TSURON TSIRIN... TSANDAURI Littafin Badia'at Ibrahim Mrs Bukhari gidan ƙamshi HARƘA TA BIYU (2) LAMBAR FARKO *Godiya ta tabbata ga Allah subuhanahu wata ala daya nuna mana wannan lokacin cikin ƙoshin lafiya. Kamar yadda muka kammala harƙa ta ɗaya lami lafiya. Ubangiji ya nuna mana lokacin da zamu kammala Harƙa ta biyu, harƙa ta uku, da harƙa ta huɗu lami lafiya amee* *Sannunku masoya da jumirin jira, yau dai jira ya ƙare in sha Allah* *Masoyan alƙalamina na duk duniya, ina miƙa saƙon gaisuwa da godiyata gareku. Ubangiji Allah ya bar mun ku son so💪🏼* *( Ina da tsokaci kaɗan kamar dai na baya. Wannan littafin yana buƙatar karatun nazari sosai da sosai. Inaso masu bibiyar wannan labarin su karanceshi da kyau domin gane haƙiƙanin inda labarin ya dosa, manufarshi, da saƙon da yake isarwa kai tsaye dan Allah.* *Sannan mu sani ba duk littafi bane ake yinshi domin jin daɗi ko nishaɗi ba. A lokacin da wasu ta ɓangarensu labarin zai tafi yadda suke so, ta ɓangaren wasu zasu ci karo da abinda zasu ji su kamar ba'ai musu daidai ba.* *Ko mu karan kanmu ba duk abinda muke so muke samu ba, ba duk yadda muka tsara rayuwa muke samu ba. Yayin da wasu yadda suke so haka Allah ya so yai musu, sabida haka yaso ba dan su yafi so ba, sai dan rayuwa shirin shi ce yadda yaso haka take tafiya* *Almuhim shine mu ɗauki darasin dake cikin labarin Hindu Duwaf da Gawata zamu amfana da abubuwan ban mamaki in sha Allah)* *sannan ƴan ƙungiyar Gawata da ƴan ƙungiyar Hindu dan Allah ayi sharhi na girmama ra'ayoyin juna. A fito a fafata a baza hujjoji ta ko wanne ɓangaren a rungumi juna ai mutuwar kasko ma in ta Allah* *Allah ta'ala yasa mu dace. Ku gyara zama da kyau yanzu zamu soma wannan tafiyar.* *Kuzo muje filin jirgi mu ji yadda zata kaya* Tawa dai zan shiga Akarami. gidana zan sauka ai da izinin Allah." Ina ganin mijinyawa na ajjiyar zuchiya a tunaninshi gidanshi nake nufi ko? Hmmmmm Ai kuwa motata na shige ni da Yaya Saratu da yaran. Akarami kuma sai yayi kara yace bari shi ya shiga na Mijinyawa, tunda dai duk mun yashe, kin motar ya miƙo ma Yaya Saratu. Ana haka Luba ƴar amana ta ƙaraso, harda gudunta. "Azgar koma motar Babanmu, ke Luba shigo daga nan. umm Luba wato kema ba za'a barki a baya ba ko dole sai anzo tan tarbi ƙawar arziki? " Cewar Yaya Saratu dake gaban mota mazaunin direba ni kuma ina gefenta. Azgar ya fita ya koma motar Abbansu Luba ta maye gurbinshi. "Ja muje Yaya Saratu Zawa ciki zaki kaimu zan dinga nuna miki hanyar da baki gane ba, ke dai mu je kawai" Cewar Luba dake magana tana dariya tare da miƙo mun hannu muka tafa cike da farin cikin ganin junanmu. Sai dai ta rame amman tayi kyau taci lashinta danƙarere harda ɗan kunnen gwal abinda masha Allah. Lallai Luba ta dawo daga rakiyar Sunusi, ta gaji da sarama kare ciyawa. "Me akeyi a zawaciki kuma Hindu, Luba kun sani a duhu fa, ke ba kince gida zaki wuce ba? Daga dawowa me akeyi a zawacikin da can za'a soma zuwa" Ta ƙarashe zancan tana kallona ƙur a dalilinta na son karantar gaskiya. Gidana nake nufi ba gidan mijinyawa ba Yaya Saratu, ke dai muje zan miki bayani ai in mun ƙarasa." Ishara nayi mata da Sabira ala tilas tayi shiru tare da yi ma mota ki muka ɗauki hanya, amman naga sai jinjina al'amarin take yi, tana ta jinjina kanta. Ni da Luba kuwa sai hira muka dirarms kawai, ai ba ƙarewa hirarmu take yi ba. Sai da muka saɓa hanyane Akarami ya kira wayar Yaya Saratu yace. " Ke Yaya, ya naga kun miƙe, mu da zamu yi kwana kuma? " "Eh kawai ku biyo bayanmu in mun ruguntsuma munje inda zamu je sai ayi magana, nima Luba ke mun idanu, bansan me zance da kai ba a yanzu. Kai dai ku biyo mu a bayan dai" Kashe wayar tayi muka ci gaba da hirar yaushe gamo, dukkanmu ukun muna da tulin magana a bakunanmu sai in mun zauna lokaci zai bada damar zantawa. Tafe_tafe har muka ƙaraso ƙofar madaidaicin gidana wanda ya sha fenti mai ruwan ƙasa da fari ta ciki. "Sabira ungo ki, ki fita ki buɗe mana get maza" Cewar Luba da ki ke hannunta. Yaya Saratu dai illahirin mamaki ya hanata cewa uffan. Sabira ta wangale gidan muka shiga, sai dai motar mijinyawa ba zata samu wajen shiga ba tsakar gidan bazai ɗauki mota biyu ba. Ki Luba tasa ta buɗe mana muka shiga asalin mashigar da zata sadamu da cikin gidan. Yanayin tsarin gidan da an shiga koridone dogo ba sosai ba, sai wajen daining daga hago Kicin daga dama suna kallon juna, falo kuma yana fuskantarmu babban falon gidan kenan. In ka ratsa Kicin kuma, wani korido ɗinne da ɗakuna uku ko wanne da banɗaki a ciki, kana akwai banɗaki a korido ɗin na baƙi maza haka, ba baƙin kwana ba na bakin zo ka koma. Ɗakin maigida masta bedrum kamar yadda suka tsara yafi girma kuma banɗakin cikinshi ma da girma. Haka tsarin wannan gida yake. Falon muka runtuma muka shiga yaji kujeru da tattausan kafet sai ƴan kayan ƙawa ba masu yawa ba amman masu tsada. "Ke Hindu dama mijinyawa ya sake miki gida shine babu ko labari, tafiyarki umara ma haka kikai mana bazata, ga wani bazatan ya sake samuwa" Dariya nayi ma Akarami nace. Akarami kenan ku shiga ku ga waje, gida yayi kyau ko?" Mijinyawa dai yana tsaya yadda kuka san ɗan rakiya maras galihu ma kuwa. Murna su Azgar suka shiga yi, Mijinyawa kuwa sai yaƙe yake yi gaban mamaki ya rufeshi. Yana biye tamkar raƙumi da akala, muka ratsa Kicin ɗin shima babu tulin kaya iyakar abin buƙata kawai aka saka komai fes dashi. Ɗakin Azgar muka tura gadone sai sib da kafet ƙarami shikenan abinda ke ɗakin. Sai ɗakin Sabira ma haka komai iri ɗaya, kala ne ya bambamta. Ɗakina na tura duk saida suka faɗi albarkacin bakinsu na kyau da tsaruwarshi rusheshen ɗakine, Banda mutuminku fa ato. Ɗakina yana da girma, dan yafi falon girma sosai, ga kafet malala ja, labulen taga ma ja ne, sai farin gado, sib bango guda daga sama har ƙasa, sai durowar kwalliya, sai durowar takalma da sandar sagale jakunkuna, da kayan kallona suma ɗas dasu, da kujera babba doguwa da teburi a gabanta harma da ƙaramin kafet a ƙasan teburin, ga wasu fulawowi domin sake ƙawata ɗakin shikenan iyakar abinda ke ciki. Luba ta kuwa shinfiɗamun farin zanin gado ɗan ƙasar sin mai bargo. Wanda na sa ta siyo mun a Ɗorayi wajen Anty Zee collections. Babu irin nau'in zanin gadon da bata siyarwa. Jinga_jinga masu barko, madaidaita, harma da ƙananu kana na ƙasashe daban_daban duk tana siyarwa ( Zanin gado ai duniyane nima a wajenta nake siya, Oga yana yabawa gaya. Ni kam a zanin gado tattalin arzikina yake ƙarewa. Na gamsu da ingancin zannuwan gadon Anty Zee collections ɗari bisa ɗari. Duk mai son burge uwarɗakinshi ya neme ta kai tsaye kawai) Kunga wannan ɗakina kenan ya kuka ga wajen to?" Mijinyawa fa yana tsaye tamkar mutum_mutumi kuma idanunshi a kaina ina sane da komai har yadda yake ƙarema ko'ina kallo yana mamaki ina kallonshi fes. "Waje yayi kyau, na taya ki farin ciki da kuka yi gidan kanku wallahi. Mijinyawa ka kyauta sosai daka raba Hindu da Asama'u a gida ɗaya gida yayi kyau Allah ya ƙara arziki. Hakan zai fi kawo zaman lafiya sosai" Cewar Yaya Saratu cike da fara'a da murna. Akarami yaba Mijinyawa hannu suka tafa yayi mishi murna shima. Da yaƙe dai aka barshi kawai mamaki kamar ya halakashi, har ƙanƙance idanu yake yi tsabar ruwan mamakin dana shayar dashi a yanzu haka. Falo muka koma su Azgar suka shigarmun da kayana sai jakar dana zubo dabino dasu bagaruwa da ruwan zam zam kawai na bari. Kayan dana turoma Luba tun ina landan, suma suna ɗakina cikin sib. Buɗe su dabinon nayi Sabira ta ɗakko tire na zube musu, tare da miƙewa tsaye. Ni kam zanje in watsa ruwa kuma in ɗan huta nagaji, ga bacci dana tara. " " Ai dole ki taro bacci, Umara ai ba wasa bane, kuma ai ba kya je ƙasa mai tsarki ki shantake da bacci ba. Nima dana gama cin dabinonnan zan wuce jirana madam take yi tana gida na kawosu, to anguwa zan kaita kuma, ga kin sabuwar motarki nan, bari ma kawai in ɗebi dabinon na zuba a leda, sai kinzo gida dan nasan gobe a gida zaki wuni ko? " In sha Allahu kuwa a gida zan karya ma. A gaishe mun da Maman Soja boi" Nan mukai sallama na amshi kin motata na fice a falon, su Yaya Saratu suka biyoni ɗakina yara duk suna nasu ɗakin suna santi. "Hindu na fahimci mijinyawa kamar baisan komai game da tarewarki ba ko, menene abinda yake faruwa tsakaninku, da Allah gidannan naki ne ko nashi ne? Luba kada ku ɓoye mun. Dukkan halamu ya nuna yana cike da mamaki" Zama muka yi akan kujerar ɗakin nace. Gidanane Yaya Saratu kuma na ɗan jima da siye gaskiya, babu wanda yasan dashi sai Luba kaɗai, shima yau yaga gidan kamar yadda kuka gani yau, gidan yana da gyara sosai Luba na wakilta ta gyaramun hatta kayannan komai da komai ita ta zuba mun. Yaya wallahi bazan taɓa zaman aure da mijinyawa ba, bazai taɓa yiwuwa ya haɗani kishi da Asama'u ba. Na bar mata shi har gaba da abada ta zauna ta cika mishi gida da ƴaƴa da suke so shi da danginshi ni a barni da yarana biyu sun isheni rayuwar duniya. Sannan ko ba dan Asama'u ba inason in zauna a gidana mallakin kaina tunda Allah ya hore mun. Taya kuke tunanin ni Hindu zan ci gaba da wannan Auren?" "Danƙari akwai kallo kenan a gaba.. Ke Hindu ashe da gaske kin rabu da mijinyawa? Duk da nasanki da taurin kai amman nayi tunanin in kika dawo zaku sasanta kanku ashe ba haka bane. Kenan in ya sakeki sai kiyi zamanki a gidanki ciki gaba da kulawa da yaranki tunda ba zaki koma gida da zama ba? Toh a gaskiya ni bazan tursasa miki ko in baki shawarar dole ki zauna dashi ba, kina da ƴancin zaɓin abinda kike ganin shine farin cikin ki. Ke ba ƙananan yara ba kina da damar ƙwatar ƴancinki gaskiya. Ina tare dake Hindu Allah ya baki nasara. Wallahi ko nice na reni yarinya tana ƙarama, ta girma mijina ya Aureta, to an tashi wasan dani wallahi. Dole in koma gefe ai. Kuma naji sha'awar in mallaki gida nima wallahi ko dan shiryama matsala, wani sa'in ko guma maka akayi sai ka buɗe gidanka ka huta. Ko wata shida ba'ayi ba saida na kashe miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu na sauya kujeru da gado da ƙyale_ƙyale namu na mata. Yanzu da hakan da nayi da ban cika ko filin miliyan biyu na siya ba? A hankali a hankali sai mutum ya soma gininshi, ɗan abinda ka samu ka watsa a gini ba, Luba abunnan ya burgeni" Luba tace. "Nima ina bayanta tunda ba ƙananun yara gareta ba. Wallahi Yaya ni kaina ɗan lokaci kawai nake jira na ba Sunusi, dole ya sakeni so nake Sadiq da Aisha su kai wani mataki kaɗan kafin in fita in barsu nasan zasu kula da ƙannensu. Zama da kishiya gida ɗaya masifa ne, wallahi ko baka son mijinka zama gida ɗayan babu daɗi, balle wuya irinta Sunusi wacce iri ce ni Luba ban ci ba? Ya kuma isa haka na kame kaina ina gefe aikina kawai na saka a gaba sai adashen manya_manya da na shiga, kuɗi nake nema idanu rufe in tara, in gina kaina da kyau" Dariya muka kwashe dashi muka yi muka yi sosai. Wanka na shiga nayi na ɗauro alwalar magriba na fito na lailaye fatata da mai na shafe jikina da khumra ƙasaitacciya irin ta gidajen sarautun daular larabawa. Wanda Anty Badiat Mrs Bukhari take yi. Wannan Khumra akwai mannewa a fata ƙamshinta ya riƙe jiki da kaya. ( Sunan wannan Khumra. (Khumrat al khaltat) Tana zuwa a 30mill cikin mazubi na ƙasaita mai nuna daraja da tsada. Tasirin ƙamshinta yana da ƙarfin riƙewa na kimanin awa arba'in da takwas. In bata miki wannan awannin ba, ki yi magana in dawo miki da kuɗin Allah. Ta samu aiki da sinadaran gargajiya masu ƙarfi da daraja. Wannan khumra sabuwar zuwa ce, wanda na shafe shekara guda ina aiki a kanta dominku. Duk mai so tayi magana) na buɗe durowata na ciro riga da wando falazo na saka, dubu arba'in na siye su masu santsi ko sawa ban taɓa yi ba, ribon ɗin kaina na sunce ina bin gashin da oil ɗin Oriflame na gashi, fuska, da jiki mai ƙamshin fiya. Wanda nake siya a hannun Mamanmu Hajara Aliyu dattijuwa mai girma da karamci. Ni sake lakuto man gashi na Mrs Bukhari gidan ƙamshi na ƙasaitattun matan da suka gane sirrin dake cikin ƙamshi. ( Sunan wannan man gashi na larabawan usil (Makhmariyatul Oud Al nafis) ke daji ba'a magana. Gashi tazo a mazubi kyakkyawa mai daraja lamba ɗaya. Wannan makhmariyya ƙamshinta na da ƙarko sosai ta yadda hatta matashin kai in kika kwanta ƙamshine yake kamashi. Masu so suyi magana. Wannan ma sabon aikinane dana jima ina aiki a kanshi, ban fito ba sai da shirya) "Hindu naga gashinki ya ninka na da me kike mishi haka. Sannan naji kin buɗe wasu kayan ƙamshi duk sun cike ɗakinnan da ƙamshi, daga Saudiyya kika tawo dasu hala? " Cewar Luba data fini maitar gashi harta taso tazo inda nake tana taɓa gashina dake kan kafaɗata gashi sai sheƙi da ƙamshi yake yi yana shan lele gaskiya. Maganin tayar da komaɗa (Supplement) na kamfanin Oriflame nake amfani dashi, da kuma wannan oil ɗin duk na kamfaninne. A wajen Hajara Aliyu nake siya" Yaya ta matso tace. "Gaskiya gashinki yayi yawa gashi ya kuma cika ni kamar har duhu ya sake yi fa, man kamfanin Oriflame ɗinne ya dawo miki da fatarki haka itama?" Wallahi Hindu kinyi kyau sosai kinyi rama naga babu tumbi a jikinki ko idanunane Luba?" Dariya muka saka kawai Yaya har tana ɗaga mun rigata dan su shaida. Fatata da ta shafa kuwa wani ƙamshine ya kama mata hannu. Nan na basu labarin mai maye gurbin abinci na kamfanin Oriprame da nake damawa in sha mai suna mil rifilesment, gwanin narka kitse, ya fatattaki tymbi da duk wata ƙiba kenan. Shima dai duk akwai a wajen Mama Hajara Aliyu. Dangane da kyan fata kuma, harda man fata na ƙamshi sirrin matan sudan na wajen Anty Badiat Mrs Bukhari, da kuma basarakiyar dilkhar ta ta asali mai dogon tarihi. Sunan man ƙamshi, da gyaran fata na mrs Bukhari shine (jamrat al dhahab makhmariyya) sarauniyar ƙamshi, taushi, da hasken fata kenan. Hajiya babu dana sani cikin wannan tafiyar ƙamshin. Shima sabon aikinane wannan) Luba tace. "Ai ta kwana gidan sauƙi, tunda ina cikin Taskar Anty Badiat. Mamanmu ma ai ta sanni, ba ta dai san ni ƙawarki bace. Anty Badiat tamu ce itama. Duk zan neme su, irin wannan ƙamshi mai ƙima" Yaya ma tace ba za'a barta a baya ba. Ai kuwa ku shirya, ku malkaki kaya masu daraja, kuma zaku canja kamar yadda na sauya. " Nan sukaita ɗaga kwalaben kayan ƙamshi na alfarma na Mrs Bukhari suna mai rantsuwar da ba dan ga sunanta a jiki da lambar wayarta ba, ba zasu taɓa yadda cewar a Najeriya ake wannan kayan ba. Yafi kama da kayan ƙamshin larabawa, wallahi ba yao bane darajarsu ta wuce yadda na faɗesu. "Zan gyara domin daɗin jikina. Hindu tuni na dawo daga rakiyar maza, ke nifa abunda mijinyawa yayi miki kaɗai yasa na gane ba'a iyama namiji wallahi. Da ace kuɗaɗenmu mu muka ci abinmu da yanzu mu hajiyoyine wallahi. To a hakanma Alhamdullilahi in da rabo kuma zamu yi. Ke wai kinga iskanci da kaɗifirin da Sunusi yake yi shi da mandiyarshi? Ummm ai tananan haihuwa ko yau ko gobe Hindu kya zo mata suna. Yaya Saratu ya kamata muje ko dare ya soma yi" Hala yau kece da turakar Sunusi, ke kike mulkin birnin zuchiyarshi" Duka ta kawo mun na kauce munata dariya kamar babu damuwa tattare damu. Kaina na taje ko tubkewa banyi ba ban kuma sa ɗankwali ba muka fito tare dasu. Mijinyawa mun baroshi a banɗakin korido dake a buɗe ya bari yana alwala. Har bakin get na rakasu mukai sallama akan gobe zan tawo musu da tsarabarsu, na dai basu su dabino da bagaruwa. A Kicin muka ci karo da mijinyawa, da Azgar zasu tafi masallaci. "Zamu je masallaci mu dawo yanzu" Ganin Azgar yasa nace Sai kun dawo" Na ratse na wuce mijinyawa sai kallona yake yi. Nayi imanin ƙamshina ya dakeshi sosai. Nima dana shiga nawa ɗakin bonar turaren wutan mrs Bukhari na kunna kawai, na zura hijabi na tayar da sallah. Ban tashi a inda nake ba sai da nayi isha tukunna. Na fito na kira Sabira muka shiga Kicin. Shayi na dafa mana kawai na tawo da kayan shayina shi na zuba mana kofi uku na buɗe robar dambun nama mai yawa na zuzzuba mana a kwano. Ɗauki naki dana Yayanki, in Abbanku yazo kice ni na kwanta kuyi adda'a ku kwanta kuma Azgar ya rufe gidan in Abbanku ya tafi" A sanyaye tace "To Ammi" Kamar tana son tace wani abun amman sai ta haɗiye, gudun kada mijinyawa yazo ya sameni yasa ban tursasa mata ba nayi shigewata, na saka sakata na baje a gado harda kunna siris ɗin da nake kallo mai suna The train ina shan shayi ina tura dambun nama bakina. Ina mamakin film ɗinnan sosai da yadda aka samar da aiki ingantacce, kuma na ƙagu inga ƙarshen yadda zata kaya. Bayan na gama nayi gyatsa sai kuma na miƙe na shiga jera kayana a cikin sib tsab. Ina tsaka da jerawanne na jiyo bugun ƙofa nayi imanin mijinyawane dan dai yara ba zasu buga mun ƙofa ba musamman da na barma Sabira saƙo. Guntun tsaki na sake ko in kula da bugun ƙofar na soma ware tsarabar ƴan gida na ɗakinmu kenan. Gobe dole saina shiga kasuwa kafin in iya zuwa gida kenan, na mance zan siyo tsarabar matan gida, da ƴan gida. Saida na wauware dukkan abinda ya dace na sake kayan jikina zuwa na bacci. Nayi hayewata gado adda'ar bacci nayi na saki ac na bi lafiyar gado zuchiyata fal farin ciki haka na wayi gari. Ashe haka gidan kai yake da daɗi gaban mamaki? Hmm mata mu dage wallahi mu saka Allah a farkon lamarinmu ko baki zauna a gidanki ba mallakar tana da amfani. Yanzu yaci ace mu waye mu dena gasar haihuwa, ko cika gida da ƴaƴa, da sunan kafin wata ta shigo, duk don sabida gado, shin ke bakya fatan samun naki kuɗin sai dai a mutu a bar miki, mu shikenan bama son mu yi kuɗi, muna jira har sai an mutu, wani mijinma sai yayi shekara ɗari bai mutu ba, har lokacin gado kike jira kina ruwa kuwa. Me yasa mu ba zamu tashi mu nemi namu kuɗin ba, ke ba kya fatan ki mutu a baje dukiyarki a kasaftama yaranki ne? Sannan wa yace miki mijinki ne zai soma mutuwa kafin ke? Kina da aiki, kuna da aiki kar ku tashi haiƙan ku nemi gumin halak ɗinku. Zuchiyata fes wasai na wayi garin ranar. Ƙat ƙat na buɗe kin ɗakina na fita, ɗakin Sabira na soma shiga, ta riga ta tashi tana kan sallaya. Azgar dai sai da na tasheshi nace yayi alwala ya tafi masallaci. Kana na dawo nayi wanka tare da alwala bai ɗaya. Nazo na gabatar da sallah, nayi azkhar ɗina na safe sannan na tashi na shirya cikin doguwar rigar yadi kwatin mai laushin gaske, na taje kaina na kuma tubkeshi da ribon na feshe jikina da turaruka bayan khumra dana shasshafa saina fita da tsarabar yara. A falo naji muryarsu saina nufi falon da fara'ata da sallama. Turus na tsaya ganin mijinyawa a kwance a ƙasan kafet yayi matashin kai da fulon kujera wandon shadda da singileti ce a jikinshi yana bacci. Idanu su Azgar suka zuba mun, Sabira ta miƙe ta karɓi kayan hannuna. Gaisawa muka yi cikin kewar juna sosai. Wannan ledar naki ne, wannan na Azgar ne. Kai Azgar zo ka ɗauki mota kayo mana cefane maza" "Ammi Abba ya kawo kayan Shayi tun jiya da daddare har da ƙwai ma" Shiru nayi ina nazari can nace. To shikenan kuzo muje Kicin ina zaune ku yi mana abun karyawa." Sabira tace, itace Zata yi, Azgar yace. "Ammi rabu da'ita kinfi son girkina na fisu iyawa ai ni zanyi mana" Muna dariya mijinyawa ya farka carab muka haɗa idanu dashi, ga matsananciyar kunyata a idanunshi ainun. "Abba barka da tashi" "Barka Azgar. Tutar so kin tashi ashe? " Ashe baka tafi ba? " Ficewa yaran suka yi, ai sai nayi yinƙurin bin bayansu yace dani. "Hindu" Juyowa nayi na zuba mishi idanuna cikin kallon ido cikin ido kallon ƙurulla, tuhuma, da takaici. "Inaso ki aramun lokaci dan Allah mu zauna mu yi magana. Duk da bansan ta ina zan soma miki ba" Nuna kaina nayi da yatsana manuniya nace. Wai ni da kai muyi magana? Kayi haƙuri ina girmamaka sabida yaranka. Sannan kayi ƙoƙari ka tafi gidanka ina buƙatar in kaɗaice da yarana kaɗai. Ina buƙatar takaddata bana son abun ya kaimu inda rai bazai yi daɗi ba" Ai jin na faɗi haka babu wasa da murya ta rashin tsoro sai ya zabura ya taso yazo har gabana daf ina jiyo ƙamshin shi balle ni da nayi wanka yanzu. Cikin muryar da yasan yana iya shawo kaina a duk yadda na hau dokin fishi yace. "Hindu alƙawari na ɗauka a gaban iyayenki cewar ba saki babu yaji. Ki daure mu sasanta muyi magana nasan nayi abinda ba zaki taɓa yafe mun ba. Hindu nasan na miki abu mummuna, amman aimun afuwa a yafe mun a bani dama" Baka yi mun komai ba ni, in kana tunanin kayi mun wani abun, to baka yi ba. Ai rayuwa ce kullum da kalan sauyin da zamani ke zuwa mana dashi. zaman ne kawai bazan yi ba nace bana yi, nasan ko a addini ba'a aure dole inna nemi saki dole a sakeni. Wallahi mun gama" Ina kaiwa haka na juya na yi wucewa ta ciki, carab ya riƙe ƙofar ɗakin da iyakar ƙarfinshi ashe biyoni yayi jikinshi har yana rawa. "Tutar so ki taimaka ki bani dama dan Allah muyi magana. Duba yaranmu dan Allah" Dariya nayi nace. Bazan bayar ba, bani da damar baka, bani da lokacin tattaunawa, kaga bana son takura ko wani cece kuce ka bar mun gidana bana buƙatar ganinka yaranka zasu dinga zuwa maka, duk sanda ka gaji da riƙe igiyar auren zaka tsinka. In kuma zaka haɗa dasu ku wuce laba'asa" Da mugun ƙarfi na fisgi hannun ƙofar a hannunshi, na datse nayi zamana akan kujera ina sauke numfashi. Shi da jin ƙarfin da na saka mishi yasan bani kaɗai bace. Wallahi ko buɗe idanuna bana so nayi inga mijinyawa, kuma bazan laminci ya sake kwana a cikin gidana ba, yaje can ya ƙarata. Na daɗe a zaune ina hasashen abubuwa masu dama. Yaya Zubaida ce ta kirani tana gida ita harta je, nace mata nima bazan wani jima ba zanzo in sha Allah, mun ɗan taɓa hira kaɗan kafin ta kashe wayarta. Azgar ne ke buga ƙofa yana kiran sunana. Naje na buɗe mishi na ganshi da shayi da ƙwai da biredi a tire ya jera komai. Nagode Allah yayi albarka, kuje ku karya" "Abba ya tafi yace zai je ya dawo" To shikenan bari in fito mu karya tare" Cikin yarana na shiga muna karyawa ina basu labarin Bbc da irin ƙaruwar da nayi, da rayuwar Landan, da makaranta dai mune har sha ɗayan rana. Bari kuga in je in shirya zamu je gida, ku shirya yanzu zamu tafi" "Ammi ni kam gaskiya bacci zanyi sosai kaina yana ciwo sosai dashi na kwana, shi yasa ko sallar dare na kasa tashi, sai dai kuje da Sabira" Kasha magani amman?" "E na sha Ammi" To shikenan Allah ya ƙara sauƙi ke Sabira ki shirya mu tafi maza" Shiryawa nayi tsab na caɓa ado muka ɗebi tsarabar su Innarmu Azgar ya buɗe mun get muka fice. Kasuwa muka soma shiga na dinga siyo tsaraba, carbi ma saida nasai dozin huɗu, dadduma dozin biyu, huluna kuwa irin na fakistan na sai fin dozin biyar na manya dana yara tsaraba dai ƙaƙas. Sai azahar nayi sallama a cikin gida. "Ga Hindu ga Hinduwa Duwaf. Hinduwa mutan Landan da makka da madina, kece kika yi kyau haka? Sai dai rama kuma Hindu" Cewar Inna Mairamu dake shara. Gaisawa muka yi da'ita tare da tambayar bayan rabuwa. Cikin falon nasu na yinƙura zan shiga tace. "Ai basanan duk sunje ganin gida Gude dai yau akayi da'ita zata dawo ai tayi wata biyu bata nan" Ayya to Allah ya dawo dasu lafiya" Shigewa muka yi na dinga bi ina gaishe_gaishe sai cewa akeyi nayi kyau na rame amma har da masu tambayar ciwo nayi ne. Hmmm Innah Kattime matar Baba Dogara cewa tayi. "Hindu sai haƙuri rayuwarnan. Kinga da ba'a aure Baba Soja bazai Auri Innarku tazo a ta biyu har a samar daku ba. Ki sararama ranki akan auren da mijinyawa yayi, bafa a kanki aka soma irin wannan auren ba. Amman ramar tayi yawa duk kin zube." Yawun baƙin ciki kawai na haɗiye na gimtse fuskata tamau, nayi ficewata ko sallama banyi mata ba sam na wuce ɓarayin Baba Alƙali. Yana zaune akan kujerar falonshi ya tusa littattafai a gabanshi yana ta nazari na shigo. "Hindu kin dawo ashe mutanen Landan." E Baba Alƙali nadawo jiya, ina wuni? " "Lafiya lau anyi Umara lafiya, ya landan da mutanen Bbc? " Murmushi nayi nace. Lafiya lau" "Kinyi kyau da kika rame sai kika dawo yarinya abun yayi kyau sosai. Ki shiga iyayen naku suna ciki. Barira ma tayo yaji jiya ta dawo amman mijinma yana hanya zai zo biko" Da mamaki na leƙa ɗakinsu Barira muka gaisa da Innah da Barira sai kallon ƙasan kayana Barira take yi, ni kuwa sai murmushi nake yi. Ina gamawa danan sai ɓarayinmu. "Hinduwa maraba lale" Cewar Innah Abida da suke gurgane a gaban Baba Sojanmu da gani shari'a akeyi kamar yadda aka saba, dan naga Innah Turai idanunta sun rune kamar ma fa kuka tayi. Tsugunnawa nayi duk na gaishesu, Sabira sai shigewa take da tsaraba ga takalminsu Yaya a cikin ɗaki. "Hinduwa mutan Landan da umara ma, nayi niyyar ma Akarami ya kawoni inga sabon gidan naku in kuma yi miki sannu da zuwa, to sassafe suka wuce Asibiti ɗanshi ba lafiya." Baba Sojanmu ina kwana, na sameku lafiya? " "Duk kowa lafiya Hinduwa barka barka anje lafiya an dawo lafiya ga mastas kin kammala Allah ya ƙaddara a Landan zaki yi mastas ɗinki. Na taya ki murna da zaki daure kiyi Phd kawai ki huta abunki ko Hinduwa? ". E Baba Sojanmu zan jona in sha Allah in kammala in san na gama kawai, bari in shiga ciki" "Ahh da saura in kika yi Phd ai sai ki zama farfeasa kuma, kinga ai dafa sauran aiki. Tunda a maza bamu da farfesa, Hindu inaso ke ki cika mun wannan burin nawa." Toh shikenan nayi maka alƙawari in sha Allahu." Miƙewa nayi na shige ciki. Tunda naji Innah Abida bata tanka ba bata yi sharhi ba to faɗa suka yi. Sharia ce ake musu. Ina shiga ciki na tadda ƴan ɗakinmu dukka matan harda Matar Yaya Soja Anty Sailuba sun zo daga Bori kam garin fatakwal har da goyonta ɗan wata biyu. Nan aka shiga murnar ganin juna tare da yi mun barka da dawowa da barka da shiga sabon gida. Babu damar tattauna abinda ya danganci sirri sai dai hirar duniya kawai. Amman naji daɗin kasancewata cikin ƴan uwana sosai. Bayan la'asar su Akarami suka dawo asibiti shi da Anti Dije muka ɗaura hira daga inda muka tsaya. Innarmu dai tana ta wauware tsarabar bataliyar gidanmu Yaya Zubaida ma yau ta kawo nata duk aka haɗe waje guda. Sai da muka ci tuwon dare kowacce ta kama gabanta ni dai gidan Luba na dosa takwas na dare na shiga gidan da sallamata. Sunusi na zaune a tabarma shi da Amarya suna shan iska ga tiƙeƙen cikinta a gaba daya sauya mata halittarta. "Hajiya Hindu kin dawo ashe babu labari? " Wallahi Sunusi na dawo ya aiki, amarya sannu da hutawa ko? A yatsine ta amsa kamar zatai kuka. Sunusi kuma sai rarrashinta yake yi. "Hinduwa mutuniyar tana ciki ku shiga daga ciki dake ta kunna inji da zata jiku ba" Ni dai wucewata nayi ciki na tadda Luba a falo yara suna cin soyayyar shinkafa da zoɓo mai sanyi, ita kuma tana zaune akan teburin aikinta na gida da shayi a gabanta da kaza soyayya ta cikin jajjagen albasa da attauhu. Ga haske fetal na inji a ɓarayinta, ɗakinta nata zuba ƙamshi ta sake ƙawata ko, ina da kayan ƙawa. Saye take da doguwar rigar lesiri kanta babu ɗankwali ta yarfa kitsonta na shuku. "Tabɗijan ashe zaki zo Hindu? Wallahi tunda dai naga Magriba tayi nayi tunanin ma ba zaki zo ba.Baba Sadiq a kawo ma Ammi soɓo mai sanyi maza." Yarane suka gaisheni Auta ta tawo wajena na rungumeta tare da karɓar ledar tsarabar Luba da yaranta. Na ciro wata doguwar riga na kara a jikin Auta tako yi mata cib habawa sai murna Auta. Sauran yaran duk na basu nasu suna ta godiya. Luba ta jani ciki da tata ledar tsarabar a hannu. A tsakiyar gadonta muka yada zangonmu. Luba duniya irin wannan gyaran waje haka waje yayi kyau. Naga kin kunna inji iyakar ɓarayinki Sunusi da Amarya suna waje sai fifita suke yi zafi zai halakasu, kefa muguwace ya ba zaki kunna duka gidan ba, ko a haƙura duka" Dariya muka tuntsure dashi muka tafa tab. Luba na dariya tace. "To tunda bashi da kuɗi ai sai suyi haƙuri man injin ɗinsu tun shekaran jiya ya ƙare dama baya iya kaisu wata, da zaran wata ya raba haka suke gurgurawa. To zan mutu ne Hindu dan kawai Sunusi bai da kuɗin man injin? Bazan mutu ba, wallahi ko cajin waya ba ko da yaushe nake saka musu ba, ke ba ma ko da yaushe suke ganin ƙofar ɓarayina a buɗe ba." (Mata wallahi mu kama sana'a. Masu takaddar da zasu iya aiki, kuma mazajensu zasu amince musu, ku nemi aiki mata. Mata mu tashi mu nemi na kanmu. Dan Allah Hindu Duwaf da Luba basu burgeki ba? Ni dai wallahi sun burgeni sosai) Mrs Bukhari https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp 07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm Tiktok link/ https://vt.tiktok.com/ZSCgTFH8o/ IMZEEDenterprises Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeed🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDENTERPRISESLTD wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account aTikTok@imzeedenterprisesltd https://vt.tiktok.com/ZSCgTFH8o/ Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima BADI’AT İBRAHİM tuni na antaya🏃TSUREN TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA BIYU (2) https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp 07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm Tiktok link/ https://vt.tiktok.com/ZSCgTFH8o/ IMZEEDenterprises Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeed🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDENTERPRISESLTD wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account aTikTok@imzeedenterprisesltd https://vt.tiktok.com/ZSCgTFH8o/ Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima BADI’AT İBRAHİM tuni na antaya🏃 "Laa ai baki ma sani ba, da sai shi Sunusin ya shigo ƙebe_ƙebe yazo yana ɗan wasa da yaranshi, tunda ai bazan hana ba. Sai kawai ta biyoshi sai su shantake a falona, wani sa'in harda kunna Tv Sunusi kenan mai gida ba. Dana gane fanka suke zuwa sha, wallahi ana magriba nake datse ɓarayina bugun duniya bazan buɗeba shine tayi zuchiya rannan tai ta maganganunta a tsakar gida. Shi kuma yana ta aikin rarrashinta, ba kiga yadda take ɓarje shagwaɓa ba, Sunusi gotai_gotai har wasan gudu suke yi fa, abun kunya wallahi, lokacin bata da ciki" Dariya muka kuma sakawa ni da Luba harda tafawa tab. Maza kenan, da yawansu gani suke yi isace, ko fin ƙarfi suke mana, shi yasa muka sanya hannu a ragamar kulawa da gidan. Basu san kyautatawace, da tausayi irin namu na mata ba. Amman gani suke isarsu ce ke sa ayi dole, sai randa su kai gar_gar aka janye musu tallafi, su dawo abun tausayi na gan_gan. Yanzu dai baki ga yadda na baro su Sunusi ba, zafi na neman rayuwarsu ba" Kai kawai ta girgiza tace. "Hmmm" Shiru nayi ina dubanta. Sabira ce ta shigo mun da abinci da wani soɓon wanda yake hannuna ma ban sha ba. Sai da na zuba lomar abinci a bakina nace da'ita. To wai bakwa rabon kwanane naji a labarinki kullum Sunusi yana can ko? Na dai san kin basu wata shida suje su gama ƙananan iskancinsu. To kinsan hirarmu a taɓa nan a taɓa canne, inajin bamu sake taɓa hirarta ba." Hannu luba tasa ta ɗauki lokacin dana ajjiye ta ɗebo abinci ta saka a bakinta tana taunawa tana cewa hmm, saida ta haɗiye tace. "Hindu kinga tunda Sunusi ya auro wannan aurakar bai raba kwana yayi na wata guda a tsakaninmu ba. Ta soma laulayin cikinta daya zube. Sai yake cemun zai koma wajenta ya kula da'ita sabida yarinyace ita tana laulayi sosai. To kinsan yanayin aikinmu yadda yake da wuya da cin lokaci. Wallahi Hindu na mayar da kaina sosai akan aikina na watsar dashi kwandon shara ƙaƙas. Bayan tafiyarki na jajje ɗakko rahoto na wakilceki aikin rahoto aikine mai wuya da ƙalubale ga ɗiya mace ga haɗari. Saina zama bani da lokaci sam, na kuma sake ƙirƙiranma kaina rashin lokacin sabida sam Sunusi bazai kai ni ƙasa ba. Gaga_gaga yaita jinyarta tsakaninmu dashi da asuba yana shigowa ƙofa a hannu mu gaisa kafin in tafi aiki. Ya bani kuɗin cefane ya tafi har dai ciki ya zube tayi jinya kamar zata mutu, kullum in zani aiki ina leƙawa in mata sannu, lokacin ƙanwar Sunusi tazo tana jinyarta. Kinsan Allah saida yayi wata shidda kafin shi a_ _kan _ karan _ kankin _ kanshi rannan da daddare ina kwance sai kawai ya shigo harda siyo kaza yadda kika san an kawo ango" Dariya na saka nice harda ƙwarewa da shinkafa saida na kora da soɓo. Naita dariyar mugunta Luba na taya ni. "Ƴar iska dariya ma abun ya baki dan nace kamar an kawo ango. Na dai taya shi muka ci kaza na kora da ruwa yayi kwanciyarshi yadda kika ga ruwa, har da makara. To kinga shekarar amarya ɗaya fa kenan. To ana haka da wata ɗaya cib muna rabon kwana babu abinda ya shiga tsakaninmu duk da ya nema sau babu adadi ina nuna mishi bazai yiwu ba. Mu kaita rikici. Ke Sunusi harda banƙareni yayi wai zai ƙulleni a katagon gado. Zo kiga damben tsiyan daya kaure a tsakaninmu" Katseta nayi ina cewa. Ai ba wajen bane, taya ma jikinki zai zama arha bayan duk wannan ƙasƙancin. Luba ni gani nake yi duk macen data sha wuyar zama da namiji da daɗi babu daɗi anfi wulaƙantata. Kesa_kesan da suke zuwa wajena wallahi Luba a cikin ɗari zaki ji iyayen gida da suka zame ma miji garkuwa a lokacin talauci su suke rubuto saƙo suna neman shawara cikin halin uƙuba. Da wuya kiji Amare a cikin uku. Bawai ba'a samun iyayen gida mugaye bane ko marasa son a zauna lafiya ba. Ana samu suma sosai, masu amfani da daɗewarsu tare da miji, da sanin abinda yake so, da akasin haka su danne Amare. Amman fa da wuya kiji haka amaren sunfi rawar kai da nuna su sunfi kowa son miji da kwantar mishi da hankali. Ko da yake da yawan mazan su ke zuwa musu da labaran ƙanzon kurege akan gazawar ta gidan. Kuma fa ƙaryace ruwa_ruwanta. Su kuma yaran a tunaninsu an aurosune su cike giɓi. Luba nifa ɗiyar da nono nane kawai bata sha ba, wai itace kishiyata abinda akeyi mun shi za'ayi mata. Yadda na haihu haka zata haihu, yarana da nata su zama wa da ƙani. Ai ya zama dole mijinyawa ya sakeni yaje ya ƙarata da abun kunyarshi, ko da yake maza babu ruwa a idanunsu sam hmmm" Wani mikine mai ciwo ya famu a zuchiyata. Ina yawan jin zafi sosai a zuchiyata musamman inna tuno mijinyawa da abinda suka aikata mun, ina jimawa a cikin yanayin zafin zuchiya da nauyinshi. "Hinduwa ko ni aka mun irin abinda akayi miki narantse da Allah in duk duniya zasu taru a kaina wallahi bazan taɓa yin auren ba na gama ya ƙare. Ina kai ki labari" Ina sha Luba duniya" "Sai kwatsam ta samu wannan ƙaddararren cikin nata. Shima nan nazo na sameshi na dawo aiki, na shawo gajiya, ranar rahoto naje na ɗakko a wudil. Yana haɗa kan ƙananun kayanshi a jaka. A nanne yake shaida mun zai koma wajenta da zama har zuwa lokacin da Allah zai sauketa lafiya. Labari fa yake bani, ba wai yana faɗamun in yadda ko kar in yadda bane. Shine aketa fama tutur har yanzu, wani sa'inma shi ke mata girki in jikin ya matsa mata, dan tabbas laulayi sosai take yi, ta kwanta a asibiti ya kai sau biyar inaga, tattalin arzikinshi yana ta yin ƙasa. To ai ita dole yayi mata, dan wataran ma ciwon bai kai wani ciwo ba zata kira ƴan uwanta a wuce da'ita asibiti. A hakanma yaso yace in taimaka in dinga zuba mata abinci. Wallahi baiga fuska bane shi yasa. Ya ɗan yi ƴan kame_kamenshi ya ɗakko taliya da kayan miya, wai in taimaka in girka mishi zai kai musu asibiti. A lokacin ma farfesun naman zabbi na sauke, ai ina jin yace haka na buɗe farfesun ƙamshin su citta ya daki hancinshi, na mayar da murfin na rufe. Na faɗa mishi ɓaro _ ɓaro cewar bazan iyaba, na gaji ban jima da dawowa daga aiki ba ya siya musu abinci a bakin titi ya kai musu, wannan hakkina bane. Wallahi yafi minti goma sha biyar a tsakiyar kaina yana surutai kinsan har zungure mun kai ya dinga yi. Wallahi kusan sau biyar fa. Ana shidanne dana juyo na kalleshi shine ya fita ba shiri. A yadda na ƙunannnan ai ba wajen bane Hindu. Kinji abinda yake faruwa fa, ina gefe na zuba idanu lokaci kawai nake jira, sabida yara gaskiya. Ina kan adashen da zan biya miliyan ɗaya da rabin da zan zuba zubin farko a bani kin gida fa. Saura wata uku ɗaukana ya zagayo. Bazanma shiga gidan ba har sai na mayar dashi haɗaɗɗe na zuba komai. Abinda yayi mun ya mun ciwo bazan mance ba. Amman jiya ya kuka ƙarke da mijinyawa tun safe naso in kira inji gulma kinsan Allah. Nace irin kallon da yake yi miki kamar zai haɗiyeki anya bai yi miki fyaɗe ba kuwa? " Harara na zuba mata na riga na cika bakina da shinkafa ina kan taunawa, ita kuma sai dariya take babbakawa tare da buɗe tsarabar da nayi mata tana dubawa. Wato ma yai mun fyaɗe? Ai wallahi ba wajen bane, wata fuskar tafi gaban mari. Yadda nake jin zuchiyata a soye bazan fyaɗu ba Allah Luba. Ai shima yasan sauran ya kusanto hannunshi jikina yaga yadda zanyi wasan kura dashi. Ai bazai ma soma ba kinga, yadda yake jin wata iriyar kunyata ta munafurci? To munafurci mana tunda ya iyayin ruf da ciki akan yarinyar da haihuwartane kawai bai yi ba, to kunyar ta mecece inba ta munafurciba. Anan falo ya kwana wallahi banma sani ba yazo dai ya buga mun ƙofa sanda suka dawo masallaci da Azgar" Nan na kwashe duk yadda muka yi na faɗa mata. "Da kin sani kin bashi dama ya fesar da duk abinda yake zuchiyarshi ba dai shikenan ba in kika ji ba Hindu?" Luba kefa kinsan ni inna gama na gama bana dawowa baya, ba wajen bane. Bazan ɓoye miki ba ni ko sunanshi naji an ambata sai zuchiyata tayi duhu wallahi. Bashi da abinda zai ce mun sam. Kuma bazai sake kwana mun a gidana ba ato Luba in tsaya ma in saurari ƙananun ƙarairayinshi ai wallahi bani da aji ma kenan. Sai kace wata jaka?" "Hindu a sassauta ma Mijinyawa haba ƙawata" Harara na sakar mata, ta tuntsure da dariya dama nasan tsokanace kawai. To ke ki ba Sunusi dama ta biyu mana Luba. Ki tausaya mishi, naga duk ya zama wani iri" "Ina ba wajen bane" Dariya muka sake sakawa muka tafa tabb. To zamu mutu ne? Mun daɗe muna hira har kusan goman dare. "Hindu ki tashi ku tafi gida. Ji yadda kika shantake sai kace wata bazawara. Ba wacce miji ke jiran dawowarta ba" Dariya muka sa dukkanmu. To menene marabar dambe da faɗa Luba?" Ba dan rai yaso ba mukai ma Luba sallama na kama hanyar gida Sabira sai bacci take yi a mota. Ina ƙarasowa ƙofar gidan naga motar mijinyawa a gefen gidana. Ƙwafa nayi nace. Zan kuwa kuikuyama mijinyawa. Bazan ɗauki wannan zaryar ba, haka siddan zai sa yarinya ƙarama ta rainani tayi tunanin kwana yake raba mana abinda yake yi mata shi yazo yi mun nima. Yazo ya kwana jiya, yauma ya dawo me zata yi tunani? Yana mana rabon kwana kenan fa hmmmmm subhanallahi. A zuchiyata nake wannan maganar inajin zafi a ƙirjina. To ko dai sabida Mijinyawane Azgar ya ƙi biyoni? Hmm in kuwa hakane yaronnan zai ga ɓacin raina. Ƙararrawa na matsa sau biyu a jere ina jiran Azgar ya buɗe mun. Sai ga mijinyawa yazo ya wangale mun get ɗin mamaki ya kamani na irin ƙarfin halin maza. Yana saye da wandon yadi, da singileti a jikinshi, ga ƙirjinnan ya haye kamar ɗan damben gargajiya. Wani muƙu_muƙun baƙin cikine ya kuma murɗeni. Kutsa kaina nayi cikin gidan shi kuma ya rufe get ɗin. Ke Sabira tashi ki shiga ciki mun iso gida" Na faɗa ina bubbuga Sabira. Murfin motar Mijinyawa ya buɗemun yana mun murmushi tare da amsar jakata. Na ko haɗe girar sama data ƙasa. "Tutar so sannu da shigowa maraba" Dubanshi nayi na girgiza kai kawai na fito nayi shigewata ciki. Sai kawai naga Qasimu a falo yana mun sannu da zuwa. Hmmm ohh shi aka ɗakko mun? Raini kenan shi wannan kamar ma baisan girman zunubin daya aikatamun ba ko? Qasimu ne zai sasanta wannan lamarin mai girman da yayi lalacewar da babu abinda za'ayi a gyarashi. Lallai na Mijinyawa wasane. "Hindu barka da dawowa sannu? " Babu wasa a fuskata kamar yadda aka saba. A hakan muka gaisa nayi wucewata naga jikinsu yayi wata iriyar muguwar mutuwa. Ina shiga ɗakina na danna sakata. Banɗaki na faɗa nayi wanka na fito. Azgar ne yazo yana buga mun ƙofata. Saida na saka kaya na buɗe mishi ya shigo. "Ammi Abba ne yace in miki magana suna falo. Ammi dan Allah kije kar ki ƙi zuwa kinji. Nasan abinda Abba yayi miki da ciwo amman ki saurareshi ko dan albarkacinmu" Kallonshi nayi muka yi murmushi a tare ina jin son su na huda ni. Azgar akwaishi da ƙoƙari da kulawa akan iyayenshi, nasan baya wuce ramar da yaga munyi ni da ubanne yasa duk jikinshi babu daɗi. Ba yara bane sun san dukkan abinda ke faruwa, ai suna gani ubansu ya auri Asama'u ni dasu dukka abun bai yi mana daɗi ba. Shine dalilin da yasa kaƙi bina, sabida ka buɗe ma Iyayenka gida su shigo ko?" Kai ya sauke ƙasa. Ai saina shaƙeshi na haɗashi da bango da ƙarfin da ni kaina nasan yafi ƙarfinshi, idanunshi suka firfito, ai sai kuka kawai ya sake. Sake shi nayi da sauri, ina harararshi ba ƙaramin haushi ya bani ba wallahi, ya zai mun haka. "Ki mun afuwa Ammi, kiyi haƙuri wallahi ya roƙeni ne in mai hakan. Amman bazan sake ba" To shikenan ganinan zuwa Azgar ya kan naka ya dena ciwon amman, ko dama shima kan baya ciwo? " "A'a Ammi ina ta shan magani amman gaskiya babu wani sauƙi, jijiyoyin kaina ciwo suke yi mun sosai" Kallonshi nayi naga idanunshi sun yi jawur dasu ga wata jijiya a gefen idanunshi daya tsaya. Duk da dai ya sha shaƙa. "Azgar akwai abinda yake damunka ne daya haddasama ciwon kannan, ko kuma karatune? Baka ƙarya baka taɓa yi mun ba, kada ka soma. Duk duniya baka da kamar ni meke damunka yarona? " Murmushi yayi ya sauke kanshi ƙasa yace. "Ammi bansan ta ina zan faɗa miki damuwata ba, amman ina cikin damuwa sosai" Murmushi nayi nace mishi. Ka zauna ga kujera ka jirani inje in dawo sai in zauna ka warwaremun matsalar kaji ko? " Na ƙarashe cike da nuna kulawata gareshi. Sai da na tabbatar ya zauna kana na fita na shiga falo da sallama na zauna a kujera. Gani Qasimu kun aika yaro kuna nema na, Allah yasa lafiya dai ko?" Na faɗa idanuna akan Qasimu shi kuma mai gayya ina jin idanunshi na yawo ajikina hakan yasa banyi gigin duban inda yake ba. Sassauta murya Qasimu yayi yace. "To Hindu ni nama rasa ta ina wallahi zan soma maganar ko kuma in kirata da roƙo." Numfashi ya zuƙo daga huhunshi ya fesar kafin yace. "Hindu duk wanda akace yayi haƙuri an gama cutar dashine. Mijinyawa ya faɗamun dukkan abinda ya faru a tsakaninku. Haƙiƙa abinda ya faru al'amarine mai girma wanda ya kai kiyi fishin da kika yi, domin ki huce babu laifi a ciki Hindu. Amman wallahi bana bayan Mijinyawa tun farkon fari, sabida dai bani da iko dashine shi yasa dole na zama ɗan kallo. Abunda ya shiga tsakaninshi da Asama'u wani abune na ƙaddarar da bawa bai isa tsallakewa ba. Dama shi shaiɗan burinshi babba shine shiga tsakankanin ma'aurata musamman masu fahimtar juna irinku. A iyakar ƙuruciya zuwa samartaka mijinyawa daidai da hannun mace bai taɓa riƙewa ba. Kuma kema shaidace tunda kun jima kuna gabza soyayya. Wannan abinda ya shiga tsakaninsu wani abune da zamu mishi kallo a matsayin ƙaddara da tsautsayi. Dan Allah kiyi haƙuri ki yafe mishi ya tabka kuskuren da bazai gyaru ba. Amman nadama muraratan a cikinta yake wallahi yayi nadama ya shiga damuwa sosai. Hindu bayan tafiyarki har zangon baƙi mijinyawa ya koma, sai ni naita tausarshi ma kafin ya dawo gida. Tunda abun ya faru har yanzu zuchiyarshi a cikin ƙunci take. Hindu kalamaina sun ƙare, yawuna ya ƙafe, harshe da haƙori ba zasu iya sarrafa miki yadda mijinyawa yake nadamar abinda duk ya faru ba. Sannan kinsan yana sonki irin son da ba ko wacce mace bace ta samu soyayya da sadaukarwa irin wanda ke kika samu ba. Ayi haƙuri ayi haƙuri. Ki tuna yara da irin zaman da kuka yi a baya. Ki auna da alkhairanshi Hindu sai a yafe mishi a fuskanci gaba. Duk wannan akan Asama'u dai akeyi to maganar Asama'u yazo ƙarshe ma ayi haƙuri. Shafinta an kulleshi abadan. Dan Allah kiyi haƙuri, abinda akayi miki da zafi" Yayi shiru yana sauraren ko akwai abinda zance. Ni kuma nayi shiru, duk maganganun da yake yi na sokiburutsu ni bama shigata suke yi ba bare har su taɓa zuchiyata in sakko ba. Sabida ba wajen bane, to Qasimu ne zai sa in sakko, ko a tunaninsu fishi nake yi ne? Wallahi da fishin nake yi in akace ya matso inda nake ma, ai bazai matsoba. Balle har ya tattagomun abokinshi sun wani sha ankon yadi kamar abokan ango, ga uban kwalli dama_dama caɓa_caɓa a idanunsu. Duk abubuwan da yace in kalla, shi mijinyawan me yasa shi bai kallesu a yayin aikata abinda ya aikata ba? Wato su maza suna da damar yin duk abinda suke so, sabida gadarar dole ne ma a yafe musu ko anƙi ko anso. Ko da yake malam bahaushe ma cewa yayi duk abinda namiji yayi adone. Mace dai itace a ƙasa duk ƙanƙantar abinda tayi sai ya taɓa rayuwarta shi kuma yaci bulus abinshi. Ado aka kira iskancin maza, a gabansu, a cikin kunnensu, tun suna yara an cusa musu wannan maganar mai cike da muni. Amman a hakan wai mijinyawa ya ba mata tausayi har suna taya Qasimu godona, wai in yi haƙuri mu ci gaba da zama. Ashe ba Hindun bace ma. Jin naƙi magana Qasimu ya sake cewa. "Sai batun sabon gida. Na taya ki murna sosai da Allah ya baki nasarar mallakar muhalli irin wannan. Amman muna roƙon ki yi haƙuri ki kuma daure ki koma ɗakin ki Hindu, a taimaka ko dan sabida gudun maganar Nanno dan nayi imani ba zata yadda ba. Yanzu haka ma gobe tana hanyar zuwa garinnan ne, kuma akan batun wannan gidanne maganar gaskiya. In yaso wannan ɗin sai ko haya ne a saka. Kiyi haƙuri duk dai akan zama da Asama'une to bata gidan a halin yanzu dan Allah Hindu kice wani abu, a duba yarannan sun girma bai dace ace har sun san abinda ke faruwa a tsakaninku ba" Mijinyawa ya ɗaura da cewa. "Giwar mijinyawa nayi miki alƙawarin zaki sameni fiye da yadda kika sameni a baya. In sha Allah bazan sake aikata abinda zai dameki ba. Giwar mijinyawa kiyi haƙuri nasan nayi kuskure mai girma. Wallahi kunyarki nake ji fiye da yadda kike tunani, kiyi mun aikin gafara ki tuno da irin soyayyarmu mijinyawa naki ne ke kaɗai har abada babu wata mace da zata... " Ƙur nayi mishi da idanuna, waɗanda sabida ɓacin rai har ƙanƙancewa suka yi, cike da tuhuma nake kallonshi, duk sai ya dibibice nasan abinda na tuno shi ya tuno irin kushe halittar nonona da ya dinga yi a wajen Asama'u da irin yabon zatinta daya dinga yi. Ya ce mun bagidajiya, itama tace mun bagidajiya. Alhalin sune gidadadawa ƴan ƙauye. Yace mun mai tumbi, yace mata suna suka tara, kenan ni Hindu ba mace bace rako Asama'u duniya nayi. Wai da duk wannan inci gaba da zama dashi? Asama'u fa in ba bacci tayi ba, bana ko runtsawa, gata da laulayi ciwo babu irin wanda batai ba. A kanta meye ni Hindu ba'a faɗamun ba. Haka zan rungumeta akan ƙirjina ina jin tsabar sonta kamar in maidata ciki in haifota. Amman yau itace ke kirana bagidajiya, sakamakon tsirara da mijinyawa yake yi a gabanta. Ya salam wai kunsan zafi da raɗaɗin irin wannan abun kuwa? Kunji amman wai shi nawa ne shi ni kaɗai. Hiye maza kenan wacce bata san yaudarar maza ba an sha da'ita. Murmushi kawai nayi da naga ya kasa iya furta wata kalmar yayi shiru yana ambaton. "Hasbunallahi wa ni'imal wakil. Billa nasan ba zaki yadda da duk abinda zai fito bakina ba. Giwar mijinyawa ki yafe mun" Har gaba da abada kuwa. Ai da ka ƙarashe yaudarar daka tasamma furtawa Magawata, da baka fasa ba. Shure_shure ai baya hana mutuwa ko?" Jin na ambaci Magawata sai suka kalleni Qasimu hannu a baki na ta'ajibi. Tasowa yayi yazo gabana kamar mai neman gafara ya tsugunna, wallahi a kan guiwowinshi yana rokona da duk kalaman rarrashi da roƙo. Nasan yana sona fiye da tunani amman narantse da Allah inji ɗigon tausayinshi banji ba. Ni sake tunzurani ma haƙurinsu ya bani, a ganina an raina ni ƙarshe da aka rasa wa za'a ɗakko sai Qasimu, Qasimu fa. Miƙewa nayi na dubi Qasimu nace. Nagode Qasimu mu kwana lafiya, dan Allah a gaishe mun da Baraka. Bari in ɗakko tsaraba a kai mata tunda dai kazo. Sannan nan gaba kada ka sake tunkarata da irin wannan surutan bana so, na ɗaga maka ƙafa sabida ƙawata Baraka ne kawai" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. "Baraka zata ji, zata ji Hindu" Haka yaita maimaitawa wallahi kamar mahaukaci fa. To ya faɗa yafi sau shidda. Na gigita Qasimu sosai ya gama faɗen duk abinda yake son faɗa amsa ce babu, bani da wannan lokacin a halin yanzu, ba wajen bane. Na fita a hankali nake takawa dan jiri ke neman kayar dani. Inaji Mijinyawa na cewa. "Qasimu ka taimaka kar in rasa Hindu mu kwana muna bata haƙuri inna rasata komai zai iya faruwa dani" Ai kuwa abinda ma zai faru da kai yadaɗe bai faru dakai ba ma. Dan Hindu ai shekararku biyu da rabuwa, na faɗa a zuchiyata. Daga cikin dogayen rigunan dana siya ma kaina na saka ɗaya a leda da dabino naba Azgar nace yakai ma Qasimu daga nan ya rufe mun gida in sun fita sai ya zo. Bai jima da fita ba ya dawo yazo ya zauna a ƙasan kafet ni kuma ina zaune a bakin gado. Murmushi nayi mai sauti nace. To ina jinka kada ka ɓoye mun komai Azgar. Ni mahaifiyarka ce inason ka sani cewar babu wacce ta fini kusanci dakai, kuma ni zanfi fahimtar abinda ke damunka" "Hakane Ammi dama akan Kubra ne sai wahala take bani kwana biyunnan. Shekaranjiya da daddare dana kirata ma namiji ne ya ɗauki wayar. Ko da sake kiranta bayan awanni shine sai take ce mun saurayinta ne yazo daga najeriya lokacin dana kirata" Tausayi ya bani ainun. Nasan zafin soyayya da wahalhalunta gaya. To amman Kubra ta dace da Azgar kuwa rayuwarsu ba zata zama daidai da juna ba sam, sannan zata yadda inya aurota ya kawota Najeriya kuma ta zauna tayi biyayyar Auren ma?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace dashi. Naji daɗi sosai daka tunkareni da maganarnan ba tare da ka rufe mun ba. Dama akwai tulin tarin tambayoyin da nake son yi maka na bari ne inna dawo sai mu tattauna. Yanzu Azgar tana ƙasar Landan kai kana nan Kano a haka zaku yi Auren ne? Shin kana ganin kun dace da junanku kuma sa'annin auren junane ku? Amman bansan yaya kuka tsara yadda zaku rayu ba" Dariya yayi mun ya ɗago yace. "Ammi ai akwai yarta dake Aure a Gombe. Mahaifinsu baya musu sha'awar auren turawa sam. Sannan ni ban rufeta ba na faɗa mata mu ba masu kuɗi bane, kuma inna gama karatuna soja nake son zan shiga da izinin Allah sabida in cika burinki. To wannan ma ya ƙara mana kusanci yadda ta nuna tana son jarumin maza sosai. Kuma a yanayin yadda take ina kyautata zaton zamu zauna lafiya bata da dogon Guri" Gashi kai ba jarumi bane amman in ka shiga soja zaka koyi jarumta dolenka Azgar. To shikenan Allah yasa mu dace, sannan kayi ta adda'ar neman zaɓin Allah akan aikin sojan in akwai Alkhairi Allah ya tabbatar, in babu ya maye maka gurbinshi da mafi alkhairi. Itama Kubra ka haɗata da Allah ka nemi zaɓinshi in itace shikenan sai kaga kunyi aurenku, tana da hankali gaskiya. Amman ka rage yawan damuwa dan kawai kaji saurayi yaje mata. Ai macece kuma kyakkyawa mai ilimi. Azgar baxai yiwu ace kai kaɗai ne saurayinta ba. Kai dai kayi naka bakin ƙoƙarin ka sace zuchiyar tata, shikenan fa a cikin dubu sai kaga ta zaɓeka. Kaima yana da kyau in biya maka kaje ka dubota iyayenta su sanka kuyi magana ido da ido. In sha Allah zanyi ma adashen kuɗin jirgi in Allah ya yadda shekara mai zuwa sai kaje ku gana lokacin ka kammala digree ɗinka, itama ta kammala nata. Dariya yayi mun sosai da sosai nasan na farin ciki ne zallah. To wa nake dashi bayan su. To shikenan damuwa ta ƙare ko akwai wani abun?" "Akwai Ammi. Zainab nake so ayi ma magana dan Allah ta dena damuna da kira ko saƙon karta kwana. Bana so in rufe layinta ne sabida zumunci" Wallahi mancewa nayi wacece Zainab ma wai ashe Zainab ta wajen Uwatale yake nufi. Ni dariya ma abun ya bani wallahi. Toh ikon Allah Zainab kuma Azgar. Yayarka fa Zainab ta wajen Uwatale? Kada ka damu zan ji da wannan amman ka sani ko bayan raina ban yadda ka auri Zainab ba, bama ita kaɗai ba duk wata mace data fito tsatson mahaifinka ban yadda ba" "Me yasa kika ce haka Ammi ko dan kina tunanin basa sonmu ne kika ce hakan? " Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Azgar kai yarone ba zaka gane ba. Amfani suke so suyi daku kawai ba wai soyayya domin Allah ko dan haɓaka zumunci bane. Wallahi ko zan yadda da auren dangi banda yaran cikin ɗakin Uwatale. Azgar ko Zainab ɗin kake so in bar ɓata lokacina akan Kubra ne? Ka san dai ta girmeka ko " Dariya yayi yace. "Allah shi taimaki Giwar Abba ranki shi daɗe Tutar so da girman kujerarki duk abinda kike so shi nake so billah" Dariya muka yi tare ina son Azgar sosai wallahi. To shikenan jeka ko akwai wani abunne? " "To Ammi kada kiga kamar na dameki akan Abbane dama. Kinsan Asama'unma bata nan tun washegarin da sukai wani faɗa da Sabira akan ki akace washegari Abba ya ɗauketa suka fita wai tana gidansu" Labari ya kwashe ya faɗa mun duk yadda akayi, ya ɗaura da cewa. "To Ammi Abba tunda kika tafi yake cikin damuwa, ramarki da tashi suna da alaƙa sabida tun tasowarmu bamu taɓa riskarku a cikin halin faɗa ba" Azgar kenan yanzu dai kazo ne mijinyawa ya turoka, yayi amfani dakai wajen shawo kaina ko? " "A'a Ammi wallahi baisan zan miki zancan ba. Ammi jiya ya daɗe a falo yanata zurga_zurga ya goya hannunshi. Tsoro nake yi kar wani abun ya sameshi" Ba shakka Azgar, ni kuma baka tsoron wani abun ya sameni ko, sabida kaima namijine kamar mijinyawa ko? To yayi tashi kaje ka kwanta kaina ciwo yake yi, ina fatan ka rufe mun gidana? " "Ammi ki mun aikin gafara. A cikin ku bana kare kowa bana ganin baƙin kowa dukkan ku nawa ne" Dariya yasa nayi dole yadda ya marairaice shi tsiyata dashi rauni, nakasune a wajen namiji rauni. Namiji a dake aka san zuchiyarshi sai wajen daya kamata yayi rauninne ya dace ace yayi. Banyi fishi ba ɗan albarka. Amman bana son ka sake saka bakinka a wannan ƙadiyar, ka rufe mun ƙofar? " "Abba ya rufe yananan bai tafi ba, yama kwaso kayan sawarshi mun jera a sib ɗin ɗakina" Kai kawai na girgiza Azgar ya tafi ya barni a tsaye ina gaban mamakin mijinyawa mai kwaso kaya. Ya kwaso kaya fa Azgar yace wai har sun jera a sib ɗin ɗakin Azgar. Na fahimci so yake mu raba abun faɗe tsakanin ni dashi kenan a gaban yara. To shikenan wallahil azeem gobe zai sha mamaki, irin wanda ya shayar dani, zai ga tambotsai na haƙiƙa kuwa. Hiye ba shakka wannan ƙarfin hali da yawa yake. Hmmm maza kenan in sukai wani abun kamar kaita dukansu. Kamar wasa bacci ya ƙaurace a idanuna abubuwa da yawa naita tubkewa da warwarewa. Ina hango rayuwarmu ta baya ni da mijinyawa, da yaranmu, a lokacin suna ƙananan yara da Azgar da Asama'un da ya mayar da'ita matarshi. To naji Qasimu yace Asama'u bata nan. Ga labarin da Azgar ya bani kuma? Gidan haya ya kama mata ya sakata a ciki kenan koko yayane? Inma gidan hayar ne tunda ita itace sai ya kama mata ai babu mamaki a ciki. Amman ni nayi juyin duniya mu sake gida, mu kama haya ko dan kaucema gori, da ƙananan iskancin Uwatale. Amman sai yace Nanno ta hana, umarninta ne dole sai dai mu zauna a gida ɗaya. Hmmmm Allah dai ya kyauta in ana cin ɓaure ba'a tona cikibshi. Ga maganar Zainab ya tsayamun a raina sosai Wannan fa duk sharrin mutuniyarku Uwatalene. Yarinya ta gama kwantai sa'anninta suna gidajen mazajensu, shine ake so a jona ta wajen Azgar ƙaninta abun kunya. Da maganganun Qasimu suma sai nuƙurƙusata suke yi da yasan irin baƙin cikin ban haƙurin da yazo yayi mun da nayi, da baima soma ba, a tunaninshi shi ya shiga yayi sulhu ne, baisan sake damalmala al'amarin yayi ba. Harda cewa in koma ɗakina sabida Nanno gobe tana hanya. To sai me dan tana hanya, ni da gidana akwai wani ikon da za'ayi munne. Ashe gobe za'a kwashi ƴan kallo kuwa tab. Karatun Qur'ani na saka a wayata idanuna a rufe inata ambaton Allah bansan bacci ya kwasheni ba sai jin kiraye_kirayen sallah kawai nayi. Na faɗa banɗaki saida nayi wanka na iya ɗauro alwala idanuna har yaji suke yi tsabaragen baccin da nake ji. A daddafe naje na tabbatar yaran sun tashi, na haɗu da Azgar tare da mijinyawa a daidai Kicin suna shirin fita. Jin motsin ƙofata yasa suka juyo. Sosai mijinyawa ke kallona. Zai ga abinda zan yi mishi, yadda ya kwaso kaya haka zai ɗebe kayanshi, yaga ina mishi sanya ne hmm. Ƙila saina shaƙeshi idanunshi sun firfito zai gane ba wasa nake yi ba. Tabb maza wallahi akwai soyewar idanu. "Kin tashi Tutar so? Mu mun tafi masallaci Sabira ma na tasheta" Adawo lafiya na faɗa a ƙasan maƙoshina ya sakar mun lafiyayyen murmushi mai muni yace. "Allah yasa mun gode da adda'a" Suka fita nabi bayanshi da harara. Ɗakin Sabira na leƙa dan tabbatar da ta tashin kuwa, tana kan sallaya tada kabbararta kenan. Ƙofar na mayar mata na rufe na koma ciki na yi sallah ido a rurrufe na koma gado ko minti biyu banyi da hawa ba bacci ya kwasheni. Mrs Bukhari. To mu jira mu ga abinda gobe in Allah ya kaimu zata zo dashi kuma....TSURON TSIRIN... TSANDAURI.. LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA UKU (3) _Idan kika sai littafinnan nawa mai suna TSURON TSIRIN TSANDAURI tamkar kinyi sadakane kai tsaye a asusun marayu._ _Littattafaina kuɗinsu sadaukarwane ga iyayen marayu har zuwa ranar da zan dena rubutu._ _Ko nawa kika cire kika saka marayu zan yima hidima dashi wallahil azeem ko kuɗin Data bana cirewa a kuɗin littattafaina, marayu kaɗai nake yima hidima._ _Saima ƙarawa da nake yi da kuɗin kasuwancina akan kuɗin da littafi ya samar mun._ _Kuzo ku siya mu samu ladan marayu tare daku, ga lada, ga karatun littafi Hajiya._ _Wannan link ɗin na ƙasa ɗaya ne daga cikin aikin da nake yi da kuɗin wajen hidimtama marayu, shafin gidan Rediyo, da talabijin na ZINARIYA TV jos ne suka ɗaura domin sun kai ziyara a lokacin da aikin tallafin yake gudana._ _Nayi hankane ba dan riya ba sai dan ina cewa marayu nake ma hidima da kuɗin, amman ku baku taɓa gani ba, shi yasa wannan karon na zaɓi ku gani, daga yanzu kuma zaku dinga ganin dukkan aiyukan da nake yi da kuɗaɗen littattafaina, hakan zai ƙara mana ƙarfin guiwa __Daga ɗari bakwai zuwa sama yadda kike jin zaki iya zubawa baki faɗi ba saima romon lada da zamu samu a tare_ _Mu tausayama marayu wallahi marayu suna cikin wani hali na ni ƴasu, har jari ina tallafama da iyayen marayu jarin ƙananun sana'a domin dogaro da kai_ Nagode sosai son so Asusun sanya kuɗi 9153081057 Buhari Ibrahim ladan Palmpay Surutu nake ji sama sama a mafarki, tun inaji a mafarki harna farka na tabbatar a cikin gidanne surutunnan yake tashi kamar hauka, ko ince yaƙi ma. Muryoyin na nutsu ina saurara tabbas na jiyo muryar Yaya Jamila, dama Qasimu yace jiya Nanno tana hanya nasan itama dole da'ita akazo, babu kaffara nasan Uwatale dole ta biyosu, ko dan taba idanunta abinci taji daɗin yin gulmar data saba. Ohh ni Hindu to wai su magulmata menene ribarsu ne ma? . Sakkowa nayi na wuce banɗaki nayi wanka na fito. Lesiri mai tsada na manyan mata na dandatso na saka, na ɗauki sarƙa da ɗankunnena tsomen zinare mai tsadan sosai wanda in ba harkar gwal kake yi ba bama zaka iya tantancewa ba, a Saudiyya muka siyo ni da Yaya Zubaida zamu ci da buguzun dashi, duk da masu tsadanne kamanninsu da gwal abun ba'a magana. ( Anty Zee collections tana kawosu daga saudiyya dandatsa_tsandatsa sai kun gani. Me so tayi mata magana) Na yi kwalliya mai sauƙi na cika turare sosai ta yadda dana fito kowa zai ji ƙamshina, babu wasa a cikin lamarina wallahi bazan ragama duk wacce ta nemi ɗaga mun hankali ba. Kafin in buɗe ƙofar ma tuni an turo Azgar wai yayo kirana hmmm. Ƙat _ƙat na buɗe ɗakina na fito. Sai naga falon kamar a cike yake da mutane haka na kitsa kai na shiga, ƙanne da yayyen Mijinyawa duk suna falon tare da Goggo mahaifiyar Uwatale da ita kanta Uwatalen harda matan su Gambo da Zainab ɗin Uwatale. Su Azgar duk suna zazzaune. Sallamata da ƙamshina yasa duk suka juyo suka zuba mun idanunsu, ni kuwa tafiya nake daɓas_daɓas irinna cikakkun manyan mata waɗanda suka san kansu, wai damma na rame da sai sun ga salo. Waje na samu na zauna a ƙasa sabida rashin waje a kujerar. Sannunku da zuwa Nanno ashe kune, kun zo ina baccine ai" "Ba shakka Hindu mulki, ke kina bacci shi kuma kin mayar dashi ɗan aiki yana madafi yana miki girki, ke da yaranki kuma kuna baccinku. Kinbi kin gama asurceshi kin kanainayeshi da kisisinarku ta ƴan boko da muggan asiranku na Kanuri, Allah yana ganinki kuma ya fiki. Kuma ni ɗinnan bazan taɓa yafe miki ba" Cewar Nanno a cikin wannan taron ga yarana a wajen, akwai abinda yafi wannan ciwo a tozartaka a idanun yaranka suna ji, suna kuma gani fa. Kallon mijinyawa nayi yana gurfane a gaban Nanno shima ni ɗin yake kallo da idanunshi masu mun kyau a da a yau saina gansu munana mayaudaran idanu, mazinatan idanu masu kallon tsaraicin yarinyar da bata da maraba da ƴa. Ina kwananku Goggo kunzo lafiya?. Dakewa nayi, basu isa sun sani ɓacin rai ba wallahi. "Lafiya lau Hindu ashe kuma kin dawo ga sabon gida kun tare a ciki babu wanda yake da ƙwayar mutunci a idanun mijinyawa da zai iya sanar dasu ya sai gida ba. Taya ɗanmu zai sai gida bai iya faɗa ma ko abokin tagwaitakarshi ba. Ranar da zaki dawo sai kawai nemanshi akayi aka rasa, to me hakan yake nufi. Kuma wannan tabbas shirinkine. Kin hanashi zama da Asama'u hankalinki ya kwanta yayi mata saki mara kome, shine kika ɗaukeshi a cikin ƴan uwanshi sabida ki raba zumuncinsu, kin janyeshi zuwa naki dangin sai yadda aka juyashi, yadda kika dama haka du suke sha. Ke ƴannan mulkinki yayi yawa kiji tsoron gamuwarki da Allah. Kina cikin gidannan yana madafi ya haɗa zufa yanata miki girki ke kuma sai dai ki caɓa ado ki fito kici abinci kin maisheshi ɗan aikin gidanki. Ashe dama tsawon wannan lokacin baki dena saka shi aikace_aikaceba' ke a gidanku haka Babanki yake yima Mamanki aikine sai yadda akayi dashi? " Carab Yaya Jamila ta karɓe zancan ta hanyar cewa. " Sabida mugunta da ƙin danginshi shi yasa tasa ya siya mata gida a nesa kuma ta hanashi ya faɗama kowa, ji nisan tafiyar da muka kwaso fa. Amman ance ya ƙara aure yaƙi yace baida kuɗi sai kuɗin siyama Hindu gida ita da yaranta. Ai kinga ko ɗakin baƙi babu a gidan sabida mune baƙin nesa da zamu zo mu sauka a gidan ƴan uwanmu, ita nata dama wuni zasu zo su yi kawai. Wannan lamari abun dubawane. Wannan aure ya ci ace ya ƙare tuni gaskiya. A gaskiya na girgiza da wannan lamarin jibi gida katafare" Ina zaune ina saurarensu ina nazarin kalmominsu, in kalli wannan in kalli wancan. Naji zafin sako mun iyayena da suka yi shine kaɗai abinda yayi mun ciwo banda sauran maganganun domin na saba da jin waɗanda suka fi wannan ɗin ma. Jahilci, da ƙauyanci zafinsu yafi na hauka wallahi. Sai mamakin wai mijinyawa ya saki Asama'u saki mara kome nake yi. Ko menene ruwana a cikin sakin oho ya saketa ya zauna da'ita babu abinda zai sauya na abinda ya aikatamun. Ta baya dai ta rago, biyu babu ne zai sameshi wallahi. Nanno wannan gidan nawane ni na sai kayana da kuɗina, ina aiki ina samu Alhamdulillahi, duk abinda kuka gani a cikin gidannan babu sisinshi. Bama gidan kaɗai ba, duk abinda kuke ganin yana faruwa da kuɗina nake yi, wallahi sai dai shi ya shiga rigar alfarmata tun muna ƙauye bare yanzu. Yana da kyau kaima danginka bayani tun farko sabida akwai mutuwa akwai rabuwa, kar ka mutu ko in mutu mu tafi mu bar baya da ƙura. Anata maganar gida ka wani ja baki kayi shiru. Gida dai mallakinane babu ko bulo ɗinshi a cikin gidannan. Sabida haka bana son wani surutai da Allah" Na ƙarashe ina kafeshi da idanu. Babu ko ɗigon ɓacin rai a fuska da muryata a nitse nake magana su ɗin me, me akayi aka yi su da zasu sani ta da jijiyoyin wuya ni kuwa. "Nanno tun kafin Hindu ta fito na shaida muku wallahi bani nasai wannan gidan ba, itace ta siya da kuɗinta, kuma bani na sake mata mota ba itama da kuɗinta ta siya, bani da kuɗin da zan sai gida da mota kamar yadda na faɗa miki. Wallahi bani da kuɗi kallon kitse kukai ma rogo. Hindu kuma bata ma san na shiga madafi ba wallahi bacci take yi Nanno" Sai ɗakin yayi shiru jikkuna sukai sanyi ni dai fuskata fes da fara'ar dole ba dan tsoro ba kuma nake yi haka kawai ni nake in so akeyi in yi kuka, to wallahi ko man taiga za'a ziraramun a idanuna zan daure. In kuma dariyar akeso in yi kome za'ayi na abun dariya a wajena bazai zama na dariya ba. "Ita Hindun har tana da mazajen kuɗin da zata sai gida ta sake mota? To in ita ta siya sai ka kwaso kayanka gandan_gandan ka biyota ta zama mijin kaine matar kenan, tunda gata ta fito fes da ita ta zuba gwala_gwalai tana baza ƙamshi, kai kuma kana madafi kanata haɗa zufa ka kaɓakin kayan abinci daka siyo ka jibge mata. Sannu ke kuma ƴar gidan ƙaruna ƙarshen kuɗi. In ba'a yawon barbaɗa ba ina zaki samo mazajen kuɗin siyan gida da mota" Cewar Yaya Jamila. Murmushi nayi nace da'ita. To sai me Jamila dan mijinyawa yayi mun girki, ai na isane shi yasa yake yi, ko na saka shi ko ban sakashi ba, kuma wallahi dolenshi yayi. Ke naki mijin me ya sameshi da baya miki, ko dai baki kai bane shi yasa ko? Hmmmm batun ɗiyar ƙaruna da kike yi. Mahaifina ba ƙaruna bane, sai dai mutumne mai ilimi, da sanin ya kamata, ga natija, ga sanin hakkin mutane, bugu da ƙari ubana soja ne. In duk kun gaji da bautar muku da ƙani da nake yi. Ba gashi ba, asa ya sake ni, ya tattare kan kayanshi ya bar mun gidana mana. Kai kuma in ka cika ka sauwaƙemun a gabansu gasu, sai ku fice mun a gidana" Gabaki ɗaya ni suke kallo, illahirin mamaki ya lulluɓesu. "Ba shakka shanyayye ai kana jin abinda ƴar boko fitsararriyar, tantiriyar matarka take cewa. Su Nanno ai kuna ji, Goggo kin gani da idanki" Mijinyawa Babba yace. "To Yaya Jamila ai dukiya a ɓoye take sai an so ake ganinta. Kuma ni banga laifi dan mijinyawa matarshi ta siya musu gida ya dawo ba. Naga duk irin arzikin da Hindu zata samu nasu ne su duka tunda karatun ma da gumin halak ɗinshi tayi. Hindu Allah ya sanya alkhairi gida yayi kyau" Murmushi nayi nace. Nagode sosai Baban Zainab, abinda ka faɗa gaskiya ne, da bai sani a makaranta naci gaba da karatu ba ƙila da ban kai haka ba a tunaninka ko? Sai dai ka sani ko dashi ko babu shi, ni ƴar karatuce a ciki na taso. Shi da dai ban shigo rayuwarshi ba, da yananan ƙila a ƙauye, ko kamarka haka dai. Alhamdullahi ko da naje Landan na haɗa mastas ɗina nayi amfani da damar dana samu." Kuka Nanno da Goggo suka fashe fa dashi ƙaƙas wallahi. Ina zaune ina kallon abun almara wallahi. Duk yaran suka rufu a kanta, ni dai da yarana muna zaune mamaki na neman halakamu. "Allah ya'isa Hindu. A gabana kike cema ɗana in ya cika ya sake ki. Gashi ya nuna miki bai cika ba, tunda har yanzu kina amsa sunar matarshi. In dai nice na haifeka nonona ka sha to ka saki Hindu a take anan, kana ka tattaro kayanka kazo mu wuce harda yaran ma wallahi " Yarana na kalla, ina gani Azgar na buɗe bakinshi da mamaki a fuskarshi. "Nanno kiyi haƙuri wallahi in duk duniya zasu taru a kaina bazan iya sakinta ba. Wallahi bazan iyaba ki mun rai. Nawata ka sa baki bazan iya bane. Sannan Hindu bata yi ma kowa komai ba. Akanme to zan saketa. Nanno kiyi haƙuri bazan iya ba, ina miki biyayyar duk data dace, amman ina son Hindu kiyi mun afuwa" "To Magawata me zance. Hindu fa kana jin maganganu miyagu da take faɗa. Yaya jamila tana faɗa itama tana faɗa. Kuma ita tace in ka cika ka saketa. Ai ko saki ɗaya ne sai kayi mata ta san ka haifu. Kasan ni ban fiye shiga shirginku ba, amman fitsarar ta.... " Kai Nawata ka shiga taitayinka dani ahir ɗinka. Ka iya bakinka kana jina ko? Ba wani ɗan abu ta kazan da ya isa ya zo har gidana yace zai tayar mun da hankali. Sabida haka ku tashi ku fice mun a gidana, ko dole ne, ko kuma zuchiyace babu?" Ranar anyi ɗauki babu daɗi wallahi dani da Jamila da Uwatale. Dan Uwatale ta tashi tsaye kamar zata dakeni. Ni kuma a lokacin jikina har rawa yake yi. Bansan sanda na zabga mata mari ba. Na kuma sharara mata mari. Inaso in sake marinta sai ga hannuna a kan ƙirjin Nawata na mara. Idanuna ya gama rufewa jira nake wani ya tunkaroni in dira a wuyanshi. Duk sun ja baya suna salati, nanno ta ƙanƙame ƙanwarta Goggo ƙam. Mijinyawa da Azgar ne suka nufo ni da zummar riƙeni. Hannayena nasa na hankaɗe Mijinyawa yaje ya zauna da ƙarfi a kujera, dashi da kujerar suka kifa. Na ɗauke Azgar da mari, na rufeshi da duka tako ta ina kawai, ya ma kasa karewa. Ita Sabira wajen Ubanta ta nufa harda kukanta. Da ƙyar ƙurar ta lafa nai musu wankin babban bargo, idanunsu duk suka raina fata. Suna takure a waje ɗaya tsoro na neman halakasu. Fuu na sa kaina na fice a ɗakin. A ɗakin Sabira na zauna ina jijjiga. Ina hango su Sabira suna kai musu kayan kari, marasa zuchiya kawai. Naga yayo cefane da yawa harda buhun shinkafa, da katon na taliya, katon na makaroni, da wake, doya, man gyaɗa, manja, maggi, ƙwai, kayan shayi. Azgar ne ya zubo mun soyayyar doya da shayi. Ɗauke doyarnan. Akwai kayan shayi a ɗakina wuce kaje ka haɗo mun dashi" Zai yi magana na nuna shi da yatsana jikina na wani irin rawa. Da sauri ya miƙe zumbur. A ɗakin Sabira na karya su kuma nace suje falo bana ma son ganinsu suma ɗin. Ina shan shayi mijinyawa ya turo ƙofar ya shigo ya zauna a bakin gadon, ni kuma ina daga ciki. Tunda ya buɗe ƙofar nayi mishi kallo ɗaya ban sake ɗagowa ba bare mu haɗa idanu. "Hindu kiyi haƙuri da abinda su Nanno suka yi miki, nasan in da sabo mun saba kiyi haƙuri kinji?" Naji, nayi kuma" Na faɗa a taƙaice, sai yayi shiru can yace. "Na saki Asama'u sabida na gane nayi kuskure mai girma Hindu. Na rantse miki da girman Allah ban kwanta da Asama'u ba tunda na aureta, san... " Da Allah mijinyawa bana son jin komai. Kada ka sake kiran sunan tsinanniyar yarinyarnan a gabana kar ka sake nace, ka kusanceta baka taɓa kusantarta a rayuwarka ba, ni fa inka lura bashi ne a gabana ba. Sakinta da kayi zaluncine kuma. Ai dama maza kanku kaɗai kuka sani, duk abinda zaku yi kanku kuke sawa a gaba. In Abdulƙadiri ne ya lalata maka rayuwar ƴa suka gama tumɓele a titi, zangon baƙi_ zangon baƙi, ya aureta ya saketa zaka ji daɗi ko? To ka sani ka zalunci ƴar mutane ni daka ganni bana bayan zalunci, Hindu bata kasance mai son kanta ba. Ka fice mun a raina babu abinda zaisa ka sake shiga mijinyawa. Bazan iya zaman aure da mutumin da bana jin ko ɗigon sonshi ba, takaddata kawai nake buƙata. Ka sauwaƙemun saki mara kome in je in yi auren farin ciki ga mijin da bazai ci amanata ba. Ko da zai ma ci ba irin wannan nakan ba. Sannan kayanka daka jera ka kwashemun ka bi danginka ku fice mun a gida tun kafin in muku korar kare. Ina ɗaga muku ƙafa sabida yaranane kawai. Amman wallahi ka kiyayeni in ba haka ba zan maka abinda abadan yaranka ba zasu iya sake kallonka ba." "Hinduuu... ni kike cema zaki auri wani? " Ya ambaci sunana da zafi da kaushin murya har tana ɗan rawa_rawan kishin nace zan yi auren farin ciki. Miƙewa tsaye. Miƙewa nayi inajin wani irin ƙarfi na zuwa mun, take na soma tunkararshi yana matsawa da baya da baya. Iyakar abinda na sani kenan na dawo hayyacinane na tarar da mijinyawa a bango, hannayena du biyun suna wuyanshi na shaƙeshi yana kakarin mutuwa, idanunshi sun firfito sosai suna ta hawaye. Da sauri na sake mai wuya na ja da baya. Ai sai ya kama haki, gami da tari yana dafe da wuyanshi. Zama nayi ina harararshi Da sauri ya fice. Na bishi da harara. Kaina sai yamutsewa yake yi. In ka gaji da kanka zaka zuchiya ka rubuta mun takaddata wallahi, aikin banza da wofi yaushe zan iya sake yadda dakai a rayuwata. Hmmmm. Jikinka na rawar iskanci dan na ambaci zan auri wani, ni da ka Auri yarinyar dana gama rainonta ka lalatata kafin ka Aureta, ka kaita har gadonmu na sunnah ashe haɗiyar zuchiya ni ya kamata ace nayi kenan. Maza da yawa basu da kunya wallahi hiye. Ban sake komawa falon ba wuni sukai cur inajinsu a Kicin sunata dafe_dafe da soye_soyen gadarar cefanan ƙaninsune yayi, ni kuwa ko a jikina in sun so su kwashe abincin dukka ma in zasu tafi. Shi su kai ma asara wallahi ina abinda ya dameni. Da su Uwatale suka shigo ɗakin Sabira yin sallah sai nayi komawata ɗakina, tare da daka tsaki, suna jina. Na shiga group ɗin gida anata shirye_shiryen bikin Salamatu har zuwa lokacin ba'a san wanda zata aura menene muƙaminshi ba, gashi mu ɗabi'ar gidanmu shine in mace zata yi aure a san muƙamin mijin nata to su Salamatu sai suka ɓoye face dai iyaye maza da su dole zasu sani. Abinda muka sani shine a katsina zata zauna. Su Nanno basu suka bar gidan ba sai bayan azahar. Ina kicin lokacin "Zanje in rakasu gida sai dare zan dawo kinji? " Murmushi nayi sabida a gabansune nace. Adawo lafiya Allah ya tsare" "Zamu je har da yaran sa dawo da uban nasu in zai dawo? " Gaku gasu Jamila wannan ma in aka faɗama ubansu ya wadatar ai. Inma dasu zaku koma laba'asa" Sallama nayi ma su Nanno nayi shigewata sai da suka tafi na fito na shiga gyaran waje. Ruwa har a kujera da ƙasan kafet sai da suka zubar mun. Ga tulin wanke_wanke da suka barmun akayi kaca _kaca da Kicin da saman gas kukan ma dan mugunta irin ta wasu dangin mijin. Kajin da ya siyo guda biyar sun soye biyu sun cinye, uku suka rage na buɗe firiza na jefa na kunna dan babu komai a cikinshi. Kayan abinci kuwa naga halamun an ɗebi kusan kwatan buhun, na cikin kwalin duk an ɗiɗɗiba, nama gani a hannun Uwatale a cikin bakko. Adana komai nayi a inda ya dace na tsabtace gidana, na ɗaura tafashen kaza kana na je nayi sallar la'asar. Ina soya kaza, ina shan shayi dana haɗa dan yinwa nake ji sosai. Kafin Magrib na gama aikina tsab da nayi sallah kuma na zauna kenan naji ana buga get babu shiri na nufi bakin get na tambaya su waye. Ashe su Baba Sojanmu ne da su Innah Abida suka zo ganin waje. Sai cewa Innah Abida tayi. "Gidan ɗan mitsitsi dashi abun sha'awa. Akace guntun gatarinka ai yafi sari ka bani, amman dai yayi kyau. Ya fiye muku gidan wan mijinki mijin Uwatale ko" Kallonta kawai nayi Innarmu ce tace da'ita. "Ai kuwa wannan gidan baiyi irin wannan ƙanƙantar da za'a kirashi da guntun gatari ba. Ke dai magana kika faɗa kawai. Gashi komai ya zauna a muhallinshi" "Ba haka nake nufi ba Ruwayya" Baba Sojanmu dai yana ta kallonsu suna mayar da zance, Innah Turai tace. "Gida kam yayi masha Allah. Kuma wallahi yayi namijin ƙoƙari a wannan zamanin da filaye ma faɗar ɗaya suke yi balle ka sai gida a tsaye" Ni dai abinci na fita na kawo musu, Innarmu tace zata kama ruwa kafin taci abincin. Ɗakina na shiga da'ita ashe ba ruwan zata kama ba. "Hindu maganace take ta cin zuchiyata shi yasa na kasa haƙuri sai kin zo gida muyi zancan. Wannan yarinyar ta faɗamun ashe ke kika sai gidannan ba mijinyawa bane ya siya ba. Ina fatan wannan makwaɗaitan iyayen nashi sun san zancan dan gudun watarana? Kinga Goggonku Yahanasu, ta taɓa siyan gida suka rayu a ciki ita da mijinta na farko, babu wanda ta sanarma gidan nata ne har Allah yayi mishi rasuwa kuma ɗiya macece a tsakaninsu, kinga danginshi na da gadonshi. To sai a wannan lokacin take sanarwa ai gida nata ne. Rikicin da akayi har kotu kuma duk da haka su sukai nasara a kanta aka samu wani baƙin azzalumin lauya haka aka