TSURON TSIRIN... TSANDAURI.. HARƘA TA UKU LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI JAMA'A BARKANMU DA DAWOWA BAKIN DAGA💪🏼💪🏼 Ina so nayi amfani da wannan damar wajen miƙa saƙon gaisuwa, da godiya a gareku masoyana na haƙiƙa. Ƴan bati ban barku a baya ba, kuna ƙure kwament sosai, ina yinku, tabbas na san soyayya ce har ta jaku zuwa bibiyar aikin ina godiya son so💪🏼 Hindu Suna kwance a tsakar gida magashiyyan, cikin neman agajin al'umma. Sun shallake lokaci mai tsayi, irin lokacin da bazai kwatantu ba. Amman dai sun daɗe sosai kafin Allah yayi ikonshi akansu. GIDANSU HINDU:. Baba Sojanmu ne ya fito cikin riga da wando, yayi zanzaro, ga hula mai fesinkab ya saka, ya nufi ɗakin Innah Ruwayya yana ɗaura agogo a hannunshi, Innah Abida na kallonshi dan tasan kwananta ne. Cikin shirin fita ya tadda Innah Ruwayya. "Sai ina naganki cikin shirin fita? " "Wallahi kuwa, akwai wani taron mata ƴan kasuwa, ƴan gwagwarmaya da zan halarta, ina daga cikin baƙin da aka gayyata, zan yi magana akan yadda ake tattala uwarkuɗi har a kai matakin nasara, mancewa kayi kafin in fita girki ai na shaida maka. Qazzafine zai kaini, motata tana gajeri har yanzu. Ina tunanin saida motarnan zanyi, Akarami yai mun ciko in sauya wata." Kai ya girgiza yayi jim, can yace. "Abinda za'ayi shine, muje ki rakani gidan Hindu Yahuza tunda yazo sai ya kaimu, Qazzafinma zai bi bayanmu, in muka gama abinda muke yi sai ya wuce dake shi Qazzafin, Yahuza kuma ya zai wuce dani wani taron tsofaffin sojoji. Kawai naji inason in kai mata ziyara, nayi mafarki mara kyau a kanta gaskiya da iyalanta, jiya ban yi baccin kirki ba, mafarkin yana da sarƙaƙiya" Shiru Innah Ruwayya tayi sai kuma tace. "To muje daga can Qazzafi ya kaini wajen taron ba damuwa" Ɗakinta ta rufo suka fito, daidai shigowar Yahuza. Qazzafi yana zaune abunshi a falo yana jiran Innah Ruwayya. Innah Abida na zaune tana shan kunu ga masa taji miya shane_shane a gabanta. Innah Turai ma tana falon tanai ma Tahira kitso. "Sannu da fitowa Janaral" Cewar Innah Turai kenan. "Yauwa Turai mu zamu fita. Kai Yahuza muje ka kaimu gidan Hindu ni da Innarku, Qazzafi ka biyo mu a baya kai" Uhum Innah Abida bata ce ba, kallo wannan basu isheta ba sam. "Tahira ƴar Fulani kitso akeyi kenan, ya karatun naki dai" "Karatu Alhamdulillahi Baba Sojanmu, karatu kam yazo ƙarshe sai batun bautar ƙasa kuma, bamu san inda za'a turamu ba" Yahuza yace. "Gashi duk ma inda aka turaki Baba Sojanmu ba ɗaga ƙafa sai kinje, shima ilimine ni a Taraba nayi nawa, kuma na haɗu da mutanen arziki acan sosai, shima ilimine mai zaman kanshi, bawai mutum ya ƙunshe kanshi yace sai a garinsu shi zai yi bautar ƙasa ba. Qazzafi a Fatakwal yayi nashi, shima haka yaje ya gamo ya dawo" Dariya Baba Sojanmu yayi kawai, tare da sa kanshi bai ko kalli Innah Abida ba, rikici take ji, jiya saida allurarshi ta sojoji ta motsa ya kusan raba dare yana turanci ma manya_manya, fitina take ji ƙaƙas. Innah Ruwayya da Baba Sojanmu duk motar Yahuza suka shiga, Qazzafi na biye dasu a baya, ya dai fahimci gidan Hindu za'aje. Suna tafe a hanya Baba Sojanmu na hirar barikin sojoji da Yahuza, yana shaida musu a shekarun baya lokacin mulkin soja irin daɗin da akaji, da irin aikin da su suka yi haiƙan, da kuma irin kwantar da tarzoma da aka tutturasu har zuwa wasu ƙasashen ma, ya zaga Najeriya sosai da sosai shi yasa yake da wayewa mai yawan gaske. Da wannan hirar har suka isa ƙofar gidan Hindu. Babban abinda ya basu mamaki ganin get ɗin gidan a buɗe shine abu na farko na al'ajabin da suka soma karo dashi. Na biyu kuwa shine suna danna hancin motarsu suka hango Hindu da Azgar a yashe a ƙofar shiga cikin gidan, ga akwati babba da jaka yashe shima. Motar Qazzafi bata samu shiga ba, a waje ya ajjiyeta ya fito da sauri. A guje suka fito a motar, Innah Ruwayya ta shiga jijjiga Hindu wacce bata ko motsi, jikinta ya sandare sosai ta zama kamar itace. Qazzafi yayi kan Azgar shima a sanƙamen yake, yana jijjiga yaron, yana kallon Hindu Innarmu na jijjigata. "Yahuza a sasu a mota mu wuce asibiti kawai dasu maza. Maza mu wuce asibitin cikin barikin Bukavu (Armed forces Specialist Hospital Kano) Cikin gaggawa asa kasa su Hindu a mota. Azgar na cikin motar Qazzafi, Hindu na cikin ta Yahuza. Innah Ruwayya ta shiga cikin gidan tana kwaɗama Sabira kira jin shiru, ba Sabira ba Mijinyawa ya tilasta mata fitowa, tare da kulle gidan suka fice Yahuza ya dawo ya rufe get ɗin gidan suka wuce kai tsaye asibiti. Dama asibitin cikin bariki suke amfani dashi a gidan, duk da ritayar Baba Sojanmu, kuma yaran sun yi girman da babu inshorar lafiya a kansu. Amman ana samun lukawa ta musamman, da magunguna masu kyau a asibitocin sojoji. "Kinga inata neman wayar Mijinyawa bata shiga kwata_kwata, kuma basa ce mun suwich ob. Allah yasa lafiya, duk da bai yi kama da lafiyar ba. To ita Sabira ko tana tare da ubanne oho" Innarmu tace da Baba Sojanmu. "Kaci gaba da gwadawa ko Allah zaisa a dace. In bata shiga ba, zuwa anjima sai a kira abokin tagwaitakarshi ai." Dukkaninsu hankalinsu baya tare dasu sam, a haka suka isa Asibitin Innarmu na bayan mota tare da Hindu. Qazzafi shi kaɗai aka bari da Azgar tsabar ruɗewane kawai. Nan da nan aka basu gado tare da cike_ciken duk daya dace ace anyi. Suna zaune a falon jira basa iya cewa uffan, sai Yahuza dake ta faman waye_wayenshi da jama'arshi. "Baba Sojanmu nace akwai wani abun da za'a kawo muku daga gidane? Dan da dukkan halamu yadda muka kawo su Hindu asibitinnan dole gadone ma za'a basu gaskiya. Kuma da gani ba lafiya, kai ina babu lafiya wani babban abu ya faru. Innarmu wai baki lura da akwatuna a tsakar gidan Hindu ba, gashi ba Mijinyawa, babu motarshi, Sabira ma bata ciki. Kuma yaran Hindu daga gida sai makaranta, ko can gida kaɗai suke zuwa" "In naga Akwati sai me Yahuza? Ya yarinya tana halin rai kwakwai mutu kwakwai amman kana kawo mun wasu irin maganganu marasa kan gado, ko dan dai ita Hindu burin kowane yaji matsala a gidanta. Abu shekara sama da ashirin an kasa zubar da makaman yaƙin haka? Ka fita idanuna na faɗama" Cikin fishi take maganar, a fuskarta babu wargi. Amman a hakan Yahuza yace. "Wallahi ba haka bane ba. Hindu ai ƙanwatace ta jini, abinda duk ya sameta ni ya sama fa. Ba abinda kike tunani bane" Ya ƙarashe murya ba kuzari. Baba sojanmu dai sai kallonsu yake yi, ya harɗe hannayenshi du biyun a ƙirjinshi yayi kurum. Qazzafi shima yayi shiru baya iya cewa uffan, zuchiyarshi sai zillo take yi mishi. Yahuza yace da Baba Sojanmu. "Ni zan tafi, ko abincine sai a kawo, zan sanarma su Innah" "A, a da dai ka barshi, Hindu ai tana da miji shine a haƙƙu ya sa a kawo mata abinci. Jeka uzirinka Yahuza shikenan" Cewar Baba Sojanmu da yake sake kwada lambar mijinyawa. Innarmu kuma tana waya da Saratu ne akan dai batun Hindu da Azgar, tana sanar mata ta faɗama sauran ƴan uwan nata. Kuma ta tawo musu da dadduma, da abinci, da ruwan zafi. Yahuza ya saka kai ya fita, yana ma Innarmu magana tayi biris dashi. Baba sojanmu yayi mata murmushi na ƙauna tare da ci gaba da gwada lambar mijinyawa. Har su Saratu da Rayya suka iso, lambar mijinyawa bata shiga. Har likita ya kirasu Baba Sojanmu, da Yaya Saratu, da Qazzafi ne suka shiga. Ananne yai musu bayanin dukkansu suna cikin wani hali gaskiya. Shi dai Azgar hawan jinine ya kamashi kuma jinin nashi ya hau sosai. Ita kuma Hindu ana kan bincike tukunna. Amman duk an musu allura suna bacci, kuma ana ƙara musu ruwa. "To shikenan likita mun gode sosai. Da fatan dai babu damuwa zamu iya shiga duk mu gansu? " "Eh sir. Zaku iya shiga ku gansu, amman kar ayi wata hayaniya a kansu, ko doguwar magana haka" Tunda suka fito suka sanarma Innarmu, tasan akwai matsala jikinta tabbas ya bata matsala. Kuma tabbas ita Hindu ciwonta bana asibiti bane duka, dole akwai buƙatar a karɓo mata rubutu a shasshafa mata. To amman abinda duk ya ɗaure ma kowa kai menene haɗin saurayin mai shirin zuwa bautar ƙasa da hawan jini, tunda shi galibi ciwone da damuwa, da tashin hankali ke haifar dashi. Tambayar da dukkanninsu suke ma kayukansu kenan, gasu a tsaye a gaban gadon Azgar, wanda lokaci guda ramarshi ta fito, idanunshi a faɗe ga busassun hawaye a gefen idanunshi na hagu. "Allah ya basu lafiya. Innarmu an sanarma ƴan gida kuwa, ko in faɗa a zaurenmu?" "Hmmm ana takai wa yake ta kaya. Duk da nasan Yahuza konfam ya faɗama Uwarshi, nunawa dai zata yi bata sani ba. Ki sanar a zauren kawai. Baba sojanku kuma ya sanarma da iyayenku maza ɗazu" Yaya Saratu tace. "To Allah ya kyauta. Yasa muji alkhairi. Gashi wayar mijinyawa bata shiga har zuwa wannan lokacin. Ni ca nayi ba mamaki ko tafiya jama'are suka yi shi da Sabiranne? " Rayya tace. "Nima nayi zargin hakan. Tunda sun taɓa tafiya tare lokacin waccan baƙar kadarar Asama'u na matsayin ƴar Hindu, da'ita aka haɗa aka tafi. Shine dalilin da yasa wayarshi bata shiga babu shakka. In ya samu nutsuwa zai kira, sai dai inje gidan in ɗakko wayar Yaya Hindun mu riƙe, Azgar dai wayarshi tana hannun Yaya Qazzafi." Ajjiyar zuchiya Innarmu tayi. Duk da ma dai hankalinta bai kama hakan ba sam. Amman tana ji inama Allah yasa hakanne. To in ta tuno akwatuna da suka gani a tsakar gidan, da get da suka tadda a buɗe, tabbas wani abunne ya faru wanda bazai ma zukata daɗi ba. Tana fatan Allah yasa ba zaman bane ya ƙare ba. Dan in zamane ya ƙare shikenan magana ta ƙare, akwai masu zuba ruwa a ƙasa da yawa su sha. To amman a lokacin da ya auri Asama'u da zafi zafi basu rabu ba, sai yanzu kwatsam, ko dai wani abunne ya kuma faruwa, ko kuma akan gidanta ne rikici ya haɗasune, ko dashi, ko da uwarmijin tunda dama taƙi jinin Hindu. Muryar Yaya Saratu ce ta dawo da'ita cikin hayyacinta. "Kuje Innarmu ni sai in zauna dashi, Rayya ta zauna da Hindu, Qazzafi ya kamata ya tafi shima, ya tafi daku ma ke da Baba Sojanmu, tunda duk an gaggama komai ku tafi gida kawai." Shigowar Rayya da Baba Sojanmu ne yasa suka juyo shi dama a wajen Hindu yayi zamanshi, shi da Qazzafi, lokacin ne ya shigo duba Azgar ɗin. "Saratu mu zamu tafi akwai yaron da zai mayar damu gida. Nayi _nayi da Qazzafi yazo ya mayar damu gida. Yaronnan yaƙi, yace bazai iya tafiya ya bar Hindu a halin da take ciki ba. To yana da gaskiyarshi in akayi la'akari da irin shaƙuwar dake a tsakani. Bayan la'asar ma zo da iyayen naku duka. Kuci gaba da tirai ɗin lambar shi Gawata, nima zanci gaba da gwadawa, in bata shiga ba har yamma, to sai a tura Qazzafi yaje can tsohon gidan nasu, ya sanarma buyunshi halin duk da ake ciki, anan zamu ji labarin shi mijinyawan da Sabira suna inane. Ibin do inaji a jikina akwai furobilem babba. Ruwayya muje ko?" Tafiya suka yi suka barsu cike da alhini. Rayya da Zubaina, da Qazzafi, suke wajen Hindu, Yaya Saratu tana wajen Azgar tana tubkewa da warwarewa, amman ta kasa tuno menene matsalar, ga dai matsala tana gani tasan akwai. Ga yaro ƙarami ya kamu da hawan jini. "Hmmm Asama'u. Wai ka reni macijiya a gidanka, ya girma ya haɗiyeka kai da zuriyarka. Ta ina Asama'u zata samu farin ciki da nutsuwa a duk ma inda take. Ohh ni Saratu Azgar da hawan jini, yaro mai haƙuri da tausayi kamar ba Hindu ce uwarshi ba, tamkar ni na haifeshi. Allah ka kawoma wannan ahali taimako" A ɗakin Hindu kuwa, Qazzafi yana tsaye idanunshi akan Hindu, sai kallonta yake yi yana mayawa. "Zubaida bana jin lafiya. Jikina yana bani tamkar Hindu lokacine yayi da zata zama tawa. Ina ji a jikina tamkar rabuwa suka yi da Mijinyawa gaskiya. Ga kuma a halin da muka je muka taddasu, ga akwati da jaka a yashe a ƙasa. Wayar Mijinyawa bata shiga, ga Sabira ba'a ganta ba. Kai ina zuwa bari kawai inje tsohon gidan nasu, inji menene yake faruwa ai ba zasu rasa sani ba, kuma lallai inaso inga Mijinyawa." Yana gama faɗin haka ya fice a mugun fusace. JAMA'ARE:. Komawa Jama'are ainihin labarinsu na baya. Mun tsaya a daidai lokacin da suka gurfana a gaban Nanno bisa wa'adin da aka yanka musu ya cika. Na ko ciki ko saki da fatan kun tuno ko? Yauwa. HINDU:. Bayan mun zauna, sai ga Uwatale, da Yaya Salihu, harma da Shafa, ita Uwatale wai tana wakiltan Mijinyawa babbane hmmm kuji wani abu. "Yanzu wa'adi ya cika yau ɗinnan, da fatan ka tawo mun da takaddar Hindu ko? Dan wallahi babu gudu babu ja da baya matsawar batai ciki ba, saki ya tabbata a kanta babu kokonto. Kai kuma aure ya tabbata a gareka, kuma tabbas babu kome a tsakaninka da Hindu abadan, ko da kuwa bayan bana numfashi ne. Tunda dai kai baka da hankali baka sanma inda yake maka ciwon komai ba. Ga Uwatale nan juna biyu gareta a yanzu haka fa, tana neman cika gida tabb da ƴaƴa. Amman kai ka ƙare a wannan mai ciwon, sai azaba makaranta suke gana maka. Bakwa wannan ƙauyen ba kwa wancan ƙauyen" Yaya Salihu yace. "Abi a hankali Nanno, tunda dai wa'adi aka basu, kuma lokacin ya cika. Duk wannan tashin tashinar bata taso ba, tana da ciki ko bata dashi, mu shine abinda ya zama maƙasudin haɗuwarmu anan. Hatta su iyayen ita Tsahare abinda suke jira kenan, ko jiya munyi taɗin da Balaji wanta akan batun Auren nasu, dama cikar wa'adin." Yaya jamila tace. "Ai bata da wani ciki ma, yaushe makaranta zasu barta ta haihu. Ai ya miƙo takaddar mu shaida kawai" Harna buɗe baki zan yi magana tare da yinƙurin zan miƙe. Carab mijinyawa ya damƙe hannayena, na koma na zauna. Ajjiyar zuchiya ya sauke, tare da cewa. " Nanno ina neman afuwarki, tare da ƴan uwana baki ɗaya. Ni da Hindu muna son junanmu sosai, ba zamu iya rabuwa ba, tayi mun halaccin da harshe da haƙori bazai iya faɗa ba. Allah ya amsa adda'ar da mukai ta yi. Allah ya azurta Hindu da samun juna biyun, ma'ana tana da ciki." Sai yai ƙasa da kanshi, yana sauke numfashi mai sanyi. Idanuna na lumshe kawai, nayi guntun murmushi kawai. Ban taɓa zaton mijinyawa zai amince da ƙudirina ba, tunda har muka kwana muka tashi baice komai ba. Lallai ya yarda ya shirya rayuwa tare dani. Nima babu gudu babu ja da baya kuwa. Daga duniya har ƙiyama can cikin Aljanna maɗaukakiya" "Me kace cikin haihuwa ita Hindu ta samu, bata samu tuntuni ba sai yanzu. Ya akayi kuka gane tana da cikin, asibiti kuka je ko yaya akayi, ko dai gidoga zaka yi mana?" Cewar Shafa wacce take riƙe da haɓa. Surukai masu fada kenan a wajen dangin miji. Ni a nazartarsu da nayi sam ba haka dukkansu suke so ba, sakin lallai suke so, rabuwar suka zaɓa muyi shi yasa suka ɓullo mana ta haka hmm. Uwatale kuwa har guntun tsaki ta ja, tare da ɗauke kanta zuwa gefe. Yaya Jamila tace. "To kunyi shiru, ku amsa mana wannan tambayar mana. Yaushe aka samu cikin ne, kuma ya akayi aka gane da gasken gaske cikin ne ba ƙaton kashi ba?" Saina ƙwaceshi ta hanyar cewa. Ni ai macece, kuma a bisa ƙa'ida mace na gane tana da juna biyune, daga lokacin da al'adarta bata zo ba, da kuma sauyi da zata ji a jikinta. To wata uku kenan banga al'adata ba" Wannan maganar fuskata a sake, ta cikina kuma ina jin wani baƙin ciki, ga Yaya Salihu a zaune ana irin wannan maganar. Dashi da mijinyawa kunya tamkar zasu nitse a wajen. Ɗakin ya ɗauki shiru na wasu lokuta kafin Nanno tace. "Shikenan ciki dai watanshi uku, ko biyu kenan za'ace. Munanan muna ƙirge daga yanzu har wata bakwai, ko takwas, inma shekaraune dai duk za'a haifa. Kuma nanda wata biyu ai ciki shi ɗan dumane zai fito ɓaro_ɓaro. Allah ya sauketa lafiya, kun haye wannan siraɗin. Sai ki kiyaye aiyukan ƙarfi kinga dai da yadda kika samu cikin. Sannan wannan koyarwar sai a haƙura da'ita zurga_ zurgar tayi yawa. In kika ji kina son wani abun ci ko sha sai ki mun magana, ko Uwatale" Ta ɗan sassauto muryarta, amman fa babu soyayya ko wani jin daɗi a yanayinta gaskiya. Haka dai akace ni an sallameni in tafi. Miƙewa nayi na fice na koma ɗakina. Saina shiga zurga_ zurga a falo ina goye da hannayena. Tabbas wannan lamarin akwai haɗari a cikinshi, to in ba'a dace da jaririn ba kuma ya zamu yi, ga ciki ance akwai iyakar daɗewarshi shekara gudane rak. Saina ƙwarara kaina akan lallai za'a samu muddin muka je gidajen marayu, zamu samu in sha Allah. Ajjiyar zuchiya na sauke, tare da lumshe idanuna ina hasaso da yanzu shikenan ni da mijinyawa ya ƙare fa kenan. Wannan kyakkyawan ginin soyayyan akeson a rushe mana hmm. Amman batun dena zuwa koyarwa baima taso ba, babu abinda zai mun shamaki da aikina gaskiya, bazan ma soma wannan gangancin da kuskuren ba. To inna zauna muci me? Gashi nan da wata takwas za'a tawo suna daga gidanmu. Miƙewa nayi, naci gaba da zagaye, zuchiyata cike da taraddadi. Ina tsaye mijinyawa ya shigo da sallamarshi. Matsowa yayi ya jawoni jikinshi muka yi shiru a jikin juna, ajjiyar zuchiya kawai muke ta aikin saukewa. Mun jima sosai a hakan kafin ya kamo hannuna muka zauna a kan kujera tare da fuskantar juna. "Tutar so, bazan iya rabuwa dake ba. Kinga wannan hannun bazai taɓa iya rubuta miki wannan kalmar mai raba masoyaba abadan. Ni nakine abadan, bazan taɓa iya haɗa ko wacce mace dake a zuchiyata ba. Halaccinki gareni babbane. Duk da nasan abinda kike so mu aikata haɗari gareshi, bana ma tunanin yiyuwarshi, ina tsoron ranar tonon asirinmu. Ranar da zan bar duniya, ko ke ki bar duniya. Wannan rana itace ranar fallasa da tonon asirin da zamu fuskanta mai girma. Da ace ɗan da baka haifa ba yana iya gadarka da wannan asirin na har abada zai zama. A hakanma Hindu kisan duk yadda zaki yi mu ɓoye wannan sirrin. Gadonma inta kama a raba da wannan yaron ko yarinyar. Amman tukunna ke kin tabbatar zamu samu jariri ko jaririya a gidan marayu, suna bayarwa?" Murmushi nayi, na kamo hannayenshi na riƙe. Nagode da wannan rufin asirin da kayi mana. Ɗakko jinjiri ko jinjira a gidan marayune kaɗai zai bamu damar kasancewa tare. To tunda bamu san yaushe Allah zai bamu haihuwar ba. Amman ka daure muje asibiti gobe ayi mana gwaje_gwaje da kyau dan Allah. Sannan inaso in mun shiga garin mu nemi Harira muji duk matakin da akebi dan ɗaukan yaro a gidan marayu. Sabida musan shirin da zamu yi tunda wuri ko?" Hancina ya lakace mun muka yi dariya. "To shikenan mai juna biyu. Sai ki bi komai a hankali. Kar ki mance da yin laulayi naku na mata, ni kuma duk zan sanar ma abokai. Batun asibiti da dai kin bari ba sai munje ba. Tunda dai ke kinje ba ɗaya ba, ba biyu ba ai shikenan." Aa kaima yana da kyau muje tare. Ai ko a maganine zasu iya ɗauramu wata ƙila. In suka sake tabbatar mana bamu da matsala ai shikenan" Shiru yayi na ɗan daƙiƙa kafin yace. "Allah ya kaimu goben ya kuma fishshemu jin kunya. Yasa ba kuskure zamu aikata ba." Shi ya tattayani muka maida kayayyakin da duk na hautsina, bamu muka gama ba sai azahar. Na gaji bazan iya girki ba. Garin rogo na jiƙa mana, ya shigo mana da soyayyan kifi gammo biyu Abdulƙadiri ne ya siya yace a kawo ma mai ciki. Har ya fesa musu ina da ciki. Abun almara har mata daga maƙota wai suka shigo suna taya Nanno barka da samun arziki. Hmm ƙauye garinsu kare. Iyayen yarinyar da aka ajjiye da sunan wa'adi ya cika. Suma suka zo ma su nanno da rikici akan su an ɓata musu lokaci ake nufi a banza. Ina zaune mijinyawa na ɓare mun kifi, ina ci in kora da garin da babu sikari, ba ƙuli bare gyaɗa, mukai ta jiyo rikicin su nanno. Uwatale ce ta leƙo wai kiran Mijinyawa. "Wai baka ji anata rikici duk a kanka ne? Ohh mata tayi ciki kuma sabuwar tarairaya sai abinda ka mance, yanzu abincinne kake bata a baki." Dariya kawai yayi mata. Itama a sigar zolaya ta nuna tayi maganar. Amman ni a zahiri nasan da gasken _gaske take. Uwatale manyan magulmata kenan. Miƙewa yayi zai fita nace. Kayi zamanka me zaka yi musu to in kaje" Na faɗa a shagwaɓe, ba shiri ya gyara zamanshi. Ba shiri uwatale ta fice haɓa a hannu baki a wangale. Da daddare shi da kanshi ya dafa mana wata shinkafa da mun mance da'ita sanadiyyar tattare kayane ma na ganta, da guntun taliya. Sabida son tabbatar da ina da ciki. Mijinyawa na ba kwano yaje wajen Baraka ya karɓo mun jallof ɗin taliyar manja tako ji kifi, harda daddawa a ciki. Ita muka ajjiye akan da safe maci, sabida abinda zamu ci ma babu. Ɗan kuɗin motar dana harhaɗa dashi zamu je Bauchi kuma zamu je asibiti. Ɗan abinda ya rage sai mu ɗan cefana cefane kafin ayi albashi. Muna kwance muna hirarmu cikin soyayya. Wai ni kam da mun rabu yanzu kana cikin wanne hali sai Allah. Ni kam uwar haka gidanmu ya ɗauka, ko ince unguwa ta ɗauka." "Ai ni kam da yanzu kusan ina asibiti ma cikin rashin haiyaci rai kwakwai mutu kwakwai. Kinsan Allah bazan iya rayuwa in buɗe idanu ban ganki a kusa dani ba. Kuma wai kina raye, nima ina raye. Ƙila ma har kije ki auri wani in zama tarihi a cikin rayuwarki" Dariya na saka na shige jikinshi. Haiƙan ya nuna kishinshi akan hakan, har muryarshi na sauyawa. Daga haka labarin ya canja salo zuwa can_ can sama jannati. Washegari da wurwuri muka shirya. Kunsan Allah itacen da zamu yi ɗumame babu. A haka muka ci abincin Baraka. Taliyace duk ta danƙare a cikin romo, ta yi danƙo, a haka muka tuttura. Muka kakkaɓi ruwa muka fito. Ni a bakin ƙofar fita na tsaya ina jiranshi. Shi kuma yaje yi ma Nanno sallama. Ya ko daɗe, daɗewar da har saida raina yayi mummunan ɓacin da ko da ya fito yazo inda nake, Bance dashi komai ba, kai har saida muka shiga motar Bauchi kafin yace. "Wai Tutar so fishin daɗewar tawa kike yi ne? Haba Tutar so aimun afuwa kinsan sha'anin Nanno sai a hankali. Wallahi a hakanma saida na ɓata mata ranta sosai. Aimun afuwa" Ya kafeni da idanunshi shaƙe da kwalli. Murmusawa kawai nayi, shi kuma ya sauke ajjiyar zuchiya. Da muka isa Bauchi kai tsaye muka tare abun hawa zuwa gidan Harira da adireshin data bani. Sai da mu ka ɗan sha wuya kafin aka gane gidan da muke nema. Ina shiga da sallama na tadda Harira a tsakar gida tana wanke gidan. "Ahhh malama Hindu kece a tafe. Ashe da gaske kike zaki zo? " Dariya nayi mata muka ɗan rungume juna. Wallahi Harira kin dai ganni. Tare muke da mijina. Ina wannan hirar da muka taɓa yi dake a makaranta akan ɗakko reno a gidan marayu? " "Naji naji" To itace ta kawoni, ina fatan zan dace? " Hannuna ta ja muka shiga ɗakinta. Zama nayi a kujerar dake fuskantar nata. Wani matashi dake taje kanshi ya gaisheni ya fita. "Kin ganshi shine yaron da gidan marayu suka bani. Kinga ya girma shekara sha uku fa." Harira tare nake da mijina a waje. Muna son ɗaukar jariri sabuwar haihuwane. Sai dai namu ya bambanta da naki. Mu zamu ɗauka ne mu nuna shi a matsayin ɗana dana haifa, ba kamar naki da kowa yasan a gidan marayu kika ɗakko shi ba. Amman Harira a rayuwarnan ciki ba dan tuwo kaɗai.... ' Hannunta ta ɗaga mun tace. "Ya isa malama Hindu. Ai wannan babban sirrine da ya zame mun dolon doliya in rufe muku shi. Nafa san zafin rashin haihuwa. Na kuma san zafin gorin haihuwa kin manta ne? Banfa taɓa haihuwa ba, ko ɓari ban taɓa yi ba. Nice nafi cancanta da in rufe miki wannan sirrin. Sai dai wannan abun yana da hatsari sosai Hindu. Ki sake tunani da kyau tukunna. Amman kafinnan ki mai iso ya shigo sai mu tattauna baki ɗaya, a tsayar da matsayar da za'a cimma nasara. Jarirai sabuwar haihuwa baƙar wuya suke yi alal haƙiƙa" Shiru nayi gabana na dokawa da jin tace jarirai na wuyar samu. A sanyaye na fita wajen mijinyawa, nai mishi iso muka shigo tare. Bayan sun gaisa da Harira sai tace. Mrs bukhari ce To sai mun haɗu kuma gobe in mai duka ya amince. 💪🏼💪🏼💪🏼MRS BUKHARI .. "Naji abinda duk yake tafe daku, amman sai dai akwai wani hanzari ba gudu ba. Ɓoye wannan sirrin abune mai ɗan karen wahala. Kasan yawancin mata a jama'are a gida suke haihuwarsu, suna dai shiga asibitin azare a duba lafiyarsu, shima ba kowa ba. To ya zata yi da batun bayyanar ciki, da canjawar da masu ciki suke yi na yanayi, gara ma laulayi zata iyayi, wannan bazai zama abu mai wahala ba. Gaku a gidan gandu, har mahaifiyarka da kishiyoyinta duk suna cikin gidan, ga facaloli. Duk ba wannan ba, in ɗaya a cikinku ya mutu ya za'ayi da batun gado, wannan shine babbar matsalar, wannan ranar itace ranar tonon silili, ranar kuka kuma. Akwai wanda na sani shekaru matsu tsayi a baya, a lokacin ilimi bai yawaita ba. Wata mahaukaciyace ta haifi yaron a rumfar gidan cikin dare, su kuma ita da mijinta su suka karɓi haihuwar, mahaukaciyar a wajen ta rasu suka riƙe yaron. Shi dai wannan yaron yaci gadonsu, tare da ƙannenshi wanda Allah yaba iyayen goyon nashi daga baya. Har gobe bashi da masaniyar basu bane iyayenshi ba. To ku ya zaku yi duk kun shirya?. Duk da nasan in sha Allah kafin wannan lokacin iyaye da manyan masu faɗe aji sun mutu, sai dai in Allah yaso gwada ƙudurarshi sai kai ka mutu, ko ita ta mutu ku riga iyayen. A wajen tashin hankali da tonon asirin yake fa" Kallona yayi, nima shi ɗin nake kallo ina nazari. "To ke Hindu kinji duk abinda akace. Kusan duk nima na jajjero mata wannan jawabin da kika yi. Musamman na mutuwar. Amman duk da haka ta nuna tana so. Ina ganin in abu ne mai yiwuwa samun jaririn, babu damuwa mun ɗauki hatsarin, matsawar zai faranta mata rai hakan, to ni babu wata matsala, ni kaina bani da burin daya wuce inga ranar da zamu karɓo ɗa a gidan marayun da sunan mu muka haifi abinmu" "To shikenan ke Hindu kinji fa abinda yace" Naji Harira, saida muka amince kafin muka zo. Dama munsan samun ɗan mutum sukun da guda abune da yake da girman gaske. Ban yi tunanin abune mai sauƙi ba gaskiya" Murmushi tayi tace. "To yanzu dai in sha Allah zan yi ƙoƙari in samu Hajiya Bara ƙanwar wacce ta bani wannan yaron Hannafi. Zan mata bayani in sha Allah sai ku dawo zuwa rana ita yau. Allah bashi In tayi mana iso sai in kai ku, in kunje sauran maganar sai ayi tsari da dokokin ɗaukar yaron abune mai yawa, kinsan yanayin duniyar sai a hankali, dokokin suna da tsauri. Ina zuwa to" Fita tayi ta bamu waje. Ni dai wallahi babu wani tsoro ko fargaba a raina sam. Mijinyawane ma ya sare, duk ya shiga ruɗu sai nazari kawai yake yi. "Kina ganin wannan hanyar zata ɓulle kuwa Tutar so? Kada mu aikata abinda asirinmu zai tonu. Kada kiyi tunanin ko bana son a ɗakko ɗa ko ƴar ne, wallahi aa ni kaina zuchiya ta kwaɗaita gaya da ganin jariri a kan kafaɗata ina jijjigawa. Wannan shine kaɗai dalili babba da zai riƙe igiyoyin aurenmu abadan" Zata ɓulle ai tsayuwar dare zamu dage dayi. Sai kaga Allah ya bamu namu kafinma lokacin wancan ɗin yayi. Ai komai na Allah ne. Shi ke da tasarrafi akan komai. Maji roƙon bawane, majiɓancin al'amuran bayine. Ina da yaƙinin Allah zai lamince mana, tunda ba saɓa mishi muka yi ba, ba kuskure zamu aikataba. Balma taimakone" Harira ce ta shigo da ɗumame da ruwan bunu ta dure a gabanmu. "Gashi kuci bamu ɗaura sabo ba. Nima dama Allah_Allah nake yi in gama in wuce wajen aiki sai gaku" Godiya nayi mata, ta fita ta bamu waje. A gaskiya bamu tsaya fulako ba, cinye abincinmu muka yi muka kora da ruwan bunu. Bamu jima ba mukai ma Harira sallama, kai tsaye muka wuce babban asibiti janaral. Muka tadda layi, zani ba zani ba har layi ya kawo kanmu, lokacin biyu harta gota, dan mijinyawa yaje yayo sallah ma ya dawo. Mun shiga muka tadda likitan macece, bayani nayi mata abinda ya kawo mu. Sannan mun taɓa zuwa asibitin sau ɗaya an bincikamu, amman mijinyawa dai bai kuma biyoni ba bare yaji ba'asin sakamakon nashi ba, duk da aikine babba ba wai zuwa ɗaya za'ayi a sanar dakai matsala ko akasinta ba. To itama dai gwaje_gwajen ta sake yi mana. Ta haɗa mijinyawa da likitan maza, akace in zamu dawo ya tawo da samfurin abinda ya dace a auna, aka bashi kwalba tsabtatacciya da zai sako a ciki. Rana ita yau mu dawo, a sake wani gwajin. Haka kurum wannan karon sai naji faɗuwar gaba kuma, tsorona Allah tsorona ace bazan taɓa haihuwa ba, gashi Allah ya jarabceni sosai. Sai dai ina kai kukana gareshi. Kafin mu shigo gida ragowar ƴan kuɗaɗen nawa haka na ƙundume muka yo jefane, nice harda siyan nama. A lokacin jama'are ta samu wutar nefa Alhamdulillahi, sai dai ba duka unguwanni ba, kuma ba wani kawo wutar akeyi ba, sai ayi sati babu, dake mu unguwarmu garine sosai muma akwai wuta. Kuma Yaya Salihu ya ja mana a cikin gidan namu. Sai mu kwan goma ba'a kawo ba wallahi. Amman dai babu laifi motsi yafi laɓewa. Ina kai ku, mun dawo mun tadda matan gida dana maƙota duk a gidan. Suna ganinmu aka shiga yima mijinyawa barka da samun arziki, harda masu kuma habaici da caɓa muggan magana. Ciki nayi babu wacce tama isheni kallo, balle in tanka mata. Uwatale na ƙofar ɓarayinta a zaune ta dasa kujera, ta ɗauki tagumi ta dasa. "Kun dawo, ashe bakya gidan? " Wallahi" Iyakata da'ita kenan. Ina kan buɗe ƙofar ɓarayina mijinyawa ya shigo, uwatale na ta faman bin ledoji da kallo. "Tsaya Tutar so, kinsan fa bake kaɗai bace. Bari inzo in buɗe miki mana." "Ahhh lallai Mijinyawa kace Hindu ita sai dai taci ta kwanta kawai. Buɗe ƙofarne ba zata iyaba. Sai kace a kanta aka soma ciki. Ai saina soma kakarin amai na shige da gudu, zuwa bayin tsakar gidana. Da gudu uwatale ta biyoni, mijinyawa ya watsar da kayan hannunshi ya biyoni yana ta faman sannu sannu. Kallonshi nayi muka yi murmushi, na rungumeshi. A kunnena ya raɗamun. "Kin ko kyauta kin aiki moɗa randa saƙon zai isa" "Sannu Hindu ko in shigo in taimaka miki ne? " "Aa uwatale kije kawai, ni aikin me nake yi da bazan taimaka mata ba" Ni dai buta ya miƙo mun na wanke fuskata na fito. Shi kuma ya cika bokiti da ruwa ya shaƙema banɗakin. "Sannu, uhmmm nace wani abun kika ci ne. Kinsan masu juna biyu ba komai suke iya ci ba. Ni wallahi nama yi tunanin duk burgace ba wani ciki, ashe dai tabbas akwaishi. Haha Allah ya inganta. Dan ko Nanno bata yadda akwai cikin ba. Ashe dai akwaishi, dan ban taɓa ganin kin yi amai ba" Ta saka kai. Ta fice. Hannun mijinyawa na ja muka shiga ciki, saida muka zauna nace. Uwatale fa sai mun san yadda zamu zauna da'ita. Duk wata maganar data danganshi cikinnan da batun asibiti, da batun gidan marayu daga yanzu ba zamu sake yinshi a cikin gida haka ba. Sai in mun fita, a hanyarka ta rakani makaranta sai mu yi" Hannayena ya damƙe yace dani. "Duk yadda kike so haka za'ayi Tutar so. Yanzu muje mu ɗaura girki, bari in karɓo itace" Nera hamsin na danƙa mishi ya fice, ni kuma ina tsakar gida ina jujjuye ɗan kayan abincin da muka siyo, ga nama na juye a tukunya, ina kan juye kayan miya ɗanye a basket Nanno ta shigo. "Haka aka koya miki a gidanku? Ya da ciki ƙarami jikinki zaki dinga durƙuso irin wannan. Alhalin yanzu uwatale tace kin gama amai? Abincin ma in kikai haƙuri sai su Shafa su dinga dafawa ana zuba miki, nan da wata biyu ko uku, zuwa lokacin cikin ki yayi wata biyar ko hudu yayi ƙwari, sai kici gaba da yin girkin ai. Amman fa sai abinda kuka ce" Har a fuska Uwatale bata ji daɗin wannan magana ta Nanno ba. Nima kuma har a cikin raina banso wai a dinga zubo mun abinci daga cikin gida ba, wannan ƙazaman ne ni zanci abincinsu. Aa zan dinga yi da kaina ko da a zaunane. Sabida ba ko wanne abinci nake iya ci ba. Zan dinga yi" "Au Allah. Kenan bakya so a dinga zuba miki, sabida dai kina mana kallon ƙazanta ko? " Uwatale ce tace haka. Ƙwarai da gaske hakane. Zan dinga girkawa da kaina" Na bata amsa sam ba hargowa, babu tsoro dan ba yankani za'ayi ba. Nanno tace. "Ba shakka. Ishasshiya, to kiji ki kuma ji, ni dama nayi hakanne dan in taimaka miki ke da kika samu ciki da ƙyar, kar yazo ya zube. Cikinnan na zubewa zaki tattara komatsanki ki kama hanyarki. Dan ni wallahi banso ma kika samu cikin ba. Ke uwatale wuce muje" Kundai ji da kunnenku abinda tace. Ita bata so ma na samu cikin ba. Ma'ana bata so haɗa zuriya dani ba fa kenan. Wanke nama na nayi, na jajjaga tafarnuwa da citta na zuba, na yanka albasa, na zuba dunƙule guda biyu na rufe. Ina aikina, ina jujjuya maganganun Nanno, da irin girman ƙiyayyarta gareni. Da ba dan mijinyawa na mun son da baya bashi da misalin musaltuwa ba, kuma nima ina sonshi, a zamanmu baya cutar dani, balma sai kyautatawa da tattalina. Wallahi da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba. Amman bazan hukuntashi da laifin danginshi ba. Mijinyawa da kanshi daya shigo ya haɗamun wutar na ɗaura tafashen nama. Na zauna kusa dashi da tiren tsintar shinkafa ya sa hannu ya karɓa" "Kije ki ɗakko takadda da biro ki rubutama su Innarmu wasiƙa Shehulle zai tafi kano gobe sassafe" Da murnata naje na yago takadda da biro. Shehulle wani maƙocinmune kuma abokin Mijinyawa Babbane. Direbane har gidanmu ya sani, in zai shiga kano ina bashi takadda yakai gidanmu, in zai dawo Innarmu takan haɗoshi da takadda da rigi_rigin kayan tsaraba. Tanan muke isar da saƙon junanmu. Wannan karon batun samun ciki shine yazo a layin farko bayan buɗewa da dubun gaisuwa, tare da fatan aikhairi maras yankewa. Saina labarta musu batun ciki, na kuma ƙarashe da gaishe_gaishen dana saba tare da tambayar Baba Sojanmu. Nace Innarmu ta sako mun man shanu in Baba sojanmu ya kawo. Duk dai abinda ya dace na rubuta, mijinyawa yasa a ajjihunshi zai kaima Shehulle in ya fita da yamma. Da taimakonshi nayi mana tuwonmu na gari, da miyar kuɓewa ɗanya. Naman gida biyu na raba, rabin na barshi a tukunya. Ina kammala girkin na kulle ɓangarena muka shige wanka tare da mijinyawa, abinda yafi so kenan. Muna fitowa ya wuce sallar magriba. Kasancewar yanayine na zafi sosai ɗinnan a tsakar gida na shinfiɗa mana daddaruma ƙatuwa, na jera mana kayan abincin namu. Wani sa'inma a wajen muke kwana gidan sauro kawai muke ɗaurawa, a gefe kuma nayi sallah ta. Ina raka'ar ƙarshe naji anata bubbuga ƙofar, kafin in sallame aka dena bugawa, ina durƙushe ina ɗiban rushi a kasko zan zuba turaren wuta naji yo muryar mijinyawa yana ambaton. "Ahh Baraka sallah inaga take yi fa. Kin bubbuga bata buɗe ba ko? " Da sauri na zuba turaren wutan, nazo na buɗe ina murmushi. "Ahh Malama Hindu kai Alhamdulillahi nayi murna da jin wannan kyakkyawan labarin." Hannunta na jawo muka shigo daga ciki. Mijinyawa ya shige falo mu kuma ya barmu a tsakar gidan. "Wannan turaren wuta naki wallahi ba dai ƙamshi ba. Ɗakina duk ya kama ƙamshi tun wannan da kika kawo mun tsarabarshi fa, inata cancanawa wallahi." Ohh na wajen Mrs Bukhari kenan, gaskiya kayan ƙamshinta ƙarshene. Wannan ma na wajenta ne ai" Kula mai hannu ta roba ta dure mun a kan kafet. "Ga abinci ƙila kiji sha'awarshi. Kuma Qasimu yace a dinga zuba miki abinci kullum dare daga nan har zuwa ranar da zaki sauka. In kika ji kina sha'awar wani abunma zaki iya faɗamun zan girka miki. Kinsan tsarabe _tsaraben ciki da yawa yake." Ahhh wannan nauyi da Qasimu ya ɗaura miki haka Baraka?" "Oo_oo ba nauyi bane. Tsakanin Qasimu da mijinyawa babu wani bambamci wallahi. Ɗazu da rana ma ai nazo na riƙo miki kwaɗon zogale Uwatale bata faɗa miki nazo bane?" Murmurewa nayi, ai ba zata taɓa faɗa ba. Na buɗe tuwo, ina kan zuba mata ne nace. Babu mamaki ta mance bata faɗamun ba. Ga tuwo da zafinshi kici" "Ahh zanci gaskiya irin yadda naga miyarnan da ƙamshinta dole tayi daɗi. Ni kam akwai wani ƙamshi da miyarki take yi na musamman dan Allah menene sirrin a sammun mana" Dariya muka yi. Ta ja kwanon tuwon ta soma yanka tana lumshe idanu. Sirrin kayan ƙamshine namu dai na gargajiya. Mu kanuri bama girki ba tare da mun sa tafarnuwa, citta, kanunfari, ɗiyan miya, masoro ba. Kinga masoro yana da wani irin ƙamshi na musamman wanda gaskiya ba duk mata bane suka san da wannan sirrin ba. To shine sirrina, sai barin miya ta dahu a nutsuwa. Tayi magana ta kasa, sai loma kawai take zubawa har saida ta gama kafin tace. "To kingani nima na dinga yin miyarku ta birni mai ƙamshi, duk da muma muna sa citta, amman tafarnuwa kam bama sawa. Itama ɗiyar miyar kam gefi_ gefi muke sawa, barinma ni ban taɓa amfani da'ita ba gaskiya. Amman kinga ita citta ai muna dakawa tare da daddawa, har a jalof inasa citta. Muna wannan hirar muka jiyo sallamar Qasimu da Abdulƙadiri. Da sauri miinyawa ya fito, ni kuma na sake gyara mayafina. Na koma gefe na shimfiɗa mana tabarma. Sai ko gasu sun shigo niƙi_niƙi da tsaraba. "Ga Tutar so ta Magawata ba da kanshi a sare yaje gida yace ya faɗi. Barka barka munji abun arziki Alhamdulillahi za'a haifo mana ɗan so, ko ƴar so" Abdulƙadiri yayi carab yace. "Mu dai koma me aka haifo na kama zan haɗasu auratayya da yarana" Ai sai wajen ya ɓalle da dariya, ni dai na dara kaɗanne. Amman zo kuga dariyar Baraka ɓaratatata. "Kai dallah. Aurenma da ko haramar yi baka yi ba. Zaka wani ce ka kama abunda za'a haifa. Ai ka bar mana dai kawai" Murmusawa yayi yace. "To zan iya bar maka. Amman nima inason haɗa jinina sosai da Mijinyawa kasan gudane da ɓari. Amman batun aure yana kusa kusa Allah na kusan fito muku da matar Aure. Hindu zan kawo miki kayan tarin nawa ma ki ajjiye a wajenki. Sabida Baba tafiya zata yi, kuma bata rufe ƙofa, kwanakin baya data tafi ganin gida kusan atampa uku aka sace mun datsa_ datsa." To shikenan Abdulƙadiri babu damuwa sai ka kawo. Bamu gaisa ba ma, ina wuninku, Abdulƙadiri ka dawo lafiya? " Nan gaisuwa ta gudana a tsakaninmu dai. Ledojin gabanshi ya turo mun wai tsarabace, Qasimu ya miƙo mun lemu da gwaiba cikin leda. Godiya nayi mishi, na ja hannun Baraka muka shiga ciki na basu waje suka ci tuwonsu. Turarukan wuta na mata haɗin gambiza dashi. A kwalbar man shafawa mai gurguwa. Saina bata jan bakin majigi ina dasu da yawa. Godiya tayi mun, tare muka yi isha da'ita a ɗaki su kuma mijinyawa suka fita zuwa masallaci. Baraka ita ta wanke mun kwanakun da su mijinyawa suka ci abinci, tayi mun shara kafin tamun sallama ta tafi. Kular da Baraka ta kawo mun abinci na buɗe. Shinkaface da miya, aka jangaɓa miyar akai ga dai nama zuƙu zuƙu. Ɗiba nayi inaci ina korawa da ruwa, a gaskiya bata wani iya girki ba, tsabta gareta sosai irin masu aljanun tsabtarnanne shi yasa ma nake cin abuncinta. Miyarnan janƙwab da ruwa a ƙasanta. Ina kan ci Mijinyawa ya shigo yana fara'a. "Uwar biyu kenan abincin akeci, kina ɗan jin daɗin bakin naki yanzu ko?" Zama yayi daf dani ya raɗamun cewar Uwatale na zaune a dokin ƙofar ɓarayinta. Bakina na taɓe kawai, yasa hannu tare muka ci abincinnan, a tsakar gida muka kwana. Washegari na kintsa bakwai da rabi na fito da zummar tafiya makaranta, Mijinyawa na rataye da jakata ciki da takaddun ƴan makaranta. Ai daga zuwa gaishe da Nanno ta dira tijara akan na bar zuwa karatu, nace mata aa fa zani makaranta ko dan rufa mana asiri. Nan ta dura tijara aka kaɗa aka raya, na kafe na ƙeƙashe wallahi bamu muka baro gidannan ba sai takwas na safe. Haka ya kaini makaranta na shiga aji, zuchiyata cike tab da saƙe _saƙen wannan lamarin. Gaga gaga gaga haka akaita tafiya, da daddare Baraka zata aiko mana da wadataccen abinci muci da daddare mu ɗumama da safe abincin rana kawai nake girkawa an rage mana wahala. Bayan kwana biyu da tafiyar Shehulle sai gashi da yamma sakaliya ɗauke da jakar bakko shaƙe da kaya, da zungurereyiyar wasiƙa. Ranar nayi murna sosai. Ina ciccira kaya, mijinyawa na karanta mun takaddar. Gaisuwace da taya murnar samun juna biyu, da kuma batun nan da watanni biyu zuwa uku tana son inzo akwai biki, sannan lallai tana son ganina kafin ace na haihu. Harda miya Innarmu tayo mun miyar jirgi, wato soyayyar miyar sutu wacce babu ruwa a cikinta, wannan wacce zaku ga har duhu tayi sabida suya, tana shan mai sosai kuma bata lalacewa ko wata zata yi ba'a ɗumama ba, muddin a tukunya take ba a robaba. Tako ji soyayyun naman saniya harda awarar nono a ciki wagashi in ji mutan togo. Ga bushasshen kifi him, gasu yajin daddawa, jan yaji, maggi mai sita da reko, da farin maggi, sai kayan ƙamshi tafarnuwa, masoro, citta, ɗiyan miya harda man shanu cikin babbar gora mai girman wan lita. Naga madara da furanto, da sikari masu yawa suma. Sai wani ƙyalle da aka nannaɗe ina buɗewa a hankali dubu talatin rafa uku ƴan ishirin ishirin sababbi miƙaƙƙu suka zubo. Daidai Shigowar Uwatale. Mayafina nasa na rufe duka kayan. Ai mun saba a gidama Innah Abida haka take ma Innarmu, muddin taga an shige da leda to sha Allahu saita bankaɗo labule ko sokiburutsune saifa tayi. Sai ta soma shirmen gangan tana yi tana sosa kai, tana dariya wai tazo ganin jikin nawa ne, haka ta fita ba guiwa. Mijinyawa ne ma ya samu zarafin mata magana, amman ni da idanu kawai na kakkafeta. Tana fita ya bita ya maida sakata. A tsakiyar wannan kuɗi sai ga wasiƙar Baba Sojanmu da turanci manya manya ya rubuta. Tabb daga layin farko zazzagane na faɗa. Akan batun makarantata, yanzu ance cikine dani tun bani da nauyin kowa mijinyawa ya ƙi cika alƙawarin da ya ɗauka. To wallahi ya rantse mun muddin na haihu Mijinyawa bai maidani karatu kamar yadda yake a sharaɗi ba, zan dawo gida in zauna har sai ya tara kuɗin makaranta kafin zai amince. Baba sojanmu yayi maganganu masu zafi da kaifi sosai dangane da yanayin yadda Mijinyawa ya saɓa mishi alƙawari. Ga ƴan uwana duk suna aikinsu, suna da albashinsu. Ni dai kasa fassarama Mijinyawa nayi wannan takadda, amman duk da haka yaga sauyi a yanayina bayyananne, sai bai tanka ba, shima illahirin jikinshi ya mutu. Rafa ɗaya na miƙa mishi a cikin kuɗin. Kai mana cefane zuwa gobe, wannan kuma sai mu adana, ga maganar jigilar zuwa Bauchi kaga Alhamdulillahi." Karɓa yayi yana murmursawa. Haka kuwa akayi washegari kafin in dawo makaranta mijinyawa ya siyo mana cefanen duk kayan buƙata, ya siyo itace da yawa wai ya samu wani abokinsune shi ne ya jibga mishi wannan itace. Nako ji daɗin itacennan gashi bushasshe. Da hakan dabara ta faɗomun akan in dinga siye ina tarawa kafin lokacin batun haihuwarnan, kuma a damuna tsakiya haihuwa zata zo. Haka dai sati ya zagayo sassafe wannan karon ko Nanno a gaskiya bamu yi ma sallama ba muka wuce. Ƙarfe takwas a ƙofar gidan Harira tayi mana, sai dai yaronta yace ta fita zata dawo daga wajen aiki zuwa azahar. Sai muka zarce asibiti kawai domin mu rage lokaci. Jikina a sanyaye yake gaya, mijinyawa ma sai naga duk ya karaya harma gara ni. Muna ta zaune har dai aka soma kiraye kirayen sunaye, layi dai yazo kanmu. Duk da haka wani ɓangaren ni aka turani wajen likitan mata, mijinyawa ma aka dai haɗashi da wani likitan maza ( (Urologist) Ni kam na sha tambayoyi bila adadin gaskiya. Nan ɗinma fa cewa akayi sati mai zuwa mu dawo zamu samu sakamako komai a ranar. Haka muka fito wajajen bayan azahar. A bakin asibiti na siya mana cincin, da doya da ƙwai a bakin titi, muka hau abun hawa zuwa gidan Harira. Mun ko taki sa'a shigowarta kenan itama, ta haɗa shayi tana sha ga wara a gabanta. "Malama ashe kunzo kun tadda bananan? Wallahi wajen aiki naje, basason wasa sam dole ka fita sassafe shi yasa. Ki ma maigidanki iso mana yazo ko shayine in haɗa muku gidan ba komai" Kinga ma mun siyo doya a bakin asibiti, shayin dai zamu sha ki haɗa mana, bari in kirashi. Fitowa nayi na kirashi muka shiga, bayan an gaggaisa haka sai muka ci abinci nayi sallah, mijinyawa yayi sallah tun a asibiti. Kai tsaye gidan ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan marayu Harira ta kaimu. Hajiya Bara Mun tadda wasu mace da namiji a zaune suma tafiyarsu ɗaya da gani ma ma'auratane kuma ba yara bane sam. Waje Harira ta nuna mana muka zauna, ni dai nayi shiru ina taraddadi a zuchiyata bayan mun gaisa da wannan bayin Allah. Can sai ga wacce muka zo gani ta shigo da sallamarta. Muka amsa baki ɗaya tare da gaggaisawa. "Harira wannan itace Hindun? " Wannan mata ta tambaya. "Itace, wannan shine mijin nata ƴan biyune shi mijin nata." "Allah sarki to bari in gana da waɗannan baƙin nawa. Kunsan harkar tana son sirri." Harira tace. "Bakomai Hajiya" Nan ta shiga da baƙinta ciki, sunfi awa ɗaya a ciki kafin suka fito, sai tasa akai kiranmu ɗan ƙaramin falonta wanda anan take ganawa da baƙi. "Harira kinyi musu bayanin dokokin da matakan da akebi a hukumance, da dokance? Kunsan bafa mu zamu baku ɗa bane haka, sai da yarda, da sahalewar masu ruwa da tsaki. Zan muku bayani daki daki amman ba abu bane mai sauƙi ba. Waɗannan bayin Allahn da kuka gani sun fita, suma jinjiri suke buƙatar su ɗauka sabuwar haihuwa, nan da wata shida haka. To samun jirarirai yana da wuya gaya, loki ne samun gaskiya, bawai ba'a samu bane amman duka ba, loki ne dai" "Banyi musu bayani ba, nace dai waƙa a bakin mai ita ai yafi daɗi Hajiya" "To muna saurarenki Hajiya ayi mana bayanin yadda zamu bi tsari da matakan in abune mai yiwuwa, sai mu yi, in ba mai yiwuwa bane sai mu haƙura mu dangana. Cewar mijinyawa kenan. Mra BukhariMRS BUKHARI ... "A sanin kanku ne samun ɗan mutum musamman jariri abune mai wuyar gaske a gaskiya. Wani lokacin kuma mu kan same su ma a kusa_kusa, kuga mun haɗa biyu uku ma. Amman ku zuwa nan da wata nawa kuke da buƙata? " Mijinyawane yace. "Wata bakwai, ko shida haka, imma ta kama wata takwas ko tara muna so, tunda ana haihuwar shekararren ɗa, ko mu shekara guda muka yi a cikin ummanmu kafin ta haifemu, harma anata zargin asiri akai mata" Sai da ta nisa kafin ta soma magana, ni dai gabana ma sai faɗuwa yake yi. "Hanyoyin da ake bi domin ɗaukar yaro (adoption) a gidan marayu a Jihar Bauchi, dama ko'ina a Najeriya, suna tafiya ne ƙarƙashin dokokin ƙasa da na ma'aikatun walwalar jama'a na jiha. Babban mataki na farko shi ne tuntuɓar Ma'aikatar Shari'a da Walwalar Jama'a (Ministry of Women Affairs and Social Development) ta Jihar Bauchi, domin su ne ke da alhakin amincewa da tsarin bisa doka. Kuma fa tsarukane masu yawa dake sa da dama sarewa, koma haƙura da abun baki ɗaya. Ɗan mutum ba wasa bane sam. Tsarin ya kasu kashi da kashi kamar haka: Sharuɗɗan Da Ake Bukata Ga Mai Neman Ɗaukar Yaro Dole ne mai neman ɗaukar yaro ya kasance yana da aƙalla shekaru 25, kuma ya girmi yaron da yake son ɗauka da aƙalla shekaru 21,. Idan Ma'aurata, kamar ku haka ne, Dole ne miji da mata su amince, kuma su haɗu tare su nemi ɗaukar yaron. Idan mutum ɗaya ne (maras aure), yawanci doka ta fi amincewa mace ta ɗauki yarinya mace, muddin ta cika sharuɗɗa. Tabbatar da Samun Kudin Shiga, Dole ne a nuna shaidar samun kuɗi ko sana'a tabbatacciya da zata ba da damar kula da lafiya, ilimi, da kuma ci gaban yaron. Matakan Da Ake Bi Wajen Aiwatar Da Tsarin. Shine Sayan Fom da Neman Izini. Zaku ziyarci Ma'aikatar Harkokin Mata da Walwalar Jama'a ta Jihar Bauchi, don bayyana aniyarku tare da cike fomin neman ɗaukar yaro na hukuma. Tantancewa da Binciken Gida (Home Assessment): Jami'an walwalar jama'a (Social Workers) za su ziyarci gidanku, don ganin yanayin wurin da yaron zai zauna, da kuma tabbatar da cewa kuna da halayya ta gari da kuma ikon kula da yaro ta fannin tunani da lafiya. Tattaunawa (Interview) Hukumar zata zauna da ku (idan ma'aurata ne) domin tattaunawa ta musamman don gano manufarku ta gaske. Ziyartar Gidan Marayu. Idan hukuma ta gamsu, za a ba ku izinin zuwa babban gidan marayu na gwamnati, ko wanda ke da rajista a Bauchi domin duba yaran da suka cancanci a ɗauke su, Lokacin Gwaji (Fostering/Attachment Period) Yawanci ana bayar da kwanaki ko watanni uku (3 months) domin ku zauna da yaron a gidanku karkashin sanya idon jami'an gwamnati, don ganin yadda zaku saba da juna, amman wannan sai in babba zaku ɗauka, ba wai jariri sabuwar haihuwa ba. Matakin Ƙarshe na Kotu (Legalization) Bayan cikar lokacin gwaji kuma, jami'an walwalar jama'a sun kawo rahoton cewa komai yana tafiya daidai, za a shigar da maganar gaban Kotun Iyali (Family Court / Juvenile Court) a Bauchi. Alƙali zai duba dukkan takardun, idan ya gamsu, zai bayar da takardar umarni ta ƙarshe (Adoption Order) wadda ke tabbatar da cewa yaron ya zama naku, na shari'a guda ɗaya da halataccen ɗan da kuka haifa. Mataki na Farko, da zaku bi, Idan kun shiga Ma'aikatar Harkokin Mata ta Jihar Bauchi, ku nemi Sashen Walwalar Jama'a (Department of Social Welfare). Neman Darakta ko Jami'i, Za ku nemi ganin Darakta mai kula da walwalar jama'a (Director of Social Welfare) ko kuma jami’in da ke kula da shirin Adoption/Fostering. Aikin Jami'an Su ne za su saurare ku, su ba ku fomi, su bayyana muku dukkan takardun da za ku kawo, kuma su ne za su gudanar da binciken gida (home assessment) don tabbatar da kun cancanci daukar yaron. Sanya Hannun Kwamishina, Neman amincewar Kwamishina ko sanya hannunta yana zuwa ne a matsayin mataki na karshe na gudanarwa (administrative approval) bayan ma'aikatanta na karkashinsa sun tantance ku, kuma sun gamsu da buƙatarku. Dakta Aisha usman Mahmood itace kwamishiniyar harkokin mata da walwalarsu, macece mai kirki da sanin makamar aiki. Na sanda sanadiyyar ƙawar Yayata ce, tare suka yi makaranta. Zan taimaka muku dan ganin tsarin ya tafi yadda suke so. Kana kafin a mika muku jariri sabuwar haihuwa, ma'aikatar walwalar jama'a tare da hadin giwar asibitin gwamnati za su gudanar da cikakkun gwaje-gwaje na lafiya (medical check-ups) ga jaririn. Wannan ya hada da duba lafiyarsa ta asali, gwajin jini, cututtuka masu yaduwa (kamar HIV, Hepatitis), da sauran matsalolin lafiya na gado, domin ku san ainihin yanayin lafiyar jaririn da kuke shirin riƙawa. Shikenan aiki ya kammalu in sha Allah. Amman fa samun jaririn shima wani hot kek ne, amman iyakar bakin ƙoƙarina a gaskiya zan yi muku in sha Allah, sabida Harira. Zan kuma taimaka muku wajen bin dokokin domin abun yazo muku da sauƙi. Amman zaku sha dai zurga_zurgane dai, da fatan ba zaku gajiya ba dai. Sabida akwai da dama da suke somawa su kakare su haƙura, furoses ɗin da yawane. Allah yasa mu dace, in kuna da rabon haihuwar Allah ya baku, in babu kuma ya sanya haƙuri da dangana a zukatanku, yasa ku samu mai share muku hawaye. Shi ɗa muddin yana jinjiri kuka ɗauka mancewa akeyi da ba'a haihuwa, ko baku kuka haifeshi ba ma. Nima ɗana na fari tsintarshi akayi, a lokacin an kai gidan mai unguwar ƙauyenmu ne, kafin a damƙashi ga gidan marayu na buƙaci inaso. Aka bani shi, bayan dana ɗaukeshi saida na shekara ashirin kafin na samu haihuwa, lokacin na girma al'adatama daf take da tsaiwa. Yana daga cikin dalilan da yasa na nace saida na samu aiki a gidan marayu. Kana na daga cikin dalilina, na yin iyakar iyawata, akan matan da suka zo gareni da nufin ɗaukar yaro." Jikin mijinyawa yayi wani irin sanyi gaya, ga karaya nan a idanunshi linkib. Ni kaina bawai ban sare bane, amman na danne kuma ina da yaƙinin inna miƙa lamarin ga Allah zan samu dacewa, Allah zai mana mafitar da bamu yi tunani ba. Nasan dai za'a sha fama da Nanno ne kawai, domin zata ga sunturin yayi yawa, amman inaga hutun makaranta zan ɗauka muyi amfani da lokacin wajen duk zurga_zurgar daya dace kawai, shine abu mafi sauƙi daya dace. Wannan Hajiya mukai ma sallama Harira ta rakamu har inda zamu shiga mota, mun yi da'ita akan sati mai zuwa zamu dawo mu soma wannan aiki da muka saka a gaba. Dafani tayi muna zaune a mota ana lodi tace. "Adda'a zaki dage dayi. In sha Allah zaki samu salama. Mijinyawa sai ka kula da'ita sosai dan Allah. Ina fatan in da rabonku zaku haihu watarana zaku riƙe ɗanku ko ƴarku a hannunku in sha Allah" In sha Allah Harira. Ina ƙara jaddada ki zama mai alƙawari, da riƙon sirri dan Allah. Yadda da aminci yasa nayi wannan maganar dake, domin kuma samun mafita. Bani da wani sirri daya wuce wannan a duniya" Murmushi tayi mun tace. "Ki ɗauka tamkar baki sanar ma kowa ba. Ki ɗauka Harira ta mutune an birneta da sirrinki Hindu" Sallama muka yi ta wuce. Mijinyawa ya dubeni da kyau yace. "Kawo kuɗi in siyo mana masar Bauchi gashi nan anata tallansu sai ƙamshi take zubawa." Kuɗin na zaro na miƙa mishi, ya dure zuwa waje, dake motar bata cika ba. Masa harda tsire mai zafi ya siyo mun da ruwan swan na gora. Motarmu ta tashi, muna tafe na ɗaura kaina a kusa da kafaɗarshi ina murmusawa harna hangoni da goyo a bayana ina jijjigawa, ko kuma yaro ya hanamu bacci munata rarrashinshi. Ko kuma yayi fitsari, ko bayan gida a cikin ruwan wankanshi, kamar yadda naga yaran uwatale, da su Shafa suna yi. Murmushi mai sauti nayi, wanda hakan ya jawo hankalin mijinyawa ya taɓani nayi saurin ɗagowa, muka zuba ma juna idanu, cike da soyayya da tsantsar nuna kulawa." "Hankalinki ya kwanta kema zaki mallaki ɗanki na kanki ko? " Yayi mun maganar kusa da kunnena. Kai na gyaɗa mishi halamun eh. "Farin cikinki shine farin cikina. Nayi murna dana amince miki kika samu farinciki. Ina fatan yaron da zamu ɗauka ko yarinya ya zame mana abun alfahari, ya tallafemu a yayin rauninmu, mu bashi tarbiyyar da ko wata rana lokaci yayi halinshi yasan bamu bane iyayenshi na asaliba. Ya zamto yana alfahari damu in sha Allah" Da waɗannan maganganun muka isa jama'are, daga tashar muka hau acaɓa har zuwa ƙofar gida. Shi ya tsaya a wajen su Abdulƙadiri. Ni kuma na shige gida, ledar masata tana cikin mayafi. Ina ajjiye mayafi Uwatale ta shigo da kwano a hannunta. Miƙewa nayi muka haɗa idanu, na ƙanƙance idanuna na tsantsar ɓacin rai. Kafin ince wani abun tace. "Yi haƙuri naga ranki ya ɓaci, dama ɗan wake ne na kawo miki ko zaki ci. Amman naji ma ƙamshin kamar masa ko tsirene kike yi." Bana cin ɗan wake, sannan in zaki shigo ɓarayin mutum a ƙa'ida sai kayi sallama an baka izini kafin ka shigo. Babu mamaki ma baki san anayin hakan ba ko?" "Me kike nufi Hindu? " Abinda kike nufi shi nima nake nufi." Wucewata ciki nayi da laidata na barta nan a tsaye tana sababi. Mijinyawa na shigowa ciki ya zauna kenan. Sai ga sallamar Nanno, tare da kwaɗamun kira. A guje mijinyawa ya fito, ni ko da ƙyar na fito ma. Ɗan wake na gani zube a ƙasa yasha ƙasa. "Yayi kyau hamshaƙiya mandiya ɗiyar ƙaruna. Sannu nace ɗiyar sarki fir'auna sarkin da yace da kanshi shine Allah ma baki ɗaya, sabida yadda duniya tayi mai daɗi. Yau kinci albarkacin cikin dake jikinki, wallahi da kinga abinda zan miki akan wannan almubassazancin da kika yi akan ɗan wakennan" Mijinyawa ne yace.. "Nanno wai me ke faruwane dan Allah, aimun bayani mana? " "Ga matarka nan zata yi maka bayani. Ina laifin uwatale dan kawai ta nuna kulawarta gareta. Karfa ka mance uwatale matar wanka ce, ɗan uwan tagwaitakarka, kuma ƙanwarkace Uwatale. Kaga matarka so take ta rabaka da uban kowa. Sai dai danginta kawai, dasu zata fi so ka samu kusanci. Inta haihu bansan wanne irin mulkarka zata yi ba. Ina tausayama a hannun wayayyar mace wallahi. Ke Uwatale ki fita sabgarta ki fita sha'aninta haihata haihata." Daga haka ta ja hannunta suka fice. Bance uffan ba, nasa tsintsiya na share wannan ɗan wake. Bance da mijinyawa bani na zubar ba, hannunshi naja muka shige ciki. Na ɗakko mana filet muka zuba tsire da masarmu, na samu ƙaramin kwano na zuba ma Nanno. In mun gama ci, sai ka kaima Nanno wannan ko? Sannan menene labari naga ka jima" Na soko hakanne dan in mantar dashi abinda ya faru, nikam bai dameni ba. Uwatale dai cikine da akace ina dashi ya dameta shi yasa take wannan ƙananun gulmammakin ba wani abun ba. "Hmmm Abdulƙadirine yazo da wata maganar banza da wofi wai Halima yake so zai aura" Masa da tsire ya haɗa, madadin ya cunkusa a bakinshi saiya cunkusamun. Shima ya ɗauka ya cunkusa a bakinshi. Dole muka hau tauna, nice harda lumshe idanuna dan daɗi. Wacece Halima kuma? " Saida ya kuma cika baki ya cinye kana yace. "A garinnan take kusan sa'armu ce tare muka yi wasa da'ita muna yara lokacin. To sai ta samu jarabawa wani saurayinta direban babbar mota ya ɗauketa suka shiga bariki fa. Ta bar gaban iyayenta. Da yawa ance ana ganinta tare dashi a maraba. Daga baya akace sun koma tafa, can wajajen ikko dandalin direbobin mota kenan. Kuma dandalin masu zaman kansu, dandalin ƴan tuwo tuwo. Ita kanta wai tayi sana'ar tuwon acan a lokacin da shi wanda ya ajjiyeta ya tsallaketa yaje yayi aurenshi. To itace ta dawo gida bayan taci maraba, taci tafa, taci Lagos wai ita Abdulƙadiri zai aura. Harma sun daidaita. Jama'a da yawa fa masu fita cirani kudu, suna dawowa da labarin sun ganta, a lokacin har ana zargin tabar Musulunci, duba da irin shigarta, da gashin doki da take sakawa. Akwai wani ɗan bariki a ƙauyennan namu mai suna Muntari ƙwallo. Ƙwallon ɗan duniyane gaya. To shima ance yayi zaman dadiro da halima a Ogere. Ya rasu amman, anata raɗe_raɗin ciwon sidane yai ajalinshi, wasu kuma suka ce tarin fukane yai sanadinshi. Ita dai Haliman ance har ƴa a haifa a bariki da'ita ma ta dawo ribar barikin kenan. To kinji zancanne Qasimu ya tareni dashi, kinga dole mu jima. Zaman garinnan fa gagarar hatta iyayenta yayi, sai Azare suka koma da zama, mahaifinta kunyace ta jama'ar gari tai sanadiyyarshi. Yanzu ma bayan Magriba zamu shigo dasu nan mu tattauna. Bai kamata mu ƙyale Abdulƙadiri faɗawa halaka ba, zamu iya iyacin iyawarmu, dan ganin mun daƙile wannan nema" Shiru nayi ina jujjuya lamarin gaskiya. Sabida dole abun dubawane. Amman me muddin ta tuba ai zai iya aurenta. Sai dai abun tsoron dake tattare da aure, yana da yawan gaske gaskiya. Ajjiyar zuchiya na ja tare da saukewa. Amman mijinyawa in dai da gaske yake sonta, kuma itama da gaske take ta tuba, zata yi zaman auren, ai tamkar jahadine wannan ko?" "Tutar so wannan gaskiyane. Amman shin wa yasan zuchiyarta ne wai. Sannan tafa jima a bariki kina ganin ta dace da Abdulƙadiri kuwa anya? Ni tsoronmu shine sha'ani na tarbiyyarta. Karfa azo ana ɗan daka ce ba'ai ba ni shine damuwata. Shi Abdulƙadiri harma ya fini sanyi da sauƙi. To yana zaman zamanshi kar yaje ya ɗakko kara da kiyashi. Kai ina Tutar so bama zamu amince da wannan lamari ba sam" Haka dai mukaita tattaunawa har saida akayi la'asar ya ɗauki kwanonnan ya fice dashi. Ni kuma na fito na soma haɗa itace zan ɗaura sanwar dare. Tuno Baraka yasa na fasa. Ai ko shida na yamma sai ga tuwon shinkafa da miyar kuka harda ɗanyen soyayyun kifi, suyar fulawa, da gani na masu siyarwane aka siyo ta watso mana biyu. Bayan magriba su Abdulƙadiiri suka shigo, nan sukaita tababa. Suna kwatanta mai, yana runtse idanunshi, shima yana kwatanta musu, Halima ta tuba, ta shiru. "Ta fa tuba, in ba'a aureta ba ruwa zata koma. Ai laifinta tsakaninta da mahaliccinta ne, shi yace yana ma bayinshi wanda su kai tuba na gaskiya gafara. To me yasa ba zamu mance komai ba. Mu matsalarmu shine, ko mutum ya tuba, bama iya dena kallonshi da fentin da yaima rayuwarta na baya. Ku tausaya mata mana. Tunda kuka ga Halima a gida ai ta tuba ne." Mijinyawa yai carab yace. "Ai bafa dole sai kaine kaɗai zaka aureta a samu yadda ake so ba. Ya idanunka suka rufe ne haka Abdulƙadiri? To ni dai Magawata ban yarda ba, ban yarda ba, ba kuma zan yarda ba wallahi." Qasimu shima ya cabke, suka buga shima dai ya buga, har yayi zuchiya ya fice ya barsu. Shi ya kafe yana son Halima aurenta zai yi, daya kammala gininshi ma kuwa. Suma sun kafe kai da fata akan basu amince ba. Haka dai akaita jiƙawa ana matsewa har ranar komawa asibiti yazo, kuma a ranarne zamu soma bin matakan ɗaukar yaro a gidan marayu tamkar yadda muka tsayar. Sassafe muka ci ɗumame da ruwan kokko sai Bauchi, amman da zummar zuwa makaranta ni na fita. Tun Juma'a na riga na ɗauki hutu. Ko da muka shiga Bauchi asibiti muka wuce kai tsaye kawai. Ni dai gabana sai bugawa yake yi dim_dim_dim matsala kam tabbas akwaita. Jiya dana kwanta nayi wani irin mafarki wanda nake zargin yana da alaƙa da sakamakon da zamu ji na asibiti. A jikina nasan sakamakon ba zai zama mai daɗi ba. Mrs BUKHARI Mu kwana anan sai zuwa gobe in mai dukka ya amince💪🏼MRS BUKHARI .... Ni dai da shigarmu akace nawa sakamakon tukunna, suna buƙatar mataki na gaba wato gwaje_gwajen jini kuma. Da zaran na soma al'ada a kwanaki biyu zuwa uku na al'ada akwai gwaji. Za'a sake neman wani jinin na sinadarin Progesterone a kwana na 21 na al'ada (don gani ko ƙwai ya fita) A baya can duk an yi mun wannan gwaje_gwajen, dasu hoton mahaifa, dana toshewar bakin mahaifa, duk nayi su. Nayi tunanin tunda zuwa na biyune ba sai anyi duk wannan ba, tunda yana rubuce. Amman likitana tace dole akwai buƙatar sake sabon gwaje_gwajen. Sunturin asibiti ya ganmu. Shima Mijinyawa wai za'ayi mishi gwajin jini tukunna, kafin muji sakamakon, amman dai yace tabbas yasan da matsala kawai dai likitan yace babu komai ne, amman jikinshi yana bashi tabbas akwai matsala babba. Muna barin asibiti muka shiga bin diddigin hanyoyin daya dace abi dangane da neman yaro. Gaga_gaga haka abubuwan sukaita tafiya, sunturi kam mun shashi, na asibiti da ƙa'idojin ɗaukar yaro. Kusan tare aka gama da batun asibiti, shi wancan na neman yaro mun gama na ɓangarenmu, muna dai jiran sakamakon daya kamata, kafin umarnin zuwa gidan marayu, duk da mu jariri zamu ɗauka. A ranar sakamakon duk gwaje_gwajenmu ya kammala. Kamar na baya, ni bani da matsalar komai. Muna murna muka nufi likitan mijinyawa bayan bin layi muka samu shiga, yana zaune, muma munyi shiru sakamakon muke son a bamu muji. "Magawata sakamakon gwaje_gwajen da duk muka yi maka sun fito. Nace ko madam zata iya jiranmu a waje in da hali?" Ai sai nayi saurin riƙe ma Mijinyawa hannu, shikenan nasan ma matsala zai faɗa. Murmushi yayi yace. "Aa madam ba zata yadda ba, kaga yadda ta riƙeni ai. Dakta ai babu komai matatace, zaka iya faɗan komai" Kuma mu musulmaine, mun yadda da Allah, mun yarda da ranar sakamako. Dukkan abinda Allah ya nufa shike wanzuwa, shike da tasarrafi da isa, da buwaya." "To shikenan, a sakamakon gwaji na farko ya nuna mana Magawata bashi da kwayoyin Halitta. A gwaji na biyu ya sake tabbatar mana da bashi dasu, ba'a halicceshi dasu ba. Amman nace a sunanka naga kamar ku ƴan biyu ne ko? " Jiki a saɓule mijinyawa yace. "Tabbas mu ƴan biyu ne dakta" Shiru likitan yayi can sai yace. "Kunyi kama matsananciya, ko irin ƴan biyunnanne da basu da kama? " "Munyi kama sosai, komai namu iri ɗayane, girma kawai nafi ɗan uwane, shine kaɗai bambancinmu" "To shi yayi Aure ya haihu kuma?" Saida mijinyawa ya lunshe idanu kana yace. "Tabbas yana haihuwa, yanzu haka matarshi juna gareta." Ajjiyar zuchiya wannan dakta yayi, sai yayi rubutu yayi rubutu kafin yace. "Ba'a fiye samun haka ga ƴan biyun da suka yi kama ba sam. Anfi samu ga tagwayen da basu da kama. A yawan lokuta, matsalar tana faruwa ne saboda lalura bayan an haife ƴan biyu, ana iya haifar ƴan biyu ɗaya kwata-kwata ba shi da kwayoyin halittar haihuwa tun daga ranar haihuwarsa, yayin da ɗan uwansa kuma aka haife shi lafiya lau. A fannin kimiyya da likitanci, akwai dalilai guda biyu na musamman da ke sa ɗaya ya zo duniya ba shi da kwayoyin haihuwa, ko masana'antar kera su, ko da sun yi kamanni da juna su ƴan biyun 1. Rashin Sauko da Maraina Tun a Ciki (Cryptorchidism/Anorchia) Yayin da jariri namiji yake girma a cikin cikin mahaifiyarsa, marainansa suna samuwa ne a cikin cikinsa daf da koda, sannan kafin a haife shi su sauko su daidaita (scrotum). 2. Me ke faruwa da ƴan biyu ɗayan? Ana samun yanayin da jinin da ke kai wa marainan ɗaya daga cikin tagwayen abinci ya toshe, ko ya murɗe tun suna cikin ciki (Testicular Regression Syndrome). 3. Wannan matsalar tana sa marainan yaron ta narke ta ɓace gaba ɗaya, kafin a haife shi (wato an haife shi kwata-kwata ba shi da maraina, ko kuma an haifeshi kwata kwata bashi da kwayoyin halittar haihuwa). 4. ɗan uwansa kuma yana saukowa lafiya lau. Canjin Kwayoyin Halitta na Mosaicism,Wannan yana faruwa ne da zaran ƙwan da ya rabe ya zama tagwaye masu kama ya fara rarrabuwa a farkon ciki. Yayin rarrabuwar kwayoyin halitta, ɗaya daga cikin tagwayen yana iya samun matsala inda kwayoyin halittarsa na maza (XY chromosomes) suke canzawa, ko kuma kwayar halittar 'Y' ɗin ta ɓace a sassan da ke kera maraina. Wannan yaron za a haife shi da matsalar Gonadal Dysgenesis, wato an haife shi da masana'antar haihuwa da ba ta nuna ba, kuma ba ta da kwayoyin kera maniyyi ko guda ɗaya tun asali. Ɗan uwansa kuma kwayoyinsa suna tafiya daidai. Tabbas bincike ya tabbatar ana samu. Sannan akwai lalurori da ake samu a yayin girma zuwa balagar yara, nan ma ɗaya zai iya samun matsala a marainanshi wanda ka iya kashe ƙwayoyin halittar. Shin kayi irin wasan rafinnan lokacin da kake tasawa?" Jikin mijinyawa yana rawa yace. "Nayi wankan rafi sosai. A cikin abokaina nafi kowa ƙwarewa" "To kaga shima yana haifar da cutar tsargiya, a sakamakon wasu ƙananun halittun ruwa dake samun damar shigewa jikin yara. Su shiga su zuba ƙwayayensu a jikin mutum, sai kaga yana haifar da zafin fitsari, ko in an gama fitsarin kaga ɗan jinin da baifi ɗigo ba. Tabbas shima wannan yana haifar da matsalar rashin haihuwa, koma ya raunata al'aurar baki ɗaya. Cikin wannan misalan ka taɓa fuskantar ɗaya a ciki?" "Likita na fuskanci duka, musamman na jini a ƙarshen fitsarin. Nayi hira da abokina Qasimu sai yace mun wai na balaga ne shi yasa" Likita yayi rubutu, yayi rubutu kafin ya ɗago ya zuba mana idanu. Can sai yace. "Babu damuwa in sha Allah. Sai dai akwai maganguna da allurai da zan ɗaurashi akai, na tsawon watanni shida, zuwa shekara guda. Ina mai tabbatar muku in sha Allah zasu farfaɗo da waɗannan sunadaran. Wannan ba matsala bace kuma ba wani abun bane. Baya ga haka kana da cikakkiyar lafiyarka ta jiki, data al'aura. Sannan kar ka ɗauki damuwa ka saka ma kanka, babu komai in dai kabi abinda zan ɗauraka akai za'a dace, harma ya zama tarihi." Allah mun gode maka, Allah mun karɓa, Allah ka fimu sanin dalili. In haihuwa alkhairice a garemu, Allah ka bamu ƴaƴan da duniya zata yi alfahari dasu, in babu alkhairi Allah mun karɓa a haka, ka fimu son kanmu, kai kake tsara komai, kuma komai yana da dalilinshi" Wannan maganganu nawa, su suka ƙwarara mijinyawa daya karaya har jikinshi na rawa inaji, hannayenshi dake cikin nawa tuni suka jiƙe. "Madam madallah dake. Irinku akeso masu bama mazajensu nutsuwa akan duk abinda zai firgitar dasu. Ku daure abi hanyar shan maganin da alluran za'a dace. Duk mako sau biyu za'ayi mishi a ƙalla. Wanda a wata za'ayi mai allura takwas. Ko wacce allura ɗaya kuɗinta zai kai dubu biyu da ɗari biyar. Zamu yi na wata uku, zuwa shida, sannan akwai magunguna da zai dinga sha. Su kuma bana tunanin zasu wuce dubu bakwai zuwa takwas dai. ( a lokacin kuɗine masu yawa gaskiya tunda a yanzu wannan zamanin allurar ko wanne ɗaya tana kaiwa dubu ashirin da biyar a wata guda kuma kuɗin kusan dubu ɗari da sittin zuwa dubu ɗari biyune) Kainane naji ya sara, kuɗaɗe ake buƙata mazajen kuɗi ba matan kuɗi ba. Mijinyawa yace. "Mungode dakta. Hindu tashi mu tafi kinji?" Ajjiyar zuchiya na sauke, jikina a mace na miƙe. Dakta zamu dawo in kuɗaɗen sun kammala in sha Allah" Tunda muka shiga mota, ni dashi babu wanda ya tanka har muka isa tasha inda zamu sauka. Shi ya biya kuɗin, ya riƙo hannuna munata tafiya, bamu hau abun hawa ba. Sai adda'a da ambaton Allah nake yi. Munyi tafiya mai nisa kafin na dawo hayyacina, harma na taran mana acaɓa muka hau. Mijinyawa baya cewa komai, sukuku ya shiga gida, wannan ganin da Uwatale tayi mishi ai saita garzaya ta je ta kirawo nanno. Ina can gaban sib ina ɓoye takaddun asibitinnan, na jiyo Nanno tana tambayarshi ko lafiya? Sannan ance kwanana nawa bana zuwa makaranta, to ina nake zuwa. Ƙin fitowa nayi, na nemi gado na kwanta shiru kawai, zuchiyata da ƙwaƙwalwata aiki kawai take yi. Kaina ya kulle, zuchiyata nauyi tayi mun sosai. Nanno ce ta kwaɗo mun kira, na amsa a hankali tare da fitowa. Mijinyawa yana kwance a doguwar kujera da gani zazzaɓine ya rufan mishi sosai. "Meke damunshi ya shigo a cikin wannan yanayin. Gashi jikinshi fa da zafi sosai, nace ko wani abunne ya samu yaron cikin naki ne? " Aa zazzaɓine kawai yake damunshi, zai sha magani yansu" "To naji zurga_zurgar duk da kuke yi, ina kuke zuwa? Ance kin kwana biyu bakya zuwa makaranta, to ina kuke zuwa tabbas wancan satin an tabbatar mun Bauchi kuka je. Me akeyi a Bauchin har haka" Uwatale na kalla, idanunta a kaina. Na juyo da dubana wajen mijinyawa wanda ya miƙe zaune. "Nine bani da lafiya asibiti muke zuwa, wannan satin kuma itace bata ji daɗi ba shine na kaita." "Amman baka da lafiya baka iya faɗama kowa ba, sai matarka ko? Ga jikinka da zafi, da sanarmun kayi nasa aka dafa maka saƙesaƙi ka sha da tuni ka warke. Me akeyi da ƙwayar bature da har zaka je asibiti. Ke ba'a zuwa asibiti a cikin gidannan kiji da kyau. Duk abinda kuma yake damunshi a tabbatar an sanar mun. Ke dai ƙoƙarin ki na raba kan dangine kawai. In ba haka ba ya yaro ba lafiya ba zaki sanar mun ba" Hmm kunji wai yaro. Mijinyawa fa take nufi, ba yaro mai shan nono ba. Na kasa buɗe baki ma ince uffan, firejar dake kaina a lokacin ta wuce gaban misali. Shima da yaso sake wata maganar hanashi tayi kawai. Ba'afi minti talatin da fitar ta ba, sai ga Shafa an aiko da magani cikin ƙaramin bokitin fenti ta dure mana. Abu kamar wasa kafin dare Mijinyawa baya gani, sai sunana kawai yake ambato. Ni dai inata tofa mishi adda'a, ban sanar da kowa halin da ake ciki ba sam. Ga jikin ina ganin yayi tsanani, har sau biyu ya suma, ina yayyafa mishi ruwa. Ruwa na ɗebo nayi mishi tofi, na bashi yasha, ragowar na shafe mishi jikinshi dashi. Naita jiƙa tsumma ina goge mishi jiki da ruwan sanyi. Sai ajjiyar zuchiya yake saukewa. Can sai bacci mai nauyi ya kwasheshi. Ajjiyar zuchiya mai nauyi na sauke. A lokacin na samu zarafin yin sallah, na jima a sujjada ina kai kukanmu zuwa ga sarkin sarakuna, sarkin adalci, sarkin da babu sarki kamarshi. Ana kiran sallar isha, na miƙe na gabatar, ina yin Azkhar mijinyawa ya ɗan farka. Zaka iya zuwa banɗaki ka ɗauro alwala kayi sallah ko a zaune ne? Ɗan guntun murmushi yayi mun, wallahi sai naji sanyi da duk damuwar data dunƙule a ƙirjina. Ku fahimci wani abu guda ɗaya. Soyayya fa gaskiya ce, so kuma hana ganin laifi ne. Manzon Allah S A W da aka tambayeshi duk duniya wa yake so, sai yace Ummuna Aisha. Akace a maza fa, yace Abubakar Assiddiq. Wannan kaɗai ya ishemu mu san cewar soyayya ba ƙarya bace. Kuma ita Ummuna Aisha bata taɓa haihuwa da manzonmu Arrasul S A W ba. Amman munji irin son da yake mata. "Zan iya, jikin ai da sauƙi. Kina shagwaɓani fa" Hmm ai dole. Kaima ai kana da raki, baka da juriyar ciwo. Amman ni nafi kyautata zaton maganinnan da kasha ne ya turo zazzaɓin naka fa. Ina da fanado in kaci abinci sai in baka kasha" Miƙewa yayi yaje ya ɗauro alwala yazo ya gabatar da sallah, ni kuma kafin ya idar na kawo abincin da ɗazu Baraka ta aikoshi. Tuwon dawane da miyar lalo taji wake da daddawa, kuma ganyen lalo ɗinma yaji sosai sai ta tubke bata yi irin tsinkewarnan ba. A baki naita bashi yana karɓa. Tausayinshi na neman halakani (umminmama kina dai ji, da Maman Jaririya, da Mamanzee, da Jamilatsafe) "Ya isheni, bani maganin in haɗiya da tuwo" Maganin na saka mai a tuwo ya haɗiye. Saida naga ya kwanta kafin na soma cin tuwon. Duk gishiri miyar amman a haka na tuttura na kora da ruwa. Kusan dare na raba ina sallah, ina karatun Qur'ani. Hakanne yasa mijinyawa ya farka, shima auwalar ya ɗauro yazo ya tada kabbara, a lokacin ina miƙa godiyata ga Allah ne, tare da roƙon Allah ya bamu ikon cinye jarabawarnan. Bayan mijinyawa ya idar sai ya zubamun idanu, ɗakin babu haske saina acibalbal ɗin da ta kusan macewa sakamakon kalanzir da yayi ƙasa. "Mun tsallake ruwa, mun faɗa ruwa Tutar so. Ba abinda likita yace bane ya kwantar dani ba. Tausayinki, da yadda zan rasaki, da tausayin nawa kan su suka kaini ƙasa. Ciwonnan da Allah ya ɗauramun Allah shine shaidana wallahi ko da likitan ya faɗamun banji wata damuwa ba ta ƙashin kaina ba. Damuwata a kanki take. Ina sonki wallahi, inna rasaki shikenan" Sai ga hawaye Mijinyawa yanayi, hakan bai mishi ba sai kawai ya fashe da kuka yana shessheƙa. Shiru nayi ina kallonshi yana kukanshi. Zuchiyata nima suya take yi mun, idanuna a bushe tamkar zasu dare. Hannayenshi na riƙe gam, sai ya zubamun fararen idanunshi masu kwalli, da ƙyalli, da tasiri. 