*🌲🌲TARBIYYA🌲🌲🌲* *©NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIAON✍🏻* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM._ *GABATARWA* _Dukkan yabou da godia sun tabbata ga Allah ubangijin tallikai,Salati maras adadi zuwa shugaban mu Annabi (SAW) da alayensa da sahabbansa ba ki daya,Allah yaqara mana rai da lafia da ikon fadakarwa akan turbar Manzon rahma Ameen._ *TSOKACHI* _Wannan littafi na TARBIYYA na rubuta shi ne domin ilimantarwa, fadakarwa, da tunatarwa,Bugu da kari na tsara salonsa domin nuni da halaye masu kyau da maras kyau,wadanda sukaci karou da addini musulunci,Banyi domin wani ko wata ba,Labari ne kirkirarre kuma kagagge,Duk wanda ya ga ya ci karou da halayensa ko dabi'un sa to ya sani Arashi ne kawai._ *GARGAD'I* _Ban yarda wani ko wata ya canja min Labari ta kowacce fuska!,Matsawar ba tare da izinina ba!Duk wanda ya aikata hakan to ya sani shi barawoun fasaha ne,kuma Mai aikata aiki maras kyau,Allah ne gatana kuma shine wanda zai sakamin._ *SADAUKARWA* _Ga Iyayenah Abin Sona,Abin Kaunata, Abin Alfaharina,Rabbil izzah yaqara masu rai da lafia tare da nisan kwana,Ya rahman ya sadasu da rahmarsa, fatana Aljanna ta zamou mazauninsu na har Abada Amin._ *SHAFI NA D'AYA* *SHIMFID'A* Da farko Ita dai *TARBIYYA* Abi ce mai muhimmanci a rayuwar Al'umma,A wannan zamani da muke ciki, Hakika *TARBIYYA* Tayi karanchi a rayuwar mu,Idan mukayi la'akari da tsantsar so da kauna da iyaye ke nunawa yaran su Ayau,Hakan agefen yara suna yawan ajiye halaye da dabi'un gidan su agefe suna aikata abubuwa son ransu....Anan na kanyi nazari akan shin meye *TARBIYYA?* Lalacewar ta da tabarbarewarta laifin waye? iyaye ko yaran?ku biyoni...ni ce taku Mai kaunar ku *Nabeela Dikko* domin sanin yadda zata kaya,Shakka babu *TSANSAR SO* ne ya sanyani nake subourboudou maku littafai masu ma'ana....Banda zabi akan ku masoyana *MATAN AURE* da 'yan mata,na nesa da na kusa domin *MATA JIGON AL'UMMA* ne,Kuma su Abin girmamawa ne akoda yaushe,Ina baku shawara ku rike hakuri saboda halin *WATA RAYUWAR....* Domin *IDAN AN CIZA HURAWA AKE* Duba ga Ukuba irin ta wasu *DANGIN MIJI* Da sannu zata zo karshe,Kamar yadda *ALMAJIRANCHI KO AIKATAU* zai zamou labari nan ba da dadewa ba,Dama caan ita *BAK'AR AK'IDA* Abin gudu ce,Allah ya dauramu Abisa tafarkin gaskiya,Ya bamu ikon yiwa yaranmu *TARBIYYA* mai kyau Ameen. ______________________________________ "Sunana Nadiya Bello, Wanda akafi sani da suna Balarabe,saboda fari ne sol, kamar zubin larabawa." "Mafi yawan kawayena na firamare da sakandare sunfi Kirana da (Naddy Balarabe)," "Tun Ina karamata na Tashi da nutsuwa gashi ,Allah yayi min baiwar kyau da farin jinin jama'a,shiyasa bakin mutane yayi yawa akaina,saboda tsabar kyau na,Iyayena akullum cikin zuba min addu'a suke, Kasancewar ni kadai ce, Allah ya basu a duniya!" "Hakika iyayena sun inganta rayuwata, tun yarinta ta har kawowa girmana, suna bani TARBIYYA Mai kyau tare da bani cikakkiyar kulawa,"Shiyasa akullum nake alfahrin Samun su arayuwata," "Sunan mahaifina Mallam Bello, asalin sa fulanin Sudan ne, fari ne tatas Mai kyaun gaske gashi da kwarjini Duk inda ake neman dattako to idan aka sameshi ansamu,dalilin shi farine tas shine kowa ke kiransa da Balarabe,Amma sunan iya Nigeria ne, sanadin hakan sunansa na ainihi ya bace bat, " Assultaan shine mahaifinsa ya mutu da dad'ewa bayan yayi wafati ne ya dawo Nigeria da Zama...,kasuwanci ne ya kawo mahaifina Nigeria,Har ya gidadan ce anan,duk yan uwan mahaifina suna caan kasar Sudan,Dalilin kasuwancin da yakeyi na sayar da gwanjou,'' "Watarana gurin tafiye-tafiyensa yaje cin babbar kasuwar nan ta garin kalgo da ke jihar kebbi, "To anan ya hadou da Ard'ou dakin gari,daga nan suka kulla abota, Mai karfi da inganci tare da amanar juna atsakanin su,Balarabe ya zamewa Ard'ou aminin gaske,bayan wani lokaci Ard'ou yayi masa tsaye batare da binciken sanin Ahlinsa ba, ya baiwa Balarabe auren kanwarsa da ya ke riqou bayan rasuwar iyayensu wato fad'imatou(Innarei)wato mahaifiyata kenan."Itama kyakkyawar gaske ce."Shiyasa agefen uwa da uba na gado fari da kyau bana wasa ba."Mamana da Babana suna zaune lafiya babu Mai jin kansu,Domin halayensu sun zou d'aya mutanen kirki ne sosai."Shiyasa da suka sameni suke inganta rayuwata da TARBIYYA, Bayan tsawon lokacin da suka d'auka basu samu haihuwa ba,Duk da soyayyar da suke nunawa agareni bai Hana su kula Dani ba tare da hukunta Ni idan na aikata laifi," " Har yanzu mahaifina bai daina sana'ar sa ba wacce da ita muke ci da sha kuma acikin ta na kammala karatuna firamare na sakandare, Wanda Halin yanzu babana yana kokarin yaga na d'ane gurbin jami'a."A kwalejin shehu shagari da ke garin sakkwato." "Dukkan mu muna rayuwa a jihar kabi,A garin argungu cikin unguwar tudun wada."Na samu kulawa da Mai kyau awurin iyayena, ilimin islama da na zamani sunyi kokarin bani."Haka suna saka min ido akan dukkan al'amurrana,da duk wani motsi na musamman Mamana,wacce komai nawa akan idon ta yake har alakata da abokaina duk mamana tana sane.Bana Komai sai da saninta ko Kuma izinin su, Domin akwai yarda da aminci atsakani na da su" "Shiyasa na kasance abin so ga kowa, da kuma alfahari awurin iyayena da malammai nah,har ma da mutan unguwa Duka Kowa Nadiya."Domin na zamou daga cikin Yan matan unguwa,",masu nutsuwa ladabi da biyayya zan zamou ta daya, da zarar ka zAuna Dani na dakika zaka fahimciina da kirki da mutunci duka sun yalwatu arayuwata," "Nadiya..!Nadiya..!Kiran da Mama ke mani NE ya fargar da ni daga tunanin wacece Ni.." "Da hanzari na amsa da na'am mama,gani nan." "Da sauri na fitou daga dakina zuwa Dan yalwataccen filin gidan mu, inda mama take zaune a tabarma,dake shimfide karkashin bishiya,rediyo ne ajiye gefenta tana sauraren gidan rediyon nan Mai farinjini wato Equity fm birnin KEBBI inda suke Shirin Nan na IN DA RANKA." "Fuskata mama ta duba, tana murmushi tare da rage karar rediyon..."ta ce ''yooo ni...Nadiya wai sai yaushe zaki daina kumshewa acikin daki kamar kunshin kaya ne!?..." "Mama kiyi hakuri zan daina zaman d'akin..nace da alamun damuwa!" "Ni kinga,idan ma kin cigaba ke zakita rub'a!"yanzu kije gidan lantana ki amso min sako."Kice mata Ina gaidata, Nace ta baki sakon, ki kawo min,kuma karki Jima nasan dai mutuniyar taki na makaranta"inji mama "To,mamana, an gama,nace Ina dariya domin idan da sabo na saba da sauraren fadan, yawan zaman da nake daki,,Wanda ya zame mani jiki..Nan dai na dauko hijab Dina,na fita zuwa makotan mu domin amso mata sakonta." Muje zuwa fans wasa farin girki🤙🏼 *Yar mutan Dikkawa ce* *SHAFI NA BIYU* ______________________________________ Gidan su Hajiya Lantana(Kawar mamana) na nufa,da sallama na shiga gidan, hanyar da zata sadani da kofarta na nufa, da yake su biyu ne, A gidan ita da Abokiyar zamanta Laraba, sai dai ba wani zaman lafiya suke ba,zaman su irin zaman nan ne, na doya da manja,kuma laraba ce Mai matsala,"A tsakar gidan ko nasami laraba, tana daka a turmi tana wakokin ta na habaici,,duk da ta ji sallamata Amma sai tayi banza dani ta Cigaba da aikinta,Da sanyi na gaidata da girmamawa,sai dai wata uwar harara ta zabga min, Domin tasan inda wacce nazou wato lantana, shine bazata amsa min sllamata ba,"Sai ma Kawar da kanta da tayi gefe cike da masifa," "Shiyasa ma taki ta amsa min sallama ta da gaisuwa,Sum sum na wuce nikam,Harara ta bini da shi tana cewa munafuncin banza irin cuta da babu asali!"An kullo bala'i an kawowa oniga!"Komai nisan jifa dai kasa zai dawo.." "Bance da ita komai ba nidai!Duk da naji zafi araina sai dai ba sa'an yina bace ina girmamata Kuma Abokiyar zaman qawar mahaifiyata ce, ita ce uwargida agidan tana da yara har jikoki,Bazan mayar mata da martani ba,Amma na lura Sam batasan ciwon kanta ba irin ballagazayen matan Nan ce Domin Bata daukar girman ta."gashi dai ko yanzu ta nuna(Gaskiya ne akwai Mata masu halayen laraba basa Amsa Sallama muddin ba wurin su ajazou ba,A kiyaye Wannan dabi',un jahilai ne) "Daga cikin dakinta ta jiyo Ina jera sallama,Da fara'arta ta tarbeni sai da na hango haurenta na makka dake walkiya kamar zinare abakinta ya bayyana,da ladabi na gaidata, amsa min tayi, tana cewa Yawwa Nadiya,Ya Innarei!"Shigo daga ciki,kujera ta nuna min afalon na zauna."Duk dai kuna lafiya Nadiya!?." "Lafiya qlaw,Hajiya da yake hakan yaran gidan ke kiranta." "Nace daman mama ce ta aikoni tace agaishe ki sannan kibata saqon.." "Allah sarki,Dan Allah Nadiya ki ce mata tayi hakuri daman Ina jiran dawowar yaran nan, ne daga makaranta,Sai na basu sukai mata,Amma Ina zuwa..."Tashi tayi ta fice uwar dakinta....Dan madaidaicin falonta dake kallon Daman falon ta shiga,Wanda ke zuba kamshi komai atsare kamar wacce bata da yara,A raina Ina jinjinawa tsaftarta..."Dawowarta ne ya dawo da ni hankali na."Murmushi nayi Ina sadda kaina k'asa." "Ta ce Karbi Nadiya kirga ki gani nawa ne!?" "Amsa nayi a nutse na kirga su yan dari biyar_biyar ne,kimanin naira dubu goma."Daga kaina nayi na dubeta nace Hajiya dubu goma ne cip." "Yawwa,Nadiya ki kaimata,ki gayamata wasu ne suka kawo mana tsaiko! basuyi zubin adashin su ba,ko yanzu ma ajikina ne na cika mata kudinta tunda lokacin kwasar adashenta yayi, kafin sukawo nasu zubin!"Kinsan Mutane basa da Alkawari!"Sai dai Hakuri kawai!" "Murmushi nayi nace to Hajiya zan gaya mata,Allah ya sauwaqa ya taimaka, su Saudat ba'a dawo ba ko!"Na tambaya." "Ameen nadiya....Eh saudatu Bata dawo ba Abokiyar yawonki, ana can makaranta,jiya fa take kirana awaya waai anfara koya masu yadda zasuyi allura,nace lalle sai anyi malamar asibiti sarkin kaudi, sai ku shirya Nadiya afara koyo gareku mukam mun yafe...Hajiya tace tana dariya..alokacin da ta bude katou firijin din ta na kwance,wanda yake cike da kayan sanyi..kunun aya,da zobou da kunun zaki ta dauko min roba uku 'yan talatin tasa a leda,ta miko min."Tace Gashi Nadiyatu NAGODE ki gaida Innerie "Da murna na amsa Ina godiya cike da ladabi saboda Hajiya akwai mutunci ga kyauta,Abinta na kowa ne,Shiyasa yan uwan miji,da makota duk ta amshewa laraba su wacce ke ganin maganin mallakar miji da Mutane ne tayiwa kowa ita yakeso da yaranta."Batasan cewa kyautatawa nasa Komai arayuwa," "Har kofar gidan Hajiya ta rakani tana bani sakon gaisuwa wurin mamana."Ni Kuma Ina kara gode mata tare da Bata sakon gaisuwana zuwa ga Saudat idan sunyi waya, saboda Ni ban ma taba rika wayar kaina ba asalima duk gidan mu Babana kadai ke amfani da waya."Bare na Kira kawayena," "Gida na dawo Ina munna na mikawa Mama sakonta tare da nuna Mata alheran da Hajiya tayi min." "Mama tace Allah ya saka mata da Alheri...Lantana akwai mutunci Shiyasa zaman mu ya daure da ita akwai kirki, Kuma batada munafunci Shiyasa nake sonta..."Mama tace cikin harshen nan na hausarta da Bata gama zaunawa abakinta sosai ba, "Ameen nace."Amma Azuciata Ina tuna kazafin da Kishiyarta laraba tayi Mana,Sai dai Banda halin sanar da mamana komai akayi,Domin tun Ina karama ta horeni Akan k'aramar magana, da kawo Mata gulma da sauran kaji ka Gani, Sam Bata saurara kuma da zarar na fara fad'a Mata zata kwabe Ni tare da min fad'a akan ba halin kirki ba NE,"Shiyasa ko Yanzu nayi shiru nabar zancen Dan Nasan gwaleni zatayi," "Mama Tace"Bani zobou kinyi zaune kina tunani kamar Mai lissafi...." "Murmushi nayi tare da kallon mamana cike da kauna.. " "Nan muka dinga shan zobou,Mama tace adashe ne na kwashe...Ina son in ba malam kudi aqara sayo min kayan Nan.."Saboda naga magi da mangyada sunyi qasa kinga babu dadi,azo sayen kaya babu su." "Haka ne mama Allah ya kara kawo kasuwa.."Nace Ina kurba kunun Aya," "Ameen,Ina son na baiwa malam dubu biyar ya qara wurin biya maki kudin makaranta." "Allah sarki Mama NAGODE,Allah ya bani abinda zan muku nima..." "Kedai Kice Allah yaqara tufa asiri kawai nidai fatana kiyi karatu Kuma ki rike addini da *TABIYYAR* da muka baki."Ko yanzu Mungode Allah domin daga ni har malaam,muna da sana'ar da muke tufawa kanmu asiri da ita Kuma akullum muna korewa bakin mu gudaji dai dai gwargadou..." "Gaskiya ne,mama Allah yakarou arziki,Bari na d'aura sanwar dare naga lokaci na tafiya."Nace tare da azamar tashi na hura wuta." "Mama tace"nima dai bara na kulla manja da magi da sauran kayan yajin nan kafin ki wuce Islamiyya."Yau naga cinikin ma yayi sanyi yara sun dan tsakaita shigowa to babu kudi ga Mutane sai addu'a."Inji mama "Nace haka ne mama ko d'azu da safe Islamiyya mallam yace yanzu kusan mako daya Yana mita akawo kudi makaranta,Amma kowa shiru saboda gari yayi zafi!" "Nan dai muka cigaba da aikin mu muna fira saboda mamana ita ce babbar Aminiyatah batayi karatun boko ba,Amma ta kwankwadi na muhammadiya,Shiyasa take da ilimi da wayewa na ainihi wayo Addini."Domin macece da taso gidan malammai batada wata makosa arayuwarta,"Magana Daya da biyu ta ambaci sunan Allah ko wa'azi." Mallam Balarabe da abokinsa Mallam musa ne atsaye suna tattaunawa dangane da zuwan Nadiya makaranta da yake Dan gidan malam musa Yana aiki a jami'ar ta shehu shagari da ke garin na sakkwato."Takardun nema min gurbin karatu na aji daya ne."A hannun baba na."Wanda Saddik ya kawo abaiwa Baba na shine mahaifinsa Mallam Musa yaba Babana."Tare da gaya masa Saddiq yace "A tura ni makaranta mako Mai zuwa Domin kuwa dadewa daliban sun fara karatun zango na daya."Lambar wayar Saddiq Baba ya karba Yana kara godewa Abokinsa Mallam Musa abisa namijin kokarinsu."Daga Nan sallama sukayi Baba ya nufo gida." "Bayan sallar Isha,mun kammala cin abinci,Baba yace Nadiya shiga dakina kina ganin takardu ki dauko min su." "To,Na amsa da toh tare da cika umurnin Baba." "Na kawo masa yace"Ki karanta ki gani Takardun ki ne,jibi zakije makaranta."Idan an kara shiryawa "Da murna mama tace madallah, Allah abin godia Mallam wato yaron nan Saddiq ya samo mata adimishan (Admission)din!?" "Ni kuma murna kawai nikeyi bakina yaki rufuwa sai jera Alhamdulillahi nakeyi azuciata."Ina ta Duba Takardun fuskata awashe bakina kuwa tamkar gonar auduga."Ina dariyar Mama "Baba yace"Ay Innerie dazun Nan Mallam Musa ke bani su,Yace Saddiq din yazo to kai tsaye ne,Tare da abokan aikinsa ne sunzo ko wani taro ne a kwalejin can ta Adamu Augie." "Oho,na gane makarantar, Nan kafin akai asibiti babba ko,Inji mama." "Eh ita,Wai suna sauri ne Shiyasa, malam Musa ma yace saddikun yaso mu hadu Amma dai yace abani lambarsa da zamu Kira kuma yace idan Nadiya taje da ita zata iya kiransa." "Allah sarki gaskiya yaron nan akwai kirki....Inji Innerie,ta Kara da cewa to kinji ko Nadiya ki rikesa ki masa biyayya yayanki ne."Kuma nasan ke da shi duk Kuna da hankali da sanin ya kamata Kinga bakisan Kowa ba sai shi," "To mama in shaa Allah."Na Bata Amsa Ina murmushi." "Baba yace Kuma kunga cikin ikon Allah yace gwamnati ta biyawa dalibbai kudin makaranta,Yanzu kudin da zamu bata bazasu wuce dubu ashirin ba ayi duk abin ake buqata," "Mama tace Haba dai mallam masha Allah gaskiya naji dadi Allah Mai tufin asirin bawa, Nan ta kwance gefen Zanenta,kudi ta fito da su,ta kirga sannan tace malam ga wannan dubu biyar ne,akara ayi mata sayayyar daman dazu na kwashe adashena na gidan lantana da na fada make kwanan baya, wadannan ragowar kuma gobe kasuwa ayimin sayayyar kayan cefane kamar yadda aka saba Amma Ina da ragowar,kuka,kanwa,da barkono,su bada suba,Uw na manta da gishiri mallam" "Dariya Baba yayi yace da kin barsu Innarei Ni kaina na hada dubu goma sha biyu Kuma Mallam Musa ya bani dubu uku tun shekaranjiya."Ke ga sai ai Miki cefanen Sana'ar ki," "A'ah malam ba komai ai yiwa kaine da kai da kaya duk mallakar wuya ne, Allah dai yaqara tufa asiri."shima mallam Musa Allah yasaka masa da Alheri." "Ameen nace Ina kallon iyayena cike da tausayin su...hawayen da nike kokarin hadiyewa ne suka kwanta a fuskata."A hankali na share su kasancewar dare ne."Nace Baba!"cikin sanyi naqara da cewa Mama NAGODE Allah ya sadaku da gidan aljanna yaqara tufa asiri."ya bani ikon muku Biyayya," "Ameen,Sukace Dukkan su,Baba ya kalleni yace"Kinga dubu goma zan ba Innarei, gobe kije kasuwa kisayo kayan abinci da abubuwan da kike buqata."Dubu biyar ki rike hannun ki,Dubu biyar Kuma naji ance malammai nacewa ku kawo kudin ko awut(handouts)sai ki dinga saye." "Dariya Baba ya sani Nace to Baba NAGODE," Duk kudaden Mama ya baiwa ta ajiye,"fatan su Nan dai zuwa jibi na gama komai na wuce makaranta." "Tashi nayi na basu wuri suna ta hirar su."Ni Kuma dakina na fada envelope din da nake boye documents dina na dauko na zuba Takardu na da baba ya bani."sannan na kwanta Ina ta tunanin yadda zanyi rayuwa a jami'ar tare da tunanin irin halin da zan shiga saboda Ban taba nisa da iyayena ba idan dai ba hutu naje garin kakanni na ba dakin gari."Kasancewar makarantar sakandare ta jeka ka dawo nayi anan Argungu."Da hakan nayi addu'a kwanciya bacci barawo ya saceni." *'Yar mutan Dikkawa ce* 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *SHAFI NA UKU* _____________________________________ "Tunda misalin karfe goma na safe na shirya tsaf ciki riga da siket na atamfa super faro kalar miyan goro da fari kayan sun amshi jikina sosai,hoda da man baki na shafa da yake Ni ba ma'abociya son kwalliya bace,nayi kyau matuka,katon hijabina na islamiya na sa ruwan kasa tare da takalmina na roba,Kudi na amsa ga mamana da yake tun kafin baba ya fita kasuwa nagama lissafin komai da zan saye." "Shiyasa Ina amsar kudin na nufi hanyar kasuwa,Mama tayi min adawo gida lafia,Daga gida banyi wata wahalar tafiya ba, Na samu napep bakin titin makarantar nan shehu kangiwa."Tsayarda shi nayi kana na Shiga, a hanya ya samu wasu yam mata biyu wanda da ba zasu wuce sa'a ta ba,sunci kwalliya, riga da wando ne sanye ajikin su Wanda suka kame jikinsu, sai Dan karamin gyale da kowaccen su ta yafa,Duk surar jikin su abayyane take,kallo daya nayi musu na Kauda kai!"Mai napep sai kallon su yake Yana washe baki Domin irin sune suke nema."Daga ganin su suma dallibai ne Domin handouts ne rike ahannunsu sai jaka da suka rataya(Wankan gefe)." "Tunda suka Shiga adaidaitan sahun muka gaisa da su ban kara bi takan su ba!",firar su kawai sukeyi ba kunya bare tsoron Allah firar samari suke da malammai(lecturers)...Haka dai muke zaune dasu wannan tace ke yau wane ya sayo min kaza munci, wane yayi min kaza,Kice wane ya kawo maki abi kaza gobe...nikam mamakin su nikeyi kamar ba mata ba!?" "Ba hankali bare nutsuwa da kamun Kai,Suna aikata zantuka banza kamar marasa *TARBIYYA* wata zuciyar nace min aykam basuda *TARBIYYA* da gani....wannan rashin kamun kai yayi yawa."Allah dai ya shirya nace azuciata"...Dai dai nan aka ajiyeni babbar kofar ko kasuwar kudinsa na tambaya yace naira dari,kudin na bashi ya wuce da su..ko ajikin su suna fira suna shaan rake ga ledojin marhaba super market cike da kayan kwalaam ajikinsu,nikam da mamaki nabar wurin..." "Addu'ar Shiga kasuwa na karatou kamar haka" _LA ILAHA ILLALLAHU WAHDAHU LA SHARIKAA LAHU LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU YUYYI WA YUMITU WA HUWA HAYYUN LA YAA MUTU WAHUWA ALAA KULLI SHAI'IN QADIR_"sannan na daura kafata na shiga a nutse na Fara abinda ya kaini har na kammala duk sayayyata."Dan dakou na nemo ya tayani daukar kayana bayan na kammala sannan na nemi adaidaita na dawo gida." "Mamana ta Duba duk kayan da na sawo a kasuwa,daman su gari ne da indomie da sabulun wanka da ta wanki sai karamar tukunya da risho sakanhan na samo masu kyau na sayo, da sauran abubuwan da ba za a rasaba."Ni da mama sai munna muke tana sa albarka."Tace sai Baba ya dawo anuna masa Kudi sunyi albarka,nikam murna ce faal azuciyata." "Da yamma bayan na idar da sallata ta la'asar Kuma na gama aikina sarai shirin zuwa Islamiyya nayi." "Sallama nayi da mama na wuce,A hankali nake tafiya kaina kasa sai sauri nake saboda karfe hudu harta gota banaso na makara Domin Nice Amira wato (shugabar dalibai mata)Kuma malamar na kasa da ni, kusan aji biyu nakewa karatu bayan anyi min nawa."Bana sanin inda nake jefa kafata saboda saurin da nake gashi daga gidanmu zuwa makaranta zanyi tafiyar mintuna goma da Dan nisa kadan."A daddafe na isa ko da na Shiga ajinmu Mallam Yunus Yana karatu nan,Nima zama nayi ya karanta min batare da wani korafi ba saboda halin karya dokar makaranta ba hali na bane,Shiyasa yayi min uzuri."Dalibai da dama suna cewa Mallam Yunus Sona yake Amma nidai ban yadda ba sai dai Ina da tabbacin Yana ganin mutuncina Kuma Yana kulawa da ni saboda hazaqa ta." "Malam yunus karatu yayi min, tare da bani umurnin naje aji biyu da uku na fada masu karatu,idan na kammala nazarin karatuna." "Lokacin Tashi yayi anan ne nake fadawa malam yunus jibi zanje makaranta a kwalejin shehu shagari da ke sakkwato." "Cike da damuwa malam ya dubeni yace haba Nadiya meyasa ba zakiyi karatun ki a Nan garin ba!?Naga dai duk makarantar daya ce meyasa zakije wani!?" "A ganina ta cikin gari zata fiye maki sauki kullum kije ki dawo." "Murmushi nayi nace malam Ay ba laifina bane Baba ne ya nema min acaan din." "Sadda kansa yayi kasa Yana nazari tare da gyara zaman hularsa irin (tabanni kasha hadisi) Nan, yace to ba damuwa Allah ya Sanya albarka Amma munyi rashin daliba Kuma malama akusa da mu." "Wani iri naji Nan take idona ya cika da hawaye nace Amin malam nagode." "Bakomai Nadiya zan sanarda sauran malamman mu...Amma dai gobe zaki shigo mana bankwana ko!?" "To gaskia da son nayi gobe na tsaya gida na shirya kayana Mallam, Amma zan shigo da yamma."nace Ina gyara zaman jikata da ke rataye akafada ta kaina akasa,Domin Ina ganin girman Mallam arayuwata." "Masha Allah." "Allah ya kaimu kinji Nadiya." "Ameen,Nagode Mallam nace, Ina kokarin tafiya tare da yaran makotanmu da nake dawowa gida tare da su." "Daaaaaf!Da magariba muka shigo layin mu,Saboda tsayin da mukai da malaam lokaci ya tafi sosai..."Kamar daga sama naji mota tayo cikin mu....sai da mukayi saurin kaucewa!!"Tuni kura ta bademu na mintoci kafin muga gaban mu." _Hasbunallahu wa ni'mal wakil_ Ita ce kalmar da ta fitou bakina..."Tsaye nayi Ina mamakin wanene wannan Wanda duniya tayi wa dadi!" har yake neman kisan rayuka!"A hankali na karkade hijabina tare da janye yaran gefen titi muka cigaba da tafiya Raina na kuna!" "Caaan sai ga motar tana dawowa daga baya."Matrix ce kalar jinin kare wadda tasha bakin gilashin," oda ake mana..."ko kallon inda motar take banyi ba!"na cigaba da tafiya taa."Duk da nasan akan mu ne ya dawo Yana fiiifiiitfit banza nayi da motar."ko hakuri zai bamu oho Amma dai kowanene bamu yafe masa ba!" saboda ya shiga Hakkin mu musamman yaran sun tsorata!"Domin agefen titi muke tafiya amma ya nemi halakar da mu."Jikina sai Bari Yake Dan fargaba!" "Ganin ba zan tsaya ba yasa saurayin fitowa, da hanzari ya sha gaban mu da Mota, Yana min kallon sama da kasa!"Ya fito afusace!" "Yace min ke yar gidan uban waye!?"Da zakiji ana magana ki share,Da hanzari na dago kaina Ina dubansa."wando three quarter da red shirt ne ajikinsa sai katon madubi baki wulik manne a kyakkyawar fuskar sa,saman kansa suma ce baka wulik kwance wadda da ganinta tana shan gyara."Baya da maraba da yaran arna!"Domin Sam baiyi kama da Ahlin Mallam Bahaushe ba!" "Dariya yayi yace "Wow!Kice ke kyakkyawar ce Shiyasa kike wani yanga kina Shan kamshi."Amma Kuma daga ganin wannan kodadden hijab naki na fahimci iyayenki basa kula da suturar ki!"Daga bana sai bad'in ba d'ad'a!" "A hasale!nace Dan Allah bamu hanya...!" "Anki abaki hanyar yar rainin wayo! wallahi naso na koyarda ke darasi sai dai ke Mai kyau ce,Kyaunki ya fansheki Domin yayi tasiri a zuciyar JAWAD,daman naga kina karkade wannan tsumokaran hijab din na kine wanda daga gani yasha omo da sabulu,Shiyasa nazo na baki Kudi ki yanko sabon yadi...Sannan ki sani da titi da gefen titi duk mallakin mu ne...saboda haka ki san inda zaki tafiya keda Allah ya daurawa tafiya a kafafuwa..."Kudi ya dauko a aljihun wandonsa Yana bani." "Amsa nayi Ina juya su sannan na dubeshi ahankali cike da kunar rai!Nace bakada abinda zaka bani Wanda ubangiji bai bani ba...na lura daga ganinka ba kasan muhimmancin Dan Adam ba KUma bakada TARBIYYA, Naga kana shiga hurumin Iyayena me sukayi maka da zaka zagesu,da kasan darajar naka iyayen na tabbata bazaka wulaqanta na wani ba!"Sannan titi na yadda naku ne amma kasani anyi gefen titi Domin irin mu bayin Allah...Ayshi arziki ba'a tutiya da shi,Domin na Allah ne, idan yaso yaba mutim ko Kuma ya amshe kayansa,Dan haka ka karbi tsiyarka bana bukata!!!!"Nace tare da watsa masa kudinsa a fuska Nan suka zube aqas, na juya na kama hannun yaran Raina abace muka wuce zuwa gida." "Kallona yayi tsaf Alokacin da nafara tafiya, kana ya kalli Jikinsa!" da kudin da ke kasa,mudubin idonsa ya cire Yana mamakin wacece Ni da na bashi kunya har Mutane na kallonsa suna shewa!".....Idonsa suka kad'a sukayi jajur...zuciyarsa na masa suya!"A fili cewa yayi lalle kin tabo ruwan dafa kanki Ni JAWAD za akira da maras *TARBIYYA!?*"meye take nufi kensn taci bulus!?" "Kudin ya tsallake ya barsu nan wurin, mota ya nufa ya fada cike da bacin rai!"Da matsanan cin gudu yabar unguwar @360 ya isa gidan su,Dakinsa ya fada Yana kaiwa da kamowa mafita yake nema yadda zai gasawa yarinyar Nan aya a hannu."lalle zai nuna mata shi din maras *TARBIYYA* ne kamar yadda ta jefeshi da kalmar." "Bayan JAWAD ya wuce,mutanen da ke zaune gefen titin wadanda akai komai akan idonsu suna kallo,sune suka kwashe kudin suka raba,sukan gaba ta kaisu gobarar titi." "Ko da na karaso gida mamana tana alwala magrib,Kallon tuhuma ta bini da shi,Shiyasa na Dan saki Raina kar ta fahimci me nake ciki." "Addu'ar kammala Alwala naji tana karantouwa kamar hakan" _Allahumma ja'alni minal tauwabin waj'alni minal mutadahirrin Allahumma Amin_" "Kallona tayi ta ce"Ina kika tsaya? meyafaru? naganki hakan?,Ajere mama ta jefo min tambayoyinta."fuskarta adaure "Sakewa nayi nace mama daman malam ne ya Dan Tsayarda Ni Ina gaya masa jibi zanje makaranta,shine yake min nasihohi har Lokaci ya kure min har fa nuna min yayi wai sai sun yi rashin dalibar da ke rage masu aiki!"Shi ne naji ba dadi Kuma Naga magrib ta gabato bana gida nasan zakiji ba dadi." "Ajiyar zucia mama ta sauke tare da gamsuwa da maganata,kana tace Allah sarki to Mallam yayi hakuri Domin koni zanyi kewarki Nadiya." "Murmushi nayi na Shiga daki kayana na ajiye na fito Domin Alwala yayinda mama ta tada sallah." "A kasan zuciyata haushi da takaicin Dan iskan yaron Nan nakeji maras *TARBIYYA* "Toufaah kubiyoni Domin Jin yadda zata kaya😊 *Yar mutan Dikkawa ce* 🌲🌲 🌲 *TARBIYYA*🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *SHAFI NA HUD'U* _____________________________________ Kayan da na wanke tun safe, nake ninkewa mama tana tayani kamar nadin nan na guga saboda wutar layin mu ta lalace kwana biyu muna fama!,Baba ne yayi sallama." "Amsa masa mukayi dukkan mu cikin fara'ah."muna masa barka da zuwa." "Jikkar nan da ake Kira "gana most go" ce rike ahannun sa da ledar kosan wake da yake sayo mana." "Da munna na amsa Ina godiya Domin nasan wadda Baba yasaya min ce nasaka kayana."Shi Kuma kosan mama na baiwa." "Kayana na kwashe duka na Shiga daki Ina shirya su acikin jakata sabuwa da Baba ya kawo min, tsaf na fake kayan da ba wani yawa ne da su ba, duka kala bakwai ne sai hijabai uku hadi da nq islamiyyata suka zan hudu Kasancewar tufin asiri ne da mu ba wata yalwatacciyar sutura ce da ni ba,Kuma ba wasu manyan atamfofi ne ba,yawanci duk roba ne."A haka na kammala duk shirina da duk wani Abu da nake buqata." Domin gobe ne tafiya ta makaranta da yardar Allah." "Alkawarin da na daukarwa malam yunus ne,na cika saboda ko yau da yamma nayi naje makaranta,Dalibai ajina nagawa karutu tare da masu bankwana,Addu'oin fatan Alheri suka dinga kwaranyo min,har sai da naji Ina alfahari do a kaina."sai dai fatan samun aljanna nayiwa jigon rayuwata wato iyayenah."Domin sune suka daurani akan turbar gaskiya Kuma suka jajirce akan kula da lafiyata."Su ma dai acikin addu'a na saka su." Bayan antashi na doshi inda naga mallaman mu suke taruwa,Da ladabi na gaida su," "Mallam Isma'eel ne ya amsa Yana fadin Nadiya Ashe gudun hijira zakiwa makaranta." "Malam bilya ya amshe cike da raha Yana fadin to malam kasan ta zabi karatun yahudu..." "Murmushi nayi tare da sadda kaina kasa." "Dariya malam yunus yayi yace ba wani ilimi dai Nadiyatu zataje nema kowa Kuma anan ya nemoshi." "Daga Nan dai Hada baki sukayi dukkan su suna min nasiha tare da fatan alheri akarshe naira dubu biyar malam yunus yabani yace hukumar makaranta ce tabani Kuma suna min fatan samun nasara da cigaba Mai daurewa arayuwata." "Cike da girmamawa na russuna fuskata dauke da kunya Ina zuba masu godiya."Sosai naji dadin yadda suka karramani tare da nuna kulawa agareni." "Nan dai mukayi sallama tare da bankwana da su sai da wani hawaye Mai zafi!"Ya sauka a fuskata!"Dama ance sabo turken Wawa!"Da hakan nabar Islamiyyar mu, ta Nurul Huda Ina qaramata kallo kamar bazan dawo ba!"Jikina yayi sanyi lakwas tamkar wacce kwai ya fashewa ajiki!"A haka na tafi!Ina kewar dalibaina da mallamai na masu Sona,Tafiya nake Ina tunani barkatai araina,Ban Ankara ba sai ji nayi kimisss naci karo da Abu duk da dai nasan ahanyata nake." "Cikin fargaba na dago kaina!"A tsorace Dan na dauka ko icce ne jin abin bai motsa ba!" "Sai dai amaimakon naga abinda nake tunani sai mutim na gani tsaye ya hade hannayensa akirji Yana kallona!"A gadarance!" "Tsaki nayi nace Mallam Kai kuma daga Ina!?" sai naga yauma akan hanyata nake!" "Mai kyau kenan kina tunanin lafiyace zata kawoni acikin rayuwarki,Ay baki neman zaman lafiya arayuwarki!"Tunda har kika kirani da maras *TARBIYYA* kisani wallahi na dauki Alwashin ko ke Yar gidan uban waye agarin Nan Kuma ko waye ubanki saina wulaqanta ki!"Sai nayiwa rayuwarki Karan tsaye wannan Alqawari ne na daukarwa Kai na!"Ke har kin isa kisa Mutane suyi min shewa!!!!"Me kike taqama da shi Kudi,mulki,ko Kuma me!?"Dole Kiyi nadamar kirana da hakan Alokacin da Zan nuna Miki Waye Ni,sai ki koyar Dani TARBIYYA TUNDA iyayena Basu min ba!' "Ko kallonsa Banyi ba na cigaba da tafiyata!!!"Saboda Naga matashin Nan Yana neman zubar min da mutunci agaban mutanen da ke ganin mutuncina akoda yaushe!..." "JAWAD ko qara cimmin yayi yace ki rubuta ki aje sai Naga bayanki!"Ke sai kinyi nadamar mayar min da martani masu zafi!"Wannan kashedi ne na karshe nazo nayi Miki saboda maganarki tayi min zafi har kin isa nayi magana kibani amsa to mu zuba Yar talakawa!"Zaki gani!"Kuma wallahi sai nasa matsiyatan iyayenki sunyi nadamar haihuwark......" "Ban Bari yaqarasa ba!"A zafafe kamar zakanya!Na dauke shi da wani wawan mari...zuciyata na kuna!" na qara mashi wani..."tuni ya dafe kuncensa!"A kidime ya kalleni!"Yana kokari magana naqara zabga masa wani Wanda sai da yaga sararin samaniya nayi masa yawo kokarin kirga giragizai yake Amma ya kasa sai bishiyoyi da ke masa yawo!"Nan take kansa ya Sara!"Idonsa da sukayi jajur ya zuba min manyan idanunsa ya dafe kuncinsa da yatsuna suka kwanta masa shaaar!!!" "Cike da gadara nace Kai wane irin mutim ne da baya da Imani da tausayi kaci zarafina na kyaleka hakan bai isheka ba!"Sai ka sanyo iyayena!?"To kasani nasan darajar iyaye na akan su Zan iya aikata komai!"Me ka dauki kanka!"Me kake da shi!"To barikaji bazan taba Bari ka wulaqanta Ni ba,Domin baka komai abakin komai arayuwata haka kawai me iyayena sukai maka!!?"kasani ko da me kake taqama shi,Kudi ko mulki to fir auna da qaruna sunyi nasu zamani sun shude bare Kai,kasani komai kake da shi wasu sun fika!!"An kiraka da hakan Domin shi ya Dace da Kai duk abinda zakayi Ina tare da Allah kuma ya fika!"Shi ne yake tsaya min aduk lamurana." "Kallon banza nayi masa nakara da cewa kaje ka koyi halaye da dabi'un kirki saboda naga rashin da'a ya yalwaci rayuwarka!!!!"Fuuuuu na wuce kamar Zan kade shi nabar wurin cike da bacin rai na isa gida,A kofar zauren mu na tsaya na kimtsa kaina da saita hankali da zuciyata da ke tafarfasa!"Kana na Shiga gidan tare da tuna kyautar da malamai sukai min sai naji farinciki araina na manta da komai." "JAWAD ko mutuwar tsaye yayi!"Rabon shi da amareshi har ya manta!"Abi da mom basu taba marinsa ba!!"tunda ya taso!"Shi bai masan zafin mari ba..Amma yau yarinyar da ya tsana itace ta zabga masa Mari har uku."shafa wurin yayi kowanne gefe yatsunta biyar ne da Allah (SWT) yayi mata suka kwanta masa a lafiyayyar fuskarsa."sake kallon Inda tabi yayi!"gefen lebensa ya ciza!"Tare da dunkule hannunsa,iska Mai zafin gaske ya furzar!!" "A hankali yabar wurin jiki a sayaye...Domin yau kam karya taqare!"Wanda kewa mata wulaqanci yau macce ta wulaqanta shi!" batare da ya waiga ko Ina ba akan kunya!"Kai tsaye Mota ya Shiga da kyar ya iya Kai kansa gida,Saboda zafin Marin!"Ga kansa dake masa ciwo!"lalle da ce yau Yana wata harkar banza ko shaye-shaye da wuce club ko zai rage zafi!"Da zogin da zuciyarsa ke masa!"Sai dai ya daukarwa Abi Alqawari ba zai Kara aikata hakan ba...Hawaye ne suke azuba a fuskarsa,rabonsa da kuka tun bayan rasuwar Abi.." "Mamakin yadda akayi har ma yabarta tabar gurin bai babballata ba!yake"Babu Wanda yataba cin galaba akansa kamarta!"yanzu ko mom tana marinsa bare wata matsiyaciya maras gata kucaka kwailar yarinya kazama da ita!." "Murmushi yayi tare da shafa fuskarsa,a fili iska Mai zafi! Ya furzar yace zaki gane kurenki Zan dauki fansha akanki!"Tabbas zakisan waye Muhammad Jawad."Daga gobe Zan fara binciken ko ke waye!"Daga nan Zan d'ana miki tarkon da zakiyi kuka da Ni!!!!"Cigaba yayi da safa da marwa a kayataccen Dakinsa Mai tsarin gaske!"A karshe ban daki ya fada ya dade Yana sakarwa kansa ruwa,daga bisani ya fito masallacin kofar gidan su yaje domin idar da sallar magrib da Isha saboda Duk rashin mutuncinsa Baya wasa da ibada,kamar yadda Abi ya koyarda shi."Kwanci yayi Yana shafar fuskarsa!"Da hannu, Yana kara duban tafin hannunsa,Nan take ya zabura...karar marukan ne keta kaiwa da komowa a kunnensa!!!"Kiran mum ne ya shigo wayarsa!"Yana gani ya kyale!"Har ya tsinke akarshe wayar ya kashe duka saboda Baya son kowacce irin damuwa nutsuwa da hutu yake buqata!!"Amma Ina zuciyarsa sai nuna masa hoton yarinyar Baya son gani ya tsana,Har yanzu ita ce laqabe a gilashin Idonsa!!" ************* "Niema dai bayan naci abinci na kammala muna fira da mamana sai ga Baba yadawo daga masallaci Nan ne mama take nuna masa alherin da malammai na sukai min." "Murna yayi tare da samin albarka da malammai na."Kudin ya amsa yace idan naje makaranta, Wadanda ke hannuna suka kare, sai nagawa Yaya Saddiq,idan yazo hutun karshen mako sai abashi ya Kawo min." "To nace,Ina murmushi domin na gamsu da dabarar Baba." "Yaron da yayi sallama ne ya katse mana zancenmu." "Amsa masa Baba yayi!" "Yaron yace"Wai ance ana sallama da Malama Nadiya." "Nan take gabana ya fadi kar dai yaron Nan ne yabiyo Ni har gida!!" "Muryar Baba ta katse min zancen zucin da nake!"Inda yake cewa yaron jeka kace wake sallama da ita!?" "Yaron cewa yayi daman cewa yayi idan an tambayeni nace Mallam yunusa ne daga madaratul Nurul Huda." "Ajiyar zuciya na sauke tare da lumshe idona.." "Mama tace Anya ko!?Lafiya Mallam ke nemanki Nadiya!?"Ba shi yabaki kudin ma kikace min ba dazun!?" "Eh,mama shi yabani su da hannunsa."nazari nake Nima Ina mamakin zuwan mallam yunus na bazata agidan mu da Daren nan!." "Baba ne yayi tari irin nasu na manya yace min maza jeki ki Sanya hijabinki kije kiji Kiran da yake maki watakila akwai dalilin zuwan nasa." "Yadda Baba ya bani umurni haka nayi sai dai Ina mamaki malam yunus agidan mu!"Wanda ciwona kawai ke kawo shi gidan."Da sallama na isa wurin sa bakin kofar gidan mu,tare da gaida shi a ladabce." "Amsa min yayi,tare da cewa Nadiya kiyi hakuri na tadoki da dare ga sanyi k0!?"Mallam yace." "Kallonsa nayi cike da ladabi nace Mallam ba komai.."Duk da ba wutar lantarki akofar gidanmu..Amma farin wata Dan daren sha biyar ya hasko min shi tsaaf...Sanye yake acikin farin yadi Dan Madina dinkin kaftan,sai wandonsa da ya tsallake it's kwarou irin sunna sak din nan,Hulla ce fara tabbani kasha hadisai zaune a kwaryar kansa,yayi kyau matuka,kamar Balarabe." "Ledar da ke hannun sa yake bani Yana cewa karbi wannan Nadiya." "A Dan tsorace na amsa,zuruuuum nai Ina sauraren me zai biyo Baya." "Murmushin da ke Kara masa kyau da kwarjini yayi,yace duk kin wani tsorata ko kin fara tsoron leda ne?"Daman tawa gudummuwa ce,ta mussamman na kawo maki,ki ci da hakuri...."Ba yawa kin San mallamin sai Masha Allah...yace Yana dariyar zolaya." "Haba Mallam ai ka bani dazu hidimar tayi yawa...na katse masa zance cike da jin kunya." "Nadiya kenan karfa ki manta Ni malamin ki ne! to meye aciki Dan nayi maki kyauta,wancan din ta dazun daban ta hadakar mallaman makaranta ce,yanzu Kuma wannan tawace daban ce,,ta mussamman,karfa ki manta ke dalibata ce ta daban da nakeji da ita,ba komai karki damu."Mallam yunus yaqarashe zancen sa da lallausan lafuzzansa nasa." "Nagode Mallam Allah ya saka da Alheri mama da baba na maku godiya sosai Allah ya qarou arziki..." "Ameen...Nadiya Habae!?"Ya isa hakan kinji Nadiyatou.. yanzu dai Ni karatun da ya kaiki nake buqatar kiyi haiqan..sannan Ina Kara Jan kunnenki akan ki maida hankali akan abinda zai kaiki ki guji kawayen banza!"Nasan kina da ilimi Addini bugu da Kari kinada hali Mai kyau."kisani jami'a gidan kowa da kowane, gida ne koyon *TARBIYYA* da halaye masu kyau Kuma gida ne na B'ata *TARBIYYA* saboda duk abinda kike taqama da shi zakaga wani ya fiki shi!" Kuma kowa yayi nasa lokaci."Saboda wasu da yawa sunyi nasu lokaci ya shude."Idan mulki, ilimi,arziki, Kudi ko Kuma talauci kake taqama da shi zaka hadou da wanda ya fika su!"Ina son ki kiyaye Nadiya."Kin dai karanta kin sani kiyi kokari ki dinga aiki da iliminki."A karshe Ina maki fatan Alheri Allah ya kiyaye ya tsare hanya,Zaki iya komawa gida kar aga kin dade!"Nagode ki gaida su umma." "A hankali na dube shi da kyar na iya motsa fatar labbana!"Nace Nagode Mallam bansan Taya Zan nuna maka godiyata ba!"Wasu hawaye ne masu zafi!suka sulalo min afuska!!"Ina jin so da kaunar Mallam yunus Yana ratsa ko Ina na jikina!"Nan take jinin jikina ya karbi sakon Zuciyata Tabbas zuciya tana son Mai kyautata mata!"silar hakan kaunar malamina ta Shiga birnin zuciyata."Ba tare da nasani baah!"Maganar sa ta tsinke min tunani.." "Ya ce Bakomai Nadiyatu yiwa kaine nidai ki kula da kanki da karatunki Kuma karki damu da kowa, saboda samun nutsuwa Mai kyau akaratunki."Karki bi kawayen banza marasa halayen kirki b'ata gari," "To nace muryata na rawa!"Saboda wani kuka da nakeji banason rabuwa da Mallam,ban San mun Saba ba!"Sai yau da muke Shirin rabuwa,Tabbas sabo wani Abu ne Mai GIRMA azuciya." "Shima na fahimci kamar yana jin abinda nikeji sai dai shi nasan na rashina amakaranta ne yake,Domin Duk yanayin fuskarsa da walwalarsa ya rikide izuwa kalar tausayi." Amma ahakan ya dake mukayi sallama da juna cike da wani bakon lamari azuciyoyin mu." "Zauren gidan mu na tsaya na share hawayena!"Sannan na Shiga inda nabar su mama anan na samesu sai dai Baba abinci yakeci...Nan na gaya masu abinda ya kawo Mallam tare da bude ledar da bansan ko meye aciki ba."Domin su gani." "Mama da Baba had'a baki sukayi suna cewa Allah ya saka masa da Alheri."Gaskiya yunus akwai kirki "Bude ledar nayi mayukan shafawa ne da turare biyu masu kamshin gaske sai babban makilin da buroshi,da sabulan wanka masu kyau,Sai kwalin cakuleti daya,Da littafin Hisnul Muslim da tasbaha Mai kyau duk acikin ledar." "Mama to Nadiya ki kula Domin malam yabaki makamin Samun nasara Kinga Hisnul muslim ki rikeshi maganin komai ne Duk abinda ya taso maki arayuwa matukar Kika lazimci karanta Azkhar da sauran addu'oin da ke ciki to bakida sauran matsala,shima tasbihi Salati, Istigfari da hailalah abine mai,ba Dan kinje makaranta kice Zaki ajiye karatu ba,"To karki Soma ADUK inda kike ki zamou Mai tuna ubangijinta,"Mallam ya kyauta Allah ya saka Masa da Alheri," "Ameen nace Ina sauraren jawabin mama "Baba cewa yayi nima in shaa Allahu gobe zan samesu har makaranta nayi masu godiya wannan hidimar har Ina." "Mama cewa tayi" Ya kamata ka tafin Mallam Domin sun kyauta yaba kyauta Kuma tukuici,Tace Kinga Nadiya tattara kayan naki kikai daki, Tashi nayi na kwashe su na koma Dakin Ina Kara shiryawa Kayana,Baba ko kokarin kunna rediyonsa yake." "Mallam yunus ma kasa sukuni yayi,A lokacin da ya koma gida!" tunanin neman mafita yake!"ya dade Yana nazari daga bisani Alwala ya daura tare da fuskantarta Alkibla Domin kaiwa Rabbil Alamina kukansa...."Ni Kuma nace mu da shi duka Rabbil Izzah ya karbi buqatocin mu." Muje zuwa fans...Shin Ina labarin Jawad ko yasamu bacci Mai dadi ko Kuma zafin Marin ya hanashi sukuni?"Hmnnnn mutuniyata faah ta sarkou da cutar so,Shin meke ciwa Mallam yunus towo a kwaryar!?" Amsa na gareku masoya na niece taku Mai kaunar KU har kullum *'YAR MUTAN DIKKAWA* *READ, COMMENTS,AND SHARE*😍 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *SHAFI NA BIYAR* *TUKUICHI NEH GAREIKU" MASOYANA MASU QAUNAR RUBUTU NA"NA CIKI DA WAJEN NIGERIA, HAQIQA INA ALFAHARI DA KU KUMA INA JIN DADIN COMMENT DINKU,GAISUWAR KU TA DABAN CE MY RAHMA,SHATOU DIKKO,DA YACEERAH HINDOU ALQALI,SAI NURATU SALIHU,HASSANA NIGER,RABI'A AMINU,MARYAMA MUHD,MAMAN YASEER DA ANNOUR,SUMEE WAZIRI,KHADIJA KAKA,VILKYN SUDAN,DA DUK JAMA'AR GIDAN NABEEHA AMINU(MARUBUCIYAR SAREENA DA GUDAI)INA GODIYA MAI TARIN YAWA A BISA ADDU'OIN KU DA FATAN ALKHAIRAN KU GARENI,FATANA ALLAH YABAR ZUMUNCHI AMEEN."❤* ______________________________________ "Rana ba ta karya akace...Domin gashi dai yau Allah yayi ranar zuwa na makaranta tazo, na shirya tsaf cikin Shiga ta mutunci da Kamala. gurfane nake agaban Babana da Mamana sunayi min nasiha kamar yadda suke min akullum, sai dai aganina ta yau tasha banbam da ta koyaushe, saboda yadda take shiga tana ratsa min jikina."Hawaye ne ke ta kai kawo a fuskata har suka game jawabinsu...Yaran makotan mu sai daukan kayana sukeyi suna Kai waje wurin Mai napep.."Nasiha,da kashedi,tare da hannunka Mai sanda,ba Wanda iyayena basu min ba, musamman akan na kare mutuncina "Ina share hawayena! nace In shaaa Allah na daukar maku alkawarin ba zan taba watsa muku kasa a ido ba, Baba zan kula da kaina sosai zanyi kokarin ganin nayi karatuna Kuma zanyi amfani da Duk nasiharku. "Albarkaa suka samin tare da fatan alheri,Ina kuka nabar gidan cike da kewar iyayena!"Haka mamana sai da tayi guntun hawaye saboda Ni da ita akwai kaunar juna atsakanin mu!"Baba ma dakiya yayi..Har kofar gida sukai min rakiya tare da fatan alkhairi da samun nasara a karatuna A karshe dai nan muka rabu da su cike da alhini su na min asauka makaranta lafiya." "Tunda muka dauki babban titin da zai sadamu da hanyar Tasha nike goge hawaye!Da suka jika min hijabi!Shishshekar kuka nake Ina sauke wahaltaccen numfashi!"Kamar wacce akayima mutuwa.."Mai napep din da nake ciki Dan Mani,,,dariya yayi yace malama Nadiya adaina kukan hakan."Da yake mun San juna Ni da shi a unguwar mu yake." "Yaqara da cewa Zaki dawo ki samesu da yardar Allah,to kuka na me!?"Kin ma bani mamaki Allah ke da gidan wani zakije watarana ki barsu, kinga ko gara kisaba da rabuwa da su Baba." "Yake Mai kama da kuka!"Nayi nace to Dan ladi na daina,Domin gudun barin abin fade a unguwa." "Dariya yayi yace Hmnnnn Ashe kin gano Domin Ida muka zauna majalisa bama sanin sanda batutuwa ke bulbulowa abakin mu tuli_tuli,babu Mai barin afishi Labari...Kinga sai na manta nayi subul da baka na antaya masu labarin kukanki...."Yaqashe zancensa Yana Dariya." "Nima dariyar ya bani nace rediyo masu jini Ashe Bari mukama kan mu." "Ya ce aike ta daban ce keda kowa ke yabo, Duk fa unguwar mu kece ta daban..."Gaskiya ana ganin kirkinki..."saboda Duk Yan tallar yam matan unguwar nan basuda kirki da mutunci kamar kebmunsan halin kowa...." "Murmushi nayi nace sanin gaibu sai Allah." "yace Hakane Kuma malama," "Ba muyi wata tafiya Mai nisa ba!Muka kawo tashar sokoto,sauke kayana Danmani yayi, yana lodawa a motar da ke layi...kudinsa na ba shi Amma yace ba zai karba ba, Allah dai ya kiyaye hanya da Kuma fatan samun nasara yayi min,Ameen nace da shi Ina kara masa godiya... "Dan kamishon ne yakaraso,da sauri wurina yace malama Bismillah,fasinjoji sun kammala ke ake jira kinzo a nasara." "Nawa ne kudin,na tambaya?" "Dari shidda ne kacal,yace Yana lissafin kudaden da ke hannunsa." "Naira dubu,na Ciro daga jikata,na bashi,canjina ya miko min." "Bayan na karb'i naira dari hudu na,wurin motar na nufa Inda ake jirana,da Addu'a na Shiga,gaban motar mu biyu Ni da wata Yar matashiya,Saura na Baya,Direba kudinsa ya karba ga Dan kamishon,,tare da basa la'adarsa,sannan ya Shiga ya tada motar da sunan Allah,Nan muka Kama hanya,Rutse ido nayi Ina Mai shakar iskar jihata cike da shauki,can Kuma na tuno iyayenah da Mallam,Nan take bugun kirjina ya canja,Idona suka cika da kwalla, Ina dubin ciyawo da itatuwan da muke wucewa a hanya." **********"Wata hamshakiyar mata ce, wankan tarwad'a duk da ba atsaye take ba,Kallo guda zakayi Mata ka fahimci tana da tsayi da jiki,Hakimce take a luntsuma luntsuman kujerun nan, na lada farare tas."Sanye take aciki wani uban leshi ruwan Zuma anyi dinki bubu data Sha uban aiki.."duk gwala gwalai ne ta Sanya tayi kyau matuka sai kamshi ke tashi ajikinta da falon duka.. "kamar wadda zataje GIDAN buki Zaune take tana fuskantarta katuwar talabijin din da ta mahe fiye da rabin bangon katafaren falon,Kallo ta ke azahiri Amma abadini tunanin tilon danta takeyi,Wanda tun jiya take neman layinsa a kashe, iPhone 11 dinta da ke ajiye saman Dan karamin teburin dake gefenta ta dauka,Layinsa ta Kara Kira....Motsin da taji gefen kofar falon ne ya sanyata waigowa ko inna ce ta dawo...." "Sai dai me!?Wanda take kokarin Kiran ne,ya shigo falon kamar an jefoshi....ba tare da sallama ba,Bata ko nuna damuwarta akan rashin sallamar sa ba,da yadda ya fadou falon kamar arne."Kallonsa tayi tana sauke numfashi fuskarta asake." ( _Hattara iyaye a kula da sallamar yara,Da Duk wani lamurana nasu Domin kawo gyara arayuwar su)_." "A hankali ta tashi, cikin kasaita domin akwai jiki Mai kyau ,ta nufe shi.." "Hannunsa ta Kama ta rike tare cewa"Jawad!"Meyasa me ka!?" meke faruwa jiya baka ci abincin dare ba anan!?Kana Ina!?"Meyasa baka d'aga Kirana ba!?"Ka fada min ko dai kana son tuna rayuwarka ta Baya ne!" kasan ayanzu banason ganin ka ahakan!?"Ta tambayesa ajere cike da damuwa..." "Ba komai mom,ki kwantar da hankalin ki,bazan karya alqawarin da na daukarwa Abi ba!" kaina ne yake ciwo alokacin, naji Kira sai dai ban duba ba, Duk fa zatona Saif ne, Shiyasa na kashe wayar, saboda alokacin zafin da nakeji akaina bazai barni na daga waya ba...Amma Yi hakuri mAh!ban San kece baah."Kuma munci abinci agidan su Saif." "Ajiyar zuciya mum ta sauke tare da tausayawa d'anta, kana Tace Meyasa bazaka gaya min ba Jawad!Ay sai nakira Dr.samir ya Duba min kai,kodai ka shaa ruwan sanyi ne ciwon ne yake kokarin tashi kasan yanayin sanyi ne yanzu!!?." "Waro ido yayi,ya ce A'ah mum kinsan ko son ganin ruwan sanyi banayi,kawai dai kaina ne.." "Ido! ta zuba masa kamar tana hango wani boyayyen Al'amari tare da yaronta..Amma cewa tayi ya kakeji yanzu!? kasha magani!?ko kuwa!?nafa sanka da rashin kula da magani!" "Mom karki damu na samu sauki faah,Jawad ya ce"Yana murmushi tare da Kama hannunta zuwa saman kujerin falon,Ya ce nasha magani Kuma ya daina ciwon garau nakejina yanzu....."Inji Jawad Yana safar sumarsa fuskar sa dauke da murmushi," "Jawad....."mom ta Kira shi da karfi! idonta akan fuskarsa!"cike da mamaki!!" "Hannunta ta aza awurin taji yayi karfi!"Kallonsa tayi cike da tuhuma!" "Me nake gani haka yayi jaa afuskarka kamar naushi!" "Raaas!gabansa ya Fadi!"A Dan tsorace ya kalleta!"Tsaf mom ta gama fahimtar wani Abu!"A tattare shi!"cikin ma yanzu kumburin yayi dama sai alamar jaa hakan Kuma ba kwancin yatsun!!!" "Duk sai yawani daburce!Oh!!mom Shiyasa nakeso ki zauna nayi maki bayani..."labarin abin da ya faru da mu ajiya!!" "Kallon tuhuma tayi ma sa tana kokarin zama,lemun da ke gabanta ta kurba kana ta dubeshi." "A gefenta ya zauna,cike da k'warewa yace wato jiya mom munga abin mamaki, muna tare da saif fa amotana zamuje na rakashi ina gidan Anty Bakaran su,To Kinsan a can cikin gari gidanta yakeyi,Muna tsaka da tafiya Bamu Ankara ba!Sai jin kawai mukayi mun kad'e tsofo kiiiiimissss misssss!!!!"A hankali ma muke tafiya mom."Shiyasa Abin yazo mana da sauki."Nan kinkaji Mota ta tayi kuuuuuuuuuuuhhhh.taja ta tsaya bayan nayi kokarin Tsayarda ita."Inji Jawad cike da kwarewa "Kai!Garin Yaya hakan yafaru my son!!?Mom Tace a firgice!" "Mukam mu gannin sa kawai mukayi agaban mota kamar dai an jefoshi,saboda nidai akan hanyar mu muke!" "Sai akayi Yaya!?"Inji mom tana kallonsa da tsoro! "Sai Allah ya tsare!Mom,Domin Ashe Tsohon ya Dan bigi motar ne sai ya Fadi qasa ya Suma saboda fargaba da firgita!" "Nan dai muka fito da hanzari tare da tallafo shi!" Dai-dai nan sai ga wata yarinya da kanenta sun aza hannu aka suna kuka!"Da alamu yaransa ne!"sun ma dauka baban su ya mutu!"Alokacin saif yaje gefen titi ya samo ruwa masu sanyi." "To fa Nan ne Kanen yarinyar ya dinga dukana da yakici a fuska,Wai na tayar masu da babansu,ita Kuma yayarsa kukan takeyi!Da farko sun bani haushi musamman yaron!"sai dai ya bani tausayi alokacin mom baki gansu ba!kamar almajirai faah!!"Nan dai Da taimakon mutanen wurin muka samu aka yayyafa masa ruwa da fifita Da Yardar Allah har ya farfadou." " Tace Wai kun auni arziki!"Jawad, mom Tace cike da al'ajabi, "Haka ne mom kaddara CE, to daga Nan dai mota nace su shiga, muka kai su,aka Duba lafiyar tsohon tare da bashi magani,sai mukayi masu sayayya muka ajiye su agida !."Shine faa har kaina ya Dan soma ciwo da daren Kuma nagaji da kyar ma na sauke saif agida."Kinga yaron duk ya naushe Ni!" "To Jawad Allah ya kara tsarewa Shiyasa nike Kara Jan kunnenka!"akan ka daina gudu acikin gari ko unguwar dake da jama'a,kaga Amfanin hakan ko!"Ay kuwa yaron Duk ya Jima ciwo abu ga aikin kurciya gaskia Bai kyauta ba!Ai da ka Mari banzah!Duk ya jimaka ciwofa!"takarashe Zancen da bacin Rai!" "Mtwsssss....Hakane fa mom to na firgita da tsohon...kar ya karasa lahira,"Jawad yace Yana Kara shafa fuskarsa,azuciyarsa Yana godewa Allah da yasa mom Bata gano shi ba." "Gaskiya anyi arziki,kasan jikin tsufa!"yanzu Gobe ko jibi zan shirya muje mu qara dubashi,tunda kasan gidan,Kasan jikin tsufa!sai muga yanda ya kara da jikin,ko mu da muke da sauran kurciya ajiki gamu sai ahankali bare dattijo!"Duk naji tausayinsa wallahi." "Dummmmn!kirjinsa ya buga tofa Ana wata ga wata!"Yanzu Ina zai Kai mom!!??"Jimnnnnn yayi na Dan dakika sannan yayi Murmushi tare da shafa sumar sa yace to mom,Ba damuwa...Duk da ba wani gane GIDAN nake ba!"Amma yanzu Bari na tashi,Zan shiga inda saif yana jirana, Daga nan sai mu neman GIDAN ko zamu gane."Muje mu gaishe sa." "Yawwa,Jawad ka gaida shi idan kun gane,ko da baku gane ba to kuyi tambaya!Amma bazaka ci abinci bane!?" "Mom bana buqatar komai yanzu idan dawo zanci nayi faam,." "Allah ya dawo min da Kai lafiya son,Akula adinga tuki ahankula....mom tace, "Ameen."sai na dawo!" "Hanyar kofar fita ya nufa dai-dai da shigowar Inna Mai aikin gidan..A tsorace ta gaida shi cikin girmamawa ko kallonta baiyi ba ya amsa." "Komawa Inna tayi da Baya ta bashi hanya ya wuce,sannan ita Kuma ta shigo daga cikin falon jikinta na rawa!"saboda tsoron Jawad,da take! tun ranar da ya sharara mata Mari ya karyewa jikarta Habi kafa!"ta shiga tsoronsa saboda Baya da kirki Ko kadan!!"Da sauri ta qaraso falon,tana gaida Mom tare da Bata Aiken da tayi mata."Amsa mom tayi ba tare da ta kalleta ba!"Inna madafa ta nufa Domin Cigaba da aikinta." Mom ko cigaba da jimamin abinda ya faru da su Jawad take cike da gasgata labarin d'anta( _A matsayinki na uwa ya kamata ace kina iyah banbamce zancen gaskia da karya a bakin yaranki,Ko afuskar SA,Bai kamata ace Duk abinda yara zasu fada ki yarda ba,A gaskiya muna sakaci iyaye sai mun gyara, mu daina karbar zancen yaran mu har sai mun raigaye_) "Shi Kuma jawad din Yana fita,Hamdala yayi da mom, Bata gane komai na gaskiya a zantukan sa"Domin tuni ya kwarai wurin tsara mom,Duk hanyar da zai daurata akai hakan take hayewa!!"Dariya yayi yana tafawa kansa yadda ya tsara zancen karya ya shimfadawa Mom,Daga nan Gidansu saif ya nufa Domin warware Masa zare da abawa." *WANENE MUH'D JAWAD.........?* Ku hakuri da wannan fans banajin dadi!Ina neman AAddu'arku pls!!!!!INA SONKU MASOYANAAH *'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍* 🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *Wannan Shafin kyauta ce,Ga kungiyata Mai albarka,(PEWA)Allah yaqara daukaka mu ya Sanya haske a alqamin mu,ya qarou baseera da kaifin ido,ya Kuma dauramu mu akan turba ta gaskiya Ameen.* _INA YIWA DUKKAN 'YAN UWANA MARUBUTA FATAN ALKHAIRI A DUK INDA SUKE, ALBARKOKIN ALLAH SU YAWAITA GARESU AMIN._ _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *SHAFI NA SHIDA* _____________________________________ "Tafiyar kimanin awa d'aya da rabi da 'yan mintoci,Ta kaimu sakkwato birnin shehu..."Inda ake ajiye mutane, a nan aka sauke mu.."Duk muka fito kowa ya Kama gabansa,masu Kaya,tsayawa mukayi direban ya sauke Mana kayan mu." "Nawa kayan na d'auke na ajiye gefe,ina sallama da mutanen da mukayi Dan fira a motar, da yake mata munfi yawa amotar.."Lambar da Baba ya bani ta Mallam Saddiq ce na Ciro acikin jakata.."Mansura wacce muka zauna tare itama tsaye take agefena tana jiran napep." "Takardar ke hannu na na duba kana na kalleta...."A sanyaye nace Mansura ko da akwai waya hannunki." "Eh,Ina da waya Nadiya."Ta amsa min "Yawwa..dan Allah Kinga Lambar Nan ki taimaka ki Kira min ita." "Ayyah...gashi banida Kati,Kinsan nayita waya amota! Amma Bari naciyo bashin MTN na Kira maki..."INJI Mansura..." "Ba za ayi Haka ba!"mansura Daman Yaya na ne,zai zou daukana to tunda na taso Babana ya kirashi yace Masa na taso, Domin ni Banda waya, Shine Baba yace idan na iso nan sai naje shagon masu sayarda Kati na biya Kudi akira min shi muyi magana."Shine Naga ke Yar uwata macce ce zaifi sauki ki Kira min,Da naje gurin mazan can!"Kinga ga kudin saimu sayi katin akirashi da wayarki." "Murmushi Mansura tayi tace Da ki barshi..."katse ta nayi da cewa ba'ayi haka ba."Ina zuwa." "Nan na tsalka titi naje nasayo katin dari 200 aka loda Lambar na baiwa Mansura tasa awayarta takira kusan sai akira na biyun aka d'aga" "Wayar ta bani,Na karba da sallama,sannan na gaida shi,tare da masa bayanin in da muke ayanzu."Da taimakon Mansura har ya gane."Yaya Sadiq kenan "Amsawa yayi da to Yana zuwa yanzun najira shi,tareda katse Kiran." "Kallona tayi cike da mamaki irin yadda ta fahimci ko wayar ban iya ba bare karata a kunnena irin na Yan gayu...Tace Wai ni na tambayeki Nadiya Sam ke bakya da waya ne?ko kuwa lalacewa tayi!?" "Yake nayi Tace ban taba rika waya ba, ta kaina dai gaskiya Mansura.......,saboda Iyayena basa so Kuma Ni kaina Bata dameni ba...."na Bata amsa Ina dariya." "Hmnnnn...Lalle nikam ban San yadda za'ayi nayi rayuwa babu waya ba Naddy,Ay ko basa Bari Zaki iya riqe abirki aboye!"Tunda su aganinsu wai...Ita ke lalata yara ko."Nikam Ina ganin ba haka bane!" Kin ganni nan wayoyin da nayi sun Kai biyar ba tare da sanin Dattijai ba!duk da mamana ba ruwanta tsohonne dansa ido"Mansura Tace tana juya wayarta da ni ban ma San sunanta ba."Amma da ganinta tana da kyau da tsada." "Numfashi na sauke nace to Allah ya kyauta." "Amma Bazasu maki fad'a idan suka Gane!? "Fad'a fa ai ita mama ba ruwanta!shi Kuma Baba ko ya fara fad'an nasa, mama ke tare min Domin ta tsani bacin ranmu Kinga Ni ko ahabar Zane na!"Yayi ya Gama Idan ya gaji ya fita.. "Mansura tace tana Dariya "Nace to Lalle Mansura Allah dai ya shiryaki,"Baki kyautawa," "Wani kallon banza ta bini da shi Tace to Ameen,Ni Kinga Nadiya zan wuce."Tana Cin chewing gum kallo D'aya zakai Mata ka fahimci Kai ya waye." "Cike da damuwa nace Ah'ah kiyi hakuri har Yaya yazo,mana!nasan idan ya karaso zai K'ara Kiranki Kinga idan kin wuce ya kenan zanyi." "Toufaah Nadiya kin fara ganin Amfanin wayar!"Hmnnnn ai wallahi kije ki nemi waya tun wuri domin tana da amfani bazaki gane ba sai kinje jami'a."Inji mansura tana juya Ido! "Dariya nayi Ina kallonta Nace Nima zan roki Babana alfarma da yayi Hakuri, ya saya min,Domin nima na shigo gari,sanan mansura ai karatun ne ya kawoni garin nan." "Da mamaki ta kalleni da kayana ta kwashe da dariya Tace makaranta faa,Nadiya!?tare da dukan kirjinta"Tace Nifa na dauka ko sakandare ne zakije ko kuma hutu Kika zo."Lalle Nadiya kina cikin duhun Kai!"yoo Nan kayan Yar jami'a ne bako !? Yar trolley din Nan ma bakisan ki saya ba ki da kudin samari!Duk kyaun nan ya tashi abanza!?Ko kinsan yanzu irin KU ke da kasuwa da farinjini."Hmnnnnnn abin mamaki kenan Inji mansura "To wace makaranta acikin makarantun?"Ta tambayeni tana Murmushi "Nace shehu shagari(COE) tare da Bata fuska saboda naga tana son kawo min raini!"da wulak'anci "Kiyi hakuri da ni Nadiya akwai ni da hegen baki da yawan magana ko,Amma Bari Kiji Kinga kayan Nan naki,ta nuna ni.."Sannan Tace karki Bari ki shiga da su ahaka harabar school, saboda akwai Yan sa ido! dan basuyi Kama da na yam Mata wayayyi ba!"Idan Kika kuskura Kika saki layi wallahi zasu gane ke JJC ce,Ke Kinsan Zane..to zasu zanaki tsaf da kayanki da Kuma abinda kinkayi ko Kika fada kowa ya gani."ga Yar kauye Mai zumbulum hijab ta shigo makaranta,"Mansura Tace tana wani kaudi,Nikam cewa nayi to ai kinsan Kowa da halinsa mansura," "Mansura cap KE nifa Nan da kike gani na Yar makarantar ce,"Nan take ta gaya min ita a Danfodiyo take karatu,Daga birnin kebbi take yanzu hakan Tana shekara ta karshe,daga nan zataje bautar kasa idan ta kammala karatu Sannan tayi aure...."Nan dai mukayi ta Fira tana ta zuba har tarihin iyayenta da komai ta labarta min acikin kankanin lokaci,Kiran Yaya Saddiq ne ya shigo,Nan muka Kara fitowa abakin titin ya hango mu Bayan mun dauki wayar......" "Inda muke ya tsaya,bayan ya fito Gaida shi mukayi dukkan mu,Mansura har da wani canja murya.."Amsawa yayi yace mu shigo motar."Nan ya bude but muka zuba kayan." "A rab'e muke cikin motar Mai kyau ga kamshi ni gaba Mansura Baya,wacce tuni ta mutu wurin kallon Yaya Saddiq Domin matashi ne Mai cikar zati da haiba Yana da kyau sai dai baki ne wulik Amma Mai sheki."Shi Kuma sai tambayata yake ya nabaro mutanen gida."Ni Kuma Ina ba shi amsa."Nan yake tambayar Mansura Ina zai ajiyeta."Saboda tun farko na masa bayani itace na aro min wayanta makaranta zataje."Tafiya mukayi Mai Dan nisa ba Mai magana sai sautin wakar ashanty ke tashi a motar asanyaye har muka karaso..." "Cike da yanga mansura Tace Nan ma ya isa yayah sadiq, cikin sigar kissa,nikam mamaki ma take bani yadda take canja salon muryarta kamar sarewa..." "Nan dai Yaya ya ajiyeta bakin kofar makarantar,akwatinta Mai tayoyi baka tajanyo ta dawo gefena Tace Nady zanyi saving Lambar Yayanmu,sai munyi yawa ko Nagode kawata,"Wani iri naji Amma yake nayi nace To...mansura nagode!"Domin na kosa ta tafi ganin yadda Mai motar yasha kunu...karya murya tayi tayi masa sallama tare da ma shi godiya tana lankwasa murya."Bakomai yace da ita."yaja Mota muka tafi."ko kallon ta bai kara ba.'' "Kallona yayi ya watsar a Dan fusace!yace Wannan yarinyar na lura Idonta ya bude!ta cika kaudi da rawar Kai!Daga yau bake ba ita!" "To Yaya Daman a Mota muka hadu nace Ina Wasa da yatsunta!"Bayani yayi min sosai Kan adimishin Dina da Kuma tsarin yadda karatuna zai kasance!"Yace sai gobe zanje makaranta,Kasancewar yau kinga lahadi ne ba aiki sai na karasa Shirin....."kiransa da akayi awaya ne ya tsayarda Zancen,Ashe Baba ne, Yaya Sadiq ya shaida masa na sauka lafiya,Yanzu ma muna hanya zai kaini gidansa har gobe ko jibi idan an samamin daki a hostel, ya gama komai sai na koma."Godiya Baba yayi masa Yaya Sadiq yace''Baba bakomai Nadiya kanwata ce...Nan ya bani Baban muka gaisa da shi tare da Mana fatan alheri....."A hankali muka shigo unguwar da naga an rubuta BAFARAWA ESTATE daga farkon get din."Hancin motarsa ya kunna aciki ahankali yake tafiya....Layi na biyu muka shiga dai-dai wani gida mai lamba sha biyu muka tsaya sai da Mai gadi ya wangale get."Babu abinda nakeji sai fargaba!da tsoro azuciyata!Yau kwana ba dasu Mama ba!"Kayana Yaya Sadiq ya fito da su tare da daukar min leda guda jikkata na kinkimo Sannan ya rufe motarsa Yana gaba Ina biye abayansa." *********Muhammad Jawad Husamaddin Shi ne asalin sunansa,Alh. Husamaddin Shi ne mahaifinsa mutumen kirki ne,Yana da tsayi da Dan jiki,wankan tarwada ne kyakkyawa." Wanda asalinsa ba Dan kasar Nigeria bane,Iyayensa ne suka turo shi Nigeria akan wani muhimmin aiki Shiyasa ya dawo Nigeria da zama,yana kasuwancin safarar Kaya kasa wa kasa, ko gari wa gari hakan Nan." Yana yawan zuwa garin su Domin isar da aikinsa, da Kuma Duba lafiyar mahaifiyar sa."Sai daga Baya ne ya daina zuwa saboda aikin gwamnati da yake,watarana yaje kasar saudiya wurin arkallarsa ya hadou da Hajia Khaltumi wato mahaifiyar Jawad,Tana da kirki sosai Itama Kuma asalin kasar su daya shi domin zama ne ya kawo iyayenta saudiyya."Shiyasa Alh.Husamaddin Bai Sha wuya ba."Wurin aurenta komai na hidiman neman aure da buki a ainihin garinsu khalthumi akayi wato KHARFOUM wato babban birnin tarayyar kasar su ta Sudan din danginsa da danginta suka taro akasha hidima da Al'adun su na aure" Bayan auren su da wata daya suka tattaro zuwa Nigeria ."Domin Husamaddin ya boyewa khalthumi wani abin dangane zuwansa Sannan ya sanar Mata Wasu dalilan zaman shi Nigeria Haka Itama ta dauki alkawarin taimakon sa Domin ganin ya samu nasara a aikinsa." "Sannu a hankali Alhaji Husamaddin ya zama attajiri a jihar kebbi wanda fadi daya za'a ganeshi,Haka Hajia Khaltumi tana kasuwancin gwal Domin shine sana'ar Yan gidansu....A hankali sukayi Kudi naji nagani na Kuma fada."A cikin G.R.A ARGUNGU ya sake Kira katafaren gida Wanda babu kawai ce ba'a zuba ba acikin gidan."Amma Duk daularsu daga su sai ma'aikatan gidan,makota keci da kuma abokan Domin basu samu haihuwa ba dangi akasar sai mutanen arziki." "Ana hakan har akayi shekaru, Ana yawon asibiti da neman taimako da Addu'oi, watarana sai khaltumi ta samu ciki, murna babu wadda basu yi ba!"tare da godiya ga Allah."Akan Wannan kyautar da yayi masu Mutane sai murna suke tayasu,Har ma'ana gidan aka Karo Domin Kula da khaltumi da abinda ke cikinta Kasancewar Alhaji ya fiye tafiye-tafiye kasashen waje,"Hajiya khalthumi da Alhaji Husamaddin na kula da Cikin sosai tare da yawon asibiti yanda ya dace," "Bayan wata Tara Hajiya khalthumi ta haifo danta Shalele...Wanda yaci suna Muhammad Jawad,Tun haihuwar SA ake tururuwa agidan masu taya Munna Duk Wanda yaje BARKAR Jawad da Swiss less ko super ko gizna Yake fitowa waaai tukuicin barka,"An kece raini ranar suna Wanda bazai misaltu ba, saboda mutane ne masu Alheri da son jama'a Shiyasa kowa ke kaunarsu da burin saka masu da abin alheri"kamar yadda sukeyi...Anyi barin Kudi ba'a ko magana."Anci an Sha an wataya,anyi hani'an... Musamman Yan gidan Nabila's fans group," "Hakan Jawad ya taso cikin gata da kulawa tare nuna masa soyayya."Musamman Hajiya khalthumi da batason abinda zai tab'a mata yaronta! "Tun tashin jawad ya taso ba kwaba,Shiyasa Baya da kunya gashi da rashin Jin tsiya Kuma Baya tsoron kowa."Yawan wasan ruwansa ya haifar masa da ciwon nan na nimoniya Wanda tazame masa kuronic sai dai yasha magani amma bata warkewa saboda tayi masa yawa sosai."A ko da yaushe cikin Shan magani Yake Wanda ya zame Masa jiki!"Iyayensa da likitoci na kula da lafiyarsa Musamman lokacin damina da Sanyi!" "Mahaifisa ne tsaye Akan sa shine ma ke kula da shi sosai da Duk wani motsinsa Yana tsawatar Masa,gashi bai cika zama gida ba wacce ke zaune agidan sai abinda Jawad keso yakeyi"Saboda Hjia khaltumi ba ruwanta Duk abinda Jawad keyi tun yarintarsa har zuwa girman sa ita awurinta dai-dai ne."Ta shagwaba shi sosai, Bata son kowa ya tabashi ko mahaifinsa ke masa fada nuna bacin ranta take! bare makota da kawaye,Akan Jawad ta samu matsala da mutane sosai."A kullum Kara nuna masa so da kauna take ga kudade da suke sake masa mussamman mahaifiyarsa."Domin daga kansa basu Kara samun haihuwa ba, Shiyasa akullum take cewa shine Allah ya hore masu ba dole su sake masa ba ya wataya" "Tun firamaren sa har sakandare a Madina international School yayi su acan ne ya samu ilimin addini sosai,Amma Sam Baya amfani da shi."Tunda ya kare sakandare ya dawo gida Nigeria,Nan ya DAUKI rayuwar sharholiya yau Yana wannan club gobe Yana wancan ga rashin mutunci kallo daya zakayi masa ka fahimci Baya da mutunci!"saboda yana iya cin mutuncin kowa Duk da mahaifinsa na iya kokarinsa sai dai Yana Gina rayuwar Jawad,Hajiya khalthum tana roshewa."Bayan sakamakonsa ya fito a Madina Alh Husamaddin yaso yasa ma wa Jawad jami'a acan Domin shi burinsa Jawad ya samu ilimi biyu ko gyaru...Amma fafur!!! shi da khaltumi sukace A'ah Dole Sai U.S zaiyi karatun institution dinsa...ahakan ya hakura ba Dan yaso ba, ya nemawa Jawad gurbin karatunsa na degree a London din,"Da aka kammala Shirin Tafiya yayi masa nasiha sosai da Jan kunnensa sosai akan ya kula da Addinin SA domin Kar ya biyewa abokai marasa jin magana....To KAWAI Jawad Yake fad'i ba Dan zancen yana shiga kunnensa ba!"Domin shi ko a London din yaje ba karatun zaiyi ba, Ahakan aka tattara ya samu biza ya wuce tun zuwansa makaranta ya Samu abokai sharholiyar SA Yake,son ransa ba Mai tsawatar masa."shekararsa uku ya dawo Nigeria hutu."Nan ya hadou da saifullahi da su Al-amin da sauran abokansa ya bude sabon aikin rashin mutunci wai shi ya Waye rayuwar turawa da ya gani acan ita ya dauko yazo da ita gida"momynsa har Dadi takeji Jawad ya Waye sosai Yana harkar manyan Yara,A ganinta duk abinda yakeyi ba damuwa bane,ga wulaqanta mutane da Yake,"Yana zagin manya da cin mutuncin su,Ko ita kanta lallabashi take saboda Idan suna magana muryata CE akasa ta Jawad asama kamar shine ubanta,komai tanayi masa Domin gudun bacin Ransa" "A lokacin da jawad ya dawo Nigeria ya samu mahaifinsa yayi tafiya Abuja wurin wani taron su na kasuwanci shi da Abokan sa."A hanyarsu ta dawowa suka Sami mummunan hatsarin Mota." "Tashin hankali marar misaltuwa Hajia Khaltumi da Jawad suka shiga."Saboda sun san Alhaji Baya tafiyar Mota sai jirgi, Amma akan daukin yazo yaga Jawad da ya dawo Bayanan, yasa ya shigo motar Abokinsa Dr.Hassan da ke kangiwa sai ya fasa jiran visa,"A hanyarsu ta dawowa NE Wannan abin ya afku! Wanda tuni shi abokinsa nan take ya rasu!."shi Kuma aka karaso da shi gida da yake a garin yabo abin ya faru..." "Cike da tashin hankali suka Isa asibitin Uduth da ke Cikin Argungu saboda tunda abin ya faru aka iso da shi Asibitin emergency" "A lokacin da khaltumi da Jawad suka ga Alhaji nade cikin bandeji jina jina Duk ya halaka! kuka suka dinga rusawa."cike da tashin hankali." "Jawad inda gadon ya isa, Yana kallon sa yace Abi Abi!Abbina kaine Haka!!!"Ya Kara fashewa da kuka." "Itama Hajia momy wurin mijinta ta karasa Tace Habibi Haka kaddara tazo Mana Allah ya baka lafiya cikin kuka!!!" "Da kyar ya bude bakinsa ya ahankali ya bude Idonsa da Duk suka kumbura.."Ya ce KU daina kuka!!"Nidai kuyi min Addu'ah!" "Momy Tace Allah ya baka Lafiya Abih...." "Khaltumi Ina ganin da wuya!idan Zan cika alkawarin da na daukarwa iyayena da Yan uwana akan aikin su...Ina son ki taimaka min ki Cigaba da yi min aikin Nan."Duk wasu abubuwan da ya dace kin San su."Haka Duk abinda za'a iya bukata kina sane da inda suke na rokeki karki koma kasar mu har sai kinyi iya kokarinki akai..."Sannan ga Jawad Nan ki kula da shi da Kuma rayuwarsa! idan yayi hankali sosai ya daina rashin ji, ya mallaki hankalin kansa ki sanarda shi ya tayaki aikim nan...Amma sai kin tabbatar ya shiryu Dan Allah"Sannan ki kula min da shi da ki cigaba da tafiyar rayuwar kamar yadda kikaga inayi...Dan Allah khaltumi ki rike min amanarsa da ta dukiyarsa."KU kula da kanku,Haba! KU daina kukan nan mana..."Ya karashe zancen cike da wahala saboda azabar ciwon da yakeji ajikinsa.. " "Khaltumi hawaye take sharewa tana Tace"To Abih ka daina Wannan Zancen zuciyata tana bugawa! In shaa Allah zaka samu sauki ka daina tsoratar da mu kaji!"Inji mommy murya a disashe!" "Murmushi yayi ya kalli Jawad da ke kuka sosai..." "Cike da dakiya yace Muhammad Jawad Dina zo Nan,"Jiki a sanyaye ya isa wurinsa hannunsa yasa acikin na Jawad din yace"Muhammad Ina son ka daukar min Alqawari zaka daina Duk abinda kakeyi zaka zamo yaro Mai addini,Jawad bana son ganin kana rayuwa irin yadda kake ba abune Mai kyau ba!"kasani ina sonka Shiyasa nake kokarin ganin kasamu rayuwa Mai inganci! Kuma ayyukan alherinka sune zasu bimu...Hakan na sharri zasu bibiyemu...Jawad ka daina zuwa club banaso zamanka da Abokan banza da yammata!,ka daina wulaqanci wa manya dama kowa,ka daina rashin mutunci wa manya."Ka rike addininka kayi amfani da iliminka,ka rike ibada ka tausayawa mommynka kaji koh...."Ina son ka samu rayuwa Mai inganci agaba!Domin TARBIYYA tana farawa NE tun yarinta har girma,"Sannan TARBIYYAr 'ya'ya tana farawa NE tun Alokacin neman Aure,"Na horeka ka zamo Mai dabi'un kirki Kuma idAn zakayi Aure kasamu maccen kirki Mai addini wadda zata Gina rayuwar yaranku Akan turbar gaske ta kula da su tazamo masu jigon rayuwa,kaji tsoron Allah jawad!a Duk inda kake karka manta da nasihata!Inji Abiyh Wanda da kyar Yake maganar!" "Jawad kansa ya d'aga alamar yaji,saboda kukan da ya ci karfinsa ganin yadda muryar Abbih dinsa ta disashe!" mahaifinsa mutumen kirki Mai son wasa da raha ne ya koma Haka kaicoh rayuwa!" "Dr.Isma'eel ne ya shigo tare duba jikin na Abi sosai, Wanda akarshe dai office dinsa momy da Jawad suka bishi bayan ya kammala aikinsa,Sunje Domin SAMUN Mafita, Dr. Ya basu shawarar cewa suyi kokarin acikin satin Nan afita da Alh. Husamaddin kasar India Domin Duba lafiyarsa.."Ciwonsa yayi tsanini Yana buqatar sai an duba Wasu kasusuwan SA,"Basu bar asibitin ba sai da aka shirts komai "Kwanan su hud'u da zancen aka samu bizar su ta zuwa kasar India dukan su...Daren ranar da washe gari zasubi jirgin India Alhaji ya ce ga garinku!!!"Sun shiga tashin hankali na tsawon shekara daya basa cikin hayyacin su sai daga bisani suka hakura da hukuncin ubangiji Duk sun rame sunyi baki sun canja saboda damuwa."Nan karatun Jawad ya dawo Nigeria saboda ba zai iya barin mom ba ita kadai!"Itama agefenta Bata iya rabuwa da Jawad shi kadai ne da ita ahalin yanzu."Sonsa sai karuwa yake,ko taso tayi masa fada Bata iyawa,shikam idan ya tuna da hudubar Abi da ta shigesa sai yayi laushi saboda ya daina wasu abubuwan wasun ma ahankali yafara dainawa."A hakan ya kammala Degree dinsa fannin Accounting har yayi service ya dawo,suna zaune da mom cikin tufin asiri tana kasuwancin ta," "Amma shi jawwad har yau baisan aynihin kasar iyayensa ba!"Da dalilin zuwan su Nigeria."Iyayensa sunki su gaya masa sirrin boye."Wannan kenan "A yanzu dai jawad kokarin zuwa masters yakeyi."shi da Abokinsa Saifullahi waziri."Wannan ita CE rayuwar Jawad da Iyayensa ta baya har kawowa yanzun ."Da Yake suna da dukiya Kuma Kullum acikin Kasuwancin kudin suke, shiyasa Bai damu da ko da yafara neman aiki da degree dinsa ba!" *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 [2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA TAKWAS*AYI HAKURI SHAFI NA BAKWAI YANA K'ASA WURIN HADAWA NE AKASAMU MATSALA! _Kyauta ce ga Daukachin 'yan uwa da Abokan Arziki Ina maku fatan Alkhairi Allah yabar zumunchi AMEEN_ _Appee Bufday🎂 Kawar Aminchi Fatty Musa tare da ta hannun damanki Pynah Buhari Ina maku fatan Alkhairi Allah ya qarou shekaru masu Albarka,Da 'yah'yah nagari,Ya barmu tare,Ameen"_ _My Cweet Baby Mufeeda ta ce"A gaida ku Fans Ana tare iya wuya."