raba gadonnan da ƴan uwanshi, da haushi ya ƙume Goggonku gadon yarinyar tata da tuminin takabar ta duk ta haɗa ta bar musu, kinsan mu Kanuri muna da zuchiya sosai. To shine nake gudun kada a kuma" Sun san ba gidanshi bane a yau da suka zo, bayan azahar suka tafi suma da sunyi tunanin shi ya siya har Nanno ta soma faɗanta" "To shikenan daga nan kada maganar ta fita ko ina a rurrufa a zuwan shi ya siya ɗin. Kinsan gidan namu ya sake lalacewa da gutsiri tsoma sosai anyi rikice_rikice da gore_gore sosai lokacin kina landan har yanzu ƙurar bata gama lafawa ba ma. Sannan sunanki ne akan takaddar gidan ko? " Innarmu sunanane, ki kwantar da hankalinki. "Muje kar su ji shiru Abida ta biyo mu" Tare muka fita muka dawo falon. Suka ci abinci sukai mun sallama suka tafi. Dukka abincin suka cinye dake dama iyakar mu nayi abincin sai shayi na haɗa na dafa taliyar ƴan yara naci nayi ƙat. Da misalin taran dare ina zaune ina kallon tashar Arewa 24 na jiyo ana buɗe get dake akwai kin get a hannun Azgar. Jim kaɗan sai gasu sun shigo da kayan shofin leda leda nan falon suka baje yahuza suya da Habib yogot nima aka miƙo mun tawa ledar. Hannu nasa na karɓa ba tare da godiya ko nuna jin daɗi ba. "Ba yanzu zaki ci bane Giwa?" Na riga na ci abinci a ƙoshe nake" Bismillah nayi na tashi zan fita. "Tutar so kin mance da ledar taki baki ɗauka ba?" Ya faɗa da murya mai sanyi. Ban kalleshi ba nace. Sabira ki saka mun a firji in kin gama" Na yi shigewata ciki. Washegari ranar aiki ce sassafe kowa ya shiga shirin fita. Na barshi ya sake kwanane sabida su Nanno suna gari basu tafi ba. Bana so suka komawarshi da komatsan kayanshi. Amman in suka tafi da kaina zan haɗa kayan in kai mishi har gidan. Shayi da biredi da taliyar yara mijinyawa ya dafa mana a Kicin ɗin na fito cikin shirin aiki na sameshi, shima a shirye yake. Cikin sut baƙa, da rigar ciki mai ruwan omo, sai baƙin takalminshi kwaba shu shayi yake tsaye yana haɗawa" "Barka da fitowa Tutar so, ki shiga falo kayan karinki yana ciki" In na je office zan karya acan" Na faɗa a taƙaice na leƙa falon a tsaye. Azgar kana da lekca da safe kenan?" "Eh Ammi takwas na safe zuwa ukun yamma" To shikenan inka dawo ka tafasamun kaza kai mun tuwon semo ni zan yi miyar inna dawo. Ke kuma ki same ni a mota in kai ki makaranta. Kai kabi Mijinyawa" "Adawo lafiya ammi Allah ya tsare hanya" Ameen Azgar nagode. Na saka kai na fice zuwa mota Sabira bata jima ba ta fito rataye da jakarta a baya. Ita ta buɗe mana get ɗin na fitar da motar. Ta koma ta rufe kafin ta shiga motar muka tafi. Na sauke ta a makaranta ni kuma na wuce wajen aikina Takwas a farfajiyar gidan rediyonmu tayi mun. Dai _dai zan fito saƙo ya shigo wayata ta akwatin turo saƙo. Da kamar ba zan bi ba ina tunanin ko kamfanin layin wayane sukai mun saƙo, sai dai na duba naga baƙuwar lamba ga abinda saƙon ya ƙunsa. _Rana da ruwa da iska sunyi kaɗan wajen raba auren soyayyar da ilahine ya ƙulla. Tattabara uwar alƙawari a wannan safiyar kinyi kyau irin kyan da harshe da haƙori ba zasu sarrafu ba wajen faɗa ba. Ina roƙon Allah ya haɗaki da dukkan Alkhairi ya rabaki da dukkan sharri, kiyi aikin ki lafiya ina miki fatan wuni cikin farin ciki. Ga dubu talatin ayi maneji kuɗin cefanen wata. Mijinki har a Aljannah in sha Allah_ Hmmm mijinyawa kenan kayi wasa da damarka ka fesamun dafin da har in mutu babu makarinshi. Bana buƙatar kalaman soyayya a wannan ƙadamin basu da amfanin komai, raina ƙara ɓaci yake yi inna buɗe idanuna na ganka kusa dani. A zuchiyata nake maganar ina hango sanda Asama'u ta shiga ɗakin Aurenmu kan shimfiɗar sunnah. Take sambatun da mijinyawa yake ma yarinyar da bata da maraba da ƴar cikinshi ya soma yawo a kaina. Da sauri na fito a cikin motar. Luba ce ta dafa ni. "Hindu Duwaf yau an dawo bakin aiki kenan, da kika rame sai kika ɗan ƙara tsayi fa. Duk da wannan shegun takalman naki masu tudu basa bari a tantance asalin tsayin naki" Da wannan abun dariyar Luba ta mantar dani baƙin cikin da nake ciki. Luba kenan da halama daren jiya Sunusi ya saki cikin farin ciki kunje aljannah kun dawo? " Dariya muka saka mun kasa cewa komai sai da muka yi muka gaji, ba amsa muka shiga ma'aikata. Office ɗin shugaba na wuce nafi awa guda muna tattaunawa dashi kafin na fito. Abokan aikina sai suka mayar dani nama, masu nuna hassadarsu kuma a lokacin suka bayyanata ƙarara, dama dai tun daga lokacin da labarin fitata landan ya fasu mahassadan ɓoye suka fito fili, ga kuma rifota dana zama da wasu hakan baiyi musu daɗi ba. Wannan sunnar rayuwace dama duk wata ma'aikata ana samu, wani ma haka kurum yaji baya ƙaunarka, wasu ma a ƙulla musu sharrin sata, ko sharrin wani abun. Yau dai bani na karya ba sai sha biyun rana da muka samu birek naci taliya da kifi da Luba ta dafo mana da shayin na'a na'a. Luba jiya baki san yadda muka ƙarke da su Nanno da Yaya jamila ba" Idanu Luba ta zazzare tace. "Sun zo ganin gida da neman ta da zaune tsaye kenan? " Har muka gama ina bata labarin yadda muka yi dasu, da kuma dawowar mijinyawa gidan. "To ke wanne hukunci zaki ɗauka akan dawowar tashi? " Da nace zan haɗa mishi kayanshi in kai mai can gidan da kaina. Amman a halin yanzu na rabu dashi sabida magana yake nema dani kuma bazai samu ba. Dawowar tashi kusa damu ɗin zai bani sauƙi wajen rabuwa dashi. Luba ina da hanyoyin shiru da halin ko in kula da zan tuƙe mijinyawa dashi da zai sa in ya gaji ya sakeni, ko nan da shekara nawa ne bani da matsala. Amman wallahi_tallahi tunda nace na gama to na gama ba wajen bane Luba. Ai aure ma Nanno take so yayi shi yake ta zulle musu. Ita kuma Asama'u ashe yayi mata saki uku kamar yadda suka ce. Hmm dake maza basu fiye kunya ba shine yake biyo ni yana ce mun tunda ya aureta sai ya gane bai kyauta ba, kuma bai kusanceta ba. Tuni na tsayar da zancan tare da jaddada mishi takaddata zai bani inje in yi auren farin ciki sabida bana jin ɗigon sonshi. Kinga wai yadda jikinshi yake rawa wai shi kishi Luba? Ni wallahi sai yanzu ma abun ke bani dariya. A jiyan baƙin cikine ya kuma turniƙeni" Mun yi dariya sosai wallahi in muna wajen aiki mancewa mutum yake yi da komai. Duk macen da ke aiki, ko sana'a tafa wuce ƙananun iskancin maza na zalunci. Azzaluman maza inji Lubna kai Lubna bata ji. Sai mace taso ya dameta wallahi in taga zai tayar mata da hankali tuni zata jingineshi gefe taci gaba da harkokinta. Ƙarfe huɗu muka baro wajen aiki. Kasuwa Luba ta rakani nayo cefane da kuɗin cefanan da mijinyawa ya turo mun. Daidai abinda ya turo dashi na sai abinda zan buƙata. Na sauke Luba a ƙofar layinsu na dawo gida a mugun gajiye sosai a Kicin na tadda Azgar yana tuƙa tuwo. Tsayuwar da nayi dashi bata shige ta mintuna ba, na wuce ɗaki. Ban zauna ba nayo wanka na gabatar da sallar la'asar kana na faɗa gado gashi gobe sassafe nake son fita ina da asament a ƙauyan wudul da zanje ɗakko rahoto. Bacci na kwanta nayi magashiyan saida kiran waya ya shigo mun na farka a lokacin ƙarfe shida har tayi. Assalamu Alaikum." Na faɗa bayan na ɗaga wayar tare da karawa a kunnena. Sai naji sautin kukan baƙin ciki da ɓacin rai a muryar matar da tayi kiran nawa. Gashi babu suna. Baiwar Allah kiyi haƙuri ba kuka bane magani, buɗe baki kiyi mun bayanin matsalar taki in sha Allah sai mu haɗu mu shawo kan matsalar in Allah ya dafa mana" Shine Allah ya taimakeni tayi shiru cikin shessheƙar kuka tace dani. "Dama Na'ilatu ce ta cikin Zaurennki ta bani lambarki shawara nake nema ki bani. Amman abun yafi ƙarfin waya in kin bani dama in tawo yanzu gidanki dan Allah bazan iya bacci ba in banzo wajenki ba" Ajjiyar zuchiya na sauke. To shikenan ina zawa ciki in babu nisa kina iya zuwa" "Ina da nisa amman zanzo yanzu in sha Allah. Inna zo wanne gida zance?" Ki kirani zansa yaro yazo titi ya jiraki inna kimanci kin kusan isowa. Daga wacce anguwar zaki tawo?" "Daga gandun Albasa zan tawo nama fito yanzu titi zanje" To shikenan nan da minti goma sha biyar zai fito bakin titi zan bashi lambar wayarki sai kin zo" Da haka na sauke wayar a kunnena na fito na tura ɗakin Azgar baya ciki, Sabira kuma tana aikin gida na makaranta jarabawa zasu soma sati mai zuwa. Kinata aiki ba? Sannu ya karatun" "Lafiya ƙalau Ammi tun ɗazu na dawo Yaya yace mun kina bacci kar in sake in tasheki a baccin" Dariya nayi mata kawai na ɗan tsaya a tsaye muka ɗan yi hira kafin na wuce Kicin na tsayar da sanwar kuɓewa ɗanya, ina cikin zuba ɗanɗano mijinyawa ya shigo da sallama, na amsa mishi ciki_ciki ban sake waigowa ba. Baice mun komai ba ya shige ciki da jakarshi ta aiki. Bai wani jima sosai a ciki ba ya fito saye da jallabiya da laptop ya wuce falo lokacin ina falon muna hira da yara. "Tutar so ya aikin ya wunin ya kasance? " Alhamdulillahi" "Masha Allah. Azgar Sabira yaya karatun ke sati me zuwa zaku soma jarabawa ko? Kai kuma jarabawar ƙarshe na tunkaroku ko? " "Eh Abba a saka mu a adda'a" Cewar Azgar. Kai ya gyaɗa yace. "Sai dai a kuma dagewa da adda'ar amman ai kullum a cikin yi muku adda'a ake. Sabira dafo mun shayi marar madara ki kawo mun" "To Baba" Ta tashi da sauri ta fice, Azgar ma ya miƙe. Azgar kaje ɗaki ka ɗakko kin mota ka fita titi zaka ɗakko mun baƙuwa. Ga lambarta ka kwafe a wayarka" Na miƙa mishi wayar ya kwafe ya miƙo mun. Falon ya rage mu biyu, yana danna laptop ɗinshi da halama aikine ya sha mishi kanshi sosai. Ni kuma zaurena na shiga sabida akwai saƙwannin wasu mata biyu da suka turo mun masu neman shawara na tura musu. Kuma inason da daddare na ɗanyi rubutu na jan hankalin maza a shafina na Facebook in sha Allah. "Tutar so kinga kuɗin dana turo miki na cefane ko?" Yi nayi kamar banji ba, saima tashi da nayi na koma Kicin na yi zamana. Magriba ake kira ma, kuɓewa na zuba dana buɗe tukunyata naga ruwan yayi ƙasa naman ya faffashe yadda nake so. Na zuba da minti biyu saina kashe wutar na tafi yin sallah. Ina tsaka da sallah baƙuwata ta shigo Azgar ya wuce masallaci. A falo na sameta a zaune yarkace_yarkace cikin ƙazanta da damuwa da gani bata da ishasshiyar lafiyar kirki. Da sallama na shiga na nemi waje na zauna. Sannu da zuwa baiwar Allah kin iso lafiya? " "Lafiya lau malama" Mrs Bukhari ce To yau kuma kunji yadda aka sha ɗauki babu daɗi da su Nanno. Sai mu kwana anan in sha Allah sai kuma gobe. https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp 07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm Tiktok link/ https://vt.tiktok.com/ZSCgTFH8o/ IMZEEDenterprises Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeed🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDENTERPRISESLTD wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account aTikTok@imzeedenterprisesltd https://vt.tiktok.com/ZSCgTFH8o/ Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima BADI’AT İBRAHİM tuni na antaya🏃TSURO TSIRIN... TSANDAURI LITTAFIN BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA HUƊU (4) https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp 07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm Tiktok link/ https://vt.tiktok.com/ZSCgTFH8o/ IMZEEDenterprises Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeed🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDENTERPRISESLTD wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account aTikTok@imzeedenterprisesltd https://vt.tiktok.com/ZSCgTFH8o/ Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima BADI’AT İBRAHİM tuni na antaya🏃 "Na iso lafiya malama Hindu. Ina cikin damuwa bani da uwa bani da uba bare inje su share mun hawayena. Mahaifiyata ni kaɗai ta haifa a gidan Babana, ina da ƴan uwa wanda ta haifa a wani gidan, su kuma babu shaƙuwa a tsakaninmu kasancewar bamu rayu waje guda ba. Kinsan irin wannan sai dai a hankali." Ajjiyar zuchiya na sauke nace da'ita. Yanzu dai abinda ya kamata kiyi sallah, kici abinci in kika ɗan samu nutsuwa sai mu tattauna" "To shikenan nagode Allah ya ƙara haɗe kanki ke da mijinki. Ya yara miki yaranki Malama" Hmmm Sabira'Sabira" Na shiga kiran Sabira. "Na'am Ammi" Ta amsa tare da zuwa da sauri" Ki kai baƙuwa ɗakinki tayi sallah ki bata abinci taci ko?" "To Ammi, taso muje bari in riƙe miki goyon" Sabira ta sunce goyonta na yarinya mace sai ƙarni suke yi daga ita har ɗiyar. Tishet ce a jikinta sai zani ballagaza a tsaye da hula komai dai daban hijabinta duk jurwaye. Ohh irin wannan matan da gaske suna kiran kansu da mata, wannan ƙazanta da me tayi kama. Haka suka wuce ɗakin Sabira. Jin sallamar Azgar da Mijinyawa yasa na tashi nayi komawata cikin ɗaki na zauna ina bin tattaunawar yadda bikin Salamatu zai kasance da ranar da zamu wuce katsina kai Amarya da su batun anko namu yaran gida dai. Sabida ƙarya irinta Salamatu leshi ta fitar na dubu hamsin a matsayin anko tasan a cikin gidan akwai marasa ƙarfi da yawa, waɗanda a wahala zata saka su, in ko ana ha maza ha mata zasu siya, sai dai a barsu da biyan bashi. Bamu taɓa cire anko mai kuɗin wannan ba sai dai ku cire iyakar ɗakinku kuyi da ƴan uwanku ku ƙara mai tsada yanda kuke jin ƙarfinku ya kai. Na fahimci za'ayi ƙarya sosai a bikin inaji ana batun gobe za'a kawo akwati da yamma ana buƙatarmu a gidan. Shigowar Sabira yasa na ɗago. Ta ci abincin? " "Taci Ammi sai kuka take yi" Da sauri na fito ina hango mijinyawa a Kicin yana zuba miya baƙin cikine ya turniƙeni akan abincina daya taɓa mun. Tsayawa nayi na dubeshi da kyau. Yana da kyau ka sani cewar nan ba gidanka bane, kuma ban siya dominka ba, balle danginka ba. Ɗazu sun zo sun ɓata mun gida na ƙyalesune sabida bansan sun ɓata ba sai da suka tafi. Sun ɗebi abinci wannan bai dameni ba sabida kai ka siyo in da sun so sun kwashe duka ma babu abinda zai dameni. Abinci yaranka ka siya ma, kuma su na girka ma sabida haka bani" Na miƙa hannuna ya ko saka mun kwanon a hannuna. Zai yi magana na runtse idanuna nace. Kul ba wajen bane, kada ka sake ka ce mun komai." Tuwon na mayar cikin kula, miyar na juye a tukuna, daga tsayen na saki kwanukan suka tarwatse dama faɗi ka mutu ne. Shiga nayi na sameta tana ta sambatu tare da ambaton Baballe. Zama nayi kusa da'ita na dafa kafaɗarta. Wannan kukan da dogaro da ɗa namiji shike halaka matan zamaninnan, sabida mazan wannan zamanin ba duka bane masu zuchiyar imanin tausayama mace ba. Mu kuma mata mun dage ko da daɗi ko babu daɗi sai mun yi zaman aure. Mun mayar da kanmu ƴan a mutu ma Aure duk tsanani. Jibi rayuwar Shanono yadda tayi kyau har ta zama lauya bayan rabuwarta da Kaila Ita kaɗanta abun buga misalice ga mata ire_iren masu zuchiyar dole sai sun yi zaman auren dole ko da cutarwa. Bama musulunci bane akwai haƙurin da cutarwane ba haƙuri bane. Ki dena kukannan ki faɗa mun ni abinda ke tafe dake kar mu ɓata ma kanmu lokaci, ina da abubuwan yi, ga aiki ban jima da dawowa ba ga hidimar gidana. Kin tusani gaba da kukan banza akan wani azzalumi da bai san daraja da kimar hawayenki ba. Wai me kuka yake amfanar muku ne?" Raina dama a ɓace yake tana neman ƙaramun fireja. Na hasala nazo iyakar wuya. Na tsani inga mace tana kukan banza kukan da babu mafita a cikinshi. Shi yasa inna tuno Sabuwan Babangida kaci gari sai inji tamkar in damƙota in hayeta yadda take hawaye akan komai. "Kiyi haƙuri malama abinda Baballe yayi munne da ciwo wallahi. Shekararmu ashirin fa da aure yara goma cib nake dasu sai dai dukka mata Allah ya bani. Tsangwamar dangin miji da shi kanshi mijin iri daban daban babu wanda ban fuskanta ba. A hakan lokacin haihuwata ta shida mahaifina ya rasu aka raba mana gado miliyan ɗaya ce na gada Baballe ya saka mata rani yai tamun barazana iri_ iri da saki akan sai na bashi wannan kuɗi ya ƙara a kasuwa. Takalman roba yake saidawa a baro a bakin kasuwar kwari. Haka na bashi ko kwandala bai bani ba Malama. Rayuwar taci gaba a haka. Yanzu kayan ɗakina kab ya kwashe ya siyar katifa ya jefar mana ni da yaran kawai. Bance mishi komai ba sai yau ɗinnan da yamma sanda na kiraki wai masu jerene suka zo jere a ɓarayin gidanmu da aka gyara ya lashe kuɗaɗe yai ta ce mun ƙaninshi ne zai dawo da iyalanshi, ashe Baballe aure zaiyi ranar Juma'a za'a ɗaura Auren da kuɗin kayan ɗakina ya biya sadakin. Wannan shine abinda ya faru bani da kafaɗar da zan jingina in yi kuka a share mun hawayena" Sai ta kuma fashewa da kuka harda jiniya tana fyace majina da bakin zane. Ƙur nayi mata a zahirance ita nake kallo a baɗinance kuma nazari nake yi tare da rarrabe kalmomi da haɗewa domin in gane kan labarin da kyau in san kuma a wacce gaɓar ya dace in tambayeta in akwai tambaya. Nisawa nayi nace. Naji duk abinda kika ce. Inna lura na fahimta danne miki hakkinki da yayi na miliyan ɗaya kuɗin gadonki, bai dakeki kamar kayan ɗakinki da ya sarayar ya kai sadaki ba ko? " Sai tace cikin rishin kukan iskanci. "Kishiya fa malama zai mun ya siyar mun da kayan ɗakina ya ƙara a hidimar shirin bikin fa. Duk baƙar wahalar da nasha a gidan Baballe ina zaune yayi gini mai kyau zai saka mace fa" Kina da Sana'a a hannunki ko wani aiki da kike yi ki samu kuɗi, ko da babu yawa ɗan taro da dai sisi? "Bana aikin komai da a baya nayi wankau sai ciwon ɗan kakkare ya tusoni gaba ba wuya nayi dole na haƙura. Ita babbar ƴar tawa kafin tayi aure ta ɗanyi suyar Awara a ƙofar gida, kuma ana samu amman jarin ya durƙushe tunda a ciki muke matsaltsalunmu. Komai fa in banyi ba, shima bayayi tunda yaran matane, yace duk wahalace zai yi a banza dasu" Inna fahimceki Baballe baya baku abinci wadatacce? " Kai ta girgiza tace. "Baya bamu sai sanda yaga dama, ca yake wai rayuwarmu bata da amfani na kama na cika mishi gida da yara mata. Sai yaso zai kawo masara ko dawa ko gero a tsabarta, ni zan nemi na niƙa da kuma na miya ko da kaɗa ƙwarya ce in mana" Hmmm makarantar yaran fa? " "Suna islamiyya itama wani bawan Allah ne yake neman marayu zai taimaka musu shine na fita na roƙeshi ya saka mun su a islamiyya, a bar bokon ma su samu na muhammadiyya. Shine suke zuwa. Babbar dai mijinta ya sakata a makaranta tana yin na bokon" Hmm to inna fahimta da kyau, kuma lissafin nawa yayi daidai. Kishin Baballe kike yi kenan, mutumin da baisan kimarki da darajar Ƴaƴa mata ba, har yaran da Allah ya bashi? Tabb akwai aiki a arewa mai girma, ko yaushe mata zasu gane ba'a zaman aure da zalunci oho' ko yaushe mata zasu gane sana'a ko aiki na da matuƙar mahimmanci a rayuwarsu oho. Ko yaushe mata zasu gane rabuwa da miji azzalumi bashi bane ƙarewar rayuwarsu ba oho. Ko da yake sai da ilimi ake aiki. Amman sana'a ba sai da ilimi akeyi ba. Ko dan na taso na tadda mahaifiyata ƴar gwagwarmaya ce oho. Yanzu ke madadin ki nemi yadda hakkin dukiyarki zai fito sai kika ruɗe a ƙarin aurenshi mutumin da baisan mutumcinki ba, baya son yaranki, baya baku wadataccen abinci shi kike runtumama kuka ƙaƙas dan zai ƙara aure, ashe ba zaki iya dakewa in duk matan duniya zai aura ba. Ƙila ma a gabanshi da zubewar aji da girma kin yi kuka tunda mu mata mun ɗauki kuka wata hanyace ta karya zuchiyar ɗa namiji ko? Su kuma suke ganin kamar logonmu kenan. To ya kamata ki farka ki dawo cikin haiyacinki ki yi watsin ruwan tsarki da sha'anin Baballe da aurenshi ki fuskanci tarbiyyar yaranki da sana'a, ki kama girma da mutumcin kanki, ki ja gefe a rayuwar Baballe. Dan tunda kince baki da kowa bazan ce ki kashe aurenki ba yara goma kam kinci gida, amman ki dinga kallon Baballe a matsayin Yaya ko Kawu kin huta. A na me zaki ɗaurama kanki hawan jini a kan aure, ku kuke bayar da mata wallahi, ku kuke sa a raina mata sama da ƙasa. Wallahi banga ɗa namijin da ya kai ya isa in yi mishi kuka ba, ko da kuwa shine wa. Sannan dan Allah ki dinga tsabtace jikinki kiyi wanka a ƙalla ko alim ki dinga gogawa a hammatarki, ko farar hoda yana ɗauke gafin hammata. Jibekki yarkace _yarkace babu yadda kike, daga ke har goyon naki babu fasali kamar ba mace ba. To yanzu ma me kike so ayi miki kina so in shiga kuɗinki ya dawone ko kayan ɗakin ki? " "In so samu ne duka biyun" Na nisa nace da'ita. To kinsan in akace za'a tafi da Baballe ofishin ƴan sanda a tuhumeshi akan kayanki da kuɗinki zai iya zuchiya ya sakeki, shin kin shiryama hakan ko da ya faru? In kin shirya babu komai tunda ko sakin ki yayi to ya zame mishi dole ya kama muku haya ya biya, kuma ya baku abinci ya kula da duk ɗawauniyar yaran, ko yaƙi ko ya so." Sai tayi jimm tana tunani. Ki bari ki nutsu kiyi nazari zaki iya kirana a waya ko ki zo ai kinga gidana duk abinda kikace za'ayi miki in sha Allah. Kiyi sallah sai muzo mu kai ki gida kuma" Na fita na barta tana ta mun godiya. Sallah nayi na ɗan tsinto mata kaya kala uku, da mayafi baƙi, sai humra na tsiyaya mata a kwalba, sai ɗan kayan kwalliya haka da basilin. Fitowa nayi da mayafi a jikina na leƙa nace mata ta fito muje. Ta fito muka jero har zuwa ƙofar falo. Azgar yana zaune yana latsa laptop mijinyawa kuma yana kallon labarai yana shan koren shayi ( green tea) Azgar bani kin mota zan kai baƙuwa gida" Tasowa yayi da sauri ya miƙa mun. "Ko in zo in tuƙa motar naga kin gaji gashi ko abinci baki ci ba" Kar ka damu inna dawo zanci. Akwai Ahmad shayi a ɗakina ka dafa mun fulebon girfa. Sai ka dafa mun taliyar ƴan yara ka kai mun ɗaki saina dawo" Ban jira komai ba na fice Mijinyawa kuwa ban ko kalli inda yake ba. Azgar ya buɗe mun get muka fice. Har muka isa ƙofar kwaraɓaɓɓen gidansu ina bata shawarar yadda zata zama mace ba muna mace ba. To shikenan Baiwar Allah mun iso gida naga waje in sha Allah. Sunanki fa? " "Ashe ban faɗa miki sunana ba, sunana Badia Malama. Kuma naji daɗin shawarwarinki, wallahi naji sanyi sosai a zuchiyata, na samu sassauci gobe zan kiraki kiji hukuncin dana yanke" Hmmmmm mata da yawa bamu fiye tunani ba, wai akan Baballe sai Badia ta zatsa tayi tunani tukunna. Murmusawa nayi na jawo ledar kayan dana riƙo na bata tai ta zuba godiya. Nan gaba kada ki kuma fitowa a haka dan Allah. Ko da baki da kaya mai kyau ki tabbatar a wanke suke fes, kuma kema ki tsabtace jikin naki. Ki shiga sai da safe" Godiya tayi sosai ta sauka saida na tabbatar ta shiga ciki ni kuma na juya na tafi. Ina tafe ina jujjuya maganganun Badia da ragowar mata da basu da aiki sai rusa ma namiji kuka. Naji inaso da ra'ayi akan kes ɗin Badia, in da tace tana son hakkinta wallahi da sai inda ƙarfina ya ƙare akan Baballe. Naji na tsanashi sabida ƙin ƴaƴa mata da yake yi. Kuma ko babu komai zai zama na farko da zan taimaka ma wata mace hakkinta ya fito ba wai a iyakar shawara ba kawai, ya kamata ace nayi gaba kuma. Da tulin tunane_tunanen faɗaɗa abinda nake kai na isa gida na danna hon Azgar ya buɗe mun na shiga na ajjiye motata muka shiga tare. Zanje in kwanta gobe ina da aiki mai wuya. In ka gama karatunka ka tabbatar ko wacce ƙofa a rufe take" "Sannu da dawowa Tutar so" Na jiyo mijinyawa ya ambata. Yi nayi kamar banji ba na wuce ina tambayar Sabira nayi shigewata ciki. Wanka na soma yi na shirya cikin kayan baccina kafin na zauna zaman cin abinci goman dare lokacin. Ina buɗewa na tabbatar mijinyawane ya dafa taliyarnan sak irin wanda yake dafa mana ni da Azgar lokacin yana shekara biyar ya shiga makaranta. Lokacin bani da lafiya ciwon makarai mai tsanani. Hakan ya dawo dani wata ranar manday a daren monday ko bacci bamu iyaba, a hakan ma Yaya Saratu tazo ta kwana dani, kwana suka yi a kaina suna mun hayaƙi da karatun Qur'ani. Ajjiyar zuchiya kawai na sauke. Na rufe taliyar ƴan yarannan dan wallahi sai naji tana ƙoƙarin fama mun miki a raina. Shayin kawai na shanye na haye gado nayi kwanciyata. Sai naji wayata tana ta ƙaran shigowar saƙo, amman ina baccine mai nauyi a kaina. Sai da na tashi sallar dare wanda ni da yarana ya zame mana jiki, kana na ɗauko wayata na duba wannan saƙon. Ina buɗewa hmmm wai kunsan me wai na gani? Mijinyawa na gani a hoto tare da wata mace. Tana kan cinyarshi yana riƙe da ƙugunta tayi hoton, gata kyakkyawa wanke hannu ka taɓa. Kunji wannan sai kuma hoton maganarsu ta hanyar chart. (Screenshort nake nufi na chart ɗin sai aka turomun hotunan chart ɗin Allah yasa bayanin ya fita kun gane? ) Hoton mama aka turoma mijinyawa. Ga abinda ya rubuta. _wayyo Babyna wato so kike ki ɗaga mun hankali dan kinsan nayi kewarki, kuma kinmun nisa ko_ Sai ta turo mishi da hoton mai gaba ɗayan. Shi kuma ya tura mata irin wannan gwaigwai ɗin me tambarin zuchiya biyu a ta ka daƴa a baki 🥰, sai na ayaba🍌, na sumba💋, da na rigar mama da ɗan duros. (aimun afuwa ba saina nuna ba, kunya zata halakani) Sai hoto na gaba shi kuma ya tura mata jikinshi, gashinan muraratan. Da kuma hoton la'anannen ƙirjinshi. _kai Jarumina gaskiya gobe zan dawo irin wannan kaya ai ba zasu barni bacci ba_ Abinda ita ta rubuta mai kenan shi kuma sai yace. _gobe mu haɗu a zangon baƙi amman ke zaki kama mana. Duk da gobe asabar, zan san yadda zan yi da Tutar so in samu in zo ko minti ashirinne in baki ai zai ishemu. Wannan zumar ina son ɗanɗanarta_ Sai ta turo mai dariya kawai. _Me yasa kike dariya?_ Sai tace. _Ai kasan me nake ma dariya, amman zan yi maganinka in muka haɗu sannan ina kishin wannan Tutar so_ Sai yace da'ita _A yanzu ai kinfi Tutar so samun gurbi, da mahimmanci a wajena_ Ɗayan hoton bai buɗe ba sam, nayi_nayi ya buɗe yaƙi buɗuwa. An goge shine kamar. Murmushi nayi kawai, na sake bubbuɗa hotunan ina kallon lokacin, da kuma kwanan watan da akayi abun. Da wayar mijinyawa akayi hoton ( screenshort) ɗin ga lambar yarinyar nan ko suna babu, sai lambobin a jejjere. Murmushi nayi na kwashe hotunan zuwa labtop ɗina, lambar kuma na kwafe a wayata na sa sunan da zan gane da kyau. Na koma kan manhajar WhatsApp na duba lambar a ƙasan lambar naga an rubuta Talatu Ibrahim First Bank. Murmushi ne ya suɓucemun. Ohh abokiyar aikinshi ce Talatu uhm Mijinyawa kenan, a.a maza ƴan gatan mata. Lambar da aka turo da saƙon na duba ƙasanta babu suna ita sam. Amman zan barma gobe ya zama dole in san wacece mamallakiyar wannan lambar. Kuma ya zama dole in san komai akan Talatu Ibrahim First Bank Alwala nayo, na ta da kabbarar sallah ƙirjina na wani irin daka tamkar zai fashe wallahi haka nake ji. Ni kaɗai nasan irin yadda nake ji, duk da ma inaji tamkar bani ɗin bace. Namiji tuwon reza miyar allura hmm. Ra'aka biyu nayi, sai nai wutiri, nafi minti goma a sujjadata ina faɗama Allah damuwata. Ko da na ɗago zaman tahiya na kai minti goma ina sake jaddadama Ubangiji na sirrin zuchiyata kafin na sallame. Sai ƙarfe huɗu da rabi na kwanta. Baccin awa ɗaya nayi kacal, na wayi gari da zazzaɓi da matsanancin ciwon kai marar misalin misaltuwa. Duk da dai hakan, bakwai da minti biyar na yi ficewata na bar yaran duk a gida Mijinyawa ya kaisu ko ya basu kuɗin mota, wannan matsalarsu ce dukkansu. A ranar na sha wuya na shiga wudil ɗakko rahoto na dawo gidan rediyo edita a ranar bata zo ba ni na zauna nayo editin da yamma kuma na nufi hanyar gida, bayan naje ofishin ƴan doka, daga ofishin ƴan doka zuwa ofishin kamfanin layin waya. Gashi na gaji in ƙi zuwa gidan ace dan Salamatu ba ƴar ɗakinmu bace shi yasa naƙi zuwa. Ga ƙirjina sai rawa kawai yake yi mun. Ai kuwa ina shan gwanar gida naga jerin gwanon manyan motoci ƙila na masu kawo akwatine. Ilay tun daga lungun Innah Mairama ake shaidamun masu kawo akwati suna ciki. Da sallama na shiga falon namu daya cika ya batse da akwatuna. Wallahi irin wannan akwatunan a soshal midiya kaɗai nake ganinsu suma a wajen yaran manya, yau sai gashi a gidanmu a gidanmun ma a falonmu kuma wai Salamatu aka kawo ma. Da ganin dangin mijin suna da wadata ya nuna ma a jikkunansu. Innah Abida sun cika falon da bokiti _bokiti na cincin, soyayyun kaji, samosa, da mutu fab, harda alkaki. Gaggaisawa nayi da baƙi Innah Abida ta dubi wata farar Hajiya mai haƙorin makka tace. "Wannan ma ƙanwar Salamatu ce. Bata jima da dawowa daga landan ba tayi aiki da Bbc landan, ta kuma hada mastas ɗinta" Tabb yau Innah Abida ke wannan maganar sabida ta ɗaga ma Salamatu darajarta. Wannan Hajiyar tace. "Masha Allah. Ashe dai zani ce ta tadda muje mu muma a gidanmu maza da mata daga masu mastas sai Phd, muna boko sosai katsina ana karatu sosai. Sai da na kalli Hajiyarnan da kyau sai naga kamar fa Mrs Bash ce, gata jajir da'ita ƙibarta tayi mata kyau dan mazaunaine da'ita haka_haka. Sai da na kuma kallonta da kyau sannan na gane kamace kawai, Mrs Bash ta fita kyau da ƙibarma. Akwatuna kam kusan kala huɗu ko wanne seti akwai mai huɗu, akwai masu uku, dizaina kuma, ga manyan Adudu shaƙe da takalmi da jakunkuna ko rufuwa basa yi tsabar tumbatsa. Hmmm kuɗi na inda suke ya ilahi da aka buɗe kayannan gaskiya babu wanda bai yaba ba, kayan kece raini sosai suka zuba harda dubu ɗari biyar wai fa kuɗin ɗinkin kaya. Sai a bakinsu muke jin ashe babban ma'aikacin hukumar fasa ƙwarine, babbane inaga kwanturola ne ma. Innah Abida da ƙannenta da dangin Baba Sojanmu suka harhaɗa har dubu ɗari biyu cib kuɗin tukuici, da kaɓakin toye_toyennan. Akayi adda'a baƙi suka tafi. Ai fitarsu ke da wuya ruwa ya ɓalle ruwan farko kenan a watan damuna da muka shiga. Dama yau an wayi gari da hadari tun safe sai yanzu Allah ya umarci ruwan da sakkowa. Kuma sai yazo da ƙarfi harda ƙanƙara tamkar watan marka_marka. Mu dai muna zaune mun yi ɗai_ɗai a falo anata sake tusa kaya masu ƙirgawa nayi. Innah Abida da dangin Baba sojanmu sai giggiwa suke yi har Goggo Tandama tana cewa. "Ruwa ya sakko alkhairi ya sauka a lungun Soja. Salamatu a kaf yaran gidan Soja tafi kowa sa'a wallahi." Yaya Saratu tace. "Ah haba dai Goggo Tandama nata dai ya fito fili ai kowa da irin ƙaddararshi, da kuma irin sa'arshi. Tunda a kaf lungun Baba Sojanmu babu wacce aka taɓa sakowa sai ita ta birekin rekot kuma" Daƙuwa tayi ma Yaya Saratu sai abun ya zama wasa, Innarmu kuma ko a jikinta danne_ danne waya ma take yi. Sun yi ne dan ta tanka tunda dama ita tunda aka aurota basa ƙaunarta sam sunfi ƙaunar ƴar uwarsu Innah Abida kuma duk dangin Baba sojanmu a wajenta suke. Shi yasa ko sha'anine na ɓarayinta sunfi dandazo. To daɗin abun ba'afi Innata dangin ba suma zuwa suke su cika falon har da ɗakunan wasu lungunan ma. Naman kaza Salamatu ta shiga rarrabawa tana bi ana ɗauka sai wani dariya take yi dangin Baba Sojanmu na wani irin zugata ɗai_ɗai nake kallon kowa bana cewa uffan. Ni da ba dan ruwa ba ma tafiyata zanyi gashi har magriba ruwan bai tsagaita ba. Badia ce ta kirani ina sallah a ɗakin Innarmu su Yaya kuma sai ƙus_ƙus ɗin gulmar mijin da Salamatu zata aura da kayan da suka narko suke yi. Ina idarwa nabi kiran Badia. Da sallama ta ɗaga wayar na amsa mata muka gaisa. "Malama dama na kirane in shaida miki na amince a nema mun hakkina amman iyakar na kayan ɗakina wancan na yafe" Ajjiyar zuchiya na sauke wallahi jiya mafarki nayi akan kes ɗin Badia da Baballe. To shikenan Badia gobe in Allah ya kaimu zan zo in ɗaukeki har gida muje ofishin ƴan sanda mu shigar da ƙara a karɓa miki hakkin ki. Naji daɗi da kika ji kina son tsayuwa akan dugaduganki. Kinga ko babu komai zaki gyara muhallinki kuma zaki samu jarin juyawa. Kafinnan ki rubuta duk abinda ya kwashe, miki ki yi musu kuɗi sai ki turo mun total ɗin kuɗin ta saƙon kar ta kwana. Ai kin iya rubutu ko? " "Eh Hajiya na'iya rubutu zan rubuto miki in turo miki nagode_ nagode sosai. Wallahi jiya baki ga bacci mai daɗin da nayi ba" Murmushin cin nasara nayi tare da jin gurina yana hanyar cika akan wannan harkar na ƙwato ma mata ƴancinsu. Wannan labarin ya wanke mun zuchiyata fes na shiga cikin ƴan uwana muka ci gaba da gulma tare da shirin biki dan da alama akwai ƙarya da ƙure adaka a bikin. Take Yaya Zubaida tace mu fitar da lashin da a lokacin shine na sama, da kyale masu tsada na lokacin, sai mu yi ankon da ta fitar. A haka muka tsayar ni harma na hango ɗinkin da za'a buga mun, shi kanshi ɗinkin zai yi dubu ashirin gaskiya inma baifi ba kenan, ina da sarƙoƙina bani da matsala da wannan ina da sabon takalmi da jaka dana siyo manya masu tsada ta gaske guda biyu a landan, zan ci waje da ɗaya. Ruwa bai tsagaita ba a wannan rana sai goman dare. Su Yaya Zubaida duk sunce a gida zasu kwana kawai. Ni kuwa yara sai kirana suke yi hanlalinsu duk a tashe. Dole na miƙe na shirya dafa har nayi kwanciyata nima, amman Azgar harda kukanshi. A raina nace Azgar zaka yi kuka har sai ka dena hawaye. Dan ubanku in shi kaɗaine Autan maza sai dai ni dashi mu kalli juna. Wallahi_billahi na rufe babin Mijinyawa abadan. Zai sha mamakin Hindu. Ku dai ku biyoni, ni bana gaggawa daki_daki sannu a hankali nake ɗaukan mataki. Kuma yanzu saina gama tattara bayanai akan abokiyar aikin Mijinyawa kafin in tsallaka mataki na gaba. Duk abinda zanyi da cikakkiyar hujja nake yi. Mata ku bini a hankali dan Allah ku dena gaggawar yanke hukunci. Ina hanya Azgar ya kuma kirana na ɗaga nace. Azgar ina hanya bafa ɓata nayi ba gida naje ruwa ne ya hanani dawowa, amman kaga ina hanya ma." "Alhamdulillahi Tutar so wallahi nayi tunanin kin sake tafiyane kin barni a karo na biyu" Naji muryar mijinyawa a kunnena ai saina yi murmushi nace. Zan dai tafinne amman ɗakin mijina sabo ba. Ka zauna kaita yaudarar kanka dai, dan Hindu tafi ƙarfin a yaudareta wallahi. Ai kafi kowa sanin in nace bana yi da mutum in duk duniya zasu taru ba zasu saka in yishi ba. Tunda na iya bijirema iyayena na zaɓeka. Kai a tunaninka in nace na barka akwai mahalukin da ya isa ya sani in yika ne" Dogon tsaki naja tare da datse wayar kawai saina juya na koma gida kawai. "Dawowa kika yi kuma Hindu lafiya? ". Babu komai Innarmu kawai naga dare yayi gaskiya gara in kwana nima kawai" Doguwar rigar Innarmu ta bacci ta miƙomun na saka na shige tsakiyar su Yaya Saratu a kan katifar da aka sauke musu muka ci gaba da hirarmu wayoyina kuwa duk na kashesu. Inajin sanda mijinyawa ya kira Innarmu wajajen goma sha biyun dare, ta shaida mishi inanan sabida anyi ruwa bai tsaya kan kari ba zan kwana a gida tare da su Yaya Saratu. Mu kuwa hirar yaushe gamo muke yi wacce bamu samu zarafin yi ba. Sai wajen biyun dare fa muka haƙura mu kai bacci. Gida shima yana da irin daɗinshi, ƴan uwa kuma sarƙar wuya. Haka muka wayi gari sassafe na soma shirin aiki. Kayan Innarmu na saka na bar nawa anan naima kowa sallama na kama hanyar aiki takwas a wajen aiki tayi mun. Sha biyun rana akace nayi baƙo yana ɗakin jira. Ina zuwa naga mijinyawane da leda wai ya kawo mun abinci sai murmushi yake yi ko na menene oho, ni kuma na sake haɗe rai. Yayi juyin duniya nace abinci dai bana so kana bana son ana biyoni wajen aikina. Na juya na tafi na barshi daga shi har ledarshi. Ƙarfe biyar a ƙofar gidan Badia tayi mun, sabida sauri yasa ban shiga ba itace ta fito ta kuwa saka ɗaya daga cikin kayan dana bata harda mayafi wallahi ashe da kyanta, wahala ce kawai da ƙwallafa ɗa namiji a zuchiya ya sukurkutata. Kai tsaye muka nufi ofishin ƴan sanda na kusa muka shigar da ƙaran Baballe akan ya siyar ma da Badia kayan ɗakinta. Akayi rubutu akai duk abinda ya dace. "Yanzu a ina zamu samu Baballe ke Badia? " Ɗan sandan ya tambayeta. "Ko yanzu dana fito yana gida" "To shikenan bari aje a tawo dashi yazo sai a sasanta in ya yiwu, in kuma bai yiwu ba, sai mu turaku kotu kawai. Kofur Bala aje a ɗakko Baballe ta baka adireshi maza a tawo dashi tace yana gida" Muna zaune dake babu nisa sai ga ƴan sanda da Baballe sun shigo. "Abu ta kazan uba... Da gaske dama Badia ke kikai ƙarata to akan nayi miki abu ta kazan me? Zaki yi ta aurenki kuwa wallahi ƴar abu ta kazan uba " To sai me dan tayi ta auren nata? Baku da aiki sai barazana da saki, ko in kun saki mace mutuwa akace muku zata yi oho. Ko kuma kun ɗauka rayuwarta tsayawa take yi ne oho" Sheƙeƙe ya dubeni ya maya baki a buɗe na fahimci kallo na biyu na mamakine, shi yasa ya buɗe bakinshi. Kafin yace um an tasa ƙeyarshi zuwa bayan kanta, mu kuma muna daga wajen kanta. "Matarka Badia ta kawo ƙararka akan ka siyar mata da kayan ɗakinta kaf ba da izininta ba, kana baka iya ɗaukar nauyinta dana yaranta. Shin gaskiya ne anyi haka ko yaya? " "Abu ta kazan ubancan. Tabbb Badia wannan bayahudiyar mai hure ma mata kunne itace ta zugaki kike son tozartani a idan duniya, abunda baki taɓa yi ba? Matar da ake cewa kwangilar rushe matan aure taje ingila ta karɓo yanzu layin har yazo kanmu? " Kunji lafazin bakinshi? Hmm baku ji yadda yake magana da ƙarfi ba, bakinshi sai yauƙi yake yi. Da gani babu tarbiyya da addini tattare dashi jahiline tsantsa. "Dallah mai firen rufe ma mutane baki nan ba wajen wasa bane, hakane ko ba haka bane? " "Ba haka bane sharri suka ƙullo suyi mun kawai, yallaɓai wannan in kana Facebook zaka santa kullum fa bata da aiki sai zagin mazan arewa da nuna ma mata gazawar maza. Ina binta ai har kwamen na zagi nake yi mata a duk sanda ta saki sabon bidiyo. Ita da Lubna boƙararriya ina yawan la'antarsu." Banci ɗan sanda ya buga Baballe ya dawo hayyacinshi. "Kace baka siyar mata da kayan ɗaki ba ko? In muka je muka duba babu kayan ɗakin zaka sha wuya har gidan yari za'a kulleka" Da jin gidan yari sai Baballe ya sakko ya hau in ina. "Da gaske na siyar amman ara nayi ranka shi daɗe, ayi haƙuri sati mai zuwa aurena taya za'ace za'a kaini gidan gyaran hali? " Muryarshi lub tamkar bashi bane yake ɗura ashariya yana ɗumawa ba. Ofisa yace. "To zamu kulleta har sai ka biya kuɗin, madam nawa kika ce kayanki zai kai? " "Dubu ɗari biyu har da hamsin, ga jerin adadin yawan kayan daya siyar mun nan duk na rubuta a bayanaina" Baki Baballe ya buɗe idanunshi jawur yana kallona cikin tsana, ji yake kamar ya sakar mun iskar gas. "To zaka biyata kuɗinta mun baka kwana biyu in baka biya ba zamu turaku kotu, daga kotu sai gidan gyaran hali. Sajen a shiga dashi babu beli har sai ya biyata hakkinta. A tuɓeshi a adana mishi wayoyi da kuɗaɗenshi." Godiya naita ma ofica ina ƙarawa yace babu komai muje kawai gobe sai mu dawo da rana ko safe. Badia jikinta duk a mace yake har muka ƙaraso Mr Bukhari ce. Tom wata sabuwa in ji ɗan caca Kuyi haƙuri gobe ba lallai ku samu Posting ba, wallahi bana jin daɗi asibiti ma zanje. Nagode sai in mun haɗu zuwa monday kuma SANNAN KU TAYA ƊAYA DAGA CIKIN ADMINS ƊINMU JIMAMI ALLAH YAYI MA MAHAIFIN AMINA MADAKI RASUWA. MUNA MIƘA TA'AZIYYARMU GARETA MUNA ROƘON ALLAHBYA YAFE MISHI, YASA ALJANNAH TA ZAM MAKOMA GARESHI🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻 9153081057 Buhari Ibrahim ladan Palmpay SANYA KUƊIN KARATUN TA WANNAN ASUSUN ƳAR UWATSUREN TSIRIN... TSANDAURI.. LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUƘHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA BIYAR (5) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DShCUZYCIFz4jkcpvChacU Shiga group dinmu domin samun ingatattun duk wani nau'ikan kaya da ake turowa daga Egypt kama daga abayas jilbab dasauransu cikin farashi me rahusa da ingataccen quality 👌💪✨💯🇾🇪 Taken mu shine shigar larabawa kai tsaye zuwa gareku🥰 Direct from Egypt to your doorstep 💯 +20 12 22791293 Sai da na dafata tayi saurin juyowa. Badia kaddai nadama kike yi na kulle Baballe da akayi? Bari kiji Badia tun wuri ki sanar dani abinda ke ranki kada kisa inji kunya, in gama haƙilon tsaya miki daga ƙarshe ki ɗebi ƙasa ki tula mun" "Wallahi Malama nadamar auren Baballe kawai nake yi. Bana dana sanin shigowarki rayuwata domin ki taimaka mun. Malama babu ranar da zata fito ta faɗi Baballe bai kutuntumama iyayena ashariya ba. Abu mafi ciwo a gaban yarana mata sai ya tsinkeni da mari" Mari Badia da yaranki goma miji ya mareki ke kuma kina zaune baza ki haƙura da auren ki nemi rayuwar da tafi ta gidanshi ba? Wai ina zamu kai son miji ni Hindu, anya matan wannan ƙarnin da muke ciki ba cutar son rijalu bace ta kamasu ba kuwa?.... Muje inga ɗakin naki mu gaisa da yara, ga magriba tayi sai muyi sallah sai in tafi." Tare muka shiga yaran suna tsakar gida ƴar babbar tana bakin murhu tana tuƙa tuwo ga miyar a rufe a gefe a ƙaramar tukunya. "Mama sannu da dawowa ina wuni? " Suka gaggaisheni na amsa da fara'ata ina ƙarema gidan kallo, da yaran gidan hmmm. Babbane sosai gidan yana da filin tsakar gida sosai, ga ɗakin Badia can gefe ga kuma tamfatsetsen ginin Amarya. Jana tayi muka soma zuwa ɓarayin Amaryar duk da a rufe cikin yake an yi jere. Yasha fenti har tsakar gidanta yayi mata. "Kinga harda tsakar gida ya yanka mata, ga bayan gida a ɗaki gana baƙi a tsakar gidanta. Ni da yara goma da banɗaki ɗaya muke amfani, wani sa'in wata na ciki wata ta matsu haka dai muke rarrafawa, muke gurgura rayuwar." Allah ya kyauta amman wannan ginin Baballe ya kashe kuɗi Badia, nace dama yana da kuɗine? " "To yana noma, noman shinkafa, da dawa, kuma abun ya karɓeshi yana ajjiye hatsi sosai kawai dai nice ba zaima ba har gidan gona gareshi ya zuba kaji sama da dubu akace shima a bakin ƴan uwanshi nake ji. Wallahi Allah bansan da wannan gidan gona ba. Dan ni ranar da naji a zaune na kwana ban bacci ba" Kina me?" "Inata tubkewa da warwarewa, gami da mamakin Baballe" Murmushi nayi kawai. Hannunta na jawo muka fito, muna tafe tana labarta mun har muka shiga ɗakinta. Manyan ɗakunane ciki da falo fulastar ɗakin duk ta farfashe ko leda babu a ɗakin fenti ma dan masifa harya sude ba'a iya gane wanne kalar ne, ga jinin kuɗin cizo ko ta ko ina tamkar ɗakin Shanno ta Kaila zance, ko ta Jega. Uwar ɗakin babu komai sai katifa da jakunkunan kaya masu yawa, rai goma sha ɗaya ba wasa ba. Tsummokarai tako ta ina saman ƙofarta shaƙe fal da kaya. A haka na ɗauro alwala ta shinfiɗamun zani nayi sallah, ko sallaya bata dashi, aka zubo mun tuwo na daure dai nayi loma uku. Badia a irin ɗakin da kishiya zata shigo ta sameki kenan abinda Baballe yake nufi kenan?. Kuma sabida wauta irin taki batun miliyan ɗayanki kince kin yafe, me yasa ba zaki ƙwarara kanki ayi mai gabaki ɗaya a wuce wajen bane. Ko akwai abinda kike tsorone?" "To ya za'ayi sai haƙuri kinga dai rayuwa. Abinda yasa na ce na yafe mishi shine. Akan wannan kuɗin Baballe zai mun sakin wulaƙanci, yarana goma ace ina riƙe dasu babu Aure, a irin al'ummar da muke ciki zai zame mun babban ƙalubale. Yaran kansu sai aure ya gagaresu za'ace yaran macene. Gani da siriki ina tsoron abinda zai taɓa rayuwar aurenta." Hmm nagane, kuma nagani Badia, zanyi ƙoƙari in sha Allah ayi miki filasta da fenti gobe masu aiki zasu zo, masu fulasta kenan su soma aikinsu. In ya baki kuɗin kayanki sai a sai masu sauƙi ragowar a rage ayi jari babu komai " Kuka ta fashe dashi kawai na shiga tausa. Daf isha na bar gidan Badia takwas da rabi na sha kwanar gida mijinyawa na tsaye ya saka hannu a ajjihu da alama tunani yake yi tunda haka ya saba, aikin banza. Get ya buɗemun na shiga. Kafin ya gama rufewa na shige gida a guje cikina ya murɗa yara na mun sannu hannu kawai na ɗaga musu na wuce a guje. Ina zama a sita sai gudawa, ba sai amai ba kuma. Wallahi kamar wasa nayi amai har bana iya tashi, mijinyawane ya shigo ina kwance cikin amai ya shigo ganin ƙofa a buɗe yasan babu lafiya. Kada ka taɓani bana son taimakon ka, ka fice mun" Nayi saurin katseshi daga shirin ɗagani da yake yi. "Haba Tutar so yama zan barki haka a cikin amai?" Daddagewa nayi na miƙe duk da saida ya riƙeni da yaga jiri na ɗibata. Fisgewa nake son yi na kasa. Da ƙarfi na fisge hannuna na tureshi, ina haki, idanuna sai rufewa naji suna yi. Kaje zanyiwanka ka fitarmun nace ma, wallahi in ba haka ba zan iya raunataka a banza. "Mai taurin kai kawai, ya ma za'ayi in barki haka" Zaunawa nayi a saman sita. Shi kuma ya goge aman tas kafin ya fita ya barni. Rarrafawa nayi na shiga wajen wankan na watsa ruwa a jikina sai naji dama_ dama saida na huta sosai na fito ɗaure da tawul ina tafiya a hankali. Har wannan lokacin ina jin cikina na haɗa shirgi, ga tashin zuchiya. Abinci na tadda mijinyawa na jeramun a kan teburi harda ruwan wanke hannu. Ƙuramun idanu yayi kamar ya cinyeni dan sha'awa har ajjiyar zuchiya yake saukewa a kakkatse maza a barsu kawai. Shi da yake da matan bariki meye na ajjiyar zuchiya dan yaga bagidajiyar mace. Kaina na kawar ba tare da nace uffan ba nayi saurin zura doguwar rigata, kana na zare tawul ɗin ta ƙasa. "Zo ki zauna ki samu ki saka wani abun a cikin ki. Ga magani na kawo miki kisha" Bance komai, kallon dana watsa mai yasa wallahi ba shiri ya saka kai ya fita kawai, harda haɗawa da sauri, tsaki naja na yane kaina da mayafi na ta da kabbarar sallah. Ina idarwa yaran suka bubbuga naje na buɗe musu sukai mun sannu da jikin. Azgar wa yayi girkinnan? " "Nine Ammi duk da bansan ko shi kike so ayi ba. Nayi ta kiran wayarki babu amsa." Yayi ba kullum mutum ke samun abinda yake so ba. Zanci abinci in kwanta sai mun haɗu kuma gobe. Ina da magana da kai zuwa gobe" Nayi sallama dasu na rufe ɗakina. Ina cin abincin amman hankalina, tunanina yana ga ɗakin Badia da irin abincinsu wanda babu tsabta a ciki gashi naci yana neman halakani. Naci ne kawai sabida in ƙarfafata, amman wallahi nasan za'ayi haka. Ni ko abincine a ido bai mun ba, in dai naci saiya dawo gaskiya. Zuchiyata tace. To namiji na neman halakata ya cinyeta da ciwon hawan jini, ta faɗi ta mutu ƴaƴanta sune da asara. Wata zuchiyar tace. To su yaran a tantagaryar ƙasa kenan suke kwana babu ko tabarma ko yaya, katifa ɗaya ce a ɗakin ai? " Iska na fuszar daga bakina kawai. Na lumshe idanuna ina jin zafi da raɗaɗin halin da mata suke tsintar kawukansu, a gidajen aurensu. Rayuwar mata abar a tausaya ce. Da mafarke_mafarken Badia na tashi dashi na wuni a wajen aiki dashi, na labartama Luba ma tace zata bini ofishin ƴan sandan taga Baballe muna hanyane wata itama ta kirani tana son ganina a yau ɗinnan tana cikin matsala. Adireshina na tura mata itama ɗalibar cikin zaurena na kan manhajar WhatsApp ce, kuma tana taimakawa wajen bama mata shawari na hankali. Banso bata adireshin nawa ba, amman bazan iya zuwa inda take ba, kuma wajen aikina bazai yiwu in ce zan maidashi wajen jin koken mata ba, akwai dai yiyuwar in samu ofishi nawa na musamman. "Hindu inaga ki buɗe ƙungiya kiyi rijista kawai kamar shawarar da a baya mijinyawa ya taɓa baki, sai ki kama ofishi kawai ki dinga jin koken mata. Amman gayyatarsu gida ba mafita bane, yadda rayuwarnan ta kasance" Kallonta nayi tare da yin guntun murmushi nace. Shi kuma aikin nawa zaki karɓa mun Luba? A yanzun ma yaya na cika ishasshen bacci ba samu nake yi ba. Ga yarana ranar hutu kaɗai suke samun lokacina. Amman gaba zan kafa ƙungiyar da matan arewa zasu yi alhafari da samuwarta. Jibi Fauziyya d Sulaiman irin ƙoƙarinta da tallafama gajiyayyu da take yi. Matar jarumace sosai. Zan samu buɗe ofishi Luba, amman sai nabi matakan duk daya dace, gudun take doka" Luba tace. "Ga Umma Sulaiman ƴan awaki Anty Baby tana ƙoƙari har gida suke ginama marayu da marasa ƙarfi, ko su gina rijiyoyin burtsatsai. Harkar taimako akwai daɗi kuma itama kinga tana wani shiri mai suna sirrin mata a Aminci rediyo tare da mataimakiyarta Hajiya Badia. Amman ita kinga aikinta sau ɗayane a sati kawai. Ba kamar mu masu aikin kullum ba. Aikin ɗakko rahoto ba ma aikin ragwaye bane, ga haɗarin dake cikinshi. Jiya ina kallon aljazira wallahi gobarace akayi a wata ma'aikata, masu ɗaukar rahoto daga wajaje daban_daban ƙasa ta rufto musu a kansu, wallahi sun rasa rayuwarsu, ta dalilin ɗakko rahoto" Har muka isa gidan Badia muna hira. Ma'aikatan dana turo har sun gama fulastar ciki da falon tun safe. Tace ma a maƙota zasu kwana zuwa gobe ya bushe sai a yi mata fenti. Sai godiya take yi tana shi mun albarka. Ko da muka isa ofishin ƴan sanda mun tadda Baballe an fito dashi wani abokinshi yazo zai biya kuɗin sai gamu abun yazo a daidai. Duk da abokin yayi ƙoƙarin tanƙwara Badia akan ta rage yawan kuɗin ta duba darajar ƴaƴa kunsan maza wajen son kansu babu damane, to Allah kuwa me yasa shi Baballe bai duba darajar Ƴaƴa ya martabata ba uwar ƴaƴanshi goma fa, yara goma ai sunfi ƙarfin wasa. Ni na zame mata baki sabida na fahimci tana tsoron Baballe, sai harararta yake yi yana ƙuta. Haka dai da suka gama surutansu wannan abokin nashi ya ciro kuɗi a leda cib kuɗinta ya miƙama kofur ya ƙirge kuɗi tas. "Hajiya kuɗi sun cika cib" To Alhamdulillahi mun gode Kofur Allah ya saka da alkhairi. Yanzu kam za'a iya ba da belinshi mun gama da wannan amman bamu san ko zamu sake dawowa akan sabon kes ba, dan duk abinda Baballe ya kuma yi mata zamu sake garzayowa" "Ƴar kwangilar yahudawa, wato kin shigo rayuwar Badia ne domin kisa ta boƙaremun? To Lubna Saleh michika ma shugabar mata boƙararru ba'a bakin komai take ba a wajena" Ai kuwa a bakin komai take da ita da ire irenta sun tsaya ma maza a wuya kamar ƙayar kifi. Kun fi so mata su kasance a cikin duhu kuita gasa musu aya a hannu ko? Ni da Badia mun riga mun zama ƙawaye babu yadda ka'iya dani." Nan dai muka gama abinda zamu yi muka baro Baballe acan sabida sai Dpo yazo kana ya basu umarni ayi belinshi. To Badia ga kuɗi sun samu a shawarce ki sai gado da katifa, sabida yaran, sai kujeru ko da rabin seti ne da abinda ba za'a rasa ba. Zan siya miki kafet ki saka a falo, zan kuma taimaka miki da jari in sha Allah." "Nagode sosai Malama Allah ya duba miki, ya raya zuriyarki, ya barki da mijinki har aljannah" Babu komai Badia nagode sosai. "To nima ina da tsohuwar katifa zan taimaka da ita ko yara sa kwanta a ƙara muku" Cewar ƙawar Arziki Luba. Nan ta shiga murna tana godiya. A gida na sauke Luba nima na nufi gida. A falona na tadda baiwar Allahn da muka yi zata zo yau. Ita kaɗaice a falon mijinyawa naga motarshi amman ƙila sabida ganin baƙuwa yasa ya tafi ɗakin Azgar. Shiga nayi a mugun gajiya. Gaisawa muka yi da fara'ata na marafceta, da ɗiyarta mace da ba zata wuce shekaru biyar zuwa shida ba. Me sunanki ƴan mata? " Na tambayi yarinyar tare da ɗan jawo hannunta. Sai kawai ta fashe da kuka. Toh ƙyuya take yi ne?" "Ba ƙyuya take yi ba. Bata da lafiya ne Hajiya bari ki gani." Sai ta kamo yarinyar ta cire mata ɗan zanin jikinta sai na ganta da ƙunguzun yara a jiki. Tana warware ƙunzugun sai wari ya cika wajen. Duburarta ta juyomun na gani a fatattake uwar sai sharce hawaye take yi, yarinyar kuwa jikinta har rawa yake yi. Baiwar Allah dena kuka waye yayi ma ƙaramar yarinya irin wannan aika aikar, ke kuma kina ina?" Sai rishin kuka kawai take yi. Mayafina na gyara na suri jakata. Taso muje asibiti duk abinda ya dace za'ayi asibitin shine farko" Kinkimar yarinyar tayi muka fito. Azgar zo ka tuƙamu zuwa asibitin malam aminu Kano dan Allah nagaji bazan iya tuƙi ba, kaina ciwo yake mun. Kema kizo muje" Duk na tattare kan yaran muka tafi malam Aminu Kano sabida nasan wata ne suka amince suka karɓemu ba tare da mun haɗa da ƴan sanda ba. Ban bar asibitinnan ba sai sha ɗayan dare, sai da na siya ma Mariya abinci, ƙanwarta tazo taya ta kwana kafin nayi mata sallama akan gobe zan shigo da safe mayi magana lokacin, dan na fahimci bata cikin hayyacinta. Ina bayan mota tunanin ƙaramar yarinyarnan ya shigeni, kes ɗinta ya gigitani inata tunanin to wanne marar tsoron Allahn ne ya hakkema yarinya ƙarama irin khadija kuma ta baya, ya fatattaka mata takashinta sosai. Kainane yaci gaba da sara mini, tamkar zai faɗo. Ni nama mance a cikin damuwar da ni nake ciki shaf. Ko da na shiga gida shayi kawai da guntun kek naci, na yi wanka a daddafe na kwanta cike da mafarkai marasa daɗi. Washegari da safe na wuce asibiti na tafi ma da Maman Khadija abinci. Khadija tana baccinta ga ƙarin ruwa a ɗaure a hannunta uwar tayi tagumi kawai. Bayan mun gaisa sai na nemi ta juya mun bayan khadija zanyi bidiyo in yaɗa. Bayan na ajjiye abincin nayi bidiyon sai muka runtuma wajen likita yarinyarnan aiki za'ayi mata nan da kwana bakwai, sabida ashe ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, aka ayi mata wannan aika_aikar ba kuɗin aiki ana neman nera dubu ɗari kusan uku da ɗoriya. Mahaifiyar Khadija ta fito a firgice tana kuka. Ki yi haƙuri maman Khadija A gurguje takwas ta kusa inaso zanje aiki shin wa yayi ma yarinyarnan wannan aikin? " "Ƙanin mahaifinta ne da yazo daga ƙauye yake zaune damu shi yayi mata wannan aika_aikar. Ki taimaka mun a ƙwato mata hakkinta dan Allah Hajiya Hindu" Kai nane naji yana ƙoƙarin bugawa da mamakin jin furucinta na wai ƙanin mahaifinta ne yayi mata wannan aikin. Lallai anyi ma zumunci riƙon sakainar kashi. Ajjiyar zuchiya na sauke murya a dashe nace. Kuma yana ina yanzu? " "Yananan tare damu Mijina baima amince cewar Musa shi yayi wannan aikin ba. Akan haka har mahaifiyarsu sai da tazo daga ƙauye taci mun mutumci sosai, kuma suka ce ko Musa ne yayi dole ayi haƙuri a zauna dashi a haka kada ayi abinda zai taɓa zumunci. Haka suka cuceni suka barni da yarinya ko asibiti ban kawota ba, wai gudun tonuwar asiri. Ni nake ciyar da kaina da kula da Khadija da yayunta" Tabbb duniya tazo ƙarshe ai yanzu lalacewar zamani har ya kai Musa yayi irin wannan abun kuma a daddanne maganar, harma a biki da sharri. Musa yana gidanku yana rayuwa kenan daku? " "Wallahi yananan Hajiya shima fa har rirriƙeshi aka dinga yi akan wai sai ya kasheni shi sharri nayi mishi" To ke ubanki kike yi da baki san yana kwanciya da'ita ba. Yarinya ƙarama irin Khadija ace ana saduwa da'ita ta baya, amman ke baki ma sani ba, har saida ta ruɓe? Zuchiyata sai naji tana tasomun tamkar zan amayar da'ita. Da ƙyar na saita kaina gudun kar in sake jefata a cikin wani taskun. Zanje aiki inna dawo zamu je dake ofishin ƴan sanda yau Musa bai isa ya kwanta a ɗakinshi ba da izinin Allah zan yi miki tsayuwar dakan da sai na ga Musa a gidan yari a garƙame kafin hankalina zai kwanta. Amman ki mun alƙawarin barazanar saki ba zata sa ki juya mun bayan da za'a soma kes kizo a zugaki ki janye ba? Zan yaɗa bidiyon Khadija tare da asusun bankina ga masu bukatar taimaka mana in sha Allah. Ki je ki zauna kuci abinci, ki kuma kwantar da hankalinki" Da haka mukai sallama na wuce aiki, a ranar ma naje gidan gwamnati na ɗakko rahoto na dawo ofis ƙarfe uku muka tashi, yau ni kaɗai na wuce Luba tana da inda zata je. Hankalina bai kwanta ba saida muka shigar da ƙara sukaimun alƙawarin Musa a hannu zai kwana gobe mu dawo. Nayi farin ciki sosai haka ma Maman Khadija tayi murmushi ko babu komai naji daɗi ganin murmushi a fuskarta. Tun daga nan ofishin ƴan sanda take bani labarin yadda abun ya faru. "Ni gidan aiki nake zuwa in yi wanke _wanke da girki da yamma in dawo gida. Ɗan abincin dana tawo dashi shi zamu ci da yarana. Ina da kishiya itama ita ke ciyar da kanta sai yaronta dake tallar fiya wata ya ɗauke mata abincin dare. Yarana ukune Khadija itace ta biyu Akwai yarsu shekararta takwas sai na goye. To inna tafi gidan aiki Rabi'a ta tafi nata aikin sai yara a gidan, Salma ita ke kula da Khadija shi na goyen tare nake zuwa dashi wajen aiki. Da rana Musa yake dawowa gida yaima khadija wannan aikin. Ranar da nake tunanin itace ranar farko naga jini a wandonta a tunanina bayan gidane nasa Salma ta wanke mata tana ta kuka nayi tunanin kukan rigima ne kawai na yara. To washegari da zazzaɓi muka tashi tayi zazzaɓi sosai daga baya ta warware, har Rabi'a na mata tsiyar daga yin ciwo tafiyarta ta canja. To sai ranar da yayi mata wannan wallahi har Yayarta tace ta ganshi itama kuma yana cewa ta sha mishi kuma tana sha" Tai ta bani labarin daki daki da irin rayuwar da suke yi wacce bata da maraba da zaman kai. Kuma da sunan aure suke yi mijin aska na cin ƙwaryar kanshi, anma ya bar rayuwar iyalinshi a haɗari. Ayi magana ace mune masu hure ma mata kunne. Yanzu dan Allah masu karatu da irin Auren da su Maman Khadija da kishiyarta suke yi ba gara zawarci ba, mace tasan bil haƙƙi dole ita zata kula da kanta ba? Tabbb Allah ka gyara mana. Wannan lalacewar zamani da lalacewar wasu mazan da yawa take. Nayi mata tambayoyi masu yawa a matsayina na ƙwararriyar ƴar jarida. Akwai kuskurenta da sakaci sosai. Ace kamar Khadija yarta ƴar shekara takwas ita ke mata wanka yarinyar da in da gata bata wuce a wanke mata kashin mazaunanta ba, wai ita ke kula da ƙanwarta. Nayi mata faɗa_nayi mata faɗa. Na nuna mata laifinta ta kuma yadda tabbas tana da lefi. Daf magriba muka iso asibitin naje na duba jikin Salma na basu kuɗin siyan abinci nayi musu sallama na shiga gida ana kiran isha. Sabira kawai na tarar a ɗakinta tana sallah. A banɗakinta na ɗauro alwala nazo na gabatar da sallah. Muna hira da Sabira ina tambayarta makaranta da gida su Azgar suka shigo. Jin muryata a ɗakin yasa suka shigo harda Mijinyawa da kwana biyunnan nake ganinshi kamar marar lafiya sai sake tsomarewa yake yi. "Tutar so kin dawo barka da dawowa ya aikin? Ban ko kalleshi ba Ɓoyayyar ajjiyar zuchiya ya sauke. Ya jima yana hira da yaranshi yanayi yana kallona ni laptop ma na buɗe na yaɗa bidiyon Khadija tare da taƙaitaccen rubutu da lambar wayata da lambar asusun bankina, masu son zuwa suga khadija domin tabbatarwa su kirani ta waya sai in kaisu su ganta. Ban faɗi asibitin da take ba gudun kar a damesu da zuwa, ban kuma yadda fuskarta ta fito ba sabida watarana zata girma itama ta zama mace, hakan zai iya zama mata tarnaƙi wajen auruwa. Ina ɗago kaina naga Mijinyawa ni kawai yake kallo ya shagala sosai yana mun wani irin kallo. Rai na haɗe tare da tura labtop ɗina a jaka na miƙe na fita zuwa ɗakina. Ina fitowa wanka Sabira ta kawo mun jallof ta taliyar manja da bushasshen kifi sai ruwan shayi na Ahmad. Zama tayi ina ci muna hira duk da na gaji amman data buƙaci hirar take so muyi saina zage nasan suna kewata, kwana biyunnan kaina yayi zafi sosai. Washegari da asuba dana tashi wallahi tallahi naga kuɗaɗe da suka shigo fin nera dubu ɗari biyar, kuma fa harda masu saka ɗari biyu. Mutanen da sukaimun magana ta manhajar WhatsApp kuwa Allah yayi yawa dasu harda wata lauya da tace mun tana da ra'ayi akan kes ɗin in za'a shiga kotu. Wannan saƙon nata yayi mun daɗi sosai da sosai. Amsa mata nayi tare da yi mata godiya mai tarin yawa. "Inason ganin yarinyar yau in babu damuwa, domin in tattauna da mahaifiyarta" Ta rubuto mun. Sai na bata amsa da. Mu haɗu a asibitin malam Aminu Kano da misalin ƙarfe huɗu zuwa biyar na yamma" A gurguje na fito daga ɗaki shayinma a tsaye a Kitchen na sha da yara suka matsa lamba. Ina kan sha mijinyawa shima ya fito cikin shirin fita ganinane yasa ya tsaya. "Giwa kin tashi lafiya? Naga bidiyon da kika yaɗa na tausayama Khadija gaya, ai itace yarinyar da suka zo jiya tare da mahaifiyarta ko? Itace" Na faɗa tare da kurɓar shayina ina tura biredi. "To Allah ya bata lafiya, shi kuma Musa In mai shiriyane Allah ya ganar dashi. Nima na tura da nawa gudunmawar duk da babu yawa dai. Ni zan wuce aiki amman inna dawo inaso zamu yi magana dan Allah" Kallon tsana nayi mishi, da sauri yayi ta hanyar haɗe hannayenshi dukka biyu halamun ban haƙuri" Bani da lokacine abubuwan da suke kaina sun sha mun kai. Kana iya bari ƙarshen sati amman a ranakun aiki bani da lokacin ɓatawa" Rai ya haɗe da halama abinda na faɗi yayi mishi zafi. A tsaye a wajen na yi ficewata na barshi cike da ta'ajibin abinda nace dashi. Nasan mamaki yake da har aka samu wani lokaci da ni Hindu bani da lokacin shi aikina yafi mun komai mahimmanci. Ina shiga motata na tayar da'ita ina zaune ina ɗan womin ɗinta. Sai kiran wayata akeyi lambobi daban daban. Azgar na buɗe mun get na fice ina ɗaga mishi hannu. Tunda na fito nake amsa wayoyi duk akan kes ɗin Khadija lauyoyi uku ne suke da ra'ayi akan kes ɗin dukkansu mata ne. Hukumar kare hakkin ɗan adam ma sun mun magana akan zasu shiga kes ɗin. Da murna da farin ciki na isa office aikinma cikin karsashi da jin daɗi na gudanar dashi. Da muka yi birek ne nake labartama Luba abinda ake ciki. "Ai naga bidiyon ya yaɗu fiye da tunani Hindu. Gaskiya kes ɗin khadija kes ne da duk mai imani sai ya tausaya ma yarinyar harma da uwar yarinyar. Yanzu nasan dai kotu dole za'a shiga kuma dole a hukunta Musa, amman ita Maman Khadija zai yi wuya aurenta yayi ƙarko da Baban khadija tunda dai ya nuna yana bayan ɗan uwanshi." Ai wannan aure ya daɗe bai rabu ba Luba. Ya saketa mu shigar da shi kotu ba. Ai hakkin ci, da sha, da tufatarwa, da neman lafiya, da baya iya musu yanzu. Wallahi daga lokacin da ya saketa zai sha mamaki" " Hindu maza sun shigo hannunki ai wallahi sun zama nama" Dariya muka saka. Bayan mun tashi a wajen aiki kuma. Sai nace da Luba taje gida akwai inda zani, inna dawo zan zo har gida in ɗauketa muje asibiti. Haka akayi, ita ta wuce gida ni kuma kai tsaye na bi adireshin gidan Talatu Ibrahim first bank. Na ko ci sa'a maigadi ya buɗe mun get na shiga harda motata, sakamakon mun yi waya da Talatu Ibrahim First Bank tun dana taso. Yadda na tsammaci gidan ba haka na tarar ba, gidan yafi mun kama da gidan matar aure, ba mai zaman kai, ko mai zama gaban iyaye ba. A haka dai na kutsa kaina na shiga. Ilay sai ga hoton Talatu, da mijinta, da yara biyu maza a bango. Ko wanne hoto mutum ɗayane a jiki. Girgiza kai nayi kawai ina ta'ajibin ashe Mijinyawa har matar aure kenan yake mu'amala da'ita. Ni dai ina zaune bayan na gama ɗaukar hoton hotunan Talatu dake jere dana mijinta a waya. Sai gata da fara'arta ƙaƙas. Ta zauna sai muka gaisa, harja jus ta ajjiyemun. "Bismillah ga ruwa ki ɗan sha" Murmushi nayi mata. Kar ki damu da ruwan Talatu Ibrahim. Nace ashe mijin naki soja ne ma, gaskiya mana" Sai ta ɗan haɗe ranta kaɗan tace. "Me kike nufi ne? " Yanzu in nace miki mijinki yana zinace zinace da abokiyar aikinshi kuma matar Aure, ke kuwa Talatu ya zaki ji? " Wannan jus dai ita ta ɗauka ta kurɓe. Murya na rawa tace. "Me kike nufi da hakan, ni na ɗauka da gaske ƙawata da muka yi karatu tare ce ke, kamar yadda kika ce mun? Taya zaki haɗa mijina da irin wannan alkaba'in. Wacece ke me kuma ya kawoki?" Murmushi nayi na ɗakko wayata na tura mata wannan hotunan chart, nace da'ita. Duba wayarki zaki ga saƙo sai kiyi mun bayani" Da sauri ta shige wata ƙofa ta ɗakko waya ta dawo ta zauna. Data buɗe ta gani, kuma na haɗa mata da hotonmu da muka ɗauka ni da mijinyawa. Sai kawai ta sauke kanta tana zufa. Can ta zabura ta dawo kusa dani. "Ki mun rai wallahi muddin mijina yasan halin da nake ciki, kashina ya bushe bindigeni zaiyi" Kallonta nake yi ƙur yadda take hawaye, jikinta na wani irin mazari. Hmmmm Talatu Ibrahim. Yaushe kuka soma nema ke da Magawata Ɗan safiyo? In kika mun ƙarya komai zai iya faruwa" Sai carab ta rirriƙemun hannayena tana godona. "Ki yi haƙuri. Wallahi zaman kaɗaici da rashin mijine yasa na soma neman mijinki wallahi. Mijina Soja ne, bashi da lokacin iyalinshi sam, kuma bani kaɗai bace matarshi ba. Kuma kinji na rantse miki Magawata Ɗan safiyo bai san ni matar Aure bace, nace mai mijina rasuwa yayi. Bazan mai ƙazafi ba, wallahi tabbas na tabbatar mishi babu aure a kaina. Kuma ni na nemeshi da kaina" Ta wacce hanya kika nemeshi to? " Kanta ta sauke tace. "Ta hanyar waya, na jima ina tura mishi tsaraicina tun baisan wacece ba. Har na bayyana mishi ni wacece, daga nan ne muka soma haɗuwa dashi. Kiyi haƙuri dan Allah. Akwai sanda muka haɗu da Ƴarshi Asama'u a zango baƙi ma. To kusan tun daga lokacin alaƙarmu ta yi baya. Daga baya yazo ya janye mun gabaki ɗaya. Ko na je ofishinshi koroni yake yi. Shikenan dai muka yanke alaƙar tamu. Nayi nadama tunda nake ban taɓa jin kunya da tsoro irin na yau ba. Ki rufa mun asiri" Shiru nayi kawai ina kallon yadda take rusa kuka tamkar ranta zai fita. Ni kuma a lokacin zuchiyatace take ta yinƙuri tamkar zan yi amanta. Mun fi mintuna goma tana kukanta, ni kuma ina rarrabe kalmominta, da batun Asama'u da tayi. A wanne zangon baƙinne kuka haɗu da Asama'u, kana a cikin irin wanne yanayin ku kuke a lokacin data gankun?" "A harabar shiga zangon baƙinne, mu kuma mun fito, hannunmu na sarƙe dana juna, har muka shiga mota shi bai ganta ba, amman ni na ganta a lokacin. Kuma taga abinda muka yi a cikin motar, a nanne Magawata ya ganta duk ya ruɗe, shine ma nake tambayarshi wacece ita, yace mun ɗiyarshi ce ta biyu" Murmushine ya suɓucemun kawai. A wanne yanayi ta ganku kuma? " A kunyace ta faɗamun, Asama'u ta ganshi a lokacin yana yamutsa Talatu, bakinsu a cikin na juna. To a lokutan aiki kenan kuke zuwa ku sheƙe ayar taku, ko ya kuke haɗuwa. Na dai san sau biyu ya taɓa fita a ranakun da ba aiki" Idanuna na zuba mata. Ina jinki, in kin zaɓi in turama mijinki ai shikenan, ina da lambarshi, harda lambar mahaifinki daya haifeki ma" Muryarta na rawa tace. "Ranakun aikine ne muke haɗuwa, sau ɗaya muka taɓa haɗuwa ranar wata asabar" Itace asabar ɗin da yazo daidai goma sha ɗaya ga wata ko?" Kai kawai ta gyaɗamun. Murmushi nayi nace. To sau nawa kuma kika kawoshi gidanki kuka kwana ne?" Kuka ta fashe dashi tace. "Sau biyu ne, kaɗai muka kwana. Daya kwana ɗaya washegari ya tafi Jama'are, daya dawo ya kuma zuwa ya kwana, washegari ya wuce shikenan wallahi, ban ɓoye miki komai ba." Kai kawai na girgiza ina jinjina girman rashin mutumcin Mijinyawa. "Dan Allah zaki rufa mun asirina, ki duba yarana" Na duba su, kuma bazan yaɗa sirrinki ba. Ke dai kiji tsoron Allah ki kuma sani Allah bazai taɓa barinku ba. Kinci amanar mijinki da yaranki, shi farkanki yaci amanar matarshi da ƴaƴanshi, kun saɓama Ubangiji kun yi zina kuna da aurenku, zina mafi muni, wa'iyazubillah. Shekararku nawa kuna wannan sheɗancin?" Shiru ta kasa magana, kuka take yi tamkar ranta ne zai fice, tana yi tana tari, ga majina ta haɗa. Miƙewa nayi na fice a falon. Wallahi itace har gaban motata, tana rusa kuka mai gadi yana kallonta. A wajen na tafi na barta. Ina tuƙi idanuna na lumshewa da kansu. Sai murmusawa kawai nake yi, ina haɗa dalilan haɗuwar iskancin mijinyawa da Asama'u. Wato ashe duk irin tarbiyyar dana ba Asama'u har tasan taje zangon baƙi, har kuma tasan yadda ake zarge wuyan wanda aka kama yana aikin da baya son a sanshi. Amman dai mijinyawa an yi baƙin ɗan iska, ƙaton banza da wofi. A daidai ƙofar layinsu Luba na tsaya, na kirawota ta fito muka wuce. Asibiti muka wuce kai tsaye isowar baristan da muka yi zamu haɗu kenan, tace tana cikin wata jar mota tana shirin fakin mu kuma muna kusa da motar. Tana gaba muna bayanta muka shigo asibitin. Tare muka fito a motar. "Wai Hindu Nagoɗi ashe da gasken dai ke ɗince, naga sunan, amman inata tantamar ko sunane ya zama ɗaya. Ga Lubabatu madaki ma wannan ƙawance da girma yake ashe har yanzu kuna tare" Saudatu Mustapha wai dama kece lauyar da muke waya dake? Luba kinga ikon Allah" Saudatu Mustapha ƙawarmu ce tare muka gama sakandare da'ita wajen zamansu ɗaya da Luba. Yawan zuwa wajen Luba ne yasa nima na zama ƙawar Saudatu. Amman dake mu gidanmu bamu fiye yin ƙawayen waje ba yasa inaga Saudatu bata taɓa shiga gidanmu ba sai dai tazo wajen Luba mu haɗu acan. Akazo kuma Aure ya rabani da Kano. "Lubabatu kinga Duwaf ai ba zata canja ba baki ji wai Saudatu take kirana ba? " Luba ta kwashe da dariya tace. "Ai sai ta tuno mun da lokacin da a makaranta in dai akace miki Saudatu har kuka kike yi" Na cabke da cewa. Wani sa'in har da kai ƙara wajen malama Aisha take yi. Wataran kuma aci uwar dambe. Rayuwa gashi yanzu duk mun zama iyaye." A nan tsaye mun yi hira tayi ta minti ashirin, da ƙyar muka yakice muka shiga har zuwa ɗakin da Khadija take kwance. Muka tarar da baƙi sun zo duba jikin nata. Gaggaisawa muka yi tare da duba jikin Khadija yau dai idanta biyu tana kwance shiru duk tabi ta rame. Maman khadija muje daga waje muyi magana" "To Hajiya. Rabi'a dan Allah ki kula mun da Khadija" Kallon Rabi'a nayi na maya. Itama duk gata ga kamarta dai abun gwanin tausayi. Gefe muka samu Batista Saudatu Mustapha ta yi mata tambayoyin da zata yi mata duk ta amsa mata. Kana muka wuce wajen Diktan daya dubata zuwanmu, amman shi akace aikin dare zaiyi sai dai gobe da safe mu dawo in lallai dai muna da buƙatar ganin nashi. Mun bari akan gobe da safen zamu dawo domin Saudatu Mustapha tace lallai akwai tambayoyin da take son yi mishi a matsayinshi na likitan daya soma taɓa Khadija a halin da aka kawota. Mrs Bukhari Jama'a jikina yayi en ob diskoshon😆 To sai Allah ya kaimu monday kuma in sha Allahu rabbi. Nagode sosai da addu'o'iinku Ubangiji Allah ya bar so da ƙauna.TSURON TSIRIN.. TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA SHIDA (6) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DShCUZYCIFz4jkcpvChacU Shiga group dinmu domin samun ingatattun duk wani nau'ikan kaya da ake turowa daga Egypt kama daga abayas jilbab dasauransu cikin farashi me rahusa da ingataccen quality 👌💪✨💯🇾🇪 Taken mu shine shigar larabawa kai tsaye zuwa gareku🥰 Direct from Egypt to your doorstep 💯 +20 12 22791293 Maman Khadija kuma nera dubu ɗari na bata nace ta riƙe a hannunta, duk kuma abinda ake buƙata ta kirani a waya kai tsaye. Daga nan muka ɗunguma zuwa ofishin ƴan sanda domin mu gana da Dpo mun kuwa ci sa'a yana shirin fita ma muka zo, dan har ya baro ofishinshi. "Hajiya Hindu yaronnan har yanzu bai amsa laifinshi ba ya daku iya dakuwa. Inaga zamu tattara mu miƙa ku kotu kawai zaifi, in bai amsa ba, acan za'a matseshi har sai ya amsa" Yauwa ofisa mu hakan muke so, ba dole sai ya amsa ba, bincike zai tabbatar dashi yayi in sha Allah. Mun kuma gode sosai " "Babu godiya wannan aikinmu ne Hajiya Hindu. Wanshi ma yayi ƙoƙarin a bashi belinshi su tafi dashi gida. Babu beli a kanshi ko kotu aka kaishi kotu ba zata sallameshi ba sai dai ta adanashi har zuwa yadda shari'a ta kaya" Godiya muka yi mishi sosai kana muka fito. "Hindu Duwaf ya kamata ace ko da ƙarshen satine mu haɗu a wani ɗan wajen cin abinci mu ɗan tattauna tare da hirar yaushe gamo, sannan mu kankare gajiyoyin ranakun aiki ko me kuka ce? Sai in Gayyaci Sumayya ma ita kam muna tare basu daɗe da dawowa Kano ba, da a Abuja mijin ke aiki" Luba tace. "Hakan yayi sosai Saudatu Mustapha, a ƙallah zamu yi hira muji daɗi mu kankare damuwowin dake zukatanmu, rayuwa ba'a rabata da damuwa" Sai Saudatu Mustapha tayi shiru har fuskarta saida ta canja. Da dai alama wani miki aka tabo mata mai zafi. Kuma ƙila haɗuwar zata zama wani abu da zan iya kira rarraba matsalolin juna. "To shikenan zamu yi magana zuwa lahadi sai mu haɗu a wani wajen shakatawar in sha Allah. Luba zan amshi lambarki a hannun Duwaf" Da haka mukai sallama ta shiga motarta ta ja ta fice, ni kuma na kai Luba gida kafin na wuce nima gida. Na gama da kes ɗin Badia. An mata filasta na saka mata kafet a falo, ta zuba kujeru rabin seti, da gadonta sai katifa da Luba ta ƙara musu ta sake labule. Nayi mata kwalimar kaya, har su Yaya Saratu saida nasa sukai mata kwalima dana yara duka dai. Sannan na damƙa mata dubu hamsin zata dinga yin awara da yamma a ƙofar gida da rana kuma shinkafa da wake da mai da yaji da salak ( inji kanawa ba suka ce salak). Hankalina ya dawo kan kes ɗin khadija. Ranar Juma'a aka tura kes ɗin kotu wanda za'a soma zama ƙarshen watan da muke ciki daya raba. Daren Juma'a tsabar gajiya da zafin kan aiki da masu turo wasiƙa dan na samu sababbin takaddu masu tsoratarwa, harda na yarinyar da mijinta ke kwanciya da'ita ta baya yayi mata illah mai yawa. Ga shirye _shiryen bikin Salamatu mun kai ɗinki, mun bada gudunmawa kamar yadda aka saba lokaci kawai ake jira. Saida na haɗiyi maganin ciwon gaɓɓai na yi wanka da ruwa mai zafi kana na gasa wuyana zafi yake yi mun sosai. Na shafa man zafi na bi lafiyar gado na saki ac na ja faiba. Rufin asiri yayi a rayuwa, mata mu tashi mu nemi na kanmu, wato kuɗin kai da daɗi yake. Ban fito babban falo ba washegari sai sha ɗayan rana, da Asuba dai inaji Mijinyawa na tashin Sabira, Azgar shima naji muryarshi. A daddafe nayi sallah azkhar wannan ban gama ba na koma na duƙunƙune a faiba idona har ƙasa_ƙasa yake yi mini tsabaragen bacci. Goma da rabi na farka, wanka da gyara ɗakinane ya ɗebeni minti talatin cib. Na fito fes cikin rigata iya guiwa da wando falazo irin wanda ake kawosu daga Turkiya. Kaina a tsafe dake tunda na dawo Landan tajewa kawai nake yi nasa ribon, ina tunanin da zuwa la'asar muje kitso da ƙunshi ni da Sabira, na gaji da kan babu kitso ina kewar ƙananun kitso inaga bayan azahar ma kawai zamu je sabida aimun guda ɗari biyu cib da ƙunshi. A falo na samesu suna hirarsu ya mayar da hankalinshi kansu suna hirarsu da nishaɗi. Ƙamshina tare da sallamata yasa duk suka juyo da murmushi a kan fuskokinsu. "Kinyi kyau Tutar so" Tare duk suka haɗa bakinsu waje faɗin nayi kyau ɗin. Murmushi nayi musu su yaran na nemi waje na zauna. Yaran suka matso muka gaisa, ganinsu a wajen yasa Mijinyawa yaci albarkacinsu muka gaisa tamkar babu komai, sai dai babu fara'a sam. Dana ganshi ma wallahi fuskar Talatu first Bank nake kallo a fuskarshi, ta wani gefen in ga Asama'u. Sabira ta haɗo mun shayi da ƙwai da biredin dashi suka karya. Azgar kuma na turashi ya ɗakko mun laptop ɗina inason in ɗan dudduba kwament dana jima sosai lokaci bai bani damar dubawa ba. A hannkali ina cin abinci ina duba kwament na dariya in yi dariya, na takaici in girgiza kai. Maza na fahimci ba tun yauba suna adawa da ire _iren mata irina badan kuma komai ba, sai dan gudun kada muita musu bankaɗa mu hure ma mata kunne a tunaninsu. A zahiri kuma muna wayarma da matan kaine domin su san cewa su ba bayi bane, zaman aure ba zaman gidan kurkuku bane. Zamane na amince, yarda, karamci, zaman ibada, zaman raya sunnar ma'aiki Arrasul S a w. Naji wani kwamen da wani yayi mun abun babu hankali da ilimi gami da gogewa a ciki. Zuriyarmu kaf saida ya zagesu ya kirani karuwa arniya. Wai ni na kasa zaman aurena shine nake son hurema matan da suke inuwar aure kunne, ya kirani da Bazawara fasiƙa. Inuwar aure, wasu kuma a inuwar zalunci suke ai. Yanzu ba zalunci bane ga matar da mijinta yayi amfani da rashin iliminta da wayonta ya dinga kwanciya da'ita ta baya ba? Yanzu haka suna asibiti mahaifanta na jinyarta, inaso ko zuwa yammane in leƙa domin in tattauna dasu inji me suke nema na taimako daga gareni. "Hindu gobe inaso ki taimaka da yaran mu fita cin abinci kamar yadda muka saba. Wannan rikicin bai kamata ya taɓa jin daɗin rayuwar yaranmu ba" Ɗagowa nayi daga duban laptop na dubeshi kamar ba zan yi magana ba dai sai nace. Jin daɗin rayuwarsu yana ta'allaƙe a zuwa gidan abinci ƙarshen sati kenan inna fahimci zancanka, ko me ɗauka a matsayin jin daɗin yara?" "Bawai nufi na kenan ba. Amman dake hakan muka saba a baya, a haka suka taso suka tadda muna yi" Hmmm Gawata kenan akwai abubuwan da a rayuwa in suka zo kuma suka wuce sun wuce