🤣 Kana tunanin zan rabu dakai, sabida ance baka haihuwane wai. Ashe kai bakasan girman sonka da nake yi bama ashe. Ruwa da iska ba zasu rabamu ba. Banyi tunanin akwai abinda zai taso maka na wata lalura da zata iya rabamu ba. Kaima baka gujeni ba a lokacin da danginka suke zargin rashin haihuwar daga gareni ne. Babu gori, ko canji dana samu a gareka, Ka bani kariya, har aure aka baka umarnin yi amman baka yi ba, duk dan ka bani kariya. Sai nice zan tafi in barka sabida baka haihuwa. Shin ƴa ko ɗan da zamu karɓo a gidan marayu bai ishemu rayuwar duniya ba ashe? Mijinyawa ka kwantar da hankalinka, akan rashin haihuwa bazan gujeka ba abadan wallahi ka rubuta a ajjiye. Kuma kaimun alƙawarin wannan sirrin namu ne mu kaɗai mu ya shafa. Bana son jin wannan sirrin a wajen kowa hatta Nanno bana so taji, har Qasimu da Abdulƙadiri nake nufi. Mu burne abinmu sabida kaga in muka tona muma mun ɗauki wuƙa mun daɓama cikinmu ne. Sabida yaron da zamu ɗakko da sunan namu. Ka kuma godema Allah a duk halin da kake ciki. Sannan ka dena tunanin zamu rabu, mutuwa ita kaɗaice ta isa raba wannan soyayyar." Hannayenshi ya zame a nawa yace. "Aa Hindu ni bazan zalunceki in tauyeki ba. Kina da damar da zaki iya auren wani mijin ki hayayyafa, me yasa zaki zauna dani da yaron da zamu ɗakko? Ai ni da cewa nayi zamu ce ma Nanno cikin ya zube kawai. Ko kuma mu faɗa musu babu cikin ƙaryace kawai muka yi, rabamu da take so ayi sai ya tafi akan wannan dalilin, kiyi haƙuri Hindu na roƙeki. Bazan iya cutar dake ba. Kina da damarki fa. Ina ina Hindu. Ban isa kashe miki rayuwa ba. Son da zan nuna miki wannan shine dasaukarwa mafi girma, kije ki yi aurenki ki ga jininki a duniya" Idanunshi sun kaɗa sun yi jawur dasu, jijiyoyin kanshi duk sun firfito, ga hawaye, harda majina. Ni mamakin kalamanshi ma nake yi sosai. Kawai saina kwanta a ƙasa na rabu dashi, yaita kuka yana mayawa. Sautin kukanshi na sawa inji kamar zan mutu. Shima filo ya kada ya kwanta a bayana. Idanunmu biyu har fa akayi kiran sallar asuba, sai dai makarai sun ziyarceni tabbas naji a jikina, ga kumburin fuska inaji. A hankali muka miƙe. Alwala ya sabumta ya fita, nima na sako alwala nazo na gabatar da sallah. Ina zaune a kan sallaya sai gashi ya shigo ba kuzari a jikinshi sam. Kwanciya ya kuma yi yana dafe da kanshi, idanunshi jawur. Na yinƙura zan tashi sai ya riƙe hannayena. Bakin gadon na dawo na zauna. "Hindu ya zanyi. Ki amince da abinda nace shine mafitarmu mai kyau. Ina miki irin son da zatonki bai zata ba. Na yarda na gamsu sonki yafi nawa yawa tun fari. Amman ki.... " Hannu nasa na rufe mishi bakinshi, sai yai shiru. Hindu takace abadan. Wallahi Allah akan wannan abun banga ranar da zan gujeka ba, ban ganta ba ban ganta ba. Muna tare har cikin aljannah, ni ɗinnan nice shugaban matanka na aljannah. Ni abinda nake so dakai kaji taoron Allah, ka godema Allah da abinda yayi maka. Musa hannu bibbiyu mu amshi ƙaddararmu, kuma in sha Allah zan ɗauki ɗan kunnena da sarƙana in siyar mu samu aima allurannan da magunguna da likita yace, sai kaga an dace bana so kana karaya dan Allah." Kamar ba namiji ba, sai ga hawaye na bin gefen kuncinshi yana zuba akan fulo. Tunda ya lumshe idanunshi, ya riƙe saitin zuchiyarshi bai sake cemun komai ba. Mun share kusan minti goma, ni ina mishi kallon tausayi, inaji dama ace ina da ikon yaye mishi damuwarshi, ko dawo da ciwon jikina, ace matsalar daga nice wallahi da nayi yanzu take. Sai dai kash, Allah shi yake yi, shi yake zaɓan wanda yaso, ba domin ƙiyayyaba sai domin jarraba imanin bayinshi. Haƙuri da rungumar ƙaddarar da Ubangiji ya ɗauroma ka iya sanyawa Allah yasa bawa a aljannah. Zan tattaleshi mu burne wannan sirri, walwalarmu da farin cikinmu nasan zasu dawo da zaran mun samu jinjiri a gabanmu da sunan ɗanmu. Bayan ya buɗe idanunshi naga sunyi wani irin ja mai ban tsoro. "Hindu me yasa kike sona haka, me yasa kike ta shan wahala sabida ni, wai me kike gani tattare dani ne haka? Naga ni bani da komai, ni ba kyau ba, ni ba likima mai zurfi ba, ni ba kuɗi ba. Ɗan ƙauye bagidaje dani" Soyayya ai gaskiya ce, in inason abu, ina sonshi ne da dukkan rayuwata, haka in naƙi abu haka nake, haka Allah ya halicceni. Babu irin sadaukarwar da bazan iya maka ba. Amman bana son cin amana daga wajen wanda na yarda dashi." "Nagode sosai da wannan soyayyar. Amman ban yarda ki saida ko da barimar hancinki ba da sunan wai ki biyamun kuɗin maganguna ba. Sannan ko ma kin siyar ba zasu isa kuɗin alluran har a gama ba. Sannan bani da amsar da zan ba su Innarmu a lokacin da zasu ankara babu wannan ɗan kunne da sarƙan. Kiyi haƙuri Hindu. Na miki alƙawarin duk inda maganin gargajiya yake zanje in nema, kuma in sha Allah zamu dace, ba sai kin mun wata hidima ba gaskiya, wacce kike yi ma ta'isa" Ajjiyar zuchiya na sauke kafin nace. Kayi haƙuri, babu wanda zai san na siyar. In haka kake gudu zan siyar da ƙananan ɗan kunnayena biyu, shi ɗan kunne da sarƙan sai in barshi. Amman batun maganin gargajiya ai bazan hana ba, sabida bansan ina za'a dace ba. Na asibitinma zamu soma. Da zaran naje gida na dawo. Ka amince dan Allah, domin Allah nayi maka bana neman komai a gareka" Tasowa yayi ya zauna da kyau muka fuskanci juna sosai yace dani. "To ni bansan me zance miki ba, bani da kalmar da zan iya gode miki, ko nuna miki farin cikina. Amman ga wani alƙawari ni mijinyawa zan miki. Ke da zama da kishiya har gaba da abada. Ke kaɗai zaki rayu a zuchiyata, rayuwata, gidana, daga ke babu ƙari in sha Allah. Babu abinda zan samu daga wata ɗiya macen wanda ban samu a wajenki ba. Hindu kin zamemun huɗu a ɗaya, ko mata huɗu ba lallai su kamo ki ba jarumata. Mijinyawa naki ne kiyi yadda kike so dashi, sai yadda kika ce. Na miki wannan alƙawarin ba dan tuwuici ba, sai dan dama a zuchiyata tun kafin wannan lamarin kinsan ina faɗa miki hakan. Duk da naga baki taɓa yadda ba. Amman a yanzu zaki yadda ai. Babu yadda za'ayima in Auro ƴar mutane alhalin nasan bana haihuwa " Laa ka adana wannan alƙawarin, zaka warke in sha Allah. Sannan kar kayi alƙawarin abinda ba zaka iyaba. Ai ba sabida haihuwa kaɗai ake yin aure ba. Nasan ribar soyayya Aure, rubar aure haihuwane. Amman ai Allah shi yayi masu haihuwa yayi marasa haihuwa. Suma marasa haihuwan sun ci ribar kasancewa a inuwar aure, kuma in suka riƙe aurensu da kyau zasu samu rabo mai kyau. Kar kasa in saka a raina wataran ina zaune inji ana shigo da Amarya kayo Aure." Jin kishi ya tsirgamun yasa na haɗiye wani yawu wanda da kanshi ya tsinko mun, duk na kishine. Mun daɗe dai muna tattaunawa, dake asabarne ba makaranta sai kawai muka kwanta tunda dama bamu samu bacci ba jiya. Ai kuwa sai sha ɗayan rana muka farka. Masar Bauchi na turara mana na dama mana kokko. Ni dai ni nake jan mijinyawa da hira, amman shi kam ya ɗauki damuwar duniya ya ɗaurama kanshi, abinda damuwar ba zata sauya ko wacce iriyar ƙaddara, ko jarabawa ba. Saima dai ta sake tura sabuwar matsala. To amman nasan lamarin yana da girman da ya kamata ace an yi tunani kam a kanshi. Koni daya fita saina zauna inata tubkewa ina warwarewa da kaina. Inna buga sai in kwashe na kasa haɗa komai. Tafe_tafe damuwa tai ta cin ƙasan ranmu, har rama muka yi, na shiga sabon ciwon makarai, kullum sai sun tashi, jikina ko ina a kumbure, ga tsami. Amman bamu kuma ta da zancan rashin haihuwa ba. Matan gida ni kam nawa sun ɗauka laulayine, dan babu laifi ina nuna yanayi na laulayi a aikace sosai. Har hannu nake sawa a bakina in ƙwaƙwalo aman dole inta sheƙashi. Gashi na zama kusan ɗanya har kaina saida ya kumbura. Gaga_gaga_gaga har ranar zuwana biki gida yazo. Na harhaɗa tsarabata, da duk kayana na kintsasu a jaka. Ɗan kunnayena biyun na saka a ƙaramar jakar hannuna. Mai sarƙar kuma na sa a wuyana. Nanno tayi faɗa kamar zata ari baki, akan ita ba za'a hau mata hanya da jika a ciki ba. Akace rashin sani yafi dare duhu. "Cikin da da ƴar da jiɓin goshi aka samu, shine zaki je ki jijjigeshi a hanyar Kano, koko mai kike nufi ne. Kai yanzu kana gani zata tafi sabida dai kai baka da kataɓus a cikin gidanka. Haka kaga Yayunka suna tafiyar da gidansu ne. Kuma sabida salo ace wai dakai zata tafi, yanzu dan zata je ganin gida sai kun tafi tare?" "Kiyi haƙuri Nanno Innarsu ce ta aiko tana son ganinta shi yasa, biki za'ayi a gidan. Ni kuma zan rakatane sabida yanayin hanya, kuma kinga ba ita kaɗai bace" "To ban yarda ba shanyayye, kaji ko nace ban yarda ba." Ai kuwa Nanno taƙi fur mu tafi tare da mijinyawa sai dai tasha ya kaini. "Kar ki manta da shirinmu, kinga yaci ace cikinnan ya fito, to a gida kuma ko kinsan tsumma za'a samu mai taɓawa ba kamar nan bane. Sai kiyi yadda muka ce ko? " Kai kawai na gyaɗa mishi ba tare da nace uffan ba. "Sati nawa zaki yi to?" Sati biyu yayi maka, ko sati ɗaya?" "To kiyi sati biyun banason daɗewar sabida kar su bugo jirginmu ne, da sai ince kiyi uku" Ba zasu bugo jirginmu ba. Ai akwai da yawan mata da ciki yake bin jikinsu, ko Mamansu, yadda nayi ma Mamana dole zasu gamsu nawa Mama yabi. Kai dai kafin in dawo ka tanadar mun gadalinnan, kar ka mance da batun itace, kuma ka zauna da shiri dana dawo sunturin Asibiti ya ganmu" Saida motarmu ta fita a tasharnan kana ya tafi shima. Gudu motarmu take yi, amman zuchiyata bata tare da gangar jikina, tunanukane fal zuchiyata. Takalmin ƙafata na kalla wanda na siya sabo, amman ba mai tsada yadda na sababa, ta fannin suturu bani da matsala sai dai fa nawa na gidane na sako masu tsada, gani da adani da tattali ni kayana basa tsufa gaskiya. Mota na saukemu a tashar unguwa uku sai na nemi abun hawa sai Na'ibawa. Ina sauka a ƙofar gida muka haɗu da Qazzafi shi da Akarami sun fito zasu masallacin magriba anata kiraye_kirayen sallah. Qazzafine ya suri buhun tsarabata ya wuce ciki yana ta kallona. Akarami kuma ya ɗauki akwatina, ni kuma ina riƙe da jakar hannuna muka ratsa gidan. Matan gidan duk suna ciki. Ni kam wannan karon na zaɓi saina huta zan bisu da ɗaya da ɗaya in gaishesu. Muna shiga falonmu aka kawo wutar lantarki wallahi sai naji tasirin wannan haske har a zuchiyata. Da Innarmu muka haɗa idanu taci kwalliya tana harɗe a kujerar dake falonmu da littafin turanci a hannunta tana nazarinshi. Mrs Bukharice Jama'a ya muka ji da jimami, ya muka ji da tausayi🤧🤧🤧 Ai mun Afuwa yanzu ba zaku dinga samun feji ranar Juma'a ba, sabida Oga yana gida duk Juma'a. Jama'a soyayya ba ƙarya bace🤣🤣. Dolena in zauna in kula da mai bada shinkafa ƴar gwamnati. Nagode son so💪🏼💪🏼💪🏼MRS BUKHARI ..... https://chat.whatsapp.com/Ewd4dGuB35VI7hqrRck8TH ✨🛍️ HAFSAT COLLECTION — INDA KYAU YA HAƊU DA SAUKIN FARASHI! 🛍️✨ Kin gaji da neman kaya masu kyau amma farashinsu ya yi tsada? 😍 Ki zo HAFSAT COLLECTION! ❤️ Muna kawo miki kayan kitchen masu kyau da inganci, laces masu kyau, atamfa, abayas da kayan zamani — duk a farashi mai sauƙin gaske! 🔥😍 💎 Ingantattun kaya 💰 Farashi mai sauƙi 🤝 Kyakkyawar mu'amala 📦 Muna tura kaya zuwa garuruwa daban-daban cikin aminci A HAFSAT COLLECTION, burinmu ba sayar da kaya kawai ba ne, muna son ki samu kaya masu kyau kuma ki dawo da farin ciki. 🥰❤️ ✨ Kada ki bari a baki labari—ki gwada HAFSAT COLLECTION yau! ✨ 📩 Ki turo mana da saƙo domin ganin kayan da suke available. HAFSAT COLLECTION — KYAU, INGANCI & FARASHI MAI SAUKI. ❤️🛍️ https://chat.whatsapp.com/Ewd4dGuB35VI7hqrRck8TH "Ga Hindu ga Hindu, ga mai ciki, ga mai ciki. Kai tubarkallah jibi yadda kika cika ta sama, wallahi cikinne gashi duk kin canja" Cewar Innah Abida da take ƙoƙarin riƙeni, nayi saurin kaucewa, sai hannuna ta samu zarafin taɓawa. Hakan yasa dole tayi turus. Kayan su Akarami suka dire, Qazzafi ya dunguremun kaina ya fice. Akarami kuma ya sakarmun murmushi. Amman inata ganin tausayina a idanunsu su su biyu, to ko me ya sa oho. Jikina na kuma kallo ni dai banga aibuna ba, takalminne ma ni yake sani jin kunya kamar in nitse. Wajen Innarmu na ƙarasa na zauna. Gaishe da Innah Abida nayi, na juyo na gaishe da Innarmu. Kafin muka miƙe tare da Innarmu. "Salamatu ma ta zo hutu tana ciki, in kika huta kya zo ku gaisa da mutan turai, sannu Hindu ya ƙauye da mutanen cikinta? " Innarmu tayi murmushi tace. "Abidah kenan ke dai ba'a rabaki da magana. Ai ke da ganin Hindu kinsan ƙauye da mutanen cikinta lafiya suke, ga tsarabanan buhu guda, kya taya ni buɗewa ai." Ni dai ciki na wuce, inata kalle_ kalle kamar fa na wanke makaranta. Ko ina ganinshi nake haɗaɗɗe. Innarmu ta sake fenti harda kujeru da labulaye duk ta sauya, da kafet ɗin tsakiyar ɗaki. "Abidah sai rigima in bata yada zance ba ita dai bata jin daɗi. Ke kuma wannan wanne irin takalmine a ƙafarki kika sako kamar wata marar galihu, ko irinshi yake iya siya mikine. Sannan zaki tawo ba zaki sa kayan da ba'a sanki dashi ba, sai ki kama ki sako kayanki tun na gida, sabida iskanci ba zaki ɗinga kayan zuwa gida ba. Haka kike ganin inayi in zani maiduguri ne? Hatta ku ɗinnan ɗinki nake yi muku, wannan ai sai ki tsinkani, wai kinga yadda Abidah ke kallonki kuwa. Ga gidan fal jama'ar biki, gashi goben dai sunan Matar Babanku Lukumanu matarshi ta haihu Amaryace yayo" Ni dai shiru nayi akan batun kaya da takalmi, na dai yi barka. To ya zanyi, bani da wani kayan da zan iya sakawa in burge, saina akwati ko wanda na tafi dasu, ba ɗinki nake yi ba. In banda ɗinkunan ankon bukukuwan gidannan bana ɗinkin komai. "Kije ki ɗauro Alwala kizo kiyi sallah" Miƙewa nayi da ƙyar ina ɗan turo ƙirjina dana sa rigar mama ƙatuwa mai cike da soso nayi him. "Tubarkallah ga cikinnan harya bayyana. Kema cikinki irin ya Yayarku ne baya girma sai dai yabi umma, amman bakya jin daɗin yanayinki ne, naga fuskarki ta kumbura. Ayya sannu ciki haka yake fa." Ni dai fita nayi bance uffan ba, ina wajen alwala da wanke wankenmu su Qazzafi suka shigo. A ɗakinmu na samesu Qazzafi na magana da Innarmu sai kallona yake yi. "Innarmu ni sai naga Duwaf ta yi girma sosai tayi ƙiba, amman wuyanta ya faɗa, fuskarta kuma ta kumbura." "Bata da lafiya ne, ta samu juna biyune abinda duk ake ta nema" Abun almara da al'ajabi sai kawai Qazzafi ya durƙusa yayi sujudul shukur, fuskarshi fal fara'a da dariya. Ina idarwa na kalleshi ina murmushi. "Allah sarki ɗan uwa abun wuya. Qazzafi na Duwaf. Ina jin daɗin yadda baka bari Mairamu ta raba maka zumunci da Duwaf ba. Ina jin daɗin yadda baka yi fishi ba lokacin da Hindu ta nuna ita ba kai take so ba. Tayi hakanne sabida ƙiyayyar Mairamu a gareta. Kuma ko ni dalilin da yasa naƙi aminta kenan. Ni ba kanwar lasa ba, Mairamu ba kanwar lasa ba, abun bazai yi muku kyau ba." Shigowar Baba Sojanmu da sallama ne ya katse Innarmu. "Hindu kece a tafe, ina Magawatan yake to, ko ke kaɗai ke kullum kike zuwa, da bazai rakoki ku tawo bibiyu ba, ga biki za'ayi?" Sai nayi murmushi nace. Yaso zuwa ma Mahaifiyarshi ce ba lafiya shi yasa. Nice ma nace ya zauna, amman yace in dai jikin yayi sauƙi zai zo in sha Allah, sai mu tafi tare." "Ashsha to Allah ya bata lafiya. Zai zo ai ya sameni ba zaki koma ba har sai yazo, naji me ya ɗaukeni. In nayi fishi abun bazai muku daɗi ba, Nagoɗi ne yake ta tauyeni shi yasa har kuka kai tsawon shekaru har shida. Da yanzu kin gama karatunki komai da komai, ko a Bauchi gya samu aiki. To yanzu gaki da juna, shikenan in kika sauka sai a bani hujjar sai kin yaye ko kuma me? Qazzafi ku zama shaida inna juya Hindu da mijinta ba zasu ji daɗi ba. Akan wannan yarjejeniyar in nace a bani ɗiyata kar aga laifina. Ko gaban malamai naje ba zasu ce nayi laifin komai ba, sabida akan doron wannan sharaɗinne harna yadda ɗiyata tayi aure acan. Jibeta fa yadda ta zama ƴar ƙauye ji wani kwalli damamme a idanunta. Ku in akabar Hindu haka wallahi watarana ba ganeta zaku yi ba. A hakanma tayi daban da sauran ƴan uwanta. Hatta yaran Dogara sun fita kyan fasali. Infosiful in saka ido ina kallonta haka. Shi is not ibin ashaim ob ha sef, jus luk at ha, bilej gel" Ya dinga faɗa yana ruwan turanci, rabi da kwatan maganganunshi da turanci yake yi. Ni dai nayi zuru _zuru gashi ance bazan koma ba sai Mijinyawa yazo. Tabb karfa asirina ya tonu lallai ina cikin tsaka mai wuyar fita. A yadda Baba Sojanmu ranshi ya ɓaci, wallahi nasan ko shekara zanyi, to fa tabbas sai Mijinyawa yazo kafin ya barni mu koma. "To ya jikin naki bakya fuskantar wani matsala ko, kuma hof dai kina zuwa awo ko?" Naje, jikinne dai sai dai a hankali kawai kullum ba lafiya" Sai kuma ya sassauto ya shiga hira dani harma yana zolayata ko na kawo musu nono da fura. Kafin inci abinci Innarmu ta juyemun ruwan wanka na wauwatsa naji daɗi sosai. Koda na fito duk a babban falo na samesu, ina shiga naga Innarmu ta ajjiyemun doguwar riga ƴar kanti ta yayi sabuwa fil. Murmushi nayi, uwa kenan mai daɗi, wallahi wanda ya rasa kulawar uwa abun a tausaya mishi ne. Innarmu Akwai tsumi da tanadi, da dabara sosai irin nasu iyayen da. Man mai gurguwa wanda Innarmu take mai haɗin gargajiya na gyaran jiki mai sirri na shafe jikina dashi. Na saka wannan riga na yane kaina da mayafin kana na fito. Innarmu bari inje in gaishe da matan gidan, babu wanda yasan shigowata." Fita nayi na dinga bin lunguna ina kwasar gaisuwa, ƴan uwa da abokan arziki ƴan biki sunanan cike da ko wanne lungu, su kuma sai ƙaremun kallo suke yi Innah Mairamu ce tace. "Duwaf kema cikin naki irinna Saratu ne baya fitowa, sai dai yabi Umma. Gaskiya zamu je asha bikin suna damu jama'are. Ranar jama'are zata ɗauka gaskiya dan har waɗanda basu je ba lokacin biki yanzune zasu je, barinma yanda kika yi jinkirinnan. Ai su Khadija ma duk zasu je. Allah dai ya raba lafiya" Ni dai na fita inata saƙawa a zuchiyata, toh ni yanzu yama zanyi da jama'ar gidanmu ta yaya zan fita kunyarsu ni Hindu. Kuma naga alamar kowa cewa zaiyi zai zo gaskiya, ai wallahi ko dan gulma, da son jama mutum jarfa nasan zasu iya yin bus uku ma cike Wannan tunanin har na kammala cin tuwo ban bari ba. Qazzafi fa sai da Innah Mairamu ta kirashi kana ya bar ɓarayinmu, a hakanna saida ya turo aka aikomun da gashasshiyar kaza ƙatuwa taji yaji jan gashi ma malam. Take yawuna ya hau gudana, innarmu na tsittsinkawa yawu na ambaliya a bakina. "Ungo ci Hindu ko zaki ji daɗin bakinki, gobe zan karɓi girki nasan kina kewa ko, me kike son ci wanda kike kewa sosai" Margi, da masar safe ta kari." "Ohh gulma, masar da kusan dole kuke cinta, yau itace in kuka bar gidan kuma babu abinda kuke kewa sama da'ita. Ai shikenan Abidah zata soya kici ki ƙoshi Hinduwa ta" To Allah ya nuna mana. Innarmu ba'a turomun yadin ankonsu Aminan ba, ko basu fitar da anko bane?" "Haba Hindu, a gidannan za'a iya biki ba anko ashe? Sun fitar da kala biyu, atampa da shadda. To Yayarku ta fitar muku da wata atampar, sai kammala ƴar senegal a madadin shaddar. Har an ɗinko dake ma, nace in kika zo kya biya kuɗin. Ko kuma ki barshi kawai na bar miki kuɗin. Amman ki sani sutura na da mahimmanci, kina ɗaukan albashinki duk wata, ki ɗan dinga siyan suturu mana, dasu takalma ki adana abunki sai in zaki zo gida ki saka. Abidah fa bata dena kallonki ba har saida taga kin saka wannan doguwar rigar, a tunaninta fa da'ita kika zo. Sannan in zaki tafi zan siya miki zannuwan jego falle_falle ki tafi dashi, kuma ki daure ki tanadi kayan zaman bakwai masu kyau. Kayan fitar suna kuma zanga yadda zanyi, ko Yayunki maza sa yi miki a ɗinka miki su daga nan, sai dai kawai ki saka." Ni dai nayi shiru kawai, ina jinjinama jarumta irinna Innarmu. Duk yadda nake da jarumta, Innarmu ta dokeni. A ranar Innarmu ta barnine na huta, nayi bacci a ɗakinmu mai cike da tarihi, ga fanka sai hurani take yi ni'ima takota ina ga wutar nefa duk inda na juya zanga haske, ga ba sauro sam, ba haushin karnuka. washegari da sassafe sai ga Yaya Saratu, da Yaya Zubaina sun zo mu gana kafin su wuce wajen aikinsu. Doya da ƙwai da miyar hanta Yaya Saratu ta kawomun, da ruwan shayi mai kyau. Kulolin data zubo abincin da basket ɗin da ta sako kulolin duk ababen kallone. Yaya Zubaina kuma farfesun ƙafar sa ta kawo mun, da biredi mai laushin gaske, ƴan uwa abun wuya, masa suka zuba a kwano ko wacce a gurguje ta wuce wajen aikinta. Ina zaune a falo ina shan farfesun ga kular a gabana, Baba Sojanmu ya fito ya zauna a falo tare da kunna tv dan soma sauraren labaran tara. "Hindu zo ga masar na kwashe ki zo ki zuba" Cewar Innah Abida. Da sauri na miƙe, zuba farfesun nayi a kwanon da nake ci na miƙa ma Baba Sojanmu, ya karɓa tare da jinjina mun. Ina fita Salamatu na fitowa daga ɗaki taci adon sufa, wuya da kunnenta duk gwal jiki duk hutu, ƙasan wuya duk madara. Ficewata nayi naje na ciko roba da masa guda goma sha biyu na zuba, na kwarara miya akai na koma ciki. Kaza na tadda Salamatu tana ci, ga kular Alala da kunun gyaɗa a gabanta kuma. "Hinduwa ashe wai kin samu ƙaruwa ɗan da ƙyar kenan " Allah ya nufa" Iyakar abinda nace kenan. "To Allah ya raba lafiya. Ba ranar komawa karatu kenan, sai lokacin reno" Saida na zauna kana nace. Ai banyi tunanin reno yana hana karatu ba, da yana hanawa da Yaya Saratu bata yi ba, dasu Khadijan lungun Baba Nagoɗi ba. Kuma ke kanki ai da baki yi aikin ba, tunda kema kin haihu. Lokaci in yayi zan koma karatu in sha Allah" Bakinta ta taɓe, Baba Sojanmu kuma yana shan wannan farfesu yana kallonmu. "Ai Salamatu zai zo ne ya sameni a wannan karon tabbas sai an tsaida mun lokaci kafinma in barta ta koma. Naga abun nashi tamkar raini ne ko menene dai oho. Amman duk abinda ke kanshi saina sauke mishi. Ba lallai ta koma wannan ƙauyen ƙayau ɗin ba" Ni dai nayi shiru ina cin masa har lumshe idanu nake yi sabida tsabaragen daɗin masar. Salamatu kuwa, sai zaro magana take yi, da misalai domin sake harzuƙa Baba Sojanmu. Ina kammalawa sai ga Qazzafi ya shigo falon, ya nemi waje ya zauna. Innarmu kuma tana daga falonta tana aikin kasafta tsarabar da nayo mai yawan gaske. Yadda nake samun damar kawo tsaraba mai yawa, tanadi nake yi duk ɗan abinda yake arha sai in siya in adana, da haka haka har in cika buhu da tsaraba. Nan kuma Innarmu tasa aka soma zagaye da tsarabarnan lungu_lungu harma da maƙota. "Abidah ga naku da Salamatu." "Aa ni kam sai dai Innah ki haɗa da nawa ni kam nagode" Cewar Salamatu kenan. Ni hankalina ma yana kan Baba Sojanmu da Qazzafi muna ta hirarmu. Zuwa sha ɗayan rana gida ya soma ɗinkewa da jama'ar taro. Bayan azahar su Zubaina suka dawo wajen aiki. Nan muka sanya kayan fitar suna, ni dai lace na saka su Yaya Saratu da su Rayya kuma Atampa ce suka saka, amman ba anko ba dai. Ƴan gidanmu sabida gulma fa, wallahi kowa sai zuwa ganina yake yi ana ta yi mun barka da arziki, kona gulmane, kona gaskiya ne ohon musu dai. Sai kusan magriba muka samu kammu ƴan ɗakinmu mu ka ɗan keɓe. "To ke Hindu wanne tanadin kika yi tun da kafin samun cikinnan. Sannan menene shirinku. Masu kurmin idanu da wuri suke soma kuka. Kinsan dai za'ayi gayya ta mamaki, kuma kowa yaje yana son ganin me za'ayi me akayi. Ko ba haka ba Saratu? " "Hakane Innarmu nima dai hankalina duk kuma sai ya koma kan yadda za'a ƙarke. Sabida muna da ƴan baƙin gida, ga ƴan uba dake son ganin faɗuwarka. Musamman faɗuwar ita Hindun. To ya kamata a san abun yi. Tunda ba lallai ta sake zuwa ba sai dai ƙila saƙon takadda. Batun wankan gida shima za'a tattauna muji yadda zata kaya" Yaya Zubaina tace. "Gaskiya kam ni tunda aka sanarmun wallahi harna soma ajjiye atampa, da kayan yara wanda maza da mata zasu iya amfani dashi ma. Innarmu duk ta koya mana tsimi." To ni dai kam muna yin namu shirye_shiryen daidai da ƙarfinmu, ta namu ɓangaren Innarmu. Danginshi ma suna yin nasu, gaku kuma dai. Ni dai Allah ma ya saukeni lafiya ji nake yi kamar ma mutuwa zanyi ba lallai in haihu ba" Nayi hakanne sabida in rage ƙarfin maganar tasu, sabida bani da abun cewa amman dai in sha Allah ba zamu ji kunya ba, zanyi iyakar iyawar abinda zan iya. Ga ɗan adashen makaranta ma na shiga. Kuma inaso in sake labule da kafet ɗin falo, kujerunma so samu in sauyasu, amman bana jin zai yiwu gaskiya" "Babu komai a bar maganar Ubangiji Allah zai saukeki lami lafiya Hinduna. Ki ta adda'a Allah zai saukeki lafiya. Akwai kayan jira jirai na fitar suna da setin jinjirare zaki haɗa ki tafi dasu. Sannan in cikin ki fa ya tsufa ki sashi ya dinga fita dake kina tattaki Hindu. Allah ya saukeki lafiya ai zanji daɗin ganin abinda zaki haifa" "Kuma Innarmu ai ya kamata ace kafin suna, a sauyama Hindu kayan ɗaki, ko da ba sababbi dadal bane, amman me kika gani shekara shida fa?" Cewar Yaya Saratu. "Eh to wannan gaskiya ne. Sai dai kuma wannan aikin naki ne. Abinda yasa nace haka, nafi son a sai kayan a Kano nan, a kai sai a kwaso natan a siyar. Zan mata ciko ko ba sababbi bane a sauya ɗin yana da kyau." Da haka zancan ya ƙare dai. Washegari da safe na shirya Qazzafi ya kaini gidan Luba. Tana tsakar gida, wanki ta tara mai yawan gaske ta duƙufa tana ta fama, ga igoyoyin gidan cike_cike fam da kayan shanya. Matan gidan kuwa Facalolinta ko wacce aikinta take yi. Masu girki nayi, masu kitso nayi, masu wankin ma dai duk suna yi ko wacce tana ƙofar ɗakinta. Luba na ganina tazo da gudu ta rungumeni sai kawai ta saki kukan farin ciki. Wani sanyi naji a raina. Ita hanyar nuna ƙaunarta da kewarta kukane, ni kuma sanyi nake ji a cikin zuchiyata annuri ya bayyana a fuskata. Jama'a ina son Luba sosai, kuma inai muku adda'a Ubangiji Allah ya haɗaku da ƙawaye na amana, ƙawancen gaskiya da gaskiya akwai daɗi sosai. "Hindu kinsan Allah jiya nayi mafarkinki wai kin haihu munje suna anata rikici da Yaya Jamila" Dariya muka saka ta jawo hannuna muka wuce. Cikin jam'u na gaishe da matan gidan. Duk suka washe baki cike da fara'a suka amsa gaisuwata. Ciki muka shige ni da Luba, ni a ƙasan ledar tsakar ɗakin da duk ta yage anbi da baƙin salateb na zauna. Wash Allah Luba ciki akwai wuya" Ihu Luba ta saka tare da godema Allah. "Hindu cikine dake, abun nema ya samu kenan? Kai na taya ki murna gaskiya na ganki kin yi ƙiba fuskarki ta ciko to ya kika ji laulayin daɗi ko? " Harararta nayi ta miƙo mun hannu muka kashe. "Mafarkina ya tabbata ashe, Allah ne yaso ya nuna mun. Kin ganni nima cikinne dani amman nawa ƙaramine sosai gaskiya, ga makaranta Hindu na koma rayuwar dai sai adda'a abubuwa sun sake damewa baki gani ba." Kin samu komawa makaranta Luba? Na taya ki murna. Ai in sha Allah in kika kammala karatun abubuwan zasu zo muku da sauƙi, da zaran an samu aiki koma wanne irine. Wuyarta a koma makarantar ai. Sunusi fa yayi ƙoƙari ni kin ganni har yanzu dai shiru. Baba Sojanmu ma wallahi cewa yayi bazan koma ba har sai mijinyawa yazo sun zauna akan batun komawata makaranta. Kinga lokaci nata ƙurewa, amman wallahi da abun yake kwana yake tashi Luba, babu halin komawa karatunne a halin yanzu. To kinsan Baba sojanmu shi babu ruwanshi da wannan labarin ma" Luba ta sauke ajjiyar zuchiya tace. "Ni kaina dafa ƙyar ake ta turawa Hindu. Bama lallai inci gaba da karatun ba. Kona abun hawa bana samu fa, to Sunusi bashi dashi, Mamanmu ce ma take yawan taimaka mana. Ɗan abinda ta tattaro saita aiko su Aisha su kawo mana. Ga wanki can na tara kuɗin omonne babu shi yasa suka taru haka. Abincin da zanci babu ko karyawa ban ba Hindu. Sunusin dai yaje ya dawo naji shiru, to fa tunda naji shiru baifa samo bane. Niyata wallahi inna kammala wankin, da aikace_aikacen gida zani. Inna ciyo na rana, na dare zan tawo mana da dafaffe." Luba ga ɗari biyu ki aiki yaro ya siyo mana taliyar murji ki ɓararraka mana muci, wannan ɗari ukun ya siyo mai da magi, ganyen shayi da sikari. Kina da itace ne? " "Ina kuwa naga itace. Ai ko wanka kin ganmu bamu yi ba. Wai kinsan Hindu rabi da kusan kwatan kayan akwatina, da wasu ƴan kayan kicin ɗina duk na siyar da wasu anci abinci da kuɗin kuwa? Hmmm. Sai idanunta yayi ƙwal ƙwal tana shirin yin kuka nera hamsin na saka kuɗin itace. Luba ashe da kanta ta je cefanen. Fitarta ke da wahala sai ga Sunusi. Da ƴar ledarshi baƙa a hannu. "Laa Hindu kece a garin. Yaushe kika shigo? Wallahi nice Sunusi shekaranjiya na shigo. Na same ku lafiya, ya aikin? " "Lafiya lau. Aiki gashinan anata lallaɓawa, yanzu haka ma daga wajen aiki nake nace bari in kawo mata abun kari, yau mun wayi gari sai godiyar Ubangiji. Ina abokina Gawata tare kuka tawo ne?" Aa yana jama'are ba tare muka tawo ba. Zai dai zo sai mu koma tare." Muna ɗan taɓa hira sai muka ji Luba ta watsar da itace sharab a bakin ƙofa, shigowa tayi da cefane a hannunta. "Sunusi ka dawo ashe? Ka ganni cefane naje yowa." Sunusi yace. "Cefane da wanne kuɗin Luba, bashi kika ciyo ne?" Luba tayi dariya tace. "Ko kaɗan Hindu ce ta bada kuɗin. Shiru shiru kai baka dawo ba to" Sai ya ɗan sosa kai ya shiga godiya. Ledar hannunshi ya miƙa mata, ya ce damu. "To ni kam na tafin ku. Hindu zaki kwana a wajen Luba ne, ni aikin kwana yau zanyi mai taimaka mun ɗin baya nan dole kwana zanyi" To babu damuwa sai mu kwanan ai hirarmu dama bata ƙare bace" Ficewa yayi Luba tabi bayanshi. Bata jima ba sai gata ta dawo da nera ɗari biyu. Ledar da Sunusi ya miƙa mata kuma Alala ce guda huɗu na gongoni an zazzage shi a leda an zuba mai da yajin akai, sai kunun gyaɗa shima a ledar. Jujjuyewa tayi ta duremun. "Cinye Hindu bari in hura wuta inzo" Ta miƙe tana murmushi. Illahirin jikina sai naji ya mutu murus _murus wallahi. Har Luba ta hura itace ta ɗaura tukunna tayi jajjage, ta tsayar da sanwa, ta shigo ta zauna kusa dani. Inata faman tubkewa da warwarewa akan wannan lamari "Hindu baki taɓa komai ba to? " Luba ke dai zauna ki karya, ni na karya ai in taliyar ta dahu naci, ki karya ga juna biyu a jikinki kina zama da yinwa" Jan kwanon tayi tace. "Ko ɗayane kici ko zanji daɗi" Hannu nasa na soma ci, kafin ta soma cin nata itama, muna ta zuba hira ba ƙaƙƙautawa nayi rashe_rashe a falo. Bayan mun ci abinci mun yi sallah, saina taya ta muka game wankin da sai da muka kai kusan magriba kafin muka gama. Wanke tsakar gidan tayi da ruwan wankin tas, muka ɗaura alwala muka shiga ciki. Shinkafa da wake da manja da yaji na wuta ta kusan nuna, daf la'asar Sunusi ya leƙo ya kawo mata. Ina sallah yaro ya shigo wai Hindu ta fito inji Qazzafi su tafi. Luba ce ta fita, ina sallamewa Qazzafi da Luba suna shigowa. "Qazzafi yau gashi naci albarkacin Hindu kazo gidana. Ina wuni ya gidan ya iyalin? " "Luba kenan iyayen baki ai kin dace da aikin jaridan da kuke da buri sosai. Ke kuma taso mu tafi sauri nake yi" Anan zan kwana Qazzafi, Sunusi bayanan gobe in Allah ya kaimu zamu tawo gida da Luban. In kaje ka faɗama Innarmu" Qazzafi bai bar gidan luba ba saida yaci abinci, gashi babu abincin da yawa shinkafa ce gongoni uku wake gongoni ɗaya rak. Sai dai da zai tafi sai ya ajjiye ma Luba dubu uku. Ya turo yaro da biredi, da kayan shayi harda tsire cikin takadda. Muka baje tsiren a saman shinkafa da wakennan muna ci muna tattaunawa dangane da batun masu zuwa jama'are in haihuwar tazo. A wannan rana mun tattauna abubuwa da yawa da Luba. Washegari bayan mun karya kuma muka nufi gida nanma wunin ne cur. Sai kuma aka shiga hidimar biki, dangi duk sun hallara, ƴan Kwantagora ma duk gasunan. Akayi biki lafiya, aka gama lafiya, sai ɗan rikicin daya kusan ɓallewa tsakanin Zubaina da Matar Yahuza, da Yaya Saratu da Salamatu. Amman Iyaye maza saida suka shiga, sabida rikicin ya yi ƙarfi sosai. Ni wallahi saida ƙurar ta lafa kana naji, ashe wai a kainane Yaya Saratu suka yi da Salamatu. Bayan kwana biyu na soma zagayen gidajen ƴan uwa, inanan Khadijan su Qazzafi ta haihu. Ranar suna sai gani ga matar Qazzafi sai wani fiskewa take yi, tana wani turanci da su Lamin su Qazzafi. Ni ko banza na ba ajjiyarta gaisuwa wannan bata shiga tsakaninmu ba. Hirarmu kawai muke yi dasu Luba da ƴan lungun Baba Alƙali. Sai dab magriba muka kama hanyar gida. Ni dai haka na share wata guda a gida, danma na nemi Inda Shehulle yake lodi na bashi wasiƙa ya kaima mijinyawa. Gashi asirina yana shirin tonuwa, yau da gobe ina mance ya kamata in ɗan dinga son jiki, da ɗan kwaɗayi haka, sannan sai inga Innarmu nata kallona haka dai. To ranar litinin muna dawowa daga kasuwa da yamma da Luba. Mun je wata ƙawarta ta fasa dilar kayan jira jirai muka je muka tsinto masu yawa gaskiya, dan tayi mana sauƙi ni kuma a lokacin da ɗan kuɗaɗe a hannuna da Akarami ya bani, Yaya Soja ma da yazo ya bani, Qazzafi ma haka. Kuma dama mun shiga kasuwa mun siyo safuna, da huluna, da wandunan jarirai abun gwanin sha'awa, har labule irin gumamannan na siya, masu kyau baku gansu ba. Inama ace da gaske haihuwar zanyi da ba haka ba. Sai dai kash. Muna shigowa na tadda mijinyawa a falo a zaune yana jiran Baba Sojanmu. Innarmu ta ajjiye mishi abinci da ruwa, da filas ɗin shayinmu na Kanurai. Idanu muka haɗa na sakar mishi murmushi, shima murmushin nayi kewarki yayi mun. Gyaran muryar Baba Sojanmu ne yasa na dawo hayyacina. Innah Abidah sai ƙarema ledojin hannayenmu ni da Luba da suke gaisawa da mijinyawa kallo take yi. "Hindu siyayyar haihuwar kike yi a nan kafin ki wuce ko? Ai yafi miki ki sai duk abinda ya dace. Wallahi kinsan fa ƙauye ba lallai ki samu irin kayan daya dace ba" Kallonta kawai nayi, bance uffan ba naja hannun Luba muka shige. Meya faru me ya faru kawai muka soma jiyo turanci na tashi a falo, Baba Sojanmu naji yana bazan koma ba, nazo kenan, sai dai shi ya koma shi kaɗai. Duk fa da turanci. Ni dai ina zaune jigum nasan dama za'a rina. Innarmu ce ta leƙo. "Ke Hindu kizo inji Baba Sojanku maza" Miƙewa nayi nabi bayanta zuwa falon. Innah Abida sai zurga_zurga take yi. Tana ganin na fito ta nemi waje ta zauna, sabida jin ƙwaƙwaf. Mijinyawa kanshi a sauke baya ko iya ɗagowa. Ga Baba Nagoɗi, ga Baba Alƙali duk Baba Soja ya kirawosu su zame mishi shaidar gani da idanu. Ga takaddar yarjejeniya a hannun Baba Sojanmu harda biro. Yaufa ake yinta. Me za'ayi da biro ni Hindu? Mrs Bukhari Sai mun haɗu zuwa gobe in Ubangiji ya amince. 💪🏼MRS BUKHARI ..... https://chat.whatsapp.com/Ewd4dGuB35VI7hqrRck8TH ✨🛍️ HAFSAT COLLECTION — INDA KYAU YA HAƊU DA SAUKIN FARASHI! 🛍️✨ Kin gaji da neman kaya masu kyau amma farashinsu ya yi tsada? 😍 Ki zo HAFSAT COLLECTION! ❤️ Muna kawo miki kayan kitchen masu kyau da inganci, laces masu kyau, atamfa, abayas da kayan zamani — duk a farashi mai sauƙin gaske! 🔥😍 💎 Ingantattun kaya 💰 Farashi mai sauƙi 🤝 Kyakkyawar mu'amala 📦 Muna tura kaya zuwa garuruwa daban-daban cikin aminci A HAFSAT COLLECTION, burinmu ba sayar da kaya kawai ba ne, muna son ki samu kaya masu kyau kuma ki dawo da farin ciki. 🥰❤️ ✨ Kada ki bari a baki labari—ki gwada HAFSAT COLLECTION yau! ✨ 📩 Ki turo mana da saƙo domin ganin kayan da suke available. HAFSAT COLLECTION — KYAU, INGANCI & FARASHI MAI SAUKI. ❤️🛍️ https://chat.whatsapp.com/Ewd4dGuB35VI7hqrRck8TH "Ga Hindu ga Hindu, ga mai ciki, ga mai ciki. Kai tubarkallah jibi yadda kika cika ta sama, wallahi cikinne gashi duk kin canja" Cewar Innah Abida da take ƙoƙarin riƙeni, nayi saurin kaucewa, sai hannuna ta samu zarafin taɓawa. Hakan yasa dole tayi turus. Kayan su Akarami suka dire, Qazzafi ya dunguremun kaina ya fice. Akarami kuma ya sakarmun murmushi. Amman inata ganin tausayina a idanunsu su su biyu, to ko me ya sa oho. Jikina na kuma kallo ni dai banga aibuna ba, takalminne ma ni yake sani jin kunya kamar in nitse. Wajen Innarmu na ƙarasa na zauna. Gaishe da Innah Abida nayi, na juyo na gaishe da Innarmu. Kafin muka miƙe tare da Innarmu. "Salamatu ma ta zo hutu tana ciki, in kika huta kya zo ku gaisa da mutan turai, sannu Hindu ya ƙauye da mutanen cikinta? " Innarmu tayi murmushi tace. "Abidah kenan ke dai ba'a rabaki da magana. Ai ke da ganin Hindu kinsan ƙauye da mutanen cikinta lafiya suke, ga tsarabanan buhu guda, kya taya ni buɗewa ai." Ni dai ciki na wuce, inata kalle_ kalle kamar fa na wanke makaranta. Ko ina ganinshi nake haɗaɗɗe. Innarmu ta sake fenti harda kujeru da labulaye duk ta sauya, da kafet ɗin tsakiyar ɗaki. "Abidah sai rigima in bata yada zance ba ita dai bata jin daɗi. Ke kuma wannan wanne irin takalmine a ƙafarki kika sako kamar wata marar galihu, ko irinshi yake iya siya mikine. Sannan zaki tawo ba zaki sa kayan da ba'a sanki dashi ba, sai ki kama ki sako kayanki tun na gida, sabida iskanci ba zaki ɗinga kayan zuwa gida ba. Haka kike ganin inayi in zani maiduguri ne? Hatta ku ɗinnan ɗinki nake yi muku, wannan ai sai ki tsinkani, wai kinga yadda Abidah ke kallonki kuwa. Ga gidan fal jama'ar biki, gashi goben dai sunan Matar Babanku Lukumanu matarshi ta haihu Amaryace yayo" Ni dai shiru nayi akan batun kaya da takalmi, na dai yi barka. To ya zanyi, bani da wani kayan da zan iya sakawa in burge, saina akwati ko wanda na tafi dasu, ba ɗinki nake yi ba. In banda ɗinkunan ankon bukukuwan gidannan bana ɗinkin komai. "Kije ki ɗauro Alwala kizo kiyi sallah" Miƙewa nayi da ƙyar ina ɗan turo ƙirjina dana sa rigar mama ƙatuwa mai cike da soso nayi him. "Tubarkallah ga cikinnan harya bayyana. Kema cikinki irin ya Yayarku ne baya girma sai dai yabi umma, amman bakya jin daɗin yanayinki ne, naga fuskarki ta kumbura. Ayya sannu ciki haka yake fa." Ni dai fita nayi bance uffan ba, ina wajen alwala da wanke wankenmu su Qazzafi suka shigo. A ɗakinmu na samesu Qazzafi na magana da Innarmu sai kallona yake yi. "Innarmu ni sai naga Duwaf ta yi girma sosai tayi ƙiba, amman wuyanta ya faɗa, fuskarta kuma ta kumbura." "Bata da lafiya ne, ta samu juna biyune abinda duk ake ta nema" Abun almara da al'ajabi sai kawai Qazzafi ya durƙusa yayi sujudul shukur, fuskarshi fal fara'a da dariya. Ina idarwa na kalleshi ina murmushi. "Allah sarki ɗan uwa abun wuya. Qazzafi na Duwaf. Ina jin daɗin yadda baka bari Mairamu ta raba maka zumunci da Duwaf ba. Ina jin daɗin yadda baka yi fishi ba lokacin da Hindu ta nuna ita ba kai take so ba. Tayi hakanne sabida ƙiyayyar Mairamu a gareta. Kuma ko ni dalilin da yasa naƙi aminta kenan. Ni ba kanwar lasa ba, Mairamu ba kanwar lasa ba, abun bazai yi muku kyau ba." Shigowar Baba Sojanmu da sallama ne ya katse Innarmu. "Hindu kece a tafe, ina Magawatan yake to, ko ke kaɗai ke kullum kike zuwa, da bazai rakoki ku tawo bibiyu ba, ga biki za'ayi?" Sai nayi murmushi nace. Yaso zuwa ma Mahaifiyarshi ce ba lafiya shi yasa. Nice ma nace ya zauna, amman yace in dai jikin yayi sauƙi zai zo in sha Allah, sai mu tafi tare." "Ashsha to Allah ya bata lafiya. Zai zo ai ya sameni ba zaki koma ba har sai yazo, naji me ya ɗaukeni. In nayi fishi abun bazai muku daɗi ba, Nagoɗi ne yake ta tauyeni shi yasa har kuka kai tsawon shekaru har shida. Da yanzu kin gama karatunki komai da komai, ko a Bauchi gya samu aiki. To yanzu gaki da juna, shikenan in kika sauka sai a bani hujjar sai kin yaye ko kuma me? Qazzafi ku zama shaida inna juya Hindu da mijinta ba zasu ji daɗi ba. Akan wannan yarjejeniyar in nace a bani ɗiyata kar aga laifina. Ko gaban malamai naje ba zasu ce nayi laifin komai ba, sabida akan doron wannan sharaɗinne harna yadda ɗiyata tayi aure acan. Jibeta fa yadda ta zama ƴar ƙauye ji wani kwalli damamme a idanunta. Ku in akabar Hindu haka wallahi watarana ba ganeta zaku yi ba. A hakanma tayi daban da sauran ƴan uwanta. Hatta yaran Dogara sun fita kyan fasali. Infosiful in saka ido ina kallonta haka. Shi is not ibin ashaim ob ha sef, jus luk at ha, bilej gel" Ya dinga faɗa yana ruwan turanci, rabi da kwatan maganganunshi da turanci yake yi. Ni dai nayi zuru _zuru gashi ance bazan koma ba sai Mijinyawa yazo. Tabb karfa asirina ya tonu lallai ina cikin tsaka mai wuyar fita. A yadda Baba Sojanmu ranshi ya ɓaci, wallahi nasan ko shekara zanyi, to fa tabbas sai Mijinyawa yazo kafin ya barni mu koma. "To ya jikin naki bakya fuskantar wani matsala ko, kuma hof dai kina zuwa awo ko?" Naje, jikinne dai sai dai a hankali kawai kullum ba lafiya" Sai kuma ya sassauto ya shiga hira dani harma yana zolayata ko na kawo musu nono da fura. Kafin inci abinci Innarmu ta juyemun ruwan wanka na wauwatsa naji daɗi sosai. Koda na fito duk a babban falo na samesu, ina shiga naga Innarmu ta ajjiyemun doguwar riga ƴar kanti ta yayi sabuwa fil. Murmushi nayi, uwa kenan mai daɗi, wallahi wanda ya rasa kulawar uwa abun a tausaya mishi ne. Innarmu Akwai tsumi da tanadi, da dabara sosai irin nasu iyayen da. Man mai gurguwa wanda Innarmu take mai haɗin gargajiya na gyaran jiki mai sirri na shafe jikina dashi. Na saka wannan riga na yane kaina da mayafin kana na fito. Innarmu bari inje in gaishe da matan gidan, babu wanda yasan shigowata." Fita nayi na dinga bin lunguna ina kwasar gaisuwa, ƴan uwa da abokan arziki ƴan biki sunanan cike da ko wanne lungu, su kuma sai ƙaremun kallo suke yi Innah Mairamu ce tace. "Duwaf kema cikin naki irinna Saratu ne baya fitowa, sai dai yabi Umma. Gaskiya zamu je asha bikin suna damu jama'are. Ranar jama'are zata ɗauka gaskiya dan har waɗanda basu je ba lokacin biki yanzune zasu je, barinma yanda kika yi jinkirinnan. Ai su Khadija ma duk zasu je. Allah dai ya raba lafiya" Ni dai na fita inata saƙawa a zuchiyata, toh ni yanzu yama zanyi da jama'ar gidanmu ta yaya zan fita kunyarsu ni Hindu. Kuma naga alamar kowa cewa zaiyi zai zo gaskiya, ai wallahi ko dan gulma, da son jama mutum jarfa nasan zasu iya yin bus uku ma cike Wannan tunanin har na kammala cin tuwo ban bari ba. Qazzafi fa sai da Innah Mairamu ta kirashi kana ya bar ɓarayinmu, a hakanna saida ya turo aka aikomun da gashasshiyar kaza ƙatuwa taji yaji jan gashi ma malam. Take yawuna ya hau gudana, innarmu na tsittsinkawa yawu na ambaliya a bakina. "Ungo ci Hindu ko zaki ji daɗin bakinki, gobe zan karɓi girki nasan kina kewa ko, me kike son ci wanda kike kewa sosai" Margi, da masar safe ta kari." "Ohh gulma, masar da kusan dole kuke cinta, yau itace in kuka bar gidan kuma babu abinda kuke kewa sama da'ita. Ai shikenan Abidah zata soya kici ki ƙoshi Hinduwa ta" To Allah ya nuna mana. Innarmu ba'a turomun yadin ankonsu Aminan ba, ko basu fitar da anko bane?" "Haba Hindu, a gidannan za'a iya biki ba anko ashe? Sun fitar da kala biyu, atampa da shadda. To Yayarku ta fitar muku da wata atampar, sai kammala ƴar senegal a madadin shaddar. Har an ɗinko dake ma, nace in kika zo kya biya kuɗin. Ko kuma ki barshi kawai na bar miki kuɗin. Amman ki sani sutura na da mahimmanci, kina ɗaukan albashinki duk wata, ki ɗan dinga siyan suturu mana, dasu takalma ki adana abunki sai in zaki zo gida ki saka. Abidah fa bata dena kallonki ba har saida taga kin saka wannan doguwar rigar, a tunaninta fa da'ita kika zo. Sannan in zaki tafi zan siya miki zannuwan jego falle_falle ki tafi dashi, kuma ki daure ki tanadi kayan zaman bakwai masu kyau. Kayan fitar suna kuma zanga yadda zanyi, ko Yayunki maza sa yi miki a ɗinka miki su daga nan, sai dai kawai ki saka." Ni dai nayi shiru kawai, ina jinjinama jarumta irinna Innarmu. Duk yadda nake da jarumta, Innarmu ta dokeni. A ranar Innarmu ta barnine na huta, nayi bacci a ɗakinmu mai cike da tarihi, ga fanka sai hurani take yi ni'ima takota ina ga wutar nefa duk inda na juya zanga haske, ga ba sauro sam, ba haushin karnuka. washegari da sassafe sai ga Yaya Saratu, da Yaya Zubaina sun zo mu gana kafin su wuce wajen aikinsu. Doya da ƙwai da miyar hanta Yaya Saratu ta kawomun, da ruwan shayi mai kyau. Kulolin data zubo abincin da basket ɗin da ta sako kulolin duk ababen kallone. Yaya Zubaina kuma farfesun ƙafar sa ta kawo mun, da biredi mai laushin gaske, ƴan uwa abun wuya, masa suka zuba a kwano ko wacce a gurguje ta wuce wajen aikinta. Ina zaune a falo ina shan farfesun ga kular a gabana, Baba Sojanmu ya fito ya zauna a falo tare da kunna tv dan soma sauraren labaran tara. "Hindu zo ga masar na kwashe ki zo ki zuba" Cewar Innah Abida. Da sauri na miƙe, zuba farfesun nayi a kwanon da nake ci na miƙa ma Baba Sojanmu, ya karɓa tare da jinjina mun. Ina fita Salamatu na fitowa daga ɗaki taci adon sufa, wuya da kunnenta duk gwal jiki duk hutu, ƙasan wuya duk madara. Ficewata nayi naje na ciko roba da masa guda goma sha biyu na zuba, na kwarara miya akai na koma ciki. Kaza na tadda Salamatu tana ci, ga kular Alala da kunun gyaɗa a gabanta kuma. "Hinduwa ashe wai kin samu ƙaruwa ɗan da ƙyar kenan " Allah ya nufa" Iyakar abinda nace kenan. "To Allah ya raba lafiya. Ba ranar komawa karatu kenan, sai lokacin reno" Saida na zauna kana nace. Ai banyi tunanin reno yana hana karatu ba, da yana hanawa da Yaya Saratu bata yi ba, dasu Khadijan lungun Baba Nagoɗi ba. Kuma ke kanki ai da baki yi aikin ba, tunda kema kin haihu. Lokaci in yayi zan koma karatu in sha Allah" Bakinta ta taɓe, Baba Sojanmu kuma yana shan wannan farfesu yana kallonmu. "Ai Salamatu zai zo ne ya sameni a wannan karon tabbas sai an tsaida mun lokaci kafinma in barta ta koma. Naga abun nashi tamkar raini ne ko menene dai oho. Amman duk abinda ke kanshi saina sauke mishi. Ba lallai ta koma wannan ƙauyen ƙayau ɗin ba" Ni dai nayi shiru ina cin masa har lumshe idanu nake yi sabida tsabaragen daɗin masar. Salamatu kuwa, sai zaro magana take yi, da misalai domin sake harzuƙa Baba Sojanmu. Ina kammalawa sai ga Qazzafi ya shigo falon, ya nemi waje ya zauna. Innarmu kuma tana daga falonta tana aikin kasafta tsarabar da nayo mai yawan gaske. Yadda nake samun damar kawo tsaraba mai yawa, tanadi nake yi duk ɗan abinda yake arha sai in siya in adana, da haka haka har in cika buhu da tsaraba. Nan kuma Innarmu tasa aka soma zagaye da tsarabarnan lungu_lungu harma da maƙota. "Abidah ga naku da Salamatu." "Aa ni kam sai dai Innah ki haɗa da nawa ni kam nagode" Cewar Salamatu kenan. Ni hankalina ma yana kan Baba Sojanmu da Qazzafi muna ta hirarmu. Zuwa sha ɗayan rana gida ya soma ɗinkewa da jama'ar taro. Bayan azahar su Zubaina suka dawo wajen aiki. Nan muka sanya kayan fitar suna, ni dai lace na saka su Yaya Saratu da su Rayya kuma Atampa ce suka saka, amman ba anko ba dai. Ƴan gidanmu sabida gulma fa, wallahi kowa sai zuwa ganina yake yi ana ta yi mun barka da arziki, kona gulmane, kona gaskiya ne ohon musu dai. Sai kusan magriba muka samu kammu ƴan ɗakinmu mu ka ɗan keɓe. "To ke Hindu wanne tanadin kika yi tun da kafin samun cikinnan. Sannan menene shirinku. Masu kurmin idanu da wuri suke soma kuka. Kinsan dai za'ayi gayya ta mamaki, kuma kowa yaje yana son ganin me za'ayi me akayi. Ko ba haka ba Saratu? " "Hakane Innarmu nima dai hankalina duk kuma sai ya koma kan yadda za'a ƙarke. Sabida muna da ƴan baƙin gida, ga ƴan uba dake son ganin faɗuwarka. Musamman faɗuwar ita Hindun. To ya kamata a san abun yi. Tunda ba lallai ta sake zuwa ba sai dai ƙila saƙon takadda. Batun wankan gida shima za'a tattauna muji yadda zata kaya" Yaya Zubaina tace. "Gaskiya kam ni tunda aka sanarmun wallahi harna soma ajjiye atampa, da kayan yara wanda maza da mata zasu iya amfani dashi ma. Innarmu duk ta koya mana tsimi." To ni dai kam muna yin namu shirye_shiryen daidai da ƙarfinmu, ta namu ɓangaren Innarmu. Danginshi ma suna yin nasu, gaku kuma dai. Ni dai Allah ma ya saukeni lafiya ji nake yi kamar ma mutuwa zanyi ba lallai in haihu ba" Nayi hakanne sabida in rage ƙarfin maganar tasu, sabida bani da abun cewa amman dai in sha Allah ba zamu ji kunya ba, zanyi iyakar iyawar abinda zan iya. Ga ɗan adashen makaranta ma na shiga. Kuma inaso in sake labule da kafet ɗin falo, kujerunma so samu in sauyasu, amman bana jin zai yiwu gaskiya" "Babu komai a bar maganar Ubangiji Allah zai saukeki lami lafiya Hinduna. Ki ta adda'a Allah zai saukeki lafiya. Akwai kayan jira jirai na fitar suna da setin jinjirare zaki haɗa ki tafi dasu. Sannan in cikin ki fa ya tsufa ki sashi ya dinga fita dake kina tattaki Hindu. Allah ya saukeki lafiya ai zanji daɗin ganin abinda zaki haifa" "Kuma Innarmu ai ya kamata ace kafin suna, a sauyama Hindu kayan ɗaki, ko da ba sababbi dadal bane, amman me kika gani shekara shida fa?" Cewar Yaya Saratu. "Eh to wannan gaskiya ne. Sai dai kuma wannan aikin naki ne. Abinda yasa nace haka, nafi son a sai kayan a Kano nan, a kai sai a kwaso natan a siyar. Zan mata ciko ko ba sababbi bane a sauya ɗin yana da kyau." Da haka zancan ya ƙare dai. Washegari da safe na shirya Qazzafi ya kaini gidan Luba. Tana tsakar gida, wanki ta tara mai yawan gaske ta duƙufa tana ta fama, ga igoyoyin gidan cike_cike fam da kayan shanya. Matan gidan kuwa Facalolinta ko wacce aikinta take yi. Masu girki nayi, masu kitso nayi, masu wankin ma dai duk suna yi ko wacce tana ƙofar ɗakinta. Luba na ganina tazo da gudu ta rungumeni sai kawai ta saki kukan farin ciki. Wani sanyi naji a raina. Ita hanyar nuna ƙaunarta da kewarta kukane, ni kuma sanyi nake ji a cikin zuchiyata annuri ya bayyana a fuskata. Jama'a ina son Luba sosai, kuma inai muku adda'a Ubangiji Allah ya haɗaku da ƙawaye na amana, ƙawancen gaskiya da gaskiya akwai daɗi sosai. "Hindu kinsan Allah jiya nayi mafarkinki wai kin haihu munje suna anata rikici da Yaya Jamila" Dariya muka saka ta jawo hannuna muka wuce. Cikin jam'u na gaishe da matan gidan. Duk suka washe baki cike da fara'a suka amsa gaisuwata. Ciki muka shige ni da Luba, ni a ƙasan ledar tsakar ɗakin da duk ta yage anbi da baƙin salateb na zauna. Wash Allah Luba ciki akwai wuya" Ihu Luba ta saka tare da godema Allah. "Hindu cikine dake, abun nema ya samu kenan? Kai na taya ki murna gaskiya na ganki kin yi ƙiba fuskarki ta ciko to ya kika ji laulayin daɗi ko? " Harararta nayi ta miƙo mun hannu muka kashe. "Mafarkina ya tabbata ashe, Allah ne yaso ya nuna mun. Kin ganni nima cikinne dani amman nawa ƙaramine sosai gaskiya, ga makaranta Hindu na koma rayuwar dai sai adda'a abubuwa sun sake damewa baki gani ba." Kin samu komawa makaranta Luba? Na taya ki murna. Ai in sha Allah in kika kammala karatun abubuwan zasu zo muku da sauƙi, da zaran an samu aiki koma wanne irine. Wuyarta a koma makarantar ai. Sunusi fa yayi ƙoƙari ni kin ganni har yanzu dai shiru. Baba Sojanmu ma wallahi cewa yayi bazan koma ba har sai mijinyawa yazo sun zauna akan batun komawata makaranta. Kinga lokaci nata ƙurewa, amman wallahi da abun yake kwana yake tashi Luba, babu halin komawa karatunne a halin yanzu. To kinsan Baba sojanmu shi babu ruwanshi da wannan labarin ma" Luba ta sauke ajjiyar zuchiya tace. "Ni kaina dafa ƙyar ake ta turawa Hindu. Bama lallai inci gaba da karatun ba. Kona abun hawa bana samu fa, to Sunusi bashi dashi, Mamanmu ce ma take yawan taimaka mana. Ɗan abinda ta tattaro saita aiko su Aisha su kawo mana. Ga wanki can na tara kuɗin omonne babu shi yasa suka taru haka. Abincin da zanci babu ko karyawa ban ba Hindu. Sunusin dai yaje ya dawo naji shiru, to fa tunda naji shiru baifa samo bane. Niyata wallahi inna kammala wankin, da aikace_aikacen gida zani. Inna ciyo na rana, na dare zan tawo mana da dafaffe." Luba ga ɗari biyu ki aiki yaro ya siyo mana taliyar murji ki ɓararraka mana muci, wannan ɗari ukun ya siyo mai da magi, ganyen shayi da sikari. Kina da itace ne? " "Ina kuwa naga itace. Ai ko wanka kin ganmu bamu yi ba. Wai kinsan Hindu rabi da kusan kwatan kayan akwatina, da wasu ƴan kayan kicin ɗina duk na siyar da wasu anci abinci da kuɗin kuwa? Hmmm. Sai idanunta yayi ƙwal ƙwal tana shirin yin kuka nera hamsin na saka kuɗin itace. Luba ashe da kanta ta je cefanen. Fitarta ke da wahala sai ga Sunusi. Da ƴar ledarshi baƙa a hannu. "Laa Hindu kece a garin. Yaushe kika shigo? Wallahi nice Sunusi shekaranjiya na shigo. Na same ku lafiya, ya aikin? " "Lafiya lau. Aiki gashinan anata lallaɓawa, yanzu haka ma daga wajen aiki nake nace bari in kawo mata abun kari, yau mun wayi gari sai godiyar Ubangiji. Ina abokina Gawata tare kuka tawo ne?" Aa yana jama'are ba tare muka tawo ba. Zai dai zo sai mu koma tare." Muna ɗan taɓa hira sai muka ji Luba ta watsar da itace sharab a bakin ƙofa, shigowa tayi da cefane a hannunta. "Sunusi ka dawo ashe? Ka ganni cefane naje yowa." Sunusi yace. "Cefane da wanne kuɗin Luba, bashi kika ciyo ne?" Luba tayi dariya tace. "Ko kaɗan Hindu ce ta bada kuɗin. Shiru shiru kai baka dawo ba to" Sai ya ɗan sosa kai ya shiga godiya. Ledar hannunshi ya miƙa mata, ya ce damu. "To ni kam na tafin ku. Hindu zaki kwana a wajen Luba ne, ni aikin kwana yau zanyi mai taimaka mun ɗin baya nan dole kwana zanyi" To babu damuwa sai mu kwanan ai hirarmu dama bata ƙare bace" Ficewa yayi Luba tabi bayanshi. Bata jima ba sai gata ta dawo da nera ɗari biyu. Ledar da Sunusi ya miƙa mata kuma Alala ce guda huɗu na gongoni an zazzage shi a leda an zuba mai da yajin akai, sai kunun gyaɗa shima a ledar. Jujjuyewa tayi ta duremun. "Cinye Hindu bari in hura wuta inzo" Ta miƙe tana murmushi. Illahirin jikina sai naji ya mutu murus _murus wallahi. Har Luba ta hura itace ta ɗaura tukunna tayi jajjage, ta tsayar da sanwa, ta shigo ta zauna kusa dani. Inata faman tubkewa da warwarewa akan wannan lamari "Hindu baki taɓa komai ba to? " Luba ke dai zauna ki karya, ni na karya ai in taliyar ta dahu naci, ki karya ga juna biyu a jikinki kina zama da yinwa" Jan kwanon tayi tace. "Ko ɗayane kici ko zanji daɗi" Hannu nasa na soma ci, kafin ta soma cin nata itama, muna ta zuba hira ba ƙaƙƙautawa nayi rashe_rashe a falo. Bayan mun ci abinci mun yi sallah, saina taya ta muka game wankin da sai da muka kai kusan magriba kafin muka gama. Wanke tsakar gidan tayi da ruwan wankin tas, muka ɗaura alwala muka shiga ciki. Shinkafa da wake da manja da yaji na wuta ta kusan nuna, daf la'asar Sunusi ya leƙo ya kawo mata. Ina sallah yaro ya shigo wai Hindu ta fito inji Qazzafi su tafi. Luba ce ta fita, ina sallamewa Qazzafi da Luba suna shigowa. "Qazzafi yau gashi naci albarkacin Hindu kazo gidana. Ina wuni ya gidan ya iyalin? " "Luba kenan iyayen baki ai kin dace da aikin jaridan da kuke da buri sosai. Ke kuma taso mu tafi sauri nake yi" Anan zan kwana Qazzafi, Sunusi bayanan gobe in Allah ya kaimu zamu tawo gida da Luban. In kaje ka faɗama Innarmu" Qazzafi bai bar gidan luba ba saida yaci abinci, gashi babu abincin da yawa shinkafa ce gongoni uku wake gongoni ɗaya rak. Sai dai da zai tafi sai ya ajjiye ma Luba dubu uku. Ya turo yaro da biredi, da kayan shayi harda tsire cikin takadda. Muka baje tsiren a saman shinkafa da wakennan muna ci muna tattaunawa dangane da batun masu zuwa jama'are in haihuwar tazo. A wannan rana mun tattauna abubuwa da yawa da Luba. Washegari bayan mun karya kuma muka nufi gida nanma wunin ne cur. Sai kuma aka shiga hidimar biki, dangi duk sun hallara, ƴan Kwantagora ma duk gasunan. Akayi biki lafiya, aka gama lafiya, sai ɗan rikicin daya kusan ɓallewa tsakanin Zubaina da Matar Yahuza, da Yaya Saratu da Salamatu. Amman Iyaye maza saida suka shiga, sabida rikicin ya yi ƙarfi sosai. Ni wallahi saida ƙurar ta lafa kana naji, ashe wai a kainane Yaya Saratu suka yi da Salamatu. Bayan kwana biyu na soma zagayen gidajen ƴan uwa, inanan Khadijan su Qazzafi ta haihu. Ranar suna sai gani ga matar Qazzafi sai wani fiskewa take yi, tana wani turanci da su Lamin su Qazzafi. Ni ko banza na ba ajjiyarta gaisuwa wannan bata shiga tsakaninmu ba. Hirarmu kawai muke yi dasu Luba da ƴan lungun Baba Alƙali. Sai dab magriba muka kama hanyar gida. Ni dai haka na share wata guda a gida, danma na nemi Inda Shehulle yake lodi na bashi wasiƙa ya kaima mijinyawa. Gashi asirina yana shirin tonuwa, yau da gobe ina mance ya kamata in ɗan dinga son jiki, da ɗan kwaɗayi haka, sannan sai inga Innarmu nata kallona haka dai. To ranar litinin muna dawowa daga kasuwa da yamma da Luba. Mun je wata ƙawarta ta fasa dilar kayan jira jirai muka je muka tsinto masu yawa gaskiya, dan tayi mana sauƙi ni kuma a lokacin da ɗan kuɗaɗe a hannuna da Akarami ya bani, Yaya Soja ma da yazo ya bani, Qazzafi ma haka. Kuma dama mun shiga kasuwa mun siyo safuna, da huluna, da wandunan jarirai abun gwanin sha'awa, har labule irin gumamannan na siya, masu kyau baku gansu ba. Inama ace da gaske haihuwar zanyi da ba haka ba. Sai dai kash. Muna shigowa na tadda mijinyawa a falo a zaune yana jiran Baba Sojanmu. Innarmu ta ajjiye mishi abinci da ruwa, da filas ɗin shayinmu na Kanurai. Idanu muka haɗa na sakar mishi murmushi, shima murmushin nayi kewarki yayi mun. Gyaran muryar Baba Sojanmu ne yasa na dawo hayyacina. Innah Abidah sai ƙarema ledojin hannayenmu ni da Luba da suke gaisawa da mijinyawa kallo take yi. "Hindu siyayyar haihuwar kike yi a nan kafin ki wuce ko? Ai yafi miki ki sai duk abinda ya dace. Wallahi kinsan fa ƙauye ba lallai ki samu irin kayan daya dace ba" Kallonta kawai nayi, bance uffan ba naja hannun Luba muka shige. Meya faru me ya faru kawai muka soma jiyo turanci na tashi a falo, Baba Sojanmu naji yana bazan koma ba, nazo kenan, sai dai shi ya koma shi kaɗai. Duk fa da turanci. Ni dai ina zaune jigum nasan dama za'a rina. Innarmu ce ta leƙo. "Ke Hindu kizo inji Baba Sojanku maza" Miƙewa nayi nabi bayanta zuwa falon. Innah Abida sai zurga_zurga take yi. Tana ganin na fito ta nemi waje ta zauna, sabida jin ƙwaƙwaf. Mijinyawa kanshi a sauke baya ko iya ɗagowa. Ga Baba Nagoɗi, ga Baba Alƙali duk Baba Soja ya kirawosu su zame mishi shaidar gani da idanu. Ga takaddar yarjejeniya a hannun Baba Sojanmu harda biro. Yaufa ake yinta. Me za'ayi da biro ni Hindu? Mrs Bukhari Sai mun haɗu zuwa gobe in Ubangiji ya amince. 💪🏼MRS BUKHARI ...... https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp 07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm Tiktok link/ https://vt.tiktok.com/ZSCgTFH8o/ IMZEEDenterprises Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeed🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDENTERPRISESLTD wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account aTikTok@imzeedenterprisesltd https://vt.tiktok.com/ZSCgTFH8o/ Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima BADI’AT İBRAHİM tuni na antaya🏃 Baba Alƙaline yayi sallama ya shigo, tare da neman wajen zama ya zauna. Tabb abunnan babbane kam. "Inason Abidah ta bamu waje in da hali, tunda dukkan abinda ya shafi yaran ɗakinta bana kutse, bare katsalandan akai. Ko kuma in da hali mu je ɓarayin Babansu Alƙali nanne babu yawaitar mata da hayaniya." Cewar Innarmu wacce ta haɗe girarta ta sama data ƙasa ta ɗaure. "In banda abinki Ruwayya da Hindu da su Salamatu ai duk ƴaƴanane. Miji ɗaya fa muke aure, menene danna zauna an tattauna matsalar Auren Duwab dani? " Har tana ƙarashewa da murmushi, ta ƙwantar da murya lunbu_ lunbu. "Ba ɗaya bane o_o kema kuma kin sani ai. Yanzu irin hidimar da kike ma Salamatu in zata koma irinta kike ma Hindu ashe?" Baba Nagoɗi yace. "To abinda za'ayi dai shine ita Abidah ta shiga ɗaki to. Ni banga wani abu a cikin wannan lamarin ba dan ta zauna. Batune na karatun Hindu ina ya kwana kawai, ba saɓani ko yaji tayo ba. Yaro ma ai yayi bazata, ita kanta Hindu ai ta ba da mamaki an fa shiga shekaru na shida da aure." Innarmu naga ta ma Baba Sojanmu wani kallo, tare da mai nuni da Baba Alƙali. Bafa cikin raini ba sam. Cikin sanin girma da mutumcin kai ga matar da take jan zarenta, kuma tasan mijinta da logonshi. Da yawa ana ganin tamkar Baba sojanmu tsoron Innarmu yake yi. Sam ba haka bane, ko wacce mace da irin baiwarta, da kuma irin matsayinta a wajen mijinta, a yadda kika ɗauki kanki, a haka kike a zuchiyar mijinki. Masu cewa Innarmu ta samu waje, su waya hanasu samun nasu wajen a wajen mazajensu? Ni dai nasan burin ko wacce mace ace mijinta yafi kusanci da'ita koda kuwa su ɗarine matanshi. Ke dai ki zauna a yadda kike so ki zauna, zaɓinki ne. Sai kawai Baba Sojanmu ya gyara murya. "Wel inaga muje lungun Alƙali ɗin tunda Ruwayya ta insistin. Acan za'afi sakewa ai" Baba Nagoɗi ya girgiza kai yace. "Ni na rasa dalilin da yasa faɗanka da tsaurinka baya taɓa hawa kan Ruwayya. Ai shikenan sai mu jenku gimbiya ta canja shirin." Baba Sojanmu da Innarmu sai suka mayar da abun wasan da dolensu suma suka ɗaukeshi a hakan. Ɗunguma muka yi zuwa falon Baba Alƙali dake shi matarshi ɗaya ce aina faɗa muku dama. Bayan mun zauna sai Baba Sojanmu ya buɗe takadda yace. "Hindu karanta mishi takaddarnan, a tunasar dashi yarjejeniyar dake tsakaninmu. Ko a addinance yarjejeniya gaskiya ce, rubutu gaskiya ne. Danme zai saɓa yarjejeniyar dake tsakaninmu? Ni nasan shine dalilin da yasa baya iya rakoki duk sanda zaki zo gida, baya so in ganshi balle in tuno. To yanzu haihuwa zaki yi a wannan ƙauyen in ban tashi tsaye ba shikenan zaki tara yara, batun karatunki ya sha ruwa. Amman kafinnan maza maza kije ki dirje wannan kwallin dake fuskarki, kaima ka dena sayo kwallinnan in zaka zo gidannan." "Aimun afuwa bazan sake ba" Mijinyawa ya faɗa muryarshi na rawa. Ni dai fita nayi ƙofar babban falon, na zare ɗankwalin atampar kaina, na goge kwallin kafin na dawo. Miƙe mun takaddar ya kuma yi, nasa hannu na karɓa. Zan soma karatun manyan turancin da akayi rubutun dasu, Baba Nagoɗi ya ɗaga mun hannu saina dakata. "Duk ba wannan ba. Yaro ai yasan da wannan yarjejeniya janaral baya musu a kanta. Al muhim shine mu tuntuɓeshi muji ta bakinshi. Janaral ka dinga sassautama boko haka nan" "Akanme, boko kam ai shima a wannan zamanin dole ne ko Nagoɗi. Yanzu yarinyar maƙotanmu yamma damu da auren ya mutu, na mayar da'ita karatu ta haɗa digiri. Kana ganin irin babban mai ɗamarar daya Aureta fa. Aurenta na farko ai maras ilimi ta aura yara nawa ta kwankwasa mishi. To sai akan Hindu ne zanyi shiru, duk irin ɗaga ƙafar da nayi. Alƙali kana jin mutuninka ko? Shifa dashi aka biye boko ma a gidannan ba yi za'ayi ha sam, sai dai a gani a maƙota. Ai yana da kyau ilimi ko sannan wannan yarjejeniya ce wacce a gabanku duk aka yita, na fa yi haƙuri ku duba" Baba Alƙali yace. "Nagoɗi a wannan gaɓar Janaral daidai ya faɗa. A tuntuɓi yaro aji inda yarjejeniya ta kwana shine kawai. Shi alƙawari girma gareshi. Ni sam banga wani laifinshi ba, in aka yi lakwa_lakwa da wannan ishu ɗin to Hindu ba zata yi karatun ba, dan babu wata alama data nuna zata yi. Da yaso tayi da yanzu ta gama, ko tana fainal ya ɗinta o somtin lik dat. Kai Magawata a ina zancen karatu ya kwana shekara an shiga na bakwai, dan an wuce shida? Muna son ji daga gareka" Mijinyawa ya ɗago muka haɗa idanu, na ɗan mai nuni da yayi magana kuma ya ƙwarara kanshi. Ai kuwa sai naga ya samu ƴar nutsuwa. Domin maganar gaskiya Baba sojanmu mutummne mai kwarjini da haiba, kwarjininshi muka ɗakko sosai. "Ayi haƙuri wallahi daidai da sakan ban taɓa mancewa da batun wannan alƙawari da yarjejeniya ba. Yanayin al'amurane da sukaita jujjuyawa damu, shine babban abinda ya kawo tsaiko a batun karatun. Amman yanzu aimun afuwa inasone in ɗan uwana ya ƙarashe gininshi daya soma anan kano ɗinnan. Zai dawo da iyalinshi, to inaso nima in roƙi mahaifiyarmu in biyoshi mu dawo nan Kano sai ta soma karatun anan Kano. Dan Allah a ƙaramun lokaci aimun afuwa, nasan an ɗagamun ƙafa sosai, amman dan Allah a ƙara" Baba sojanmu da yayi ƙur yana kallonshi yana nazari, sai can Baba Nagoɗi yace. "Zuwa shekaru nawa kenan tunda kaga gini yake yi ai ko? Kuma kasan gini ba abu bane mai sauƙi ba, shin sai yaushe kasa lokacin da kanka, sabida babu ɗaga ƙafa tsakaninmu." "To bana ce ba. Baba Nagoɗi aimun alfarma har zuwa a gama ginin mu dawo in sha Allah da zaran mun dawo zata soma makaranta. Ayi haƙuri bana son saka lokacine ya zamana kuma lokacin yayi bai gama ginin ba. Dan Allah a bani lokaci" Baba Sojanmu zai yi magana. Baba Nagoɗi ya dakatar dashi da hannun. Amman ina sai takadda ya miƙo da biro. "Amshi ka rubuta mata takaddarta. Iskancine a kanka na fahimceka. Infosibul ace wai sai an gama gini, o somtin lik dat, sannan ku dawo, a lokacin ne zata shiga makaranta. Lissafin hau meni ya kenan kake mun. Yaro kasan a inda kake, da waɗanda kake magana dasu kuwa? Sallamarmun ɗiyata ka kama hanyarka kawai" Da sauri duk muka ɗago muna kallonshi da biro da takadda. "In hankali ya gushe, hankali ake turawa ya nemo shi. Ai daɗina da gobe saurin zuwa, duk fa abinda aka saka mishi rana zai zo janaral. Inaso ka dinga sassautama zuchiyarka akan batun karatun yarannan. Akan karatu aure bai kamata ya mutu ba? " Cewar Baba Nagoɗi kenan. Baba Lukumanu yayi gyaran murya yace. "Kai Magawata wannan lissafin naka yayi nisa, gini ba abun wasa bane. Me zai hana ku kama haya, kafin shi ɗan uwan naka ya kammala ginin nashi. Sai kaga harta gama makarantar ba lallai ya kammala ginin ba. Ai ina ganin haka zaifi ko? Sannan mu zamu ɗauki nauyin makarantar tata" "Neba, infosibul mu ɗauki nauyinta. Ka mance a rubuce shi zai ɗauki nauyinta. Sannan ni na tura moda ɗinta har jama'are akan zan ɗauki nauyin karatun wai bikos na tausaya. Cewa yayi ya gode, amman zai iya ɗaukar nauyin matarshi. Sabida haka ya rubuta takaddarnan kawai" Hawayene naga yana bin kuncin Mijinyawa, baki Baba Sojanmu ya buɗe kawai. Aka buga, shima ya buga akan saifa an sakeni. Mijinyawa yaita magiya, hawaye shaɓe_shaɓe akan bazai iya rayuwa babu ni ba dai. Ni ko ji nayi alƙiyamata tamkar ta tsaya. "Shikenan Ubangiji Allah ya amince Magawata. Allah ya nuna mana lokacin da ranmu da lafiyarmu. Kai janaral haƙurin da kayi a baya har aka kai wannan matakin, ka ƙarashi akai. A bashi dama tunda ba mancewa yayi ba, ba kuma ƙin cika sharaɗin yayi ba. Ɗaga ƙafar yana da kyau sosai. Ko me kace Alƙalin alƙalai iyayen boko?" "To Yaya Nagoɗi tunda haka kace shikenan ba zamu yi jayayya ba. Amman ace sai an kammala gini abune babba fa. Gini a wannan marrar masu kuɗinma jjigasu gini yake yi. Balle wanda bai tara ba. Amman in akayi la'akari da irin yadda ya riƙe Hindu. Babu rashin sha, babu naci, babu rashin sutura, ga ƙoƙarin shi akan lafiyarta sai dai ace son barka. Amman muddin aka gama gini basu dawo birni ba, kuma ba'a ta da zancan karatun ba. To ta ɓangarena kaɗai zan iya datse igoyiyon auren ba sai janaral ba, ka amince?" "In sha Allah ma ba zamu kai ga wannan jallin ba. Zan yi iyakacin iyawata" "To shikenan ke Hindu ki kaishi ɗakin samarin gidan ya huta, a kai mishi abinci. Yaushe zaku koma kuma?" Mijinyawa ya dubi Innarmu yace. "Gobe sassafe zamu juya in sha Allah. Nanno bata da lafiya wanda yake kanta ma bata ganewa" Innarmu tace. "Ashsha Allah Ubangiji ya bata lafiya" Baba Sojanmu sai rubutu yake ta faman yi. "Ungo yasa hannu, kema ki saka, sai ki ba Nagoɗi, da Lukumanu su saka hannu suma." Sharaɗine akan batun gini da yace da an gama zamu dawo, da mun dawo zan shiga makaranta. Hannu nasa, na ba Mijinyawa shima ya saka, saina miƙama Baba Nagoɗi. "To ayi mutum komai sai yace a saka hannu, yanzu wata takaddar ka sake rubutawa, wannan uban rubutun, kaddai duk abinda aka tauna ka rubuta? " Obkos shi na rubuta, ma firen sain" Nan taron ya ƙare, muka fita tare. Baba Sojanmu ko magana ya dena yi, sai harɗe hannayenshi kawai da yayi ƙirjinshi yana ta jijjiga. Mukaita ratsa gidanmu domin zuwa shagon samarin gidan namu. Wallahi duk inda muka gilma sai kallo ya dawo garemu, har sai sai da muka fita, kafin hankalinsu ya kwanta. Kai subhanallahi tur da gidan yawa irin namu, da wanda ma yafi namu. Shagon su Akarami na da na kaishi, sai tulin tarin tsummokarai a hanga irin ta bangonnan, ko wacce katifa da hangarta a gefen gadonta. Kaya kuwa ba damane, katifun duk a tuɓe babu zannuwan gado. A ɗaya daga cikin katifun nai mishi nuni ya zauna. Komawa ciki nayi na tadda Innarmu na harhaɗamun komatsaina buhu guda. Luba na taya ta. "Ga miya a saman gaushi ki karɓo shinkafa a wajen Abidah sai ki haɗa mishi. Miyar Innarku Abidah bata ciyuwa ɗanyar miyar tumaturi take yi duk tsami ga ruwa." Dariya muka yi dukanmu, na ɗauki kwano na fita ta zubo mun farar shinkafa, ga miyar nan ta ɗaura a wuta tsululu tumaturinnan. A babban tire na haɗa mishi komai, na aika aka siyo mun lemun kwalba na limca na saka mishi. Da sallama na shiga na taddashi ya ɗauki tagumi ya ɗaura a kumatunshi. Bayan na dure abincin saina zauna daf dashi, nasa hannuna saina cire tagumin ina mai murmushi mai sanyi. Bani labarin zuchiyarka. Ka tsorata ko? " "Ai dole in tsorata kina jin Abinda Baba sojanmu da Baba Alƙali suka ce fa. Ke kinji ƙirjina kuwa sanda Baba Sojanmu ya miƙo biro da takaddarnan kuwa? . Sannan batun dawowa birni tare da su Nawata. Wannan tunaninane kawai bani da tabbaci in Nanno zata amince mun, ko kuma akwai sarari a cikin gidan ma da zamu iya zama. Wallahi na faɗane domin in kuɓuta kawai" Ai sai nazo wuya, inaji har makaraina na neman su dokeni, dalilin daya hanani cewa uffan kenan na lokaci mai tsayi. Shi yaga canji a tattare dani, dan take idanuna sukai luɓu_luɓu suka zama jawur. Ga abinci bismillah kaci, sai ka huta ni zan shiga daga ciki." Miƙewa nayi, yayi carab ya miƙe tare da shan gabana. "Hinduna me na faɗa wanda ya sosa ranki haka har kika kasa zama in ci abinci dan Allah? " Sai naji na sakko ganin yadda ya tashi hankulanshi. Komawa nayi na zauna tare da zuba mishi abincin. Zauna da kyau kaci ka ƙoshi sai ka huta ka shawo hanya. Ya jikin Nanno naji kace ba lafiya kuma cuta mai tsanani ko?" "Ke dai ki bari Nanno na kwance ana jinyarta baki ganta ba, abun tausayi. Ai bayan tafiyarki da kwana biyu ta soma ciwon. Abu kamar wasa daga ciwon kai, sai jiri, sai kawai ta faɗi bata san ina kanta yake ba. Akaita magani dai har zuwa yanzu bata iya tantaceni tsakanina da Nawata in faɗa miki" Shiru nayi ina jinjina lamarin Ubangiji. Mutum fa ba'a bakin komai yake ba. Allah yaso nuna mishi iyakarshi, yanzune kawai kafin ƙiftawar