ki damu”.     “Amma Alaja.....” “Basai kince komai ba zan ninka kuɗinta sau uku. Domin zanyi ƙyauyar girma ne”.         “Uku?”. Madam ta faɗa cikin waro idanuwa da sakin murmushi. Amsa Alaja ta bata da, “Yes nan gaba ma idan aikinta yay ƙyau har ƙyauta ta musamman zaki iya samu. Dan gidan girma za'a kaita dake kanki sai kin san kin zama mai sa'a a wannan gaɓar”.        A take kuwa Madam ta sallama. Babu ɓata lokaci matar tai kiran waya driver ɗinta ya shigo da jakkar da bamu san minene a cikinta ba. Daga ganin yanda yayma Hajiya gaisuwa kasan shima ɗan gida ne. Suma sauran duk sun zaɓi ƴammatan ɗaɗɗaya. Bayan suma an kawo tasu jakar da bata kai ta Alaja girma ba Mama ta umarcemu da mu fito. Ni gaba ɗaya ma sai naji kamar an ƙara ɗaureni da sarƙa. Sannan yanda nake jina ko wuta Hajiya tace na faɗa zan iya hakan. Sabbin kaya Mama ta bamu mu ukun nan wai mu saka. Bayan mun kammala tace muyi sallama da sauran ƴan uwanmu dan zata iya yiwuwa rabuwar kenan, idan iyayen gidanmu sunji daɗin zama damu ba lallai mu sake waiwayen nan ɗin ba. Mu dukanmu tamkar waɗanda ake sarrafawa da remote mukai sallama da su. Sai dai ƙasan zukatanmu mu kaɗai muka san halin da muke a ciki sai UBANGIJINMU. Haka muna ji muna gani aka fiddomu harabar gidan inda hamshaƙan motoci suke har guda uku. A ta farko da tafi kowacce ƙyau da tsaruwa akace na shiga gaba. Yayinda aka buɗema Alaja baya ita kuma ta shiga. Sauran ma duk shiga sukai motocin suka fice.      Haka kawai wasu hawaye masu zafi suka shiga sakkomin. Duƙar da kaina kawai nayi na cigaba da kukana batare da na bar sautin ya fita ba. Haka kawai nake jin takaicin kaina da sauyawata. Jina nake tamkar bani Samraah Abdul-wahab Gwarzo ba. Gaba ɗaya tamkar an kashemin zuciya da kuzari. Abinda kawai nake ganewa shine bin umarni. Munyi tafiya mai nisa kafin na share hawayena na ɗago. Bansan lokacin dana furta (Masha ALLAH) ba a zuciyata ganin wata irin ginanniyar anguwa da muka shigo. Sam tsarin anguwar baiyi kama da a cikin ƙasata Nigeria ba. Victoria island na gani rubuce a babban symbol. Hakan na nufin sunan anguwar kenan. Tun a farkon shiga street da shima aka rubuta a symbol sai dai banga farkon sunan ba securitys suka tsaidamu. Sai dai ganin Alaja yasa suka bamu damar shigewa alamar dai sun riga sun santa.......✍️       _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒆𝒏_ _______________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 ____________ .......Su Alaja na ficewa a gidan dasu Samraah Madam tai wani ƙasaitaccen murmushi da cije lips ɗinta. Wayarta ta shiga daddanawa tana tafiya har ta shige ciki. Dai-dai tana kai wayar kunnenta takai cikin kujera. Cikin wani salon gogaggun matan bariki ta shiga jera kirari ma wadda tai kira a maimakon gaisuwa. Bamu ji abinda aka faɗa mata daga can ba. Sai dai yanda ta saki siririyar dariya zai baka tabbacin mai daɗi ne. Sai da tayi mai isarta sannan ta ɗaura da faɗin, “Ina godiya da wannan ƙyauta hajjaju masu Lagos da wajenta. Kai Africa ɗin ma duka taku ce. Na kiraki ne domin wani babban albishir da nai imanin zai faranta miki ranki matuƙa”. Ta ɗan yi jimm alamar saurare. Wani murmushin mai faɗi ta sake saki da cigaba da faɗin, “Godiya nake hajjaju. Dama akwai babbar haja da a yanzu akai cinikinta zuwa gidanku. Na tabbatar irin kalarki ce shiyyasa ma na sayar babu ja'inja bayan na gane daga ina masu sayen suka fito. Na tabbata idan kikaga wannan hajar sai kin sake min sabon biya dan ni kaina buƙatar kuɗi kawai ta sakani sallanawa amma raina ya biya sosai.”       Amsar da Hajiyar ta bata daga can ya sata sake sakin dariya. “Ayyah! Hajjaju Ayya. Ai ku manyanmu ne. Kodan girmamawa ma kauda kai ga abinda ya dace daku. Sai dai kinga kayan dan na tabbatar yanzu suna gab da zuwa gidan naku. Duk da dai tace zata bada as gift ne. Kuna wani shagali ne a gidan naku babu gayyata Hajjaju?”.      Shiru alamar saurare, sai kuma ta tashi zaune da ƙyau tana furta, “Woow fantastic Hajjaju. Ai dolene muzo wannan birthday party kuwa kodan ke. Dan haka sai kin gammu”.     Daga haka sukayi sallama ta yanke wayar tare da ajiyeta gefe tana wata kalar shaƙiyyar dariya. A ranta tana ayyana (lallai yarinyar nan tazo da arziƙi. Ai tun da na ganta nasan mabuɗin arziƙina ce ita, dan zoben da babalawo ya bani yay wani irin haske da bai taɓa yi akan sauran yaran da nasarata ke samowa ba. Sai dai fa nima yawuna ya biya, dan komai yaji a jikin yarinyar nan, ga wani shegen fata kamar na dorinar ruwa. Dan haka sai na ɗanɗana koba yanzu ba) ta saki wata dariya a zahiri. Hakan yay dai-dai da shigowar Janny. Ko kaɗan batai mamakin gani da jin dariyar da Madam ɗin tata keyi ba. Sai ma takowa da tai cike da yauƙi jiki na girgiza ta faɗa mata a jiki...... (Hummm🥱)         💥💥💥💥       *_MAASH MANSION_* Shine rubuce da manyan baƙi da akai da kalar ruwan gold a jikin babban makeken baƙin gate ɗin gidan da ya mamaye kaso mai yawa na street ɗin. Ƙirjina yay wata irin masifar harbawa, ba sai an min bayani ba, hakan na nufin wannan katafaren gini shine gidan su Maash ko gidan Maash. (Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un) to yaya hakan ta faru? Maash ɗin dana sani ne a Lagos ko kuwa wani ne mai irin sunansa?. Bani da mai bani amsa sai jikina dake rawa sosai amma babu wani yinƙuri da zan iya yi. Dan tuni wasu garɗa-garɗan securitys dake tsaren ƙofar sun miƙe, sai da suka gama kallemu ɗaya bayan ɗaya da gaida Alaja cikin girmamawa sannan ɗaya daga cikinsu ya danna remote da ke hannunsa, a hankali gate ɗin ya shiga zuge kansa. A jere motocin uku duk suka shiga makeken compaund ɗin da sam baida iyaka ga mai kallo, kowacce ta tsaya a muhalin da ake son ganinta. Dolene ka shigo wannan gida ka tsarkake sunan UBANGIJI mai rahama mai jinƙai, dan shike samarwa ga wanda ya so a lokacin da yaso. Gini ne daya ginu karkashin mahaukatan maƙudan kuɗaɗe da sam zaka iya rantsuwa da ALLAH ba'a Nigeria kake ba idan kana a cikinsa. Dan a iya compaund kawai da abinda ke zagaye da gidan, da kallon ginin a tsaye ya isa tabbatar maka da naira tayi kuka. Wani irin ɗunƙulallen gini ne mai matuƙar armashi da ƙayatarwa. Ga wasu irin korayen ciyayi da furanni masu azabar ƙamshi da sanyaya gida da ƙawatashi da sukaima ko'ina ado. Ga jibga-jibgan motoci jere a cikin rumfuna kusan biyar a tsare acan nesa sosai, wasu ma rufe suke da tempol. Sosai ma'aikata ne ke kai-kawo, dan dole irin wannan gidan yana da masu kulawa ta kowanne fanni. Driver ne ya fara fita a motar ya buɗema Alaja. Kafin ita kuma tai min nunin na fito. Jikina a matuƙar sanyaye na fito ina mai bin katafaren harabar gidan da kallo. Brain ɗina gaba ɗaya ta gama kwancewa, dan tunanina ya rabu biyu ne tsakanin haɗuwar gidan da sunan dana gani rubuce ɓaro-ɓaro matsayin mamallakin gidan.       “Oya muje”.    Furicin Alaja ya katse min tunani. Tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki na fara takawa a hankali ina bin bayansu. Drivern ta ne yay saurin buɗe dankareriyar ƙofar mai wani irin zubin ƙyau da ɗaukar hankali da duk mai kallo zai iya tabbatar da an sayeta da kuɗaɗe masu nauyi. Alaja ce ta fara shiga da sallama, yayinda ni kuma ke biye da ita kamar bindi. Sai sauran abokan tafiyarmu biye damu. Sai dai babu sauran yaran da aka ɗakkomu tare da alama an barsu a mota. A haɗaɗɗen falo dake matsayin main perlor muka fara ratsawa. Komai na cikinsa a tsaftace yake ga ƙamshi da sanyin ac kamar ka ɓingire barci. Sai dai babu kowa a cikinsa ko television ma a kashe yake. Bamu tsaya anan ba, mun shiga falo na biyu daya kasance katafaren gaske. Haɗuwar falon ba'a magana. Dan ya ƙawatu da ƙawatuwa ta musamman. Komai sai ƙyalli da ɗaukar ido yake tamkar ba'a talauci a duniya. Shima dai ƙamshin ke tashi mai nutsuwa, sai ƙafar bene da suka zama mahaɗar sassan gidan guda uku. Gashi ƙaton gaske bana wasa ba, dan duk da set na kujeru kusan biyar da ke cikinsa group-group zama a iya kawo wasu set goma sha biyar duk ya ɗauka batare da wasu sun matsi wasu ba.       Anan kam akwai mutane. A hankali dattijuwar matar dake zaune cikin kujera 1sitter da laptop a gabanta tana sarrafawa a group na set ɗin kujerun dake farkon shigowa ta ɗago fuskarta ƙawace da murmushi, laptop ɗin da tun shigowarmu ta dakata da sarrafawa ta ture gefe, cikin ƙasaitacciyar muryarta ta furta, “Idanu na ne kemin gizo ko kuwa mafarki nakeyi? Da ganin Auta”.       Dariya Alajah tayi tare da nufarta ta rungumeta. Dai-dai nan wasu ƙyawawan ƴammata uku dake can ɗayan rukunin kujerun suka taso suma a guje suna faɗin, “Oyoyo Aunty Mamah. Juyowa tai ta rungumesu suma cike da kulawa da farin ciki. Sai da suka gama murnarsu suka nutsu kafin su maida hankalinsu garemu. Ni suka fara zubama idanu, kafin su maida ga sauran hajiyoyin fuskokinsu a washe da murmushi suna musu barka da zuwa cikin nuna girmamawa. Ni dai ina daga tsaye gefe dan haka kawai naji shakkar ƙarasawa garesu har sai da Alajah tai kirana tare da nuna min na zauna. Inda ta nuna min ɗin nakai zaune ƙasan carpet. Kaina a ƙasa batare dana kallesu ba na shiga gaishesu. Hajiyarce kawai ta amsa, amma ƴammatan nan ko kallo ban ishesu ba. Musamman ma babbar ciki wani kallon tsana data wurgamin tun farko sai da najisa har a ƙasan raina. Dan haka nima sai banbi takansu ba...        Munyi zama na kusan mintuna talatin a wajen kafin hajiyoyin nan biyu da muke tare da su su miƙe alamar zasu wuce. Hajiya da Alajah ne sukai musu rakkiya. Yayinda ni kuma aka barni nan maƙure waje guda ƴammatan nan na bina da kallon banza. Kusan mintuna biyar sai gasu sun dawo. Basu zauna anan ba, sai umarni da suka bama ƴammatan cewar ai kiran Mama Bilki shugabar masu aikin gidan taje dani sashensu zasu nemeta. Hakan kuwa akayi, dan atake babbar cikin ƴammatan ta ɗaga telephone tai kira, cikin gadara da izza ta isar da saƙon Alajah da tuni sun haye upstairs ta ɗaya daga cikin ƙafar bene ukun data ƙawata makeken falon na alfarma. Ba'a ɗauki wani lokaci mai tsaho ba sai ga wadda nake ƙyautata zaton Mama Bilki tazo. Babbar mace ce sai dai baza'a kirata tsohuwa ba. Abin mamaki kuma jikinta fes kamar bamai aiki ba, amma tabbas zata iya haihuwar kamata. Cikin fara'a da kulawa ta bani umarnin tasowa na bita. Nima sai na miƙe jiki a sanyaye nabi bayanta ina mai sakin ajiyar zuciya. Dan dama zama a tsakiyar shegun yammatan duk ya gundireni. Ina jin wata a cikinsu na sakin tsaki amma sai nan juyoba balle naga wacece.          