TSURON TSIRIN.. TSANDAURI.. LAMBA TA ƊAYA LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) GIDAN ƘAMSHI Da fatan mun yi sallah lafiya. Mata barka da gajiyar aikin sallah Ubangiji Allah ya bamu lada, su kuma mazajenmu Allah ya ƙara musu arziki mai albarka ameen🤲🏻 Ina kuke masoyiya littattafan Mrs Bukhari gidan ƙamshi? Nace gashi na sake fitowa da wata tafiya mai rikitarwa. Marubuciyar taku dai kunsan irin salon rubutunta da jerin littattafanta kamar haka. GISHIRIN ZAMAN DUNIYA MATA IYAYEN GIJI MAI IDO A TSAKAR KA DUNIYA NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA. IDAN KAYA YA GAJI GAMMO MA YA GAJI. TO YAU GANI DA WANI MAI TAKEN TSIREN TSIRIN TSANDAURI KU BIYONI DAN JIN YADDA TSIRIN ZAI FITO A TSANDAURI, KU GYARA ZAMANKU TAFIYACE MAI DOGON ZANGO WANNAN KARON MA SANNAN TAFIYAR TA MUSAMMAN CE SOSAI. DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINƘAI Ranar litinin wanda yayi dai_dai da ɗaya ga watan ɗaya a lissafin nasara. Masu iya magana sukan kira ranar litinin da tushen aiki wanda ko bature ke tsoronta. Ni macece mai ra'ayi sosai Zan iya cewa tsattsauran ra'ayi to, amman ina da sauƙin sha'ani gaya. Sannan duk inda na shiga burina in dishashen taurarin kowa ya zama nawane yake da ƙarfin haske sama dana kowa. Ni macece Ƴar gyaye da ƙwalisa tamkar Maigogul ne ya haifeni wajen bama ado da kwalliya muhimmancinsa, duk abinda zan saka a jikina nafi son ya kasance mai tsada wato daraja. Dan ko ankone aka fitar babbar atampar nake zuwa in nemo, ko in tura samfurin har garin Lagos sai an nemo mun. Kuma tun ina budurwa haka nake, saina kasance ta daban cikin ƙawaye, ta daban kuma a cikin dangina, harma da dangin mijina. Na kasance mace mai guruka masu yawan gaske, gani da naci da ƙwallafa abu a raina, inna kafe ina da taurin kai musamman akan hanyar cimma gurina. Bana damuwa da wahala, ko barazana wajen cimma guri hakan yasa na kasance mace jajirtacciya, jaruma, mai kama da mikiya wajen fita ta nemo da kanta. Ita mikiya fita take yi ta farauto naman ƴan uwanta tsintsaye dashi take kalaci, bata da tsoro sam, kuma tafi son tayi da kanta ba dai ta ƙarashe aikin wani ba. Ba ungulu mai jiran a mutu ta zo ta cacciki naman mutum ba. marar tsoro kuma kona misƙala zarratin. Ni ɗinnan ina alfahari da kaina gaya. Ina da kama mutuncin kaina da kiyaye abinda zai zubar mun da kimata, hakan yasa ko magana zan furta sai nayi jim tare da nazari kafin in furta. Domin a furuci ake gane nauyin ƙwaƙwalwar mutum, da harshe mutum ka iya samun daraja, da harshe mutum ka iya furta abinda zai zubar mishi da kima abadan. Amman ƴan gidanmu dama gama garin jama'a suna mun kallon mai shegen girman kan tsiya, dangin miji, da maƙotana duk haka suke mun kallo, sai dai duk wannan baya damuna, nasan mutum ba'a taɓa iya mishi, a yayin da ka burge mutum ɗari, haƙiƙa sai mutum ɗari biyu da hamsin sun sokeka. Na kasance baƙace ni ba fara ba dan ko a sahun wankan tarwaɗa bazan fito ba, ni ɓakace mai lallausan fata. Ina da hancina daidai gwargwado amman bashi da tsayi kamar biro. Abu mafi kyayu a fuskata shine idanuna da siraran shiryayyun haƙorana masu ɗauke da tsagun wushirya sama da ƙasa. A ɗakinmu nafi kowa gashi sabida irin nacina da kuma ɗaukar gashi da mahimmanci da nayi, duk wani mai na gashi duk tsadarshi saina tara kuɗina na siya, yadda nake mutunta gashina ko fatata bana gatantata haka sabida Innarmu takance damu shi gashi rabin kyan mace ne, sai na ɗauki wannan kalmar na azata bisa kaina. Har bafulatana mai nono a bakin layinmu ta shaidani dan duk satin duniya saina sai manshanu ɗanye na mulke gashina dashi tsabar inason gashi, Alhamdullahi gashin ya samu, ko ina nake a cikin taron mata zan iya buɗe kaina in yi shafar kai hankali kwance. Sannan in kitso zanyi bana manyan kitso ƙananu nake yi sosai wanda a ƙalla zasu kai guda ɗari da hamsin zuwa ɗari biyu, kuma kullum da lalle a tafukan hannayena da tafukan ƙafafuna. Bani da tsayi can ɗinnan gaskiya ni gajerace ƴar dandaɓasa mai faɗin ƙugu da mazaunai masha Allah. Kun gane Fati Baffa ƴar wasan hausa tsohuwar jarumar da suka yi zamani dasu Abida Muhammad? To tsayinmu zai yi ɗaya kunga ai kuwa gajera ce ni ko? Sai dai kash bani da girman nono, ƴan mamunana basu shige na bera ba, su dai banyi gigin cewa zan ƙarasu ba naji ina da ra'ayin barinsu a hakan. Ina da tumbi cikina ba'a shafe yake ba ko ba gaskiya ba dan tumbina yana iya fitowa ta cikin riga ana hangowa, yatsun hannuna dana ƙafafuna gajerune kamar yadda nake gajera Hindu duwaf ƙawayena ma da muka taso tare suke kirana har ƴan gidanmu suma suka kama anfi cewa duwaf ɗin ma, kuma ina amsawa domin ban ɗauki hakan a matsayin rauni ba sam. Sai dai mu gajeru Allah yana yi mana baiwa ta diri fiye da dogayen mata. Ku lura da kyau da wuya kuga gajerar mace wacce bata da diri, shi yasa ko gajerun mutane waɗanda ake kiransu da wada Allah yayi musu diri da mazaunai. Amman dogayen mata kafin kiga mai diri goma kinga hamsin babu cinya babu sharaɓa ko ba gaskiya bane?" ( bafa ni nace ba Hindu duwaf ce take magana) Ina ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan rediyon Kano ni edita ce, wani sa'in ina yin labarai musamman na yamma. Amman a aikin gidan Rediyo nafi sha'awar aikin fita ba na zama a ofis ba, sai dai ita rayuwa ba duk abinda kake so kake iya samu ba. Yauma ni na karanto labaran yamma fitowata daga cikin ɗakin watsa labarai kenan sai naga wayata nata rauji. Da sauri na duba wayar kafin in ɗauko ta tsinke. Mijinyawa ke kirana kuma ya kirani fin sau goma. Take naji gabana ya faɗi dan tabbas ba lafiya ba. Mijinyawa baya kiran waya sau uku ma, biyu kawai yake yi ya haƙura sabida yasan yanayin aikina ba ko da yaushe yake bani damar amsa waya ba, wani sa'inma kasheta baki ɗaya nake yi. Kafin in gama tunanin da nake yi wayarshi ta sake shigowa a karo na goma sha ɗaya. A sanyaye na ɗauka tare da sallama da sassauƙar murya. Ilai kuwa sai naji muryar wani daban ba mijinyawa ba. "Assalamu Alaikum madam sunana Aminu Jibrilu in babu damuwa muna buƙatar ganinki a asibitin malam Aminu Kano" Take naji hantar cikina tana kaɗawa tare da duk tsokokin jikina. Lafiya meya samu me wayar dan Allah? " "Ki kwantar da hankalinki ɗan abinda ya sameshi ba mai yawa bane. Kuma a wajen kiran wayarshi munga har dake kuka yi waya dashi da misalin ƙarfe ɗaya, kuma da halama ke iyalinshice shi yasa muka kiraki. In kin shigo ki tambaya ward ɗin maza manya ɓangaren ƴan haɗari na taimakon gaggawa. Amman ki kwantar da hankalinki baima wani ji rauni sosai ba." Da sauri na zame wayar a kunnena na suri jakata dake ajjiye akan teburin aikina. Luba zanje Asibiti Mijinyawa ya samu haɗari kya sanar ma oga" A guje na fita zuwa harabar gidan rediyon. Motata na hau illahirin jikina babu inda baya kakkarwa, bama a cikin hayyacina nake tuƙin ba, daga gidan Rediyon Kano zuwa malam Aminu Kano sai naga yayi mun wani irin nisa gaban mamaki. A guje motata ta shiga cikin asibitin, in tsaya in pakata da kyau wallahi na kasa. Da sauri_sauri gudu_gudu naita kutsa kaina ina tafe dake nasan ward ɗin mazan nan da nan na ƙarasa. Mutane sai darewa suke yi suna bani hanya duk wanda yaga saurin da nake yi yasan bana lafiya bane sam. Wasu ma har dakatawa suke suna kallona. Dana isa cikin babban falon ward ɗin maza saina rasa inda zan nufa ga dai marasa lafiya da yawa a kwance a ɗakin ɓangaren ƴan hatsarine subhanallahi Ubangiji Allah yai mana rowar ciwo. Wayata na ciro da sauri na kira lambar mijinyawa, sai na jiyo raujinta daga can ƙarshen ɗakin a wajen wani gado da aka rufe da labule halamun ana dubashi kenan. Saina ga likitan ya fito. A guje naje gabanshi. Nice wacce muke waya dakai ɗazu. Dr dan Allah wanne hali Mijinyawa yake ciki kace ciwon nashi babu yawa ko?" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. "Kiyi haƙuri yanzu muna kan aikinmu ne, ɗaki ma za'a sake mishi tukunna. Zaki iya jiranmu a waje, ƴan sandan da suka kawo mana shi sunje zasu dawo yanzu. Yana dai fil ko kati tare damu ne? " Kai kawai na girgiza Halamun A_a. "To ga Sista ki bita duk abinda ya dace ayi" Wata ma'aikaciyar jinya nabi har zuwa bakin wani taga anan na cike komai jikina da hannuna sai kakkarwa suke yi duk da jarumtata. Ina zaune shiru a kan dogon bencin dake kallon ward ɗin, nan aka zo aka wuce da wani magidanci ya ƙone har kanshi, sai wani irin ƙara yake yi. Ai take zuchiyata ta kuma tsinkewa, to ko shi mijinyawa a cikin wanne hali yake oho, ya Allah ga bawanka kai kasan yadda zaka yi dashi. Wayata na zaro na daddanna sunan wan Mijinyawa Hassan ɗinshi kenan mai suna Nawata, shi kuma Mijinyawa ana kiranshi Gawata. Sunayene na ƴan biyu wanda a ƙasar hausa a da ake sanyama tagwaye. Anyi tagwaye sakaruna a shekarun baya a Kano ta dabo NAWATA DA GAWATA. Nawata da Gawata sune sarakunan kano daga alif dubu ɗaya da ɗari ɗaya da talatin da huɗu zuwa alif dubu ɗaya da ɗari ɗaya da talatin da shida. Sarakunan tagwayen sunyi Sarautar Kano a tare har sai da ɗaya daga cikinsu wanda littafin tarihin Kano bai ambaci wanene daga cikinsu ya rasu ba. Ya rasu watanni bakwai bayan hawansu kan karagar sarautar. Ɗayan tagwayen ya rasu a shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari ɗaya da talatin da shida bayan yayi mulki shi kaɗai na watanni goma sha bakwai. Tagwayen Ƴaƴan Gijimasu da Munsada ne. A yanzu sunan ya ɓata gaskiya, ba kasafai ake samun tagwaye masu irin sunan ba, inma an samu zaku ga yawanci dattijaine. Shi kuma mijinyawa da ake cewa dasu, Nawata shine Mijinyawa Babba, Gawata mijina kenan shi kuma mijinyawa ƙarami ake kiransu harma sunayensu ya ɓace ɓat. Asalin waɗanda ake kira da mijinyawa yaron da aka haifa kakanninshi dukka suna raye na wajen uwa da uba musamman ma matan, to waɗannan yara su ake kira da Mijinyawa. Bansan ya ɗauki wayar ba sai jin sallamarshi nayi a kunnena. A sanyaye na amsa. Dama Mijinyawane ya samu hatsari yanzu haka ma ina asibitin malam Aminu Kano, ko ganinshi ba'a bari nayi ba." Duk wannan abunfa babu ɗigon hawaye a idanuna sabida gaskiya ni macece mai dakiya sosai ba komai ke sani kuka ba, kuma duk ƙwaƙwarka baka iya gane logona. "Subhanallahi ganinan zuwa yanzu. Kafin in ƙaraso Ado zai zo tunda ya fini kusa, kin sanarma su Nanno? " A_a ban faɗama kowa ba. Naga ba jin daɗin jikinta take yi ba, ba a faɗa mata ba " Sai yayi jim kafin can kuma yace. "Gaskiya ne. To sai nazo dai" Ya datse wayarshi. Cikin ƙasa da minti talatin sai ga Ado ya ƙaraso ƙaninsu Mijinyawane amman ba Nanno bace ta haifeshi ba kishiyarta ce ta haifeshi, gidanmu ɗaya tare da iyalanshi shima. Jigum_jigum dai muka yi daga ni har Ado, can sai ga Mijinyawa Babba da Gambonsu shima tare muke a gida ɗaya da iyalanshi. "Yana ciki har yanzu ba'ai kiranki ba? " Cewar Mijinyawa Babba da duk ya shiga damuwa. Basu kirani ba, nafi awa ɗaya a zaune anan dan Allah ka shiga ka dubo shi" Ai bamma rufe baki ba ya kutsa kanshi cikin ɗakin dan wata iriyar shaƙuwace mai ƙarfi a tsakankaninsu, damma Matarshi nason kassara zumuncin nasu. Bai jima da shiga ba sai gashi sun fito tare da likitan. "Gambo ka shiga ka zauna tare da Mijinyawa Ƙarami, Hinduwa ke kuma muje" Da sauri na miƙe na bisu har ofishin likitan. "To a gaskiya ya samu mummunan haɗari, sai dai da taimakon jama'ar gari da taimakon ƴan sanda an kawoshi akan kari. A binciken da muka yi a kanshi, ya samu raunuka da yawa irinsu kujewa daujewa, sai gilashi daya ratsa tsakiyar cinyarshi ya lume, wannan ne dai sai anyi mishi ƙaramar tiyata kana ya zubar da kusan rabin jinin dake jikinshi, abinda ya zama mai sauƙi babu buguwa a kanshi ko wani rauni mai tsanani da zai zama barazana, sai kunnenshi daya tsaye shima za'a ɗinke mishi in sha Allah. Motar tashi gaskiya tayi kwatsa_kwatsa a yadda su ƴan sandan suka nuna mana a waya sai dai muce ya auna arziki dan bakwa ce mutum mai rai zai iya fitowa a motar ba" Jin irin hali da raunukan da Mijinyawa ya samu ya firgitamun lissafina, sai dai babu hawaye, na rasa kuma kalmar da zance sai Allah kawai nake ambato, lokaci guda idanuna duk suka farfaɗa. "To Dr yaushe za'ayi mishi aikin, sannan a halin yanzu me ake buƙata? " "Aikin sai zuwa gobe za'ayi mishi, babban abinda ake buƙata a halin yanzu bazai wuce jini ba. A yanzu dai yau muna buƙatar kamar leda huɗu da za'a soma saka mishi, sai kuɗin allurannan muna buƙatar a biya, da kuma shi kanshi kuɗin aikin za'a rubuta muku takadda kuje ku biya gobe sai a shiga dashi ɗakin tiyata" Takaddun biyu yasa hannu ya amsa. "To yanzu Dr akwai ƙannena za'a iya ɗaukar jininmu ayi mishi amfani dashi a shirye muke" "To babu damuwa sai kuje lap a auna aga lafiya da dacewar jinin, in yayi falillahi hamdu" Mijinyawa Babba, bani takaddun ni sai inje in biya ku kuje lab ɗin" Shiru yayi, nasan ba lallai bane in yana da kuɗin da zai iya biya ba, rayuwar dai ƙarfin haline zuchiya dai garesu ba dukiya ba. Bashi da tsumi bare dabara dole ya miƙa mun. Da sauri duk naje na biya na dawo na ba Dr. Lokacin dana shigo naga Mijinyawa Babba da ƴan sanda a tsaye suna tattaunawa akan zasu je inda haɗarin ya afku. Dr zan iya shiga in ganshi ko? " "Madam zaki iya in kika daure kika ƙarfafa zuchiyarki dan yana cikin wani hali. Sannan ga wayarshi sai ki riƙe a hannunki, sauran abubuwan da suke motar yana hannun ƴan sanda tukunna." Godiya nayi mishi na fito zuwa ɗakin da mijinyawa yake ciki. Daga nesa na hangoshi a kwance a gado, gefen fuskarshi ya kumbura ta wajen kunnenshi daya yage, ga bandeji a kunnen, cinyarshi ma an rufe da wani farin saƙa, ga ciwuka duk an wanke mishi. Fuskarshi na ƙurama idanu sai lokacin naji naji rauni sosai ya shigeni ganin irin yadda lokaci guda halittar Mijinyawa ta sauya tamkar bashi ba kundukukina na shafa ina nazari da girmama ƙudurar Allah. Na ja doguwar kujera na zauna, babu ko riga fa a jikinshi, wandoma gajerene kawai shi yasa aka katange gadon da labule. Numfashinshi yana hawa da sauka a hankali. Wayata ce ta soma ruri da sauri na ciro Azgar babban yarona ɗan jami'a ke kirana. Azgar ya akayi kana ina?" "Ammi da gaske wai Abbanmu ya samu haɗari kuna asibitin Malam Aminu Kano? " Idanu na lumshe nace. Hakane Azgar sai dai kuyi ta ma Abbanku adda'a. Kazo ka sameni a asibiti, su Asama'u da Sabira su zauna a gida kada suje ko'ina" Sai naji duk Azgar ya kiɗime duk da dai dama ba jarumi bane sam. Sai lokacin na tuno ai ya kamata in faɗa a gidanmu nima. Yaya Saratu babbar yarmu na kira na sanar mata halin da ake ciki. Ki sanar ma su Inna da Baba Soja Yaya Saratu" Itama duk sai hankalinta ya tashi. Ina zaune ga marasa lafiya iri_iri wani inka kalleshi ma wallahi ba zaka sake ba, in kaga halin da mijin wata, uban wasu, ɗan wasu, wan wasu, ƙanin wasu ke ciki, sai kaga majinyacinka shi kamar ma lafiyarshi ƙalau. Tunani na shiga yi zuzzurfa. Azgar ne ya dafa mun kafaɗata sai zuchiyata ta tsinke dana ɗago na kalleshi naga ya toshe baki hawaye na sauka a kundukukinshi. Murmushi nayi. Azgar banda kuka adda'a zaka yi mishi. Allah ga kayanka kai kasan yadda zaka yi dashi, zauna ga kujera kaji ko?" Zama yayi tare da share hawayenshi mukai jigum_jigum har Mijinyawa Babba yazo dashi da Uwatale matarshi da basket na abinci, harda su fulo da tabarma. Suna isowa Yaya Saratu suka iso ita da Akarami shima wanane ɗakinmu ɗaya. "Abinda ya faru kenan? Ɗan adam ba'a bakin komai yake ba" Cewar Yaya Saratu kenan tana jinjina kanta. "Am dan Allah kuje daga waje mutum ɗaya ya zauna dashi ba lokacin ziyara bane yanzu" Faɗin wata ma'ailaciyar jinya. Ajjiye kayayyakin da suka zo dashi Uwatale tayi, Yaya Saratu ma sun tawo da abinci itama ta ajjiye "Ammi kije sai in zauna ni" A_a Azgar kuje kawai kaji? " Akarami ya riƙe hannunshi suka fita dukkansu. Wayar Mijinyawa dake jakata ta shiga ruri, bani da lokacin amsa wayar koma waye zaro wayar da nayi da zummar sakata a shiru ta yadda ko an kira bazai dami mutane ba nayi. Sunan da yake yawo a kan wayar ne yasa na kalla da kyau. Sweet L naga an rubuta harda jan zanen zuchiya a gaban L ɗin. Gabanane naji ya yanke ya faɗi. Sweet L kuma a wayar Mijinyawan? Kai ina idanuna ne suka samu matsala gaskiya, in kuwa hakan na gani to tabbas ƙila lambar Nanno ce, ko lambar mijinyawa Babba. Tuni na saka waya a shiru na mayar jakata naci gaba da kallon hawa da saukan numfashin Mijinyawana. Kamar wasa sunan dana ga ya kira wayar nafa kasa mancewa sai canki cankar wanda ya dace a saka ma sunan nake yi, sai zuchiyata taƙi kwanciya. Ni gashi ba ɗabi'ata bace bin diddigi da son ji ko ganin ƙwaƙwaf ba, sai naji zuchiyata na jana ala dole ya kamata in san waye Sweet L ɗinnan. Tsintar kaina nayi a bisa bin umarnin zuchiyata ta hanyar zaro wayar wanda yayi daidai da shigowar saƙo a manhajar whatApp kuma duka daga wannan Sweet L ne saƙon. Wajen kira na soma shiga ta kirashi sau takwas, kafin ya kirani ƙarfe ɗayan rana. Ya kirata kun kai minti arba'in suna waya. Zuchiyata na rawa ina gangarawa ina duba tarihin waɗanda yake kira da waɗanda suke kiranshi har na tsawon sati guda. A cikin sati gudannan a rana yana kiranta fin sau bakwai, kuma suna daɗewa, jiya ma ƙarfe biyun dare sun kai awa guda suna waya. Sai naji kaina ya ɗaure zuchiyata ta buɗe iska na shigata takota ina wallahi kunji na rantse. Ina daga cikin matan da basu taɓa ɗaukar wayar miji da sunan bincike kamar yadda matan wannan zamanin suke yi ba. Ina ganin wallen masu yi da mamakin abinda ke ɗarsa musu rashin yadda da mazajensu da har suke bincika musu wayarsu. A matsayina ta ma'aikaciyar gidan rediyo wacce ta karanci aikin jarida tabbas nasan wayar mutum sirrinshi ce. Ni da Mijinyawa muna da wani irin yadda da junanmu na ƙin ƙarawa, ƙarewar yadda yasan nawane tarina a asusun bankina, nasan tarinshi a asusun bankinshi, babu bashi a tsakaninmu ko nawane zai iya cira daga asusuna ya kashe ba tare dana tambayeshi me yayi dasu ba haka nima ina iyayin yadda naso da dukiyarshi. Babu shiri na kori shaiɗan ta hanyar cewa A'uzubullahi minal shaiɗanun rajin. Na jefa wayar a ajjihuna tare da kyautata zatona akan lambar. Ina zaune shiru ashe har magriba tayi ni ko ko la'asar banyi ba. Jini wata ma'aikaciyar jinya ta zo ta ɗaura mishi tace dani. "Amman bake zaki zauna dashi ku kwana ba ko? Kinga nan ward ɗin mazane mazane masu jinyarsu" E nasani yaronshi zai zauna dashi" "To ya kamata ki soma shirin tafiya gida magriba harma ta wuce zance tunda an fito daga masallaci." Da sauri na miƙe tare da surar jakata. Na matsa daf kuskar mijinyawa nace. Allah ya baka lafiya Mijinyawana Allah ya tashi kafaɗunka, kayi haƙuri gobe shidan asuba anan zata yi mun" Kamar yana jina haka nake magana. Haka na juya na fita. Su Azgar suna zaune dashi da Mijinyawa Babba, sai Yaya Saratu da Akarami. "Yauwa kin fito ba? Dama yanzu nake so inje in miki magana ya kamata ki koma gida. Ni da Azgar zamu zauna dashi. Ungo nan Atm ɗinshi ne da ƴan sanda suka bani, na'urarshi da sauran tarkacen kayayyakinshi suna gida an kai." Karɓa kawai nayi bance komai ba. Su Akarami sukai musu sallama muka fita. Akarami ne ya ja motata suka mayar dani har gida har ɗaki, Yaya Saratu kuma ita ta jawo motar Akarami tana biye damu a baya har gida. Yaya Saratu ta kaini ɗakina. Bata tafi ba saida nayi wanka na rama sallolina tasa Asama'u ta kawo mun shayi da tuwo ta tusani a gaba saida naci dan dole ba dan daɗi ba." "To zamu tafi Duwaf. Ku kuma Asama'u sai ku dinga leƙo Umman taku, kui tama Abbanku Adda'ar Allah ya tashi kafaɗarshi, Hindu aita adda'a da kai lamura wajen rabbil izzati shine sarki ɗaya da zai share miki hawayenki. A rungumi ƙaddara" Tai ta bani kalma daga ƙarshe sukai mun sallama suka tafi. Yara suka zauna dani har wajen goman dare kafin nace suje su kwanta ƙarfe ɗaya su tashi suyi sallah su roƙama mahaifinsu samun waraka Allah yasa ayi mishi aikin da za'ayi mishi a sa'a. Ina zaune a tsakiyar gado kamar mai jego ƙarfe ɗaya ƙarfe biyu ba bacci ina ta ambaton Allah. Ga zuchiyata sai saƙa da baƙin zare take yi mun dangane da lambar Sweet L. Tsintar kaina nayi da ɗauko wayar a karon farko a rayuwata kenan dana shiga abinda ba'a gaigaceni ba. Kuma sai naji take nayi ma mata masu binciken wayoyin mazajensu uziri. Ashe wannan duba waya shine sanadin tarwatsa rayuwata da karya alkadarina. Hmmm ina buɗe manhajar WhatsApp ɗin saƙon Sweet L ne a farko wanda tayoshi tun yamma lokacin ina asibiti. Shiga nayi ga abinda na gani a rubuce. "Babyna wai da gaskene ka samu haɗari ko ko dai wasane dan Allah. Hankalina ya tashi sosai kasan irin son da nake yi maka ba irin na tsohuwar bagidajiyar matarka bane. Dan Allah ka kirani ko hankalina zai kwanta" Dariya nayi ina girgiza kai ina maimaita kalmar tsohuwa bagidajiya data kirani dashi. Lallai maza ƴan Babansu. Wallahi na ɗauka mahaifiyar Mijinyawa ce kaɗai zata iya aibatani a gabanshi ba tare daya tare mun ba, baya ga ita na ɗauka babu mahalukin daya isa, ashe budurwarshi ma ta isa ta rubuto mishi kalmar Bagidajiya tsohuwa wai ni?" Sai kawai na shiga haurawa can saman chart ɗin naita haurawa amman na kasa ƙurewa a daidai wasu hotuna na tsaya. Hoton tsaraicin mijinyawa na gani tsirara haihuwar uwarshi da ubanshi, harda bidiyo yana kwance a gadona yana wasa da gabanshi yana mata nishi da sambatu har yana cewa tazo tayi mai ita kaɗai yake jin sha'awa baya ko ƙaunar kallon matarshi mai ƙiba da tumbinnan." Wallahi a lokacin alƙiyamata tsayawa fa tayi, kunnene sai naji ya ɗauke sai wani shuuu_shuuu yake yi mun, kaina kuwa shima sai naji yayi wani irin dum. Ashe haka mazan suke, ashe haka matan da suke kama tsaraicin mazajensu suke ji. Daurewa nayi na dake na buɗe bidiyon yarinyar ita data fishi wayo babu fuska sai al'aurarta cike da ni'ima tana wasa dashi kamar yadda yayi mata. Sai bidiyo na mamanta suma tunjun_tunjun dasu, ga cikinta a shafe kamar bata cin abinci. Saida na ajjiye wayar na miƙe na shiga zagaye ɗakin ina safa da marwa na fin awa guda. Mrs bukharihttps://chat.whatsapp.com/JI1IGIBFHYm64hr6IfVfqR TSURON TSIRIN.. TSANDAURI LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA BIYU. BARKANMU DA DAWOWA Hindu: Na jima sosai ina zurga_zurga tare da murmushi na gaban mamaki. Bawai ban taɓa jin labarin matan da suka amince da mazajensu kuma sukai musu budulci ta hanyar raba tsaraicinsu ga matan waje bane. A.a Ina da youtube chanal da nake wayarma da mata kai duk da bani da yawan mabiya a YouTube ɗin nafi karkata akalata da izuwa Facebook. ina da zaure a shafin Facebook da nake wayarma da mata kai tare da ba da ginannun shawarwari dan taimakon ƴan uwa mata. A whatApp ma ina da zauruka guda biyu shima duk aikin da nake yi kenan zauren ma na kuɗine nera dubu uku ake biya kafin mace ta shiga, babu abinda bana koya musu da hanyoyin kama zuchiyar miji ta hanyar kirsa da maɗe, nice koya magana, nice koya salo _salo na kwanciyar Aure domin duhu da ƙauyanci, da kunya dake kan da yawan matanmu na Arewa yasa na zaɓi wannan hanyar dan ganin an rage yawan zinace_zinacen da mazan wannan zamanin suke yi sabida ƙorafin yayi yawa. Mata in suka kawo mun ƙorafin mazajensu na charting da matan waje suna tura tsaraicinsu, ko kuma mace tace miji inya dawo bata samun hankalinshi, wallahi ni sai inga kamar matan in da laifin mazan sai inga kamar laifin na matan yafi yawa. Ashe akwai ragowar karatun maza da ban buɗe shafin ba, sai yanzu Mijinyawa ya buɗe mun gashi ina biyawa da manyan baƙi. In dai duk kulawar da nake ba mijinyawa bai katangeshi da nuna tsaraicinshi ga wata ba, bai hanashi jin sha'awar wata ba. Babu abinda mace zata iyayi ta katange mijinta face ta miƙa ma Allah shi yayi mata maganinshi babu tsumi babu dabara sai dai mace ta gyara kanta ta kasance ta musamman domin kanta da kanta kada tayi domin burge ɗa namiji dan ba lalle ta burgeshi ba. yarinyar da bata kai mace ba saita ɗauke hankalin magidanci, yarinyar da kika fita da komai da komai fa. Hmm wai maza ku wanne irinenene, daku nake? . Kayan gyaran Aure wallahi bana ƙasata najeriya nake sha ba mafi yawanci, ina dai shan kayan sirrin tsirrai nasu Abokiyar hira da su pinkish kayansu na da inganci sosai. gyaran jiki babu irin wanda banayi, ina amfani da basarakiyar dilka ta Mrs Bukhari wacce take sanya santsi da laushin fata, da hasken fata mai kyau sirrin matan Sudan. ( Nakune mata masu daraja na haɗa muku kuzo ku sameni domin mallakar wannan dilka bata lalacewa ko shekara zata yi duk mai so tayi magana) Man shafawa mai tsada nake shafawa, haka sabulun wankana mai darajane. Turarukan jiki, kulaccham, humrori, turaren wuta na alfarma masu ƙamshin sanyaya rai na Mrs Bukhari dasu nake amfani gidana, duk da mahaifiyata tana da nagartattun turarukan wuta da take yi da kanta amman na gamsu na yadda da nagartar na Mrs Bukhari ɗari bisa ɗari. dukkannin kayan sakawana na gida cike suke da ƙamshin kabbasa turaren turara kaya da na feshi a kaya, sib ɗina kina buɗewa ƙamshi zai daki hancinki. Duk na wajen Mrs Bukhari ne fa. Ina da ƙananun kaya da rigunan bacci masu kyau da bada haɗin kan da duk akeso masu tafiyar da damuwa da sanya fara'a gani da zati na faɗa muku a baya. salon mu'amala kullum a cikin kashe kaina nake dan in faranta ran Mijinyawa. Kullum cikin ƙirƙirar girki nake in zuba kuɗina nayo cefanen da gumina dan kawai yazo ya zauna yaci yana santi. Kuloli kuwa ina dasu da yawan gaske danma ina fitarwa, nike nan cikin sake mishi kulala filet, cokali, kofin shan ruwa aikina kenan. Kullum maganarshi shine Tutar so bakya tsufa kullum kamar amarya nake ji da ganinki. Abu ɗaya nasan ya tsuro dashi shekara ɗaya kenan akan shi yanason in cire wannan tumbin nawa duk da da sigar wasan gaske yayi kalaman kuma bata hanyar zafi ko kaushi yayi furucinba cikin lalama da salama yayi maganar kuma sau ɗaya tak bai kuma ba. Wallahi kullum a cikin siyan ganyayyakin shayi nake na zaizaye kitse da tumbi dan kawai in faranta mishi yaji daɗi kawai, har motsa jiki na koya na rage tumbi dan kawai farin cikinshi. Danginshi sun tsaneni gani suke son da yake yi mini yayi yawa gani suke yi kamar asiri nayi mishi kasancewar ni Kanuri ce cikakkiya sai suke ganin ban barshi haka ba. Ni kaina nasan mijinyawa na sona babu wata iriyar sadaukarwa da baiyi mun ba a rayuwa. Farinciki harda kuɗi yake cirewa ya siyo ya kawo mun domin jin daɗina. Rayuwace babu irin sauyin da bata zuwa dashi. Yau ga sakamakon dagon ƙaunar Mijinyawa na samu. Zama nayi na ɗauki wayar naita haurawa har saida nazo farko, duk da bashi bane farkon maganar tasu ba. A hankali naita bi inajin yadda suke musayar kalaman ƙauna, da irin yadda yake mararinta da kuma irin yadda yake kushemun baiwata a gareta labarin gazawata ko da yaushe yake haska mata, ni kuma nayi imani da Allah babu ta inda na gaza bance ɗari bisa ɗari nake ba amman ni macece wacce ta yadda da kanta sharrin wasu mazanne kawai ya hau kaina nima. Abunda ya buga mun kwanyata yawuna ya ƙafe ƙaf shine hoton wacce na gani ɗin. Itace suke wannan abun da mijinyawa dama, itace take ta nanata mishi tsohuwar matarka mai tumbi da wasu kalmomi na aibantawa. Allahu Akbar duniya tazo ƙarshen ƙarshe wallahi. Saƙwannin duk na kwafe na dawo dasu kan wayata, ba tare dana karashe bi ba, ai wannan hoto dana gani ya ƙonemun jinin jikina ƙarƙaf, ya tsiyayemun man kaina tas, bani da buƙatar ƙarashe bi sam Wayar na kashe na buɗe durowar gefen gadona na jefa. A lokacin ko tsaga jikina akayi ba za'a tadda jini ba. Murmushi wanda yafi garwashi zafi nayi. Da ƙarfina na miƙe na shiga banɗaki na sakarma kaina ruwa ko kayan jikina ban samu zarafin cirewa ba, saina tsinci kaina da murmushi. Idanuna na ɗaga sama nace. Allah ga kayanka nan kai kasan yadda zaka yi dashi. Murmushi na sake yi a karo na barkate na sake kallon sama nace Ya Allah! Zuwa gare Ka nake kai kukan raunin ikona, da ƙarancin dabarata, da kuma walakancina a idon mutane.Ya Mafi jinkan masu jinkai! Kai ne Ubangijin mafiya rauni, kuma Kai ne Ubangijina.Ga wa kake barina? Shin zuwa ga bare na nesa ne da zai riƙa nuna mini fushi? Ko kuwa zuwa ga abokin gaba ne da Ka mallaka masa al'amarina?Idan har ba Ka yi fushi da ni ba, to ban damu da kowace wahala ba. Amma lafiyarka da kariyarka su ne mafi yalwa a gare ni.Ina neman tsari da hasken fuskarka—wanda duffai suka haskaka da shi, kuma al'amarin duniya da lahira ya gyaru a kansa daga saukar fushinka a kaina, ko kuma tabbatuwar fushinka a gare ni.Gare Ka nake tuba da neman gafara Ubangiji har sai Ka yarda. Kuma babu wata dabara ko ƙarfi sai da taimakonka. Ina kaiwa haka na saka hannu na cire kayan jikina na jefasu a bokiti ruwan sanyinnan ya shigeni sosai kana na ɗauro alwala na fito. In nayi sujjada sai infi minti talatin goshina a ƙasa ina magana da Ubangijina ina nuna mishi abinda akaimun. Ga adda'ar da naita nanatawa kema ki riƙeta. Zan yi haƙuri mai kyau (marar gunaguni). Kuma Allah shi ne abin neman taimako akan abin da kuke siffatawa na yaudara da ƙarya. Ita naita nanatawa Haka inna zauna zaman tahiyar da sallama zanyi nake fin minti goma sha ina ƙara nanata ma Allah halin da nake ciki. Babu fa hawaye ko sofane a idona wallahi bana jin zan iya zubar da hawaye sabida bashi da amfanin da zai mun. Ina da jarumta irinta wacce naci sunanta wato Hindu bin utbah matar Abu sufyan mahaifar Mu'awuyya. Kunsan suna akace linzamine ni na gani a karan kankin kaina Ga yadda zuchiyar Hindu ta kasance. Zuciyar Hindu bint Utbah wajen jarumtaka ta kasance mai naci, maras tsoro, da kuma karsashi na ban mamaki, ko kafin ta musulunta ko bayan ta musulunta.Malamai da masana tarihi sun siffanta zuciyarta da abubuwa guda uku: 1. Zuciya Mai Cikar Kamala Da Juriya Hindu ba ta da tsoro ko kaɗan. A al'adar Larabawa, ana ɗaukarta a matsayin mace mai "Zuciyar Maza" saboda yadda ba ta firgita a lokacin tsanani. Ko a lokacin da yaƙin Yarmouk yai ɗumi, kuma manyan jarumai maza suka fara ja da baya saboda yawan sojojin Romawa, zuciyar Hindu ba ta girgiza ba ko kaɗan. 2. Zuciya Mai Juya Akalar Mutane (Leadership)Tana da zuciya mai tasiri da kwarjini. Idan ta yi magana ko ta yi tsawa, maza ba su iya jurewa saboda kwarjinin zuciyarta. Wannan ya sa ta iya tsayar da dakaru maza da suke gudu, ta canza musu tsoro ya koma jarumtaka da kunya. 3. Sauyawar Zuciya Zuwa Ga Gaskiya Babban abin mamaki game da zuciyarta shi ne yadda ta canza lokacin da ta musulunta. Zuciyar da ta kasance cike da gaba da ƙiyayya ga Musulunci ta koma cike da kishin addini da ƙaunar Allah da Manzonsa S A W. Jarumtakar da ta yi amfani da ita da can wajen yaƙar Musulmai, ta dawo tana amfani da ita wajen kare Musulunci. Nima haka nake wallahi. Saida nayi sallar asuba kana na haye gado kaina kamar zai tarwatse ga zazzaɓi_zazzaɓi dake taso mun. Asama'u wacce ita ke bin Azgar ce ta shigo da sallama yarinya nutsattsiya kamila mai ƙoƙarin aiki, tafi Sabira aiki sosai, amman Azgar in ɓangaren girkine ya fisu iyawa. "Ammi kinyi sallah kuwa?" Ta faɗa tana kai hannunta wuyana. "Ammi zazzaɓine a jikinki sosai. Subhanallahi kiyi haƙuri Ammi Allah zai ba Abba lafiya. Mun yi sallah mun roƙa mishi lafiya. Murmushi nayi tare da rufe idanuna. Babu komai Asama'u baccine ba zazzabi ba. Kuje ke da Sabira ku gyara gida, Azgar yayi abincin da zamu tafi dashi asibiti, kuna da lekca ne da safennen?" "A_a Ammi bamu da lekca sai ƙarfe ukun yamma. Bari muje mu soma aikin. Azgar kin mance ai a asibiti ya kwana." Kai kawai na ɗaga mata. Kafin ta fita. Sabira ta gaisheni hannu kawai na ɗaga musu. Cikin minti uku bacci ya kwasheni mai nauyi bani na barka ba sai takwas na safe lokacin Sabira ta tafi sukul. Ogana na soma kira a waya na sanar dashi ina buƙatar hutun sati ɗaya sabida lalurar mijinyawa. "Babu damuwa Hindu ki nutsu ki kula dashi ai Mijinyawa gudane harda ɓari, Allah dai ya bashi lafiya" Hmmm Murmushin gefen baki nayi tare da yi mishi godiya mukai sallama. Asama'u ce ta shigo mun da shayi da soyayyar doya da miyar ƙwai. Kai na ɗaga mata dan lokacin na riga na kira wayar Baba Sojanmu harya ɗauka nagagga kiran mutane da yawa harda kiran Azgar. "Hinduwa ya jikin shi Mijinyawan? " Baba Sojanmu jikinshi Alhamdullahi yanzu ma nake shirin zuwa asibitin." "To shikenan muma yanzu muke kintsawa Akarami zai kawo mu tare da iyayen naki, sai munzo. Ko akwai wani abu da kike so a tawo miki dashi? " A_a bana buƙatar komai Baba Sojanmu" "Shikenan Hinduwa sai mun zo" Haka mukai sallama saida na fito wanka na kira Azgar ina karyawa. "Ammi kun tawo ne? " Tukunna nima banji daɗi bane amman nan da minti talatin zamu ƙaraso in sha Allah. Yaya jikin Abban naku ya farka kuwa? " "A_a bai farka ba yanzu ma cuku cukun shiga dashi ɗakin Tiyata akeyi shi yasa nake ta kiranki kizo kafin a shigar dashi" To shikenan Azgar gamunan zuwa" Na kashe wayar tare da karyawa a gurguje na kintsa na fito Asama'u na riƙe da basket. Wai saida matar Gambo da matar Ado suka gammu mun fito a tsakar gida dan kuturun wulaƙanci suke tambaya ya mai jiki. Da sauƙi mun gode" Na basu amsa a ɗaure nayi wucewata. Muna tafe ina tunane_tunanen da ni kaina bana iya tantance komai. So nake yi ƙwaƙwalwata ma ta huta amman ina sai tafasa take yi. Muna shiga ɗakin muka tarar ana ƙoƙarin jan gadon da Mijinyawa yake kai za'a wuce dashi ɗakin tiyata. Jikinshi ya kumbura sosai har fuskarshi da babu rauni saida ta kumbura suntun. Hannun Azgar na riƙe kawai. Mijinyawa Babba yace. "Hindu ayita adda'a dan Allah kuyi haƙuri da ganin idanunki baki samu bacci ba shi yasa ma baki zo da wuri ba" Kai kawai na ɗaga mishi bazan iya cewa uffan ba. Haka aka fice da Mijinyawa muka bisu har gaban ɗakin tiyatar sai dai sun umarcemu da mu koma bakin can babban ɗaki. Haka muka dawo Asama'u ta zuba musu kayan karyawa suna kan karyawa Su Baba Sojanmu suka iso shi da Inna Ruwayya wato Ruƙayya ake nufi da yaren Kanuri itace mahaifiyata. Doguwar baƙar kanuri mai gajeren hanci da zanen fashin goshi dogo, hancinta hagu da dama duk a ɓule suke ta saka barimar zinare a duka hudar biyu, gata da gashi, son gyara, ƙafarta kullum da baƙin lalle dan mu dai bamu taɓa ganin fararen tafukan hannayenta dana ƙafafunta ba. Inna Ruwayya ba kyakkyawa bace in kallo ɗaya zakayi mata. Amman tana da abubuwan da suka saka tafi Inna Abida kyau gashin da take dashi mai yawa, domin ko da yaushe tana faɗa mana gashi yana ɗaukar kaso hamsin bisa ɗari na kyau. To wannan gashi da salon kitsonsu na Kanuri ya fito mata da martabarta, haka zalika hujin hancinta ya haskata sosai, uwa uba laushin fatarta da sheƙin da fatar take yi shima wani abune. Muma duk ta ɓula mana hancinmu hagu da dama kuma tun muna yara ta maƙala mana zinare a hancin namu, hudar kunne kuwa huɗune damu a jejjere. Innarmu itace ta Biyu a wajen Baba Sojanmu yaranta goma cib, Shida mata huɗu maza, mazan ɗakinmu gabaki ɗayansu Sojojine. A ɗakin Inna Abida tana da Yahuza shine kaɗai soja. Sai inna Abida itace uwargidan Baba Sojanmu wacce akayi musu Auren zumunci iyayensu wa da ƙanine a gidansu Inna Abida Baba sojanmu ya girma Mahaifin Inna Abida shi ya saka shi a aikin Soja inna Abida da wannan take ƙafafa sosai. Inna Abida macece gajera mai ƙiba, gata da ido da hanci kamar biro. Yaranta goma sha huɗu cib. Bakwai maza bakwai mata. Sai Inna Turai itace Amaryar Baba Sojanmu, ita ba tsohuwa bace gata da kyau fara sol da'ita. Yaranta huɗu duka ƙananane babbar Ƴarta Tahira a js 2 take, ga cikin na biyar a jikinta goɗai_goɗai dasu. Gidanmu gidane na yawa da tarin al'umma da tarin matsallalun da sannu zaku gane kan gidan da ɗabi'un kowa. "Hindu, Mijinyawa Babba sannunku ya shi Mijinyawa da jikin? " Cewar Baba Sojanmu dake miƙa ma Mijinyawa Babba hannu. Duk da yaso nokewa saida Baba sojanmu ya bashi wannan hanu suka gaisa harda Azgar. Su Inna suka tsallako suka taddani akan tabarma harda abinci suka tawo niƙi_ niƙi Nan aka shiga gaishe_gaishe. Baba Sojanmu yana zaune a benci tare dasu Azgar. "Hinduwa to ki kaimu muje mu ganshi mana ko tunda abinda ya kawo mu kenan. Cewar Inna Abida tanaso ta ganshi sabida ta samu damar barbaɗa zance a cikin gida ba.. " Ai bama sai mun ganshi ba, a gabanki Akarami yake sanar mana ko sutura babu a jikinshi, ina ke ina kallon siriki a haka" Cewar Innarmu wacce Hausarta take a gurɓace da irin harshen garinsu. "Nima dai haka na gani, ni ɗakinma bazan iya shiga ba" Cewar Inna Turai da irin tata Hausar ta Fulanin usil. Basa ma ciki an shiga dashi ɗakin tiyata bamu san yaushe za'a fito dashi ba" Hakan yasa zancan baiyi tsawo ba. Masa da miya suka kawo mana masar da ita muka ci muka rayu duk kwanan duniya da safe ita muke ci, wasu suci da miya, wasu da sikari, wasu da ƙuli. Guda biyu Innarmu ta zuba mun bayan ta zuba ma Azgar da Mijinyawa Babba. Ban musa mata ba na karɓa na cinye. Sun ɗan jima isowar su Gambo da matansu ne yasa Baba sojanmu ya miƙe. "Mu zamu wuce Allah ya bashi lafiya ni da daddare zan dawo' Kuɗi ya ƙirga dubu ashirin ya ba Innarmu ta miƙo mun. Akarami ya bani dubu sha biyar, Innarmu ta bani dubu goma su Inna Abida sai taɓe baki kawai suke yi. Har wajen motarsu muka rakasu ni da Azgar da Asama'u da Baba Sojanmu yake ta tsokanarta tana dariya. Suna fita motar su Yaya Saratu ta shigo ƴan ɗakinnmu. Yaya Saratu, Yaya Zubaida, da Firdausi, Rayya, da Jinjin, nike bin Zubaida sauran duk ƙannena ne, Yaya Saratu kuma itace babba a ɗakinmu Obarol. ( Maman Twins gafa obarol ta mata kuma an samu) Sun tawo da abinci kula kula suna nan har aka fito da Mijinyawa daga tiyata aka dawo dashi ɗakin hutu, sai dai sun hana a shiga a duba shi. Azgar da Mijinyawa Babba tun safe suka tafi, mijinyawa aiki ya wuce, Azgar kuma wanka yaje yayo, sai ya tawo da Sabira wacce ta dawo daga makaranta. Wajajen azahar su Yaya Saratu suka tafi daidai lokacin Ƴan jama'are suka iso mata biyu da namiji guda. Inna Dubu itace kishiyar Nanno mahaifiyar mijinyawa, sai matar ƙanin Nanno Inna Duduwa, sai ƙanin mahaifinsu Mijinyawa Kawu Tanko. Cikin girmamawa da kame kaina na gaishesu tare da tambayarsu hanya, suka tambayi mai jiki na ce musu da sauƙi. Ban sake bi ta kansu ba, sunata hirarrakinsu a tsakankaninsu harsu Ikilima matar Gambo da Sajida matar Ado suka ƙaraso nan Inna Dubu ta shiga nannan dasu sune surukan arziki, ni kuwa ko a kwalar rigana bana neman yaddar kowa a da balle a yanzu da akayi walƙiyama halin Mijinyawa ya fito, badan albarkacin Ƴaƴa da bani da amsar da zan basu ba wallahi Allah da babu abinda zan sake takowa inyi a asibitinnan. To bana so kima da darajar Mijinyawa ta zube a idanun ƴaƴanshi da basu da tamkarshi, inna danne na daure ai zai dawo gida kuma abinda ya faru ya daɗe da faruwa ba gogewa zaiyi ba. Sannan bazan nuna damuwata ta yadda za'a gane logona ba sam Namiji bai isa yasa mun hawan jini ba sai dai in saka mishi ina dalilin da sai dai muita ƙona kanmu muna haska rayukan maza? Mijinyawa zan bashi mamaki wallahi zai girgiza da lamarina. Ƙarfe uku nayi Azgar da Asama'u sukai mana sallama suka wuce makaranta. Maƙotanmu na layi suka yo gungu guda suka tawo dubiya. Wajajen magriba aka bamu damar shiga duba Mijinyawa amman da ɗaya da ɗaya, a lokacin Mijinyawa Babba dasu Ado duk sun zo. Haka akaita shiga nice ta ƙarshe dana shiga Nayi shiru ina kallon fuskarshi ƙwaƙwalwa kuma na aikin ɗora mun bidiyonshi na tsaraici da irin sambatun da yake ma yarinya ƙarama a waya. Ya zubar da kima da duk darajarshi, nima ya zubarmun da daraja da kimata wacce har abada bana jin zata dawo wannan kimar. Maza basa tsoron Allah da tuntuntuni akan mutuwa. Allah ne fa yaso tunama Mijinyawa asirinshi dalilin ma da yasa yayi haɗarinnan kenan har wayarshi ta iso hannuna. To wai yanzu in bai farka ba ya mutu me zaije ya faɗama Allah? Jiya gashi da ƙarfinshi da lafiyarshi yau kuma gashi a kwance baisanma a duniya ko a lahira yake ba. Wannan ayace agaremu wallahi. A tsayen da nake na tuno wata baiwar Allah da take neman shawara a wajena tayi mun saƙon murya take faɗa mun irin zinace_zinacen da mijinta yake yi sai nace mata ta bani lokaci zanyi tunani akai kafin in bata shawara. Bana so kai tsaye ince ta kashe aurenta a samu matsala. Dan na fahimci mata zasu kawo maka ƙaran mijinsu yana cin zarafinsu ƙololuwa amman da zaran kace su haƙura da auren wata ba zata sake kulaka ba. Wata saita soma maka lissafin ita yaranta take ji, ko kuma kuji tana cewa adai duba a bata wata shawarar. Mijinyawa ya dawo ya sameni a ina nazari ya zauna a gefena. "Bani labarin damuwar dake shinfiɗe akan wannan Kanuriyar fuskar mai annuri da nagarta Tutar so." Murmushi nayi a kullum kalamanshi suna sanyaya mun ruhina tare da faɗaɗamun sadari na. Nan na bashi labari kaji_kaji abinda ke faruwa bani shawara in bata. Hmmm kunsan me yace?. "Duk macen data zauna da mazinaci jakace bata san ciwon kanta ba, bata son lafiyarta, kuma kice bata ma kanta adalciba inta zauna" Sai gashi yau na kamashi dumu _dumu da nuna ma mace tsaraici, anyi zinar, ba'aiba ban sani ba tunda ban gama bin chart ɗin ba. Sannan ba lallai a chart in samu tabbacin anyi zina ko ba'aiba. Amman ina da tabbacin sunyi zinar hannu, sunyi ta ido, sunyi zinar waya kuma. Mininyawa kenan wallahi idanunka sai yayi kiliya. Wucewa nayi na fita dan zuchiya sai take cemun in shaƙeshi ya mutu duk mu rasa amman dake ni na mallaki zuchiyata ba ita ta mallakeni ba saina fita, da'ace zuchiyata ke da ni da tuni na ƙarashe mijinyawa. Azgar zamu wuce gida sai gobe, ga abincinan ya isheku, ku kuma ku kwashe kayannan muje." Mijinyawane yace. "To Inna duk ku ɗunguma muje in kaiku wasu su shiga motar Hindu maza in sauke ku in dawo. Haka ko akayi Inna Duduwa da Inna Dubu suka shiga motata muka dawo iyakarsu dani a tsakar gida dama a ɓarayin Uwatale suka saba sauka. Ina shiga cikin falona na mayar da sakata. Kuje ku kwanta, in kuma zaku ci abincine ku girka kuci" "Ammi kefa kinci abincinne" Murmushi nayi ganin yadda Asama'u ta damu. Akwai kayan shayi a ɗakina zansha in kwanta kar ku damu" Ina shiga ɗaki nanma na saka sakata. Wanka nayo na zura rigar baccina doguwa, na ɗan dafa shayi a butar zamani mai aiki da wutar lantarki, na sha zallan shayin na kwanta nayi lamo a gado, inata tubkewa da warwarar yadda zan ɓulloma wannan babban Al'amarin daya tunkaroni, da wasa bazan taɓa iya tunkarar wani ko wata da wannan maganar ba, dole in ci in cinye tare da ɗaukar matakin daya dace ni kaɗai dama ni ba mai faɗar sirri ko matsalar gidana bace, ni da kaina nake yanke hukunci da kaina bana buƙatar shawarar kowa. Sai kawai na tsinci kaina da son yin bidiyo mai ɗauke da sassanyar magana ga matan da suka tsinci kawukansu a irin halin da nake ciki. Nayi bidiyo mai zafi da tasiri dake ina cikin zafin abun, na fesar da maganganu cikin ilimi sosai. Editin ɗinshi nayi da kyau na ɗaurashi a youtube chanal ɗina da shafina na Facebook. Ajjiyar zuchiya na sauke na kwanta. Na dai fi awa guda ina juyi daga baya bacci ya ɗaukeni. Washegari takwas a asibiti tayi mun ni kaɗai na tawo na dai shiga ɓarayin uwatale a gurguje na gaishe da su Inna Duduwa na fito na wuce asibiti. Sabira ta wuce makaranta, Asama'u kuma sai tara take da lakca. Ina isa Asibiti na tadda mijinyawa ya farka shayi ma Azgar yake bashi a hankali. Hmmm mutumin naku fa ya farka bai mutu ba. Mrs Bukharihttps://chat.whatsapp.com/JI1IGIBFHYm64hr6IfVfqR TSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA UKU. Ga Mijinyawa Babba a zaune shima dai karyawar yake yi. "Abba ga Ammin ta ƙaraso, Ammi tunda Abba ya farka sunanki yake ta ambata" Hmmm wasu maza sun shiga ukunsu da yaudara da munafurci. Ni dan baƙin ciki ma sai nake ji kamar in zazzagama kaina gas ko fetur. Ɗan murmushi nayi na ƙarasa bakin gadon Mijinyawa ya dubeni nima shi nake kallo ina kallon wannan bidiyo na tsaraicin a fuskarshi. Sannu mijinyawa ashe ka farka? Allah yasa kaffarane ya tashi kafaɗunka sannu kaji" "Ameen Tutar so kinga yadda Allah yayi dani ko? Na buɗe idanu ban ganki a gefena ba shine Mijinyawa Babba yake faɗamun ba'a barin mata jinya" Sai tari ya sarƙe shu ba tare da ya samu zarafin ƙarashe abinda yake son faɗi ba. "Sannu mijinyawa ka dena yawaita maganar haka akace. Hindu ƙarasa bashi shayin, mu kuma mu samu muje mu kintsa zan fita kasuwa Azgar yaronnan ko bacci bayayi duk sanda na farka zan ganshi a zaune ya tusa uban yana mai addu'a" Zama nayi a bakin gadon na amshi kofin shayin a hannun Azgar. Kaje kaima Azgar ka shirya ka tafi makaranta ƴar uwarka daga gida zata wuce. In kuma ka sameta a gidan sai ku tafi tare. Amman ga abinci kuci tukunna naga wanda kuke ci na siyarwane" Lafiyayyen abincin dana kawo su ka zuba su ka ci sukai ƙat kana sukai mana sallama. Mijinyawa kuma tsomen biredi da dingayi mishi ina bashi da cokali. Hannuna ya riƙe yana kallona. "Ya'isa Tutar so amaine yake yinƙuromun" Kafin ma ya rufe baki ya soma amai kamar zai amayar da ƴan hanjinshi. Ina tsaye ina mishi sannu, daya gama aman na zuba ruwan zafi a bokitin wanka dasu Azgar suka siyo, na surka da ruwan gora, ɗankwalina na cire dashi na goge mishi aman tas na goge mishi jikinshi da kyau, ina gamawa su Ado na shigowa. Tare dasu na fita na barshi da tambaya na isa inda majinyata suke wanke kayansu da wanke_wanke. A nan na wanke dankwalin nawa da zallan ruwa na wanke bokitin tas, ɗankwalin na shanya a igiya na dawo da bokitin na sake zama a bakin gadon, lokacin ma'aikaciyar jinya tana kanshi tana bashi baki akan ya daure yaci wani abun sabida magani da zaisha. Naga ma har an ɗagoshi bayanshi na jingine a jikin gadon. "Madam ki bashi abinci yaci zuwa anjima zan kawo mishi maganinshi, sannan za'a wanke mishi ciwukan dake jikinshi." To mungode" Iyakar abinda na iya cewa kenan. Abinci na zuba mishi a hankali yake buɗe baki ina bashi, muna cikin haka sai ga su Yaya Jamila da su Inna Duduwa ko yaushe ita Yaya Jamila tazo oho. Zuwansu yasa su Ado su kuma sukai mana sallama kowa ya tafi aikinshi. A cikin jam'u na haɗa dukka na gaishesu Yaya Jamila dai bata amsa ba, dama banyi gaisuwar dan ta amsa ba. Sai cewa tayi. "Hala a garin sunturin kai Zinariya Hindu wajen aikine ka gamu da wannan iftila'in ko? Dan nasan ta cika Zinariya sai anje an dakkota" Kuma wai har dariya take yi tana nufin bada faɗa take maganar ba tsokanace kawai. Ni dai abinci na sake saka mishi abakinshi sai da ya cinye kana yace. "Ko ɗaya ita ranar ma da motarta ta tafi aiki, na fito daga bankinmu ne zanje wani wajen abun ya faru" Da ƙyar yake magana a kuma mugun raunace. Sai kuma tayi dariya tana kallona, murmusawa nayi nima na nuna mata ai banma san nufinta ba. Yaya Saratu ce tayo ma su Inna Mairamu jagora su shida dukka matan yayye da ƙannen Baba Sojanmu kenan, duk gidanmu ɗaya dasu kuma ko wacce tana da kishiya. Sakamakon ba lokacin dubiya bane gaisheshi da jiki kawai suka yi suka ajjiye basket cike da abinci har biyu, ga leda biyu cike da lemo da ayaba. Miƙewa nayi nabi bayansu muka fito, suma su Inna Duduwa suka fito Yaya Jamila ce take wajenshi. Sannunku Inna mairamu nagode sosai jikin da sauƙi ma" Nan suka ɗan jima dai haka suka tafi, ban kai ga komawa ciki ba abokan aikina suma suka zo duba jikin nashi suma da kayansu na arziki harda kuɗi da aka haɗamun masu tsokar gaske, suna bani wannan kuɗin Yaya Jamila ta fito idanunta akan kuɗin ya sauke. "Hindu Mijinyawa na nemanki, ya daga rakiya baki dawo ba kin barshi sai faman nunfarfashi yake yi wannan wanne irin jinya kenan?" Gafa abokan aikina tana gani amman dake bagidajiyace saida ta tsinkani abunka da ƴar ƙauye. Baki ganni da baƙi bane, dubiya suka zo kinga ai bazan barsu a tsaye su kaɗai ba ko?. Kuma yanzu ba lokacin dubiya bane balle ince dasu mu shiga ciki ba? " Na mayar mata ina kallon cikin idanunta dan na tsani a tsinkani. Sai dai babu harigido ko nuna jin zafi sam a cikin muryata da kuma salon isar da saƙon. Tattaki nayi musu na rakasu duk dan in cunkusa musu haushi tunda su dangin miji ba'a iya musu da yawansu. Duk yadda zaka kai ga tautatawa ba lalle su gani ba sam. Aiko ina dawowa na tadda Yaya Jamila tana ta ruwan faɗa da zage_zage shigewata ciki dai nayi kanzil bance ba. A zaman jinyarnan na haɗiɗiyi baƙin cikin dangin Mijinyawa ƙari akan halin da nake ciki fa. Musamman Yaya Jamila da bata ƙaunar ta buɗe idanunta ta ganni tare da ɗan uwanta. Dangina wanda muke uba ɗaya, da yaran yayye da ƙannen Baba Sojanmu duk saida suka zo asibiti kuma duk wacce zata zo saita riƙo abinci ko kayan marmari ta tawo dashi, haka sukai ta nuna fariya da gasar kawo abinci kai harma da gasar kuloli dan kawai ace ai wance tana jin daɗi a gidan Aurenta. Wasu ma hannayen mazajensu suka riƙo suka tawo tare da rigi_rigin arziki. Kada kuce zaman lafiya ko zaman haɗin kai da zumunci fa akeyi ko wacce ta cikinta na cikinta da sannu zaren zai jamu har mu isa wajen. Maƙotanmu maza da mata suma haka sukaita sunturin zuwa. Sabida ina zaune da kowa lafiya, gashi suna mugun mutumtani gaya. A wannan zaman asibitin komai daya danganci kuɗi ni Hindu ake zuwa aima magana, ma'ana ni nake biyan kab kuɗin jinyar Mijinyawa ba tare da saka hannun danginshi ba sam. Su Yaya Jamila su kuma suka samu duniya wuni suke ciye_ciye a asibitinnan duk abinda aka kawo sai sunci, inma ban musu tayi ba sai ya zama rigima yadda kuka san gidan biki. Mijinyawa yana ji da ganin duk abinda yake wakana sai aka barshi da rarrashina da bani baki kamar yadda ya saba tun baya. Ni baisan ma a yanzu nafi ganin farinsu sama dashi ba, baisan dawar garin bane sabida ba ƙaramin dannewa nayi na ɓoye damuwata ba, dama ina da zurfin ciki kuma ni duk bala'i bana nuna na karaya, ba'a sanin logona kuma duk ƙwaƙwudubar mutum. Haka dai tafe_tafe har sati ya zagayo kuma jikin da kyau yana samun sauƙi. Sai Monday na koma bakin aikina na tawo na barshi dashi da danginshi da suke ganin sunfi kowa sonshi. Hankalina a zahiri a kwance babu wata damuwa mai yawa da zaka gane girman abinda ke zuchiyata, sai dai fa ina shiga office Luba tace mun. "Kin rame Hindu Duwaf duk jikin Mijinyawanne, naga idanunki sun farfaɗa." Murmushi nayi wanda ke kawar da tunanin wani abun a kaina. Zirga_zirgan asibiti ma kaɗai ya'isa yasa na rame, gashi warin asibiti yana sani tashin zuciya da ƙyar nake iya cin abinci ke kin sani. Ga miji babu lafiya Luba dole in rame" "Kuma hakane zaman jinya akwai wuya sauƙinta ma bake kike kwana ba. Wani ciwo da Sunusi yayi saida mukai wata huɗu a asibiti cur. Kinga yadda na fita hayyacina, gashi lokacin ba kuɗi bane damu nice nake ɗan aikin ma, wallahi bayan an sallamomu saida nayi jinyar jikina na zurga_zurgar da nayi ta yi ai lokacin ma kin zo gari kin same ni a wannan halin bazan mance ba" Sai muka ɗanyi shiru na fahimci tana cikin damuwa sosai gaskiya kuma ita macece mai son a tattauna, bata iya ɓoye damuwarta ta ko wacce fuska raguwar zuchiya gareta. Amman naga kamar a cikin damuwa kike, dan har a muryarki da kike karanto labarai babu irin wannan karsashin kinsan hakan koma nakasune ga aikinmu. Dole ka burne damuwarki a yayin da kake kan aikin ki musamman ku da ake jin muryoyinku" Sai kawai naga tana sharɓe hawaye wanda yazo mata babu shiri. To nasan bazai wuce Sunusi bane ya guma mata ba. Mata basu da aiki sai kuka akan maza hmm wannan fa ragon salone sosai wallahi mata. Ba Ko yaushe kuka ke zama mafita ba, ba kuma dole sai kinyi kuka kike nuna kin raunata ba, kuma ba dole sai kinyi kuka za'a tausaya miki ba. Amman naji ana cewa mace da rauni aka santa harma ana cewa wai kukan mace na karya alkadarin maza. Amman bana jin alkadarin mazan irin wannan zamanin ake nufi mazajen da da yawa yawansu basu san ma darajar matan ba balle har su tausayama zubar hawayensu ba. Ai da kukan suke cuta mana da wannan kukan suke kaimu ƙasa warwas. "Hindu kinsan ashe Sunusi aure yake nema? " Ni kaina saida na nuna mamaki. Amman wallahi kaɗan daga aikin maza. Ba gara Aure ba da abinda na kama Mijinyawa nayi ba? Na faɗa a zuchiyata a fili kuma nace. Aure Luba shine kike kuka a kanki zata zauna ne, ke da kike aikinki me zai dameki ne? " "Ba auren bane yasa ni kuka ba. Karfa ki mance gidan da muke ginawa tare dani dashi muke ginawa, wannan watan in ya saka kuɗi a ginin, wata na gaba ni zan saka. Muka koma rayuwar turawa hamsin_hamsin (50_50) haka muke rayuwarmu duk dan mu tsira da mutuncin kanmu mu tashi a gidan gandu mu huta da gori da tsangwama. Sai kawai ace yanzu tare da wata ƴar iska zan tare a gidanmu da muka gina? Shin da kaina na gina da yanzu banfi haka ba, da yanzu ban mallaki gidan nawa na kaina ba? Hindu sau nawa Zarah abokiyar aikinmu zata kawo suturu aita ɗauka da takalma ni bana ɗauka sabida adashe _adashe da nake yi sunfi uku, saida muka gama tabka gida ana shirin tarewa zai zo mun da batun aure, ko kuma ince danginshi zasu dinga yar mun da magana a tsakar gida" Haƙiƙa Sunusi yayi mata zalunci mai girman gaske. Mace ta gama bautama miji amman inya tashi ɗiban albarka a kanta yake nuna ƙarewa. Ni ɗin meye banayi a gidana, meye banyi ma Mijinyawa ba, wacce iriyar sadaukarwace banyi mishi bane a rayuwarmu da zai sakamun da raba tsaraicinshi harda mugayen maganganu masu ciwo a kaina. Ajjiyar zuchiya na sauke kana nayi murmushi nace. A bakin facaloli kika ji labarin kenan bai faɗa miki komai ba ke? " "To na isane ya faɗamun Hindu? A bakin fanfo naji suna faɗan irin lefen da yayi ma matar, da ƙyar na kawo kaina wajen aiki. Hindu jiya_jiya na biya kuɗin makarantar yaranmu uku dubu ɗari da hamsin fa hmmm" Wasu sababbin hawaye suka sake zubo mata. Shiru muka yi kowanne cikinmu na ƙunshe da baƙin ciki da takaicin ɗa namiji ɗa namijinma wanda ka sadaukar da komanka domin shi yayi rayuwa mai kyau. Girgiza kai nayi nace. In nice ke idanu zan ɗauka in zuba ma Sunusi kana duk wani tallafi in janyeshi sai wanda nasan zai iya cutar mun da yara, domin bazan ɗaura yarana a kan dogon laifin mahaifinsu in wofantar da lamarinsu ba, sabida akaina ma akwai hakkinsu. Kinga idanu? Basa ci basa sha amman mashine. Saifa kin dena wannan banzan kukan ke da kanki zaki samama kanki ƴanci wallahi bani zanje in miki faɗa a gidanki kamar yadda na saba tare miki faɗa a makaranta ba. Aure kuma yaje yayi kowa da halinta zata zauna in kika janye tallafi ita kanta amarya saita ɗanɗano kuɗarta kisa farin cikin ki dana yaranki saman nashi, ki ba banza ajiyarshi. Kada ki sake kuka har facaloli su gane rauninki kada kiba maƙiya ƙofar da zasu ga wallenki. Ke da kanki zaki yi yaƙi ki kwaci kanki Luba. Kina aikin ki daidai gwargwado kina samun albashinki kada ki bari ciwo ya kamaki kima ɗiyayonki asarar lafiyarki wannan shine. Ki ɗauki ido ki zuba zaki ga ƙwal uwar dakane." "Nifa da cewa nayi zanje in faɗama uwarshi abinda ake ciki" Baki na buɗe nace. Laa ashe baki san bayan ɗanta zata bi ba? Wallahi da kinje saita faɗa miki cutar da sai tayi ajalinki ko tai miki sanadin ciwo. Dashi da dangin nashi watsasu a kwandon shara. Nifa in kamun saina yi maka ko da daga baya zamu sasanta sai dai mu tashi da ɗaya da ɗaya (1_1) Matar Aure ba fa baiwa bace Aure bafa Bauta bane sunnahce ta ma'aiki Arrasul S.A.W, inda zasu yi koyi da shugaban soyayya na duk duniya Arrasul s.a.w da duniya ta zauna lafiya." Na daɗe ina tausar zuchiyarta duk da nima tawa zuchiyar cikin miki take ɗanye. Lokacin barina aiki nayi na ɗauki haramar fita. Ogane ya kirani na shiga ofishinshi na sameshi. "Hindu sannu da ƙoƙari fa a gaskiya muna jin daɗin aiki dake kina da jajircewa da gogewar aiki sosai. Kuma ina bibiyar aikin ki musamman a shafinki na Facebook duk da naji yawancin kwament ɗin maza zagine da albatawa tunda a tunaninsu yaƙi kike yi dasu. " Dariya kawai nayi bance komai ba. "Amm akwai semina da za'a gabatar a Abuja Bbc ce ta haɗa seminar, ke da Ibrahim ne zaku wakilcemu ko kuma ke kaɗai ma to sai ki zauna da shirinki in sha Allah." Wani daɗine ya lulluɓeni sosai har fara'ar gaske ta wanzu a fuskata. Nagode sosai oga Ubangiji Allah ya nuna mana babu matsala a shirye nake lokacin kawai zamu jira" Da haka nayi mishi sallama na nufi asibiti. Harna isa ina cike da fara'a da jin daɗi inason halartar irin tarukan ƙarama juna sani sosai sabida yana sake wanke mun kaina tas.kuma inason in ganni ina cuɗanya a cikin manyan mata. Musamman Bbc ai burin duk wata ma'aikaciyar rediyo baya wuce son tayi aiki da Bbc ko DW waɗannan manyan gidajen rediyo suna da girman daraja, ni dai burina in kasance ma'aikaciyar Bbc sashen hausa, ban cire raina ba har yanxu in da rai to da rabo. Kamar kullum Yaya jamila ana zaune anata ciye_ciye. Kullum daga gidanmu ana kawo abinci rana dare, abincin safe kawai nake yi musu in kawo musu kafin in wuce wajen aiki. Mijinyawa yana zaune suna hira da abokinshi Nura na shigo. "Madam kin taso kenan yanzu muke maganarki yana yabawa da ƙoƙarinki sosai." Murmushi nayi tare da cewa. To in banyi mishi ba wazai yi mishi Nura, ai mijinyawa yafi haka a wajena guda ne shi har da rabin mutum. Ranka shi daɗe ya jikin naka, duk da naga jiki da kyau ciwon nata kamewa" Idanu ya lumshe tare da mun murmushin da ada in yamun sai inga kamar nafi uban kowa dace a duniya. A yanzu in yayi mun sai inga kamar ma kuka yake yi tsabar baƙin cikinshi. "Da sauƙi sai cinyarne ya rage kawai har yanzu bana iya takawa, kuma likita yace saina taka sun tabbatar babu wata matsala kafin ya sallamemu, gashi duk na gaji da zaman asibitin. Wayar tawa kin tawo mun da'ita kuwa?" Na tawo da'ita da safe ma mancewa nayi ne shi yasa" Jakata na zuge na bashi wayarshi ya kunna. Sallama Nura yayi mana ya tafi. Yaya Jamila tana ganin fitar Nura ta shigo ta zauna ta shiga janshi da hira. Sabida ita bata so yayi hira ne dani, shi kuma idonshi akan wayarshi har murmushi naga yanayi idanuna ƙur a kanshi ita kuma Yaya Jamila sai zuba take yi, jifa_ jifa yake amsata, yama mance da wata banza a zaune a gabanshi, ni kuma inata nazartarshi. Take na sake shaƙa sai ɗan girgiza ƙafa kawai nake yi amman fa a fuska ba'a gane asalin halin da nake ciki. Zuwa kamar bayan la'asar ina yin sallah nace. Zan wuce ni Allah ya ƙara sauƙi sai kuma gobe" Idanshi na kan waya ya ɗago yace. "To shikenan Tutar so nagode da ɗawainiya ki gaishe da yaran" Sallama nayi ma Yaya Jamila na fita. Ina tuƙi ina mamakin Mijunyawa sai dai inyi murmushi kawai abun ma ya dena bani mamaki. Gaga_gaga har tafiyarmu zuwa semina ta matso gobe ne tafiyar, nazo asibiti bayan na taso aiki sai lokacin a gaban Yaya Jamila da bata iya bamu waje ba nace. Gobe zani Abuja akwai semina da zan halarta wanda Bbc ta haɗa, kuma an zaɓeni a matsayin wacce zata wakilci gidan rediyonmu. To gobe da sassafe zamu kama hanya" "Ba shakka, sabida rashin imani mijinki na kwance baida lafiya amman aikin ki ne a gabanki har tafiya ma zaki yi. Kinfi sha'awar ki dinga ganin kanki a cikin maza kuna cuɗanya" Mijinyawa Babba ne yace. "Yaya jamila Hindu tana ƙoƙari duk ɗawainiyar asibitinnan ita ke yi da ajjihunta. Kuma aikinta yana da mahimmanci, Mijinyawa ƙarami jiki da sauƙi ƙafarma ɗazu ya takata." Harararshi tayi, ni dai abinda mijinyawa zaice nake jira. "Babu damuwa Yaya Jamila taje na yarje mata" "Kai dai shanyayyene. Ya zaka bar mace ta dinga takaka yadda taso, kana kwance a gadon asibiti tana zuwa aiki bai isheta ba har sai ta tafi semina ke Hindu zuwa Seminar to dole ne. Wai me yasa ƴan boko basu fiye girmama aure bane su, ko dan kinga an barki a gidan ke kaɗai shi yasa kike yadda kike so ko?" Allah ya huci zuchiyarki Yaya jamila. Ni kam saida safenku." Na miƙe nayi juyawata ina jinjina lamarin ƙiyayyar wannan mata a gareni, ko uwa na kashe mata sai haka. Ina zuwa gida na zube a falo Sabira ce kaɗai a gidan tana zaune tana karatunta. "Ammi yau kin dawo da wuri ya jikin Abba? " Jiki da sauƙi. E nadawo sabida gobe zanje Abuja sassafe, ku kuma zaku je gidan Baba Sojanmu ku zauna kwana biyu kacal zanyi." Shigowar su Azgar yayi daidai da shigowar kiran Baba Sojanmu cikin wayata. "Hinduwa Duwaf nima in ɗana to yaya jikin shi mijnyawan yana dai samun sauƙi ko? " Da sauƙi sosai yauma ya taka ƙafar tashi. Ni gobe ma zanje Semina ne Abuja Na Bbc hausa" "To allah ya taimaka haka nake so ku zama jajirtattu kuma ku riƙe aikinku kada ku zamema mazajenku da yaranku nauyi. Kunga mahaifiyarku dai malamar boko ce har matakin princifal ga kasuwanci da take yi, kafin ta tambayeni kuɗi sau ɗaya tayi da kanta sau goma. Kuma kunga bambancinta da ragowar abokan zamanta. Ya maganar mastas ɗinki ai ya kamata kiyi Hinduwa ko? Kada kisa ƙyuya ke ba yaran goye ba. Saratu da goyon ɗiyarta ta soma mastar ba gashi ta gama ba, ki dai yi tunani mijinki dai ba hanaki zaiyi ba" To shikenan Baba Sojanmu in sha Allah shekara mai zuwa dani za'a soma nima abun yana raina kuma inaso shi dai Mijinyawa bashi da matsala da hakan. Baba sojanmu gobe su Azgar zasu tawo gida saina dawo sa dawo" "To ai babu komai su zo irinsu sunfi ashirin a gidan ai. Allah ya kaimu goben Allah ya tsare miki hanya, amman ki dawo da tunaninki lallai kan mastas ɗinki Hinduwa" Na amsa mishi da amin tare da yi mishi godiya. "Ammi kin dawo, naji kina zaki yi tafiya? " E Azgar tafiyace ta taso mun daga ofishinmu kuma ni aka zaɓa amman kwana biyu zanyi in dawo. Zaku je can ku zauna Na'ibawa bazan barku a gida ɗakina a buɗe ba Yaya jamila nanan" Asama'u tace. "Ko yau Ammi saida tai ta zagin Azgar wallahi kuma bai mata komai ba" Hmm to dama me zaiyi mata shi da uwashi, kuyi ta haƙuri watarana ma ba zasu ganku ba. Kuma kuci gaba da basu girmansu sabida duk tsiya sune bangonku. Bari in shiga ciki in watsa ruwa in fito in mana girki yau taliyar hausa nake son ci ta manja mai kifi" Nan na tafi na barsu sunata cece kucensu nayo wanka na zauna a gaban mudubi ina shafe jikina da kulaccham. Saina tsinci kaina da miƙewa tsaye tare da cire tawul ɗin jikina na ƙurama zatina idanu ina so inga inda nake da wata tawayar da har Mijinyawa zai kirani da tsohuwa, karuwarshi kuma tace dani bagidajiya, banyi tunanin akwai abinda budurwa zata nuna mun ba daya wuce sabon budurci ba. Ƙoƙarin gyaran jikina da nake yi ba duk kai ba a yaran matan ma. Sabida gyaran da nake yi ya ɓoye haƙiƙanin shekaruna. Fuskata na kalla ba'a taɓa cewa ni mummuna bace in ba'a kirani kyakkyawa ba to za'a kirani tsaka tsaki. Rama nagani sosai a fuskata wuyana harya fitar da ɗan ƙashi a cikin kwanakin da basu wuce kwana ashirin da wani abu ba. Namiji kamar bom yake wajen iya tarwatsa rayuwar mace yayi mata dameji. Shafe jikina nayi da mai na bi da humra. Doguwar rigar yadi na saka na shafe kaina da man chebe. Kiran Innarmu nayi na sanar mata zanje Abuja gobe kuma inna dawo gidan zan nufo kai tsaye in ɗakko yara. Saida na gama wayata da'ita na fito na shiga Kitchen duk yaran suna Kitchen ɗin sunata hira suna dariya. Tare muka yi girkin a tukunyar yau muka ci abincin a cikin Kitchen ɗin muka zauna Asama'u ta shinfiɗa mana ƙatuwar tabarma. Kitchen ɗin yana da girma dan yayi falona girma inajin daɗin aiki a ciki sosai, kuma ana sha'awar Kitchen ɗin sosai. Gaga_gaga washegari sassafe muka fito na garƙame ɓarayina, har ƴar ƙofar dake sada mutum da ɓarayin nawa saida na kulle. Dake sassafene ban bi takan matan gidan ba Azgar ya tuƙani zuwa gidan rediyonmu su kuma suka wuce da motar gidanmu. Mota aka bamu da direba ni da Ibrahim yana gaba ni ina baya ni kaɗai muka shiga Abuja wajajen biyun rana. Kai tsaye hotel muka nufa kowa ya shiga ɗakinshi, washegari muka halarci Samenar data kawomu. Naji daɗin ganin Badariyya Tijjani Ƙalarawi mutumiyar kirki ga fara'a gata da kirki, ƴar gaye iya gaye. Dariya da aji ya ƙare a wajen Madina Ɗahiru mai shanu gwanar iya sarrafa harshe gwanata. Mun ƙaru da abubuwa da yawa wanda zai taimaka mana ta fannin aikinmu, munyi hotuna munci mun sha kafin taro ya watse, muka koma Hotel washegari sassafe muka nufo Kano ɗaya da rabi a Kano tayi mana kai tsaye na wuce Na'ibawa. Duk fa wannan bidirin da akeyi ban ɗaga waya na kira mijinyawa ba. Ya dai kirani a ranar da muka tawo yaji ko na isa lafiya. Shigewata nayi cikin gidanmu. GIDAN NAGOƊI SHINE INKIYAR GIDANMU KUMA SHINE INKIYAR FAMILINMU. MRS BUKHARI 📚 SPEAK ENGLISH WITH MRS JAY Assalamu Alaikum. An buɗe rajistar shiga Online English Class. 