😍 ______________________________________ "Tunda na farka asuba ban koma bacci ba!"Karatun Alqur ani nayi tare da azkhar."Bayan na kammala wanka nayi da misalin karfe bakwai na ta da yaran saboda nasan cewa suna zuwa makaranta domin jiya kafin su bacci sun sanar min."Da kyar Mufeeda da ke gefena ta tashi can na koma agadon Mufeed Ina tashe shi ahankalin ya tashi wanka nayi masu daya bayan daya."Sannan nace suyi Alwala Amma wai basu iya ba!"Da taimakona sukayi cikakkiyar Alwala...Sai na shirya su tare da saka masu uniform dinsu da suka dauko a lokarsu."Cewa nayi suyi sallah Nan take Mufeeda ta Bata rai!" "Wai ba za tayi sallar ba,''Saboda mumyn su Tace Basu Isa sallah ba!"sai sun girma," "Shi kam Mufeed ta da sallar yayi domin ya Gaya min Abbansa Yana zuwa masallaci da shi magrip da ishaa kawai idan yadawo aiki amma ranakun mako yanayi duka." "Nadai lura dukkan su basu son sallar domin Nan da nan Mufeed ya gama tashi sallar."Ya dinga zuba kamar famfo, banji ko Aya Daya abakinsu Amma Nasha surutu da labarin series da wakoki abakinsu." "Da kyar da wa'azi da Komai na samu Mufeeda tayi sallar nan tana fushi!"Da taga ma har da hawayenta Domin na takurata ne sai da tayi dole! "Bayan sun kammala nasiha nayi musu akan duk Wanda baya sallah Dan wuta ne!"RANAR tashin alqiyama wutar jahannama za'a SA Maras sallah,"Kuma Yara ma suna sallah basai an girma kamar yadda momynsu ta fad'a,"Domin idan sunyi Abbansu da momy za'a sakawa Lada." "Sun tsorata matuka,suna hada baki sukace zasu dinga yin sallah kullum ka da Allah yasa su wuta bal-bal!!"( _Hattara iyaye mafi yawa bama tilasta yara sallah musamman asuba akwai wata yarinya da nagani tace ita Sam batasan akwai sallar asuba ba!acikin salloli,ko da na bincika Ashe Bata taba ganin sanda iyayenta ke sallar ba,A lokacin tana bacci Kuma idan an tasheta ba za'ace tayi ba,Mu sani ana koyawa yara sallah tun suna kanana domin ta shiga Jikinsu sosai basai sun GIRMA ba!"Shi Icce tun yana danye ake tankwara shi ) "Bayan mun shirya tsaf nasa atamfata Riga da zane da hijab masu dama saboda yau ne shigar farko da zanyi Dolene Nima in kure wanka,"Kar araina Ni naji ance Yan jami'a akwai wankan,"Hijabina sabo Shima na zuba Mai yalwataccen girma,daga cikin turaren da malam yunus ya kawo min na bude daya arebian ne jamylah na saka Ni da yaran sunyi kyau sosai acikin uniforms dinsu black and blue,"sannan muka fito falon suna rike da school bag din su." "Anty Jalila muka Fara Cin karou da ita wanda tun jiya Bayan shigowarmu Ni da Yaya ban sake daurata a idona ba! afalon take tana kokarin shigowa Dakin mu, tashin ta kenan Daga bacci tana idar da sallah komawa takeyi bacci sai yanzu ta fito.."murmushin Jin dadi tayi da ta gansu tsaf!!Tare da sauke ajiyar zuciya."ta kalleni tace, Nadiya kice har kun shirya gaskiya kinyi kokarin Shirin su day wuya!.....kullum fa sai sunyi latti akan kafin na shirya su lokaci ya kure!"Tunanin ma nake yanda zan shirya su yanzun!!" "Mufeed oya jeka Kichen ka dauko basket din KU...Anty Jalila tace.." "Mamaki abin ya bani yadda ko gaishe da maman nasu basuyi ba,Ni kadai na gaida ita Kuma Bata damu ba!"( _Zamu ga yara da dama basa gaida iyayensu,wasu har baki suka Gani baza su gaishe da bakin ba,Sai dai suji ana fira su sakou bakinsu su amshe zancen!"Wai anan iyayen suna dubin abin duk yarinta ce, ba za'a tilasta yara ba akoyarda su gaisuwa,"Iyaye na ganin idan sun GIRMA zasu daina................,_) "Mufeed ne ya dawo falon hannunsa dauke da basket biyu ya ba Mufeeda nata."Ya CE momy yau waina mukeso..." "Ni bana son waina doya da kwai Abba zai saya min..." "Nidai waina..mufeed yace Yana ma Mufeeda dariya." "Mufeeda Tace mumy Ni bana so tana kokarin kuka!" "Zo Nan kiji."Mufeeda taje wurin da momyn take zaune...ta wani hade fuska..."Tace Kinga Mufeeda duk abinda kikeso ki gayawa Abba zai saya maki kibar Mufeed Baya Jin magana.."Doya kike so ko!!" "Eh,mumy da Indomie ko Zaki dafa Mana..!?" "Kin jiki da rigama Mufeeda wane indomie Kuma Ana zaune kalau,Kinsan ban samun lokacin dafa maku abincin zuwa makaranta."Wa yayi min bacci wa ya shirya min ku,Mufeeda Tunda aka sakaku amakaranta ban Kara samun nutsuwa ba!"Ni wallahi na k'osa ayi maku hutun Nan ko na ji sarari Ina lokacin dafa indomie gareni idan ita kikeso ki gayawa Abba kubiyata teburin Mai shayi sai asoya maki kinji Yar mama"Inji Anty jalila tana ma mufeeda cakulkuli "Kyalkyala Dariya Mufeeda keyi tana momy...." "Nidai sai saurare da Kallo NE aiki na Ina gefe zaune..." "Yaya Saddiq ne ya shigo ga alamu ya shirya Dan har jakar zuwa aiki ya ratayo a kafadarsa yayi kyau sosai..."A hankali na gaida shi ya Kuma amsa min fuska asake...Yana mamakin yau anyi saurin shirya yaran ko ba'a fada ba yasan nice Dan gimbiyar bata dade da fitowa ba." "Kayan shayi Anty Jalila ta hada daman akwai ruwan zafi!"Tea ta hadawa Yaya da yaran Ni Kuma tace na hadawa kaina ita Kuma dakinta ta nufa Domin tashin ta kenan Daga bacci!"Haka muka Sha sayin da biredi...Ina mamakin Anty Jalila duk da ban waye ba Amma dai nasan a karin safe ana cin Doya da kwai..Wanda na gani zube acikin Kichen dinta Wasu har sun Fara lalacewar Musamman dankalin turawa harda hunhuna "ko indomie katin katin nagani jere ga yaranta naso amma saboda tsabar son jikin tsiya da lalaci bazata iya girkawa ba!"Nace araina saboda koni dai bakuwa Ina son na lasa," "Haka muka gama Karin muka fita,Anty Jalila fitowa tayi tana Mana Allah ya kiyaye!"Sai mun dawo...Domin ta k'osa mu wuce ta tafi zuwa bacci!" "Yaya tambayata yayi na dauko duk takarduna?" "Eh,na amsa masa saboda komai nawa Yana acikin jikata tana GIRMA.. "Sai da muka fara biyawa aka sayawa yaran abinci da yake akwai biscuits da drinks acikin school bags dinsu sai suka had'a..."Daga nan Hanan Academy muka nufa da ke kan titin Ali bagodu...Aka sauke su a makaranta.."Sai hannu suke min suna cewa.....bye-bye Anty,ahakan muka rabu nima Ina murmushi,Yaya cewa yayi na dawo gaba,saboda daman Mufeed ne agaban.."Ni da Mufeeda abayan."Nan na dawo gaban muka wuce," "Tunda muka dauki hanya Yaya Saddiq ke min nasiha akan nayi karatu sosai kada nasa wasa Kuma kada na kuskura ya ganni da abokai barkatai."Ya CE in Sami qawa d'aya wacce na yaba da hankalin ta da kamun kanta kuma wacce ke karatu sosai."Sannan ya Kara da cewa zai samu dalibi daya namiji Mai hankali ya hadani shi ya dinga koya Mana karatu muna group Assignment."Haka dai Yaya Saddiq ya dinga min Bayanin komai yadda zangane...."Zuciyata Bata Kara tsinkewa sai da muka shigo get din makarantar." "Ba laifi makarantar tana da kyau Inda aka rubuta admin da manyan bakake can muka nufa parking place yaya ya nufa ya tsaya." "Bayan mun fito Mota,Inda office dinsu Yaya yake muka nufa."Bayan mun shiga office din nasa."Mai tsari, wasu Takardu ya d'auko acikin file."Sannan muka fito Nan ya dinga gaisawa da Yan uwansa malammai da muke haduwa da su Nima Gaida su nake ba Dan nasansu ba."Da muka fito harabar makarantar muka nufa Ina bayansa, Dalibai sai gaida shi suke..."Nima fa na zama Abin Kallo awurin su irin yadda muke tafiya da Yaya Saddiq."Gwanin burgewa Ina Jin Wasu na gulmar mu..Wasu na fad'in ai matar mallam ce,ko budurwa sa ce, can wani yace ko dai kanwarsa ba! Ina jinsu saboda shi Yaya waya yakeyi Tunda muka fito Admin din."Nidai komai banayi sai aikin kallon makaranta..." "Bayan Yaya ya kammala wayarsa, magana yayi min Amma Ni nayi nisa wurin kallon 'ya'yan duniya Wasu da shigar mutunci maza da Mata wasun ko tamkar mahaukata idan Naga wasun Kuma kamar ba yaran Mallam bahaushe ba."Kabilun ma sun fisu shigar mutunci."Wani nayi murmushi wanin Kuma nayi tsaki," "Ke hankalinki na Ina!?"Inji Yaya." "Sunkuyar da kaina nayi cike da kunya...Ya ce ga to ga faculty DINKU Nan."Eng/Sos aka baki Adm.no gata nan 22741/18/Sk."karbi wannan Takardun komai naki na aciki computer form da clearance Duka." "Amsa nayi da girmamawa Nace to Yaya nagode,"Is okay!yaya yace atak'aice Yana Cigaba da Danna wayarsa tare da dubin agogon da ke daure a tsintsiyar hannunsa.." "Wani matashi ne...ya iso wurin mu cike da ladabi.."ya gaida Yaya tare da musabaha atsakanin su." "Nima gaisawa mukayi da shi....Nan Yaya Saddiq yace'' Naseer ga kanwata nan Nadiya da nayi maka bayanin zata zo."A kula sosai kamar yadda nayi maka Bayani." "Naseer murmushi yayi da ladabi yace ba damuwa Mallam in Shaa Allah,"Sannan ya kalle ni da walwala yace Malama Nadiya da fatan Zaki bani hadin kai domin bana wasa da karatu." "In Sha Allah Yaya Naseer Zan kula sosai."Nace kaina ak'asa "Naseer yace Yawwa,Allah ya taimake mu "Ameen Nace Ni da Yaya "Yaya Saddiq yace min Kinga office Dina dai,Ina son idan kin gama lectures dinki duka kije mu koma gida, yanzu Zanje nayi Miki Maganar hostel.."Naseer sai ku Tafi Sannan kuyi kokari tayi coping time table dinsu.ka fahimta yadda komai zaizo da sauki" "Ni da Naseer ro muka Fadi atare Sannan Yaya ya wuce mu kuma tafiya mukeyi nan Yake min Bayanin alakarsa da Yaya suna mutunci Sannan yardadden yaronsa NE, Yaya Saddiq ne ma ke kula da karatunsa..."Nan yake shaida min sun fara karatu tun last 2 weeks da suka wuce sai nasa himma da sauran su." "Mun dawo daga inda ake buga time table wato shagon kwanfuta,.Direct MW3 block 2 muka nufa kai tsaye Domin muna da GSE 115,min samu aji tinjim da jama'a Nan take cikina ya dauki ruri ganin idon Mutane sun min YAWA ban saba ba!Tsoro da fargaba ya darsu araina har Ina ayyanawa araina Anya zan iya! karatun nan Jiki Mutane Bila adadin...Nan jikina ya Soma rawa har takardar dake hannuna da biro suna kakkarwa...Naseer ya fahimci Ina Cikin tsoron rashin sabo shiyasa ya dinga wayar min da Kai har Mallam ya shigo ajin namu"Haka dai muka Cigaba da daukar karatu aranar cike da rashin sabo...Naseer nayi min Bayani handouts dinda aka fitar bana Nan Domin na saye da yake na fito da Kudi."Haka da Assignment din da aka bayar saboda Naseer ya Gaya min shi ne C.A Kuma Yana taimakawa sosai awurin Cin jarrabawa." "Sai da mukayi lectures 5 sannan muka tashi wuraren 6:pm."Sallama mukayi Da Naseer bayan yayi mani rakiya har office din Yaya."Mutane da gulma da sa ido sai kallon mu sukeyi."'Daga cikin yAn ajin mu na fahimci wata Alokacin da ake lacca sai hararena takeyi....,Ashe Naseer take so sai da muke dawowa ahanya yake Gaya min sunan Aleesha Wai sonsa take."Na lura yammata nayinsa saboda akwai shi da kwakwalwa(Gifted)NE ajin farko."Shiyasa kowa yake son ya rab'e shi." "Gida muka koma ahanya Yaya Saddiq yake Gaya min."Cewa an samu hostel Ina shehu shagari house block D rum 6."Murmushi nayi Duk da araina Ina Jin tsoron makarantar Nace to Yaya." "Da isar mu gidan Anty Jalila muka samu tana kallon Zee world Inda ake wani series."Ko sallamar mu da kyar ta amsa Mana."Tana cigaba da kallonta."Yaran suka tarbe mu da murna."Yaya Saddiq d'aki ya nufa, Nima inda akai min masauki na nufa...ina zuwa na fad'a bayi nayi Wanka da wanke bakina da man goge hakora...saboda na gaji!"Ga yunwa duk da munje cafeteria munci abinci Ni da Naseer Amma Ina jinta"Bayan na shirya hijab na zuba na fito falon Ina kamshi....Dai da fitowan yaya,Inda teburin Cin abinci Yake ya nufa yaci abinci..Nima abincin naci da taimakon sa Domin shi ya kula da yayi min tayin abincin da ko wani Dadi bayada ci nakeyi Ina dura ruwa har na kammala shima Tuni ya gama inda suke naje na zauna muna kallon sai dai akarshe daki na koma Ina duba handouts Dina da na saya." *************** "Bayan sallar magrip Saifullahi da jawad suka shirya tsaf cikin shiga ta Kamala da mutunci."Kaftan suka sa milk Mai kyau." "BAKIN masallaci suka tsaya Inda dattijawa sukayi dandazo."suna Hira a ladabce suka isa wurin suna tambayar Mallam Balarabe."Kamar yadda suka samu aduniyar binciken su." "Tasowa yayi,yace gani yan samari da mamaki ya Kara da cewa.....nace day lafiya!?" "Lafiya qlaw Baba..."Daman wurin kane muka zo Kuma kaie muke nema."Saif yace Yana sadda Kai kasa domin shine ma iya koyon dabi'un kirki da ladabi shi Jawad har ma ya gaji da durkusawar da sukayi tun sanda suka zo,"Domin shi Baya jimirin wad'annan dabi'u." "Mallam Balarabe tashowa yayi Daga cikin jama'ar Suma tashi tsaye sukayi...saif ya rike hannun Jawad ya matse Yana murmushi Alamar dai Jawad yayi Hakuri subi KOMAI asannu kamar yadda suka tsara." "Dan karamin benci Mallam Balarabe ya aza gefe domin sun fito cikin mutanen ya zauna..."Ya kalle su Yace Yan samari kafin Nan Kai...ya NUNA Jawad da hannu yace"KU dauko dayan bencin KU Domin na fahimci da magana abakin KU....'' "Jawad banza yayi da shi!"Domin shi fa yafara hasala!"Saif NE yayi sauri ya dauko benci ya aza suka zauna suna fuskantar BABA BALARABE."yana murmushi "Gyaran murya yayi irin na manya yace Ina sauraron ku,Daga Ina kuke!?Me ke tafe da KU!?"Da fatan dai lafiya!?"Ya jero masu tambayoyinsa ajere." _Muje zuwa fans agaskiya rubutun Hausa sahihinta da wuya! Ashe bazan iyah ba!Ana fadakar da mu cewa duk marubuncin Hausa ba'a bukatar kalma daya ta ingilishi arubutunsa😀Abin mamaki Ina iya kokari na domin ganin bansa kalma ko daya arubutuna! Amma Ina! wani gurin sai da nasa na kasa yadda zanyi sai da turancin ya fito,Pls my FANS kui taimako min da zafafan Kalmomin Hausa domin ganin na Kai gachi. Nagode😀_ *'YAR MUTAN DIKKAWA CE* [2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* SHAFI NA BAKWAI :SHINE MUKA SAMU KUSKURE! *SADAUKARWA GA MAMANA TA KAI NA UWAR BIYU DA YARDAR RABBIL IZZA, MUMMY JUWARIYYA BAWALE WARA(EQUITY FM) INA MIKA SAQON GAISUWATA DA GODIYA TA MUSAMMAN ALLAH YAQARA ARZIKI DA NISAN KWANA YA KAWO ZURIYA MAI ALBARKA TAKWARAR MAHMIE❤* _____________________________________ "Yaya Saddiq ne gaba, Ina binsa Baya,Har muka shiga babban falon gidan da yake akwai mukule a hannunsa."Bayan munyi sallama har sau biyu gidan shiru..." "Kayana ya ajiye tare da nuna min daki gefen hagu ya ce na shiga na ajiye kayan acaan."shi Kuma dakin da ke gefen dama ya shiga." "Duk kayan na kwashe kaf na tsibe agefen dakin da aka nuna min tsoro ya hanani zama dakin ni daya Abu ga bakunta kar wani Abu yafaru ace nice,Shiyasa nadawo falon na zauna ni kadai kumshe acikin hijabina." "Bayan kamar minti biyar sai ga Yaya Saddiq ya fito,Kyakkyawar Matar sa Anty Jalila A bayansa." "Gyara zamana nayi cike da girmamawa..."Da ladabi na gaida Anty Jalila." "Wani kallon tayi min Wanda na kasa banbamce meye ma'anar SA!?"na rasa da wane suna zan danganta shi." "Ta ce,Yawwa 'yan makaranta,ya ma sunan!?" "Murmushi nayi nace da ita Nadiya..."Saboda nasan babu wani dalili da zata sanni Tunda zumunchi abotakaar iyaye ne kawai."Amma jiya na Gaya Mata wataqil ta manta ki tayi NE Domin ta garani agaban mijinta oho..." "Okay,Allah ya taimaka."Anty Jalila tace da ni." "Ameen,Nagode nace kaina na dubin lallausan kafet din da ke shinfide a tsakiyar falon."Wanda yayi datti har ya canja kala saboda rashin sharar kwarai," "Honey...Kin dafa abincin ko kuwa....!?"Yaya Saddiq ya tambaya" "Haba Habibi!Kasan yau su mufeed sunje gidan mama ba girki zanyi ba!Kuma ina da tabbacin yau lahadi (weekend) ne,Fita muke waje mu ci abinci, nima fa yunwa nikeji tun dazu nake jiranka,kamar yadda aka Saba!"Jalilah tace cike da shagwaba."Saboda ita adunia ta tsani girki,ba abinda takeso illa ta wanke goma ta tsoma biyar gangariya ta kwashi girki!"Ta zauna tayi Kallo ko bacci." "Kallonta yayi ya Kuma fahimci tunanin girkin take!!!"Kansa ya girgiza yace"To yanzu Kinga ga bakuwa munyi bazan iya kwasar ku muje restaurant ba!"Nagaji sai kiyi hakuri ta tayaki! KU dafa ko Wanda zamuci yanzu ne." "Ni zanje na watsa ruwa na kwanta kafin ku gama. Kaina na min zafi kin sani Kuma yunwa CE ke janyo hakan.."Inji Yaya Saddiq ''Wani Kallo jalilah tayi masa adakile tace To!"Amma Kasan dai Banyi Shirin abinci ba yanzun ba!"Bari ko taliya ce nadafa Mana." "Ba damuwa saddiq yace atakaice! tare da wucewa abinsa saboda shi ko sunan abinda ya danganci fulawa bayaso ji,"domin har ya gaji da cin indomie,Taliya,da macaroni Wanda akullum abincin gidan nasa kenan idan anyi gwaninta ake shinkafa da miyar ja."Amma shi tuwo har ya manta sai dai suci a wani gurin," "Nikam Bance KOMAI ba Ina zaune akasa sai wasa da zoben hannuna nake." "Am...Nadiya kizo ki tayani girki Nifa ba ayi min zaman banza agidana..."Anty Jalila tace a gadarance."saboda taji takaicin zatayi aiki," "Yake nayi nace haba Anty muje ki nuna min ma, ko me kikeso agirka babu damuwa." "Ajiyar zuciya tayi tana Murmushi,"Tace to muje"Daga gefen wurin cin abinci (Daning) sai madafa(Kichen)muka fad'a,"Tsaye nayi Ina kallonta, firiji Anty Jalila ta bude ta dauko kayan Miya masu yawa,Ta bani na gyara mata Bilanda ta miko min domin in nika kayan, gas take kokarin kunnawa..." Har ta kunna Ina kallonta saboda in ga yadda ake kunna shi,Dan Ni ko abin nikan duk bansan yadda ake amfani da su ba."Amma nan Anty Jalila ta nuna min yadda duk zanyi." "Aiki muka fara muna taba Hira can KUma sai haushin aikin ya dawo mata,Nima taimaka Mata nayi da dauko nan ajiye wancan,yankan wannan...",Har ta kammala dafa taliyar da taji kayan lambu da su magi da sauran su"Ana magrip naje dakin da akayi min masauki nayi wanka da sallah Nan na zauna Ina lazimi."Bayan Yaya Saddiq yadawo masallaci ya samu kanen Anty Jalila ya kawo yaran."Nan dai gidan ya kacame da wasan su da fadan Alewar da uncle dinsu Tahir ya saya masu."Ina Jin duk abinda suke a falon har ficewar Tahir din.," "Sai da aka zo cin abinci a daining place,Anty Jalila ta kirani...Bayan na fito gaishe da su nayi,Tace na zauna tare da nuna min kujera gefenta,na zaune sai dai na kasa sakewa..."Nan yaran ke Kallo na,Waton Mufeed da qanwarsa Mufeeda suna tambayar Daddynsu wacece Ni ." "Antyn ku ce Daga gidan su Baba Musa..."ku gaida ta." "Juyowa sukayi gareni Anty Ina wuni." "Lafiya qlaw nace da su." "Anty Ina Baba Musa"Inji Mufeed!?" "Yana can Argungu yace"Agaishe KU.." "Anty Nan Zaki kwana!?"Inji Mufeeda "Eh,nace Ina Daria." "Anty adakin Yeeeeeh ki zamanki anan muna sonki ki dinga kwana Dakin mu tsoro mukeji!!"In Mufeeda tana dariya." " A gajarce!!"Nace to saboda Naga Anty Jalila ta damu da hayaniyar su,Na Kuma kula tanada saurin daukar zafi!sosai,Na Kuma kula bataso Ina yawan magana da mijinta."Shiyasa na Kama kaina da bakina." "Shima dai dariyar yaran yake..yadda suke wani kaudi akaina.," "Abinci kowa ke ci cike da raha da Jin dadi musamman Yaya Saddiq da yaransa, duk da nidai taliyar ta Anty batayi min wani dadi ba,Duk da Tasha kayan lambu da magi bare man gyada."Ba a ko magana."A zuciata nace da ace nice na girka kila zan iya ci Kuma bazan Bata kayan da ta suburbuda aciki ba!Wai duk Domin tayi dadi."Hmnnnnn nikuma nace girki tsari da kwarewa yake buqata ba zambada kayan kamshi ba.."Ina amfanin kyau a fili babu abaki akula lol."Sai dai Nadiya bata sani ba ko daga bakinta ne fans ku dandana kuji😀." "A gurguje ni kam na dan tsakura naci na tashi saboda ban Saba da cin irin wannan kalar abinci ba!"A hankali nabar wurin Dakin Wanda ga alama na yaranta ne, na koma na zauna Ina jiran sallar Isha."Tunanin Malam yunus ya darsu azuciyata na tabbata shima yau zaiyi kewa ta rashin ganina a makaranta "Cikin sa'a ko ya samu Abokin sa alambun gidan su kamar yadda yadda yadda sanar masa."da yake kafin ya zo sunyi waya." "Bayan ya zauna,yasha ruwa da lemu sun danbtaba raha."Shi ne Jawad ya zayyanewa Saif duk abinda ke faruwa atsakaninsa Yarinyar da ta mare shi!"Sai dai ya boye zancen marukan da ya Sha saboda tsarou😄"Ya dai gayawa, Saif ta kirasa Maras *TARBIYYA* Abin ya daki zuciyarsa!!"Sannan yarinyar ta masa rashin mutunci ta zazzage shi"Shiyasa yanzu yake so yayi mata wulakanci naji nagani na fada agari!!!."Amma fa ba Wanda zaisa mom ta gane ba!"tayi magana akai..."Nan shaidawa Saif karya!Da tsarinda yayiwa mom." "Nazari Saif yayi kana ya kalli Jawad Yana murmushi ya ce"ya naga ka wani had'e fuska kamar tana agaban ka." "Bana son rainin hankali,Shawara nazo nema wurinka ba iskanci ba!"Jawad yace yana kallon Saif tare da Harara." "Mai da wuqar nawan, yanzu dai mafita d'aya ce nake ganin zamu bi muyi maganin iskancin ta shine mu nemi sanin gidan su,iyayenta akarshe muje masu a mutanen kirki!"Daga nan zamu daura su akan tarkon mu da zarar ya Kama su Ina da tabbacin zamuyi nasara akanta,"Abokina Albishirinka."Daga ranar na tabbata ta tashi da aiki domin ba makawa zamuyi maganinta!" sauran bayani Kuma basai na gaya maka ba yanzun sai zuwa gaba." "Da wata irin dariyar k'eta Saif ya kalli Jawad da ke wani Shan kunu Yana huci da hura hanci!"Yace Baba you hakuri! tare da miko da shi tsaye....muje yakin neman Gidansu yarinyar domin mu santa da labarinta, Allah ya taimake mu yasa iyayenta kashe money ne.. " "Ameen,yace." "Tsaki!"Jawad yayi azuciyarsa yana tuna maruka, Amma afili yace waton Saif idan har ta shigo hannu na banma san irin kalar wulakanci da zanyi Mata ba!" "Jawad ay babu babi ko days ko Kuma labarin irin abinda zansa ka aikata mata aduk cikin labaran rashin mutuncin wannan zamani..."Inji Saif yana kokari shiga Mota..." "Da motar Saif din suka fita yayinda Jawad ya bar tashin agidan su Saif har su dawo Kai tsaye unguwar tudun wada suka shiga sai dai Jawad bai Bari suka tsaya inda abin ya faru jiya ba!"gaba suka Kara hanyar da ya ga yarinyar na bi." "Sai da sukayi Danyi tafiya sannan suka tsaya "Wani shago da ake dinkin tela suka nufa."Suna tambayar yarinyar!?"Sai dai matsala daya!basu San sunanta ba!"Wanda duk kowa shi yake tambaya ko na mahaifintA."Wuri uku suna zuwa babu nasara..."Har sun hakura sun jiyo suna cikin tafiya a motar sai Jawad ya hango yaro daya Daga cikin yaran da ya tab'a gani tare da wancan yarinyar." Yana ta wasa tare da abokansa yara." "Da sauri Jawad yace DakAta Saif!"Na hango makamin tafiyar Nan." "Da mamaki ya dubeshi yace a Ina!?"Jawad "Ga yaro daya ce daga cikin kannanta muje mu tambaye shi."Jawad yace da sauri "Fitowa sukayi Daga Mota wurin yaran suka nufa...tunda yaron ya hango su tafe ya gane Jawad...nan take yaron ya fiddo ido cike da tsoro yacewa abokan sa ku!!! mu gudu!!!ga mugu Nan tafe!...Nan take Duk yaran suka archeee da gudu." "Jawad Bai San sanda shima ya archeee ba ya kamo yaron da tuni ya Kama kuka!" "Saif dariya abin ya bashi yadda Duk miskilanci da iskancin Jawad ya sheqa da gudu." "Jawad yace "yanzu zanyi maka allura ko kana son mu tafi da kai ne!" "Ah'ah!"yaron yace Yana girgiza Kai. "To ka fada min gaskiya idan na tambaye ka! Ina wacce na ganku tare ranar!?"Inji Jawad "Yaron,yace taje shakkwato makalanta,cikin maganarsa ta yarinta."Yana hawaye "Ya sunan ta ne!?" "malama Nadiya!."Yaron yace cikin tsoro domin yashiga tsoron Jawad Jikinsa har Bari yake!" "Jawad ya ce kasan gidan su?" "Eh,nasani."Inji yaron. "To yanzu muje ka nuna Mana sai kadawo Kai wasan Ka."Saif da ke tsaye yace." "Nan suka saka shi gaba Yana tafe suna binsa har kofar wani gida na laka Wanda daga gani Basai an fada ba kasan tufin Asiri ne agidan." "Saif ya kalli yaron tare da dauko naira dubu ya bashi yace maza kaje ka kashe." "Washe baki yaron yayi jiki na Bari yaje ya kashe kudin."( _Sabo akace turken Wawa Daga Ni yaron ya Saba da kashin kudi_ ) "Sai dai saif rikoshi yayi yace''Sarkin son kudi!!"Ay sai ka tsaya mana..."Ya sunan babanta ita Malama Nadiya?" "Mallam Balarafe(Balarabe),Inji yaron" "To ya sunan mamanta?" ''yannere(Innerei)Mai manja" "Yawwa yaro to jeka mun gode." "Da gudu yaron yabar gurinsu Yana munna da tsalle sai kanti...."Dariya saif yayi yace shege Dan talaka ya ga Kudi." "Kallon junan su sukayi Bayan yaron ya wuce,sun gama mamakinsa." "Sannan suka dubi kodadden gidan cike da haushi!!!." "Saif yace "cikin sigar rarrashi Babban yaro da ka hakura da wannan kwailar ka yafe Mata me zamuyi awannan gidan ba girman mu bane!"Ka barta iyaka mu dauki hayar Yan iska suyi maganin iskancin ta kawai!!!" "Wannan zancen Bai taso ba!Domin na dauki alqawarin wulaqanta ta da kaina."Tabbas ba girman na bane in tsaya ma awannan kofar gidan Amma kaddara ta riga fata!"Dan kuwa dole na dauki fansa!!!" "To shi kenan Baabaa muje can shagon mu Gaya masu sunanta da na babanta musha Labari." "Suka shiga shagon Kudi suka raba musu 1k Duk Wanda ke shagon Nan take shagon ya dauki shewa suna GODIYA...Nan ne Saif ya tambaye su labarin Nadiya da iyayenta." "Cikin mintuna suka basu labarin KOMAI tsaf hadda karerayi da kare Karen Dan gishiri...."Sai dai babu abin ashsha ko ki acikin labarinsu da halayensu sai ma furuci da shaidu na Alheri." "Nan suka bar shagon jiki yayi sanyi saboda kowa yace tanada kirki Amma shi gashi tayi masa rashin mutunci!!!" "A hanyar su ta dawowa sai mamaki suke yadda hakan tafaru,yarinyar ta masa hakan!"Bayan ance musu tana da kirki Shi kam saif sai yake ganin kamar laifin Jawad din ne." "Jawad a zuciyarsa sai tusushin baki ciki da damuwa yakeji yadda yar talakawa ta wulaqanta shi!"A gaban mutane!!!"Ashe ma ba Yar gidan kowa ba CE!Jin Motar ta tsaya ne yasa ya fahimci an kawo gidan su Amininsa Saifullahi galadima Wanda hali da rayuwar su kusan daya."Sallama sukayi nan tare da Alqawari gobe zasuyi shiga ta Alfarma su ziyarci Mallam Balarabe wato mahaifin Nadiya."Daga Nan Tunda ba wani haline da su ba,suyi masa barin naira domin cikar burin su." "Bayan na kammala Shirin bacci Addu'ar azkhar na karanto kana na kwanta bacci saboda nasan gobe litinin makaranta zanje...Nan naji wasu zafafan hawaye na ambaliya a saman lafiyayyar fuskata."Kukan rashin sabo,kewa da soyayya ne nake rusawa Amma fa marar sauti saboda yaran Duk sunyi bacci." "Duk lokacin da na tuna iyayenah da irin rayuwar su sai naji nakara kujan can na tuna sayyadi Nan ma kukan ya Kara kwaceni!!!"sai da muryata ta daina fita ga ciwon kai idanuwana Duk sun kumbura saboda Kuka." "Ina son in bacci Amma na kasa har karfe dayan dare sabod tunani da kawa zucin mamana...Hakan yasa na tashi nayi Alwala nayi sallah bayanna idar karatun alqurni na fara,Tabbas Alqur ani rahma ne Kuma maganin komai ne,Nan wurin na samu nutsuwa na shigo ni ahankali,Lazimi na dinga yi da hannu na daga nan bacci barawo ya saceni Ni."( _LITTAFIN manzon tsira rahma ne Kuma saukine Sannan waraka ne Daga dukkan komai_) "Ana wata ga wata kenan domin Yana cikin bacci ya dinga jiyo sautin karatun Alqur ani ahankali Yana tashi acikin gidan,sabon lamari kenan saboda abinda Bai tab'a faruwa ba agidan,sautin muryar mace tana karatu....Juyowa yayi ya kalleta tana gefensa tana sharar baccinta azuciyarsa yace Daman nasan ba anan ba ne..."A hankali ya isa bakin kofar dakin da yake tsammani...Yana sauraro tun Yana tsaye har ya Kai zaune,muryata ta na shiga jinin Jikinsa Yana wurin har sai da yaji Shurin nata Sannan ya tashi ya koma dakinsu cike da tunani azuciyarsa agaskiya Ina son macce Mai addini yarinyar ta burgeshi,Ina ma ace jalilarsa ce ta ia karatun alqur a ni hakaaan....."Yaya Saddiq shima Alwala yayi ya tada sallah,Abinda ya dade baiyi ba!"Domin A Da Yana da kokarin ibada,Azumin nafila tsayuwar dare da tilawar alqur'ani sai yanzu akan yasamu macce marar addini batayi kuma shi idan yanayi tace Yana takurata hakan dai shima ahankali shaitan ya rinjaye shi!!"Amma gashi yau yaji komai ya dawo masa, Jin da yayi Nadiya tana rera karatu kamar balarabiya...Nan shima ya dinga nafilfili da istigfari har wajajen uku da rabi Sannan ya kwanta... Jalila ta farka bayi ta shiga da ta ganshi zaune Yana Jan carbi tsaki tayi tace Hmnnnnn su Huda Huda sarkin sallah yau an tuna da ibadar Ni Motsin ka ma ya hanani baccin kirki!"Kwanciyar ta tayi tare da Cigaba da baccinta."( _Tabbas akwai Mata kawayen Jalila masu wannan irin wannan halin! ya kamata mu gyara!idan kinsamu miji Mai addini da ibada to yi kokari kibi sahunsa ki Kara karfafa masa gwuiwa KU Cigaba da ibadar atare domin KU tsira atare,idan ma sabanin hakan ne kiyi kokari kiga Yazan mai ibada yadda ya kamata,Saboda da yawa mazan wannan karnin suna da raunin ibada ko ta farilla bare nafilar Allah yasa MUDACE Amin._!") *'YAR MUTAN DIKKAWA CE* [2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA TARA* _SADAUKARWA GA AMAREN 👰🏻DECEMBER🌙,DA KUMA NA SABUWAR SHEKARA📆 INA MAKU FATAN ALKHAIRI ALLAH YASA AYI LAFIYA A WATSE TAROU LAFIYA_ _SANARWA!SANARWA!!SANARWA!!!IINA MASOYAN OFFICIAL NABEELA DIKKO,INA MAKARANTA NOVELS DINA...DUK INA GAYYATAR 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI DA KUMA MASOYANA ZUWA AUREN KANWATA TA KAINA ❤ PRINCESS YASEERA DIKKO👰🏻 WANDA ZA'AYI ON 28/DEC/2019 ,BAN DAUKEWA KOWA BA NA NESA DA NA KUSA AZO LAFIYA ALLAH YA KAI MANA RAI AMEEN._😍 ______________________________________ "Har yanzun Yaya Saddiq Bai Kara min zancen komawata Hostel da Zama ba."Har nayi sati daya agidansa." domin na kula yaya Yana Jin dadin ganina agidan.Shakka babu Tabbas an samu canji agidan mussaman agefen girki,ina yiwa yaran abincin safe kullum suje da shi makaranta, kuma duk kalar Wanda su keso shi nake girka masu."Sannan idan na dawo da Wuri Ina daura sanwar dare,Ina tuwon semo,shinkafa da miyar taushe da kubewa da sauran su"mufeed da Mufeeda suma yanzu suna jin dadi sosai sun sake da Ni sosaii, sun daina hayaniya atsakanin su,sunayin Kuma sun iya gaida Mutane idan sun gan su, har iyayen nasu yanzu suna gaidawa safe,Rana,da yamma Yanzu kam kowa agidan ya fahimci yaran sun samu canjin RAYUWA Gashi kuma Ina kokarin koyar da su karatun Islamiyya da na boko."Yaya Saddiq Yana jin dadin yadda nake kulawa da taimakon da nakewa yaran, aransa sai fatan Alheri yake min,Yana son zamana gidan sosai Domin farin cikinsu ya karou dani ta kowanne fanni,Gashi Yana sakewa da Ni sosai tamkar kanwarsa ta jini,komai mukeso Ni da yaran Yana saya Mana,Haka kullum suke ganin kamar kada na tafi saboda canjin da akasamu agidaan Kuma kowa na nuna min kulawa cikin Yan kwanaki Anty Jalila ta sake min komai na gidan." "Anty Jalila sai dadi take ji aranta tasamu ma'aikaciya agida,Iyakacinta tayi bacci,ko Kuma Kallo daga nan ta wanke goma ta tsoma biyar"KOMAI ni nakeyi agidan idan dai banje makaranta ba da Wuri,ko Kuma kafin na tafi tun Wuri sai na kammala aikin duka Sannan na wuce saboda wataran da karfe goman safe ko da Rana ko Kuma karfe hudu na yamma nake fita."Daga Baya ne kawarta Subbyh ta shiga atsakanin mu alokacin da tazo gidan tasameni,Shine ta hurewa Anty Jalila kunne,akan na bar gidan kada na aure Mata miji."Duk da Ina Mata biyayya Ina kula da yaranta,Bai hanata daukar shawarar aminiyarta ba,saboda tana da tsananin kishi!"Akan Yaya komai zata iya aikatawa."Hakan akayi domin kuwa Anty Jalila ta takewa Yaya Saddiq burki dole saina bar gidan na koma Inda yace Mata tun farko zan zauna!"Ba domin sunso ba,shi da su Mufeeda."Yace na tattara kayana zan koma makaranta da Zama,A cewarsa acan zanfi karatu,Sayayya yayi na koma hostel da kwana.."Sai dai kullum mu kanje ofishinsa Ni da Abokina Naseer mu gaida shi."Wataran ya bamu kudin abinci Wataran Kuma bama samu saboda yau da gobe sai lillahi." "Na kwantar da hankalina sosai Ina karatuna yadda ya kamata Kuma Ina ganewa sosai."Dan kuwa muna group discussion da Naseer da abokinsana Deeni." "A hakan na Cigaba da tafiyar da rayuwata akwalejin shehu shagari.."Sai dai Banyi sa'ar abokan kwana ba, wato Yan Dakin mu da yake mu hudu NE adaki daya."Hali na ya babbanta da nasu."Hakan Rayuwata ta fita daban acikin tasu." "Su uku ne Esha Hayat wato (Aisha Hayatu)sai Kuma Deejah Yak(Khadija Yakubu) sannan Deeyarh Bas(Badiya Basiru) sai Ni Nadiya BB da yake ko Nan ma hakan suke Kirana wato Nadiya Balarabe Bello." "Kullum Yan Dakin mu ganina suke ban waye ba a matsayin Bagidajiya!"Sune suka waye suka San duniya da Abin da duniya take ciki."Ni Kuma Ina masu kallon Wasu iri,A ganinsu saboda bana shigar banza irin tasu Kuma bana kula maza Bana Wannan shirmen soyayya kamar yadda sukeyi shine ban waye ba,A Kullum kirana suke gara ko ustaziyya"Su Esha sam basu da kamun Kai da yake na lura mafi yawa hakan yam matan suke na kwarai masu hankali da kamun Kai"Kalilan ne acikinsu abin mamaki har matan auren ba'a barsu Abaya ba a Wannan zamanin me cike da tsoro,yadda mafi yawan Mata suka ajiye sure gefe suna abinda ransu keso bare yammata sai dai har gobe akwai na Nagari b'ata gurbi ne sukafi yawa!"Wannan halayen da nake gani yasa na Kara yarda da kuma gasgata Maganar Mallam yunus Dina,Da ya CE"Jami'a gidan kowa da kowa ne."Nako gani saboda akwai shege akwai Dan banza Sannan akwai nagari aciki,kowacce kalar rayuwa akwai Kuma ko da me kazo amfika."Na tabbata hakan."gidan ban Kashi ce," "Rayuwar mu da su wata iri Cce suna tasu nikuma Ina tawa koyaushe SU Esha cikin Kudi suke, da sayen sutura masu kyau da tsada,Har gasar wanka da saka manyan Kaya masu tsada sukeyi da sauran d'alibai" ga su duk sun San manyan mutane da malammai suna shiri da su sosai,da duk wani Mai fad'a aji acikin makarantar." Iyakacin su,Fashion da budawa amakarantar,Ba karya sun iya wanka naji nagani na fada,saka mayafi Bai damesu ba,ga kayan suna kamesu sosai tare da fidda tsiraicin su, Amma su aganinsu wayewa ne Wannan fitar ta rashin mutunci ita ake yayi,"Shiyasa suke fita yawon su,Abinci mai kyau sukeci su Sha Mai kyau,Ina ji Ina gani nazama doluwa Yar Kallo acikinsu." ko sun ce min in zo muci abinci tare da su banaci hakan bana nuna bukatar komai Daga garesu."Ba yadda basuyi ba domin su ga na shiga acikin harkar tasu Ayta sha'ani tare,Amma naki!"Sun nuna min sutura saboda sun fahimci banida ita da yawa Mai kyau."sun nuna min kud'i sun bani abubuwan kwadayin duniya duk nayi banza da duk abinda suka bani."Nace da su nagode banaso Domin nafison abinda nasamu ta dalilin iyayena!!"Hakan Na Cigaba da karatun da ya kawoni makaranta." saboda su na gane basu damu da wani karatun ba Kuma basu da niyyar yinsa." sharholiyar su kawai sukeyi ta duniya."A kullum fatan shiriya nake masu."Su kuma suna min kallon lusara Wacce batasan komai ba bagidajiya Yar kauye." "Saifullahi Aminin Jawad ne sosai Kuma Abokin shawarar sa."Sun shaku da JUNA sosai sai dai shi Saif yafi Jawad dama Amma dai dukkan su yan gatane."Sun taso acikin so da kauna." Saifullahi shine karami agidansu,Saboda duk yayyensa Mata ne su biyar shi kadai ne namiji Kuma auta agidansu yayyensa Duka manya ne,Haka iyayensa manyan Mutane ne,Kuma yayyansa suna auren mazaje masu kudi.shiyasa ta ko ina,yake damawa da kudade son ransa Dan gata ne Dan auta Kuma autalele Sha leleh awurin iyayen sa da yayyensa ." ************* "Yanzu kimanin sati biyu da zuwan su wurin Mallam Balarabe wato mahaifin Nadiya Tabbas sun Sami karbuwa kwarai da gaske agurin Baban nata Haka kawai yaji jininsa ya hadou da Jawad kaunarsu na ratsa jini da jikinsa,Duk da ya kula yaron sai ahankali Amma dai ya karbe su hannu biyu kuma ya gamsu da kudurinsu."Aykuwa sunji Dadi sosai sai dai sun fahimci Baban bayada kwadiyin Abin duniya."saboda sun bashi masa kudade yaki ya karba ranar." "Shiyasa suka canja dabara ta hanyar Sayayyar kayan masarufi sukai masa yau,Saboda sun Kwana biyu basuje gaida shi ba!"Kuma wannan Yana Daga cikin shirinsu...Shiryawa sukayi tsaf acikin jallabiyoyi da huluna farare tas sunyi kyau kamar larabawan Sudan da yake dukkan baqaqe ne masu Dan haske."Da misalin karfe hudu na yamma hanyar tudun wada suka nufa kamar yadda suka Saba, Bayan duk kwanaki uku sukanje da sunan kawo gaisuwa ta mussamman agurin mahaifin Nadiya ko Yanzu hakan CE ta kasance." "Tun Malam Balarabe na sanyi-sanyi da su har ya Fara sake masu saboda ya lura yaran na da kirki,da sanin girman na gaba dasu shiyasa suke girmama shi Kuma suka dauke shi da muhimmanci, Wannan NE yasa Mallam Balarabe ke ganin mutuncin su, tun Baya amsar abubuwan da suke kawo masu har ya fara amsa har cikin gidan suke shiga su gaida mama fad'imatou(Inneirei) suyi fira sosai da ita har take masu zancen kewar Nadiyarta, Haka sukeyi dai har aka Saba da JUNA."Kamar kullum yau ma zaune suke rashe rashe agidan Bayan an kammala shigo da kayan da suka kawowa su Mallam Balarabe." Sannan suka cigaba da firar su daga bisani suka fito."Mama Da Baba sai albarka suke saka masu da dimbin GODIYA." "Dariya sukayi alokacin da suka fad'a Mota,suna tafawa Jawad yace"Wallahi da farko sai Naga kamar bazan iya ba!"Saif "Hakuri ne bakada shi Jawad Shiyasa.. Saif yace Yana Dariya." "Yanzu nafara koyon hakurin adalilin daukar fansa!" "To Jawad yanzu dai kaga Shirin mu Yana tafiya dai-dai." "Haka NE faa...Wai kasan da kyaar na tsara momy na d'aurata akan layin iska,Domin ta daina zancen zuwa ganin mutumen Nan da na Mata Bayani na karya...."Sai da nagaya Mata yaji sauki munje dubashi Baya gari yayi tafiya kauyen su..sannan NE fa ta hakura Tace sai yadawo ta tafi."Nace Mata to da kanmu zamu kaita har gidan."Inji Jawad dake tuki cike da kwarewa," "Kace munyi arziki da mummy Bata B'ata mana shiri ba!nji Saif yana dariya "Kai Baaba...Ai kuwa da ta tab'a komai nifa na rasa Ko Meyasa mom ta damu da taje, ai idan ta dage sai taje sai ta wargaza Mana shiri."Jawad yace."Saif Kam muryar wakar Davido dake tashi amotar ya Kara tare da rawa Yana tafawa...yace bazamu rasa yadda zamuyi Mata wayo ba!Domin mu Yan zamani....yace yana Cigaba da bin wak'ar." "Tafiya suke suna Hira da shewa,Saboda a yadda Shirin nasu ke tafiya, kamar yadda suka tsara."Daa kamar wuya Nadiya ta kubuta Daga tarkonsu."Sai dai ta zama Abin tausayi a hannun su, Domin Bata sani ba, ta tafi makaranta tabar Baya da kura." *************"""" "Zaune nake Ni kadai adakin mu Ina dafa abinci Ina karatu da yake yanzu mun fara gwaji(test)." "Shigowa sukayi Dakin ko sallama basuyi ba da yake yanzu sun daina kulani sosai kamar baya."Ko kallon su Banyi ba!"Na Cigaba da karatuna." "Esha CE Mai raha acikin su."Tace Sannu Malama Nadiya." "Yawwa,Sannunku Nace da ita! "Baiwar Allah Naddy Karatu,kawai ake ta sha..."Inji Deejah tana dariya. "Banza nayi Mata..tashi nayi na Duba abincina shinkafa da wake ce,Na had'a ta da Mai da yaji,zubowa nayi da su Nace suzo muci,Ba kunya Esha da Deejah suka zauna mukaci tare Dan ba kunya da zuciya ne da su ba!."Deeyart Ita dama akwaita da Jin kan tsiya Kuma bata wani yina sosai Tunda taga bana layin su." "Nan muka dinga cin abinci suna bani labarin yawon su da suka fito dana samarin su na malamai da Yan makaranta har na cikin gari ba'a barsu Abaya ba...nidai Daga Eh,sai Ehimnn ke hadani da su,Ina cin abincina su Kuma sunata zuba"Har muka gama nan ne nake basu Shawara akan su dinga shiga aji suna karatu,saboda idan har suka cigaba da hakan Sam basu yiwa iyayensu adalci ba,"Idan dai Haka rayuwar su zata cigaba basa Zama makaranta bare su shiga aji suyi karatun kirki Domin ga gwaji Nan anfara basada labari'' "Deeyart da ta cika faam tace"Ke Malama kisani mufa ba yara ba NE!"Da Zaki wani zo kina Mana surutun banza to ki ajiye gaskiyar da shawarar ki agefe!"watarana zatayi Miki amfani."Naga kina Mana kallon Wasu iri!"Me kike nufi Nadiya!?"Mu sakarai ne marasa Hankali ko kuwa!?To idan bakisan Wacece Badiya ba bari na sanar maki Kuma idan har zakiyi min adalci to Zaki iya Kirana da Mai Ilimi ba jahila ba,Wacce iyayenta suka Bata kulawa yadda ya Dace"Deeyart ta d'aki kirjinta...Tace Ni nan da kike gani da kaina na ajiye masu kayansu agida kafin na koma na DAURA Daga Inda na tsaya."Domin naga anan bazatayi min amfani ba!"Ni Badiya na kasance yarinyar kirki Babana limamin unguwar mu ne,Duk garin gwadabawa ba wanda Bai San shi ba,Haka mamana Malama ce matan aure take karantarwa Ni da yayye na duk malammai ne."Ko da na shigo makarantar nan da mutuncina da komai na yaran kirki, sai dai haduwata da Esha yasa nafara canja rayuwata saboda wannan CE mafita agareni matukar inason in Zama babbar yarinya kamar kowa Nan muka hade da Deejah."Ba komai yasa Ni canja rayuwata ba!"Illah!nagane a jami'a idn baka budawa kana wanka,to Kai ba kowa bane Kuma ba za'a Sanka ba ko Kai Mai basira ne!"Kuma ba Wanda zai San da zamanka..malammai ma da kansu basa kula ka bare ka nemi Alfarma ayi maka da sauri."Amma yanzu ki Duba kigani bama shiga aji Amma muna da sakamako Mai kyau ajiye,Wanda ma yafi naki ke Mai ikirarin kinzo karatun Hmnnnnnn Amma Ahakan kike Mana kallon tarbiyya.Ki zauna ki gani zamu amshi Takardun NCE lafiya qlaw."Ba tare da Wani wahala ba!"Ko ba Haka Eshaa."Deejart Tace tana kallon abokanta cike da bacin rai!Domin Naddy ta hasalata sosai akullum kallon mutanen banza take masu!" "Tabbas Hakane Deeyah Domin Ni kaina gidan mu an bani matakan kulawa da kaina amatsayin na macce sai dai ni ban dauka ba tun farko,Ni tun Ina gida Nike sharholiyata kuma da taimakon mamana,Sai dai Tace min Aysha ki kula, saboda tana Sona batason bacin Raina ko Baba yaso hukunta Ni ita ta ke tarewa."Kullum cikin bani kariya take,Domin ganin kada aga nayi laifi!"Shiyasa Duk abinda nake tana sane Domin da taimakonta."Kuma idan nasamu kudade awaken samari tare muke cinyewa, Shiyasa rawar Kai tayi yawa,Ina da Mai dafa Mani baya,Duk Abubuwan da samarina ke kawo min tare da ita mukeci har kaji,nama,da sauran kayan kwalam....Bari kuji watarana ummana ke tsara min yadda zanyi nasamu kudi shiyasa idona ya bude Banda Kunya Kuma Bana shakkar Kowa arayuwata" "A lokacin da na shigo makarantar sai na Cigaba da harkokina!"Na fahimta kokarinka da dagewarka akan karatu wani lokaci bashi kesa kaci jarrabawar ba!"A wannan zamani saboda tun Ina sakandare nasan da hakan masu karatu daban masu Cin jarrabawar daban....Wannan ne dalilin da yasa nake abinda Raina ke so Dan Nasan Banda kokarin ko dagewar nayi bazanci ba to gwara naci ribar rayuwata." Nadiya ki gane muma fa kamar ke muke muna da ilimin mu saurin Dauka ne banayi Duk da hakan ki daina Mana kallon da kike mana"Esha taqare zantukan ta tana dafani." "Deeja dariya tayi Tace nikam agaskiya idan Nace iyayenah sun min TARBIYYA To hakika banyiwa kaina adalci ba!"Saboda Ni ko gidan TARBIYYAR ban taso ba bare nagani anayi na koya."Iyayena rikakkin Yan boko ne."Duk abinda mukeso agidan mu shi mukeyi Daga mu har iyayen mu kowa sha'anin gabansa yake."Shiyasa Ni da kannaina Duk abinda mukeso shi mukeyi."Kowa Yana da right dinsa agidanmu,rayuwa muke tamkar rayuwa akasar turai, hakan rayuwar gidanmu take tafiya,Nifa ko Islamiyya bana zuwa agida anan makaranta na koyi ibada saboda masallaci da muke zuwa,Kuma anan nakejin karatun alkur'ani da waa"Azi tare da koyarda mu ibada duk anan na koya,Agida iyayena Basu san komai ba bare su koyarda mu Sannan Basu damu da muyi karatun addini ba boko dai suka sa agaba."Kinga nikam amakarantar nan na fara koyon ibada,Halaye da dabi'un kirki....saboda akan ina ganin wasu nayi Nima na Kama,saboda Haka zamana da KU da Kuma rayuwar jami'a ya koyar da Ni Ibada Kuma na more." "Shiyasa Tunda na taho na samu su Esha da Deeyah amatsayin kawayena sai muka dace da JUNA!"Babu Mai Jin kanmu muna zaune lafiya qlaw, harkar mu mukeyi Kinga kowa ya ganmu yaga manyan yara,mun samu sutura,Kudi,wayoyi masu tsada ki Duba kigani kowaccen mu Infinix take riqe da ita."Muna business dinmu wanda har iyayen muke taimakawa." "Hmnnnnnn yanzu motoci ne kawai suka rage Mana mu saya!"Kwanan nan zamu Kama gidan kanmu Domin munfi karfin zama hostel."Kuma Nan da kike ganin mu Duk abinda muke iyayenmu basada Labari musamman Ni da nake a zamfara."Yanzu zamani ya canja abubuwa da yawa mukeyi Batare da sanin su ba."Domin kuwa sune suka haife mu Amma mun fisu wayo da dabaru."Ko karatun mukayi karshe kadamu za'ayi abaiwa wasu can da basa karatu muna Kallo,da musha haushi gwara mu bada haushi Nadiya."Kedai da kikaji Kika Gani kuma Zaki iya rayuwar jami'a a Haka kamar bagidajiya da Kyaunki da kyaun jikinki sai kiyi."Amma kisani Nadiya zamanki ahakan bakida Wanda zaiyi maki tsaye a makarantar Nan babban hadari NE."Saboda kowa amakarantar Nan yasan halin Wanda kike ganin ya isa gareki KUma zai iya tsaya maki"Shifa malam Sadiq na daban NE acikin malamman makarantar Nan."Yana Daga cikin Yan tsirarun mutanen da ake ganin masu mutuncine Kuma ake mutuntasu.."Sai dai Yana matsala daya Baya neman Alfarma ga kowane malami Kuma Baya yiwa kowa Alfarma."To ta Yaya Mallam Saddiq zai taimake ki ahakan Nadiya.!"Kina ganin Zaki iyah cinye jarrabawa ahakan Bayan akwai iri irenmu da akeyiwa alkawarin sakamako Mai kyau shi kenan?"Iyakachi saiki tanadi ko me kike so kicewa iyayenki idan har ba ki ci jarrabawar ki ba!?"Duk da mun fahimci Duk acikin mu iyayenki sunfi namu rauni!"Ba kuda shi kuma dagani talakawa NE!"Sunyi kokarin turoki karatu kin fad'i...ai ba Dadi Amma gashi Allah yayi Miki baiwa bakya amfani da ita Dan kawai akiraki Mai mutunci Mai kokari Mai kamun Kai."Kisani acikin duniya akwai na kwarai kuma akwai Dan iska,Duk yadda ka zama bazaka wuce zagi ba awurin mutane!"Yanzu hakan ke kanki Nady akwai masu zaginki..Dan Haka kowa yayi abinda yakeso Kuma yake ganin mafitace agareshi,Wannan Shine nasara arayuwa Nadiya."Mu da kike Gani ba Wai mun zubar da mutuncin mu bane ko kuma muna aikata ba dai-dai ba!"A'ah Duk wanda yace Yana son mu Amsa Masa muke saboda Kudi mukeso da an sake Mana zamu canja sheqa da sauran abinda ba za'a rasaba....." "Numfashi na sauke Mai nauyi!tare da kallon su tabbas wadan su zantuka na su hakika gaskiya ne,Kuma sunyi tasiri azuciyata ganin yadda rayuwar makarantar take tafiya..." Sai na kasa cewa komai!"Kallon junan su, sukayi suna murmushi..."Tare da Cigaba da zantukan da zasu janyo hankalina garesu."A karshe hannu suka aza tare da yimin inkiya na daura nawa akai saboda suna Sona sosai." "Duban hannayen su nayi tare da Kawar Kaina!Tuni na nutse a cikin kogin duniyar tunanin zamanin mu ayau."Shiru nayi na Dan lokaci Ina nazarin amsar da zan basu saboda karatun Yanzu sai da dabaru ko mu hade da su ne?"Ina son iyayena Ina Bbukatar suyi alfahari Ni da Kuma karatuna...Kodai mu raba hanya da su!?"Shi nake tunani, Domin ina Gudun watarana."Yanzu meye mafita agareni na shiga tsaka Mai wuya Ina son karatuna sosai,Amma Kuma Ina Jin asarar watsi da halayen da nafito dasu agaban iyayena!"Daman da basirata da Kuma taimakon Yaya Saddiq na kwantawa gashi ance Baya neman Alfarma Ni ya zanyi Yanzu bare aimin ta dalilin sa!" *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 [2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 12* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ ____________________________________ "Da Misalin karfe shidda na yamma ranar litinin yayi min ne. Abakin kofar hostel dinmu."Idona duk sun kumbura!" Su Eshaa ne suka taimaka min na kwashe duka kayana!..."Nayi bankwana da makotan Dakin mu nagaya masu zan koma cikin gari da Zama!."Muna nan tsaye muka hango motar Yaya Saddiq na tahowa inda muke atsaye..."Nan take Deeyart ta juya baya suka Esha da Deeja suka bita!"A gurguje mukayi sallama da su suka bace Daga gurina!"da zummar zamu hadu gobe!" "Wurinsa na karasa na dinga zuba kayana but da yake ya bude Amma Yana Daga cikin motar..."Bayan nasa na shiga motar tare da gaida shi." "Amsawa yayi batare da ya dubeni ba!"sannan muka wuce." "Mun dauki lokaci muna Tafiya babu abinda ke tashi sai sautin karatun sheik Ahmad suleiman...Inda yake karanta Amanarrasulu..."Da kuma sheshsheqar Kukana da ke tashi...koda ci kanki Yaya Saddiq baice min ba!" "Yau dai mom ta tura kewar saif da Jawad agaba sai gidan Mallam Balarabe domin taje Duba lafiyarsa."kamar yadda Jawad din suka tsara "Da yake sun kirashi awaya kafin su zo shiyasa suke da Tabbas akan Baba Yana gidan Kuma sun samu bakin zaren." "Da Sallama suka shiga gidan,Dukkansu." "Amsa masu Innarei tayi tana masu maraba da zuwa" "Tabarma ta shimfada masu tare da kawo masu ruwan leda da Baba ya sayo masu kafin ya shigo."Ta ajiye fuska asake tana Kara gaisawa da Mom." "Momy ta yaba da halin mutanen duk da Kasancewar su talakawa Amma suna da halin GIRMA." "Musayar Gaisuwa sukayi.."Da mom da su Baba." "Nan mom Tace"Baba ya gida ya karfin jiki."Da fatan kasamu lafiya." "Lafiya qlaw Hajiya jiki da sauki ay naji dama sosai!" Yaran Nan suna kokari sosai...Allah dai yayi albarka." "Ameen...innerie."Tace tana Murmushi." Jawad da Saif kallon JUNA sukayi...Tare da yake na Jin Dadi domin sun sami mafita..."Dayake shi malam Balarabe kwanakin baya yayi maleria har ya sanarda su Jawad Lokacin da sukazo gaida shi."Shiyasa ya dauki shine suka sanarda mom tazo masa ya jikin." "Mom taji dadin zantukan Baba"Ta CE Ba komai Baba yiwa Kaine domin azatonta ko wani dattijo ne mai shekaru." batasan cewa wahala da rashin hutu tare da cutar talauci ne ya tsofar da Mallam Balarabe tun Wuri." "Innerei Tace Hajiya ayni nasamu yarana masu son mu,Su jawad kaam Akwai mutunci." "Raaas gaban mom ya Fadi domin Innerie CE,mutum ta FARKO da ta ambaci mutunci tattare da su Jawad." "Mom mamaki take yadda su Jawad suka canja suka koma kalar kirki tun Daga shigarsu gidan har kawowa yanzu...Ba suyi wani abin rashin mutuncin ba!"Ko meye sila!?"Amma dai Akwai wata akasa Tunda har taga sun Sanya sutura ta mutunci,Wato Kaftan da hula..."Abinda Bata taba ganin sun sanya ba!" "Jawad ne ya dawo da mom Daga duniyar tunanin da take."Ya ce mom mu wuce Koh!?" ''Dariya tayi tace"To mutafi Baba Allah Kara sauki Kudi ta bashi 10k Daman sun shigo da manyan ledojin kayan fruits ahannunsu sun ajiye."Tace aci da Hakuri Allah ya baka lafiya ya tsare gaba!" "Ameen,Baba yace Yana ta jera GODIYA da fatan Alheri wa mom da yaranta." " Saif yace to Baba sai mun dawo fira jibi."Yana Dariya "Malam Balarabe yace yawwa saifullahi sai na ganku fa Hajiya angode Allah ya saka da alkhairi,Muhammad sai kunzo cewa da Jawad."." "Ameen..mom Tace." "Jawad yace Baba sai mun dawo," "Innarei tace gaskiya kuna kokari mun gode ay ba Haka ake ba!"Gashi 'yarta taki tana makaranta har yau ba ta dawo ba." "Mom Bata fahimci me Innerie ke nufi ba.."Yake kawai tayi ta shige suka bita Abaya..Nan suka isa Mota Baba har can ya rakasu Yana masu GODIYA." "Innerie Koh Daga zauren gidan ta tsaya tana musu Sallama."Tare da tunanin kirki irin na wad'annan mutanen..."Tsoronta daya kada Nadiyatou ta dawo asamu matsala!"Koh da yake tana da yakini akan halinta kuma a yadda sukayi Mata tarbiyya bazata taba girgiza masu ba!"Bare Jawad baida aibu ko makosa ko kadan."Domin ya nuna masu halin kirki yaron kirki ne kawai zai fitou agefen da Jawad ya bulkowa lamarin!!"Da tunanin ta shige Daga cikin gidan tana Cigaba da ayyukan ta."Tana yiwa Allah GODIYA da yakawo haske arayuwarsu." "Baba Yana ganin tashin motarsu Jawad, shagon unguwar ya nufa domin sayen abubuwan da suke buqata, Daman kudin sun zo masu alokacin da suke nemansu."Shiyasa ubangiji ya kawo masu su Jawad a sanadin tufin asirin su."Ikon Allah kenan da Amfanin Kai Kuka awurinsa, Allah kenan Al-ahad Al- samad."Sai ya kawo mafita ba zato ba tsammani da zancen zucin Malam Balarabe ya isa kantin ya fara sayen kayan da yake bukata!" "Dab da magriba suka iso kofar gidan su...Horn suka yiwa Mai gadi ya bude gidan Mom suka sauke sannan suka shiga masallacin gidan domin an fara Kiran sallah." "Mom shiga tayi tafara watsa ruwa sannan tayi sallah tana dawowa falon, suna shigowa..." "Daning place suka nufa domin abincin dare ya Dade da kammala."Har an jera komai akai." "Da mom da su abincin suka bude kowa ya zuba suka fara ci..."Suna taba fira. "Nan mom ta kalle su ta fahimci suna cikin farinciki." "Tace Saif.." "Na'am mom ya amsa." "Nace wai...meye sirrin? ko dai mun fara Yar boyen sirrine da KU?.." "Yace kamar ya mom!?" "Kun fara neman aure Banda Labari ne..!?" "Jawad yace aure fa mom!?" "To sarkin tsari...Ba da Kai nakeyi ba da Saif nake."Inji mom tana hararen Jawad "Kansa ya Sosa Yana murmushi.."Tare da cigaba da cin abincinsa." "Saif ma dariya suka bashi yadda suke wannan da mom..." "Na dawo kanka saif kasan bana son wasa ko to kagaya min Gaskia meye alakar KU da wadan can mutanen..?"Anya kad'aiwa ce kawai!?"Wannan hankali da kukayi asanadin su!?"Na k'asa ganewa Domin naji Wannan matar tana fad'in yartawa Bata Nan kaina ya daure saiku min Bayani..."Inji momy "Kallon Jawad yayi da ke cin abincinsa ko ajikinsa." sannan yace"mom kiyi Hakuri a gaskiya Jawad ya fad'a son yarinyar gidan ne." me suna Nadiya..."To har yanzu Bai sanarda ita ba!"Iyayenta dai sun sani,Saboda ance halin kirkine kafara neman macce awurin iyayenta kafi Ka sanar da ita,"To yanzu dai su sun san da maganar Kuma Jawad aurenta Zaiyi ba da wasa ba!"