Tafiya mukai mai tsaho sosai data bani mamaki dan kamar bama a cikin gidan muke ba. Kasancewar bata hanyar da muka shigo dasu Alaja bane yasa ban iya na fahimci komai ba. Sai ma sake zama wata baƙauya nayi dan kalle-kalle nakeyi iya iyawata. Sosai nake sake girmama girma da ƙudira ta UBANGIJI. Dan wannan gida sai ka rantse ba hannu ne ya gina shi ba saboda ƙawatuwa da ɓannar dukiya da akai wajen saka masa kayan alatu. Ban sake tabbatar da gidan ƙaton gaske bane sai da muka ɓullo wata hanya data fiddomu wajen ginin tanan ma. Ashe ta gaban girmansa ba komai bane. Ta can baya da ginin apartment na masu aiki yake ɓangaren maza daban na mata daban shine ainahin ƙaton gaske. Dan shi ta can gefe akwai ƙaton garden da ko ba'a faɗa maka ba kasan shi ɗin ne. Sannan daga hannun dama akwai wani ƙaton wajen wasanni na yara da manya. Akwai wajen ƙwallo, wajen..... Kai dama wasu daban da ban gama tantancewa ba dan iya abinda idona ya hango kawai nake sanar miki Bily. Shi kansa sashen masu aikin da muka shiga sai da notikan kaina suka nema kwancewa. Dan tamkar ba na masu aiki ba. Komai fes akwai kuma kayan ƙawar suma duk da basu kai na sashen masu gidan ba ko kusa ko kaɗan. Amma dai duk mai hankali ya kalla yasan an girmamasu an mutuntasu. A tare ƴammata kusan takwas da muka samu a falon zaune suna kallo suka zuba min ido fuskokin wasunsu da fara'a, wasu ko kallo ɗaya sukai min suka ɗauke kawunansu. Sannu wanda suka nuna kulawar su suka shiga yi min, hakan yasa nima na amsa musu da kulawa tare da gaishesu duk da sukansu bazasu wuce sa'anni na ba har ma da waɗan da zan iya girma..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒍𝒆𝒗𝒆𝒏_ __________ _Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_ https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ___________ ......Wajen zama Mama Bilki da naji sun ambata da Mama ta nuna min, babu musu na zauna. Ta nuna wata dake gab da inda nake tana faɗin, “Sayyada kawo ma baƙuwarmu ruwa da abinci ko”. Cike da fara'a wadda aka kira Sayyada ta amsa tana miƙewa. Wata ƙofa dake a falon can inda ƙaton dining table yake na katako ta nufa, mintina ƙalilan kuwa sai gata da tire madaidaici a hannunta. A gabana ta dire tana murmushi da faɗin, “Sister ga abinci ko.”          “Nagode”.        Na faɗa a hankali nima ina murmushin yaƙe. Wajen zamanta ta koma ta zauna. Yayinda ni kuma na zuba ma abincin ido nai shiru har sai da Mama Balki ta zungureni sannan na kawo numfashi. Abincin ta nuna min alamar naci, na ɗan sauke ajiyar zuciya. Sai kuma cikin tausasa murya nace, “Mama dan ALLAH zan fara salla tukunna”.      Cike da fara'a tace min, “Lah ai babu komai ɗiyata. Kinga A'i tashi ki rakata ɗakinku sai tayi a can kunga kun samu abokiya kuma kun zama ku uku kamar kowa. Ɗan tsuke fuska wadda aka kira da A'i tayi, sai dai kuma batace komai ba ta miƙe. Nima miƙewar nayi nabi bayanta ɗan lungun da naga ta nufa. Dogon corridor ne mai ɗauke da ƙofifin ɗakuna kusan goma. Hannun dama biyar haggu ma biyar. Babu yabo babu fallasa bayan mun shiga ɗaki na biyu a hannun dama ta nuna min ƙofar bayi. “Ki shiga nan”. Daga haka ta juya ta fita. Komai bance da ita ba nima, face cikowa da idona yayi da ƙwalla. Ji nake komai ya ƙwace min, gaba ɗaya nama gagara hasashe balle tunanin komai akan wannan rayuwa dana jefa kaina. Dan a yanzu kaina nake zargi ba kowa ba. Ina ma kaina kaico akan bin hajiyar nan da nayi, sai naji inama tashar na nufa koda roƙo na samu kuɗin motar zuwa Kano. To amma bakin alƙalami ya riga ya bushe. Ni bama wannan ne tashin hankalina ba. Son sanin wanene mai wannan gidan shine tashin hankalina. Karfa ya zamto ANYI GUDUN GARA ne AN FAƊA GIDAN ZAGO. Kai amma da nayima kaina kaico. In sha ALLAHU ma bazai kasance hakan ba.       Bayan na idar da salla na jima zaune a wajen shiru, dan har sai da A'i ya biyo bayana sannan na miƙe na bita. Kamar yanda na barsu haka na samesu. Sai dai an sake samun ƙarin mutum uku suma duk manyan mata dan da kaɗan Mama Balki zata iya girmarsu. Gaishesu nayi a ladabce, duk suka amsa min babu yabo babu fallasa. Na ɗan ji jikina yay sanyi, sai dai ban bari al'amarin nasu yayi tasiri a raina ba na fara cin abincina. Ka ɗan na tsakura nace na ƙoshi, Mama Balki tai murmushi da faɗin, “Ƴar nan baƙunta zakiyi mana?”.       Murmushi kawai nayi kaina a ƙasa batare da nace komai ba. Itama sai tayi ƴar dariya da cigaba da faɗin, “To ai shikenan. Bara nayi wani karanbani duk da Aunty Mama bata sanar min ke wacece ba ko matsayinki. Amma dai duk wanda aka kawo nan mun san namu ne ai. Minene sunanki?“.        Shiru nayi jimmm kamar bazance komai ba. Sai kuma na sauke ajiyar zuciya a hankali na furta Kandala”.     Su dukansu sai da naga alamar shock a fuskokinsu game da jin sunan nawa. Amma ganin yanda na fiske abuna ya sasu basarwa. Wasu a cikinsu suka furta Masha ALLAH. Yayinda wasu suke taɓe bakuna a yamutse. Mama Balki ce ta katse yanayin da nuna kanta. “Ni sunana Balkisu, amma suna kirana da Mama Balki kamar yanda kika ji. Ni ce shugabar duk wani ma'aikacin wannan gida musamman mata. Mijina kuma shugaban ma'aikata maza. Wannan kuma ta kusa dake Sayyada, sai Afrah, sai Sumayya, sai A'i, sai Asiya, sai Bintu, sai Mansura, sai Kairat, sai Bahijja, sai Sadiya suna kiranta Aunty Sadiy, itama tana da miji. Ta nuna ɗaya daga cikin manyan matan nan uku da suka shigo daga baya. Sai Aunty Kubrah itama tana da miji, sai aunty Falilah. Dukanmu muna aiki ne a wannan gida. Kowa kuma da fannin sa. Wasu gyara, wasu wanke-wanke. Kowa kuma da sashen da yakema aiki dan komai a ƙa'idarsa yake. Idan har kema tamuce zamuji fannin da aka kawoki ki kasance”.        Sosai ƙirjina ke wani kalar luguden daka tunda ta fara. Sai dai inata dauriyar danne yanayin nawa. A rain kuwa komai ya dagule min, babu abinda nake ambato sai kalmar (Na shiga uku. Yanzu kuma boyi-boyi na koma kenan? Mike shirin faruwa dani ne haka?). Bani da mai bani amsa, dan haka na maida hankalina ga Mama Balki dake cigaba da min bayani. Sai dai sam bana fahimta har tayi ta gama. Mun cigaba da zama har akai kiran sallar la'asar. Sai a sannan dukanmu muka miƙe. Ɗakin dai ɗazun naje tare da wadda ta rakani A'i sai abokiyar kwananta Bahijja. Bahijjar akwai fara'a, dan sai jana take jikinta cike da kulawa. Muna idar da salla ta kwashe tarkacen kaya da suka jibge a ɗayan gadon ɗakin dan uku ne ta ce, “Nan shine gadonki Kandala”. Yanda tayi maganar da murmushi ya sani nima mayar mata da murtani ina jinjina kai, kafin na ɗora da mata godiya. A'i dai na jinmu amma tai kamar bata ɗakin. Bahijja dake ƙoƙarin saka uniform ta sake kallona da faɗin, “Kiyi kwanciyarki ki huta mu zamu je can sashen yin aikin yamma. Idan kuma zakiyi kallone to muje falo”.       Da sauri na girgiza mata kaina. Sai kuma na murmusa da faɗin, “A'a bari na kwanta ɗin, ai bazaku jimaba ko?”.      Tsaki akaja kafin ta bamu amsa, atare muka kalla A'i dake ƙoƙarin ficewa alamar itace tayi tsakin. Murmushi Bahijja tayi da maido idonta gareni. “Karki damu da ita haka take kamar mai aljanu. Nima farkon zuwana haka ta dinga min kamar mai jin haushin mutane. Amma bari kiga nan da kwana biyu zata fara kulaki. A'in ce kamar mai aljanu wlhy”.          Murmushi nayi yayinda ita kuma ta ƙare maganar da sakin ƙaramar dariya. Daga haka ta cigaba da faɗin, “Ya danganta da yanayin aikin da zamu tarar. Musamman ma ni, dan iyayen gidan nawa mutuncinsu ragaggene bare ma idan akace miki Aunty Azizat. Tana abu kamar mai jin warin mutane. Bari naje dan in nayi latti zan sha maruka gashi ƙa'idarta ne iyanzu take wankan yamma”.        Kasa cewa komai nayi, sai kaina dana ɗaga mata kawai sunan wadda ta kira na min kai-kawo a rai batare dana san dalili ba. Bayan ficewarta na saki nannauyar ajiyar zuciya. Sai kuma na miƙe cikin kasalar jiki zuwa gadon da tace nawa dake a farkon shigowa. Na can ƙarshen bango na A'i, na tsakkiya nata. Sai ni a bangon ƙarshe na farkon shigowa.....       ❤️★★★❤️    Tsakanin Halime da Dady dai tun wannan ranar ba'a sake haɗawa ba. Dan washe gari uban aiki taci kamar kurar wasa. Dan kaf girke-girken da aka tanadama Alhaji Rufa'i itace tayi su. Tayi kuma gyaran gidan musamman falon tarar baƙi da Mom ta sakata ƙalƙalewa kamar za'a canja bangonsa. Ita dai bata san dalilin uban aikin da taci ba sai da yammaci take ji a bakin auta wai Baby ce tayi baƙo. An kuma ce ta saka hijjab da niƙab takai masa abinci falon baƙi. Bata da yanda zatai dole tabi umarnin Mom tayi shigar da akace taje takai komai. Da ɗunbin mamaki ta fito mara misali. Yayinda taketa jarumtar danne dariyar dake cinta har sai da ta shiga ɗakinta. Bata tsaya a tsakar ɗakin ba ta shiga toilet ta rufe kanta duk dan kar a jita sannan ta fara kwasar dariya harda hawaye. “Kambu taƙashin nan. Yanzu ni Halime ina Baby ta samo wannan tulun giyar, wlhy cikinsa kamar an kifa masakin Baba Lauren gidanmu na Daudawa. Gashi sanƙameme kamar samudawan da suka zo mana a labari. Tab ɗi jan, daga dai ganin wannan kasan sai dai a so shi dan kuɗi duk da dai ƙyaƙyƙyawa ne a fuska.” kiran da Mom ke ƙwala mata ya sata fita a guje dan tasan idan tai na uku sai ta sha maruka a wajenta.       