💵 Kudin shiga: ₦2,000 early bird Normal price ₦3,000 📱 Za a gudanar da karatun a WhatsApp Group. Za ku koyi: ✅ Grammar ✅ Vocabulary ✅ Sentence Construction ✅ Daily Conversations ✅ Reading & Writing ✅ Pronunciation Domin yin rajista: 📞 08136013866 Limited slot ✨ hurry and grab your sit 🪑 https://chat.whatsapp.com/G6bk3L1w6NQGHsERPqG0PbTSURON TSIRIN.. TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA HUƊU *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. GIDAN NAGOƊI Gidane gidan Gandu mai matuƙar girma da yawan taron yara. Gidan rikici da munafurci, gidan rarrabewar kai da son ganin kaine a sama. Gidan da kusan ƴan wannan ɗakin na son ganin beken ƴan wannan ɗakin. Kai gidan yawa gidan masifa, gidan yawa gidan munafurci da girmama ƙaramar magana izuwa babban al'amari kuma mara gogewa duk tsawon zamani. Wannan dalilin yasa ko wanne ɗaki suna tattalin maganar da zata fita, abun arziki kaɗai ake shela na tsiya kuwa sai dai ya fito da ƙarfin gaske. Baba Nagoɗi shine babban wansu Baba Sojanmu, amman asalin sunan Nagoɗi sunan mahaifinsu Baba Sojanmu ne, bayan ya haifi yaronshi na fari sai ya saka mishi sunanshi suna ya bishi Nagoɗi. Shine ya soma fitowa cirani zuwa Kano asalin mahaifarsu kwantagorane dake jihar Naija su ƴan asalin canne. Lungun Baba Nagoɗi shine a farkon gidanmu. Yana da mata huɗu da yara ashirin da shidda. Sana'arshi itace saida kayan kwalliyar dawakai, da alkyabba, da takalma, da mafici da duk abinda ya danganci kwalliyar dawakai da sarakuna. Shaguna biyu gareshi a jere da juna shi yana cikin ɗaya yaranshi maza na cikin ɗaya waɗanda basa aikin kaki, ko aikin gwamnati kenan. Sai Lungun Baba Kumainu dake da matan aure uku yara goma sha shidda. Sana'arshi itace saida su kibiya da manda, da mangul a nan kasuwar kurmi shima. Sai Lungun Baba Sogiji mai mata uku shima da yara ashirin cib. Shi kuma shagon niƙan garine dashi a cikin kasuwar Ƴan lemo nan Na'ibawa. Sai lungun Baba Sojanmu. Shi kuma ritayat sojane har ya kai genaral kafin yayi ritaya. Yana da mata uku da yara talatin maza huɗu daga ɗakinmu duk sojojine su. Sai lungun Baba Alƙali Shi kuma macen Aurenshi ɗaya ce tilo da yaranshi shida kasancewar ɗan bokone sosai alƙaline a kotu. Shi da Baba Sojanmu ne kaɗai sukai karatun boko kuma suka ɗauki boko da mahimmanci musamman dai Baba Sojanmu da bashi da aiki sai son yaga ana ƙaro ilimi. Baba Alƙali yana da zurfin ilimi sosai. Sai lungun Baba Dogara. Lungun masifa da bala'i kenan shi dai matanshi huɗu amman ko yanzu yaga wata zai dawo ya saki wata ya kawo wata. Yaranshi shima zasu yi talatin harda waɗanda iyayensu basa gidan. Yana siyar da kayan marmari Anan ƴan lemo dangin su kankana, mangoro da dai sauransu. Kunji yadda tsarin gidanmu yake. Ko wanne lungu abincinsu sukeyi ba wai ƙatuwar tukunya ake ɗaurawa guda ɗaya ba. Gidanmu yana da girma sosai ga filin tsakar gida fetal. Da Inna Meramu na soma cin karo tana zaune a ƙofar babban falon da shi ya haɗe kan ɗakunan iyalan gidanta tunda duk lungunan irin gini ɗayane sak. Wanki take yi, Inna Baballiya Kishiyarta kuma tana daga cikin madafi. "A_a Duwaf kin dawo daga Abujanne. Akace mana kinje wani taro da Bbc ta gayyaceki, ince Bbc zaki koma da aikine?" Cewar Inna Mairamu, ai kuwa Inna Baballiya na jin haka tace. "Ai ina Bbc ta manyan kaice fa Yaya Mairamu ai sai dai taje taron kawai. Duwaf ya jikin mijin naki?" Murmushin mamaki nayi tare da cewa. Jikinshi da sauƙi ina wuninku? " Nan aka gaggaisa ragowar abokan zaman nasu ma saida na bisu har ɗaki na gaishesu. Duk lungun daka shiga sai kabisu ɗaya bayan ɗaya ka gaishesu da waɗanda suke yinka da waɗanda bama yin naka suke ba basu ƙi su ganka a ƙasa ba. Ga shegen kallon ƙasan zani, da takalmin daka sako, da mayafinka. Allah cikin ikonshi ni da yarana dai kullum cikin sutura muke dan bana wasa da siya mana sutura sabida gidanmu ana yawan yin sha'ani ni kuma akan in fita kunyar ƴan gidanmu na gwammaci inci bashi kuɗi ya hau kaina a ganni dai fes. Ƴan ɗakinmu gaskiya ko wacce a cikin rufin asirinta take tunda gaskiya muna karatu sosai ko wacce tana da aikinta harma da kasuwanci. wata iriyar rayuwar gasa da son kowa ya nuna shi shine haka muke yi daga kan iyayen namu mata, har zuwa kanmu. Muma a hakan muka tsinci iyayenmu akai su kuma iyaye madubaine ga ƴaƴansu. Wata rayuwar ƙaddara ke zaɓama tasowa kake yi ka ganka ciki. Sai wanda Allah yaso shine sai ya kasance shi na dabanne. Yaran lungun Baba Dogarane kaɗai basu yi karatu mai yawa ba iyakarsu Sakandare kawai sai Kakale data ƙuƙuta a gidan mijinta tayi NCE shine ma ta samu aikin koyarwa a wata firamare ta cikin unguwar da take aure. Baya ga ƴan lungunsu gaskiya kowa yayi karatu daga masu digiri sai masu mastas a maza kuwa harda masu PHD amman babu a mata sai ni da nake tunanin in sha Allah da ikon da Allah yaima Annabinmu Arrasul sallalahu alaihi wasallam saina yi PHD bazan sake zaman bautama miji da son ganin na burgeshi ba. A waɗannan lungunan akwai soja wasu ba ɗaya ba, ba biyu ba. Saida na gama zagayena na dawo Lungunmu. Da ɗakin Inna Abida na soma itace a farko. Babban falone sosai mai ɗauke da ɗakuna falle_ falle guda biyar. Kowacce ta ɗauki ɗaya Baba Sojanmu ma ya ɗauki ɗaya ɗayan daya rage kuma ake ajjiye shirgi da kayan abinci dai haka. Falon kujerace doguwa guda ɗaya sai kafet malale a falon, sai tv da wata kwaba mai cike da littatafanmu da jaridun Baba Sojanmu. Da sallama na ɗaga labulen ɗakin Inna Abida da Iyami muka haɗa idanu tana tsakiyar gado tana ba jaririyarta nono, Inna Abida kuma tana zaune tana ƙulla sikari abinda take saidawa kenan. "Duwaf kin dawo daga taron Bbc ɗinne? " Nadawo Inna Abida, na sameku lafiya? " "Ah lafiya lau ya Mijinyawa da jikin? " Jikinshi da sauƙi Iyami wankan gida tazo yine? " "E wallahi Duwaf wanka nazo yi nima inji abinda ake ji" Murmushi nayi nace. To in banda abinki ai wankan gida yanzu ƙauyancine yaushe zaka baro ɗakinka ka dawo gidanku kusan wata biyu" Na ƙarashe ina taɓe bakina. Inna Abida tana dariya tace. "Ato faɗa mata dai. Gata ga gidan taci uwar da akeci faɗan Baba Sojanku ma ya isheta" Da haka na leƙa ɗakin Inna Turai muka gaisa kafin na shiga ɗakinmu. Kasancewar ɗakunan suna da girma yawanci duk sun rarraba da kwali, wasu da gini kamar na ɗakinmu an cirema Innarmu falo ƙarami kujera doguwace kaɗai a falon sai kayan kallo, uwarɗakin kuma da girma. Tana zaune tana shan shayi ga turaren wuta a gabanta a kasko yana tashi, ƙafarnan sai sheƙin mai take yi ga lallenta shar. Yaya Saratu da Yaya Zubaida suna kan gado sunyi ɗaiɗaya da atampopi da lesuka sunata surutai. "Hindu kina tafe ashe har kun dawo daga Abujan? " Zama nayi a gaban innarmu nace. Innarmu kinsan me Inna Baballiya take cewa a gabana kuwa? " Nan na labarta musu abinda tace. Yaya Saratu tace. "Gidannan ba zasu taɓa dena hassada da baƙin hali ba. Kuma in da rai da rabo sai kiga kin zama ɗaya daga cikin ma'aikatan Bbc ɗin badai aikin da kike yi suma suke yi ba? Kinsan ai mijin Kandenta ma'aikacin Bbc ne shi yasa take ganin Bbc tafi ƙarfinki. Hindu kin haɗu dasu Badariyya tijjani ƙalarawi kuwa? Baiwar Allahnnan tana burgeni gaya wankanta yana fita" Ai kuwa mun haɗu har ma da hotuna da bidiyos gajeru da muka yi." Wayar na miƙa musu ni kuma na shiga shan shayi muna hira da Innarmu. "Batun mastas ɗinki kiyi ƙoƙari shekara mai zuwa ku soma ke da ƴar uwarki Baba Sojanku ya matsa jiya inaji yana ma ƴar uwarki tsiya akan karatun itama to ita tace mijinta yaƙi yadda amman yace zaije ya sameshi su tattauna dole ya barta ta ƙara karatu tunda ya iya barinta tana aiki me yasa ba zai barta tayi karatu ba" Gaskiya kam zan jona in sha Allah ni so nake ma inna soma inyi har Phd kawai in wuce wajen Innarmu nasan Baba Sojanmu zaiyi murna sosai. Nan mukaita tattaunawa daga baya su Fhatsima suka shigo. Ba ni na bar gidan ba sai bayan isha tunda munyi waya da Azgar yace an sallami Mijinyawa suna gida hakanne ma yasa na miƙe ƙafata a cikin ƴan uwana naita hira ina jin sauƙin abinda ke cin ƙasan zuchiyata. Da muka tashi gidan muka nufa kai tsaye. Ai kuwa falona a cike da su Yaya Jamila dake yana da ɗan mabuɗi a wajenshi, hamshaƙin yana kwance a kan goduwar kujera muka shigo. Da ƙyar suka amsa sallamata harda Uwatale yau itace a zaune a falona anata hira hiye, sabida sunga bananan. Fuskata kadaran kadahan na nemi waje na zauna. Ina wuninku" Na faɗa babu yabo babu fallasa. "Kin dawo Tutar so? Ai ni da naga tara saura banyi ma tunanin kun dawo ba, na kikkira wayarki baki ɗaga ba." Wayar tana cikin jaka banma gani ba. Mun dawo tun yamma yara naje ɗakkowa acan gida, kuma motatama tana gidan" Buɗar bakin Yaya Jamila sai cewa tayi. "Sabida son yara shine har sai kinje kin ɗakkosu ma su ba zasu tawo da kansu ba? Batun mota kuma ai ta fita daga sahun taki dole ki bama mai mota motarshi tunda dai yanzu bashi da mota tashin tayi rugu _rugu sai dai a yayyankata." Miƙewa nayi saɓe da jakata nace. Son yara ai Yaya Jamila ban kaiku ba" Ina dariya na mayar mata da martani" "Muna son yaran zamu bar Mijinyawa da matar da ita ba juya ba ita ba mai haihuwar ba, wannan tsirarin yaran har yarane gasu Uwatale da akayi bikinku tare sabida jarumtarta har gwarne ta dinga yi" Wato wannan kalmar ta dokeni sosai amman bance mata komai ba taci bashi dan wallahi saina mayar mata da martani. Ɗakina na shige na watsa ruwa na sallaci isha na saka kayan bacci nayi kwanciyata ina jiyo muryoyinsu ko tare dashi zasu kwana ohon musu dan bai dameni ba sam. Sai can wajajen sha ɗayan dare naji fitarsu shiru mijinyawa zai leƙone naji shiru har sha biyu. Miƙewa nayi na leƙa ta gefen ƙofata da ban rufeta kirib ba. Na hangoshi yana ta danna wayarshi yana murmushi. Nima murmushin nayi kawai na saki labulen nayi kwanciyata ƙirjina na soya mun Duniya in akace akwai ranar da mijinyawa zai iya rikiɗewa ya koma haka wallahi bazan amince ba. Irin son da nake yi mishi fa bana wasa bane da kanshi yasan son da nake yi mishi baya mun irin wannan son yana dai yin irin nashi, amman nasan shima yana matuƙar sona sosai kuma yana tsaya mun a ko wanne hali. Leƙawar da zan kuma yi naga Mijinyawa baya falon ya shiga ɗaki. Hmm sai ga Asama'u saɗab_saɗab ta fito daga ɗakinsu ta nufi turakar mijinyawa har tana sake waigowa ta tabbatar babu wanda ya ganta. Kaina sai naji yana juya mini ohh dama tana kai mishi ziyarane ɗakinshi ban sani ba, aina zaci a waya kawai suke iya neman junansu, sai kuma inda suka san suna haɗuwa. To amman ni ai ko da yaushe ina ɗakin mijinyawa, sai dai shi nakan farka inga baya kusa dani kuma baya banɗaki, cikin hukuncin Ubangiji ban taɓa fitowa nemanshi ba, kafin ya shigo sabida gajiya ma tuni na koma baccina, kuma bana zargin komai a cikin kaina. Zuchiyata dake dokawa da ƙarfi inaji numfashina yana karkatsewa kamar mai asma. Sai take nabi umarnin zuchiyata na fito nima saɗab _saɗab naje daidai bakin tagar turakar na tsaya. Ba ganinsu nake yi ba jinsu nake yi. Wani irin yanayi Asama'u take ciki sosai duk ta fita hayyacinta, sau biyu a kunnena naji mijinyawa yayi wani numfashi daya saba yi in muna tare cikin aminci da ni'imar dake cikin Aure. "Bani insha ƴan biyuna nafi kewarsu sosai, kinsan na Hindu a zube suke kuma babu tsoka haka irin wannan, ni kuma Allah ya jarabceni da son ƴan biyu" Ya faɗa da wata iriyar murya mai cike da shauƙi. "Wai daka tursasani nazo in ta zo ni ya zaka yi dani Sikari?" "Yanzu zan sallameki inje wajenta kewarki ce ta isheni kema ai naga yadda kika yi kewata." Ina jiyo yanda yake ma jikinta sai sambatu yake yi ita kuma tana wani irin sauti. "Da ace duk mata haka suke kamarki da maza sun more Sweet L komai naki mai kyau da kwalitine, mata sunansu ne kaɗai iri ɗaya." Sai naji shiru suna musayar sumba. Ji nayi sun yi shiru sai wani abu da nake jiyowa. Barin wajen zuwa ɗakina nayi ruf da ciki tare da yin shiru ina sauraren zuchiyata dake dokawa da dukkan rassan jikina dake wani irin ɓari. Yarinyar da Mijinyawa shi ya sai ragon sunanta shi ya raɗa mata suna. Tun tana ƴar shekara biyu take bacci akan faffaɗan ƙirjinshi, tayi kuka ya rarrasheta, wai yau da ita suke wannan abun har yake cewa ta bashi.. ya sha nawa a zube suke. Lallai maza da yawa babu ɗigon kunya da halacci da amana a tattare dasu. Babban abinda yake baƙanta mun raina shine ace wai yarinyar dana riƙeta na raineta tun tana shekara biyu ace itace take aibata halittar jikina. Shi kuma mijinyawa mutumin banza babu kunya babu tsoron Allah tattare dashi subhanallahi. Ina jin tsananin zafin mijinyawa da azabar ƙyamarshi mai cakuɗe da mikin tsanarshi a zuchiyata. Idanuna na ɗaga sama nace. Allah ga kayanka nan kai kasan yadda zaka yi dashi Allah ka ɗauke mun son Mijinyawa cak a rayuwata ya Allah ka kawo mun ɗauki" Turo ƙofa yayi ya shigo da sanda yake dogarowa har zuwa bakin gadona ya zauna har yana wash sabida ciwon dake cinyarshi tafiyarma da ƙyar yake yi fa. Hannunshi ya ɗaura a mazaunaina da suke tafiya da nutsuwarshi amman fa ada kenan, banda yanzu da yake matsa na ɗanyen jini. Hannunshi sai naji kamar garwashin wuta wallahi, ko wata narkakkiyar dalma. "Tutar so ta Mijinyawa baccinki ma kika yi kika barni ni kaɗai inata jiranki?" Idanuna na buɗe tare da juyowa muka fuskanci juna idanuna ina jinsu suna mun mugun yaji babu ko ɗigon ruwa a cikinsu. Kallon mamaki nake yi mishi mai ɗauke da faɗuwarshi ƙasa warwas. Shi kuma kallon yaudara yake yi mun wanda ada yake sawa inji kamar nafi duk matan duniya dace. "Menene ya ɓata miki ranki Yaya jamila da maganganunta ne ni na sani. Kiyi haƙuri tun farko na faɗa musu mota da kuɗinki kika siya yarda ne basu yi ba. Amman zan sake ma Nanno bayani. Naga tunda kika shiga ciki baki fito ba. Hankalina yana kanki amman Yaya Jamila ta hanani tasowa sai hira suke yi mun" Ajjiyar zuchiya na sauke wani ɗaci na tasomun. Babu damuwa yaya jikin naka to?" "Jikin da sauƙi ƙafar dai ko da sandar gaskiya tana mun tsananin ciwo amman Alhamdullahi. Ya semina ta kasance? " Wayancewa nayi da zubo hamma. Bacci nake ji sosai Mijinyawa duk jikina ciwo kawai yake yi mini" "To taso muje ɗakina inji ɗuminki da nake ta kewa anya zan jure jinki a jikina ba tare da munje gona ba kuwa? " Murmushi nayi a zahiri a baɗini kuma nace. Ni da kai zuwa gona har gaba da abada ai ba'a garin gaɓa_gaɓa muke ba. Kai dai ka warke tsab tukunna. Miƙewa nayi tsaye na nufi sib dan ɗakko hijabina, a hankali ya samu ya tashi tsaye muka fito tare. Daga Kitchen Asama'u ta fito. "Ammi sannu da fitowa Abba sannu da jikin" Hmmm kallon Mijinyawa nayi naga wani irin kallon kar ta san kar da sukaima junansu wayyo suna mun kallon biri ina musu kallon ayaba. Yauwa Asama'u me kike yi da har yanzu baki yi bacci ba? " "Farkawa nayi inajin ƙishi shine na fito nasha ruwa" Kai kawai na gyaɗa mata muka wuce muka barta makirar yarinyarnan tana tsaye bata wuce ba. Nina soma shigewata ciki dan in bashi dama ya kalleta ta sanyaya mishi ruhinshi. Ilai kuwa ina shigewa na juyo shi kuma ya juya harda ɗaga mata hannu. Juyawa nayi na haye gadon ina jin zafi da ƙyamar ɗakin ma baki ɗaya. Harna kwanta sai naji ƙamshi turarenta da halamun yadda ya tumurmusheta da gudu na duro ina ambaton Allah tare da runtse idandunana. Riƙeni yayi da kyau. "Lafiya menene a gadon Tutar so? " Da ƙyar nunfashina ya dawo daidai saida na saisaita kaina. Ɗakina zan koma mijinyawa in zaka biyo ni muje, in ba zaka biyoni ba ni kam saida safe" Ina gama faɗin haka na fito sai naga kamar gilmawar mutum da sauri bazai wuce Asama'u ba. Bata da laifi ga gona_gonan mai laifi mijinyawa yaci amanar yarinya yaci amanar abokantaka yau da Abdulƙadiri mahaifin Asama'u da ranshi yaya zaiji ace Mijinyawa da kanshi ya lalata mishi ɗiya wanda ya dace ace sai inda ƙarfinshi ya ƙare akan ganin tarbiyyar yarannan ta ginu. Ina shiga ɗaki ya biyoni yana ta tambayata a mugun tsarge yake hakan yasa na aro nitsuwa na yafa. A kusa dani yazo ya kwanta da dabara muna fuskantar juna. "Nace wani abunne a kan gadon Tutar so ko mutanen naki ne suka dawo miki ne? Kinsan makarai ba'a alƙawari dasu" To babu mamaki su ɗinne dan ji nayi kamar na hau ƙaya" Da haka na manna mishi hauka shine harda kunna karatun Qur'ani a ɗakin, ya dinga mun tofe_tofe daga ƙarshe ma idanduna na rufe da nake jinsu tsabaragen bushewa kamar zasu tsattsage wallahi. Ya jima yana mun tofi kafin daga bisani ya kwanta. Sai can da dare ya shura na buɗe idandunana na sauke su akan murɗaɗɗen faffaɗan ƙirjinshi wanda yana daga cikin abinda ke fusgata a jikinshi. Kafin muyi Aure ƙirjin nashi bai kai haka buɗewa ba sanin inasone yasa ya dage ya ƙaramun faɗinshi, ko kallo muke yi na irin fina_ finan amurka haka nafi son ganin jarumin shirin murɗaɗɗe mai kama da namijin gaske, bana son ganin namiji babu faɗin ƙirji ko da ba'a murɗe yake ba. Wannan ra'ayinane tun ina budurwa dana mallaki hankalin kaina nake sha'awar maza masu ƙatti_ƙattin ƙirji. Hasaso Asama'u nake yi a lulluɓe a wannan faffaɗan ƙirjin da ya ke a matsayin duniyata. Yanzu shikenan kimata ta zube a idanun Asama'u kallona kawai take yi tasan babban sirrina shikenan. Bakinshi na kalla ina hasaso jikinta da yace zaisha a bakin nashi. Tunowa nayi da mai ɗungurungun ɗin kuma Idanuna na runtse jijiyoyin kaina suka amsa. Ina mamakin yadda akayi har aka soma wannan alaƙar tasu, waye ya soma neman wani a tsakaninsu? Sakewar da Asama'u tayi da Mijinyawa abun yayi yawa na kuma yi mamaki. Yarinyar dana ci alwashin haɗata Aure da azgar gashi Mijinyawa ya lalatata ya buɗe mata idanu. Tunda na kulle idanuna na kasa buɗesu adda'a kawai nake yi ƙirjina na curewa tamkar dutse. Sai wajajen asuba na iya bacci. Da asuba naji Mijinyawa na shafani babu shiri na zabura na miƙe zaune, ji nayi kamar gaushi ya watso mun. "Tashin hankali makarannan su da suka yi alƙawarin sun rabu dake Tutar so dawowa naga suke shirin yi fa" Miƙewa nayi ba tare dana ce uffan ba na shige banɗaki idanuna kamar zasu zazzage sabida bacci da tarin damuwowi. Wanka na soma na fito nayi sallah. Ina zaune akan sallaya Asama'u da Sabira suka shigo sai kallon gadona Asama'u take yi, ƙuri nayi ina kallonta. "Ammi ina kwana ya gajiyar hanya? " Lafiya lau Sabira ya karatun? " Asama'u tace. "Amminmu ina kwana ya gajiyar hanya?" Gajiya tabi lafiya, kuna da lekca ne yau?" "Eh muna dashi amman sai yamma zan shiga ni, Azgar dai yana da lakca da safennan. To yayi kuje ku nemi abinda zaku ci, kuyi da Abbanku ni zan shirya in fita aiki" Miƙewa nayi na isa bakin madubi su kuma suka fita a gaggauce na shirya na fito kamar babu damuwa tattare dani. Ina fitowa falo Mijinyawa na shigowa. "Me zan gani aiki zaki je yauma ashe, aina ɗauka zaki huta na kwana ɗaya kafin ki koma aiki" Murmushi nayi nace. A.a zanje ni na shirya zan wuce saina dawo. Ke kuma Asama'u kafin ki tafi makaranta kiyi girkin dare shinkafa da miya" Sai cewa tayi. "Ammi babu nama kifinma ya ƙare" Ban gane ba, wani abun akayi da namanne nasan dai na bar kifi da nama ai? " Sabira tace. "Inna Jamila ne suka yi girki jiya a Kitchen ɗin muma sanda muka shiga muka ga kwanuka duk anci abinci to inaga su sukayi amfani da naman" Shiru nayi ina girmama girman muguntar Yaya Jamila. Bananan shine zasu shigarmun Kitchen suyi mun girki harma su ɓarnatar mun da nama? To kiyi miyar a haka Asama'u. Wucewata nayi na barsu a gida ko Sabira ban jiraba. Kallon ɓarayin Uwatale banyi ba ina jiyo hayaniyarsu Yaya Jamila. A gaban motata naga Azgar ya wanke mun ita fes yana gogewa sai naji sanyi da tausayinsu kuma. Gaisheni yayi nayi mishi godiya tare da shi mishi albarka. Na shiga motata na fice a gidan. Shikenan zuwa anjima sai suci karensu babu babbaka gidan daga su sai su in sunga dama kada su rabe in suka haɗe. Idanu na lumshe kawai na ƙudure a raina inna dawo zan karɓi wayar Asama'u inga ta inda suka soma wannan alaƙar waye ya soma ra'ayin wani cikinsu. Da wannan tunanin na ƙarasa gidan rediyo na gabatar da aikina tamkar babu matsala tattare dani nice harda daɗa kwantarma da Luba hankali da take faɗamun asabar zata tare a sabon gida asabar ta sama kuma auren Sunusi. Na bata shawarwarin da saida ta saki ranta Alhalin ni ƙirjina da kaina kamar zasu tarwatse haka nake jinshi. Na dawo gidan na tadda Mijinyawa da Azgar da Sabira Asama'u na makaranta. Sai bayan magriba na ɗakko wayar Asama'u daga caji a ɗakinsu, na shiga ɗaki basa nan suna wajensu Yaya Jamila. mijinyawa ma yana can suna hirar zumunci wai gobe zasu koma. Zaman shirshen nayi na shiga manhajar Whatapp ɗin Asama'u saƙonshi ne a farko an rubuta Sikari Shiga nayi ina girgiza kaina na dinga haurawa sama har nazo farko, da dukkan halamu nata saƙwannin cikakkune. Asama'u ita ta soma tura mishi da saƙo kamar haka. _Allah ya sani Abba na daɗe ina jin sha'awa da mafarkin ganina a manne a faffaɗan ƙirjinka ka matseni. A kullum mafarkina kenan kuma ina fatan ya tabbata ya zama gaskiya. Nima ka sammun soyayyarka ko da kwatan_kwatan wanda kake ba Ammi ne. Haza wassalam daga Asama'u mai mafarkinka ko da yaushe_ Yawu na haɗiya mai ɗaci da kauri, lallai yaran zamaninnan idanunsu a mugun buɗe yake in ubantane zata rubuto mishi wannan saƙon, yanzu duk wahalar da nayi da Asama'u ta rasa abinda zata yi mun sai farautar mijina? Duniya tazo ƙarshe. Ga amsar mijinyawa _Haba Asama'u shaiɗan ke ƙawata miki ni kawai aini ubane a gareki har gaba da abada mafarkinki a iyakar duniyar mafarki zai tsaya_ Sai ya tura mata. Sai ta sako mishi gwaigwai ɗin kuka da hawaye. A haka dai taita jero mishi kalamai kusan kullum, har ya soma jin daɗin hira da'ita tun tana batsa yana jin nauyi har ya dena jin nauyi. Sai kawai ya tura mata da hoton mazantakarshi yana nuna mata a cikin halin da yake a daidai lokacin. Shikenan ya buɗe mata ƙofa saiga bidiyonta ta turo mishi tana wanka ruwa da kumfa na sauka a jikinta. Da_ haka_ da haka _dai ashe a Hotel suke haɗuwa ya jagwalgwalata yadda yaso sai dai bai taɓa shigarta ba amman yana saka hannunshi dai. To yanzu roƙonshi da take yi ta nace shine ya kwanta ita da'ita tagaji da jan ran da yake yi mata. Shima kuma yana so amman dai ba'a je can wajen ba. Yana jin nauyi a haka dai har suka haɗa ranar da zasu haɗu Abinda ban gani ba shine shin sun haɗun sun biya buƙatar juna, ko kuma basu haɗun ba? Babu lallai bare tilas in gani a chart. Allah al hakim iyaye saifa mun dage mu dunga bin diddigin yaranmu, mu dasu babu ɗaga ƙafa mu dinga bincikarsu tamkar yadda mai kaya ke buncike ɓarawo, sannan mu dage da adda'a wallahi mu hana idanunmu bacci muita roƙon Allah ya riƙa mana akan tarbiyyarsu. Hotuna da bidiyon tsaraicinsu Allah yayi yawa dasu a cikin wayar. Kwafe komai nayi na tura a cikin wayata, daga wayata na adana a na'urata laptop jiri ne kawai yake tamaule dani ina tsantsar mamakin mijinyawa ashe raguwar zuchiya gareshi baya iya sarrafa zuchiyarshi akan mace kenan, ashe maza haka suke da rashin tsoron Allah da yawansu? Hmm Babu komai ( Dan Allah kuyi haƙuri kalmomin sunyi tsauri da yawa aimun afuwa yanayi ne yazo da hakan) Mrs BukhariTSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMMA TA BIYAR *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. Nayi bincike sosai a cikin wayar ko zanga tana mu'amala da wani, irin mu'amalar da take yi da Mijinyawa. Amman bangani ba, sai dai saurayi ɗaya da suke ɗan soyayyarsu soyayya mai tsabta babu kalaman batsa sam a hirarrakin nasu. mayar mata da wayarta nayi jikin caji har lokacin suna ɓarayin uwatale, Mijinyawa babu mamaki yana masallaci dan anata kiraye_kirayen sallah a lokacin. Sallah nayi na haye gado na kwanta kamar gawa, kaina fa ku gane a kulle yake har zuwa lokacin ina canki cankar matakin da zan ɗauka akansu ne mai mugun zafin da sai nadama gami da dakace ma basu san junansu ba. Sannan bani da garaje nafi son bin komai daki_daki domun bana son kalmar faɗuwa, sai dai nasara. Yawan garaje nasa yawan faɗuwa. Bin komai a kan tsari tare da ba ƙwaƙwalwa da zuchiya damar gudanar da tunani mai kyau yana sawa a fidda sakamako duka ɗauka. Dukkan abinda zanyi tunanina bai gushe ba, ina jin kunyar yaranmu suji irin wannan ɗumasariyar da ubansu ya aikata, kuma ace musu da Asama'un da suka ɗauketa tamkar jininsu babu bambanci tako ta ina. Ana idar da sallah yara suka dawo sukaita murɗa ƙofata a rufe ina daga kwance na tambayi waye. Munafukar itace tace. "Mune Ammi? " Lafiya" Na tambaya dan ita da sake shigowa ɗakina har abada wallahi. "Dama zamu gaisheki ne" Ji nayi kamar in lailayo ashariya in narka musu dukkansu ma. Kuje a kwance nake bazan taso ba bana son hayaniya" Ya suka ƙare oho sai na jiyo muryar mijinyawa a dokin ƙofa yana kiran sunana. Da ƙyar na tashi cikin jarumta na buɗe mishi ƙofar ya shigo. Saida ya zauna yace. "Naga sai rufe ƙofar kike yi yarannan zasu kawo mana abincinmu ko kinci naki ne? Miƙewa nayi tare da cewa. Banci ba, bari in karɓo da kaina yaran sun kai minzilin da in kana ɗaki tare dani bai kamata su riƙa shigowa ba" Har nakai dokin ƙofa yace dani. "Waɗannan kuci_kucin cakuri cicin yaran? " Kusan a hasale na juyo nace Su fa" Nayi ficewata da ƙarfina a jikina. Tiran abincin na gani a hannun Asama'u tana rawar kan kawowa cak nasa hannu na zare na juya Azgar na saman Daining shi da Sabira suna cin abinci suna hira kallonsu banyi ba dan ji nake kamar in cinnama gidan wuta duk mu ƙone baki ɗaya. Sai dai kash bazan yi hakan ba sam. Shiru na shiga ko sallama na kasa yi na dire abincin a kan gado. In zuba maka ne? " Ƙur ya bini da idanunshi jikinshi duk a mace. Hannayena ya kamo nayi sauri na fisge tsoro ya kuma shigarshi da irin ƙarfin da yaga na saka yayi tunanin bani kaɗai bace. A ɗabi'ar ɗan Adam yana samun ƙarfi in yana cikin matsanancin ɓacin rai musamman ma in shine da gaskiya. Murya ba ƙarfi yace. "Tutar so wani abun ko dai ya faru ne a lokacin ina kwance a asibiti? Me ka gani? Na tambaya da murya sassauƙa harda murmushi. " Naga tunda kika dawo kika canja ba kamar yadda na sanki ba a satikan baya ba. Nasan baki fiye jituwa dasu Yaya Jamila ba nasan kuma dole ko a lafazi zata cutar mun dake. Amman kiyi haƙuri in akan nama da kifi da suka ɓarnatar miki ne nasa an kawo kifi da nama bayan tafiyarki. In akwai matsala ki faɗamun dan Allah sabida in samu nutsuwa" Murmushin baƙin ciki da takaici nayi, har Allah ya'isa saida na jawo a zuchiyata. Babu fa komai gajiyar tafiya cakuɗe da gajiyar asibiti ne kawai, sai ciwon kai da nake cikinshi dai" "Na fahimci kamar mutanenki ne suke son su sake dawowa kinsan basu fiye alƙawari ba. Amman babu komai zan koma wajen malam da kaina gobe zan rarrafa inje in karɓo miki rubutu' Allah ya nuna mana goben." Abincin na zuba mishi, na haɗa shayi da biredi nasha da naji ban ƙoshi ba na saka Azgar ya dafo mun Indommi naci na ƙoshi abuna, to kashe kaina zanyi in ƙi cin abinci sabida Mijinyawa gona_gonan mazinaci, mayaudari, mai budurwar zuchiya, wanda bai gode Allah bisa ni'imar da Allah yayi mishi ya tsaya a iyakar halalinshi ni ba. Ya ɓige da aikin ashsha da yarinya ƴar cikinshi, kuma yake kwashe mun albarka a gabanta, ya bata ƙofa itama ta zauna a tabarmar rashin darajar daya shinfiɗa mata a kaina. Washegari kuwa ina dawowa daga aiki naga rubutu da hayaƙi da saƙe_saƙi ya karɓomun. Haka lamura suka ci gaba da tafiya wasa_wasa dai har Mijinyawa ya koma bakin aikinshi, ni kuma ina dako, da sanya idanuna a duk motsinsu na cikin gida fa amman. Ni ke saukeshi a wajen aiki in wuce wajen nawa aikin nima. Ya nemi hakkin auratayya na nuna mishi bana jin daɗin jikina sai ya ƙyaleni tunda yaje wajen malam ya haɗo mishi magangunan makarai ya kawo mun, saina fake da wannan naita guje mishi. Shi da Asama'u suka ci gaba da iskancinsu ina sane da duk motsinsu ina kallonsu sosai. Kwatsam rannan na dawo aiki na tarar Nanno tazo tana ɓarayin Uwatale dama nan take sauka in dai tazo. Ina ajjiye jakata na nufi ɓarayin na Uwatale matan su Ado duk suna ciki. Ina shiga Nanno ta rage fara'arta ɗan yaƙe dana saba yi mata albarkacin ɗanta da jikokinta bata samu ba ina gaisheta na miƙe sai cewa tayi. "Dawo zauna" Na dawo na zauna sai tace. "Mijinyawa ya faɗa miki Asama'u zata koma hannuna?" Sai naji mamaki amman sai nace. A.a bai faɗa mini ba babu mamaki ya mance" "To gobe zamu wuce ni da ita riƙonta zai dawo hannuna da makarantarta da komai" To Ubangiji Allah yasa hakan shine mafi alkhairi" "To ameen shikenan jeki" Miƙewa nayi na fice. Karo muka ci da Mijinyawa da mijinyawa Babba suna shigowa zasu je wajen Nanno. Gaisawa muka yi na shige ko duban mijinyawa banyi ba. A falo na zauna cikin su Azgar da Sabira, Asama'u kuma tana ciki. Ina asama'u take?" "Tana ɗaki tana haɗa kaya Ammi wai gobe zasu tafi jama'are da Nanno" E hakane gobe zasu tafi" Azgar yace. "Bamu ji daɗi ba wallahi to Ammi acan zata ci gaba da karatun nata? Ni dai da Nanno ta bari inta gama karatun ta koma, jama'are ƙauyene sosai Ammi dan Allah kisa baki komawar tata tamkar kashe mata rayuwa za'ayi, mun saba sosai babu wanda yake tunanin Asama'u ba ƴarki bace me yasa za'a ɗauke miki ita? " Sabira ta amshe. "Dan Allah Ammi" Murmushi nayi musu nayi farin cikin tafiyarta, amman akwai abinda nake son sani meye dalilin tafiyar tata, tuba Mijinyawa yayi yake son nisantarta ko kuma, wani shirin ake ƙullawa, ko kuma menene?" Sai kawai ma na share nace da yarana. Kuyi haƙuri Nanno ba yadda zata yi ba tunda ta riga tace to dole ayi mata biyayya" Shiru suka yi, ina zaune harta fito idanunta yayi luɓu_ luɓu tazo ta zube a gabana sai kuka. Yaran duk hankalinsu ya tashi. Ƙur ni kuma nayi ina kallonta ina tausayin halin data jefa rayuwarta a ciki, wannan kukan dai na rabuwa da Mijinyawane. Ina son Asama'u sosai kuma tausayintane yasa nake sonta, na bata pawa sosai a gidana ƙila hakanne yasa ta samu waje, ni Allah shine shaidata dominshi nayi kuma Amana aka bani na saka hannu na karɓa. Ana cikin haka sai gashi ya shigo da sallamarshi ya nemi waje ya zauna. "Ita kuma wannan kukan rabuwarne aka soma? Kiyi haƙuri ai zaki dinga zuwa mana hutu kinji ko, nima kuma zan dinga zuwa wajenki, sannan duk abinda kike so ki bugo waya ki faɗama Amminki zata sanar mini, ko ki faɗama mutuminku Azgar." Asama'u kiyi shiru. Ki kuma riƙe mutuncinki ki tsayu akan tarbiyyar da Abbanku ya baku dama wanda nima na baku, ke macece dole watarana dama za'a rabu, da kin gama jami'a aurenki zaki yi. To sai kiyi haƙuri ki rungumi sauyin da kika samu" Ina gama magana na ƙule ciki na barsu sai rarrashinta suke yi yadda kuka san wacce jaki ya kada. Sai da akayi isha muna zaune muna cin abinci Mijinyawa ya kirani a tsanake na dubeshi ba tare dana amsa mishi ba. "Nifa na kasa gane kanki sam Tutar so nafa san halinki ki fito ki faɗamun kawai abinda nayi miki da kika ƙaurace ma turakata da abubbuwa da yawa da kika yi watsi dasu a cikin gidannan rayuwar gidan ta soma rashin daɗi, na damu da yawa duk sanda na tambayeki sai kice babu komai, amman kuma akwai wani abun da kike ɓoyewa Tutar so nayi miki sanin da babu mahalukin da yayi miki irinshi ki faɗamun menene matsalar na roƙeki da girman Allah" Mijinyawa kenan, in da akwai zan faɗa maka ai. Kuma kasan ba haka nake fishi ba tunda babu abinda bana yi maka face kwanciyar aure da muka dena shima kuma lalurace ni kaɗai nasan abinda ke damuna fa" "Aa ba mu'amalar aure kaɗai aka dena ba harda hira, da cefane da kike yi, a da in abu ya ƙare bakya tambayata sai dai ki siya har sai nayo wani cefanen in sabon wata ya shiga, wani sa'in ni dake gogoriyo muke yi wajen cefanen gidannan. Sannan da ko da al'ada kike yi kinsan hanyoyin gamsar dani tunda ke kinsan halittata. Ga motarki kina mun rowarta harma na yi zuchiya na dena cewa ki bani ko a jikinki, na fa soma gajiya kina neman ki sukurkutamun tunanina, wannan abun ya soma taɓa aikina Tutar so, in akwai abinda nayi miki ki sanar dani in baki haƙuri mu dawo da farin cikin gidanmu. Gidan yaushe rahama da haske zai sauka sarauniyar gidan tana nuna halin ko in kula" Ummmm babu komai maganar cefane da kake yi ai ratayayyen hakkinka ne ni taimakawa nake yi, a yanzu bani da halin taimakawanne sannan batun hira da kake yi me ka taɓa cewa ban tanka maka ba" A daren ranar faɗa muka yi ƙaƙas, shi ala tilas yayi fishi dani, ina ɗaga mishi hankali da sabon salon ko in kula da nake nunawa gabaki ɗaya na canja. Kuma ina fara'a muna hira, kwanciyar aure da wasa da dariya na dena kamar yadda ada muke yi, sai ya dakeni, in dakeshi wallahi ko mu kama kokawar soyayya a ɗaki haka muke rayuwarmu mai tsabta kafin ya shigo da wannan bidi'ar. Yayi rikici sosai yayi rarrashin duniyan,damma ban biye mishi ba. Zuchiya ma yayi ya koma ɗakinshi nima na kulle ɗakina nayi kwanciyata. Sabida samun waje har ƙorafi kake yi akan mota da cefane sabida na wawantar da kaina ka ɗauka bansan me nake yi bane? Ai baka ga komai ba inka gaji sai ka ɗauki matakin duk da kake ganin shi ya dace aikin banza. Washegari kafin bakwai Asama'u tazo tace mun zasu wuce har gaban motar Mijinyawa Babba muka rakasu ni da yara. Mijinyawa yana gaban mota ashe dashi za'aje. Ni dai nayi musu Allah ya tsare hanya na ɗakko dubu biyar na damƙama Nanno nayi wucewata. Sai naji gidan yayi mun sarari sosai. Mijinyawa bai dawo ba saida ya kwana uku, ko sau ɗaya bai kirani a waya ba. Sai ranar da zai dawo a ranar ni kuma ina wajen aikina cike da farincikin kwantiragin da Bbc landan ta ɗaukeni suka ji suna son suyi aiki dani na shekara biyu kuma gidan rediyon kano masu karamci basu yi mun baƙin ciki ba tuni suka amince, gashi a yau ɗin ake sanar dani an maidani ɓangaren masu ɗauko rahoto wato rifota kenan aikin dana fi ƙauna a aikin jsrida kenan. Na ƙudurce a raina ko a gidanmu bazan sanar ba har sai lokacin tafiyata landan yayi tukunna. Ina cikin wannan murnar naita ganin kiran Mijinyawa wallahi nayi funfuruncus naƙi ɗauka daga gidan Rediyo ma madadin in dawo gida wallahi sai naƙi nayi wucewata gidan Yaya Saratu dan in wanke ƙuncin zuchiyata. Gidanta ita kaɗaice da yaranta takwas duk sun girma Autanta ma shekara sha uku. Tana zaune tana kallon tashar Arewa 24 ta jiyo sallamata. "Tabb yau kune a gari inji maƙi baƙo? Ban kuma daɗe da dawowa daga gida ba Inna Turai dai na barota tana naƙuda. Abinda yasa na dawo Baban Nafisane ya kirani yana hanya shi yasa kika ganni na dawo yanzunnan na gama girki shine na zauna" Zama nayi ina cire mayafina. Ahh kice yau amarya ce ke, banji turaren wuta na tashin ƙamshi ba, sai ƙamshin kaza" "Tukunna dai ai sai nan da awa biyu ko uku ma zai dawo, zo mu shige ma daga ciki" Miƙewa nayi muka shige ciki yaran duk basanan. Zama nayi a gadonta nayi dirshan. "Ina zuwa bari in ɗebo kayan ɗa'a in dama na damawa, kinsan fa ba wasa sai da tada komaɗa" Fita tayi muna dariya sai gata da kayan ɗa'a cikin basket Na Surayya Dee marubuciyar Halin yau. Su sanyi fuloshane, harda gimbiyar zabuwa a dafe cikin tsabta da ganin komai kasan cikin nagarta da ilimi aka haɗashi. Ga nasu garine dana ruwa duka dai. (08032773332) Duk mai so ya tuntuɓi Surayya Dee kai tsaye zaku dawo ku gode mun. Taita damawa tana sha, tana bani ina kaucewa sabida ai nima ina amfani da kayan matan Surayya Dee kuma nasan nagartarsu da ingancinsu bazan taɓa sha ina kan wannan ƙadamin ba. Ke dai kisha ni kinsan ina da nawa bani na haɗaki da Surayya Dee ɗinba ma. Amman sabida Allah saida miji yana hanya zaki soma shan magani shi da akeso kamar saura sati guda sai kasha yabi jikinka ai yafi aiki ma" "Ke nafa shassha wannan ƙarine fa sanyi fulosha ma da shan lemo nake yi mishi tsabar yadda yake fatattakar sanyi. Hinduwa ai dole in dage insha magani in gyara jikina har dilka duka nayi wanda na siya a wajen Mrs Bukhari sirrin gyaran jikin matan Sudan, na matsi duk nayi amfani dashi shima na wajen Surayya Dee ɗinne. Ni so nake yi ma inje aimun ɗinki a ɗinkeni gam wallahi. Nace. Ai kuwa akwai wacce na sani ta'iya sosai nata gashi da saurin warkewa kuma tasan aikinta sosai, duk da ban taɓa yi ba ta dai taɓa yima Luba kuma ta yaba sosai." "Allah sarki saida kika ce luba na tuno mijinta yayi auren ko? " Hmmm yayi aure munje mun yi biki. In banda sha'anin maza sai su baki ga amaryar ba babu wayewa sam sakandare kaɗai ta gama. Na dai siya mata kayan mata basket guda na Uwargida a hannun Surayya Dee tana kan gyara kanta zuwa lokacin da Allah zai sa miji ya waiwayo kanta" Muna cikin hirarmu muka jiyo kiran Innarmu a wayar Yaya Saratu wai Inna Turai ta haihu ɗa namiji. Mun jima sosai muna hira sai dab magriba na wuce lokacin Baban Nafisa ya faɗa mata ya shigo kano. Bani na isa gida ba sai bayan magriba. Ai kuwa a falo na samu Mijinyawa ya cika yayi fam kamar zai fashe. Yarane sukai mun sannu da zuwa na amsa musu, Abinci Azgar ya kawo mun ko wanne ya nufi ɗakinshi. Sannu da dawowa ashe yau zaka dawo ka baro su lafiya? " Wani mugun kallo yayi mun. "Daga ina kike kuma baki ga kiran wayata bane? " Daga gidan Yaya Saratu nake bayan na baro wajen aiki. Kiranka kuma ban gani ba" Ai sai ya miƙe ya soma nuna ni da yatsa. "Ke bari kiji bazan ɗauki wannan sauye_sauyen da kika ɓullo mun dashi ba. Na fahimci sauƙin kaina yasa kin soma rainani. Wallahi idan kika yi wasa aikinma ajjiyewa zaki yi tunda nina biya miki kuɗin makarantar kuma ina da ikon hanaki zuwa. Na lura a wajen aikin ku ake zigaki. Ya kike nema ki kassaramun kuzarina Hindu kin hana ma zuchiyata salama, na roƙeki da girman Allah ki sanar dani me nayi miki ni mai baki haƙurine kema kin sani. Amman kin ƙi sai lulluɓeni baibai kike yi" Dariya ma ni wallahi ya bani yadda yake haƙilo akan ɗan canjawata. Au ashe duk abubuwan da nake yi muhimmaine kuma anaso duk wata mace ta yisu? Maza kenan nasan kunanan wasu na ganin wautata kuna ganin tamkar bazan ɗauki mataki ba ko? Mataki da hukunci sunanan tafe kubi karatun cikin nutsuwa karatune na nazari bana zallan nishaɗi ba. Hmmm mijinyawa duk abinda ka faɗa gaskiya ne. Kai ka biya mun kuɗin makaranta badan a gidanmu ba zasu iya biya mun ba. Aiki kuma a gidanmu aka nema mun, aikinnan babu abinda bai yi maka ba. Aikina yana da mahimmancin da babu abinda zaisa in barshi wallahi idan sama da ƙasa haɗewa zata yi aikina yana hannuna babu gudu babu ja da baya. Babu shakka ashe ka'iya gori har ƙwaƙwalwarka ta iya tuno maka kai ka biya kuɗaɗen karatuna ashe?" Abincina na ɗauka na shige ɗakina na yi zamana a kan gado. Sai gashi ya biyo ni waje ya samu ya zauna na lura jikinshine yayi sanyi. Banyi niyyar cin tuwon ba amman naita turawa ina haɗiyewa dan in cusguna mishi. "Tutar so" Ya kirayi sunana da murya mai kauri. Bai jira na amsa ba babu buƙatar hakan yasan bazan taɓa amsawa ba. "Ba haka kika saba yi mun ba. A baya ni ɗan gatankine wanda kike gatantawa ta fannoni daban_daban ta fannin abinci, ta fannin mu'amalar aure, ta fanni kulawa dani, da gidan baki ɗaya. Ki duba rayuwar da muke gudanarwa mai kyau, a baya kaɗan har guje_guje muke yi da juna musamman ranakun hutu. Asabar da lahadi kuwa muna fita da daddare muci abinci a waje tare da yara ayi nishaɗi. Amman tunda na dawo daga asibiti ba'a sake yin wannan ba. Bakya zuwa ɗakina kona kwana a naki ɗakin babu ko hira a tsakaninmu, dan Allah me nayi miki ki sanar dani mu haɗu mu gyara rayuwar gidanmu tayi kyau. Duk kin rikirkitamun lissafina yana neman kwancewa duk wanda ya kalleni yasan ina da damuwa, ni tsorona kada su Azgar su gane halin da gidan yake ciki" Shiru yayi yana saurarena Bada ban ina duba abubuwa da yawa ba ai da wani labarin akeyi ba wannan ba. Mijinyawa nace maka babu komai yanayin rayuwane kawai. Ai dama ba zamu taɓa dauwama a haka ba inta riritaka ina tarairayarka kamar dan kai nazo duniyar ba. Wannan duniyar Allah ya haliccemune domin mu bauta mishi" Miƙewa nayi na shige banɗaki na wanko hannuna da bakina na fito. Ban ganshi ba amman nasan masallaci ya tafi. Ko da ya dawo bai shigo ba, ni kuwa harna garƙame dama ɗakina. Da safe dake ranar asabarne sai ƙarfe takwas na fito fes dani nayi wanka na saka atampa riga da siket. Naga falon babu kowa amman Sabira ta gyare ko'ina sai ƙamshin Halud lamba wan na mrs Bukhari yake tashi. Na jiyo muryoyinsu a Kitchen saina nufi can. Hmm mijinyawa yana gabas gas kuka yana ta aikin suyar doya ga miyar ƙwai sai dahuwa take yi.. Azgar kuma yana haɗa kofuna da filet da zai fita dasu. "Kin tashi barka da fitowa, kije falo kiyi zamanki Tutar so yanzu zan kammala in fito, kiyi sarautarki yadda kike so, takawarki lafiya" Kai na gyaɗa kawai yaran duk muka gaisa na fita. Laptob ɗina yana kan cinyata ina duba asament ɗin farko da aka bani monday zanje wani taron ƴan siyasa in ɗakko rahoto su suka turo da gayyatarma da kansu. To bayanai nake karantawa suka fito tare da dure komai a gabana. Dani mijinyawa ya soma, nasa hannu na karɓa. Nagode" Nace dashi, naci doyata da miyar ƙwai na kora da shayi, yanata jana da hira, ina amsawa a taƙaice kuma babu fushi, ko ɓacin rai bare damuwa tattare dani sam, abinda yafi komai ɗaure kai kenan. Da naga tara tayi nace dashi. Zani gida Inna Turai ta haihu zanje" Baki ya washe. "Me muka samu, yaushe ta haihu? " Namiji, jiya ta haihu." Mayafina da jakata na shiga na ɗakko takalmina na hannu na fito. Naso in tafi da yaran duka, Azgar yace mun karatu yake so yayi saina barshi Sabira kuma ta bini muka je. Haka mukaita sintirin zuwa gida har ranar suna. Asament ɗina na farko na gane aikin rahoto ga ɗiya mace aikine mai ƙalubale ainun, hakan naba mace damar shiga maza, sanin manyan mutane, shiga inda batai tunani ba, da shiga inda baima dace ace tana mace ta shiga ba, tsaiwa a wajen da batai zato ba, tambayoyi ga wanda bata taɓa tunanin zasu haɗu ba. Taron ƴan siyasa na farko da naje ɗakko rahoto ƴan jarida da gidajen tv da rediyo sun halarci taron sosai. Amman mu biyu ne mata a masu ɗaukar rahoto ɗayarma ba musulma bace. Kuma dole ka kutsa kaima kayi taka tambayar ka tura bututun magana domin naɗewa. Nasha wahala ranar sosai, amman dake abinda nake sone wahalar bata dameni ba, kuma gwagwarma shine abun burgewa na farko mafi girma a rayuwata, ni nafi sha'awar abubuwa masu wuya. Al'amura haka suka ci gaba da cukurkuɗewa ana cikin haka Zara'un Inna Abida ta haihu nanma mukaita sunturi, mun gama da wannan Baba Nagoɗi ya kwanta a asibiti shima muka ɗaura, ga aikin rahoto aikine na yawo sosai har gari_gari inta kama sai kaje ƙauyuka kuwa babu inda bana kutsawa duk Mijinyawa fa bai sani ba. Ranar wata asabar sunje Jama'are da yara sun dawo ina falo a zaune ina kallon labarai a NTA labaran tara sai gasu sun shigo. Sannunku da dawowa ya hanya? " A gajiye ya amsa mun. "Hanya Alhamdulillahi mun sameki lafiya? " Lafiya ƙalau ya aka baro su inna da Nanno? " "Kowa lafiya sunce a gaisheki ma" To ina amsawa, ya Asama'u take? " "Lafiya lau take tama samu gurbin karatu." Miƙewa nayi na soma fito da kayan abinci ina jerawa a ƙasa. Duk muka baje a ƙasa tuwon semo nayi da miyar karkashi bushasshe yana son miyar sosai. Tun daga lokacin dana ga wannan aika aikar muka raba kwanon abinci. Muna ci ina hira da yara shi dai na ganshi sanyi ƙalau. Mun jima muna hira a falo dan sai wajajen goman dare ko wannensu ya wuce ɗaki zasu yi wanka su kwanta. "To bari inje in yi wanka ki sameni a ɗakina zamu tattauna muhimmiyar magana" To kadai yi wankan ina falo sai muyi maganar" Kallona yayi yace. "Da gaske guduna dai kike yi daga ni har ɗakina Tutar so. Mijinyawanki nefa wanda kullum dare kina maƙale a ƙirjina" Dariya kawai nayi fur naƙi binshi dole yaje yayi wankan ya fito saye da jallabiya fara. A inda ya barni ko shurawa banyi ba. Zama yayi a ƙasa inda ya tashi. "Hindu" Naji ya ambata. Na tabbatar wannan magana babu wasa a cikinta tunda ya ambaci sunana. "Wata ƙaddarace ta hau kaina nima bansan da maganar ba saida naje Jama'are Nanno ta kawo mun zancan. Akan dai rashin sake haihuwarkine take ta ƙorafi akan yara biyu gashi sun girma shiru abokaina sunata hayayyafa. Shine ta umarceni da ƙarin Aure.... " Sai ya ja fasali, ni kuma ko ɗar banji ba a zuchiyata domin nasan dole sai anzo wajen kuma tunda ya kwaso baragadarsa nasan akan Aure zai sauketa. Murmushi nayi mishi kawai ina saurarenshi ya ƙarashe. Sai kallona yake yi da gaske har cikin zuchiyata banji komai ba ganin hakanne yasa yaci gaba. "To shine dole na amince mata nan da kwana arba'in za'ayi bikin. Amman wallahi Hindu" Sai nayi sauri ɗaga mishi hannu muƙus yayi da bakinshi. Mijinyawa rantsuwa ai ba taka bace babba gareka. Sannan ƙarin Aure ba laifi bane Ubangiji shi ya baku wannan damar, bin umarnin Iyaye wajibine Allah ya sanya Alkhairi. Ni bacci nake ji zanje in kwanta" "Amman baki tambayeni wacece wacce zan Auran ba? " Dariya nayi nace. Akwai buƙatar hakan ko? Ai dake naga Aure dai kaine zaka ƙara nauyinta da komanta ai kamar a kanka yake ba kaina ba ko" Kai ya gyaɗa halamun eh akwai buƙatar in santa ɗin, harna tashi saina koma na zauna. Wallahi saida muka kusan zarce minti goma sai zaiyi magana sai ya fasa, ni kuma idanuna ƙur a kanshi, da ƙyar dai yace. "Asama'unki tace in Aura, kiyi haƙuri dan Allah ban karɓa dan in tozartaki ko inci zarafinki ba wallahi. Matsawa Nanno tayi dole hakan take so ayi. Ni kunya da damuwa duk ta aureni wallahi. Shin da wanne idanu duniya zata kalleni ne? Naso in fahimtar da'ita Asama'u ɗiyace gareni babu Aure a tsakaninmu ubane ni sosai a wajenta, amman ina. Kuma babu macen da zata iya kamoki matsayi a zuchiyata na sani da zafi amman kiyi haƙuri ki taya ni muyi ma Nanno biyayya." Sokiburutsunshi tun ina iya ji har kunnuwana suka dena ji sakamakon hankalina da baya wajenshi. Irin girgizar da zuchiyata tayi har abada bazan mance ba, ga girgizar abinda suke aikatawa, ga sabuwar girgiza. Kuma na ƙudurce daga yau baccina na ƙarshe kenan da zanyi a gidan Mijinyawa. Miƙewa nayi cikin dakiyar zuchiya tare da nuna halin ƙi faɗi cikin halin ko in kula nace. "Allah ya bada zaman lafiya" Juyawa nayi nayi shigewata ɗaki da ƙyar nake ganin hanya. Ina jinshi yana bina tare da ƙoƙarin cin mani yanayi yana kiran sunana. Ina shiga ciki na bugo ƙofata na jingina bayana a jikin ƙofar, ɗakin na juyawa dani. Ji nake kamar in bar gidan a daren in tafi gidanmu. Amman ina ba lokacin bane, ba yanzu na tsara abinda zan yi ba tukunna dai. Tsugunnawa nayi da rarrafe na isa bakin gadona sabida inason lafiyata ji nake yi zan iya faɗuwa. Allah naita ambata kawai ina jina kamar ba ni ba, yarinyar dana ci kashinta naci fitsarinta na koya mata tarbiyya, tasan sirrina ciki da waje itace za'a auromun a haɗani zaman kishi da'ita bayan ya gama kwashe mata albarkatun jikinta, kuma ya gama watsar mun da darajata. Kuma wai ni yake ma ƙaryar umarni aka bashi. Hmmm oh dalilin da yasa aka ɗauketa daga gabana kenan ashe a matsayin kishiya za'a dawo mun da'ita? Kunji sabon shafin da mijinyawa ya buɗemun alhalin ban gama biya wancan ba. Dan Allah zaku ga laifina inna soma buɗe mishi nawa shafukan kuma nayi mishi rinto? Hmmm ambaton Allah shi ya ragemun nauyin ƙirjina sai nake jin kamar zan hau iska tsigar jikina sai buɗewa take yi. A taƙaice saida na sha wahala cikin wannan daren da ƙyar nayi bacci makaraina ina jinsu a kusa_kusa. Amman da gari ya waye saina dawo cikin hayyacina sabida tsabar ƙarfi da tasirin ambaton Allah da salatin ma'aiki Arrasul SAW. Tashi nayi na gabatar da sallah, na rasa wacce adda'a zanyi sabida nayi adda'a a daren jiya kamar babu yau. Sai kawai nace. Allah ga kayanka kai kasan yadda zaka yi dani" Ina kaiwa haka na miƙe na shirya tsab duk da zuchiyata ciwo take yi mun amman fa a fuska babu halamun rauni ko damuwa tattare dani. Dama masu suna Hindu jarumaine kuma suna da bushewar zuchiyata ga kafiya. Bushewar zuchiyarne yasa Hindu matar Abu Sufyan kafin ta musulunta ta saka wahshi ya kashe mata Sayyadina Hamza ta ciro hantarshi ta ci. Fitowa nayi na tadda Mijinyawa a zaune a falo da shirinshi na zuwa office tsaf. Ina kwana" Na furta ban jira amsarshi ba nayi ficewata ina jiyoshi kamar biyoni yake yi dashi da yaran. Sai kawai naga su Uwatale suna leƙowa ana nunani da baki. Wannan abun sai ya zamemun tamkar fitilar data haskamun hanya, take tunanina da ƙudurin dana fito dashi a zuchiyata ya sauya salo. Da sauri na isa harabar gidan kafin su zo harna tashi matota maigadi ya wangalemun get nayi ficewata da mugun gudu. A tsaye nabarsu a wajen in sunga dama kada Allah yasa su je makarantar shima kada yaje aikin. Takwas da rabi na ƙarasa Na'ibawa na ajjiye motata a kusa da Motar Akarami na shiga gidan da sallamata. Anata hada hadar karyawa ko wanne Lungu cike fam da hayaniya. Haka naita shiga ina gaishesu a ɗakin Inna Abida nake jin labarin samarin gidanmu mutum biyu an saka ranar bikinsu wata uku masu zuwa. Murna na taya su dan nasan bana ma ƙasar za'ayi bikin. Innarmu na tarar ita da Akarami yana juya mata masa. Wannan shine ana wata ga wata. Kai jama'a Ubangiji Allah ya datar damu Mrs Bukharihttps://chat.whatsapp.com/JI1IGIBFHYm64hr6IfVfqR TSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA SHIDA. *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. Turmi na jawo na zauna a kusa da Akarami. Baba Nagoɗi ne ya shigo ɓarayin namu da sallamarshi. Cikin ladabi muka gaisheshi ya amsa da fara'a. "Hinduwa ina labaran na ganki sassafe a gidan, ince dai lafiya ko? " Lafiya lau Baba." To_to_ to ya jikin shi Mijinyawan ya warware ko? " Da sauƙi sosai Baba" "Allah ya ƙara sauƙi Ruwayya kirawo mun Soja wani abunne ya taso a ɓarayin Dogara. Zamu je yanzu kice ya sameni a lungun Dogara" "To shikenan bari a taso shi. Ke Hinduwa zo ki zuba masarnan a tanda ina zuwa" Wucewa ciki tayi Baba Nagoɗi ya ɗauki masa biyu ya wuce Lungun Baba Dogara. Su Baba Lukumanu sukaita zuwa suna wuce wa Baba Sojanmu ne ya fito shima. "Hindu kece sassafe haka lafiya dai ko? " Baba Sojanmu ina kwana? " "Lafiya lau bari inje in zo sai mu gaisa da kyau" Wucewa ciki yayi Innarmu ta zauna ta kalleni tace. "Duk da ke me ƙoƙarin ɓoye damuwace ni mahaifiyarki ce na tabbatar kina da damuwa" Idanu suka zuba mun. Hakane Mijinyawa ne zai ƙara Aure" Murmushi Innarmu tayi, Akarami kuma ya harareni. "Kishiyar kike tsoro kenan ke da kike da tauri kamar tsandauri? Mu bar maganar bari in sallami mutan gidan in mun shiga ciki ma tattauna inba haka ba kinsan halin gidan namu" Cewar Innarmu Ni dai bance komai ba ɗaki na shige nayi kwanciyata, daga nan ban san me kuma ya faru ba sai buɗe idanuna nayi naga Innarmu da Akarami a kaina suna tayi mun tofi. "Innarmu sun saketa. Sannu Hinduwa dama ashe baki rabu da ciwonnan ba har yanzu? " Innarmu tace. "Allah ya kyauta kawai dama su basu fiye barin mutum gabaki ɗaya ba. Sannan sukan kawo ziyara a lokacin da mutum yake cikin ɓacin rai ko cikin murna, to duk macen duniya bata son kishiya, babu wacce take murna da zuwanta sai dai fa dole, kaga kuwa dole su motsa. Bari inje in samu matan gidan munafukai kowa ya baza kunne yana son jin ƙwaƙwaf" Fita tayi ina jiyota tana musu bayanin mutanena ne suka tashi ba wani abun bane. "Wani abunne ya faru da'ita da suka tashi?" "Me zai faru da'ita yau Hinduwa ta soma hawa makaraine Abida, koko dai son jin abinda babu ruwan mutum a ciki. In da matsala ai dole zaku sani balle matsala bama fatanta. Na zaci kun cire rai da jin matsala daga gidan Hindu shekara sama da ashirin ai shi kaɗai ya'isa abun nunawa babu yaji, babu kawo ƙara" Shigowa tayi tana maganganu, Innarmu bata da daɗi kuma bata barin ta kwana sam. "Hinduwa tashi ki zauna muyi magana kinga nema kike yi ki tona mana asiri a cikin wannan gidan, Allah ma yasa makaran basu yi tonan silili ba ihu kawai sukai tayi suna nannaɗeki" Ina daga kwance nace. Innarmu na baro gidanne bazan taɓa komawa ba har abada na rabu da Mijinyawa" Bakina tayi saurin rufewa tace. "Kul kada ki bari ko ƴan uwanki suji wannan maganar balle Baba Sojanku. Hindu sabida zai ƙara aurene zaki ce kin rabu dashi, yaranki fa sannan saida kika gina gidanki kika gina shi kanshi mijin zaki tsallake ki barshi da wacce zai aura ta more ita kaɗai. Kada ki mance nifa nice ta biyu a wajen mahaifinku bayan ni yayo wata matar, ke kishiya fa ba wata abar tsoro bace in dai mace tasan kanta. Kaga Akarami bamu waje maza wannan ba karatunka bane" Fita yayi ba tare da yace komai ba. Innarmu Asama'u fa zai Aura yarinyar da tsugunnawa in haifeta ne kaɗai banyi ba. Wallahi aurenta da zai yi ko kusa bai tayar mun da hankaliba, zamanne yazo ƙarshe kawai" Zama ta gyara da kyau tace. "Hindu kenan, ai wannan kaɗan daga cikin butulci da sakayyar wasu mazan kenan. A fuskar addini baiyi laifi ba tunda akwai aure a tsakaninsu. A al'adance ana barin halak dan kunya. Nasanki da jarumta da dakiya sosai banyi zaton wannan abun zai tashi hankalinki ba sam, kuma na yarda dake Auren Asama'u bazai girgiza duniyarki ba. Duk da kishi halittane, kuma kishin abun so gaskiya ne. Yarinyar da rainonki ce itace zata ɗaukeki a gidan da da tallafinki ya tsaya da ƙafafuwanshi, mijin da kike da tasiri a rayuwarshi shi zaki bar mata akan me? Dangin mijinki da facalolinki da suke son ganin faɗuwarki su zaki bama ƙofa suga bayanki? Hindu yanzu duk idanu a kanki suke kuma kowa ya baza idanu da kunne dan son ganin irin haukar da zaki yi, ko wanne irin mataki zaki ɗauka. In da nice ke kuma in kin yadda na isa baki umarni to ba shawartarki nake yi ba umarnine ki koma gidanki ki ɗauki idanu ki zuba ayi komai a gama kamar yadda ba'a iya sanin logonki har ƴan uwanki kada ki sake asan kina da rauni akan kishi. Kada ki ɗauka amanarki aka ci. Ki daure ki danne Hindu ki rufa mun asiri ki tuno da yadda akayi auren da sharaɗin Baba Sojanku a kanki in kin mance na tuno miki kinsan a sharaɗinku babu yaji babu kawo ƙara kin sani. Kuma in sama da ƙasa zata haɗe kinsan babu mai sauyashi, kaifi ɗayane shi. Daga nan ki wuce gidanki kije ki zauna ki lallashi zuchiyarki kada ki bari damuwar komai ta taɓa lafiyarki, kinga makaranki har sun soma kawo ziyara, da sannu zai yi nadamar abinda yayi miki ke dashi sai kun zama tamkar sirikarshi tsabaragen kunyarki da zai dinga ji, me akayi akayi Asama'u, me kuma akayi_akayi Mijinyawan shi kanshi, ai yasan alfarmar da akayi mishi, ya kuma san kin mai tazara. Irin tazarar da in ba rayuwarshi da kika shigaba ba lallai ya kamoki ba. Yanzu haka ma da sauranshi bai kamoki ba sai ya jira wallahi. Kuma ki sani ko da taji daɗinshi na ɗan lokaci ne akwai lokacin da zai zo in ance ya kalleta ma sai yaji kamar an haɗashi da aiki, in akace ya taɓata sai yaji tamkar ƙasa ta tsage ya faɗa." Miƙewa tayi ta fita. Ni kuma na lumshe idanuna ina nazarin maganganunta da sharaɗin dake kaina da irin kafiyar, da dogiyar Baba Sojanmu wanda na gado daga wajenshi na ƙara a saman na mai sunana. Ga kuma abubuwan da suka wanzu tsakanin Asama'u da Mijinyawa dake dawo mun wanda wannan sirrin na burneshi har abada ƴan uwana ba zan bari suji ba, ko babu komai dan yara da irin yadda ya soni a baya zan alkinta mishi mutuncinshi, duk da shi bai alkintamun nawa ba, amman a idanun yaranshi yana da girman darajar da ya kamata in basu dama suci gaba da girmamashi abadan. Amman batun in zauna ni da Asama'u mu haɗa miji, wallahil azeem babu shi, babu_babu, ba kuma za'ayiba wallahil ƙudrat, hukuncin dana ƙudura a zuchiyata shine mafitata babu mai hanani aikata wannan abun face ƙudurar Allah. A hankali naji ina samun sauƙi a zuchiyata. Murmushi kawai nayi tare da girgiza kai ina hasaso yadda zanma mijinyawa. Saiya gaji da halayena yaji ya tsani kanshi, dama rayuwar baki ɗayanta, zan fice fit a cikin rayuwarshi, ko da daga kanshi maza sun gama ƙarewane. Kuma nayi imanin sai rayuwarshi ta girgiza, ta dawo salab. Shigowa Innarmu tayi da masa da miya ta ce. "Tashi kici Hinduwata ki sha maganin ciwon jiki kiyi kwanciyarki, in yamma tayi kya koma gidanki. Shi mijinyawa yasan gida kika gudo?" Bai sani ba, tunaninshi wajen aiki naje" "To na dai san a lokacin da yace miki zai ƙara aure, kuma ya faɗa miki Asama'u zai Aura. Fatan alkhairi kawai kika yi mai ba tare da nuna karaya, ko mamakin lamarin ba, ina da yaƙini a kan ki" Ajjiyar zuchiya ta sauke. miƙewa nayi na karɓi masar na soma ci kenan Baba Sojanmu ya leƙo daga bakin ƙofa ya tsaya yake tambayar Innarmu abinda ke faruwa" "Naji gida ya ɗauka wai Hinduwa gidanta babu lafiya har makaranta sun tashi. Dama ihun da nake jiyowa nata ne? Mu mun ɗauka a wajene ai" "Ohh ni Ruwayya. Su dai dake fatan da suke yi ta samu matsalane a Aurenta sabida sun san dambarwar da akayi kafin auren. To iyakar shekarun da suka shuɗe baici ace sun haƙura da son ganin bayan Aurenta ba? Ciwonne kawai ya tashi babu komai a tsakaninta da mijinta." "Ke Hinduwa hakane? " Eh Baba Sojanmu babu komai. Dama tun ina hanyar zuwa nake jin wani iri" Kai ya gyaɗa yace. "To Allah ya ƙara sauƙi sai ku koma wajen mai maganinku ai" Eh mun koma ina kan shan magani kwana biyunnan abun na taɓani" Shiru yayi baice komai ba, sai can yace. "Allah ya kyauta ya bada lafiya. Ya batun Mastas ɗinki Hindu yafa kamata ki jona karatunnan yana da matuƙar amfani '. Ilimi jogone babba" Zan jona in sha Allah nayi maka alƙawari zaka yi farin ciki dani" Murmushi muka yi dani dashi ɗin Ya saki labule ya fita. "Kinga ni kuma kinji ko? Dama ai kinsan babu auren da idanun kowa yake kanshi irin wannan auren naki. Ki daure ki rufa mana asiri dan Allah" Innarmu sai duk ta tashi hankalinta. Shikenan Innarmu nayi haƙuri zan kuma koma zanyi duk abinda kika ce" "Yauwa Hinduwa nagode miki. Shi kuma mijinki a tsakaninku kinsan irin yadda zaki tafiyar dashi ke macece, duk macen data zama wulaƙantacciya ƙasƙantacciya ita taso, ba'ace ka wulaƙanta kanka ba, ke kika san logon mijinki. A baya Mahaifinku ya taɓa yi mun wani abu lokacin daya Auro Turai ranar girkina ya shigo yake roƙona in siyar mishi da kwanana. Hindu ranar itace rana mafi zafi da muni a gareni, kuma shine dare mafi tsayi. Banyi musu ba na siyar mishi, sabida in ban karɓi kuɗinba ma zai tafin sabida a lokacin Amaryace ludayinta shi ke kan dawo. Inma ya zauna a wajen nawa ni dashi ba zamu mori daren ba asarar daren za'ayi. Gashi ko da wasa bana son yasan menene logona. Kuma nasan dole ya sanar mata zai zo siyan kwana. Kema kinsan ina ji da kaina, na kuma san mutumci, da kimar kaina gaya. Hindu ranar na gane dare da tsayi yake. Turai ta gama kwanaki biyunta, ita kuma Abida ita ya dace ta je turaka, tako shirya tayi girki taje. Hmmmm in taƙaice miki saida na shekara uku cur ƙafafuna basu sake taka turakar Babanku ba na yafeshi gabaki ɗaya ya kaɗa ya raya naƙi fur wallahi, gashi a fuska babu canji, a girmamawa babu canji, a kwalliyata da abincina duk babu canji. Hindu da ƙyar da jiɓin goshi na haƙura muka shirya a hakanma saida ya bani miliyan guda yace in ƙara jari banda alkhairai da yake tayi mun. Kinga a cikin ruwan