..."Daman muna son ta dawo Daga makaranta ya sanarda ita ne Daga Nan idan ta aminche sai mu sanarda ke!"Amma kiyi Hakuri mom...Inji Saif Wanda a cikin sigar rarrashi yake maganar da kunya." "Wani Abu Jawad yaji tamkar an cika Masa mashi ak'ahon zucia..Alokacin da yaji Amininsa na fadin waaai...ya kamu da son wacce yafi tsana adunia! wacce ya tsani ganin ko da Mai sunanta ne!Wacce yake burin daukar mummunar fansa akanta!"Wacce yake da kudurin ya wulaqanta dukkan rayuwarta!!!"Tuni Idonsa suka rikid'e zuwa ja abincin ya ture tare da tashi ya fice yace ka sameni part dina saif kaina na min zafi zan kwanta!!!"Jawad yace tare da tafiyan sa abinsa..." "Da yake saif Dan duniya ne Tuni ya hango bacin ran abokinsaa!!!"Sai ya fashe da dariya yace su kunya manya bawani ciwon Kai....sai dai nazon..." "Ya kalli mom yace"Ai mum yau kin hada rigima saboda munyi da Jawad sai Nadiya ta aminta za'a sanar maki."Kinsan mutumen nawa yanzu fushi NE yayi saboda na gaya maki Gaskia alkawari ne." "Murmushi mom tayi Tace"A Gaskiya naji Dadi wannan zancen idan har da gaske Jawad na sonta Kuma Zaiyi auren da gasken...zanyi murna da hakan Saif,domin na k'osa Naga kun Zama mutane kunyi aure ya fiye muku wannan shirmen banza da kukeyi!" "Yanzu dai mom karki damu In shaa Allah mun Zama mutanen kirki..."saboda mun fara hankali..ki dai tayamu da addu'a Allah yasa muyi nasara." "Saif zanyi maku Addu'a da fatan shiriya, sannan idan ta kama har ni zan shiga zancen domin ganin ya samu abinda yakeso, duk da ba Yar gidan talakawa naso ya aura ba!"Na ci buri akan auren Jawad naso ya samu Yar gidan manyan mutane masu Kudi na asali ya aura mu daki JUNA da naira,Nayi had'ashi da yaran qawayena, da 'ya'yan Abokan marigayi Babansa d'iyan masu Kudi Amma kana sane Saif duk yace baya son su.." sai Wannan zaice Yana so!?" "Mom may be ita ce zabin da Allah yayi Masa." "Hakane Saif,Allah yasa ita CE Alheri,Zanyi munna da hakan Daman shine burin mahaifinsa,yaje da burin son ganin auren Dansa."Mom ta karashe zancen cike da damuwa." "Allah ya gafartawa Abi." "Ameen Saif..." "Shima abincin ya ture tare da Shan ruwan faro da ke ajiye...yace mom Bari nasamu nawan..."Sai da safe." "Yawwa Saif ka gaida Mamie Kwana biyu bamu hadou ba Amma muna waya sai na shigo..." "Yawwa zataji mom.." "To sai da safe Nagode sai naji yanda dik kukayi adinga sanar min." "To Mom zakiji saif yace ya nufi sashen Jawad ." "Mom abincin ta Dan ci kana ta Kira Inna tare da Bata umurnin ta kawo Mata kayan fruits." "Jiki na rawa Inna ta dauko su afirijin Daman ta gyare su sun dauki sanyi...ta kawo ta ajiyewa Mom..."Sannan ta wuce dakinta..."mom falon ta dawo dauke da filet din ta,kallo takeyi tana chat da kawayenta tana Shan kayan lambun." "Horn yayi kusan sau uku Alamar da yake masu idan ya dawo..."Sannan yayi parking motar a Inda yake ajiyeta..."Aykuwa fitowar mu ke da wuya sai ga yaran da gudun su.."Suna oyo yo Abba." "Ganina yasa suka daka tsalle da kuwwa suka rugumeni Anty Nadiya oyo yo..."Cike da murna suka dinga daukar Yan kananan kayan da suke iya saukewa abut din." "Mufeed da Mufeeda sai munna sukeyi...ganin hakan yasa naji Dan sanyi araina na sake fuskata...Saboda a hanya Yaya Saddiq yayi min tatas tare da kashedi da sharudda akan na kiyaye na kula da kaina "A karshe Baba ya Kira awaya yabani shi muka gaisa har nace yabani mamana yace Yana kanti wurin sayayya."Kuma Daga can masallaci zaije alokacin." "Da taimakon yaran na kwashe duk kayana Yaya Saddiq Tuni ya shige gida yabar mu..."Rufe motar nayi Bayan mun kammala."A Lokacin da na shiga gidan naji wani iri araina.."Hakan dai na adana kayana adakin yaran nadawo falon."Ina tambayar Anty Jalila?" tana wanka Inji yaran."Nikam zaune nayi shiru sukuma sai zuba suke.." "Tana wanka ta dinga jiyo hayaniyar yaran suna fadin sunan Anty Nadiya..."Nan take taji wani sanyi aranta..."Tuni ta manta da wanka take ta dinga tikar rawar India har da su shoyki tana Alhamdulillah gobe zanyi baccin safe, Addu'ata ta karbou."Nan da Nan ta watse ruwan ta fito ko Mai Bata shafa ba tafito Sanye da jallabi.A falon Inda muke." "Yaran na jikina suna surutu ta karaso cike da fara'ah Tace A'ah Nadiyatou CE Wai... " "Nace"Eh.....Anty Ina wuni,tare da sunkuyawa Daga kujerar.." "Ta ce"Lafiya qlaw,ya makaranta!?" "Nace Alhamdulillah." "Kallona tayi Tace anzo Mana kwanaki NE?" "Eh,nace."Da sanyin muryata "Anty tace Nadiya to yau ake zuwa weekend NE! jiya sukace zaki ko Ranar jumma'a?" "Eh,Anty,Daman naso nazo wani sati weekend ne,Yaya ne dazu yace in shirya ya wuto da Ni." "Tooo....Anty jalila tace tana Murmushi Domin murnarta taqasa boyuwa," "Nace,Anty... Bari nayi sallah muna hanya akai sallah..." "To sai kin fito ga Tafiya can kichen sai ki zubo ku ci idan kingama idar da sallar" "Nidai na koshi gaskiya Anty domin na ci abinci a hostel."nace Mata saboda nikam bana son komai ayanxu." "Mufeed Ina Abba!?"Anty Jalila ta tambaya." "Ya tafi masallaci Mufeeda ta baiwa maman su amsa." "Tashi nayi yaran SUKA bini sai dadi sukeji kamar an gafarta masu."Alwala nayi tare da tada sallar magrip da ishaa da yake lokaci yayi muna hanya akayi sallah gashi motar mu tayi faci ahanya muka samu tsaiko..." "Ni da yaran mukayi sallar magrip sannan Ishaa...Bayan mun kammala Azkhar mukayi Ina koya masu...Nan SUKA dauko littafan su suna nuna min ayyukan da aka basu da taimakona sukayi aikin..."Sannan nace suje falon suyi kallo Inda mamansu saboda nikam Ina bukatar hutu mussamman da na tuna da qawaye na su Esha Nan naji Wasu zafafan Hawaye na zuba a idona." "Duk sai naji komai ya fita Raina!!!" "Amma ahakan zan hakura na Cigaba da Zaman Hakuri agidaan Yaya Saddiq...." Kui hakuiryh fans Ina ganin comment naku Ina godia zakuji Ni hiru a Yan kwanakin nan cos zan shiga busy ana auren kanwata Amma idan nasumu time zan Dan tsakurou muku ko read more 1 ne,Ina neman Addu'oin KU wa auren Habibartynah😍 *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 [2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 11* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *TUKUICHI NEH GAH* _Mesona,farin cikinah Hasken idaniyatah Abin alfaharinah Nagode sosai da kulawa Allah yabar zumunchi da Zaman tare Ameen_*FATAN ALKHAIRI*😍 ______________________________________ "Ta Kama yau ranar litinin CE,Ranar da ko bature Yana tsoronta!"Tunda na kammala shirina tsaf acikin wata atamfa metro ruwan miyon goro da fari,dinkin riga da siket ne yayi min kyau sosai."Da yake su Eshaa suka dinkama ita dinkin ya amshi jikina sosai."Hijab fari nasa irin wannan da ake daurewa baya."Yayi min kyau,Takalmi na saka sannan na dauki jikata,Na fita da zummar su Esha zasu sameni facultyn mu."Saboda tun adaren jiya na sanarda su zasu rakani Inda Yaya Saddiq muyi masa barka da zuwa." "Ina fita Inda muke haduwa da Naseer na wuce Banyi minti biyar awurin ba sai gashi ya sameshi Ina duba littafaina." "Yace "Malama kiyi hakuri kinata jirana ko tare da zaunawa gefena..." "Murmushi nayi nace bakomai antashi lafiya." "Yace"Lafiya qlaw yace,Gaskia Nady yau kin fito kamar balarabiya ko dai kin hada Da su ne."Wannan kyaun." "Dariya nayi wadda sanadinta sai da dimple dina suka lutsa..nace ehhhhh...Ni balarabiya ce...kaga bana son zolaya muje tun ba Kai min format din abinda na rike ba.." "Naddyh kenan kefa karfe ce..na yadda da karatunki bazai taba zuwa ko'ina ba.." "Nan dai muka wuce muna Tafiya muna firar da yake jinin mu ya hadu sosai da Naseer...Haduwata da shine na fara rage tunanin malam yunus.."Yana debe min kewa mutum ne Mai mutunci da sanin darajar Dan Adam," "Acikin awa Biyu muka kammala gwajin mu(test)."Cikin ikon Allah duk abinda aka tambaya na amsa saboda nayi karatu."Da munna na fito Daga Hall din Ina dubin ko Naseer Ya fito da yake bama Zama guri daya uztaz ne baya chakuda acikin Mata ya zauna sai idan takama dole." "Bayan ya fito ya sameni zaune Ina jiransa..."tambayoyin juna mukeyi akan test din da yadda malamin ya rikita Mana lissafin saboda tambayar a hikima yayita idn mutum Bai fahimta ba sai ya fad'i."Daga nan Dakin karatu muka shiga muka Duba Wasu littafai acan nabar Naseer saboda munyi da su Esha idan Sha biyu tayi zamu hadu muje Inda Yaya Saddiq." "Banyi wahalar samun su ba domin nasan Inda sukafi yawan Zama.Nan na samesu sai ciye_ciye kayan kwalaam suke maza da Mata."Da nesa na tsaya ayko Nan take suka tashi suka sameni...Kallon su nayi ba laifi duk jallabiyoyi suka saka..."Sukayi rolling da mayafin rigunan."Sunyi kyau sosai da yake ba karya dukkan suna da kyau ga mayukan gyaran Jiki da suke amfani da su masu tsada kowacce sai sheki take Sunyi tatas da su. "Deejah tace Nadiya har kin karaso mu Tafi ko, "Esha ta ce"Ya test din koda yake nasan ku masu kwanya ne zakuci..." "Murmushi Deeyart tayi batace komai ba." "Bamuyi doguwar Tafiya ba suka isa admin din."Office din Yaya Saddiq mukayi knocking..."Sai da naqara yin wani sannan yace Mana Yes come in (Alamar mu shiga)" "Da Sallama muka shiga office din.. "A hankali ya amsa Mana tare da ajiye wasu files a side drower dinsA." "A hankali muka gaida shi..." "tuni su Esha suka sha jinin jikin su saboda kwarjininsa da cikar zatinsa Domin shi Sam bada case da Kowa mutum ne mai Kare mutuncinsa" wani irin Kallon yayi Mana ba yabou ba fallasa Yaya Saddiq ya bimu da shi."A lokacin da ya dago kansa ya ganmu..."Tare da amsa gaisuwar mu adakile!" "Da sanyi nace Yaya Daman mun zo mu gaishe ka ne.." "Yawwa to kun kyautah..."Ya karatu!?" ya tambaya "Lafiya qlaw....nace da shi" "Wad'annan fah!"yace tare da nuna su da hannu.." "Rass!"Gabana ya fad'i!"Cikina ya dauki duri kada ya wulaqanta su..."Domin sunyi suna da tashen rashin mutunci a makarantar "Da....Da.....Daman 'yan Dakin mu ne yaya!"na bashi amsa." "Okay...yayi KU Nagode Kuna iya Tafiya zanyi magana da ita."yace da su Esha "Kamar jira suke kowaccen su ta tashi Daga kujerar da take zaune.,sum sum suka fita jiki na kyarma!"Saboda duk iskancin basa wasa da irin su Yaya Saddiq." "Suna fita ya kalleni...sama da kasa!"Ya ce"Da kyau! haba biri yayi Kama da mutum...Shiyasa naganki kin wani canja Ashe da marasa kamun Kai kike rayuwa dasu!"wad'annan yaran da muke gani Kowa ya sansu a makaranta Nan sune abokanki bakisan idan Kuna yawo da su za'ayi maku Dauka D'aya!"Dan an hadaku d'aki D'aya dasu saiki dinga fita dasu meyasa ma Baki gayamin ba ai sai nasa ahadaki da mutanen kirki.... inji Yaya Sadiq a fusace! "Kina ganin kinyi wa iyayenki Adalci Nadiya!?"To wallahi bazan lamunce ganin ki da wadan Nan 'yan iskan yaran ba!"Sai dai ki koma gida da karatu saboda Baba Ni ya baiwa amanarki!" "Meye alakarki da su Bayan Zama guri Daya!?"Ya tambayeni a fusace!" "Kuka!nakeyi yayin hawaye na ke malala a fuskata!"Nace wallahi Yaya Sam bana rayuwa irin tasu Dakin mu ne daya!"Kuma nifa ko yawo bamayi tare ko yanzu Dan kace nakawo su ka gansu ne..."Naqarashe maganar muryata na rawa.." "Saboda naga kin canja ne ya sanyani tuhumarki!"Shiyasa na nemi ganin su.."hankalina ya tashi alokacin da na hango wayewa da canji a kwayar idonki...sannan tsadar chocolates dinda kika baiwa su Mufeed ne ya bani mamaki...domin Ina sayen irinsu nasan kudin su..."Amma ace Wai kawayenki. Zasu iya KYAUTA da su amatsayinsu na dalibbai." "Daga yau karna Kara ganinki da yaran nan saboda lectures da dama sun nuna min su amatsayinsu na makaranta."Duk makarantar Nan ansan da labarinsu da Zaman da suke school dinnan."Kina tunanin ba za'ayi muku dauka daya ba!?"To kisani babu ke babu su!"Kuma na baki Nan zuwa yamma ki tattara komai naki Zaki koma gidana da Zama saboda ko an raba maku daki nasan zasu iya binki har Inda kike su canja makin rayuwa kamar Yadda suka fara...." "Dai-dai Nan nakara fashewa da Kuka saboda na shaku da su Eshaaa,Ban son rabuwa da su..."Jin kukana!ya tsananta yasa Yaya Saddiq yace na fice nabashi guri karfe shidda ya sameni bakin get din hostel da kayana." "Fita nayi cike da kunci azuciyata!Nasan bana rayuwa irin ta su Eshaa Amma Ina da burin cetou su daga halinda suke ciki!"Ban Kai ga cika burina ba!"Yaya ya yanke min kuduri!!!"Tafiya nake Batare da nasan Inda nake kada kafata ba!"Banyi aune ba sai Jin nayi karaf an rikemin hannu." "A zabure na dubi gabana ...wani ne. Wanda ga alamu kamar malami ne.." "Hannuna na kwache a nasan tare da bashi hanya ya wuce!"Haushin rikeni da yayi yasa na watsa Masa harara da tsaki!Nace haba Mallam Bai kamata ka rikeni ba!sai Kai min magana!" "Murmushi yayi yace"Yammata Kiyi Hakuri Amma laifinki ne,kisani Kuka Bai kamace ki ba!"Kina da kyau hakan har za'a ga hawaye kwance a fuskarki Kuma kina 'yar jami'ah..." "Ya Kara kallona Yana murmushi yace ki gayamin damuwarki zan taimake ki wanene ya kadake!? ko ya cuceki!?" "Takaici ya bani bansan sadda nayi na koma tsaki ba!"Na wuce abina saboda yabani haushi tabanin da yayi!" "Tsaye yayi Yana kallona...."Yace Kai!Ni wannan yarinyar zata yiwa tsaki!"Hmnnnn zan nemoki yarinya Zaki shigo hannu...Tabbas watarana zaki San waye malam Dan Bala!"Ya wuce office dinsa Yana mamakin yadda Mai kyau ta masa tsaki duk yadda yake jin kansa." "Ko da na fitou fili Banga su Eshaa ba!"Duk da muna da lecture 4_6 ban tsaya ba hostel na wuce saboda ban San abinda ke min Dadi bA!" "Na Saba da rayuwar hostel tsawon watanni biyu..."Naji dadin rayuwa acikin mutane!"Na fara iya mu'amala da mutane da yadda AKE zama da su Naga wadanda nafi komai Naga Wanda suka fini ilimi,da addini har Ina kwaikwayon su Amma yanzu Yaya Saddiq Yana son ya rabani da su!"Saboda su Eshaa da nasan a mazaunin da na ajiye su arayuwata." "Da tunanin na isa Dakin mu....Gabana ne ya fad'i alokacin da na kalli fuskokin su...kowacce ba fara'a ita Deeyart har da hawayenta..." "Banyi kasa agwuiwa ba!"Nace Eshaa, Deeyah, Deejah Dan Allah kuyi hakuri da abinda Yaya Saddiq yayi muku, kunga koni yanzu yayi min! wannan halinsa ne KU kanku kunsani Kuma kunji aschool ana fada!!!" "Ba komai duk abinda yayi Yana da dama domin mu muka Kai kanmu!"Inji Deeyart da bacikin Rai!" "Eshaa tace wallahi saboda ke kawai mukaje Naddy..."Kuma Dan kawai kince mu rakaki ne!"ya ganmu a office dinsa but idan yakara ganinmu ya Yankee kafafuwan mu!" "Inda ba domin Hakan ba! me zai kaimu!? mu da sai ma an gayyace mu muke shiga office!k'oshi sai mun Sami time,Bare shi waye shi!?"Me Kuma ya dauki kan sa" "Deejah kenan."KU daiyi hakuri koma menene nice sila!"Nace da Deejah wacce ta gama zancenta tana cika tana batsewa.." "Shiru sukayi Ni Kuma tashi nayi Ina had'a kayana..." "Eshaaa tace Naddy Ina zakije Naga kina had'a kayanki ba dai akan wannan maganar ce zaki bar Dakin ba!?" "Hawaye masu zafi!suka zubou min,na dubeta Ina ninke kayana nace Eshaa Yaya Saddiq yace"Gidansa zan koma da Zama duka...!!" "Menene!Naddy!?cap lalle bawan Allah nan anyi mugun gaske,!"Saboda kawai yaga shi aka baiwa kula da ke shine yake Miki hakan ai Wannan mulkin mallaka ne!..."Inji Eshaa "Ni kaina Ina son zamana anan Eshaa Gidansa bazan sake ba!"Bazanyi karatun kirki ba!"Amma ya zanyi? Ina gudun ya Kira Babana ya Gaya mashi wani Abu akaina ran iyayena ya baci...Dole nabi umurninsa..."Nace idona ya ciko da kwallah!!" "Hmnnnn...Tabbas zai Gaya masa kin lalace Tunda kina rayuwa da mu lalatacci!"Inji Deejah "Ba Haka bane Khadija...."DakAta! Naddy, Hakane mana!"Saboda kowa a makarantar nan ya ajiye mu a marasa kirki da kamun Kai!"Dan kawai muna tafiyarda rayuwar mu irinta zamani!ba Halin wanka da sa kayan zamani, "Tabbas hakane Deejah!"Nidai duk Wanda ya zarge mu akan abinda bamayi Allah ya isa!Domin baka shaidun mutum Ayau!" "Tabbas Deeyart!"Inji Esha wacce ta tashi Daga Inda take zuwa wurin da Dan firijin dinsu karami yake!"Ta bude tare da dauko lemun kankana Mai sanyi ta kurba kana Tace" mudai Allah ya wanke mu,Daga zargin da ake Mana!"ke Kuma Naddy kiyi hakuri ki yafe Mana domin Zama da mune yasa ake ganinki kema kin lalace har aka Bata maki Rai!"Daman Zama da madaukin kanwa ke Sanya farin Kai!" "Nidai Har ga Allah Nady Ina sonki Kuma Ina kaunar Zama da ke ko bakomai muna karuwa da iliminki Inji Deejah .." "Kuka ne ya kwace Deeyart da yake akwaita da saurin Kuka da hasala!" "Tace"Yau akan mu ake kokarin raba Naddy da Zaman hostel!"Tabbas Akwai gyara arayuwarmu saboda shaidun duniya shine na kiyama..."Hakan da akayiwa Naddy ya zame Mana izinah!"Kenan babu masu Mana shaidar kirki!"Mun b'ata record dinmu Tunda har mukayi watsi da halayen kwarai tun farko, yanzu koda munso mu nunawa mutane abinda suke zargi ba shi bane ba bazasu taba amincewa damu ba....! "Hakane Deeyart mun makarou Inji Eshaa itama tana zubar da hawaye!!" "Deejah kam tuni jikinta yayi sanyi..."Tana nazarin rayuwa!!" "Nace kuyi hakuri kawayenah!Kusani na shaku da KU bazan iya barinku ba!"Muna tare yanzu ma naji Ina son zumunchi daku!!"Sai dai Kusani shi Zaman duniya iyawa ne Kuma duk abinda zakuyi kuyi nazari kuyi amfani da addininku da al'adarku ta amince da shi,.Saboda idon mutane ma'auni ne...Shiyasa tun farko nake kokarin sanarda KU gaskiya gashi yanzu kowa Yana zarginku alhalin KU abinda ake nufi da KU ba Haka bane!" "Nady ki yarda damu!yakacin mu mu ci kudin samari ana soyyaya da yawon gari ko Muje muyi sayayya da su, muyin shiga irin yadda ranmu ke so Amma Sam bama watsi da mutuncinmu.."Sannan farin jini ne Allah yayi Mana,Nasan munasa Gashin doki,da kunba,da girar Ido...Amma Duk KWALLIYA ne Sannan saka Kaya masu kame Jiki bamu kadai keyi ba,gyalen ma da muke rikewa a hannu har matan auren nayi Dan hakan Nikam Nasan zamani ya kawo Wannan rayuwar Amma rashin mutuncin mu anan ya tsaya!"saboda mu aganin mu wayewa CE!"Inji Deejah." "Na dubeta!Nace Babu wayewa Deejah sai tsabar halaka!"Wacce yanzu sanadinta ana maku kallon marasa kamun kai,"Babu amfani kabar koyarwa Allah da manzo Domin kawai kabi rudun zamani!Itafa macce wata Abu ce Mai daraja Bai kamata ta dinga sakin jikinta ba Domin Al'aurace itya fuska,kafafuwan da hannayenta aka cire ajerin Abubuwan da ya kamata tabari ajikinta,Amma tun kan shigarku halayenku da dabi'unku Sam basuyi Kama Dana Mata masu kamun Kai ba!Ta yaya za'ayi maku shaidun kwarai!Bani da buri irin in ganku Kuna karatu Kun Kama kanku Kun dinga shigar mutunci Domin itace Tafi Dacewa da buduwar kirki wacce watarana zata zamo uwa Tagari da maigidanta da yaranta zasuyi Alfahari da ita Kuma ta zame masu jigo silar Farin cikinsu.....Aysha...Badiya..Khadija Dan Allah ku zamou Nagari KU ajiye komai ku fuskanci karatunku,Domin Rana dubu ta b'arawo ce Rana D'aya Kuma ta Mai Kaya,Allah shi ke bayarda nasara da Sa'a ba wani ba!Na yarda da ALLAH Kuma na amince da basirata idan nayi karatu na roki ubangiji zaisa naci jarrabawa Amma meye amfanin kazo karatu anci amanar Wasu Dan kawai a faranta maku!?"Suma Mallaman watarana Amana zarta waiwayo su,Sannan idan akwai irin su Yaya Sadiq masu adalci a makarantar Nan Nasan watarana komai zai Dai-daita fatana Allah ya yafe Mana yasa mugane Amin ." "Ameen Nadiya mungode Kuma zamu kiyaye...Inji Deejah,Esha Tace ai idan anyi b'ari ba'a kwashe Dai-dai ba!"Allah ya yafe Mana laifin mu na baya,"Deeyart Tace Amin mungode.''Jikin ba kwari "Jikina na sanyaye nace dasu bakomai Nan na kammala shiri na tsaf acikin akwatina..."Lokacin Tafiya ta kawai nike jira.." "Tsittth!!!!Dakin yayi kamar wadanda ke Zaman makoki....Mun Sha Kuka!"Har mun gode Allah"Sai yanzu nagane su Eshaa nada kirki!"Hakan Suma sai yanzu suka Kara tabbatar da mutuncina..." *'YAR MUTAN DIKKAWA* [2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 13* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ ___________________________________ "Wannan karon zamana ya sauya a gidan Yaya Saddiq saboda na daina sakewa sosai da shi!" "Bana son muna yawan haduwa da shi a gidan,Sai dai idan zamuje karanta ko mundawo,Idan Yaya Saddiq Yana falo bana Zama!"Ina Dakin mu Ni da yaran." "Hakan yayiwa Anty Jalila Dadi,Ganin yadda nake nisanta kaina da mijinta." "A gefe ban bar komai da nakeyi ba agidan,Sai dai Idan bana Nan Ina makaranta."Kuma yawanci kafin na fita sai na kammala dukkan ayyukana.."Shara! mopping da girki,da yake wanke2 tun acikin dare nakeyi." "Su Mufeeda da Mufeed ba laifi akwai soyayya sosai atsakanin karatun boko da na zamani Ina koyarda su.."Musamman gefen sallah da Halaye masu kyau duk Ina kula da su sosai."A yanzu kwakwalwar su ta bude ga ladibi da biyayya da suka koya agurina." "Yaya Saddiq Yana jin dadin yadda al'ummara ke Tafiya agidan sa..."Dawowata agidan ya kasance sanadiyyar farincikinsa Haka kawai yaji ya Sami nutsuwa da kwanciyar hankali arayuwarsa." ****** "Kimanin watana HUD'U da kwanaki a sakkwato birnin shehu Ina karatuna a kwalejin shehu shagari."A yanzu hakan mun kammala (C.A) din mu duka sai batun fara zana jarrabawar zango na D'AYA wato(FIRST SEMESTER)."Saboda hakan ne na Kara mayar da hankalina akan karatuna." "Alaqata da kawayena su Eshaa,Dejeeh da Deeyart tana Nan daram ba Inda ta canja sai dai aboye nake zaune da su.."Ina zuwa faculty su da dakin su a hostel."Muna zumunci sosai Ni da su saima ayanzun kawancen mu yaqara tasiri azukatan mu."Duk yadda muke mu'amala da su munayi ne aboye saboda Yaya Saddiq ya Sanya Abokina Naseer da saka idanuwansa akan duk wani motsina a makarantar ya sanar Masa."Shima Naseer Tuni ya daukarwa Yaya Saddiq alqawarin Gaya masa gaskiya in dai akan su Eshaa ne saboda ya tsani ya ganni tare da su."A ganinsa lalatacci ne wadanda beraye suka gama wankewa idanu."Bai kamata aganni da su ba!"Musamman ayanzu da zuciyarsa ta Dade da tabbatar Masa da ciwon Sona da ya kamata!"sai dai har yanzu ta kasa furtawa abin sonta saboda labban baki sun ki bayarda wata kafa ta furuci!"Sai dai Tuni idaniya suka nunawa abin sonsu me zucia take nufi!" "Hakan na cigaba da rayuwata da ciwo da Dadi Ina karatuna tare da taimakon Naseer...."Kuma Ina ganewa sosai." ******************* "Wayar hannunsa ya ke latsawa ga alama lambar da aka rubutawa My man ita ce yake Kira...."tare da karawa a kunnensa.." "Hello!"A kace adayan BANGAREN." "Jawad yace Kai kana Ina ne Kai nake jira fah.. "Oh!sorry man gani a low-cost Mami ta aikeni na karbou Mata sako!Inji saif" "To,Ya za'ayi!?"Jawad yace Saif yace "Ka jirani Ina zuwa yanxun..." "Ok!"Sai ka shigo."Ina jiranka Jawad ya Fadi tare da kashe wayarsa Yana game da dayan wayar. "Jimnnnnn yayi zaune Sannan Ya duba wayarsa tare da kallon tsintsiyar hannunsa domin Duba agogon da ke daure a hannun nasa Mai kyau da tsadar gaske." "Bayan mintoci talatin da dakiku sai ga Kiran abokin nasa ya shigo...Iska ya furzar tare da manna bakin gilashinsa a fuska Wanda ke Kara fito da Masa da kyawunsa." "Dakinsq ya rufe tare da Daga wayar yace gani Nan sannan ya kashe tare da fita Daga sashen nasa duka..."A harabar gidan ya Sami Saif tsaye ya hade hannayensa a kirji yana kallon Amininsa da yayi kyau matuka wato Muhammad Jawad Husamaddin." "Tafawa sukayi tare da gaisawa sannan suka fad'a a SABUWAR motar Jawad PRADO kalar kasa Mai kyau." "Tafiya suke suna sauraren wakar M Sharif ta SAREENA."Saif hadda bin wakar cike da sauki."Jawad da ke Driving kallon titin yake..."Yana Dan fira da Saif.."A hankali ya karya kan motarsa a kwanar Tudun wada layin gidan su Baba Balarabe suka."Ba suyi wata Tafiya suka karaso kofar gidan."Tsayawa sukayi kana suka fito.." "Da Sallama suka karasa Daga ciki.. " "Innarei ce ta Amsa alokacin da take kwashe tuwon dawa da ta kammala tukawa." "Tarbarsu tayi alokacin da suke gaidata..."Tabarma ta SHIMFID'A masu tare da kawo masu fura da ruwan leda da Baba BALARABE."yake sayowa agidan ruwa da ke saman tudun layin nasu." "Bayan Innerie ta ajiye masu daki ta shiga tare da gayawa Mallam gasu Jawad Nan..."Kimtsawa yayi fito da yake ya kishingida NE." "Innerie ko tuwonta ta Cigaba da kwashe tana adana komai a mazauninsa..." "Su Saif Tuni aka bude Sabon babin fira da Mallam Balarabe kamar yadda suka saba."Tun suna kyamkyemi akan abuncin gida har suka daina akan dadi da dandanonan bincin gashi sun yaba da tsaftarsu matuka..."Nan Innerie ta zubo masu tuwon dawar da danyar kubewa Kore Shar da Tasha kayan kamshi da daddawa......."Ay Nan su Saif aka hau kwano ana ci ana Santi,Jawad sai Kora furar Nan Mai Rai da lafiya ta shinkafa kabawan kanta yake."Mai Dadi da gardin gaske Wacce akayiwa damun kyale mouda." "Suna cin abincin suna yabawa Innerie akan dai abincin yayi Dadi." "Innerie tayi dariya tace mu da abincin namu miya sallaba CE,Ba Nama aciki ai abincin masu kudi yafi namu Dadi...." "Ina mama fati da yake hakan suke kiranta...Saif ne katseta ya qara da CEwa a gaskiya mama abincin Nan ko gidan shugaban kasa Albarka... Saboda duk Wanda yaci bazai fahimci ba Naman dawisu ko jimina aciki...Ai mun dauka da giwa kikayi miyar Nan Mama..." "Jawad ya amshe zancen...yace" mama gaskiya Ni ban ma fahimci ba nama aciki bah...Saboda kamshin miyar sai ya nuna nama da kifi ne suka yalwaceta..." "Baba Dariya yayi kana yace zaku gama santin KU Yan nema masu salo...Ai kuwa 'yahtah Nadiyatou tafi ta iya Miya saboda ta kware sosai agurin girki kunga ko Sabon hannu yafi tsohon hannu...." "Innerie ta karbe zancen tana dariya ta ce da dadin miyar kake tutiya Kuma da shi aka reni 'Yar taka shine taci ta girma...kaima anjuma kadan zaka daura santin naka daga Inda su Jawad suka tsaya..." "Dariya sukayi cike da jin Dadi dukkan su...Nan aka dauko firar Nadiya..."Baba ya shaida masu saura mako biyu ta dawo a yadda Saddiq ya sanar Masa da sukayi waya ajiya."Saif yace agaskiya Baba da Nadiya ta dawo hutu sai dai kayi Hakuri zamu saya Mata waya..." "Jawad yace "Duk da na fahimci baka so Baba Amma ya kamata ka hakura saboda tana fama da kewar mu sanadin rashin wayar!" "Ajiyar zuciya Baba ya sauke yace''Abinda yasa bana son Nadiya da waya shine saboda kula da rayuwarta Domin macce ce na Duba nagani rashin Amfanin wayar yafi amfaninta yawa!"Tana batawa yara da dama rayuwa Haka yara da yawa sukan fad'a wata rayuwa sanadin waya!"Sai kuga yaro Yasan abubuwan da dama Kuma ya iyasu adalilin wayar Nan ta zamani."Shi NE nake Jin tsoron barin Nadiya ta rike waya domin kare mutuncinta da kula da rayuwarta "Gyaran murya yayi a kausashe!"Ya ce"Baba na tabbata hakan bazata faru ga Nadiya ba!"Saboda nasanta da mutunci da sanin ya kamata!"Bazata taba zubarda kimarta da mutuncinta sanadin waya!"Inji Jawad." "Saif ya CE"Baba gobe zamu sayo waya mu kawo maka,Kaine zaka Bata da hannunka yadda bazata zargi wani Abu ba!"Kuma idan ka Bata da kanka zatabi umurninka da kashedinka akAn duk wani Jan kunne naka!"Da GARGAD'in da zakayi Mata." "Hakane Baba yace cike da gamsuwa da bayanin su.'' "Innerie Tace Allah yasa MUDACE,Amma gaskiya munyi kewar Nadiya saboda yau kusan mako daya ba mujita ba!"Sai Idan Saddiq din Yana kusa da ita ne."muke jinta watarana sai dai yace Bata kusa da shi."Amma da ace tanada waya da munjita...." "Tabbas Mana Fatty,Jawad yace cikin Jin Dadi."Abisa karfafa masu gwuiwa da tayi," "Saif yace ku kwantar da hankalinku Baba da mama. ba abinda zai faru...Mudai ku tufa Mana asirin mu awurin Nadiya idan ta dawo." "Babu matsala saifullahi karku damu komai zai zo kamar yadda muka tsara Inji Baba." "Innerie Tace "yadda kukazo Mana da manufar ku jawad itace ta sanyamu karfafa muku gwuiwa.."Domin Hakan shine Dai-dai." "Dariya sukayi tare da inkiya da ido cike da kwarewa ta wayayyi..."Sannan sukace Mu zamu koma,Bayan sun wanke hannunsu, Jawad daurin kudi ya fito a aljihunsa ya ajiyewa Baba atabarma..."Yace"Baba ga wannan afara Shirin tarbon Nadiya." "GODIYA!"su Innerie sukayi ma su tare da rakiyar su har zaure..."Tana Mika sakon gaisuwar ta awurin mommy da Mami." "Ficewa sukayi Baba da Innerie suka dawo gida cike da murna da godewa yaran."Su Jawad ko suna fad'awa mota suka dinga murna...turare suka feshe jikinsu da shi,tare da jefa sweet Mai kamshi a bakinsu,Domin Kamshin daddawar ya fita jikinsu Sannan suka Kama hanya," "Baba Balarabe yace "wallahi Innerie Ina Jin so da kaunar yaran Nan Shiyasa bana iya Koda Girgiza masu..."Musamman Jawad Ina Sonsa har zuciya kamar d'ana gudan jinina!"Shine dalilin da yasa nakeson ganin na aura Masa Nadiya da zuciya D'AYA."Kudinsu basa rudani illa halin su na kirki na burgeni..." "Innerie Tace"Nima dai na yaba halayensu da kirkinsu Allah ya nuna Mana mun saka masu da auren Nadiya ai duk Wanda yaso abinka dole kaima ka so shi, Musamman ta yadda suka bullowa lamarin Nan yasa naji Ina kaunar sa ALLAH dai yasa mudace." "Ameen..."Mallam Balarabe yace tare da dibar kudin ya baiwa Innerie sauran yace ta ajiye masu da basu san ko nawa bane KAMAR yadda ko Wanda ya basu kudin bai kirgasu ba." *'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍* 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA TARA* _SADAUKARWA GA AMAREN 👰🏻DECEMBER🌙,DA KUMA NA SABUWAR SHEKARA📆 INA MAKU FATAN ALKHAIRI ALLAH YASA AYI LAFIYA A WATSE TAROU LAFIYA_ _SANARWA!SANARWA!!SANARWA!!!IINA MASOYAN OFFICIAL NABEELA DIKKO,INA MAKARANTA NOVELS DINA...DUK INA GAYYATAR 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI DA KUMA MASOYANA ZUWA AUREN KANWATA TA KAINA ❤ PRINCESS YASEERA DIKKO👰🏻 WANDA ZA'AYI ON 28/DEC/2019 ,BAN DAUKEWA KOWA BA NA NESA DA NA KUSA AZO LAFIYA ALLAH YA KAI MANA RAI AMEEN._😍 ______________________________________ "Tun ranar Yaya Saddiq Bai Kara min zancen komawata Hostel da Zama ba."Har nayi sati daya agidansa." domin na kula yaya Yana Jin dadin ganina agidan.Shakka babu Tabbas an samu canji agidan mussaman agefen girki,ina yiwa yaran abincin safe kullum suje da shi makaranta, kuma duk kalar Wanda su keso shi nake girka masu."Sannan idan na dawo da Wuri Ina daura sanwar dare,Ina tuwon semo,shinkafa da miyar taushe da kubewa."mufeed da Mufeeda Kuma yanzu suna jin dadi sosai sun sake da Ni kwarai, sun daina hayaniya,suna sallah yanzun,Kuma sun iya gaida Mutane idan sun gan su, har iyayen nasu yanzu suna gaidawa,Yanzu kowa agidan ya fahimci yaran sun samu canjin RAYUWA kuma Ina kokarin koyar da su karatun Islamiyya da na boko."Yaya Saddiq Yana jin dadin yadda nake kulawa da taimakon yaran, aransa sai fatan Alheri yake min,Yana son zamana gidan sosai Domin farin cikinsu ya karou ta kowanne fanni,Gashi Yana sakewa da Ni sosai tamkar kanwarsa ta jini,komai mukeso Ni da yaran Yana saya Mana,Haka kullum suke ganin kamar kada na tafi saboda canjin da akasamu agidaan Kuma kowa na nuna min kulawa cikin Yan kwanaki Anty Jalila ta sake min komai na gidan." " Anty Jalila sai dadi take ji aranta tasamu ma'aikaciya agida,Iyakacin tayi bacci,ko Kuma Kallo sai ta wanke goma ta tsoma biyar"KOMAI ni nakeyi agidan idan dai banje makaranta ba da Wuri ba,ko Kuma kafin na tafi tun Wuri sai na kammala aikin duka Sannan na wuce saboda wataran da karfe goman safe ko Rana ko Kuma karfe hudu na yamma nake fita."Daga Baya ne kawarta Subbyh ta shiga atsakanin mu,saboda ta zugaa Anty Jalila,akan na bar gidan kada na aure Mata miji."Duk da Ina Mata biyayya Ina kula da yaranta,Bai hanata daukar shawarar aminiyarta ba,saboda tana da tsananin kishi!"Akan Yaya komai zata iya aikatawa."Hakan akayi domin kuwa Anty Jalila ta takewa Yaya Saddiq burki dole saina bar gidan na koma Inda yace Mata tun farko Zan zauna!"Ba domin sun so ba shi da su Mufeeda."Yace na tattara kayana zan koma makaranta, ya Kara min sayayya na koma hostel da kwana.."Sai dai kullum mu kanje ofishinsa Ni da Abokina Naseer mu gaida shi."Wataran ya bamu kudin abinci Wataran Kuma bama samu saboda yau da gobe sai lillahi." "Na kwantar da hankalina sosai Ina karatuna yadda ya kamata Kuma Ina ganewa sosai."Dan kuwa muna group discussion da Naseer da abokinsana Deeni." "A hakan na Cigaba da tafiyar da rayuwata akwalejin shehu shagari.."Sai dai Banyi sa'ar abokan kwana ba, wato Yan Dakin mu da yake mu hudu NE adaki daya."Hali na ya babbanta da nasu."Hakan Rayuwata ta fita daban acikin tasu." "Su uku ne Esha Hayat wato (Aisha Hayatu)sai Kuma Deejah Yak(Khadija Yakubu) sannan Deeyarh Bas(Badiya Basiru) sai Ni Nadiya BB da yake ko Nan ma hakan suke Kirana wato Nadiya Balarabe Bello." "Kullum Yan Dakin mu ganina suke ban waye ba!"Sune suka waye suka San duniya da Abin da duniya take ciki."Saboda kawai bana shigar banza irin tasu Kuma bana watsewa da maza kamar yadda sukeyi."Sam basuda kamun Kai da yake na lura mafi yawa hakan yam matan suke na kwarai kamun Kai"Kalilan ne acikinsu abin mamaki har matan auren ba'a barsu Abaya ba!"Shiyasa na Kara yarda da kuma gasgata Maganar Mallam yunus Dina,Da ya CE"Jami'a gidan kowa da kowa ne."Nako gani saboda akwai shege akwai Dan banza Sannan akwai nagari aciki,kowacce kalar rayuwa akwai Kuma ko da me kazo amfika."Na tabbata hakan." "Ina ganin SU Esha Kullum cikin Kudi suke da sayen sutura masu kyau da tsada,Har gasar wanka da saka manyan Kaya masu tsada suke." ga su duk sun San manyan mutane da malammai suna shiri da su sosai,da duk wani Mai fad'a aji acikin makarantar." Iyakacin su,Fashion da budawa amakarantar ga yan jaan wanka cikin fita ta rashin mutunci,su fita yawon su,sucii mai kyau su Sha Mai kyau,Ina ji Ina gani nazama doluwa Yar Kallo acikinsu." ko sun ce min in zo ci abinsu banaci Kuma bana nuna bukatar komai Daga garesu."Ba yadda basuyi ba domin su ga na shiga acikin harkar tasu Ayta sha'ani tare,Amma naki!"Sun nuna min sutura saboda sun fahimci banida ita da yawa Mai kyau."sun nuna min kud'i sun bani abubuwan kwadayin duniya duk nayi banza da duk abinda suka bani."Nace da su nagode banaso Domin nafison abinda nasamu ta dalilin iyayena!!"Hakan Na Cigaba da karatun da ya kawoni makaranta." saboda su na gane basu damu da karatu ba Kuma basu da niyyar yinsa." sharholiyar su kawai suke ta duniya."A kullum fatan shiriya nake masu."Su kuma suna min kallon lusara Wacce batasan komai ba bagidajiya Yar kauye." "Saifullahi Aminin Jawad ne sosai Kuma Abokin shawarar sa."Sun shaku da JUNA sosai sai dai shi Saif yafi Jawad dama Amma dai dukkan su Maras *TARBIYYA* ne."Sun taso acikin so da kauna, ga gata da ake basu." Saifullahi shine karami agidansu,Saboda duk yayyensa Mata ne su biyar shi kadai ne namiji Kuma auta agidansu,saboda iyayensa manyan Mutane ne,Kuma yayyansa suna auren mazaje masu kudi.shiyasa ta ko ina,yake damawa da kudade son ransa Dan gata ne Dan auta Kuma autalele Sha leleh awurin iyayen sa da yayyensa ." "Yanzu kimanin sati biyu da zuwan su wurin Mallam Balarabe wato mahaifin Nadiya Tabbas sun Sami karbuwa kwarai da gaske agurin Baban nata Haka kawai yaji jininsa ya hadou da Jawad kaunarsu na ratsa jini da jijiyarsa,Duk ya kula yaron sai ahankali Amma dai ya karbe su hannu biyu kuma ya gamsu da kudurinsu."Aykuwa sunji Dadi sosai sai dai sun fahimci Baban bayada kwadiyin Abin duniya."saboda sun nuna masa kudade yaki ya karba." "Shiyasa suka canja dabara ta hanyar Sayayyar kayan masarufi sukayi yau,Saboda sun Kwana biyu basuje gaida shi ba!"Kuma wannan Yana Daga cikin shirinsu...Shiryawa sukayi tsaf acikin jallabiyoyi da huluna farare tas sunyi kyau kamar larabawan Sudan da yake dukkan baqaqe ne masu Dan haske."Da misalin karfe hudu na yamma hanyar tudun wada suka nufa kamar yadda suka Saba, Bayan duk kwanaki uku sukanje da sunan kawo gaisuwa ta mussamman agurin mahaifin Nadiya ko Yanzu hakan CE ta kasance." "Tun Malam Balarabe na sanyi sanyi da su har ya sake masu saboda ya lura yaran na da kirki,Kuma sanin girman na gaba ne yasa suke girmama shi Kuma suka dauke shi da muhimmanci tun Baya amsar abubuwan da suke kawo masu har ya fara amsa har cikin gidan suke shiga su gaida mama fad'imatou(Inneirei) suyi fira sosai da zancen kewar Nadiyar Haka sukeyi har aka Saba da JUNA."Kamar kullum yau ma zaune suke rashe rashe agidan Bayan an kammala shigo da kayan da suka kawowa su Mallam Balarabe." Sannan suka cigaba da firar su daga bisani suka fito."Mama Da Baba sai albarka suke saka masu da dimbin GODIYA." "Dariya sukayi alokacin da suka fad'a Mota,suna tafawa Jawad yace"Wallahi da farko sai Naga kamar bazan iya ba!"Saif "Hakuri ne bakada shi Jawad Shiyasa.. Saif yace Yana Dariya." "Yanzu nafara koyon ahakurin adalilin daukar fansa!" "To Jawad yanzu dai kaga Shirin mu Yana tafiya dai-dai." "Haka NE faa...Wai kasan da kyaar na tsara momy ta daina zancen zuwa ganin mutumen Nan.."Sai da nagaya Mata yaji sauki munje dubashi Baya gari yayi tafiya kauyen su..sannan NE fa ta hakura Tace sai yadawo ta tafi."Nace Mata to da kanmu zamu kaita har gidan." "Kace munyi arziki da mummy ta Batamana shiri,Inji Saif." "Wallahi kuwa narasa Ko Meyasa mom ta damu da taje, ai idan ta dage sai taje sai ta wargaza Mana shiri."Jawad yace." "Tafiya suke suna Hira da shewa,Saboda a yadda suka kaga Shirin nasu na tafiya kamar yadda suka tsara."Daa kamar wuya Nadiya ta kubuta Daga tarkonsu."Sai dai ta zama Abin tausayi, Domin Bata sani ba, ta tafi makaranta tabar Baya da kura." "Zaune nake Ni kadai adakin mu Ina dafa abinci Ina karatu da yake yanzu mun fara gwaji(test)." "Shigowa sukayi Dakin ko sallama basuyi ba da yake yanzu sun daina kulani sosai kamar baya."Ko kallon su Banyi ba!"Na Cigaba da karatuna." "Esha CE Mai raha acikin su."Tace Sannu Malama Nadiya." "Yawwa,Sannunku Nace da ita!" "Baiwar Allah Naddy Karatu,kawai ake ta sha..."Inji Deejah tana dariya. "Banza nayi Mata..tashi nayi na Duba abincina shinkafa da wake ce,Na had'a ta da Mai da yaji,zubowa nayi da su Nace suzo muci,Ba kunya Esha da Deejah suka zauna mukaci tare Dan ba kunya da zuciya ne da su ba!."Deeyart Ita dama akwaita da Jin kan tsiya Kuma bata wani yina sosai Tunda taga bana layin su." "Nan muka dinga cin abinci suna bani labarin yawon su da suka fito dana samarin su na malamai da Yan makaranta har na cikin gari ba'a barsu Abaya ba...nidai Daga Eh,sai Ehimnn ke hadani da su,Ina cin abincina su Kuma sunata zuba"Har muka gama nan ne nake basu Shawara akan su dinga shiga aji suna karatu,saboda idan har suka cigaba da hakan Sam basu yiwa iyayensu adalci ba,"Idan dai Haka rayuwar su zata cigaba'' "Deeyart da ta cika faam tace"Ke Malama kisani mufa ba yara ba NE!"Da Zaki wani zo kina Mana surutun banza to ki ajiye gaskiyar ki agefe!"watarana zatayi Miki amfani."Naga kina Mana kallon Wasu iri!"Me kike nufi Nadiya!?"Mu sakarai ne marasa TARBIYYA!?"To idan bakisan Wacece Badiya ba bari na sanar maki Kuma idan har zakiyi min adalci to Zaki iya Kirana da Mai *TARBIYYA* wacce iyayenta sukayi Mata *TARBIYYA* Mai kyau,Sai dai tuni ni na ajiye masu kayansu agida kafin na koma na DAURA Daga Inda na tsaya."Domin naga anan bazatayi min amfani ba!"Ni Badiya na kasance yarinyar kirki Babana limamin unguwar mu ne,Duk garin gwadabawa ba wanda Bai San shi ba,Haka mamana Malama ce matan aure take karantarwa Ni da yayye na duk malammai ne."Ko da na shigo makarantar nan da mutuncina da *TARBIYYATA* sai dai haduwata da Esha yasa nafara canja rayuwata saboda wannan CE mafita agareni matukar inason in Zama babbar yarinya kamar kowa Nan muka hade da Deejah."Ba komai yasa Ni canja rayuwata ba!"Illah!nagane a jami'a idn baka budawa kana wanka,to Kai ba kowa bane!"Kuma ba Wanda zai San da zamanka..malammai ma da kansu basa kula ka bare ka nemi Alfarma ayi maka da sauri."Amma ki Duba yanzu hakan bama shiga aji Amma muna da sakamako Mai kyau ajiye Wanda ma yafi naki ke Mai ikirarin kinzo karatu Kuma kinayi.Ki zauna ki gani zama amshi Takardun NCE lafiya law."Batare da Wani wahala ba!"Ko ba Haka Eshaa."Deejart Tace tana kallon abokanta cike da bacin rai!" "Tabbas Hakane Deeyah Domin Ni kaina gidan mu an min *TARBIYYA* sai dai ni ban dauka ba tun farko,Ni tun Ina gida Nike sharholiyata kuma da taimakon mamana,Sai dai Tace min Aysha ki kula, saboda tana Sona batason bacin Raina ko Baba yaso hukunta Ni ita ta ke tarewa."Kullum cikin kareni take Domin ganin kar aga nayi laifi!"Shiyasa Duk abinda nake tana sane Domin da taimakonta."Kuma idan nasamu kudade na kan tsakura na sammata." "Shiyasa da nazo makaranta na Cigaba da harkokina!"Na fahimta kokarinka da dagewarka bashi kesa ka ci jarrabawa ba!"A wannan zamani saboda tun Ina sakandare nasan da hakan,Wannan ne dalilina da yasa nake abinda Raina ke so."Amma Nadiya ki gane mu ma fa kamar ke muke muna da ilimin mu ki daina Mana kallon maras *TARBIYYA*"Esha taqare zantukan ta tana dafani."cike da gamsarwa." "Deeja dariya tayi Tace nikam agaskiya idan Nace iyayenah sun min *TARBIYYA* To hakika banyiwa kaina adalci ba!"Saboda Ni ko gidan *TARBIYYAR* ban taso ba bare nagani anayi na koya."Iyayena rikakkin Yan boko ne."Duk abinda mukeso agidan mu shi mukeyi Daga mu har iyayen mu kowa sha'anin gabansa yake."Shiyasa Ni da kannaina Duk abinda mukeso shi mukeyi."Kowa Yana da right tamkar rayuwa akasar turai hakan rayuwar gidanmu take,Nifa ko Islamiyya bana zuwa agida anan makaranta na koyi ibada saboda masallaci da muke zuwa idan muna Nan,Kuma anan nakejin karatun alkur'ani da waa"Azi."Kinga nikam amakarantar nan na fara koyon *TARBIYYA* "Shiyasa Tunda na taho na samu su Esha da Deeyah amatsayin kawayena sai muka dace da JUNA!"Babu Mai Jin kanmu muna zaune lafiya qlaw, harkar mu mukeyi Kinga kowa ya ganmu yaga manyan yara,mun samu sutura,Kudi,wayoyi masu tsada ki Duba kigani kowaccen mu iPhone 11 take riqe da ita."Muna business wata anan har iyayenta take taimakawa." "Hmnnnnnn yanzu motoci ne kawai suka rage Mana mu saya!"Kwanan zamu Kama gidan kanmu Domin munfi karfin zama hostel."Kuma Nan da kike ganin mu Duk abinda muke iyayenmu basada Labari musamman Ni da nake a zamfara."Yanzu zamani ya canja abubuwa da yawa mukeyi Batare da sanin su ba."Domin kuwa sune suka haife mu Amma mun fisu wayo da davaru."Ko karatun mukayi karshe kadamu za'ayi abaiwa wasu can da basa karatu muna Kallo,da musha haushi gwara mu bada haushi Nadiya."Kedai da kikaji Zaki iya rayuwar jami'a a Haka kamar bagidajiya da Kyaunki da kyaun jikinki sai kiyi."Amma kisani Nadiya zamanki ahakan bakida Wanda zaiyi making tsaye a makarantar Nan babban hadari NE."Saboda kowa amakarantar Nan yasan halin Wanda kike ganin ya isa gareki!"Shifa daban NE acikin lectures din makarantar Nan."Yana Daga cikin Yan tsirarun mutanen ake ganin masu mutuncine Kuma ake mutuntasu.."Sai dai Yana matsala Baya neman Alfarma ga kowane malami Kuma Baya yiwa kowa Alfarma."To ta Yaya Mallam Saddiq zai taimake ki ahakan Nadiya.!"Kina ganin Zaki iyah cinye jarrabawa ahakan Bayan akwai iri irenmu da akeyiwa alkawarin sakamako Mai kyau!?"Me kike so kicewa iyayenki idan har ba ki ci jarrabawa ki ba!?"Duk da mun fahimci Duk acikin mu iyayenki sunfi namu rauni!"Ba kuda shi ku talakawa NE!Amma gashi Allah yayi Miki baiwa bakya amfani da ita Dan kawai akiraki Mai *TARBIYYA* Mai mutunci Mai kokari Mai kamun Kai."Kisani acikin duniya akwai na kwarai kuma akwai Dan iska,Duk yadda ka zama bazaka wuce zagi ba awurin mutane!"Yanzu hakan ke kanki Nady akwai masu zaginki..Dan Haka kowa yayi abinda yakeso Kuma yake ganin mafitace agare shi,Wannan Shine nasara arayuwa Nadiya." "Numfashi na sauke Mai nauyi!tare da kallon su tabbas wadan su zantuka na su hakika gaskiya ne,Kuma sunyi tasiri azuciyata ganin yadda rayuwar makarantar take tafiya..." Sai na kasa cewa komai!"Kallon junan su, sukayi suna murmushi..."Tare da Cigaba da zantukan da zasu janyo hankalina garesu."A karshe hannunsa suka aza tare da yimin inkiya na daura nawa akai saboda suna Sona sosai." "Duban hannayen sau na Duba tare da Kawar Kaina!Tuni na nutse a cikin kogin duniyar tunanin zamanin mu ayau."Shiru nayi na Dan lokaci Ina nazarin amsar da zan basu saboda karatun Yanzu sai da dabaru ko mu hade da su!?"Ko Kuma mu raba hanya da su!?"Shi nake tunani, Domin ina Gudun watarana."Yanzu meye mafita agareni na shiga tsaka Mai wuya Ina son karatuna sosai,Amma Kuma Ina Jin asarar watsi da *TARBIYYA* ta!!Daman da kokarina da Kuma taimakon Yaya Saddiq na kwantawa gashi ance Baya neman Alfarma Ni ya zanyi Yanzu!!" *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA GOMA* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ _____________________________________ "Kimanin wata D'AYA da barina gidan,Anty Jalila ta shiga damuwa saboda Duk ta daina ayyukan da ta saba da yai sanadin zamana agidan,sai Yanzu ne ta gane cewa tayi wauta! na cewa na koma hostel da Wuri,Akan zance subyh saboda basu ko ga yaya Saddiq Dinma yace Yana Sona, hasashe ne kawai na zucia,meye ma Habibinta zaiyi da Ni karamar yarinya!"A gaskiya subyh tayi Mata asara Domin gashi Dan hutawar da takeyi ta daina aiki ya dawo Mata sabou!"Hakan gefe yaran sun damu da akai su wurina sosai.Shiyasa Yaya Saddiq Ya shirya ranar lahadi suka kai min ziyara wuni sukayi min a hostel,Su Esha sai yawo suke da su Mufeed block by block suna nunawa Yan faculty dinmu Wai ga yaran malam Saddiq."Da yake yaran barkallah akwai farin jini Domin sun biyo haske da kyaun maman su."Sai hotuna ake masu."Nidai Ina daki suka dawo da su,Kayan kwalam su Esha suka baiwa Mufeeda da Mufeed."Masu yawa har bakin get suka rikamu, nida su muka nufi office din Yaya Saddiq." "Da isar mu muka samu Yana rufe office,Masinja ya baiwa keys din office suna sai da safe da shi."Kudi Yaya ya bashi da munna ya Yana godiya.."Da gudu suka karaasa wurin Yaya tare da nuna masa kayan da aka basu na chocolates masu yawa.. "suna cewa Abba kawayen Anty Nadiya ne suka bamu."Itama Kudi tabamu tare da nuna masa Yan hamsin da na basu na naira dari." "Kallona yayi yace su waye kawayen naki!"Fuskarsa a daure." "Daman ba qawayena bane Yaya!"Dakin mu D'AYA da su." "Gobe ki Kawo su office Dina na gansu."KU Kuma KU shige Mota mu tafi." "Mota yake kokarin shiga ni kuma Ina bayansu gefen Mota, yaran sai hannu suke Daga min."Suna yaushe zAnzo,nace sai wani sati zAnzo weekend."Ina masu Bye kamar kar su tafi!" "Wayar Yaya ta dauki ruri Ina kokarin tafiya..A zuciata Ina Jin tsoron Kawo masa su Esha saboda sunyi popular sosai a school din."Nasan sarai Raina zaiyi mugun baci." "Ke tsaya!"na ji Yaya yace da Ni."Har na fara tafiya." "Juyowa nayi Adan razane!Rass!!!Kirjina ya buga na karaso gareshi..." "Ya ce"Amsa Allah!Wannan yarinyar ce,Fitinanniya!!!!ta dameni kamar batasan bakida waya ba!"Ki gaya mata karta Kara kirana banson damuwa!!" "Amsa wayar nayi jikina na rawa ko ba'a fad'a nasan mansura CE." "Da Sallama na Kara waayar akunne nah!." "Amsa,min tayi cike da iyah yi." "Tace"Alo kawas ya kike ya karatu?.." "Lafiya qlaw.."nace agajarce!" "Bayan mun gaisa nace mansura mata itama ya nata karatun?." "Lafiya qlaw,Nady nayi missing dinki da na Yayanmu kina Ina NE sai ki kwatanta min zan zo?" "A tsorace nace Mata Ay Ina zaune a hostel."Nan dai na kwatanta Mata." "Tace yawwa zan shigo mu gaisa...." "Ke ban wayata bAnson shirmen banza..."Yaya ya katseni."Haushi ya Kama shi aransa Saboda shi Sam ya tsani Wannan heqaqqiyar yarinyar Mai Kama da figaggiyar kaza."Zaiyi kokarin ya raba Nadiya da ita domin kareta da miyagun kawaye!"Ka da su lalata Mata *TARBIYYA* Mai kyau." "Da sauri nAce mansura karki Kara Kirana da layin Yaya zan kiraki da Lambar Yan dakinmu nagode sai anjuma.." "Ban jira amsarta ba!"Na katse Kiran tare da ba Yaya wayarsa Wanda har yayi nisa cikin tunani...Kallon tuhuma ya bini da shi." " saboda ya lura a Yan kwanakin nan na kara wayewa a kwayar idona da kuma yanayi na ya fahimci hakan."Amma azuciyarsa cewa yayi zai yiwa tufkar hanci."Mota ya shiga mukayi sallama da su ya wuce." "Ajiyar zuciya na sauke saboda yadda Naga Yaya ya canja min na tsorata sosai."Hanyar hostel nayi,A hanya sai gaisawa nake da masu kaunar min magana,saboda Ni ban damu da kowa ba!" Ina tafiya Ina zancen zuci har na Isa Dakin namu." "Fira sukeyi...Amma da na shiga Dakin sai shiru ya biyo baya..kamar da wata akasa."Littafaina na dauko Ina Dubawa."Nan suka canja fira ban dai koma ta kansu ba,Duk da ayanzu Ina shiga cikinsu muyi fira tare muna cin abinci tare kuma har dinkuna sun fara yimin Ni da su har wani suna naji ake Kiran mu da shi Wai 4Stars,A yanzun dai zance nasamu canji sosai na sutura da hijabai da takalma har akwati Mai Taya sun saya min Yanzu dai Nima Ina Jan wankana Kuma Duk abinda na saka ajikina Yana amsana sosai."Nan take na Kara kyau da haske ba laifi sai dai har Yanzu bana fita Daga cikin makaranta Kuma ban daina karatu na ba,sannan ko sun bani Kudi bana karba,Sutura da abinci dai Ina amfani da su Kuma muna mutunci sosai da su tun ranar da sukayi min taron dangi wurin bani Shawara da mafita."Sai dai banaji araina zan iya yin watsi da *TARBIYYAR* da iyayena suka bani akan Abin duniya." "Bayan na gama karatu abinci mukaci sannan na fita sallar magrib sai da nayi isha na dawo."Sabon karatu nake saboda gobe Litinin muna da gwajin EDU 113." "Jin Naddy ta katse kiranta da sauri yasa taji haushi da takaicin Domin tasan nata ne sila wato(Yaya Saddiq) mamaki sosai takeyi ko dai baya son alaqarta da kanwarsa,Yana Mata wulaqanci! shin me mutumen Nan ke nufi!?"Ko Naddy CE ta katse Kiran!?"Shin Yanzu shi Bai fahimci cewa na fad'a sonsa ba!?"Kullum ina kiransa Domin in gaida shi but ya kasa fahimta ta!?"Cap lalle akwai aiki agabana saboda Ni kam Duk duniya ba Wanda zai iya rabani da Yaya Saddiq dina."Da nakeso da kauna Wanda cutar Sonsa ta hanani watayawa."Tabbas na dauki damara kuma na shirya fad'a da kowaye akansa,dole NE ya so ni kodai Domin kissata da kisisinata nayi alqawarin sai na sanya soyayyarta abirnin zuciyarsa."Duk wannan zancen zucin mansurah ce ke yinsa Wacce Abin duniya ya taro akanta yayi Mata katutu azucia."A karshe tunanin mafita take sai zarya take a Dakin su." "Ko da suka koma gida sun Sami Anty Jalila tana kallon Zee world Inda ake series dinnan Amma." "Tayi zurfi wurin kallon ko Jin Kira batayi..." "Yaran da murna sukazo gareta suna nuna Mata kayan da aka basu Amma cewa tayi tagani suje su Sha Batare da ta ko kalle su bare Abbansu."T.v ya kalla kana ya dubeta tsaki yayi ya wuce abinsa." "Takaici NE fal azuciyarsa ace macce takai macce amma batasan yadda zata Kula da mijinta da yaranta saboda dakarchi da lalachi...."Allah wadai yake da rayuwar matarsa saboda wani bangare na rayuwarta Sam baiyi ba!"Wanda basai an fad'a Masa ba!"Yasan abinda ya shuka NE yake girba!Saboda ya san gidan da ya dauko ta!"Ba *TARBIYYA* ne da su ba!"Bare ta koya!"Bariki da kyaunta ne ya rudesa har ya aurota, Ashe tuni yayi zaben tumun dare!"Bai ankare ba sai Yanzu..."Da Dana sani ya fad'a toilet yayi wanka ya fito ya shirya."Falon ya dawo ya zauna." "Kallonta yayi Tama gyara sabon Zama tana kallon wani sabon series da suka sa married again."Wanda Shakka bayayi magrip da Isha na Nan kanta batayi ba!"Saboda sai zata kwanta take ramakon sallolin."Ya lura duk lokacin sallar magrip da Isha Jalila batayin su saboda sannan NE ake saka Sabon series." "Yaran ya kalla da sukayi bacci Duk sun hargitsa falon da ledojin minti da biscuits."Ko kayan jikinsu basu cire ba!" "Jalila....ya Kira sunanta." "Ehyeeeeh....Tace tana kallonta " "Idan kin dafa abinci ki kawo min..yace ahasale!"saboda ya fahimci hankalinta baya gareshi." "Habibi ban dafa komai ba!"Naga yaran basa Nan Kuma Kai kanaci awaje Nima tea da biredi nagama Sha yanzun Nan kagama cup ..Tace tare da nuna Masa saman stool dinda ke gabanta..." "Tsaki yayi Akan haushi baice komai ba! tashi tsaye yayi tare da nunata!"Ya ce''Nagaji da iskancin ki jalilah wai ke wace irin macce ce da batasan ya kamata ba!"Me Kika daukeni!?"Ya dace ace zuwa Yanzu na huta saboda akwai yara!"Idan da can mu kadai ne zan iya hakuri!" Amma Banda Yanzu Kisani dole kiyi girki bazan lamunci Zama da yunwa ba nida yara ga abinci agida."Shi kenan Ni kullum ahanyar restaurant kamar tuzuru!!"to Nagaji Kuma ba Inda zan Kara zuwa sayen abinci Bayan komai akwai agidana."ki Duba kiga yaranki sun kwanta da yunwa!"Wallahi sai hakkinmu ya kamaki!"Ke kice Daga bacci sai Kallo kamar ibada Kiji tsoron Allah ki daina barin Jin dadin dunia na hanaki aikin lada."Kuma Daga yau abinci wajibi ne agidana..."Ya karashe zancen tare da wucewa daki ya banko kofar azuciye!" gado ya fad'a ransa abace Yana neman mafita da abinyi!!!" "Ko agefen zaninta Bata ji shi ba!" Domin da Harara ta bishi!"Tare da tsaki saboda surutunsa ya hanata jin me ake."Sai da tagama kalonta tsaf...sannan ta kwashe yaran ta Kai Dakin su..."Haka Nan ta shinfide su da sabbin kayan nasu ajiki." ta wuce Abinta( _Ni Kuma nace ko addu'a bazata shafa masu ba!saboda neman tsari Daga shaitanun aljannu,Hattara iyaye masu halin Jalila,musani addu a wa yaranmu babban makami ce agaresu_) "Da kyar ta Isa Dakin su Bata tsaya komai ba ta fad'a gadon tana wash!"Alamar ta gaji da Zaman, ga hamma da tabiyo baya sai jerawa takeyi saboda yunwa Nan ta kwanta bacci Abinta Batare da tunanin komai aranta ba!."( _Ni Kuma tunanin sallolin da ake bin Jalila nake Anya ko ta rankasu fans!?"Tabbas Mata da yawa Kallo na hanasu sallah acikin lokacin ta musamman series din nan da ake sawa time din sallah,Ya kamata muji tsoron Allah mu dinga ajiye komai alokacin ibada har sai mun kammala IDAN KUNNE YAJI......_ ) "Zaune suke suna fira da Rabin ransa!"Sai dariya da shewa sukeyi cike da kaunar JUNA!" "Kallonsa tayi tace yaushe zamuje duba bawan Allah nan nasan dai Yanzu ya dawo."Inji mom tare da kafe sa da idonta masu saurin Kama zaren zance." "Gabansa ya Fadi!"Ya kalleta tsaf shi take Kallo..."Murmushi yayi yace mom sai..sai....ki saka ra...rana muje mugani idan sun dawo!"Jawad yace cike da inda-inda na rashin gaskiyar Nan!" "To na saka Rana,gobe zamuje ka shirya da yamma."mum tace." "To,Allah ya kaimu tare da tashi..."Ya ce"Zanje na kwantar mom..sai da safe." "Allah ya kaimu...My son mom Tace tana Murmushi cike da kaunar danta." "Yana shiga Dakinsa wayar Saif yake Kira sai dai akashe!!"Ya rasa me Zaiyi!"Saboda shikam Yanzu baisan meye mafita ba!" *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*[2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 12* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ ____________________________________ "Da Misalin karfe shidda na yamma ranar litinin yayi min ne. Abakin kofar hostel dinmu."Idona duk sun kumbura!" Su Eshaa ne suka taimaka min na kwashe kayana!..."Nayi bankwana da makotan Dakin mu nagaya masu zan koma cikin gari da Zama!."Muna nan tsaye muka hango motar Yaya Saddiq na tahowa wajenmu..."Nan take Deeyart ta juya baya suka Esha da Deeja suka bita!"A gurguje mukayi sallama da su suka bace Daga gurina!"da zummar zamu hadu gobe!" "Wurinsa na karasa na dinga zuba kayana but da yake ya bude Amma Yana Daga cikin motar..."Bayan nasa na shiga motar tare da gaida shi." "Amsawa yayi batare da ya dubeni ba!"sannan muka wuce." "Mun dauki lokaci muna Tafiya babu abinda ke tashi sai sautin karatun sheik Ahmad suleiman...Inda yake karanta Amanarrasulu..."Da kuma sheshsheqar Kukana da ke tashi...ko ci kanki Yaya Saddiq baice min ba!" "Yau dai mom ta tusa kewar saif da Jawad agaba sai gidan Mallam Balarabe domin taje Duba lafiyrsa." "Da yake sun kirashi awaya kafin su zo shiyasa suke da Tabbas akan Baba Yana gidan Kuma sun samu bakin zaren." "Da Sallama suka shiga gidan,Dukkansu." "Amsa masu Innarei tayi tana maraba da su." "Tabarma ta shimfada masu tare da kawo masu ruwan leda da Baba ya sayo masu kafin ya shigo."Ta ajiye fuska asake tana maraba da Mom." "Momy ta yaba da halin mutanen duk da Kasancewar su talakawa Amma suna da halin GIRMA." "Musayar Gaisuwa sukayi.."Da mom da su Baba." "Nan mom Tace"Baba ya gida ya karfin jiki."Da fatan kasamu lafiya." "Lafiya qlaw Hajiya jiki da sauki ay naji dama sosai!" Yaran Nan suna kokari sosai...Allah dai yayi albarka." "Ameen...innerie."Tace tana Murmushi." Jawad da Saif kallon JUNA sukayi...Tare da yake na Jin Dadi domin sun sami mafita..."Dayake shi malam Balarabe kwanakin baya yayi maleria har ya sanarda su Jawad Lokacin da sukazo gaida shi."Shiyasa ya dauki shine suka sanarda mom tazo masa ya jikin." "Mom taji dadin zantukan Baba"Ta CE Ba komai Baba yiwa Kaine domin azatonta ko wani dattijo ne mai shekaru." batasan cewa wahala da rashin hutu tare da cutar talauci ne ya tsofar da Mallam Balarabe tun Wuri." "Innerei Tace Hajiya ayni nasamu yarana masu son mu,Su jawad kaam Akwai mutunci." "Raaas gaban mom ya Fadi domin Innerie CE,mutum ta FARKO da ta ambaci mutunci tattare da su Jawad." "Mom mamaki take yadda su Jawad suka canja suka koma kalar kirki tun Daga shigarsu gidan har kawowa yanzu...Ba suyi wani abin rashin mutuncin ba!"Ko meye sila!?"Amma dai Akwai wata akasa Tunda har taga sun Sanya sutura ta mutunci,Wato Kaftan da hula..."Abinda Bata taba ganin sun sanya ba!" "Jawad ne ya dawo da mom Daga duniyar tunanin da take."Ya ce mom mu wuce Koh!?" ''Dariya tayi tace"To mutafi Baba Allah Kara sauki Kudi ta mike masa 10k Daman sun shigo da manyan ledojin kayan fruits ahannunsu sun ajiye."Tace aci da Hakuri Allah ya baka lafiya ya tsare gaba!" "Ameen,Baba yace Yana ta jera GODIYA da fatan Alheri wa mom da yaranta." " Saif yace to Baba sai mun dawo fira jibi."Yana Dariya "Malam Balarabe yace yawwa saifullahi sai na ganku fa Hajiya angode Allah ya saka da alkhairi,Muhammad sai kunzo cewa da Jawad."." "Ameen..mom Tace." "Jawad yace Baba sai mun dawo," "Innarei tace gaskiya kuna kokari mun gode ay ba Haka ake ba!"Gashi 'yarta ki tana makaranta har yau ba ta dawo ba." "Mom Bata fahimci Innerie ba.."Yake kawai tayi ta shige suka bita Abaya..Nan suka isa Mota Baba har can ya rakasu Yana masu GODIYA." "Innerie Koh Daga zauren gidan ta tsaya tana musu Sallama."Tare da tunanin kirki irin na wad'annan mutanen..."Tsoronta daya kada Nadiyatou ta dawo asamu matsala!"Koh da yake tana da yakini akan *TARBIYYAR* da suka baiwa Yar su bazata taba girgiza masu ba!"Bare Jawad baida aibu ko makosa ko kadan."Domin ya nuna masu halin kirki yaron kirki ne kawai zai fitou agefen da Jawad ya bulkowa lamarin!!"Da tunanin ta shige Daga cikin gidan tana Cigaba da ayyukan ta."Tana yiwa Allah GODIYA da yakawo haske arayuwarsu." "Baba Yana ganin tashin motarsu Jawad, shagon unguwar ya nufa domin sayen abubuwan da suke buqata, Daman kudin sun zo masu alokacin da suke nemansu."Shiyasa ubangiji ya kawo masu su Jawad sanadin tufin asirin su."Ikon Allah kenan da Amfanin Kai Kuka awurinsa, Allah kenan Al-ahad Al- samad."Sai ya kawo mafita ba zato ba tsammani da zancen zucin Malam Balarabe ya isa kantin ya fara sayen kayan da yake bukata!" "Dab da magriba suka iso kofar gidan su...Hon suka yiwa Mai gadi ya bude gidan Mom suka sauke sannan suka shiga masallacin gidan domin an fara Kiran sallah." "Mom shiga tayi tafara watsa ruwa sannan tayi sallah tana dawowa falon, suna shigowa..." "Daning place suka nufa domin abincin dare ya Dade da kammala."Har an jera komai akai." "Da mom da su abincin suka bude kowa ya zuba suka fara ci..."Suna taba fira." "Nan mom ta kalle su ta fahimci suna cikin farinciki." "Tace Saif.." "Na'am mom ya amsa." "Nace wai...meye sirrin? ko dai mun fara Yar boyen sirrine da KU?.." "Yace kamar ya mom!?" "Kun fara neman aure Banda Labari ne..!?" "Jawad yace aure fa mom!?" "To sarkin tsari...Ba da Kai nakeyi ba da Saif nake."Inji mom tana hararen Jawad "Kansa ya Sosa Yana murmushi.."Tare da cigaba da cin abincinsa." "Saif ma dariya suka bashi yadda suke wannan da mom..." "Na dawo kanka saif kasan bana son wasa ko to kagaya min Gaskia meye alakar KU da wadan can mutanen..?"Anya kadaiwa ce kawai!?"Wannan hankali da kukayi asanadin su!?" "Kallon Jawad yayi da ke cin abincinsa ko ajikinsa." sannan yace"mom kiyi Hakuri a gaskiya Jawad ya fad'a son yarinyar gidan ne." me suna Nadiya..."To har yanzu Bai sanarda ita ba!"Iyayenta dai sun sani,Saboda ance masu *TARBIYYA* ta kwarai kafin su Sami yarinya da zancen so iyayenta suke sanarwa domin ayi komai amutunce!"To ya zu dai su sun sani Kuma aurenta Zaiyi ba da wasa ba!"..."Daman muna son ta dawo Daga makaranta ya sanarda ita. ne Daga Nan idan ta aminche sai mu sanarda ke!"Amma kiyi Hakuri mom...Inji Saif Wanda a cikin sigar rarrashi yake maganar." "Wani Abu Jawad yaji tamkar an cika Masa mashi akahon zucia..Alokacin da yaji Amininsa na fadin waaai...ya kamu da son wacce yafi tsana adunia! wacce ya tsani ganin ko da Mai sunanta ne!Wacce yake burin daukar mummunar fansa akanta!"Wacce yake da kudurin ya wulaqanta dukkan rayuwarta!!!"Tuni Idonsa suka rikide zuwa ja abincin ya ture tare da tashi ya fice yace kasameni part dina saif Cikina ya murda zan kwanta!!!"Jawad yace tare da tafiyan sa abinsa..." "Da yake saif Dan duniya ne Tuni ya dago bacin ran abokinsaa!!!"Sai ya fashe da dariya yace sun kunya manya bawani ciwon ciki sai nazon..." "Ya kalli mom yace"Ai mum yau kin hada rigima saboda munyi da Jawad sai Nadiya ta aminta za'a sanar maki."Kinsan mutumen nawa yanzu fushi NE yayi saboda na gaya maki Gaskia." "Murmushi mom tayi Tace"A Gaskiya naji Dadi wannan zancen idan har da gaske Jawad na sonta Kuma Zaiyi auren da gasken...zanyi murna da hakan Saif,domin na k'osa Naga kun Zama mutane kunyi aure ya fiye muku wannan shirmen banza da kukeyi!" "Yanzu dai mom karki damu In shaa Allah mun Zama mutanen kirki..."saboda mun fara hankali..ki dai tayamu da addu'a Allah yasa muyi nasara." "Saif zanyi maku Addu'a da fatan shiriya, sannan idan takama har ni zan shiga zancen domin ganin ya samu abinda yakeso, duk da ba Yar gidan talakawa naso ya aura ba!"Na ci buri akan auren Jawad naso ya samu Yar gidan manyan mutane masu Kudi na asali ya aura mu daki JUNA da naira,Nayi hadashi da yaran qawayena, da 'ya'yan Abokan marigayi Bavansa diyan masu Kudi Amma kana sane Saif duk yace baya son su.." sai Wannan Nadiya zaice Yana so!?" "Mom may be ita ce zabin da Allah yayi Masa." "Hakane Saif,Allah yasa ita CE Alheri,Zanyi munna da hakan Daman shine burin mahaifinsa,yaje da burin son ganin auren Dansa."Mom ta karashe zancen cike da damuwa." "Allah ya gafartawa Abba." "Ameen Saif..." "Shima abincin ya ture tare da Shan ruwan faro da ke ajiye...yace mom Bari nasamu nawan..."Sai da safe." "Yawwa Saif ka gaida Mamie Kwana biyu bamu hadou ba..." "Zataji mom.." "To sai da safe Nagode sai naji yanda dik kukayi adinga sanar min." "To Mom zakiji saif yace ya nufi sashen Jawad ." "Mom abincin ta Dan ci kana ta Kira Inna tare da Bata umurnin ta kawo Mata kayan fruits." "Jiki na rawa Inna ta dauko su afirijin Daman ta gyare su sun dauki sanyi...ta kawo ta ajiyewa Mom..."Sannan ta wuce dakinta..."mom falon ta dawo dauke da filet din ta,kallo takeyi tana chat da kawayenta tana Shan kayan lambun." "Horn yayi kusan sau uku Alamar da yake masu idan ya dawo..."Sannan yayi parking motar a Inda yake ajiyeta..."Aykuwa fitowar mu ke da wuya sai ga yaran da gudun su.."Suna oyo yo Abba." "Ganina yasa suka daka tsalle da kuwwa suka rugumeni Anty Nadiya oyo yo..."Cike da murna suka dinga daukar Yan kananan kayan da suke iya saukewa abut din." "Mufeed da Mufeeda sai munna sukeyi...ganin hakan yasa naji Dan sanyi araina na sake fuskata...Saboda a hanya Yaya Saddiq yayi min tatas tare da kashedi da sharudda akan na kiyaye na kula da kaina "A karshe Baba ya Kira awaya yabani shi muka gaisa har nace yabani mamana yace Yana kanti wurin sayayya."Kuma Daga can masallaci zaije alokacin." "Da taimakon yaran na kwashe duk kayana Yaya Saddiq Tuni ya shige gida yabar mu..."Rufe motar nayi Bayan mun kammala."A Lokacin da na shiga gidan naji wani iri araina.."Hakan dai na adana kayana adakin yaran nadawo falon."Ina tambayar Anty Jalila?" tana wanka Inji yaran."Nikam zaune nayi shiru sukuma sai zuba suke.." "Tana wanka ta dinga jiyo hayaniyar yaran suna fadin sunan Anty Nadiya..."Nan take taji wani sanyi aranta..."Tuni ta manta da wanka take ta dinga tikar rawar India har da su shoyki tana Alhamdulillah gobe zanyi baccin safe, Addu'ata ta karbou."Nan da Nan ta watse ruwan ta fito ko Mai Bata shafa ba tafito Sanye da jallabi.A falon Inda muke." "Yaran na jikina suna surutu ta karaso cike da fara'ah Tace A'ah Nadiyatou CE Wai... " "Nace"Eh.....Anty Ina wuni,tare da sunkuyawa Daga kujerar.." "Ta ce"Lafiya qlaw,ya makaranta!?" "Nace Alhamdulillah." "Kallona tayi Tace anzo Mana kwanaki NE?" "Eh,nace." "To Nadiya Monday ake zuwa weekend jiya sukace zakizo wani mako?" "Eh,Anty,Daman naso nazo wani sati weekend ne,Yaya ne tare yace inzo ya wutou da Ni." "Ok,Tace." "Nace,Anty... Bari nayi sallah muna hanya akai sallah..." "To sai kin fito ga da wake can kisaka ku ci." "Nidai na koshi gaskiya Anty domin na ci abinci a hostel."nace Mata saboda nikam bana komai ayanxu." "Mufeed Ina Abba!?"Anty Jalila ta tambaya." "Ya tafi masallaci Mufeeda ta baiwa maman su amsa." "Tashi nayi yaran SUKA bini sai dadi sukeji kamar an gafaerta masu."Alwala nayi tare da tada sallar magrip da ishaa da yake lokaci yayi muna hanya akayi sallah gashi motar mu tayi faci ahanya muka samu tsaiko..." "Ni da yaran mukayi sallar magrip sannan Ishaa...Bayan mun kammala Azkhar mukayi Ina koya masu...Nan SUKA dauko littafan su suna nuna min ayyukan da aka basu da taimakona sukayi aikin..."Sannan nace suje falon suyi kallo Inda mamansu saboda nikam Ina bukatar hutu mussamman da na tuna da qawaye na su Esha Nan naji Wasu zafafan Hawaye na zuba a idona." "Duk sai naji komai ya fita Raina!!!" "Amma ahakan zan hakura na Cigaba da Zaman Hakuri agidaan Yaya Saddiq...." Kui hakuiryh fans Ina ganin comment naku Ina godia zakuji Ni hiru a Yan kwanakin nan cos zan shiga busy ana auren kanwata Amma idan nasumu time zan Dan tsakurou muku ki read more 1 ne,Ina neman Addu'oin KU wa auren Habibartynah😍 *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 [2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 11* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *TUKUICHI NEH GAH* _Mesona,farin cikinah Hasken idaniyatah Abin alfaharinah Nagode sosai da kulawa Allah yabar zumunchi da Zaman tare Ameen_*FATAN ALKHAIRI*😍 ______________________________________ "Ta Kama yau ranar litinin CE,Ranar da ko bature Yana tsoronta!"Tunda na kammala shirina tsaf acikin wata atamfa metro ruwan miyon goro da fari,dinkin riga da siket ne yayi min kyau sosai."Da yake su Eshaa suka dinkama ita dinkin ya amshi jikina sosai."Hijab fari nasa irin wannan da ake daurewa baya."Yayi min kyau,Takalmi na saka sannan na dauki jikata,Na fita da zummar su Esha zasu sameni din faculty mu."Saboda tun adaren jiya na sanarda su zasu rakani Inda Yaya Saddiq muyi masa barka da zuwa." "Ina fita Inda muke haduwa da Naseer na wuce Banyi minti biyar awurin ba sai gashi yazo da gareni." "Yace "Malama kiyi hakuri kinata jirana..." "Murmushi nayi nace bakomai antashi lafiya." "Yace"Lafiya qlaw,Gaskia Nady yau kin fito kamar balarabiya ko dai kin hada Da su ne." "Dariya nayi wadda sanadinta sai da dimple dina suka lutsa..nace ehhhhh...Ni balarabiya ce...kaga bana son zolaya muje tun ba Kai min format din abinda na rike ba.." "Naddyh kenan kefa karfe ce..na yadda da karatunki bazai taba zuwa ko'ina ba.." "Nan dai muka wuce muna Tafiya mina firar da yake jinin mu ya hadu sosai da Naseer...Haduwata da shine na fara rage tunanin malam yunus.." "Acikin awa Biyu muka kammala gwajin mu(test)."Cikin ikon Allah duk abinda aka tambaya na amsa saboda nayi karatu."Da munna na fito Daga Hall din Ina dubin ko Naseer Ya fito da yake bama Zama guri daya uztaz ne baya chakuda acikin Mata ya zauna sai idan takama dole." "Bayan ya fito ya sameni zaune Ina jiransa..."Firar tambayoyin mukeyi da yadda malamin ya rikita Mana lissafin saboda tambayar a hikima yayita idn mutum Bai fahimta ba sai ya fad'i."Daga nan Dakin karatu muka shiga muka Duba Wasu littafai acan nabar Naseer saboda munyi da su Esha idan Sha biyu tayi zamu hadu muje Inda Yaya Saddiq." "Banyi wahalar samun su ba domin nasan Inda sukafi yawan Zama.Nan nasamesu sai ciye_ciye kayan kwalaam suke maza da Mata."Da nesa na tsaya ayko Nan take suka tashi suka sameni...Kallon su nayi ba laifi duk jallabiyoyi suka saka..."Sukayi rolling da mayafin rigunan."Sunyi kyau sosai da yake ba karya dukkan su Sunyi kyau da yake suna shafa mayuka masu tsada kowacce sai sheki take Sunyi tatas da su." "Deejah tace min muje Malama Naddy." "Esha ta ce"Ya test din ko da yake nasan ku masu kwanya ne zakuci..." "Murmushi Deeyart tayi batace komai ba." "Bamuyi doguwar Tafiya ba suka isa admin din."Office din Yaya Saddiq mukayi knocking..."Sai da naqara yin wani sannan yace Mana Yes come in (Alamar mu shiga)" "Da Sallama muka shiga office din.. "A hankali ya amsa Mana tare da ajiye wasu files a side drower dinsA." "A hankali muka gaida shi..." "tuni su Esha suka sha jinin jikin su saboda kwarjininsa da cikar zati." wani da wani irin Kallon Nan na ba yabou ba fallasa da Yaya Saddiq ya bimu da shi."A lokacin da ya dago kansa ya ganmu..."Tare da amsa gaisuwar adakile!" "Da sanyi nace Yaya Daman mun zo mu gaishe ka ne.." "Yawwa to kun kyautah..."Ya karatu!?" ya tambaya "Lafiya qlaw....nace da shi" "Wad'annan fah!"yace tare da nuna su da hannu.." "Rass!"Gabana ya fad'i!"Cikina ya dauki duri kada ya wulaqanta su..." "Da...Daman 'yan Dakin mu ne!"nabashi amsa." "Okay...yayi KU Nagode Kuna iya Tafiya zanyi magana da ita." "Kamar jira suke kowaccen su ta miqe Daga kujerar da take zaune.,sum sum suka fita jiki na kyarma!"Saboda duk iskancin basa wasa da irin su Yaya Saddiq." "Suna fita ya kalleni...sama da kasa!"Ya ce"Da kyau! haba biri yayi Kama da mutum...Shiyasa naganki kin wani canja Ashe da marasa *TARBIYYA* kike rayuwa!" "Kina ganin kinyi wa iyayenki Adalci Nadiya!?"To wallahi bazan lamunce ganin ki da wadan Nan 'yan iskan yaran ba!"Sai dai ki koma gida da karatu saboda Baba Ni ya baiwa amanarki!" "Meye alakarki da su!?"Ya tambayeni a fusace!" "Kuka!nakeyi yayin hawaye na ke malala a fuskata!"Nace wallahi Yaya Sam bana rayuwa irin tasu Dakin mu ne daya!"Kuma nifa ko yawo bamayi tare ko yanzu Dan kace nakawo su ka gansu ne..."Naqarashe maganar muryata na rawa.." "Saboda naga kin canja ne ya sanyani tuhumarki!"Shiyasa na nemi ganin su.."hankalina ya tashi alokacin da na hango wayewa da canji a kwayar idonki...sannan tsadar chocolates dinda suka baiwa su Mufeed ne ya bani mamaki...domin Ina sayen irinsu nasan kudin su..."Amma ace Wai kawayenki. Zasu iya KYAUTA da su amatsayinsu na dalibbai." "Daga yau karna Kara ganinki da yaran nan saboda lectures da dama sun nuna min su amatsayinsu tsagerun makaranta."Duk makarantar Nan ansan da labarinsu da Zaman da suke school dinnan."Kina tunanin ba za'ayi muku dauka daya ba!?"To kisani babu ke babu su!"Kuma na baki Nan zuwa yamma ki tattara komai naki Zaki koma gidana da Zama saboda ko an raba maku daki nasan zasu iya binki har Inda kike su canja makin rayuwa...." "Dai-dai Nan nakara fashewa da Kuka saboda na shaku da su Eshaaa,Ban son rabuwa da su..."Jin kukana!ya tsananta yasa Yaya Saddiq yace na fice nabashi guri karfe shidda ya sameni bakin get din hostel da kayana." "Fita nayi cike da kunci azuciyata!Nasan bana rayuwa irin ta su Eshaa Amma Ina da burin cetou su daga halinda suke ciki!"Ban Kai ga cika burina ba!"Yaya ya yanke min kuduri!!!"Tafiya nake Batare da nasan Inda nake kada kafata ba!"Banyi aune ba sai Jin nayi karaf an rikemin hannu." "A zabure na dubi gabana ...wani ne. Wanda ga alamu kamar malami ne.." "Hannuna na kwache a nasan tare da bashi hanya ya