Gab da magrib taji ihun Bibaa da Abbas ya cika gidan. Ta kitchen ta kasa kunne sai ta jiyo ihun nasu wai duk murna ne akan Alhajin nan ya bama Baby makulin mota, tare da alƙawarin kujerar maka gareta da Mom da Dad da kuma Abbas, su kuma  su Bibaa da Auta da Nabil yay musu ƙyautar wayoyi iphones. Hakan dai na nufin su duka banda Yaya Musaddiq bawan ALLAH kowa ya samu alkairi daga Alhaji Rufa'i. Baki ta yaɓe ta cigaba da aikinta. Daga haka bata sake bi takansu ba sai washe gari da kakarsu tazo take jin har ƙyautar kuɗi yay ma yaran gidanta itama wai naira miliyan ɗaya. Itama kuma kakar tasu harda ita a zuwa saudia, da yaje gidanta kuma ya bata waya mai ƙyau ƴar dubu ɗari biyu harma ta sayar da ita yau. Sosai Halime ta jinjina kwaɗayin wannan mutane da mamakin maganganun da taji suna tattaunawa. Dan sai da Mom ta farga da ita sannan tasha maruka aka korata waje, daga haka bata san mi suka ƙarasa tattaunawa ba. WASHE GARI kuwa bata ma san lokacin da Mom ta fita a gidan ba tare da Baby. Sai Bibaa da Auta da suka wuce makaranta. Shi dama Abbas ba'a sakashi a lissafin gidan. Yaya Musaddiq kuma ta lura jiya kamar bai kwana a gida ba. Tana a falo tana shara da raira waƙarta cikin zazzaƙar muryar nan tata taji kamar ana kallonta. Ɗan jim tayi cikin nuna tsarguwa. Sai kuma ta cigaba da shararta amma ta daina waƙar da take rerawar ta (kwanana ya kusa ƙarewa a gidanmu zan tafi ɗakina. A gidan mijina zan rayu zaman kaɗaici ya kusa yankewa).       Cikin sauke ajiyar zuciya da rashin jin daɗin daina raira waƙar tata Abba ya ƙarasa fitowa daga jikin ƙofar ɗakin barcinsa da yake maƙale.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_ _____________ _Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_ https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 _____________ ......Daga ni har Mama Balki ƙasa muka zube gaban Alaja dake zaune cikin kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya tana daƙilar tab. Gaisheta na shiga yi, batare data ɗago ba ta amsa min. Kusan mintuna biyu muna zaune kamar masu neman gafara sannan ta ɗago tana cire eyeglasses ɗin idonta da bana raba ɗayan biyu na ƙara gani ne. A kaina ta zube idanun nata, sai kuma ta ɗan saki murmushi. “Ƴammata sorry fa. Tunda mukazo ban sake waiwayarki ba ko? Nayi busy ne da yawa.”         “Ba komai Mama”.     Na faɗa kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hanuna ta cikin hijjab.     “Ohkay, yanzun ma bani da isashen lokaci. Maman Nana kije da ita wajen Sunusy ya gwadata a ɗinka mata uniform itama. Sauran kayan da zata iya buƙata kuma sai ki shirya zuwa anjima kuje shopping. Zata cigaba da zama a hannunki kafin tasan aikin da zatayi”.          “To Hajiya in sha ALLAHU yanda kikace haka za'ayi. ALLAH ya ƙara nisan kwana da rayuwa mai albarka”.     A hankali ta amsa da amin. Jin godiyar da Mama tayi nima sai nayi godiyar. Duk da kuwa wani irin abune mai masifar nauyi ke neman riƙe min ƙirji. Ban san a wace kalar rayuwa kuma na jeho kaina ba. Lallai na tafka kuskure. Inama Kano na nufa abina. Kai anya kuwa kuskuren nawa ba daga baro asibiti bane da nayi. (Tun daga baro gidan mijinki dai a Kano) wani gefe na zuciyata ya ayyana min. Jinai tsigar jikina yay wani irin tashi sama. A saman lips na maimaita kalmar “Miji”. (Kai ina ai bazan taɓa zama matar kowa ba sai Mansoor in ALLAH ya yarda)..         “K! waye wannan kika hayo mana har sama da shi?!”. Muryar dana tabbata naji irinta a jiya ta faɗa cikin daka mana tsawa dai-dai muna sauka steps na biyun ƙarshe. Ganin yanda Mama Balki ta dakata da sauri cikin nuna shakka ya sani mamaki. Cike da girmamawa da sauke kai ta furta “ALLAH ya huci zuciyarki Aunty Azizat. Dama mun cika umarnin Aunty Mama ne. Dan itace ta buƙaci ganinmu”.        Fuska ta wani yamutse tana balla mana harara. Da alama dai bata da abincewa. “K kuma uwar miye kike wani kallona? Shegiya mai kama da mayu!!”. Ta sake faɗa a fusace tana wani ware idanu a kaina sosai cike da nuna tsagwaran tsanar da ban san laifin dana mata ba. Duk yanda naso jin na bata girma a matsayin wadda na shigo gidansu da kuma girmata da tayi  a shekaru dan zata iya kaiwa sa'ar Yaya Musaddiq amma sai naji hakan ya gagareni. Sai ma tsareta nai da idanu ina ƙare mata kallo daga sama zuwa ƙasa....       Tauuuu!!! Naji saukar wani shegen azabebben mari asaman fuskata babu zato babu tsammani. A take ta rashin jin ya yunƙuro, bamma san lokacin dana ɗaga nawa hannun ba na sauke mata nawa yatsun biyar nima a saman fuskarta dake fara sosai a dama da haggu kuma. Daga gani kasan akwai ƙarin farin kanti dan har wani yellow-yellow takeyi. Tamkar mutuwa ta ratsa gidan haka yay wani irin tsittt na wuccin gadi. Kafin tai wani irin zuba min ido like wadda tai suman tsaye. Bama ita ba hatta da Mama Balki wani irin waro idanu tayi da ɗaura hannuwa duka a saman kai bakinta buɗe. Cike da dakiyar nan tawa da taurin kai na watsar da su tamkar banga komai ba na raɓa zan wuce. Dai-dai nan ta wani saki kururuwa da girgiza tamkar tsohuwar dodanniya ta damƙo min hijjab ta baya. Sai kawai ji nai an shaƙureni tare da jawoni baya. Tabbas da banyi azamar damƙe hijjab ɗin ta gaba ba da zamesa da sauri babu abinda zai hanata kaini ƙasa a wajen. Idan kuwa na faɗi zan iya buguwa, idan ma da tsautsayi zan iya rasa rayuwata. Gaba nayi gaba ɗaya, dan yanda ta fisga ni kuma na fisge sai yay kamar an hankaɗoni ne. Na gama sallamawa babu makawa a wannan gaɓar sai na kai ƙasan mayen marbles ɗin nan mai tsananin sheƙi da ɗaukar idanu tamkar zakaga fuskarka a cikinsa. Dan haka na runtse idanuna gaba ɗaya ina mai ambaton sunan ALLAH da sallamawa baki ɗayana......                 ★★★★     Cikin mintuna ƙalilan Halime ta dawo ɗauke da tray. Haka kawai take ji bazata iya tsallake umarnin Abba ba. Duk da tana jin shakkar uwar ɗakinta tasan ta ƙetare umarninta. A hankali ta dire tray ɗin a gaban Abba dake zaune a dining. Tun fitowarta kuma yake famar binta da kallo ta gefen ido tamkar zai cinyeta. Ƙoƙari barin wajen take yi tamkar mai raɗa ya furta, “Baza'a zuba min ba?”.       Duk shirmen Halime sai da taji zuciyarta ta tsarga. Hannunta na rawa ta shiga zubama Abba abincin. Ta kammala tana ƙoƙarin barin wajen ya katseta da faɗin, “Uhhm Kinga zo mana”. Nan ma ƙiri tai tana kallonsa, kafin cikin sanyin jiki tai ƙoƙarin durƙusawa a ƙasa. Amma sai yay saurin girgiza mata kansa da mata nuni da kujera. Gabantane ya sake faɗuwa. Tai masifar waro idanu waje tana jijjiga masa kanta alamar dai bazata iya ba. Ƙyaleta yay, cikin gyara yanayinsa ya ce, “Minene sunanki?”. Ganin yanda yaci serious ya sata nutsuwa itama. Kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta amsa masa da, “Halime”.      “Halimatussa'adiyya kenan?”.    “Eh ta faɗa a hankali”. “Ina ne garinku?”. “Ƴan tumaki”. Ta bashi amsa kai tsaye.       “Ƴan tumaki?”. Ya maimaita da ɗan waro idanu a kanta a tunaninsa shaƙiyanci ne. Amma sai a mamakinsa yaga ta jinjina masa kai na tabbatarwa. Kasa haƙuri yayi sai da ya furta “A wane state ne?”. Girgiza masa kai tayi da faɗin, “Katsina ne. Amma dai muna kusa da Musawa”. Jin sunan Musawa ya sashi fahimta Katsina state kenan ɗin dai da gaske. Humm mutanenmu da ganganci, ka turo yarinya mai cikar halitta jiki kamar wannan aikatau har wata jiha. Cigaba yay da faɗin, “Miyasa kike aikatau?”.       Idanunta ne suka ciko da ƙwalla. cikin rawar murya ta ce, “Inna ce tace Baba ya turani na samo kuɗin kayan ɗakin aurena”.        “Ita Innar mamanki ce?”.   “A'a gwaggona ta rasu tun ina ƙarama. Matar Babana ce, amma uwarsu ɗaya ubansu ɗaya da Gwaggona. Bayan ta rasu aka aurama Babana ita dan ta riƙemu ni da ƙanina. Sai dai kuma ta tsanemu, kullum cikin mana mugunta take, gadonmu ma da Gwagginmu ta barin mana duk ta cinye. Gashi Baba baya iya cemata komai, shima tsoron masifarta yake ma”.    Haka kawai yaji wani abu mai nauyi ya tsikarar masa zuciya. Tamkar walƙiya hoton Maman su Samraah yazo masa a cikin idanu. Da sauri ya ture zancen zucin gefe ya cigaba da faɗin, “ALLAH ya gafarta mata. Toke kina da saurayi ne da aka turoki samun kuɗin kayan ɗaki?”.        Ƙasa ta ƙara yi da kanta sosai alamar jin kunya. Wasa ta farayi da yatsunta sannan cikin in ina ta ce, “Duk wanda yazo wajena Inna korarsa take yi. Tace saina haihu a gida ɗan shege ko zata bari nayi aure. A hakan ma sai su Lami sun gama yin nasu auren”.       Sosai zuciyar Abba ta sake raunana da tsinkewa. Da ƙyar ya iya furta, ”Wacece ita Lami ɗin?”.     “Ƙanwata ce ita ta haifeta da su Lailah”. Kasa sake magana Abba yayi tsahon lokaci. Sannan yace ta tashi taje ta cigaba da aikinta. Shima sai ya miƙe dan ya gagara cin abincin kuma ya koma ɗaki. Shirin fita yayi zuciyarsa na masa kaikawo. Bai wani jimaba ya kammala ya bar gidan batare da ya sake neman Halime ba.... Duk yanda Abba ke son yaƙar zuciyarsa game da abinda take ƙwaɗaita masa hakan ya gagara. Tun yana iya danne al'amarin har yana son fin ƙarfinsa. Yakan rasa sukuni a duk ranar da baiga Halime cikin idanunsa ba. Al'amarin tun yana bashi mamaki har ya koma bashi tsoro. Dan haka kawai yanzu rana tsaka zai baro kasuwa yayo gida dan kawai yaga Halime. Tun Mom na masa uziri idan yace mantuwa yayi harta fara tsarguwa da tunanin ya saka mata ido ne akan yawan yawon da take kwana biyun nan. Hakan ya sakata ɗan nutsuwa a waje guda. Yayinda shi kuma Abba zaman nata a gida ya zame masa takura. Dan idan tana nan ko giccin Halime baya gani saboda yanda take jin tsoron saɓa umarninta. A haka da ƙyar akai kwana huɗu. A daren cikar na biyar ya gagara haƙuri ya nufi gidan abokinsa Alhaji Sadisu mai-agogo. Tsaff ya kwashe komai ya sanarma Alhaji Sadisun. Shiko ya dinga dariya yana tsokanar Abba har sai da yaga ya ƙulu sannan ya bashi haƙuri tare da bashi shawarar yanda ya kamata suyi dan ganin komai ya tafi dai-dai. Sosai shawarar tayima Abba kuwa. Ya tafi gida cike da farin ciki....              ★★★       Wata irin ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi jin na faɗa kan abu mai taushi saɓanin inda na gama sadaƙarwa zan faɗi. Rawar tsorata dana riga nayi jikina keyi, dan haka na sake ƙanƙame abinda na faɗawar ina mai sake matse idanuna dake a kulle. Sai dai me, wani kalar wakitawa ƙitjina da zuciyata sukayi a lokaci guda, a take tsigar jikina ta fara mimmiƙewa. Gabana ya sake faɗuwa jin yanda wajen ya koma tsitt tamkar babu wani rai mai numfashi. Gaba ɗayan numfashina ne ya ɗauke daga illahirin gangar jikina nima, tare da wata irin girgizawar zuciya taban mamaki. Sake ƙanƙame abinda na faɗawar dai na sake yi. Wani irin jifff!! Ƙirjina ya sake bugawa a karo na biyu jin tabbacin mutum ne, mutum ɗin kuma daga ji ba jikin mace bane, sannan ƙamshin dana shaƙa na neman jirkice min tunani gaba ɗaya. Ga tsitt ɗin da wajen ya ɗauka lokaci ɗaya tamkar an tsaida numfashin kowa da komai na gidan. Sassauta riƙon da naima koma minene na fara yi, sai kuma na shiga ɗago kaina a hankali ina ƙoƙarin buɗe idanuna. Akan farin riga armless ta sport wear fara tas na fara saukewa. Sai ƙaton damtsen hannu dake a murɗe sosai fari mai ɗan duhu kaɗan dan fatar batai irin tas ɗin nan na mahaukacin fari ba. (Jikin namiji) zuciyata ta ayyana min, dai-dai da bugar hancina da ƙamshin turarensa ya sake yi. Cikin wani irin sauri da shiga tsananin tashin hankali na ɗago gaba ɗayana na sauke idanuna akan fuskarsa.........✍️ _🥺🥺Hukumar tawada da alƙalami tace a tafi yajin aiki.🥱_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒍𝒗𝒆_ __________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 ____________ .......Ƙamshin turarensa mai armashi daya bigi hancin Halime ya sata ɗagowa a zabure. Hakan yay dai-dai da isowar Abba inda take. Aiko suka kusa cin karo. Tsalle tayi baya jikinta na rawa. Tako tafi zata zube ƙasa yay saurin riƙota. Rawar jikinta ce ta ƙaru sosai sai faman zazzare idanu take tamkar bazazzage a hannun kanawa (😂😜lol).         “Please kinga calm down nutsu”. Abba ya faɗa da sauri ganin yanda duk ta gigice. Kasa nutsuwar tai, sai ma mutsu-mutsun son ƙwacewa da take kawai daga hannunsa. Sakinta yay, aiko ta kwashi tsintsiyarta ta zura da gudu hanyar kitchen dan nan ne kawai takema kallon wajen ɓuya. Murmushi Abba ya saki mai haɗe da ƙaramar dariya yana girgiza kansa da jinjina wawtarta. Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya mai kauri zuciyarsa na sake tabbatar masa da yanayin dake son hawa kansa batare daya shirya ba. Dan duk yanda yake son ƙaryata zuciyar tasa hakan ya gagara. Dole ya haƙura a yau tare da tabbatar da da gaske fa son yarinyar nan da ko sunanta bai sani ba yake. Lallai yasan shima ya taro match babba, mai aikin gidansa fa. Randa Jalilah tasan wannan sirrin nasa sai abinda ALLAH yayi ai. Maybe yankan raguna zata musu shi da yarinyar nan....        📯📯📯📯📯        Zancen Bahijja ya tabbata. Dan kuwa bata dawo ba sai bayan sallar magrib. Haka ta shigo idanunta balo-balo alamar taci kuka. A take zuciyata ta motsa. Sai dai bance da ita komai ba ganin itama ta dake tana min murmushi. Dan cike da kulawa ta shiga faɗin, “Lah baki je falo ba bayan gasu A'i can duk sun dawo su tun ɗazun. Su Mama Balki ne kawai su sai anjima saboda girkin masu gidan kowa da abinda yake so. Balle ma Uncle Boss yana gida aikin yafi tsamari kodan gayyar yaransa”.      Dariya sunan data faɗa ya bani, wai Uncle Boss. Amma sai haka kawai naji gabana ya faɗi, cikin ƴar in ina nace, “Waye Uncle Boss kuma?”.        Numfashi ta sauke mai nauyin gaske. Sai kuma tai murmushi da faɗin, “Uncle boss shine gidan dama ƙarfin ikon kidan baki ɗaya. Shine babban ɗa a gidan kuma. Bari dai kada na shagala da yawa banyi sallar magriba ba, har an kusa isha'i. Kuma Malam da anyi isha'i idan ka makara zuwa makarantar dare duka yake yi”.     Da kallo kawai na bita dan babu abinda na fahimta a zancen nata. Sai kawai na cigaba da lazimina harta fito ta kabbara salla ban sake cewa komai ba. Tana idarwa ana kiran sallar isha'i. Dan haka muka tashi a tare muka kawota. Muna idarwa ta miƙe ɗauke da Alkur'ani tace na taso muje wajen karatu. Ban musa mata ba na tashi na bita kuwa. Mun samu duk kusan ƴammatan nan sa'anninta suma sun fito, a tare muka rankaya waje. Can muka nufa cikin wajen wasannin nan dake ƙwanyar da hasken lantarki tamkar rana. Hakama tsakar gidan yake tako ina. Ga hasken ya sake ƙawata gidan tamkar ba'a duniya ake ba. Mun samu malam har ya iso, dan haka babu wani ɓata lokaci muka zazzauna a ƙatuwar dardumar dake shimfiɗe a wajen. Yayinda shi kuma yake zaune a saman kujera abinsa. Kamilun mutum dattijo. Dan shekarunsa da gashin fuskarsa zuwa kansa dake fari fat ya isa tabbatar maka da shi ɗin ba yaro bane ba. Mun gaishesa a tare, ya amsa mana da kulawa kafin a fara karatu babu ɓata lokaci dan kowa ya riga yazo. Naji daɗin karatun, duk da kuwa nayi sauka tuni. Kusan awarmu ɗaya da rabi dan sai takwas da kusan arba'in muka tashi. Sai dai yanata kallona amma baiyi magana ba balle tambayar dalilin shigowar baƙuwar fuska ajin karatunsa. Can sashen muka koma, sai dai wasu basu zauna ba suka shiga canja uniform wai zasu koma can sashen su ƙarasa ayyukansu, ciki kuwa harda Bahijja da tafi kowa rawar jikin komawa. Sun bani matuƙar tausayi, amma dai bance komai ba dan bani da abin cewar. Shiru babu wanda ya dawo a cikinsu ni dai har na fara hamma saboda sabon barcin wuri da nayi tun fil azal. Mama Balki data rigasu dawowace tace naje na kwanta. Babu musu na miƙe na wuce ɗaki kuwa, dan ni kaina nasan ina buƙatar barcin, amma ba lallai tunanin dake danƙare a zuciyata ya barni yinsa ba. Koma dai yaya ne zanyi yaƙi da zuciyata wajen ganin na yisa kodan na samu nutsuwar fuskantar abinda ke gabana. Dan Alhmdllh, ɗan zuwa islamiyyar nan ta ɗazun da nayi sai nake jin kamar yanayin da nake jin kaina sanda nake a gidan Hajiya ya fara sakina...        A hankali na buɗe idanuna da sukai min matuƙar nauyi irin na mai barci. Akan Bahijja na sauke su. Da mamaki nake kallonta. Ta sakar min murmushi da nuna min agogon ɗakin. Sosai na waro idanun waje mamaki fal raina na ganin asubahi. Kenan nayi barci sosai yau. Tab ɗi, abinda na daɗe banyi ba a rayuwata. Dan ko kwanciya asibitin da nayi ni shaida ce akan allurar da suke min ke bugar da ni bawai normal barcina ba.     Bayan mun idar da sallar asuba muka gaisa da Bahijja. Itama A'i dake faman ɗauke min kai gaisheta nayi. A mamakina sai naga ta amsa da sauri har ma abin nata ya bani dariya. Amma sai na danne banyi ba sai dai guntun murmushi kawai. Alkur'ani na ɗauka na fara karatu, yayinda A'i ta shiga wanka, ita kuma Bahijja ta fara ƙoƙarin gyara mana gadajenmu. Ina nan zaune harta kammala tace na koma saman gado zatai shara. Hakan kuwa nayi, tana kammala shara A'i ta fito, a gurguje ta ƙarasa morping itama ta shiga wanka. Bata jima ba kamar A'i ta fito. Su dukansu shiri sukayi a cikin Uniform ɗinsu wankakku harda guga dan na fahimci suna dasu ne da yawa ba ɗaya bane. Suna kammalawa harda fesa turare, na fahimci hakan kamar yana cikin dokar aikinsu a gidan zama cikin tsaftar jiki. Fuskar Bahijja da murmushi ta kalleni. “Sis.. mu zamu wuce aiki. Ki kwanta ki hutama ranki kafin a kawo break fast. Tunda kinga har yanzu ba'a sanar da aikin da zakiyi ba, ALLAH dai yasa ba tafiya dake aunty Mama zatayi ba”.        “Waye aunty Mama?”. Na tambayeta cikin sanyin murya. Kai tsaye ta bani amsa da, “Itace wadda kukazo tare. Ita ba'a Nigeria take zaune ba. Yanzu ma nasan bikin birthday ɗin Hajiya Babba ne ya kawota. Dan ana yinsa ne tamkar bikin aure duk shekara. Ana gamawa kuma zata koma ita da nan sai babbar salla”.     Kai na jinjina mata cikin nuna gamsuwa. Sai kuma na sauke ajiyar zuciya ganin itama ta nufi hanyar fita dan tuni A'i ta fice dama...      *_10:30am_*     Ina kwance a ɗaki da littafi a hannuna ina dubawa na Hadith nasu Bahijja ɗaya daga cikin ƴammatan jiya da ban gama tantancewa ba duk da an faɗa min sunansu ta shigo tai kira na. Tare muka dawo falon. Na rissina cikin girmamawa na gaida Mama Balki da muka samu ita kaɗai zaune. Ta amsa min da kulawa tana murmushi. Sai kuma ta nuna min dining table tana faɗin, “Kije kiyi break fast gashi can kar ya huce. Dan Ban sani ba ko'a buƙaci ganinki yanzu da safe. Ina fatan dai kinyi wanka?”.       Murmushi nayi mata, dan haka kawai naji ƙaunar matar na shigata. Kaina a ƙasa na amsa mata da, “Eh mama nayi wanka, kayane dai ban canja ba”.      “Karki damu da wannan. Nasan Hajiya Mama na sane da ke zata kawo kayanki in sha ALLAHU. Yanzu dai ki karya sai ki dawo nan ki zauna kisha iska ni zan koma bakin aiki kada yaran suyi shirme”.     “Na gode mama ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara girma”.          “Amin ya rabbi ɗiyata ALLAH yayi miki albarka kinji”.     Yanda ta faɗa ɗin ya bani tabbacin taji daɗin girmamawar da nake bata. Zama nayi naci abincina, duk da dai bawani na kirki bane naji yamun daɗi. Bayan na kammala falon na dawo kamar yanda Mama ta umarceni. Ina zama sai ga Mama ta dawo. Cike da kulawa ta ce, “Yauwa to taso ɗiyata, dama nace miki Aunty Mama zata iya buƙatar ganinki”. Da girmamawa na amsa mata da to ina miƙewa nabi bayanta. Sosai nake ƙara tsarkake sunan UBANGIJI daya bama waɗanda suka tsara ginin wannan gida fiƙrah da fasahar yinsa tamkar an ɗakko an dasa ne ba hannu yayisa ba. Ashe jiya kallon tsoro nayi masa. Lallai na yarda masu arziƙi na inda suke. Ashe su Mom iyayen alfahari da kuɗin Abba basu wuce ƴan aiki ba a wani wajen. Ashe duk kuɗin da take kallon iyayen Mansoor suna da shi ba komai bane ba. Zuciyata tai  wata irin jijjiga dalilin tuna masoyina Mansoor. A take naji hawaye sun cika min ido. Amma ban bari sun zubo ba na haɗiyesu.         Mayataccen ƙamshi da sanyin ac ke fara maka sallama tamkar ba safiya ba. Ga wani irin shiru da gidan ya bada tamkar babu wani rai mai motsi a cikinsa. Wata irin ajiyar zuciya ce ta kufce min batare da nasan dalilin hakan ba. A cikin takun nan nawa na nutsuwa da rashin hayaniya na cigaba da bin bayan Mama. (Ya Al-malik) na furta a zuciyata lokacin da muke gama haurowa upstairs ɗin tsakkiya. Ashe saman ma wasu shegun faluka ne da sukafi na ƙasan ƙawatuwa da barazana tamkar ba duniya za'a mutu a barsu ba. Rasama ina zan nutsu na kalla nayi nikam. Tako ina na gama diriricewa. Sai dai a zahiri baka isa tabbatar da yanayin nawa ba dan na shanye komai a raina ni da zuciyata mukeya bidirinmu kawai a baɗini.......