sanyi na dafashi ba hargowa ba fishi, daga ranar bai sake bari abu makamancin haka ya shiga tsakaninmu ba, fishi wannan baya so inyi gudun kar kwanana ya zagayo in ƙi zuwa turaka. Hindu in kin yadda kina da abinda ke gamsar da ƙishin ruwan Mijinyawa, kuma kin yadda ke macece cikakkiya wacce tasan kanta, in kin yadda kina da kima da daraja, kuma kinsan ƙwallonki tana shiga raga da kyau. To ki koma ɗakin ki kiyi yaƙin gidanki da kanki kamar yadda kika saba al'amuranki ba tare da sanin kowa ba. Na sanku bakwa bin bokaye dan ban ɗauraku a wannan gwadaben ba, nasan bakwa sharri shima. Amman ban yadda kuyi zaman boranci ba. Kin ganni ban taɓa zuwa kai ƙara gida ba, a dangi har misali akeyi dani. Kuma babu abinda ban ƙunsa ba da kike ganina saida na tashi tsaye na dena shakkar kowa na zama mafaɗaciya haiƙan kana na zama mai cikakken Ƴanci. Da ba haka nake ba a lokacin kuna yara baku san komai ba" Innarmu ta dinga wanke mini kaina da dabarbarunsu na manya na dinga tarawa da nawa dana sani da gogewar da nake dashi, tuni naji babu duk wani ƙunci a cikin raina illa iyaka na zafin Mijinyawa da bana jin akwai ranar da zan dena ji. Amman fa inanan kan bakata wallahi bazan zauna ba. Innarmu ta harhaɗomun magungunan gargajiya, itace harda bani kyautar atampa da mayafi duk dan ta sanyaya mun raina. Uwa kenan. Haka ta wuni tana lallaɓani. Allah sarki duk wanda ya rasa kafaɗar uwa dole a koka mishi, in banda uwa wa zaima wannan? Sai da yamma lis na bar gidan, dama bani da asament yau duk da ya kamata in kasance a wajen aiki bazan rasa abinda zanyi ba ko da editin zanyi. A hanya na tsaya na sai banƙararriyar kazar gidan gona, da masa, na biya shago na sai jus na cikin kwali na nufi gida. A tsakar gidan na tadda Mijinyawa a zaune a kujera yayi shiru yana kallon fulawowi yaga na shigo. Fitowa nayi da ledata duk maiƙo na nufoshi da fara'ata. Ranka shi daɗe ango hutawa akeyi ne? " Kallona yayi muka zuba ma junanmu idanu na ɗan lokaci. Shigowar Uwatale ne yasa duk muka juya sabida sunana data ambata. "Ashe kuma Mijinyawa ya kai sadakin Asama'u har an saka rana? Allah mai iko kenan, girman ɗan mutum babu wuya" Wallahi ai inata so ma inna dawo in shiga in faɗa muku to dawowar tawa kenan " Da fara'a a fuskata ta kalleni da kyau taga babu damuwa a tattare dani. Mijinyawa muje daga ciki na kwaso gajiya" Tsohuwar munafukar a wajen muka tafi muka barta sai daga baya ta biyo mu a baya a baya. Sabira ce kaɗai a falon tana zaune tana kallo. "Sabira ku shirya ke da wanki in anyi sallah zamu je cin abinci ko? " Cewar Mijinyawa. "To Abba dama mun riga mun shirya Ammi kawai muke jira ta dawo" Murmushi nayi ma yarinyar nace. Gashi Ammi babu inda zata iya zuwa aikin da suke kaina da yawa kwa tawo mun dashi. Bari in kwatsa ruwa" Na faɗa tare da shigewa ciki. Banɗaki nayi shigewata shi kuma ya zauna a kan gado. Harna fito yana zaune, da ɗan ƙaramin tawul a jikina nayi zamana a gaban madubi na dinga bin fatata da love neture na kamfanin Oriplem wanda nake siya a Hannun Mamanmu Hajara Aliyu da lotion ɗin da oil ɗin harma da sabulun wankansu na ruwa dashi nake amfani fatata kullum cikin sheƙi da laushi. ( ni kaina Mrs Bukhari shi nake shafawa kuma yana gyara fata sosai ga laushi ga sheƙi, ga ƙamshi mai daɗi da riƙe jiki) Yana zaune harna saka kaya riga da wando falazo na saka ƴan kanti na feshe kaina da humrar gashi na saka hula. "Tutar so wannan shirun yana dafani sosai" Juyowa nayi nace. Wanne shiru kenan, naga duk abinda kace saina baka amsa ko? " Sai ya zabura ya iso inda nake a tsaye ya mannani a bango tare da riƙe ƙunƙuruna. "Kiyi haƙuri wallahi nasan abinda akayi miki da zafi sosai. Amman Tutar so umarnin Nanno nabi dole inyi abinda take so in dai inason in rabauta. Ko ɗigon son yarinyar babu a raina, ni bansan ma ya wannan lamarin zai faru ba, bana ji a jikina Aurennan zai yiwu. Ni yarinyar ce ma nake jin kunyarta bansan ta yadda zan iya rayuwar Aure da'ita ba yarinyar da take kallona a matsayin uba" Ammm Mijinyawa naji zafi, zanji zafi duk bashi bane. Aurene dai babu fashi Allah ya sanya alkhairi bana son maganar ma aita nanatawa dan Allah" Ina kaiwa ƙarshe na cire mishi hannayenshi a ƙuguna na koma banɗaki nayi zamana akan sita har saida naji ficewarshi zuwa masallaci kana na fito na tada kabbara nayi sallah na jawo ledar kazata na baje na hau tutturawa ina korawa da jus nice harda saka film a labtop ɗina inayi ina kallo A haka ya shigo cikin shiri ya sameni. "Da gaske ba zaki zo muje ba? " Gaskiya na gaji kuma ina da abun yi" "To mun tafi me za'a tawo miki dashi? " Ni kam Alhamdulillahi nagode Allah ya tsare" Haka yayi ficewarshi. Daga wannan rana na sake canja takuna sosai anata tsogumi a danginsu Mijinyawa, da dangin iyayen ita Asama'unma. Ranar asabar saiga masu fenti sun wuce can cikin gidan ɓarayin dake kulle sun soma fenti haiƙan wuni suka yi suna abu ɗaya. Washegari sai ga mota tazo mijinyawa ya sameni a ɗaki yake sanar dani za'a kwashe komai na falona da cikin ɗakina zuwa gobe kuma za'ayi fenti jibi za'a kawo wasu sababbin kayan. To kawai nace mishi. Aka kwashe komai har maƙota sun shigo tsogumi a tunaninsu ko na tada fitinane aka sakeni shine ake kwashe kaya. Sai da suka shigo su munafukan gidan da duk suka fito tsakar gida shine suke shaida musu gyara za'ayi mun. Ni da yara gidan Yaya Saratu muka wuni sabida fentin da za'ayi. A nanne nake sanar mata abinda ke faruwa daga ni sai ita. Jin Asama'u za'a auromun ta hau zage_zage ni kuwa sai kallonta kawai nake yi. Ita ta kira dukka ƴan uwana take sanar musu halin da ake ciki. Nan fa duk suka ɗauka Yaya Zakiya ma garzayowa tayi tazo ta samemu sukaita zage zagensu ita da Yaya Saratu. "Shi yasa ni tun farko banso aka bata yarinyar ba, yarinya da uwarta a raye ace an wani kyautar da'ita dan kawai ubanta ya mutu. Babu mamaki dama sun daɗe da son haɗa auren fa ƙila ma tun tana tsumma aka bashi ita" Rayya tace. "Nifa in nice wallahi Allah sai dai mu rabu yaje ita ya aureta ko ya haƙura da'ita muci gaba da zama." Yaya Saratu tace. "A.a in tayi haka kuma dama haka danginshi suke son ayi fa. Saida ta gama wahalarshi tukunna zata rabu dashi? Ai a wannan gaɓar in tace sakin take so da yanzu ya tafa mata takaddarta. Gara tabi a hankali ta ƙwaci ƴancinta lokacin da zata ce ya zaɓa yana nan zuwa" Sukaita tattaunawa ni dai ina tsakiyarsu ina jinsu kawai sai wajen magriba na ɗauki yara muka tafi. A mota suka tutsiyeni da tambayar Aure wai Abbansu zaiyi. Na sanar dasu har kwanakin daya rage ranar auren amman ban iya sanar musu wacce za'a aura ba tukunna dai bansan bayanin da zanyi musu su gamsu ba. Munje gida ko ina yasha fenti mai tsada da kyau, har fentina yafi na wancan ɓarayin na Amarya kyau da tsada. A katifu muka kwana washegari litinin sassafe Mijinyawa ya fita. A gurguje na fito nima dan yau ƙauye zan shiga ɗakko rahoto ma, gashi saina je office tukunna. A bakin titi naga mijinyawa na taran abun hawa yana ganina na miƙe abuna wallahi kallo bai isheni ba, motata ce dai ya bar hawa. Dana je office ogana yake sanar dani tafiyata ranar Juma'a wanda yayi daidai da ranar da mijinyawa zai angwance da amaryarshi. Muna zaune ni da Luba nake shaida mata auren da Mijinyawa zaiyi da wacce zai aura ɗin. Luba harda kukanta ni dariya ma ta bani. Haba Luba menene na kuka Aure fa nace miki za'ayi ba wa jo ko ba" "Hindu mazan wannan ƙarnin haka suka lalace wai. Yanzu duk irin wahalar da kika sha da Asama'u itace zata zama kishiyarki daga ƙarshe ki shiga turaka ta shiga itama wannan turakar? Allah ya kiyaye wuce nan nu Hindu, ta shiga turaka dai. Ai ko yanzu bana tarayya dashi balle in sun yi aure. Luba kenan kin mance wace Hindu ne ma. Ai ni da turaka har abada" Murmushin takaici tayi tace. "To aure yana yiwu ne babu tarayya Hindu ballan tana nasan ke mabuƙaciyace sosai? " Luba in kika ji ana ƙi gudu sa gudune baizo ba buƙatuwar abu ta kazan... Kinsan inna juya ma abu baya har abada bana waiwaye Luba. Ai aurenmu ba na zobe bane duk ranar daya gaji zai sakeni. In kuma bai gaji ba saimu dauwama a haka. Ba zan kashe kaina akan ɗa namijin da baisan darajata ba." "To Hindu gida ɗaya zaku zauna? Dariya nayi mata. A. a ba zamu taɓa zama inuwa ɗaya da Asama'u ba Luba har shi mijinyawan ma." "Ƴan hayar gidanki zaki tasa ki koma ciki kenan Hindu? " Ashe kin gane Luba. Ke zan ɗaura akan aikin gyaran gidan sabida ni ranar da za'a ɗaura Auren ranar jirgina zai tashi zuwa landan. Kafin in dawo an gama komai an zuba mun komai sai tarewa a ciki kawai" Shiru tayi tace. "Yanzu da ace nayi dubara irin taki wallahi nima da babu abinda zaisa in tare a gidan Sunusi. Ke Hindu ina kwasar baƙin ciki" Luba ke kika so ki kwashi baƙin ciki. Kinga gidannan dana siya ban siya da tunanin zan zauna a ciki ba, wannan dalilin yasa ban sanarma kowa ba face ke, na siyane sabida su Baba sojanmu. Nasan ko mu jima ko mu daɗe akwai ranar da dole sai gidanmu ya tarwatse kowa ya kama gabanshi, sabida gidan na Baba Nagoɗi ne kinga daga ranar da Allah yayi mishi cikawa zaman gidan gandu ya ƙare. Yayuna maza sojojine rayuwarsu da iyalansu a bariki suke yinta albashin nasu sai godiyar Allah. Kinji da tunanin da na sai gidannan domin iyayena su amfana da dukiyata ba iyakar miji da yarana ba. To kema da kin yi wannan tunanin da yanzu kin huta. Amman bata ɓaci ba, ga gidaje ana ginasu madaidaita wanda zaki bada kaso mai tsoka daga farko duk wata zaki dinga biya a hankali har ki gama. Kuma in kika bayar dana farkonnan zaki iya shiga gidanki takaddune ba za'a baki ba har sai kin gama biya. Inmaa na fili kike so duk anayi. Ki tuntuɓi oga Rashid kiji." Luba taji daɗi shawarata kuma ta yaba. Ina hanyar zuwa ɗakko rahoto mijinyawa ya kirani yana shaidamun ƙarfe huɗu za'a kawo kaya zuwa lokacin na dawo. Eh kawai nace mishi na datse wayata. Su Yaya Saratu na faɗama munyi dasu zamu haɗu a gidan. Ƙarfe uku da ashirin na shiga gidan na tadda basu isoba. Ina shiga suna isowa Sai santin fenti suke yi duk da dai jukkunansu a mace yake sosai. "Labarin aure ya baza gida sai gulme_gulme in faɗa miki akeyi daga gidan muke ma yanzu haka anata yagalgala zancan an samu nayi" Zasu yi su gama wuyarta a ɗaura amarya ta tare." Huɗu da kwata motar kaya ta shigo har harabar gidanmu akaita shiga da kaya su Yaya Saratu na jerasu. Dan kyau kaya sun yi kyau amman ni a wajena asarar kuɗine kawai. A tsanake nake ta tarkace suturuna ni da Luba muna kaiwa gidana muna adanawa na riga na tashi ƴan hayan gidan babu kowa. Ana saura sati guda biki sai ga su Yaya Jamila daga jama'are sun kawo kayan faɗar kishiya dama ya sanarmun zasu zo zasu kawo kaya, saina sanarma su Yaya Zakiya suka tawo. Ni sanda suka zo ma ina hanyar dawowa daga ɗakko rahoto a gidan gwamnati. Na shigo na samu an bubbuɗe akwatuna har biyu da jakarshi. Dangin miji sai kallona suke yi, sun yi mamakin ganina gadagau ba rama ba damuwa sai fara'a ma tare da yi musu sannu da zuwa nice harda godiyata" Washegari suka kama hanya suka koma. Nayi ma Mijinyawa godiyar kayan dannar ƙirji sosai. Ya ɗakko dubu ɗari biyu da hamsin ya bani wai kuɗin ɗinki. Ya waro wasu daban wai na cefane in inaso zanyi tarone. Sabuwar kunyata yake ji sosai baya yadda mu haɗa idanu sam. Abokanshi sai zuwa suke suna mun nasiha da godiya ina ta binsu. Ana jibi ɗaurin aurene nake sanar mishi ina da semina da Bbc a Abuja gobe ya kamata in wuce. Kallona yayi yace. "Amman kinsan jibi gidannan a cike yake ko, ya kuma za'azo ke bakya nan Tutar so? Kiyi haƙuri da Semina ɗin dan Allah. Ki daure a samu a tarbi baƙi bana son ƙananun maganganun su Yaya Jamila". Murmushi kawai nayi mishi nayi shigewata ciki. Naci gaba da haɗa kayana a tunaninshi na haƙura ne sabida baiji nayi gaddama ba, saida na haɗa komai na fito na shiga ɗakin Azgar na sameshi nace ya kirawo mun Sabira, yaje ya kirawota suka zo muka zauna ina kallonsu. Gobe zanyi tafiya zuwa Abuja jibi zamu wuce landan na samu kwantiragi da Bbc Landan zanje inyi shekara biyu in dawo, zanyi amfani da damar zanyi mastas ɗina acan in sha Allah. Amman bana so ko da wasa ku faɗama Abbanku har saina tafi. Sannan inaso in sanar muku wacece Abbanku zai Aura Asama'u ce ta gidannan " Da sauri Azgar ya ɗago muka haɗa idanu idanunshi naga sunyi jawur dasu, Sabira kuwa jikina ta faɗo ta sau kuka. Shima Azhar hawaye yake yi ni kuma ina kukan zuchi. Kuyi haƙuri ai ba haramci bane akwai aure a tsakaninsune. Sannan na horeku da kada ko a labari inji kunyi mata rashin kunya ko wani abun. Ranar da aka gama biki ku tarkata ku koma gidanmu har saina dawo. Kuyi haƙuri kamar yadda nayi. Kai gobe zaku wuce Jama'are ko? " Kai ya ɗaga mun kawai, ya kasa magana amman fa naga jikinshi yana wani irin ɓari gaskiya. To shikenan ke Sabira gobe zan kaiki gida shima in sun dawo jibi sai ya tawo ya sameki. Ku mayar da hankalinku akan karatunku, dana isa na samu nutsuwa zan kiraku" Hannuna Azgar ya riƙe yace. "Ammi amman ba shirin barinmu kike yi baki ɗaya ba ko? . Ammi bazan zauna ba ni dai, ba kuma zani bikin ba gaskiya. Asama'u fa ƙanwata, Asama'u fa Yayar Sabira wacce kika raineta, yarinyar da nake kama hannunta muje miki aika itace za'a kawo miki" Ai sai ya fashe da kuka mai gunji tamkar ba namiji ba har yana dafe ƙirjinshi. Wannan maganar tashi ta matuƙar raunata mun zuchiyata ainun sakamakon wani birnannen mikin daya fama kanshi a zuchiyata. Mrs Bukhari. Masu neman lambar wayata gatanan 08179523215 WhatsApp kaɗai nake yi da'itaTSURON TSIRIN... TSANDAURI LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA BAKWAI *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. Ai ban isa ba Azgar. Ko Aure kayi ba zamu rabu ba, Sabira ce kaɗai zata tafi gidan nata mijin bani da yadda zanyi. Kuyi haƙuri ku kula da kanku a kula da karatu duk ranar lahadi ka kamo ƙanwarka kuzo ku duba Abbanku ku wuni tare dashi. Kuyi haƙuri da ƙaddarar Auren Asama'u mahaifinku ya duba maraicintane shi yasa yayi hakan." "Ammi me yasa bai haɗani da'itaba in dai maraicinta yake dubawa. Ammi ko kina ganin bani da nagartane? Nasan kun bamu tartibiyar tarbiya kamila. Kuma kin kula damu da duk wuyar aikinki baki taɓa yin ƴar aiki da zaki sakar mata yaranki ba. Ammi wannan aure.... " Ya'isa Azgar kaji maganata sami'ina wa ɗa'ana. Na baku tarbiyya Allah yana kallo, bansani shi zai ƙyara kusakuraina in ina dashi. Kabi mahaifinka ayi ɗaurin aure tare da kai kaine babba a gidannan. Ka koya ma kanka dakiya wannan laushin zuchiyar naka yayi yawa Azgar ɗina. Sabira a maida hankali akan karatu ki kula da kanki, kiji tsoron Allah ba tsorona ba, kiyi domin Allah na ganinki ba dan ni nake ganinki ba. Ki ƙiyi domin Allah ba dan kar inji in hukuntaki ba. Allah yai muku albarka ya ɗaga darajarku" Mun jima sosai kafin nayi musu sallama na fita. Maganar Azgar ta tsayamun a maƙoshina sosai ita naita jujjuyawa ina kwance babu irin tunanin da bana yi a haka har bacci ya sureni. Wajajen takwas na safe Mijinyawa ya shigo da shirinshi na tafiya jama'are mu haɗa idanu ya kasa kanshi a gefe yace. "Zamu wuce kiyi mana fatan alkhairi Tutar so sai mun dawo. Kuma ina mai jaddada baki haƙuri a bisa wannan auren wallahi babu son raina. Kuma babu wata mace da zata iya gogaiya da matsayinki babu ita Hindu" Murmusawa nayi nace. Allah ya tsare Allah yasa a ɗaura a sa'a ya bata ikon yi maka biyayya, taita haifo maka yara su cika gidannan fam" Kasa cewa ameen yayi ya saki labulen a sanyaye ya juya. Azgar ne ya shigo muna haɗa idanu ya fashe da kuka. Kai dai baka da jarumta a haka Akarami yake ta son ya sakaka a soja. Banda kuka shekara biyu ai kamar yaune shalelen Amminshi" Hannayena ya riƙe gam yaita mun adda'a kafin ya sake ni ya juya. Azgar" Na kirayi sunanshi ya juyo. Ka kula da ƙanwarka ka kula da kanka sosai " "In sha Allah. Ina roƙon Allah ya amintar dake" Ya saka kai ya fice. Duk gidan aka watse baƙaƙen munafukai sai leƙowa sallama suke mun. Sun tafi kamar da minti talatin na fito da akwatina na rufe gidana Sabira ta wuce kici _kici da kayayyakinsu duk ta saka a bayan mota. Na fito mai gadi ya wangale mana get muka fice. Wata iska na shaƙa mai sanyi har saida na lumshe idanuna. Muna tafe ina ma Sabira nasiha akan ta kula da kanta sosai har muka isa gidan. Haka mukaita gaishe_gaishe sai mamakin ganina suke yi a gidan Inna Mairamu data kasa haƙuri saida ta biyoni ina zauna a falo gaban Baba sojanmu tace. "Hindu mu da muke shirin tahowa gidanki biki kuma sai na ganku kun tawo ina Azgar mai gidan da babu cefane? " Ai ba a gidan za'ayi bikin ba suna can hanyar Jama'are acan za'ayi bikin amarya kawai za'a kawo" Cike da dariyar gulma ta fice a falon, muka gaisa da Baba Sojanmu da Innarmu dake gefe Sabira kuma ta shiga shigar musu da kayansu ciki. "Lafiya waɗannan kayan kuma fa na menene? " Kaina na ɗago na dubi Baba Sojanmu nace. Tafiyace ta kamani zuwa landan zanyi aiki da Bbc na shekaru biyu jibi jirginmu zai tashi yanzu dai Abuja zamu wuce" Ai sai Innarmu ta washe baki tare da yin hamdala" "Landan fa kika ce Hinduwa? " Jin haka yasa Inna Abida ta fito. "Naji ana kiran Landan?" Saina labarta mata haɓa ta kama tace. "Landan har shekara biyu to shikenan ita Amarya zaki barma mijin har shekara biyu? " Murmushi kawai nayi bance komai ba. Baba sojanmu yasa albarka sosai yayi adda'a. "Gobe asussubar fari zamu wuce can jama'aren. Akwai abokina acan landan ɗin tare muka yi aikin soja zan baki lambarshi tacan in kika je ki neme shi zai taimaka miki ki samu gurbin karatun mastas a can jami'ar landan ɗin duk taimakon da kike buƙata sai ki yi mun waya Allah yayi albarka. Ko babu shirin yin mastas a tsare_tsarenki? Kinsan bazan barki kije Landan ba tare da kin ƙaro karatuba. In ful time zaki yi ma shekara ɗaya ya isheki kin gama wata sha biyu ba. In kuma fat time ne shekara biyunne karatunsu akwai sauƙi. Lallai ki riƙe mutumcinki da kimarki. Kinga jajircewa da ƙwarewa inda ta kai ki ko, sai ki sake saka idanu da kyau ki fahimci irin aikin nasu na Bbc Allah yayi albarka. Godiya nayi sosai ya rubutamun lambar abokin nashi Innarmu ta rakani lungu_lungu nayi sallama da matan gida. Gida duk ya ɗauka zanje Landan abinda ba'a taɓa yiba a famili yau gashi a kaina ya faru. Kin motata na damƙama Innarmu nace taba Azgar zai dinga zuwa makaranta da'ita sannan zai dinga kai Sabira makaranta. Ɗan sahu na hau zuwa gidan rediyonmu har muka iso. Mota manajanmu ya bayar aka kaini Airport. Bayan ya sake ƙarfafamun guiwata tare da yi mun fatan alkhairi, da shawarwari masu yawa. Acan na haɗu da Shamsiyya ita ma'aikaciyar wani gidan rediyonce a Kano mun san juna tun muna jama'a a lokacin da muke karatun jarida, kana muna haɗuwa sosai musamman dana soma fita ɗakko rahoto. Itama ashe Bbc ce ta nemi zata yi aiki da'ita kamar dai ni, sai muka ji daɗin haɗuwa da juna. Cikin awa guda jirginmu ya sauka a Abuja Bbc ita ta bamu Hotel tsadadde a Abuja. Ina kwance a ɗakin hotel ɗinnan rayuwata tana ta dawomun da irin dukan da mijinyawa yayi ma rayuwata. Yarana na tuno sai idanuna suka lumshe Da tunane_tunane mai yawa bacci ya ɗaukeni nayi bacci sosai har sai magriba na farka a gurguje na yi wanka nazo nayi sallar la'asar nayi isha. Shamsiyyace tazo ta buga mun ƙofa na buɗe mata ta shigo. Munyi hira tare kuma muka ci abinci wannan hirar ta aiki da irin gwagwarmayar da masu ɗakko rahoto mune har ƙarfe goman dare kafin tayi mun sallama ta koma ɗakinta. Naji daɗin haɗuwar tafiyar tare da Shamsiyya itama ganina yasa ta saki jikinta harma take jin itama zata yi amfani da damarta wajen ƙarin karatu. Washegari sai kusan azahar mota ta zo suka ɗaukemu. Ina jinjinama Bbc yadda a kullum suke tallafama tafiyar aikin jarida. Gidan Rediyo ɗaya tamkar da dubu kenan gidan Rediyon daya kasance alfaharin mutan arewa dama duniya baki ɗaya gidan Rediyon da baya yaɗa farfaganda kenan, gidan Rediyon da duk wani ma'aikacin tv ko rediyo ko jarida ke da burin aiki dasu ko da kuwa na kwana guda ne. Gidan Rediyon da ma'aikatanta suka kasance ababen marmarin son ji dama gani. Ƙarfe uku dot jirginmu ya ɗaga izuwa ƙasar Ingila. Muna zaune a filij jirgi ɗakin jira daidai misalin ƙarfe ɗaya daidai na buɗe wayata na shiga manhajar whaTApp dina nayi ƙaramin rubutu cikin ƙwarewa irin ta ɗan jarida mai iya sarrafa harshe. Ga abinda nace. Wannan itace rana mafi daɗi a cikin rayuwarka samun mace mai ƙarancin shekaru mai ɗanyen jini, mai tsayayyun cikakkun mamuna ba irin na Hindu Duwaf da suka zube babu tuwo a ciki ba, nasarace a gareka. Sai dai kashh kun riga kun kassara zumuɗin wannan ranar ta hanyar lashe zumar juna a hotels, turakarka, a waya tare da sanin sirrin duk saƙo da lungu na Kutumbun juna. Tshohuwar mai tumbin matarka gajera tana muku fatan samun Zuriya ɗayyiba. Hindu ce" Na tura mishi, sai na haɗa da dukkannin chart ɗinsu, hotuna da bidiyonsu da murya da suke turama juna, da komai da komai ma. Daga ƙarshe na rubuta. Ga gudunmawar Aure daga Hindu Tsohuwa, mai yamusassun mama, , mai tumbi, kuma Duwaf. Ɗif na kuma datse wayata dana tabbatar saƙwannin duk sun shiga. Na jefa a jakata sai nake jin wani irin salama na gaskiya tamkar mutumin daka tsaya kareshi a gaban alƙali kuma kuka zo da hujjoji ƙwarara haka nake jin kaina. Awanni goma cib ne ya kaimu muka sauka a birnin Landan. (Anan nake son yin ɗan tsokacina. Mata mu riƙe sana'a, mu riƙe ilimi da aiki. In baki da ilimin da zaki iya aiki, ki nemi sana'a duk ƙanƙantarta ya zama kina juya kuɗi ko da ribar babu yawa kada mu raina. In muka bi a hankali muka tattala uwar kuɗin da ribar gaba sana'ar zata haɓaka ta girma, kowa da kaɗan ya fara, kowa kaga ya zamo gwani yabi hanyar koyo, kuma in kaga wane ba banza ba. Mu dake haiƙan mu yi sana'a mu riƙe mutumcinmu, mu kula da dukiyarmu, mu ji tsoron Allah a duk abinda muka saka gaba. In sana'arki wacce ke kika haɗawane da kanki, misali cincin, kunun zaƙi, soyayyar Aya, wara, dambu..... Ki tsayar da gaskiya kiyi domin Allah banda ƙazanta banda amfani da gurɓataccen ruwa, ayi mu'amala da masu siya mu'amala hasana. Riƙe mutumci yana da mahimmanci. In kuma aiki kike fita ki sani ke matar aurece, aikine ya fitar dake kije aikinki, ki dawo lami lafiya ba ruwanki da kule_kule maza abokan aiki a riƙe kai, a riƙe mutumcin Aure ayi shiga ta islama, a nuna tarbiyyar islama, a ɗaga darajar tartibiyar tarbiyyar da iyaye suka bamu. Waɗanda suke da damar komawa makaranta in mazajenku sun amince ku koma makaranta. Mata ku tashi mu koma islamiyya wallahil azeem dolenmu ne muyi ilimi ko dan rayuwarmu, da gyara ibadarmu, da gyara alaƙarmu da Allah mu sani ilimi musamman na addini wajibine, mu tashi mu koma makaranta kada jahilci ya cimu da yaƙi. Macen da take da ilimi tasan inda addini ya martabata, ya gatantata, ya ɗaga kimarta da darajarta, tasan abinda yake na hakkinta, tasan wanda yake bana hakkinta ba. Magana wannan tasan me zata furta, tunaninta zai kasance mai kyau. Abu ukunnan yana gyara rayuwar ɗiya mace yana cire mata damuwa gaya. 1 aiki 2 ilimi 2 hanyar shige da ficen kuɗi, juya taro ta dawo sisi, wato sana'a. Mu ƙara da haƙuri sai an nace ake dacewa in Ubangiji ya kama mana) MIJINYAWA. Jama'are cikin unguwar Dako_Dako cikin Gidan Malam Ibrahim Ɗan Safiyo Ranar ɗaurin Aure. Mijinyawa yana kwance a ɓarayinsu dake cikin gidan nasu ga jeren Hindu tunna Aurensu sanda take Amarya. komai yananan fes dake kafin su iso an share komai an goge komai. Wayar Hindu ya sake bugawa a kashe tun jiya yake ƙoƙarin samunta a waya abun ya faskara ya kuma ci tura. Sai yaji duk komai ya fice mishi a kanshi yana jinshi wani iri kamar a ɗaga Auren yake ji. Tun ranar daya sanar ma Hindu batun biki yake jinshi a cikin yanayi na wasi_wasin Auren sosai Abokan wajen aikinsu ke sake ƙarfafa mishi yuiwa, suna karanto mishi falalar dake cikin Auren yarinya mai ɗanye jini. Tsaki yayi ya kalli babbar rigarshi dake kan kujera wacce ta sha aiki, da ita zai yi amfani wajen ɗaurin Auren. Sai yayi shiru yanata aikin nazarin abinda bashi da wani amfani domin kusan lokaci ai ya ƙure. Yana ta jiyo hayaniyar mata da yadda aketa aikin tuwon ɗaurin Aure. Yaya Jamila da su Yaya Tabawa ne suka yo ayari kusan su biyar duk ƴan ɗakinsune cikin Nannonshi. "Mijinyawa ƙarami kana ciki ashe Hamusu yazo akace mishi baka nan, nifa na ɗauka kana wajen abokinka Ƙasimu ashe kana nan? " Cewar Yaya Jamila kenan. "Ina ciki dake jiya ban samu ishasshen bacci ba shine da safe nayi banma jima da tashi ba. Yaya akayi ne Yaya Jamila? " "To menene ma ba'ayi ba Mijinyawa kayayyakin akwatinnan gaskiya sai yanzu dasu Inna Larai suka isone shine ake ganin kamar yayi kaɗan babu manya_manyan atampopi masu yawa a ciki. Takalma da jakunkunan ma basu da tsada can can ɗinnan kuɗi zaka kawo a yi maza aje kasuwa a ƙaro kafin isowar dangin uwa da uban yarinyar. Kaga kai ka riƙeta zasu iya tsammatan abinda yafi haka daga gareta. Tunda a Aurenka na fari da waccan gajeruwar matar taka bajintar da akayi bata wasa bace duk da su kushewa ma sukaita yi. Ko ba haka ba Tabawa? " "Sosai kuwa mayafai ma sunyi ƙaranci a hakanma Inna Zakiya ta kawo biyu an ƙara. Kaga matarka suturu kake siya mata manya sosai gata da sarƙar gwal damfareriya itama tun wuri ai ya kamata ace an sai mata ko ƙaramace gaskiya da bata wuce dubu ɗari shida ba sabida yanzu inta shiga ba lallai bane fa ta samu ba. Dan wallahi yadda idanun Hindu suke a tsaye ya maman maza ba yadda zata yi a siya ba" "To yanzu dai nawa kuke buƙata in sallameku in samu in bar gidannan in kuna ganina ba zaku dena tatsata ba" "Ai gara mu tatseka wa yasan nawa Hindu ta tatseka tunda taƙi nuna Auren na gabanta ma. Milliyan ɗaya zaka bamu har da kuɗin sarƙar gwal ɗin sai mu shiga Bauchi a gurguje a siyo abinda ya dace kafin ɗaurin Auren mun dawo Ajjiyar zuchiya ya sauke ya lura su Yaya Jamila wani hanyar cin kuɗi suka samu tun jiya ake sakashi ture_ turen kuɗi in ya nuna babu a soko maganar Hindun da kafin yayi mata hidima tayi mai sau goma sha biyar. Kafin ya sai mata sutura ta saima kanta sau ashirin koma fi. "To shikenan zan tura ta asusun bankin ki ni zan shiga wanka" Basu bar ɗakin ba saida ya tura musu. Yana cikin banɗaki yana wanka kanshi ya ɗauki ɗumi sai yake ta jin ƙaran wayarshi harya fito wayar na kiɗa Asama'u ke kiranshi. Zama yayi tare da ɗaukar wayar ya kara a kunnenshi. "Ranki shi daɗe yaya akayi ne? " "Lafiya lau Angon Asama'u yau dai alƙawari zai ciki ko? " Murmushi yayi mata kawai baice komai ba. "Dama kuɗin dinki zaka tura mun zamu je mu karɓo kafin ƙofar gidan ya soma cika da dandazon ƴan ɗaurin Aure. Dubu sittinne" "To shikenan zan tura miki yanzu ranki shi daɗe sweet L" Da haka sukai sallama ko daya duba account ɗinshi dubu ɗari bakwai gareshi kacal, banda dai asusun da yake tari a ciki, su kuma waɗannan kuɗaɗe na cizo ne ajiya yake yi. Dubu saba'in ya tura mata ya shafa mai ya kintsa cikin farar shadda ɗinkin malum_malum yana fesa turare abokanshi na wajen aiki suka kirashi gasu sun iso jama'are. Ai babu shiri ya fito dan zuwa ɗakkosu nan filin gidan yawan ya karaɗe da guda tare da faɗin "Ango kasha ƙamshi. Shi dai yana yaƙe ya fita kin motar Mijinyawa Babba na hannunshi kawai sai suka je suka tattago baƙi mota guda shi da Ƙasimu. A gidansu Ƙasimun aka saukesu anata hada_hadar ɗaurin aure Abokanshi na ƙuruciya duk suma sun taru anata hira ana dariya da yawansu ma ba'a jama'aren suke da iyalansu ba nema yasa duk sun warwatse sai dai sukan shigo bikin Aure ko bukukuwan sallah haka. Ƙarfe ɗaya daidai ƙofar gidan malam Ibrahim Ɗan Safiyo cike dam da Al'umma su Baba Soja dasu Akarami sune a gaba_gaba aka ɗaura Auren Gawata da Amaryarshi Asama'u a bisa sadaki nera dubu Ɗari biyu ha da hamsin. Ta faru ta ƙare wai anyi ma mai zane ɗaya sata. Nan mijinyawa ya soma gaishe_gaishe da jama'a anata yi mishi Allah ya sanya alkhairi yana amsawa tare da dariyar jin daɗi. Baba Soja da Akarami daya gani yaji daɗi sosai kuma yasa an karramasu an saka musu abinci a mota dan sunce juyawa zasu yi, ai kuwa Azgar ya sulale yabi su Baba Soja suka juya zasu je su kwana a Bauchi washegari su wuce Kano. Da ango da abokanshi kuma suka ɗunguma zuwa cikin gidansu Ƙasimu dan anan akaba matar Qasimu kwangilar yi musu girkin biki. Yana duba saƙon Asama'u sai yaga saƙwannin Hindu sunata shigowa ai babu shiri ya fita daga son bama Asam'u amsa ya duba yaga Hindu tayi mishi saƙo fin ɗari nawa. Sai yaji jikinshi ya mutu mus jikinshi ya zare ya nufo gida ya kusa kai ya shiga ɓarayinsu ya kulle ƙofa ya zauna a kan kujera. "To me Hindu take cewa har ɗaruruwa haka, ko dai ta zazzagar mun abinda ke ranta ne? To bari dai in cire fargaba in duba. Buɗe saƙon yayi ya soma da taya shi murna da tayi sai yaga saƙwanninshi shi da Asama'une da duk abinda sukaita cewa da duk bidiyo da hotunan tsaraicin juna da sukaita turama juna. Miƙewa yayi tsaye tare da kama haɓarshi yayi shiru yanata nazari mai zurfi da tsayi. Malum_malum ɗin jikinshi da hula da agogon hannunshi ya cire duk yayi fatali dasu a tsakar ɗakin. Hannayenshi ya goya a bayanshi wayar na riƙe a hannunshi. Haƙiƙa yaji kunya, nadama, damuwa irin wanda bai taɓa shiga ba a rayuwarshi ba. Baya ji ko kusa in zai iya haɗa idanu da Hindu. Kuma duk da yasan son da Hindu take yi mishi ba ɗan ƙarami bane amman ya gasgata tabbas macece mai kawaici da danne damuwa da baƙin ciki. Saiya soma tuno wannan zaburar da tayi a ranar daya shigo da Asama'u turakarshi a karon farko ya tumurmusata akan gado. Kenan ta gansune shi yasa daga ranar bata kuma shiga turakarshi ba kana bata sake bari mu'amalar aure ta kuma shiga tsakaninsu ba? Yanzune ya shiga nazari akan sauye_sauye masu nauyi da girma da yake fuskanta daga wajen Hindu. Tana da dukka wannan hotunan da bidiyon baiwar Allah amman take iya bacci taje aiki harma tayi ma Mijinyawa murmushi yayi magana ta bashi amsa? Wayar ya jefar akan gado ya ɗaura hannayenshi a ka yana jin jiri na neman kwashe ƙafafunshi ya nanashi da ƙasa. Yanzu yaya zaiyi ya gyara tunda shine ya ɓata? Yasan Hindu da riƙo da taurin kai, gata da ra'ayin riƙau yanzu ta wacce hanya zai gyara komai ya zaiyi Hindu ta mance da duk abinda taji ko ta gani? Wata zuchiyar tace. "Ai har abada bazata mance ba. Kuma har abada ka rasa yadda da zallan tausayi a wajen Hindu. Kuma har abada mutuncinka bazai dawo ba" Ai sai yaji jiri ya jefashi kan kujera ba tare daya shiryama hakan ba. Shiru yayi a kujerar yana tunanin to tun farko shi kuwa meye abinda ma ya ruɗu dashi a jikin Asama'une tunda yasan babu abinda ta isa ta nuna ma Hindu sai ƙuruciya kaɗai. Mema yasa harya biye mata a matsayinshi na uba suka shiga aikin ashsha, ya Auri ɗiyar da matarshi ta riƙe ta raina taci wahalarta. Shi kuwa ya dace ace ya aureta ko da tafi kowa kyau a duniya? Sai yanzune fa duk yake waɗannan tunanin a lokacin da tunanin bashi da amfani sam, a lokacin da komai ya damalmale ya rugusa farin cikin da suka shekara sama da ashirin suna ginawa. Wannan na daga cikin illolin da muke samu. Yana da kyau kafin kayi komai a rayuwa ka duba abinda zaije ya dawo ba masalahar kanka itace kaɗai abar girmamawa ba, masalahar iyalinka shima abun dubawane. "Yanzu da gaske duk ni na aikata wannan charts ɗin da Ɗiyata wacce bata da bambanci dasu Azgar a wajena, ni nake buɗe tsaraicina nake nuna mata, itama ta buɗe nata ta nuna mun, in kaita hotel in sha komai na jikinta? Ya subhanallahi ya subhanallahi Allah na tuba ka yafe mini Allah ka yafe mini. Aminina ka yafe mini na lalata maka yarinya. Wanda nayi imani in kaine yarana suke hannunka ba zaka aikata wannan aikin ba. Hindu ki yafe mun ki gafarta mun Hindu" Lokaci guda Mijinyawa ya zama majinuni na dole inya tashi saiya zauna. A yaune ya gane irin illata rayuwarshi da yayi da irin abinda yayi ma haularshi. Ba Hindu ba har su Azgar sai yana jin baisan da wanne idanu zai kallesu ba na Auren Asama'u da yayi duk da ba haramci ya aikata ba, amman a babi na mutuntaka da dattijantaka Azgar ya kamata a haɗa Aure da Asama'u ba wai shi ya Aureta ba, bama auren ne babbar damuwar ba irin biye matan da yayi, shaiɗan ya shagaltar dashi ya biyema kaidin mace yaita aikata abinda bai taɓa aikatawa a rayuwar ƙuruciyarshi ba sai yanzu da girmanshi. Damma Allah yasa duk yadda take mishi magiya da yadda take nuna buƙatuwarta gareshi baisa ya taɓa gigin kwanciya da'itaba sai dai yayi mata wasanni harta samu nutsuwa. Dana sanine ya shigeshi na ɗakko riƙon Asama'u ma tun farko Allah ya sani daya san bala'in da zai faɗa kenan da ya barma mahaifiyarta riƙonta ya ɗauki nauyin komansu kawai. Saiya tuno sanda ita kanta mahaifiyar Asama'un data matsa akan ya Aureta ya kare mutuncin iyalin marigayi Amininshi. A lokacin ya nuna ma Hindu har taita mamaki ƙarfin halinta dan wannan shi yai sanadiyyar rugujewar zumuncinsu ma, tayi naci sosai har Allah ya ɓullo mata da miji da dai taga mijinyawa yaƙi karɓarta saita haƙura tayi aurenta tana gidan wani tanata hayayyafa abunta. Yau gashi ya lalata Asama'u ya kuma yi Auren cin Amanar Hindu, yanzune ya samu zarafin yin nazari harya gane girman cin Amanar da yayi ma Hindu, damma tana da dagiya da ƙi faɗi yasan da tuni zuchiyarta ta buga. Shi a halin yanzu tsoronshi Allah, tsoronshi rabuwa da Hindu bazaima iyaba sam. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da yake ji anata ta faman yi Qasimu bai jira an bashi izini ba ya kutsa kanshi, sai dai a irin yanayin daya riske Aminin nashi tabbas yasan akwai matsala. Kafaɗarshi ya dafa suka ƙurama junansu idanu. "Nasan dole za'a samu matsala Gawata. Bari kaji tunda dai Nanno ta shiga rabon alawa da goro na gayyatar biki Baraka matata babu irin kukan da bata yi ba. Gawata har zaginka Baraka saida tayi burki na taka mata, ta haukace kamar dai ita za'aima kishiya. Bafa auren bane matsalaba, ba kuma ca akwai kar kayi auren ba. Amman ka rasa wacce zaka Aura sai ɗiyarmu yarinyar da a babi na dattijantaka ko kai da'ita kuka rage saidai ku kalli juna kamar yadda zaka yi in ku biyu kuka rage a duniya kaida Sabira. Hindu mutum ce da rabin mutum jibi rayuwar da kuka gudanar a ƙauyannan shekara sama da ashirin baya jama'are ta jiya bata yau ba fa data samu ci gaba sosai. A rasa dame za'a saka mata sai auren yarinyar da mamane kaɗai bata bata ba. Ba'a duba ma Hindu ba sam, baka duba ba Gawata" Idanu mijinyawa ya lumshe kanshi na wani irin tururi. "Qasimu nayi wauta na tabka babban kuskuren da ba lallai in wanku a idanun Hindu ba abadan. Kai abokinane ko mutum na kashe zan faɗama nasan zaka taya ni birneshi. Qasimu kafin in Auri Asama'u saida muka gama lalube junanmu zinace kaɗai bamu aikata ba. Ashe Hindu tasan komai bayan ɗaurin aure duk ta turo mun komai a wayata" Shirune ya biyo baya na lokaci mai tsayi. Da ƙyar Qasimu ya ja hannun Mijinyawa suka zauna a saman kujera duk sukai tagumi, sai can yace. "Gawata ka kwafsa ma Hindu ka ɓarar da kimarka, mutumcinka abadan. Lallai baka da abinda zaka iya wanke kanka ko sakin Asama'u kayi, kayi a banza wai man kare. Me ya shigeka Gawata tunda nasan soyayyar shan minti ba naka bane ba halinka bane wannan zan iya shaidarka a ko'ina to ya akayi ita Hindu ta mallaki komai? " "Wallahi ban sani ba Qasimu. Nifa yanzu komai ya fice mun akaina bazan iya zaman aure da Asama'u ba, illahirin kunya nake ji. Asama'u ita ta ribaceni ta ja hannuna zuwa wannan. Qasimu daba dan na kai zuchiyata nesa ba da yarinyarnan tasa na aikata zina da'ita" Idanu Qasimu ya runtse yace. "Ashsha Gawata ashsha ni yanzu wallahi damuwata da wanne idanu za'a kalli Hindu ne kawai. Amman da idanun cin amanar zamu kalleta mu bata haƙuri amman fa ina da tabbacin ba zata taɓa haƙura ba" Mijinyawa yace. "Ko da na rabu da Asama'un? " "Ko da ka rabu da'ita. Kasan mata suna da yafiya amman basa mantuwa. Bazan ɓoye maka ba ni kaina haushinka nake ji Gawata ji nake kamar a busa ƙaho kamar zai iya fin sauƙi a wajenka. Kuma in ka rabu da Asama'u ka tanadi abinda zaka ce da Nanno ne akan dalilin sakin, da su Yaya Jamila da basu ƙi su ingiza Hindu wuta ba? Kada ma ka soma sake kwaɓa wani abun. Amman ina mai tabbatar maka ba lallai muje mu samu Hindu a gidanka bama tunda kaga ta turo maka saƙwannin abinda kuka aikata mata, shikenan ka rasa Hindu mace mai karamci da ɗa'a. Yanzu daure mu je cikin abokanmu aci asha zamu san yadda zamu ɓullo ma matsalar. Ka tara jama'a kaine uban biki, dole ka daure" Mijinyawa turjewa yayi akan bazai fita ba, a sallami kowa kawai, shi bazai iya zama da Asama'u ba. "Gawata wannan duka aikin banza ne. Wallahi Hindu rabuwarku ma shine mutumcinka, ta bala'in yi maka da ƙauna. In kaci gaba da riƙe igiyar aurenma, rayuwar ta gama muku daɗi. Wacce macece zata kama irin wannan iskanci da abu ta kaza... Da kuka yi ta rufa maka asirinka ma. Wallahi ko Barakace misali ta kamani haka, wallahi Jama'are da kewayanta kab sai sunji mena aikata. Bata ƙara zama gidana." "Qasimu ni ya zanyi dan girman Allah. Taya zan wanke laifina a wajen Hindu. Da wacce siga ma zan sameta mu tattaunane Qasimu? Wallahi Hindu bata rageni da komai ta ɓarayin ɗakinmu ba. Asalima kullum tamkar sabunta kanta take yi. Ga wani ƙamshi na dindindin da take yi. Wallahi babban tashin hankalina baya wuce, yadda naita zagi gami da aibata albarkatun jikinta. Wallahi kuma abunda nake ta cewa ba gaskiya bane. Hindu cikakkiyar macece wacce tasan kanta a ta ko ta ina. Qasimu ba gaskiya nake ta faɗa ba. Kuma wallahi bansan me ya fusgeni nake ta wannan shirmen ba. Me yasa na biye ma Asama'u? " "Son zuchiya mana Gawata da rashin tsoron Allah subuhanahu wata ala. Yarinyar da tayi maka tayin wannan lamari babba. Ai kamata yayi taci na jaki, kuma kada ta wuce wata guda tim a aurar da'ita tunda dai an samu matsala. Amman dake ka zama ɗan babbar abu ta kazan.... Sai kawai ka biye ma kiɗan kukaita canja salo_salo na rawa. Tur wallahi ka bala'in bani kunya. Wallahi Hindu ba zata taɓa ma uziri ba, jarabawa kawai zamu yi" Qasimu kam ya sulle Mijinyawa soso harda sabili. Ya sake ɗora mishi damuwa mai tsananin gaske. Ganin damuwar tayi yawane yasa Qasimu ɗan sassautowa daga fishi mai tsananin daya shiga. Yaita bashi baki kuma. Haka dole Qasimu ya jashi suka koma gidanshi akaci gaba da gabatar da liyafar cin abinci. Ya gagara kiran Hindu a waya sam. Asama'u sai kiranshi take yi tare da tura mishi wasu irin saƙwannin batsa. Tare da fayyace mishi yadda take ɗoki da zumuɗin su kasance daren gobe tare. Ranar mijinyawa ya gane dare da tsawo yake dan da ƙyar garin Allah ya waye mishi Tunani, gami da namadar komai su suka aureshi, kokkone ya haɗe mishi da giya. Da ciwon kai ya tashi mai tsanani, ga zazzaɓi kau a jikinshi, tsokokin jikinshi da hantarshi har kaɗawa suke yi. Bazai iya rayuwa mai kyau babu Hindu a gefenshi ba. Abu ɗaya ke sake sassare mishi guiwa tare da tsittsinka mishi gaba, sanin sarai wacece Hindu mace mai tauri, da ra'ayin riƙau, da dagiya akan gaskiyarta. Ƙarfe takwas daidai aka gama loda jama'a a mota da kayan Amarya da Nanno dasu Yaya Jamila suka cajeshi kuɗaɗe masu kauri Haka aka tawo a jere motoci ƙananu huɗu guda biyu ta Mijinyawa da abokanshi, biyu kuma amarya da ƙawayen Amarya sai kuma bus babba da aka zubo dattijai da yaran mata gayya suka yi mai yawan gaske suka ɗauki hanya. Tunda aka kama hanya Mijinyawa dake kusa da Qasimu a zaune ya jingina bayanshi da jikin kujerar motar ya rufe idanunshi ba bacci yake yi ba asalima yana jin abokanshi suna hira masu cewa ya buɗe musu ƙofa suma zasu shiga neman Aure na biyu, sai masu ganin da dai ba Asama'u ya Aura ba. Sai kuma masu tunasar dasu ba haramun ya aikata ba nan suka raba kansu uku akaita musu ana dariya gami da ɗaga murya. Ango shi kuma babu abinda yake yi mishi daɗi mafita da makomar zaman lafiyarsu kaɗai yake hange. Ji yake yi yana jin nauyi da kunyar haɗuwa da Hindu fiye da kima, har wani tsoronta ke ratsa jikinshi. Fatanshi, burinshi Allah yasa ta yafe mishi, in taƙi baisan ina zai tsoma ranshi ba. Asama'u kam sun gama bazan taɓa iya riƙw igiyoyin aurenta ba tabbas. ƙirjinshi sai dokawa kawai yake yi fat_fat_fat. A haka Allah cikin ikonshi da buwayarshi suka shigo garin Kano da yamma, ruwa akeyi sosai a Kano damunar farko farko ce amman ruwan da ake makaɗawa kamar irin watan agusta ɗinnan tsakiyarshi watan marka_marka. A haka suka shiga cikin gidan kayan Amarya kam ba'a fito dasu ba suna cikin mota rufe ruf da tamfol. Su kan abokan ango da ango kasa fitowa a cikin ruwan suka yi. Dan ruwane ake makaɗawa mamakon gaske. Amma mata tuni suka fito sukai ciki a guje a cikin ruwan. Su kuwa saida ruwan ya tsaya cak wajajen magriba kana suka ɗunguma suka fito kai tsaye ɓarayin Hindu suka nufa. Dangane da sunan Azgar asalin sunan ( Asghar) ne ba Azgar ba. Na hausantar dashine ya zama Azgar sabida hausawa a haka suke kiran sunan, ni kuma nafi sha'awar aiki da zallah hausa da fatan kun fahimta? Mrs BukhariTSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI. LAMBA TA TAKWAS *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. "Bata ciki ne Hindun Yaya Jamila? " Cewar Mijinyawa da yake jin faɗuwar gabanshi ya tsananta yana jin juwa na neman kayar dashi. "Bata ciki bugun duniya da muka yi bata ciki. Fisabilillahi mun kwaso yinwa ace ana bikin mijinki guda, ko aikin ta tafi oho dan dai naga Hindu na mutuwar son aikinnan nata. Kuma ba komai bane sa take ta tozartaka a idanun abokai ta nuna musu iyakarka. Ai muddin namiji ya Auri macen data wuce da ajinshi, kuma mai zuwa aiki ta cakuɗu da maza. Wallahi dashi da banza duk ɗaya" Batulu tace. "Yarinya sai girman kai da taurin kai. Da naga ai bata nuna auren ya dameta ba ashe dai ya damentan, da ba tace bata ji ba. Amman dai ta tabka mana tsiya ga ruwa ga dare" Qasimu ne yayi magana. "Yaya Jamila ku je ɓarayin Uwalate ku jira, Nanno kuyi haƙuri. Bari muje a kawo muku abincin da zaku ci kawai. Gawata mujenku" "Au bazai kirata tazo ta bamu abinci ba sai dai ku siyo mana? Hindu ta samu dama taci galaba a kanmu ta wulaƙanta banza? Kaga yadda ruwa ke dukanmu muna tsiyayar ruwa fa" Waje ya kaure da sowar mata, Nanno da kishiyarta dai babu kalma a bakinsu, cika suka yi sukai fam. Hannun Mijinyawa Qasimu yaja abokansu suka biyosu Sai a babban gidan ci da siyar da abinci suka siyo musu soyayyar shinkafa da dafadukan shinkafa sai zoɓo da kunun aya ai kuwa Mijinyawa yaji a ajjihunshi sosai. Basu koma ba saida Qasimu ya siya ma duk abokansu abinci a cikin ci ka yar da abun sha kana ƴan wajen aikinsu sukai musu sallama suka wuce ƴan Jama'are kuma suka koma can gidan mijinyawa Qasimu ya basu abincin, nan ya tarar Nanno tana masifa itace harda kuka wai Hindu taci mutumcinta, ta tozartasu a idanun ƴan Jama'are. Mijinyawa kuma ya saka ɗan mabuɗi ya buɗe musu falon Hindu fes_ fes dashi gwanin sha'awa komai na zaune akan tsari. Ga ƙamshin turarukan wuta na Mrs BUKHARI yana tashi a ko wanne kusurwa, ya cakuɗe da ƙamshin fenti, da ƙamshi sababbin kaya. Ƙoƙarin buɗe ɗakinta yayi sai yaji ɗakin a kulle ya duba duk safaya ki ɗin ƙofofin gidan ya gansu amman banda na ɗakin Hindu kuma yasan yana dashi har a jikin kin ƙofar ɗakinshi ko daya duba bai gani ba, kanshi ya jinjina lallai yasan ya taro mach. Masallaci suka wuce suka yo sallar isha sunyi magriba a hanyarsu ta dawowa daga siyo abinci. Sai da suka dawo kowa ya baje yana cin abinci. Mijinyawa ya zare jikinshi ya shige ɗakinshi ya shiga kai kawo. Wayarshi ya ɗaga ya kira wayar Hindu ya jita a kashe jiki a mace ya sauke wayar zuchiyarshi tana bashi gidan ya kamata yaje ya dawo da'ita zaifi kawai, amman baisan yadda zata kaya ba a gidan. Ga Baba soja da tauri, in kuma ta sanar musu shikenan ya kaɗe har ganyenshi. Amman duk da haka kwanciyar hankalinshi shine zuwan dai. Ai kuwa a ƙagauce ya fito tare da zaran kin mota a ajjihun gaban rigar Qasimu yayi waje da hanzari. Sai ji sukai an wangale mishi get ya fice, haka yai ta tuƙinnan cikin rashin hayyaci. Zuchiyarshi kamar zata tawarwatse a cikin ƙirjinshi haka yake ji, har wani amai ne ke taso mishi kawai. Ajjiyar zuchiya ya sauke ganin motar Hindu a ƙofar gida, hakan yasa ya shiga gidan kai tsaye da ƙarfin guiwa. Bai tsaya gaishe_ gaishe ba kai tsaye a lungun Baba Soja ya tsaya ya shiga yin sallama. Baba Soja ne ya leƙo hannunshi riƙe da jarida ga kakin soja a jikinshi, da hular sojoji mai malama. "Mijinyawa kaine a darennan ga sanyi, kaddai su Azgar kazo ɗauka ne? Shigo daga ciki mana sai kace wani baƙo." Ya riƙo hannunshi suka ratso falon, su Inna Turai da Inna Abida suna falon suna cin abinci a ƙaton tire, Innah Inna Ruwayya kuma littafin turancine a hannunta tana karantawa, ita mai son karance karance littattafan turancice sosai. Tsugunnawa yayi ya gaishe da iyayen mata. Suka amsa tare da taya shi murnar aure. Shi dai da yaƙe aka barshi, kunya kamar zatai ajalinshi. ƙarasawa yayi ya zauna a ƙasa gefen Baba Soja. "Dama nazo in tafi dasu Hindunne naga dare yayi ga ruwa" Baki Baba soja ya buɗe yana kallonshi galala. Inna Ruwayya dafa ta fahimci da matsala saita taso tace. "Muje daga ciki Mijinyawa ganinan shigowa" Miƙewa yayi ya shige cikin falon, Inna da Baba soja suka bishi suka zazzauna. "Hindu bata faɗa maka tafiyar da zata yi bane Mijinyawa, naji kace kazo tafiya dasu, ko Sabira kake nufine?" Ajjiyar zuchiya ya sauke daya tuno ashe semina tace zata tafi fa sabida shi ya mance shaf, idanu ya lumshe yana jin daɗi na ratsashi sosai. "Ta faɗamun na mance ne shaf wallahi, dake nace ta haƙura da tafiyar" "Ta haƙura fa kace? " Suka haɗa baki dukkansu suna tambayarshi. A wulaƙance cike da kallon ƙasƙanci Baba soja yace. "Ta haƙura da tafiya Landan mijinyawa, sabida baka san darajar karatu da ci gababa ko me.? Hindu ai ta daɗe tana mafarkin son yin aiki da Bbc sashen hausa, kuma wannan damar data samu ba kowa ke samun irinta ba ai. Shekara biyu kamar kwanane ai bazai yiwu ma ace ta bar tafiyar ba ina, wannan ai son kai ne da rashin mutumci a gidana za'ayi haka." Inna tace. "Tunda kana da macen da zata kula da kaima ai da sauƙi, wannan yana daga cikin amfanin mace sama da ɗaya a gida, in ɗaya bata nan miji bazai tagaiyaraba. Mu dai mata adda'ar Allah yasa ta gama aikinta a sa'a ta dawo cikin aminci kawai." Shiru yayi kanshi a ɗaure yaji ana maganar Bbc ga maganar shekara biyu, ga maganar Landan, an saka shi a duhu gashi bazai iya musu tambaya ba dole Hindun zaita kira har ya sameta tayi mishi bayani. Amman ji yake yi alƙiyamarshi ta tsaya. A lokacin in aka tsaga jikin mijinyawa ba zata tadda jini ba ya ƙafe tsabar yadda ya hautsine. "Babu damuwa, su yaran fa su fito mu tafi" Baba soja yace. "Ai zamansu anan yafi dacewa tunda dai acan babu mai saka musu idanu. Ita yarinyar daka aura ba zata iya tsawatarwa ba ƙarshenta su ɓige da yi mata fitsara, tunda kaga Azgar ya girme mata, ai zamansu ba gyatumarsu gwarine. Zan fita inje in ji labaran tara saika fito" "To shikenan nima tafiyar zanyi. Inna saida safe" "Allah ya tashemu lafiya" Fita yayi tare da yima su Inna Abida sallamar sai kallonshi suke yi. A ƙofar gida yaci karo da Azgar hannunshi ya ja suka isa gaban motar Hindu. "Azgar ina Hindu taje nasan dole kun sani"? " Hakane Abba mun sani. Tana Ingila ta samu aikin kwantiragi da Bbc sashen Hausa landan. Shekara biyu zata yi" "Me landan fa kace Hindun, shine ba zata faɗamun ba sai kace zaman kanta take yi. Landan Hindu, landan fa Azgar? shikenan" Sai kuma yayi muƙus dan haƙiƙa yasan abinda ya aikata yana da girman da dole Hindu saita horashi. Amman baya jin zai iya shekara biyu ba tare da yaji ɗuminta ya sakata a idanunshi ya roƙi gafararta ba, shekara biyu ai mutuwa zai. Tabbas ya fahimci in yaci gaba da riƙe igiyoyin auren Asama'u to tabbas Hindu zata iya rabuwa dashi shi kuma akan ya rasa Hindu gara ya rasa duk abinda ya mallaka ya rasa kowa da komai, ko da wasa bazai ba maƙiya daman ganin bayansu ba, yasan da yadda akayi aurensu ya kuma san matsayinshi a gidansu Hindu, da irin ɗauki babu daɗin da akaita faman yi, da tataɓurza, wa ma ya taɓa tunanin za'ayi auren. Ajjiyar zuchiya ya sauke. "Shikenan kaje Azgar, ga wannan ku riƙe a hannunku" Ya miƙa mishi kuɗi masu yawan da ko ƙirgawa baiyi ba. Azgar ya noƙe yace. "Ka barshi Abba. Ammi ta bamu wadatattun kuɗin da zasu ishemu har ta dawo. Sai da safe" A tsaye ya barshi baki a sake, bai bar wajen ba har saida Azgar ya shige shagon kwanan samari na gidan kamar ma kuka yake yi, kuma da ƙyar yake magana, idanunshi sun yi jawur har jijiyoyin saman idanunshi sun kumbura, yanayin da bai taɓa ganin yaron nashi a ciki ba kenan. Da ƴar Mijinyawa ya shiga mota ya ja ya koma gida. Yana shiga Ƙawar Nanno Innatu tana kiran wayarshi sai faɗa take yi wai taji labarin Hindu bata gida shine ya kwashi jiki ya bita abinci ma sai a gidan cin abinci aka siyo. "Kiyi haƙuri Innatu bata nanne tayi tafiya aikine ya taso mata naci gaba babba, kuma da izinina ta tafi kiyi haƙuri." "Shikenan ai sarki mai Hindu dama haka suke da baƙar zuchiya masu sunan ko a tarihi jarumtarsu ba irin ta mata bace. Yarinya ta samu ta sakata ta wala kafin ta dawo. Sannan ko da wasa Asama'u ba zata yi aiki ba sai dai sana'a a gida ita waccan data fifita boko sama da Aure shi yasa ma yaran take ganin biyu sun isheta ai, shekara da shekaru ance ma mahaifar ta tursasa maka kuka juya mu dai a haka ruwayar tazo mana. Shikenan sai taje ta riƙe boko Asama'u zaman aure zata yi duk shekara banƙi in tawo suna ba" Illahirin kunya saita cika mijinyawa. Bai iya cewa komai ba har ta kashe wayarta. "Qasimu ga ɗakunan yara zaku iya kwana a ciki kaina ciwo yake yi zan haɗiyi magani in kwanta" "Ai ba sai mun shiga ko'ina ba nan falon ya ishemu gobe sassafe mu kama hanyar ƙauyanmu kuma. Ai kuwa hakan akayi wanka ya shiga banɗakinshi yana yi babu nutsuwa tattare dashi sam, haka ya fito babu komai a jikinshi sabida yana tunanin babu mai shigo mishi ɗaki yana fitowa yaga Asama'u kwance a tsakiyar gadonshi tayi ruf da ciki da wasu fitinannanun kayan bacci masu nuna sura. Da sauri ya koma baɗakin ya ɗauro tawul a ƙugunshi ya fito. "Me kika zo yi ɗakina gida cike da baƙi, falo cike da maza, wannan wacce iriyar fitsara da rashin ta'ido ce Asama'u wai ubanme yake damunki ne haka?" A yadda yayi maganar babu wasa bare wargi ya ɗaure girar sama data ƙasa tamau, tare da kawar da kanshi daga kallonta. Zama yayi a kujerar gaban madubinshi Asama'u ta taso tazo bayanshi ta tsaya baiyi Aune ba ta rungumeshi ta baya, yana jiyo ƴan biyu, sai yaji kamar ta ɗana mishi garwashi yayi saurin zabura ya miƙe nanma ta sake rungumeshi tsam harda saka mishi kuka. Shiru yayi yana sauraren kukan, tare da sauraren zuchiyarshi amman tuno abinda suka aikata kafin auren da kuma tuno fuskar Hindu yasa ya ɓanɓareta da sauri ya rirriƙe hannayenta tare da daka mata tsawa dan sai wani dire_diren shagwaɓa take yi mishi mamanta na rawa na iskanci. "Ki nutsu ina magana dake dan abu ta kazan..." Ya daka mata tsawa. Babu shiri ta nutsu dan tunda take bai taɓa mata tsawaba bama ita kaɗai ba kaf yaranshi. Sai taji ta tsorata. Hannayenta ya sake ya wuce wajen durowarshi ya zaro jallabiya ya zura. "Ɗauki hijabinki ki zura maza ki koma ɓarayinki. Kada ki sake biyoni nan wannan sirrinane ni da Hindu Mamanki" Da mamaki ta dubeshi amman taji haushin abinda ya aikata mata saita fice fuu. "Aikin banza ko menene ribar auren wannan mitsitsiyar yarinyar oho ita ba kyau ba ma. Nayi nadama da dana sani, bazan iya haɗa jikina da wannan yarinyar a matsayin matar Aure ba, wallahi bazan iyaba, bazan iyaba Hindu na tuba." Wata zuchiyar tace mishi. "Yarinya bata fa da laifi kaine ubanta ka fita hankali da sanin abinda ya kamata. Ka dai rushe farin cikin gidanka da kanka. Muddin Asama'u zata ci gaba da wanzuwa cikin rayuwarka a matsayin mata, to tabbas kaida Hindu har gaba da abada" Zama yayi a bakin gadonshi da ƙyar ya haɗiyi maganin ciwon kai ya kwanta shiru yana sauraren zuchiyarshi, dake daka. Haka dai gari ya waye dasu asussubar fari Yaya Jamila tazo akan abinda za'a karya dashi. Firjin Hindu ya buɗe ya basu nama da kayan miya yace ko taliyace su dafa, suka wuce masallaci dasu Qasimu. Suna dawowa aka shiga sha'anin wanka da sake kaya, shida da rabi aka kawo musu taliya da lafiyayyen shayi yaji madara suka karya banda Mijinyawa. Bakwai daidai duk suka fito aka shisshiga mota harda dangin Asama'un duk suka watse gida ya rage daga su Uwatale sai Asama'u. Nanno taƙi fur tayi magana da Mijinyawa har suka tafi. Su Uwatale su suka gyara mata ko'ina harda wanke_wanke. "Kin ji labarin kishiyar taki tayi tafiya bata gidan akayi bikin ko? Sai fa kinyi da gaske kishi da Hindu sai mutum ya shirya gata da kafirin girman kai" Cewar Uwatale, Matar Gambo sai cewa tayi. "Naji fa ana cewa yaji tayi ta tattare yaranta ta tafi dasu, bayan mun dawo Mijinyawa ƙarami ya tafi biko a ruwannan ƙin biyoshi dai tayi kun santa da taurin kai" Uwatale tace. "Zaiyi wuya tayi yaji tunda har ta bari aka ɗaura auren batai rigima ba, nifa na ɗauka saita kusan ƙona gidannan amman dake makirace saita nuna da Asama'u da banza duk ɗaya, kema kinsan tasan meta taka. Kiga ko fenti na ɓarayinta yafi tsada, jibi wasu royal kujeru daya saka mata kota ko ina ɗakinta yafi na Asama'u kyau da girma fa hmm" Asama'u take taji wani ƙwollon kishi ya tsaya mata a zuchiyarta tana kuma jin kota halin ƙaƙa saita mayar da Hindu ba komai ba a wajen Mijinyawa. Wuyarta ya ɗanɗana zumarta dan mahaifiyarta ba ƙaramin shiri na magunguna tasa akayi mata ba. Cire kunya tayi ta koya mata yadda ake ƙwace miji kamar yadda gidan data shiga ta tadda mata biyu ta kwace misu miji take juya mijin yadda take so, yake fifitata tako ta ina. Ga kuma kulawa da tattalin miji, da haƙuri data koya a aikace a wajen Hindu. Sai take ganin ƙwace goriba a hannun kuturu abune mai sauƙi sirrin Hindu a tafin hannunta yake, haka duk abinda mijinyawa yake so ta sani sarai. Murmushin mugunta kawai tabi su Uwatale dashi. A ɓarayinta suka wuni cur, uwatale ta dinga kwance ma Hindu zane. "Asama'u ai ya kamata kije ɗakin kishiyarki kima Mijinyawa magana yayo miki cefane ya kamata ki yi girkin tarbarshi ke a daɗinki ma Allah yasa Hindu ta tafi kenan har gaba da abada, dama ni tun farkon da aka haɗamu kafinma a Auromu ikon Allah jinina da nata sam bai haɗu ba. Tana da iyayi da yawa da girman kan tsiya. Wannan da ace ita kaɗai ke da Digiri a surukan haularnan da an boni." Nan sukaita zuga Asama'u ta shiga ta feffesa turare a jikinta ta gyara ɗaurinta ta nufi ɗakin Hindu. A rufe ƙofar take hakan yasa dole ta shiga ƙwanƙwasawa kamar ba za'a buɗe mata ba dai sai kuma aka buɗe mata. Ranshi a ɗaure yace. "Lafiya me ya kawoki kuma? " "Sikari dama cefane nake son ayo mun inaso zan ɗaura girki" "Ina zuwa" Iyakar abinda yace da'ita kenan ya mayar da ƙofa ya kulle bai jima ba ya fito da basket guda na kayan miya da sukai ƙanƙara harda su nama ya miƙa mata ya kuma kulle ɗakin ya shige. Ji yake yi uwa yayi shekara da shekaru bubu Hindu a rayuwarshi gidan jinshi yake yi tamkar wata babbar katanga ta rushe. Ba Hindu ba yara sai Asama'u a matsayin mata ba'a matsayin ɗiya da take a wajenshi da ba. Idanu ya runtse kawai Haka ya wuni cur a ɗaki cike da kaɗaici sai dai ya fita masallaci ya dawo. Da bayan la'asarne ma yayi wanka ya tafi gidan ɗaya daga cikin abokanshi na wajen aiki sai bayan isha'i ya koma gida ziƙau daga shi sai halinshi. Ɗakin Hindu ya kuma buɗewa ya shiga yayi kwanciyarshi a kujera tare da kunna tv ya nemi tasha ya saka, bama kallon yake yi ba kawai dai ya kunnane. Wayar Hindu ya sake kira bata shiga, ya duba whatApp ko zai ganta saiya fahimci kamar fa ta kulle layinshine a whatApp ɗinta. Zabura yayi nan take ya buɗe sabon WhatApp da ɗayar wayar tashi da number daban. Sannan ya ganta, bata kai amman bata fi awa uku da sauka ba, hakanne ya tabbatar mishi da kulleshi dai tayi. Bugun ƙofar falon ne yasa ya miƙe yana tsaki Yana buɗewa yaga Asama'u a tsaye. "Ashe da gasken dai kaine ka dawo, to ya ka dawo nan ka zauna ga abinci yana jiranka kuma yau ai ranace ta musamman a wajen, ka man... " "Ke bana son fitsara da iya shege kinji ko, wai lafiyarki ƙalau kuwa Asama'u? " Shiru tayi tana ƙunƙunni ƙasa_ƙasa. "Kije ki ci abinci ki yi kwanciyarki kinji ko? " Wannan karon da rarrashi yayi mata maganar saita fashe da kuka ta ruga a guje zuwa ɗakinta. "Allah na tuba, Allah ka yafe mini" Ya faɗa a fili ya koma ciki. Ranar ma a ɗakinshi ya kwana sassafe ya shiga shirin tafiya aiki, ya fito tsab cikin shirin aiki yana kiciniyar rufe ƙofa Mijinyawa Babba yace. "Ohh ashe da gaskenne a ɗakin Hindu ka kwanta kabar ƴar mutane sai kuka take runtumawa ta kira Nanno ta faɗa mata wallahi Nanno tace ka kiyayeta duk abinda kake ciki tace ka kwana a ɗakin matarka yau ni dai saƙo ta bani. " Ƙarata takai kenan Mijinyawa Babba? Bana jin daɗine kwata_kwata fa. Kuma kaga yanzu haka ma tafiyace a gabana an turani first bank na garin kaduna akwai wani abu da zamu gudanar ka ganni a ƙagauce na fito" "Kuma na ganka ba jaka amma? Mijinyawa Babba ya tambaya yana kallon ɗan uwan nashi. "Mancewa nayi bari in shiga in ɗakko" "To Allah ya tsare a dawo lafiya in ka nutsu saika kira Nanno dan ranta ya ɓaci" Mijinyawa yana shiga ya tattaro kaya ya danna a akwati ya fito da sauri. Ɗakin Asama'u ya shiga tana Kitchen tana ɓuruntu kiranta yayi daga tsayen da yake. Da murna ta fito tayi tunanin ya dawo ɓarayinta ne. "Ina kwana? " Fuska babu annuri ya amsa mata. "Zanje Kaduna tafiya ta kamani. Zan turo a kawo miki kayan miya, zan tura miki kuɗi a account ɗinki saina dawo" A sanyaye tace. "Me zai hana mu tafi tare dan Allah, tsoro nake ji wallahi" "Bazai yiwu ba. Kima Uwatale magana ta baki Zainab ta dinga tayaki kwana" A wajen ya barta ya ja akwatinshi ya fice ɗan sahu ya tare ya kaishi babban hotel ya kama ɗaki, yana ajjiye akwatin ya wuce wajen aiki zuchiyarshi cike da tunane_tunane masu yawa. Ba kadunan da zashi ya haɗa ɗaki da Asama'une wai bazai iyaba kimunin. A wajen aikin ya kira Nanno yake faɗa mata tafiyar da yayi saida ta gama faɗanta tayi mishi adda'a kana hankalinshi ya kwanta. Qasimu ya kira a waya. "Qasimu dan Allah inason ganinka inda hali amman bana gida inka shigo Kano ka kirani kuma kada ka faɗama kowa zaka shigo kano" Cike da mamaki Qasimu yace "Allah yasa ba wata matsalar bace ba ko? " Kai tsaye yace. "Itace Qasimu kai dai sai ka iso kawai, ƙila ma kafin ka iso na mutu Qasimu" Saida yayi dariyarshi ma'ishi kana yace. "Duk wanda yace zai yi guga danya ɗebi duniya, ƙarshe ko ya janyo bazai janyo komai ba. Gawata tsalle ɗaya akeyi a shiga rijiya, amman wallahi sai ayi dubu ba'a fito ba. Kasan Allah bacci wannan ɓarawone ya kwasheni. Baraka sai tambayata take yi damuwata amman ina na kasa magana, sabida wannan sirrinkane Aminina." "Ka kasheni kawai ka huta zai fi maka" "Ka kashe kanka dai, ni in kasheka ka rataya a wuyana da wannan zunubin daka aikata? Allah ya kiyaye. " Hmmm" Kaɗai yace. Qasimu yace dashi. "To shikenan saina zo, Allah ya kyauta." Da wannan Mijinyawa ya ajjiye wayarshi ya shiga aiki, amman ina aikin yaƙi samuwa, baya ganewa har lokacin tashin shi a aiki yayi dai. kai tsaye ya wuce Hotel ɗin da ya ya da zango. A ciki yayi sallah, ya yo odar abinci aka kawo mishi tuwon sakwara da miyar Egusi. Ya tusa a gaba kenan Qasimu ya ƙaraso dan ya riga yayi mishi kwatance kuma ya bashi lambar ɗakin. Sakawa yayi aka ƙaro tuwon sakwarar suka ci tare kana sukai sallar isha'i kafin tattaunawarsu ta soma gudana" Mrs Bukhari. To sai mun haɗu ranar Monday kumahttps://chat.whatsapp.com/JI1IGIBFHYm64hr6IfVfqR TSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA TARA *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. "Qasimu bazan iya zaman Aure da Asama'u ba. Kasan Allah in shiga inda take ma bazan iyaba, na kuma kasa. Kaga kayana nan nazo nake nufin tarewa, to amman nasan dole akwai buƙatar in koma gida komai daren daɗewa. Jiya kaɗai da ban shiga ɗakin yarinyarnan ba saida ta kira Nanno ta faɗa mata, Mijinyawa Babba ma yasan halin da ake ciki bare matarshi. Qasimu wai yaya zanyi ne dan Allah kaimun mafita. Sannan ya zanyi da Hindu? Ni dai bazan iya zama da Asama'u ya ƙare tsakaninmu. Ni tsoro ma yarinyar take bani wallahi. Kuma kasan uwarta ke zigata, ina da tabbacin ita ta rusa duk ginin tarbiyyar da Hindu tayi mata. Ta koma maras kunya, maras mutumci, yarinya yadda kasan zatai mun fyaɗe fa" "Zauna Gawata muyi magana ta fahimta dan Allah, zauna kaji" Zama yayi suka fuskanci juna. "Ita Asama'un ka dena sonta ne ko ko dama can sha'awarta kake ji ne? " "Bazan iya tantancewa ba. Daga lokacin da Hindu ta turo mun waɗannan saƙwannin daga lokacin naji bana son Asama'u kuma ko kusa bazan iya haɗa jikina da nata ba" "Inna fahimceka da kana sonta kenan ko sha'awarta kake ji? " "Wallahi Allah Qasimu bazan iya cewa ga haƙiƙanin abinda ke zuchiyata dangane da yarinyar ba, sai dai daga lokacin da muka soma haɗa jiki na dena iya mallakar kaina muddin muka keɓe." "To Hindu ka samu damar magana da'ita ne, ko dai ta dawo ne? " Nan ya kwashe labarin tafiyarta landan ya labarta mishi da komawar yara gidansu. " Tabb Landan fa? Gawata bazan rufeka ba ka kwabsa ba ɗan kaɗan ba. Hindu tayi halacci nine shaidar hakan. Ka duba irin rayuwar da kuka gudanar a jama'are bafa rayuwa bace mai daɗi duka tako ta ina Hindu ta karɓeshi a wajen danginka, amman a haka ta jure ta kawar da kanta ta