idanu. "Hmm Ubangiji Allah ya bata lafiya. Amman anje asibiti ko ko dai a gida aka barta? " "Ba'aje ko'ina ba. Kawu dai yana rubuto mata rubutu cikin jarka ana aikowa duk sati. Yaya Salihu yaƙi amincewa aje asibiti. Shima Kawu yace ciwon bana asibiti bane. Ana zaton jifanta akayi, ta taɓa samun haka a lokacin tana da cikin Autarmu. Tunda dai ta kwanta ciwonnan sai da ta haifeta Allah ya kawo yankewar abun. Jujjuyata akeyi fa kamar jinjira. Yaya Jamila da Yaya Zakiya duk suna gidan suke jinyarta. Magunguna kuwa baki gani ba, duk inda muka ji labari tafiya muke yi mu karɓo. Har yanzu dai babu makari." Shiru nayi ina nazarin wannan wanne irin ciwone haka. Gashi sun canfa wai jifane to wa zai jefi Nanno ni naga bata da komai. To Ubangiji Allah ya tashi kafaɗarta kawai zamu ce. Amman ai da an jarraba na asibiti sai kaga an dace" Dariya yayi ya girgiza kanshi kawai. Saida yaci shinkafa loma biyu kafin yace. "Hindu sha'anin mutan ƙauye sai haƙuri, kedai ki bari kawai. Shi Yaya Salihu yasan tarihin ciwon na Nanno. Kuma ance yana da asaline da kishiyoyinta tunma mahaifinmu yana da rai haka ake jiƙawa a matse. Sabida Nanno macece mai rikici sosai. Hatta mahaifinmu yana shakkarta. Kuma ta kasance silar arzikinshi. A lokacin mahaifinta mai garine mai darajar gaske. Ya tallafama mahaifinmu sosai a bisa aikin Safiyo ɗinshi, kuma gonakan da duk muka gada ya samesu ne sanadin mahaifin Nanno. To hakan yasa sai Babanmu ya fifita, ya ɗaga darajar Nanno a cikin sauran kishiyoyinta. Kuma tana taƙamar ita ɗiyar mai garice. Mai gari a lokacin darajarshi ta kusan ta sarki gaskiya. Kuma mai gari zaki ganshi da tulin dukiya. Suna kiran ragowar gama garin jama'a da bayinsu. To a wannan gaɓarne kishiyoyi akace sun jefeta. Ciwon yana tashi mata lokaci zuwa lokaci. Sanda aka haifemu Nanno kusan hauka tayi fa tuburan, sabida ta haifi ƴan biyu kuma du maza, ke dai Allah ya kiyaye kinji tarihin da tsayi sosai. Mu kanmu Allah ne ya rayamu har muka zama mutane kawai. Amman menene abinda ya sosa miki ranki ɗazu? " Batun da kace wai baka san ko Nanno zata barmu, mu dawo birni bane ya sosani. Ai wallahi muddin Nawata ya ɗauko Uwatale suka dawo birni. To na rantse maka da wabillahillahi la'ilaha illahhuwa, ni Hindu zamana nima a Jama'are ya ƙare. Ko an ƙi ko anso, shine kawai" Shiru yayi yana kallona, yadda yaga na ɗaure fuskata tamau. Sama da ƙasa Allah bai bashi ikon tankawa ba. Shigowar Luba da Sunusi ce ta katse mana wannan zance. "Sunusi ashe dai rai kan ga rai. Hajiya Luba ikon Allah alƙawari ya cika" Cewar mijinyawa dake yashare baki. Zama suka yi nan aka shiga gaishe_gaishe da tambayar yaushe gamo. Mun jima a ɗakin ana hira sosai kafin Sunusi yace. "To mu kam zamu wuce in kaita gida, kafin in wuce wajen aiki" "Sunusi kayi babur ne?" "Inafa Mijinyawa a ƙafa ma zamu murza, ai rayuwar watarana dai sai labari. Muna sa rai inta kammala karatu ta soma aiki al'amuran zasu ɗan sassauta. Kasan fa ta koma makaranta. To wallahi kuɗi ya zauna a hannuna ina ba dama. Ga ƙaramin juna a tattare da'ita lamarin dai sai godiyar Ubangiji nake faɗa maka kawai" Miƙewa muka yi muka tattaka musu har titi. Kafin mukai sallama da juna. Muna tafe mijinyawa yace. "Kin sake yin kyau sosai. Kuma har ƙiba naga kinyi, sai kikai zubin masu cikin sak. Ga idanunki duk sun kumbura." Murmushi nayi kana nace. Kuma kullum a ɗarare nake kar a gano shirinmu, inka ganni kullum da hijabi hatta bacci dashi nake yi. In ana kallona sai inta tsarguwa kamar za'a bugo jirginmu" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. "Ai kuwa a gaskiya da mun shiga uku. Ta Nanno mai sauƙine tunda bata da lafiya. Amman Baba Sojanmu ƙila sai ya sa bindiga ya harbemu, yai fata_fata da namanmu" Dariya muka kwashe dashi kawai. Gaga_ gaga_gaga washegari motarmu ta ɗaga sai garin Badariyya. Da yamma lis sakaliya muka isa garin. Abdulƙadiri da Qasimu su suka taimaka mana wajen shigar mun da kayana ciki. Ni kuma na wuce kai tsaye ɓarayin su Nanno. Nan na taddata babu yadda take. Su Yaya Jamila duk suna cikin ɗakin da ƙanwarta Akulu ma tazo. Gaishesu nayi da mai jikin. "Matar Magawata ko? Tubarkallah gatanan kuwa yanayinta duk yayi na masu juna biyu, naga ta kumbura ta ɗanyance." Kai kawai na sauke ƙasa, jiyane na tashi da wannan kumburin. Sakamakon maganganun da Innarmu ta cunkusamun wanda yai sanadiyyar motsawar makaraina. "Ai kuwa gata nan fa. Da cikinnan tayi tafiya mai tsayi irin wannan bata ko tsoro ma" Cewar Yaya Jamila. Mijinyawa na shigowa na miƙe ina tafe irin na masu ciki harna fice. Matan gida sai wani hararata suke yi. Ni kuwa Hindu ko in kula. Zaman dirshan nayi a gaban buhunhunan da muka tawo dasu har saida Mijinyawa ya shigo. Nan ya shiga sunce kaya, yana jujjuyewa a mazubin kayan hatsinmu. Kayayyakin jarirai dana siyo, da wanda Innarmu ta bani duk na tura jakar cikin ɗaki, shi wannan sai dare ya raba zamu buɗe. Danma nazo na iske Uwatale bata nan, wai sunje Birni ita da Nawata gano gini. To haka na kasance kullum jikina babu daɗi, yau ciwo gobe lafiya. Makaraina suna kusa daf dani, mijinyawa ya shiga sunturin maganina. A haka na lallaɓa muka koma asibiti. Na ƙundume ƴan kuɗaɗen dana riƙo muka koma ma likita. Nan ya bamu magani na tsawon wata biyu tukunna, itama Allurar ta wata biyu ce, in aka gama, sai a dawo a sake gwaje_gwaje, kafin a sake ɗauramu akan magani da allurai. Sai dai zuwa ɗaya, biyu sai likitan ya bamu shawarar in dinga yi mishi a gida in dai zan iya, ya nuna mun inda zanyi tunda a hannuce, yace allurar kan jijiya itace tafi ko wacce haɗari. In kuma bazan iyaba, to mu nemi wani kemis mafi kusa damu a dinga yi mishi, alluran kuma sam basason zafi, mu ajjiyesu a waje mai sanyi. Haka akayi mai allura muka dawo gida. Muna zaune Mijinyawa ya ɗaurama ranshi damuwar duniya. Gani yake rayuwarshi ma ta ƙarene baki ɗaya. Haba mijinyawa yana da kyau ka dangana. Ka sani in Allah ya nufi zaka samu lafiya, to zaka samu ko da baka so. In Allah bai ƙaddari zaka ga ɗanka a duniya ba, wallahi ko kanaso, ko baka so ba zaka gani ba. Na sha faɗama ka riƙe istigifari, da tsayuwar dare, da karatun Qur'ani. To bayan wannan sai ka dangana, ka barma Allah kayanshi. Amman bana son wannan haɗa kai da guiwar da kake yi, dubi har ka soma ramewa fa." Kanshi ya ɗaga sama, sai naga hawaye na shatata ta gefe da gefen kuncinshi. Ƙanƙameshi nayi mukai shiru na lokaci mai tsayi. Kafin na zame jikina, muka haɗa idanu. Na dinga bashi kalma, ina ƙarfafashi, tare da tausarshi. "Hindu nayi miki alƙawarin rayuwa a birnin zuchiya, filin gidana ke kaɗai daga ke sai yaran da zamu ɗebo a gidan marayu. Raina fansane a kanki. Ki ji daɗinki babu ke babu kishiya, kuma zan sake ƙara kyautatawar da nake yi miki bisa wanda nake yi miki. Zan so duk abinda kike so, zan miki duk abinda kike so. Ke matar rufin asirice sosai. Kin sadaukar da duk jin daɗinki kin biyoni ƙauye, kin jure tsangwama da takurar dangina, duk dan mu rayu tare. Na kasance juyi, amman duk da haka kika sake sadaukar da duniyarki domin kawai ni Mijinyawa ki zauna ki rayu dani. Kuma kina da damar da zaki iya neman saki, dan kije ki auri mai haihuwa ku rayu tare. Ni ko naso ace Nanno tasan da zaman wannan al'amarin tattare danine ba tattare dake bane. Sai dai kash, muna son rungumar yaran da zamu dinga ganinsu muna jin daɗi. Hindu wallahi a yanzu nafi ki son a karɓo jaririnnan, na fiki sonshi wallahi. Sabida gara ma ke, ko yau inna mutu zaki iya aure ki rungumi naki. Nifa, in kika mutu kika barni fa" Sai ya fashe da kuka, kuka mai gunji, gabaki ɗaya ya tashi hankalinshi, ya tashi nawa hankalina. Haka naita tausarshi, ina bashi kalma. A ranar mijinyawa da zazzaɓi mai zafin gaske ya kwana cur. Dangane da shawarar likita, haka kuwa akayi, sau biyar akayi mai a kemis, na shidanne ni nayi mishi, da haka harna ƙware, har zuwa lokacin zazzaɓine kau a jikinshi, sai da muka je asibiti. Likita ya kuma kwantar mishi da hankalinshi. Abubuwa sukaita tafiya, da daɗi babu daɗi dai. Cikin ƙudurar Ubangiji yanayi na ciki duk ya bayyana a jikina, sakamakon kasa baccin dare da nake yi, kusan dare na shiga nake faɗawa wani yanayi. Ga damuwar maganar samun jariri ko akasin haka. Rannan da safe muka shirya tsab muka nufi ɗakin Nanno jikin da sauƙi, tana gane kowa, tana iya magana, amman babu kuzari a jikinta sam. Sannu Nanno ya ƙarfin jikin naki? " "Da sauƙi. Wai nace har yanzu ba zaki haƙura da zuwa koyarwa ba, ciki kusan wata bakwai. Ko sai kin shiga watan haihuwar zaki dena zuwa? " Babu fa ƙwari a jikinta, amman saida tayi mun wannan batun. Kaina a lokacin sabida tsananin ciwon da yake yi mun tamkar zai faɗo haka nake ji, ga fuskanta tayi wani irin kumburin da idanuna ma sunyi mun nauyi. Babu damuwa Nanno zan iyane, kuma inna zauna ma jikin babu daɗi" Yaya Jamila tace. "In naƙuda ta kamaki a titi kinga ai shikenan. Gashi duk kin kumbura kin sauya kamanni ma" Cikin gatse ta faɗa, sai nayi dariya nace. Ai shikenan Yaya Jamila. Fatanmu shine sauka lafiya. Nanno Allah ya ƙara lafiya. Na tafi ni" Na miƙe da ƙyar ina jin wani irin juwa na ɗibana. Wallahi in sauka a ɗan tudun ɗakin Nanno saina kasa ɗaga ƙafata. Bauchin da ba'aje ba kenan sai washegari da na ɗan samu baccin awa uku cikin dare, sai jirin ya sassauta mun. Asibiti wajen likitan Mijinyawa muka koma, allurai da magunguna sun ƙare. Wasu tesa_tesan aka kuma yi mishi, akan nan da sati guda mu dawo. Hajiya Bara tana ofis sai gamu mun shigo, ina turawa da ƙyar, ga ƙwarya lailaye a cikina, ga ciko a ƙirjina. "Hindu kune a tafe da safe haka, kunga zuwana kenan nima gidan. Bismillah ga waje" Zama muka yi, ina dafe da kaina. "Lafiya naga duk kin kumbura, kamanninki sun sauya, Mijinyawa meke damun madam ne haka? " "Wallahi gata nan dai. Damuwa ta ɗauka ta ɗaurama kanta, duk akan sha'anin ɗaukar jariri ne. To dake tana da makarai shine suka matso kusa. Kin ganmu ko baccin kirki bama samu. Jiyane ma ta samu baccin awa uku. Jiyan muka so zuwa, amman jikin yaƙi" Hannayena Hajiya Bara ta kama. "Kar kiji komai in sha Allah zaku samu. An sassamu jira_jirai a makonnan har uku. Muje ku gansu, sai dai ina fatan kafin wa'adin wata taranki a samu wasu jariran. Muje ku gansu." Nan muka bi bayanta, tana ta nuna mana yanayin gidan, da yaran cikin gidan, dama ma'aikatan cikin gidan. Har muka zo ɗakin da jarirannan suke ciki, ga mai kula dasu tana zaune. "Baba an basu madarar ko, naga wancan yayi bacci, iyayenshi ma suna hanyar zuwa ɗaukarshi" Cewar Hajiya Bara da take magana da ma'aikaciya, mai lura da jariran. "Yayi kuka sosai, jiya kwana muka yi ba mui bacci ba. Ya hana bacci samuwa, ya sha madararma yaƙi sha" Kai na girgiza, sai ganina nayi a gaban kyawawan yaran, inata ƙare musu kallo, inaji tamkar in ce a bani su dukka. Mijinyawa ya dafani, duk mukai shiru muna kallon yaran. Ashe hawaye mijinyawa kawai yake ta faman sharewa abun tausayi wallahi. Da yawa ba lallai su gane, ko su fahimci irin nauyin da zukata suke shiga ciki ba, a yayin da suka kasa samun haihuwa, harma aka tabbatar musu a asibiti ba lallai su haihu ba. A hakanma magungunan hausa ko kafin dawowata mijinyawa ya dafa wasu da yawa, ko shekaranjiya yaje wani ƙauye ya karɓo maganin haihuwa, ana dai ta sha, mun zubama sarautar Allah idanu. Sai dai bamu fidda rai ba. Dafani da Hajiya Bara tayi ne ya sa muka juyo tare. "Kinga da ace cikin ki ya shallake wata takwas, ko da kwana biyar ne, da sai kin zaɓa. Wannan namiji ne, waɗannan mata ne biyu. Gasu kyawawa kuma lafiyayyu, basa ɗauke da ko wacce cuta mai cutarwa." Murmushin dole na ƙwaƙwalo, idanuna a bushe tamkar babu ɗigon ruwa. Babu dama ciki wata bakwai, ace na haifi taranni ai akwai ƙura kuwa. Amman ni tsorona Allah tsorona kada lokaci ya cika, a rasa jariran tunda yanzu an samu anya ba zamu yi amfani da damarmu ba kuwa? " Mijinyawa ya riƙe mun hannayena, dan ya fahimci hankalina a mugun tashe yake, ga ba ishasshiyar lafiya bace gare ba" "Hakane zancan Hajiya. Kina ganin babu ta yadda za'a iya bamu ɗannan mu tafi dashi kawai ace ta haihu? " Murmushi tayi tace. "Allahu Akbar. Nasan a cikin ruɗu da tsoro kuke, har kuke ganin ga wata dama ta samu kuna tsoron kar ta kubce a samu matsala ko? Kuyi tunani, ɗaukan yarannan da sunan haifarshi akayi da cikin wata bakwai, magana ta domin Allah asiri zai iya tonuwa. Hindu ke macece kinsan yadda ake haifar bakwaini fa." Ajjiyar zuchiya na sauke a hankali. Na ambaci Allah sai nutsuwa tazo mun. Wannan gaskiya ne Hajiya. Idan muddin muna da rabo zamu samu in sha Allah. Babu damuwa muna faɗama Allah" A gabanmu wannan mata da mijin da muka haɗu dasu a gidan Hajiya Bara zuwanmu na farko suka zo ɗaukar jaririnsu, ita cikinsu ya wuce wata takwas. Kyakkyawan namijin suka ɗauka yaro ɗan Fulani gashinshi lub_lub ina kallon yaron a idanun zuchiyata har yanzu. Matarnan ta rungume yaronnan ƙam a jikinta, ta durƙasa guiwowinta a ƙasa tana godema Allah maɗaukakin sarki. Murmushi kawai na sha'awarta da ɗan ya kamani sosai. Mijinyawa na kalla, idanunshi jawur jijiyoyin kanshi sai tashi suke yi. A haka muka koma gida, zukata cike da sabon zulumi, in kuka ganni ko da yaushe ambaton Allah, istigifari, karatun Qur'ani, sallar dare. A zaune nake yin sallah sabida azabar ciwon kai, duk halittuna sun sauya, kamannina sun koma wani iri daban, wallahi sharrin makarai har kaina saida ya sake girma. Ta wani fanni hakan yayi mini, sabida ya ɗauke zargi a kaina. Ta fannin ciwon jiki kuma, ina abun ba'a cewa komai sai godiyar Ubangiji. Kunsan masu makarai da zaran sun shiga damuwa, ƙunci, ko tashin hankali. Makarannan sai su matso kusa sosai domun su baka kariya. Wannan dalilin ne yasa suke yawan tashi, kuma dalilin da yasa nake ta kumbura kenan. Masu makarai irin nawane kaɗai zasu gane. Mu kwana anan sai gobe in Allah ya kaimu. 💪🏼💪🏼MRS BUKHARI ....... https://chat.whatsapp.com/Ewd4dGuB35VI7hqrRck8TH ✨🛍️ HAFSAT COLLECTION — INDA KYAU YA HAƊU DA SAUKIN FARASHI! 🛍️✨ Kin gaji da neman kaya masu kyau amma farashinsu ya yi tsada? 😍 Ki zo HAFSAT COLLECTION! ❤️ Muna kawo miki kayan kitchen masu kyau da inganci, laces masu kyau, atamfa, abayas da kayan zamani — duk a farashi mai sauƙin gaske! 🔥😍 💎 Ingantattun kaya 💰 Farashi mai sauƙi 🤝 Kyakkyawar mu'amala 📦 Muna tura kaya zuwa garuruwa daban-daban cikin aminci A HAFSAT COLLECTION, burinmu ba sayar da kaya kawai ba ne, muna son ki samu kaya masu kyau kuma ki dawo da farin ciki. 🥰❤️ ✨ Kada ki bari a baki labari—ki gwada HAFSAT COLLECTION yau! ✨ 📩 Ki turo mana da saƙo domin ganin kayan da suke available. HAFSAT COLLECTION — KYAU, INGANCI & FARASHI MAI SAUKI. ❤️🛍️ https://chat.whatsapp.com/Ewd4dGuB35VI7hqrRck8TH Yau na wayi gari jikin nawa da ɗan dama babu laifi kam. Dan da kaina nayi share_share, mijinyawa lokacin yana ɗebo mun ruwa ya ciccika mun randunana. Nanno sai zazzaga faɗa take yi, amman yau abun nata akan su Shafa yake, wata gulmace Shafa ta jagoranta, shine abun ya zame musu matsala. Sarkine ma ya aiko ayi kiransu fa. Haka fa ake ƙyanƙyashe ƙwai tara tsinana a wannan gida namu. Gulma fa zaman daɓaro tayi ƙaƙas a gidan. Da ƙaton cikina a gaba na fito saye da mayafi a jikina. "Kin shirya zuwa wajen Barakan ne?" Wallahi kuwa, ƙafafuna duk sunyi nauyi amman inna tattaka zan ɗan warware, ai gara a wanke kayayyakinnan a adanasu ko?" Murmushi yayi mun yace. "Sosai kuwa. Dama inason zamu yi magana dake, ina sone inna gama ɗiban ruwan dama sai muyi. Nama mance da batun zuwa wankin kayan jarirai shab." To bari mu gama maganar ba sai inje ba. Ai ba sauri nake yi ba." Zama nayi saida ya kammala yazo ya zauna muna fuskantar juna yace. "Aiki Qasimu ya samo mana mu uku a cikin garin Bauchi. Na lura da gidan gonan wani babban mai muƙami. Kuma babu laifi akwai tsoka kuɗin. To kinga kuɗinnan muna da buƙatarsu ko ba gaskiya ba? Ga batun siyen rago, ga fita kunyar dangi, abincin suna duka dai, ga batun kayan fitan sunanki dole akwai buƙatar in fita aiki. Danma munyi dabara mun tara itace, ga abinci da kika tara duk dan kar a ji kunya. Tutar so dole in matsa duk da ina jin tsoron a yanayin da zan tafi in barki, sabida baki da lafiya, ga ƙullin da muke ɓoyewa. Amman me kika gani shawara. In tafi, ko in yi zamana dake? " Shiru nayi ina nazari. Ni kaina nayi tunanin hakan, amman duba da yadda ko bacci bana iya samu yasa ban mishi maganar fitan ba. Babu damuwa wannan shawarace mai kyau. Kaje Allah ya tsare, zan kula da kaina in sha Allah. Amman yaushe zaka dinga dawowa kenan?" "To Amin. Wannan dai tafiyar in muka yi Gombe zamu je kai tsaye, na tsawon wata guda. In muka gama da gidan gonarshi na Gombe, sai mu dawo Bauchi. To in muka dawo Bauchi kam ai duk sati ina gida. In kika ce kullum ma zan dawo sai in dawo ai mayyata" Ya faɗa cikin sigar zolaya mu kai dariya. To shikenan Allah Ubangiji ya dafa, ya baku abinda kuka je nema. Yaushe ne tafiyar to? " "Jibi ne in Allah ya kaimu cikin masu rai." To Ubangiji Allah ya nuna mana. Bari inje wajen Baraka. Ku sai yaushe zaku je Azaren ne? " "Yanzu dana kammala zamu wuce ai babu mamaki ni suke jira ma mu wuce. Zan wanke miki tsakar gidan kafin muje" Sallama mukaima juna, na fito zuwa babban tsakar gidan ina tattakawa a hankali. "Kaga mai ciki, ciki sai girmanshi yake yi. Kai zamu sha suna a gidannan, tsiranku da Uwatale babu nisa." Cewar Shafa kenan tana tsakiyar mata ana ɓarin gulmar da aka saba. Ita da kes ɗinta yana gaban sarki ya nemesu su zo gobe. Dariya kawai nayi, muka gaisa. "Sai ina haka Hinduwa? " "Wajen Baraka zani Tatsaure, kina da saƙone wajenta? " Na faɗa da gatse, sai ta ɗauki abun wasa. "Oo_oo bani da saƙo. Ai gara ki dinga miƙe ƙafar haka akeso. Haihuwar fari baka jaɓe waje ɗaya ba" A zaure ma na jiyo ƙarashen zancan ni kam. Ina sa ƙafa a gidansu Baraka na tarar da igiyoyin gidan shaƙe_shaƙe da kayan jarirai igiya biyar cike dam, da kayan jarirai da na yaro ko yarinya wacce ta ɗan tasa. Sun gama wanke komai safuna suke wanke wa. "Kaga Uwar biyu in sha Allah. Ai wallahi dama zamanki kikayi kinga Lamiso ta tayani mun wanke fes, safuna ya rage." Waje na nema a benci na zauna da ƙyar, ga goro ina ɗan ɓantara abu dai irin na masu dashi. Baraka Lamiso nagode shine baku jirani ba. Allah ya saka da alkhairi" "Laa ai babu komai Hinduwa yima kaine. Lallai wannan yaro ɗan gatan Baba da Mamane, irin wannan tulin Kayan wallahi ban taɓa ganin an yima wani jariri ko jaririya irinsu ba. Tubarkalla ji kaya fa reras." Dariya kawai nayi, ina daga zaune muna ta hirarmu, da haka muka jiyo muryar Mijinyawa yazo wajen Qasimu amman ba zama suka yi ba waje suka yi ficewarsu. Na jima a wajen Baraka sosai, saida ta kammala abincin rana shinkafa da wake da manja da yaji. Zuba mun tayi cikin kula. Nan nace ba sai ta yi na dare damu ba wannan ya ishemu, da ƙyar ta amince. Gaga gaga gaga gaga. Ranar dasu Mijinyawa zasu tafi nice rakiya har ƙofar gida, Uwatale bakinta a washe sai farin ciki take ta faman yi. Ni kuma makaraina tamkar jira dama suke yi Mijinyawa yasa ƙafarshi a gidan ya tafi. Sai ya zamana bana iya baccin dare sam idanuna a soye, ga faɗuwar gaba, ga matsanancin ciwon kai subhanallahi. Gashi da safe ne nake jin bacci, inna kwanta makarantar fa? . Haka dole nake lallaɓawa inje makarantar in bada ilimi. Kafin in iso gida ji zanyi kamar in yi bacci a hanya. Inna dawo ko abinci bana iya ci, sai bacci, bana sake sanin kaina sai daf magriba, kuma idanuna sai kuma soyewa suke yi. Sai inji kamar babu ruwa sam a cikinsu. Shi yasa yanzu duk ɗan abinda zan iyayi da daddare nake yi. Ina riƙe da kaina, ko in ɗaure jiƙaƙƙen tsumma a kaina tamau. Wani irin tafasa kullum kaina yake yi. Tsumman fa ɗumi yake yi inna ɗaura, gishina in kuka luma yatsa kwatan yatsanku zai iya lumewa, in kika cire yatsan a haka wajen zai tsaya tamkar an huda sakwara, yadda kukasan babu ƙashi. Duk yadda bana son hayaƙi sai gashi da kaina nake yi. Cikin sati biyu nayi wata iriyar rama ta ban mamaki, a sati na uku zuwa na huɗu nayi wani irin kumburin da wallahi idanuna rufewa suka yi ruf, saina ɗan ɗaga girata kafin nake iya gani. Allah ya raba kowa da ciwon makarai. Sun wuce tunanin masu tunani. Baraka hankalinta ya tashi ranar da ta kawo mun abinci da kanta. A guje ta kirawo Nanno. Ita kanta taji tsoro a karo na farko. "Wai wannan Hindun ce Baraka? Ciki kenan masu gari jibi yarinyar mutane yadda ta koma abun tsoro ni ƴasu, kuma haihuwar da shingen kusan wata biyu inaga. Nace ke Hindu shi Magawatan yayo miki aike ne ko yaya, duk da wannan makon ake sa rai da dawowar tasu? Ga juyin ɗaki kinyi kina da ciki irin haka menene na juyin ɗaki. Da kin bari ma ƙawayenki su Uwatale ai zasu yi miki" Kunji wai ƙawayena su Uwatale fa hmm. Bai yi aike ba. Wannan satinne satin dawowar tasu, an shiga sati huɗu." "Umm nace wannan fantimotin kuma na waye. Kaddai kice ke Magawata ya kuma siyama na haihuwa? Dan wallahi nasan ba hankali bane dashi ba tsab zai aikata." Aa na Abdulƙadiri ne ajjiyace ya kawo mun, yana tara kayan Aure ne" "Ita Gwamma kuma ta barshi ya ɗebo uba uban kaya ya kawo miki. Allah mai iko. Ke dai kece uwar kowa, hatta abokan miji sai yadda kikai dasu? To bikinma ai ya riga ya zo, suna dawowa bikin za'ayi ta faru ta ƙare" Tana girgiza kai harta fice. Da haka su Uwatale sukaita tururuwar zuwa dubiya. Da ɗaya biyu suka zo saina dawo tsakar gida nayi kwanciyata. Duk wanda ya shigo ina tsakar gida a kwance. Wannan kenan. Washegari asabar ne, tun asuba nayi bacci, bani na farka ba sai sha biyun rana. Kumburin ya ɗan saɓe tunda ina gani ba saina ɗaga girata sama ba. Taliyar hausa nake jin sha'awar ci, ta manja da bushasshen kifi. Ina da kifina tun wanda Innarmu taimun aikenshi kafin inje biki, da naje bikinma na kuma tawo da wani kusan cikin leda mai zane. Adanashi nayi tare da shinkafa karolin dana tawo dashi daga gida ta kusan rabin buhu, wake, maggi, farin mai, garin tuwo sabida dai batun haihuwarnan ne, in fita kunyar masu son in gaza. A ciki na ɗakko kifi babba na wanke, nayi jajjagen kayan miya na tsaida sanwata. Ashe da rabon jarumin maza, jan gwarzo na Hindu ba da kanka a sare. Ina ƙoƙarin zare itace in samu gaushi zan yi turaren wuta kafin in kashe, naga ƴan tsaka tsakin matasa sun dure buhu a ƙofar ɓarayina. Leƙawa nayi na tadda Uwatale a tsaye a ƙofa itama tana kallon kayan. "Ba mamaki ɓatan kai suka yi Nawata ne ya dawo kenan, shine suka jingine buhun a bangonki" Baki na taɓe nayi komawata ciki, har ta janye buhu ta shige dashi ɓarayinta. Saiga Qasimu da Mijinyawa jaye da babban rago ƙaton gaske mai murɗaɗɗun ƙaho. Ciki na koma na zaro mayafi na fito. Qasimu ashe kuna tafe?" "Hindu Subhananallahi cikinne du ya mayar dake haka, kina shan magungunan zaƙi da duk wanda ya dace, Baraka ta dafo miki kuma kina sha? " Ɗan murmushi nayi. Goga naku kuwa sakan igiyar ragon yayi ya nufoni yana taɓa fuskanta. Hanlalinshi in yai dubu ya tashi gaya. Musamman da yaga shatin hannayenshi sun zauna akan fuskar tawa basu baje ba. "Tutar so lafiya kika koma haka, shi yasa jikina duk bai bani ba, wallahi kaga abinda nake faɗa maka ko? Ni dai ku barni har Hindu ta haihu nanne zanfi gane kaina, har in tafi neman kuɗi" Uwatalece ta shiga da sauri taji kukan rago. Nanno kuwa anci gagarumar sa'a batanan taje Azare akan batun bikin Abdulƙari, daga can zata biya har misau wata guda zata yi. Bata nan ma za'ayi bikin tunda mun shiga satin bikin ma. "Aa_aa wannan ƙatoton ragon ai ko ni Nawata bai yankamun lokacin haihuwar Zainab ba. Mijinyawa yanzu kaine da wannan rago hoɗijan" "To ai Nawata kika ce, shi daban ni daban. Ke da baki da aiki sai neman Sababin tsiya. Na fahimci Uwatale baki da kirki sam. Ayi magana ki kwashi jiki ki sanarma Nanno. Tutar so ina buhun kaya da yara suka shigo dashi? " "Laaa ai wallahi nayi zaton Nawata ne ya dawo. Kaga fa harna soma buɗewa. Kukan ragone ma ya zaburo dani ka ganni nazo." "Har kin soma buɗewa fa kikace? " Kusan dukkanmu ukun muka haɗe baki wajen faɗin haka, saini daga ƙara da cabɗijan" Sumi_sumi ta fice sai gata da buhun ta jawo kiiii zuwa inda ta ɗauka. Turke Qasimu yaima ragonnan a rumfa, ya taya shi suka shigar da kaya cikin ɗakin da muke adana hatsi. Nayi nayi ya tsaya suci abincin Qasimu yaƙi fur. Sallama yayi mana ya ƙara gaba abunshi. Ni kuma naja hannun Mijinyawa zuwa ciki. Saida yayo wanka kafin muka zauna zaman cin taliyarnan, tako yi daɗi, kifinne baimun laushi yadda nake sonshi ba gaskiya, sai manja daya gaza. "Hindu makaranne suka mayar mun dake haka wai? Ni kam wannan makarai suna cutarmun da mata. Wallahi gabaki ɗaya kamanninki duk sun sauya, sai naga kamar kanki ma fa ya ƙaru sosai hakane? " Hakane, nima ina jinshi gingiringin dashi, sai dai haƙuri. Ya aikin naga dawa tayi mai har rago ka siyo? " "Dawa tayi mai. Ga Hatsinan shinkafa mai kyau marar ƙuƙus kusan kwatan buhu, wake mudu bakwai, garin tuwoma wani dana gani mai tsabta na cikin leda na siyo, tuwonshi da daɗi ga danƙo. Sai ƴan abubuwan da baza'a rasaba dai inmun gama sai mu duba. Wannan rago a can gidan Gonar da muka je kulawa dashi yake. Alhajinne ya ware ragunan da shanun da zai siyar. Fin guda ɗari, Kamar wasa nace inason wannan, a dubu bakwai ya barmun, amman fa sai nayi aikin kuɗin ragon kusan a bashi ya fito, sai dai aikin wata guda zai biya wannan bashi. Bana son abinda ƴan uwanki zasu zo suyi ƙorafi akaine, kinga ai babbane sosai. Shinkafa ma zamu ƙaro a gulmare ranar kasuwa, da mai da maggi duk zamu ƙaro da ragowar canjin hannuna. Fatanmu shine Allah ya dubemu ya ji ƙanmu, game da abinda muka saka a gaba." Mukaita tattaunawa, muna ni shaɗinmu. Bayan la'asar muka bubbuɗa kayan abincinnan duk muka juye komai a inda ya dace, muka adana komai. Alhamdulillahi kayan abinci kam muna dashi, ga itacen wanka shima akwaishi mai kyau faskare bushasshe. Gaga_gaga_gaga _gaga Muka shiga hidimar bikin Abdulƙadiri. Wajen Harira nasa Mijinyawa ya kai mun ɗinkin kaya kala biyu, da atampa mai kyau da Abdulƙadiri ya bani, wai tukuicin riƙe kaya, kuma haka suke yi dole yasa na karɓa. Harira tasa akaimun ɗinki mai kyau. Ni da Baraka a haka ina tutturawa, ni aka ba kwangilar girkin maza ƴan ɗaurin Aure. Dafadukan shinkafa, da soyayyun kaji muka yi, sai soɓo da kunun zaƙi da muka yi musu. Soɓo robar fenti ɗaya, kunun zaƙinma robar fenti ɗaya. Baraka ita kaɗai duk ta ƙuƙƙulla a leda. Abincin na juye a manyan kuloli biyu, matan gidan duk na basu nasu. Nayo wanka kenan, na sa sabon ɗinkina riga da zani. Saiga Mijinyawa an sha ankon yadi mai ruwan jinin kare. Ya shigo a hanzarce shi da Balele, da Qasimu ɗaukar abinci. "An ɗaura auren kenan Qasimu har kun dawo?" Cewar Baraka dake zaune tana zura abinci, kwanonnan yayi tsoro. "An ɗaura, sai da yamma kuma zaku je ɗakko Amarya. Hindu kam ba sai taje ba, gobe wuni ta leƙa dai ayi da'ita" Ai kuwa hakan akayi, bayan la'asar sakaliya suka tafi ɗakko Amarya. Basu suka dawo ba sai wajajen taran dare. Mijinyawa bashi ya shigo gidaba sai goman dare, amari ƙirjin biki ake faɗa muku. Washegari da yamma na biya ma Baraka muka je wunin biki. Lasiri na saka ja, mai adon baƙi mai tsadane sosai yana daga cikin anko ankon gidanmu. Na sa baƙin takalmin da innarmu ta sai mun, shi nake fita dashi unguwa bama ni da wani, na ɗakko mayafina baƙi na saka. A gidan wuninnan muka tadda su Shafa, da Uwatale dai. Kutsawa muka yi wajen Amarya. "Amarya sunana Baraka matar Qasimu, wannan kuma Hindu ce matar Magawata" Da fara'arta ta tarbemu. Idanunta tsabar yagewa har ɗayan ya haɗe da ɗayan. Ga wani kitson gashin doki da tayi, ga ƙawayenta karuwai nan duk sun halarci wannan biki. Ni dai sai jinjinawa nake yi dai. Shinkafa da miya, da alala aka bamu, sai kunun zaƙi yako ji sikarin. A haka dai taron biki ya ƙare. Gaga_gaga_gaga_gaga. Ciki yana shiga wata tara, a ranar da lissafinmu ciki ya cika wata tara. Ina zaune a ƙofar ɗakina ina karanta littafin hausa, da yammane, mijinyawa suna Bauchi na samu na lallaɓashi ya koma, wannan shine tafiyarsu ta uku, kuma Alhamdulillahi ana samu. Kwatsam sai na jiyo muryar Yaya Saratu a tsakar gidan har tana cewa "Ga can kwanar da zaku yi? " Ai ba shiri na fito da saurina, in rungumeta na kasa asiri zai tonu taji ƙqarya, ganin Akarami da Qazzafi ya sake faɗaɗa murnata gaya. Kayan kujeru suka kawo mun sababbi dal wallahi, waɗanda suka fi nawa kyauma. Ai fa Jama'are ta ɗauka, kafin kuce kwabo ɓarayina ya cika da mata, harda Nanno saida ta shigo ganin ƙwaƙwaf. Uwatale kuwa mai zata yi in ba habaice _habaice da ƙunci ba. Ai kuwa a tsakar gida aka dire kayayyakin, wasu kuma duk aka ɗaura wasu kan wasu. Nan suka shiga aikin fitar da tsofaffin kayan nawa, na riƙe kafet ɗin falona inaso a kaima Luba da labulayena dan Allah. "Karki damu, ai gidana kai tsaye za'a kai kayan zan cire mata ni da kaina zan kai mata. Amman kayannan sai zuwa gobe gaskiya zamu jera miki, kafin mu kama hanyar garinmu kuma. Amman su Akarami zasu samu wajen kwana a gidannan Hindu? " To bazai gagaraba ko a gidan maƙota zasu kwana. Zanje inma maman Qasimun Baraka magana za'a samu. Inaso Yaya inba Baraka labulayen uwarɗakina akwai wanda na siyo a kano na gumama suna da kyau sai in sakasu a uwarɗakin" "Ai babu komai zaki iya cirewa ki bata. Abinci fa, shayi zaki dafa mana mun siyo kajinmu da masar Bauchi" Akarami yace. "Ina mai gidanne Hindu?" Ai ya tafi nema Yana Bauchi, gata muke sa ran dawowar tasu. Qazzafi ga filas ɗin ruwan zafi nan ɗan miƙo bari in kawo kofuna da sikari, da ganyen shayin." "Wato nine marenin wayonki ko Duwab, me yasa baki ce Akarami ya miƙo miki ba. Yana ƙanina" "Kai waye ƙanin naka, wata takwas fa kawai ka bani" Dariya dukkanmu muka saka, ƴan uwa abun wuya. Miƙewa nayi da ƙyar na kawo musu kofuna, sikari, ganyen shayi, da babban tire. Tabarmace babba na shinkafa mana akai duk muke zaune, mukai da'ira muna cin masa da kazarnan Qazzafi dai sai kallona kawai yake yi. "Wannan irin kumburi haka, amman dai a asibiti zaki haihu ko? Sabida bana lafiya bane wannan kumburin ba" A can zan haihu ai koma ban kumburan ba gaskiya, haihuwar fari yaushe zan yadda in haihu a ƙauyennan." Haka dai mukaita tattaunawa, muna hirarmu ta zumunci, Akarami da Qazzafi sai zolayata suke yi. Da daddare bayan munci tuwo miyar kuka, yaji bushasshen kifi da daddawa , Yaya Saratu ce ta girka mana, Baraka ta kawo ma baƙi dafadukan shinkafar manja da ganye. Wajen nanno naje na tambayi batun kwanansu Akarami. Da naci sa'a sai tace a buɗe ɗakin samartakan Mijinyawa tunda su Lauwali basanan sun tafi cirani. Ilai anan suka kwana. Mun yi hira sosai da Yaya Saratu. Harma take sanar dani irin ɗinke_ɗinken fitar sunan da Innarmu tayi mun, har Baba Sojanmu ya siyo mun kayayyaki. Washegari sassafe, koma ince asussuba suka soma mun aikace aikace, ni kuma ina gaban murhu ina tuyar doyar da suka kawo mun tsaraba, jiya na aika aka siyomun ƙwan kazar hausa a wajen Shafa guda huɗu. A wannan lokacin huɗun du nera sittin in manyane, in ƙananane hamsin. Kafin takwas na safe kuma ɗaki ya kammala sun gamamun komai da komai, komai ya fito shar dashi sosai, damma ba'ai fenti ba. Komai na kalar kayan ɗakin mai ruwan ƙasane, da ruwan madara. Bayan sun kammala na zuba mana doya da toyayyen ƙoyi, da shayi muka karya. "To Hindu, mu kam zamu koma, sai munga wasiƙa daga Shehulle ƙila ma gobe mu sake juyowa kin haihu, Ubangiji Allah ya raba lafiya? " Ameen Yaya nagode sosai. Akarami Qazzafi, nagode sosai Allah ya bar zumunci" Akarami ya bani dubu biyar, Qazzafi ya bani dubu goma. Na rakasu har ƙofar gida inda motar Qazzafi take, saida suka ɓacema ganina kana na dawo. Ga durowar turarukan wutana an kuma batsemun ita da turarukan wuta na jego. Hmmm nan kuma aka soma zuruftun zuwa ganin waje. Allah ya soni Nanno bata ce Mijinyawa bane yayi mun wannan kayan ba, tana gani daga gidanmu yayuna suka kawo. Mutuniyarku gunɗu kuwa ko a cikin gayyar masu shigowa ganin ɗaki bata zo ba. Ni dai bama na cikin haiyacina, tafiyar su Yaya da kwana bakwai saiga Mijinyawa. Wannan karon kam tsaraba Nanno ce ta raba ta bamu, sai kayan jira jirai daya siyo, shima ta raba ta ba Uwatale rabi. Na shaƙa na shaƙa dan har cewa nayi ya ɗauka ya haɗama Uwatalen baki ɗaya tukunna. Saida yace in yi haƙuri zamu je ni da kaina in siyo kafin na haƙura. "Wannan kaya da aka kuma narka miki tubarkallah. Gaskiya su Innarmu suna sonmu babu laifi. Jibi gadonnan mai kyau." Murmushi kawai nayi mishi. Ni kam kaga ya fa kamata gobe sasafe muje wajen Hajiya Bara tun wuri kafin hankalinsu Nanno ya dawo kanmu. Wata tara da kwana tara yau cikinnan cif, ya kamata mu san me muke ciki kar asirinmu ya tonu, duk da ina ta faɗama Allah" "Hmmm Tutar so, ai ni wasu mafarkai dana dingayi a Bauchi a jejjere nama gama sarewa. Yaromnan abune mai wuya mu samesu fa. Mafarkin ba kyau nake faɗa miki" Haba mijinyawa, sai kace wani mai fassarar mafarki, kuma mafarki ai ba ko wannene yake zama gaskiya ba. Ni ina ganin muje kawai goben muji me ake ciki. Daga nan sai mu siyo setin bowon wanka, dama kace saika dawo tukunna" Kai ya girgiza yace. "To shikenan Allah ya kaimun Tutar so. Allah yasa mu dace. Ya kamata ki tafi ma da Harira kayan da za'a ajjiye a wajenta na batun haihuwar, in muka siyo riyo sai a cire a haɗa mata dashi ko kuwa? In Allah yaso ma sai kiga mun dawo da jariri, ko jaririyarmu a hannun?" Allah yasa, amman ka mance yadda aka tsara kaine zaka koma ka faɗa musu ina asibiti, saima na kwana? " Kanshi ya shafa kawai yace. "Hmm Allah fidda A'i daga roro. Akwai kwantaccen rikicin da bansan a ina zai tsaya ba Tutar so. Allah ya bani ikon cinye wannan jarabawar. Nanno ba zata ɗauki haihuwa a asibiti da sauƙi ba. Sannan mahaifa ya zamu yi da batun buso, jinin da ake buƙatar a gani a zani wanda nake ganin in su Shafa sun haihu ana wauwankewa a tsakar gida duk ya za'ayi dasu Hindu?" Idanuna na lumshe, ƙirjina da zuchiyata suna ta kokawa. Ni duk babu wannan a tunanina. Tunanina shine a samu yaron tukunna shine mai mahimmanci. Kai dai muci gaba da adda'a. Allah zai mana mafita" Haka muka kwana da zulumi, ni kam akan sallaya na kwana cur, idanuna a kangare, a soye, a bubbushe, ƙayau_ƙauyau. Ƙarfe takwas Nanno na fita maƙota karɓan haihuwa, muka fice cikin hanzari, da leda a hannun Mijinyawa, kayan jira jiraine a ciki wanda zamu kaima Harira. Kasuwa muka soma zuwa muka sai setin bahun na wankan yara, da riyo babba mai murfi daban, sai ƙarami mai murfi biyu dake manne gefe da gefe, me ruwan omo muka samu. A wajen na sai tawul ɗin nabkin, ledar labkin, da kayayyakin da muka samu. Kai tsaye sai gidan Harira, fita ma take shirin yi, ganinmu ne ya kawo mata tsaiko. "Allah gwanin hikima. Nace ko wata hikimar kika yi ne, har kika rikiɗe sak mai cikin gaske, irin wannan kumburin ma ai yayi yawa. Allah sarki Ubangiji Allah ya rufa asirinku a samu wannan jariri a baku, wallahi tunda aka shiga wata tarannan ni kaina sai faɗuwar gaba nake yi." Hmmm Harira, ciwone ke sani wannan kumburin, wannan yafi ƙarfin na masu ciki ai." "To Ubangiji Allah ya sauwaƙe. Yanzu dai muje gidan marayun mu samu Hajiya Bara mu san halin da ake ciki" Muka ɗunguma zuwa gidan marayu, Hajiya Bara na zaune a ofishinta ta gammu kwatsam. Itama ta jinjina halin data ganni a ciki sosai. "Toh labari marar daɗi, har zuwa yanzu ba'a samu jarirai sabuwar haihuwa ba. Ke ko sati ɗaya da haihuwa ko biyu, ba'a samu ba. Dama ban rufe muku ba ba'a fiye samu ba. Mata da yawa sunyi irin naku daga ƙarshe sai cewa suka yi an haihu ɗan babu rai kawai. Wasu kuma da haka asirinsu ya tonu. Abinda zance daku ku ƙara wata guda wata goma kenan, in ba'a samu ba shikenan zan taimaka muku a samu gawa a asibiti wanda suke mutuwa iyayensu su gudu su bar gawar a asibiti, asibiti kuma ta adana a mutuware. Inaga sai dai ayi hakan. Kuyi haƙuri" Tabbb akwai kwantaccen rikici fa mu dai je zuwa Mrs BUKHARI. Sai Allah ya kaimu gobe kuma💪🏼MRS BUKHARI ........ In miƙe tsaye mu fita na kasa, tun ina ganinshi bibiyu, uku_uku har na dena ganin hasken duniya baki ɗaya. Irin tashin hankalin da muke ciki yafi gaban misali jama'a. Ni dai buɗar idanuna nayi kawai na ganni a mota, ga Harira ga Mijinyawa, harma da Hajiya Bara. "Alhamdulillahi ta buɗe idon nata. Sannu Hindu Ubangiji Allah ya yaye miki, ya kuma kawo mafitar wancan abun. Mijinyawa ni ko akwai gidan wata mai magani a can wani ƙauye mai nisa a Katsina. Ina ganin in bayan wannan lamarin an gamashi akwai buƙatar ka ɗauki Hindu ka kaita wajen. Ana dacewa sosai, kaga yanzu haihuwa zaku yi ace tana shiga cikin irin wannan halin tana da ƙaramin goyo ɗanye abun fa bazai zama mai kyau ba. Kuma ana dacewa sosai, sai dai da nisa sosai kamar zaku shiga nijar haka wajen yake, inma ta kama ta riƙeku ne zata riƙeku har Allah ya bata lafiya. Har mahaukata matar take karɓa. Ta jibiya akwai hanyar shiga ƙauyen" Cewar Hajiya Bara. "To ai ko Hajiya mun gode sosai. Ai ko cikin nijar ɗinne zamu je, lafiya ai tafi gaban wasa. Kuma anan ɗinma duk wajen da naji magani ina zuwa in karɓo mata, zamu je in sha Allahu. Bari dai mu gama da wannan lamarin tukunna." "Wannan dole sai taga maras lafiya kafin ta ba da magani gaskiya. Amman ana dacewa, ko sulhune sai ayi musu, su shafa mata lafiya, uwa zata zama. Da ba dan na tausaya ba ma, wannan safgar ba zata yiwu da irin mai lalurarta ba. Tarbiyyar yaron abun dubawace sosai da sosai" Ni dai ina jinsu bance komai ba, harshena yayi nauyi ko motsi baya iya yi. Mun sauka a inda mota take saukewa bus sitop kenan. Daga nan muka hau acaɓa har ƙwar gida, inda majalisar matasan unguwar suke zama. Tare dukka muka shiga gidan, da sallama a bakinsu. Nan hankalin kowa ya dawo bisa kanmu suka shiga ware idanu, sabida ganin baƙuwar fuska, dan ko Harira basu sani ba. Muna shiga mijinyawa ya zari kula babba ya fita. Nasan abinci zai siyo musu. Ku shigo Hajiya Bara" Na faɗa a sanyaye jikina babu laka. Shigowa suka yi duk suka zauna. Hajiya Bara sai ƙarema ɗakin kallo take yi. Mijinyawane ya leƙo ya miƙo kularnan shaƙe dam da dambu yaji man shanu da yaji. A gabansu na dire, na ɗebo musu ruwan sanyi. Ga abinci kuci, ni zan yi sallah kafin ku gama. "Sannu Hindu, mungode sosai. Harira zuba mana muci, muma sai muyi sallah kafin mu kama hanya ai, kinga uku saura. Ta dubi agogon dake tsintsiyar hannunta. Alwala na ɗauro na fito na gabatar da sallah, na ɗaga hannu nace. Allah ga kayanka nan, kai kasan yadda zaka yi dashi." Shikenan na sauke hannuna na fito, sai na jiyo maganar su Hajiya Bara a tsakar gida kamar alwala suke yi, inajin motsin ruwa da buta. Da sallama suka shigo. "Wato Hindu ɓarayinki ya ban sha'awa ko'ina a tsabtace, kuma a killace, ɗakinki tamkar a birni, gashi ko ina sai ƙamshin turare, hatta butocinki ƙamshin turaren wuta suke yi, ni har ruwan alwalarma ƙamshi yake mun" ( kina da turaren mrs Bukhari ko kema ƙarnin kifi komai na gidanki yake yi? Ko turaren wuta mai warin sigari kema kike iya siyane Hajiya. Maza ga lambar wayata ki mun magana in baki ingantattun turaruka 08179523215) Murmushin dole nayi. Sallamar Nanno muka jiyo, tare da ɗaga labulen ɗakin, duk muka juyo muka kalleta. "Au baƙi kika yi daga birni ne?" Eh baƙi nayi?" Gaggaisawa suka yi, Nanno sai fara'a take yi. Tayi tunanin daga Kano ne tabbas. Harma data fita ta aiko yara da fura cikin kwanon sha mai murtala. Bayan sun idar da sallah Harira ta miƙomun ƙunshin leda. Na karɓa, ta soma mun bayanin magungunan. "Ganyen nonon kurciyane, ki dinga damawa da nono kina sha harna tsawon sati biyu, ruwan ummanki zai kawo lafiyayye da izinin Allah da zaran yaro ya kama. Nima dashi nayi amfani, sannan ki dinga yawan shan ruwa, ki yawaita tafasa hulba kina shan ruwan da zuma kamar shayi, ummanki zai kawo lafiyayyen madarar da zaki shayar da yaronki ko yarinyarki cikin aminci. Sannan ki dinga matsa kan umman a hankali a hankali ki ɗan dinga mishi tausa. Kuma ko jaririn yazo ko umman bai zo ba, ki dinga bashi zai zo. Wannan kuma na koriyar ledar da ruwan zafi zaki kaɗa, ko ki kaɗa a cikin kunu zazzafa ki sha. Shi wannan jini yake ɓallowa. Amman baya wuce sati biyu zai tsaya, ya danganta. In kuma da kika sha jinin ya ɓalle ya wuce ƙa'ida, sai ki kaɗa manda gatanan a kofi ki shanye ruwan, jinin zai dakata in sha Allah. A wajen wata wanzamiya ƴar na gada, ba haye ba na karɓo miki. Magungunanta suna da kyau. Hajiya mu sha furarnan mu kama hanya kuma" Godiya nayi mata, suka kammala shan furarsu suka fito na rakasu, lokacin ana masallaci an shiga sallar la'asar ne. Dawowar da zanyi Nanno ta tareni. "Su ɗin daga ina suke, ai nayi zaton ƴan uwanki ne daga Kano. Sai gashi sun tafi. Ke ƴannan wai lafiya kuwa, kwanaki can har sau biyu a jere wasu sun shigo gidannan kamar duba gari, harda namiji a ƙofar gida, sau biyu suka zo, kuma uwatale ta tabbatarmun dube dube taga suna ta yi. Yau ga wasu sun zo me kuke ƙullawa? " Babu abinda muke ƙullawa dukkansu abokan aikinane kamar yadda na faɗa miki tun lokacin. Waɗannan ma ɗaya abokiyar aikinace itama malamace, ɗayar kuma ƴar uwartace ni ban ma santa ba. Kuma ai bance miki daga kano suka zo ba ko?" Na gama kaiwa iyakar wuya har tsuma jikina yake yi ina tsaye. Da ba dan addini, da tarbiyya bata ba da damar a raina babba, ko a lailayo ashariya a ƙundumama mutum ba, ko a tsinka mishi mari ba, da Nanno yau taga tsiya. Amman kash, ina da tartibiyar tarbiyya, iyayena sun ɗaurani bisa gwadabe mai tsafta. Itama tana tsaye ƙiƙam tana zazzaremun idanu, a haka Mijinyawa ya shigo ya taddamu, kai tsaye wajenmu ya nufo. "Nanno lafiya meke faruwa? " "Akan baƙin da suka fita yanzu ne. Daga tambayarta su waye, shine fa take zazzagina ita ga sallamammiya" Murmushine ya suɓucemun na takaici da baƙin ciki. Jan sawuna nayi da ƙyar na koma ciki. Kabbarar sallar la'asar na tayar harna idar Mijinyawa bai shigo ba. Kular dambunnan na jawo in duba ko sun rage, dan raina ya biya gaskiya. Aiko baifi rabi suka ci ba, cokali na ɗakko, na dawo na jujjuya dambunnan. Loma ɗaya loma biyu sai ga Mijinyawa ya shigo. Zama yayi a gabana tare da yin tagumi hankalinshi baya jikinshi, gangar jikinne kawai anan. Idanu na ƙura mishi a gaskiya domin Allah Mijinyawa ya rame sosai, yayi duhu kuma. Juyowa yayi muka haɗa idanu. "Akwai abinda kike sone, ko jikinne? " A lokacin raina fansane ga Mijinyawa maganganun bakinshi sun shigeni sosai da sosai. Babu komai, ga dambu kazo mu ci basu ci da yawa ba" Lokali na miƙa mishi, in yayi loma ɗaya sai ya ban loma biyu, yana yi yana bani ruwan rubutu ina sha har muka gama. "To Nanno ta soma tambayata batun haihuwa, tana lissafe wallahi da komai cib da kika sani. To tace za'ayo miki rubutun naƙuda kisha zuwa sati na gaba in baki sauka ba. Ni gobe zamu wuce Bauchi sati ɗaya kacal zanyi, zan biya can wajen Hajiya Bara. Kusanma shine ƙarfin zuwan nawa. Ga damuna tana ta kawo kai, wannan karon zamu dai yi noma na faɗa miki Abdulƙadiri ya yankamun gona ni da Qasimu zamu noma, shi zai yi amfani da gonar Yayansu mai rasuwa. Ki samu a adda'a noma tayi kyau, harma munje jiya mun yi sharar gona lokaci kawai ake jira, gero da gyaɗa zan noma in sha Allah. Qasimu kuma masarar zallah yake tunanin nomawa dai ƙila da wake dai." To Ubangiji Allah ya baku sa'a Allah yasa yabanya tayi kyau. Nima da ace akwai waje ai da nayi nomannan nima. Baraka tace duk shekara ita ke noma musu shinkafar da zasu ci ko?" "Ƙwarai kuwa. Amman ke kam ban isa in barki kiyi noma ba. Ke da a lokacin kina jego ma. Kuma ko babu jego kalarki batai kalar noma ba. In shinkafar kike son in noma sai in noma ai Giwa. Amman ita sai ruwa ya daki ƙasa sosai, sannan ƙasar garinnan bata fiye yin shinkafa me kyau ba." Dariya muka yi baki ɗayanmu. Ai gyaɗarma abune mai kyau sosai, tana da daraja" "Ƙwarai kuwa tana da daraja sosai ma kuwa. Yanzu in Allah ya taimaka sai kiga mun samu gyaɗa fin buhu goma sha biyar fa, gero buhu goma kinga ina lefi zamu shekara ba yinwa" Hayaniyar oyoyo_oyoyoce tasa mukai shiru. Nawatane ya dawo, sai bayan damina kuma, an nome amfanin gona, hatsi ya koma rumbu tukunnah. Gaskiya naga Uwatale ta sha lalle, ga cikinta har yafi nawa girma ta shiga na wata bakwai kenan. Kafin Magriba sai ga tsaraba Uwatale ta leƙo ta miƙo mana a bokiti. Hmmm shinkafa ce mudu guda, sai magi, da bushasshen tattasai da tumaturi bushasshe. Sai mangwaro, uku, lemo uku. Tunda na ajjiye bokitin a cikin ɗakin ajjiye abinci ban sake bi ta kanshi ba. Ina kan sallaya na idar da sallah, ga turaren wuta na tashi a kasko, na ɗanyi wanka nasa riga doguwa zafi akeyi kamar me ruwan sama ya kusan sauka, sai ga Baraka. A tsakar gida ta zauna a tabarma dana shinfiɗa mana. Saina fito na taddata da kular abinci. Yau ke da kanki ina Ya'u da bai kawo ba? " Na faɗa da fara'a ina zama. "Maman biyu kenan. Babu mamaki biyune a cikinnan. Wai nace ashe lokacin haihuwar taki tayi, naji Uwatale sai surutu take a gari. Tana ta roƙon Allah yasa kar ki haifi ƴan biyu sai ta haifa" Bakina na taɓe kawai. Haihuwa kam ko yanzu, ko anjima an shiga watan har ya ɗan gota. Fatan shine mu samu mai albarka da jin ƙai, ba biyu ko uku ba dai." Tana kallon rago dake ta zaƙar harawa ya sake girma, dan gaskiya abinci Mijinyawa yake bashi haiƙan. "Hakane kam. Nima dai nayi mamaki nace in banda uwatale ai ba'a jayayye da ƙudurar Allah ko? " Sosai kuwa Baraka. Allah dai ya saukemu lafiya shine kawai" Dariya tayi tace. "To ameen Hinduwa. Ga nan abincin bari in koma gida. Ya'u ai bayanan ya raka Babarmu ɓoto. Shi kam ma da damina ta wuce zai tafi almajirci, dama shayi ake jira ayi, kuma kinga anyi harta warke, yaro ya girma." Kai kawai na gyaɗa dan bani da ta cewa. Ko'ina da al'adarsu. Su sunfi gamsuwa su tura yaransu nemo ilimi a nesa, kamar yanda ake tura ƴan bodin na boko. "To bari in je uwar biyu sai da safenku" Bokitin tsarabar su Uwatale na juye mata komai a leda na damƙa mata, sai godiya take yi. Tsakanina da Baraka ai babu godiya alkhairansu baya misaltuwa sam. Tana fita bata jima ba sai ga Mijinyawa ya shigo. Abincin na zuba mana. Tuwon dawa da miyar karkashi bushasshe ya ko ji bushasshen kifi. Ci muke yana wucewa, amman hankali da tunanikanmu duk basa jikinmu ma. Ranar tafiyarsu Mijinyawa zuwa Bauchi yazo, ya tafi ya barni daga ni sai halina, daga kwanciya sai kwanciya. Nanno kullum saita zo dubani ko naƙuda ta tashi, harfa cikin dare turowa take yi azo a duba. Wannan damuwar saita ƙaru mun gaya, sati na zagayowa saiga mijinyawa yazo mun da mummunan labari kam cewar har wannan lokacin babu jaririnnan fa. Jikinmu duk a sanyaye gaya. Rubutu aka soma yo mun ina sha da shafawa Nanno tace. "Babu mamaki cikin ƴan biyune a jikinta, dan kuma shekara kuka yi tim a ciki, itama naga halamu shekara zata yi." To wannan hasashen shi ya ɗan riƙemu, har hankula suka sauka a kaina, masu jiran tsammani suka tura. Ta ɓangaren su Baba Sojanmu kuma nayi musu wasiƙa akan har yanzu haihuwa shiru, kuma munje asibiti sun bani wa'adi akan in wa'adin ya cika ban haihu ba to za'a ciro ɗan ko ƴar. A wasiƙar da Innarmu ta turone take tambayar ko a turo Inna Yahanasu tazo ta zauna dani. Ranar kwana muka yi muna canki cankar abinda zamu ce ma Innarmu a matsayin amsa. Da ƙyar muka cimma matsaya. Muka ce babu damuwa Nanno na kulawa dani, da Shafa Matar Yaya Salihu. Hankalinmu in yai dubu ya tashi fa jama'a. Tafe_ tafe _tafe har wata goma sha ɗaya ciki ji kuke shiru, Mijinyawa yaje gidan marayu yafi a ƙirga shiru babu labari harma dai mun sare gaskiya. Mun kuma yanke hukuncin zamu je kawai asibiti kamar yadda Hajiya Bara tace zata taimaka mana a bamu gawar jariri. Ina ya Allah babu ya Allah, abu har ciki ya shiga shekara. Wata ranar asabar wacce abadan ban isa mancewa da'itaba, koda hauka nayi bana jin wannan ranar zata gogemun a rayuwata. Ranace mafi zafi da tsanani a tare dani. Dama dai jiya banyi bacci ba, daga ni har goga naku. Makaraina sun tashi sunata buge_buge suna kururuwar da saida kaf ƴan gidan suka taru a ƙofar ɓarayina dan jin ba'asin abinda ke faruwa, da dalilin zuwansu. Nasan baya wuce baƙin ciki suka zo taya ni, na abinda ya samemu. Mijnyawa shi ya tsaya kai da fata a kaina, ba nuna gajiyawa, babu nuna ƙosawa da lamarin. A haka har garin Allah ya waye damu ranar asabar ɗin kenan da fatan kun gane. Gashi jiyan dai muka karanta wasiƙa Innarmu, cewar Innah Yahanasu tana hanya daga Maiduguri zata zo ta kaini asibiti, inya kama ma a tawo dani kano ne duk dai yadda ta kama, inma gurin maganin gargajiya za'a kaini dai duk zata zo ayi duk wacce za'ayi a gabanta. A cewar Innarmu bai kamata ace babu wani nawa a yanzu a wajena ba, dole a nuna ma su Nanno gatana. A hakanma sun makara da turo mutum. Ana wata ga wata kenan, ranar tonon asiri, ranar da ramin ƙarya zai ƙure. Sukuku haka duk muka kusan wuni, ni babu inda baya yi mun ciwo ma a jikina, hatta akaifa dake hannayena da ƙafafuna ciwo kawai suke yi mun, jinsu nake yi kamar suna ɗurar ruwa. Wajajen la'asar ina gaban murhu na dasa tagumi, bana gane komai bana jin komai. Ashe Nanno ce a kaina tana ta magana, sama da ƙasa Allah bai bani ikon jinta ba sam. Har saida Mijinyawa ya zungureni dawowarshi masallaci kenan. "Nace wai lafiyar matarka kuwa, shekara guda ciki anƙi a haifeshi, ga can Uwatale fa naƙuda take yi awa uku kenan tana abu ɗaya. Cikin jikin matarka fa kusan wata uku yaba na Uwatale. Ni inaga makarantane suka danne cikinnan suka kifeshi gaskiya. Gobe ni da shafa zamu ɗauketa zuwa can Burra, wani ƙauyene a Toro, akwai wani bafullace mai ba da maganin mayu, da muyagun makarai. Dan haka ka shirya har da...... " Shafa ce ta shigo da saurinta. "Nanno kizo ki ga Uwatale, abun fa yana ta sake kankama. Wannan karon gaskiya abun sai a hankali." "Kin bata hannun maryam ɗinnan dana jiƙa kuma? ( Shajaratu Maryam) Shahararriyar bishiyace wacce ake jiƙama mace mai naƙuda tasha ruwanta, domin samun sauƙin haihuwa da rage raɗaɗi. Yawancin unguwannin zoma na al'ada ke amfani dashi, dole a kwai hannun Maryam a ƴar jakar unguwar zomansu. "An bata ta sha Nanno" "To damo tsakin kuka maza, da ta sha bakin mahaifar zai buɗe, maza Shafa" Da sauri suka fice dukkansu. Mijinyawa na kalla rauni linkib a idanunshi. "Taso mu tafi Tutar so, maza taso matata" Miƙewa nayi, ban tambayeshi ina zamu je ha, banyi tababa ba, shiga ciki nayi sabida ƙarfin hali nice harda sake sutura, na saka mayafina mai kyau, ƴar jakar da kuɗaɗena, da magungunan da Harira ta bani, suke ciki na ɗauka, na zura ɗan kunnena da sarƙa na gwal a cikin jakar na fito. Ɗan makulli yasa ya rufe ƙofar ɓam. Ya amshe jakar hannuna. "Kiji da kanki" Tare muka fito dashi, ƙofar ɗakin uwatale cike da takalma. Ga dutsen niƙa a ƙofar ɗakin an ajjiye. Wannan wani canfine na mutan da, ajjiye dutsen niƙa a ƙofar ɗakin mai haihuwa dan kareta daga mayu, ko makarai. Ficewa muka yi suɗuɗu. Babu ko kowa a babban tsakar gidan, har muka fice babu wanda ya ganmu. Sai dai kash muna fitowa sai ga Abdulƙadiri da Halima, dama yace zai kawota ayi zumunci, tunda dai tun bayan aure bama mu sake haɗuwa ba. Su Barakane ma suka je, har mijinyawa yake tsokatamun Halima tace dani ya kamata tayi ƙawance nice wayayya basu Baraka ba. "Kai Magawata har kun mance da zuwan namu ne zaku fita tattaki. Gamu mun zo ai dole sai a koma ko? " Cewar Abdulƙadiri da yake magana da karsashi. Halima ma tayi carab tace. "Gaskiya kam ai gara mu koma ciki tunda dai mun haɗu ba ku yi nisa ba. Ni da ƙawata hira kam yau sai abinda na manta" Mijinyawa ya dubeni, nai mishi nuni da idanuna akan kar mu koma, tuni ya ɗauki haske, renon Innarmu ne fa mu ɗin. Wallahi sabida soyayya da fahimta, da karantar juna ko da hanci kayi magana miji yasan inda ka dosa, shi yasa ko ɓacin rai innarmu take yi da Baba Sojanmu bata dena mai komai data saba, a idanunta kaɗai yake gane tayi fishi, kuma ya shiga taitayinshi. Ai mace mai aji tayi. Ga wani hadisi kyauta na baku. Manzo rahma Arrasul S A W yace da ummuna Aisha. "Lallai ni na san lokacin da kike farin ciki da ni (ba kya fushi), da kuma lokacin da kike fushi da ni." Sai Aisha ta ce: "Ta yaya kake gane hakan, ya Ma'aikikin Allah?" Sai Annabi (S.A.W) ya ce: "Idan kina cikin farin ciki (ba kya fushi), idan za ki yi rantsuwa kina cewa: 'A'a, na rantsu da Ubangijin Muhammadu' (Wa Rabbu Muhammad). Amma idan kina fushi da ni, sai ki ce: 'A'a, na rantsu da Ubangijin Ibrahim' (Wa Rabbu Ibrahim) (A lura: Lafazin rantsuwar shi ne "Ubangijin Ibrahim" ba "Ubangijin Ka'aba" ba, kamar yadda bayani ya zo a cikin sahihan littattafai) Jin haka, sai Sayyidatuna Aisha ta yi murmushi ta ce: "Haka ne, ya Ma'aikakin Allah! Amma wallahi, ba abin da nake bari illa sunanka kawai (amma soyayyar taka tana nan a zuciyata)." Allahu Akbar wato ummuna Aisha macece mai hikima, macece wacce ta iya jan zaren soyayyarta da ma'aiki Arrasul S A W Itace macen da aka tambayi Annabi wa yafi so duk duniya yace Aisha. Akace a maza fa yace mahaifinta. Tsarki ya tabbata ga Ubangiji Annabi Ibrahim da Haruna. Ke ki zauna dai kina cewa ai mijinyawa ko Baba sojanmu tsoron matansu suke ji, juyasu akeyi, kar ki iya jan zarenki kinji ko? Maza dai zauna samadora, bodara. "Kai Abdulƙadiri ai fitowar bata motsa ƙafa bace ma, fitowace ta zuwa asibiti, jikin yayi nauyi sosai, ciki shekara guda. Gara muje asibiti muji abinda likitoci zasu ce. Kafin ace na gargajiya za'ayi." "To kace wani abu. Amman me zai hana ka bari su Nanno su yi da kansu? Kasan fa ba'a son batun asibiti musamman ta a wajen haihuwa. Kar ku tafi ku bar baya da ƙura" "A'a Abdulƙadiri. Dole nine a haƙƙu da in kula da'ita. Nanno tana karɓar haihuwar matar Nawata, sai su iya kwana ma ana abu ɗaya, kai fa ka sani. Zamu je kawai Amarya tazo barka da suna kawai." Da haka dai muka zulle musu, kai tsaye wajen motar Bauchi muka isa. Saura mutum uku mota ta cika, zuwanmu sai ya rage saura mutum guda. Ni dai kaina na jingine a damatsen mijinyawa naku mai ƙirji him hahaha😆. Har motarnan ta cika muka hau titi. Shiru motarnan tamkar ruwa ya cinye kowa. Wani irin sabon al'amari nake ji a jikina, wani iri zuchiyata take yi mun. Abun almara ana daf shiga cikin tasha, munfa riga da mun iso cikin Bauchi. Sai numfashi yai halinshi na suma. Mijinyawa:. Jin jikin Hindu ya saki ne yasa ya juyo da sauri, taɓatan da yayi sai yaga ta koma baya halamun babu numfashi a tattare da'ita. "Hindu! Hindu?". Shiru babu Hindu babu ɗan dalilinta. Riƙeta gam yayi. Ya shiga yi mata karatu a kunnenta yaji shiru. Jikinshi take ya soma rawa daidai tsayuwarsu a cikin tasha, harma an soma sauka. " Baiwar Allah ki taimaka mun mu sauka da'ita. Iyalinace ta suma ne, asibiti kuma zamu je dan Allah" Wata mata dake kusa da Hindu yaima magana. A motar ya barsu ma, ya fita ya nemo mota ƙarama aka sa Hindu a ciki, yana riƙe da jakarta. "Magawata lafiya Hindun ce babu lafiya ne?" Juyowar da Mijiyawa zai yi sai yaga Harira ce. "Harira Hindu babu lafiya bata ma san inda kanta yake ba. Dama wajenki muke son zuwa ki mana jagora wajen Hajiya Bara" "To ai ni ɗinma ganinnan da kayi mun, wajen naku zani. To ai sai mu shiga mota mu je asibitin" Harira ta shiga gaban mota, mijinyawa yana baya tare da Hindu, kanta na bisa cinyarshi. Jama'are:. Da magriba Inna Yahanasu tayi sallama ta shigo cikin gidan. Matan gidan duk suna tsakar gidan. "Ahuwanku dai masu gida, da fatan mun same ku lafiya? " "Yauwa maraba lale baƙuwa." "Wajen Hindu nazo, ni ƙanwar mahaifiyarta ce" Shafa ta washere baki tace. "Ayya, to Tatsaure kaita ɗakin Inna, Nanno tana wajen mai naƙuda bara a kirawo miki ita" "Subhanallahi, naƙudar tazo ne. To Allah ya buɗi idanunta lafiya" "To Ameen, amman ba Hindu bace matar Abokin tagwaitakanshi ne ke naƙuda. Muje in kai ki ciki" Cewar Tatsaure. Kayanta suka kinkima jaka uku zuwa ciki. "Baƙuwace da daddare haka Tatsaure? " "Hmm ai ko dai Innah. Ƙanwar mahaifiyar Hindu ce tazo. Shine Yaya Shafa tace in kawota wajenki kafin a kira Nanno" "Ayya, to ku shiga, baƙuwa maraba" Shiga da Inna Yahanasu ciki akayi. Tana zaune ta jima, itace har bayan isha, kafin Nanno ta shigo. "Hi haƙuri baƙuwa, ina wajen mai haihuwane, tun rana sai yanzu ta sauka, an samu ɗa namiji. Ance wai wajen Hindu kika zo ko? " "Eh wajenta nazo" "To basanan. Tun ɗazu muka fahimci basa gidan, kuma ɓarayinsu a kulle yake. Amman babu mamaki gidan Abdulƙadiri suka je. Zan aika yara su yo kiransu. Yauwa ai gara da Allah yasa kika zo. Gobe zan ɗauketa zuwa Toro akwai wani mai maganin gargajiya, to wajenshi zamu je ko za'a dace. Abunka da mai makarai babu mamaki su suka riƙe cikin. To kinji" Innah Yahanasu tace. "Wanne irin maganin gargajiya ne kuma? Ai asibiti gobe zan ɗauketa in kaita. Babu wani maganin gargajiya da za'ayi." "Au Allah ishasshiya, a matsayinki na wa kenan? Ashe ba da arziki kika zo ba kenan? " "A matsayina na uwarta, banzo da arziki ba. Duk abinda kike ji dashi kin tara kin samu, alo tsiya alo danja. Kano ma zan tafi da Hindu kuma ko mijinta baida fawa, balle ke" To mu kwana anan sai in Allah ya kaimu Monday kuma in sha Allah Son so💪🏼💪🏼💪🏼MRS BUKHARI ......... Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JVdGBW8N6iFFBHyPGYXdrF?s=sw&p=a&ilr=0 *Kin Dade kina neman Adashin gatan da zaki shiga ki rika Tara kudi kadan kadan ki kwashi idan nace Miki kaya hajiya ta ina nufin komai ga Anty zee nazo muku da Tsarin adashi ki rika Tara kudin ki kadan kadan ki kwashi duk abunda kike so, akwai bangaren kayan sawa na Yara Dana manya, akwai kayan kitchen, akwai sarkoki ,takalma , jakuku Nan Yan gayu, mayafai dadai sauran su me kuke jira maza ku shigo ku fara tari tun yanzu* 💃💃 "In mijinta bai isaba, ni uwarshi na isa har nayi yawa ma. Babu inda za'a ɗauke mishi mata a kaita wallahi. Kinsan Allah ko wankan jego bata isa taje ba. Asibiti dai bama zuwa akan Hindu kuma ba za'aje ba to kinji. In sama da ƙasa haɗewa zata yi, to sai dai ta haɗe babu asibiti a gidannan" Innah Yahanasu ta dubi Nanno tace. "Zaki ga inda ake mulkar mutum har fadarshi kuwa. Hindu ɗiyata ce, ƙafata ƙafarta zan tafi da'ita Kano, ke Maiduguri ma zan wuce da'ita inga ta tsiya. Tunda ke kam baki da mutumci tabbatacciyar maras ɗa'a" Innah Dubu ce ta shigo da sauri tace. "Haba baƙuwa, haba Yaya ku yi haƙuri. Mufa surukan junane, ai bai kamata ma ace ana wannan hatsaniyar ba. Baiwar Allah Hindu dai sun fita zansa Tsalha yanzunnan yaje ya kirawosu su dawo. A yi haƙuri wannan faɗace_faɗacen a watsar dashi" Kafin Nanno tayi magana Yaya Jamila ta leƙo. "Nanno jini ya ɓallema Uwatale fa, sai kin zo." Fita tayi da sauri tana "Ina kofi a jiƙa manda, a ɗebi ganyen gwanda dana dafa da tsamiya, ha haɗa da mandan, ta kafa kai tasha maza kafin jininta ya ƙare. Wannan yarinya taji jiki." Nan Nanno ta wuce ta bar Innah Yahanasu. Innah Dubu kuma ta tura Tsalha kiransu Hindu a gidan Abdulƙadiri, duk tunaninsu can suka tafi. Tuwo ta kawo ma baƙuwa, tuwon masara miyar bushasshiyar kuɓewa da naman rago a ciki yanka ɗaya jol, sai kakide da aka sa mata da yajin daddawa. "Ga abinci dan Allah kici. Duk abinda ya faru kiyi haƙuri. Yaya ce bata da haƙuri sam" "Babu komai nagode, ni ɗinnan da kika ganni na fita rashin haƙuri, nata ai wasane. Da Allah inaso zan yi alwala in yi sallah kafin ita Hindun tazo" Innah Dubu ta nuna mata wajen alwala, ta dawo ta shinfiɗa mata tabarma ta fita zuwa bakin murhu tana raba tuwon dare. Asibiti:. "Harira taimaka mun mu fito da'ita kinji sai in goyata mu shiga, na cire mata ƙwaryar cikinta. Jikinta yayi zafi sosai." Cewar mijinyawa wanda duk ya ruɗe ya fita hayyacinshi ganin Hindu kwance babu yadda take. Harirace ta zagayo ta buɗe ƙofar ta riƙe jaka da ƙwaryar cikin Hindu. Shi kuma daya fito saiya zarota ta kafaɗa ya fito da'ita. Harira ta taimaka mishi saiga Hindu a bisa kafaɗar mijinyawa yayi mata riƙon yara wanda kai da ƙafa suke reto a kafaɗa, ba dan bata da nauyi ba, aa sai dan yana ganin dole yayi hakan, sabida yayi sauri a ceto mishi rayuwar mata. Harira na biye dashi. Suna shiga ma'aikatan babban asibitin Bauchi masu karanmci suka ba Hindu gado. "Magawata bari inje wajen Dr AA Nafaɗa in mata magana aminiyar Hajiya Bara ce zan zo yanzu." Ina hankalin nashi ma baya tare dashi sam, har Harira ta dawo ita da Dakta AA nafaɗa farar dakta ƴar duma_duma baima san anayi ba. Adda'a kawai yake yi yana zurga zurga. Jin an buɗe ƙofar ɗakinne yasa yayi zuruf yabi bayan Dakta AA nafaɗa. Harira na kiranshi ina. Mata ya gani a kwakkwance a gado kawai, ga mata biyu a tsaye a gaban gadon Hindu suna dubata. "Kaine Mijin Hindu kenan ko?" "Eh nine likita. Dan Allah ki taimakeni Hindu ta tashi, kar wani abu ya sameta, gara ni komai ya sameni wallahi" Murmusawa tayi, kafin tace. "Babu abunda zai sameta. Asibiti ai gidan warakar ciwone da yardar Allah. Yanzu kaje daga waje ni da kaina zan duba Hindu." Fita yayi jikinshi a sanyaye, amman ya zauna ya kasa zama. "Mijinyawa zanje in tawo da Hajiya Bara yanzunnan akwai buƙatarta a wajennan. Sannan dama ai itace ta turani wajenku nai kiranku" "An samu jaririnne Harira, dan Allah kice mun eh an samu?" "A'a ban sani ba. Ni saƙwan kira kawai ta bani. Yanzu ka jira zanje yanzu zamu dawo tare. Nasanma ba za'a tambayeka komai ba tunda tana wajen Dakta AA nafaɗa" A haka Harira ta tafi ta bar mijinyawa cikin zulumi sosai da sosai. Yana tsaye sai karatun Qur'ani yake yi, ba da ƙarfi ba, amman ba a zuchi ba a bayyane yake yi, harma wani bawan Allah da aka shiga da matarshi ya dinga tayashi suna yi tare. Fitowar Dakta AA nafaɗane ya zaburar dashi. "Biyoni muje mijin Hindu" Da sauri ya bita, yana tafe yana waigen ɗakin da aka shigar da Hindu. "Ka kwantar da hanalinka, duk taimakon gaggawan da take buƙata an riga an mata, an ɗaura mata ruwa, anyi mata abinda ya dace. Bacci da hutu sosai take buƙata, kusan cutar damuwace taso ta kamata, amman dai zamu shawo kan matsalar, sannan kayi ƙoƙari wajen rage mata nauyin zuchiyarta, ta ɗauki damuwar abu ta ƙwallafa a ranta. Ko duk akan batun ɗaukar jaririnne. Dan Hajiya Bara shekaranjiya ta mun magana akan zan bata gawar jariri daga mutuware, irin yaran da aka haifesu babu rai, sai iyayensu su gudu su bar mana su. Mu kuma saimu adanasu a mutuware, wasu suna dawowa daga baya rashin kuɗine ke sawa su gudu. Wasu kuma zasu haifi jariran ma da ransu zasu gudu su bar mana su, sabida ba zasu iya kulawa dasu ba, wasu dama bata hanyar Aure aka samar dasu bane, to ire irensune bayan duk mun gama musu gwajin lafiya sai mu turasu gidajen marayu, na gwamnati, ko masu zaman kansu." "Wallahi likita akan batun da ta tashi hankalinta kenan. Nama dakkotane sabida mu zo wajen ita Hajiya Bara akan batun gawar jaririn, sabida yadda mahaifa suka matsa, shekara guda tana kife da ƙwarya a cikinta" Kai ta girgiza tace. "Nasan komai dangane daku, Hajiya Bara aminiyatace, mace mai tausayi, da mutumci kenan. Ai lamarinku ya tsaya mata a wuya fiye da yadda kuke tunani. Itama Hindu tayi namijin ƙoƙari. Abun mamaki yadda naga ta kumbura tamkar mai cikin gaske, yafi komai ɗauremun kai gaya" Ƙofar ofishin aka ƙwanƙwasa, ba'a jira neman izini sai ga Hajiya Bara duk a firgice. "Ya ake ciki ƙawata ta farfaɗo? " "Kibi a hankali kinfa san sarai lalurarki. Mun shawo kan lamarin in sha Allah. Ya jaririn an samu kuwa? " Mijinyawa ya ƙura mata idanu yana son yaji to me zata ce. "An samu har biyu, mace da namiji, shine dalilin da yasa na tura Harira tai mun kiransu" Zubewa mijinyawa yayi, tare da yin sujjadar godiya ga Allah da wannan babban asiri da ya rufa musu. Da kuma murnan samun jaririn, dan kusan yafi Hindu ƙwallafa rai akan samun wannan jaririn. "Allah sarki bawan Allah. Kuna ta faɗi tashi, sai yanzu Allah ya nufa. Ina fatan asiri bai tonu ba dai ko? " Kai kawai mijinyawa ya girgiza halamun asiri bai tonu ba. Dakta AA nafaɗa ce tace ya basu waje, ya koma can ɗakin da Hindu take zaima iya shiga. Ai kafin ta ƙarashe ya fice da saurinshi, har yana zamewa. Ɗakin ya shiga ya tadda baiwar Allah a kwance, ga ruwa yana shiga jikinta a hankali a hankali. Fuskarta ya ƙurama idanu, yayi shiru kawai yana jin dama ita ta tashi shi ace shine a kwancen. Amman yasan haka Allah maɗaukakin sarki ya hukunta musu. Ya jima a tsaye kawai a bakin gadon yana aikin kallonta ƙirjinshi na hawa da sauka. Ina ma Hindu irin son da bashi da abun misali. Duk da har kullum ya yarda kuma ya gamsu, son da Hindu take mai ya ninka wanda yake yi mata. Duk wanda ya kalli ƙwayar idanun Hindu, yasan tana sonshi gayatan. Da ƙyar ya nemi farar kujerar dake gefen gadon ya zauna, tare da yin tagumi. Fatanshi da burinshi shine farfaɗowar Hindu, da kuma irin farincikin da zata yi a yayin data buɗe idanu taga jaririnta a gefenta. Dakta AA nafaɗace ta ba da umarni aka maida Hindu wani ɗaki na musamman wanda gado biyune kacal a cikin ɗakin, daga na Hindun sai na wata baiwar Allah data haifi ƴan biyu, ga jarirannan a wani gado daban sunata bacci, itama uwar bacci take yi, ga ƙarin ruwa anayi mata, sai mai jinyarta guda ɗaya mace. "To Magawata anan Hindu zata ci gaba da kwanciya har zuwa lokacin da zata samu lafiya, amman ya kamata kaje ka sanar a gida cewar ta haihu ko? In yaso Harira sai ta zauna da'ita. Kai namijine ba zai yiwu ka zauna kai mata jinya ba, dama ɗakin dai ku kaɗaine. Hajiya Bara zata kawo jaririn yanzu" "To Dakta mungode sosai Ubangiji Allah ya bar zumunci. Sai dai zan so a barni sai zuwa gobe da safe in naga farfaɗowarta, to sai in je in sanar musu. Kuma inaso in kwana ko da a ƙofar ɗakine sabida in dinga dubata jefi_jefi. Aimun wannan alfarmar" Murmushi tayi tace. "To shikenan Magawata, Ubangiji Allah ya bata lafiya ko? " Sai ta saka kai ta fice. Harira tace dashi. "Inason zuwa gida in ɗakko riyon kayan jaririn, sai ruwan zafi a filas. Da abinci zaka iya zama kafin inje in dawo" Nan Harira ta fita ta bar Mijinyawa a zaune yana ambaton Allah. Ko magriba bai yi ba, ga isha ma ta wuce. Ganin wannan mata ta shiga banɗakin cikin asibitin tayo alwala shine ya tuno ashe fa bai yi sallah ba. Yanzu dole ya jira Harira ta dawo tukunna. Can sai aka turo ƙofa, Hajiya Bara riƙe da jariri a cikin farin abun ɗaukan yara, tana isowa ta miƙama Mijinyawa yaron. Jikinshi na rawa ya karɓi yaron, baima iyaba saida aka gyara mishi kan yaron. Durƙusawa yayi guiwa a ƙasa, sai hawaye yana kukannan hawayen na ɗiga a fuskar yaronnan. "Alhamdulillahi Allah nagode ma da wannan kyautar da kayi mun. Ya Allah mun karɓa mun gode ya Allah. Allah ka raya mana wannan ɗa da imani. Kasa duniyar musulunci tayi alfahari dashi" "Ameen Magawata, ka daure ka tashi, kawoshi a shinfiɗeshi kusa da Mamanshi" Hajiya Bara ta karɓi yaron daidai shigowar Harira da kaya rigi_rigi tamkar gaske. "Allah sarki Ubangiji Allah ya raya. Hala sun ɗan jima basu samu haihuwar bane ko?" Cewar wannan mata da take jinyar uwar biyu" Harira tace. "Suna cikin shekaru na bakwai kenan Allah ya basu" "Allah sarki dole su yi murna. Ubangiji Allah yasa hanya ta buɗe kenan" Duk suka amsa da Ameen." Hajiya Bara ta fito, Magawata ya bita. "To shikenan in Allah yasa ta warke zata zo ofishinmu ta sanya hannu, kaima ka sanya bisa doron ƙa'ida. A kuma ji tsoron Allah a riƙe yaro da kyau dan Allah. Ni zan tafi, na biya komai na asibitinnan ba'a buƙatar komai daga gareku" Godiya Mijinyawa ya dinga yi mata, shine rakiya har gaban mota. Saida ya tabbatar da fitar motarsu, kana yabi wasu fulani suka yi sallah a wata ƙatuwar tabarma. Ya daɗe a sujjadar ƙarshe, da tahiyar ƙarshe yana godiya ga Allah da wannan rufin asirin da yayi musu, yana roƙon Allah ya tashi kafaɗun Hindu." Bayan ya sallame ma ya dinga zubo adda'a, daya tuno fuskar wannan farin jaririn sai yayi murmushi. Wato Allah cikin ikonshi da hikimarshi ji yake yi a zuchi, da gangar jiki, tamkar shi ya haifi yaronnan. Kuma yaji yana jin sonshi da tausayinshi suna shigarshi tamkar yadda ake ƙarama mara lafiya jini, da ruwa. Lallai Ubangiji mai girma da ɗaukakane. Hukunci sai mai tsaga idanu. JAMA'ARE:. "To kinji dai an dudduba gidajen abokanshi ko sunje, amman ba'a samesu ba. Amman duk inda suka je zasu dawo. Kiyi haƙuri ala bashi ko zuwa gobe da safene za'a san inda suke, tunda ba ɓata suka yi ba. Abokinshi Abdulƙadiri ma yace ya gansu da yamma lis. Har bayan la'asar tana cikin gidannan dake bama mai yawan fitowa bace, dama haka take yi." Innah Dubu ce ke magana da Innah Yahanasu, wacce take zaune tana cin alkakin da ta tawo dashi, dan anyi juyin duniya taci abinci taƙi ci. Hatta maƙota an kawo kusan kwano huɗu na mabanbantan abinci, bata ci ba. Kasancewarta macece mai ƙyama sosai, a birninma ita ba abincin kowa take iya ci ba, balle a nan ƙauye. Nanno ce ta shigo tana cewa. "Kinga fa abu kamar wasa Dubu babu Hindu babu Mijinyawa ko ina suka je baza su sanar ma mutane ba sai Allah. Duk sai naci mutumcinsu in suka dawo marasa hankali. Kuma nasan aikin Hindune itace zata jashi su kama hanya. Tunda nake yarana basu taɓa zuwa wani wajen ba izinina ba sai gashi yau Hindu ta zama sila" "Tunda shi wawane ai dole kice Hindu ce sila. Wato ke dai har kullum son kanki ne dake. Kina nan amman kin yanke hukunci. Madadin ki musu fatan alkhairi, sai cewa kike yi zasu dawo su sameki mutanen banza. Ke wacce iriyar uwace ke haka ne? Kai Allah ya sauwaƙe" "Kinga baiwar Allah bafa zaki zo har gidan mijina ki nemi farfaɗamun maganganu ba ehe. In ba Hindu bace zata ja shi, da can yayi hakan mana. Kinzo sai wani daɗɗagama mutane kai kike yi. Duk abinda aka baki kinƙi ci, ku ga zuriyar ƙaruna ko?" Innah Yahanasu ai saita miƙe tsaye, gata doguwar kanuri ingarma. Innah Dubu tace. "Bafa za'ayi haka ba. Dan Allah ku sakama zuchiyoyinku risilama. Muyi fatan Allah ya dawo mana dasu lafiya tukunna. Ke Yaya ki tafi abunki" Ai ina wuta Nanno tasa Innah Dubu tunda dama tsoronta suke ji, maraina wayonta ne. Danma ruwane a haka ya doki babban zakara, in da canne tama isa ta shiga safgar Nanno ne, balle har ta shigar mata magana. Innah Yahanasu kuwa ta dinga zazzagoma Nanno baƙaƙen maganganu masu zafi, da ƙyar husumarnan ta lafa. Dan da kuka wiwi Nanno ta wuce, a hakanma saida Yaya Salihu yazo ya dinga ba da haƙuri, ya kuma sa aka jaye Nanno. Su Qasimu da Abdulƙadiri sukaita sunturi a jama'are ko Allah zai sa su ci karo dasu amman ina, dole sukai haƙuri akan a barma gobe ko asibitinne sai su leƙa tunda dai Abdulƙadiri ya faɗama Qasimu shi kaɗai cewar ai Magawata yace Asibiti zai kai Hindu ɗazu da suka zo. Amman bai sanarma su Innah Dubu ba, yasan akwai