wuce!" "Murmushi yayi yace"Yammata Kuka Bai kamace ki ba!"Kina da kyau hakan har za'a ga hawaye kwance a fuskarki Kuma kina 'yar jami'ah..." "Ya Kara kallona Yana murmushi yace ki gayamin damuwarki zan taimake ki wanene ya kadake!? ko ya cuceki!?" "Takaici ya bani bansan sadda nayi tsaki ba!"Na wuce abina saboda yabani haushi tabanin da yayi!" "Tsaye yayi Yana kallona...."Yace Kai!Ni wannan yarinyar zata yiwa tsaki!"Hmnnnn zan nemoki yarinya Zaki shigo hannu...Tabbas watarana za San waye malam Dan Bala!"Ya wuce office dinsa Yana mamakin yadda Mai kyau ta masa tsaki duk yadda yake jin kansa." "Ko da na fitou fili Banga su Eshaa ba!"Duk da muna lecture 4_6 ban tsaya ba hostel na wuce saboda ban San abinda ke min Dadi bA!" "Na Saba da rayuwar hostel tsawon watanni biyu..."Naji dadin rayuwa acikin mutane!"Na fara iya mu'amala da mutane da yadda AKE zama da su Naga wadanda suka fini *TARBIYYA* ilimi,da addini har Ina kwaikwayon su Amma yanzu Yaya Saddiq Yana son ya rabani da su!"Saboda su Eshaa da nasan a mazaunin da na ajiye su arayuwata." "Da tunanin na isa Dakin mu....Gabana ne ya fad'i alokacin da na kalli fuskokin su...kowacce ba fara'a ita Deeyart har da hawayenta..." "Banyi kasa agwuiwa ba!"Nace Eshaa, Deeyah, Deejah Dan kah kui hakuri da abinda Yaya Saddiq yayi muku kunga koni yanzu yayi min wannan halinsa ne KU kanku kunsani Kuma kunji aschool ana fada!!!" "Ba komai duk abinda yayi Yana da dama domin mu muka Kai kanmu!"Inji Deeyart cije da bacikin Rai!" "Eshaa tace wallahi saboda ke mukaje Naddy..."Kuma Dan kawai kince mu rakaki ne!" "In dan badomin Hakan ba! me zai kaimu!? mu da sai ma an gayyace mu muke shiga office! Mutim ko provost sai ya nememu muke zuwa bare shi waye shi!?"Me Kuma ya dauki kan sa" "Deejah kenan."KU daiyi hakuri koma menene nice sila!"Nace da Deejah wacce ta gama zancenta tana cika tana batsewa.." "Shiru sukayi Ni Kuma tashi nayi Ina had a kayana..." "Eshaaa tace Naddy Ina zakije Naga kina had a kayanki ba dai akan wannan maganar ce zaki bar Dakin ba!?" "Hawaye masu zafy!suka fito min nace Eshaa Yaya Saddiq yace"Gidansa zan koma da Zama duka...!!" "Menene!Naddy!?cap lalle bawan Allah nan anyi mugun gaske,!"Saboda kawai yaga shi aka baiwa kalihunki shine yayi Miki hakan..."Inji Eshaa "Ni kaina Ina son zamana anan Eshaa Gidansa bazan sake ba!"Bazanyi karatun kirki ba!"Amma ya zanyi Ina gudun ya Kira Babana ya Gaya mashi wani Abu akaina ran iyayena ya baci...Dole nabi umurninsa..."Nace Ina Kuka!!" "Hmnnnn...Tabbas zai Gaya masa kin lalace Tunda kina rayuwa da mu lalatacci!"Inji Deejah "Ba Haka bane Khadija...."DakAta Naddy Wallahi hakane!"Saboda kowa a makarantar nan ya ajiye mu amarasa *TARBIYYA* da kamun Kai!" "Tabbas hakane Deejah!"Nidai duk Wanda ya zarge mu akan abinda bamayi Allah ya isa!Domin baka shaidun mutum Ayau!" "Hakane Deeyart!"Inji Esha wacce ta tashi Daga Inda take zuwa wurinda Dan firijin dinsu karami yake!"Ta bude tare da dauko lemun kankana Mai sanyi ta kurba kana Tace" mudai Allah ya wanke mu,Daga zargin da ake Mana!"ke Kuma Naddy kiyi hakuri ki yafe Mana domin Zama da mune yasa ake ganinki kema kin lalace har aka Bata maki Rai!"Daman Zama da madaukin kanwa ke Sanya farin Kai!" "Nidai Har ga Allah Nady Ina sonki Kuma Ina kaunar Zama da ke Inji Deejah..." "Kuka ne ya kwace Deeyart da yake akwaita da saurin Kuka da hasala!" "Tace"Yau akan mu ake kokarin Naddy da Zaman hostel!"Tabbas Akwai gyara arayuwarmu saboda shaidun duniya shine na kiyama..."Hakan da akayiwa Naddy ya zame Mana izinah!"Kenan babu masu Mana shaidar kirki!"Mun b'ata record dinmu Tunda har mukayi watsi da *TARBIYYAR MU* tun farko yanzu ko mun so mu nunawa mutane abinda suke zargi ba shi bane ba bazasu taba amincewa ba!" "Hakane Deeyart mun makarou Inji Eshaa itama tana zubar da hawaye!!" "Deejah kam tuni jikinta yayi sanyi..."Tana nazarin rayuwa!!" "Nace kuyi hakuri kawayenah!Kusani na shaku da KU bazan iya barinki ba!"Muna tare yanzu ma naji Ina son zumunchi daku!!"Sai dai Kusani shi Zaman duniya iyawa ne Kuma duk abinda zakuyi kuyi nazari kuyi amfani da *TARBIYYA* da kuma addininku...Saboda idon mutane ma'auni ne...Shiyasa tun farko nake kokarin sanarda KU gaskiya gashi yanzu kowa Yana zarginku alhalin KU abinda ake nufi da KU ba Haka bane!" "Wallahi Nady iyakacinmu mu ci kudin samari muyi sayayya da su muyi shiga irin yadda ranku ke so Amma Sam bama watsi da mutuncinmu.."Sannan farin jini ne Allah yayi Mana Iyakacin mu rashin mutuncin anan ya tsaya!"saboda mu aganin mu wayewa CE!"Inji Deejah." "Na dubeta!Nace Babu wayewa Deejah sai tsabar halaka!"Wacce yanzu sanadinta ana maku kallon marasa *TARBIYYA* Allah dai ya yafe Mana yasa mugane ." "Ameen..."Deejah Tace. "Nan na kammala shirina tsaf acikin akwatina..."Lokacin Tafiya ta kawai nike jira.." "Tsittth!!!!Dakin yayi kamar wadanda ke Zaman makoki....Mun Sha Kuka!"Har mun gode Allah"Sai yanzu nagane su Eshaa nada kirki!"Hakan Suma sai yanzu suka Kara tabbatar da mutuncina..." *'YAR MUTAN DIKKAWA* [2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 13* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ ___________________________________ "Wannan karon zamana ya sauya a gidan Yaya Saddiq saboda na daina sakewa sosai da shi!" "Bana son muna yawan haduwa da shi a gidan,Sai dai idan zamuje karanta ko mundawo,Idan Yaya Saddiq Yana falo bana Zama!"Ina Dakin mu Ni da yaran." "Hakan yayiwa Anty Jalila Dadi,Ganin yadda nake nisanta kaina da mijinta." "A gefe ban bar komai da nakeyi ba agidan,Sai dai Idan bana Nan Ina makaranta."Kuma yawanci kafin na fita sai na kammala dukkan ayyukana.."Shara! mopping da girki,da yake wanke2 tun acikin dare nakeyi." "Su Mufeeda da Mufeed ba laifi akwai soyayya sosai atsakanin karatun boko da na zamani Ina koyarda su.."Musamman gefen sallah da *TARBIYYA* duk Ina kula da su sosai."A yanzu kwakwalwar su ta bude ga ladibi da biyayya da suka samu agurina." "Yaya Saddiq Yana jin dadin yadda al'ummara ke Tafiya agidan sa..."Dawowata agidan ya kasance sanadiyyar farincikinsa Haka kawai yaji ya Sami nutsuwa da kwanciyar hankali arayuwarsa." "Kimanin watana HUD'U da kwanaki a sakkwato birnin shehu Ina karatuna a kwalejin shehu shagari."A yanzu hakan mun kammala (C.A) din mu duka sai batun fara zana jarrabawar zango na D'AYA wato(FIRST SEMESTER)."Saboda hakan ne na Kara mayarda hankalina akan karatuna." "Alaqata da kawayena su Eshaa,Dejeeh da Deeyart tana Nan daram ba Inda ta canja sai dai aboye nake zaune da su.."Ina zuwa faculty su da dakin su a hostel."Muna zumunci sosai Ni da su saima ayanzun kawancen mu yaqara tasiri azukatan mu."Duk yadda muke mu'amala da su munayi ne aboye saboda Yaya Saddiq ya Sanya Abokina Naseer da saka idanuwansa akan duk wani motsina a makarantar ya sanar Masa."Shima Naseer Tuni ya daukarwa Yaya Saddiq alqawarin Gaya masa gaskiya in dai akan su Eshaa ne saboda ya tsani ya ganni tare da su."A ganinsa lalatacci ne wadanda beraye suka gama wankewa idanu."Bai kamata aganni da su ba!"Musamman ayanzu da zuciyarsa ta Dade da tabbatar Masa da ciwon Sona da ya kamata!"sai dai har yanzu ta kasa furtawa abin sonta saboda labban baki sun ki bayarda wata kafa ta furuci!"Sai dai Tuni idaniya suka nunawa abin sonsu me zucia take nufi!" "Hakan na cigaba da rayuwata da ciwo da Dadi Ina karatuna tare da taimakon Naseer...."Kuma Ina ganewa sosai." "Wayar hannunsa ya ke latsawa ga alama lambar da aka rubutawa My man ita ce yake Kira...."tare da karawa a kunnensa.." "Hello!"A kace adayan BANGAREN." "Kai kana Ina ne Kai nake jira fah.." "Oh!sorry man gani a low-cost Mami ta aikeni na karbou Mata sako!" "To,Ya za'ayi!?" "Ka jirani Ina zuwa yanxun..." "Ok!"Sai ka shigo." "Yawwa" "Tnx...Ka gaida Mommy "Zataji.."Yace agajarce tare da katse Kiran.."Zaune yayi Yana duban wayarsa tare da kallon tsintsiyar hannunsa domin Duba agogon da ke daure a hannun nasa Mai kyau da tsadar gaske." "Bayan mintoci talatin da dakiku sai ga Kiran abokin nasa ya shigo...Iska ya furzar tare da manna bakin gilashinsa a fuska Wanda ke Kara fito da Masa da kyawunsa kamar irin na bakaken fatar Nan ta kasar Sudan." "Dakin ya rufo tare da Daga wayar yace gani Nan sannan ya kashe tare da fita Daga sashen nasa duka..."A harabar gidan ya Sami Saif tsaye ya hade hannayensa a kirji yana kallon Amininsa da yayi kyau matuka wata Muhammad Jawad Husamaddin." "Tafawa sukeyi tare da gaisawa sannan suka fad'a a SABUWAR motar Jawad PRASO kalar kasa Mai kyau." "Tafiya suke suna sauraren M Sharif ta SAREENA."Saif hadda bin wakar cike da sauki."Jawad da ke Driving kallon titin yake..."Yana Dan fira da Saif.."A hankali ta karya kan motarsa a kwanar Tudun wada layin gidan su Baba Balarabe suka."Ba suyi wata Tafiya suka karaso kofar gidan."Tsayawa sukayi kana suka fito.." "Da Sallama suka karasa Daga ciki.. " "Innarei ce ta Amsa alokacin da take kwashe tuwon dawa da ta kammala tukawa." "Tarbarsu tayi alokacin da suke gaidata..."Tabarma ta SHIMFID'A masu tare da kawo masu fura da ruwan leda da Baba BALARABE."yake sayowa agidan ruwa da ke saman tudun layin nasu." "Bayan Innerie ta ajiye masu daki ta shiga tare da gayawa Mallam gasu Jawad Nan..."Kimtsawa yayi fito da yake ya Dan kishingida NE." "Innerie ko tuwon ta ta Cigaba da kwashe tana adana komai a mazauninsa..." "Su Saif Tuni aka bude Sabon babin fira da Mallam Balarabe kamar yadda suka saba."Tun suna kyamkyemi akan abuncin gida har suka daina akan dadi da dandanonan bincin gashi sun yaba da tsaftarsu matuka..."Nan Innerie ta zubo masu tuwon dawar da danyar kubewa Kore Shar da Tasha kayan kamshi da daddawa da busheshshen kifi..."Ay Nan su Saif aka hau kwano ana ci ana Santi,Jawad sai Kora furar Nan Mai Rai da lafiya ta shinkafa kabawan kanta yake."Mai Dadi da gardin gaske Wacce akayiwa damun kyale mouda." "Suna cin abincin suna yabawa Innerie akan dai abincin yayi Dadi." "Innerie tayi dariya tace mu da abincin namu miya sallaba CE,Ba Nama aciki ai abincin masu kudi yafi namu Dadi...." "Ina mama fatyh da yake hakan suke kiranta...Saif ne katseta yaqara da CEwa a gaskiya mama abincin Nan ko gidan shugaban kasa Albarka... Saboda duk Wanda ya ci ba zai fahimci ba Naman dawisu ko jimina aciki...Ai mun dauka da giwa kikayi miyar Nan Mama..." "Jawad ya amshe zancen...ya ce mama a gaskiya Ni vanma fahimci ba nama aciki bah...Saboda kamshin miyar sai ya nuna nama da kifi ne suka yalwaceta..." "Baba Dariya yayi kana yace zaku gama santin KU Yan nema masu salo...Ai kuwa 'yahtah Nadiyatou tafi ta iya Miya saboda ta kware sosai agurin girki kunga ko Sabon hannu yafi tsohon hannu...." "Innerie ta karbe zancen tana dariya ta ce da dadin miyar kake tutiya Kuma da shi aka reni yarta taka...kaima anjuma kadan zaka daura santin naka daga Inda su Jawad suka tsaya..." "Dariya sukayi cike da jin Dadi dukkan su...Nan a dauko firar Nadiya..."Baba ya shaida masu saura mako biyu na dawo a yadda Saddiq ya sanar Masa da sukayi waya ajiya."Saif yace agaskiya Baba da Nadiya ta dawo hutu sai dai kayi Hakuri zamu saya Mata waya..." "Jawad yace "Duk da na fahimci baka so Baba Amma ya kamata ka hakura saboda tana fama da kewaemu a sanadin wayar!" "Ajiyar zuciya Baba ya sauke yace''Abinda yasa bana son Nadiya da waya shine saboda kula da *TARBIYYAR* na Duba nagani rashin Amfanin wayar yafi amfaninta yawa!"Tana batawa yara *TARBIYYA* Haka yara da yawa sukan fad'a wata rayuwa sanadin waya!"Sai kuga yaro Yasan abubuwan da dama Kuma ya iyasu adalilin wayar Nan ta zamani."Shi NE nake Jin tsoron barin Nadiya ta rike waya domin kare mutuncinta da "Gyaran murya yayi a kausashe!"Ya ce"Baba na tabbata hakan bazata faru ga Nadiya ba!"Saboda nasanta da mutunci da sanin ya kamata!"Bazata taba zubarda kimarta da mutuncinta tare da *TARBIYYAR TA* Ba,A sanadin waya!"Inji Jawad." "Saif ya CE"Baba gobe zamu sayo waya mu kawo maka,Kaine zaka Bata da hannunka yadda bazata zargi wani Abu ba!"Kuma idan ka Bata da kanka zatabi umurninka da kashedinka akAn duk wani Jan kunne naka!"Da GARGAD'in da zakayi Mata." "Hakane Baba yace cike da gamsuwa da bayanin su.'' "Innerie Tace Allah yasa MUDACE,Amma agaskiya munyi kewar Nadiya saboda muna mako ba mujita ba!"Sai Idan Saddiq din Yana kusa da ita ne."muke jinta watarana sai dai yace Bata kusa da shi."Amma da ace tanada waya da munjita...." "Tabbas Mana Fatty,Jawad yace cikin Jin Dadi." "Saif yace Duk KU kwantar da hankalinku...Mu dai KU tufa Mana asirin mu awurin Nadiya idan ta dawo." "Babu matsala saifullahi karku damu komai zai zo kamar yadda muka tsara Inji Baba." "Innerie Tace "yadda ku kazo Mana da manufar ku jawad itace ta sanyamu karfafa muku gwuiwa.." "Dariya sukayi tare da inkiya da ido cike da kwarewar su ta Zama Yan duniya wayayyi..."Sannan sukace Mu zamu koma Jawad daurin kudi ya fito a aljihunsa ya ajiyewa Baba atabarma..."Yace"Baba ga wannan afara Shirin tarbon Nadiya." "GODIYA!"su Innerie sukayi ma su tare da rakiyar su har zaure..."Tana Mika sakon gaisuwar ta awurin mommy da Mami." "Ficewa sukayi Baba da Innerie suka dawo gida cike da murna da godewa yaran." "Baba Balarabe yace "wallahi Innerie Ina Jin so da kaunar yaran Nan Shiyasa bana iya Koda Girgiza masu..."Musamman Jawad Ina Sonsa har ajinina kamar d'ana gudan jinina!"Shine dalilin son ganin Naga na aura Masa Nadiya da zuciya D'AYA." "Innerie Tace"Nima dai na yaba halayensu da kirkinsu Allah ya nuna Mana mun saka masu da auren Nadiya ai duk Wanda yaso abinka dole kaima ka so shi...Hakan ta yadda suka bullowa lamarin Nan yasa naji Ina kaunar sa ALLAH dai yasa mudace." "Ameen..."Mallam Balarabe yace tare da dibar kudin ya baiwa Innerie sauran yace ta ajiye masu da basu san ko nawa bane KAMAR yadda ko Wanda ya basu kudin bai kirgasu ba." *'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍* [2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 14* *Hakika Samun Masoya Babbar Nasara ce, Haka Zaman lafiya Babbar Sa'a ce, Bazaka San meye so bah sai ka samu masu sonka, Ina miqa Gaisuwa tare da jinjina ta musamman gareku MASOYANAAH, Masu kaunar Rubutu na, Tabbas Ina ALFAHARI da ku Bazanyi dana sanin Samun Ku rayuwata ba, Kun min komai bansan da me zan biyaku ba, Fa ce fatan Alheri gareku wa zuriyar ku, Wannan Shafin TUKUICHI ne na baku, Allah yabar Ni da ku Ameen, Ku chigaba da bibiyar littafai na, Ay comment, Share and post, A karshe Taskata abude take domin karbar korafi ko kuma kawo gyara a kundin alqalamina NAGODE😍* _Nayi mamaki alokacin da nasamu kaina atsakiyar Masoya na,Alokacin da na tafi wani tarou ne,Naga yadda Masoya suka nufoni tare da min rumfah suna nuna farin cikin ganina awurin,Tabbas Abin ya burgeni sai naji Banda kamar ku,A duk Inda na ganku bazan barku bah, Alhamdulillah Alaa kulli yaumn...😊_ ______________________________________ "Mansura ce zaune akan kujera da ke falon,ta daura kafa daya kan daya,Daurin Nan na ture kaga tsiya ne kwance akwaryar akanta,Wanda yaji kwalli har ya gaji,Daram yake yayi kyau... "Simple makeup ne Zane a fuskarta ba laifi tayi kyau da yake black beauty sai dai siririn jikinta da rama suka mata cikas..."Chewing gum take tauna kas..kas...kas tana Danna wayarta mayafinta da jikkarta gefe suke ajiye...Dinkinta A shape ne,ya matseta sosai tamkar idan ta motsa rigar zata yage..." "Karasowa tayi jikinta asanyaye hannunta dauke da Dan ture ruwan pure water ne da lemun fanta sai glass cup..."Ajiyewa tayi akan stool dinda ke wurin tare da matso shi wurin mansura." "Tace mansura Bismillah ga ruwa ki Sha tare da nuna ruwan da hannunta..."Ta ce,Ashe dai kinsha wuya kafin ki gano gidan..." "Haba!zancen wuya ay baima taso ba!"A gaskiya Nady baki iya kwatance ba!"Mansura Tace tare da tsiyaya lemun ta Kai bakinta..." "Nadiya tace"to kinsan nikam ban San gari ba!"Kuma Anty Jalila Bata Nan bare ta kwatanta min...." "Hmnnnn. Mukam mun Zama kudajin sakkwato domin cike da wajenta ba Inda bamu sani ba!"Inji mansura tana dariya..." "Nadiya tace"KU Manya ne mansura ba'a gasar ku....." "Wai Ni Naddy Ina Yaya Saddiq ne,Naga gidAn shiru....Kuma fa akan nasan ranar weekend kowa Yana gida shiyasa na zabeta aranar da zan kawo muku ziyara na gaida Yayanmu..." "Ayyah!Kinga ko yau gidan Ni kadai ce sunje bikin suna matar abokinsa ta haihu...Nima cewa nayi bazanje saboda karatu Kuma gashi tun jiya kin kirani Zaki zo....."Katseta tayi ta hanyar cewa kin San gidan!? "Da mamaki Nadiya tace"A'ah bansani ba!"Meyafaru..." "Murmushi mansura tayi tace''wai da munje na maki rakiya..." "Yake Nadiya tayi tare da kallon mansura, tace''nikam bazanje ba!"yanzun ko da nasan gidan,saboda tun farko ya kamata naje tare da su,Kinga nifa Ina da abin yi karatu NE nasa agaba!..."A zuciyarta ta k'osa mansura ta fice saboda Lokacin dawowar su yayan ya kusa." "Mansura ta katse Mata tunani ta hanyar dafata tana cewa"Nadiya Ina damuwa azuciyata sai dai ban san ko da wace fuska Zaki dubeta ba!"Amma Ina son ki min uzuri...."Sannan ki taimake Ni!" "Dubanta nayi cikin yanayin rashin fahimta nace"Na taimake ki!Kuma mansura!?"Ni Ina da abinda zan iya taimaka maki ne!?" "Kina da shi Nadiya...!"Ay taimakon iri iri ne qawata..."Mansura Tace "To Ina jinki....sai ki fad'a min naji...." "Yawwa...Naddy...Daman tun ranar da na daura idona mukayi ido HUD'U da yayanki Saddiq!"Sai naji duk duniya ba Wanda nakeso kamar shi..."Nasha kiransa Ina gaida shi...Ina Nina Masa afakaice..Sai dai Banda wulakanci ba abinda yake biyo baya...Nayi iya kokarina Naddy domin Abbakar ya fahimce Ni Amma Sam yaki ya kulani..."A ranar da kaddara ta farmin nakira shi na gaya Masa....Tatas yayi min na Sanya lambata ablack list!!!"Naje makarantar ku office dinsa ya korou Ni yanzu gani Gidansa Shakka bana yi ko yanzu ya sameni zai koreni....."Ajiyar zuciya tayi tare da Kama hannayen Nadiya ta rike gam, da wacce Tuni tayi mutuwar zaune ba abinda take sai kallon mansura..." "Wannan dalili ne yasa nazo domin ki taimake Ni ko Dan uwanki zai so ni!"Duk abubuwan da suka faru Abaya na boye maki ne domin Naga ke kina tsoronsa na dauka zan iya saye zuciyarsa da kalamai da Kuma irin salon nawa kissar...."Amma yanzu tura ta Kai bango"Saboda na kasa...." "Sanyin Hawayen mansura NE suka digo min a hannu Wanda yayi sanadin Dawowata hayyacina...Tabbas yau na shaida mansura tafi karfina kuma ta wuce sanina...." "Da kyar na motsa bakina da ya hade gum....Nace nikam Wannan al'amarin yafi karfina mansura saboda bazan iya tunkarar Yaya Saddiq da Wannan zancen ba!"Kiyi Hakuri kawaai...." "DakAta Nadiya karki sa Nayi Dana sanin tunkarar ki a mutum ta FARKO kamar ya!Nayi Hakuri ya kamata ki gane shi so kaddara CE Kuma baisan Hakuri Wallahi!Bazan hakura da Saddiq Dina ba!"Sai Inda karfina da iyawata ya kare...." "A firgice na kalleta tare da zame hannuwa na daga natan nace Mansura Tabbas giyar so ta bugar da ke!kinsan me kike fad'a kuwa!?"To Bari kiji Yaya Saddiq ba Yayana bane na jini Dan gidan abokin Babana ne..."Kin ga bazan taba shige Masa domin alaqarmu Bata Kai ga Nayi Masa shishshigi arayuwa ba!" "Hmñnnnn....Bari yayi Kama da mutum Naddy kice akwai aure atsakanin KU watakila kema Sonsa kike!" "So Kuma Mansura!?" "Eh!Mana idan ba Sonsa kike ba ko Kuna tare me zai Hana ki taimakeni....Shiyasa ma Kika tare agidansa...yanzu na fahimce ki." "Da mamakin na kalleta nace ka da ki min sharri Ni Babu abinda ke tsakanina da shi fa CE zumunci...Tayaya zan daurawa Kaina dala ba ganwo...Ay ruwa ba sa'an kwandou bane!"Na tsaya a Inda Allah ya ajiyeni bana kankamba bare shiga hurumin da ba nawa ba!" "Ni Kuma kin ganni Nan Naddy Ina shiga hurumin da ba nawa ba!"Kuma Ina kokarin har ya zama mallakina...kedai ki zuba ido ki gani!"Domin duk abinda nasa agabana sai na same shi.... "Tuni idona sukayi jajur cike da kunar rai!"Ina Allah wadai da mutane irin su mansura da basa son azauna lafiya...."Kayanta ta dauka Tace Ni zan tafi Naddy NAGODE..." "Komai bance da ita ba!"Kuma ban motsa ba!"Jin tsayuwar motarsu Yaya Saddiq ne yasa naji wani fargaba!Kenan sun dawo na shiga uku na!!!" "Mansura ko murmushi tayi Tace madallah turare ta dauko Jakarta ta fesa tare da gyara fuskarta..."Glass dinta ta manna afuska mayafinta ta rike a hannu tare da turo kallabinta gaba...Ta kalle Ni muje ki rakani kada ki mayarda agogo Bayan hannu...kinsan yaba kyauta TUKUICHI...Haka bako rahama ne..." "Jikina ba kwari na tashi nabi bayanta Tafiya take kamar zata karye...Azuciya ta na k'osa ta tafi....Dai dai kofar falo Mika ci karou da Anty Jalila da yaran sun bode kofa!!!"Ledoji a hannunsa..."Wani Kallo tayi ma mansura..hakan mansura ta mayar Mata da martani..."Kallona tayi cike da tuhuma yayinda nake Mata sannu da zuwa..." "Nan da Bata CE Mana komai ba ta wuce mu Kuma muka fita...Yaya Saddiq muka samu Yana kokarin rufe motarsa...Da hanzari na gaida shi.." "Hakan mansura cike da yanga da kwarkwasa ta gaida shi..." "Ko kallonta baiyi ba!"ya CE Nadiya Wannan fa!?"Daga Ina!?"Ina Kuma Zaki tafi Bayan ke kadai CE agidan...." "Cike da razana nace Yaya,"Mansura CE,Daman anan zan ajiyeta ba ko Ina zamu tafi ba!" "Ok,shige gida mu tafi..."Da sauri na koma gidan..."kallonta yayi yace Kar nakara ganin kafarki agidana!"Bana son iskanci!" "Mansura Tace"Have Yaya Saddiq meye illar so!?"Kodai tare da Nadiya kake!?"Saboda Naga kwaryar sonta a mazaunin idonka!" "Mari ya watsa mata...Sannan ya Kira Mai gadi cike da fushi yace ka dubeta da kyau...Kar na Kara ganinta gidan Nan ka fita da ita waje!!!"Sannan ya shige gida!" "Angama yallabi mudi Mai gadi yace"tare da CE ma Mansura to Malama kina iya fita ko!?" "Anki afita Kai acikin kayan Miya wa kake!?"Dan Abi yarima asha kid'a kawai...." "Mudi maigadi ya zarou ido da Yake ko shi kansa matashin kauye ne...yace ke Ni zakima rashin kunya to kinzo gidan kisani tun a 1960 nike rashin mutunci akauyen mu har yanxu ba'a haifo kamata ba!"Wallahi ko ki fita da kafar ki ko na tallabeki Nayi waje da ke ko wajenma ajuji zan jefar da ke!"Kinganki ba nama ne da ke ba!"kamar an fige figaggiyar kaza Mai Dan hoda..." "Mansura ta saduda Dan taga sai fama gyara rigarsa yake da wondo zai kinkimeta!"At da gudu rabar get din gidan Takalmi da mayafi ahannu.. " "Dariya yayi yace da kitsaya kiga aiki da cikawa ayke karamar Yar iskace kina acikin Dalibai na yarinya..."komawa yayi kan aikinsa Yana Waka Yana Shan rake..." "Nadiya Ina Kika samo Wannan yarinyar!?"Inji Anty Jalila "Wallahi Anty Daga shiga mota ne da zAnzo shine ta laqabe min..." "Mtwsssss...to ki kiyaye saboda bana son kwashe kwashen kawayen banza agidana...!" "To,Anty in shaa Allah zan kiyaye..." "Mufeeda KU kawowa Antynku kayan bukin ma kun wani zauna kunaci KU kadai..." "Dawowar Yaya Saddiq afalon ne yasa naji..dif Ina jiran yace wani Abu sai dai baiko nuna damuwa...ba"Da yake ko da ya shigo Ina Kichen Duba girkin da nakeyi..."Shiyasa bangan shi ba sai da shiga bedrum ya fito yanzu." "Kayan bukin nakeci ahankali duk na tsorata... Yaran ko sai fira suke min Sam hankalina baya kansu...tunanin ta'asar da mansura ke son yi nikeyi da Kuma hukuncin Yaya Saddiq gareni... "Mansura da sassarfa ta karasa bakin titin estate din..."Lalle yau ta hadou da gamonta!!"Sai haki take saboda gudun da tayi alokacin da mudi ya biyota!"Napep tasamu Dan fodio Tace ya kaita!"Sai alokacin tasamu sarari ahankali wulaqancin Saddiq ya dawo Mata Hawaye ke zuba afuskarta!!"Lalle Dole ta dauki mataki akan Saddiq da kawarta Nadiya!"Wacce ta fahimci suna kaunar JUNA atsakanin su!!!" "Da misalin karfe 7:30am na safe na shirya tsaf nida yaran Tuni na kammala abincin Karin mu Dana yaran."Mun zauna munci mun koshi su Yaya Saddiq harda kari.."Nan da muja kammala muka fita domin zuwa makaranta..."Ita Kam Anty Jalila tana can tana sharar baccinta batasan ma me ake ba!"Da yake yanzu Yaya Saddiq yama daina tashinta da zarar mun shirya wucewa muke sai dai ya kulle gidan ta waje idan ta tashi ta bude ta ciki..."Hakan ya fiye Mata komai Dadi arayuwa domin itakam tafi so kullum yazan tana hutawa..." "Bayan an sauke yaran...Titin makarantar mu Yaya Saddiq ya hau ta gudunsa..."kallona yayi kana ya kauda kai..Nikuma kamar munafuka..sai sadda Kai nake saboda nasan fassarar kallon sa..." "Nadiya..ya Kira sunana." "Na'am Yaya na Amsa "Ina son naja maki kunne Kar naqara ganin Wannan Kawar Taki agidana...tunda Nayi kokarin rabaki da Yan iskan makaranta!"Yanzu Kuma kin samu wata banzar!!!" "Cike da bugun zuciya nace Yaya Dan Allah Kai Hakuri hakan bazata koma faruwa ba!" "Daga yanzu na daina tilasta ki Kiyi abinda ranki keso Nadiya tunda Ni ba jininki bane ban Isa da ke ba!" "Kukan da nake hadiyewane ya balle min...nace ka isa da Ni Yaya na dauke tamkar Yayana najini kayi Hakuri na daina Daman ta dameni da tazo mu gaisa ne,Shiyasa Nayi Mata kwatance tazo Amma Wallahi bazan Kulata Yaya!" "Kallona yayi akarou na biyu Sannan ya CE "Shi Kenan...share hawayenki ya wuce!" "NAGODE nace muryata adisashe idona sun kumbura ga kukan da Nayi ga Kuma kumburar rashin baccin da bansamu ba adaren jiya saboda karatun jarrabawar da zamu fara yau." "Faculty dinmu ya ajiye Ni tare da yimin Addu'oin Samun nasarar jarrabawar." "GODIYA Nayi Masa ya wuce..."Ni Kuma Inda muke Zama da Naseer na nufa kafin lokaci yayi..."Sai dai su Esha, Deejart da Deeja nasamu zaune suna jiran karasowata..."Da murna na fad'a kansu cike da kewar juna..." *Toufaah wasa farin girki Inji"YAR MUTAN DIKKAWA* [2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 15* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM._ _Kui min uzuri fans Ina ganin sakonku,A whtap,Text mssg da Kuma masu Kirana,Ina godia, sai dai tun farko na Gaya maku Ina busy a watan nan, Ina iya kokarina domin ganin na maku post akan lokaci,Daga SHAFI na 12,13,zuwa 14 har zuwa na gaban duk nt Edit ne sai kunyi hakura da MESONKU😍_ ______________________________________ "Rana akace Bata bar komai ba!"Yau dai Allah yayi na kammala dukkan jarrabawar mu lafiya..."Na k'osa na koma gida Duk da yamma tayi Amma Ina ji ajikina kamar bazan Kara ko AWA daya agarin sakkwato..."Ban kwana mukeyi da Yan department din mu."Su Esha ma fatan Alheri mukayi musaya da su."Naseer abokina kamar ka da mu rabu saboda munyi sabou da JUNA..."Sai da Nayi Hawayen rabuwa da kawayena da Kuma Abokin karatuna!!!" "Hakan dai kowa ya watse da Yake akwai wadanda basu kammala ba!"Suma sai jibi zasu wuce gida.. "Na amshi lambobin su Deeja da zummar zan dinga kiransu da wayar Baba." "A hanya ne Yaya Saddiq ke Gaya min sai gobe zamu tafi *ARGUNGU* saboda Shima ya kwana biyu baije duban su Baba Musa."Tare zamu tafi Zaije har ma da yaran, da Yake sunyi hutu.. saboda Daman ita Anty Jalila ba zuwa take ba." "Sai da yanayin fuskata ya canja da naji maganar kamar saukar guduma akahon zuciyata!!"domin na k'osa banje Naga Innata da Babana ba.."Da Kuma malamina Yunus." "Hakan na hakura,Sai goben Duk da banji dadin hakan din ba!"Jimami da jajantawa Kaina na Cigaba da yi araina!" "A ranar kuwa Bayan mun koma gida naci abinci na huta Ni da yaran na kammala dukkan shirina da na su saboda na matsu gobe tayi nabar birnin shehu izuwa jihata ta *KEBBI* "Anty Jalila Bata so na tafi gida hutu ba!Taso ace agidan zanyi tunda ba wani tsayi ne da hutun namu ba!"domin kuwa alokacin da taji Labarin tafiyata...Jin tayi tamkar an watsa Mata ruwan zafi!A zuciya!"Nan take jikinta yayi sanyi domin tasan cewa zatayi kewata ba kadan ba!"A gefe Kuma Sai tunanin tulin ayyukan gidan takeyi, wadanda mafi akasari suka tashi kanta yanzu kuma zasu rataya akanta!"Domin Yaya Saddiq yanzu ya tsaya kyaam!"Akanta ya daina wasa Dole tayi aiki!"Ga Kuma haushin zuwan da za'ayi da su Mufeeda da Mufeed a Argungu..Saboda ita sam batason dangin miji su rabeta da yaranta..."Da hakan dai ta hakura Domin tasan tunda Habibinta yace Zaije da su ba makawa sai sunje din..."Ko rayuwar juna ta baci domin ya canja ba kamar da can baya bane,da take hanashi zuwa garin su,gaba D'AYA." "A gidan malam Balarabe tamkar a yau take sallah...Domin sun Shiryawa tarbou yarsu daya tilo..." "Innerie anyi shinkafa da Miya har da su Naman kaji,Wadanda su jawad suka kawo,Domin Duk cefanen su suka kawo adaren jiya harda waya Spark 4 dal akwali,da Kuma layin(Sim card)Wanda akayiwa register."Domin abani idan nazo Har katin din faro da fanta."Da dai sauran tarkace..." "Malam Balarabe kuwa dawo ya sayo mai kyau da nono kindirmou... Innerie tayi zaune ta dame shi sarai kwarya...Irin Damun Nan na da ake Kira na"kyale mouda...( _Hmnnnn fans Kar na tada maku da shekararren kwadayi😋kunsan *KABAWAN KANTA* ba Abaya ba!fagen iya fura Mai Dadi da gardi_) "Misalin Sha biyu na Rana muka iso Argungu..."Sai kallon garin nikeyi kamar ya canja min..."Murna ce fal araina..."A hankali ya juya akalar motarsa zuwa titin da zai dauke *TUDUN WADA AREA ARGUNGU*."Karya kwana yayi alayi na bakwai..."Dai.dai kofar gidan su ya tsaya..."Wani iri naji Amma na daure muka fitou kamar yadda yadda ya fiton... "Hannun yaran na na kama Yana gaba muna bayansa har muka shiga gidan..."Da murna gwaggo inno ta nufo mu tare da tarbe su Mufeed tana Yan sakkwato allura da zare!"Lale marhaban da maigidana da kishiya..."To Mallam dai baya Soo...cike da zolaya ta Kama yaran da munnarta...Ni da Yaya Saddiq sai dariya muke.." "Baba Musa ne ya fito daga uwar daki, Yana cewa" A'aaa su Nadiyatou ne sannu da zuwa 'yan makaranta...Saddikun har Kun iso..." "Da ladabi na gaishe su alokacin da Inno ta gama SHIMFID'A Mana Tabarma." "Yaya Saddiq ma gaishe su yayi da girmamawa.. "suka Amsa cike da munna." "Su Mufeeda da Mufeed har kasa suka Kai suna gaida kakanninsu Gwanin burgewa...."Sannan muka zauna dukan mu atabarmar har Yaya Saddiq cike da fara'ah." "Baba Musa saman kujerar nan ta roba ya zauna Yana fuskantar mu tare da Mana ya ban gajiya... "Inno,ko ruwan leda da fura ta ajiye Mana ajug, Yaya Saddiq shi Kuma alangar Sha ta fura."Nan dai akaita musayar Gaisuwa..."Mun Sha ruwa Ni da yaran, Daga Nan su Mufeeda acichi sai banbamar fura suke..."Su kuma su Yaya Saddiq sai firar su sukeyi....nikam na k'osa Yaya ya kaini gida.." "Kayan tsarabar da akayiwa su Inno da Baba."Yaya Saddiq yace muje mu bude but mu kwaso amota, Ni da yaran..."Amsa keys din motar Nayi muka fice...ba da jimawa ba, muka dawo da Ledoji manya uku...Nan ya warewa Baba nashi,Yadi NE uku Masu kyau da tsada,sai turare biyu,da rediyo da fitila caji,Itama Inno ya bata natan zannan atamfa biyu,da turaren ruwa da na daki,sabulan,wanki,Dana wanka,da sauran tarkace."Saboda Gwaggo Inno akwaita da kirki ita ce Wacce ta maye Masa gurbin marigayiya karima! watou mahaifiyarsa ta aynihi."Amma idan ba Wanda yasani bane!"zaka dauka ko inno itace uwarsa,Saboda Babu bambanci atsakanin Saddiq da yaranta."Shiyasa Shima ya riketa uwa wacce baya da kamarta Aduniya."( _Ayshi D'a na kowa ne....Mai wayo kadai ne, zai iya gane hakan...Domin da nakan da na wanin bakasan Mai amfaninka ba"Inji 'yar mutan Dikkawa_) "GODIYA suka hau yimasa tare da sa Masa Albarka..."Daga Nan yace mu tashi yaje ya saukeni gida..." "Zumbur na Mike Ina musu Sallama,Ai kafin Yaya Saddiq ya fito har na Kai Mota..."Saboda daukin zuwa gida..."Daman Zaman ya gundure Ni!" "Murmushi yayi alokacin da ya same mu,Ya shiga motar Sannan yace"Kin cika kakkabi Nadiya sai kace gidan zan barki!"A yanke namanki danye!"Sai wani hanzari kike!"Tsaki yayi tare da tada motarsa..." "Nikam kunya ta rufeni...saboda Yaya Saddiq Yana saurin dago lagona SOSAI... "Tsit Nayi har muka karaso kofar gidanmu....Inda matasan unguwa ke zaune a karkashin bishiya suna fira...yaran makotan mu ko wasa sukeyi a kofar gidan namu..." "Parking yayi muka fito...Da yake na Dan Kara haske da jiki...yaran sai kallona suke..Sai da nace su madou ne...sannunku Aiko da gudu suka tareni suna fadin ashe Malama Nadiya CE....."Rungumesu Nayi batare da na kula da dattin jikinsu ba!"Niema dariya nake nace Baku ganeni bane madou.?" "Eh,malama kin canja...sukace dukansu..." "Yaya Saddiq da yaransa sai kallon mu suke...Nan yaji yaqara son yarinyar saboda halayenta..." "Matasan tasowa sukayi suna min sannu da zuwa ya makaranta na Amsa musu tare da GODIYA nan mutum biyu suka dauki dukkan kayana zuwa cikin gida.'' "Mu Kuma muka bi bayansu...Tun a zaure muka hadou da mamana wacce takasa Hakuri...Nan na rungumeta Ina murna sakeni tayi ta Kama su Mufeeda da Mufeed tare da Mana sannu da zuwa..."Saboda mamana ta Dan ji kunya ganin Yaya Saddiq....Domin fulani akwai kunya musamman ta diyan farin..." "Alwalar sallar Azzahar muka Sami Baba nayi...."Dukkan mu gaida shi mukayi..Bayan mun zauna....Mamana ta rasa Inda zata sa ranta Domin Dadi,sai kallona takeyi taga nakara kyau na murje kamar ba Ni ba.."Kayan abinci ta ajiye mana... Nan na zubawa Yaya Ni Kuma na zuba da su Mufeed, sai da muke ci sosai,muna Santi..."musamman furar Nan Mai Dadi." "Duk da Kasancewar ba ako'ina Yake cin abinci ba! Amma ya kasa hadiye yawunsa ga abincin nan na Innerie, da ke ta faman tururi da zuba kamshi...hakan ya Sanya shi sakewa ya kwashi gara...Nan ya gane iya girki abin Daga jini ne domin dai ita Nadiya gadowa tayi awurin Mamanta...( _Shakka Babu matsawar Kika kwarei afannin girki Kuma kinayi akan idon yaranki,kina koya masu ahankali da dabaru to Lalle watarana su zasu kawo maki wani Sabon salo har su zarce ki,Iyaye mu kula adinga koyawa yara girki domin gudun watarana."_) "Bayan mun kammala cin abinci tsarabar da Yaya Saddiq ya sayawa su mama da Baba na dauko na basu har alherin da yayi min...Nan SUKA dauki GODIYA da saka Masa Albarka har zuwa irin kokarin rikon da Yake min tsakani da Allah,Da Kuma kulawa da *TARBIYYA TA*." "Murmushin yayi,yace bakomai Baba ai yiwa Kaine, Nadiya kanwata CE karku damu..." "Iyayena sun nuna Masa karamci abisa kokarinsa Nan akayi fira yace ya tashi...."cewa Nayi abarmin su Mufeeda har zuwa yamma na kaisu gidan Inno...Domin Suma sun nuna awurina ma waiii sukeso su kwana...Nan dai Yaya Saddiq ya barsu tare da Mana Sallama...Katoun jug Innerie ta cika Masa da fura ya wuce da ita Yana GODIYA."Tare da Baba suka tafi saboda zai wuce masallaci." "Nan muka bude rumbun magana Ni da Mamana domin an Dade ba'a hadou ba!"Labarin makarantar mu nake Bata,tare da tambayarta ina makota da kawata sauda Yar gidan mama lantana."Duk mama Tace min tayi kowa na lafiya...."Sallah mukayi mukayi daga bisani Kara cin abinci Nayi saboda nakasa ci in koshi agaban Yaya Saddiq din,kayana na kimtsa adakina..tare da fito da tsarabar minti..na Kira yaran makotan mu su madou ina basu..tare da jikkar lollipop guda D'AYA, nace su kaiwa su badaru matasan nan na waje..."Ina cikin gida na jiyo shewarsu suna GODIYA...Suma yaran sai murna suke kowa ya tafi gida ya nunawa mahaifiyarsa." "Su Mufeeda da Mufeed an Saba da mama sai fira ake Mata da Yake yaran suna da saurin sakewa...Da yamma makotan mu sai shigowa sukeyi suna min sannu da zuwa tare da godiyar alawa da balanbalan da na baiwa yaran nasu..." "Sai wajajen magrip...na kwashi yaran na Kai su gida, Bayan Nayi masu wanka sunci abinci...Sannan na basu alawa da biskit."Kamar kada murabu da su...hakan na barsu agidan kakanninsu su na koma gida..."A hanyata ta dawowa, na hadou da Mallam bilya na Islamiyyar mu,Nan na tsaya Muka gaisa Yana cewa yaushe nadawo nace Masa yau dinnan...yace to ya makaranta ya exams nace Alhmdllh''...sosai da naji da sanyi araina da na ganshi domin nasan yanzun Nan zai labartawa Mesona labarin Dawowata...."Domin Ni kunya ta hanani na tambaye shi ya Mallam yunus din yake..." *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 [2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 16* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ _Saqoun Gaisuwa Gareku manyan Writers_ _Saudat Zariya(SAJ),Marubuciya Waye Sila_ _Nabeeha Ameenu,Marubuciyar Gudai_ _Nabilancy luv Marubuciyar,Marainiya_ _Nabila Lady, Marubuciyar Alkali Ne_ _Ina muku fatan Alheri Allah yabar zumunchi Amin🤝🏼_ ______________________________________ "Muhammad Jawad Husamaddin ne Sanye acikin riga da wando 3quater,Yayi kyau matuka sai dai Yana zuwa jikin mirror da ke manne a kayataccen Bedroom dinsa,Yana Duba kansa ajikin madubi yaji kamar shigar batayi Masa,A Yan kwanakin Nan da Yake Sanya manyan Kaya na Mallam bahaushe sai yaga tamkar sunfi amsar ajikinsa amaimakon kananun Kaya.." "A zuciyarsa mamaki yake yadda ahankali ra'ayinsa yake canjawa... musamman na gefen shigarsa da mu'amalarsa da mutane..."Can gefen zuciyarsa yake gaya Masa cewa kwaikwayon halaye *NADIYA* kakeyi ne!saki yayi Wanda ya fitou fili tare da furzou iska waje!" "Dubin kayan ya karayi sai kawaai yaji baya,son fita da kayan... Wardrobe dinsa ya nufa gefen da yake ajiye kaftan din da aka dinka Masa na musamman domin zuwa gidan Mallam Balarabe ya dauko kala daya shadda gizna fara Sol,ya Sanya tare da feffesa turare ajikinsa..."Kara Duba kansa yayi kana yayi murmushi alokacin da Yake ajiyar zuciya...kansa ya kalla tare da shafa sumar kan nasa yace"Ya kamata na nemi hulla ko guda CE na dinga sakawa,Ina rufe gashin Nan nawa..." "Dakinsa ya fito,A falon sa ya sami Saif,da Al-amin suna jiransa..." "Jawad yace"Guys muje ko na shirya..." "Da mamaki suka kallesa ,Saif yace"muje Kuma Baba ahakan!?" "Eh,Mana...ko kuwa!?inji Jawad. "Al-amin yace Wai meke faruwa Naga ka canja Jawad!" "Meyafaru NE!?"ya tambaya "Yanzu Kai zamuje birthday Babynah zaka wani sa Kaftan..kasan fa harkar ta masu aji CE...Wallahi zaka koma abin dariya..." "Saif yace haba Jawad ba fa inda muka Saba zuwa da Kaftan NE zamu tafi ba!"Pls!Alhaji ka koma ka canja zubin wanka karka Bata Mana lokaci!" "Murmushi yayi na gefen lebe ya dubi abokansa tare da kallon Jikinsa sarai...shafar gashin zajensa yayi tare da d'an rike gemunsa irin na matasa..."Kana yace kunga Guys Ni yau ahakan zanje birthday idan yaso Ilhaam din ta korouni.."Sai me!?"Kunga muje ko nace nafasa ahakan nake ra'ayin Tafiya!" "Kallon JUNA sukeyi!"cike da Jin haushin canjin rayuwar Jawad din." "Tashi Saif yayi Daga zaunen yace"Al-amin muje ko!" "Jiki ba karfi Shima ya Mike suka bi hanya cikin rikitattar shigar su tamkar ta diyan kabilu...Bayansa Jawad yabi cikin hadaddiyar motar sa Prado suka shiga direct Miema Celebrity Hall suka nufa domin hallarta birthday din Ilham maina."Duk da ba hakan Saif da Al-amin suka so ba!"Iya kwafsawa ya kwafsa masu to meke faruwa!?" "Tunda aka game sallar Isha Nike baza kunne akan sauraren Kiran Mallam Yunus..."Amma shiru kamar an aiki bawa garin su." "Zaune Nayi Ina tunani na zabga uban tagumi cike da damuwa!"Ko dai malam Bilya Bai sanarwa Mallam Yunus din na dawo ba!?" "Banyi aune ba sai Jin sanyi tafin hannun mamana Nayi tana dafani.."Zumbur na kalleta!" "Nadiyatu!"Ta kirani." "Na'am,Mama na Amsa "Tunanin me kike Mallam nata kiranki Ni nama dauka ko bacci ne ya saceki saboda gajiya..." "Daburcewa Nayi Nan dabara ta fadou min...nace bakomai mama Daman tunanin jarrabar mu nake..." "To ke banda abinki ay Addu'a ce kan gaba adai-dai Wannan gabar,Allah ya Baku nasara in shaa Allah zakiyi nasara...muje muna son magana da ke." "Raaaasssa!!!!gabana ya fad'i!cike da fargaba!"nace Amin..."A sanyaye na bi Bayan mamana izuwa waje Inda Baba yake zaune Yana sauraren rediyo." "A sanyaye cike da rud'u na zauna gefen iyayena nace Baba gani." "Yawwa,Nadiya...Daman magana nakeson muyi da ke." "Gyaran murya yayi Sannan yace, Nadiya Ina son kibani hankalinki...Bayan tafiyarki makaranta akwai wani bawan Allah da yazo wurina amatsayin Mai neman aurenki!" "Difffffh ....naji na dauke wuta arazane na dagou Kaina Duk da duhun dare NE sai da iyayena suka ga yanayin nawa." "Baba ya Cigaba da cewa"To agaskia na yaba da hankalinsa da Kuma *TARBIYYAR SA* tunda har yafara neman mu amatsayin mutane na farko...kAfin ya ganki Kuma yazou maki da zancen...Kinga kuwa Wannan yaroun ya cancanci ayaba masa." "Bugu da kari yace"Mana bazai shiga rayuwarki ba!"Har sai kin kammala karatunki duka!"Saboda baya son ya kawo maki cikas arayuwarki...Wannan uzuri nashi Kuma yayi min Dadi sai dai yace"A Gaya Miki zaku dinga waya..." "Innerie,ki Bata wayarda ya saya mata..." "Mamana wayar ta mikou min kamar yadda Baba ya Bata umurni..." "Amsa,Nayi jikina Yana rawa saboda tsoro da fargaba...."murtar mama na jiyo tana cewa"Nadiya kinsan bazamu cutar da ke ba!"A gaskiya Muhammad Jawad yaron kirki ne,Kuma Yana sonki bakiga yadda yake hidima da mu ba!"Mu dai mun yaba da halayensa Duk da Kasancewar sa Dan masu kudi...baisa yaji wani abu ba!"Har mahaifiyarsa ya kawo Nan gidan Duk fa saboda ke." "Saboda Haka Daga ke har mu Addu'a zamuyi Allah yasa Jawad ne Alheri gareki,ki bude wayar yace zai kiraki..." "Sannan kashedina akAn wayar nan....Baba katse maganar Innerie, yace shine...Ka da Naga kinyi abubuwan Nan da ake da waya,daga ki Kira sai akiraki bana son shirmen banza!"Idan nasami kina ba dai-dai bazan karbeta Daman Ni ba so nake ba ko yanzu Alfarma CE jawad ya nema agurina..."Kinji ko!" "kada Kaina Nayi Eh,." "Yayi kyau ki kula sosai Allah yayi Miki Albarka..." "Ameen,nace cike da kidima." "Ya ce kina iya Tafiya,yau dai untuwa tayi Zane..." "Mama ta amshe da cewa biyar gari ya tashi..."Dariya sukayi dukkan su cike da farinciki...."Mama takara da cewa"wayar Nan da aketa maita to ansamu Amma adai kiyaye Kinji saboda Kashi 70% na lalacewar *TARBIYYA* sanadin waya ne...Domin ta zamou tamkar wata uwa Mai kawo gyara asada zumunta da Kuma hanyar tabarbarewar addini da Kuma al'ada." "Shiri Nayi Ina nazarin zantukan mama Tabbas na yarda da hakan domin nagani amakaranta...ko style akagani awaya ace shi akeso da sauran su." "Nan dai na tashi...na shige daki Ina mamakin waye *Jawad*!?Me yake nufi da Ni!?"Shin Ni yakeso ko kuwa Iyayena!? " *MUHAMMAD JAWAD* na Cigaba da nanatawa,A cikin Zuciyata...Wayar na bude ba laifi tayi min kyau, kuma Daga gani irin wacce ake yayi CE,Naji dadin Samun Kaina da waya..."Saboda Dan faso gari..in fita acikin duhun Kai!"Sai dai kashedi da gargadi Baba na tuna...Nan naji jikina yayi sanyi lakwas...Layin nasa acikin wayar saboda Ina ganin yadda Anty Jalila keyi shigen wayarta CE,"Bayan nasa zaune Nayi Ina shafa wayar saboda ba komai na iya ba na waya..." "Da nagaji da Danna wayar kwanciyar Nayi Ina tunani barkatai!a Raina game da *JAWAD* Daga Nan malam yunus ne ya fadou min arai!"Bakomai gobe zan shiga Islamiyya da yamma..."Sai kuma kewar Naseer da su Esha ce ta darsu azuciyata!!!"In shaa Allah gobe zan Kira su musha fira........." *'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍* [2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* _1st Jan 2020_😍 _Alhamdulillah Alaa kulli Halin....Da farko Ina taya Yan UWANA da Masoyana Munna shigowa shekarar bature....Sannan Ina Kara baiwa MASOYAN *TARBIYYA* Hakuri abisa korafe2nku, masu turoun min text,Kira,da comments duk Ina gani Kuma Ina GODIYA...kamar yadda kuka sani Na tsayarda rubutun ne akan wani uzuri...Amma gashi Allah ya nufa nadawo kuma Ina muku fatan Alheri..Masu Addu'ah wa kanwata muna GODIYA sosai Allah yabar zumunchi Ameen._ *Alhamdulillah,Anyi Auren Princess Yaseerah Dikko da Angonta Prince Uzairu LAFIYA, Ina maku fatan ALKHAIRI MY KANNAI Allah ya baku zaman lafia da zuriya Dayyaba Mai Albarka Ameen.* *GODIYA TA MUSAMMAN A gareku 'Yan uwana, Dangina,Kawayenah da Kuma masoyana Na nesa da na kusa wad'anda suka zo tayamu murnar aure,Allah ya sakawa kowa da mafifichin alkharie ya mayarda kowa gidan sa lafiya ya huce gajiya Ameen,Mun gode kwarai da gaske irin sosain Nan, Allah yabar zumunchi Amin.😍 _Appee Bufday❤ My Dear Rahma m sanie, U re d first born,nd U born in first Jan,1st+1st=Special oneof the world so u r special,it's ur special day of the year,Wsh u Allah's khaira's nd Noor in ur lype,More many money in ur bnk.act...Allah ya qarou shekarou masu Albarka Amaryar 29 Feb 2020,In shaa Allah,Kuma Allah ya kawo Yara nagari masu Albarka ,Ina maki fatan Alheri MRS.ABDUL MALEEK GADO, Allah ya qara danqoun kauna ke da yayanmu Ameen.WLLP BESTIEHNAH🎂_ _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *SHAFI NA 17* "Tunda safe na shirya tsaf acikin shiga Mai kyau da tsari nayi kyau ba karya,Hijab Dina na Islamiyya na saka...Fitowa nayi na samu Mamana tana kokarin daura dumamen tuwo a madafa....Nace Mama zan wuce Islamiyya..." "Kallona tayi cike da mamaki tace Nadiyatou...Tun yanzu baki ko karya ba!?" "Mama na makara ne!" "To...Shi kenan Allah ya tsare hanya adawo lafiya ki gaida min da yunus." "Yawwa mama nace cike da Jin kunya saboda na lura kamar ta ganou rawar jikin da nakeyi saboda Naga malamina ne." "Murmushi tayi tare da cigaba da aikinta Ni Kuma na wuce abina." "A hanya ma na k'osa na ganni a kofar makarantar Nurul Huda...Sanda na shiga makarantar Sai Naga tamkar ta canja min....Farin ciki NE fal araina alokacin da na hango malam yunus a ajin mu Yana bayar da karatu...."Da Sallama na shiga ko kallona Mallam baiyi ba...Yan aji suka amsa min fuskar su asake sai ya makaranta suke min." "Zama nayi Nima na Cigaba da daukar karatu agefena na hango wata kyakkyawa matashiya baka ga alama sabuwa CE saboda ban wayeta ba....sai faman hararata takeyi tana ya tsina fuska..."Nikam da mamaki na ke kallonta akarshe karatuna na Cigaba da yi...." "Da lokacin tashi yayi akayi addu'ah muka tashi...Nan na Cigaba da gaisawa da Yan ajinmu da Yake Ana hutu kowa ya dawo gida yammatan makarantar har da kawata Saudat Yar gidan hajia lantana." "Tare da ita muka fito muna firar mu....Gabas da ajin mu na samu Mallam da Wannan yarinyar atsaye Yana rike da hannun Yara biyu namiji da mace WADANDA ke matukar Kama da Wannan budurwar Mai hararena...Ras naji kohon zuciyata ya koka!"Nan take Kaina ya Sara!Ganin yadda Mallam yunus da ita ke magana cike da fara'ah...A hankali nake Tafiya idona ya rufe zuciyata tayi duhu bana ji bana gani har sai na tabbatar da abinda nake zargi!"FATANA kar ya zamou gaske!"Saudat magana take Amma bana Jin me take batu a Kai!" "Da sanyi na Isa garesu na CE Mallam Ina kwana!" "Mur...yasha kunu kamar Mai cin magani ko Wanda yaga wani sharri!"Ya nufoshi....Da kyar yace lafiya qlaw... Nadiyatu ya makaranta!?"Fuska ba walwalah "A wahalce muryata na rawa nace Lafiya qlaw Mallam,saboda fargaba da tsoron da ya darsu azuciyata...." "Ya Dan kalleni ya watsar!"Sannan ya ce Saudat duk Kuna lafiya!?" "Saudat tace Lafiya qlaw,Mallam..." "To....Madallah Allah ya taimaka..."Nagode ko!"yace tare da cigaba da magana yaran." "Nikam Tuni na sandare...Saudat Amin Tace"Kana taja hannu nah saboda na kasa Motsin kirki!...muka wuce...A nan nale hango farinciki shimfide a fuskar yarinyar da muka barsu tare da Mallam yunus, WACCE bansan ko Wacece ita ba!" "Tafiya muke Amma kukan zuci nakeyi!!na kasa jurewa sai da na tambayi Saudat shin wai Wacece wannan yarinyar da ke tare da Mallam yunus!?..." "Hmnnnnn Nadiya kenan Nima ban santa ba!"Ko da na dawo daga Health (makaranta)na gansu tare Amma naji Ana gulma Wai ita CE zai aura har anyi masu baikoh...Sunanta BADI'ATU Lawal Wai ance takarin makka NE akwaita da ilimi ga hazaqa Tuni ta hadda CE Alqur ani Mai GIRMA ke idan tana larabci zakice balarabiya CE...Bugu da qari ta Tara sanin littafan musulunci Ina ganin akanta NE TAURARUWARKI ke neman disashewa can makarantar nan saboda malam yunus naji da ita kinsan shi da son Dalibai masu Hazaqa...." "Innalillahi wa Inna ilaihir raju'un!!!!!"Nace a firgice!!Wani jiri ya kwasheni sai da na jini a jikin Saudat tareni saboda firgichi....A zaune ta ajiyeni na mintoci hankalina yadawo kwakwalwar Sannan tace in tashi mu wuce..."Bance komai ba sai Hawaye da ke min ratata!!!! Sauda dai da kanta ta fahimci na kamu da ciwon son Mallam alokacin da Shima ya fad'a tarkon son Badi'atu...Tabbas ta tausaya min domin son maso wani mu ke yiwa juna akace koshin wahala..." "Duk da nayi kokarin boyewa Saudat damuwa ta Amma a hankali sai da ta fahimta...A karshe dai KAFIN mu Isa gidaa kwashe komai na labarta Mata...Hakika ta tausaya min Amma tabani Hakuri saboda shi Mallam Bai taba furta min kalmar so ba!"Sai dai ya nuna min Alamar hakan..."Sannan ta fahimtar da Ni shi mutum NE Maison ganin dalibi Mai hazaqa Sannan Tace min Ni Kaina nayi wauta da na fad'a Sonsa har na kamu da yawa hakan...Gashi Nan shi ya canja wata da Ni Kuma batare da ya damu bah!"Na shiga tashin hankali sosai Amma yanzu Naga darasi domin nagane kuskure na."( _Hattara Yan Mata da yawa kuna wauta irin ta Nadiya,Sai kiga saurayi Yana nuna Miki so Amma ya kasa furta miki,A maimakon kema ki share sai ki fad'a so,shiyasa sonki zai fi nashi son to akiyaye domin gujewa wulaqanci_) "Bayan RABUWAR mu da Saudat gida na shiga,dakina na nufa...."Ban sanda na fashe da Kuka bah!" "Sai da nayi Mai Isa ta na koshi Sannan na fito bansan meke min Dadi bah!"Na kasaci da Sha zuciyata taimin nauyi!"A hakan na hakura na Cigaba da ayyukan gidan..."Saboda tun jiya mama ta gaya min zata fita unguwa..." "Ko da ta dawo ta sameni Ina aiki Amma Raina ba Dadi!"Idanuwana sunyi jajur...ko da ta tambayeni lafiya!"Nace Mata ba komai bacci na tashi..." "Kyaleni tayi duk da ta fahimci da wata aqasa Amma tasan cewa a hankali zata San meye damuwata..." "Da Rana ma Yaya Saddiq ya shigo da yaran sa sunyi Mana bankwana zasu koma sakkwato..." "Mama ta bada kayan yaji da SAURAN tarkace akaiwa Anty Jalila." "Kamar Kar su wuce naji!"Nan dai Nima na shirya Naje Gidansu Saudat.'' "Ban jima ba!"Aka turou min sakou kamar kullum na gaisuwa tare da fatan alkhari Wanda akarshe ake rubuta ... min Daga mesonki M.JAWAD."Banyi mamaki ba domin idan da sabo na Saba..."Tun ban mayarwa har nafara mayar Masa da reply na NAGODE."Fira mukayi sosai ni da saudat tare da bani shawarwari akan Jawad da Kuma Juyawa malam yunus baya." "Tuni na dauki alqawarin mantawa da soyayyar Mallam.. sai dai Nikam bana Jin masoyin boye amatsayin masoyi domin bazan iya Sonsa ba."A yanzu da ace za'a bani zab'i da Abokina Naseer zan zaba domin shine mukafi dacewa da shi." "Mommy zaune a bedrum tana ninke kayan ta....sai Gashi ya fadou ba ko Sallama...duk da ta Dan tsorata akan baiyi Sallama ba!"Amma sai ta share shi...''Yace mum gani!" "Jawad!!"Daman Ina son muyi magana Mai muhimmanci da Kai!"Zauna anan ta Nina Masa gefenta." "A gefen gadon shima ya zauna Yana fuskantar mahaifiyarsa..." "Jim tayi na wani lokaci Sannan ta dubeshi shi da sanyi Tace"Jawad ya kamata muyiwa Abba Adalci!Lokaci Yana Tafiya fah! yanzu Naga hankalinka ya dawo jikin ka kayi hankali!ka daina shashanci ka fara Zama yaron kirki Mai Kamala kamar yadda Abba Yake son kazamou Mai *TARBIYYA*...Sanadin neman auren Yar gidan *TARBIYYA* ya canja kaf rayuwarka ta Daa yanzu ta dawo sabuwa kamar kowane D'a nagari Mai *TARBIYYA*"Yanzu NE Ya kamata mu Ida nufin Abba..."Ina son muyi kokari mu fara neman abinda ya Sanya agaba kafin mutuwarsa!..."Mu Idar da aikin da ya kawo shi wannan kasa ta Nigeria,Kaga kakannin ka suna can suna na jiran tsammani!." "Sanin kanka ne...Abba ya barmin wasiyya!"Ya Kuma barmin amanarka da ta dukiyarsa ka da Kuma ta aikinsa." Ina son ka cika Masa burinsa jawad lokaci yayi da ya kamata na warware maka komai yadda zaka gane Wanene Kai meye asalinka da kuma Danginka..." "Ajiyar zuciya yayi yace"To mom zanyi kokarin hakan."Nagode Allah da ya kawo Wannan lokaci da na Dade Ina jira..." "Yawwa,Jawad zan Gaya maka komai nidai kayi kokari kayi aure domin shine mabudin warware maka abubuwa kamar yadda Abba ya tsara da Yana Raye!!" "Ba komai mom aure kamar gobe NE,zanyi da yardar Allah." "Masha Allah Tace tare da sauke ajiyar zuciya so da kaunar tilon danta Yana fizgar numfashinta." "Cike da kauna tare..yanzu ya zancen Nadiya ne!?"Jiya saifullahi yace min ta dawo tana gida hutu take." "Tana lafia.....mom Eh...na manta na sanarda ke tafa dawo." "Yaushe zaka kawo min ita na ganta." "Duk Ranar da kikeso mum." "To...kamar Jibi akawo min ita zaifi." "An Gama mom,zan kawota...." "Shi kenan Allah yayi maka Albarka." "Amin...my Dear.." "Tashi yayi Yana kokarin fita...mom taqara da cewa Nifa na kosa ne inga surukar tawa saboda nidai Tuni na yaba da tushenta nasan cewa Nadiya yarinya CE Tagari wacce nutsuwa Ta wadaci rayuwarta..." "Haushi yaji acikin zuciyarsa saboda ya tsani! yaji ko da sunanta NE!"A fili Yake yayi yace"Hmnnnnn mom kenan Lalle kinaji da yarinyar nan..." "Kwarai da gaske Jawad." "Duk da Kasancewar ta Yar talakawa!?"mom "Ayni Tuni Na daina tsanar talakawa Tunda na hadou da ahlinta Jawad saboda mutuncin su ne ya saye son duniyata..."mum taqare zancen tana dariya." "Dai dai KOFA ya juyo ya Kara kallon mom..Yana murmushi Sannan yace"To Allah yasa ta soki itama kamar yadda kike sonta."Domin Ni nafara KISHI!"tun ba a ganta ba!An fara santi hakan..." "Amin...Jawad Ayna San yarinyar kirki CE zata so ni kamar me.." mom Tace alokacin da yake kokarin fita daga Dakin." "Cigaba tayi da gyara Kayanta aranta ta kosa taga ko Wacece Nadiya..." "Shi Kuma Yana fita wani tsaki yayi tare da cizon yatsa!"ya ce azuciyarsa"hmnnnn Nadiya ta shigo hannu kawai sai tayi Kuka da hawayenta Wallahi!sai tayi Dana sanin kirana da abinda ta ambata Abaya wani Hawaye ya zubou Masa Mai zafyh!"Hannunsa yasa ya goge tare da jera ajiyar zuciya." "Sashensa ya nufa wayar Saif ya Kira..."Nan sukayi waya Mai Dan tsayi kana suka rabou da zummar zasu hadou an juma da yamma." "Tunda Naje Islamiyya da yamma na canja domin ko kallon malam yunus Banyi ba!"Na daina sakewa da KOWANNE malami..Abinda ya kaini shi nakeyi na dawo daga Ranar na canjawa kowa."Kullum Ina waya da Naseer..."Da su Esha,Deeja,Da Kuma Deeyart ayanzu ba abinda ke damuna domin na jingine duk wani son malam yunus gefe..."Saudat da kanta sai da tayi mamakin irin dakiyata ta Kuma jinjina min..."Saboda Sam batayi tsammanin zan debe komai araina da Wuri hakaan." "Haka na Cigaba da rayuwar Hutuna lafiya qlaw Bani da damuwa domin Naseer ya Gama min komai mun Kara shakuwa sosai awaya." "Hakan agefen Jawad ko yaushe Yana turo min text Nima Ina tura Masa Sannan muna waya sai dai ba sosai ba!" "Na fahimci Jawad mutum NE Mai hankali ilimi da Kuma tsari Wanda gayu da kwarjini ya wadaci rayuwarta Wanda Kuma alamun cikar kima da hankali ya bayyana agaresa duk da bamu San juna ba!"Amma halayensa da Yake nuna min awaya ya Sanya naji Yana burgeni..."Sai dai har yau Babu Sonsa ko da kwayar zarra azuciyata." "Ana hakan kwanaki sai Tafiya sukeyi har lokacin komawa na sokoto yayi domin hutun mu ya kare har naqara mako biyu...Shiyasa Yaya Saddiq ya Kira Ni Yana fad'a Nan NE iyayenah suka tattara abinda suke da shi nayi Sayayyar Kaya na koma makaranta..."Sai dai Wannan karon karatu NE agaban mu domin mun fara darussa masu wuya shiyasa na ajiye komai nafara FUSKANTar karatu na haikan ba da wasa ba." "Saif da Jawad NE Cikin shiga ta Alfarma..kokarin fitowa sukeyi Daga hadaddiyar motar su..."Dai dai Inda aka rubutawa Admin suka nufa tare da want malami Wanda ga alama Dan jagoran su ne...."Ba da wani jimawa ba suka Isa kofar wani office da aka rubutawa M.BALA da farin fenti...manne akofar." "Knocking sukayi Bayan an basu damar shiga Daga ciki...Sai suka shiga Bayan sun gaisa..." "Wanda ke tare da su yace Mallam Bala wadan Nan sune samarin da kuke waya da su Jawad da saifullahi Daga kebbi." "Dariya Wanda aka Kira da Bala yayi irin ta rashin mutunci Sannan yace"Ba dai kace sun jika ba ko sahabi?" "Sosai...ko ay manyan yara NE ranka ya Dade Wanda aka Kira da sahabin yace Yana murmushi da zumudi." "Gud...malam Bala yace Sannan yakara da cewa naji duk bayanin KU awaya Sannan sahabi ya fad'a min komai...Wannan bukatar taku duk Mai sauki CE...matukar zanji damen kudi atafin hannuna to zan iya aikata komai Aduniya..." "Sahabi ya karbe Tabbas hakane oga ai duk fadin makarantar nan Babu Mai ja da kai.."Duk Wanda yaja da Kai xaici kasa..." "Dariya yayi tare da zuqar tabar hannunsa kana ya hurou hayakin waje cike da gadara yace ku nuna min hoton yarinyar zansa anemo min facultyn su da duk wasu details nata duka Nan zuwa jibi komai zai wakana sai dai KU saurari sakamakonsa aikin ku..." "Da sauri Saif yasa Hannun sa a aljihu ya dauko hotonta biyu ya mikawa sahabi ya duba da kyau kana ya baiwa M.Bala..." "Ido ya turou fili tare da zuge gilashinsa sa yaqara mannawa Yana kallon hoton...dariya yayi Sannan yace Wannan yarinyar sunanta sorry...Domin Ni Kaina ta taba min rashin kunya ko da Baku kawota wurina nasan watarana zamu hadou da ita a makarantar nan....Kenan yanzu can hada Mata zafy! biyu saboda Nima Ina da takaicinta!!!" "Jawad yace mudai aikin mu kawai muke bukata kayi Mana kuma ya tafi daidai." "Saif yace saboda akwai Dan uwanta ko Mallam Saddiq bama son ya shiga Cikin lamarin Nan yakawo Mana cikas...." "Haba yaro ay duk farin makarantar Nan ta shehu shagari ka bincika Babu Mai fad'a aji kamar m.Bala Nan da kake ganinsa shaidani NE ko shaidan da kansa yana Sara Masa Kai duk makarantar Nan tsoronsa sukeyi har provost da kansa Sara Masa yake...saboda Yake mutum a halaka wurin bokaye Bakomai bane awurinsa...Sahabi ya karashe zancen cike da Jin Dadi da Kara Koda da kambaba ubangidansa." "Kallon JUNA sukayi sannan Jawad ya zarou Damen kudaden da shi kansa baisan adadin su ba ya ajiyewa M.Bala..."Saif ya Mike tsaye yace to Mallam mu zamu KOMA sai munji Daga gareku..." "Sahabi washe baki yayi shi da M.bala Ana rige rigen daukar kudi Tuni M.Bala ya kwache ya tura aljihu shi Kuma sahabi cewa yayi haba yallabai ay sai kabari na kirga Dan gudun kuskuren biyana kudin aikina..." "Jawad wasu kudi ya zarou ya mikawa sahabi..da Tuni ya Kai kasa Yana GODIYA...Nan sukayi Sallama da m.Bala suka fito sahabi baimasu doguwar rakiya ba ya KOMA office din Amna Ina Tuni M Bala ya kargame kofarsa da makuli...Sahabi cike da haushi yabar wurin saboda yayi ta bugawa malam Bai bude ba!"Sai CE Masa yayi ai anbiya shi kudin aikinsa sai dai ahadou wani aiki idan yasamu... hakan ya hakura yabar wurin Yana ma M.Bala Allah ta Isa!" "Su Jawad na fita suka dinga zaga harabar school din ko da kadara zata hadasu da Nadiya Amma Ina...Har yamma Basu ganta ba!"Hakan suka hakura suka Kama hanyar Argungu cike da farinciki aransu." _Share and comments my fans_ *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 [2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 19* _DAN TSOKACHI"GAISUWAR BAN GIRMA GAREKU ABOKAN TAFIYA, WATOU MASOYANA,DAN ALLAH KUI HARURIE MASU NEMAN BUKS D'INA, ZAKU IYA SAMUN SU, A NABILA'S FANS GROUP KAI TSAYE" KO KUMA KU BINCIKI SHAFUKA NA, FCBUK, INSTAGRAM,DA KUMA WHTSP NAGODE."👍🏼👍🏼👍🏼😍_ _Masu comments ina ganie kuma ina jin dadi musamman masoyan Nadiya naga kamar kun damu da yawa,Yoo nie ita mansura banji ana tabou chapter ba,Masoyan jawad yana godia,Wasun ku kuma na bar maku jalilah domin nikam tafi karfina sai ku fans🤣🤣🤣_ _*LITTAFAN MARUBUCIYA*_ _*WATA RAYUWAR..._ _*TSAN-TSAR SO_ _*MATAN AURE_ _*BAK'AR AK'IDA_ _*ALMAJIRACHI KO AIKATAU?_ _*DANGIN MIJI_ _*IDAN AN CIZA..._ _*MATA JIGON AL'UMMAH_ _*AUREN DOLE!_ _*SAI KUMA TARBIYYA.....✍🏼_ _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ ______________________________________ "Mansura kam tana kare chashewarta gidan su kawarta Safna, saurayinta Bimboy ta Kira awaya yazou ya kwasheta sai mabera."Bayan tulin kayan birthday din da safna ta hadata su tare da godia"...karya tayiwa Bimboy da cewa Zata biya ta gidan kawarta Suhaila da ke unguwar ta amso sakou..."Nan ya tsaya gefen titi Yana jiranta amota har ta dawo, ita kuma tana fita wani lungu ta shige Mai hanyoyi daban2 ahankali ta shiga wani Babban zaure..." "Da hanzari ta zube gabansa tana kwasar gaisuwa...Da fara'a malam ya taryeta domin sun Saba da ita SOSAI." "Gyaran murya yayi tare da kallonta "yace mansura yau kece a zauran namu...To meke tafe da ke."Matsalar jarrabawar ce to taso?ko malaman ku ne!?Ko Kuma iyayenki nasan Tuni muka Gama da zancen su....Ko samarin ki ne ko Kuma Abokai!?"Ajere Mallam zakiru ya tambayarta..."yana cigaba da Jan carbinsa." "Gyara zamanta tayi tare da cewa"Ay malam yanzu sai abinda nace iyayena keyi, aiki yayi kyau domin tsorona ma sukeyi yanzu Tuni nayi watsi da *TARBIYYAR* da suke kokarin yimin...Haka exams sun fitou Duk sunyi kyau na lashe...samarin ma biye suke abayana..."Sai dai malam yanzu mijin aure nagani Ina so,Ina ga lokacin aurena yazo Ina son kaimin aiki..."Mai kyau akansa Mallam Nike Sonsa shi Kuma ya tsaneni!..."Ina bukatar agaji da taimakon ka!"Gobe zanxou da matarsa wato uwargidan sa inason ka had'a min kullin da zan mallake shi duka Amma fa da sunana sai dai ita kabata amatsayin Yar aiken mu..."Ina son ka janyo min hankalinsa ya aureni Kuma Sai abinda nace da shi zaiyi da matarsa Jalila harma yaransu su kasance kamar bayina...."Ita zaka baiwa maganin tayi amfani da su Amma aiki yazamou nawa..."Da fatan ka fahimta Babban goro." "Dariya yayi irin ta shaidanu wacce tayi sanadin fesou goron da ke kimshe a wangalelen bakinsa..."Sai da ya watsawa mansura afuska..."Ya ce bakida matsala yau aikinki zanyi na tsawon dare!" Amma Zaki bada kudin aikinki tun yanzu kinsan yankan wuqa alokaci daya..." "Murmushi tayi Tace bakada matsala mallam zip din Jakarta ta zuge tare da doubou kudade tace ga Wannan Ta mika masa Nan yasa hannu ya karba tare da zuba su a aljihunsa Yana washe baki..."yace yanzu sai kunzou da Yar rakiyarki zan shirya komai." "Yawwa malamin mallaimmai GODIYA nake Allah YABAR ZUMUNCHI ya qarou sani..." "Ameen, mansura,Ay bakya da matsala tunda kinka rikemu tamau..."Mallam zakiru yace Yana munna." "Inda Bimboy yayi parking ta nufa kai tsaye,motar ta fada suka nufi makaranta." "Tsaye nake ina knocking kusan yafi akirga amma shiru ba motsin komai...."Gajiya nayi da tsayi na zauna abakin kofar falon tare da ajiye ledojin da jikata...Wayata na fitou da ita domin na kira layin Anty jalila sai dai kiran baya zuwa..."Nan na cigaba da buga kofar....Motsin keys na jiya alamar za'a bude...." "Da karfi aka bude kofar...Wanda sai da na dan tsorata!"Rasheeda ce kanwar Anty jalila na gani...ta bude min kofar ko kallona batayi ta juya daga ciki...Su mufeeda ne a sanyaye sukayo kaina suna Oyo yo Anty Naddyh....Da taimakon su na shigo da kayan..."sai dai turus naja na tsaya ganin irin yadda Anty jalila ke harare na!"Ita da kanwarta da kuma yayarta Anty talatu...." "Duk da naji wata irin fargaba da tsoro araina!"Bai hanani zubewa agaban su ina gaishe su cike da ladabi..." "Dakata munafuka!!!"Ki ajiye gaisuwarki nan gaba idan da sauran rayuwa zatayi maki amfani...Anty talatu tace tare da daga min hannu..." "Rasheeda da bazata wuce sa'a ta ba!"Sai hararena take tare da daure gyalenta a kugunta ta hade hannayenta akirji!!!" "Rasss gabana ya fadi!na rasa me zance!"saboda naga Anty jalila ko kallona batayi ba!kuma tamkar tasha kukan wahala!"kamar ba ita ba!" "Ban motsa da inda nake ba ban kuma tashi ba!"jikina sai rawa yake ga cikina sai qara kugi yake!!!"A karshe tashi nayi tsaye da nufin shiga dakin mu...." "Karaf rasheeda ta cab'e min kafafuwa sai kasa tif....Dagowar da zanyi a firgice naji saukar zafafan maruka uku ajere wanda sai dai Anty jalila ta daddage ta watsa min su..."Cike da zafyn!nama...." "Durkushewa nayi ina fadin Innalillahi!Wa inna ilaihir raju un!!!" "Oh!!!Bakinki ma da sauran magana nan ta hayeni ta dinga dukana ita 'yan uwanta wanda tuni suka rufe min baki bana ko iya magana bare kuka!!!" "Su mufeed sai kuka!!!suke suna cewa momy Anty kuyi hakuri!!"Amma ina dukana suke ta ko'ina!tun ina jin me suke fada har na fita hayyacina...'' "Ta ko'ina jibgata suke...kamar daga sama sai ga shi ya shigo falon sai dai yayi mutuwar tsaye ganin ana kokarin kisa agidansa!" "Da hanzari ya isa wurin su inda yayi wurgi da rasheeda wacce sai da ta dan bugu da kujera...nan ya hankade jalila tare da watsa mata mari!!!" "Anty talatu ko tuni ta daburce ta sauya kamar mai kokarin hana fadan...." "A firgice ta dago kai ta kalle shi!"Ni zaka mara!"