shanye harya wuce. Ka duba ragamar ɗawainiyar gida da ɗawainiyarka data yara da Hindu bata jin ƙyuya sam. Gawata Hindu tayi maka rana a lokacin da kake biɗar inuwa, ta soka a lokacin da matan Jama'are suke ganin ba zasu iya baka ɗiya ka Aura ba, bazan mance sanda Nanno taje ta tambayo maka Auren Uwatale ba. Amman aka ƙi fur duk da dangantakarku, kuma yadda zaka gane farin jinine baka dashi ana cewa a ba Nawata a guje aka bashi, yau ga Uwatale nan ta haɗa garken yara. A haka Hindu ita kuma ta soka, ta ɗaga darajarka. Hindu bawai matar Aurenka bace kaɗai ba. Itace koman ka" Hindu ta riƙe Asama'u tamfar ita ta haifeta. A lokacin da mahaifin Asama'u Amininmu kenan ya rasu matarshi ta shiga wani hali, nina soma tunanin ɗaukar Asama'u in kaima mai ɗakina Baraka dan a lokacin ita shayarwa take yi Hindu kuma ta riga ta Yaye Azgar tuni. Mai ɗakina kwana muka yi muna rikici akan ita tunda mahaifiyar Asama'u na da ranta ba zata shayar da'ita ba. (Ina fatan karatun nazari kuke yi ba karatun jin daɗin rai ba? Wannan littafin ban yishi dan nufin daɗi ba, ku nutsu ku saurara har na kai ga manufar domin anan ribar take) Haka na haƙura washegari nazo Asibiti kake labartamun ka amshi Asama'u ni dakai muka kaima Hindu Asama' u a farin tsumma bazan manta ba. Hindu ta saka hannu ta amsheta ta rungumeta tsam a ƙirjinta. Ba tare da ka nemi shawararta ba, ta riƙeta da zuchiya ɗaya ta sota sosai, gashi ta jima bata samu cikin Sabira ba Asama'u ta jima a saman cinya da kafaɗun Hindu. Babu irin siratsin rayuwar da baku tsallake kai da Hindu ba, Gawata babu shi. Amman kash bayan shafe duk wannan tarihin ace da Asama'u za'aima Hindu kishiya. Ba kishiyar tafi ɗaga mun hankali ba halin da aka tsinci kai kafin Auren. Gawata tunda ka bani labarinnan ranar ɗaurin Aure nake tubkewa da warwarewa. Hindu fa ta barka har abada ko ta dawo Landan ba zata taɓa dawowa gidanka ba bare ta sake samun gogewar aiki da buɗewar idanun rayuwa, kuma kaima ka sani Hindu ta fika wayewa nesa ba kusa ba. Soyayyace kawai ta zargeku kaida a ƙauye ka kasa Auruwa Gawata" "Ya isa Qasimu ya kake neman tayarmun da hawan jinine dan Allah? Ni na kiraka domin kaimun mafita kai kuma kana neman tarwatsamun zuchiyata. Qasimu inaso in sallami Asama'u ta koma gidan mahaifiyarta da zama. Ko zan samu salama. Na aikata babban laifi, naci Amanar Hindu, na zubar da darajata, na saɓama mahaliccina, kana naci amanar Abdulƙadiri. Kaicona Qasimu kaico" "Gawata ka nutsa da kyau tukunna kada ka daddama lamura da yawa mana, sannan abinda nake faɗa ai duk gaskiya ne. Yanzu inka saketa ka kirama kanka ruwa wallahi. Ka daure ko wata biyar tayi saika sallameta. Amman fa ka shirya shiga tashin hankali, sannan saika zama kurma makaho. Amman tabbas sakin Asama'u zai rage kaso ashirin bisa ɗari na fishin da Hindu take yi da kai, sai dai fa ba zata zauna da kai ba. Amman dai kayi haƙuri a ɗan miƙa tukunna gudun rikici kaga in Sabirace akai Aurenta kwana biyu miji ya sakota ta dawo duk rashin gaskiyarta baza ku taɓa jin daɗi ba. Gani zaku yi kamar an tozartaku ne ma, to sai ka daure Gawata. Jarabawace taku kuma a haka tazo, da tsantsar son zuchiyata, da son kai, da rashin jin tsoron Allah bare abinda kaje kazo. Kayi haƙuri da kalmomina ni Qasimu nine zan iya tsage maka gaskiyar data dace. Amman matarka Hindu tana sonka so mai tsamari, ka sani, nima na sani Gawata, in ka waiwaya baya. Ni damuwata mata zasu ɗaukeka su kafa hujja akan wannan kalma da suke jaddadawa ta namiji ba ɗan goyo bane. Kuma sun canfa cewar duk namijin da akaima halacci, sai yayi butulci. Kuma mata ku dena waɗannan kalmomin wallahi bamu taru mun lalace duka haka ba. A ko wacce iriyar al'umma akwai nagari akwai na banza. "Na sani Qasimu wallahi na sani. Haka Hindu take cewa Mijinyawa anya ba asiri kayi mun ba kuwa sonka kullum ninka kanshi yake yi a zuchiyata. Qasimu da Hindu bata sona da ta tona mun asirina a duniya. Amman wallahi ko iyayenta basu san abinda ke faruwa ba a irin yadda suka ƙi jinina da sun sani inaga Baba Soja da kanshi zai koreni inna shiga gidannan, ko yasa a kulleni a firzin na sojoji. Ni dai Qasimu landan zani in samu Hindu me kake gani?" "Landan fa? To kana da kuɗine Gawata da zaka bita. Sannan in ka bita me zaka tarar ka sanine? Kai dai kayi ƙoƙarin sakin Asama'u da zaran tayi wata biyar zuwa shida. Kuma kayi ta istigifari wala Allah aurenku ya zauna. Amman binta Landan bazai haifar da ɗa mai ido ba. Irinsu Hindu in sukai fishi abun babu kyau. Gata da makarai in kaje suka tashi wallahi tsab sai su shaƙeka ka mutu a banza. Ka daure ta dawo kawai" Sun ɗauki lokaci mai tsayi suna tattaunawa sai da Qasimu yasan yayi duk yadda zaiyi ya kwantar ma da Mijinyawa Hankali. Washegari da safe bayan sun karya sun gama shiryawa Mijinyawa ya nufi wajen aiki Qasimu kuma ya nufi Jama'are. Kwananshi huɗu a ɗakin hotel kana ranar Juma'a ya koma gida da yamma. Har zuwa lokacin bai samu damar magana da Hindu ba, ko da yayi mata magana da number shi daya buɗe whatApp saita kulleshi kai tsaye. Sai rubuce rubucenta ne suka zame mishi abokan rayuwa, bidiyoyinta suka zama ababen nishaɗinshi sai dai wasu abubuwan in yaji ta furta sai yaji duk ya tsargu sosai dan wallahi dashi take yi. Asama'u kuma duk yadda take kallon al'amura da sauƙi sai suka zame mata wani iri. Mijinyawa ya zame mata abun tsoro dan baya ko sakin fuskarshi, kallo wannan bata isheshi ba. Gashi ta kasa faɗama kowa halin da take ciki. Ɗakinshi na ɓarayinta yake shiga ya kulle kanshi yayi baccinshi washegari ya fice sai dare yake shigowa gidan. Asabar su Azgar suka zo suka wuni dashi amman falon Hindu ya buɗe musu acan suka wuni ko kallo Asama'u bata ishesu ba, itama nunawa tayi kamar bata sansu ba. Ranar monday yana fita aiki ta kira mahaifiyarta a waya" "Asama'u kuna lafiya ina fatan komai na tafiya daidai ko, kuma Hindu bata takura miki ba ko? " "Mama ai Hindu ta tarwatsamun duk wani shiri da mafarkinmu Mama." Mama daga cikin wayar tace. "Asama'u sai kin buɗe idanunki kinyi da gaske, ai dama zama da kishiya zaman yaƙine. Ko ki yaƙeta ko ta yaƙe ki, kina ganin yadda na kafa gwamnatina a gidannan har mota ya siya mini matanshi dana zo na samu ko tayar keke basu da'ita. Babu boka ba malam kirsa da kisisina da maɗe kawai ya ishi maza, wallahi ba sai an bi bokaye za'a mallakeshi ba Kiyi amfani da hikima ki tabbatar kin mallakeshi kamar yadda na ɗauraki akai. Ai anyi mai wuyar tunda har kuka yi Aure" "To ai Mama yaƙi kusantata sam ɗaki ma yaƙi mu haɗa ita kuma naji ƙishin_ƙishin tayi yaji bata ma gidan shekaranjiya dai yaran sunzo sun wuni wallahi Mama ko kallona basui ba" "Danƙari ai kuwa bazan yadda ki zama bora ba wallahi. Zanyi duk yadda zanyi sai kin mallaki mijinki. Gobe zan tawo in sha Allah ki jiraci zuwana. Ki kuma kwantar da hankalinki." Da haka suka ƙarƙare wayar. Washegari kuwa da yamma sakaliya Asama'u na riƙe da kaskon turaren wuta tana turara gida sai ga Mamanta ta iso ita da ƴarta da take goyo da kanta tayi tuƙin. Su Uwatale suna ganin shigarta. Sai ga uwatale harda kularta ta abinci. "Halima ikon Allah yau kece a gidan namu. Hindu ta raba zumunci amman yanzu yaya ta'iya ɗiyarki na aure a gidan? " "Uwatale kenan baki da dama. Hindu kam sai dai ta ganni ta barni ai tunda ɗiya sukutum naba mijinyawa. Yaya gida ya yaran? ". Uwatale na dariya tace. "Lafiya lau sai kika ji labarin Hindu dai tayi yaji tabar gidan. Iyayenta kuma madadin su dawo da'ita sunƙi sun riƙeta harda yaran. Dama kinsan ƴan gidansu da nuna gadara, ga shegen son boko gani suke sunfi kowa" Sun daɗe suna tattaunawa har saida akai kiran Magriba kafin uwatale ta koma shashenta. Halima na sallah a falo mijinyawa ya shigo da sallamarshi harda ledarshi na kayan marmari. "Sannu da dawowa Sikari, ga Mama tazo ganin waje" Dai_dai Halima ta sallame sallarta. "Mijinyawa maraba ka shigo? " Fuska ya ɗan sake yace. "Halima kece a tafe, ya mai gidan naki? " "Yana lafiya, nazo ban samu Hindu ba ince dai ba akan Aurennan bane ta tafi ba ko? " "Ahh ko ɗaya ba tafiya wani wajen tayi ba. Aikinta ne ya taso mata, bari in shiga daga ciki" Ya wuce ciki yana jiyo Halima tana cewa. "Maza bishi ki haɗa mishi ruwan wanka" Murmushi kawai yayi yana zama a kan gado ta shigo ta wuce ta haɗa mishi ruwan wanka. "Na haɗa maka ruwan wanka kaje kayi wankan" Dariya yayi mata na takaici ya wuce banɗakin kamar zai mutu, ita kuma ta fita tana murnar yau har dariya yayi mata, bata san dariyar takaici bace. A falo ta tarar da Halima tana cin abinci ita da ɗiyarta ta goye. "Kin haɗa mishi ruwan wankan? " "Na haɗa mishi yau har dariyarshi na gani mutumin da ya dena mun dariya sam Mama" Murmushi tayi na samun nasara. "Akwai wasu surrukan dana kawo miki na magungunan mata ya rage naki kiyi amfani da hila ki karkato hankalinshi kanki.wallahi wallahi in ya kusanceki Hindu saita dawo mishi nama mara maggi da gishiri ba zai sake jin ɗanɗanonta ba, zaki ta baza mulkinki a cikin gidan, zaki cika gidan da yara dam mu mallake kab illahirin dukiyarshi. Magungunan matane wanda nima su na riƙa a matsayin makamina" Magungunan duk ta miƙa mata tace taje ta adana da safe tayi mata bayanin yadda za'ayi dasu. Mijinyawa ne ya shigo da sallama ya zauna suka sake gaggaisawa Asama'u ta kawo mishi abinci duk da tasan ba ci yake yi ba a tunaninta ko ganin idon Halima zaisa yaci. Sai yace yaci abinci a wajen aiki kayan marmari daya shigo dashi kawai zata kawo mishi ta ɗebi nasu. Dama kullum hakan yake dawowa a ƙoshe, da safe kuma baya karyawa yake fita abunshi. Data kawo mishi kayan marmarin sai yayi musu sallama ya koma ciki. Halima kuwa kusan raba dare suka yi tana ɗaura ɗiyarta akan hanyar yadda zata kafa gwamnatinta a gidan ta ture gwamnatin Hindu. (Akwai fa kallo a cikin wannan turka_turkar ku dai ku gyara zama ina fatan kuna gane inda muka dosa?) LANDAN:. Mun sauka a Landan cikin aminci da kwanciyar hankali. Mota aka turo ta ɗaukemu zuwa masaukin da Bbc ta tanadar domin ma'aikatanta Gaskiya Bbc ɗayace tamkar da dubu kuma gagara gasar masu gasa. Gidane mai kyau da tsari ko wanne ciki da falo ne, akwai kaya da duk wani abun buƙata na rayuwa a ɗakin dangin su gado, kujera, kayan kallo, kayan Kitchen da dai abubuwan amfani yau da kullum. Ɗakina yana jere dana Shamsiyya. Ki nasa na buɗe na shiga ajjiyar zuchiya na sauke mai nauyi, na nemi waje na zauna akan tiri sita dake falon ina daɗa ƙarema tsarin wajen kallo, tsarine irinna turawan asali, babu tarkace da yawan kaya a ɗakin amman dake sun iya tsara waje wajen yayi kyau da sha'awa Sosai hakan zai baka dama ka samu lafiyayyen bacci ta yadda zaka gudanar da aikin ka yadda ya dace. Miƙewa nayi naja akwatunana zuwa ciki, kai tsaye na wuce banɗaki nayi wankana na fito. Saida na rama sallolin da ake bina kana na samu nutsuwa da zarafin shirya kayana a sib dake mun ci abinci a Airport bana jin yinwa, kuma ina da dambun nama da cincin dana tawo dasu. Washegari da safe bayan nayi wanka na fito zuwa ɗakin Shamsiyya akan ya zamu yi muyo cefanen kayan abinci tun wuri kafin monday mu koma bakin aikinmu. A kan titin layin da muke akwai kantuna na saida kayan abinci wata balarabiyace ta nuna mana, itama ma'aikaciyar Bbc ce fannin larabci. Ita tai mana jagora muka yo cefanen duk abinda muke buƙata kowacce ta jibge a ɗakinta. Da daddare shinkafa da miyar kifi naci, na ɗanyi miyoyi kamar kala uku na adana a firji sabida rage aiki. Ranar monday muka ɗunguma Bbc domin soma aiki. Gaskiya ma'aikantansu suna da kirki da haba_haba da baƙi sosai haka sukaita janmu suna zagayawa damu suna nunnana mana waje. Rigiji gabji ashe Bbc girma gareta hawa_hawa ko wanne hawa da ma'aikatansu. Bbc Hausa Bbc shashen turanci Bbc shashen faransanci Bbc shashen larabci Gasunan da yawa kuma ko wanne fanni hawansu daban kuma akwai soyayya da halaƙa a tsakankanin ma'aikatan sabida al'umlace ƙasa_ƙasa yare daban_daban haka ma addinai daban_daban amman aiki kuma ya haɗeku ya dunƙuleku a waje guda kun zama ƴan uwan juna a ƙasar da baku da kowa sai kawunanku. Madallah da shugaban shashen Hauwa shugaba mai mutunci da karamci da sanin ya kamata. Gaskiya ita kanta Bbc wata jami'a ce ta ɗaukar ilimi na musamman bazan rufeku ba. Aikina dasu na kwana ɗaya rak ya haskamun abubuwa da yawan gaske. Babban abinda yafi komai burgeni dasu yadda tuƙuru suke son ci gaban aikin jarida, da ci gaban ma'aikatan gidajen tv da rediyo wannan dalilin yasa suke karɓo ma'aikata daga gidajen rediyo daban_daban mutum yazo yayi aiki dasu ya sake gogewa akan aikinshi ya sake samun horo na musamman. Kai madallah madallah da Bbc da ma'aikatanta baki ɗayansu. Lokacin tashi nayi muka wuce gida, mu bamu soma aikin ba tukunna dai, ana dai kan nunnuna mana yadda al'amuran suke ne tukunna. Abinci na ɗumama na zauna a lokacin na sake kunna wayata na kira wayar Innarmu ta manhajar whatApp a bidiyo ma na kirata nako taki sa'a tana ɗakin Baba Sojanmu itace da kwana suna tare. Mun gaisa dasu cike da farin ciki inata basu labarin yadda ma'aikatan Bbc suke da karamci, da irin yadda suke murna in suka ga sabon ma'aikaci daga Najeriya. Bayan mun gama wayar dasu nan na kira Azgar da Sabira mun jima sosai dasu a waya muna gaisawa. Muna gamawa na kira Ƴan uwana mata. "Ai munyi fushi sai jin tafiya kawai muka yi Hinduwa babu ko sallama? " Yaya Saratu ba haka bane a dai yi haƙuri yanzu ba gashi na kirawo ba" "Yanzu Hinduwa kin barma Asama'u Mijinyawa kenan gashi kin tafi tafiya mai tsawo wanda in da rabo kafin ma ki dawo ta haihu?" Murmushi nayi mata tare da cewa. Aikinane a gabana Yaya Saratu. Ko da inanan Mijinyawa ai mijintane itama, babu abunda zan tare mishi tunda a tsakaninmu dole yayi mana adalci. Bari in nuna miki ɗakin da nake" Na bagarar da hirar ta hanyar haska mata wajen zamana tana ta santi da taya ni murna. Da haka muka ƙarƙare wayar tamu dasu na ajjiye wayar tare da ajjiyar zuchiya. Take kuma Yaya Saratu ta hautsinamun lissafina a ranar kwanan baƙin ciki da tunane_ tunane kala_kala nayi. Haka rayuwar Landan taci gaba da tafiya cikin jin daɗi da kwanciyar hankali sai ranar lahadi na samu damar zuwa gidan Abokin Baba Sojanmu. Su sukaima ɗan tasi kwatance ya kaimu ni da Shamsiyya. Gidansu mai kyau da tsari sosai gidane na ƙasa ga matarshi mace mai kirki da sanin ya kamata sunyi mana tarbar arziki, har Baba Soja ya kira a waya ya sanar dashi zuwanmu. "Zata samu gurbin karatun mastas ɗinta Soja in P. H. D ma take so data gama mastas ɗin ta jona ai sai tayi babu laifi. Amman in sha Allah zata samu shiga na fahimci tana da hazaƙa da son karatun babu laifi, zanyi iyakar yina Soja Hindu ai tamu ce na tuno lokacin da aka haifeta mu kuma muna filin kwantar da tarzoma" Dariya suka yi Baba Soja yaita mishi godiya. Bamu muka bar gidan ba sai dare su suka kaimu har gida suka ga waje har ɗakina suka shiga na kawo musu dambun nama da abun sha. Rayuwa taci gaba da garawa duk ranar Lahadi ina kiran ƴan uwana muna gaisawa harma da wasu daga cikin ƴan gidanmu. Rayuwar a Landan taci gaba da garawa, ta ɓangaren aiki kuma ilimin da muke kwasa ba na wasa bane gaskiya, kaina ya sake buɗewa sosai akan aikina. Allah cikin ikonshi da Amincewarshi ni da Shamsiyya muka samu gurbin karatun mastas ɗinmu a jami'ar Landan a lokacin Shamsiyya mijinta yazo suna zaune tare sabida yawanci ma'aikatan suna zamane tare da iyalansu, ko kuma iyalan su su kawo musu ziyara. Nakan tuno Mijinyawa da Asama'u kaɗan bamai yawa ba sabida na riga na shafesu a babin rayuwata ni ba mace bace mai ɗaura damuwa araina ta hanani cikar gurina ba, kuma inna wuce da sanin abu na wuce da saninshi har gaba da abada. Sai dai fa a ranar da Shamsiyya mijinta ya iso mu muka je filin jirgi muka tawo dashi tun a mota naga irin soyayyar da suke gudanarwa sai jingina nayi da kujerar motar na lumshe idanuna inajin sabon ciwon da Mijinyawa ya jima zuchiyata da irin butulcin da yayi mun, da irin yadda suka yaudareni dashi da Asama'u. A haka har muka dawo gida na shige ɗakina na zauna shiru ƙwaƙwalwata ta shiga aikin tariyomun rayuwarta ta baya da farkon haɗuwata da Mijinyawa da yadda har muka ƙulla halaƙar soyayya. Shekarun baya:. Ina tsaye a ɗakin Innarmu sassafe saye da kayan makarantar Asiya bayaro. Ina gyara zaman hijabina. A lokacin ina SS2 kuma nice shugaba a ajinmu sabida ina da ƙwazo da hazaƙar karatu sosai. Duka yaran Baba sojanmu ba daga nan ba sabida duk dare in sha Allah saiya koya mana karatu tare damu da yaran gidan baki ɗaya harma da yaran maƙota da iyayensu suka zo suka roƙa musu. Bikine damu na Ƴan mata goma a ɗakinmu akwai Yaya Saratu da Yaya Zubaida ɗakin Inna Abida Akwai Haula, akwai Mabaruka, sauran kuma daga ragowar lungunanne. A lokacin shine karo na farko da za'a aurar da mata a gidanmu. An Aurar da maza guda biyar suma lokaci guda wannan shine Aure na biyu wanda iyayenmu mata suka ci buri ko wacce so take tayi ma ɗiyarta kayan ɗaki na bajinta da burgewa sosai. Mu kuma Ƴan matan gidan burin ko wacce shine saurayinta ya fito da'ita. Fargabata guda ɗaya ce ina Gawata zai samu kuɗin da zai fitar dani kunyar ankon da aka fitar har kala uku a gidannan, banda takalmi, kuɗin ɗinki mayafai, da sarƙa da duk zamu yi amfani dasu. Su Fatsiman Inna Abida da muke tsararrakun juna, da Aminan Inna Mairamu, da Khadijan Lungun Baba Nagoɗi duk samarinsu sun sallamesu da komai da komai harda kuɗin liƙi ƴan ashirin Ashirin. Saurayin Fhatsuma ma ya kawo, Inna Abida da kanta ta fito da kayan ta nuna a tsakar gida. Rayya ce ta dafani tace. "Yaya Hinduwa kizo Innah tana waje tana jiranmu tafiya zata yi in baki fito ba" Jakata na rataya na fito falonmu riƙe da takalmina a hannuna sai a bakin ƙofa na saka na ratsa gidan namu muka fice. A motar Innarmu Honda ladys kwaraɓaɓɓiya na tadda su Akarami da su Yaya Saratu a ciki, a lokacin suna jama'ar bayaro kano. A cinyar Yaya Saratu na Zauna, Akarami ya ɗauki Rayya a gaba mu goma sha ɗaya ne cib a cikin motar harda Innarmu dake tuƙamu. Itama malamace a makarantar tana ɗaukarmu darasin islamic sutodis a wannan lokacin, kuma tana ɗaukarmu darasin turanci. Kamar kullum muna tafe muna hira har muka iso makaranta. Idanu muka haɗa da Gawata yana wajen sana'arshi ta sai da lemo a ƙofar Asiya Bayaro. Murmushi ya sakarmun mai kwantar da hankali. Idanuna na lumshe ina mai sakar mishi da nawa murmushin. Wannan murmushin shi ya riƙeni har akayi tara. Luba muje ki rakani in kaima Gawata wainarnan dan Allah in ɗan ganshi inji daɗi." Dariya tayi tace. "Hindu Duwaf amman kina yaudarar Gawata dan nasan in sama da ƙasa zata haɗe a gidanku baza'a taɓa bari ki Auri wanda ba ɗan boko ba kuma talaka ma. Yadda Baba Sojanmu yake girmama boko da masu karatun boko hmm wallahi ki kiyaye naga kunyi zurfi sosai shekara ɗaya kuna soyayyarnan ina jiye muku ranar rabuwarku. Kinsan fa a gidanku babu mai goya miki baya ki Auri ɗan cirani" Illahirin jikina sai ya mutu mus. Abinda duk Luba ta faɗa gaskiya ne sabida da wasa nasan ba za'a taɓa yadda da Gawata a matsayin surukin gidanmu ba, bana tunanin ma yayi karatu fa gaskiya amman zan tambayeshi. Abunda na sani shine duk runtsi duk wahala bazan taɓa yadda a rabani da Gawata ba, dan zan iya rasa raina. "Duwaf tunanin me kike yi ne haka? " Hmmm tunanin makomar wannan soyayya da duk wanda yayi yinƙurin rabata tamkar ya rabani da rayuwatane nake yi." Ƙarasowarmu bakin get ne ya katse mana hirar tamu gaishe da Baba mai gadi mukayi kasancewata ɗiyar malama Ruwayya yasa yake barinmu fita duk sanda muka zo kuma yana gani iyakarmu wajen Gawata ne ba wani wajen muke tafiya ba. Gawata na zaune a gaban teburinshi na kayan marmari yana shan lemo. Ganinmu ne yasa yayi murmushi idanunshi farare cike dam da farin kwalli wanda baya taɓa rabo dashi duk ya caɓe ya zazzago ( wa ya tuno da Yaya Hambali a daidai wajennan?)Rigace ƴar shara a jikinshi, na wani yadi mai ruwan kunun kanwa, ya goɗe harya gaji da koɗewa, sai dai tas dashi babu ko sofane na ƙazanta. Luba dai tace kwalline na asirin ƙifil shi yasa ma nake mutuwar sonshi. Amman sharri take yi mishi sabida bata sona dashi, ranar data soma faɗi nayi dariya harda fitsari. "Tutar so ta Gawata, ƴar makaranta barkanki da isowa. Luba sannunku da zuwa ga benci ku zauna" Bencin ya tashi ya bamu muka zauna shi kuma ya zauna a kututturen itacen dake fuskantarmu, yayi banza da kanshi wajen kallona. Masar na miƙa mishi dake leda taji ƙuli da albasa yasa hannu ya karɓa yana godiya. Sai muka zuba ma junanmu idanu, ni dai sai kallon ƙirjinshi mai tudu nake yi wanda a gaskiya yana daga cikin abinda ke burgeni gaya a tattare dashi. Murmushi yayi mun shima ya dubi ƙirjin nashi ya dawo da kallonshi wajena. Luba ta miƙe ta koma ciki ta barmu. "Ya shirye_shiryen biki Tutar so? " Anata shiryawa biki saura sati guda. "Allah ya nuna mana, gobe da rana zan shiga kasuwa in siyo miki angon in sha Allah da duk abinda ake buƙata. Amman Tutar so... " Nasan abinda zaka ce in sha Allah ranar biki zaka zo ƙofar gidanmu, daga lokacin zaka ci gaba da zuwa gida muna zance tunda na shiga SS2 saura shekara guda muyi kandi, ya kamata a san da zamanka." Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. "To aimun alfarma gobe da daddare inzo har gida in kawo miki ankon mana. Nasan unguwar taku wajen zuwanane acan nake saro kayan marmari. Kimun kwatance zanzo" Murmushi nayi mishi tare da mai kwatancen gidanmu. Saida aka buga ƙararrawa na tashi na koma makaranta. A haka muke zancan Gawata bai taɓa zuwa gidanmu ba tsawon shekara guda muna soyayya duk ranar da akace asabar da lahadi ne babu makaranta, tofa haka duk zan damu, danma yana rubutamun wasiƙa mai daɗi ranar Juma'a da'ita zan tawo gida, inta nanatawa, gashi ya mugun iya rubuta kalaman soyayya masu kaifi. Ranar da zamu yi hutu kuwa ba ƙaramin ɗagama Gawata hankali nake yi ba, haka zai ta rarrashina idanunshi duk suyi jawur a haka muke rabuwa. Ana tashi a makaranta muka tarkato Innarmu ta dawo damu, yau Juma'a ne babu islamiyya babu karatun dare na Baba Sojanmu, da wuri muke bacci. Wannan kenan To kun dai soma jin asalin gundarin labarin Mijinyawa mai lemo ko? Ina Ummin mama, da Fulani, da Mamanmu, da Mamanzee, da Maryama, na Munira. Mutumin naku ashe mai lemone a ƙofar Asiya Bayaro Mrs Bukharihttps://chat.whatsapp.com/JI1IGIBFHYm64hr6IfVfqR TSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA GOMA *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. Washegari da safe muna ɗakinmu muna karyawa su Yaya Saratu suna gwada kayan da aka karɓo musu na cin biki daga wajen tela. Ni kuma ina zaune inacin masa da aka saba kamar kullum, shi ne dai abincin karyawan babu ranar fashi kuwa. Jinjin kuma a tsaye take tana karatunta, Akarami kuma yana zaune yana kurɓar shayinshi. Muka jiyo muryar Inna Mairamu ba shiri Innarmu tace. "Ɗakko zanin gadonnan ku rufe kayannan, maza ke ciro ɗankwalin kanki, saida nace dama ku bari saida daddare ai kun san yanayin gidannan sarai" Da sauri Jinjin dake tsaye ta yayimo zanin gado ta rufe kayan. Babu sallama kuwa Inna Mairamu ta faɗo haka akeyi a gidanmu dan son ganin ƙwaf, kai gidan yawa ko babbar masifa. "Ruwayya barka da safiya, ahh amare ana karyawane? " Nan muka gaisheta kana ta miƙo mun ledar hannunta. "Duwaf gashi Qazzafi ne ya turo kuɗi aka sai miki kayan ango harda ma kuɗin ɗinki dana liƙi a ciki shine na kawo da kaina. Qazzafi dai ya dage wallahi kamar kamar wasa tun da ƙuruciya, mu mun ɗauka duk wasane to abu dai na shirin tabbata" Ƙin karɓan ledar nayi sai Akaramine ya karɓa yana mun dariyar mugunta. Innarmu tayi jim kafin tace. "Mairamu ni ina ganin da Qazzafi ya bar wannan hidimar ya samu soyayyar Hinduwa tukunna, sabida bana son rigimarki ba iyawa zanyi ba. Kar azo ana kai ruwa rana... " "Haba Ruwayya ai Qazzafi ba ƙashin yarwa bane menene a ciki ma dan yayi hidima da ƙanwarshi? Zasu daidaita ma tunda ai banga wani na zuwa wajenta ba. Karfa ki mance sabida Hinduwa Qazzafi duk falonnan naku yayi dabdalarshi, tunma ina hanawa harna miƙa wuya. Kusan kaf ƴan matan gidannan samarinsu sun sai musu Anko banda ita dake bata da kowa sai Qazzafin dai" Kallonta kawai nayi na kawar da kaina. "To shikenan angode kiyi mishi godiya" "Ai babu komai yima kaine Ruwayya" Daga haka ta fice abunta. Yaya Soja wanmu ne shima ya shigo ya taddamu su Yaya Saratu sai babbaka dariya suke yi akan Qazzafi da irin ƙarfin halinshi da uwarshi. "Innarmu wannan dariyar da yarannan suke yi ta meye harda Saratu fa? " "Uhm kaga wai Qazzafin Nagoɗi ne yayo ma Hinduwa anko ya dage ita yake so, ni dai har cikin raina bana son wannan haɗin yadda Mairamu take da gadararnan sannan mu ba zaman daɗi muke yi ba, waye baisan jaraba da tatarar jarfa a wajen Mairamu ba" Yaya Soja yace. "Ai a irin taurin Hindu da murɗaɗɗen halinta Soja ne ya dace da'ita ya kaita bariki ta koyi hankali, in allurarshi ta motsa ya jibgeta." Ai kuwa wallahi bana sonshi bazan taɓa saka kayan daya kawo ba sai dai aba Jinjin nima yau za'a kawo mun nawa ankon ai, da take cewa bata taɓa gani anzo wajena ba zata gani kuwa yau" Dariya suka kwashemun dashi ni kuwa ko gezau naci gaba da cin masata. Saratu ta buɗe kayan harda su ɗankunne da sarƙa da dubu uku na ɗinki sai dubu biyar na manni ƴan goma_goma sababbi. Ai kuwa Innarmu na gama karyawa ta fita da kayan ta zagaye gidan dashi tas tana nunawa hakan ya sake ƙular dani, da wannan ɓacin ran nakai har dare. Tun yamma na cancara ado nice harda shafe jikina da humrar Innarmu ba wacce muke shafawa ba. Yaya Saratu ce ta shigo itama taci ado wanda zata Aurane yazo. "Ke kuma sai ina kinyi zuchiya saurayi zai soma zuwa zance ne? Ai kuwa kinma kanki alamnashara in ba haka ba Qazzafi zaki Aura yarinya, gashi da rashin fara'a ko a cikin sojoji wallahi Qazzafi zai yi mugunta. Kuma duk bala'in Innah Mairamu haka zata zama surukarki" Dariya kawai nayi mata na gama shafe_shafena ina zaune ina jiran shigowar yaro. Ga isha ta kusa yau muna da karatu da Baba Sojanmu. "Assalamu Alaikum wai ana kiran Duwaf inji Gawata" Wani daɗine ya lulluɓeni ɗan halak yaƙi ambato ashe yana hanya. Ina jiyo Innarmu daga babban falo tana raɗa mun kira. Da sauri na fito riƙe da mayafina. "Maza kije ana kiranki kada ki wuce minti goma sha biyar" Maki take yi a littattafan ƴan makaranta inna Abida ta taɓe bakinta tace. "Qazzafin kuma ko yaya za'ayi dashi oho ni Abida. Lallai ashe akwai yaƙi da mairamu a cikin gidannan" "Saita tara rundunar yaƙinta ku kenan tun yanzu ai Abida sabida Hinduwa dai allurace a cikin ruwa mai rabone kaɗai zai ɗauka. Kuma ce miki tayi tana son Qazzafin ne ko ke zaki bashi tunda ai ƴarki ce ko? " Innarmu mafaɗaciyace bata da kawaici bare barin ta kwana kullum cikin rikici ake da'ita kuma tana yawan nuna musu gadara da isa sosai, domin tana jan zarenta kasancewarta mace mai ilimi cikin kishiyoyinta, gata da tattalin miji, kuma tana da kuɗinta daidai gwargwado ga koyarwa, ga kasuwancin sutura da take yi. Itace tilo a cikin iyaye mata dake aiki, itace mace tilo dake da ilimin boko, kana itace mace tilo mai mota a gidan. Gaskiya idanu yana kan Innarmu da yawa, koma ince idanun kowa a cikin gidannan a kanmu yake baki ɗaya. Ba ƙaramin hassada, da kishi suke yi da Innarmu ba. Gashi duk surutar da zata siya mana mai tsadace, mune yara na farko a gidan da muka soma saka zinare, hatta ɓulukan hancinmu zinaraine Innarmu ta saka mana, haka kunnenmu. Daga nan matan gidan suka soma siya ma yaransu suma. Akan ɓulin hancinmu kuwa ansha artabu da ɗauki babu daɗi. Su Innah Abida sune ƴan gaba_gaba masu cewa. "Ɓulin hanci duka ramukan hancin biyu sai kace wasu karuwai, wannan ai sai ayi musu mummunan fassara kisa a haɗa harda yaranmu." An sha gumurzu danma Baba Sojanmu tsayayyene sosai shi yasa maganar ma ta wuce. Ni dai ratse gidan namu nayi na fita. A raɓe a gefe can hagu da gidanmu na hango Gawata a tsaye da ledarshi baƙa yana saye, da yadi mai ruwan omo a jikinshi da hularshi tashi ka fiye naci, wasu na kiranta tashi ka fiye ƙwaƙwa ɗaya_ ɗayar hular da tun sanina dashi da'ita na sanshi. Ina ƙarasowa na jiyo ƙamshi turaren Alhaji Abdullahi a jikinshi yana tashi sai murmushi yake faman yi. "Tutar so Allah ya nufa yau gani a ƙofar gidanku, ina fatan wata rana ki kasance a cikin nawa gidan. Barkanki da dare, wannan shine karona na farko dana ganki ba'a kayan makaranta ba. Sai kika sake yin kyau zatinki ya fito sosai, ashe yadda nake hasashenki kin wuce haka" Dariya kawai nake yi mishi. Bamu jima muna hira ba yace. "Yana da kyau ki shiga gida, ga kayan ankonki nan da duk abinda za'a buƙata yana ciki kiyi haƙuri da kuɗin da zaki tsinta a ciki babu yawa a yi haƙuri." Mai yawan kenan akace kwabon masoyiya yafi nerar maƙiyi kuma ai nasan baka da ƙarfi. Amman zaka zo mana party da zamu yi ko, ko wacce saurayinta zai zo bana so a barni a baya? " "In kika gayyaceni ban isa inƙi zuwa ba. Allah ya nuna mana lokacin zan zo miki Tutar so in haka zai faranta miki kuma zai fitar dake" Albishir ɗin da zan zanyi maka daga yau kaci gaba da zuwa gidanmu zance, lokaci yayi da ɓoyeka zai iya haifarmun da matsala Gawata. Amman duk sanda zaka zo dan Allah kazo ana idar da magriba sabida bayan isha muna karatu da Baba Sojanmu" Yayi murna sosai fiye da yadda nake tunani. Ana kiran sallah yaimun sallama yace zai tafi in yayi sallah zai koma inda yake kwana sai kuma gobe in yazo. Naso in tambayeshi ina yake kwana dan wallahi bansan a inda yake kwana ba sam. Da murna ta na shiga gidan saina tarar ana ɗauki babu daɗi da Inna mairamu da Innarmu ga kayan da Qazzafi ya kawo har Innarmu ta watso mata su suna gabanta a barbaje. "Ga tsiyarku nan. Hinduwa ma ba zata taɓa auren Qazzafi ba ko da tana sonshi, ai ƙaddarace kaɗai zata sa ai surukunta dake Mairamu, matan da zasu zo a surukanki ma wallahi abun a tausaya musu ne" "Lallai Ruwayya kin samu waje dama ai kin riga kin shanye har Soja ballantana Su Abida da kika maishesu ababen takawarki. In sha Allah sai Qazzafi ya cika burinshi na auren Hinduwa domin ɗabbaka zumuncin da burinki kiga ya ruguje. In kuwa bata aureshi ba abadan ba zata samu kamarshi ba in sha Allah. Mata sai girman kai da ɗaga ma mutane kai sabida kawai kina koyarwa a kanki aka soma koyarwane, ko a kanki mace ta soma fita aikine" Innarmu tace. "Ko ba'a soma a kaina ba, a gidannan dai a kaina aka soma. Ilimin da nake dashi kuke ma baƙin ciki, kuma wallahi na shige da saninku, ko yanzu aka ƙara mata ƴar boko a gidannan sai dai ace itace ta biyu bata ɗaya ba. Wawuya jahila" "Yayi kyau Ruwayya matar wan nawa kike kira da Jaliha ko? " Cewar Baba sojanmu daya iso shi da Baba Nagoɗi da Baba Lukumanu. "To ita Mairamun ba ita tazo ba duk abinda akayi mata ai ita taja. Ke Hinduwa shige mu tafi ciki" Innarmu taja hannuna muka shige ciki. Ina jiyo Baba Sojanmu na faɗa da hargagi a falon an rasa mai tanka mishi. "Allah ya kyauta, Mairamu kwaso kayan muje. Tunda yarinya bata son Qazzafi sai yayi haƙuri ai. A gidannan ba'a Auren dole kuma kinsan dai Soja bai isa da Ruwayya ba illar Auren ƴar bokon kenan shi ya kasa ganewa burinshi ayi boko ayi boko, duk ya mayar mana da yara ƴan boko ya hure musu kunne suma bokon suka fi so, gasunan duk a wahale sunata sunturin zuwa makaranta" Cewar Baba Nagodi kenan. Mairamu ta tattare kaya da kuɗin tabi mijinta suka tafi. Mu kuma Baba sojanmu ya soma kiran a fito ayi karatu. Littattafaina na ɗauka na fice abini. Nan nabar Innarmu na ƙirga kuɗin da Gawata ya zubo a cikin ledar dake na fasa asusuna na ƙara kuɗin a cikin ledar a zatona ba wasu kuɗin kirki ya sako ba, ashe kuwa yayi bajinta. Sai da muka gama karatunmu muka dawo ciki Innarmu tace. "Dubu goma cib ya zuba miki a ciki Hinduwa gaskiya yayi ƙoƙari sosai ya fitar dake kunya sabida babu ƴar da aka saka mata dubu goma. Ga takalmi da mayafi harda ɗan kunne da sarƙa da kayan kwalliya duka ya saka. Rigar mama da gwari na tsuma da ɗan kamfai kawai zan sai miki gobe ki tarkata kayan in an nuna ma matan gida ki kai gidansu Luba ɗinki." Bayan mun hallara a tsakar gida Baba sojanmu ya kama koya mana lissafi muna zaune muna aikin daya bamu ga fitilu irinna sojoji masu bala'in haske an kange kowanne ƙoƙarinshi ya amsa tambayoyi biyar ɗin da Baba Sojanmu ya rubuta. Muna rubutun ina jiyo hatsaniyarsu da Innarmu lallai ranta ya ɓaci dan bata fiye ɗaga muryarta a saman na Baba Sojanmu ba, mun dai san ba kanwar lasa bace shi kanshi Baba Sojanmu na kiyaye rikici da'ita. Nasan fishinta na da nasaba da maganganun da Baba Nagoɗi ya yayyaɓa mishi a gaban su Inna Abida. A fusace ya fito ya sani aikin karɓan takaddun kowa akan gobe da daddare in anyi maki za'a babbamu. Mun shiga zamu kwanta muka tadda Innarmu sai faɗa take yi a tsaye hancinta har hunhuna yake yi tsabaragen faɗa. Washegari ma da sabon rikicin dai aka kuma tashi sabida Innarmu ta zagaya ta nuna abinda Gawata yayi kamar yadda kowa yayi, nawa sai ya zama gutsiri tsoma ni nama tafi gidansu Luba kai ɗinki Ashe har rirriƙe Inna Mairamu aka dinga yi wai zata daki Innarmu sabida tace in duk maza sun ƙare bazan auri Qazzafi ba. Shine tace mai zaiyi dani gajera dani mai kama da agwagwa wajen gajarta kuma wai mummuna. Na riƙe wannan maganar sosai dan a kunnena ta dira ni kuma nayi alƙawarin in dani da Qazzafi ne kaɗai mutane da muka rage a duniya saidai mu mutu a haka ina da riƙo sosai da rashin mantuwa, sai dai zan yafe in an matsamun a hakanma ba komai nake iya yafewa ba. Haka dai wunin ya kasance Innarmu tana ta girke_girke ga fenti anayi mana na lungunmu da duka ɗakunanmu dan baƙin Biu ma suna hanya yau dangin Innarmu haka akayi dasu zasu iso sabida su taimaka ma da Innarmu wajen hidimar siyayyan kayan ɗakin Amare Baba Sojanmu da safe ya basu abinda yake a hannunshi na kayan katako da duk abinda ya dace uba yayi mai son yin bajinta saita cika, ya ɗakko atampa da shadda ya ba Innarmu yaba Inna Abida, kayan Kitchen dama iyaye ke yi. Innarmu ta jima tana tarinta a ɗakin Innarsu Luba ƙarƙashin gadonmu da saman sib ɗinta cike da kayayyaki. Saman sib kuma zannuwan gadone masu bargo shaƙe da buhu biyu. Wajajen magriba sai ga dangin Innarmu su Inna Yahanasu da Inna Yalewa da Inna Hewa. Dukkansu ciki ɗaya suka fito da Innarmu kuma a Biu suke Aure sai Inna Hewa dake aure a chad tana Auren hamshaƙin mai kuɗi. Abin daɗin shine dukkansu da iliminsu kuma suna aiki. Ai gida kam ya soma ɗaukar haramin yare dan dai a falo suka bace sukaita yara yaren kanuri anayi ana dariya ga biski da miyar margi Innarmu ta tarbesu dashi. Ana idar da sallah yaro yazo yayi kirana na sulale na fice. Mun daɗe sosai da Gawata muna hirarmu a tsaye cikin jin daɗi da kwanciyar hankali. Kayan marmari da balangu ya kawo mini harma muka isa inda Luba suke zance da Sunusi suka gaisa kana Gawata ana isha yai mun sallama ya wuce. Gidanmu ya ɗauki haramin ƙamshi fa washegari aka soma yi ma amare gyaran jiki namu na al'ada, su Innarmu da Inna Yalewa kuma suka shiga kasuwa ganin kayan gado wanda tunda aka kawo sadakinsu Yaya Saratu Innarmu ta bama kafintan aikin kayan gadon. Kafin su dawo Ƴan kwantagora da su Zaria ne dangin su Inna Mairamu da ƴan kaduna, katsina sukaita zuwa gida ya cika ya tumbatsa sosai. Ranar sakun lalle aka zaɓi masu zuwa jere ai kafin washegari ranar ɗaurin aure maƙota da ƴan cikin gida sai tattauna irin kayan da akaima su Yaya Saratu akeyi, gaskiya Innarmu akwaita da ƙoƙarin fidda ɗa kunya ko da kuwa bashi zata ciyo dan ko sallane ana azumi saura wata biyu ta game mana ɗinki an goge an adana kuma kaya masu tsada. Munyi daban sosai da yaran cikin gidan namu. Ga Baba sojanmu in dai zaka yi karatu sakamakon jarabawarka zata yi kyau to zai iya maka komai sabida yadda yake son karatu. Shi yasa su Yaya Saratu duk ƴan boko zasu aura. Ranar Juma'a aka ɗaura Auren ƴan mata gomannan rigis anata zolayarmu akan muma ba zamu shige shekara huɗu a ƙasa ba sabida mune masu tasowa. Sai rawar kai sa'annina suke yi masu neman suma su samu suyi saurayi. Tun ranar laraba muka wayi gari da ƙunshin gargajiya da Inna Yalewa tayi mana. Tare da Amare kitso ma su sukai mana guda ɗari da hamsin akayi mun irin kitso na al'adar kanuri wanda wasu zasu yi baya wasu zasu yi gaba gefe da gefe na amare dai yafi namu siri_siri shine bambancin, ragowar Amaren kuma gidajen kitso da gyaran jiki da lalle suka je. Biki yayi biki ƙawayen Innarmu malaman makaranta da lauyoyi duk sunzo sun kuma bata gudunmawa sosai kasancewarta mai yi ce sosai itama. Abincin da akayi a ɗakinmu kala uku akayi saɓa'in ƴan cikin gida daga masu shinkafa da miya sai masu fate, da masu yin jalof da kifi haka Amman mu munyi masa, munyi tuwon shinkafa da miyar taushe, mun yi burabusko da miyar margi wanda akayita da kifi karfasa ɗanye tillafiya kenan. Bayan ɗaurin Aure da yamma muka wuce wajen walima. A wajen walima ma mun raba masa, da cincin, da abinci harda tsokar nama sai jus. Ana tsaka da walimar Luba ta taɓani na juyo muka haɗa idanu. "Gawata yana waje yazo tun ɗazu kizo muje muna waje da Sunusi ne. Da sauri na miƙe da leda biyu a hannuna wanda nayi mishi zubi na musamman. Tun daga nesa muke jifan juna da kallon_ kallo kafin in ƙarasa inda yake sai kawai naga Qazzafi a gabana yana mun murmushi yana saye da kayan sojijinshi da anininshi biyu. "Giwar mata wannan irin kyau haka sai kace ranar bikinmu gaskiya kinyi kyau sosai sai ƙamshinku na al'ada kike yi wanda yana daga cikin abinda yafi ɗaukata, amman a cikin abubuwan da suka ja ra'ayina harda gajartannan taki wacce ta dace dake" Kallonshi nayi nace. Yaya Qazzafi yaushe ka dawo? " "Yau na dawo dani aka ɗaura Aurenma. Ina zaki je kike gaugawa haka? " Baƙone dani bari inje in sameshi kada yaga kamar nayi mishi wulakanci " Kafin ma yayi magana nayi gaba zuwa wajen mijinyawa yana saye da yaji mai masifar arha da wannan nacacciyar tashi ka fiye nacinnan dai da baya sauyata. "Barka da isowa Tutar so. Tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya tsara wannan halittar. Tutar so wato wannan gajartar taki da yanayin yadda zubin zatinki yake bazan ɓoye miki ba dole ya ɗebi hankalin duk lafiyayyen namiji, kitsonnan yayi mun kyau ina fatan in dinga ganinshi a kanki ko da yaushe idan munyi Aure" Gawata kenan kalamanka suna mun daɗi sosai. Sai inji na sake son wannan gajartar tawa da wasu mutanen suke amfani da'ita wajen zagina basu san da Allah suke yi ba ni Hindu menene nawa tunda haka Ubangiji na yaso ya ganni. Gashi sai Allah ya bani dogon miji ingarma" Murmushi yayi ya dube kanshi yana kallona. "Na fahimci kamar yadda jikinki yake burgeni kema haka jikina yake burgeki musamman ƙirjina ko? Kada ki damu zan kula miki dashi zan ci gaba da ɗaga ƙarfe, wannan ɗinma a ƙauye ne da bamu da abun yi shine muka saka kanmu wannan aiki ni da su Abdulƙadiri" Yauwa ka tuno mun ni kam menene matakin karatunka naga dai ka iya rubutun hausa sosai kuma ina yawan ganinka kana karanta littatafan yaƙi, kwanaki ma na ganka da littafin dare dubu da ɗaya" Yana wasa da zoben azurfan hannunshi yace. "Iyakata makarantar sakandare na kammala ta gwamnati a ƙauyenmu iyakar matakin karatun nawa kenan a hakanma mun samu, karatun ma sai a hankali an dai kammala" Banji komai a raina ba sai jinjina yadda zan bayyana Gawata a matsayin miji. Ni dai a wajen soyayya na lalace har aka tashi a walimarnan bashi ledar walimar nashi, nabi ayarin ƴan gidanmu muka koma gida. Da daddare a gidan Yaya Saratu ni dai na kwana ragowar suna gidan Yaya Zubaina Washegari aka yi wunin biki shikenan taron biki kuma ya ƙare. Bayan kwana biyu da gama biki baƙi duk suka watse mu kam dama tun monday muka koma makaranta. Qazzafi yaso in bashi lokaci na amma naƙi fur na dinga mishi yawo da hankali. Sau uku yana ganina da Gawata a ƙofar gida muna zance a haka hutunshi ya ƙare ya koma bariki a kudu yake. Gaga_gaga A haka har Watan Azumi ya tsaya ga karatu, ga rana, ga azumi. Ƴan matan gidanmu samarinsu suka soma musu bajintar azumi Gawata ma yayi mini daidai ƙarfinshi ba'a raina ba, duk da dai Innarmu ta ɗanyi ƙorafi kaɗan, a hakanma bata san wasu abubuwan ni na ƙara ba. Da sallah yayi mun atampa da shadda da takalmina sukos ja mai kyau da jan mayafi. Haka dai tafe_tafe. Sannu sannu ar mun zana jarabawarmu ta ƙarshe a makaranta mun bar makanta muna murna kamar yadda sauran ɗalibai ke murna. Bamu cika sati ɗaya da gama karatun ba Baba Nagoɗi yasa aka tarkato kawunanmu kusan mu goma muma. "Ko wacce cikinku ta turo mana wanda take so zuwa jibi mu ganshi mu yi mishi tambayoyin daya dace, ayi bincike a kanshi kafin manya su shigo ciki, batun ci gaban karatunku kuma, Soja ya tsaya muku, sai kun soma jami'a za'ayi Auren kuma bai ɗaura nauyin karatunku akan mazajen da zaku aura ba. Shi yaji zai iya zai dinga biya har ku kammala, shi yasan cukurɗa kurɗar da zai yi aikinma ya samu in kun kammala karatun. Ko a cikinku akwai wacce bata da tsayayyene? " Duk mukai shiru ko wacce tana da masoyinta. Baba Dogara yace. "Ko wacce tana fita zance, kayan azumi da samarin suke kawowa ai yana isowa kunnuwanmu." Baba Sojanmu yace. "Ni naso a barsu su soma jama'a ko matakin na uku ne sai suyi Aurensu sa ƙarashe a gidajen mazajen nasu, kada ayi sharaɗi da wani ya saɓa amman in sun riga sun soma sun yi nisa kaga ba zasu hana ba. Kamar dai yadda akayi dasu Saratu gashi Sunci gaba da karatunsu ga goyo ma abinsu wannan shekarar zasu kammala. Ni kar azo ana rikici dani da surukaine dan wallahi kunji na rantse wallahi sai sun yi karatu kuma sai sun yi aiki. Gara ku sani tun wuri fa" Hannu Baba Nagoɗi ya ɗaga mishi. "A_a kaga waɗannan sunfi su Saratu girma da rawar kai Hinduwace kaɗai bata wannan farfar irin nasu gara a Aurar dasu karatun sayi a ɗakin mijinsu, duk wanda yaƙi amincewa sai ya tafi wani yazo ai sharaɗi za'ayi" "Ai ko ya Aureta daga baya yaƙi karatunta sai dai su rabu bazan zuba idanu a danne musu hakkinsu a dankwafar da rayuwarsu daga ɗaki sai tsakar gida ba. Ina kai ai ya waye sosai yaushe zan ɗauki wannan iskancin ni" Kai kawai su Baba Nagoɗi suke ta girgizawa dan basa tare da irin ra'ayin Baba Sojanmu na tsaurin karatu da kallon wanda baiyi karatu ba a matsayin ba mutum ba. Da sunyi magana yace dan basu san daɗin karatun bane. "Ku tashi kuje an sallameku, ke Hindu banda ke Qazzafi a shirye yake tuni ya gama haɗa kayan akwatinshi ma" Take idanu suka dawo kaina, girar sama da ƙasa na haɗe baka isa gane yanayin da nake ciki ba. Nasan babu wanda zaimun Auren dole Ƴaƴan maƙotama da za'ayi musu Baba Sojanmu yayi uwa yayi makarɓiya yasa a fasa bare kuma ɗiyarshi? Duk bazawara a unguwa da aurenta ya mutu zai ɗauketa ya maidata makaranta yace tayi ilimi tafi ƙarfin wulaƙanci zata fi daraja. Gaskiya yana ƙoƙari ina girmama ƙoƙarinshi sosai. Yaran unguwa da yaga yaro na gararanba sai ya sashi a makaranta yana alfarmomi a wajeje da dama. In saurayine kuwa to soja sai jefa mutum yayi tirenin shikenan. Zaurawa unguwa da sun gama idda zasu zo har gida su sameshi, sai mayar dasu kamaranta, ya nema musu aikin yi. Kuma cikin ikon Allah sai su yi aurensu rayuwa tayi musu kyau. Ya sauya rayuwar al umma da yawa. Madallah da tsayayyen uba. Washegari Gawata na zuwa na sanar dashi saƙon ana nemanshi, zuchiyarshi cike da murna tawa cike da fargaba dan nasan matakin karatunshi shine zai haifar da matsala, ni kuma akan wannan bazan canja ra'ayina ba tunda dai ni zan zauna dashi ba kowa ba, kuma yayi saukar Qur'ani shi ba jahili bane. Ranar da aka yi kiransu wasu sun iso kafin isha wasu kuma sai bayan isha suka ƙaraso. Kusan dukka samarin tara ko wanne ya mallaki abun hawa kasancewar ƴan bokone aiki suke yi Gawata ne kaɗai yazo a Bus. Duk suka hallara a babban falon Baba Nagoɗi, Baba Sojanmu har da littafi da biro sabida yaji daɗin rubuta abinda za'ayi. Tun jiya yake ta rubuta tambayoyin da zai yi musu da sharuɗa. Ni dai ina ɗaki a kwance ina jiran sakamako. Mra BukhariFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F5JwhdwbtCQ6qdo4LA4kyE TSURON TSIRIN... TSANDAURI LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA GOMA SHA ƊAYA *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. Sun jima sosai dan sunfi goman dare suna abu ɗaya, Baba Sojanmu gaskiya bayayin ta daɗi. Nasan sai da safe kuma za'a neme mu koma menene Lokacin zamu ji. Wajajen goma da arba'in bacci ya soma ɗibata muka jiyo muryar Baba Sojanmu yana ta zage_zage da turanci ranar ba hausa halamun ɓarin rai mai tsanani kenan in muka ji yana zuba turanci. tom yau dai nasan lallai ranshi ya ɓaci a zafafe ya shigo ɗakinmu Innarmu ta miƙe da sauri Matsar da'ita gefe yayi yasa hannu ɗaya ya fincikoni a maulidi, sai gani a ƙasa a gabanshi. Duka ya rufeni dashi yana tattakani da ƙafarshi da dukkan ƙarfinshi yake dukana, ni kuma inata kwarmata ihu. Bel ya zare ya dinga labtamun tako ta ina inata ihun ceton rai dan wallahi dukan sa'a yake yi mun, kuma duk wannan dukan babu ƙidon hawaye a idanuna sai dai idanuna sunyi jawur a halittatane da wuya abu ya sakani kuka zuchiyata bata fiye tsinkewa ba ina da dakiya da jarumta sosai gaskiya. Cikin ƙanƙanin lokacin aka taru a ɗakinmu Innarmu na zaune a bakin ƙaramin gado ta hau tayi fam, magana wannan bata yi. "Wai lafiyarka ƙalau kuwa Ganaral ka saki yarinyarnan haka in ba kasheta zaka yi ba, da ƙarfi irinna sojoji zaka daki Hindun" Cewar Baba Dogara da ya rirriƙe Baba Sojanmu da ƙarfinshi na gidan soja ya fincike da ƙarfi sosai. "Ai gara in kasheta data kasheni da baƙin ciki kai kaga komai a kan idanunka komai ya faru, yaro bazai kasheni da baƙin ciki ba, sai dai shi ya mutu" Da turanci irin manyannan fa yake magana yaƙi hausa fur. Buɗar bakin Innah Abida sai cewa tayi. "Ciki tayo ne hala? " Wannan kalmar ta girgiza zukatanmu ni da Innarmu amman dake a cikin maɗaukakin fishi take bata tanka ba amman martani dole ne kamar cin bashine da ko ka mutu sai an biya maka. Baba Nagoɗine ya balbaleta da faɗa duk ya kori matan da suka cika falonmu suna son jin gulmar me ya faru. Baba Lukumanu ne ya fito da Baba Sojanmu yana ta gwarancensu na sojawa. Ina durƙushe na kasa ko da tashi ne jikina yayi laushi kuma ya farfashe. "Tashi Hinduwa koma me kikayi baki cancanci duka haka ba. Bari ina zuwa" Fita tayi sai gata da ruwan ɗumi da tawul ta dawo a bakin gadonmu ta zaunar dani ta gasamun jikina a Lokacin zazzaɓine kau a jikin wanda ita kanta saida ta tsorata, a darennan a kaina kusan duk ƴan falonmu suka kwana makarainane suka motsa irin motsawar da basu taɓa yi ba, a da basa magana sai dai su rabkeni in ta shan wahala amman a wannan rana sukaita zage_zage da alwashi iri_iri sukaita bige_bige da fisge_fisge dan da ƙyar aka iya danneni. Shi Baba Sojanmu bai yadda da makarai ba. Ko kuma ince bai yadda makarai na shiga jikin mutane ba, tunda duk musulmi yasan akwai Aljanu tunda sura garesu sukutum a Qur'ani, kuma su suka soma zama a duniya kafin bil'adama. Baba Lukumanu ne suka rufu a kaina akaita mun adda'a ana tofamun kafin suka lafa na samu bacci bani nasan me nake ciki ba sai bakwai na safe. Fuskata ta kumbura sosai abun tsoro da Innarmu ta fito dani zanyi alwala sai da hankalin kowa ya tashi harda Baba Sojanmu dan hatta kaina saida ya ƙara girma baka isa kace nice ba. Amman Baba Sojanmu dakewa yayi, ya nuna ko a jikinshi sai turanci yake yi. Alwalarma yi mun akayi na dawo nayi sallah a zaune. Jikina babu daɗi sam, matan gida sukaita shigowa dubani tare da jajanta abinda ya faru. Da Innah Abida ta leƙo tana gaisheni da jiki banza muka yi da'ita har ta saki labulen ta koma. Jamila ce tayo sallama ta leƙo. "Innarsu Saratu ana nemanki dake da Duwaf a falon Baba Nagoɗi" "Jeki gamunan, Hindu zaki iya rarrafawa muje ko inje ni kaɗai? " Ni ba raguwa bace duk irin ciwon dake jikina da irin yadda makarai suka luguiguitamun gaɓɓai baisa na sare ba nace. Zan iya Innarmu" "Rayya kamo ta ku tawo ni bari in yi gaba" Miƙewa tayi ta fice mu kuma muka fito a hankali sai kallona akeyi a cikin gida kai tur da gidan yawan daya haɗa haula iri da kala. Masu mayar da ƙaramar magana ta zama babba. A cike falon yake babu ma masaka tsinke dan da ƙyar muka kutsa na rakuɓe a jikin Innarmu. "To maƙasudin wannan taron akan bikin waɗannan yaranne. A gaskiya mutum takwas daga ciki yarane na sanannun mutane anan cikin garin Kano face Saurayin Jamila daya kasance ɗan Gombe bamu da masaniya akan asalinshi amman yana da mastas ɗinshi ma aiki yake yi anan garin Kano. Sai kuma shi wanda Hindu ta rakito yace ɗan ƙauyen jama'are ne amman asalin iyayenshi daga Jimeta suke jihar Adamawa. Kuma lemo yake saidawa shine sana'arshi. Matakin karatunshi yayi sakandare ta ƙauye shikenan, dan tambayoyin da Soja yayi musu da turanci. A gaskiya bai amsa ko ɗaya ba, yace baya jin turanci sam" Nan ɗakin ya hau hayaniya da ƙus_ƙus. Innarmu tayi mun wani irin mummunan kallon da saida nasha jinin jikina ba shiri na ɗan muskuta daga kusa da'ita. "Sabida haka ita Hindu an soke Aurenta da Gawata zamu haɗata Aure da Qazzafi wanta shi yafi cancanta da'ita. Yarannan sati mai zuwa iyayensu zasu tawo mu gana zamu tsayar da lokaci amman bazai ɗauki lokaci ba ku zauna da shirinku kawai. Kuma sun amince ba batun karatu da aiki da Soja ya sharɗanta musu. Da sharaɗin ko gaba suna son yin mastas ko phd zasu basu dama, duk kuma sun amince kasancewar suma daga gidan boko yawanci suka fito" "Ina da magana. Ban yadda da wanda Hindu ta kawo a matsayin miji ba hauka tayi ma shi yasa ta kawo mana shi sabida rashin hankali. Amman kuma ban yadda ta auri Qazzafi ba. Babu ta yadda za'ayi a haɗa wannan Auren wallahi" Cewar Innarmu dake yinƙurin tashi. Baba Sojanmu yace. "Sabida ke kaɗai kika haifeta ko? " "Ko bani kaɗai na haifeta ba ina da hakki nima a kanta. Banga abinda zaisa ka shiga lamuran yaran maƙota ka ƙwato musu hakkinsu ba. Sai da yazo kan ɗiyarka kace ba zaka tsaya mata ba. Ba wanda za'aima Auren dole ehe nasan rait ɗina kuma ina da rait a matsayina na uwa" Ficewa tayi fuuu ni dai ina zaune tsamo _tsamo dani. "Ai kaga illar bokon da aketa nuna maka baka ji. In banda Ruwayya cikin matanka wake maka wannan fito na fito ɗin? Babu sabida su ƴan boko daka taɓasu zasu ce sun san ƴancin kansu suna da hakki. Ke kuma Hinduwa kinga abinda kika jawo mana akan wani bagidajen ɗan ƙauye tantagarya." "Hmmm ai kamar yadda Ruwayya ta nuna ƙin kinina a fili to muma mun fasa auren sai dai a haɗata da wani a gidan ga samarinan iri da kala a cikin gidan kuma ko wanne da iliminshi" Wani kallo da Baba nagoɗi yayi mata ai ba shiri ta kame bakinta. "Kuje an sallameki" "A_a Baba kuyi haƙuri ku bani Gawata wallahi shi nake so mutuwa zanyi in ba'a bani shi ba. Qazzafi bana son shi" Salati falon ya ɗauka kawai ni kuwa ko gezau iyakar gaskiyata nake faɗa dan yanzune na ɗaura ɗambar son Gawata." Miƙewa Baba Sojanmu yayi aka yi saurin riƙeshi. A daddafe na shige ɗakinmu na kwanta Innarmu bata ɗakin sai Yaya Saratu da suka zo babu mamaki sunji labarin abinda ke faruwane. Luba ce ta shigo a sanyaye bayan sun gaisa da su Yaya sai akai kiransu suje Inji Baba Nagoɗi. Suna fita Luba tace. "Kinga abinda nake ta jiye miki ko Duwaf? Dama nasan babu mai ƙaunar Gawata a gidannan inata jan kunnenki ƙin ƙi ji dama taurin kan tsiyane dake. Jiya ihunki har waje duk unguwa ta ɗauka anata surutai iri da kala. Gawata bai daɗe da barin gidanmu ba Hinduwa ya bani takadda yace in baki, yazo tare da abokinshi mai lemo dake sana'arshi a cikin kasuwar ƴan lemo." Me yace miki Luba? Kinsan Allah sai dai a kasheni ko in dauwama babu Aure in basu bani Gawata ba." "Na sanki da taurin kai ai. Takadda ya bani in baki yace mun shi ya koma garinsu baki ɗaya" Ai sai ganina nayi a zaune daɓas. Takaddar na fiske na buɗeta. "Hindu duk duniya in sun taru ba zasu iya raba wannan ƙaunar ba. Allah shine masanin abinda ke sama, kuma shine masanin abinda ke ƙasa, dana ƙarƙashin ruwa. Shi ya halicci zuchiyar dake gaban ƙirjina Hindu sonki rayuwatane ƴan gidanku suna son kasheni sunce ba zasu bani ke ba Hindu, sunce ilimina bai kai ba, ni baƙauyene, talaka kuma. Hindu ina sonki har abada amman kiyi haƙuri na koma garinmu sabida in nisanta dake in yi jinyar dundumin sonki. Gawata ne naki mijinki na har abada" Yawu na haɗiye na duƙunƙune takaddar na kwanta ina nazari. "Baki ce komai ba Hindu kin kwanta"? Luba kinga bani da lafiya zan rubuta miki saƙo da kuɗi dan Allah abokinshi ya taimakeni ya san yaya za'ayi saƙon ya isar mishi, inya haura kwana bakwai da kaina zanje garinsu Gawata kuma inna tafi na tafi kenan har abada bazan taɓa dawowa ba." Baki Luba ta rufe mun. Motsin shigowar Innarmu ne yasa mukai shiru. Zama tayi tana fuskantarmu. "Ke Luba ina Hindu ta haɗu da ɗan iskan yaron data kawo mana nasan kinsan komai ko ki yi magana ko in haɗa dake in dakaku? " "Mai lemon dake ƙofar makarantarmu ne Innarmu" "Ke ban gane me kike cewa ba. Mai lemon zaƙi na ƙofar makarantar da nake koyarwa shine dama duk tsawon wannan lokacin yake zuwa wajen Hindu? Amman Hindu baki da hankali baki san abinda yake yi miki ciwo ba ke yarinyace ƙarama shi yasa. Ina ke ina auren jahili ace mijin da kike son Aure sakandare kawai ya gama a gidannan kuma kike ganin zamu amince? Har abada wallahi babu ke babu shi ki nemi duk wanda kike so banda wannan yaron" Shigowar su Yaya ne yasa Innarmu tayi shiru sai Yaya tace. "Akwai abokin mijina daya nuna yana sonta sai nace mishi tana da wanda take so. To ko shi zanyi ma magana ne kawai ya turo tunda dama a shirye yake. Ma'aikacin hukumar fasa ƙwauri ne yana jibiya amman iyayenshi mazauna Kano ne" Innarmu dajin haka ta yi na'am harma hankalinta naga ya kwanta. Nan suka fita suka barni ni da Luba na yagi takadda na rubuta saƙo na bata ta kaima abokin Gawata. Ai kuwa tana dawowa take sanar dani saƙo ya faɗa inda akeso ya faɗa domin akwai bawan Allahn da gobe sassafe zai tafi Jama'aren kuma basu da nisa tsakaninsu da Gawata. A wannan ranar haka aka wuni ana abu ɗaya a kaina har rubutu Baba Nagoɗi daya dawo da yamma ya karɓo mun da na sha ne ma na samu salama har nayi wani irin baccin da sai da safe na farka tun shidan Yamma shima fa tashina ma akayi. Sai suka ga na yi fari na saɓe wannan kuburin sai ya zo da rama sosai idanuna kuma suka jujjuya ya zama kamar mai harari garki wallahi. Makarai sukaita sauya mun halittata kamar almara. JAMA'ARE:. Da yamma sakaliya Nanno na gaban murhu ita ke da tuwon dare ranar kishiyoyinta duk ko wacce tana ƙofar ɗakinta suna aikace_aikacen dake gabansu dai. Kwatsam sai ga Gawata da buhun kayanshi. "Ahh Gawata ikon Allah ai kuwa Nawata yau ɗinnan ya koma ɓoto yazo kusan satinshi biyu kai kuma sai gaka yau" Cewar Inna kenan kishiyar Nanno." Tsugunnawa yayi har ƙasa cike da ladabin mutan ƙauye ya gaishe da iyayen nashi. Nanno tace. "Shiga daga ciki bari a kawo maka fura yannzu akwai wacce Bala ya rage" Miƙewa yayi yana sosa kai ya shiga ciki. Gadone guda biyu a ɗakin lamba wan da kuma bono ya sha shinfiɗar zanin gado mai ɗawisu, ga kwaba bango guda shaƙe da jeren samiru da tasoshi an lulluɓe bangon ɗakin da kwatin ga kwatin bot zagaye da ɗakin jere da takalman masu ɗakin. Ƙasa leda ce shinfiɗe sai alkuki da aci balbal a kai. Jingina yayi da jikin bangon ɗakin yana jin babu kuzari da ɗanɗano sam a bakinshi. Ko wanne hali Hindunshi zata shiga in wasiƙarshi ta isan mata oho. Yasan yana ma Hindu so mai girma, amman da kanshi yasan yadda take son shi yafi yadda yake sonta. Amman yana ganin sai dai suyi rayuwarsu a matsayin gwagware babu Aure domin babu rabuwa a tsakaninsu. Basu soma dan su bari ba, tunda iyayenta sunfi fifita iliimin boko fiye dana addini yasan ba zasu iya bashi Auren Hindu ba. Dama Qasimu ya faɗa mishi gaskiya Dundumin so ne kawai ya makantar dashi. Nanno ce ta shigo da kwanon sha ta ajjiye a gaban Gawata. "Mijinyawa lafiya kuwa na ganka babu kuzari sam a jikinka, ko wani abun ya faru a binni ne? " "Babu komai Nanno gajiyace sai rashin jin daɗin ganawar da bamu yi da Nawata ba naji haushi sosai." Kwanon shan ya buɗe ya saka ludayin duma ya soma shan furar. Duk son shi da fura ɗaci yau take yi mai. "Mijinyawa faɗamun gaskiya ko dai saɓani kuka samu da yarinyar da kake nema ne? Kaga dama jiranka nake yi ka zo muyi magana. Nawata sun daidaita da Uwatale muna shirin saka rana tunda Allah bai yi dakai za'ayi ba, amman dole tare za'a haɗaku a Aurarku zaifi ga waje nan sai ku yanka ku soma ginawa tun wuri." Ɗagowa yayi ya dubi Nanno yace. "To matsala aka ɗan samu daga gidan nasu. Amman in sha Allahu zamu shawo kan matsalar Nanno. Ni zanje masallaci daga nan zan wuce wajen Qasimu ya kaini gidan Yaya Jamila mu gaisa tunda ita a kusa take. Su Shafa kuma gobe na zazzaga. Banga Auta ba tunda dai na shigo gidan? "Autar Nanno. Tana can gidan Yayar taku dake ta haihu jiya tana taimaka mata da riƙon shi Habu ɗin tunda shekararshi ɗaya ne kawai" Kai ya jinjina kawai ya fita. A masallaci ya haɗu da abokan nashi bayan an isar da sallah suka dawo ƙasan bishiyar dirimi suka baje. "Gawata na Hindu bada kanka a sare kaje gida kace ya faɗi. Ya Hindun take to? " "Jazuli baka da dama. Hindu tana ƙasan zuchiyata a kwance lub" Dariya suka kwashe dashi Ashiru yace. "Baka da dama Baban soyayya ina mamakin a inda ka iya soyayya" "Ahh ka mance dai. Shi da yake karanta littafan yaƙi harma dana soyayyan. Su wannan littafin me yake da suna? Soyayya tafi kuɗi na Hadi Abdullahi Alkanci Su kulɓa na ɓarna na Umaru ɗanjuma katsina Su kwabon masoyi Su in da so da ƙauna na Ado Ahmad gidan dabino Duk fa ya karanta jiya nima na soma karanta wani littafi mai suna. Matar mutum kabarinshi na Bashari Faruku Roukbah Wasan kwaikwayone na Nura da jummai gaskiya jarumin yayi ƙoƙari gaya" Murmushi Gawata yayi yace. "Ashe zan sha karatu mutumina ba da ina baka shawar ka jaraba karatun ba kaƙi. Nima zaka bani matar mutum kabarin nashi in karanta, na tawo da sababbi sai in baka ka karanta ɗaya" Sun daɗe suna hira har dai suka yi isha Qasimu ya ja Gawata can gidansu anan suka ci dambu suna kan cin dambunne Qasimu ya lura duk son Gawata da dambu baya wani ci, ya fahimci tun a wajen hirarsu hankalinshi baya jikinshi. "Gawata kun samu saɓanine da Hindu ko? Naga hankalinka baya jikinka sam ina lure dakai sosai. Meke faruwa? " "To Qasimu hadda ma rashin farin jinina ni tunda a dangi duk wanda aka taya ma baya so yace zan auri ƴarshi ko ɗiyarta. Yanzu Nawata suka ba Uwatale shi sun amince zasu bashi, amman ni da akaso a tambayamun ita a shekarun baya ƙiri da muzu Goggo ta kakkauce zancan bata bari ma Uwatalen taji ba. Baƙin jininane ya bini har birni iyayen Hindu sun rabamu a yadda suka ci mutumcina ko sama da ƙasa zata haɗe nasan ba zasu yadda su bani ita ba. Kaji yadda mahaifinta yake turanci kuwa? Yaƙi hausa fur wallahi ga kayan sojoji ya saka. Labarin komai ya zaiyana mishi. "Lallai kuwa Gawata kana cikin damuwa. Amman in da rabon aure a tsakaninku wallahi saika Aureta nake faɗa maka. Ina mamakin abinda yasa ƴan binni basu ɗaukemu a bakin komai ba suke kallonmu a matsayin wulaƙantattu." Sun daɗe suna rabe ɗayan biyu ko gidan Yaya jamilan ma basu je ba sun barma gobe. Har gida Qasimu ya biyo Gawata dan yau kam anan zai kwana har zuwa lokacin da Gawata zai tattare inashi inashi ya koma. Tare suka shiga ɗakin Nanno da sallama. "Qasimu kaida mutuminne? Gandan_ gandan daku ba aure kun saka fita Binni a gaba. Wallahi kuma kanku faɗa fa. Ku zauna kuci tuwo" Zama suka yi suna dai bin Nanno da dariya kawai. Tuwonma Gawata ya dai ɗan taɓa dan kada Nanno tayi faɗa. Nan ya janyo buhunshi ya ciro tsaraba kashi_kashi harda ta maƙota haka suke yi. Shima in zai tafi mai biyar mai goma duk sai an harhaɗa mishi, to shima fa dole yayo tsaraba wani abun sai ƙauye, amman ko babu komai hakan na ƙara danƙon zumunci da soyayya a tsakankanin maƙota gaya. Saida ta bari sun kammala cin abincin tas kana tace. "Matsalar me kuka samu da kai da yarinyar da kake nema ɗin Mijinyawa? " "Daga ɓangaren iyayenta ne su ɗan boko suke son su bata ni kuma gashi banyi boko ba" "Baka yi boko ba kuma. Duk bokon da kuka shafe shakara sama da goma daga firamare har ta gaba da'ita. Kana gani in banda ku ɗin waye yayi boko a cikin gidannan ga ƴan uwanku nan na ragowar ɗakin babu wanda yayi karatun. To akwai bokon data wuce wannan ne, ga Qur'ani izifi sittin a kanka, me suke so, ko dai kora da hali suke yi maka ne? " Qasimu yace. "Akwai karatuka masu yawa a gaba waɗanda muka yi sune dai tsanin hawa na gaba, amman karatu an dai yi yaƙi da jahilci. Irin karatun su Dauda shine karatu" "Dauda ɗan wajen Tine da yake shigowa ƙauyannan da mota wanda akace yana aiki a binni?" Gawata yace. "Yauwa Nanno irinshi suke so Nanno, to shine aketa turka_ turka gashi tare akeso a aurar dasu su kusan goma a rana ɗaya. Yanzu dai halin da ake ciki sunce ba zasu bani ba gaskiya a haka muka rabu dasu" Ya ɓoye ci mishi mutuncin da suka yi sabida gudun abinda kaje kazo. Sama da ƙasa Nanno ta rasa abinda zata faɗi ita a tunaninta matsalar daga Gawata ne tunda a cikin dangi da abokan arziki da dangin abokan zamanta babu inda bata tallata Gawata ba ko za'a dace amman duk wacce akaima maganar sai ta ƙi ko iyayensu su ƙi. Amman Nawata yayi budurwa rasuwa tayi, ta biyun da yayi kuma cikin shege tayi daga ƙarshe zaman garin ya gagareta ita da iyayenta suka bar garin. To a baya har Uwatale Nanno tasu ta haɗa da Gawata amman mahaifiyar ta nuna taƙi, amman da tace a ba Nawata da gudu ta amince ba kwana_kwana. Duk da shi Nawata yana da kuɗinshi inda yake aiki yana samu sosai saɓanin Gawata da lallaɓawa kawai dai akeyi dan kada a zauna. "Hmmm Allah ya rufa asiri. In suka dage sai ka haƙura ka nemi wata. Bana ga laifinsu ba su da ɗiyarsu ga mutumin binni da raina na ƙauye, ni kuma nace in kuka yi aure ko a ina aka Auro yarinya to a nan ƙauyen da gidan zaku zauna bana son zaman bariki irin na Dauda kawai a je a shanye maka ɗa sai yadda danginta sukai da shi." Su Gawata dai sukai shiru babu ta cewa. Maƙotane sukaita aiko da kwanukan abinda na baƙo kusan kwano goma aka kawo. Gawata dai lallaɓawa yayi suka fito zuwa ɗakinsu shi da Qasimu. Matan gidan da yaran kab suna tsakar gida manyan sun ware kansu yaran ma. Gaggaisawa aka kuma yi anata zolayar Qasimu yau yaga aboki. Ko da suka shiga ɗakin mai katifar yayi da tabarma karauni Gawata bashi da sukuni. Duk yadda Qasimu yaso ya ribaceshi ya mance damuwar tunanin Hindu wallahi ya kasa cin nasara. Kafin kuwa Safiya ya wayi gari da zazzabi da ciwon kai mai tsananin gaske. Daddaurewa yake yi baya son Nanno tasan halin da yake ciki. Shi yasa ma sha biyun rana a gidan Yaya Jamila tayi musu, da sukai azahar suka wuce gidan Yaya Zakiya itama sai zuwa la'asar suka baro gidanta suka nufo gida. Suna tafe a hanya shiru_shiru Qasimu yace. "Baka karɓi littafin matar mutum kabarinshi da kace zaka karanta ba. Bari in ɗakko maka tunda mun iso ƙofar gidan jirani kawai" A jikin bishiyar ƙofar gidansu Qasimu ya tsaya yana ƙarema unguwar kallo. Tunano yadda Hindu ta tsara musu yadda zasu gudanar da soyayyarsu da yadda zasu reni yaransu yayi. Murmushi kawai yayi daya tuno irin yadda Hindu take matuƙar sonshi kuma yake burgeta. Fitowar Qasimu ce ta dawo dashi daga tunanin daya lula littafin ya karɓa suka wuce majalisarsu ta matasa aka shiga musu, Gawata dai ya kalli wannan ya kalli wancan ya rasa tacewa. Acaɓa ne ya ajjiye Zakari a daidai majalisar da buhun kayanshi. "Yauwa Gawata wallahi dama dalilin saukata anan kenan sabida kai zo mana" Da sauri Gawata ya ƙarasa wajen Zakari dashi da Qasimu. Hannu yasa a ajjihu ya zaro takadda a ambalob mai ruwan ƙasa ya danƙa mishi. "Musa mai yalo shine ya bani taladdarnan kuma ya roƙeni ta iso hannunka daga isowata to gashi na damƙa maka ita. Saƙone ƙawar Hindu Luba ta kawo tace a baka" Zakari na faɗin haka ya saɓa bakkonshi a kafaɗa ya ƙarasa majalisar matasan aka gaggaisa ya gangara unguwarsu. Sai da akayi sallar magriba Gawata ya maƙale a gefe ya buɗe takaddar ga abinda ta ƙunsa. _ka sani zuchiyata in ta buga kaine sanadiyya. Gawata a duk sanda wasiƙata ta iso gareka ka tabbatar washegari ka kamo hanyar Kano kazo na ganka mu tattauna, in ba haka ba da kwatance zan biyoka mijina. Wallahi babu mai rabamu sai mun yi Aure da izinin Allah. In kazo, kazo gidansu Luba zata zo da dabara ta kirani. Ko kuma in zauna in jiraka a gidansu Luban. Gawata ina jiranka dan Allah kada ka gujeni a lokacin da nafi buƙatarka yanzu haka bani da lafiya a kwance nake ciwon sonka ya kwantar dani. Matarka Hindu_ Ai da ganin saƙonnan Gawata hankalinshi ya tashi washegari sassafe yaima kowa sallama Qasimu ya rakashi har tasha saida motarsu ta tashi ya juyo. Sabida lalacewar mota a hanya basu suka shiga Kano ba sai taran dare ga alƙawarin shi da Hindu ko kusa baya son saɓawa. Bashi ya iso ƙofar gidan ba sai wajajen tara da rabi, matasa suna zazzaune a waje ana shan iska. Da ƙyar ma ya samu ya aika yaro gidansu Luba yace ana nemanta. HINDU:. "Hindu ya kamata kizo muje in kai ki gida kinga har tara da rabi bai zo ba ƙila ma takaddar bata iskeshi ba" Zai zo Luba bari goma tayi mu gani" Kafin ma in rufe bakina yaro ya doka sallama. "Wai ana kiran Luba tazo inji Gawata" Miƙewa nayi da sauri duk ciwon da jikina yake yi sai naji duk babu. Ina fita muka haɗa idanu da Gawata ga bakkonshi a riƙe a hannunshi. "Tutar so, na cika miki alƙawarinki nazo kin ganni na ganki. Amman mu barma gobe lokaci bazai bamu wata dama ba. Nasan muna da tarin maganganu a bakunanmu. Gobe bayan la'asar zanzo." Lallai ka cika alƙawari kaje ka samu ka kwanta ka huta sai gobe mijina" Murmushi mukaima juna muka ɗan jima muna kallon juna. "Ina sonki wallahi kuma zan jure duk wahala dan in mallakeki. Ko me za'ayi mun a gidanku Hindu zan aureki. Saina maidaki abar kwatance a fagen so da ƙauna." Mrs BukhariTSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA GOMA SHA BIYU *INA GODIYA SOSAI MASOYANA. DALILIN DA YASA AKA JINI SHIRU RASUWA AKAYI MUN TA JIKI SOSAI* *A NAN KUMA NA SAKE GANE MASOYANA MASU BIBIYAR AIKIN NAWA, NA SAMU KIRAYE_KIRAYEN WAYA DAGA NAN GIDA NAJERIYA HARMA DA ƘASASHEN WAJE. WAƊANDA BAN SAMU DAMA DA IKON ƊAUKAR WAYARSU BA INA MAI BA DA HAƘURI AIMUN AFUWA.