har abada kenan. A ciki harda abinda ka kake godona akai. Magawata na lura kuma na fahimceka tsaf, a shirye kake da ka tona ma kanka asiri da kanka, baka duba suturar rufin asirin dana lulluɓeka dashi ba" Ina gama faɗin haka na miƙe tare da barin labtop ɗin a wajen na tsaya a Kicin na ɗaura sanwar shinkafa da wake kana na shiga ɗakin Azgar na zauna. Gado na gani a gefe wanda da dukkan alamu na mijinyawane gadon. Kallon tuhuma naima Azgar shi kuma yayi saurin kawar da kanshi dugun kar in jefo mishi tambaya akan gadon dana gani. Magungunan asibiti na gani a gefen gadon. Waye babu lafiya kaine ko Abbanku? " "Abbane baida lafiya kwana biyu yanata zuruftun zuwa asibiti, sai jiya suka bashi magani. Amman na tambayeshi ma abinda ke damunshi bai faɗa mun ba. Ammi dan Allah kiyi haƙuri da duk abinda Abba yayi miki ku dawo kamar da, muma zamu fi jin daɗi dan Allah Amminmu. Gashi Nanno kullum a cikin matsanta mishi take dole sai yayi aure kullum saita kirashi wallahi. Shi kuma sabida ke ne yaƙi yadda yayi auren" To me yake ce mata, ca yake bazai yi auren ba sabida ni kome? " "A'a haƙuri yake bata akan bashi da kuɗin da zai iya ƙarin aure a halin yanzu. Yana dai ta cewa a bashi lokaci in Allah ya ƙaddara zai ƙara auren, zai ƙara ɗin" Dariya nayi mishi. Azgar komai zai wuce ai ba zamu dauwama a haka ba, akwai lokaci. Ku dai duk rintsi kuci gaba da yima mahaifinku biyayya, kuma wannan maganar ba taku bace. Ya Nafisa kun sasanta kuwa?" A ƙoƙarina na bagarar da wancan batun Saida ya sosa kayinshi irinna samari masu jin kunya yace. "Mun sasanta Ammi kuma na faɗa mata da zaran na kammala bautar ƙasa zanzo. Amman tace mun ma kafin lokacin su zasu zo Najeriya. Kuma tama ce babu buƙatar dole saina zo, tunda a Gombe maɗaurin auren yake to can ya kamata muje a nemi auren, zuwa lokacin da zan gama bautar ƙasan." Kai na gyaɗa ina farin ciki. To ita Zainab fa ta rabu dakai ko har yanzu dai taci gaba da kiranka? "Ta rabu dani sai jifa_ jifa haka. Anma kawo sadakin Nasibansu har an saka bikin." Baki na mele ni wallahi har na mance da su Uwatale a rayuwata sam. Rayuwa kenan komai na duniya mai wucewane wannan gaskiya ne. Allah sarki, Ƴan baya kuma Allah ya duba musu yaba ko wacce budurwa miji nagari wanda yasan mahimmancin mace da darajarta. " "Ameen" Kawai yace mun, na ɗan jima a ɗakin kafin na fito na zuba shinkafa a cikin wakena dake wuta yayi rabin dahuwa. Ɗan goge_ gogen yana, da goge _gogen taga da ƴan ɗage_ɗagen dana saba duk nayi, dana fahimci mijinyawa baya cikin gidan falonma na shiga na yi ƴar ƙaramar kwalima, haka sib ɗin ɗakina na gyara kayayyakin dana wargaza, nayi goge goge da ɗage_ɗage, na zuba wanki a injin wanki na zamani dake cikin banɗakina, na gyare ko'ina na kunna turaren wuta ne mix na Mrs BUKHARI wanda nake yi sau ɗaya a sati. Ƙarfe ɗaya na gama shinkafa da wakennan. Sai da mukai sallah na zuba mana a tire muka baje a falo muna ci muna nishaɗi zuchiyata fes ina cikin ƴaƴana bani da damuwar komai. Wajajen ƙarfe biyu, na ba Sabira ta shanyamun kayan dana wanke a bayan ginin ɗakina, inda anan igiyoyin shanya suke sai muka tafi gidan kitso can sheka gidan wata shuwa da Yaya ta bani labarin iya kitsonta. Da kwatance da kwatance muka je gidannan da sallama muka shiga mun samu mata da yawa amman yawancinsu lalle akeyi musu, sai masu kitson basu da yawa yawanci matan aurene ƙila ma'aikata, da basu da lokaci sai irin wannan ranakun da dole saika daure in kuwa ba hakan ba ƙazami mutum zai zama, in dai zai biye ma gajiyane. "Ahh baƙuwa muka yi. Sannu da zuwa kitsonne ko lalle za'ayi muku? " Cewar wata yarinyar mace dake yarfa ma wata farar mata kitso ƙanana amman na ƙarine ga lalle jajir a zane a farar fatarta. Kitso da lallen duka. Amman kece Maman Idi? " Dariya tayi tare da riƙo hannuna ta zaunar dani a kujera ƴar tsugunno. "Nice Maman Idi mai kitson ƴan gayu kaf garin Kano babi wanda bai sanni ba. Nice kitso, nice ƙunshi, nice gyaran jiki, nice magungunan mata" Shewa matan dake wajen suka saka ni kuma murmusawa kawai nayi ina mamakin surutun Maman Idi. To mutum nawa ne a gabanmu yarinyata ma kitson za'ayi mata, amman ni kece zaki mun" "To shikenan mutum ɗayace a gabanki sallah ta shiga tana yi, kuma bata kitso mai yawa yanzu zan gama mata. Yanzu Hajiya ke kika haifi wannan budurwar ƴa amman naganki caras dake kamar budurwa? " Farar matar da akema kitso tace. "Hmmm nima tambayar zanyi sai naji kin rigani. Kuma muryarki baiwar Allah kamar sananniyar muryace inata tunanin a ina nasan muryarki tunda na ji sallamarki" Dariya kawai nayi mata. Na sha haɗuwa da mutane ko a kasuwa, ko a wani wajen da zaran nayi sallama sai suce kamar sun san muryar tawa. Saina gama abinda nake yi a wajen nake sanar musu wacece ni, sai na tafi in barsu da mamaki. Salon maganata yasa masu saurarena suke mun kallon babbar macen da shekarunta suka haure nawa gaya. Kuma da yawa sunce muryata tafi dacewa ta hau da mace mai ƙiba irin sosai ɗinnan, sai kuma abun mamaki bani da irin ƙibar da suke tunani, gashi yanzu ma na rame. Ni dai da murmushi kawai nake binsu gami da godiya da nuna ƙauna. Ina zaune dai mata wannan su tafi, wannan gungun su shigo. Abinda na fahimta Maman Idi asalin magulmaciyace kuma tsuliyar duniyace tasan labaran kowa. Wata yarinyace ta fita bayan an gama mata gyaran jiki sai ƙamshi take yi shine tace. "Wannan yarinyar fa itace Amaryar da za'a kaima Maman Safwanun gidan lashe_lashe, amman kunga rashin sani har canjan lamba suka yi basu san dodo ɗaya suke ma tsafi ba. Tunda Maman Safwanu ta shigo take hira da Hassana kunsanta da shegen kwashe_ kwashe, da kuma son mata ƴan gayu. Da ace tananan Maman Sabira tazo wallahi saita amshi lambarta. Maman Safwanu ai ƙawayen da tayi a wannan gidan kitso sunfi gaban ƙirge" Wannan farar matar dana shigo na sameta ana mata kitso tace. "To ke ya akayi kikasan itace mijin Maman Safwanun zai Aurane. Wai ni Maman Idi duk matan duniya kin sansu ne? Ni naga kullum kina gida a ƙunshe kina kitso ko ƙunshi. Amman duk abinda ke faruwa a waje kinsan komai." "Maman idi idan gari ake faɗa miki. Baba na ɗaka gemu na waje. Ai a wannan gidan nawa aka ƙyanƙyashe ƙwai tara tsinana. Kinga gidannan magama sunanshi, maganar dukkan wani sirri wallahi, abar kaza cikin gashinta kedai kawai" Ni dai illahirin Mamaki bai sakeni ba, ina dai saurarensu ana yarfamun kitsona, ga ƙunshi har an gama mun, jira kawai nake a gama kitson in wanke. Sabira tuni aka gama mata nata ƙunshi da kitson ni kawai take jira. Sai yamma lis muka baro gidan Maman Idi ba dan ta gwanance wajen iya kitson ba da ba lallai ta sake ganin ƙyayata ba, gulmar tayi yawa, maƙota ma a gidanta suke zuwa su shantake, wasu kuma an gama musu kitson amman sun kasa tafiya. Naga wacce tayi miyar darenta a gidan tsabaragen ana gulma bata son tafiya a sha babu ita. A Asibitin Malam Aminu Kano na yada zango zuwa ɗakin da Jamila take kwance babu yadda take. Ko da naje bacci take yi, duk da ban santa ba haƙiƙa ta rame fuskarta da wuyanta sai ƙashi, hatta ƙashin awazanta ana ganin layi layinsu. Mamanta da Babanta suna zaune tare da'ita. Ita Uwar kuka take yi Uban na rarrashinta a haka muka shigo ɗakin. Tun daga shigowata nake ta gaishe da marasa lafiya harna ƙaraso gadon Jamila da sallamata. Mama ta ɗago ta dubeni tace. "Hindu ko? " Kai na gyaɗa nace. E Mama nice, Baba ina wuni ya Jamila da jikin?" "Ƴar nan babu sauƙi jikin Jamila sai dai mu taya ta da adda'ar Allah yasa ta cika da imani. Yarinya dubu ɗari kusan uku jinyarta zata ci harda tiyata da za'ayi mata. Mu kuma ba masu ƙarfi bane" To Baba shi mijin nata da yayi mata wannan aika aikar yana ina? " Kuka Mama ta fashe dashi tana rishin kuka, Baba yace. "Ya tattare inashi_ inashi ya bar ƙasarma haka mai gadin gidan yace damu Hindu ƴata" Da mamaki na dubesu nace. In ya gudu ai dole yana da iyaye ko Baba?" "Baiwar Allah abar tone_ tone kawai, wannan yaron kuɗi muka bi muka bashi Jamila wallahi. Yarinyarnan tana da wanda zai aureta har an saka musu rana, wannan Alhaji Adinanu yazo ya sake mana kuɗi da iyayen bogi na ɗauki aurenta na bashi, shi kuma yaita zubar mana da kuɗi tare da alƙawarin in munje aikin Hajji mun dawo kuma sai maganar siya mana gida. To munje dai aikin hajjin gidan bai kai ga samuwa ba Jamila ta shiga wannan halin da kika ganta a cikinshi. Gyatumarta gata nan wallahi dukiyar bata tsone mata idanu ba, haka ma ita jamilar Biyayya kawai tayi mana. " Sai ya fashe da kukan nishi. Kunji irin halin da gidajenmu na arewa suke ciki a sakamakon talauci da rashin tawakkali ko? Ace har aure a ƙasar hausa yayi lalacewar da uba zai ɗauki ɗiyarshi ya aurar da'ita ga mutumin da baisan sarsalarshi ba, mata muna ganin rayuwa wallahi Allah. Kunji dai yadda mahaifin Jamila yayi amfani da isarshi ta uba ya aurad da Jamila ga mutumin da bata so, ya danne mata hakkinta, ya take ma uwar Jamila nata hakkin. Shin musuluncine yace ayi auren dole, ko kuma ra'ayoyinmu da son zuchiyoyinmu ne?. Haƙiƙa akwai auren dole mai fa'ida da kyakkyawar manufa wanda ake haɗawa domin ita yarinyar an hango mata zata samu kyakkyawar rayuwa mai inganci, a hannun wanda aka bata. Wani malamine, wani kamiline, wani nutsuwarshi da tsoron Allahnshi ke sa iyaye su kwaɗaitu da haɗa haula dashi. Amman wani auren dolen zaluncine tsantsa, irin dai na Jamila da mahaifinta ya damƙata ga mutumin da bai san waye shi ba. Jikina yayi sanyi ƙalau, amman ban sare ba zan taimaki Jamila iyakacin iyawata. Bidiyo nayi mata Mama ta rakani wajen likita, nayi mishi alƙawarin kuɗin aikin bazai wuce kwana biyu ba zan kawo. A haka muka tsaya da zancan na kawo dubu goma na basu nace suci abinci mukai sallama, tare da nufan gida a lokacin isha ake kira. A farfajiyar gidan muka tadda mijinyawa a zaune a farar kujera ko me yake yi ohon mishi, Azgar ne ya buɗe mana get tare da shige mun da jakata zuwa ciki. Wuceshi nayi ko kallo bai isheni ba, na ƙule ɗakina a gurguje nayi sallah na watsa ruwa na fito falo da laptop ɗina A falon na samu mijinyawa a zaune Azgar ya kawo mun jallof ɗin shinkafa da bushasshen kifi da zoɓo ina ƙoƙarin yaɗa bidiyon Jamila kiran mahaifiyarta ya shigo ina ɗauka ta saki kuka. Mama ki daure menene ya faru kuma? " "Ƴata Hindu Allah yayi ma Jamila rasuwa kaiconmu mahaifin Jamila ya cutar da'ita, wallahi sai Allah ya saka mata" Idanuna na rufe kawai mutuwar Jamila ta dakeni ainun, naji zafi fiye da tunani. Ƙwarara kaina nayi nace. Kiyi haƙuri Allah yayi mata rahama yasa ta huta. Mama idan akwai abinda kuke buƙata ƙofa a buɗe take kuyi mun magana dan Allah. Ki dena kuka Mama" Na kashe wayar tare da sauke ajjiyar zuchiya nayi shiru ina numfashi jikina ya mutu sosai. "Watace ta rasu Tutar so" E watace da mijinta ke saduwa da'ita ta baya ta mutu. Maza ai dama da yawansu neman hanyar kashe mata suke yi. Kuma kayukansu kaɗai suka sani, in buƙayarsu ta biya, to uban kowa ma ya mutu" Na ƙarashe tare da jan guntun tsaki abincin, da zaman falonma ya fice mun a kaina. Miƙewa kawai nayi na dawo ɗakina. Madadin in zauna saina shiga safa da marwa da ƙulafacin tunanin da ace ina da muryar da za'a saurara da na kawo canji a arewa mai yawan gaske. Da ace ni wata ce wallahi da sai maza sun gane kurensu, adalan mazane kaɗai zasu tsira amman wallahi duk wani azzalumi saina kaishi ƙasa. Sai dai kash, tunanin matanmu na Arewa yana kashe ma ire_irenmu guiwa. Mu ake bari da wahala, mu ake zalunta, mu ake kashema rayuwa. Amman abun baƙin ciki da takaicin, mata basa son ƙyas a taɓa maza sai su koma bayan maza, suna aibata mace ƴar uwarsu. Da anyi magana sai su ce ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, ciwonki ciwonkine dai ni da abinda nafi yadda kenan. Matuƙar muna goyon bayan zaluncin maza, wallahi bamu ga komai ba. Ba dai mata kunce duk bala'i gara mace ta zauna a ƙarƙashin azzaluman mazan ba? Harma yanzu lalacewar mata takai lalacewar da sun cire tsammani da rahamar Ubangiji. Wai cewa suke yi in kika fita a gidanshi, baki san hannun wanda zaki faɗa ba, gara ki zauna. Sun mance Allah baya zalunci, baya bayan azzalumai. Sun manta Allah maji roƙon bayine, sun manta da cewar indai kika fito a gidan Auren da baki zalunci mijin ba, Allah zai baki inda zaki je ki huta. An yanke tsammani da rahamar Ubangiji. Ko da yake jahilci, da rashin wayewa irinta addinin Musulunci ke sa ayi wannan mummunan furucin. Wallahi azeem babu wata mace mai kamilin hankali, mai addini, ƴar islamiyya da zata ce in ta fita a gidan azzalumin namiji, bata san ina zata faɗa ba. Laaa wai a tunanin ku babu mazaje kamilallu, masu jin tsoron Allah, ma'abota kiyaye dokikin Ubangiji ne? Kunyi kuskure kun zalunci maza, in kukai musu kallon azzalumai duka. Allah yasa mu dace kawai, sai mun tashi mun gyara zamu ga daidai. Ajjiyar zuchiya kawai na sauke zuchiyata na jin zafin mahaifan Jamila. Allah kaɗai yasan irin halakar da iyaye suka sanya yaransu a ciki, a kan dalilin da ba addini bane yazo dashi ba. Da yawan iyayen mutuwar Auren basa sone sabida kar ace sun gaza wajen tarbiyya. Ko kar a ce wance bazawarace. Su kuma matan suna tsoron in sun fito wacce tarba iyayen zasu yi mata, sannan suna tsoron irin ɗan kiran da al'umma zasu dinga musu. Bazawara_bazawara dai Su gani suke yi wannan sunan ƙasƙancine sun mance fiyayyen halitta Arrasul saw matanshi in aka cire uwar mumunai Aisha ɗiyar sayyadina Abubakar al siddik duk zawarawane matanshi. Nana khadija Uwar Ƴaƴan ma'Iki Arrasul wacce harta mutu, yace da Aisha wallahi Allah bai musanya mun da wacce tafi Khadija ba, sabida girma da matsayinta, da irin yadda ta ma Musulunci hidima. Allah da kanshi ya aiko mala'ika da saƙon gaisuwarshi zuwa ga Nana Khadija. Duk da an tambayi ma'aiki Arrasul saw a duniya wa kafi so yace Aisha, akace a maza fa yace Abukakar mahaifinta kenan. Kunji mata masu asalin kafacity ko, muce Allahu Akbar dan Allah. Jama'a Musulunci fa addinine mai sauƙi da daɗi, mu ne dai muke ɗaukan duman magaji da nishi wallahi. Ina cikin wannan safa da marwan mijinyawa ya shigo harda neman waje ya wani zauna. "Hindu zauna muyi maganar da nace inaso muyi dake. Na fahimci baki da lokacin komai da kowa a yanzu aikinki kawai kika ba mahimmanci, sama da komai da kuma kowa." Wani kallo nayi mishi daman kuma a wuya nake da maza ji nake kamar in karkashesu kowacce mace dake ƙarƙashin zalunci ta samu ƴanci. Bani da lokacin magana kaina ya ɗauki zafi kaɗaici nake so ka barni" Sai kawai ya zabura cikin fishi da zare idanu. "Baki isaba Hindu nagaji da wannan ƙananan iskancin naki. Mai kika ɗaukeni ne lusari wanda baisan abinda yake yi ba kome? Kina matsayin matata amman bani da iko dake kullum kina tafe baki nan baki can taimakon mata, amman kin kasa taimakon mijinki ki yafe mishi laifin da yayi miki. Ya kamata mu kawo ƙarshen wannan rikicin kin kasa bani damar da zan nemi yafiyarki bare ki yafe mun" A'a ya'isheka Mijinyawa. Harma kana da bakin cewa kagaji da ƙananun iskancina. Ai baka ga komai ba indai kana riƙe da igiyar aurenane wallahi. In so kake komai ya ƙare ai sai ka sauwaƙemun. Fita kuma ina da ikon fita duk inda zani ba dole saina faɗa maka ba. Tunda a baya kasan yarjejeniyar dake a tsakaninmu, ka bani dama inje duk wani lungu da saƙo domin in yi aiki, ko in taimaki mata, ka barni in dinga zuwa gida a duk sanda buƙatar hakan ta taso mun, ka yarjemun in yi tafiya ko wanne gari in buƙatar hakan ta taso mun. Ka mance kaine inna tambayeka zani wani wajen kake fishi harma kake cemun na wuce haka a wajenka. Ka mance da izininka nake komai, ka bani duk wani lasisi. Shekara fin ashirin a haka muka shinfiɗa rayuwar Aurenmu, kai ka sani? Ohh naganoka da kai da magoya bayanka ai dama abinda kuka riƙa kenan a matsayin hujjar da zaku kafa abun kunya. Batun aiki da kake yi shi nasa a gaba, kamar ba kai ka nuna mun in ba aikina mahimmanci ba a baya. A da na tsaya na kula dakai, na kula da yarana uku, na basu tarbiya, ko ƴar aiki ban taɓa yi ba, aikina daban, kula daku da nake yi daban, ban taɓa tauye hakkin aikina, ko hakkinku ba. Duk wuyar aikina bakwa kuka da komai, inayi da lokacina, ƙarfina, dukiyata. Asalima kai gatane, da soyayya tayi maka yawa shi yasa ka zama ɗan iska irin yadda ka zama" " Aure ba abun wasa bane Hindu, nifa mijinkine. Akan laifi ɗaya jol sai garani kike, kin haukatamun nutsuwata, kina farautar rayuwata Hindu. Tabbas ni na baki damar zuwa duk inda aiki ya kama kije, da duk inda aikin agajinki ya kama kije, kiyi haƙuri dan Allah ruɗewa nayi ne. Sannan baki taɓa tauyeni a komai ba, in nace gata inda kika gaza na miki sharri. Amman taurinki yayi yawa" Murmushi nayi ina kallon yadda yake faɗa yana ɗaga murya. A daki mutum a hanashi kuka kenan. Ga mari ga tsinka jaka, wani iskancin sai maza. Wayata na wawuro na shiga manhajar WhatsApp, na ciro wannan hoton chart na nuna mishi. Wallahi babu shiri ya zauna daɓas a kujera, shine harda dafe zuchiyarshi, yana haki tamkar zai mutu. Kunsan meye abun farko da yayi? Fsshewa yayi da kuka, yana ta ambaton Allah kawai. Ni kuma ina tsaye babu inda baya rawa a jikina, haƙorana sai haɗuwa suke da juna. Zuchiyata kuwa tamkar zata faso ƙirjina ta fito, ta faɗi ƙasa ta fashe haka sak nake ji. "Hindu ki mun rai, ki tausayamun, ki taimakamun dan darajar Allah. Haƙiƙa naci amanar da kika damƙamun, na zalunci ƙaunar da kika nuna mun. Wallahi Allah baki gaza tako ta ina ba. Ina jin daɗin rayuwar aure dake, kina mun biyayya, kina gyara jikinki, kullum cikin ƙamshi, da gyaran jiki kike, ta ɓangaren kwanciya babu ta inda wallahi kika gaza. Tarbiyyar yara wallahi Hindu nasan kin basu tarbiyya, ni na ɓata komai. Alƙawarinki da kika ɗauka kin sauke. Wallahi nine na gaza. Hindu ki dubi raunina ki yafe mun, raunine dani. Kinga Talatu wallahi ita ta neme ni, ni kuma rauni gareni wallahi, Asama'u ma ita ta neme ni. Ki yafe mun, haƙiƙa na cutar dake, naci amanarki Allah bazai barni ba. Hindu ki yafe mun ki yafe mun baiwar Allah Ki yafe mun" Ya sake fashewa da kukan iskanci. Hmm da gaske kaine ko dai Mijinyawa Babbane ka dai duba" A zabure cikin ɗimuwa yace. "Nine Hindu, nine wallahi nine, a ina kika samu? " Halima surukarka uwar Asama'u itace ta turomun. Abinda baka sani ba, har gidan Talatu naje, ashe har kwana kayi a gidanta, kuka kwana kuna aikin ashsha. Da matar Aure Magawata hmmm" Wani ƙwallo na haɗiye. Kanshi na ƙasa kawai, jikinshi sai rawa yake yi. Hmmm mijinyawa kenan. Kana maganar sanin darajar aure ko darajar miji. Shin kai kasan darajar matarka da ka kai wata ɗakin baccinta ka turmusheta kana shan ƙirjinta kana sambatu a kunnen matarka. Kana kwanciya ka tura tsaraicinka zuwa duniya. Itama ta turo maka, ku biya ma kanku buƙata kuji daɗinku, ka ɗauki yarinya zango_baƙi_zangon_baƙi ku gama sheƙe ayarku. Yarinyar da haihuwarta ne kaɗai ni da kai bamu yi ba, yarinyar data rayu a tsakankanin cinyoyina da kafaɗarka. Yarinyar dana ɗaga darajarta fiye da darajar Ƴaƴana. Yarinyar dana fifita sonta fiye da son ƴaƴana. Ita ka Aura mijinyawa kuka ƙarashe abinda baku gama ba. Talatu ma ka game gane komai nata, kaje har sau biyu ka kwana a wajenta, kune kwararo_kwararo, harma ya yawonku Asama'u taci karo daku, saika yima Talatu ritaya, ka ɗauki Asama'u ka ɗaura daga inda wanda yake kaita zango baƙi ya tsaya. Ubangiji shine shaidata duk wata tarbiyya na ba Asama'u, daga Jami'a take ɗiban jiki ta tafi yawon bin mazanta, acan ta haɗu da ubanta, mijinta kuma. Wai rauni ne dakai ko, ashe watarana zaka hakkema Sabira tunda kana da rauni, duk wacce tayi ma tayi, shikenan ciniki ya faɗa ko. Na rantse maka da Allah saika sakeni, na gama da babinka tuni, ba zajen bane wallahi. Meya rage a mutumcinka a idanuna ka faɗamun, nace ka faɗamun ka faɗamun" Cukukeshi nayi na shiga ihu ina nanata kalmar. Ka cuceni ka shayar dani guba abadan bazan yafe maka ba, bazan iya zaman aure dakai ba wallahi. Ko zaka mutu sai mun rabu, ko kaine Autan maza sai ka sakeni" Dukan ƙirjinshi nake yi cikin rufewar idanu, da fitar hayyaci. Shi kowa yana durƙushe kamar dutse. Wani ihu naji daga can nesa nake jiyoshi ashe ni nake yi." Mijinyawa:. Ihun Hindu ya karaɗe dukka gidan gabaki ɗaya har su Azgar sun iso cikin ɗakin a lokacin data sulale ƙasa tana bige_bige aljanunta suna farfaɗar maganganu, tare da rantsuwa, da cin alwashi. "Kuje Azgar zan zauna da'ita. Kuje kawai babu komai zan mata adda'a" Da ƙyar yaran suka futa jikinsu a sanyaya suna jiyo hayaniyar iyayen nasu duk da ɗakin da zurfi basa iya sanin me suke cewa, kafin wannan ihun ya biyo baya. Mijinyawa na sunkuyawa Hindu ta kama wuyanshi ta cabke yaita kokawar ya ƙwace abun yaci tura ya kasa ƙwacewa, abinka da ƙarfin junnu. Ayatul kursiyyu ya soma karantawa suka sake tsananta riƙon da sukaima maƙoshin nashi. Yanata haki da kakarin ɗaukewar numfashi. Sai suka sakeshi tare da kyakyacewa da wata dariyar mugunta. Bai yi aune ba Hindu ta tashi tsaye ta tokareshi a bango, tana neman shaƙeahi, shi kuma yana ƙoƙarin riƙeta ya kasa. Hannu ta saka mishi a idanunshi du biyu, take ya dena gani, ta saki wani ihu, tasa hannu ta wurgashi kan gado, yaje ya haɗu da kan gadon bayanshi ya daku. Sai kuma suka shiga bige_bige da maganganun da kamar yare suke yi badai ya gane me ake cewa ba. Adda'a ya shiga yi mata yana tofawa daga kan gadon, gashi basu da hayaƙi a gidan ko kaɗan. Rabon Hindu da shiga irin wannan irin yanayin tun a jama'are lokacin da ake ganiyar yi mata gorin haihuwa. Shima aljanun hausa suke yi, saɓanin wannan da yare suke yi haiƙan. Wannan tunanin da yazo mishi sai ya dawo da tunaninshi baya lokacin da suka je gaban Nanno shi da Hindu akan batun ciki ko saki. Kai ya girgiza yasan sun tsallake siratsi masu yawa, kuma Hindu tayi rawar gani a rayuwarshi. Da ƙyar ya sakko ya nufota, tana ƙasa, ƙafarshi ta jawo ya faɗo kanta, nan suka shiga birgima ta kama mishi kunnuwanshi du biyun tamkar zasu tsinka mishi su. Tirƙashi, bari nima in yi nan tun kafin a haɗo dani. 🏃🏻‍♀️ Mrs BukhariTSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA BAKWAI (7) https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp 07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm Tiktok link/ https://vt.tiktok.com/ZSCgTFH8o/ IMZEEDenterprises Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeed🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDENTERPRISESLTD wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account aTikTok@imzeedenterprisesltd https://vt.tiktok.com/ZSCgTFH8o/ Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima BADI’AT İBRAHİM tuni na antaya🏃 Sun jima suna mirginawa, ga kunnuwanshi a riƙe gam. Idanunshi a runtse suna zubar da hawayen azabar hannu da aka saka mai a ciki, ga kunnenshi da aka kama, irin kamun da bazai rubutu ba, balle ku gane, ƙarfin aljanu ya wuce gaban kwatance sai wanda aka kama ne kaɗai zai gane. Addu'o'i kawai yinsu yake yi sai wanda ya manta, inya kama wannan ya sake wannan, har dai jikin Hindu ya saki, ta sake kunnuwan nashi hannayenta suka faɗi yaraf. Yana durƙushe a gaban Hindu, yana kallonta dishi_dishi yana sske jin zafin laifin daya aikats. Sai dai kash dama ana dawo da hannun agogo baya da kuskure ɗaya tak da yayi ma Hindu bai aikata ba. Babu riba a abinda shaiɗan da dange_dangenshi suka jefashi ciki sai ƙunci da zafin zuchiya. A hakanma Asama'u bata daina bibiyarshi da sharri ba, yayi ƙoƙari sosai wajen tosheta ta duk kafar da yasan zata sameshi, sanadiyyarta ya soma amfani da turu kola a wayarshi sabida yadda take nemanshi da lambobi da daman gaske. Ga matsaltsalun dangi, gana Nanno da tayi tsayuwar daka akan dole sai ya ƙara aure. Bashi da wannan ra'ayin a baya ma baisan abinda ya shigeshi ba ya Auri Asama'u ba. A yanzu kuma yayi ma zuchiyarshi alƙawarin babu maccen da zai bari ta shigo cikin rayuwarsu ta sake rura wutar rikicin da har yanzu ci take yi tamkar ana ƙara mata fetiri. Hindu ba ƙashin da za'aci a siɗe a yar bace. Ya tuno da faɗi tashin da ta dingayi a zamantakewar auren nasu. In banda tana sonshi fiye da tunani shi sai yaga to wai wanne daɗi shi yake ba Hindu ne, menene ribar data tsinta a Aurensu ne ma? Wallahi ya yaba, yana kuma yabawa, alkhairanta suna da yawan da sai an sake tsunduma cikin ainihin ci gaban zamansu a ƙauye za'aji. Ita alkhairice tako ta ina a rayuwarshi. Ya yadda sonta yafi nashi yawa, ya yadda ta fishi sadaukarwa. Sai dai kash ya kassara wannan yardar amman ya lashi takobin duk daren daɗewa saiya wanke lefinshi tas a wajen Hindu, wannan shine aikin da yake so yara su taya shi, dan dole saida taimakonsu. Kallonta ya kuma yi da ƙyar ya buɗe idanunshi, sai ƙasa_ƙasa suke mai na ciwo, daya buɗe sai su cika tab da ruwan hawaye mai ɗumi. Kafin yayi mata tayi mishi sau dubu, duk wani abun gwaninta da bajinta gogoriyo suke yi a tsakankaninsu, ko wanne cikinsu na son ganin murmushin abokin rayuwarsu. Ihun da Hindu ta kuma sakewa mai ƙarajine ya dawo dashi cikin hankali da nutsuwarshi yayi saurin riƙeta tana ƙoƙarin fisgewa danneta yayi iyakacin ƙarfinshi amman ina dake ƙarfin ba nata bane sai ganinshi yayi a jikin kujera an wancakalar dashi gefe. Yaji zafi sosai har saida bayanshi ya amsa dama ba lafiya gareshi ba, ga ido sai ambaliyar ruwa yake yi. Amman a hakan ya kuma tunkarar Hindu dake ƙoƙarin illata kanta ya riƙeta da ƙarfi ta sake fyaɗashi da ƙasa, ya faɗi rim ƙirjinshi ya daki ƙasan ɗakin. Saida ya huta sosai, kafin ya shiga karatun Qur'ani yana tofa mata a haka a haka har jikinta yayi sanyi ya jata ya kwantar da'ita kuma ta yadda ta kwanta ɗin. A hankali ya dinga shafar kanta tare da ƙure mp da karatu a hankali a hankali idanunta suka rufe ta shiga sauke ajjiyar zuchiya akai _akai tamkar yaron da yasha kukan banza ya gaji yayi bacci dan kanshi. Ajjiyar zuchiya ya sauke nannauya ya lumshe idanunshi cike da kewar rayuwarsu ta baya ainun. Babu abinda baya kewa a zamantakewarsu ji yake yi tamkar yayi hauka ko zai samu salama. Wata rayuwa mai kyau da tsafta suka gina a dawowarsu birni. Wannan rayuwa wani ɓangare ne wanda tarihi bai isa ya gogeshi ba abadan. A wannan zamanne Hindu ta nuna bajintarta gaya, ta taka muhimmiyar rawar da han yanzu take kan takawa. Hindu wani ɓangarene na cikon rayuwarshi, a yanzu ya sake tabbatar da haƙiƙatan Hindu ta fita daban a cikin mata. Kusan a zaune a jingine da fuskar gado ya kwana za'ace. Kwana Hindu tayi tana zabura sai ta miƙe zaune saiya maidata. Sai ya soma gyangyaɗi, saita miƙe yayi carab ya riƙeta ya maidata bata dai yin gardama take komawa cikin rashin haiyaci. Kiran sallah asubahi ne ya farkar da Hindu cikin hayyacinta. HINDU:. A hankali na buɗe idanuna da nake jiyosu luɓu_luɓu halamun a kumbure suke sunyi mun nauyi. Jikina babu inda baya tambayata. Na riga nasan abinda ya faru tunda na jini a cikin nauyin jiki. Ina buɗe idanuna na jini a kan gado nayi zargin hakan. Waigawata ke da wuya naga mijinyawa a jingine a fuskar gado wuyanshi a sama yana bacci rigarshi ta ƙirji a yage har Mamanshi ɗaya na waje duƙui. Ƙurama ƙirjinshi idanu nayi ina hasaso abubuwan Masu yawa da nauyi. Mijinyawa yayi mun cutar da mata sun kasa ganewa, mata sun kasa fahimtata. Jin motsina yasa ya motsa, nayi yinƙurin tashi amman na kasa ji nayi kamar am daddanneni da ƙarafai. "Kar ki motsa bari in haɗa miki ruwa mai zafi sai in zo in kai ki banɗaki" Haɗe rai nayi nace. Ka kirawo mun Sabira" Har zai yi magana mai ya tuna ohon mishi abun baƙin ciki sai wani nannan yake yi dani. Idanunshi sun kumbura sun yi jawur, gashi naga ɗingisawa ma yake yi. Yana fita Sabira ta shigo da sauri da halama a bakin ƙofa ma suka haɗu gaskiya. "Ammi sannu ya jikin? " Idanu na lumshe ina hango hoton Jamila a kwance a gadon mutuwarta. Da sauƙi haɗamun ruwan wanka mai zafi" Na faɗa a hankali, kes ɗin Jamila ke damuna kuma inaso in samu iyayen Jamila in musu tambayoyi ko za'a samu wani labari da zaisa a gano wannan azzalumin mijin nata. Mijinyawa na riga na rufe babinshi. Tuno da barista yasa na sauke ajjiyar zuchiya. "Ammi na tara miki ruwan" Kamani a hankali ki kaini bayan gida Sabira" A hankali muka isa na zauna a cikin bawon wankan nace mata taje. Da kaya a jikina na dinga zuba ruwa tun daga kaina zuwa ƙafafuna, kafin na samu ƙwarin da na iya cire kayan jikin nawa naita gasa jikina ina ƙara ruwan. A zaune na yi sallah na samu man zafi duk na mulke jikina. Sabira na kira ta haɗo mun shayi mai madara na sha na haɗiyi maganin ciwon gaɓoɓi na koma gado na kwanta sai bacci mai nauyi ya ɗaukeni, bamma san inda kaina yake ba, bai yi kama da bacci ba ma dai. Mijinyawa:. Suna dawowa daga masallaci ya tadda Sabira na wanke hannu wajen wanke_ wanke. Gsisheshi tayi ya amsa da fara'arshi tare da tambayarta Hindu. "Tana ciki amman bacci ta koma na shiga bata sanma na shiga ba. Na kai mata shayi tasha tare da maganin ciwon jiki. Baba idanunka yayi ja, kuma ya kumbura yana ta ruwa, ciwo yake ma? " " Sabira kenan, ciwo yake mun, garin yi ma Amminku adda'ane ta sa mun hannu a ido bata sani ba. Sannu Sabira da ƙoƙari. To me muke dashi a suto na abinci da za'ayi mana?" Ya tambaya yana kallonta, Azgar bai tsaya ba, yayi wucewarshi ciki ɗakin Amminshi ya shiga duk da yaji ance ta koma baccin. "Abba akwai ɗumame a tukunya shayi zan dafa kawai. Ammi kuma inta tashi sai Azgar ya dafa mata taliyar yara" "To Sabira tunda ma ɗumamene kije kema ki kwanta, ba ku yi bacci ba. Nima magani zan haɗiya in kwanta kinji ko? " "To Abba Allah ya baku lafiya dukkanku" Idanu ya lumshe yana yabawa da irin tarbiyyar da Hindu ta bama yaranta, duk da kasancewarta ma'aikaciya baisa ta bar yaranta sakaka ba, ƴar aiki bata taɓa rayuwa a tsakaninsu ba. Tuno wata rana yayi da safe misalin shidan asuba. Zuwa tunani. Hindu na tsaye a Kicin da misalin ƙarfe shidan asuba, ta gama suyar dankalin hausa, ga miyar jajjagenta a wuta tana soyawa taji kifi shawa. Kicin ɗin fes tamkar ba a ciki akayi aiki ba, babu wanke_wanke ko na cokali. Da sallama mijnyawa ya shigo, ta juyo da sauri suka sakarma juna murmushi. "Ka taso ashe, yau ai kaƙi taya ni girki, sai ni kaɗai, yaran kuma Yanzu suka tafi wanka, na yi ma Sabira har ta sa kayan makaranta" Ƙarasawa yayi yana mata dariya. Saida ya jawo kwanukan da zata raba abincin ya soma rabawa, ita kuma ta komawa miyarta tana juyawa, kana yace. "Ke dai ki bari Tutar so. Jiya kin hanani bacci da rigimarki, karatunne baya wani shiga kaina ke gashi kin nace. Wallahi da kin barni naci gaba da tuƙin motana da yafi mun. Ina shan wuyar karatun, gashi malaman suita mana wasu manya_manyan turanci." Dariya suka kwashe dashi, tana zuba miya a dankalin yara daya raba, shi kuma yana juya musu sikari a shayi. "Mijinyawa kenan, shi yasa duk gajiyar dana kwaso, da duk ɗumin da kaina ya ɗauka nake tsayawa muyi bitar abinda kuka karanta, in maka filla_fillah da hausa yadda zaka gane. Ko nima nawan baka ganewa ne?" "Ina gane nakin, a cikin ajinne bana iya sakewa, turancinne yake damuna" "Kar ka damu da wannan, kai dai kawai ka iya abinda akayi muku, shine al muhim kayi haƙuri wannan shekarar bana son kari oba. Bari inje in yi wanka, kai kayi wanka da ruwan da na kai maka? " Kai kawai ya ɗaga mata, ta fita da sauri zuwa wanka. "Hindu baiwar Allah kenan. Allah ka bani abinda zan saka ma wannan baiwa taka. Wannan soyayya abar kwatancece. Zuwa bakwai da rabi, hatta da abincin rana Hindu tayi, ta zuba a kula, suka ɗebi yara suka fito titi. Ita ta wuce da yaran makaranta, shi kuma saida ya tabbatar da tafiyarsu, shima ya tari abun hawa zuwa makaranta. Ita ta bashi na mota, ita ta bashi na abinci, da ta bashi ma kuɗin abun hawan dawowa, ita wai ta dawo a ƙafa, shine yaƙi karɓa yace mata shine namiji shi ya kamata ace ya tako a ƙafa. Yana zaune a bus, saye da wani yadi da Qasimu ya bashi kwance, ƙafarshi da wani takalmin fata da ake haɗawa na hannu, Hindu ce ma ta siya mishi shi kaɗai gareshi, dashi aketa murzawa har ya kusan hujewa ma ta dunduniya. Ajjiyar zuchiya kawai ya sauke. Dawowa daga tunani: Wucewa yayi ciki yana ɗingishi, ya zauna a bakin gadonshi tare da jawo ledar magungunan shi, ya ɓalla ya ɗakko goyot ɗin da ya siyo domin shan magungunan dashi, irin mutanen da in suka haɗiyi magani da ruwa yake dawowa ne, shi yasa sai dai yasha da kokko ko nono. Magungunan ya watsa ya bisu da nonon. Duka ya shanye nonon kasantuwar rashin abinci a cikin nashi. Ya kwanta kenan Azgar ya shigo ɗakin ya zauna ya sake gaishe da uban banda gaisuwar da suka yi a masallaci. "Azgar tana bacci daka shiga ko? " A sanyaye ya tambaya. "E Abba bacci take yi. Amman Abba ya kamata kaimun kwatancen wajen mai maganinta sai inje zuwa rana in karɓo hayaƙi tunda kaima ba lafiya bace dakai ba, baccin dai sai a hankali gaskiya. Abba sai ramewa kake yi fa. Kaƙi ka faɗamun damuwarka, kaki ka sake Abbah" Murmushi Mijinyawa yayi ma Azgar yace. "Zan lallaɓa muje tare sai ka tuƙa motar mu karɓo mata. Da yauma naso zuwa jama'are Nanno bata ji daɗi ba itama. Amman yanayin jikin Hindu bazai bani damar zuwa ba, zan kirasu a waya dai inji yanayin jikin nata. Ka kwanta in kana jin bacci nima kwanciya zanyi" "Um zan mana wankine sabida da daddare in samu in goggoge mana. " Tashi Azgar yayi ya cicciro kot ɗin Baban da fararen na cikin da nashi kayan ya fice. Akwai injin wanki a Kicin, wannan nasu ne, nan ya shiga wankin yana gyaran Kicin ɗin. Sabira kuwa tana can tana gyaran ɗakinta da gyaran sib. Hindu: Bani na farka ba sai wajajen sha ukun rana shima wayatace aketa aikin kirana a waya ashe Luba ce keta kirana. Cikin muryar bacci na ɗauka. "Hindu mutuniyar taki fa ta haifo ƴan biyu dukka maza wallahi. Ke kinga yadda Sunusi yake ta gigi yadda kika san a kanta aka soma haihuwa kin ganni a asibiti ina hanyar zuwa gidanki" Dariya na saka tare da cewa. Dama a danginta suna da ƴan biyune? " "Sosai kuwa itama ƴan biyu take bi Gambo ce ai. Mahaifiyartama Usainace. Ashe sabida ma hakan Sunusi ya Aureta. Ke dai saina ƙaraso a ajjiyemun abinci dan wallahi yinwa kamar zata halakani" Tsaki nayi mata na datse wayata kana na miƙe na nufi banɗaki, ina jin jiri, na sake gargasa jikina na ɗan ji dama_ dama ba laifi. Riga da siket na jar super na saka bayan na gama lailaye fatata da mai. Kwalli kaɗai na zirara a kumburarrun idanuna da har yanzu basu yi haske ba sunanan a rine. Na shafa humra na ɗan gyara gadon na jona bona na zuba turaren wuta, dana gabatar da sallah, saina fito a hankali dan jikin sai a hankali kawai, ko ta ko ina ciwo ne. Shiru naji halamun babu kowa a gidanne ko bacci suke yi ne oho dai, amman ko'ina a gyare yake fes. Ina tsaye cike da tunanin ina zan dosa falo ko ɗakin Sabira sai naji ta turo ƙofar ɗakinta ta fito. "Ammi kin tashi ashe inata leƙawa sai inga kinata baccinki" Murmushi nayi mata kawai. Me kuka dafa Sabira? " "Ɗumame muka ci Ammi. Amman nace in kika tashi sai in dafa miki taliyar yara akwai shayin Ahmad a filas kije falo yanzu zan gama miki minti goma" Ta ƙarashe da sigar zolayata, dariya nayi mata dan taji daɗi kamar yadda nima tasa naji daɗi. Yarana su suke yayemun damuwar duniya wallahi. Allah yaba duk macen dake neman haihuwa masu albarka. Ki dafa da Ummanki Luba tana hanya kar ki cika yaji. Nasan ma in dai taga taliyar yara wallahi babu abinda zai hanata mita" Ina maganar ina tafiya har zuwa falo. Wayata na buɗe na shiga manhajar WhatsApp domin ganin me ke tafiya a zauren gida game da bikin Salamatu da suka tasamma ƙarya. Nan naga saƙwanni sunfi dubu da ɗari biyar, dariya nayi nasan akwai lallai abinda ya faru tabbas jikina har tsuma yake na shiga. Da hoton motar Salamatu naci karo sabuwar mota fil da rubutu a ƙasanta kamar haka. "Wannan tukuicine Zauji ya bani na amincewa da Aurenshi da nayi a saka mun albarka" Kallon motar na shiga yi a ƙofar gidanmu ma akayi hoton mota ta iso kenan su Salamatu gaskiya ta samu dama tana ta damawa. Gangarawa naci gaba dayi masu zumunci da'ita sosai kamar ƴan ɗakin Inna Mairamu kenan sai habaici suke sakarwa tare da taya ta murna. Waɗanda gaisawa kawai akeyi wasu Allah ya sanya alkhairi suka rubuta wasu ma stikar taya murna kaɗai suka turo harda masu emoji na jinjina. Ƴan ɗakinmu kyakkyawar adda'a sukai mata duk da irin zaman doya da manjan da akeyi. Ayarin masu mata fatan alkhairi da taya murna na shiga. Wannan saƙwannin na jiya da daddarene, da safe misalin goma sai ga hotunan Aure kuma har uku zafafa ta turo shima mijin gashinan yasha kayan hukumar fasa ƙwarri a jikin rigarshi naga matsayin da yake kai, ummm Salamatu tayi kowa ya samu dama dama ya dama. Dake goduwace sosai ta fishi tsayi shi kuma irin siraran fulaninnanne ita kuma ta haɓaka nama wuyanta cike da gwai mai rawun ba mai kwaɗo ba kun dai gane. Kasantuwarta ƙatuwa sai shi ɗin ya zama tsurut a gabanta kamar bakwaini. Anata masha Allah, masha Allah, ni ko ina zaune ina dariya na jiyo muryar Luba suna yi da Sabira. Shigowa tayi tana haki. "Wai Hindu nima wannan taliyar yaran na jaraba zanci? Wallahi bazan iyaba kinsan basir gareni yaushe ma zata riƙe mun ciki tsakani da Allah, kinsan na tsani taliyarnan fa" Ta ƙarashe tana neman waje a ƙasa tare da cire mayafinta ta jefar ta cire ɗankwalinta ta jefar shima. Luba kenan dama nasan da mita zaki shigo wallahi kuwa. Akwai biredi saita soyo miki ƙwai ki haɗa ai Maman Nawata da Gawata" Dariya muka kwashe dashi mune harda tafawa taf tamkar bamu da matsalar komai. "Hmmm tana asibiti dai ta haihu yau ta yaba ma aya zaƙinta ai taji maza, wai kinga bakinta yadda ta saki yake zubar da yawu kuwa ga laɓɓan sun yi dama girma sabida ciki." To ke ya akayi kika kaita asibiti kuma naga kin caɓa ado ke da kika kai mai haihuwa?" "A'a nifa dama na fito zan tafi gidanmu ne acan zan wuni, in barista Saudatu Mustapha ta kira ta bamu adirrshin inda zamu haɗu sai in tawo daga gida, yara tun Juma'a suka tafi gidan ma. To ina kulle ƙofa na hangota tana rarrafe a ƙasa fa wai in taimaka mata zata mutu. Dana fahimci haihuwa ce saina kamata ta miƙe tsaye nace mata lokacin haihuwarta yayine? Wai ranar wa'adin da likitoci suka yanka mata ya cika. Ina kayan yaro wai bata haɗaba suna saman akwatin saman sib ɗinta. Haka na jata muka je har uwarɗakin nata na zaunar da'ita a kan gado, ni kuma na taka gadon na sakko da akwatin na harhaɗa duk abin buƙata ita dake ƴar gaban goshin miji ce komai da ake siyan ɗaya ita biyu aka siya mata. Ta cika gana mas go da kayan jarirai baki gani ba Hindu. Ni nawa yaran da figi da yagi na haifesu kayan fitar suna tun haihuwata ta fari nake yima kaina Sanusi bai taɓa yi mun ba. In banda zuchiyar musulunci yaushe zan kai mishi mata asabiti." Shigowar Sabira da tiren abinci ya katse mana labarin da Luba ta kwalo bani ina amsa. A gaban Luba ta dure abincin harda ragowar ɗumamen da suka ci ashe yayi saura. To shikenan ƙorafi ya ƙare tunda kin samu ɗumame ko? " "Sosai ma wannan taliyar ba ci zanyi ba sai dai kici kayanki, ato yaushe zan iya nifa wallahi a ƙirjina take mannewa ta zamemun olsa ina dalili" Dariya muka saka Sabira ta fita ta bamu waje, na gyara zama ina kan zuba taliyar nace. Kuma danginta dashi Sunusi sun yaba da namijin ƙoƙarin ki ko kuwa a banza man kare? " "Hindu ai ba'a burge kishiya, ba kuma a birge dangin kishiya, kazalika mijinma ba'a burgeshi akan kishiya, duk abinda zaki yi a mazaunin munafurci ko ganin ƙwaƙwaf yake. A gabana yarta take cewa abu baiyi kyau ba kishiya da karɓan haihuwar kishiyarta, babu fa ɓoye ɓoye ni take faɗama hakanma. Sunusi ban tsaya bi ta kanshi ba ƴan uwanta na zuwa nayo nan. Kuma ni wallahi ranar sunane kaɗai zan zauna a gida. Ko mun taso aiki haƙiƙa gidannan zan zo in tare sai dare zan dinga komawa gudun kada ai mun abinda zuchiyata ba zata iya jurewa ba" Dariya na kuma yi kawai. Muna cin abincin ina bata labarin abinda ya faru dani da mijinyawa, amman iyakar gajiya da yace yayi da ƙananun iskanci, da ƙananun labaran da zata iya ji. Tace shi yasa taga halamun bani da lafiya, tasan mutanen sun kawo ziyara. dana gama na shiga nuna mata motar Salamatu da hoton mijinnata. "Hindu ki ɗan sassauta ma mijinyawa kiyi nazari ki kuma hakaito irin rayuwa mai daɗi da kuka gudanar a baya" Dakatar da'ita nayi har ina ƙwarewa. Dakata Luba ke da Sunusi wacce iriyar soyayya ce baku buga ba a rayuwa wanne irin duniyar soyayyane Sanusi bai kaiki ba, ada gani kike yi kinfi ko wacce mace sa'a duk duniya. Me ya faru daga lokacin da Sunusi ya ga mace ƴar uwarki wacce abinda yake jikinta da wanda yake jikinki duk anko ne. Ba baya ya juya miki ba ya dawo da ragamar komai na gidan hannunki ba? Ɗan hamsin da hamsin ɗin da kuke yi ya dena. Me ya hanaki yafe mishi ku dawo kamar da in kunce ni ina da baƙar zuchiya ke mai farar zuchiya ki yafe ma Sunusi. Luba mijinyawa ya cutar dani ba zaku gane girma da zafin ciwon dake zuchiyata ba. Luba amman zaki iya hakaito irin zafin abinda akayi mun. Yau ko gobe mijinyawa yayi Aure ace babu rikicinnan a tsakaninmu Luba bazan taɓa zamemai damuwa ba, bazan canja mishi ba, zamu zauna lafiya sai dai kinsan bazan ɗauki danne hakki da mayar dani koma baya ba, ba kuma zan ɗauki wulakanci ba kema kin sani. Amman Luba ki gane Mijinyawa Asama'u fa ya Aura, bayan ya Aureta ya haɗa jiki da'ita, yaji daɗi da'ita, yayi mata ƙila fiye da abinda yayi mun. Luba mai tausar zuchiyata ta yi sanyi ban ganshi ba ne kawai ba wajen bane" "Amman Hindu bakya tunanin ya bi Umarnin su Nanno yayi Aure, ya watsar dake kamar yadda kika yi mai. Hindu baki san menene asalin haƙiƙatan ɗin me ake nufi da kishiya ba. Kuma babu mai iya kwatanta miki ya masu kishiya suke ji. Daga lokacin da akace bake kaɗai bace a wajen miji ba to ke da kwanciyar hankali ɗorarre har abada fa haƙuri kawai akeyi, musamman masu zama gida ɗaya irinmu" Dariya nayi mata nace. Bambamcina dake kenan Luba. Ni kinsani in abu ya siremun ya siremun kenan komai zaiyi bazai taɓa burgeni ba sam. Ke kina iya jin zafin kishin Sunusi a ƙirjinki, ni kuma ko yanzu mijinyawa ya auro mata uku dashi dasu basa gabana. Luba wallahi so nake yayi auren sannu _sannu tasa ya mance dani daga ƙarshe ya shafeni a rayuwarshi,ya huta in huta. Ni ko ya sakeni wallahi Allah kinji na rantse bazan taɓa ƙara Aure ba, neman kuɗi kawai zan sake sakawa a gabana. Hajiya nake son in zama ƙaƙas" "Wallahi na sani Hindu, nasan kin rufe da mijinyawa tarihinshi ya ƙare. Amman na tausaya mishi" Harararta nayi, tana ta dariya. Me yasa baki wai yafe ma Sunusi bane Luba to?" "To yaushe yazo yace in yafe mishi ne wai. Sunusin da sai dai ya leƙo mu gaisa, daga bakin ƙofa yake tsayawa fa. Wallahi Hindu na tsani Sunusi. " To bare kuma ni" Mun jima muna tattaunawa kafin muka shiga hirar bikin Salamatu har da nuna mata motar Salamatu da hoton Auren nasu na kuma yi, Anata magana a zaure sai tara magana akeyi masu kambabata nayi,masu saka alkhairi nayi nima dai danna hoton nayi nace. Masha Allah ga ango a gaban amarya abunshi." Na tura tare da ajjiye wayar muka ci gaba da hirarmu daga baya ma Kicin muka koma muka ɗaura girki muna yi ina bata labarin mutuwar jamila da kuma bin diddigin mijin da nake so nayi. "Allah sarki na tausaya mata iyayenta sunyi wasa da rayuwarta sosai. Amman Hindu ni kam ki bar kes ɗinnan kawai" Dariya kawai nayi mata ina yanka latas da zamu ci shinkafa da miya. "Nasan ai tunda kika ce zaki yi babu mai hanaki wannan naci da taurin kai naki ba dama" Harararta kawai nayi. Bayan mun gama girkinmu muka sake bajewa a falo sai wajejen bayan la'asar Saudatu Mustapha ta kira wayata take shaidamun mu haɗu a Calido top roof ƙofar mata. Wani gidan cin abinci ne mai kyau gami da tashe. Mijinyawa na yawan kaimu wajen asabar da lahadi kowa yaci abinda ranshi ke so. Muna kan shiryawa kenan bayan munyi la'asar muka jiyo shigowar mijinyawa da Azgar. Atampa super mai ruwan ganye na saka ɗinkin riga da zani, na ɗakko mayafina baƙi, takalmi da jakata ma baƙi, suna daga cikin wanda na siyo a landan na zizara sarƙata ta gwal da ɗankunne da ƙaramin zobenta dama akwai zoben gwal a yatsana wanda yake da'iman dan tunda na siya ban taba cireshi a hannun nawa ba. Humra na shafa mai sanyi wacce ba zata dinga tasowaba ita nake shafawa duk sanda zan fita masu ƙarfin a gida nake shafasu, bata da ƙarfi Anty Badiat tana yinta ne musamman domin mata masu fita aiki, da kuma masu cutar asma. Sam babu ƙarfi sai mace ta matsoki sosai ne zata iya ɗan jinta ato kafin a kafurtani, na san me nake yi. Tabarauna na ƙara gani na saka. Muje Luba biyar saura ƴan jarida basa wasa da lokaci. Da ɗan jarida da lauya, da likita bansan wanda yafi girmama lokaci a cikinsu ba" Dariya tayi tare da ajjiye man bakin data gama shafawa tana gyara zaman mayafinta. Tare muka fito da'ita muka tadda masu gidan a falo mijinyawa yayo siyayya kowa da ledarshi. "Hajiya Luba kece a gidan namu? " Ya faɗa harda tasowa haƙiƙa mijinyawa na girmama hatta ƙawayena. Idanunshi jawur, har sun soma kwantsa. Gaisawa suka yi sosai ya dubeni yace. "Ga rubutu da magunguna na karɓo miki, Azgar zai kai miki ciki" Saida na kawar da kaina nace. Nagode Luba muje ko? Azgar zo ka rufe get" Na juya na fita na bar mijinyawa a tsaye da Luba. Sun jima sosai. Ni dai na faɗa mota na zauna na jirata har suka gama ta shiga mota muka fice sai ƙofar mata. Haurawa muka yi sama ko zamu ga su Saudatu Mustapha, amman bamu gansu ba. Maza da mata, ƴan mata da samari, magidanta masu ra'ayin fito da iyalinsu suci abinci duk gasunan ko wanne da abinda yake yi. Luba bari in kira inji suna ta inane? " Wayata na kara a kunne kuka ɗaya biyu tayi Saudatu Mustapha ta ɗaga tare da cewa. "Gani a bayanku ina hangoku ku dawo baya kaɗan" Juyawa muka yi tare da Luba muka hangota can nesa tana ɗago mana hannu. Baya can muka je sai na fahimci wajen shi na musamman ne babu yawantar mutane kujerun wajenma na musamman ne. A wani tebiri na gaba can muka hango Sumayya ta zama ƙatuwa sosai ta zama babbar mace tamkar ba ita bace wannan doguwa fara siririyar a makaranta ba. Da dariya muka ƙarasa wajen Sumayya ta taso da sauri ta rungumeni tsam muna dariya ta sakeni, ta rungume Luba sai farin ciki muke da junanmu, yaushe rabon da mu haɗu ai an jima gaya kuwa har gara Luba duk sunje bikinta shekara ashirin baya fa kenan. Sumayya kece kika zama babbar mace haka? Gaskiya oga ya tsaya miki Hajiyata" Na faɗa bayan na zauna." Sumayya tace dani. "Hmmm jikin dai na ƙibane amman Hindu Duwaf halin da nake ciki yaci ace na dawo ƙashi wallahi, amman dake kurman jiki gareni kin ganni dumimi dani" Saudatu tace. "Hmmm ai sha'anin rayuwar yanzu sai godiyar Allah. Matsalar dai bazai wuce ta kishiya, dangin miji, ko shi kanshi mijin ba" Murmushi nayi nace Ai a cikin wannan matsaltsalun da kika karanto da wuya kiga mace tace miki bata da ɗaya daga cikinsu. Wacce kuwa bata cikin wannan layin to da sauranta a duniyarnan Saudatu." Murmushi Saudatu tayi da gani mai ciwone idanunta take suka kawo ruwa suka taru sai ajjiyar zuchiya take saukewa. Dukkanmu sai muka shiga girgiza kayuka ko wacce da abinda ya famu a zuchiyarta. Ko wacce tana da tabo ko in kirashi miki a zuchiyarta. Wallahi rayuwar mata ɗamfare take da tarin ƙalubale. Jama'a mu kwana anan, sai in Allah ya kaimu gobe. (Dan Allah a dinga karatun nazari, ba karatun nishaɗi kaɗai ba) Mrs BukhariTSURON TSIRIN... TSANDAURI LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA TAKWAS (8) TSUREN TSIRIN... TSANDAURI.. LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUƘHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA BIYAR (5) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DShCUZYCIFz4jkcpvChacU Shiga group dinmu domin samun ingatattun duk wani nau'ikan kaya da ake turowa daga Egypt kama daga abayas jilbab dasauransu cikin farashi me rahusa da ingataccen quality 👌💪✨💯🇾🇪 Taken mu shine shigar larabawa kai tsaye zuwa gareku🥰 Direct from Egypt to your doorstep 💯 +20 12 22791293 Saudatu Mustapha ta ɗanyi murmushi a ƙoƙarinta na kawar da damuwar dake ranta, sai dai masu azanci suka ce labarin zuchiya a tambayi fuska. Tuni fuskarta ta tona asirin damuwar ƙasan zuchiyarta. "Kafinnan bari mu saka odar abinda, ya dace ana tauna ana labari abun zaifi daɗi" Luba ce ta sauke ajjiyar zuchiya tare da cewa. "In labarin masu daɗinne ba Saudatu Mustapha. Ni a halin yanzu, da kuma yadda duniya take jujjuyawa sai inga mata kamar rabinsu da kwata a cikin rayuwa mai ƙunci suke" Sumayya tayi carab tace. "Sati ɗaya dana soma bin shafukan Hindu ya ragemun damuwata gaya, dan ada gani nake nafi ko wacce mace tarin matsaloli da shiga damuwa a gidan Aure. Saida na karanta labarin wannan matar da silar Hindu ta samu wanda ya aureta, ya riƙeta da yaranta, na fahimci matsalar gidan aure ko matsalar ɗa namiji nawa na sani. Hindu na taɓo abubuwa muhimmai sosai, a gaskiya tana ƙoƙari, duk da dai tun can mai ƙoƙari ce, gata da nacin karatu na masifa. Akwai tarin matan da wala Allah in suka ji labarina suce daɗine yayi mun yawa. Kamar yadda sukaita ganin daɗine yaima Lolo matar Babangida Kacigari yawa" Saudatu Mustapha tace. "Ai ni ina ganin a wannan zamanin ko duk macen da ta samu miji nagari ta godema Allah, kuma itace mace mafi sa'a a duniyarnan wallahi" Hmmmm" Shine kaɗai abinda ya fito bakina na rasa kalma kwata_kwata zukatanmu sai ƙonewa suke yi suna mai cike da ƙunci da damuwa mai yawan gaske. Saudatu Mustapha ce da kanta taje tayo mana odar abinda zamu ci, mu sha. Dariya nayi nace. Wannan teburin da alama yayi kama da teburin tattauna matsaloli da gani" Dariyar suma suka saka Sumayya tace. "Wala Allah in muka tattauna mu samu sauƙin nauyin zuchiya. Wallahi a gidanmu babu wanda yasan a cikin rayuwar da nake. Kinsan yanzu a cikin ɗakinku ma sai ki samu mai son ganin bayanki. Shi yasa matsaltsalun gidajen auren suka dawo yanar gizo_gizo ai kune malama haid my id Hindu, ke kinsan komai. Da yawa_yawa matsalar cin rayuwarsu take yi. Sun kuma kasa fuskantar gidansu, ko ƴan uwansu, bare ƙawa da wannan batu. Ku kuma sai kuka sauƙaƙema mata hanya. Kuma ana samun maslaha. Ina Bibiyar Lubna da Aisha Falke sosai. Ina son matar, turancinta da yadda take wuji_wuji da turanci yana burgeni. Gata da fahimtar juna sosai da mijinta, yakan taya ta abubuwa da dama. Hindu ma naga Mijinta yana taya ta abubuwa, akwai bidiyoyi da yawa dana ganku tare ke da mai gidan naki. Dariyar muka kuma sakawa harda tattafawa taf tamkar bamu da wata damuwar komai. Mai kawo abinci ne ya dure mana ƙaton tire ɗauke da shinkafa irinta larabawa mai nama gashasshe manya manya harda bushasshen inabi a cikin abincin. Sai lemo da ruwa, da soyayyen dankalin turawa mai gashasshen kifi tarwaɗa lafta lafta biyu. "To Bismillah mu soma ci ana hirar yaushe gamo. Luba na dai san gidanki a baya, na kuma san kina aikin gidan rediyo yaronki ɗaya na sani Baba Sadiq naje suna ma. Daga nan na bar ƙasar bamu sake ji daga juna ba. Ya rayuwarki ta kasance wajen faɗi tashin cimma gurin abinda kike so ki zama, ga aure ga yaro a lokacin ga miji? " Cewar Saudatu Mustapha fa kenan murmushi nayi mata bakina cike da kifi da dankali nace. Saudatu Mustapha kenan kaga manyan lauyoyi irin wannan tambayar haka? " Luba tace. "Rabu da'ita in dai fagen tambayane da ƴar jarida da lauya ƙwaryar sama ke dukan ta ƙasa nima zan yi mata nawa. Mu da muke rufta mutum yai suɓul da baka ma" Mu kai ɗan dariya, duk hankalinmu akan abinci yake munata yaga muna ƙona yatsunmu. "To gurin zama ƴar jarida ya ginu a zukatanmu ni da Hindu tun muna yara gaskiya inga ni tun ina da shekaru goma sha biyu. A lokacin kullum a gida ana sauraren Bbc Hausa safe da yamma. Babban abinda yafi komai birgeni a lokacin dake da yarinta yadda suke karanto labaran ba tare da ɓata ko gargadaba shi yafi ɗaukata sosai. Ita kuma Hindu abinda yafi burgeta shine wannan muryar da Bbc suke kwaɗa hira da'ita mai taken landan take kira sashen hausa na Bbc. Kinsan Bbc sha ƙundumce, ta tattare ƙunduna, kuma abar koyice, Bbc masu gaskiya da yaɗa labarun gaskiya, ingantattu. Dan ko labaraine a da, da ma yanzu muddin kace ai a shafin Bbc ka gani, ko Bbc ne suka faɗa, musu ya ƙare kawai an gama yadda. To ina ya Allah babu ya Allah. Mun soma sakandare duk da haka muna hira gurin bai canja ba saima, sake ƙaruwa da yake yi. Toh mun yi Aure da Sunusi dama ya riga ya san da zaman gurin nawa, kana yayi alƙawarin barina in cimma gurina, kuma inaso ya barni in yi aiki duk kuma ya amince ko da bashi zai biya mun kuɗin karatun ba. To muna auren kuma sai ciki kunsan ciki da goyo na daga cikin manyan dalilai masu ruguza gurin ƴaƴa matan da sukai sake, da yawa. Ni ban bari hakan yayi tasiri ba duba da Innarmu mahaifiyar Hindu da nake kallo a matsayin allon kwaikwayo, da yadda tayi zarra ma sauran abokan zamanta da Jama'ar gidansu, a cikin malamanma bata da tamka kun san wannan dai, ta iya koyarwa, ta iya duka. Sadiq na da wata takwas lokacin na soma zuwa jami'a. Sabida tsabar son karatun a ƙafa nake zuwa in dawo a ƙafa rana, ɗaɗɗayane nake samun kuɗin abun hawa a wajen Sunusi. Rijistireshon ma da ƙarma_ ƙarma ya biya na farko aka barshi da biyan bashi da mitar tsiya, ya doshi mita, yaita mita yana ciccika yana batsewa. Na soma karatuna da kamar shekara ɗaya na samu wani ciki mai laulayin tsiya wanda dole ya taɓa karatuna na dakatar dashi na shekara guda, akan inna haihu sai inci gaba. Na haihu ina yin arba'in na koma karatu, a wannan lokacin Sanusi a gida yake babu sana'ar ma bare in yi tunanin ya biya mun rijistireshon sai ƴan atampopina na siyar na suna, na gagganɗa na biya naci gaba da karatun a wahale. Me yasa nace a wahale? Babu kuɗin mota, babu abinci ishasshe da zanci in tafi makaranta, ga jego, ga tunanin inna dawo gidan me zan zo in tarar in ci, ga rana na shawo, in kika ga ƙafata a lokacin duk ƙura. Sabida tafiyar ƙafa da nisa tsakanin gidan Aurena, da makaranta har faso saida ƙafata tayi. Ina tafe kawai naji ƙafata kamar an sa reza an tsaga mini kes, sai ga jini. Shikenan ya zama ciwo, a haka dai. A haka akaita bugawa ina ya Allah babu ya Allah, duk na rame na fita hayyacina kafin shekara ta zagayo nayi lalacewar da koni bana sha'awar kaina wallahi, in kalli madubi bana so. Gidanmu kuwa bana son zuwa sabida ƴan uwana sai suita magana akan ramata. Ni kuma nayi gum naƙi faɗa musu sirrin gidana, haka muke ɓoyewa, haƙawa, mu burne tare da Sunusi, soyayya kam muna bugawa, duk da rashin kuɗin, yarona na biyu ma ba'ayi mai haƙiƙa ba. Baba Sadiq ɗinma firjina na siyar a lokacin duba goma sha biyar, na bashi a ciki aka siyo rago dubu takwas, ragowar kuɗin dashi ya fiddani kunyar abincin suna, dake akwai kayan akwati, ni kuma na ɗiba na ɗinka kayan fitar suna. A hakan akaita turawa har Allah yasa ya samu gadi a zangon baƙi, wataran aikin safe, wataran aikin dare na kwana, sai muka ɗan samu sauƙi har Sadiq ya shiga makaranta shima. A haka na gama karatuna na shiga faɗi tashin neman aiki hmm Da ƙyar na samu aiki a wani gidan jediyo, haka bayan wasu shekaru kenan fa. Ko kuma ince na nuna ni ko kyautane zanyi musu aikin sai aka ɗaukeni akan wani shiri sabo, na soma ana ɗan tsakuramun abinda ba za'a rasaba, koma in kirashi da na mota. Kafinnan na ɗan yi koyarwa a wata makarantar sakandare, ana biyana dubu huɗu da ɗari uku. Sai mu haɗe da kuɗin Sunusi muyi hidimarmu ta yau da kullum. Kunji yadda akayi a ɗan taƙaice kenan, har aka iso wannan matsayin da ake a kai yanzu, sai dai mu miƙa godiya ga Allah" Ajjiyar zuchiya Luba ta sauke tare da ɗiban shinkafa da nama ta zuba a bakinta tana taunawa. Sumayya tace. "Toh yanzu da kika cimma gurinki ya rayuwarki da Sunusi taci gaba?" Dariya tayi tana kallon Sumayya data kafeta da idanu. "To bayan komai ya warware shekaru sun sha sosai, Sunusi shima ya samu faraga daidai gwargwado muna rayuwarmu babu matsala harma Allah ya huwace mishi ya sai filinshi babba, ko ince dai muka sai filinmu babba, dan inajin in ban mance ba. Ni na kawo miliyan ɗaya, shi kuma ya saka dubu ɗari huɗu, da dubu biyar akai, muka mallaki fili da sunan zamu gina, mu shiga ni da yarana mu wataya. Tare dani dashi muke zuba kuɗi mu ka yi ginin dai, ko kuma ince da kuɗina ni na soma ginin kafin ma shi Sunusin ya soma zuba nashi kuɗin. Dani dashi muka zauna, mukaita tsara yadda zamu yi gidanmu, har dai muka cimma matsaya. A wannan matsayarne muka kira masu zane suka zana mana hmm. Ragamar gida data yara kusan saba'in talatin muke yi a lokacin (70/30) ban damu ba duk wani nauyin kaina a hankali ya singa sakarmun ƙaƙas. Wataran ya biya kuɗin makarantarsu duka, wataran ya biya rabi, ni in biya rabin, duk ban damu ba. Hindu ma cemun take yi ai babu komai dan mun taimaka ma mazajenmu in akayi duba da cewar sai da yaddarsu da amincewarsu za kayi karatun, kuma duk namijin daya barka kana aiki kana samun kuɗaɗenka baida mugunta. Dan a cikin maza akwai baƙaƙen mugaye masu hassada da samun matansu, masu dankwafar da matansu. Lokaci guda Sunusi ya sauya sabida Aure da ya saka a gabanshi, ya dena mana komai. Ya shiga karantamun shafukan rashin mutumcin daya buɗe bai biya mun ba a baya. Naci gaba da jurewa har na tare a sabon gida amarya tazo itama. A lokacin na gane Allah ɗayane, na kuma yadda ba kowanne namiji ake goyawa ba wallahi. Sunusi ya nuna mun ni ba kowan kowa bace, ni ba komai bace a rayuwarshi ba, ta Amarya kawai yake ya mance yana da uwar ƴaƴa ni Lubabatu dana Aureshi baida ko biyar yake yi. A yanzu da nake yi muku maganarnan rayuwa nake yi sunan ina da miji ko rabon kwana ba'ayi dani. Ni dama bai dameni ba, amman a ƙalla a kwana a ɗakin naka ko da a falo namiji zai kwana gobe ya fice, a ƙalla ya siya ma ɗan mutumci. Amaryar ta haihu ta haifi ƴan biyu dukka maza. Hankalinshi ya sake karkata ya koma kanta. Wallahi da Sunusi ake zaman barka ƙaƙas, yana cikin mata ai ni naga abinda yafi zare tsayi" Dariya nayi har ina ƙwarewa, suma su Saudatu Mustapha dariyar suke yi. (inaso ku nutsu sosai, kuyi karatun nazari, ku fito mu tattauna sosai. Wannan haɗuwar bawai hira da cin abinci bane kawai ba. Hirar bawai hira bace wacce zata wuce a hira kawai ba. Mu buɗe zukatanmu mu yi karatun da kyau) Sumayya tace. "Ikon Allah Luba lallai ko wacce aka ganta cikin sutura ba'asan abinda ta fuskanta ba kafin a ganta cikin suturar ba. Kowa ka taɓa yana da abun faɗe. To ta nawa ɓangaren labarin. Ni da Auwalu a tsangayar Aminu Kano muka haɗu shi yana fafutukar haɗa mastas, ni kuma ina ta damben kammala digirin farko, ina karatun likitanci. Gashi gida an matsamun in fidda mijin aure. Sun gaji da zaman karatu da nake yi a gidan ɗalibai hostel dan gaskiya Babanmu ya fiso ka zauna a gidan ɗalibai ka nutsu kayi karatu, duk ƙarshen sati sai ka koma gida. Dangi sun damu Mamana da surutu akan so suke su maidani ƴar boko inzo ince ni nafi ƙarfin maza su basu yadda ba. Sabida nayi jinkirin soma jama'a gaskiya, ban shiga da wuri ba. To dama ina soma karatu, sai aka matsama Mama lamba, ita kuma sai ta ɗauramun firejar duka a kaina, inna dawo hutun ƙarshen mako. Ina cikin wannan firejar muka haɗu da Auwalu, hmmm lokacin an turani asibitin koyarwa na malam aminu Kano domin in yi aiki dasu, to shima ashe a cikin irin wannan firejar tawa yake a gida, dan ba yaro bane gaskiya, iyayenshi suna Bauchi karatune ya kawoshi Kano yana zaune gidan Kawunshi ƙanin mahaifiyarshi, kuma da aikinshi a hannunshi karatun yake son ƙarawa sabida samun ƙarin girma dai da sha'awar karatun ma. Irin wannan matsin lambar da iyaye ke ma yaransu yake sawa mace ta zaɓi mijin da ba daidai da rayuwarta bane ma'ana tayi zaɓin tumin dare. Kazalika namijin na iya zaɓar macen da ba tai daidai dashi ba kuma ya sani, amman sabida gudun kar wa'adin da aka ɗibar mishi ya cika a gida sai ya zaɓi wacce duk tazo mishi, domin kar ace za'a bashi ko wacce irice a dangi. Abinda ya faru dani kenan a zaman hira biyu kacal na fahimci Auwalu ba irin ra'ayinmu ɗaya ba, kuma na gane wani irin bauɗaɗɗen mutum ne mai saurin fishi, da tsattsauran ra'ayi, rashin fara'a, da rashin nuna damuwarshi a kaina. Amman tabbas a baki in muka haɗu yana furta mun yana sona. baya gajiyawa, amman fa a iyakar fatar bakinshi ne a aikace babu wannan son kwata kwata. A hakan na gabatar dashi a gidanmu na kaishi har gida ya gana da iyayena, aka tsayar da maganar Aurenmu akan dana kammala karatun sai ayi bikinmu. Kuskurena na farko kenan dana tabbatar na aikata. Hmmm tafe_tafe na kammala karatuna asibitin malam Aminu Kano suka riƙeni a matsayin gama garin likita wacce a yaren nasara ake kiranmu da General practitioner (Gp) Sai mukai aure da Auwalu duk da halin rashin damuwa dani da yake nunawa, ni kuma dake aiki ya sha mun kaina sai bana damuwa sam. A hakan mukai Aure ya ɗaukeni mukai Bauchi yuu dole na bar aikina amman dai mahaifiyarshi ta nema mun aiki a babban asibitin Bauchi naci gaba da aikina da daɗi babu daɗi, inata turawa Auwalu kuma ya ɗan canja babu laifi yana ɗan iya kirana a waya haka sau ɗaya a rana, shi soyayyarshi bata motsawa sai yana son ya kwanta dani kaɗai, da zaran ya gama, aikina yake ƙarewa kallo ban isheshi ba, wallahi. Sai kiga ya sauya tamkar ba shi bane wannan na kan gadon ba. Ina goyon yarona na farko ya samu aiki a Kano babba da yafi nashi na Bauchin, muka ɗungumo muka dawo naci gaba da aiki da Malam Aminu Kano a matsayina na gama garin likita. Lokacin dana samu cikin yarinyata Fati a lokacin komai ya cukurkuɗemun ni da Auwalu, babu zaman lafiya ko kaɗan kullum cikin fishi da ƙunci yake, mu zauna mu fahimci junanmu, ya hanani wannan damar ga aikina baya bamu ishasshen lokacin daya dace, a lokacin harya soma ƙorafi akan aikin ya isheshi shi kam in ajjiye. To kunga ai anzo wajen ko? " Kai na jijjiga nace An zo wajen tabbas ki bar aiki a matsayin wacce tayi rantsuwa zata kare rayukan al'umma, Auwalu yazo da abinda zai kawo haɓakar rashin zaman lafiya a aurenku. Ina mamakin mazan da zasu auri mace tana aiki, ko tana Jami'a, yazo ya ce a dena aiki, ko ta gama karatu yace, ba zaki yi aiki ba. To wai tun farko bai ga ƴar sakandare itace ta dace dashi bane wai? Sumayya tayi murmushi tace. "Sak kuwa abinda yake so kenan dan daga haka ya tsiri gaba dani Hindu. Sai ayi wata baice mun komai ba. Duk ranar da yake buƙatata zai neme ni, ni kuma ban taɓa hanashi kaina ba. Ke sai yai wata biyu, fin haka ma, in kinga yayi magana dani to zai amfana da albarkar da Ubangiji ya halittoni dashi, kinga fa kenan a fakaice, ya maidani injin ɗin walwala da fulejonshi kenan fa, daga haka sai in yi ƙyanƙyasa, iyakar kwantiragin daya auroni in yi kenan fa. Wannan rikicin sai da ya ɗaukemu shekara biyu. A lokacin duk na rame na lalace Hindu, duk wanda ya kalleni saiya tambayeni ciwon me nake yi. Ana haka ya samu aiki a Abuja aikin daya canja mu daga tsaka_ tsaki zuwa mataki na sama_sama, aikin daya ɗaga darajar Auwalu wanda ya samu ta dalilin mijin ƙawata kuma ni naima ƙawar tawa magana kamar wasa aka ɗauki Auwalu, lokacin yarana uku na kuma yanke na gama harna ɗaura robar tsarin iyali. Bazan iyaba, itama ta ukun Allah yayi zata taka doron duniyane wallahi. A lokacin dana sama mishi aikin yana tsaka da gaba dani. Rayuwa tayi kyau, taci gaba da tafiya damu. Nima ina aikina a wani asibiti mai zaman kanshi ana biyana da kyau. Zaman namu dai kadaran kadahan, ga tarin dukiya amman ni da Auwalu har lokacin bamu fahimci junanmu ba, bansan me yake ciki ba, baisan me nake ciki ba ,muna rayuwa a gida ɗaya a matsayin miji da mata. Bayan shekaru sai ya sake tsuro da wannan fishi na rashin dalili a tunaninshi zai gasani. Sai naƙi gasuwa sabida na riga da na ƙuna a lokacin ko gezau bana ji, zuchiyata ta bushe ta kangare. Madadin ma damuwar abun ta dameni saina koma karatu naje na haɗa mastas ɗina a Jami'ar Abuja, ga aikina ga yarana da suke ɗebemun kewata. Ranar laraba na dawo da safe kasancewar aikin dare nayi Auwalu da yara sun gama shiri zasu tafi ya ajjiyesu a makaranta. Sai cewa yayi. "Sumayya inaso zamu yi magana dake, inata son muyi maganar amman duk sanda zaki dawo a gajiye kike dawowa, ga lokaci yanata ja. Gara muyi maganar tunda lokacin da zan dawo ke kuma lokacin kike shirin zaki koma ƙaddararren aikin da yafi miki kula da yaranki da mai gidanki" A gaban fa yara. Sai Ahmad ya saka ƙannenshi gaba suka fita, a lokacin sun girma shekara biyar yanzu da yin hakan, Ahmad yana Jami'a yanzu haka. Ai naji abinda yace, kuma ni nasan ban rageshi ba, ina yaga lokacin nawa ma. Zama nayi kamar yadda ya umarceni, banyi raddi akan abinda yace game da aiki ba. "Aure nake so in yi dama shine nake ta son in faɗa miki. Sabida tunda mukai aure haƙuri nake yi dake ta wajen mu'amalar aure gaskiya, in kin lura shi yasa sai in yi sati, wata ɗaya, wata biyu, har uku, ban nemeki ba. Ba dan bana so bane ko bani da lafiya bane. A'a sai dan rashin gamsuwa da bana yi ne kawai, baki da ɗanɗano sam, kuma ni bama na dai ganewa dai. Sannan baki da lokaci kullum a gajiye kike, ga yawan amsa waya da yawan bama marasa lafiya lokacinki. Sai dai bawai bana sonki bane in zaki gyara ta yadda zan dinga gamsuwa shikenan. Sannan in ki ajjiye aikinki sai in fasa auren. Ki zauna kiyi nazari na kwana uku zai kama ranar sati da muke gida sai mu zauna mu tattauna" Zazzaro idanu waje muka yi dukkanmu ita kuma Sumayya idanunta suka cika tab da ruwan hawayen baƙin cikin fama miki mai raɗaɗin zafi dake ƙasan zuchiya. Sabida jarumta murmusawa kawai take. Wato abinda na lura kamar yadda aka tsara zuchiyar namiji da faɗin da zata iya ɗaukar soyayyar mace huɗu, kuma ko wacce a muhallinta. Haka Allah ya tsara zuchiyar mace da faɗin shanye damuwoyi da matsala harma da jimiri. Sai dai wannan haƙurin da yawan shiru da mata suke yi su bar magana a ciki, shi ke faɗa musu ya wanzar musu hawan jini, ciwon zuchiya, da buguwar zuchiya mai shanye ɓarin jiki, ku harda ma rasa rayuwar baki ɗaya. In ba mace mai taurin zuchiya aka samu ba. Yanzu dai ku jibi furucin Auwalu tamkar yaci kashi dan Allah, ko da yake mata zasu ce, ai maza sunfi haka na Sumayya kaɗanne. Harma su buga misalinsu da matan da akai musu fiye da hakan. To ni tambayata anan shine, tunda anayi, dole ayi shiru, ko kuma dole yadda wance tayi, wance ma dole haka zata yi? Ni kam aban amsata ni Hindu a kwament sekshon. Nisawa nayi kawai Luba ce ta samu zarafin cewa wani abu da murya mai ɗauke da amon tausayi, gami da ɗaura kai a matsayin da mai labari ya ke kai. "Yaya kika ji a lokacin dan Allah Sumayya. Ace Namiji ya kalli tsabaragen idon matarshi bayan shekaru da aure yace bai taɓa jin daɗinta ba, shi yasa ma bai fiye nemanta ba? Ya ilahi rijalu suna sharafi" Dariya Sumayya tayi tare da share hawayenta da dabara bata barsu sun kai da sakkowa ba, hakan ya burgeni, kunsan ance bana ji, kamar yadda nace Ummin Mama bata ji😉. Saida ta nutsa hannunta a cikin shinkafa ta gutsiri ƙaton nama ta saka a bakinta ta tauna ta cinye, mu kuma illahirin nutsuwa da hankulanmu suna kanta. "A lokacin Lubabatu da za'a tsaga jikina ba za'a tadda jini ba. Maganarnan ta dakeni ta mari rayuwata. Wallahi nafi awa uku a tsaye a gaban mudubi tsirara ina duba zatin da Allah yaimun, ina hasaso tsabtata, iya girkina, kula da muhalli, kula da gida da gyaran gida, tallatin dukiyar miji, bada gudunmawa ta kuɗi a lokacin da ake buƙatar hakan, na hakaito fuskar Auwalu a lokacin mu'amalarmu bazan iya tuno komai ba. Ni ba ƴar ƙauye ba bare ace ban iya sarrafa miji ba, ko ban iya sarrafa jikina yayin mu'alamar bane, ni ba ƙazama ba bare ince da datti nabar jikina da muhallina. Ni ba wai bana shan magungunan matan bane, duk da ban yadda dasu ba a matsayina na likita akwai abubuwa na musamman da jiki yake buƙata domin ƙarfafa sha'awa da tada komaɗa, ina haɗawa dasu zogala, alayyawo, rama, kayan ganye da irinsu kanunfari, citta da sauransu da sauransu. Kuma ni ba kasalalliya bace a ko da yaushe Auwalu in yazo da buƙatarshi ina biya mishi ko da wanne irin gajiya nayi sabida gudun ƙorafi da kiyaye abinda zai iya harzuƙashi, akan aikina muzo afi wata ɗaya ana rikici, tunda dai na fahimci shi irin mazannanne masu tattalin rikici da janjanin kar ya ƙare. Akan kalma ɗaya tak sai afi sati biyu yana ƙorafi da ƙoƙarin ƙera maganar ta dawo garma. Kuma ni likitace, nasan lafiyata ƙalau, ni'ima dai in tana ma mace yawa to ni Sumayya tawa tayi yawa. Ina tara buƙatuwa sosai kafin Auwalu ya waiwayeni, hakan yasa da zaran munje sama jannati, sai in ta yoyo kawai. A baya ina nemanshi, sai ya gwadamun ba haka yake ba, saina ɗauki ido na zuba mishi. Hmmm a cikin kwana ukunnan tunanukan da nayi sai wanda na mance, ga kuma aiki inna fita shima babu sauƙi. Ga masu son ganin faɗuwarka musamman a wajen aiki, dama haularka, abinka da ƴan dangi in magana ta shigo haularmu to a rufe ƙofa kawai. Bamu sake magana ta fatar baki da Auwalu ba satin duk aikin kwana nayi, ranar asabar da safe muka haɗu a wajen cin abinci da yara kamar kullum. Doya da miyar kwai nayi mana, sai ruwan bunu da lemun tsami sabida danne maiƙon abun suya da muka ci, in akasa madara a shayi ga kayan soye soye tayar mun da zuchiya yake yi, maiƙon ai sai yayi yawa gara shayi mai lemun tsamin yafi shiga. Yara na gamawa suka bamu waje. Sai kallona yayi mukaima juna murmushi. "To ya ake ciki da fatan kin rubuta musu takaddar barin aikin kafin ki baro wajen ko, ko sai monday zaki rubuta musu? " Dariya nayi nace dashi. In har na zaɓi abinda kake tunanin ba? To ban zaɓi barin aikina ba. Auwalu in mata uku zaka auro bana jin zai shafeni bare aikina. Ai gara ka auro wacce zaku ji daɗin rayuwar auren da'ita, tunda anan baka samu ba, bazan tauyeka ba, ta yiwu halittatace hakan, shi yasa baka gamsuwa. Shari'a ta ba da wannan damar ni Sumayya bana jayayya. Amman kafinnan, inaga akwai buƙatar ka soma shan magungunan ƙarfin maza kafin tazo, inaga basir ko cutar sanyi sun cinyeka faɗamane banyi ba. Kar ka kawo yarinyar mutane a haka, tunda kana kallon kanka a matsayin gogarma" Ina gama faɗin haka na suri kwanon abincina da kofin shayina na ƙule ɗakin yarana. Maganar bata ƙara tashi ba, naci gaba da aikina shi kuma yaci gaba da shirin aurenshi da gyare gyaren inda zai ajjiye ƴar mutane, wallahi ko a jikina kamar an tsikari kakkausa. Bai mun kayan faɗar kishiyaba ban tambaya ba, ya gyara ɓarayin amarya ya tsarashi fes, nima na zuba kuɗi na gyara nawa ɓarayin fes. Kuma naci alwashin, na bar ma Amarya Auwalu Abadan. Bai isa duk ranar da yazo in saurareshi ba sam. Ranar wata Juma'a aka ɗaura auren, asabar Amarya ta tare naga gulma da makirci irinna dangin miji ashe haka suke babu kyau babu daɗi. Shikenan ranar lahadi ango ya tare a ɗakin Amarya, da ta kwana ɗaya ban santa ba babu wanda ya kawota wajena. Ashe shigowar Amarya cikin gidannan a lokacin ne zan gane ainihin mijin da nake aure, da duk bansan waye Auwalu ba. Hmmm da safe ranar monday na buɗe ɗakina zan fito cikin shirina na zuwa wajen aiki. Sai nake jiyo tashin maganar Auwalu a falo da Amarya suna magana a hankali yana bata labarina. Dan tabbas jin sunana daya amtaba ya jani da son laɓewa inji me yake faɗa mata. Namiji namiji tuwon ƙaya miyar allura. Ya ilahi. Mrs Bukhari (A cikin labarin Lubabatu, da labarin Sumayya duk da bata ƙarasa ba, wanne darasi kuka ɗauka. Inason jin ra'ayoyi sosai. Ayi karatun nazari sosai, a fito a tattauna domin Allah)TSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA (8) "Hmmm wai kunsan me Auwalu yake faɗama Amarshi suna zaune a falo? " Su Luba suka amsa mata da "Aa" Ni kuma na yi ƙur ina kallonta kawai ina nazartarta. "Cewa yayi da'ita" "Ai a kwana ɗaya da nayi dake Amarya kin mantar dani komai in faɗa miki. Yau ɗinnan nasan nayi aure na san kuma na kwanta da cikakkiyar budurwar data tattalamun tantanin budurcinta, ta kawo mun ɗakin sunnah na alkinta abuna." Sai naji gabana ya faɗi ras sabida a iyakar sanina nasan Auwalune namiji na farko da ya taɓa tarayya dani. Saina shiga tunanin to me ya tauye mun nawa budurcin Auwalu yake nufi? " Amarya sai ta sauwaƙemun ta hanyar cewa. "Bazawara ka Aurane Diya, naji a batunka kana maganane kamar bata kawo budurcinta bane, ko bazawarace, ko dai tsalle_tsalle tayi?" Idanuna na lumshe hawaye suka zubo mun masu ɗan karen zafi. "Budur bazar ce. Abinda yasa nace dake hakan, ta jima batai auren ba, sai kuma ta zama likita. To kinsan ni'ima da albarkatun jikin mace tana girma suna ja baya. Sai da abokaina suka ce in inaso in more Aure in ɗauki ƴar sakandare wacce take kan ganiyar balagarta masassaƙin budurci hankalinshi ya dawo kanta. To a lokacin yarintace bana so, saida na aureta sai na gane yarintar da shagwaɓar tana da matuƙar amfani. Ko gidanmu can Bauchi naje in naga su Nazifa suna ma Dadanmu shagwaɓa sai abun yai ta bani sha'awa auren yara duniyane. Kema harda shawaɓarki a cikin abinda ya sake gigitani. Kinga wannan kukan shagwaɓar? Ba dama ne" Dariya suka yi, da jin amon muryarta tayi farin ciki sosai da jin wannan labari daga bakin Auwalu. Bakin da a tunaninta bazai mun ƙarya ba. Ni bansan ma ya iya hira da mace hakan ba, dan ko zamanin da muke budurwa da saurayi bamu yi fiye hira ba, yadda na sanshi baida sakewa kullum a ɗaure yake, ga saurin fishi, da maida ƙarami ya zama babba. Abun mamaki sai gashi muryarshi zaƙwai_zaƙwai, yana hira shine harda sharri, da aibatani a gaban matarshi, matar tashi ma wacce kwana ɗaya tayi kacal a cikin rayuwarshi fa. Hmmmm ya salam. Da ƙyar na jawo ƙafafuna na fito bayan na saisaita kaina, na share hawayena. Murmushi na ƙaƙaro na yafa a fuskata muka gaisa da Amarya ina daga tsaye. Shima gaisawa muka yi ina ƙare mishi kallo hannunshi a sagale ana Amarya yana ta wasa dashi. Inda ranka dai zaka sha kallo. Abun almara. "Dama ke muke jira mu yi kalaci Maman Abba" Cewar Amarya dake nuna mun dainin ɗin babban falon. Ayya ayi kalaci lafiya ni inna je ofishina nayi acan ni sai na dawo" "Ahh dama inaso in haɗeku muyi ƴar maganar da akeyine jiya babu lokaci" Kallonshi nayi na dubi agogona nace. Ita ƴar maganarnan a barta zuwa in dawo bana wasa da aikina. Amarya saina dawo a kula da gidan da mai gidan" Na kwashi yarana muka tafi. Hmmm wasa farin girki tun daga lokacin har izuwa yanzu zuchiyata bata huta ba, Auwalu ya tsiro da abubuwa iri_ iri abinci wannan ya dena ajjiyewa, yana dai kulawa da yaranshi. Ni ɗinma zaman jiran lokaci nake yi kawai. Bayan ya gama kwanaki bakwai yazo neman daɗi, wai tafiya