✍️ _😂Ku cigaba da haƙuri dai, ni kaɗai nasan yanayin da nake ciki😞._     _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_ .......Cak numfashina ya tsaya, illahirin jikina ya saki gaba ɗaya. Da ga ni har shi muka zubama juna ido. Yamutsawa kaina ya farayi saboda wani sinadari mai ƙarfi dake fitowa daga cikin cat ayes ɗinsa yana shiga cikin nawa. Wani irin kallo yake min mai kama da gargaɗi koma tsanace ban sani ba. Dan duk yanda naso dakewa hakan ya gagara. Tuni naji wani irin kwarjininsa ya gama mamayeni da cikani tamkar mu kaɗaine a wani matsatsen lungu. Hatta da iska ma ta fara min wuyar shaƙa neman komawa fisgar numfashi nake yi. Wani matsiyacin kallo daya dalla min tare da ƙoƙari janye jikinsa daga nawa ya sani tafiya gaba ɗayana baya zan faɗi. Bamma san na fasa ƙara ba da komawa gaba ɗaya jikin nashi na ƙanƙamesa tamkar zan huda shi na shige ciki...         Kusan kowa dake a wajen sai da ya sake waro idanu. Yayinda tuƙuƙin baƙin ciki da kishi mai tsanani ya gama mamaye zuciya da ruhin Azizat. A yanda take jin bawan ALLAHn nan a ranta ko macen sauro ta tsani ta taɓa mata shi, ai tuni idanunta sun sake rufewa. Batama san lokacin data isa gabansu ba. “Wlhy sai na kasheki ƴar iska. Bayan maita ma harda bin mazan mutane”. ta faɗa cikin ihu mai ƙaraji tana damƙo hannun Samraah da ƙoƙarin janta baya daga jikin Maash. Wani mugun kallo ya watsa mata. Sai kawai ta fashe da kuka tare da sakar min hannun tana ƙoƙarin kaimin mari. Nima tamkar wadda aka farkar a barci dai-dai nan na dawowa a hayyacina, Cikin wani irin sauri da shiga tsananin tashin hankali na sakesa gaba ɗaya tare da turashi. Sai da me ko gezau, yana nan a tsayensa ƙyam saman ƙafafunsa tamkar dasashiyar bishiyar data kafu a muhallin daya dace da ita. Kallo ɗaya yay min da shegun idanun nan nasa kalar na maguna ya janye tamkar wanda ba'ai komai ba ma. Ga fuskar tsamm babu alamun rahama ko sassauci balle ma kai tunanin ya taɓa sanin mai kama dani a rayuwarsa. Duk yanda naso janye nawa idanun daga kansa na gagara hakan saboda tsabagen shiga ƙololuwar baƙin ciki, ruɗani da mamakin makirci da mugun halin mutumin nan, kenan da gaske shi MAASH ɗin ake nufi da sunan gidan nan?. Tayaya ma to hakan ta kasance?, farkon labarin a kano, cigabansa a Abuja, ƙarashensa a Lagos. Duka a ƙarƙashin ikonsa, kenan da gaske yayi winning kamar yanda yake iƙirari da cika bakin shi ba'a game da shi baiyi winning ba. Kai impossible...       Mugun zagin da Azizat ta lailayo min da sake yo kaina ya maidoni a hayyacina, raina a dugunzume na janye idanuna a kansa na dawo da shi gareta, dan wlhy tana sake taɓani duk haushi da takaicin mugun nan saina juyesu a kanta yanzun nan. Tana gab da kai hannunta jikina aka kira sunanta da ɗan faɗa-faɗa. “Azizat minene haka wai?!”. Mu dukanmu kalon Aunty Mama da tayi maganar mukayi, yayinda itama ta dakata tana hararata da famar huci sai kace wata kububuwa. Cikin sake bada umarni daga inda take tsaye ta dubi Mama Balki. “Kuje inda na turaku”.        “Godiya muke ranki ya daɗe, ALLAH ya ƙara girma”. Mama Balki ta faɗa tana risinawa tare da kama hannuna. Tamkar wadda aka zarema illahirin lakar jiki na shiga binta zuciyata na wata kalar suya da raɗaɗi mai zafi. Yayinda idanuna ya kasa daina kallonsa, nama rasa wana kalar tunani kuma ya dace nayi. Muna gab da fita muka haɗa ido, wani irin lumshe nasa yay da yamutse fuska ya motsa lips ɗinsa a hankali, (First Game) sai kuma ya cije gefen lips ɗin da wani salo ya ɗauke kansa gaba ɗaya daga garemu.       Da ƙarfi na rumtse idanuna dake cikowa da ƙwalla. Cikin ɓacin rai na shiga ƙoƙarin son fisge hannuna daga na Mama Balki. Dan bazan iya haƙuri ba sai na maida masa murtani. Kai yau ma duk abinda za'ayi sai dai ayi wlhy. Sake damƙe min hannu Mama Balki tayi tare da jawoni gaba ɗaya daga cikin falon muka fito cikin main falo, sai da muka fito anan ma gaba ɗaya wajen compaund sannan. Cikin lallashi da ɗan faɗa ta furta, “Ya isa mana. Ki ƙyaleta. Banda abinki ina ke ina faɗa da ƴar masu gida. Kin san kuwa fitinar Azizat musamman akan bawan ALLAHn nan. Zuciya ba taki bace ba ɗiyata, anan a ƙarƙashinsu muke dole muyi haƙuri da koma mi zamu gani. Kima godema ALLAH Alhaji ƙarami yazo wajen da wlhy abinda zai faru ALLAH kaɗai ya sanshi. A hakan ma ALLAH ya taƙaita duk barci jama'ar gidan suke. Ita kuma Aunty Mama tana da sauƙi a cikinsu da ko gidan nan bazaki sake kwana ba. Kema dai na lura akwai ƙarfin hali, ki daure ki sauke wannan zuciyar taki kada ki sake kwatanta abinda kikayi yau”.        Zantukan Mama Balki sake ƙona min rai suke. Dan haka na sakar mata kuka kawai tare da faɗawa a jikinta na ƙanƙameta. Itama sai ta riƙeni hannu bibbiyu tana lallashi na.....      Su Samraah na gama ficewa a falon Azizat tayo kansa. “Yaya Please kace afitar mana da ita a gida. ALLAH yarinyar nan mayya ce. Tun jiya da aka shigo da ita gidan nan naji na tsaneta, jinake kamar ma na kashe banza. Dan bazan taɓa yafe mata rungumar da tayi maka b.....”       Ko kallon inda take baiyi ba, sai ma motsa lips ɗinsa da yay a hankali cikin silent voice ɗin nan tasa ya furta, “Good Morning Aunt” yay wucewarsa. Wani irin tsayawa tayi cak jikinta na tsuma. Duk da ba yau ne farau ɗin hakan ba a tsakaninsu sai take jin na yau ɗin ya mata zafi. Da kallo ta bisa idanunta nayin narai-narai alamar gab take da sakin kuka. Murmushi Aunty Mama tayi da ɗan girgiza kanta tana binsa da kallo. Har sai da ya ɓacema ganinsu ta janye idanun, ganin Azizat ta zabura zata bisa ta sakko ta kama hannunta batare da tace komai ba ta jata suka koma saman dan tasan bin nasa bazai haifar da ɗa mai ido ba. Dama ga wata wutar dake neman tasowa akan matsalarsun....            ★★★ Cike da nishaɗi Abba ya koma gida. Sai dai me, yana shiga ya samu Mom na jibgar Halime har Bibaa na tayata. Yayinda Baby ke kwance a kujera wanwar alamar tasha kayan nata. Tuni yay wata irin zabura batare daya sani ba ya hankaɗesu su duka. Sannan ya ɗauke fuskar Bibaa da mari. “Kinci gidanku Habiba. Dan uwarki wannan ɗin sa'arki ce?”.      Kafin Habiba dake kuka ta bada amsa Mom data sake shiga cikin matsanancin ɓacin rai ta hayayyaƙo masa. “Mitai maka zaka daketa. Akan ƴar aiki wulaƙantacciya da iyayenta ma suka sallama ma duniya saboda baƙin talauci”.       Wani irin ɓacin rai ne ya tasoma Abba. Cikin rufewar ido ya furta, “Jalilah! Halimatussa'adiyyar ce wulaƙantacciya?”.           “Kuturun ubancan! Imamu harma sunanta ka sani? Harda ƙara masa wani ƙaimi. To ko dai kana zagayowa ne ban sani ba ta zama karuwarka. No wander yanzu kullum sai ka dawo gida da rana. Idan ka zauna kuma kata waige-waige kenan...”       “You are vary stupid Jalilah! Ni kike dangantawa da fasiƙanci?”.     “Yo in ba fasiƙin ba minene kai? Taya akai kasan wannan tsinanniyar yariyar anan gidan ma? Bayan na mata gargaɗi kaima kuma nayi maka. To wlhy kuwa zaku mutu yau ku duka...” ta ƙare maganar da rarumo flower base tai kan Halime dake maƙure gefe tana kuka. Damƙota Abba yayi da masifar ƙarfi, aiko ta juyo gaba ɗayanta ta buga masa abin a kai. Lokaci ɗaya Bibaa da Halime da Baby da hayaniyarsu ta sakata buɗe ido suka ƙwalla wata irin masifaffiyar ƙara da duk maƙwaftansu sai da suka jiyo. Yayinda fuskar Abba ta gama wankewa da jini. A take ya faɗi wanwar ƙasa. Ai sai su Bibaa suka sake ƙwala wata ƙarar da tafi ta farko. Itama Mom ta yadda guntun flawer base ɗin daya rage a hannunta tayi wani uban tsalle gefe tana ware idanu. Halime kuwa tuni ta gigice tazura waje a guje.......        💦❤️💦❤️       Komai na daina ganewa. Komai ya tsaya min cak. Ba brain kawai ba, hatta zuciyata da gangar jikina komai dake taimaka musu ya tsaya cak. har muka baro inda Alajah ta sakamu zuwa anan cikin gidan bana iya gane komai. Bin kowa kawai nake da kallo tankar wadda ke a duniyar mafarki. Koda muka koma can sashen Mama Balki bata shiga ba. Tace na shige ciki ita zata koma kan aikinta. Shiru sashen babu kowa, hatta tv a kashe take. Ban zauna a falon ba na shige ciki, saman gadon dana kwana na kai zaune, cikin gushewar tunani na dafe kaina tare da fasa wata irin ƙara illahirin jikina na rawa har ta kaini da faɗowa ƙasa....         Da gudu Bahijja data shigo sashen domin shiga toilet ta ƙaraso ɗakin, dan da farko ma ita tsorata tayi, sai da tajiyo ihun kamar daga ɗakinsu ne sannan cikin ɗari-ɗari ta nufi can. Sosai ta waro idanu, sai kuma ta zabura kan Samraah tana faɗin, “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!. Kandala! Kandala! Miya farune haka?...”       Ƙanƙameta Samraah tayi sosai tana cigaba da kuka mai tsuma rai da zuciya. Sai kawai itama Bahijjar ta sanya kuka. Dan yanzu su Sumayya ke bata labarin abinda ya faru tsakanin Samraah ɗin da Azizat. Sun kai kusan mintuna biyu a haka kafin su sassauta kukan nasu. Cikin lallashi Bahijja dake rungume da ita ta fara faɗin, “Kiyi haƙuri Kandala kinji. Haka take sam bata da mutunci. Bata ɗauki ɗan adam komai ba sai abin wulaƙantawarta. Sai kace itama ba cin arziƙi tazo yi gidan ba. Tunda ba gidan ubanta bane ba. Ai wlhy naji daɗin abinda Uncle Boss yay mata, azzaluma. Nima kullum sai ta mareni ga bautar gyara mata ɗaki da nake kamar jaka, hatta da pants ɗinta nike wankewa. Amma sam bata gani, komai akai mata ba'a iya ba, bayan ita ɗin ma babu abinda ta iya sai barcin tsiya da gantali. In sha ALLAHU Uncle Boss bazai aureta ba zamu gani”.         A hankali na ɗago ina kallon Bahijja, haka kawai kalamanta sukai wani irin tasiri a zuciyata. Har ban san sanda na furta kamar ya ba ƴar nan gidan bace Bahijja?”.