?"Saddiq akan wannan yar iska!?" "Bai ko dubeta ba!"Tallafota yayi tare da jijjigata amma ina bata numfashi...Da gudu ya nufi fridge ya dauko ruwa ya dinga zuba mata duk bakinta da fashe!"fuska ta kumbura...."A hankali na bude idona gajimare kemin yawo!"Bansan inda nake ba!"A hankali naga yaya sadiq kamkame shi nayi nace yaya ka taimakeni!"Zasu kasheni!!"Yaya zasu kasheni Anty jalila da yan gidan su!"Ka mayarda ni inda Mamana..." "A hankali ya jinginar da ni ajikin kujera saboda duk sun halakani,sun min rauni a fuska,hannu da kafa..saboda harda cizo na sukai!!!"Da inda Anty jalila take tsaye sai kawai tayo kukan kura kaina ta shakeni sai dai naga wuta..."Nan take kuka ya kufce min...Yaya saddiq kam iya karfi nai!"Ya hankadeta sai kasa! tare da watsa mata lafiyayyen mari!"Nan Anty talatu itama ta kashe shi da mari!"cike da takaici da zuciya!!"Rasheeda da gudu tayo kaina ta hayeni tana duka!...A kufule yaya saddiq yayi wurgi da Rasheeda! harda kwallo da ita!!"Nikam da kyar na rarrafa na tashi na koma bayansa ina rusa kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro...."Saboda naga manyan namun daji sunyo kaina suna batun cinyeni...sam ba imani da tausayi azuciyarsu...." "Anty Talatu tace tabbas saddiq ka canja!"yanzu akan bare zaki nemi halaka min kannai!!"" "Karfa ka manta jalila uwar yayanka ce kuma matarka tafi wannan banza munafukar yarinya!!!" "Anty kibar shi wallahi zaiyi da nasani ke kuma kibar min gidaana ko kuwa tsoffin da kike ambata su zo su dauki gawarki!!"Wato bakinki ma da sauran magana baki kasu ba!!!" "Ransa abace Ya ce" haka kawai zaku daketa!me tayi muku!"Anty talatu wannan haukar ba girmanki bane!"Ay saiku sanar da ni idan ma wani abin ta aikata!"Domin nine jigonta ba ku dauki mataki ba!"Na hauka da zalunci!!!"Irin hakan!! "Ka kirani da mahaukaciya saddiq!Me ya rage!ko kuma kazo ka dakeni sai ka rage zafi saboda an daki Dadironka..!!"Anty talatu ta fada cike da rashin mutunci!" "Dadirona na Kuma jalila.....Saddiq ya nanata tare da dafe kai!!" "Nikam tuni na daura hannu akai ina ambaton sunan Allah ina hawaye!!"Saboda jin wannan mummunan zarafin..." "Eh...ko karya ake maku wato ni zakuci amana acikin gidan nan saddiq wallahi ban yafe ba!kuma sai Allah ya saka min...sannan sai dai ka zaba ko ni ko yarinyar nan babu ni ba ita na tsaneta ko Lahira kada Allah ya hadani da shegia irinta banza mayya yar talakawa...."Allah ya tona asirin ku duk abinda kukeyi an gaya min maci amana kawai!ke kuma da bakisan halacci ba!"Ashe Sam bakiyi kama da wadanda za'a baiwa amana ba.....!!!" "Ya isa Hakan jalila bana son rainin wayo.....yanzu kuma abin ya kai ga aymin sharri kuma har da ita Nadiya!?...ya kamata kisan waye ni ba sai wani yabaki labarina ba!"Kawai an shirya karya an gaya maki saiki dauka batare da bincike ba!!?"Yanzu kina nufin akan Wannan dalili maras kan gado zaku daketa!!!" "An daketa din Ay horata ne akayi domin tasan cewa ba a shiga hurumin mu akwashe lafiya...Wallahi sai kinyi dana sani Nadiya...Rasheeda tace cike da tsiwa tana hararana..." "Baice da su komai ba!"Ya kalleni..." "Nadiya tashi muje asibiti aduba lafiyarki.."A hankali na tashi ina dingishi...yaran rikeni sukayi suna kukan tausaya min...Anty talatu fizgo su tayi sai da na kusan faduwa akan mangajeni da tayi...yaya saddiq ne ya tareni..tare da rike hannuna...."Tafiya nake sannu ahankali saboda zafi!"Dai dai bakin kofa Anty jalila ta cimma mana tare da sha gaban yaya saddiq hannu tasa afusace ta yage masa riga tun daga sama har kasa tace"Wallahi ba inda zaka!"Ta kira ubanta ya kaita asibitin mana!" "Kallon jikinsa yayi tare da mamaki!" kuma ta kame rigar tamau taki sakinsa....yace Sakeni!!"kinji ko!yace da mutukar bacin rai!" "Sai dai ka kasheni bazan saki ba!"Anty jalila tace afusace tana zubda hawayen bakin ciki!!"Da girgiza jiki!Da hurar hanci." "Nikam bayansa na koma na labe jikina sai rawa yake tuni na nemi zawayi na rasa!!"Saboda tashin hankali..." "Saddiq bafa inda zakaje!!"Na gaya maka!fita tare da ita tamkar fitar numfashi na ne!!"Wallahi bazan barka ba! Macuci kawai!!"Wato in barka akara cin amanata agama da rayuwata!!"Hmnnnn tace tare da riqe kugu da cimuimuye masa wuyan rigar da ta yage!!"Tace waini zakuci amana!!"Harda zancen aure bana da labari! To ni ai gwara ka sakeni!!" sai ka aureta amma kasani amanata baza barku ba har abada!!!" "Da karfi ya kwace kansa daga jalila!"Yace mtwsss!!!kin haukace!!"Ke Nadiya mutafi...Tafiya nafarayi...Banyi aune ba!sai jin saukar sandar humtiyata da nayi akaina wanda Anty jalila ta ratsa min..."Tuni na fadi wurin somammiya!!" "Tana huci tace idan na kasheta zaka san sonka ne silar haukata!!"Kuma kishinka zai iya SA na aikata!komai "Jalilah!ya fada da karfi!"tare da duban Nadiya akasa ba rai!"Ganin hakan Ya sanya jikin su Anty talatu da rasheeda rawa da faduwar gaba!!"Amma Anty jalila ko ajikinta fatan ta yarinyar nan ta mutu ita kuma zata iya jure zaman gidan kasou har karshen rayuwarta!!" "Yaran kuka sukeyi suna kallon iyayen su....Amma jalila hawayen farin ciki take!!"Kallonta yayi yace kibi yan uwanki sai na nemeki "sannan ki saurari sammaci!!" "Wallahi ba inda zanje ina gidan nan...Ba'a haifi wata da zan bar gidan nan akanta ba!"Babu ta aduniya ni da kai mutu ka raba takalmin dan kaza!!Ayi arziki tare da ni aci da wata banza...wannan mafarki ne!!!"Jalila ta qarashe zancen tana surfa masifa!!" "Hannun yaran sa yaja zuwa mota!"tare da kinkimar Nadiya wacce tuni numfashi ya dauke!" da sauri ya ajiyeta mota yaja zuwa specialist hospital...."Yaran sai kuka sukeyi...." ( _Hattara iyaye mu sani duk abinda mukeyi yaran mu suna fa kallon mu,A matsayin ki na uwa bai dace kina wasu abubuwa akan idon yara ba!Shi yaro baisan dacewa da rashin dacewa ba,Zaki iya manta kin aikata abi sai yaronki ya tunatar da ke ko labarin ya maimaita kansa hairan ko sharran Akiyaye!_) _A cigaba da zubou min zafafan commets_ *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 [2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 18* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ _SADAUKARWA A GAREKU 'YAN UWANA 'YA'YAH MATA NIKAM DAI BAZAN RAINA MATA BA ADUK INDA KUKE ALLAH YA SANYAWA RAYUWAR KU ALBARKA YA KAWO CIGABA MAI DAUREWA ARAYUWAR MU AMEEN._ ______________________________________ "Da zarar ka kunno kanka a unguwar sama road, da ke garin sokoto, kunnuwan ka zasuyi arbah da sautin kid'a da ke tashi..."A katafaren gidan Alh.Badamasi Dan canji,Attajirin gaske ne Wanda naira ta zaunawa atafin hannun sa.. "Muryar fasihin mawakin nan KB show ke tashi Wanda ke ta faman wake Hajiya Asabe wato uwar gidan Haji Badamasin wacce dubban jama'a suka zo murnar tayata bukin cika shekaru Hamsin Aduniya..." "Manyan kujeru ne na Alfarma naji na gani da fad'a aka jera....sai kayan makwalashe da abinci da drinks da aka jera akan ... teburan"Manyan mata ne zaune Cikin shiga ta Alfarma hakan harabar filin gidan Sai chasu yaran na Hajiya Asabe keyi da qawayen su tare da sauran Dangi Yan uwa da Abokan arziki...." "Mansura sai kwasar shoyki ake Ana karairaya Ana juyi...Cikin shigar material green da white head kusan su shidda ne da Wannan dressing din iri daya sunyi kyau matuka an Kuma matse Cikin dinkin taaam..." "Hajiya Asabe da kawayenta sai liki suke masu hakan mawakin shima sai azama yake wurin wake uwar gayya Mai Birthday wato Hajiya Asabe Badamasi." "Mansura rawa take tana juyi!"Juyowar da zatayi idonta yayi tozali da matar da ta tsaya Mata arai!"Wacce ko a mafarki bazata rasa tantance ta ba!" "A hankali ta dinga fitowa Daga Cikin filin rawar...karaf taji an Kama hannunta...tare da cewa Ina zakije mansura Bayan kinsan kice Mai jagorantar rawar Nan ko zuman naki yazo NE!?..." "Murmushi tayi tare da dafata tace ko daya.." Ina zuwa Safna yanzun Nan zan dawo Kinga Daman wata Yaya ta na hango zanje mu gaisa da ita ne...."Inji mansura "Owk...karfa ki makale kin sanki da zuba kamar ruwa...Safna Tace tana dariya." "Aha Ina zuwa bazan juma ba... Mansura Tace tare da hanzari tabar Safna wurin tana kwasar rawa ummanta nayi mata liki da Yake ita ce autar gidan.." "Cikin kwarewa da kwarkwasar take Tafiya daki-daki kamar hawainiya da yake takalmanta masu tsini ne SOSAI..."Ga kayan jikinta duk sun matseta..."A Inda take zaune tana kallon duk shagalin da ake..."Abinci take ci tare da motsa baki." mansura....ta nufota Cikin sanyin murya Tace Ina wuni Anty.. "Kamar bazata kalleta baa domin ta hangota tana zuwa wurinta Kuma ita Sam yarinyar Bata burgeta!"Tun haduwar su ta FARKO taji Bata yinta!...sai dai sadda Kai tayi tare da cigaba da Danna wayarta Tace "Lafiya!Ina gajiya agajarce..." "Yake tayi tare da janyo kujera ta zAuna Sannan Tace Lafiya qlaw Anty,Hmnnnnn mansura ce faah ko baki gane Ni ba!?"Inji mansura "Uw... gaskiya ban gane ba!Daga Ina kenan!?"Ta tambaya "Haba!?"Kinga nikam na ganeki ya gida yasu Mufeeda da Yaya Saddiq!?" "Duuuumnnnn gabanta ya buga Nan take ta canja sauyin walwalar fuskarta Tace lafiya..."A Dan kufule!!" "Madallah Daman kinsan su Safna kenan Ay kawata ce tare muke karatu a university...Daga can ne ma na hango ki nace Bari nakawo gaisuwa gurin babbar Anty..." "Allah sarki..Nako gode...Niema dai Hajiyar su Safna nan Kawar Mamana CE SOSAI mun shigo bukin tare da Yan gidan mu..."Inji Anty Jalila." "Am Bari na tashi na tafi,Anty Ashe Naddy tana gida na dauka Kuna tare da ita ne ko da Yake ba magana take min ba!ko da ace mun hadu anan ba Amfanin hakan.." "AshSha!meke faruwa ke kuwa!?"Ba kawarki bace!?"Inji Anty Jalila da mamaki." "Hmnnnnn Anty kenan Ada can baya Naddy kawata ce amma Banda yanzu domin tafi karfina saboda nikam bana goyon Bayan cin amana Wannan daliline yasa muka ware!..."mansura ta karashe zancen cike da kissa da makirchi." "Cin Amana kuma ita Nadiya CE taci amanarki!?"Inji Anty Jalila cike da tuhuma." "Gyara zamanta tayi tare da fuskantar Anty Jalila fuskarta dauke da damuwa...Tace kiyi Hakuri da Abinda Zakiji Daga gareni Anty Amma tsakani da Allah taimakon zanyi domin ki fita Cikin matsala Kuma ki kwatou mijinki Daga shu'umancin Naddy..." "Fidda ido tayi waje da mamaki Tace wama kike!?Bangane ba!?"Me kike nufi!?"Mijina Kuma!?" "Mansura sunana....."Hmnnnnn Anty kenan me kike ci nabaka na zuba...Ki saurareni da kyau Kiji." aranar da Kika ganni agidan KU Daga wurin malamin Naddy muke!"Inda yabata kullin mallakar Yaya Saddiq Wanda sanadin hakan ke kuma za'ayi waje da ke!"Ganin hakan Bai Dace ba yasa na nunawa Naddy ta dai aure shi Tunda sun Dade tare da shi Saddiq din Kuma suna son juna Wanda azahiri ita Naddy ce ta mutu Sonsa domin Tasha gaya min."Shiyasa nace Mata zata iya auren Saddiq Ba sai tarabaki da yaranki da mijinki ba!"To fa Daga Fadan gaskiya fa Anty...sai kawai Naddy ta ci mutuncina ta koreni Daga falon! Ina Fitowa na ci karou da Saddiq Kuna dawowa anan shima ya Kara min wani wulaqanci harda nunawa get man Ni Wai kada yaqara barina na shiga gidan..."Saboda daman Saddiq Yasan cewa bana goyon Bayan cin amanarki da sukeyi Bayan ke da zuciya daya kike zaune da su musamman Naddy da Kika dauka tamkar kanwarki!!" "Daman Ina nemanki na warware maki zare da abawa Kuma na nemi alfarmar ki yafeni na tuba domin wani wa'azi naji akan zuwa neman magani ba kyau,Akan hakan na dauki alqawari aduk Inda na ganki zan Gaya Miki gaskiya Kuma ashirye nake domin na kaiki har Inda mukaje muka amso maganin Nan."Domin a walwale kullin asirin..."Hawayenta da ke Mata zuba ta goge cike da kicihi Tace Anty Jalila na kasa nutsuwa saboda mun cuceki..."Nidai Dan Allah ki yafe min." "Tamkar mahaukaciya Sabon kamu Haka Anty Jalila ta hargitse duk ta rikece ta tashi tsaye! tana huci sai gumi da ke fetsou Mata ta kowacce kusurwa ta jikinta!!!!"Hawaye ne sharaf a fuskarta Tace yanzu Ni yarinyar Nan zata zalunta!"Ni Jalila za'aci Amana!Wallahi sai tagane shayi ruwa NE yau ba sai gobe ba!zatayi laushi Kuma tabar min gidana...Ina Mata kallon kirki Ashe Yar iska CE! marar mutunci! to da shi har ita zanyi maganin su...."Jikarta ta dauka ta kalli mansura tace Nagode kinji...yanzu ya za'ayi muje gidan Mallam din!?"KOMA muje yanzun nan kinji Dan Allah mansura ki taimakeni!!!"Ni nayafe maki ke Mesona CE.." "Numfashi ta sauke tare da cewa yanzu yamma tayi sai dai gobe mu hadou na kaiki Anty yanzu dai kibani lambarki sai muyi waya!"Kinsan bazanje gidanki domin gudun wulaqanci!!" "Karki ji komai mansura Ni yanzu Kaina ya dauki zafi!bansan ya zanyi ba!"wucewa zanyi bazan iya jiran su Hajiya ta ba!"Inji Anty Jalila hankalinta atashe "Musayar lambobin juna sukayi har Anty Jalila tafara Tafiya mansura ta cimmata Tace Anty ko gobe Ina baki shawara ki daina sakewa kowa ragamar gidanki da amanar mijinki domin yanzu Babu Amana kingani wacce kikewa kallon kirki itace ke kokarin cutar da ke tare da ci Miki Amana sai ki kiyaye gaba..." "Wasu zafafan Hawaye ta hadiye tare da Girgiza Kai Tace hakane mansura Nagode..." "Nan SUKA rabou mansura ko farin ciki NE fal aranta domin hakarta ta kusa cimma ruwa hakan ta Koma filin rawa ta Cigaba da rakashewa "itama Anty Jalila da kyar tasamu taxi din zuwa gida sai rusa Kuka takeyi ga bakin kishinta ya motsa Jin takeyi tamkar ta hadiye zuciyarta ta mutunci saboda kunar rai!"A daddafe ta Isa gidanta da ke BAFARAWA ESTATE ta sallami Mai taxi din tana shiga gidan faduwa tayi a tsakar falonta ta dinga Kuka kamar wacce aka aikowa sakon mutuwar iyayenta...A zuciyarta takasa shirya irin bala'i da masifar da zatayi da Saddiq!"agefe Kuma Tasha alwashin halaka Nadiya idan ta shigo gidan..." "Sautin dariyar su da shewa ke tashi a falon da karar spoons da suke cin abinci a dining place." "Yanzu dai mom an kawo karshen zancen...Jawad yace Yana murmushi..." "Wane zance kuwa yazou karshe Bayan an Saba Alqawari..."Ayni kaji abinda na fad'a bazan Kara cewa akawo ta ba..." "Mom...ki yarda da mu agaskiya Ranar da mukaso kawo maki Nadiya aranar aka Aiko ta koma makaranta."Amma bazata wani Dade ba zata dawo sai akawo ta...Saif yace Yana Cigaba da cin abinci..." "Lemu mom ta kurba tare da lunshe idanuwanta...Tace to Saif Ni yanzu ai sai Ranar da na ganta..." "Jawad ya ce''Yanzu dai mom ayi kokari kafin ta dawo atura magabatana agidan su ay komai agama Kinga da ta kammala karatu Shi kenan..." "Dariya mom tayi Tace naji SARKI tsari...Zanyi magana da aminin mahaifin ka Alh.malami sambo da Mainasara sai suje ayi duk abinda yadace..." "Mom zan gayawa Abban mu domin Wannan Tafiya yadace ayi ta shi...Inji Saif cike da Jin Dadi..." "Yawwa Saif hakan yayi Amma nifa Rana daya nakeso ku angance Kai da nakan...Ya zancen ita samhan naka?"Mom Tace tana kallon Saif "Momy ay na daina zancen samha da dadewa saboda yarinyar sai ahankali batada kirki nagane samha batasan meye ya kamata ba, saboda"Samari ne da ita barkatai da nayi magana sai ta nuna min ban Isa ba!"RABUWAR mu shine mafita domin dukkan mu muna gadara da arziki..."Saif ya kammala zancen Cikin sanyin murya..." "Jawad ya karbe yanzu dai zamu fara lalabou wata mom Sai ayi tare ko ba Haka ba!?Nawan...." "Hakan shi yafi dacewa Inji mum tana Murmushi taqara da cewa nifa Kuna bani mamaki ga yam Mata Nan kamar janfa ajos sai Kun darje!"AKWAI Yayan arziki da talakawa akwai Kuma masu tufin asiri...Amma garin ruwan idonku na banza har KU kwasowa kanku maras *TARBIYYA* ko da ruwa baya tsami banza..." "Mom abar zancen aymu Duk mun daina komai yanzu Inji jawad." "Allah yasa mum Tace." "Saif yace Amin... " "Nan SUKA Cigaba da tattaunawa akarshe mom tashi tayi ta barsu suna fira ita Kuma waya ta dinga yi da hamshaqan kawayenta Kuma Abokan business dinta gold." "Daga Nan Alh.malami sambo ta Kira WATOU aminin marigayi mijinta All.Husamaddin tayi Masa bayanin SOSAI akan neman auren Dan su Jawad."Sai da ya Bata tabbacin gobe zai dawo daga Abuja Amma jibi zasu shigo ayi zancen komai Sannan suje neman auren." "Fatan adawo lafia tayi Masa tare da GODIYA ta musamman Sannan sukai Sallama..."Murmushi mum tayi tare da kallon gilashin wayarta tana tunani Tabbas Alh.malami sambo akwai mutunci Kuma ya rike su da amana tamkar jinin Abba." "Bayan mun Gama lectures din mu duka direct office din Yaya Saddiq na nufa..."Sai dai akulle yake Bayan Naga motarsa a parking place na admin din..."Fitowa nayi tare da jinginawa ajikin motarsa Bayan mintuna sai Gashi Yana sauri tace Kai shige mutafi..." "Duk da Kasancewar bana Jin dadin jikina tamkar Mai zazzabi Duk jikina yayi zafi!"Ga wata fargaba da ta darsu araina!"Bai hanani hango bacin Rai a fuskar Yaya Saddiq ba!"Da alama kamar an tabou shi a office din da yafitou..." "Gudun fitar hankali yake shararawa a titi kamar Mai Shirin tashi sama ko kallon Inda nake baiyi ba!"Sai Nan da Nan yaja tsaki tare da duka sitarin motar...."Na tsorata matuka domin ban taba ganin shi a irin Wannan yanayin ba!"Tsorona da fargaba ya ninkou!!"Domin kamar muyi karou a hanya Nan take cikina ya shiga kugi abukace nake da shiga bayi Shiyasa na kosa na ganni agida..."Addu'oin tsari nake jerowa Allah ya sauke mu lafiya Dan Tuni kwallah yafara min zuba saboda tashin hankali...."Ajiyar zuciya nayi alokacin da na ga mun shigo layin gida tare da fadin Alhamdulillah...." "Waigowa yayi ya kalleni...bansani Ashe zancen zucine ya bayyana...Dai dai gidan yayi parking yace ke matsoraciya fice Dan Allah ki dauki ledojin nan ki shige da su Ni zan tafi masallaci...." "To nace jikina na rawa saboda zawayi da ya matse Ni da kyar na kwashe kayan da jikata na nufi gidan...shi Kuma juya akalar motarsa yayi izuwa hanyar masallacin da ke Cikin Estate din...." 👍🏼Share👍🏼 comments👍🏼My fans *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 [2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 20* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ _Wannan safin kyauta ce,mallakin ku ne my people's😍_ _Zulaihat Abadany_ _Maimuna Ladan_ _Ummu Alisha_ _Momy Jega(Zeeman)_ _Mummy Yusuf(Fattyh)_ _Hindou Alqali_ _Aysha Bagudu_ _Ayush Iliyas_ _Nabeeha Ameenu(Sareena)_ _'Yar Father_ _'Yar Hussai_ _Hadiza Yusuf Buzu_ _Duk ina mika saqon gaisuwata agareku nagode irin sosain nan_❤ *Jinjina da gaisuwarki daban ce Babbar Yaya mai kamar Oummah😍 Allah yaqarou arziki da nisan kwana YAYA RALEEYAH MUHAMMAD AMINU,Allah yayi miki jagora ya zamou gata agareki Amin...Muna yinki Over*👍🏼👍🏼👍🏼 ______________________________________ "Alh.Malami Sambo da mom ne zaune afalon tare da Jawad da Kuma aminin Alh.malamin,Suna tattauna akan zanjen neman auren Jawad..."Mom kudade ta BAIWA Alhajin Amma fafur yaki karba tare da daukarwa Jawad alkawarin zai zame Masa uba kamar Marigayi Husamaddin..."Alh.malami sambo ya Kara da cewa komai shi zaiyi na auren..." "Mom da Jawad sai GODIYA suke Masa..." "Ya ce ku daina GODIYA iyalan marigayi sun wuce GODIYA a ko'ina ba girmanku bane domin arziki da kansa jinjinawa Humaddin yake Sannan Alheransa NE ke bibiyar ku in shaa Allah Bazaku taba wulaqanta ba Aduniya domin marigayi mitum NE Kuma ya dasa alherai Aduniya "Wasu Hawaye masu zafi!"suka zubowa momy habar gyalenta tasa ta share!"Tace hakane malami mun gode DUK da hakan da ka riqe Amana.." "Jawad ma Idonsa ya kada yayi jajur!"Saboda tuna baya Tabbas sun Rasa wani bangare na rayuwar su sai dai Hakuri!" "Alh.malami yace"yanzu kubamu address din gidan gobe sai muje...." "Nan Jawad yayi musu gamsasshen bayani har suka fahimci komai kana sukayi Sallama da mom suka wuce...Jawad har parking place yayi masu rakiya cike da girmamawa...." "Hannu Alh.sambo yaba shi sukayi musabaha..."Ya ce a gaskiya Muhammad Jawad naji dadin ganin irin sauyin da kasamu arayuwa inama ace marigayi zai dawo duniya yaga yadda nasa ya zamo kamili Mai cikar kima dA haibs kamar yake buri...."Ko kaifa jawad baka ga sauyi arayuwarka ba!?"Rayuwarka ta baya Bata Dace da Kai ba kuma batada amfani...Amma shigar mutunci da Kamala,sanin girman manya da mutunta su tare da amfani da ilimin nan biyu shine gishirin zaman duniya Duk Wanda ya ganka zai San kana da hankali da ayanzu.....Allah yayi maka Albarka ya shiryar suwa...." "Amin...Abba nagode...Jawad yace Cikin sanyi da ladabi..." "Nan SUKA wuce shima sashen sa ya nufa cike da mamakin zantukan Abba malami..."Ya Rasa ma Taya zai fassara Wannan shin wa'azi ne ko Jan kunne....Tsaki yayi tare da haye gadonsa wayarsa ya dauko Yana Kiran Nadiya Bata zuwa akarshe Baba Balarabe ya Kira tare da shaida Masa gobe magabatan sa zasu zo Inda yake..." "Malam Balarabe cike da Jin Dadi yace to Allah ya kawo su lafiya ya Sanya Alheri...Nan SUKA taba hirar su Sannan sukai Sallama..." "Sauya Kiran yayi zuwa layin abokinsaa saif...tare da labarta Masa Duk yadda sukayi da su Abba malami sambo..." "Shima Saif din fatan samun nasara yayi masu...tare da yiwa Jawad Albishir din aikin M Bala na shehu shagari ya kammala dazu ya Kira shi ya tabbatar Masa da komai ya daidaita..." "Dadi Jawad yaji SOSAI tare da dariyar mugunta yace aikin mu Yana kyau kace an kusa cimma wurin Baba.." "Tabbas Nawan an kusa Mata shakar dambu..Inji Saif Yana kyalkyala dariya..."Fira suka dinga yi Jawad har da labartawa Saif nasihar aminin mahaifinsa...." "Saif yace Basu San tubar mazuru CE kayi ba!" "Jawad yace Duk da hakan nagane zama mutumen kirki wani Babban jigone arayuwa komai iliminka da kudinka da kuma wayewarka idan bakada tarbiyya Kuma Bata wadaci Rayuwarka ba saif Ashe ba ZA'A daraja ka ba!"A gaskiya idan nayi watsi da komai Banda halin kirki da na koya ayanzu.."Domin shine burin iyayenah nazamo nagari "To Jawad Allah yasa MUDACE halayen sunyi karamci arayuwar mu..."Saboda bama koyon su Koda an koyarda MU..."Inji Saif.." "Jawad yace na Kira mutuniyar wayarta akashe.." "Wa Kenan..."Saif ya tambaya "Matar faansa!!"Jawad ya bashi Amsa..." "Dariya Saif yayi yace to may be batada caji!" "Ita tasani...." "Kodai me sonta yasani ba.!" "Tsaki jawad yayi tare da datse Kiran yace banza night!!!" "Jifa yayi da wayar gefen gado...cike da haushin zancen saif Nan wani Sabon takaicin Nadiya yadawo Masa sabou..." "Bansan yadda akayi sai gani na nayi kwance a gadon asibiti....Kallo nabi Dakin da shi..."Tare da Salati ahankali na dubi gabana Yaya Saddiq NE,A tsaye ya hade hannuwa Yana kallona agefena yaran NE tsaye suna Hawaye!"Wasu Hawaye NE suka dinga min zuba ahankali na tunano abubuwan da suka faru da Ni!!!" "Hannuna na motsa tare da yiwa Yaran Alamar su zo...Nan suka matso kusa Dani...Da yake hannuna daya ansa min drip!"Da dayan na dinga share masu Hawaye..." "Anty Naddy sannu...mufida Tace." "Kallonta kawai nake domin ko magana bana iyawa!saboda axabar zafin da nake ji akaina Wanda aka nadiye da bandeji!!" "Mufeed yace Anty Naddy kiyi Hakuri ki yafewa momy da su Anty Wallahi sun ci amanarki...." "Da sauri na rufe Masa baki tare da Girgiza Masa Kai Ina Hawaye...Nan na Rungumesu muna ta Kuka..." "Tausayin yarinyar ya Sanya shi zubda Hawaye!!"Kallon su Yake cike da tausayin su day Kauna!"A zuciyarsa Yana Allah wadai da halayen Jalila!"Sam Bata cancanci Zama uwa ba!"wacce zata iya kula da yaran "Dr.ne ya shigo yace"Saddiq ta farfadou NE!" "Eh...Dr.ta farfadou.." "Hannu Dr.ya bashi yace congrts Saddiq...Anyi nasara gaskiya saboda dogon Suma NE tayi." "Wurina Dr.yazou yace sannu..." "Da kyar na kada Kaina Alamar Amsawa..." "Kallona yayi na mintoci tare da janye yaran jikina...yace kingane su!?" "Nan ma Banyi magana ba!"sai Alamar da nayi Masa..." "Kallon Yaya Saddiq yayi..yace"Ina ga ba wata damuwa Saddiq kamar zafin kanne Yake hanata magana..."Abin yazou da sauki tana gane komai...saboda ta Bugu SOSAI akai..."Inji Dr.yana murmushi." "Masha Allah..."Dr.mun gode.." "Yanzu muje office Sai na rubuta magani...Ina ga Nan zuwa gobe ZA'A iya sallamar KU..." "Ok!Yaya Saddiq yace tare da bin Bayan Dr.." "Har ya Kai KOFA ya dawo tare da dubina yace sannu Nadiya!"Ki Hakuri kinji..." "Mufeed KU jirani asayowa Anty magani...Banda surutu kunji ko..." "To Abba sukace Sannan ya fita...su Kuma dawowa sukayi kan gadon suka zauna sunata faman jera min sannu...." "NIKAM na kosa nabar asibitin Tuni na kudurta abinda zai fiddani..."Domin gujewa halaka da haukar Anty Jalila...A hankali Hawayen ke kwaranyo min a fuska...Wani Abu nakeji idan na Tuni kazafin da tayimin tare da mugun alkaba'i da tayi min...Allah ya saka min nace Wanda ya fitou fili..." "Ameen Anty naji yaran sunce....Nan na kama bakina nasa Masa linzami..." "Haba Anty talatu Ni Wallahi ba Inda nayi nadama...Akan Wannan Dan Abu kima daina Wannan zancen Dan Allah." "Jalila kinsan kaddara ake gudu!"Anty talatu tace "Kaddara da kanta tsorona take..."Inji Jalila "Rasheeda ta karbe Nima fa Da farko na tsorata!"Amma yanzu nasan da sauki domin idan anji shiru lafiya CE!!" "Tsaki Jalila tayi Tace kamar da ba jinin umma ba!Naga yanzu tsorou ya shiga jininku Ni Wallahi ko ajikina Allah yasa ta mutu! sai me!?" "Anty talatu mayafinta ta yafa kana Tace"Allah ya sauwaqa sai dai kinji jawabin umma ko...Koda wasa karki raga Masa ki bude Masa wuta Kuma itada gidan Nan sai a mafarki..." "Duk na hadda CE komai Anty...karku damu Zanyi maganin komai!" "Allah yasa hakan..."Inji Anty talatu.." "Amin... Jalila Tace..." "Nan tayi musu rakiya har kofar falon Sannan ta dawo...wayarta da dauka tare da Kiran layin mansura..." "Ba da jimawa ta Daga wayar da Sallama tare da gaida Jalila cike da ladabi kamar tana agaban ta..." "Amsawa tayi tare da cewa mansura ya makaranta ya karatu!?" "Lafiya qlaw Anty Jalila...Mansura Tace ya Hakuri!?" "Hmnnnnn....Bari kedai nafara rage zafi!"Nan ta labartawa mansura komai harda karin Dan gishiri..."Cike da Jin dadi da gadara..." "Mansura kaam kamar an gafarta Mata aranta"A fili ko Ta ce A gaskiya Jalila banji Dadi Duk Naddy itace ta ci amanarki Amma na tausaya Mata!" "Haba Mansura karki sa nayi Dana sanin kiranki Mana!!!" "Anty Jalila banso ki daketa!saboda gudun abinda zai biyo baya.." ''kamar me Kenan mansura!?" "Anty Ina gudun matakin da Yaya Saddiq zai daukar maki...kinsan fa zai iya cewa dole anan zata zauna..." "Katseta Jalila tayi tare da cewa"Mansura Saddiq na Sona bazai taba iya rabuwa Dani ba!"Daman na bashi zabi koni ko ita!"Idan ya dawo zan Masa barazanar ya sakeni nasan dole ya korata hostel domin bazai iya aikata hakan ba!" "Cap di jaam...mansura Tace azuciyarta cike da haushi da takaicin Jalila...Yake tayi da cizon yatsa kamar tana gaban Jalila...Tace to Anty Jalila Allah ya gyara..." "Ameen...Daman nace gobe wanne time zamuje gidan malamin...?"Anty Jalila ta tambaya" "Murmushi tayi tare da hararar wayar Tace"Da misalin Sha biyu na Rana...sai mu hadou Nan makaranta saimu wuce..."Inji mansura." "To sai nazo mansura NAGODE..." "Ba komai yiwa Kaine Anty.." "Nan sukayi Sallama kowannen su da irin abinda Yake cin ransa, Yake Kuma kullawa da kuncewa...."Musamman mansura da takaicin Jalila ya cikata...." "Tun fitar Yaya Saddiq Mufeeda da Mufeed ke ta faman jera min sannu cike da damuwa..."Har Abbansu ya dawo hannunsa rike da Ledoji..." "Kujerar da ke gefena ta janyo ta zAuna tare da bude ledojin fresh milk CE da kayan fruits..." "Tea ya hada min Mai zafyh nasha Sannan ya bani magani nasha..."Fresh milk ya Miko min...Duk da da kyar nasha maganin da tea ba Dan Ina so ba!"Hakuri nayi na karba Ina washa da kwallin a Hannu na..."Kayan fruits din yaba yaran da fresh milk din saboda suna Jin yunwa..." "Sannu Yaya Saddiq ya dinga jera min tare da tambaya to ya jikina!?"Me nake Ji!? "Amsa na bashi da sauki..." "Baki ya Cigaba da bani tare da rokona alfarmar Kar na sanarda su Baba meke faruwa ko da awaya NE!Nayi Hakuri zai dauki mataki Mai kyau Akan Anty Jalila..." "A sanyaye nace Yaya ba komai in shaa Allah bazasu ji ba!" "Kallona yayi tamkar Bai Saba ganina ba!"tare da sauke Numfashi yace nagode kanwata Ina alfahari da ke!" "Juyawa yayi awurin yaran SA yace"Mufeed muje masallacin asibiti mu kwana...Ke kuma Mufeeda ki kwanta awancen gadon..." "Nan Yaya Saddiq yayi Sallama da mu ya wuce...Ni da Mufeeda Cigaba mukayi da zama har bacci ya dauketa...Nikam tunani duniya ya dameni Ni Nadiya!!" "Yadda Anty Jalila ta rufe Ido ta ci mutuncina harda kirana karuwa!!"Kalma Mafi Muni!!" "Hawaye!ya dinga min zuba shin waye ya sanarda ita Yaya Saddiq so na Yake!? "Wace alama tagani da ke nuna hakan!?" "Meyasa zata yanke hukunci Akan abinda batada Tabbas!? "Meyasa Anty Jalila zaki mana kazafi!?" "Meyasa!!!!" "Kuka nake rusawa Babu Mai bani Hakuri..Nan take Kaina ya dauki zafi!"Ciwona ya Taso....jikina sai rawa Yake Ina kakkarwa...."Nurse Lubna CE ta shigo ta sameni awannan halin Tuni tabani agajin gaggawa tare da min allurai..."Daga Nan komai ya lafa bacci ya kwasheni..." "Akai akai Nurse tana zagayo Ni tana dubani Ina bacci normal da Yake asibitin akwai TSAROU nurses NE da kansu ke jinyar patient DINSU..." *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 21* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM._ _Sadaukarwa gareku manyan gobe😍_ _Mufeeda, Jiddartyh ,Zarah, Ikhram, Minal,Teemah, Juwairiyyah, Umairah,Khadija, Afra, Ramlat, Iman,da kuma Afnan Allah ya raya min ku Ameen😍_ ______________________________________ "Bakin ciki da b'acin ran da ta kwanta da shi adaren jiya!"Da shi ta wayi gari!"Tabbas Sadiq ya Bata mamaki Kuma ya wulakanta ta!"Ace saboda Nadiya zai kwana wani wurin ba agida ba!"Da sunan Yana garin sokoto!"Dan Karin tasko da wulaqanci harma da yaranta..."Tabbas masifar da ta tanada Masa sunada yawa..." "Ko karyawa ba tayi ba!"Da misalin 11:30 na safe ta shirya Akan sauri da kyar ta had'a tea da kwai ta Dan tsakura saboda yunwa, Nan tabar kayan ko'ina a ya mutse!"Ta na fita.."Kai tsaye Dan fodio university ta nufa...."Wuri tasamu ta zAuna kana ta dannawa mansura Kira..." "Mansura ta Daga wayar Nan Jalila ta shaida Mata inda take tazo ta sameta tana jiranta..." "Duk da tashinta kenan Daga bacci amsawa Anty Jalila tayi da to tana zuwa yanxun..Sannan ta ajiye wayar..." "A gurguje ta wanke jikanta tare da Saba tufafi tsaf ta fente fuskarta aka zuba uban turare aka fito..."A zuciyata nace Wannan tsaka tsamin...kamar kawalliya Uwany lol😄 "Cike da yanga take Tafiya har ta karaso a inda Anty Jalila ta kwatanta Mata..."Bayan ta qarasou gaisawa sukayi sannan suka nufi titi domin samun taxi da zata sauke su Mabera Iddi...." "Tunda safiya ta waye Yaya Saddiq ya hada Mana tea Ni da yaran mu ka Sha tare da bani magani na..." "Bada jimawa ba Dr.yazo ya dubani Sarai tare da min wani Sabon dressing akai..."Ba laifi nasamu sauki Daga Nan Sallama ya bamu da zummar Bayan kwana biyu mudawo a kwance daurin...." "GODIYA SOSAI Yaya Saddiq yayi Masa tare da bashi tabbacin ZAMU dawo in shaa Allah..." "Nima muryata a sanyaye nace mun gode Dr. "Dariya yayi cike da kulawa yace"Yawwa ma patient ay yiwa Kaine..." "Sunkuyar da Kaina nayi saboda yadda Dr.kai kafeni..da Idonsa masu min kwarjini..." "Yaya Saddiq yan tarkacen kayan yafara hadawa Sannan yace mu tashi mu wuce..." "Da taimakon Dr.Mu'ab muka Kai kayan Mota...Shi da kansa ya rufe min Mota yayin da na shiga tare da cewa''My Patient sai nakawo ziyara an juma ko Yana kallona tare da jefa min murmushi" "Nima murmushi na mayar masa..."Yaya Saddiq baice damu komai ba!!"Sai dai sauyin fuskarsa da ya canja..." Daga Nan motar mu ta tashi Yana Mana Bye su Mufeeda na mayar Masa cike da kewarsa domin Dr.mutum ne Mai mutunci da son mutanen..." "Tsaye yayi Yana Cigaba da Daga Mana hannu..."Har muka wuce..." "Nurse Nussyh...Da ke gefe tana kallon Duk abinda ake ta cika da haushi...sai cizon baki take tana surutai ita daya.."Har suka wuce Bata dawo a hayyacinta ba!"Tunani take wata da wattani tana tufka Amma acikin kwana daya Nadiya zata warware..."Tirkashi!...Dole ne tayi maganin abin domin ta dawo da abinda ta Dade tana kiwo har ya gawurta ahannunta...."Wasu Hawaye suka zubo Mata...Tace Dan Allah Dr. Mus'ab karkayi min Haka Ina sonka Ina kaunarka Amma Daga ganin wata banza kakeson canja sheqa!"A gaskiya Bazata taba sabuwa ba!" "Maganar Dr.Mu'ab CE tadawo da Nusaiba a hayyacinta yace yadai "Nussy...." "A zabure tayi saurin goge hawayenta tare da murmushi Tace normal..." "Dr...mus'ab yace"Ok,Muje Daga ciki..." "Bayansa tabi suka shige Daga ciki..." "Office dinsa ya nufa Kai tsaye binsa tati...tana wani kaudi tace....Lafiya Dr.naga kamar Bakaji dadin tafiyar su abokinka Mufeed bane!?" "Ba su Mufeed bane banji dadin tafiyar su my patient Nadiya tabani tausayi..." "A zabure ta tashi tana huci Tace Dr.ka Gaya min gaskiya Kodai sonta kake!?"Nusy tace cike da tsiwa..." "Kallonta yayi sororo...domin idan da abinda ya tsana a halayenta Bai wuce tsiya da rashin Hakuri ba!" "Tace"Shiyasa Naga kawani laqabe Mata ita Kuna shegia munafuka sai wani sangarta da iyayi take...Wallahi Dana San kafada sonta da nayi maganin ta KAFIN tabar asibitin Nan.... " "Hmnnnnn...Nusy kenan nagode Allah da yasa Kika gane nine nakamu da sonta ba itace ta laqabe min ba da nacin soyayyar ta Kinga kenan ta cika macce Mai aji wacce batasan ta cusa soyyayar ta azuciyar namiji ba...ko da karfi...."Inji mus'ab Yana kallonta ba yabo ba fallasa" "DakAta....''Mus'ab ba sai kayi min fade ba!"saboda Allah ya hadani da aikin sonka...Wallahi da zan iya ciresa da na debe ko Dan wulaqanci ka!!!"Nussyh Tace cike da takaichi!!!" "Kinsan da hakan har zaki ga laifina saboda Nima na hadou da cutar son Nadiya!?"Dukkan mu Hakuri zamuyi muga abinda Allah zaiyi!"Amma kisani Ni ban wulaqanta ki ba Nussy rashin kamun kanki da tsiwa ne bana so!"Ina son macce Mai kamun Kai da nutsuwa wacce Zaman mintina da ita za'a fahimci kamun Kai ce.." "Kana nufin Ni ban cancanta ba!?" Nussy Tace tana zubda Hawaye!" "Kina da Halaye masu kyau saboda an baki !"Sai dai bakya nunawa akoda yaushe....Dr.mus'ab yace tare da daukar wayar SA ya fita Daga office din ransa ba Dadi..." "Nurse Nussyh nan ta had'a Kanta da table din office din tana rusa kukan bakin ciki!!!Tare da Dana sanin son mus'ab arayuwarta domin ya Gaya Mata abinda ke ransa ayau saboda kawai ta tabou Nadiya!!!"To wannan Wacece ita!?"Dole ne ta nemo bayanai akanta da halayanta, Kai Koma da kalamai ne tayi nasarar burge Dr.nan take zata sani domin ta kwaikwayon su itama ya sota!" "Taxi na ajiye su agefen titi suka tsalka izuwa wani lungu Tafiya suke suna tsallake gotoci har suka Isa zauren...." "Mansura Tace Yawwa Anty Jalila Kinga Nan NE..."Amma Ina zuwa bara nagayawa Mallam mun karaso..." "Badamuwa mansura...Inji Anty Jalila..." "Zauren ta kusa kanta Nan sukayi magana da Mallam harda shewa Sannan ta fito Tace"Anty Jalila Yace ki shigo..." "Jiki na mazari Jalila ta shiga zauren wuri tasamu ta zAuna Cikin karamar murya ta gaida malam zakiru..." "Amsawa yayi tare da maraba da zuwan na Jalila.." "Nan mansura ta lakwashe murya cike da kissa Tace"Mallam Wannan itace yayata Kuma Yar uwata da nayi maka bayani akanta da Kuma Matsalar ta...Asirin da na rikawo kawata Naddy mukazo awarware tare da Bata taimako Akan mijin mata...." "Mallam zakari Jan carbi Yake Yana wani muzuru da ido Yana kada Kai...Yace to agaskiya taimakonku Zanyi bana Aiki na warware Amma saboda kinta rokona mansura zan MUKU Alfarma...Hankada tabarmar kaba da ke shimfide adakin yayi tare da dauko garin magani ya mikawa Jalila..." "Wata kwarya ya dauko acikinta ya fitou da kwalbar turare ya Mika Mata..." "Yace Kinga garin Nan ki dinga turaren wuta da shi...Sannan Wannan na ruwan ki dinga sakawa ajikin ki da yardar Allah ba dai Wannan yarinyar ba!"Zai tsaneta!zai daina sonta!" "Washe baki Anty Jalila tayi jiki na rawa ta amsa Tace nagode Mallam..." "Mansura ko kashewa Mallam Ido tayi sukayi murmushi Tace yayi Mallam Aiki dai ya kammala Allah yasa muga sauyi da haske!"Magana tabi hanya...Mungode..." "Dariya yayi yace"karkiji komai mansura kamar gobe ne..." "Jalila Tace gaskiya Mallam ka taimakeni ka taimaki rayuwata Allah yaqarou sani..." "Ameen...Mallam zakiru yace...."Nan SUKA tashi....Anty Jalila kudi ta dauko ta aza Masa asaman kwaryarsa...." "GODIYA yayi Mata Sannan suka fita...Har sun fara Tafiya mansura Tace lah!"Anty Jalila Allah ya gyara Kinga nabar wayana azauren Mallam Bari nayi sauri na dauko..." "Anty Jalila.... Dariya tayi domin tana Cikin farin ciki Tace Lalle Mansura kin cika sakarya!to maza jeki ki dauko na tare Mana adaidaita..." "Wucewa Anty Jalila tayi bakin titin...ita Kuna mansura ta wuce zauren Mallam..."Daman karya takeyi wayarta na Jikarta ta sata a silent..." "Dawowa tayi da sauri ta zAuna agaban"Mallam tace injin komai ya kammala!?..." "Kwarai kuwa sai dai ki jira ki ga Aiki da cikawa...Ga Wannan ki tabbata ki Sanya shi atufafinki kije inda yake da tufafin ajikin ki...." "Amsa mansura tayi tana murna...yayi kyau Mallam nagode ai na fahimci signal dinka Shiyasa nadawo amsar nawa tsarabar....tana dariya... " "A inda Anty Jalila take tsaye da Mai Napep ta karasa da sauri tana dadin bakinta har suka shiga suka wuce kowanne murna fal aransa...." ***** "A wajen gidan suke zaune karkashin bishiyar cediya..."Suna tattaunawa akan abinda ke tafe da su...." "Mallam Balarabe yace"To agaskiya ba zan iya amsar Auren Nadiyatu Ni kadai ba."Sai dai ku bari na Kira liman da makocina ayi agabansu da Kuma abokina Mallam musa...Domin sune Yan UWANA a wannan garin bani da kowa sai su...."Alhaji malami Gyaran Murya ya yi yace"Ah bakomai a kirasu,Nan ya kirasu a waya ba dadewa ba!"Sai ga liman ya qaraso Daga bisani Mallam Yusuf da Mallam musa su ka zo...Bayan an gaisa, Nan liman ya bude taro da addu'a. Sannan malami sambo ya KOMA yin jawabi Akan abinda ke tafe da su wato nemawa dansa Jawad Auren Nadiya..." "Ba tare da wata matsala ba!"Akayi magana suka biya kudin aure naira dubu ashirin kacal kamar yadda liman ya bukata..."Sunyi zancen sadaki sai dai Malam Balarabe baiyi na'am ba!"A cewarsa yafiso sai an saka Ranar aure Sannan a karbi sadaki saboda yanzu yarinya karatu take...Kuma ba kyau yawo da sadaki aka"Sun dai amshi kudin goron baikoh NE,saboda atsayar Mata da mijin..." "Su Alhaji malami sambo da Haji shehu sun gamsu da bayanin malam Balarabe sosai,Nan aka kammala komai suka wuce Cikin Aminchi..."Suna yabawa da halin dattako na dattijawan, Tabbas yarinyar ta samu cikakkiyar kulawa....idAn dai hakan ne hakika Jawad yayi Dace..." "Shima Mallam Balarabe GODIYA yayi ma abokansa tare da fatan alkhari... "Cikin gidan ya shiga Yana shaidawa Innarei dukkan abinda ya faru...." "Itama murna tayi da Sanya Alheri...." "Kudin ya Bata ta ajiye da zummar Ranar kasuwa zai sayo goro arabawa Yan uwa da Abokan arziki...ita Kuma Nadiyatu ta sayi alawa ta rabawa kawayenta idan tadawo...." "Da Haka suka cigaba da tattaunawa akarshe fatan Alheri sukayiwa yaran nasu..." ************** "Hajiya khaltumi ce hakimce a kayataccen falonta tana kallon AREWA 24.. sai ga Kiran waya ko da ta Duba Alh.malami sambo NE....Da fara'ah ta amsa Kiran..." "Bayan sun gaisa ne Alhaji malami sambo ke sanarda ita dukkan abinda ya farua tsakanin da iyayen yarinyar,ya kuma yaba da halayar mahaifinta...." "Hajiya khaltumi taji Dadi matuka GODIYA tayiwa Alhajin tare da fatan Alheri Daga Nan Sallama sukayi da shi ta Kara godewa.." "Da murna takira wayar Jawad tana shaida Masa yau Ranar Murna CE Anyi baikonsa da Nadiya..." " ya nuna Jin dadinsa a fili sai dai a ransa yaji wani haushi ya Kama shi!tamkar anyi Masa Albishir da mutuwa..."Yanzu amaimakon ace zai fara auren so arayuwarsa da wacce yake so Amma Wai da makiyiyarsa zai fara kafa tarihin aure!"Kuma wacce yafi tsana Aduniya!"....Hmnnn Anya Ni Jawad ban tafka kuskure ba!!!?Ta Ina hakan zata faru!?"Karfa ka manta da kalmar da ta kiraka saboda ta rainaka!"Dole ka koyarda ita darasi arayuwarta,Dole ta Sha wuya!Hmnnnn ka nuna Mata ta tafka Babban kuskure! Zancen zucin ya dinga yi tuni ya manta da waya yakeyi......." "mom ta fahimci ita kadai ke surutunta....Jawad watakil ya ajiye wayar,Shiyasa not Kira sunansa...Amsawa yayi Nan ta kammala duk zantukan ta da murnarta... akarshe datse Kiran tayi da zummar sai yadawo suyi celebration..."Shi Kam wani Abu yaji ratsa jikinsa,"Wasu Hawaye suka zubou masa wanda baisan ko na menene ba." ******* "Tun da muka shigo unguwar ido na suka kawo kwallah!"Fargabata ta karou!"Ina ji ajikina Babu alheri a Dawowata gidan, sai dai ba yadda Zanyi banajin zan iya Girgizawa umurninsa..." "Duk da ya lura da irin damuwar da na shiga baisa shi ya nuna min komai ba!"A fuska ko kuma ayanayin sa..." "A kofar get din gidan muka tsaya Mai gadi ya bude get din muka shige!" "A hankali ya kunna kan hancin motarsa acikin gidan...Bai tsaya a mazauninta ba saitin kofar falon yabi Sannan ya kashe injin motar..."Fitowa mukayi dukkan mu...." "Mai gadi barka dawowa Yake Mana tare da min ya jiki!?" "Amsa Masa Yaya Saddiq din yayi.."Nima da sauki nace Masa..."Ya wuce bakin aikinsa..." "Kayan da ke motar Yaya da su Mufeeda suka kwashe..."Tsaye nayi Ina rarraba Ido...Har sun Kai KOFA ya juyo inda yabar ni atsayen Ina Nan...." "Ke anan din Zaki zauna!?" Yaya Saddiq yace da Dan tsawa!" "Da sanyi nake Tafiya Ina bin bayansu har muka karasa bakin kofar, mukulli yasa ya bude...." " _Bismillahi Tawakaltu Alallahi_ Na Fadi Sannan na shiga falon...." "Yaran shiga sukayi sai raba ido suke ko zasu ga momyn su Amma shiru...sai kawai suka basar domin bawani sa su ajiki take ba..bare su damu...wasan su suka cigaba da yi afalon..." "Yaya Saddiq Kichen ya fad'a Babu komai aciki sai dai ya ga kayan da akayi breakfast da su ajiye awurin....A ransa mamaki yake wato Jalila tana gidan!?"To Ina ta tafi !?"Da tunanin ya daura sanwar jallof na taliya..." "Ko da ya dawo falon a inda nake zaune kasa atakure Nan ya sameni...Tausayi na bashi cike da rarrashi yace Nadiya Kuka fah!?"Ko baki hakura bane!?" "Sai alokacin na fahimci kukan nake, hawayena na share Sannan nace Nidai Yaya Dan Allah ka mayarda Ni hostel da Zama, nagode da kokarin...ka saboda hankalina zaifi kwanciya acan......."Katseni yayi "Yace bana son shirmen banza!"Kece Zaki Gaya min yadda Zanyi!!!?...ki tashi kije kiyi wanka ki sauya kayan jikinki idan kin kammala ki fito ki ci abinci kisha magani sauran idan kinje ki Cigaba da kukan ko kuma ki Bari har sai na Aiko su kifiton!...."Yaya Saddiq ya idar da maganar fuskar sa adaure..." "A hankali na tashi nabar falon Ina Kukan xuci!!!"Dakin mu na nufa...Toilet na shiga tare da hadawa Kaina ruwan dumi nafara wanka..." "Su Mufeed da Mufeeda ya tasa agaba sai toilet din bedroom DINSU..." wanka yayi musu tare da sauya masu Kaya...."ya gyara bedroom din da ke hargitse ya kuma wanke toilet din fes.. Sannan NE shima ya fad'a...suna fitowa tsaf acikin shiga Mai kyau...Daning area suka nufa har Ni din dake zaune falo Ina jiran fitowar su....''Yaya Saddiq ne ya zuba kowa abincin"A hankali kowa ke cin abincinsa musamman yaran sai da suka cinye tatas harda Kari...Domin rabon su da abincin kirki tun kafin muje asibitin..."Nima na ci saboda girkin yayi Dadi da Dan yaji ga marar lafiya da son Dan barkono😋ba Dan Kar nace Yaya Saddiq ya karamin ba masoyana suyi min Dariya,Mai ciwo da cin tsiya _Kamar SHATOU Dikko acicih_ Da nace akarou min...Amma Hakuri Zanyi nayi na masu ciwon🤣 ************ "Ana sauke mansura a makarantar su...ita Kuma Gidansu aka nufa da ita..."Nan l Bayan ta Sha ruwa ta huta ta labartawa Mama Atika(Hajiyar su)Labarin daga inda take da maganin da mallamin ya Bata.."Jinjinawa Jalila mama Atika tayi harda Sanya Mata Albarka tare da fatan Samun Nasara Aikin yaci..."(Hattara iyaye a dinga Sara Ana duba bakin gatari,kuso yaranku a lokacin da duniya takisu, hakan ku kisu a lokacin da taso so) "Cike da Jin Dadi ta tafa da ita tana nuna Mata maganin...Tace Ina ALFAHARI da ke Jalila hakika Kece Kika gajeni...Saboda kina da zuciyar daukarwa kanki fansa..Basai an TAIMAKA maki ba!"Nima Nan ba zAma Zanyi ba!"Zan daura Daga inda Kika tsaya.... "Haka akeso Jalila hakika kin biyani goron haihuwarki da Nayi Allah yasa kifi hakan,." "Ameen...Hajiyata...Jalila Tace cike da Jin Dadi suka tafe da Hajiyar..."Tana Mata bayanin duka garukan da malam zakiru ya Bata.." "Anty Talatu da ke kwance Akan gado tana Jin su...sai dai batace masu kanzil ba!"Saboda ta lura idan har Hajiya taga Jalila agidan yanzu zata sauya masu tana yabon Jalilar...domin kawai tana damka Mata yan kudade...."Lumshe Ido tayi tana tunano ita ma alokacin da take zaune agidan nata mijin yadda Hajiyar su ke nuna Mata so...Gashi tayi nasarar kashe mata auren yanzu ta dawo gida zawarci sai wulaqanci take mata da sauran kannanta..."Hmnnnnn rayuwa kenan...wasu Hawaye suka dinga zubowa Anty Talatu..." "Can sai ga Ga Rasheeda wato Autar gidan...Da fara'ah Tace Anty Jalila saukar yaushe..."Da Dan gyalenta a Hannu.." "Tace yanzu na shigo na tambayeki ai,Hajiya Tace kina makota sarkin yawo!"Baki dai barin halinki uwar gulma!''..Ita Yaya Babba Naga sai bacci takeyi.." Jalila Tace tare da nuna Anty Talatun da baki tana Dariya..." "Haba...Anty jalila!Nafa rage gulmar nan..."Nifa banason cin fuska duka yanzu gidaje shidda ko bakwai ne nake shiga kaf layin nan....Hararen wurin gadon Rasheeda tayi tare da tsaki Tace aikinta kenan ita Kuma Wannan Daga bacci sai ci!!"Ko ba Anty Tala ba uhmnnnn!" "Hajiyar su Hannu ta baiwa Rasheeda suka tafe suna dariya"Tace auta Wannan bakin naki ko!!"Sai ta jiki taci mutuncinki, Ina gefe kin san Sarai kunnen ji ne da ita..."Yanzu hakan kwantou ake Mana Ana daukar rahoto.." "Hakane kaam...Amma Wallahi Hajiyata. sai dai mu ci mutuncin juna Ni da ita ...rasheeda Tace tana murgudar baki...." "Duk Anty Tala...na jin su da Kuma SAURAREN su Amma sai ta lafe domin idan ta tashi ta samu damar cin mutuncin Rasheeda..."Saboda ko ita ma ba baya ba!wurin rashin mutuncin da masifa,yanzu ne Kura tayi lafiya.." "Tana Jin su aka bud'e sabuwar tashar zagin Nadiya da Saddiq, a gefe sai yabon mansura ake da irin taimakon da tayi masu tare da yabawa da halayenta..."A karshe Hajiya da Rasheeda shawarwari suka baiwa Jalila tare da koyar da ita wani babin rashin mutunci...."Sannan sukace ta tafi gidanta kawai ba wani abinda zai faru. zuciyarta fal da murna ta fito da karfin gwuiwa har ta isa gidan..Akan murna ko canji Bata tsaya ta karba ba awurin mai Napep Tace ya wuce kawai ta bar Masa...." _Hattara iyaye!!!....A gaskiya muna sakaci da izgili!"A yau...,"Tabbas akwai iyaye masu rayuwa irin ta mama Atika...Mu sani fa, Wannan ba rayuwa bace!" Mai Wannan hali na ko in kula Akan yara Kisani watarana zakayi Kuka da idonki biyu!😭" Wai ace lalacewar ta kai yaronka ma alfahari kake da shi idan ya iya aikata rashin mutunci,Da Rashin kunya! ko Kuma wasu halaye na banza!🤔?"Sai dai Kuma ba abin mamaki ba NE,Domin kuwa uwa Tagari kawai CE zata iya haifo d'a nagari,Kuma ita *TARBIYYA* Daga gida ake tasowa da ita,Babban tushe CE,Kuma tubali CE,Wanda tun asali ake samunta...Allah ya shirya mana Ameen_ *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 22* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ _KYAUTHAH CE GARE KU MANYAN WRITERS INAJI DA KU ALLAH YABAR ZUMUNCHI_ _Anty Murja Na'ikkeh_ _Hassana Dan Larabawa_ _Zuwairah(Ummu Maryam)_ _Nabila Lady(Takwarata)_ _Nabilancy luv(Tawan)_ _Kamal No Luv_ _Nordin_ _Hassan Tanko_ ____________________________________ *WACECE JALILA?* "Jalila Nura gwaranyo 'ya CE awurin Alh.Nura gwaranyo,tsohon principal na Nana girls da ke garin sokoto...."Wanda aiki gwamnati NE ya zaunar da shi sakwatto har ya Tara iyali..."Amma ainihinsu shi matarsa Yan karamar hukumar garin sokoto ne..""Mallam Nura p.c Mutumen kirki NE wanda Tuni matarsa Atika tafi karfinsa acikin gidansa.."Domin irin matan Nan NE marasa sanin ciwon kai Duk da Yana iya bakin kokarinsa wurin tsawatar Matarsa da yiwa yaransa tanadi Mai KYAU arayuwar su..."Amma Tuni ta rinjaye shi saboda shi mutum NE marar son hayaniya.." Zaman SA da Atika Zama NE na wahala da rashin sanin girma da mutuncin juna!"batasan darajar miji ba!bare aure..."Bakin cikinta ne yayi sanadin ciwonsa dake addabar rayuwarsa hawan jini..."Tunda ya kwanta ciwo ba ruwan su da Shi sai abinda suka ga damar yi agidan..Mahmud ne Mai kirki Amma Yana makaranta.."Kuma shine Mai taimakon mahaifinsa.." "Suna da Yara biyar maza biyu Mata uku..."Anty Hajara wacce suka ma alkunya (Talatu)ita CE tafari...Itama dai rainon Atikan CE bawani kirki ne da ita ba!Rashin biyayya shine silar fitowarta agidan mijinta inda tabar yaran ta uku duka Mata..."Da taimakon Hajiya Atika Anty Talatu ta kashe aurenta saboda kawai mijinta Mustafa yaqara aure...yanzu hakan Amaryar SA Halisa ta rike yaran tamkar nata ta hadasu da yarta ta riqe su gaam.."Yayinda Ita kuma Anty Talatu ke Zaman Dana sani agidansu wato (Zawarchi..)Domin tayi biyar tsohon mijinta ya mayarda ita da sauran igiya daya amman yaki..."Kasancewar ita batayi karatu ba iya sakandare NE da ita..Shiyasa take zaune Zaman banza..."Ba aiki ba sana'a kudin gadonta Tuni suka Zama kashi..."( _Sai naji na tuna da baitin tauraruwata Allah ya jikan Rai...Barmani chogi...In take cewa "kowa ya Kama sana'a wacce Bata sana'a ta boni...Duk wacce ke zaman zaune abata ta boniyh wulaqanchi da takaichi zai ZAMOU ajalinta"_) "Daga Anty Talatu Sai Jalila ita ke binta..."kyakkyawa CE fara Sol anyi bleaching har angaji...Tana da jiki Mai KYAU idan ba kaga Jalila tana tsiya ba! bazaka taba yarda da ko hannu akasa Mata a Baki zata ciza ba!"saboda (silent in face ce...)"Amma kaf rashin mutuncin Talatu Bata Kai na Jalila ba,domin ita copyn Atika CE harda dauri akan wasu halayen banza..."Tayi karatu a Danfodiyo sai dai har yau result yaki karbou saboda akwai carry-overs da yawa Kullum Cikin process take ko zata Amsa Amma ba labari..." "Sai Tahir shima dai ba laifi ya dauko halin gado ba SOSAI ba!"Shima ya kammala Degree dinsa Engr.ne Yana aiki a nepa Ya fara gini sai dai Bai fara neman auren ba har yanzu....."( _Ni dai Engr.Tahir ga qawata DANMUSA itama Duk kune 'Yar mutan Dikkawa na center🤣lol_) "Mah'mud shine na hudu agidan kuma bawan Allah acikinsu Yana da kirki matuka ga Tausayi Duk halayen mahaifin su shine ya kwaso saboda Yana da nutsuwa da hangen nesa..."Shi Kam ya fita daban agidan saboda Yana dama acikinsu."akullum Yana nunawa mahaifiyarsa da Yan uwansa akan abinda sukeyi..."Domin shi sam baya Jin Dadi..."Shima ya kammala karatun sa Mass com..Yana aiki a rima redio.." "Rasheeda ita CE auta agidan kaf gidan idan ancire Jalila ba Mai nuna Mata rashin mutunci tayi karatun NCE ta kammala shekaru biyu kenan ba aiki ba miji..." "Tun kafin auren Jalila mahaifin su Mallam Nura Allah ya yi masa..rasuwa,sai dai komai na auren ya tanada tun Yana kwance..."Da Yake yana da tufin asirinsa ga aikinsa da Yake kuma ga kadarori yan kudaden da Yake samu ribar feeding na makaranta da yake..."Shiyasa basu Sha wata wuya ba." suna da gadon su mai tsoka...Gashi Kuma Bayan auren na Jalila kudin sa suka fito Nan aka raba gado kowa yasha sha'aninsa..."Abin yazo masu da sauki saboda marigayi ya Gina rayuwar yaran sa da ilimi kowa yayi karatu..."Daga lokacin ne ragamar kula gidan da yaran tadawo a hannun Hajiya Atika." Daman marigayin NE ke Dan tsawatar masu Duk da ba so take ba Tana nuna bacin ranta saboda ta tsani ayiwa yaranta fad'a ko so kanka!"....."Aykuwa Daga lokacin suka Kara lalacewa gidan ya dawo gidan macce Tuni yaran suka fandare mata saboda ba Mai tsawatar masu..."Mutanen unguwa ba Mai tofawa Hajiyar Atika da yaranta Mata Alheri saboda Sam basu San meye mutunci ba.."Ko an zo nemen auren su idan aka BINCIKI mutan unguwar gaskiya suke Fadi yaran Hajiya Atika irin sakakkon ne sun kasance 'ya'yan macce Komai suke so shi sukeyi..." "A hakan suka Cigaba da tafiyar da rayuwar su tun Bayan rasuwar mahaifin su har zuwa yanzu ba abinda ya rago saima karuwa..."Domin Hajiya Atika kwadayinta,da dogon buri...tare da son abin duniya sai gaba yakeyi..."Shiyasa har yanzu Rasheeda Bata Sami miji bA!"Itama Talatun shekaru shidda tana zawarchi har abin ya fara damunta...."Hajiya Atika ta shiga ta fita Amma Babu Labari shiru kakeji tamkar an aiki bawa kan saqou garin su..." Wannan kenan. *CIGABAN LABARI* "Tunda abin nan ya faru Bata taba Jin faduwar gaba ba!"sai yanzu da ta shigo gidan kuma taga motarsa a parking place..." "Da sassarfa ta isa bakin kofar falon..."Murd'a kan kofar tayi gam..."Alamar an rufe Daga ciki...." "Knocking...Tayi kusan sau uku shiru Nan ta dage ta banki kofar da karfi...." "Yaran da ke bacci falo azabure suka tashi saboda tsoro!..." "Mufeeda ta Kama hanyar kofar tana murza idonta da magagin bacci!..."Da sauri ya fito daga Daki shima baccin Yake knocking din ya tashe shi! Yana cewa DakAta Mufeeda...kuje Dakin ku, ku karasa baccin ku inda Nadiya bara na duba..." "Komawa tayi tsakiyar falon yana tashin su Dakin nasu su ka nufa da sauran baccin a tattare da su..."Shi Kuma kofar ya nufa ya bude...." "Tsaye take ga alama ta kawo iya wuya!"Wani kallon banza tayi Masa ta watsar!"Shi ma kallonta yake batare da yace Mata uffan ba..." "A fusace Tace"Dan Allah bani guri na wuce!!" "Ki wuce kuma!?"Daga ina!?"Ina Kuma zakije!?"Saddiq ya tambaya "Kamar ya Daga Ina nake!?Ay baka bukatar sanin inda na fito saboda baka damu da Ni ba!"Bare lafiyata!?"Ni ban tambayeka Daga Ina kake ba!?"Awanne Wuri ka kwana!?"Saini zaka tambaya!?""Ai kaine abin tuhuma da zargi ba Ni ba!Kuma Dan wulaqanci za'aje yawon banza harda yarana!?"Kai da Allah!Saddiq Wannan ba Rayuwarka bace!?"An Riga anyi maka asiri!"Nasani...To Bari kaji Abbakar! Wallahi na fad'a na kara fad'a Ni Jalila ka CI amanata Saddiq bazan yafe maka cuta ta da kukeyi!" ta karashe maganar da kumfar Baki..." "Kokarin tureshi take ta wuce Daga ciki...Amma tureta yayi waje!"Fuskarsa a turmuke ya nunata da yatsa yace"Ke har kin Isa ince ga yadda za'ayi kice Ah'a!waye ke!?"To Bari kiji ki koma inda Kika fito saboda bakida wani sauran muhalli a gidan Nan..."Naji anyi min asiri sai me so ba yau aka Saba samin gari a abinci ba!"Idan so kuddi ta Aiko...." "Ay Daman na Gaya maki kibi 'yan uwanki sai na nemeki!?" "Anki abisun ai gwara ni da Azzalumai masu cin amanar aure..."Jalila Tace tana nuna SA da yatsa...."Kuma Kasan wake maka asiri ba dai Ni da Hajiyata ba!" "Ganin mudi Mai gadi Yana kallon su yasa ya juya ya shige falon tare da kokarin rufe kofar..." "Iya karfinta ta tattare ta bude kofar kafin yasa key....Tana shiga falon da gudunta ta fad'a Dakin yara... Shima da gudunsa ya bita Yana kwashe jallabiyar sa kada ya Fadi...."Ta Kai hannunta ta chakumou Nadiya kenan ya cafe Mata kafa ta Fadi tif agefen katifar...."Tare da fadin wash!wallahi ko zaka karye!kafar zan kasheta!!!"Da hargagi tana neman damkou Nadiya....." "A zabure na tashi Cikin tashin hankali Naga Yaya Saddiq da Anty Jalila na kokuwa tana neman damkou Ni....saboda daman Jalila irin matan Nan Yan masifa masu karfin tsiya...."Ido na fitou da su waje ina Salati..." "Maruka Yaya Saddiq ke sakarmata Amma Taki sakinsa....Nan yaran suka tashi suna kallonsu suna Kuka..."Nima na takure jikin bango Ina Kuka..." "Janta Yaya Saddiq yayi tare da rufe mu adakin ta waje Ni da yaran..."Ita Kuma sai falo yayi jifa da ita Cikin fushi!" wayar Kebul din t.v ya zarou ya dinga aunawa Anty Jalila ta ko'ina tun tana DAUREWA har tafara kururuwa tana zaginsa Babu mugun furuci kazafi d alkaba'in da Bata jera Masa ba!" "Sai da yayi Mata likis ya turata waje Cikin Jin haushi..."Yace na soki Jalila!nayi Hakuri da ke da mugwayen halayenki!Amma a karshe kazafi Kika yi min....Kin cutarda yarinyar mutane saboda me!?"Hakurina yaqare kije gidan KU na sakeki saki daya Babu Ni Babu ke!"ki fita yanzu tun bansa ayi waje da ke ba..." ni Jalila ka wulaqanta hakan Saddiq!!? Ni zaka saka!?Wallahi sai na dauki fansa bazan barku ba!"!Zan dauki mataki mafi Muni agareku!" mugu KAWAI...." "Tsaki yayi yace kiyi Duk abinda zakiyi Allah ya fiki!Kisani ban taba cutarki ba!Allah ne shaidata!" komawa Cikin gidan...ya rufe kofar da key!" Nan ya durkurshe shima Yana zubda Hawaye....Shine ya saki matarsa uwar yaransa agaskiya Sam baiji Dadi ba!"A rayuwar SA...."Amma rashin Dace da macce Tagari ya Kai shi ga Dana sani Tabbas yanzu Kam yaga izinar auren macce marar *TARBIYYA* daman abokansa da mutan unguwar su Jalila sunyi Masa gudun hakan Amma ya tubere sai da ya kawo cuta agidansa...Gashi Yana Hawaye!"saboda ita...." "Itama ta jima wurin tana rusa Kuka!!"Babban bakin cikinta kudaden da ta kashe wurin neman maganin!"Amma ko AMFANI batayi da shi ba ace wai ya saketa!"Har yanzu ganin take abin kamar amafarki ne...saddiq da ke tsananin sonta zai saketa!"Lalle zancen mansura dutsi ne!Ashe da gaske Nadiya ta Gama da Saddiq Kuma burinta ya cika an saketa!" Nan ta lallaba tabar gidan har wani jiri ke dibanta saboda bacin Rai!....Da tsamin jiki"Tafiya take dishi dishi take gani....Hajiya ayi Hakuri da rayuwa...Mai gadin yace"Zuciyarsa fes yana kallonta har ta fita gidan...Rawa yayi har da shewa Yana cewa Allah ya raka Taki gona!"Yasa mai gida ya auro gangariya Mai dafa abinci Kullum...."Ita kaam bata bi ta kansa ba ta wuce..." "Tashin hankali maras Adadi na samu kaina alokacin da naji irin hayaniyar da akeyi tsakanin Anty Jalila da Yaya Saddiq Wai duk saboda Ni...."Innalillahi Wa'Inna ilaihir Raju'un!!!"Nake ta maimaitawa araina...."Na shiga uku Ni Nadiya,Wannan wace irin rayuwa CE!?..."A hankali na dinga tattara duka Kayana na zuba a akwatina da bakko..."Kai na hade da gwuiwa Ina rera Kuka Wanda shi kadai nakeyi naji sanyi da sauki a birnin zuciyata..."Wayata da ke kashe na kunna domin Kiran su Eshaa...."Sai dai texts NE ke shigowa Duk na Jawad barkatai Duk dai akan rashin samuna NE na tsawon kwanaki uku Haka Naseer da su Eshan Duk sun turou min domin sun kirani waya arufe har da sheda min anata gwaji (tests)bana nan...."Numfashi na sauke tare da Kiran Eshaa...Nace Mata anjuma zan shigo makaranta da yamma Banda lafiya Shiyasa suka jini shiru...." "Hankalin Esha ya tashi Jin yanayin magana ta Amma hakan ta danne damuwarta Tace"sai kin zo..." "Ina kammala wayar na kashe wayata na saka ajikata tare da SA hijab Dina...."Yaran na kalla har wani Tausayi suke bani domin suna Cikin tashin Hankali..."Duk sun koma wasu iri!" "Da sanyin muryata Nace Mufeeda menene kuzo Nan...tare da janyo su jikina..."Ina lallaba su..." "Tuni ya manta da ya rufe bayin Allah adaki ahankali ya qarasa wurin kofar Dakin tare da budemu..."Da gudu yaran sukayi Jikinsa suna tambayar sa ummansu..." "Yake yayi yace ta tafi gidan umman Tahir..."Saddiq ya Basu amsa..."A takaice "Mufeed yace Abba mommy ta daina Kuka!?"meyasa ka daketa....!?" "Mufeeda ta katse shi.... tana cewa Kai bakaga mommy Jiya ta daki Anty Naddy batai Mata komai ba Har Taji Mata ciwon Nan Shiyasa Abba ya Rama Mata ko Abba!?" "Ya Isa bana son shirmen KU....kuje falo kuyi kallo ga ice creem can da sweet...Wa ya Gaya maku dukanta nake ay na wasa NE!"Saddiq yace Yana murmushi cike da jansu ajiki Dan su manta..."Fall ya fita da su sai murna suke..da surutu" "Ina nan zaune adaki naki fita falon har akayi la'asar jiran magrip tayi nake..."Domin da zarar Yaya Saddiq yaje masallaci sallah na guduwa zan na bar gidan saboda na tsani rayuwa acikin gidan...." "Mansura har wata karamar liyafa ta had'a ita da Yan Dakin su... "Murna take da farin ciki ta kusa kammala karatun ta tabar hostel zuwa gidan mijinta Saddiq..."Allah SARKI Ashe da rabon ta Cigaba da rayuwa a sakkwato..."Anci an Sha anyi hani'an ita da kawayenta..."Ta kosa gobe tayi ta kira Anty Jalila taji ko tayi turaren kamar yadda malam zakiru ya umurta...." **************** "Jawad Kam tun lokacin da momy ta sanar Masa labarin baikonsa da Nadiya..."Jikinsa ya mutu..wani zazzabi ya Taso masa ga ciwon Kai...Allah ne ya kawo shi gida lafiya, sashen sa ya wuce batare da sanin momy ba."Saboda wata irin azabar ciwo da Yake ji ajikinsa..."Da kyar ya kirawo Saif awaya ya gaya Masa...." "Nan take Saif ya dirou gidan tare da Dr...." "Saif da kansa ya shaidawa momy Jawad ba lafiya!"aikuwa arikice ta fadou falon nashi...Hankalinta atashe saboda bata hada kowa da tilon danta ba da take so kamar kwai.." "Bayan Dr.ya dubashi magani ya rubuta da drip Nan take Saif ya fita clinic mafi kusa da su yaje ya sawo komai da ake buqata..."Bayan yadawo taimakawa Dr.yayi akasama jawadi din ruwa tare da bashi tea da magani yasha..."Daga Nan Bacci Mai nauyi ya kwashe shi.." "A hanyar fita Dr.yace ma mom da Saif sai an baiwa Jawad kulawa sosai saboda ya kamu da ciwon zuciya...Wanda idan ba'ayi ahankali ba!"Zai iya Zama silar rayuwarsa...." "Kuka mom ta fashe da shi tana kallon Saif cike da tuhuma..." "Har bakin get Saif din yayiwa Dr rakiya da biyansa kudin aikinsa da masa godiya..."Ya wuce." "Dawowa yayi yasamu momm tana zubda Hawaye! Zama yayi kusa da ita Yan kokarin kwantar Mata da hankali tare da cewa in shaa Allah Jawad zai samu lafiya... "Momy cike da damuwa Tace"Saifullahi Dan Allah ka Gaya min meye damuwar Jawad!?" wane Tunani yake!?"Nasan cewa Kasan Matsalar SA!"Bansan me yayi zafi ba!Da har zai sawa kanshi damuwa irin hakan!..." "Rassss!Kirjinsa ya koka!"Tabbas tsanar Nadiya ita CE damuwar Jawad...Inji Saif azuciyarsa...sai dai zAhiri ya Dubeta da Tausayi..Yace gaskiya bansan Jawad da wata damuwa ba! Bayan rashin Abbu, Ina ga abin NE ya SA aransa musamman da ya ga yanzu lokacin auren SA yayi..." "Wani sabon Kuka! mom ta bude tana cewa dole ya hakura koni Nan Hakuri nakeyi domin ya Riga da ya tafi inda ba'a dawowa..." "Tausayin mommy ya Kama shi sai da yayi kwallah!"Lallaba ya dinga yi har tayi shiru. har sashenta ya kaita tare da Bata tabbacin Yana tare da Amininsa har sanda ya samu sauki...." "GODIYA tayi Masa tare da SA Masa Albarka..." *********"Tun a kofar falon tayi jifa da takalmi,da gyale harma da jikkata kamar mahaukaciya ta fad'a jikin Hajiya tana rusa Kuka Mai tsuma zuciyar mutum...." "Da tashin hankali Hajiya ke tambayarta lafiya!?" "Amma Ina ba bakin magana sai...wani sabon kukan.." " 'yan uwanta da ke tsaye sunyi jugum jugum cike da tashin hankali da tsoro..suna kallonta kamar Mai hawan iskokai..." "Rasheeda Tace"Laaah!!!Hajiya KU dubi jikinta ashe dukanta yayi!"Tare da taba jikin na Jalila wacce in Banda Kuka ba abinda take...." "A zabure Hajiya ta mike tare da Duba dukkan jikin na Jalila da yayi jajur da kwancin buloli!!!" "Hajiya Tace"Akwai bala'i Ni wani katon banza!zai dakarwa 'yah!?"Wallahi bazan k'yale ba, Sam ba zan lamunta ba!...Ina Tahir....Tahir Kai Tahir....Hajiya ke Fadi atsawace..." "Da sauri ya karaso Daga dakinsu...Shin Lafiya Hajiya...? Ganin Jalila kwance akafet tana Kuka yasa shi karasowa da sauri yace''Ita Kuma Wannan fa!?"Lafiya meke faruwa!?" "Rasheeda cike da kad'ad'i da masifa Tace"Wai Abban su Mufeed NE ya daketa!"Saboda Nadiyar nan da nake Baku Labari..." "Kai...Amma ko anyi d'an wulakancin za ya yi Bayani,ba Domin na daina d'aukar hukunci da adda da zabira ba,da yau Sadiq ya yi nadama Amma ko yanzu zai wahala!..."Inji Tahir tare da qara Duba jikin yayarsa..."Tsaki yayi yace"Ke kuma Ashe Haka kike sakarya!?"Ki zAuna aita jibgarki kamar Jaka...Anya ke jinin mu CE...!?"Wallahi yau akwai yaki da bala'i da masifa!!"Domin zan tadda rashin mutunci na!"zai Gane bayada wayo. "Hajiya Tace"Duk akwai su, Tahir bana fatan a yayyafa Masu ruwa matukar bana fetur bane akwai bala'i Saddiq ya tabou masifa!...Amma kafin mu d'auki mataki mu saka hukuma gaba,duk da ba komai zatayi ba,Kun ga idan hukuncin da akayi Bai Mana ba,ai sai mu d'auki matakin da ya Dace da shi. Yanzu Maza ka tafi police station ka Kai report"sai mu hadou gidan matsiyaci Kuma Duk uban da yayi Masa tsaye shi da makirar yarinyar Nan, sai sun kwana a cell ke kuma sai ya sakeki!"Idan yaso ya aureta ita Nadiyar..." "Hajiya kafin can da kubari muji ta bakinta saboda bamu San yadda abin yake ba!"Kar mu aikata Abu mu koma Dana sani!!"Inji Anty talatu." "Kece da Dana sani banza! wacce batasan ciwon Yar uwarta ba!"Ban San meke damunki ba!"Sakarai kawai, Kai ku shige muje Rasheeda dauko min mayafi!!"Hajiya Tace Rai a bace!" "Kokarin ta da Jalila tsaye Hajiya keyi...Tace share hawayenki Jalila zai gane Kuran sa!!" "Da kyar ta bude bakinta Tace Hajiya yafa sakeni!"sannan Ya dakeni!"Yayi jifa da Ni waje kamar wacce bai sani ba!"Kuka NE ya ci karfinta..."Tayi shiru....." "Hannu Anty talatu ta aza akaa tare da fashewa da kukan tausayin kanwarta tana fad'in Innalillahi wa Inna ilaihir raju'un mun shiga uku jalilah..." "Hararanta Hajiya tayi Dan Allah rufemana Baki bakiyi kukan ciwukan jikinta ba!"Sai Dan kawai ya saketa!?To meye aciki!?"Saki nawa yayi Miki ta tambayi Jalila!?" "Cikin Kuka tace"daya..."Nan Rasheeda ta zo da mayafin Hajiya..." "Hajiya Tace"muje ai sai ya qarasa biyun matsiyaci!"Ta kalli Talatu tace ke Kuma ki tsaya Ki fake Mana gidan..."Ku shige muje!" "Da kyar Jalila ke Daga kafarta saboda fargaba!"Tasan halin Hajiyar su Sarai bata wasa idan ranta ya baci..."Ita dai Allah Yasa Kar Saddiq ya qara Mata wani sakin...."Nan take ta manta a hanya suke ta fashe da wani sabon Kuka!"Hakuri Hajiya da Rasheeda ke bata har suka samu taxi."Tuni Tahir ya isa police station..." _Toufah muje zuwa 'yar mutan Dikkawa ce😍_ [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 23* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *An karb'ou Daga Daga Abiyh hurairah(R.A) Yace"Annabi Muhammad (SAW)Yana cewa:"Idan Dan Adam ya mutu..Dukkan Ayyukan SA sun yanke,Face Abu 3"Sadaqa Mai gudana,(Jariyat)Ko ilimin da ake aiki da shi,Ko Kuma D'a na gari Mai yiwa iyayensa Addu'ah"Daga Imam Muslim."* _"Abin Tambaya....?Taya D'a zai ZAMOU Nagari?Dole sai an bashi TARBIYYA MAI KYAU Domin ita ce jigon rayuwa"Ya Kamata IYAYE mu daure mu baiwa Yara TARBIYYA MAI KYAU wacce za'ayi ALFAHARI da Su watarana."