umara yake so yayi da'ita in suka je suka dawo sai nima muje yayi mun alƙawari wa ya mutu wa ya dawo. Abinda yasa zai soma tafiya da'ita akan wannan alƙawarin ta amince da aurenshi. Babban abinda yake ƙaramun mamakinshi. Yadda ya sauya tamkar ba shine wannan auwalun me ɗaure fusa, shiru_shiru, saurin fishi, gaba ba?" Ya warware annurin fuskarshi baya ɓoyuwa sam. Ba sai ka kaini ba Allah ya huwace mun abun biya, dama na riga da na biya faɗamane banyi ba, sai yanzu dai data kama, amman lokacin tafiyar kawai nake jira in yazo ƙila kafinnan ka shigo wajena sai in faɗama. Batun ƙara kwana wallahi Allah ni sumayya na yafe mata kwanan, tunda dama ni dai lallaɓawa akai ta tayi dani, zan mayar da hankalina a kan tarbiyyar yara da kulawa da aikina. In kuma sallamata zaka yi duk ɗaya Auwalu. Tunda sai inga zamana kamar zai iya takura muku. Ni dai kaga ba amfanin komai zanyi ma ba, daga nan har duniya ta naɗe" Kunji wannan? Kuma a lokacin ban biya kuɗin umara ba wallahi, biya dai nayi bayan fitar Auwalu, dake ina da fasfo ɗina a ajjiye. Na kira abokiyar aikina ta haɗani da egen. Azumi na goma sha bakwai jirginmu ya ɗaga zuwa umara ta kano ni na tashi, ta ina suka tashi can ta matse musu dan ban sani ba, na dai san Allah ya dafa mun na rigasu tashi. Babban abinda zaisa kisan mata basu da kirki da yaya_yawansu. Wai wannan bushasshiyar Amarya saita tsiri rigima da Auwalu akan wai damme zai biya mun umarah, alhalin ita yayi ma alƙawarin zata soma zuwa, wai take ce mai da ta san yana son matarshi da yaranshi ai da bai aurota ba. Ita taga inna dawo aiki duk sai ya sha jinin jikinshi, alhalin ya faɗa mata zaman haƙuri kawai yake yi dani hmmm. Naje umara, nayi ma Allah kuka, nayi mishi kirari akan ya dubeni, yana kallon Auwalu yai mun maganinshi. Shikenan Aurena ya zama haka inje aiki in dawo, in ma yarana girki mu ci mu kwanta aikina kenan. Auwalu ko ɗakina bai ƙara shigaba, Shekara data zago shi da'ita suka tafi aikin hajji wata shekarar na tafi nima to ina da kuɗina, amfanin neman kenan, rayuwata nake yi fes dani, Auwalu dai ya jingineni kamar yadda Sunusi ya Jingine Luba, amman gara Luba sau biliyan. To su fa amman dangi gani suke duk Auwalu ke mun komai, suturu, motar hawa, hajji, da umara, duk ni naima kaina da gumin halak ɗina. Amman sai albarka iyayena suke bashi, yana karɓa. Kaje biki a ganka kayi firesh, kasa kaya mai tsada, ga mota, ga gudunmawa mai tsoka duk tunaninsu miji dai. Dangishi ma haka suke gani kamar ma a kaina ya ƙare suke gani. Dan wulaƙanci an san kuma kana aiki fa. Kwatsam yace ni da yara mu dawo Kano a lokacin yaro ya samu gurbin karatu a Kano. Shikenan muka dawo gidanshi daya gina a Kano ya tashi ƴan hayan fat ɗaya muka dawo. Watanshi bakwai ban sakashi a idanuna ba, mukan fi sati bamui waya ba dan daga wannan ranar ban sake ɗaga wayata na kirashi ba, in ya matsu shi yana kirana. Da Amarya ta haihu banje ba, yayi juyin duniya naƙi fur haihuwa ta biyun dai naje ana gobe suna nayi mata barka a ranar na juyo. Amman zama tsakanina da Auwalu babu bazan yi ba in shine Autan maza. Kuma yaronnan yana kammala jami'a, ƙanwarshi lokacin tana mataki na biyu a jami'a, to lokacin sai in nemi takaddata auren ya ƙare, in ci gaba da rayuwata, dan nasan zaice bazan riƙe yara ba. Shi yasa naita turawa har zuwa wannan lokacin. Allah yasa nima bani da ra'ayin riƙesu, kuma Allah bai yini da ƙulafacin yara ba sam. Hmmm wannan shine labarina, iyakar wanda zaku samu" Kaina na shiga girgizawa kawai, Saudatu ce tace. "Kenan ke babu wani hira ta fahimtar juna a tsakaninki da Auwalu?" Kina ji fa tace ita bata sanma ya iya hira da laluma ba har saida amarya tazo" Na tari Saudatu. Sumayya kuma tace. "Ai dariya wannan zan iya ƙirga sau nawa yayi mun tun farkon aurenmu. Amman bayan zuwan amarya kullu yaumun suna babban falo suna hira nake dawowa in taddasu. Wallahi Auwalu ashe har dariyar mugunta yanayi irin ta Uzairu zuchiyata." Murmushi nayi ma Sumayya tare da cewa. A hangena ke da Auwalu ruwan kashe gobara kuke nema a lokacin da iyaye suka ɗaura muku fireja. babu haƙiƙanin soyayya da dacewa da juna a tsakaninku, balle fahimtar juna. Ko ko dai ke kina sonshi Sumayya a lokacin? Sabida in akayi la'akari da yadda aka haɗun da kuma yadda komai ya tafi banga soyayya ba gaskiya, ni ko ku kun gani Luba? " Luba tace. "Gaskiya shi dai Auwalu bana jin yana sonta, kawai ya amshi Sumayyane domin faranta ran iyayenshi" Saudat tace. "Ba za'a rasa son ba tunda ba dole sumayya tayi mishi ba, ba kuma dole iyayen nashi suka yi mishi ba" Sumayya tayi dariya duk ta bibbimu da kallo kafin tace. "Auwalu ya soni ne sabida kawai iyayenshi wa'adi suka bashi akan in wa'adin ya cika za'a aura mishi ƴar uwarshi, har yarinyar na sani a Bauchi take duk wani sha'ani inya tashi na famili muna haɗuwa da'ita, tayi aure harma Auren ya mutu yanzu haka zawarci take yi. Harma naji labarin Auwalun na zawarcinta. Nayi kuskure mai girma dana amince mukai Aure da Auwalu a irin halin ko in kular da yake nuna mun gaskiya. Amman ko babu komai ai na soshi kuma na kula dashi, na ciyar dashi, na tufatar dashi, na rungumi aurena a lokacin da bashi dashi. Na shanye abubuwa da yawa sabida bakin mutane bana so yayi tasiri a kaina tunda sai cewa suke yi idona ya buɗe bazan iya zaman auren ba ma" Ai kinji irinta ko Sumayya? Nifa bana yin komai dan in burge kowa da komai. Duk yadda kika so ki burge mutane baki isa kin burgesu ba. A lokacin da kike ganin kin ƙure burgewarki, a lokacin zaki ji kushe daga wajensu. Bazan kashe kaina sabida ku ba wallahi " "Ai ke Hindu zuchiyarki na da jumurin kawar da kai daga komai ma. Nabi shafinki ai naga yadda maza suka saka miki jakar tsaba sunata caccakarki kamar me" Dariya muka saka dukkanmu nace da Sumayya. Kuma ni kinga bana ma karanta kwament bare in gani ba. Ko lokacin da nake dubawan, nifa zagina da akeyine yasa na gane abinda nake yi saƙwan na isa. Yarane ma suke damuwa musamman ɗanki Azgar. To shima na huta da mitarshi tunda nace ya dena bin shafin nawa ya sakama zuchiyarshi risilama. Hukuncin da kika ɗauka yayi daidai na rabuwa da Auwalu, nayi farin ciki da baki taɓa yadda kun kuma sake haɗa jiki dashi ba. Kinga batun rigasu zuwa umarannan? Ya tafi dani Sumayya. Amman kinsan da kece kika jingine Auwalu, kika hanashi kanki shekara da shekaru. Da yanzu an jaki an jefaki a wuta, amman fa mutane. In namiji yayi shi sai ace miki kiyi haƙuri, ai naki ma kaɗanne, ko kuma ace in dai namijine zai yi yafi haka. Shikenan iyakar maganar ta gama ƙarewa kenan." Agogo Saudatu ta duba tare da girgiza kanta hakan yasa nima na kalli nawa agogon kunsan wai ƙarfe nawa? Ƙarfe takwas da minti biyar. Lallai hira tayi hira lokaci ya ja haka bamu ma sani ba." Saudatu ta dubeni tace. "Abun mamaki kamar yanzu muka zo kinga dai lokaci. Yanzu abinda za'ayi mu barma sati nagaba domin jin nawa labarin dana Hindu. Sai dai zan so mu haɗu a gidana da wuri domin nawa labarin yana da tsayi babu laifi." Luba tace. "Mai makon kuce a haɗu a gidana? " Sumayya tace. "Ko nawa gidan ba" Duk mukai dariya tare da miƙewa muna tafe muna hirarmu, har muka fito harabar wajen cin abincin. A gidan Luba muka tsayar zamu haɗu zuwa sati mai zuwa in Allah ya amince wanda yayi daidai da ranar sunan Kishiyarta. Saudatu da Sumayya ko wacce ta shiga motatarta ni kuma da Luba muka shiga tawa kamar yadda muka tawo, har ƙofar gida na kaita munata tattauna matsalolin maza har dai ta sauka hirar ba ƙarewa take yi ba, duk kwanan duniya da sabon maudu'in da zaka ji Allah dai ya iya mana kawai. Sai wajajen taran dare na shiga cikin gida. Mijinyawa da yara suna tsakar gida a zaune a tabarma babu wuta ko'ina duhu sai hasken tocilar waya kawai. Sakkowa nayi jakata a hannuna. Muka haɗa idanu da Mijinyawa da yai ƙuri yana kallona kamar zai cinyeni. Barkanku da gida kuna zaune a duhu? " Nayi maganar da sigar tambaya ga dukkansu. Sabira tayi saurin amsar jakata, Azgar kuma yana wajen get yana rufewa. Mijinyawa bai ce dani uffan ba har na shige yaran na biye dani. Dama dai yasan da yarana nake magana, naga kuma ya ɗan kama kanshi tun bugu da yaci. A falo na yada zango duk jikina ciwo suke yi mini dama. Ya naji kujerar dana zauna kamar a jiƙe?" "Eh Ammi yaron Goggo Zakiya ne yayi fitsari a kai kafet kuma duk sun zubar da ruwa" Sun zo gidanne?" "Sunzo kin fita baki daɗe ba. Maman Zainab ce ta haihu, shine suka tawo barka da suna" Naji zafin yadda suka jiƙamun waje danma yara sun gyara, kuma sun zuba bakin fauda domin ɗauke warin kafet. Uwatale ikon Allah anata cika gidan Nawata da yaƴa to Allah ya raya. Me kuke yi a waje da baku kunna inji ba ga zafi sosai?" Azgar daya shigo yace. "Abba yace babu kuɗi a wajenshine, man cikin injin kuma ya ƙare bashi ma da lafiya ko yau na kaishi asibiti." Sai na tuno lokacin da nake cika fasta biyu da mai a ajjiye a wajen injin, a kunna injin ɗin duka gidan kowa yaga haske, in ya ƙare kafin mijinyawa ya kai ga siyowa zan cire kuɗina in siya aci gaba da amfani dashi. Girgiza kai kawai nayi nace. To Allah ya kyauta ba kuna da fanka ƙananu masu caji ba? Sai ku je ku kwanta gobe akwai makaranta, nima kwanciyar zanyi sai da safenku" A bakin falo muka ci karo da mijinyawa ya sakar mun murmushi hannunshi na cikin ajjuhunshi, idanunshi dai ciwo suke yi ƙaƙas. girgiza kaina nayi kawai. wucewata cikin ɗakina nayi, abuna mutuminku dai ya kama kanshi, saura sallamata. Wanka nayo kafin in zauna jikina ya mutu, fanka na kunna ina shafan mai ina nazari akan labarin Sumayya da Auwalu, da abinda ni na hango wanda nake tunanin ita Sumayya bata hangoshi ba duk yadda akayi. Rigar baccina na saka na shafe jikina da Humrar mrs Bukhari mai musulmar sassanyan, tattausar ƙamshi, madadin in hau gado in huta sai naji ina sha'awar duba zaurukana domin ganin meke faruwa. Da Facebook na soma ban jima a ciki ba na koma WhatsApp zauren gidanmu anyi magana fin dubu biyu, to me kuma ya sake faruwa ko duk batun motarne, gashi naga an taɓa rubutuna anyi magana domin in gani ko in san dani akeyi taggin. Ga kuma wani saƙwanni biyu da suka ɗauki hankalina mai ɗauke da sabuwar Lamba. Na farkon na shiga sai naga bidiyone guda biyu a jere iyakar abinda aka turo kenan. Dannawa nayi suka buɗe na shiga na farkon. Mijinyawane a kwance a ɗakin hotel shi da Asama'u dake jikinshi a kwance ita ke yin bidiyon. "Sikari mai zaƙi faɗamun yadda kake ji game dani" Sumbatar bakinta yayi yana dariya ga jin daɗi ƙarara a fuskarshi. "Amfanin me zai miki duk irin yadda nake faɗa miki matsayinki sai kin kafe waya kina bidiyo zaki tambayeni Sweet L?" Dariya suka saka ya saka hannu ya karɓi wayar sai bidiyon ya katse. Shiru nayi ina nazari mai zurfin gaske da irin yadda duniya taima su mijinyawa daɗi hankalinshi kwance yana lalata yarinyar mutane da girmanshi zangon baƙi_ zangon baƙi yake ɗaukarta, ya kaita su sheƙe ayarsu ni ina gida gaho yarinya na mun kallon tsirara. Shi nasan yana ofis, ita kuma nasan tana makaranta. Kuma bata taɓa yowa dare a waje ba, shima bai taɓa saɓa lokacin dawowa ba sam. Mijinyawa ya zubar da duk kima da darajarshi a idanuna, babu sauran ganin girma, rabuwar mu itace mafi alkhairi. Ajjiyar zuchiya na sauke ina jin wani irin nauyi a zuchiyata. Ɗayan bidiyon dana buɗe a kwance yake yana bacci daga shi sai shimi da gajeren wando ita kuma babu fuskarta sai hannunta da take shafan ƙirjinshi. Idanuna na lumshe ina ganin wani irin duhu_duhu. In faɗamun akayi daidai da sakan mijinyawa zai iya kallon wata mace da sigar sha'awa bazan yadda ba. In faɗamun akayi akwai ranar da Asama'u zata iya shafa jikin mijinyawa bazan yadda ba. In akace mun akwai ranar da Asama'u zata bar hannuna, to ɗakin Azgar na zaci za'a kaita. A yadda mijinyawa yake nuna mun soyayya, kulawa, nunawa yake yi tamkar nice duniyarshi, bazai iya gudanar da tartibiyar rayuwa ba in bana gefenshi. Ashe baibai kawai yake ninkeni Allah ne kaɗai yasan adadin matan da Mijinyawa ya tuɓe suka ganshi suka jishi kuma. Wa yasan su nawa yake mu'amula dasu sai shi sai Allahnshi. Ni inata hauka akan na samu nagartaccen miji kuma uban ƴaƴa, kaico ashe da kanshi zai dagula farin ciki da jin daɗinmu, ashe akwai ranar da zata zo mu zama a yadda muke a yau, ashe akwai ranar da zanji na tsani mijinyawa na tsani ganinshi na tsani kowa nashi? Murmushi nayi wanda yafi kuka ciwo, yafi ciwo ciwo wallahi. Lambar mijinyawa na duba a whatApp na buɗeshi daga kullewar da nayi mishi na ɗauki waɗannan bidiyoyi da hotunan da aka turomun ina Landan na tura mishi tare da rubutu ƙarami kamar haka. Ga Zunubinka nan." Suna gama shiga na rufeshi na jefar da wayar na hau gado ina jujjuyawa abubuwa masu girma da nauyi a zuchiyata. Ban gusheba inata ambaton Allah har nutsuwa ta sakkomun tare da baccin da na fidda raina da samunshi, sai gashi ƙarfin ambaton Allah yasa nayi baccina na wayi gari lafiya sai ɓacin rai da damuwar da tunda abinda zai faru ya faru dashi nake kwana nake tashi. Saye na fito cikin doguwar rigar materiyal mai santsi kaina yane da mayafin daya dace da takalmina da jakata, sai agogon baƙin fata dana saka a tsintsiyar hannuna na hagu. Ko da na fito yaran kaɗai na tadda a falo wai mijinyawa ya fita sassafe zuwa wajen aiki. Kai kawai na girgiza na zauna na karya muka fito, na sauke yara a makaranta na wuce wajen aikina. Muna yin birek sai ga wayar Innarmu ta shigo. Ɗagawa nayi da sallama sai naji muryarta babu daɗi. "Wai Hindu me kika cema Salamatune da aketa cece kuce tun jiya a gidannan harda dambe?" Da mamaki a muryata nace. Gaskiya babu Innarmu ai kinsan kanwarmu bata jiƙuwa kofi ɗaya shi yasa ko waya bama yi fa" "Wai a zaurenku na yaran gidane kika faɗa mata baƙar magana, shine fa aketa abu ɗaya har yau da safennan da zancan aka tashi, Mairamu sai sake tura abun take. Wai yau zama ma za'ayi duk akan batun" Ikon Allah to ni bansan wata baƙar magana dana yi ba Innarmu, nifa sanya alkhairi kawai nayi mata banma sake bi kan wayar ba." "To kinsan Abidah da son girmama magana, sai yi take yi tun jiya take habaice_habaicen baƙin ciki kike ma Salamatu. Ai shikenan Allah ya kyauta ya aikin naku? " Ajjiyar zuchiya na sauke kafin nace. Alhamdulillahi yanzu muka fito birek zamu ci abinci kenan da Luba wayarki ta shigo" Warce wayar luba tayi bakinta cike da doya da miyar ƙwai a haka suka gaisa da Innarmu, sukai sallama ta kashe wayar tare da miƙo mun. Luba kinji wai ni na faɗama Salamatu baƙar magana jiya ba a gabanki na tagin hotonsu nayi musu Allah ya sanya alkhairi ba? To sabida bita da kulli wai na faɗa mata baƙar magana tun jiya Innah Abida take ta habaice habaice, ace kishi tun da jajayen sahu akeyi har ƙadamin tsufa ke Luba kishi masifa ne azabane wallahi " Dariya Luba tayi tace. "Duwaf kishi wani irin halittane mai raɗaɗin da kwatancenshi baya yiyuwa, karatun kishi wani karatune mai faɗin da baya ƙarewa. Dubu gidan Arrasul S A W suma an buga kishi, Kishi bashi da kyau. Kuma duk irin ƙoƙarin da namiji zaiyi akan yaga ya faranta miki ya maidaki sarauniya dole sai anyi miki wani abun da dole sai zuchiyarki ta sosu" Hakane Luba nima na ɗanɗani ɗacin kishi. Ɗanɗano mafi muni da ɗaci. Zuchiyata ta samu matsalar da abadan ba zata iya dawowa daidai ba In duniya da abinda ke cikinta mijinyawa zai bani, in biyayya da so zai nuna mun sama da so da biyayyar da su Azgar suke yi mun, bana jin daidai da sakan zan iya ganin mutumci da darajarshi a idanuna. Ashe hausawa sunyi gaskiya da suke cewa mutumci madarane muddin ya zube baya iya kwasuwa duka. To haka mijnyawa yake a wajena" "Matsalarki Duwaf baki iya so ba baki iya ƙiyayya ba. Ni kuma sai naji zafin mijinyawa. Sai inji na bashi uziri sabida yadda ya haƙura da Asama'u sabida ke, ya kuma ƙasƙantar da kanshi ya toshe kunnenshi ya biyoki gidanki, kuma yaci gaba da ƙoƙarin yaga kun dawo yadda kuke da. Ni na samu haka Duwaf? Nifa Sanusi baima san abinda yayi mun laifi bane bare har yayi tunanin yin karatun ta nutsu. Sabon iskancin daya buɗe na faɗa miki wallahi dashi ake zaman bakwai duk matannan da suke zuwa da maƙota, masu shigowa Sanusi yana tsakiyar mata da yara a ƙwaƙwube a hannunshi, yadda kika san sune yaranshi na fari fa" Hmmm kawai na iya ce mata a wannan karon. Zuchiya kowa da irin wadda Allah ya dasa mishi sunanta dai kawai iri guda. Ni kuma ina ganin girman laifin Sanusi bai kai kwatan na mijinyawa ba, amman dake Luba bata san irin wainar da Mijinyawa da Asama'u sukaita toyawa kafin su yi auren bane shi yasa take mai uziri. Kuma take ganin wai ya sauke kanshine ya biyoni, kuma wai sabida ni ya rabu da Asama'u. Wallahi bai rabu da'ita sabida ni Hindu ba, ai bani na haɗasu ba. Auren ba laifi bane duk abinda sharia ta kawoshi ta yadda dashi baya zama laifi. Amman ashe bani da daraja da kimar da mijinyawa zai iya kawar da kanshi akan Asama'u, ya auro yarinya daidai dashi wacce zata zo mu rayu cikin farin ciki ta haifa musu yaran da suke so? Hmmmm taya wai zamu sasanta da mijinyawa ne. Masu cewa in yafe mishi, to na yafe mishi na sake na yafe mishi, na sake na yafe mishi, amman zaman aurene babu mahalukin daya isa yasa in zauna dashi. A haka muka gama aikinmu muka taso ƙarfe ukun yamma. Kai tsaye gidan makokin Jamila muka je ni da Luba ta hanyar kwatancen da mahaifiyarta tayi mana. Ƴan tambayoyi nayi mata ta bani amsa sabida akwai binciken da nake son yi in Allah ya dafa mun sai mijin Jamila yazo hannu da izinin Allah. Zan ta bibiya, ga lambar waya ma na samu, duk da bata shiga, babu mamaki ma ya cillar da layin wayar. Daga nan muka wuce asibiti wajen Maman khadija itama jikin nata da sauƙi, sati mai zuwa zamu soma zaman kotu da izinin Allah. Ƙarfe shida daidai muka shiga gida ni da Luba, Mijinyawa baya nan motarshi bata ƙofar gidan ma hakan yasa muka barbaje a falo tare da Sabira, Azgar dai bayanan ya shiga gari dubiyar abokinshi da suka yi hatsari. Saida Luba tayi magriba taci tuwo kana ta tafi gida. Ina zaune ina cin tuwo ina duba saƙwannin mata tare da nazarin matsalolinsu idanuna na lumshe kaina na wani irin turirin zafi, haƙiƙa mata a wannan zamanin muna cikin damuwa da matsaloli da dama. Sannan da daman matan da suke shiga irin matsala mai girma ko samun matsalolin cin zarafi da tozarci. Basa sana'a, basa aiki, basu iya juya taro ya koma sisiba, da mazajen suka dogara kawai. Ga ba safot na iyaye da dangi. Mata a wannan zamanin fa ya zame mana dole mu yi aiki, ko sana'a a cikin gida, domin kare mutumci da darajar kanmu. A halin da ake ciki ko iyaye sunfi ji da yaransu masu ƙumbar susa, ƙiri _ƙiri a ɗakinku zaki zama saniyar ware in bakya sana'a ko aiki, wani abunma sai ya faru amman ke ba'a fada miki ba sabida babu abinda zaki iyayi. Zauren gidane yake ta ɗaukar hankalina irin yadda aketa saƙwanni sai zuwa lokacin na tuno da wayar da muka yi da Innarmu. Ai babu shiri na shiga zauren na gane ma idanuna me nace daya tayar da tarzoma haka. Wai ashe da nace ga ango nan a gaban amarya abunshi. Shine abun baƙin ciki. Khadijan Innah Mairamu itace ta soma kwamen akai akan. "Me kike nufi da wannan kalmar Duwaf ya hausar ga ango a gaban Amarya abunshi?" Ai tana faɗa sai aka soma taɓa maganata, ana mayar mun da raddi akan me yasa zance haka. Yaya Saratu ce tace. "Ni banga wani abu a kalmar da Hindu tace ba. Shin ba a gabanta yake ba daman? " Khadijan Innah mairamu sai cewa tayi. "Kamar baƙin ciki take yi da hakan, dama ku kun saba ƴan ɗakinku sunfi so ace komai sune akan gaba." Sai Salamatu tayi saƙo mai murya na kusan minti ashirin. "Dole kice haka Saratu tunda dama ku ƴan ɗakinku bakwa laifi. Sai ku faɗama mutum baƙar magana ku nuna akan daidai kuke. Tun ranar da aka kawo akwatunana kuke nuna baƙin ciki da hakan, sabida a tarihin gidanmu babu wata mace data taɓa samun irin kayan dana samu. Hindu tasan nafi ƙarfinta da ɗan ƙauyan mijinta wawa. Sannan da take cewa ga ango a gaban amarya abunshi ita da take gajera kamar a kifeta da kwando ita ba ƴar tsurut take a gaban mijinta ba, abunma babu tsari. Me ta fini dashi, gajerar mace, sannan me Mijinta yafi nawa dashi faɗin ƙirji da jikin samudawa ko? . Ku dama taƙamarku Innarku itace mace wacce tayi boko a iyayenmu, sai kuka ɗauki wani irin girman kai kuka ɗaura ma kanku. Shi kuma Baba Sojanmu yana jin tsoronta, yafi ji da'ita ƴar boko hakan ya baku dama kuke ta tsula tsiyarku" Ta dai inda dai ta shiga ba tanan take fita ba. Tai ta zazzagar ƴan ɗakinmu. Ai kuwa ta sha baƙaƙen maganganu a wajen Yaya Zubaina, zafafan saƙon murya saida ta jero uku masu zafi duk saida na saurara. Ta ciccire mata aiki, ta zagesu tatatas. Ɗakina na koma,naci gaba da sauraren abubuwa. Ƴan ɗakin Innah Mairamu suke ƙara tura abun, su da ƴan lungun Baba Lukumanu. Ƴan lungun Baba Alƙali kuma suna karemu. An yi abubuwa sosai har takai da zage_zagen juna a tsakanin Yaya Saratu da Salamatu tunda ita Salamatu kai tsaye da Innarmu take yi, duk haushinta a kanta yake tana mugun taya Innah Abida kishi da Innarmu. Innarmu kuma taci dubu sai ceto zaren wallahi ba kalan yadin bane. Ni da abun ma ya gundureni, saina fita a zauren na koma Facebook na yi rubuce_rubuce akan mata su tashi tsaye wajen sana'a ko aiki, inda hali a haɗa duka biyun. Na buga musu misalai masu yawa akan matan da suke tsaye da ƙafafunsu ba'a iya kafaɗar miji suka jingina ba, suma kafaɗune ababen jinginar wasu. Na kuma buga musu misali da macen da bata aiki, bata sana'a, da ƙafafun miji take tsaye komai sai ta jira anyi mata bata da ikon siyan komai ko canja komai sai abinda ta gani. Gashi yanzu a zamaninnan ba dukkan mazan ke sauke ratayayyen hakkin kulawa da mata da yara ba. Sai dai ɗabbaka sunnar ƙarin aure kaɗai da yawa suka iya. Iyaye basa son a dawo musu da ƙorafi, to me ya kamata mata suyi? A nemi ilimi arabi, da boko, ayi aiki, ayi sana'a. Na nuna musu muhimmancin sana'ar mace da darajar da take yi a cikin dangin miji, nata dangin, dama shi kanshi mijin. Na kuma buga musu misali da Nana Khadija da irin gudummawar da ta baima addinin musulinci da dukiyarta da lokacinta. Addinin musulunci bai barmu sasakai ba. Babu a inda akace kar mace tayi aiki ko sana'a matsawar zata kare kima da mutumcin kanta. Bari mu ja nunfashi anan sai kuma gobe in Allah ya kai. Mrs Bukhari 08179523215 Ga masu son magana dani kai tsaye ga lambata Banda kira dan AllahTSURON TSIRIN... TSANDAURI.... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA TARA (9) 08179523215 Ga masu son magana dani kai tsaye ga lambata Banda kira dan Allah Mace tayi sana'a ko aiki. Al muhim shine a duk inda take ta tsare darajar kanta a matsayinta na musulma, mace, matar aure, uwa, ƙanwa, ya, kaka. Shine kawai madamar mace zata tsare mutumcinta shikenan, tasan iyakokinta, ta tsare mutumcinta na musulma, ta kame daga hulɗa da mazan wajen aiki, ko mazan kasuwa, ta kama girma da darajarta ta ɗiya mace. Har kullum ina buga misalina da Layla, in kuma mace ƴar gwagwarmayar iya tallata kayane a barma FMK kayanta. Wai mata kunsan daɗin kuɗin kai kuwa? Da kin sani da kin kama sana'a kinyi adda'ar Allah ya dafa miki, da kin sani da kin yi aiki kin roƙi ilahi ya riƙa miki. Je ki bibiyi tarihin FMK, Layla Ali Othman zaki ɗauki darasi, ita Layla misalin bugawane ga zawaran da suke ganin ƙarshen rayuwane yazo musu shi yasa. Ku bibiyi tarihin Layla zawarawa sai ku sauke numfashi, a yanzu tana da Aurenta fa ato ( ranki shi daɗe ina miƙo gaisuwata💪🏼) Nayi rubutu mai jan hankali sosai kafin na sauka na ajjiye wayar tawa, nayo wanka na kwanta. Haka dai abubuwan suka ci gaba da tafiya rubutun da nayi jiya sai ya samu wani irin farin jinin da babu inda bai shiga ba, sai yaɗashi mata suke yi domin mata ƴan uwanmu su amfana da abinda na rubuta. Na fito da shirin fita aiki na tadda yaran na jirana duk sun shirya, sai lokacin na tambayi Mijinyawa, sabida banji motsinshi ba, ina fatan inji sunce ya tattara kayanshi, ya ɗauke gadonshi ya tafi. A lokacin Azgar ke faɗamun ya tafi Jama'are jikin Nanno ya tsananta sosai, shine aka kirashi suka wuce tare da su Yaya Zakiya, da suka kwaso jiki zuwa sunan Uwatale. Allah ya bata lafiya nace kawai na kwashesu na saukesu a makaranta nace dasu su wuce can gidanmu in an tashesu nima can zan wuto inna taso aiki. Hakan kuwa akayi daga wajen aiki kai tsaye na wuce gidanmu Luba kuma na barta zata shiga kasuwa zata siyo takalmi da jaka na sunan kishiyarta. Ina ƙoƙarin fitowa a mota wayata ta shiga ruri da baƙuwar lamba. Kamar ma bazan ɗauka ba dan lokacin anata kiraye_kirayen sallar la'asar maza sai wucewa zuwa masallaci suke. Sai da wayar ta kusan tsinkewa kafin na ɗaga. "Alhamdulillahi Malama Hindu Lantana ce ina ɗaya daga cikin memba ta zaurenki dan Allah in babu damuwa so nake ki sakamun lokaci in zo ko ofis ne in sameki, inaso zamu yi magana dake. Kishiyace za'ayimun kuma bazawara mai buɗewar idanu shine nake son a saka ni a hanyar mutumta kai" Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace. Haba Lantana in dan wannan ne ai bama sai kinzo ba. Akwai rubuce rubuce da nayi a zauren da shafukana musamman na uwayen gidane, ai waɗannan kaɗai ya ishi duk wata macen da take son sanin hanyayin kare mutumcinta ko? " "Eh hakane duk na karantasu kuma na haddace, tare da ɗaura ɗambar yi, ina dai son ganin naki ne tafe da wata matsalar duk akan aurenne dai, dan Allah Malama ganin naki zai mun amfani, kuma zai sanyayani" To naji gobe ƙarfe uku ki kirani lokacin na taso aiki sai kizo gida ki sameni zan tura miki adireshin gidana" Godiya ta shiga jero mun gami da yima iyayena adda'a. Naji daɗin adda'arta ga su Innarmu sosai. Ina kashewa wayar mahaifin Jamila mai rasuwa ya kirani. "Ƴannan da fatan ban katse miki aikinki ba ko?" AA Baba ba damuwa, ya ƙarin haƙurinmu, da fatan kuma an dace samun hoton nashi Baba?" Baba yace. "To a gaskiya bamu samu ba wallahi. Ƴata inaso ki taimaka mana dan Allah. Mutuminnan mugune sosai. Bai yadda ya bar mana wani alama ba sam." Idanuna na lumshe nace. To Baba kwatanta mun yanayinshi, duk da nasan ba abu bane da zai yiwu ba. Amman ya yanayinshi yake?" "Yananan mai ɗan ruwane siriri haka, tsayin nashi ma ba can sosai bane." Idanuna na buɗe da sauri, wani abune yazo kaina. Am Baba yana da zane a fuskarshi haka, farine ko baƙine to?" Baba yace. "Yana da haske ƴata. Kuma kamar dai yana da kalangu a gefe da gefen kuncinshi, dake ba ƙura mishi idanu nake yi ba. Kinsan masu kuɗi da kwarjini" Kai na girgiza baƙin ciki na neman halakani da jin abinda yace. To shikenan Baba zanci gaba da bunciken, duk yadda ake ciki zan sake tuntuɓarka" Da haka na sauke wayar. Nayi shiru ina dogon nazari, na buɗe wayata na duba abu, na kulle idanuna nayi nazari kamar na ƴan mintina, kafin na buɗe idanun nawa. Sakkowa nayi, na rufe motata na shiga gida da sallama. Duk matan gidan kamar suna can cikin gida a nan nake jin hayaniyarsu ko me akayi kuma sai Allah, ni da nasan ma haka zan zo in tarar da gidan da gidana na wuce ya fiye mun. Ko in bi Lubana kasuwa. Ina shiga lungunmu na gane a lungun Baba dogara ake wani abun, gasu Innah Mairamu can muryarta tafi ta kowa tashi. Gidan yawa babban masifa kai Allah ya rabamu da gidan gandu, babu daɗin zama, babu sirri, ƙyas ake jirace da kowa. Falonmu na shiga na tadda wata shariar aketa fafatawa an cika an cika. "Yauwa ga Hinduwan ta ƙaraso. Ke Hindu zo ki zauna ayi wannan maganar ta ƙare kawai, nagaji da yadda aketa mayar da wannan maganar babba, da wani sharrin dai ake neman mu, duk yadda akayi." Cewar Innarmu da suke zaune a gaban Baba Sojanmu, ga Salamatu, ga Yaya Saratu, ga Habiban su Salamatu, ga Yaya Zakiya, ga Khadijan Innah Mairamu, ga Sailuban Baba alƙali. Su Innah Abida duk suna zaune. Waje na samu na zauna ni da Salamatu muna fuskantar juna. Harara ta sakar mun harda tsaki marar sauti, ni kuma nayi murmushi tare da girgiza kaina irin na cusa haushi. Ashe Baba Sojanmu akan gidanshi akayi komai yana kallonmu yana nazartarmu. Can yace. "Ke Salamatu me Hindu ta rubuta miki da aketa abu ɗaya yau kwana biyu magana taƙi ƙarewa, ga gida ya soma ɗinkewa da baƙin nesa. Wannan wacce maganace da girmanta yakai a kwana biyu ana yinta, duk lungunan gidannan ya ɗauka zance guda ɗayane Hinduwa tayi kaza, Hinduwa bata kyauta ba. Me Hinduwannan tace ne, inda babu ƙasa anan ake gaddamar kokawa" Innah Abida na kalla na dubi Salamatu dake ƙoƙarin soma magana. Ni dariya ta bani wallahi, sai kace wata ƙaramar yarinya. Ko da yake Innah Abida ma haka take yi. "Baba Sojanmu daga na turo hotunana da mijin da zan Aura shine Hindu take cewa gashi ɗan tsurut a gabana. Kuma dama tunda aka kawo akwatina suke ta nuna abubuwa, ga Innah ai tana ganin komai. Hatta Innah Ruwayya ma sai habaice_habaice take saki a falonnan. Daga magana a zaure, su Saratu suka goyi bayan ita Hindun. Rikicin da yaƙi ƙarewa dama a zaure ne ake ta sake tayar da zancan" Ta ƙarashe tana huci harda runtse idanu, dama muguwar mafaɗaciyace hancinta mai zufarnanne na mafaɗata. "Shikenan iyakar bayanin ko akwai wani?ki gama kab inajinki, wannan lamari ace harda dambe tsakaninki da Zubaina, gotai_gotai dake. Ke kuma Zubaina zaki ci gidankune. "Ta nawa ɓangaren akwai wani. Tun jiya da ƙannena su Ladidi suka ƙaraso Ruwayya take harararsu, tana musu wani gani ganin da dama can ta saba muddin ƴan kwantagora zasu zo, saita nuna ƙyamarsu a fili. Abinda yayi ni, shi yayi ka. Su Ladidi ƙanenka ne kuma ƙannenane ta ko wanne ɓangare, danme su da gidan wansu ba zasu zo a wanye da matarka lafiya ba? " Kafin yace wani abun sai ga Goggo Shirwa ta ƙaraso yayar Baba Sojanmu ce daga ita sai Baba Alƙali. "Haka su Ladidi da Talatuwa suka ce, tunda suka shigo falonnan Ruwayya take kallonsu ɗaiɗaya, ni da sabida ita da yaranta da basa ganin mutane da gashi wallahi banso zuwa bikin ba. Sabida ita ko kwantagora tazo biki saita raina mana arziki, bare mun biyota har fadarta. To fadarta mana A gaskiya Soja Ruwayya matarka bata fiye son a zauna lafiya ba. Kuma a kan turbar data ɗaura yaranta kenan. Ba dai kaga su Saratu sun shigo cikinmu sun zauna a sake ana hira ba. Sai dai su shigo a gaisa kawai sunfi gane su haye gadon uwarsu suita shewa, kasan wannan jini na Maiduguri na yawo a jikinsu matan Maiduguri raini garesu sosai, ga girman kan tsiya." Goggo Shirwa haka dama take duk sanda tazo wani sha'ani na gidannan in sha Allahu sai sun tunzura Innarmu. Bance laifin nasu bane susu kaɗai ba. Innarmu ba mace bace mai haƙuri ba, kana ba mace bace wacce in akayi mata ba zata rama ba. Sa'a kaɗai mutum zai taka har ya yar da magana ta ƙyaleshi. Amman bata hargowa da ihu cikin sanyin murya da murmushi zata rama baƙar maganarta, wanda ke kusa ba lallai ma yaji muryarta ba. Amman nasan kab dangin Baba Sojanmu basa ƙaunarmu ta dalilin ƙin Innarmu da suke yi. Shi kuma yaro bazai taɓa shiga inda kullum kyararshi da aibata mahaifiyarshi akeyiba. Wannan shine musabbanin da ko sunzo sun sauka a ɗakin Innah Abida iyakarmu dasu gaisuwa. Innarmu ma da taga mun jima bamu fito ba zata kwaɗama yaro kira ya dawo ɗaki, ba wanda take jin tsoro. Kuma ita kanta Innah Abida sau nawa ta sha korarmu in mun shiga ɗakinta, lokacin muna yara. Wannan tun muna yara kenan fa ake abu ɗaya duk akan rijalu. Baba Sojanmu yace. "Amman Yaya Shirwa ni banji wata magana mai zafi da Hindu ta faɗa da har zai kawo rikicin da za'a kwana biyu anayi ba. Shin mijin ba ɗan tsurut ɗin bane? Nima fa da kaina nace da Abida shi kuma mijin Salamatu haka yake ƙanƙani, gata ai. Ke Ruwayya me kike dashi na cewa akan wannan maganar? " Goggo shirwa saita juya ta wuce ɗakin Innah Abida tana zage zagenta. "Hmmmm ƙauyanci yaƙi sakin Shirwa, gata dai gotai_gotai ji yadda take tafiya bagazan_bazagan. Innarmu tace. "Ban dai sani ba ko su yaran suna da abun faɗe tunda rikicin nasu ne bana iyayeba. Amman banga wani abun faɗe da zance ba" Baba Sojanmu yace. "Ke Hinduwa me kika rubutoma ƴar uwarki? " Wayata na ciro na dubo rubutun da nayi na karantoma kowa, na kuma nuna ma Baba Sojanmu ya gani, ya karanta. Na kuma danna muryar Salamatu a lokacin da take mayar da martanin da yasa har Innarmu saida ta sako a ciki, dashi kanshi ba tace yana tsoron Innarmu ba, da muryar Nanan Lungun Baba Nagoɗi da take ƙara zuga Salamatu tare da kambaba abun. Na kunna mishi muryar Yaya Saratu na martaninta ga Salamatu, da muryar Yaya Zubaina itama na martaninta, da muryar Khadijan Innah Mairamu duka dai. Na ɗaura da cewa. Iyakar abinda nasan na rubuta kenan. Dake akwai wani ƙulli a zukatansu shi yasa ta fassara kalmar da wani abun daban. Da kuma kike maganar baƙin ciki akeyi miki tunda aka kawo akwati, to ai Salamatu munsan ba ke kika yi akwatin da kuɗinki ba, kawo miki akayi banga abun baƙin ciki ba kowacce tana da nata rufin asirin daidaiya. Koni zan iya ma Azgar wannan akwatin ai. "Ungo naki ƴar nema. A gabana ma faɗan zaku ci gaba ke Hinduwa? " Cewar Baba Sojanmu kenan. Sai nayi shiru tare da cewa. Aimun afuwa Baba Sojanmu. Itama Salamatu tayi haƙuri bana nufinsu da komai wallahi" Su ba haka suka so ince ba, shi yasa nace hakan. So su kai mu tada rikicin da zasu tabbatar ma mutane baƙin cikin mukeyi da Auren, shi yasa na bada haƙuri dan in kashe maganar gabaki ɗayanta. "Ni ki dubi tsabar idona da girmana kice wai ina tsoron Ruwayya, sabida Abidah na saki a keken ɓera. Sannan Ruwayya da kike magana a kanta, sa'arkice, ba uwarki bace?" Nan turancin sojoji ya tashi, ya kaima Salamatu mari, yasa ƙafarshi ya take mata yatsu ya kuma murza. Ya saba yi mana haka tun muna yara, lallai ranshi ya ɓaci gaya. Yai ta manya_manyan turanci yana nuna Salamatu da Innah Abida. Sai haƙuri suke bashi, da ƙyar yayi shiru da Innarmu ta tausheshi. "To maganarnan bana so a sake tadata a cikin gidannan. Ke Salamatu duk sanda wani abu ya sake faruwa kika sako Ruwayya a cikin maganarki, balle ni, zaki sha mamakin hukuncin da zanyi miki ni yaro baya girma da duka a hannuna, sai in zaneki ciki da bai, ko in sa sojojin gidannan su baki kashi wallahi. Kuma kiyi gaggawar basu haƙuri sabida uwarsu da kika taɓa. Maganar kuma na kasheta wanda ya kuma tadata ni da shine mutuniyar banza, mutuniyar hofi. Ke Khadijan Mairamu ashe kema baki da mutunci, daku su Nana ko? In na kuma jin bakinku akan abinda babu ruwanku, sai na sa Qazzafi ya ɗaure mun ku a bishiya kun wuni" Tunowa da irin hukuncin gidan soja da Baba Sojanmu yake ma su Akarami nayi, lokacin yana ganiyarshi. Bafa haka Inna Abida taso ba. Ni suke son aima kaca_ kaca sai ya ƙare musu a kansu, Salamatu sai kuka ƙaƙas. Taso tayi magana Baba Sojanmu ya ɗaga mata hannu dolenta tayi shiru. Salamatu kuwa dole ta bamu haƙuri ta kuma ba Innarmu haƙuri. "Babu komai Salamatu. A dai shekarunki yana da kyau ace kina da ladabin magana. Gashi zaki shiga babban famili dole sai kin dinga tauna magana kafin ki fesar dan ke Magana kike yi kamar kashi, baki da tarbiyyar magana sam. Babu mamaki abinda ya rabaki da mijinki ma kenan" Da haka dai taron ya watse duk muka yi ɗakinmu muka ci gaba da tattaunawa musamman akan maganganun Goggo Shirwa da kuwa yaji zafinsu. "Ga ɗinkunan biki nan na karɓo mana sunyi kyau zamu ci waje gaskiya." Cewar Yaya Saratu da take buɗe ledar kayan. Innarmu tace. "Gashi naji ana batun akwai dina ranar da muka isa katsinan. Su kamar biki sosai suka shirya a katsinan fa" Nace da Innarmu. Ni ba wannan ba me akeyi a ɓarayin Baba Dogara naga duk matan gidan suna can? " Innarmu ta taɓe baki tana ɗaga ɗinkinmu tace. "Aure auren daya saba yayi wannan karon a ƙauye yaje ya kwaso matar. Jere dangin amaryar suka zo yi. Wai bazawara mai yara takwas kuma wannan karon ya auro. Kai wannan Baba naku bashi da dama." Mamakine ya lulluɓemu dukkanmu. Bamu muka bar gida ba sai daf magriba na tarkata yaran muka leƙa ɗakin Innah Abida nayi sallama dasu Goggo Shirwa sun amsa basu amsa ba Allah masani ni dai banji amsar tasu ba. A ƙofar gida muka tadda motar Mijinyawa, data mijinyawa Babba. Azgar ya fita ya buɗe mun get muka shiga. Ashe harda Nanno ma da Yaya Jamila akazo, da Musa yaron Shafa. Falon na shiga da sallamata mijinyawa Babbane kaɗai ya amsa sallamata mijinyawa kuwa sai sake sunne kanshi ƙasa yayi na zame mishi kamar suruka. Nanno ya jikin naki?" "Jiki da sauƙi bamu daɗe da shigowa ba munje asibiti shine nace a kawoni nan in kwana ɗaya in fa kin amince kenan dan ke kike juya gidan. Ki mun wannan alfarmar sabida gidanki yafi kusa da Asibitin, inci albarkacin su Azgar, kwana ɗaya zamu yi. Wannan yarinyarce ma ta kawo tunanin hakan, ni da a ɗakin Uwatale zan zauna. Ina jin haya_hayar jikoki" Ɗan murmushi kawai nayi, dan jiki kam tana jin jiki, sai nishi take yi. Dan dai su kwana su wuce, zan barta a wannan karon, sabida ciwo, sannan ita uwa koma yaya take uwace. Duk yadda misali zan takurama matar Azgar misalifa. Bazan so ace naje gidan Azgar matarshi ta koroni ba. Duk da nasan su Nanno basa ƙaubata a mataki na ƙololuwar ƙarshe. Yau in muka rabu da ɗansu ai shikenan. Na gaishe da su Mijinyawa Babba a jam'u shi kaɗan ya amsa Yaya Jamila kuwa bata ko kalli ma inda nake ba bare ta amsa dan ko gaisuwar su Azgar bata amsa ba. To bari in shiga daga ciki in yi sallah. Azgar ka shiga da jakunkunan su Nanno ciki" Na miƙe na fita Azgar ya biyoni da jakar su Nanno ya saka a ɗakin Sabira. Saida nayi wanka nayi sallah a tsanake kana na fito. Saina tadda Yaya Jamila a Kicin tana yinƙurin kunna gas ni kuma shigowata kenan. Zaki ɗaura girki kenan jamila? To bari in shiga daga ciki" Harna juya ta kira sunana a gadarance. "Ke malama in zaki zo ki ɗaura girki kizo ki ɗaura dama ruwan shayi zan dafa ma Nanno. Meya aikeni yin girki a gidan ƙani" Taja dogon tsaki tare da kwaɗama Sabira kira ta tawo a guje. Ita ta kunna mata gas ɗin ta dafa ruwan zafin, kafin ruwan nata ya tafasa na jona ruwa a buta ina jingine da firji ina jiran ruwan ya tafasa. Nima shayin zan sha. "Ciromun kayan shayi in haɗama Nanno Sabira yinwa saita kashe mutum a wannan gidan naku na ma'aikata." Cicciro mata gwangwanin madara dana milo tayi, ni kuma na juye ruwan dana tafasa a kofi. Ina tsaye ina kallon ikon Allah manyan cokula huɗu harda tsoro Yaya Jamila ta juye a shayin, haka taima milo ma ta wuce tana hararata Sai bayan isha na kammala girkin indomi na zuba ma su Sabira, na haɗa komai nawa a tire, na wuce falon, na nemi waje na zauna. Nanno tana zaune tana kallon wani shirin hausa da ake gudanarwa a tashar hausa bakwai, tana shan ti a hankali a hankali. Ni ko ina cin indomina ina danna wayata.. Har zan miƙe in fita su Mijinyawa suka dawo masallaci. ina kallon mijinyawa irin kallon da Yasan dalilin da yasa na mishi, sauke kanshi yayi a hankali. "Hindu kinji Haihuwar Uwatale kuwa, baki zo mana barka ba? " Cewar Nawata harda fara'arshi. A gintse nace dashi. Naji labari" Iyakar abinda nace kenan. Yaya Jamila ta ja dogon tsaki tace. "Azgar kai da ɗan uwanka da Sabira ku bamu waje zamu tattauna" Zamana na gyara jin tace haka, da ina bakin kujera, yaran kuma suka fita jikkunansu a mace har cikin ransu basa jin daɗin abinda dangin mahaifinsu suke yi mun. Tun basu san me ake ciki ba, yau da gobe da girma gami da mallakar hankalin kai yasa sun gane irin zaman takun saƙan dake tsakaninmu. Nanno ce tayi gyaran murya irin na girma kafin tace. "Hindu nayi duk yadda zanyi domin Mijinyawa ya sake Aure tunda ke ba haihuwa kika sake yi ba, ga yarinya har ta kai aure, amman yaƙi fur sabida tsoronki. Ya auri yarinya kun shiga kun fita kin musu farraƙu saida kika tabbatar aikin ki yaci... " "Nanno.... " Mijinyawa ya kirayi sunanta da sigar roƙo" "Kaci gidanku dan abu ta kazanka. Wato so kake in zuba idanu in barka da yara biyu alhalin matsala ba'a jikinka take ba, kana da ƙwayayanka na haihuwa ko? Jibi wanka yaranshi nawa ga Uwatale ta sake haihuwa. Matar Gambo haihuwa ko yau ko gobe, amman kai sai yaushe zan sake ganin jininka saina mutu kake so? " Ni dai kasaƙe nayi ina kallon Nanno ina haɗiye wani abu mai tauri daya tokare mun maƙoshina. Ni da ai tausayi ta bani a matsayinta na uwa, ga ciwo naga bai dace ace na koresu ba, ga dare. Ashe a hakanma tijarar zatai mun. Allah mai iko. Juyowa tayi kaina. "Alfarma nake nema ki umarceshi dan Allah yabi umarnina ya ƙara aure dan Allah na roƙeki wannan alfarmar a karon farko, tunda kece kaɗai ishasshiya a wajenshi tsoronki yake ji, da an yo maganarki zai soma baki kariya. Ni na rasa wannan wanne irin so mijinyawa yake yi miki ke ba yara kika cika mishi da gida ba, bare yace albarkacin yarane. A wannan karon matsawar baki barshi ya ƙara aure ba, kema zaki rasashi dan zai sakeki kinji na faɗa miki ehe. Duk sabida ke ciwona ya tashi. Ki duba halin da nake ciki, ki barshi yayi aure tun ina da raina in ga daɗin yaranshi. Ai ko su Azgar zasu so ganin ƙannensu" Illahirin mamakine ya hanani ko da haɗiyar yawune, sai kawai Nanno nake kallo da irin son zuchiyar da tazo dashi. Yanzu tsakani da Allah ita ta saka kanta a matsayina, surukarta ta mata abinda tayi mun yanzu wanne hali zata shiga, ace ana zaune lafiya fa kawai yara biyune ake ganin sun yi kaɗan. Shin ko auren dole muka yi ace in roƙeshi ni da bakina yayi mun kishiya? Kishiyar da na taso naga irinsu iri da kala a gidanmu, kishiyar da ko yau saida naga sharrinsu, kishiya kishiyar kishiyar. Ai sai dai miji yace zai yi aurenshi da kanshi kai mishi fatan alkhairi. Ina wannan lissafinne ace lafiya muke zaune, babu wani tarnaƙi fa, da fatan kun gane. Kishiya bana tsoronta, bata gabana wallahi, amman azo ma mutum da irin wannan maganar kamar rainin hankaline ai. Ajjiyar zuchiya nayi naji a raina shikenan Nanno ta nemamun hanya mafi sauƙi da mijinyawa zai sakeni salin alin, in tace zata tsine mishi zai sakeni ai ko? . A fili kuma sai nace. Nanno inaga kin mance nice a ƙasanshi ba shi bane a ƙasana ba. Sannan kece a samanmu dukka aljannarshi na tattare da yi muku biyayya. In yaji yana da ra'ayin ƙara aure sabida tara yara, shi namijine zaiyi ko da ba'a sakashi dole ba. In kuma yana jin bashi da ra'ayi shima babu dalilin da za'a sakashi aure dole. Ni a nawa ɓangaren duk abinda yaga yafi mishi shi zaiyi, shi yasan kanshi zai iya riƙe mata biyu da ɗawainiyarsu, ko bazai iyaba. Wannan ba hurimina bane kiyi haƙuri cikin girmamawa. Gashi naga baki da lafiya ma" Yaya Jamila jira dama take yi sai kawai ta dira a kaina da zagi harda zagin iyaye a wannan karon lamarin daya sake dagula kan zancan kenan da yasa su Mijinyawa saka baki. Akul Yaya Jamila da wasa kada ki sake zagin iyayena ko aibatasu wannan ya zama na ƙarshe. Aurene ya kawoni Haularku so ba zai zama ƙiyayya ba" Mijinyawa Babba da mijinyawa nan suka saka baki. "A'a Yaya Jamila bai kamata azo har gida aci zarafinta ba, sannan ke kanki ba zaki so ta rama zagin da kika yi mata ba. Gaskiya banji daɗin wannan kaifafan maganganun naki ba" Mijinyawa Babba ya cabke da cewa. "Abi komai a sannu dan Allah su Azgar ba zasu rasa jin halin da ake ciki ba. Irin wannan ke wargaza kan haula kuga yaran can ɗakin na jin haushin wane da wance." "E lallai babu shakka. Wuyanku yakai yanka. Yau ni mijinyawa ke ma iyaka da iyalinshi ni ɗinnan dana saɓaku a baya, naci kashinku da fitsarinku, kar ka mance da dukkan abubuwan da nayi maka a rayuwa yayin ƙuruciyarka, amman yau har lalacewata takai kaimun iyaka. Ke kuma ki ƙarama bokanki kuɗi aikinshi kamar yankan wuƙa. Amman ki sani in ana tafiya tsirara tsabar fatara tabbas saina rabaki da mijinyawa, rabuwa irinta har abada mu zuba" "Babu mai rabani da matata sai mutuwa Yaya Jamila, ke ya kamata kisan iyakarki bafa ke kika haifeni ba. Baki da aiki sai zuga Nanno kije kiyi mulkin da kika saba a cikin gidanki mana kuma...." Tas Nanno ta matso ta ɗaukeshi da mari da bahagon hanunta, kuma ba bayan hannu. Bata da lafiya fa wallahi. Aini a lokacin jina nake yi a sama, tsigar jikina tashi kawai suke yi. Dafe kuncin yayi kanshi a ƙasa cikin rawar murya yace. "Allah ya huci zuchiyarki" "Ashe haka rashin ɗa'arka ta tumbatsa mijinyawa a gabana kake ma Yayarku wannan ɗiban albarkan, akan matarka wacce ita da juya bambamcinsu ƙalilanne? Babu shakka harni nan gaba zaka zaga. Hindu burinki ya cika. Ke taso muje mu kwana wajen uwatale kinji. Bazan kwana a cikin gidannan ba, bama zata sake ganina ba" Tace da Yaya Jamila da take ta huci tana cika tana babbatsewa. Ni kuwa Allah nake ambato ciwonane yake ƙoƙarin tashi dukkan tsigogin jikina a tashe suke, iska ke ratsani har ɓargona hakan ya haifarmun da rawar jiki hantata gigir_gigir take kaɗawa ina ji. "Ina wallahi muna nan Hindu bata isa ta koremu daga gidannan ba. Ta nan kuma bokanta ba zai ci nasaraba Nanno, munanan har sai kin gama ganin likita mun gama duk abinda muke yi zamu tafi. Ai dama ita ba son zamanmu take yi ba. In so samu ne bata ƙi ace ita da mijinyawa da ƴaƴansu bane a duniyar kaɗai ba." Ajjiyar zuchiya ta sauke. Ni kuma da zuchiya ke cewa in shaƙe Yaya Jamila in ɗagata in nuna ma Allah in saketa tamkar an yi mun wahayi, sai na miƙe jikina babu ta inda baya rawa. Tana cikin wannan hargagin sai taji na riƙeta mata hannu gam. Daga haka bansan komai ba kuma. Mijinyawa:. Ganin idanun Hindu kaɗai yasan ba'ita bace. Da sauri ya matso kusa da'ita. Hannu tasa ta matsar dashi, ta kashe Yaya jamila da mari, ta kuma turata bango ta maƙure mata wuya, tuni ta shiga kakarin amai. Tana ihun ceton rai. Mijinyawa Babba, da mijinyawa wallahi sun kasa ɓamɓare Hindu, har saida su Azgar da Musan Shafa suka zo. Da ƙyar aka ɓamɓare hannunta a wuyan Yaya Jamila. Ai da tayi wani girgiza, sai suka wancakalar da Azgar, da Musa. Su Mijinyawa kuma sai tofi suke yi mata, suna tofa mata. Ita yinƙurinta shine ta sake kamo Yaya Jamila wacce take durƙushe tana kakarin amai, tana sake matsawa. "Kaga irin matar daka ɗakko mana ko? Yanzu inta nufo kaina yaya zanyi? Mijinyawa ka saki matarnan ka huta" Ai sai Hindu ta juyo da mugun ƙarfin da saida ta ƙwace a hannunsu Mijinyawa. Ta nufi Nanno, Allah sarki suma makaran sun san uwa wani sa'in. Cak kawai suka tsaya suna huci a gaban Nanno, suna nunata da yatsa kawai. Itakuma ta duƙunƙune a kujera, hannayenta biyu tasa ta kare kanta saukar duka kawai take jira. Azgarne ya iso a hakan ya rungume Mamanshi ya fashe da kuka, ya riƙeta ƙam yana mata adda'a. "Nanno ku tafi ku bamu waje. Kuna ɗaga ma mahaifiyarmu hankali yana yawa. Nan gidanta ne, kije ki sauka a wancan gidan da muka baro. Ku barmin ita ta huta dan Allah. Ku barta ta huta. Abbah ku barta tana buƙatar hutu" Ya sake fashewa da kuka, Hindu ta sa hannu ta fincikeshi a jikinta, yaje ya rungumi Mijinyawa, daga ɗago yaga shine sai ya maida kanshi saman ƙirjinshi ya kuma raujewa da kuka. "Jimala taso mu tafi. Anyi ta yanke ta guntsile, watara kashemu za'ayi a gidannan" Hindu:. Kaina na dafe, ina jin wani irin mugun jiri. A hankali na fice ko ganin gabana banayi. Duk abinda nake yi a lokacin tamkar umarni zuchiyata take bani ne, haka mutanena sukaita umartata. Karo naci da wani abu ina shirin faɗuwa naji an yi saurin caɓeni. Dishi_dishi nake ganin Mijinyawa na riƙe dani. Da sauri na miƙe a jikinshi inaji kamar an watsamun narkakken ruwan dalma a jikina. Daga saman kaina naji murya na cewa. "Su fitar ma goɗiyarmu a gida. Su fita a rayuwarta. In ba haka ba, ba wanda zaiji da daɗi, ba zamu sake ragama kowa ba." Wucewa ɗakina nayi kawai na zauna a kujera idanuna a lumshe inata ambaton Allah A hankali a hankali. Zuchiyata sai tunzura take yi, tana yinƙurowa tamkar zan yi amanta. Na dawo daidai a hankali, saina buɗe idanuna da suka rine sukai jawur dasu. Banɗaki na shiga, sai amai haka na Mayar da duk indomin da naci tas, bakina na wanke, na ɗauro alwala tare da saka hijabi. Ina cikin yin Sallah mijinyawa ya shigo da tire ɗauke da abinci harda ruwan zafi a kofi yana ta turiri. Sallamewa nayi, nako jima a kan sallaya ina kai ƙarar duk wanda yake neman damun rayuwata, nayi azkhar ɗina, na yamma kana na tashi na naɗe hijabina na maidashi muhallinshi na haye gadona, da ƙyar nake iya ɗaga hannayena. Kafaɗata tayi mugun nauyi gaya. Hannu nasa na ɗakko laptop ɗina dake durowar gefen gado. A lokacin fa ina ji anata tausar Nanno ita tafiya zata yi ana ta cewa ta bari sai gobe. Tace zasu tafi tun kafin in shaƙeta ta mutu. "Hindu ga abinci ki daure kici, zama da yinwar bazai haifar da ɗa mai idanu ba. Inaso zan je in raka su Nanno ne" Hmmmm" Kawai nace, ya taso ya duremun abincin akan gadon. "Ahmad shayinki bansan inda yake ba, na dudduba ban gani ba inaso in saka miki a ruwan zafi... " Zan saka inna tashi" Nayi saurin katseshi dan maganarshi ma ba son ji nake yi ba. Fita yayi, inaji suna fita da kayan su Nanno, naji tashin motarsu, shi kuma ya dawo jiki a saɓule. Ga wani kes da ya ɗauki hankalina na wata mata da mijinta yai mata kafurin dukan da idanunta gabaki ɗaya sun kulle tsabar kumburi, abunka da farar fata saman idan da ƙasan idon jini ya taru sosai Bakinta ya farfashe. Numfashi kawai na ja tare da saukewa. A hankali na sauka na ɗakko Ahmad Shayi a durowar ganyen shayina da na tarasu iri da kala, na ɗakko sikari mai iyali dunƙule uku na dawo na zauna na zuba a kofin shayin. Kana naci gaba da bin kanun labaran a daidai lokacin tana ɗakin maƙota da ƙyar mijin maƙociyarta ya ƙwaceta a hannun mijin, kasheta ma yaso wai yayi. Ai da ganin dukan kasheta yaso yi. Wallahi in kuka ga irin dukan da miji yaima yarinyarnan zaku tsorata. Gata fara kyakkyawa wallahi. Kai ya salam, yansu in tace tana neman hakkinta sai ace tayi fito na fito da maza ko? Dan Allah ga tambayata, in ya kasheta shi me sunan abinda yayi? Ban ma tambayeta abinda ya haɗasu ba na barma gobe wannan, kuma nayi mata alƙawarin sassafe zan zo ta ajjiyemun Adireshin gidan kawai. Duk da ciwon da nake ji a jikina, amman zanje, lallai tana buƙatata. Kwatancen mijin Jamila da mahaifinta yayi munne ya sake faɗo mun. Lumshe idanuna kayi kawai. Laptop ɗin na kulle na jawo tiren abincin na buɗe filet ɗin naga shinkafa ce da miya. Na saka cokali na soma ji, dan cikina kamar an mun yasa haka nake jinshi. Cokali biyu nayi, na ɗauki shayin ina kurɓa a hankali. Hmmm shinkafa da miya ya musu kenan. Su Jamila manya. Wannan karon uwatale ana jego da sai taga ƙwal uwar daka. Hakan sai ya tuno mun da wata ranar talata da daddare dana dawo aiki da zazzaɓi sosai a jikina. Ina shigowa na tadda yara a gidan. "Ammi kamar baki da lafiya ko? " Asama'uce ta tambayeni cike da kulawa fitowarta daga Kitchen kenan. Bana jin daɗi kam da ƙyar na ƙaraso gida zan kwanta in mijinyawa ya shigo kuce mishi ina ciki" Ɗakin mijinyawa na buɗe na shiga, shigata ke da wuya aka ɓalle da ruwa kamar da bakin ƙwarya dama hadarine baƙi a garin ya saki sanyi da duhu sosai. Ƙarfe huɗun yammane amman zaku yi tunanin magribane sabida yadda garin yayi duhu sakamakon mun shiga tsakiyan watan marka_marka. Ruwannan daya ɓalle sai sanyi ya ƙaru a garin babu shiri na duƙunƙune a faiba ina rawar ɗari, a haka wani wahalallen bacci ya kwasheni wanda har a cikin baccin nawa ina jin zazzaɓi sosai. Bani na farka ba sai shidan yamma a lokacin saura ƴan mintuna a kira sallah, jikin nawa ya sake tsananta ainun. Ina zaune Mijinyawa ya shigo da sallama hannunshi riƙe da leda fara. A gefen gadon ya ajjiye tare da zama a bakin gadon. "Da halama bakya jin daɗi ya nuna a idanunki ma" Hannu yasa ya taɓa jikina sanyin hannunshi ya ratsani, shi kuma zafin da jikina ya ɗauka ya ratsashi. A jiƙe yake ruwa ya jibgeshi a hanyar dawowa. "Subhanallahi zazzaɓine ya rabkeki haka shine ko yara basu kira sun sanar dani ba? Daure ki ƙoƙarta muje asibiti maza man Allah. Mrs Bukhari To jama'a sai Litinin in Allah ya kaimu cikin rakayyu masu lafiya.TSURON TSIRIN... TSANDAURI LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI. LAMBA TA GOMA (10) SADAUKARWA _Na sadaukar da wannan shafin zuwa gareki masoyiyata, ƙawata, mai son ci gabana. Aisha Haladu. Masoyiya alkhairin Allah ya ishe miki a duk inda kike._ _Ya yara miki haularki, ya dauwamar miki da farin ciki a rayuwarki maras yankewa._ https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl?s=cl&p=a&ilr=1&amv=1 ✨ DA YAWA SABABBIN KWASTOMOMI SUKAN TAMBAYA... ✨ "Shin kayan naku suna da kyau kuwa?" Amsarmu ita ce: Ku gwada sau ɗaya, ku zama shaidun ingancinmu. 🥰 A HAFSAT COLLECTION, muna kawo muku: 🌸 Kayan Kitchen masu inganci 🌸 Atamfa masu kyau 🌸 Laces na musamman 🌸 Abaya masu ƙayatarwa 💯 Inganci tabbatacce 💯 Farashi mai sauƙi 💯 Amana da gaskiya 💯 Ba cuta ba cutarwa – gamsuwar kwastoma ita ce fifikonmu. Kar ki bari a ba ki labari. Ki yi odarki yau, ki ga bambanci da idanunki. 📲 Order yanzu: ☎️ 08131850861 ☎️ 07076403211 HAFSAT COLLECTION – Inganci, Kyau da Amana. 💖 Kallonshi nayi tare da cewa. A'a ka bar asibitin in nasha magani na samu bacci shikenan. Yanzu in asibitin zamu je a ruwannan zamu tafi, mu ba abun hawa ba? Jibeka a jiƙe kaima ka dawo ruwa ya dokeka" Hannayena ya kama yana kallona. "Ina fatan ba ruwa bane ya dakeki ba ko, kinsan fa jikinki baya jurar dukan ruwan sama? Zan ƙoƙarta in sai abun hawa akwai wata mota da abokin aikina yaimun tayinta dubu saba'in sai dai gyara gareta da matsaloli sosai, kuma bani da kuɗinma ke kinsan komai, tsohuwace sosai tasi ma da akeyi da'ita daga baya aka ajjiye ta dai. To guntun gatarinka akace yafi sari ka bani. Amman bari in sauya kaya sai in samu Mijinyawa Babba ya aramun motarshi in kai ki asibiti, hakan zaifi" Tashi yake yinƙurin yi ina nishi na riƙe hannunshi. Ka bani magani in sha da shayi mai zafi ma ya'isa. Ko fa munje asibitin bamu da kuɗi yadda wata ya raba ɗinnan kuɗin motar hannuna ma ya ƙare gobe sai dai in tafi a ƙafa. Kaga batun zuwa asibiti ai bai taso ba. Nafi zargin gajiyace" Shiru yayi baice uffan ba yana dai ta nazari, can dai ya sauya kaya yayi alwala ya fito. Fanado ya ɓalla ya bani nasha, ya haɗo mun shayi baƙi ya kawo mun. "Bari dai muje masallaci mu dawo zamu san yadda zamu yi, ke dai babu damuwa. Kinsan bazan barki baki da lafiya a gida ba, rashin kuɗi ba hujja bane, nifa namijine Tutar so ki jirani ke dai, zan san ya zanyi dole muje asibiti" Fuskata ya shafa ya fita na bishi da idanu kawai, tare da lumshe idanuna ina jina tamkar zan tashi sama tsabar yadda nake jin daɗin irin sa'ar da nayi da miji nagartacce. A lokacin ina ganin nafi duk matan duniya dace, da samun nagartacce, tsayayyen mijin da muka fahimci junanmu gaya. Mijin da ya zame mun abokin birne sirrina. Mijin da ya yarda dani, na yarda dashi. A daddafe na ɗauro alwala da ruwan ɗumi, na gabatar da sallah kana na jawo ledar daya shigo da'ita na buɗa, shinkafa ce kwano ɗaya da wake gongoni huɗu. Kai na girgiza kawai na sha'afa babu hatsi a gidanma gobe dole zan san abunyi kafin a biyamu albashi gaskiya. Daddagewa nayi na miƙe da ledarnan a hannuna na fito. Da sauri Asama'u ta tareni tare da karɓar ledar a hannuna. Ki dafa shinkafar rabin kwano, aci har safe, wake bazai nuna a darennan ba ayi shinkafar aci da manja da yaji, in yaso gobe nayi mana mai waken da kaina" Lokacin basu tasa sosai ba, amman suna aikace_aikacen gida da har su Yaya Saratu suna mamaki. Musamman Azgar dake son yaga an sakar mishi yayi girki, har tuwo zai talga ya tuƙa. Idanu na lumshe sabida irin zazzaɓin da nake ji. Azgar ne ya shigo da sallama ina zaune a falo, matan suna Kicin sai musu suke yi, da hayaniya dai irin da yara daidai sa'anninsu. Shi kuwa Azgar duk saiya ruɗe ganin yanayin da nake ciki, yaita yi mun sannu ina amsawa a hankali. Can saiga mijinyawa ya shigo a gaggauce. "Tutar so taso muje asibiti maza, Azgar ku kula da gidan ba zamu daɗe ba" Haka na miƙe muka fito, dama da mayafi a jikina. Muna fitowa ya riƙe mun hannayena, yana riƙe dani ga lema a hannunshi har zuwa wajen motar mijinyawa. Har lokacin ana ruwan sama, amman ba mau ƙarfi ba. Ya sakani gaban motar ya zagaya a gurguje ya shiga sai asibiti. Akaimun dai gwaje_gwajen daya dace rashin hutune kawai ke damuna, aka rubutamun magani muka tawo. "Ki daure ki ringa hutawa Tutar so. Jibi jikinki fa yadda ya rikice, bakya samun wadataccen bacci, sabida zaurenki da fashin Facebook ɗinki. Washegari kuma ki shirya ki tafi aiki ki dawo kuma ki shiga aikin gida. Anya bazan hana wannan wayar da kan matan ba kuwa? Aikine shima mai zaman kanshi yana da buƙatar lokaci ga risach da kike yawan yi, na ƙananun kosis da kike yi ta yanar gizo, ki dinga hutawa, kinga ya soma shafar lafiyarki. Kullum a cikin ciwon kai kike." Idanuna na lumshe tare da buɗewa nace dashi. Ai ana samun lada sosai, irin addu'o'in da suke yi mana muna ganin hasken su mijinyawana" Murmushi yayi tare da saka tafukan hannayena cikin nashi. "Wannan gaskiya ne, shi yasa nima wani sa'in nake shiga cikin bidiyonki ayi dani ai. Sabida inason duk abinda kike so, shi yasa nake baki gudunmawata, amman a dinga hutawa. Me kike sha'awar ci tun kafin mu shiga gida in siya miki? " Tukunna Kafin mu kai wannan jallin, ina aka samu kuɗin, kaddai a wajen Mijinyawa babba ka karɓo? " "Kai haba dai wayata dai na siyar sabida dai lafiyarki madam ɗina, nasan ba zaki ji daɗi ba in na tambayo mijinyawa babba kuɗi ba. In dai ya bani zan karɓa, in ya hanani bazan ji haushi ba. Tunda yayi mana sutura, da tuni muna gidan haya muna gwagwagwa." Murmushi kawai nayi mishi. Miyar sutu nake so kayi mun inci da shinkafa, asa ɗanyen kifi ko bushasshe in kuɗin zai isa. In muka je gida Azgar sai ya siyo kayan miyan a maƙota" "An gama ranki shi daɗe da girman kujerarki" Dariyar ƙarfin hali kawai nayi. A hanya muka tsaya ya sai mun kifi guda biyu ƙananu. Muna isa gida Azgar na shigowa shi da su Gambo daga masallaci suke. Aikenshi nayi maƙota siyo kayan miya, mu kuma muka shiga cikin gidan ɗaki na wuce na kwanta ina jiran abinci Sai wajajen tara sai ga mijinyawa da tiren abinci shinkafa da miya da shayi sak irin na yau ɗinnan ya dire mun a gabana. Bai gushe ba ya dinga bani a baki ins ci, har saida ya samu tabbacin na ƙoshi tukunna. "Toh ga maganin ɓalli ki sha, ko zaki iya wanka?" Kai na girgiza mishi. Akwai sanyi, bazan iya wanka ba" Maganin ya ɓallamun, na zuba a baki na kora da shayi. Kayan baccina ya ciromun, ya fita wajen yara, ya ɗan zauna dasu ina jiyo hirarsu. Sai bayan ya sallamesu sun tafi sun kwanta, kafin ya shigo da sallamarshi. Saida yayi wanka ya hayo gadon, muka shige jikin juna, yana shafamun bayana har bacci ya kwasheni. "Tutar so! " Kiran sunana da mijinyawa yayine ya dawo dani cikin hayyacina, ya kashemun tunanin da nake yi. Na kalleshi yana zaune akan kujera. "Dan Allah kiyi haƙuri da dukkan abubuwan da suka faru ɗazu a falo, ki daɗa haƙuri da kalaman su Yaya Jamila har Allah kawo ƙarshen komai. Wallahi Tutar so kunyar Ubangijina nake yi, kan abinda shaiɗan yai riƙo da hannayena na aikata. Kema kin zamemun tamkar suruka. Naga hotunan zunubina da kika turomun, ina ƙara daɗa baki haƙuri. Ina kewa da mafarkin rayuwarmu mai daɗi da muke gudanarwa a baya, a kullum cikin tunani da mafarkan Giwata ta da nake, bata yanzu ba, wacce nake jin kunyarta tamkar zan nitse. Nina ruguza komai da hannuna. Amman nayi miki alƙawarin matsawar kika bani dama ta biyu zan gyara duk abunda na lalata. Albishir mafi daɗi da farin ciki shine, nayi miki alƙawarin ke kaɗaice sarauniya a fadata, baki da abokiyar tarayya, babu gurbin wata macen a zuchiyata. Wannan gangariyan alƙawarine ba irin gama garin alƙawarurrukan da ƴan uwana maza suka saba yi ma matayensu bane, a lokacin da suke ganiyar soyayya ba, ba kuma romon baka bane, ba kuma toshiyar baki bane Hindu cancantarki ce, da sadaukarwarki." Fasali ya ja yana yamutse fuskarshi halamun yana jin wani irin zafi a ƙasan zuchiyarshi na taso mishi. Sai dai kash nawa zafi da ciwon ya wuci gaban misali, tunda zuchiyata ta kama da wuta har yanzu ci take yi, daidai da sakan ban taɓa mance komai ba, komai da komai yananan ƙyam a ƙwaƙwalwata, a kullum saina yi bita da nazarin dukkan abubuwan da suka faru. Maganganun yaudaran da mijinyawa yake yi mun sai nake ji tamkar ya raina ni ne, ya raina kuma tunanina Hakan yasa nayi murmushi kawai nace. Naji duk abinda kace mijinyawa, zaka iya fita" Miƙewa nayi ɗauke da tiran abincin na fice na kai Kicin, Ɗakin Sabira na leƙa tana zaune tana karanta littafin labari na turanci. Ke kaɗai kike zaune, kina karatu ƴan matana? Na tambayeta ina murmusawa. "Karatu nake yi, Ammi tun jiya nake son gama wannan littafin, amman saura kaɗan, yau zan gama in sha Allah, ya jikin ki Ammi? " Da zaran goma tayi kiyi adda'a ki yi bacci. Akwai Makaranta gobe. Azgar shi yana falon ne?" "A'a yana ɗaki tare da Yaya Musa. Shiru nayi ina nazari Azgar kenan yaron kirki. Leƙawa ɗakin nashi nayi na taddashi yana waya yana gadon Mijinyawa a kwance. Musa kuma yana kan gadon Azgar ɗin yayi bacci baki a buɗe sai munshari yake ja kawai. Kai na girgiza kawai. Ina jinjina ƙarfin maita irinta su Yaya jamila. Ysnzu menene dalili, da amfanin barin Musa ya kwana, tunda tare suka zo, ai ya kamata da zasu tafi sun wuce dashine. "Ammi kina son wani abunne"? Ya tambayeni harda toshe wajen jin sautin murya a wayar. Kai na girgiza mishi kawai na karkashe wutar korido data Kicin na koma ciki da sallama a bakina. Mijinyawa na zaune inda na barshi, har naje nayo wanka nayi zaman daɓaron shafa mai, na gama inajin idanunshi na yawo a jikina harna sanya rigar baccina, na shafe jikina da sassanyar humra mai sanyi da taushin ƙamshi ta wajen MRS BUKHARI nayi hayewata gado. "Nayi kewar shaƙar wannan humrar ta dare mai sanyaya ruhi da kwantar da gajiya gami da sakko da shauƙi" Hmmmm Mijinyawa kenan. Ashe baka fita ba, nayi tunanin ka fita ai. Ka kashemun wutar in ka fice, in kuma anan zaka zauna, ni sai in bar maka gidanma baki ɗaya" "Aa wane mutum inji mutuwa. Kaina bisa wuyana zan fita." Miƙewa yayi da sauri ya fice" Juyawa nayi na soma adda'a ina shafawa bacci ya sureni ban sake sanin komai ba sai da wayata ta tasheni da alama, na ƙarfe biyun dare. Dake jikin nawa babu ta inda baya ciwo. Mayar da idanuna nayi na kulle kawai. Ƙarfe huɗu daidai kamar yadda alamar cikin wayata ya kuma kaɗawa na tashi idanuna a rurrufe, na nufi banɗaki na watsa ruwan zafi a jikina tare da ɗauro alwala na fito na shiga sallah kamar dai kullum. Na faɗa na sake faɗa muku ƴan uwana mata. Dukkan abinda kike yi a rayuwa ko minti sha biyar ne ki tashi kiyi alwala, ki faɗama Allah damuwarki ko buƙatarki, muddin kika ga buƙatar taki bata biya ba babu alkhairine a cikin abinda ke baki da sani akai, kike roƙon Allah ya baki. Sallah dare makamine babba wanda ya kamata mu riƙe. A lokacin da kowa ke bacci, kin ɗauke haƙarƙarinki a ƙasa, in fuskanci alƙibla kuna faɗama Allah damuwar da ta dami rayuwarki. Kina godiya bisa ƙofofin ni'ima daya buɗe miki. Ki riƙe salatin Annabi saw, da istigifari. Ko su kika yi, bakya buƙatar sai kin jeroma Allah buƙatun da kike ɓoye a zuchiyarki, Allahn shi ya halicceki, ya halicci zuchiyar dake gaban ƙirjinki, shi yafi kowa sanin rauninki. Kiran sallar farko mijinyawa ya buɗe ƙofar ɗakina ya shigo, dake a buɗe ta kwana, tunda ya fita ban kulle ba. Juyowa ban ba, inata jan jarbi abuna. ", ashe kin tashi, nayi tunanin ko nauyin jikin zai hanaki tashi ai" Shiru. Mun tafi masallaci Tutar so" Har ya juya, ya juyo ya dubeni. "Rabon da inyi bacci mai ni'ima, harna mance, ƙamshin Humrarkinan mai sirri yayi tasiri jiya a jikina, iskar dana shaƙa a cikin ɗakinan, cakuɗe da iskan numfashinki da wannan Humra taki harna manta yaushe na jini a irin wannan yanayin. Ina kewar komai daga gareki inaji inama mafarki nake yi zan farka ace duk komai a mafarki ya kasance. Inama ki kasance mai yafiya, mantuwar zunubina dana nayi farin ciki. Allah ya shaida na tuba, mala'ikun Allah sun shaida nayi tuban gaskiya. A kullum na kai goshina ƙasa ina roƙon yafiyar Ubangiji, ina roƙon Allah ya sanyaya miki zuchiyarki, ki yi haƙuri mu ƙarashe ginin da muka gina ya rage ƙarashe kawai" Kallonshi nayi zuchiyata na tunzura inaji tamkar in zazzageshi a ƙalla ko na ɗan huce. Wallahi bazan taɓa iya ci gaba da rayuwa da mijinyawa ba. Amman naga halama so yake ya kaini bango, shikenan zan ɗauki matakin rabuwa dashi a shariance, dama mutumcin shine a gaban yaranshi bana so ya zube, amman na lura tonuwar asirin yafi so, zai ko ga sammaci. Masu ganin na zafafa, ko naƙi in yafe ma mijinyawa, ku dakata har zuwa lokacin da kuka gama jin ƙarashen labarin rayuwarmu ta baya. Sannan ni nace na yafe mishi, ko ban yafe mishi ba, in yayi tuba mai kyau Allah zai yafe mishi. Ku fahimceni zamanne bazan iya ci gaba dayi dashi ba wallahi. Kuma banyi laifiba. Kin taɓa rainon ƴa mijinki ya nemeta sukaita aikata aikin ashsha, kin taɓa renon ƴa mijinki ya gama zageki a gabanta, ya kuma aureta da ranki. Kinsan raɗaɗin, kinsan zafin? Nayi imanin matan da suke maganganu akan Hindu ta zafafa wallahi in watace saita mutu, ko hawan jini ya doketa, ko ta ƙona gidan, ko tayi musu terere bankaɗa musamman a lokacin data kamasu akan gadonsu na sunnah hmm. Fita yayi dama baya buƙatar jin abinda ke bakina, yafi kowa sanin bazan taɓa tankawa ba. Bayan na idar da sallah nayi azkhar, sai nayo wanka na shiryo fes na fito dan mu gaisa da yara. Saida na tsaya a kicin na jona ruwa a buta, nan naga ƙwai da biredi sinƙin_sinƙin mijinyawa ya ajjiye. Ƙwai Azgar ya soya mun, ni kuma na dafa shayi, a kicin ɗin muka gaggaisa, naji lafiyarsu. Musa ya leƙo ya gaisheni, na amsa mishi kadaran kadaham tare da miƙa mishi kayan kari. A gurguje nake komai inayi ina kallon agogo. Shida da rabi na fice ba tare dana yi sallama da kowa ba. Na dai faɗama Azgar ya tabbatar sun fita da Musa sun kulle gidan. mijinyawa a waje na wuce shi yana motsa jikinshi, da kallo kawai ya bini, kai tsaye sai gwammaja adireshin da wannan baiwar Allah da miji ya bata kashi ɗinnan. Ina isowa unguwar na tambayi yara sunan inkiyar gidan data bani suka nuna mini ina kusa da gidanma. Gidan harda get babba kusan ma yafi ko wanne gida kamar dama_ dama a unguwar. Ba mugun kyau gareshi ba, a ɓuɓɓule ma yake get ɗin shima ko fenti babu kamar yadda gidanma babu fentin sai dai gidan babbane a tsukukun shine yafi kyau. Tura ƙofar gidan nayi na shiga mata yama_yama a tsakar gida anata hada hadar safiya ga yara kamar tsaki. Wata matar ƙabila na tambaya wajen Hajara nazo. "Ummm tana ɗakin Maman Junaidu, ga ɗakin can mai jan labule, amman dai tafiya kika zo kiyi da'ita dai ko? In ba haka ba mugun mijinnan nata sai ya halakata, sannan hankalinshi zai kwanta" Murmushi nayi nace. E tafiya nazo yi da'ita" Harna wuce ta dawo dani da cewar. "Baiwar Allah daga can garin nasu kika tawo, a waya ta kiraki ne? Lallai wannan karon abun yaci tura tunda har Hajara ta iya neman agaji, matar da ko ihu bata fiye yi ba in mijin ya sha giyarshi yana jibgarta yana amai" Idanu na zare bansan sanda na furta. Giya fa kika ce, au giya ma yake sha ya jibgeta kenan?" Saurin rufe bakinta tayi alamun tsabar gulma dake cintane yasa tayi suɓul da baka. Sai kawai na girgiza kaina na nufi ɗakin data nuna mun bayan na dakata mun gaggaisa da bataliyar matan gidan. Sai kallona suke yi kamar zasu cinyeni. A dokin ƙofar da aka nuna mun nayi sallama wata murya ta bani izinin shiga na shiga a hankali. Hajara na kwance a doguwar kujera fuskarta ta aune, ga wani jini daya taru mata a kusa da fuskarta, bakinta a fashe da saman idanunta. Mai ɗakin kuma tana zaune a ƙasan kafet tana yanka tuwon ɗumame ga risho a gabanta, shayi sai tafasa yake yi yana fidda ƙamshin citta. "Sannu baiwar Allah ga waje zauna. Hajara matsa mata" Kasancewar kujerar ita kaɗaice a ɗakin. Yi kwanciyarki ƙasa ma ya isheni nagode" A ƙasan kafet na zauna muka gaisa da wannan mata, kana Hajara ta gaisheni na amsa ina kallon yadda mijinta ya sauya mata halittarta. Ke kuwa Hajara me kika yi da mijinki ya jibgeki haka, da alamu ba yauma ya saba dukanki ba, sabar mishi kika yi yaita jibgarki kamar ubanki da sunan aure. Wai me yasa mace da kanta take ɓarar da damarta, kimarta darajarta? Har kullum ina faɗe ina mayawa wata fuskar tafi gaban mari. Wanne irin laifi mace zataima mijinta in da soyayya, da darajarta, yai mata irin wannan dukan sa'an, kuma yayi tunanin zasu ci gaba da aure harma suci gaba da mu'alamar aure? Baiwar Allah kiji mun wannan abun, wai ashe lalacewar da muka yi da son nuna ma maza sai dasu dole zamu rayu, duk irin cutarwarsu a garemu ashe har ya kai irin wannan matakin? Jibi fuskar Hajara fa wanne kamilin magidanci, nitsattse,wanda yasan darajar jinsin mata, mai daraja iyayenshi, da matar aurenshi, mai addini, da sanin ya kamata ne zai yi wannan ɗanyen aikin" Ajjiyar zuchiya ta sauke Hajara kuma sai kuka mai nishi take yi. Wannan mata tana sassaka tuwo a cikin miya tace. "Baiwar Allah wallahi Mijinta tantirin mugune, azaba kaɗai yake gana mata, duka kuwa ta mayar da kanta tamkar jaka, dan tana karɓarshi taƙi ta sanar a gidansu balle a duba irin matakin da za'a ɗauka, ni nayi mamaki ma da take sanar mun tayi magana dake zaki taimaka mata. Yanzu duk dukannan da yayi mata kuma yace ta bar mishi gidanshi a daren, sabida babu kishinta a ranshi balle tunanin abinda kaje kazo game da fitar ta a cikin duhun dare, in akayi la'akari da ita ba ƴar gari bace, shima zuwo ne uwar ɗaki kaɗai gareshi, kuma ba nan kusa take ba. Da mugun zazzaɓi ta kwana saida Baban Junaidu ya siyo mata magani ta haɗiya ta gargasa jikinta tukunna ta iya bacci" Jikinta na taɓa yananan yayi zafi sosai. Hajara tashi muje in kai ki asibiti a duba lafiyarki, ina da aiki daga can wajen aiki zan wuce, bansan wa zai zauna dake a asibitin ba" Matarnan tace. "Baban Junaidu ya yarje mun akan duk inda zaki je da Hajara in biku, bari in sallami yara da abun karyawa sai mu tafi". Jiranta nayi ta kammala sallamar yara, taba Hajara taci amman ta kasa ci jikinta ma rawa yake yi shayin kaɗai nasa ta daure ta sha badan tana so ba. Fitowa muka yi riƙe da'ita Maman Junaidu na kiciniyar rufe ƙofarta, muka ji an ɗumo wata ashariya mai ƴaƴa da jikoki an ɗumama Hajara. Da sauri na juyo, ita kuma tayi saurin komawa bayana ta maƙale. Kallo na ƙare mishi daga shi sai gajeren wando da singileti, kanshi kuwa wani irin gashi mai dada ya tara wallahi har wuyanshi yadda kuka san bommali, wannan mawaƙin da yayi sharafi. Haƙiƙa iyayen Hajara sun yi kuskure mafi muni da suka ɗauki ɗiyarsu suka bata wannan miji, da irin wannan sufa tashi ta rashin daraja. Wai iyaye muna tunowa ƴaƴanmu nada hakki akanmu kuwa, ko mun mance kiwo ilahi ya bamu na yaranmu, akwai kuma ranar da zamu tsaya gaba gareshi ya tambayemu akan ababen kiwonnan daya bamu? Ko da yake kada in yi saurin yanke hukunci, ta yiyu Hajara ce ta liƙe ta kafe sai shi, iyayenta suka ja ta ja suka sake mata kamar dai yadda ya faru dani. Ta yiyu sun gaji da'ita burinsu su kaita ɗakin aure, ta yiyu kuma abun hannunshi suka bi da sauransu_da sauransu. "Ke dan abu ta kazan.... Daga ina a dangin Hajara bansan wacece ke ba da har kike yinƙurin fitarmun da mata" "Haba Figo wannan irin zagi haka ya'isa mana asibiti zamu kaita ba wani abun ba, baka ganin yadda idanunta ya tara jinine? " Cewar Maman Junaidu ni dai ina tsaye mamaki zai halakani, Allah mai iko ashe lalacewarmu har ta kai a ɗauki mace a ba Figo? "Babu to inda zaku je in dai ni nake aurenta. Zaki zo ki wuce ki girka mana abinda zamu ci ne ko saina tattakaki ne? " Matan gidan duk suka dena abinda suke yi suka rufu a kanmu suna kallon ikon mai saukar da ruwa da iska. Yinƙurowa yayi Hajara tayi saurin riƙeni tana kuka. Kai lafiyanka ƙalau kuwa a hakanne zata yi maka girki, har kana ikrarin kuma dukanta a tunaninka baiwa ko Jaka ce Hajara? Girki ba zata yi ba, asibiti kuma dole saina kaita ko aman wuta kake yi wallahi. Hajara wuce muje" Wata dariya yayi tare da yin kasaƙe yana kallona. Ina jan hannun Hajara, tana noƙewa tana son bina tana tsoron me kaje kazo kunji irin tsiyar da irin baƙin cikin da muke ƙunsa ko. Fisgeta nayi muka ratsa matan gidan muka wuce. "Wallahi na rantse miki da Allah kika kaita asibiti dake da'ita duk sai kun kwana a sell, ke har kotu saimun shiga saina ƙulla miki sharrin da baki zata ba, makirine ni na gaske wallahi. Ke kuma kinsan gamona dake." Da Hajara da Maman Junaidu duk sai sukai turus a bakin ƙofar fita. Juyowa nayi na dubeshi ina murmushi nace dashi. Wanda ya fasa abu ta kazanshi ni da kai. Baka san waye Hindu bane. Ke Hajara kin shirya da duk abinda zai biyo baya, da fatan ba zaki ba dani ba ko? " Kai ta ɗaga mun halamun i duk da jikinta har rawa yake yi. Fisgarta nayi muka fice na sakata a bayan mota Maman Junaidu ta shiga gaba muka je asibitin Malam Aminu Kano. Saida na tabbatar an basu gado na basu kuɗi a hannunsu, na yi musu sallama tare da ba Maman Junaidu lambar wayata Da ba dan an sanni a asibitin ba, bama zasu karɓemu ba sai da hukuma dukan da Figo yaima Hajara dukane na sa'a. Ina zuwa wajen aiki na fita ɗakko rahoto, amman sauƙinta a cikin garine taron siyasane da aka gayyacemu ɗakko rahotanni. Mun jima muna jira tare da ƴan jarida ƴan uwana daga mabambamtan gidajen yaɗa labarai. Saida taro ya ƙare kana muka yinƙura muka soma aikinmu. Wato aikin ɗakko rahoto aikine mai wuya da haɗari ga ɗiya mace sosai, yawancin masu ɗakkon rahotannin dai mazaje, kana waɗanda zasu bada bayani akasari mazane. Dan wannan taro har gwamna yayi magana damu duk da ba wannan bane farau ba. A gajiye tulus na dago gidan Rediyo a hanyar dawowane na samu zarafin kiran Maman Junaidu dan jin me ake ciki. Kafinnan, naje kotu, mun yi magana da alƙali akan kes ɗina da mijinyawa, bazan sako Saudatu a cikin lamarin ba, sai dai in ɗauki lauya daban gaskiya. Bayan nan, na je wajen Baban Jamila na nuna mishi hoton Mijin Salamatu. Kuka kawai ya fashe dashi, yanata furta. "Allah ya'isa Allah ya isa, bazan yafe ba. Duk da nasan nina cuci kaina. Amman yarinya ya akayi kika gano hotonshi? " Baba wannan da kake ganinta Babanmu ɗaya, itace nan da ƴan kwanaki zata aureshi. Mu a Katsina ya nuna mana yake. Kuma da dukkan halamu a wannan karon yayi amfani da iyayenshi na gaske. Sabida sunzo an gansu, akwai kama. Sannan anyi bincike ɗan manyan mutanene, ya fito a familin yawa, kuɗi, da muƙami. In sha Allah zamu ƙwato hakkin Jamila da izinin Allah Baba. Duk sauran bayani zaka ji." Da haka mukai sallama kafin na kira Maman Junaidu. Wannan ƙasar tamu wallahi akwai gyara, Wai a asibiti an sallamesu an mata duk abinda ya dace basu wuce ƙarfe uku a asibiti ba suka koma gida. Figo ya ɗakko ma Hajara ƴan sanda harma sun tafi da'ita, nima wai suna hanyar zuwa wajena. Bata da lafiya, da ciwuka a jikinta, a haka aka wuce da'ita. Illahirin mamaki da ƙyar ya barni na shiga ciki cikin ɓacin rai na miƙa aikina na ranar, ko zama bam ba sai ga kira wai ana nemana ƴan sanda suna waje. Luba hankalinta duk ya tashi ta shiga ruɗu tare da tambayata dalilin neman. Dariya nayi ina jinjina rashin daraja irinta Figo. Miƙewa nayi nace da'ita. Kar ki damu akan kare hakkin wata baiwar Allah ne mai miji ɗan hau, Luba bari inje ayi duk wacce za'ayi." Ina gama faɗin haka na suri jakata na fita suna harabar gidan rediyon har ma'aikata sun soma leƙe, harma da masu kai kawo kunsan dama a wajen aiki baka rasa maƙiya duk yadda kuka kai ga haɗin kai. To ina da tulin maƙiya sosai. Ba fa kuma dan komai ba, sai dan jajircewata a fannin aikina ne kawai lefina. Sai cancantata data kaini landan kuma. "Mun kamaki da lefin sa matar Figo yi mishi bore, sannan kin fitar da'ita daga gidan dan ki koya mata bariki a bisa wannan dalilan zamu kamaki. Kofur Aisha ki kamata muje" A'a basai ta sha wuya ba. Bazan gudu ba muje babu damuwa" Muna kan tafiya zuwa wajen motarsu sai ga Luba ta ƙaraso da sauri. Kin motata ta zare da jakata a hannuna wayata kaɗai ta barmun. "Nazifi zai tuƙomu mu biyoku a baya Hindu" Dariya nayi mata. Lallai Luba kiyi tafiyarki gida, wannan ai ba wani abu bane, ni da ba da laifin kisa aka kamani ba. Waɗanda sukai kisanma a wannan ƙasar tamu wanne hukunci mai gamsarwa akeyi musu daya wuce aje a adanasu, gwammati ta dinga ɗaukar nauyin ci da shansu, da lafiyarsu." Kofur Aisha ta daka mun tsawa tace. "Ma firen shiga muje kina ɓata mana lokaci" Motarsu na shiga gaban motar ta zauna a gefe na sai direba, ragowar suna baya aka wuce dani. Su Luba na biye damu har zuwa ƙofar gidansu Hajara. Hmmm ashe Maman Junaidu muka zo ɗauka. Haka aka tuso ƙeyarta tana kuka da ihu, sanadin da yasa unguwar ta cika ta batse kenan. Sai mayafina nasa na rufe fuskata sabida darajar ƴaƴana. A bayan mota aka watsata muka wuce ofishin ƴan sanda na wajen. Aka sakamu a bayan kanta Hajara na zaune a benci bacci take yi a zaunen kasancewar jikinta babu ƙarfi. Kunji wata ƙaddarar kuma, wannan labarin in ya shiga gidanmu ai na zama nama, ga su Nanno suna garin suma labari zai karaɗe jama'are da kunnauwansu uwatale, in suka ji. Sai dai lallai babu mai jin wannan lamarin. Ni abubuwane ma cunkushe a kaina, musamman kes ɗin Mijin Salamatu yafi bugani. Yanzu a wanne matsayin ƴan gidanmu zasu ɗauki lamarin sai Allah, sai kuma su. (Kuyi haƙuri ku bini sannu_ sannu har zuwa inda nake son kaiku. Wannan labarun tafe suke a cakuɗe a cikin rayuwa, da gwagwarmayar Hindu, in zan rubuta rayuwar Hindu, dole aikinta na yau da kullum ya shigo cikin labarin nata, harda aikace_aikacen agajinta. Akwai ilimi da ɗunbun darasin ɗauka gaya a cikinshi. Ku bini sannu kan hankali, ba rubutun gaggawa bane, ba kuma karatun gaggawa nake son kuma kuyi ba. Tafiyar fa da tsayi) Mrs Bukhari........TSURON TSIRIN.... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA GOMA SHA ƊAYA (11) _(Tsokacina a kullum zaku ji ina cewa ayi karatun nazari, kuma a karanta a tsanake domin asan abun nufi, mu isa ga manufar anan ribar take_ _mui aiki da hankali da fikira wajen gane ina labarinnan ya dosa dan Allah_ _na fahimci da yawa sun juya manufar labarin izuwa mahanga, bigire daban, duk da bani da tasarrafin da zance kowa saiya fahimta irin tawa fahimtar, a tawa mahangar. Amman a dena juya manufar dan Allah nagode._) _Saƙwannin gaisuwa, gami da jinjinarku gareni yana zuwa mun. Kuma ina yabawa gaya, nagode da soyayya Ubangiji Allah ya bar so da kuma ƙauna_ https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl?s=cl&p=a&ilr=1&amv=1 ✨ DA YAWA SABABBIN KWASTOMOMI SUKAN TAMBAYA... ✨ "Shin kayan naku suna da kyau kuwa?" Amsarmu ita ce: Ku gwada sau ɗaya, ku zama shaidun ingancinmu. 🥰 A HAFSAT COLLECTION, muna kawo muku: 🌸 Kayan Kitchen masu inganci 🌸 Atamfa masu kyau 🌸 Laces na musamman 🌸 Abaya masu ƙayatarwa 💯 Inganci tabbatacce 💯 Farashi mai sauƙi 💯 Amana da gaskiya 💯 Ba cuta ba cutarwa – gamsuwar kwastoma ita ce fifikonmu. Kar ki bari a ba ki labari. Ki yi odarki yau, ki ga bambanci da idanunki. 📲 Order yanzu: ☎️ 08131850861 ☎️ 07076403211 HAFSAT COLLECTION – Inganci, Kyau da Amana. 💖 Hmmm ina zaune na tallafe Hajara jikinta kau da zafi, ina mamaki da ta'ajibin irin tashancin mijin Hajara Figo, ni ko zan so sani da dalilin yin wannan ƙaddararren aure meye silar ƙulluwan. Ƴan doka sai cike_cike suke yi anyi banza damu a kanta, sai ga Luba ta shigo duk a dame gashi ta ganni a bayan kanta. Shigowarta ke da wuya figo ya shigo yana wani harararmu harda tsaki. "Ka ganta itace take bi gida _gida tana hure ma matan mutane kunne, tana faɗa da maza sabida kawai tayi boko, ita ta fitar mun da matata tana son ɗaurata a harkar bariki, dan haka ni nafi son a kaimu kotu kawai dan wallahi bazan taɓa yadda ba" Mamaki cike da kaina na ɗago muka haɗa idanu da Luba da tayi kasaƙe tana kallonshi. "Bawan Allah kaji tsoron Allah Hindu bata zuga mata, sai dai ta wayar musu da kansu, kuma ta saurari matsalarsu, kuma Alhamdulillahi suna ganin haske. Kana matar aurece da yaranta, macen data fito gidan mutumci da karamci kuma. Bai kamata ka bita da sharri ba dan kawai matarka ta nemi agajinta akan dukan da kayi mata ba. Ai kaine wanda ya dace ace an ɗaure kai da baka san darajar mace ba bare darajar.... " "Ma firen ya'isa nan ba wajen hayaniya bane me ya kawoki daga kuma ina? " Cewar wata macen ƴar doka wacce da'ita aka tawo damu" "Sunana Luba nazo in yi belin su Hindu ne in da hali" "To babu hali tattarasu zamu yi ayi kotu dasu, kes dinsu babbane tunda mijin matar da taje har gida ta dauka yace bai amince ba. Sannan wacce dokarce ta bata damar shiga har cikin ɗakinshi ta fitar mishi da mata? A yadda ya faɗa mana ma ita kanta matar tashi bata son binta ba, ƙarfi ta gwada mata kawai. Rose a saka su a sell, su cire ɗankunne da sarƙa da mayafansu, wayoyinsu, jakunkunansu, in suna dashi domin kiyaye doka. Ki haɗesu a cikin wannan sell ɗin da aka kulle wannan matar mai adashe ta jiya" Murmusawa nayi, tare da jinjinama ƙasata.... Luba kije gida abunki, da baki wahalar da kanki ba tun farko. Ko da mijinyawa yazo nema na ko ya kira wayata kar ki faɗa mishi halin da ake ciki. Duk yadda zai kaɗa ya raya kice aiki ne dai muka tafi wani garin. Luba luba hmm" Na dubi wannan ƴar doka nace. Yanzu har da wannan maras lafiyar, da jikinta duk shatin duka, rauni linkib a jikinta itama kulleta za'ayi? " Ci kanki babu wanda yace dani. A kiɗime Luba tace. "Yanzu Hindu ciki za'a kai ku a kulle, to a haɗa dani mana, tunda nima ina bayanki ai? " Murmushi nayi nace Matakin nasarane kisa hakan a ranki Luba, ba fa kisa aka kamani nayi ba. Ke ɗaukaka da nasara basa zuwa da sauƙi ai. A cikin sell ɗinma wani sabon darasinne" Tasa mu gaba akayi zuwa wannan sell, da mace ɗaya ke ciki da gani Hajiyace haƙoran makanta har uku biyu a sama sai ɗaya a ƙasa. Sai na tuno da Maigogul, itama fara ce sol kuma kyakkyawar gaske. Babu komai a ɗakin sai zarni, da ƙazanta kawai ga jinin kuɗin cizo duk an kashe a bango. Shi kuma saiya tuno mun da Shanono Naroro, rayuwa kenan. Hajara daure ki zauna babu komai.zai yi dana sanin abinda ya aikata mana. Maman Junaidu kuka babu mafita a cikinshi, adda'a kawai ya kamata ki dinga yi. Duk wani mafita a wajen Allah yake" Jansu nayi muka zauna a gefe. Baiwar Allah ina wuni? " Na gaishe da wannan Hajiyar dan babbace zata kai Yaya Saratu a shekaru. Babu fara'a ta amsa dama bana tunanin fara'a a fuskar duk wanda zai shigo wannan ƙazantaccen waje. Dawo da dubana nayi kan Hajara dake nishi kamar numfashinta zai fita wallahi tsabar baƙin cikine ɗamfare a zuchiyarta, sai da naita basu baki kafin ta share hawayen da suke ta shatatowa da kansu. Yauwa ko ku fa. Wannan bafa shine ƙarshen rayuwarku ba sharia kuma daya ambata kuka ruɗe ,Hajara Figo baisan sharia bane baisan yadda reshe ke juyewa da mara gaskiya a kotu bane. Ko ya janye ni zan shigar da ƙaran ƙoƙarin lalatamun sunana da yayi. Amman ni bama wannan ba Hajara yaya akayi kuka yi aure da Figo dan Allah, sannan har lokacin da kuka yi nema kuka yi aure, da wannan gashin na dada a kanshi ko ko dai daga baya ya tara, duk da nasan dada na ɗiban shekaru da dama kafin taruwarta, shin ko hula yake sawa ta sanyi ya rufe dadan?" Kai ta girgiza da gani wani sabon baƙin cikin ta tuno kuma murya a sanyaye tace. "Anty ƴan mata da yawa sukan tabka kuskure, idanunsu na rufewa akan soyayya kaɗai, basa tuno cewar aure tafiyace mai dogon zango da yake buƙatar guziri mai yawan gaske. Iyaye suma suna wasarere da kiwon da Allah ya basu akan ƴaƴansu. Soyayyar yara da son faranta musu, ya rufe idanun iyayenmu da yawa na yanzu." Shiru tayi sai ta saki rishin kuka, ni kuma kunsan ban fiye shiri da masu kuka ba. Idanuna na lumshe kawai ba tare da nace uffan ba. Maman Junaidu sai girgiza kanta take yi. "Anty kinsan Allah in kika ga irin dukan da yake yi mata abun ya wuce misali, bel yake zarewa yaita dukanta har tsakar gida. Muna ji muna gani Hajara za'a wuce mata da mata cikin ɗakinta, wallahi ta fito tayi musu girki a ƙofar ɗakinta, dake duk a ƙofar ɗaki muke girki wasu kuma suyi a cikin ɗakunansu sabida guje ma gulmar leƙa tukunya irin na gidan haya masu raina arzikin mutum. Wai nan ƙawayenshi ne matan tare yake mu'amala dasu, kasancewar a gidan wasa yake aiki amman bansan wanne irin aiki yake yi ba." Gidan wasa gala ake cewa ko?" Maman Junaidu ta ɗaga mun kai halamar eh. Hajara ta numfasa tare da furta. "Ai har gadona yake basu su kwanta su huta, har kwana suke yi a ciki. Kuma bani da damar ɓata rai balle ƙorafi, a gabansu zai ci mutuncina ya zazzageni. Gadararshi shine yasan a gidanmu ma neman kai akeyi damu, kusan cusa mishi ni akayi, halamu sun nuna kamar dama da yaudara yazo sai Babanmu ya cusa mishi ni tare da rangwanta mishi aurena cikin rahusa. Ji da ganin rahusar ne ya amince dan da ya soma kawo uzirinshi na bogi. Badan komai yasa ake neman kan damu ba sai dan yawanmu. Mahaifinmu na ganin mun yi yawa a gabanshi gashi mun ɗanyi nauyi, da wuya azo neman auren ɗaya a cikinmu. Kinji yadda akayi Anty da abubuwa da dama da suka faffaru kafin auren. Yayuna biyu da aurensu ya mutu ko Anty? Wallahi su suke ciyar da kansu, su shayar da kansu, suima kansu sutura da komai. Mamanmu zata ɗaura tukunya suma ko wacce ta ɗaura tata tukunnar, a haka har ɗayar ta shawo kan mijin nata ta koma, itama kuma duka yake haɗata ita da kishiyar ya kulle gida yaita narkarsu kamar yaranshi, bayanta duk shatin bulalane. Amman a haka ta koma, sabida yara, da kuma rashin madafa. Ɗayar Yayar tawa karuwar gida ta zama, da yinwa da takura tayi mata yawa, tazo tafi ƙarfin kowa. Tun mota na zuwa ɗaukarta ta dawo da'ita har ya zamana in aka ɗauketa sai afi sati bata gidan, babu wanda yasan inda take. In akayi mata batun aure sai tace in anayi a lahira zata yi amman in namiji irin na duniyane bata so. Aure huɗu tayi dukka babu daɗi labarin ko wanne gida tana da ɗa Anty. Na sani itama tana da tulin nata laifuffukan. Bawai mazan bane masu matsala su kaɗai ba. Ni kinji irin rayuwar da nake tsoro wallahi Anty. Shi yasa nake ta zaman haƙuri da Figo" Kasaƙe nayi ina kallon Hajara kawai, illahirin mamaki ya hanani cewa uffan sai nazari kawai nake yi, tare da tubke maganganunta, ina warwaresu filla_filla Ashe har lalacewar tamu ta kai lalacewar da iyaye zasu dinga neman kayuka da yaran da Allah ya basu kiwonsu, ashe akwai uwa da uban da zasu amince ma Figo ya auri ɗiyarsu harma da sauƙaka mishi auren dan ana gudun kada a rasashi. Shin iyaye basa zurfin tunani da hangen nesan goben yaran nasu ne, sai dai burin su kawar dasu, tare da binsu da barazanar kada su sake su kaso aurensu su dawo musu gida? Wani uban ko uwarma cewa suke yi duk rintsi gidan miji yafi gidan uba, ashe harda miji irin Figo, ashe harda azzalumin namiji shima gidanshi yafi zaman gidan uba, wai me aka fahimta da kalmar aure da kuma ta saki ne?" Bana nufin duk iyaye haka suke fa. Ku fahimceni, wasu iyayen nace. A kullum ina faɗin duk lalacewar al umma akwai nagari, balle lalacewar ba ta kai lalacewa irin wanda muke zato ba. Ɗan aiki matsaltsalun suke buƙata kaɗan, da izinin Allah zamu samu sauyi. Mace tasan darajar kanta ta fuskar addini. Tasan iyakarta, tasan abinda yake hakkintane, tasan abinda yake ba hakkinta bane a aure. Sannan zama a tattauna matsala a tsakanin ma'aurata. Misali abu kaza da kaimun banji daɗinshi ba. Kema abu kazannan da kika ga nayi miki, abu kaza da kikai munne yasa nayi miki. To kowa ya fesar da ra'ayinshi, daga nan sai a ɗauki hanyar gyarawa. To rayuwar aure zata yi kyau. Samun rashin tattaunawa a tsakanin ma'aurata, yana taka muhimmiyar rawa wajen rugujewar auren baki ɗaya. Sai a rabu azo ana begen juna, sabida soyayyar akwaita ai, rashin zama ayi maganane. Ba rashin kunya, ko rashin biyayya bane yake sa mace tace da mijinta abu kazannan da kaimun banji daɗinshi ba. Asalima son zaman auren, da son zaman lafiya, da mutumta kai, da sanin ciwon kaine ke sanya haka, da sanin darajar kai. Duk kuɗin mace da iliminta, madamar bata san darajarta ba. Ba miji ba hatta ƙawa, ƙanne, abokan aiki, abokan karatu. Babu mai ganin darajarki, balle mijinki da zaku kwana ku tashi, yafi kowa saninki kuma. Haka macen da bata da ilimin, amman tasan darajar kanta. Tafi gaban wulaƙanci, ba a wajen miji ba a wajen kowa nake nufi. Allah yasa an gane hadafin. Idanuna da suke mun zafi kawai na lumshe jina nake da ace ina da iko dana zamema mata garkuwa ko da bazan iya cire dukka a matsalar gidajen aure da azzaluman maza ba, a ƙalla zan taimaka. Azzaluman maza nace, ba dukka maza ba. "Lallai iyayenki yarinya kiyi haƙuri basu san darajarku ba, haƙiƙa haihuwarku kawai suka yi. Kiyi haƙuri na shigar muku magana ba tare da an kasa dani ba. Amman sun saku a makaranta ta mahammadiyya da boko kuwa? " Cewar wannan Hajiya da muka zo muka taddata a sell ɗin. Kai na gyaɗa domin tayi mata tambayar da nima ita zanyi mata daman. Hajara ba Hajiya amsarta. Hajiya baki yi laifi ba ai ke uwace wala Allah zaki iya bamu shawara tunda Allah ya haɗamu. Kuma Allah shi yasan nufinshi na haɗamu. Komai na duniya yana da sababi" Hajara ta dubeta tace. "A_a bamu yi karatun boko ba, mun yi amman makarantar allo shima iyakar na sallah aka samu. Kasancewar mahaifinmu baya iya sauke nauyin ci, da sha, da tufatarwa, ga bashika da rikice_rikice da sukaima Ummanmu katutu a ƙoƙarinta na ganin asirinmu ya rufu, amman ina. Wannan dalilin yasa ta tafi ƙauyensu aka bata wani kaso daga cikin gadon iyayensu, ta kafa jarin sana'a. Wannan ta ɗauki kunun zaƙi, wannan ta ɗauki tallar shinkafa da wake, wannan ta ɗauki tallar dafaffen rogo, ni Awara nake soyawa a bakin kwatar ƙofar gidanmu a nan ɗinma muka haɗu da Figo, ya nuna yana sona a lokacin. Kuma ko danginshi bamu sani ba, yana dai da uwar ɗaki a garinmu, to amman da auren yazo yayyunshi maza biyu sunzo daga mai mujiya, shi ɗan asalin mai mujiyane. A kanon ma uwar ɗaki gsreshi." Allah mai iko da hikima, yanzu Hajara tallah kawai kika sani kuma a haka aka baki Figo ya tawo dake Kano, ba tare da an san danginshi ba, wannan wanne irin rashin gatane iyayenki suka gwadama Figo baki dashi, ai kusan sune silar halin da kike ciki ma. Shi figo dai bai riƙe ki da amana ba sam" Idanuna na kuma lumshewa ni wallahi zaman cikin wajen bai dameni ba kamar abinda iyayen Hajara suka yi ba. Na kuma fahimcesu su a ƙoƙarinsu na son ganin tayi aure asirinta ya rufu ne. Sai dai kash mama da Baba ba ko wanne aurene yake zama rufin asirin mace ba. Kuma juma'ar da zata yi kyau ai tun daga laraba ake ganeta. "Ai kuwa Figo dole ya dinga jibgarki iyayenki sun nuna mishi rashin mahimmancinki, duk shi yasa. Amman yarinya da kanki zaki tashi ki tsaya da ƙafarki ba da ƙafar kowa ba, ke zaki nema ma kanki gata ki maida kanki mai ilimi da sanin ciwon kai, da daraja kai. Ki tsaya kai da fata, kada ki sake bari yai miki irin wannan dukan. In bama zaki iya ramawa ba, ki gudu ko maƙotane, ki samu dattijan anguwa. In abu yaci tura sai ki haƙura. Namiji goma ba fa uba goma bane. Kin ganni anan? Nayi aure ɗai_ ɗai har goma da kike ji da gani, nayi digirin digirgir a harkar sanin maza, da harkar zama da kishiya, da harkar zawarci, da gogewa duka. Idan Allah yasa anan zamu kwana duka ni kuwa zan baku labarina kaɗan daku da masu karatu zaku ƙaru ko da babu yawa. Kuma Mahaifiyata ita ta ja mana komai a sakamakon talauci, mu namu ma bai kai irin na gidansu Hajara yawa ba, gasa da kishiyoyi kusan shi yafi yawa. Kuma duk macen da tayi aure domin abun hannun miji ta shirya ganin komai da komai. Duk namijin da aka aura domin kuɗi ya sani, bazai taɓa girmama iyayenki ba bare kuma ke, ba kuma zaki taɓa burgeshi ba. A zamanin da muke ciki mata ku tabbatar kun yi ilimi arabi da boko, ku tabbatar kuna sana'a ko aiki, ku tabbatar kun san darajar kanku, mutumta kai, ku tabbatar zaku iya rayuwa ba dole sai kun sa damuwar namiji a zuchiyarku ba. Ni dai daga mahaifiyatane laifin, da nawa kusakuran danai ta tabkawa. Ni da kaina na cuci maza, na zaluncesu basu suka zalunceni ba. Kinsan wani sa'in mu mata baki muka fi su. Jarabawa kam ina cikinta na alhakin mazajen dana zalunta. To amman Mazan zamaninnan da yawa zuchiyarsu a mace take murus, shi yasa ma suka rungumi tsarin hamsin_hamsin 50/50 wajen gudanar da rayuwar iyali, to kayi aikin ma, kayi sana'arma, ya kuka ƙare bare ana jibge. Babu laifi dan an taimaka ma miji, amman komai yana da iyakarshi, sannan ki dinga yi kina gina naki kan, da yaranki. Kuma duk abinda zaki yi, ko kike yi. Kada kiyi tunanin samun sakamako a wajen miji, kada kiyi tunanin hakan zai hanashi aure, ko ya hanashi ɓata miki ta ko wacce fuskar. Kiyi domin rabbil izzati, shi zai baki lada ba miji ba, shi dai albarka zai sanya miki. Dake dashi duk Allah kuke bautama, a wajenshi duk kuke neman gafara. Hajara iyayenki suka ja miki kamar yadda iyayena suka ja mun halin da nake cikinnan" Kunji wata sabuwa kuma ko ohh ni Hindu duwaf. MIJINYAWA:. Da sallama ya shiga cikin gidan da yake jiyo hayaniyar Nanno kusan tun daga get. Dawowa suka yi suka zauna? Shi dai yasan tace zasu biya a ɗauki Musa, dalilin daya kashe ma Azgar makaranta ma kenan. Idanu ya lumshe kawai bashi da yadda ya'iya, amman dama yasan tunda aka tawo da Yaya Jamila kuma suka ce anan zasu sauka to dole yasan da matsala, duk da zaman nasu bai yiyu ba, ga yadda aka kwashe, yaci ace basu ma kuma waiwayen gidan nan kusa ba. Duk damuwar da yake ciki tuno Hindu kawai, da rayuwar baya sai hakan yasa ya saki guntun murmushi duk da a cikin wata matsalar yake babba a wajen aiki. Amman a wajenshine hakan yake matsala, a ƙa'ida da dokar aikin banki ba matsala bane, kuma ba yau farau ba Hindunshi iya rigima kawai yake ji. Murmusawa ya kuma yi. Rayuwarsu ta baya tana burgeshi, yana kewa. Yana shiga ya tadda Nanno a babban falo, ita dasu Yaya Jamila da matan su Gambo. "Lafiya Nanno ashe baku tafi ba. Ai ni na ɗauka yanzu kun kama hanyar jama'are. Kuma baki da ishasshiyar lafiya, tun daga waje nake ta jiyo muryarki fa?" "Ya ba zan yi magana ba mijinyawa Hindu fa tunda ta saka ƙafa ta bar gidannan Musa yace sun duku_duku har yanzu bata shigo ba. Ƙarfe nawa yanzu nace ko a can take kwanane?" Agogo ya duba shida saura yasan duk yadda akayi tana hanya wani abunne ya riƙeta, wani sa'in tana kaiwa magriba, isha. Amman misali Uwatale da take aiki a asibiti, ai ta saba yin aikin kwana kuma bai taɓa zama matsala ba. Muryar Yaya Jamila ce ta dawo dashi daga tunanin da yake yi. "Kiyi haƙuri Nanno tana hanya duk yadda akayi wani abunne ya riƙeta. Amman zata dawo ne. Yaya Jamila ai naga zata iya girka muku duk abinda kuke son ci, ga matansu Gambo ma, naga ga kuloli alamun sun kawo miki abincine. To in kunci sai muje in maidaku gidan Mijinyawa Babba" "E ai dole kace gani sa'arka zan shiga Kicin ɗin matarka mai shegen raini da girman kai, da take mana gadara da dukiyarka, dan wallahi ƙarya kuke yi da akace wai nan gidanta ne. Kace dai gida ka siya mata da kuɗinka, akasa sunanta a takaddun gidan. Sannan ni jinyar Nanno nake yi babu Kicin ɗin da zan shiga dole itan zata dawo ta girka wallahi" Kafin yace wani abu Nanno tace. "Kai mun shiru akan macen da yara biyu jol ta haifa maka kake wannan abun baka da aiki sai bin bayanta, da kakkareta kai ga majanunin sonta ko? To ita dole zata girka mun abinda zanci. Nan fa gidan ɗanane, babu wata suruka data isa hanani zuwa wajen ɗana, ba'a yita ba. In iska take taƙama dashi, ga matar Gambo nan itama tana da makaran. Uwarta ma magani take bayarwa ƙarke kenan. Jibeka duk yadda ka lalace, ka rame, fuskarka tayi fiyau sabida rashin kwanciyar hankali. To ba'a barka haka ba nayi_nayi ka sake wani auren kaƙi. Ko jiyannan sai da mukai waya da uwar yarinyarnan Asama'u har yanzu da ƴar da uwar suna fatan aure ya sake haɗaku ko da gabane, in tayi wani auren ta fito. Mijin uwar ya ba ita Asama'un ɗanshi babba ya aureta yanzu yarinyarnan da ace Hindu bata shiga ta fita ba da yanzu ta haihu ƙila harma da wani cikin" Ta dinga maganganun da a matsayinta na uwa bai kamata sam ace tayi ba. Uwatale, da mijinyawa Babba daya dawo bayan matarshi, su suka zuga su Nanno akan dole su dawo. Kuma su nuna ma Hindu iyakarta. Uwatale ta dinga zigi da sharri, shine dalilin dawowarsu, basu zo domin su tafi yanzu ba ma. Illahirin kunya, babu shiri ya sauke kanshi ƙasa yana saita nunfashinshi a hankali, dan har kanshi ya soma ciwo. Sum_sum_sum ya fice daga ɗakin ba tare da ya waigo ba. Ɗaki wajen Azgar ya leƙa yana ciki yayi tagumi akwai abunda ke damunshi, yana da nasaba da taɓa uwarshi da akayi ƙur Mijinyawa yayi mishi. "Sannu da dawowa Abba" "Azgar tunanin me kake yi haka? " Ɗan murmushi yayi ma uban, shima ya ɗan murmusa kaɗan. "Babu komai ina ta kiran wayar Ammi bata ɗauka nasan ma tana hanya duk da sai faɗuwar gaba nake yi" Shiru mijinyawa yayi ya ɗan yi jim kana yace. "Babu komai yau garin akwai go slow sosai, babu mamaki itama shi ya riƙeta kaga nima ai na jima. Sabira fa? " "Tana ɗaki abinci ma taso ta ɗaura kamar yadda muka saba, Nanno ce ta hana ta shine ta koma ɗaki." Kai kawai ya girgiza ya saki ƙofar ya juya ba tare da yace da Azgar komai ba. Ɗakin Hindu ya tura yaji a rufe ɓam dole ya dawo wajen Azgar yana tambayarshi kin ɗakin Hindu, anci sa'a yaron yana dashi ya zaro ya miƙa mishi. Yana shiga ƙamshinta na asali ya doki hancinshi duk damuwowin dake kanshi saida yaji wata nutsuwa a jikinshi. Ko'ina fes komai na zaune a muhallinshi, ɗaki kamar zangon baƙi. Kayanshi ya rage ya shiga banɗaki yayo wanka tare da ɗauro alwala dan lokacin sallah ya kusa, yana ta adda'ar kar ta dawo ta ruskeshi. Kewarta ke cin rayuwarshi kawai. Shi ya amsa yasan yayi laifi, kuma yasan halin abarshi. Amman sam baisan haka fushinta zai jima ba. Yana fitowa ya shiga kiran wayar Hindu gashi dai tana shiga amman ba'a ɗagawa daga ƙarke ma sai yaji wayar a kashe, da gaske bai yi zargin komai ba dai har suka je sallah suka dawo. Ya tarar da Nanno na kiran Mijinyawa Babba akan ya tawo ya kawo musu abincin dare. Matan su Gambo basa nan sun riga sun tafi kafin magriba. Sai lokacin jikin mijinyawa ya soma bashi ya shiga kiraye kirayen waya sabida wayar Hindu a kashe take. Duk inda yake tunanin zata je saida ya kirayi lambobinsu amman bata nan har akayi isha suka dawo, kira kawai yake yi, su kansu Yaya Saratu sai hankalinsu ya tashi sakamakon a tsakankaninsu ma sunyi waya da juna babu wanda ma yace ya ji muryar Hindu yau, ga gidansu Baba Sojanmu cike da Jama'ar bikin Salamatu, ƴan nesa duk sun zo. Mijinyawa ba shiri ya fice a gidan ya hau titi sai tuƙi kawai yake yi, yama rasa inda zaije gashi yana ta kiran wayar Luba taƙi ɗagawa kiran daya sake mata na ƙarshe bayan fitiwarshi ne yasa ya karkata akalar motarshi zuwa gidan Luba kai tsaye. Ga tunanin irin fitinar da Uwatale da Yaya Jamila suke kunna mishi a gida. Abun ya isheshi ya fita kanshi, nanno uwace babu yadda zai yi da'ita. Ita da gasken gaske take yi, gani take yi tamkar an shanyeshi. Uwatale itace babbar munafukar dake kai dukkan rahoto, a yanzunma bata bari Hindu ta huta ba. Yanzu in Hindu ta dawo ta tadda su Nanno baisan ya zata kaya ba. Kuma bazai taɓa iya korarsu ba uwa ba abun wasan yaro bace, duk rashin gaskiyarta, duk faɗanta kuwa, ita anan gani take yi iyakar soyayyar da zata nuna mishi kenan. Ko da tasan gaskiya ta take, bashi da yadda zai yi da Nanno, gida ko ba nashi bane, tunda Hindu har gobe, da gaba da abada matarshi ce, dole su Nanno suna da alfarma a wajen Hindu ko da sun rabu, ɗan alkhairi ke rama sharri da alkhairi. Da waɗannan tunani tunanen, da batun wajen aikinshi ya iso ƙofar gidansu Luba. A ƙofar gidan yaci karo da Sunusi. "Ahhh ahhh wa nake gani yau kamar dai Magawata? Allah mai hikima kaddai har sun faɗa maka na samu ƙaruwar ƴan biyu ne, kazo mun barka? Ƴan biyu kyautar Allah, kai da yake biyu ne kai zaka gane. Kaga yanzu haka ma kayan shayi zan siyo ma ita mai jegon, kai ka shiga ciki Luban ma suna tsakar gida" Sanusu bai ba mijinyawa damar cewa uffan ba ya wuce yana zumuɗi da zakwaɗin ƴan biyu. Kai mijinyawa ya girgiza yayi shiru a tsaye a wajen, yana tuno irin soyayyar da Luba suka buga da Sunusi. dama akwai wata haihuwa da za'ayi mishi ko da ta ƴan huɗu ce da zaisa ya mance da farin cikin samun ɗanshi na farko a duniya da Luba? Ko da yake gara shi, murnar samun ƴan biyu yake yi. Ni nawa laifin ai babbane, na aikata wauta, kuskure mafi girma da muni. Zuchiyarshi ce tayi magana a madadinshi. Mijinyawa yana tsaye yana karanta wasiƙar jaki har Sunusi ya dawo da leda mai zane zane a hannunshi. "Baka shiga ba Magawata kana ta tsaye? " "Bai dace ace in shiga kai tsaye ba tare da kayi mun iso ba, wannan dalilin ya hanani shigar. " To to mu shiga taren babu damuwa ai gidane" Sanusi yana gaba mijinyawa na biye dashi a baya turyan_turyan har ɓarayin Luba, suna tsakar gida ita da yaran suna cin abinci. Dama tasan ƙarshenta sai anyi haka tunda taji kiran Yaya Saratu da Innarmu suna tambayarta game da Hindu, ga mijinyawa shima ya biyo sahu. "Mijinyawa kaine a tafe da darennan? " Cewar Luba dake gyara zaman kan Hijabinta. Farar kujera ta nuna mishi ya zauna. Yaran suka shiga gogoriyo wajen gaishe da Abban nasu, yana amsawa ɗaya bayan ɗaya da kulawa. "Sai ka fito Magawata in ka fito ma shiga kaima Amarya barkan ƴan biyu" Luba ta ɗago ta zuba ma Sanusi idanu, a yayin da mijinyawa yake karantarsu du su biyun. Sanusi bai sake cewa uffan ba ya nufi hanyar fita. "Ku je ciki ku ƙarashe cin abincin ina nan zuwa" Sai da yaran suka watse mijinyawa yace. "Luba Hindu ba zata taɓa yin wata tafiya ko ta aiki ko na raɗin kai ba tare da ke kin sani ba. Kima Allah ki sanarmun ina Hindu take, kuma ina fatan ki faɗamun gaskiya sabida girmanki da nake gani, sannan ina fargabar kice mun Hindu ta fice daga ƙasar sabida bani da kuɗin binta zuchiyata ba zata kuma jure rashinta na lokaci mai tsayi kwatankwacin lokacin data shafe a waccan tafiyar ba. Luba ki riƙe mun mu shawo kan Hindu ta yi haƙuri mu dawo yadda muke da dan Allah. Nasan kin fini sanin kafiya da taurin Hindu Luba. Amman ta wacce hanyar zamu bi mu bata haƙuri ta haƙura ta bani dama ta biyu? Alkhairanta a rayuwata da yawa, da ba Hindu cikin Rayuwata da yau bansan inda nake ba, bansan yadda rayuwa ta kaini ba. Duk wani matsayi ko ko matakin rayuwa Hindu itace tsanin da na hau ta cicciɓani. Luba munyi rayuwa da Hindu a ƙauye irin rayuwar da a sanin da naima Hindu ko zata labarta miki ba zata iya labarta miki duka ba. Hindu ta jure babu, ƙorafi, babu nuna gajiyawa bare sarewa. Luba ina son mu ci gaba da rayuwa da Hindu rayuwa ta gaba da abada, ma'ana har a cikin aljannah ta zama shugabar matana. Sam ba gazawa bane namiji yaima matarshi laifi ya nemi tayi haƙuri ba. Hindu ta taka rawar da mata dubu basu taka a gidajensu ba, kuma ba zasu iya takawa ba abadan. Macece mai tsoron Allah, tsusayi, riƙon amana, riƙon sirri, mai so domin Allah, mai sadaukarwa dominshi. Luba ni kam ki taimaka mun ki bani satar amsar yadda zan shawo kan Hindu" Shiru yayi kawai yana sauke ajjiyar zuchiya yanayinshi take suka sauya. Luba tayi shiru to ita yanzu ƙaƙa zata yi Hindu tace kada ta faɗa ma Mijinyawa inda take, ta kuma san halinta sarai. Shi kuma gashi yazo ya cikata da tausayinshi kana ya ɗaɗɗaureta da jijiyoyin jikinta. Mrs Bukhari Mu kwana anan sai kuma gobe in Allah ya kaimu.TSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA SHA UKU (13) Aimun afuwa na samu kuskuren lambane, nayi lamba ta takwas har sau biyu, jiya lamba ta sha biyu ya kamata in rubuta saina rubuta lamba ta sha ɗaya Afwan dan Allah Ajjiyar zuchiya Luba ta sauke tare da cewa. "Haƙiƙa nasan inda Hindu take mijinyawa, amman kayi haƙuri zuwa gobe zaka ganta ta dawo gida wani ɗan abune ya taso kayi haƙuri, amman tana ƙasarnan cikin garinnan namu mai albarka na Kano" Ɓoyayyar ajjiyar zuchiya ya sauke yaji sanyi mamaye da zuchiyarshi jin Hindu na ƙasar cikin garin. Amman haƙiƙa ya zame mishi dole yasan inda take me kuma ya faru. "Dangane da taimakon ka da kake son nayi dan taya ka shawo kan Hindu, a gaskiya ni shawarata anan shine ka ɗan nesanta da'ita, ka bata waje ta sha iska sai inga kamar zata yadda tayi haƙuri ta yafe maka, kuci gaba da zumunci. Mijinyawa bari kaji kaganni ko nice Sunusi yayi mun irin abinda kaima Hindu, ta reni ɗiya ka aureta a ƙarke, to na gama auren dashi abadan. Abune mai wuya Hindu a irin sanin da nai mata ta yadda ta zauna dakai a gaskiya. Amman ka jarraba bata iska. Wannan dai shine". "Luba ki yi ma Allah, domin darajar Allah ki sanar dani ina Hindu take a wanne halin take? Na roƙeki dan Allah. Sannan in bata waje zai sa ta sakko, Luba a shirye nake, dama nayi tunanin hakan ko dan in sama mata farin ciki ko dan sabida su Nanno, ke kinsan abubuwa da yawa ai. Amman Luba ni ɗin komai zai iya faruwa dani. Ki gane Hindu tayi mun irin sadaukarwar da ko Nanno a girmana dai ba zata iya mun ba, ballantana ƴan uwana. Akwai dalilan da yasa lallai na damu da rarrashinta, nake son ta haƙura Luba. Allah shine shaidata inna haƙura na biye ma Hindu muka rabu, Luba nayi mata zalunci mafi munin zalunci. Kinsan abubuwan data sadaukar domina kuwa? Ko da yake ku kun ɗauka tamkar maza basu san ai musu karamci ba ko Luba. A tunanin mata da yawa namiji ba ɗan goyo bane ba ko Luba. A tunanin da yawan mata mu azzalumaine waɗanda kawunanmu kaɗai muka sani ko? Wallahil azeem ba haka bane, ba haka muke ba jostis fo rijalu Luba. Duk ɗan halak yasan halacci, duk ɗan halak ɗin da matarshi ta sadaukar dominshi Luba ya sani. Kuyi kwalliya dominmu mun sani, kuyi girki mai daɗi dominmu mun sani, ku yi cikon cefane mun sani, kuyi kitso ko ƙunshi mun sani, duk abinda mace zata yi dominmu idanunmu yana kai. Kuma tana tarin ɗunbun ladanta ita a wajen Allah. Wallahi firejar aikin yau da gobe ke sa wasu mazan da yawa kauda kansu, badan basu gani ba, ba dan basu yaba a zuchiya sunji daɗi ba. Firejar tana da yawa. Wani daya shigo gida dukkkanin wata gajiya sakko mishi takeyi Luba. Wani ma magana wannan baya so ai mishi sai ya huta, kanshi ya ɗauki caji, kune kaɗai kuke iya saukemu fa. To a cikin mata na faɗa na kuma Hindu ta dabance. Ko wanne namiji tai mai sadaukarwar da tayi mun, bazai iya rabuwa da'ita sasakai ba wallahi. Ta wuce ƙashin yadawa." "To Mijinyawa duk kasan da haka me yasa ka auri Asama'u? Ka gane ba ƙarin aurenka bane ya zama matsala a garemu ba. Wacce ka aura itace matsala. Haba mijinyawa ai ana barin halas dan kunya. Ko da yake wannan karatun malamai sunce kuskurene, kuma a wajenku kuskurene. Bazance Hindu ɗari bisa ɗari take ba ajizace. Amman ƙoƙarinta ba duk kai ba. Bazance zata zame maka uku a ɗaya ba ta yadda zaka kauce ganin wasu matan ba, ko aurosu ba, itama bata jayayya da ikon Allah. Macece mai tawakkali, da miƙa lamuranta ga rabbil izzati. Amman in zaka auro mace sai ka auro macuwat wacce zata dace da Hindu, azo a buga a kwashe, wacce ta biya allonta sai ta wanke. Sabida lokuta da dama yaran matan duk bulace, a waje dai soyayya ƙaƙas, yarinya data soma haihuwa fa magana ta ƙare." Murmushi yayi ya dubeta. "Luba ki bar aikin ƙaddara. Kuna wasa da ƙudurar Ubangiji, da kuma rubutaccen al'amarin Ubangiji. Ke dai nayi kuskure kuma ɗan ba ƙara" "To shikenan rubutaccen al'amari ba? Hindu tana ofishin ƴan sanda a kulle. Sanadiyyar taimakon wata baiwar Allah da tayi. shine mijin ya haɗa harda matar tashi ya kullesu. Wayarta na hannuna motarta kuma tana wajen aikin mu. Kayi haƙuri itace ta buƙaci bata son a sani ciki harda kai. Kaga abinci na tusa a gaba amman wallahi sam na kasa ci tunaninta kawai nake yi" Kai ya dafe yayi shiru na lokaci mai ɗan dama. "Nagode Luba zanje in sameta mu yi magana, dana sani da wuri ai ba zata kai haka a kulle ba." Yana kaiwa nan ya fice da sauri lo bi ta kan Sanusi bai yi ba ya shige mota, sai ofishin ƴan sanda na wajen. Da sallama ya shiga ya sanar dasu wacce yazo gani,ƴan dokar suka shaida mishi dare yayi sai dai gobe ya dawo. Ya buƙaci belinta ma shima suka ce gobe ya dawo bazai gagara ba duka. Yana ji yana gani, ya baro ofishin ƴan sandan da zummar asubar fari ma a wajen zata yi mishi a bashi belin matarshi, inma kotu za'a shiga koma menene shi zai ɗauki sintirin yi da kanshi. Abinci ya siya musu na mutum biyar harda nama da ruwa. Nanma saida yaita roƙo suka amince zasu miƙa ma su Hindu abisa sharaɗin sai yaci a gabansu sun gani kamar yadda ƙa'idar take, haka dole ya ci loma ɗaɗɗaya ya kama loma biyar, kafin suka amince suka kaima su Hindu wannan abinci. Yana hanyarshi ta komawa gidane Mijinyawa Babba ya kurawo wayarshi idanu kawai ya lumshe tare da ɗaga wayar. "Ina kuka shige da kai da matar taka Mijinyawa? Gani a gidan naka na kawo ma su Nanno Abinci, yanzu iriyar rayuwar da kuka zaɓama kan ku kenan aikin jarida haukane dama bamu sani ba? Kuna ina yanzu nace? " "Ina hanya na kusa isowa." "Ita kuma Hindun fa shafaffiya da mai?" "A_a Mijinyawa kar muyi haka da kai. Kai ka sani bazan taɓa aibata maka matarka a kunnenka ba, ko da kuwa mai ta aikata maka kuwa. Bai kamata ka biye ta su Yaya Jamila kaima ka shiga gaba a sahun masu kushe mun mata ba. Yana da kyau ku san bafa haifata kuka yi ba. Ya kana neman zaƙewa da yawa, sabida munafukar matarka tayi maka huɗuba ko" "Yayi daidai" Cewar Mijinyawa babba. Mijinyawa yace "Ƙwarai kuwa yayi daidai, yadda kake jin Uwatale a ƙoƙon ranka, ina jin fiye da haka a kan Hindu. Wai me Hindu ta tsare muku ne da kuka tsaneta? Kuma abu mafi zafi ace harda abokin tagwaitakata. Ko da yake matarka kake biyema shi yasa duk kabi ka sauya mun. Amman ni da kai mu zuba in dai akan Hindu ne. Inna ƙyale su Yaya Jamila, da Yaya Zakiya wallahi bazan ƙyaleka kana sakona kaci kashi akan matata ba. Turar kowa ta kaini bango, nagaji abu kamar cin ƙwan makauniya" Sai jiyo kukan Nanno yayi gami da salatinta tana ambaton "Ɗan uwan naka wanka kake caccaɓama magana, akan wannan baƙa gajeruwar matar taka, wacce yara biyu kaɗai kuka haifa baku haifi duniya ba? ". Wayar ya kashe yana ji tamkar ya ciro zuchiyarshi ya yayyafa mata ruwa tsabaragen zafin da take yi mishi, abu ya gwale mishi goma da ashirin cikin taimakon Ubangiji ya samu ya shigo gida dan gabanshi wannan dishi_dishi yake gani tsabar fireja. A tsakar gida yaci karo da mijinyawa Babba da Gambo. Ƙarasowa yake son yayi su gaisa da mijinyawa, amman shi yinƙurin ficewarshi yake yi, yayi mishi banza kamar bai ganshi ba. Bai daddaraba yaje gabansu tare da miƙa mai hannu bakinshi ɗauke da sallama. Ya dai amsa mishi sallamar hannun dai bai miƙa mishi ba, haka suka wuce suka barshi saroro a wajen. Cikin gidanma babu daɗi nanno tafi awa guda tana zazzaga mishi ruwan faɗa, Yaya jamila tana sake ingiza lamarin abinka da ɗa da uwa sai ta sassauta da taga yadda duk ya birkice idanunshi suka sauya launi. "Kiyi haƙuri Nanno laifin nawa ne shaf na mance Hindu ta faɗamun zasu yi wata ƴar tafiya daga wajen aiki, har saida na kirata a waya tukunna na tuno" "To shi fitar da kayi ka jima aina zaci nemota kaje yi. Matarka ta bar gidan dai sabida zuwanmu ƙiri da muzu Hindu ke nuna bata son mu raɓeka, tabi dukiyarka duk ta handame tayi kane_kane har umara Hindu taje da kuɗaɗenka kai baka je ba, ni baka kaini ba bare ace na neman ladane ko, amman ita shafaffiya da mai har mota ka sauya mata ayi magana kace ita tasiya da kuɗinta alhalin uwatale ta faɗamun ma'aikatan gidajen rediyo albashinsu bai kai ma nasu Uwatalenba su ma'aikatan jinya ba. Ita uwatale banga ta sai mota ba, banga taje umara ba ko suturar da take sawa bata kai ta matarka ba ai. Dan ko ranar da muka zo, wannan yarinyar tace mun zinare ne a kunnen matarka, atampar jikinta mai tsadar gaske ce. Wallahi Mijinyawa kaima kanka karatun tanutsu ka kiyayi duniya, ka kiyayi matarka. Uwatale tayi gaskiya" Kasa cewa yayi uffan. Dama yasan Yaya Jamila da Uwatale su suke sake cusama Nanno ƙiyayyar Hindu, ta hanyar farfaɗa mata ƙarairayi da gaskiya bai ɗaya. Haƙuri yaso bata amman ta hanashi, hanyar waje ta nuna mishi bai musu ba ya fita kanshi na sara mishi tamkar zai tarwatse. A daddafe ya duba su Azgar ya tabbatar sun ci abinci kafin su kwanta dai ko. Kana ya shaida musu Ummansu tayi tafiyane amman ba zata wuci gobe zuwa jibi ba zata dawo. Ya umarci yaron da yayi ƙoƙari gobe in su Nanno sun tafi, ya haɗa mishi duk kayayyakinshi a akwati, ya ɓalle gadonshi ya jingine mishi. Abinci Azgar ya taso ya bashi a tire shayine mai zafi da jallof ta taliya mai bushasshen kifi. Godiya yayi ma yaron ya shige ɗakin Hindu, tare da rufo ƙofar😆 HINDU: ofishin ƴan doka. Bayan mun gama ta'ajibinmu na labarin Hajara. Da lokacin sallah yayi na magriba a cikin wannan sell mai cike da zarni da ƙasanta, cikinshi duk mukai sallah ko wacce ta shinfiɗa ɗankwalinta. Na zauna ina lazimi har lokacin isha yayi, na ta da kabbarar sallah na yi wani irin jimawa a sujjada ina ganawa da Ubangiji na ina kai mishi ƙarar tozarcin da Figo ya tasanma yi da kuma ƙazafin da yayi mun, ina so zan nemi hakkina ta fuskar shari'a domin bazan yadda da ɓacin suna ba a matsayina ta mace kana uwa, kuma madubin mata da dama. Wai da zaran mace ta yinƙura a arewa domin kawo wani sauyi, shikenan bata tsiraba matan ƴan uwanta iyayen hassada da shegiyar ƙeta, sune sahun farko wajen kusheta da yayata farfagandar kwangila ta karɓo a hannun turawa. Maza kuma su tsoronsu kada a ƙwace musu ƙarfinsu mata su samu wayewa da muƙami su fito a dama dasu. A matsayina ta mace musulma, na tashi na ƙwana da sanin kome mace zata yi namiji na gabanta, domin Allah subuhanahu wata ala shiya ɗaukesu ya sasu a gabanmu domin su zame mana wani garkuwa, ita mace a halittarta bama a yita domin shan wahala ba, Musulunci ya gatanta mace gaya. Namijine aka yoshi da ƙirar gwagwarmaya, da faɗi tashin neman na tuwo, da ganin ya gina ahalinshi sun samu tsayuwa da kyau, sun samu dukkan abinda akeso. Ya haɗa da yaran, da matan aurenshi ya rungume ya musu tarbiyya mai inganci. Ni kushen maza baya gaba na sam, kushen mata yafi damuna gaya, amman ita mace ƴar son kaice, itama fa mace ƴar dama nice wance ce. Shi yasa duk abin a yaba da ƴar uwarta mace zata yi, in ba zata iya wannan abun ba, sai ta shiga kushewa da lalata abun, hassada da ƙyashi sun cika zuchiyarta fal. Akwai wacce a kwamen sakshan ta rubutamun wallahi na tsani matarnan, mugun haushi take bani sai shegen gajarta kamar turmi. Ke me ya kaita kallon aikina, in ba sha'awar dama itace ba? Ina fatan kun gane wannan karatun. Bayan na idar da sallah sai na miƙe na basu dama sukai sallah ɗaya bayan ɗaya ɗaki ba girma gareshi ba, tsukukune a takure muke sosai ga sauro sun soma farautar jininmu ɓula_ɓula dasu. Wata ƴar sanda ce ta zo buɗe wata mata da suke cikin sell ɗin dake kusa da namu. Magana nake son nayi mata akan abinci ko Hajara zata samu taci ta sha maganinta, amman bansan ya tsarin nasu yake ba sai kawai nayi shiru. Allah cikin ikonshi sai ga wata ƴar sanda da kular abinci ta sulba mai hannu ɗinnan ta buɗemu tace. "Hajiya ga abinci inji Alhaji Salmu yace a baki" Da mamaki tace. "Alhaji Salmu kika ce fa?" Bata kulata ba ta dure abincin tare da mayar da ƙofar ƙarfe mai huji huji ta rufe tayi tafiyarta. "Ke Hajara tunda ba daɗi kike ji ba kici abincin sai ayi musu magana su baki maganinki." Jawo kular nayi gaban Hajara ina ma Hajiya godiya. Na buɗe tuwone na shinkafa da miyar kuka taji ɗanyen kifi sosai ga man shanu. Amman Hajiya tuwon yayi mata yawa guda biyu ne manya ko zaki ci ɗayan? " "To saka mun a murfin kular ma ya isheni' rabi zaki saka mun kuma ku lasa zaman duk na haƙurine." A murfin na zuba ma Hajara malmala ɗaya na zuba ma Hajiya a abun miyar rabin karin na saka a cikin kular na tsiyayama Maman Junaidu miyar, duk na mimmaƙa musu na miƙe ina buga ƙarfe da sunan neman agaji. Ƴar doka ce ta ƙaraso. "Ya dai Hajiya kuna buƙatar wani abunne? " E dan Allah akwai maganin Hajara a kan kanta lokacin shan maganinta yayi sannan muna buƙatar ruwa" Jim tayi tace. "Bata da lafiyane kuma aka kulleta? " Murmushi nayi kawai, na fahimci masu aikin dare ne su, dan duk bamu gansu ba ɗazu. E bata da lafiya daga asibiti ma aka sallamota amman kin ganta anan" Na gifta ta leƙo ta ganta babu yadda take abincin ma taƙi ci sanyi take ji sabida a tantagaryar ƙasa muke ga kuma ya haɗa da mara lafiya. "Zan kawo mata maganin Wacece Hindu a cikinku? " Nice Hindu' Ƙofar ta buɗe ta miƙo mun leda nasa hannu na amsa ina tunanin Luba ce ta aiko sai kawai tace. "Mijinyawane ya kawo yace a baki" Tana kaiwa haka ta kulle ƙofar ta juya. Mamaki ya kamani, a hankali na ajjiye ledar abincin ina tsaye harta kawo magungunan na karɓa na ɓaɓɓalla ta wuce da sauran, da fiya wata guda ɗaya tak. Hajara daure ki cinye tuwon ki sha magani. Ga wani abincinma an kawo bari in buɗe ko zai baki sha'awa. Saifa kin zama jaruma Hajara ki zage a ƙwatar miki ƴancinki in kuma kinsan kin zaɓi rayuwar gidan mijinki duk wuya in zame hannuna tun wuri. Bance ki kashe Auren ba, a dukkan bayananki ai ya nuna kina son Figo. Amman ayi muku iyaka ayi a rubuce ba zai kuma bugunki ba, shi nake nufi." Na ƙarashe maganar raina a ɓace, tare da buɗe ledar abincin a roba biyar aka zuba, na ba kowa roba ɗaya, ɗayar na ajjiye in da mai son ƙarawa. Shinkafi ce da miya da nama manyan yanka bibbiyu. Hajara tuwon taci ta sha maganinta ta takure waje guda na rufeta da mayafina, dana roƙa aka miƙo mana mu kai sallah. Maman Junaidu kuwa bata ko iya magana sauro kamar ya jamu ya fitar damu waje sabida yawansu da girmansu. "Hmmm nace zan baku ɗan labarina domin ku tsinci darasin da zaku tsinta marasa anfanin ku watsar tare da su Jamila tsafe da Mamanzee, da su Munira, da Umminmama, da fulani, da Maman Daddy. Kun ganni kyakkyawa fara tas ga kalangu a gefe da gefen fuskata, wanda mutane da dama suna faɗin basu taɓa ganin wacce kalangu ya zauna ya zame mata ƙarin kyau kamata ba. Allah ya yoni da farin jini duk da bai kasance daga Allah ba. Mahaifiyarmu ce take karɓo mana rubutu na farin jini a wajen wani tsoho, muna sha tun muna yara, da kwallin idanu, da turaren gogawa a goshi na farinjini. A bisa dalilinta guda ɗaya zuwa biyu. Dalilin farko burinta mu huta mu auri masu kuɗi, mu miƙe ƙafa mu kula da'ita. Dalilinta na biyu shine tana so kamar yadda mata biyu daga cikin ɗakin Yadikkonmu wato Matar Babanmu suka auri mazaje masu kuɗi hamshaƙai, suka samu duniya suke juyata a tafin hannunsu muma mu samu. Sun yi aure muna yara kasancewar su aka soma haifa sune manya ita babbar yayar tamu ma Hajiya Kulu a Dubai sukutum suke tare da mijinta da ƴan yaranta. Ta kai mahaifiyarta, umara, ta kaita aikin hajj. To a lokacin suna ma mahaifiyarsu hidima gaya saita fito tsakar gida tai ta nunawa kishiyoyi da fariya, kasancewar mahaifinmu malam Baballe Baduku matan aurenshi huɗu, yama rabu da kusan mata goma akace ma'ana yayi aure aure sosai kafin dai ya haƙura, sakamakon tattalin arzikin nashi da ya ƙare kab ta dalilin aure aurennan da yaita fama dashi. Wannan kenan. to ita uwa abinda kullum take faɗa kunnen yaro yana saurare inma jariri inma yaro zaku ga ya taso ya tasirantu da wannan abu, ba tare da shi kanshi yasan yadda akayi ba. Abinda ya faru damu kenan musamman ni da nake ganin nafi sauran ƴan ɗakinmu diri da hasken fata. Kacokan sai Ummanmu hankalinta yafi karkata a kaina fiye da ragowar ƴan uwana. Mu mu shida ta haifa mata mune manya, sai maza huɗu ƙannenmu. Amman duk wannan abun fa iyakar karatunmu sakandare ce, mahaifinmu ma a iyakar firamare ake tsayawa da karatun. Iyayenmu mata ke idasa ragowar aikin har mu kammala sakandare. Mun taso cikin wata iriyar wayewa ta ban mamaki gamu da son maza masu mota mun raina samari daidai da ƙarfin gidanmu, yankinmu. An ɗauramu a gwadaben son maza masu kuɗi. A haya yayarmu ta auri wani mai ɗamara akayi gagarumin biki na alfahari da nuna ma kishiyoyi muma mun isa. Haka lamuran cikin gidanmu yaci gaba da tafiya mahaifinmu bai san wainar da ake toyawa ba da safe ya fita, sai dare zai dawo a gajiye hutawa kaɗai yake buƙatar yi, da safe muka fi haɗuwa dashi gaskiya sabida baya dawowa da wuri. Bayan auren Kande da shekara biyu taje hajji taje umara har tana tuƙa ƴar motarta ta zamanin. Sai nima Allah ya ɓullomun da mijina Alhaji Sango ɗan canji ga kuɗi ga kyau mukai aure muka tare a gidanshi dake birget. Rayuwa mai aminci, gida na alfarma katafaren gaske. Sai dai kash jarabawar data faɗomun shine ashe Alhaji Sango matsolone mai kuɗin lugudi naje na taddashi da matan aure biyu dan ba yaro bane. Sutura ma su ke yima kansu, yaya kuke ganin za'a wanye dani da mahaifiyarmu lafiya ni da mu kai auren domin abin hannunshi? " Shiru tayi tana dubanmu ɗaya bayan ɗaya ido a cikin ido. Murmusawa tayi kana tace. "Mama da taji shiru wata ɗaya da aure babu wani motsi ina zaune ko a safiyar ranar munyi rikici dashi na ban mamaki akan biredin nera hamsin da yake siyamun, a ranar yake cewa shi ya gaji da sarama kare ciyawa, ni gashi ko garar da ake kawo mace daga gidan iyayenta banzo dashi ba. Yai mun tatas yana ɗaga murya matanshi sarai suna ji. Ni gashi wata ɗaya nayi bare ince gishirine ya sire akan kaza, amman inna tuno a shimfiɗa yadda yake yabawa sai in ji dama_dama, domin a lokacin da gaske ina sonshi sai dai bana jin tafiyarmu zata iya nisa da wannan mammaƙon nashi. Burina in mallaki manyan kuɗaɗe masu kaurin gaske. Katsaham sai ga Mama tazo gidana tare da Yayata dake Aure a Abuja, tunda dai tazo biki bata koma ba, na rasa yadda zan tsomasu dan murna amman fa jikina har rawa yake yi sabida bansan ta ina zan soma labarta musu halin Sango ba. Abinci na girka na kawo musu babu kifi babu nama babu lemo ƙasa kamar ta tsage in faɗa dan kunya. Sabida yadda na ciccika baki, nake da dogon buri kuma. Ɗan kwali Mama ta turo gaban kanta tace. "Kan Uba Bibalo me nake gani nan kin kawo mana shinkafa ce tsurarta daga magi sai mai sai kayan miya, ba kifi ba nama ba ko ƙwai?" Nan Mama da Yata suka shiga kallon kallo, suna rarraba idanunsu a kaina Mrs Bukhari Mu kwana anan, sai in Allah ya kaimu gobe kumaTSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA GOMA SHA HUƊU (14) https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl?s=cl&p=a&ilr=1&amv=1 ✨ DA YAWA SABABBIN KWASTOMOMI SUKAN TAMBAYA... ✨ "Shin kayan naku suna da kyau kuwa?" Amsarmu ita ce: Ku gwada sau ɗaya, ku zama shaidun ingancinmu. 🥰 A HAFSAT COLLECTION, muna kawo muku: 🌸 Kayan Kitchen masu inganci 🌸 Atamfa masu kyau 🌸 Laces na musamman 🌸 Abaya masu ƙayatarwa 💯 Inganci tabbatacce 💯 Farashi mai sauƙi 💯 Amana da gaskiya 💯 Ba cuta ba cutarwa – gamsuwar kwastoma ita ce fifikonmu. Kar ki bari a ba ki labari. Ki yi odarki yau, ki ga bambanci da idanunki. 📲 Order yanzu: ☎️ 08131850861 ☎️ 07076403211 HAFSAT COLLECTION – Inganci, Kyau da Amana. 💖 "Ke Bibalo lafiyarki kuwa, ya da kyanki da wayonki kina Amarya me zaki yi da wannan abincin a cikin irin wannan katafaren gidan."? Na rasa yadda zanyi dasu dole na faɗa musu gaskiyar halin da ake ciki. Hmmm Mama tayi rantsuwar ban isa bata kunya a idanun kishiyoyi ba, dole in kashe auren in dawo gida. Amman kafin kashe auren tana so in mallaki manyan kuɗaɗen da zasu taimakama tafiyar zawarcina. Da zasu tafi Mama saida ta cika bako da kayan abinci, Sango shi kuma mutum ne mai bin diddigi da maƙon tsiya, yana shiga Kicin ya gane an ɗibar mishi abinci, kuma yaji labarin Mama ta zo. Ya shiga rashin albarka da gore_gore iri da kala bari in baku a taƙaice akan shinkafa mudu biyu dana aunar na siyar na sai nama na zuba a miya, ya sakeni da daddare misalin taran dare. Amman fa kafin wannan lokacin, da asiri, da ƙulunboto, saida na mallaki kuɗaɗe masu yawan ban mamaki. Asirine baya tasiri a kanshi, kasancewar malamin Mamana ya sanar mata, shima yana bin malamai sosai, sabida tafiyar kasuwancinshi, da gogayya da gaggan ƴan kasuwa. A daren na harhaɗa komai nawa na tafi, dama sutura kaɗai nazo dashi gidan. Na nemo mota ta kwashemun akwatunana kab, su Mama suna tsakar gida na shigo a lokacin Baba bai ma dawo ba ranar yayi dare sai washegari ya ganni, yayi ƙoƙarin sasantamu Mama ta buga kai a faranti tace bazan koma ba, ai Sango dukana yake yi, baya bani abinci, mane min matane, dukka baya ɗaya sharri ta bishi dashi. Kunji wannan, ashe Mama ta ja mun duk abinnan data lissafo shi zan tadda a gidan Alhaji Namadina ina kammala iddata washegari aka ɗaura aurena sai birnin taraiyya, Shima nayi rub da ciki kan dukiyarshi, na asirceshi, hatta uwarshi saida muka mallaketa, kishiyoyi da yaran gida ni Bibalo bana ma ta tasu sam, in suka ganni tsoro_tsorona suke yi. Yana duka, yana bin mata, amman dake ba zama ya kawoni ba, wallahi ko a gyalena na bashi dama yaje ya fantama. Ni dai kawai inji dumusu. Hala naita Aura ina saki, saida na Auri bakwai, waɗanda na dinga buga kansu a faranti wallahi. Na tara arziki sosai, na zama Hajiya, kyauna ya sake fitowa, na zama ƴar duniya ƙaƙas. Daga wannan mazaje bakwai sai ƙurata ta lafa, alkadarina ya karye. Amman nayi zamani. Unguwarmu kawai na shiga da mota ansan Bibalo ta shigo. Har mataimakin wani gwamnan wani garin na aura, bazan kama suna ba. Ina ya Allah, babu ya Allah. In gajarce muku labarin. Saida na zama ƙasƙantacciya wulaƙantacciya a hannun maza, saida na zama abar tausayi abar kwatance yau ina gidan aure gobe ina gaban Mama, abun duniyar na samu a hannun wasu, wasu na sata da kaina. Amman me duk wannan ya farune sabida talauci, da gasa ta iyayenmu mata kawai, sai muka ɗaura auren a turbar kwaɗayi, kuma masu iya magana suka ce in da kwaɗayi to da wulaƙanci. A aurena na takwas shine nayi aure domin rufin asirina ba domin kuɗi ba. Sabida matar da zata auri mazaje har bakwai, zawarci zai gana mata azaba sosai. Sabida ta saba da maza gaya. Da wannan dalilinne kuma, aka soma yawo dani, daga wannan zangon, zuwa wannan zangon baƙi. Daga ƙarshen _ƙarshe, mai tuƙa kurar ruwa ni Bibalo na aura a miji na takwas, kuma da gaske zaman auren zanyi jikina ya mutu, na fahimci muddin kace a kafaɗar ɗa namiji zaka jingina kina harin abun hannunshi, ba wai abinda ke kika mallaka ba a wannan zamanin, in ba zaɓaɓɓun maza ƴan aljannah kikai katari dasu ba zaman bazai yiwu ba. Inma ya yiwu dole ki haɗiye baƙin ciki da takaici kala da iri, duk macen da ta auri ɗa namiji da sunan kuɗi tana cikin matsala. A lokacin ga Mama ta rasu, Babanmu Allah yayi mishi rasuwa, babbar yarmu kuma miji ya shafa mata cutar ƙanjamau a sanadiyyar neman matan bariki. Kuma ta sani sarai tunda ba'a ɓoye yake yi ba, ta fifita son kuɗinshi sama da lafiyarta, kishi wannan bata yi. Amman kufa sani jahilci ya taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwarmu sosai da sosai. Hmmmmmm dare yayi sosai ku bari zan ƙarashe muku labarinnan gobe da safe, dan ina kyautata zaton gobe zan fita a wajennan in sha Allah." Ajjiyar zuchiya na sauke tare da jinjina kaina. Wannan al'amarin babbane. Duniya ta cika tab da son abun duniya, ba mazan ba, ba matan ba, ba iyayen ba, ba surukan ba. Amman kamar yadda nake faɗa kullum ma ƴan uwana mata, haka Hajiya Biba itama ta faɗa. Duk rintsi ki nemi ilimi arabi da boko, in boko bai samu ba wajibine ki nemi na arabiyya ko dan ibadarki, in mijinki yaƙi barinki dole shi ya koya miki, in kuwa bashi da ilimin koya miki dole ya barki ki fita neman ilimi. Sannan duk runtsi duk bala'i ki riƙe sana'a, ko aiki ko duka biyun, kuma kisan darajar kanki. Ga sana'o'inan birjik, akwai na gida, akwai na shago, akwai na waya, ko wanne irine ƴar uwa ki faɗa. Wallahi matar da take juya kuɗi ba ɗaya bace da wacce ta zauna tana jiran abinda miji ya farauto ya bata ba. Hakaza matar da tayi ilimi ba ɗaya take da jahila ba, hakaza matar da tasan darajar kanta kuma, ko bata sana'a bata aiki, batai zurfin ilimi ba, tafi ƙarfin wulaƙanci a ko ina wallahi, mace mai kuɗin kanta ba ɗaya take da mace mai kuɗin miji ba. Duk yadda kuka kai da fahimtar juna kina da iyakarki a kan dukiyarshi, dukiyar da kika tara da gumin halak ɗinki babu wanda zai miki shamaki ke da abunki. Shi yasa ni Hindu zan sake zagewa in nemi kuɗi bakin rai bakin fama, zan kuma tsare kima da mutumcin addinina, ƙabilata, ƴaƴana, iyayena. Mata mu farka bafa lokacin bacci da miƙe ƙafa bane a gidan miji kina jira ya samu ya baki ba, duk ranar da bai samo ba shi zuru ke tagumi. Mazan yanzu kaɗanne masu zuchiyar ɗauke nauyin daya rataya a kansu, nace madallah da waɗannan mazaje ƴan aljannah. "Kash banso labarinnan ya tsaya a haka ba, Hajiya haƙiƙa na ƙaru matuƙar ƙaruwa, zan kuma dagewa akan sana'ata ta sai da omo, da sabulun wanki, da nake yi. Sha'awa da kwaɗayin komawa islamiyya ya kamani, ga islamiyya kusa_kusa da gidanmu in sha Allah zan shiga" Cewar Maman Junaidu kenan. Murmurewa nayi tare da jin wani ƙarfin guiwa akan aikina nace. In kika yi haka kin kyauta ke kanki zaki gyara abubuwa da yawa a zamantakewar aurenki, zaki san yadda ake zama da miji, kuma zaki san haƙƙoƙunki da kyau, zaki san irin haƙurin daya kamata kiyi, da irin wanda bai kamata ma kiyi ba, zaki san iyakarki, shima yasan nashi iyakar. Sana'a kuwa jigone babba, ita rayuwar dole sai da kuɗi take tafiya. To a matsayinmu na mata bai kamata ace mun zauna bama sana'a ba, shi juya kuɗi ai akwai daɗi, sannan kema zaki koyi yima kanki da yaranki hidima tun miji yananan ba sai ya mutu ya barki da yaran zaki koya a lokacin ba. Mata da yawa na sansu waɗanda suka samu damammaki mai yawa, Allah ya hore musu mazaje masu kuɗi, amman matan basui amfani da damarsu ba, babu sana'a wata babu karatun, sai dai taci tasha ta kwanta, ta ɗinka manyan suturu ta hau mota. Bata aikin fari bare aikin baƙi, bata san yadda ake juya kuɗi ba. Mazajen kuma suka mutu suka bar dukiya mai suna dukiya. Amman dake bata san zafin kuɗi da gwagwarmayar tarawa ba, sai kuɗin ya lalace harma kiji ana cewa ai dukiyar gado bata da albarka. Ta yaya zata yi albarka? alhalin zara akeyi a cinye ba juyawa ba, shi kuma zara baya barin dami. Sai kiga cikin ƙanƙanin lokaci komai ya ƙare ya zama tarihi, wahalar rayuwa ya soma, iyaka ƴan unguwa kiji ana yanzu yaran wane ke talla, ko kiji suna cewa Allah sarki rayuwa yanzu yaran wane ke gararamba a anguwa. Amman wannan yana faruwane kaɗai a ƙabilar hausawa, mu daure mu faɗama kanmu gaskiya, kuma mu karɓi gaskiya. In muka duba matan yarbawa ba haka suke ba, matan inyamurai, matan arago, matan ibira, matan yaruka da yawa, sana'a suke yi haiƙan. Kuma duk matsayi da muƙamin mijinta zaki ga ko ba ita zata zauna ba, tana da masu zama mata a shagunanta. A karɓa da haƙuri. To muyi amfani da lokaci da damarmu tun kafin mu zo muna cizon yatsa. Rayuwa bata da tabbas, gidan miji babu tabbas. Ki dogara da kan_ kin_ kanki, ki tsaya da dugaduganki bana wani ba, ki zama bangon da za'a jingina dake, ba wai ki zauna kina ganin wani a matsayin shine bangonki ba, daya faɗi zaki ci ƙasa. Ke Hajara kina son a shiga kotu a kwato miki hakkinki kuma Figo ya sakeki, ko dai a barki da mijinki ai muku iyaka akan wannan duka?" Ina da dalilai da yasa kuka ji inata nanacin zance, ku tambayi masu gulɗa da matsalolin aure, zasu baku labari sai ka dage ka tsaya ma mace daga ƙarshe sai tace a janye ƙarar ita tana son mijinta. "Haba Anty wallahi na haƙura da auren Figo saki kawai nake buƙata, in koma gida in nutsu. Makaranta zan shiga in samu ilimi, da gogewar rayuwa a hankali Allah ya ɓullo mun da wani mijin in yi aurena, miji nagartacce" Murmushi nayi na dafa ta. Hajara kinyi kyan kai, zan tsaya miki har ki samu takaddarki. Amman kiji tsoron Allah a duk abinda zaki saka a gaba. Kina take dokar Allah kin kaɗe har ganyenki. Ki sani sai kin girmama kan ki duniya zata girmamaki gwargwadon yadda kika ɗauki kanki da mahimmanci, gwargwadon muhimmancinki a idanun al'ummar dake kewaye dake, da waɗanda zasu tsallako su shigo rayuwarki." Gaga gaga haka muka kwana cikin sauro da kuɗin cizo gabaki ɗaya zarni muke yi wallahi, bacci ɓarawone su ya kwashesu ni kam kwana nayi ina ambaton Allah, tare da istigifari ƴar uwa kinsan sirrin istigifari kuwa? Matso kiji a duk bala"in daya tunkaroki, ko wata buƙatar kike nema Allah ya dafa miki, ko ma babu komai so kike rayuwarki ta yi inganci, tayi albarka komai ya dinga zuwa miki cikin sauƙi? To ƴar uwa ga istigafi nan ki tayi a rana kiyi sau fam taɓa sama, wallahi ko baki ɗaga hannu kin roƙi Ubangiji komai ba, Allah yana ji yana gani zai zama majiɓancin al'amuranki, abubuwa za suita zuwa da sauƙi a rayuwarku, harma aita cewa asiri kake yi nan ko Allah ka riƙe, ki ƙara da sallar walha, da tsaiwar dare, to Hajiya ai kin gagara ba dai mutum ba sai dai Allah wallahi, shi yasa surutun mai surutu baya tasiri a kaina, kushen mai kushe baya taɓa ni. Wannan na daga cikin sirrin Hindu wanda muka koya a wajen Innarmu, madallah da iyayenmu nagartattu, masu natija. Masu tambayar munyi Islamiyya wai ko bamu yi ba, kunsan Kanuri wajen karatun addini mun cire tuta. Tun muna ƙananun yara ƴan firamare mukai sauka, a gidanmu sai yaro ko yarinya ya haddace Qur'ani kafin ya shiga sakandare. Amman bama zuwa islamiyya, a gida aka samar da karatun, dama sauran littattafan da su wannan lokacin muns sakandare. Amsar ta fita? To shikenan. Innarmu ta koyar damu riƙo da addini a aikace, shi yasa ta gagara. Da Allah ta dogara, sai sanin darajar kai, sanin sirrin ƙamshi, gyaran jiki, ado da kwalliya, da girke girke baraitis wanda gidan yawa baisa tace ba zata yima mijinta ba, wai dan sabida mun yi yawa. Wannan kenan. Bayan mun yi sallah ina zaune inata lazimi, a cikin inda ɗakunanmu suke ƴan sanda su kai su kawo, mu dai mun yi shiru kamar ruwa ya cinyemu kwatsam ga yinwa ga wani irin rashin daɗi na jiki dana zuchiya sai wajajen tara da rabi aka zo aka buɗe mu. "Ke da ke da ke kuzo mu je" Ƴar sandannan ta nunamu muka taso saida na taimakama Hajara ta miƙe. Hajiya Biba tace. "In ta ɗauro ba'a dawo daku ba, gidana yana ceɗiyar ƴan gurasa layi na biyu gida mai lamba tamanin da tara, ko yaro kika tara kika ce a nuna miki gidan Hajja Biba komai da ruwanka, za'a kawo ki, nima ki bani adireshinki inma baki ɓullo ba ni da kaina sai in zo ai" A gurguje na bata adireshina muka fito. Luba da mijinyawa su na soma hangowa a tsaye, mijinyawa idanunshi a kaina, ni ko nayi kicin_kicin da raina ita kanta Luba sau ɗaya na dubeta ma, a wannan gaɓar ita nafi jin haushi. Ga Figo, da wani dattijo haka da wata mace kamar tafiyarsu ɗaya. "Zo ki saka hannu anan daga yau babu ke babu Hajara, kada ki sake shiga rayuwar gidan Figo, da ba dan mijinki ba da kotu ma za'a turaku ungo nan" Ya miƙo mini alƙalami, mijinyawa na kalla, na dubi Luba naƙi karɓan wannan alƙamalin dan wallahi sai naga abinda ya ture ma buzu naɗi. Yallaɓai na fi so a kaimu kotu, Hajara tamkar ƙanwa take a gareni cutarwar da wannan bawan Allah'n yake mata yayi yawa. In ban shiga kotu akan Hajara da Figo ba, zan shigar da ƙaran Figo akan ƙagen da yayi mini, ko kuma ya janye yanzunnan anan" "Hindu ki karɓa ki saka hannu tunda dai mijinta baya son alaƙarku. Hindu dubeni kinji? " Banza nayi dashi idanuna akan Hajara da take kuka. "Yarinya so kike ki gutsire mata igiyar auren nata ne? Ni mahaifiyarta ce, mu muka ɗaura aurenta da Yahuza dan haka ki fita sabgarta. Irinku ne masu hure ma mata kunnensu kar suyi zaman gidan miji, masu ta'adar yahudawa maƙiya Allah da ma'aiki." Murmushi nayi kawai na zare alƙalamin daga hannun ƴar dokar. Kinga a ina zan saka hannun, Mama Allah ya baki haƙuri? Amman wallahil azeem sai nayi sharia da Figo. Bazan kwana cikin sell a banza haka ba" Nayi tambayarne cikin zafi da ƙunan zuchiya. Wajen da zan sa hannun zan sa kenan, Hajara ta riƙe hannuna tamau. "Anti dan Allah kar ki saka" Ƙur nayi mata ina kallonta, tausayinta kamar zai halakani. "Kunji ba ta riga tayi mata huɗubar shaiɗan, tana son kashe mata aurenta alhalin ita ga nata soloɓuyon mijin shanyayye. Dan shanyayyene kaɗai lusari zai iya barin matarshi na wannan aikin" "Ya'isheka kada ka sake aibatani, ya ana ƙoƙari shawo kan matsala kana ta maganganu tun ɗazu, dan kaga ina tausarka" Nan rikici ya ɓalle tsakanin mijinyawa da Figo, saida ƴan sanda suka tsawatar musu. "Ki sake mata hannunta ko in miki baki wallahi" Cewar fa mahaifiyar Hajara. Hannuna na fisge dan baƙin ciki, inata tausar zuchiyata kada in mata rashin kunya, duk da haka bayan na saka hannun Maman Junaidu ma ta saka hannun ana bamu kayanmu nace. Mama ga Hajara nan a maidata gidan miji, in ya halakata sai ya kiraku yace sa'i yayi, ku sai kuzo ayi jana'izarta daku. Ku sani mu ababen kiwone da Allah ya baku, kuma akwai ranar da zamu tsaya a gabanshi ya tambayeku kiwon daya baku" Na fito daga cikin bayan kanta na fice waje ina ji tamkar in haɗiye zuchiyata in mutu, ni sai yafi mun, ga Hajara tana ta kuka sai kiran sunana take yi, nayi mata banza. Motata da na gani a can gefe wajen na ƙarasa na jingina, sabida tausayin da naji na Hajara kada in ƙara sata a cikin masifa yasa na jaye ƙudirina na son maka Figo a kotu, amman wallahi da ni dashi har kotun Allah ya'isa. Ina hangosu Mahaifiyar Hajara sai zaginta take yi, Figo kuma sai rikici suke yi da Mijinyawa, har yana dukan ƙirjin mijinyawa, Luba nata aikin ban haƙuri, bakina na taɓe na kawar da kaina kawai. Mijinyawa yazo da sauri ya buɗe mun motar na shiga baya, na zauna tare da rufe idanuna ko'ina a jikina rawa yake yi mun a haka Luba ta shiga motar mu ka ja. Tun suna maida zance ina jin muryoyin nasu a sama, wallahi kamar wasa kafin mu isa gida bana ganin komai sai duhu, ana haka inata ambaton Allah ni dai ban sake sanin inda kaina yake ba daga wannan ɗaukewar ganin, mutanen sun kawo ziyara sakamakon ɓacin rai su dama haka suke ko da yaushe. Kunji wannan ai ko? MIJINYAWA:. "Mijinyawa shikenan mutanenta sun rabketa ni dama nayi tunanin za'a rina, la'akari da irin yadda Hindu take da nacin abinda ta saka a gaba. Haƙiƙa ni kaina wannan yarinya ta bani tausayi. Muje ka saukemu a gida kayi tafiyarka wajen aiki kasan yanayin aikinku ba aiki bane na wasa ba" Gabaki ɗaya mijinyawa a dame yake, yama kasa magana sai karatun Qur'ani ya saka ƙira'ar malam Sulaiman maja baƙin malam Kabiru Gombe, a haka har suka iso gida ga ofis sai kiranshi akeyi a waya, wasa da aikinshi su suke ganin yanayi, babu mamaki yana da alaƙa da abinda ya taso a wajen aikin ma ga wannan fargabar a ranshi, ga kuma halin da Hindu ta shiga ga damuwar su Nanno, damuwa ce fal kanshi goma da ashirin fireja na neman halakashi. Su Nanno suna tsakar gida Yaya Jamila na musu wanki mijinyawa ya buɗe babbar ƙofa, kana ya fita ya shigo da motar Hindu suna zaune suna kallon ikon Allah, suka fito da Hindu ranga_ranga babu yadda take suka yi ciki aka shimfiɗeta a gado. Nanno da Yaya Jamila ne suka shiga har uwarɗakin Hindun. "Wai lafiya aka dawo da'ita a cikin wannan halin ne. Yanzu mijinyawa rayuwar da kai a naka hankalin kake ganin ya dace kaci gaba da gudanarwa da wannan yarinyar kenan? Iyayenta sun zuba maka idanu sai aikin wahala kake yi da'ita, wannan wacce rayuwace haka. Ka saketa kaƙi, ka sake aure saika taramun dattawan gari suita godona. Yanzu ta fita ta kwana a waje, kaida ka fita aiki ka baro aikinka kazo sarama kare ciyawa...." Shi da Luba adda'a kawai suke ta ma Hindu, har Allah yasa ta dawo hayyacinta. Hindu:. Da Nanno da Jamila na soma haɗa idanu. Jamila sai kallon ɗakina take yi tana mayawa. Na dubi Luba, na dubi Mijinyawa. Kafin ince komai Yaya Jamila tace. "Duka wannan mimmiƙewar ta borin kunyace ai. Sabida taje ta kwana a wajen gantal.... " Muƙewa nayi sai gani a gabanta. Me kike cewa? Na faɗa cikin ɗaga murya. "Ai kinji me nace, kuma kin gane me nak...." Tas na gaura mata mari, na sake dallah mata mari. Na dubeta nace. Kinci abu ta kaza kazan...... Daga yau in kuka sake shigomun gidana na rantse da Allah zaku sha mamaki. Wai ku wanne irin mutanene, me nene laifin da nayi muku dan kawai na so ɗanku, ashe soyayya na zama ƙiyayyane" Jamila a fusace ta ɗaga hannunta zata sauke a fuskata. Mijinyawa yayi saurin matsowa, yana ƙoƙari riƙe hannunta, na fishi zafin nama tuni na caɓe hannun, na murɗashi zuwa bayanta, wallahi saida ta saki tusa. Daga haka ina na zama bani ba. Mijinyawa:. "Kana kallo zata kashema ƴar uwa kana gani. Kana jin duk abinda take cewa ai? Wallahi komai yazo ƙarshe saika saketa. Ƴar iskar yarinyar ƴar mutanen banz...... " Wallahi kafin ta ƙarashe Hindu ta sureta ta bugata da ƙasa, taje bayanta ya daki katakon kwalliya, sai ga Nanno daɓas a ƙasa tayi zaman daɓaro wanda ya haddasa sai da ƙashin ƙugunta yayi ƙara ƙaƙaƙaƙaƙa_ raɓaɓaɓas. Hindu bata yi wata _wata ba, ta shaƙe Yaya Jamila Mijinyawa da Luba suka yi suka yi suka kasa ƙwace Yaya Jamila, idanunta sai firfitowa suke yi. Da Luba da Mijinyawa sun sha duka duk wanda ya matso sai a zubar dashi ƙasa, idanun Hindu sun kafe babu baƙi ko ɗis sai wani irin gurnani take yi na rashin hayyaci. Bai taɓa ganin idanunta a haka ba. Nanno da rarrafe ta fita waje tana kukan a kawo musu ɗauki, amman dake unguwar ba irin wannan unguwar bace babu ruwan kowa da kowa, kowa na cikin gidanshi ƙofa a ɓame. Nanno ta bugu iyakar buguwa, ko miƙewa tsaye ba zata iyaba sam, bayanta tana jinshi tamkar ba nata bane, kuka take yi ƙaƙas. Hayaƙinta Mijinyawa ya lalubo ya wuce Kicin a guje nan ya tadda Nanno a zaune tana kuka wiwi, bai bi ta kanta ba ya kunna gawayin kanti ya koma ya bunke ɗakin da hayaƙi yana karatu yana tofa ma Hindu tana kawo duka da hannu ɗaya, ɗayan hannun tana riƙe da wuyan Yaya Jamila wanda a halin da ake ciki ta riga da ta sume ma. Dan da dokata da ƙasa da akayi har sau biyu, har fitsari tayishi a tsaye. Mijinyawa ma bakinshi a fashe yake, Luba kuma hannunta ta murɗeshi zuwa baya, harya samu targaɗene ko tsagewar ƙashi, ba'a dai sani ba, amman harya aune ya kumbura, banda mari da tasha, idanunta ya tara jini. A hankali riƙon ya soma sassautawa har dai ta soma shirin faɗuwa luu, mijinyawa yayi saurin tareta, wallahi yama mance da Yaya Jamila sai ji kuke rututum ta faɗi, da aka ce tsautsayi baya wuce ranarshi, ai saita faɗi a hannunta ya karye ɓararars hatta su Luba sunji rushewar ƙashi. Shikenan mijinyawa yasan komai na iya faruwa kuma, gado ya mayar da Hindu ya lulluɓeta ya koma kan Yaya Jamila da Luba take ta yinƙurin yayyafa mata ruwa, isowarshi wajen farfaɗowar Yaya Jamila amman fa kafin ma idanunta su gama buɗewa ta sake sumewa. "Luba taimaka mun mu kaita mota gara aje asibiti da dukkan halamu hannunta ne ya karye." Da ƙyar suka iya sakata a mota kaya hamago guda, ita kanta Nanno tana buƙatar ganin likita, bata sume ba, amman ta shiga cikin yanayi sai maganar bebaye take yi, idanunta basa ko buɗuwa. "Luba zan turo Azgar yazo ya taya ki zama da Hindu zan dawo zuwa anjima, ko da ta tashi bata dawo daidai ba hayaƙin yana ajjiye a gaban madubi, da kin turara zata samu bacci. Zamma dawo zan dawo Luba, ki kirani, zan dawo zan dawo" Mijinyawa ya zauce fireja iya fireja yau. Nanno ta fashe mishi da kuka da sauri ya shige motar, dama ya riga da ya buɗe get ya fice da motar sai Luba ce ta rufe ƙofar. "Ciɓiri nannagi wannan karon bayin Allahn nan sun ɗebo mana da zafi Allah masanin abinda ka iya faruwa. Dama su da suke neman dalili bare sun sameshi mai girma kuwa, dan wallahi tsohuwa ta sha bugu Allah yasa sifana kot ɗinta bai zare ba, ga waccan tsohuwar maras mutumcin ni wallahi daɗin abinda suka yi mata naji, suma dama suna da cikin makira. Makaran Hindu yau sun burgeni. Duk da nasan rikicine zai ɓalle gagarumin gaske. Igiyar aurensu tama ɓalle Allah ta gama" Wucewa ciki tayi da sauri Hindu dai bacci take yi lokaci zuwa lokaci kuma tana ɗan zabura. Waya luba ta ciro ta kira Yaya Saratu ta sanar mata Hindu fa ba lafiya. "Yaya Saratu in da hali ki baro ofis kizo wallahi Allah da akwai babbar matsala sosai" Hankali tashe tace. "Ganinan tawowa Luba" Ƙit ta kashe wayarta Luba na tubkewa da warwarar abubuwan da suka faru, Azgar ya dawo gidan, bai jima da dawowa ba sai ga Yaya Saratu ta'iso itama. Bayan duk an gaggaisa Sai Luba tace da Azgar yaje ya ɗaura abincin rana, dan Hindu da yinwa zata farka bata tsammanin ta karyama. Yana fita Yaya Saratu tace. "Menene Luba naga dai Halamun mutanenta ne suka motsa me ya jawo hakan, naga ko'ina kaca kaca halamun anyi dambarwar tsiya" Luba ta kwashe labari silar komai duk ta faɗama Yaya Saratu. Ta nuna mata hannunta yadda yake ta daɗa kumbura. Mayafi ta cire tsabar ruɗani. "Tabbb lallai wannan karon sun ɓaro aiki babba, dukan suruka da Yayar miji, ai aurenma ƙarshenta dole igiya ta tsinke. Luba ko ni sai inda ƙarfina ya ƙare ace yau matar ɗaya daga cikin ƙannena ta hau iska ta dakar mun uwa, gaskiya za'ayi abunda dai bazai yi daɗi ba gaskiya dai wannan makarai sun jawo mana wata rigima narkakkiya, wannan tarihine da abadan bazai gogu ba, anyi ta gorantama yaran Hindu kenan. Duk da Kinga wannan Jamila tsohuwar maras mutumci kenan dama ita ba wannan ne karon farko da haka ta faru da'itaba. Bana mance lokacin sunan Azgar ne ko irin yadda tai ta abubuwa, tai ta cakale_cakalen rigima har sai da akayi tukunna. Haka lokacin biki ma meye bata yi ba." Luba tace. "Ai ita take zuga ma uwar akan Hindu. Baƙin ciki ke cin ƙasan ranta, zamanine muke ciki wallahi in ba sa'a kaci ba wanda kuka fito ciki ɗaya ma sai ya nuna baƙin cikinshi a bisa ni'imar da kake ciki, ko wata ɗaukaka. Yanzu fa baka isa miji ya soka ya nuna miki kulawa ba, sai ace asirine kayi sabida soyayya ta mutu a ra'ayoyinsu. In kuma kashi miji ke baka kana ɗiban gashi, sai kiji ana Allah sarki Murja Kabiru mijinta bashi da mutumci baki ga yadda yake wulaƙantata ba. Yayin da a gefe guda dariya suke yi miki. Da yawan dangin miji sunfi so suga matar yayyensu ko matan ƙannensu a tagaiyare, suna musu dariya harma a ba wata ɗan kwancan kayan sakawa ko ita ko yaranta. Amman infa cikin rufin asiri suka ganka shikenan ka zama abokin yaƙi. Magana ta domin Allah Nanno ta bani tausayi dan ta bugu sosai, saida bayanta ya amsa da rarrafe ta fita kuka wiwi. Amman uzirin daya kamata aima Hindu shine ba'a cikin hayyacinta take ba, in a cikin hayyacinta take ko sa'insa bata da lokacin yi dasu bare har akai ga haka. Amman wannan uzirin shine zai yi wuya Yaya Saratu. Kuma sun ƙureta sun kaita ƙarshen tuƙewa" "Hmmm Luba lamarin fa da girma Allah kedai bari kiga in kira Innarmu tasan halin da ake ciki, amman Allah yasa muji alkairi jikina yana bani za'a samu matsala babba." Wayar Yaya Saratu ke ruri ta ciro a jaka. "Kinga ga Zubaida na kirana" Ɗagawa tayi bayan sun gaisa take sanar da'ita halin da ake ciki, ai take tace gatanan zuwa. Tana kashe kiran ta kira Innarmu ta sanar da'ita halin da ake ciki. "Wannan maganar tana da girma sosai gaskiya. Zan sanarma Baba Sojanku domin yasan halin da ake ciki, wannan lamarin yafi ƙarfin ya tsaya iyakar Hindu da mijinyawa, dole manya sai sun shiga lamarin gaskiya, amman in sun so adalci sai su duba yarinyarnan ba lafiya gareta ba shi yasa ta aikata hakan. Amman tunda uwar Mijinyawa ba mace bace mai son a zauna lafiya ba nasan abunnan zama zaiyi babban abu. Kinga ga Baba sojanku ya shigo zan kiraki bari in yi mishi bayanin halin da duk ake ciki" Innarmu ta kashe wayarta, Yaya Saratu ta sauke a sanyaye ta zuba ma Hindu idanu sai zabure_zabure take yi tana ɗan mimmiƙewa kamar ciwo zai sake tashi ai Yaya Saratu da gudu ta bar ɗakin tana haki, tana mugun tsoron masu aljanu a lokacin da aljanun suka tashi musu. Ganin fitowarta da Gudu Azgar dake tsaye a Kicin yana girki sai yayi ɗakin Ummmanshi da gudu, daidai lokacin suna turka _turka da Luba tana yinƙurin fita Luba na tareta. Azgarne ya rungumeta yana kuka ya ruƙunƙumeta ƙam yana ta karatun Qur'ani. A haka Luba ta fita ta kunno gaushi ta dawo lokacin Hindu ta wancakalar da Azgar, harta falla mishi mari bakinshi ya fashe idanunshi ya tara jini shima, sai dukanshi take yi tako ta ina. Shi kuma karatu yake yi mata da ƙarfinshi. "Subhanallahi. Haba bayin Allah wannan ɗanku ne Azgar fa. Ku bar Hindu ta huta taji da bom ɗinma da kuka haɗa mata mana." Hayaƙi ta barbaɗa a wuta, daga nesa Hindu ta soma shaƙar ƙamshin, azgar yayi saurin tareta yaga tana yinƙurin faɗuwa. Hannunshi ta faɗo ya riƙeta sosai hannunshi na rawa dan tayi mishi nauyi, luba ce tazo ta taimaka mishi suka mayar da'ita gado. Wayar Azgar tana ta ruri lokacin da ake wannan abu saida suka shimfiɗe Hindu kafin ya zaro wayar a ajjihunshi. "Abbanmune tun ɗazu yake ta kirana" Ya faɗa yana kallon Luba, hawaye kaca_kaca fuskarshi, gaban rigarshi duk jini. "Ɗauki kace mishi da sauƙi jikin kaji? " Kai ya ɗaga mata tare da ɗaukar wayar. "Azgar ya jikin Hindu ta farka kuwa ko har yanzu bata farka ba, sannan basu dawo ba dai ko? " "A_a bata farka ba Abba, bacci take yi babu wani matsala Umma Saratu ma tazo duk muna tare" "Toh shikenan zan kiraka anjima inji ko ta farka. Muma yanzu aka shiga da su Nanno ciki jikin Nanno ya tsananta sosai ku taya ta da adda'a, da ƙyar