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒆𝒆𝒏_ 💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥 *_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K'ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K'ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* .http://wa.me/+2347069711327 *_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *Hadin amarya budurwa ko zawara* *Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)* *Maijego package (virgin gain)* 📦 *Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji* *Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci* *Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa* *Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji* *Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa* *Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,* *Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni'ima sha'awa da dandano* *Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki* *Kalolin Zuma masu saukar da ni'ima Nan take da gamsar da maigida* *Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni'ima da dandano irin wadda akeso* *Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano* *Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar danna wannan blue rubutun* 👉🏻 http://wa.me/+2347069711327 *Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni'ima da jimawa sosai ajikin mace* *Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha'awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha'awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura* http://wa.me/+2347069711327 *Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto* ============= .......Zama Bahijja ta gyara fuskarta cike da gulma. Sai kuma ta miƙe ta leƙa waje sannan ta dawo ta rufe ƙofar. Hannuna ta kama muka koma saman gadon A'i dake can ciki. Cikin sake sauke murya can ƙasa tace, “Eh mana ba ƴar gidan nan bace ba. Uncle Boss shi da ƙaninsa kawai aka haifa a gidan nan. Ita ɗin da ƙanwarta Hindu mahaifiyarsu yayar Baban su Uncle Boss ce. Ni na rasa gane musu, ko bata da mijine yanzu oho mata, dan nidai tunda nazo anan gidan nake ganinta zaune ita da ƴaƴan nata. Sai Ashna, ita kuma agola ce. Matar Baban Uncle Boss ta yanzu itace mahaifiyarta. Bata nan sunyi tafiya ne ita da Baban Uncle boss ɗin amma nasan yau zasu dawo. Itama wadda tazo dake Aunty Mama ƙanwar Baban Uncle Boss ce ba'a Nigeria take aure ba. Ƙanin baban dai da shima yake da nasa iyalan anan gidan basa nan sunje Niger biki suma yau zasu dawo yaransu uku. Suma duk basu da kirki musamman babbar su da suke takara da Azizat akan Uncle Boss dan itama sonshi take kamar zata mutu. Shiko ko kallo basu ishesa ba....”         “A'a, to shi ina mahaifiyar Boss ɗin ko ta rasu ne?”. Na faɗa cikin tare numfashinta. A take naga jikinta gaba ɗaya yayi sanyi, sai kuma idanunta suka ciko da ƙwalla. Cikin raunin murya irin ta tausayi ta ce, “Tana nan raye bata rasu ba. Amma bata da lafiya....”     Sagade nayi kawai ina kallonta. Sai kuma cikin ƙarfin hali na furta, “Tana asibiti kenan tana jiyya?”.       Nan ma idanunta ne suka sake cika da kwalla. Sai kuma ta girgiza kanta. “Tana a cikin gidan nan kulle a sashenta. Babu mai shiga inda take sai masu kula da ita, suma basa haɗa wata a gidan nan suke guduwa duk da ɗunbin kuɗin da ake biyansu na albashi, mun rasa miyasa basa zaman. Idan kinga masu gidan sun shiga su kuma to sai dai an ɗaureta ne ko an mata allurar barci mai ƙarfi”.            “Ɗaurewa kuma? Sai kace wata dabba?”.      Shiru tayi dan hawaye ne sosai ke ɓulɓulowa daga idanunta. Har tana jan ajiyar zuciya kamar zata shiɗe. Sosai hankalina ya sake tashi, sai dai ban iya cemata komai ba na dai riƙe mata hannu alamar lallashi. Kusan mintuna biyu ta haɗiye kukan da ƙyar. Sannan ta cigaba da faɗin, “Humm bazaki ganeba Aunty Kandala. Amma ni dai zuciyata na ayyana min abubuwa da yawa a gidan nan wlhy, sai dai bamu da wani ƙarfin iko ne shiyyasa kawai na zama cikin masu kallo. Mahaifiyar Uncle Boss tana da ciwon hauka ne, shiyyasa suka killaceta ba'a bari kowa ya shiga inda take sai masu kula da ita. Sai kuma likiticin dake dubata duk bayan sati biyu. Duk randa kikaga masu gidan sun shiga inda take to an ɗauretane, dan sunce duka take yi.....”        “Har su ƴaƴan nata?”.     Yanda nai maganar a ɗan tsawace yasa ta zabura. “I'm sorrry”. Nace mata dan na fahimci na fara rasa nutsuwata. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi, alamar samun nutsuwa. “Ai Uncle Boss ne kawai. Shi ɗayan baya ƙasar, nima tunda nazo ban gansa ba sai a hoto kawai.....”      “Shi ɗin baya shiga kenan?!”.   “Yana shiga, sai dai ba koda yaushe ba. Saboda shigar tasa bata haifar da ɗa mai ido ne. Yau ma bakiga abu a gefen girarsa ba. Shekaran jiya ne daya shiga dubata bayan ya dawo ta jimasa wannan ciwon. Da ƙyar aka fiddosa a ɗakin ma”. Ta kare maganar tana hawaye. Cikin kukan ta cigaba da faɗin, “Wlhy yana bani tausayi aunty Kandala. Dan abubuwa da yawa idan yanayi zai tabbatar maka da yanda yake matuƙar son mahaifiyarsa. Itama kuma zakiji tana kuka duk dare tana kiran sunansa. Amma al'amarin nasu kamar wani abun sihiri basu isa haɗuwa a waje ɗaya ba kamar maƙiya. Wlhy da ace inada abinda zan taimaka masa koda da duk abinda na tara ne zanyi aunty Kandala. Ki duba fa kiga yanda ya inganta rayuwarmu a gidan nan tamkar ba ƴan aiki ba. Muhalli mai ƙyau, ilimin addini dana zamani kullum akwai malaman dake zuwa karantar damu. Ga albashi mai tsokar gaske. Rayuwarmu a killace ta yanda wani bazai taɓa ganinmu a ƙasƙance ya wulaƙantamu ba. Cimmu, shan mu, sutura, magani idan muna ciwo bai taɓa gazawa ba. Dan ALLAH dami zamu sakankama wannan bawan ALLAH?. Har sonake naga wace mai sa'a ce zata dace da samunsa matsayin mijin aure? ALLAH zan tayata murna harda azumin godiya ga UBANGIJI. Nasan bazaki gane duk abinda nake nufi ba. Amma nan da wata ɗaya kacal duk zaki maimaita abinda na faɗa, dan ma ba zama yake ba sosai saboda harkokin kasuwancinsa dana mahaifiyar tasa ance duk sun koma hannunsa, dan itace mai kuɗin fa. Ko wannan katafaren gidan ance ita ta fara gina shi sannan Uncle Boss ɗin yana ƙarami, sai da ya girma shi kuma ya ƙarasa saboda ita ciwo bai barta ba”. Tana kaiwa nan ta miƙe zaram idanunta akan agogon ɗakin. “Tabɗi na shiga tara, Aunty Kandala bari na koma wlhy minti biyar ta bani, nasan zansha mari”.      Kafin nace wani abu ta fice a guje. Shiru kawai nayi ina kallon ƙofa tamkar zan zuƙota da idanu. Akaf labarin data bani wanda ya shafi mahaifiyarsa ne kawai ya tsaya min a rai. To dama tana a haukan ta haifesu? Kokuwa daga baya ne haukan ya sameta? Bani da mai bani amsa dan haka na zabga tagumi kawai. A karo na farko naji ina kwaɗayin jin labarinsa. Ko shiyyasa baya son a tambayesa tarihinsa? Randa nai hira da shi ya shiga dawo min a rai. Tabbas a ranar bai amsa koda kalma ɗaya data shafi privet life ɗinsa ba. Na sake tuna ranar taron buɗe kamfaninsa. gargaɗinsa akan ƴan jarida baya buƙatar kowace tambaya sai akan kasuwanci. Hakan na nufin akwai abinda yake ɓoyewa ko baya son a sani dangane da shi. Kai dolene nasan komai, to amma ta yaya? Wannan shine tsallen baɗaken a gareni. Gashi ba wani jituwa muke ba, to wannan ma jiji da kansa zai barsa huɗɗar arziƙi da mutane....               ★★★   Tunda Samraah tabar gidan ya sake zama sukuku. Wani lokacin ma ya gwammace ya kwana a gareji kawai. Yakan yi kwana biyu bai shiga cikin gidan ba. Duk da kuwa bai fasa musu dukkan abinda yake musu na hidimar yau da kullum ba mussaman cefane da ya dawo bisa kansa. Idan har bazai zo ba yakan bama wani almajiri dake a garejinsu ya kawo cefanen. Duk da asha ruwan tsuntsaye da yakema zuwa gidan Abba bai taɓa tambayarsa ko cigiyarsa ba. Sai hakan ya sake ƙona masa zuciya da jin komai yama fice a ransa. Yakan ɗan ji sanyi ne kawai idan ya kira Hafizzullah ko mijin Samraah yaji yaya jikinta. Yakan so a bata su gaisa, sai dai hakan baya faruwa kasancewar duk sanda zai kira tana barci. Amma dai mijin kan kirasa video call ya ganta a wasu lokutan. Harga ALLAH yana son zuwa ya ganta, sai dai ta bakin su Kawu Musa baya son mijin nata ya ga kamar an nuna ya gaza ne shiyyasa ya haƙura yake kawaici. A kwanakin nan kuma sai ya koma baya samunsa duk sai hankalinsa ya tashi, yana shirin zuwa Abujan sai ga shi ya kiransa yana mai bashi haƙuri akan jinsa shiru wai yayi wata ƴar tafiya ne, amma yana gab da komawa gida idan ya koma zai haɗashi da Samraah. To tun daga ranar kuma basu sake waya ba dai har yanzu...         Yana cikin damuwar rashin ji daga mijin Samraah ɗin sai ga ogansa yazo masa da wani batu. Wai Companyn Maash na ƙera motoci da aka buɗe kwanaki sunzo garesa suna buƙatar matasan kanikawa masu kwalin secondary. Shi kuma ya bada sunansa dan yasan yana da su. A yanzu haka kuma sunce zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu suna buƙatar ganinsa interview. Rasama abin faɗa yay, sai hawaye da suka cika masa ido yana kallon ogan nasa kawai. Bai san mizai sakankama bawan nan da shi ba a rayuwa saboda ɗunbin ƙaunar da yake nuna masa da alkairan da yay masa...       “Wai namiji da kuka Musaddiq?”.    Ogan nasa ya katse masa tunani cikin nuna damuwa. Hannu yasa ya share hawayen da shi kansa bai ma san sun zubo ba. Sai kuma yay murmushi tare da buɗe baki zaiyi magana. Da sauri ogan nasa ya dakatar da shi da faɗin, “Basai kace komai ba Musaddiq. Ka cancanci fiye da haka a wajen nan domin kai ɗin ɗan hakal ne wlhy. Da ace inada abinda yafi hakan zan maka a rayuwa. Fatana dai ALLAH yasa wannan canjin da zaka samu ya zama sanadin alkairin ka a rayuwa kai da zuri'ata. Kuma ina mai farin cikin sanar maka nima basu barni haka ba. Akwai aikin dazan dinga musu, dan haka zasuzo su gyara wannan wajen ya koma na zamani kamar yanda suka faɗa”.       A take farin ciki ya sake mamaye Musaddiq. Sujidar shikur ya farayi kafin yaje ya rungume ogan nasa. Dariya ya shiga yimasa, dan har ga ALLAH yana matuƙar ƙaunar Musaddiq saboda gaskiyarsa da riƙon amana. Ga biyayya da kwazon aiki, da wahala kaga fushi a fuskarsa koda kuwa faɗa yay masa. Mutum ne mai juriya da shanye komai koda bai masa daɗi ba....     