gagarumin rikici muddin suka ji inda Magawata ya kai Hindu. Akwai narkakken rikici. Asibiti. Mijinyawa Harira tayi juyin duniya ya zauna yaci abinci, amman ina yaƙi yadda yaci. Yana ƙofar ɗakin da Hindu take, lokaci zuwa lokaci yana shiga ya dubasu, bacci Hindu da yaronta suke yi, sai wani sa'in inya leƙa ya tadda Harira tana gyangyaɗi. "Ka daure ka yi kwanciyarka ba sai kana leƙowa ba. Allurarran fa da akayi mata, sai ta kai gobe zata saketa. Sai zurga_zurga kake yi. Gashi cikinka babu komai" Murmushi mijinyawa yayi. "Ai babu komai Harira, ba ma zan iya wani bacci ba gaskiya" Daya fitane baiwar Allahn dake jinyar wacce ta haifi ƴan biyu tace. "Inama Alhaji Dauda zai zo yayi koyi daga wajen bawan Allah'nnan. Yazo yaga yadda maza suke damuwa, da nuna kulawa da matansu. Shi ya ɗauka namiji babu abinda zaizo yayi a asibiti dan matarshi zata haihu, ko ta haihun. A cewarshi aikin namiji shine kawai ya biya dukkan kuɗin ɗawainiyar asibitin, wanzuwarshi bata da mahimmanci. Kaico" Harira tayi shiru tana nazari kafin ta san me zata furta. "Ai kulawama wani abunne sosai. Kuma wannan kulawar, da damuwar. Halamun soyayya, da tausayine a zuchiyar namiji. Amman shima Dauda bashi da laifi. Babu mamaki haka ya taso yaga ana kulawa da mace, ta hanyar bata kuɗi ta magance matsalolinta, lokacinshi ba nata bane, na kuɗine da kasuwancinshi, ko aikinshi kaɗai. Ita mace ɓangarentane dole ta kula da namiji, tai mai gadin gida, ta ɗau ciki, ta haihu, taci gaba da kulawa da yaran, mijin, gidan. Ita bata buƙatar kulawa, da lokaci sam." Shirune ya wanzu a tsakankaninsu kawai. Ji kake kurum. Wajajen asubane jaririnnan ya soma kuka kamar ranshine zai fita. Yana hannun mijinyawa yana aikin jijjigashi, idanunshi akan yaronnan. Wannan kuka shine ya zama wasila na farkawar Hindu daga nannauyan baccin data tafi, na allurai. Allah take ambato tunma kafin ta buɗe idanunta. "Harira Hindu ta farka, naji muryarta" Hindu:. A hankali na soma buɗe idanuna, ina jin kukan jariri a kunnuwana har zuwa cikin ƙwaƙwalwata, wani muhimmin saƙo sai isa cikin zuchiyata yake yi. A kan mijinyawa da jaririna na sauke idanuna. Na dubeshi, na dubi jaririn dake jikinshi yanata canyara kuka. Saman ɗakin na kalla, a hankali nace. Ubangiji nagode, ka fiddani kunya, Allah Alhamdulillahi da wannan kyauta daka bamu. Ubangiji dama ina da yaƙinin ka amsa adda'armu, lokaci ne sai yanzu yayi." Hannayena na miƙo daga kwancen da nake. Miƙoshi inji ɗuminshi. Bani shi in rungume abuna" "Hindu jikinki babu ƙarfi ba zaki iya ɗaukarshi ba, bara in kira ma'aikatan jinya" Cewar Harira. Murmushi nayi mata. Zan iya, ai ciwo ya kau, farin ciki ya mamaye ƙuncin. Mijinyawa bani ɗana" Harira ta fita kiran Dakta, shi kuma ya manna mun yaron a saman ƙirjina. Idanuna na lumshe, inajin ƙirjina na wani irin bugawa na ban mamaki. Kukan yaron yana ratsamun dukkan rassan jikina. Hannuna na saka a bayan yaron, mijinyawa yasa nashi hannun a saman nawa. Yaronnan wallahi kamar almara sai yayi shiru yanata ajjiyar zuchiya. Ashe haka soyayyar uwa da ɗa take, ashe haka uwa take ji game da ɗanta, ashe haka ɗa yake da daɗi? Madallah da ubangijin Halittu. Take yaronnan ya samu kyakkyawan gurbi a cikin zuchiyata, ya kwanta yai lub, take naji tausayinshi mai ƙarfi ya shigeni. Idanuna na buɗe na zubasu a cikin na mijinyawa. Murmushi muka sakarma juna, a kunnena ya raɗamun. "Shikenan hankalin iya rigima ya kwanta. Burina in faranta miki ranki ko da ni nawa zai yi baƙine" A hankali na furta. Raina fansane a gareka. Ina maka so irin wanda uwa take ma ɗan data tsugunna ta haifa. Bana tunanin a duniyarnan zaka iya samun macen da zata soka rabin son da nake ma. Nagode da dukkan kyautatawarka gareni. Madallah da nagartarka" Idanunshi sai suka kawo ruwa, ya ɗago inya kalleni sai ya kalli jaririn dake ƙirjina, ga hawaye fal guraben idanunshi. Shigowar Harira da ma'aikaciyar jinyane yasa ya miƙe ya matsa. Harira taso ɗauke yaron a jikina, amman ina naƙi yadda, dariya kawai tayi mun. Wannan ma'aikaciyar jinya taimun tambayoyin duk daya dace dangane da yadda nake ji. Nifa jikina ma ya warware bana jin komai wallahi kumburi kuma dama a cikinshi nake. Ruwan da ake ƙaramun ma ya ƙare, ta cire mun. "A bata shayi mai madara ta sha ta warware hanjinta, kafin a bata abinci taci, zuwa anjima zata sha magani. Allah ya ƙara sauƙi" Sallama tayi mana ta fita. Mijinyawa ya ɗauki yaron a jikina ya zaunar dani tare da jingina mun bayana a fuskar gadon, fulo ya saka mun na jingina a jiki. Na miƙa hannu akan a dawo mun da ɗana jikina. Dariya duk suka yi. Mijinyawa ya saka mun yaronnan a cinyata na tallafeshi. Harira ta haɗamun shayi mai kauri. Ita ta dafo ruwan zafin, mijinyawa kuma ya siyo kayan shayin madara, sikari, furanto. Na kafa kai na shanye shayinnan. Ta sake kaɗo maganin jininnan ta bani na shanye. "Sannu Hindu, yanzu dai asuba ta riga da tayi, in gari yayi haske sai a siyo miki abinci kici. Kinga tuwon Mijinyawa dana kawo mishi yaƙi ci fur, haka ya kwana yana zurga zurga tsakanin waje da cikin ɗakinnan. Shi bawan Allah ki kawoshi tunda ya samu bacci, kema ki kwanta nan da kamar awa guda wannan maganin zai soma aikinshi, ga tsumman ƙunzugu na tanadar miki" Mijinyawane ya shinfiɗe jaririn a gefena kafin ya tafi masallaci. Ni a kan gadon nayi sallata ina tunanin yadda zan dinga zamewa in yi sallah in muka koma gida, wannan jinin kam nasam bazai hanani sallah ba, tunda gayyatoshi akayi. Amman duk da haka zanyi tambaya, to wama zan tambaya ni Hindu. Nasan dai jinin istihadha jinine na cuta, ko na magani, wanda wannan jinin dana gayyato yana cikin jinin da bazai hanani sallah ba. Tabbas nasan wannan, sai dai in da zan samu malamai inason a ƙaramun sani bisa ga ɗan sanin da nayi. Ina daga kwance nake wannan tunanin, ina kallon matar da muke ɗaki ɗaya tana ba yaranta umma. Ɗayan ya gama sha an miƙo mata ɗayan. Naga sai runtse idanunta take yi, ko dai da zafine ba da umman? "Ki daure, kinsan shan farkon akwai wuya, da zaran sun saba shikenan zaki dena jin zafin, in sun gama sha ga nan man kaɗanya sai ki shafa a saman umman. Sannu Balarabu" Tamkar matar tayi ne dan inji amsar tambayata. Mijinyawane ya shigo da tuwon shinkafa miyar taushe mai zafi, babu mamaki yanzu aka gama wannan tuwon. "Ga tuwo da zafinshi yanzu ta gama. Inaso in kika gama cine, sai in je in sanar a gida halin da kike. Jiya bazan iya tafiya in barki ba tare da kin farfaɗoba. Amman yanzu da zaran na tabbatar kinci abincin sai inje, babu mamaki ma Innah Yahanasu ta iso tun jiyan" Sai kaci malmala guda, sannan sai ka bani inci, amman infa kanaso inci" Murmushi muka yi ma juna dukkanmu. Baiyi musu ba yaci malmala ɗaya, ya dinga bani a baki naci malmala guda, da nama yanka uku, gashi miyar taji gyaɗa ga man shanu. Wannan matar da ta haifi ƴan biyu, sai kallonmu take yi, yadda mijinyawa ya zage yana bani, abinci a baki, yanata hilatata da hira. Jakata ya buɗe ya ciri kuɗin ciki duka, ya mayar ajjihunshi. Yasa hannu ya ɗakko yaron. "Wanne suna kike da sha'awar a sanya mishi Tutar so, zanyi mishi huɗuba? " Azgar nake so ka sanya mishi, na jima ina dakon wannan suna mai Muhimmanci a Tarihin Musulunci Suna ne na ɗaya daga cikin Sahabban Manzon Allah (S.A.W) mai suna Asghar bin Qais Haka kuma, ana yawan tunawa da sunan a tarihin Musulunci saboda jikan Manzon Allah (S.A.W), wato Ali al-Asghar (Ali mafi ƙankanta), wanda yake shi ne ɗan gullan Imam Husain (R.A) mafi ƙanƙanta, duk da akwai saɓanin malamai akan sunan, wasu sunce Abdullahi ne sunan. Shi nake son ka sanya ma ɗanmu" "An gama Giwar mijinyawa, yaro zai amsa wannan suna mai daraja." Huɗuba take yaima yaron da suna Asghar wanda hausawa suke kira da Azgar. Harira ya miƙama, yai mana sallama akan shi sai ya dawo. Yana fita sai jini ya ɓallemun, magani ya soma aikinshi, tsumma Harira ta bani, na shige banɗaki cike da farin ciki nayi ƙunzugu na fito sai murna da zumuɗi nake yi. Ban jima ba bacci mai lauyi lafiyayye mara fargaba a cikinshi ya kwasheni. Jama'are:. Daga ƙofar gida Mijnyawa ya hango su Qasimu. Ganinshi yasa suka zabura suka nufoshi. "Yanzu muke shirin shiga cikin Bauchi asibiti mu duboku, me ake ciki haihuwarce koko dai wani abunne? Ni wallahi nama kasa faɗama Nanno wai kace mun asibiti zaku je, kuma a tunanina ba kwana zaku yi ba. Jiya fa da ƙyar ƙura ta lafa, ga Innar Hindu tazo daga Maraya. Kai in kaga rikicin da sukaita yi ita da Nanno hmm. Yanzu ma basu daɗe da gamawaba Nanno harda kuka" Kafin yace musu wani abun Mijinyawa Babba ya fito. Ganin ɗan uwan nasa yasa ya nufosu. "Yaushe kuka dawo, kuma kai haka akeyi koma ina zaku je ba zaka sanar ba. Ga can Innar Hindu sai ta da husuma suke yi ita da Nanno" "Wallahi asibiti muka je can Bauchi. Kuma lokacin daidai Uwatale tana naƙudannanne Nanno na ciki. Hindunma ta sauka, an samu ɗa namiji shine nace bari inzo in sanar ma mata" "Haihuwa a asibiti kuma a gidannan? Tabb yau na yadda baka gudun magana. Duk da dole aima uziri Hindu ƴar birnice ace dole dole saita haihu a gida tauyewane gaskiya. Yanzu dai kazo mu shiga mu samesu, Qasimu Abdulƙadiri sai kuzo ai a shiga daku" "Kafinnan, ina zuwa zanje in samu Shehulle zan bashi saƙon wasiƙa ya kai gidansu Hindu" "Ai ko kayi sauri, dan naga ya fito da motarshi tun lokacin sallar asuba. Babu mamaki sammako zai daka" Ai da hanzari mijinyawa yaje wajen Shehulle, sai a wajenshi ya samu takadda da biro, ya rubuta wasiƙa ya bashi ya ba Innarmu. Godiya yayi mishi, ya dawo wajensu Qasimu. Suna shiga suka ci karo dasu Nanno a babban tsakar gida. "Yauwa ga ɗan halas ɗinnan ma. Ina Hindun take?" Cewar Yaya Jamila, Nanno dasu Innah Dubu da Innah Yahanasu idanunsu na kan Mijinyawa. "Tana asibiti ta haifi ɗanta namiji jiya da daddare" Innah Yahanasu ta ɗaga hannu tace. "Alhamdulillahi, yaro Allah yayi maka albarka daka ɗauki matarka salin alin ka kaita inda ya cancanta. Allah ya raya" Nanno tace. "Ba shakka ka ɗauketa ka kaita asibiti, ni ina cikin gidannan, ina unguwar zoma wacce a kaf faɗin garinnan duk wacce zata haihu ni nan ake kira, surukan gidan kab ni nake karɓar haihuwarsu. Amman dake Hindu ita gwalce komai nata na musamman ne, shine ka ɗauketa ka kaita ta haihu a asibiti kalan su kashe maka ɗan da da ƴar ta zuchiya ta sameshi ko?" Yaya Jamila tayi saurin caɓewa da cewa. "Lallai a gaisheka Magawata. Hindu na juyaka yadda suke so su da danginta. Dama ga Babarta nan da aka turo ta ɗauketa ta kai asibiti tazo tun jiya. Ashe an riga an kaita ma. To Allah ya raya ɗan da aka samu" Nanno dai fuu ta wuce ciki wiwi da kuka mai jiniya, su Jamila suka mara mata baya. Innah Dubu tace. "Baka kyauta ba. Wannan abun da ka aikata babbane, kuma dole Nanno tayi fishi dakai. Da kai da Hindu bakwa son zaman lafiya. Jibi irin asarar gonarka da kayi a aurenta. Yanzu kuma ai shikenan tunda ta haihu dakai ai sai inda take so zaka zauna. "To dama a inda ke kike so zai zauna? Wai ku kuma haka kuke da zuzuta ƙaramar magana ku ƙerata ta zama babbane? Kai mijinyawa ɗakko mun kayayyakina a ɗakin wannan mata, maza in kulle a ɗakin Hindu sai mu koma ka kaini asibitin inga uwata, da sabon miji" Mijinyawa da Abdulƙadiri ne suka tafi ɗebo kayan. Qasimu kuma ya karɓi ɗan mabuɗi yaje ya buɗe ɓarayin, suka kawo kayan. "Bara in ɗan watsa ruwa sai mu tafi" "To shikenan Innah, nima zan karɓo mata abincin da zamu tafi mata dashi, a ɗan ɗaukar mata zannuwa" Cewar mijinyawa daya fita. A ƙofar ɓarayin nasu ya tadda su Mijinyawa Babba dasu Qasimu. Wai ga Nanno can sai kuka take yi ƙaƙas wai an haifar mata jika a asibiti abun kunya. Ko da Mijinyawa yaje, korarshi tayi tace bata son ganinshi ya fice mata kawai. Jiki ba laka ya fito. "Sai haƙuri dama munsan za'a rina. To dole a dubama Hindu fa. Bari inma Baraka Magana ta haɗo abinci sai mu je asibitin tare ai." Mijinyawa Babba bayan Qasimu ya tafi tawo da abinci yace da ɗan uwan. "Kasan uwatale ma jiyan ta haifi namiji, bana an samu namiji, sunan haɗawa ma za'ayi. Zanso suma asa musu Nawata da Magawata ko me kace?" "Aa akwai sunan dana zaɓa mishi harma nayi mishi huɗuba dashi gaskiya. Sabida ai banma tuno komai ba, kuma bansan Uwatale ta haifi namiji ba" "To ai shikenan babu damuwa Allah ya raya mana. Batun mahaifar yaron fa, ka tawo da'ita nanne za'a burne kusa da namu, kasan na yaran gidannan ma duk a waje ɗaya suke.?" "Ai ni na burne a can, sabida da daddare ta haihu, in nace zan bari saina tawo da'ita, warima zai ishi kowa a mota" Kai yake ta girgizawa, yana jinjina girman rikicin muddin Nanno ta kuma jin wannan magana. "Nima bari in shiga in sauyo kaya sai muje" Tare da Abdulƙari aka barsu. Basu jima ba, saiga Qasimu da Baraka, da kulolin abinci an ƙulle a ɗankwali, sai filas ɗin shayi. Innah Yahanasu ce itama ta fito, da ledar kayan Hindu a hannunta, ta sha lafaya fara sol. Mijinyawa babba bai fito ba. Qasimu ko da yaje kiranshi, sai cewa yayi Uwatale jikinta ya ɗan tashi, suje zai biyo bayansu. Haka suka hau acaɓa zuwa tasha, daga tasha suka hau motar Bauchi. Mrs Bukhari. Sai mun haɗu zuwa gobe, son so💪🏼MRS BUKHARI .......... Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JVdGBW8N6iFFBHyPGYXdrF?s=sw&p=a&ilr=0 *Kin Dade kina neman Adashin gatan da zaki shiga ki rika Tara kudi kadan kadan ki kwashi idan nace Miki kaya hajiya ta ina nufin komai ga Anty zee nazo muku da Tsarin adashi ki rika Tara kudin ki kadan kadan ki kwashi duk abunda kike so, akwai bangaren kayan sawa na Yara Dana manya, akwai kayan kitchen, akwai sarkoki ,takalma , jakuku Nan Yan gayu, mayafai dadai sauran su me kuke jira maza ku shigo ku fara tari tun yanzu* 💃💃 Hindu:. Ina zaune Harira ta sani gaba na sama Azgar umma a baki, yana tsotsa a hankali. Amman dai da dukkan halamu babu ruwa tukunna dai. Karɓarshi tayi ta bashi ruwan zam_zam, ta miƙo mun dabino "Tauna ki saka mishi a bakinshi da yawu yawunki maza" Karɓan dabinon nayi na tauna na tura mishi da harshena a bakinshi ya hau tsotsa. "To shikenan Allah ya raya, ni da zaran dangin mijinki mata sun zo sai in tafi in sha Allah ko? " Hakane Harira, nagode sosai da dukkan taimakonki, dama ƙoƙarinki a gareni, Allah ya bar mana zumuncinmu, ya nuna mana ranar da zan aiko miki goron gayyatar Auren Azgar in sha Allah. Dariya muka yi dukkanmu daidai shigowar Innah Yahanasu da Mijinyawa da abincinshi ɗaure a ɗankwali. "Allahu Akbar Hindu Duwab an zama uwa, Ubangiji Allah ya amince kai madallah. Baiwar Allah sannu, kece kike zaune da'ita?" "Nice Mama sannu da zuwa, ga angon naki nan fari sol dashi tubarkallah" Harira ta miƙama Innah Yahanasu Azgar, ta rungumeshi tana dariya tace. "Barka da shigowa duniya sabon mutum. Masha Allah, gashi ƙato tubarkallah masha Allah. Hindu sannu kinji, amman da kanta ta haihu ko? " Innah Yahanasu ta ƙarashe zancan tana mai kallon Harira, fuskarta yalwace da fara'a. "Eh da kanta ta haihu, ai zuwa yamma ma za'a sallameta da zaran likitanta tazo. Ni kam bari in tafi kuma, sai in nazo suna kuma" Nagode Harira sai kin zo" Harira tayi mana sallama ta fita. "A zubo miki abinci ko? Tare da su Qasimu muke an hanasu shigowane suna waje amma, harda Baraka ita ta dafo abincin ma" Zubomun abincin yayi shinkafa ce, ni kuma bana son ci dama tuwone gaskiya. "Ahh wannan bushasshiyar shinkafar mai jego? Ai bazai mata kyau ba. Ai inaga gara a nemo mata tuwo ko Uwata?" Eh Innah bakina babu daɗi sam, bazan ma iya cin shinkafa ba, dama tuwone" Na ƙarashe ina yamutse fuskata" "To shikenan ai sai a nemo miki tuwon yanzu, bayan tuwon dame kuma kike so Hindu? " "Ka haɗo mata da farfesu in ya samu, in bai samu ba a kawo iyakar tuwon, amman yaji nama asa man shanu yaji, kayi maza" Innah Yahanasu ta faɗa bisa Umarni. Da sauri ya fice a ƙoƙarinshi na son cika wannan umarnin. Yana fita saiga Baraka an barta ta shigo, dama akace kar a wuce mutum biyu. "Sannu Hinduwa, an sauka ashe? Allah ya raya me muka samu? " Innah tana murmushi tace. "Gashi namijine ɗaukeshi mana, ba ƙawarki bace Hindun ƴannan? " Ta miƙa mata Azgar, ni dai sai bin yaron da kallo nake yi, inaji kamar mafarki ma nake yi. Innah Yahanasu inta kalli Baraka sai ta kalleni, kome take kallo ohon mata, amman dai naga tana ta girgiza kanta, harda ajjiyar zuchiya take yi na damuwa. Lokacin sallar azahar ban samu nayi sallah ba, har saida ma'aikatan Jinya suka ce su ba da waje za'ayi goge_goge shine na samu da sauri na ɗauro alwala nayi sallahta a gaggauce. Uwar biyu bacci take yi, ita da gani jiki take ji sosai. Ko ɗazu tana ta kukan ciwon ciki sosai. Har zuwa lokacin ba dangin mijinyawa, babu dalilinsu har ya dawo da tuwonshi lafiyayye tuwon shinkafa da miyar kuka ta ko ji nama da man shanu harda yajin daddawa. "Yauwa maza zauna kici da kyau kinji ko? Kar ki barshi yayi sanyi. Bari in haɗa miki shayi tunda naga da madara." Mijinyawa dai yana zaune da Azgar a hannunshi. Ita Baraka Qasimu ya maidata gida. Abdulƙadiri da Mijinyawa Babbane suke waje. Ƙarfe uku aka bada izinin shiga dubiya sai gasu sun shigo sun ga Azgar. Ni dai ina kwance idanuna a rufe, naci tuwo har wuya, ina baccin dole. Wajajen biyar na Yamma Dakta AA nafaɗa na zuwa ta ce ta sallamemu, amman kafinnan akwai gwaje_gwaje da zata kaini aimun. Innah Yahanasu tace. "To kai rakata bari ni in haɗa kayan kafin ku dawo. Nace ko ta wacce hanya su Ruwayya zasu san anyi haihuwar? " "Na rubuta ma Shehulle takadda tun safe lokacin dana koma, ai yanzu ina mai kyautata zaton labari ya riga ya iskesu in sha Allah" Bata ce uffan ba mu dai muka fita. "Ba gwaji zan miki ba. Maza kije Hajiya Bara na jiranku kuje ku sa hannu sai ku zo ku kama hanya." Ai kuwa cikin minti talatin muka je, muka dawo nan muka tattare kayanmu, mijinyawa yayi shatar mota har ƙofar gida. Yana daga cikin babban abinda ke burgeni inga mace ta tafi haihuwa asibiti. An dawo da'ita har ƙofar gida, ga bebi, ga filas ga riyo maƙota na mata barka da dawowa, tazo ta shiga ɗakinta tsab dashi shima. Sai dai mu motarmu na tsayawa ruwan sama ya ɓalle, dama garin ya riga da ya ɗinke yayi duhu sararin samaniya tayi baƙiƙƙirin sai rugugi take yi. Bismillah damuna ta sauka, rashin ƙyan hanya, da caɓewar gari salamu alaikum. "To wannan ruwan fa dole sai ya ɗan sassauta kafin mu fita, ga jinjiri, gashi kema jikin naki ɗanyene, wannan jego a damuna caɓe_caɓe zamu yi shi ni Yahanasu a wannan jar ƙasa. Allah mai iko wai Hindu ce a cikin wannan rayuwar hmmm. Mamaki yasa na kasa haƙuri har saida na furta wani abu daga cikin zuchiyata, da yake damuna gaya" Ni da mijinyawa tari wannan mun kasa yinshi, A gefena take, Mijinyawa na ɗaya gefen nawa. Mijinyawa Babba, da Abdulƙari suna gaban mota. Babu wanda yace uffan sai mai mota da yace. "Inaga a lulluɓe yaronnan kawai gaskiya ni zan koma. Allah kaɗai yasan yaushe ruwannan zai ɗauke Baba, ayi haƙuri ina da uziri gaskiya" Da faɗa_faɗa yake magana. "To shikenan bari in ɗakko leda babba a cikin gidan in yaso sai a lulluɓe Innah da jaririn, inna kaisu ciki sai inzo in ɗauki Hindun" Cewar mijinyawa da yai saurin ɓalle murfin motar ya fita, mijinyawa babba ma ya bishi a guje zuwa ciki. Bai jima ba ya fito da ƙatuwar leda Innah Yahanasu ta fito da Azgar a hannunta suka shiga ya kaita. Kafin nima yazo ya ɗaukeni. Baraka na barandar da murhuna yake ta girka tukunya ƙatuwa ta wankan jego, tana cikin barandar tana iza wuta, ga murhu ƙarami ta ƙara a gefe girki ma take yi. "Mai jego irin albarka an dawo, ga ruwa ya tsuge kuma. Wannan jego a damuna ƙaƙas zaku yishi." Saida na shiga daga ciki nace. Sannu Baraka ashe kina ta aiki? " "Wallahi kin ganni, ai tunda na baro asibiti inanan, ruwa na ɗaura, da girki. Ɗakinma naso in gyara saina ganshi tsab, turare kawai na kunna" "Shige daga can ciki jikinki ɗanyene, ki hau gado, in an juye ruwan wanka na miki magana. Yaronnan a bashi Umma yasha sai mutsu_mutsu yake. Ruwan umman ya kawo kuwa?" A kunyace nace da'ita. Aa bai kawo ba tukunna' "Bashi a haka ya kama, zai zo ne. Bari in kunce kayan dana zo dashi akwai kifi bai ƙarashe bushewa ba sabuwar gashi ne, kar yazo yayi tsutsa" Fita tayi a guje zuwa ɗakin shirgi. Ni kuma na shiga ciki Azgar na kan gado sai mutsu_mutsu yake ta faman yi. Ina zama Mijinyawa ya shigo da riyo a hannunshi, da abincin Baraka daya kawo da safe. Ina ba Azgar Umma, shi kuma yana zaune ya tanƙwashe ƙafarshi yana cin wannan abinci, idanunshi a kanmu, sai murmusawa yake yi. Yanzu a ina zaka dinga kwana tunda nasan innah kam sai mun yi arba'in kafin ta tafi?, bansan ko zani wankan jego ba. Amman a nawa ra'ayin zuwa wankan jego baya burgeni, baya cikin tsarin rayuwata, da zaɓi za'a bani ko? Zan zaɓi in yi zamana a ɗakinane. "Tutar so. A ɗakin kayan abinci zan dinga kwana. Ai har mun ɗakko katifar yayi ni da Qasimu, ya taya ni mun gyara, kafin dai su Yaya Saratu su ƙaraso. Sabida in Azgar ya farka zan dinga zuwa in taimaka muku. Um bari kiga in gama in fice kar a sani a bakin duniya" Dariya nake mai Baraka tayo sallama da gaushi rigis a kasko ta dure mun ta fice. "To ni kam na fita sai zuwa anjima zan leƙo. In akwai abinda kike so ki faɗama Baraka" Yasa kai ya fice, ni kuma na sauke ajjiyar zuchiya daidai da zuwan umma ina ji Azgar ɗina yana zuƙa, take zuchiyata naji tayi wani irin harbawa da mugun ƙarfi saida na runtse idanuna. Sai naji bana iya gani. Da sauri na soma kiran Innah mutanenne suka motsa, ga jariri a jikina. A guje ta ƙaraso, tunda taji kiran tasan bana lafiya bane. "Subhanallahi Hindu, ke Hindu" Cewar Innah Yahanasu kenan, wuf ta zare yaron daga jikin Hindu. Mijinyawane dai ya daddage ya cire kunya ya leƙo Innah na riƙe da Hindu sai dariya da guɗa take yi. "Kaga zo maza ka taya ni. Farin ciki su ka zo nunawa, yaro na tsaka da shan umma" Nan ya ƙaraso ya zauna, tare da soma karatu yana tufa mata. Kan yaron suka shafa, suka shafa fuskarshi sai murmushi kuma. Shikenan iyakar abinda suka yi sai bacci ya ɗebeta. Mijinyawa ya shinfiɗeta. "Shikenan Innah sun tafi, bacci take yi da zaran ta tashi shikenan" Bata ce mai uffan ba. Shima ɗari _ɗari yake yi da'ita dan babu ko ɗigon wasa a fuskarta. Yana juyawa ta saki tsaki. "Aikin banza da wofi kenan. In banda ƙaddara da rabon wannan yaron me zai kawo ni wannan ƙauyen da sunan wai wajen ɗiyata nazo. Kai wannan ƙaddarar tana da girma. Hindu Allah ya kawo miki silar barin wannan ƙauye" Sum_sum_sum ya fita zuwa ɗakin kayan abincinsu, nan ya shiga zurga_zurga goye da hannayenshi a bayanshi. Dukkan maganganun Innah Yahanasu a kunnenshi tayi su. Yana tsoron ranar da dangin Hindu zasu rabashi da Hindu. Duk da yayi imanin yadda ya tsaya ya kasa barin danginshi su rabasu, itama yasan zata yi abinda yafi nashi dan ganin sun rayu tare. Bashi da wani buri a yanzu daya wuce burin ganin ya ɗauki Hindu da ɗansu zuwa birni. Daga ranar da Mijinyawa ya sa ƙafarshi ya ɗauki iyalanshi zuwa birni. Daga lokacin zai ta da nashi tafiyar ko da sama da ƙasa haɗewa zata yi, dan yasan yaƙin basasa za'ayi da Nanno. Amman in adalci zata yi mai, babu dalilin da zaisa ta bar Mijinyawa babba ya koma birni da iyalinshi, ace shi ta hanasu komawa da nashi iyalin, Yana roƙon Allah ya dafa mishi, kuma ya kawo mishi lamarin a cikin sauƙi in lokacin ya gabata. Yana so ma ya tuntuɓi mijinyawa yaji a ina zancen ginin ya kwana. Yana kuma so yaji, shin zai iya samu waje shi da matarshi, tun wuri gara yaji, in babu waje sai ya tanadi kuɗin haya, domin cika sharaɗin aurensu na mayar da Hindu makaranta. Ya yaya Nanno zata ɗauki wannan lamarin oho. Amman yasan ba abune mai sauƙi ba, yana jin bama abune wanda zai yiwu cikin daɗi ba. Ajjiyar zuchiya ya sauke kawai. Muryar Yaya Jamila yaji tana rakaɗa mishi kira. Da sauri ya fito, Baraka na tuƙa tuwo, Innah Yahanasu na zuba ruwan wankan jariri a bawo. "Kai nace gyatumarka da sauran matan Babanka, da duk jama'ar gidannan basu san mun dawo daga asibiti bane? Naga babu wanda yaje asibitine, mun dawo ma babu me zuwane, koko basa farin ciki da zuwan wannan bawan Allahn ne, ko kuma al'adarkuce ta shar'anta hakan inason ji tun wuri kafin danginka da kai kanka ku ƙarashe kaini bango" A mugun ɗaure take magana, bama ka isa ka kawo ma Innah Yahanasu wani wargi bane, ba wajen bane. Gata da kwarjini. "Basu sani ba. Yanzune dai zan je in sanar musu da dawowar tamu, sabida mun shigo ana ruwane sosai. Zasu shigo Innah kiyi haƙuri" Ci gaba da ɗiban ruwan zafinta tayi, Shi kuma ya fita gabanshi na dokawa. Ruwafa akeyi kashirɓan saima abinda ya ƙaru, koshi mijinyawan a jiƙe yake sharkab. Haka ya shiga ɗakin Nanno, ya tadda Yaya Jamila, Yaya Salihu, da mijinyawa Babba. "Yayi hamshaƙi tabbatacce. Inaso a gaban yayunka ka faɗamun menene dalilin da yasa ka ɗauki Hindu ka kaita ta haihu a asibiti. Ina unguwar zoman da duk wata haihuwa kusan ni na karɓeta sai Deluwa da itama ta kasance daɗaɗɗiyar unguwar zoma. Shin in ni bakwa so in karɓi haihuwar me yasa baka kira mata Deluwa ba. Wato kai komai saika nuna ita wannan matar taka tafi uban kowa kenan. Duk surukan gidannan babu wacce ranta bai sosu ba akan abinda ka aikata. Dama ai ita waccan maras kunyar ƙanwar gyatumar tata tace ko naƙi ko naso sai ta ɗauketa ta kaita asibiti. Ashe haka suka maka huɗuba shi yasa ko? Sannan ina mabiyar yaron take, ai ya kamata a birne a wajen da taku take, kusa da yaran ɗan uwanka, da kuka haifa rana ɗaya ko?" Nanno ke magana da faɗa, ɗaga murya, da fishi duk a lokaci guda. Ɗakin yayi shiru. Mijinyawa dai baima san me zaice ba. Da Nanno ta cika, sai Yaya jamila ta caɓe itama, tana gamawa Yaya Salihu ya ɗaura, shine harda zagin Hindu da cewa gajeriya da'ita, mahaukaciya mai makarai da'ita. "Babu mamaki ma makaran nata ne suka aureshi suke juyashi yadda suke so. Wai haukane auren mace a burni. Ko kuma a kanka aka soma ne. Naga ga yaran birninnan an aurosu sun saki rayuwarsu ta birni, sun rungumi yadda Allah yayi dasu. Ita matarka wacce irice da ba zata bari kayi komai irin yadda akeyi ba?" Shi dai baice uffan ba. Bai kuma shirya cewa ba, to me zaice musu. "Ni dai a madadinshi nace kuyi haƙuri ba dan naji daɗin abinda yayi ba, ba kuma dan ina goyon bayanshi bane. Zai kiyaye gaba. Amman in kuka duba itafa Hindu daga babban gida ta fito ko da a birninne. Mahaifinta da yayyunta duk sojojine. Hatta mahaifiyarta malamace ta makarantar sakandare, kamar dai ita Hindun. Ita wannan ƙanwar gyatumar tata fa ance babban hamshaƙi take aure a maiduguri. Kuyi haƙuri tunda Allah ya sauketa lafiya sai a gode. Batun mahaifa, ya riga yayi kasadar birnewa a asibiti, wai sabida kar ta kwana tayi wari. Ni shine ma babban abinda yafi damuna". Ai Nanno sai ta tarwatse da kuka, har tana bubbuga ƙafafunta. Yanda du suke jaddada batun mahaifarnan, zaku ɗauka Azgar ɗinne akace an birne da ranshi. Wato ƙauye suma suna da nasu al'adun masu wahalarwa, yanzu menene laifi dan an burne mahaifa a asibiti, da har zai zama babbar matsala irin wannan. "Shikenan yaro ya zama ba jikin gidan ba. Dama ita Hindu burinta shine ta rabaka da danginka. Bazan taɓa yafema wannan yarinyar ba, akan saka da tayi ka burne mahaifar jikina a asibiti ba, abadan bazan yafe ba" Nanno ta ƙarashe da ƙyar kuka yaci ƙarfinta. Innah Dubu ce ta leƙo jin kukan Nannon yayi yawa. Jamila ta labarta mata halin da ake ciki. "Tabb amman wannan yaro ya faɗa hannun ƴan asiri. Yaya ai wannan asirceshi akayi. Ina mai tabbatar miki ya kamata a mai hayaƙi da rubutun da zai dinga sha. Ina wannan ba lafiya ba. Ya burne mahaifa a asibiti fa. Kai nace zaka gane wajen daka burne, aje a tono a dawo da'ita muhallinta? Wannan da kake ji da gani umarnin mahaifinku ne fa. Mu so kake mu tsallake umarnin malam kenan?" "Kiyi Haƙuri Innah. Bazan iya ganewa ba, da daddare na burne, kuma asibiti ba zasu yadda a musu tono a ciro wani abu da aka burne ba" Ai ina wuta Nanno, da Jamila su saka mijinyawa. Kallonsu kawai yake yi, yana sake ƙarfafa zargin anya shi kuwa ɗan wannan gidanne, Nanno ce da gaske ta haifeshi. Ko dai kamace kawai yayi da Mijinyawa Babba? To ina asalin mahaifanshi suke? Tunowa da mahaifinsu, da irin ƙaunar da yake nuna musu, shi ke kore mai zargin ba Nanno ta haifeshi ba. Idanunshi sun kaɗa sun yi jawur. Mijinyawa Babba ne yake ta ban haƙuri, da bayani. Yaya Jamila ce ta katse mijinyawa Babba da cewa. "Gafara dallah shashasha Hindu ta maida mutane banzaye, amman kana sake jaddada mana cewar ta fito babban gida. Ku ba daga babban gida kuka fito ba kenan. Kasan waye mahaifinmu a ƙauyennan kuwa, kana da tarihin mahaifin Nanno kakanku kuwa, har an isa a nuna mana asali, mu da sarauta ce kakanninmu. Mahaifin mahaifin Nanno mai garine kakanta. Mahaifinta mai garine, kakanmu, Babban wanta mai garine, ita kanta da Namijice da zata yi sarautar" Kuka Nanno ta saka ta nuna Mijinyawa tace. "Ka tashi ka fice mun daga ɗaki, kaje ni na barma Hindu, da danginta kai. Kuje ku ƙarata taci gaba da juyaka. Yaro kuma Allah ya rayashi, amman bazan ma iya zuwa barka ba" Baki ya buɗe da zummar bata haƙuri, ta ɗaga hannunta ta kwaɗa mishi mari, tare da nuna mishi ƙofa. Babu shiri ya fita jikinshi duk a sanyaye. A cikin ruwan ya fita har waje, kai tsaye gidansu Baraka ya wuce, Qasimu yana bakin ƙofa yana juye ruwan sama a babban duro ya hangi Mijinyawa ya shigo zauren. "Lafiya kake tafe haka a jiƙe. Batun asibitinne ko? Ai nasan wallahi ba zaka samu sauƙi a ko inaba. Babanmu ma baka ji yadda take ta mun faɗa ba, yadda kasan nine na ɗauki Hindu na kaita asibitinnan. Cewa tayi zaka zo ka sameta ne." A zauren ya ɗakko mishi kujera ya zauna, shima ya zauna daga dokin ƙofar Baraka sukai shiru, sai ƙaran saukar ruwa kawai ke tashi a garin baki ɗaya. Idanu Mijinyawa ya lumshe kawai, zuchiyarshi na mishi suya, tuno farin cikin dake shinfiɗe a fuskar Hindu, da kuma tuno fuskar Azgar, ya tilasta mishi yin murmushin da bai shirya zuwanshi ba. Qasimu dai yana ta kallon shekara. Ajjiyar zuchiya ya sauke, sai yaji duk damuwar ma ta kau, fuskar Hindu kaɗai ta wadatar da zuchiyarshi. "Babu komai Qasimu, duk suyi haƙuri aikin gama ya gama." "Ni inaga ka bar musu gidan kawai, ga ɗakinmu na samartaka kazo ka buɗe ka shiga babu kowa a ciki" "Aa dole ana buƙatata, kasan jinjiraye da kukan dare, dole in dinga taimaka musu" Idanu Qasimu ya zare yace. "Wallahi ka kula, littattafan hausa da kake karantawa zasu kaika su baro, a ƙauyennan ba zasu ɗauki wannan ba" Murmushi mijinyawa yayi yace. "Ai addininmu ma ya riga ya koya mana yadda zamu rayu da iyalanmu. In muka duba gidan ma'aiki arrasul SAW ai kaga zance ya ƙare. Duk wani soyayya da tattalin iyali a nan ya ƙare. Kaga ba a littattafan hausa na soma karantawa ba, dan dai kai baka tsaya ka mayar da hankali a karatun bane. Kuma zan taimaki Hindu iyakar ƙarfina, wanda yake da abun faɗe Qasimu ya faɗa. Da kasan kalar cin kashin da yanzu aka gama mun, bama zaka ce komai ba. Ni mu bar wannan zancan Qasimu. Yau yanda ake Ruwannan Balele zai yi gashin balangu da tsire kuwa?" "Mai zai hana. Ai kasan a yanayi irin haka na damuna anfi cinikin nama da zafi zafinshi. Rumfarshi tana da kyau ko yanzu kaje zaka tadda yana gashinshi gaskiya, dan ɗazu ma na wuce ta rumfar yana ta aikin nama. Zaka siya ma maijegone kafin gobe a siyo naman ƙauri ba?" Nan sukaita hirarsu dai magriba na kawo kai cikin ƙudurar Ubangiji sai ruwannan ya sassauta sai yayyafi, amman sabon hadarine ganga_ganga sosai a garin yau da alamu za'a sha ruwan dare. Hindu:. Bani na farka ba sai bayan magriba, ko dana farka Innah bata ɗakin ina dai jiyo ɓuruntunta a tsakar gida, ga Azgar har an mai wanka an sake mashi seti sabo fil wanda ina kyautata zaton Innah ce tazo mana dashi, yayi kyau sai baccinshi yake yi. Ga tocila mai manyan batura taiga wannan tocilar ta ƙarfe nasan wacce ta haure shekaru talatin da biyar zuwa arba'in ta san wannan tocila, ko a hannun mahaifinta, ko a hannun dattijan anguwa. Ɗakin yayi ɗumi ga iska bababa ana ta yi a waje. A tsanake na tashi na shiga banɗaki na gyare jikina na ɗauro alwala. Fitowa nayi na duba Innah bata falo, tana waje wajen Murhu kamar kifine take sake gasawa. Sallar magriba nayi, dana duba agogo isha tayi saina yi, ina sallamewa Innah ta shigo da sallamarta falo. A guje na cire mayafin nayi wurgi dashi gado. "Kin tashi Hindu, ya jikin?" Da sauƙi Innah ya gajiyar hanya? " Kallona take yi cike da kulawa tace. "Gajiya ta bi lafiya Hindu. Bari in zuba miki abincin ki samu kici, na dama miki kunun geroma ɗazu kafin Baraka take ko ta tafi. Gaskiya tana da ƙoƙari hatta kayan jinin da muka tawo dashi a asibiti taso ta wanke sai nace ta bari, shi irin wannan kayan jinin haihuwa na jikine sosai yake yi, sai dai in na jikin basa kusa suna nesa ne." Kwanon da tuwon yake ciki ta jawo ta zuba mun. "Innah ya'isa haka bakina babu daɗi" "Ikon Allah irin jegon Ya Ruwayya zaki yi kenan, cikinta cunkushewa yake yi bata iya cin abinci. Kyanta ma ai kici gashasshen nama mai ruwa ruwa. Dan naga da yamma muka dawone ga ruwa. Shi yasa bance mijinki ya siyo ba, gobe dai ya siyo." Miya ta zuba mun da bushasshen kifi guda guda, ta jawo wani kwanon muttala dogo mai kamar bokiti yana ma da hannu, ta ɗaura a wuta cike yake fam da soyayye nama a cikin kakide. Daya soma narkewa ta ɗebo namannan ta zuba mun, ta sake ɗaura irin kwanon, shi kuma cike fam da soyayyar miyar tumaturi da nama yake shaƙe, ta sake ɗebo naman miyarnan ta saka mun, ta miƙo mun tuwon. "Maza kici, sai ki sha kunu, wanka kuma ko a bayinki na ɗaki ki ɗan gargasa jikin Allah bashi gobe mayi na ganye a bayan gidan tsakar gidanki ko? " Saida na ɗauki nama na tura a bakina kana nace. To Innah" Miƙewa tayi ta shinfiɗa dadduma, ta ta da kabbarar sallah. Ni dai ina cin tuwonnan ina kallon fuskar Azgar sai nake ji tamkar bani da wata damuwa a nan gidan duniya. Ga mijina ga ɗanmu, to me kuma zai damemu? . Nan da nan na cinye tuwon tunda bashi da yawa kifi ne da nama ya cika kwanon, ina ɗan kurɓan kunun Azgar ya farka da kuka, Innah nake kallo, ita kuma carbi take ja. "Ki ɗaukeshi ki bashi yanzu kam ya sha ya ƙoshi sosai, ɗazu ma da kukan ya tashi kina bacci." Kunun na ajjiye na ɗaukeshi na bashi Umma yana ta tsotso, Innah tana ta kallona, can dai tace. "Yanzu Hindu ke naga ko a jikinki irin wannan rayuwar ƙauyanci da kike ciki. Dan Allah jibi ƙauyannan, da gidan, da mutanen gidan, da suke kewaye dake. Ke amman kinsan kin koma ƴar ƙauye futuk irinsu amman?" Shiru nayi tare da sauke kaina. "Ba magana nake miki bane dan abu ta kazan.. Kinga yadda kika koma baƙauya futuk kuwa, kinga takalmin da kika je asibiti dashi, da wani irin riyo zubin ƴan ƙauye da kuka je dashi, ke irin rayuwar da kika zaɓa kenan su Ya Ruwayya suna kallo sun zuba miki idanu ko? Shima yanzu wannan yaron a irin rayuwar da zai taso kenan haka kika zaɓa mishi ko? Batun karatuma an yi magana yace har sai ɗan uwanshi ya gama gini. Amman a yadda naga uwarshi a tsaye ya maman maza, ba zata taɓa barinku ku koma birni har ta barki ki koma makaranta ba. In Janaral ya yadda da zaman ƙauye, kinsan bazai yadda da rashin komawa karatu ba. A cikin ƴan uwanki kin fita zakka, kece kaɗai kab gidanku ma kike rayuwa a ƙauye, yadda kika san asiri akayi miki. Ai shikenan tunda haka kika zaɓa. Shi ɗan uwanshi ba gashi har yayi tunanin ya koma kano da nashi iyalin ba, ya sai fili yana ginawa ba. Yanzu inma an barku kuje birnin tare dasu, a gidansu za'a raɓaku kenan. Ko shima ya sai nashi filinne zai gina yana fama da kwalli sai kace boka?" Aa bai siya ba tukunna dai, amman in muka koma shima zai siya Innah. Kiyi haƙuri yayi alƙawarin zai sani makaranta kamar yadda akayi mishi sharaɗi. Kuma Innah bai ragamun da komai ba, yana bani dukkan kulawa, bai barni babu ci ba, bai barni babu sha ba, bai barni da rashin sutura ba. In banda lafiya yana tsayamun, bai gajiya da makaraina ba. Yana bani dukkan lokacin shi" Wata uwar harara da tsaki ta ja duk a lokaci guda. Murmushi nayi mata kawai, wani ƙududu ya tokaremun wuyana. "A cikin gidannan babu wacce ta shigo barka ciki harda surukarki. Nayi tunanin ko ruwane ya hanata fitowa jikin tsufa. Sai dai kash ina kan shanyar zannuwan jinin biki sai gata a guje ta shige ɓarayin ɗayar mai jegon, mata a hakan suke ta shiga mata barka. Amman na zuba idanu mu gani zuwa gobe da safe zata shigo ko ba zata shigo ba. Wallahi babu abinda zai hana in farfaɗa mata magana ni da ita babu wanda zai iya rabamu. Duk yadda kakanni suke son jikoki, amman ace babu wanda ya biyomu asibiti, mun dawo ma babu wanda yazo, babu wanda ya kawo abinci ko dai ya nuna kulawa hmmmm" Ni dai na kasa cewa komai. Sai dai naji wani irin ciwo dangane da abinda su Nanno suka yi. Shin wai ƙiyayyar da suke mun ashe har yarana ma ba tsira zasu yi ba kenan. To shikenan, bama zasu rayu a kusa da su ba, balle suma su ga ƙiyayya da mugunta. A zuchiyata nake wannan batun. Saida Azgar ya ƙoshi yayi bacci, na zare Umman a hankali zan kwantar dashi Innah tace. "A kafaɗa zaki sakashi, ki dinga shafar bayanshi har sai yayi gyatsa umman ya faɗa mishi kenan sai ki kwantar dashi. In kuma goyon ƴan ƙauyen zaki yi sai ki kwantar dashi, ya dinga kwaro miki tumbuɗi duk ku jagwale" Kai Innah" Na faɗa a hankali. Ina kan shafar bayanshi Mijinyawa ya shigo da sallamarshi. Ya tsugunna har ƙasa ya gaishe da Innah, tare da tambayarta hanya" "Bamu samu gaisawa da kyau mun tambayeki ya gajiyar hanya ba Innah." "Gajiya tabi lafiya. Gobe naman ƙaurin ka kawo da wuri. Sannan inason ƙafar saniya da jelar sa zan mata farfesu ta sha, mu kasan a al'adarmu haka muke ma mai jego." Ga manyan dalilan da yasa kanuri suka riƙe sirrin girka ma mai jego ƙafar saniya da jelar saniya, musamman a satin jegonta na farko. Wannan daɗaɗɗiyar al'adace ta matan kanuri, wanda har yanzu da yawa basu yi watsi da'itaba. Kasancewar an san kanurai d riƙo, da girmama al'adunsu, wannan dalilin yasa sukai fice. Sinadarin Collagen, da Sinadaran Gyaran Jiki. Kafar saniya da jelar sa suna ɗauke da sinadarin collagen da kitse mai gina jiki. Bayan haihuwa, gabobin mace da jijiyoyinta suna bukatar abubuwan da zasu dawo dasu yadda suke, sannan kafar saniya tana taimakawa wajen rage radadin ciwon gwiwoyi, da ƙashin baya, da mace ke ji saboda nauyin ciki.Kayan Yaji na Musamman da ake amfani dasu. Ba a dafa ƙafar saniyar haka kawai, ana zuba mata kayan yaji masu zafi sosai kamar citta, masoro, kanumfari, da kimba, gyaɗar miya, tafarnuwa, habbahan, habbatussauda kaɗan, hulba kaɗan ƴaƴan. Wannan farfesu mai zafi yana taimakawa wajen gasa cikin maijego daga ciki, sannan yana sanya mata dumi domin fitar da dukkan gudan jinin dake cikinta, wanda ya rage a mahaifa. Karin Jini da Kuzari. Jelar saniya tana da nama mai dadi da taushi wanda ke cike da sinadarin iron (mai karin jini) Mace tana zubar da jini lokacin haihuwa, shan wannan romon yana dawo mata da kuzarinta a cikin sauƙi. Karuwar Madarar umma. Shan romo mai zafi na kafar saniya, da jelar sa, yana bude hanyoyin umma, kuma yana karawa uwa yawan madara domin ta shayar da jaririnta cikin sauki. Wannan wata hikimace daga tsofaffi masani sirrin gyaran jikin mai jego. Mijinyawa ya nisa kana yace. "To to gobe za'a kawo in sha Allah. Ga wannan kaza ce, da balango nasa akai mata gashi na musamman ta samu taci kafin gobe. Sai da safenku" Haka ya fita yana satar kallona. Ni kaina hankalina yana kanshi. Ni naman ma kaɗan naci, Innah ta zuba mun yajin daddawa ta sake zubo mun kunun gero dai, haka na samu dai nasha na kwanta. A wannan daren, wani irin nutsattsen bacci nayi lafiyayye wanda rabona da yin irinshi dai na mance. Sai da Asuba naji Ɓuruntun Innah tana hura itace, asubace, ina jiyo mijinyawa na jidan ruwa. Jikina na kuma gyarawa na ɗauro alwala nayi sallah. Miƙewar da zanyi mai zai faru, ai sai jini ya ɓallemun, na soma ganin juwa ɗakin na jujjuyawa dani. Jinine mai yawan gaske yake zuba kamar an buɗe fanfo, ga jiri na neman kayar dani, ina faɗuwa Azgar zan danne, in buɗe baki in yi magana na kasa. Mrs BUKHARI Mu kwana anan sai gobe in Allah ya kaimu💪🏼💪🏼💪🏼 *Ina mai farin cikin sanar daku basarakiyar dilkharmu ta matan sudan ta kammala* *Zan turo muku hotonta ku ganta, da nera dubu bakwai ɗinki zaki mallaki wannan basarakiyar Dilkha Hajiya, a haɗe take ruwan ɗumu da ƙwai kawai zaki saka mata ki kwaɓa ki shafe jikinki dashi, zaki dawo ki bani labari. Ga wani sirrin ƙamshi mai riƙe fata a tattare da wannan dilkha Hajiya* *siyan nagari maida kuɗi*💪🏼💪🏼MRS BUKHARI ........... Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JVdGBW8N6iFFBHyPGYXdrF?s=sw&p=a&ilr=0 *Kin Dade kina neman Adashin gatan da zaki shiga ki rika Tara kudi kadan kadan ki kwashi idan nace Miki kaya hajiya ta ina nufin komai ga Anty zee nazo muku da Tsarin adashi ki rika Tara kudin ki kadan kadan ki kwashi duk abunda kike so, akwai bangaren kayan sawa na Yara Dana manya, akwai kayan kitchen, akwai sarkoki ,takalma , jakuku Nan Yan gayu, mayafai dadai sauran su me kuke jira maza ku shigo ku fara tari tun yanzu* 💃💃 Jininnan zuba yake yi sosai, gabaki ɗaya sai naji na rasa dukkan kuzarina. In kira Innah ma na kasa, jirine yake neman kaini ƙasa Kukan Azgar ne ya shigo da mijinyawa da sauri. Ganin jini a ƙasan kafet yana zuba kamar bawali daga jikin asalin ƙunzugun dake jikina. Faɗuwa nazo yi akan kuma Azgar dake kwance yana kuka, daidai shigowar Innah Mijinyawa yai saurin tareni muka faɗi ƙasa. Innah tayi ihu ganin na kusa faɗawa kan bawan Allah, har idanu saida ta runtse tasa hannunta bisa kanta. "Subhanallahi ai jinine ya ɓalle mata. Hindu sannu, kai yi maza nemo maganin tsayar da jini na gaggawa tasha kafin mu kaita asibiti. Subhanallahi sannu Hindu" A guje mijinyawa ya fita, ni dai da ƙyar nake nishi sabida yadda jini ke bulbula a jikina. Inaso ma ince akwai maganin tsaida jini, ina dashi amman harshena yayi mun wani irin nauyi. Dama Harira tace akwai yiyuwar ɓallewar jini tabbas. Ai kuwa bai jima ba sai gashi da ruwan ganyen gwanda da tsamiya, da manda wanda aka dafama Uwatale Shafa ta kamfato mishi. "Kafa kai kisha maza." Cewar Mijinyawa wanda ya saka mun kofin a bakina, Innah tana riƙe da Azgar sai kuka yake yi. Runtse idanuna nayi na shanye duka. Banfi minti biyar ba, Allah cikin ikonshi jinin sai ya daidaita. Amman ko iya tashi zaune bazan yi ba. "Jeka tunda jinin ya tsaya zan gyara wajen" "Innah kije daga falo zan taimaka mata, kiji da jaririn" Ni dai da ƙyar nake numfashi sai naji mijinyawa yayi sama dani zuwa bayi, ya ajjiyeni a kan kujerar wankana da nake zama. Kuma fa wallahi nauyine dani sosai. Ƙarfin haline, da kuma sabon ɗaganin a duk lokacin da makaraina suka rabkeni. Ai Anty Badiat ta rarrage muku abubbuwa da yawa, na dangane da ciwon makaraina. Tace kanta sara mata yake yi in tana rubuta waje. Shi ya ciremun kayan jikina, ya fita ya ɗebo ruwan zafi sirkakke cikin bokiti yaita kwaramun yana wankeni. Tsumma da ɗan diras ya kawomun nayi sabon ƙunzugu ya dawo dani gado. Jina nake yi sakayau, sai jiri. Ya saka tsumma ya dinga aikin jininnan, wallahi babu ƙyama sam a fuskarshi, da kuma yadda yake dama hannunshi a jininnan. Yasa sabulu da soso ya dirje wajen tas. Kana ya ɗauki bokitin ya fitarma da Innah dashi. Azgar tazo ta shinfiɗe tanai mun sannu, gaushi ta fita ta ɗakko a kasko, ta ajjiye ta kuma fita sai gata da bawo na wankan jariri da ruwan zafi. Sabulun salonta ta ɗakko dashi tazo cikin roba na jariri daban, nawa ma daban anyi mishi haɗe haɗenmu sirrinmu sosai a ciki. Lita biyar haka ta kawo mun a farin bokiti mai murfi. Sai ƙamshi yake zubawa. Ta cicciro manya manyan kwalaben turarukan wuta wasu lita biyar, wani lita uku, humrorin lita uku uku gasunan kusan kala bakwai. Wannan kayan ƙamshin jegone, shima daɗaɗɗiyar al'adace har a garar abincin da ake kawowa daga gidansu maijego, tare da suturu ana saka turarukan wuta bokiti bokiti manya manya sosai. Haka humrorinma ake sakasu. Innah ta harhaɗa itacen turare ta watsa a wuta, tare da farcen turare, turare mai dogon tarihi, turare mai sirri wanda ya kamata ace ko wacce mace ta mallakeshi. ( kizo in baki Farce Hajiya sunanan hawa uku nake dashi masu kyau da inganci, mai daɗaɗɗen tarihi) Take ƙarnin jininnan ya gushe, ƙamshi ya maye gurbinshi. Baraka ce ta shigo da sallamarta. "Innah dama wankan nazo yi mai, kya ji da maijego ke kam" "Allah sarki ƴannan, ai ko nagode sosai. Kinga yanzunnan jini ya ɓallema Hindunma. Inaga sai mun koma asibiti zuwa anjima, amman tasha magani jinin ya daidaita" "Ashsha sannu Hinduwa, ai Innah ba sai anje asibiti ba. Bari in ɗakko mata wani jiƙo na ƙarin jinine sadidan. Sai taci abinci ta ƙoshi zata sha, jinin data zubar zai dawo. Ai ko jiya an dafama Uwatale irinshi, domin itama ta samu wannan ɓallewar jinin harma ake tunanin kamar ba zata kai ba. Amman ko yanzu na ganta a ƙafafunta zata shiga wanka. Bari in ɗakko mata. Haka sittin ma in mace ta haihu ko jini bai ɓalle mata ba, ana bata tasha. Nanno ce ya kamata ace ta aiko mata" "To shikenan. Ai sannunki da ƙoƙari Baraka. Wannan yarinya ba dai kirki ba. Ita Nannon da kika ce, jira nake in gama ma Hindu wanka, zanje ɓarayin nata inji mutum nawa Hindu ta kashe mata da ta kasa zuwa ganin jikinta. Na fahimci bata da mutumci, inda mutumci yake ma ba saninshi tayi ba sam." Baraka dai ta rasa ta cewa. Fita tayi, ita kuma Innah saita fita kwashe ruwan wankana, ni dai gabana sai faɗuwa yake yi. Baraka na dawowa na yafa zane muka shiga wanka. "Bansa miki ruwan da zafi ba, sabida jinin da kika zubar yanzu, in ruwan yayi zafi zai iya ɓalle miki sabon jini. In jikinki yayi sauƙi kika samu kuzari ma dinga yi dana zafin, tsumma zansa in gargasa miki jikin" Ai ko tsummane take tsomawa inta ciro sai a gadon bayana, ko ƙasan marata. Amman dake ba tafashasshe bane, kuma jikin babu inda baya mun ciwo, babu inda baiyi tsami, da kumburi ba, sai naji wannan gashi na mugun mun daɗi, yana shigata sosai. Ta jima tana yi mun. "To ga sabulu kiyi wankan soso, zan kawo miki ruwan da zaki shiga ki zauna na magani yanzu." Fita tayi ta bani waje, na saɓi haɗin sabulun salonnan na sille jikina tas dashi, har wani santsi fatata take yi. SIRRIN GYARAN FATA. HAƊIN SABULUN SALO NA MUSAMMAN DOMIN HASKASUWA DA SULBƊIN JIKIN MAI JEGO. Wannan haɗin sabulun salo na musamman ne ga macen da ke son fatarta ta yi sumul, ta yi sheƙi, kuma ta yi sulɓi ba tare da ta yi bilicin ba. Yana da matukar kyau wurin kwashe tsofaffin ƙofofin fata da dawo da ainihin kyawun kalar chocolate ko wankan tarwada. ( BANDA FARAREN MATA DAN ALLAH) Abubuwan da Za a Buƙata, Sabulun Salo, A daka shi a turmi, a samu zuma mai kyau, Rabin kofi. Don ba da damshi da laushin fata) Manori / Man Kaɗanya (Shea Butter) Cokali 3 na girki (Don maganin bushewar fata da kariya). Man Kwakwa, Cokali 2 (Don ƙarin kumfa da sulɓi) Girislin, na Ruwa: Cokali 2. Kurkum na gari Cokali 1 (Wurin goge tabo da fito da hasken fata). Garin Jan Itace (Camwood/Majigi) cokali 2 Sandalwood.Cokali huɗu (Sirrin sulɓi da sili-sili na jikin mace, da sirrin riƙe ƙamshi). Dilkha haɗaɗɗiya ta mutan kanuri, dunƙule huɗu, ko uku. Domin sake murje fata, da dauwamammen ƙamshi. Sai madarar turare mai daɗin ƙamshi gaya. Matakan Haɗawa Daki-Daki Mataki na Farko, Fasa sabulun salon na Gana kashi-kashi, sannan a zuba shi a cikin babban turmi ko kwanon roba mai faɗi.Mataki na Biyu. A narke Shea Butter da Man Kwakwa a kan wuta mai ɗumi (kar a bar su su ƙone), sannan a juye ruwan man a kan sabulun salon da aka daka. Mataki na Uku. A zuba Zuma da Glycerin a kai. A zuba dilkha. Waɗannan sinadaran su ne za su tabbatar sabulun bai busar da fatar mace ba.Mataki na Faɗu. A zuba garin Kurkum da kuma Camwood (Majigi) da Sandalwood a saman haɗin.Mataki na Biyar, A zuba turaren mai irin ƙamshin da yayi miki, amman ba mai yawa ba, wannan basarakiyar Dilkha itace gamawan da zata riƙe miki ƙamshi a jikinki, sabida anyi mata dukkan haɗin gargajiya ( kizo in baki Basarakiyar Dilkha ɗin mrs Bukhari ta haɗa miki a kan farashi mai rahusa) Mataki na shida A daka su duka a cikin turmi ko a juya su da muciya sosai. A tabbatar komai ya gauraye har sabulun ya zama da laushi sumul (kamar dambu ko ɗanƙo) Mataki na Ƙarshe. A kwashe sabulun a zuba shi a cikin mazubi mai kyau da ke da murfi A bar shi ya zauna na tsawon wata guda, kafin a fara amfani da shi, domin sinadaran su haɗe da kyau. Hanyar Amfani da wannan sabulu. Lokacin wanka, a jika jiki da ruwa, sannan a shafa sabulun ta amfani da soso mai laushi. A goge jiki duka a hankali, musamman wuraren da suka fi fuskantar dukan rana kamar hannaye da ƙafafu. Bayan an gama murzawa, a wanke da ruwa nan da nan (kar a bar shi ya daɗe a jiki). Bayan an fito wanka, a shafa kulaccam mai danƙo bata loshon ba. mai kyau don kiyaye sulɓin fatar Da adana ƙamshi. Matan Kanuri suna yin wannan sirrinne domin goge datti da kanɓori_kamɓorin baƙi da mai ciki take fuskanta a yayin juna biyu, da irin duhun da bayanta da wuyanta yake yi. Kafin ranar suna sai mai jego ta fito tana wani irin haskawa da sheƙi ruwan zafin da Innah ta ajjiyemun ban shiga a haka ba zubar da rabi nayi, na zuba wannan na babban bawo wanda taimun wanka dashi dake ya huce, nayi zamana. Ya ko sha magani, harda itacen dorot a ciki😉 Sai naji daɗin jikina sosai da sosai. Ina fitowa tun kafinma in shiga ɗaki aka ɓalle da ruwan sama, dama garin yayi kamar irin jefin asubannan yayi duhu. Baraka na gaban gaushi tana gashin cibi da cokali, ni dai ji nake tamkar a jikina ake ɗana cokalin, tsigar jikina har tashi take yi. Sababbin kaya na atampa mai kyau ɗinkin zamani na gani akan gado innah ta ajjiyemun. Ina ɗaga rigar na tabbatar ni ta ajjiyema. Ohh gata mai daɗi. Kulaccam mai danƙo ta wajen Mrs Bukhari na mulke jikina dashi. Saka rigar nayi, na ɗaura zanin rigar, na yi ɗaurin ɗankwali, na saka kwalli, da ɗan mai mai gurguwa dana shafa a leɓena Humra na shafa a jikina, da kayana. Saina haye gado. Innah ta shigo da sallama hannunta da kwano, da kofin silba. Ta miƙo mun. Tare da jawo babbar kwalbar turaren gabgab ta zuba a gaushi, take ɗakin ya kaure da ƙamshin al'adarmu. Ta ɗebi gaushi guda ɗaya ɗan ƙarami ta zuba wani haɗin turaren tsugunno mai gyara dausayi ta saka kaskon a ƙasan kujerar da aka fafe samanta. "Zo ki zauna maza akai na minti biyar ma ya isheki. (Kema kina da buƙatar turaren Dausayi Hajiya. Mrs Bukhari tana dashi gangariyan asalin na matan kanurin. Wannan haɗin na kwana bakwai ake buƙatar mai jego, uwargida ta zauna akai. Banda Amare na macen data taɓa haihuwane. Kizo in baki zaki ba da labari). Minti biyar nayi, na sauka na koma gado. Kwanon dai farfesun bushasshen kifine manyan nannaɗe uku, sun kwanta a kwanononnan ga wani ƙamshin kayan ƙamshi, kofin kuma kunun gyerone na marɗon yaji nonon da dama dashi ta tawo. Ina zaune dirshan a kan gado, sai ga sallamar Uwatale a cikin ruwa, gulma na cizonta dole haka ta shigo, ga balangon jiyanan da kaza Innah na juyewa a faranti, zata sake sarrafashi nasu bai yi daɗi ba. Ga farfesu nayi zaman masu jego a tsakiyar gado ina sha. "Uwatale mai jego, ke da jikinki yake ɗanye, ina ke ina fitowa kinji irin ruwan da ake zugawa kuwa? " Cewar Baraka wacce ta gama gashin cibin Azgar tana sauke mai rigarshi. Idanun uwatale akan farfesun dake gabana, ga nama tana gani innah ta juye. "Wallahi nazo ganin baƙon duniyane. Hinduwa ashe kin sauka, ikon Allah ashe asibiti ya kaiki, ga yaronan tittiƙeƙe abunshi, shekarau kenan. Dake ya shekara a ciki yafi na wajena girma sosai." Murmushi kawai nayi mata, uffan bance ba. Tama rasa me zata kalla, gata a uwarɗakina tana ƙarema sababbin kaya kallo, da yadda na canja fasalin zaman komai. Gashi ta ganni da sabuwar atamfa. Abubuwa goma da ashirin. "Ga yaron ki ganshi, ki zauna ga kujera nan" Uwatale bata sanma Baraka nayi ba. Sai da Innah tace. "Dake fa ake magana, ga jaririn ana miƙo miki" Sai tayi firgigit ta amsa, tare da zama a kujera wan sita dake cikin ɗakin. "Innah bamu gaisaba. Kinzo lafiya, ya aka baro birni kuma? " "Lafiya lau, da fatan kema kin sauka lafiya, ance rana ɗaya kuka haihu" Sai tayi dariya. "Wallahi rana ɗaya fa, shikenan suna za'a haɗe duk an huta. Ga yaro tiƙeƙe dashi wallahi" Nan dai tai ta zarar zance, ni tunda na duƙufa cin kifinnan banma bi ta kanta ba. Hindu bari in shiga daga bayan gidanki in wanke wannan kayan jaririn da naki wanda kika cire" Haba Baraka shiga mana. Akwai omo a ciki, sabulunma akwai a banɗakin" "Ahh su Baraka an yi ɗa shekara ta bakwai, ai dole kya yi. Bari in tafi kar Baban masu gida ya nemi umma. Gashi Hindu Allah ya raya mana su baki ɗaya" Hannu nasa na amshi ɗana. Ameen nagode" Ai saita riƙe haɓa. "Na shiga uku ni uwatale, ai ba'a amsawa da ameen haihuwar fari. Shiru akeyi" Wani kallo da nayi mata babu shiri ta fice a ɗakin tana dariya ƙasa _ƙasa ta tantiran munafukai. Ai in kowa baizo ba, dole uwatale saita zo, wai danma haihuwa tayi ƙila dan munafurci da a nan zata tare. Ni dana gama shan farfesunnan da kunun baccina nayi, tunda dai na samu Azgar yana ta baccinshi ya sha gashi. A wannan bacci nawa ashe Innah Yahanasu taje ɓarayin Nanno, jin ba'asi anko yi ɗauki babu daɗi rikici sosai suka gwabza. Ance Nanno sai ɗaki aka shige da'ita tana kuka wiwi akan anzo har fadarta ana ci mata mutumci. Innah dai sai da taima duk matan gidan tatas, ƙofa ƙofa ta dinga zuwa cikin ruwa fa, duk ta sille kowa ta kuma ɗaura da cewa. Bata son ganin ƙafar uban kowa yazo mata da zummar ganin ɗa. Hayaniyar matan maƙota masu shigowa barkane ya tasheni. Nan suka shiga gaisheni da jiki, tare da taya ni barka. A lokacin azahar ta kusan kawowa, amman har lokacin babu a maza, balle a mata na dangin mijinyawa da suka zo barka, harfa da Nanno. Ni bansan anyi wannan gurmin ba lokacin. Yinƙurawa nayi na fito, ruwan zafi nake so zan kama ruwa. "Koma garin da sanyi, me kike so? " Innah ke tambayata, tana bakin magudana tana wanke ƙafar saniya, da jela. wanda mijinyawa ya jido, ga naman ƙaurinan har ya hau kaskon gashima. Shima ƙafar saniyar ta ɗaura wani sai dahuwa yake yi ƙamshi duk ya kaure gidan. Ruwan zafi nake so zan kama ruwa" "Jeki zan kawo miki maza" Farin cikine ya lulluɓeni, nice harda ajjiyar zuchiya da ganin irin bajintar da mijinyawa ya nuna, ya fiddani gagarumin kunya, Allah yaci gaba da rufa mana wannan asirin, har a gama a watse. Ruwan zafi ta bani a butar ƙarfe na shiga na kamo ruwa. Fitowar da zanyi sai naji kamar muryar Innarmu, kamar harda Baba Sojanmu. Kafinma in fita saiga Mijinyawa ya shigo. Ganina yasa yayi turus yana bina da kallo. "Kinyi kyau sosai Tutar so, kin fito a amaryar ƙarni sak. Kizo su Baba Sojanmune suka iso." Azgar ya ɗauka, nabi bayanshi zuwa falo. Su kuma sai lokacin suke shigowa. Baba sojanmu ne, da Yaya Sojanmu, sai Innarmu, da Luba. Baba Sojanmu yana saye da riga da wando na ƙananun kaya, rigar mai dogon hannu mai kwala, sai zanzaro da yayi, harda hular fosinkab a kanshi, da hula da bel duk na sojojine. "Ahhh kawo shi ni zan soma ɗauka, rabu da Ruwayya ta huta" Cewar Baba Sojanmu dake ta murmushi. Gabanshi Mijinyawa ya koma ya miƙa mishi Azgar ya karɓa. Gabansu na koma na zauna sai baki nake washema Innarmu. Itama tana ta murmusawa, harma ta shafi kaina.. "Sannu Hindu, bakya jin ciwon komai ko? " Aa bana ji Innarmu, Yaya Sojanmu barka da zuwa. Baba Sojanmu maraba." Na dubi Luba da ƙaton cikinta nai mata sigina, itama tayi mun. "Hindu, yaronnan kamar fa dani yake kama, baki ga hancinshi dogo kamar nawa ba, kuma kinga yana da haske" Dariya muka yi dukka, tunda cikin sigar zolaya yayi. "Oh mai diya konguratuleshon. Amman bakya jin ciwo ko?" Aa bana jin komai. Ya hanya, kun shawo tafiya" Idanu ya kanne yace. "beri bat hanya. Musamman hanyar shigowa wannan ƙauye naku, anyi ruwa ko ina mol. Motarmu ma mol sai riƙe mana take yi. Bot wi sobaib." Innarmu ya miƙama Azgar. "Ga sabon ango kin samu. Shikenan dai hankali ya kwanta ko?" Dariya kawai tayi mai, shima ya maida mata, yana ƙare mata kallo kuma fa na soyayya duk gamu a wajen. Innarmu ce ta soma shigo da abinci, sai Luba ta miƙe ta tayata kawo kwanuka, da ruwan sha. Baba Sojanmu sai ƙarema ɗakina kallo, damu kanmu yake. Mijinyawa yana gefe a takure, a ido a ido yake kallon Baba Sojanmu. Ajjiyar zuchiya Baba sojanmu yayi. Eni way inaga sai mun yi sallah kafin muci abincin ko, kai Magawata, moda ɗinka bata san munzo bane, ni banga kowa naka ba. A tsakar gidama naga sai kallonmu akeyi. Ko akwai furobilem ne? " Kafinma ya bashi amsa sai ga Nanno, labari ya isheta. Labulena yana hannunta, ganin fuskar Innarmu, da Baba Sojanmune yasa ta shigo, har tana ɗan washe baki. "Baƙi muka yi daga burni haka Hindu, ya jikin naki. Kinga ban shigo ba, bana jin daɗine zazzaɓi ya rabkeni" "Aa baki dai samu shigowar ba dai, ko da ma da zazzaɓin. Ai ke kinsan sauran" Cewar Innah Yahanasu. Nanno sai tayi kamar bata ji ba. "Bayin Allah sannunku da zuwa, ya hanya kuma?" Innarmu tace. "Hanya Alhamdulillahi. Ashe an samu ƙaruwa to Allah shi raya. Wannan shine mahaifin ita Hindun, wannan kuma babban wansu ne" Nanno ta dubi Baba Sojanmu, ta sake kallonshi da mamaki sosai bayyananne a fuskarta. Sai ta murmusa tace. "Allah sarki. Ai wannan yanzu shi ya haifi wannan, ya kuma haifi Hindu, shine ya sako ƙananun kaya harda hula kamar tubabbe? " Ƙur Baba Sojanmu yayi yana nazartar kalamanta, sai ya girgiza kanshi kawai, kallon tausayi ma naga yana ma Nanno. Mijinyawa yayi carab yace. "E ai kinsan tsohon sojane, sojoji saida ƙananun kaya" Nanno sai ta kame bakinta tayi shiru. Yaya Sojanmu da luba suka gaisheta ta amsa. Innarmu ta miƙo mata Azgar ta sa hannu ta amsheshi, har tana mai tofin da ita kaɗai tasan me take karantawa. Innar Yahanasu kafin ma ace Nanno ta gama tofinnan, saiji tayi ta zare Azgar a hannunta. Kallon_kallone ya wanzu a tsakaninsu. Idanunsu cike dam da son mayar da martani. Ƙuta dai Nanno tayi, ba tare da ta tanka ba. "Kai ashe kana nan, dakai ake karɓar barkar ne, dan rashin kunya, ko rashin tudun dafawane" Cewar Nanno bayan ta kasa tanka Innah, saita juye akan Mijinyawa. "Eskus me, lefine dan yazo ya gurfana a gaban illos ɗinshi o wat do yu min?" "Muje masallacin ko Yaya Sojanmu, an kusan shiga sallah" A tsaye su Baba Sojanmu suka wuce, suka bar Nanno itama tana tsaye. Baba Sojanmu sai turanci yake ma Mijinyawa. "Dis kwalli yu han to ridus is to muc." Baba Sojanmu da Mijinyawa kenan. Nanno tana tsaye ƙiƙam. Hannayenta ta tattafa. "To wata sabuwa, ana wata ga wata" "Magana kike yi ne? " Inji Innah Yahanasu. Da sauri Nanno tabi bayansu Baba Sojanmu. "Allah ya kyauta. Wai lafiyar uwar mijinnan naki ɗaya kuwa, jibi abubuwan da take yi. Duka fa baya wuce akan sunga janaral da ƙananun kayane. Shima nayi nayi dashi kar yayi zanzaronnan, yace baiga daliliba, haka ya saha haka zai yi. Ina jinsu da Nagoɗi ma suna yi kafin mu tawo. Yana ce mai baisan menene hamimmancin zanzaro a boko, da kuma gidan soji ba. Allah ya kyauta. Yaha Allah ya baki haƙuri, sai kin kauda kai akan abubuwa da yawa hmmm. Hindu ce duk taja mana komai, mai haɗawa haihuwa ta riga ta haɗamu dasu." "Wai kinsan Ya Ruwayya. Matarnan tunda Hindu ta fito asibiti sam bata zo ganin jikanta ba. Babu fa wanda yazo a cikin gidannan. Sai matar wan shi Magawatan itama gulma tazo yi. Ai sabida janaral ne wallahi kinsan Allah da bata isa ta ɗauki yaronnan ba, saina mata wankin babban bargo. Ɗazu ai na bisu ɗaya bayan ɗaya nai musu sul soso da sabulu, taci kukanta ta ƙoshi, nai mata wuji_wuji dan na fuskanci bata da mutumci, kuma gaskiya na faɗa mata. Gaskiyar da ba kowa zai iya faɗa mata ita ba. In jununta rashin mutumcine, ni wuta nake fitarwa." Baki Innarmu ta taɓe, ta dubi Luba. "Luba a bani ruwa zan yi alwala kinji. Bazan iya da wannan rigingimu na familin mijin Hindu ba." Miƙewa Luba tayi ta kaima Innarmu ruwa, wai bayan gidan waje zata shiga. Tana fa fita, sai ga gungun su Yaya Jamila, da ƴan ɗakin Innah Dubu sun tawo gulma, dan ba barka zance ba. Harda Uwatale itace akan gaba_gaba Miƙa musu ɗan Innah Yahanasu tayi. "Sai yanzu kuka zo barka bayin Allah. Tun jiya fa muka dawo cikin gidannan, ai ko baku zo dan ita Hindun ba, kwazo dan ɗan uwanku dashi jaririn ko. Hakan kuna ganin ya dace kenan. Ace sai naje na sulleku zaku kwaso tsofaffin zannuwa da sunan ganin jariri da uwarshi?" "Aa ayi haƙuri Mama. Dake yanayin ruwannan da akaita zugawa jiya da yau shi ya hanamu shigowa. Ni yanzune ma shigowata gidan, shine Nanno tace yanzu itama ta shigo, ashema har mahaifin Hindun shima yazo ganin sabon jini? Gashi tubarkallah shekarau kenan" Yaya Jamila ta ƙarashe da dariya, ta saki fuskarta ƙaƙas tamkar ba itaba. "Zakiya, gafa Shekarau" Ta miƙama Zakiya, nan aka shiga karɓan karɓa, sunata yabawa da girman Azgar. Shigowar Innarmu yasa suka tsayar da hirarsu suka gaggaisa. Shigewarta ciki tayi, Luba tabi bayanta, ga ƙaton cikinta a gaba tana tutturawa. Su Baba Sojanmu ne suka shigo, to ɗakin ba ɗaukarsu zai yi ba. Dole suka miƙama Innah yaron suka miƙe. "To bari muje, ga Baba sun dawo daga masallaci" Fita suka yi, a tsakar gidan na jiyo suna gaishe da Baba Sojanmu da Yaya Sojanmu. Buhu Mijinyawa ya shigo dashi, buhun bakko biyu ciccike da kaya ya dure a gefen kujera. Yana sa kai ya fita. Yaya Sojanmu shima ya shigo da wasu kayan. "To bari a saka muku abinci kuci kuma" Innah ta zuba musu jalof din shinkafa mai bushasshen kifi, harda farfesun ƙafar sa, sai turiri yake yi. Nima ta zubo mun cikin kwano ta dure mun. Innarmu da Luba ma ta zuba musu, suka fito duk muka haɗu anacin abinci ana ɗan hira haka sama_sama. "Ai da safe jinine ya ɓalle mata sosai, gaskiya mun tsorata da harma zamu je asibiti. To an karɓo maganin tsayuwar jini a wajen uwarmijinta. Matar abokin mijin ma ta kawo mata maganin ƙarin jini. Da naso ma muje asibiti dai to, amman naga jikin da sauƙi" "No no ai dole a kaita asibiti, jini fa kikace ta zubar fa Yaha? Yana da kyau a kaita asibiti. Ni duk wannan kokoshon ɗin bana yadda dasu, yarinya ta shirya in zamu wuce tunda A Bauchi zamu kwana, sai Yayanta ya kaita Asibiti, inma gado za'a bata a bata. An ma yi ai gaggawar sallamarta a asibitin gaskiya." Innah Yahanasu tace. "Ai ya tsaya. Kuma anayin hakan sosai. In dai tana cin lafiyayyen abinci shikenan, wannan farfesun zai taimaka mata. Gashi mijin ya kawo da yawa harma baza ragowar nayi a buhu, na sake gargasawa, zan soya sama sama sai in baza a wancan fallen ɗakin." Innarmu tace. "Eh Janaral tunda jinin ya daidaitu ba sai anje asibiti ba. Akwai abubuwan dana kawo mata waɗanda zasu taimaka ma jikin nata ma. Sannu kinji Hindu? Ko bakya jin daɗin bakinki ki daure romo romon ki dinga sha yana da matuƙar amfani gaya." Baba Sojanmu dai lallai yaso aje asibitinnan, da ƙyar aka tausheshi ya aminta. Ruwan samane ya dawo , a wannan ruwan sai ga Yaya Jamila an aiko da damammiyar fura tako ji nono. Sai kallon farfesun da Luba take ƙaramun take yi, ga lafiyayyar jalob taji manja da bushasshen kifi. Haka dai ta fice tana waige. A falo muka bar su Yaya Sojanmu da Baba Sojanmu Azgar na kan cinyarshi. Yajin daddawa a bokiti mai lita goma cike Innarmu tayo mun. Yajin daddawa mai kilishi, da nama a ciki yaji magi, da daddawa. Man shanu cikin kwano mai kamar bokiti kusan lita uku. Ga kayan mata na gyaran maijego cikin bakko guda. "Wannan gumbar kullum ki dama ki sha zata yi saurin ciko dake, a kunu zaki dinga dama mata Yaha. Ko a cikin madara mai ɗumi. Karfa tayi wasa dashi sam. (Ga yadda kuma zaku haɗa taku kumbar son so domin Allah) HAƊIN GUMBAR MADATA MAI DABINO (Ta mai Jego da Gyaran Mata na musamman) Wannan babban haɗi ne na musamman domin mata masu jego, amare, da ma duk matar da ke son dawo da ni'ima, matsi, da samun ƙari na kuzari da ƙarsashin na musamman. Abubuwan da Zaki Buƙata. Garin Madata (ko Geron Mata) Kofi 2 Dabino (Busasshe) Kofi 1 (a cire ƙwallon) Kwakwa da Aya Busasshiyar kwakwa da ayar da aka soya sama-sama Kayan Ƙamshi. Kanunfari (cokali 1) da Citta dakakkiya lokali ɗaya. Garin Asuwakin Mata (ko Gyadar Mata) Cokali 2 (domin matsi da samun farin ciki. Kuyi haƙuri in kalmar tayi tsauri)Zuma ko Mazarkwaila – Domin zaƙi da ƙarin inganci. Garin Madara – Kofi 1 babban kofi. Yadda Ake Haɗawa. Gyaran Kayan. Cire ƙwallon dabino. Daka dabinon, kwakwar, da ayar a haɗesu tare a niƙa, har su zama garin laushi. Haɗa Garikan waje guda A cikin kwanon haɗawa, juye garin madatarki, sannan ki zuba garin dabinon, kwakwar, da ayar da kika daka.Saka Magungunan, Sanya garin kanunfari, citta, garin asuwakin mata, da garin madararki duka a waje guda. Idan mazarkwaila ce, daka ta ki gauraya a ciki. Idan zuma ce, zaki zuba ta ne yayin da zaki kwaba gumban. Dakawa. Mayar da duka haɗin a turmi ki daka su sosai har su haɗe jikinsu ya zama guda, kirɓawa zaki yi tamkar kina dukan sakwara, wannan ba wai aikin wasa bane, ba ƙaramin aiki take yi ba, ba ta tuƙawa a wuta bace. (dabinon, da zuma, ko mazarƙwallar, zai sa gumban ta fara dunƙulewa da kanta) Shikenan sai ki soya riɗinki ki sake cakuɗawa a ciki shikenan kin haɗa gumbarki ta mata masu aji a cikin gidanki Hajiya. Yadda Ake Amfani Da Ita. Sha Da Nono/Madara. Zuba cokali 2 na gumban nan a cikin madara mai kyau ko nono, ki juya sosai ki sha. Ana iya mulmulata a dinga taunawa kamar alewa lokaci zuwa lokaci hmmm. A riƙa sha da safe kafin karyawa da kuma da daddare kafin barci. Yana da kyau sosai wajen sa damshin dausayi da dawo da martabar mace. "Wannan tsumine na ƴar gata. Shima da madara kar ki yi wasa da komai anan Hindu, Yaha ke kinsan komai." Ga haɗin tsuminnan. TSUMIN MAI JEGO MAI KAURI DA INGANCI (Gyaran dausayi mai ingamci) Wannan tsumi ne na musamman wanda ke ƙara wa mace kyan dausayi, yana kwashe sanyin dausayi, kuma yana sa mace ta dawo fafur kamar ba ta taɓa haihuwa ba. Abubuwan da Zaki Buƙata. Ganyen Magarya da Ganyen Sidir – Shi ne asalin ginin tsumin (ganyen magarya cokali 3 na garinsa, ko ɗanyen busasshe cokali 3). Kanunfari, da Citta Suna sa kauri da daɗi kuma suna dumama mahaifa.Habatussauda, Cokali 2 (yana warkar da duk wata cuta da sanyi). Namijin Goro – Guda 3 (a daka shi, yana da kyau sosai wajen matse dausayi da dawo da ƙarfin dausayi). Dabino, da Ɓaure, Shi dabinon (kofi 1) shi ke kawo kaurin tsumi, ɓaure kuma yana matsin dausayi, Garin Jirjir, ko Bagaruwa cokali 1, tana busar da jiƙan dausayi. Zuma ko Mazarkwaila Shi ne sirrin kaurin! Zaki buƙaci zuma mai kyau cokali 5 ko mazarkwaila guda 2. Yadda Ake Haɗawa yayi kauri. Wanke ganyen magarya, dabino (wanda aka cire ƙwallo), namijin goro, kanunfari, citta, da ɓaure. Zuba su a tukunya. Zuba ruwa dai-dai gwargwado (kamar kofuna 3 zuwa 4). Bar shi ya tafasa sosai a wuta marar ƙarfi, na tsayin minti 20 zuwa 30 har sai dabinon ya farfashe a cikin ruwan. Ruwan kuma ya ragu ya yi duhu sosai. Tace ruwan da kyau ta amfani da rariya mai laushi ko tsumman tata, duka raguwar kayan su fita. Zuma/Mazarkwaila Mayar da ruwan tsumin da kika tace a kan wuta, sannan ki zuba zuma mai yawa ko mazarkwaila da kika daka. Dahuwar Ƙarshe. Bar shi a kan wuta yana dahuwa a hankali Zakii ga ruwan yana ƙara yin kauri sosai yana kumfa kamar zum. Da zaran ya yi kauri yadda kike so, ki sauke ki bar shi ya huce. Juye shi a jarka mai kyau. Yadda Ake Sha. Ana shan cokali 2 zuwa 3 na wannan tsumi a cikin babban kofi na shayi ko madara mai zafi. Safe da daddare kafin barci. Yana sa jikin mace ya haɗe, dausayi ya matse, tana jin dumi kuma yana wanke dattin mara duka. Sai turaren tsugunno na musamman, ingsntacce, mai gyara dausayi, ya dawo da martabarshi. (Wannan ki cire nerarki dubu goma in baki Hajiya, harda kyautar kwalbar farin miski ɗan asali ƙarami yake zuwa) Zaro wata robar tayi basarakiyar daka ne a ciki shi kuma, sha da nono, ko madara. Cikui ne da dabino, sai geron mata, da garin idanun zakara. Dakesu zaki yi su zama gari, a dinga damawa da madara, ko nono, wannan dakan gamawane kat. (Mata na baku wannan sirrine domin gyaran gidajen Aure. A yanzu siyen maganin mata barkate ba naki bane. Mu kula da lafiyarmu, da abinda zamu dinga ɗibgama kanmu in di nam ob maganin mata😆. Lafiyarmu abar kiyayewace. Wannan haɗin in kika daure kika haɗa abunki, bakya buƙatar ko wanne irin maganin mata na siyarwa. Da wanda zan kakkawo muku a gaba in sha Allah. Saura kuma kuce yau na cika musu fejinne da sharhin magunguna nasan zaku aika🤣 to da Innah Yaha zan haɗaku ehe son so domin Allah. Burina inga na taɓa rayuwar auren mata da yawa kuma na gyara musu zamantakewarsu. Mata mu san kanmu, mu kula da kanmu, mu mutumta kanmu, musan girma da darajar da Allah yai mana. Mu yi karatu, mu kama sana'a., mu yi aiki in mazajenmu sun bamu damu. Mu tsare mutumcinmu a wajen aiki, mu tsabtace sana'armu mu sa gaskiya. Mu riƙe adda'a tare da miƙama Allah lamuranmu tare da yaƙini. Sai mun haɗu gobe) Nasan yau wasu zasu rahaba kasuwa🤣🤣🤣🤣 To basarakiyar Dilkha dai taku ce mata masu aji💪🏼💪🏼💪🏼 Mrs BUKHARIMRS BUKHARI ............ Innah ta sake zaro Ƴaƴan hulba shima tace ƙwaya ashirin kullum in haɗiya in bi da ruwan ɗumi. "Shikenan sauran kayan fitar suna, da gara suna tafe, su Saratu zasu zo miki da komai. Ina ganin da mun yi la'asar zamu kama hanya kuma. Gashi sai ruwa akeyi. Yaha ya batun wankan gida amman, girkannan za'ai mata ko? " "To naga kamar bata son batun wankan gidan gaskiya. Amman zamu tafi da'ita Maiduguri ko kwana gomane tayi, sai mu dawo mu ɗaura wanka. Dole kinsan ai mata gyara na musamman, jikinta ya rasa martabobin da gyarane kaɗai ka iya dawo mata dashi. Amman sai mu bari tayi talatin, sauran goman sai in tafi da'ita. Amman me kika ce?" "Aa ki dai tafi da'ita da zaran suna ya ƙare, a ƙalla itama za'a gane da gatanta, kar dangin mijin suga kamar ko neman kai akeyi da'ita. Zasu iya goranta mata tabbas. Kuma ai kinsan dole a girketa, hankalina ya kwanta sosai da kikace Maiduguri zaki tafi da'ita. Itama nasan gidanne can bata son zuwa. Akwai ƴan gutsiri tsoma sosai. Gulmace za'aitayi inta dawo. Bana son kowa ma yasan zaki tafi da'ita. Sai an watse kab, sannan ku tafi. " Ni dai ban iya cewa uffan ba. Azgar ne yayi kuka, innah ta karɓoshi, Luba na zaune sai ƙashi take ta faman gwagwuya ƙaƙas abunta. "Bashi Umma. Naga yaron yana da haƙuri kamarki. In ya biyoki ai zaki yi lafiyayyen goyo, kefa bakya kuka, ko a bacci kika tashi sabida haƙurinki, sai dai kisa hannunki a baki kawai kita tsotso. Bana mancewa har Asibiti Ya Ruwayya ta kaiki wai bakya kuka. Likitocin suka ce in dai kin yi kuka lokacin da aka haifeki shikenan, in daga lokacin ma anji kin kuma kuka babu damuwa. Wasu yaran haka Allah yayi su da kuka, wasu kuma masu dauriya" "Um ai wannan gashi yana ta canyarawa. Ai itafa irin wannan canyara kukan ban taɓa ganin tayi ba gaskiya. Yana dai da haƙuri shima irin nashi" Umma na bashi ya sha ya ƙoshi, muna ta hira da Luba, tana bani labarin irin nata zaman da falalolinta, da tafiyar karatunta da a yanzu ta dingine zuwa ta haihu kuma. Halima ce tayo sallama, ita da Baraka. Inajinsu a falo suna gaisawa da su Baba Sojanmu. Kafin daga bisani suka yo sallama suka shigo, Azgar na kafaɗar Luba tana shafar bayanshi. Gaisawa muka yi da Halima, ta yafo ɗan mayafinnan ƙarami irin na ƴan mata. Ta caɓa ado kanta da ƙarin gashi anyi mata kitso dashi. Da yayi gyatsa saita miƙa musu yaron. Bakara ta karɓa ta ba Halima. "Ya jikin Hindu? " Da sauƙi Baraka sai jiri da nake ji kaɗan. Yanzu ma wani irin sanyi nake ji duk da ga gaushi." "Ai hadarine ganga_ganga a garin. Halima na rako tayi barka inaso inje in zuba ma su Qasimu da mijinyawa abinci sun fito gona" Aa bari Luba ta zuba sai ki kai musu, tun tuni ma nake son magana da Mijinyawan fa. Ko dan Allah zaki mun Magana dashi, in yaso ma ya tafi da abinci? " Hakan ko akayi, sai ga mijinyawa amman a ɗakin kayan abinci ya tsaya, Luba ta miƙo mun kwanan abincin na fito. Allah ya soni basu kulani ba. A tsaye na shiga na sameshi, dana dure abincin saina faɗa banɗakin tsakar gida na gyara jikina da ruwan zafi, nayi alwala na shige da sauri. Hadarine sosai a garin. Sallar azahar da la'asar nayi. Yana zaune a saman katifar yayi yana kallona. A gurguje ina ka samo kuɗi haka, Innah tace ka jido ƙafar saniya da jela, ni kuma nasan kuɗin cikin jakarnan daka ɗiba ba zasu isa wannan hidimar ba. Ko bashi ka ciyo ne? " Murmushi yayi. "Banci bashi ba. Dama naje ne da zummar siyo ƙafafuwan saniya guda, kinga huɗu kenan ƙafafun, da jelar. To harma munyi ciniki yana daddatsawa dake Azare muka shiga mahauta. To sai Qasimu yace a ƙara kamar wanda na siyan. Shi kuma Abdulƙadiri ya sai naman ƙauri kinji yadda akayi kenan. Amman dama akwai ƴan wasu kudaɗen a jikina, in sha Allah ba zamu ji kunya ba. Kije kar aga kin daɗe ya zame mana magana, kyakkyawata kinga yadda kika yi wani kyau" Miƙewa nayi ina ƴar dariya. Ga abinci nan, ka dinga aikowa ana zuba maka naka, ai dakai akayi girkin, babu mai hanaka cin abinci. Dan Allah ka saki jikinka" "Ke tsoron Innah nake ji, kinsan Allah ko ganinta nayi sai naji faɗuwar gaba. Tana ganina take sake haɗe girar sama data ƙasa fa. Ke dai muje" Tare muka fito, yayi maza ya fice ni kuma na shiga ciki. "Ma firen inaga wi hab to go. Banason ruwannan ya taremu a ƙauyannan mol yazo ya sake riƙe mana mota. Allah ya raya ya ƙara lafiyar shayarwa ko? Tek gut kiya ob yo sef. Kinga yanzu kin zama uwa, dan Allah a dage. Kuma ya kamata yayi makaranta mai kyau, nasan bai den kun dawo Kano kema har kinyi nisa a karatunki, za mu tattauna da Magawatan. Ga wannan ki riƙe a hannunki" Ya bani kuɗi masu yawa. Yaya Sojanmu ma ya bani kuɗi, ya kira Luba itama ya bata kuɗi, Baba Sojanmu ya ƙara mata. Lafaya na naɗa, na sake lulluɓa da zani, Luba ta zauna da Azgar tare da su Halima. Mu kuma muka ɗunguma rakiyarsu Baba Sojanmu, gari sai sanyi mai ruwa_ ruwa halamun ruwa na daf da sakkowa. Muna fita Mijinyawa ya hangomu, abincima suke ci a ƙarƙashin bishiya. Ba shiri ya taso, shine harda gudu_gudunshi. Baba Sojanmu ya dafashi kanshi a ƙasa. "Ma firen wannan kwalli yu hab to ridus it is to muc filis" Murmushi kawai yayi, ya daddaki kafaɗarshi. "Ma diya mun tafi mu kam Allah ya raya" To Baba Sojanmu, Allah ya tsare hanya. Innarmu Yaya Sojanmu Allah ya kiyaye hanya. Anty zasu zo ne tare da su Yaya Saratu? " "Ameen Duwab zata zo. Ai masu zuwan da yawa. Gayyar da zasu yi bata wasa bace. Mun barosu anata rubuta sunayen masu tawowa aikin Khadija ne wannan kema kin sani" Kai kawai na jinjina ina yaƙe, ji nayi cikina ya ƙulle. Wallahi da yawa ba taya murna bace zata kawosu ba, gulmace da son ganin ƙwaƙwab. In sha Allah ba zamu wulaƙanta ba, masu son ganin gazawarmu da faɗuwarmu ba zasu gani ba. Rikici ne dai nasan sai wanda su Yaya Jamila suka mance. Har sukai nisa ban gaji da yi musu adabo ba. Sai da sukai nisan da yayi yawa, kana na sauke hannuna. Innace tayi gaba, na faki idanunta na damƙama mijinyawa kuɗin da Baba Sojanmu ya bani, tunda sunfi yawa suna da kauri sosai gaskiya, na wajen Yaya sojanmu kuma na soke su, suma da kaurinsu. Muna isa ƙofar gida, muka ga gilmawar Nanno da gudunta. "Ikon Allah. Wannan kamar fa surukarki ce take hangenmu, da taga mun juyo shine ta rufa da gudu" Saukar ruwan sama da ƙarfi shi ya katse mana bayanin, a guje muka shige. Ita a wajen ruwan zafi ma ta tsaya. "Ki shirya kizo ki sameni a banɗakin waje zamu yi wanka." To" Kawai nace da'ita ko dana shiga ciki, tsabar duhu har acibalbal suka kunna. Baraka nayi ma Azgar wanka, sai ga Innah Dubu nan ta shigo da sallama wai tazo itace zata dinga ma yaro wanka. Ita take ma na Uwatale ma. "Aa ki dai je kiyi ma na Uwatalen kika ce ko? Ya yaron da ko barkarshi baki zo bane, zaki ce wai wanka kika zo kiyi mishi. To bazai ma yiwu ba ehe" Cewar Innah daga falo muke jiyosu, mu muna daga ciki. "Aa baiwar Allah. Ai ba batun ƙin zuwa barka bane. Kuma in kika duba ai fishi dukkanmu muke yi da batun haihuwarnan da akayi a asibiti. Kuma shi mijinyawa yaje ya birne mahaifa mabiya a asibiti. Ai dole muyi fishi haƙuri ma ya dace a bamu" "Nace anƙi a baku haƙurin. Yarone dai Baraka na yi mai wanka ta wadatar. Ku je kuci baƙin halinku. Sabida na fahimci baƙin cikine kawai kuke ma yarannan. To ko ku so ko kar ku so, Hindu dai ta haihu da ɗanku babu abinda kuka isa kuyi. Wannan Auren damu daku ya zame mana TSURON TSIRIN TSANDAURI, ya gagaremu ba dai mutum ba sai dai Allah. To kinji wallahi. Haka kurum a baki yaron anaji ana gani ki dannamai kai a ruwa, ko ki shiɗa mishi sabulu a hanci. To kin ji" Innah ta dirarma mita, dan wallahi mita gareta, saita kwana ta wuni tana abu ɗaya. Dole ƙanwar naƙi Innah Dubu ta fita dan anfi ƙarfinta. Kuma ita ba mafaɗaciya bace sam. "Ke in zaki fito ki fito mu je wanka. Wannan abubuwan na gidannan ya fitarmun aka. Wallahi su bini a hankali kar su tunzurani rikicina babu kyau. Akanme suke ire iren wannan abun da girmansu da komai" Faɗa Innah take yi kamar me. Ni dai kaya na cire, na yafo zani na fito. Ai na shiga banɗaki, Innah na shirin shiga sai ga Nanno da Inna Kulu, da mahaifiyar Uwatale, sai Innah Dubu, sun shigo. Ƙugu Innah ta riƙe. "Ke dubu shiga ki karɓi jaririn a hannun Baraka ki mai wanka, jikanane ubanshi ma nawa ne, ita kanta Hindun bata isaba nafi ƙarfinta." Sai Innah Tine, mahaifiyar Uwaatale sunayene da'ita kusan uku amman mu ɗauki Tine ɗin tace. "To ma in banda kwaɓa ina wata Baraka da wankan jariri, nawa Barakan take. Mu a al'adance dattijaine ke ma jirajirai wanka. Kuma ta ɓangaren dangin miji a dattijanma. Alhakin wankan daya rataya a wuyan dangin mata wanke ɗiyarsu mai jegone kawai." Ai sai Innah ta cire ƙafarta ɗaya dake cikin banɗaki ta fito, a dokin ƙofar shiga ɗakina ta tokare. "In mata ta isa, tana jin tana da ƙarfi tazo, wallahi saina kwantar da'ita. Ke da kike maganar iko ke kika sanshi. Ke me al'adu shi yasa gaki kamar al'adarku ta neman magana da zuzuta ƙaramar magana ta zama babba. Kunsan Allah banga a cikin dangin Magawata daya isa yaima yaronnan wanka ba. An kaita asibiti babu ƙeyarku. An dawo da'itama haka har saida na wanke ƙafata naje jin ba'asin wa Hindu ta kashe muku a dangine. Ai kun riga ƙiyayyarku, da hassadarku, ta fito fili. Sai kawai dan bani da hankali sai a baku yaro ku mai wanka ko? Baku isaba to kunji" Ni wallahi wankana na dingayi, jikina na wani irin mazari makaraina na shirin tashi. Ni wannan masifa dame tayi kamane. Ina jin Luba na ta ban haƙuri ita da su Halima. Wallahi cikin ƙanƙanin lokacin ɓarayina ya cika maƙil da mata, harda maƙota. Azgar ɗinma har an gama mishi wankan fa. Ga ruwan samannan duk a kansu yake sauka. Muryoyin su Yaya Salihu da mijinyawa Babba, da mijinyawa, dasu Qasimu dama sauran da ban riƙe muryoyinsu ba nake ta jiyowa. "Kuyi haƙuri Nanno wannan fitina a barta haka. Tunda basason wankan a bar musu ɗansu. Mijinyawane ya nuna musu tun fil azal danginshi basu da martaba. Da ba dan haka ba, hakan bama zata faru ba. To tunda naka shi ke ba da kai sai ayi haƙuri. A barsu da abinsu. Ai duk wani sha'ani in aka haɗu Mijinyawa da matarshi to dole sai sun nuna isa" Yaya Salihu kenan wanda ya kamata ace ya yayyafama ƙura ruwa, saima ya zaɓi tayar da'ita ta bule kowa. "Aa Yaya Salihu kar kace haka. Wannan rikicin na matane. Magawata babu ruwanshi. Mu fa hayaniyace muka ji tayi yawa shine muka ce bari muzo. Magana ta domin Allah babu ta inda magawata ya nuna danginshi basu da kima. Tunda basason wankan a haƙura dan Allah. Kuma ai ba'a kyauta ba, da aka kasa zuwa a duba Hindu a gida ko a Asibiti. Mufa faɗama kanmu gaskiya. A cikin gidannan abubuwan da akema Mijinyawa sun wuce misali. Kun wareshi tamkar ba ɗan gida ba. Duk abinda zai yi yana tsoro a ɗarare yake yi. Saɓanin Nawats da zai yi komanshi gaba gaɗi shi da matarshi. " "Dallah rufa mana baki. Ai kai ko kisa abokinka yayi kana bayanshi. Shima ai waremu yayi shi yasa. Uwatale kuma ai jininmu ce dole mu sota sama da Hindu. Nanno ku tawo muje a barsu da halinsu. Hindu dai ba zata je wankan ma gida ba tananan anan ƙauyen, abinda yake damun iyayenta kenan. To wallahi babu inda zata je tananan" Cewar Yaya Jamila da yanzu naji muryarta. Murmushi kawai nayi. "To tunda kece mijinta ko uwarta da ubanta ai dole. Ku ku fice mun da gani kafin in muku ɓarin makauniya wallahi" Akaita rikici, ɗauki babu daɗi iri da kala. Na gama wankana fes na fito babu wanda na kalla, nayi shigewata ciki abuna, Luba dake tsaye na jawo muka shige ciki an barmun yaro shi kaɗai yanata kuka bawan Allah. Ɗaukan abuna nayi na saka mishi umma. Babar su Qasimu ce ta dinga basu haƙuri, tana ba Innah haƙuri tana riƙeta, zata daki Innah Kulu harma ta zabga mata mari wai ɗankwalinta ya cire. Daga ƙarshe dai tace ita zata amshi wankan jaririn. Shikenan rikici ya lafa. Innah tace. "Ai Barakannan data nuna kulawarta, wallahi itace zata ci gaba da yin wankannan har zuwa lokacin da zamu tafi wankan gidan da ko mutuwa zasu yi sai dai suyi. Ni banƙi sanadin wankan gidanma auren ya mutu uban kowa ya huta ba. Banzaye gidadawa" Shigo da'ita Baba tayi. Su Nanno kuma suka rufu akan Mijinyawa sukaita zazzagarshi. Sai da makaraina suka tashi, Innah Yahanasu ma ta hau makarai, babu shirin gayyar ta watse harda masu fita da gudu akace. Dan wajen ruwan zafin dake kan wuta ta nufa, dole taron ya watse, ƙurar ta lafa dan dole. Amman su Nanno sun ƙullaci wannan hanasu wankan jariri da akayi gaya. Kuma rikici lafawa yayi, ba ƙarewa ba. Ni banma sake sanin inda nake ba sai washegari da safe. Ina buɗe idanuna naga mijinyawa a jingine a fuskar gado ga Qur'ani a hannunshi, yana ta gyangyaɗi. Motsinane ya farkar dashi. "Alhamdulillahi. Innah ta farka. Sannu Hindu kinji" Innah tayi saurin shigowa rungume da Azgar. "Sannu Hindu, kiyi haƙuri kema kinsan bazan iya ganin wannan iskancin in zuba ido ba. Ke da makaranki Allah ya baku haƙuri. Robona da tashin makarai nima na mance, tunanina ma sun rabu danine. Jeki gyara kanki akwai ruwan zafi a ciki. Kai kuma kaje kafin gyatumarka ta tsinema, sannunka da ƙoƙari" "Innah kiyi haƙuri da duk abinda suka faru. Da wanda ma zasu faru a gaba. Dan Allah ki dena tankawa, nasan rigimarnan ba'ayi komai ba. To kuyi haƙuri dan Allah" "Au haba ba'ai komai ba. To me jaki ma yace ayi tsere bare mai doki? Ni kaɗai na ishesu. Yi tafiyarka kawai yaro kar in sauke kwandon jalala a kanka" Zai kuma magana ta ɗaga mishi hannu. Dole ya miƙe a hankali ya fita. Ya sake rama sosai wallahi, gashi bama samun keɓewa yadda ya kamata. Haka lamura sukaci gaba da cukumurɗawa dai har ya rage saura kwana biyu suna wanda ayau muke sa ran zuwan Yaya Saratu, da Yaya Zubaina sune zasu soma yowa gaba. Har zuwa wannan lokacin sabida rigingimu, su Nanno da su Yaya Jamila sun sha'afa da tambayar wanne suna akaima Azgar huɗuba dashine. Hmm tsugunne nasan bata ƙare ba, tunda ranar raɗin suna za'ayi shelar sunan a ƙofar gida, tare da makaɗan kalangu. Tun bayan munyi wanka Innah da Baraka da Halima suke ta girke_girke. Tasa mijinyawa ya siyo kaji zata yi miya dasu. Banda ƙafar saniya da tace ya ƙaro. Sai Baraka na ƙullema kuɗin ta fita ta kai mishi ya siyo ya kawo. Innah babu ruwanta, aikinta shine ya siyo wannan, ya ƙaro wancan. "Hindu kunyi magana da Mijinyawa akan abincin suna kuwa, ya kamata kuyi magana sabida naga ƴan ɓarayin facalarki harsun soma tsintar shinkafa. Ko zamu jira zuwansu Yayane? Ya kamata da wuri asan me ake ciki. Tunda kinga nasan zamu yi namu girke_girken daban. Sannan shima ai zai kawo nashi cefanen ko?" Hakane Luba, ni kaina inata so in ganshi muyi magana, sabida asan me ake ciki. Bari anjima in ya shigo zan mai maganar muji me ake ciki. Wannan ciki Luba haihuwa ko yau ko gobe" "Fatana ma kar inzo in haihu a ƙauyennan Nanno tace dole ita zata karɓi haihuwata" Dariya muka sa tare da tafawa tabb. Baki da kirki Luba. Zaki haɗu da Nanno babu ruwana" Muna wannan hirar sai ga sallamar mijinyawa, ya leƙo yace. "Kuna nan abinku. Luba sannu fa. Tutar so zo muyi magana ga Qasimu zai yi magana dake, kuzo da Luba" Miƙewa nayi na kamo hannun Luba muka fito. Duk sai suka tusamu a gaba. "Qasimu baku ce komai ba. Ko dai in baku wajene? " Cewar Luba dake yinƙurin miƙewa. "Aa wallahi. Ai in zan iya shiga gaba akan sabgar Magawata. To kema zaki shiga gaba a sabgar Hindu. Ƙawance ba ƙarya bane. Hindu nasan abinda zamu faɗa ba daɗine dashi ba. To amman yaya zamu yi lokaci yanata ƙurewa dolene mu sanar dake halin da ake ciki dangane da batun abincin suna." Sai ya ja tunga, yana ta ƙunƙunda. Ni tuni na riga na bugo jirginsu. Na kuma zo iyakar wuya. "Kaci gaba da bayaninka Qasimu" "To Luba. Wallahi birni muka shiga ni da Magawata, da Abdulƙadiri mukayo cefanen kab abincin suna sabida dai a samu a fita kunyar baƙin birni. Har nama muka siyo mai tarin yawan gaske dan ya kai cikin robar fenti babba wallahi. Duk wani cefane munyi duk mun kashe kuɗaɗenmu. To amman me? Wallahi acaɓa na saukemu saiga Nanno da Innah Kulu a ƙwar gida. Nanno haka tace dole mu shige mata da duk cefanen ɓarayinta, ita abincin suna su Yaya Jamila ne zasu yi tare dana Uwatale sai dai a kai kwalla, a zubo muku abincin. Hatta kayan soɓo da ledar ƙullawa mun siya, akan mu sallameku da wuri bamu san shirinku ba. To kunji dai abinda ke faruwa. Kuma babu kuɗi a hannayenmu balle mu sake baku wani. Sai dai mu bari zuwa gobe, muga mai zata haifar. Kunya duk ta kamamu" A lokacin da za'a tsaga jikina ba za'a tadda jini ba. Da mai kukace ni da tuni hawaye sun gama jiƙamun fuskata. Amman sai naji kawai idanuna sun bushe kamar zasu dare halamune na ƙarshen maƙurar ɓacin raina. Jikina har rawa yake yi. Amman murmushi nake yi, mijinyawa dai sai na zame mishi suruka. Ina tuno irin surutan da ƴan gidanmu zasu yi akan wannan lamari. Innah ba bafa zata yadda ba, abunne bai yi ba sam. "Amman a gaskiya ba'a kyauta mana ba. Kuma ai ba'a haka. Yanzu Innah na jin wannan labarin ba ƙaramin gagarumin rikici zata tayarba. Kuma ko ta tayar dafa gaskiyarta, magana ta domin Allah. Ace shikenan mu duk yawanmu sai dai a dafo abincin suna a bamu, muna zaune jigum_jigum kenan. Me zai hana a bamu namu, muna fa da yawa sosai. Ko yau mutum nawa ne zasu zo" Cewar Luba. Ni ko tunda nayi gefe da kaina, ban juyo ba. "Tutar so kiyi haƙuri, ki tausayamun. Wallahi da kinsan firejar da take kaina nasan zaki yi haƙuri. Kinfi kowa sona, kinfi kowa yi mun uziri. Kinfi kowa fahimtata" Babu komai Mijinyawa, su yi babu damuwa. Qasimu ba komai. Watarana mai bada labarin wannan abun ma ba za'a samu ba. Ni zan shiga daga ciki" Leda Mijinyawa ya miƙomun babba da kaya sosai a ciki" "Kayan fitar sunane nayi miki. Babu dai yawa, amman nasan zaki yi alfahari dasu sabida ya fito daga hannun masoyinki" Ƙwarai kuwa. Nagode Ubangiji Allah ya ƙara buɗi, ya raya mana Azgar. Qasimu nagode. Kuma in sha Allah babu wani hayaniya da zakuji dangane da batun abincin suna" "To mungode matar rufin asiri. Luba mungode. Kaga taso mu tafi kafin azo a riskemu mu shiga uku" Figar hannunshi yayi suka fice, sai waigena yake yi. Har saida nayi mai halamu da idanu na abinda shi kaɗai yasan sirrin. Kafin naga ya sauke ajjiyar zuchiya. "Yanzu ya zamu yi da Innah Hindu. Amman dai wannan tsarin bai yi ba. Taya ma za'ace wai su Yaya jamila ne zasu yi mana girki ma, mu sai dai mu yi jingum_ jingum kenan? " Inafa Luba. Babu komai akwai wasu kuɗaɗena zan ƙirgesu in danƙama Innah yanzu. Abinci kam ko sun kawo ki tabbatar ba'a karɓeshi ba, a mayar musu da kayansu wallahil azeem bana so." Dafani tayi tace. "Hindu na sanki, kuma bazan bari a karɓa ba in sha Allah. Muje ki harhaɗo kuɗin a danƙama Innah su nuna a hannunta" Shigewa muka yi ciki. Na buɗe nan in ciro kuɗi, in buɗe can in ciro haka na harhaɗa harda ƴan kuɗaɗen adashen dana ɗauka dama na hidimar sunanne. Na gagganɗa kuɗaɗe dubu hamsin ta wancan lokacin fa. Ni da kaina na fita na kirawo Innah, suna ta aiki ita dasu Baraka. Falo ta shigo ta zauna na damƙa mata kuɗinnan. Kuɗin cefanen abincin sunane. Yace ayi amfani da shinkafar karolai dake jingine a wancan ɗakin dama sabida sunan ya siyo. Wannan na cefanene" Ta juya kuɗin ta ƙirga ta ƙirga tace. "To gaskiya sun yi kaɗan wannan fa sai dai ayi girki ɗaya. Tunda kinsan dai ba za'ayi gajiyayyen abinci ba. Abinci za'ayi na fita kunya yaji nama yaji kayan lambu ko?" Shiru nayi daman nasan za'a rina wallahi, ko nawa aka ba innah ko ya kai dubu ɗarine saita raina. Mu hidimar sha'aninmu na Kanuri muna cin nama da abinci masu kyau sosai. Amman nasan ai in su Yaya Saratu suka iso, za'asan duk yadda za'ayi abinci dai na fita raini za'ayi kala biyu. "To shikenan dai bari su Saratu suzo sai mu yanke abinda ya dace." Miƙewa tayi ta fita ta soke kuɗinnan a mararta ta fice. Shadda na koma na samu Luba na buɗewa abun mamaki shadda mai tsada, kuma wallahi ta sha surfani na zamanin, ɗinkinma riga da zanine, rigar ɗinkin hannun fanka, Allah yasa kunsan ɗinkin? har a zanin an yi surfani mai kyau, kuma sabon samfurine na surfani dan gaskiya ban taɓa ganin irinshi ba. Shaddar mai ruwan baƙin bulu ce, sai akayi mata surfani da zare mai kamar ja, kamar kalar hoda dai gashinan. Harda takalmi na ƴan burni baƙi, da mayafinshi na yayi shima baƙi. Sai sarƙa da ɗankunne mai ruwan gwal, sai ɗan diras guda shida, rigar umma guda shida. Sai atampa dinkin riga da siket, kuma koddibuwa atampar mai ruwan ganye, da ruwan madara. Sai kayan jarirai na hanga masu tsada kala biyar, harda takalmin yara. Murmushi nayi, nayi farin ciki nayi mamaki, mijinyawa ya sammaceni, kaya yayimun masu daraja. Madallah da mijinyawa. "Gaskiya surfanin shaddarnan yayi kyau sosai Hindu. Sosai gashi shaddar mai tsadace mai gidan kashe kalace fa." Wata nau'in shaddace mai wannan sunan, wadda aka buga yayinta a shekara ta dubu biyu, ko dubu biyu da ɗaya. Nasan wasu sun santa. Mai Gidan Canza Kala" (ko wacce wasu ke kira da Mai Gidan Kashe Kala) tana daya daga cikin shaddodi mafi ban mamaki da kayatarwa a wancan lokacin. Ga yadda take da kuma abubuwan da suka sa ta shahara. Sauya Launi, Babban abun da ya ba ta wannan sunan shi ne, yadda take sauya launi dangane da haske. Misali, idan kana cikin daki ko inuwa tana iya nuna kalar kore amma da zaran ka fita zuwa cikin rana ko karkashin wutar lantarki mai haske, sai ta koma kalar shudi, ko ruwan gwal. Tayi zamani sosai wannan shaddar. Mamakin inda har aka samu kuɗin wannan shaddar nake yi gaskiya. Amman koma yayane nasan daga baya zaimun bayani. Iyakar kunya ya fiddani, ni bamma sa aka zaimun kayan fitar suna ba, sabida bashi dashi na kuma sani. Zuwa la'asar sai muka jiyo tsayuwar mota ta bayan tagar ɗakina. Can kuwa sai yara suka soma shigo da kayayyaki a buhu, buhu suna durewa a tsakar gida. A lokacin duk muna ciki an kammala aikin Baraka nayi ma Azgar wanka ma lokacin. Su Yaya Saratune muka jiyosu ana gaisawa dasu Shafa a tsakar gida. Can sai gasu da sallamarsu sun shigo. Murna da jin daɗi ya kaure, akaita raha, ana dariya. Baraka na kammala wankan jariri ta miƙa musu, sukai mana sallama ita da Halima. Dama nace Baraka ta Ɗibi abinci ta tafi dashi, Innah da kanta ta zuba mata da nama zuƙu zuƙu. Saida su Yaya sukai sallah, suna cin abinci ana zuba hirar yaushe gamo da yadda suna zai kasance. Yaya Zunaiba ce ta jawo babban buhu ƙato shaƙe da kayan maijego atampopi da kayan jariri, su omo da sabulu kuwa suma buhunsu daban tare da tawul ɗin nabkin da ledar nabkin kun tunota mai ruwan hoda, wata mai ruwan madara ko? Rayuwa kenan. Atampopi, shaddajo, materiyal, leshi sunfi kala talatin wane talatin shi kanshi Azgar ya sami riguna masu tsada ni dai bansan guda nawa ba. Harda su takalmi da jaka fa. Sai kuma kayan cin suna Yaya Sojanmu da Akaramine sukaimun. Shadda biyu, lesiri biyu, atampa biyu, komai mai tsada fa. Shaddar ta gida ita kuma wagambari ce irin ta da mai tsada. Dan a wannan lokacin wagambari sai masu kuɗi, ko mulki ke sakata me kyan kenan. To mu dama kanuri har gobe wagambari tunƙawo da darajarmu ce, hatta a bukukuwanmu na al'adu. Du biyun itace. Ga lafayu masu kyau guda uku. Atampar daya holan daya hitaget ce manyan sosai. Leshin kuma mai gidan kwamfuta da mai wuri da azurfa wanda a wannan lokacin sune abun tunƙawo da alfahari. Sun yo cefanen girkin suna da duk abinda zasu buƙata hatta da man girkin da zasu yi sun tawo dashi. Su albasa, attaruhu duka dai, Sun tawo da lemukan kwalba kiret kiret. Harda hofuna mai ɗauke da sitika a jiki dake an faɗama su Innah sunan yaron ga sunanshi nan ɓaro ɓaro a jiki, wanda za'a rabama mutane, guda ɗari da hamsin akayi. Wacce aka rubuta tayi Rayya ce. Kayan gara da ragowar sauran gudunmawowin ƴan gidanmu, da abokan arziki Innah Abidah itace zata tawo dashi. Wannan da suka tawo dashi iyakar na ƴan ɗakinmu ne, dana Innarmu, da jama'arta na makaranta. Ga zanin gado mai bargo babba sun tawo mun dashi ja wanda zan saka ranar suna in sha Allah. Su Yaya Jamila saida Nanno ta turota ganin ƙwab, uwatale ma saida ta shigo wai gaida baƙi, Nanno dai wannan karon bata shigo ba dai anci sa'a. Kuma rikici sosai take ji, sau nawa suka yi da Innah akan batun wankan jariri da ake turo Innah Dubu, ita kuma Innah ta kafe tayi rantsuwa harda dukan ƙasa ta lashe. Kusan raba dare akayi anata shirye_shiryen yadda suna zai kasance cikin daraja. A lokacin ni kuma Innah tana yarfamun kitso ƙananu namu na al'ada, ga lalle lallaɓe an ƙunsamun a ƙafafuna da hannayena. Washegari akaci gaba da hada hada. Su Yaya Saratu suka tafi kasuwar cikin Bauchi da wannan nera dubu Hamsin ɗin, Innah ta ƙara dubu talatin a kai, su Yaya sunce zasu cika ashirin ɗin ya zama dubu ɗarin. Jama'a mu riƙe zumunci gam gam wallahi. Ƴan uwa abun wuyane. Ai ko rago sukutum suka siyo da ranshi tiƙeƙen gaske, da uba uban cefane rigijib. Gabaki ɗaya matan gidan sukai cirko_cirko a tsakar gida cike da illahirin mamaki. sai yamma sakaliya motoci ƴan gida suka ƙaraso bus biyu sukayi na masu ruwa suna. A lokacin ko minti ashirin su Yaya basu yi da dawowa daga cefsne ba. Ana wani irin ruwa kamar da bakin ƙwarya suka ƙaraso. Dama tun rana ake wannan ruwan ko abincin da za'a tarbesu dashi a ruwa su Yaya Saratu suka girka. Shinkafa ce dafa duka taji naman rago. Dan sun tawo da ɗanyen naman rago him, tun jiyan suka tafasashi sama_ sama aka barshi a tukunna, ko ɗazu da suka gama girkin ƴan gida sun kuma tafasa naman gudun kar yayi tsami. Ta ɓangaren Nanno a tsaye take a tsakar ɗakinta ta goya hannayenta a bayanta, tana ji damuwa, baƙin ciki na neman rayuwarta. "Rago fa mijinyawa ya ba ƴan uwan matarshi suka ƙaro mai, banda wanda ya siyo tiƙeƙe. Ga buhun kayan cefane da suka shigo dashi fa" Innah Kulu tace. "Yaya tun jiya ake wucewa da buhunhuna. Kina gani bus biyu ƴan uwanta suka kwaso suka zo, suna cikin bus ɗinma ruwa ya hanasu fitowa. Yaronnan an gama asurceshi nace ko a ina yake samo kuɗinma oho Yaya. Amman lallai saikin tashi tsaye. Kuma muddin kika bar yarinyarnan ta tafi wankan gida, to fa an dinga tatsarshi kenan. Babu mamaki har gidannan ya siyar ya mallaka mata kuɗi, ga ɗan gwal wanda ba'a taɓa haihuwar irinshi ba an haifo" Nanno ta juyo a fusace tace. "Ruwa na tsagaitawa aje a kwaso ragunannan dukka biyu, da cefanen da suka shige dashi a ruwannan ɗazu. Ke Zakiya a ruwannan kije ki nemo mun Magawata yazo yanzu yanzunnan. Zan iya mai baki in bai yi wasa ba" To jama'a da alkhairi. Sai mun haɗa ranar litinin in muna cikin masu rai da lafiya son so💪🏼💪🏼💪🏼💪🏼💪🏼 Mrs BukhariMRS BUKHARI ............. *Wai kina da labarin Gidauniya ta mata, farin cikinsu, da walwalarsu, mai suna *MURYAR MATA (FARIN CIKIN AL'UMMA)*🧕🏻👩🏻‍🎓 *Wanda ni Mrs BUKHARI muka yi haɗin guiwa wajen buɗewa, tare da sauran shuwagabannin Taskar Badiat Ibrahim?* *ku matso kusa ki kasance a cikin wannan tafiyar ta Alkhairi, tafiyar da zata gyara rayuwar Aurenki, tafiyar da zata gyara miki tunaninki, tafiyar da mace zata gane ni'imominta, tasan kima da darajar kanta, gidauniyar da zata koya miki sana'ar da zaki dogara da kanki, gidauniyar da zata koya miki tattalin uwar kuɗin kasuwancinki, da yadda zaki tattali ribarki ta yadda zaki ƙarfafa kasuwancinki, sha'awar son komawa makarantar addini, ko na boko kike so? To biyomu muje wannan gidauniyar taku ce mata, gidauniyar ta ƙunshi abubuwan da zatonku ma bai zata ba.* *Ga lambar wayata ga matan da basa cikin Taskar Badiat group 1 group 2 group 3 sai kui mun magana in sha Allah zaki kasance a cikin wannan tafiyar ta manyan mata* (08179523215) *Ƴan taska kuma zaku iya tuntuɓar Admins ɗinmu ta pc domin kuji yadda tsari da dokokin kasancewa memba a cikin wannan shahsrarriyar, garnaƙaƙar gidauniya wacce ta haɗa manyan masana zamantakewar aure, malamai, manazarta, mahukunta, ƴan gwagwarmaya, masana ta ɓangaren gyaran aure, ƙwararrun ƴan kasuwa, da gogaggun ƴan boko, wanda ya haɗa matan arewanmu da kudunma baki ɗaya, zamu kasance a duk faɗin Najeriya da izinin Allah* *Hindu ma tace mata mu farka, musan menene yake mana ciwo, kuma tana sa ran za'ayi wannan tafiyar tare da'ita*💪🏼💪🏼💪🏼💪🏼💪🏼💪🏼 Zakiya ta miƙe a ruwannan ta tafi kiran Magawata. Fitarta ke da wuya, ta tarar dangin Hindu sun soma shigewa ciki a guje, ga kaya niƙi_niƙi sunata shiga dashi. A madadin ta wuce aiken da akayi mata, saita ja tunga har saida taga sun wuce kaf ɗinsu, ga kayayyaki sosai wanda suka tawo dashi. Gasu da yawa sunfi su ashirin, ko wacce kuma cikin shiga ta kece raini. Sai ta gansu kyawawa dasu tamkar wasu halittune daban. Tana tafe tana girgiza kai. A zauren samari na ƙofar gidansu Qasimu Yaya Zakiya ta tsaya. Aiko alai mijinyawa yana ciki, kiranshi tayi suka fito tare jikinshi a mace. Suna zuwa ƙofar gidansu Innah Abidah tace. "Yauwa Magawata ga buhunhunan kayan abincinnan shige mana dasu, mai motan sai ya taya ka" "To Innah. Yaya Zakiya kije ganinan zuwa" Ya saɓi buhun shinkafa irin mai mudu tamanin ɗinnan yayi ciki, mai mota ya biyoshi da wani irinshi a kafaɗa. Nan fa kallo ya koma Sama, sai ga Uwatale tsulum_tsulum a cikin ruwa ta fito ganin abinda a rayuwa basu taɓa gani ba. Manja wannan babban galan mai ashirin aka kawo mata, haka ma mangyada, maggi mai tauraro katan guda. Haka akaita shigewa da kaya, saida aka gama mijinyawa ya shiga ɓarayin Nanno. "Wallahi Nanno ke kinga kayan garar da suke ta shigewa dashi kuwa? Ahh dole Hindu ta raina mutane ta dinga musu kallon waɗanda basu san abinda suke yi ba. Gaskiya iyayenta haƙiƙa suna da arziki, shi yasa gaskiya girman kanta yayi yawa. Maganar gaskiya Aurennan nasu bama su dace da juna ba sam. Shima Mijinyawa dole ya liƙe musu suna nuna mai gadara, shi yasa ma ya kuma siyo musu rago sabida ya nuna kalar tashi gwanintar" Kanshi kawai ya girgiza, Uwatale kenan bata so aso Hindu kona misƙala zarratin, ya rasa a duniya mai Hindu ta tare mata. Kishi take yi da'itane. Ko ko dai a yanzu tana sonshi ne ba Nawata take so ba? Shi ya kasa gane irin wannan bita da ƙullin da Uwatale take ma Aurensu, da irin yadda take yi mai wani kallo in suka haɗu, shine ma yake dakewa in ya ganta, baya sa fuskar wasa sam. Da sallama ya shiga ɗakin Nanno na tsaye ta kasa zama sam. "Kaje yannzunnan dukka raguna biyunnan ka kawomun su da hannunka. Da cefanen da kaba ma ƴar gwal ɗiyar ƙaruna ƴan uwanta suka je suka yo, sabida ka nuna musu ni bani da darajar da zan hanaka, ko in sakaka. Yara nawa ta haifa da zaka siyo raguna har biyu gabza_ gabza. Sannan nace maka abincinnan Yayunkane zasu yi dukka dana Uwatale. Yayan naka ma Nawata, kaga nashi cefanen ya dure mun ka gansu nan, tunda shi ai ya auro matar da yafi ƙarfinta ba ita tafi ƙarfinta ba" Ya juya ya kalli cefanen. "To ragon da za'a yanka ma gashinan a ɗaure a ƙofata nan ya kawo, ya gwadama a aikace ya fika sanin darajata. Kayan suna da za'a kaima uwatale na ɓangaren miji. Ka gansu a leda ya kawo mana, zamu gagganda da abinda maƙota, da ƴan uwa suka kawo asa a bawo akai, ashiri duka ya rufu. Amman kai da ka kake komanka tamkar baka da iyaye, wallahi ragunannan dukka biyu sai an kawosu, da duk abinda kasan ka kaima Hindu na suna, kuɗi ko sutura saika karɓosu. Ai dole kasha wahalar aure, ganin uban Hindu ya tabbatarmun bata fito gidan tarbiyya ba. Ni dai hana ƙarya lokacin da turawa suke ɗaukar yaranmu su sasu a makaranta, na taɓa ganin turawa da irin hularshi da wannan zanzaron. Ya dattijon mutumci zai sayo ƙananun kaya, da hula irin wannan da zanzoro ya fuskanci surukai. Banma taɓa ganin uba yazo barkar ɗiyarshi ba, ai ko uwa in ido da kunya bata zuwa, sai dai kishiyoyinta suje. Sai turanci yake yi shi ga ɗan boko ko ince ɗan duniya, dan yafi kama da baduniye" Kallon Nanno kawai yake yi, yana tunanin shi yaushe zai taɓa iya burgeta. Me zai yi ta soshi, menene laifinshi ya roƙa a yafe mishi. Mai Hindu tayi musu, laifinta shine tana sonshi, tana tattalinshi ta yadda ta rayu dashi duk runtsi? Kawai sai yaji damshi a kumatunshi. "Kinga wai kuka yake yi. Ai wallahi in kukan jini zaka yi sai an karɓo komai, ni da kaina zan karɓo bama sai yaje ba. Babu mamaki sabida kin sako uban Hindune yake wannan kukan. Tunda kowa tsoronshi yake ji, shima jikinshi ai har rawa yake yi daya ganshi. Kai dai baka san darajarmu ba sam" Cewar Yaya Jamila fa kenan. Innah Kulu tace. "Abi a hankali dai. Kai kaje ka kwaso komai kamar yadda kyatumarka ta faɗama shine kawai" Kafin yace wani abun sai ga Nawata da nama cikin leda mai zane. "Ga nama na ƙaro sabida naga dangin matar Magawata yawane dasu kamar tsaki, su kuma ƴan birnine yanzu sai su raina duk abinda za'ayi na ƙoƙari" Da idanu Mijinyawa yabi abokin tagwaitakar tashi yana mai kallon tsam ko zaiga wani abu daya rabasu domin ya ƙaryata su ƴan biyu ne, ya kuma ƙaryata ɗan ɗakin Nanno ne shi. Sai dai kash basu da wata maraba saita hasken fata shima kaɗanne, sai ƙirji him daya fishi, shima ba haihuwarshi akayi dashi ba, shi ya gadarma kanshi a sakamakon yawan karance_ karance littatafan Hausa, musamman na soyayya. "Kagani ko, kai kana nan ka siyo nama dan ka rufama ɗan uwanka asiri. Shi kuma rago ya kuma basu kuɗi suka siyo. Dana karɓi cefanen nace ayi girkin tare, sai ya basu suka siyo wani baka ga kaya ba him" Buɗar bakin Nawata yace. "Sabida baka da hankali rago fa. Kai wai me Hindu tayi ma ne? " "Sabida bani da hankalin. Kai wa ya tambayeka mai uwatale tayi ma. Uwatalen da kowa juyawa take yi a cikin gidannan. Take mulkarka, sai Hindu itace karkatacciyar kukarku. Me muka yi muku ne, in bakwa son ganinmu ku bamu dama mu bar muku gidan mu huta ku huta na roƙeku. Tura tana neman ta kaini bango. Nanno ya kamata a dinga tausayamun, kuma a dinga bari anajin ta bakina koma yayane. Wallahi ni yanzune dana shiga naga ragon. Bani na basu kuɗin ba, kuma bani na ba da kuɗin cefane ba, wallahi bani da ko sisi. Ina naga kuɗin wannan hidimar, yaushe na soma fita aikinma da har zan samu kuɗi haka. Ko cefanen da kika karɓa, su Qasimu ne ƙarfin siyayyar" Uwatale sai baki take buɗewa, itace harda salati da tafa hannaye. Mari yaji tau a fuskarshi. Yana juyowa yaga jamila ce ta mareshi. Ai sai kawai yasa hannu ya rama. Itama taji tas a kumatunta. Da mamaki ta dubeshi, Nanno ta fashe da kuka wiwi. Nawata kuma ya rungumeshi da dambe, ya dira a wuyanshi. Ai kuwa dambe gagarumi ya kaure a tsakaninsu, dake dama ran mijinyawa a tunzure yake, Mijinyawa ya dinga naushin Nawata iyakar ƙarfinshi harda fasa baki. Ruƙunƙumeshi Nawata yayi ya runtumashi da ƙasa rim, nan suka hau birgima yana koƙarin cirema Mijinyawa kunne. Dan kunnenshi ya riƙe yake fisga. Yaya Salihu da Qasimu ne suka shigo a guje, Nanno kuwa Zakiya ta riƙeta tana ta kuka harda doka ƙafa kamar yarinya. Innah Kulu sai bari_bari take ma su Magawata., Innah Dubu ba shiri ta saki abunda take yi ta garzayo. "Haba nagaji ya isheni. Cikinku babu wanda zai iya haƙurin da nayi da irin abubuwan da akemun nifa kullum mai laifine fa" Marinshi Yaya Salihu yayi. Nanno tace. "Ka ƙara mishi" Ya ƙara mishi, "Ka kuma ƙara mishi nace, dan abu ta kazan...." Ya ɗaga hannu zai ƙaramai dashi da Qasimu suka riƙe hannun carab. Idanun mijinyawa ya tara jini sakamakon naushin da Nawata yayi mishi a ido, kanshi ma ta gefen wajen ciwo yake yi. Hannunshi ya zare, ya bar Qasimu riƙe da hannun Yaya Salihu, wanda yayi saurin fincikewa. "Kai Qasimu fice ka bamu waje, ashe kaima baka da mutumci. In Bala ne zaka riƙe mishi hannu in yana dukanka ne? " "Aa bazan riƙe mai ba. Sabida bazai mun dukan zalunci irin wannan ba. Magawata wuce muje, ka barsu suje su ɗakko, tunda kai basu yadda da gaskiyarka ba. In sun basu shikenan. In basu basu ba shikenan" "Amman Qasimu danme za'aje a tsinkata a gaban danginta alhalin bani na siya musu komai ba, wanda na siyo an kwace. An taru fa danginta bus biyu rigimace kawai dai za'a ɓalle ba za'a bar zuchiyata ni ta huta ba" "Wallahi sai mun karɓo. Kuma sai kayi nadamar wannan marin da kayi mun" "In baki yafe mishi ba, nima ban yafe mishi ba" Jin wannan furuci na nanno ya kassara mijinyawa sosai. Babu shiri ya zube a guiwa yana roƙon gafarar Yaya Jamila. Aka kaɗa, aka raya, da ƙyar tace ta yafe mai. Qasimu da yazo har wuya ya finciki hannunshi suka fice. Suna fitowa motar ƴan Maiduguri na ƙarasowa suma a cikin wannan ruwan. "Qasimu yanzu haka zasu je su tsinkamu Hinduna a cikin taron dangi irin wannan. Ya kake tunanin zata ji? " "Ai bazai kwatantu ba yadda zata ji. Nasan rikici har maƙota tsakaninsu, amman da Innah Yahanasu kaima ka san bama zaka ji muryar Hindu ba, sai dai a assasa mata wani baƙin cikin, da makarai zasu doketa ƙilama ayi sunan bata ma san inda kanta yake ba. Zan baka shawara duk runtsi muddin Nawata yasa ƙafa ya ɗauki tsinanniyar Uwatalennan suka koma birni, to tabbas kaima ka kama hannun Hindu da ɗanku ku ƙara gaba. In sama da ƙasa zata haɗe. Nasan haka Allah ya halicceka da sanyin hali, rauninka yana da yawa. Da rauninka Nanno take amfani tana sa ƴan uwanka su tozartaka. Kayi haƙuri watarana sai labari. Muje ƙarƙashin bishiyarcan mu jira zuwa da dawowan yau ruwannan a kanmu nasan zai ƙare. Yaƙin duniya dai suke son tayarwa. Ji irin rikicin da akayi akan wankan jariri ma. Wai kasan yadda na tsani Uwatale haka na tsani mutuwata. Ni zarginta nake yi ƙila yanzu tana sonka ne, sakamakon yadda kake kyautatama Hindu, da soyayyarku. Ada tayi tunanin ba lallai ka samu kamarta ba, sai gashi Allah ya musanyama da Hindu mace wayayya, ƴar birni, mai ilimi. Shine cutar hassadarta ta tashi, ta lashi takobi akanku" Hannunshi ya ja zuwa wannan bishiya, ruwa akeyi a jiƙe suke kashirɓan, yadin jikinsu duk ya maƙalƙale a jikinsu dama ba nauyi ba. "Wai sun san da sunan da akaima yaro huɗuba?" Qasimu ya tambayeshi. Yana goge idanunshi wanda ya tara jini dan sai ruwa yake yi yace. "Ai Nanno ta mance bata tambaya ba. Babu wanda ya tuno. Itama Uwatale bata tuno ba, data tuna musu tunda itace annamimiyar da take son tarwatsamun gidana. Nasan akan sunanma sai Nanno taji dalili. Balle wancan yaso mu sama yaran sunanmu" "Wanene wancan kuma? Qasimu ya tambayeshi. " Wa kuwa In ba Nawata ba" Dariya Qasimu yasa yace. "Ja'iri ai ya daku. Gara daka turmusheshi wallahi, ni wallahi naso kaita dukan hancinshi da bakinshi, kai mishi irin jina jinannan" Dariya suka yi, amman fa zuchiyarsu cike fal da damuwa ainun. Hindu:. Ana wannan ruwa muka jiyo sallamarsu Innah Mairamu, dasu Innah Abidah, da ƴan gida harma da waɗanda in ba dole ba bama magana, amman duk sun harhaɗo sun zo. Wallahi kuma nayi farin cikin ganinsu, baka sanin yawan dangi na da amfani sai kayi aure, sai kaji kana alfahari da yawan danginka. "Ahh sannunku Abidah kun ƙaraso, anata ruwa haka dai muke ta aiki a ruwan ma. Sannun ku da zuwa kun riga ƴan Borno isowa su da sukace asubar fari zasu tawo, a hanya ma zasu yi sallah Asuba" Innah Abidah dake ta faman kalle_ kalle ko magana ma ta kasa yi, sai da Innah mairamu tace. "Magana fa akeyi. Ai Yaha mun sha hanya. Ga hanyar shigowa nan ɗin bata da kyau sam. Ga laka motarmu sai cijewa take yi. Ai dake lokacin da muka kawo ita Hindun da ranine hanyar bata kai haka lalacewa ba. Hindu ina sabon maigida?" Sannunku Innah Mairamu. Kun shawo hanya ga ruwa." "Ke Halima ku shige ɗakin can na gaba, nan ɗin duk ya cike. Hindu sai fa an nemo musu matsugunin kwana, amman a yanzu dai haka duk zamu zauna." Cewar Innah Yahanasu Nan aka rabu, duk ɗakunan an cikesu maƙil da jama'a. Gida ya kaure da hira da abubuwa dai na ƴan uwa. Tunda na miƙa Azgar na fito zuwa barandar da su Yaya suke suna ta zuba abinci tire _tire ga nama nashasha. "Hindu za dai a samu masauki ko a wajen Baraka ko? Kinsan ba zasu so su yi nisa ba?" Za'a samu duk a maƙota da za'a saƙasu. Su innah Mairamu su anan zasu zauna ne?" Kafin inyi magana Innah Abida ta fito. "Zanje direba ya shigo da kayan kawai in an samu matasa sai su kawo mai. Hindu ashe kayan ɗaki kika sauya haka uban ubansu? Gaskiya mijinki yayi ƙoƙari gaya irin wannan kaya a ƙauyennan ai ko a birni sai haka. Nace amman a Bauchi aka siya ko, ko dai daga Kano ne?" Ta kakkafeni da idanunta. A Bauchine" Na faɗa a taƙaice. "Ai ashe Bauchi za'a iya samun irin wannan kaya na zamani haka, gaskiya ya gwangwajeki, ai da gani zasu yi tsada dai. Ta ƙarashe tare da ficewa a guje. Ni dai cikin ƴan uwa na koma ni da Luba muna gado, Azgar dai yau zai sha ciwon jiki gaskiya. Ga hayaniya yau dai yasan yazo duniya, ya faɗo a ɗan dangi. Anti matar Yaya Sojanmu ce tace. "A miƙa yaronnan haka Fatima yasha ɗauka" Fatima tace. "Ai da su Murja zan kaima shi suna ɗayan ɗakin" "Ana ruwannanne zaki fita da jinjiri ai bazai ma yiwu ba" Inji Rayya" "To rasa kunya. Gashi Hindu kwantar dashi" Sai Luba ce ta karɓeshi, na kalleta na watsar, ni dama tun tasowarmu Fatiman Lungun Baba Doraga bama shiri sam. Ficewa tayi a ɗakin. "Ai gara kije, ni banso ma ta biyomu ba wallahi" "Zainab ɗin Baba Lukumanu tace. " Maza ki bari uwarta Innah Yabi ta jiyoki wallahi" Ni dai kallonsu kawai nake yi. Yaya Zubaina ce ta shiga miƙo turen abinci. "Saura ɗaya Zubaina anan ciki" Cewar Anti, saima ta tashi ta fita kawai karɓowa. Can sai muka jiyo sallamar Su Yaburra dasu Falmatan Innah Yalewa, dasu Fannah, da Yakura. Sai sabon murna da yaren Kanuri kake ji yana tashi. Falmata ƙawatace ai tana shigowa ta haye gado da goyonta. Hamshaƙi mai kuɗi take aure, tana zaune a Chard. Ita dai tsiyarta bata hausa sai yare. Inajin komai, amman amsar bana iyayinta zur zur inta yi, sai dai ingausa dai. Amman nafi Mrs BUKHARI, ita iyakarta gaisuwa da yaren Kanuri. Nan aka shiga hirar zumunci ta rungumeni sai ƙamshin kabbasa take yi, ta ci lallen gargajiya ga kitsonta na gaɓa yis_yis_yis. Kiran Innah Yahanasu naji, na fito da sauri Tana tsaye ita da Innah Yalewa kamarsu ɗaya sak tamkar ƴan biyu. Rungumeni tayi tace. "Kajinya" Kalmace ta nuna tsananin ƙauna. Annuri kawai nake yi, naga dangin Innarmu cikin ummansu sunyo tattaki domin nuna ƙauna da ƙarfafa zumunci. "Yauwa uwar ɗakinnan naki dole mu za'a barma, kinga iyayen gidanku sun haɗu a can ɗakin, su Yabi da Abidah, yaran matan aka bari a naki ɗakin. To uwar ɗakinnan mu zamu mamayeta sabida tattaunawa ta musamman. Ga niƙan sunasun ɗinnan wa zai kai. Da niƙan kayan miya, ko bari zanma Baraka magana ta shiga gaishe da su Abidah. Kó dúa ganyí, Yaya ( ko ba haka ba Yaya) Ta tambayi Innah Yalewa. Kai ta gyaɗa tace "Hárúgú tàvás ( hakane tabbas) "Fáto adə́ sáwábe kárgá-bé-rSync kózə́ndé shíoró landányé. (Su bar mana ɗakin ko dan mu yi hirarmu ta zumunci) Muna cikin wannan magana, ni ina daga dokin ƙofa, su Innah Yahanasu suna daga waje. Sai ga Yaya jamila ta shigo. " Baraka kinga niƙannan na bokatannan uku muke son akai a niƙo mana yanzu. Sai kuma inda za'a aro tukwanen girki manya manya" Cewar Innah Yahanasu data watsar da Yaya Jamila. "To Innah, bari a kira yara su zo su ɗauka. Hindu ni kam na tafi, gobe da asussuba sai in dawo. Masu zuwa kwana kuma zuwa dare Qasimu zai zo ya tawo dasu in sun gama hirarsu" Tana sa kai ta fita sai Yaya Jamila tace. "Ke Hinduwa shiga ki kwasomun kayan da Magawata ya kawo miki na barka. Da cefanen da aka baku kuɗi kuka yi na fitar suna. Wannan ragunan kuma zan wuce dasu. Kai Nawata shigo mana kake tsaye kazo ka sunce mun ragunannan du biyun" Cike da hadara da taƙama irin ta dangin miji, isar rashin isa kenan, har wani daddaƙile wuya takeyi. "Wacece wannan haka take magana da isa da gadara? " Cewar Yalewa. Ni mamaki ma yasa motsi wannan na kasa, har Nawata ya shigo ƙebe_ ƙebe ya kama igiyar rago. Aiko farantin dake hannun Innah yahanasu ji kuke ƙwal a hannun Nawata. Ba shiri ya saki igiyarnan, yana yarfe hannunshi. "Ubanwa ya aiko ki maras kunya fitsararriya? Ke na lura baki da kunya baki da mutumci, hala dai bazawarace ko, kin kasa zaman naki gidan shine kike baza mulkinki a kan matan ƙanne? Ke Hindu wannan ba mijinki bane? Duk da naga ba kwalli a idanunshi" "Yayanshi ne, shi yana waje. Sannan mahaifiyarmu ce ta aikomu mu kai mata komai da komai" "Tunda ita take aurenta ai dole ta aikoku, to kuje ku faɗa mata babu mahalukin da a wannan duniyar ta maliki yaumuldin daya isa ya kwashe ragunannan ya kai mata. Ko shi Magawatan yake ko magarana ne bai isa ba. Na fiku tauri da zafi wallahi" Ni dai ina tsaye ina waige. Aiko sai gasu Innah Abidah, da Innah Mairamu, da Innah Yabi, sun fito. Idanu na lumshe kawai na buɗesu akan Yaya Jamila dake cewa. "Ai kuwa dole mu ɗauka wallahi. Nanno ta isa da ɗanta, kuma ta isa da kayanshi. Ke baki haihu bane ko baki san yadda uwa tak.... " Tas Yaya Saratu ta ɗauke Yaya Jamila da mari. Marin da ya zama, wasila ta janyo hankalin ɗaukacin ƴan gidanmu. Su Innah Yalewa dama su suna tsaye. Dasu Yakura, da Fannah Innah Abidah tayi saurin shiga tsakanin Yaya Jamila da Yaya Saratu. "Kinmun daidai. Kai kuma ƙaton banza zo ka wuce kafin insa a tuɓemun kai wallahi, aita dukanka kamar kwarto" Ai ba shiri ya tsallake ya fita. "Menene yake faruwa baiwar Allah yi mun bayani. Ke kuma Saratu haka akeyi zaki zo ki haddasama ƴar uwarki fitina a dangin mijinta." "Haka fa, ai dama zaki aika Abidah dole kice haka ai. Munafuka kawai mai hassadar tsiya. Kema maza kizo ki fice kafin in saka wannan yaran su miki na jaki. Maras kunya kawai. Yanzu in saka Yanuna tai miki duka" "Ai wallahi sai an bamu kayannan. Ke kuma zaki san kin daki jamil... " Ai bata ƙarasaba Yaya ta dira a wuyanta ta ruƙunƙumeta, Falmata ma ta mara mata baya. Dambe ya kaure ya kacame. Aka hautsine, kowa ya firfito daga masu taɓe baki, sai masu murna, da masu alhini. Ni dai ina tsaye kawai kamar dutse. "Kai subhanallahi. Yalewa ke kizo mu saka hannu. Fanna kuyi mata magana ko zata ji karta kashe ƴar mutane fa, kunfa san Saratu sarai akan batun dambe, dama ita bata cacar baki tun da can" Ai kafin kace kwabo an cika ɓarayinnan maƙil da ƙyar su Nanno suka kutso kai suka shigo tsabar cikowa. Da ƙyar su Khadija da Anti suka raba faɗannan. Duk su Yaya sun farfasama Yaya jamila baki, Yaya ta kusan cire mata kitso ɗaya. Dan janshi tayi ya ɓanɓaroshi. "Ya salam ke Nanno menene yake faruwane yara sunce ke kika aikosu menene kiyi mana bayani dallah_dallah" "Wanda zaku ɗauki rahoto ba. Ai sai tayi miki bayani ki bata amsar daya dace Abidah. Uwargidan janaral. Ai batun ayi bayani kike yi, to ke Nanno yi mata bayani." Innah Abidah dai bata ce komai ba, sai Innah Kulu ce tayi mata bayanin raguna, da cefanen suna aka aiko su Jamila su karɓo, da kayan barka da mijinyawa ya ba Hindu. "Haba dai an taɓa yin haka ne ace baza'a barmu muyi abincin suna da kanmu ba. To menene amfanin yawanmu. Shin ko al'adarku ce ta baku wannan damar ai sai mu sani ko Mairamu? " Cewar Innah Abidah. Yalewa ce ta karɓe duk da hausarta bata da kyau tana mayar da mace namiji, namiji ya koma mace. "Ai ko al'adarsu ce ta basu wannan damar, wallahi bama za'ayi wannan aikin ba. Mun yi musu kala da waɗanda zasu ma girki har muci? jibesu ƙazamai gidadawa dasu, tama ina za'ayi haka. Ke tsohuwa kuje dai yaro ya baku kuɗin cefanen abinda zaku dafa, ba dai wanda zaku dafa mana ba" Innah Yahanasu zata yi magana. Yalewa tayi mata yare ta yi yare, sai ta ja ta riƙe ƙugunta bata ce uffan ba. Sai hura hancinta take yi. Uwatale a guje ta shigo, tana dube_ dube. "Shin wannan ragon da aka ƙaro da cefanen da aka shigo dashi Mijinyawa ne yayi ko bashi yayi ba? " Cewar Innah Kulu. "Shi yayi mana wa zai mai. Kuma in kuna tunanin wata gwanintace, mu kam mun raina. Kune matsiyata da har kuke ganin ɗanku wata bajintar yayi, wanda har kuke jin hassadarku ta motsa ku bama zaku iya haƙuri ba. Kuma Munci kayannan sai dai ku mutu wallahi ƙauyawan banza da wofi." Nanno da kanta ta ja ragon, Innah Kulu tace Zakiya ta kinkime kwandon tumaturinnan. Nan rikicin ya samo asali. Nanno ta ja ƙafar rago, Innah Yahanasu ta ruƙe ƙahon ragon suka shiga jani in jaka. "Cika tsohuwa" "Bazan cika ba sai na tafi dashi" Zakiya da zata ɗauki kwandon tumaturinnan, Fannah sai ta dafe. Tana fincikan kwandon Fanna da Rayya na fincika. Nanno saida ta karya ragonnan ɓaras wallahi sabida yadda take ja, Innah Yahanasu na ja. Rago sai kuka kawai yake yi. An cika danƙam su Uwatale ba damane. Ai Innah saita saki ragonnan da Nanno da ragon suka tafi suka faɗi rigija. Innah tayi kanta ta kinkimeta, na faɗa muku ƙatuwace ta jefata cikin kwanukan wanke_wanke ji kuke kwakwaracam. Kuka Nanno take yi wiwi. Kanta saida ya daki gini ƙum, tana nunoni tana cewa. "Kina gani Hindu abinda duk akeyi akan ki ko?" Innah Kulu ma zata je ɗagata Yalewa ta tareta ta hanata wucewa ta ingizata taje ta daki buhun shinkafa da bayanta. Nan ta shiga haki. Ta damƙo Zakiya ta danna mata kai cikin tumaturinnan dake kwando. Da ƙyar su Anti suka ceceta, Yalewa ta daketa a ƙirji tab. Akaita rikici da dambarwa da su Yaya Jamila, da su Innah Yalewa da ƴan ɗakinmu, ragowar ƴan gida sai kallo, su Innah Abidah dai suna ta hanawane, amman Innah Mairamu wallahi gefe ta ja sabida wai ta riƙe Jamila ta fincike, wai kar ai mata illah tana fama da ƙafa. Matar Yaya Sojanmu itace gaba wajen ba da haƙuri. Sai maƙota dattijan da suke ta ƙoƙarin yayyafama ƙurar ruwa, suna nusar da Nanno hakan ba daidai bane. Koma menene da Mijinyawan akasa ya karɓo da kanshi duk ba ayi wannan rigimar ba, an riga da an zama ɗaya. Rikici fa yaita ƙamari, dokanni in doka ƙaƙas tsakanin dangina da danjin Mijinyawa. Kwandon tumaturi ɗaya ma an yi kaca_kaca dashi. Rayya ta jefa Uwatale kan attaruhu, sukaita murginawa, a ƙoƙarin uwatale na ceton ranta ne, duk tayi watsi da tumaturinnan, jama'a suka tattake. Akaita abu ɗaya, Jama'are ta ɗauka, al'umma a ƙofar gida tamkar ana yaƙi. Wannan rana tana daga cikin ranakun da bazan mancesu ba abadan, tana cikin ranakun baƙin ciki, da jin kunya mai ƙarfi a gareni. Ba abu bane mai sauƙi ba, lamarine wanda bazai kwatantu ba, amman ku hasaso ace rikici da doki in doka harda suruka, ga Innah Yahanasu itama ta ɓalle rikici duka kawai take kaiwa, ya faɗa kan mai rabo. Innah Yahanasu da Innah Yalewane suka turasu waje, koma ince suka watsasu waje suka danna sakata a ɓarayin nawa. Nanno sai kukan mutuwa take yi. Maƙota dasu Shafa suna ta rarrashinta kamar wacce jaki ya doka da ƙasa. Duk wannan fa abun ina tsaye ni da Luba Azgar yana rungume a ƙirjina. Bakina ya kullene, na kasa furta kalma, da idanu kawai nake bin mutane nayi_ nayi in buɗe bakina na kasa, sai kawai na haƙura nayi shiru. Amman ta ciki zuchiyata ci take kawai da wuta wallahi. Ƴan gidanmu sai ƙus ƙus suke ta faman yi, sun harhaɗe kansu anata sharafin gulma dama itace ta kawosu, Nanno ta basu akan sari. Shikenan sai an shekara fin nawa duk wani taro da za'ayi suna ko biki, sai an jaddada labarin wannan rikici tamkar lokacin abun ya faru. Balle Aurena da ƙiris ake jira aji yayi targaɗe, sai gashi sun tadda karaya. Wannan abune da bai taɓa faruwa da wata ƴar gidanmu ba, ace tana da babban saɓani da dangin miji irin wannan ba, ace har ta kai ana faɗa harma da suruka a ciki ba. Sai akai na Hindu ya faru. "Aikin banza da wofi. Ke buɗemun ƙofarnan duk wacce ta isa ta sake shigowa, in bansa itace na gabɗeta ba wallahi. Ku kuma munafukan banza duk kunyi cirko_cirko sai ƙus_ ƙus kuke yi, an samu nayi madadin ku shigo ko ayi daku ko ku raba, aa kuna tsaye kuna ɗaukan rahoto. Ke kuma Abidah burinki ayi miki bayani ta yadda zaki samu abun faɗe da hujjarki. Kai tur Allah ya sauwaƙe." Innah Yalewa itama da yare take tata maganar tana zaginsu Innah Abidah, dasu Nanno. Abun baima Innah Yahanasu ba. Sakata ta zare ta fice babu ko mayafi a kanta. Yaya da Yalewa suka bi bayanta Nima dolena na fita, ko takalmi babu a ƙafata ga ruwa anayi. Ashe waje ta nufa, a ƙofar gida ta tadda Nanno ta tusa Mijinyawa tana kuka tana bashi labarin abinda akayi mata. Kuma cefane yace bashi yayi ba ashe shi yayi. Yana kan rantsuwar bashi yayi ba Innah Yahanasu ta isa wajen. "Kai kayi mana yaro faɗa mata gaskiya, ita gaskiya ɗaya ce, ko babu hakkin wannan a wuyanka ne? Sannan wallahi ke ki kiyayeni ina faɗa miki kenan. Muddin ƙafarki ta sake takowa ɓarayin Hindu da sunan neman fitina, wallahi saina ɓallaki kamar yadda kika ɓalla ragonnan. Tunda na lura ke ba tsohuwar mutumci bace. Madadin kece mai hanawa, aa kece kan gaba wajen ƙulla wutar rikici kina wai uwa, anya ma yaronnan ke kika haifeshi kuwa? ." Tana yi ne fa tana dungurema Nanno kai har sai da Yalewa ta ƙarasone ta shiga tsakani. Nanno ta wani fashe da kuka, tana girgiza kanta. Ni dai mijinyawa na kalla, ya dubi ƙafata ba takalmi, gani ba mayafi, ga ruwa anayi. Kawai sai ya lumshe idanunshi yana tausata ta idanunshi. A fuskata bazai iya karantar komai ba, kadaran kadahan. Kunyatace an riga da an kunyatamu, an kwaye mana baya, sai nake ji abinda ya tafasa to yama daɗe bai ƙone ba. Da ace bakina ya buɗe da su Jamila zasu yi mamakin maganganuna, Ita nanno uwace na barta a hannunsu Innah Yahanasu. Nanno sai girgiza kai take yi. Mijinyawa ya ɗago yama kasa ɗagowa sam. Qasimu ne yake ta ba da haƙuri. "Dan Allah ayi haƙuri. Nanno, Innah ku yi haƙuri. Ke kam damo sarkin haƙuri Hindu bamu ma da kalma, Allah yai miki albarka. Innah ku shiga da'ita ruwa sai taɓata yake yi, ga babu takalmi bare mayafi a jikinta." Sai lokacin ma suka ankara dani, da ƙyar ya lallaɓasu Innah Yahanasu muka shigo ciki, nanma sai da ta bangaji Nanno ta kusan faɗuwa, Qasimu ne yai saurin tareta. Innah na riƙe dani tana ta faɗa. Ni dai basu ji ko tarina ba. Ɓarayin nawa shiru ko tari ba'ayi, kowa yayi jigum. Inaji ina za'ace ƙasa ta tsaye in faɗa da yafi mun. Illahirin kunya. Baraka ce ta shigo da ƴan matasa suka ɗauki niƙa kayan miyanma saida aka kuma wankewa. Tumatur kwsndo guda anyi asararshi shi kam. Innah Yahanasu tace wasu su bi Baraka gidan yayi kaɗan. Ɗuuu suka bita, su Innah Abidah dai suna falo su huɗu iyaye. Sai su Khadija a ɗakin ajjiye abinci. Su Yaya kuma sune zasu kasance a uwarɗaki tare dani. Amman suna tsakar gida. Ni kwantawa nayi na rufe idanuna kawai. Luba na gefena tayi tagumi kuka take yi kamar ranta zai fita. Yaya ma tayi kuka sosai Anti, ce tai ta basu haƙuri dai. Sai tashi nayi naga gari ya waye harya soma haske, kwana akayi ashe a tsaye a kaina. Da magriba rikici da dawo sabo, sakamakon dangin Nanno da suka zo, ai labarin abinda ya faru shi ya tunzurasu, nan akaita ɗauki babu daɗi, ni kuma magashiyyar a sandare ma aka shigo dani, ina ihu da fiffusga, wannan kenan. Ga ƙamshin girke_girke ina jiyowa da hayaniyar mata a tsakar gida. Makarai sun yi nasu aikin. Wainar duk da aka ƙarasa toyawa bani da masaniya. Yaya ce ta shigo da kaskon Turaren wuta. Innah Abidah ta biyota da babban buhu shaƙe da kayan barka. Khadija na biye da'ita da wasu kayan a leda. "Jiya husuma yasa ban samu damar damƙa muku kayan barka da dangi da ƴan uwa suka bayar ba. Kai munja galala jiya, ni dai wallahi ban yi bacci ba. Ke Saratu kirawo Yalewa dan Allah banda Yaha ni fitinarta ta isheni , jiya raba dare tayi tana mita. Bamu san yau mai zata haifar mana ba. Dan dangin mijinnan naki a shirye suke. Yaya bata ce uffan ba ta fita. Bata dawo ba sai da shayi mai zafi, ta zaunar dani.. "Sha Hindu kafin ki soma komai kinji" Banyi musu ba sabida inajin yinwa gaya. Innah Yalewa ce ta shigo. "Ga kayayyaki nan na barka wanda dangi, da ƴan uwa na cikin gida, harma da maƙota abokan arziki suka yi. Wannan kuma kuɗine gashi Hindu" Ta miƙomun su masu kauri. "Iyayenki mazane suka harhaɗa suka ce in kawo miki nasu gudunmawar kenan. Wannan kaya da suke daban gasu a hannun Khadija, Qazzafi ne yace a kawo miki nashi gudunmawar kenan, tunda har yanzu bai gaji da rigar zawayi ba. Ga buhun shinkafa uku, manja, farin mai, maggi, garin tuwo, man shanu, komai na gara dai gashinan daga dai Yayyu mazan gidan kafataninsu, kamar dai yadda aka saba wannan a kansu yake. Allah ya raya yaro da imani" Innah Yalewa tace. "Madallah Abidah angode sosai, saƙo ya iso munji daɗi sosai. To zan koma ina kan suyan Sunasun ne aka tasoni. Hindu ya kamata ki yi wanka ki shirya kafin a soma shigowa ai. Sannan kiyi haƙuri, babu komai" A banɗakin ciki nayi wanka, dole na fito a gabansu na gabatar da sallolin da ake bina. Ina idarwa Yaya tace. "Jini harya tsaya miki Hindu, ikon Allah. Haka fa Zubaina tayi kwana huɗu jini ya tsaya mata. Sanyi naji a raina. Shiryawa nayi cikin shaddar da mijinyawa yayi mun, Yaya ta miƙomun ɗan kunne da sarƙarta na gwal a lokacin babu kowa a ɗakin. " Saka wannan kimun loncin sabone na canja babu wanda ya sanni dashi" Dariya nayi na saka, nabi jikina da humra, Yaya taimun ɗauri na fito shar. Azgar shima yana kwance shar_ shar dashi yaci sabon farin seti na kanti mai kyau. Ɗaukarshi Yaya tayi muka fito falon anan na tadda su Innah Mairamu. Take kallo ya dawo kaina. Ƴan gida sai kallon wuyana da kunnena suke yi. Gaggaisawa dasu nayi, sai wani koɗani suke yi. "Su Abidah na can ɗakin sai ki shiga ku gaisa. Nima hutawa nazo yi, tun huɗun asuba muke tsugunne ana aikin abinci kala kala." Miƙewa nayi na fita tsakar gidan nawa. Ga tukwane nan a wuta. Wata lafiyayyar dafaduka naga Yaya suna juyewa a ƙatuwar fanteka. Ga Sunasunnan rabin fanteka Yalewa tana kan suya bata ƙareba. Da wannan ragon du suka yi girke_girken harda naman da suka zo dashi, naga kai da ƙafan ragon a gefe. Ga kuma ragon haƙiƙa yananan ba'a fita dashi ba tukunna. Mra Bukhari. *Wai kina da labarin Gidauniya ta mata, farin cikinsu, da walwalarsu, mai suna *MURYAR MATA (FARIN CIKIN AL'UMMA)*🧕🏻👩🏻‍🎓 *Wanda ni Mrs BUKHARI muka yi haɗin guiwa wajen buɗewa, tare da sauran shuwagabannin Taskar Badiat Ibrahim?* *ku matso kusa ki kasance a cikin wannan tafiyar ta Alkhairi, tafiyar da zata gyara rayuwar Aurenki, tafiyar da zata gyara miki tunaninki, tafiyar da mace zata gane ni'imominta, tasan kima da darajar kanta, gidauniyar da zata koya miki sana'ar da zaki dogara da kanki, gidauniyar da zata koya miki tattalin uwar kuɗin kasuwancinki, da yadda zaki tattali ribarki ta yadda zaki ƙarfafa kasuwancinki, sha'awar son komawa makarantar addini, ko na boko kike so? To biyomu muje wannan gidauniyar taku ce mata, gidauniyar ta ƙunshi abubuwan da zatonku ma bai zata ba.* *Ga lambar wayata ga matan da basa cikin Taskar Badiat group 1 group 2 group 3 sai kui mun magana in sha Allah zaki kasance a cikin wannan tafiyar ta manyan mata* (08179523215) *Ƴan taska kuma zaku iya tuntuɓar Admins ɗinmu ta pc domin kuji yadda tsari da dokokin kasancewa memba a cikin wannan shahsrarriyar, garnaƙaƙar gidauniya wacce ta haɗa manyan masana zamantakewar aure, malamai, manazarta, mahukunta, ƴan gwagwarmaya, masana ta ɓangaren gyaran aure, ƙwararrun ƴan kasuwa, da gogaggun ƴan boko, wanda ya haɗa matan arewanmu da kudunma baki ɗaya, zamu kasance a duk faɗin Najeriya da izinin Allah*MRS BUKHARI .............. *Wai kina da labarin Gidauniya ta mata, farin cikinsu, da walwalarsu, mai suna *MURYAR MATA (FARIN CIKIN AL'UMMA)*🧕🏻👩🏻‍🎓 *Wanda ni Mrs BUKHARI muka yi haɗin guiwa wajen buɗewa, tare da sauran shuwagabannin Taskar Badiat Ibrahim?* *ku matso kusa ki kasance a cikin wannan tafiyar ta Alkhairi, tafiyar da zata gyara rayuwar Aurenki, tafiyar da zata gyara miki tunaninki, tafiyar da mace zata gane ni'imominta, tasan kima da darajar kanta, gidauniyar da zata koya miki sana'ar da zaki dogara da kanki, gidauniyar da zata koya miki tattalin uwar kuɗin kasuwancinki, da yadda zaki tattali ribarki ta yadda zaki ƙarfafa kasuwancinki, sha'awar son komawa makarantar addini, ko na boko kike so? To biyomu muje wannan gidauniyar taku ce mata, gidauniyar ta ƙunshi abubuwan da zatonku ma bai zata ba.* *Ga lambar wayata ga matan da basa cikin Taskar Badiat group 1 group 2 group 3 sai kui mun magana in sha Allah zaki kasance a cikin wannan tafiyar ta manyan mata* (08179523215) *Ƴan taska kuma zaku iya tuntuɓar Admins ɗinmu ta pc domin kuji yadda tsari da dokokin kasancewa memba a cikin wannan shahsrarriyar, garnaƙaƙar gidauniya wacce ta haɗa manyan masana zamantakewar aure, malamai, manazarta, mahukunta, ƴan gwagwarmaya, masana ta ɓangaren gyaran aure, ƙwararrun ƴan kasuwa, da gogaggun ƴan boko, wanda ya haɗa matan arewanmu da kudunma baki ɗaya, zamu kasance a duk faɗin Najeriya da izinin Allah* Aiki suke ta ta faman yi babu kama hannun yaro. Ko ina hada_hada akeyi, gwanin sha'awa. Baraka ce ta shigo da ƙatuwar fanteka "Yauwa Amaryar ƙarni, ga angon ƙarni can a waje, yace ki leƙa duk da wajen cike yake dam ta taron maza danƙam, ƴan raɗin suna. Duk da haka yace kizo zaku yi magana" Murmusawa nayi. Na dubi su Yalewa nace. To shikenan bari in leƙa." Ɗaki na koma na sako takalmi da mayafin da mijinyawa ya sako a cikin wannan kayan fitar suna. Na saka kaina na kutsa mata na fito tsakar gidan. Lungunmu danƙam da mata anata aikace_aikace. A tsakar gidanma matane gungu_gungu anata aikin yankan ganye, da wankin shinkafa kowa dai da aikin da yake gabanshi. Anata shewa, gidan suna ya ɗauki harami, suma da sassafe koma ince asuba suke aikin abincin suna a gidan gaskiya. Sannunku da aiki" Shine abinda nace dasu, ni kallo wannan basu isheni ba, nayi waje. Inaji anata ƙus_ƙus ƙasa_ƙasa, harda masu cewa. "Wannan mai gidan gilashi ce fa. Lallai Magawata yana ji da wannan mata tashi, tana tatse duk kuɗaɗenshi hiye" Babban mamakina a wannan wajen shine. Wai me yasa son zuchiya yake damunmu musamman mu mata? Ai kowa yasan mijinyawa bashi da hali, kuma fa ansan ina koyarwa. Wai an taɓa tambayar duk zaman da muke yi mijinyawa baya aiki, wake ci da shayar damu ma kuwa? Amman a hakan babu dama mace ta fito fes sai ace sai mijinta. Wata ma wannan fes ɗin zata kalla kwaɗayi yasa ta biyo, sai ta shigo gidan kana idanunta suyi kiliya. A zaure na tadda mijinyawa cikin farar shadda sabuwa kar, harda kularshi dara mai ruwan jinin kare mai kyau. Murmushi duk muka sakarma junanmu. "Kinyi kyau sosai Maman Azgar. Kinsan Allah jiya ko runtsawa banyi ba, sabida damuwa da irin yanayin yadda kika fito babu ko takalmi. Ga irin tsinkamun da su Nanno suka yi a taron jama'a, muna ƙoƙarin rufe kanmu da bargon sutura. Kiyi haƙuri Tutar so, nasan ke me haƙuri ce ki daɗa. Zamu girbe ribar haƙurinnan. Nayi alƙawarin ko da Nawata bai bar ƙauyannan ba, mu zamu bari, ba kuma zamu kai shekara huɗu ba. Zuwa wannan lokacin ina fatan zamu tattara mu bar jama'are sai ziyara." Ya dinga bani baki, ni ko nayi shiru ina saurarenshi kawai. Can na nisa. Babu komai ai. Ita rayuwa kowa da irin tashi. Sannan ni da kai muna zaune lafiya, kuma ina fatan duk runtsi mu riƙe amanar juna kamar yadda Yarda tasa muka mallakama junanmu amanar rayuwarmu, mu riƙe wannan amanar. Na yarda dakai irin yardar da ko wacce mace bace zata iya ma mijinta ba. Zuwa anjima za'a fito muku da abinci, da zaran an kammala. Ni zan shiga cikin gida, ana raɗin sunanne? " Ai kafinma ya bani amsa muka jiyo maroƙi yana shelar. "Allah ya raya Ɗan safiyo da Azgar. Ƴaƴa tagwaye, iyayensu ma tagwaye" Sai kiɗa ya biyo baya. Fuuu Yaya Salihu ya zo ya wuce mu. "Azgar kuma, menene to Azgar ɗin" A haka ya fice yana sambatunshi. Murmushi muka sake, na juya na koma ciki abuna. Ai nan naga anata surutai a tsakar gida. "Azgar kuma wannan wanne kuma irin sunane, wannan haka kamar sunan yare? " Inji wata zabiya daga dangin Nanno. Sai wata tace. "Ai yarenne ma, anfa ce babarbariyace, ga danginta sai yare suke yi, ga lafaya kina gani duk wannan aikin tana jikinsu fa. Shine ai sunan wani nasun aka saka ma yaron ai. Shi ko irin karar nan ma bazai iyaba. Matarnan in aka sake ta cika gida da ƴaƴa wallahi saita mulki kowa, yaranta ma haka zasu taso in uwatale ba ta yi da gaske ba sai sun mulki ɗiyoyinta. Nanno ta tabka kuskure da ta yarda da aurennan tun fil azal." Ni dai banma nuna nasan abinda suke cewa ba, na sake kutsawa. A bakin ɓarayinmu na tadda Yaya Jamila da Uwatale. Uwatale tana saye da atamparta mai kaza da ƴaƴa kun ganeta ai, mai ruwan jinin kare sai kaza da ƴaƴan nata kuma mai ruwan madara. Ƙafarta caɓe da lalle duk ya hauro mata. Yaya Jamila kuma fefa lesiri ne a jikinta. Mai ruwan bula ta yi lallenta a hannu da ƙafa shar dama dai bata rabo da lalle gaskiya. Kafeni da idanu suka yi, ga bakinta a kumbure harma an baɗa mata magani, ita Yaya jamila fa tsarabar rikicin jiya. Uwatale ma naga ciwo babba a wuyanta, babba sosai. "Hindu daga ina haka. Sai muka ji sunan yaro Azbar amman wannan suna bana hausawa bane ko? Ni ban taɓa jin irin wannan sunan ba, nace sunan wani yaren naku ne hakan, ko asalin sunan kenan azbar Allah da iko yake" Inji fa Uwatale wanda a yau dariyar munafurcin ya gagara. Fuskarnan tata a murtuke wallahi ƙwallace fal guraben idanunta. Sai kallon mai gidan gilashi take yi tana mayawa, ni kaina sai nasan nayi kyau. Ko kaɗan bana hausawa bane, kema ai bai miki kama da na hausawa ba ko. Zan wuce ko? " Na dubi Yaya Jamila da ta yi bankan_bankan a hanya" "In naƙi naki matsawa, tureni zaki yi ki wuce ne, koko Yayarki zaki turo mu daku, maras kunya kin shanye mana ɗan uwa jibi shadda mai gidan gilashi ya ɗinka miki, harma da gwal a kunnenki kina jin tsoron Allah kuwa?. Yaro an ƙaƙaba mishi sunan da bamu san wanne iri ne ba, ni bama zan iya kiran sunan ba sam" Sai na ƙare musu kallo tsab. Ina nazarin abinda zance kafin na yi murmushi. Hmmm Jamila kenan. To in ban mallake mijina ba, naki mijin kike son in mallake? Naga kema mulkinki kike yi a gidan aurenki, ance sai yadda kika yi da mijinki, a wata ruwayarma cewa akayi har talla kike ɗaura mishi. Yana kai miki duk ranar kasuwa, Ke akwai tsoron Allah a lamarinki ne. Ko kina jin cikar isarki ce tasa kike juya mijin naki? In isarce to nima da ita nake taƙama da gadara, in ba ba'ita bace hanyar duk da kika shanye mijinki kika dawo dashi jani talau, shine ake ramawa akan naki ɗan uwan. Ko rabuwa nayi da ƙaninki nayi mishi tasirin da abadan bazai samu irina ba, sai dai wata kalar daban" Ji nake kamar in rufeta da duka wallahi. "Amman Hindu baki da.... " Kina ƙarashewa zaki tare haƙoranki da hannunki dan wallahi saina zubar miki dasu, dan babbar abu ta kazan... Ina daidai da zamanin ko wacce shegiya a cikinku. A tunaninku zaku hanani kwanciyar hankaline a gidan mijinane, ƙarya kuke wallahi. Kunci ƙarya kun kwana da yinwa. Ƙyaleku kawai nake yi sabida bani da lokacin wannan shirmen naku. Karkacewa nayi ƙirjina da ƙirjin Yaya jamila suka gogi juna, na matseta a bango, a lokacin saranda tayi, ina ganin tsoro a idanunta. Nayi wucewata ina ji tana ƙungumama iyayena zagi, domin batasan darajar iyaye ba sam. Anata hada hadar girke_girke, kowa ya duƙufa a bakin aikinshi. Ɗakin kayan abinci na shiga, muka gaggaisa da ƴan uwa, anata wanka, wasu kuma bacci ma suke yi hankalinsu kwance. Ƴan gida sai ƙaremun kallo suke yi. Ga wannan haɗin sabulu ya murjemun fatata a cikin kwana bakwai nayi wani irin kyau shar shar dani. "Hindu kenan irin wannan zinare haka, kai ɗinkinnan ba damane gaskiya yayi kyau kin fito shar dake." Uwarɗaki na koma nanna tadda Luba da falmata suna kwalliya, ko wacce ta ƙure adakarta. Nan nayi zamana cikinsu, su Rayya, da Fannah suka shigo muna ta hirarmu gwanin sha'awa. Muryoyin su Qasimu na ke jiyowa a tsakar gida. Da Yaya ta shigone take faɗa mana rago suka zo ɗauka za'a yanka. "Wato Luba kuna gado ko, gara ke cikine dake ita kuma Falmata bata ƙaunar aiki sai son jiki. In aka kawo hanji ku zaku gyara ayi miya dashi ai. Ga tuwo can mun ɗaura daga shi mun gama komai. Zuwa sha ɗaya muna fatan mu kammala komai. Ga hadari harya soma haɗewa. Allah yasa kar ayi ruwannan dan caɓewa gidan sunan zai yi sosai" Luba tace. "Ai ni Yaya ji nake yi ma cikina na jujjiyawa tun jiya, Allah dai yasa a gama taronnan lafiya dani. Jibi zamu koma ko? " "Jibi kan uwar haka mun ma yi nisa, duk abinda zamu ƙarashe gobe zamu kammala komai da komai, jibi sai tafiya in sha Allah" Ƴan gida da suka kwana wajen Barakane suka soma tuttuɗowa. Ashe anko suka yi mai kyan gaske sun ko yi kyau, Babu laifi in dai wankane gidan aka tarar. wajajen goman safe shiru har lokacin ba'a aiko kayan ciki ba. Sai Innah Yahanasu ta tura Yaya da Fanna suje su karɓo, ko suji me ake ciki, shirun yayi yawa. Suna fita Innah Kulu da Innah Dubu suka shigo uwarɗakina. Da ganinsu neman magana ya kawosu. "Ke Hindu wannan wanne irin sunane kuka sanyama yaro, babu sanarwa ba komai, a cikin ƙauyannan wa zai iya kiran wannan suna sabida Allah fa. Sannan kuma tun asussuba muke ta jin ƙamshi abinci, mun shigo mun tadda anata girke_girke shin ba'a sanar muku a can ɓarayin Nanno za'ayi abincin suna haɗe dana Uwatale bane, ince akan wannan batun jiya akayi duk rikicin da akayi ko? Me yasa kuke da neman fitinane wai ni kam, ayi magana kuga kamar an matsa. Da Nanno da kanta taso zuwa, jama'a ne suka tausheta. Ji wani irin sunan yare da aka ɗauka aka sa ma yaro fa sabida Allah" Yaya ce tace. "Ai ba'a hana ku yin abincin acan ɓarayin Nannon ba. Muma ai ba zaku hanamu yin namu ba Baba. Batun suna kuma ai ba Hindu zaku tambaya ba ɗanku ya kamata ku tambaya. Wai me yasa komai sai Hindu ne ni kam itace ke Auren ko ita aka aurk ne?" "Kusan abinda kika faɗa hakane yarinya. Ai itace mijin, ɗanmu shine matar, shi yasa komai ake tunkararta aji ba'asi" Cewar Innah AKulu Innah Yahanasu wacce ta shigo yanzu yanzu, wacce saida tayi magana ma muka gane ta shigo tace. "Yanzu iyakar abinda ya kawoku kenan batun sunan yaro da batun girkin suna wai? To maza ku fice mun da gani marasa kai da tunani. Kafin in sa itace duk in doddoke muku kwanyarku. Ƴan masu ƙorafin tsiya" Wannan maganar itace wasila ta wanzuwar gagarumin faɗan da wallahi tsaiwa rubutashi ɓata bakine, dan rikicin ƙin ƙarewa yayi. Sai da Innah Yahanasu ta rakasu har ƙofar fita ɓarayin baki ɗaya. To dake gidan a cike yake. Yaran Innah Dubu sunzo suna, na Innah Akulu ma haka. Sai rikici ya ɓalle, zagi in zaga tsakaninsu dasu Yaya. Wannan karon ƴan gida sun taɓuka dasu akaita musayar zagi, dake sunga dangin Nanno suna da yawan gaske. Kunji wannan babin? An yi akan kayan ciki. Da aka kuma turawa a karo na biyu, su Falmata sun tarar har su Zakiya sun soma ma hanji kitso. Innah Yahanasu da kanta taje har ɓarayin ta kinkimo bawon kayan cikin, tazo ta dureshi. "Kuci gaba da aikin Saratu. Wacce take jin kanta wuta yake fitarwa tazo ta ɗauka, kamar yadda naje na ɗakko" Aka gama wannan, sai maganganu da sukaita zagaye. anyi akan naman ragon suna sabida mu a al'adarmu a girki duka ake zuba naman a cinyeshi. Innah yahanasu tasa aka raba ragonnan uku aka ba su Nanno kashi ɗaya a ɗanye, kayan cikin ma aka raba uku aka basu ɗaya. Nan rikici ya ɓalle aka dawo da naman, aka mayar musu. Aka kuma aikowa. Sai da Yaya ta rutsa Shafa. "Wai menene dalilin dawo da namannan da kuke yi ne? " "Sabida soyawa ya kamata ace kunyi, mu a soye ake raba nama ba a ɗanye haka ba. Sabida haka mu ba zamu karɓa ba, kuma wannan ɗan naman a rago biyu, wa za'a ba, wa za'a hana?" A cewar Shafa. Yalewa da kanta ta mayar musu da naman. Ta faɗa musu al'adarmu karace ma akayi aka basu a ɗanyen, sabida dai ba za'a basu abinci ba. Nan dai akaita rikici sun dai karɓi naman sabida sunce ɗansune ai yayi. Ana suna, ana hirar rikicin su Yaya Jamila. Ƴan gida an samu labarin adanawa. Innah Abidah ba damane, ta kafa ta tsare ita a tsakar gida ma take zaune kawai. Sai nishaɗi da fara'a sosai take yi. Sai ƙus_ƙus da Innah Mairamu suke yi. A wannan rikicin, sai ga Harira tazo suna, harda atamparta da rigar yaro itama, haka Halima, da Baraka atampa da rigar yaro, harda omo ana Baraka, Halima kuma harda sabulu sanda uku kore. Akazo rabon abinci, suka ga ana fitarma dasu mijinyawa abincika na alfarma tire_ tire manya. Ko wanne tire akwai dafadukan shinkafa, akwai shinkafa da miya, akwai tuwon shinkafa da miyar yakuwa, akwai sunasun da miyar kuɓewa ɗanya. Haka al'adar take, kuma a cikin babban tire aka haɗa komai da komai. Kamar na mutum huɗu, ko uku, ko biyu, in madaidaitan tiran robane, sai ayi kowa da nashi. A cikin ko wacce miya namane faca_faca kawai. Nama duk a abinci aka kididdaba, har Dandaru anyi ds cinyoyin baya biyu. Haka aka fice musu