_ *SADAUKARWA GA IYAYENAH ABIN KAUNATA*😍 ______________________________________ ************* "Kamar munafuka Haka nake Tafiya Ina sanda a falon..."Wayo nayi ma Mufeeda dake zaune tana kallon cartoon.. nace taje tayi Alwala ta gabatar da sallah lokaci yayi..."Domin daman shi Mufeed din Yana tare da Yaya Saddiq sunje masallacin..." "Tana shiga bedroom din Ni kuma na fito da kayana dana boye Bayan labulai..."Ja in ja nake da akwatina da bakkona..."Sauri-sauri gudu-gudu nake Tafiya zuciya ta na bugawa..."Cikin Sa'a na fito get din gidan gashi Mai gadin shima baya nan Yana masallaci Aykuwa da sauri na qarasa Titin Estate din..."Nan nasamu Napep ta kawo wata Mata da sauri na shiga nace Masa Shehu shagari Zai kaini..."Sai da muka fita estate din naji wani sanyi da nutsuwa..."Wayata na fito da ita tare da dannawa Esha Kira..."Nace su fito bakin get din hostel gani Nan zuwa yanzun...." "Bayan an kammala sallar magrip kamar kullum Tsayawa sukeyi a masallacin Ana gaisawa atsakanin su makota..."Yau ma hakan CE Tafaru Shiyasa ya dan jima Bai koma gida ba!" "Mai gadi ya Kama hanyar gidan..."A bakin kofa ya samu Hajiya jalilah da mamanta da kanwarta tsaye kamar itatuwa.." "Mudi yace"Ah Hajiya sannunku an dawo...Ay gidan abude Yake ku shiga Mana Daga ciki oga yana masallaci.." "Harara Rasheeda ta watsa Masa tare da cewa BA ZAMU shiga ba!" "Tsaki Hajiya tayi tare da Duba agogon wayarta.."Tace"Shi kuma Tahir ya jima Bai zo ba, ko me ya tsaya oho?" "Mama kin san lokacin magrip yayi Ina ga Shiyasa basu karaso da Wuri ba!"Inji Rasheeda tana tauna chewing gum tare da Danna wayarta..." "Mudi asawaki KAWAI Yake Yana hararen su ta gefen ido...Aransa yaji haushin dawowar Hajiya wato Jalila..tun Wuri hakan..." "Juyawa yayi da yanayin ko in kula.. "Ya ce to akawo maku benci? Naga Hajiya zaune kasa Yana nuna Jalila da abinda duniya ya dameta,wanda ya hanata magana..."Ya Koma cewa"Kunsan ban iya hakurin barin Hajiyarmu zaune ga banza!" "Kai bama buqata munafuki! in Banda iskanci akace maka mun gaji NE!?ko Dole NE zaman!?"Ita Jalila tagaya maka tagaji NE!?Hajiya Tace cikin masifa!" "Ya numfasa kenan domin ya fesowa Hajiya Amsa, sai dai Jiniyar motar Yan sandan da yaji tana shigowa estate din ne tayi sanadin katse Masa hanzari...."Cike da mamaki ya fito da Ido!abinda Bai taba faruwa ba acikin Estate din Jiniyar Yan sanda sai dai su jiyo a waje...." "Bai qara mamaki ba sai lokacin da yaga motar tana qarasowa wurin su tana tada kura!ay da gudunsa ya shige gidan tare da rufe get din..."Saboda tsoro!"Yana mamaki abinda Yan sanda suka zo yi akofar gidan..Yana cewa Hajiya kuyi ta kanku tiyagas!!!"Tuni yaran da suka dawo masallaci harda matasa sukayi tsaye suna kallon Hajiya da ke faman baiwa Yan sanda Labari harda na karya da kazafi!" "Tun Daga nesa ya hango mutane akofar Gidansa..Bai Kara tabbatar wa sai da ya qarasou..."Yan sanda ne da motarsu ya hango..."Sakin hannun Mufeed yayi tare da dafe kansa da ya Sara yayinda ya hango Yan Gidansu Jalila atsaye kofar gidan..." "Jiki a mace ya iso..tare da masu Sallama.." "Hajiya Ina wuni yace muryarsa asanyaye..." "Tsaki Hajiya tayi tare da dauke Kai!" "Tahir da Rasheeda, Sai hararen shi sukeyi..." "Tahir ya CE"Yawwa officer Gashi Nan tare da nuna Saddiq.." "Mufeed wurin momynsa yaje Yana surutu wacce Kuka kawai takeyi..."Suka Rungume juna..." "I.D card Officer Bashir ya nunawa Saddiq tare da cewa Daman sun kawo karar Kane ka daki Yar uwarsu harda jimata ciwo!"Hakane Kaine kayi Mata dukan har da targade!?" "Cike da sanyin murya da kunyar jama'ar da ke wurin suna SAURAREN su, yace"Eh.. yallabai na daketa Amma bansan da targaden ba!"Inji Saddiq "Good"Officer yace, tare da cewa ka shige Mota..zamuje Office da Kai akwai sauran jawabi..." "Yallabai a kashe maganar Nan anan, Dan Allah ba sai munje ko'ina ba!" "Wallahi sai ka kwana acell anki akashe matsiyaci Dan ba jaka na Haifa ba! ...Inji Hajiya.." ********* "Murmushi yayi Wanda yafi Kuka!ciwo yau shi ne matsiyaci Bayan goma na Arziki da ya ke masu. Ya dubi Dan sanda ya ce "ba damuwa yallabai Zan bi ku amma Ina son kabani dama in gayawa kanwata abinda ke faruwa shima yarona ya shiga gida kafin mutafi...." "Yallabai harda yarinyar da yake magana akai ya kamata afitou da ita domin ba kanwarsa bace Yar iska CE!ya ajiye agidan!"Akanta ne ma ya daki yayata harda saki! Kuma ita CE silar lamarin... Rasheeda Tace da masifa!" "Duk da abin ya yi Masa zafi!Amma ya kasa magana saboda Yana son adaina maganar a INDA ake masa kallon mai mutunci, Duk da ko yanzu girma ya Fadi!" "Officer yace wa saura Yan sandan biyu...KU bishi afito da kowa da ke gidan..."Sara Masa sukayi tare da bin Saddiq din..."Sai da yayi magana sannan Mai gadin ya bude get atsorace,shiga Saddiq da police din."Tuni Mai gadi ya shige Dakinsa ya boye!"Kar kaftu ta kafto shi.'' ********** "A hankali ya bud'e Idonsa da suka yimasa nauyi tare da karewa Dakin nasa kallon..." "Hannunsa yaji a hade da na abokinsa, ya kalle shi acikin yanayin irin na ciwo da damuwa.." "Yace saif meyake faruwa da Ni!?" "Jawad...Baka jin Dadi NE!Yanzu ya kake jin jikin naka!?" yace Cikin damuwa. "Hmnnnn..Saif kenan kafi kowa sani damuwata ai Dole na kamu da cuta!Saboda Naga Zan cuci Kaina da kaina!A gaskiya nayi Dana sanin Wannan mataki da zan dauka!"tayaya ma zan auri makiyiyata!?"wai Wacce nafi tsana adunia.."Sai naji sam bana son ganinta bare mu zAuna agida daya...da ace na d'auki mummunan mataki a kanta da yanzu komai ya wuce Amma yanzu idan na aureta ai ko Bayan rabuwar mu Kai da ma ace ta mutu labari zai Cigaba da Tafiya ta tab'a Zama matata!Ni Kuma Bana son a dangantani da Wacce ta kirani marar tarbiyya,maccen da ta zabga min mari har uku."Tashi yayi tare da jingina bayansa jikin gadon...Ya qara da cewa Inda na sani tun farko maganinta Zan sa Yan ta'adda suyi!"ko Kuma nasa ayi Mata dukan tsiyah a karyata a halakata!"A nakasa Mata rayuwa!Ka ga Zan debe haushinta Da yanzu ba ni da mugun tabonta a Rain.."Amma yanzu idan na aureta Saif,ai ta kwareni. "Gyara zamansa yayi tare da fuskantar Jawad, yace Wannan ba mafita bace!"Ka daina Tunani irin Wannan karfa ka manta da abinda Ta kiraka!"Ay ka aureta ka gasata Kai Mata azaba shine fansa Daga Nan zata koyi sawa bakinta linzami idan zatayi furuci!" Sannan akarshe ka sata Dole sai ta koyar da Kai *TARBIYYAR* saboda Kai ba Mai ita ba NE..."Kamar yadda ta fad'a,Itama za'a kirata bazawara."Kaga anan ka gasata!Kuma ka lalata Mata rayuwa, "Zan iya sata tayi min hakan ko da ban aureta ba..! "Tayaya!?"ya tambaya "Ta hanyar SA asato min ita,Zan iya boyeta sai lokacin da naso na fito da ita Kuma masara idan taji wuta ita ke nunawa." "Ka daina Wannan zancen abokina ai mafita daya CE ka auri Nadiya domin huce haushinta..."Saif yace Yana kallon Jawad.." "Numfashi ya sauke tare da furzou iska abakinsa yace "Shi kenan Saif na gamsu Kuma na amince.." "yace"Yawwa Dan Allah ka cire Wannan aranka kaga mom ta damu da rashin lafiyar Nan naka"Ka manta da komai.." "Yanzu Ina momyn!?" "Tana sashenta Bari ka ci abinci kasha magani sai muje kadan motsa jikinka...Ba tama Jima da fita ba!Ba ka ganta ba!"Duk ta damu sai da na lallabata nace damuwar rashin Abbu ne ranka, Saboda lokacin aurenka ya zo bashi a duniya.." "Allah SARKI Mamana Jawad yace afili..A ransa Kuma tunanin irin kaunar da mahaifiyarsa ke Masa yake..."Allah dai yasa ya Gama da momynsa lafiya shine burinsa..'' *********"Yana gaba 'yan sandan na bayansa bakin falon suka tsaya tare da cewa ka fito da kowa a gidan idan ba haka zamu shigo da Kan mu..."Baice komai ba ya shiga Daga ciki...Mufeeda ya samu zaune tana Kuka!" "Ke Kuma me akai Miki!?"Ya tambayata "Da gudu ta isa wurinsa Tace"Abba tsoro nikeji Ni kadai CE agidan.." "Ke kadai Ina Nadiya!?" "Nima ban ganta ba!tun dazu fah nake nemanta na Duba banganta harda Kayanta ta kwashe!" "Diiiif...ya dauke wuta!Ana wata ga wata kenan!To Ina Nadiya ta tafi!?"Kenan ta gudu!?" "Abba ko ka ganta a waje?Mufeeda ta tambaya!?" "A'ah...Bari na Duba da Kaina Mufeeda wakil shirmen ki NE..."Nan Saddiq ya rawaye gidan kaf ba Nadiya ba ko tsinken ta..." "Jikinsa a sanyaye ya janyo Hannun Mufeeda tare da rufo gidan...Ko kallon yan sandan baiyi ba!"Ya wuce suka biyo shi baya.." "Inda Mai gadi ya tsaya "Bacin ransa ya bayyana ran maza ya baci...Fuska turmuqe yace"Mudi zanje in dawo ka kula da gidan..." "Angama Mai gida Allah ya tsare ka ya kareka Daga sharrin mahassada.." "AMIN yace agajarce..Ya fara Tafiya tsam ya tsaya tare da waigowa..Mudi." "Na'am yallabai yace tare da qarasowa da gudu." "Ko kaga fitan Nadiya daga gidan Nan!?" "Gaskiya yallabai Banga malama Nadiya ba.." "Okay..saina dawo Saddiq yace suka wuce.." "Adawo lafiya Mai gida, ba dai mutum ko Aljan ba!"Wallahi Tama zaka dawo gidan Nan mu Cigaba da zaman mu,Allah ya rabamu da sharrin bakar shiga.."Inji mudi "Inda suke tsaye har yanzu suna Nan.." "Officer yace Kai sajaan..Ku wai..wad'an me irin shashashai NE kunje kunyi zamanku kamar Kun bar itatuwa a waje!" Fad'a masu yallabai....Inji Tahir "Sara Masa sukayi tare da cewa sorry sir!" Saddiq yace yallabai motarku bazata ishemu ba har yarana Ina ga bara na Dauko tawa Muje ko? Ba damuwa go ahead.inji officer "Nan Saddiq ya KOMA Cikin gidan ya fito da motarsa,Mufeed da Mufeeda ya dauka amotarsa...Su kuma Hajiya da Jalila da Rasheeda amotar police suka shiga Tahir da Yan sandan biyu abayan motar.."Saddiq NE agaba police na binsa Abaya sai jiniya ke tashi..."Wasu zafafan Hawaye suka zubo Masa yanzu shine police suka Taso gaba!"Lalle ya hadou da irin wahala!"Jalila ba Alheri bace arayuwarsa,Silarta ya shiga wata rayuwa..."Ga tarin kunyar mutane da dama masu ganin girmansa a kansa.."Wannan kazafi da tonon silili da Hajiyar su Jalila tayi Masa..A gaban idon makotansa da Yara..." "Maganar Mufeeda ta dawo da shi hayyacinsa...Abba Ina zamuje Naga Yan sanda na bin mu Kama mu ZASUYI?" "Mufeed yace Abba Ni tsoronsu..nakeji,kuma mummy Tace min ka zasu Kama su dakeka kamar yadda ka daketa!"Da gaskiya ne? "Kuyi shiru bana son surutu.. Saddiq yace ahasale wayarsa ya dauko tare da Kiran layin abokinsa Ali.." "Cikin Sa'a Ali ya Daga Nan yayi Masa bayani tare da cewa yasa me shi a station din.." "Rai ba Dadi Ali yace to Yana zuwa.."Da Yake Yana cikin unguwar juya akalar motarsa yayi zuwa police station din." "A Mota Hajiya Atika sai zagin Saddiq take tare da fadin karerayi domin Officer yaji ya Basu gaskiya.." "Police station din suka nufa, karasawar su ke da wuya sai ga Ali ya qaraso shima da sauri..."Saddiq yace Yawwa Ali Dan Allah ka wuce min da yaran Nan gidanka su ci abinci suyi wanka Sannan ka dawo, su Kuma yaran kabar su can..." "Ali yace gaskiya banji Dadi ba Saddiq..Wai meke faruwa ne!?" "Babu lokacin Wannan bayanin Ali..Ni dai kafita da yaran Nan daga wurin Nan..."Sai ka dawo kaji yadda abin Yake.." "Ba damuwa,yace tare da Jan yaran suka wuce!"Jalila idonta na kansu aharabar station din, sai dai ba halin magana. Dan ta lura ko da wasa Saddiq Bai kalleta ba!"Gashi dazu Akan ta Kula Mufeed Hajiya ta Mata fad'a wai ta fita harkar yaran dan Saddiq din zaifi Jin haushi..." "Wuri aka tanada kowa ya zauna nan Officer ya karanta Duk statement din da aka dauka Akan abinda Saddiq ya aikata..Tare da tambayar Saddiq din hakane!?" "Abinda Ya san ya fada ya Kuma aikata yace hakanne abinda ba gaskiya ba Kuma ya karyata..." "Ali NE ya dawo shima Wuri yasamu ya zauna kusa ga Tahir..Jalila da Rasheeda sai hararensa sukeyi..." "Officer yace meye dalilinka na dukan matar ka batare da tayi maka laifin komai ba!?"A karshe Kuma ka hadata da guzurin saki!" "Saddiq yace ranka ya Dade neman kisan Kai!"tayi shine nayi kokarin hanata!.." "Kamar ya kisan kai!" "Gyara zamansa yayi Cikin ilimi da dabara Saddiq ya zayyane wa Officer Duk abinda ya faru!"Daga FARKO har karshe...Ya qara da cewa idan Kuma tayi musu..."Ina da shaidu yanzu Haka yarinyar akwai raunukan da sukayi Mata ita yayarta da Wannan marar kunya ajikinta,ya nuna Rasheeda. Sannan ina so muje asibitin da aka kwantar da yarinyar a nemo file dinta..nasan zaku samu dukkan bayanai daga bakin likitan da ya dubata..." "Yau ma tayi yunkurin hallaka yarinyar Shiyasa nayi kokarin hanawa har na daketa, yallabai ina ma son akafa shaida anan domin ta ci alwashin sai ta kashe yarinyar!"Daman Ina niyyar kawota Kara koda ita Bata kawo zancen nan ba!"ta fita harkar Yar mutane abinda take zargi ba haka bane,k'anwata ce Wallahi duk abinda ya sameta itace. akafa shaida nan.." "Tahir...yayi sarou saboda shi Sam bai san sun daki yarinyar ba!"Kallon su yayi duk sunyi wani zuru-zuru.." "Hajiya Kam sai fidda ido take!" "Tuni Cikin Rasheeda ya dauki ruri sai murdawa yake.." "Cikin tsawa Officer yace Ke Jalila kinji bayaninsa hakane!?"Ko akwai abinda Baki yadda da shi ba!?" "Hawayenta ta goge da gyale..Tace nasan mun daketa dai..." "To kince sai kin kasheta!?"Inji Officer "Wallahi Ni ba da gaskiya nake ba barazana ce!"Officer taya can Zan iya kashe mutim!"Dan Allah kuyi Hakuri wasa nakeyi.." "Officer....yace Kai rubuta.."Nan Mai rubutawa ya rubuta Duk bayanan..." "Kallon su officer yayi yace to naji Duk bayanan KU...Kai Saddiq Ina yarinyar..!?" "Yallabai dazu da naga Jalila taso ta halaka Shiyasa na mayarda ita hostel Daman kanwata CE tazo karatu ne ba ANan garin take ba!To yanzu da Naga masifar tayi yawa ga rauni ajikinta!kuma Ina gudun Jalila tazo Daga baya idan bana gidan ta Ida nufinta..."Ta kashe Yar mutane...Shiyasa da yamma na mayarda ita makaranta tana can.." "DakAta masharranci!ka daina hada diyata kisa!"Inji Hajiya afusace tana goge gumi da mayafinta!." "Officer yace"Hajiya! karki manta diyarki tayi furuci kuma ta amsa mu Kuma mun dauki report Dan watarana.." "Yanzu Saddiq zAka fad'a Mana abinda ka kashe...na jinyar ita Nadiya zasu biya ka ko nawane..."Sannan kuma zasu bayarda naira dubu goma ta Cigaba da Shan magani..."Tarar da akaci su saboda sun daketa batare da hakkinta ba!" "Y'allabai....." "DakAta! Hajiya nasan me nakeyi..."Ai hukunci na lalama ne nayi maku. "Ke Kuna Jalila zamuje asibiti kema aduba ki!"Saddiq zai biya duka kudaden da za'a kashe maki..." "Ke Rasheeda ke da yayarki da ace tun Ranar da abin ya faru ne aka kawo mana labari!to da sai mun kargameku a cell har wannan jalilah!"Saboda kunyi kokarin kisan Kai!"Kuma Kun taka doka!"Daga yanzu Baku ba Nadiya munyi maku kashedi na karshe!" "Yallabai da subar kudin kawai saboda na fiso akashe zancen Inji Saddiq.." "Duk abinda nace shi za'ayi Saddiq Wannan shine dai-dai. saboda mu bama sabawa doka!"Kai ma karka k'ara daukar hukunci da kanka! "Bakin Hajiya ya Kara tsini... Rasheeda ta Matsu subar wurin tun ba'a tasa kiyarta cell ba!"Jalila Kam taga ta kanta Baki Mai yanke wuya domin tana Cikin tsaka Mai wuya.." "Daga Nan asibiti suka nufa aka Duba Jalila tare da rubuta magani Saddiq din ya biya, tare da Basu dubu goma na Shan magani..."Amma fir Tahir yaki karba yace ya rikesu kudin tarar Nadiya." "Hajiya Kam ta kasa cewa komai taga Sami taga Rashi! Daman Talatu tayi masu gudun hakan.. "Gashi akarshe Sune da kunyar!"Da jin haushi da takaichi!" "Saddiq dubu biyar yaba Officer da yaransa tare da Masa godiya suka wuce..."Ko duban su Hajiya baiyi ba!" "Hajiya Tace DakAta Saddiq idan Kai Dan halal ne!ka Ida sakin Jalila yanzu ba sai anjuma ba!" "Murmushi Yayi tare da cewa kiyi Hakuri Hajiya iya sakin da Naga damar yimata kenan..."motarsa ya shiga, Ali ta da nashi motar yayi Nan SUKA wuce suka bar su Hajiya na daddalar sayyada horn sukayi masu na sai da safe suka wuce abinsu..." "Tsaki Rasheeda tayi Tace shegu wa zakuyiwa karyar Mota..." "Ke Mana banza! ke sukeyiwa?keda gaki Nan akafa...wallahi sai na karyeki wato kunsan kun daketa, kukasa na zo Ashe bakuda gaskiya...Tahir yace Yana kumfar Baki.." "Dan Allah kubar ni da zancen haushi da wanne zanji..."ke Kuma sakarya Sonsa ma kikeyi ko!?"marar zuciya yace bazai sakeki ba!"ke bakisan kalar rashin mutuncin da zakiyi Masa ba!Har ya hasala ya sakeki!" "Shiru Jalila tayi Amma azuciyar ta tasamu sauki da ba'a Ida daga Mata red card dinta ba!"kamar yadda Hajiya ta so."Sai da sukayi Tafiya Mai nisa Kasancewar dare yafara Sannan suka Sami abin Hawa kowanne da bacin ran da ke damunsa..." *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍😍 *2020*✍🏼 *Share & Comments* [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 25* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM._ *DAN TSOKACHI..."A duk lokacin da masoyana ke min Wannan tambayar na kanyi😄Wai Dan Allah Nabeela Dikko 'yar mutan katsinawan Dikko ce?"My Fans Ni Yar KEBBI ce, Ba 'yar katsina ba,Kamar yadda kuke tsammani😍 Nidai 'yar jihar kebbi ce a garin ARGUNGU,Nagode sosai fans,Da kulawar ku, da Kuma soyayyar ku,Allah yabar zumunchi Ameen,Duk Wanda zai zo kebbi Inda nake, ina maraba.*😄 _A koda yaushe mu masu kuskure neh awurin ku,Mu writers muna fuskantar kalubale awurin ku readers, Dan Allah idan munyi ba dai-dai ba amatsayinku na fans ku fitou ku bamu shawara, ba kuyita zagin mu ba,Kusani laifin mutum daya zai iya shafar kowa,Sannan ta wani gefe kuma Kuna bayarda goyon baya Akan abinda ke faruwa,FATANA Allah ya yafe Mana ya daura mu akan tafarkin gaskiya Ameen,Anatare iya wuya fans_ ______________________________________ ************* "K'arar Wayata ta sani karasowa da sauri!"Inda na sanyata caji na nufa,Ina kokarin d'ebeta acajin!"Sai dai Lambar da ta bayyana da sunan Wanda ya kirani ajikin wayar ya sani tsorata!"Juyowa nayi na kalli Esha da tsoron Ina fadin Yaya Saddiq NE!" "Kiyi sauri ki dauka mana!Inji Esha" "Da sauri..Na d'aga tare da Sallama hannuna na rawa da muryata!" "Ki fito bakin hostel din ku, Ina jiranki,Shine Naji adodon kunnena,Dif Kuma ba'a Kara cewa komai ba!Wayar na duba Ashe ya datse kiran." "Idona ya kawo kwallah!Ina kokarin yiwa Esha bayani me yace,Sai ga Hindou ta rum 6 da maman hostel abayanta sun shigo Dakin." "Bayan mun gaisa da su,"Maman Hostel tace"Nadiya kiyi sauri!Tun dazu nake neman Dakin ku Bangane ba! Mallam Saddiq ke nemanki,Yana waje Yana jiranki!" "Da kyar na hadiye kukana!Nace to mama Gani Nan!"Juyawa sukayi suka fice!" "Ni Kuma Esha na duba!"Ko Zaki rakani!?" "Ni Naddy?Allah ya kiyaye!wato na karaki asirinki ya tono!kina son ya gane muna tare har yanzun ko!?" "To Ay yanzu Kun canja Daga yadda ya sanku Adaa can baya Eshaa!"Kuma Duk Wanda zai tambaya zai fad'a masa hakan!" ''Amma ba damuwa bara na tafi nace Muryarta na rawa! na sab'a hijab Dina,na nufi hanyar waje!"Tun Daga nesa na hango motar sa, Addu'oin nake idan na Kama Wannan na manta karshenta, na dauko wata har na Isa jikin motar," "Tsaye nayi Ina kallon su saboda duk glass din motar arufe Yake ko sallamar da nayi basuji ba, sai dai nasan sun ga baki na Yana motsi,kusan mintoci Basu fito ba!Ni Kuma Ina tsaye!"Nan Kuka ya zo min na hau shafe Hawaye na da hijab." "Daga Cikin motar kuwa,Ali,yace ko Yanzu an horata nikam agaskiya ta bani tausayi,ka dubeta Wallahi duk atsorace take!." "Saddiq yace"Daman halin ta NE, Kuka ba!" "Fitowa sukayi Daga Cikin motar ahankali nayi kasa da murya ina gaida su, "Yaya Ali ya Amsa min tare da tambaya ta ya makaranta ya karatu?" "Lafiya kalau nace Masa" "Yace"Nadiya Daman mun zo mu duba shin ko kina makaranta?"Alhamdulillah,Mun sameki,Amma Meyasa Zaki fita batare da iznin Saddiq ba!?Bayan kinsan amanar kula da ke tana hannunsa!"A gaskiya Baki kyauta ba!"Ay ba'a hakan! da kinyi Hakuri idan ya dawo Daga masallacin, kice ya mayar da ke hostel din!"Sannan komai ya wuce kiyi Hakuri kinji!?" "Sunkuyar da kaina nayi nace to Nagode,"Na Kara da cewa Yaya Saddiq nasan nayi laifi Dan Allah kayi hakuri!" "Duk da ya yaji ciwon abin da yarinyar Nan tayi Masa Amma Akan ta bashi Hakuri sai yaji wani Sanyi aransa." "Yace ba komai Nadiya Allah ya tsare gaba Yanzu anan kike son Zama kenan!?" "Eh....!"Yaya nafi son nan saboda Ina shiga library karatu,gashi anfara Mana (C.A) Ina bukatar Samun nutsuwa Domin karatu" "Ya CE to Shi kenan Ali kaji yadda Tace.." "Ali yace to ba damuwa,Nadiya Allah ya taimaka,Ayi ta karatu banda wasa, ya dauko kudi acikin aljihun sa, ya bani yace ga Wannan ki sayi sabulu." "Amsa nayi Ina GODIYA tare da nunawa Yaya Saddiq din." "Shima godiya yayiwa Ali."Yana murmushin jin dadi Sannan "Ya kalleni a wane daki kike Zama!?" "A dakin da nake Ada!na bashi Amsa cike da tsoro, "Ba Nace kibar Zama da yaran Nan ba!?" "Yaya Wallahi sun daina komai Yanzu karatu NE agaban su Kuma ka bincika!" "Ay gurbi ya Bata Sha,Domin ko sun gyara ba za'a daina masu Kallon banza ba!Kuma idAn an ganku tare dauka daya za'ai maku ba ayi b'ari a kwashe daidai ba." "Ali yace Haba Saddiq yau me zaka yiwa mutanen duniya da Bazasu zage ka ba!?Kawai kabar su Tunda sun daina din Wannan tsakanin su,Da ubangijin su,ke Kuma ki Kama kanki." "To in Sha Allah Yaya, Nagode." "Mota ya bude, kudi ya fitou da su ya bani,Ya ce"kinga Wannan kiyi sayyaya abinci abinda ya rage ki Bari zuwa jibi idan anyi salary na sayo maki, Sannan ki mayarda hankali ga karatu Daga Wannan hutun TP(Teaching practice)zakuje sai ki turou min courses din da akayi test Baki Nan zanyi magana da malamman."Ya dubi abokinsa yace"mu wuce ko." "Amsa nayi Ina GODIYA na koma hostel su Kuma Mota suka shiga suka wuce." "Eshaa na samu tsaye bakin rum dinmu tana jiran Dawowata, da murna na rungumeta Ina labarta Mata yadda mukayi tare da nuna Mata kudin da suka bani,karba tayi ta kirga na Yaya Saddiq tace dubu goma NE cif,sai dubu biyar na Yaya Ali."Nan Nace sai zuwa anjuma su rakani kasuwa na sayi abubuwan da bama da shi."Tace"To Shi kenan kafin Nan su Deeja ma sun dawo Daga saloon din da sukaje wankin Kai." ***********Katafaren gidan da mom ke ginawa Jawad tun Bayan rasuwar mahaifin sa,Can sukaje dukan su komai an kammala na gini,Yanzu kaam kayan part dinsa kawai ya rage azuba,Suma tuni tayi maganar ayi oder su,da zarar lokaci yayi kawo su za'ayi." "Jawad da Saif sai murna suke saboda rabon su da zuwa gidan tun ba'a karkare shi ba gashi yanzu gida ya hadu iya haduwa." "Sun shiga ko ina na gidan sama da kasa ba laifi,Daga Nan gida suka wuce."Momy suka sauke,Alheri shopping plaza suka nufa, Sayyaya kayan masarufi da sauran tarkace sukayi,gidan Mallam Balarabe suka nufa." "A irin lokacin da suka san cewa zasu same shi agida,Lokacin suka Isa."Kamar kullum sun samesu zaune a farfajiyar gidan da aka share tsaf,kamar ba mutane agidan saboda tsaftar su,Fira suke shi da matarsa, Sallamar su Jawad ta katse su." "Maraba sukayi masu." "Nan aka shiga musayar gaisuwa, "Ruwa Innerie ta kawo masu saboda yau Kam gidan sai Hamdala,Yanzu NE take kokarin girki," "Fira sukayi sosai,da Innerie da Mallam Balarabe sai wajajen yamma sukai masu Sallama tare da basu kayan da suka kawo masu." "Godiya sosai suka yiwa su Jawad din tare da saka masu Albarka." "A hanyar su ta dawowa Saif yace"Gaskiya Jawad iyayen Nadiya mutanen ARZIKI ne sosai,Ina son irin dattakon Su." "Hakane Inji Jawad."Ni Kaina Ina jinsu tamkar wani bangare na jikina,Kasan ance sabo turken Wawa!" "Tabbas...Saif Yace Yana murmushi." "Tafiya suke suna fira har suka Isa gidan su Saif." "Da misalin karfe 6:00 pm na yamma ta lallaba ta fita Daga Cikin gidan su ba tare da sanin kowa ba,Abin hawa ta nema sai Bafarawa Estate ya sauketa."Bakin kofar get din gidan ta tsaya tana bugawa,Bude kofar yayi." "Mur yayi da fuska tare da cewa"Barka Hajiya." "Murmushi tayi Barka dai mudi ya aiki?" "Ta Kasan Ido yake kallonta sheqeqe yace"Aiki Gashi Nan munayi yanzu bakin Aikin nake." "Mamakin mudi take irin yadda ya canja Mata da rainin wayo, sai kallon Ina na sanki Yake ma ta,Wanda take garawa tana juya shi son ranta shine ke Mata kallon banza!"Hadiye bacin ranta tayi tace bani hanya in wuce." "Mudi,Kara tare hanyar yayi tare da zaro ido,Yace"To Hajiya kimin gafara Amma mai gida ya CE"Kar na kuskura ko da wasa na Bari wani ko wata ya shiga gidan nan batare da izininsa ba!"Mutim daya ce ya bani umurnin na barta ta shiga idan tazo wato malama Nadiya." "Kai Dan Allah rufe min baki!"wato Ni din ce ma wata ko!?"Lalle mudi ka kusa rasa aikinka!Zaka San da Ni kake zancen.."Jalila Tace Cikin masifa tare da makale Jakarta akafada."Gyara tsayuwa tayi Tace"Wallahi ka bani hanya ko Yanzu in maka rashin mutunci ko Mai gidan yayi kadan ya hanani daukar Kayana agidan Nan bare Kai banzA Dan taho na taho cin ARZIKI Shiyasa duk yadda akayi da jaki sai yaci Kara kauyanci babbar cuta ce." "Dariya yayi har da shewa,yace na dai ji Hajiya Kinga bakauye ya samu matsayin sai da umurni na Kuma idan naso Zaki shigo gidan nan. Amma Yanzu naji magana Zan Miki alfarma,shigo Mana ay bansan kayan NE akazo kwasa ba!"Inji mudi tare da Bata hanya." "Tsaki tayi tare da hararsa ta wuce,aranta ta ci alwashin sai tasa Saddiq ya Kori mudi idan har ta dawo gidan jibi!"Zai gane ruwa ba sa'an kwandou bane." "Mukullinta tasa ta bude gidan,Bedrum dinsu ta nufa ta had'a Kayanta acikin akwatin ta karama, Dakin yara ta nufa..Wani Dadi taji da ta ga ba komai wayam,na kayan Nadiya,Dariya tayi Tace"Ruwa su iza harda matuka jirgi,Na rabu da shegia mayya,To ko'ina yakai su Mufeed oho!Wani sauyi taji Azuciayarta saboda tana son ganin yaranta!" "Inda kayan su ta nufa sai dai Babu dayan akwatin su,da wasu tufafin su,Shakka batayi yaran suna gidan Ali,idan hakane Kuma zataje har gidan ta dauko yaranta zuwa gidan su kafin ya maidata" "Ajiyar zuciya tayi tare da komawa falon share shi,tayi tsaf,bona ta jona tare da zuba turaren,ta ko'ina hayakinsa ke Tashi afalon."Zama tayi tana kallo sai da 6:35pm tayi Sannan ta Tashi ta dinga murza na jiki Domin tasan duk inda Saddiq din Yake Yana hanyar dawowa gida."Domin a masallacin Estate din Yake sallar magrip." "Gogawa take da murzawa ta ko ina..Jin Horn dinsa yasa taji dadi,gabanta ne ya fAdi ga koshi ga kwanan yunwa." "Da sauri ya fito motar,mudi na Masa sannu da zuwa ya wuce,baiko tsaya ba!"Lokacin sallah yayi kusa gashi Yana son ya watsa ruwa kafin yaje masallaci." "Janyo akwatinta tayi tare da tsayi abakin kofar, Tuni ta koma rufe kofar da key ta zare abinta,shima Yana isowa makullinsa yasa ya bude gidan,Yana murda kofar Jalila ma murdawa tayi,Shi zai shigo Daga ciki ita Kuma sai tayi kamar tana kokarin fita ne,A yadda suke tsaye kowannen su Yana jin Numfashi da bugun zuciyar dayan sa." "Ido ya zuba Mata cike da mamakin, me ya kawo ta gidan!?." "Ita Kuma kallon sa take,yadda yayi haske ya Kuma rame!"kamar bashi ba!" "Wani masifaffen turare yaji kamshin sa na fita ajikinta da gidan,Wanda yayi silar sarawar kansa."Ga kuma hayakin da ke Tashi afalon,kallonta yake cike da mamaki da Kuma tuhuma." "Hmnnnn, Saddiq kenan meye abin mamaki Dan na zo Naga gidana hargitse na gyara!?Meye Dan uwar yaranka tayi ma Shara ta saka turare!Karka manta ba kada Mata,Ay Taimakon ka nayi,Karka damu saboda har gobe Kai na Jalila ne ya kaga gidan ya sauya sosai zaman gidan ka Lafiya Dani a gidan nan da yarana ba tare da kowane bare ba!" Wani kallo ya ke Mata baiyi magana ba. "Am Saddiq Dan Allah kayi hakuri nasan abinda duk nayi sonka da kishinkai ne sanadi!"Amma kasani Wallahi an gaya min cewa soyayya kukeyi Kai da ita.." "DakAta Jalila idan kin Gama abinda ya kawo ki kina iya Tafiya... yace fuskarsa adaure!" "Wani shu'umin murmushi tayi na jan hankali, Tace" Shi kenan Nagode, Ina Mufeeda da Mufeed NE!?" "Bansani ba! ya Bata Amsa afusace!"meye damuwarki dasu yanzu Kika San dasu. "Murmushi tayi Trolley dinta taja tayi tafiyarta... ********* Sai ga Saddiq ya biyota da gudunsa Yana haki ya Fadi agabanta Yana Hawaye yace,My Jalila kiyi hakuri na mayarda auren mu Dan Allah karki tafi." "A Dan fusace Tace"Habibi ka barni na wuce mana kaifa kace na tafi na barmaka gidanka!" "Na tuba kiyi Hakuri kece Hasken gidana Kuma farin cikina Jalila ki taimakeni, Saddiq yace Yana rokonta!" "Dai-dai kofar mudi ta tsaya tare da Kallonsa Ina son ka,Kuma Zan zAuna da Kai har abada Saddiq,Amma ka amince duk abinda Nace bazaka musa min ba!?"Inji Jalila agadarance "Na yadda ranki ya Dade!"Saddiq yace Jikinsa na rawa."Ya rike akwatinta har da rataya jakkarta akafadarsa." "Mudi!mudi! ta Kira da karfi, "Da sauri ya zube agabanta domin ko Mai gida Gashi nan akasa bare shi,Yace Gani ranki ya Dade."Ayi Hakuri na tuba." "Dariya tayi harda shewa,Tace zaka San matsayina agidan Nan mudi,Ay nagaya maka." "Saddiq ta duba tace"Habibina ka gaya Masa ya daina Aiki Daga yau bana son ganinsa agidan nan..." "Kuka mudi Yake Yana rokonta." "Ita Kuma dariya take har da tafawa....." "Ganin da yayi Har yanzun shi take kallo tana kyalkyala Dariya,tana lumshe Masa ido!"Ya Kara tunzura shi!" Bangajeta yayi gefe! ya wuce ciki,tare da tura keyarta waje da akwatinta.."Yace Ina ga kin samu Matsalar tabin hankali Allah ya Baki lafiya..Inji Saddiq ya rufe kofar falonsa da key.." "Hannu Jalila ta aza aka, lokacin da hankalin ta ya dawo jikinta,Ta ce Yanzu Ashe ba gaske bane tunani nakeyi inama ace da gaske ne..."Inda mudi yake zaune ta kalla,Kuru ya zobou mata Ido Yana murmushi." "Kwafah!tayi tare da Jan akwatinta ta fita afusace!"Mudi Yace Allah ya kiyaye tare da rufe get din gidan." "Jalila tafiya take saman titi Hankalinta atashe, Trolley dinta take ja tana Hawaye!"Ga abin Hawa yayi wuyar samu!"Tunanin take shin, to me hakan ke nufi!?"Gashi dai ya shaki duka turaren Amma wulaqanci ya biyo baya!"To ko sai zuwa Bayan kwana biyu maganin zai fara Aiki!?"Kai anya maganin ya Kama shi kuwa!?"Saboda Yanzu Saddiq Yana da kokarin Ibada da tashin dare."Duk wad'annan tambayoyin da Jalila keyi batada Mai Bata amsar su."Dan Haka wayarta ta Ciro a jaka Domin ta Kira mansura ko zata Sami Karin haske." *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 *2020* *Share and comments* [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* _________________________________ ® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ _________________________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/ *SHAFI NA 24* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *"An karb'ou Daga Abiyh Hurairah, (R.A)"Yace"Manzo (S.A.W)Yana cewa"Lalle Allah ma daukakin SARKI,Baya Duba zuwa ga jikun kunanku,Ko Kuma Siffofinku,Sai dai Yana Duba zuwa ga zuciyoyin KU da Kuma Ayyunkan KU...."(Muslim)* _"Yaa 'yan uwanah Muyi kokari mu kasance masu zuciyoyi da ayyukan alkhairi, Mu gujewa bakin ciki da Hassada domin babbar halaka ce, Mu so Yan uwa, muyi zumunchi domin Allah, Idan Cigaba ya samu Dan uwanka ka Taya shi Munna domin Allah, Haka idan zamuyi ibada da aikata aikin Alheri muyi domin Allah, Fatana Allah ya dauramu Akan tafarkin gaskiya Ameen."_ _____________________________________ ***********$$** "Bayan sun taimaka min na shigo da kayan nawa,Tayani gyara su, sukayi tsaf a mazaunin su na da"Domin har yanzu ba kowa a dakin sai su,Tun Bayan tafiyata,Abinci Deejah ta zuba mana tare da su muka ci sosai,Wanda Rabona da in ci abinci da yawa irin yau har na manta." "Bayan mun kammala magunguna na fito da su nasha,Sannan na gabatar da sallar Isha." "Alkibla na fuskanta Na Dade Ina jera Addu'oin tare da neman mafita da sauki arayuwata." "Wayata Na dauka Na Kira layin Babana,Cikin Sa'a ya D'aga muka gaisa ya hadani da Innata mun Sha fira sosai da su,Har suke tambayana su Anty Jalila da yaran." "Nace lafiya qlaw." "Alkawarin da Na daukarwa Yaya Saddiq ya Sanya Ni Jin karfin boye masu damuwata har muka Gama wayar da su, Addu'oin fatan Alheri da nasarar karatu, Iyayena suka min." "Cike da Jin Dadi nayi masu godiya nan mukayi sai da safe." "Da murna tare da saukin kaunar su na ajiye wayar,sai Kuma Hawayen!da ke min sintiri a fuska,Tabbas ba kamar Iyaye Aduniya!"Wanda ya rasa Iyaye ya zamo abin Tausayi."Gashi yanzu naji Dadi da nutsuwa dalilin jin sautin muryar su." "Kawayena na Duba, suma dukkan su Ni suka zubawa ido,Tausayina NE kwance afuskar su,sai Zaman jirana suke domin na kwance masu kullin abinda ke faruwa..." "Inda suke na zauna,Ina fuskantar su na labarta musu komai Daga farko har karshe"Akan abinda ya faru da Ni." "Deeyart Tace"A GASKIYA Anty Jalila Bata kyauta ba!"To ita wa ya Gaya Mata hakan...!?" "Esha Tace shine fa tunda ke Naddy kince ko da zata fita bukin lafiya kalaw Kuka rabu da ita!" "Nace gaskiya hakane Bata nuna min komai ba! har fa abincin da Zan dafa sai da ta fad'a min,me Zan girka kafin ta wuce,nayi mata dawo lafiya.." "Deejah ta nisa tare da cewa to Naddy Ina ganin kamar awurin bikin birthday Nan aka hure Mata kunne, Sannan aka dasa makaman tsanarki da zarginku azuciyarta!"Dole mu binciki lamarin nan duk wacce ta hadaku tana da manufa akanki ko Kuma ta tsani Zamanki gidan!" "Nima hakan nake tsammani Inji Esha.." "Hakane gaskiya,Amma Ina ganin kamar kanwarta Rasheeda ce! saboda Bata wani yina sosai,Gani take na tare Mata komai agidan,Ada can rabin zamanta duk agidan NE!"To Tunda na dawo da Zama gidan, ita Kuma tayi hijira ta daina zuwa,Sannan kunga Anty Talatun nan Itama masifaffiya CE,tun farko ma ita ke kishina!A gidan bama Anty Jalila ba!"Nasha kamasu suna nunawa Anty Jalila illar zamana agida Suna yawan gulmata,cewa sukeyi tayi sakacin barina agidan!Ay yanzu an daina barin Yan matan Wannan zamani su zAuna maka agida,To inaga sunci galaba Akan Anty Jalila ne!"Amma Allah NE masanin gaibu ." "kun san wani Abu? nifa duk tsanata da suke wallahi ba komai yayi min zafi ba!"Sai kazafin da sukayi min, ita da Yan uwanta...nan take muryata ta kama rawa saboda kukan da ya zo min." "Kiyi Hakuri Naddy Allah zai saka maki!"Da ace Yaya Saddiq Bai dauki mataki Akan Jalila ba!"Wallahi da sai munyi maganinta mun ta da rashin mutuncinmu ita da shegun Yan uwanta jahilai duk sai sun gane KAWAI Daga Jin zance sai su hau kai!"Wataqila labarin wasu ne ma suka jiyo agidan bukin zasu huce kanki Inji Deeyart tana huci!."Tare da dafani tana rarrashina. "Eshaa Kam idonta ya cika da kwalla!"Tace Yanzu Naddy kina ganin ba matsala!?"zaman ki a nan.da kinyi Hakuri kin Koma tunda an d'auki mataki akanta. "Bazan iya Zama gidan Nan ba!Esha,Ina ganin hakan da nayi shi ne kwanciyar hankalina!"Amma ko da Yaya Saddiq, yayi min fad'a Zan Amsa laifina! Kuma na nemi afuwarsa, Amma fa Daga baya kenan!"Saboda na nuna Masa Ina son nadawo banga ya ce dani komai ba." "To Allah ya kyauta Inji Deejah. "Ameen,suka CE dukkan su, Daga Nan Kowacce tafara Shirin kwanciya, jiki dai ba Dadi! saboda an tabou Rabin ransu Naddy."Ko wayar da sukeyi tsawon dare da samari yau Kam an kasa!" "Tunda misalin karfe goma na safe Kiran mansura ya shigo wayar Jalila wacce ke kwance tana tunanin duniya.!" "Hello,Ta Daga wayar." "Anty Jalila ko bacci kike na Tashe ki?"Kiyi Hakuri! "A'ah mansura na Tashi.." "An Tashi lafiya ya gida Ina Yara da oga!?" "Hmnnn Nidai Ina lafiya sauran kuma ban San awane hali suke ciki ba!" "Waro Ido tayi waje!Da mamaki Tace Anty Bangane ba!Meke faruwa!?" "Jalila gyara Zama tayi ta labartawa mansura komai har da Karin Dan gishiri,cike da nadama take zancen har da Kuka Wai domin mansura ta tausaya Mata, ta taimaketa!" "Mansura kamar tayi gud'a dan murna,Amma kannewa tayi,Tace Yanzu ya sakeki akan Naddy fa Kika CE!?"Allah ya rabamu da sharrin wasu yan Matan zamani!"Ta zo gidanki ta fidda ke!Lalle Naddy bazata Gama lafiya ba,kuma ta cika maciya Amana!"Mansura Tace murya na rawa!" "Jan majina tayi alamun Kuka take,tare da canja murya zuwa kalar Tausayi Tace"Anty Jalila kiyi Hakuri in shaa Allah zaki koma gidanki!"Yanzu kiyi kokari kije gidan anjuma da yamma ko gobe,Da sunan kayanki Zaki dauko na sawa kingane!?"Hello Anty!kina jina!?" "Eh mansura Ina tare da ke!"Inji Jalila tana sheshshekar Kuka!" "Yawwa Anty,Idan kinje gidan sai ki turaren da maganin Duka,Amma fa ki daidaita time din da baya nan,Sannan kiyi zamanki agidan sai lokacin dawowar shi Yaya Saddiq din yayi,ki shafa Wanda akace kisa ajikinki,Ki tabbata ya shaki duka biyun,na jiki da na gidan."Sai ki dauko kayanki ki dawo."Sauran bayani zai biyo baya." "Kai!Kinfa kawo shawara Mai KYAU,Nagode kanwata Kinga ko tun Jiya na kasa bacci Ina tunanin ya zanyi!"Da maganin nan Amma gashi kin Samo Mana mafita Nagode."Jalila Tace cikin Jin Dadi da gamsuwa, "Haba!Anty Jalila ba komai,Sai jibi Zan shigo Ina ne ma unguwar ku!?" "Nan Jalila ta kwantata Mata tare da Kara Mata godiya ta datse kiran.,Sai yanzu tasamu karfin jiki, Tashi tayi domin ta watsa ruwa,ta Sami abinda zata jefawa cikinta." "Mansura ko Ina ruwan kankara ta fad'a domin Dadi abinda takeso ya samu godiya tayiwa Allah Sannan ta dinga Shirin fita class cike da Jin Dadi." "Hayaniyar da taji anayi afalon gidan NE ya sanyata fitowa,Ko Mai Bata shafa ajikinta ba!"Jallabiya KAWAI ta sabo ta fito da faduwar gaba!,Tahir ta samu afalon Yana ta zuba,Har da Marin Rasheeda!"Anty Talatun ma Sai sa'in sa suke da ita, tatas yayi musu tun kan Hajiya har Rasheeda." "Da sanyi tace Wai meye hakaTahir!?" "Ke munafuka kimin shiru ko na babballaki!"Sakarai! Wallahi kinyi asarar Miji!Baki sani ba!"Kuma sai kinyi Kuka,Wanga da kikeyi ba kuka bane!Har da danasanin ki,ya na nan tafe!"Kun san baku da gaskiya."Zaku wani tasani gaba na biku,To Gashi Nan munji kunya!"Wallahi naso ahada da ku, ukun nan ayi muku dukan tsiya arufe KU sai Kun ji ba Dadi..." "Sororo Jalila tayi tana kallonsa bata da halin magana saboda yadda yake tujara duk Wanda yayi magana zai iya mazgeshi Dan ba mutunci ne da shi ba!"Daman tun suna Yara ita ke Shan wuya hannunsa,saboda shi ke Binta"Kuma Tahir akwai zuciya Amma fa sai antabo shi!"Mutim NE Mai son yin rashin mutunci da hujjarsa!Shiyasa tayi ruf da bakinta." "Hajiya a fusace Tace Tahir ka fita idona na rufe! Iskancin ka ya isheni!Ita Rasheeda idan kanwarka ce!To Talatun da Jalilan ba yayyenka bane!?Sunji sun gode!" kaje ka bani guri yanzun Nan, tun ban maka rashin mutunci ba!" "Hajiya ai kin san ba ku da gaskiya!"Da Yake ba sonta kike ba!shine ni Zaki ga laifina Bayan ga 'yan ta'adda nan agabanki!" "Tatas!tas!tas! sautin saukar Marin da Hajiya ta saukewa Tahir ka keji!"Wanda sai da ya ga wuta!Tace naji Nagode fita daga falon nan,tare da nuna Masa hanya." "Idonsa sunyi ja! yace Zan fita Amma Daga yau bani ba shiga sabgar su! Tunda su basu tsare gaskiya! kuma ahakan kike goyon bayansu,Ni nafi son inyi masifa da dalili! da Kuma hujjata!"yadda bazanje inji kunya ba!kuma ba ZA'A Raina Ni ba!" Ke kuma duk kika Kara dauko gulmarki to kada ki dosoni,Yace ma Rasheeda Cikin fushi ya wuce Dakinsa tare da bugo kofar da karfi." "Ina nan tsaye Ina kallon Dan wahala!"Rasheeda Kam sai Kukan Marin da Tasha take,Anty Talatu da zagi ta bishi tana zatayi maganin rashin mutuncin SA!" "Hajiya Tace"KU barni da shashasha!"Ay mu ba kyalewa zamuyi ba!"Dole ne mu dauki mataki!Nan dai ta Cigaba da borin kunyarta ta gama!" "Kichen din gidan Jalila ta nufa,domin samun abin Kari,Sai dai kunu tasamu, bata fuska tayi cike da haushi!"Ta Dan diba a cup,ba ko suga!bare kosai!"Tana Sha sau daya ta aza hannu aka! Tana Hawaye!Saboda rabonta da shi tun tana jego!"Amma gashi yau Shi take Sha bako kosai!"Amma gidan Saddiq sai abinda Ranta keso Mai Dadi take ci ta Sha har ta aikowa Hajiyar ta." "Gashi ba halin magana ko korafi yanzu Hajiya tayi mata cin mutunci saboda ta lura tun Jiya tafara canja mata,saboda ita Hajiya idan dai ba bata zakayi ba!To zaku Sami matsala!."Idan Kaine zaka nema awurinta "Saddiq kam tun Jiya ya kasa sukuni,Abubuwa sun taru sun Masa yawa,shiri yayi, ya nufi gidan Ali, Domin ya ga yaransa."Ya samesu sun baje afalon gidan, basu da wata damuwa sun hade da yaran su Ali, Salma da Salim sai wasa suke da Yake duk tsara NE,"Numfashi ya sauke tare da basu sweets da ice cream din da ya saya masu da gudun su suka nufi bedroom Inda matar Ali take Umaimah suka nuna Mata!" "Amsa tayi ta rarraba masu da murnar su suka wuce wurin wasar su,A hankali ta tashi daga gaban madubin,mayafi ta yafa ta nufo hanyar falon.."A sannu take Tafiya saboda tsohon Cikin da take dauke da shi." "Da fara'ah ta samesu suna fira Tace"Manyan Baki sannu da zuwa." "Saddiq yace"Yawwa,Umaimah ya gida, maman Yara,Inji basa rigima!?" "A'ah basa rigima aini Kasan teacher ce nasan ta Yara.."Umaima Tace tana Dariya." "yace"Daman nazo na tafi da su ne!"Nasan su da rigima Gashi kina fama da kanki!" "Ina zaka Kai su Saddiq Idan ka dauke su Daga nan!?"Bayan ka Gaya min bazaka mayarda Jalila ba!?"Kuma Nadiya ta koma hostel!Kaine zaka zAuna da su ko kuwa!?"Inji Ali "Shiru Saddiq yayi,tare da sauke Numfashi yace"Ali ka fahimce Ni, rike Yara hudu ga lalurar ciki ba abune Mai sauki ba.."Awurin Umaimah "Umaima ta katse shi,Tare da cewa Saddiq kada ka damu Ni Banda damuwa na Saba da kula da Yara tun agidan mu,Ciki Kuma ay Kasan na daban ne!Bare ma jibi Suhaila kanwata zata zo hutu daga Kano,Anan zata zAuna har sai na haihu,kaga kafin nan ma ka mayar da Jalila." "Tana Dariya Tace"Kasan Ni da mijina ba yinmu Jalila take ba tun da muna fad'in gaskiya. naso na kirata na Bata shawara!Amma Ina da Tabbas ba dauka zatayi ba!"Sai dai Ina rokon ka kayi Hakuri ko domin yaran Nan!" "Wallahi Jiya Saddiq da kukana da hawayena! alokacin da nake jin Labarin nan awurin Abban Salim."Banso ka saketa ba!" "Shiyasa ma ba'a so gaya min ba!Dan kawai na matsa NE, da tambaya saboda Naga yaran wujiga wujiga afirgice!"kuma da dare!"Shine fa ya bani Labari Kuma su ma sun fad'a min duk kuskuren da Kuka Aikata a Gaban idon su." "Ali yace"yanzu dai koma meye ki tashi ki kawo Masa breakfast kinsan ya koma gwauro..sai da taimako Yana Dariya "To Bari mu taimakesa Tace cike da zolaya tana Dariya." "Saddiq ma dariyar yayi yace ba komai,amaryata na nan zuwa kwanan Nan."Zolayar zata zo karshe!" "Ba wata amarya shiryawa za'ayi da tawan,Ai Fadan masoya hutu ne Inji('Yar mutan Dikkawa)Umaima Tace tana dariya tare da kokarin Tashi." "Bayan ta wuce Ali yace"Karka damu Saddiq zamu kula da yaran ai abin ya zo da sauki Tunda a school daya suke karatu, ka hadou kayansu har uniform,ka kawo Mana,zamu rike yaran mu kafin kusan ciwon kanku.." "To ba damuwa,Zasu zauna anan idan anyi hutu Argungu Zan kaisu hutu,Ina son na shiga weekend din nan naje nayi masu bayanin komai,Saboda nikam aure zanyi ba Zan dawo da Jalila ba!"Yanzu ina son muje makaranta nasa anemo min Nadiya saina ci mutuncinta,Dan Nasan tana can!" "Kamar ya!?"Saddiq "To Tayaya Ali, zance kada ta fita sai bayan bana nan ta fita!?"In Banda rainin wayo!" "Karfa ka manta ka gaya min yadda kukayi da ita Kaine ka hanata Kuma taga Jalila tadawo inaga ta firgita da ganinta ne ta wuce Abinta!"Sam nikam Banga laifinta ba!"Kada ma ka soma ganin laifinta."Inji Ali "Nan Umaima ta dawo d'auke da kayan Kari,Amsa yayi ya dawo kasan kafet din hau ci harda su Santi sai da ya koshi." "Umaimah da Ali,sai dariya suke Masa tare k'ara zolayarsa." "Saddiq Yace"Sai kuyi ai ba abin kunya nayi ba!Domin agidana bana samun abincin yadda yadda dace,Zuwan Nadiya ne ma nasamu sararin yunwa." "Ali Yace"To Allah yasa MUDACE." "Amin,sukace dukkan su "Saddiq ya kammala cin abincin ya tashi suka fita,zuwa makaranta." "Umaimah ko kayan ta kwashe tare da gyara falonta, Saboda macece Mai tsafta,ga kirki da mutunci bugu da kari ta samu kulawa Mai kyau awurin iyayenta musamman mahaifiyarsa macece Mai kula da dagewa Akan yaranta" Shiyasa har yanzu Umaima ta kasance tauraruwa Mai haskakawa agidan Aliyu suna zaune lafiya da kuma yaranta masu matukar nutsuwa da tarbiyya. ********* "Zaune nake sun sani tsakiyar a faculty mu,suna min ya jiki da fatan samun lafiya, Nan ne suke bani Labarin gwajin(tests) da akeyi bana nan GSE 214,EDU 212,da Kuma ENG 222,."Duk sai naji banji Dadi ba!" "Saboda Yaya Saddiq ne ya gaya min cewa zaiyiwa malamman bayanin bana da lafiya, ya Kuma rokar min Alfarma agurinsu suyi min.."To Gashi yanzu na Masa laifi!"Yanzu ban San ya zanyi." "Naseer ne yayi Sallama wurin Amsa Masa mukayi Nan muka gaisa Daga bisani Wuri muka kebe muna tattaunawa tare da min ya jiki,Naseer yace a gaskiya Naddy Baki kyauta ba!ko Baki da lafiya ai sai ki bude wayarki Mana!Amma ayi ta neman ki akashe!"A gaskiya na shiga damuwa da tashin hankali!"Gashi Mallam Saddiq din ma ba shigowa Yake ba!sai da na Kira Yake sanar min bakijin Dadi." "Kayi Hakuri Naseer ba gani ba!?"Nasamu sauki." "Amma meyasa Bai sanarda Ni Kuna asibiti ba!?" "To Kasan kana karatu Kuma lokacin gwaji ne inaga Shiyasa baya so ya D'aga maka hankali!" "Allah yaqara sauki."Yace "Amin My Nass Nagode da kulawa."Nace Ina murmushi "Abubuwan da akayi bana Nan ya dinga koya min har su Esha suka zo suka samemu Nan Suma suka zAuna aka Cigaba da koya mana,saboda yanzu sai San barka sun fara hankali Zama tare da Ni wasu halaye nasu da dabi'u maras kyau duk sun ajiye su,A hankali fadakarwar da nake masu ta fara shiga jikin su."Hankalin mu kwance muke karatun mu"Malamin mu Naseer Kuma sai kokarin fahimtar da mu komai Yake daki-daki." "Yau Kam bakin mumy har kunne,Ta Sanya Mai aiki ta girka abinci kala-kala,Ta Sanya Saif da Jawad agaba aci Wannan aci wancan cike da nishadi."Lafiya kalau Jawad an warke kamar bashi ba!"Hankalinsa kwance ya cire duk wata damuwa,da tunani aransa ya sake sai fira da tsare-tsaren buki suke." "A yanzu kam ba abinda ya Sanya agaba sai auren Nadiya Balarabe."Haka mommy tana nan sai shirin yadda bukin zai kasance takeyi."Saif Kam shine atsakiya ko'ina shine gefen mom da Jawad,Domin ya zamou wani bangare na rayuwar su." "Malam kana jina!?" "Eh,Ina jinki." "Yawwa malam yanzu dai kaji duk yadda ake ciki." "Dariya yayi yace"Tabbas mansura kina da kwakwalwa Mai kyau,Ai kamar yadda Kika gayawa sakaryar,To shi ne mafita." "Kenan ba matsala!?"Inji mansura "Babu Nidai ya kasance shi Saddiq din ya shaki turaren na jiki da na gidan."Inji malam Zakiru Yana Dariya." "Malam nifa duk hankalina atashe yake Dan Naga ba'ayi turaren ba!Kuma dai naso ace Ina gidan zai saketa,nafiso Yama bani sakon sakin abaki ko a hannu na Gaya Mata!"Amma sai Gashi wawuyar tayi Masa iskanchi ya korata!" "Sheqewa yayi da wata dariya yace"Mansura kenan kina da Ni hankalinki ke Tashi!"Yanzu da yadda Kika Gaya Mata hakane!"Da zarar tayi turaren zaiji ya tsaneta Daga ita har Nadiya bazai Kara kula su ba!''Ke zaiji fa da ya gansu da Idonsa gwara yaga mutuwarsa Ido biyu." "Shewa tayi har tumami...Tace Nagode Mallam akwai goro na musamman sai na kayo maka." "Allah yasa Albarka sai kin zo mansuratu." "Tana ajiye wayar ta dinga tikar zawa har da su shoyki,Tana fadin _Idan babu kai Nima ba'a ganni ba!Yaya Saddiq mansura baby_ "Har bakin get din hostel din suke shi da abokinsa Ali,Maman Hostel wato Mai kula da Yan matan, Saddiq ya gaisa da ita kana ya bata cigiyar Nadiya."Amsa Masa tayi da yabari ta shiga ta bincikota." "Tsaye sukayi tsawon mintoci suna jiran fitowar mama,Amma shiru tsaki yayi yace"Ali mu koma Mota mu jirata,nifa cika son tsayi anan ba!"Kasan mata ba hankali ne da su ba!" "Ali yace hakane musamman Yan matan yanzu basu San darajar suturta jiki ba!"Ay ko iya su matan ne Ana son su rufe tsiraicin su."Amma aganin su sakin jiki agani burgewa ne sai kaga Mata na fitowa ba Kaya a jikinsu Wai hotel ne duk sune da hakan sure Lalacewar Suna bibiyar Yan uwansu mata." "To Ali abin sai dai Addu'a Inji Saddiq." "Hira suka Cigaba da yi Akan Abubuwan da ke gaban su."Can dabara ta fadowa Saddiq yace Ali Bari nakira yarinyar nan na manta tana da waya,Bari mu ga ko zan sameta, may be mama bata gane a inda take ba!"Wayar sa ya fito da ita iPhone 11 fara sol "Dialing...No *NADIYA* yayi Wanda Tuni ta shiga.........." *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 *2020* _Share nd Comments_ [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* _________________________________ ® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ _________________________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/ *SHAFI NA 26* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ _An karb'ou daga Abdullahi d'an Anas(R.A)Yace"Manzon Allah(S.A.W)"Ya ce"Zagin musulmi fasik'anchi ne,Yakarsa kuma kafirchi ne,(Bukhari da Muslim)_ ______________________________________ "Bayan wata d'aya, abubuwa da dama sun faru, Musamman agefen Saddiq, Wanda a halin Yanzu ba abinda yafi tsana! irin Jalila ko ganinta baya son a rayuwarsa bare ayi Masa zancenta." "Haka idan ya shiga makaranta, Nadiya ta same shi a Office dinsa domin ta gaida shi, duk sai yaji ya kosa Bata fita ba!"Saboda wani Abu da yakeji idan ya ganta kamar an daura masa dutsi aka,Duk sai ya damu,Shiyasa ko kallonta baya so saboda fargaba da Yake!." "Haka kawai ya rasa meke Masa Dadi a duniyar nan,Gaba d'aya jinsa Yake tamkar an canja shi,Tun Ranar da Jalila ta bar Gidansa ya shaki turaren gidan ya kasa samun nutsuwa da sukuni.."yaji Kuma ya tsaneta da Nadiya baya son ganinsu bare su zo kusa da shi. "A Hakan yake rayuwa Yana fita Aiki,Idan yadawo ya tafi restaurant ya ci abinci,sannan ya koma Gidansa,In Banda Tunani ba abinda Yake,Amma Yana ji azuciyarsa akwai wani Abu da take so na daban Wanda ya kasa gane ko meye." "Tsaye tana nazari magana ale Mata, Amma Ina Bata jin komai Dan tuni ta nutse duniyar Tunani..." "Jalila!ta sake Kiranta akarou na biyu"Da karfi! "Tagumin da tayi, ta cire da sauri tare da kallonta,A zabure...da sanyin murya Tace Na'am Anty! "Murmushi tayi sannan ta dafata,Zama tayi kusa da ita,Tace"Kullum fa Ina ji Hajiya na maki fad'a Akan tunanin Nan!Ki dubeki Dan Allah...Har kin wani canja wata daya kacal!"Duk kinyi bak'i kin rame Jalila!"kamar kanki aka fara fita gidan miji!karki manta Nima nan Daga can na fito kuma yarana Duka na Bari,kin sani har yanzu ban Kara ganin su ba!"Kiyi Hakuri Haka Allah ya nufa da mu!Daman abinda nayi Miki gudu kenan!"Inji Anty Talatu cike da damuwa da tausayin kanwarta, "Jalila Ta sauke ajiyar zuciya!Tace"Anty kina fa ganin yadda su Rasheeda ke mana cin Kashi agidan Nan,Amma Hajiya Bata Gani!Shi kenan Dan muna zaman gida sai adinga wulaqanta mu!''Nikam kowa ban daukarwa!Duk wanda yayi min zan rama!"Haba!Da me zamuji!?Da takaichi ko da Danasani!?"Wallahi Anty nayi nadamar zaman gida,ki duba fa duk abinda kake so gidan Nan Kai zaka saye da kanka Ni Yanzu ma kudina ya Kare ko naira bani da ita, Ban san ya zanyi ba!!!"Hawaye ne suka zubou afuskar ta, Tace Anty kina Gani Kayana kaf sunyi datti Banda sabulu! Kuma Ni rabona da nayi wankin da kaina har na manta." "Hmnnnn...Jalila kenan Hakuri zakiyi da Duk abinda Zakiji ko ki Gani agidan Nan,Shawarata daya ce ki kwaso kayanki,Abinda ya Kamata ki sayar asayarda shi,kudin kina samun na Jan jari,masu dama a ajiye Miki su,Ki dauko injin wankinki ki dinga wanki da abinki,Kuma Duk shegia ko katou, karki ba dama Dan za'a halaka Miki shi,abarki da cizon yatsa tunda ba mutunci ne da su ba!" "Yanzu Anty, tala, shi kenan bazan koma gidan Saddiq ba!?" "To Jalila,Sai naga Yanzu fa an kusan wata d'aya da faruwar abin nan ba labarin komai,kinga ko gara mu hakura,ki kwashe kayanki."har zuwa gaba idan da rabo Zaki Koma. "Nikam gaskiya ba Zan taba fidda Rai da komawa gidan mijina ba!"Ina Sonsa Ina kaunarsa ban taba zato ko tsammanin saddiq zai iya sakeni ba a yadda nayi imanin Ina so na!"Ban zaci zai iya rabuwa dani Rana Daya ba,Ya Allah kasa ya maidani ko Domin darajar su Mufeeda!!"Jalila ta karashe maganar tana zubda Hawaye masu d'umi. "Daina Kuka!karki sani zubda Hawaye!Ni Kaina Ina maki fatan hakan ki koma gidanki,saboda ko Yanzu mun ga izinah,kina Gani yadda Hajiya ta saka kayan dakina gaba sai da komai ya Kare!"Badan raina yaso ba!" shi ne nake jiye maki!"kinga tun hankalin ta Bai karkata Kan kayanki ba!Kiyi yadda na Gaya maki,Domin Inda shanuwar gaba Tasha ruwa ko ta baya can ta nufa......., "Amma Ina mansura!? ba naji Ranar kamar tace''zata dawo ba!?" "Anty Tala,Banda labarinta tsawo mako biyu,Kuma ko na Kira wayar mansura akashe nake samunta! Tunda na Gaya Mata nayi amfani da maganin nan,Ta zo gidan nan ta sameni mukayi magana, kina gani Babu ta, ba labarinta Daga lokacin,Kuma munyi da ita, zata yiwa mallam duk bayanin komai." "Da Naga an dauki lokaci ban ganta ba!Shi ne, na tafi da kaina,Wurinsa na Masa korafi akan magani baiyi ba,To nan nake jin wai mansura ta tafi gida saboda mamanta batada lafiya,Kuma an sace wayarta."Ina ga shine Matsalar!"Inji Mallam." "To shi Mallam me yace da ke da kika Masa bayanin!?"Anty Talatu ta tambaya "Yace min Yana Nan Yana iya kokarinsa ba dare ba Rana har sai anyiwa tufkar hanci,yace ba Domin tsari yayi yawa ajikin Saddiq ba da tuni an wuce gurin.Yawan ibadar da Yake da shiyasa abin yaki ya kamashi!Amma yace in Kara Hakuri!" "Ina gaya maki Anty ban bar wurin Mallam ba, sai da ya tatseni dubu bakwai shiyasa kinka ganni Banda komai,Ranar fa dubu biyar na ba mansura ta Kai mishi,Duk fa Yan kudaden NE da nake tatsar Saddiq na cefane!"Sune na hada kansu,sai ga Matsalar Nan ta samu."Yanzu Duk sun Kare!" "Yanzu dai Jalila ki raba kanki da yawon neman magani kina Gani duk can takalmina suka tsinke Kuma ba riba,sai tarin asarar arziki,ga dinbim zunubi,meye amfanin shirka!?" Wallahi nikam na tuba na daina saboda ko abin neman maganin banida shi."Daman can rashin ilimi ne,Yanzu Islamiyyar nan da nake zuwa na Gane Gaskiya. Addu'oin azkhar na safe da yamma sunfi duk wani magani da za a Baki Dan haka Ina maki tayin kema ki dinga zuwa islamiyya,zaman gidan nan Kara halaki zaiyi, ba uwa ba riba. Yanzu zamuyi ta Addu'a Allah ya yafe Mana, kuskuren mu na baya, yasa mazajen mu, su maida mu ga yaranmu Domin mu Basu kulawa Mai kyau." "Ameen,Hakane Anty,Nima nayi hankali Yanzu!"Abinda ake maki yau Nima shi ake min agidan Nan."Tun farko Mallam (Baban su) yayi Mana gudun hakan shiyasa yaso ya Gina rayuwar mu ta inganta amma Hajiya ta rusheta gashi Yanzu muna nadama Munyi Kuka har da Hawayen mu."Inji Jalila tana goge kwallah!' "Anty Tala ma,nata Hawayen ta share Tace"Hakane Jalila Allah ya gafartawa mallam."Bari na duba abinci, kin san Da zarar ta dawo gidan nan abin masifa take nema, ta nufi Kichen Inda take dafa abinci,saboda kamar ita CE Mai aikin gidan! Kullum Cikin aiki take." "Tsaki Jalila tayi Tace"Allah ya raba kowa da zaman irin na gidan Nan..Nima Shara Hajiya ta sani Bari na Tashi."Tsintsiya ta kwasa tun Daga bedrum din Hajiya har nasu da falon ta share tatas Ta kwashe sharar, Taje ta Fara mopping,tana Cikin gogegogen taji ta gaji Tsaki tayi ta ajiye Tace"Wallahi na gaji idan bazan ba! idan banzar can ta dawo Aiki, tayi idan zata iya,tana nufin (Rasheeda) saboda Yanzu tana fita aiki a wata firamare,shiyasa iskanci ya karu tana Jin sakon kudi Duk wata."shiyasa Daga ita sai Tahir akeyi agidan,shi Mahmud Yana MAKARANTA bawan Allah." Hajiya Atika ko sunyi tafiya ita da kawarta Anty saratu,sunje buki agarin shagari su dawo." "Zara akace bata barin Dame,Yau da gobe Kuma Bata bar komai ba,Cikin ikon Allah, Umaimah an haihu ta samu yarinya barkallah wacce ta ci sunan mahaifiyar Aliyu wato(Asma'u)inda suke Mata alkunya da (Khairat) ."Suhaila kanwar Umaima tazo an Sha shagalin suna an Gama Mai jego da yarinya suna lafiya." "Suhaila tana da kirki da hankali kamar yayarta,saboda tun asali sun samu tushe Mai kyau Awurin jigon rayuwar su Wato *MAHAIFIYA* Wanda *MAHAIFIN* su yayi nasarar samu a matsayin Macce Tagari ginshik'in gida." "Tun da Suhaila tazo gidan mafi yawan ayyuka suka dawo hannunta,sanda taga yaran,Nan take kaunar Mufeeda da Mufeed suka d'arsu a zuciyarta, saboda ta lura yaran na da hankali da gasu farare kyawawa barkallah"Ita Kuma Yara shiyasa ta hade su, da su Salim da salima,"Kuma tana kula da su sosai."Rayuwar gidan hakan ta Cigaba da Tafiya lafiya qlaw,gefen su Mufeeda da Mufeed ko Tuni momy Umaima ta maye masu gurbin Momynsu,Haka Anty suhai (da Yake hakan yaran suke kiranta )ta maye masu gurbin Anty Naddy,Dama can Duk Bayan kwana d'aya ko biyu Abbansu Yana zuwa gidan cin abinci,ya kawo masu alawa,Kuma ya gaya masu Momynsu ta kusa dawowa daga tafiyar da yace tayi."A hakan suka yarda tare da jiran dawowar Jalila da tsarabar da zatayo masu ba Adadi." "Tun lokacin da Anty jalilah ta sanar da ita cewa, Saddiq ya tsaneta,taje gidan sa yayi mata wulaqanci! taji wani Dadi ya mamayeta, saboda Aiki yayi kyau kenan, Daga ranar ta karya sim dinta, ta canja wani,Domin ta Riga da ta Gama da babin Anty Jalila kuma ta huce haushi Nadiya dan ta ci duka,Yanzu ta rufe babinsu na karshe basa gabanta."Kebbi ta tafi weekend asatin, sannan ta dawo"Wannan dawowar da tayi ta zo da Shirin tunkarar Saddiq."Saboda Haka da shirinta ta dawo na musamman,dama can Mallam ya Bata makaman Kare Dangi." "Duk wasu (C.A) namu mun kammala yanzu jarrabawar karshen zango na biyu ke gaban mu.."Karatu nakeyi sosai saboda naji ance Yan NCE 2 sunfi kowa carryovers a kwalejin,saboda anga zasuje (TP) first semester,Shiyasa na dage ba dare ba Rana Ina karatu,tare da taimakon Naseer."Har lokacin exam yazo,muka fara Cikin ikon Allah duk jarrabawar da na zana sai na amshi tambayoyin duka kamar yadda AKE buqata,daman na shiryawa exams din duka ga Addu'a inayi." "A yanzu ba abinda Yake damu na, sai yadda yaya Saddiq din ya canja min ga halin ko in kula da yake nunawa akaina,kamar bashi ba!"Sai dai ina masa uzuri Domin Yanzu ba shi da Mata nasan abubuwa NE suka taru su kai Masa yawa."A Cikin Raina har Tausayin SA nakeyi."Fatan mafita mafi Alheri nake Masa akullum."A gefe Kullum Sai Anty Jalila ta turo min texts din tsinuwa da Allah ya isa!"Sai nake ganin Tabbas Haka NE Domin nice sila!!!"Ba abinda nake so arayuwata face Yaya Saddiq ya mayarda Anty Jalila dakinta,shi NE damuwata,Wasu hawaye!Na share afuskata, Allah SARKI su Mufeeda ko Awanne hali suke!?" agaskiya Ina Tausayin yaran.."Nidai Allah ya daidaita Kan iyayensu su shirya Amin."Nace Azuciata cike da rashin Jin dadin Wannan kaddarar." "Cikin Dan lokaci muka kammala exams Nan aka bamu t.p form dinmu,Domin mu zab'i Inda muke son zuwa." makaranta uku na cika mafi kusa ga unguwar mu,da ke Argungu,Sannan mukayi submitting,Ranar da muka kammala exams, Ban kwana mukayi da abokan karatun mu cike da kewar juna,." "Muna Tafiya da su Esha zasu rakani Office din Yaya Saddiq Domin na fada Masa Zan wuce gida, na Gama exams dina." "Ni da su tafiya MUKE muna zancen Duniya,Da Yake Yanzu Ina zuwa Office dinsa da su, shi da kansa Yasan kawayena sun tashi daga watsattsu Marasa ta Ido sun dawo masu hankali da nutsuwwla. Dan Ni da su ba bambanci tun kan shigarmu har halayen mu iri dayane."Ko munafuki ya dubesu yasan cewa sun canja Kuma sun tuba sun daina komai," "A hanya muka hadu da malamin da ake Kira M.Bala,gaida shi mukayi Dukkan mu da girmamawa,Amma Idonsa na Kaina." "Da kyar ya Amsa Mana gaisuwar muka wuce." "Ashe kowa acikin mu cike da tsoron sa yake." "Deeyart Tace Wallahi Ina jin haushin Dan iskan malamin nan!"Idan na ganshi kamar na halaka shi,mugun son Mata da kallon tsiya gare shi,Allah dai ya tsare mu da maitarsa." "Esha, Tace hmnnnn Amin, inda ke kadai CE da nayi maki Barka!"Bai da mutunci, yafi na hannun Daman shaid'an bala'i!" ya rike mutim har ya manta da Takardunsa na NCE,ba komai ba nei!"A wurinsa saboda shi Sam bai san mutunci ba!"Kinsan ko ya taba turo student affairs wurin mu tun muna FARKON shigowa makarantar Nan ko kin manta!?" Deeyart tace kwarai kuwa na tuna, a lokacin Muna Cikin hayakin mu, Ammah ko yanzu Allah ya tsare mu da masifarsa." "Ameen,Wai Kun san me,shi fa" M.Bala da zarar yace Yana sonka kace baka Sonsa, shi kenan,Ka shiga matsala!Ga shi mugu sai a NCE 3 zai fara daukar mu...Inji Deejah "Hmnnnn,mu akwai Dan iskan malamin da zai Mana iskanci!? sai dai yaba wasu carry-overs ba dai mu ba..ko dan k'ura tayi lafiya gaskiya mun bar recard ko Yanzu"Deeyart Tace tana Dariya." "Murmushi nayi nace Allah ya shirya." "Ameen,Ustaziya Nadiya Balarabe ai Mungode maki Dan sanadin ki muka dawo Hala har ake Mana kallon mutanen kirki sabanin a da.."Inji Esha tana Dariya tare da rika hannuna." "Nan muka Isa Office din Yaya Saddiq da Sallama muka shiga muka zAuna."Tare da gaida shi "Ko kallon mu baiyi ba fuska ba yabo ba fallasa yace"ya akayi..!?"Yana Cigaba da rubutunsa akan takarda. "Daman Yaya na Gama zana jarrabawa ta yau,Zan wuce Kebbi shi NE nazo na Gaya maka." "Okay,muna gaida su Baba idan kinje,yace tare da bude wallet dinsa dubu biyu ya Ciro amshi Wannan ki shiga Mota." "Da ka barsu Yaya ina da kudi a hannuna, Nace Raina ba Dadi! saboda naga kamar Wanda akayiwa dole!" "Mayarda abinsa yayi yace"To ALLAH ya kiyaye."kuna iya Tafiya." "Bani ba!har su Esha Sunji wani iri ahaka muka jawo takalman mu muka fito Daga Office dinsa."Ba Wanda yayi magana sai da mukayi nisa Sannan Deejart Tace"Nifa Ina ganin kamar Mallam sakin matar nan da yayi ya tabesa." "Hakane,saboda tun lokacin ya canjawa Nadiya Inji Eshaa "Yadda naji zuciyata na suya ko magana bana Jin Zan iya." "Haka suka dingA zuba bance da su komai ba saboda ban taba ganin Yaya Saddiq yayi niyyar kyauta Dan Kawai ance ana da, ya mayar da abinsa! ay idan da NE cewa zaiyi to ki Kara kan Wanda kike da shi." "Allah Mai iko.."Da tunanin na shirya tsaf tare da had'a duk kayana, Ni da su Esha su wuce napep D'aya muka shiga sai Tasha,daga Nan kowa ya shiga motar garin su harda Hawayen mu na rabuwa saboda Yanzu zamu Dade bamu dawo makaranta ba." "Tun Bayan sallar Azahar take fidda kalar tufafinta sunfi akirga da ta dauko Wannan ta mayar ta canja,Sai can ta sake fito da wani material kalar lemu Mai fulawowi farare Wanda aka kawata da stones ruwan kwai,yayi kyau sosai dinkin Riga da siket NE mayafi ta dauko da takalmi ruwan kwai."Kayan ta SA ajikinta sun amshi jikinta tsaf,Daman tayi simple makeup,gyalen ta yafa tare da daukar karamar jikkarta,Turare tasa ajikinta ta fice Daga Dakin." "Tafiya take kamar zata Karye Dan yanga!" "Haduwa tayi da jamcy kwalba,Tace A'ah su mansura lashe money sai ina Wannan wanka haka!?" "Murmushi mansura tayi tace''Cikin gari zani! Kedai kwalba sai na dawo?" "To Allah ya ba da nasara, ta kwana CE ko dawowa lashe su tatas!?"Inji jamcy kwalba "Tsaki tayi Tace bansani ba!" "Dariya jamcy tayi,tace to shi kenan kifi dai na ganinka Mai jar home, sannan ta haye saman dakinsu da Yake su mansura Daman dakinsu akasa yake." "Kyaji da su idan kaya ne....inji mansura ta fice abinta Sauri takeyi karta je bata sameshi ba,saboda Mallaman admin wasu basa Kai yamma a makaranta."Kamar yadda aka kwatanta Mata Office dinsa,Haka ta sameshi manne da sunansa da aikinsa." "Knocking tayi kusan sai a na uku Sannan aka Bata izinin shiga,zuge jikkarta tayi ta dauko turaren Mallam ta shafa ajikinta Sannan ta shiga da kafar hagu kamar yadda Mallam yace"Idan Kuma zata fito sai ta fito da kafar dama." "Ba damuwa tattare da ita ta tura kofar ko sallama batayi ba!"Domin Mallam yace ko auren Saddiq din tayi karta kuskura tayi Sallama Dan kuwa zata Kore shaidanu da ke taimakonta." "Tunda ta shigo ya zuba Mata Ido,jinsa yayi tamkar an sauke masa wani katon Abu akansa,Wata walwala ya samu ajikinsa,kamar an kwance masa shi,Daga dauri kwana da kwanaki.." "Ta lura da halin da ya shiga,shi ya Bata karfin gwuiwar Zama Akan kujerar da ke fuskantarsa."Hankalinta kwance, "Cike da yanga ta gaida shi,Yaya Saddiq Ina wuni." "Kamshin ta shi yafiso fiye da komai ahalin Yanzu,A wahalce ya amsa Mata."yawwa mansura!"tare da lumshe Ido. "Da mamaki ta dubeshi shi Jin ya ambaci sunanta kamar ta buga shewa, Dan murna sai dai kannewa tayi Tace"Daman nazo mu gaisa ne,saboda bana iya rayuwa banganka ba!Dan Allah Yaya Saddiq kace"kana Sona ko sau daya NE!"Saboda sonka baya Bari Naga wulakancin da kikeyi min Kuma baya barin nayi fushi dakai hakan ba zai barni na barka ba. "Hawaye NE suka zubou Mata!tana kokarin shafewa da gyalenta, Tissue ya Bata yace share hawayenki mansura,Na yarda da soyyayar ki saboda Allah NE mai daurawa mutim nasan ba yinki bane,Da yinki NE da kin d'ebeta tun Ranar da na fatattake ki!"kiyi Hakuri na amshi tayin soyyayar ki Mansura." "Murmushi ya bayyana a fuskarta,Cikin kissa Tace"Nagode Yaya Saddiq,in shaa Allah na daukar maka alkawarin Zama da Yaya Jalila da yaran mu lafiya."Idan har zaka aureni "B'ata fuska yayi alokacin da ta ambaci Jalila!...sai dai Kuma yak'e yayi yace Nagode." "Tashi tayi to Yaya Ni Zan koma Daman tahowa nayi na ganka Kuma na ganka harda tukuicin ziyara an bani Ni kunya ma ta kamani,A gaskiya zuciyata batayi min Adalci ba, Duk samarin da nakeda su, da irin aji na a matsayina na babbar yarinya Mai farin jini amma take zugani Ina yawon maular masoyi Bayan Ina da dubban masoya agefe Mansura Tace cikin sigar Jin haushi da takaicin kanta tana goge hawaye." Kiyi Hakuri da rayuwa mansura Daman hakan ta gada, muje in saukeki Daman Shirin fita nake." "Fitowa sukayi ya rufe Office mota suka nufa,A hanya sai da suka tsaya AGG MALL yayi mata shopping Sannan ya ajiyeta get din makarantar su tare da amsar lambarta." "Godiya tayi Masa tana wani narkewa kamar saliha ta gari." "Shi kam aransa cewa ya ke hakika ya samu matar aure,Nan ba da jimawa ba!"saboda duk yadda yake son macce ashe Mansura ta wuce nan."Da farin ciki ya isa restaurant ya ci abinci direct gida Ali ya nufa." *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 _Fans nasha wuyar typing dinnan....Comments naku shi zai fanshe ku, nayi wani post da wuri,yanzu Kam Dabara ta ragewa Mai......._😊 [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* _________________________________ ® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ _________________________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/ *SHAFI NA 27* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *SADAUKARWA GAREKU" 'YAN MATA ADON GARI, NAJAH, ZARAH, MAMIEH, MADAWAKI SAI RAMLAT,NAJAH,KHADIJA DIKKO,TARE DA USAINAH JOLLY DA FARIDA JEGA ALLAH YA SANYAWA RAYUWAR KU ALBARKA AMEEN, YA NUNA MIN RANAR AUREN KU 'YAN MATANA❤* _DAN ALLAH KUYI HAK'URI DA TYPING ERRORS DA AKE SAMU,A GASKIYA INA IYA K'OKARINAH WURIN EDIT, AMMA DUK INDA AKA SAMU KUSKURE KUNA IYA GYARAWA, PLS!,KUN SAN ANCE" DUK MUTUM D'AN TARA NE, BAI................