Nanno ta yi rai. Azgar kayi Alwala yayi sallah ka roƙa mana Allah ya tashi kafaɗun Nanno, da Hindu" "Allah ya basu lafiya duka Abba, in sha Allah zanyi yanzu" Ciɓiri nannagi kenan Mu kwana anan sai in Allah ya kaimu gobe. Amman ba lallai in yi sabon shafi gobe ba ƙila sai monday, idanuna ya tasamma ciwo yana buƙatar hutu, amman sai yadda ta kaya dai. Mrs BUKHARITSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA GOMA SHA BIYAR INA GODIYA A GAREKU MASOYANA NA FAƊIN DUNIYA. IDANUNA ALHAMDULILLAHI INA SAMUN SAUƘI. NAGODE SOSAI DA ADDU'O, INKU SON SO💪🏼 MIJINYAWA: Asibiti_ Yana zaune idanunshi sun kaɗa sun yi jawur kanshi ya ɗauki zafi sosai, duk wata fireja ranar tana kanshi ba sauƙi. Ga Mijinyawa Babba da Gambo duk ya kirasu sun baro wajen aikinsu suna tare. Mijinyawa Babba ya ɗaga wayarshi ya sanarma ƴan jama'are halin da ake ciki. Wai Hindu ta daki Nanno da Yaya Jamila, gasu a asibiti cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai. Sai huci kawai yake yi, yana ji tamkar ya rufe Mijinyawa da dukan mutuwa ko hankalinshi zai kwanta da ɗan samu sassauci na dangane da abinda yake ji, ga wutar ɗaukar fansa sai ruruwa take yi a zuchiyarshi. Gambo kuwa dake shi a ƙasansu yake ya birne abunda ke ranshi, kawai ya ɗauki idanu ya zuba. Gashi Mijinyawa sai kiran Azgar yake yi yana jin ya jikin Hindu, lamarin daya fusata Mijinyawa Babba yake jin an ƙure gejin haƙurinshi ya ƙare, ya zare wayar a kunnen mijinyawa ya rakaɗata da ƙasa ta fashe. Da idanu kawai ya bishi bashi ba tacewa. "Sabida iskanci mahaifiyarmu ba lafiya tana ciki likitoci na kanta, bamu san halin da take ciki ba amman ta matarka kake yi sabida tambaɗaɗɗene, kai sallamamme, wanda Hindu ya rako duniya. Matar da itace silar faruwan duk abinda ya faru, har baka jin tsanarta a ranka sai kiran yaro kake kana tambayarshi jikinta me kake nufi, nace ubanme kake nufi damu ne Mijinyawa. Anya kana da kai kuwa?" "Amman kai baka san aljanunta ne suka yi wannan aikin bane? Nayi imani da Allah ko giyar wake Hindu ta sha ba zata iya ma Nanno wannan abun ba, gara ma Yaya Jamila tunda taƙi fur ta kama girmanta, sannan akanme zanga lefenta ai wallahi ko ina akace muddin iyakar gaskiyar za'a tsage to bamu da tace wa. A wannan halin da Hindu take ciki babu wanda ba zata iya duka ba. Kada ka shiga surutan mata har suyi maka tasiri ɗan uwana. Ka fahimceni, ka fahimci Hindu." "Wallahi baka isa kareta akan abinda ta aikata ba. Gawata ko dai da gasken dai asirin Hindu tayi makan kamar yadda aketa faɗa ne? Ahh asirine wannan nima yau na tabbatar da haka. To bari kaji in faɗa maka aurenku dole ya ƙare, babu wanda zai karɓi abinda tayi kana taci gaba da zama a cikin rigar alfarmar aurenka ba, kana ta hidimta mata, dukiyarka da rayuwarka duk akanta ka ƙarar. Sarki mai Hindu jibi yadda ka rame dan jarabar son Hindu daka ɗaurama ranka. Inna hanga na hango sai ince ribar mai ka tsinta a wannan ƙaddararren Auren. Ya zame maka dole ka rabu da'ita ko kuma a tsameka a dangi, wallahi sai dai ka zaɓi ɗaya ahh iskancinku yayi yawa, ina mahaifiya fa" A fusace ya miƙe cikin ɗaga murya yace. "To sai me a tsameni mana Nawata. Hindu dai a ko'ina akaje zan kareta tunda uwar ƴaƴanace, kuma bata cikin hayyacinta tayi abinda tayi. Sannan in an bi ta ɓarawo abi ta mabi sahu. Yaya akeso in yi ne, wai me muka yi muku ne. Shikenan sabida dai Hindu ta yadda ta aureni ina ɗan ƙauye, wanda na kaita ƙauye muka rayu. Ko kawai sabida ta samu jinkirin haihuwa a farko kuma daga biyu haihuwar ta tsaya shine matsalarne, ko kasancewarta ma'aikaciya shine matsalarne Mijinyawa, ko sona da take yi nima nake sonta muna zaune babu mai jin kanmu shine matsalar ne? To bari kaji kada ka sake shiga sabgata da matata, domin bana shiga sabgarka da Uwatale. Bama kai kaɗai ba, bana son kowa ya sake shiga sabgarmu ni da iyalina. Ni dai a barni in huta in ba haukacewa kuke da burin kuga nayi ba, ace muku gani ina yawo tsirara ba. Haba haba, wallahi turarnan ta riga da tai kuma kaini bango. Ohh so kake in dena kira ina tambayar jikinta, tunda ba hakkina bane kula da lafiyarta ba ko, in uwatalene kenan ba zaka yi ba? To ni zanyi kai da kake bagidaje ɗan ƙauye a soyayya sai kar kayi. Dan kana abokin tagwaitakana ba yana nufin ka takani son ranka bane. Bama ka isa bane. "Ƙarya kake wallahi saika saketa maras mutumci, wanda baya kishin dangi" Mijinyawa yace. "Tunda kaine Ubana ba ai dole ka haƙiƙance, kasa in rabu da matata, sannu Baba" Ya koma ya zauna ya adana layin wayarshi a ajjihunshi. "Ni kake faɗama haka ina matsayin Yayanka? " "Laa gware muka yi muka zo duniya, Nawata kana mantawa son girma na rufe maka idanu, baka girmeni da komai ba. Kayi haƙuri kayi shiru bana son jin muryarka wallahi Allah, ka riƙe matsalolin iyalanka sun isheka, ka barni inji da ciwon mahaifiyata da matata" Ya ja bakinshi ya tsuke ba tare daya sake cewa uffan ba. Mijinyawa Babba kuwa ai da wa Allah ya haɗashi in ba Mijinyawa ba, yaita amayar da maganganun da suka jima a ƙasan ranshi wanda uwatale take tattarewa tana faɗa mishi, ya jima da jin haushin ɗan uwan nashi wannan haihuwarsu da akayi tare, tasirinshi ke danne jin zafin da yake yi akan ɗan uwan nashi. Burin uwatale ya gama cika yau sai dai ta saka ruwa a ƙasa ta sha. "Gambo kaine shaida in har Gawata zaici gaba da auren Hindu babu ni babu shi har gaba da abada, kuma bana fata da sake ganinshi a rayuwata, bazanje inda yake ba, kar ya sake ya sake zuwa inda nake. Ku in zaku yi zumuncinku kuyi" Gambo ya buɗe baki yace. "Nima h...... " Kallon da Mijinyawa ya watso mishi ne yasa ya tsuke bakinshi yayi shiru bai ƙarashe ba, likita ne ya fito da zummar komawa ofishinshi, suka miƙe du su ukun suka nufeshi. "Dakta ya cikin nasu? " "Da sauƙi ita Mama sai anyi mata hoton bayanta inda take kukan ciwonshi gashi ya kumbura sosai ma. Mun dai mata allurai yanzu haka tana bacci, amman a gaskiya tana jin jiki, ayi ta adda'a. Ɗayar kuma Dr yana kan dubata zai fito ba da jimawa ba. " Haka wannan ahali sukai ta zama cikin maganar kurame har kusa da Azahar, Uwatale ce ta kawo abinci bisa umarnin mijinyawa Babba, da goyonta a baya. Ta zuba ma Mijinta, kana ta zuba ma Gambo, tana ƙoƙarin zaran wani kwanon taji amon muryar mijinta irin amon da ita kanta bata san ya mallaki irin muryar ba. "Wa kike yinƙurin zuba ma abincin nace? " Cike da mamaki tace. "Abokin tagwaitakarka wanda bashi da tamka a rayuwarka" Sai da ya haɗiye abincin bakin shi kana yace. "Kul kika zuba mishi kamata yayi daga gidansu Hindu a kawo mai abinci, su gatantashi kamar yadda ya ƙare a ƙarƙashinsu, baya ji baya gani." Har a fuska Uwatale ta kasa ɓoye farin cikinta, wannan ranar take jira sai gashi yau ranar tazo Mijinyawa Babba ke cewa kada a sama Mijinyawa abinci? Tab duk abinda zaisa Mijinyawa Babba yace haka ga Usainin da bashi da tamka, to babbane. Cike da jin daɗi gami da kannewa tace. "To amman Baban Zainab mijinyawane fa naka, kuma naji shima ance wai Hindu na kwance babu lafi... " "Kada ki sake kiran sunan Hindu a gabana in ba haka ba zaki karɓi hukunci mai tsanani, kinji na faɗa miki. Ki shiga ki tadda matar Gambo ku zauna tare da su Nanno, ba ki zauna kina son jin ba'asiba Munafukar banza da wofi." Murmushin gefen fuska Mijinyawa yayi kawai yaci gaba da ƙoƙarin kiran abokinshi Qasimu, yana hanyar zuwa tare da su Yaya Zakiya. Labarta mishi yadda ƴan jama'are suka ɗauki lamarin yake yi, sakamakon sun tsaya cin abinci a wani gidan mai shike riƙe da tuƙin motar, ɗan sanyin da Mijinyawa yaji jin an tawo tare da Kawu ne kawai, duk da ƙasan zuchiyarshi cike da taraddadin ya kawun zai ɗauki lamarin yake, ta yiwu ya ɗauka da sauƙi kamar dai yadda ya saba, ta yiwu ya ɗauka da zafi kasancewar yasan dole al'amarin da girma. Amman bawai kare Hindu yake yi ba, kare gaskiya kawai yake yi. Hindu bata da laifin komai ko sanda aka shiga da'ita gidanma bata san inda kanta yake ba. Wucewa yayi zuwa masallacin cikin asibitin yayi nafila, ya jima goshinshi a ƙasa yana munajati da Ubangijinshi. Haka a zaman tahiya yaita faɗama Allah damuwarshi kan ya shiga lamarin ya taɓa, kafin dai ya sallame. Yayi sallah azahar yana kan sallar tare da tsirarun mutane su Mijinyawa babba suma suka shigo ko da ya sallame zama ya gyara, yaci gaba da ambaton Allah, can kuma yai kurum yana tuno irin rayuwar da suka shinfiɗa a baya. Wata rayuwace tamkar ta turawa tsabaragen fahimtar junansu, amman kash yau gashi ya rusa duk yaddar dake tsakaninshi da Hindu. Tuno wata rana yayi da rana ƙwal ya dawo daga wajen aiki da cefane Hindu na zaune a tsakar gida tana mishi wankin kayanshi, Azgar na tsaye a dokin ƙofa da motar roba mai ruwan omo a hannunshu, Asma'u kuwa tana bayanta tana ta sheƙar baccinta. Ganin shigowarshi yasa Hindu ta taso da saurinta tana goge kumfar hannunta a zaninta. "Sannu da zuwa ya akayi ka dawo da wuri haka? " Ta tarbeshi da kayan ta kai madafinta na langa langa dake manne a ƙofar ɗakinta. "Wash Allah ke dai bari Tutar so ai dole in dawo nasan ban ajjiye miki komai a gidan ba, in ba garin kwaki ba, cefane na cefano mana ki ɗakko ki bubbuɗa. Azgar tawo to" Ya ƙarashe zancan da miƙa ma Azgar hannu, yana zaune a kan kujera ƴar tsugunno ya tawo ya hau cinyarshi ya zauna. Hindu kuma saida ta kawo mishi ruwa mai sanyi, kafin ta ɗakko ledojin cefanen da tiren silba, kujerar da take kai tana wanki ta jawo ta zauna ta soma bubbuɗa cefanan. Kayan miya ta soma gani tattasai, attaruhu, tumaturi, albasa mai lawashi. Ɗayar ledar shinkafa ce gongoni huɗu da wake gongoni ɗaya, sai farin mai rabin gongoni, maggi mai tauraro guda goma sha biyu lokacin yana shida goma sai maggi ajinomoto leda ɗaya lokacin yana nera goma baidan kuma nera biyar yake. Sai bushasshen kifi karfasa. "Ahh yau dawar tayi mai Mijinyawa Ubangiji Allah ya ƙara maka buɗi da wadatar dukiya data zuchiya." Murmushi yayi mata yana kallonta da kyau. "Hindu baiwar Allah ban kawo miki abinda ya taka kara ya karyaba, ba jan nama, ba kaza amman sai murna kike yi wai harma dawa tayi mai. Hmmm Ubangiji Allah ya nuna mun ranar da zan dinga cika kaji da naman kasuwa a gidan ƙanƙara da kayan miya, abinci cikin sito, sai yadda kika so haka zaki yi. Ga injin ganin haske ga komai na ƙawar rayuwa, Hindu kici ƙoyi ki kora da haɗin murtuk, ki daki mummuƙi yadda kike so" Dariya suka yi dukkansu daidai lokacin Asama'u ta tashi a bacci ta shiga canyara kuka. "Suntota macen duniya, ga kuma soja an sai laɓewa yake a jikina, wannan yaron anya zai zama sojan kuwa? " "Aiko dai yana da sanyi da yawa fa. Kuma Akarami da gaske so yake Azgar ya shiga soja hatta Baba sojanmu haka yace" Ajjiyeta tayi a cinyar uban, ya karɓeta ya shiga yi mata wasa yata dariya. Hindu kuma ta tsaya kallonsu tana ayyana wani abu a ranta dangane da Mijinyawa da yaran duka. "Yau kam na tashi aiki, har Shehulle ya fita da motar. Sai dai zanje kantin Alhajiji kamar dai yadda aka saba ko na karin safe ma samu ko tutar so, ko bakya son ɗan ƙoyin da Alhajiji yake ƙunsowa yace a kawo ma uwargida ta soya ma yara" Dariya suka yi dukkansu mijinyawa ya miƙe yai musu sallama ya fita yana ta zuba warin rana to yanayin sana'arce dole sai da warin rana, duk tsabtar mutum danma Hindu na rage mishi ƙarfin warin ranar da ruwan alim ko ta goga mishi lemun tsami a hammatarshi ta dirje mishi, kuma bata barin hammatar tashi da gashi sam duk sati take aske mai ta yanke mishi faratunshi." Dawowa Murmushi yayi ya girgiza kai kawai ya sauke ajjiyar zuchiya mai cike da kewar rayuwarsu ta baya. Miƙewa yayi cike da rashin ƙarfin jiki ya fita, ya koma can wajen zaman nasu suna leƙawa duka su dubo marasa lafiyan amman basu farkaba har magriba, a hanyar dawowan mijinyawa daga masallacine ya hango su Kawu su biyar shi yai musu jagora har zuwa ɗakin da su Nanno suke kwance, Yaya Zakiya da Innah sai hararar mijinyawa suke yi." Inna Akulu data kasa haƙuri sai cewa tayi. "Ina fata marar mutumcin i yanzu tana gidan iyayenta an bata dai takaddarta ko? " Uwatale mai neman ayi sai firit tace. "Inaa ai yace babu wanda ya isa ya.... " Kallon da mijinyawa Babba ya watsama Uwatale shi ya tilastata jan bakinta ta tsuke kawai. Kawu yace. "Wanne irin saki dan dai ku yaran zamani sakin aure babu wahala a wajenku ko. Shin yarinyarnan ba makaranta bane suka tashi ba, koko da gangan tayi hakanne Mijinyawa? " Mijinyawa yace. "Ko kusa Kawu ai ita kanta har zuwa yanzu bata farfaɗo ba, bata cikin hayyacinta har yanzu. Hindu tana girmama Nanno wallahi ko ba aure muke yi ba ba zata taɓa aikata wannan ɗanyen aikin ba, ta samu nagartacciyar tarbiyya, Kuma Yaya Jamila itace ta jawo komai, itace mai kunna wutar fitina. Amman Uwatale itace idanunsu. Kawu ya dubi Yaya jamila dake kwance wuya a aune ya girgiza kanshi baice komai ba, su Yaya Zakiya da Inna Akulu sukaita rantsuwar sai an saki Hindu Kawu baice musu Uffan ba. Mijinyawa tun yana rarrashi har ya soma faɗa tamkar dambe zai kaure a tsakaninshi da Mijinyawa Babba, Kawune yace Mijinyawa ya wuce ya tafi gida duk abinda ake ciki gobe sai a tattauna ya tsawatarma kowa dai, Qasimu ya ja su Kawu zuwa gida, Uwatale da matar Gambo aka bari a asibitin kowa ya kama gabanshi. Murna da jin daɗin da Uwatale take ciki yaƙi ɓoyuwa sam ko me Hindu ta tare mata oho, ko in an saketa me zai ƙareta dashi ita kaɗai ta barma kanta wannan sanin. HINDU: A hankali nake ƙoƙarin buɗe idanuna amman tsabaragen yadda ya kumbura yayi nauyi na kasa buɗeshi sam. Bakina ma da ƙyar na motsa na ambaci Allah, wallahi ko hannuna bazan iya ɗagawa ba. Abubuwan da suka faru a ofishin ƴan sanda na shiga tunowa, ni dai nasan ina zaune a motane amman yanzu kuma a kwance nake jina. Yanayin nauyin jikina ya riga ya bani amsar abinda ya faru tunda in da ana sabawa dana saba. "Alhamdulillahi zubaina Luba ta samu kanta fa. Hindu kin kasa buɗe idanun naki ne ko?. Bari a ɗan gargasa miki fuskar da ruwan ɗumi kumburin dama yayi yawa. Luba ɗebo ruwan ɗumi da tawul." Yaya Saratu ke magana hannunta a cikin nawa, daurewa nayi na buɗe idanun da jarumta sosai in tashi dai na kasa har Luba ta ƙaraso bance komai ba. Ita da kanta tai da mun ruwan ɗumi harma da jikina shine ma harna iya tashi na jingina a kan gado, da taimakon Luba da Yaya Zubaina. Yaya Saratu dama uwar tsoroce duk sanda ta ganni a cikin wannan yanayin to ɗari ɗari take yi dani bata iya matsowa inda nake. Meke faruwa Luba. Hajara ta koma gidan Figo ɗin ko? " Na furta ina kallon luba. "Hindu ajjiye wannan zancan na kunna ruwan zafi a banɗaki Muje in taimaka miki ki gargasa jikinki a kawo miki abinci kici, yanzu fa ƙarfe takwas ne na dare" Cewar Luba dake ƙoƙarin ganin ta kamoni ta taimaka mun. Ita da Yaya Zubaina suka kaini banɗaki na zauna zaman daɓaro a banɗakin suka ja mun ƙofar suka fita. Naga hannun Luba a ɗaure da tsumma. Tuƙuƙin baƙin cikin mahaifiyar Hajara yana kamani, Allah kaɗai yasan adadin yawan iyayen da suka tursasa ɗiyoyinsu zaman aure mai cike da zalunci, sabida kawai dalilin ƙin zawarci da kunyar idanu, ko abinda za'ace. A hankali nake watsa ruwan yana shiga cikin jikina da kyau ina tuno irin yadda Figo ke shigowa da mata har kan gadonshi kuma yasa Hajara tayi musu girki. Wallahi wasu mazan haɗuwarsu da Allah ba kyau babu daɗi, sabida irin zaluntar matayensu da suke yi. Hmmmm Allah yasa mu dace ina fata wannan ya zamemun matattakalar nasara akan tafiyata ta tallafama ƴan uwana mata, wanda a zahirance maza ke yaƙi da mata ire_irenmu. Na jima sosai a banɗakin ina gargasa jikina kana na ɗauro alwala ga wata iriyar yinwa da nake ji kamar me, har wani juwa nake gani. Na fito ɗaure da tawul a jikina, Yaya Saratu na zaune suna waya da Baba Sojanmu. Yaya Zubaina da Luba tuwo suke ci sun yi mun ɗare ɗare a gado. "Hindu tawo muci tuwo kafin kiyi sallah ga shayi mai zafi ki soma warware hanjinki" Doguwar riga mai sauƙi na zura a jikina. Ke Luba ba zaki zo ki tafi gida ba koko sai Sanusi ya kiraki ya soma faɗa tukunna? " Na faɗa cikin sigar zolaya ai ko ilai sai ga kiran Sunusi ina zama. Shayina na ɗauka na soma kurɓa. "Sai kirana yake yi kuma na faɗa mishi zan kwana a nan, sabida yanayin jikin naki, harfa na tura Zulaiha ta kwana da yaran gudunma magana ko me yake son yace mun kuma oho" Tsakanin mata da miji sai Allah. Yaya Saratu yaushe kuka zo? " Gama wayarta da Baba Sojanmu Kenan. "Hmmmn Hindu kedai bari yau ni naga abinda yafi zare tsayi. Ke dai ci abinci ki rama sallolinki sai ayi magana." Bance komai ba nasan bazai wuce akan batun Hajara da kuma tashin da mutanena suka yi ba. Soma cin ciwon nayi ina tambayar Yaya Zubaina banji motsin yaran ba" "Hmmmm Surukarki tana asibiti, Azgar da Ƴar uwarshi sun tafi asibitin kai abinci. Ke dai ci abinci za'ayi miki bayanin komai Hindu. Naci abinci sosai dan saida na ƙara cin malmala guda bayan wanda naci, na shanye shayina, jikina babu kuzari a zaune na rama sallolina ina kan daddumar ina ambaton Allah Yaya Saratu ta labartamun halin da ake ciki da abinda makarai suka sa na aikata. Ga hannun Luba data samu tsagewar ƙashi ma. Allah shine shaidata ni banji wani ɗar a zuchiyata dangane da abinda ya faru ba, in aka duba sababin faruwar da kuma ai bani bace suma sun sani, mutum bashi da ikon hana aljanin da ya hau jikinshi aikata abinda yaga dama. Asalima makarai na yaƙar maƙiyan mutum ne, akasari in banda ɗaiɗaiku da suke aiwatar da son nasu zuchiyoyin, zagina suka yi, su kuma suka bani kariya a tunaninsu to menene na girmama abu in ba dai rashin son a zauna lafiya ba. Haƙiƙa bance abinda ya afku daidai bane, kuma bani da iko akai adalci kaɗai nake son aimun. Hmmm Yaya Saratu shine duk kuka damu akan abinda ni Hindu bani da iko akai, kuma ban isa in saka ko in hana ba, asalima a lokacin da abun ke faruwa bani a cikin ainihin duniyar mutane? Ni a hangena wannan ba wani abun damuwa bane, da har zai zama babba ba, lalurace tana iya faruwa kuma da kowa, amman in suka ce zasu ɗauki mataki babu mai iko akai daga ni har ku. In dai dan wannan ne ku koma kan iyalanku babu komai abinda duk ya faru muƙaddarine na dogara da Allah shine majiɓanci al'amurana alƙalin alƙalai. Amman ni ko gezau banji ba gaskiya. Kuma na kasa tuno komai" Shiru nayi ina ji a raina Allah yasa sanadiyyar wannan abun auren nawa ya mutu, ko zan shaƙi iska mai ni'ima. Su suna tsoron kar auren ya gutsirene ni kuma a wajena gutsirewar nake so. Amman magana ta domin Allah na tausaya ma Nanno domin Uwace, kuma dama ba lafiya gareta ba nima bazan taɓa so hakan ya faru dani da matar Azgar ba, ko ya faru da Innarmu da Matar Akarami ba, wannan shine gaskiya amman akwai abinda baka da iko sai ido kawai. "Hindu ai matsalar shine su Dangin mijinki da yaran ɗakinsu Mijinyawa Yaya zasu ɗauki lamarin, shine abun hangen. Ba lalle su yi hange irin nawa da naki ba" Katseta nayi da faɗin. Musamman in suka saka son zuchiya da ƙin karɓar gaskiya a lamarin ba. To Yaya Saratu yaya zaku yi in damuwar kuka yi? " Luba tace. "Daɗina dake Hindu duk girman abu a idanunki maidashi kike yi ƙarami, amman wannan lamarin fa babbane wallahi tsohuwar ta bugu sosai, ni bana ta Jamila ma dan ita a cikin hayyacima za'a iya dakuwa babu kuma abinda zai faru, girma da darajar uwane kaɗai yake tsoratamu duk da akwai fahimta tsakaninki da gogan naki" Yaya Zubaina tace. "Da fa gaskiyar Hindu wani abun ƙarfinka yake fi, dole ka mayar dashi ba komai ba sabida babu yadda zaka iya goge wannan abun, ya zamto babu shi. Hindu da gaskiyarta" Dama Yaya Zubaina tafi sauran ƴan ɗakin namu fahimtar halina, da ra'ayoyina da yadda nake tafiyar da rayuwata. An daɗe ana tattaunawa kafin Yaya Zubaina da Yaya Saratu suka yi mun sallama mun tsayar da matsayar gobe da safe Baba Sojanmu yace zai biyo ta nan gidana, shi da Akarami su ɗaukeni zuwa asibitin mu dubo su Nannon. Ni da ta tawa za'abi wallahi da ba sai sunje ba, dan nima ko babu inda zani. Luba na kwance a gefena tana aiki a laptop ɗinta da hannu ɗata, nima kawai sai na hau Facebook nayi rubutu mai taɓa zuchiya na dangane da halin da Hajara take ciki da irin tauyeta da mahaifiyarta tayi, ban faɗi sunanta ba, kawai labarin na bayar tare da ɗaurawa da tsokacina a bisa nazari da nayi akan iyayenmu na Arewa musamman mata_matan. Rufe laptop ɗin nayi ina shirin kwanciya na jiyo su Azgar suna kwankwasa ƙofa, Luba ce ta buɗe musu suka shigo. Bakin Azgar nake ta kallo daya kumbura ga ciwo. Azgar me ya sameka haka a baki haɗarin mota kuka yi ne, naga bakin ka da ciwo kuma har an wanke ma an saka maka jibi? " Murmushi yayi yace. "Ammi ya jikin naki? " Da sauƙi faɗamun abinda ya sameka" Luba ya kalla kamar yana mata ishara da ta sanar danine. "Ai kuwa jama'ar taki yau basu bar yaron nasu ba idanunsu ya rufe, ta goɗiyarsu kawai suke, duk sun nakasamu" Shiru nayi kawai tare da girgiza kaina, to me zance sai fatan Allah ya basu lafiya kawai. Basu wani zauna ba sukai mana sallama suka je suka kwanta. "Umm bari nima in haɗiyi maganin ciwon gaɓoɓi hannuna duk sun yi mun nauyi ɓallo mun biyu" Mai ya samu hannun naki, tsagewar ƙashinne? " Madadin ta bani amsa sai muka tuntsure da dariya kamar bamu da matsalar komai. Luba ke ai muguwace bani labarin irin dakuwar da Yaya Jamila tayi" Dariyar muka kuma kwashewa da'ita tana hawayen mugunta, tana bani labarin yadda ta kaya. Hmmm Allah ya kyauta ya yaye ma duk masu ɗauke da lalurar makarai" "Ai baki sani ba Hindu wallahi ni sai yaune naji dama ana aron makarai, dana ara a wajenki kinga Sunusi Allah irin dukan da zaici ko ƴan gidansu ba zasu ganeshi ba" Da dariyar mugunta ta ƙarashe zancan nata, nima dariyar nake yi sabida ta mugun bani dariya bata san wahalar da gangar jiki ke samu bane, a yayi da iska ya hau kanshi ba shi yasa, gani kawai take ji amman bata taɓa ɗanɗana zafin ba. Adda'a nake ma masu irin lalurata Allah ya basu lafiya. Mun jima muna tattauna matsalolin Hajara kafin mu ka yi bacci, cikin baccin tabbas na ji dawowar mijinyawa dan har ɗakina saida ya murɗa yaji a rufe bai dai ƙwanƙwasa ba. Da tausayin Nanno na kwana wallahi a raina duk tsiya uwace, kuma ita ta haifi uban ƴaƴana ko da bama tare da ɗanta, wallahi bazan so abinda zai taɓa lafiyarta ba musamman kuma ace nice sila. Haka dai bacci mara daɗi mai cike da mafarki kan mafarki garin ya waye mana, kuma ya kasance ranar asabar ne babu makaranta yara, muma bamu da aiki. Da misalin ƙarfe bakwai na safe fitowata wanka kenan na ke jiyo hayaniya da zage_zage ana dukan get ɗin gidanmu. "Hindu lafiya wannan doke_doken ƙofar kuma daga ina? " Wallahi kafin ince wani abun muka jiyo hayaniya a tsakar gida Luba dai da gudu ta fice ni kuma na tsaya na zura dogon wando da riga doguwa na fito. Muka ci karo da Mijinyawa daya zuro jallabiyya jikinshi duk kumfa da halama wanka yake yi ma. Motar su Baba Sojanmu na tsakar gidan Baba Sojanmu da Akarami, sai Innarmu da Yaya Saratu. Masu wannan ihun kuma su Yaya Zakiya ne da matan su Gambo harda Uwatale wai dukana suka zo su yi a bisa abinda ya faru. Uwatale da goyonta fa a bayanta, sunci ɗamara. Baba Sojanmu in ya kalleni, sai ya kallesu, ya harɗe hannayenshi a ƙirjinshi kawai, ga hula mai malafa a kanshi ta sojoji, yayi zanzaro da bel ɗin sojiji. Wuuu akwai ƙura. Mu kwana anan sai Allah ya kaimu gobe. (Masu tambayar turaren wutan da Hindu take amfani dashi, dasu makhmariyya, na jiki, ta na gashi, kuimun afuwa zuwa gobe zan sanya muku farashinsu in sha Allah) Mrs BukhariTSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI. LAMBA TA GOMA SHA SHIDA (16) ✨ MAKHMARIYYAH OUD_ AL _NAFEES MRS BUKHARI ƘAMSHIN ALFARMA DA GYARAN JIKI! ✨ Kuna neman ƙamshin da zai riƙe jikinku kuma ya daɗe, kina neman man da zai gyara miki fatarki ta dinga walwali da sheƙin kyau. Ƙamshi kike so ki dinga yi mai ɗorewa da kama fata da kaya yayi daram? Ga samfurinmu na musamman da aka tace shi don mata masu aji da son tsafta. Riko a Fata, shafawa kaɗan yana manne wa fata na tsawon lokaci, In na jikinki ya manne a kayanki yana daɗewa a kaya har sai kin wanke tasirin ƙamshinshi zai gushe. yana fitar da daɗaɗan ƙamshi a duk lokacin da kuka juya kwalbar kawai. Kula da Fata Saboda ingancin haɗin, yana taimakawa wajen lafaza jiki, yana ba da taushi, kuma ba ya barin kowace irin matsalar fata. Adon Sarauta. Ta zo a cikin babban akwatin gilashi mai kauri da adon gwal na gaske wanda ya dace da darajarku. (Farashin wannan makhmariyya mai suna a sama shine 28k ce Hajiya. Siyan nagari maida kuɗi gida) Jahilci akace yafi hauka ciwo inji masu iya magana. In da ranka akace ka sha kallo. Wallahi yau dangin mijinyawa sun kankaremun haddata tas. "Menene haka Yaya Zakiya kuke yi iye? " "Abu ta kazan.. Muke yi ɗan ta abu kaza kazan wanda yaima kazan dan ta kazan.... Ashe babu daɗi mu ta dakar mana uwa? Wallahi babu abinda zai hana mu bata kashi a gidannan, kai in bakai wasa ba har kai zamu haɗa mu doka wawa wanda baisan zafin uwarshi ba, sai zafin Hindu da iyayenta ko? " Tana kaiwa haka ta yo kukan kura wai zata nufo ni. Baba Sojanmu fa yana tsaye ya harɗe yana kallon komai. Innarmu kuwa tazo wuya_wuya. Mijinyawa yayi carab ya riƙeta suka shiga kokawa a ƙoƙarinshi na hanata ƙarasowa gareni. Dambe ƙaƙas a tsakaninsu, bai hanata dukanshi ba, bai kuma yadda ya rama dukan ba, kariya ce yake bani kawai. Ni ko uwatale ma nake hari wallahi. Baba sojanmu ya dubeni da kyau tare da nuna mun Mijinyawa da Yaya Zakiya. "Irin abubuwan da akaita ji miki kenan, amman sam kika kasa ganewa. yanzu in ba jahilai ba wa zai aikata abinda ƙauyawan matannan suka zo suka aikata? A ƙofar gidanki fa har maƙota sun soma leƙowa, burinsu su yi inbarasin ɗinki, wandaful ji wannan yadda take faɗa da mijinki? Wanda shal neba ent" Shiru nayi kaina a ƙasa kawai, a lokacin inda za'a tsaga jikina ba za'a tadda jini ba. Ji nake jikina na wani irin mazari. Luba na ƙoƙarin ƙarasawa wajensu Uwatale da suke zage zage suna cema mijinyawa ya sake Yaya Zakiya, Baba sojanmu yai mata daƙuwa. "Ungo naki Lubabatu, ke kika haɗa balle ki raba? Ai Hindu zata iya na turustin ɗinta" Nuna mun su yayi halamun inje. Ai kuwa tamkar alakatane a hannunshi, nayi kukan kura na finciko Uwatale, kafin ta ankara na fusge goyonta na miƙo ma Luba. Habawa, cikin rufewar idanu na hau dukan Uwatale tako ta ina kuwa, musamman bakinta na gulma daya jima yana ƙulla sharri. Tama kasa komai, sabida ta tsorata a zatonta makarainane suke aikin, amman nice haukar gangan kawai nayi. Sai dai kash ana hakan na gasken suka kawo ziyara, ni dai inata jin ihu da ele a kaina kawai. Bazan tuno komai ba gaskiya. Sai can na ganni a gefe a zaune a dokin ƙofa Akarami na riƙe dani shi da Yaya Saratu. " Gud Hindu, gud, Ku shiga ku sako mayafinku mu wuce asibiti, Hindu ta dubo surukar tata" Shigewa ciki muka yi hayaniyar sai sake tashi take yi, maƙota fa duk sun yi cirko_cirko a bakin get. Innarmu bata ce uffan ba, amman naga jikinta yana ta kaɗawa, Baba Sojanmu ya riƙe hannunta gam. Luba kina ganin irin abinda dangin mijinyawa suke yi, ssu inga kamar basu da cikakken hankali fa. Wai shin menene musamman da yawa_yawan gabar da take tsakankanin dangin mata da dangin mijine? Nifa a duk binciken da nayi, da karatukan dana yi bincikena ya nuna mun dangin miji kishine da baƙin cikin matar ɗan uwansu, da mugunta itace ta cika fal cikinsu. Muddin za'a ganki cikin suturar arziki ke da yaranki, miji na ji daku, kina zaune a muhalli mai kyau, ba'a ganinki kina cin abinci mara kyau, kina ɗaura sutura mai kyau, mijinki na da rufin asirinshi. To idanun danginshi rankatakaf yana kanki sai kiji wani a gabanki ana cewa ai wance kin miƙe ƙafa da yawa aure zamu yima wane gaskiya. In kuma aka ganka a wahale miji na wulaƙantaka, babu abun dariya da gulma da zunɗe kamarka. Wai yaushe wannan al'ummar tamu ta lalacene. Wai yau ni Yaya Zakiya dasu Uwatale suka yo zuga wai zasu dakeni har cikin gidana." Ai sai na sake zaburewa inason in fita in kuma haɗama Uwatale jini da majina. Luba ce ta ƙanƙameni. "In kina ma Allah ki rabu da Uwatale haka, Hindu duk kin farfasa mata baki fa. Wallahi da kika finciko goyonnan, kamar zuchiyata kika finciko na zaci makaranki zasu doka yaron da ƙasane, yazo ya mutu mu shiga bakin duniya, sai suka miƙo mun bayan sun karyamun ɗan hanun nawa. Wata dariyar takaici nayi ina ɗaura ɗankwalin doguwar rigar atampar dana zura. "Ni mijinyawane ya bani tausayi Hindu, bawan Allah dame zai ji ke ba shiri kuke yi ba. Da ƴan uwan nashi ba shirin yake yi ba. Ke baki lura duk ya rame ya lalace bane wai? " Kasaƙe na nayi ina hararar Luba mamakin kalaman tausayin data nuna ma mijinyawa na kamani. Ko da yake dama dai mu muke ba da kanmu. Nace shi Sunusi bakya jin tausayinshi ne Luba? Ki bashi dama mana yaci gaba da yin tamaule da rayuwarki, tunda ke ƴar iska ce. Dallah ni bani waje" Na tureta nayi wucewata ta biyoni mayafi a hannu tana dariya. Ashe Kawu ya'iso shi da mijinyawa Babba suna tare da Baba Sojanmu. Ganin Uwatale a wannan yanayin, anata wanke mata jini a fuskarta, ai sai ya cacimi mijinyawa da damben rashin mutumci. To in ƙarfine dai ya fishi, gaskiya ya dakeshi sosai, duk da shima ya daku babu laifi. Kawu sai kiran sunayensu yake yi. Baba Sojanmu yanata ambaton wandaful, wandaful wandaful. Da ƙyar ƙurar fa ta lafa wallahi Allah. Jagorantarsu Mijinyawa yayi zuwa cikin falona, bisa umarnin Kawu. Muma akace duk mu shiga Yaya Zakiya kuwa, sai da Kawu ya zazzare mata idanu ta wuce tana runtuma kuka kamar wacce akace ma Nannon mutuwa tayi, ohh in ba mutuwa bawa yayi ba yayi ta haɗuwa da abubuwan almara kenan. Baba Sojanmu da ƙyar siɗin goshi ya amince ma Kawu suka shigo, sai turanci yake sakarma Kawu, shi kuma kawu ba bihim. A ƙasa duk muka zazzauna mata_matan mazan duk suna sama sai Innarmu da take sama itama, ƙafarta ɗaya bisa ɗaya. Kawu ne yayi gyaran murya yace. "Dattijo ayi haƙuri dan Allah kasan sha'ani na mata, wani sa'in ragaggen tunani garesu. In ba haka ba taya Zakiya zata jagorancesu suzo dukan matar ƙaninsu, akan abinda su kansu sun yadda Hindu ta aikatane ba'a cikin saninta ba. Ayi haƙuri Kema Hindu, da kai Mijinyawa ƙarami, kuyi haƙuri tayar muku da hankali da akayi da safe haka. Kai kuma Mijinyawa Babba ka cika tabbatacce wato ashe kaima a bayan matarka kake. To mana daga shigowarmu dan ka ganta cikin jini sai ka hau kokawa da abokin tagwaitakarka, anya kuna da lafiya" Baba Soja yace. " Well, To wai in ba dan shi mijinyawa yananan ba dukan ita Hindun zasu yi, su zo har gidanta. Shin a doka sun san menene hukuncin ka biyo mutum har gida kace zaka dokeshi kuwa? Shiga gidan wani wanda a turance muke kiranshi da ( Housebreaking/Burglary) In da ranane mutum ya shiga gidan wani da zummar ya dokeshi, ko aikata wani babban laifin zai iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekaru tara zuwa goma a kurkuku. In da daddare kuwa ya shigo, kuma akaci sa'a laifin da yazo da zummar aikatawa ya aikatan to fa doka na kiran wannan da Burglary, kana hukuncin na iya kaiwa ga ɗaurin rai da rai ma baki ɗaya. Duk da basu aikata abinda suka so ba, ma'ana basu taɓa jikinta ba, tana da hakki a bisa ɓata mata sunanta da suka so yi, sabida dukan ƙofarta da sukaita yi, da hayaniyar zage_zage yasa maƙota sun firfito ga firgitata da suka yi, dis is an insolt, Sannan ko kotu muka kaisu sai anci tararsu kana kuma su sha ɗauri. Bazan yadda da wannan ƙasƙancin ba. Shi nou ha rait, kuma zan tsaya mata, Yayanta zai tsaya mata. An den ko da Hindu ta kashe waccan baƙar ta kar banza, sabida su suka take doka suka shigo mata, ai sun shigone da zummar dukanta wanda hakan can tek ha lif u nou" Murmushi nayi dan naji daɗin wannan bayani na Baba Sojanmu, kuma gabaki ɗayansu babu wacce bata ruɗe ba. Bare suna ganin Akarami da kakin sojoji a jikinshi,sun san duk abinda yake faɗa zai iya samun su. Kawune yace. "Assha Dattijo ayi haƙuri, ai rashin hankaline kawai irin na mata da shashanci in ba haka ba ina Zakiya, ina yin zuga da zummar dukan matar ƙaninsu. To yanzu da abinda suka zo da niyyar yi ya yiwu kuma fa? " "Ai Baba da yanzu wani labarin akeyi, domin gaskiya da wallahi ba zamu yadda ba, sabida Hindu abinda ta aikata a bisa rashin lafiya ne, kowa ya sani. To damme su da hankalinsu zasu zo suce zasu doketa, sabida itace mara gata ko me ake nufi? Tana da cikakken gatanta wallahi, da sun taɓata a nanne zasu gane gatan nata dan wallahi gidan yari kam sai sun cita ko wanne matakine zai biyo baya na dangane da aurenta bazai dameni ba. A yanzun ma sun taro mach tunda ai sun shigo, sun kuma yi yinƙurin dukanta, basu ci nasara ba ita wacce ta daki mijinta, shima wannan ai ya dakeshi on ha bihaf, sabida haka ba zamu bar wannan maganar sasakai ta wuce ba" Cewar Akarami da ranshi yai masifar ɓaci, Mijinyawa yace. "Balle wannan lamarin bazai taɓa auren Hindu ba, muddin nine mijinta. Zan iya shaidar tarbiyyar Hindu a gaban idanunta da bayanta, da gangan kuma cikin hayyaci ba zata taɓa aikata abinda ta aikata ba. Suma rufewar idanune abinku da an taɓa mahaifiyarmu. Amman ni da Kawu muna masu bada haƙuri Baba Sojanmu Innarmu, Akarami, Yaya Saratu, Luba, da ma Hindun ayi haƙuri" Baba Sojanmu yace. "Am furoud ob u Mijinyawa, ka nuna mun kai tsayayyene akan Hindu, kuma kana da ra'ayin kanka. Amman uhmm lallai zamu ɗau mataki." Kawu ya daka ma Yaya Zakiya tsawa wacce jikinta duk ya mutu yace. "Ki ba Hindu da iyayenta haƙuri yanzunnan, ko kuma in sassaɓa miki. Jamila tana can wuya a kumbure amman bata dena haɗa husuma ba. In banda neman sale salin magana ma, a wajen Uwatale da mijinta yafi cancantar su zaunane ko a nan wajensu Mijinyawa ƙarami domin Allah?" Sai nace dashi. Ballantana Kawu wannan gidan nawane, nice mamallakiyar gidan, ba gidan Mijinyawa bane, takaddun gidan sunane a jiki, lokacin dana sai gidan shi baima sani ba. Yana da kyau ku sani, sabida halin rayuwa naga abun ya wuce gona da iri" Mijinyawa ya dubeni, kafin ya dubi Kawu yace. "Gaskiya ne, gidannan, da motar da take hawa natane, ba nawa bane. Kuma har Nanno na faɗama yaddane dai basu yi ba. Ko na mutu yau wannan gidan ba nawa bane'" "Dis is siriyos, u a de ona ob is wandaful, biyutiful haus, fantasti,. To kun ma ji, laifin ya ƙaru akan wanda suka aikata a baya." Tsawa Kawu ya kuma dokama Zakiya akan ta ba da haƙuri. Baki na rawa, a bisa dole duk suka bimu da haƙuri Baba Sojanmu ya ruɗa musu cikinsu. Mijinyawa Babba ma ya ba da haƙuri bisa dole, wallahi kallo basu isheni ba. Yau Innarmu sarautar take ji, sarakaine a kanta yau, taƙi cewa uffan. Kawu yai ta haɗa Baba Sojanmu da Allah akan abar maganar ta mutu a haka. Mijinyawa ma yaita bin baki, haƙuri kawai suke ta bayarwa dai. "Kagane ni zanso aje Ofishin ƴan sanda a saka hannun da wajewa, duk abinda zaije ya dawo ya biyo baya sune silarshi. Ni ina ganin hakan zaifi abi doka a zauna lafiya." "A_a Soja maganarnan a batta hakanan, a rufeta Allah ne ya haɗamu a waje guda da muna so da bama so baga mu a zaune ana tattauna matsala ba. Ka daure a duba, nama alƙawarin babu abinda zai kuma faruwa, ba zasu sake zuwa ba ma" "Well naji, amman ka sani, tabbas suka sake zuwa mata gida, ko ciwon kai tayi fa to tabbas sune, shari'a daga nan har kotun Allah ya'isa zamu je gaskiya, ka amince? " "Na amince, ba zasu sake zuwa ba. Wallahi nayi maka alƙawarin duk wacce ta sake tako gidannan, ranta sai yayi mummunan ɓaci. Kuma mun shaida mun gamsu gida nata ne, muna mata fatan alkhairi. Ku taso mu tafi ma kawai" Nan ya tusa ƙeyarsu suka fice, Mijinyawa yabi su kawu. "Allah ya kyauta ai kiyi zamanki Hindu asibitinnan bama sai kinje ba gaskiya. Wannan dangin mijin naki suna nemanki da sharri, danma mijinki ba irin mai goyon bayan danginshi bane, ko yasan sune ba a daidai ba. Shin kin dena shan magungunan naki ne ko yaya wannan abun har yanzu basu sakeki ba? " Innarmu tace. "Kasansu da naci ai ko sunce sun tafi laɓewa kawai suke yi, baga dangina sunata fama ba. An tsufa ma amman har yanzu anata abu guda. Ke dai Hindu ki dinga kiyaye duk abinda zai dinga ɓata miki ranki, tunda ku lalurarku bata son ɓacin rai. Sannan wannan nacin da taurin kan naki ya kamata ki rageshi. Duk wanda kike son taimakama in mazajensu ko danginsu suka nuna basaso, sai ki haƙura tunda ba dole bane. Ina amfanin da yaranki da aurenki ace an kulleki a ofishin ƴan sanda, ya kike ganin wannan maganar ta shiga cikin gida yadda za'aita jujjuyata ana kacancanata, masu neman ganin faɗuwarka hankalinsu ya kwanta." Akarami yace. Uwatale kuwa ni naso ace bata motsine a fita da'ita ranga ranga. Duk da gaskiya nasan ta daku. "Sannan tunda shi mai matar yace kar ki fitar mishi da mata, ai sai ki haƙura, wasu ma kina zaune zasu zo neman ɗaukin ki, ke ba hukuma ba ke ba gidauniya ba, ke ba takaddar shaida ba sai taurin kai da rigima da an sake an barki kin shiga aikin sojannan, tabbb za'a sha daga dake wallahi" Cewar Akarami. Dariya duka muka saka Baba Sojanmu yace. "To Hindu ki samu takaddar shaida mana ki fitar da suna, da komai in kika bi komai a tsarin daya dace zaki fi samun taimako harma daga wajen hukuma, kuma kema za'a san da zamanki in wani taimakon za'a ba yar, kema ta ƙarƙashinki za'a samu ki rabama jama'a. Kuma ya kamata ace kina da lauya ai. In kika shirya kimun magana nasan manya duk wani gudunmawa sai in baki, amman ki tabbatar kafin kizo kin tawo mun da albishir na samun gurbin karatun PHD ɗinki tukunna, kema Luba ki nemi gurbin karatu kiyi digirinki na biyu kuna wasa da karatu yadda rayuwarnan ta lalace, mazan ma da yawa suka lalace, ku tsaya da ƙafafuwanku fa. Halin rayuwar gaba ake jiye muku, ko mutuwa miji yayi ya barku da yara sai kuga baku tagayyara ba, ko rabuwace tazo shima mace ba zata lalaceba, kuma tafi kima da daraja a idanun duniya, Kema Saratu kar ki bari in kuma magana ga Innarku ma makarantar nake so ta koma itama. Luba kar ki sake in zo gidanki akan batun komawarki makaranta, ranki bazai yi kyau ba" Dariya duk muka kwashe dashi, Baba sojanmu yana dariya ya miƙe tsaye ba dai a haɗu bai yi batun karatu ba, dole sai yayi zancan a koma makaranta, nasan ina gama Phd kuma zai soma zancan batun zama Dikta ta ilimi, in sha Allah a mata a gidanmu nice Dakta ta farko bazan yi sake irin wanda nayi a baya ba. Har gaban mota muka rakasu Luba ta buɗe musu get suka fice zuwa Asibiti gaisuwar masu jiki. Su Azgar suna can. Wash Luba jikina ciwo sosai wallahi." "Hmmm Hindu, Ai dole jikinki yayi ciwo, damma ƙarfin hali gareki sosai. Hmm zamu koma makaranta dai tare wannan karon, inna soma babu tsayawa saina ƙure kullum Baba Sojanmu in muka haɗu sai ya kwaɗa mana gudumar son karatu, a wannan zamanin karatun yana da matuƙar amfani sosai. Dangane da samun takaddar shaida akan aikinki na agaji ina bayan su Baba Sojanmu gaskiya hakan yana da kyau. Wai ya batun kes ɗin Jamila marigayiyane? " Sosai Luba nima dama lokaci nake jirane shi yasa kika ji ban tada zancan ba, amman dama zanyi takadda dolena tunda inason wannan aikin da nake yi, gaba kaɗan ma aikin jaridar bar muku zanyi fa in nitse a aikin agaji, inason kuma in samu ilimi sosai. Wai Luba ba zaki koma gida ba mai jegon wai dawa kika barta ba zaki je ki dinga ɗaurawa kina sauke tukunyar ƴan barka da kunun kanwar miƙama maƙota ba" Dariya muka saka Luba har tana hawaye tace. "Da'ace bani da abun yi haka dole zaka yi wannan aikin ko kaƙi ko kaso, bama aikin bane wahala tunda ladan gidan aure kake nema babu mai yaba maka duk yadda kayi sai an zageka, dangin kishiya da dangin miji wallahi bansan waɗanda ba'a iya musu ciki ba" Ai duk inda kika taɓa wutane Luba kina ganin abinda a gabanki yau ya faru, na jiyanma akan idanunki ya faru fa ke da ba dan su Baba Sojanmu ba, bamu san yanzu wanne zancan akeyi ba da yanzu unguwarnan ta tashi, naso ki barni in sake jibgar Uwatale nifa a wajena bata daku ba. Batun kes ɗin Jamila ai ya sauya salo, zan baki labari" Wayata ce ta shiga ruri na jawo na duba Hajara ke kirana, da sauri na ɗauka tana kuka tamkar ranta zai fita a gangar jikinta, tayi magana ta kasa ta kashe wayar ta kasa. Shiru nayi ina nazari da tunanin shin mu mata wai a haka rayuwarmu zata ƙarene cikin ƙunci da takaicin mazane? Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace. Hajara ki ƙarfafi kanki da kanki, ki zama jaruma ki nemi ƙafar tsaiwa da kanki, zan taimaka miki da jari sannan duk bala'i ki shiga islamiyya zaki gane haƙƙoƙin miji akan matarshi da naki haƙƙoƙin a kanshi, da yadda ake haƙuri mara cutarwa da yadda ake neman ƴanci kinga addininmu na Musulunci addinine mai sauƙin da babu irinshi. Hajara muddin kina irin wannan kukan akan wanda baisan darajarki ba, to kina cikin wuya, takaici, baƙin cikin da ni dake bamu san yaushe zaki fita ba, ƙila ma iyakar tsahon rayuwarki. Sai kin dakar da zuchiyarki, sai kin saba shanye duk abinda zai faru dake duk bala'i kada ki sake kuka to daga lokacin ne zaki iya tsayama kanki. Me Figo yayi miki kuma ina Mama take? " Ajjiyar zuchiya take ta saukewa da ƙyar tace mun. "Mama muna dawowa ta kama hanya ta tafi. Anty wallahi farfasamun jikina yayi yanzu haka ko iya tashi bazan yi ba" Yawu na haɗiye kuma wai irin mazajennanne akeso ai musu biyayyar yi nayi bari na bari alhalin su kansu basu san me ake nufi da kalmar aure ba basu san ya ake zaman auren ba? Tur da ire iren mazaje irinsu Figo tur da mazinatan maza masu buɗe tsaraicinsu ga matan bariki tur da mazinatan maza masu zinar wayar ire iren su Mijinyawa. Hajara kada ki sake bari Figo ya dokeki, ki haulace mishi duk abinda kika samu ki tabbatar kin buga mishi, ko kuma in kina da halin guduwa ki gudu, in kina da ƙarfi ko da cizo da yahushi ki ƙwaci kanki, in yaga kina ramawa zai bari ko yace kije ya sauwaƙe miki ki huta. Yanzu nasan Maman Junaidu ba zata sake taimaka miki ba tunda kinga daga taimako abinda hakan ya haifar miki, ki ƙarfafa jikinki ko da rarrafene kije ki watsa ruwan zafi in kina da magani ki sha na ciwon jiki ki kwanta, in babu ki aiki yara su siyo miki. Anguwarku unguwace mai tarin dandazon matasa me kike ganin zaki yi na sana'ar cikin gida? Ko da yake ki bari ki warware tukunna zan neme ki da kaina kinji ko? Ki ƙara haƙuri." Albarka tai ta shi mun tana ta godiya tamkar zata ari baki. Haka mukaita tattauna matsaltsalu masu yawa dai har wajajen azahar Luba ta shirya ta wuce gida, bayan ta gyara mun gida har girki tayi mun, hannu a kumbure fa a ɗaure. Wato samun ƙawar da zuchiyarta take a tsarkake irin Luba sai an tona, na dai jinjinama iyabo da Uwani ta balbalin a wajena Luba har ta fiye mun Tabalbalin wallahi. Wajajen dab la'asar ina zaune a falo da labtop a cinyata ina duba abu naji an yage get mota ta shigo nasan ma mijinyawane. Ina zaune kuwa suka shigo da yara. A hankali na amsa sallamarsu kusa dani sosai mijinyawa ya zauna. "Yaya jikin naki Tutar so" Kunji makircin maza ko? Wannan kaɗanne. Hmm da sauƙi ya masu jikin kuma? " Ajjiyar zuchiya ya sauke da yaji na amsa, harda tambayar masu jiki, kana yace. "Da sauƙi sosai. Luba ta wuce gidane? " Kai kawai na gyaɗa mishi. "Ammi akwai abincine yinwa muke ji? " Cewar Azgar. Akwai Innarku Luba ta dafa muku kuje ku ɗiba kuci" Har zasu fice mijinyawa yace shima a zubo dashi. Ina zaune har dai suka gama suka wuce masallaci ni kuma na yinƙura na ƙule ɗakina,naci gaba da harkokina. Wajajen taran dare naji bugun ƙofata a hankali nayi tunanin Azgar ne shi yasa nace a shigo, dake na leƙo nace ya dafo mun ruwan zafi inason shan bunu. Ƙamshin turarenshi yasa na juyo muka haɗa idanu ina bakin mudubi ina taje gashin kaina ɗaya daga cikin abinda Mijinyawa yafi wasa dashi a jikina kenan, ya nutsa kanshi cikin gashin yaita shaƙar ƙamshin dadaɗan ƙamshin makhmariyyar gashi da jiki, da nake sakawa mai suna JAMRAT AL DHAHAB MAKHMARIYYA, daga kamfanin mrs BUKHARI. Kallona yake ta faman yi daga tsaye inda yake. Kafin yayi magana Azgar ya shiga bubbuga ƙofar shima, mijinyawane ya bashi izinin shigowa ya turo ƙofar da turen shayi a hannunshi ɗauke da kofi cike da ruwan zafi. "Abba sannunku da hutawa" Azgar ya faɗa yana wani murnar ya ganmu a tare. Shima ya saki wani fara'a harda wani dafa kafaɗar yaron. Ajjiye a kan taburi Azgar nagode ko?" "To Ammi sai da safenku zan ɗan yi karatune in kwanta." Juyawa yayi ya ficewarshi, ni kuma na ɗakko sikari da ganyen shayin Ahmad nazo na zauna a bakin gado, jikina ko ina ciwo, zazzaɓine mai mugun zafi a jikina. mijinyawa ya zauna a kujera muna fuskantar juna. "Hindu" Ina saurarenka" Na faɗa a taƙaice sai yayi shiru idanunshi ƙur a kaina. Ina jin kaifin idanun nashi amman dai ban ɗago ba. "Na samu canjin wajen aiki kamar yadda aka saba kinsan sha'anin aikin banki, yau kana wannan gari gobe kana wancan garin. To shine nace bari in sanar dake ke da yaran ku zauna cikin shirinku karshen wannan watan in sha Allah zamu wuce. Katsina wannan karon aka lulamu kuma" Ya ƙarashe yana guntun murmushi. Allah sarki Allah yasa ka koma a sa'a, Allah ya ƙaro dubun nasarori" Na faɗa a taƙaice tare da ɗaukar shayina na soma kurɓa a hankali. "Ban gane ba Hindu, amman kinsan tare daku zan tafi ko, kinfi kowa sanin babu inda zanje in bar iyalina a nan ko?" Aikin nawa sai in yi yaya dashi, in ajjiye gani ƴar daɗi mijin da baisan darajata ba, ƴar daɗi mijin da bani da abinda nake burgeshi dashi ko me kake so ne mijinyawa? Bagidajiyarnan mai yamutsattsen nono ce a gabanka, ba Asama'u Sweet L ba, ba kuma Talatu Fist bank bace, wacce tafi tutar so matsayi ba" Kallon ƙuda muka shiga yima juna idanunshi lokaci ɗaya suka sauya launi daga fari zuwa ruwan ja. "Hindu wai ke wacce iri ce da ba kya yafiya bare mantuwane, yanzu duk irin sauke kaina da nake yi dan mu dawo mu sasanta bakya gani. Yanzu duk irin yadda nake sonki bakya gani Hindu sai gasani kike yi. Amman ai kinsan a ko wacce jiha akwai gidajen rediyo, a irin ƙwarewarki abune mai wuya ace kin nemi aiki kin rasa Hindu, kuma kinsan zanyi iya kacin iyawana akan aikin naki taya zan samu wani nutsuwa bana tare da iyalaina? " Bance mai komai ba dan a lokacin in nace zan buɗe baki in yi magana wallahi komai zai iya faruwa ji nake yi kamar in dira a wuyanshi in kekketa mishi kayan jikinshi. "Dake nake magana wacce iriyar zuchiyace dake, baƙa wacce bata yafiya ne? Nace kiyi haƙuri nayi nadama bazan sake ba, inata istigifari ban dena ba to Hindu saina kashe kainane zaki gane nayi nadama koko mai kike so ne, jibi iriyar rayuwar da muke yi ina matsayin mijinki amman tare da ɗana nake kwanciya ke kuma hankalinki kwance bakya ko jin nauyin haka yara na kallo. Shin haka rayuwar aurenmu zata ci gaba da tafiya ko me kike nufi Hindu, tura na neman kaini bango haba dame kike son inji, da damuwar dangina, ko da halin da muke ciki ni da ke akan wani kuskure dana aikata. Wannan ƙananun iskancin sun isheni na gaji, nace miki nagaji." Sai kuma ya sauke murya tare da furta "Hindu Asama'u wallahi Allah ɗaya kenan tunda na aureta ban haɗa shinfiɗa da'itaba. Tun sanda kika turomin saƙwanninnan Hindu har zuwa yanzu ban sake farin ciki ba, Hindu ba farin ciki kaɗai ba ban sake lafiya ba, a kullum da baƙin ciki da damuwa nake kwana nake tashi, ga ciwon gangar jiki shima shirin kayar dani yake yi, sai neman rayuwata yake yi, kuma duk a kan ki Hindu dan Allah na roƙeki ki yadda dani a karo na biyu bazan baki kunya ba. Kinsan ina sonki kin sani Hindu shi yasa ma kike ta wahalar da rayuwata." Fasali ya ja tare da miƙewa tsaye ya juya mun bayanshi yace. "Sai azabtar dani kike yi ki buɗe baki ki amayar da abinda yake cikin ki Hindu kin ƙi, sai faɗuwar gaba nake ciki a duk sanda zan kalleki, kina ta mun gashin ƙuma, Ki tausayama zuchiyata Hindu" Miƙewa nayi ina murmushin da wallahi yafi kuka zafi da ƙuna, taku biyu nayi kawai na ja na tsaya. Mijinyawa kenan bari in tambayeka mana. Da ace Asama'u namiji ne, ka kawoshi na rene shi, sai ka kamamu da irin abinda kuka aikatamun kai da tsohuwar matarka kuma ɗiyar amininka, shin yafe mun zaka yi inna ce maka nayi nadama kenan, sai ka mance komai ka sasankance kaci gaba da rayuwa dani cikin yadda da aminci. Mutumcina bazai taɓu a idanunka ba, sona da ƙaunata zasu ci gaba da guda.... " "Hindu ki dena irin wannan kwatancen kafin kisa kaina ya juye mun, kasheni kike son yi ne wai? Gani kasheni Hindu ki kasheni" Ya juyo a fusace harda nuna ni da yatsanshi jikinshi na rawa na iskanci, wai kishi ne ya kamashi. Dariya ma ya bani amman banyi ba sai cewa nayi. Batun tafiya Katsina babu inda zani ina mahaifata. Aure na faɗa maka na gama, na shigar da batun ma kotu" Sai na koma na zauna naci gaba da shan shayi na. Shima dawowa yayi ya zauna. "To yaya kike so ayi Hindu, wallahi bazan iya tafiya ko'ina in bar iyalaina ba kinsan bazan iyaba Hindu" In kaje sai kayi aure tunda iyali kake nema ai. In kaso kuma sai ka maido Asama'u ko, ka ajjiye daduro.... " "Ya'isheki haka Hindu. Naga halama kin rainani, to bari kiji dole ki bini, ko kuma in kwashe yarana in tafi dasu wallahi" Bazan bika ba, kuma yara in kaga ka fice dasu a gidannan to takaddata ka bani, kana da damar da zaka ɗaukesu tunda ba dasu nazo ba, basa gabana daga kai har su" Na faɗa cikin ruwan sanyi. "Takaddar kike so, burinki mu rabu ko Hindu? " Burina kenan babu amfanin aurenmu mijinyawa, babu in akwai amfani ka faɗamun, dan haka ka sauwaƙemun ka kwashi yaranka in birnin sin zaka koma ka koma" "Shikenan zan miki abinda kike so Hindu. Amman wallahi in muka tafi ba zaki sake ganinmu ba a rayuwarki ba, na faɗa miki kenan sai dai hotuna su zama ababen kallonki, kuma ba zaki sake waya da yara ba kin yadda? " Yara sune rayuwata, amman babu yadda za'ayi mijinyawa ya shiga rigar yara yayi mun barazana wallahi bai isaba. Duk da nasan sharia zata ba yaran zaɓin inda suke so, amman bazan yi faɗa akan duk abinda ya shafu mijinyawa ba. E na yadda, ka kwashesu, ni ka bani takaddata in ba dai so kake in shiga wuta ba" Na furta a ido ko a jikina, amman ta ciki hantar cikina kaɗawa kawai take yi. Taya za'a raba uwa da yaranta tana raye ace ko a waya ba zan sake jinsu ba. Taya haka zata kasance ni Hindu? Amman in dai wannan shine sharaɗin da zai sa mijinyawa ya rabu dani ya sauke mun ƙaddararren aurenshi, na yadda ba gudu ba ja da baya. Fita yayi a ɗakin fuu ya barni ina karanta wasiƙar jaki Tabbb to mu kwana anan sai gobe Mrs BUKHARITSURON TSIRIN.. TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI. LAMBA TA KOMA SHA BAKWAI (17) ✨ SABON TURAREN WUTA. ALFARMA DA ƘAMSHIN CIKIN GIDAN DARAJA. OUD AL MALAKI ✨ Kuna neman ƙamshin da zai canza yanayin gidanku, ya dawo kamar fadar sarauta? Ga sabon haɗin Turaren Wuta na musamman da kowace mace mai aji ya kamata ta mallaka don burge maigida da baƙi. Inganci Na Musamman Yana da inganci sosai, zai fitar da ƙamshi mai daɗi da taushi, a yayin ƙonawa. Ƙamshi Mai Kafuwa Hayaki kaɗan a kan garwashi zai mamaye kowane kusurwa na gida, yana zama a cikin labulaye da kafet na tsawon kwanaki.Mazubi Na Alfarma, Ya zo a cikin kyakkyawan mazubi mai adon lu'u-lu'u da kristal wanda zai ƙawata gidanki Hajiya (Farashin wannan turare shine 25k ne) Mijinyawa:. Yana fitowa daga ɗakin Hindu, falo ya nufa kawai ya zauna ya kasa zama, yana tsaye a waje ɗaya yayi shiru kanshi na sarawa tamkar zai tarwatse. Can ya goya hannayenshi a bayanshi ya shiga safa da marwa, yama rasa tunanin me zaiyi lissafi ya ƙwace mishi baki ɗaya. Hindu ta riga da ta kaishi ƙarshen_ƙarshe ya rufe babinta kwata_kwata ko da hakan na nufin mutuwarshi ne. Shima bawai bai iya taurin kan bane ba, aa abubuwan da suka faffaru na sadaukarwa iri_iri da tayi mishi wanda ne, wanda a tsarin rubutun layi baizo kansu ba shi yake dubawa kawai, yake ɗaga ƙafa, kuma ya doge yake son kare Aurensu. A baya ita ta kare musu Auren, sun so su faɗi su rushe, Hindu ta cicciɓosu tace. A'a ba zamu faɗi ba da izinin Allah, zamu rayu abadan. Ajjiyar zuchiya ya sauke, ya girmama taurin kan Hindu, da baƙar zuchiyarta wacce ta shafe dukkannin alkhairanshi, akan laifi ɗaya ko kuskure ɗaya. Duk da yasan laifinshi yana da girman zunubin da dole Hindu taƙi yadda dashi a karo na biyu. Yasan ba ita yayi ma laifi ba, kuma ya roƙi Allah gafara, yasan Ubangiji mai rahamane mai jin ƙaine, ya yafe mishi. Yana neman yafiyar cutar da zuchiyarta da yayine, da yaddar data bashi ya karya. Da amanar abokinshi da yaci, ya lalata Asama'u da yayi, yayi mata fata_fata da rayuwarta. Masu iya magana suna cewa tsalle ɗaya akeyi a shiga rijiya, amman sai ayi dubu ba'a fito ba. Haƙiƙa zina bala'i ce zina ƙazantace, zina saɓama Allah ne. Tunda ya aikata abinda ya aikata, bai sake samun nutsuwar zuchiya data gangar jiki ba, aikin nashi ma ba maida hankali yake yi ba, ga rigimar Hindu da shirunta da yake gasa duniyarshi. Zuchiyarshi ce ta bijiro mishi da wata tambaya data gigita tunaninshi. Yanzu Mijinyawa inka tafi ciwon Hindu ya tashi wa zai iya kularma da'ita, bayan kasan da irin sharaɗin da iyayenta suka amince da aurenku, Hindu dai inka rabu da'ita ba gidansu zata koma ba zamanta zata yi a gidanta, ka zaɓarma uwar ƴaƴanka zaman kanta kenan koko yaya? " Zuchiyarshi ce tai mishi wannan tintuntinin, sabida girman soyayyar Hindu. Yasan shi wawane akan soyayya, kuma shi da Hindu sunyi wata iriyar shaƙuwar da, rabuwa da'ita a ƙanƙanin lokaci ba abu mai sauƙi bane. Kuma yasan ta fishi jarumta, amman tabbas yasan itama tana gasuwa iyakar gasuwa. Babu shiri ya sulale ya zauna a saman kujera, yasa hannayenshi biyu bisa kanshi ya tallafesu a fili ya furta "Hindu me yasa zuchiyarki take da tauri tamkar tsandauri, da mance alkhairi akan kuskure guɗa ɗaya rak da kika kama mijinki dashi? Gashi a dalilin taurin kanki kina son ruguza mana iyalinmu, ki ruguzamun nutsuwa da walwalar yarana ya Allah" Wata zuchiyar tashi ta tare shi da cewa. "Amman Hindu tana da gaskiyarta, domin anyi mata cin amana ƙololuwar gaban mamakin da ya wuce ace ta yafe a iyakar fatar baki kawai. Ka saketa kawai sai kafi mutumci a idanunta, muddin kaci gaba da riƙe igiyoyin aurenta ma kaida shawo kanta a irin zuchiyarta har abada, kenan rayuwarku zata wanzune cike da ƙunci da ciwon ruhi mai raɗaɗi. Amman in kuka rabu shikenan zaka auri wacce zata ga mutumcinka, itama ta auri wani mijin da zata mutumtashi kamar dai yadda take yi maka a da wannan shawarace. Amman samun mace irin Hindu ba abu mai sauƙi bane, kafi kowa sanin wacece Hindu, ya son da take ma yake. Kuskure anyi. Kuma kai ka rushe gidan gaskiya. Ka saketa kawai, ka saketa" Haƙiƙa yasan duk abinda zuchiyarshi ta faɗa mai gaskiyane, domin zuchiyarshi itace shi tafi kowa gane karatun damuwa da ƙuncin da suke karantawa tare, kuma yana ganin shawarar daya tsayar kenan na sauwaƙema Hindu ya kwashe yaranshi ya nisanta da ita,ko Allah zaisa watarana albarkacin yara ta huce, in shan ruwan Auren bai ƙare ba sai a dawo, in ya ƙare shikenan sai ya gina sabuwar rayuwa, itama ya bata damar gina sabuwar rayuwa. Gara a rabu cikin mutumci, bama zai yadda a shiga kotu dashi ba. A rayuwarsu bai taɓa zato ko tunanin akwai wani dalilin da ka iya zuwa ya raba wannan auren ba, ashe akwai ranar da zata zo Hindu ta rufe idanunta ta runtse taji ta tsaneshi akan laifi guda ɗaya, ba laifuka birjik ba. Yadai sani abadan babu wata mace da zata iya ture matsayin Hindu a zuchiyarshi, kamar yadda aka rasa macen da zata iya hawa matsayin iyabo tsuntsun soyayya a zuchiyar Gwadabe. Yana ma Hindu fin son da Hamma ya nuna ma Iyabo. Hindu ta mishi fin son da Iyabo tayi ma Hammanta. Idanunshi da suka soye yake jinsu inya ƙibta tamkar zasu yage, ya lumshe a hankali wani raɗaɗi ya tsirga mishi har cikin zuchiyarshi. Shiru ya kwanta a saman doguwar kujerar yana sauraren zuchiyarshi, dake aikin watsa jini zuwa gangar jikinshi da sauri sauri. Ya jima gaya a cikin wani irin yanayi daɗewar da shi kanshi baisan iyaka ba. Alwala kawai ya ɗauro sabida bacci ya ƙaurace mishi sam, sai wajajen huɗun asubane da sanyin asuba ya soma ratsa duniya ya sulale akan sallayarshi kanshi da zuchiyarshi suna shirin yin bindiga. Azgar ne ya leƙo falon ya tadda mahaifin nasu a kwance a ƙasa ya takure kamar marar lafiya, take tausayinshi ya dirar mishi ya ƙarasa kusa dashi daf ya tsugunna. Taɓa jikinshi da yayi yaji zafi kau, gashi babu ishasshen lokaci sun kusan makara ma zuwa sallah. "Abba lokacin Sallah yayi ka tashi, Abba kayi haƙuri zan baka wata shawara ka ɗan bama Ammi lokaci zata huce. Amman Abba ka koma can gidan Baba Babba kaci gaba da zama. Zan yi iyakar iyawata inga kun daidaita da Ammi, kuma nasan yadda zanyi kaji Abbanmu? " A raunace idanu tab da ƙwalla yayi maganar, yasan Ammi ce ta caza mishi kanshi tunda shi dai yasan a ɗakinta ya barshi. "To Azgar bari in yi alwala kaga bansan sanda bacci ya kwasheni ba, sallah nayi akan inna idar sai in shiga ciki. Batun sasanci ka bar wannan zancan kada kace ma Amminku komai. Kar ka tunzurata Azgar, rabu da'ita zan tafi bama zata sake ganina ba in dai na bar cikin gidannan. Ya kuma isa haka, ya isa haka Azgar." A hankali ya miƙe ya fita, Azgar ya fito dokin ƙofa yayi tsaye har mijinyawa ya fito suka wuce masallaci. Sai kawai yaji alƙiyamarshi ta tsaya jin furucin Abbansu. Hindu:. Kaina na dafe da nake jinshi yana mun wani irin motsi tamkar mutanen zasu motsa, a haka na rarrafa ko idona bana iya buɗewa na kwanta ruf da ciki kawai sai ambaton Allah a zuchi nake yi ina karatun Qur'ani mai girma. Can sai bacci ya ɗaukeni baccin da yasa na makara ban tashi ko sallar dare ba ranar, motsin ƙofar Azgar da maganarshi ne suka tasheni a lokacin ƙarfe shida saura ashe harma sunje masallaci sun dawone. To dake jikin ba ƙwari sai na sakko a hankali, na faɗa banɗaki ina jin jiwa na ɗibana halamun mutanen suna kusa dab dani basu matsaba, mun kwana mun hantse tare dasu. A zaune nayi sallah ina jingina a gefen gado naji bacci na ɗibana, ban gama jan carbi da yatsuna ba na koma gado nayi wani irin bacci wanda babu lafiya a cikinshi, kunsan sai yaushe na farka wai? Dab magriba gari ya haɗe iska na tashi bababa_bababa halamun ruwa ya kusan sauka. Azgar, Sabira Mijinyawa duk suna ɗakin mijinyawa na zaune a kan gadon kusa dani ya jingina bayanshi a allon gadon ga Qur'ani ƙarami yana ta rera karatu. Sai na jini fayau dani wallahi tamkar an sauke mun dutsen dala a kayi na. Salati nayi a hankali na dubi su Azgar sannan na dubi agogon bango naga lokaci, ni saima na kasa gasgata lokacin da gaskene ko nice dai har yanzu ban dawo daidai ba. "Lokaci ya ja kinyi bacci mai tsayi da nauyi, kina ta firgita zaki iya tashi ki ɗauro alwala ko a kawo miki baho kiyi a gadon?" Mijinyawa ke magana dani da wani irin girmamawa na musamman, dan ya shige irin girmamawar dana san muna ma junanmu a baya. Zan iya bana jin ciwon komai. Yaya kuna nan kuma kun kasa sukuni ko? Hmm watarana sai labari watarana kuma inna kwanta nayi kwanciyar da babu tashi sai an busa ƙaho" Sauka nayi na wuce banɗaki ina jina sayau dani, su kuma jikkunansu sai yayi wani irin sanyi na ban mamaki. Wanka da goge baki na soma yi, kana na ɗauro alwala. Jikina na goge tas na maida kayan jikina tunda bansan yaran ko suna zaune har zuwa lokacin ba. Tura ƙofar nayi na shiga babu ma kowa a cikin ɗakin gashi fes komai na zaune a muhallinshi. Riga na sauya zuwa baƙar abayata dana siya a saudiyya, na feshe jikina da turaruka kusan kala huɗu na wajen mrs Bukhari, masu ƙamshin gaske, da jumuri, na yayyafama sallayata humra mai sanyin daɗi duk nata ne, kana na ta da kabbarar rama sallolin da aka bini bashinsu. Ina ta jin shige da fice a ɗakin ni dai ban tashi a wajen ba saida nayi magriba ina zaune ina adda'a, Mijinyawa da yaran suka shigo. "Hindu baki taɓa abincin ba kizo ki ci shayinma harya huce ai" Ban ce uffan ba na taso nazo na zauna a gaban abincin. "Ammi ya jikin naki? " Azgar ya faɗa yana taɓa wuyana dan yaji a yanayin da tamfarecata take. Jiki da sauƙi Azgar ɗin Ammi ya karatun amman? Kuyi haƙuri wannan ƙarshen makon bamu samu zama ba aimun afuwa. Gashi wannan satin za'a shiga bikin gida ba zama mune har katsina" Sabira tayi carab tace. "Gashi bamu da hutu a makaranta ai da gidan zan koma sai an gama bikin tas" Dariya kawai nayi mata ina kallonsu yadda suke jin daɗin hirar dani, Allah yaba duk wata mace dake son haihuwa kuma bata samu ba, jama'a ƴaƴa rahamane. "Azgar abar Ammi taci abinci maza kuje kuma ku bamu waje" Na lura Azgar na farin ciki yaga mun keɓe da Babanshi, farin ciki har a fuskarshi yake bayyana. Shayi nake sha saida na ɗumama ƴan hanjina, kafin na zuba abincin tuwon shinkafa miyar kukane taji naman rago tana ta ƙamshin man shanu. Malmala ɗaya babba na saka da nama uku na soma ci Mijinyawane yayi abincin ba Azgar ba, wannan miyar kukan tashi ce mai ɗan karen daɗi da yasan ina so ina santi akai kuma. "An sallami su Nanno ɗazu da yamma. Kawu yace in sake jaddada baki haƙuri tare da su Baba Sojanmu, Nama kira Baba Sojanmu na kuma bashi haƙuri." Ayya Allah ya ƙaremu da lafiya baki ɗaya, ya kiyaye na gaba" Saida ya bari nayi rabin cin abincin kana yace. "Ni da kaina nayi miki wannan miyar ta soyayya mai tarihi a zamantakewarmu. Hindu, kullum sai nayi mafarkin rayuwarmu ta baya, wanda ada nake jin babu wani magidanci daya fini kwanciyar hankali, da tsantsar fahimtar iyali kamata. Sai dai kash na ruguza wannan tarihi da zunubaina. Damuwata shine kada wannan yaci gaba da zamema mata hujjar faɗin namiji ba ɗan goyo da zani bane. Ko kuma matan da suke tallafama mazajensu suji tamkar labarinmu ya zame musu madogara. Wallahi Hindu ina sonki so mai yawan da harshe da haƙori ba zasu iya furtawa ba, alƙalami da tawada ba zasu iya rubutawa ba. Naso mu sake gina sabuwar rayuwa mai tsabta, mai cike da alƙawarin zaki sameni fiye da irin samun da kikai mun a baya. Naso ki yadda mu sake gari, ki bini Katsina sabon gari sabuwar rayuwa, sabuwar soyayya wacce babu nadama ko dana sani a cikinta. Naso na sake baki kariya, ta ko wacce fuska zan kuma kare miki kaina in sha Allah. Amman kash kin ƙi aminta, kuma banga laifinki ba. Na gode da yafiyar da kikai mun, ki ɗan bani lokaci kaɗan kafin in tafi Katsina zan miki abinda kike so. Inaso ki janye batun ƙarar da kika shigar, zan miki yadda kike so. Fatan alkhairi da samun nutsuwar rayuwa a gaba" Murmushin takaici da baƙin ciki na saki, har saida ya ba da sauti. Inama duka waɗannan kalaman zasu iya samun muhalli a zuchiyata har naji na nutsu, na gamsu dasu harma inji kaina na yawo a sama ina faɗin babu wacce tayi dace kamata. Sai dai kash duka waɗannan kalaman a mazaunin yaudara suke da borin kunya a wajena. Mijinyawa kenan, baka bani abinda zan riƙa wanda zaisa in sake amincewa da kai ba. Ka sani damammaki a rayuwa galibi sau ɗaya take zuwa ma ɗan Adam, in wannan damar ta suɓuce ya rasata har gaba da abada. A fili abun yake kamar kofin tangaranne da aka saki a ƙasa ya tarwatse kana tunanin zai dawo yadda yake a baya wajen kyau, ƙarko, harma da sheƙi? Ka ɗauka haka darajarka, da kimarka, da sonka suka faɗi suka fashe, kuma ni banyi yinƙurin tattarewaba ya gama amfani a wajen Hindu. Hukuncin dana yanke nayi imanin in kaine saika yanke mun hukuncin da yafi wannan tsauri da muni. Ka fahimta da ace zan iya haƙuri, da bamu kai haka ba zan haƙura mu zauna. Allah shi ya haliccemu, kuma yayi mu mabambanta, masu ra'ayi mabambanta. Wata wannan ba komai bane a wajenta, ni kuma komai ne a wajena. Bana nufin a zamanmu ni daidai nake yi ɗari bisa ɗari. Hindu mai yawan zunubice, kuma mai yawan neman gafarar Ubangiji ce. Zaman mu wuta zai kaini, kana son ace hakan ta faru?" "Ko kusa bazon so hakan ba. Haba Hindu, taya zan so waninku bake ba ma ku shiga wuta" To nagode, Batun kotu na janye in sha Allah. Na yafe maka har gaba da abada. Ni Hindu inai maka fatan alkhairi da samun kyakkyawar rayuwa a gaba, wacce tafi ta baya. Bazan gushe wajen yima fatan alkhairi ba. Na kuma baka lokacin kamar yadda kace kafin ka bani takaddar, ina fatan ka cika alƙwari" Na ƙarashe ina cizon leɓena na ƙasa, wallahi matar data kama mijinta da laifin zinar cin amana, itace kaɗai zamu iya raba wannan ciwon harma ta gane me nake nufi, ku kuwa da baku taɓa kamawa ba, bana ma ko maƙiyiyata wannan fatan. Balle ni duka biyu a lokaci ɗaya aka bani, ga laifin zina, ga cin amanar da akaimun, ka reni yarinya da hannunka mijinka ya lalatata kuma yayi miki kishiya da'ita, ya gama aibata miki halittarki a gabanta, ta zageki, ya zageki shima hmmm. "Hindu.... " Dan Allah naji, wallahi ni bana son ganinka bare jin amon mayaudariyar muryarka babu abinda zai karyamun zuchiya sai ƙudurar Allah" Na faɗa a tsanake amman ta cikin jikina zafi nake ji kamar zan halaka. Ai sai ya buga kai a faranta. "Hindu bansan wacce iriyar zuchiyace a jikinki mai tauri da tsauri ba, riƙonki yayi yawa Allah ma munai mishi laifi ya yafe mana ballantana ke Hindu. Tunda dai nayi miki duk wata laluma kinƙi bani haɗin kai, haƙuri da junanmu shi yafi mana kamar yadda kike fata da buri, ina fatan ko a gaba wani abun ya taɓa zuchiyarki ki tuno dani, ko dan yaranmu. Amman wallahi ki sani yarana dasu zan tafi kuma ba zaki sake sakamu da idanunki ba, na rantse miki da Allah saina nuna miki ƙaryar taurin kai kike yi. Maras mutumci, mai shegen taurin kan tsiya. Yara kun rabu kenan, nima kin rasani. Mijinyawa yayi miki wuya harda maƙogoro. Zaki ga taurin kai da baƙin halina. Kin kaini geji" Anan zancan ya tsaya mana. Ya fice ya bani waje. Washegari kuma Monday, nan kowa ya shiga hada_hadar fita. Da masu zuwa biɗar ilimi, da masu zuwa biɗar kuɗi, haka yake a ko wanne gida dama duniyar baki ɗaya. Abaya na saka mai daraja da tsada ruwan jinin kare wato marun kala, da surfani baƙi a jikinta naso rigar sosai a Saudiyya na siyeta. Bayan na busar da gashina na shafeshi da man gashi mai sanyi mai ƙamshi, na saka baƙar hula a kaina tare da yane mayafin abayarnan a kaina, takalmi da jakata baƙaƙene, sai zoben gwal dana ƙara ɗaya a hannuna suka zama uku, na shafa Humra mai sauƙin ƙamshi wacce musamman nake siya a hannun mrs Bukhari, wannan tana yi ne ga mata masu fita aiki in ba daf jikinki aka zo ba babu mai jin ƙamshin, daga nesa za'a jiki bakya ƙamshi mara kyau mai cakuɗe da ƙamshin ƙashinki, wata ƙashinta na da zafi yana sakata wani irin wari marar daɗi, to shi sanya humra mai sanyin ƙamshi na taimakawa ka wuni sumul ko zufa kayi ba zata yi wari ba, sannan masu lalurar asma suma irin wannan ɗin take siyar musu. Ɗakina na kulle muka haɗu da yara a Kicin suna karyawa, nima Azgar ya bani nawa a kula na kwashesu nayi ficewata aiki abina, bayan na saukesu a makaranta mutuminku bamu haɗu ba sammako yayi yau. Duk da ya kasance ranar sunan kishiyar Lubane amman itama hakan bai hanata zuwa aiki ba, sha biyun rana muka baro wajen aiki zuwa gidan Luba inda gida ya cika, cikowa bata wasa ba mata har ƙofar gida ana zazzaune. Sunusi da abokanshi kuwa suna gefe a wajen an shinfiɗa babban tamfol saniya ce shinkafe a kai suna ta aikin daddatsata. Tsakar gidan kuwa a lokacin an sauke tukwanen abinci guda biyu ɗaya alala ce akayi, ɗaya kuma jallof ɗin shinkafa taji kayan lambu kamar ba abincin suna ba tsabaragen kyau. Ga raguna tiƙa tiƙa a rataye a ƙusa a wajen wanke_wanke anata suyar kayan ciki, ga masu suyar kifi nan kusan katan uku ni dai na gani, gida ya kaure da ƙamshin gidan suna. Dangin Sunusi kuwa har daga ƙauye suka zazzo bikin wannan suna. Ga rumfa an kafa guda biyu harda fararen kujeru kamar dai ƙaramin biki za'ayi ba mamaki. Haka mukaita ratsa mata muna wuce wa idanu a kanmu. Muna shiga muka tadda ƙannen Luba a Kicin suna ta yankan kayan lambu. Tabb Nasiba sinasir kike mana ashe duk kun hallara? " "Wallahi Anty Hindu sinasir nake yi muku da farfesun kan saniya, har na kammala farfesun sannunku da zuwa Anty Luba an zo fa an karɓi kula wai za'a zuba abinci. Baban Sadiq kuma ya turo wai a bashi ƙaramar robar fenti za'a zubo miki nama" Na kalli Luba itama ni take kallo. Kafin ma tasan me zata ce sai ga Sadiq da nama cikin ƙaramar robar fenti, da kifi sukumbiya ɗanye guda shida. "Mama gashi inji Baba wai namu ne" "Hmmm ba Nabila su gyara su soya muku, in zasu iya. In sun gaji su saka a firji. Hindu mu je ciki in samu in yi wanka, kai kuma in ka fita ka rufemun ƙofata." Hannuna ta figa muka yi ciki ta zube a gado tana tunani kawai. Ni nasan sunan yaranta take tunowa ta haihu a talaucin, ta haihu a kuɗin, hidima kwatan wannan Sunusi bai taɓa yi ba. Luba karma ki damu kanki akan komai, ita rayuwa haka take da yawan mata matan da akayi gwagwarmaya tare dasu yawanci bama morar dukiyar, wata ce ke samun mijin a ɓagas aita kashe mata dukiyar ke kina jin zafi, amman zafin zai illatakine in baki da abunyi na aiki, ko sana'a shiyasa Luba mu dage mu nemi kuɗi kawai ni sana'ar motoci inaga zan soma" Dariya wajen Luba harda hawaye, a guje ta shige banɗaki nayi murmushi kawai mata wallahi mu dage mu miƙe tsaye da neman kuɗi kada ki sake kice wai dan namiji na ɗauke dukkannin buƙatunki zaki kwanta ba zaki nema ba. Ke bakya son kuɗin kanki ne? Kuɗin kai daɗi garesu, kiyi abinda kike so a lokacin da kike so babu mai ce miki sai wata ya ƙare ko a.a yanzu babu kuɗi a hannuna. Wajajen bayan azahar muna zaune da ƙannen Luba muna hira muna cin sinasir sai ga kiran Saudat a waya cewar gata ta taso, ta iso baifi da minti goma sha biyar ba sai ga Sumayya Sadiq yayi mata iso har uwarɗakin Luba ita da Mariya Habibu, da Nana Kabiru, tsofaffin ƙawayenmune wanda mukai makaranta tare, mun kuma yi ƙawance sosai, Mariya Habibu zaku santa ƴar wasan kwaikwayoce tayi tashe a zamaninta sosai, duk da ta daina daga baya sanadiyyar Aure da tayi. "Mene Mariya Habibu wai dama kina garinnan Sumayya ina kika samo wannan? Ga kuma Nana Kabiru" Cewar Luba kenan ina dariya nace. Wai Mariya Habibu kina garinnan ko ko dai shigowa kikai garinne. Nana Kabiru idonki kenan?" Duk mun cikasu da tambayoyi, Mariya Habibu kuma sai dariya take yi mana ta rame ta lalace sosai. "Nayi kewarku sosai ƙawayena. Shegiya Hindu kece kika zama Hajiya haka? " Dariya muka yi ta miƙo hannu muka tafa taf ta zauna kusa dani, Nana Kabiru ta miƙo mun hannu muka gaisa zukata fal farin ciki. Sumayya tace. "Wallahi ni na neme ta a waya nace ta shirya muzo. Na samu lambartane sakamakon asibitinmu da tazo wata huɗu da suka wuce, bata da lafiya. Nana Kabiru jiya ta shigo gari. Wannan fitar ma da muka yi mancewa nayi ban sanar mata ba. Amman ai a jihar Delta tayi Aure kun manta ne?" Mariya Habibu tace. "Hmmm da labari mai zafi a bakina wallahi. Hindu da Luba ashe dai kun cika gurikanku na son zama ƴan jarida? Na muku murna daga cikin gurina huɗu ɗaya na samu na cika, na son zama jaruma a masana'antar wasan kwaikwayo, ashe ɗaukaka zuwa take da tarin ƙalube iri da kala. Ashe ɗaukaka marmarine daga nesa. Ashe ɗaukaka wuya gareta. Hmm da zan shigo gidannan rufe fuskata nayi a hakan a kunnena naji wasu suna cewa wannan kamar Mariya Habibu. Ku duba yadda na lalace na zama tsohuwa. Gashi banyi zurfin karatu kamar ku ba ɗaukaka ta ruɗeni banyi wani abu mai amfani ba" Shiru muka yi muna dubanta. Nice ma nayi ƙarfin halin cewa. Abinda za'ayi Mariya kuzo a zauna aci asha, ayi sallah, sai a soma wannan labari dama muna bin Saudat bashin labari nima gani a layi" Ai kuwa haka akayi muka haɗu akaci abincin zumunci ga sinasir ɗin yayi daɗi sosai, abincin suna dai ko da aka kawo bamu ci ba. Bayan mun yi sallar azahar ƙarfe biyu dot muka zauna zaman jin labari, Luba ta kawo mana sassanyan zoɓo da soyayyan naman saniya da aka gama soyawa yanzu. "Wa zai soma labarin? " Cewar Luba. Har kin tuna mun da hadisin ummu zar'in, da naga wannan zaman namu. Inaga Saudat ta soma ko Mariya Habibu ce, ga Nana Kabiru" "Saudat ta soma nawa da tsayi sosai" Cewar Mariya Habibu. Zama Saudat ta gyara da kyau domin somawa. To mu kwana anan sai zuwa gobe in Allah ya amince mana. Ina godiya, ina muku fatan alkhairi. Mrs BukhariTSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA GOMA SHA TAKWAS (18) ZUCHIYAR DA BATA NUFIN KO WACCE ZUCHIYA DA SHARRI..... Kuna neman ƙamshin da zai riƙe zuciyar maigida kuma ya sa gida kullum ya kasance cikin sanyaya da soyayya? Ga samfurina ni mrs Bukhari na musamman, da kowace mace mai aji ya kamata ta mallaka don burge miji.