da tire kusan goma manya manya. Ga koka kola kiret ɗaya aka wuce dashi. Nan kallo ya dawo ɓarayina. Kuma matan malaman makarantarmu sun ssmu zuwa, an babbasu wannan kofuna sobeniya da aka tawo dashi daga gida, duk suna gani. Ga kayan fitar suna in sa wannan in sa wancan hankalin kab ƴan gidan yana gareni. Musamman dana saka wagambarinnan, ta haskani, na fito da kyau. Kuma a lokacin na fito tsakar gida, rakiyan malama. Kunsan Allah leƙe har ta katanga. Uwatale kuwa, data fito firit muka ci karo da'ita a hanyar shiga ɓarayinmu, kasa motsawa tayi. Ni dai wallahi har sanda nazo dokin ƙofa, dana waiga Uwatale na ƙame motsi wannan ta kasa, ta juyo ma ta kasa. Kai kawai na girgiza. Akan abinci ma da suka ga ba'a basu ba, an zuba an kakkaima maƙota, ga su Khadija a babban tsakar gida suka zauna suna cin nasu, kuma dama neman fitinane, hatta su Innah mairamu babban tsakar gida suka fito, suka shimfiɗa babbar tabarma, anata cin abinci. Nama kawai baja_baja a abincin. Nanma sabon ɓalli ya tashi. Ɓallin da hatta maza manya wallahi saida suka shigo raba wannan rikicin. Sunan dai bai yi armashi ba, rigima da hassadar dangin miji ta motsa ƙaƙas, haka akaita dambarwa, innah Yahanasu kuwa babu damane. Ni kam dama tun bayan la'asar na soma jin wani irin sanyi kamar yana shiga ɓargona, take na soma rawar sanyi. Sai Baraka aka turo da kayan barka na dangin miji. Sabida Innah yahanasu ta hana kowa shigowa, kujera tasa a bakin ƙofar tayi zamanta fa. Kunsan irin wannan rigunan na da can masu kala kala duk a jiki, mai gajeren wando, zaku ganta akwai ja a jiki, akwai yalo, akwai bulu , akwai shuɗi layi layi kun ganeta? To irinta har guda goma sha biyu, sai omo kwano ɗaya, sai sabulu sanda biyar, da wata atampa ruwan kwara_ kwara. Shikenan kayan dangin mijin. Ni kuwa kayana saida aka cika bahun manya uku, maƙil_maƙil wallahi kamar za'a buɗe kanti. Haka aka wakilta su Anti suka kai ɓarayin nanno, a lokacin kuwa ana kan ganin na uwatale bahun guda ƙarami anata zuzuta goshin da yaron yayi. Dai _dai nan aka kai musu nawa, Nanno riris ba lafiya ma, ita kam bata samu ganin kayan ba ma. Idanunta a kulle sai hawaye kawai suke yi. Zazzaɓi fa riris ya rufeta matarnan abun almara. Haka suka ɗakko suka dawo, muka dai ƙarashe sunan babu armashi. Ruwane ma ya tsuge kamar da bakin ƙwarya, shikenan rigimar ta ƙare kuma. Magriba na shiga aka kasa gane kaina sam. Washegari ma mager_mager na wuni duk aikace_aikacen da su Yaya suke yi da idanu kawai nake binsu. Dan jiya ruwa ya hana wanke_wanken suna. Abincin daya ragu da safe suka ɗumama, shi suka ci, ragowar suka lodama Baraka Innah tace su raba da matan gidansu. Saida suka gyaramun komai suka kintsa komai washegari asubar fari suka kama hanyar Kano. Ƴan Maiduguri suka kama tasu hanyar. Gida daga ni, sai Innah Yahanasu, da Azgar Innah Yahanasu tana gaban murhu tana soya naman kai sabida busarwa take so tayi. Mijinyawa kuma yanata faman jidon ruwa. Ni kuma inata haɗa duk kayan da nake buƙata a jaka, nawa daban na Azgar daban. Saida mijinyawa ya gama jidon ruwan kana ya shigo ya taddani, duk fuskata ta aune. Jikina babu laka sam, da ƙyar nake iya ɗaga hannuna, kaina da zuchiyata nauyi sosai. Anan muka zauna muna ɗan tattauna abubuwan da suka faffaru marasa daɗi, wanda ni bana ma son tunosu sam. Tayani yayi muka ƙarashe haɗa kayan yana yi yana ma Azgar wasa, shi baima san me ake yi ba, bawan Allah. Haka dai kafin gobe duk abinda ya dace Innah ta killace, ta killace mun. Ɗakin kayan abinci ta gyaremun tas, kayan garata ta shigar dasu Kicin ɗin falona tasa ki ta datse, da kayayyakin suna, manya manyan atampopin tace dasu zamu tafi za'a ɗinkamun acan, ɗananun ma ta tsinci wasu. Harma ta cirema Baraka atampa da sabulun gib na wanka. ragowar kayan abincinmu anan ɗakin da muke ajjiyewa ta barshi. Gandar nanma data soya a ɗakin ta bari, tace mijinyawa ya dinga dubawa. Washegari da safe wajajen tara furob ya ƙaraso mijin Innah Yahanasu, ashe a Bauchi jiya ya kwana. Ai baima shigo ba, mijinyawane ya shigo yake sanar mana da zuwanshi. Shi da Qasimu suka fitar mana da kayanmu zuwa cikin mota. Ina saye da sabuwar lafayata da takalmina da jakata sababbi. Na kumbura, na aune sosai fa. Innah Yahanasu tana riƙe da Azgar ta runguneshi muka fito. Itama ta ɗauki wankan haɗuwa da furob, jiya da daddare saida ta sake tusa lallenta ma. "Ga kin ɓarayinta nan sai ka kula kaga da dukiyarta a ciki. Kar azo ana wallahi tallahi" "Aa kuje dashi, zan dinga kwana a gidansu Qasimu babu damuwa" Innah tace. "To shikenan hakan ma yafi. Da fatan dai zaka zo kafin ace ta dawo ko? " "In sha Allah zan zo Innah. Allah ya tsare mungode sosai." Wuf uwatale ta fito. "Komawa zaki yi ne Innah? " Wani harara Innah ta sakarma Uwatale ta ja tsaki kawai. Ta shiga mita Innah ce fa. Sai ni nace mata. Zanje wankan gidane ni saina dawo" "Wankan gida? To to shikenan sai kin dawo" Wucewa muka yi muka barta tana sosa kai. Da ƙyar Mijinyawa ya shawo kan Innah akan muje inma Nanno Sallama. Ta dai ga mutumcinshi munje. Nanno dai cewa tayi.. "Sam ba da yawuna ba wallahi. Babu inda zata je ta zauna a ɗakinta. Duk tatseshin da kuka yi bai isheku ba, sai kun tafi da'ita gida kun sake tatseshi ko tausayinshi bakwa ji, dubi duk yadda ya rame, hidimar da akayi a wannan suna, da irin suturun da yayi ma yarinyarnan na fitar suna, ni tunda ummana ta haifeni ban taɓa ganin irinsu ba. Ga wani irin suna babu kan gado. Ni tunda naji sunan yaron na kwanta jinya, kuna gani ba lafiya bace dani ba sam" Innah Yahanasu tace. "Shi mai aurenta da yawunshi ai. Ke Hindu wuce mu tafi kinji? Saida nace muku ai bazan zo ba. Ayi mace ke dole sai kin yi son zuchiya ko son kanki, kai tur subhanallahi" Ina, harma ta fice a ɗakin. Miƙewa nayi nabi bayanta muka fice. Naima su Shafa, da maƙota da suka saba kafa majalisa a tsakar gidan sallama" "Au wai ashe zaki je wankan gida Hindu? Tabb Allah buwayi" Ku da bakwa wajen, In kun tanka, to nima na tanka. A zaure muka tadda Uwatale tana tsaye. Data ganmu ne wai take cewa aike tayi tana jiran yaron yazo ne. Ina isa bakin motar, ga mijinyawa ga Qasimu da Abdulƙadiri a tsaye. Sai ga Nanno ta fito, wallahi harda ɗan gudunta. Ta riƙe hannuna carab wai bazan shiga motar ba. "Babu inda zaki je kinji na faɗa miki. Kai kuma yanzunnan ka bata umarnin komawa ciki" "Wallahi bai isa bada wani umarnin hana tafiyarnan ba. Ko ya yarda ko bai yarda ba sai na tafi da'ita. Bari kiga. Ni banƙi ma auren ya ƙare ta bar wannan ƙaddararren gidan ba. Ke ɗinnan kinfi zaman ƙauyennan zamewa ƙaddara a rayuwar Hindu" Zagayawa tayi ta miƙama furob Azgar ta zagayo ta finciki hannuna, ta jani, Nanno ta jani itama. In Innah yahanasu ta ja, sai Nanno ta ja. Ga jikina babu laka sam, ni kaɗaima ji nake zan iya faɗuwa. Su Qasimu aka bari da ban baki. "Kiyi haƙuri ki barta su je, kamar yadda aka bar su Shafa, dasu Tsahare suka tafi. Kamar yadda su Yaya Jamila da sauran mata _mata na cikin gida suka tafi suma. Da izinina zasu tafi Nanno, kiyi haƙuri kinga baki da lafiya ma" Ai sai ta saka salati. Innah ta fincikeni ta dannani a mota. Furob ya fito yace. "Ma lob akwai furobilem ne. Ba da yardar mijinta dama za'a tafi da'ita ba? Kinsan ba kowa ke son wannan al'adun ba. Ibin mi to i dont lik it." "Aa furob shiga mota abunka, zanma bayani a mota. Rigimace irin ta matan karkara" Har motarmu tayi nisa, su mijinyawa na ba Nanno haƙuri. Ajjiyar zuchiya na sauke a yayin da muka hau kan titin Bauchi. Zuchiyata cike fal da tunane _tunanen abubuwan masu daman gaske. Zuchiyata tayi tauri sosai, ina girmama ƙiyayyar da dangin mijinyawa suke yi mun, ina kuma yawan hasashen abinda ya assasa tsanar, wanda a wajena sam ba dalilin da za'ayi riƙo dashi, aita cusgunamun sama da shekaru shida bane. Motarnan na garawa, daidai da yadda ƙwaƙwalwata take ta lissafe_ lissafen rayuwar baya, da wacce kuma zamu fuskanta a gaba. Har bacci yayi awon gaba dani. Awanmu Takwas da minti arba'in cur a hanya, kafin muka isa maiduguri, da gidansu mai kyau na ƴan boko, wanda babu hayaniya sam. Wannan rashin hayaniyar ya bani damar samun hutu sosai, daga ni har Azgar bamu da aiki sai bacci, da safe Innah da furob suke fita aiki. Daga ni sai Furera mai aikin Innah dattijuwar data saba da mitar Innah shekaru sama da goma suna tare, da duk wannan faɗan na Innah, dake ta kasance mai tausayi da yawan kyauta, da son shiga lamuran mutane. Saida na huta gaya, dangi suka soma tururuwar zuwa dubani, tare da yi mun barka. Duk wanda zai zo da abun hannunshi, waɗanda basu dashi sai su ƙullomun turaren wuta a kwalba su kawo mun ko humra. Nanma fa haka na tara kayan barka. Ga daɗi da ake sa Furera ta dafamun, magungunan gyaran jikina ina shansu sosai, kuma ina jin kyansu a jikina. Cikin kwana goma nayi ƙiba ni da Azgar mukai ɓulɓul. Azgar irin yarannanne da gani masu ƙiba, girmanshi sai mamaki yake bamu, lokaci guda ya soma haɗa kumatu fa. Na murje nayi wani irin kyau sosai. Furob ya kwashi manyan atampopina tela namiji akaba ya zubomun ɗunkunan da suka sake fito da martabar kayan. Tun lokacin ma teloli maza ɗinki maza suke yi banda na mata, sai ɗaiɗaiku dake ɗinkin mata. Shi wannan ma ɗan sinigal ne, kun sansu dai da iya sarrafa sutura. Saida aka ɗinka mun kala sama da goma, kuma a cikin kwanaki bakwai dake yana da yaran ɗinki, kamar kamfanine haka da suke yin ɗinkunan manyan matan masu muƙami matan ƴan siyasa, ana siya a ɗinke, akwai wani ɗinkin shadda mai haɗe da lesiri ma da Furob ya siyo mana ni da Innah Yahanasu daga zuwa karɓomun ɗinki yace ya gansu sunyi mai kyau. Muna cika kwana sha takwas sai ga mijinyawa kwatsam da yamma daf magriba. Da adireshin da Innah ta rubuta mishi, dake a maidugurinma gidanta sanannene sabida furob sanannen mutum ne sosai, kuma lekcarane a jami'ar Maiduguri, kuma yana harkar siyasa sosai fuskarshi sananniyace ga al'umma. Innah na zaune tana karanta littafin Hausa, dan tana karatu sosai, litattafanta waje ta ware musu a sib ɗinta zan iya cewa basu da iyaka. Anan na karanta wazai auri jahila, allura cikin ruwa, mata da miji, Da sauran littattafai masu koyar da ɗunbun ilimi gaya. A lokacin su Anty Bilkisu Funtua ke tashe, Ado Ahmad gidan dabino, Nazir Adam Salih, Bala Ahmad Babinlata, Balaraba Ramat, Kamilu Ladan koki. Sai ga maigadi ya doko sallama wai anyi baƙone yace Mijinyawane daga Jama'are. "Kace ya shigo, mijin Ƴatane Maman Azgar" Naji irin daɗin da bashi da abun kwatance, wannan kalmar Maman Azgar ta faranta, ta wanke, ta haskaka mun zuchiyata ƙwarai. "Maza wuce ki murzo Humra ki gyara fuskarki kafin ya shigo" Miƙewa nayi, na ɗaura mata Azgar a jikinta na wuce ciki. Humrarta mai rikita furob na murzo, na gyara ɗaurin ɗankwalina, na murza kwalli, amman ba cikawaba irin yadda Innah Yahanasu take zizarawa. A wannan kwanakin ni da kaina wallahi na sauya, kuma tabbas ashe na canja kaɗan a ƙauye. Zaman Maiduguri, da samun sababbin littattafai na marubuta masu raya Aure a Ƙasar Hausa, yasa na sake gyagijewa. Zamana nayi har saida Furare tazo ta kirawoni kana na fito. Wannan shaddar ta ranar suna, ita mijinyawa ya sako, da hular yayi shar dashi, sutura na gyara mutum sosai gaya. Sai satar kallona yake yi. Ga Innah Yahanasu na shirin miƙewa, Azgar na hannunshi. "Ki kaishi masauki, wancan ɗakin na hagu, yayi wanka, yayi sallah. Ki sameni a kicin" Tana gama faɗar haka ta wuce. Sai lokacin ya samu damar ɗagowa muka haɗa idanu. Zukatanmu fal farin ciki, sai kallonmu yake yi ni da Azgar. To taso mu shiga daga ciki, wannan bakin akwai magana tabbas" Dariya kawai yayi mun, na ɗauki buhun kayanshi, zan ɗauki babbar ledar yace ai tsarabace da yayo ma Innah Yahanasu. Furare na kira ta shiga dashi. Ɗakin da muka shiga gadone, sai kafet malala da har da talabijin da bidiyo. Muna shiga ya haɗani ni da Azgar ɗin. Dariya yayi yana kallon tsakiyar idanuna. "Rayuwata lamice tamkar miyar da babu ɗanɗano, matsawar bakya cikinta. Jina nake yi tamkar kin mun tazarar shekaru masu yawa. Gaku kun yi kyau, kun sake haske da kumari. Menene wannan sirrin? " Zamewa nayi na zaunar dashi akan gado, na zauna gefenshi. Sirrin jegone kawai. Ina samu cikakken gata sosai. Kuma kasan ma ko baka zo ba jibi zamu dawo. Sabida Innah Yahanasu zasu tafi umarah ita da Baba Furob. Shine tace zata dawo dani kafin su tafi" Ai wannan maganar ta sashi farin ciki sosai. Banɗaki na shiga na haɗa mishi ruwa a bokiti zafi akeyi sosai ruwan sanyine na tara mishi. Saida na tabbatar ya shiga banɗakin kana na fito, da Furare naci karo zata kawo kaskon turaren wuta. Karɓa nayi na shigar mishi dashi. Saina wuce ciki, Furare ta riƙe Azgar, ni kuma nayo wanka tare da alwala. Saida nayi sallah na ɗauki riga da zani na materiyar lokacin ana yin zani, da wani irin hannu mai tsayi har guiwa. Humra na kuma shafawa na yi kwalliya sama sama,na fito kai tsaye zuwa Kitchen, acanne na tadda Innah Yahanasu tana jera tuwon Ndalayi a fulas. A tire ta zuzzuba daya sha iska shine take maidashi filas. "Zuba miya a waccan kular maza ki kaima mijinki abinci, yaci kafin furob ya shigo" Miyar margi ce wacce tun safe aka ɗaura a gaushi kaɗan sai bayan la'asar aka sauke. A babban tire na jera komai na tafi na kaima mijinyawa. Na kunna tibi na saka mishi bidiyo kaset na shirin IN DA SO DA ƘAUNA shirin Ado Ahmad gidan Dabino uban marubuta ba. Na zuba mishi abincin, yana ci muna hirarmu cike da farin ciki. Lokacin sallar isha da yayi saina tafi ɗaki naje nayi sallah. Muka ci abinci da Innarmu. Muna kan ci ma furob ya shigo Shima saida yaci ya ƙoshi kafin Innah tasa nai kiran mijinyawa muka shiga falon furob yana shan shayi. Nan suka gaggaisa. "Ai dama jibi suke shirin komawa, mu zamu je Umarah. To faɗuwa tazo daidai da zama sai ku tafi tare kawai. Gimbiya gobe sai ki shiga mata kasuwa ayi mata siyayya, a siyo mata bushasshen kifi ma" Godiya nayi mishi sosai, muka fito Azgar na hannun furob ya shaƙu da yaron sosai. Nima shigewarmu muka yi ciki mukaita hirarmu ta soyayya mai daɗi, sai wajen taran dare nayi mai sallama na dawo ɗaki na kwanta. Innah Allah ya soni bata ɗakin tana wajen Furob Ko da ta kawo Azgar tayi ƙwafa. "Ai na ɗauka kina canne ince futsararriyar kawai. Ga shi shinfiɗeshi ki kashe wutar sai da safe. Gobe zamu fita da sassafe a zazzagaya dangi, ki musu sallama, sai mu shiga kasuwa" Ai kuwa haka akayi , bamu shigo gida ba sai wajajen sha ɗayan darema duniya na kwance abunta. A wannan daren Innah Yahanasu tai mun kwalimar suturunta masu riga da zani, dake rigunan irin dogayennanne zuwa cinya. Dana gwada wata ni ta wuce mun guiwa sosai, dake doguwace, sun mun yawa amman dama su a haka ake sakasu. Sai rigunan bacci, da wasu turarukan wutan, banda wanda duk gidan da muka shiga ake bani ko kifi ko turaren wuta, da kayan shayi. A wannan dare ta tayani muka haɗe duk kayanmu. Ta kuma yi mun lalle, dama an mun kitso kwananshi biyar. Washegari ana fitowa sallar Asuba muka kama hanyar jama'are. Na sha sabon ɗinki, sabuwar lafaya mai tsada, ta Innah Yahanasu ce na sanyo bata ce mun uffan ba. Ta samu irinsu har uku kalane ya bambantasu, ga sabon takalmi mai jaka, ko yau ace za'ayi bikin gida na mallaki abubuwa da yawa na ado. Hatta ɗan kunnena da sarƙa na gwal Innah Yahanasu ta karɓa ta canjomun, nayi ciko na ƙara gram uku akan na da. Ni kam ma tafiya na nisawa nayi bacci, sabida jiya bamu yi baccin kirki ba. Wuni muka yi cur a hanya, da yamma sakaliya irin dab magriba muka isa jama'are kuma a hakan Furob yace yau zasu wuce Bauchi su kwana a zangon baƙi, gobe sassafe su juya. Matasan dake ƙofar gidane suka taimaka wajen shigar da kaya. Mu kuma muka shiga da sallama. Gidan ko damƙam da mata, wai Zainab ɗin Uwatale ce ta faɗa rijiya an dai ci sa'a an cirota kuma da ranta. Shine aketa maida zance. Haka suka saba barin yarannan suna wasa a bakin rijiyarnan, ko a jikinsu. Ai muna sallama kallo ya dawo kanmu. Uwatale ta shaƙi numfashi ta cika, Nanno tayi ma Mijinyawa ƙur da idanu cike da tuhuma. "Hindu kece kika dawo, har an gama wankan ba dai arba'in ba dai ko?" Cewar Tsahare kenan. "Haba ƴarnan ba dai arba'in ba. Kwananta ashirin cib. Mijinta ne ya matsa, yaje har Maiduguri. Shine dai nace bari in kawo mishi matarshi." Inji Innah Yahanasu ranta ɗaya harda dariya. "Au dama Maiduguri ya tafi mijinyawan kenan? " "Au ke baki da labari ashe? Ai zuwanshi biyu, sunturin ya isheni, wannan soyayya daga Allah ne Da fatan mun sameku lafiya" Shafa ce tayi wannan tambayar Nanno tayi ƙwafa tare da barin wajen. Muma ɓarayina muka dosa. Nasan Innah yahanasu ta kirama mijinyawa ruwa tab. Mijinyawa ya buɗe mana muka shiga ciki. Mrs BUKHARI To asha sharhi lafiyaMRS BUKHARI ............... *Wai kina da labarin Gidauniya ta mata, farin cikinsu, da walwalarsu, mai suna *MURYAR MATA (FARIN CIKIN AL'UMMA)*🧕🏻👩🏻‍🎓 *Wanda ni Mrs BUKHARI muka yi haɗin guiwa wajen buɗewa, tare da sauran shuwagabannin Taskar Badiat Ibrahim?* *ku matso kusa ki kasance a cikin wannan tafiyar ta Alkhairi, tafiyar da zata gyara rayuwar Aurenki, tafiyar da zata gyara miki tunaninki, tafiyar da mace zata gane ni'imominta, tasan kima da darajar kanta, gidauniyar da zata koya miki sana'ar da zaki dogara da kanki, gidauniyar da zata koya miki tattalin uwar kuɗin kasuwancinki, da yadda zaki tattali ribarki ta yadda zaki ƙarfafa kasuwancinki, sha'awar son komawa makarantar addini, ko na boko kike so? To biyomu muje wannan gidauniyar taku ce mata, gidauniyar ta ƙunshi abubuwan da zatonku ma bai zata ba.* *Ga lambar wayata ga matan da basa cikin Taskar Badiat group 1 group 2 group 3 sai kui mun magana in sha Allah zaki kasance a cikin wannan tafiyar ta manyan mata* (08179523215) *Ƴan taska kuma zaku iya tuntuɓar Admins ɗinmu ta pc domin kuji yadda tsari da dokokin kasancewa memba a cikin wannan shahsrarriyar, garnaƙaƙar gidauniya wacce ta haɗa manyan masana zamantakewar aure, malamai, manazarta, mahukunta, ƴan gwagwarmaya, masana ta ɓangaren gyaran aure, ƙwararrun ƴan kasuwa, da gogaggun ƴan boko, wanda ya haɗa matan arewanmu da kudunma baki ɗaya, zamu kasance a duk faɗin Najeriya da izinin Allah* Yau wacce rana mun tadda wutar nefa kuwa. "Bari inje ko wajen Baraka ne in karɓoma Innah Abinci" "Laa barshi, aini da nayi sallah tafiya zamu yi. Akwai biredi da miya a mota ya ishemu, kaje ka samu furob. Ke kuma bara in yi sallah" Ta miƙe ta shige ciki. Kallona mijinyawa yayi ya saki murmushi. Kana yasa kai ya fice, sai zumuɗi yake yi. Bayan Innah Yahanasu ta rama sallolinta tace. "Ni kam Hindu da alkhairi, nan da wata takwas akwai biki na gidanku. Sai mun haɗu acan. Duk wacce ta miki, ki mata kar ki sake ki ɗagama ko wacce ƴar abu ta kazan uba ƙafa, na faɗa miki kenan. To kinji, Azgar zamu yi kewarka yaro mai shiga rai." Har waje na rakata, saida motarsu ta yi nisa muka shigo gidan. Uwatale na cikin tsakar gidanmu da kwano a hannunta muka shigo, tayi saurin zabura. Leda ce baƙa a hannunta ina ganin sanda ta tura a mararta jikina ya riga ya bani bata da gaskiya wallahi. Kada ki sake ƙafarki ta sake shigomun cikin gidana, tsakar gidana ba tare da nice nan na baki izini ba. Ɓacemun da gani, dake da ƙazamin abincinki, ni kin taɓa gani naci abincin ƙazantarki ne? Ki fita nace" Na daka mata wata tsawa, uwatale ta isheni na gaji da iskancinta. Ina da yaro yanzu bazai yiwu uwatale ta dinga shigomun haka sasakai ba, dan ni bamma yadda da'ita ba. Sum _sum ta fice Mijinyawa ya jani muka shiga ciki. Azgar ya ajjiye a doguwar kujera, nasan kun biya karatun da kyau kuma. Mun yi nisa a karatu, yana nuna mun darasin kewa. Kawai muka ga labulenmu a sama. Juyowar da zamu yi, mukai idanu huɗu da Nanno da Uwatale. Wallahi alamu ya nuna, ya tabbatar,sun jima a tsaye a wajen. Babu mamaki tun karfon karatun har zuwa inda karatun yayi zafi, kaina ma baya ɗauka sabida nauyin baƙin, wasu wasalinsu a sama, wasu wasalin na ƙasa, ƙila suke tsaye suma suna jin karatun. Rigata na gyara, na ɗauki ɗankwalina a ƙasa, nayi shigewata ciki. "Babu shakka tabbatacce. Kananan ana maka zizizi da zazaza. Ta ya wannan makirar zata barka kaga mutumcina Magawata hiye" Ta dai yi mai faɗa tai ta zazzaga, tamkar ta kamashi yana saɓon Allah. Aka dawo batun zuwa Maiduguri shi dai haƙuri kawai ya bata, dole ya karɓi laifin da Innah yahanasu ta ƙaƙaba mishi. Ta gama ta tafi. A wannan dare, mun yi karatu masu wasali, sosai nake fahimta ta dalilin magangunan washin ƙwaƙwalwa dana shassha😉. Rayuwa taci gaba da cukumurɗawa, abubuwan suka ci gaba da faruwa, masu daɗi da marasa daɗin ma. Na kunce gara na ba Nanno rabin buhun shinkafa, komai saida na ɗiban mata, na bata atampa, sabulu, omo duka. Kuma ranar dana dafa naman kai saida na ba kowa ma a cikin gidan. Gaga gaga gaga Abubuwa suka ci gaba da garawa, mu jiƙa mu matse dai. Bamu da matsalar abinci sam, daga nan har shekara biyu ma inaga koma fi, tunda jalauta abunmu muke yi, gani da bushasshen kifi mai yawan gaske. Mijinyawa suna tafiya aiki wannan gidan gona, ko su tsaya a Gombe, ko a Bauchi. Mafi ƙaranci sati biyu yake yi in a Bauchi suke, in a Gombe ne kuma wata guda, shi zai yi ya yawo. A nanne na fahimci Nanno kasancewarmu tare ne sam bata so, taga Mijinyawa a gida ni dashi muna nishaɗi, shine bata ƙauna. Da zaran ya dawo take kafa ƙahon zuƙa. Daya sa ƙafa ya koma take sakarmun marata in yi fitsari, sai ƙorafe_ƙorafen da ba'a rasasu. Tunda Uwatale na kai rahoto, bata sauya zane ba, sai ƙiyayya data ƙara a sanadiyar fita da Mijinyawa yake yi, da yadda taga hatsi ya wadacemu, abinci sai da kifi, in Mijinyawa zai dawo kuma in saka nama. Kar ku mance kuɗaɗen dana samu na suna, sunanan a adane nayi musu kyakkyawan ajiya gaya, kuma ina ƙarawa akai duk randa na ɗauki albashina, tunda abubuwa da yawa sun warware mana, Azgar ya shigo rayuwarmu da alkhairi gaya. Azgar yana samun kulawa sosai, kuma har Nanno na turawa a ɗaukeshi, shi da yaron Uwatale da suke kira da Baba. An mammai mugunta sosai, sai dai in kauda kaina. Daga ranar dana zo mai wanka zamu tafi makaranta koyarwa, sai naga tabo kamar na cizone ga haƙora reras a cinyarshi wallahi. To ban kuma ba da shi ba ko an aiko. Haka daya soma rarrafenshi iyakarshi tsakar gidana bai taɓa fita babban tsakar gida ba. Azgar na da wata tara muka je biki gida, a lokacin dabo ma yake yi, in yayi ɗaya biyu sai ya faɗi. Da taro yai taro a gida jama'a aka cika, ƴan kwantagora ma duk sun zo. Sai hirar dambarwar sunan Azgar ya tashi. Harda masu miƙewa su kwatanta yadda akayi, da irin rikicin Nanno da Innah yahanasu. Ni ko ko in kula, to me zaice da gaskiyarsu su yi abinda suke so. Naji daɗin zuwa bikinnan sabida yadda na fito ba damane a cikin dangina, haka yarona kowa na son ɗaukarshi ƙato dashi yaro mai cikar lafiya da kuzari. Sati uku nayi na koma, Baba sojanmu baya nan yayi tafiya wannan dai karon bamu haɗu ba, sabida shi na ƙara sati ɗaya, amman dake Allah bai nufa da rabon ganawar ba, bamu gana ba. Na koma jama'are da kwana biyu Mijinyawa ya dawo daga nema. Azgar daya ganshi sai murna da zabure_zabure. Haka muke ta gudanar da lamuranmu. Ina ya Allah babu ya Allah Kwanaki, satika, watanni sukaita matsawa. Har bakin Azgar ya soma buɗewa, yana cemun Maa, a lokacin Mijinyawa kuma yana iya ce mai Babba. Bari in dawo daku baya a farko nayi magana cewar tsawon shekaru shidda nayi a Jama'are. Mantuwace sakamakon abun ya jima amman nafi wannan shekarun Afwan masoyan Hindu, duk da ma Magawata a halin yanzu ya fini fada. Wannan kenan. Sannan Asam'u bata yi shekara biyu a hannun mahaifiyarta ba afwan shima duhu ya shige mun, a yanzu abubuwan da suke kaina suna da yawa ne ( inji Hindu ne da fatan kun gane?) A cikin wannan kwacuɓen da Azgar yake yi Halima ta haihu ɗiyarta mace fara kyakkyawar yarinya santala. Kullum ina zuwa inna gama da makaranta. A wannan zuwanne na tabbatar da irin babbar matsalar da Abdulƙadiri ke ciki da Halima. Dama Mijinyawa na labartamun wasu. Bata mishi biyayya, a gaban kowa yaɓa mai magana take yi. Ya rame, ya lalace, cikin ƙanƙanin lokaci kamar ba Abdulƙadirin da muka sani ba. "Ai da ba dan mu ba da tuni Abdulƙadiri ya saki Halima, kinga wannan cikin data haifeshi shi ya tseratar da igiyoyin aurensu gaskiya. Amman har cukumeshi Halima take yi. Ita bariki take son komawa ma gaskiya. A hakanma yana zarginta da wani tsohon bazawari da suke zaune a maƙota, ga gida ga gida. Rannan da muka dawo Gombe, mun soma biyawa ta gidanshi. Hmmm wannan ƙaton ɗan iskan a falonshi fa wai hirace kawai suke yi. Shine dalilin wannan damben dana baki labarin sunyi, ta ɗauki tukunya ta danƙara mishi a kanshi wallahi. Abdulƙadiri yana cikin jarabawa mai girma. Har kuka yake yi inya tuno da irin baƙin cikin da Halima ke ƙunsa mishi a wajen aiki fa. Illar auren ƴar bariki yana da yawa. Ba duka bane suke tuba na gaskiya ba. Kuma kinsan basu ɗauki maza da daraja bane, wannnan yana ƙara assasa wutar rikicinsu Ta saba da zaman daduro. Duk baƙin cikin da zaisa magidanci kuka akan iyalinshi, Tutar so abun da girma to yake." Mun jima sosai muna tattaunawa, washegari ma da naje gaskiya saida nayi mata nasiha, wani ashar data lailayo ta danƙarama Abdulƙadiri, kawai dan ƙanwarshi tace a bata kanwa zata saka a miya. Shikenan ta dinga zagin Abdulƙadiri. Danginshi sai muƙus suka yi, a lokacin ne na dinga nuna mata ba daidai bane. Tunda tana mugun ganin mutumcina sosai, kuma sosai take son ƙawance dani. Shi yasa ma tace ma Abdulƙadiri ita a bani kuɗin kayan yara in siyo mata a Kano lokacin zanje. Ai ko ilai ni na siyo mata duk kayan da ake buƙata nice harda ciko. Shi kuma Abdulƙadiri sabida yadda yake martaba amininshi Mijinyawa ne yaima ɗiyar huɗuba amman dai su suka zaɓi sunan da zasu saka ma ƴarsu. Ranar suna yarinya ta amsa suna Asama'u. Akayi taron suna lami lafiya, aka kammala. Harda su Uwatale a wajen suna. Lokacin tana fama da laulayin ciki, ga goyo, ga shayarwa. Sai duk ta canja kamanninta ma sai da suka sauya. Duk da dai tana ji da wannan ciki. A gidan sunanne naji tana faɗin tana haihuwa zasu koma birni, cikin data samune ma ya kawo tsaikon komawar. Amman tana haihuwa, akayi bayan suna zasu tattara yanasu_yanasu su koma birni. Nan na soma farin ciki, muma lokacinmu ya kusa kenan, dama bana fata ko kusa ace Azgar ya soma karatu a wannan ƙauye. Kuma duk sanda za'a turo wasiƙa, Baba Sojanmu na jaddada mana batun komowarmu birni, sannan yana jaddada a kiyayi ranar da turarmu zata kaishi bango. Duk sanda aka turo wasiƙarnan bana iya rutsawa sam. Nasan Baba Sojanmu, nasan fishinshi babu kyau. Sannan ni kaina hankalina kacokam ya koma kan karatu. Ga Luba ta gama karatunta harma ta samu gidan rediyo ta maƙale tana aikinta. Ga irin ci gaban da ƴan uwana suke ta samu, da ƙarin matsayi duk ta dalilin karatu. Matar Akarami, matar Qazzafi, da Anti matar Yaya Sojanmu. Duk fa sun koma makaranta dukkansu mastas garesu, dake suma tamkar wata gasace a tsakankanin mazan. Na cewar matar wane bazan bari tafi matata ilimi, ko wayewa, ko kyan gani ba. Wannan yaja matan yayinmu maza suna fitowa sosai, kece raini suke yi gaya. Kuma sun samu guraben aiki mai kyau. Matan suma gasace lafiyayya a tsakaninsu, a zahiri basu da matsala za'a haɗu ayi hira. Amman a baɗini gaskiya kowa cikinsu bata son ace ai a sunan wance, ko a bikin wane matar wane ce ta cinye taron a surukan gida kenan. Matan da iyakarsu digiri, dasu akafi gabzawa da masu mastas, duk da dai anata musu ɗauki ɗai_ɗai wajen jefasu a makaranta. In naje biki ko suna gida na kallesu, ko inji suna hirar ai ofishinmu kaza ne ya faru, aa masana'antarmu kaza. Sai inji tamkar allura suke yi mun. Batun asibiti kuma, mun gama shan magunguna, allurai duk an kuma ma Mijinyawa. Muka koma akaita gwaje_gwaje shiru babu wani labari. Daga ƙarshe ma likitan cewa yayi ya sallamemu muje mu dangana. Ai kuwa shikenan muka burne wannnan sirrin. Ina ya Allah babu ya Allah. Har shekara ta zagayo cib Ranar asabar muka wayi gari da mutuwar Abdulƙadiri. Wanda shaidu suka tabbatar faɗane ya kaure a tsakanin Abdulƙadiri, da Halima. Kuma dama baƙin cikinta ne ya kaishi ƙasa ciwo yake yi kusan kwananshi bakwai a kwance ƙaƙas. Amman sai aka rurrufe lamarin mahaifiyarshi tace kada a ɓata mata gawar ɗanta, ai mai wanka a kaishi lokacine yayi. A ranar Uwatale kuma ta sauke cikin dake jikinta ɗanta namiji ta samu. Allah al hakim, wasu na kuka, wasu na murna. Wasu sun rasa, wasu sun samu, faɗuwar wani, tashin wani. Duniya makaranta a ranar da kai ka gama, a lokacin wani nata murna farawa zai yi. Wannan kaɗai ya ishi mai hankali tsoron Allah. Su Mijinyawa da Qasimu sun yi kuka, sun yi kuka har saida aka rufu a kansu anata rarrashinsu. Ita kuma Halima wannan ne yai sanadin rashin lafiyarta, har aka gama wannan makokin tana kwance. Tasan ta cutar dashi, kuma dai dasa hannunta wajen mutuwarshi. A haka aka watse aka barta da ɗiyarta. Su Mijinyawa ne suka ci gaba da ɗaukar ɗawainiyarsu. Ga Asama'u yarinya ce mai laulayi babu wuya ta kwanta ciwo, sai an dangana da asibiti. Inata saka idanu inji yaushe su Uwatale zasu koma gidansu, tunda dai an yi suna an watse. Sai nake ji a bakin Baraka, wai an ɗaga tashin tukunna dai da saura. Gaga_gaga_gaga_gaga. Ina zaune a ɗaki, nayi kwalliya shar, littafin hausa nake karantawa, hankalina ya tafi soyayya. Har wani narkewa nake yi a sakamakon yadda ake gudanar da wata iriyar soyayya mai sanyi. Allahn daya halicceni ina mugun son soyayya, da riritawa gaya. Shi yasa nake son kasa kasan indiya gaya. Azgar yana zaune sai wasanshi yake yi, yana surutai ya samu kayan wasan yara, mota da jirgi Baba sojanmu ne ya aiko mishi dashi. Da sallama Mijinyawa ya shigo rungume da yarinya a kafaɗarshi a tsumman goyo. Azgar ya tashi yaje ya ruƙunƙume ƙafafunshi. "Oyoyo Abbah" Hannu yasa ya ɗagoshi ya haɗasu hagu da dama a kafaɗarshi. Littafin na ajjiye ina kallonshi da yaran. Shima ni yake ta kallo. Saida ya sauke Azgar, ya miƙomun Asama'u. Hannu na miƙo mata. Ta kalleni, sai tayi dariya ta miƙo jikinta, na ɗauketa na ɗaurata a cinyata. "Ga yarinya na baki ita duniya da lahiri, na sanki da amana" Rungumeta nayi tsam a ƙirjina inajin son Asama'u na ratsani sosai. Na karɓeta Ubangiji Allah ya raya mana ita da imani. Mahaifiyarta fa?" "Kema kinsan ba zamu barma Halima yarinya ba wallahi. Tana gadon asibiti ma bata da lafiya, shine na nemi ɗaukar yarinyar gaskiya. Abinda zan iyama Abdulƙadiri kenan" Kunu na dama ma Asama'u, a baki na dinga bata. Bata da kuzari irinna yara, kuma gashi bata girma, jikinta babu ƙarfi alanƙosa haka take. Nanno yaje ya sanarma riƙon Asama'u ya dawo hannuna. Ai sai gorin haihuwa ya ɓalle, ta dinga tijarar haihuwa shiru daga Azgar shikenan. Ita wallahi, ita tallahi. A daren ranar da aka kawo mun Asama'u bamu rintsa ba. Jikinta yayi kau _kau da zazzaɓi, sai kuka take yi a hankali. Na kasa zaune na kasa tsaye. Goyota nayi na dinga jijjigata. Na sauketa na sakata a kafaɗa. Na jiƙa tsumma na dinga goge mata jikinta zazzaɓin dai ya sassauta. Mijinyawa shi ke taya ni sata a kafaɗa. Runtsawa bamu yi ba, sassafe sai asibiti. Zuwan farko aka bamu gado jikinta zafi sosai. Ashe baƙon dauro ne ke damunta ana bata magunguna sai ko ƙurajennan duk suka feso. A lokacin Mijinyawa bashi da kuɗi a hannunshi, duk sun ƙare a maganin Halima. Ni na biya komai na asibiti. Kwananmu uku aka sallamomu. Mun dawo gida mun tadda Uwatale na bin maƙota anata sallama. Jibi zasu tashi. "Inaga bari in jaraba zuwa yima Nanno magana, Allah bashi ta barmu mu tafi tare. Ni ko hayace sai mu kama Tutar so" To shikenan Allah yasa a dace, nima nafi son hayar. Fita yayi, ni kuma na dawo da kallona kan Azgar dake ba Asama'u ƙuli_ƙuli a baki sai tura mata yake yi. Allah sarki. Watarana da girmanku zaka ciyar da'ita abinci a baki na soyayya. Matarka ce baka sani ba" Ajjiyar zuchiya na sauke. Na shafi kan Asama'u ta juyo baki duk yawu tana ta mamular ƙuli_ƙuli tai mun dariya. Fuskarta duk saɓar baƙon dauro. Haka Mijinyawa ya shigo ya taddani ina wasa da yarana. Yadda na ganshi a sanyaye na tabbatar da matsala. Sai ban bi ta kanshi ba, naci gaba da wasa da yaran. A hankali Azgar ya sakko ya koma jikin Babanshi. Itama sai ta bishi duk ya haɗasu a jikinshi. Dogon wando na ɗakko na sanya ma Asama'u naji garin da ɗan sanyi, na sanya musu hulunan sanyi. Shiru Mijinyawa yayi da yarannan rungume a jikinshi. Uwatale ce take ta doka sallama daga can ƙofar shigowa ɓarayina. Fita nayi na sameta. "Dama sallama Nanno tace inzo in miki. Shan ruwanmu a ƙauyannan ya ƙare. Zamu koma birni mun barku lafiya, sai in mun zo ziyartarku kuma mazauna ƙauye. Amman kayana duk sunanan in mun zo anan zamu dinga sauka" Sai gatsine take yi, wai ita shegiya. To Allah ya tsare yasa ku koma a sa'a ko?" Bam na rufe ƙofata na koma ciki. Su Uwatale suka tafi muna kallo. Nan Mijinyawa ya shiga godon Nanno, amman wallahi ta kafe mai. Sai haƙuri yake bani. "Kiyi haƙuri ina jiran wani lokaci ne, in dai har bata amince da komawarmu ba. Zan ɗaukeki mu tafi kawai. Allah yana gani nayi duk wata biyayya daya dace. Ki ƙara haƙuri na ɗan lokaci kaɗan." Akaita cukumurɗawa fa. Harma Nanno tace in ya ɗaukeni ya koma dani birni bata yafe mai ba. Kuma saita ɗaga mishi Umma. A ranar na haɗe kayana, dana Azgar da Asama'u da tayi mugun sabo dani gaya. Nima inason yarinyar sosai kamar yadda nake jin Azgar ɗina. Na lashi takobin bazan zauna ba wallahi. Tunda Nanno bata da dalilin hanamu tafiya. Mijinyawa ya shiga damuwa sosai da sosai, yaita roƙona akan kwana bakwai kawai yake buƙatar in bashi kacal. To shikenan na baka, daɗina da gobe saurin zuwa" Munyi haka dashi da kwana huɗu kwatsam da safe misalin sha ɗayan rana, ranar asabar sai kawai muka jiyo muryar Baba Sojanmu a tsakar gida ana gaggaisawa. Zumbur muka miƙe a kwance daman muke, muna tattaunawa duk akan tafiyarne. Kafin in fito har sun shigo ɓarayina da sallama. Babu wasa ko wargi a fuskar Baba sojanmu. A sojanshi ya fito tamkar yana filin yaƙi. Kayan sojojine ma a jikinshi. Gabana ya yanke ya faɗi ras. "Innarmu, Baba Soja sannunku da zuwa. Ku shigo mana daga ciki" "No nid. Hindu nazo ɗauka mu tafi, tunda alƙawarin daka ɗauka ka saɓa. Ɗan uwanka da kace a baka taim in ya gama gininshi, zaku dawo birni yarinya ta shiga makaranta. Yanzu watansu nawa da dawowa birni? Naje zan kaima Shehulle wasika ya kawo muku, yake bani labari. I was shok, an safrais. I am dibli dis'afointent. I neba esfet dat furom yu, bot is ol Nagoɗis folt. Hi yu bilej gel go insait an girab yo tins" Ya dinga turanci yana zazzare idanu. Da ƴar Mijinyawa ya iya motsa bakinshi da zummar magana Baba sojanmu cikin tsawa yace. "Wil yo shotob an bi bilemful?" Saida hantar cikina ta kaɗa. Ɗaki na shiga a guje. Dama kayan dana haɗa ban suncesu ba nawa. Na yaran na kuma haɗawa. Innarmu ta biyoni har ciki. "Hindu yi maza kinji? Nayi juyin duniya da janaral akan abi a hankali yaƙi. Yanzu sai kawai aga mun dawo gida dake, me za'ayi tunani dan Allah? Duk da Mijinyawa ya saɓa alƙawari gaskiya. Ƴan uwanki sai samun ci gaban rayuwa suke yi kinga, amman ke ace har yanzu iyakarki fa sakandare. Ina wannnan abun zai yi mana kyau" Kafin ince wani abu Innarmu idanunta yakai ga Asama'u dake zaune a gado. "Wannan wacece Hindu?" Yarinyar marigayi Abdulƙadiri ce abokin Mijinyawa. Riƙonta ne ya dawo hannuna. "Allah sarki hakan yayi kyau. Lallai ta samu uwar riƙo tagari ba dan kin kasance tawa ba." Innarmu yanzu wannan gidan zan koma, to me za'ace musu innah koma dan Allah fa?" "To Hindu shima Mijinki bai duba mun ba. Dan ni za'a saka a matsala, Abida ma ta isheni ga Salamatu da yaranta sun kawo ziraya, shi kanshi Daktan yana ƙasar baki ga yadda yake musu facakar kuɗi ba. Jiya muka shiga Bauchi. Tun jiya yaso mu ƙaraso mu ɗaukeki, in yaso ma kwana a Bauchin tare. Motace ta ba Qazzafi matsala, shi ya tuƙomu yana waje" Baba sojanmu me ya buɗe labule ya ƙura mana idanunshi. "Wandaful" Ai ba shiri na rufe akwatin. Innarmu ta ɗakko Asama'u. Ni kuma na jawo Azgar da jakar kayansu. A ƙofa na dure jakar, na koma na ɗakko tawa. Na fito ni bamma samesu a tsakar gidan ba. Ƙofar na jawo na fito. A tsakar gida na tadda Innarmu da Nanno a tsaye. "Au tafiya da'ita zaku yi sabida wanne dalilin, yarinya na aure za'ace an ɗauketa haka siddan?" "Mijinta zai miki bayanin daya dace. Mu kam yarinya dai tamu ce ai ko? To mun ɗauki abinmu" Cewar Innarmu. "Aurenne ya ƙare kenan ko yaya, sannan da ƴar mutane zata tafi? " "Kusan hakane. Aure kam girgiɗi yake yi. Yarinya kuma ai bata akayi" Nanno ta girgiza kai tana almara. Kallona tayi tace. "Giringiɗishi wato kuma yau mahaifinki da mahaifiyarki, da abunda kuka ɓullo ma wannan yaro kenan, anata wahalashi tamkar kece mace tilo a duniya ko? To wallahi aure zai yi kina tafiya. Ke daga haihuwa ɗaya ma baki kuma ba. Dama shima wannnan ɗin da yaya ya samu. A cikin gidannan bayan haihuwar Azgar, saida ko wacce ta haihu. Ga Uwatale mutan birni tare kuka haihu, amman gata da goyonta na wata nawa ma" Dawowa Innarmu tayi ta riƙe hannuna muka tafi. Mijinyawa yana tsaye a gaban motarmu. Ta gabanshi na wuce na shiga mota, Innarmu ta zuba kayana a bayan but, ta miƙamun Asama'u na rungumeta, ita kuma ta shiga ta rungume Azgar, Baba Sojanmu na gaban mota. Mijinyawa ya matso ta gefen da nake ya dubeni idanunshi sun yi jawur dasu. Zai yi magana Baba sojanmu yace dashi. " Wi a don listinin tu yu. Mub de ka Qazzafi" Ba shiri Mijinyawa ya haɗiye kalamanshi. Yana tsaye shiru motarmu ta bar wajen, ya goya hannayenshi a bayanshi, idanunshi sun kaɗa sosai. Kunji wata ƙaddarar ko? Mrs BukhariMRS BUKHARI ................ *Wai kina da labarin Gidauniya ta mata, farin cikinsu, da walwalarsu da ni Mrs BUKHARI muka buɗe tare da sauran shuwagabannin Taskar Badiat Ibrahim?* *ku matso kusa ki kasance a cikin wannan tafiyar ta Alkhairi, tafiyar da zata gyara rayuwar Aurenki, tafiyar da zata gyara miki tunaninki, tafiyar da mace zata gane ni'imominta, tasan kima da darajar kanta, gidauniyar da zata koya miki sana'ar da zaki dogara da kanki, gidauniyar da zata koya miki tattalin uwar kuɗin kasuwancinki, da yadda zaki tattali ribarki ta yadda zaki ƙarfafa kasuwancinki, sha'awar son komawa makarantar addini, ko na boko kike so? To biyomu muje wannan gidauniyar taku ce mata, gidauniyar ta ƙunshi abubuwan da zatonku ma bai zata ba.* *Ga lambar wayata ga matan da basa cikin Taskar Badiat group 1 group 2 group 3 sai kui mun magana in sha Allah zaki kasance a cikin wannan tafiyar ta manyan mata* (08179523215) *Ƴan taska kuma zaku iya tuntuɓar Admins ɗinmu ta pc domin kuji yadda tsari da dokokin kasancewa memba a cikin wannan shahsrarriyar, garnaƙaƙar gidauniya wacce ta haɗa manyan masana zamantakewar aure, malamai, manazarta, mahukunta, ƴan gwagwarmaya, masana ta ɓangaren gyaran aure, ƙwararrun ƴan kasuwa, da gogaggun ƴan boko, wanda ya haɗa matan arewanmu da kudunma baki ɗaya, zamu kasance a duk faɗin Najeriya da izinin Allah* Tunda muka ɗauki hanya Baba sojanmu yake faɗa babu ƙaƙƙautawa. Yayi hausa ma yaƙi fur, yana ta rantsuwar matsawar bamu dawo birni da zama ba, ko da aljanu zasu saceni suƙi dawo dani, a wannan karon babu ɗaga ƙafa. Ko dawowa birni, da ci gaban karatuna, ko takaddar saki. Qazzafi ya kalleni da kyau ta madubin mota, yai mun lallausan murmushin da kai tsaye na fassarashi a matsayin na farin ciki. Na sani Qazzafi yana sona fiye da tunani. Amman baimun ba, namiji mara faɗi da damatsa bana mishi ma kallon namiji. Kuyi haƙuri ra'ayinane wannnan tunma kafin in san ciwon kaina, har nazo na sani. Na biyu Innah Mairamu bata ƙaunata, ta kuma kirani gajerar da bata san mai Qazzafi zai yi dani ba. Innarmu kuma a lokacin tace. "Allah ya ɗaura mishi son wannan gajerar da bata yi kanta ba, gajerar da take hamdala ga Allahn da yaji yana son kallonta a gajera. Sannan kuma ya rasata, kuma sonta ya guyabeshi. Ke da kike da tsayi, sai dai kash tunaninki gajerene" Ranar munga jarfa ganin idanunmu. Idanuna na lumshe, tare da gyarama Asama'u kwanciya akan ƙirjina. "Allah ya kyauta. Ni naso abi a hankali ta yadda ba sai an kai ga zuwa gida ba. Kaga fa in muka je gida da Hindu haka za'aita gutsira ana tsomawa" "An so? Ai ta gutsura mana. Ai kema kinsan nayi haƙurin da wama yayi zaton zan iya irinshi ne? A wannan karon ƙorafinki bazai taɓa samun gurbiba dole a cika wannan sharaɗin, ko a rabu shikenan. Akanme zai mayar mun da yarinya ƴar ƙauye. Ki duba Hindu yadda ta koma. Ibin do i no shis tirayin ha bes taga ta lulluɓe wannan ƙauyancin. Amman ya bayyana sosai a jikinta. Yanzu shima Azgar inya taso anan ke kina ganin zai shiga ajinne ma? Sannan tunda ɗan uwanshi ya ɗakko ƴar ƙauyen matarshi da yaranshi suka dawo ƙwaryar kano, sai shine sabida raini zai zauna bayan ga rubutun da muka yi. Sa'a yaci ma ban zanesu ba" Ya nuno mata takaddar. A nanne ya ƙilla idanunshi akan Asama'u dake ta ja mun mayafina tana kirana Amma, daga baya ne ta dawo cewa Ammi, Ammin ake cemun kenan. "Wannan kuma fa, haihuwa Hindun ta kuma yi, sabida kar in yi magana aka kasa sanarmun?" Nan ya sake buɗe wuta, idanunshi sun rufe baki ɗaya, baya ko buɗesu. Qazzafi ya ɗan yi dariya. Tsawa ya daka mishi, cikin yaren Sojoji yace dashi. "Aje waya" Qazzafi ya ɗan ƙame tare da sara mai. "Ba haihuwa tayi ba. Yarinyace akayi mata kyautarta. Marainiyace mahaifinta ya rasu. Ka dinga sassautawa." Baice komai ba, ya koma ya zauna. Tare da ɗaurawa daga inda ya tsaya. Bamu muka shiga Kano ba sai ƙarfe bakwai na dare. Motarmu ta tsaya a ƙofar gidanmu. Idanu na kuma lumshewa. Shikenan hankalin kowa sai ya kwanta, wallen mijinyawa ake son gani, to shikenan su sa ruwa a ƙasa su sha. Da ƙarfin guiwata na taka ƙofar gidanmu. Asama'u na ɗafe a jikina, Azgar na wajen Innarmu. Da Innah Mairamu muka soma karo, tunda sune ƴan farko. "Ga Hindu ga Hindu. Ga kuma maigida Azgar. Aa Hindu ɗiya kika yi ne, naga mace a hannunki? Eh wallahi ɗiya nayi. Bani ita akayi" "To to muje ciki, kya zo ku gaggaisa daga baya, lokacin sallah harya wuce. Mairamu Nagoɗi ya dawo kuwa? " Cewar Baba sojanmu. Ni kam gaba nayi, bansan ko me tace mishi ba. Ina shiga falo na tadda Salamatu ita da Dakta. Ga kuloli masu kyau an mishi girki, dan wannan bama abincin gida bane. Salamatu ta zuba mishi yana ci, tana ta narkewa. "Mutan jama'are kune a tafe da yammannan, ko ince darennan maraba" Cewar Salamatu harda dariyarta ƙaƙas sabida tana gaban Dakta. Dariyar nima nayi mata, na tsaya muka gaisa da Dakta, itama muka gaisa sosai kafin na shige, sai kallon Asama'u take yi. Innah Abidah dake suruki na falo, bata fito ganin ƙwaƙwab ba. Nima ina ajjiye Asama'u a kan gadon Innarmu saina fito na leƙa muka gaisa. "Lafiya kuwa Hindu, ni dai nasan kinfi zuwa a yanayi na biki, ko suna duk da sunan ma baki fiye zuwa ba. To na ganki yanzu ko wani abunne? " Lami tana zaune tana cin abinci. "Innah to menene dan tazo gida haka kurum dan Allah. Nasiru maza cinye Abbanka ya kirani yana hanyar zuwa ɗaukermu, ya je gareji dubomun motatane shi yasa bai zo da wuri ba." Murmushi kawai nayi, tare da miƙewa Lami kenan saƙon ya iso. Na furta a zuchiyata. A falo na tadda Baba Sojanmu tare da Dakta suna tattaunawa, ni kuma na shiga na tadda Innarmu tana wasa dasu Asama'u. "Wajen Abidah kika shiga ko, nasan dole saita tsareki da tambayoyi danma Dakta yananan. Hmmm ai abun nema ya samu a gidannan Hindu. Amman babu komai rayuwarki muke dubawa, ina daidai da ko wacce ƴar... " Hmm tambaya take yi ta ganni ba suna ba, ba biki ba, kuma ko lafiya. Na dai ce mata lafiya. Sai Lami dake sanarmun tayi mota. Mota Jamilun ya sai mata kenan? "Mota ya danƙaro mata babba sosai, an kawo mana ma mun sanya albarka. Kinsan ta sake aiki, yanzu aikin kamfani take yi albashinta babba sosai, shine ya siya mata wai ta dinga hawa taje aiki kada a rainata. Tunda wajen aikin nasu duk masu motane. Wai inji Abidah fa" Ficewa tayi abunta, ni kuma na maida hankali ga yaran. Ga tunanin halin da Mijinyawa yake ciki a halin yanzu. Innarmu na shigowa nima na fita na ɗauro alwala, na rama sallolina. "Bari in ma yarannan wanka ko zasu ji daɗin bacci. Kema kije ki ɗebi ruwa ki gargasa jikinki sai kizo kici abinci ki bi iyayenki da gaisuwa, kafin Janaral ya haɗa miki mitin. Duk da ya sanar ma ƴan uwan nashi batun ɗakkokin tunma kafin mu tafin. Allah dai ya kyauta. Ni fatana mijinki yazo ayi magana ga fom na jam ana ta siyarwa, kema ya siya miki. Janaral ya samu ya sallameku" To ai Innarmu Nanno ce bata amince da dawowar tamu birni ba. Bawai daga mijinyawa bane, kuma ba makarantar bane bazai sani ba fa. Amman nasan in sha Allah zai shawo kanta, in dai ta amince shikenan faɗuwa tazo daidai da zama, sai ya siya mun fom ɗin. Sai dai in bata amince ba to bansan yadda za'ayi ba" "Kin sani mana takaddarki zai baki, a siya miki fom ki zana jam, ki koma karatu kema ai kin sani. Wallahi in bata yadda da zaman ku birni ba sai dai a rabu. Kuma ko ta amince da zamanku, karatuma shima wani rikicin zata saka. Balle danme ma zata hanaku dawowa birni, alhalin ga ɗan uwanshi, da matarshi, da yaranshi a birni? Ko kune dai take so ta kashema rayuwa, ta dankwafar daku? To ke in baki da hankali, mu da hankalinmu. Hindu banso duka wannnan abun ya zama haka ba. Sabida Abidah tayi rantsuwa da maganganu, akan Mijinki bazai taɓa iya dawowa birni ba yadda ta san uwarmijinki, sannan ba zaki yi wannnan karatun da aketa burin kiyi ba. Maganganun rikicin sunan Azgar kuwa, hatta baƙi in akayi da, sai ta zauna tai ta basu labari suna la'antar surukarki da dangin mijinki. Alhalin ba daidai bane haka, ita kashin bayanta ta zauna akai dan gudun kar ta tashi aji ɗoyinshi. Amman shawarar da zan baki kibi Baba Sojanku a hankali in kina son zaman lafiya. Hmmm kije ki yi wankan" Fita nayi kai tsaye zuwa kicin na ɗebi ruwan wanka, na sirka da ruwan randa na gargaso jikina, na fito. Na gama shafa mai kenan, sai ga Innah Mairamu ta yo sallama. "Shigo Bismillah Mairamu" Da sauri ta shigo ta nemi gefe ta zauna. "Ashe sabida wannnan dai alƙawarin makatanta ne Hindu kuka je kuka ɗakkota? Ai ban sani ba da ba'ayi hakan ba" "Au haba sabida kece mai iko da'ita ko Mairamu? " Innarmu tayi saurin katseta, ko kallonta bata yi Azgar take shafa ma mai, ta gama da Asama'u har ta sa mata wando. "Aa sabida dai ai auren yafi karatun Ruwayya. Babansu ma sai faɗa yake yi baiji daɗin abun ba. Amman nace in bai cika sharaɗin ba, da gaske sakin nata za'ayi tazo tayi zawarci kenan fa? Itace zata kasance bazawara ta farko a cikin gidannan kenan? " "Me yasa shi Nagoɗin baki tambayeshi wannnan ba. Tunda naga ai acan bakinshi kika ji wannan ma. Har a ranku kunsa makarantar ma ba zata yi ba, shi yasa har ake lissafin ta zama bazawara ta farko? To saime a tunaninku zawarci ai ƙarshen rayuwane ko? Kinga Mairamu tashi kiyi tafiyarki. Hindu dai ba zata rabu da mijinta ba. Karatu kuma ko bakya so zata yi, aka biyama wasu ma suka yi har suke ƙafafa dashi balle Hindu" Ai itama saita fusata. "Kamar su wa kenan kike nufi.? " Ai kema kinsan kamar waɗanda nake nufi, tunda kinsan bana tsoronki ko? Kamar ƴaƴan cikin ɗakin ki, dama sauran kab ɗakunan gidan. Dan haka jeki tun kafin raina ya ɓaci in faɗa miki mutuwa" Ta miƙe tana son yin zazzaga. Sai ga Qazzafi ya shigo, ga ledar nama a hannunshi sai maiƙo take yi. Harararshi tayi ta fita tana jan tsaki. "Aikin banza, kai dai anya ba canjamun kai akayi ba kuwa? Innarmu tayi tsakin itama. "Aikin banza. Ke saka musu kaya kinji. Kai kuma nemi waje dallah ka zauna, kai mun tsaye a kai. Ni nagaji da halin Mairamu irin wannan bin diddigin da me to yayi kama?" Qazzafi dai ya zauna yana zare idanu. Ba yau farau ba. Duk faɗan bala'in da za'ayi Qazzafi yana ɗakinmu, dokace Baba Nagoɗi yayi ma Innah Mairamu akan babu ruwanta da son raba Qazzafi damu, ko hanashi yin alkhairin da yaso. Dan akwai rikicin da aka taɓa yi. Qazzafi fa da girmanshi Innarmu taje har ɗaki ta damƙo hannunshi ta dawo dashi ɗakinta. Sabida Innah Mairamu tace in ya kuma shiga saita ɗaga mishi umma. Innah Mairamu tazo da rikici akan dole sai ya fito an asirceshi. Tace in ta isa ta shigo tace zata rabasu ta gani. Sannan umma ta daɗe bata ɗaga ba. Da ummanta dana Akuya duk ɗaya. Kai ranar munga abinda yafi zare tsayi, saida man kanmu yai ta tsiyaya. A ranarne Baba Nagoɗi yayi wannnan togacciyar, shine dalilin da yasa ta sarara mai. Ni anan na bar Qazzafi da Innarmu, da yara. Na dinga bi lungu, lungu zuwa gaisuwa. Duk labarin dalilin dawowata yana bakunansu, sun haddace sai biyamun suke yi, masu jimami nayi, masu cewa daidai ne hakan nayi. Ni dai da idanu kawai nake binsu. Dama an sanni in magana bata gameni ba, duk girmanta bana tankawa, ko da an so in tanka ɗin bana yi. Haka aka kwana aka hantse. Baba Sojanmu fur yaƙi amsa gaisuwata, sai ƙur yake mun da idanu. Wannan kenan Mijinyawa:. "Ai sai ka shigo kazo mu je kayi mun bayani. Jibi yadda mahaifinta yake maka tsawa. Iyayen arziki ne zasu zo su ɗauki ɗiyarsu babu gaira babu dalili." Wucewarta ciki tayi. Qasimu dake gefe ya dubi mijiyawa. "Kar ka faɗa mata sabida karatune, ƙurar buleka zata yi. Ka kafe akan batun komawa birnine. In taƙi amincema ka tattare muku suturarku kabi matarka, kaje ku rayu. Ka dinga zuwa kana neman yafiya. Ballema kaje ka fito muje mu samu Kawu mu zauna. Dole a dubama wannan baiwar Allah. Ji yadda mahaifiyarta ta damƙa mata Asama'u ta rungumeta a jikinta. Magawata kar kayi wasa da lamarin Hindu, da lamarin karatunta. " "Kazo muje tare Qasimu. Nanno a fusace take sosai" Qasimu ya dubi mijinyawa yace. "Muje to ya zanyi. Inma dukanne a kashemu tare" Shiga suka yi, suka tarar anata tattauna zancen. Anata gutsiri tsoma. A zaune a kan gadon bono suka tadda Nanno tayi shiru. Zama suka yi a ƙasa. "Nanno kiyi haƙuri dan Allah ki barmu muma muje birni mu zauna. Kamar yadda abokin tagwaitakata yaje. Ada nayi zaton dukanmu ne bakya so mu bar gabanki kamar yadda kika ce. Amman tunda Nawata ya soma gini baki hanashi ba, ya kwashi su Uwatale zuwa birni baki hanashi ba. Me yasa muma ba zaki barmu mu tafi ba Nanno? Ki duba nima aimun adalci, wannan alfarmar kawai nake nema a wajenki. Sannan in akwai wani laifi da Hindu tayi miki, ko ni nayi miki, ki faɗa mana a shirye muke mu baki haƙuri mu nemi gafararki' Sai ya ja fasali. Qasimu yayi gyaran murya yace. "Dalilin zuwan iyayen Hindu su tafi da'ita Nanno shi kuma. Akan batun komawa birnine. Tunda dama Mijinyawa yace musu zasu soma zama ananne kafin daga baya su koma birni. Tunda a birnin suka haɗu, shima kuma yana samu sosai akan sana'ar lemunshi da yake yi acan. Da wannan iyayenta suka yarje musu suka zo Nanno. Magawata ya riga Nawata shiga birni. Kuma a birni yaso ya zauna kece kika ƙi shine ya ba iyayen Hindu haƙuri, akan su bari zai rarrasheki in yaso Allah bashi daga baya sai su koma birnin. Kinji wannan dalilinne yasa, da suka ji labarin ai Yayanshi ya koma birni, to shine suke ganin danme shi da yayi alƙawari zai karya alƙawarin. Waima misali in bakya so su zauna a wani waje daban. Ba sai Nawata ya basu waje duk su haɗu su yi zumuncinsu ba. Ga Uwatale ga Hindu" Magawata ya ɗago ya dubi Qasimu. Qasimu ya ɗan mai nuni akan ya kwantar da hankalinshi, a dai je a hakan. "To kinji Nanno. Kuma in suna taren hankalinki zai kwanta sosai _sosai, ki duba wannan lamarin dai ayi adalci. Ke Uwace, ki duba a duba wannan al'amari" Shiru tayi tana kallonsu, sun jima a haka kamar ma ba zata ce uffan ba. Maganar shiganta yayine, ko yaya dai oho. Shigowar Yaya jamila kusan za'ace shi ya tarwatsa komai. Kafinma ta zauna ta yaɓa mayafinta a ƙarfen gado maulidi, sai zufa take yi. "Sannu Qasimu wato kaine bakin Magawata ko? To da kake cewa a barshi zuwa birni da matarshi. Ita Nanno duk yaranta majiya ƙarfin sai su kama hanya su tare a birni kenan. Wa zai lura da'ita to." "Kema kya faɗa ai wannan yarinyar.". Cewar Nanno wanda ada fa ku gane bata ce komai ba. " Haba Yaya Jamila, naga ga manyan yayu a cikin gidannan. Yanzu kamar Yaya Salihu, da Yaya Garbati, da su Muttaƙa, da du suke gidannan basu isa kula da Nanno ba har sai Magawata. To ke kanki aikin me kuke yi ke da Yaya Zakiya, da ba zaku kula da Nanno ba ga baki ga hanci. Ga su Shafa, Tsahare, gasu innah Dubu. Koni nan bazan kula da'ita bane. Ko ko dai sai shi Magawatanne ƙwararren wanda zai iya kulawa da'ita, ko aikinshine shi kaɗai ne? Mu dinga cizawa ana hurawa" Mijinyawa yace. "Kuma naga da can a birnin dai nake. Nawata ne ma yake shiga ƙauyuka ko yanzu ai a tsakanin Bauchi da Gombe nake. A cikin gidannan ma nine kaɗai na soma shiga birni" Qasimu yayi carab yace. "Ga wani gidan gonan da Maigidanmu ya buɗe a can Kano ɗin. Kanonnan ko ba Hindu fa aikinmu ƙarfinshi ya koma Kano, da Gombe ne. A duba wannan lamarin yarannan a sakar musu mararsu su yi fitsari ai inaga zaifi. Ko kuma shima Nawata ya dawo a kula da Nanno tare kawai. Tunda ai kowa ladannnan yana so. Kuma naga Nanno fa gadagau take da lafiyarta, kullum tana yawon karɓan haihuwa ko ba gaskiya ba" Nan Yaya Jamila ta hayayyaƙo musu. Qasimu shima ya hayayyaƙo ta inda ya tsikara ba tanan yake ja ba, mafaɗacine sosai. "Kefa ke kike jan duk wannan masifar. Kin kori kishiyarki, kina azabtar da yaran miji, mijinki kab garinnan kwatancenshi akeyi. Yadda yake ɗaukan miki talle kasuwar ƙauye_ƙauye. Asirce_ashircenki fa duk an sani a ƙauyannan. Kallonki kawai akeyi. Shi yasa ma ake tunanin wai ko asiri akayi yima Magawata. Abinda mutum yaima na wasu ne kawai baya so ayo mishi. Ni wallshi gaskiya ɗaya ce" Yaya Jamila ta shiga cashe Qasimu, bil haƙƙi yake ramawa ƙaƙas. Har saida Innah Dubu ta leƙo. "Kai gidanku da wannan sa'insar, yayar taku kake ma wannan ɗiban albarkar. Itace uwa yau in ƙasa ta rufe ma Yaya idanu fa. Shin bakwa bin komai a hankali ne. Yau ga shegantaka noma da babbar riga. Wai batun tallarnan da Ubale ake cewa yanayi da gaske ne kenan Yaya?" "Ahh da gaske ne. Har tsokanarshi fa akeyi. Ubale akwai bashi ne? Sai yace Jamila ta hana bada bashi, kuma ta ƙirga" Cewar Qasimu daya kwanto kura. Nanno ta fatattakesu, tare da rantsuwar babu zuwa birni itace harda dukan ƙasa. Ta kuma cashema Innah Dubu dama ta saba. Kai tsaye Qasimu ya ja Mijinyawa zuwa wajen Kawu. Suka tadda Kawu bayanan an gaiyaceshi wani biki na babban mai kuɗi da za'a gudanar a garin Kaduna, amman gobe zai dawo. An yi an yi dasu su tsaya su sha fura, ko suci abinci ma, amman ina. Mijinyawa bashi da sukunin cin wani abinci. "Qasimu gobe asubar fari zan kama hanyar Kano in sha Allah. Ko da ban samu mafita ba, ai ya kamata ace naje naga halin da Hinduna take ciki. Nayi imanin hankalinta da tunaninta yana nan tare dani itama" "Hakane to amman me zaka riƙa musu ta magana wanda har mahaifinta zai gamsu dakai. Ba zaka jinkirta Kawu ya dawo ba, sai kaga ma kayi tafiya mai cike da ƙwarin guiwa" "Kayya Qasimu bari dai in soma zuwa tukunna. Wannan lamarin ai sai an yi yaƙi tukunna" Qasimu yace. "Hakane. Kuma kaga wannan Jamilan hmmmm kusan itace Nanno wallahi, sai Uwatale mitsiyaciya kenan. Kaje ɗin in ka dawo sai mu sake komawa wajen Kawu. Ka rufe mata ɗakinta da kyau kasan dai sauran Shafa nanan. Kuma dogon hannu gareta" "Daɗina dakai baka sakaya abu Qasimu. Jibi abinda kayi ma Yaya Jamila" "Hahaha kyaleta zan kai da? Wallahi da nice da yayu irinsu haukace zan manna musu, inta tambotsan da takalata ma ba'aso ayi. Sabida kar inta tumɓele. Amman kai dake haƙuri gareka shi yasa, suke zuba kashi a kwanyarka suci. Jamilan me, dan a yayata tazo, sai mulki. Tayi a gidanta, tayi a gidana ina. In zaka gyagije wallahi ka gyagije" Haka sukaita tattauna wannan matsala. Sassafe mijinyawa ya fice a gidan. Wajajen bayan azahar irin ukun yamma sai ga Mijinyawa ya shiga gidansu Hindu da sallamarshi. Saye da yadinshi mai ruwan makuba, da hularshi tashi da ƙwaƙwa an ko ci sa'a bai sayo kwalli ba. Sai ragowar wanda ya saka jiya dake idanun nashi shima fa fes dashi kamar ba kwananne ba. "Magawata kaine a tafe? Za'a rina, sintiri ya aureka kuwa, in ba kayi ma janaral abinda yake so ba" Innah Mairamu ke wannan maganar a yayin da Mijinyawa ke neman gurbin tsugunnawa su gaisa. "Innah mun sameku lafiya, ya gajiyarku ta suna? " "Laaa ashe rabonmu tun sunan wannan yazo Azgar. Kai wannan suna munga masifa mai ƙafa huɗu. Ina Nanno sarakan ba da umarni? " Qazzafi ne yace. "Haba Innah" Fitowarshi kenan. Hannu yasa ya ɗaga Mijinyawa, ita kuma ta hau sosa hannu. "Muje daga ciki, Hindun suna ciki ai" Mijinyawa ya bishi suka ratse gidan. Ana tafe ana gaisuwa har zuwa falonsu Hindu. Hindu:. Tattaunawa muke yi ni da Luba, Yaya Saratu tana gado sai bacci take yi. Daga wajen aiki yau kam ta gudo, shine take ta wannan baccin sabida ciwon kai. Innarmu kuma bata nan To ke Luba ai koma yayane kina aikinki, ba albashi ake dubawa ba. Ilimin da gogewar da zaki samu. Sannan in kika horu kinanan wata rana Bbc hausa zata kiraki. Kinsan dai ko wanne matashi, da babban ɗan jarida burinshi Bbc Hausa ne, sabida sha ƙungum ce" "Hmmm Hindu hakane maganarki. Amman aikin kam gaskiya ba sauƙi albashin babu yawa, amman Alhamdulillahi ana gurgurawa. Kuɗin motane da yake cinye kuɗin albashin. Wallahi da fa harda bashi ma nake haɗawa. Sunusi ne yace in dinga tafiya a ƙafa shine ma kuɗin yake ɗan afki. Adashen wata nera ɗari biyar nake yi. Dashi kaɗai nake tsira Hindu. Kuɗaɗen duka a cefane yake tafiya. Takalmana duk sun suɗe, amman a hakan dai aketa gurgurawa" To amfanin neman kenan ka taimaki iyalinka. Allah dai yasa mu dace. Hankalina yana kan mijinyawa ko a wanne halin yake sai Allah Luba. Amman lallai inason karatu ko dan inganta rayuwar yarannan namu Luba. Inaso su yi karatu mai kyau. Karatun Qur'ani nake son su soma kamar yadda Baba Nagoɗi yayi mana. Kai ai yafi jan karatu sosai sabida Qur'ani ya huda ƙwaƙwalwar sosai" Sallamar Innarmu ce ta katse mana hirarmu. "Luba manya har kin garzayo kenan wannan yaran" "Innarmu danma dai shekaranjiya na zo naci abinci nayi bacci" Dariya Innarmu tayi. Ta warware lafayarta. "Ita kuma wannan gajiyar aikine yasa take bacci, ko ciwon kanne?" "Ciwon kanne amman gajiyar aikice. Aiki akwai wahala akwai daɗi Innarmu" "Gaskiya ne Luba. Ga wannan yaran suma sai baccinsu suke yi abinsu" Baba Sojanmu ne ya leƙo, Qazzafi na biye dashi. "Kizo ga mijinki yazo yana so kuyi magana." Cewar Baba Sojanmu, wanda sai yanzu ne ya kulani tun jiyannan. Miƙewa nayi ina murna a cikin zuchiyata. Lafaya na naɗa na ɗan murza humra na fice. Mijinyawa yana zaune a ƙasan kafet. Baba Sojanmu yana zaune a kan kujera ya harɗe ga jarida a hannunshi, halamun babu inda zaije ya bamu waje. Zama nayi daga ɗan nesa muka gaisa. A tsorace ya kalleni, murmushinma ya kasa sam. Yara dai ya tambayesu nace sun yi bacci. Sai muka yi shiru. Juyowa nayi muka haɗa idanu da Baba Sojanmu idanunshi ƙir a kanmu, ba karatun jaridar yake yi ba tsaronmu yake yi. Shiru falon yayi, fitowar Innah Abida, da Luba ne ya ɗan motsa falon ta hanyar gaggaisawa. "Fom ɗin kazo siya mata ne Mijinyawa?" "Aa Innah tukunna dai, amman za'a siya in sha Allah ayi haƙuri zan siya" Hmmm Innah Abidah kenan. Sai murna take yi wallahi ta kasa ɓoye farin cikinta ma. "To Allah ya yassare. Amman daga baya ma ance maka za'a ɗauki nauyinta tayi karatun, tunda ka kasa ka nuna gazawa, kuma ansan baka da ƙarfi. Sai kaƙi gashi dai har yanzu anata abu ɗaya ai gara ka bari mahaifinta ya ɗauki nauyinta. Kaima a ƙalla ka samu sauƙi, kuma wannan dai alƙawarin ya cika a samu a baka matarka" Ɗagowa nayi na dubi Baba Sojanmu mu dai yake kallo, jaridarshi a sama tamkar karatun yake yi. Amman baice uffan ba. Innarmu ce ta leƙo tace. "Ko kusa baice miki ya kasa ba, ba gazawa bace tasa bai cika alƙawarin nashi ba. Kuma tunda yace zai cika alƙawari Abidah ai sai a barshi. Batun a mayar mishi da mata wannan ba huruminki bane, tunda ai ba ke kika ɗaukota ba" "To hakane Ruwayya. Allah ya kyauta zamu ce. Allah yasa a soma karatun a sa'a" "To ameen Abidah" Luba ta miƙe ta shiga ciki, Innah Abidah ma ta fice a lungun ma. Mijinyawa na kalla kawai, idanunshi yayi jawur sosai. "Kizo Hindu ga abinci ki ba Mijinki yaci, wannan yarinyar ta tashi fa". Miƙewa nayi na shiga ciki, idanun Baba Sojanmu a kaina.. Asama'u na ɗakko na kawoma mijinyawa. Na koma ciki na ɗakko tire nazo na dure a gaban mijinyawa, na koma na ɗakko langar dake kan gaushi cike da nama a kakide na dawo. Shinkafa da miya na zuba mishi, na tsami namannan guda huɗu tuƙu_tuƙu na zuba mishi. Baba Sojanmu yake kallo shima idanunshi a kanmu yake. "Naƙoshi" Ya faɗa gabaki ɗaya ya kasa sakewa, sai ɗari_ɗari yake yi. Komawa ciki nayi. Innarmu ki ce ma Baba Sojanmu ya shiga ciki dan Allah" "Ke ki raba kanki da tsokano tsuliyar dodo. Kinga a ciki yake daku. In ba so kuke yi ya zaneku, ko yasa a banƙareku ba. To wallahi yaci abincinshi kawai ya kama hanyarshi, in dai ba fom yazo siya miki ba ato. Zuchiyarshi a kusa take, dan ya amayar muku ba komai bane. Babu ruwana. Jiya kina jin yadda ya kusan kwana yana turanci, da safe kinji Baba sojanku yayi hausa yau? To ki kiyaye. Anfa ƙureshi dan ƙurewa" Luba dariya harda faɗowa a gado. "Wayyo dariya zata halakani. Harna tuno sanda ake banƙare su Qazzafi in suka yi wani laifi. A barsu a rana kamar an gasa kilishi suita gumi." Qazzafi ya tuntsure da dariya kawai. "Luba bakya ji wallahi. Lokacin haka zaku zo kuita tsokanarmu, harda mintsini fa. Muma in aka sakemu muita dukan yara, duk wanda ya kulani ranar saina fasa bakinshi. Hindu ce kaɗai zata kulani in amsa. Itafa har ruwa take kawomun. Gashi sai ta hau turmi take iya bani ruwan in sha. Rayuwa kenan" Ni dai komawa nayi na barsu sunata hirarsu. Mijinyawa ya kasa cin abinci. Sai cewa yayi fa. "Zan tafi zan dawo nan da kwana uku, sai ayi batun fom ɗin. Banga Azgar ɗina ba. " Yana ta bacci yaci tuwon matarshi. Ka daure kaci abincin mana" Baba Sojanmu ya kuma kallo. Da sauri ya sauke kanshi, ganin yadda yake muzurai. Miƙewa yayi ya miƙomun Asama'u, na karɓeta. "Baba Sojanmu zan koma. Kayi haƙuri nan da kwana uku zan dawo, sai ayi batun fom ɗin in sha Allah. Dan Allah kayi haƙuri." In kun tanka, to ya tanka. Idanunshi rarrabasu yake yi a tsakanin mu biyun. Inya kalleni, sai ya kalli Mijinyawa. Yaƙi cewa uffan, tunda muka ga yana hura hanci babu shiri ya miƙe ya fita babu guiwa. Miƙewar da zanyi, naga Baba Sojanmu yana jijjiga ƙafarshi. Duk da haka na dake na nufi fita da zummar raka mijinyawa. Ai wallahi sai jin ihun Baba Sojanmu muka yi, Irin ihun sojaji da suke yi, in rayukansu ya kai bango. Ya miƙe ya nufo kanmu a guje wallahi. Yana zuwa ya ruƙunƙumeni ni da Asama'u. Ai sai ya zare bell ya zuba mun a gadon bayana. Yana ruƙunƙume dani. Mijinyawa ya shigo da sauri, dan da harya ruga da gudu, dawowa yayi, da yaji saukar bell a bayana. Aiko ya ɗaga bell ɗinnan ya sauke mishi a kafaɗarshi shima. Ka gudu, ka gudu, ka gudu mijinyawa kaje" Na faɗa da ƙarfi, idanuna a rufe jikina yana wani irin kaɗawa kar_kar_kar. "Aa Hindu bazan iyaba" Bell ya kuma ɗagawa yana shaƙe dani, Asama'u sai ihu take yi. Innarmu taƙi fitowa, sai Qazzafi, Luba, Yaya Saratu, da Innah Abidah, suka tawo a guje, harda Salamatu ashe tana ciki. Aiko ya kuma sauke mana bell ɗinnan du mu biyun. Mijinyawa saida ya gantsare. Wani irin ihu na saka ihun da ba gidanba, ungywarmu kab saida akaji wannan ihun nawa. Mrs Bukhari ce. To sai Allah ya sake sadamu ranar litinin kuma Son so💪🏼💪🏼MRS BUKHARI *Wai kina da labarin Gidauniya ta mata, farin cikinsu, da walwalarsu, mai suna *MURYAR MATA (FARIN CIKIN AL'UMMA)*🧕🏻👩🏻‍🎓 *Wanda ni Mrs BUKHARI muka yi haɗin guiwa wajen buɗewa, tare da sauran shuwagabannin Taskar Badiat Ibrahim?* *ku matso kusa ki kasance a cikin wannan tafiyar ta Alkhairi, tafiyar da zata gyara rayuwar Aurenki, tafiyar da zata gyara miki tunaninki, tafiyar da mace zata gane ni'imominta, tasan kima da darajar kanta, gidauniyar da zata koya miki sana'ar da zaki dogara da kanki, gidauniyar da zata koya miki tattalin uwar kuɗin kasuwancinki, da yadda zaki tattali ribarki ta yadda zaki ƙarfafa kasuwancinki, sha'awar son komawa makarantar addini, ko na boko kike so? To biyomu muje wannan gidauniyar taku ce mata, gidauniyar ta ƙunshi abubuwan da zatonku ma bai zata ba.