😊_ *NAGODE.* ______________________________________ ************* "Ba'a d'auki lokaci sosai ba, sai gamu mun sauka garin Argungu lami lafiya, Unguwar mu na wuce da Mai Napep,Cikin Jin Dadi da daukin dawowa gida, alokacin da aka ajiye Ni, na sami Yaran da zasu shigo min da Kayana Cikin gida." "Da Sallama na shiga gidan, Innata na sharar tsakar gidan,ta jefar da tsintsiyar da Murna ta tarbeni,Tace"min sannu da zuwa."Yan makaranta,malama uwar 'yan Yara." "Dariya nayi Wacce ta qara bayyanar da murnata fili,Nace" "Yawwa,mama ya gida ya Bayan rabuwa."tare da rungumeta," "Lafiya qlaw, "Nadiya ya MAKARANTA an Gama jarrabawar ko!?" "Eh mun gama...Mama Ina Baba?"nace Tare da duba gefen kofar dakinsa sai dai arufe." "Mama Tace"Yana nan,tun dazu Yana zaman jiranki,yanzu dai ya fita ya dawo, yace wai"Kafin ki iso." "Allah sarki Babana." "Kayana yaran suka dingA shigowa da su." "Amsa Ina kaisu dakina,Tare da masu godiya,Naira dari na zaro ajakata na basu nace"su Sha alawa Dan yau ban samu yin tsaraba ba." "Amsa sukayi,suna murna suka fice."Ni Kuma tsintsiyar da mama ke Shara da ita na d'auka na share dakina tas,na kunna turare,har filin gidan na ida sharewa Sannan na shiga bayi na watsa ruwa,Ko da na fito na samu Mamana ta ajiye min abinci da sauran tarkacen kayan kwalam,Tace duk Baba NE ya saya min." "Shiryawa nayi tare da saka atamfa Super batik Mai ja da baki,dinkin doguwar Riga ce,ta amsheni sosai,Duk da ba kwalliya nake ba amma nayi kyau da haske,fitowa nayi Dakin Ina zuba kamshi,"Mama sai faman kallona take tana washe baki,Nima dai wani Dadi nakeji araina,ganin yadda iyayena ke kaunata,Basu da buri illa su ganni a cikin farin,Zama nayi kusa da ita,abincin na fara ci sosai tuwon farar shinkafa ne,da miyar taushe,agefe an had'a min fura,Da soyen nama."santin abinci nakeyi mama ko dariyata takeyi." "Sai da nayi hani'an Sannan na dauki raken da mama ta gaya min Baba ya sayo min,Da magarya ga kuma yalo duk Ni daya''A hankali komai sai da ci na kayan kwalam."Cikina ya cika sosai,Sabon babi fira muka bude Ni da mama."Na Bayan rabuwa da Yan uwa da Abokan arziki, ''Mama Tace shin Ina Mai gida da kishiya ko saqon gaisuwa Babu?" "Murmushi nayi nace"mama kinyi gajen Hakuri amma duk fa sunce agaishe ku,mantawa nayi Ban fad'a da Wuri ba,A gaskiya mama Anty Jalila da Yaya saddiq suna da kirki kwarai, sun d'aukeni kamar k'anwar su ta jini,komai sunayi min sai dai Ku bisu da Addu'a," "Dariya mama tayi Tace"Nadiya Barewa batayi gudu d'anta ya gaza rarrafe ba,"Ai Jinin Mallam musa,Dole ne yayi kirki,Kina ganin yadda yake kula da malam,Abota CE fa,Amma tamkar Yan uwanta ka ta jini, Allah dai ya saka masu da Alheri." "Amin,Nace Ina Danna wayata." "Amma Nadiya Naga kamar kin rame!"Mama ta tambayeni da yanayin damuwa tana dubina "Mama Dole ne, Na canja ai! wahalar jarrabawa ce!Kuma nayi zazzabin mura na kwana biyu."Yaya saddiq har asibiti ya kaini aka bani magani." "Bawan Allah, lalle ya dauko halin mahaifinsa,Haka ko marigayiya mamansa take da Alheri,da mutunci,Kin ga ko Yanzu matar ubansa gwaggo akwai mutunci da Alheri,Shiyasa Saddiq ya samu *TARBIYYA* mai kyau awurinta, a gaskiya yayi sa'ar uwar riqou, Allah dai ya saka masu da Alheri ya bisu da halayen su masu kyau" "Wayar da nakeyi ne ta katse zantukan mama." "Tashi tayi ta nufi tsakar gidan,Tana aikace-aikace Domin lokacin daura sanwar dare ya gabato." "Ni Kuma su Esha na Kira dukkan su, kowannen su ya shaida min ya sauka gida lafiya,Nima na shaida masu gani a gida Cikin aminchi. Naseer na Kira na fad'a Masa na iso lafiya, Shima godiya yayi min tare da cewa sai anjuma idan munyi waya," Yaya Saddiq ko sako na aika Masa da shi, kamar haka ; Assalamu Alaikum, Yaya ya gida? ya aiki? Alhamdulillah Allah ya saukeni gida Lafiya. Nagode, su Baba sunce gaida da kai da su Mufeeda._" "Daga nan sauran Abokan karatuna na dinga Kira har sai da katin wayana ya kone Duka, Sannan na Tashi na nufi madafa Domin Taya Innata Aiki,Tare da shaida mata duk kawayena na gaidata." "Ina Amsa masu,Allah ya Baku Sa'a da nasarar jarrabawa yayiwa rayuwar KU ALBARKA."shine amsar da mama ta bani." "Cikin Jin Dadi Nace Amin mah." "Tace Da kin ajiye aikin Nan Mana ki huta!"Haka, "A'ah mama Bari in daura ba tuwon garin masara NE ba!" "Shi ne, Kinga sai muyi amfani da sauran miyar Nan ko?" "Eh,naga kamar zata ishemu,Bari Kawai nayi tuwon mama."Nace Ina murmushi "Itama yake tayi,Tace to shi kenan bari naje nayi kullin kayan yaji Kar azo saya babu kullalli."Inji mama tana kokarin fita Daga madafar, "Fita tayi zuwa had'a Kan kayan sana'arta,Ni Kuma kokarin talgen garin nake,Dan ruwan na ta tafasa."Sak'o naji awayata Ina dubawa screen din, sunan Jawad NE ya bayyana, murmushi nayi,Na k'osa na Gama tuka tuwon na bude sok'on boyayyen masoyina,saboda Yanzu Ina jin dad'in karatun sak'onninsa na soyayya,Saboda ya iya tsara zantuka da kalamai masu shiga Rai,Kuma Nima Ina mayar Masa da martani masu dadin gaske."Amma a zuciyata Babu wani sonsa araina kawai Ina kokarin biyayya ne." *********** "Kamar yadda Anty Talatu ta baiwa Jalila shawara hakan ce ta faru,Domin yau tun da safe sukaje ita da Tala da Rasheeda ta kwashe kayanta kaf,Agidan Saddiq,Har kayan su Mufeeda da Mufeed ma wadanda ta samu ta kwashe su Sarai, ta dawo da su gidan su."DOMIN ko su Shirin zuwa gidan Ali take, ta dauko yaranta su dawo hannunta." "Bayan an Gama loda kayan Duka a Mota,shiga sukayi Domin barin gidan,Yaran Estate din sai kallonta sukeyi,Abu ga bariki ba Wanda ya damu da Jin ba'asi,bare ma ita da ba ruwanta da kowa,Duk abinda ya faru Murna ko jaje ba zuwa take ba, yawonta Cikin gari ne,"Motar na Tashi Nan zuciyar Jalila ta tsinke! batare da saninta ba!Ta dinga Hawaye kamar an bude famfo!"Anty Talatu ta tausayawa kanwarta itama hawayen takeyi."Tare da Bata baki,." "Rasheeda Kam sai tsaki take da kwafa tare da cizon yatsa."Yadda Yan uwanta ke Kuka Akan wani katon banza!" "Jiki ba kwari suka isa gidan su,inda aka sauke Kayanta,Dakin marigayi aka loda kayan Duka, katon mukulli jalila tasa ta rufe Dakin,tare da boye mukulli ta,"Hajiya cike da mamaki Tace"Yanzu ke Jalila Kuka NE kikayi!"Ita wannan har da tayaki!"Tana nuna Anty Tala da jiki duk yayi Sanyi," "Kallon Rasheeda tayi afusace Tace"Anya Rasheeda kina gamawa lafiya,Ace Baki zauni komai ba, sai kaji, ka Gani!"Yanzu da dawowar mu ko Zama bamuyi ba,Har kin samu kin yad'a gulma....Inji Anty Talatu."Cike da takaichi." "Bawani Anty Tala ai dai gaskiya na fad'a ko kuwa bakuyi Kuka ba!?tun kofar gidan Sadiq kuke rusa Kuka har muka iso gidan nan"Rasheeda ta CE tana yatsina fuska," "Ita kam Jalila tsaki tayi tare da hararen Rasheeda,mangajeta tayi ta shige dakinsu Kai tsaye,Domin ita kadai tasan meye Matsalar ta." "Hajiya mita da fad'a ta Cigaba da yi, ta inda take shiga ba ta Nan take fita ba!"Tare da Allah wadai da sauyawar halayen su,da sukayi sanadin mutuwar aure!" "Anty Tala ma gajiya tayi da saurareta,ta fice zuwa sha'aninta."Tana mita da zagin Rasheeda" "Nan fa Rasheeda ta zAuna sai abinda ta manta zuga Hajiya kawai takeyi,A falon Tahir da ya dawo Aiki ya samesu,Tambayar Hajiya yayi lafiya da wa take masifa hakan!?"Tun waje Yake jiyo harshenta! "Ba Dole ba, Tahir Ni da su Talatu ne Mana, ba nan jiya Nace ka bani dubu biyar akwaso kayan Jalila ba!"to shine sukaje dauko kayan hadda Kuka agaban Mai gadin gidan da Yara!"suna kallon su kamar Yara salon Dan iskan yadawo su fad'a Masa yaji Dad'i!.."Hajiya ta karashe zancen da karaji cike da bacin Rai!" "Hajiya ai Dole suyi Kuka Mana!Yanzu Akan shi kike kumfar Baki!?"Haba mutuwar aure!Babban abune,Allah dai ya Basu Nagari Idan da gyara Kuma ya gyara saboda Duk mazajen su na da kirki, musamman shi Saddiq din Ina yinsa over..."Inji Tahir "Dan Allah kai DakAta!Gyara fa kace!? Allah dai ya Basu wasu masu kudin gaske,yanzu kai jibgi Yar uwarka kamar Jaka! zakace Yana da kirki,Wallahi Ni bana fatan su koma,shi wancan Dan iska ko diyan bai kawowa Talatu ta Gani,Banza komai Daren dadewa Yara sukasan ciwon kansu zasu kawo kansu gidan nan ko da Zai mutu ko!."Shi Kuma Saddiq ko ya kawo yaran nan sai nayi masu wulaqanci Domin yaji zafi,ba Dan ban sonsu ba!"Dan kawai aymasa bakin ciki!" "Hmnnnn,Hajiya ita fa Anty Jalila, Yanzu hakan ta kwaso duka kayan su Mufeeda, Wai dauko su zatayi naji tana Fadi ko gidan Umaimah ohonta dai,... Rasheeda Tace tana tabe Baki,tare da nunin kofar Dakin da Jalila take da idanu da baki" "Shureta! Tahir yayi da kafarsa iya karfinsa! yace"kinji munafuka Ahlin Dan ubayyu!Sai munafunci ya kasheki banza!ki fita falon nan ko na halaki,Mai bakin jakkai..." "Haba Tahir Wai meye Wannan, Haka kawai!"Wallahi Karka k'ara ai zalunci ne Dan Allah bana so!Kun tsani yarinyar nan me ta tare maku,Nidai Allah ya nuna min kayi aure kabar gidan nan ko ta huta."Inji Hajiya. "Rasheeda sai b'ata fuska take!harda su hawayenta Domin taji shurin a kugunta sosai,Amma Cikin sanyin murya da alamar Kuka!"Tace wallahi Hajiya ko aure yayi can zamu bishi aci arziki damu, Dan bazata sabou ba, ki haifowa uwar wata D'a,ta ci moriyarsa fiye da ke,gara muje akwashi gara da mu.."ai gumin jinin mu ne...." "Tabbas hakane Rasheeda ta.''Inji Hajiya tana Murmushi Tace kin kawo shawara Mai kyau Dan bazanyi haihuwar nan ta da ka aifi dan sarki gwara matar sarki.to ni Tahir Dina sarki ne Wanda Ni Atika Zan mulka ba wata ba. "Tsaki yayi, ya Nuna Rasheeda yace Ke ai ko gawarki bazata zAuna agidana ba!Dan zata iya kashe min aure a kwance"Can dai Allah ya kawo Mai so," "LaaaaaahHajiya kinji shi ko!.." "Bata karasa ba, ya Taso gadan-gadan yayo kanta Aiko da gudunta ta shige Dakin su, tare da rufe kofa tana haki!" "Yace,Da ki tsaya in karyeki!"Uwar gulma."Kayansa ya kwashe ya nufi Dakinsa."Yana tsaki, "Hajiya Tace" ai ba gulma gaskiya ta FAD'I,Kuma Ina ganin hakan ma za'ayi,Dan bazan lamunce da haihuwar nan ta, gwamna gara matar gwamna ba,"Dole in kula da dukiyar D'ana." "Wayarta ta janyo tare da Kiran mah'mud Tasha Hira da shi,sosai Nan ma yake shaida Mata zasu dawo jibi idan sun gama final exams (jarrabawar karshe)." **********"Haba!Haba!!Haba!!Wace Nadiya Kuma!?" "Karka SA nayi nadamar fad'a maka zancen Nan Ali."Saddiq yace fuska a turmuke! "Murmushi Ali yayi tare da kurb'a drink,ya mayar da cup Kan stool din da ke gabansu a cikin kayataccen falon su ruwan purple Mai haske ." " ya dubeshi tare da nazari na Yan dakiku Sannan,Yace" Saddiq Ni agaskiya banji Dadi ba!" saboda Nadiya nakeso ka aura!kaga Kun Saba da ita Kuma yaranka zasufi Jin dadinta,Kai da kanka ka Gaya min cewa itace tayi namijin kokari awurin kula da rayuwar yaranka!"Da kulawa da abincinka da na yaran Nan, "Na tabbata wannan mansura da kake magana akanta baza tafi Nadiya ilimi ko Kuma wani abu ba, Duk da bansanta ba, ban Kuma San halayen ta ba,"Amma nasan samun halayen kirki irin na Nadiya a duniyar Yan matan zamani,to sai an sha fama,Amma kayi tunani!" "Numfashi ya sauke da yanayin ko in kula,yace a gaskiya naso Nadiya amma alokacin da Jalila batayi Mana Wannan kazafi ba Ali,Yanzu Kam bana jinta araina,saboda Idan na aureta yanzu kaga zargin Jalila ya tabbata kenan,Ace da gaske NE muna tare!,Alhalin ko da wasa Babu maganar soyayya atsakanin mu,Asalima nine naji tana burgeni akan halayenta da Kuma *TARBIYYAR* ta,Silar hakan naji na kamu da sonta,Ada kenan Banda Yanzu," "Kuma Kai kanka Kasan bana son raini, Nadiya yarinya CE,da zarar na aureta zata rainani ta daina bani girmana,kaga ita mansura na san da gani ta girmewa Nadiya, Duk da bansan shekarunta ba!"Amma basuyi Kai daya ba,Had'uwar Mota CE silar abotar su da Nadiya,kaga ko shekaru ba daya ba...!" "Saddiq kana nufin ita mansura Kawar Nadiya CE!?"Inji Ali da mamaki "Eh,kawarta CE, hasalima Akan Nadiya nasanta,tana zuwa gidana,Amma yanzu kamar basa tare, Saddiq yace Yana kallon Ali,da ke Masa dubin wani iri," "Me ya had'asu to!?" "Tsakanin su ne,nikam bansani ba!Kuma bana buqatar sani, yace Yana kokarin Kai kofin lemo abakinsa." "Ina son ka fahimce ni Dan ka auri Nadiya ba shi zaisa ta rainaka ba,sau nawa akayi miji ya auri sa'an yaransa...Yaya ya auri sa'an kannansa,Meyasa ka cika son girma ne!?" "Ni gaskiya Ina son ka mayarda Jalila Sannan ka auri Nadiya,ka hadasu biyu Domin wanke kanka, iyakaci kayi tsaye agidan ka,nasan ko Yanzu Jalila ta horu saboda zaman gida sai dole!" "Dan Allah ka rabani da zancen auren matan Nan biyu Idan zakayi min fatan Alheri Ni da Mansura kayi min,ita nakeso,Amma na tsani Inji KO da sunan Jalila NE!bana so,Nadiya Kuma Nace banaso Idan zaka iya Kai ka aureta!"Nasan me nakeyi Ali,Ka adana shawararka Nagode!"Inji Saddiq afusace tare da dire kofin ya Tashi tsaye Ni Zan wuce,Naga yaran basu dawo ba!" "Tashi yayi tare da sanya hannuwansa a Aljihunsa yace"Saddiq na gane kayi nisa acikin duniyar so,bakajin kira,Amma bakomai Allah ya SA hakan Alheri NE," "Kasani,Da ace Umaima na buqatar Abokiyar Zama, da nazo gareka kamun kafa kabani auren Nadiya, domin na yaba da halayenta, Amma Kasancewar Kasaitacciyar macce Tagari kamar Umaimah, Bata buqatar Karin Abokiyar Zama,shine kawai dalilana da bazan auri Nadiya ba. Allah yasa mansura ta zamo Alheri gareka Ina maka fatan Alheri," "Dariya Saddiq yayi yace haba Yanzu naji magana Mai ma'ana,To Ameen."Ka tayani Addu'a kawai,Amma fa ko Yanzu kofarka abude take, Dan hud'u akace kayi,ga d'ayar sauran uku,"Amma kasan Nikam Ina layin Umaimah,Ba ruwana da wani kamun kafa,Kuma Bazanyi rabon yak'i ba! Saddiq ya karashe zancen Yana dariyar zolaya," "Ali,shima dariyar Yake yace"Umaimah Bata kishin hauka irin na matar ka ta daban ce Ina da Tabbas akanta.." "Hanyar waje suka nufa dai-dai parking place suka tsaya suna tattaunawa, sai ga motar Umaimah ta kunno Kai,Mai gadi ya bude Mata get din,A harabar gidan tayi parking gefe suka fito,Da fara'ah Tace"Baki mukayi NE,An jefemu da dutsi kwana biyu munyi fushi,tana dariya." "Suhaila da ke Rungume da Khairat,da sanyin muryarta ta gaida su cike da girmamawa."Ta wuce "Amsawa Saddiq yayi shi dai yarinyar tana burge shi."Gashi kamar su har ta baci da Umaimah "Yaran sai hayaniya suke Masa shi kuma daukan su Yake sama Yana ajiyewa kasa daya bayan daya,dariya kawai Sukeyi..Nan ya dauko alawa a motar sa,ya ba yaran."Da murna suka shige gida Dukkan su." "Ali ya kalli Umaima,da ke ta zuba ita da saddiq, yace Gimbiya gwarou fa yayi Mata," "Tace Haba prince,kace zamu Sha buki,Amma kafin Nan Dole sai an maido min da tawan ko!?" "To hakan muke so in shaa Allah,Ni bamma so su kwashe kayansu tun Wuri haka ba, Inji Ali "Tsaki saddiq yayi,yace bakuda aikin yi nikam na tafi,Kuma sunyi min dai-dai, Kai sai munyi waya,Ke Kuma hajiaya sai na kawo maki sabuwar kawa," "Umaima Tace to Allah ya kawo ku lafiya, Duk da Ina kishi!" Amma gwara Naga Wace iri CE,Kar dai batada kyau, SABODA da wuya asamo kamar mu, anaso Ana Kai kasuwa,gama ta zakuyi KU dawo hanya Domin sai da tsohuwar Zuma akanyi magani eheee..." "Sai dai kin ganta 100% Hajiya ba ta da makosa ko a gurin ku Yan sa ido komai iya kushewar ku zaku yaba da Mai kalar fanta kirar Coca-Cola Saddiq yace Yana Dariya tare da shiga motarsa ya tada injin." "Ali da Umaimah dariyar suke Masa,Tace lalle ka shige da yawa Toooo....Allah ya kyauta,ta fice abinta Cikin gidan,Shima Ali Sallama sukayi da shi,yabi sahun Gimbiyar SA."Ko ya gajiyar fita unguwa Bai mata ba." *********** "Sai kusan magrib,Baba ya dawo da murna na tarbeshi tare da karb'ou ledar hannunsa ina gaishe shi," "Shima yaji dadin ganina tare da nuna farin cikinsa,Yana min sannu, da ya makaranta ya karatu," "Nace duk lafiya law." "Yace to Allah ya bada nasara muna nan muna Addu'oi." "Nace Amin Baba to mungode."tare da barin wurin." "Yace"Innarei kin ganni sai yanzu?" "Shi ne Mallam daga kaje ka dawo," "To Innerie kesan batun duniya baya karewa,Ina can Mallam Musa ya rikeni,Yana bani labarin Matar Saddiku,Ashe batada kirki,ita Nadiya Bata Gaya Miki ba ko?" "Rassss!gabana ya Fadi Jin abinda Baba ke fad'a,sai da kofin hannuna ya subuce ya fadi kasa." "Dauke kofin nayi na wanke, tare da k'arasa cikon butocin, da nakeyi."Buta d'aya ta Baba na d'auko tare da ajiye Masa gefensa Domin yin alwala."Saura kuma a hanyar bayi na jera su," "Baba ya CE"Wallahi Innarei malam Musa na Gaya min abin ba Dadi saurare Ashe Saddiqu yazo makon can,Yake Basu labarin komai, Ashe batada mutunci,hakuri yakeyi sai da yaron nan yabani tausayi,Yanzu haka in karashe maki zance bata gidan sun rabo!" "Subhanallahi!"Innerie Tace"tare da buga kirji,ta kalleni inda nake zaune gefen su,nayi tsuru-tsuru,Tace"Amma ke Nadiya wace iri CE,Ashe jalilah Bata gidan!"D'azu Mallam muke zancen su da ita,harda yabonta Yar nan keyi Wai sunce a gaishe mu Aiko zakiyi zurfin ciki bazaki boye Mana Dan muma Sadiq ya zamo danmu sai mu kirashi muyi Masa fad'a mu bashi hak'uri yanzu watakil Yana dubinun san komai ," "Mama bansan Bata gidan ba!Nima Yanzu nakeji wurinku"saboda da lokacin jarrabawa yayi, Makaranta na koma da zama Domin karatu,kuma daga makaranta nadawo ban biya ta gidan ba!"Yaya Saddiq din Bai kaini ba!Kuma ni ba komai nasu na Sani ba,amma gaskiya nikam banji Dadi ba!"Nayi maganar kalar tausayi,"kamar gaske,sai Addu'a nake Kar su gane komai," "Baba yace"To ALLAH ya sauwaqa Daman malam Musa yace min shi tun farko baiso Saddiq ya auri yarinyar ba,Dan diyar macece Sam basuda mutunci Amma ya Nace sai ita,Yanzu Haka nuna min yayi da ba'ayiwa Nadiyatu Miji ba,Da mun hadasu aure da Saddiq din, nicce to ai tuni gurbi ya b'ata shaa Dan an baiwa yaron nan." "A firgice Nace Baba aure fa!?"Wallahi nikam Wannan masifaffiya ko makiyina bana fatan ya zauna da ita! har Yan gidansu basu da mutunci."Ai sai su kasheni!" "Innerie Tace"Yo Ashe Kinsan HALINTA Amma ko da wasa Baki taba aibata ta ba!" "Sai lokacin nagane tsoro da fargaba ya Sanya Ni subul da baka,"Allah dai ya gyara, iya Nan na tsaya."Nace ni ai batayi min ba Kuma batayi Masa a gabana na dai San yayarta da kanwarta Suna zuwa gidan Yan bala'i ne. "Baba yayi dariya yace"tsorou kamar farar k'ura Ni Kaina naji dadin hakan,saboda Bazasu nemi Alfarma agareni na kasa masu ba,Amma Kinga Yanzu Jawad ya raba gaddama, yace Yana Dariya."Alwala ya fara Yana gamawa ya wuce masallaci," "mama kam ta dinga mamakin Jalila,Nima dai bayani na Kara Mata saboda nasan zata tuhumeni ko Jalila na kuntata min zamana gidan,Gaskiya na Gaya Mata yadda zaman mu yake,sai dai na da na gaya mata."Muna zaune lafiya." "Nan nace mama Wai shi Wannan Jawad din naku bazai zo in ganshi ba,naji Baba yace"An yi mini Miji !?"Har an Basu ni kenan?" "Dariya mama tayi har da tafawa Tace Kai kurci dangin hauka!"Nadiya to Dan ankawo kudin shiga gidan,sai an Gaya maki,Yanzu da Kika dawo ai Zakiji komai,shi jawad din Bai Gaya Miki ba!?" "Daure fuskata nayi harda hawaye na,Nace Ni ba Wanda ya Gaya min,nifa ko saninsa Banyi ba mama," "To ki yafemu laifin mu NE ko Nadiyatu,Lalle wannan zamani abin tsoro,mu da aka yiwa auren ko mijin bamu sani ba,Amma Kuma muka zAuna sai ku yaran zamani!?"To shi kenan bari Mallam yadawo zamuyi magana." "Riketa nayi tana kokarin Tashi!Nace Mama Kiyi Hakuri Duk abinda kukayi dai-dai NE,Allah yasa hakan NE Alheri." tare da share hawayena." "Amin Daman Haka ake son D'a Nagari,Muje muyi sallah," "Tashi mukayi zuwa daura Alwala muyi sallah," "Mama dakinsu ta nufa Nima nawa na shiga Domin idar da sallah." "Ina kammala Sallah Nan wurin na zauna Ina Hawaye!"Wannan wane irin aure NE,Ikon Allah Ni Nadiyatu Naga ta Kaina,Cigaba da kaiwa Allah Kuka na!"Nakeyi ahakan na kwanta wurin Ina jiran Kiran sallar Ishaa." *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 29* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *SADAUKARWA GA:" ZURIYATAAH, KUMA DANGINAH, FARIN CIKINAH,DIKKON KEBBI & MADAWAKIN KEBBI FAMILY'S HAK'IK'A INA ALFAHARI DA KASANCEWA GUDAN JININKU A RAYUWATAH,ALLAH YA QARA HAD'A KAN MU YA SANYAWA ZURIYA ALBARKA,ALLAH YAQAROU DANK'OU K'AUNA DA ZUMUNCHI MAI D'AUREWA AMEEN, FATAN ALKHAIRI.''😍* *KYAUTAH CE,GA:"NANCY, MAMAN NANA,SAI KUMA FAUZIYYA HAMZA SHEHU NAGODE DA K'AUNAR KU ALLAH YA SANYAWA RAYUWA ALBARKA AMIN."😍* ______________________________________ Bayan mako biyu "Wannan Rana ta kasance min bak'ar Rana arayuwata!Ranar bak'in ciki agareni!"Ranar da bazan manta da ita atarihin rayuwata!"Ranar da na sha Kuka!har nagodewa Allah,Tun lokacin da akai min waya aka shaida min Wannan labarin nake gunjin Kuka!"Mai shiga Rai!Hakuri mama ke bani tare da mita Amma naki na hakura,Baba ma yayi iya yinsa akarshe fita yayi yabar gidan Domin na k'asa hakura," "Bazasu gane irin rad'ad'i da tuk'uk'in bacin Rai!da bakincikin da nakeji arayuwata ba!"Da ace nasan Banyi karatu ban mayar da hankali ba,aka kadani jarrabawar Nan!"Ba zanji ciwo ko zafi ba!"Amma Nasha karatu Nasha wuya nayi iya kokarina Ina da Tabbas Akan karatuna,Yanzu Rana tsaka akirani a shaida min banci jarrabobina ba!"Kai duniya Wannan cin Amana da zalunci yayi yawa arayuwar mutane!" "Wannan abin shi yafi komai damuwata,Duk wani buri nawa Akan karatuna ya rushe,Nayi Kuka har muryata ta disashe! Idanuwana sunyi luhu-luhu sun kumbura har wani ja fuskata tayi,Duk Wanda ya ganni Ranar sai ya tausaya min Shiyasa mamana Kuka har da hawayenta,Ba abinda ke damunta sai yadda taga naki na dangana da ikon Allah tayi bani Baki da nasiha Amma naki barin kukan!" "Baba Yana fita gidan mallam Musa ya nufa tare da shaida Masa abinda ke faruwa,wato abokan karatuna sunje sun dubo jarrabawa da aka manna Amma duk sunci amma ance Nadiya ta fad'i"tana Daga Cikin korarrin makaranta ma" "Mallam Musa Sam baiji Dadi ba!"Nan ya Kira saddiq ya shaida Masa," "Saddiq ya shaida masu Naseer abokina yaje tun jiya ya sanar Masa Kuma yayi iya kokarinsa,na Riga da na Fadi jarrabawa sai dai ayi hakuri na koma a NCE ONE,"Rai Babu Dadi suka ajiye wayar,Mallam Musa Hakuri yaba Baba, Baba yace,Bakomai Haka Allah yaso,yanzu Kam Nadiyatu tayi Hakuri da karatu tayi aure,"Duk da Mallam Musa, baiji dadin faruwar hakan ba,Amma DAUREWA yayi Yana ba Babana hakuri," "Jiki Babu kwari Baba ya dawo gida ya samu mama a madafa tana sama Mana abincin dare,Zama yayi saman turmin da ke wurin tare da yiwa mama bayanin komai."Itama Bata ji Dadi ba Akarshe Addu'a sukayi min." "Da dare Bayan Baba ya kammala cin abinci mama tana gefensa tana dama Masa fura,Daga dakina na jiyo shi Yana kirana," "Da kyar na Tashi saboda matsanancin ciwon Kai da jiri da ke debana,Ina had a hanya na fito Daga Dakin a INDA suke zaune na durkusa Ina kukan zuci!"Domin nasan Duk abinda zai fito daga garesu to ban hakuri ne!," "Baba"Ya dubeni da kulawa yace"Nadiya Ina son kiyi Hakuri,ki yarda da ikon Allah,ki duba ki Gani mu fa iyayenki NE,Amma mun hakura bare ki,kinsani da Dadi da ciwo mun hada abinda Muke da shi kinje makaranta,To Dan ance baki ci bae,me zamuyi,Kisani mun yarda da kaddara Kuma BAZAMU ja da ikon Allah ba!"Kema ki bar komai Allah yayi Miki mafita,D'azu nakira Sadiq ya Gaya min yayi iya kokarinsa,sai dai ki koma ko aji daya,niKam bana goyon Bayan ki koma,matsawar ba cigaba zakiyi ba,A gaskiya bamada wad'annan kudaden kin sani,Dan Haka kiyi Hakuri mu saurarin hukuncin ubangiji..." "Mama ta amshe zancen Baba tana cewa"Wannan gaskiya NE Mallam Nima tun d'azu nake Bata Hakuri,Amma da Yake kafiya da saka Abu Rai gareta,Taki hakura!Mu Kam ba Dadi mukaji ba!saboda cigabanki shine farincikin mu,Allah yayi maki masanya ta Alheri," "Ameen Innerie Baba yace Yana kuskure bakinsa da ya Gama Shan fura," "Tunda suka fara maganar su hankali na ya Tashi mussamman da naji maganar NCE1 wani Kuka Yazo min da kyar na hadiye shi!Kar iyayena suga kasawata!"Bayan rarrashi na da suke!" "Mama Tace"Ga ganta Nan har abinci Bata ci ba!saboda Kuka!" "Ungo Wannan Sha,Baba ya Miko min langar furarsa tare da tsare gida ranshi abace!" "Jikina na kyarma!"Na Amsa tare da kafa Kai,Allah sarki Babban ma'aji ba'a Masa garaje Domin baisan Babu ba(CIKI)Nan take ya dauki Kuka Yana amsaemr saqo,Sai da Nasha sosai na ajiye kwanon,Ruwa Baba ya bani Nasha sannan yace kar na sake Jin ance kinki cin abinci ko kinyi Kuka!" "To Baba in shaa Allah na daina,nace muryata na rawa,Tashi yayi ya shiga Dakinsa fitowa yayi da magani Panadol ya balla ya bani,yace kisha Tunda kinyi Kuka har kin godewa Allah,Amsa nayi Nasha." "Mama Tace"Ai ka taimaketa Mallam da baka barta ta kwana Bata ba CIKI ba,Ni nasan Daren farin zai hanata bacci,Dole ta ziyarci talle." "Tashi nayi tare da masu sai da safe," "Ina shiga dakina wayata na bude wadda na kashe tun lokacin da kawayena Yan sokoto suka kirani suka Gaya min sakamakona,wadanda bazan manta da bakin labarin su ba!" "Sakonnin su Esha,Naseer harda Yaya Saddiq na ci karou da su Duk na jajanta min da ban hakuri,Nan sai ga sakon Jawad ya shigo tare da cewa yaso ya turo min pics dinsa sai dai bana chat bare ya turo in bude whasp ko Kuma inyi Hakuri har ya dawo Daga tafiyar sai Yazo."Nan dai na baiwa kowa amsar sokonsa,"Sannan na kwanta Rai Babu Dadi!" Bayan kwana biyu "Tunda aka yiwa yaran hutu saddiq ya tattaro yaran da kayan su ya mayar da su Kebbi." "Gidan su ya mayarda su inda gwaggo,Da Yake yaran sun Saba da kakannin su,Basu wantli damu ba,suka Cigaba da zamansu Nan Argungu,Duk abinda zasu nema kayan kwalam da Indomie da drinks Sadiq ya saya masu da sauran sabulai,Abubuwa dai ya hada,Tare da baiwa mallam Musa kudade kamar yadda saba,"Ya kuma shaida masu zancen neman Aurensa," "Mallam Musa yaji Sanyi aransa alokacin da Sadiq ya Basu tabbacin Mansura Yar Kebbi CE Kuma sunada Dangi anan Argungu." "Gwaggo ma taji Dadi,Tace auren Yan gida yafi kaje can wata jiha ka auro yarinya ba'asan tushenta ba!"Amma gwara auren kusa,A KARSHE fatan Alheri sukayi Masa tare da saka Masa Albarka ya wuce." "A hanya sai dai ya tsaya wani store yayi Yar sayayya Sannan ya nufi gidan mallam Balarabe Haka kawai yaji Yana son ganin Nadiyatu Saboda Yana Jin tausayinta,ya Kuma santa da son karatu,a gaskiya abin ba Dadi baison ta Fadi jarrabawa ba!" "Sallama yayi kusan Sau uku kafin a Amsa." "Malam Balarabe NE ya fito Yana dubawa Mai Sallama sai ya yaci karou da dansa,Da murna yace"A Sadiq Bismillah shigo Daga ciki.. " "Sadiq Cikin ladabi ya gaida Mallam Balarabe," "Amsa Masa ysyi, Innerie bda jiyo muryarsu Tuni ta SHIMFID'A Masa tarbarma suna musayar gaisuwa da Bayan rabuwa," "Baysman kowa ya zauna fira sukeyi Nan Innerie ta dinga Kiran Nadiya da ke daki," "Tun shigowar Yaya Saddiq nake jiyo su,sai dai bana son ganinsa,Saboda sun karatuna yasa Naga kamar Bai taimaka min ba!"Jin mama na kirana yasa na rashi jiki ba kwari,na zuba hijab na fita,Ina Amsawa." "Gaida Yaya Saddiq din nayi tare da tambayar su Mufeeda," "Yace,Duk kowa lafiya sai gobe naje nazo da su ya kawo su hutune," "Sakin fuskata nayi,Domin har cikin Raina Ina son ganin yaran,"Mama Tace,kije ki kawowa yayanki Ruwa Mana!" "A'ah,mama ai a hanya nake Nagode,Yanzu Nasha Ruwa a gida,Inji Yaya Saddiq Yana murmushi," "Baba yace"Ayi Haka Saddiq!?" "Bakomai Baba Daman nazone na Baku Hakuri na Kuma jajanta akan yadda jarrabawar Nadiya ta kasance, Wallahi Baba nayi iya kokarina Amma abin ya faskara,Duk binciken da nayi aka dauko LITTAFAN jarrabawar ta aka nuna min adadin makin ta Bai Kai ba!"Naso agyara Amma bazaiyi ba!"Nasan tana da kokari da SA Kai Amma tahowar abune,Lamani daya da akayiwa masu Matsalar su shine su dawo baya...," "Saddiq ba komai mungode da kokarinka Nadiyatu tan fad'a Mana,karka damu haka Allah ya rubuta,mun fad'i Mata ta hakura da karatu,Yanzu ma dai aure zatayi.. " "Aure Kuma Baba!?Meyasa bazata koma ba!?"Ba damuwa Baba Ni na dauki alqawarin Zan dauki nauyin karatun ta!"Inji Saddiq Rai ba Dadi. "Saddiq kenan gaskiya Ni har nayi magana da magabatan yaron da ke nemanta jiya,su turou asaka Ranar aure,komawar me zatayi,Aure Zan Mata allashi idan mijinta Naso sai ta Cigaba da karatun agidansa,Baba yace Yana Dariya," "Innerie,ta daura da cewa ai komai ya wuce mungode,Ashe kaima wani Abu ya faru tsakaninka da Jalila!?Allah ya sauwaqa ya gyara!lamarin." "Ameen, Saddiq yace Jikinsa Duk ya dauki Sanyi!" "Nidai komai bance ba!"Sai dai dago Kaina mukayi Ido biyu da Yaya Saddiq Yana kallona cike da tausayi!"Yace kiyi Hakuri kinji Nadiya," "To Yaya Hakuri ya Zama dole Nagode," "Mama Tace sai ki Tashi ki dauko sakon Nan ," "Tuni na kamo zaren mama Tashi nayi nashiga dakina,na dauko ledar alawa,na ba mama,Tace"Saddiq ga naku alawar baikon Nadiya." "Amsa yayi Yana GODIYA,yace Ay Baba yayi min bayani d'azu,Allah ya Sanya Alheri, "Ameen,sukace dukansu." "Ledar gefensa ya ajiye da kudi yace Baba ga Wannan Ni Zan wuce," "To harda hidima Kuma? ba ka gajiya Inji Baba "Mama Tace to mungode Allah yayi Albarka," "Nima Allah ya kiyaye nayi Masa,suka wuce shida Baba Yana ta Masa GODIYA," **********"Knocking(Kwankwasa)kofar takeyi Amma shiru ba'a bude ba!"Sai can wata matashiyar Kyakkyawar yarinya ta bude kofar falon,wadda dagani ba sai an fad'a ba,tana da alaqa da matar gidan," "Sannu da zuwa Tace muryarta a sanyaye kamar Ana busa sarewa," "Yawwa,matar ta amsa tare da cewa Mai gidan tana Nan," "Eh,tana ciki Bismillah." "Shiga sukayi falon Mai kyau da tsafta ga kamshi,kamar ba Yara agidan komai tsaf," "Matashiyar Tace"ki zAuna Bari na Gaya Mata,"Ta wuce "Zama tayi tare da cigaba da dubin falon da hotunan,yaran gidan Nan ta gano har ansamu karuwa Domin ga hoton new baby ta Gani,manne da iyayensa," "Matashiyar budurwar ta dawo dauke da tray,drinks da snacks NE aciki,Tace ga Ruwa kisha tana zuwa," "Yawwa Nagode,Tace da ita tana kokarin Kai lemon abakinta." "Ita Kuma yarinyar da can gefe ta zAuna tana kallon Zee world,Itama hankalinta takai wurin t.v kamar Mai kallon sai dai akasan zuciyarta ta kosa taga bullowar gudan jininta!" "Riga da siket NE sanye ajikinta na atamfa super exclusive Mai kalar pink da blue,dinkin ya amsheta sosai,Kirjinta manne da babynta da ta rungumo,"suna zuba kamshi," "Sallama tayi lokacin da ta shigo falon,tana dariya ganin bakuwarta,"tare da Mata maraba," "Zama tayi Tace yoo su Jalila NE agidana,Amma Batan hanya kikai!?"Inji Umaima tana Murmushi "Eh....Batan Kai NE ma ba na hanya ba! Jalila tace ta na kokarin amsar baby Khairat Daga hannin Umaima,tana cewa Ashe kin haihunki Bako sanarwa!?"Masha Allah, tubarkallah Yar Baby. "To Jalila kin jefemu da dutsi,Ina ko Zaki San na haihun ko na gaya maki yadda Kika hasala da mu nasan bazaki zo ba!"A gaskiya Jalila banji dadin al'amarin Nan ba!Ay wani Abu Ana Hakuri,A danne KO Domin Yara,,Kuma zuciya mugun nama CE,sai Ana Sara Ana duba bakin gatari," "Hmnnnn, umaima kenan Allah dai ya sauwaqa,na gane abinda Ali da Sadiq suka tsara maki shine kinka hau Kai,Inji Jalila da sanyin murya," "Ba haka bane, Jalila Amma...." "Umaimah bashi ya kawo Ni ba!mubar Wannan zancen!"Ina su Salim da salima NE. "Umaima ta kalleta da yanayin tausayi saboda Duk tayi Baki ta rame ta canja kamar ba Jalila ba!"Sai dai taga canjin nutsuwa da Kamala atattare da ita," "Dan yake tayi Tace suna Nan lafiya sunje tahfiz,Amma Baki isuwa tambayarta ba!"Domin nasan diyana kikazo nema Gashi ko Kunyi sabani,yau suka wuce Kebbi da Abbansu," "Innalillahi Wa'Inna ilaihir Raju'un!!! Jalila Tace tare da dafe gefen kanta!"Nan take idonta ya kawo Ruwa,da Sanyi ta kalli Umaima Tace"Ba dai suna lafiya ba?" "Lafiyan su kalau,sai dai kunyi masu Karan tsaye arayuwa,Banda buri Ni da Ali irin mu ga Kun mayarda aurenku ko Domin yaran Nan,Kullum Cikin maganarki suke,"Ki Cigaba da Addu'a Jalila,Daman shi ne nake guje maki! Amma kina ganin na cika iyayi da neman asani,har Kika gujeni Kika zabi wasu da kike ganin sun Dace da rayuwarki.Ba gashi ba yanzu wa gari ya ways?" "Komai ya wuce Umaima Ni Zan wuce Daman nazo ne domin Naga yaran idan da Hali naje da su suyi min kwana biyu!" "Gaskiya Kam d'azu Nan ya daukesu da safe,"Sunje Kebbi," "Kenan zasu jima ko Naga sunyi hutu!a makaranta?" "To sun dai tafi da kayan su ban san yaushe zasu dawo ba!"Gaskiya Kuma ban tambayi shi saddiq din ba,Amma idan Abban Khairat ya dawo Zan tambaya. "Shi kenan sai ki bani lambarki Dan na canja waya wancan faduwa tayi na sayi karama Nan. Murmushi umaima tayi Domin ta gane kamekamen da jalila keyi da wata akwalar wayarta (Sha kidinka bakauye)lambar tasa sannan ta ba jalila Tace ki kirani in ga Taki lambar. Ehimnnnn gashi Banda Kati dazu nayi waya ya Kare Inji jalila Umaima Tace okay Bari ki bani nasa sai na Kira,Nan ta karanto lambobin umaima ta sa takira sukayi saving lambobin su. Godiya jalila tayi ta ce to Ni Zan wuce, tana kokarin Tashi, Umaima Tace Ina zuwa, kayan Mai da turare da sabulai ta hadou mata har da kudi, Godiya Jalila tayi Mata jiki na rawa,ta amsa,Gwanin tausayi."Tace sai anjuman ku na gode. "Suhaila Tace,To sai Anjuma Anty, "Yawwa, Jalila Tace tare da cewa Umaima Wannan kanwarki CE!?" "Eh, Suhaila CE,Mai bin Rahma," "Ok,Rahma na sani kesan tafi yawan zuwa inda nike Amma Wannan tafi Kama da ke," "Dariya Umaima tayi Tace ko Jalila,Kinsan yaran sai saurin girma,"Tace Suhaila ga maman mutanenki su Mufeeda," "Dariya suhaila tayi Tace haba magana CE Banyi ba Anty naga suna Kama da Mufeed Allah." "Kara gaisuwa sukayi Jalila da Suhaila Sannan ta wuce,"A zuciyar Jalila tana Jin kaunar Suhaila mussamman da Taji ance tanayin su Mufeeda."Da Haka ta nufi gida jiki sanyaye!" ********** "YUNIN yau Mansura busy take saboda tana hada-hadar shiryawa Saddiq abin tarbon dawowar SA,"Abinci take hadawa,Dawowar Saddiq kawai take jira saboda tayi waya da shi ya shaida Mata Yana hanya," ************ "Alh.malami sambo ya Kira momy awaya yayi Mata bayani,tare da shaida Mata cewa,Iyayen Nadiya sunce aturou,"Saboda wani uzuri da gitta Yanzu aure zasuyiwa yarinyar." "Momy taji Dadi,Sosai matuka tare da fatan Alheri,Nan Alhajin yace in shaa Allah,zasuje gobe,sukai sadaki Bazasu dawo ba,sai da Ranar auren Jawad da Nadiya,"Momy Tace to Allah ya ida nufi. ************ "Da dare Ina Danna wayata sai ga Kiran Jawad ya shigo wayata,Ina dauka muka gaisa ya shaida min Yana waje Mota Yana jirana," "To,na Amsa,tare da saka hijab Dina,turare da powder na shafa,Dakin mama na shiga tare da fad'a Mata,yau dai Allah yayi Jawad nazo mu gaisa,"Da Yake Baba baya Nan,mama umurnin fita na sameshi tabani,tare da Jan hankalina Akan na Kama Kaina," "Tafiya nakeyi a lokacin gabana sai faduwa Yake, fargaba Mai yawa ta darsu Azuciata,"Har na isa wurin motar," "A hankali ya bude motarsa,ya fito hadadden guy ne,Cikin shiga ta Alfarma,"Kaina na qasa muka gaisa da shi,tare da yimin ya makaranta," "Wani Abu yaji aransa,ganin Nadiya azahiri agaskiya Shi Kam ya yaba da nutsuwarta bazai iya yaudararta kamar yadda Jawad ke nufi ba." "Saif gyara tsaguwarsa yayi yace"malama Nadiya nasan zakiyi mamakin ganina amatsayin Wanda zai aureki, "K'asa nayi da Kai,Ina wasa da zoben hannuna," "Yace"Kamar yadda Kika sani suna MUHD Jawad Husamaddin,Nayi karatu har bautar k'asa na kammala,yanzu hakan Ina kula da kamfanin mahaifina na fata,"Na ganeki tun ba Yanzu ba,Shiyasa na nemi iyayenki mukayi magana da su har Allah ya bani nasara,kiyi Hakuri na boye Miki Kaina da nayi,saboda bana son in Zama sanadiyar lalacewar karatunki,na sameki kina karatu Kinga gwara na Bari har ki kammala,"Sai Gashi na ci Karo da sakonki Wanda yayi sanadin zubar hawayena!"Amma albishirinki my Nadiya in shaa Allah zakiyi karatu Bayan auren mu." "Ajiyar zuciya nayi,tare da Jin wani sanyi arayuwata,nace bakomai Nagode Allah yasa hakan NE alheri." "Ameen,yace Yana murmushi akasan zuciyarta tausayinta NE aransa,Amma in shaa Allah zaiyi iya kokarinsa Kar Jawad ya cutar da Nadiya sosai." "Ledoji ya fitou da su amota,yace kinga Wannan,"Sannan Ina son kiyi min texts abubuwan da kike buqata," "Sunne Kaina nayi,nace nagode,tare da amsar ledar." "To Ni Zan koma Duk abinda kike buqata ki turou min text ko Kuma sai munyi waya Nagode ki gaida su mama." "Murmushi nayi nace to,Amma ya zancen hoton...." "Shiru Yayi....yace to ba damuwa zanzou na tura maki, format wayata tayi Shiyasa,Duk hotunan sun goge,Amma later Zan turo but Nadiya Meyasa Baki chat," ya tambaya "Baba ya hanani saboda karatu,Kuma yace Ana daukan halaye marasa kyau. nace Cikin sanyin murya," "Dariya Yayi yace,okay ba damuwa niKam da munyi aure zan barki ki sada zumunci,"Da abokanki ay sai kaso halinka zai lalace,"Domin shi hali zanen dutsi. "Hakane Kam. "To ni Zan wuce,"Rabin Raina Haske Mai Haskaka zuciyata "Nace,Yayi nagode."Allah ya tsare ka da tsarewarsa. "Sallama nayi da na koma gida shi Kuma ya wuce abinsa." "Wani Sanyi naji araina da kwanciya hankali,ganin Jawad dina Mutumen kirki ne Mai Sona da nuna kulawar sa akaina,ba irin Jawad din da na tab'a Samun matsala da shi ba...Tsaki nayi nace wancan Kam marar mutunci ne" Allah nayiwa godiya da ya bani miji nagari Domin Yanzu kam hankalina ya kwanta na Sami nutsuwa," "Saif Duk Jikinsa Yayi Sanyi Alokacin da ya samu Jawad inda ya ajiye shi,daukarsa Yayi suka nufi gida,Nan Saif ya labartawa Jawad Duk abinda ya faru tsakanin sa da Nadiya. "Yace,A gaskiya na tausayawa mata,irin yadda zakayi Mata kamar abin Yayi yawa,Duk sai naji ban kyauta Mata ba!" "Dariya Jawad Yayi tare da kaima saif dukan wasa,yace"Kai Dan iska ne,meye to!?"Sai ta dauki matakin da take ganin zata iya,banzar yarinya nifa manage ma Zanyi mu zAuna gida daya da ita,"Inji Jawad "Numfash ya saukei yace Nidai Dan aike nake ko da takanje ta dawo,saboda mommy da iyayen Nadiya Basu cancanci mu yaudare su ba!"Muyi masu karya da wasa da hankali,"Ada ban dauki abin komai sai da Naga zancen auren yazo da gaske Kuma manya sun shigo cikin lamarin Sai Naga kamar bamu kyauta ba!"Kayi nazari Mana Jawad, "Ba wani nazari da Zanyi Dole na auri yarinyar Nan na Rama iskanci da wulaqanci da tayi min,"Shine kawai Zan huce haushinta,Auren ma na Dan lokaci NE sakinta Zanyi nasamu wacce ta Dace da ajina ba irin Wannan kwaila kucaka ba,"Jawad yace." "Saif Yana driving yace "Hmnnnn....Jawad kenan baka gane ko abinda na hango ba'' "Ba abinda ka hango Baaba,sai Alheri."ya Kai Masa dukan Wasa. "Da haka suka Cigaba da fira,har suka karasa gida,Saif sauke Jawad yayi Sannan ya wuce nasu gidan." *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 *SHARE, & COMMENTS*👍🏼 [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* _________________________________ ® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ _________________________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/ *SHAFI NA 28 _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ _INA GWANI WANI....,GA NAWAN, 'YAN MAGANA KANCE GASKIYA DOKIN KARFE, HAKA BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE,INA MASOYANAH...? KU FITOU K'WANKU, DA K'WARK'WATAR KU, KU NEMI LITTAFAN MAYAN MATA, MAGANIN K'ANANAN MATA, WAD'ANDA ALLAH YAYIWA BAIWAR RUBUTU KU NEMI NAKU KADA KI/KA, BARI ABAKU LABARI,DA YARDAR ALLAH ZAKUJI DAD'I LABARAN MASU ILIMANTARWA, DA KUMA FAD'AKARWA,SU NA DAUKE DA DARASI MAI D'IMBIN YAWA, BUGU DA K'ARI ZAKU NISHAD'ANTU SOSAI,ALLAH YASA MU DACE AMIN._ _LITTAFAN SUN HAD'A DA_ _HASSANA DA HUSAINA_ _(NA HASSANA DAN LARABAWA,Qawar Aminchi)_ _GIRMA YA FAD'I...(NA NABILANCY LUV, Abokiyar Aiki Kuma ta hannun damana, Takwarata,)_ _GUDAI....(NA NABEEHA AMEENU, Tawan sonki daban ne, Aminiyar Nabeela Ameenu,)_ _____________________________________ Bayan mako D'aya "Abu kamar wasa karamar magana ta zamou Babba,Domin alaka mai karfin gaske ta dinke atsakanin saddiq da Mansura." "A yanzu babu abinda saddiq ya Sanya agaba face,Aurensa da abar Sonsa da qauna wato mansura." "Haka gefen mansura abin nema ya samu,Har ta gayawa mamanta cewa tayi sabon kamu,Wanda takeso ta aura kwanan nan zai shigo gida Domin zancen aure ne da gaske."Mamanta tayi murna matuka musamman da taji akwai kaya a Aljihunsa." "Duk Bayan kwana biyu saddiq sai ya hadou da Mansura sun Sha Fira aje shopping da sauransu,Ko da yaushe suna waya idan dai ba Aiki ya fita ba." "Hankalinta ya kwanta ta sameshi yanzu atafin hannunta sai yadda taga dama da shi,"Shiyasa ta dauke nauyin abincinsa Sarai,Duk abinda yake son ci ko sha Naseer kawai zai Aiko da cefane,Nan mansura zata baje basirarta ta hada masa girki naji nagani na fad'a,''Saddiq Yana Jin dadin hakan domin wasu kalolin girkin da Mansura ke masa baima Saba ganinsu ba,wasun ko Yana ci agidan Abokinsa Ali."Tabbas burinsa zai cika yayi Dace da macce wadda ta iya girki ga tsafta,ko yaushe Yana alfahari da Mansura idan ya tuna Wannan." "Itama dai mansura acikin abincin da take dafawa tana bashi,ta nan take samun nasara zuba Dan kulle-kullenta a abincin ko abin Sha." ( _Oh ni yar mutan Dikkawa, Mansura dai,hmnnn ke kam kakarki ta yanke saqa,tsuntsu ya fadou maki Daga sama gasasshe,To Allah ya fidda A'i ga rogo_) "Tun dawowarta har zuwa yanzun suna da labarinta, tunanin mafita suke Domin jiya sunyi waya da jawad din har Nadiya take nuna masa tana son ta ganinsa azahiri da kuma ahoto dan kawai tasan Waye shi." "Tirkashi to Yanzu jawad kana nufin bazata game ka ba!?Inji saif da mamaki "Jawad yace "Yadda bazan manta da ita ba,Saif Ina da tabbacin itama bazata manta da Ni ba!"Ko a hoto zata shaidani,"A Murya ne bazata saurin daukowa ba Dan Ina canja maganata kamar ta ustazai. "To,ya zamuyi Yanzu, Kuma wace Amsa kabata?" "Neman mafitar nazo awurinka,sai dai na Gaya mata yau zamuyi Tafiya Abuja tun da safe,Shiyasa na cire layin da nake amfani da shi a dayan awayana,Wanda nasaya kawai saboda ita,"Amma na gaya mata da zarar mun sauka na huta zan turo Mata pics din," Kuma nayi nazari akai "Kennan hotonka zaka tura mata!?Meyasa zaka watse mana lamari!?"Saif yace da Dan hasala "Dariya yayi tare da tafawa da Shi yace"Ba abinda zai faru mutume na ba nawan Zan tura ba,Hotonka zan tura mata amatsayin Ni, sannan Bayan kwana biyu Kaine zakaje gidansu,Sannan Ina son ka daukota ka kawowa momy ita ta ganta," "Tayaya hakan zata faru Jawad!?"karyar da yaudarar tayi yawa!?"Saif yace cike da damuwa." "Murmushin keta yayi,Karfa ka manta da sunan da ta kirani yarinyar ta Gama dani dole na nuna Mata nidin cikakken marar *TARBIYYA* ne,"Babu tausayinta acikin raina ko kad'an,saboda hakan Ni ba ruwana da Duk halin da zata samu kanta aciki,"Ina son ka shirya saboda Duk wata hidimar aure Kaine Ango,sai Ranar auren mu idan an kawota nake son tagane Waye Angonta na gaskiya!?"Sai na gabatar Mata da kaina na kuma tabbatar Mata da *MUHAMMAD JAWAD HUSAMADDIN* shine mijinta. Nayi tunanin idan ta ganni yanzu na sani bazata aureni ba,zata fad'a iyayenta gaskiya Bata Sona,ka ga Burina na daukar fansa ba zai tabbata ba kenan. "Saif,yace"A gaskiya bakada dama jawad,Amma Kuma........To shi kenan dai ba damuwa hakan za'ayi." "Rungume shi yayi cike da murna yace Nagode Saifullahi Tabbas Kai wani B'ari ne na rayuwata."Jawad yace Yana Dariya,shima saif din dariya yakeyi yace Kai Dan uwana ne,ka wuce Amininah." ********""Tun Ranar da iyayena suka zaunar da Ni,sukayi min nasiha akan mijin da zasu aura min na hakura da komai Kuma nayi biyayya akan zabinsu." "Kwantarda hankalina nayi na cigaba da sha'ani nah,Tare da neman mafita awurin ubangiji." Washe gari "Tun da wayewar safiyar yau mama,tabani katuwar leda cike da kayan alawa," "Tace"Kayana ne na shiga gida wanda Zan rabawa abokaina." "Nace,To nikam mama Wannan yayi yawa wama zanba tunda ba wasu qawaye NE da Ni ba,Anan garin Kuma danginta suna Bagudo,Baba ba Yan uwane da shi ba!"Bare ace dangina Zan rabawa su Saudat NE kawai Zan debewa." "Mama Tace Dan kawai bakida dangi shi zai Hana kibawa yaran makota tsaranki,Sannan abokanki na Islamiyya da can sokoton bazaki Basu ba!"Meyasa kinka cika wauta Nadiya!?"Ta karashe maganar tana faman yimin mita" "Bata fuska nayi da sangarta,Nace to kiyi Hakuri Amma idan kina buqata ki ragemin su."Sai na debewa kowa yau ma sai naje Dana Islamiyya nabasu." "Mama Tace"Nadiya duk mu rabawa mokota da abokai,Mallam goro ya sayo da alawa masu yawa, kowa an ba, ya shaida ay shalli ne,ko dangina mutanen Bagudo da dakingari da yawa Mallam ya aika masu," "Amma ki tabbata kin debewa su Saddiq da yaransa,Sannan ki debewa su Mallam yunusa ko!?" "To mama Haka za'ayi Nace Ina murmushin karfin hali Amma niKam bazan iya baiwa Mallam yunusa alewata ba!Mutumen da ya wulaqanta ni agaban budurwarsa na Riga na rufe shafinsa." "Ina Cikin tunanin sai ga mama da Ledoji farare a hannunta Tace"karbi Wannan sai ki kullawa kowa nashi aleda ga Kuma manya baqaqe." "Amsa nayi tare da yin yadda Tace "Har na kammala."Ajiye su nayi har zuwa lokacin da zan fita, makaranta."Nasu Esha da yaya Saddiq ajiyewa nayi har na tashi."Sai dai na Kira Duka kawayena na shaida masu da anyi min baikoh,fatan Alheri sukayi min."Naseer Kam kasa Gaya Masa nayi Sak'o na tura Masa wanda nasan zai Sanya shi acikin wani Hali,"Sai dai yayi Hakuri Domin kaddara ta riga fata."( _Inji''yar mutan Dikkawa_) ************* "Zaman gidan Hajiya zama ne Wanda ya koma tamkar dandalin 'yan siyasa saboda ita fa Hajiya Duk inda taga maikou acan take,yau tana nan,jibi tana can,"canza sheqa awurinta kamar kiftawar gira NE,' "Abin Gwanin mamaki,saboda Tunda Tahir ya samu Karin girma,Hajiya ta daina yin Rasheeda ta koma gefen Tahir kullum Cikin yabonsa da saka Masa Albarka take."Duk wasu lalurorin gidan shine,Ga gini yanayi ba da wasa ba,saboda Yanzu hankali yafara shigo shi."Mahmud ma ya dawo gida,sai Shirin zuwa bautar kasa."Jalila da Anty Talatu sun dawo Yan kallo agidan." "Kullum falon Hajiya cike Yake da manyan mata, da matasan unguwa sa'an su Rasheeda sai Fadi banza Fadi wofi,ake Wanda dama al'adarta gidan ne, Gidan Mama Atika ko gidan uwar Daba shine sunan gidan."Tun Bayan rasuwar mijinta ta mayarda gidan dandalin gulmar unguwa."Shiyasa su Jalila ada Zama sukeyi ayi dasu bare Rasheeda da ta kware ta fannin."A gidan ake ci asha har sai an tushe."Ba ruwan Hajiya ita har ma Dadi takeji gidan ya fita daban a unguwa kowa MAAMAH,har wasu banzayen mata,ke dafa abincin mazajen su agidan,Da kayan Aikin abincin suke zuwa tun safe sai yamma,Domin maza na wurin Aiki,Idan sun gama girki su zuba akuloli idan sun Tashi,awuce gida saboda tsabar rashin sanin ciwon Kai." "A hankali su Jalila suka gane hanya sanadin Islamiyya da suke zuwa Ana FAD'AKAR da su,Shiyasa suka dingA canjawa matan fuska,haka Tahir yace"ya daina ci da matan banza da kudinsa,ya daina ba Hajiya kudin abinci."Ayko Hajiya Ba Dan Taso ba!Itama ta canjawa matan fuska har suka daina shigowa gidan su Jima."Sai dai idan Sunji gulma da zafi!suzo su gayawa Hajiya su fita." "Haka rayuwar ta cigaba da tafiya, Jalila tayi nasarar sayarda yan Kayanta masu wuyar ajiya,ta dauko zannan atamfa,takalmi da hijab,tana zuwa da su Islamiyya tana sayarwa,bashi karshen wata abiyata kudinta,"Cikin ikon Allah jarinta yayi Albarka ta ko'ina kudade na fitou Mata,tana lalurorin ta,Sannan tana taimakawa Anty Talatu,da Mahmud da ke imo state wurin service."Nan fa Hajiya aka dawo gefenta ba laifi tana tsakurawa Hajiya,Jalila ta dukufa ga zuwa Islamiyya,,ta mayar da hankakinta ga ibada da rokon Allah tare da tuba,Sauran watan ta daya ta cika iddarta,Ta shirya zuwa ta dauko yaranta mako Mai zuwa saboda yafiye zamansu gidan Umaimah Duk da tana da Tabbas akan zasu samu kulawa Mai kyau Amma ayanzu batada wani buri illah tasa yaranta ajiki,ta kula da Duk wani motsinsu da kula su kamar Yadda malamin su ya ja hankalin su." "Yanzu dai gidan yayi dama Kasancewar Jalila da Anty Talatu suna da ilimi ga halin kirki da suke samowa a makaranta,Tahir ma ba laifi ya Zama kamili har ya fara neman aure."Hajiya ma ta rage fita saboda ayanzu gidan in Banda cin Dadi ba abinda suke Tahir ya tsaya masu,Asiri ya qara tufowa."Anty Talatu ma Tahir yayi Mata alqawarin kudin da zata ja jari albashin watan Nan idan anyi,tayi murna sosai, ta gama shiryar kalar sana'ar da zatayi,"Rasheeda Kam tun Ranar da tayi wani munafunci akazo har cikin makaranta agaban dalibanta akai Mata dukan kawo wuqa,Tun Ranar ta sanyawa bakinta D'an mukulli ta rage gulma sai dai can ba'a rasa ba,tazamo Jinin jiki." ***************** "Na shiga Islamiyya,Lafiya qlaw mukayi karatu har aka Tashi,Daman tun agida na kaiwa Saudat nata kayan,na yan ajin mu Kuma da Mallaman mu Duk na damka mata,Ana Tashi ta rabawa kowa,Naso ace yau Badi'atu tana ajin abata,sai dai Bata zo ba,kawarta munira, Saudat taba Tace ta ajiye Mata,murna da Allah Sanya Alheri yan ajinmu sukayi min tare da godiya."nima Godiya nayi musu. Muna fita saudat ta wuceni taje ta Sami Mallam Bilya da yunus tabasu tare masu bayani,har da iyayi,Daman tayi da biyu,Ay ko nan malam yunus ya hade Rai!"Ko meye dalili oho!"Mallam Bilya Allah Sanya Alheri yayi mana,har inda nake tsaye nesa da su, yazo Yana min murna godiya nayi Masa muka wuce ajin Dalibai na muka raba masu alewa,sai murna suke suna cewa malama Nadiya AMARYA."Saudat Dadi kamar ya kasheta saboda yau dai mun Rama abinda Malam yunus yayi Mana agaban Badi'atu." "Tunda muka fito ajin idon Mallam yunus akan mu yake, Yana nan INDA muka barshi dazu ko dagau,Shi Mallam Bilya ya wuce abinsa."Ko kallon shi bamu yiba nida Saudat muka wuce,Muna kokarin fita get din sai gashi gaban mu yace''Nadiya Ina son magana da ke!" "Shiru nayi bance komai ba ita Kuma Saudat kokarin bamu Wuri take." "Yace Saudat ki tsaya agabanki Zanyi magana,Nadiya bazan boye maki ba!Wannan Rana da Naga baikon ki,bazan manta da ita ba a tarihin ranakun bakinciki na!"Kiyi Hakuri nayi miki hukunci ba tare da hakkinki ba!sai yanzu nasan cewa nayi sakacin barinki!"Wallahi Nadiya Ina sonki Kuma Banga wacce zanso kamarki ba!Ko da kika tafi makaranta kin barni da ciwon sonki,Ina kokarin da kin dawo na fada maki."Sai Gashi wasu matasa sun sameni sun gayamin cewa samarinki NE,Ba abinda Basu Gaya min game da ke ba na b'atanci!"Da Duk halayenki da Kika sauya a Dalilin zuwanki makaranta."Ni Kuma bacin rai da Kashin ki ya tunzurani har naji haushinki,Ina maki kallon Mai kirki Ashe kin samu kawayen banza kinyi watsi da tarbiyyar ki,da duk nasiha da jawabin da nayi maki,haka tasa naji na tsaneki! Bana sonki! harna huce haushi akan BADI'ATU Ido rufe na amshi tayin soyayyarta."Sai Bayan komai ya faru,kinzo hutu kin koma,A Yan kwanakin nan nayi tunanin ban Miki Adalci ba!"Saboda Banda Tabbas akan abinda akazo min da shi akanki!daga lokacin na shiga damuwa"Saudat kuyi min uzuri Amma na Yadda da kaddara."niKam nasan nayi asarar mace wacce zata iya Gina rayuwar yarana da gaskiya,yanzu shi kenan na rasaki a lokacin da nake kokarin gyara kuskurena! malam ya idar da zancen yana Hawaye!" "Ni Kaina kukan nakeyi Kai duniya!su Kuma su waye!?me na tare masu!?"sune tambayoyin da nake ma Kaina Azuciyata har suka bayyana, "Mallam yunusa yace da rawar murya,Nima ban sansu ba!"saboda Bayan isha NE suka zo wurina!"Amma samari NE su biyu Kuma acikin shigar banza na gansu Shiyasa abin ya bani takaichi, ace samarinki NE!, "Saudat ta Share hawayenta tare da rika hannuna Tace"Mallam ka yadda da Wannan itace kaddarar rabuwarku Domin ta Zama sila!Amma Sam ba halin Nadiya bane!"Duk wanda yayi mata Wannan sharrin Allah ya isar Mata!Sunyi NE domin su b'ata mata suna ,Kuma su shiga tsakanin ka da ita sai gashi Sunyi Nasara, in Sha Allah zasu Gani ko ma su waye da yardar Allah. Saboda Duk karya NE sukeyi babu gaskiya acikin zantukan su,Nadiya batada samari hasalima Bata kula kowa,mallam kamar ka manta Wacece ita!? Da halayenta da Kuma dabiunta ,Numfashi Saudat ta sauke da Tace mu zamu wuce Allah yasa MUDACE,sai da safe." "Dan Allah Nadiya kiyi Hakuri Ina maki fatan Alheri,mallam yunus yace fuskarsa dauke da dinbim nadama Mai dauke da damuwa!" "Bakomai mallam Nagode Nace da shi,muka wuce Yana kallon mu har muka bace Masa!"Jiki a sanyaye ya nufi hanyar gida yana tunanin abubuwa da dama!"Mallam yunus kenan." "A hanya Raina ba Dadi Nace Saudat me nayiwa mutane da suka tsaneni!mutane sun sakani gaba,mutane sun hanani sukuni nikam dai kaddarar rayuwa ta da mutane acikinta Wai me nayi masu ne?" "Saudat su waye?sukai min Wannan aikin!?Me na tare masu!?Meyasa ZASUYI min kazafi!?"Sun cutar da Ni sun Bata min suna a INDA ake ganin mutuncina da cikar kirki na,Yanzu fa su Mallam Bilya kilan ma da wasu malamai na sun san da Wannan maganar!?"Kuka ne ya ci karfina!?'nayi shiru Ina gunjin bakin ciki!" "Dafani saudat tayi tace"kiyi Hakuri! Nadiya a hanya muke bai kamata kina Tafiya kina Kuka ba! Duk Wanda yayi Miki sharri Allah ya saka maki, Domin shi sharri Dan aikene wataran zai dawowa Mai shi. Gashi anyi walkiya gari ya haska,Allah ya wankeki!"Yazo ya sanar maki abinda baki san da shi ba!"Kuma Duk Wanda yaji Wannan maganar Yasan ba halinki bane,ko shi malam zafin so da kishinki yasa ya yarda Amma Allah Yana nan...Saudat ta ida zancen cikin sigar rarrashi da tausayin kanwarta!" "Ajiyar zuciya,nayi tare da goge hawayena Nace bakomai ko su waye Allah zai saka min Saudat!" "Hakane,ki Cigaba da Addu'a Nima Zan tayaki Allah yayi Mana mafita ta Alheri,kowa baya wuce jarrabawarsa a rayuwa,Kinga Nima rashin mijin Nan da banida shi Yana damuna Nadiyatu,kullum sai abokiyar zaman mamana! tayiwa maman mu fade! Wai anje boko an dawo Babu Miji,ba kalar kazafin da batayi min,Wallahi Nadiya da Ana sayarda Miji a kasuwanni da mamana Lantana ta zuba dukiyarta ko nawa ne ta saya min ko Domin gorin Yan gidan mu."Inji Saudat tana zubda Hawaye!, "Na dubeta da tausayi Nace"Allah yasa MUDACE kiyi Hakuri komai Yana da lokaci da karshe! mutane NE suka jahilci hakan,Amma Idan Allah yace ka zamou ai ko Ana mazuru Ana shaho sai ka zamou."Da aure da haihuwa da mutuwa duk hukuncin Allah ne. "Kwarai da gaske to su mutane basuda gadonka Amma suna da na zancenka Allah ya iya Mana kedai Nadiya." "Ameen,Dai-dai Nan muka karaso kofar gidan mu, Sallama nayiwa Saudat tare da Bata SAK'ON gaisuwa ta zuwa ga mama lantana,hakan Itama Tace na gaida Mata da Innata,Tare da shaida min zata shigo da yamma,mu rabawa yam matan layinmu alawa,To nace da ita tare da godiya, Sannan na shiga gida, ita kuma saudat ta karasa gidan su, Daga gaba kadan domin makotanmu NE." *********** "Mansura Anci kwalliya taji ta Gani ta fad'a acikin wani Swiss less kalar omo da Baki,dinkin A sharp ne,yayi kyau sosai takalmi da jika,ta saka tare da mayafi,A hankali take Tafiya har ta isa inda motar Saddiq take,Jikinta tamkar anyi barin turare," "Da Sallama ta karasa bakin motar Wanda tun Daga nesa yake kallonta ta glass,ta burgeshi sosai."Bata Kara gamawa da shi ba sai da ta karaso wurinsa yaji kamshinta." "Lumshe Ido yayi da kyar ya Amsa Mata sallamar Yana murmushi,shima dai ba laifi yayi kyau sosai acikin gizna kalar kasa." "Bayan sun gaisa motar ta shiga,ya tada injin mota suka Kama hanya,A wata plaza suka tsaya ta sayi kayan kwalam suka fito suka wuce." "Bayan mintoci suka Isa sama road,inda gidan Ali yake,A Layi na uku suka tsaya gaban wani gida Mai kyau da tsari suka tsaya da Yake unguwar ba laifi ta masu shi CE,"Horn yayi Nan take Mai gadin gidan ya bude tare da dagawa Saddiq hannu,Kan motarsa ya kunno acikin gidan parking place ya nufa ya ajiye motarsa,kana suka fito, mansura sai rabon Ido ake Ana kallon gidan,Bata Kara tsinkewa ba,sai da suka shiga gidan, Saddiq Yana gaba tana binsa, har da canja Tafiya Ana wani kaudi da iyayi,"Falon suka shiga,da fara'ah Ali ya tarbe su tare da ba mansura wurin Zama Yana zolayarta." "Mansura Kam tayi nisa duniyar tunani Domin Wannan gidan shine irin gidan da takewa kanta mafarki,Wai aljannar duniya..."kalaman Ali suka dawo da ita hayyacinta inda Yake cewa shin ko amaryar kurma CE!?" "Murmushi Mansura tayi Tace"Hmnnnn...Da Ni kurma CE da bakuce Kuna so ba!" "Ayko ke kurma CE my mansura zance Ina so,Inji Saddiq cike da Jin Dadi," "Dariya Ali yayi yace"To ance ki zauna kinyi tsaye,Shiyasa nace anya Lina ji kuwa,Yawwa Bari na Kira madam suna ciki,tun d'azu fa muke ta jiranku."Hanyar bedrum Ali ya nufa." "Kuruuu..mansura ta bishi da Ido kamar mayya,A zuciyarta tana tunani da ace da Wuri taga Ali da shi zata so ba Saddiq ba,Shakar Sanyi da iskar falon tayi Mai dauke da nau'in kamshi ba Adadi."Lumshe Ido tayi..."Sai yanzu ne taji me Saddiq,ke Mata bayani,Ashe bayanin irin yadda abotakaar su,take da Aliyu take." "Yake,mansura tayi saboda hankalinta na Kan katafaren falon,Tace gaskiya Dear abokatarku ta burgeni Allah yabar zumunci." "Ameen Saddiq yace,Yana Dariya,sai ga Umaima gaba Ali abayanta,Yana Rungume da Khairat,"Ta K'asan Ido taga matar gidan,Aykuwa sai da ta Raina kanta,saboda ta hango manyan Mata na tafiya," "A'ah sannu da zuwa amarya,ayi Hakuri Ango Ina can Ina shiri,Inji Umaima tana Murmushi sannan ta zauna" "Nan suka gaisa da Mansura,wacce jiki yayi sanyi Domin taga iya taku,da wanka Wanda yafi nata,Domin less din da Umaimah ta saka ba karya. balle ma kayan adon da ke jikinta kamar wacce Zataje gasar kyau,shi kamshi ba'a magana."Shiyasa Ali ya take Mata baya," "Umaima sai Wasa take da zolayar Sadiq sai sannan suka D'an taba fira da Mansura,a hankali takewa mansura kallon kurilla cikin taku,Mansura ko sai wani sunne Kai kasa takeyi,Ali da Saddiq ma fira suke," "Umaima Tace"Bismillah muje aci abinci ko,"Cikin yanayin Isa da kasaitah," "Saddiq yace"kamar kin san Ina Jin yunwa,"Gimbiyar Ali," "Daman ai Dole kaji yunwa saboda kazama empty!"Inji Umaima "Ali dariya yayi yace"Hakane ranki ya Dade,To Malama Mansura kin dai ji,abinda Mai samma mijinki kalaci Tace" mu dai fa mun, shirya ki taimaka Mana Dan Allah ki dauke Mana nauyin nan," "Murmushi mansura tayi cike da kunya Tace"To Idan hagu Taki basai akoma dama ba! Yayata tana Nan ai." "Daga Ali har Umaima sun gane mansura bata san komai ba,Saddiq suka kalla da mamaki,signal ya aika masu,Nan suka canja magana,abinci suka ci da drinks,zafafa suka k'washi gara mai dadin gaske,sai dai mansura kunya ta hanata ta ci rabonta,saboda girkin ya hadou kamar ta tafie da shi,Bayan sun gama Suhaila tazo da yaran falon,Suka gaisa da Mansura, nan su Mufeeda da Mufeed suka dingA murnar tsarabar da Mansura ta Basu,tare da tambayar Saddiq Wacece," "Umaima Tace"Sabuwar Antynku CE Mansura," "Mufeed ya Bata fuska yace ummi Anty Nadiya fa!?"itaace Antynmu." "Mufeeda Tace"Eh ummi kice Abba ya kawo Mana Anty Naddy," "Gaban mansura ya Fadi Tace kaji min munafukai zakuyi bayani"Azuciyarta har ta kissama yadda zata dagargaje su idan sun shigo hannunta!" "Amma afili murmushi tayi tare da rikou su Tace,Nima Antynku CE kunji yarana,har Salim da salima ta dinga wasa da su,Khairat na Rungume ajikinta,har hotuna tayi da su,Nan wurin yaran suka sake da ita, Saddiq Dadi kamar ya kashe shi!"Umaima Kam Tuni tagano takun kissa irin na mansura Domin ta fahimci Bata Kai ciki ba!" "Suhaila ta mayar da hankalinta gurin t.v tana kallonta,tun da suka gaisa da Mansura Bata Kara bi ta kansu,har suka Tashi wucewa." "Kaya Umaima ta hadawa mansura tabata,kayane yan dubai mayukan shafi da turaruka masu kamshi da tsada,"Har wajen gidan sukayi masu rakiya tare da yaran," "Mansura sai karairaya takeyi,tare da masu godiya cike da gogewa," "Mufeed yace"Abba yaushe Momy zata dawo ne,!?"Mufeeda ta amshe da cewa Abba idan bazata dawo ka Kai mu da su salima mu ganta mu amso tsarabar mu ka mayar da mu ko ummi!?" "Umaima dariya tayi cike da Tausayin yaran Tace ,Eh." "Saddiq ko wani kallon tuhuma mansura ta watsa Masa Wanda ya razana shi,yace Zan Kai KU sai na dawo,"Nan suka shiga Mota suka wuce." "Aliyu da Umaimah Nan sukayi tsaye suna tattaunawa Akan Wannan feqaqqiyar yarinyar Mai idon rashin mutunci da Saddiq ke neman kwasowa kanshi,"Domin adan zaman awa biyu sun fahimci mansura Yar duniya CE,"dan idonta a tsaye suke Nan dai sukayi masu fatan abinda yafe Zama Alheri suka shige Daga ciki,su sami yaran sai hayaniya suke Wai story book NE, Suhaila ke karanta masu tana masu tambaya,shine ake rige-rigen Fadi amsa,Wuce su sukayi izuwa falon Umaima da ke gefen Bedrum dinta daya," ****************** "A hanya ta wani Sha kunu sai cika take tana batsewa!" "Gefenta ya kalla sai dai,Kawar da fuskarta tayi gefe!" "Ranki ya Dade Idan nayi laifi ai min afuwa!"Menene!?"Inji Saddiq da sigar damuwa, "Hawayene suka zobou Mata tare da turo Baki,Tace Yanzu Dear,Su Mufeeda da Mufeed Basu ma sanni ba ko ahoto baka nuna masu ni,ba!?"Ana masu zancena suna na wata Nadiya!?"Gaskiya banji Dadi!ba," "Kiyi Hakuri my Kinsan sha'anin kurciya,Kuma ita sukafi sani Amma ai Yanzu Kinga sun sanki!?" "Me suke agidan nasu Aliyu,Naga yau akwai school bama weekend ba!?"Kuna Wai Anty Jalila tayi Tafiya ko ka gayamin,Ni Kama bani lambarta na kirata nayi Mata ya hanya,"Mansura Tace tare da fiddo wayarta tana kokarin Dialing no..." "Wani takaici yaji Jin an ambaci Jalila..!" "A hasale yace,ba zan bayar ba!" "Saboda me!?"ta tambaya," "Saboda batasan da labarinki ba!" "Kenan baka sanarda ita zakayi aure ba!"ko kana Jin Tsoronta NE!?" "Hmnnnn,tsoro fa!Ay Babu Wannan mace Aduniya da zanji Tsoronta,Mahaliccina ubangina shi nake tsoro ba kowa ba!" "Nar nar mansura tayi,tare da kauda kai Alamar fushi take,shi Kuma Saddiq driving Yake Amma hankalinsa na kanta har suka iso, Makaranta." "Kokarin bude motar take afusace sai dai yasa Lock amotar," "Cikin fushi tace" ka bude min na fita," "Murmushi yayi yace"Ranki ya Dade maida wukar Zan Miki bayanin komai Saboda fushinki tashin hankalina NE!"Daman yaran sun Jima gidan Ali kusan wata daya da dauri,Na saki Jalila!..." "Me kace!"mansura ta katse shi tare da zaro ido da mamaki..." "Mun rabou da maman su Mufeeda saboda wani Abu da gitta Yanzu hakan tana gidan su,Shiyasa nakai,yaran gidan Ali,Amma da anyi hutu next week Zan mayarda su Kebbi inda iyayena,kafin ayi auren mu nadawo da su saboda karatun su." "Hannu mansura ta aza akai,Kuka take rerawa marar sauti Wanda azahiri na kissa,akuma badili na farin ciki,' "Hakuri Saddiq ke Bata tare da rarrashi yace meye abin Kuka kamar ke aka saka!"