* *NAGODE SOSAI GODIYA MA TA GODE SON SO*💪🏼 *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. Gawata saida ya tabbatar na shige gida kana ya saka kai ya tafi. Washegari muka tashi da tashin hankali mai tsanani wanda tarihi bazai iya mantawa ba abadan. Abokin mijin Yaya Saratu yazo da safe kuma harma ance an bashi ni lamarin daya burkita ciwona naita bige bige da ihu, a ranar dai har waje naci nasarar ficewa a guje bansan ya akayi aka dawo dani gida ba. Wallahi ranar murɗeni makarai sukai ta yi yadda kuka san babu ƙashi a jikina. Sukai rantsuwar ɗaukeni zasu yi a neme ni a rasa tunda anƙi a farantama goɗiyarsu rai. Baba Soja ya dinga faɗa yana jaddadama Innarmu Aure babu fashi an riga an ba Sadisu ni ko gawatane sai an ɗaura wannan Auren da'ita an kaini a mace. Shi bai yadda da makarai ba sam amman tunda sunce zasu ɗaukeni a barsu su ɗaukeni nanne zai tabbatar da lallai makarai suna iya shiga jikin mutum. Kunji tauri da irin rashin tsoron Baba Sojanmu ko? Ranar makarai sun jijjigamun jikina sosai sai da kowa ya tausaya mun Innarmu harta sare ganin irin wahalar da nake sha, ga jikina duk ciwo ko iya tashi zaune bana yi sai su Rayya sun taimaka mun nake iya tashi. Maƙota sai shigowa suke yi domin suji menene matsalar dake damuna. Amman zancan bai sauya zane ba Baba Sojanmu ya kafe baya ko ɗigon tausayina. Mako guda da wannan maganar sai ga sadaki an kawo nawa ya ɗare na kowa harda akwatin nagani inaso. Biki aka tsaida wata biyar masu zuwa da izinin Allah an fasa batun sai mun soma jami'a an ajjiye a gefe, ƴan matan gidanmu da iyayensu sai haushina suke ji. Amare ko wacce tana cikin farin ciki saɓanin ni da a kwance nake yau ina duniyar mutane gobe ina ta aljanu. Tsakanina da Gawata sai wasiƙa wacce Luba ta zama manzo a tsakaninmu ita ke kai saƙwannin dukka. Labarin ɗayane dani dashi a halin damuwa da ciwo kawai muke rai kwakwai mutu kwakwai. Dama_dama shi yana ɗan baza kayan sana'arshi. A wasiƙar daya turomunne yake sanar dani ya dawo bakin titin layinmu da saida Lemo Innarmu tasa an koreshi a ƙofar makaranta tasa anci zarafinshi sosai an watsar mishi da kayan sana'arshi. Takaddar ban haƙuri da lallashi na tura mishi. Biki nata ƙaratowa niko duk na zube a tsaye nice kullum a shan rubutu da yi mun hayaƙi nake, hatta ruwan wankana wallahi na maganine, abinci wannan in zanci dole sai an zuba mun magani. Abun ya wuce yadda kuke tunani a rana sai makarai su bigeni sau biyu uku, sai in kwana ana guda gani dai nice amman kuma bani bace, tun innarmu bata iya bambancewa har tazo ta soma ganewa in bani bace zata ga da kuzari a jikina sosai kuma idanuna juyewa yake yi, in kuma nice babu kuzari a jikina kuma idanuna zasu dawo jawur. Ranar dai Innarmu tana makaranta Baba sojanmu yaje wani bikin wani babba da aka gaiyaci manyan sojin ƙasar. Inna Abida ma bata nan lungunmu babu kowa duk suna makaranta marasa zuwa makaranta kuma sun fita. Sulalewa nayi na fito. Wallahi duk ƴan gidanmu in suka ganni sai su shige ɗaki a guje tsorona suke yi sosai sabida abubuwan da nake yi da yawa sosai, kuma muddin na riƙe mutum ba'a iya ƙwatarshi, mahaukaciya dai na zama tuburan fa. Gashi Baba Sojanmu ya saɓule hannunshi a kaina Innarmu da ƴan uwanta ne suke ta faman nema mun magani shi kuwa ko gezau wallahi. Ina fita na nufi titi samɓal har gaban teburin Gawata yana tsaye yana ba wani lemo. "Tutar so kece kika koma haka?" Ai saiya saki ledar lemon dake hannunshi lemun suka bi titi a guje. Damƙama mai siyan lemon kuɗinshi yayi, ya dawo inda nake a zaune a benci nayi shiru, ashe a lokacin bani bace. "In ka bari Hindu ta Auri Sadisu zaku rasata dukka sai mun ɗauketa sabida kai take so. Kaci gaba da zuwa zance wajenta ko da korarka za'a dinga yi" Iyakar abinda suka ce dashi kenan na kama hanya na dawo gida na kwanta nayi lamo a kan gadonmu. Daga wannan rana kullum sai Gawata ya aiko inzo sai dai a kori ɗan aiken, ko Baba Sojanmu ya fita da kanshi yaita turanci yana yi tamkar zai doki Gawata, sai in su Baba Nagoɗi nananne sai ƙurar ta lafa. Shi kuma wannan jan kunnen da makaraina suka yi mar yake jin tsoron ranar da za'a wayi gari ace an neme ni an rasa. Bari in muku a taƙaice wuya babu wacce bamu sha ba, biki ya rage saura sati biyu tim jikina yayi tsananin da ko idanuna bana iya buɗewa ko'ina a jikina ya kumbura yai suntun. Ranar asabar suka wayi gari babu ni babu dalilina ni kaina bansan a wacce duniyar nake ba. Akai neman duniya ba'a ganni ba. Har kulle Gawata akayi a ofishin ƴan sanda akan sai ya fito dani. Makaranne sukai magana ta jikin Innarmu tunda itama tana dasu kusan na gadon gidansu ne ma ya shafeni, amman gaskiya basu taɓa tashi ba, ace har an yi magana dasu irin haka ba. "Ku bar wahalar da kanku a banza, Hindu mu muka ɗauketa tana hannunmu ba zamu dawo da'ita ba. Mu mun fika taurin kai" Baba Sojanmu yayi dariya kawai yace. "Kuna dai da kalar naku baku san kalar nawa ba. Nifa bana tsoronku bare kuyi mun barazana. Babu yadda za'ayi goɗiyarku ta auri wannan yaron ina da raina. In kun so ku riƙeta ni yafi ye mun" A wajen ya bar Innarmu da makaran yayi ficewarshi. Sai su Baba Dogara Inna Abida ta kirawo suka shiga lamarin da ƙyar suka yadda da sulhu, tare da sharaɗi. A cikin kwana na tara cib da ɓacewata suka dawo dani. Innarmu na makaranta, Baba Sojanmu baya nan ƙofarshi a kulle take da kwaɗo yana buɗewa ya ganni a kwance a gadonshi. Nan ya kikkira su Baba Nagoɗi, Innarmu ma ta dawo ta tarar da lamarin gani a kwance ni dai. Ran da alkadarin komai zai karye kenan. Baba Nagoɗi da yaga irin halin da nake ciki na rai kwakwai mutu kwakwai jikina yayi wani iri, fuskata tamkar ba tawa ba sai yace. "Na soke Auren Sadisu da Hindu, shi wannan yaron ace yazo ina son ganinshi yanzunnan a aika Rayya taje tayi kiranshi yazo maza." Ajjiyar zuchiya Innarmu ta sauke tace. "Alhamdullahi Allah yasa ƙarshen wahalar kenan amman iya wuya Hindu tasha wuya, maganin akeyi amman kamar sake turasu akeyi yadda take da kafiya haka makaranta suke da shegiyar kafiya. Alhamdulillahi tunda Ƴata ta dawo. Nima na amince da Aurenta da mai lemun" Baba Sojanmu dake zaune a kujerarshi shi Baba Nagoɗi da su Baba Dogara duk suna tsaye yace. "Tunda kaine maɗaurin Aurenta kuma ka janye da wanda kayi ma alƙawari shikenan bazan ma musu ba, amman ina da dokokin da zan shinfiɗa kuma dolensu ita da makaran subi sabida ni ba tsoronsu nake ji ba. Ba zasu maidani jani talau ba wallahi dan ka yanke hukuncine a gaban kowa amman da sai dai Hindu ta mutu uban kowa ya huta, ko su dawo su ɗauki abunsu." "Dama wannan taurin naka ne dana gyatumarta duk ta haɗa ta ɗakko shi yasa abun yayi mata yawa, ga makarai dake sake tura abun. Amman ya kamata ace ka tausayama uwar yarinyar da yarinyar harma da ƴan uwanta kullum su Saratu a cikin zirga _zirga suke dan duba jikin nata. Kwana tara yarinya bata gida, kuma da suka tashi dawo da'ita aka kawota ɗakinka aka ajjiyeta, ɗaki a rufe kuma kana da tabbacin kai kaɗai kake da ɗan mabuɗin ɗakin. Ai wannan kaɗai da suka nuna maka ya'isa ka gane makarai gaskiya ne. A dai bata abinda take so ai shikenan kanwa takar tsami ƙwannafi dole ya lafa suma da suke ikrarin zasu raba ta da cikin bil'adama sai su janye tunda kaɗanne daga cikin aikin makarai, ji yadda suka sake mata kamanninta fa. Tunda Qazzafi ya haƙura Sadisu dole ya haƙura Auren bazai haifar da ɗa mai idanu ba, kada azo ana dana sani. Kai na fahimci ba dana sanin da zaka yi a cikin damuwa mu kaɗai zaka barmu" Duk wannan maganar acan sama nake jinta tayi nisa sosai da kunnuwana. Ruwan rubutu Innarmu ta shasshafamun bayan fitarsu, ita da kanta ta mayar dani ɗakinta. Sai zuwa kallona ƴan gidanmu suke yi. Kai gidan yawa bala'i ne. "Shikenan Hindu burinki ya cika kin tanƙwara iyayenki kan abinda kike so. Ai gara a haɗaku kowa ma ya huta, kema da makaran naki ku huta. Shikenan ai marar ilimi zaki aura muna da ranmu da lafiyarmu. Bawai ban amince bane, na amince sabida inaso rayuwar Aurenki tayi kyau. Na sani auren dole ba'ayi ko a Musulunci. Ko batun uba ya nema ma ɗiyarshi budurwa miji da akace. Ana nufin ya zame mata ido, ya nema mata abinda ya dace da'ita a kawo mata ta gani, in yayi mata shikenan,in bai yi mata ba shikenan sai a nema mata wani har sai ta samu wanda yayi matan. To amman ba hakan akeyi ba, iyayenmu na da can sai an kai mace ma gidan auren take ganin mijin, amman zata zauna ta yi biyayya. Amman in mace bata so babu laifi sam danta faɗa hakkinta ne, tunda ita zata zauna shi aure amincewar mutum biyu ne tunda sune zasu yi rayuwar tare. hmmm" Tayi ƙwafa ta fice. Sanyi ne naji yana ratsa jikina takota ina, ina jin guɗa a kaina anayi da shewar mata da yawa sosai harda kaɗe_kaɗe. Cikin minti ashirin idanuna suka buɗe tangararan sai dai a kumbure suke ainun. Innarmu ce ta shigo. "Hinduwa taso iyayenki na nemanki a falon Nagoɗi." A hankali na miƙe nabi bayanta zungui_ zungui har zuwa falon Baba Nagoɗi. Ƙarfin haline kawai amman ji nake inna taka ƙafata tamkar zata ɓalle. Ina kuma jin yadda iska ke shiga har ɓarona, a haka na kai kaina da kaina. Zama nayi nesa da Gawata amman muna fuskantar junanmu yana saye da yadinshi fari ɗinkin ƴar shara da hularshinnan da kuka sanshi da'ita itace ɗaya_ɗaya "To kai ganaral sai ka soma bayaninka da zaran na gama. Gawata kace sunanka ko? " "Eh Baba sunana kenan" "Kana da sana'ar da zaka iya riƙe Hindu da'ita ne bayan siyar da lemon da kake yi. Sannan kayi karatun addinine? " "A'a bani da wata sana'ar bayan wannan in sha Allah zan riƙeta da kyau iyakar ƙarfina kuma, amman ina da gonar gado wacce take haɗaka da abokin tagwaitakana, mu kan noma dawa. Batun karatu kuma na yi saukar Qu'ani mai girma, na yi haddar hadisai daidai gwargwado in sha Allah" "To amman a rana kamar cinikin nawa kake yi, ribar nawa kake samu da har kake tunanin iya riƙe mace kamar Hindu, kasan dai matsayinku ba ɗaya bane ko? " "Zan riƙeta in sha Allah ba zatai kuka da riƙon ba in sha Allah. Duk da na kasance ba mai ƙarfi ba" Baba Nagoɗi yace. "To Ganaral kaji iyakar magana sai abinda zai biyo baya na ƙarshe kuma in ka gama naka" Baba Soja ya muskuto yana dubanmu cike da ɓacin rai da baƙin ciki fal zuchiyarshi yace. "Yaro inna baka Hindu babu saki, babu yaji, babu ƙorafin da zaka kawo mun gidana, ko ta kawomun gidana, sannan dolenka ka mayar da'ita makatantar jami'a ka biya mata ta gama ta samu aikin yi tayi, kamar yadda akeyi a cikin gidannan, ni nake biya ma ko wacce ƴa kuɗin makaranta ki da tana gaban mijinta. Amman ita wannan kai zaka biya mata. Ko da wasa kada in ga ƙafarku da sunan matsalace ta kawo ku, zuwanma na lafiya bana so a cika zuwa mun gida ana ci mun abinci. Sannan zaka biya nera dubu ɗari sadakin Hindu, kayi mata kayan akwati kamar yadda za'aima sauran ƴan uwanta. Mun baka nan da kwana uku a kawo wannan sadaki cikin gidannan. Wannan shine sharaɗina akan ka da kanta kun amince." Shiru nayi ina tunanin ta yadda Gawata zai samo dubu ɗari a cikin kwana uku da akwati daidai dana ƴan birni, wannan korace kawai da hali sabida ansan bazai iyaba inya saɓa kwanakin sai su samu hujjar cewa basu suka hanashi auren ba gazawarshi ce. A lokacin sadaki baya wuce dubu goma, su Yaya Saratu ma da sukai tsada dubu ashirin ce da biyar masu daraja irinna shekarun baya. "Na amince Baba Allah ya nuna mana. Sannan in sha Allah zamu zauna lafiya albarkarku kawai muke bara a sanya mana. Sannan ku yafe mana ɓata muku da muka yi" Ya faɗa a sanyaye muryarshi har rawa take yi sabida kaɗuwa Baba Nagoɗi ya ɗaura da cewa. "Sati biyu ne yayi ragowa ayi bikin, muddin aka wuce kwana uku babu sadaki da kayan lefen baki ɗaya to Aure zai sauka a kanka zata auri Qazzafi tashi mun sallameka. Ke Hindu ki bishi kuje ku tsara yadda komai zai kasance" "Ina ai zai yi cike_ciken takadda" Cewar Baba Sojanmu. Baba Nagoɗi yace. "Haba janaral sai kace wani wanda aka ɗauka aiki. Wai kai me yasa komai sai kace sai an yi rubutune" "Manzon Allah SAW ma yace duk abinda zamu yi musamman abinda ya shafi yarjejeniya muyi rubutu. Babu damuwa zan rubuta" Cewar Gawata kenan. Baba Sojanmu ya ƙura mishi idanu tare da yin shiru, shi kam kanshi na ƙasa. "Ma firen saka sunanka anan, nan kuma ka saka hannu. Ka nutsu ka karanta takaddar" Da sauri ya karɓa, rubutun turancine nasan ba duka zai gane ba, haka dai ya saka hannu da sunanshi, Baba Sojanmu ya riƙe takadda ɗaya shima Gawata aka bashi ɗaya ya riƙe a hannunshi. Godiya yai ta yi musu. A hankali ya miƙe ya fito tsakar gida, nima na biyo bayanshi, Innarmu ce ta leƙo tace. "Hinduwa kuje daga falo can ku yi abinda zaku yi jikin ki ba daɗi bane dashi ga rana" To Innarmu" Gaba nayi Gawata ya biyoni mukaita ratse gidanmu ana ta leƙenmu ana al'ajabin abinda na gani na liƙema Gawata ɗan ƙauye futuk. Tabbas baƙauye ne amman babu duhun ƙauyanci tattare dashi kasancewar yayi karatun arabi da bokon matayassara. A ƙasan kafet muka zauna muna fuskantar juna cike da murmushi zukatanmu fes da farin ciki. "Kinga kudurar Allah ko Tutar so? Tunda abinnan ya faru na hana idanuna bacci ina roƙon Allah yasa ki zama mallakina duk da isata bata kai ta mallakeki ba, kwanana uku a kulle a sell, shima adda'a kawai nake yi ina kai kukana wajen rabbil izzati. In sha Allah zan zame miki huɗu a ɗaya zan zame miki madadin uwa, zan zame miki madadin uba, zan zame miki madadin miji, zan zame miki mijin nuna ma sa'a namijin duniya Hindu. Ubangiji Allah ya bani ikon tsallake jarabawar da aka ɗauramun. Gobe sassafe zan wuce jama'are inaga sai ranar ɗaurin Aure in munzo an ɗaura Aure kafinnan muga juna kuma. Hindu gashi babu kuɗi a hannuna da zan baki na hidimomin biki amman waɗanda zasu kawo sadaki da kayan Aure zan basu saƙon kuɗi su baki kiyi duk abinda ya dace" Ina murmushi nace dashi. Allahu shi kaɗai muke ma bauta Gawata, shi ya ƙaddara gareka nazo mata ko munyi daidai da juna ko bamu yi ba. Damuwata a ina zaka samu waɗannan kuɗaɗen a cikin kwana uku shine fargabata. Sannan batun wajen zama fa" "Tutar so baki da damuwa ko kaɗan hankalinki ya kwanta zaki ga ikon Allah in sha Allah. Wani hanzari ba gudu ba shine a Jama'are zamu zauna sabida Nanno taƙi yadda mu zauna a binni da matanmu zaki yi haƙuri da wannan bansan ko zaki iya rayuwa dani a ƙauye ba. Sannan na kasa sanarwa a gabansu Baba Sojanmu wallahi bazan ɓoye miki ba a lokacin da nake falon in da za'a tsaga jikina ba za'a tadda jini ba." Ashe tsugunne bata ƙare ba kenan jama'are, ni Hindu na shiga uku duk yadda akaso ɗaga mana ƙafa abun zai yiwu kuwa? A zahiri nace. Baka da matsala dani duk inda zaka ajjiyeni zan zauna da sharaɗin ba ajjiyeni zaka yi ka dawo birni ba, kuma zaka tsaya mun duk runtsi? " "Wannan ratayayyen hakkin soyayyane a wuyana ina da wuyan ɗauka. Na kuma sake yadda da wannan ƙauna zan nuna miki soyayya zan riritaki, zan tarairayeki har sai kin manta kowa da komai" Mun jima muna hirarmu daga bisani yayi mun sallama ya tafi, ni kuma na koma cikin ɗakinmu. JAMA'ARE:. "Kinji halin da ake ciki Nanno, wannan dalilin yasa na tawo afujajan sabida a samu ayi abinda ya dace, zan yi magana da Qasimu yayi ƙoƙari mu gina inda zata zauna" Cewar Gawata da isowarshi kenan ko ruwa bai sha ba ya tari Nanno da wannan magana ga Nawata a zaune yana jinsu. Ga kuma Goggo Akulu ƙanwar Nanno itama tazo daga Misau acan take Aure. "Mijinyawa ni gaskiya in shawara zan baka ka haƙura da yarinyarnan kawai ka huta ma ranka. Iyayen yarinyarnan sun nuna basa sonka to dole ne, ni a halin da ake ciki wallahi ko ƙaunar yarinyar nima bana yi. Ya za'ayi suce dubu ɗari kuɗin sadakinta sai kace zinari ko lu'u lu'u zamu siya, gonaki nawa zaka cire ka siya da dubu ɗari. Sannan ina zamu samu dubu ɗarin sadaki ga na kayan akwati tsakani da Allah fa. Ni dai kawai kayi zamanka a nan ƙauyen ita kuma ka barta ta Auri wanda iyayenta suke so. Bikinku tare kasan za'a haɗa dana ɗan uwanka. In fa a ƙauyannan ne baifi a kashe dubu ɗarin ba da sadakin da lefe na alfarma da gini dukka dubu ɗari zata yi fa. Wannan maƙudan kuɗi har ina. Akulu kina jin yaron naki fa irin jarabar duniyar da zai kwaso? " Goggo Akulu tace. "Wallahi naji Yaya ni amman ina gani tunda su yaran suna son junansu Yaya ki sa mai haƙuri kawai ayi a wuce wajen. Kora da hali suka yi mai sabida ya nuna gazawarshi su samu hujjar cewa dama ba auren bane ya kaishi ba. Kinga ita yarinyar zai zama ya tsinkata sosai. Jibi fa yadda duk ya fice a hayyacinshi ya rame kamar wanda yayi ciwo fa. Yaya kiyi haƙuri kawai suje su samu iyayensu su sanar dasu halin da ake ciki. In yaso ba sai a haɗa auren ba kawai shi Nawata da kuɗinshi sannan Uwatale dubu saba'in ma ya isa a gama hidimar komai na bikinta." Nanno tace ai ina ita bata yadda ba ba za'a Auri Hindu ba, a taƙaice ta tsani Hindu kamar yadda iyayenta suka tsanar mata ɗa. Damma duk wannan dambarwar kulleshi a sell bata sani ba, da batun takadda da yasa hannu, dama abubuwa da dama. Gawata sai ya zama kamar majinuni sai sambatu da roƙon Allah yake yi. Qasimu da Nawata, da Abdulƙadiri ne sukaita rarrashinshi. "Ka sassautama kanka in Allah ya kaimu gobe muje Azare mu samu Kawu Saminu mu yi mishi bayanin komai shi kaɗaine zai iya rarrashin Nanno tunda shine makwafin uwa da uba a wajensu." Cewar Nawata kenan. Wannan maganar bata sa Gawata zuchiyarshi ta nutsa ba har saida washegari suka isa Azare su uku suka gurfana a gaban Kawu Saminu tukunna su kai mishi bayanin duk abinda ke tafe dasu ga ba lokaci kwana biyu kaɗai ya rage musu na wa'adi. "Toh naji bayananku Mijinyawa ƙarami gaskiya iyayen yarinyarnan babu dattijantaka tattare dasu ko kaɗan. Amman ba zaka kunyata ba in sha Allah. Sai dai fa a siyar da gonakinku na gado a raba a baka naka kayi hidimar da zaka yi dashi tunda kwanaki ma ɗan wajen Ladi ya tayar da maganar konakin. Yanzu abinda za'ayi duba da ƙarancin lokaci bari in shiga in kintsa sai mu kama hanya umm" Tashi Kawu Saminu yayi ya shiga gida ya shiryo suka kamo hanyar jama'are sai yamma suka iso. Tunda Nanno taji muryar wanta a tsakar gidan yana gaisawa da abokan zamanta ta ɗaure fuskarta tayi kicin_ kicin dan ta riga da tasan zuwa da dawowar zancan ilai kuwa ko da ya shiga aka gaisa sai ya shiga tausarta yana bata magana bata musu dashi dole ta amince amman fa ta ƙullaci Hindu sosai. Kunji inda ƙiyayyar ta samo asali ko? "To shikenan Yaya na amince. Amman a ina zai samu kuɗin lefe da sadakin da suka yanka mishi, ga batun gini? " "To Habiba tunda gadon yarannan ba'a gama rabawa ba, kwanaki ma ɗan wajen Ladi ya tayar da ƙayar baya to a saida gonakin a raba aba kowa tunda ba nomar suke yi ba a ciki, hayarsu kawai akeyi. In yaso ko guda ɗaya ce babba sa bari su mijinyawa Babba da mijinyawa ƙarami ko gaba in sun tara ahali zasu yi noma. Amman kafin a siyar ai ga Akulu tana nan bata rasa kuɗi tunda adashen gonakai take ma maza magidanta banda mata da take yi ma. Sai ta ara mishi ya kashe wutar gabanshi in aka gama saida gonakan aka raba sai ni da kaina in cire miki kuɗinki. Hakan yayi muku? " "To shikenan ai Yaya babu damuwa bazai gagara ba ai kamar dubu ɗari biyar ya isheshi ya riƙe a hannunshi a gama komai da komai ko?" "Lallai wannan yarinya tsadarta tayi yawan da ya wuce tunani amman yaya zanyi tunda Yaya yasa baki hmmmm dubu ɗari biyar fa Akulu? Tunda nake ban taɓa ganin maƙudan kuɗaɗe irin wannan ba" Haka dai maganar ta ƙare Goggo Akulu dai a kwai kuɗi dubu ɗari biyu a jikinta take ta ɗauka ta ba Gawata akan a soma shiri. Babu shiri suka wuce gidan magajiya wacce kusan kaf layin ita ke haɗama samari kayan Aure har adashe take yi musu, shi kanshi Nawata ya soma zubi a wajenta daga baya ya soma zubawa a asusu, babu shiri ya ɓalle asusun suka je wajen magajiya. "To yanzu kaya kace za'a haɗa kamar na dubu ɗari da hamsin zuwa ɗari biyu harda akwati. Kai kuwa Gawata ƴar gidan sarkin ina zaka Aura? Yarinyar sarki Aminu ado bayaro ce? Tunda nake haɗa lefe a ƙauyannan ban taɓa haɗa na dubu ɗari tim ba" Magajiya ta jinjina abun sosai da sosai. "Magajiya ai Tutar so tafi ɗiyar sarki a wajena. Wannan lefen a gidansu za'a karɓa da haƙurine kawai sannan dan Allah a ɗebo atampopin masu haske ruwan binni, pamtimotinma a ɗakko ruwan ƴan gayu" "To naji. Akwatuna dai ina dasu seti uku daban daban bari insa Indo ta jawo maka ka zaɓa, gobe sassafe zan shiga Bauchi in siyo duk abinda ya dace kada ma kaji komai" Nan ta kira Indo ta tuƙo akwati mai taya sonsonet a wannan lokacin su ake yayi. Mai ruwan madara ya zaɓa hawa uku babban lamba 1 sai mai binshi, da kuma na saman mai turawa, magajiya ta bada shawarar ya siya da wannan ɗan kutumburin na can saman wanda yawanci daddamu da Qur'ani ake sakawa wasu kuma su shaƙeshi da ɗankunnaye da sarƙa. Nawata kuma kayan dubu hamsin yace a haɗo mishi akwati ɗaya da mitsitsin na saman haka akeyi a lokacin shima hakan na yara ƴan gata ne. Washegari da yamma kuwa saiga Magajiya da akwatuna ciki_kici ta shigo dasu, kafin kace me maƙota suka cika gidan suna mamaki. A lokacin su Gawata suna can cikin gida anata gini sun siyo bolo ɗin laka sabida babu lokacin da zasu buga bulo da kansu. Tsarin yadda suka ɗakko ginin nasu da bambamci shi Nawata banɗaki da madafi duk a waje yayi ma uwatale, sannan ɗakunan falle _falle saɓanin Gawata da yayi Kitchen a falo, banɗaki a uwarɗaki amman iyakar na wanka, sai akayi na tsugunno a tsakar gidan sabida ita ƴar binni ce ba a ƙauye ta rayu ba da estira ɗaki falle ɗaya a gefe, sai wani kwarmi da akayi da rariya a wajen kamar wajen wanke _wanke dai haka, da kuma wani gini da akayi Kitchen ne na tsakar gida na murhu. Dukkansu abokansu ke tayasu aikin ginin sabida ayi sauri ayi abinda duk ya dace. Suna cikin aikin ginin suka soma jiyo hayaniyar mata. NANNO:. "Yanzu ke Habiba duka wannan kayan kamar za'a buɗe shago haka za'a kinkima a kai Binni wannan maƙudan kuɗaɗe? Wallahi a shekaruna ban taɓa ganin lefe na alfarma irin wannan ba, kin yi ganganci da kika bari akayi wannan aikin. Wannan yarinya ita wacce irice a binnin da za'a kashe mata dukiya jibi atampopi dandatsa_dandatsa haka takalma jaka, rigunan mama da ɗan kanfai dozin dozin fa hatta janbaki majigi dozin guda aka saka da gazal" Wannan kaɗanne daga cikin cece kucen matan ƙauyen su Yaya jamila da Yaya Zakiya ma da suka zo gida akan zasu kwana asubar fari su wuce sun tsorata da ganin kayannan sai surutai akeyi tako ta ina, da masu zumuɗin suga wacece Hindu sannan wanne irin kaya za'a kawota dashi. Yaran ragowar ɗakunan kishiyoyin Nanno kuwa rasa ma ta cewa suka yi tsabar yadda aka ɓarnatar da dukiya wajen lefen Hindu. Haka dai da suka gama sututansu da daddare aka kai akwatin Uwatale canma aka dasa labarin irin kayan da Gawata yaima Amaryarshi akaita cancana zancan. Har wajajen goman dare mata na zuwa kallon lefennan wannan gayama wannan abunka da ƙaramin gari. (Ƙauye garinsu kare. Shima kare da yaji sai yace shima kai shi akayi) Washegari sassafe Qasimu ya karɓo mota aka ɗebi maza ƴan kai sadaki su biyu, mata su uku sai Qasimu a gaba suka kama hanyar Kano da adireshin gidansu Hindu a rubuce a takadda. Sai bayan tafiyarsu ne Nanno ta leƙa ganin gini taga irin tsarin da Gawata ya ɗebo har fenti ya siya musu shi da Nawata su ba farar ƙasa zasu saka ba. Kai kawai ta girgiza tace da Gawata. "Anya yarinyarnan da iyayenta haka suka barka kuwa mijinyawa Ƙarami? Abun naka yayi yawa jibi irin ginin daka yanka ma wannan yarinyar dole sai ka bambamtata da surukan gidannan dai harda siyo fenti ko? " Nawata ne yace. "Nanno ai babu komai ita wannan yarinyar kinga bata ma taɓa rayuwar karkara ba a hakanma haƙuri zata yi. Dan Allah Nanno ki kawar da kanki ayi komai a gama, ki dena biye ta matan karkararnan. Yanzu jiya da naje wajen uwatale sai fishi take yi wai banyi mata lefe irinna Gawata ba, shine nake faɗa mata shima kamawa tayi" "Hmmm ba shakka kam" Iyakar abinda tace kenan ta wuce. Ko data shiga ɗaki kasa zama tayi ta kai mari takai gwauro a haka Inna ta shigo ta sameta. "Yaya Habiba wannan abun na Mijinyawa ƙarami na hankaline kuwa, naji ance dubu ɗari biyar aka danƙa mishi yake ta facaka dasu akan mace ɗaya, kinga irin ginin da yake yi mata kuwa? Naga tsakargidan nashi ma siminti zai saka ga fenti ya siyo haka ƙyaure ma madadin ayi na langa_langa na katako yasa aka yo mishi fa abun ya wuce misali a kanshi ne aka soma auro yaran maraya ne. Guda nawa aka Auro daga Bauchi? Kinsan ance fa matan Kano wayo garesu gasu da buɗewar idanu" "Hmmm bari Ladi sama da ƙasa na rasa abinda zance da kika ganni a tsaye. Nayi dana sanin amince ma Yaya wallahi, amman babu komai Allah ya kawo yarinyar lafiya Ladi" Sun jima suna jimanta lamarin yadda kuka san anyi mutuwa mai girma" Kano: Mrs Bukhari Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JeGDRQ8mO6FFQgNGk3VCtA *NIZWA ASAL SHIFA!* (WARAKA DAGA TUSHE) Albishir ga masu neman magungunan da aka samar da su da ingantattun tsirrai ba waɗanda suka gama gantali a kasuwa ba, kayan Companyn NIZWA ASAL SHIFA (Waraka daga tushe) kaya ne tafiyayyu tun daga kasar Oman, muna da maganin sanyi test and trust, muna da maganin ulcer natural wanda aka samar da shi daga ingantattun tsirrai waɗanda ake shuka su musamman domin Companyn. Ina masu fama da kasala, ciwon ciki, tashin zuciya, ko cushewar ciki? Kukanki ya zo ƙarshe, ki zo ki gwada Nizwa Asal Shifa ki ba da labari, a farashi mai rahusa za ki yi maganin matsalarki. Babban reshenmu yana kasar Oman, kuma akwai reshe a jihar Kano, tuntuɓi lambar nan kai tsaye domin mallakar naku. Oman: +968 9536 8260 Nigeria: 08039666871TSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI SHAFI NA GOMA SHA UKU *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JeGDRQ8mO6FFQgNGk3VCtA *NIZWA ASAL SHIFA!* (WARAKA DAGA TUSHE) Albishir ga masu neman magungunan da aka samar da su da ingantattun tsirrai ba waɗanda suka gama gantali a kasuwa ba, kayan Companyn NIZWA ASAL SHIFA (Waraka daga tushe) kaya ne tafiyayyu tun daga kasar Oman, muna da maganin sanyi test and trust, muna da maganin ulcer natural wanda aka samar da shi daga ingantattun tsirrai waɗanda ake shuka su musamman domin Companyn. Ina masu fama da kasala, ciwon ciki, tashin zuciya, ko cushewar ciki? Kukanki ya zo ƙarshe, ki zo ki gwada Nizwa Asal Shifa ki ba da labari, a farashi mai rahusa za ki yi maganin matsalarki. Babban reshenmu yana kasar Oman, kuma akwai reshe a jihar Kano, tuntuɓi lambar nan kai tsaye domin mallakar naku. Oman: +968 9536 8260 Nigeria: 08039666871 Tun safe aka soma shigowa da lefe cikin gidan daga masu akwati biyar shine dama saitin sai masu huɗu babu masu ƙasa da hakan. Duka dai sonsanet ne kaloline suke bambamta da kuma irin kayan da aka danƙara a ciki. Cikin gidan namu duk Inda ka wulga ƙamshin kaji da toye_toyen kayan fulawa kawai akeyi. Banda lungunmu da yake tsit kamar ba kayan lefena za'a kawo yau ba abun mamaki da ɗaurewar kai. Shinkafa da miya da naman kasuwa Innarmu tasa su Yaya Saratu suka girka, sai zoɓo da akayi shikenan iyakar abinda tasa akayi, tana zaune tana waye _waye da kafinta. Saɓanin sauran lungunan da aketa soya kaji da abubuwan arziki. Nasan duk dan a tozartani ne yasa akayi hakan ko, ni kuma a lokacin ban damu da komai ba ni dai cikar burina shine kawai Gawata ya zama mijina daga haka bana neman komai, kuma ina ganin samunshi tamkar duniyata ne. Luba tana gefena muna aikin ƙus_ƙus. Sai kiran Innarmu akeyi tazo an kawo akwatin ƴan matan gidan barin da akayi la'asar yamma sakaliya, abubuwan arziki ba kama hannun yaro gaskiya. Sai daf da magriba muka jiyo shigowar dangin Gawata mata da kayan Akwatinsu Inna Abida ta basu izinin zama a falo. Mazan kuma suna falon Baba Nagoɗi. "Saratu kuje ku same su ganinan zuwa dallah" Cewar Innarmu da ranta ya sake ɓaci ita so tayi Gawata ya gaza da kanshi ya janye sai hakan bata faru ba, dama ni nasan shirin Baba Sojanmu kenan shi yasa aka gabza mishi kuɗin sadaki. Haka dai aka amshi akwatunan aka gabatar musu da abinci babu yabo babu fallasa ni da Luba muna ɗaki muna jiyo maganganun matan gida a falon amman bama iya jin me suke cewa. Sai da sukai sallar magriba da isha kana sukai musu sallama suka tafi akan sai ranar ɗaurin Aure in sun biyo ƴan ɗaurin Aure domin tafiya da Amarya, Allah ya taimakeni basu fasa ƙwan a Jama'are zan tare ba. Suma su Innarmu babu wanda yace dasu ina zan zauna. Innarmu ce ta shigo ta nemi waje ta zauna tare da yin tagumi tayi shiru. Yaya Saratu ce ta shiga shigo da akwatin tana masifa. "Wannan kwashen kayan abun kunya sune suke tunanin zamu ɗauki tukuici mu basu, har wata mai bakin surutu tana cewa ba'a basu tukuici ba yaba kyauta tukuici. Wa yace mata an yaba oho. In banda ƙaddara ina Hindu ina waɗannan ƴan ƙauyen. Ga kayan naki nan Hindu babu atampa ɗaya mai mutumci a ciki. Nayi shirune a falo sabida su Innah Abida amman kin faɗo kunya kuma kin gama bamu kin kai kanki ƙasa darajarki ƙasa warwas tayi." Innarmu tace" "Da nasan irin tsinkanin da za'ayi kenan da lefennan ba'a buɗe ba har saida suka tafi da mun watsa abubuwan arziki a ciki. Shikenan gida kuma ya ɗauka kenan har cikin unguwa cece kuce bazai taɓa ƙarewa ba sai dai ya lafa." Ambulan Yaya Zubaina ta jefo mun kan cinya tace. "Gashi nan shi shagon yace a baki. Ace kaya babu guda ɗaya da aka ɗinka a haka suka kawo mu suke so mu ɗinka miki kenan? " Innarmu tace. "Ai gara dai da basi ɗinka ba Zubaina, ma zabtare rabi a kai kasuwa a tsinto mata manya ko koddibuwa babu bare kuma super daga mai kaza sai mai tabarma sai soso shikenan fa. Allah dai ya kyauta. Saratu a ciccire kawai ki jefa a durowar can, akwai manyan atampopi a saman sib ki ƙirga ki zuba mata, sai a haɗa mata da ƴan masu dama_daman a cikin nasu, sabida dai ta saka su gani kar ya zame mata wata jarfar, dan naga danginshi basu da dama ne" Ni dai ban samu zarafin cewa uffan ba wasiƙar Gawata ma sai da dare ya raba na buɗe harda kuɗi dubu ashirin a ciki na kayan fitar biki. Washegari kuwa na haɗa da kuɗaɗena da nake ɓoyewa suka cika dubu talatin na damƙama Innarmu baki a taɓe tace. "Zan haɗa in siyo miki duk abinda ya dace yau ki samu ki kai ɗinki Amman da biye ta halinki za'ayi wallahi babu abinda za'ayi miki. To ina da mutane na kunya dole zan fita kunyarsu ga ƴan sa'ido da suka sakama auren ido suma, ga ƴan uwana da dangi duka dai" Haka akaita shirin biki ana saura kwana huɗu ɗaurin Aure gidanmu ya cika dam da ƴan uwa na nesa anata hidimar yin cincin da su nakiya na amare da shirye_shirye. Na dawo daga karɓo ɗinkuna kenan Innah Yahanasu take tambayata ai ya kamata in ma Gawata magana asan a wacce unguwar ya kama haya sabida batun jere ko? Yace sai ranar ɗaurin Aure in suka zo za'ayi komai amman bansan inda ya kama ba" Na faɗa gabana na faɗuwa burina a ɗaura aurenne koma menene ya biyo baya zai zama mai sauƙi jin a jama'are zan zauna zai iya sawa a ɗaura aurennan da wanin Gawata amman ba shi ba. Ana gobe sakun lalle akaita zuwa jeren Amare ko wacce anyi mata kaya na kece raini amman inaji su Yaya Saratu suna faɗin kayana yafi na ko wacce Amarya kyau da yawa. Da daddare aka soma mun kitso bamu muka gama ba sai asuba kwana akayi cur wallahi ana yi mun kitso irin namu na Kanuri. Bayan mun yi sallah kuma sai muka soma lalle ai kuwa ana gama yi mun makarai suka bigeni a kwance na wuni ga hidimar biki anata yi ni bansan inda kaina yake ba wai sunzo taya ni murna sai guɗa suke yi. Da daddare aka saka amare a lalle ni kuwa sai su Innah Abida ne suka saka ni a nawa lallen Sabida a gaskiya dangin Gawata basu zo ba sabida nisa, kuma basu da wanda zasu wakilta. "Yarinya sai kace bazawara ace ba sakun lalle wannan wanne irin Aure ne? " Inji Inna Abida Innarmu dake ɗauke da cikin maganganu da yawa na Innah Abida tace. "Aurene kamar ko wanne Aure ai sakun lalle al'adace ba addini ba bare ya zama wani abun dan Hinduwa bata sameshi ba. Abida duk yadda kike ji game da Aurennan dake da duk munafukan da kuke ta gutsiri tsoma sai aurennan ya zame muku tsuron tsirin tsandauri wanda baku da yadda kuka iya dashi sai Allah. Aikin banza da wofi ke Hindu tashi mu tafi Allah ya sanya alkhairi a cikin wannan Auren in sha Allah maƙiya kunya zasu ji kawai mu dai da amincewarmu akayi wannan Aure" Ni dai ina cikin mayafi Luba ta taimaka mun na miƙe muka shiga ciki. Washegari ranar Juma'a kenan aka tashi da tuwon ɗaurin Aure wanda akayi na dukka gidan, sai abincin da kake so kuma sai kayi da jama'arka anyi shinkafa da miya, anyi alala da kunun gyaɗa amman dai dangin Gawata masu zuwa ɗaukar Amarya tuwon aka ajjiye musu. Kayan akwatina kuma Innarmu kusan komai ta canja a zannuwan ragowar turamen masu haske ta bar mun su, ta yi mun kayan fitar biki kala takwas tayi mun. Ƙarfe biyu da rabi aka ɗaura Aure a ƙofar gidanmu. Ƴan uwan Gawata kusan mota gudane suka kutso kai suka shigo, ga ciki ga goyo duk a caɓe dai ga rana ƙata. Haka akai musu jagora zuwa ciki ni kuma ina gidansu Luba da ƙawayena biyu na unguwa dan ƙawayenmu na makaranta gargaɗin Luba nayi da kada a faɗa musu ni ban son fitina. Ina saye da lace fari mai adon zare ruwan zuma. Na sanya takalmi da mayafi da gyale ruwan zuma wanda a cikin akwatina yake shine babban seti a cikinsu, ɗan kunne da sarƙata itama ta cikin akwatine na sanyane sabida dangin Gawata su san na girmamasu sun kawo kuma na saka dan har cikin raina banji daɗin yadda aka sake mun turamen zannuwana dan kawai a nuna musu gazawarsu ba, ina da yaƙinin shi kanshi Gawata bazaiji daɗin hakan ba, ta yiwu ya haddace abinsu kuma yana so ya ga na ɗinka na saka. Ina fesa turare Luba ta shigo tana guɗa ta faɗo a guje. "Alƙawari ya cika Hinduwa ta zama matar Gawata ga kayanki nan a mota an zo dasu ƙofar gida ana zuba kayan Kitchen ke kinga kayanki kujerunki manya manya masu ɗan karen kyau wallahi, gaskiya an gwangwajeki gaskiya Hindu wai kinga kaya kuwa. Talatu kuzo dan Allah ku taya ni mu kwashe kayan Kitchen ɗin Amarya mu fita dashi maza" Ana cikin fitar da kayan ina zaune zazzaɓi na ɗebeni ina jin mutanen nawa a kusa dani sosai. Innah Abida da Innah Yahanasu suka shigo suka fito dani tare da innarsu Luba, ƙofar gidan danƙam ga motocin ɗaukata a jejjere bus _bus ne dukka gajiyayyu wahalallu. A haka muka ratse mutane muka shige ciki kaina a ƙasa sai hayaniyar biki akeyi mutanena suna sake matsowa kusa_ kusa. Muna shiga ɗakinmu saka ƙafar da zanyi naji Innarmu na rantsuwar sai dai a sakeni ba zani ƙauye ba. Ihu na daka na faɗi tim a ƙasa ina burburwa, mutanena suka tashi a gidan biki, da ƙyar akaita basu haƙuri suka tafi ni dai na dawo hayyacina dai_dai sanda Baba Sojanmu ya leƙo yana cewa. "Ku fito da'ita ko a sumen ne a wuce da'ita ko ina zai kaita ai mijinta ne kuma shi yace ya riga ya sanar mata acan zata zauna dan haka ku fito da'ita Hinduwa Allah ya bada zaman lafiya ya kaɗe fitina a tsakaninku ya baki wuyan ɗaukar matsalolin da duk suka taso miki. Ruwayya kema ki saka mata albarka fishi ya ƙare Aure ya riga da ya ɗauru" Ajjiyar zuchiya Innarmu ta sauke kana tace. "Allah ya basu zaman lafiya da zuriya ɗaiyiba Yahanasu kamata kuje" Nan fa dangin Innanmu suka miƙe tsaye suna wallahi bazai yiwu akai ni ƙauye a kashe mun rayuwata ba. Hannuna Baba Sojanmu ya damƙa, ba shiri na miƙe tsaye. Yana faɗa dasu Innah Yahanasu. "Wallahi sai ta je. Idan a bangon duniya zasu zauna menene naku? Yarinya dai ta san da maganar kuma ta amince ai shikenan." Baba Nagoɗi ne ya leƙo da sallama. "Ku fito mana a kama hanya waje ba kusa ba. Jama'are da fa nisa. Wai nace a ina Jama'are take ne ma janaral? " " Jihar Bauchi ne Nagoɗi. Muje zan kaita mota matan su biyo bayana." Baba sojanmu ya miƙo mun sadakina a hannuna harma yaimun ƙarin dubu ashirin akai, Innarmu ma ta bani dubu ashirin tare da ƙaramin da akwatin ɗan kunne ƙarami na gwal haka tai ma su Yaya Saratu ma. Tanadi ne da'ita sosai dan hatta su Rayya da Jinjin ta siya musu ɗan kunnen yana adane tana jiran lokacin bikinsu yayi ta basu, kamar yadda ta bamu. Allah sarki uwa mafi uba ko da uban sarki ne. Fitowa dani Baba Sojanmu yayi ayarin dangin Gawata da dangina suka rufa mun baya. Ko da muka fita mun tadda Yaya Zubaida da Yaya Jamila suna cacar baki faɗa ne ma ya kaure a tsakanin dangina da dangin Gawata akan motar da za'a saka Amarya sabida duk bus suka kawo. "To menene wai dan ta shiga bus shin wai ita wannan ɗiya taku da aketa yi mana wulaƙanci tun a kawo akwati ɗiyar gwal ce ko kuwa itace tafi sauran mata ne baiwar Allah amsarki nake jira? Duk Gawata ne ya jawo mana wannan yarinya sai kace zinare dan bala'i da masifa " Cewar Yaya Jamila da take son rikicin ya ƙara tsayi. Ai kuwa Yaya Saratu ta amshe da cewa. "Ai ko ba gwal bace tafi ƙarfin ɗan uwanku kuma kun sani wallahi. Ya za'ayi ace babu motar amarya sai a bus za'a kaita kamar kowa? " Inna Abida da Inna Mairamu ne suka iso wajen. Baba Sojanmu ya girgiza kai kawai ya shigar dani mota ya ajjiyeni. Zai saki hannuna saina riƙe hannun nashi, juyowa yayi muka haɗa idanu mukai shiru. "Hindu kije ki zauna da haƙuri, duk wata tarbiyya da iya zama da miji kin koya daga Ruwaiya bana jinku. Allah yayi albarka, ni da mahaifiyarki duk mun saka ma Aurenki albarka kuma da amincewarmu akayi." Hannunshi ya zare ya wuce ya koma cikin su Baba Dogara. Su kuma a waje anata rikici fa ƙata. Inna Abida tace. "Ko a amalanke akace muje sai mu je ai Saratu. Allah dai ya kyauta ko jeeb suka kawo ai dai a ƙauye zamu barota dai ko? To ku shisshiga muje kawai Yahanasu kuje ku shiga waccan ta gaban. Yarinya dai ta ja ma kanta, ita da cikar guri sun yi hannun riga. Bama tasan menene ƙauye ba wallahi, hakanne ya sanya ma ta amince. Ga kaya da Ruwaiya ta dandatsa sai dai a dawo da wasu dole" Luba ce ta shigo ta zauna kusa dani, da matasan ƴan matan gidanmu. Amaren da aka ɗaura aurenmu tare duk suna waje ganin gulma motar kaya ta wuce tare da su Akarami harda Qazzafi shima ya bisu abinda Inna Mairamu bai mata daɗi ba kenan. Ƙarfe uku da ashirin ayarin motocin amare da angwaye ta kama hanyar jama'are fuu muka fice a na'ibawa ajjiyar zuchiya na sauke sassanya har wata iskace naji tana shigata tako ta ina, sai naji kamar an saukemun Kano a kaina ne. Soyayya kenan. Haka mukaita tafiya a titi ƙawayen Amarya da su Inna Yahanasu sai abinci suke ci suna nishaɗinsu sai hira akeyi ana dariya da abincinsu suka tawo kula babba. Jallof ce lafiyayya da naman kaza da Innarmu taima ƙawayenta malamai. "Hinduwa ga abincin daure kici tafiyace mai yawa a gabanmu Allah kaɗai yasan yaushe zamu isa dan daga nan zuwa Bauchi ma nanda isha'i albarka bare mu ɗauki hanyar ƙauyan naku" Cewar Innah Yahanasu. Dake motar duk mune babu dangin miji ko ɗaya sai direba da yake bare saina sa hannu na karɓa rabona da abinci tun jiya da daddare babu ma wanda yake tani bare a bani abincin inci. A hankali nake tauna abincin ina tunano yadda muka tsara rayuwar Aurenmu yadda zata gudana. Ina fatan kada mu samu cikas dan zama da uwarmiji dole sai mutum ya kiyaye da duk abinda zaiyi, mu kuma rayuwa mai kyau cike da soyayya muka tsara. Murmushi nayi ina hango ɗakina a idanuna muna guje_gujen soyayya ni da Gawata, ko muna cin abiinci muna hirarmu ta soyayya. Da wannan tunane_tunanen harna gama cin abincin ta miƙo min mirinda na karɓa na shanye tas nai gyatsa dan na ƙoshi dam. Mun daɗe muna tafiya duhu ya rufa, gudu muke yi babu sararawa a jajjere muke tafiya motoci biyar huɗu ta mata ɗaya ta ango da abokanshi. Bamu muka tsaya ba sai takwas na dare a wani ɗan ƙauye a cikin gidan mai. Anan mukai la'asar magriba isha ina fitowa daga masallacin mata Gawata ma yana fitowa idanu muka haɗa muka sakarma juna tattausan murmushi mai ɗauke da ma'anonin da mu kaɗai mukasan abinda hakan ke nufi. Zuwan Yaya Saratu tasa ya wuce sum_ sum ni kuma na lumshe idanuna tare da binshi da kallo. Motarmu muka koma Yaya Saratu ta siyo mana gurasa da tsire da yawa ta miƙo mana. Abokan ango suka miƙo mana ruwa da kaji da Lakasera motarmu ta sake ɗagawa bamu muka shiga jama'are ba sai wajajen sha ɗayan dare gari yayi duhu dunɗum ya ɗaure babu wutar lantarki ko kaɗan. A ƙofar gidan motocinmu suka tsaya. Mata da tsaffi suka tare mu da guɗa yiriri_yiriri. A mugun galabaice duk muka sakko mukai ayari aka shiga daga ciki kai tsaye ɓangaren su Nanno aka wuce dani ga hayaniyar ƴan biki nan muna jiyowa daga ragowar ɗakuna. "Maraba lale kune a darennan sannunku da zuwa ku shigo mana" Cewar wata mace da bansan wacece ba. A tsakiyar ɗakin Nanno aka zaunar dani ina cikin mayafi kirib. Gaisuwa ta gudana a tsakankaninsu kafin Inna Mairamu tace. "Ga Amarya mun kawota. Tana hannun Allah tana hannunku a riƙeta da Amana dan Allah Hindu yarinyace mai hankali" Innah Yahanasu tace. "Ƙwarai kuwa tana da hankali da kuma biyayya. Allah dai ya basu zaman lafiya" "To Ameen dare yanzu yayi kamata yayi kuje ku kwanta zuwa safiya a zagaya da'ita ɗakunan sauran mazauna cikin gidan bisa al'ada. Akulu a bisu da abinci a nuna musu ɓarayin nata, ga acibalbal nan ki tafi musu dashi." Miƙewa nayi jikina a sanyaye tarara ni tunda muka shigo ƙauyen naga yadda yake damma darene ga duhu duk saina karaya fuskar Gawata kaɗai nake tunowa inji salama sai ƙarfi yazo mun, kuma ni jarumace gaya. Nifa in a rami zai sani muddin tare nake dashi babu komai. Ƙarasawa akayi damu ɓarayin nawa gasunan guda biyu nawa yasha fenti ruwan omo haka muka kutsa kai muka shiga ɗan ƙaramin tsakar gidan. "To ga ɗakinnan ku shiga can kuma Amaryar wanshi ne a ciki abokin tagwaitakarshi tare duk akayi bikin." "To mun gode sosai" Yaya Saratu ta faɗa. "To bari a kawo muku abinci da taburmai" Ta faɗa tare da miƙama Yaya Saratu aci balbal ɗin dake hannunta. Mu kuma muka shiga da sallama zuwa ciki. Nan naji su Yaya Saratu suna salati da hmmm da hmmm abakunansu akwai magana mai yawa nasan da ba dan idanun su Innah mairamu ba da naji maganganu a darennan. Wani irin turirin zafine a ɗakin kamar gidan biredi. "A gaskiya inaga sai dai mu yada zango a tsakar gida kawai ɗakinnan bazai zaunu ba. Kuzo muje tsakar gida kawai. Dole muka fice tsakar gidanma ba zata ɗaukemu ba mun cika tsakar gida mun cika ɗakunan sai kwasar wasu akayi zuwa sassan gidan. Tabarma manya manya aka baje mana duk muka zauna Yaya Saratu ta shiga rabon wata jalof ta masifa ƙandas babu man kirki bare kayan miyan kirki babu maggi sai gishiri cakwai harda nama tsoka guda guda yankan firit firit. Nima aka miƙo mun loma ɗaya da nakai bakina na tauna ƙuƙus kusan uku a jere da dabara na haɗiye shinkafar kawai nayi gum amman ban kuma gigin sake sanyawa a bakina ba. Wallahi kowa kasa ci yayi dole aka jujjuje a fantekar da suka kawo mana ga yinwa ga dare. Har su Yaya Saratu saida suka fita ko zasu tarar da masu abun siyarwa amman babu kowa sai karnukan ƙauye. Haka suka dawo gashi motar kaya bata isoba bare muci gara, ko su Qazzafi su shiga gari su nemo mana wani abun,kunji wannan? Bayan ko wacce ta kwanta da yinwar cikinta sauro da zafi suka hanamu bacci dole kowa ta miƙe zaune ni dai ina kwance ina ɗigar zufa ko kaya ban sake ba da lace a jikina zafi kamar zai halakani. Sai jefin asuba gari yayi sanyi muka samu muka runtsa asubar fari muka tashi shida da rabi sai ga motar kaya tare da su Akarami su kam a wani ƙauye suka nemi waje sukai kwanciyarsu sai da sukai sallar asuba suka tawo. Ina cikin uwarɗaki ina kallon silin ɗin saman ɗakin da tagogin ɗakin su Qazzafi suka soma shigo da kaya tare da abokan Gawata. "To ai wallahi kayannan ba zasu yi ma ɗakinnan ba wannan gandama gandaman royal yaushe zasu zauna a ɗakinnan. Akarami ku fita da kayannan waje zamu soma shinfiɗa kafet a ciki da waje tukunna. Mu yinwa ma muke ji sai mun karya mun yi wanka ya kamata ayi wannan aikin" Cewar Inna Yahanasu. Qazzafi yace. "To bari a jibge kayan a tsakar gidan asan an sallami mai motan" Ni dai ina tsaye, su Luba ne suka zari bokatai aka nuna musu rijiya suka soma jidon ruwan wanka kowa na watsawa yaji daɗi a jikinshi. Nima aka saka mun naje nayi na fito Inna Yahanasu ta bani wata koriyar atampa mai tsada na saka da sabon ɗankunne da sarƙa humra ta miƙo mun daga cikin humrorin aurena da suka tawo dashi daga Biu na mutsuttsuka ko ina ta ciki da wajen kayana, banyi kwalliyaba kwalli na zirara kawai na zauna a tabarma. Sabida dangin Gawata sun so tozartamu abincin da muka kasa ci wallahi shi aka ɗumamo aka haɗo da ruwan kokko babu ko sikarin kirki aka kawo mana. Hmm nasan ramawa suke yi suma layi ya zagayo kansu. "Hmmm mutanannan da rigima suke neman mu Innah Abida jibi abincin jiya suka sake ɗumamo mana dan wulaƙanci. Kunga bari in fita in nemo wannan ango da abokanshi su kawo mana abinda zamu ci ko mu dafa da kanmu" Fuu ta fice bansan yaya suka ƙare ba sai ga shayi da madara cikin babban robar fenti da biredai da ƙosai cikin fanteka abokan ango sun shigo dashi. Ƙanwar Nanno ce ta shigo dan taga an wuto mana da abinci. "Au shinkafarce bakwa so shine ba zaku yi magana ba zaku sa yaro irin wannan kashe kuɗi haka duk yawanku ace da shayi da madara harda mummuƙi zaku karya da ƙosai? " Innah Abida tace. "In da ma basu kawo ba kinga ko wacce lalitarta a cike take sai mu ciyar da kanmu tunda mu ba mitsiyata bane. Su da suka je namu gidan haka akayi musu ko haka akayi musu? Wa zaici wannan shinkafar" Hatsaniya dai ta ɓalle duk da batai nisa ba su Akarami da suke tsakar gidana sun shiga maganar kuma duk su biyun kayan sojojine a jikinsu. Ai na rage muku sai shigowa kallonsu Akarami akeyi tun sakkowarsu garin sabida an gansu da kakin soja. Anata tambayarsu a waje suna cewa su yayu nane. Haha ƙauye garin su kare shima kare da aka tambayeshi yace kaishi akayi, wannan kakin Sojoji ya sake ɗaga daraja a Jama'are bayan na lefena. Bayan duk an gama karyawa dangin Innarmu suka kamo hannuna muka shiga cikin gidan domin inje in gaishe da Nanno da ragowar matan gidan. Gidan a tumbatse yake sosai kasancewar yau buɗar kai, muna tafe suna gaisawa da jama'ar biki har zuwa shiyyarsu Nanno a falonta suka dureni aka gaggaisa babu fara'a sam a muryar Nanno nasan har a fuskarta ma babu yadda naji muryarta a daddaƙile. Nan dai aka shiga yi mun nasihohi akan in zauna da kowa lafiya. Aka kira Shafa matar babban wansu wanda suke zaune a gidan ta zazzagaya damu tun daga kan kishiyoyin Nanno har izuwa surukan gidan su su tara tare da matar Nawata mutum goma kenan saini ta sha ɗaya. Har ɗakin Amarya aka kaini a cewar Shafa ai itama matar wan mijinace dole in bita in mata biyayya kunji fa. Haka mukai sallama muka shiga tana ɗakin gadonta daga ita sai ƙawayenta wani gadone na ƙarfe mai madubai dunƙulallu na fulani kun ganeshi? Yauwa to shine a ɗakin gadonta yasha zanin gado sule ango ruwan hoda irin bau dinnan kun gane sule ango ai? Wani zanin gado da ake yayinshi da wanda ko jingina akayi a jikin gado zai sulalo ya faɗo ƙasa to shi. Sai sib ɗinta bango guda da wajen kwalliya sai jeren kuloli da kicin waya harda kofuna tarkace dai harda randar shan ruwansu baƙa mai giwa ƙarama, duk fa a uwar ɗaki, na zaune baiga gari ba. "Uwatale ga matar ƙaninki nan mun kawo miki, nasan taku saita fi zama ɗaya ɓarayinku yayi kusa kuma tare aka auroku gashi kune yaran mata a gidan sai matar Rabi'u." Buɗar bakin uwatale tace. "Ayya Amarya Allah ya bamu zaman lafiya da haƙuri da juna. Amman ni ai matar Rabi'u ce ƙawata Yaya Shafa" Anan ai kun gane mai take nufi ko? Nan muka tashi muka koma nawa ɓarayin a lokacin anata shigar da kaya ciki an gaggama malala kafet mai ruwan bombota turarre a ƙasa ciki da waje wasu na jera kujeru wasu na kafa gado har sib an shiga da'ita. A gefe na zauna ni da su Luba. "Hinduwa kinga ƙauyen kuwa jibi gidan fa da zaki zauna kiyi rayuwa ke da aka haifa a maraya, jibi matan gidan ƴan ƙauye fituk dasu ga ɗan karen nisa ke kuwa Hinduwa" Luba kenan ai babu komai babban burin ɗiya mace ta samu miji nagari nagartacce wanda zai riƙeta da mutunci watarana in sha Allah zamu bar ƙauyannan ko Bauchi saimun koma" "Hmmm da kamar wuya jibi fa Shafa take ko wa harma ta tsufa amman ba gasu suna zaune ba sai kece za'a bari ki janye Gawata. Batun ci gaba da karatunki da cikar burinmu na son zama ƴan jarida ma'aikatan tv ko rediyo gaskiya gurine wanda bazai cika miki ba ki haƙura ki watsar da karatu kawai. Kuma sai kinyi da gaskene zaki fita daban a cikin gidannan wallahi in ba haka ba sai kin dawo kamarsu ba tare da kin sani ba. Ni da naga Rabi Nass da tai aure a ƙauye ita da take Kaduna a cikin ƙanƙanin lokaci hatta fatarta saida ta sauya ke kinga wai yaranta ma kuwa hmmm" Duk da haka babu karaya tattare dani ni bana kwan gaba kwan baya gaba gaɗi nake lamurana in eh ne to eh ne haka in a'a ne to a'a ne. Murmushi kawai nayi mata bance mata uffan ba. "Hinduwa zo kiga falonki babu masaka tsinke baifi mutum uku suyi sallah a ciki ba kinsan kujerunki manya ne" Hannuna ta ja muka shige ciki. "Kinga yadda suka yi, kuma uwarɗakin naki ma dake shida da bakwai ne gadonki shima babu waje ko za'a mayar da kujeru biyu ne can gida ko a bar miki haka? " Innah Yahanasu tace. "Tunda sun zauna a bar mata su kawai kayan kallonma sun zauna komai sai a bari haka Allah dai ya bada zaman lafiya kawai, babu wuta ma sai dai in ci gaba ya riskesu za a ja musu. Amman kayan Kitchen da durowar turare guda ɗaya, da su teburin tsakiyar ɗaki dole zamu koma dasu. Hatta zannuwan gado zamu koma da wasu. Ko da yake tunda tana da ɗaki daban a rage kaya a jera a ɗayan ɗakin kawai in yaso ko Bauchi kwa shiga a siyo kafet a malala duk da akwai tarin tulin gara da za'a zuba a ɗakin" "To shikenan Innah a barshi hakan shikenan. Amman batun wani kafet a barshi kawai a tura mata ragowar kayanta shi ɗakin da za'a saka mata garar a ciki kawai. Ƙawayen Amarya ku nemo mana rushi a cikin gida ya kamata asan kanuri aka kawo cikin gidannan tunda an gama dandatsa jere" Ni dai ɗakin na shige na tadda su Qazzafi sunata haɗa zufa suna aikin zaman sib Qazzafi ya ɗago ya zuba mun idanunshi da gaske ina kallon so na a idanunshi asalima tsananin sonne yasa ya biyoni har ɗakin Aurena rakiya. Kaina na kawar na zauna a bakin gado. Da aka gama gyara komai kujera ɗaya ta samu shigowa ƙurya kuma tayi kyau. Nan da nan aka banka turaren wuta namu na gangariya, Ga na Mrs Bukhari ma na siya Amarya package dan turarenta ƙamshinsu na musamman ne, wani irin ƙamshin fadar larabawa nata suke yi, kunsan turare fa iri iri ne wallahi ko Innah Yahanasu data ɗan ɗauki itace ɗaya ana mrs bukhari ta saka a gaushi ta gane kayan kamfani daban dana shago, ta bashi maki sosai kuma ta jinjina ma mrs bukhari, harma nake tsokanarta da cewa ai itama Kanuri ce ta ɓangaren mahaifinta Waɗanda suke siyen kayan ƙamshin mrs bukhari su baku labari wallahi, ƙamshin turarenta ba iya labule da kafet yake kamawa ba hatta bango wallahil azeem yana kama ƙamshi gida ya riƙe ƙamshi ƙaƙas ( in kin siya bai miki ba ki zo in mayar miki da kuɗinki) Su wannan bama yanzu zan soma amfani dasu ba sai ranaku na musamman, zan dai turare uwarɗakina kafin ango ya shigo. Unguwar baki ɗaya ta ɗauki ƙamshin daɗi. Akarami da Qazzafi dai wajajen azahar sukai mana sallama suka tafi Dubu ashirin ashirin suka bani cikin rashin jin daɗin rai na rabuwarmu muka rabu Qazzafi sai rarrashina yake yi idanunshi sun tara ruwa kamar zai zubar mun da hawayen ƙauna, yana ji yana gani kamar wasa ya rasani. Tausayina cike da yanayinsu, ni kuma ina mamakin yadda suke ta tausayamun Innah Yahanasu ana zaune kawai sai ta hau sharar hawaye da an magana sai tace tausayin yadda zasu barni take yi. Allah buwayi Mrs BukhariTSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA GOMA SHA HUƊU *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JeGDRQ8mO6FFQgNGk3VCtA *NIZWA ASAL SHIFA!