* *Ga lambar wayata ga matan da basa cikin Taskar Badiat group 1 group 2 group 3 sai kui mun magana in sha Allah zaki kasance a cikin wannan tafiyar ta manyan mata* (08179523215) *Ƴan taska kuma zaku iya tuntuɓar Admins ɗinmu ta pc domin kuji yadda tsari da dokokin kasancewa memba a cikin wannan shahsrarriyar, garnaƙaƙar gidauniya wacce ta haɗa manyan masana zamantakewar aure, malamai, manazarta, mahukunta, ƴan gwagwarmaya, masana ta ɓangaren gyaran aure, ƙwararrun ƴan kasuwa, da gogaggun ƴan boko, wanda ya haɗa matan arewanmu da kudunma baki ɗaya, zamu kasance a duk faɗin Najeriya da izinin Allah* Tun daga wannan ihun da na jishi a saman kaina tare da saukar bel, ban sake sanin me ake ciki ba. Ɗib na dena ji, ko ganin komai ma. Gidansu Hindu:. Ɗaga bel Baba Sojanmu yayi ya sake sakar musu du su biyun. Ita dai dama Hindu ta sandare tamkar itace. An rasa wanda zai iya matsowa gudun ta ɓare dashi. Sai sake dai taruwa akeyi, abun nema to ya samu. Qazzafi ne yazo da sauri, yana son zare Asama'u wacce ta shiɗe da kuka, ga tsoro. Aiko ji kake tabbb saukan bel a gadon bayanshi. Baba Soja ya zuba mishi. A haka ya ɓanɓare Asama'u a hannun Hindu, da ƙyar sabida tayi wani irin sandarewa na ban mamaki. Ya miƙata ga Luba, Luba ta shige ciki da'ita a guje. Sai hawaye take sharɓewa. Aka cika maƙil kab matan gidan, sai ƙus_ƙus akeyi. Su Innah Abidah da Innah Yabine ma suka samu ƙarfin guiwar ba da haƙuri. Sauran kam sai dai kallo kawai. Masu jin daɗi nayi, waɗanda abin bai musu daɗi ba ma, gasunan dai. Mijinyawa kanshi a ƙasa kawai hawaye na ɗiga yana ƙoƙarin makanta ganinshi. Ba kukan dukan yake yi ba. Jin zafin fulalar ne ya gigitashi daya tuno cewar irin yadda yake jin raɗaɗi, Hindu dake a matsayin mace zata iya jin fin nashi. Gashi duk yadda Hindu ta kai da son rufin asirinsu. Yau gashi an tozartasu a idanun maƙiyansu, masu burin son ganin faɗuwarsu. Wannan shine manyan dalilan zubar hawayenshi. Gashi su Baba Nagoɗi basa cikin gidan, balle su kawo ɗauki. Su Qazzafi sun yi kaɗan su yi wani agaji. In ana babbakar giwa ba'a jiyo ƙaurin zomo. "Ai musu Afuwa wani abunne ya kuma faruwane? " Heyyyyyyyyy Aje waya" Ya daka ma Innah Mairamu tsawa, jikinshi fa rawa yake yi. Wata faɗuwa da ƙara Hindu ta kuma yi. Ji kake tum ta faɗi. Da mijinyawa da Qazzafi har suna gwara kai wajen ceton Hindu. Zubb Baba Sojanmu ya kuma zuba musu bel ɗinnan tare. Saida yawu mai yawa ya zubo a bakin Mijinyawa, ya zuba a jikin Hindu bai yi aune ba. Shigowar Baba Nagoɗi a guje ne yasa aka daddare. "Yauwa Alhamdulillahi gara da kuka dawo" A lokacin wani irin ƙara Hindu take yi, kamar irin na mage haka abun tsoro. Tana wani irin kanannaɗewa. Amman a hakan Baba Sojanmu ya kuma zuba mata bel ɗinnan, ai sai suka nannaɗeta suka cureta waje ɗaya tamkar babu ƙashi a jikinta. Allah al hakim, babu wanda bai tsorata da yanayin halittar Hindu yadda ta nannaɗe a wannan rana ba. Take ƴan cikin falon suka soma matsawa, harda masu zuba ihu. Iyayene kusan suka cika falon dama. An cika sosai, harma mahaifiyar Luba tayi ƙarfin halin shigowa. Dake ba yau ake tare ba, kuma ta jima tana shigowa ceton su Qazzafi, da ragowar yaran maƙota. Baba Nagoɗi ya matso yana ƙoƙarin ƙwace bel ɗinnan amman ya kasa sam, ƙarfin soja da farar hula bazai zama ɗaya ba. "Ka kyaleni in kashesu in huta Nagoɗi. Let mi fut him in his fi-les. Laifinka nake gani akan komai da yake faruwa anan. Ni yaronnan zai kwaso jiki wai shi loba boi yazo babu tartibiyar magana hi tink am sutufib o wat? Don eba disresfet mi lik dis agen. E militiri haushold is not e filegiraunt. If yu don hab news abaut de sukul, don sho yo fes hiya agen. Ni zaku nuna ma soyayya. Ni zaka nuna ma kai jarmai ne a soyayya? Je ka tambayi Moda ɗinku kai da'ita Hindun, i min yo inlo. Zata baku labarin irin soyayya da muka buga. Da irin yadda jarumtata take. Soja ba gidan wasa bane. Ashe kazo ka ganta ne kawai ya kawoka. A tunaninka ku saurayi da budurwane oh wat.?" Ai sai ya ɗaga bel ɗinnan ya nufi Mijinyawa dake ƙoƙarin soma karatun Qur'ani ma Hindu, ya tsorata ganin yadda kanta ya shige tsakiya tamkar macijiya. Gashi an rasa wanda zai ma iya matsowa inda take, daga shi sai Qazzafi kawai. Ai kuwa sai jin saukar bel yayi, a mazaunanshi kaɗai ta sameshi harshen bel ɗinne, Baba nagoɗi shi aka zugama jikin bel ɗin. Idanu mijinyawa ya runtse da ƙarfi, tare da girgiza kai irin na wanda zafi ke ratsa ɓargonshi. Baba Nagoɗi kuwa ihu yasa. "Ahhhh wayyo Allah na" Jirine yake shirin kayar dashi to jikin tsufa. Ya haɗu da bel ɗin soja. Baba Dogara da Qazzafi, da Yahuza da suka shigo yanzune suka riƙe Baba Nagoɗi. Aka zaunar dashi a doguwar kujera. Baba Soja na tsaye yana tsuma. " Qazzafi, Yahuza ku mai yaren sojoji ko zai huce. Janaral kashemu zaka yi ne. Ku bani ruwa. Kaima Allah ka ƙyale yarannan haka koma me suka yi maka" Baba Lukumanu ne da yazo, suka ruƙunƙume Baba Sojanmu da shi da Baba Dogara, akasa Qazzafi da Yahuza su karɓe bel ɗin. A lokacin mijinyawa ya soma ma Hindu karatu ga kuka yanayi wiwi yana jin danshin jini a bayanshi. Baba Sojanmu ya dinga kawo ma su Qazzafi naushi da ƙafa suna kaucewa. Sun kasa ƙwace bel ɗinnan. Ƴan gidan an nutsu anata naɗe labari. Suna ta kallon Mijinyawa da Hindu, ga kuma kallo a wajen Baba Soja. Yaya Saratu dai kuka kawai take ɗirka. Luba ma kuka take yi mai gunji sosai. Su Salamatu sai murmushi suke sakarma juna ita da Innah Abidah uwarta. Su hakan yayi musu fari sosai. Da abun zaifi haka ma suna maraba dashi. Hindu da mijinyawa sun matuƙar ba Saratu tausayi wallahi. "Janaral kaima Allah ka sassautama kanka. Kayi haƙuri wannan yaron sirikinka ne fa. Ka daure. Ya'isa haka wannan ai dole ya koma gida yayi jinyar jikinshi. Ni kaina Yahuza sai kun kaini asibiti, babu yawu sam a bakina. Ga jiri daga zaune ɗibata yake yi. Wajen fa ya ɗaye ko Yahuza? " Cewar Baba Nagoɗi da yake ta faman haki, Baba sojanmu na kallonshi yana ƙanƙance idanu na masifa. Baba Nagoɗi ya kuma cewa. "Saratu tawo ki taimaka mun in miƙe, dena kukan, ya zamu yi da janaral. Yaranne ma abun a duba. Janaral yau allurarnan tunda ta tashi yau sai Allah kuma. Kuma nima nayi tunanin in yaronnan yace zai zo cikin gidannan ba za'a kwashe lafiya ba." Saratu tayi sauri ta taimaki Baba nagoɗi ya miƙe tsaye. "Duk kowa ya watse bana son ganin kowa a falonnan, ko bakin ƙofar falonnan. Hindu ku kinkimeta ku shiga da'ita ciki, wajen gyatumarta. Tananan ma kuwa? " "Tana ciki Baba" Cewar Saratu dake riƙe dashi. "Ruwayya manyan ƙasa, ta janaral ikon Allah. Kai Magawata kaje kaji. Kayi haƙuri kuma, na roƙeka kayi haƙuri dan girman Allah. Duk da janaral ubane, ko baka auren Hindu zai iya maka hukunci. Kuma ka cika mai biyayya daka nuna shi asalin ubane gareka, kamar yadda Qazzafi da Yahuza basu isa yin tari in yana dukansu ba. Allurarshi ce ta tashi. Kaje in ka shirya batun makarantar, da batun dawowa birnin ka neme ni dani zaka yi magana daga yau" "Hel no dani zai yi magana ba da kai ba. Bazan kuma yadda ba ehe wallahi bazan yadda ba. Ai duk kai kaja har aka kai wannan shekarun." "Ai ni na bashi auren ɗiyar ba kai ba. In iyakata zaka nuna mun sai in zare hanuna." "Go ahed an rumub yur han an so wat?" Kuma harzuƙa ma yayi. Yayi kica_kica zai ƙwace suka kuma cabkeshi gam. Mijinyawa, da Qazzafi ne suka kinkimi Hindu a cure suka shiga da'ita ciki. Innarmu tana zaune shayi take sha, ga Azgar a cinyarta Asama'u kuma tayi bacci, sai ajjiyar zuchiya na wahala take yi. "Ku shinfiɗeta a gado Qazzafi". A gado suka shinfiɗeta, mijinyawa yana waige har ya fita, sai ya dawo ya tsaya a gaban Hindu. Hawaye kawai yake zubarwa. Innah ta miƙe taje ta tsaya kusa dashi. " Kaje kaji, kayi abinda Nagoɗi yace maka. Jeka abunka. Ka bari in ka shirya sai ka dawo" "Innah dan girman Allah kar a rabani da Hindu. Bazan iya ɗauka ba. Zan dawo mu sai fom ɗin a bani ita, zan je nan da kwana biyu zan dawo" Fita yayi da saurinshi. Innarmu ta girgiza kanta. Ta dubi Qazzafi dake ma Hindu adda'a ƙur tayi mai da idanunshi. Taga irin ruɗu da ɗimuwar da yake ciki. Kanta ne ya soma yamutsewa tana ganin jiri jiri. Ga ƙara mai kama dana mage da Hindu take yi, da ƙaran haɗuwar haƙoranta suna sake sosa mata ƙwaƙwalwarta. "Innarmu lafiya. Naga kina ta kallona. Kinga halinda Hindu take ciki?" "Babu komai. Bari in yi tofi a ruwa ka shasshafa mata. Zasu tafi. Dama Janaral a kusa yake hmmm, tun jiya yake son dukanta bai samu zarafin bane, sai yanzu" Zama tayi tana dafe kanta da takeji kamar rabewa yake yi. Mijinyawa ya fito falon ya samu anci nasara Baba Sojanmu ya miƙa bel ɗin, amman fa jikinshi sai rawa yake yi idanunshi yayi ja sosai. Sum _sum _sum mijinyawa yazo wucewa Baba Sojanmu ya zabura, kica_kica. A guje mijinyawa ya fice har yana bigewa. Yana ratsa gidansu Hindu, ana kallonshi, harda masu dariya da ƙyar ya fita a cikin gidan. Ji yake yi inama ƙasa ta buɗe ya afka. Har cikin ranshi baya jin zai iya jin zafin abinda Baba Soja yayi mishi. Kamar yadda Nanno ke tozarta. Kuma tayi haƙuri ba tare da ta taɓa yin ƙorafi ba. Shima yayi biyayya. Ko yankashi Baba Soja zai yi, yana tare da Hindu iyakar runtsi. Shiru yayi tare da kallon saman layin, ya kalli ƙasan layin sai ya lumshe idanunshi. A hankali yake tafiya tamkar majinuni. Bai san me yake ciki ba, babu tsimi babu dabara. Allah ne yasan karatun kurma. "Malam rayuwarka eh ta isheka ne eh? In eh ta isheka, ba ga babban hanya ba, ka hau tirelar eh lemo ta take ka mana" Cewar wani mai acaɓa mashayine mai jan ido. Ashe mijinyawa hanya ya shiga gadan _gadan bai sani ba, harma Acaɓa ta kusan bigeshi. "Kayi haƙuri dan Allah" "Kai kauce eh dallah" Yai saurin matsawa, tare da ɗan seseta kanshi amman dai ina. Da taimakon Allah ya isa wajen Abokinshi Auwali mai gwanda. Ganinshi kawai Auwali yayi ya zauna a benji yana haki, wani irin tiririn zafin zazzaɓine ke damunshi gaya. "Ahh wa nake gani kamar Mijinyawa mai Lemo? Ko da yake ganinka babu mamaki cikinshi, tunda dai matarka da kake Aure tananan." Zama yayi kusa dashi bayan ya sallami wani mai siyan ayaba. "Ai jiya ma Nawata muna tare dashi anan, Uwar haka. Harda Shehulle an haɗu anyi zumunci wallahi. Kaima zaka dawone ka kafa teburin lemunka a titi ko yaya? Shi Nawata ya samu aiki a tasha yana gurgurawa, Shehulle ne yai mai hanya. Ai ya kamata kuma ku baro ƙauyannan haka" Idanu mijinyawa ya lumshe kawai. Cikin dauriya suka gaisa. "Baka da lafiyane naga idanunka kamar ma fa kuka kayi. Laa kaga ai jinine a rigarka fa. Kaga zo zo muje" Auwali ya ja hannunshi zuwa shagon da anan suke kwana. Ga tarin buhunhunan kaya, kaca kaca ɗakin dai babu kyan gani. "Zauna in kawo maka tuwo da magani" Shi dai baice uffan ba, Auwali na fita ya ɗauki buta ya leƙo ya ɗaura alwala ya koma ciki, tare da tutture kaya. Nan ya shiga sallah inya yi sujada sai yayi kamar bazai ɗago ba. Haka ya dinga yi. Har isha tayi. Tuwon Auwali ya tursasa mishi, loma biyar yayi, ya watsa magani bakinshi yabi da ruwan shayi mai madara, da Auwali ya kawo mishi. Kafin kace me, zazzaɓi ya lulluɓeshi mai zafin gaske jikinshi babu ta inda baya rawa, hawaye sai bin gefen idanshi yake yi yana sauka a fulon tsumman da Auwali yai mishi matashin kai. "Ko dai inje in kirawo Nawata ne yazo yaga halin da kake ciki ne. Naga kamar hatsari fa kayi ai ya kamata aje asibiti. Da ƙyar ya tashi zaune yana jin ciwon zanannan yanzune ma yake shigarshi, sabida tsamin da yayi. " Aa ba sai ka kirashi ba. Gobe da asussuba zan koma garinmu hatsari nayi Auwali. Babu damuwa ba sai naje asibiti ba. Asibiti basu da maganin da zasu bani. Sannan wannan ya tsaya a tsakaninmu. Kar ka faɗama Shehulle, ko Nawata nazo. Basu san ma nazo ba. Dan Allah abokina.:. Gidan Nagoɗi.:. "Sabida Allah sai ka kamasu kaita lafta, nima gashi na samu tsarabata. Yarannan sun wuce duka, kaima ka sassautama kanka, girma yana ta hawanka. Tunda ka dawo da'ita gida shikenan sai ka zuba idanu aga zuwa da dawowan. Ni a wajena dakkotan baimun ba, nayi _nayi ka ƙi yaddane shi yasa na barka. Wannan dagiya taku daka gado, itama Hindu ta gado a wajenku, ku sassautata. Yanzu jibi Ruwayya duk yadda aka taru ana wannan dambarwar, mulkinta dake yana kanta ai bata ma leƙo ba fa." Qazzafi ne ya leƙo. "Baba Sojanmu zo kaga abinda Innarmu da Hindu suke yi" Yana zazzare idanu yace. "Me suke yi, ta kyale Hindu inma tafiya da'ita zasu yi sai dai su tafi da'ita. Babu abinda zanyi akai ni. Makaranta ne dole ta koma. In kuma basa ƙaunarta shikenan sai su ɗauketa suje can su rayu da'ita a duniyarsu" Baba Nagoɗi ya girgiza kai. "Kai me yake faruwa? " "Baba Innarmu ce ta shiga wani hali, sai jijjiga kanta take yi, ga Hindu sai wani irin abu take yi" Baba Sojanmu da jin haka ya miƙe sai gashi a tsaye a ɗakin. In ya kalli Hindu, sai ya kalli Innah. Baba Nagoɗi ne yayi sallama ya shigo. Innarmu na riƙe da kanta, sai jijjigashi take yi, idanunta tamkar zasu zazzago mata. "Jeka Janaral adda'a za'ayi musu. Kai Qazzafi zo kayi ma Ruwayya. Ni bari in ma Hindu" Baba Sojanmu yana tsaye ƙiƙam idanunshi akan Innah Ruwayya. Qazzafi yaita ragargazo karatu, Baba Nagoɗi nayi. Duk da ƙarfi suke yi. Hindu ta shiga kurma wani ihu ƙasusuwanta suna wani irin ƙara. Take gidan ya kuma birkicewa, aka cika falonnan har ƙofar shigowa. Karatunsu kawai kake ji da ƙarfi yana tashi. Warware Hindu suka yi, ta sauke ajjiyar zuchiya a jajjere, sai numfashinta ya daidaita a hankali. Innarmu kuwa ta dena jijjiga kan nata tayi shiru tana kallon Qazzafi. Baba Sojane ya riƙo hannunta ya ɗagata. Baice komai ba ya fito da'ita ƙofar ɗakin a cike dam da mata, harda Innah Abidah data cika ta batse. Ganin Baba Soja ya riƙo hannun Innah. Baba sojanmu bai dureta ko'inaba sai turakarshi, ya zaunar da'ita. Ya tsiyaya mata ruwa a kofi ta karɓa tasha. Zama yayi yana fuskantarta da kyau. "Ma lob ɗago ki kalleni ko zanji daɗi. Ki faɗamun menene, na ɓata miki raine akan abinda nayi ma Hindu, ko kina ganin bai dace in tsaya rayuwarta ta inganta ba? Nine nan mai tsayama yaran maƙota, marayu, da zawarawa, da yaran ƴan uwa fa" Kallonshi Innah Ruwayya tayi da kyau. Bata ce komai ba, amman yaga komai a cikin ƙwayar idanunta. Murmurshi ta sakar mishi. Sai yayi ajjiyar zuchiya, tare da yin wata ƴar dariyar basawa amman can ƙasa_ƙasa. "Ai baka laifi gogan Ruwayya jarumin maza, maza gumbar dutse. Lallai naji kana ba gidan labarin irin soyayyar da muka buga. Wannan yanayin kuma yana da nasaba da su Hindun, amman bai shafi hukuncin da kayi mata ba. Taruwan ƴan gidannan, da maƙota_maƙota shi ya hautsinani kasan dama so akeyi a gansu a ƙasa. Amman duk da haka basa ƙasa, yaron zai share hawayenta. Ina da yaƙini a kanshi." Ɗan juya idanu yayi yana girgiza kai halamun tunani kafin yace. "Nayi farin ciki da ba nine silar shiganki wannan halin ba. Kiyi kwanciyarki anan, kafin su Nagoɗi su gama abinda suke yi. Akwai abinda kike sha'awar ci ko sha da daddare in kawo miki? " "To kaza gashasshiya nake so, da nono mai sanyi in zan samu" "Me zai hana Gimbiya zaki samu, ai ko babu ko rugane zanje in nemo miki. Matar janaral tauraruwar zuchiyar Janaral" Murmusawa tayi. Nan sukaita tattaunawa, Innah Ruwayya ta dinga tausarshi tana bashi kalma har ya huce. Amman yace baya ma son ganin Hindu ko jin halin da take ciki. A haka aka samu nasara wannan allura ta lafa. Innah Abidah kuwa a wannan ranar kusan alƙiyamarta ce ta tsaya. Ganin irin yadda Baba Soja yake ta ririta Innah Ruwayya. Da kuma maganar daya faɗa ɗazu wacce take ta mata ƙaiƙayi a ruhi. Kazarma a mota ya sakata suka je suka siyo. Itama ya siyo mata nata, amman ita a wajenta da kazar, gara ma kunu maras sikari. Hindu kuma tunda dai ta samu wannan bacci fa, bata farka ba. Har washegari babu labari. An yi tunanin tashinta ma sabida sallah, amman gaskiya bata tashi ba. Asama'u sai hayewa jikinta take yi tana kuka. Azgar shi baya kukan amman du yaran haka suke manne da Hindun. Abu fa har magriba. Hindu ga numfashi dai tana yi, amman taƙi tashi jijjigawar duniya. Innah Ruwayya tayi ma Baba Soja magana akan halin da Hindu take ciki. Tana so suje Durumin iya da'ita wajen wani malami mai ruƙiya. Yace shi babu ruwanshi, in sun ga dama suje, in aljanun sun so su saceta ma uban kowa ya huta. Haka dai Qazzafi ya tuƙasu zuwa Durumin iya, da rakiyar Saratu da Zubaina. A gidan maganinne aka samu ta farka bayan adda'a da ya dinga yi, yana yarfa mata tuwan tofi. Ta farka, amman babu baki, sai idanu. Ga jikinta yayi tsami sabida makarai, da kuma yadda ta sha nannaɗa. Ta miƙe ma ta kasa miƙewa sai su Yaya Saratune suka taimaka mata ta miƙe, aka kaita mota. Ko da suka dawo. Innah Abidah na falo ranar kwananta ne, ta kallesu ta watsar, a cikin gidannan babu wanda ya tako yaji jikin Hindu, ta farfaɗo ko bata farfaɗo ba. A maza mazan kuwa harda samarin gidan saida duk suka shigo. Da yaran maƙota da suke kwana a shagunan gidan, tare da mazan gidan duk sun shigo. Qazzafi kuwa sai da aka tilasta mishi, aka guyabeshi kana ya tafi. Amman yana kiran lanlin yaji ya jikin nata. Yaya Saratu bayan sun dawo ta samu tawul duk ta goge ma Hindu jiki da ruwa mai zafi, bayanta daya fashe ma ta gasa mata, Innah ta ba da man zafi aka shafa mata. Sallolinta tayi abunta a zaune, ba baki dai, sai magana ƴan uwanta suke yi, duk sun ruɗe, Innah ce take ta ƙarfafasu. A baki Innah ta ba Hindu kunu, yaranta suna jikinta, annuri fal fuskarsu ganin uwarsu ido biyu. Azgar sai magana yake yi mata, amman ina ba bakin magana. Innah sai girgiza kai tayi yi. Tausayin yaran duk ya cikata. Hankula sosai suka tashi gaskiya.:. Mijinyawa.:. Washegari sassafe ya nufi tasha. Yamman sakaliya sai gashi ya sauka a Jama'are. Kai tsaye a ƙofar gidansu Qasimu acaɓa ya saukeshi, ya biyashi ya tsallake kwata ya shige. A zaure yayi sallama. Sai ga Qasimu zuruf. "Tun ɗazu nake ta zuba idanu ko zanga dawowarka, kaga yanzu shigowata kenan. Mijinyawa ya riƙe hannunshi zuwa waje. Shagon kwana ya tura suka shiga. Nan ya labartama Qasimu abinda ya faru. Tare da cire rigarshi ya juya ma Qasimu bayanshi, duk ya fashe. Dariyar mugunta wallahi har fitsari saida Qasimu ya soma a wando. Mijinyawa yayi kasaƙe yana kallon abinda yafi zare tsayi. Rigarshi a hannu. A guje Qasimu ya fita, ko miƙewa baya iya yi. Yaje ya sako kaya ya dawo da wasu a hannu. Mijinyawa kuwa kwanciya yayi zazzaɓi sosai yake ji. "Tashi ka sauya kaya kafin ka shiga, in Nanno ta ganka da jini a riga sabon rikici ne kawai. Wai amman dan Allah kayi ihu sanda yake dukanka? Soja fa" Ai sai dariya kamar zata halakashi. Tsaki mijinyawa yayi, tare da miƙewa ya sauya riga, wandoma bai sauya ba. Anan kwance yabar Qasimu dariya na shirin halakashi. Har ya isa ƙofar gida yaji tub_tub Qasimu ya tawo da gudunshi, tare suka shiga bai ko kalleshi ba. Bafa daina dariyar yayi ba, yana yi. Tsakar gidan sunci sa'a ba mata sai yara. Ɓarayinshi suka wuce. Ya buɗe ƙofar suka shiga. Qasimu yace. "Ai alwala zamu yi muje sallah in mun dawo sai kayi wanka, kasha magani, na karɓo maka ruwan zafi a wajen Baraka sirikin Soja." Hararshi kawai yayi, bai tanka ba. Kafin a idar da sallah fa jikin Mijinyawa ya rincaɓe a daddafe aka idar dashi. Ana sallamewa ya fita kawai Sai daga baya Qasimu ya bishi ya samu yana ta rawar ɗari. Ruwan zafi ya karɓo mishi a wajen Shafa sabida yaji labarin Nanno jiya tayi tafiya. Taje biki, daga can wai sunyi da Nawata zai kai Uwatale bikin, in an gama sai su koma Kano da Nanno, taga waje. Jin wannan labarin ya kuma hautsina Mijinyawa tunda yanzu dole sai sun jira dawowar Nanno. Shagon gidansu Qasimu suka koma acan suka kwana jikin dai kau. Bayan ya gargasa jikin nashi, Qasimu yabi layi_layin shatin bel ɗin daya kwakkwanta raɗau a allon bayanshi. Ga ciwo ga rashin bacci, yana kwance tunanin tutar so kawai yake yi. Yama rasa inda zai saka ranshi. Tunaninshi ko ta farfaɗo, ko tana nan cikin halin daya barta? Inta farfaɗoma yasan tananan tana amsar zafin dukan da akayi musu, ga kuma ciwon jiki na tashin makarai. Idanu ya lumshe, tare da miƙewa zaune akan katifar yayin da yake kai. Idanu ya kuma lumshewa, tare da tuno Hindu a lokacin da suke halin yarda da juna. Azgar da Asama'u ya tuno suma. Saida Qasimu ya farka fitsari ya ganshi a jingine yanata karatun Qur'ani. Kai Qasimu ya girgiza, ya fito wajen inguwa a talatainin dare, ya tsula fitsarinshi a gaban kwata yayi tsarki ya koma ciki da butar a hannunshi. A haka washegari suka wuce wajen Kawu da hantsi suka isa. Kawu na zaune yana rubutun Qur'ani a allo a ƙofar gida yana zaune akan buzu sai gasu. "Qasimu kune kuka sake dawowa kenan? Na dawo iyali sun sanar mun da zuwanku. Nasan dama dole da wata matsalar ko?" "Eh Kawu da matsala ita ke tafe damu. Ina wuni kawu? " Nan suka gaggaisa suka kwashe bayanai kaf suka labarta mai, harda tafiyar Hindu gida. Amman banda batun karatunta, amincewar komawa birnin kawai suke da buƙata. "To akanme zata hanaka alhalin ta barshi shi ya tafi. Ɗan gwalne shi ko duk ba ƴaƴanta bane? Zan sameta muyi magana. Amman yanzu kam suna wajen bikin ɗiyar Amadudu, iyali ma suma sun tafi jiya. To in suka dawo zanje da kaina mu yi magana in ji dalilinta in sha Allah. Ba zai gagara ba, zan mata magana. Bata kyautawa abubuwan da take yi. Wasu na dawowa kunnena ta bakin Gude, wasu kuma bana sani. Ita Jamila itace take ƙulla wasu abubuwan. Inda ace ita a matsayinta ta mace kuma ya. In uwarku ta kauce sabida tsufa, ko wani abun. Ita ya dace ta dawo da'ita hanya. Amman Jamila halinta sai ita. Wani daga cikin gadonku ma na wasu manyan gonakai da Ɗan Safiyo ya mallaka, da da aka danne anata rikici akansu. Allah yayi sun fito an ma siyar kuɗaɗen suna hannuna, Salihu dashi akayi komai" Sun dai jima, Qasimu sai bashi wasu labaran matsaltsalu yake ta yi. Kawu yayi tsam yanata nazartar kalma bisa kalma. Kafin daga bisani dai suka mai sallama tare da komawa gida jiran dawowar Nanno, wanda baisan yaushe bane. Shi dai yananan an barshi da dakon tunani da jumurin jiran dawowar Nanno, da baisan yaushe bane. Aka tura har kwana huɗu, jikinshi da sauƙi, zuchiyarshi ce babu sauƙi sam, damuwa da tunani ne ya aureshi gaya. A kwana na biyar da daddare kawai mijinyawa yace gobe sassafe Kano zai wuce, Qasimu ya rakashi zai je batun siyan fom ko Allah zaisa yaga Hindu da yara. "Ni kam bafa zani ba, tsoro nake ji inje ya rufe ɗaki damu haka siddan. Sannan akwai kuɗi a hannunka ne ma na fom da kudin motarmu? " Akwai na fom ɗin. Na mota yana wuyanka. Kuma wallahi sai munje. Inma kashemu za'ayi a kashemu" Qasimu ya kafe. Mijinyawa ya rantse sai yayi rakiyarnan. Cikin sarayar da rai suka kamo hanyar kano, sun ko sha ankon yadi mai ruwan bula, sai gasu da magriba a ƙofar gidansu Hindu. Amman me? tsoro ya hanasu shiga, sun kasa aika yaro. Suna wannan raɓe ɗayan biyunne, suka hango Baba Soja da wasu matasa da kayan sojoji suna tawowa. "Ga mahaifin Hindunnan ma zuwa. Qasimu gabana faɗuwa yake yi. Kaga yadda yake yi mana muzurai kuwa? Hindu:. Abu kamar da wasa ya zamana ni da su Innarmu sai idanu kawai. Bakina baya magana, ina buɗewa inci abinci, in sha ruwa, in sha magunguna da Innarmu take ta karɓomun. Dukkan abubuwan da ake tattaunawa inaji. Da rikice_rikicen gulme gulmen da aketa yi. Inaji in su Innarmu na hirar. Suna cikin tashin hankali mai girma. Ni kaina na shiga damuwa, Allah kaɗai nake ambato a zuchiyata. Ruhina yana azabtuwa irin azabtuwar da ban taɓa ji ba. Ina dai ta faman tunanin abinda ya hana mijinyawa zuwa. Ko dai jinya shima yake yine? Nayi imanin in lafiya yake zai zo ko da kasheshi za'ayi, zai zo sai dai a kasheshi. Idanuna na lumshe. Tsoron Allah ya sake shigata wato mu godema Allah da yayi mu masu yin magana, ma'ana furuci, kuma yayimu masu ji da kunnuwanmu, ma'ana amo. Lallai baiwace mai girma. Allah Ubangijin masu ji, kuma Ubangijin kurame, Allah alhakim nagode maka da dukkan ni'imominka gareni. Allah buwayi ka buɗemun bakina, harshena yai furuci ko zuchiyata zata rage nauyi. Haka akaita murɗawa, nice wankan magani, nice hayaƙi, sha da kunu, ci a abinci. Ga maƙota sai zuwa dubani suke yi, tare da zuwa ganin ƙwaƙwab. Cikin kwana biyar na rame na zama wata iriya sai kun ganni, dole sai kunji tausayina. Bana fatan maƙiyina ya gamu da cutar makarai wallahi, amman Alhamdulillahi nasan a kwana a tashi Ubangiji zai yaye mun nima. Kwatsam da magriba muka jiyo muryar Baba Sojanmu, daga falo. Mrs BUKHARINRS BUKHARI .................. *Wai kina da labarin Gidauniya ta mata, farin cikinsu, da walwalarsu, mai suna *MURYAR MATA (FARIN CIKIN AL'UMMA)*🧕🏻👩🏻‍🎓 *Wanda ni Mrs BUKHARI muka yi haɗin guiwa wajen buɗewa, tare da sauran shuwagabannin Taskar Badiat Ibrahim?* *ku matso kusa ki kasance a cikin wannan tafiyar ta Alkhairi, tafiyar da zata gyara rayuwar Aurenki, tafiyar da zata gyara miki tunaninki, tafiyar da mace zata gane ni'imominta, tasan kima da darajar kanta, gidauniyar da zata koya miki sana'ar da zaki dogara da kanki, gidauniyar da zata koya miki tattalin uwar kuɗin kasuwancinki, da yadda zaki tattali ribarki ta yadda zaki ƙarfafa kasuwancinki, sha'awar son komawa makarantar addini, ko na boko kike so? To biyomu muje wannan gidauniyar taku ce mata, gidauniyar ta ƙunshi abubuwan da zatonku ma bai zata ba.* *Ga lambar wayata ga matan da basa cikin Taskar Badiat group 1 group 2 group 3 sai kui mun magana in sha Allah zaki kasance a cikin wannan tafiyar ta manyan mata* (08179523215) *Ƴan taska kuma zaku iya tuntuɓar Admins ɗinmu ta pc domin kuji yadda tsari da dokokin kasancewa memba a cikin wannan shahsrarriyar, garnaƙaƙar gidauniya wacce ta haɗa manyan masana zamantakewar aure, malamai, manazarta, mahukunta, ƴan gwagwarmaya, masana ta ɓangaren gyaran aure, ƙwararrun ƴan kasuwa, da gogaggun ƴan boko, wanda ya haɗa matan arewanmu da kudunma baki ɗaya, zamu kasance a duk faɗin Najeriya da izinin Allah* Leƙowa Baba sojanmu yayi. "Ya tayi magana kuwa ko har yanzu?" "Bata yi ba tukunna dai. Muna fatan tayi in sha Allah" Kallona yayi tare da girgiza kanshi, ya ɗagomun hannu irinna kurame. Nima na ɗaga mishi. "Kizo ku gaisa da mijin nata, gasunan shi da abokinshi. Ki tawo mai da yaran banma gansu ba" Wani irin sanyine naji ya ratsa dukkan rassan jikina Alhamdulillahi. "To barka Alhamdulillahi. Yara suna wajen Saratu ta tafi dasu. Damun Hindu suke yi da surutu. Ga Asama'u na lura laulayine da'ita, jiya ma saida na kaita asibiti. Shine Saratu tace zata tafi dasu" Miƙewa Innarmu tayi ta fita. Nabi bayansu da idanuna kawai. Ina jin wani irin farin ciki. Falo:. Su mijinyawa ana gurfane a ƙasan kafet. Ga Baba Nagoɗi, ga Baba Alƙali sai shi Baba Soja. Fitowar Innah yasa su Mijinyawa juyowa, yaji irin ƙamshin turaren wutan da Hindu ke ma kayanta kabbasa. Ashe Innace, amman mayafin Hindunne a jikinta. Ƙamshin Hindu kawai da yaji ranshi yayi fari sosai. Har ya samu nutsuwa a zuchiyarshi gaya. Gaisawa akayi, Innah ta nemi waje ta zauna. "To iyakar fom ɗin yanzu kazo batunshi, shi batun dawowar taku sai yaushe za'a tsammaceka to?" Cewar Baba Nagoɗi kenan. "Bazai wuce sati mai zuwa ba in sha Allah. Daman dai nace bari a soma wannan ɗinne kafin ayi maganar tarewan nata. Dake ina tsoron ƙurewar lokaci. Hannu yasa a ajjihu ya ƙirgo kuɗi ya ba Qasimu, Qasimu kuma ya miƙama Baba Nagoɗi, ya karɓa ya ƙirga. Ya ciri iyakar na fom ɗin, ragowar ya miƙa mishi. "Sunyi yawa, na cire na fom ɗin shikenan. Ranar duk daka shirya batun tariyar sai kazo ka sanarmun. Inma kazo bana gidan to ka jirani" Mijinyawa tunda ya ɗago ya ga sun haɗa idanu sau uku da Baba Soja, sai ya sauke kai bai sake ɗagowa ba. Yana son ya tambayi yaranma ya kasa. Sai Qasimune yace. "Su Azgar basananne bamu ji ɗuriyarsu ba?" Shima a ɗarare yake sosai, kusan sau biyar suna haɗa idanu da Baba Soja. Gashi cikin idanunshi ba wasa. Irin siriyos mutanennanne shi Baba Soja. Kusan bama shi kaɗai bane. Haka kafatanin masu Ɗamara suke. Amman na Soja dabanne. Innah tace. " Basanan suna gidan Saratu" Takadda Baba Soja ya miƙo ya nuna mishi wajen da zai sa hannu, ya saka. Ya miƙama Baba Nagoɗi shima ya saka. Hannu, yana mita a fili kan batun sake_saken wannan hanu shi kam. Baba Soja bai tanka mai ba, sabida hankalinshi na kan takaddar yana rubutu. "To shikenan u kan go ko?" Baba Nagoɗi zai yi magana. Baba Soja yace. " I beg yu in da naim ob Allah don se enitin. Let dem lib bifo i lus ma temfa." Haka suka fita jikinsu a mace mus. Kai tsaye mijinyawa ya aika gidansu Luba yace mijin Hindune so yake a rakashi gidan Luba. Mamansu da kanta ta fito dan tabbatarwa. Bayan sun gaggaisa ta turo Aisha tai musu rakiya har gidan Luba. Sunusi ne ya jagorancesu zuwa cikin gida. Yana ta musu maraba. Luba ta kawo musu abinci, suka ci suka sha ruwa. "Dama naje gidane can wajen Hindu. Baba sojanmu bai bani damar ganinta ba. Na kai kuɗin fom ɗinne. To shine nace ko zaki taimaka zan rubuta wasiƙa ki kai mata ko da gobe ne. Inaso inji amsa daga gareta kafin in bar garinnan. In ba haka ba bazan samu nutsuwa ba Luba. Ko yara ban iya gani ba" Ajjiyar zuchiya Luba ta sauke. "Hmm ai kuwa Hindu tana cikin wani hali, tun ranar daka tafi ka barta, cikin wannan halin take. Bata sake magana ba har zuwa yau ɗinnan, bansan amman yanzu da daddarennan ko ya take ba. Amman da rana dana baro aiki na biya. Har zuwa lokacin makaran nata basu buɗi bakinta ba. Hindu sai ido. Banda gidan magani da aka kaita, yanzu ma haka akan magunguna take" Tuni mijinyawa ya ruɗe ya shiga matsanancin tashin hankali. Yama so komawa gidansu Hindu. Qasimu da Sunusi ne suka nusar dashi haɗarin hakan, kafin ya haƙura da ƙyar. Ya rubuta doguwar takaddar rarrashi, da soyayya, tare da albishir ɗin dawowarsu birni, duk da Nanno tana nan Kano, amman yasan kawu zai tanƙwarata su ci gaba da adda'a. Ya ba Luba akan gobe inta kaima Hindu, ta karanta, ta bata saƙo zasu haɗu a teburin Auwali mai Gwanda. Shagon Auwali mai Gwanda suka koma, mijinyawa ya kasa zaune ya kasa tsaye sam. Qasimu tun yana rarrashinshi ya dawo faɗa, ya kuma dawowa lallashin dan ganin abun azimunne. Sha'anin ya soma tsorata Qasimu duba da yadda Mijinyawa duk ya tashi hankalin kanshi. Sai sambatu yake yi shi kaɗai kawai. Hindu:. Komawa gado nayi na kwanta tare da lumshe idanuna. Ina maƙale a jikin labule naji duk abinda aka tattauna. A daren ranar a sallaya na kwana ina roƙon Allah ya buɗe mun bakina, ya sassautamun nauyin da zuchiyata take yi mini. Innarmu na gefena ta idar da nata sallar tana karatun Qur'ani ne cikin ƙira'a mai daɗin amo. Baba Sojanmu ne ya turo ƙofar ya shigo, dake ba sakata ake sakama ƙofofin ba. Ƙofar babban falo kaɗai ake sakama sakata, sai turakar Baba sojanmu. Shigowa yayi da jallabiyya a jikinshi. "Da daddarennan ina ka baro Abidah Uwargida sarautar mata? " "Tana bacci. Ƙira'arnan taki da take ƙara mun sonki ita ke tashina a duk daren duniya. Inma muna tare, inma bama tare. Alwala zan ɗaura in yi sallah nima huɗu saura yanzu, bacci yayi mun nauyi. Gaki ga ɗiyarki kuna raya dare. Ubangiji Allah ya ɗaga darajarku, ya haskaka sadarinku, ya baku abinda kuke so fid duniya wal akira. Masu tsayuwar dare Ubangiji yana haska musu gabansu sosai, yana cikin lamuransu face_face. Ko da wannan kaɗai kinyi zarra. Balle kyawawan, natijajjun halayenki yawa garesu. Dubanshi ya dawo dashu gareni. Ya ɗan murmusamun, nima na mayar mishi da murmushin. Kaina ya ɗan bubbuga halamun rarrashi, jin daɗi. Miƙewa yayi ya fita, yana murmushi. Ai ko sai muka jiyo muryar Innah Abida har da kukanta wallahi. Kai kawai Innarmu ta girgiza taci gaba da karatunta. Kishi masifa ne wallahi mata. Tsawon waɗannan shekarun gidanmu yaƙi samun zaman lafiya, da haɗin kai. Tsawon wannan lokacin an kasa sanyama zuchiya risilama. Shin sai yaushe kenan komai zai ƙare kenan? Wani ɓangare na zuchiyata yaimun matashiya da cewa. Dukkan abun duniya yana da iyakarshi. Ita wannan iyakar zata zo, ko da shiri, ko babu shiri. Watarana za'a wayi gari ɗaya ya mutu, ƙura ta lafa. Ko a wayi gari ɗaya ba lafiya cikin rashin zato da tsammani. Komai ya lafa. Inma ba haka ba. Akwai ranar da sai dai a kalli juna kawai, an kai matakin tsufan da kowa nafsi_nafsi ne kawai. Ajjiyar zuchiya na sauke. Jama'a ina tsoron Allah, ina tsoron ranar mutuwata, ina kuma tsoron day wan a kabari. Allah alhakim. Bani na kwanta ba sai da nayi sallar asuba. Ban samu farkawa ba har sai da luba ta zo, lokacin Innarmu ta tafi aiki ne inaga. "Hindu! Hindu!! bacci kike yi" Kamar almara bayan na buɗe idanuna, dana motsa harshena da zummar amsawa, kamar yadda nake yi kullum bana gajiyawa. Sai kawai naji na haɗa kalma. Na'am Luba. Ihu Luba tayi ta rungumeni, ni kuma saina kama dariya inata ambaton sunanta. "Alhamdulillahi naji daɗi dana kasance wacce taji muryarki a fari. Kafin nan mijinyawa ya aikoni da takadda, ki karanta kafin a shigo ki bani amsa in kai mishi yana bakin titi maza_maza." Wasiƙar ta zaro ta banin Cikin gaggawa na warwareta. *Zan soma da sallama irinta addinin musulunci. Amincin Allah ya tabbata a gareki.* *Dama ace ina da damar dawo da lokaci baya, da banzo na zama silar shiganmu mawuyacin hali irin wannan ba.* *Inama ina da dama dana riƙeki a jikina na rarrashi abuna.* *Hindu babu wanda yake da damar rabamu tunda Allah shi ya haɗamu.* *Mun zame musu tsuron tsirin tsandauri kafin Allah, bana mutum ba.* *Naji irin halin da kika tsinci kanki na ɗaukewar murya, irin wanda kika taɓa yi a baya.* *Kiyi haƙuri, ki yi haƙuri, kiyi murmushi, mijinki na miki adda'ar samun lafiya a kullum.* *Ina mai baki haƙuri, kinga na kwana har biyar banzo ba ko?* *Nasan baki yi wannan tsammanin ba, bani da lafiya tun ranar dana bar gida, har zuwa yanzu da nake gidan Luba ina rubuta miki wannan takadda.* *Na kawo kuɗin fom ɗinki, a zuwa na biyu in sha Allah zan zone in ɗaukeki mu koma gidan mu anan Kano.* *Naje na samu Kawu munyi magana muna jiran Nanno....* " Sallamar Yaya Saratu ne yasa nayi saurin ɓoye takaddar a ƙasan filo. "Luba kece kika zo duba jikin ƙawa? Nima aiki zan wuce nace bari inzo in dubata. Asama'u ba lafiya harma an kwantar dasu Innarmu ma tana can ita da Baba Sojanmu. Me ya sameta Yaya? ' Jin muryata yasa itama tayi hamdala tana ta murna. Nima murmushi kawai nayi mata. "Ban dai san meke damunta ba. Dama tunda na tafi dasu take ta laulayinta, tunma dai ban ɗaukesu ba. Sannu kema Allah ya ƙara sauƙi. Ga farfesu na kawo miki kici. Ni zan tafi aiki, inna dawo zan biyo" Nan tai mana sallama ta fita. Luba muje ki kaini inga mijinyawa " "Wa wallahi baki isaba, ƴar mai taurin tsiya. Dan wallahi masifa kike shirin ja mana mai tsayi. Ki yi gagawar rubuta mishi amsarshi in kai mishi, tun kafin Baba Sojanmu yazo ya rutsamu. Ke da yasan an kawo takaddarnan har zan mayar da amsa ke ya kike ganin abubuwa zasu kasance ne. Zaneni zaiyi ƙila harda Sunusi" Luba duk ta rikice. Takadda da biro na nema nayi rubutu na naɗe. Jakata na buɗe na zaro kuɗaɗen dana nannaɗe a zani, na ɗiba na mayar cikin ƙasan kaya, mai yawan kuma na nannaɗe a zanin ba tare da Luba tasan menene ba. Na nemi leda na jefa zanin. Na bata. "Bari in kai mishi in dawo mu sha farfesunnan. Yaushe rabon mu gamu." Tayi sauri ta fice. Ajjiyar zuchiya na sauke. Sai nake jina tamkar wata sabuwar halitta. Sai na shiga tausayin bayin Allahn da Ubangiji ya haliccesu ba Magana. Allah buwayi gagara misali. Mai yin yarda yaso da bawanshi. Allah Ubangiji ya bamu ikon tsarkake harsunan namu. Domin akwai tarin tulin al'ummar da harshe zai halakasu, ya jasu izuwa wuta. Luba taje ta dawo muka sha farfesunmu, mukaita hirarmu, aikinma bata je ba. Hankalina ya dawo kan yarana kuma. Da yamma sai ga Innarmu an sallamo Asama'u a Asibiti, tana goye da'ita Azgar kuma ta riƙeshi a hannunta. Ba Innarmu ba, hatta su Azgar sun yi farin cikin jin amona. Duk da kasancewarsu yara. Sukaita wasa a jikina, Asama'u babu kuzari a jikinta sam sam. Ita kuma haka Allah yayita laulayi ne da'ita sosai, wannan laulayi yasa bata girma sam, kamar yarinya ƴar watanni, hatta ƙafafunta basu da ƙwari sosai, data miƙe saita faɗi. Sai ta ɗan soma tafiya ƙafar ta ɗanyi ƙwari. Sai ciwo ya kwantar da'ita, shikenan sai ta dawo ba. Gaga_gaga_gaga_gaga. Haka abubuwan suka ci gaba da cukumurɗawa. An siyo mun fom na jamb na cike, tare da manna fasfo ɗina. Mijinyawa kawai nake jira, inji inda zancanmu ya kwana. Gulma da tsigudidi fa sai wanda ƴan gidanmu suka manta. A cikin ƴan gida, duk wacce ta kawo ziyara sai labari ya dawo sabo. Akaita caccanja labari, tare da ƙawatashi dan yafi armashi, kai subhanallahi, tur_tur da wasu gidajen yawan. Mijinyawa.:. Ko da luba ta kawo mai wasiƙa da leda yayi farin ciki sosai. Musamman daya karanta wasiƙar. Layi uku ce rak, amman wannan layi ukun tana da girman da yafi ace shafi uku aka cika. Murmushi yayi, tare da buɗe ledar. Kuɗin da suka ganine yasa su buɗe baki, musamman Qasimu. "Wannan maɗuɗun kuɗaɗenfa na menene? ' " Hmm baiwar Allah. Babu mamaki ta bani ne sabida jigilar dawowa, da kwaso kaya. Kasan Hindu akwai tsinkaye, da hangen nesa." Shiru Qasimu yayi tare da dafa kafaɗar Mijinyawa. "Bari in maka nasiha ba dan na fika sani ba. Ba dan na fika haƙuri ba, asali ni bama mai haƙuri bane, yau faɗa da Baraka, gobe shiri. Haƙuri kawai aketa yi. Nasan ka kai mai sanyine, mai haƙurine ko akan su Yaya Jamila za'aima wannan shaidar. Dan wallahi in nine basu isa su mun abinda suke ma ba. Kana da riƙon amana tun muna ƴan yara kai ake kawo ma ajjiyar kuɗi, kuma bai taɓa ɓata ba, baka taɓa cinyewa ba. Kaga Hindu matarka? To ka riƙeta hannu ɗari_ɗari. Ko da sauyin zamani da lokaci zai sauya maka ita. Kai kayi ƙoƙari kaita kyautata mata. A gaskiya tana sonka. Kuma naga ƙokarin iyayenta sosai da suka ɗauketa suka baka ita. Hindu mutum ce har da rabin mutum" Qasimu yai ta mai nasiha da kwatance kala_kala. Mijinyawa na zaune a mota, amman minti_minti sai ya warware takaddarnan ya karanta, yayi murmushi ya damƙe a hannunshi. Anjima ma ya maya. Satarshi Qasimu yayi, ya warware kenan ya fisgeta, tare da sawa a ajjihu. Murmushi yayi mishi. "Sabida kunyi faɗa da Baraka shine zaka huce a kaina"? Dariya suka saka baki ɗayansu. Gaga_gaga_gaga_gaga. Nanno dai a ranar da ta cika sati biyu da tafiya. Sai gata Nawata ya dawo da'ita. Tace sam ba zata hawo mota ita kaɗai tun daga binni har Jama'are ba. Sun dawo yau washegari sai ga Kawu da misalin irin sha ɗayan safe yazo. Yaronshi ne ya kawoshi, dake yana da mota da yake yin lodin ƙauyuka haka. Shi da Malam Liman Kawu yasa aka tattaro kan ƴan gidan, da waɗanda suke gidan mazajensu. Waɗanda suke da nisa ƴan uwansu su wakilcesu. Bayan an cika an batse ga Malam Kalla Liman kenan a gefe, sai kawu yace. "Dangane da waɗannan katafarun ganakai biyu da shi Ɗan safiyo marigayi ya bari ne dama. Shi Salihu kusan dashi akayi komai. Dama saidasu akazo yi abinda ya faru ya faru. To Alhamdulillahi gonakai sun fito an siyar ga kuɗin magada za'a ƙarashe raba musu. Malam Kalla gareka" Nan Malam Kalla ya kasabta kuɗi bisa doron sharia, aka cirema kowa kasonshi ga kuɗinan muna_muna aka danƙama kowa nashi. Dake yawa garesu dai maza sun tashi da nera dubu ɗari da sittin sai matan kuma suka tashi da dubu tamanin. To a gaskiya wannan kuɗi a wannan lokacin kuɗine mai yawa, ba kamar yanzu ba. Bayan Kawu ya sallami kowa, ya sallami Kalla, su Jamila ma yace kowacce taje gidanta, zai yi magana da Nanno, Salihu, Mijinyawa, sai Mijinyawa Babba. Bayan sun shiga ɗaki yace. "Yaro yaje wajena da ƙoƙon bararshi, dangane da batun son komawa binni kamar yadda ɗan uwanshi gashi ya koma. Wanda kika je kika dubo inda suke" Sai kawai ta fashe da kuka wiwi. Kawu yayi kasaƙe yana kallon abun almara. Baice uffan ba. Mijinyawa sai kallon Kawu yake yi shi kuma. Yayin da Yaya Salihu ke harararshi. "Ƙarata yakai zaka ce Yaya. Ni banaso yaje ko'ina. Ni dai kawai ya zauna" "To shikenan. Kai Nawata zan bata umarni ita ta baka, cewar ka dawo da Uwatale nan ƙauye nan da sati ɗaya. Ka tabbatar ka siyar da gidan kafin ku dawo. Ki bashi wannan umarnin na baki umarni. In kuma ban isaba ga yaranki a gabansu ki nuna musu iyakata. Ni kuma daga yau ni dake mu raba hanya, ta yadda ko kin ganni a hanya ke baki isa yinƙurin nuna ni a matsayin ɗan uwa ba" Nawata yayi saurin ɗagowa. Yaya Salihu shima ya ɗago. "Kawu duk ba haka bane. Akwai daliline da yasa bata so ace ya koma birnin. Sabida matarshi ta riga ta mallakeshi sai yadda tace dashi a gabanmu. To ina ga sun koma binni? kuma garin da danginta suke. Watarana wahalar gani ma zai mana musamman in yayi kuɗi. Kuma fa yarinyarnan bata da kunya, bata da kirki..... " "Bata da kirki ko, maras kunya ce irin Shafa wacce ta kama Uwarka da dambe farko_farkon kawota, a sakamakon uwarka na son juyata kamar yadda ta juya gidanta a lokacin da mahaifinku yake raye ko? Ko juyashi take yi kamar yadda Jamila ke juya Ubale ko? Shin kun taɓa tsawatarma Jamila kan cuta ma Ubale da take yi, da su kansu yaran Ubalen data kaɗa uwarsu? Ko da yake ita da gatanta kam. Hindu ce bai dace tace ma mijinta ayi kaza ba. Bai dace Mijinyawa ya bata dama, irin damar da Ɗan safiyo ya ba gyatumarku ba kam. Uwarku ce ya dace ta tsara musu yadda zasu rayu tabbas, ya dace sai abinda tace. Ke kefa nake jira" Nanno tayi shiru ba amsa, sai haɗiyar zuchiya take yi. Ita bafa zata iya barin mijinyawa da Hindu bane a binni. Kuma bata isa musu da Yaya ba. "Yaje tunda kace yaje. Sai dai bana son ƙara ganinshi da iyalinshi Abadan" Murmushi yayi mata. "To kai kaji. Tashi kaje ka soma shirin binni. Duk ranar da yazo sai ki koreshi. Ranar da Nawata yazo da iyalinshi ki ɗauki Uwatale ki maidata ciki kinjo ko? Kai kuma inta koroku sai ku wuto gidana kai tsaye, ta bari ƙafafuna su taka gidannan akan kunzo ta koreku. Allah ya tsare muku hanya" Kai yasa ya fita. Mijinyawa na zare idanu ya miƙe. "Koma ka zauna dan babban, tsinin, abu ta kazan..." Cewar Nanno da bata taɓa shiga irin wannan halin na ɓacin rai ba. "Dama zan rakashine" Harararshi tayi, tana kuka. "Kaje ka rakashi ka dawo munafuki" Cewar Yaya Salihu. "Kada ka sake bakin ka ya sake furta mun kalmar munafuki. Zan iya jure komai banda wannan kalma mai muni" Mijinyawa an ɗan taɓuka yau. "To in ya kuma me zaka yi mishi? Yanzu in farfasa maka baki" Inji Nawata "Fasa baki, to ko zaka zo ne? Ai kasan karonmu dakai, kaga in bar kwantar dakai a nan ba" Har zai fita Nanno ta kirawoshi ta miƙa mai hannu halamun ya bata kuɗin wajenshi. Ledar ya miƙa mata babu musu, yaje ya raka Kawu ya dawo gaban Nanno. "Na gode da tursasani da kasa Yaya yayi. Watarana ma zaka sa ya tursasani akan in barma Hindu kai ita kaɗai tabbas. To naji ku tafi tunda an mun dole, amman bana so, kuma bazan taɓa so ba abadan. Na kuma gode da yadda ka nuna mun ban isaba" Mijinyawa zai yi magana Nanno ta ɗaga mishi hannu. Kallon Nawata tayi tace. "Kana da wajen da zaka basu su zauna ne, ko babu tunda naga ba du ka kammala gidan ba?" Ta dubi Nawata. "To akwai babu kuma. Sabida akwai ciki da falonnan na can gefen da kika gani, to shi wannan kinga yarane a ciki kuma ƙananune, sai inda muke ciki. Sai wannan ɗaki ɗaya dake zaure. Sai dai in shi za'a basu kuma to" Yaya Salihu yace. "Ai sai ka basu wannan ɗayan" "To ai akwai kayan shirgin Uwatale a ciki. Amman ai" "Ba sai ya bamu ba. Zan kama haya ma nagode ƙwarai" Mijinyawa ya katse Nawata. Nanno ta ƙirgi wannan kuɗi rabi cib ta ajjiye gefe, rabin kuma ta miƙa mishi dubu tamanin kenan. Yasa hannu ya karɓa yana kallonta. "Kaje ka kama haya, ka kuma tabbatar gidan da zaka kama bashi da nisa da na ɗan uwanka, kafin asan yadda za'ayi dan dole a gida ɗaya zaku zauna, ba zai taɓa yiyuwa kane gefe dangin matarka su samu zarafin yin yanda suke so ba. In har ba'a samu haya a layin ba, sai ku jira har zuwa lokacin da za'a samu. Wallahi akan wannan ko Yaya bashi da yadda zai yi dani. Ko bayan raina tare nake son ku zauna a waje ɗaya, sabida ƙarfafa zumuncinku da yaranku. Sannan dokata ta biyu kayan kicin da sututa kaɗai na yadda ku ɗauka. Duk wani jere daka sani anan za'a barshi sabida duk lokacin sallah ƙarama, da babbar sallah dole kuzo da iyalinku ku yi sallah tare damu anan, wannan dolen dole ne kaji na faɗa maka" Hankalin mijinyawa ba ƙaramin tashi yayi ba, amman ya ya'iya da abinda yafi ƙarfin wuta inji kishiyar ƙonanniya. Baici ta zama ba, ɗaki ya koma ya shiga sunturi yana kallon kyawawan kayan gadon Hindu da sabuntarsu. Murmushin baƙin ciki yayi, wani yanayi na taso mishi. Ya kuma kallon kuɗin gadon nasu, murmushi ya kuma yi mai cike tab da damuwa. Nawata ne yayi sallama, tare da shiga falon Hindu. "Nace gobe zan koma. Ka biyoni akwai sababbin gidajen haya har biyu a cikin layinmu, ɗayanma wani ƙaramin gidane a tsakaninmu, in yayi maka ai sai ka kama. Akwai kuma wanda ba sabon ba ma" Murmushi yayi mai. "To shikenan Allah ya kaimu goben, sai mu tafi tare. Bari in ma Qasimu magana tafiyar tamu ce tare" Qasimu ya nemo ya sanar dashi duk halin da ake ciki. Qasimu yaso su koma wajen Kawu, mijinyawa ya nuna mishi haɗarin hakan. Dole ƙanwar naƙi yayi haƙuri. Yaita dakon tunani, da nazari har zuwa wayewar gari. Sukai sallama da Jama'are sai gasu a gidan Nawata da yamma. Dake Unguwar Kurna Uwatale na tsakar gida da itacenta tana tuƙin tuwo ta ga shigowarsu. Gasu Zainab da ƙannenta suna ta wasannin guje_guje duk sun cika gidan fal da hayaniya. "Ahh Qasimu kune tafe, tare kuke? " "Tare muke Uwatale. Mun same ku lafiya? " Fuskar Qasimu kadaran kadahan. "Waje yayi Allah ya sanya alkhairi. Kai masha Allah" Cewar Mijinyawa. Alwala ma dai suka ɗaɗaura sabida anata kiraye_kirayen sallar magriba ne. Masallaci suka wuce, tare da ƙarema unguwar kallo babu dai laifi za'ace ga mutumin daya shigo daga ƙauye ga wutar lantarki tanwar. Bayan sun idar da sallah a wani ƙaramin masallaci. Sai Nawata ya gabatar da Mijinyawa a wajen limamin masallacin. Tare da sanar dashi gida suke nema na haya. "Ai kuwa ga kamanninan sosai faɗi kawai zai nuna ma. To zamu iya zuwa ku ga wajen, wannan bawan Allah ma haya zai kama ai sai mu ɗunguma tare ko Bilya? " Limamin ya dubi wannan bawan Allah da a wajen dama suka samesu, suna tattaunawa. Gidaje uku aka nuna musu, biyu daga ciki sababbine, wanda ya shiga shi zai soma shiga. Ɗayan kuma tsohone, amman ɗakunanshi sunfi girma, irin gininanne na masu dashi, wanda akayima ƙawa da ginin jan bulo ta wani ɓangaren. Sai dai sai anyi fenti, anyi gyaran ƙofa da dai sauransu, tagogin na gilashine masu murfi biyunnan. Ga tsakar gidan da yalwa sosai. Gidane na mutum huɗu kawai, mutum biyu bayan gidansu daban, mutum biyu ma haka, sai madafi babba a tsakar gidan. Sababbin kuma gidajene kamar na mutum takwas ɗayan kuma na mutum shidda. Mijinyawa yayi shiru yana ta nazari. Nawata yafi son sabon musamman na kusa dasu, Mijinyawa kuma yana ganin tsohon shi yafi dacewa, ɗakunan lallai da girma, gashi ko wanne ɗaki yana da ƴar baranda a ƙofar ɗaki. Kuma yalwa na da kyau. "Inaga zan ɗauki wancan na farkon tsohon, sabida kaga ɗakunan manyane sosai in yaso nayo fentin, kuma naga akwai rijiya a gidan. Duk da sauran akwai famfo, shi kuma nan babu" Qasimu yace. "Nima shi ɗin na zaɓa naga gaskiya suna da girma. Kawai a ɗaukeshi" Ai kuwa anan aka tsayar da magana. Kuɗin haya suka biya. Liman ya danƙa mishi ɗan mabuɗin gidan, da kuma ɗan mabuɗin ɗakin. "To shikenan Allah yasa ku shiga a sa'a Malam gaskiya zaɓinka yayi kyau sosai. Gidane mai kyau ginin masu kuɗi, tsufane dai kawai yayi. Bilya ko kaima shi zaka ɗauka ne? " "Gaskiya ina tunanin. Hakan, duk da ni wani auren zan kuma. Amman amarya ma tana son yalwa a bani kawai" Nan su Mijinyawa sukai ma liman sallama suka tafi. Sunje sun samu uwatale da yaran duk suna yashe a tsakar gida, suna ta yarɓar tuwonsu miyar kuka tako ji kalwa. Ga nasu Nawata a gefe kan tabarma an jera musu a kan farantin silba sabo 555. Sai langoginta tuwo da miya, da babban farantin da zasu juye. Ai kuwa Qasimu ya juye musu tuwonnan, tare da kwalala musu miya akan tuwon. Ruwan wanke hannu Nawata yace ta kawo, ta ɗebo musu a bokitin ƙarfe haɗe da buta. Bayan sun soma cin abincinne Uwatale take tambayar su Hindu da ragowar ƴan ƙauye. "Ai tana hanyar dawowa binni, harma mun kama mata waje, abinda ya kawo mu kenan. Baki ga gidan ba babba dashi, ga rijiya a gidan" Cewar Qasimu dake karantar Uwatale. Ai sai ta tsaya cak ta dena lashe miyar dake bin yatsunta. "Hindun, mijinyawa binni zaku dawo kuma Nanno ta amince muku, babbar abu ta k...." Mai ta tuno sai ta wayance da cewa. "Babbar magana kai abu yayi kyau sosai. Na ta ya ku murna. Kuma a wacce unguwarne, duk da ba sanin sunayen unguwannin nayi ba? " Nawata dake ta cin abincinshi yace. "Ta farko_ farkon layinanne, da ɗan nisa amman a layinnanne. Ina wani gida dake kusa da wannan shagon da kike zuwa siyan kayan miya? To gidan na kallon shagon." "Naji naji ai ko gidan babbane a haka a ido. me jinin jan bulo ko?" Nan dai Uwatale ta tsame hannunta ta shige ciki, abincinma ya fice a kanta. Sai tari take yi, sakamakon ƙwarewa da tayi da yawu. Qasimu ya girgiza kanshi kawai, tare da takalar Nawata da hirar me yake yi ne a binni, amman yaƙi faɗa fur, sai kau da zancan yake yi. Bai san Auwali ya sanar musu ba. Ɗakin su Zainab aka basu, su kuma akai musu shinfiɗa a falo. Mijinyawa bai kwanta ba, saida ya zaro takadda da biro da yayi dakon abunshi, ya rubutama Hindu duk abinda ke faruwa, tare da neman shawarinta. Sassafe suka nufi gidansu Luba. Tare da Luba suka zo layin, amman su iyakarsu wajen Auwali mai lemo. Luba bata jima ba ta fito mishi da amsarshi. *Dukkan abinda kake ganin ya dace ka siya.* *Ba sai ka bani kuɗim na siya ba, tunda ba'asan muna iya jin juna ba.* *Tunda ta amince, komai ai mai sauƙine jarumin jarumai* Ta faɗi a cire mata labule, a tawo mata da kefet, da kayan kallonta. Gaga_gaga_gaga_gaga. A cikin sati guda, duk gyare_gyaren da gidan yake buƙata saida Mijinyawa da Qasimu suka tabbatar ya kammala. Ranar da akayi fenti ne yaga Bilya ana buga ma matarshi amarya madafi na katako. Sai shima ya tambayi Liman shima yana so ya buga madafin. Liman ya amince mishi, tare dana Bilya aka gama fes. Haka su Mijinyawa suka kuma kwasa zuwa jama'are. Nan suka shiga tattare_tattaren duk abinda ya dace su tattare, na sawa a buhu suka sa, wasu a cikin randuna duk aka saka. Ya cire kafet ɗin uwarɗaki, na falon yace a barshi. Labulayen ma na Uwarɗakin kaɗai ya samu zarafin cirewa. Kwanansu biyu dai suna aikin, ana ukunne suka nemi motar kaya daga Azare, tazo ta kwashe kayan duka. Sallama Mijinyawa yayi da Nanno, dama mutan gidan. Su Yaya jamila duk sai da ya bisu har gidajensu yai musu sallama. Kadaran kadahan dai aka rabu. Cikin motar kaya, a bayan motar suka zauna, direba da mataimakinshi suna gaba. Ba su suka isa Kano ba sai wajen taran dare, motarnan tsohuwa zata ba zata ba dai shi ya kawosu izuwa daɗewarnan. Masu motar ne suka taimaka musu wajen shigar da kayan ciki. Kayan kicin ɗin duk aka loda a cikin kicin ɗin langa langarnan. Ragowar kayan kuma suka shiga dasu cikin falon. A saman kefet ɗinnan suka yi kwanciyarau. Mu kwana tare dasu a nan sai in Allah ya kaimu kuma gabatar be. Mrs BUKHARIMRS BUKHARI ................... *Wai kina da labarin Gidauniya ta mata, farin cikinsu, da walwalarsu, mai suna *MURYAR MATA (FARIN CIKIN AL'UMMA)*🧕🏻👩🏻‍🎓 *Wanda ni Mrs BUKHARI muka yi haɗin guiwa wajen buɗewa, tare da sauran shuwagabannin Taskar Badiat Ibrahim?* *ku matso kusa ki kasance a cikin wannan tafiyar ta Alkhairi, tafiyar da zata gyara rayuwar Aurenki, tafiyar da zata gyara miki tunaninki, tafiyar da mace zata gane ni'imominta, tasan kima da darajar kanta, gidauniyar da zata koya miki sana'ar da zaki dogara da kanki, gidauniyar da zata koya miki tattalin uwar kuɗin kasuwancinki, da yadda zaki tattali ribarki ta yadda zaki ƙarfafa kasuwancinki, sha'awar son komawa makarantar addini, ko na boko kike so? To biyomu muje wannan gidauniyar taku ce mata, gidauniyar ta ƙunshi abubuwan da zatonku ma bai zata ba.* *Ga lambar wayata ga matan da basa cikin Taskar Badiat group 1 group 2 group 3 sai kui mun magana in sha Allah zaki kasance a cikin wannan tafiyar ta manyan mata* (08179523215) *Ƴan taska kuma zaku iya tuntuɓar Admins ɗinmu ta pc domin kuji yadda tsari da dokokin kasancewa memba a cikin wannan shahsrarriyar, garnaƙaƙar gidauniya wacce ta haɗa manyan masana zamantakewar aure, malamai, manazarta, mahukunta, ƴan gwagwarmaya, masana ta ɓangaren gyaran aure, ƙwararrun ƴan kasuwa, da gogaggun ƴan boko, wanda ya haɗa matan arewanmu da kudunma baki ɗaya, zamu kasance a duk faɗin Najeriya da izinin Allah* Washegari sassafe su Mijinyawa suka tashi. A rijiyar gidan suka ja ruwa, Qasimu ya siyo soso da Sabulu, kafin ya dawo Mijinyawa shi yayi nashi wankan, da nasu soso da sabulun. Suna shiryawa kai tsaye suka nufi wajen Nawata. Ɗumamen tuwo miyar kuɓewa ɗanya Uwatale ta saka musu, sai ruwan kokko. Sai kuɗin mummuƙi Nawata ya bata, yace su sha sha shayi da mummuƙi tunda ɗumamen ya ƙare ba'asan da zuwansu ba. "Jiya kuka shigone? Dan jiyan ma naso in kai Uwatale taga gidan. To a rufe yake shi yasa dai bamu shiga ba." "Jiya da daddare muka shigo ai shi yasa. In Hindu ta tare ta shigo ai taga wajen. Yanzu kam ai babu komai a ciki." Nawata yace. "To ita Hindun ka sanar mata cewar kayan jerenta an barsu acan kamar yadda muma namu yake can, sabida in munje ya zamana muna da masauki? " "Na sanar mata. Babu matsala zata sai wasu kayan ɗakin tace" "Iyayenta ne kenan zasu yi mata, babu matsalar da kai ka hanga akan hakan? " Qasimu yayi carab yace. "Su zasu yi mata mana. Kuma tace ai babu matsala, to babu matsalarne." Dole zancan ya tsaya a haka. Uwatale dai sai barbaza kunnuwa take yi, ta kasa zaune balle tsaye. Sai zurga_zurga kawai take yi. Suna gama karyawa, su Mijinyawa suka nufi wajen Auwali mai gwanda, Nawata kuma ya nufi tasha wajen aikinshi. Auwali ya ba da jiran kayan sana'arshi, ya rakasu inda ake saida kujeru, da gadaje sababbi, dama na hannu waɗanda basu sha jiki ba. A zahirin gaskiya sababbin kujerun basu yi mai kyau da ma halamun ƙarko ba. Amman yaga wasu setin kujeru, da gado, da sib, masu kyau sosai, kuma basu sha jiki ba, da gani masu tsadane. Su dannma ance musu na hannune suka gane tsabar yadda suka nuna sabunta. Mijinyawa yaji su yake so, sune suka dace da irin zaɓin Hindu. Waɗannan sababbin basu da ƙarko, kuma yadunansu gasunan burwatsai dai haka. Cinikinne ya ɗaukesu lokaci mai tsayi. Ta yarda har Auwali ya barsu a wajen ya koma bakin sana'arshi. Da ƙyar suka ƙarƙare a kuɗin da mai kayan ya kafe akai, bayan ya ɗan yi ragin kaɗan. "Kayannan masu kyaune, kuma aurene na wata shidda ya mutu. Shine iyayen yarinyar suka siyar dan dole, sabida basu da wajen ajjiya, ga takaici. Da ace munso ma a sababbi zaku siyesu gaskiya. Dan dai gaskiya da gaskiya muke komai ne" "To shikenan babu damuwa mun siya a hakan. Za'a samu mota da zata kai mana kayan ko?" "Kyauta kuwa, bari in kira wannan. Kai mu'azu zo ka kai musu wannan kayan can kurna." A wajen Mijinyawa ya sai kafet babba na falo sabo, duk da kuɗin da nauyi, amman a haka ya siya. Aka lode komai a mota, suna gaban mota har Kurna. Da ƙyar suka gane layin ma, mai mota yana ta rantsuwar shi sai sun ƙaramai wani abun, shi wallahi, shi tallahi dai. Bayan ya taimaka musu wajen shigar da kayanne, mijinyawa ya ɗauki ɗari biyar ya bashi, sai lokacin yayi dariya, gami da godiya ya ja motarshi kuma. Sallah suka yi a tsakar gida, kana suka fita nemo abinci. Duk wannan aikin Qasimu bai nuna gajiyawarshi ba sam. Kunji abota abun a yaba, ba irin abota ta yanzu da hassada ta cika mana ciki ba ko. A ranar suka kafa gado, suka ajjiye sib inda ta dace, suka ajjiye dires miro. Falo ma suka jera kujeru, suka saka kayan kallo. Komai fes sai dai babu labule a tagogin falo, ya mance shab. Amman tunda Qasimu shi gobe yake son komawa, satinsu kusan biyu suna kai kawo. Ko shi kaɗaine kafin yaje ɗakko Hindun ya siyo ya saka. Kicin kuma ya barta da aikinta in ta dawo ita tasan yadda zata jera, a yadda take so. Suturuma duk a saman gadon ya jibge mata. Washegari sassafe sai ga su Mijinyawa a tashi Qasimu zai tafi. Kuɗi Mijinyawa ya saka ma Qasimu a ajjihu, baisan kuɗi bane shi yasa ya barshi. Komawa sabon gidansu yayi sai ƙarema falon kallo yake yi. Yana mai farin cikin dawowarsu birni. Zuchiyar tashi cike da zabarin son ganawa da Hindunshi. Wasa, ne gaskene, sun doshi wata biyu basu sa juna a ido ba. Shi tun sanda suka kai kuɗin fom basu sake zuwa ba, yadda suka yi da Baba nagoɗi shine sai randa ya shirya tariya sai yaje ya sameshi. Dan haka ana magriba zai fita yaje. Murmushi yake yi, yana hasaso irin tarbar da zaima Tutar so da yaran baki ɗaya. Har kaza ma zai siyo musu gashasshiya a sabunta amarci. Tunda dama a darensu na farko Hindu ce ta siya musu, wannan karon zai siya duk kayan da ake buƙata na siyan bakin amarya ya tanadar mata. Kafin magriba ya shirya cikin wagambari shadda, wacce Hindu ta ɗinka mishi bayan sunan Azgar. A cikin kayan suna ta sassamesu, sai ta bashi kala huɗu duk aka ɗinko mishi, biyu ya taɓa sakawa suma da sallah ne kawai. Mai ruwan ƙasan ya saka, ya tsaida jar dara, ya shafe jikinshi da Alhaji Abdullahi, yabi da kulaccam ɗin Hindu. A masallaci suka haɗu da Nawata, saida aka idar sun fito ya tareshi da zuba. "Na ganka kamar ango gidansu Hindu zaka je ne, tariyarce tazo?" "Eh zan je in tawo dasu, tunda an zuba mata kayan har an jejjera dawowane kawai." Baki Nawata ya buɗe. "Au har an zo an mata jere, shine baka sanar dani Uwatale ta musu girki ba? Yanzu ma da zaka je ɗakkota sabida Allah ba sai ka sanarmun muje tare ba. Kuma ko naman miyane a siyo a haɗe sanwar dare daku. Nace ko zumuncinmu ya samu tangarɗane? Kaifa ɗan uwanane bani da tamkarka. Abubuwan da duk kaga sun faru a gida can, naƙi goyon bayanka akan abubuwa da yawa, sabida Nanno taji cewar muna bayanta, ba dan bana jin zafi, ko ko tausayin abinda akeyi maka ba. Kayi haƙuri ɗan uwana ka watsar da komai mu yi rayuwarmu mai kyau, mu rungumi junanmu. Baka da kamata, bani da kamarka. Kuma kada mu bari mata su gilma tsakaninmu" Mijinyawa yayi shiru yana nazari. Take yaji wani sanyi a ranshi, ya kuma gamsu da bayanin biyunshi, kuma yayi mishi uziri. Ya tabbatar tabbas yana sonshi, baya nufinshi da sharri, uwatale ce ke neman farraƙa kansu. Amman bazai iya zuwa dashi tawo da Hindu ba. Wannan ranar tasu ce, Hindu ma ba zata zo azo mata da kowa ba. "Na fahimceku daga kai har su Yaya Jamilan. Na kuma yi ma kowa uziri akan abunda yake yi. Ni bazan so ace duk kuna bayana, ita ana kallonta a matsayin ba daidai take yi mun ba. Nanno uwace, soyayyace tabbas yasa take nuna mun haka. Kaza na take ɗanta ba dan bata sinshi bane. Kuma, kuma babu yadda za'ayi ace kullum kareni kuke yi." "Hakane nagode da fahimta. To muje in watsa ruwa sai mu tafi ai ko? " "Aa babu damuwa tunda ba dakai aka shirya tafiyar ba, ka bari inje ni kaɗai ɗin. Ai bama shiga ciki zanyi ba. Yaro zan tura ta fito mu dawo. Gobe dai kwa zo a gaggaisa ku ga waje.' Da haka ya lallaɓashi suka rabu salamun_salamun. Ko da yaje ƙofar gidansu Hindu lokacin sallah gashi yayi, sai kawai ya zarce masallaci. Sahunsu ɗaya da Qazzafi ma, ga Azgar a gefenshi sai riga yake ja yana nishi. Su Baba Nagoɗi sune a gaba gaba. Bayan an idar, masu yin nafila sun yi, marasa yi sun fita, masu karatun Qar, ani sun soma. Mijinyawa ya miƙama Qazzafi suka yi musabaha. Azgar yana ɗago kai ya ga Babanshi. "Abba Abba Abba." Ya miƙe a guje tare da faɗawa jikin Mijinyawa. Tsam yayi mishi a jikinshi, sai ƙamshi turaren wuta yake ta faman yi. Sanyi da tsantsar son yaronne yaji yana hudashi. Shi ko yayi lub a jikinshi. Miƙewa yayi da yarin a hannunshi suka fita. Baba Nagoɗi yabi a baya a hankali. Su Baba soja, dasu Baba Lukumanu suna gaba. Saida akaje ƙofar gidan Mijinyawa yace. "Barka da dare Baba' Da sauri ya juyi. " Mijinyawa kaine Ka dawo kenan? To bismillah muje falona. Hindu:. Haka dai naci gaba da gudanar da rayuwata ni da yarana a gidanmu. Kullum Innarmu taza je aiki ta dawo ta iskeni. Zaman gabaki ɗaya ya isheni, ya gama gundurata. Gashi ni bana zuwa ko'ina ina gida a ƙunce. A gidanma iyakata falo, falonma saida Innarmu suka yi ta sosai da Innah Abidah. Da inna fito sai ta hau labarin abinda ya faru, ita kaɗaifa taita dariya. Ko ta fita babban tsakar gida tasan yadda zata yi dai har sai ta sanarma jama'ar gidan ai gani a falo. Su kuma suita gilmawa, ko su shigo wai tambayar wani abun, ko kuma sun zo wajen Innah Abidan dai, musamman Innah Mairamu. Ita kam in ta shigo kai tsaye dani zata ta maida mun yadda akayi, da irin zanan da Mijinyawa ya sha. Rikicinnnan saida yaje har kunne iyayenmu maza, dan ba ƙaramin zazzaga innarmu tayi musu ba ranar, anyi ɗauki babu daɗi sosai, ta zazzagar da buhunhunan maganganu sosai. Ina ya Allah babu ya Allah, lokaci yana ta shurawa dai, Asama'u ta saba a cikin gida, ta sake da Innarmu da Baba Sojanmu. Ita da Azgar ai ko muryarshi suka jiyo da gudu suke ficewa. Gashi dama kullum zai shigo musu da ƴar tsaraba. Watarana har dani za'ayoma tsarabar ɗan abun ci, ko abun sha haka. Wataran kaza ce zai miƙo mun gashasshiya da wata damammiyar fura mai lafiya. Na yi ƙiba, kuma nayi haske sakamakon zaman waje ɗaya. Kwatsam da daddare rannan sai ga Baba Sojanmu ya shigo. Lokacin ina zaune idar da sallata kenan, ina sauyama Asama'u kaya, zuwa masu sauƙi, bacci ya soma zuwa, tana ta ɗan kukakkakin rigima. Ɗakinmu ya leƙo. "Ruwayya mijin Hindu ne yazo. Nagoɗi ya buƙacemu ni dake a falonshi. Muje ko?" Miƙewa Innarmu tayi bayan ta amsa. Lafaya ta naɗa, ta ɗauki Asama'u suka tafi tare. Ajjiyar zuchiya na sauke. Alhamdulillahi yau dai zan kwana a ɗakina. Nagaji, duk yadda gidanku ya kai da daɗi, ko muƙami. Gidan mijinki duk ƙasƙancinshi yafi miki. Ina nufin gidajen da akwai nutsuwa da fahimtar juna, soyyayya, tausayi mai ƙarfi, sadaukarwa a tsakankaninsu. Ba ko wanne gidan miji ke fin na ubaba, kafin kuce idanunane suka rufe da soyayyar mijinyawa ehe. Dukkannin saƙwannin da Luba take turomun daga Mijinyawa, babu wanda ya sani, a tsakankaninmu mu huɗu ya tsaya kawai. Kuma dangane da barin kayana a jama'are. Da kuma kamamun gidan haya, da zubamun wasu kayan da nace mijinyawa yayi salin alin. Wannan sirrinmu ne, ƙila Qasimu ya sani. Amman ni ta ɓangarena ban kasance mai faɗan komai ba. Cikina na iya shanye abubuwa da yawa, bana jin wai saina fitar nake samun nutsuwa. Ƙirjina na da faɗin adana magana abadan, ko na wani lokaci mai tsayi gaskiya. Kuma ni na ɗauki rayuwar aurena sirri babba. Innarmu babu abinda take sanarma danginta, na game da dukkan abinda ya taɓa rayuwar aurenta. Face abinda tasan na farin ciki ne zallah. Hakan ya wanzar da girmamawa, farin ciki sosai. Kusan halinta da kyau na ɗebo, komai shanye abunta take, ta nema ma kanta mafita da kanta, ta koya mana tsaiwa ma kanmu a gidan aure, ba kowa bane zai shigo rayuwar aurenki da sunan ya gyara miki gidanki, ko zamantakewar ba. Ta koya mana shanyewa da haɗiyewa sosai. Duk da ta kasance macen da bata barin takwana, amman ba komai take tankama ba. Anan ni da ita hannun rigane, ni Hindu ba karta kwana ba. Tayi shekaru ma bana tankawa, haka kuma nake ni. Su Yaya Saratu aka barma wannan halin, shiyasa ake yawan rikici dasu na famili. Kafin kuji muryar Hindu kam da wahala. Ni in tankawa kake so inyi, to bafa zan tanka ba, kome za'ayi. Amman in kuma nayi ra'ayin tankawa babu ɗar a lamarina. Bance ni da Innarmu akan daidai muke ba, sai dai kowanne ɗan adam da yadda yake tafiyar da rayuwarshi. Ban kuma ce mu bama kuskure ba, bance abu baya shige mana duhu ba. Aa a fahimci Hindu, a karɓeta da halinta. In mutum ya kasance da tsaurin ra'ayi mutane ne suke kallonshi tamkar ya mayar da kanshi gwani na gwanaye, alhalin shi ba haka yake nufi ba. Kawai abinda irin Hindu suka sani shine, zan iya samun mafita ba saina bayyana halin da nake ciki ba. In raina ya ɓaci nafi zaɓan in yi shiru, in na gama rufewa nake yi, bana kuma buɗewa. Zan iya tunani in ɗauki abinda ni nake ganin ya dace dani, ko da wasu zasu kalleshi a matsayin kuskurene. Baya damuna yawan cece kucen Hindu kaza, Hindu tayi kaza. Miƙewa nayi da sauri_sauri na gyara fuskata na sauya kaya, na zauna ina jiran a kirani in fito. Kunji wani ƙarfin hali ko? Mijinyawa:. Mijinyawa na gurfane a falo, Azgar na cinyarshi, yama cire mishi hularshi yana wasane da'ita. Baba Nagoɗi yana zaune a kujera. Sai ga Baba Soja da innah sun shigo. Asama'u ta sauke kusa da Mijinyawa, tayi saurin zuwa wajenshi. A tsanake Mijinyawa ya sake shaishesu. Sai kuma falon yayi tsit na wasu ɗan lokuta. Baba Nagoɗine ya katse shirun ta hanyar cewa. "Sai kayi mana bayanin abunda ke tafe dakai, muna saurarenka" Firit Innah Mariamu ta fito ta fita waje. Baba Nagoɗi ya girgiza kanshi. Zata kuma shigowa yace. "Mairo jeki can wajen Abidan ki zauna in mun gama kya dawo" Zata yi magana ya ɗaga mata hannu cikin rashin wargi, dole ta juya ta koma. "Dama batun tarewarne nazo." "Can gidan ɗan uwan naka kenan ko? To yaushe ka tsayar ranar da za'aje a kwaso kayan nata, da kuma tariyar? " Mijinyawa yayi gyaran murya yace. "Ai komai ya kammala, kayanta duk suna gidan na kwaso, harma an jejjera mata. Sannan gidan ɗan uwan nawa bai samu ba, sabida inda zamu zauna ɗin ginin bai kammalu ba. Shine na kama haya nan kusa dashi" Sai ya ja fasali a wajen. Baba Soja yana ji baice uffan ba. Innah tace. "To masha Allah, Allah ya sanya alkhairi" Falo ya ɗauki shiru. Baba Nagoɗi yace. "To yaushe kake so a rakota?". Kai ya kuma sunnewa kafin yace. " Dama nazo ne in ɗaukesu mu koma yanzu, tunda duk an gaggama komai" Baba Soja yayi murmushi kawai. "To Janaral kaji abinda yaro yace. Ke Ruwayya sai ki sanar da Hindu ta shirya ta fito ko?" Innah tace. "Inaga ya dai bari zuwa kamar jibi haka, in mun kammala kintse kintsenmu na mata, sai yazo ya ɗauketa" Baba Soja yace. "Wa yace miki yanzu Hindu zata koma gidanshi wai? Ba zata koma yanzu ba wannan shine gaskiya" Baba Nagoɗi ya kalleshi yace. "Kamar ƙaƙa kuma sai yaushe kenan? " "Sai admishon ya fito an biya kuɗin rijistireshon in sha Allah, sannan zata koma, wannan shine dahir a wajena. Yanzu fom kawai fa aka siya, ko jamb ɗin bata rubuta ba" "Janaral nace ko boko ya taɓa maka kaine anya kuwa? Taya zaka riƙe mishi mata da yara har tsawon wannan lokacin? Bazai yiwu ba kaji na faɗa maka. Ruwayya a kirawo Hindu tazo su wuce. Dan Allah bana son wata magana." Baba Soja yace. "Ob kos boko ya taɓani kace ko? To shikenan ni dai Hindu ƴata ce. Duk wani uziri nayi mai shekaru sama da shida, sai kawai yanzu dan nace sai komai ya kankama, kafin in mayar mishi da matarshi sai ya zama furobulem a wajenka." "To amman ayi haka dan Allah Janaral?" Innah tace. "Ni ina ganin Nagoɗi a madadin ayi haka, a bar janaral akan abunda yace. Kamar yaune. Kai mijinyawa kaji abunda Babanku yace." Baba Nagoɗi zai yi magana Mijinyawa yace. "Aa Baba, babu damuwa zan jira zuwa lokacin in sha Allah. Kuyi haƙuri ni zan tafi. " Babu komai, ka kuma yi haƙuri kaji. A wacce unguwar gidan yake?" "A kurna ne" "A kurna wacce unguwar takamaimiya, ai Kurna da girma"? "Kurna babban layi. A cikin unguwar bakin kasuwa" "To faɗi lambar gidan, ko kuma bari kuje da Tasi'u yaga gidan. In lokacin biyan rijistireshon yayi, ba sai ka zo ba, ni zanzo" Miƙewa yayi da hanzari, ya miƙama Innah su Azgar ya fita. Baba Nagoɗi ya sa aka kira Tasiu dan ya kai mijinyawa gida, ya gano gidan. Nan Baba Nagoɗi ya tayar da faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba sam. Mijinyawa dai haka Tasiu ya kaishi har ƙofar gida ya saukeshi, ya ga kuma gidan. shirinshi ya rushe, yaso sau ɗayane asa Hindu ta leƙo su gana ma. Washegari sassafe sai kawai ga Uwatale da Nawata. Sukaita ƙwanƙwasa ƙofa, a mugun gajiye mijinyawa ya buɗe ƙofar tare da dogewa a ƙofar ɗakin. "Bacci kake yi ne har yanzu. Dake Hindu ta dawo dole kaita bacci." Mijinyawa ya ɗan yi dariya kawai. Uwatale tace. "To ka bamu waje mu shiga a gaggaisa ko? Jiya na ajjiye muku abincin dare, baka zo ka ɗaukan muku ba. Gashinan an ɗumama na tawo muku dashi, bansan ko Hindu zata yadda ta ci ba dai." Ta ƙarashe maganar tana kallon girman gidan, da kyan tsaiwar ginin, sai dai ace tsohon gidane kawai. Amman gidan ya burgeta a ina ma ta taɓa ganin gida mai kyau irin wannan itakam. Muryar mijinyawa da abinda yake cewa ne ya dawo da'ita hayyacinta. "Ai bata dawowa ba. Sabida bata jin daɗin jikinta gaskiya. Shi yasa nace a barta, magani ma aketa mata" Ya ƙarashe zancan yana sosa kai. Ji yake kamar zasu gane zahirin abinda ya faru. "Allah sarki. Wannan makarai suna azabtar da'ita duk yadda akayi mazane a kanta shi yasa" "Meye haka Uwatale kike yi? " Nawata yai saurin katseta, ta ja bakinta tayi gum. "To Allah ya bata lafiya. In ta samu sauƙi ta dawo ma zo mu ga wajen. Ni daga nanma kasuwa na nufa" Nan suka yi sallama da juna. Ina ya Allah babu ya Allah, lokaci akace alƙali. Hindu;. Innarmu ce ta shigo da yaran a hannunta, ta nemi waje ta zauna. "Hindu hoo wato harma kin shirya, tafiya kawai kike jira ƴar nema. To Janaral yace sai admishon ya fito, an biya kuɗin rijistireshon kafin ki koma" Murmushi nayi nace. Babu komai Innarmu Allah ya kaimu" "To ameen. Hindu nasan janaral yana da zafi da kuma tsauri. Amman kinga duk wannan abun da yake yi? Ba wai so yake aurenki ya mutu, ko ya samu tangarɗa bane. Ba kuma yana nufin saida ilimi mutum ke samun ɗaukaka, ko daraja ba. In Allah yaso ɗaga bawanshi, yana ɗagashine a duk sanda yaso, ko wannan bawan yana da ilimi ko bashi dashi. Darajar amman mai ilimi daban take, musamman ilimin addini, shi wannan daidai gwargwado nasan kina dashi, kuma kina ƙoƙarinki wajen bin dokokin mahaliccinmu, ga tsayuwar dare da kike yi, wanda shima wannan mai tsayuwar daren in domin Allah yake yi, dan neman yardarshi darajarshi daban take a wajen Allah. Na horeki da haƙuri, ki koya daga gareni Hindu. Ki jira lokaci alƙali tamkar yaune" In sha Allah Innarmu. Nagode, kuma wallahi nasan Baba Sojanmu ba ƙin Mijinyawa yake yi ba, nima ba ƙina yake yi ba. Kuma tunda har yace haka, nasan babu mai mishi dole. Mijinyawa kuwa nasan bazai dawo ba har sai lokacin da wa'adi ya cika." Innarmu ta gyaɗa kanta, halamun ta gamsu da abinda nace. Gaga_gaga haka akaci gaba da cukumurɗawa. An yi jarabawar Jamb a ranar ashirin da takwas ga Afirilu. Cikakken sakamakon hukumar jami'ar BUK ta zauna don tantance maki ( cut off maks) na kowanne kwas da sashe, inda aka fara kafe sunayen ɗalibain da suka samu nasara a jikin allon sanarwa na makaranta. A tsakankanin watan satumba, Nuwamba, na wannan shekarar. Ina gada cikin waɗanda suka samu gurbin karatuu Sai dai mu ce alhamdulillahi. Duk wani cike cike, da duk abinda ya dace Baba Sojanmu shi ya shige mun gaba, tare dashi muke zuwa duk inda ya dace aje. Har dai lokacin biyan rijistireshon yayi. A nanne ya sanarma Baba Nagoɗi ya nemi mijinyawa. Baba Nagoɗi. Baba Nagoɗi da magriba yasa samarin gidanmu suka kaishi Kurna, cikin ikon Allah sun haɗu da Mijinyawa ya fito masallaci kenan. Nan suka gaggaisa. "Lokacin biyan kuɗin rijistireshon yayi. Kamar yadda na ɗauki alƙawarin nemanka shine nasa yaro ya kawoni. Inaga ka bani kuɗin bama sai kazo ba. Sannan ka bani ɗan mabuɗin gidan, da ɗan mabuɗin ɗakin ita Hindun. Da kaina zan kawo maka ita. Sai haƙuri Baban naku akwaishi da zafi" Mijinyawa yaita goɗiya. Tambayar kuɗin rijistireshon ɗin yayi, a take ya shiga ya ƙirgo kuɗin, da ɗan mabuɗin ya bashi. Suka yi sallama Baba Nagoɗi ya kamo hanyarshi suka dawo. Ya danƙama Baba soja wannan kuɗi. Hindu:. Yau cike nake da farin ciki marar abun misali. Yau itace ranata ta farko a cikin ajin ɗaukar darasi, tare da ƴan uwana sababbin ɗalibai. Galibi ƴan matane, matan auren a wannan lokacin bamu da yawa, bamu wuce ace ɗaya, biyu, uku ba an gama ƙirgamu. Kuma ayau zan koma ɗakina Baba Nagoɗi yace ina dawowa in jirashi zai dawo daga kasuwa ya maidani da kanshi. Nayi lalle, na yi ƙunshi, nayi dilka duka, magungunan ta da komaɗa ma duk nasha, kafin in tafi makaranta na gama kammala kayana tas. Ina dawowa Baba Sojanmu ya tareni. "Ya lakca Hinduna? Sai yanzune na samu nutsuwa da kwanciyar hankali. Ina miki fatan alkhairi, tare da adda'ar gamawa lafiya. Nagoɗi tun tuni ya dawo yana ta so kizo ya kai ki gidanki. Amman nace dani za'aje da Innarku" Ameen Baba Sojanmu nagode ƙwarai da jajircewarka." Tashi nayi na shiga ciki, innarmu na tarar ta shirye tsab, yaranma ta saka musu kaya sababbi siya musu tayi gaskiya. Ban ko zauna ba akace in fito. Jakata na ɗauka kawai su Azgar na tafe da ƙafafunsu. Matan gidan duk sun fito rakiyata har gaban mota. Ni dai motarmu na hawa titi na lumshe idanuna kawai. Tafe tafe sai gamu a ƙofar gidan. "Ga gidannan ka ganshi tsaya gefe Tasi'u" Yaya Tasi'u ya kyara tsaiwa duk muka sakko a tsanake. Ɗan mabuɗi Yaya Tasi'u ya saka ya buɗe gidan, muka shiga da sallama. Tsakar gidan lallai akwai yalwa. Sai dai ashe Tasi'u bai shigo ya ga inane ɗakina ba ranar da yazo sauke Mijinyawa ba. Muna wannan tsaiwar cirko_cirko a yayin da Baba Sojanmu yake ta ma Yaya Tasi'u turanci na faɗa. Sai ga uwar Gulma Uwatale da alayyawo cikin leda ta shigo, kwaram_kwaram. Yatsunta sun fito har suna taɓa ƙasa ta gaban takalmin. Ga mayafi an yafa. "Ashe dai ke ɗin na gani Hindu? Ai ina wajen Shitu mai kayan miya, kawai naga tsayuwar mota. Sannunku ina wuninku?" Su duk sun amsa, ni kuwa sai ido. "Ga ɗakin can ai, ba nan inda kuke tsaye bane" "Ayya to mun gode ko?" Cewar Innarmu, data amshi ɗan mabuɗi a hannun Yaya Tasi'u, ta nufi ƙofar ɗakin ta buɗe. Uwatale dai taƙi tafiya. Ganin na haɗe raina ne yasa tace wai zata je ta dawo. Ni dai jakata na ɗauka nabi bayansu muka shiga. Masha Allah falo yayi kyau, kujeru sun haska gaskiya. Innarmu sai ƙarema falon kallo take yi. Ni dai waje na samu na zauna. "To Hindu mu kam za kuma mu koma, mun dawo dake ɗakin mijinki, zai dawo ya taddaki. Allah ya ba da sa'a akan karatunki. Ubangiji Allah ya sanya albarka a ciki" Cewar Baba Nagoɗi kenan. Baba sojanmu shima ya sanya albarka, tare da Yaya Tasi'u da sai tattaɓe bakinshi yake yi. Innarmu dai ganin iskancin da Tasi'u yake yi ni nasan shi ya hanata magana, kusan tama riga kowa ficewa. Bayan ta ajjiyemun soyayyar situ ɗin da tayi mun mai cike da nama. Har saida motarsu ta tafi na koma ciki. Ina shiga falon na sauke ajjiyar zuchiya wani irin farin ciki marar musaltuwa nake ji. Saida nayi sallar la'asar na soma gyaran sib, ya ci mun lokaci sosai, sai daf magriba na gama. Inata mamakin banga kayan kicin ɗina ba. Kwatsam sai na jiyo sallama. Mrs BUKHARIMRS BUKHARI .................... *Wai kina da labarin Gidauniya ta mata, farin cikinsu, da walwalarsu, mai suna *MURYAR MATA (FARIN CIKIN AL'UMMA)*🧕🏻👩🏻‍🎓 *Wanda ni Mrs BUKHARI muka yi haɗin guiwa wajen buɗewa, tare da sauran shuwagabannin Taskar Badiat Ibrahim?* *ku matso kusa ki kasance a cikin wannan tafiyar ta Alkhairi, tafiyar da zata gyara rayuwar Aurenki, tafiyar da zata gyara miki tunaninki, tafiyar da mace zata gane ni'imominta, tasan kima da darajar kanta, gidauniyar da zata koya miki sana'ar da zaki dogara da kanki, gidauniyar da zata koya miki tattalin uwar kuɗin kasuwancinki, da yadda zaki tattali ribarki ta yadda zaki ƙarfafa kasuwancinki, sha'awar son komawa makarantar addini, ko na boko kike so? To biyomu muje wannan gidauniyar taku ce mata, gidauniyar ta ƙunshi abubuwan da zatonku ma bai zata ba.