Ƙamshin Ɗaki da Jiki: Feshi kaɗan a jiki bayan wanka ko a cikin tufafin barci yana ba da ƙamshi mai taushi da ratsa zuciya.Dorewa na Tsawon Lokaci, Yana daɗewa a jiki yana fitar da daddaɗan tattausan ƙamshi mai sanyaya rai, wanda zai sa maigidanki kullum yaji yana son zama kusa da ke. Aji da Kwalliya,Kwalba ce ta alfarma (50ml) mai kyawun gaske wacce za ta ƙawata wurin kwalliyarki. (Farashinshi 25k ne.) In kika fesama tufafi har sai in an wanke zai fita, in kuma fesawa kika yi a kayan, baki wanke ba kika mayar cikin sib, da kin buɗe ƙamshi zai daki hancinki, kuma zai harbi kayan sib ɗin. Wannan garanti ne in sha Allah. "To tunda kun bani dama bari in soma labari mai taɓa zuchiya. A zahiri duk macen da kika ga ta taka wani bigire ba'asan irin gargadar data fuskatanta a hanyarta ba. Shi yasa nake mamakin masu faɗin Allah ya samu a danginki. A haka gani sak cikin walwala amman a baɗini ba lafiyayya bace ni kwata_kwata, godiyar Allah ce da salatin ma'aiki Arrasul s.a.w" Muka haɗe bakunanmu wajen faɗin sallalahu alaihiwasallam. Kana ta tsunduma cikin tafiyar labarinta mai ban tsoro da firgitarwa ya salam. Duk muka yi shiru kowa Saudat yake kallo kawai. LABARIN SAUDAT:. "Mun yi Aure da Nazifi a lokacin ina aji matakin dubu biyu ( 200 level) ina karanta fannin shari'a wato ( low) a harshen nasara. Ranar da muka haɗu ruwan sama akeyi kamar da bakin ƙwarya, ni kuma inason zan koma gida Mama nayi mun kiran gaggawa daga makaranta, haka na fito a cikin ruwan zuwa titi ruwa na gudu a titi ina ɗiga haƙorana sai kakkarwa suke yi. Nazifi shi kuma yana cikin napep shi kaɗai a baya shi yaba mai adaidaita sahun da yazo wucewa izinin tsaiwa a ɗaukeni, duk da hanyarmu ta saɓa. Amman sai yace a soma kaini tukunna. Ashe shi a lokacin shigowarshi Najeriya kenan ya kammala karatunshi na digiri na biyu a tsantsayar Amurka, babban likitan fata ne kuma ƙwararre, jajirtacce, jajircewarshi cema tasa suka ji suna son yin aiki dashi a can Amurkan. Nan aka saukeni a ƙofar gida nayi godiya na shiga gida a guje, kuɗin ɗan sahun ma ca yayi in barshi harda sake mun murmushi mai kyau. Ni wannan kulawar da wannan murmushin a yayin rabuwa, shine abinda ya soma jan hankalina gareshi. Kunsan mace raguwar zuchiya gareta, sannan da yawanmu abu ɗaya zuwa biyu kaɗai ya ishemu wajen zaɓin mijin aure, sabida a lokacin bamu san meye aure ba balle musan yadda lamura zasui ta jujjuyawa bayan mun shiga auren, sai daga baya ake gane zaɓen tumun dare akayi, wasu kuma nasu zaɓin ya zame musu na alkhairi. Suma mazan sun iya ƙirƙirar halin da ba nasu bane su yafa, a ƙoƙarin ganin sun mallaki mace, ita kuma in wannan abinda ya ƙirƙira shine sababin zaɓarshi da tayi, sai anyi aure sai taga akasin hakan, daga nan ake soma samun matsala. Ina da ƙawar da muka haɗu da'ita a Amurka gidanmu ɗaya bafulatanace ita sabida barkwancin mijinta kaɗai yasa ta aureshi, kada ku daɗa kada ku raga. Amman ita duk yadda mace takai mai sa'a wallahi Allah ya bata. Akace wai ko wacce mace da irin tata matsalar a gidan Aurenta ko? Harma ake cewa duk wacce tace bata da matsala ma ƙarya take yi. Akan wannan bafulatanar na gane wannan maganar ba haka take ba. Duk yadda ake neman miji kamili, adali, salihi, mijin baiwar Allahnnan ya kai, kuma ya cika gwarzon namijin da yasan kima da darajar matarshi. In dai a gidan aurene bata da matsala ko wacce irice, salamun_salamun suke zaune, sun shinfiɗa rayuwa tartibiya, sun gina yara masu tarbiyya, nutsuwarsu ma dabanne, kai ilimin addini, da kuma aiki dashi a aikace yayi a rayuwa." Mariya Habibu tace. "Ai baki san baɗinin rayuwarta ba. Kinsan fa akwai fek lib Saudatu, anya a wannan marrar, da wannan ƙarni za'a samu matar da take zaune bata da matsalar komai a gidan miji kuwa, namijin wannan zamanin kuma? Kai ina" Kallon Mariya Habibu nayi, tare da yin murmushi nace da'ita. Haba Mariya akwaisu fa bila adadin billah. Kinsan matsalarmu itace, mun fiye raki mu mata. Sannan in kina da matsala a naki gidan auren, sai ki haɗa mata ki musu kuɗin goro kice duk wuya ake sha. Mazan duk basu da halacci, azzalumaine, basu san darajar mata ba. Wannan ƙarara zaluncine, kuma kuskurene mafi girman gaske. Kinga na Allah ba zasu taɓa ƙarewa ba. Azzaluman Maza akwaisu, Salihai ma akwaisu basu da iyaka. Ni sai ince miki ma Salihan maza natijajju sunfu na banzan yawa. Matane suke sake tura lamarin fa. Matsalarmu shine in ke mijinki mazinacine misali, ko ɓarawo, ko madokine. Sai kawai kice maza ai ƴan iskane, duka maza fa. Gaki da mahaifi, mahaifinki na da mahaifi, mahaifiyarki na da mahaifi, kina da Baffanni, kina da yayu, kina da ƙanne, ke kina da Ƴaƴa mazan ma. To duk kin haɗa dasu, da malamanmu, da manya_manyan bayin Allah. Wannan kalmar hatsari gareta. Kuma mata suna so in mijinki azzalumi kika samu wai dole kiyi shiru hanyar shiga aljannarki kenan. Sannan in in kika koka, sai kawai mace ta dubeki tace. Nawa yafi naki, an mun abinda yafi naki, ke wacece da ba zaki haƙura ba. Ko anma wance' an ma wance kema kiyi haƙuri, ya zama ruwan dare. Sun mance Allah maɗaukakin sarki shi ya yimu mabambanta. Wasu masu sanyi, wasu masu zafi, wasu masu sauƙi, wasu akasin hakan. To ke kina da sauƙi, gaki da saurin sakkowa a yayin fishi. Ba yin kanki bane, bake kika zaɓa ba. Ubangijin daya halicceki shi ya yoki a haka. Ba kuma ki isa kice kowa sai ya zama kamarki ba, kuskurene. Ga wata mafaɗaciya, mai saurin hasalace, haka Allah ya yota. Sai wata tace wai dole sai ta zama mai sanyi, da taushi. Alhalin ba ita tayi ta ba, itama ba ita tayi kanta ba, haka Allahnnan yaso ganinsu. Babu damar ɗaya ya tanƙwara ɗaya ta ƙarfi, sai da nasiha, da nuni. Kama da wane akace bata wane. In Allah yaso sai ya juya lamarinshi yadda yaso. To dan Saudatu tace ƙawarta na cikin Nutsuwa, baya nufin fek lib, sai fa mun cire waɗannan dattin a cikin kayukanmu. Abinda kika samu, ba kowa yake dashi ba. Naki naki ne, na wani nashi ne. Allah yasa mu gane mu karɓeshi a haka, ko da zamu karɓa da haƙurine" Ajjiyar zuchiya duk suka sauke. Nana Kabiru tace. "Madallah dake Hindu Duwaf. Wannan bayanin naki cike yake fal da ilimi sosai. Ko ni Nana ganinan. In aka zauna dani akace namiji ba ɗan goyo bane, to Allah zai iya saka ma maza. Wallahi Mijina duk inda ake neman miji ya kai. Shekararmu ashirin da shidda jiya jiyannan cib da Aure. Cin amana, zalunci, tauye hakki. Ban taɓa kamani da ɗayan wannan ba. Rayuwace muke yinta mai tsabta. Rayuwar sanin darajar kai. Ni dashi mun zama abu guda, wallahi ya washeni na washeshi. Bari in muku ta mahaukaci. Ban taɓa kuka ta sanadinshi ba wallahi. Muna saɓani a farko, farkon aurenmu a lokacin muna kan karatun fahimtar kawunanmu. Da kuma lokacin da yara suke ƙanana haka, ni mai duka ce, shi kuma sanyi gareshi. Bari dai kar mu haɗe labarin, Saudatu tace gaba. Saudat:. Bari dai in ci gaba kar in sauka akan maudu'in da nake kai, kamar yadda Mrs Bukhari take yi labari cikin wani labarin, wani sa'in inta shige cikin wani labarin sai ya danne labarin farko wanda kuma shi ya haifi wannan. To a haka muka ƙulla alaƙar soyayya ni da Nazifi sosai mai ƙarfi. Naga bahaushen bature, ma'abocin son turanci da rayuwar wayewa ta masifa. Kuma shi a lokacin iyayenshi suna son ƙulla Aurenshi da ɗiyar ƙanin mahaifinshine, shi kuma baya so yace bata waye sosai ba, bata cikin kalar tsarin rayuwarshi har hotonta ya nuna mun, naji kishi sosai sabida ta fini kyau sai dai in nuna mata wayewa, da manya manyan turancin dana dinga nacin iyawa tun muna sakandare ai kun san wannan gurin nawa. Mun shirya zamu yi aure zai barni a Najeriya in ƙarashe karatuna, kafin yazo ya ɗaukeni mu koma Amurka in jona mastas ɗina acan, ya kuma nema mun aiki. Ai kuwa dake Abbanmu ma yasan familyn Nazifin bincike bai zame mana wahala ba, kuma bamu ji mummunan tarihi akan Nazifi ko zuriyarsu ba, bai koma Amurka ba saida aka ɗaura Aurenmu, amman kash a ranar ya bar ƙasar ko ɗaurin auren bai samu halarta ba. yana Abuja sabida ta can jirginsu zai tashi. Amarya ita kaɗai a katafaren gida sai abokanshi ne suka zo suka sayi baki, suka sallami ƙawayen Amarya ni kuma daga ni sai Magena kuliyana tare muka tare yana gefena. Ni dai nayi shiru a kan sabon gadona inata nazari akan Nazifi, da irin burin da yaci na wannan ranar ashe bazai kasance tare dani ba. Murmushi nayi kawai na miƙe naje na yi wanka na sauya kaya na kwanta a bayan Usama magena ɗan Amana fari sol dashi ɗan ƙasar waje. Bacci ranar nayi harda makara, ba sabamba anyi gidan kai" Mariya Habibu tace. "Hmmm ɗakin kai akwai daɗi yafi ko wacce duniya daɗi, amman fa in an dace. In ba'a dace ba kuma yafi ko wacce duniya tashin hankali da matsala, mace inta rasa farin cikin gidan aure rayuwarta taɓuwa take yi." Kai kawai Saudat ta girgiza ta kurɓi zoɓo kana taci gaba. "Hmmm a waya ni da Nazifi tamkar zamu haɗiye juna haka muke soyayya, kullum zani makaranta in dawo, ban nemi komai na rasa ba ban taɓa kukan komai ba. Har Allah cikin yaddarshi, da amincewarshi, na kammala digirina tas a fannin lauya sai ya rage shirye_ shiryen tafiya Amurka kawai aketa yi mun, daga dangin Nazifi kuma ni kaɗai zan tafi babu ɗan rakiya daga ɓangarenshi ko nawa" Tsaya kada ki mana rinto baki faɗa mana sau nawa ango yazo aka darje Amarci ba? " Na tambaya ina tuntsurewa da dariya. Luba tace. "Hindu rigani kika yi gaskiya, kinsanni da shegen son labari, gani da wutar ciki" Ita kuma sai tayi dariya tace. "Bai zo ba ko da sau ɗaya ne. Haƙuri dai kullum yake bani akan yanayine na aiki" Ƙur nayi mata ina nazari can nace. Kuma ke a lokacin baki yi zargin komai ba, a matsayinki ta lauya ba. Namiji mai lafiya ya auri mace ya ajjiyeta bai waiwayota ba. Ke a lokacin da kuka yi auren zuwa kammala karatun naki shekara nawa ne a tsakani? " "Duwaf kenan shekara uku da wata shidda cib da aurenmu, jirginmu ya sauka a Amurka. Ki fahimta a lokacin ban samu damar saƙa komai ba. Dalili kuwa shine Nazifi na ƙoƙarin bani lokacinshi ga kalaman soyayya da yake yi mun. Kana yana yawan nuna mun ma shi da ƙyar yake bacci dauriyace kawai yake yi. Sau biyu yana ja mun rai cewar zai zo daga baya zancan sai ya shiririce. Hmmm ina kai ku dai, Umma ta turo mun Yayata Kulu muka kwana tana harhaɗamun kayana kuɗaɗe na cire na sai ƙananun kaya masu tsadar gaske da kyau, ni a lokacin ma atampa uku na ɗauka, lesiri biyu, kayan burge miji Anty Kulu ta loda mun kawai in faɗa muku. Ƙaramin akwati cike da magungunan mata, na gida dana tada komaɗa kala kala. Washegari ta rakani har Abuja da yamma sakaliya jirginmu ya ɗaga zuwa Amurka Ya sauka a washington DC. Duk da sai da jirginmu yayi mana juye a burtaniya, muka huta muka ci abinci kafin muka sake hawa jirgin Washington DC ɗin. A taƙaice sai da muka kwana har muka kai rana kafin muka sauka. lamarin daya sauya mun tunani da rayuwa kenan. Amarya ta galabaita ta dahu sosai. Babban abinda ya tashi hankalina shine ganin Nazifi a cikin halin rashin ɗoki da zumuɗin ganina a matsayina ta Amarya fil a leda, ya dai riƙo wata uwar fulawa a hannunshi gari guda, yana tsaye ƙiƙam har na iso gareshi kafin ya buɗe mun hannu na shiga jikinshi muka sauke ajjiyar zuchiya. Ina kallon wata bahaushiya wacce muka hawo jirgi ɗaya daga Burtaniya ita nata gogarman fulawarma zubarwa yayi ya tafi a guje sukai kaciɓis a hanya, amman banda Nazifi. Mijin wata bana wata bane. Ko da muka shiga tasi zuwa gida shiru motar ta ɗauka kowanne cikinmu da tunanin da yake yi. Wallahi tun kafinma in ƙarasa gida naji nadamar baro iyayena da dangina ta kamani ƙaƙas, sabida na fahimci tabbas da matsala. A haka muka je gida ya saukeni har girki dai yayi mun amman fa babu wannan fara'ar da ita ta soma jana ga nazifi sai ɗaure fuska. Tambayar duniya yace babu komai aikine fal kanshi, shi yasa in yi haƙuri. Sai da na kwana ɗaya Nazifi ya ɗan sake. Babu karsashi a jikina. Ta ɓangaren mu'amala kuwa tun a daren na tsorata da salon Nazifi, ace saurayin da bai taɓa aure ba, bai taɓa sanin mace bane zai kasance a haka? Daren naci wuya sosai bai ragamun ba ina irin abunnan na saina fanshe wahalata da kuɗina, irin abinda Nazifi yayi mun kenan akaita Amarci ƙaƙas Ango ba fara'a babu nuna yabawa, a rana ta biyar da daddare ya shigo mun da ƙorafinshi da wasu sharudɗanshi duk akan mu'amalar aure fa. Shi yafi son mace mai sake jiki wayayya ta haƙiƙa, amman ni sai in dinga ƙin sakin jikina dashi sannan bana yi mishi kaza wa kaza wa kaza. Shiru nayi ina nazari har dai ya gama kafin nace dashi. "Ita mace da kunya aka santa sosai. Sannan inka duba ni ban sababa amman a hankali zan zo in saba, zaka samu abinda kake so tunda kaine malamin nawa" Sai ya haɗe ranshi wai kunsan wacce kalma ya jefeni da'ita maras daraja wanda yasa har yanzu ina kallonshi da wannan baƙin? Dukkanmu girgiza mata kai muka yi muna son ji. Murmusawa tayi ta girgiza kai tace damu. Cewa yayi . "Haba Saudatu kada ki raina mun hankali mana, kina nufin akwai wata mace da zata haɗa digiri ba tare da tasan kala_ kalan maza ba ne? Ke dai kawai wulaƙancine kawai ke damunki in zaki sake ki sake muci duniyarmu da tsinke kawai. Abubuwan da mu ka yi a baya mu ajjiye a gefe, muyi mai lada shine maganar gaskiya. Amman ya zan rayu a wannan ƙasar in koma gida da tunanin na samu wayayyar mace, daga ƙarshe kuma ki dinga nuna mun kamar baki waye ba haba ke kuwa. Kiga abinda kikai mun jiya harda amai kenan ƙyamata kike yi, ko me a gabanki nayi wanka kuma ko a fuska ai kinsan ni ba ƙazami bane, da wayewata ina likita mai daraja lamba ta ɗaya" A lokacin in da za'a tsaga jikina ba za'a samu jini ba daskarewa nayi kawai ina kallon Nazifi, ina gaban mamaki. Wato ashe da yawa yawan jahilan maza, irin kallon da suke ma macen da tayi jami'a kenan ko dai Nazifi bai same ni a mace cikakkiya bane? Kallonshi nayi na kira sunanshi nace. "Baka same ni a matsayin mace bane Nazifi, ko kuwa lissafinkane ya baka duk matar jami'a mazinaciyace, ko kuwa sabida kasan ka lalata mata bila adadinne yasa kake tunanin irinku su suka cika Jami'ar, harma kake hasashen babu wata macen Jami'a da zata tsira da mutumcinta?" A kausashe nake magana idanuna tab da ruwan ƙwalla. Hmmm cikin wata kwaɓar yace dani "Haba Saudat ke dai ayi sha'ani kawai, amman matan Jami'a ai ragowar laccarorine da abokan karatunsu. Nifa a jami'a mata ke bi suna roƙon in kwanta dasu, sai dai ba ko wacce take mun ba. Da wannan dalili na kafa hujja nake ji tamkar budurcinki bai cika na asalin budurwar da bata san komai ba. Kawai dai in zaki saki jiki ki dinga farantamun, kawai ki saki, ni wayayyene ina son harkar wayewa." Hawayen da suka cika guraben idanuna tuni suka shiga zuba a kumatuna, kaina da zuchiyata sukai mun dundurundun dasu yawu a bakina ya ƙafe. Naziru kuwa ko a kwalar rigarshi hankalinshi kwance yaita sarrafani yana ɗora hannayena a duk inda yake son in taɓa shi. Amman ina baƙin ciki gami da nadamar aurenshi sun hanani sukuni, a ƙarshe ma tureshi nayi a kaina na juya baya. Ranshi a wannan daren ya ɓaci sosai dan bai kwana a gidan ba ni kaɗai na kwana ina kuka, babu sallah babu salatin ma'aiki arrasul S A W, haka gari ya waye dani kaina kamar zai tarwatse tsabaragen ciwo. Ga gari ni bansan kowa ba, daga tawowa dawa zaka soma raba matsalar gidan aurenka? Nayi tunanin yin haƙuri in danne domun muyi zama na aminci da Naziru, sai dai abadan girmanshi ya gama zubewa bashi da wani kwarjini ko kima a idanuna sam. Dake nice mace kuma inason sanin daɗin aure, saina tattare komai na mayar dashi ba komai ba, na kuma saki jikina na dinga yi mishi abinda yake so, wallahi shafuka_shafuka na koyan mu'amalar aure iri_iri babu wanda bana shiga, in karanta in kuma kalli bidiyo duk dan in zama gwana kuma ƙwararriya a shinfiɗa, sabida na fahimci babu abinda yake faranta ran Naziru sama da mu'amalar aure. Duk da dai zuchiyata cike take da wasi_wasi da taraddadi amman ban tabbatar da gaskiyar abinda nake zargi ba sai wata ranar Juma'a da safe dana tashi da amai. Kuma ga zazzaɓin dare daya tusoni gaba a lokacin watana huɗu da zuwa. Muna zuwa asibiti gwajin farko akace ƙaramin ciki gareni sati biyar, yana cikin na shida. Matsalata a gidan naziru na farko kenan gagarumar matsala kuwa. Ni ina murnar samuwar ciki, shi kuma sai ya ɗaure fuska yayi tamau dashi har muka iso gida bai kulani ba, ni kuma a lokacin ko ƙwaƙƙwaran motsi tsoron yi nake yi sabida kar wani abun ya samu cikin jikina. Muna shiga ciki na nemi waje na zauna kusa daf da Nazifi domin naji menene damuwarshi. "Damuwata shine wannan cikin a zubar dashi Saudatu, bana buƙatarshi yanzu kuma kar ki manta makaranta zan mayar dake inata fafutukar nema miki gurbin karatu, kinsan da kin samu ciki kika yadda kika haihu shikenan cikar burinki ko? Ni kuma bazan iya zama da macen da iyakarta digiri ɗaya ba, kinsan gidanmu ƴan bokone sosai, matan yayyene daga me mastas sai masu phd bazan kasance a ƙasa dasu ba, ni da nayi karatuna a waje, nake aiki a waje kuma. Dan haka dole a zubar da cikinnan" Ai sai na fashe da kuka sabida bani da abun cewa, ni gashi bani da kowa a ƙasar ya hanani kuma mu'amala da kowa yace baya so. A kusa damu akwai wata bahaushiya mai yara dana taɓa ganinta ta taga, hausa sosai suke yi harma da zanenta na uku_uku irinna kanawa a hagu da daman fuskarta, tsoron fishin Nazifi yasa na kasa fita mu gaisa. Nayi kuka tamkar raina zai fita wallahi ko uhum Naziru bai ce ba, saima fita da yayi ya barni a zaune a wajen kawai. Ni na rarrashi kaina na ƙwarara jikina na tashi na gyara gida, nayi mana girki. Haka na wuni sukuku saida na kira gidane ma na ɗan samu sassauci a raina amman na rasa ya zanyi da raina ni dai inason cikina, kuma inason mijina ina, kuma son karatu, shi kuma yace sai dai in zaɓi ɗaya ko a zubar da ciki in ci gaba da karatuna kuma babu ni babu kishiya, ko kuma in haihu in koma gida najeriya, kuma bazai barni aiki ba bazai barni karatu ba, sai dai inta haihuwa in kula da yara shi kuma ya auro wata macen mai ilimi. Satinmu biyu muna rikici duk na rame na fita a hayyacina haka dole na amince zan cire cikin shine fa muka samu zaman lafiya. Allura yayi mun ta zubar da ciki. Nayi ciwo nayi ciwo har shi a karan kanshi ya ɗauka mutuwace zanyi in faɗa muku." Fasali ta ja tana share hawayen da suka wanke mata fuskarta. Luba ce ta miƙo mata tishu ta amsa ta yago kaɗan ta goggoge fuskarta kana taci gaba. Na jima babu lafiya a jikina nafi shekara bana jin daɗi sam, ga magunguna kullum Naziru yana bani jiki dai babu daɗi ga yawan ciwon mara. A haka harna samu gurbin karatun digiri na biyu a Jami'ar Georgetown university center Wacce take a tsakiyar birnin Washington DC kusa da koton ƙoli ta Amurka (u.s supreme court) da kuma majalisar dokoki wanda hakan na taimakawa mu samu hoton aiki cikin sauƙi ( internships) haka na soma karatuna cikin aminci, harma da tafiya tayi tafiya nafi ƙaunar makaranta sama da gidana, dan Nazifi ya tsiro da sabon ɗabi'ar yawon dare koma ince kwanan waje ya kan shigo gida a sanda yaga dama, ko na ɗaga waya na kirashi baya ɗauka amman baya bani hutun mu'amalar aure madamar ba jinin al'ada nake yi ba, ko rashin lafiya nake yi sai ya kwanta dani. To karatunmu yana da wuya, in nace zan ɗauki matsalarshi in saka a zuchiyata zan samu matsala da karatuna, ni kuma bana fatan abinda zai bani matsala a karatuna sai na ɗauki lamarinshi na watsar na mayar da hankali sosai akan karatuna. Gaga_gaga karatu nata tafiya na saba da mutane sosai, a makaranta maƙociyata maman Haifa itama muka saba sosai takan shigo gidana nima in shiga gidanta, harma in yi bacci ba tare da sanin Nazifi ba, ina shekara ta ƙarshe a makaranta sai ga ciki nayi farin ciki nayi murna. Na muku tsallake ashe daga cikin magungunan da Nazifi yake ɗurkamun kullum akwai na hana ɗaukar ciki a ciki bansani ba. Gashi bai amsheni ba ashe shine yake ta muƙurƙusan jikina ranar da asirin zai fasu, maman Haifa ta shigo mun ni kuma na ɗakko magunguna zan haɗiɗiya duk na ɓalla sai tace. "Lallai matarnan ashe maganin hana ɗaukar ciki kike sha sabida karatu, ba zaki haihu ko da sau ɗaya bane, yarannan watarana su zasu tagajemu a lokacin da mukai rauni, me zai sa ki sha maganin hana ɗaukar ciki" Ai sai naji gabana ya yanke ya faɗi ras, to a lokacin naso ɓoye mata halin da nake ciki amman ruɗun dana shiga sai gani washegari a gidanta, na zayyana mata halin da kab nake ciki kab nan tasa hannu ta tsamemun maganin hana ɗaukar cikin. "Kibi a hankali maza da yawa suna cutar da matayensu da suka ƙetare wata ƙasar dasu. Ni ɗinnan da kika ganni babu irin abun da ban fuskanta ba, kainane ya waye na daina ɗaukar komai, shi yasa na samu lafiya. Amman a da lokacin da ban samu aiki ba ina zaune ba kuɗi, da iya miji na dogara ga matsin lamba daga iyaye da dangi, su gani suke yi wani kuɗine a ƙasar waje basu san wahalarta tafi daɗin yawa ba, jibi a wajen da muke rayuwa. A hakanma mu ƴan gata ne sosai. Ki kwantar da hankalinki ki lulluɓeshi baibai kawai ko cikin kika samu kada ki sake ki sanar mishi har sai ya bayyana kanshi, a lokacin da bashi da abinda zai iyayi sai dai kawai ya zubama sarautar Allah idanu" Maganganun maman Haifa su suka ƙwararani sosai har na kammala karatuna na mastas sakamako ya fito mai kyau Alhamdulillahi, harma Nazifi yayi mun alƙwarin zai tuntuɓi abokinshi Alex baturen Burtaniya ne lauwa anan Washington DC ɗin akan batun aiki. Shiru aiki yaune gobe ne shiru in nayi mishi magana sai yace samun aiki a wata ƙasa ba abu bane mai sauƙi ba, in sa haƙuri watara kwatsam aikin zai samu. To haka dai naita jiƙawa ina matsewa da daɗi babu daɗi inata turawa da ƙarfin ikon Allah. Cikin ƙudurar Allah sai da cikina yayi wata bakwai kafin Naziru ya gane ciki gareni shima ya farune ta dalilin na fito wanka ina tuɓe ina shafa mai ya shigo bagatatan shine ya gani. Wai kunsan sai da Nazifi ya dokeni da wannan ciki duka tamkar Allah ya aikoshi, ya dinga ma cikina mahangurɓa, ya fice a gidan ya barni ina murƙususu ga jini ya ɓallemun bani da mai tagazamun in taƙaice muku dai sanyin asubane ya farfaɗo dani na ganni cikin jini mai yawa daskararre. Da dabara na iya shiga bayi nayi wanka na kintsa na tafi asibiti yaro lafiyarshi ƙalau galabaita yayi shi yasa baya motsi, amman yana lafiya haka likita ta ce mun. Na kaɗo kaina na dawo. Nan na shiga sabuwar rayuwa sai in fi sati bansa Nazifi a idanuna ba, in zai zo ma sai in ganshi a bige yana tumɓele wallahi. Akwai sanda aka buga mun ƙofa ina buɗewa naga matan turawa biyu sun dawo mun da Nazifi, babu yadda yake, dare daga cikin darare masu muni kenan a rayuwata a daren na soma naƙuda sai Maman Haifa na kira ta kaini asibiti na haifi yarona Ahmad. To a lokacin sai na samu gata mahaifiyar Nazifi da Anty Kulu sun tawo kafin suna basu tafi ba sai da na gama wanka tas, kafin suka tafi. Naso in bisu amman Nazifi yaƙi fur. Haka naita murzawa Nazifi ya bayyanamun ɓoyayyen halinshi da ya ɓoye mun a baya. Mane min mata, mai shaye_shaye, mata har gida yake kawosu su zauna a ɗakinshi, abun takaicin mata kala_kala yake kawowa duk wacce ta tafi ba lallai kiga ta dawo ba, sai dai gobe ya kawo wata. Watsewa dai tamkar ba ɗan musulmai mai tarbiyyar islama ba. In zan tsaya baku labarin irin azaba da uƙubar da nazifi ya bani kan ku bazai ɗauki duka ba, da ilimina da wayewata amman na taku na daku sosai, zuchiyata ta samu ciwo hawan jini da ciwon zuciya duk suna tattare dani, yanzu haka kafin Allah ya kuɓuto dani na dawo gida Najeriya da zama a lokacin yarana biyu suna karatunsu mai inganci na haƙura na zauna sabida gobensu, ilimi acan ya bambanta da ilimin nan gida magana ta domin Allah kenan. Kwatsam yace in tattare dani da yara zamu koma gida aimun magani a gida tunda ciwona yaƙi ci yaƙi cinyewa. To ta yaya zai cinye alhalin kana ji kana gani miji ya ajjiyeka baya ta taka, sai ta karuwanshi kawai danma taimakon da Allah yaimun da yaran suka tasa sai karuwan suka dena zuwa gidan, sai dai shi ya fita ya same su kamar dai lokacin amarcina. Kullum da irin ƙalubalen da zan fuskanta, hakan yasa ciwo yaƙi ci yaƙi cinyewa. A lokacin da muka tawo ni da yara babu ɗigon so ko ƙaunar Nazifi a zuchiyata asalima zaman na dole kawai nake yi sabida Hajiyarmu da take jaddadamun in riƙe mijina hannu bibbiyu, in dai inason farin cikinta to in farantama Nazifi ita na sallameta. Kunsan sabida me?" "Sai kin faɗa Saudatu" Cewar Mariya Habibu kenan wacce take shara ƙwalla. "Sabida ya gama siye dangina da nuna karamci. Hatta gidanmu saida Nazifi yayi musu gyara ga kuɗi da yake yawan turama Hajiyarmu, sannan duk abinda ya faru a dangina aka faɗamun shi da kanshi zai buƙaci lambar asusun bankinsu ya tura musu kuɗi mai tsoka. Ya toshe duk wata kafa da zan tsugunna in kai ƙorafina shi yasa ma ban gwada kai ƙorafin ba na haƙura na zauna a kan yarana. Na gina rayuwata na samu aikina, ina zuwa sai ya zamemun farin cikina. Duk sanda Nazifi ya kirani in ɗauka, in shekara za'ayi bai kirani ba inanan aiyukan dake gabana sune a gabana wallahi. Ya jingineni tsawon shekaru, yadda kuka san babu hakki." Ajjiyar zuchiya ta sauke tare da jawo jakarta ta ciro mana tulin magunguna bature ta zubesu a gabanmu. Waɗannan dasu nake rayuwa Nazifi ya illatar dani, ya salwantar mun da lafiyata, ya ɗagamun rayuwa a haɗari. Ribar aure na samun yarana biyu ne kawai sun girma sunata karatu. Mrs Bukhari. Mu kwana anan sai zuwa gobe. Wanne darasin kika ɗauka a labarin Saudat? Menene a tunaninki kuskuren Saudat?TSURON TSIRIN... TSANDAURI.... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI. LAMBA TA GOMA SHA TARA (19) ✨ JAMRAT AL_ DHAHAB MAKHMALIYA: SIRRIN ƘAMSHIN GASHI! ✨Kuna neman ƙamshin gashi na alfarma wanda baya gushewa? Ga sabon haɗina na musamman a cikin kyawawan kwalabe masu adon gwal da glitter. Matuƙar Ɗorewa. Yana manne wa gashinki yana fitar da daɗaɗan ƙamshi na tsawon kwanaki.Aji Da Alhari Ɓoyayyen sirri ne na mata masu son kamshi mai sanyaya rai da burge na kusa da su. Kada ki bari a ba ki labari, sanya naki odar ( farashin wannan makhmariyya 27k ne Hajiyata) Inna kallesu sai inji sanyi a raina. Iyaye sun tauyeni, sun hanani rabuwa da auren. Tun ina ɓoye damuwata, harna fito na fayyacema Anti Kulu halin da duk nake ciki. Sai haƙuri ta dinga bani dai, akan inna kashe aurena ma, bansan gidan wa zan faɗa ba. Gara Nazifi shi yana girmama dangina. Wata mijinta ya zageta, ya zagi iyayenta amman tana zaune. In dai taƙaice muku haka nake rayuwata da yarana sanyin idaniyata. Shi kuma Nazifi yana can, duk randa yazo ina maraba dashi, ina kuma sauke mishi hakkinshi da duk ya rataya a wuyana. In ya tsallake ya tafi sai na ganshi. Kuɗi dai kam, yana sake mun, ni da dangina dana dawo Najeriya. Baya son aga gazawarshi tako ta ko ina." Wannan shine labarina amman na tsallake abubuwan da suka kwanta mun da dama. In da mai tambaya akan inda ya shige mishi duhu bismillsh." Duk muka yi shiru ita kuma sai raujin kuka take yi zuchiyarta ta taɓu, ta fama babban miki a zuchiyarta mai ciwo. Duk muka tsaya akan bamu da tambaya. Ni dai ina da tarin tulin tambayoyi wallahi, amman na dannesu da zoɓo, da nayi magana sai tawa ta yi raɗaɗi. Nana ce ta numfasa tace. "To ni dai bani da ƙalubalen komai. A wajen aikine kawai nake fuskantar matsalalo da abokan aiki. Ina aiki a gidan ruwa water bot. Amman ta ɓangaren miji, suruka, dangin miji na zame musu abun marmari da so tamkar watan Ramadana. Ina aji na uku a jami'ar ATBU Bauchi muka haɗu da Ibrahim, a lokacin ina zaune a dutsen tanshi gidan Kawuna. Ibrahim yana daga cikin ɗaliban ilimi masu so da sauraren karatuka da bin majalisin Dr Idris dutsen tanshi, Allah yayi mishi rahama ameen. Kamar wasa yace da Kawuna ai shi yana sona. Shi kuma Kawu yace yaje ya nemo yardata. Ya ko zo muka daidaita kanmu, ina gama karatu muka yi Aurenmu anan garin Bauchi muka soma gudanar da rayuwar tamu, dake yana daga cikin ma'aikatan gwamnatin jihar ta Bauchi. To rayuwa mai kyau, kamila tartibiya muka gina, mai cike da fahimtar juna. Ya taya ni grki, inya rigani dawowa office ya ɗaura girki, asabar muyi wanki, lahadi muyi guga. Haka muka tsara komai nama rayuwa na tafiya sumul. In nayi ba daidai ba, zai zaunar dani mu tattauna. Zan bashi haƙuri in karɓi lefina. Haka in shi yayi mun laifin ma, zan zaunar dashi mu tattauna, ya bani haƙuri. Shi ya bani wannan damar. A haka har muka tara yara guda Biyu, mace da Namiji. Namijin sunan mahaifinshine, macen kuma Sunan Mamane Binta. To inaga sabida yarane har Ibrahim yake mun faɗa, ni ina da duka, shi kuma sanyi da sauƙi gareshi. Bayan faɗa da ɓacin rai akan dukan yara. Gaskiya bani da matsalar komai. Yana sauke dukkan hakkokin dake kanshi. In kinga na sai abu a gidan, ta ganin daman kainane. Ina taimaka ma mahaifanshi, da nawa mahaifan sosai. Ina da cikin Balaraba Ibrahim ya shigo ranar wata Juma'a jikinshi a mace. "Lafiya na ganka ka shigo tun ɗazu wani iri? Na tambayeshi, bayan na bashi abinci, na rakashi yayo wanka, muna kwance ne ina taya shi hutawa lokacin. " Babu komai, wani al'amarine ya taso mun, bagatatan ban shirya ba. Ke kuma bansan ya zaki ɗauki lamarin bane. Shine dalilin damuwar" Dariya nayi, kana nace. "Babu komai, na yarda da rayuwa shirin Allah ce. Menene koma menene sanar dani. Nice a haƙƙu da insan damuwarka". " Aure zan ƙara Nana. Ba dan kin rageni da komai ba. Bazan kin gaza ta ko ta ina ba. Sai dan lokacin ƙarin aurenne yayi. Kuma ina fatan zaki tsaya mun"? Kukane yaso ya cuceni. Wallahi bazan ɓoye muku ba, Hindu ce ta soma faɗo mun a raina. Saina dake, na mayar da hawayen nace. "Ɗari bisa ɗari ma kuwa zan goyi bayanka. Wannan ai abu mai kyaune Abban Binta. Ubangiji Allah ya sanya alkhairi. Ya bamu zama lafiya, yai mana suttura da'iman" Gaga_gaga aka shiga gyaran gida, ni kuma na shiga siyan kayan lefen amarya. Miliyan huɗu ya bani cib, akan amarya miliyan biyu, nima miliyan biyu. Ita dai nayi mata kaya na gani a kuma. Ni ko ƴan kuɗaɗena cib na danƙama Yayana na zuba hannun jari a katafaren shagonshi dake singa, dama Yayata ce naga tayi. Duk sati, ko wata yana tura mata kuɗi. Akaita tsoratani da sunan shikenan na rasa Ibrahim. Hatta ƙannenshi sai da suka ce haka. Ni dai Allah kawai nake faɗama. Kuma ya amsamun, Ibrahim bai taɓa wulaƙantani dan yayi aure ba. Akayi biki, na sake samun daraja a wajen dangin Ibrahim. Amarya ta tare. Ta ko zo da rawar kanta sosai. Ganina ne ya kashe mata jikinta sosai. Wannan ɗokin angwancin Ibrahim ya ɓoye, har ga Allah ban gani ba. Haka suka gama Amarci aka soma rabon kwana. Tana aikinta, nima ina nawa, ga ciki ma yana ta faman bani wuya. Shekararta uku, sai zaman yaƙi daɗi, a tsakaninsu. Duk da tayi wata shida cib nima tana mun wasu abubuwan da ban gane musu ba. Habaice_habaice kullum cikin yinsu take. Saina fita harkarta, to ba wajen bane. Ranar da abun zai faru dai, bayan ya saketa sai take cewa. "Dama kasan mijin tace ne kai shine ka auroni. Kasan kana son matarka, da yaranka to menene amfanina? " Kunji tunanin da yawa yawan matan da suke shiga gidan Aure a matsayin mace ta biyu ko?" Amman Hindu kina ganin daga ina ake samun matsalar ne?" Tai mun wannan tambayar, sai nayi murmushi. Luba bata amsa, zaki fi yin bayani" "Hmm daga Mazanne a yayin da suke zuwa wajen matan zance. Wani a ƙoƙarinshi na shawo kan macen yake wannan furucin, yace ai matata ta gida, bata iya kwanciyar aure ba. Ni bata iya girki ba, ƙazamace, bata da wayewa, ko lob yu lob yu bata iya ce mun. Inna aureki na samu aljannar duniya. In ta shigo gidan kuma ya nuna mata a aikace, cewar baki da daraja, ke ba'a bakin komai kike ba, dake da banza duk ɗaya, ke matar ƙaddarace. To kinga wannan mashin, su matan suka riƙa. Ko da namijin bai faɗa musu cewar matarshi ta gaza ba. A ranta haka ta ɗauka, ai gazawarmu ce ke sa mazan ƙaro aure. A kunnena naji Sunusi na ce ma Amarya. "Ni yanzu ne nasan nayi aure. Dama gazawar Luba ne yasa duk aure ya fitar mun a ka." Sai kawai taja fasali. Nana Kaburi tace. "To a haka wannan aure ya ƙare, da rabon yarinya mace ɗaya. Ba'a rufa shekara ba Ibrahim ya sake auro wata Bazawara da mijinta ya rasu. Muna zaune lafiyar Allah, muna mutumta junanmu sosai. Har dai yanayi na aiki ya dawo damu nan garin Kano. Muna tare dukkanmu baki ɗaya. To kunga ai babu abinda zance na ƙaras na takaicin ɗa namiji ko? " Saudat tace. "Ba'a yabon ɗan kutu... " Kash hakan kuskurene fa, yafa kamata mu dinga gyara kalamanmu. Saudat baya kufin dan ke baki dace ba, Nana ma dole sai ta ƙi dacewa. Ba haka rayuwa Allah ya tsarata ba. Shi yasa aka ƙagemu mabambamta. Masu kuɗi da talaka. Musulmai da kirista, maza da mata, yara da manya fa. Masu hankali da marasa hankali. Masu ilimi da jahilai. Nana madallah da Ibrahim, kuma na taya ki murna. Fatan rayuwa cikin aminci ɗorarre. Mariya Habibu gareki." ita kuma Mariya Habibu ta soma bamu nata labarin kamar haka...... Labarin Mariya Habibu To kun dai sani a makaranta Dr Mariya ma ake kirana, ina amsawa da karsashi cikin alfahari. A wannan lokacin a raina na saka ni likita nake son in aura tsabar soyayyata da aikin jinya. Ga yawan saka fararen kaya duk sabida gurina, ashe wannan guri bamai cika bane sam." Saurin katseta nayi na muskuta tare da cewa. A'a lokaci bai ƙure ba har yanzu Mariya Habibu. Ai ba'a tsufa da ilimi kuma in sha Allah in dai kina so, to burinki zai cika. Ke dai kici gaba muna saurarenki" Dariya tayi mun tare da cewa. "Hindu Duwaf iyayen son karatu na ƙwaƙwuduba kenan. Haka dai kike gani amman ƙwaƙwalwata a yashe take ita da fankon ashana babu maraba, ke naga rayuwa, rayuwa ta ganni fa. To a haka dai anata buga_buga ga iyaye ƙarfinsu ya ƙare har ta kai ta kawo mahaifinmu ya dena fita kasuwa, Babban wanmu ne ya maye gurbinshi a kasuwar. Haka aketa gurgurawa an gama karatu babu kuɗin ci gaba da karatu na gaba, kuma fa akwai yara da yawa da suke gama sakandare babu kudin wucewa Jami'a duk iliminsu haka za'aita zaune har ƙwaƙwalwar ta toshe, son karatun ya fice a ran mutum, shikenan duk iliminshi an salwantar mishi dashi. Talauci kenan bashi da daɗi sam, Allah dai yasa mu dace Ameen. Wata ranar asabar ina zaune wata ƙawata jarumace a masana'antar fina-finan hausa, tazo tace in karata wajen shirin film da kamar bazani ba dai sai na miƙe muka fita, saboda zaman gidan wallahi ya gama isata. A hanya muna cikin bus nake sanar mata nima ai da da hali da na shiga wannan masana'anta ta fina_finai, in ɗan dinga samun kuɗin da zan rufa ma kaina asiri, ai kuwa tace. "Shikenan Mariya in sha Allahu zanyi ma furodusanmu magana za'a ɗaukeki yadda kike masha Allah ɗinnan." Dake na fita kyau gaskiya, haka ko akayi rabon za'ayi, wallahi muna shiga wajen ga jarumai waɗanda na sani, dama waɗanda bansansu ba, ƴan bayan kemara kenan sai furodusan yace. "Ga ainihin wacce zata dace da Talatu nan gaskiya, kuma dama sabuwar fuska akeson amfani dashi. Ke a gida za'a barki kiyi film? " Gabana ya tattake ya tsinke, nama kasa magana sai kallona akeyi a wajen. Ba shiri ƙawata tayi carab tace. "Dama abinda ya kawota kenan shiga film, kuma babu matsala muna tare maƙotanmu ne." Wallahi dake ƙaddara bin me ita take yi tamkar inuwa, a ranar ita batai aiki ba dama sabon film ne nina ja shirin ita tazo a matsayin ƙawata, akayi film ɗinnan nice har a gaban Ali Nuhu ananne na gane sarki sarkine. Mutumne shi mai dattaku, natija, jan na ƙasa a jiki da ƙarfafa sababbin ƴan koyo, gashi da kwarjini sosai ya riƙe mutumcinshi irin riƙewar da baka isa ka kawo mishi wargi ba. Na koya daga Ali Nuhu sosai. To daga wannan film ƙaddarata ta soma aiki, Duk inda na ratsa laƙanina na cikin shirin ake ambata. A lokacin ɗaukakar daɗi wallahi. Har gida ake zuwa ganina, tsofaffin ƙawayena duk suka dawo, da samarina waɗanda muka rabu suma duk sai suka dawo hmmm. Ke Hindu a lokacin kina daf da yin Aure in ban mance ba mun haɗu daku a kasuwa, na rufe fuskata sai nice na kulaku kun tuna ke da Luba? Dariya Luba tayi tace. "Mu ko muka tuna jama'a aka taru a kanmu, wani mai shago fa da muka tsaya gaban shagonshi muka gaisa, bayan kin tafi wallahi da muka shiga saida yayi mana kyauta gwaggwaɓa, sabida dai mun sanki kuma ya tambayemu muka faɗa mishi tare mukai karatu fa" Dariya duk muka saka kafin taci gaba da cewa. "Haka na ɗaukaka naita fina_finai kuttun farin jinin al'umma ya fashemun. Kuskuren da mu muke yi ƴan wasan hausa, rashin tsari da hangen nesan me kaje kazo. Sabida a lokacin da mace take ganiyarta tana samun kuɗi tana da alfarma iri_iri madadin tayi amfani da alfarmarta ta yadda ta dace sai kiga bata yi ba. To garama na yanzu suna buɗe shago, sai dai abun takaicin kusan duk abu ɗaya suke saidawa shagon abaya, maganin mata, turaren wuta mafiya yawansu. Basa komawa makaranta suyi karatu mata_matan suyi amfani da alfarmar da suke da'ita su samu aiki, suyi ma al'umma hidima. Sai dai kiga basu wannan ƙasar, basu waccan ƙasar, mota, waya mai tsada, gidan haya mai tsada, siyan kayayyaki marasa alfanu tunda zaki ga wata bata da gida, bata da gwala gwalai amman duk sabuwar waya ko mota burinta ace a Kannywood ita ta soma hawa. Mu zamaninmu a lokacin da sauƙi, ba kuɗin da yawa amman akwai albarka, kuma ga girmama juna. Kannywood yanzu ai ta zama raka_raka amman akwai arziki cikinta. Amman Mariya Habibu masu wayo cikinsu irinsu Rahama sadau, Fati washa, maryam both, nafisa Abdullahi. A matan kenan kinga ai sunyi karatu a wasu ƙasashen ma ko?" Dafani tayi tace. Yauwa to ai basu da yawane, kinga shi yasa Rahama take burgeni sosai, yarinyar tana da masifar wayo kiga yadda ta ɗaga famili ɗinta, kuma Allah ya taimaketa ta samu uwa mai fahimta. Kinga ai tana riƙe da muƙamin da ilimine ya bata. Amman sauran fa? Wasu da ilimin nasu suka shigo, amman sai su ajjiye ilimin a gefe su saka film a gaba. Sai ciwo ya zubar dasu azo ana kafe hoto ana maula ai ba daidai bane. To haka nima ɗaukakata tazo na saima iyayena gida, Yayana na buɗe mishi shago a kasuwa, na cika mishi kaya muna raba riba, gani da ƴar motata kuma duk inda zan shiga ina da alfarma, wannan shine kaɗai daɗin ɗaukaka Alhamdullillahi har yanzu ina da wannan alfarmar duk da dai ƴan zamani basu wani sanmu ba abun ya jima. To a dawo ɓangaren mijin aure, sabida tsabar ruwan idanu da ƙyar na zaɓi wani Alhaji tare da iyalanshi suna Lagos. Mun yi soyayya kamar babu gobe, gaskiya ina son shi sosai, wallahi Aure sai ya gagara mahaifiyarshi, danginshi, suka ƙi fur abu mafi ciwo harda karuwa Mahaifiyarshi saida ta kirani. Ni kuma nace in shine Autan maza na haƙura dashi wallahi. Haka muka rabu. Na faɗa soyayya huɗu sai anzo batun aure da gabatarwa iyaye, sai su ƙi. Daga wannan lokacin na tsinke da lamarin harkar film, abun ya fita a kaina gashi ita harkar kamar shan taba ne dainawa yana wahala gaskiya. Shi yasa nake so a dinga ma matan film uzuri in anga basui aure ba, ko sun kasa zaman auren. Wallahi ba tulin maneman ba, mijin Auren. Ba Auren ba abinda ke cikin auren. Mufa munfi shanye baƙin cikin gidan Aure fiye da gama garin matan da basu da ɗaukaka domin me? Mu idanu na kanmu da mun fito sai ace dama bama zaman Aure sam, Ko kiji ana ai dama wance ce zata zauna a gidan Aure? Wance matar gwamna tafi ne, ko matar shugaban kasa tafi, ko matan sarakuna tafi ne da su sukai zaune a gidan Auren nasu? Wallahi rashin fahimta ce da yanke hukunci akan rayuwar mutum ta baɗini, tunda ai ba fitowa zaka yi duniya kace dole sai ka gamsar da jama'a ba. To a taƙaice wancan Alhajin nawa wanda mahaifiyarshi ta hana auren shine ya dawo, bayan mahaifiyarshi ta rasu. Ni kuma a lokacin Mamanmu an gama zigata akan in yi Aure ai ƴan film basa aure, kuma ta yadda wallahi ko gaisuwata bata amsawa ga Abbanmu Allah yayi mishi rasuwa. Ai yana zuwa nace to ya turo tunda mun riga mun fahimci juna, ai kuwa cikin sati guda aka saka biki, amman na zaɓi yin bikin da ba sai an yi sharholiya ko bikin da za'a kama hall ba, sai akayi biki a gida ƴan film sun mun rana su suka cika gidan bikannan waje ma haka maza duk mune ƴan film, su suka kaini ɗakin aurena, suka durƙusar dani a gaban kishiyata sukai mana nasiha mai kyau. Buɗar. Bakin kanwar kishiyata sai ca tayi. "Asabe dama ƴan film suna da tarbiyyar da zasu zaunar damu wai nasiha suke yi mana ƴan film fa?" Buɗar bakin margayya bazan ambaci sunanta ba, sananniyar mata mai mutumci tace. "Suna da wannan tarbiyya sabida suma ƴaƴane kamar kowa, ba bishiya aka girgiza suka zubo ba. Mariya ke dai kiji duk abinda muka ce miki ku taso muje mu kaita ɗakinta" Sabida kara da irin haɗin kai na Kannywood a wannan lokacin wallahi dangina ƴan kallo suka zama kawai, sun ƙwace biki tas sai dai san barka. An yi biki an watse ashe ƙaddarata anan zata soma ya Allah. Ta ɓangaren miji a lokacin gishiri na kan kaza, shi bani da matsala dashi sam sai da kishiya. Wautar da nayi shine saina ɗauki matsalar Asabe ba'a bakin komai ba, duk abinda tayi in shanye, duk sharrin da tayi in bata haƙuri, mafi girman kuskuren da hatta yanzu inajin zafi inna tuno kenan. Tafiya tana ta tafiya a haka anata gurgurawa da daɗi babu daɗi dai. Ta ɓangaren dangin miji basa sakani a lissafi basa mun kallon mutum zance, ne ko me oho. Sai dai ina zaune Asabe tayi mun sallama ta tafi bikin dangin miji dake danginshi da yawansu suna Legas musamman ta Agege, da idiraba, da obalande dai haka. Ita Asabe tana jin daɗi dangin miji da'ita suke yi, kunga ai ba zata faɗamun ba. Shi miji yana tunanin an faɗamun girman kai na ɗaurama kaina shi yasa nake ƙyamatar shiga danginshi, sabida ni ƴar film ce dai. Wannan labarin banfa sanshi da wuri ba har sai da bikin ƴar ƙanwar mahaifiyarshi ya tas, to ita a Taraba suke a cikin jalingo, wannan dai na tsinci zancan bikin a bakin wata maƙwabciyata wacce jininmu yazo ɗaya da'ita, mutuniyar Argungun ce masu kifi. To da naji banyi ƙasa a guiwa ba sai da kwana ya zagayo kaina saina tambayeshi, domin inji daga gareshi. Ashe ni daga ranar matsalata zata soma da miji. Nayi muku tsallake Asabe wata iriyar macece maras lissafi, muguwa wacce ta iya takura mutum. Akwai wani film nawa da wata waƙa ni nahau waƙar bazan faɗi sunan mawaƙiyar ba dan kar ku canko wacece ni. To wannan waƙar kullum itace abun wasan Asabe da fina finai na. Ina zaune zan dinga jiyota da maƙota suna tsinewa, da aibata ƴan film ƙage da sharri babu irin wanda basa yi mana. Ni a lokacin ne na gane girman ƙyama da al'umma tayi mana. Ko kuma ince ana sonmu a tv, anason ganinmu kuma, amman ba'ason a auromu sai mu zama bare tamkar ma ba musulmai ba. Kuma a hakan har zuwa kallona akeyi, ana murna in aka ganni, dole in musu fara'a in tarbesu, ga damuwa ni fal raina. Wallahi yaran Asabe har zagina suke yi a idona suna ce mun ƴar film mara tarbiyya, dake yaran ƴanmatane kuma mata, bana ko son fitowa mu haɗu babban abinda ke haɗamu Kicin. Kowa na da Kicin a ɓarayinshi sai babban Kitchen a tsakar gida babba sosai, cikinshi da ƙaton suto shaƙe da kayan masarufi. To anan ko wacce in ta shiga girki zata yi, kuma girki a haɗe. Asubar fari ran kwanana zan zare jikina in nufi Kicin, gashi ƙa'idar gidan abun tuya akeyi da safe, doya, dankalin hausa, dankalin turawa, sai ƙwai da ya zama dole. Kuma zaki yi cincin ko mutufib, ko fanke da yara sazu tafi dashi makaranta. Hmm to wannan ma kullum zai shigo yaita azalzalata, Asabe kuma ta dasa mita duk in birkice basa dubamun, cewar ni ba sabawa nayi da hidimar kowa ba, lokaci ɗaya hidimar yara bakwai gani,ga miji, ga kishiya, ba abu mai sauƙi bane. Tunda ko ita Asaben ai da sannu sannu aikin yaita hawa kanta ba lokaci guda bane. Amman sunƙi fahimta sam, duk da itace ke kambaba abun da'ita da babbar ɗiyarta. To mu dawo inda na tsaya cewar na tareshi da batun bikin Taraba. Dana tambayeshi. "Ashe za'ayi biki a Taraba shine ba'a faɗa mini ba, bare in soma shiri." Ai wallahi kamar na ɗana mishi wutane. "Menene amfanin sanar miki tunda ko an sanar miki ba zuwa zaki yi ba, ke da kike ƙyamar dangina? Asabe ce ta dace dani, kuma itace ta damu da dangina, da yarana ai. Wai ke da na Auroki na rufa miki asiri, yau ni kike tozartawa Mariya? To babu inda zaki je, suma dangina basa fatan ganin ƴar film a cikinsu ke baki san da yadda akayi auren naki bane. Na gama gajiya da ɗabi'unki, da yadda kike ma iyalina gani_gani, ga barin yara da yinwa da kike yi, kullum kekenan a cikin yin lattin girkin safe, da rana ma sunce har su dawo bakya gamawa, sai wajen huɗun yamma kike gama girki, na dare kuwa sai bayan isha wataran har gaba da isha kike kaiwa nima ina gani ai. Wannan shine tsiyar auren ƴar film. Baki iya uban komai ba sai rawa" Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba wallahi. Ya barni in yi magana in wanke, kaina abu yaci tura, ya barni in bashi haƙuri ma, yaƙi yadda sai fuffuka yake yi. Ni kuma ƴar adam ce kamar kowa kuma babu ta inda ya zama ratayayyen hakki a kaina yima matarshi da yaranshi hidima. Sai naji na kawo wuya haƙurin da nake bayarwa na ja bakina nayi shiru kawai. Daga ranar yadda kuka san an mana farraƙu haka muka kasance tamkar musa da fir'auna. Asabe ta haɗa makirci, ta shiga ta fita, da asiri ta rabamu. Naje bikin Taraba saida nayi ɗan da kace banje ba, irin wulaƙanci, da tozarcin da akaimun a bainar nasi ba ɗan kaɗan bane. Gashi zuwana bikin yasa maƙwabta na nesa dana kusa sun hallara sabida ni, kunsan Allah yayi mu da farin jini. Wannan faɗama wannan, wannan faɗama wannan, akaita zuwa kallona sai wani ɗaki na shige na adana kaina saida nayi kuka kafin na samu salama. Haka muka dawo naci gaba da karɓar gashi, ga laulayi ya sameni inata gurgurawa a lokacin ko ɗakina miji ya dena shiga, ya ganni mu gaisa abun yaci tura, yaci abincina babu dama, duk ran girkina Asabe da yaranta kawai nake yi ma. Shi kuma Asabe zata fito tayi mishi girki na musamman. Tana yi tana cewa. "Gida nawa ne, na yi zantsuwar babu wata shegiyar da zata zo ta miƙe ƙafarta. Ramin kura sai ƴaƴanta. Inata laulayinnan har cikina ya tsufa a haka ban taɓa zuwa awo ba, ɗan maganin zaƙinnannan ban sha ba, in faɗa a gida nakasa sabida an riga an yima Mamanmu famfo akan bama zaman Aure, mun riga mun saba da kuɗi. Inaso in haskama duniya ba saboda kuɗi ko son film ke fito da ko wacce ƴar film ba, a. a wallahi ina da ja. Aure muke ke yi kamar kowa, da niyyar mutuwace zata rabamu, bawai auren jeki ki dawo ba. Ƙaddarar data haɗa Aure, ƙaddarar ke raba Auren, bawa kuma bashi da tsumi bashi da dabara, mu kaɗai muka san me muka fuskanta, me kuma muka shanye dan dai duk kada ace Aure ya mutu duniya ta ɗauka. Asabe ta azabtar dani, amman haka naita turawa, nace zan zauna a haka. To ina zaune da safe sai Mama tayi kirana akan Inna Mairiga ƙanwarta gata nan a tasha zata tawo ta zauna dani, tunda ciki haihuwa ko yau ko gobe. A lokacin da ta kirani kafin Innah mairiga ta taso zan hana, amman sai bayan da motarsu ta taso take sanar dani. Dana jiyo motsinshi zai fita sai naje na sameshi a gaban motarshi shi da Asabe nace. "Dama Mamace ta kirani tace dani Innah Mairiga ta taso, zata zo ta zauna dani." Sai nayi shiru dan a lokacin wani tsoronsu nake ji sosai dukkansu, ƙur yayi da idanu yana kallona can yace. "Sabida ban isaba harma saida ta tawo kafin zaki faɗamun, ke ɗin yarinyace da sai anzo an zauna dake ke da kika gama tsufa, kika rasa mai tayawa, ba zaki iyama kan ki komai ba? "Zan iya, wallahi nima Mama bata faɗa mini ba har sai da ta taso tukunna kayi.. " "Rufa mun baki dallah, akanme za'azo wani kula dake, kenan Asabe duk kulawar da take baki kin raina kenan ko?" Kaina ya ɗaure dan Asabe gaisuwata ma bata amsawa, bata ɗauke mun komai na ɗawainiyar girki da aikace_aikacen cikin gida ba, a haka nake gurguwara inyi komai. Naji kuma ana batun kulawar da take yi dani. "A.a Baban Murja ai ana zuwa a zauna in haihuwar fari ce. Tazo ta zauna in akayi suna ba sai ta tafiyarta ba, inma da'ita zata tafi wankan jego ba shikenan bama" Sai yace. "Ai shikenan tunda bayanta kike goyo, wato harma da wankan gida?" "Iyi sai taje ai tunda kaga tunda akai Auren bata je ganin gida ba" Ni da nake daskare a waje ɗaya mamakin kirsar Asabe nake yi. Wato kishiya bata kaɗan bar ganin kinfi kishiyarki komai da komai, wallahi tsab zata kai ki ƙasa. Innah Mairiga ba ita ta shigo ba sai washegari da azahar tazo ta sameni ina naƙuda na kasa neman tallafin Asabe sam, tare suka shigo suka taddani a durƙushe babu yadda nake. To mu kwana anan sai kuma in Allah ya kaimu litinin sai mu ɗaura. Nagode da kulawa. Ayi ta haƙuri da rayuwa, ayi haƙuri da juna kuma. Tim mijinyawa, ƴan a mutu mai su Anty Faty, Anty Hafsat, Maman Muhibba, mrs jay da sauransu, da sauransu ina gaisuwa. Tim Hindu. Ƴan a mutu mata Su munira Nasir. Umminmama Mamanmu Hajara Aliyu. Maman Dady Mamanzee Da sauransu, kai tim Hindu da yawa kuke afwan waɗanda ban kiraba, bamma isa kiranku duka ba. Son so masoya labarin Hindu💪🏼💪🏼💪🏼💪🏼💪🏼 Mrs Bukhari YAR UWA MENE MATSALARKI KINSAI MAGUNGUNAN NONO DA NA KARIN MAZAUNAI HAR YAU ALLAH BESA AN DACE BA TO INSHAA ALLAHU MATSALAR KI TA KAU INJINI NI AUTAR AMBATO MAGANIN NONO Kina fama da zubewar breast komai lalacewarsa kokuma dai Allah be azurtaki dasu sosai ba to ni na baki guarantee kwana 7 kachal zakiga chanji idan har kikai amfani da magani na 🥱🙅🏽‍♀️🤌🏽🙌🏻 MAGANIN HIPS Kinasan ki kara mazaunai ki kaddara matsalar ki takau DOMIN maganin mu sadidan ne inkinyi amfani dashi Saikin dawo ko kin kawo wata wannan shine taken maganin mu masu bukatar karin bayani ko samun maganin mu zaku tuntubemu akan wannan number ta WHATSAAP number 0812 681 3773 SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA 🤭INJI AUTAR AMBATOTSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA ASHIRIN (20) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F5JwhdwbtCQ6qdo4LA4kyE Adashen hijabin ƴan gayu ɗinkin ƴan kaduna kike so Hajiyata? Ga masoyiya, aminiyar da bata da tamka, Ummu inteesar kenan farar aniya laya. Ki shiga group ɗinta zaki samu yadukan hijabai ƴan gaske na kaduna, wanda zaki ta da taro. Kaduna sune Hijabi a bar musu kayansu. Ummu inteesar hijabs and more, mai adashen gata. "Subhanallahi kinga ma kin zo a gaɓa ai kamar naƙuda take yi ma? " Asabe ta iso a guje wajena tana wani tarairayata, yadda kuka san zaman lafiya muke yi haiƙan ɗinnan. Inna Mairiga dai hijabin jikinta ta cire tazo ta kamani, tana kwatantamun in dinga ambaton summas saliba yassara. Saina kama inata nanatawa ciwo ya ƙi ci, yaƙi cinyewa. Asabe na kaina tayi kane_kane. "Inaga kije Uwargida zan kula da'ita, kinga in banda abu na lalura babu yadda za'ayi kishiya ta tsaya kan kishiyarta yayi naƙuda, ko ba gaskiya ba? Kuma wannan dalilinne yayi sanadin zuwana ma. Amman kiyi haƙuri ƴannan" Ga ciwo na cina amman sai naji daɗi. Asabe ta fita ba guiwa To haihuwa in yita a gida abu ya gagara. A asibitin ma da suka ga dugu, dugu wajajen asubahi kawai suka ce a saka hannu aiki za'ayi mini. Ina miji, bayanan wayarshi a kashe, sai lokacin Asabe take cema Innah mairiga ai tafiyace ta kamashi ta kwana huɗu. Ni dai bammasan inda kaina yake ba, ita ta saka hannu a takadda aka ciromun yarona sunkucece lafiyayyen gaske. Asabe ce ta biya duk ɗawainiya, ashe ita ya danƙama kuɗi uba_uba a hannunta. Kwananmu huɗu a asibiti aka sallamemu. Dake na jigata gaya. A ranar da muka koma oga ya dawo daga tafiya ana jibi suna, na kira anyi mun kitsona, gobe nake so nayi ƙunshi. Muna zaune da daddare Innah Mairiga tana zaune tatusani gaba inacin tuwo miyar kuka, yaji manshanu ga yajin daddawa an gabzamun, wanda Innata tayo mun. Sai kunun kanwa a gefe ina korawa. Muka jiyo sallamarshi ya shigo kadaran kadahan. Innah mairiga ta miƙo jariri ta bashi ya karɓa. Duk da jaririn shine jaririnshi namiji na farko baisa ya samu salama a fuskarshi ba, bani ba hatta Innah mairiga ta tsinke da wannan lamari. Miƙewa tayi ta shige ciki ta bamu waje. "Gashi nayi mishi huɗuba da sunana. Allah ya raya. Dukkan abinda kike buƙata sai ki ma Asabe magana. Kuma washegarin suna a bisa al'ada da yamma zaki tafi gida wanka kuma. In kika gama sai in zo in ɗakkoku" A jikina nake ji ba lalle in sake dawowa ba, haka na dinga ji har zuwa ranar suna. Ragone aka yanka ma yaro Haruna, dake kudune kuma danginshi ba yina suke yi ba. Shinkafi mudu uku kacal aka dafa da lemun kwalba, shima sabida kara da maƙota suka yi ne. Ni ina kwance ma babu lafiya mamana ya suntuma kan yana tsagewa harda jini_jini, gashi a haka nake cirowa in ba Haruna zafi kuwa har maɗigata nake jinshi. Zuwa bayan magriba Innah mairiga ta dinga tattare mun kayayyakina tana adanasu, ni kuma ina haɗa akwatin kayan Haruna da abubuwan buƙatana. "Naga duk kin sakko da akwatunanki dasu zaki tafi ne" A, a atampopina masu tsada zan cire da dai duk wasu abubuwa masu tsada Innarmu, kinga cewa yayi aba Asabe kin ɗakin" Shiru tayi taci gaba da aikinta can kuma meta tuna oho sai ca tayi. "Ki ɗauki duka kayan akwatin naki, da duk abinda kika sani mai tsada. Kinga kayan sawanki na ciki? Kada ki bar ko ɗaya jiƙaƙƙun ƴan kamfanki da kika wanke ɗazu ki zuba a leda mu tafi dasu. Amman taya za'ace aba kishiya kin ɗakin Kishiya ne ma? " Allah ya kyauta kiyi haƙuri aure babu da irin turka_turkar da baya xuwa dashi. Matsalar wannan daban da matsalar wannan. Wama ya zaci ƴar wasan kwaikwayo dake zaki yi irin wannan haƙuri, ku da ake cewa zaman aure na gagararku. Sai gashi ke baki da fada a gidanki, kishiya ke mulkin gidan, amman kin daure kin... Burum Asabe ta shigo babu ko sallama da jakar buhu kano ta ɗau zafi a hannunta. Ganina da akwatuna na baje su a gaba sai tayi turus. Me ta tuno_ me ta tuno, ohon mata sai ta yashe baki, ta gaishe da Innah mairiga itace har da zama a bakin gadona. "Mai jego irin albarka ga kayan suna inji Baban boi. Atampa uku, sai mayafi da rigar yaro biyu da pampas me takwas. Wallahi kunji rantsuwar ɗan musulmi, shikenan abinda aka bani na suna. Sai atampa da sabili da dubu hamsin na Innah mairiga. Wannan ma kam tace ita tayi ma Innar ba Haruna bane yayi mata ba." Fasali Mariya ta ja tare da ɗebe hawayen dake fuskarta a ƙoƙarin ganin ta danne damuwar, amman ina sai kawai ta fashe da kuka mai gunji. Duk dana dubesu hawaye suke taya ta sharewa. Ajjiyar zuchiya na sauke kawai tare da cewa. Duk wacce kuka gani tana da labarin bayarwa a rayuwarta. Mata muna ganin rayuwa a hannun mazajen da basa jin tsoron Allah. Waɗanda suka more ire_iren Nana Kabiru kuwa, su da rijalu sai son barka. Matan da suka auri masu koyi da Arrasul SAW, ku gode ma Allah, kuma kuyi musu biyayya. Har kullum ina daɗa jaddadawa mata a nemi na kai, kar ki sake da wasan _wasa ace baki da sana'a a hannunki. Wacce taji ba zata iyaba, ga waje tayi zaman daɓaro. Sannan a nemi ilimin sanin Allah, kuma ayi ilimin boko. Ko kuma ki kasance ma'aikaciya, sannan banda raina sana'a ko riba." Ajjiyar zuchiya na sauke kafin nace. Mariya bayan kin dawo gida, Haruna baizo ba sai takaddarki ya turo miki ko? " Na tambayetane sabida ta dena kukan haka. Tun kafin ta kaini wuya. "Kamar kin sani Duwaf. Daga wankan gida shikenan Aure sai ya ƙare. Kafin auren ya mutu maƙota da ƴan unguwa tuni sun soma gulmammaki, labari ya baza unguwa kan doron jita_jita, a lokacin wata uku nayi a gida kunga ai wanka ya ƙare. Tun anayi a ɓoye har aka soma shigowa tambayar yaushe zan koma, dangi suma suka matsa sosai, akan batun komawata, musamman Dangin Babanmu. Dana cika wata na huɗu. Sai ƙanin Babanmu yace in bashi adareshin gidan namu na can Lagos, tunda wayar Haruna bata shiga sam. Na rubuta mishi adireshin, a ranar ya kama hanyar Lagos kwananshi biyu sai gashi da yamma sakaliya ina tuƙin tuwo a tsakar gida. "Ke Mariya zo mu tattauna a gurguje." Muciyar na ajjiye na nufeshi yana zaune a tabarma a ɗakinmu. "To naje Lagos yadda kikai mun kwatance, na tarar da kishiyarki Asabe ko? " Eh kawu Asabe" "To shi Haruna sanda naje baya gidan, Asabe tayi mun tarbar kirki har Harunan ya shigo muka tattauna. A yanda yace wayarshi ce aka sace mishi shi yasa kika jishi shiru. Kuma akwai tafiya da zaiyi na wata biyu in ya dawo dakanshi ma zai zo ku tafi. To Amman ni Kattume saina fahimci ba lallai yaronnan yazo ba, a yadda ya tarbeni. Ke Mariya me kika yi mishi ki gayan gaskiya, dama ku ƴan wasan ƙwaiƙwayo baku fiye zaman Aurenku ba. Shi yasa mu dai bamu so wannan sana'ar ba. Nifa a unguwarmu wallahi har nuna ni akeyi, ga uban ƴar fim" Haka dai Kawu yaita sababi, kafin yayi mana sallama. Ni dai a ranar akan sallaya na kwana. Bana so Aurena ya mutu sabida yadda Dangin Babanmu suke zuwa suna matsama ummanmu, har kuka take shigewa ɗaki tai ta yi. Nima inna jiyota tana kukan ranar haka zan wuni a ɗaki cikin damuwa matsananciya. Ranar da muka cika wata shida sai ga kiran Haruna ya shigo wayata. Da gudu naje ina nuna ma Ummanmu. "Maza ɗauka Mariya. Allah nagode ma. Abinda tace kenan ina ɗauka bayan mun gaisa sai cewa yayi. " Na sakeki in kin samu miji kiyi aure. Yarona kuma in kika yayeshi zan zo in karɓeshi in haɗashi da ƴan uwanshi" Mama ta karɓi wayar a hannuna ta kashe. Mukai shiru a tsaye a wajen a haka Innah mairiga tazo ta taddamu cirko cirko, wallahi munfi minti talatin a tsaye kafin zuwan Innah Mairiga. Da ƙyar Mama ta labarta mata halin da ake ci. "Mairiga babbar damuwata shine ki duba da yadda akayi Mariya tayi Aurennan. To yanzu gashi ya mutu, dama anata cewa ba zata zauna ba. Dangin mahaifinsu laifina suke ta gani. Kawunsu kullum cikin sunturin jin ba'asi yake. A unguwa an takura mana da gulma, Mairiga ki tafi da Mariya dan Allah. Kuma ban yadda ta koma harkar film ba." "Yaya ki dena damuwa da maganar mutane mariya zan tafi da'ita. Kuma mu yadda da ƙaddara, mu sa a ranmu ba sabida ta kasance ƴar film bane Aurenta ya mutu ba. Ke Mariya haɗo kayanki muje ba shikenan ba ne. Haka na haɗa kayana sanadiyyar konawata hannun Innah Mairiga kenan. To bafa ni na fita idda ba sai bayan shekara ɗaya tim da sakina da Haruna yayi. Sabida saida na yaye Haruna kafin na soma al'ada na sauke iddata. Sai rayuwa taci gaba gaga_gaga, ga maneman amman ba batun aure sam. Zamam waje ɗaya ya dameni, ba karatu, ba sana'a, kwatsam za'ayi wani shiri sai ƙawata ta kirani tace inzo odishon gashi_gashi. To Mama da ƙyar dai ta yadda sai na sake tsintar kaina a masana'antar a karo na biyu, akaci gaba da damawa damu rayuwa ta yi kyau fiye da lokacin farkon ma. Masoyana basu mance dani ba, anata murnar ganin dawowata. Akaita ɗaurani akan fina_finai alhamdulillahi ina samun na rufin Asiri. Haruna kuwa yana ganin fina_finaina yazo ya karɓe yaronshi, harda faɗamun da yayi niyyar barmun shi, amman a yanzu tsoron kar in sakashi harkar fina finai yasa dole ya rabamu. Luba tace. "To yaya kika yi kika sake Aure, ya fitowar taki ta kasance?" Katse Luba nayi ta hanyar cewa. Ni a wannan lamarin Asabe tafi bani mamaki a matsayinta ta mace. Itace matsalar auren kacokan. Ina mamakin abinda mata suke yi akan maza wallahi. Sai mace ta cutama ƴar uwarta mace, mace ta hana ƴar uwarta mace zaman aure, kuma ita tana so ta zauna akan nata auren, tana so kuma a Auri nata yaran suma su zauna. Dukkannin matsalolin ƴan uwa mata da sanya hannun mace a ciki. Mata wai yaushe kukai irin wannan lalacewarne? Ko da yake Manzon Allah yayi gaskiya da yace yaga mata danƙam a wuta." Saudat tace. "Gashi Asaben ƙware sosai. Amman duk yadda akayi Asabe bata aiki, bata sana'a ko Mariya? " "Bata yi, nima banayi. Shi Haruna gani yake yi aiki ko sana'ar mace na da alaƙa da gazawar mijinta, wannan itace fahimtarshi gaskiya. Kuma dani da Asabe bamu da ilimi, da takaddun shaidar karatu ma balle muce zamu yi aiki, tunda baya son sana'a. Ai abu mafi girma da nake yin dana sani shine, rashin yin karatu mai zurfi da zan iya aiki, da rashin gina sana'a a lokacin da ake daddamawa dani. Aure na biyun wanda na Aura har yafi Haruna kuɗi gaskiya, ma'aikacin hukumar fasa ƙwaurine babba, ko ince babban ɓarawo, wanda bai ɗauki kuɗi da kashesu a bakin komai ba. A bodar jibiya yake iyakar nijar da Najeriya. Matarshi da iyalinshi suna zaune a Katsina, yana zuwa duk hutun ƙarshen mako, wani sa'in sai yayi wata ma bai leƙo ba. Adamu sunanshi, yana da yara maza manya matan ƙananane. A wannan karon yaran miji da kishiya ba sune matsalata ba, daidai gwargwado muna zaune dasu lafiya. Sabida matarshi ta kafu gata hamshaƙiyar ƴar kasuwace, babbar mace wacce bata da lokacin kishi, kullum tana cikin lissafi ko waye_waye da abokan ciniki. Da Adamune matsalata. Zargina yake yi, haka suddan bai taɓa kamani da komai ba. Sabida kawai na kasance ƴar shirin film. Wallahi naso duk wuya duk zargi in jure in zauna ko dan sabida Mama, da maganganun dangi, da jama'ar gari yadda aka shafe ƴan film da kashin kajin rashin son zaman aure. Babu dama a kira wayata, sai yace wai ƴan iskan dana ke mu'amala dasu su suke nema ba. Wallahi ko zan haɗiyi Qur'ani yaji ina aman surori bazai yadda dani ba" Amman a wajen da bai dace ba kuka haɗu ko Mariya, in ba haka ba wannan zargin na menene? Idanu ta lumshe kana tace. "Hakane Duwaf a inda bai dace ba muka haɗu, amman ni aikinane ya kaini wajen wallahi. Amman wannan zargin shi ya kawo ƙarshen auren, Banda cutar ciwon hanta daya shafamun, ashe dashi da matarshi duk cutar garesu, duk da dai itanma shi ya shafa mata, kunsan ita ana iya ɗauka a lokaci, in mai cutar yawunshi ya taɓa, ana iya ɗauka ta gumin jikin mutum. Bayan ya gama wulaƙantani da tozartani. Na azabtu da bugu tamkar galila in faɗa muku. Ni kuma nayi biyayya, na kwantar da kaina, dan dai kada a sakeni. Amman har sunan Mama da Baba yake kira zai mun zaginsu na katsinawa mai goyo. Gashi da shan tabarmasifa yadda kuka ga bummali. Aure ya ƙare na dawo gida kunji biyu? Ga tsarabar ciwo dana kwaso. Sai matsaltsalu al'amura suka daddamemun, zawarci babu kyau, sai aka hau mun ɗan kira a unguwa ana zinɗen Innah mairiga. Wato ina mamakin yadda ƙalibar hausa suka ɗauli aure, saki, da zawarci. Wato ni a mahangata gani suke yi tamkar wani aibune ace mace ta kasa zaman aure, alhalin basusan menene dalilin daya fiddota a wannan gidan Auren ba. To ni kuma nawa yayi ƙamarine a sakamakon ina da fentin ni ƴar film ce. Murmushi nayi mata nace. A hangenki kenan. Ni a nawa gane_ganen da irin koken mata da nake saurara sun ɗauki zawarci tamkar kafurcine wasunmu da yawa. Kuma daga iyaye ake soma samun wannan matsalar, dan su suke soma nuna ƙyamarka muraratan. Sai kiga uba wai baya amsa gaisuwar ɗiyarshi sabida an saketa. A tunanin su ta aikata zunubin da za'a dinga ganinsu dashi, ko kuma kai tsaye ta nunama duniya gazawarsu a tarbiyya, ko kuma ta nuna rauninta ko wani tunanin nasu na daban. An fifita al'adu fiye da addinin. Wai macece zata kama mijinta yana zina fa sabida kar a saketa magana wannan sai ta kasa yi mishi, balle azo batun ɗaukar mataki ko ƙwatar ƴanci. Da kin fito kince a ƙwaci ƴanci kan zaluncin da akayi miki fa, yanzunnan kwaf ɗaya za'a kafirtaki, kiji ana cewa kwangila kika karɓo ake biyanki dan ki tarwatsa tunanin mata, da addinin Musulunci. Mariya ai irin yadda al'ummarmu ta dawo a yau abun ba'a cewa komai. Da yawan mata sun mutu wallahi, baƙin cikin ɗa namiji ne, da yawa suna kwance a asibiti, da yawa suna ɗauke da wani miki marar warkewa a rayuwa, dan bana ce zuchiya ba yafi ƙarfin wannan. Akwai jajawur ɗin aiki a gabanmu, akwai buƙatar ayi ilimi arabi da boko wallahi, da yawan abubuwan nan jahilci ke taka muhimmiyar rawa. A haka dai ga yawaitar malamai, karatuka a sauƙaƙe amman wallahi akwai jahilci da rashin wayewa, uwa uba rashin tarbiyya. Aure kawai akeyi, ayita haihuwar yaran da ba za'a iya ɗaukar nauyinsu ba. Wallahi wata mata dana bata shawara su huɗu ne a wajen miji, kuma wai mai gyaran takalmine mijin. Yaranshi ko sha uku. Hmmm ni dai jari na bata na haɗata da shawarar komawa islamiyya. Awara take soyawa a ƙofar gida, tace mun tana ciniki babu laifi, kuma harta saka yaranta a makarantar allo sabida basa karatu, abinci ma sau ɗaya ake iya basu. Ba muhallin kirki, babu suturar kirki. Ya ba zasu lalace ba damin Allah fa? Luba tace. "Ai sha'anin al'ummarmu ta wannan ƙarnin gaskiya akwai gyara mai yawa, son zuchiyoyinmu yayi yawa, da kuma son burge mutane. Shi kuma ɗan Adam ba'a taɓa iya mishi. Saudatu Lauya anyi shiru anata ɗaukan darasi" Dariya muka yi dukkanmu Saudat tace. "Rayuwar Mariya da tausayi sosai, kunsan sabida me? Sabida rashin karatun dake tattare da'ita, gashi ita ba wata sana'a take yi mai gwaɓi ba. Ga ƙaddarar dake bibiyarta, amman bari mu kammala jin labarin kar mu katsi hanzarinta. In yaso in aka gama sai a tattauna baki ɗaya. Hindu kam sai dai wani jiƙon ta bamu nata labarin lokaci ya tafi sosai. Mariya Habibu taci gaba da labarinta da cewar. Bayan mun rabu da Adamu inata zaune bana harkar film ɗinma, sabida ba'a kirana aiki tauraruwar ta disashe an samu yalwar sababbin fuska. Dama sunnar masana'antar kenan cin moriyar ganga, duk da muma da kalan namu kusakuran na rashin amfani da dama a lokacin da tauraronka yake kan ƙyalli. Na yanzu dai suna ƙoƙari sosai wajen kasuwanci da karatunma. Na sake faɗawa gidan mai mata uku ni Mariya Habibu ta huɗu, abun mamaki bama a birni ba. A ƙaramar hukumar bunkure yake cikin kumurya. Kumurya garine babba mai tarihi da ke da fadar kansa (Gunduma) garin kumurya sananne ne sosai a fannin tarihi, har ma an bayyana cewa shine garin kakannin tsohon shugaban kasa na soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida IBB. A unguwar Fada wacce take a ƙwaryar garin ganan fada take, kuma wannan unguwa itace matattarar sarautar gargajiya, shi kanshi mijin dana Aura mai sarautane jinin sarauta, amman bazan faɗi sunan sarautarshi ba, duk da ba wata babbar sarauta bace, kuma yana siyasa sosai ɗan, gwagwarmaya ne a wajen gwagwarmayar siyasa ma muka haɗu mun je wani taron siyasa an gayyaci ƴan film shine ƙawata ta kirani muka je. Ashe wannan ƙaddarar Aure shi ya kaini wannan taron. Soyayya ta gaskiya, tarairaya gata, dattaku babu wanda ban gani ba kafin auren. Ya matsa ya takura shi ayi a gama kawai ya ganni a ɗakinshi zai fi kwanciyar hankali, shi yana da fina finaina da yawa ya jima yana ƙaunata, wa kaza wa kaza. Toh dama ni ga firejar iyaye da dangin Abbanmu a kaina tuni na haɗashi da Kawunmu. Da haɗuwarmu da Aure duka duka wata ɗaya cur aka ɗaura aure sadaki dubu ɗari, ya bani miliyan ɗaya yace in haɗa akwati. Da wannan kuɗin na sai kayan Kicin, ɗan abinda nake da buƙatar ƙari tunda ina da komai na aure a adane. Dubu ɗari biyar na tafi dashi da zummar yin wani abun duk da yayi mun alƙawarin ci gaba da gwagwarmayar siyasa. Hmmm ranar dana kwana ɗaya tak na gane Allah da girma yake. Yanda kuka san mijin kofur Zubaina na Ghana wajen matsolanci, ashe kuɗin lukudi gareshi sau ɗaya tak ake girki a gidanshi tuwone za'ayi da daddare, ku ci ɗumamenshi da safe a haɗa da kokko ba'a maganar sikari gara Mijin Zubaina ma ana haɗa kokko da ƙuli_ƙuli har a haɗa a mazarƙwaila. Da rana ba'acin komai ba'a ko hura wuta haka ake wuni halen_halen da yinwa. Mata, da yaran gidan duk a rame. Gashi gidanshi ginin zamani babba, kuma ba'a sana'a a cikin gidanshi. Ranar Juma'a ana dafa shinkafa da wake da mai da yaji shine shinkafa da akeci sau ɗaya tak a sati, kuma shine abincin rana da akeyi sau ɗaya tak. In aka niƙo dawa buhu guda tuwonta za'aita ci har sai ta ƙare. In masarace haka, in gerone haka shima. Naga rayuwa, naji yinwa kamar zan mutu sanadin da cutar yinwa mai tsanani ya kamani kenan har gobe yana tashi mun. Ta ɓangaren auratayya kuma babu matsalar komai gaskiya shi matsalarshi ta kuɗine, ace za'a kashe yanzu zaku hau sama a diro. A haka naita gurgura rayuwar naita birgima cikin wannan ahali da zummar duk rintsi zan zauna. In ko naje ganin gida mayinwaciya haiƙan nake dawowa, in zan tawo a haɗoni dasu garin biskit da ƙanzon masara sai in adana abuna da rana in dinga yafita, da ya ƙare shikenan. Wannan kuɗi dana tafi dashi in ƴan uwana suka kawo mun ziyara sai in zara a siyo musu abinci ko wara kamar yadda naga matanshi na yi. Kishi fa a gidannan zaku ɗauka zai yi sauƙi ko? Wallahi kullum sai an yi cacar baki a gidannan a tsakankanin bataliyar yara kai naga duniya, naga makirci, naga aya. Ana cikin wannan cukumurɗar sai ga laulayi na samu cikin Asiya. Kunsan ciki da tsurfa, bana iya cin tuwo da miya wallahi sai gayan tuwo da ruwa har na tsawon wata shida cur. Na rame na fita hayyacina. Duk wani ƙwaɗayin ciki ban sanshi ba. Asibiti awo sai Innah Mairigace ta kaini sau biyar shima a ɓoye. Ina jin halamun haihuwa na gudu gidan Innah tsoro nake ji kar in mutu. Ai ko jakar kayana ban cire ba sai naƙuda yanke take. "Ikon Allah Mariya naƙudar kike yi shine kika tawo? Tabawan sabo zo ki kamamun Mariya mu shiga ciki" Kishiyar Innah mairiga ta rirriƙeni muka shiga ciki. Awa shidda ina gumurzu, nayi zufa, na galabaita har na soma jijjiga. "Mairiga a kira mijin yarinyarnan a kaita asibiti, kinga ta soma jijjiga kar ta yi tsinka_tsinka" Hmm aka kirashi suka sanar mishi halin da ake ciki. Wai kunsan me yace? Cewa yayi shi bazai biya kuɗin asibiti ba, sabida matanshi duk a gida suke haihuwa ko?" Na faɗi ina jinjina kaina, ai kuwa Mariya Habibu tace. "Kamar kina wajen wallahi Duwaf. Har ɗorawa yayi da faɗin shi an isheshi, tunda na samu ciki nake ta tsurfa, sannan shi ba da yawunshi za'aje asibiti ba kuma bai yafe ba in aka kaini asibiti" Haka akaita waye_waye daga ƙarshe Yaya Habune yazo ya kaimu asibitin yace shi da yawunshi. Muna zuwa akaita faɗa likitoci, gashi kai tsaye suka ce tiyata za'ayi mun. Kiran Duniya Yaya Habu yayi mishi amman wallahi bai ɗaga ba. Shi ya rantaɓa hannu aka wuce dani tiyata aka ciromun Asiya. Ga jinina ya hau ainun ashe na auna arziki sosai, amman saida na kwana huɗu cur na dawo hayyacina na fahimci a ina nake. Inna baku a taƙaice, har aka sallameni babu Alhaji Adamu babu wani nashi, haka aka maidani gidan ina gani. Mun koma ana gobe suna wallahi akan abincin suna saida Alhaji Adamu ya dinga sa'insa da Innah mairiga shinkafa mudu biyar ya bayar, da ajino rabin jaka, mai tauraro kwatan leda, mai kwalba biyu harda na suyan wata tinkiya da aka yanka ta haƙiƙa kayan miya a ƙaramin kwano albasa biyu ce akai. Ni kuma turmin zani, da rigar yarinya, da tawul ɗin ƙunzugu shikenan abinda ya rabani dashi. Abubuwa dai babu daɗi wallahi a haka nayi wannan goyon cikin yinwa Da baƙin ciki. A gaskiya a wannan auren ni da bakina nace ya sake ni ina kwance a gadon asibiti cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai ciwon damuwa, ga ciwon hanta ya matsamun lamba, a lokacin hantata har ta kumbura, ga ciwon yinwa yana neman rayuwata. Bai ja ba, ya rubuta mun saki tare da faɗamun kalma mafi zafi da muni wai. "Ai dama Ƴan film basu da tarbiyyar zaman gidan miji, da jumurin haƙuri" Wallahi bansan sanda nace dashi abu ta kazan ubanshi ba. Aminiyata tana gefe na itama ƴar film ce, ita ta biya komai na asibiti na. Wannan shine ƙarshen labarina amman a yanzu haka saura wata guda aurena da wani sabon mijin bayan shekaru biyar ina cashe zawarci. Ga ciwon hawan jini dake ta jujjuyamun yanayina" Hmmmm ni abinda yake bani mamaki da hangen mutane baya wuce yadda suke haɗa mutane sui musu kuɗin goro, alhalin a musulunce hakan ba daidai bane. Wai shin ƴan film ɗinnan wasu al'ummane daban da gama garin mutanene. Ko ya abun yake nenene? " To anan zamu kwana. Nayi Posting yaune sabida in kawo ƙarshen labarin ƙawayen Hindu, mu dawo kan ainihin labarinmu zuwa Monday in sha Allah. Son so💪🏼💪🏼💪🏼 Mrs BukhariTSURON TSIRIN... TSANDAURI.. LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA ASHIRIN DA ƊAYA (21) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F5JwhdwbtCQ6qdo4LA4kyE Adashen hijabin ƴan gayu ɗinkin ƴan kaduna kike so Hajiyata? Ga masoyiya, aminiyar da bata da tamka, Ummu inteesar kenan farar aniya laya. Ki shiga group ɗinta zaki samu yadukan hijabai ƴan gaske na kaduna, wanda zaki ta da taro. Kaduna sune Hijabi an bar musu kayansu. Ummu inteesar hijabs and more, mai adashen gata. Gaga gaga haka Mariya Habibu ta bamu nata labarin ya ƙare, zuchiyata fal da tunanuka. Nana Kabiru kuwa sai dai san barka. Lallai tana daga cikin matan da a duniyarta sai dai tace Alhamdulillahi. Allah ya azurtata da miji kamili, adali, mai mutumci, da dattijantaka. Mai bin koyarwar ma'aiki arrasul S A W, madallah dakai Ibrahim. Na jinjina maka, da kai da ire_iren maza natijajju kamarka dama waɗanda suka fika. Saudat ce tace. Allah yasa mu dace. Lallai Nana na jinjinama Ibrahim gaya. Kin samu sa'ar rayuwa. Domin farin ciki a gidan Aure shine duniyar ma'aurata." Murmusawa nayi tare da kallonsu nace. Ni labarin Mariya Habibu, da yadda ta dinga ƙona kanta danta haska al'umma. A wajen Hindu kuskurene babba. Yanzu wacce riba dai za'ace ta tsinta a zaman auren da tayi, in banda guzirin ciwuka, kana wannan suna da bata so lallai a kirata dashi, kalmar Bazawara, sai da ta amsata. To ni ina ganin mu daure mu dinga yin abu domin Allah, domin kanmu, domin gobenmu. Ba wai domin gudun maganganun al'umma ba. Kinga mutum? Allah ke iya mishi badai mutum ba. Duk yadda kike son ki burge, ko ki fahimtar baki isa an fahimceki rabi ba, dama duka bai samuwa. In dubu sun gamsu dake, dubu biyu da ɗari biyar basu gamsu ba, ya zaki yi da su waɗannan ɗin? Ga aure zaki kuma yi, nayi tunanin nutsuwa zaki yi ki gyara kusakurenki, ki gina rayuwarki, ko dan tsallake maimaita halin da kika shiga a gidajen aurarrakin naki. Ki duba Shanono yadda aure ya bata wuya. Yara nawa ta haifa kafinma ta koma karatu, kafin karatunma ai kinga kayan gwari take siyarwa a cikin gida tana kuma ciniki. Yanzu barista ce mai zaman kanta, yaranta duk sun yi Aure sai matasa biyu a gabanta kawai, mijinta Jega ya tsaya mata, suna rayuwarsu mai kyau. Ke me yasa ba zaki koya daga gareta ba, auren kika fi son ki kuma ne? Ni ina ganin ki huta, banda gaggawa" Ajjiyar zuchiya Mariya Habibu tayi. "To Hindu a hakan ai na gyara. Kuma ina ɗan sana'ar takalma da mayafai. Kuma babu laifi ina samu arziki gaskiya. Inaga zanci gaba da sana'ar. Kinsan Allah kona shiga makaranta, kaina ya riga yayi tsatsa, babu abinda zai iya shiga" To amman ki tabbatar kin koma Islamiyya, ai wannan kanki zai ɗauka. Dama ni bance lallai sai boko ba. Sannan wannan koke, koken Saudat, Mariya Habibu a rageshi dan Allah" Dariya suka yi dukkansu, ni kuma na jefesu da harara cikin sigar wasa. Saida na sauke ajjiyar zuchiya, kana nace. Allah ya dafa mana, ya kawo ma ko wacce mace farin ciki da nutsuwa a gidan aurenta. Amman akwai gyara da aiki jajawur a gabanmu, akan zamantakewar aurenmu. Kuma aure a arewa duk kwanan duniya mutuwa yake yi, ɗaura wasu akeyi. Komai da ka akeyi ba tare da neman ilimin abun ba. Musamman Aure, yana da kyau maza, da mata, ace su dinga zama a aji ana koya musu yadda ake aure a addinance, ba a al'adance ba. Kowa yasan hakkokin ɗan uwan rayuwarshi, Tunda ba kowa yake da ilimin da za'ace yasan tarihin ma'aiki arrasul s a w yadda yayi zamantakewa kamila, tsaftatatta, da iyalanshi ba. Da kuma koyan dabarun zama da mata, da musalai masu tarin yawa. Musulunci addinine na adalci wanda ba'a tauye komai ba, duk yadda muke tunanin canji da murɗewar zamani, da duk abinda ake ciki Qur'ani ya riga ya zo mana da komai, kuma komai yana faruwa daki_daki. Bafa da ka muke rayuwa ba, shi yasa ko wacce al'umma tana da manzo wato ɗan aike. Mu kuma aka aiko mana manzo, Annabi mafi girma da ƙololuwar daraja. Aka saurar mishi da littafi mafi girma da tsarki, shine annabi daya karɓo mana sallah. Allahu Akbar. Aure tafiyace mai tsayin da ake fata, burin mutuwa ce kaɗai ka iya rabawa. Ai kuwa shine a haƙƙu da aje aji a koyi iliminshi, a wajen masana. Wai wanne irin tunani a ƙwaƙwalenmu ne? Ko da yake jahilci da rashin wayewar addini, da wayewar rayuwa, da gogewa kusan shine wasila. Wallahi in bamu koma tafarkin koyarwa ma'aiki arrasul s a w ba yanzu muka soma shiga tasku. Dangane da makaruntun koyon auren, naga yanzu gaskiya babu laifi a nan kano akwaisu, naga Malama Zara'u tana da makatantar koyon yadda za'aiyi zaman aure da aji, na maza daban, na mata daban, ga koyon girki. Tana da gogewa sosai, kunsan itama tana daga cukin madubaina, shigarta ta lafaya irinta mrs Bukhari tana burgeni sosai. Akwai wata makarantar a Gombe wacce Anty A'A Nafaɗa tana daga cikin malaman makatantar. Tananan a cikin Taskar Badi'at Ibrahim anan ma in an gama littafi suna gabatar da shirye_shirye na gyaran aure da hulhu tsakanin ma'aurata. Ga Hajara