* (WARAKA DAGA TUSHE) Albishir ga masu neman magungunan da aka samar da su da ingantattun tsirrai ba waɗanda suka gama gantali a kasuwa ba, kayan Companyn NIZWA ASAL SHIFA (Waraka daga tushe) kaya ne tafiyayyu tun daga kasar Oman, muna da maganin sanyi test and trust, muna da maganin ulcer natural wanda aka samar da shi daga ingantattun tsirrai waɗanda ake shuka su musamman domin Companyn. Ina masu fama da kasala, ciwon ciki, tashin zuciya, ko cushewar ciki? Kukanki ya zo ƙarshe, ki zo ki gwada Nizwa Asal Shifa ki ba da labari, a farashi mai rahusa za ki yi maganin matsalarki. Babban reshenmu yana kasar Oman, kuma akwai reshe a jihar Kano, tuntuɓi lambar nan kai tsaye domin mallakar naku. Oman: +968 9536 8260 Nigeria: 08039666871 Har ƙofar gida muka rakasu ayarin ƴan ɗakinmu. Na kalli unguwar da kyau na kuma kallonta da kyau hmmm akwai aiki ja ƙau. "To Hinduwa mu kam dai sai kuma sanda kika zo Kano zamu sake haɗuwa in Allah ya ƙaddara kinzo lokacin muma munzo kenan, tunda ba zama muke yi ba" "Tunda ku gwagwarene bare a biku duk garin da kuke ba. Ya kamata kuyi ma kawunanku faɗa ku nemi matan Aure" Cewar Yaya Zubaida kenan. Dariya Akarami yayi yace. "Ni kam da tawa a hannu shekara bazan kuma yi babu Aure ba. Sai dai kuyi ma Qazzafi magana ya nemo wata a cikin gida ko waje kunga muma sai a gangama ai mana auren tare ko wanne ya tare a bariki da matarshi, to yanzu ƙila ya mayar da hankalinshi akan Sailuba ta lungun Baba Lukumanu, ta jima sosai tana nuna mishi so duk da bata furta ba bama zata iya ba. To yanzu tunda ba Hindu sai yayi maneji ai." Qazzafi dai bai kula wannan zance na Akarami ba. Mun ɗan jima a tsaye harma Gawata daya fito a wani gida ya tawo aka gaggaisa fuskarshi sai hannuri take yi yanata satar kallona. Shi ya raka su Akarami mu kuma muka shige ciki ƙofar gidan danƙam da yara suna kallon su Akarami da kakinsu na sojoji. Mun shigo mun tadda faten shinkafa aketa sha na manja babu kyan gani. Muna shiga ɓarayina muka tadda Inna Yahanasu na haɗa murhun dutse. "Saratu aje a nemo mana cefane zamu ɗaura ko taliyace aci munfi ƙarfin wulaƙanci fatensu kuma a mayar musu dashi babu mai sha." Ai kuwa yadda akayi kenan sai cefane akayi suka dafa jallof mai lafiya da nama har dare suka yi ta, bamu muka ci abinci ba sai la'asar. Wannan girki yasa anyi rigima mai ƙarfi har maƙota Yaya Jamila ta shigo taita rashin mutumcin wai an rainasu ana ƙyamarsu lamarin daya haifar da rikicin da sai da maza dattawan gidan da su Gawata suka shiga aka kwantar da tarzoma Bayan lafawar komai Gawata ya shigo yanata bada haƙuri akan da daddare zasu sa ayo girki a kawo haka ma da safe. "Ai ku barshi wallahi bama so munyi girkinmu har dare kuma gobe ma zamu yi na safe muyi kuma na rana kafin mu kama hanya mu koma garinmu. Ai babu komai yaro kuyi duk yadda kuke so yana da kyau" Shi dai yaita bayar da haƙuri fitarsu babu daɗewa suka aiko nono jingim da fura kowa yasha ya more, ni dai ina gefe kamar kunne tunda ni suka fi haushi sama da kowa a hakanma tausar zukatansu kawai suke yi. Nan aka shiga rabon kayan fulawa aka kai na ɓangaren su Nanno komai randa guda aka aika musu harda ƙaramin buhun shinkafa aka kai musu. Wajajen Magrib akaita shigowa ganin ɗaki kamar hauka gungu_gungu aketa zuwa harda ƴan unguwa mai nisa da daddare sai gasu gungu _guda wai sunzo ganin waje mu dai mamaki ya ishemu kai subhanallah. Washegari sassafe suka dafa taliya da shayi akaci akayi hani'an Gawata ma yasa an kawo koko da ƙosai. Gidan babu hayaniya sosai sabida baƙi sun warwatse. Suma sha ɗaya nayi suka gama shiryawa basu yi girkin rana ba sunce a ƙoshe suke, sai dai kafin su tafi anyi mun cefanen kayan miya da yawan gaske harda ɗanyen nama da kai da ƙafafun rago. Har ƙofar gida na rakasu har saida naga tafiyarsu Gawata ya rakoni na shiga ɓarayina. Jikina yayi wani irin sanyi ƙalau, sai na jini babu guiwa. Ina shiga na saka sakata nayi shigewata ciki ina ƙarema ɗakin kallo yanzu ne na samu zarafin kallon komai cikin nutsuwa. Wani sanyi nake ji yana gangaromun kawai yanzu nan ɗakin aurenane ni da Gawata da yaranmu zamu rayu a ciki. Masha Allah, Allah shine abun godiya mai girma da ɗaukaka. Kitchen ɗina na shiga komai fes dashi kaya a jere gwanin sha'awa sosai tire na ɗakko tare da basket mai hannu na fito tsakar gidan nawa na baza kai da ƙafafun ragonnan a tire na ɗaura bisa katangar ɓarayina dake ba bisa gareta ba sosai danma bani da tsayi da zan iya hango mutanen cikin gidan. Kayan miyan kuma na juyesu a basket masu kyau dasu gwanin sha'awa. A gefe can wajen inuwa na ajjiyesu Naman kuma na shige dashi ciki na kunna risho na ɗaura tare da saka musu kayan ƙamshi tunda babu wutar lantarki a jama'are ga firji da kayan kallo amman dai sun zama abun ado kawai. Gawayi na fita na ɗakko wanda suka yi girki suka kashe na kara biyu a jikin rishon na koma na share tsakar gidana tas nice harda saka ruwa da omo na wanke sumintinnan tas har wani ɗan rumfar gini da akaimun da ginannen murhun itace a wajen saida na wanke, wajen wanke_wanke na da wanki wani ɗan rami akayi kamar bawon wanka na turawa da rariya a ciki, daga gefenshi kuma radunanane guda uku shaƙe da ruwa, sai buta ɗaya da suka ajjiye mun sabida ban ɗakin waje. Kunji Amarya da gyaran gidanta da kanta ko? Tsakar gidan yayi mugun dattine, bafa ƙaramin tururuwar zuwa ganin ɗakina aka dinga yi ba. Shima wannan ya taka muhimmiyar rawa a zaman jama'are gaskiya. Ina sauke naman na ɗaura ruwan wanka kana na turare ko'ina da turaren wutana irinna mrs Bukhari turaren wuta ɗan gaske wanda sai dai kace tsada ba dai rashin riƙe ɗaki da musulmin tattausan ƙamshi ba, kuma dama abu mai kyau da nagarta yana da tsada sosai. Ƙamshi wani babban sirrine na ma'aurata sosai macen da tasan kanta dole a ganta da humrori da turaren wuta na gasken ba wannan itace da ruwan banzan ba. Wanka nayi na sallaci azahar. Sai murmushi ke kubce mini wallahi har sanda nake sallar. Sabida murna ji nake zuchiyata kamar zata fatso ta fito Ina kan sallaya ina jan carbi naji anata doka ƙofar ɓarayina da sauri na cire hijabina na fito na caɓa ado nasa sabuwar atampa mai tsadar gaske na sha ɗauri ga ƙamshin Humrori ina bazawa. Ina zare sakata naga wai matan maƙotane da basu samu shigowa ganin ɗaki ba suka shigo kusan su bakwai ko wacce da goyo kamar haɗin baki, sun dame da ƙazanta wani ƙarni_ƙarnin Mama suke yi dake masu shayarwane. "Amarya munzo ganin wajene dama a tsanake maƙotankune, lokacin da ake tururuwar mu bamu zo ba, mun fi son mu zo a tsanake mu kashe ƙwarƙwatar idanunmu" Murmushi nayi musu tare da musu iso har ciki duk suka lalleƙa suna santin waje, tare da labarai iri da kala. Na ƙolla musu kayan garar fulawa sukai mun sallama Na bisu zan rufe ƙofa kenan aka aiko yara da kwanon abinci wai ya kawo mini. Nasa hannu na karɓa dama yinwa nake ji sosai gashi kayan fulawar ko son ganinsu banayi na kasa ci gashi jingim kuma. Ina shiga na buɗe kwanon. Taliyar hausa na gani a cikin ruwan manja tana iyo. Rufewa nayi nayi jigum wallahi bazan taɓa iya ci ba gashi yinwa nake ji, zuchiyata take ta soma tashi ma. Agogo na kalla biyu har ta gota ai saina miƙe na shiga Kitchen na fita da turmina waje na ɗauki roba da wuƙa na fita. Jajjayen kayan miya nayi na koma ciki na tsaida sanwar shinkafa jallof gongoni uku na wadatata da nama da maggi mai star, ga jajjagen yaji tafannuwa nan da nan gida ya ɗauki ƙamshi, ina cikin girkinnan naji ana wani irin bubbuga ƙofa kamar za'a cire mun ita. Fita nayi na buɗe ƙofar Inna Ladi kishiyar Nanno nagani. "Hindu kece kika ɗaura girkine gida ya karaɗe da ƙamshi? " Murmushi nayi nace. Eh wallahi nice na ɗan ɗaura sanwa" "Wa yace miki mu haka muke yi wannan wacce iriyar fitsarace yau daga watsewar ƴan biki miji bai ko shiga ɗakinki ba zaki nuna rashin kunyarki da zumuɗinki akan bainar idanun surukai? Lallai mijinyawa da jajawur ɗin aiki a gabanshi. Ki jini kada ki sake ɗaura ko ruwan shayine in ba sati guda kika yi a gidannan ba. Mu ba haka muke yi ba gida duk ya ɗau magana. Haka akeyi yau ɗinnan biki ya watse fa amman sabida ƴan boko ku dama baku da ta ido shine har ƙamshi ya karaɗe gida" Tana dasa aya ta wuce fuu. Ni kuma nayi tsaye kawai illahirin mamaki ya cika ni. Nasan amarya bata girki saita kwana bakwai amman babu laifi a ciki danta ɗaura girkinta. Lallai dole saina kiyaye sha'anin ƙauyawa abun azimun ne zama da sirikan kenan takura da saka idanun tsiya. Komawa ciki nayi na sauke abincina na zuba a kwano naci na sha ruwa abina. Ina zaune ƙwalam har bayan isha duhu ya rufa sosai na kunna acibalbal ɗin da tunda muka zo aka bamu na ɗaura a saman alkuki. Kafin magriba na shiga da kayan miya da wannan naman kai cikin ɗakin dake kusa da namu. Ina jiyo hayaniyar abokan mijinyawa Babba da suka rako ango amman ni sai wajajen sha ɗayan dare Gawata ya shigo da abokanshi hannun Qasimu riƙe da leda ƙarama ta jiƙe da mai Abdulƙadiri kuma yana riƙe da hannun Ango. Nan aka gaggaisa dai suna nuna farin cikinsu da ganin wannan rana suka ɗaura da yi mana nasihu, kana sukai mana sallama suka fita. Ɗagowa nayi muka soma kallon ƙuda ni da Gawata da naga yayi wani irin kyau na musamman. Murmushi muka sakarma juna ya riƙe hannayena biyu a cikin nashi. A karon farko da wani namiji da ba ɗan gidanmu ba kenan daya riƙe mun hannuna. "Tutar so tunda kika mun irin wannan sadaukarwar kika baro birni kika biyoni ƙauyanmu ni kuma zan zame miki garkuwa bango abun jinginar rayuwarki, na yadda in ƙuntata ke ki samu farin ciki. Nayi miki alƙawari duk daren daɗewa zan mayar dake Kano mu rayu acan tare da yaranmu in sha Allah su samu karatu mai kyau ginanne kuma. Nafi ko wanne namiji sa'ar mace a rayuwata. Kin fi ƙarfin in haɗaki da wata mace ko da ana ha maza ha mata ke kaɗaice tilo a gidan Gawata daga ke babu ƙari" Sai yayi shiru ya sauke kanshi ƙasa me yake tunawa oho ban sani ba. Sai na katse shirun ta hanyar cewa. Mu godema Allah daya ƙaddara wannan auren duk da iyayena basaso Gawata ko kuma daga yau ka zama mijinyawa kamar yadda naji ana faɗa maka" Murmushi yayi mun yace dani. "Nima iyayena ba so suke yi ba ansha dambarwa Tutar so mai yawa. Zamane bamu samu yi ba bare in labarta miki halin dana shiga nima" Nan ya labartamun duk abinda ya faru bai rufe mun komai ba ya ɗaura da cewa. "Amman yanzu komai ya wuce mun samu nasarar kasancewa da juna. Yanzu dai ki tashi muje muyi alwala mu gabatar da nafila sai mu dawo ko?" Kunyace naji ta kamani sosai miƙewa yayi ya riƙe hannayena na miƙe tsaye nima a tare muka ɗaura alwala muka fito shi ya ja mana sallar mukai raka'a biyu yai mun ƴan tambayoyi game da addinina na bashi amsar ko wanne, abinda ya ƙara faranta mishi ranshi kenan. "To muje muci nama wallahi tsire muka samu kazar taƙi samuwa fur kuɗaɗenmu duk sun ƙare akan biyan masu mota kiyi haƙuri a bini bashin wannan kazar dole zaki ci." Ai da kayi mun magana akwai kuɗi a hannuna sai in baka ka siyo bana son abinda zai ɓata mana tarihin wannan daren mai tarihi daren da shi zai mai damu mu cure mu zama ɗaya" Dariya yayi mun. "To shikenan ki aramun dubu biyu inje in siyo zan dawo miki dashi da zaran na samu" Kunji fa a daren farko Dubu biyar na miƙa mishi nace. Ragowar ka barsu a ajjihunka" Nan da nan ya fita, kafin ya dawo na sanya doguwar rigar bacci marar nauyi na zauna a bakin gado ina murmusawa tare da ƙarema ɗakin kallo. Haka ya dawo ya taddani muka baje muka ci kazarmu muka haɗe da tsiren muka cinye tas muka sha mirinda. Bayan mun wanke bakunanmu lamura dadaɗa masu tsaiwa a rai suka shiga wakana. A iyakar karance karancen littattafaina anan na gano gwarzantakar Gawata da irin yadda ya bini a hankali har komai ya wakana cikin aminci. Sai dai mamakina ɗaya duka duka da komai minti talatin akayi ruwan aka ɗauke saɓanin yadda marubuta suke zuzuta lamarin wannan daren ta hanyar nuna mana an kwana ana abu guda, an suma, an cika gida da kiran umma da Abba. An kasa tashi da sauran surutai masu tarin yawa da tsaiwa a zukatan ƴan mata sababbin yankan rage. (Marubuta saifa mun gyara wallahi. Ko ƙirƙirarren labarine a ƙirƙireshi daidai da mizanin da hankali zai ɗauka. Allah ya bamu ikon gyarawa) Sai gashi da mamaki da asuba ni da kaina na dafa mana ruwan wanka nakai banɗaki na sirka mana Gawata yayi nashi wankan ya fita masallaci ya dai tambayeni zan iya sabida inna haɗe ƙafafuna ina jin zafi tafiyata ta ɗan taɓu ba sosai ba fa ehe. Nace dashi zan iya sai yai mun sallama ya tafi masallaci. Ina gargasa jikina na dawo garau sai ɗan zafi da kumburi wanda bai wuce misali ba. Kwalliya nayi na saka doguwar rigar lesiri mai ruwan hoda sabone fil na bi jikina da humrori. Tsakar gidan na fita na ɗakko gawayi na saka a shiro ya ruru na bangama gidana turare na sake gyara komai. Wanke wanke na fita tsakar gida nayi, na share gidan na wanke shi tas na fito da naman kannan na shanya a katanga. Yau Gawata zai shigo bashi ya shigo ba sai takwas da rabi. Tare da wata yarinya suka shigo tana riƙe da kwano shi kuma riƙe da kofi. "Masha Allah a gaskiya kinyi kyau sosai Tutar so. Kuluwa ajjiye kwanon maza kije ko? " Ajjiye kwanon yarinyar daya kira kuluwa tayi ta gaisheni ta fita abinta. Miƙewa nayi naje na dakko mana kofuna da filet na zuba mana kokko na juye ɗumamen a filet tuwon masara miyar kuɓewa bushasshiya sai warin kalwa koriya fatau babu mai babu halamun kayan miya shine abun karin Amarya. "Kiyi haƙuri nayi yinƙurin siyo mana kayan shayi Nanno taƙi jiya ma wai kinyi girki an miki gargaɗi akan kada ki kuma Tutar so kiyi haƙuri zama da iyaye sai haƙuri." Wani ƙwallone yaje maƙoshina ya tokareni amman sai nayi murmushi nace dashi. Babu komai muci yinwa nake ji" Muna ci muna ɗan taɓa hira jifa jifa ni dai turawa kawai nake yi, wani irin ƙaurin kalwa miyar take yi kawai. Tunowa nayi da su Yaya Saratu har farfesu innarmu ta dafa aka aika musu har kwana uku ana kai musu. Da kalaman soyayya da ƙauna da labaran kasancewar darenmu na jiya Gawata ya ja hankalina har muka cinye tuwonnan bamu sani ba wallahi. Shi ya wanke kwanukan yace in saka mayafi muje mu gaishe da Nanno da Mijinyawa Babba. Tare muka fito matan gidan surukan gidan kenan duk suna tsakar gida anata aikace_aikacen yau da kullum Masu wanki nayi, masu wanke wanke nayi, masu shara nayi, masu kitso nayi, masu karyawa nayi, gidan dai cike da mata da yara. Suna hangomu aka soma tsogumi Yaya Shafa ce tace. "Kaga ango kasha ƙamshi Amarya sai yanzu aka fito kenan? " Ina kwananku an tashi lafiya? " Na faɗa ina murmushi, ashe su a ƙa'ida saina rufe fuskata na nuna jin kunyata sabida miji ya kwana a ɗakina kwanan farko. Sai suka ga saɓanin haka kunji wannan? Gawata na cikin gaggaisawa da surukan gidan su Mijinyawa Babba suka ƙaraso sai yau Allah yasa muka haɗu kamarsu harta ɓaci bambamcinsu ɗayane Mijinyawa yafi Babban faɗin ƙirji da murɗewar jiki sai haske kaɗan daya ɗarashi. Uwatale tana rufe ruf a mayafi ba'a ko ganin fuskarta. Gaishe da mijinyawa Babba nayi ya amsamun da fara'a cike da kulawa. "Kaga amare masu kunya ba irin matar mijinyawa ƙarami ba ƴan binni" Kallon Yaya Shafa nayi kawai Mijinyawa nawa ya dubeni baiji daɗi ba. Rankayawa muka yi zuwa ɓarayin su Nanno inata mamaki Sai da muka gaishe da kishiyoyinta da suke tasu hada hadar a tsakar gidansu, idanuna a buɗe ina kallon kowa Uwatale kuwa kirif da'ita. Ɗakin Nanno muka shiga da sallama a ƙasa na zaune gefen gadonta duk suma sauran suka zube a ƙasa. "Sai yanzu kusan goma saura ne zaku zo gaisuwa ku da yanzu ya kamata ace bakwa gidanma sun fita sabida mata nan da anjima zasu shiga sunturin zuwa ganin Amare" "Zamu fita yanzu Nanno ina kwana? " Mijinyawa ya katse mata maganar tata da fara'a ta amsa mijinyawa Babba da uwatale suka gaisheta ta sake faɗaɗa murmushinta. Ina kwana Nanno an tashi lafiya? " "Lafiya" Iyakar abinda tace kenan shima a gimtse ni ko ko a kwalar rigata nasan babu yadda dai suka iya dani aurene dai an riga an ɗaura Ina zaune suna ta hirarsu ni dai dake nice bare ina saurarene kawai. "To ina ganin ku ku koma ɓarayinku ko, ku kuma ku zauna zamu tattauna" Ni nama riga Uwatale yima Nanno sallama na fita abuna. Ina shiga ɓarayina na sauke ajjiyar zuchiya kawai. Kitchen na shiga na duba sai naga wannan nama dana tafasa ya so yayi tsami ɗaurawa nayi a wuta na ɗumama kawai saina tsiyayi mai na hau suya. Wallahi ko kaskon farko ban sauke ba Nanno da kanta ta shigo sai ganinta nayi a ƙofar Kitchen tace. "Ke wai wanne irin taurin kai da rashin kunyane dake jiya Ladi bata faɗa miki cewar mu anan sai an kwana bakwai ake girki bane? " Kiyi haƙuri Nanno namanne zai lalace in ban soya ba, kuma naga da kuɗi aka siya" "Nama waya siyo miki wannan naman mai mugun yawa ba dai Gawata ba dai ko? " Da sauri nace. "Dangin Innatane suka siya mun to tun jiya na tafasa harma ya soma lalacewa" Gawata ne ya shigo da sallamarshi. "Yauwa gara da Allah yasa ka shigo kuma a gabanka za'ayi. Yarinyarnan daga namanannan kada ta kuskura ta sake ko da dafa ruwan shayi ne in ba haka ba zan saɓa maka, zan muku babu daɗi" "Kiyi haƙuri Nanno ba zata sake ba" Ta saka kai ta fita, ya kalleni nima na dubeshi muka sakarma juna murmushi. "Ina muka samu nama haka cikin babbar tukunya haka? " Wallahi Innah Yahanasu ce ta siyo mun ga kan rago can ma shima zan soya sai in barshi ya bushe." "To ni kam zan fita sai da daddare zan dawo akwai abinda kike buƙatane zamu shiga Bauchi ni da Qasimu da Abdulƙadiri? " Ɗan shagwaɓewa nayi nace. Kuma sai yaushe kenan zaka dawo? " Ba shiri ya jawoni na fito a Kitchen ɗin ya kama ƙuguna dukka biyun yace. "Ba daɗewa zanyi ba kafin la'asarma mun dawo in sha Allahu. Ki kula mun da kanki sosai in kin gama ki kwanta ki huta bai kamata kina aikinnan ba dan Allah kinji? " Kai kawai na ɗaga mishi nayi mishi adda'a na rakashi har bakin ƙofar fita kana na dawo naci gaba da suyana har kan ragon saida na soya na mayar faranti na baza shi. Leda na samu na ɗebama Nanno cikin leda ƙarama na zuba ma uwatale nata. Yarane da suka shigo na basu suka kakkai na sake ƙullawa a leda nace a kaima Yaya Shafa ta raba musu, suma yaran na daddanƙa musu a hannu. Maƙota mata da yara sukaita shigowa bani na samu kaina ba sai Magrib cincin naita loda musu. Na gyara gidana fes na kunna turaren wuta wani mix ne na gabgab da sandal lamba wan da farce dolar da kajiji wannan in kika haɗesu kika ƙona akwai wasu surruka masu yawa tattare dasu Akwai mix ɗin a wajen mrs Bukhari 15k kacal zaki samu mix ɗin dukka itatuwan turarennan hajiyata. Saida na fito wanka na yi sallah na zauna na tsantsara kwalliya na saka doguwar rigar materiyal mai laushi ina fesa turare naji yo sallama ƙofar falona ina leƙowa naga uwatale ce a tsaye tun kayan dake jikinta da safe suɗinne a jikinta. "Dama nazo ne in faɗa miki Nanno tace zamu dinga cin abinci tare to an kawo abincin wajena in mijinyawa yadawo sai ki shigo muci" To shikenan sai mun shigo" Na faɗa ina murmushi a baɗini naji zafi sosai kuma naji damuwa sai dai dake mai shanye ɓacin raice saina nuna babu damuwa. Ko da bayan isha Mijinyawa yazo bayan mun gaisa na yanka mana kankanar daya shigo mana dashi nake ce mai. Muje ɓarayin mijinyawa Babba acan zamu ci abinci yau. Muje ko? " Haɗe rai yayi na fahimci kamar ma yasan da maganar bai ce mun komai ba har muka je muka ci tuwon muka dawo tare da kankanar da na kai aka taɓa hira mukai musu sallama muka dawo. A nanne yake bani haƙuri akan batun cin abinci umarnine na Nanno. Bagarar da zancen nayi kawai na kawo mana soyayyen nama muka ci mun kai kusan sha biyun dare muna hirar biki da abubuwan da suka faru damu. Daren shima mai tsada ya kasance muka wayi gari cikin farin ciki. Haka amarci yaci gaba da tafiya da safe muna zuwa gaida Nanno abincin dare in yau munci a ɓarayin uwatale gobe a ɓarayina za'aci haka dai har kwana bakwai ta cika. Cikin kwanaki bakwai ɗinnan wata sabuwar shaƙuwa da soyayya muka sake ginawa ni da mijinyawa bana so ko da wasa ya fita ya barni in kuwa ya dawo da rana ina manne dashi ko da yaushe bana bari mu zauna ba a manne da junanmu ba. Kuma yana taimaka mun da wanke wanke yau ma wanki yayi mana amman a banɗakinmu na ciki dugun kada a ganshi saida ya shirya ya fita tukunna na shanya kayan a katanga. Saida na gama gyara ɓarayina na yafa mayafina na nufi ɓarayin Nanno acan na tadda Uwatale gaishe da Nanno nayi ta amsa babu yabo babu fallasa tace. "Yau ke zaki yi muku girki ke da uwatale, zaki yi na kwana biyu in kika fita saita karɓa, haka zaku dingayi safe rana dare. Sannan wannan risho naki sai dai ki dinga dafa ruwan zafi amman a itace zaki yi girki kamar yadda kowa yake yi za'a aiko miki da itace da kara, sannan za'a aiko miki kayan miya. Sannan zaku dinga zuba mun abinci da mahaifiyar Uwatale da daddare kaɗai sauran mun yafe" Kunji wani salon takura da neman magana sabida in ba'a sonka dole sai an nemi hanyar da za'a bi a takuraka. To shikenan Nanno babu damuwa ɗazu ma da zai fita nake yi mishi batun itace. Dama rishon na ɗan dafa ruwane kawai. Babu damuwa shikenan wanda kike son a zuba ma abincin?" Na faɗa da murmushi a fuskata sosai. Sai tace. "Mu kenan sai kamar yau da zaki yi girkin farko zaki yi da ko wanne ɓarayi ki basu a kwano amman daga yau shikenan sai in abun ɗaukani kika yi shine zaki basu" Na ɗan zauna kaɗan kana nayi mata sallama na shiga ɓarayina ina huci dan raina ba ƙaramin ɓaci yayi ba. Naman kannan na wanke na jiƙa a ƙaramin bokiti na jawo kujera na zauna a dokin ƙofata ban bari tunani ya dameni ba na zauna ina karanta wani littafin hausa mai suna SABALULA na marubuciya Sa'adatu Saminu kankiya Ina tsaka da karatun aka turo ƙofar tawa ba ko sallama.. Su Yaya jamila ne da su Yaya Zakiya da Autar ɗakinsu. Sannunku da zuwa" "Yauwa dai sannu Amaryar binni" Murmushi kawai nayi na shiga ciki suka biyoni zama suka yi na ɗebo musu ruwa da cincin harda soyayyan nama. Gaisawa muka yi sama sama duk mukai shiru na lokaci mai tsayi sai can Yaya Jamila tace. "To Allah yayi wannan aure dai ya ɗauru sai kiyi ƙoƙarin zama da kowa lafiya ki kuma san a gidan surukai kike, sannan ba zaki ta ƙunshe kanki a ɗaki kina karance karancen litttafan da babu abinda ake koyawa sai bijirema miji ba Ga uwatale can a tsakar gida tana hira amman ke kina nan kina karatu. Kina so ki nuna cewar kinfi kowa tun kafin aje ko'ina kenan? " Bance komai ba harta gama maganganunta suka ce in basu leda zasu juye cincin ɗinsu. Miƙa musu nayi suka juye suka tafi. Na koma nayi zamana naci gaba da karatuna dan ina jin daɗin littattafan Sa'adatu saminu kankia sosai ta iya rubutu na kece raini da feƙe ƙwaƙwalwa. Ba'a jima ba sai ga yaro an turo da kayan miya da itace da kara. Shinkafa da miya naso nayi sai naga a cikin cefanan an haɗo mun harda karkashi sai nace to bari in yi tuwo da daddare. Kunji ƙaddara ta farko ko? A cikin gidan fa kowa girkinta take yi, sai waɗanda suka haɗa miji sune masu tukunya ɗaya. Amman ni sabida a ƙuntatamun an haɗa mun girkina da Uwatale, kuma wai tare ma za'a dinga cin abinci fa. Duk wannan salon takurawane da hanaka sakewa da miji. Ku dai muje zuwa shafi na gaba kuga yadda zanyi wannan tuwon ni Hindu Duwaf sai anjimanku Mrs Bukharihttps://chat.whatsapp.com/JI1IGIBFHYm64hr6IfVfqR TAURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA GOMA SHA BIYAR Na samu kiraye_kiraye daga masoyana manyan mata har a gari uku, sun manyanta sosai kuma dukkansu suna fama da lalurar idanu, ɗaya a cikinsu ma tsohuwace bata iya karatun Hausa ba jikarta ke karanta mata tana saurare. Nayi farin ciki sosai da naji daga garesu, suka ji daga gareni Alhamdulillahi Hajiyoyi ina godiya marar adadi godiya ma ta gode. Kakarmu Hajiya Rabi nagode Ubangiji Allah ya baki lafiya ya ja da ranki ameen. Nagode sosai godiya ma ta gode, wallahi bani da kalmar da zan iya nuna muku irin farin cikin da kuka sanyani ciki. Allah shi ke haɗa soyayya mutum kawai yaji yana sonka har yana so ya kira waya kuyi magana ya ji daɗi. Hajiya Rabi Kakarmu fa wallahi jiya har magidantan yaranta maza sai da suka tambayeta lafiya yau sunga jikin nata da sauƙi. Shine take sanar dasu waya tayi da Badiat wannan marubuciyar shine take cikin murna. Allah mai girma Wannan yafi komai faranta mun raina wallahi. Nagode sosai wallahi son so💪🏼💪🏼💪🏼 *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. Da rana taliya nayi mana jalof na saka mana soyayyen nama, na saka mayafi na miƙa ma Uwatale tana ciki da ƙawayenta na miƙa mata, saida na tsaida sanwar miya na daka daddawa wake, tafarnuwa na zuba. Da rana dai ƙata bazan ci abinci haka kurum da uwalate ba wallahi. Na darenma dama na gani, da bazan ba tunda ko mijinmu ɗaya ba za'ai mana tilas ba. Na zauna kenan zan ci abinci sai Uwatale ta leƙo wai abincin bazai isheta ba tayi baƙi in zuba ma baƙinta. Harna ɗago zan zazzageta saina fasa. Duk iyakar kawar da kan da zanyi bazan yadda a rainani ko a nemi takani ba, ko a keta mun rigar alfarma ba, ba komai ni Hindu zan iya ɗauka ba ni nasan kaina. Kawai sai nai bismillah na soma cin abinci na dan wallahi in nace magana zanyi saina zagi uwarta da ubanta tukunna, kunga kuwa ai akwai rikici in nayi hakan kuma Mijinyawa nake tausayama. Da taga dai bazan kulata ba saita nufi ɓarayin Nanno ni kuwa nayi rantsuwar ko kaɗani gida za'a sa Mijinyawa yayi sai dai yayi amman bazan taɓa ma ƙawayen Uwatale abinci ba wallahi, ai tunda nace bazan yi ba, bafa zanyin ba ne. Nanno haka ta tako ta sameni ina kan cin abinci na hankalina kwance. "Hindu me ya haɗaki da uwatale ne ta kawo mun ƙararki akan abinci nace da somawa da iyawa, ina fatan kinsan matsayin Uwatale a wajena ko? " Babu abinda ya faru nayi abincin na kai mata nata yanzu nima nake cin nawa" Na nuna ni bansan komai ba ma ai. "Amman kina ganin tayi baƙi ai, ya zaki bata abinci a kwano ƙarami?" Banyi tunanin da baƙi za'a dinga girkin ba Nanno. Na zaci ita zata ma baƙinta abinci tunda wajenta suka zo, ni kuma bani da wanda ma zasu zo wajena balle tayi musu. Baƙinta bai kamata su rataya a wuyana ba" Sai tayi shiru tana nazari. Wannan maganar fa da salon ladabi da ɗaure mutum da jijiyoyin jikinshi na haska mata bazan iya soma abinda zai zame mun lalura ba wallahi, duk abinda bazan iya ba, gara tun wuri in haska su san da zamanshi. "Uwatale muje zan san matakin da zan ɗauka akai wannan yarinyar sai anyi maganinta. Idanunta a buɗe yake da yawa. Ji yadda take mun magana kamar mai karanto labarai" Taja Uwatale suka fita na bisu da harara. Kafin magriba na gama tuwona duk na zuzzuba ma waɗanda suka dace har dana gidan su Uwatale da kaina duk na mimmiƙa ma kowa, na Nanno na haɗa da kwanon gidansu Uwatale na kai mata. Namu kuma na jera a falona na ajjiye dukkan abun buƙata na kunna turaren wuta ragowar gaushin kuma na ɗaura ruwan shayi daya tafasa na juye a filas na mayar dana wankan mijinyawa, ni nayi wanka na turare jikina da turaren jiki dan kore ƙaurin hayaƙin girki a jiki haka naga Innarmu take yi, kuma akwai wata doguwar riga ta musamman wanda da'ita take shiga madafi yin girki tana gamawa zata wanketa in ta shiga wanka tana fitowa ta shanya ta turare jikinta da turarenta mai ƙamshi na jiki dan ƙaurin itace yana da ƙarfi in mace batai da gaske ba sai ya riƙe mata jiki sosai. Amman naji jiki hannayena duk sun sage tuwone gari guda na tuƙa babu matayi, babu kowa banma taɓa abinci mai yawan wannan ba. Sai dai ban samu wata matsala ba tunda muna taya su Innarmu girki, da su jajjage, yanka ganye, ɓare maggi da sauransu dai. Ina kan sallaya har akayi sallar isha nayi jigum ina tunanin ƴan gidanmu na jiyo sallamar mijinyawa ya shigo. Da sauri na tafi na tarboshi harda tsarabarshi ta kankana ƙwallo guda, zama yayi ni kuma na juyo mishi ruwan wanka na taimaka mishi yayi wankan da kaina na zura mishi jallabiyarshi muka fito tare. Ina tsaye a Kitchen ina yanko mana kankana su Uwatale suka shigo muka zauna ni dai tare a kwano ɗaya na zuba mana namu abincin Uwatale kuma ta zuba ma mijinta daban itama daban. Sai cewa tayi. "Nayi tunanin ai a faranti ɗaya zamu ci, kamar yadda muka a ɓarayina ai? " Mijinyawa Babba yace. "Ai hakanma yayi Uwatale" Murmushi nayi nace mata. To ai dake shi ba mijina bane, kema Gawata ba mijinki bane babu yadda za'ayi ace muna cin abinci a faranti guda wannan ba musulunci bane sam. Wata al'adace kawai. Amman ke kici da mijinki nima haka shine dacewa" Bata iya cewa komai ba, ai na wuce da tunaninsu na riga na kashe zancan. Ana cin abinci suna ɗan taɓa hirarsu ni da uwatale bama cewa uffan kusan har aka kammala cin abincin. Mijinyawa dai yana kallona tare da sakarmun murmushi nima haka. Wajajen tara suka tafi ni kuma na tattare kayan na kai Kitchen na dawo muka buɗe shafin hira shine yake tambayata yadda muka yi da Nanno na mishi bayani tas tun daga kan girki da abinda ya haɗamu da uwatale. "Sai haƙuri ki ƙara haƙuri komai zai wuce watarana sai labari kusan haka suke yi a gidan waɗanda amman suka haɗa mijine kawai sai su haɗe girki suyi. Mu din so take yi shaƙuwarmu ta ƙaru kawunanku su haɗe sosai shi yasa" Kada ka damu da ba dan ka jiyo ba zancan ma ai bazan yi maka ba. Yanzu gobe da nayi shikenan zan kuma huta na kwana biyu shikena, ai da daɗi sosai " Jawoni yayi ya gyara mun kwanciyata yace. "Daɗina dake ke bakya fishi Allah yayi albarka. Gobe zan gayyaci abokaina kamar mutum biyar muci abinci tare dasu girkin bazaiyi miki yawa ba? Duk da gobe zan kasance a gida na kama miki aikin ma. Kuma inaso zamu fita dasu Mijinyawa Babba zuwa gidan Yaya jamila zuwa bayan isha in mun kammala cin abincin sai gidajen abokai da zamu ɗan zagaya" Allah ya nuna mana goben da rai da lafiya mijinyawa nawa ni kaɗai" Da haka labarin ya canja salo zuwa eh kun gane ai. Washegari da zai fita na bashi kuɗin kaji uku, da kayan miya nace in zai shigo tunda yace azahar nayi zai shigo sai ya kawo mana, sabida babu ko sisi a hannunshi sai yace in yi amfani da na wajen nawa. Shayi da ɗumamen tuwo na miƙa ma su Uwatale na safe, da rana na dafa jalof ɗin shinkafa da wake ta manja na ajjiye mana namu ni da mijinyawa na ba uwatale nata. Ina zaune ina wanke_wanke mijinyawa ya shigo. Wajen wanke_wanken ya iso ya ajjiye cefanan a gefe, nayi mishi sannu da zuwa ya amsa harda shafar fuskata. "Bari in kwaɓe in zo muyi girkin ki saka sakata a ƙofar gidan" Sakata na saka na dawo sai da muka ci abinci kana na gyara kayan miya ina jajjage yana wankemun kajin daya siyo yasa an fige an yanka daga can. Muna aikinmu muna hirarmu harda dariya abin sha'awa. Sai da la'asar tayi ya tafi masallaci yana dawowa muka ci gaba da aikinmu kafin magriba mun gama komai shi ya shimfiɗa babbar tabarma muka jera kulolin abincin da cokula da kwanuka dukka dai shinkafa da miyar kaji nayi musu ana idar da magriba suka shigo ni kuma ina ɗaki dan na zuba abincin uwatale na miƙa mata nima ina cin nawa a ɗaki, yau dai ba zaman cin abinci. Saida suka gama na fito muka gaisa sukayi godiya tare da yi mun sallama. "Tutar so ki shirya da mun dawo zamu tafi" Kafin ya dawo na shirya muka rankaya gidan Yaya jamila mun kuwa jima a can, daga nan muka ɗan zagaye abokansu gida na ƙarshe gidan Qasimu ne aka kaini wajen Baraka na ganeta sau biyu tana rako maƙota zuwa ganin ɗaki. Yaya Jamila mutuniyarku tai ta habaici da turo maganganu iri_ iri, ni kuwa Hindu nayi biris. Gaga_gaga rayuwar taci gaba da shurawa a haka da daɗi a wajen miji babu sauƙi a wajen matan gida da dangin miji sam, Nanno kuwa ba'a ma magana wallahi. Duk abinda akayi ace kuskurene hatta ruwa da mijinyawa yake jidarmun ya ciccika randuna kullum sai Nanno tayi ƙofari, wata ɗaya da aurenmu Nanno ta damu akan Mijinyawa ya koma kan sana'arshi inma bazai koma Kano ba sai ya nemi abun yi ba kullum yana maƙale dani ba ina bautar dashi yadda nake so ba. Sabida a lokacin mijnyawa Babba ya koma inda yake aiki shi. Da daddare bayan mun gama cin abinci ni dashi tunda Uwatale tunda mijinta ya tafi sai dai in kai mata nata abincin taci ita kaɗai. Ai da sabida kawai a baƙanta mun in bijire yasa basu tuno da cewar mazajen namu ba mazauna bane, kunga ai gara dana biye ma abun, ba ko da taushe faɗa da hauragiya ke zama mafita ba. Sai Mijinyawa yake mun ƙorafi akan baya son tafiya neman kuɗi ya barni bisa sharaɗina, shi yasa amman Azare yake son zuwa zai ci gaba da ciraninshi acan duk sati biyu ya dinga zuwa. Jikina duk ya mutu nasan ko da muna da abinci dole muna da buƙatar aiki rayuwa ba zata ɗore a haka ba, ƴan kuɗaɗen hannun nawa babu yawa duk sun ƙare dama dai tunda nazo da kuɗaɗen muke amfani tunda shi ba kuɗi bane dashi a hannunshi ba. To amman ai Nanno ta fimu gaskiya duk da bana son kayi nesa dani mijinyawa amman dole ka fita nema, sai dai akwai kuɗi ne a hannunka? " "Shine damuwar babu kuɗi a hannuna amman inaso in nemi Aro a hannun Abdulƙadiri tunda tare dashi zamu tafi can Azaren, shi a can yake tashi sana'ar sai in dinga kama mishi kafin in samu jarin ƙashin kaina." A'a ba sai ta kai ga haka ba ina zuwa" Miƙewa nayi na shiga ɗaki na ƙirga kuɗaɗen hannuna duka_duka dubu arba'in ya rage mun. Sai na rabata biyu na kawo mishi rabi yasa hannu ya karɓa ya ƙirga. Sana'a naso in yi da kuɗin, to amman a ƙauyen na rasa gane wacce sana'ace zata karɓeni ma. To gashi kuɗi kam sun ƙare zance. "Naga har dubu ashirin ya zaki kwashe kuɗin ke da zan tafi in barki kuma" Murmushi nayi na shige ƙirjinshi ina kallon idanunshi mai kyau da kwalli nace. Akwai komai na abinci kayan miya kawai zan dinga siye akwai kuɗi a hannuna fatana shine ka kula mun da kanka kuma kar ka wuce sati biyu ka dinga waiwayowa kasan ka sabamun da kwanciya a jikinka kana yi mun hira mai daɗi, ni inta kama duk sati ma ka dawo abunka." "Hmm Tutar so kenan Allah ya hore mun in kula dake yadda ya dace in kaiki birni in sakaki a makaranta ki cika burinki na son zama ƴar jarida, a lokacin ko aiki na fita nayi kuɗin sukutum zan dinga baki wallahi sai yadda kika yi dani. Kai da kaya duk mallakar kuya ne" Dariya muka yi dukkanmu nan muka ci gaba da tattaunawa, kwana biyu da wannan maganar Mijinyawa yabi abokanshi suka wuce Azare ya rage ni kaɗai sai karatun littattafai suka zame mun ababen ɗebe mun kewa, na koyi abubuwa da yawa a karance karancen da nake yi kusan ma littattafan hausa shi ya wayar mun da kaina fiye da tunani kuma nasan bani kaɗai bace. Marubuta madubaine ko kuma walƙiya masu iko da tararrafin hasko rayuwar Al'umma su haska ma duniya su wayar da kan matan da basu da damar da zasu iya fita suyi cuɗanya da mutane su samu wayewar kai. Basu da damar da zasu san abubuwan da dama saita hanyar karance_karancen a karatune marubuciya zata kutsa cikin rayuwar wasu ma'auratan ta haska muku, wata sai taga kamar da'ita akeyi a sannu tana karantawa tana bi har ta samu warwaruwar matsalarta cikin kwanciyar hankali da izinin Allah. Littatafin hausa jami'ace mai zaman kanta wanda yake da shashe_shashe ya rage ga makaranci ya zaɓi shashen da yake so haka ya rage ga marubuci yasan me yake haskama al'umma ya sani shi madubine abun koyi, shi malamine mai gyaran tarbiyya da gyaran gidajen aure, in wannan ɓangaren ya zaɓa. In kuma yabi masu tutuya da adabin bariki, masu haska mana rayuwar mata ƴan maɗigo, da mata karuwai, ba tare da nuna illar hakan ko da a ƙarshen labarin bane, to kunga wannan aikinsu na wargaza tarbiyyar al'ummane da nuna ma yaranmu kai tsaye hanyoyi da dabarun biya ma kai buƙatar sha'awa da Allah ya halicceta a jikin ɗan adam. Wa'iyazullali. Madallah da duk marubutanmu na da dana yanzu, madallah dake Mrs BUKHARI. Bayan tafiyar Mijinyawa da kwana biyu na isa ɓarayin Nanno nayi mata share_share bata ko yaba ba, bama ta nuna tasan nayi wani abun yabawa ba. Ƙorafinta shine ni kullum ɓarayina a kulle sannan in an ganni a tsakar gidan ruwa nazo ɗiba ko kuma na fito a gaisa da safe ne. Audiga nasa na toshe kunnena domin bazan iya wannan zaman ba, sai kuma ta tsiro da cewa mu haɗu ni da uwatale mu dinga hira, nanma na nuna bana so Baraka ce ma dai jininmu ya haɗu da'ita. Ta shigo mun sau biyu bayan tafiyar su Mijinyawa, ni bamma samu damar shiga ba, nafi sha'awar zama ni kaɗai littattafan Hausa su zamemun ƙawaye. Tun ana jibi sati biyu da tafiyar mijinyawa na soma gyaran jikina dilka dama da'ita nazo mai dunƙule dunƙule wanda baya komai ko shekara zai yi ( Dilkar sirrin matan sudan kenan. Mai saka laushi da fito da ainihin kalar mace, mai danƙarar, dauwamar da ƙamshi a fatar mace, musamman ki haɗa da turarenmu na turara jiki wato dukkhan Hajiya tare set ɗin nasu yake. Akwai wannan Dilka a wajena da kin shirya ki yi mun magana ni Mrs BUKHARI ga lambar wayata 081_79523215 saina jiku) Magungunan matana nagartattu, ingantattu na wajen Surayya D (08032773332) dana zo dasu bansha ko ɗaya ba, in banda sanyi fulosha na dama nayi ɗibge ɗibgene sai na shiga tsifar kaina Baraka tace zata rakani gidan wata mai kitso data iya itama ƴar garinmu ce Maiguduri, ta iya kitso cikin kwana ɗaya na tsefe kitsona fes da daddaren na tashi da lalle yayi duhu kalar jinin kare dashi, dake akwai ragowar na biki da bai fita ba, yi ɗaya nayi amman ya kwanta yayi lub. Wajajen ƙarfe goman safiya Baraka ta shigo bayan na fito sai na tafi neman izini wajen Nanno. "Mijinyawane zai dawo aka ce mun tun shekaranjiya kike juyin ɗaki ko yaya, ga kitso kince zaki je? " E haka nake saka rai sati biyu yace mun zaiyi ya dawo" "Sati biyu, ke Baraka sati biyu Qasimu yake yi ne ya dawo daman?" Baraka tace. "A'a wani sa'in wata ɗaya wata biyu ma kafin ya dawo amman bai taɓa dawowa sati biyu ba" Shiru tayi can tace sai mun dawo. Muna tafe muna hirarmu a ƙafa muka je unguwar dake babu nisa kuma inason ganin gari. Gidan kitson munje mun tarar da wata mata anayi mata amman ita baƙuwace ma ta shigo ziyarane shine tazo ayi mata kitso. Bamu daɗe ba aka gama mata ni kuwa sai da akayi awa biyar ana abu ɗaya danma tana da sauri sosai guda ɗari da shittin akayi mun wajajen dab magriba muka isa gida, Nanno tai ta faɗa kishiyoyinta na tayata daga baya kuma suka shiga bata haƙuri. Raina ya matuƙar ɓaci sosai amman haka na bata haƙuri na tafi shashena. Washegari wajajen azahar na gama girkina tsab na zuba kwalliya ko ina tsab ga ƙamshi ta ko ta ina, ina jiran miji shiru_shiru sai dab magriba na jiyo ihun yara suna mishi oyoyo ajjiyar zuchiya nannauya na sauke. Jakar kayanshi aka shigomun dashi, shiru_shiru shine har sai bayan isha ya shigo hannunshi da tsarabar da yayo mun Nanno ta ɗibi nata dana matan gidan. Babu walwala sam a tattare dashi duk da ganina cikin ado da kwalliya ya sanyaya ranshi amman damuwarshi ta kasa ɓuya. Wanka na taimaka mishi yayo na kawo mishi abinci na tusashi gaba inaji kamar yau sallah. "Tutar so kinga yadda kika yi kyau abunki, fatarki sai sheƙi take yi. Kamar kitso kika sake ko?' Kafin ma nayi magana ya zame mun ɗaurin nawa ya shiga shafa kan nawa wanda ya sha kulaccam ta gashi mai bala'in taushin ƙamshi sai da ya lumshe idanunshi. ( maza dai ki zauna Abulle kada ki motsa ki lalo kuɗi kizo in fiddaki kunya da kayan ƙamshi. Su Khadija da Kattime anata abun arziki ke an barki a baya. In kinga dama ga lambata ki kirani in fiddaki 081_ 79523215 mrs BUKHARI GIDAN ƘAMSHI) "Kitso da lalle yayi kyau wanda akayi dominshi ya yaba, gashi ko ya kika motsa ƙamshi kawai ke fitowa a jikinki, mala'ikun Allah ku shaida Allah yai ma Tutar so albarka ni mijinta na ɗaga ƙafata ta shiga aljannah. Nayi kewarki fiye da kewar daddaɗan girkinki harma bansan da wanne zan soma ba" Da ƙyar na lallaɓashi yaci abincin muka wuce ɗaki. Sai da asuba na tattare komai. Yau saina wayi gari garau dani sawai nake jina babu nauyi. Da kaina nayi ma Mijinyawa abun kari duk da uwatale ke da girki ban tsaya jiranta ba, ɗumamen tuwo ta miƙo mun babu ko shayi bare kokko. Muna karyawane mijinyawa yace dani. "Tutar so jiya dana dawo Nanno tayi mun faɗa sosai akan dawowata, ta dinga take tsikara ba tanan take jawowa ba. Sannan ta kafa mun dokar sai dai in dinga yin wata biyu kafin in dawo kamar yadda Qasimu da Abdulƙadiri suke yi. Hankalina ya tashi sosai ko da safennan da zancan naje mata taƙi fur wallahi. Ya zanyi da kewarki da rashinki nisan yayi yawa Tutar so ina buƙatar matata a kusa dani, sannan na miki alƙawari bai kamata in saɓa ba. Bansan mabuƙaci bane ni saida na aureki na ɗanɗani zumarki sati biyunnan ma a daddafe nayi shi ina ga wata biyu daga yin aure ko amarcin bamu more ba." Ajjiyar zuchiya na sauke domin a lokacin kaina ɗaurewa yayi na rasa abinda zance. Kar ka damu zamu tattauna a nutse kaji? Yanzu ka daure ka ture duk wata damuwa babu abinda zai gagara, Allah shi ke da tararrafi akan bayinshi" "Ai bazan iya turewa bane inaso gobe zan kai ma Kawu ziyara in faɗa mishi halin da ake ciki ko akwai taimakon da zai mana shine kaɗai mai tafarrafin faɗama Nanno taji" Amman kai kana ganin yin hakan daidaine kar taga kamar ƙararta aka kai kuma ya zama wani abun daban mijinyawa, naga a wajen Nanno komai na faɗa ne. Ka daure kawai kaje ɗin ayi yadda tace ɗin wata rana sai labari babu abinda yake dammawa face ƙudurar Allah shine mai tasarrafi da buwaya, kuma gagara misali" Da ƙyar na shawo kanshi ya amince ya bar maganar. Badan komai na hanashi kai ƙara ba sabida abu biyu ne bana son su san logona domin dashi za'a iya kaini ƙasa, na biyu bana so hakan ya sake ruru wutar rikicin da kullum ruwa nake yayyafa mata. Bayan dawowarshi da kwana biyu da safe yana mana wanki a banɗaki ni kuma na dasa kujera muna hira shine yake sanar mun ai ba Azaren ma suka je ba cikin garin Bauchi suka shiga anan suke ciraninsu Mijinyawa yace shayi yake siyarwa da ƙwai. "Wani mai shayine zai koma garinsu shine ya siyarmun da komai nashi naci gaba da yin shayin a inda yake yi dake na shiga da canjina a hannuna. Shi kuma Qasimu teburin lemo ne dashi Abdulƙadiri kuma aiki yake yi a tasha sai dai duk wajen kwananmu ɗaya. A tasha muke kwana rumfar wata mai tuwo_tuwo a saman bencinta washegari kuma mu biya nera goma_goma muyi wanka mu kimtsa ko wanne ya fita wajen nema kinji sana'ar da nake yi, kuma da riba babu laifi in faɗa miki kinga in Allah ya dafa sai kiga mun koma Bauchi da zama na saka ki a makaranta kin cika gurinki na son zama ƴar jarida" Shiru nayi ina tallafe da kumatukana dukka biyu. Kumfa ya watso mun nayi firgigit na kalleshi. "Tunanin me kike yi kika barni inata zuba Tutar so? Ni na zaci murna zaki taya ni tunda ba ɗaukar kaya nake yi a ka ba. Ko kina tunanin kamarki ace mijinki shayi yake saidawa ko? " Ko ɗaya bana wani abu daya danganci nadamar kasantuwata iyalinka abadan. Ni dai fatana mijinyawa ka riƙe ni da amana kaga na rabu da ƴam uwana, na rabu da kowa sabida inzo nan in rayu dakai" "Kar ki damu mijinyawanki mai ƙoƙarin yaga ya saka miki da mafiyin alkhairin da kika yi mishi ne. Nayi miki alƙawarin zaman Ƙauyannan lokacine zan mayar dake burni" Nan na sake muka ci gaba da hirarmu tare muka yi shanyar ya taya ni muka gyara gidan kana ya fita ni kuma na shiga hidimar girki. Gaga_gaga haka rayuwata a Jama'are taci gaba da kasancewa littattafai suna tusa a gaba karatuna nake yi haiƙan kuma inajin daɗi sosai da sosai. Nanno bata taɓa gajiya da ƙorafin rashin fitowata ayi hira dani ba. Haka matan gidan da yaransu kallona suke yi a matsayin baƙuwa kullum ni kaina na kasa sake jikina dasu sam amman kullum zamu gaisa in abun jajene ina leƙawa haka inna taya murnane dani shima akeyi. Amman ina fama da hayaniyar yara, gashi su Shafa sai suita shewa a tsakar gida. Gidan fa wani matattarane na matan ƙauyen Baraka take sanar dani a gidan aka ƙyanƙyashi ƙwai tara tsinana na gulma. A gidan komai na cikin ƙauyen yake fitowa Shafa itace wuman lidar magulmatan garin. Ana cikin haka Zakiya ta haihu ranar suna kuwa muka ɗunguma har da Baraka muka je suna. To a lokacin Uwatale na da cikinta harma ya fito nan Yaya Jamila ta dubi tsabaragen idona tace dani. "Hindu ke kuwa shiru ko ɓatan wata baki taɓa yi ba Aure wata shidda ga Uwatale nan da ciki wata biyar ke kuwa sai dai kici kiyi ƙaton kashi. Allah dai yasa ba juya Mijinyawa ya ɗebo mana ba dan mu kaf zuriyarmu suna haihuwa haka surukan gidanmu babu wacce ta taɓa kaiwa wata shida bayan Aure bata yi ciki ba" Ashe haka matan da basu samu ciki da wuri ba suke ji in akai musu gorin haihuwa? Ranar naga tashin hankali ido da ido. Sabida tsabar ɓacin rai kawai sai na dena ganin kowa kaina naji yana motsawa, duk yadda naso in mallaki kaina ina makatan kainane suka tashi suka bigeni a gidan sunannan suka shaƙo wuyan Yaya Jamila da ƙyar aka ƙwaceta akace, a ranar masu makarai a gidan sunannan sun faɗi har da waɗanda ba'a san ma suna dashi ba sai da suka bigesu. Gidan sunannan ya hautsine sosai, makarai suka karɓe sha'anin sunan baki ɗaya ni dai da ƙyar na dawo haiyacina ina gane inda kaina yake na koma gida bakina alaikum ina shiga da Nanno na soma cin karo labarin duk abinda ya faru a gidan suna duk ya dawo musu. A yanayin data ganni ba arziki ta bani hanya na wuce dan idanuna sun yi jawur sosai kuma sun juya kamar irinna masu harari garke. Da ta yi mun magana da saina fyaɗata da ƙasa, ko in haɗa kanta da danga. Ina zuwa daf rijiya na sake zubewa na shiga burgima da tambotsai suna faɗin ba zasu yadda na ɓata mun rai da akayi ba. Ya akayi ya akayi ni dai na ganni a ɗaki Baraka na kusa dani. "Sannu Hindu Allah yasa dai wannan mutanen sun tafi wahalar tayi yawa" Naji ta faɗi gashi duk jikina ciwo yake yi ko zaune na kasa miƙewa sai daga kwancen nace. Meke faruwane Baraka yaushe kika zo? " "Hmmm labarin da tsayi Hindu yanzu dai ki lallaɓa ki tashi ki ɗan watsa ruwa mijinyawa nasan yau duk inda yake yana hanya tun rana aka tura ɗan aike ya sanar dashi halin da kike ciki, sabida an kasa shawo kan matsalar. Babu wanda bai tsorata da irin yanayin da kika tsinci kanki a ciki ba. Nima dake mahaifiyata ciwonta kenan tun tasowarmu shi yasa na iya zama dake dan bana tsoronsu wahala babu irin wanda mahaifiyarmu bata sha ba" Shiru nayi ina ƙoƙarin tuno abinda ya faru take kuwa na tuno ni dai nasan na baro gidan suna na dawo gida na tadda Nanno a tsakar gida iyakar abinda zan iya tunowa kenan. Sallamar mijinyawa yasa Baraka ta miƙe da sauri. "Maraba ka ƙaraso kenan? Hindu Allah ya ƙara sauƙi" "Na iso Baraka dan Allah in babu damuwa ko zaki faɗamun abinda kika sani dangane da abinda ya jefa Hindu a halin da aka bani labari" Kallona Baraka tayi kana ta dubeshi tace. "Abinda zan faɗama shine Hindu bata da lefin komai bata cakali kowa ba taɓata akayi. To kasan mutanannan in suna tare da mutum ba dama ayi ma mutum abun ɓacin rai sai kaga sun kawo ziyara. Allah ya kiyaye gaba" Ta saka kai ta fita. Shi kuma ya zauna a bakin gadon ya riƙe hannayena du biyun ya kuramun idanu ya kasa cewa komai naga firgici sosai a cikin yanayinshi. "Kiyi haƙuri Tutar so babu inda zan sake zuwa in barki zan kafa sana'ata a jama'are abinda muka samu shi zamu tattala. Ni kaina ina azabtuwa sosai da rashinki. Ki faɗamun abinda ya faru kada ki ɓoye mun komai domun insan wanne matakin zan ɗauka akan Yaya Jamila. Zan iyayin komai a kanki. Ka taimaka mun in watsa ruwa in yi sallah tukunna, kaima kana buƙatar hutu ai." Da kanshi yaimun wankan ya gargasa mun jikina sai wash_wash nake yi sabida ciwon jiki. Agogon dana kalla ne ya tabbatarmun da kwana ɗaya nayi da wuni ɗaya bansan inda kaina yake ba. A zaune na soma rama sallolina ina jiyo ɓuruntun mijinyawa a Kitchen daga baya naji fitarshi. Bayan na gama rama sallolina harda magriba da ake yinta yanzu saina koma na kwanta a kan gado maganganun Yaya Jamila na dukan kaina. Nima sai yanzu na tambayi kaina ni har yanzu ban samu ciki ba, to sai yaushe zan samu nima inji ɗumin jinina, to dai juya ce? Yaya Saratu ce ta faɗo mun ita da kunika ma tayi abunta na sake tuno ƴan gidanmu da akai musu aure lokaci ɗaya da su Yaya Saratu babu wacce ta shekara ba da goyonta ba amma ni gani wata shida cur babu ko ɓatan wata gashi har nima na shiga sahun matan da rayuwarsu take yin tsanani sabida rashin samun rabo kenan? " Da sallama mijinyawa ya shigo ɗauke da tire da pilet cike da taliya da ruwan shayi sai maganin ciwon jiki kati ɗaya. A kan gadon ya dure mun a gabana. "Taso kici abinci kisha magani Tutar so sannu kinji" Nanno ce ta leƙo yana rungume dani. Da sauri ya sakeni, nima na sake shi a firgice" Ji nayi tamkar ƙasa ta dare in faɗa dan kunyar a yanayin data same mu. "Ba shakka zinariya ba lafiya ciwonta ya hana kaje ka dubo Yayarka data shaƙe wuyanta har yanzu bai saɓe ba, ya kumbura. Kai da kace mun bari kaje ka ajjiye ledar kayanka ko? Shine ka ɓige da lallaɓata" Miƙewa nayi a hankali dan takaici na nufi hanyar banɗaki. "Kibi a hankali jikinki babu ƙwari Tutar so" "La'ilaha'illallahu Mijinyawa a gabana, sannan ina maka magana hankalinka na kan juyar matarka" Da sauri na juyo muka haɗa baki wajen maimaita kalmar. "Juya?" "Eh juya ko nima shaƙenin zaki yi kamar yadda kikaima yar mijin naki yarinya sai rashin kunya da taurin kan tsiya kin gama shanye mun yaro. An gama asirceshi a turaren wutan da baki da aiki sai bankashi. Kai kuma ka wuce kaje ka duba ƴar uwarka da baka da kamarta ko yau na faɗi na mutu itace makwafina. Ita kuwa wannan juyar ko yanzu naso saika saketa wallahi" Banɗaki na shiga na tsaya kawai ina murmushi wallahi sai ji nayi na doku da ƙasa tim, wuji_wuji suka yi dani suka danfarani da ƙasa. Kunji fa sabuwar ƙaddarar data sake dirar mana. Ohh ni Hundu ɗiyar Baba sojanmu Mrs Bukhari.TSURON TSIRIN... TSANDAURI... LAMBA TA GOMA SHA SHIDA *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. Da sauri na miƙe ina ambaton Allah. Ji nake yi kaina kamar ana mun yawo dashi a sararin samaniya, ga wani kururuwa da nake ji a kaina. Shiru nayi idanuna a runtse inaji yadda Nanno take fama da mijinyawa, sai bambami take yi. "Kiyi haƙuri Nanno bai kamata in fita in bar Hindu a wannan halin ba amanarta a hannuna take, ki yi haƙuri dan girman Allah na roƙeki. Dan Allah kiyi haƙuri zanje in dubo Yaya jamila a darennan amman inason sanin halin da Hindu take ciki, kinga bamu samu zama da'ita ba" Sai ganina nayi a cikin ɗakin cikin dakiya da nuna rashin kulawa da abinda ya faru nace. Babu abinda ya sameni kaje ka dubo ƴar uwarka baka da kamarsu a rayuwarka, ni zaka iya rabuwa dani, ita kuma har abada taka ce" Zama nayi a kan gado, na jawo tiran abincin gabana, jikina tamkar zai tsattsage jini ya fatso ya fito, sabida ciwo. Nanno ta tusashi gaba suka fita, da murmushin baƙin ciki da takaici na bisu kawai. Ni Nanno mamaki take bani, bama ita kaɗai ba harda ire_iren surukai irin Nanno. Da ƙannen miji, da yayun miji masu ƙara tura rigima, su kuma so suke a so su, a ƙaunace su a nasu dangin mijin fa. Amman kai in ɗan uwansu zai nuna darajarka, sai dai in asiri kayi mishi kawai hakan zai iya faruwa. Son kai irinna mata abun azimun. Ashe bayan samun damar rayuwa da zaɓinka akwai ƙalubale masu yawa zagaye da Auren? Ni da nayi tunanin duk damuwar duniya ta gushe mun matsawar na samu mijinyawa a matsayin abokin rayuwa, ashe tsugunne bata ƙare ba. Yanzune zan soma ganin rayuwa. Wata shida kaɗai an soma gorinta mun haihuwa. Murmushi na kuma yi kalmar juya na yi mun yawo a jinina yana tuƙamun a ƙirjina. Shayin na soma sha dan yinwa kamar zata halakani jikina babu kuzari sam. Taliyar kaɗan naci naje Kitchen na rufe na ɓalli ƙwayar bature guda biyu na watsa. Saida nayi sallar isha na shafa humra na saka kayan bacci na kwanta. Ban wani jima da kwanciya ba mijinyawa ya shigo babu daɗi sam a fuskarshi idanunshi sun kaɗa sun zama jawur ƙirjinshi sai hawa da sauka yake yi. Hayowa gadon yayi ya jawoni nayi lamo a ƙirjinshi sai lumshe idanuna nake yi. Shi kuma ƙirjinshi nata dokawa. Mun jima a haka sai shafar bayana yake yi yana sake shigar dani jikinshi kamar irin za'a ɓanɓareninan haka yakeyi. A hankali cikin wata murya mai zurfi da kauri ta cikar mazantaka yace dani. "Zan iya fito na fito da duk wanda ya nuna miki ƙiyayya ko ya nuna baya ra'ayinki. Bazan zuba ma Yaya Jamila idanu tana aibanta mun ke ba tana kuma sake zuga Nanno a kanki ba. Wallahi Tutar so Nanno kaɗai zan iya ɗaga ma ƙafa a kanki, banda ita bazan iya ɗaga ma kowa ƙafa ba." Kaina na ɗago na dubeshi ƙur sai can nayi murmushi kaɗan nace. Yaya akayi kuma, ta sake tayar maka da zancanne ko ko dai ita ta tayar da zancan da kaje dubo ta? Kada ma ka ɗaga hankalinka in dai Yaya Jamila ce ta daɗe tana faɗamun maganganu na wannan karonne suka dakeni irin dukan da abadan bazan warke ba matsawar zan buɗe idanuna in ganta. Babban abinda yafi komai zama zunubi a wajena shine a tsinkani a cikin mutane, ballentana ita tasakani a halin da bansan ya kaina yake ba, na bayyana tsaraicina, ko ban bayyana ba duk ban sani ba, ga gidan dam da taron mata" Ajjiyar zuchiya na ja na sauke. "Kiyi haƙuri ina tare dake kuma zan tsaya miki sai iyakar inda ƙarfina ya ƙare. Mu zuba dani dasu Yaya Jamilan tunda haka ta zaɓa. Mijinta dake shanyayyene shima har yana cemun ya kamata in ɗauki mataki a kanki in da makarai da iskanci ya zaki shaƙe yar miji kiji fa. Itama Yaya Shafa sai sake zuga Nanno take yi dake duk bakinsu ɗaya Yaya Salihun mijin ita Yaya Shafan shima mun haɗu masallaci yake cewa tun wuri in ɗauki mataki a kanki in ba haka ba watarana Nanno zaki shaƙe kiji mun wannan magana fa sai yayata magana akeyi. Ita kam Yaya jamila bamu rabu da arziki ba nasan gobe sassafe zaki ganta ta tawo gida tazo haɗin faɗa. Duk da wuyan nata ya aune. Naje na samu mijinta ma yana shafa mata man Ayu kinsan yana maganin kumburi" Shiru nayi sai can nace. Wata shida da aure baiyi wuri ace har an soma kirana da juya ba, kenan in ni juyar ce danginka ba zasu iya karɓata ba kenan mijinyawa? Nifa a duk halin dana tsinci kaina ina godiya kana ina son kaina a hakan. Duk rintsin da zan shiga ni Hindu inason kaina, kuma ina godiya ga Allah, rashin haihuwa ai ba gazawa bace shirin Allah ne." "A duk yadda kike inma mai haihuwa inma mara haihuwa ni dake har abada, muna tare babu gudu babu ja da baya. A duk tsawon zamani zanyi alfahari dake ƴar matata. Wallahi ko ki haihu ko ki kasance juya Hindu ni Mijunyawa ina tare dake abadan" Da dadaɗan kalaman yabon halayena da zatina ya mantar dani damuwa, amman sunan juya yaƙi ya kwanta mun sai ma maimaita kanshi da yake yi. Washegari kamar yadda aka saba ina idar da sallah na koma na kwanta jikina sai ciwo yake yi. Cikin bacci nake jiyo tashin murya a falo babu shiri na duro a gado na leƙo. Yaya jamila ce a zaune akan kujera ta tusa Mijinyawa a gaba tana mai sababin faɗa ga Mijinyawa Babba daga bakin ƙofa shi da gambo suna bata haƙuri. Wuyanta ya aune gaya Mijinyawa kuwa yana zaune a ƙasa ko ɗagowa bayayi. "Ya dace kenan ita fa sanda na leƙa tana gado tana bacci, shi kuma yanata faman yi mata soye_soyen doya sabida rashin kunya da rashin mutumci. Ɗan uwanka haka kaga yana yi ma matarshi ita da take da ciki ma, me zai aikeshi shiga madafi sai dai in ciwo yayi tsanani a nemo ƙannenta su zo su zauna da'ita ai" Mijinyawa Babba yace. "Yaya Jamila a dai taru ayi haƙuri kai kuma kada ka sake gaskiya. Ai gara ma ka shiga cikin gida ka nemo mata abinci. Ga uwatale canma tana suyar ƙosai har daku nace mata tayi. Me zai kai ka madafi in ba neman sababi ba, dole sai ka kiyaye, madafi ai sai mata. Gaskiya banda ciwon da zai sa in shiga in ma mace girki a madafi ba. Yaya Jamila ke kuma kiyi haƙuri hakanan muje Nanno tana nemanmu har da kai da Hindu tace duk muje, Yaya Zakiya da Yaya Adamu, da Yaya Salihu ma duk suna ciki da iyalansu." Miƙewa Yaya Jamila tayi ta fice, idanu na zuba ma mijinyawa muka sakarma juna murmushi kawai. "Taso muje kinji inzo in ƙarashe miki girkinki. Kinji ƙauyanci wai mijinyawa Babba ina shi ina shiga Kitchen ko? Ƙauyancine yake ɗawainiya dashi. A littattafan Hausa dana kakkaranta maza na yin fiye da hakan" Ni dai babu ruwana kar kasa Nanno ta leƙo ta ganka" Jawoni yayi ya matse gam a ƙirjinshi muka sauke ajjiyar zuchiya yai ƙasa da muryarshi raɗa_ raɗa yace. "Kada ki damu da kowa da komai. Duk abinda za'a tattauna kar ki bari yayi miki tasiri ni ɗinne dai mijinki mai riƙe da igiyoyin Aurenki uku wanda akaima ƙullin da babu kuncewa ko a Aljanna kece shugabar matana nacan" Idanu na ɗago nace. Anan duniya ma nice shugaban matanka? " Hancina ya lakace dan bai isa ya gane da wacce siga nayi mishi tambayar ba, fuskata ba zata iya fassara mishi manufataba. "A nan duniya ke kaɗai kike mulkin birnin zuchiyata yanzu dai ba wannan ba muje mu dawo in baki labari mai daɗi" Tare muka fito muna murmushi madadin aganmu cikin damuwa sai ga akasin hakan. Wannan abu na dafa dangin Mijinyawa sosai haka sanda nake gida wannan halin nawa na shanye damuwa inyi murmushi a madadin ɗaure rai yana damu ƴan uwana wanda muke ƴan uba da waɗanda muke ƴaƴan wa da ƙani kuwa, kirana suke munafuka miskila wacce ba'a iya gane me tafi so ko menene bata so. Da sallamata raɗau na shiga ɗakin ina biye da mijinyawa. Waje muka samu a ƙasa muka gurfana kamar yadda sauran suka yi. Nanno kaɗai na gaisar daban amman sauran duk kuɗin goro nayi musu. Sun amsa basu amsa ba, banyi da nufin dole sai sun amsa ba. Taro aka haɗa mana. "Abinda yasa na taraku anan akan maganar wannan makirar yarinyar da take yinƙurin farraƙa zumuncin ɗakinnan tasa kishiyoyi da yaransu sai zunɗena suke yi. Gari ya ɗauka anata yamaɗiɗin matar mijinyawa ta shaƙe wannan yarinyar da ƙyar aka ƙwaceta. Yau kuma gashi an ganshi yana girki a madafi. Kuma naji a majiya mai ƙarfi har wanke_wanke da wanki du yana mata, ya wanke mata tsakar gida ta maisheshi lusari dai". Sai kawai ta fashe da kuka ƙaƙas fa wallahi abun dariya, abun baƙin ciki. Iko sai mai yi mana iska harda ruwa kuma a lokaci guda, menene abun kuka a wannan lamarin in ba dai so ake a nuna mun iyakata ba. Matan suka shiga bata haƙuri ni da Mijinyawa babu wanda ya tanka sai ido kawai illahirin mamaki. "Ki yi haƙuri Nanno tunda muka je kai lefe muka ga irin tarbar da uwar Hindu tayi mana nasan akwai matsala, kawune yayi ruwa yayi tsaki shiyasa bamu da yadda muka iya. Amman fa dan shanyewa wallahi ta gama shanye mijinyawa dama Kanuri haka suke jan mazajensu a ƙasa, an tabbatar mana uwarta ma sai abinda tace ma tsoho" "Bana son sake ganinka a Kitchen ko yima wannan juyar hidima. Wanka gashi matarshi a cikin laulayi take amman ita take yin komai na gidanta, amman dake ita ƴar gwal ce shafaffa da mai sabida tayi makarai na ƙarya shine ta shinfiɗe kake mata girki, ga rashin mutunci da kaje har gida kaima yarka duk akan wannan abar ko? Kai wannan yaron ku shaida wallahi akan Hindu zan iya sallama Mijinyawa domin yadda yake nuna fifiko akan matarshi abun yayi yawa. Nan ko tsaraba ya kawo na karɓa na raba sai ya nuna rashin jin daɗinshi da hakan yafi so ita a bata ta raba, duk yadda na dinga kwatanta mishi ta dinga fitowa tsakar gida ayi hira da'ita sai shima ya dinga kwatanta mun a barta tunda haka tafi so na lura tsoronta yake ji shi kanshi bijirema umarnin shi take yi. Girkin haɗakar da suke yi ma da uwatale na soke shi kowacce tayi abunta, dama uwatale tace tunda ta samu ciki take hassada abincinma bata yi sai ta yi niyya wani sa'in sai dai taci a wajensu Shafa. Ke kuma Hindu in dai kina son zaman Aure na gaske to dole ki riƙa fitowa tsakar gida ana hira dake duk abinda ya tashi ayi dake in ba haka ba wallahi zaki koma inda kika fito ni dai na faɗa miki kenan. Sannan kada ki sake kunna risho a gidannan ko ruwan zafi ban lamince miki ki dafa a risho ba, sabida baki fi kowa ba a cikin surukan gidannan kuma duk a itace suke girkinsu. Ki tashi kije na sallameki ragowar bayanin zan ƙarashe da yarana" Miƙewa nayi ko a kwalar rigata na shige cikin ɗaki ina rantsuwar in dai dole saina fito tsakar gida anyi munafurci dani wallahi sai dai auren igiyar ta tsinke, ta daɗe bata tsinke ba. Kuma ban ba da haƙuri ma kowa ba, sabida babu abinda nayi ma kowa wallahi. Duk da fa ina mugun son mijinyawa kuma gani nake yi dole sai dashi a cikin rayuwata rayuwar zata yi mun kyau. Amman kuma bazan wulaƙanta kaina, ko in yi abinda bazan iya ba. Kitchen na shige na tattaro doyar da bai gama soyawa ba na fito tsakar gidan na hura wuta naci gaba da suyan. Nayi shiru ina sauraren zuchiyata ina tunano ƴan gidanmu yau gashi a sanadina a gabana ana aibanta mun Innata wacce bani da kamarta. Ko dai a bakin Inna Abida suka ji cewar Innarmu ta mallake Baba sojanmu ne, dan naga Inna Abida ta shige dangin Mijinyawa da suka zo sosai. Ni dai harna gama komai na maida sanwar rana mijinyawa bai shigo ba sai wajen sha biyu sai gashi ya shigo ni kuma ina tsakar gida nayi shiru ina tunanin rayuwa da makomar aurenmu in ban samu ciki ba. A lokacin har girkin rana na gama na kwashe a filas. A haka ya shigo ya sameni ya zauna daf dani jikinmu na gugar juna. "Kin karya ina fatan ko? " Ko kusa ya zan karya alhalin kasan in kana nan tare muke karyawa?" "To zuba mana maza mu karya zanje maganar benci da za'a buga mun da rumfar shayi ne da zafi_zafi ake dukan ƙarfe" Saida na zuba mana muka soma ci kana nace. Ka sanar da Nanno ta amince ne da zaman naka kar hakan ya sake zama wata damuwar fa? " "Ba wannan ba sharrin da uwatale tayi miki yafi komai damuna Tutar so dan nayi imani da Allah babu abinda zai sa kiyi hassada da cikin jikinta" Murmushi kawai nayi na tura doya a bakina bance komai ba dan na ƙullace uwatale da Yaya Jamila sosai sun shiga littafina da nake adana mutanen da suke ƙina. Wannan ya wuce sai aka dawo maganar kafa teburin shayin mijinyawa. Nan aka yi mun ca a kaina, wannan ta zageni wannan ta aibata mun iyayena, maganganu harda maƙota akan na shanye mijinyawa baya son fita gari aiki shi yasa ya zaɓi ya zauna anan tare dani. Akan wannan maganar ma ciwona ya tashi yafi a ƙirga a lokacin ne aka haɗa mijinyawa da mai magani dake Azare yake zuwa karɓo mun rubutu da na hayaƙi. Babu dama dare yayi aimun hayaƙinnan babu bacci ranar na dinga ihu da tambotsai kenan, masu ganin makaran na ƙaryane ai dole suka amince na gaskiya ne dan a cikin kwana bakwai saida halittata gabaki ɗaya ta sauya hatta kamannina saida suka canja na dawo wata iri na kumbura idanuna a ciki kamar an huda sakwara. A lokacin mijinyawa shi kanshi babu nutsuwa tattare dashi ishasshen bacci wannan baya samun yi, ya kuma dage akan bazai iya dinga zuwa birni aiki ya barni in ciwona ya tashi babu mai kulawa dani ba. Ana cikin haka kawu da matanshi suka zo dubani da jiki harma ya tawo da magani shima hayaƙin ne dai da na sha da wanka yace in anji daɗinshi sai mu zo ya kaimu. To a wannan zuwanne aka samu masalaha kawu yace Nanno ta ɗauke idanunta akan mijinyawa da matarshi, a halin da nake ciki bai kamata ace ya tsallake ya barni ba tunda bani da kowa a ƙauyannan. Nan dai ala tilas ta haƙura ya kafa teburin shayinshi. Nanma kuma zama a teburin ya gagareshi ciwo babu dama duhun almuru ya ratsa sai ciwo ya tashi har da gudu nake fitowa. Rannan anyi haka da magriba shima na danna da gudu zan fita Mijinyawa babbane ya riƙeni da ƙyar ya shigar dani ɗakina aka tura yaro yai kiran mijinyawa. Nanno sai faɗa take yi wai dama ansan mahaukaciyace ni shi yasa aka liƙa ma ɗanta, ita ta gaji ya ɗaukeni ya mayar dani gaban iyayena aimun jinya mana. Shi kuma bai nuna gajiyawa ko gazawa ba, duk inda magani yake zaije ya karɓo mun ya kawo mun, sai nayi kamar lafiya zata ɗore, sai abu inya tashi motsawa yafi na da. A haka mijinyawa yaji labarin wata macce mai bada maganin jinnu ai kuwa da safe yace mu shirya mu tafi. Tare muka shiga ɗakin Nanno tana zaune tana karyawa. A gefe na zauna na gaisheta, ta amsa harda tambayar jikin nawa. Dan rannan ta shigo tana faɗa, ni kuma ina kan ganiyar abun. Sai na kamo zaninta ta ƙugu. Ba shiri ta sunce zanin ta danna a guje, Allah yasa ma tana da gwari na tsuma ta ciki. Shine ta ɗan sassauta. "Jikin dai gashinan amman bama samun bacci sam yanzu ma Abdul ƙadiri ne zai kaimu can wani ƙauye a cikin ɓoto wajen wata mai magani ko Allah zaisa a dace" "Ya dai kamata kam dan in abun yaƙi dole ta koma gaban iyayenta ayi mata jinyar acan tunda wannan lalurar da'ita ka aureta ba a gidanka ta samu ba. Ni da naje wajen Malam Idi ma nayi mishi bayanin lalurar ita Hindun. A gaskiya cewa yayi ma biri boko akayi mana, ba'a Auren mace da irin wannan ciwon ba tare da amincewar dangin mijin da za'a Aura ba. Da kuma shi mijin da za'a bashi ba. To in ma ba'ayi haka ba. Iyayenta su ne a haƙƙu su nema mata lafiya ba kai ba. Wahalar da kake yi tayi yawa fa. Uwatale ma ta dawo nan ɓarayin namu tana ɗakin Ladi tace firgita take yi cikin dare in makaran matarka suka tashi to abunka da mai juna biyu kar su shiga jikinta su sake ɗan cikin nata su mayar mata da ɗan ruwa. Kasan suna yi ai" Murmushi mijinyawa yayi kawai mukai mata sallama muka nufi ɓoto bisa jagorancin Abdul ƙadiri mahaifin Asama'u fa. Daga ɓoto muka hau mashin saida mukai tafiyar awa uku a acaɓa kafin muka isa ƙauyen akace mun makara sai dai mu karɓi lamba gobe sai mu zo sassafe. Lambar ma lamba ta sha uku muka samu. Kwatsam muna isowa ƙofar gida a Acaɓa muka tarar da motar gidanmu isowarsu kenan Yaya Saratu da Innarmu sai Akarami da Yaya Zubaina, da Jinjin. Nayi farin cikin ganinsu gaya su kuma sun tsorata da ganin yadda na lalace. "Hindu ciwo kika yi ne haka duk kika tsiyaye?" Murmushi nayi ma Innarmu kawai. Mijinyawa sai ɓare_ɓaren jiki yake yi kamar zaima Innarmu sujjada amman ita tani take yi bata ma ta tashi. Hannunta naja muka ɗunguma cikin gidan da sallamarsu suka shiga. "Maraba baƙi muka yi ne da yammancinnan? " Cewar Shafa kenan harda fara'arta kamar gaske. "Baƙine mahaifiyar Hindu ce da yayunta, shi Yaya Akarami ai kun sanshi Soja dashi aka kawo Hindu" Innarmu ta gaishe da matan gidan aka gaisa faram_ faram kamar dai gaske. Mijnyawa yace. "Innarmu muje ku gaisa da Nanno dan Allah" Innarmu bata ce komai ba tabi bayanshi muka wuce ɓarayin Nanno su, Yaya Jamila ma tana nan. "Maraba baƙin birni muka samu ne mijinyawa kaddai surukan naka ne?" Cewar Inna Ladi kenan bayan sun gaggaisa sai mijinyawa yace. "Mahaifiyar Hindu ce da Yayunta" "Allah sarki ga kamanninan sai dai ita doguwa sosai masha Allah. Ku shiga ciki bari a kawo fura" Shiga muka yi ɗakin Nanno itama harda fara'arta ta tarbi Innarmu aka gaggaisa a mutumce sosai. "Dama nazo ganin ɗakine wata nawa da Aure nace ya dai kamata mu biyo sahu muga halin da take ciki, nayi tunanin in tayi wata shidda zai kawota taga gida sai muka ji shiru shine muka biyo sahu" Cewar Innarmu kenan. Nanno tace. "Mu anan dake sai yarinya ta shekare a ɗakinta take zuwa ganin gida, wata ma sai dai a kaita wankan gida ma, to ita ko cikin ma babu tukunna wallahi" Ta ƙarashe tana dariya amman magana ta caka ma Innarmu, ita kuma a matsayinta na wayayya malamar makaranta sai tayi murmushi tace. "Allah sarki ai gara su more ƙuruciyarsu kafin yara su soma zuwa. Mu dake a birni sai yarinya ta shekara uku a ɗakinta ma batai haihuwar fari ba. Yarjejeniya ma akeyi tsakanin mata da mijin, shi yaronki ya san da hakan. Bari muje mu huta mun shawo hanya" Murmushi nayi dan na mugun ji daɗin martanin Innarmu. Garzayawa muka yi ɓarayina sai kallon gidan Innarmu take yi tana taɓe baki. A tsakar gidana ta tsaya ƙiƙam tana ƙarema murhuna kallo kafin ta ɗauke idanta daga murhun ta dawo da kallonta gareni. "Hindu rayuwar da kika jefa kanki a ciki kenan irin rayuwar da soyayya da taurin kai suka zaɓar miki kenan? Jibakki yadda kika rame kika ƙwanjame da jin yadda surukarki take yaɓo maganganu na tabbatar ba zaman daɗi kuke yi ba" Innarmu mu shiga ciki dan Allah gidannan cike yake da munafukai. Mu yi a ciki dan Allah" Gabaki ɗaya jikkunan ƴan uwana duk ya mutu murus wallahi. To ina fatan kafin tafiyar Innarmu Allah yasa kar a rabu dutse a hannun riga ita da Nanno. Dan Innarmu ba kanwar lasa bace sam. Mrs BukhariTSURON TSIRIN.... TSANDAURI.... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA GOMS SHA BAKWAI *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F5JwhdwbtCQ6qdo4LA4kyE Assalamualaikum Kina son ki mallaki zafafan hijabai masu kyau da inganci Amma baki da halin siya kai tsaye kizo GA sauki na samar Miki na adashin hijabai Kala kala da kadan kadan zaki Zuba ki kwashi hijabin ki cikin Aminci da yarda Allah ki fito fes abunki ki baza capacity ki hajiya Allah dai ya soni batai musu ba muka shiga daga ciki suka zazzauna ni kuma na kawo musu ruwa kana na zauna. Yaya Saratu, Yaya Zubaina, Jinjin, Akarami sannunku da zuwa kun shawo hanya gaskiya. Na ko ji daɗin ganinku sosai. Innarmu ina wuni ya hanya yasu Baba Sojanmu bai biyo ku ba, ni na zaci duk randa zaki zo ganin ɗaki tare zaku zo dashi ai? " Saida ta gama shan ruwan ta miƙo ma Saratu kafin tace. "Lafiya lau hanya, wannan gari naku kamar za'a bar duniya dama haka jama'aren take ƙauye Hindu ke kuma ƙaddarar soyayyar nan ta jawoki Allah al hakim yanzu kece a cikin irin wannan gida da irin wannan rayuwa?" Murmushi kawai nayi mata ina kallon Akarami dake mun murmushi shima, wallahi tausayina yake yi gashi nan ɓaro ɓaro a idanunshi. "Innarmu ina ganin kubar maganarnan da daddare in kuka keɓe ƙafa ta ɗauke sai ku tattauna tunda tare zaku kwana ai, kinga tace miki a shigo daga ciki, kuma gidan yawa dai kinsan yadda ba'a rabashi da gutsiri tsoma. Hindu yinwa mu muke ji wallahi ko taliyace a sulala mana mu rage hanya kafin ai mana girkin jama'are" Cewar Akarami daya ƙarashe yana murmushi tare da ƙarema falon nawa kallo. Da sauri na niƙe tsaye dama mayafina na jikina. Ina zuwa bari a ɗaura abinci danma bansan da zuwan naku bane." Fita nayi saida na saka leda na hura itace da kara kana na fita, daidai zan fita na hangi Yaya Jamila da kwanon sha babba zata kaima su Innarmu fura ni kuma a bakin ƙofar fita can waje naci karo da mijinyawa rigijib da kayan cefane. "Ina zuwa ke da baki da ishasshiyar lafiya kuma?" Dama wajenka zanzo sabida bansan me zan girka musu ba" "Muje ga cefane nayo harda ma na dare, muje in kama miki ayi a gama" Ba dai ka kamamun ba ka rufamun asiri so kake Nanno ta barmun kai? " Dariya muka saka dukkanmu, tare muka shiga ciki, shi ya wuce wajen su Innarmu ni kuma na jawo tire na baje kayannan. Zabbi nagani guda biyu an yanka ba'a fige ba saina soma ɗaura ruwan zafi. Ga kayan miya, ga kifi soyayya na mutun ƙauye wanda ake soyashi da fulawa dama dashi nake miya na nera ɗari kullum nake ɓarewa ko a miya ko a jalof yau gammo biyu ya siyo. Ina jajjage ya fito Yaya Saratu jin daka yasa ta fito tsakar gidan ta nemi kujera ta jawo ta zauna. Da kanshi ya juye ruwan a bawo ya tsoma zabinnan ya hau figa ni kuma na tsayar da sanwar jalof ta taliya. Kusa da Yaya Saratu da tayi tagumi naje inta kalleni ina ɓare kifi saita kalli mijinyawa daya daddage yana ta fige zabi me take nazari Allah masani. Allah ya taimakeni harya gama ya yayyanka babu wanda ya shigo bare ya ganshi har ya fice a gidan ya bamu waje. "Hoo ni Saratu Hindu kece mai girki a murhu sai kace tsohuwa? " Yaya Saratu kenan ai naga a gidan Baba sojanmu ma da itace muka taso muka gansu suna girki ko, ni banga aibu dan nayi girki a murhu ba. Muna zamanmu lafiya kuma ina samun dukkan kulawa" "Ba shakka ai nima naga kulawa kam shi yasa gakinan duk kin tsiyaye sai kumburarriyar fuska jiki ya tsotse kai Allah wadaran soyayyar da zata ɗakko na maraya zuwa ƙauye, manzon Allah ma ya hana Hindu sai dai a ɗakko na ƙauye zuwa maraya. Babu babban koma baya irin a ɗakko mutumin da yayi rayuwar maraya a kawo shi ƙauye tur cutarwace mai girman gaske fa, wai baki da hankaline Hindu, ke yanzu kin zaɓi wannan irin zaman" Miƙewa nayi naje na zuba taliya a tukunya na zuba kifin. Sabida bana son hirar tayi tsayi saina ɗakko tukunya na zuba zabbinnan a ciki, guda miya zanyi musu, gudan kuma tafasawa zanyi in ajjiye gobe naga me zanyi musu da'ita. Ina sauke taliyar na ɗaura tafashen nama a babban tire na juye mana taliya biyu sai mijinyawa dana ɗibanma da kaina nasa mayafi naje na kai mishi har teburin shayinshi kana na dawo na tarar suna ci ana hirar yaushe gamo. Saida suka ƙoshi sukai wanka suka rama sallolin da ake binsu. A lokacin duhu ya riga da ya rufa. Shinkafa da miya na girka musu na zuba a kwano na aikama da Nanno nata dan gudun magana. Akarami saida yaci abinci ya ƙoshi sannan ya miƙe. "Ni kam Innarmu zan shiga cikin Bauchi sai jibin zanzo mu wuce. Hinduwa Innarmu zata baki tsarabar da nayo miki. " Godiya nayi mishi ni da Yaya Saratu, da Jinjin muka rakashi har gaban mota sai lokacin muka sakko da kayansu da uwar tsarabar da suka yo mana muka shiga dasu cikin gida, Akarami kuma ya wuce. Muna kwance a tsakiyar ɗakina muna hira Innarmu tace. "Dama ƴan uwanki ne suka dameni akan muzo mu dubaki shi yasa muka zo tunda ke baki yi hankalin da ana yin wata shida kice ya kawoki gida ba, ƴar daɗi miji, kinfi so duk shekara ne zaki zo gida kenan? Kina gani duk wani suna biki ina zuwa Biu inje in sada zumuncina da Ƴan uwana. Ko yanzu haka daga can muke kwananmu bakwai kuma nanda wata uku komawa zamu yi bikin ɗiyar kawuna in anyi na su Akarami da sati guda, tunda kina nan lokacin sai muje tare ma dake. Hindu ki kiyaye zumunci ba abun yarwa bane. Kinga Jinjin ita tai ta mafarkai munana a kanki, ranar da safe tazo tana shigowa ta saki kuka kawai, cewa take Innarmu muje mu dubo Hindu." Baki na washe nace. Akarami bikin ya matso kenan su nawa zasu yi Auren?" Yaya Saratu tace. "Su Bakwai hadda Qazzafi Innah Mairamu ta shiga ta fita ta haɗashi Aure da ƴar gidan manya gidansu sanannun mutanene sosai, kuma gorin kin ƙishi bata dena ba, da labarin ƙauyannan iri_ iri a bakinta har da wanda bana gaskiya ba in faɗa miki. Za'a sha biki dan angwayen a shirye suke sosai baki ga akwatin Akarami ba Innarmu ce taje Lagos da kanta ta siyo kayan akwatinma wasu daga Lagos wasu kuma daga Dubai taba ƙawarta ta siyo mata. Mun tawo miki da ƙyallen ankon ƴan ɗakinmu amman gaskiya ba lallai mijinki ya iya siya miki leshin da muka fitar ba" Innarmu tace. "Harma atampar super ce fa ai ta saka abinda yake daidai ita kawai zai fi mata. Yanzu ba da bane ai. Ni kuma bazan iya siyar da Akuya ta dawo ci mun danga ba. Ta suturta jikinta da kayan akwatinta zai fi mata" Naji wani irin zafi da baƙin cikin kalamansu ainun. Amman saina murmusa nace. A bani ƙyallen zai siyo mun. Daidai gwargwado ban rasa komai ba ƙauyan kawai kuke kallo shiyasa. Innarmu wallahi muna zaune lafiya duk wata nutsuwa da ake buƙata a zamantakewa daidaiya ina samu" Ciro ƙyallen Yaya Saratu tayi a jakarta ta miƙo mun. Suka nunnunamun tsarabar da suka kawo mun, harda lafaya mai kyau Inna Yahanasu ta bayar tace a kawo mun, sun sake yo mun guzirin turaren wuta da Humra daga maiduguri naji daɗi sosai. "Nace ba Hindu meke damunki ne kika lalace aurenne babu daɗi, ko garinne, ko dangin miji, kar ki sake ki ɓoye mana wani abu zurfin ciki a zamantakewar Aure in yayi yawa tura mutum ga halaka yake yi, ke kuma na sanyi da tauri da zurfi." Wallahi Innarmu babu ɗaya mutanenne kawai suka matsamun lamba ko bacci bana iyayi" Ai kuwa ina ambatonsu sai naji tsigogin kaina suna tashi saina shiga zare idanu. Abunda nake yi cikin daren haka yauma ta faru a gaban idanunsu sun shaida tabbas. Yau kam Nanno harda zuwa a lokacin Mijinyawa ya shigo sun daddanneni ana shafamun ruwan magani a jikina Mijinyawa yanata adda'a. Da abun ya ɗan lafa bayan an kwashe sama da awa uku ana abu ɗaya. Mijinyawa na riƙe dani yana ta mun karatu yana tofamun ina harararshi, duk na yakusheshi gefen wuyanshi ma jini ke fita. "Kinga halin da kullum muke kwana dashi kenan Allah yasa kun gani. Dama kunsan tana da wannan lalurar ne? " Nanno ke wannan maganar suna falo su uku da Innarmu da Innah Ladi. "Mun sani shima ya sani ba rufarshi akayi ba Aure ne dai na ƙaddara kawai. Amman ai mun wuce matsayin rufa_rufa bama neman kai da'ita manema gareta masu daraja da ɗamaru. Kutse yayi mana kawai" Sai Inna Ladi tace. "Ni ina ganin ku tafi da'ita kawai a nema mata magani Allah bashi inta warke sai a dawo da'ita inaga hakan shi yafi. Yaronnan yana wahala, wajen nemanshi ma bashi da nutsuwa, ga kasuwarshi ta dare ce, namiji bazai iya wannan jinyar ba" Innarmu tayi dariya tace. "Ku ai iyayen Hindu ne bai kamata ace shi Gawata zaku bari da jinyar Hindu ba. Kune zaku taimaka mishi har Allah ya bata lafiya. Amman tayi jinya a ɗakinta shine abu mafi cancanta. In kinga mun tafi da'ita to sai dai in da takaddar sakinta a hannunmu domin auren bai dokamu da ƙasa ba taurin kaine irin ya yaran zamani ma. Ina malamar makaranta mahaifinta na matsayin babban soja ace ɗiyarmu na aure a wannan kufai ɗin" Sai Inna Ladi tace. "Me yayi zafi shi ba wuta ba? Abun bai kai nan ba Allah ya huci zuchiyarki Nanno taso muje kinji, na lura Hindu gadon taurin kai tayi kinji mahaifinta shima soja ne ashe. " "Ƙwarai kuwa gado tayi babu yadda za'ayi ta zauna ku takata yadda ranku yake so. Tana da iliminta tasan hakkinta. Ku yanzu baku ji kunyar kwaso jiki kuna cewa wai a tafi da'ita ayi jinyarta a gida ba ko? Ashe ɗanku bai nuna muku takaddar yarjejeniyar da akayi dashi ba ko" Nan rikici mai zafi ya ɓalle tsakanin Innarmu da Nanno. Wallahi har kai Innarmu tai ta dungurema Nanno. Ita kuma Nanno sai zazzaga take yi. Yaya Salihu ne ya shigo shi da Shafa ya janye su Nanno yana ba Innarmu haƙuri domin sai fesar da manganganu take yi. Nanno dai bata samu zarafin cewa komai ba kuma jikinta ya mutu, ashe ita ba jaraba ta iyaba ƴar koyo ce. f Fita kawai suka yi. Saida bacci ya ɗebeni a lokacin ɗaya da rabi ma na dare ne, sannan mijinyawa ya iya fitowa ya baro ni, ya tsugunna yana ba Innarmu haƙuri akan abinda ya faru a tsakaninta dasu Nanno. Bata ce dashi ci kanka ba harya gama ya fita jiki ba laka. Yana fita ciwo ya kuma tashi a kaina su Innarmu suka kwana cur. Washegari sassafe harda Innarmu muka wuce gidan maganin su Yaya Saratu kuma suka zauna zasu yi mun kwalima. Munje mun samu mata da yawa masu irin lalurata ni nawa da kyau ma tunda ina cikin hayyacina a lokacin, wasu kuma da yawa basa cikin hayyacinsu ma. Tunda na zauna a kan layi nake jin kaina na jujjuyawa sai ambaton Allah kawai nake yi har layi yazo kanmu. Ni dai muna haɗa idanu da mai magani na zube a wajen na fita cikin hayyacina. Mijinyawa:. "Ku shigo da'ita ai dole su zubar da'ita wannan fadar bata wasa bace. Ku matso da'ita kusa dani" Cewar mai magani tana yi tana murmushi ga haƙoran makka a bakinta kusan shida, ga zobuna da awarwaro marasa iyaka, sarƙoƙi a wuyanta babu dama ne, ita kanta tayi zubin aljanu kuma da kun haɗa idanu gabanka zai tsinke ya faɗi. Tattago Hindu suka yi zuwa gabanta ta shiga yarfa mata ruwan magani nan take Hindu ta soma kakari tana sambatun cewar ko kashesu za'ayi ba zasu fita a jikinta ba, kuma in ba'a dena mata gorin haihuwa ba ba zasu dena zuwa ba. Su asalinsu makaraine na gadon gadon gidansu Innah suna tare da kaf zuriyarsu ko ita Innah suna tare da'ita su ba masu cutarwa bane ayi sulhu dasu kawai in kuma anason zaman lafiya kada a sake kiran goɗiyarsu da juya" Da wata iriyar murya mai sauti biyu suke magana da kuma wani irin amo mai tsoratarwa. "Au juya suke kiranta wata bakwai da ɗan wani ɗoriya kacal da aure dan bata samu ciki ba? Allah mai iko, ƙauye kenan" Cewar Innah kenan tana girgiza kanta. Mai maganin tace. "Amman ai kuna cutar da'ita dayawa me yasa kuke son kashe mata Aurenta ku barta hakanan ta huta tunda ku mallakin zuriyar gyatumartane mana kuyi alƙawarin barinta ta huta ko in haɗaku da babbanku" Makaran suka ce su babu inda zasu matsa suna tare da Hindu kullum kuma basu ga wanda zai iya matsar dasu ba" "Ashe ba sonta kuke yi ba kenan kunce ku ba masu cutarwa bane amman kun hanata ita da mijinta samun farin cikin dare, sannan ziyarar da kuke zuwa mata cikin dare zai iya hanata samun rabon da akeyi mata gorin akai ai. Ku matsa ku bata waje kuyi haƙuri na roƙeku ku barsu su mori gajiyar aurensu" Da haka dai ta shawo kansu suka ce zasu dena bigeta in aka dena mata gori amman duk sanda akace mata juya tabbas zasu zo kusa su kuma. Kuma sun kusa soma juyar da bakin duk wanda ya sake cewa da Hindu juya" Hayaƙi ta zuba a cikin kaskon dake gabanta ɗakin ya turniƙe da hayaƙi mai tuƙuƙi mai maganin tace da Innah. "Kiyi haƙuri na kanki ba zasu motsa ba, naki dattijaine basa tashi miki tunda kika tsallake abubuwa da yawa ba zasu tashi miki a yanzu da girma ya hauki ba. Amman sabida ke suke bibiyar yaranki dukkansu suna tafe da abinsu ita nata ne suke da tsauri shiyasa suke tashi mata. Su kuma kalar tasu nuna ƙaunar kenan. A zuriyarku akwai masu hawa makarai kamar inda ita wannan take yi? "Eh akwai hatta gyatumarmu itama tayi ciwon makarai sosai. Akwai ƙanwarmu da suka hanata zaman auren saida tayi aure shida ana bakwanne ta dace da magani, mai maganin ma dai ta aura dashi suka ci gaba da rayuwa, amman bata taɓa samun haihuwa ba, ko ɓatan wata gaskiya bata taɓa yi ba Sai ɗaiɗaiku a cikin yaran ƴan uwa." "Gadon gidankune ta ɓangaren mahaifiyarku, sai dai ba masu cutarwa bane kuma musulmaine ba kafirai ba, ta dage da magani sannan a guji ce mata juya sabida dugun abinda kaje kazo ita ba juya bace tana da ƙwanta na haihuwa, kuma zata haihu lokacine bai yi ba. Kai kuma ga wannan hayaƙin duk magriba da zaran almuru yayi a turare ɗakinta dashi, sannan wannan ruwan maganin a dunga sirka mata ta dunga wanka dashi a bawo, kada ta goge jikinta in tayi wankan ta barshi ya bushe a jikinta, zasu barta ta huta. Sai a kiyaye a dena aibantata ana kiranta da suna juya kasan makarai suna da naci da rashin yafiya, kuma sukan taya wanda suke karewa faɗa kota wanne siga, amman ba masu cutarwa bane, kada ace za'a rabata dasu bisa dole zasu iya cutar da'ita da duk makusancinta a wannan gaɓar. Sannan in aka kaisu bango zasu soma hana duk wanda zai kira musu goɗiya da juya sukuni, kaji da kunnnenka me suka ce zasu soma yi ai? " Hayaƙi da na wankan ta miƙa mishi ta ɗebi ruwa a tafin hannunta ta yayyafama Hindu" Hindu:. Ji nayi ruwa ya sauka akan fuskata da sauri na miƙe zaune idanuna naji suna mun wani irin yaji da raɗaɗi kawai. "Sannu yarinya ya kike jin jikin naki? " Mai magani ta tambayeni da jajayen idanunta. Kasa magana nayi, sai tayi dariya ta dubi mijinyawa tace. "Sun riƙe mata bakin basa so tayi magana dani. Fishi suke yi dan nace su baku iska. Kada ku damu da kun bar wajennan bakinta zai buɗe. Kuma sun haƙura" Mijinyawa yace. "Mungode sosai nawa zamu bayar kuɗin sadaka to? " "Ai bama faɗa abinda Allah ya tsaga rabonmu ne shi muke samu ka ajjiye kawai ku tafi" Hannu ya saka a ajjihu ya ɗebo dubu huɗu ya ajjiye mata, shi da Innarmu suka kamani muka fito. "Kai da ita sai ku hau Acaɓa ka riƙeta da kyau" Cewar Innarmu, ita ta taimaka mun na hau mijinyawa ya hau bayana, ita da Abdul Ƙadiri kowa ya hau nashi muka tawo. Wani sanyi ne yaketa ratsani jikina har kakkarwa yake yi. Ƙam mijinyawa ya riƙeni yanata mun karatu a kunnena can sai na sauke ajjiyar zuchiya na dena jin wannan sanyin. "Sannu Tutar so Allah ya inganta lafiya" Ameen' Kawai nace dashi nayi shiru ina sauraren zuchiyata. Sai bayan la'asar muka shiga gida, fuskata tun a hanya naji ta sawai ta saɓe ban gasgata hakan ba saida na fito wanka na tsaya a bakin mudubi sai na ga na rame sosai fuskata kamar ta ƴar mage. Magriba na dosowa Innarmu da kanta ta bunke ɗakina da hayaƙi ta zagaya lungu da saƙo. Muna yin isha tasa nayi wankan magani Alhamdullillahi yau kam nayi bacci harda makara nayi saida Innarmu ta tasheni kana nayi sallah muka gaggaisa. "To mu kam anjima kaɗan zamu ɗauki haramar komawa inda muka fi wayau. Kada kiyi wasa da magungunanki Hindu ki dinga yin hayaƙin kuma ki dinga yin wankan kinji ko Allah zai baki lafiya. Kuma kar ki saka damuwa a ranki dan kawai kinyi wata takwas baki samu rabo ba, baki ma ƙarasa takwas ba wata bakwai ne kamar da kwana goma sha uku, kowa da lokacinshi masu goranta miki in sunyi zuchiya su baki mana tunda a gidansu ana bada ɗan mutum kyauta. Ki maida hankali akan abinda ke gabanki. Yaya batun komawarki karatu da mijinki yayi alƙawari? Ai yanzune ya dace ya sakaki ki kammala digiri ɗinki kafin ku soma tara yara ko, ko kuwa ya janye alƙawarinnen sai musan me zamu ce da Baba sojanku dan wallahi akan karatunki kinsan Aurennan zai mutu ko? Bazai yiwu ba wallahi Allah kinji na rantse miki. Sai dai muji da ɗaya kasancewarki a ƙauye amman dole kiyi ilimi ba zaki haɗa biyu ba ga ƙauyanci ga jahilci ba. Ni naji daɗi ma da baki yi ciki da wuri ba. Nifa bana jin akwai ranar da zan so Aurennan naki. Ga Saratu harta samu aiki ta soma ɗaukar albashinta mai tsoka. Ku bani amsar abinda zanje ince ma Baba Sojanku saƙon daya bani in kawo shine yaushe za'a soma karatunne." Mijinyawane ya shigo da sallamarshi yazo duba Innah a kuma gaisa ya tarar tana maganar karatu. Bayan sun gaisa tace. "Gara daka shigo dama inason ganinka akan maganganu da yawan gaske. Na farko yana da kyau danginka su sani cewar Hindu ba juya bace tunda ba dole bane saita haihu a cikin shekara guda da aure ba, ni sanda akaimun aure saida na shekara uku kafin Allah ya bani rabo. Ikon Allah ban taɓa ji daidai da rana ɗaya an kirani da juya ba, sai Hindu wata takwas kawai, anan garin bata da gatan kowa sai kai yana da kyau ka tsaya mata ka tsawatar ma danginta su guji kiranta juya a gabanka. Kaji abinda mai magani tace, suma makaran kaji abinda yake kawosu, domin samun nutsuwarku da lafiyarta sai ka gargaɗesu. Sannan batu na biyu menene dalilin da yasa abincin cikinku ku biyu ba zaka dinga siyo ma Hindu kalanzir tana aiki a risho ba saita kunna itace abincinku kuku biyu? " A hankali mijinyawa yace. "Kiyi haƙura Innah in sha Allah zamu tattauna da masu ruwa da tsaki a gidan babu mai sake kiranta da wannan sunan. Dangane da batun aikin girki a murhu umarnin mahaifiyata ne muka bi tace bata yadda ita Hindu ta dinga aiki da risho ita kaɗai a gidan ba, sai dai tayi a murhu kamar kowa shine kawai dalilin." "To batun komawarta karatu daka ɗauki alƙawarin zata ci gaba da karatunta in ka aureta fa, shi wannan mahaifiyar taka zata amince dashi kuwa, kasan fa akan karatunnan wallahi sai dai aurennan ya mutu, zamu iya yadda da komai amman banda zama babu ilimi kuma ba ilimin da mace zata yishi ace ta zauna ƴaƴanta ne kaɗai zasu amfana ba, a'a ilimin da zata fita ta bayar dashi al'umma su ƙaru da'ita tayi aiki kamar ni, kamar ƴan uwanta. Kasan yana cikin sharaɗin aurenku ai. Kai Magawata yaushe zata koma bakin karatunta? " "Ban manta da alƙawarin ba. In sha Allah zata koma makaranta nayi wannan alƙawarin bazan saɓaba. Ina jiran sana'ar da nake yi ta tsaya da ƙafafunta ne tukunna, sannan ita kanta ta samu lafiya" "To zuwa yaushe kenan dan in sanar ma mahaifinta ko ba gaskiya ba? Dan ina ganin yanzune ya dace a ɗebe mata kewar raɗaɗin zaman ƙauyennan da karatun ko? Kuma kaga ai gara ta soma tun kafin ta shiga laulayi ko, in kuɗinne babu sai na tallafa maka na ɗauki nauyin karatun mu dai fatanmu shine a samu ilimin yara su dogara da kawunansu." Shiru yayi har a fuskarshi ya nuna rashin jin daɗinshi, nima naji wani irin kunya gaskiya. "Kiyi haƙuri zata yi karatu in lokaci yayi kuma in sha Allah ni zan ɗauki nauyin karatunta harta kammala, kuma zata yi aiki kamar yadda kuka buƙata in sha Allah nima zanyi alfahari da hakan" Innarmu tace. "Amman... " Yaya Saratu ce ta katseta ta hanyar cewa. "A bashi lokaci kamar yadda yace tunda yace zai ɗauki nauyin karatun kamar yadda dama haka sharaɗin yake. Kuma ya nuna baya buƙatar tallafinki akan karatun ai shikenan Innarmu" Ajjiyar zuchiya ta ja tare da saukewa tace. "Shikenan mun baka lokaci lokacin shi zai mana alƙalanci. Amman yana da kyau ko koyarwa a firamare ka nema mata ga makarantun gwamnati nan a garin naku da zaman banzan da take yi, ko nawa ne albashin a ƙalla zata samu, sannan ko babu komai fitar zata rage mata damuwar cikin gidan, ko babu albashi gara ta dinga yi, a ƙalla karatun ba zai bar kanta ba" "To shikenan zan nema mata wannan baida matsala, akwai wanda na sani in sha Allah zan mishi magana zai sama mata gurbin koyarwar" "To madallah mu zamu wuce akwai biki nan da wata biyu da sati biyu na yayunta maza munaso ka barta tazo, sannan akwai bikin ɗiyar ƙanwata a Maiduguri shima zamu je tare da'ita in an gama bikin gida da sati guda, muna saka idanun ganin ka barta tazo" Kai ya sosa yace. "In sha Allah zata zo Allah ya nuna mana lokacin rai da lafiya mungode sosai Innarmu da wannan ziyarar" Tare dashi muka ɗunguma muka raka su Innarmu har gaban motar Akarami da yaƙi shigowa sai yaro ya aiko wai su fito su tafi. Ɓarayin Nanno muka leƙa suka yi sallama babu yabo babu fallasa. Saida motarsu ta ɓace ma ganinmu kafin ya rakoni muka shigo gidan a tsakar gida muka zauna na kawo mishi kayan karyawa, kana na jibge mishi tsarabar da suka kawo komai da komai harda kuɗin ɓatarwa da Baba Sojanmu ya aiko mun dasu, na miƙa mishi ƙyallen ankon gidanmu duka dai. Yana cin doya yana korawa da shayi yace. "Gaskiya sun yo tsaraba da yawa, wannan doyar da suka kawo akwai gari gata da haske, mungode sosai ga wake ma mun samu" Ina dariya nace. "Kuma kaga kayan abincinmu shinkafa kaɗai ta rage itama bata fi kwana biyar ba. Bari in samo ledoji in zuzzubama matan gida tasu tsarabar. " Hannuna ya riƙe yace. "Baki karyaba kizo muci Tutar so, naga jikinki da sauƙi sosai" Sai naji ƙaunarshi ta sake yin lub a ruhina nayi murmushi nace. Naci tare da su Yaya Saratu wannan ai du naka ne kaci ina zuwa" Ciki na shiga na ɗebo ledoji na zuzzuba waken diyar na samu wuƙa na yanka na sakama kowa Su Nanno ma na cire musu nasu, na cire ma Baraka nata dan tayi hidima dasu Innah sosai da kaina na mimmiƙama kowa na Baraka na ba yara suka miƙa mata. Da kwana ukun wake, doya huɗu muka tsira. Turaren wuta dama ban samma kowa ba adana abuna nayi a durowar turarukana. Saida na kammala na zauna kusa da mijinyawa muna fuskantar juna nace. Kayi haƙuri da duk maganganun Innarmu nima ba sui mun daɗi ba balle kai" "Ko kusa, ai kamar yadda Nanno take yaɓo mana ni dake mu shanye, itama Innarmu dole mu shanye nata, in kikai la'akari dukkansu da hujjojinsu salone nasu na nuna soyayyarsu garemu. In sha Allah zaki zama abinda kike son zama da gumin halak ɗina zan biya miki karatu. Kuma zan nema miki gurbin koyarwa a makaranta kamar yadda Innarmu ta buƙata gobe_gobennan kuwa zan shiga in samu hedimasta muyi magana da takaddunki ma zan tafi in sha Allah zaki samu koyarwan in dai hakan zai baki farin ciki. Masu miki wannan gorin kar ma ki sake kulawa ke ba juya bace zaki haihu har ma sai kince da kanki kin gaji. Kuma in so samu ne yara nawa zaki haifo mun ne?" Ina dariya nace. Bakwai ma ai sun isa ko?" Shima dariyar yayi mun yace. "Baki da burin tarawa ma sai nuna damuwar kawai dai". Mun jima muna hirarmu cikin farin ciki da annashuwa. Daga bisani yace yana son zai yi ƙaikula, ya shige daga ciki ya kwanta ni kuma na shiga aikace_aikacen gida inayi ina girkina na rana faten wake da doya nayi mana munci shinkafa munci dama har mun gaji. Washegari kuwa da yamma Mijnyawa yaxo mun da albishir na samu gurbin koyarwa a makarantar yara ta firamare jama'are sentaral makarantar firamare da sakandare ta gwamnati duk wata ina da albashin nera dubu huɗu ta wancan lokacin. Nayi murna sosai nayi farin ciki, duk da an sha daga da Nanno amman daga ƙarke ta amince dan nayi rantsuwa da Rabbil ka'aba akan dole in koyar tunda har naci sa'a suka ɗaukeni, akan wanne dalilin za'a hananu. An sha artabu dani sosai, banyi da wasa ba sam, nasan muddin nayi sake kuma na amince na zauna. To wallahi batun karatuna ma babu ina ji ina gani zata zaune mun. Kunji yadda al'amura suke ta cukumurɗewa ko? Ku dai ku ci gaba da biyo Duwaf ɗinku. Mrs BukhariTSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIA'T IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA GOMA SHA TAKWAS *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. Ranar Litinin kuwa na soma zuwa koyarwa a Babbar sakandare Government Day sakandare Jama'are. mijinyawa shi ya rakani har cikin Ofishin Shugaban makarantar ya ganni muka yi magana aka bani ajin turanci ina ɗaukar aji ɗaya jiniya kilas kenan ba siniya ba. Da ai makarantar firamare aka tambayomun, harma munje gwajin da akaimunne yasa aka dawo damu sakandare. Sabida akwai turanci a bakina sosai, kuma gwajin ta nuna musu nayi karatu ingantacce, tunda a gida ma Baba Sojanmu yana gurantar damu. A lokacin ba'a cika ɗaukan koyarwa a sakandare da takaddar sakandare ba, sai da Takaddar NCE gaskiya, amman ni dake kwana nayi ina adda'a an ɗaukeni sabida ana ƙarancin malamai gaya gaskiya. To taimakon Allah ne, kuma sunga nasan abubuwa da dama, gashi babu tsoro a maganata turanci zur_zur kamar ( Mrs jay malamar turancinmu da take horas damu) Kuma a lokacin takaddar sakandare mai ɗauke da sakamako mai kyau tana da daraja gaya, ba irin yanzu bane. Mijinyawa misali ko a firamare ba'a ɗaukeshi ba, karatun dai anyi ne ba ace ba'ayi ba. Wannan kenan. Nayi muku bayani da kyaune dan kada ku ƙalubalenceni wannan labarin a gaske ya faru a_kan karan _kan_kin kaina ya faru wallahil Azeem. A shekarar 1999 sunan makarantar Government Arabic college GAC) jama'are har zuwa shekara ta dubu biyu da ɗaya kafin aka sauya sunanta. To ni sanda na shiga tana a matsayin kwaleji larabci an kusa sauya sunan daf, dan watanni kaɗan nayi aka sauyata zuwa Government Day Duk da kasancewarta kwalajin larabci an haɗa ta da darussan boko na ɓangaren Arts don ba ma ɗalibai damar rubuta SSCE na WAEC ko NECO Darussan da suke bayarwa sun haɗa da turanci, lissafi, da tarihi hausa. Amman babu darussan kimiyya masu zurfi irinsu fizizs, kemistiri a tsarin karatun makarantar a lokacin da take amsa kwalejin larabci fa Allah yasa kun fahimta. Su Mijinyawa sune suka yita tana matsayin kwalejin larabci. Makarantar ta yaye manya_manyan masu riƙe da madafan iko na cikin gida Najeriya wanda in sunayensu za'a jero za'ayi mamaki. An kafa makarantar a alif dubu ɗaya da ɗari tara da tamanin da ɗaya. Nan mukai sallama da Mijinyawa aka nuna mun aji na shiga da Bismillah zuchiyata har tsalle take yi domin murna. ƙarfe ɗaya aka tashi A lokacin malaman mata mu uku ne duk sauran malaman maza ne. Cikin amincewar Ubangiji na soma koyarwa kuma abun daɗi da sha'awa yaran suna gane karatun nawa sai dai ƙalubalen farko dana samu shine na ciwon kai har jiri nake gani inna dawo gida sabida ihun karatu da ƙoƙarin nutsar da ɗalibai su saurari karatunma. Makarantar ƙauye ta bambamta da makarantar birni, haka ma yaran akwai bambamci. Kuma babu laifi ana karatu a jama'are ko wanne aji cike yake fam da ɗalibai babu laifi. To wannan koyarwar ta shafe mun kwatan damuwata sosai duk da gorin rashin haihuwa kusan sake tsananta yake yi barin in akayi haihuwa a dangi zamu je taron suna gabana har faɗuwa yake yi dan zaiyi wuya aje a dawo lafiya dole sai anyi mun shaguɓe ni kuma dana dawa makaraina zasu rabkeni, waɗannan sukai mun gorin kuma mutum biyu bakinsu ya karkace, sai da suka kwana biyu a haka kafin akaita roƙona bakin ya sake. A ciki harda Shafa matar Yaya Salihu. To wannan ja'ibar ta ɗan sassauta gorin gaya. Haka mijinyawa zai kwana a kaina yana yi mun adda'a babu wanda ya sake sanin halin da nake shiga mijinyawa shi ke ci ya cinye, haka in zai kaini gidan magani mu amso babu mai sani. Tafe_tafe har lokacin bikin gidanmu ya gabato saura sati biyu, ni kuma inaso saura sati guda in tafi. Atampopina guda huɗu na cira ni da mijinyawa muka shiga Bauchi muka sako su leshinne ban samu ba, amman supern na samu na bada ƙananun super guda biyu an bani super babba irin ta ankon sak sai sauran kuma na karɓo kuɗinsu muka dawo gida naci gaba da haɗa kayana. Ranar da zan tafi da sassafe na fito zan ma su Nanno sallama na tadda Uwatale zata haihu tana naƙuda. Bikin yayi daidai da hutun ƴan makaranta da aka bayar. "Kije Allah ya tsare muna cikin halin kula da mai haihuwa ne" Cewar Inna Ladi. A babbar tasha mijinyawa ya saka ni a mota kai tsaye zuwa kano. "Naso ace na rakaki sai in dawo to amman kuɗinne babu shiyasa kawai na haƙura watarana a motata zan tuƙaƙi in kai ki in da rabo." Ƴan kuɗaɗen jarinshi ya tarkata ya danƙamun dan ya fiddani kunya kawai. Idanu na lumshe kawai inaji uwa in zubar mana da hawaye, rayuwar fa tayi mana tsauri sosai hatsin da zamu ci sai dai mu auna, ranar daya carke mishi kuwa sai dai mu sha shayi da biredi mu kwanta, ko in Mijinyawa Babba ya dawo yana ƙoƙarin kawo mana tsaraba da hatsi sosai duk da uwatale na adawa da hakan amman dai bata isa shiga tsakanin ƴan uwan ba, shaƙuwar dake tsakaninsu da ƙarfi sosai. Babu wanda yasan halin ƙuncin da muke ciki a gidan muna iya bi da talaucinmu muna ɓoye sirrinmu sosai. Albashina na farko tare dashi muka shiga kasuwar Galdimari wacce take ci ranar talata anan muka siyo hatsi da kayan miya bushasshe da duk abinda muke da buƙata. Shine mukaita amfani dashi har watan ya ƙare, aka sake wani biyan a lokacin kuma ina shirin wannan tafiyar da zanyi sai ya hana in taɓa kuɗin a hakanma bani da kuɗin motar da zan dawo gida na tafiya kaɗai gareni da kuɗin ɗinkin biki sai kuɗin lesiri dana ƙullo, kuɗin daya bani kuma su takalmi, mayafi, ɗan kunne da sarƙa zan siya, ga tafiya Maiduguri shima bikinne. Motarmu saida ta cika kana yaimun sallama, kafin ya tafi na siya mishi rogo da ƙuli yayi mun godiya ya fita a tashar, dan nasan baida ko ficika, muma motarmu ta fita muka ɗauki hanya fetal tunanuka cike da kaina. Rayuwar a haka zata ci gaba da tafiya ƙila rayuwata a cikin wannan ƙauyen zan gamata babu lallai in samu cika burina dana iyayena fa. Ga lamura sai sake taɓarɓarema mijinyawa yake yi ina ganin dole in bashi shawara ya fita nema kamar yadda sauran ƴan uwanshi da abokanshi suke fita sabida gaskiya samarin garin basu fiye zama ba in ba lokacin damuna bane shine suke dawowa domin gabatar da noma da zaran hatsi ya dawo gida zasu tattare nasu ya nasu su koma inda suka fito. A haka cikin wannan tunanin muka shiga Kano da yamma sakaliya muka sauka a tashar unguwa uku. Ni dai magriba na shigo layinmu anata kiraye_kirayen sallah na shiga da sallama da akwatina da ƴar tsarabar da bata taka kara ta karya ba a bugu aka dai ce motsi yafi laɓewa. Dake su Innah Mairamu sune ƴan farkon gida dasu na soma gaisawa. Sai kallona take yi tana dariya. Jin muryata yasa Qazzafi ya fito yana washe baki. "Ahh manya ashe zaki zo kune ƴan farkon zuwa kenan, ya mai gidan naki? Yana lafiya ba dole in zo ba auren manyan yayu guda" "Ah lallai Duwaf kenan muje in kai miki akwatin mana. Yanzunnan Baba Sojanmu ma ya dawo sunje aiki Gombe sun dawo" Tare muka wuce na dinga gaisuwa lungu_lungu har muka iso lungunmu a falo muka tadda Baba Sojanmu yana zaune da kakin sojoji ga tsarabar manshanu da nono harda fura yayo musu. "Hinduwa kece a tafe har kin zo bikin? " Na gurfana a gaban Baba Sojanmu muka zuba ma juna idanu muna murmushi da jin daɗin ganin juna. Nice mace ta farko a gidanmu a lokacin da take Aure a uwa duniya, sai daga baya Salamatu Mijinta ya samu aiki a ƙasar waje ya tafi da'ita. "Ya Gawatan ba tare kuka zo bane, ke kaɗai kaddai ya bari kika niƙo gari?" Ba tare muke ba ni kaɗai nazo Baba Sojanmu yanzu Qazzafi yake faɗamun dawowarka daga Gombe kenan ga man shanu na samu na wanke kaina" Dariya yayi mun kawai. Muka gaggaisa da su Innah Abida Innarmu tana madafi can na barota ita ke da turaka yau tanata hidimar tarbar miji. Ciki muka shiga ni da Qazzafi a ciki muka tarar da Yaya Soja da Akarami suna shirin tafiya sallah dan yanzu za'a shiga. Akwatina Qazzafi ya ajjiyemun suka rankaya har da Baba Sojanmu zuwa masallaci. Mayafina na cire na zauna a bakin gado ina sauke numfashi inajin wata iska na shigana ga hasken lantarki tauwar ya mamaye dukkan ɗakin. Waje yasha gyara an raba ma Innarmu ɗakinta ya zama ciki da falo ga fenti da kujera an saka mata a falon waje yayi kyau gaya. Ga atampopinan bandir bandir na anko innarmu ta jibgo dama ita ke kawo duk atampar ankon bikin gidan. Ina zaune tamkar wacce ta wanke makanta Innarmu ta shigo da nata kason tsarabar Baba Sojanmu. "Hinduwa ashe zai barki kizo da wuri haka? Hmmmm kije kiyo alwala kiyi sallah kici biski" Baki na washe mata na tashi na fita na ɗauro alwala na dawo na gabatar da Sallah ina kan sallaya Luba ta shigo da sallamarta. Ahh Luba duniya ashe har labarin zuwana ya shiga gidanku? " Dariya muka yi duka ta zauna kusa dani tace. "Kinsan dake ƙawancan Innah Mairamu ya sake ɗinkewa da Innarsu Sadiƙa harta shiga ta fesa musu zuwanki wai kin rame kin lalace ƙafafuwanki harda kaushi. Ni kuma dana shigo saina samu akasin hakan, gashi kinsha ƙunshi ƙafarki shar." Jikina na kalla shar dani atampa mai tsada ce a jikina sabuwa ban taɓa sakata ba, takalmina da jakata ma sababbine fil haka lafayar dana naɗo sau biyu kacal na taɓa sakawa shar dani ko na birni ba zasu nuna mun komai ba wata takwas a ƙauye baici ya ragargazamun yanayina ba. Sannan duk da bana ta'amali da wayayyu ina karance_karancen littattafan hausa wanda babu duniyar da basa leƙawa babu wata iriyar wayewa da basa kawo mana, tare suke tafiya da zamani kafaɗa da kafaɗa. Ikon Allah Innah Mairamu dai zafi take ji dan naƙi Qazzafi kuma ni bana nadamar kasancewata a ƙauye Luba wallahi Aure daɗine dashi babu abinda ya kaishi daɗi musamman in mace tayi dace da miji mai tausayi" Shewa Luba ta saka ta bani hannu muka tafa tabb. "Nima Aurenmu da Sanusi saura wata huɗu in faɗa miki har an fidda anko an shiga shirye_shirye ka'in da na'in" Ahh kice Allah yayi Sanusi ya doke duk manemanki? Gaskiya na taya ki murna sosai ashe dawowa biki nan da wata huɗu ya kamani Luba Allah dai ya nuna mana lokacin. Kuma a garin nasu zaku zauna ko nan Kano?" "To har yanzu bamu sani ba yana dai ta fafutukar hakan to iyayenshi sunfi son ya zauna acan amman duk inda ta faɗi sha ne Hinduwa, nima fa ƴar ƙunar baƙin waken ce" Muna cikin hirar mu su Akarami suka dawo sallah har da Qazzafi aka shigo duk muka gaggaisa suka tambayeni mai gidan nawa. Innarmu ce ta leƙo ta kirawo Luba ta shigo ma dasu Akarami abincinsu ta ɗakko mana namu muma muna ci anata hira duka Innarmu dai babu zama tana can kula da miji. Luba sai bayan isha ta tafi lokacin ƴan matan ɗakin namu sun dawo suna ganina suka soma murna nan aka shiga hirar yaushe gamo. Gida mai daɗi yau nayi baccin farin ciki a cikin ƴan uwana na wayi gari cikin gatana gaba da baya. Ƴar tsarabar albasa dana kawo Innarmu ta karkasa, ta haɗa da sabulun wanki mai ƙamshi dan dai a fita kunya. Ni na dinga shiga ina kaiwa ina gaisawa da iyayenmu maza sai in bada albasar da sabulun, haka har maƙotanmu kaf Innarmu tasa na rabar da albasar a hakanma bata isaba ko su Yaya Saratu bata ajjiyema ba. Muna kan suyar masa ni da Innarmu muna hira tana tambayata yanayin zaman namu da yanayin jikin nawa sai ga su Yaya Saratu tana murna yau a motarta da mijinta ya canja ya bar mata tsohuwar tazo. Haka muka ɗunguma muka fita sanya alkhairi dukka gidan, masu murna da masu baƙin ciki dai. Daga haka kullum sai sunzo gida mun shiga kasuwa siyayyar abubuwan biki ana saura kwana biyu biki gidan ya ɗinke tam da baƙin nesa harma dana kusan. Sun sha mamakin yadda na tawo da ankona, kuma na lale kuɗi na ba Innarmu kuɗin lesiri ta bani. washegari aka shiga biki. Mune har Kaduna kai lefe sabida matar Akarami ƴar Kaduna ce kasanxewar a Jaji yake aikinshi dalilin haɗuwar kenan itama wanta soja ne abokin Akaraminne. Sun mana tarba ta girma da ƙarya sosai. Muma mun nuna bajinta da harkar girma a lefe sosai sukai mana tukuice mai tsofar da saida mukai mamaki, na fahimci Kaduna suna da ƙarya da son girmama sha'ani dan biki sosai suka haɗa na tarbar lefen kuma basu bamu shinkafa ba sai kayan fulawa da soyayyun kaji da ruwan gora da abun sha na kwalba kiret biyu. Muka kamo hanya muna jinjina girma da karamcin mutan kaduna. Sai magriba muka dawo a lokacin za'a tafi kai kayan lefen Qazzafi dasu Babawon lungun Baba Lukumanu, ai sai juyawa muka yi aka sake wucewa kai lefennan na samari uku. Ragowar an riga an tafi kaiwa amman ba'a dawo ba. Bamu muka dawo ba sai wajen sha ɗayan dare muka dawo tulus ni dai ina kwanciya sai bacci. Washegari innarmu ta miƙo mun dubu talatin tace kasonane na kuɗaɗen salalar lefen da muka kakkai shine aka kididdiba aka raba kowa abinda ya samu kenan. Nasa hannu nayi godiya na adana abuna. Ranar ɗaurin Aure muka saka atampar da muka fitar a ɗakinmu ai kuwa mun ɗauki magana sai cece kuce akeyi a cikin gida, ko wanne ɗaki fa sunyi nasu amman namu shine mafi tsada kuma sun san ƙa'idane mu ƴan ɗakinmu komai muna nuna mu mune wannan a haka Innarmu ta ɗoramu akai, shi yasa duk abu in ba mai tsada bane bai fiye damunmu ba. Daga cikin iyaye aka wakilta suka wuce kaduna ɗaukar Amarya zuwa barikin sojoji dake cikin Jaji. Mu kuma muka wuce aka ɗakko matar Qazzafi zuwa gidan daya kama A Ɗorayi duk da ance inya tashi tafiya zai wuce da'itane. Masha Allah gidan na zaman mutum ɗayane, kuma iyayenta sun kwankwatsa mata kaya sosai babu laifi, wajajen goman dare Yaya Saratu ta tuƙomu muka wuce gida a motarta. Washegari kuma muka wuce wuni a barikin sojoji jaji gidan Yaya Akarami. Ranar muka saka leshinmu muka fito shar damu, itama danginta da ƙawayenta duk leshi suka daka masu tsada. An sha wuni anci an sha wajajen ukun yamman muka baro bariki zuwa gidan ƙawar Innah Yahanasu dake malali anan muka kwana washegari muka koma gidan Amarya da safe wajajen goman safe a lokacin Akarami ango yana gidan jiyan aka rakoshi bayan isha. Su Innah Yahanasu suka haɗasu sukai musu nasiha muka ga waje a tsanake sannan Akarami ya dafo mana shayi da wainar ƙwai muka sake karyawa,sannan fa muka ɗauki hanyar gida. Biki ya ƙare ƴan nesa sun kokkoma mu kuma muka ɗauki haramar tafiya Maiduguri. Ranar da zamu tafi Baba Sojanmu ya titsiyeni da batun komawa makarantata. Ta inda yake shiga wallahi ba tanan yake fita ba. Tsabaragen faɗa har hunhuna yake yi. Saida na sanar dashi ma ai na soma koyarwa a sakandare ne fa ya sassauta mun, na bashi haƙuri sosai kafin muka wuce. Nanma anyi biki sosai na manya an kashe nera satinmu biyu muka dawo kano na kuma yin sati guda ya kama sati huɗu kenan na hau haramar komawa gida kuma. Kafin na tafi saida muka sake gazaye gidan angwaye, na yi sabon kitso na sabunta ƙunshina dake lallaɓe nake yi ba mai fulawa ba. Innarmu ta harhaɗamun tsaraba sosai harda su garin tuwo da shinkafa, dasu man shanu da kifi bushasshe da mukai guzirinshi da yawa daga Maiduguri, banda wanda aka babbamu tsaraba, muma ko wacce ta cire kuɗinta ta siya, da komai na abinci saida ta ɗibamun tace nayi tsaraba dashi Baba Sojanmu yace aimun miya ya siyo kaji biyu Innarmu tayi mun miya nice harda kuma yin cincin na ƙara akan wanda na tattara na biki, ana gobe zan tafi na shiga kasuwa na siyo abubuwan da nake da buƙata, su Yaya Saratu yaji ta dakamun ta bani dubu goma, Yaya Zubaina kuma kuɗi ta bani da dambun nama tace naita ci a hanya, Jinjin kuɗi ta bani, Fulawa na siya na ba Innar su Luba taimun Gurasa mai gishiri da mai sikari ta kwano biyu dama sana'arta kenan Ranar talata sassafe nayi sallama da Kano muka ɗauki hanyar Bauchin yakubu. Da misalin ƙarfe shiddan yamma Acaɓa ya saukeni a ƙofar gida da akwatina da buhun kayan tsaraba rigi_rigi. Mijinyawa yana zaune a kututturen dake ƙofar gida yayi tagumi, duniya tayi mishi ɗaurin lemar minti, ganina ne yasa ya miƙe da sauri ya taya mai acaɓa suka sauke buhun kayan tsarabar garin tuwo kamar ya fashe a cikin buhun ma dan harya soma zuba. "Taimaka mu shigar ciki kawai bawan Allah" Cewar Mijinyawa, tare suka shiga ni kuma na biyosu da akwatina a baya da sallama a bakina na shigo cikin gidan. Duk suna tsakar gidan sai bina da ido suke. Ana washe mun baki na bogi. Ɗakin Nanno na wuce da sallamata su Inna Ladi suna zazzaune a tsakar gida. "Tica uwar karatu yanzu kike tafe kenan? Sunan da suka dawo ce mun kenan. Wallahi kuwa innah na sameku lafiya? " "Ahh lafiya lau ya kika baro angwaye da iyayen naki? " Duk suna lafiya sunce a gaisheku ma" Muka gama gaisawa nasa ƙafa da sallama na shiga ɗakin Nanno Uwatale tana bakin gado a zaune tana ba jaririyarta nono sunyi kyau uwatale tayi ƙiba sosai. Kallonta nayi da jaririyar suka bani sha'awa sosai ko ni sai yaushe zanga nawa ɗan ko ƴar oho wata Tara da Aure. Nanno na zaune tana kaɗin lagwani Uwatale mai jego masha Allah mai muka samu ne kawota" "Baki ga Mama take sha ba ai kya bari inta ƙoshi sai ki karɓeta" Nanno ta tsinkani ba shiri naji wani abu ya tsargamun. Zama nayi muka gaisa da Nanno uwatale ko kallona bata yi ba gudun kar in shareta ace ina baƙin ciki shi yasa nace. Uwatale ina wuni kin sauka lafiya? " Kunga yadda tayi da baki kuwa tace. "Lafiya ya kika baro ƴan gidanku? " Lafiya sunce a gaisheku. Nanno bari in shiga in huta" Na miƙe nayi tafiyata, ko ƴar ban tsaya ɗauka ba. Tozali da nayi da mijinyawa a tsakar gida ya ciro kayan buhun ya adanasu a ɗakin shirgi yana juye garin tuwon daya zube a buhu a cikin bawo, ya sanyaya ruhina. Wani kallo yayi mun mai fassarori da dama. Murmushi na sakar mishi na ƙarasa kusa dashi ya damƙe hannuna muka lumshe idanu. "Tutar so ashe zaki iya irin wannan daɗewar ba tare da kin duba wanne hali ni zan shiga ba? Sati huɗu fa" Sai kunya ta kamani Ai kuwa da daddare na yadda mijinyawa yayi kewata sosai sau uku ya neme ni duk da ba wannan bane na farko ba amman da wannan daren ya bambanta sosai. Washegari dashi muka kunce tsaraba ina mishi bayani tsarabar yana taya ni muna juye kayan hatsin a robobin da muke adana kayan abinci. Tare muka ƙulla cincin da gurasa muka bama matan gida da tsirarin maƙota. Sai da muka je gaishe da Nanno na samu aka bani Zainab na ɗauketa nayi shiru ina kallonta amman a ƙasan zuchiyata inajin ni sai yaushe zan rungumi nawa ɗan ko ƴar, yaushe ma ciki zai shiga cikin marata ya kwanta, ko dai juyar ce da gaske? Mijinyawane ya katsemun tunanin nawa ta hanyar karɓar Zainab ya riƙeta yana jijjigata ni kuma sai kallonsu nake yi ina jin sha'awarsu. Sai abun ya tasirantu sosai a zuchiyata. Wasa_wasa sai rashin haihuwa ya soma damuna ainun kullum cikin tunani nake. Sai ciwona ya soma takuramun gashi a lokacin kusan da koyarwar da nake yi muka dogara nike yin komai a gidan har murjin taliyar hausa ake kawo mun na kuɗi inayi ina ɗan samun kuɗin shiga. Mijinyawa ba wai zama yayi ba dole ya haƙuri da sana'ar shayi ya shiga bin su Qasimu, dubu Ashirin na kuma dunƙula na bashi, yana duk abinda ya samu wahala dai ana shanta babu wadataccen kuɗi sai yayi wata guda a wani ƙauyen ko cikin Bauchi inya tashi dawowa baya dawowa da wani abu mai yawa kuɗin da yake dawo dashi baya isata inci abinci na wata in an haɗa harda kuɗin albashina to a ciki nake siyan itace, da kayan miya, sabulun wanka sabulun wanki, harda omo nayi wanka da tafiya tayi tafiya. Bikin luba ma naso zuwa Allah baiyi ba babu kuɗi a lokacin dole na haƙura. Bani na sake zuwa gida ba saida na kuma shekara guda kafin na sake komawa ganin gida. A lokacin naje na tarar da su Yaya Saratu duk ƴan gidanmu babu wanda bai haihu ba harda matan su Qazzafi. Can gida jama'are ma dukkan facalolina sun haihu har Uwatale ma ta sake haihuwar ɗiyarta mace. A zuwana gida na biyu hatta su Innah mairamu saida suka yar mun da magana, kuma akan matsalarnan har asibitin cikin Bauchi saida mijinyawa ya ɗaukeni ya kaini. Amman babu ta inda aka ga wata matsala a jikina ko jikinshi sai dai likita ya ɗauramu akan magani da zasu taimaka harna Hausa dana matsa mijinyawa ya barni ni da Baraka muka je muka karɓo na dinga sha amman shiru kake ji. Baba sojanmu ma saida ya tambayi Innarmu akan ko naje asibiti akan matsalar haihuwan kuwa? Lokacin kwanana biyu da zuwa gida. Naje asibitin Bauchi Baba Sojanmu" "Kuma to me suka ce ciwon me yake damunki akace, ko daga shine matsalar? " A'a dukanmu lafiya akace har magunguna aka ɗauramu akai amman babu canji nasha na hausa ma dukka dai shiru" Na ƙarashe maganar ina haɗiyar zuchiya damma ni ba mai saurin kuka bace a duk wannan son haihuwar da gorance gorancen da akeyi mun a gaban idona da bayan idona ma bai taɓa sani kuka ba sai dai ya sakani a damuwa kawai shima da mijinyawa ya rarrasheni shikenan zan mance da komai." Harna gama ganin gida zuchiyata sam babu daɗi. Haka na dawo jama'are abubuwa suka sake ɗaure mana sosai. BAYAN WASU LOKUTA:. Ina zaune a gaban mirhu girki nake yi amman damuwowine masu yawa suke dukan zuchiyata. Gorin rashin samun haihuwa ciwone dake cinye rayuwar duk macen da ake gorantama, zafin gorin rashin haihuwa ya shige duk tunanin mai karatu, macen data taɓa saka ƙafa a takalminane kaɗai zata gane abinda nake nufi. Shekara biyar da aure haihuwa ta ƙi samuwa har ankai Nanno ta bama mijinyawa dama ta ƙarshe akan ina cika shekara shida ban haihu ba, ko ban samu ciki ba babu shakka Mijinyawa zai sallameni yayi wani Auren dan bata ga amfanin ya riƙe igigoyin aurenmu ba. To a cikin wannan ƙadamin muke kuma watanni baifi uku zuwa huɗu ya rage mana ba wa'adin ya cika. Gashi shiru ba wani motsi duk inda mijinyawa yaji labarin masu maganin haihuwa baya ƙasa a guiwa zaije ya karɓo mana muyi ta sha amman shiru kuke ji. Ƙwallo ce aka jefo mun ta bige mun miyar da yanzunnan na gama ƙaɗawa shikenan abinda muke dashi nayi mana tuwo da miyar kuma ta zube tas. Zainab ce da Tasi'u yaron Rakiya suka shigo a guje ashe su suka jefo ƙwallo. Zabori na zare na ɗan cauɗe hannayensu bafa mai zafi ba suka fita suna kuka. Ni kuma ina takaicin miyar da suka zubarmun domin nayi imanin yau sai dai mu dama tuwonnam mu zuba sukari mu sha itama sikarin kaɗan garemu. Sai ga Rakiya da Uwatale sun shigo suna zage zage. "Kece kika dokar mana yara sabida baki san zafin yadda ake naƙuda ba ko, to me suka yi miki ma?" Murmushi nayi nace. Allah sarki uwatale gyara kayanka baya zama sauke mu raba. Sannan ba rawa kika yi aka baki yaran ba, kuma kinsan dai ba'a gidanku ake rabawa ba balle kice baza ku bani ba. Ɓarna sukaimun shi yasa na dokesu, kuma ko yanzu suka sake saina dake su, ku kanku baku fi ƙarfin dukan ba" Buɗar bakin Rakiya tace. "Sabida mugunta dai ko da yake makawo ma cewa yayi ido da wari sabida yasan ba samu zai yi ba. Ni dai in kuna ƴar tsamarku da Uwatale ki dena dukanmun yarona wallahi in Babanshi yaji labari bazai yadda ba" Saida suka gama gasa mun magana kana suka fice fu. Wallahi saida nayi awa biyu cur a tsaye jikina babu inda baya ɓari maganganun su uwatale sai shigata kawai yakeyi zufa ce sharkab a jikina ko da mijinyawa ya juyo dani yaga ina zubar da zufa har fa ɗiga nake yi ba ƙaramin damuwa ya shiga ba domin zan iya cewa wannan shine karonshi na farko a zamanmu da yaganni a cikin irin wannan yanayin, kakkarwa sosai nake yi jikina na sandarewa. DAWOWA LABARI: HINDU: Murmushi nayi mai ciwo ina hango lokacin tamkar yanzu abun yake faruwa dani. Mijinyawa ya cutar dani cutar da bazan taɓa yafe mishi ba, kuma ni dashi har gaba da abada. Ya zalunci rayuwata. Yasa ƙafa yayi fatali da sadsukarwata, da soyayya dana nuna mishi mara algus a cikinta. Da duk faɗi tashin da muka tsinci kanmu a ciki, muka tsallake. Zama na gyara dan yanzune zamu shiga asalin labarin ba'ai komai ba tukunna. KOMAWA LABARI:. "Hindu lafiya kike kakkarwa da zufa irin haka Hinduna menene abinda yake damunki dan Allah" Nuni nayi mishi da miyar data kwarare kawai saina wuce ciki na zauna a kujera kaina a sama ina ƙoƙarin mayar da hawayen da suke so su zubo mun. Tun jiya nake ta saƙa wani abu a raina amman tabbas nasan abune marar yiyuwa zuchiyata ce dai kawai take yaudarata akai. Amman abinda ya faru yanzu ya sake assasamun tunanin nawa. Ga firejar da Baba Sojanmu yake ɗaura mana akan batun karatu abun yayi yawa. Shigowa mijinyawa yayi ya zauna kusa dani yasa hannu ya riƙo wuyana muka fuskanci juna. "Sabida miyar ta zube ne kika shiga wannan halin? Ko kusa wannan bazai zama dalili ba, ban taɓa ganinki a haka ba, tun kafin zuchiyata ta buga ki faɗamun abinda yake damunki Tutar so. Wallahi zan iya fito na fito da koma waye ya taɓo mun ke" Mrs Bukhari *KADA KU MANCE WANNAN LABARIN LABARINE WANDA YA FARU A GASKE. BABU RIBAR DA ZANCI INNA FAƊA MUKU ABINDA BA HAKA BANE IN CE DAKU HAKANE. BA YARDAR KOWA NAKE NEMA BA, IN DAI ALLAH YA YARDA DANI SHIKENAN*TSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA GOMA SHA TARA: *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. Labari na bashi akan abinda ya faru. Jikinshi har rawa yake yi naji ya fita fuu ina kiranshi amman ina baiko ji ba. Sai jiyoshi nayi a tsakar gida yana faɗa akan bazai lamunci taka mishi mata da akeyi ba ya gaji ya kuma isa. Da sauri na fito gidan harya ɗinke da jama'ar gidan ƙarason nayi nace. Babu komai kayi haƙuri wata rana zai zama labari" "Labari in kika haihu ba, baki da aiki sai zaunar da miji kina kwatanta kishi yadda zai ƙyamaci danginshi, so kike a zuba miki idanu ki illata musu yara sabida baki san zafinsu ba ko?" Cewar Yaya Jamila tana yi tana bubbuga cinyoyinta da tafukan hannayenta du biyun. "Ke Yaya jamila nace ya isheki ya isheki, haka wanne irin jahilci ke sa kuke mana gorin haihuwane. Shin kuna ganin ku Allah ya fi sonku ne daya baku haihuwar? Wallahi ba haka bane sau nawa muke haifar yara su zame mana masifa ko silar zubar hawayenmu. Hindu dai matatace, zamana take yi, na rantse bazan lamunci cin fuska da cin mutuncinta ba akan abinda bata da ikon bama kanta. Shin in matsalar rashin haihuwar daga nine fa, me yasa ba'a ma maza gorin haihuwa dole sai mata, shin mata na iya ma kansu ciki ne koko yaya? " Murmushi nayi kawai, nace. A tunanin ƙauyawan gidadawan danginka ni zan ba kaina haihuwa ai. Ke kuma Jamila kul ki shiga taitayinki ki kuka da kanki, wallahi zan miki abinda zaki jima kina kwance kina jinyar da babu wanda zai iya baki magani." Na juya na shige ɓarayina. Na bunka hayaƙina na shafe jikina da maganina dan naji halamun mutanen a kusa kusa ni kuma yau nake son amayar ma da mijinyawa buƙatata ko Allah zaisa na dace ya amince mun duk da ni akan karan kankin kaina nasan zaiyi wuya satar ɗan mace mai ido ɗaya. Ashe wannan rikici bana ƙare bane dan saida takai mijinyawa Yaya Jamila ta mareshi ya rama, ya bata lafiyayyun mari biyu. To kunsan a ƙauye babban wa namiji, ko babbar Yaya mace, jinsu suke yi tamkar su suka tsugunna suka haifi ƙannensu, fawar da suke da'ita yawa gareta shi yasa ake samun matsaltsalu dasu, saɓama umarninsu ma tamkar zunubi ne. Dambe ne ya kaure a tsakankanin Mijinyawa da gambonsu ina zaune naji hayaniya gida ya cika fam amman na kasa fita in tashi ma na kasa ni bansan a wanne halin nake ba har sai washegari shima da rana. Anyi ɗauki babu daɗi sosai saida na dawo hayyacina mijinyawa yake labarta mun abinda yake faruwa kuma Nanno ta umarceshi da ya ƙara Aure sannan wa'adin data ɗaukarmun yana cika muddin ban samu ciki ba zata sa ya sakeni in tafi dan yanzu haka ta bashi umarnin ya turani gida bata son ganina har sai sanda ta neme ni, tayi kuka harda tumami akan dole sai na tafi gida bata ƙaunar ganina, nazo ni zan tarwatsa mata gida" Amman kasan a kan sharaɗin da iyayena suka gindaya maka babu batun saki, bare yaji ko, kuma a gabanka suka ce muddin hakan ta faru to dole sai dai in nemi inda zani ko? To bari kaji in faɗa maka ka sake ni kawai, nagaji da waɗannan iskancin da ake yi mun a cikin gidannan Mijinyawa ta faru ta ƙare kaje kayi aurenka" Na yi maganar ina ƙanƙance idanu na ɓacin rai. Kuma ɗaurawa nayi da cewa. Nifa mijinyawa wannan jafa'in yafa isheni ka sakeni kawai kaje ka auri wacce zaku haihu kuyi rayuwarku nima inje in auri miji daidai ni na koma makaranta na cika gurina dana iyayena. Dan wallahi in dai kai nake Aure na tsallake kowa na zaɓeka to fa daga ranar da ka yadda zaka ƙara Aure, daga ranar ka rasani har gaba da abada." Zafi kan zafi na haɗa ma Mijinyawa duk inda ya buga babu daɗi dan nima na kafe akan mu rabu na gaji bazan je gida ba sai da takaddata na kuma kafe akan matsayata yasan bana juyuwa ba'a canja mun ra'ayina. Wannan shine karon farko dana taɓa botsare mishi na fitittike na tashi hankalinshi, na saka shi a uku. Saida aka kwana bakwai cur ana abu ɗaya, Nanno na cewa ya sallameni in tafi, ni kuma ina cewa a bani takaddata, har umarni ta bashi sau uku akan ya bani takaddata in tafi tunda shima ba ganin mutumcinshi nake yi ba. Ni kuwa ko gezau na ƙeƙashe ƙasa nace. Daga ranar daya tafa mun takaddata, daga ranar Nanno kin bar ganina har gaba da abada. Sai yaje ya auri mata ɗari ma in ana Aura" Inayi ina zazzare idanu. Duk da a tsorace take saida ta nuna kanta da ɗan yatsa tace. "Ni kike faɗama wannan maganar? " E" Itace kalmar dana faɗa ba ko ɗar. "Hindu kiyi shiru" Ai saina miƙe da a zaune nake fa, na cire zanina ya faɗi daga ni sai gwari na tsuma nace. Bazan yi shirun ba, nace bazan yi shirun ba Magawata" Sun ɗauka makaraine, sum_sum_sum Nanno ta fita, ni kuma ras nake turace kawai ta kaini bango. Matsowa yayi kusa dani ya riƙe mun hannu, na saka dukka hannayena biyu na tureshi da dukkan ƙarfina ya faɗi yib a kan kujera. "Subhanallahi" Ya miƙe da sauri, na kuma tureshi ya koma, na tsaya a kanshi ina huci tamkar kumurci. Karatun Qur'ani kawai yake ta rerawa yana tofeni da yawu. Wallahi ranar yaga abu sosai. Sai da Kawu yazo yaima tubkar hanci akayi sulhu tsakanin Yaya Jamila da mijinyawa ya bata haƙuri itama ta bashi, ya kuma tursasa Nanno akan ta janye batun in tafi gida babu ruwanta. Ina zaune a kan tabarma ina tuno gida da ƴan uwana da yadda rayuwarsu take ta ci gaba suke ta samun ɗaukaka, ga yaransu a gefensu. Ni inna tuno nawa rayuwar Auren da soyayyar miji kaɗai na tsira, soyayya bana jin zata iya riƙeni a yanayin da idanuna suka gama rufewa ɗa ko ƴa kawai nake da buƙata na gaji da gori har kunyar haɗuwa da dangina nake yi ko wani sha'ani ya kaini gida, dan kafatanin ƴan gidanmu babu wanda baimun gorin haihuwa ba. Damma a tsaye nake, duk wanda yai mun gori na dena ƙyalewa saina faɗama mutuwa, tunda kai cuta ka faɗamun wallahi. Gwauron numfashi na ja tare da amsa sallamar mijinyawa wanda shigowarshi kenan fishi muke da juna magana wannan bama yi face gaisuwa yau kwana bakwai Kenan kuma wannan shine karo na farko a rayuwarmu da muka yi faɗan da muka kasa shirya kanmu kafin gari ya waye. Duk da mijinyawa ya buƙaci haka nina matsa lamba badan bana gasuwa da hakan ba sai dan dauriya da jumurin ɓoye damuwa dana fishi. Wallahi a cikin kwana bakwai saida yayi ramar da duk wanda ya ganshi yasan ya rame. Miƙewa nayi zan tafi bayan na ce dashi. Ga abincinka nan sai da safe" Na juya zan shiga ya riƙo hannuna ba shiri na lumshe idanuna ina ma mijinyawa wani irin so marar abun misali, ina tsananin kishinshi fiye da tunanin mai karatu, batun matar da aka bashi yafi komai yi mun ciwo sosai kuma bana ji a jikina da zuchiyata zan iya raba mijinyawa da wata macen na gwammaci ya rabu dani matsawar bazai iya rayuwa dani ni kaɗai ba, inanan daram akan matsayata. Balle wannan auren da akeso a yishi a matsayin hujjar na kasa haihuwa shine akaso a auro mishi wata macen a bashi ita dan tazo ta sama mishi yara ni in zauna a matsayin me to? Duk wuya da bijirewar da nayi sai in tashi a tutar babu a gidan mijinyawan dana ɗaukeshi na shure ɗan uwana Qazzafi. Wanda a yanzu ya sake samun matsayi, ya sai mota mai kyau ya samu sukuni da nutsuwa sosai, ga matarshi da yaranshi biyu dukka maza, kuma har gobe sona na yawo a jikinshi. "Tutar so kwana bakwai cur kina azabtar dani, tako ta ina babu daɗi shin ba zaki ma mijinyawanki mai yawan ƙaunarki afuwa ba. Tutar so shin ta ina nake da lefin da harna cancanci kiyi watsin ruwan tsarki dani? shin bakya ganin ƙoƙarina da jajircewata akan lamarin aurenmu? Fishi da gaba dani shine sakamakon da zan samu a wajenki kenan? " Sai yayi shiru ni kuma ban juyo ba ina dai ta nazarin maganganunshi. Tabbas baida wani laifi tunda ba ƙashin kanshi bane yace zaiyi aure sabida bana haihuwa ba. Amman indai mace aka kawo mishi a matsayin mata watan watarana dole sai yayi ruf da ciki a kanta babu mamaki ma a ranar da aka kawota. Shikenan in suka zama ɗaya ta haifa mishi yara to mecece makomata, matsayina kuma na menene a gidan? " A hankali nace. Idan matar da za'a Aura ma ta shigo cikin gidan ta sama muku abinda na kasa sama muku kai da danginka, to ni menene makomata ko amfanin zamana da kai. Ƴar reno zan zame ma matarka, ko ƴar aikinta zan zamane, ko kuma a matsayin me zan zauna? Mijinyawa bazan rufe maka ba daga ranar da aka ɗaura aurenka da wata mace bisa dalilin danginka na ganin gazawata tabbas kafin Nanno tasa ka sakeni a wulaƙantani ni da kaina zan nemi sakin kuma dole ka sakeni wallahil azeem ko da a gaban kuliyane. Hannuna na fisge na shiga ciki na kwanta a gadon rigingine inata lissafin dokin rano. A haka ya shigo ya hauro gadon shima ya kwanta rigingine yace. "Banyi tunanin akwai ranar da zata zo ke da kanki ki dinga furta mana kalmar rabuwa ba. Tutar so kamar kina mance da yadda akayi aurenmu da alƙawarin dana ɗaukarma iyayenki. Babu abinda na mance Tutar so, sannan bazan bari wani nawa ya wulaƙantaki ba, na fahimci bakya ganin duk ƙoƙarin da nake yi. Hindu irin son da nake miki ruwa da iska basu isa sun rabamu ba, ko su Nanno sai dai suyi haƙuri kin zame musu tsuron tsirin tsandauri babu yadda za'ayi dake. Bazan taɓa auren Kandala da suke son in aura tazo ta haihu mun ba. Ba ita kaɗai ba, babu wata mace a duniya da zata haɗa miji dake, mijinyawa naki ne, wannan shine kaɗai sakamakon wannan sadaukarwa taki gareni, matan duniya a matsayin maza jinsina nake kallonsu, kece kaɗai mace tilo a idanuna, zuchiyata, gidana, rayuwata. Yaranki nake so, in kuma Allah ya ƙaddara ba zamu ga ƙwanmu ba shikenan ba dole bane haihuwa ba, auren kanshi ba dole matsawar mutum yasan zai iya riƙe kanshi wallahi Hindu ina girmamaki ina girmama lamarinki. Tunda mukai aure komai nawa ya ƙare sau uku kina bani jari yana lalacewa har gobe a ƙarƙashin inuwarki nake. Ni har kunya nake ji irin yadda dangina suka ɗaukeki, da irin nuna gazawata ta kasa riƙeki in kula da komanki, kin tattarw komai na ɗauke dukkan ɗawainiyar gidanmu. Hindu in na samu kuɗi zaki ji daɗi sosai gabaki ɗaya kuɗin zan dinga jibge miki kiyi yadda kike so da shi ni kaina sai dai in karɓi na kashewa a wajenki" Mirginowa nayi na rufe bakinshi da nawa tuni yai ma laɓɓana riƙon alawar yara. A wannan daren mun wankema junanmu duk wani tsatsa da dattin dake zukatanmu. Take naji dukkan wuya da tsangwama ina tare da mijinyawa babu gudu babu ja da baya. Abinda na ƙunshe a raina kuma na ɗan ƙara lokaci kafin in fitar mishi dashi zan sake gayama Allah tukunna, dan lamarin da girma yake ni kaina ina jinjina lamarin. Washegari sassafe na gama komai har girkin rana na gama mana kasancewar ranar monday ne. Muna gama karyawa muka fito tare zuwa gaishe da Nanno. Muka shiga taga muna fara'a muna cikin godiyar Allah. Yana daga cikin abinda ke damun dangin Mijinyawa su kullum burinsu su ganni a ƙasa, ni kuma duk girman abinda ya tunkaroni sai in nuna musu ko oho na gwammaci in kwana a cikin tunani. "Kaje zance wajen Kandala kuwa? Kasan fa wata huɗu kaɗai kuke dashi da zaran watannin sun cika to babu makawa za'ayi auren ita kuma zaku rabu baku dai mance ba ko? " Bamu manta ba Nanno muna nan muna lissafawa duk abinda Allah yayi mai kyau ne rayuwa shirin Allah ne" Na ƙarashe ina murmushi tamkar wacce akaima bushara da gidan Aljannah. Ita na bari da haɗe rai tamkar hadari. Nan mukai mata sallama muka fice. Muna tafe muna tattauna matsalolinmu har muka iso bakin makaranta. To zan shiga kaga yara suna asambili sai kazo ɗaukata