* *Ga lambar wayata ga matan da basa cikin Taskar Badiat group 1 group 2 group 3 sai kui mun magana in sha Allah zaki kasance a cikin wannan tafiyar ta manyan mata* (08179523215) *Ƴan taska kuma zaku iya tuntuɓar Admins ɗinmu ta pc domin kuji yadda tsari da dokokin kasancewa memba a cikin wannan shahsrarriyar, garnaƙaƙar gidauniya wacce ta haɗa manyan masana zamantakewar aure, malamai, manazarta, mahukunta, ƴan gwagwarmaya, masana ta ɓangaren gyaran aure, ƙwararrun ƴan kasuwa, da gogaggun ƴan boko, wanda ya haɗa matan arewanmu da kudunma baki ɗaya, zamu kasance a duk faɗin Najeriya da izinin Allah* Ina jin sallamarnan, na fito a tsanake daga uwarɗaki babu ko ɗan kwali a kaina, yara na biye dani. Mijinyawa yana tsaye a falo muka fito. Illahirin mamakine ya kamashi, yara suka nufeshi suna kiran Abba Abba. Abba hankalinshi na kaina, tsugunnawa yayi ya ɗauki yaran dukansu, miƙewar da zaiyi ya haɗa dani yai mana riƙon alawar yara. Ajjiyar zuchiya muka sauke, ya shafi ƙananun kitsona, ni dashi muka soma kallon ƙuda, har saida yara suka gaji suka shiga mutsu_mutsu kafin ya dawo hayyacinshi. Duresu yayi yana ta fara'a. "Yaushe kuka dawo, ashe yau zaki dawo? Jina nake yi tamkar maraya, kullum cikin tunaninku nake. Gashi bana so inje gida ya zame mana matsala dukanmu. Alhamdulillahi komai aka sa mai lokaci zai zo Tutar so." Kaji kiran sallah, ka samu kayi alwala ka tafi masallaci, in ka dawo ma zauna. Ai da labari" "Yau kam kwana zamu yi muna hira ai gaskiya." Muna dariya ya fice a ɗakin. Yana fita aka kawo wuta ya haske ko'ina. Ɗakin na kuma kallo, na juya na kalli uwarɗakina. Yanzu shikenan na baro jama'are. Zaman ƙauye ya zama tarihi. Haƙiƙa Allah shine abun godiya, Allah kasa mun dawo a sa'a, ka bamu rufin asirin da zamu fi ƙarfin tozarci. Allah mun faɗi rub da ciki a gaban maƙiyanmu, sunga wallanmu. Ya Allah ka ɗagamu suna gani, mu tsaya da ƙafafunmu irin tsaiwar tsirin tsandauri, ta yadda babu mai iya tugemu. Kai Azgar kuzo muje mu yi alwala ko? " Jaye su nayi muka fito tsakar gidan, ga hasken wuta nan tantar. Alwala. Muka yi ni da yara, a wani waje da tabbas an tanadeshine domin wanke_wanke, wanki, da duk abinda dai ya danganci ruwa. Sallah muka yi, ina ta zaune har nayi isha Mijinyawa bai shigo ba, harma na soma jin yinwa, danma farinciki na ɗauke mun hankali. Sai can ya shigo da ledoji cike _cike fa. Yana direwa ya fito, sai gashi da tire. Kajine biyu manya_manya ya saka a tire. Carab na karɓi ledar a hannunshi na ciro gurasa, harda lemun kwalba guda huɗu. Ɗayar ledar kayan shayine da biredi harda ƙwai. "To wannan daren amarcine zamu maimaita. Inaso wannan daren ya kasance a cikin darare mafiya tarihi a rayuwarmu." Ilai hakane ya tabbata. Wannan daren darene wanda yake tsaye ƙyam a raina, babu daren da zai iya kankare wannan, sai dai wani daren shima ya kafa nashi tarihin. Sai bayan mun nutsa, sai nace dashi. Kayan kicin ɗina ban gansu ba. Naga babu kicin a ciki, hala na tsskar gidane ko?" "Ga kicinnan na buga miki na langa_langa komai yana ciki. Akwai kalanzirma dana siyo yana ciki, ina ɗan tafasa ruwan bunu, da ruwan wanka. Kinga kaya, kinga wajen ko da fatan yayi miki? " Idanuna na kaɗa cikin sigar soyayya. Kuma tabbas saƙo yaje. Nagani, kaya sun yi kyau sosai, banyi zatonsu haka da kyau ba, ai kayane masu kyau. Lallai kayi ƙoƙari sosai. Ɗakunan gasu manya_manya sunyi kyau sosai, nagode, Allah ya saka da alkhairi. Yanzu dai muje ka rakani in kunna risho in ɗaura ruwan wanka." "Naƙi ɗin. Da izinin wa zaki je ɗaura ruwan"? Daga haka shikenan kuma ni Hindu. Washegari sassafe misalin shidan safe, harna dafa ruwan shayi, na soya ƙwai, na ajjiye a teburin tsakiyar falon. Saina koma na gyara Uwarɗakina na share duka ɗakin. Gashi ni bani da gaushi inason turara turaren wuta, dama ina da gawayinne sai in karashi a risho ya ruru. Shida da arba'in Mijinyawa ya shigo. Ganin ko'ina fes_fes, ga yara nayi ma Azgar wanka, Asama'u kam harna shiryata. "Har kin soma aiyukanne Amarya? " Ai dolena zani makaranta ina da lakca tara da rabi, ga yara zan kaisu gidan Yaya Zubaina in ajjiyesu" "Aa yau kam ki barsu, babu inda zanje. Sai jibi in sha Allah zan kafa teburin lemona, na tambaya to shi Alhajin dana tambayeshi bai ce mun komai ba tukunna. Kinga tunda ƙofar gidanshine sai abinda yace. Amman in har zuwa jibi baice mun komai ba, sai in nemi wani abun da zanyi, ko in sake gwada wani wajen" Shiru nayi, can nace. To shikenan Ubangiji Allah yasa a dace. Bari in kammala sai in tafi, dan saina biya ta gidan Yaya na faɗa mata yau bazan kawosu ba." Shiryawa nayi, muka karya gabaki ɗaya, ƙarfe takwas da rabi daidai, harmun ƙarasa titi zan hau abun hawa, sabida da ɗan tafiya daga Kurna zuwa Buk tsohon shashi. Gashi zan tsaya a gidan Yaya Zubaina dake Kabuga. Inda a ƙofar Kabuga motoci suke ajjiyemu, kuma gidanta a kan titi yake sauƙin dana samu kenan. Bani da wata matsala da yara. Ita tana da mai aikinta dake kula mata da yara, ko da batanan. Ƴan gwangwani bus na hau zuwa ƙofar ruwa, wasu a Bata suke tsaiwa. Daga nan ƙofar ruwa kuma, na sake hawa kai tsaye inda zan sauka a Kabuga anan motocin suke tsayawa, wasu suna shiga har cikin buk tsohon shashi, a lokacin babu mota ta kai tsaye daga Kurna zuwa Buk. Ganin tara saura yasa ban tsaya gidan Yaya Zubaina ba. Ina sauka na shiga ɗaga ƙafata kawai. Tara da minti biyar ina cikin aji. Ƙarfe biyu na gama da makaranta. Kai tsaye gidan Yaya Zubaina na nufa, anko ci sa'a ashe bata je wajen aiki ba, kanta na ciwo a kwance a ɗakinta na isketa. "Tun safe nake ta zuba idanu inga kin kawo yara naji shiru. Nayi tunanin ma ko baki shiga makaranta ba" Ai ko dai na shiga, dake Mijinyawa bai fita aikin ba, yace sai jibi shine na barsu tare a gida. Baki je aikin ba yau?" Na tambaya ina miƙewa, yinwa nake ji sosai tunda nayi sallah a makaranta ai gara inci abinci kafin in tafi. "Ciwon kannan ne dai ya uzzuramun, tun safe ni ko falo ban fita ba. Bansan ma wainar da ake toyawa ba. Ni dai naji ɗuriyar yara sun dawo boko, sunci abinci Islamiyya tayi kira" Ladi na kira ta zubo mun abinci, shinkafa ce ds miya da kifi, inaci muna hira. Biyu da arba'in nai mata sallama na fita. Bani na shiga gida ba sai la'asar. Na shiga gidan na tadda anata shigowa da kayan ɗaki, da dukkan alamu dawowa akayi ɗaya daga cikin ɗakunan. Ga mata a tsakar gidan anata aiki. Sallama nayi, muka gaggaisa da matan da na gani a tsakar gidan. A kicin naji ɓuruntun mijinyawa, Asama'u na zaune a dokin ƙofata, Azgar na tsaye a bakin kicin. Gyaran kicin ɗin kake ta yi ne, me yasa baka jira na dawo nayi ba?" Murmushi kawai yayi mun. Asama'u data matso na ɗauketa, Azgar kuma inata shafa kanshi. Ka shiga ciki, kaga gidan cike da mata k0? " "To gimbiya sarautar mata. Ku shiga da yaran ganinan zuwa" Hannun Azgar na ja muka shiga, na gaji sosai kuwa. Amman hakan na tashi na fita na ɗauro alwala, mijinyawa kuma ya tafi masallaci. Ina zaune ina ɗan nazarin karatunmu na yau, mijinyawa ya shigo da sallamarshi, ga cefanen kayan miya a hannunshi. Kayan miyan na karɓa muka gaisa. Nan muka shiga hirar makaranta, da bayan rabuwa halin da kowannenmu ya tsinci kanshi a ciki. Na tambayeshi mai suka ci da rana, yace dani ragowar kazar jiya da daddare suka ci da biredi. Hirar dai taƙi ƙarewa muka koma kicin, shi yana zaune a kujera daga waje. Ni ina daga cikin kicin ɗin, na kunna risho. Ya gyara kicin ɗin fes, ya jera komai, a kantocin sama da aka kewaye kicin ɗin dashi, ƙasa kuma kayan abincine, da risho, sai kwandon kwanuka. Shinkafa na dafa mana fara, na juye miyar dana tawo dashi a tukunya na ɗumama. Sai na tafasa ruwan zafi na cika filas. Dake zafi akeyi da ruwan sanyi, da magriba nayi wankana a bayangida, ina fitowa na ɗaura alwala saina shige. Mijinyawa na ƙoƙarin fita na shigo. Inason gawayi zan samu nan kusa, inason in turara ɗakinne ya ɗauki ƙamshi" "To in zan shigo daga masallaci sai in tawo miki dashi." To shikenan adawo lafiya, Allah ya tsare" Da "ameen" Ya amsa tare da ficewa. Saida nayi kwalliya na kintsa. Wani yadi nasa mai taushi ɗinkin riga da zani, rigar iyakar guiwa, na karya ɗankwali, nabi jikina da humrori kafin na ta da kabbatar sallah a uwarɗaki. Ina kan sallah na dinga jiyo sallama, can kuma sai naji shiru. Bayan na idarma saida na kuma gyara tsaiwar ɗankwalina. Hmm ina fita mutuniyarku tana zaune dafa'an a kujera ta yi tagumi wallahi kunji na rantse. Ta yi mugu_mugun zurfi a tunani. Ni ko raina fa yayi maƙurar ɓaci. Zama nayi a kujerar dake fuskantarta, bata ma san na fito ba, bance mata uffan ba. Fitowar yara da gudune ya dawo da'ita hayyacinta. Tana ganina kuma sai ta shiga washe baki tana wayancewa. "Ashe kin fito ban sani ba. Ikon Allah wannan sababbin kaya haka Hindu? Gaskiya waje yayi kyau. Iyayenki suna da kuɗi gaskiya. Wai nace Hindu ni kam inaso in zaki gidanku in biki aje a gaggaisa" Ni dariya ma ta bani da ƙyar na dake. Abinda zan soma miki dashi shine. Ba'a shigowa ɗakin mutum a zauna ba izininshi, kinyi sallama ba'a amsa ba sai ki haƙura. Amman kin shigo kin yi zamanki, kuma kika yi shiru? Bari kiji kada ki sake" Sai tayi dariya. "Laa to shikenan dama tunanina ko kina sallah ne. Kin dawo lafiya. Ohhh Asama'u yarinyar Hindu. Kin samu yarinya a ɓagas wallahi. Yanzu shikenan an rabata da gyatumarta ana haka in ba mutuwa ba kuwa" Sai kuma ta ɗan yi dariya kamar taɓaɓɓa. "Ammi abinci zanci" Azgar ya katseta. "Kinji yaronnan baki raɗau, ko da yake Ɗan safiyo ma abokin tagwaitakarshi yaro baki ji surutu ba. Ni banma taɓa jin muryar yaronnan ba, dake baya fitowa tsakar gida." Ta ƙarashe da dariya. Miƙewa nayi, na nufi kicin Uwatale ta biyoni fa "Ay wannan madafine ashe. Kai amman yayi kyau ga kayan alatu rigis" Tana yi tana kallon miyata mai cike da zuƙu_ zuƙun nama. Azgar na zuba ma abincin na bashi, Asama'u ma na zuba mata nata na bata. Sai na zuba ma Uwatale data bisu suka shiga ciki. Ga abinci fa" "Laaa sai dai in tafi dashi na ƙoshi, na ci tuwo kamar cikina zai fashe. Gashi miyar jawur da'ita ta bani sha'awa, ji nama wani babban yanka." To shikenan " Iyakata da'ita kenan, sai ga Mijinyawa ya shigo da sallama. "Shigo mana Nawata bismillah" Nawata ya biyo bayanshi suka shigo. Ni dai tunda muka gaisa ban kuma cewa komai ba. Kwano da cokali na ƙaro musu, mijinyawa ya zuba musu abincinnan. "Azgar ana cin shinkafa da miya?" Cewar Nawata, saida ya cika bakinshi dam da abinci ya soma ɓarin zance. "Yanzu mijinyawa shikenan an raba Halima da Asama'u kenan, ko kuwa dai zaka mayar mata da ƴarta in ta tasa? " Ya kuma cikowa ya kai baki. Mutuniyarku itama saita soma cin nata kawai. Suna hirarsu tana saka baki, ni dai idanune nawa kawai, hirace da bata shafi Hindu ba. Dana miƙe ma sai na nufi kicin. Gawayi na gani ƙulli ɗaya, na ko karashi a risho ya ruru kana na dawo ciki na ɗauki kasko na koma. Tunda na shige ciki, ni kam ban sake bi ta kansu ba. Daga uwarɗaki nayi musu sallama tare da godiya. "To sai kin shigo mana. Daga wannan gidan naku gida goma sha huɗu ne, da babban layi a tsakani" Sai mijinyawa Babba yace. "To in banda ke Uwatale ai Mijinyawa zai kawota in ta huta kema dai" Ya fita rakasu, ni kuma na fito na gyara wajen da suka ci abinci. Asama'u na tarar tana amai. Da sauri nayi kanta jikinta sai zazzaɓi kau. Asama'u akwai laulayi ƙarshe akan saman ƙirjina ta kwana, ni kam baccina rabi da rabi, gashi dama ban kwanta da wuri ba, ina karatu mijinyawa na sanar dani mai gidan daya tambaya zai dinga saida lemo a ƙofar gidanshi, yau yayi mai magana bai amince ba. Dan haka gobe zai fita buga_ buga. To amman yanzu yaushe kasan gari da har zaka shiga buga_buga?" "Tutar so ho. Ga Nawata da bai ma taɓa shigowa birni irin na Kano ba. Amman yana fita buga_bugarshi. Ai binni ba kamar ƙauye bane kingani, akwai sana'o'i iri da kala, aikin ƙarfinnan gasunan suma. Kinga batun karatunki bana son a samu wata matsala, ga hayar gida, ga Nanno dole in zamu je da sallah mutum zai riƙe wani abu. Ga yara a gabanmu" Hakane Ubangiji Allah ya sauƙaƙe maka ya buɗa maka" Washegari da yaran na tafi na saukesu a gidan Yaya, ni na wuce makaranta. Uku na shiga gidan Yaya, bata ma dawo ba. Na tadda wai su Nana sun tafi islamiyya dasu Azgar. Ladi ya jikin Asama'u kin bata maganin kuwa na rana, sannan taci abinci?" "Jikin da sauƙi taga yara ta ware sosai. Sai dai abincin da taci ta dawo dashi gaskiya. Amman na dama mata kunu da ta ƙoshi saina bata maganin" Wannan shine mafarin shigan su Azgar islamiyya Tare da su Nana. Mijinyawa kuma a fitar farko dako yayi a kasuwa, fita ta biyu shugaban leburori yace ya sake kasuwa ya kauce ƙa'ida dokarsu. Sai ya shiga buga_bugar duk abinda ya samu zai yi. Yayi wannan buga_buga kusan na watanni shidda. Kafin ya samu aikin kwandastan Bus, kuma babu laifi ana sallamarshi da kyau. Sai dai kuma sai wajen sha ɗayan dare yake shigowa. A gajiye tulus kullum, kafin ya dawo na tanadar mishi ruwan zafi, zan gargasa mishi jikinshi da kaina, yaci abinci mu ɗan taɓa hira sai bacci, wataran ma hirar sam bata samuwa. Ranar lahadi ne kaɗai muke samun lokaci kanmu. Ɗakunan hayan gidan duk mata sun shiga, amarya guda ɗaya, sai masu yara kamata haka dai. In mun haɗu a tsakar gida, muna gaisawa, ni dake ba zama sosai nake yi ba ma, bama haɗuwa. Ranar wankin bayangida in ya zagayo kaina, zan wanke kafin in tafi aiki, haka ma sharar tsakar gida. Wajen da muke wanki, wanke_wanke ni ce kaɗai nake sa tsintsiya da ruwan kumfa in zirje tas bayan na gama wankin da nake yi duk ranar lahadi. Uwatale dai kullum da yamma saita shigo, in tazo siyan kayan miya. Hana ƙarya na shiga sau biyu gidansu. Na farko tare da Mijinyawa. Na biyu ni kaɗai bata ji daɗi ba, na shiga na sameta ta na ta zuga amai. Ƴan gidanmu sun zazzo da yawan, sau uku suka zo, sun rarraba tafiyar. Ƴan kuɗaɗen hannuna duk saida suka ƙare ayi musu hidimar girkin fita kunya. Kuma alhamdulillahi an fita kunyar. Gida kuma ina zuwa dubo su Baba sojanmu, musamman daga makaranta nake wucewa. Sai da uwatale duk yadda zata yi ta naniƙi matar gidanmu, Maman Zailani. To shikenan a lokacinne tasan kullum ina fita, Maman Zailani ta faɗa mata. Itama ta gani da idanunta, na dawo makaranta da yara nazo na sameta a zaune a tsakar gidanmu. Tana ma Maman Zailani wanke_wanke fa. Daga ita sai ɗaurin ƙirji, ga hijabinta rataye bisa igiyar shanya. Matan gidan duk suna tsakar gidan suna shirye_shiryen sanwar dare, kamar yadda kusan kullum a haka nake samunsu. Sai Amarya da take kicin ɗinta, tunda ni da'itane masu kicin ɗin langa_langa. Su a ƙofar ɗakunansu suke girkin, ga kicin shirgege na tsakar gida, shirginsu kawai suke sanyawa. "Ahh Hindu kin dawo, ai na shigo wajen ƙawata ban sameki ba. Ashe kin kuma samun koyarwa ananma? " Ƴar dariya nayi mata kawai. "Kin dawo maman Asama'u?" Su haka suke ce mun. Nadawo Maman Fatu sannunku da gidan" Na wuce tare da buɗe ƙofata na shiga. Nagaji sosai, ga yinwa inaji. Faten doya Yaya suka yi, ni kuma lalatamun ciki yake musamman mai wake da ganye a ciki. Gashi bana siyan komai a makaranta, abinci nake dafawa in tafi dashi, in zan kai yamma a makaranta. In nasan bazan wuce biyu ba nasan zanci a gidan Yaya. Sai da na huta kana na fito, na saka ɗan mabuɗi na buɗe kicin ɗina. Sai naga cefane a cikin bokiti mijinyawa ya ajjiyemun, Allah sarki ya zagayo kenan, dake yasan babu kuɗi a hannuna, kuma ba cefane. Kuɓewa ɗanya nagani, sai attahuru, albasa, tumaturi, tattasai, sai ɗanyen kifi jela ɗaya, da maggi, ina da mai. Risho na kunna na ɗaura ruwan tuwon nawa. Sai nayi zaman gyara kayan miyana ina jefawa a turmi. Jajjagawa nayi na juye a tukunya, na zuba maggi, manja ina da daddawata da kayan ƙamshi a cikinta aka haɗa aka daka, sai kawai ɗiba. Na yanka kifinnan na zuba. Sai na juye ruwa a bokiti naima yara wanka, na sauya musu kaya, suna wasansu daga ƙofar ɗaki cikin barandata. Su Zainab kuwa sai uban guje_guje da ihu suke yi. Tamkar ana kaɗasu da ruwan hanji. Azgar sai karatu yake yi, sai Asama'u itama ta soma karatun, suna yi suna nishaɗinsu. Ƴaƴa rahamane wallahi jinsu nake a cikin rayuwata tamkar ni na haifi abuna. Ita Asama'u dake mai laulayice dole zata fi shiga raina, zanfi damuwa da'ita. Amman son da Azgar yake mun gurbin yaron na musamman ne. Murmushi nayi na tuno sanda Baba Sojanmu yake kawo musu tsaraba, yaita rungumarsu Asama'u tai ta birgimarta a jikinshi. Uwatale sai labarin jama'are take basu, muryarta kuwa nayi imani har maƙota. Naga a gidanmu tayi jajjayen kayan miyanta ta zuba a leda dan jar jarsba. Sai da taga duhu fa ya soma rufawa, a lokacin harna sauke tuwo na maida miya, na ja ruwa na tafi wanka. Kafin Uwatale kuma ta kwasa a guje wai ta shiga uku bata san yamma tayi ba. Kai kawai na girgiza, na yi wankana, ina fitowa nayo alwala. Kalanzir ɗina na fita na tadda ya ƙare miyar ko tafasa bata yi ba. Ina da gawayina, saina janye kurfotina na ƙasa laka nake nufi, banma taɓa amfani dashi ba, sabida rami biyu gareshi ma'ana yananan kamar irin risho mai kai biyu. Gashi da nauyi. Fito dashi nayi baranda na kunna da leda. Kafin na shiga ciki na shafa mai, na zura doguwar rigar yadi dinkin umburela amman doguwa. Saida muka yi sallah da yara na fito.. Na tadda murhun ya ruru sosai garin sai iska ba_ba-ba_ba ga hadari har walƙiya akeyi. Mun shigo watan damuna Allah yasa mu samu ruwan dare. Ai kafin in idasa tunanin, sai ruwa mai iska aka soma shi. Haka na ɗauki kurfotinnan na mayar kicin, ɗayan gefen ruwan wankan mijinyawa na saka, na zuba gaushi a kasko na turare ɗakin nawa, ga yinwa, gashi bani da komai na taɓin gishiri, sai bayan isha na kammala miyarnan. Nako ci tuwo sosai, yau dai ban jira mijinyawa ba. A cikin ruwannan ya dawo ya jiƙe sharab. Kai tsaye ma ruwan wanka na juye mai yaje yayo. Yana cin abinci, muna taɓa hirar karatu. Ga kuɗaɗen aikinshi da kullum yake zubemun su, ni zan bubbuɗasu in jejjerasu, sai yace in adana in ya ɗan ɗauki wani abun, watarana ma baya ɗauka. Muna ta hirarmu ta karatu, wuyarshi da daɗinshi, da wuyar neman kuɗi da daɗinshi. Nan nake sanar mushi Uwatale tasan ina fita gashi_gashi. "To ai sai mu barsu a hakan. Ai duk sun san dama kina koyarwa a barshi a hakan. Allah ya taimakemu" Murmushi kawai nayi mishi. Haka dai gidanmu shikenan ya zama gidan zuwan Uwatale wuni zuryan fa, daga haka Uwatale sai tasa mata ke zuwa su saka kujera aita hira. Ta fa baro gidanta, ta tare a nan gidanmu. Ni yau dana shigo hirar takin dausayi suke ta yi, ko wacce na faɗin irin nata takin, suna ta shewa. Muryar uwatale wallahi har waje. Ina shiga sai suka ɗan daburce basu zaci ni bace. "Hindu to kuma da yaran duk kike zuwa koyarwan, ki dinga kawosu mana ai ba sai kin sha wahala ba. Ni kullum ma inanan" Aa nagode, babu wahala a cikin tafiya dasu ai Uwatale. Bana ɗaurama kowa nauyi." Yau dai harna gama dafa dukata ta bushasshen kifin da aka aiko mun da tsarabarshi, Uwatale tana gidan. Nayi wanka, naima yara, na bulale ɗakina da ƙamshin turaren wuta. Ina zaune ina nazarin karatu. Amman uwatatale manya tananan ana zuba. Ko sai yaushe take kammala girki oho. Asabar data zagayone na gane lallai wuni uwatale take yi a gidan tun safe take zuwa, tun kafin fitar Mijin Maman Zailani, dake Nawata sassafe yake fita, inaji tace wai ya samu wani babban aiki. Jarabawa mu kam ma mukeyi na samestan farko, duk na rame sabida karatu, da wuri nake shiga makatanta mu zauna da abokan difatiment muita karatu, zuwa wannan lokacin an shaidani wajen naci da ƙwaƙwar karatu, ga tambayoyi da nake damun lakcarorin dashi, wasu su yaba da ƙwazon, yayin da wasu suke ganin iyayin nawa ai ai yawa. Hakama a ajinmu kowanne da fassararshi. Ni bana bi ma takan kowa, ni ai karatune ya kawoni, in banyi tambaya ba me zanyi to?. Gaga gaga gaga, aka shiga azumi, muka gabatar da ibadarmu cikin nutsuwa, kwanciyar hankali, abu mafi daɗi lokacin buɗe baki yadda iyali ke haɗuwa ayi buɗa baki, da kuma yadda ake tafiyar sallah a masalci maza da mata. Ana jibi sallah muka wuce Jama'are, su Uwatale ai tuni su azumi na ashirin suka tafi, kamar masu zuwa umara. Da yamma lis sai gamu a jama'are, su Shafa ana tsakar gida, naci adona da kaya na alfarma, haka ma yarana. Nan akaita kururuwan murnar zuwanmu. Bayan mun ajjiye kayanmu, muka nufi ɓarayin Nanno. Hmm Uwatale tana can ɓarayin tana damama Nanno kunu. Ni ko sau ɗaya ta amsa gaisuwata, ta kawar da kanta. Tashi nayi bayan na ajjiye mata tsarabarta, harda kayan sallah, da hijabi, da takalmi da muka yi mata. Na wuce shashena. A daren sai ga Baraka da abinci, dariya mukaima juna, mun taɓa hira babu laifi gaskiya. Washegari sai ga Halima tazo ganin Asama'u. Tayi farin cikin ganin yadda Asama'u ta koma sosai, itama muna ta hirarmu tunda mun saba sosai, kuma yanzu shaƙuwar ta ƙaru sakamakon riƙon Asama'u. Ashe ita, Tata manufar zuwan dabanne. A daranne tace ma mijinyawa tana sonshi, tunda yana riƙe da ƴarta, mai zai hana ya aureta sai riƙon yarinyar ya dawo hannunta? A daren take faɗa mai ita da auren Abdulƙadiri ma tana jin motsin son Mijinyawa duk ranar data ganshi, kuma tana so ta kasance a inuwar aurenshi. Cike da mamaki yazo yake sanar dani yadda suka yi da Halima. Murmusawa kawai nayi, to me zance ni kaza? Mijinyawa yaita faɗa fa, yanata ɓaɓatu. Daga lokacin ban kuma sake ma Halima fuska ba, har akayi sallah aka gama muka tattare yanamu_yanamu muka koma. Gashi sai ta caɓo ado tazo, ta barbaza kitson ƙari, sabida a tunaninta ai bansan mijinyawa take farauta ba. Na muku tsallake, ai saida Nanno ta titsiyeshi akan batun koyarwar da nake yi, da sunturi da yara da nake yi kullum wai ita bata so, kar mu zo da babbar sallah ace mata naci gaba da zuwa koyarwannan. To ashe tsugunne bata ƙareba. Da babbar sallah tazo banje Jama'are ba, shi dasu Uwatale suka je. Yace ƙaramar sallah kawai zan dinga binshi, babbar sallah nima inyi tare da dangina yana ganin zaifi, tunda suma suna da buƙatata. Nace mishi to, ai kuwa hakan akayi. Nanno kashe mijinyawa ta dawo dashine kawai bata yi ba, faɗa kam tayi_tayi shi babu iyaka. Wallahi ya dawomun idanunshi duk ya faɗa. Gaga gaga kamar wasa har na shiga lebul na biyu a jami'a. Baba Sojanmu sai jin daɗi yake yi, musamman in naje gida sai yace. "Hinduna ta farfaɗo, ta dawo ƴar gayenta, ƴar birni ke da ƙauye har abada, sai dai ziyara" In sha Allah Baba Sojanmu" Abunda nake cewa dashi kenan. Kuma muddin naje gida dubu biyar ɗinnan alƙawarine sai ya bani, to da naga bani dana mota, naje makaranta a ƙafa, na dawo a ƙafa sai in kai musu ziyara. Innarmu kuma tana bani dubu biyu da tarkacen kayan alawa, da biskiti na ƴan makaranta. Ana tsaka da zafin karatu Luba ta haihu. Sunturi salamu alaikum, ga babu kuɗi a hannunmu, mun biya haya a lokacin. A ƙafa da kuka sani wallahi nake niƙan gari inje duk inda zani. Tunda Luba ta haihu a ƙafa nake zuwa kusan kwana nawa. Sai ranar sunane dake na biya gida na samo wannan nera dubu bakwai da nake samowa. Ranar suna nakai mata atampopi biyu, na siya mata omo da sabulu na dubu biyu. Ina ya Allah, babu ya Allah. Ranar da Uwatale zata gane ashe jami'a nake zuwa ranar asabar da yamma, ina jan ruwa a rijiya ga hadari baƙiƙƙirin a garin. Kwatsam sai ga Alawiyya wata abokiyar karatuna kilas mait ɗina ce ma ƙarewarta. "Hindu Nagoɗi dama ashe gidanku ɗaya da Maman Zailani? Ikon Allah" Ai kuwa Alawiyya mai Rago gidanmu ɗaya, ƴar uwarkice?" Hankalin Uwatale na kaimu. "Ƙanwar mijinace ai. To ya karatun, karatu yanata zafi. Ko da yake kune gurayen aji ai gaskiya ai kanki yana ja" Dariya kawai nayi mata. "Anti Alawiyya ina kikasan Maman Asama'u?" "Ai makarantarmu ɗaya, ajinmu ɗaya muna karanta kwas ɗaya" Uwatale na kalla, sai zazzare idanu da susar kai take yi. Ina aikin girki inata tunane_tunanen abinda zai je ya dawo dan nasan akan wannan al'amari tsab Uwatale zata ko shirya zuwa Jama'are. Ai kuwa kamar da ƙasa. Anyi haka da kamar wata guda kenan. Lokacin babu mota a hannun ogan mijinyawa, bige_bige kawai yake yi. Yau tun daga Kurna har zuwa makaranta da ƙafata na dawo, bani da kuɗin motar, ni kuma bazan iya ɗaukar huƙa in huda cikina ba, shi yasa ban tambayi Yaya Zubaina ba. Abubuwan sun yi mana yawane su Azgar ma an sasu a makaranta, ga Islamiyya sun ma dena zuwa an ɗakkoma su Nana malamai har gida suke zuwa su karantar dasu, karatu mai kyau hadda suke yi na Qur'ani sosai, inajin daɗin yadda bakin Asama'u ya buɗe da karatu, Azgar kam ba'a magana in yana karatun Qur'ani muna mamaki wallahi, dake ƙwaƙwalwar da Qur'ani aka buɗeta. Ina shigowa cikin gidan da sallamata, muka haɗa idanu da Uwatale, in waiga Gefen kicin ɗina naga Nanno a zaune da jakarta ta buhu. "Ba shakka shanshani. Wata baki dena zuwa makarantar ba ashe? To ƙarshenki yazo wallahi wallahi, yau zaki sha mamaki" Na kalleta, na kalli matan gida duk mu suke kallo, Uwatale kuwa fara'a sosai a fuskarta. Mrs Bukhari.MRS BUKHARI ..................... Ƙaƙas fa Nanno take faɗa da wani irin ɗaga murya. Ni wallahi baƙin ciki, takaici, sun hanani cewa uffan. Hannun yaran kawai na ja zuwa ƙofar ɗakina. Ina kiciniyar buɗewa Nanno ta ƙaraso, ko gani da kyau banayi. Baƙin ciki ya makanta ganina, jina nake yi tamkar in haɗiye zuchiyata in mutu kawai. "Sannu ƴar gidan ɗan boko, ubanki mai zanzaro da hula. Eh nace sannu ko, ɗiyar ƴar boko, ke ticha, uwarki ticha. Sannu shanshani" Kallonta muke yi dani da yaran dukka. "Ko zanji saukan aradune, naga irin kallon da kike yi mun, nasan saura duka tunda wuyanki ai ya riƙa, kin dawo binni, cikin gatanki, jibi a irin gidan da kike rayuwa shirgege ma malam. Wanda ko su Uwatale da suke rayuwa a gidan kansu albarka. Ke dai a komai sai fa kin nuna kinfi uban kowa" Ƙofata na buɗe ina jin juwa. Ina buɗewa ta wuce ciki da buhun kayanta. Uwatale na shirin ratsawa ta wuce ni, na damƙi kafaɗaarta, irin riƙon da yaro kema abun wasan da ake shirin ƙwace mishi. Baya na dawo da'ita idanuna sun riga sun sauya launi, sun juya. Kada ki sake ki shigarmun ɗaki, in kika shiga wallahil ƙudrat sai dai a fito dake ranga_ranga. Ke bama yanzu ba na rantse miki da Allah duk ranar da gigi, ko hauka yasa kika kuma shigarmun ɗaki, sai dai a ɗeboki a karairaye, ko in kakkaryaki in watsoki waje" Cillata nayi taje ta kusan faɗuwa, tayi taga_taga, nayi shigewata ciki, sai naga daga Uwarɗakina Nanno ta fito. "Ba shakka irin wannan dukiya da aka narka miki yayi. Ya ƙarar da kuɗin gadon nashi akan inganta rayuwarki, da ɗanki tilo, ga ɗan uwanshi ya sai babban fili da nashi kuɗin, ya gagganɗa da tarinshi da dama ya jima yanayi, tabkeken fili ya siya. Amman dake shi shanyayyene, shine ya ƙare a kashe miki nashi gadon haka" Ina wuni Nanno kinzo lafiya?". Na gaisheta, ai ita uwace, kuma ko wanne tsuntsu kukan gidansu yake yi, ta bani tsiya, ni kuma in maida mata da arziki, abinda kake dashi ai shi kake bayarwa. Ko bata ci albarkacin komai ba, taci na haihuwar Mijinyawa. "Ƴar nema, gidan asiri da ban wuni ba nace kya ganni ne? Kujera ta samu ta zauna. Ni ko ɗaki na shiga na ajjiye jakata, ina yinƙurin sauya kaya zuruf ta shigo. " Nace ba zaki kawo mun ruwa bane bare abinci? Dama ai Uwatale ta faɗamun ko ranar da suka soma zuwa wajenki, ɗaki kika shige kika barsu, su ga marasa amfani a wajenki ko, shine nima zaki mun wannan shariyar taki? " Zan zo, zan sauya kayane. Abinci kam babu sai in na girka tukunna" Labule ta sauke, ina jiyota tana kiran uwatale. Nayi saurin zura riga na fito. Wabillahi in kika shigo ɗakinnan saina karyaki ɓaras, sai dai ayi miki ɗori, in kin ɗauka wasane ki shigo kiga yadda zanyi wasan kura dake, ba kince bakya ji ba" Ƙafa ɗaya dama ta sako, ba shiri ta mayar da ƙafarta.. "Dama dake naga Nanno ce ta kirani. Naga ai ta'isa damu mu duka ko? Amman tunda haka kika ce shikenan. Zumunci kam Hindu bakya so, ina Matar wan mijinki ni kike jujjuyam.... " Nufarta nayi gadan_gadan batai wata wata ba ta arce. Naso in samu in dira a wuyanta in jijjigata in bugata da ƙasa, inga wacce za'ayi. Nanno na tsaye tana salati nayi ficewata waje. Ruwane dai na cika kofi na kai mata, na fito na tsaida sanwar abinci. Ina kan yin girkin Nanno ta fito da buhun kayanta. Uwatale na tsakar gida fa, tana ɓarin zance sai fi'ili data buɗe sabon shafi, wai ita ƴar abu ta.. "Ke zo Uwatale muje ki kaini gidanki. Ke kuma in ɗana yazo kice mishi yazo ya sameni a gidan Uwatale, na dai faɗa miki" To zan faɗa mishi." Iyakar kenan. Dafadukan shinkafa da kifi nayi, harna gama girkinnan hankalina baya tare dani sam, na rasa wanne irin tunani zanyi ni Hindu. Matan gida gulma suke ta faman yi, basu da laifi gaskiya. A haka dai nayi duk abinda na saba. Na saka ma yara abinci suna ci, ni kuma idar da sallah na Kennan inaso in kaima Nanno abincinta dana zuba. Sai gata ta shigo, in tayi sallama to banji ba, ina mai tabbatar muku banji bakinta ya motsa ba. Ai yanzu ma nake son in kai miki abincin sai gaki kuma" "Haka fa, to ai sai ki kawo mun inci, inanan har ya dawo." Abincin na ajjiye a gabanta, na kawo mata kwano da cokali. "Wannan turaren wutan mallakan daya turniƙe ko'ina, ɗaukeshi ki fita dashi. Ni bazan mallaku ba, na sha tabara, na sha yasin. Ɗana ma da kika mallake ina roƙon Allah ya kuɓutar dashi, a hannunki azzaluma" Ɗan murmushi nayi nace. To ameen, Allah ya kuɓutar dashi" Na ɗauki kaskon na fitar, na dawo na sameta tana magana akan kifin cikin abincin, da kuma yadda taji kayan miya. Ni dai gefe na koma na ɗauki Qur'ani na soma karatu. "Wannan abinci haka, ji kifi yadda aka ɓaɓɓareshi, ga kayan miya yaji yayi baja_baja, irin wannan almubazzaranci da yawa yake. Babu shakka ni inacan ƙauye, ku kunanan miji ya ƙare a kanki, dama danginki ko munasara" In kun tanka Hindu ma ta tanka. Ni da yarana muna ta karatunmu, nasu rabi da kwata wasa, kwata karatu, amman da zarrafe ake tashi. Uwatale ce tayo sallama tare da buɗe labule, daga wajen ta zuro langunanta biyu tuwo da miya. "Ki shigo mana tsoronta kike jine, ke da kike matar wan mijinta? ' " Hmmm ca tayi in na shigo saita ɓallani. Zata aika in Nawata ya dawo ma shigo tare ai. Ga tuwonnan" Ta saki labulen. Nanno ta ɗakko tuwon ta soma ci. Ina gani loma uku tayi ta rufe, taci gaba da cin shinkafar. Wajajen bayan isha sai ga Nawata ya shigo, ai Uwatale bata iya biyoshi ba, taji irin riƙon da naima kafaɗarta ai. Bayan sun gaisa, nima mun gaisa sama_sama. Saina ɗauki Asama'una data ɓingire tayi bacci. Azgar kuma gyangyaɗi yake ta yi. Azgar ɗin Ammi zo muje ka kwanta ko?" Tashi yayi ya biyo bayana na shinfiɗesu. Inaso zan siyama Azhar ƴar katifa da zai dinga kwanciya a kai gaskiya, ya ƙara girma yaci ace ba a gado yake kwana ba. Duk ranar da za'a zuba taki, sai dai mu kaisu falo mu shinfiɗesu. Ai gara ma in siya musu ƙananun katifa kawai in dinga musu shinkiɗar a falo. Shiru nayi da tunanin jin abinda Nawata yake cewa ƙasa_ ƙasa da murya. "To muma bamu san makaranta take zuwa ba wallahi nake faɗa miki. To da zanyi mai magana. Ita Hindunce tace ma Uwatale koyarwa take yi. Sai daga baya abun ya fito. Magawata baya kyautawa ya zama jani talau, sai yadda akayi dashi. Yanzu ya dace ace Hindu ta hana Uwatale shigowa kuma a gabanki fa ko ɗar bata ji. Shikenan zumunci take so ta raba mana, bazai yiwu ace Uwatale bata shigowa wajenta ba, ita ba shigo mana take yi ba dama. Yaronnan Azgar sam bai saba da su Zainaba ba sam." Zama nayi da kyau na shiga nazartar maganganun shi, ina jin yadda nanno ta sake buɗe ruwan faɗa tana mijinyawa zai zo ya sameta. Gaga gaga mijinyawa ba shi ya shigo ba sai sha ɗaya da mintina na dare. Bari kuji abinda ya faru, sai kawai ya shigo da ledar kayan shayi da biredinshi, gongonin madara ta pick ta gari fa, da furanto na leda, da sikari mai iyali mai zaki. Ga kuma kaza gashssshiya guda ƙatuwa, da abinda ya shigo kenan. Ku faɗamun wa zai fiddani ba sai Allah ba. Inajin sallamarshi sai na fito. Yana tsaye Nanno na ƙare mishi kallo, shima da mamaki yake kallonta, amman sai murmushi yake yi. "Ungo wannan ledar kai kicin Hindu" Yayi saurin miƙomun, kafin hannuna ya isa na Nanno ya isa, ta fisge. Ta buɗe taga wannan kayan da nima bansan daga ina bane. Tunda bawai siyowa yake yi ba, rayuwarma lallaɓawa muke yi, muna adana sirrinmu muna lulluɓe babunmu. Ni ban kasance mai roƙo, ko huda cikina ba. Shi kuma daidai ƙarfinshi yake yi, bazan iya haɗa karatuna da koyarwa ba, sabida yanayin lokaci, kuma munfi karatu da safe ma. "Babu shakka, madara ƙaton gongoni haka, ga kaza muƙeƙiya, shi kake kawo mata kullum, shi yasa kuka haɓaka ƙiba ji wani haske da Hindu tayi. Ni ina can ina sharɓar miyar kuka da wake. Kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi fa kenan." Ai sai ta zauna ta soma huci, shi kuma ya gurfana gabanta kanshi a ƙasa. Juyawa nayi zan koma ciki. "Dawo dan gidanku, ai kece musabbabin zuwan nawa munafuka." Zamana nayi daga dokin ƙofar mukai shiru. "Wato kai mai mata shine ka sakata a makaranta tana karatu, ni da ƴan uwanka kace mana koyarwa take yi, tunda haka ta kitsa maka kace k0? To alkadarinku ya karye, asirinki ya tonu, kun kuma ji kunya, sabida haka dole a ajjiye karatunnan, ko kuma ka sallameta ta kama gabanta. Inaji ina gani surukata bazan bari tayi zurfin karatu a boko ba. Ƴan bokon da basu san addini ba, mu karatun muhammadiyya muka sani, sai ilimantiri da akeyi da can, in yarinya tayi sakandare mace ma mu bata cika auruwa ba, kuma a ƙauye da kuka gurgura kukai karatun a lokacin da kuke yi wanne surutune banji ba. Madadin ace ta sake haihuwa, yaro Asbar ya girma ga Ɗan safiyo mai gida ƙani za'a kuma mishi biyu fa kenan, amman ita tana ɗaya, ga boko zai kuma kangarar da'ita, haihuwarma taƙishi. To wallahi bazan yadda ba ta gama zuwa makaranta, kai koyarwanma ban yarda ba, ba kuma za'ayi ba. Wannnan kenan. Batu na biyu shine. Sai batun wannan uban gida, da uban kayan alatu daka ma Hindu irin wannan. Yanzu irin wannan gidan ka kama kake biyan hayanshi daga kai, sai ita, da ɗa ƙwalli ɗaya wanda dashi da babu kusan ɗayane, to menene marabar? bata da yawa kake wani buɗe baki nafaɗa. Wallahi sai kun bar gidannan, sai kun barshi ni dai na faɗa muku makaranta kuma dole ta daina, ji irin kayan alatun da kake kawo mata fa" "Kiyi haƙuri Nanno. Wallahi wannan kayan da kika gani bani akayi, babu sisin kwabona a ciki. Sannan dan Allah kiyi haƙuri ki dena batun barin makaranta alƙawarine na ɗauka nake ƙoƙarin saukewa. Sharaɗine a kaina" Ai ina wuta tasa Mijinyawa, ta dinga surfa faɗa harfa da kukanta. Ta jima tana faɗannan, wallahi data gama faɗanta fes, sai ta mimmiƙe a saman kujera wai anan tare damu zata kwana. Mijinyawa ya kalleni nima shi nake kallo kawai babu baki sai idanu. Yafitoni yayi muka fita waje. "Yanzu ya zamu yi ko in je in nemi wajen kwana in bar muku nan ɗin?" Hmm aa ka shiga kayi kwanciyarka da yara a ciki, ni zan kwanta a falon, dare yayi, ai gara ka shiga, ga gajiya ka kwaso. Amman fa zanje makaranta kasan jarabawa nake yi, kuma zan iya juran komai banda batun daƙile karatuna, ko aikina wallahi kaji na faɗa da manyan baƙi" Ina faɗin haka nayi shigowata, ciki na shiga na ɗakko fulo da bargo na shinfiɗa, Asama'una na ɗakko, na shinfiɗe a gefena shi da Azgar kuma suka kwanta a ciki. Munsharin Nanno bai barni na runtsaba, da nayi karatu sai na dinga nafila kawai sai wajajen daf asuba na kwanta. Safiya nayi na haɗa duk wani abun kari na ajjiye a falo, Nanno na zaune tana kallona. Na shirya ƴan makaranta. Ni dai ficewata nayi na barsu ita da ɗanta nayi shigewata makaranta. Nasan dai cinyeshi ne kawai ba zata yi ba. Me akayi, ya suka ƙare? Ban sani ba sam. Ku tambayeni mai ya faru to bayan dawowata. Ina dawowa na shiga gida da sallamata, sai naci karo da bokitina na wanka a fashe, a kuma yashe a tsakar gida. "Hala baki san kun tashi a gidan bane ko Maman Asama'u? Ai kun koma gidansu Maman Zainab tun safe" Cewar Maman Zailani ƙawar uwar gulma. Sai naji abun yana jujjuyamun a kaina, mun koma gidansu Uwatale, sabida me, me yasa to? Bani da amsar wannan tambayar, saida na shiga na tabbatar da zancanta kafin na juya, su Azgar na biye dani. Ina fita naci karo da Mijinyawa idanunshi sun kaɗa sunyi jawur kuma tabbas yayi kuka, ganin irin matsanancin tashin hankalin da yake ciki, sai na sake fuskata sawai, sabida ya samu sanyi, salama daga gareni, duk da ni ɗin bai sanyayashin, nima fa a cikin zafi da zugi nake. Barka yallaɓai daga ina, yau babu aikinne? " Sai ya ɗan murmusa. "Yaushe zanje aiki Hindu, ai tun fitarki ake ɗauki babu daɗi. Harma dai yanzu mun koma gidan Nawata bisa umarnin ko in koma ko Nanno ta ɗaga mun nono. Kuma sharaɗine ta bani akan ko mu rabu, ko ki dena makaranta, ko kuma mu koma gidan Nawata. Shine na zaɓi komawa can ɗin. Nasan zaman gidan ƙuncine, takurane a garemu bai ɗaya. Amman me? Allah yana ji, Hindu yana ganin komai" Ba zamu ga haka ba. Allah yasa haka shine mafi alkhairi. Amman wallahi bazan ajjiye karatuna ba, kuma zanyi aiki inata jaddadawa" "Har yanzu roƙon da nake ta faman yima Nanno kenan. Amman wallahi ta kafe a wannan karon tace babu gudu babu ja da baya. Amman ina kan lallaɓata kafin ta koma dan jimawa tace zata yi. Kinsan mun fa gama magana ta ban sharaɗi. Tana komawa gidan Nawata, sai kawai tace ita bata yarda da wannan sharaɗin ba, kawai karatun take so a ajjiye. Mujenku yaran Abba" Ya kama hannun su Azgar ina gaba suna bani kariya. Kunsan menene? Bana wani iya kallon gabana, ƙafata nake jefawa kawai, kana ko wacce adda'a na tuna yinta nake yi kawai har muka isa ƙofar gidan. "Hindu" Juyowa nayi na dubeshi, sai muka yi murmushi kawai, ya haɗiye abunda zaice, ni kuma bance mishi me yake son cewa ba. Babu abunda nake buƙata face in yi sallah in kwanta kaina tsagewa yake shirin yi. Ga karatun jarabawa dake jirana. Da sallama na shiga gidan fuskata sawai sawai tamkar ba'a gumamun ba. Nanno na tsakar gida tana tankaɗema Uwatale garin tuwo, ita kuma mandiyar wanke_wanke take yi. Gidan kaca_kaca da tsummokarai, da tarkace kona menene oho. "Ahh kin dawo ashe, kinje can gidanku na da kika tarar kun dawo nan ko?" Eh naje, kai nayi murna sosai gidan haya ai sai dole, kinga nan ko hankalinmu kwance, mutum bashi da fargabar notis, ko na kuɗin haya. Sannu Nanno da aiki" Uwatale sai tayi turus, ba haka taso ba, so tayi in nuna ɓacin raina, ko inyi faɗa ita dai ta kai Hindu ƙasa, batasan ba wajen bane. Nanno dai bata tanka mun ba, ina tsaye mijinyawa ya shigo ya buɗe mun ɗakina na shiga da ƙafar dama bakina da adda'a ta neman tsari. Ɗakin na ƙarema kallo, kayan kujeruna duk sun zauna, sai dai babu filin tsakar ɗaki baifi mutum uku suyi sallah ba, iyakar filin kenan. Uwarɗakina na wuce kayan kicin ɗina suna zazzaune da ƙafafunsu, gadonma ba'a ko kafa ba. Ga sib mai ƙofa shida suturu duk a gefe dai. Inaso in yi alwala, kuma kamar ba ruwa ko?" Na dubi mijinyawa dake ta wasa da yara. "Akwai a bokiti a falo dana ɗebo kaɗanne" A bawo nayi alwalata na kabbara sallah, na daɗe sosai goshina a ƙasa. Wallahi kafinma in sallame Ubangijina maji roƙon bayinshi, ya yayemun duk wani damuwa, da ƙuncin zuchiya. Da ƙarfina na shiga aikace_aikacena. Mijinyawa kam kafin in idar Nanno ta doka mai kira ya fita a guje. Inaji tana farfaɗamai magana. Haka naita aikinnan kayan Kicin wasu a ƙarƙashin gado, ragowar duk na ɗura a sib ƙofa biyu cike da kayan kicin ɗina, sai kurfo ɗina na ajjiyeshi a gefe can wajen sib. Saida na share ko'ina dako ina, kana na fito da wannan bawo na zubar da ruwan alwalar a magudana. Ba kowa a tsakar gidan, ga abinci dai a murhu garin tuwo kaca _kaca a kan duwatsun murhun, dama bakin tukunyar. Ƙaramar randata na buɗe sai naga cike take tab da ruwa. Ciki na koma na ɗakko bokiti ina zuba ruwa Zainab ta fito. Ke inane bayan gidanku? Ta nuna mun da yatsa. Toka da omo na ɗauka na shiga banɗakin, a wanke dai yake babu laifi, sai zarni da ƙarni da yake yi. Zagewa nayi na wanke tas, na ɗebi ruwa nayi wanka tare da alwala. Na fito kenan Uwatale itama ta fito daga bayin ba haya, dake a rabe suke. "Ashe kece kike ta wanke banɗaki, ai a wanke yake tas Nawata yasa na wanke sabida ku" Funfurunfus nayi mata, nayi shigewata ɗaki, lokacin magriba ma tayi, ga wuta ma an kawo. Risho na kunna na rura gawayi na kunna turaren wuta. Ban ko shafa mai ba, na nemi rigar yadi mai sauƙi kwatin na saka, tare da gabatar da sallah. Ina ƙoƙarin rufe taga dake a layi tagar take ba irin ta cikin gida bane, tagar falo ne take cikin tsakar gidan. Mijinyawa na gani a wajen tagar da ledojin cefanenshi. "Yauwa inata adda'ar Allah yasa baki rufe tagarnan ba. Ungo kayan cefanennan ga kalanzir a gora ma na siyo, ɗan abinda ya samu ki girka zanje in taɓa aikin dare ni saina dawo kawai" Karɓa nayi, tare da mai adda'a. Ina tsaye a jikin tagar ina kallonshi yana tafe a tsanake. Rufewa nayi kawai na shiga aiki. Shinkafa da wake na ɗaura, bana jin zan iya jajjage kaina ciwo yake yi sosai. A uwar ɗakina na kunna rushona dan wannan datti bazan iya dashi ba, ko babu datti bazan iya girki a tsakar wannan gidan ba, uwatale na leƙamun tukunya, tana kallon abunda zata tattara ta kai rahoto ba. Sai bayan isha na kammala girkina, na toya mai. Saida na zuba ma yara nasu, kana na ɗauki kwanon dana zuba ma Nanno na fita. Suna tsakar gida, sai tuwo suke ci, a faranti ɗaya dukkansu suke cin abincin harda Nanno. Kwanan na ajjiye. Ga abinci Nanno" Bata ko kalleni ba, dama na ayyana hakan tabbas. Shigewata ciki nayi, na samu Asama'u taƙi cin abinci. Zo uwata mu ci tare to" Sai ta soma murna, tare muka ci abincin inayi ina ɗan karatuna. Yara sun yi bacci wajajen takwas da kaɗan bayan sun gama aikin da aka basu na makatanta. Ni kuma karatu nake ta faman ci, har zuwa wannan lokacin ina jiyo hirarsu Nanno a tsakar gida, harma da Nawata duk ina jiyosu, dan sosai suke ɗaga murya harma na saba nikam. Sai wajen sha biyu saura naji an ƙwanƙwasa mun taga, da sauri na isa wajen. Waye" "Mijinyawa ne" Da sauri na buɗe. Leda ya miƙo mun, baice uffan ba ya zagayo zuwa ciki. Ai kuwa Nanno na jiranshi, ashe a tsakar gidan ta soma bacci ita dai sai taga shigowarshi taga mai ya tawo dashi. Falo na dawo na zauna. Ina jiyo bambaminta amman bana gane abunda take cewa. Da ƙyar ya yakice ya shigo, idonshi kawai na kalla nasan ya galabaita gaya. Tarbanshi nayi da ledar hannunshi na zaunar dashi, tare da yi mai hidima. Naso ya soma wanka, amman yace mun rabonshi da abinci tun karin safe, yako ci abinci sosai na zuba mishi tsiren daya kawo akan abincinshi, nawa na bari sai da safe sai muci da yara. Na tambayeshi shin ya ba nanno nata tsiren.? "Kaza ma na sai mata rabi, wannan tsiren nasan inta gani duka zata haɗa shiyasa. Muita haƙuri har Allah yasa a rabu lafiya. Nace dashi. Watarana ai sai labari. Wanka yaje yayo, mun jima sosai muna tattaunawa kana mukai baccinmu. Washegari ma sassafe nayi ficewata, na barshi akan ya kullemun ƙofata in zai fita, na ɗauki sifiya ki. Ai ina fitowa Nanno ta riƙeni carab wai babu inda zani harda kukanta. Aka buga, aka buga, aka kaɗa, aka raya taƙi, ga lokaci na ta tafiya, kuma jarabawa garemu. A ranar da ni mai kukace, da kuka zanci wallahi harda birgima, amman dake ba mai kukan bace, sai ido kawai. Uwatalece ta saka baki ta dinga lallaɓa Nanno, kana ta sakeni, na ja hannun yara muka fita ko tari ban ba. Har naje makaranta na dawo, inata tubkewa da warwarewa. Wai shikenan ni Hindu babu wani ƙwanciyar hankali da zan iya samu ko da na ɗan ƙanƙanin lokaci ne daga dangin mijinyawa? To yaushe wannan ƙoyayyar zata zo ƙarshene? Yaushe zasu gane Hindu bata nufin kowa da sharri? Wata zuchiyar tace. Muddin Uwatale, da Jamila, suna raye. kuma suna amsa sunan dangin mijinki, to tabbas babu ranar da zaki samu sauƙi. Amman mijinki yana sonki, kuma yana kyautata miki, yana miki adalci tsakaninki da danginshi. Kuma in kikai la'akari shi kowa ya juya mishi baya, amman ke duk rintsi danginki suna tare dake. Soyayyarku abar sha'awace, da abar kwatance. Zamun miji mai irin nagartar mijinyawa sai an tona, kamar yadda samun mace mai irin, haƙuri, da nagartarki sai an tona. Ajjiyar zuchiya na sauke, tare da lumshe idanuna da nake jinsu tamkar zasu tsaye tsabar rashin ruwa a cikinsu. Zama nayi a bakin gado ina jin hayaniyar matan unguwa, su Maman Zailani da suka mayar da gidan tamkar yadda uwatale take yi a lokacin da nake can. Adashe ma Uwatale ta kafa musu kamar yadda Shafa take uwar Adashe a ƙauye. Wannan adashe shi yai silar da yasa kullum mata cike da tsakar gida, acan jama'are, aita gulma ana faɗa. To irinshine Uwatale ta biyomu dashi kuma. Wannan ja'iba da mai tayi kama. Hayaniyarsu ta hana ƙwaƙwalwata hutawa sam. Turmi na ja zuwa falo, da wuƙa. Kafin in zauna zaman jajjage na ɗaura tafashen namana. Daga zaune na jajjage kayan miyana tsab. Saida na tsayar da sanwa, kana na fita tsakar gida na ɗauro alwala. Su Maman Zailani na mun sannu nayi kamar banji ba, sabida ina gani akan idona Maman Zailani na ma sauran matan zunɗena kafin ta gaisheni. Na gani, na kuma ji, sai na mayar da ganin nawa, da jin tamkar ma banji ba. Har saida na zo zan koma ɗakine Uwatale tace. "Hindu ƙawayena suna ta gaisheki baki ji ba" Na dubesu na watsar tare da cewa. Ayya" Nayi shigewata ciki. Sai gidan duk ya ɗauki shiru ji kake ƙus_ƙus. Duk wannan abun fa Nanno tana cikin gidan, tana falon Uwatale a zaune labule a rataye a ƙofa, koni da zan wuce na ganta yi nayi tamkar ban ganta ba. Bayan nayi sallah, na tsaida sanwar shinkafa ga magriba ta gabato, ni da yara mukai wanka fes, na sauya musu kaya. Ai ina fitowa ɗiban ruwa a randa sai naga Uwatale na ma yaranta itama wanka. Su kansu abun ya ɗaure musu kai, sai Zainab cewa take yi. "Mama mai yasa kike mana wanka da daddare yau? " Uwatale sai rufe ma yarinyar baki take yi, ni dai na ɗebi ruwana nayi shigewata. Da daddare da mijinyawa ya dawo, nanno ta kuma riƙeshi sai kusan sha biyun dare ta sakeshi ya shigo, anata artabu akan lallai ita tana kan bakarta saina dena karatu, shi Kuma mijinyawa sai haƙuri yake bata, yana ta kwatanta mata abubuwa. "Nonno ke fa kika ce tunda zata ci gaba da karatu sharaɗine mu dawo gidannan, to mun dawo kuma naga kinci gaba da batun Hindu ta ajjiye karatu, kefa kika ce ko mu dawo gidannan, ko Hindu ta ajjiye karatu, ko mu rabu. Na zaɓi mu zauna anan ɗin, kuma kika ce dokace baki yadda mu raba gida da Nawata ba, mu zauna a gida ɗaya duk runtsi, shima nace na yarda. Nanno me yasa abubuwa in akaina da Hindu ne kika fi zafafawa? Hindu fa bata ƙinki, bata ƙin kab dangina, me yasa kowa yake ƙinta ne. Da kince rashin haihuwane, an haihu tsugunne bata ƙare ba. Nawata kace wani abu, wallahi kaina ji nake kamar zai fashe, inaga ma mutuwa zanyi" Nawata yace. "Hakane duk abinda yace. Kuma nima inata baki haƙuri ki barta tayi karatunta Nanno. Kuma sharaɗi kika bashi na abu uku ya zaɓi ɗaya. Kuma ya zaɓa dan Allah ki bar maganarnan hakanan." Sai shiru ya ratsa tsakar gidan kafin tace. "Shikenan na bari, kar ka mutu, amman ba dan ina so ba wallahi. Da kake cewa da nace haihuwa ne yanzu an haihu. Ai har yanzu Hindu fa bata da maraba da juya in faɗa maka. Kaga matan arziki nan, yanzu haka da kake ganinta cikine a jikinta, Ɗan safiyo ƙani na biyu kenan za'a haifa mishi. Kake wani batun haihuwa. Yaro ɗaya rak ya girma baki raɗau har ya shiga makaranta, amman ko halamun ciki tattare da Hindu babu. Wannan baƙaƙen makaran nata zasu bari ne ta tara yara" Ni da nake jiyosu illahirin kunya sai da naji tamkar in nitse, ace uwace ke faɗama yaranta maza irin wannan magana mai nauyi da kunya, ita ko a jikinta. "To naga sabida munafurci a uwarɗaki fa Hindu take girkinta. To ban yarda ba, ta fito ta kafa dutse a tsakar gida kamar yarda matar mai gidan ta kafa nata. Ban yarda ba, ban lamunci aiki da kalanzir ba, dole da itace zata yi aiki wallahi ban amince ba. Ko data kawo mun abincinta sau biyu, Uwatale ce gata taci, da ƴan jikokina. Ni bana cin abincin risho ance cuta yake sakawa. To bazai yiwu ta kashemun jikana da ɗana ba, kaji na faɗa maka" Idanu na kuma lumshewa, na miƙe na koma uwarɗaki na gaji dajin wannan maganganun. Da ƙyar aka sallameshi ya taso ya shigo. Yana cin abinci yana son mun bayani, na katseshi. Naji komai, kar ka damu zan dinga yi a tsakar gidan, amman ba'a itace ba, a gawayi. Duk na ɗauka zamu mata biyayya. Abu ɗayane shine zanci gaba da karatu, kuma zanyi aiki wannan kam babu abunda zai canjashi sau ƙudurar Allah." Ajjiyar zuchiya kawai ya sauke, yayi magana ma ya kasa sam. Gobe su Innarmu zasu zo, tare dasu Yaya su ga waje, tunda babu aiki asabar ne." Ai sai ya ƙware harda tari. Da sauri na tsiyaya mishi ruwa ya sha. "To fa gashi Nanno tananan, Ubangiji Allah yasa a rabu lafiya. Nasan abune ma mai matuƙar wahala a wanye lafiya" Haka dai mukaita jimantama juna. Da Allah ya taimakemu, mun wayi garin asabar sassafe sai bugun ƙofa. Ina buɗewa naga Nanno da shirinta tsab harda buhunta. Ta kalleni ta harareni yarda take so, taƙi ma amsa gaisuwata. "Maza je ki kirawomun wannan maras kunyan, ya ƙule ɗaki da safennen bazai fito ya fice ba, ɗan uwanshi tuni ya fice. Shi yana ciki kina mai Zizizi da zazaza" Ni dai komawa nayi na tasheshi, da ƙyar ya buɗe idanunshi da suka rune sabida tsantsar gajiya. Nanno na nemanka, kamar ma tafiya zata yi" Jawoni yayi na faɗa mishi. "Ba shakka, tabbatattu" Cewar Nanno data ɗage mana labule yana hannunta. Da sauri na sakeshi kaina a ƙasa. Shi kuma ya miƙe da sauri ya bita. Ashe tafiya tayi. Ni kuma suna tafiya na fito da teburina dake ɗakin shirgina na jama'are, da mijinyawa ya tawo mun dashi. Na fito dashi waje, gefen randunana na ajjiye. Akai na ajjiye kurfona mai rami biyu, na saka gawayi na kunna, kana na shige ciki. Na dawo da tukunyane, Uwatale ta fito da tuwonta tana yankawa. Ban kalleta ba, bata kalleni ba sam, ni daɗi hakan yayimun. Yau da iskanci ta tashi, cika take tana babbatsewa. Shayi da ƙwai na soya nayi shigewata bayan na ɗaura ruwan shinkafa. Ƴar lisuwa kamar zata halaka Uwatale. Wajajen goman safe Mijinyawa ya aiko yaro da kayan miya da kifi jela huɗu manya. Na soya su, nayi miya gidan ya kaure da ƙamshi Uwatale ta rasa sukuni sai zurga_zurga take yi haka ma yaranta. Ni dai na gama komai na, har wanka da sa turaren wuta, da wanke kayan kwanuka dana ɓata. Su Innarmu sai bayan Azahar suka samu shigowa. Sunga waje dai, innarmu da ma ƴan uwana sake ƙarfafani suka yi, Innarmu harda tsaraba cikin bako. Uwatale kam, ai tun kafin su Innarmu su zo ta zari mayafinta suka fice ita da yara yawon barbaɗa. To yawon barbaɗa mana, wa take dashi a ƙwaryar kano da kewayenta? Gaga_gaga_gaga_gaga. Abubuwa da yawa sukaita cukumurɗawa, makirci, munafurci, ƙarya, sharri. Yau kwatsam na fito zanje gidan abokin Baba Sojanmu shima janaral ne, inama yaranshi karatun boko a gida, ranakun asabar da lahadi. Baba Sojanmu yaje gidanne yaji suna neman malamin turanci, da lissafi, shine yace zan iya. Duk ran asabar da lahadi nake zuwa, wata a bani ƴan canjin da yake mugun sauƙaƙe mana rayuwa. Na shirya tsab zan fita, harna kulle ƙofata na jiyo ihu da nishin Uwatale a ɗakinta. "Hindu! Ki taimakamun naƙuda nake yi haihuwa zanyi, wayyo Hindu zan mutu ki taimakamun na tuba" Na jiyo Uwatale sai maimaicin sunana take yi, haihuwa tazo. Mrs BukhariMRS BUKHARI Mun jima sosai a haka kafin yayi shiru. "Me yasa kike ta wahalar da kanki a kaina ne?" Ba wahala bace, ai duk abinda zanyi na alkhairi ma wani, ko wata zan samu lada mai yawan gaske. Ballantana abinda zan yi maka kai da kake uban ƴaƴana. Babu asara a yin alkhairi, ko da kai akasin hakan aka baka. Baya nufin naka alkhairin ya zube, yananan yadda yake a wajen Allah" "Uban ƴaƴanki? " Sai yayi murmushi ya sauke kanshi kawai. A wannan daren, mun tattauna abubuwa masu yawan gaske, da ƙyar ma bacci ɓarawo ya sacemu. Daren ya kasance mana wani irin dare mai cike da gurika, gami da yaƙini akan Allah zai shiga cikin lamarin karatun mijinyawa ya taɓa. Da safe dai na ɗumama mana wannan masa, da naman kan saniya, sai shayi mai kayan ƙamshi dana dafa, Iya Halima kawai, sikarin ta ashirin ce aka siyo. Mu kuma ruwa muka sha abunmu, sai mijinyawa dana ɗan tsiyayama shayin. "To ni kam mijinyawa zan tafi, naga Hindu ta kintsa zata tafi aiki, ga yara duk sun shirya suma. Am Magawata nace in Asama'u suka samu hutu, inaso in zo in ɗauketa, ina wannan barar" "Aa Halima ai basa samun hutun da har zata yi wata tafiya, kana suna karatun Islamiyya sosai, yarannan basu da wani hutun da har zaki ɗauki Asama'u. Kuma in taje Azgar irin shaƙuwar dake tsakaninsu, bazai ji daɗi ba. Kamar dai yadda aka saba kya dinga zuwa ganinta" Murmushi tayi mai fassara, ni naso ma ya amince kar Halima taga kamar an tauyeta. "Ka duba dai dan Allah" "To zan duba zuwa lokacin da kika yi Aure. Kinsan ai bazan baki yarinya bakya gidan iyayenki ba, bakya gidan mijinki ba. Wannan ganganci kenan Halima" Ai kamar an sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi sai ta miƙe. "To inason ganinka a waje kafin in tafi, akan batun aurenne. Hindu ni zan tafi" Ki gaida gida Halima" Mijinyawa yaso ƙin zuwa, ni nace mai yaje yaji koma menene. Nayi mai ishara da idanuna. Saida ya gallamun harara kana ya fice. Zancan na aurenne dai, dan rai a ɓace ya shigo yana ta faɗa. Ni ko sai dariya nake yi mishi. Gaga_gaga_gaga Haka akaita bugawa, rayuwa taci gaba da tafiya. Har Allah ya kawomu ranar da mijinyawa ya zauna a ajin jama'a ranar farko. Ya samu bizines admistireshon, na mance ban faɗa muku fannin da yake ba. Nan aka soma buga karatu. Ranar farko haka ya dawo daga makaranta idanunshi jawur. Na tambayeshi ya karatu. "Karatu ko wahala, kinji wani turanci wai da malaminnan yake mana, itama wata mace da bata wuceki ba, baki ji turanci ba. Ni bana ma gane komai" Mijinyawa hoo wato yanzu turancin yafi karatun wahala kenan?" Idanunshi ya zare. "Ina gara ma turancin ina ɗan gane ƙanana, amman karatun, bama zan iya ce miki dame_dame akayi ba. Ɗan ƙarfin guiwar dana samu ma ɗayane. Bani kaɗaine babba a ajin ba, akwai kamata, harma da wani magidanci wanda gaskiya babbane" Dariya na fashe dashi, shi kuma sai hararata yake yi. Kace da sauƙi tunda kaga wanda ya fika. Jami'ace fa, ai sai kaga tsoho ma" "Woo ba zaki gane bane Hindu, su sun iya turanci fa. Harma gabatar da kanshi wani yayi a gaban duka ajin. Ke kinji turanci? Wallahi yayi masifar burgeni. Ƙiris yarage in yi tafi fa" Dariyace taci ƙarfina. Ai sai ya ɗauki jakarshi ya shige ciki, a guje na bishi ina ci gaba da dariyata. "Haka fa Qasimu yake mun. Duk bala'in da zan shiga, wallahi duk masifa sai yayi dariya" Ni naita ƙarfafashi ina nusar dashi. Nan muka shiga yin lesin, darasi sosai muke yi, zan iya cewa kusan tare muke karatun, wani digirin nima nake haɗawa kuma hakan ya taimakeni gaya. Ƴan gidanmu babu mahalukin da bai yi mamakin komawarshi makaranta ba. Haka danginshi da abun ya iskesu, Yaya Jamila ce tazo tai ta zazzaga, Nanno dai wai tana ƙauye zazzaɓi ya lulluɓeta, tana ta kuka wai za'a kafurta mata ɗa. Saida yaje ƙauyen Kawu ya shawo kan lamarin. Uwatale kuwa irin ruɗun data shiga yana da girma, wallahi bazai rubutu ba. Zazzaɓine ya bigeta, jikinta yaita rawa kakakar_kakakar. Ranar asabar na ƙarshen satin Mijinyawa na farko a makaranta. Da yamma muna zaune muka jiyo sallamar Baba Sojanmu da Innarmu, sun zo ta ya mijinyawa murna. Rungumeshi Baba Sojanmu yayi, yana ta bubbuga bayanshi. Ni dai farin ciki tamkar ya halakani wallahi. Yau ga Baba Sojanmu rungume da mijinyawa suna cikin aminci. Fita damu Baba Soja yayi, zuwa wani gidan cin abinci. Yayi mana odar abinci, muna ci yana ƙarama mijinyawa bayani akan amfanin ilimi, da ribar auren mace mai ilimi. Yace dashi da ba dan ya auri mace mai ilimi ba, ba lallai ne yayi tunanin inganta rayuwarshi ba, babu lallai yayi tunanin komawa karatu. Baba Sojanmu harda kyauta ya kawo mai na agogo, da turare. Gaga_gaga_gaga Nike riƙe da komai kamar yadda nayi alƙawari, da daɗi babu daɗi dai haka aketa gurgurawa, kamar yadda na alƙarwanta. Wataran naje aiki a ƙafa, shima mijinyawa yaje makaranta a ƙafa, haka dai. Ganin wahalar da muke sha, da irin dariyar da Uwatale ke yi da habaici, shi ya tura mijinyawa ya dage akan karatun haiƙa. Nawata ma cewa yayi asarar kuɗi da lokaci. Wannan kalmar ta dakeni sosai. Shigarsu mataki na biyu ke da wuya na samu aiki a wani gidan rediyo buri ya cika. Albashin dai babu yawa, amman yafi na koyarwa. Watana shida da wannan gidan Rediyon Baba Sojanmu ya sama mana wani gidan rediyon ni da Luba. Sai abubuwa suka soma mun sauƙi, suna warwarewa a hankali. Rayuwa kenan shirin Allah. Sabira ta girma, ga surutu sai ta shiga Islamiyya da wuri, da'ita su Azgar ke tafiya su ajjiyeta gidan Yaya. Rayuwa tai ta haske, wahala tana raguwa. Allah cikin ikonshi da Amincewarshi har mijinyawa ya kammala karatunshi, munci kwakws tabbas. Sai yawon neman kuma aiki, ga yara sun girma suna taimakona sosai, musamman Azgar dake da karanbanin son girki, a hankali a hankali ya dinga koya, yana maida hankali. To kwatsam sai ciwon makarai suka dawo sabo ta yarda har saida na rasa aikina. Ciwo magashiyyan nake yi. A lokacin na sake sanin daɗin ƴaƴa, mijinyawa ya samu wata makaranta yana ɗan riƙon aji, dole zai fita sabida ni bani da aiki, yaranne zasu yi mun komai Sabira na biye dasu, shi kuma in ya dawo daga koyarwa, zai mana wanki, da abincin dare. Inajin daɗin irin haɗin kansu, da irin yadda suke son junansu a kusa. Ina ba matan da basu taɓa haihuwa ba shawarar, ko ƴaƴan ƴan uwa, ta roƙa a bata ƙarami sosai. Ko ta sanarma danginta da mijinta, ta ɗakko a gidan marayu da yardarsu, bance dole sai kinyi irin na Hindu, dama ire _iren mata irina da suka zaɓi ɓoyewa ba. Irinmu sunanan suna rayuwa a cikinku, ba tare da kunsan ƴaƴansu daga gidan marayu suka ɗakko ba. Ƴaƴa rahamane sosai, kar ki zauna kita tunani, ki kashe rayuwarki akan abinda Allah kaɗai ke yi. Ɗakko riƙo ki riƙe da zuchiya ɗaya. Ina mai ba ki shawara in zaki ɗakko ki ɗakko namiji, kada ki sake ki karɓi mace, ni dai na faɗa miki ne bes ob esfiriyans. Haka dai nayi kusan wata huɗu yau lafiya, gobe ciwo. Ko kuma dare nayi ba bacci, gari na wayewa kamar bani ba. Duk na kumbura na fita hayyacina, hankalin su Baba Sojanmu da mijinyawa duk a kaina. Bamu nan, bamu can gidajen magani. Gaga_gaga_gaga Rayuwa ta shura, mijinyawa ya samu aiki a bankin farko, ta dalilin wani abokin Baba Sojanmu. Ni kuma Baba Sojanmu, ya sake nema mun aiki a gidan rediyo Kano tare da Luba. Wannan samuwar aikin shine warwarewar komai na rayuwarmu, silar shiga sabuwar matsala. Haka fa Ubangiji yake ikonshi. Da sannu, muna ta samun ƙarin albashi, da sannu munata adashe, da sannu rayuwa nata shurawa. Mijinyawa yana siyo komai na hatsi ya ajjiye, cefanen kayan miya, kifi nama yawanci nafi yi ni. Sai in abu ya ƙare ni zan yi saurin siyowa. Ya sauyamun komai na ɗakina a wani adashe daya soma yi, tare da abokan aikinshi. Yasan nawane tarina, nasan nawane tarinshi. Zan iya cire kuɗi a asusunshi, in yi abinda zanyi. Bai taɓa jin menene dalili ba. Haka zalika nima, haka zai cire kuɗi, me yayi, mai zai yi? Bana tambaya. Mun yarda da juna, mun gamsu da juna, sam_sam bana tunanin akwai abinda a duniya zai sauyamun mijinyawa ba. Amman sai dai kash, kaico. Mijinyawa Shine siyan man injin babba daya siya, kowa na gidan in an kunna yana amfana, sabida yace Nawata shima yayi nashi ƙoƙarin, na bamu wajen zama, ruwan famfo, wutar lantarki. To a wannan gaɓar da muke zuwa aiki dukkanmu ne, Uwatale mutuniyarku, naga masoya gareta ko? wata dai tace tana hangota a mai sakakken baki. Ta samu aikin asibiti a wani asibiti mai zaman kanshi a matsayin. Ward atendans, masu tura gadajen marasa lafiya, masu kai gwajin jini lab, masu shinfiɗa zanin gado, duk dai sune ward atendans ɗin. Wannan shine aikin uwatale a wani katafaren asibiti mai zaman kanshi, wanda an ɗauketane sanadin shi Nawata yasan mijin mai Asibitin, asibitin na mace ne, kuma itama Uwatalen ya kaita gidan matar, sai aka bata aikin sabida sanayya, tunda aikine wanda ba dole sai da kwalin karatu ba akeyi. Kuma suma suna yin tsarin karɓi in karɓa wannan yasa take aikin dare. Tunda muna fita aiki, tofa itama shine dole sai tayi. Dakta ma wani sa'in Nawata ke kiranta in iskancinshi ya motsa. Dan mugun bugun ƙirji yake yi da wannan aiki. Uwatale kab unguwa ƙarya take musu a matsayin wani aikin take yi babba, ba irin wanda ake tunani ba. Tana sa fararen kaya, da guntun hijab irinna sistas ɗin asibiti, tamkar nos haka zaku ɗauka, in kuka ganta. Hatta su Nanno tunaninsu kawai uwatale malamar jinyace. Wannan kenan, yau dai kunji hankalinku ya kwanta dai ko? Hahahhh... To tun kafin al'amura su gama warwaremun da kyau, na ɗan soma yin gajerun bidiyoyi na ba mata shawarwari, akan yadda zasu inganta rayuwarsu, da yadda zata kula da kanta ma ita macen. Sabida a aikina da nayi na gidan jarida, ai ina zuwa hotu ɗakko rahoto, na ƙara sanin Allah da girma yake, na ƙara sanin mata na buƙatar mai taimaka musu ko da shawarane. Da haka na soma, ina ɗan watsawa shafukan sadarwa, sannan akwai wani shiri na zamantakewa dana yi riƙon ƙwaryarshi, shima yayi mun ido, ta yadda nafi tattauna matsalolin mata akan abubuwa biyar da suka fi dakushe ma da yawan mata rayuwa. ( zaku ji a gaba) Wani bidiyo da muka yi da mijinyawa shima ya tofa albarkacin bakinshi, wannan bidiyo ya taɓa zukata. Akan wata ce da mijin ya maidata kamar injin ɗin buga kuɗinshi. Haɗata yake yi da maza manyan masu muƙami, taje ta kwanta dasu, a bata kuɗin sai ta kawo mai. Data gaji sai ta neme ni ta kirani a waya ta labartamun. A dalilin wannan kes ɗinne, muka yi bidiyo muna masu jan hankalin iyaye akan mahimmancin bama yara ilimi, da mahimmancin jan yara a jiki su shaƙu da ku. Dan wannan harda ƙarancin ilimin addini, da rashin sanin madafar rayuwa. Wannan bidiyo shine mabuɗi, ko ince matattakalar dana tattaka na shiga lamarin mata sosai. Wasu shawara kawai suke so, wata rarrashinta kawai take so in yi. Wata so take kawai ta bani labarinta inji, dan ko na bata shawara ba ɗauka zata yi, labarin kawai take so ta bayar. Mun yi bidiyo biyu uku da mijinyawa. To bidiyo har jama'are aka kaima Nanno ta gani. Da muka je zo kuga rikici da cin kashin da Nanno tayi mun, abun ba'a cewa dai komai. Saina dawo bidiyona ni kaɗai. Bidiyonma sai na daina sai ɗan rubutu dai haka. Da haka na dinga tara mata ina sakasu a zaurena dana buɗe. Wannan shine tarihin aikina na agajin mata da nake yi. BAYAN SHEKARU..:.. Tsaye nake a gaban madubina ina shafe jikina da man kamfanin Oriplame na madara da zuma. Cikin sauri na zura doguwar rigata Abaya ja mai taushin yadi. Baƙin agogon fata na ɗaura, na saka takalmina baƙi, jakatama haka. Ɗakin na kalla komai na zaune a muhallinshi sai ƙamshi ɗakin ke zubawa. Ga zanin gadona mai tsada, irin mai santsinnan, a wajen Anty Zee na siya tana shigo dasu daga Saudiyya, china, dama sauran ƙasashen. Asama'uce ta shigo da sallamarta. Anata rawar kai yau za'a soma jami'a ko? To Ubangiji Allah ya dafa. Asama'u kinsan ke macece dole ki ƙara kula da tarbiyyar dana baki. Jiya nasan mun daɗe daku, ina muku nasiha ke da Yayanki. Asama'u ki riƙe kanki, ki dinga tuna in mu bama tare dake, babu idonmu Allah daya haliccemu yana ganinki. Ki riƙe mutumcinki, ki tsare matantakarki, shine darajarki, in kika rasa baki da wata daraja, a idon duk mai daraja. Allah yayi muku albarka, duk wata nasiha ai nayi muku" "Ammi in sha Allah bazan baki kunya ba. Kinga kyan da rigarnan da kika siya mun tayi mun. Ammi takalmin ma da kika siya mun ɗinnan? Shi na ciro zansa. Komai dai sabo zansa. Azgar ma naga kayan da Abba ya siya mishi ya saka." Mijinyawane ya turo ƙofar. "Kunanan anata nasiharne, Tutar so sai kace yarannan wata ƙasar zasu je karatunnan?" Saye yake da baƙar sut, sai rigarshi ƴar cikin fara sol, da takalminshi sau ciki irinna ma'aikatan banki, da kwallinshi a idanunshi, amman shima kwallin ya zama ɗan boko gaskiya, zirarashi yake yi baya tusawa, ga ƙamshi yana zubawa ƙirjinnan hmmm, na faɗa ku sa mun gas hahaha. "To fito mu ci abinci, in samu in sauke yarannan kar muyi latti fa Hindu, nima kusa in makara" Asama'u ta suri turarena, ta feffesa na dunguri kanta. Tare muka zauna a teburin cin abinci. Ko'ina tsab, sai ƙamshin turaren wuta, cakuɗe da ƙamshin mai soyayye. Azgar yana ganina ya hau zuba mun abincin. Soyayyan dankalin turawane, da miyar ƙwaai, ga biredi mai laushi, shayi duk madara. Rayuwa kenan, komai wucewa yake yi tabbas. Muna cin abincinnan ina ƙara jaddada musu nasihata har dai , muka kammala muka fito tare. Azgar tuwon shinkafa miyar kuɓewa ɗanya da bushasshen kifi zaka yi mun. Asama'u ke kiyi mun wannan lemun na su abarba da lemo, Sabira ta ƙara share falo, tasa turaren wuta. Ke Asama'u sai kiyi wanke_wanke. Ƴar motata na hau na fita, suka biyoni a baya. Da gudu na wucesu da aka saki danja har ina latsa musu hon. Ina ganinsu, harda Baban a dariya. Shima haka yake mun, duk ranar ni zan kaisu makarantar. A ciki na tadda Luba karyawa ma take yi. Taliya da miyar ƙwai take ci. Ganina yasa tayi mun murmushi mai taushi, kafin in bata amsa Mijinyawa ya kira wayata. "Ranki shi daɗe kin isa ofis lafiya ko?" Idanuna na lumshe. Lafiya lau, kaima ka'isa lafiya, ya sabon ofis, da sabuwar kujera to?" Dariya yayi. "Kin ganni inata jujjuyawa akai, ofishin yana da kyau. In akayi birek zan zo in ɗakkoki kizo ki gani, sai ki shirya zuwa sha biyun rana." Agogon hannuna na kalla. To shikenan Allah ya nuna mana, zan kasance cinin shiri. Yanzu dai kayi aikin ka, nima ka barni in yi nawa aikin" Da haka mu kai sallama. "Soyayya daɗi Hindu, irin wannan maƙale murya har ina" Dariya muka saka, tare da tafawa. Luba kenan iyayen sharri, to yama akayi kika rigani zuwa ne?" "Au sabida kinsan na saba latti ko Wallahi nasiharki naji, shine dai nace in dinga zuwa ina karyawa anan kawai" Mu ka dai tattaɓa hira, kafin kuma kowa ya kama aikinshi. Sha biyu nayi, sai ga kiran Mijinyawa wai ya fito. Kafin ya ƙaraso, na buɗe mana alala da kunun gyaɗa dana tawo mana dashi, muka ci da Luba. Yana ƙarasowa, na fita na sameshi, ya kaini sabon ofishinshi na matsayin Akawun cikin gidan, na sa albarka. Ga hotona da nashi a saman teburin, muna dariya. Gaga_gaga_gaga A kwai wani gagarumin rikici da'akayi a gida, wanda akaita gore _goren gida su Innah Mairamu. Wannan ya ɗarsamun tunanin siyan gida da sunan su Innahrmu, sabida halin rayuwa, ban siya domin in zauna ba, ban siya dan ina tunanin watarana zan shiga ba. Babu wanda yasan da gidannan sai Luba kawai Wannan shine dalilin siyan gida danayi. Ba zaman kaina naso yi ba, kuma ba fito na fito nayi ga maza, ko Aure ba. Ina tunanin nayi haƙurin da ba lallai ke da kikace ina da zuchiyar kafurci kiyi ba. Na kawar da kan da ke da kike kirana mara tausayi ba zata yi ba. Nayi sadaukarwar da ke da kike ganin inada tauri, jiji dakai, nuna ni nice wanda ke ba lallai kiyi ba. In kece ni irin hukuncin dana yanke na haƙura da mijinyawa, ko da shine Autan maza zakiyi. Ko haƙuri zaki yi kuci gaba da zaman auren naku? Inaga iyakar abunda ya sauwaƙa daga cikin waiwayen bayan kenan. Amman kar ku mance Asama'u ɗiyatace, haihuwarta ce kaɗai banyi ba. Ni an riga da an kawoni ƙarshen tuƙewa. Dukkannin haƙurina, tunda ni ba Annabi bace, ƴar adamce, banzo kuma a sahabiya ba. Haƙurina dole yana da iyakarshi. Ba dan ni mai kawar da kai bace, ba dan ni na jure komai ba, sai yake nufin dole in zauna saina ƙarashe da mijinyawa bane, shine zan cika ba. Ku fahimci wani abu guda, mai haƙuri, da kawaici, bai iya fishi ba, wanda yake miƙa rayuwarshi ga masoyinshi abokin rayuwarshi da zuchiya guda, irin wanda ni nayi, a ranar daya ce bayayi, to yana nufin bayayi. Ban iya so ba, ban iya ƙiba. Zuchiya zata iya shekara ɗari tana ƙunsan damuwa, ko tana ƙunshe da ciwo. Kuna da labarin abinda zai iya buga wannan zuchiyar ba dole sai mai girma ba, ba dole sai anyi babban abu ba ko? Abu kaɗanma da kika raina ƙanƙantarshi ka iya kai mutum maƙurar bango, har ya buga zuchiyar tashi baki ɗaya ma. An yi ma zuchiyata irin turin da aka riga aka kaita bangon ƙarshen tuƙewa. Amman me kuke gani? A labarin ina da kusakuraina irin na cikar ɗan adamtaka, irin naki kema, irin nasu suma. Ni ba ma'asumiya bace, bare ince nice akan turbar gaskiya da gaskiya ba. Dukkanin alkhairan mijinyawa ni na zaiyano muku da kaina, ban zama mai son zuchiyar da zan ɓoye alkhairanshi dan yayi mun budulci ba. Wannan shine ɗan kaɗan ɗin haƙurin da nayi, kaɗanne bashi da irin girman da ku kuke tunani yana dashi, domin Allah nayi haƙurin. Yanzu ma da nace bazan iya biyayya ba a rabu dani, shima domin Allah ne. Akan mijinyawa bazan halaka kaina izuwa wuta ba. Muddin naƙi mishi biyayya, to Allah fa zai hukuntani tabbas. To a wajen Hindu rabuwar tamu itace mafi alkhairi. Kefa? Na faɗa tun farkon labarina cewar son da nake ma mijinyawa, ya haɗiye wanda yakemun. Wabillahi, shima ya faɗa, kuma ya sani. A ƙarshe nake cewa da duk waɗanda suka kirani da zuchiyar kafurci, da waɗanda suka ce kwangilar yahudawa muka karɓo ni da marubuciyar, da waɗanda suke cewa a rabu da Hindu, me take son koyama mata, tana son koya musu ko wacce ta fito daga gidan aurenta ne ta koma makaranta, ko ta kama sana'a Hindu bata da aiki sai cewa kuɗin kai duniyane. To ku shaida, mala'ikun Allah su shaida na yafe muku, nasan rashin fahimtane da saurin yanke hukunci. Shi yasa babu kyau saurin yanke hukunci, da saurin faɗar magana mai kaifi akan mutum. Ni kam na yafe wallahi. Sannan mu sani dukkan hukuncin da zamu yanke, muyi nazari sosai a kanshi. Yawan magana bashi da kyau. Manzon Allah SAW yace akwai alkhairi a cikin yawan yin shiru. Ka faɗi alkhairi ko kayi shiru. Na sani ɗabi'ace ta ɗan'adamtaka bazan burge kowa ba. Ni bana yin komai dan in burge, asalima ni kushewar mai kushe taki yake zamema rayuwata. Bana dariya da ƙaddarar kowa bana isgilanci akan ƙaddarar kowa. wani zaiji duk duniya Hindu ya tsana, binciken laifinta ma yake yi idanu rufe. Akwai waɗanda sunasan ganin Hindu, suna ji Hindu na burgesu. Nima ina sonku domin Allah ( yau a tayar mun da dibet mai zafi domin Allah. Yau ranar faɗan dukkan wani ra'ayine, tunda kun gama haɗa dukkan hujjojinsu da kuka riƙa) Nima anan na naɗe tabarmar wannan littafin Harƙa ta Uku, biyoni a harƙa ta huɗu dan jin dawowa asalin turban labarinsu Hindu. Na tsallake abubuwa da yawa, muka miƙa zuwa ga hamimman da fatan kun fahimta? Kuskuren da nayi Ubangiji Allah ya yafe mun. Daidai mai amfani dana rubuta mata suka amfana dashi, Allah ya bada lada. Godiya ta tabbata ga sarkinnan Allah mai girma Ƴan bati ina miƙo saƙon godiyata gareku. Ina miƙa saƙon godiyata a gareku Ɗakin sharhi 1 Ɗakin sharhi 2 Ɗakin Sharhi 3 Da ace lokaci zai bani dama dana lissafo muku sunayen wasu daga cikin makaranta waɗanda kai tsaye zan miƙa musu lambar yabo. Amman kash babu lokaci, sai dai inyi kuɗin goro wajen miƙa jinjinata ga dukkan masoyan labarina, masu bibiyar aikina na faɗin duk duniya. Ku gyara zaman jiran Harƙa ta 4 domin yadda lamurannan zasu ci gaba da tafiya. Me kika koya daga cikin labarinnan? Wanne darasin rayuwa kuka ɗauka. Menene abu mafi ƙololuwa daya taɓa zuchiyarki. Zaɓi team ɗaya tak Team Hindu Ko Team mijinyawa kike? Faɗi dalilin zaɓen wanda kika zaɓa, da hujjojin da kika dogara dasu. Lallai inason dukkan masoyana su tofa albarkacin bakinsu, kuce wani abu. Sannan idan akwai inda na ɓata muku, ku yafemun. Nima na yafe muku. Ina godiya son so fisabilallahi.