Rasa inda Musaddiq zai kai wannan farin ciki yayi, har ya danna Number Abba sai kuma ya fasa sakamakon tsoratar da shi da zuciyarsa tayi kodan halin Mom. Haƙura yayi, sai da yamma ana tashi daga aiki ya wuce Dawanau wajen Gwaggo Gudidi. Ita ya kaima wannan labarin farin cikin, ai ko baiwar ALLAH harda kukanta tana ƙara godema ALLAH. Daga ƙarshe ta gargaɗesa akan kada ya sanarma Abba yanzu kodan mugun halin matarsa zata iya shiga ta fita ta jefesa da wani sharrin. Yana dai ganin halin da aka shiga game da auren Samraah abu kamar a film ko a labaran hikayiyin marubuta. Ya yarda da shawarar Gwaggo ɗari bisa ɗari. Daga haka suka koma hirar Samraah. Itama Gwaggo ta shiga damuwa sosai hankalinta kuma ya fara tashi, anya kuwa basuyi gangancin aurama Samraah mutumin nan ba? Duk da dai a fuska yazo musu da suffar mutanen kirki. Amma dai zatai magana da Kawu Musa domin a tuntuɓi magabatansa da sukai masa waliccin auren.........✍️              _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒊𝒙𝒕𝒆𝒆𝒏_ _Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_ https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ______________ ......Sosai hirarmu da Bahijja ya tsaya min ƙyam a rai da zuciya. Duk yanda nake yaƙin son turesa hakan ya gagara. Gashi tun ranar ban sake ganin makirin ba. Hakama cikin gidan ban sake shiga ba. Bahijja dai ta sanar min Babansa da matar babansa sun dawo daga tafiya, hakama ƙanin baban nasa da iyalinsa sun dawo suma dai. Sannan yau gaba ɗaya sunyi busy wai ana aiki ne acan sashin saboda bikin birthday da za'ayi wai na mahaifiyar tasa. Ni al'amarin ma sai na ɗaukesa hauka. Yo inba hauka ba, koma nace sunfi ita mai ciwon haukan zama mahaukata mara lafiya dake buƙatar addu'a ce wai za'ama wani shegen birthday party. Kai yawudanci ma baiyi ba. Ko kuwa dukiyar tasu ce ke neman zauta musu ƙwaƙwale ma oho musu. Sosai takaici ya kumeni, ji nake kamar na buɗe ido na gansa a gabana. Wlhy da ko zai tsireni sai na faɗa masa gaskiya sai dai ya mutu shiya sani. Ina nan kwance ina ƙullawa da kwancewa wajen ƙarfe biyu su Mama balki suka fara dawowa. Hayaniyarsu tasa na fito falo nima. Sannu na shiga musu, wasu su amsa wasu su shareni batare dana san mina musu ba. Mama Balki ce ta dubeni da murmushi, cikin kulawa ta ce, “Ai kema daga gobe za'a fara miki sannun. Dan Aunty Mama tace zaki fara aikinki. Kinga sai ki shirya idan mun gama zamu wuce dake tare wajenta kamar yanda ta bada umarni”.        Sosai naji wani irin abu mai nauyi ya soki zuciyata. Na dai danne da ƙyar ina murmushin yaƙe. Da girmamawa na amsa mata da “To mama nagode”. Daga haka ban sake cewa komai ba saboda baƙin ciki. Ni kuma haka rayuwata zata ƙare. Wahalar gidan Abba. Rabani da masoyina, auramin azzalumin mutum irin wannan mutumin da bai san komai ba a rayuwa sai kansa. Daga ƙarshe ma maimakon na shigo gidansu matsayin matar aure a ƴar aiki nazo. Nasan shine ya tsara hakan, kuma zan tabbatar masa ya tsara ramin muguntar da shine zai afka ciki daga ƙarshe. Dani yake magana Samraah Abdul-wahab gwarzo.....        _Hummm Sam-G tamu. Koda yake aunty kike tunda matar Yayanmu ta🥱🥱🚴_       ❤️ Kamar yanda Mama Balki ta umarceni wanka nayi nima. A'i da yanzu ta ɗan fara kulani itama ta kawo min doguwar riga ta farin Material da suma naga sun saka a jikinsu inji Mama Balki. Nayi mamakin kayan, dan sababbine ƙal kuma daga gani ba ƙanana bane ba. Haka dai na shirya ina zancen zuci. Ganin yanda Bahijja ta tsaya tana kallona ya sani mata alamar lafiya? Da idanu. Murmushi tayi da sauke ajiyar zuciya. “Wlhy Kandala baki ganki ba. Sam bakiyi kala da masu aiki ba. Kayan nan sun sake fiddo da ainahinki na ƙyaƙyƙyawar mace wayayya. Dan ALLAH idan bazaki damu ba ki sanar min labarinki. ALLAH sai nake ji a raina ko sunanki ba gaskiya kika sanar mana ba”.       Idanu na ɗan waro mata kamar zanyi magana sai kuma na fasa nayi murmushi kawai. Dan babu abinda na ɗauki zancen nata sai shirme. A girme zan iya girmar Bahijja, amma yanayin inda take rayuwa da kuma halitta ta na mutum mai jiki yasa a ido zaka iya cewa sa'anni ne mu. Riƙoni tayi zata sake yin magana Afrah ta shigo. A wulaƙance tace, “Malamai ku Mama ke jira kuka wani zo nan kuka haɗe kawuna dan munafunc....”       Ta gagara ƙarasawa saboda saukar idanunta a kaina. Ɗauke kaina nayi tamkar banga kallon da take min ba. naja ƙaramin mayafin Bahijja na yafa nai ficewata na barsu..          “Kan uba Bahijja kinga kuwa abinda na gani tattare da yarinyar nan?”. Afrah ta faɗa cikin jimami da shiga ruɗani. Ƴar dariyar shaƙiyanci Bahijja tayi. “Yo mi kika gani?”.       “Bahijja anya ba ƴar leƙen asiri bace ba. Sam yarinyar nan batai kama da wadda ta fito a cikin wahala ba. Musamman kwana biyun nan da tayi a gidan nan jikinta ya sake murjewa sai ainahinta ya fito. Duk da muma yawancinmu badaga ƙauye aka kawomu ba rashin gata ne da neman rufin asiri amma yarinyar nan fa ta fita daban a cikinmu wlhy.”       Cikin son basar da zancen Bahijja ta ce, “Babu wani leƙen asiri. Itama dai neman rufin asirin ne ya kawota. Acikin ƴaƴan talakawan ma ai akwai ƙyawawa da yawa irinta har ma da wanda suka fita. Kin san dama irinsu gatan ne kawai babu, amma da sun samu kulawa sai ki gansu tarr da su”.      Badan Afrah ta gamsu da bayanin Bahijja ba tai shiru. Dan Bahijjar na gama bata amsa ta nufi hanyar fita itama. Kai kawai Afrah ke jinjinawa da sake tabbatar ma kanta dole ne ta sakama yarinyar nan ido a gidan nan, dan sai ta san ko ita wacece....       Koda na fito falon ma gaba ɗayansu suka zubomin ido. Hatta da Mama Balki naga alamar shock a tattare da ita. Tuni na ƙara gyara yanayina, dan na fahimci fa nima sai na yarda na ari wata rayuwa kafin na cimma burina akan mutumin nan dama zaman gidan nan. Sam bana fatan zama a cikinsa na dogon lokaci. Amma ina da burin son sanin sirrin cikinsa da mutumin nan keta faman ɓoyema duniya. Hakan kuma bazai taɓa ya kasance ba sai na zauna a matsayin da kowa ke kallona a yanzu na ƴar aiki. Ta wani gefen kuma begen ganin mahaifiyarsa da tausayinta na tsungulin min rai da zuciya. Sai dai ban san ta ina zan kama ba har yanzu. Gaishesu nayi kawai na koma gefe kaina a ƙasa...       “Tab ɗi lallai akwai rigima a gidan nan. A banga laifin Hajiya Azizat ba. Anya kuwa babu alamar tambaya anan gurin?”. Aunty Falilah ce tai maganar cikin nuna baƙin cikinta muraran a kaina. Dama na fahimci ita da sauran ƙawayenta su Aunty Kubrah basa ƙaunata sam. Kafin wani ya sake magana Mama Balki tace muje. Dole kowa ya haɗiye abinda ke a ransa muka fice. Cikin raɗa Bahijja dake ta gefena ta ce, “Kiyi haƙuri karki damu da su. Su dama su Aunty ƴan neman fitina ne, sam basa riƙe girmansu a cikinmu saboda suna gadarar yaran Mammah ne a gidan. Itace mai juya akalar kowa a gidan kuma hatta da mai gidan kansa da matarsa”.       Murmushi kawai nayi batare da nace komai ba. Dan ta gefena su Afrah ne idan har nayi magana zasu jini. Sosai an sake ƙawata gidan. Tako ina ka kalla kasan za'ayi shagali ne. A maimakon cikin gidan yau garden muka nufa. Bamma san sanda na furta “Masha ALLAH” ba a zahiri. Dan tsayawa muku misalin haɗuwa da tsaruwar da garden ɗin nan yayi ma ɓata lokaci ne. Sai dai abin mamaki bamu tsaya anan ba. Ta wata ƙofa da ganyen flower ya baibaye muka sake ratsawa sai gamu a wani killataccen waje da yafi wancan ƙatoton da muka ratso, wani irin shiryayyen adon furanni da koriyar ciyawa akai masa tako ina masu ƙamshi. Ga ƙaton swimming pool da ruwansa ke wani kalar ƙyalli da walwali tamkar ba normal ruwa ba. Ƙasa-ƙasa Bahijja dake kusa da ni ta furta, “Wannan sashen garden ɗin babu mai shigowa cikinsa sai a irin wannan ranar. Sau ɗaya a shekara kenan kawai”.       Da mamaki nace mata, “Saboda mi?”.       “Saboda bana kowa da kowa bane. Bakiga an zagayesa da waya ba. Uncle boss kaɗai ke shigowa cikinsa, dan tanan shine jikin part ɗinsa”. Ta ƙare maganar da ɗan nuna min wata hanya da aka ƙawata da koriyar ciyawa tamkar a irin lambun mafarkin gaibu ɗin nan. Na jima ina kallon ƙofar abubuwa masu yawa namin kai-kawo. Sai dai bance komai ba face ɗan kalle-kallen garden ɗin da nake yi. Komai a tsare a tsaftace. ga Docorretion ɗin da akai masa ya bala'in sake ƙawatashi. Hannuna da mama tazo ta kama ya sani kallonta firgigit, murmushi tamun da faɗin, “Zo muje ke anan zaki zauna har sai an buƙaci ganinki”.        “Mama saboda mi?.     “Saboda Aunty Mama bata bada umarni na shigo da ke har nan ba”. Komai ban sake iya cewa ba har taja hannuna muka fito a wajen. A ƙaton garden ɗin na farko muka dawo. Ta kaini can wani ɗan lungu ta ce, “Zauna anan. Kar kije ko ina dan ALLAH dan akoda yaushe zan iya zuwa kiranki”.     Kaina kawai na jinjina mata. Dan koda bata roƙeni ba ma bazan tashin ba. Nakai zaman mintuna talatin a wajen dukan tunanina naga Yaya Musaddiq. Yau wani irin kwaɗayin son jin muryarsa nake shi da Hafizzullah. Tamkar wadda hankalinta ke dawowa jikinta a wajen nake jin ƙarfin zuciyata da komaina dake neman ƙwacemin a kwanakin nan na fara dawowa. Sai kawai naji harshena ya ɗauki ambaton sunayen ALLAH. A jere na ringa sauke ajiyar zuciya kai kace a barci na farka. Ratsa kunnenna da sautin muryar malam tayi yana karanto addu'a ya sani lumshe idanuna a hankali. Ji nake hatta da jinin jikina yamutsawa yake yi har a cikin farautana har malam ya kammala. Ajiyar zuciya na sake saukewa a karo na babu adadi, dai-dai nan sai ga Mama Balki ta dawo kirana.        Nasha mamakin ganin wajen yanzu dan cike. Dan komai da alama an tsarashi ne hatta da mutanen dake a wajen. Ɗan bin kowa da kallo nake ƙasa-ƙasa nima har muka isa inda su Bahijja ke tsaye jere. Dai-dai nan mc ke shelanta fitowar mai gayya mai aiki tare da tabbatar da shi a madadin  mai birthday ɗin. Tsitt wajen yayi kowa ya sake maida hankalinsa ga hanyar da Bahijja ta nunamin ta sashensa. Duk da yanda zuciyata ke tafasa na kasa ɗauke idanuna daga kallon wajen nima. Ƙanjamammiyar baturiyar nan mai shegen iyayi da yaje da ita wajen taron buɗe companynsa ce ta fara fitowa sanye cikin doguwar riga milk da wasu shegun dogayen takalmanta. Siririn tsaki na saki tare da ɗauke kaina a wajen gaba ɗaya.        “Woow masha ALLAHU”. Da Bahijja dake a gefena ta faɗa ya sakani ɗagowa na kalleta. Ganin yanda ta saki baki da hanci da idanu tana kallo ya bani mamaki, kaina kawai na girgiza zan ɗauke caraf ta kamo hannuna. ”Dan ALLAH ki kalla ado ya namijin ɗawusu Aunty Kandala. Wlhy Uncle Boss na kasheni da salonsa, komai ya saka a jikinsa sai kiga kamar danshi dama akayi kayan, wani lokacin sai nakeji kamar na ciza uwawuna”.       Takaicin shirmenta ya sakani dalla mata harara. Nai ƙoƙarin fisge hannuna amma ta sake damƙeshi. Haushi ya sakani kallonta, amma sai naga ma ita hankalinta sam baya a kaina. Takaici ya sani girgiza kai kawai nakai dubana ga abinda take zuzutawar batare da nasan dalili ba nima..........✍️       _Bayin ALLAH kuyi haƙuri dani Please. Wlhy biki gareni na ƙanwata asabar ɗin nan. Jiya kuma rasuwa akai mana data bugeni sosai. Amma in sha ALLAHU komai ya kusa dai-dai da amarya taje ɗakinta zaku cigaba da ganina yanda ya kamata. Kuyi hakuri da asha ruwan tsuntsayen nan nawa na yanzu🙏_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏_ ......Akan takalman ƙafarsa na fara sauke idanuna, yanda suke sheƙi da ɗaukar idon mai kallo ya isa tabbatar maka almubazzaracin da akai da kuɗi wajen sayensu. Coffee brown suit ne a jikinsa, sai rigar ciki milk color. Kamar kullum botiran farko a buɗe har ana iya hango jikinsa kaɗan. Luf-luff gashin kumatunsa ke kwance a saman fuskarsa tamkar masu barci, sai wani irin sheƙi suke suma. Hannunsa ɗaya a cikin aljihun wandonsa ɗayan riƙe da wayar dake manne a kunnensa yana wani motsa ƙananun pinkish lips ɗinsa a hankali kamar wanda akaima tilas. Kamar kullum kunnensa ɗaya manne da ɗan kunne, daga tacan saman kansa zane da kitso ƙwara biyu zane ata gefe da gefe, tsakkiya wiving kusan biyar, cikkune dan haka ɗaure yake a tsakkiya ƙarshen kitson kuma gashin a warware ba'a kitseba dan haka ya sakesa kawai a baya yana lilo. Wani irin takaici da haushi ya sakani kallon fuskarsa duk da nasan tabbas yayi ƙyau. Karaf kuwa idanuna a cikin nasa. Bamma san lokacin dana balla masa harara da murguɗa nawa bakin ba. A mamakina sai kawai naga ya lumshe nasa idanun tare da buɗesu a lokaci guda yana cije gefen lips ɗinsa ya ɗauke kansa. nima ɗauke nawan nayi kamar zan fasa kuka, ji nake tamkar naje gareshi yanzu na zazzage masa abinda ke a raina. Amma dai na dake, sai harara dana sake jefama jelar PA ɗinsa dana fahimci tunda idonsa ya sauka a kaina yay suman tsaye. Niko na ɗauke kaina tamkar ban san da zamansa a wajen ba. Tunda nasan dai duk abinda mugun ogansa ya ƙulla tare da shine makirin shima. Addu'ar da aka fara gabatarwa ya saka kowa a wajen sake nutsuwa. Mu dai marasa gata duk muna a tsaye kan ƙafafunmu, yayinda suko ke zaune a kujerun da aka ƙawata wajen. Sosai yanda akai addu'ar wa kowa harda iyayenmu ya sake saka min nutsuwa har idanuna na tara ƙwalla. (ALLAH sarki rayuwa, da ace muma namu iyayen na raye babu yanda za'ai mu tsinta kammu a cikin wannan gararin rayuwar. Amma ko yanzu ma alhmdllh, koba komai mun rayu cikin aminci tunda gallazawar rayuwa batasa mun lalace ba). Kewar su Yaya Musaddiq ce ta sake taso min sabuwa har na zurfafa a tunani batare dana farga ba. Taɓanin da Bahijja tayi ne ya maidoni a hayyacina. A hankali na sauke ajiyar zuciya da nannauyan numfashi. Cikin raɗa-raɗa a saitin kunnena ta ce, “Aunty Kandala muje zamu fara bada drinks”. Kaina kawai na iya jinjina mata, dan gaba ɗaya babu wani ƙarfi a tattare da ni. Ta wajen babban table ɗin da aka shirya nau'ikan abinci dana lemuka da ruwa muka nufa. Bahijja ta zari handglob guda biyu ta miƙamin tare da mun nunin na saka. Itama ta zara ta saka a nata hannun sannan ta buɗe ƙatuwar kular da kayan ruwan ke ciki ta ɗiba lemunan da ruwa duk ta loda a babban tray data jawo guda biyu. Sai da ta gama zuba nata da nawa sannan ta ce, “Yauwa to muje. Kowa a gabansa zaki fara ajiye ruwa sannan ni kuma na ajiye lemon da suka buƙata”.        “Kamar ya?”.    Na tambaya cikin rashin fahimta. Ƴar dariya tayi. Kafin ta ce, “Na zuba miki ruwa ne dan kar su baki wahala. Shi ruwa zaka ajiye ne kawai. Amma lemo dole sai mutum ya zaɓa sannan”.        Kaina na jinjina mata alamar gamsuwa, sannan na kama tray ɗin na ɗaga ina ɗan taɓe baki. Ai da sauri na maida na ajiye ina waro idanu. Ai wlhy bazan iya ɗauka ba yamun nauyi. Ragewa na fara yi, hakan ya sata zaro idanu waje alamar nuna mamaki. “Lafiya kike ragewa?”.       “Yamun nauyi wlhy Bahijja bazan iya ɗauka ba”.     Sake waro idanu tayi, niko ban sake kulata ba na rage fin rabi sannan na ɗauka. Kallo take mun na tama rasa abin faɗa. Ni ko na sake ɗauke kaina gefe kamar ban ganta ba. Dole itama ta barni muka bar wajen tana gaba ina biye da ita. Suma sauran kowa ya fara aikinsa dan komai a tsare yake. Mun fara da table ɗin farko. Mai ɗauke da mutane huɗu kamar ko ina. Maza biyu masu tsananin kammani, a fisge kuma suna kama da mutumin can Maash. Sai dai kawai su baƙaƙe ne. Tabbas nasan mai irin fuskar nan amma na manta a ina. Sai mata guda biyu ƙyawawa suma, ɗaya fara tas ɗaya black beauty. Su duka sunci ado sosai mai tsananin ƙawa. Ganin kallon da suke min na rashin sani yasa naji kamar duk na daburce. Amma sai na dake kaina a ƙasa na shiga haishesu ƙirjina na bugawa da sauri-sauri. Mazan ne kawai suka amsa min, yayinda baƙar matar ta dubi Bahijja a gadarance ta furta, “Wannan fa?”.           Jikin Bahijja har ɓari yake. Cikin in-ina ta amsa da, “Au...aun..Aunty Mama ce tazo da ita randa ta iso”.     Su dukansu ɗan kafeni sukai da kallo, sai kuma duk suka janye cike da basarwa. Jiki a sanyaye na bar wajen, batare da ina kallon gabana ba saboda zancen zuci na iso table na gaba. Ganin nayi tsaye kawai Bahijja ta ɗan zungureni, firgigit na kawo numfashi, ɗagowar da zanyi na sauke idanuna a kansa. Zaunensa yake a harɗe fuskar nan kicin-kicin tamkar ba wanda ya tara jama'a ba. Gaba ɗaya hankalinsa na akan tab dake a hannunsa ne. Yanda yay serious a kanta zai baka tabbacin abinda yake yi mai muhimmanci ne. Ga uban ƙamshin turarensa da ya mamaye wajen gaba ɗaya. Fuska na yamutse tare da ɗauke kaina. Harara na ballama ɗan koren PA ɗinsa dake table ɗin bayansu. Ƙasa naga yayi da kansa yana murmushi. Jinai zuciyata ta ƙulu da murmushin nasa, amma sai na danne tare da cije lips ɗina kawai....         “Woow! fine girl ko ana mana rowan ruwan ne?”.      Ɗaya daga cikin waɗan da ke zaune a table ɗin tare da shi ya dawo dani a hayyacina. Ni sai ma yanzu na lura da sauran dake zaunen a tare da shi. Su duka su nasan fuskokinsu a wajen taron buɗe Companyn sa na Kano. Dan ALLAH ya bani baiwar da dawahala nai maka gani ko ɗaya ne na manta fuskarka koda ace ban riƙe suna ba ko a inda na sanka ba. A hankali na ɗan yamutse fuska ta. Batare da nace komai ba na fara ajiye musu ruwan. Uku na ajiye abina batare da nashi ba, dan kowa a gabansa na ajiye amma shi banda shi. Na ɗaga tray ɗin zan bar wajen wannan dai da yay maganar ya ɗan waro idanunsa yana nuna min shi. “Beauty baki ajiyema boss ba fa”. Yi nai tamkar ban jisa ba sai da Bahijja tasa hannu ta ɗauka ruwan ta ajiye masa jikinta har yana ɗan rawa. Harararta nayi batare dana san dalili ba. Itako ta waro idanunta na nuna mamakina. Tray ɗin na sake ɗagawa da nufin barin wajen ina dallamasa harara ta gefen ido dan tunda mukazo wajen ko sau ɗaya bai motsa ba balle kai tunanin yama san da zuwan namu, batare da nasan yanda akai ba, ta yaya kawai tray ɗin ya suɓuce min na tafi gaba ɗaya na. Idanu kawai na runtse tare da sallamawa, amma sai na jini zaune jikin mutum, yayinda shi kuma tray ɗin ya suɓuce a ƙasa sauran ruwan suka tarwatse. Wani irin zuƙa da nayima mayataccen ƙamshin turarensa ya saka gabana faɗuwa. Da sauri na buɗe idanuna dake a rufe. Sai kawai na waro su tare da yunƙurawa da sauri zan miƙe amma hakan ya gagara. Dan sake zamewa nayi na koma jikin nasa gaba ɗayana har ma fiye da farko.        “Sai kice son hawa kike ba sai kinyi pretending ba”.     Naji saukar muryarsa a cikin kunnena. A wani irin zafafe na sake yunƙurawa gaba ɗaya na na miƙe jikina har tsuma yake, sai da Bahijja data gama firgita ta riƙoni. Jinai bazan iya daurewa ba, idanuna na tara ƙwalla na watsa masa harara, sai dai ina motsa lips ɗin na nufin juye masa abinda ke raina naji na gagara hakan. Sakamakon wani shegen kallo daya tsatstsareni da shi tare motsa lips ɗinsa a hankali, “Kina cewa tak sai kowa yasan ke MATAR MAASH ce”.     Da masifar ƙarfi na cije lips ɗina hawaye na sake ciko min idanu. Badan na samu horo akan aikina game da salon da yay maganar ba da bazan fahimta ba. Amma gamu ƴan jarida yaren magana da ido ma an karantar da mu balle na motsa lips. Da wani irin salon rainin hankali ya kai yatsarsa manunuya saman goshinsa tamkar zai gyara silin gashi yay salute tare da sakin wani matsiyacin murmushi gefen baki ya kanne ido ɗaya.      “Sai na tarwatsa rayuwarka”.   Na faɗa nima a saman lips ɗin ina haɗiye hawayen da suka ciko min idanu. Sanin zasu iya zubowa na kai durƙushe nima ina taya Bahijja tsinci ruwan daya tarwatse. Sai faman haɗiyar zuciya kawai nakeyi dan ni kaɗai nasan abinda nake ji a cikinta, nu mutumin nan zai cema ina son hawa masa jiki ne dama. Ƙasa-ƙasa Bahijja ta furta, “Aunty Kandala kice masa yayi haƙur....” ruff ta rufe bakinta tare da haɗiye sauran abinda ke bakin nata saboda hararar dana balla mata. A fusace na miƙe tare da sunkutar tray ɗin nabar wajen. Mama Balki ce tai min nuni da nazo inda take. Dole na nufi inda muka ɗebo ruwan. Amsar tray ɗin tayi tana faɗin, “Badai kiji ciwo ba ko ɗiyata? Alhamdullah ma Alhaji ƙarami na kusa ya taimaka miki da kinyi muguwar faɗuwa ai. Sai naci ƙaniyar Bahijja kuwa, tunda bance harda ke za'ayi aikin nan ba amma ta jaki”.           Sosai naji raina ya ƙara zafafa. Wato su abinda suka fahimta kenan nazo zan faɗi ya taimakeni, alhalin ina zargin taɗeni akayi da ƙafa, tunda karo naci da abu a bazata, kuma babu wani dutsi ko ƙarfe balle ace shine. Ko rantsu nayi ba'a bina bashin kaffara mutumin nan shine silar faruwar komai, dan shine ya taɗeni da ƙafarsa........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*