Aliyu ( mamanmu Adala kamila) itama tana cikin malaman gyaran Auren. Sai mrs Bukhari itama tana ciki farar aniya laya kenan ( afwan amman ni ƴar koyo ce, yanzu ne nake ƙara faɗaɗa karatun zamantakewar, tare da risach mai zurfi akan zamantakewar aure, musamman na Arewa, a taya ni da adda'a domin Allah) Akwai Anty Zee musa kolektshon, mai kayan ƴan gayu, kama daga tufafi, kayan Kitchen, kayan jira_jirai komai akwaita. Itama malama ce cikin taskar Badiat. Muna da Maman Safwan, itama malamace, maman Muhseen, Ga Maman Inteesar, mai Hijaban matan manya in dai marsidi ne a bar miki kayanki, tana da gogewar rayuwa, gata da tsinkaye. Akwai Mum khairi itama malama ce nagartatta. Ga kuma Hajiya Nabila mrs Bash fara duma_duma, itama malama ce jajirtacciya, gogagga, mai hangen nesa sosai. Madallah da dukkanninsu, madallah da aiyukansu na alkhairi, Taskar Mrs Bukhari taskar Alkhairi. Gasu da Malama Maman muhibba, mace mai ilimin addini, da baiwar tsara zance. Saudat tace. "Wato Hindu ina girmama tunanin ki sosai, in dai aka zauna dake dole sai an ƙaru sosai. Zanso ace ina aiki tare dake. Dariya nayi sosai, ni a tsarina bani da sha'awar aikin haɗin guiwa, sai dai a taimakamun da abinda ya sauwaƙa, sai dai dole a tafiyar da nake son yi ina buƙatar mutane amintattu da zasu raka tafiyar gidauniyar matan da zan buɗe. Amman ace gundarin kuɗi, da sunan gidauniya, da komai na kuɗi, nafi so ni kaɗai na kasance akai, bawai ace namu bane, a'a nawa nake so ace mallakina. To Saudatu tunda ke lauya ce, ki zama lauyana mana, da kuma lauyar Gidauniyar da zan buɗe. Luba da su Habiba duk sai su taya ni aiki ai, kinga ita Mariya fuskarta a matsayinta na jaruma zai taimaka mana abun yaje inda zato ma bai zata ba. Amman mai kuka ce? Sai dai inaso in juya akalar abun ta hanyar tallafama mata da jarin da zasu ɗan dinga jujjuyawa, shine babban jigon Gidauniyar, sai basu shawarwarin yanda zasu san darajar kansu, da yadda zasu juya kuɗin sana'ar da zan ɗan dinga basu. In akayi musu wannan da kansu zasu iya tsayama kansu. Zan je Katsina wajen Maman muhibba mu tattauna ta ƙaramun kalan nasu dabarun yadda suke tallafin mata da jari, da yadda aka ɗaurasu a hanyar juya kuɗin. Sai dai kash ita a tim ɗin Mijinyawa take, sai dai abinda zai kaini dabanne" Take duk kowa ya amince da tayin da nayi mishi, mun tsaya akan zamu sake haɗuwa ta musamman, amman in sha Allah sai komai ya girma ya tsaya da ƙafafunshi tukunna. Tunda da kaɗan zan soma, ofishi zan kama da ba zai wuci ɗaya ba, da ma'aikata da basu wuce biyu zuwa uku ba. Komai kuma zai biyo baya a hankali in sha Allah. Da wannan muka tsaya akan sai wani lokacin in muka sake haɗuwa zan basu nawa labarin, tunda dai lokacin bai bamu wannan damar ba. Har wannan lokacin jama'ar gidan suna sunanan, sai dai raguwa da suka yi. Da dukkan alamu kishiyar Luba ƴar dangice sosai, duba da irin taron da akayi na suna. Sunusi kuwa yayi bajinta irinta kere sa'a. Sallar la'asar muka gabatar, kana muku sake cin jallof ɗin shinkafa mai hanta. Kafin mu fita Luba ta kaimu ɓarayin mai jego mu mata barka, mun shiga mun samu Sunusi a kan gado da yaran a hannunshi, yayi zaman daɓaro a tsakiyar gado, shi da maijego ankon shadda ce a jikinsu iri ɗaya sak, ga yayu da yannen maijego suna cin tuwon dare. Dan magriba a lokacin ta kusan kawo kai. Luba tayi kyau fiye da maijegon ma gaskiya, kuma lesirinta ya danne kuɗin shaddarsu, gezna ce ta tsakiyan suka ɗinka. "Ahh Hajiya Hindu kun fito kenan? " Idanu Luba ta ƙura mishi irin kallon Allah wadaran naka ya lalace ɗinnan. Wallahi ka ganmu mun fito shine muka ce bari mu ma maijego barka kafin mu tafi" Na faɗa kadaran kadahan. "Ayya ai kuwa nagode sosai. Maman Sadiq naga atampopi da kayan yara an gode. Yaya ku ma Maman Sadiq godiya" Cewar Amaryar Luba kenan data ƙarashe tana kallon ƴan uwanta. Tana wani magana taɓa_taɓa, tare da karkace baki gefe. "Ayya ai dama zamu shiga har ɓarayin mui mata godiya ma. Maman Sadiq muna godiya sosai wallahi kayan Tubarkallah. Allah ya kauda shaiɗan a tsakaninku." Nan suka soma godiya wannan ta ja ta cika ta ba wannan. Kuɗi na ƙirgo dubu goma sha biyar na ajjiye akan gadon. Gashi a siya musu ƙunzugu" Dukkanmu muka ajjiye mata kowa da nata. Nan suka sake kaurewa da godiya harda Sunusi fa yana cikin mata ƙaƙas haka muka fito. A waje ma mun jima muna ta faman hira, da ƙyar dai muka yakice mukai ma juna sallama na shiga motata na nufi gida. Ina jujjuya sitiyari amman ƙwaƙwalwata na jujjuya mini rayuwar su Saudat da Mariya, da irin dacen da Nana Kabiru tayi, a haka na isa gidan. Mijinyawa:. Yana tashi daga aiki ya juya akalar motarshi izuwa gidan Mijinyawa Babba, da tunanin acan zai ƙarashe ƴan kwanakin da suka rage mishi, kafin ya bar garinma baki ɗaya. Ya jima yana matsa hon, Mijinyawa Babba ne ya leƙo ta ƙaramar ƙofa. Ganin mijinyawane hakan yasa ya koma ciki. Kafin can mai gadi ya fito ta ƙaramar ƙofa. "Baban Azgar ashe kai ɗinne? " "Nine Yahuza buɗe mun in shiga daga ciki." Jim yayi kafin yace. "Wallahi bansan me zance maka ba ma. Yanzu haka motar ɗiban kayan ɓarayin Mamansu Azgar tana tsakar gidan kwashe kayan akeyi. Dama na ɓarayin ita Asama'u Nanno tasa an kwashe ba tun yanzu ba. Sannan ɗan uwanka ya bani umarnin karma in barka ka sake shiga. Dan Allah kayi haƙuri, nasan abun babu daɗi. Ni kaina abun yayi mun nauyi sosai, amman ya zanyi." Murmushi Mijinyawa yayi ma Yahuza. "Ai babu komai Yahuza. Ita rayuwa haka take. Babu matsala bari inje" "Ka tsaya yace dani ince maka zai fito. Au kama ganshi ya nufo mu" Ya nuna mishi Mijinyawa Babba da yake nufosu. Shiru yayi kawai, yana sake ƙarema ɗan uwan tagwaitakar nashi kallo, har ya iso gareshi, ya dafa tagar motar tare da zura kai ciki. "Ashe baka ji gargaɗina ba Magawata? Lallai ka ɗauka wasane, ai muddin Hindu matarka ce, ni da kai ya ƙare abadan. Uwatale har yanzu jinin daya taru a idanunta bai baje ba. Nanno yanzu bata iya takawa sai da sanda, Yaya Jamila kuwa jikinta har yanzu yaƙi daɗi. Sabida kaine ɗan daɗi Hindu, kace aljanunta ne suka yi, ba ita ba. Kawu ya goyi bayanka, ai shikenan ni dai na sallama. Nanno dai tace ta yafe maka, ba kuma zata yi maka baki ba. Amman muddin da ace bakina zai bika, wallahi saina lalataka da bakina, na tsinema albarka daga kai har zuriyarka." "Kace haka bama sabida kana baƙin ciki da samuna, ni da matata ba? Ban taɓa tunanin in kowa zai juya mun baya har dakai ba Nawata. Tur da Uwatale wacce ta zama wasila ta faruwar wannan tashin hankalin. Batun tsinemun da kake yi da zuriyata kuma, kash gashi ba kai bane ubana ba. Ni da kai duk haifarmu akayi. Kuma na gane girman hassadarka, kai da matar akanmu. Wato a ƙarƙashinka kaso muci gaba da rayuwarmu ko? Sai kaga Allah yayi mana liɗifi shine cutar hassadarka ta motsa, a baya ma bata motsa bane sabida a ƙarƙashin inuwar arzikinka muke. Ashe wannan ne dalilin da yasa duk sanda zan ma batun siyan fili, sai kace kai baka yadda ba, kai in faɗama in Uwatale ce tayi mana wani abun. Kai in ba zumunci zan yanke dakai ba in zauna tare dakai. Ashe duk ƙaryane, sha'awa kake yi ka ganmu muna ƙarƙashin alfarmarka. Kaji kunya ka yaudareni, kaci amanata. Amman Allah zai sakamun in sha Allah" Sun yi rikici da musayar kalamai masu zafi, da ɗaci sosai. Daga ƙarshe motar kayan Hindu ta fito a gidan. Kai tsaye Mijinyawa yace motar tabi bayanshi. Wajen ƴan kayi nayi masu shago ya kai kayan kawai. Nan kuwa suka yi siyan wulaƙanci sababbin kaya masu darajar gaske amman milliyan biyu kacal suka siya gabaki ɗaya. Bai ja da yawa ba, sabida ranshi a jagule suke, kayanma baya ko ƙaunar ya buɗe idanunshi ya gansu, sabida tunanin abubuwa da yawa. A akawunshi suka sanya mishi kuɗin, ya sallami masu mota, kai tsaye Hotel ya wuce, ya kama ɗaki ya shiga ya kwanta. Shiru yayi, dan a lokacin baya son hayaniyar komai da kowa. Jijiyar gefen kunnenshi aiki kawai take yi, ta kumbura ta cika, haka tai ta yi. Kunnuwanshi wani irin ƙara kawai suke yi mai, yayinda zuchiyarshi ke wani irin harbawa wanda ya wuce ƙa'ida. Idanunshi a lumshe suke rub. Gaga_gaga_gaga_gaga. Hindu:. Ko dana shiga gidan, banga Mijinyawa ba, bamma bi ta kai ba sam. To satin da muka shigannan dukka bamu zauna ba sabida bikin Salamatu. Kafin a ɗaura auren, naje ma da Innarmu da Baba sojanmu da maganar Mijin Salamatu, da sassafe naje gidan. Harma na haɗa Baba Sojanmu da mahaifin Jamila a waya suka zanta. Baba Sojanmu sai yace in bar mishi komai a hannunshi, shi dasu zai yi magana dasu. "Amman gaskiya bana so sunana, ko na Hindu ya fito, sabida Abida mummunar fassara zatai ma abun, fiye da yadda kake tunani. Ga danginka, da jama'ar biki fal gidannan, kaga fa abun ba kyau zai yi ba sam. Ni kuma bazan zauna a taka ni ba, da an faɗi cuta zan faɗi maganinta. Ni da ace Hindu dani tayi shawarar wannan lamarin da cewa zanyi abar Salamatu tayi aurenta kawai. Wannan maganar fitarta tamkar ƙaramin yaƙine na ƙasa da ƙasa, yadda suka cin buri akan angon da bikin" Baba Sojanmu yayi kurum yana nazari, can yace. "Ai bai dace ace Hindu taga matsalar da ka iya cutama ƴar uwarta taja baki tayi shiru ba. Nima kuma bazan saka sunanta a ciki ba. Salamatu ba yarinya bace, kana ba jahila bace da za'a nemeta ta baya ta amince ba, madamar a hayyacinta take. Sannan banji cewar za'a sanar mata da wannan lamarin ta amince da auren ba. Ni nawa faɗane kawai. Daga kan Hindu na dena matsin lamba akan aure, balle Salamatu shi hab a rait da cuzin wanda take so, islamikali ma tana da rait ai. Disishon na hannunta weda ta zaɓeshi inna mata bayani, o not. Don boda yo seib. Ke Hindu kinyi abinda ya dace, i will diskos wit Salamatu." Da haka na barsu dai. Amman ko da Baba Sojanmu ya kai zancen Innah Abinda ta hau ta dire tace Allah ya kasheta. Bai ja ba, sai ya cika, da sharaɗin duk abinda zai biyo baya da Salamatu babu hannunshi shi a ciki. Innah Abida, da Salamatu suka amince, shikenan zance kuwa ya mutu mus. ranar Juma'a aka ɗaura aurenta da safe, ƙofar gidanmu cike dam da maza a haka na kutso kai na shigo ban samu shigowa sassafe ba, kwana naso in yi ma a gidan to mata masu ƙorafine suka zo ɗayarma sabida nisa ga yanayin jikin ba lafiya anan ta kwana damu a ɗakin Sabira, da sassafe na kira Luba tazo suka wuce Asibiti ni kuma na nufi gida. Wai ƙannen mijine sukai mata duka, shima mijin daya dawo suka labarta mishi ƙarya da gaskiya, shikenan ya hau kai. Yana dawowa ya zare belet ya dinga narkarta, abunda zai tsorata ku wallahi jego take yi kwana biyu da yin suna. Akan naman suna wanda yake hakkinta akai mata irin wannan cin zarafin. Inata tunanin yadda zan yi da kes ɗin ita a yadda ta nuna danginshi ne basa ƙaunarta, kuma su suke zugashi yayi mata duk rashin mutumcin da yake yi. "Ahh Duwaf ashe ba a gidan kika kwana kamar sauran ƴan uwan naki ba? " Cewar Qazzafi. Kenan iyayen ƙoƙari a kan zumunci. Dake ni nayi baya dashi sosai. Kafinma in bashi amsa matarshi tazo ta wuce harda jan guntun tsakin da mu kaɗai zamu iya jinshi. Kishi ƙaƙas take yi dani, wallahi mamaki take bani, gashi har takwara yayi mun Hindu, Innah Mairamu ta dinga maganganu a tsakar gida sai da Baba Nagoɗi ya taka mata burki tukunna. Inason Qazzafin ita har ta isa ta sameshi, mutumin da har yanzu ga soyayyata nan a kwance a ruwan dake gulbin idanunshi? Mata a barsu wajen kishi, da zubar da daraja. Ban kwana ba hakan dai naso. Amman kana naka Allah yana nashi. Ya gida ya iyalan, duk da yanzu tazo ta wuce. Ina Hindu" Shiru yayi, yana so ya bani haƙuri sai ban bashi dama ba na bagarar da shirun ta hanyar cewa. Bari in shiga ciki nasan anata shirye_shiryen tafiya Katsina ta dikko ɗakin kara. Auran naga an ɗaura" "Anko ɗaura ai su Khadijanmu ma har sun wuce Katsinan, su kam tun asussuba sabida ƙarashe gyare_gyare. Takwararki ma ta bisu, ɗiyar Abbanta shalelenshi kuma ba. Ku je ku fito sai in kaiku, da dai ban wani yi niyyar zuwa ba gaskiya dan harna ce ma Madam ba zani ba" Wucewa ciki nayi ina tafe anata gaishe_gaishe sai kallona suke yi nasan sabida ɗinki, da ankon da muka yi ƴan ɗakinmu aketa mun wannan kallon, na ɗauki wanka iyakar wanka, iyakar man baki, da kwalli ban muttsuka hoda ko wacce iri ba. Amman sai mace ta kalleni ta kuma. Da sallama na shiga Falonmu dai _dai dangin mijin Salamatu sun fito da'ita. Ta sha ado na kecewa tayi kyau. Amman duk da haka sai kallon jakata da takalmina take yi dan tabbas yafi nata tsada a matsayinta na Amarya. Ina ganin sanda ta taɓe baki ina gaisawa da dangin Baba Sojanmu. Innarmu ce ta fito cikin wani farin lesiri mai adon ruwan zuma, ta ɗanɗasa kyau tamkar ba ita ta haifemu ba, gashi ta mugun iya ɗauri ya zauna tamkar ta kafa hula. "Toh Hajiya Rahila mu jenku na kammala. Ke Hindu muje su Saratu suna ɓarayin Babanku Dogara." Fitowa muka yi yuuu tare da tawagar Amarya zuwa ƙofar gida. A can na hango su Yaya Zubaina da Yaya Sojanmu, da su Rayya, suna tsaye anata tauna zance harda Qazzafi dake shi gaskiya yafi sabawa da ƴan ɗakinmu sama da kowa, a dandamalin ɗakin Innarmu yayi dafdalar ƙuruciyarshi tas. Dana soma tasawa, sai sonshi da ɓarayinmu ya ƙaru. Duk abinda Qazzafi ya samo na Hindu ne. Ina tuno lokacin da zai tafi aikin soja irin sallamar da muka yi dashi. Shi kam ma sai da idanunshi suka cika tab da ruwa. Innah Mairamu ce ta ruguza komai, duk da ni soyayyar ƴan uwanta nake ma Qazzafi, bashi a tsarin kalan mazan da ni Hindu nake so. Amman daga baya, bayan nayi aure saiya fahimci shi bashi da abinda ni yake ganin shi nake so. Sai yayi ƙoƙari ya dinga cin ƙarfe har sai da ƙirjinshi ya buɗe ya haye sama him, duk da yasan fa ya rasani. "Hindu da mota zaki je, ko a gida zaki barta? " A gida zan barta katsina ba nan kusa ba gaskiya." Ina kallon Yaya Soja, na miƙa ma Azgar da ƙarasowarsu kenan kin motar. Ke Sabira kizo muje tunda Innarmu ma da'ita za'aje" "Qazzafi ai sai ka kaisu a motarka. Ni zan ɗauki madam da yara, Sabira tazo muje zata fi sakewa a motata tunda akwai sa'arta." "Ammi nima inaso inje ai sai in rage mutane" Ya ƙarashe yana susar kai. Yaya Saratu tace. "Ki barshi tunda dai shi yaji zai iya. Ga su Shafa'atu can bari in kirasu ya tafi dasu. Ku kuma su Jinjin ku shiga muje a motar Qazzafi. Ai kuwa hakan Akayi nice ma a gaba a motar Qazzafi. Azgar kuma ya ɗauki su Khadijan Baba Alƙali dasu Shafa'atun lungun Baba Lukumanu, da Batulu ɗiyar Yaya Zubaina. Motar Azgar na gaba muna biye da'ita a cikin tawagar ƴan kai amarya kusan mota goma sha uku ni dai a iyakar ganina, kuma ko wacce ta cika, wasu ƴan gida ma basu samu zuwa ba. "Hindu saina tuno wata tafiya da muka yi da Baba Sojanmu zuwa kwantagora lokacin da Kawu Gwani ya rasu. Muna tafe Baba Sojanmu na sissiya mana kayan ciye_ciye na hanya." Dariya na tuntsure dashi nace. Harma muka tsaya a wani gari haka ya siya mana kaza ƙatuwa mu mu uku da ni da kai da jinjin. Su Yaya Saratu kuma suna cikin motar Yaya soja. Wallahi ban mance ba kazarnan tayi daɗi sosai. Dariya muka tuntsure dashi dukkanmu Yaya Saratu tace. "Ai tun kuna yara sosai ake zuwa damu wajen kazarnan. Tumma bamu dawo Kano ba a lokacin Baba Sojanmu yana maiduguri sai dai mu kawo ziyara nan gida Kano wajen su Innah Abida, ku su Hindu kuna yara lokacin. Lokacin bana mancewa in muka zo yaran gidannan suita zuwa kallonmu hadda Qazzafi fa yadda kuka san nama. Dake gaskiya Innarmu akwai kashema yaro kuɗi. A lokacin wani zuwanne aka zo Hindu lokacin tana da shekaru huɗu dawowar da muka yi kenan Baba Sojanmu yace mu zauna lokacin an turasu wani daji na tsawon lokaci. Qazzafi yaita hidima da Hindu duk kuɗin taranshi akan Duwaf ya ƙare. Alewar madara, kafi tsire, yashin madina sune abubuwan da Duwaf tafi so. In rigima yaga tana yi Innarmu ta doketa duk ya fita hayyacinshi ya addabi kanshi. Allah sarki a gaskiya Qazzafi ya so Duwaf, dake Allah ya ƙaddari ba matarshi bace shi yayi aurenshi itama haka" Yaya Zubaina ce ta cabke suka ci gaba. Qazzafi kallo ɗaya yayi mun naga idanunshi har launi suka sauya, an fama mishi babban miki, wallahi shi yasa sam bana son muna haɗuwa dashi, sabida irin halin da yake tsintar kanshi a ciki. Matarshi ma na ta kiran wayarshi ina bai samu zarafin amsawa ba. Juyawa nayi mukaita sheƙa hirarmu da tuno irin tafiye_ tafiyen da muka sha daga wannan barikin zuwa wannan barikin. Daga haihuwa ta dai tafiyar ta kusan ƙarewa sai dai Innarmu takan je wajen Baba sojanmu tayi hutu in an yi hutun ƴan makaranta. Innah Abida ta dinga faɗa kenan tana aibata Innarmu. Itafa bai taɓa damunta ba, ba ita ta zauna ba sai da ta Haifi Rayya tukunna. Lokacin Innah Turai bata zo ba. Da Auren Innnah Turai da Ritayarshi shekara uku Adamawa aka turasu anan ya gano ƴar fillo, sai ganinshi Akayi da mata da cikinta na wata biyu ni a lokacin mun dawo Kano ni da Gawata da zama in ban mance ba. Allah komai mai wucewa ne a rayuwa. An sha dambarwa da Innah Abida. Innarmu kuwa ko ta kula, kuma wallahi tafi Innah Abida kishi akan Baba Sojanmu. Tafiya mukaita tiƙa har dai Qazzafi ya tsaya a wani gari ya sai mana balango lafiyayyen gaske da masa. Mijinyawa sai kiran wayata dake ajjiye a jikina yake yi, bana ko kulawa naman nake ci ina jin daɗinshi gaya. Ƙarfe biyu muka shiga cikin garin katsina Unguwar Yari Ƙofar soro. Idan ana maganar masu kuɗi na sarauta, gadon gida, tsofaffin ƴan kasuwa na gargajiya, wannan yankin shine gaba_gaba. Unguwar Yari tana ɗaya daga cikin tsofaffin unguwanni na asali dake yammacin cikin birnin katsina ta dikko ɗakin kara. Unguwace mai dogon tarihin gaske sabida yana da alaƙa da lokacin mulkin sarautar Fulani ( Dallazawa) da kuma farkon mulkin turawa. An kafa unguwarne kusa da gidan yari na garin, inda manyan bayin sarki da masu riƙe da madafun iko ( kamar wazirin katsina na da) da suka gina gidajensu na Alfarma a lokacin. Misali manyan mutane kamar mahaifin shahararren attajirin nan Dr. Lema jibril. Dama tsofaffin janar_janar na soja suna da tushe a wannan yanki har ila yau Kusancinta da fadar sarkin katsina ( gidan korau) wanda aka gina tun ƙarni na goma sha huɗu hakan yasa ya zama babban mazaunin masu daraja da dukiyar gado A wannan unguwa ƙarƙashin wani babban gida mai kyau Salamatu zata zauna. Ba sabo bane gidan ginine irin na masu kuɗin da, gidan akwai yalwar tsakar gida da shuke_shuke masu tarin yawa gaskiya, duk jama'ar biki muka fito muna kallon gidan gamu da yawan gaske wasu motocin ma suna waje basu shigo ba, mata ne dai suke shigowa. Haka muka ɗunguma zuwa cikin ta wata ƙofa babba data sadamu da falon Salamatu. Nan muka tadda dangin mijinta, da su khadijan gidanmu, ƴan gidanmu dai su biyar harda Innar su Dije matar Baba dogaranmu kenan. Mu dai a falo muka ya da zango, Amarya kuma su Innarmu sukai ciki da'ita gida kam tubarkallah. Nan akai mana saukar girma ta manya, munga karamci gaskiya babu laifi asuwaki mukaita yi da kaji. Da daddare akayi Dinner mai nutsuwa ta macuwat mutane.. A gajiye tulus muka dawo gidan amarya wajajen sha biyun dare sai bacci Washegari na farka na tadda kiran Luba kusan sau bakwai. Ina kan sallaya nan inda na idar da sallah a ɗakin Salamatu na manta wayar. Luba Allah yasa lafiya, wallahi nace zan kiraki in muka dawo daga Dinne nadawo a gajiye. Ya mai jikin to amman kaddai jikinne" "Hmmm wallahi Hindu jikinne ko kinsan yarinyar nan abu kamar wasa a asibiti muka kwana. Idanunta ɗaya ya samu matsala gani ma bata yi a sakamakon naushin da yayi mata. Sunce dai in akayi mata aiki akwai yiwuwar ganinta ya dawo. Ɗayanma bata gani da kyau fa. Ni kam gaskiya Hindu ki makashi a kotu ya saketa kawai. Tunda tace ta haƙura da Auren har abada". Ajjiyar zuchiya na sauke tare da ambaton Hmm maza kenan. Shikenan Luba yau zamu dawo da wuri muna karyawa. Duk abinda ke akwai zamu yi magana. Zan yi magana da saudat ma ta shiga lamarin in yaso sai a tsayar dashi a kotu in yaƙi sakinta ta laluma. In kuma ya saketa zamu rabu dashi da halinshi, duniya zata yi mai karatu. Amman fa sai da yadda da amincewar iyayenta, da ma danginta. In babu amincewar wasu daga cikin danginta, luba haka zan tsame hannuna, in nema mata lafiya ta koma ɗakin aurenta ato. Ita baiwar Allahn ta na sana'a ko aiki ne? "Tana koyarwa a makarantar firamare da dibloma. Nata kinga bazai bamu wuya ba zata iya kulawa da rayuwarta. In ta samu tayi digiri ma kinga shikenan zata nemi wani aikin. Ta jingine auren agefe a yanzu ta maida hankali akan aikinta, da saita shiga makaranta da izinin Allah miji nagari zai zo ya aureta a lokacin itama tana da madafa. Zaluncin yayi yawa. Ba yau ya saba dukanta ba, har sumar da'ita ashe yake yi, to gashi yayi mata sanadin ido ɗaya, dan wannan ido da ƙyar zai yi aiki gaskiya. Gaba inta koma ba'asan me zai mata ba kuma. Macen da bata da madafa ke fakewa da zaman ƴaƴa. Kinsan Allah talaucine yawanci da rashin sanin inda za'a dosa. Ba ilimi, ba sana'a, ba aiki ba dole a zauna zaman yara ba. Yana lasa mata abinci yana zaginta ya zagi ahalinta. Tana ji tana kallo an maidata juji, an jingineta ana soyayya da wata matar. Hmmm Luba sai mun iso asibitin zan wuto kai tsaye, kafinnann Saudat zata zo." Da haka mukai sallama. Nan aka soma gaishe_gaishe da juna a falo kuma su Yaya Soja da Azgar da Qazzafi ina jiyo muryoyinsu. Su Yaya Saratu da su Jinjin anata raba kayan kari da aka aiko daga gidan iyayen miji dake saman layin da gidan salamatu yake. Zuwa tara mun gama komai har mun shisshiga mota Salamatu da mijinta sunata ɗaga mana hannu har muka fice a jere a gidan. Ni kuwa sai kallonsu nake yi ina mayawa. Haka kurum nake ganin tamkar ganina da Salamatu na ƙarshe kenan wallahi. Ƙarfe ɗaya muka shiga gida, kowa a gajiye yake ga gidan cike da baƙi musamman ɓarayinmu, ni inayin sallah ma na tarkace yaran suka kaini asibiti wajen Luba anan na tarar da labarin wai mijin Kaltume ya saketa ta waya ya turo da sakin. Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Duk da haka ya kamata kamar mu tsaya a kotu dashi sabida lafiyar idanunta bai dace ace sunci bulus ba Luba. Luba abun yayi yawa" Wallahi haka akayi muka maka mijin Kaltume a kotu dake mun tattara hujjoji ƙwarara kuma mun haɗu da ƙwararriyar lauya da alƙali adali. Zama uku akayi kacal shari'ar ta ƙare. Shi zai ɗauki nauyin komai na asibitin ta, sannan in akayi aikin idonta bai buɗe ba za'a hukuntashi hukunci mai tsauri harda ƴan uwan nashi ma. Bayan mun fito kotu iyayenta sukaita mun godiya mamanta har tana kuka dan jin daɗi. Ranar da aka saka na aikin ya zagayo ban bar asibiti ba har saida aka fito da'ita. Dr kuma ya nemi ganawa dani, naje na taddashi a ofishin shi, ya nuna mun waje na zauna. "Hajiya Hindu an yi aiki dai muna fatan ta samu lafiyar gani in sha Allah. Duk da dai dole zai kasance mai raunin gani sosai, da rashin jure haske mai ƙarfi. Nan da kwana bakwai zamu buɗe bandejin in sha Allah, mu ga yanayin aikin muna fatan samun nasara. Amman nace faɗuwa tayi ne ko kuma garin yaya hakan ta faru? " Garin zaluncin wasu maza, azzaluman maza inji Lubna michika. Ka ganta mijinta da danginshine suka naɗa mata na jaki gata nan dai ka ji ka kuma gani ai" Shi kanshi ji nayi na tsaneshi, ai shi kanshi ma ya gane hakan shi yasa yayi muƙus da bakinshi. Gaga_gaga haka dai Barira sati ya zagayo aka warware idanunnan wallahi ya mutu fa bata gani saida ɗaya dishi dishi shi ɗinma take gani, amman an yanka mata tabarau da kuma bata magunguna, harma da sake saka ranar sabon aikin da za'a kuma jarabawa. Ina rufe wannan kes sai ga sabon kes na wata mata Haule wacce miji garin neman matan banza ya kwasa mata ciwon sida wata ƙanjamau HIV. Tazo da safe ranar asabar muna gida dukkanmu mijinyawane ya buɗe mata ƙofa ta shigo. Da safen yazo wai yazo ganin yaranshi, kamar wasu masu shan mama, tana falo tana jirana Azgar kuma yana ta haɗa musu kayan tafiyarsu gobene tafiyar, inaji mijinyawa na ambaton sassafe zasu tafi, yana waya da Qasimu. Shine dalilin zuwan nashi, zai taimaka ma yaran su harhaɗe kayansu waje guda, washegari kuma su kama hanyar katsina. Ni kuma in yi firi. Mrs Bukhari To mu kwana anan sai kuma gobe in Allah ya kaimu.TSUREN TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA ASHIRIN DA BIYU (22) Da sallama na shiga na sameta a gurfane tana sharar hawaye. Shekarunta a ido ba zata wuce shekaru arba'in haka ba dai. Ga wata ƴar takadda a hannunta. Waje na samu na zauna muka gaisa. To gani nasan zai yi wuya ace lafiyace zata sa ki dogo irin wannan muƙu_muƙun sammakon. Ina saurarenki" Na ƙarashe maganar ta ƙarshe haɗe da jan numfashi. Tun jiya gabana yake faɗuwa, a kan dadduma na kusan kwana ina sallah, da yin salatin ma'aiki Arrasul s a w, kan ya sassautamun, ya cire mun kewa, ko jin ƙulafacin yarannan da zasu tafi a zuchiyata. Na ɗaga hannu nace da Ubangiji na. Allah kana gani ni akaima laifi, kuma nayi haƙuri. Allah duk macen kirki biyayya dole ne a gareta taima mijinta, Allah kai ka haliccemu, ka yomu jinsi biyu. Allah kai ka ce muyi Aure domin bin sunnar ma'aiki arrasul s a w. Allah kai kasan dalilin da yasa ka sanya saki a tsakankaninmu. Kuma aurenma ya kasance ba dole ba, madamar mace ko na namiji, zasu iya riƙe kansu ba tare da sun aikata zina ba. Allah kai mai adalcine baka son azzalumi, Allah kana gani bazan taɓa iya ci gaba da zama Mijnyawa ba, bazan taɓa iya sonshi a karo na biyu ba, bazan yarda dashi ba. Ya Allah kana ganinshi yanaso ya ruguzamun rayuwata, ta hanyar rabani da ƴaƴana. Allah ka bani haƙurim rasasu da zanyi, Allah ka ƙara ƙarfafamun zuchiyata kasa kar in raunata. Allah kai musu albarka, ka sadasu da mutanen arziki ya Allah" Nayi adda'ar da bansan iyakarsu ba. Muryar baiwar Allahn dake gabane ya dawo dani daga dogon zango dana tafi. "Anty haƙiƙa na zalunci kaina, na cuci ƴaƴana, gashi rayuwata tazo ƙarshe shikenan." Kaico, me ya faru da har kike yanke tsammani da ci gaban ruwaya? Tsanani ba mutuwa bane. Faɗuwa ba yana nufin gazawa bane, jarabawace daga Allah, in kikai tawakkali in Allah ya tashi ɗagaki zaki yi tsaiwar da babu mai iya kai ki ƙasa. Duk abinda kika ga rayuwa ta baki, ɗaukeshi a matsayin jarabawa, ko ƙaddara. Kinga wannan biyun? Sune abokan tafiyar rayuwa, dole dasu muke rayuwa" Kuka ta fashe dashi na raɗaɗin abinda ke mata zugi a ruhinta. Shiru nayi ina lumshe idanuna gabana yana ci gaba da tsananta bugu, yarane sune rayuwata amman bana jin mijinyawa zai karyani ya tanƙwarani ta hanyar amfani da yarana. Nayi imani da Allah yayi ne kawai domin ya tilastamun binshi Katsina. Hmmmm maza da yawan san kansu shi ne matsalarsu. "Anty na jima da sanin mijina yana biyar matan banza na kama a waya. Abun tashin hankalin shine yadda naga mata da yawa da yakemu'amala dasu, da yadda yake biyansu kuɗin zunuban nasu. Babban kuskuren da nayi shine rasa tudun dafawa, da tuno makomata data ƴaƴana. Anty ban rasa duk wani jin daɗin rayuwa ba a gidan mijina ba. Ina samun ci sau uku a rana, kuma ko abinci ba nama bana ci. Sutura ta alfarma inna shiga cikin matan abokai nasan ba'a fini gata ba. Gidana mai kyaune, yarana suna karatu mai kyau. Naso daya aureni tun kan nayi haihuwar fari in koma makaranta, sai ya nuna mun baya sha'awar macen da tayi digiri, sabida buɗewar idanu. Dalilin da yassa ya auroni kenan. Masu digiri ɗin nemanshi suke ya auresu yaƙi. Na haƙura, sai nace zanyi sana'a bayan na haifi ɗiyata ta fari har ina da cikin ta biyu. To nan ya dinga mun faɗan wai zan zubar mishi da mutumcinshi, da kamarshi, ace matarshi na siye da siyarwa." Majina ta ja sama idanunta kaca_kaca da hawaye. Saida ta saisaita kanta ta ɗaura cewa. "Anty kasancewar nasan bani da gata kuma gani a cikin rufin asiri. Yasa dana kamashi a waya da ƴan matanshi na kasa magana. Shi ban tunkareshi ba, a gida ban kai kukana ba. Ƙawata dana faɗa mata sai cewa tayi ita mijinta da maƙociyarsu bazawara ta kamashi a kan gadonta. Amman tana zaune sabida bata da inda zata je, kuma inta rabu dashi ƴaƴanta fa. Hmmm shawararta nabi na ja bakina nayi kurum Anty, sai na dinga tashi ina mishi adda'a, duk na rame na fita hayyacina. A sanadiyyar damuwar dana shiga da rashin baccin da nake fama dashi na kusan shekaru uku cur, dan na kamashi lokacin da ciki a jikina, harna haihu shekara biyu na yaye na samu wani cikin na haife. Ina dakon baƙin ciki, na kusan shekaru shidda. Kwatsam ciwo yaita cina, inata sunturin asibiti jiki yaƙi daɗi to jiya dai aka tabbatarmun ina ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato cida, ƙanjamau, HIV Anty." Ai sai kuka ya kubce mata tai ta rabzarshi, har saida mijinyawa ya bar abinda yake yi ya leƙo. Ni nayi jigum na tusata a gaba. Ita tana zaune ta cusa kanta a tsakankanin cinyoyinta kawai kukan fitar rai take yi mai zugi. "Hindu lafiya take irin wannan kukan? " Wani mugun kallo na bishi dashi wanda wallahi saida na hango ɗan tsoro a fuskarshi. Lamarin shi da Asamu'u ya dawo ɗanye. Kunsan dai tashin miki tsoho yafi sabon miji zugi, dama wuyar sha'ani. Sai naji numfashina har wani karkatsewa yake yi. In buɗe baki inyi magana na kasa, ji nake uwa in nayi magana mutuwa zan. Wucewa yayi babu guiwa, nabi bayanshi da hararar baƙin ciki. Kinga kuka duk ba naki bane. Amman kinyi kuskure irin kuskuren da nake ji tamkar in rufeki da duka ko zan huce. " Miƙewa nayi tsaye naje na kulle ƙofar falon na shiga zagayawa hannayena goye a bayana. Sabida baki da tudun dafawa kika zauna da miji mazinaci, har yaje ya kwaso cuta ya kwasa miki kina ji kina gani, ke ba ƴar iska ba, ke ba komai ba. Sabida ana baki ci da sha da tufafi mai tsada ko? Wannan duk abubuwan da kika lissafo ba hajja bane na ki zauna da miji mazinaci, kuma kinsan mazinacine ba. Ba gara ya sakeki, dangi da iyaye su ƙi ki ba, amman kina da lafiyarki. Kinsan matsayin lafiya da arzikin lafiya kuwa? Kin zauna kin kamu da hawan jini, kin samu cutar ƙanjamau, kuma gashi a yanzu na tabbatar sakin kike nema, wanda a baya ya kamata ki nema da lafiyarki. Wai mata me muka ɗauki zawarci, da mutuwar aurene? Shikenan su maza duk kwaɗon da suka daka haka mata zasu shanye. Ko sun ƙi ko sunso ne. Me yasa muke kashe rayuwarmu, sabida makomar yaran da ke idoce a tarbiyyarsu kawai, shiriya kuma a hannun Allah take. In kika faɗi kika mutu shin kinsan yar'dda zasu rayu ne? Cikin faɗa nake maganganuna, ina jin matarnan kamar wani ɓangarene ita na jikina, ina jin makamancin irin zafin da take ji a ƙirjinta. Sassauta muryata nayi tare da cewa. Yanzu ga abinda kika samu a sakamakon haƙurinki, cikuwa biyu masu durƙushe rayuwa. Bance Allah ba zai saka miki, ko ya duba miki akan haƙurinki, ko zaluntarki da akayi bane ba. Amman wannan ƙaddarar kusan ke kika gaiyatota, da a lokacin da abun ya faru kin nemi sakin ki, kin kuma sa a zuchiyarki zaki fita kina da yaƙinin Allah zai miki mafitar da ya fi miki wannan baiwar Allah. Nayi mamakin ƙawarki data baki wannan gurguwar shawarar, kuma itama ta zauna da mijin data kama da mace a gadonta. Mun mayar da kawunanmu dabbobi, jahilci, da ƙauyanci yana farautar rayuwarmu, ya subhanallahi. To yanzu me kike so in miki? " Na faɗa muryata a maƙoshi, tare da neman wajen zama na zauna. "Shawara nake nema dan Allah ya zanyi. Ji nake yi na tsani kaina" Ai dole ki tsani kanki, shawarata kai tsaye shine ki nemi lafiyarki kawai. Domin a wannan gaɓar sakin bazai miki mafita ba. Amman mudding kika ci gaba da zaman to zaki iya mutuwa lokacinki bai ma yi ba, sabida baƙin ciki. Duk macen data kana mijinta yanaa zina ita da jin sanyi in dai a zuchiyane to har abada. Ko da rabuwar akayi kuwa, abun zai ci gaba da bijiro mata. Da za'a buɗe miki zuchiyoyin da yawa_yawan mata, da kinga mikin zinar mazajenshi cunkushe a ciki. A halin da ake ciki da yawa _yawan maza mazinata ne. Banfa ce duka ba bare a sanya mun jakar tsaba aita caccaka. Nasaan me nake yi sarai, kuma da ilimina, nasan duk yadda al'umma ta kai da lalacewa akwai nagari a cikinta. Musulunci bai yadda kayi kuɗin goro kace al'umma kaza dukka masu laifine ba. Ki nemi takaddarki ya sakeki in kina ganin haka kike so, amman ni banga amfanin rabuwar ba a wannan gaɓar da kuka kai ba. Ciwo dai ya shafa miki, ki haƙura ku ƙarashe juna kawa. ki mayar da kanki a kan shan magani, da zuwa asibiti akai_akai. Ciwon Sida ba ƙarshen rayuwa bane baiwar Allah, sannan duk tsanani sauƙi na bayanshi. Zan rubuta miki addu'o'in kije ki durfafesu, sannan in so samu ne a rana kiyi istigifari dubu, in zaki iya fin haka kiyi wannan sirrinane, zaki ga yadda rayuwarki zata sauya. Duk abinda kike buƙata zaki iya zuwa ki sameni. Sannan zan tallafa miki da jarin da zaki ɗan godara da kanki. Amman kiyi haƙuri ƙila har iyayenki su nuna miki ƙyama sabida lalurarki, amman in kika daure zai zama labari" Mun daɗe ina bata magana, ban barta ba saida ta karya ta huta, kana na bata dubu goma nace ta tafi gida. Alhamdulillahi a kullum ina godema Allah daya bani baiwar iya magana, da bada shawarwarin da al'umma suke amfanuwa dashi. Gani face_face cikin damuwa, amman gashi wannan baiwar Allah na sa ta fita harda musmushi a fuskarta duk da nauyin ƙirjinta. Wucewa ciki nayi, ina ji su Mijinyawa suna ta ɓuruntu, yana ɗakin Sabira ƙila taya ta haɗa kaya yake yi ohon mishi dai. Haka ranar na wuni tuntunini akan lalacewar wasu mazan da zinace_zinacennan da ya zame mana bala'i, tarbiyya ta lalace, na rasa daga ina aka samu gazawa daga iyaye mazanne, ko daga iyaye matanne, ko gwammatice, koko dattijan unguwane? Mu faɗama gaskiya matsalar daga tushe take tun farkon fari, a tarbiyyane matsalar, sai kuma wajen zaɓan miji ko matar auren. Ai tunda mukai watsi da koyarwar ma'aiki Arrasul S A W to matsala ma bamu ga komai ba gaskiya. Wajajen la'asar ina zaune ina shan magani, zazzaɓine naji yana tasomun tun azahar da nayi wanka, gashi naji sai ƙaruwa yake yi. Yawun bakina in banda ɗaci babu abinda yake yi, ko abincin rana na kasa ci, yadda Sabira ta ajjiyeshi gashi nan ban ko buɗe ba. Azgar ne yake doko mun sallama daga dokin ƙofa can.. A hankali na tashi na nufi ƙofar nasa hannu na buɗe. "Ammi wai kizo inji Kawu Qasimu suna falo" Kai kawai na gyaɗa mishi na koma. Sai nake ji kamar muryar mace bansan ko kunnena bane. Saida na isa falon naga ashe Baraka ce. Ganinta yasa na saki fuskata tare da shiga da sallamata. Na nemi waje na zauna duk aka gaggaisa. "Hindu Tutar so. Gamu a karo na barkate mun sake zuwa, amman wannan shine karo na ƙarshe in sha Allah. Haƙurin dai muka yo tattaki mu sake bayarwa. Hindu mutumin da duk kika ji anata nacin bashi haƙuri, ko ya sani ko bai sani ba to an cuceshi ne" Qasimu kafin kace komai inaso kai da shi in muku tambaya ɗaya tak" Dum yayi yana kallona ya kasa magana. Mutuminku kuwa ko kanshi bai ɗaga ba tunma dana zauna. Sai cika yake yana babbatsewa. "To muna saurarenki" Ace kaine da Baraka ka ɗakko ɗa namiji ka bata ta raina, sai da yaronnan ya girma sai ka gane Baraka na kwanciya dashi, kuma har tana cewa yanzu ta san namiji, yanzune ta haɗu da jarimi... " "'A'uzubillahi minalshaiɗanunrajin. Hindu wannan wanne irin kwatancene kuma mai muni, mafi girma? " Au da girma tambayar, ko kwatancen, sannan me yasa? " "Hindu in sha Allah na zare hannayena akan lamarinki da Gawata. Ki mun adalci kar kiga kamar ko ina goyon bayan Gawatane akan kuskure ɗaya tak daya aikata miki ba. Ga Baraka nan ta zame mun shaida Hindu" Murmushin nasara nayi kawai na dawo da idanuna kan Baraka. "Hindu wallahi Qasimu kullum a bayanki yake ba bayan mijinyawa ba. Mu babban abinda muke hange shine yanzu duk wannan faɗi tashin da irin sadaukarwarku ga junanku, a haka labarim wannan soyayyar zata tsaya, to menene makomar yara da yace dasu zai tafi, kuma ba zai sake dawowa ba, makomar karatunsu fa? Hindu ki duba lamarinnan da kyau ku daure. Ki yafe ma Mijinyawa dan Allah ki yafe mishi" Baraka kenan. Ba ko wanne labarin soyayya yake samun ƙarshe mai daɗi ba. Da in zauna in shiga wuta ta dalilin na kasa sauke haƙƙoƙin auren da suka rataya a wuyana, da mu rabu kowa yayi rayuwa cikin aminci fa? Yara da kike magana akai sun girma Azgar ya samu matar Aure, ita kanta Sabira damace bamu bata ba da yanzu tana da tsayayye. A kansu kike magana me to ya rage na tarbiyyarsu da banyi ba. Karatunsu kuma mahaifinsu zaka tambaya? Qasimu ka ba abokinka umarni ya sauwaƙemun kafin ya tafi. In ba haka ba duk inda yake sai mun yi shari'a wallahi dashi. Baraka zo mu shiga daga ciki" Qasimu muryarshi a dashe na tashin hankali da rashin tsumi bare wata dabara yace. "Zai sauwaƙe miki kafin ya tafi Hindu, kiyi haƙuri wallahi an baƙanta miki, an miki ba daidai ba. Dole ai miki uziri. Ta yiwu wani rabon ke kiranki a wani gidan. Ta yiwu hakan yasa a gaba ku dawo da aurenku ku gudanar da rayuwa mai kyau, kuƙarashe abinda kuka soma. Ai shi tuni ya haƙura. Ko wannan zuwa nawa ne ba nashi ba. Kuma sai da yayi, yayi damu kar mu sake tunkararki da maganar, nine nace aa tunda munzo zamu yi maganar. Amman Hindu wannan yafiya wacce irice kika yi ne. In an yafe ai sai a yi haƙuri ace gaba da zama ko? " Ai ina wuta Magawata naku yasa Qasimu sai ya dira a wuyanshi da faɗa. "A yanzu bana buƙatar Hindu cikin rayuwata, kamar yadda bata buƙatata. Kada kiyi zaton ni na turosu, gaban kansu suka yi. Daga gobe kin gama sakamu cikin idanunki gaba da abadan. Zaki gane bake kaɗai kika iya taurin kai da zafin kai ba. Inna murɗe babu mai iya juyo dani" Ni wallahi dariya ma ya bani, na ɗan dara kaɗan. Kafin na kalli Qasimu nace. Bari in baku hadisi ingantacce. (a cikin Sahih al-Bukhari 4072) cewa lokacin da Wahshi ibn Harb ya zo wurin Manzon Allah (SAW) ya karbi Musulunci. Wahshi shine bawa mai neman ƴanci ido a rufe, wanda Hindu tayi amfani dashi wajen kashe sayyadina Hamza. Manzon Allah ya yafe masa (ba'a bashi hukunci, ko a zartar masa da wani mummunan nufi ba. Saboda Musulunci yana shafe abin da ya gabace shi) Amma Manzon Allah S A W ya ce da shi. "Shin zaka iya boye mini fuskarka? wato ka rika yin nesa dani" Dalili Ganin Wahshi yana ta da tsananin bakin ciki da kuma tunatar da Manzon Allah (SAW) kisan shahidi Hamza ibn Abdul-Muttalib (RA), wanda yake shi ne kawun Annabi kuma wanda yake ƙauna a zuciyarsa sosai. Halayyar Annabi (SAW) Wannan bai nuna cewa Manzon Allah (SAW) bai yafe masa ba ko ya ƙi amincewa da musuluncinsa ba, a'a, kawai tsantsar raunin dan Adam ne da kuma radadin da zuciya ke ji a duk lokacin da aka tuna wanda aka Fi so da aka rasa. Bayan Haka Daga baya Wahshi (RA) ya rayu yana kokarin fanshe kansa da aikata alheri a tafarkin Musulunci, har ma ya kashe Musailama Al-Kadhdhab (makaryacin da ya yi ikirarin Annabta bayan rasuwar Annabi) a yakin Yamama, inda yake cewa ya kashe mafificin mutane (Hamza) a lokacin jahiliyya, kuma ya kashe miyagun mutane (Musailama) a lokacin Musulunci. Wannan kaɗai ya isa ku gane cewar, yafiya daban, ci gaba da zama daban. Wannan hujjar ina fatan ta fito ai? " Bance komai ba na fito, Baraka na biye dani a baya har zuwa ɗakin Sabira, tana gaban akwati tana dannawa, ga jakunkuna biyu duk ta gama cikawa ta rufesu. Sabira kije ɗakina ki zauna. Amman kafinnan ki kawo ma Baraka abinci taci. "To Amminmu muma haka zamu dawo cewa kamar yadda kuke cewa Innarmu" Dariya kawai muka yi da Baraka, itama ta fita tana dariya. Kai Baraka ta girgiza tace. "Da dukkan alamu yarannan basu san dawar garin ba, naga fuskokinsu ɗauke da jin daɗi. Ko yaya zasu kasance zuwa gobe in lokacin tafiyar tasu tayi suka ga banda ke a tafiyar oho. Kai amman Asama'u tayi asara ji yadda baƙar zuchiya tasa Asama'u tarwatsa kan wannan ahali" Sallamar Sabira ce ta katseta dan bata sauka a inda take son sauka ba sam. Abinci ta ajjiye mata ta fita. Baraka kenan ai Mijinyawa shine babban shaiɗani, mu faɗa ma kanmu gaskiya. Laifin waccan yarinyar ƙaramine da ace a ranar data soma nemanshi ya sanar dani. Ko da bazai iya tunkararta ba. Haba ku riƙa aunawa a mizanin hankali, uzirin da muke baima maza yayi yawa. Zina duk zina ce, kuma hukuncin duk ɗayane. Shin Baraka ko mata ne kaɗai Ubangiji yace kada su kusanci zina, ko akwai inda akace macece kaɗai in tayi zina rayuwarta take lalacewa ne? Ko da yake sabida tsabar yadda ire_iren mijinyawa suke da yawa a wannan zamanin ma naga wasu matan sunce gara ka zauna sabida in ka fita baka san inda zaka je ba, kuma wai mazan haka suke duka. Amman nasan ba adalci bane wannan maganar da gyara. Maza ba duka haka suke ba, daga ciki harda mahaifina dan ba mazinaci bane, daga ciki harda yayuna, da ɗana Azgar. Da akwai bayin Allah maza nagartattu masu gudun famfalaƙi tsakaninsu da zina. Sannan Baraka in akace duk mazan haka suke wallahi ni Hindu na haƙura da Aure zan zauna in rayu, kuma zan kiyaye kaina. Ni bansan ma kinsan wannan aikin ɓarnar ba " Abincin ta zuba a bakinta ta tauna kafin ta haɗiye. "Hindu yanzu yarannan haka kina gani za'a rabaki dasu? " A'a ni dai naso Baraka. So yake yayi amfani da yaran ya tursasani zama dashi, ya ɗauka mutuwa zanyi in babu su, ko yana tunanin bazan iya rayuwa ba sai dasu, kin gane? Ai nasan kotu, kuma nasan uwa ita akeba raino duk da su Azgar sun yi girman da zaɓi za'a basu sai inda suke so. Na sallamashi dashi da yaranne su je. Rayuwata daga lokacin da suka tafi na dena ganinsu, zan soma wata sabuwa, ba tsayawa rayuwata zata yi akan mijinyawa ko yara ba. Ada can haka nake ni ni kaɗai na bansan mijinyawa ba, bansan yaran ba daɗa." Dafani tayi" "Hindu burgeni kike yi babu ɓoye_ɓoye da ace haka mata suka san ƴancinsu kuma suke nuna ma maza ba zasu iya rayuwa da mazinaci ba ko. Da rabi da kwatan maza sun tsoraci zina, duk da nasan basu ji tsoron mahaliccinsu ba. Lokacin da Qasimu ya sanar dani abinda ya shiga tsakanin mijinyawa da Asama'u, na tsorata. Na kuma yadda da masu cewa nono guba ne. Dariya nayi nace. Hmmm Baraka kenan, ina jinjinama matar da zata zauna da miji mazinaci, ni nawa ma zinar da ƴar da tsugunnawa mu haifeta ne kawai bamu yi ba, mu ta buɗe idanu ta gani a rayuwarta." kurum muka yi zuchiyoyi na zafi da murɗa girman lamarinnan. A haka ba madafa su Baraka suka kama hanya suka tafi. Da yamma sakaliya na kira yaran zuwa ciki dan tunda Mijinyawa ya fita tare dasu Qasimu bai dawo ba. Kallonsu kawai nake yi ina tunanin to ni mai zance musu ne? Kuma dolen dole akwai buƙatar in yi maganar dasu tunda dai gobe zasu wuce" Babanku ya faɗa muku wani abu game da tafiyarku gobe ne? " Azgar ne ya ɗago kanshi muka haɗa idanu, sai yayi mun murmushi mai taushi, irin na ƙauna mai tsanani tsakankanin uwa da ɗa. Sabira kuwa bata ɗago ba kanta na ƙasa. "A'a baice mana komai ba gaskiya ya dai ce mu haɗa kayanmu an mai tiranfar aiki zuwa garin katsina" Shikenan abinda yace daku? " Suka ce Eh shikenan." Shiru nayi naita karanto adda'a a zuchiyata kafin nace. To zaku bi mahaifinku ku je Katsina aikinshi ya koma can. Ni kuma zan zauna anan inci gaba da aikina, sannan zan jona PHD na in sha Allah" Sai nayi tsam ina nazartarsu da yadda zasu karɓi abun. Kallon kallo suke yi a tsakaninsu su su biyun nima su nake kallo kawai. Sai kuma suka dawo kallona nima su nake kallo nayi kurum. Ai ba wani abu bane. Babban abinda zaku yi mun shine wannan tarbiyyar da muka baku ni da mahaifinku, kar kuyi fatali da'ita. Ku tsaya tsayin daka kuima mahaifinku biyayya da matar da zai auro muku ta shigo rayuwarku a matsayin matar uba. A duk inda kuke ku wakilceni, me nake nufi da wakilci shine ku nuna ma duniya an baku tarbiyya kuma kunsan girman nagaba daku. Kunga ibada? Ku riƙe sallah, ku kiyaye dokokin Ubangiji, ku dinga sanya Allah gaba gareku akan komai na rayuwarku. Ku riƙe Azkhar safiya da maraice, ku riƙe sallar dare, walha, da nafilfilin da muka saba gabatarwa kafin azahar, bayan azahar daf la'asar, bayan magriba, data bayan isha. Kana in kukai sallar dare ku cika da wutiri. Duk rintsi ku dinga karatun Qur'ani kamar yadda kuka saba kafin kwanciyar bacci, da kuma kafin sallar asuba. Sabira ke macece kina da rauni sosai. Ki riƙe kimarki da darajarki ta ɗiya mace. Menene wannan daraja taki budurcinki, matantakarki shine mutumcinki da darajarki. In kika baiwa wani namiji dama ya lalataki tun kina waje bata hanyar aure ba, kinma rayuwarki giɓi kin cuci kanki da kanki, akwai azzaluman mazan da aikinsu kenan kawar da budurcin ƴan mata. Ta hanyoyin yaudara da dama. Sai kin nutsu sosai kin zama mai wayo, da ɓoye wayon kafin ki gane mayaudarin namiji. Kai Azgar namijine, kada ka sake ka zama daga cikin maza masu kawar da budurcin matan da suka yarda dasu. Zuchiyarka ta zama mai taushi da sanyi, da tausayin ɗiya mace sosai. Kar ka bari a gabanka ka zalunci ko wacce mace, bare kai da kanka ace kai kayi zaluncin. Kuyi haƙuri naga kuna ta jin kunya sabida maganar tana da nauyi ko? Ni uwace in ban wayar muku da kai ba, wa zai wayar muku dashi abokai? Ai nasan ba yau na saba yi muku irin wannan nasihun ba ko? Azgar tun kana yaro inayi maka irin wannan nasihar na kada ka bari ko abokinka ya kalli al'aurarka. Akwai abinda ya taɓa faruwa dakai a makarantar Islamiyya ba zaka iya tunawa ba kai. Amman ni gashi nan ina kallo Wani malaminku ke saka muku hannu a al'aura yaita wasa dashi, amman kai a ranar da ya saka maka kana dawowa gida bazan manta ba ina wanke wanke, sai ka faɗo jikina kana kuka zazzaɓi kau a jikinka. Kake faɗamun malaminku ne ya taɓa ma gabanka. Hmmm ranar munga tashin hankali ko da muka bi ba'asi ashe wannan malamin ya lalata yara a makarantar fin goma, yara maza ya kwanta dasu ta baya, harma yaran sun saba sanadiyyarka alkadarinshi ya karye. Sanadiyyar barinka makarantar kenan, kuma sanadiyyar haka a lokacin saida ake kulle makatantar sakamakon shige da ficen da Baba sojanmu ya dinga yi. To yanzu da ban koyar dakai ba, kaima da ya lalata mun kai an cuceni a banza. To dan Allah ku kula da kanku, kuma duk runtsi kuima mahaifinku biyayya akan duk abinda zaice ku yi, to kuyi. Abinda duk yace ku bari, to ku barshi kar ku tambayeshi dalili. Kamar yadda bana son ku tambayeni dalilin da yasa ba zan biku ba. Kuma ku sani ba lallai mu dinga waya ba. Bama lallai ku sake ganina nan kusa ba. Amman nasan duk daren daɗewa watarana Allah zai sada fuskokinmu da alkhairi. Innah mutu kuma ba tare da naga wannan lokacin ba, ina mai neman yafiyarku. In kuma kun dawo kun sameni zanyi farin ciki gaya. Kuyi haƙuri ku yafeni, nima na yafe muku har abada. Na yafe muku, kuma ina roƙon Allah yaima rayuwarku albarka, ya ɗaukaka darajarku. Ke Sabira Allah ya baki miji nagari adali, ki rayu dashi da farunciki, ku zauna lafiya kamar yadda kika buɗi idanu kika ganni ina zaune lafiya a gidan mahaifinku, kafin wannan abun ya lalata komai. In mahaifinki baiso kizo wajena da mijinki ba, ki yi biyayya. Azgar kaima Allah ya baka mace tagari wacce zata maye gurbina a rayuwarka. Kaima in mahaifinka bai yadda kazo da matarka wajena ba, shikenan kar kuyi gaddama kuyi biyayya. Ban yafe muku ba in kuka zo ba da yawunshi ba." Carab Azgar ya cabkemun hannayena yana kuka tamkar ƙaramin yaro. Murmushi nayi na sauke kaina ƙasa kurum. Bansan me zance ba tausayinsu tamkar ya halakani, musamman Azgar nasan yafi kusa dani, ya kuma fi nuna mun ƙauna gaya. Sabira dai hawaye naga tana sharɓewa ta ɗago ta kalleni ta kasa. "Ammi dake zamu tafi, babu inda zamu je sai tare dake Ammi. In kuwa ba zaki je Katsina ba Ammi muma babu inda zamu je. Ammi kiyi haƙuri kinji? " Murmushi nayi na janye hannayena tare da rungume hannun nawa a kirjina. Dame zanyi haƙuri Azgar? " Sai yayi ƙasa da kanshi yace. "Ammi nima ina jin zafi da ciwon Auren Asama'u da Baba yayi. Kuma wannan abun shi ya tarwatsa mana nutsuwa da farin cikinmu, kuma na kasa dena ganinsu a idanuna. Ammi bance ki yi haƙuri ki zauna dashi ba, nasan ba zaki iyaba ba zaki iyaba. Ammi ni na kasa manta komai a cikin kaina. A gabana a makaranta Asama'u take waya da Baba ba tare da mun sani ba, a gabana take maganganun soyayya dashi. Ammi ina tuno lokacin da nake riƙe hannunta muje Islamiyya, in tayi tsokana ta gudo bayana in bata kariya. Kika rene ta reno na haƙiƙa amman yau ace itace ta taɓa Auren Abbanmu suka rayu na shekara guda a tare. Wallahi har gobe ina mafarkan abubuwa da yawa. Ammi amman ba zamu rabu dake ba, duk inda kike ana..... " Azgar kar ka dinga kuka kai namijine inaso ka zama jarumi, sai dai kashbSabira ce ta kwaso jarumtakata, saurin kuka zai kai ka ƙasa fa" "Ammi zan zama soja kamar yadda kike so, jira nake in kammala Digirina tukunna, duk da na gama kusan zance bautar ƙasane yanzu a gaba. Wataran zaki ga Azgar a gabanki da kakin sojoji yana muzurai" Dariya muka yi harda Sabira mai share hawaye. "Ammi ki yafe ma Abba. Ki yi haƙuri ki bar komai ya wuce, kamar yadda Asama'u ta zama tarihi a rayuwarmu. Rashinta da abinda tayi miki duka yana taɓamu.' Kiran sallar Magrib ya katse mana zancan. Azgar yayi alwala ya tafi masallaci. Ni da Sabira mu kai sallah a ɗakina da Azgar ya dawo ya zubo mana abinci muna ci a tire. Duk sai mukai shiru dukkanmu abu ɗaya muka tuno, tunani ɗaya muke yi shine tunanin Asama'u a irin wannan da'ira ta cin abinci da muke samun yi jifa_jifa. Wannan dalilin yasa hirarmu batai armashi ba. Azgar ma tashi yayi ya fita, ina kiranshi ma bai juyo ba kamar kuka yake yi. Hmmm Sabira na ƙoshi in kin gama kije ki rufe a Kicin, ni zan kwanta sai da safe in mun haɗu kafin ku tafi ko? " Magana zata yi na hanata dole ta haɗiye maganar a cikin lomar abinci. Tana fita, na jiyo muryar Mijinyawa yana rakaɗa musu kira. Dama naji buɗe get ɗinshi. Ni dai ina zaune, da ƙarfin ikon Allah nayo wanka na fito na sake komawa kan sallaya ina jiran isha tayi. Ana kira a masallaci kuwa na miƙe na ta da kabbara na sallaci isha, sai na yi tagumi a kan sallaya ina tuno abubuwa masu dama na rayuwarmu ta baya. A da in akace haka ƙarshen soyayyarmu labarin zai tsaya, wallahi ko waye ya faɗa sai mun ƙaryatashi. In nace kowa ina nufin kowa. Sai gashi yadda ƙarshen ya kasance. Ƙila a daren yau in karɓi takaddar saki ta kwana a hannuna ƙila kuma zuwa gobe ne zan karɓa. Bayan na sauke ajjiyar zuchiya, saina ɗaga hannu nayi kutse cikin sunayen Ubangijina kyawawa na dinga ragargazo mishi kirari. Nayi tawassali da aiyukan jin ƙai da nake yi nace In dai dominka nake yi ya Allah, ba dan neman suna ba. Ubangiji ka haskamun sabuwar rayuwa mai cike da aminci, ka sanya hannu a lamarina kasa nayi murmushi, murmushi mai kyau wanda babu kuka a gabanshi. Allah kai ka halicci Hindu, ka halicci zuchiyar dake gaban ƙirjin Hindu, Ubangiji kaine Ubangijina kasan bazan iya zama da Mijinyawa inci gaba da yi mishi biyayya ba. Na kuma san sakamakon da zan samu in nazo gabanka a matsayin mace maras ɗa'a ga mijinta. Shi yasa na zaɓi rabuwa domin in rabauta. Ubangiji Allah kai riƙo da hannayena, ka sanya mun nutsuwa, tawakkali, haƙuri, ƙarin juriya, ka haska mun. Yarana Allah ka kula mun da rayuwarsu, Allah ya basu matar uba ta gari wacce zata zame musu uwa, Allah ka gani ban ma yarinyar dana riƙe mugunta ba, saima itace ta ƙulla mun cutar da abadan zafinta nanan daram." Na dinga magana da Ubangiji na ina bashi labari cikin salon adda'a, domin ni a nanne nake feɗe duk cikina, sabida nasan ina wajen maganin. Hannayena ina saukesu, wallahi sai ga ajjiyar zuchiya wacce ita tayi kanta da kanta. Sai naji kamar an zare mun wani dogon nannauyan abu daga ƙirjina. Naji na dawo sakayau wanda ada nauyin da nake ji kwatankwacin mai ɗaukar dala da gwauron dutse ne nauyin. Mijinyawa:. Bayan sun yi doguwar magana sosai da Qasimu bai shigo gidan ba sai bayan Magrib yana haɗe hanya kanshi ji yake yi tamkar zai tarwatse dan ciwo, babu ɗanɗano a harshenshi ko ɗis, yana zama ya shiga kiransu Azgar lokacin sallah bai basu damar zaman ba har saida sukai sallah suka dawo, ya tarasu a ɗakin Azgar. Yana bakin gado su suna zaune a gabanshi. Shirune yaita wanzuwa a ɗakin wanda a ƙalla saida aka shafe minti goma baice uffan ba. Sautin numfashinsu kaɗai suke ji. Can yace. "Gobe zamu koma Katsina kamar yadda kuka sani. Abinda baku sanin ba shine ba da Hindu zamu tafi ba. Ita zata ci gaba da zama anan. Kuyi haƙuri nasan dole zaku tuhume mu, ni dai ta ɓangarena zan muku dukkan bayani in muka isa, ku yi biyayya, nasan kun samu tarbiyyar da bani da haufi. Kuyi haƙuri ƙaddarace kawai zan iya ce muku. Wallahil Azeem ina son mahaifiyarku har gaba da abada bazan iya dena sonta ba. Tana da matsayi mai girma a rayuwata. Amman a yanzu kune zaku maye mun gurbinta. Sabira kije ki kwanta, kai kuma ka kawo mun ruwa in sha magunguna bana jin daɗi sam" A sanyaye Sabira ta fice, Azgar ya fita ya kawo mai ruwan ya ɓaɓɓalli magunguna ya watsa yabi da ruwa. A wannan daren a cikin wannan ahali babu wanda ya runtsa. Amman babban abinda ya zama abun burgewa da ƙawa a kan sallaya suka kusan kwana. Kowanne cikinsu ganawa yake yi da Ubangiji babu hijabi, sai dai akwai babbanci adda'a. Asussubar fari Mijinyawa ya tattaɓa Azgar dake bacci a zaune da carbi. Sai yaji jikin yaron kau, shima yaron yaji jikin Baban nashi kau. Babu wanda yace da ɗan uwanshi komai. "Kaje ka yi wanka kayi alwala" Sai da Azgar ya shiga banɗaki mijinyawa ya jawo takadda da biro, yayi shiru ya rasa ya zaiyi hannunshi na ɓari ƙirjinshi na dokawa yayi rubutu ya nannaɗe. Azgar na fitowa Mijinyawa ya faɗa banɗaki, alwala kawai yayo ina ya kasa wanka jiri ɗibanshi ma kawai yake yi. "Muje masallaci Azgar. Da mun dawo zamu wuce Qasimu zai zo shi zai tuƙa mu." Suna fitowa ya nufi ƙofar ɗakin Hindu ya soma ƙwanƙwasawa a hankali. Ganin haka yasa Azgar ya fita zuwa tsakar gida yana jiran uban nashi. Hindu:. Ina sallame sallar ra'aka tanil fajir naji ana lillisa mun ƙofa a hankali. Nima a hankalin na tashi na je na buɗe, ina da tabbacin mijinyawane ne babu makawa. Ilai ina buɗewa muka haɗa idanu baki na ɗan taɓe kaɗan haka. Hannu ya saka a ajjihu ya ciro takadda ya miƙa mun. Allah na ambata na sanya hannu na karɓi takaddar, ya juya ya wuce da sauri. Illahirin jikina sai yayi sanyi kamar an watsamun ƙanƙara. Take sai sanyi naji yana huda har ɓargona. Wallahi hannuna har jiƙewa yayi da ruwa sharkab. Juyawa nayi na koma ciki, na buɗe durowar gefen gadona na adana takaddar sakin, ina wani murmushin da ni ni kaɗai nasan fassararshi. Sallah na kabbara, na yi adda'a nayi adda'a nayi ma Allah kirari, nayi godiya, na nemi nasara a rayuwar gaba. Ina zaune ina sauke ajjiyar zuchiya a hankali a hankali sai na jiyo magana a tsakar gida kamar dai Qasimu, da gagamniyar yara suna fitar da kaya suna sanyawa a mota. Sai can naji an buga mun ƙofata. Wani abune ya tsirgamun daga kayina zuwa babban yatsan kafata ta hagu. Ina buɗewa naga yaran a bakin ƙofa kawai jikinsu kamar an watsa musu ruwa. "Zamu tafi Ammi" Rungumesu nayi du su biyun a jikina, wallahi ina jiyo yadda jikin Azgar yake ɓari, Sabira ita kuma kuka take yi abunta kashirɓan. Kiran da mijinyawa yayi musu ne ya tilastamun sakinsu tare da jan hannayensu har filin tsakar gidan. Qasimu yana ta jijjera kayan nasu a mota cikin dabara, dan motar tayi ma kayan kaɗan. "Hajiya Hindu ta Gawata ikon Allah. Tsuron tsirin tsandauri Allah ke fidda shi." Murmushi nayi haƙorana yana wani irin rawa. Da ƙyar nace. Qasimu ashe baku tafi ba?" "Dama yau zamu tafi. To sai ga kiran Gawatanki akan ni zan kaisu Katsina shi jikin nashi babu daɗi, yana ganin Azgar kamar bazai iya tuƙin ba" Azgar ɗin? Kallon yaro yake yi mishi. Ai kuwa shi ya tuƙamu lokacin bikin Salamatu har katsinan, kuma shi ya tuƙo ya dawo da mota" Mijinyawa dai baice damu ci kan ku ba asalima kanshi a juye yake, ko me yake kallo oho. Yaran naja na shigar dasu cikin mota, na ɗan ƙara musu nasiha. Shigar mijinyawa da Qasimu gaban motar yasa na musu sallama na matsa, ga get an wangale. Ina gani suka ta da motar, gabana na dukan uku_uku ƙafafunane naji suna neman gagarar ɗaukana, ba shiri na yi saurin ƙoƙarin barin wajen. Ina zuwa daf ƙofata sai naji Azgar ya kwaɗamun kira da ƙarfi, muryarshi na wani irin rawa. Juyowa nayi da saurina. Mrs Bukhari.TSURON TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA ASHIRIN DA UKU ( 23) YAR UWA MENE MATSALARKI KINSAI MAGUNGUNAN NONO DA NA KARIN MAZAUNAI HAR YAU ALLAH BESA AN DACE BA TO INSHAA ALLAHU MATSALAR KI TA KAU INJINI NI AUTAR AMBATO MAGANIN NONO Kina fama da zubewar breast komai lalacewarsa kokuma dai Allah be azurtaki dasu sosai ba to ni na baki guarantee kwana 7 kachal zakiga chanji idan har kikai amfani da magani na 🥱🙅🏽‍♀️🤌🏽🙌🏻 MAGANIN HIPS Kinasan ki kara mazaunai ki kaddara matsalar ki takau DOMIN maganin mu sadidan ne inkinyi amfani dashi Saikin dawo ko kin kawo wata wannan shine taken maganin mu masu bukatar karin bayani ko samun maganin mu zaku tuntubemu akan wannan number ta WHATSAAP number 0812 681 3773 SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA 🤭INJI AUTAR AMBATO Ina juyowa naga Azgar a tsaye akan ƙafarshi ya fito daga mota. Wani abune ya tsirgamun. Allahu Akbar Azgar na Ammi, dama nasan zai yi wuya Azgar ace ya tafi ya barni. Yana ƙarasowa ya durƙusa a gabana ya fashe da kuka. "Ammi ko ki zo mu tafi, ko in zauna in ƙare rayuwata dake, ko Abba ya zauna tare damu" Kafin in bashi amsa Qasimu da Mijinyawa sun ƙaraso inda muke a tare suka ɗaga Azgar. Mijinyawa na shirin juyawa dashi, yaron sai ya turje. Da mamaki gami da tsoro ya dubi yaron. "Me kake nufi Azgar a hannun Amminka kake son in barka. Ko ko me kake son faɗamunne?" Qasimu yace" "Abi a hankali Mijinyawa. Azgar menene yake faruwa. Menene matsalar?" Ya kasa magana sai ajjiyar zuchiya kawai yake yi. Ni dai ina tsaye ina kallon ikon Allah. "Nace ne tazo mu tafi. Ko ni in zauna a wajenta, ko kuma Abba ka haƙura da zuwa Katsina. Bazan iya barin kusa da'ita ba wallahi, bazan iyaba. Kuyi mun rai" Qasimu ya dubeni, ni kuma Azgar nake kallo. Inaji da ana iya kyautar rai a bawa wani. To raina fansane akan Azgar, akan wannan abun da yayi. Ya burgeni sosai. "Hindu kinji abinda Azgar yace. Me zaki ce game da abinda yace" "A'a Qasimu kada mu yi haka da kai, Azgar dole zai bini, bai isa ya juyani ba wallahi bai isa ba. Shi da Hindu ai ba haifata suka yi ba. Kai nafi Hindu taurin kai da ƙwaƙwaduba" "Ya ko isa tunda yara na uwane a musulunci, har sai sun mallaki hankalin kansu suke da zaɓi kamar dai Azgar da yake da cikakken hankali. Ai ko kotu akaje baka da ikon tursasama Azgar. Tunda dai yaro ni ya zaɓa baka da iko. Wallahil Azeem naso su zaɓeka kamar yadda suka nuna. Ni da kake ganina babu wanda dan ya shigo rayuwata, fitarshi zai girgizani kai ka sani. Amman yaro a barshi da kamilin hankalinshi ya zaɓama kanshi abinda yake so shine kawai" Kallona Mijinyawa yayi da maɗaukakin mamaki, ni ko ko gezau ina kallonshi sheƙeƙene dan bana mishi kallon mutumci sam, ina raga mishi domin yaranshi ne kawai, da kuma alkhairan baya. Fuuu ya isa wajen mota ya jawo Sabira yazo ya dure mun ita ya juya, cikin maɗaukakin fushi marar misaltuwa "Baba" Sabira ta kirashi, cak ya tsaya bai ko iya juyowa ba. Sai itace ta isa inda yake. Muna tsaye muna kallon almara, wallahi yarinyarnan ta rufe idanunta ruf. "Ni kai zan bi Baba" Hannayenta ya riƙe ya kaita mota, har yana murmushi, tare da juyowa ya dubi Azgar, ya dubeni. A sanyaye Qasimu yace. "To shikenan yara sun raba kansu. Sai dai kash naso ace Sabirace ta zaɓeki ba Azgar ba. Riƙon mace sai mace Hindu. Kash ni banso wannan tarihi ya yanke a iyakar haka ba. Amman a jikina inajin tarihin rayuwar soyayyarku hutu kawai zai tafi, da zaran kun huce, zukata sun yi kewar juna, zaku yi mannewa iriyar wacce zaton wani bai zata ba" Hannayen Azgar na riƙe kawai ya dawo gefena. Qasimu ne ya sauke mai kayanshi daga motar, suka ja suka wuce. Muna tsaye mun yi shiru. Juyowar da zanyi sai naga Azgar na layi zai faɗi ƙasa. Kafinma in tallafoshi ya faɗi ƙasa sumamme. Nan na shiga jijjigashi ina ambaton sunanshi, ina jin kaina na yamutsewa makarai na neman dokeni, ga yarona sanɓal a kwance. Sai jijjigashi nake yi ina ambaton Allah. Kawai sai naji na dena ji, na dena gani ɗif na rasa numfashina. Kunji wani ƙudurar Allah. Mijinyawa:. Yana kallon Hindu da Azgar har motarsu ta fice daga cikin gidan. Sabida damuwa da ruɗu yasa Qasimu ya mance da batun rufe get a haka suka bar get ɗin a hangame sukaita gudu bisa hanya. Babu me magana a tsakankaninsu tunani kawai mijinyawa yake faman yi, da irin yadda tun a baya lokacin da Hindu bata samu haihuwa ba, akaso a rabasu, aka saka musu wa'adi ko samun ciki, ko sakin Hindu da yin sabon Aure. A lokacin alƙiyamarshi ce ta tsaya. Sai gashi yau bagatatan sun rabu da Hindu rabuwa irinta har abada, rabuwar da babu batun dawowa aci gaba da rayuwar Aure. A cikin ranshi ya ƙudure sai dai shi da Hindu su haɗu a darrussalami. Idanunshi ya rufe tare da jingina kanshi yasa hannu ya dafe zuchiyarshi yana tuno ɗumbun alkhairan Hindu a cikin rayuwarshi. Hindu mutum ce, yasan tana da taurin kai. Kuma yana girmama taurin kanta tunda bata raina kowa, kuma akan gaskiyarta take taurin kai, bata yadda a takata ko a tauyeta ba. Yasan da taurin kan nata tafi mata dubu, ta yi biyayyar da marasa taurin ma bafa zasu iya ba. Murmusawa yayi daya tuno ciwon da yayi ta faman dashi, da yadda tayi mishi jinya. Tunani: Ina kwance jikin nawa babu daɗi gaskiya. Gambo da mijinyawa Babba su suke jinyata ta ɓangaren kaini banɗaki, tsarki, wanka. Ba dan gazawar Hindu ba, sai dan suma suna ganin iyakar tallafin da zasu yi mun kenan, su ba kuɗi garesu ba shi yasa suke yi da ƙarfinsu. Hindu kuma itace sha ƙundum na jinyata, tayi da jikinta, tayi da aljihunta, tayi da lokacinta. Itace fita aiki, itace abincinmu, itace kuɗin maganina, ga kuɗin makarantar yara. Watana shida cib a kwance sai an kwantar sai an tayar. Ina tuno sanda ta ɗauki gwal ɗinta ta siyar ranar komawa asibiti ta kaini asibiti, taita jigila dani, a lokacin ma gado aka kuma bamu haka taita turawa ba gajiyawa. A lokacin su Gambo da Mijinyawa duk sun watsar sun gaji, suna dai shigowa da safe abinda nake buƙata su mun, ko wanne ya kama gabanshi. Ko Baba sojanmu ya tambayeta matsala sai tace duk babu matsalar komai, komai anayi mun a gida. Kuma a lokacin ko su Yaya Jamila sau biyu kaɗai suka zo asibitin suka duba ni, babu abinda akayi mun daga gida, tsayuwar kirki basu iya akan jinyarba. Hindun dai jurau ita aka bari da zama dani" Dawowa daga tunani:. "Mijinyawa wannan tunani haka daka lula na menene? " Cewar Qasimu daya katse mishi zaren tunanin nashi. A hankali ya buɗe idanunshi da sukai jawur dasu ya dubi Qasimu. Ya juya ya dubi Sabira wacce har lokacin kuka take yi amman marar sauti, idanunta sun kumbura sun yi jawur dasu. Laɓenshi ya lasa wanda ya bushe ya zuba ma titi ido kawai. "Ka kira Lauwali ka sanar dashi mun taso kuwa Gawata? " Girgiza kai yayi kawai. "To taimaka dai ka kirashi sabida asan da tasowar tamu ko ba gaskiya ba. Gawata bazan ce komai ba, amman in muka isa sai mu tattauna. Danne ka kira Lauwali. Sabira kun karya ma kuwa? " Qasimu ya tambayeta a sanyaye, sabida yanayin yarinyar dole a tausaya mata. Shi dai yaso yarinyarnan an barma Hindu ita gaskiya. Kai kawai ta ɗaga alamun aa basu karya ba. Kafin mijinyawa ya kira Lauwali wayarshi ta shigo shi. A hankali ya ɗauka murya a sanyaye yace. "Lauwali yanzu nake shirin kiranka" Lauwali yace. "Da jin muryarka haƙiƙa iyalinka bata amince ta biyoka ba Gawata. To ni abinda nake so dakai tunda Asama'u ka riga ka saketa, ita matarka ta nuna itama ba zata zauna dakai ba, ba shikenan ba Gawata sai ka sauwaƙe mata kawai ka huta. Nasan baka kyauta mata ba daka Auri yarinyar data riƙe ta rene ta ba. Amman ai ƙaddarace yanzu saita riƙe wannan a matsayin dalilin da zata horas dakai. Ka rabu da'ita kawai dan Allah. Kazo Katsina mu da muke da fararen mata. Matana suna da ƙanne kyawawa in kazo ba sai ka zaɓi ɗaya ba? " Da dariya ya ƙarashe zancen nashi. Murmushin takaici kawai Mijinyawa yayi. Lauwali baisan dawar garin ba, iyakar Auren Asama'u ya sani duk da ya kasance abokinsu tare suka taso, amman ba ko wanne aboki bane Amini. Wannan labarin a tsakanin Gawata, Hindu, Qasimu, Baraka sai ita Asama'un aka burgeshi kawai. "Lauwali kenan. To matan naka har nawa ne haka da kake dukan ƙirji? " Dariya Lauwali yayi sosai dake ɗan yine shi sosai dama. "Ai kai dai Allah ya kawo ku lafiya. Nifa ba matsoraci bane daka ganni, ɗan taran aradu da ka ne" Da haka sukai sallama Mijinyawa ya sauke wayar a kunnenshi. Ya kalli Qasimu, shima kallonshi yayi sukaima juna murmushi kawai. Shi kaɗai yasa me yake ji. Saƙone ya shigo wayarshi. Da mamaki ya buɗe saƙon, gafa abinda saƙon ya ƙunsa. _ina mai farin cikin sanar maka, ni Asama'u Aurena ya mutu. Sabida Allah ya ƙaddara ni taka ce har abada. Da zaran na kammala iddata zan soma farauto soyayyar mijina, kuma Babana, wannan mai yawan tausayin nawa_ Shiru yayi, tare da lumshe idanunshi, baisan me zaice ba, bai kuma san me zai yi ba. Mamaki Asama'u take bashi, duk da yasan Halimace ta lalata komai, amman bazai daina mamamaki ba. Abinda Asama'u da Halima basu sani ba shine. Idan duk duniya zasu taru a kanshi shi da Asama'u har abada. Yanda bazai iya auren Sabira ba. Haka bazai iya auren Asama'u a karo na biyu ba. Tafiya kawai suke yi babu magana, sai jujjuya lamura a kanshi yake yi. Allah cikin ikonshi da amincewarshi suka shiga garin katsina lami lafiya cikin aminci. A ƙofar ƙaura gidan Lauwali yake. Tsakanin ƙofar ƙaura zuwa kan titin Ibrahim Babangida IBB way inda babban reshen first bank yake a katsina babu nisa. Ba wannan ne kaɗai firat bank ba, akwai sauran dake wasu wajajen amman wannan da aka turo mijinyawa shine Babba. Akwai bankuna da dama a wannan yanki, ga gidajen ma'aikan gwamnati irinsu Lauwali kenan. A hankali motarsu ta sulala cikin unguwar ana maƙale da Lauwali a waya yana fasalta musu hanya har suka iso inda yake tsaye, a gaban gidan da yayi kama da nashi, saye da jallabiyya mai ruwan toka, da tumbinshi kaya guda a gaba. "Kaga Lauwali masu gidan ruwa na jihar katsina ba. A taɓaku a kwana da ƙishin ruwa" Dariya Lauwali ya saka ya miƙa ma Qasimu hannu suka tafa taf har suna tsalle dan jin daɗi. Mijinyawa da Sabira suna cikin mota basu sakko ba, kallonsu Mijinyawa yake yi yana ji ina ma shine su da basu da damuwar komai . "Qasimu koma mota a shiga da motarnan ciki kaji. Gawata sai kallonmu yake yi muna ƙular dashi, yadda kasan mu muka kar zomon" Komawa Qasimu yayi cikin mota. Maigadin gidan ya buɗe musu get suka shiga cikin madaidaicin farfajiyar gidan, ga motoci fake guda huɗu a tsakar gidan a cikin ƴar rumfa. Su Mijinyawa sai a gefe suka saƙala tasu motar, a kaikaice sabida tsakar gidan ya cushe. Fitowa suka yi daga motar. Lauwali yace. "Sabira kece kika zama haka? Qasimu yarinya ai budurwace sosai" "Kai da ƴarka ashe baka san ma ta girma haka ba Lauwali, ai ta gama sakandare gamawar kenan. Ta soma jami'arta anan. Shi kuma wanta da muka baro a can ya kammala jami'ar za'ace saura bautama ƙasa kuma." "Ha'a Azgar ko, to shi ina aka baroshi ne. Ba tare akace za'azo dashi bane da. Ko Hindu taƙi ba da shine, ko sai ya kammala bautar ƙasan?" "Maimakon ka shiga damu amman ka tsaya sai zance kake mana, kai kuma kana ta biyeshi a gaban ƴarku" Cewar Mijinyawa da yake jin haushinsu kamar me. "Ina wuni Baba" Sabira ta faɗa a sanyaye. Tausayinta ya kuma durama mijinyawa kamar ya zubar mata da hawaye. Oh ko yaya rayuwarta a cikin ahalin da bata san su ba zai kasance mata oho. Shi tsoronshi Allah kada a lalata mishi tarbiyyar ƴa shine abinda ke yawo a zuchiyarshi. Da ace Sabira na da saurayi kuma ya cancanta Aurad da'ita zai yi ya huta, wallahi yafi mishi kwanciyar hankali. "Lafiya lau Sabira sannu ko? Ku biyo ni, in yaso kayan zuwa anjima in kuka huta sai a sakko dashi" Suna biye dashi har izuwa babban falon gidan inda ga kulolinan an zubesu a ƙasa da kayan sha na tarbar baƙi, da duk abinda za'a buƙata. Matan gidan su biyu suna falon a zaune. mijinyawa suka shigo. "Baƙi sannunku da zuwa maraba" Cewar Amaryar Lauwali ƴar katsinawan dikko kenan. "Yauwa sannunku, da fatan mun same ku lami lafiya ko?" Nan aka shiga gaggaisawa sai ga Sodangi uwargidan Lauwali kenan ƴar mutan Gombawa, tare da Yayanta namiji da ya kawo mata ziyara. "Ah Sodangi Yaya Jaddo ba dai tafiya zai yi ba ko? (Jaddo a al'adar fulani ana nufin mutum mai daraja, jarumi, ko dangi nagari) . " A'a ba tafiya zai yi ba. Yana son kaima wani abokinshi ziyarane. Yama zo ɗaukarshi yana waje. Gawata, Qasimu sannunku da zuwa kun shawo hanya, ashe rai kan ga rai. Ƴata Sabira sannu da hanya. Taso muje kinji? " Sabira ta miƙe a tsanake ta gaishe da Sodangi, ta juya ta gaishe da Jaddo wanda tunda suka fito idanunshi a kanta. Juyawa yayi suka gaggaisa da su Qasimu ya fita akan zai dawo da Magriba bazai kai isha ba. "Sodangi Sabira ta zauna a wajenki, tunda a ɓarayinki akwai ƴan mata har huɗu zata fi sakewa." "To maigida in sha Allah babu komai zan riƙeta amana. Ina kayanta suke fa? " Lauwali ya shafi tumbinshi yace. "Kaya suna mota ko anjima sai asa yara su kwaso" Hannun Sabira ta kama suka shiga ciki. Tsoro da fargaba duk sai ya shigi Mijinyawa. Sai da matan Lauwali suka basu waje falo ya rage daga su sai su. Mijinyawa yace. "Lauwali kana da yara mata kuma kake barin namiji ya shige har can can cikin gidanka? " Qasimu ya tuntsure da dariya shine harda ƙwarewa dan shi tuni ana wannan dudumar gaishe_gaishen yana ta aikin zuba musu tuwo. Mijinyawa ya dubi Qasimu idanunshi suna layin ciwo, wani irin ciwone yake bijiro mishi ainun. "Namiji baya shigarmun can cikin gidana. Jaddo da kake gani ɗan uwan Soda ne, baima daɗe da dawowa daga ƙasar waje ba, yayi phd ɗinshi. Likitane babba, sai dai bansan fannin daya karanta ba. Harma ya buɗe ɗan asibiti nashi, muma damu akaje akayi bikin buɗe wannan asibiti. Dalilin barinshi da nayi zuwa ciki shi mutumne wanda in nutsuwa da hankali suna ma mutum yawa to sun yi mishi. Wannan shine karonshi na biyu kacal daya taɓa kawo mana ziyara. Kaji dalilin da yasa na aminta dashi har ya shiga ciki. Akwai ƙannen ita Soda da nake riƙewa su biyu, suna makarantar Jami'a a garinnan, to kaji. Shiru Mijinyawa baice uffan ba, bashi da abun faɗe, sai kawai juya tuwo a cikin miya da yake yi. Loma uku yayi kacal ya sha kunun ayan da ɗan dama. Jinshi yake yi tamkar ba shine ba sam. Bai tabbatar da haka ba har saida suka koma muhallin saukar baƙi, ciki da falo da banɗaki harda kicin, kuma akwai abun girki, da tukwane. "Kaga in girkinka ma kake son yi akwai komai har kayan abinci akwai. Akwai wani bawan Allah da yazo daga garin Kano ya zauna damu na shekara biyu. Ya kasance mai kiyayewa da tsoron Allah, kai harma da mutane tsoronsu yake ji. Rubutu yazo yayi na littafin hausa wanda ya tattare irin matsalolin da suke kawo mace macen aure, yana da burin ya buga in Allah ya bashi dama. Amman kai kam daga cikin gida za'a dinga kawo maka abinci" Mijinyawa bama ya jin me yake faɗa gabanshi sai sake tsananta faɗuwa yake yi. Sannan jikinshi na bashi tamkar za'a lalata mishi Sabira, gata mace balle yace zasu dinga kwana tare. Azgar ne ya faɗo mishi. Murmushin dole yayi kawai, baisan wanne fassara zai ba murmushin ba, shi dai yayi ne kawai. Amman fa fat_fat gabanshi ke faɗuwa sai sake tsananta yake yi. Tunanuka sun cika kanshi, yana hango Talatu bankin farko da Asama'u da suka zama wasilar tarwatsa mishi ginin soyayyar da ya shekara ashirin da biyar zuwa shida yana ginawa. Amman yasan ya fisu girman laifi, hukuncin da Hindu ta yanke mishi, da Azgar hukuncine mai kyau wanda ya dace dashi. Bai ga laifinsu ba sam. Sai dai ya tabbatar zuchiyarshi ba zata iya ɗauka ba, rayuwarshi babu ta yadda zata tafi da kyau babu Hindu da Azgar a cikinta. Abun kamar da wasa kafin Magrib mijinyawa baya iya gane wa yake kanshi ma kwata_kwata, ranga ranga a sume cikin fitar hayyaci su Qasimu suka wuce dashi asibiti a motar Jaddo har da Sabira, sai kuka take yi. Dukane a kanta tako ta ina kawai. Anan ƙarshen harƙa ta biyu yazo ƙarshe. Sai mun haɗu a harƙa ta uku sabuwar tafiyar da zaku ji ƙarashen tarihin rayuwar Gawata da Hindu zai zo muku a tafiya ta uku. Ƴar uwa ki buɗe zuchiyarki sosai, a cikin karatun nazarin da kika yi, ke wanne babban darasin kika koya. Sannan me kika koya daga Hindu Wanne darasi a dunƙule zaki ce littafin na bayar Menene babban jigon labarin? Wanne saƙo labarin ƙawayen Hindu ya isar miki ke a karan kan ki kanki? Shin kin jinjinama mrs Bukhari kuwa? Tsokacina ga masu ganin sharhin da nake yi yana yawa. Ga amsarku ayau na zaɓi in baku dan ku fahimta. Ko wacce marubuciya da salo, da tsarin zubin rubutun data fi sha'awar yi. Ni wannan yana daga cikin salon rubutuna. A wannan sharhin nake sake faɗaɗa tunanin mai karatu ta yadda zai fahimci asalin inda na dosa. Naga wasu suna tunanin sharhin bashi da amfani, ko kuma yayi yawa. A wajen mrs Bukhari bai yi yawa ba, kuma yana da matuƙar amfani, musamman a labarin Hindu wanda al umma suka kalleshi ta fuska biyu. Nagode muku sosai. Haƙiƙa kuna bibiyata da kyau, kuma ƙorafi halamace ta son aikin da mutum yake yi, kuma halamace ta tabbas ana bibiya. Ko wanne irin saƙo kuka aiko yana zuwa gareni, kuma ina godiya. Son so masoyana💪🏼💪🏼💪🏼💪🏼 Inason yau inji kwament sosai, ku tattaɓo abubuwan da baku taɓo ba. Ku jira fitowata a cikin tafiya ta uku dan jin yadda zata kaya. Ina mai tabbatar muku yanzune zamu dulmiya sosai, zaku tsinci abubuwan ban mamaki a gaba wanda baku yi zato ba. Ta ɓangarena ina miƙa godiyata ga masu jajircewa wajen sharhi tim mijinyawa da tim Hindu Haƙiƙa kun yi rawar gani sosai wajen sharhinku, madallah daku, Mrs Bukhari na godiya shi kanshi oga mai daraja lamba ta ɗaya eh mr Bukhari ba Abu khalil yace in gode muku, in sake gode muku, godiyarma da kanta ta gode💪🏼💪🏼💪🏼💪🏼💪🏼💪🏼 Akwai wata gaɓa da nake jira wacce in anzo zan muku magana, zan muku bayani dogo in sha Allah, game da babban dalilin daya ja ra'ayina naji na zaɓi labarin da Hindu ta bani a matsayin littafina na gaba in sha Allah. Na faɗa na kuma littafin Hindu labarine na gaskiya. Akwai Hindu, akwai Mijinyawa da duk waɗanda aka lissafo akwaisu. Babu abinda na ƙara, saima ragewa da nayi, sabida wasu dalilan da ni da Hindu ne kaɗai muka san dashi. Zamu sarara na kwana biyu, sai kun ganni kawai. Kuyi haƙuri hutun zai ɗan yi tsayi ba kamar yadda aka sababa. ❤️❤️❤️❤️❤️❤️🤺🤺⚔️⚔️⚔️⚔️⚔️⚔️🤺🤺 Wuya a tafa, wuya a mararraba wuya a gida, wuya a eh daji. Inji Gaza Baban eh Rahine, rabin ran Rakiya eh kayi eh nayi😆😆😆😆