ko? " "To shikenan Allah ya amintar mun dake Tutar so sai na zo ƙarfe ɗaya a nan zatai mun kamar yadda aka saba." Da haka mukai sallama na shiga ciki na tsaya a saman baranda kamar sauran malaman sai da aka gama asambili malama Tani take shaidamun shugaban makaranta firinsifal yana nemana a ofishinshi. A hankali nake tafiya har zuwa ofishin firinsifal na shiga da sallamata ya nuna mun wajen zama na zauna. "Malama Hindu abinda yasa na kirawoki shine akwai malamin mu daya samu sauyin wajen aiki yana ɗaukar ƴan sakandare aji biyu. A bisa ƙoƙarin ki da gogewarki wajen iya turanci dama koyarwar shine muka ga ke kika fi cancanta ki maye wannan gurbin na malamin daya tafi, akwai wata malama sai mu kirata ta maye naki gurbin kinga za'a samu ƙarin albashi kuma munsam zaki iya" Nayi farin ciki sosai take na amince da tayin da akayi mun harma na soma ɗaukar ƴan aji biyu a ranar kuma Alhamdullillahi karatu ya tafi yadda ake so kuma na samu haɗin kan yaran gaya. Saida muka fito tara ne muna zaune a rumfar makaranta muna hirarmu da malama Tani, yara ƴan makaranta na ta harkokinsu a haka har muka koma aji. Ana tashi a makaranta na hango mijinyawa a zaune tare da maigadi suna zantawa harna iso wajen, ya karɓe jakata dake cike da littattafan ƴan makaranta muka wuce. Tun a hanya na faɗa mishi alkhairin daya samemu mukaita murna da jin daɗi. Sallar azahar muka yi nan muka zauna zaman cin abinci shinkafa ce da wake jalof harda bushasshen kifi. "Shinkafarnan tayi daɗi wallahi zata kaimu har dare ne mu ci ba sai kinyi girkin dare ba ki huta kema? " Dariya nayi mishi nace. Ai iyakar abincin da muke dashi kenan na girka har safe ma zamu samu amman bamu da ƙwayar hatsi a Kitchen komai yayi ƙarƙaf" Sai muka yi shiru sabida wata dai yau yayi rabi, akwai sauran kwanaki goma sha kafin ayi albashi. Mijinyawa ya kamata mu sake tsara yadda zamu dinga cefanenmu yadda kuɗin da muke samu zai dinga isarmu har zuwa wani watan. Wahalar tana yawa ace komai ya ƙare a rabin wata, yanzu shikenan mun shiga jula jula kenan fa. Kai ya kake ganin zamu yi?" "To Tutar so ke a tunaninki me kike ganin za'ayi kece mace kuma ke kike girkinnan ko ba gaskiya ba, ya za'ayi sai yadda kika ce" Murmushi kawai nayi mishi nace. Ina ganin garin tuwo da fulawa kaɗai zamu iya siya a kayan hatsi kenan Ragowar kuɗin sai mu sai bushasshen kayan miya da su maggi da sauran abinda ya dace. Tuwo da daddare sai muci ɗumamenshi da safe, da rana muci taliyar murji ko da mai da yaji ko jalof, sabida mu guje ma yinwa da ƙarewar abinci zuwa lokacin da Allah zai yanke mana" A haka muka tsayar da matsaya a daddafe muka ƙarashe ƙarshen wata talata kuwa muka wuce kasuwar Galdimari muka siyo duk abinda ya dace mijinyawa da daddare ya gama murje mana taliyarnan tsab washegari da tasha na zuba a robar da muke adana kayan hatsinmu shine rayuwar tayi mana sauƙi abinci yake kaimu wata cur. Uwatale kuwa kullum da nama ko kifi take miyarta sabida Allah ya buɗa ma mijinyawa Babba Kano yake aiki ya samu Ubanggida a kasuwa kuma yana samun alkhairi harma muke jin raɗe_raɗin yana gini acan yana so nan da wani lokacin in ya gama zai ɗauke iyalanshi zuwa Kano sabida yana so su samu ilimi mai zurfi sosai. Duk sanda zai zo yana tawowa da kayayyakin alatu amman bamu fiye samu ba kasancewar Nanno ke raba komai ba ko wanne zuwa bane ma in yayi muke samun tsarabarshi ba. Ya na dai bama ɗan uwan nashi kuɗi to wannan dai muna samu. Uwatale ta sake yin kyau ta samu sukuni har kayan ɗakinta mijinyawa babba ya sake mata, cikine ƙaramima a jikinta sai feleƙe take yi. Damma Allah yasa ina da tattalin sutura da tuni suturuna sun lalace. Amman sunanan gadagau ko yau na saka wasu kayan kamar sababbi haka suke zama amfanin siyan kaya masu tsada yana da yawan gaske. Takalma kaɗai nake fatararsu guda biyu kaɗai gareni masu kyau na fita unguwa haka na zuwa makaranta guda biyu, suma inata manejinsu tunda mukai aure in banda ankon gidanmu da nayi ban sake yin ɗinki ba, ta kai ake bata kaya ba. Gaga_gaga al'amura suka ci gaba da shurawa wasa_wasa lokaci har ya kusan motsowa saura wata ɗaya tak wa'adin da Nanno ta gindaya mana ya cika. Mijinyawa duk ya rame ya fice a hayyacinshi ni dai tuni na sadudu na zubama sarautar Allah idanu duk abinda yayi dani mai kyau ne babu tsimi bare wata dabara. Kuma na roƙeshi ya zaɓamun abinda yake mafi alkhairi Da daddare bayan mun gama cin tuwo nace. Mijinyawa kusan watanni uku kenan inason mu tattauna wata muhimmiyar magana amman nauyinta ne yake hanani furtawa sai nayi kamar na haƙura sai in fasa." Hannayena ya riƙe yana matsawa yana kallon idanuna, nima idanunshi nake kallo tunda nake ban taɓa ganin namijin da kwalli ke zama a idanunshi ya zamemai ado kamar mijinyawa ba. "Me kike son faɗa mun har tsawon wata uku Tutar so? To koma menene ki faɗa zanyi miki in dai zai sama miki nutsuwa da farin ciki" Shiru nayi kaina na kallon kafet ɗin ɗakin namu. So nake mu ɗauko yaro a gidan renon yara mu riƙe a matsayin nina haifa mijinyawa ta wannan ne kaɗai zamu tsallake sharaɗin Nanno kuma nagaji da gorinnan da akeyi mun mijinyawa" Shiru muka yi kusan na minti talatin yayi tsam yana kallona yama rasa me zaice dani. Miƙewa yayi ya fita tsakar gida. Sai gaji da kasko cike da rushi ya ajjiye a gabana ya bankamun hayaƙin makarai tare da kama kaina yana ta mun tofi. Sama da ƙasa saina kasa cewa uffan sai hawaye ne suka cika tab a guraben idanuna, amman basu zubo ba. Lokaci guda fuskata ta kumbura tayi suntum. "Dama nasan kune kuka furta wannan maganar ba dai Hindu na ba. Na roƙeku ku barmu muji da abinda ke damunmu dan Allah" Miƙewa tsaye yayi ya miƙar dani ya kaini gado ya kwantar ya kunna mun kaset na karatun Qur'ani a rediyo mai manyan batura tiger. Idanuna na lumshe ina kukan zuchi zuchiyata tamkar zata tarwatse. Shikenan na rasa mijinyawa kenan sai dai ya zama tarihi a rayuwata kenan?" Haka naita tubkewa yana warwarewa da kanshi. Ban sake yima mijinyawa maganar ba sai ana jibi wa'adi ya cika na sake maimaita mishi maganar. "Wai dama da gaske Hindu kece da kanki kika yi wannan maganar ba makaranki ba? Ni na ɗauka mai hankali ba zaiyi irin wannan maganar ba. Taya za'ayi mu mayar da ɗa da ba namu ba ya zama namu kin taɓa ganin anyi hakane? Hindu kada mu yaudari kanmu dan Allah" To shikenan babu damuwa mijinyawa Allah yasa rabuwar tamu shine mafi a'ala" Na juya na koma ɗaki makarantar da banje ba kenan. Ko da ya dawo da yamma ya samu duk na harhaɗe kayayyakin Kitchen ɗina na ɗuresu a manyan buhunhuna suturuna duk nayi wanki sun bushe na jejjerasu a akwati waɗanda nake ji zan kyautar duk na ware su a gefe guda. Wallahi a daren ko abinci bamu nema ba kusan kwana muka yi akan sallaya, haka washegari ma bansan abinda ke cikin ran mijinyawa ba bai bani dama mun yi magana ko da ta ban kwana bace yana riƙe da carbi Yaya Jamila ta shigo babu ko sallama sassafe fa. "Kazo kai da Hindu inji Nanno. Yau wa'adi ya cika alƙawari shima zai cika duk wani aure ribarshi haihuwa ne ba soyayya ba" Juyawa tayi ta fita fuskarta cike da farin ciki da jin daɗi. Murmushi kawai nayi na zari mayafina na dubi mijinyawa nace. Ya kamata muje ko sabida in samu in tafi da wuri kar dare yayi mun a hanya" Idanunshi masu kyau da tozali ya zuba mun sun yo jawur suna ƙoƙarin zubar da ruwan hawaye. "Wai ke ashe da gaske kin shirya rabuwa dani Hindu alƙawarin da mukai ma juna fa? " Alƙawari? Ai ba faɗar Allah bace faɗarmu ce. Muje dan Allah ayi abinda za'ayi tun kafin ka tunzurani" Shiru yayi yana salati zuchiyata wani irin rawa take yi to ya zanyi tunda dai da Allah suke faɗansu ba da ni ba. Sanin kowa ne bazan iya bama kaina haihuwa ba. Allah shike da tararrafin komai da isa da kuma buwayarsa. Fitowa muka yi zuwa tsakar gidan matan gida anata ƙus_ƙus na munafurci har muka shiga ɗakin Nanno. Na zaci taro zan gani sai naga su su ukune kaɗai a ɗakin Nanno, Yaya Jamila, Yaya Zakiya sai kuma mu da muka shigo muka samu waje a gefe guda muka zauna. Sai carbi mijinyawa yake ta ja. Ni ko ina kallon kowa hankalina kwance, ai wanda ya dogara ga Allah ya gagara. HINDU: DAWOWA LABARI:. Murmushi nayi mai ciwon gaske wannan ranar tana daga cikin ranakun da suke da tarihi baƙi wanda bazan iya mancewa ba abadan. Bari in tsayar da labarin a nan, amman zamu ci gaba, an sha gwagwarmaya mai tarin yawa sosai. A iyakar haka kaɗai zaku iya hanke mana hukunci ni da mijnyawa. Ni dai na riga da na rufe shafinshi a rayuwata. Inna juya ma wuri baya wallahi ko sama da ƙasa zata haɗe bana waige. Miƙewa nayi na faɗa banɗaki na cire kayana na saki ruwan ɗumi a jikina idanuna a lumshe ina sake kallon wannan ranar kamar yau abun ya faru. Gashi dai daga ƙarshen ƙarshe mai afkuwa ta afku na bar mijinyawa har gaba da abada yaje ya rayu da Asama'u ta taci gaba da haihuwa mishi tunda na samu haihuwar har yara biyun amman ban tsira ba. A yanzu bana tunanin akwai abinda zai dameni, ko na misƙala zarratin. Gaga_gaga_gaga_gaga Haka rayuwa a landan taci gaba da tafiya yadda ya kamata. Gurbin karatun mastas dana samu ya sake sawa zaman ƙasar yayi mun daɗi sosai. Sosai na mayar da hankalina haiƙan akan ci gaban rayuwata, na rufe komai da komai na ɗauki lokacina na rabashi gida hudu gashi ɗaya na ibadar Allah da rayuwar Ƴaƴana, kashi na biyu naba aiki na da dangina, kashi na uku na ba karatuna da ci gaban rayuwata, burina in shahara in zama mace mai arziki, da yalwar ilimi, kashi na huɗun shine na ba rubuce_ rubucen wayar dakai da nake yi dan a yanzu nafi samun damar rubuce_ rubucen fiye da yin bidiyo lokaci zuwa lokaci ina yin gajerun bidiyoyi in ɗaura a Facebook. Bayan dogon nazari, da yawan bincike yasa na gano, rubutun yafi saurin isar da saƙwannin da akeson isawarwa. Menene daliki? Sabida ƴan uwa mata sunfi gane manhajar WhatsApp da Facebook sosai, kuma suna son karance_karance A halin yanzu ina da tarin mabiya masu son aiyukana dama masu sukan aikin nawa. Ina samun lokaci ishasshe a duk mako in bibiyi sharhi da yawan masu yaba mun abun mamaki maza ne, matan sunfi ƙarfi wajen aibatani da kirana ƴar kwangilar yahudawa da sunaye marasa daɗi makamantan haka dai. Amman maza in aka kasasu kashi ɗari saba'in a cikinsu yabamun suke yi kaso talatin ke sukana saɓanin mata da kaso mafi tsoka shine na albatawan, bayan duk a kansu nake yin komai amman basa tare dani. Sai dai dake na faɗa muku ba'a samun cikar guri ta sauƙi kana kwance, dole a hanya akwai gargada da ƙalubale masu tarin yawa a yayin tafiyar, kuma ni cece kuce a kaina baya damuna, yana daga cikin dalilin da yasa nake yin Hajiya Laila Ali othman, da Lubna boƙararriya, duk da nasan a wasu lokuta ra'ayinsu na cin karo da addininmu, amman in aka ɗauke wannan ina yinsu. Kuma sara da sassaƙa baya gashe gamji. Abu mafi daɗi shine dana saki bidiyo ko rubutu kafin kace wayewar gari abun yayi shurar da ni kaina sai abun ya soma bani tsoro. Dake mafi yawancin saƙwannina da daddarene sune na ƙarshe wanda da nayi nake ajjiye wayar sai kuma gobe. Ɗan ragowar Lokacin dashi nake zumunci da dangina da yarana. Hankalina a kwance yake sosai sau biyu ina turama da Luba kuɗi kuma tana yi mun bidiyon yadda sabon gidana yake ciki, da duk abubuwan data siyo ta zuba mun. Tafe_tafe da wasa_da _wasa har yau gani shekarata guda cur a landan gani cikin hukuncin Ubangiji nasha ruwan landan fatata ta yi kyau ta murje maina na kamfanin Oriplame dai ban sake shi ba sabida mayukane masu tsada da sirrin kyau duk wata babbar mace mai jin itace zaka ganshi a jakarta ko a gaban madubinta hatta turaren fesawa da nasu nake amfani sai na wajen mrs Bukhari da shima na yadda da ingancinshi in ka fesa har ka wanke kaya yana ƙamshi itama nata, tana da manya _manyan kayan ƙamshi wanda ake musu laƙabi da Luzziri😃kun dai gane turancin ko? Kamar kullum dawowarmu daga aiki kenan na yada zango a saman kujera ina sauke numfashi na gaji sosai gashi gobe asabar muna da lakca akwai buƙatar in yi karatu ga takaddun mata dana tara fin goma suna jiran amsata tare da basu shawara ni da mabiya shafukana. Wanka nayo na saka sassauƙar doguwar riga. Na kwanta nayi bacci sosai sai magriba na tashi na gabatar da Sallah. dake bana jin yinwa sai kawai na dafo shayin ganyen shayin Ahmad ti mai ƙamshin gwaiba. Nazo na zauna a saman kujera tare da shigar da ƙafafuna cinyata na ɗaura laptop ɗina a cinyata na kutsa tsafina na Facebook na ɗan yi dube_dube kafin kuma na shiga whatApp ɗina, yauma Qasimu yayi mun sallama hmm baya gajiya wajen taya abokinshi godona. Ganin sunanne ma yasa na tuno da mijinyawa da Asama'u ƙila yanzu sunanan suna renon ƙani ko ƙanwar Sabira hankalin Nanno da su Yaya Jamila ya kwanta. Nasan ko ta haihu babu mai faɗamun daga su Yaya Jamila har su Azgar. Tunda na tawo babu wanda ya sake yi mun maganar mijinyawa su Azgar dai suna faɗamun sunje sun dubo Baban nasu a bisa umarnin dana gindaya musu basu taɓa tsallakewa ba, basu taɓa bani labarin halin da Babansu da matar Baban nasu ke ciki ba, sabida ba irin tarbiyyar dana ginasu akai kenan ba. Ni kasancewarmu a gidan gandu yasa duk abinda muka gani har rige_ rigen zuwa faɗa muke yi, iyayen namu suma kuma su biye mana, sabida kowa na son ganin gazawar abokin adawarshine. To in ka taso ka samu iyayenka sun yi kuskure a tarbiyyar da suka baka ka girma ka mallaki hankalin kanka, bai kamata kaima Ka sake aikata irin kuskuren akan yaranka ba. Amman mai hankali kaɗai ke gyara abinda iyayenshi suka rusa ko lalata a tashi tarbiyyar. Yawanci abinda muka taso muka samu iyayenmu da kakanninmu suna yi muma shi zamu yi. Imma, mai kyau, imma mara kyau. Wannan tunanin shi ya hallaka su Abu jahal da sauransu masu bin addinin iyaye da kakannin. Mrs Bukhari.TSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA ASHIRIN _Idan kika sai littafinnan nawa mai suna TSURON TSIRIN TSANDAURI tamkar kinyi sadakane kai tsaye a asusun marayu._ _Littattafaina kuɗinsu sadaukarwane ga iyayen marayu har zuwa ranar da zan dena rubutu._ _Ko nawa kika cire kika saka marayu zan yima hidima dashi wallahil azeem ko kuɗin Data bana cirewa a kuɗin littattafaina, marayu kaɗai nake yima hidima._ _Saima ƙarawa da nake yi da kuɗin kasuwancina akan kuɗin da littafi ya samar mun._ _Kuzo ku siya mu samu ladan marayu tare daku, ga lada, ga karatun littafi Hajiya._ _Wannan link ɗin na ƙasa ɗaya ne daga cikin aikin da nake yi da kuɗin wajen hidimtama marayu, shafin gidan Rediyo, da talabijin na ZINARIYA TV jos ne suka ɗaura domin sun kai ziyara a lokacin da aikin tallafin yake gudana._ _Nayi hankane ba dan riya ba sai dan ina cewa marayu nake ma hidima da kuɗin, amman ku baku taɓa gani ba, shi yasa wannan karon na zaɓi ku gani, daga yanzu kuma zaku dinga ganin dukkan aiyukan da nake yi da kuɗaɗen littattafaina, hakan zai ƙara mana ƙarfin guiwa __Daga ɗari bakwai zuwa sama yadda kike jin zaki iya zubawa baki faɗi ba saima romon lada da zamu samu a tare_ _Mu tausayama marayu wallahi marayu suna cikin wani hali na ni ƴasu, har jari ina tallafama da iyayen marayu jarin ƙananun sana'a domin dogaro da kai_ Nagode sosai son so https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=pfbid0auC21yurVzFgZB5dArWgYZNDLpSLDWWNyMVfhw5pjfoThFSJepavmiD8NMy2sUmgl&id=100084908716368&mibextid=Nif5oz *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. Hmmmm rubutu nayi mai jan hankali dangane da halin maza da irin son kan da maza da yawa suke dashi, bance duka ba kafin a caccakeni. Sai na bi tsokacin da rubuta takaddar da wata baiwar Allah da mijinta yai mata zalunci, daga ƙarshe yai mata sakin wulaƙanci, da dai sauran labarai akan rayuwarsu marar daɗi har idanun yaronta ɗaya ta rasa ta dalilin uban ɗan da kanshi. Tayi ƙorafi ance to ai Ubangiji ne. Kuma yaron yazo tare uwarne a yayin da uban yake mata dukan galila. Na ɗaura a shafina na Facebook na tura a zaurukan whatApp ɗina da nake dashi guda uku. Har zan ajjiye wayar tawa in gabatar da sallar isha sai naga shigowar saƙo da buƙuwar lamba naga kuma an kirani da Hindu Nagoɗi, a tunanina ƙawatace ta makaranta wannan yaja ra'ayina na buɗe saƙon. Hotuna uku na gani ɗaya Asama'u ce a jikin mijin yawa yana rungume da'ita tsam idanunshi cike da buƙatuwa sun lumshe sun fito da wani mai_mai Asama'unce da kanta ta ɗauki hoton. Hoto na biyu na ranar ɗaurin Aure ne da gani. mijinyawa na ƙurama idanuna banga annuri da zaƙwaɗi tattare dashi ba sam. Amman yayi kyau fatarshi lub ga wannan tozali dake sake gayanta gayenshi ya fito ras idanunshi, amman na banza a wajena, tur da Mijinyawa. Ta ɓangaren Asama'u kuwa tamkar wacce akaima bishara da gidan Aljannah. A kanta na zurfafa kallona tamkar ƴar sandar dake son gano gaskiya ta idanun mai laifi. Na fassara dalilan annurin fuskarta fin kashi talati. Murmushi nayi tare da cije gefen leɓena na ƙasa ɓangaren hannun hagu. Hoto na uku kuma Asama'u ce a kan cinyar mijinyawa a ofishinshi har hotonmu dake kan gaban teburinshi ina hangowa, da atampar da Innarmu tayi musu anko da Sabira a jikinta, kanta na kan wannan ƙirjin dashi yafi komai ruɗata shima dashi yake taƙama in dai a gabanane, a da can da duniyarmu take kwance nake nufi. Tuno sanda aka miƙomun Asama'u nayi, na sanya hannu na karɓeta na rungume, yarinyar tayi lub a kan ƙirjina, irin lub ɗin da tayi a ƙirjin mijinyawa a jikin hotonnan. Sai rubutu a ƙasan hoton _Hindu Nagoɗi_ _Yaya akaji da zafin rasa miji, yaya akaji da zafin yadda Asama'u ta ƙwace mijinyawa a wajenki. Nan _nan kusa zaki ji kyakkyawan labarin haihuwar Asama'u_ _Kinga yaranki guda biyu kacal da kike tunanin su kaɗe zasu mamaye gadon dukiyar mijinyawa sai ki sauya lissafi wannan karon anci Kanuri da yaƙi._ Shikenan iyakar abinda aka rubuta. Ko dana duba sama dan ganin hoto sai naga kamar an kulleni bulokin. Dannan lambar nayi ya kaini wajen suna Alhamdulillahi aka rubuta a wajen sunan. Lambar nake ta kallo kamar a jiki zan samu bayani. Luba na kwafe lambar na turama da ɗan taƙaitaccen rubutu. Ki bincika mun waye mai lambarnan Luba. Turomun hotunan mijinyawa da Asama'u akayi kana aka kulleni" Shikenan abinda nace na ajjiye wayar nayi sallah isha na zauna da Qur'ani shiru a cinyata ina rabe ɗayan biyu, zuchiyata tafi tunanin Uwatale ce. To ni menene nawa, itama menene nata Uwatalen? Mijinyawa dai in yaso ya mayar da Asama'u cikinshi ya adanata ƙarshen zama tashi kenan. Kai amman ba Uwatale bace bata san wannan lamarin ba, kuma ba sani zata yi ba. Babu mamaki Asama'unnce tana ganin karanta ya kai tseko, tasan sirrina, ta kwanta da mijinyawa gani take yi tamkar ƙarshena kenan. Murmushi nayi zuchiyata cike da mamaki da raɗaɗin zafi. Wani turiri da wasu munanan hasashen da banso zuchiyata ta hasasomun ba na shiga yi. Murmushi na kuma yi har ina rufe bakina da hannuna. Mijinyawa kenan an dai faɗi babu nauyi gaskiya, an kuma ci baya wallahi. Wani irin ciwo dake cikin ƙirji ke tuƙamun a cikin zuchiyata yana murɗamun notukan kaina, inaji suna kuncewa man kaina na tsiyaya. Sai ajjiyar zuchiya nake saukewa kawai, tare da ambaton Allah a fili. Tunda muka rabu da Mijinyawa rabuwar da suka tafi ɗaurin aure ban sake kallon hotonshi ba sai yau. Na gaban tangaran ɗin wayata dana gaban laptop ɗina tuni na daɗe da cirewa na maye gurbin da hotunan kyawawan nagartattun ƴaƴana, ababen alfahirina, nutsuwata, farin cikin ruhina. Hasken fuskokinsu da adadin yawan ƙaunarsu ne ya dishashen hotunan Asama'u da Mijinyawa a idanuna tuni na danne maiƙon tunanin su da tunano nishaɗinmu da yarana. Ajjiyar zuchiya na sauke na tashi naje na dafa taliyar yara da kifin gwangwami da kuma waken gwangwami, sai baƙin shayin Ahmad mai ƙamshin girfa. Kiran Azgar ne ya shigo ta manhajar WhatApp ɗina. Ai ni na mance shaf yace mun gobe akwai yarinyar da zata zo ta sameni a makaranta zamu gaisa da'ita. Nasan shi da nacin zance tunatar dani yake son yayi. Ɗazu aikine yasha kaina yasa ban yi mishi tambayoyiba akan ita yarinyar. Azgar bana hana ka kiran dare ba shine ka kirani ko. Nasan akan yarinyar da kace zamu haɗu a makaranta ta gaisheni ne, kai da kake da nacin zance ko? " Ɗan murmushin samartaka yayi mun yace. "Ummi har da shi ɗin. Amman rubutun da kika yi a Facebook ne naga anata muhawara akai anata zaginki, shine duk zuchiyata ta tsinke. Ammi mutane basa ganewa, kuma suna da saurin zagi. Abokinane ma yace in duba yaga anata muhawara, kuma anata yaɗa rubutun zuwa groups daban_ daban na mata" Ƴar guntuwar dariya nayi mishi kana nace mishi. Kada ka damu da duk abinda mutane zasu ce a kanka, muddin kana son kaci gaba a rayuwa, kasan domin Allah kake yi, Iyakar wannan yaɗawar kaɗai ya isa ɗaga darajata dana sunana Azgar. Matakin duk nasara, ƙalubale da cin karo da abubbuwa marasa daɗine. Kasan adadin bulogas da suka dena yaɗa abubuwan alkhairi sabida wannan gutsiri tsomar kuwa? Ni bana duba abinda zasu ce kaima kama dena damuwa nasha faɗa maka, ni bani da matsala da hakan. Sai maganar yarinyar menene alaƙarku, sannan wanene tsanin haɗuwar taku? " Ajjiyar zuchiya ya sauke jikinshi duk yayi sanyi saida na ƙarfafashi. Azgar yana jin zafi gaya in yaga ana zagin rubutuna sosai. Su masu zagin, basa duba wanda suke zagin cewar suna da haular da suke son su, kuma basason abinda zai taɓaka. Sun san ni uwace tunda har yarana sun sani da damansu, amman basa duba darajar ƴaƴana su ɗaga mun ƙafa dole sai sun yi zagi, banda masu cewa suna sona. "Ni bazan sake bibiyar shafin naki ba zuchiyata zata iya bugawa watarana Ammi" Allah yasa hakan shine mafi alkhairi. Amman nasihata shine kai namijine ka zama mai juriya da wuyan ɗauke dukkan matsala, ka fiye sanyi da tsoro Azgar ba'a son namiji haka. Da wannan dalilin yasa dole ma in ma Akarami magana da ka gama jami'a a sakaka a aikin soja. Nafi sha'awar namiji jarumi mai zuchiyar dake da jumurin ɗaukar ko wanne yamutsu. Faɗa mun ita yarinyar fa?" "Ammi dama a Facebook muka haɗu da'ita zai kai wata shida haka. Ni na roƙi lambarta ta bani muna gaisawa sama_sama. Shine take faɗamun ai tana Landan tana karatun digiri a jami'arku. To shine nima na faɗa mata mahaifiyata tana mastas tare da jami'ar, kina aiki a Bbc Landan, to itace ta buƙaci tana son ta ganki ku gaisa tunda ni sai dai a hoto ta sanni na santa" Idanuna na lumshe kawai tare da girgiza kai Azgar kenan. Toh shikenan zamu haɗu da'ita ta sameni a ɗakin karatu nasan inta ganni zata ganeni shikenan ko?" "Tana da hotonki ma har da na Abba, da Sabira" Toh shikenan sai goben ka kula dai banda yawan magana da mata, sannan banda maganar da bata dace da addini da tarbiyya ba. Ka riƙe girmanka da mutuncin iyayenka, ka kula da kanka ka kula da ƴar uwarka har zuwa sanda Allah zai dawo dani" "Ammi" Kada kace komai ka adana wannan tambayar har sai na dawo najeriya kamar yaune shekara ai kamar kwanane" Nasan tambayar ɗaya ce inna dawo gidan Abbansu zan koma, shine tambayar da suke matsa mun da'ita shi da Ƴar uwarshi. Ni kuma bana son raba musu hankalinsu. Duk da na fahimci kamar basason in koma gidan Abbansu. Amman dole zuchiyarsu zata yi ƙunci ko babu komai uba ubane, kana akwai shaƙuwa mai yawan gaske a tsakankanin mijinyawa da yaranshi sosai, har nakan rasa gane cikin mu biyu dawa suka fi shaƙuwane su suka barma kansu sani kawai, amman shi Mijinyawa yace Azgar yafi sona sama dashi. Karatu nayi sosai dan bana wasa da dukkan abinda na sanya a gabana. Washegari bayan mun fito daga lekca muna zaune a ɗakin karatu muna hutawa dan yau wuni cur zamu yi a makaranta. Bamu da wajen zuwa ni da Shamsiyya sai nan wajen kasancewar itama mayyar son karatuce gata guruwace sosai kamata. Mun sake haɗuwa da wasu ƴan najeriya mata biyu Nabila da Nafisa. Amman mazauna landanne a yanzu aiki ya kawo mazajensu shine sukai amfani da damarsu wajen ƙara karatu sai dai su digiri suke gwagwarmayar kammalawa, amman a shekaru zamu yi sa'anni da juna. Son karatunsu ya jone mu waje ɗaya duk da a wata ƙasar in ka haɗu da ƴan ƙasarku ko masu jin yarenka sai kaji kamar ka suma dan daɗi. Sau uku muna ziyartarsu su kam sun ziyarcemu yafi a ƙirga muna mutumci sosai harda mazajen nasu, sabida kusan su suke yawan mayar damu gida duk ranakun da muke shigowa makarantar. Dankali da ƙwan da Nafisa ta kawo mana muke ci muna labarin wani littafin turanci da yadda jarumar take jan zarenta a wajen mijinta. Muka ji sallama da wata matashiyar sassauƙar murya a bayanmu. Nina soma waigowa kasancewar nasan zanyi baƙuwa. Tana saye da abaya irin ta zamani ta yane kanta da mayafin abayar a mutumce dai sosai. Kece baƙuwar Azgar ko? " Sai tayi murmushi kawai tare da ɗan risinawa ta gaishemu da girmamawa. "Nafisa dama kinsan Hindu Nagoɗi ne? " Cewar Nafisa ƙawarmu. Kin santa ne, kaddai itace Nafisan da kike kira da takwararki _takwararki tsarar zamanki sit meit?" Nafisa tayi dariya tace. "Itace fa gata da ƙoƙari gaskiya tana taimaka mun sosai akan karatu." Kai na kaɗa nace. Duk guruntakarkinnan Nafi..?" Muka ɗanyi dariyar mu ta wayayyun mata ƴan boko. Hannun Nafisa na jawo ta zauna kusa dani daf har muna jin ƙamshin junanmu. Azgar yaronane ya haɗani da Nafi, shi ya turota ma. Nafi ya karatu ya iyayen naki, kina jin labarinsu? " Murmushi tayi tace. "Suna lafiya tare muke dasu anan ba'a Najeriya suke ba Ammi" Gaban mamaki. masha Allah nayi tunanin turoki karatun suka yi. Nan aka haifeki ne Nafi? " "A'A a Gombe aka haifeni mu fulanin Gombe ne Ammi. Abbanmu aikine ya kawosu nan bamu daɗe da dawowa ba mu, amman shi ya kai shekara ashirin yana zaune anan" Magana take yi hausa_hausa turanci_turanci ( kun tuno da Uzairu Zuchiyata? Dariya zata halakani). Mun taɓa hirarmu cike da wayewar kai. Azgar na kira a waya na haɗamu mukai magana a tare harma na ba su Shamsiyya suka gaggaisa kana yayi mana sallama. Muma lokacin komawarmu aji yayi muka ɗunguma muka koma, nan muka bar Nafisa da Nabila tunda su ba lekca garesu ba abu suka shigo yi. Tilis muka koma gida yau dai kam na gaji sosai. Ina shiga gida kiran Yaya Saratu ya shigo mun. Bayan na ɗaga mun gaisa tace. "Mutan landan baki fiye shiga group ɗin gida ba. Qazzafi matarshi ta haihu tun shekaran jiya. Innah Turai ma ta haihu, sai Auren Salamatun Innah Abida daya mutu anata tattaunawa a group." Baki na buɗe ga murnar samun ƙaruwa, ga ta'ajibin mutuwar Auren Salamatu. Yanzu Salamatu duk yadda take ɓare soyayya da Dr sai da ya saketa. Ita da take ganin babu macen data kaita sa'ar Aure a gidanmu ita da tayi Aure suna rayuwa a ƙasar waje? " "Ke dai bari ai gidan ya ɗauka in faɗa miki, da zaman gidanma gagararta yayi, ko tsakar gida bata isa ta fito ba kin dai san yanayin gidan namu. Ai kunya take ji sabida irin ƙafafa da jiji da kan da take yima mutane in suka zo. Tai ta saka suturu masu tsada tana ganin kamar mu wuya ma muke sha. Komai tace Dr Dr to Dr dai ya sallameta kuma dukka igiyar ta ƙare" Baki na buɗe. Kika ce igiyar ta ƙare me tayi da har zai mata saki uku haka? " "Hmmm Hindu gidanmu ana munafurci ƙaƙas wallahi, shi yasa duk runtsi tunda kana aiki ka zauna a ɗakin aurenka. Ashe a baya sau biyu yana sakinta Innah Abida suna rufewa hatta Baba Sojanmu bai san da wannan saki na baya ba. Ina wani zuwa da suka yi tayi kusan wata biyu a gida? To lokacin ma ashe ba auren. Aka shiga aka fita kafin iddar ta sauka a kanta aka dawo da'ita. To kinji abinda yake faruwa aure da Dr ya ƙare" Kaina na jinjina ina mamakin gidanmu da jama'ar cikinshi. Gidan yawa masifa ne wallahi. Da yawa ƙalilanne mai daɗi amman gutsiri tsoma sunnar gidan yawa ce. To Yaya Saratu yaran fa? " "Waɗanne yara kuma da sun riga sun girma Ummi tana jama'a ita da Baba Sadiq ragowar suna ɗakin mijinsu. A can ta barosu daga ita sai kayanta danma ta tsira da gwala gwalan da take zuwa tayi mana ƙarya dasu. Hmmmm Hindu Mijin Zubaida fa ya ƙara Aure jiya Amarya ta tare" Ai ba shiri na buɗe idanuna da suke rufe ina saurarenta. Sai naji abun wani iri. Aure kika ce fa Yaya. Shine bata ko faɗa mun ba?" "Hindu kenan ai zaucewa Zubaida tayi damma Innarmu nata ƙarfafata. Wallahi yayi aurenshi yarinyar mai gidanshi na wajen aiki ya Aura. Wai ashe yarinyar tun tana shekara goma a duniya aka bashi aurenta yake ta renon soyayyarta yanzune takai munzulin girbi. Yarinya ƙarama Sa'ar Batulunta fa kayan takaici. Ai ko kishin za'a haɗaka gara a ɗakko maka wacce zaku goga macuwat. Amman daɗin ma tana aikinta ta sake samun matsayi a ma'aikatarsu yaranta sun girma ba haihuwa yanzu take yi ba. Mu dai shawarar da muka bata shine ta ja gefe ta basu waje suci karensu ɗanye babu babbaka. Gidane taci gida, yaranka koma menene duk inda aka buga sune manya babu wani ɗa da za'a haifa ya fisu matsayi. Kafin a mori ƴaƴan Amarya an mori naka, ba da abinda Innah Abida take gadara ba kenan harma take ganin mu ba ƴaƴa bane? " Hmmm ni ai tuni na dawo daga rakiyar rijalu suna yin abinda suke sone a sanda suke so. Mune muke da hanya ɗaya su hanyoyine dasu. Abinda na fahimta da maza a binciken da na yi maza suna da son kai, sannan su a kullum sun fi son abu sabo. Wannan son abu sabon ya ja ma mata matsaltsalun da mazan kuma suka gujesu kuma asalin abun dominsu ya faru. Mata na shafa man sanya fari domin maza, mata na shan ƙwayoyin bature sabida jikinsu da zatinsu ya fito domin maza, mata na kashe kansu da zumar ƙiba,masu ido da kwalli kuma a saka musu ruwa, ko ai musu allurar ƙiba da farin, mata na zuwa ai musu ɗinki, mata na shan magungunan mata da suke birkita musu yanayin tsarin halittarsu, mata na cushe _cushen magungunan mata domin su tsuke al'aurarsu wanda daga ƙarshe ake barinsu da ciwo, naga wacce gabanta ya rifta, naga wacce gabanta ke fitar da mugunya, naga wacce gabanta ke ɗoyi wallahil azeem. Ku tambayi likitoci ku sha labari. Nima a baya nayi kuma na samu matsalar da nasha zuruftun asibiti sosai kafin Allah yasa na dace, cutar sanyi ce ta kamani na sha baƙar wuya. Mune ƙarin gashi, duk abinda mace fa zatayi sabida ta burge saurayi, miji ne, da duk wannan abun haka zai ajjiyeki ya ɗakko wacce bata kai rabin rabinki ba ya faɗaɗa darajarta gaban mamaki. Duka waɗannan ababe dana lissafo, ba hasashe ko shaci faɗe bane abune da yake faruwa damu mu mata, in bai faru dake ba, ya faru da maƙociyarki, ƙawarki, yarki, mahaifiyarki, ƙanwarki, ko ƙanwar mijinki. Mata wallahi mu yi ma kanmu faɗa nifa yanzu ko murmushi nayi wallahi nayi ne a ƙashin kaina bana buri da fatan in burge uban kowa face kaina. Muma sai mun koyi son kanmu a duk yadda muke. Babu abinda ma yafi komai takaici kamar irin matan da suka ɗauki aure yi dole ko mutuwa. Suke ganin rayuwa ba zata kai musu ba sai da namiji A kullum ina buga misalina da layla Ali othman. Kuga yadda rayuwa ta kai mata bayan mutuwar aurenta, ku dubi yadda ta tsaya ta mayar da hankalinta ta jajirce ta tsaya da ƙafafunta. Mijinta na yanzu kuga yadda yake girmamata, ku duba wayewa da fahimtar rayuwa tattare da'ita. Gogewarta tana bani sha,awa da ace mata haka muke son kawunanmu muke rabuwa da mazajen da suke neman halaka rayukanmu da ba haka ba. Hmmm bari in tsaya kafin ace mun kwangilar yahudawa na karɓo kamar yadda ake ce ma Layla ta raina maza hahaha harna tuno rikicinta da magaji. ( Ummu Nabeeha, dake muka tattauna Rikicin Layla da magaji, a lokacin da abun ya faru) Wanda ya san zancan mu haɗe a kwament sekshan. "Hindu kina jina kuwa? " Naji muryar Yaya ta ratsa dodon kunnena. Inaji na tafi wani tunanin ne kawai Yaya Saratu" "Hindu inaso dama nayi miki magana akan mijinyawa. Nasan halinki da tauri, da kafiya, Hindu da kuma fishi, Wannan dalilin yasa kowa ya ƙyaleki baya ko yi miki maganar mijinyawa bare Asama'u" Idanuna na lumshe kawai inaji da ana iya mayar da zamani baya irin yadda na taɓa gani a wani shiri na Indiyawa yadda suke murɗa agogo a dawo baya da tuni na murɗa makarantar da mijinyawa ke sana'ar lemo ma wallahi bazan yadda in shiga ba. "Hindu ina fatan kuna waya da mijinyawa dai yanzu ko? Bai sake zuwa ya kawo ƙorafinki a wajeba ba dai tun wannan zuwan na farko, kuma batun tafiya da kika yi babu saninshi, wallahi yace ya lamunce miki, ya kuma yafe mala'ikun Allah su shaida, dan haka ba kya cikin tsinuwar mala'iku. Hindu ni ko dan sabida Asama'u bana so ki rabu da mijinyawa wallahi" Murmushi nayi nace. Me yasa sabida ita Yaya Saratu? Na ja numfashi tare da gyara zamana. "Yauwa bana son uwarta, ko ita, ko Uwatale ɗaya a cikinsu yayi nasara a kanki. Hindu ba zaki iya nuna kamar baki san Asama'u mijinyawa yake Aure ba ki zauna ko dan maƙiyanki ba? Wallahi nasan kaɗan daga cikin dakiyarki ne wannan. Na sanki farin sani tun kina yarinya ƙarama, nasanki da shanye abu, da dakiya" Dariya nayi gajera. Yaya Saratu kinsan tunda na taso ni bana yin abu sabida mutane zasu ce, ko gudun suce. Bana daga cikin matan da suke kashe kansu dan su burge maƙiyi, kana ai su Uwatale na riga na gama dasu. Ni naso zama da mijinyawa, ni kuma nace na barma Asama'u shi har abada dan wallahi billah bazan taɓa iya mishi biyayyar aure ba, ba kuma zan taɓa bari ya kwanta dani ba. Kinga kuwa wuta zan shiga in nace naji na gani zan zauna dashi dan kawai in burge su Uwatale. Naji sitatiment ɗinki ma na ɗasu da kika ce wai gara duk runtsi mutum ya zauna a gidan mijinshi, sabida gudun gulmace_gulmacen ƴan gida. Hindu ba haka take ba Yaya Saratu. Ni bana yin komai domin kowa. Yaya Saratu Asama'u fa" "To yaya zaki yi da sharaɗin Baba Sojanmu? " Saina dawo zan san yadda zanyi" "Amman uwar Asama'u ba ƴar halak bace. Hindu narantse miki da Allah zan nemi har garin da take aure inje in gargasa mata maganganu ko Allah zaisa in huce, zuchiyata tayi sanyi. Ko yaya mijinyawa yake iya gudanar da mu'amalar Auratayya da yarinyar da shi ya zaɓa mata suna ta girma a gabanshi. Hindu dole ki ƙi shi kaiii ina wallahi ina bayanki Hindu" Dariya muka kwashe dashi da haka mu kai sallama na ajjiye wayar na wuce banɗaki nayi wanka na ɗauro alwalar magriba, ina fitowa Shamsiyya na shigowa da waya a hannunta. "Hindu Nagoɗi kinga irin zagin da maza suke yi miki kuwa akan rubutun da kika yi. Dan Allah bakya jin wani iri? " Lallai shamsiyya sai kace ba ƴar jarida ba? Mu da aka sanmu kamar aljanu dan naci da kafewa. Jibi yadda muke saka mutum yayi aman abinda ke zuchiyarshi ya fesama al'umma, in bai yi wasa ba sai dai ya shiga ɗaka yayi kuka mun ruftashi. Hmm wannan zagin ni ko buɗewa banyi ba. Saima ranar da nafi nishaɗi nake dubawa. Wannan zagin a wajena matattakalace ta ɗaukaka. Ana cikin haka sai ga kira ta whatApp ɗina kamar bazan ɗaga ba dai sai kuma na ɗaga. Da sallama a bakina. Namiji ya amsa a tsanake, ya tambayeni dan Allah nice Hindu ko, na amsa mishi da Eh. "Dama dangane da wannan mar'atussaliha da kika ɗaura labarinta ne maƙasudin kiran. Ni sunana Ibrahim haifaffen garin Kano amman, yanzu ina Abuja ina sana'ar canji. Inaso in babu damuwa ki haɗani da wannan baiwar Allahn inaso in Aureta, kuma zan riƙeta harda yaran nata, amman nima ina da yarana uku mahaifiyarsu shekararta goma sha biyar da rasuwa, amman sai yanzu ne naga wacce zuchiyarsu asin da asin da matata." Wannan rana na daga cikin rana mafi girma da daraja a rayuwata a karon farko da zan haɗa Aure. Take na tura mishi lambarta ita kuma na kirata ta whatApp ɗin mai shagon da suke karɓan kaya ina tura mishi kuɗin kasancewar bata da babbar waya. Nayi mata bayanin zata yi baƙo gashi gashi Wallahi kuka ta fashe dashi. Ba'ayi sati biyu ba duka duka akayi auren ya kwashesu zuwa Abuja wai kunga gidanta? Wani hanin ga Allah baiwane, wannan darasine ga matan da suke tauye hakkin rayuwarsu sabida a nasu tunanin basu san inda zasu faɗa ba. Allah na ɗauki kalmarnan a matsayin rashin tawakkali eh na faɗa ku saka mun gas in kun so". NAJERIYA:. Mijinyawa To ƴan team mijinyawa gobe ranarku ce kuma Mra BukhariTSURON TSIRIN... TSANDAURI.... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHIN LAMBA TA ASHIRIN DA ƊAYA *Bojuwa herbs* *By* *Surayya Dee.* *08032773332.* *Sanyi flusher!* *Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.* *Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. *Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.* *Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*. *Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.* *Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.* *Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.* *Tuntubeta a wannan lambar* *08032773332* *Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.* *Nation wide delivery*. MIJINYAWA:. Ta ɓangaren mijinyawa duniya tayi mishi ɗaurin lemar minti, jinshi yake yi tamkar ɓari ba guda ba. Hindu dai dama ya kwana da sanin wani ɓangarece a rayuwarshi sosai kuma jigo. Sai yake jin rayuwar tashi da wani wawakeken giɓi wanda bazai iya cukowa ba matsawar Hindu bata ɓangarenshi gaskiya. Da zaran yayi tuntuntuni akan abubuwan da suka shiga tsakaninshi da Asama'u illahirin kunyar Allah da nauyin Hindu da taga komai sai ya lulluɓeshi, ji yake yi tamkar ƙasa ta dare ya faɗa ciki. Watan Hindu huɗu da tafiya amman yayi iyakar yinshi dan ganin ya rage tunaninta amman sai abinda ya hauhawa. Gashi ta toshe mai duk wata hanyar jinta ko labarinta. Ta ɓangaren Asama'u ta ɗauka yaƙin shine na samun zuchiyar Mijinyawa shine mafi wahala. Sai ta samu ƙoshi da kuma kwanan yinwa, gata a matsayin matarshi, amman kuma ta rasashi harma take jin ɗan da kace basui auren ba watsewar kawai suka ci gaba dayi. Gashi tayi mugun sabo ta tasirantu da abubuwan da ya shiga tsakaninsu kafin Aure. Amman a yanzu a yanzu gashi ta rasa duk da cewar Nanno tazo tace in ya sake kwana ɓarayin Hindu bata yafe mishi ba, sannan zata ɗaga mishi Nono muddin ya sake raba ɗaki da Asama'u. Da wannan dalilin ya lallaɓa ya baro ɓarayin Hindu duka ya dawo wajen Asama'u wanda a yanzu yake ganin baƙinta. Gashi dai a ɗakin amman doguwar kujerar cikin ɗakin nanne gadonshi. Sannan babu fuskar da Asama'u zata yi yinƙurin yi mishi wani abun, duk da a baya tayi yinƙuri har sau biyu a na biyun dai tayi nasarar cire mishi wandonshi ranar hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba. Kamata yayi ya mammareta tare da mata gargaɗi mai zafi, sai zazzare mata idanu yake yi. "Waike wacce iriyar rashin kunya da fitsara yake damunki ne? Ni dai nasan Hindu ta baki tartibiyar tarbiyyar da Uwarki ma ba zata iya baki ba, wannan dalilinne yasa tun fil azal bamu bar amanar tarbiyyarki a hannunta ba." Ya gargasa mata maganganu kaifafan gaske. Washegarin da abin ya faru sai ga kiran Halima tana son titsiyeshi dan jin menene yayi zafi da ya zama har da duka, da kuma aibatata a gaban yarinyarta. "Me yayi zafi Mijinyawa da zaka dukan mun ƴa, kuma kana neman sunce mun zane a kasuwa. Shin ku abu baya wuce wa a wajenku ne mijinyawa? " "Baya wuce wa Halima, dalilin da yasa a cikinmu kab abokan marigayi babu wanda yayi yinƙurin aurenki, shi kanshi Abdulƙadirin kara da kiyashi ya ɗauko ɗaukan maras sani. Kuma ai kinsan babban dalilin da yasa muka karɓe Asama'u a hannunki ko? Da ace nasan riƙo Asama'u haka zai zame mun da tun farko gidan raino muka kaita taje ta rayu acan wallahi. Yanzu ke har kina da bakin kirana kina mun titsiye akan ƴar ko Halima? " Rikici ne babba ya ɓalle a tsakanin Mijinyawa da Halima, dama akwai magana a danƙare fa. Bayan sun gama wayar yayi tsaki. "Aikin banza da badan na zubar da girmana ba tayaya Halima zata kirani tana faɗa mun magana. Ita kuma yarinyar dake bata da kunya cema uwarta tayi wando ta cire mun kenan? Dan a maganganun Halima ya nuna tasan musabbabin marin harma shi yasa take tambayar nenene laifi a cikin abinda tayi ko? Hmmm Allah wadaran naka ya lalace, ashe dai da gaske barewa ba zata yi gudu ɗanta yayi rarrafe ba." Haka dai wannan zaman doya da manjan yaci gaba da tafiya. Kamar ko da yaushe da safiyar asabar yana zaune a saman Daining da laptop a gabanshi yana aiki da misalin ƙarfe sha ɗayan safe. Asama'u kuma tana Kitchen tana neman abunda zata ɗaura musu na rana sabida biredi da shayi kawai suka ci da safe. Kwatsam sai ga sallamar su Sabira har da Baba Sojanmu. Da sauri mijinyawa ya miƙe bayan sun shigo, Baba Sojanmu na sake da riga da wando na ƙananun kaya da fosinkaf ta sojoji harda zanzaro da bel ɗinshi irin na sojoji. "Sannu da zuwa Baba Sojanmu kune ashe a gidan, ni naji shigowar mota na zaci ko Mijinyawa Babbane ya fita ashe kune? " Ya ƙarasa yana shirin tsugunnawa Baba sojanmu ya katseshi tare da miƙa mishi hannu su gaisa irin na boko. Ala tilas ya miƙa hannun suka gaisa cikin fara'a, kana suka zazzauna yaranma suka gaisheshi ya amsa da kulawa yana tambayarsu karatu. "Dama cewa suka yi in rage musu hanya ni zan wuce yanzu akwai wani taron ritayat sojoji da zani ne. Inna gama zan biyo in ɗaukesu mu koma tare kamar yadda muka fito." Asama'u ce ta fito a Kitchen. Azgar ya ƙura mata idanu kamar zai halakata dan ƙiyayya Mijinyawa na kallonsu yaga sanda Asama'u ta zuba ma Azgar hararar da yaji kamar ya tashi ya zuba mata mari. "Ina kwana Baba soja, ya su Innarmu? " Muryarshi ya saisaita tare da cewa. "Lafiya lau Asama'u ya gidan ya haƙurin zama?" Ɗan murmushi tayi kanta a ƙasa. "Ta dena karatune ko ko dai ta koma ta ɗaura karatunta? Kasan fa karatu na da mahimmanci kuma Asama'u ai tana da ƙwazo" Kai mijinyawa ya sosa tare da cewa. "Bata koma ba, dake Nanno ce tace a barta a gida kawai ta zauna, ta kula da Aure" "Wat no no akanme yarinya a irin wannan shekarun ace wai ta zauna Aure, au dama aure na hana karatune? Kai ke nan ka auri mace ka jibge a gida sai an kai ruwa rana kafin a koma karatu? Ka mayar da yarinya makaranta. Nanno mai ta sani akan karatu tunda batai ba" Mijinyawa dai kanshi a ƙasa yana tuno artabunshi da Baba Sojanmu akan makarantar Hindu an yi ɗauki babu daɗi gaskiya. Baba soja ya fita Mijinyawa ya bi bayanshi aka bar Asama'u da su Azgar. "Wallahi in sha Allah sai alkadarinki Ya karye Asama'u ashe da Abba kuke wannan wayar da kuke yi kullum a gabana? In kina tunanin kinyi domin ki ƙuntatama Amminmu ne wallahi Allah bazai baki iko ba. Ammi tayi miki nisan da iyakar rayuwarki baki isa kin kamota ba" "A matsayi na duniya ba, bana fata in zama mai cuɗanya a cikin maza. Amman a matsayi a zuchiyar mijinyawa sai dai ta biyo bayana. Abinda muka aikata ai ba haramun bane kuma in kukai mun haka ba kui mun adalci ba, sabida babu wanda yake a haƙƙu ya aureni sama da mijinyawa ai" "Wallahi ƙarya kike. Ammi ta riga ta rufe ƙofar zuchiyar Abbanmu babu wata macen duniya da zata iya buɗe zuchiyarshi. Ai da ganin zaman babu daɗi kuma ba zaki samu nitsuwarshi ba har sai farin cikinshi ta dawo gidan. Bar miƙe ƙafa yarinya Ammi tananan dawowa da zaran ta gama abinda take yi a landan zata dawo ɗakin aurenta, kinyi tsararo ki raba wannan ƙaunar da Allah ne ya ƙulla. Sabida baki da daraja da Mijinyawa kike kiran Abba" Azgar bai saka baki ba, kuma bai hana Sabira amayar da gubar da Asama'u ta shayar dasu ba, sabida ita macece rauni gareta. Amman ya fita jin zafi da ɗacin abinda ya faru, kuma a idanunshi yana tuno wasu kallon_ kallo daya wanzu tsakankanin Asama'u da Abbansu wanda sai da abinda zai faru ya faru ya iya fassara kallon. Ji yake kamar ya shaƙe Asama'u, ba dan biyayyar iyaye ba mai ma zai kawo shi wajen Abban kanshi. Miƙewa Asama'u tayi taja tsaki tare da cewa. "Aikin banza aikin wofi kada ki sake zuwa har ɗakina kice zaki faɗamun magana ina matar ubanki" Ai wannan kalmar ta MATAR UBA ita ta tunzura Sabira, tana miƙewa ta dira a wuyan Asama'u dambe sosai ya kaure a tsakankaninsu. Uwatale ce ta ƙaraso a guje tana shigowa mijinyawa na shigowa. Damben yaƙi rabuwa a tsakaninsu Uwatalate ta kasa rabawa Sabira ta ɗafe Asama'u sosai. "Jeki abinki uwatale ki rabu dasu" Ya faɗa yana kallon yadda Asama'u take naushin bakin Sabira, ita kuma Sabira ta riƙe wuyanta tamau idanunta sun firfito. "A barsu mijinyawa a dai rabasu. Ga babban banza a zaune ya kasa rabasu, sai kallonsu kawai yake yi. Duk ba ƙannenshi bane" Ta nuna Azgar dake kallonsu. "Naga matar Aure ce kinga ai bazan iya taɓata ba shi yasa" Azgar ya kashe bakin Uwatale, mijinyawa kuma yana ta kallon yaron yayi tsam yana nazari. Tim suka ji Sabira ta kayar da Asama'u ta hayeta da sauri Uwatale ta ƙarasa mijinyawa yace. "Uwatale nace ki barsu ki fita dan Allah kar kiga ɓacin raina" Tsawar daya daka ita ta tsayar da damben, uwatale tayi saurin fita Sabira ta jeru da ɗan uwanta daya miƙe tsaye. Asama'u ta miƙe tana kukan makircin ƙafarta ta goce. Hannaye ya goya a baya yana ta kallonsu Sabira ƙirjinta nata hawa da sauka, Asama'u nata kuka fuskarta duk yakushi kaca_kaca. Bai tuno irin wannan zai iya faruwa ba, iyakar son zuchiyoyinsu ya hanga. Baiyi nazari kan mutanen da abun zai taɓa ba, bai tuna zai iya cusa ma yaranshi tsanarshi ba. "Yayi kyau Asama'u kinji yayi kyau. Azgar kuzo mu fita" Ciki ya shige da saurinshi. Azgar ya kamo Sabira suna shirin fita Asama'u tace. "Sabida waɗannan ƴan iskan yaran kake mun faɗa, yarinya ta dakeni kuma kazo kana ce mun yayi kyau... " Tau Azgar ya ɗauketa da mari daidai fitowar Mijinyawa da sauri, sarai yaji abinda ta faɗa abinda ya fito dashi ma kenan. "Ƙara mata a ɗayan kuncin" Mijinyawa ya ba Azgar Umarni. Tau ya kuma ɗauketa da mari a ɗayan kuncin nata. Hannun ƴar uwarshi ya riƙe jikinshi na rawa suka fita. Asama'u ta bi Mijinyawa ciki ta sameshi yana sake riga harya sake wando. Bata iya ce mishi uffan ba, haka zalika shima. Kuka take risga kamar zata mutu. Kin mota ya zara ya fice. Suna tafe da su Azgar a mota ya rasa me zaice dasu har suka ƙarasa kantin da suka saba siyayya suka shiga. Azgar na biye dashi a baya da basket ba ƙaramar siyayya yayi musu ba, ya shiga gari dasu sukaita zagaye, tunani kawai yake tatayi ta yadda zai bama yaranshi haƙuri dan so yake abun yazo ƙarshe a gama. Hotel ya wuce dasu kawai ya kama ɗaki suka shiga. Ciki da falo ya kama musu, yana zaune a kujera su suna zaune a gabanshi a saman kafet. Azgar kuka yake yi kamar me. Hawaye kawai ke fita a idanunshi idanunshi jawur. "Abba... " "Shisshshsh.... " Ya ɗaura yatsanshi a laɓɓanshi halamun tayi shiru. Babu shiri ta haɗiye kalamanta. "Azgar, Sabira" Ya kira sunansu murya na rawa. "Na'am Abba" Suka amsa a tare. Azgar jikinshi sai rawa yake yi. Numfashi mijinyawa ya ja tare da lumshe idanunshi. Ya kallesu da kyau. Ya jima yana ƙare musu kallo kana yace. "Kuyi haƙuri ku yafe mun da zafi da baƙin cikin dana yi muku silarshi, da kuma zumuncin dana rushe muku da ƴar uwarku da kuka taso a gaban Amminku tare. Dan Allah ku yafe mini kuma kada ku riƙeni. Banyi dan cin zarafinku, ko dan ɓata muku zuchiyarku ba. Nanno ce ta tursasamun akan in aureta, biyayya nayi mata. Amminku tayi fishi mai girma dani. Tsawon shekara ɗaya cur banji ko da muryarta bane, ta toshe duk ƙofar da zan iya jin muryarta. Amman da dabara ku taya ni bikonta. Da ace ina da damar iya kallon Hindu da tuni Hindu ta ganni a landan to bani ƙarfin guiwa ne. Kuyi haƙuri kunji? " Kayukansu du su biyun suna ƙasa Azgar ne ya ɗaga ya dubi uban nasu, bayan ya share hawayenshi yace. "Babu komai Abba. Ciwo kam munji shi marar misalin misaltuwa. Amman tunda kace zaka kawo ƙarshen abun ai shikenan Abba mun yafe matsawar zaka kawo ƙarshen komai, ka dawo mana da farin cikinmu, mu zama kamar yadda muke da" Sabira tace. "Hakane Abba mun yafe in dai komai zai dawo kamar da. Duk da abinda ya faru ba abu bane wanda za'ace ya shuɗe a tarihin rayuwarmu ba. Abba hatta maƙota abun yayi musu zafi, su Innah uwatale ne kaɗai suke murna da Goggo Jamila. Suma dan basa son ganin farin ciki da walwalar Amminmu ne. Kayi haƙuri faɗan da nayi da'ita bazan sake ba, amman dan Allah ka saketa mu kam shine kaɗai kwanciyar hankalinmu, kuma shine zai kawo ƙarshen komai" Murmushi yayi guraben idanunshi fal ƙwallar baƙin cikin abubuwan daya damalmala, da ace yayi tsinkaye tare da duba da idanun basira gami da hange irinna girma kan abinda zai haifar, da tun farkon_farko da Asama'u ta soma mishi ƙananun iskanci, da ya maidata hannun uwarta. Wanda sai yanzu yake ganin sanya hannayenta dumu_ dumu akan abinda ya faru. Shi yasa manzon Allah Arrasul S A W yace ka zaɓa ma ƴaƴanka uwa ta gari, bayan jero nasaba, kyawu ya haska cewar mai addini tafi alkhairi. Ina addini tattare da Halima in banda bankaura, dama dai can tubabbiyace ta bariki bata isilama ba. Yana daɗa ganin wautarshi tare da jin haushin kanshi ainun. Abu guda ke ɗan sanya shi jin daɗi tare da saka tsammani akan Hindu. Rashin kwanciyar aure a tsakaninshi da Asama'u. Amman abu mafi girma da ɗaukakar kashe rassan jikinshi, bai shige aibata maman dake ƙirjin Hindu ba da yayi. Duniyar tashi, wajen dabdalar jin daɗinshi, da nutsuwar nashi. Itama kuma abun ya doketa tunda har ta aiko mishi saƙon tuna mishi da kalmar. Idanu ya lumshe. "Ku yi hakuri komai yazo ƙarshe zan gyara ko da bai kai irin na da ba, balle ina fatan yafi na da sosai. Kuyi ƙoƙarin shawo mun kan Hindu in tace hukuncin rabuwane a tsakaninmu, zaku iya rasani a gidan duniyar ma baki ɗayanta." Da sauri yaran suka ɗago suka zuba mishi idanu shi kuma ya gyaɗa musu kai halamun tabbaci. "Ba zata rabu dakai ba Abba. In sha Allah zamu yi ƙoƙarin ganin hakan duk da Ammi an ji mata rauni, irin raunin da baya warkewa, ko ni bana jin zan iya warkewa Abba. Amman dai bama fushi da ƙudurar Ubangiji. Tunda ba haramun bane, babu dai daɗine shi yasa" Cewar Sabira, Azgar kam bazai iya cewa komai akan wannan maganar ba. Mijinyawa ya jima yana rarrashinsu har suka sake dashi amman fa ta ciki na ciki musamman a cikin Azgar, ita Sabira kasantuwarta mace yasa dukan bai mata rauni ba, sabida mata rauni ne linkib a tattare dasu, kuma ita kamar tafi son ubanta, shi Azgar na Ammi ne. Sai yamma lis suka fito ya mayar dasu hatta Sallah a ɗakin hotel ɗin suka yi, suka ci abinci tare. Ya tarar da Baba sojanmu ya dawo gidanma, shine yake faɗa mishi ai ya koma zai ɗakkosu, ake cewa basanan. Ita Kuma Asama'u an kaita Asibiti harma an bata gado wai Sabira ce ta doketa. "Nayi mamaki gaya. Taya Sabira zata iya ma Asama'u dukan da zai kaita gadon Asibiti, kana mai ya haɗasu ma, kai kana ina Azgar?" Faɗin Baba Sojanmu dake zaune yana cin tuwo da miyar margi sifeshal ta matan Kanuri. " Saɓanine ya haɗasu har ta kai su ga dambe. Amman nayi ma tubkar hanci. Bamu da masaniyar ma tana asibiti a kwance ni babu wanda ya faɗa mun, kuma gaskiya ni banga abinda ya faru harna kwanciya a asibiti ba" Innarmu tace. "Hmmm Allah ya kyauta. In banda sha'anin yara ina Sabira ina faɗa da matar Babanta? In Hindu taji abinda kika yi zaki sani kuwa" "Ayi haƙuri innarmu kada ta sani, ita Asama'un ce ta soma takalar Sabiran, dama suna yi lokaci zuwa lokaci. Ayi dai haƙuri ni zan wuce" Nan yai musu sallama ya kama hanya yana faman mamakin abinda ya kai Asama'u harda kwanciya a asibiti. Yana daf da gida wayar mijinyawa tai ta shigowa ya ko ƙi ɗagawa sabida haushin matarshi Uwatale na neman ya shafeshi ainun. Yana shiga gidan ya tadda motar Mijinyawa a fake. A ƙofar ɗakinshi suka haɗu. "Ina ka shiga ne Mijinyawa inata kiranka baka ɗaga mun waya ince dai lafiya ka fita da yara tun rana? " "Umm lafiya wani abunne ya faru, ya aikin da gani a gajiye ka dawo? " Ɗan tsaki yayi ya ce. "Shigo daga ciki mu tattauna" Bai jira amsarshi ba ya ja hannunshi suka shiga falon Uwatale. "Uwatale bata nanne?" "Tana can ɗakin matar Gambo haihuwa zata yi" Sai su ka yi shiru na ɗan lokaci, can mijinyawa Babba yace dashi. "Mijinyawa menene dalilinka na auren Asama'u tun farkon fari ne, ince kai kaje ma da Nanno batun aurenta, ba wani bane ya tursasaka ba, naga kai ka nuna kana mutuwar sonta harma Nanno ta amince maka. Shin ko dan Hindu ta tafi ta barka ne shi yasa ka kasa sukunin da zaka kula da ƴar mutane, kullum ranka a ɓace kabi ka sauya sai rama kake yi. Menene matsalar ne, ba ji kayi kana sonta bane shi yasa kukai Aure ba? Uwatale tace dani a gabanka Sabira ta kayar da'ita tai ta jibgarta. Kuma bacin an gama hakan kayi ficewarka da yaranka, ita kuma Uwatale ta runtuma da'ita Asibiti. Sunce sun kira wayarka yafi sau a ƙirga baka ɗauka. Nima na kiraka kaƙi ɗauka har Halima na ikrarin zata zo gobe ta tafi da ɗiyarta ita ta gaji, tunda kana gani ɗiyarka zata kashe mata ɗiya. Ni dai na shiga na kashe zancan. A nanne ma nake ji wai baka taɓa kwanciya da ita Asama'un ba ma. Halima ce fa babu kunya take faɗamun maganarnan. Yanzu ya dace ace ni ta faɗamun haka? Shiru mijinyawa kawai yayi ya rasa abinda zaice. Sai can yace. "Babu damuwa mijinyawa Babba zan yima tubkar hanci in sha Allah komai yazo ƙarshe. Sannan ka dena biye kunji_kunjin mata, Hindu fa aiki ta samu na kwantiragi da Bbc Hausa tana landan kamar yadda nayi maka bayani a baya, da zaran ta kammala zata dawo ɗakinta. Su uwatale ke cancana zancan". "Na fahimci uwatale ke ririta wannan lamarin ita kanta zan maganinta gudun kar ta aikata abinda zai tarwatsa ahalinnan. Kaje ciki Asama'un tana ciki an sallamota mun dawo da'ita gida" Godiya yayi mishi ya fita izuwa ɓarayin Asama'u. A ciki ya tadda Uwatale tana mata wasu huɗubobi marasa kyau akan su Azgar. Girgiza kai yayi kawai tare da yin sallama. Da sauri Uwatale ta fito tana dariyar munafurci ta fita. Shiru yayi yabi bayanta da idanu. Ya jima a wajen har sai da Asama'u ta leƙo taga yana wajen kana ya tattaka ya sameta a bakin gado tana wash_wash ɗinta. Yayi mamakin huɗubobin Uwatale da irin maganganun bakinta akan Hindu. Duk Asama'u ta yaɗa shi ita ba'a kwanta da'ita ba, Allah mai iko. Ajjiyar zuchiya ya sauke kawai. "Damben da kuka yi kenan har ya kai a baki gado a asibiti Asama'u? Allah ya kyauta ki shirya suturunki kaf ɗinsu kar ki bar ko silifas akwai inda zamu je gobe" Daga haka bai ce komai ba. Asama'u tai ta haɗa kaya wasu a akwati, wasu a buhu, wasu a jakunkuna saida ta kammala fitar da komai. A daren ya dinga loda kayan cikin mota ba tare da kowa ya ganshi ba saida ya saka komai a motar, ya dawo yayi wanka ya sha ruwan bunu ya kwanta. A daren Qasimu ya iso daga Jama'are yana kwance a ɗakin Azgar, an buɗe mishi. Washegari da wurwuri yasa ta shirya tsab shima ya shirya suka fito harda Qasimu. Sai da ta shiga ɗakin uwatale suka jima kafin ta fito. Shi kuma suna tsaye da mijinyawa babba da Gambo, da Qasimu a wajen mota suna gaisawa tare da shaida musu zasu yi tafiya. Ta iso wajen ta gaishesu ya buɗe mata mota ta shiga. Sun ɗan jima suna tattaunawa al'amuran yau da kullum kafin su ka shiga motar yaja suka fice a gidan. Ta fahimci kamar garin mahaifiyarta zasu je da taga hanyar da aka miƙa. Sai jikinta ya sake sanyi gashi ya zame mata dodo tsoronshi take ji sosai. Tana son tambayarshi me yasa zasu je babu fuska, ya ɗaureta tamau. A tunaninta tunda har ya iya wasa da sassan jikinta bazai iya mata irin abubuwan da yake yi mata a yanzu ba. Aure shekara guda amman ta kaɗa ta raya wata mu'amala ma ta haɗasu. An yi tafiya mai nisa kawai ya tsayar da motar a gaban gidan mai. "Qasimu ka tuƙamu mu ƙarasa juwa nake ji" Canjen waje suka yi, Qasimu ya ja suka wuce. A haka dai suka isa ilai garin mahaifiyarta suka je. "Kinsan gidan da take Aure Halima ko?" "Eh na sani, amman... " Hannu ya ɗaga mata dole tayi shiru. "Ki dinga nuna mun hanyar ance sun sake sabon gida, cewar Qasimu" Turyan_turyan ta dinga nuna mishi har suka iso bakin tangamemen gidan auren Halima. Hon ya matsa mai gadi ya wangale musu get suka shiga da rana ƙata. Halima ce ta leƙo daga babban Kitchen ɗin tsakar gidan nasu ta hango ɗiyarta a bayan mota. Ba shiri ta nufo su. "Mijinyawa ita da bata da lafiya shine kuka yo miƙaƙƙiyar tafiya haka ko ita tace zata zo? " "Kamawa tayi Halima zamu iya shigowa ciki mu yi magana?" Cewar Qasimu. "Zaku iya nan gidan ai ba baƙonku bane, Mijinyawa maigidan ma yana ciki mujenku" "To kafinnan akwai kayayyakin ita Asama'u a baya a sa yara su shigo dashi" Jim Halima tayi jikinta a sanyaye tasa yara suka soma shiga da kayan ciki. Kishiyoyinta nan suka fito suna tambayar baƙi akayine. "Au Asama'u Amarya kece da angon naki? " Cewar uwargidansu Halima. A sanyaye aka gaisa kowa babu laka a jikinshi dai. Suka shiga falon suka tadda mijin Halima yana zaune yana shan shayi da dambun nama yana kallo, ga turaren wuta na tashin hayaƙi a hankali. "Asama'u kece a tafe akace kina asibiti babu lafiya ko? " Cewar Alhajin Halima. Miƙa ma mijinyawa hannu yayi suka gaisa, ya kuma miƙa ma Qasimu ma. Asama'u ta gaishe da mijin gyatumar tata sai falon ya ɗanyi shiru. "Lokacin sallah yayi muje masallaci kafin mu dawo Halima a ajjiye mana abinci" Fita suka yi masallaci suka je suka dawo, sun kuwa samu tuwon shinkafa miyar zogale an ajjiye musu. Sosai mijinyawa ya take cikinshi yasha zoɓo sosai kana yasa akayi kiran Halima ita da mijinta. Qasimu dai jikinshi duk a mace. "Dama ga Asama'u nan na dawo da'ita hannunki. Kamar yadda na ɗauketa tana shekara ɗaya da rabi ne ko biyu na mance dai. Gata na dawo miki da'ita zanci gaba da ɗaukar ɗawainiyarta har illa masha Allah amman ta zauna a hannunki. Qasimu a gabanka na sa hannu na karɓi Asama'u, yanzu a gabanka na dawo ma da Halima ɗiyarta. Sai yayi shiru. Alhaji yace "Bamu gane ba, to mijinyawa Auren kuma fa, ko dai abun yaƙi daɗine? Duk da ba abun daɗi bane a wajen mata ba, ka kuma sansu da kacalcala zance. Ni kaina a lokacin da Halima ta zo mun da zancan auren haƙiƙa na kaɗu" "Hakane, zama kam bazai yiwu ba Alhaji na sauwaƙe mata inta samu yaro daidai ita tayi aurenta" Hannu yasa a aljihu ya ciro takaddar ya miƙa ma Halima. Idanunta sun kaɗa sun yi jawur dasu tasa hannu ta amsa tace. "Amman ka cuci yarinyarnan mijinyawa cuta mai girma. A matsayinka na uba, in mahaifintane ya auri Sabira yai mata irin wannan sakin tozarcin zaka ji daɗi? Yarinya tunda ka aureta babu abinda ya shiga tsakaninku, Hindu ta asirceka, ta shanyek, ta hanaka rawar gaban hantsi, nan Saratu Yayar Hindu tayo tattaki har nan tazo ta zauna ta ci mutuncina yadda take so duk sabida aurannan. Aure kuma ku kuka sasanta kanku babu wanda yayi muku dole, kuma naga ba haramun bane. Yanzu yaya zanyi da Asama'u Alhaji kana ji fa" Mijinyawa baice da'ita komai ba amman yaji zafi sosai da maganganun data yaɓa ma Hindunshi. Ta ɗauki zafi sosai har da yi mishi adda'ar in sha Allah sai an yi ma Sabira abinda yayi ma Asama'u. Ya harzuƙa ainun amman kuma yasan duk shi yaja har Halima ke mishi rashin kunya haka. "Halima batun alkaba'i baima taso ba domin Allah. Ni tun farko da mijinyawa ya ɗauki shawarata da ba'a zo wannan munzilin ba. Babu ta inda Auren Asama'u zai haifar da ɗa mai ido. Ke kanki son zuchiyarki kika bi, amman ai Hibdu tafi ƙarfin haka a wajenki. In kika duba irin riƙon da taima ita Asama'u. A dai karɓa da Haƙuri kawai." "Ya'isa Halima shi aure raine dashi fa. Ni tun farko auren bai kwanta mun ba, kuma naso in yi miki tarin tulin tambayoyi baki bani damar hakan bane. Yarinya ayi mata fatan alkhairi. Shi kuma ayi mishi godiya a bisa ɗaukar ɗawainiyarta da yayi tsawon shekaru" "Naji ya tashi ya fita ko a lahira bana fatan sake haɗa idanu dashi. Kuma kada yayi tunanin sake yin wata hidima da Asama'u tana da gata ba irin yadda take tunani bane. Allah ya isa tsakanina da Hindu" Halima fa ta shaƙa har saida tayi kwakwazon da abokan zaman nata suka san halin da ake ciki. Alhaji ya ja Mijinyawa da Qasimu har cikin motarshi. "Kayi haƙuri kasan Halima ni kaina haƙuri nake yi da'ita. Hatta abokan zamanta haƙurin suke yi da'ita. Dan Allah kuyi haƙuri in da hali ka daure ka mayar da Asama'u ɗakinta mana" "Babu damuwa na fika sanin halaiyar Halima ba tun yanzu ba. Halin dawo da Asama'u babu shi har abada ayi haƙuri kawai" "To shikenan babu komai ka gaida yaran da kowa da kowa" Nan sukai sallama ya fito a motar, mijinyawa da Qasimu kuma suka kama hanya. Sai yake jin kamar an sauke mai wani gingimemen dutsene a kanshi. Ya kashe wannan ɓangaren amman yasan ya bar baya da ƙura ko yaya zasu kwashe da Nanno kuma bai sani ba, ga kuma Hindu daya fi kowa sanin irin taurin kanta da kafiyarta. Duk da haka cikin nishaɗi da nutsuwa yake tuƙinshi har ya shigo kano da daddare sai hira yake zuba ma Qasimu Sai dai me zai biyo baya? Mrs BUKHARI _Idan kika sai littafinnan nawa mai suna TSURON TSIRIN TSANDAURI tamkar kinyi sadakane kai tsaye a asusun marayu._ _Littattafaina kuɗinsu sadaukarwane ga iyayen marayu har zuwa ranar da zan dena rubutu._ _Ko nawa kika cire kika saka marayu zan yima hidima dashi wallahil azeem ko kuɗin Data bana cirewa a kuɗin littattafaina, marayu kaɗai nake yima hidima._ _Saima ƙarawa da nake yi da kuɗin kasuwancina akan kuɗin da littafi ya samar mun._ _Kuzo ku siya mu samu ladan marayu tare daku, ga lada, ga karatun littafi Hajiya._ _Wannan link ɗin na ƙasa ɗaya ne daga cikin aikin da nake yi da kuɗin wajen hidimtama marayu, shafin gidan Rediyo, da talabijin na ZINARIYA TV jos ne suka ɗaura domin sun kai ziyara a lokacin da aikin tallafin yake gudana._ _Nayi hankane ba dan riya ba sai dan ina cewa marayu nake ma hidima da kuɗin, amman ku baku taɓa gani ba, shi yasa wannan karon na zaɓi ku gani, daga yanzu kuma zaku dinga ganin dukkan aiyukan da nake yi da kuɗaɗen littattafaina, hakan zai ƙara mana ƙarfin guiwa __Daga ɗari bakwai zuwa sama yadda kike jin zaki iya zubawa baki faɗi ba saima romon lada da zamu samu a tare_ _Mu tausayama marayu wallahi marayu suna cikin wani hali na ni ƴasu, har jari ina tallafama da iyayen marayu jarin ƙananun sana'a domin dogaro da kai_ Nagode sosai son so