? "Tace,Dole nayi Kuka!Dear Meyasa zaka saki Yar uwata,nasan watarana akaina zai dawo,Tunda kafara yi akan ta, wallahi Ina sonta!,Sam bai kamata ba!Duk abinda tayi maka sai kayi Hakuri ko domin yaran namu!"Wa zai kula da su?wazai Basu tarbiyya? Shine su Umaima ke magana ban gane ba,yaran ma suna tambaya Bangane ba,na dauka tafiyar CE da gaske Ashe hakane!"niKam gaskiya Dear bazan lamunce Wannan bacin sunan ba! kana son adinga fadin saboda zakayi aure ka saki matarka!?"Ko Kuma ace nice sanadi!?" "Duk ba Haka bane mansura share hawayenki kiyi Hakuri Nike aure Kuma banayi in dai da Jalila NE,Dan Allah karki Kara min maganarta!"Yace ransa na Masa daci!" "Goge fuskarta tayi da gyale,tare da daukar Kayanta Tace"Bakomai Dear Allah yasa mudace,Nidai kayi tunani akai,"Allah ya huci zuciyarka. "To, Nagode ki saki ranki sai munyi waya," "Fita mansura,tayi amotar azuciyarta farinciki ba'a Magana,"shi Kuma wucewa yayi ransa Babu dadi!" *'YAR MUTAN DIKKAWA CE* *SHARE* *VOTE* *&* *COMMENTS* *2020*✍🏼 [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* _________________________________ ® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ _________________________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/ *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFA NA 30* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *GODIYA MARAS ADADI GA NABILA'S ONLY GROUP FANS, INSIDE AREWA,NABEEHA NOVELS, SISTER'S OF JANNAH,004 HAUSA NOVELS, TABBAS INA JIN DADIN COMMENTS DINKU, ALLAH YABAR ZUMUNCHI AMIN* ______________________________________ Bayan wani lokaci "Yanzu Kam Abubuwa da dama,sun faru Kasancewar a kullum lokaci kara Tafiya yake,haka kwanaki gudu suke," "Yau da gobe Bata bar komai ba,komai an kammala na shirin auren Nadiya da Jawad," "kullum suna manne da WAYA,Yana tsarata da kamalai masu dadi!"Wanda akasan zuciyarsa jin yake kamar ana watsa masa garwashi!"Saboda ya tsani jin sautin muryarta,hakuri kawai yake har yaga ta shigo hannu," "Haka Saif Yana zuwa Inda Nadiya amatsayin Jawad,shi kuma jawad yana kiranta awaya tare da turo mata texts" "Momy tasa an hadouwa Nadiya kayan lefe na idon duniya daga dubai saitin akwati biyu masha Allah,"An gyara gidan ango tsaf,Alh.malami sambo ya zuba komai na furnitures sabbi fil aleda sashen amarya dana ango sama da kasa ko'ina angyara,Kuma Ya fad'awa Mallam Balarabe Basu BUQATAR komai sai amarya da 'yan tarkacen ta Wanda ba za'a rasa ba,"ita ma Momy ya ce"Ta amso kudeden ta na kayan furniture da ta tura oder,taji Dad'i sosai Kuma tayi ta godewa Alhaji malami. "Malam Balarabe ya nuna RASHIN yaddar SA,sai dai Alh.malami ya rinjaye shi,saboda yace ba komai da Nadiyatu da Jawad Duk yaransa NE kuma shine ya dauki nauyin yimasu komai,karsuji komai Allah dai yabar zumunci." "Haka Malam Balarabe ya hakura amma yaso abari su kaiwa yarsu duk abinda Allah ya hore masu dan gudun bar mata abin fade,Amma fafur Alh.malami ya hana ayi komai, shi yayi komai na auren." "Momy taji dad'in abinda Alh.malami sambo yayi musu kullum cikin Masa GODIYA take,Saboda samun abokai irin sa awannan zamani sai an tona" Ta Kara shiryawa harkar auren,ta gayyaci kawayenta da sauran Abokan kasuwancin da danginta ta,taso ta Kira dangin mahaifin Jawad sai dai RASHIN cika alqawarin marigayi Babansa yasa tafasa sanarda su,"Amma tana burin bayan aure taje da jawad da Nadiya har kasar su domin su gana da kakannin jawad din da kuma sauran danginta." "Saboda daman ta kosa taga auren Jawad, Domin burinta da na marigayi ya kusa cika,bugu da kari Idan ta tuna surukarta sai taji dad'i,tun Ranar da Saif ya kawo Mata Nadiya ta ganta taji tana sonta,Kuma ta kwanta Mata arai,Bugu da k'ari nutsuwarta ta burgeta"Sannan Idan ta Dad'e tana dubin Nadiya sai taga tana Kama da Jawad din haske NE kawai bambancin su."Amma tafi yarda da zancen nan na idan so yayi so Yana Sanya Kama," "Ankai lefen Nadiya agidan su da ke Tudun wada area Argungu,Hankalin Innerie da Kawarta Hajiya lantana da sauran jama'a ya Tashi ganin Kaya kamar shago,"Abin ba'a cewa komai,"Akace ido kannan kai," "Kawayen Hajiya khaltumi (momy)sun Sha mamaki ganin irin gidan da Jawad ya d'auko Matar aure,yadda suke da arziki Amma ya tsaya ga auren Yar karamin gida talakawa,"Duk da mafi akasari acikin su sun kawo tayin ya auri yaransu masu aji, manyan Yara,da wayayyi,Amma ya kafe, yace bayaso,"Ashe da rabon ya kwaso yar marasa arziki," "Hmnnn Abin nema ya samu Nan Hajiya Salma da Hadiza suka dingA gulmah,suna yiwa su lantana wani kallo,Hajiya Maryam(matar malami sambo) murmushi tayi saboda ita ta daban CE acikinsu,"Daman halinta na kirki daya da mijinta,," "Bayan dangin Innerie sun Gama duba kayan,cike da murna sai sa saka Albarka suke da fulatanci Dan ko Hausa basuyi," Sannan ne Hajiya Maryam, ta CE to KU Tashi mu tafi Hajiya Hadiza,Idan Kun Gama," "Kunya CE ta Kama su saboda sun gane Maryam ta fahimce su,Amma fuskewa sukayi sai wani hurar hanci suke, suna yiwa bayin Allah Yan uwan su,kallon hadarin kaji, saboda kawai suna talakawa ( _Sai kace arzikin nasu sune,ko su suka baiwa kansu,Hattara dai wulaqanci ba kyau!!Rana 1 Allah Zai amshe Daga gareka yaba Wanda yaga dama_) "Hajiya Maryam da fara'ah tayi Sallama da sauran jama'ar gidan suna kokarin tafiya" "Ay kuwa Hajiya lantana da Baba kiruwa (Yayar Innerie)kayan tukuici suka damkawa Hjia Maryam daidai karfinsu suna godiya da Allah Sanya Alheri." "Baba Kiruwa Cikin hausarta da ba dai-dai ba ta fulani,Tace Hashiya Dan Allah kushi da Hakuri kinshan harkar talaka!"Sai ahankaki,mungode!kaya shunyi kyau Allah shanya albarka," "Ameen,Hajiya maryam tace tana dariya,tace ba komai suma sun gode," tayi musu sallama tare da karba kudin tukuicin dubu ashirin Wanda da kyar aka had'a aka Basu da Sauran Tarkace,Tayata kwasar kaya sukayi wasu daga cikin gidan sukayi ta fice,"Ko da Hajiya Maryam ta fito su Hajiya Hadiza da Salma sun shige Mota da makotan momy sai tsegumi suke,ganinta da Yan Kaya dariya suka kwashe da ita,suna fadin Allah ya raba kowa da harkar tsiya,''Nan suka wuce gidan momy ran Hajiya Maryam ba Dadi saboda Sam batason irin rayuwar ta su." "Yanzu Kam aski ya kusa Kai gaban goshi Domin Nan da mako biyu za'a daura auren Muhammad Jawad Husamaddin da Nadiya Balarabe."Su Saudat da Mardiyya Yan matan amarya anyi anko Duk da WALIMA kawai za ayi na auren,Su Esha ma Nan da wani mako zasu dirou Argungu shagalin Aure."Naseer ma Tuni ya hakura da Nadiya yabarwa Allah komai Daman Yasan Nadiya tafi karfinsa,karambani NE irin na so," ************A gefena ba laifi Mama lantana da mamana suna kula da Ni sosai tare da gyara min jikina,Duk mama tana Jin Kunya sosai Abu ga fulani....Amma tafara min gyara kafin Yan uwanta Suzi suci gaba daga inda ta tsaya. A Cikin kwanaki uku fatata tafara sheki da haske,nayi kyau sosai harda jiki nayi saboda Yanzu hankalina ya kwanta,Jawad na bani kulawa sosai,"Haka komai nakeso agidan mu ina samu," "A BANGAREN mansura da Saddiq suma anyi baikoh har Ranar aure an saka,Idan akayi Auren Nadiya da sati Daya za'ayi nasu,"Mansura ta Sami kud'ade masu dama awurin Saddiq tuni tafara dilka da gyaran jiki,Ta kammala final exams dinta,Shiyasa ta koma gida Kebbi,suna Shirin aure,"suma dai Ranar aure kawai ake jira."Har yanzu Nadiya batasan waye matar yaya sadiq dinta ba,Saboda tuni ta manta da labarin mansura arayuwarta tun alokacin da sukayi fada,"Bata kara jin labarinta ko kuma ta ganta." "Dukkan wasu shirye shirye da akeyi na aure Saif shi ke zuwa a matsayin babban abokin ango haka saudat abokiyar amarya da sauran yaran makota kawayen su. A gefe kuma saif ya nunawa su saudat Jawad har gaisawa sunyi da shi a matsayin ango,"Kuma ta yaba da hankalinsa da kuma kyaunsa azuciyarta," "Saudat ta baiwa Nadiya labarin jawad,kuma ta yaba da shi sosai cike da jin dadi,"Nadiya ma tayi murna da hakan,"Saboda ita baifi sau biyu ko uku ba haduwarta da angon nata ba,kuma har yanzu batada hoton shi shima bayada nata hoton," "An kammala komai na shirin aure nan da mako mai zuwa za'a sha shagalin bukin auren jawad da Nadiya,Yan uwa da abokan arziki har sun fara zuwa taron taya murna."Mussaman dangin innerie fulanin Dakin gari da Bagudo." ********"Umaima da mijinta Ali suna zaune lafiya da yaranta tare da kanwarta suhaila,"Bayan sunyi nasarar samun amincewar ummah akan ta hakura suhaila tayi karatunta a nan sokoto,"Da kyar umma ta amincewa su umaima Akan zata bar suhailat ta zauna a gurinsu,Saboda tafi son suhaila tayi karatunta a kano(BUK),"a inda take ganin 'yarta yadda zata sa mata ido akan duk wani motsinta da kyau. "A karshe dai umma ta amince amma sai da umaima da Ali suka daukar mata Alqawarin kula da suhaila."Sannan ta yarda." "Umaima taji dadi sosai,saboda bata san kowa ba a sokoto aure ne ya kawota,Tana neman dan uwanta agefenta,Fatan ta Allah ya baiwa Suhaila miji a sokota sai tasamu 'yar uwa a gari." "Ali yayi kokarin samawa suhaila gurbin karatu a state university sokoto, tafara zuwa daukar karatu hankalinta akwance,"Umaima na kula da duk wani yanayin na kanwarta,da shigarta da kuma irin kawayenta,"Tasa ta ajiki sosai ta zame mata abokiyar karatu da shawara ta hakan ne zata fahimci duk wani motsinta," *******"Tahir do kansa ya samu dangin mahaifinsa har garin gwaranyo,Ya shaida masu cewa yasamu matar aure,yana son suje su nema masa aurenta a garin Cikin unguwar Bado,Haka kannan mahaifinsa suka shirya suka shigo sokoto domin nema masa aure,Anyi nasara kuma an bashi yarinyar har baiko sai da akayi."Tahir yayi masu Godiya tare da masu Sha Tara na Arziki,Daman Yanzu Yana zuwa Kuma yana masu aike duk da Hajiya bataso Amma ya Gane duk Dan kwarai yafi kadari da daraja agidan ubansa. *************** "Hajiya jiki yayi laushi saboda tayi neman magani har ta gaji,Har yanzu Tala,jalila da rashida babu labarin maza kamar anyi ruwa an dauke," "Mahmud anyi service an gama,Yanxu hakan ya samu wani karamin aiki,A kamfanin robobi da ke cikin garin" "Jalila kam ta samu lafiya yanzu a hankali ta debe komai aranta,tayi jiki da haske tana cigaba da sana'ointa,"Amma tana jin so da kaunar sadiq aranta agefe kewar yaranta na damunta,"Tun ranar da ta fito gidan sadiq rabonta da yaran,"Wannan shi ke sata kuka!"Idan ta tuna,Tabbas Anty Talatu tayi juriyar rashin ganin yaranta shekara da shekaru!"Allah sarki wai abinda ka mallaka yake kokarin maka nisa," *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 _"Kuyi hakuri da wannan fans rashin caji ya sanyani gaba saboda muna fama da rashin wutar kantarki,Kawai ayi manage🙈"_ [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* _________________________________ ® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ _________________________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/ *SHAFI NA 31* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *SADAUKARWA GA MAI GIRMA KUNGIYATA MAI ALBARKA✍🏼 PEN WRITERS ASSOCIATION ALLAH YA QARA HAD'A KAN MU YA SANYA MANA HASKE DA CIGABA MAI ALBARKA ACIKIN AL'AMURAN MU YA QARA KAIFIN BASIRA DA ZAKIN HANNU AMEEN, ANATARE🤝🏼ABOKAN ARZIKI ALLAH YABAR ZUMUNCHI,INA MAKU FATAN ALHERI DA SAMUN NASARA MAI D'AUREWA A RAYUWA😍UP UP UP PEWA* _Only the exquisite and whizkid writers are opportune to be PEN writer_ *SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!! INA MASOYAN MU...INA MA'ABOTA KARATUN LITTAFAN MU....MUNA KIRAN KU DA BABBAR MURYA,MUNA SHAIDA MAKU CEWA KUNGIYRMU MAI ALBARKA PEWA TA SHIGA GAGARUMAR GASAR NAN TA WOMEN24 TV WHATSAAP GROUP(AWARD),MUNA SON KU FITOU K'WANKU DA K'WARK'WATAR KU,DOMIN KU ZAB'EMU PEWA,DOMIN SHIGA SAHUN GANI GA IDO A RANAR VOTING, SAI KU TUNTUB'I WANNAN LAMBAR,INA MASU SON MU DA K'AUNAR MU KUFITOU KU ZAB'E MU GA LAMBAR.KARKU MANTA DA SUNAN PEN WRITER'S ASSOCIATION MUNGODE👍🏼* ______________________________________ "Rana bata karya..."Yau Allah Yayi dubban jama'a na birni da karkara sun shaida da daurin Auren Muhammad Jawad Husamaddin da Amaryarsa Nadiyatu Bello (Balarabe)A Kan sadaki naira dubu Hamsin kacal," "Yau Rana CE ta farin ciki awurin Yan uwa da Abokan arziki musamman iyaye,Haka Kuma Rana ce ta bakin ciki da tashin hankali!"A wurin Jawad da Nadiya," "Tun Alokacin da aka Gama d'aurin Aurensa abokansa da Aminan marigayi mahaifinsa sukayo Masa caa aka,suna taya shi murna da nasiha,Sai yaji wani bacin Rai!"Ya ziyarci Rayuwar shi,"Danasani ne fal aransa,Saboda Yanzu Shi kenan an fara kiransa da mijin Nadiya Kuma an damka Masa Amanarta! yarinyar da ya tsana Aduniya!" "Suna barin masallaci da akayi d'aurin Auren,Gida suka koma,nan jawad ya samu ya kebe acikin jama'a da Abokan sa,Kuka!ya ke tamkar karamin yaro,ya rasa meke damunsa,Da kyar abokinsa Saif,ya lallaba shi yayi Hakuri suka shiga Cikin abokai," "Hajiya khaltumi Kam Baki har kunne duk Wanda ya ganta zai hangin farinciki kwance a fuskarta,Burinta da na mijinta ya cika Ina ma ace Yana duniya ya ga Wannan RANAR alokacin da aka dawo d'aurin Auren momy har Kukan Dadi sai da tayi" "sashen Jawad ta shigo tana dariya da shewa tare da ma'aikatan ta,Kayan abinci da Abin Sha aka jerawa Abokan ango,kala-kala,"Sannan momy ta kira Ango domin yazo ya gaisa da abokanta da sauran bakinta,Jiki ba kwari saif da jawad suka bi Bayan momy,tana ta Jan su da Fira har suka shiga Babban falon ta da ke cike timjin da manyan Mata masu shiga ta Alfarma,Cikin ladabi ya dinga gaisawa da su,Albarka da fatan Alheri suke Masa,Harda hotuna da shi,"Momy an canja wani kayataccen wanka,Cikin ado na Gani na fad'a,"Tayi kyau matuk'a kamar wata yarinya Nan itama ta jone aka dinga daukarsu hotuna,harda Maman saif da yayyensa Mata,Gwanin burgewa,"Murmushin dole NE jawad keyi Ana daukar pics Amma akasan zuciyarsa kamar mad'aci," "Anci an sha anyi hani'an komai akwai naci da Sha agidan Hajiya khaltumi Husamaddin,Tayi rabon Kaya kamar hauka,"Tabbas ta barwa mutane abin fad'a Domin bukine akayi na kece raini da ban mamaki, Wanda yasamu halartar Wannan bukin kawai zai iya bayar da shaidar irin yadda tsaruwarsa da haduwarsa Yake, sai sam BARKAH." "Tun da Naga Yan uwa da Abokan arziki na shigowa Taya Mamana Fatima(Innerie)murna na dinga rusa Kuka!"Haka kawai naji fargaba da faduwar Gaba!ya d'arsu azuciyata!komai ya tsaya min a rayuwa,wani k'unci nakeji azuciyata,Na rasa meye dalili? Saudat CE tayi tsaye akaina har na hakura na daina Kuka!" "Da misalin karfe 2:30 na rana aka shiryani acikin wani tsadadden material Arsh da head Bak'i,nayi kyau matuk'a,Mayafi da takalmi da jaka da sauran kayan ado nasa wad'anda suka Dace da shigata ta Alfarma,"Babban Hall din Adamu Augie muka Hallara inda za'ayi WALIMA,"Sheik Akhram Hamza Madawaki,NE malamin da zaiyi walimar,An k'awata wurin Gwanin sha'awa da decorations, Haka kawayen mumy sun Hallara har ita kanta Uwar gayya Mai gayya,"Cikin shiga Mai kyau ta kece raini,"Nima ba laifi kawayena da yan uwana kowa yayi shigarsa ta Alfarma karfi baifi jiki ba!"Da aka fara walima malam yayi min nasiha sosai akan rayuwar Aure da hukuncinsa,"Yace"Nayi biyayya,Hakuri,Sannan na dinga Kawar da Kai,da Kuma juriya,"Haka mallam ya janyo hankalin Mata sosai Akan su daina aikata ayyukan ashsha!"Su kula da bakin su adinga rufawa aure Asiri a daina tona asirin aure da mazaje,yace a kula Baki mugun Abu ne adinga saka mashi linzami,Mallam ya Kara da cewa Mata su dinga Kai zuciyoyin su nesa Akan mugun kishi!"Zargi da Kuma bincike!"Da ganin kwakwaf saboda Babu kyau,"Mallam Akhram Hamza ya qara da Jan hankalin Mata su zamo masu kula da yaran su Domin su zamo abin alfahari a ko'ina a dinga kula da tarbiyyar Yara adaina sangarta su ana sake masu yace Mata aji Tsoron Allah adaina satar kudi satar fita da leqen garka da guma da sauran dabi'u Marasa kyau,"A KARSHE malam fatan Alheri yayi Mana acikin rayuwar auren mu,tare da Addu'oin kariya Sannan aka shafe Addu'a,"Malam da tawagarsa suka wuce,Mu Kuma Hotuna muka dinga yi da su momy. sai murna Yan uwana keyi saboda ba laifi Babu makusa gurina, shigata ta amshi jikina nayi kyau matuka"Ina jiyo Abokan ta sai yabani suke nayi kyau sosai selfie kawai mukeyi Ni da su da Yake Yan duniya NE,"Nima wayancewa nayi muka jone karsu Raina ni,"Ay kuwa na basu mamaki su da feqaqqin diyansu da suka zo gogawa da Ni,Wanda Tuni suka Sha mamakina,Haka aka tafiyar da bukin walima cike da Jin Dad'i,"Anci an Sha anyi guzuri anyi hotuna,An baza wanka."Acan na hango Yan group din NABILA'S fans acikin wani ankon rantsattsen less Mai black and red da white stones,"Kowacce tayi dinki Mai kyau,suma Yan gidan NABEEHA novels an Sha kyau, sunyi Nasu anko na musamman sai hotuna suke da Kawar su NADIYA,"Tayi masu godia sosai kayan aure tasa Saudat tabasu Suma sunji Dadi matuqa Baki har kunne yadda aka karrama su," Bayan angama gaisawa da selfie kowa ya nufi gida na nesa da na kusa," "A gajiye muka dawo gida ni da kawayena kowa sai fad'in ALBARKACHIN bakinsa Yake dangane da irin haskawar da nayi ayau da Kuma yadda surukar tawa ta burge mutane da dama yanda take nuna kulawarta da soyyayar ta agareni, kowa fatan Alheri Yake Mana kada momy ta zo ta canja min Daga baya." "Ni Kaina naji dad'in hAkan,Dan Momy ta Nuna ta na Sona sosai Ina ganin Banda matsala tunda na samu soyyayar mijina da surukata,A gefena su Saudat suka zAuna sai zolayata sukeyi,Fadi banza Fadi wofi cikin annashawa,Innawuro Yar gidan Baba k'iruwa CE ta shigo d'akina da abinci,"Da sauran k'annai na,"Da suka zo daga Bagudo wasun Kuma Dakin gari,Shigowa su kayi tare da ajiye Mana abinci da abin sha da fulatanci suke magana Dani Ina Basu Amsa,Saboda Nima na iya tun Ina karama mamana da wuya tayi min Hausa sai da ta tabbata inaji Ina Kuma iya mayarwa. Saudat da Mardiyya abincin suka zuzzuba a flats harda matsa min dole na sa hannu muci ba Domin Ina so ba,nima na Dan tsakura naci saboda komai bana Jin dad'insa,"tun sanda naji Ana Shirin kaini gidana jikina ya sauya,Da yake Al'adar garin namu sai Bayan Isha ake Kai Amaarya." "Da misalin 8:30pm na dare motoci ne bila adadin a kofar gida,Bayan iyayena da Yan uwa da Abokan arziki sunyi min huduba!Ina Kuka Wanda da kyar aka rabani da jikin Mamana!"Nasha Kuka haka mamana kunyar ta fulani CE tahanata Kukan!!"Amma zuciya tayi laushi!"su Saudat Duk dariyata suke da farko sai like da suka ga Abin da gaske ne sai suka tausaya min harda Hawayen su!"Nan aka tattara aka wuce da Ni gidan momy aka fara kaini ta Sanya Mana Albarka tare da yimin huduba ita da Hajiya Maryam da malami sambo,da sauran kwayenta a katafaren falon baki da ke gidan,Da zamu wuce kyautar Kaya tabani acikin akwati. Wanda bansan ko meye aciki ba!" Baba kiruwa da lantana suka rike kayan,Alokacin Ina kudundune acikin katon mayafina,su na Godiya da Allah Sanya Alheri,Daga nan katafaren gidana da ke millionaires quarters Argungu,"Aka kaini." "Tunda aka shiga harabar gidan jikina ke b'ari saboda tsoro!"Haka mutane suka dinga kauyanci da santin gidan,"Da Addu'a da salatin manzo na shiga Cikin falon gidan da sunan Allah da Kuma kafar dama," Bayan iyayen sun kaini,nasiha da fatan Alheri sukayi sannan suka wuce,"Ya yi saura Daga Ni sai yan Matan Amarya, aka Bari a dakin,Bayan mintoci sai ga ango da abokansa sai dai Daga jinsu Bazasu wuce Mutim uku ba,"Abin yabani mamaki yanda naji angona Yana zuba surutu da su Saudat,"Wani iri naji ango Babu Kama Baki a Ranar farko kamar rediyo!"RAS!!!gabana ya Fadi Alokacin da naji an zAuna kusa da Ni,"Nan aka kammala Addu'oin da ake, kowa ya watse!"Kara hade Kaina da gwuiwa nayi Ina rera Kuka marar sauti ganin su Saudat sun tafi sun barni,"Shi kenan an rabani da mama da Baba!" "Tsakin da akayi da karfi NE ya dawo da Ni hayyacina," "Ko da na dago kaina Banga kowa ba ga alama ya fita,Shiyasa Ni kuma na cigaba da kukana!"Da Naga abin ba rawa ba tumami,Ango shiru kamar an aiki bawa Kai sakou garinsu,"Ba shi ba labarinsa,Shiyasa na Tashi nayi Alwala nayi sallah Ina Addu'oi,nutsuwa na samu araina Daga Nan sauya Kaya nayi da Yake Naga akwatuna na,adakin Bayan na shirya azkharul naumy,nayi na kwanta zuciyata cike da tunanin abubuwa masu yawa." ********* "Mansura taji Dadi Sosai Alokacin da Saddiq ya shaida Mata Zaije Kebbi auren Nadiya,"Saboda aganinta Yanzu ta samu Sadiq har abada batada sauran damuwa ko fargaba,"Sha'anin Shirin Aurenta Yanzu shi tasa a gaba,"Tuni akayi dinkunan aure,Da wakokin Aure, INVITATION CARDS ma an buga ba kalar bidi'ar da ba'a zuba aciki ba,Har an fara inviting mutane,Gidan su mansura ba baya ba wurin chasu Shiyasa aka zuba HARKAR da za aje ayi chasu, "Su Mufeeda da Mufeed an Sha shagalin bukin Anty Naddy saboda kwanan su uku da gwaggo suna yawon zuwa gidan Innerie har Ranar aure,"Saddiq ma yayi kokari sosai wurin bayarda gudummuwar SA,"Daga Malam Balarabe har Innerie sai dai fatan Alheri Domin sun Sami alherai da dama awurin Yan uwa da Abokan arziki." "Ana wata ga wata!Domin Tuni saukin Soyayya Mai karfi ya rinjaye su batare da sun farga ba!"Har yayi nisa da tasiri azukatan su,"Kauna Mai yawa ta d'unke tsakanin Saif da Saudat adalilin had'uwar su auren Jawad da Nadiya,"Saif baiyi k'asa a gwuiwa ba,ya sanarwa Saudat irin sonda Yake Mata,tare da labarta Mata Duk abinda ke faruwa Dan kada ta zargeshi Nan gaba!" "Saudat ta nuna rashin Jin dadinta sosai har tana tunanin gujewa soyyayar Saif!"Sai dai bazata iyaba!Domin Daman abinda take nema NE Ido rufe"Wato mijin aure Gashi ta samu agaskiya bazata iya Wannan sakacin ba!"Amma ta nunawa saif bacin ranta da rashin Jin dadin yadda suka yaudari Nadiya."Tare da wasa da hankalin su day na iyayen su Kuma ta Nuna Masa Wannan halayen ba masu kyau bane,Kuma ba dabi'un kirki bane." "Hakuri saif ya Bata tare da daukar Mata alqawarin zaiyi kokari ya taimakawa Nadiya Kuma ya kubutar da ita Daga cutar ta da Jawad ke kokarin yi!"saboda ko shi Yanzu ya saduda Nadiyatu na bashi tausayi,ba ta cancanci hakan ba." "Hankalin Saudat ya kwanta amma ba taso hakan ba!"Mafita suke nema Mai sauki ita da Saif,yadda Zasu iya shawo kan matsalar!"Wanda har suka rabu da juna Basu nemota ba wata hanya Mai sauki ba da zasu Gane bakin zaren!"Saudat tasan labarin Jawad da dadewa awurin Nadiya kamar yadda Saif Yasan Labarin Nadiyatu awurin Jawad,"Wanda kalmar *TARBIYYA* ta zamou Silar hamayyar su" *********"Al'amurra da dama sunyi masu sauki agidan,Haske suke Gani kamar yadda Mallam ya Gaya masu,matukar suka dogara ga Allah Kuma sukaji tsoronsa tare da barin sabawa umurnin Allah da manzo to hakika zasu ga sauyi.'' Tabbas shawarar Mallam tayi masu aiki da Addu'oin da ya Basu na AYATUL SHIFA," "Tun sanda Jalila tafara karanta su, ta dinga Jin sauki arayuwarta,Har wani kunci ta daina Jin yana damunta kamar baya,"Haka gefen Anty Talatu bautar Allah tasa agaba da neman zabin ubangiji,Ga business da takeyi domin Tahir ya Bata jari,Tana sana'oi Cikin ikon Allah,sai Gashi Allah ya bude masu kasuwa ita da Jalila sai San BARKAH Abu Daya ke ci masu tuwo akwarya rashin samun Miji har Yanzu, Anty Talatu kusan shekara hudu ita Kuma Jalila wata biyar a na shidda kenan ba amo ba labari," "Rasheeda Kam wani Alhaji Dauda Dan kasuwa ne Mai Mata biyu ya fitou nemanta,A hakan ba Domin irinsa takeso ba,ta hak'ura saboda shi dinne tasamu," "Hajiya ma ba Sonsa take ba!"sai Domin tagaji da ganin su, su dukansu agabanta!"Amma aranta saurayi taso Autar ta samu ta aura Mai dan kud'i inda zata huta," Sai dai tun ran gini ran Zane."Su Hajiya dole a hak'ura,"Da hukuncin ubangiji," "A yanzu babu jayayya acikin lamarin Domin kuwa Jalila ta gane gaskiya ta fahimci mansura ta yaudareta!" saboda har Yanzu bata k'ara samun labarin mansura ba!"Taje har makarantar su Danfodiyo ance mata mansura ta KAMMALA karatunta wata uku,da suka wuce!"har ta koma Kebbi da Zama anan ta jiyo bayani ga wadanda take tambaya a hostel din,cewa mansura ma aure zatayi Amma anan sokoton za'a kawota," "Sam Jalila bataji Dadi ba!"Duk da bazata koma wurin Mallam zakiru ba!"Ta so ace taga mansura saboda taji dalilin da yasa zata yaudareta. Daga ta taimaketa sai ta karbe Mata kudi, Babu ita ba labarinta,"A Haka Jalila ta koma gida Rai Babu Dadi!"Tana tunanin irin asarar da tayi sanadin neman magani!Ba biyan buqata ba kudinta sannan Kuma ba Yar aikenta!," "A hakan jalila ta hak'ura Daga Nan ta dukufa da Addu'oin AYATUL SHIFA, da KUN FAYA KUN,da sauran Addu'oin tsari tare da nafilfili ba dare ba Rana,"Domin samun nutsuwa da cigaba da neman mafita awurin Allah (SWT)." Washe gari ********Tun adaren jiya da Jawad ya fita Daga sashen Amaryarsa har Yanzu da gari ya Waye bai Kara waiwayenta ba,"Yana Dakinsa Yana Kuka har bacci ya kwashe shi!"Yanzu ma yana Tashi wanka yayi ya shirya saboda Daga yau Zai fara baza makaman yaki agidansa," "A gefena ma tun Daren jiya da nayi kukan bakin ciki har na hakura,"Amma Ina mamaki ace Ango yayi min tsaki ya fice ban kara ganinsa har Yanzu!"Wannan wane irin rayuwa CE!?,wane laifi na aikatawa Jawad da Zai min hakan!?"ko dai duk masu Suna Jawad hakan suke Basu da kirki? "Jikina ba Dadi na Tashi na fad'a rantsattsen bayina nayi wanka,Bayan nayi sallah,komawa baccin nayi sai kusan 11:00am na Tashi,inda aka ajiye ledojin kaji da lemuka har yanzu Suna gurin ban Kara bi ta kansu ba. Bayan na Gama shirina tsaf Cikin wani boyel less maroon nayi kwalliya sai zuba kamshi nake, fitowa falon nayi Ina k'ara gyara guri,Nan ne nakara yiwa gidan kallo,ba karya gidan ya tsaru Kuma ya burgeni musamman falona Mai kalar maroon da milk,bedrum Dina Daya milk ,dayan Kuma maroon,ba laifi gidan yayi,Sama ko inaga gefen Jawad NE Shiyasa banyi kokarin hawa saman ba,"Bare naga duniyar da ke can," "Bayan na kammala goge da share-sharen K'asan nawa turare gidan nayi ta ko ina ya d'auki k'amshin turaren na Maman QURAISH Yar mutan maidugurin barno wacce ta shahara wurin hade amare da kamshin jiki,tufafi,da gida," "Kichen dina na shiga komai atsare,sai dai ba komai na abinci,Shiyasa na dauko flats na Koma dakina kaza Daya na bude naci na koshi sannan na aza lemu. Daga nan falona na Koma na zauna Ina jiran su Saudat Domin nakira ta Tace min tana Nan zuwa." "Idona na Kan t.v Ina kallo naji karar takalmi na saukowa Daga saman benen,Ban dauke idona ba!"Saboda ko ba'a fad'a nasan Jawad NE ke kokarin saukowa," "Da gadara yake Tafiya,sai wani kamshi Yake Sha,"Yana saukowa Yana waya," "Wani faduwar gaba ya riskeni!"Duk da ahankali Yake maganarsa Amma muryar da naji ce taja hankalina zuwa inda yake!" "Cike da tashin hankali na dubeshi Tabbas Idan idona ba gizou yake min ba shi ne!"Sanye yake da wando 3quarter,da riga ba inda dressing dinsa ya sauya a yanda nasan shi a day duk da yanzu ba Suma akansa Kuma ya rage Jiki Amma tabbas shi ne," "Wani kallon banza yayi min up and down,Nima kauda kaina nayi Daga gareshi tare da d'aura kafata d'aya Kan d'aya cike da k'asaitah, na Cigaba da kallon t.v Nan take bugun zuciyata ya tsananta!." "A k'aramar kujera zaman mutim d'aya ya zauna..."Yana Danna waya, Shi ma ya d'aura kafarsa D'aya Akan dayan, waya yakeyi Yana Dariya da shewa,"Sai da ya Gama ya dubeni yace Amarya Abokin Ango Saif yace agaida ke," "Banza nayi da shi!" "Yace"Ke wace irin banza CE!Ana magana kina kyale mutane saboda bakida hankali ko gaisuwa ma Baki iya ba!"ko ba ayi miki tarbiyyar gaida mutane bane? "Kallon SA nayi cike da bacin Rai!"Nace Ni zakayiwa magana cike da raini? "Yace"Eh...Anyi maki marar tarbiyya da ke, da ace kina da ita da kin nuna min alokacin da na shigo!Amma saboda ba'a koya maki ba!"Baki San mutuncin kowa ba!kin kyale mutim," "Naji nagode Amma ahakan Yayan naka ya Gani ya auro Ni,"Na karashe zancen muryata na rawa saboda ban zaci Wannan ne kanen mijin nawa!"Amma Kuma shi yayan shi sunan su D'aya Jawad to tayaya hakan ta faru?na tambaya a Raina. "Kokari Tashi nayi in shige Daga ciki sai dai gabana yasha yana kallona har munajin sautin bugun zuciyoyin mu!" "Meye haka kabani hanya bana son rainin hankali!"Nace a fusace," "Tsaye Yake Yana murmushin mugunta Yana kallona..."Na bude Baki nayi magana Kenan....Sai naji saukar Mari uku zafafa!"A fuskata!" "Cike da gadara ya qara wanka min wasu biyu...Hankalina tashe na dubeshi idona na zubda kwallah!"Hannayena Duka dafe da fuskata!"A firgice...Ina mamakin iskanci irin na kanen mijina to shi Jawad din Yana Ina NE,da baiji hayaniyar mu ba!" "Nuna Ni yayi da yatsa yace"Daga Yanzu ki sanyawa bakinki linzami,kisan me kike fad'a Saboda na fahimci bakinki yana sakaki amasifa!Domin nafi karfinki da iskancin ki!"Ni Zaki mayarwa martani!Zaki San koni Waye! bana barin bashin gaba!" "Kuka nakeyi Ina son bude bakina na bashi Amsa Amma na k'asa irin yadda yake min kallon tsana da takaici na tabbata Zai iya kasheni,Gashi ba kowa agidan!"Shiyasa na dinga rera Kuka Ina Kallonsa kawai!" "Dariya yayi marar sauti yace"naji Dadi yau gaki agaban mijinki Muhammad Jawad kina Kuka Nadiya abinda nafi kaunar ganin kenan a tare dake wato bacin rai,Kinsani Kuka!kin mareni shekaru biyu da suka wuce,Gashi arana daya na mayar maki da su,harda dauri!"kisani Wannan shine Babban burina,Kuma soman tabine kalolin wuya da azaba marar Adadi na Nan tafe arayuwarki!"Zan nuna Miki nidin cikakken Maras *TARBIYYA* NE kamar yanda Kika fad'a Abaya!" "Wani jiri ya dinga dibana Jin irin kalaman Jawad,meke faruwa!?"Mafarki NE!?ko Kuma gaske!?"Idan mafarkine Allah ya tasheni Daga nannauyan baccin da nake!"Kaina na dafe! ahankali saman falon ya dinga min yawo, Faduwa nayi k'asa somammiya!"Batare da sani na ba!" "Murmushin Jin Dadi Jawad yayi,yace farawa ce,Nine hawan jininki!tsallaketa yayi,Saman SA ya wuce abinsa Yana sauraren wakokinsa na Hip-hop,"cike da Jin Dadi." *'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍* *VOTE,SHARE,AND COMMENTS MY FANS❤* [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFA NA 32* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *Hawayen ka Littafinka ne,masu sonka ne kadai suke iya karanta shi Dai-dai.* *Kada ka zamo kamar alawa a shanyenka,Kuma kada ka zamo kamar madacci a furzar da Kai,mafi alherin al'amurra shi ne na tsakiya.* *Ka koyi kawaici kamar yadda kake koyon magana, Domin Alokacin da magana ta k'asa amfani kawaici zai iya Kare ka.* _DUNIYA MAKARANTA_ ______________________________________ ******** "Knocking.....D'in da ake a falon k'asa ne ya dameshi ahankali ya sauko Daga saman...Turus ya ja ya tsaya!ganin mutim a kwance kamar gawa!" saboda shi har ya manta da akwai somammiya a kwance,Tsaki yayi tare da isa inda fridge din falon yake,"Robar faro ya dauko Mai Sanyin gaske,"Isa yayi gadan-gadan cike da mugunta inda take,"Kara Kwankwasa kofar akayi...."Da hanzari ya Bud'e ruwan ya dinga zuba Mata su,Ta ko'ina ajiki,"A hankali na sauke wani nannauyan Numfashi!tare da bude idona,"Ina duban jikina!"Sunan Ubangijina na kiraya!" "Wani kallon tsana!na watsa mashi tare da kokarin Tashi sai dai kasa tashin nayi!"ga jikina da ke tsuma Yana kakkarwa saboda Sanyi!" "Ke banza!ballagaza!!kwaila..kucaka Yar kauye!!Kafin na dawo kin fita daga falon Nan,Jawad yace tare Juyawa zuwa bakin kofar ya bude," Mai aikin momy CE tsaye!"dauke da basket din abinci ta ce inji Hajiya."Tare da gaida shi,"da ladabi," "Amsa Jawad yayi tare da cewa ta gaida momy,saboda baya son taga halin da Nadiya take ciki!"yaki barinta ta shigo daga ciki,' Ko da ya dawo na Tashi Daga falon,Dining ya nufa ya zubawa kansa abincin,ya hada tea da chips din da pepper soup din hanta da koda ya dinga ci yana chat har ya koshi sannan ya Cigaba da sha'aninsa," "NiKam da kyar na k'arasa dak'ina na kwanta Ina zubda Hawaye!"Wato dai da gaske NE,wannan guy da na tsana shine Jawad Kuma mijina,Abokinsa Saif shine ya yaudareni Yazo min amatsayin Jawad din!"Tabbas sunci amata Kuma ubangijana Zai saka min!"Sallamar su saudat CE ta dawo da Ni hayyacina da sauri na Rufe bedrum Dina,saboda naji su afalo," toilet na fad'a na wanke fuskata sannan na sauya wasu tufafi zuwa atamfa,"Ko da suka karaso bude masu kofar nayi tare da Rungume su naji dad'in zuwan su ita da Mardiyya Ina murna," "Abincin suka zuba min Wanda suka zo min da shi,nayi zaune muna ci.''Na lura Saudat na yawan kallona Shiyasa na basar muka dinga fira suna zolayata, Mardiyya Tace munga ango da Saif a falo,Abinci suke ci!"Ke Kika girka?" "Momy ta Aiko Mana shi!banci ba na karashe zancen Ina kallon Saudat tare da dariyar karfin Hali wacce tafi Kuka zafi!" "Saudat Tace Hmnnnn...Amarya "Nan muka ci muka koshi tare d adauko sauran kajin da lemu munci sosai muna fira daga nan Mardiyya ta wuce da Yake wani Buki gareta dangin mamanta shiyasa tayi Mana Sallama ta fita ,Ya Zan daga Ni sai Saudat adakin," "Saudat ta kalleni Tace Nadiya kinki ki hakura ko!?" "Nace"me Kika Gani,"Saudat!?" "Murmushi tayi ba komai,Naga kamar Baki daina Kuka ba!"But nasan zaki daina yanzu dai muje falo ga Saif da Jawad can,sai muyi fira Mana ya fiye Mana zAma anan Inji Saudat..." "Bazanje ba!"Na Bata Amsa atak'aice! "Saboda me!?"ko bazaki girki ba!?" "Eh...girkin me Zanyi nasan momy zata dinga Aiko Mana da shi,sai Nan da wani mako Zan fara aiki Domin Ina buqatar hutu!"Amma idan ke kina buqata muje ki girka. "Dariya Saudat tayi tace"to Gimbiya Naddy..Sarkin son hutu,Gashi dai Allah ya yarda Zaki huta,Allah ya samu adanshin ki,niKam a koshe nake. "Nace...Hmnnnn Saudat kenan wani hutun Alheri wani Kuma cuta ne kedai Allah yasa mudace Ameen." "Dagewa Saudat tayi da sai mun fita!Shiyasa na hakura,muka nufi falon Aykuwa na shiryawa tunkarar Saif akan tambayar SA meye dalilin sa nayi min karya akan shine Jawad!" *********"Mansura amaryar wani mako,An shigo sokoto Domin gayyatar Yan uwa da Abokan ARZIKI, musamman kawayen ta da ta Bari a school,Wasun Kuma har gidajen su ta zazzaga ta Basu alawa da katin gayyata," "Ta had'ou da Angonta, Saddiq sun sha fira,da tsare-tsaren su,A KARSHE inda ake pre-wedding pics,suka nufa,"Mansura trolley daya aka cika da kayan hoto,Wurin Deenee Mai hoto,sukaje akai Mata makeup,Daman ya kware sosai mai hoton,Nan ya dinga daukar su hotuna ita da Saddiq taso suyi banzan styles sai dai shi Saddiq Bai amince ba,"Amma sun canja tufafi Sunyi kyau matuka,"Bayan an Gama aka tura masu awaya tare da wanke na katin aka Basu,"Mansura jikinta har rawa Yake ta zAuna ta watsa pics din su a social media."Daga Wurin Mai hoton,gidan kawarta Lubna ya ajiyeta da zummar gobe zai mayarda ita Kebbi,"Tunda Saddiq ya ajiyeta ko ruwan da lubna ta kawo Mata Bata Sha ba, ta zAuna ta dinga turawa kawayenta pics dinsu,Nan ta aza adpnta na Instagram,facebuk,whasp,da sauran chat nata,"Status dinta ma duk pics din ne"Nan fa mutane kowa ya gani sai San barka,Wannan satin kam duka na Mansura da Saddiq NE,Domin Nan take media ta d'auka ko'ina sune ake azawa,"tamkar fashin kwai da Yake popular ce nan labarin Auren mansura lashe money ya bazu ko'ina. Ana ta masu fatan Alheri,"Mansura sai dad'i takeji tana masu godiya,"Domin ta samu miji Mai kyau ga kudi ba k'arya Sunyi kyau a hotunan fiyema da zahiri. "Ali da matarsa Umaimah suma sun bi sai Shirin SHAGALIN Auren sukeyi. Domin sun ga Ango Saddiq ya riga yace sai Rabin ransa mansura Yar mutan Kebbi,"Shiyasa Suma suka shigo dumudumu Domin Taya shi murna,"Komai na Shirin bukin auren an shirya shi tsaf, Umaimah ce zatayi abinci da snacks din Abokan ango da duk wasu hidima,"Saddiq ya kammala katafaren Gidansa a Nan unguwar su Ali,"Amarya mansura kadai ake jira da Kayanta,Domin shi ya gyare sashensa da na Yara tsaf ya zuba furniture madu kyau da tsada sai San BARKAH." **********"A falon muka samesu suna fira harda dariya da shewa...Ganin mu yasa sukayi shiru,Saif sunkuyar da kansa Yayi Yana sosar keya cike da kunya,"Jawad ko wani mugun kallo ya bini da shi, murmushi nayi Masa,"Nan muka zAuna Ni da Saudat," "Nace Abokin Ango saukar yaushe Ina gajiya," "Yake Yayi a Dan daburce yace"Amarya ya bakunci!?" "Nace...Alhamdulillah saifullahi,tare da Kallonsa na Dan canja yanayin walwalata na Kawar da kaina gefe!"Nace" Ashe Daman Kaine na hannun Daman Ango sai akai min basaja!?" To ba damuwa hakan yayi kyau Wannan ma wani sabon salon tsarine Mai dauke da wata manufa! ,Amma a kiyaye Gaba Domin gudun matsala!"Idan anyiwa Mai *TARBIYYA* an kwashe lafiya za'a iya haduwa da b'ara gurbi maras *TARBIYYA* Kasan kuwa sai wani ikon Allah Domin komai ta fanjama fanjam!"na karashe zancen Ina murmushi," "Wani Abu Saif yaji kamar Yana cikin Ruwa Don kunya..."Saudat ma taji dadin yadda Nadiya ta dauki mataki acikin ruwan Sanyi ta mayarda martani!" "Tashi nayi na dauko drinks na zuba Nace yallabai ga Ruwa saifullahi Bismillah Nan na zubawa Saudat da Ni muka Sha," "Jawad wani haushina ya kamashi mamaki Yake wato har Yanzu bakina da sauran magana,zaiyi maganin komai,"Yace azuciyarsa "Bayan ya kurba lemon Mai Sanyi ajiye Glass cup din yayi Kan stool tare da sauke Numfashi,Yace Allah Nadiya kiyi hakuri Daman suprise ne mukayi maki,"Amma ki manta da Wannan Duk abinda Kika Gani plan din Jawad ne,"Dariya Saif yayi irin ta rashin gaskiya yace"Jawad yace zai gwada ki ya gani ko Zaki so shi ko da baki sanshi ba!" "Murmushi nayi tare da cewa,Ay Yanzu yaga zAhiri saboda Ina amfani da umurnin iyayenah,Kasan su Baba sun tsaya maku dole ne nabi idan har na kasance Mai biyayya "Ajiye kofin yayi da karfi ya kalli Saif yace" mu wuce gidan Momy, tana jirana tun d'azu fa Nace Mata zamu zo Kai nake jira" "Daman saif ya kosa su bar gidan Dan Haka Tashi yayi suka wuce, jiki ba kwari," "Suna fita na fashe da wani irin Kuka Mai tsuma zuciyar Mai sauraro!"Saudat gefena ta dawo tana rarrashi na,da bani Baki!"Da sanyin muryata da ta disashe!"Nace Bari kawai Saudat kuka shine zaisa na rage zafin abinda Jawad da Abokinsa su Kai min!sun yaudareni da Iyayena,sun zo masu da sigar kirki da Kamala. Saudat nifa har na manta da shi tuni na shafe babinsa a rayuwata Ashe shi Kam ya kullaceni har ya yi nasarar aurena. Ba komai inda rabbana ba wahala komi zai wuce.Nan na k'ara bata labarin abinda ya hadani da shi daga farko har karshe. "Saudat ta Jinjinawa lamarin!Amma Hakuri da nasiha ta Cigaba da yimin tare da fad'a min irin dabarun da zanbi Kar jawad yaci galaba akaina!" naji sauki sosai Azuciata da Jin kalaman kawata,Nan itama Saudat ta sanarda Ni Duk abinda tasani da Kuma abinda ke tsakaninta da saifullahi."Da irin Shirin da su ke son kawowa a tsakanin mu. "Da FARKO na nuna Mata rashin amincewata aganina Jawad da saif halinsu Daya,Kuma Duk sune marasa *TARBIYYA* wataqil yaudararta zaiyi,sai dai tuni na fahimci Saudat tayi nisa aduniyar son sa Shiyasa na barta tare da Masu fatan Alheri,"Amma Ina jiye Mata auren kaddara!kamar nawa," Bayan Kwana Biyar "AURENA da Jawad Zan iya misalta shi da auren daukar fansa!"Domin tun lokacin da mutane suka D'aga Mana k'afa nake Shan wuya da azaba a hannun Jawad!" "Bugu da k'ari Duk yawan gidan Nike share shi nayi mopping nayi abinci ga gyaran Kichen,kaf ayyukan gidan nice!"Zagi da Mari kullum Cikin shansu nake awurin Jawad,Ya mayar da Ni kamar wata baiwarsa,Banda tsimi Banda dabara dole na hakura na Cigaba da Masa biyayya. saboda na dauki Alqawari araina ko da Jawad zai kasheni!"Bazan fadawa kowa ba!"Face mahallicina!"A kullum wurinsa nake Kai karar Jawad ba dare ba Rana!" "Kasancewar kusan kwanaki hudu Babu nepa a unguwar, Transformer din layin nasu ta lalace sai yau aka gyara,Murna sukeyi Domin an samu karamcin Ruwa da cajin wayoyi a Dan kwanakin Nan,"Sai yanzu da aka gyara wutar suka ji sanyi," "Nan kowa ya saka cajin SA da Yake kowannen su Yana da Yar k'aramar waya,shiyasa abin yazo masu da sauki!" "Zaune suke afalon suna kallon Arewa 24,Hajiya An hakimce a kujera Ana cin Naman kaza,Ana Kora fanta," "Anty Talatu itama Naman takeci tana kallon Gidan Badamasi da akeyi,"Sai Dariya suke," "Mahmud system dinsa Yake operating shima dai Rabin hankalinsa na Kan t.v." "Rasheeda gaban t.v take wayarta na caji tana dannawa Domin tayi missing din chat kwana biyu,"Hankalin kowa a falon Yana gurin abinda yakeyi!" "Tunda ta bude data sakonni ke Shigowa wayarta Babu Adadi da status a WHATSAAP dinta, Danna wayarta take tana murmushi sai dai Abinda idonta suka gane mata NE ya yo bala'in firgita ta!"A zabure ta mike tare da cewa jabbala'i! Me Zan gani!"Cin Amana ko Kuma meye!?" "Tsaki mahmud yayi tare da cewa Wallahi kin kusa haukacewa Rasheeda!"Waya na neman haukata ki!"Ke Kam kullum chat Zama online kamar ibada Allah yasa battery dinki ya buga,waya ba caji Kuma kina chat..mtwssss yayi Tsaki. "Tashi Rasheeda tayi Tace"Anty Talatu duba min shin mansura din nan ce ko kuwa!?" "Wayar Anty Talatu ta amsa,sai dai azabure ta Tashi ganin Saddiq da Mansura ne sun Sha kyau!" "Innalillahi Wa'Inna ilaihir Raju'un!!"Anty Talatu Tace tare da cewa yanzu Ashe daman mansura batada kirki!?"Hajiya duba kigani!" "Hajiya na dubawa ta auna ashar Wanda yayi sanadiyar fitowar Jalila Daga dakinsu a sukwane!"Mah'mud yace shin meke faruwa!" "Rasheeda ta ce"Anty Jalila duba ki Gani Mansura da Saddiq dinki NE maciya Amana Wai aure zasuyi Ranar jumma'a!"Kinga harda i.v da pre-wedding pics dinsu Yanzu nagani awani group,ko status Dina Duk sune mutane su ka aza daga Yar k'arya ce Dan duk Yan gayu Naga sun azasu!" "Kallon hotunan tayi Sarai!ko'ina mansura ta washe baki!wani Wuri harda kallon soyyaya, styles iri-iri na masoyana!"Dafe kanta tayi Nan Hawaye suka sauko mata fuska!"Zama tayi kusa ga Hajiya tana gunjin Kuka!" "Duk Wanda ke falon ya tausayawa Jalila irin yadda ta amince da Mansura!" "Hajiya Tace"Kibar Kuka Jalila!Allah zai saka maki!" "Anty Talatu Tace"nayi mamakin yadda hakan tafaru,Duk da Ni dama can ban yadda da ladabin Mansura ba!"saboda ta iya bakinta sosai,"Da ganin Idonta na fahimci Yar duniyace Kuma gogaggiyar Yar bariki..." "Rasheeda ta amshe Nima haka Anty Talatu,Sam batayi min ba!"lalle mutim abin tsoro ne, ya shigo jikinka ya san sirrinka yayi amfani da shi wurin kashe ka!"Anty Jalila kibar su ga Allah shi zai saka maki amma Sadiq ya cuceki!"Ya rasa wacce zai aura sai wadda tasan sirrinki!Ni na d'auka Nadiya zai aura!"Sai Labari ya canja kuma mafi munin canji!" ''Jalila ajiyar zuciya tayi tare da share hawayenta,Daga Nan komai ya dawo Mata sabou!" "Muryarta na rawa Tace"Hakika na aikata kuskure arayuwata na yadda da Mansura Kai tsaye!Batare da na karanceta ba!"Na Bata amanar sirrina!"Na mallaka Mata Amanata!"Sai yanzu na fahimci makamin kashe rayuwata da ta gidana na Bata!"Domin Gashi tayi Silar mutuwar AURENA,da rabani da yarana!"Nan Jalila ta zayyanewa Yan uwanta komai tun haduwarta da Mansura har kawowa yanzu,Kuka take Mai ciwo Tace Nadiya ki yafeni,Ina Zan ganeki na rokeki na ci amanarki bada alhakinki ba!"Wallahi sai yanzu na Gane k'arya mansura keyi Kuma tana haushinki da na Nadiya shi ne ta huce,bazan manta ba tayi fad'a da Nadiya ko da na ganta,Amma iya makircinta yasa na yadda da ita a lokacin kishi ya rufe min Ido.... "Mah'mud ajiye system dinsa yayi gefen kujera yace"Anty Jalila kinyi kuskure babba Amma Alhamdulillah Tunda Allah yasa kin gane Daga baya kenan,Bayan komai ya faru,"Wallahi Mata Kuna bani mamaki da kuke saurin yadda da mutane har Kuna basu amanar ku!"Kun manta cewa makashinka Yana tare da Kai!"Duk Wanda zai cuceka toufa sai ya kusantoka!"Yanzu Gashi ta fidda ke zata aure mijinki,"Allah ya saka maki sai Hakuri kawai,yana Gama zancensa ya wuce abinsa Dakinsa!" "Zaune sukayi zugum suna Jimami,Anty Talatu da Hajiya har zubda kwallah!"Rasheeda ma taga bala'in da yafi nata,"Shiru ma magana CE" "Jalila hawayenta ta goge!Da hannun..tare da sharce majina idonta yayi jajur!"Tashi tayi Daga falon daki ta nufa,ruf tayi da ciki tana kukan takaici! Da nadama! da Kuma Danasani!"Tunanin mafita takeyi domin kuwa Tabbas sai ta dauki wani mataki saboda mansura bazata cuceta abanza ba!Sai ta nuna Mata bataci bulus ba!"Duk da aski ya kusa kawowa Gaban goshi bazatayi k'asa a gwuiwa ba. "Tashi tayi ta daura Alwala salloli ta dinga jerowa, da nafilfili tare da karanto dukkan Addu'oin da malamin su na islamiyya ya Bata tana Kuka tana jerawa Allah kirari tare da Kai karar mansura awurinsa,Akarshe salatin manzo da istigfari da hailala,"Tayi Nan wani Sanyi da sauki ya ziyarci zuciyarta,"Sannan tayi azkhar ta kwanta."Da zummar da safe ta nemi mafita mafi sauki." *'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍* [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFA NA 33* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *Kayi kuskure ba shi ne matsala ba!Ka yarda kayi kuskuren shi ke da muhimmanci,Abinda yafi shi muhimmanci shi ne ka koyi darasi Daga kuskuren ka.* *Duk mutim bawa ne,Ko ka Zama Bawan Allah,ko Kuma ka Zama Bawan shaid'an ko na son zuciya,Wanda baiyi sharan masallaci ba!Hakika Wataran ya Shari kasuwa.* _DUNIYA MAKARANTA_ _____________________________________ Bayan gari ya Waye "Kosawa tayi Rana Bata fito ba, da kyar ta ga karfe Sha biyu na Rana yayi, sauri-sauri, gudu-gudu,take Tafiya a sukwane da kyar ta samu abin Hawa,Tana shiga Napep din sama road,Tace ya Kaita Bayan tsawon lokaci suna Tafiya sai gasu a unguwar,Layin gidan su Umaima suka nufa,A kofar gidan aka sauketa,Nikab din ta janyo ta rufe fuskarta tare da sallamar Mai Adaidaitan," "SHIGA tayi gidan,sai dai Mai gadin su tare ta yayi da tambaya!"Saboda kafafunta safane baqaqe,ga Hijab har k'asa,da nik'abi," "Yaye Nikab din tayi,sannan ya dubeta tare da gaidata,"Nan yabata hanya ta shiga," "Gabanta ya fad'i ganin motar Ali agidan,A hankali ta karasa kofar falon...sai dai canja Shawara tayi sai tabi ta Bayan wacce zata sadata da hanyar Cikin gida,gefen Kichen...." "Gabanta fad'uwa yake Kar dai yau ne d'aurin Auren can take tuna jumma'a akace..."Kofar tafara bugawa ahankali,Cikin Sa'a sai ga Umaima ta bude hannunta dauke da jug,"Ganin wacce ke bugar kofar yasa taji tsoro yanayin shigarta komai dark blue,"Yasa Umaima jin tsoro,tana Addu'oin acikin zuciyarta Kar dai Aljana CE!" "Riketa tayi tare da yaye Nikab dinta,Tace nice Umaima karkiji tsorou!"Nice!" "Da mamaki..ta kalleta tare da Juyawa baya Bataga kowa ba!"Janyo hannun tayi zuwa bedrum dinta,"Tace,Jalila kice da Rana tsaka!lafiya dai!?" "Babu lafiya Umaima zuciyata tana neman rugujewa Nan zuwa Anjuma jinina zai hau!"Taimakona zakayi!?"Inji Jalila tana zubda Hawaye!" "Murya kasa-kasa Umaima Tace"Saddiq da Ali suna Falo,Abin Sha ne Zan Kai masu da Abinci,suna jira zAuna Ina zuwa,"Ki kwantar da hankalin Jalila "Kama hannun Umaima tayi!"Tace Dan Allah Umaima ki taimakeni Domin fad'uwa tazo dai-dai da Zama,Bude jikarta tayi tare da fitou Robar faro da Ruwa aciki," "Kallonta Umaima keyi..." "Tace Umaima ki TAIMAKA min ki zubawa Saddiq ruwan Nan, acikin abin Shansa Dan Allah!" "Tayaya Jalila gaskiya bazan iya cutar da Saddiq ba!"Kuma tare da Abban Salim suke fa abinci zasuci!"Inaji Ina Gani bazan aikata hakan ba!"Umaima Tace da Dan fushi!" "Umaima kina nufin ahalin Yanzu Zan iya aikatawa Saddiq wani mugun Abu!?"Ko Zan cutar da shi!?"Wallahi Duk halayena da Kika sani na canja su Sarai!"Ba kamar da ba!nayi hankali Kuma duniya ta koyar da Ni darasi!"Babu cuta Babu CUTARWA acikin ruwan Nan Addu'oin ne akayi da ruwan zam-zam da ma'ul khal,na AYATUL SHIFAH,"Wallahi Umaima na karye sihiri NE,ki taimakeni mansura tayiwa Saddiq Sihirin da Zai tsaneni!!"Mallamin Islamiyyar mu Sheik Affan,Da kansa Yayi istihara Akan lamarin Kuma shine yabani Addu'oin nan na kariya ne da karya Asiri,Ni kaina tayi min Kuma Anyi Nasara nawan ya karye suran nashi"ki taimake Ni sauran bayani Zanyi maki Daga baya,Kuma Dukkan su suna iya sha Bari ma kigani,Nan Jalila ta bude Robar Tasha ruwan,Taba Umaima jiki a sanyaye tace''kema Kisha ki yarda da Ni Umaima bazan cutar da kowa ba!!"Kukane ya ci karfin Jalila ta k'asa karasa maganarta!" "Umaima Ta hango nadama tsantsa a fuskar Jalila Shiyasa ta amshi ruwan Bismillah tayi ta Kora,Jin tsamin su ya tabbatar Mata da AKWAI ma'ul khal din aciki," "Nan ta koma hanyar Kichen zobou ta had'a da ruwan tare da saka kankara,Kayan Abinci ta had'a,Tana sauri taje falon,har Yanzu fira sukeyi!" "Saddiq yace"mun d'auka an manta da mu!"Yana Dariya" "Ayyah!kuyi Hakuri Khairat ta motsa Daga bacci ta hanani sukuni Daman yau fitina takeji," "Kayan Abinci ta jera masu tsaf,A dining sannan ta koma bedrum su Kuma abincin suka hau ci,"Daman Umaima tasan Aliyu baya Shan zobou Shiyasa ta had'a kadan,Nan fa Saddiq ya Shanye kusan Rabin jug,"Ali ko Drink yasha da Ruwa." "Tun farkon had'uwar Jalila da Mansura har karshe da yadda neman maganin ya kasance tsaf, Jalila ta labartawa Umaima tana Kuka!" "Umaima taji haushi da takaicin Jalila matuka saboda tayi sakaci!"Tun farko da ta yarda da Duk plan din mansura ba tare da ta bincika ba!"Amma kaddara ta Riga fata!" "Jalila Tace"Yanzu Kinga Nidai Duk wani Abu da yafaru Umaima ya Riga da ya wuce!"Nidai burina Saddiq ya samu lafiya, Allah ya kubutar da shi Daga cutar tsanata!" "Umaima Tace"Jalila tun Ranar da Saddiq ya kawo shegiyar yarinyar Nan naji batayi min ba!"Kinga hotunan su da yaran,kuma jiya fa da kanta ta turo min pics DINSU na aure gobe ma ake dinner jibi aure,"Nan Jalila ta karbi wayar Umaima tana dubawa,Hawaye na Mata zuba!"Tace lalle mansura ta cika mayaudariya!" "Umaima Tace"Ba zamu barta ba!za tasan ta cutar da ke!"Yanzu Zan sanarda Aliyu komai Daga Nan zamu Sami mafita,Kodai Saddiq ya mayar da ke!Dakinki Kafin jibi Ranar auren!"ko Kuma ya fasa aurenta,nasan Idan yaji Wacece ita zai tsaneta saboda fuska biyu tayi Masa!"kin Shan shi Kuma ya tsani haka in fact BASAI na fad'a Miki halayenta ba kissani baya son munafunci da k'arya. "Umaima kenan ba zai yarda ba!"zaice sharri nayi Mata!"nasan Waye Saddiq!"Nidai ya mayarda Ni ko da Zai auri mansura saboda na rike yarana na kula da su,"* "Ajiyar zuciya Umaima tayi tare da daukar Khairat da ta Tashi Daga bacci tana jijjigata Tace"Jalila Addu'a kadai zatayi Mana maganin Wannan Matsalar!saboda Nima nagane Saddiq yayi nisa duniyar son yarinyar nan idan Allah ya nufa ya mayarda ke Jalila sai ki kula Domin ta iya kissa da abubuwa da dama Wanda ke bakida ilimi Akan su!"Ga Kuma neman magani oh ni Yan matan yanzu Abin Tsoro ne. "Hakane komai gogewarki yanzu kiga karamar yarinya ta fiki iyawa watakil ma tafi ki sanin duniya,Aini ina Cikin tashin hankali da matsala!"Ni da mijina uban yarana amma na koma baran SA!"Kai duniya makaranta Umaima Ni Kam na samu darussan rayuwa!Dan Allah Koda Kun hadu da Nadiya Wurin auren ki nema min gafararta nayi ta kiranta da layin ta da nikeda Bana samunta akashe,kinga saboda rashin sani yasa na cutar da ita,Ni da Yan uwana,Ina Jin kunyar Ido hudu da Nadiya yarinyar kirki," "Murmushi Umaima tayi,Ay ina ga satin can ne Saddiq yaje Auren Nadiya,"Tayi aurenta su Mufeeda ance sun Sha shagali," "Haba Dai!?"Inji Jalila "Gaskiya!"Kuma wani Dan Masu kudi ne ta aura kamar Jawad sunansa Dan Saddiq ya kawo Mana littafan aurensu da memo" "Allah sarki Nadiya ta wajena!"ban kyautawa bautar da kikayi min ba!"Allah ya Basu zaman lafiya!"Kai zargi baiyi ba!"Ashe tana da ma mijinta!"Allah ka rabamu da sharrin zuciya!"Inji Jalila "Ameen...Shiyasa komai nason Kyakkyawar fahimta,Daman da Dan gari Akan ci gari"Inji Umaima" "Hakane,Yanzu goben zaku wuce Kebbi ko!?"Jalila ta Tambaya kamar tayi Kuka!" "Bata fuska tayi,Tace"Jalila a gaskiya niKam bazanje auren Nan ba!"Ko Aliyu Hana shi zuwa Zanyi!"Daman niyyar su muje gobe ayi dinner mu kwana idan anyi walyma da daurin aure sai muzo da Yan kawo Amarya,Kinsan Kun dawo gidanku na Nan unguwar,Kuma har part dinki akwai aciki"Umaima Tace cike da zolaya," "Gidan Amarya mansura dai,Domin Ba'a b'ari akwashe dai-dai," niKam Ina gefe,"Hmnnnn... Yanzu har an kammala ginin nan!Allah sarki Dani aka tsara gidan Allah baiyi ashiga Dani ba!"Daman mugunta akace fitsarin fakou,Jalila Tace cikin sanyin murya," "In shaa Allah ko ba'a shiga da ke ba!"za'a Ida rayuwar ciki gidan da ke Jalila ki kwantarda hankalinki!"Ba'a taba canjawa tuwo suna!"Har gobe ba za'a iya yanke alakarki da Saddiq ba!"saboda AKWAI gudan jini!" "Ajiyar zuciya tayi tare da mayar da Nikab dinta Tace"gobe Zan dawo naji yadda ake ciki,ki duba min da yanayin canjin Saddiq,sai munyi waya, Nagode! Umaima TABBAS ke Abokiyar Shawara CE,saboda kin taimakeni na yarda ciki da gaskia wuka Bata iya hudawa...Nayi danasani akan kuskure na nq wargaza alakata da ke kiyi Hakuri."Ni Zan koma Daga Islamiyya nake!" "Itama Umaima Tashi tayi Tace"Yawwa Jalila karki damu Allah ya bamu nasara,Har kofar da ta biyo Umaima tayi Mata rakiya,Nan Jalila take tambayar Suhaila da yaran " "Umaima Tace, Suhaila tana makaranta,yaran ko Sunje kitso da Lalle gidan k'awata Amina a rinjin sambo."Nan sukayi Sallama kowa ya wuce da abinda ke cin ransa," **********Kaddara ta Riga fata!"a gurin Nadiya Dan kuwa rashin mutuncin Jawad sai abinda ya karu!"Duk yanayi shigarsa ta da ayanzu hakan da ita yake yuni ya kwana acikin gida,sai Idan zai fita yake saka tufafin kirki," "Momy(Hajiya khaltumi)tana bani kulawa da sosai komai ta samu ta aiko min Sam batson na wahala,burinta nidai bugun zuciyarta mu kasance acikin Jin Dadi da walwala ba kalar gatan da batayi mana,"Har gidan tazo ta ganeni tare da shaida min Duk abinda nakeso arayuwa,na sanar Mata Abinci ma Tace in daina Masu aiki su dinga dafowa Ana Aiko Mana. Amma nace Zan iya dafamana hakan tayi zancen kawo min Yan aiki nace a ah a hakan momy ta Hakuri ta barni da ayyukana. "TABBAS Albasa batayo halin Ruwa ba!"Domin nagane momy tana da girki sosai," "Zama na da jawad Sai Kara lalacewa Yake,Domin ya sani agaba!"Duk wani aikin wahala burinsa ya sani!"A wuni sau uku nake Shara da mopping kaf gidan,Ga abinci Yana sani dafa kala hudu biyar ba Wai domin ya ci ba!"Acewarsa ba zai ci girkina ba kwaila Dani kazama! Har lokacin da ya diba min na adadin zamana agidan ya rubuta ya bani a takarda yace in ajiye Domin aranar zai sakeni ya yi min korar Kare. IDAN nayi abincin,sai da yaba masu gadi ko yace akaiwa almajiran kan layi,"hakan naketa wahala da fama da ayyukan gidan. "Na yarda wuya Bata kisa!Domin nayi Hakuri na danne Duk irin wulaqanci!Zagi,Cin zarafina da Jawad ke min,"Ba Wanda ya sani agidan mu,hakan gefen kawayena Saudat CE tasan wani Abu,wanin Kuma Daga Ni sai shi," "A cikin Yan kwanaki Duk nayi Baki na rame na lalace kamar bani ba!"Tsabar damuwa da bakin Cikin zaman agidan na neman salwantar da bugun zuciya ta!"Kuka da Addu'oin da karatun kur'ani su ne kadai ke min maganin zafin hawayena!" "Ba karamin Dadi da nishadi yakeji ba!"Ganin Yana azabtar da Ni gashi ba Wanda ya sani,saboda Yana Dan Jin tsoron momy da kunyar su Baba,"Yanzu ko da na taimake SA,na tufawa kaina Asiri Yana cin karensa ba babbaka,sai wani Dadi Yake ji, Restaurant Yake zuwa ya ci ya koshi,yayi fari ya Kara kiba ga Kamala da kwarjini sun karou ajikinsa kamar ba shi ba,"kowa sai sa Albarka ake. *************************** "MANSURA amaryar jibi an Sha gyara tayi wani irin kyau,sai baza sheki take!"Qawayenta na nesa Dana kusa Duk sun karasou bukin auren,"Yauma akwai event din friends Day da za'ayi a gesse phase ii da ke Birnin Kebbi." "Fadar irin Shirin da Amarya da kawayenta sukayi fatar baki zata iya bae,saboda sunyi kyau acikin red and Arsh dress DINSU,Amarya Kam white wedding gown tasa,An cashe ba'a ko magana,Anyi hotuna mansura sai Jin Dadi take, mussamman yadda ta bada kala,A taron bukin ta haska sosai,"Abinka da 'yar son karya da bud'awa,"Kawayen nata Suma ba baya ba!sai wani karairaya ake Ana yanga!"kamar a karye dan kuri,"Haka aka Gama program din aka dawo,Sai Kuma na gobe dinner da akayiwa shiri fiye da kowanne Domin Abokan Ango zasu zo da uban gayya na mansura,"( _Nikam nace nasan gobe za'a sha kallo)_ ***************** "Tun lokacin da Nadiya tayi Masa magana Mai zarar bunu,Jikinsa Yayi Sanyi,yaji Bai KYAUTA Mata ba!"Da har ya amince da zuwan Mata amatsayin mijinta Jawad, Daga Ranar shi da Saudat suke tsare-tsaren yadda zasu gyara zaman Jawad da Nadiya su tafiyar da rayuwar su kamar kowanne Mata da miji Nagari,"Saboda Sam zaman doya da manja da ake agidan Amininsa Yana Bata Masa Rai!"Domin ya gane gaskiya Basu KYAUTA ba!rashin tunani Mai kyau ya haddasa hakan," "Tsoron SA Daya Kar ya rasa Rabin ransa Saudat adalilin abinda su ka Aikata, Shakka ba yayi idan asirin su ya tonu iyayen Nadiya suka ji abinda sukayi sai mama Lantana taji,hakan Idan tasan Waye shi bazata bar Saudat ta aure shi ba!"Wasu zafafan Hawaye Saif ya share tare da sauke Numfashi Daga nisan kiwon da ya fitou a duniyar tunani!" "Allah na tuba!"Allah ka yafe Mana!"Allah Karka Bari na rasa Saudat ya Allah,shi kadai Yake Addu'oin tare da Daga hannayensa sama yana Kuka!" **************** "Bakin ciki marar misaltuwa Baba laraba ta samu kanta aciki!"tun Ranar da D'anta Almu ke gaya Mata wani saurayi Mai Mota babba ke zuwa inda Saudat," "Har Kuka sai da tayi Domin kaf mazajen diyanta Babu Mai Keke bare Mota," "Daga RANAR bakin habaici ya mutu awurinta,Sai dai Babu kalar kazafin da batayiwa lantana da Saudat,Akan zancen saifullahi." "Hajiya Lantana Kam ko a habar zanenta,Domin Idan da sabo sun Saba da tujarar laraba,Kasuwancinta ta Sanya agaba!"Da dadewa tagane Hassada ga Mai rabo Taki CE,saboda har Yanzu laraba da yaranta Basu Zan komai ba!" "Amma ita Alhmdllh ga Saudat na aikin asibiti yaranta na karatunsu maza da Mata, Itama dai sana'arta takeyi,"saboda hakan NE taja kunnen su Saudat Akan su Kara kawarda Kan su Akan al'amurran laraba da yaranta,kowa ya rike Addu'a Kar Wanda ya kula su da Duk abinda zasuyi, Kar Wanda ya Koma ko yabi ta kansu." "An saka RANAR auren Tahir da Rasheeda Rana daya,"Hajiya Atika sai shirye-shiryen buki ake,Tahir ya Kamala Gidansa Mai kyau,A unguwar Arqilla."Itama Rasheeda a tudun wada sokoto za'a ajiye a Babban Family house din gidan chairman na Yan kasuwa wato Alh.salisu Wanda akafi sani da sunan (Kai da kudi)," Daren "Ranar dai Jalila Bata runtsa ba!"Addu'oi da salloli take jerawa har asuba,"Tasha Kukan nadama har ta godewa Allah,Babu abinda take tunani sai sabon gidan su da ta Sanya arai,mijinta da yaranta!"( _Duniyar kenan daman abinda ka raina sai ka dawo nemansa_) "Shima dai Saddiq, tun da yabar gidan Ali yaji Jikinsa ya sauya!"Ranar kwana yayi nafilfili da rokon Allah mafita!"Abinda ya Dade baiyi ba!"Saboda tun da Nadiya tabar gidan ya daina tashin dare,"ko yaso ya Tashi sai ya k'asa!"Sai dai yau yasamu kanshi da Tashi,"Yayi ibada sosai da tilawar Alkur'ani Mai GIRMA,Domin YUNIN yau Duka ya k'asa fahimtar meke faruwa da shi!" *'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍* *SHARE,VOTE,& COMMENTS👍🏼* [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* _________________________________ ® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ _________________________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/ *SHAFA NA 35-40* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *TALAKA BA SHI NE, WANDA BAIDA KUD'I BA,TALAKA SHI NE MARAR LADABI DA TARBIYYA, ITA KUMA TARBIYYA BA'A SAYENTA, KUMA BA'A SAIDA TA, KOYONTA AKEYI* ______________________________________ "A hankali Numfashi na ya dawo gangar jikina,Sai dai ko ya tsana bana iya d'agawa saboda na lakadou sosai!" "Ko da na Bud'e idona arba nayi da Hajiya Maryam,tana faman sha'fa fuskata!" Alhamdulillah ta CE"Tare da goge hawayenta,tana Dan murmushi Jin Dadi tare da"Kokarin tayar dani zaune," "A hankali na bisu da kallo!"Nan komai ya dinga dawo min,kokarin tuna komai da ya faru nake!"Sai dai kaina da ke min zafi na D'an dafe! Ina lumshe idona," "Momy rike min hannu tayi tana ta faman jera min sannu tare da goge min Jinin hancina da Baki da milk din gyalenta!"Batare da kyama ba!" "Ko kallon inda Jawad Yake momy batayi,A hankali ta tayar da Ni tsaye,Tace "Hajiya Maryam mu Kaita Mota,Muje asibiti," "Da kyar nake tafiya Ina dingishi saboda har kofafuna Jawad ya Shure ya take Yana kwallo da Ni,A lokacin da yake mazgata!"Shiyasa naji ciwo sosai," "Parking place muka nufa,muna Tafiya Jawad na bin Bayan mu Yana zubda Hawaye!cike da kunya!nadama!da Tausayi," "Mota su momy suka sani sannan Hajiya Maryam ta shiga tana kokarin ta da Motar,Jawad ya koma gefenta,"Da sanyin murya yace"Dan Allah momy Maryam kuyi Hakuri Kada Baba malami yaji,Wallahi na tuba!"Raina NE ya baci!Domin Yarinyar Nan bansan Haka take ba!" Batada kirki!nagaji da Hakuri! shi ne ta tunzura!" Ni bansan Lokacin da nayi Mata wad'annan raunukan ba!"ya karashe zancen SA Yana sosar keya na rashin gaskiya..." "Tsaki momy tayi,"Cikin bacin Rai!"tace haba Hajiya Maryam ko na dawo na amshi driving din!?"Dan Allah Muje aduba min lafiyar 'Yar Mutane!" "Wani shock!jawad yaji ajikinsa! yanda momy ta turmuke fuska tana magana afusace!"kallon su Yake,Har Hajiya Maryam ta saka glass din Motar tana kokarin fita batare da sunce da shi uffan ba!" "Nikam duk na k'osa muje inda zamu,su sallame Ni nakoma ga iyayenah,"A hanya ma Sai tattaunawa momy da Hajiya Maryam keyi Akan sanadin Wannan ta'asar,Rai ba Dadi mukaje asibitin,"Likitan ya dubani sosai tare da bani magani har na ciwon zuciya!"Saboda ya Gaya masu Ina fama da hawan jini da ciwon zuciya!"Kuma ayi Hattara! saboda zuciyata zata iya bugawa sau biyu!A lokaci daya!"Ya ce, da zarar taqara irin Wannan muguwar bugawa tofa Zan iya rasa Raina!" "Ba Ni kadai ba!"dukkan su hankalin su ya Tashi!"mussamman momy da ke zargin d'anta NE sila,"Jiki ba kwari muka fitou asibitin,Gidan momy muka wuce,Nan Wasu Hawaye suka dinga min zuba!saboda nikam gidan mu Naso mu tafi!"Amma momy tayo gidanta da Ni,ina Jin nauyinta da kunyarta Shiyasa ba Zan iya musu da ita ba!"Naso na shaida Mata ta mayarda Ni gidanmu, Kuma ta SA danta ya sakeni Domin ko lahira bana fatan Allah ya sake sadani da macuci irin shi!" "Kulawa nake samu sosai awurin momy da ma aikatan gidan,Har abinci ta dinga bani abaki,d'aki daya tasa Mai aiki ta gyara min tsaf,A hankali ta rakani Dakin tare da umurtar Inno ta had'a min ruwan wanka!"Ina fitowa na samu Kaya sabbi momy ta fito min da su!"Na saka,magani ta bani Nasha sannan Tace na kwanta!"Inno ce Tace" ta tsaya ta lura Dani ko da na farka Ina buqatar wani Abu!" "Hajiya Maryam tana ganin na samu sauki sukayi Sallama da Momy Rai Babu dadi!"Saboda Duk da Basu San meye mafari ba!"Amma sun San Jawad ne Bai kyauta ba!"Da hakan dai suka rabou suna alhini abin," "Bayan an kammala sallar la'asar limamin masallacin Sheik Musa masani da sauran jama'ar unguwa da Yan uwa da Abokan arziki suka shaida da an sake daura auren Saddiq da Jalila akan sadaki naira dubu asirin," "Aliyu da waliyin Jalila Malam Habu Sunji Dadi matuka,"Haka Tahir da Mahmud godiya suka yiwa Allah." "BARKAH jama'ar Wurin suka dinga yiwa Saddiq da bakinsa yaki rufuwa saboda Jin Dad'i,"Tare da fatan alheri." "Suna barin Wurin direct shi da Mallam Habu,da Tahir da Mahmud,da Kuma Amininsa Aliyu,Gidan Hajiya Atika suka nufa,Nan ta dinga murna da godiya tare da masu fatan Alheri cike da kunya,"Saddiq yaqara ganin canji sosai awurin surukar Tashi da Yan uwanta,"Shima godiya yayi Mata cike da girmamawa,sannan suka bar gidan shi da Aliyu," "A hanya Saddiq ya Kira Lambar mahaifinsa Mallam Musa,Hankali kwance, ya bayyanawa babansa Dukkan abinda ya faru,"Har zuwa mayarda auren sa da Jalila!"Aliyu ma amsar wayar yayi ya qara yiwa Baba Musa bayanin komai tare da bashi Hakuri Akan an mayarda auren ba tareda sanin su ba!" "Baba Musa yace"Bakomai Allah yasa hakan ne ALHERI,ya Kuma tsare gaba," "Ameen,Ali ya amsa Cikin murna,"tare da ba Saddiq waya" "Baba Musa yace"Saddiq Ina son magana da Kai idan ka samu ka nutsu!"ko da zuwa da dare!NE ZANYIWA gwaggo bayanin komai!"Idan na koma gida," "Saddiq yace to Baba Babu damuwa nagode sai munyi waya," "Wani Sanyi yaji aransa,da mahaifin SA ya fahimce shi,"sabon Gidansa suka nufa Kai tsaye!" "Ko da suka Isa su Umaima,Anty Talatu,da Rasheeda an dage,sai aikin gyaran gidan sukeyi!"Amarya Jalila ko tana jinsu ta boye!"Wai acewarta ango bazai ganta ba sai shirts,Anja Masa wankan k'wallabou," "Masu aikin jeren kayan furnitures din sai faman hada Wurin suke,Inda two bedrooms dinta green da orange ne,tun Kan gadajen har zuwa komai na Dakin Wannan green ne, Wannan Kuma orange ne,falonta ko dark purple NE,"tun Kan kujeru har daning da labulai kala Daya NE,A gaskiya Jalila Kam sai San BARKAH Domin ko Amarya bazata nuna Mata komai ba,"Ga Dakin Mufeed da Mufeeda Tuni Saddiq ya gyare masu an zuba masu komai na decorations da bed din Yara," "Babban falon gidan ma Saddiq ya zuba komai aciki da bedrum daya nashi," "Daman falonsa babba aciki Bedrum dinsa yake Sai kofar da zata sadaka da gefen Jalila d'ayar kofar kuma gefen Amarya sannan Dakin Yara Wanda Duk acikin Babban falon suke,"Gidan Kam ba karya yayi kyau,komai an kammala,gefen Amarya NE kawai ba'a kawo kaya ba!har yanzun acewar su sai Ranar aure zasuyi jere!"Da angama akawo Amarya,"kada ayi mata barbade Kafin tazo( _Hakan neman magani ya gada,A duk lokacin da kakeyi ganin kake anayi maka,Allah ya tsare mu da fadawa halaka!Amin_) "Cikin tashin hankali Yake driving Yana tunani da zancen zuci! kamar zai kife ya Fadi daga Cikin motar,Gudu Yake shararawa na fitar hankali!!kamar zai Tashi sama ya kosa ya isa Kebbi!"Domin yayi arba da Mansura!" "Ranshi sai suya Yake,Yana cikin damuwa da tashin hankali!"yadda mansura zata yaudare shi!"Lalle bazai taba barinta ba!"Sai dai kowa ya rasa Wallahi Domin ya shirya fallasa komai ya tonawa kowa asiri Akan zancen Auren,Abdul-Rahman(Bimboy)kenan tsohon saurayin Mansura," "Tun da yamma tayi kowa ya shirya acikin ado da kwalliya Mai kyau,Wurin da ake event din kowa ya hallara ba laifi komai ya tsarou Domin harka CE ta Yan karya,Kuma wayayyi,"A hankali wani sassanyar sauti ke Tashi Wurin,"Komai an bajewa Mutane a table,"Suna hiding suna motsa Baki,zuwan Amarya da ango da sauran kawayenta kawai ake jira wasa ya fara," "Ganin har 6pm ta gota yasa jikin mansura yin Sanyi,Gashi an damesu da Kira su karasou tarou ya fara Basu,"Nan dai ta hak'ura suka Isa Wurin ita da kawayenta!"Sai karairaya suke Ana rangwada kamar za'a Kare!"Bayan ta zAuna awurin da aka tanada Domin Amarya da Ango,Wayarta ta fitou da ita tana kokarin Kiran layin Saddiq," "Hayaniyar da taji anayi kusa ga Angonta yasa ta murmusa Domin tasan cewa shi da abokansa NE,watakila ma sun karasou,"Sallamar CE ta dawo da ita hayyacinta," "Tace"Nace har Yanzu Banga Kun zo ba!"Kuna hanya NE,Dan Allah my kuyi sauri Wallahi Mutane sun taru Kuma kune ake jira...mansura ta Gama zancen da sangarta da nuna damuwa tamkar Yana agabanta!" "Sauke Numfashi yayi yace"kiyi hakuri Daman Yanzu nake Shirin kiranki,Gaskiya BAZAMU samu zuwa ba!"sai dai goben ki bawa kowa Hakuri wani uzuri ya gitta Mana... sannan Umaima ma batajin Dadi Shiyasa bazata zou ba!"Kuma......" "Datse kiran Mansura tayi batare da k'arasa Jin me zai fad'a ba!"wasu Hawaye NE suka zubou Mata!"Ranta Idan yayi dubu ya baci!"me Saddiq ke nufi da ya canja Mata hakan,kwana biyu,dole NE ta dauki matakin Kare Dangi akansa!" "Sai ware Ido take tana kallon Mutane!"ranta ba Dadi!"Can sai ga kawarta Hindou ta karasou Yar fara lukuta da ita,Mai manyan mazaunai,tana tambayar ta yadda Sukeyi da Saddiq," "Mansura labartawa Hindou komai tayi,"tana kokarin Kuka!" "Hindou Tace to meye aciki mansura ki Masa uzuri Mana! muje mu chashe kawai kinsani da rawa kamar mazari!"Kiyi Hakuri!muje Ayi pics share hawayenki..!" "Har sun Kama hanya sai ga Sahura tana rangwad'a ta tare su,"Hindou Daman ba shiri take da su Sahura ba, Shiyasa ta sake hannun mansura ta Kama gabanta! Domin ta dabance acikin su ita tana da kirki," "Sahura tambayar mansura tayi ya ake ciki!" "Mansura ta Gaya Mata yadda sukayi da Saddiq din Sarai ranta abace!" "Sahura zarou ido tayi waje!"cike da mamaki Tace"Wallahi ke lusara CE,mansura da har kinka Bari Saddiq yafi karfinki,Har da Masa Hawaye!?"Kinga nikam bazan Baki Shawara ki biye masa ahaka ba,Kina mallakar cutar d'a namiji!"Ay namiji da kike Gani mansura,ba Dan goyo bane,Kuma allurar guba NE,Gashi yasaki bakin ciki tun Yanzu,Wallahi idan kin dauki Saddiq uba to karshenki Zama marainiya!"Bari kiji SHIFA Namiji tuwon kayane,miyar allura ka gutsira ya soke ka,ka hadiye Kuma sai lahira,"Yanzu muje ki fuske kamar komai Bai faru ba!"Duk Wanda ya tambayeki Ango kice suna hanya motarsu ta lalace,yace"zasu sauya Mota suna tahowa!"Ni kuma An juma zanje gidan malam na Kan tudu na amso maki Mai kankat,Dariya Sahura tayi ta shaidanu...Tace Daga Nan Hajiya Mansura Labari zai canja,saboda zakiyi maganin iskancinsa,Ai yayi kadan ya samu bakin ciki,"Muje tawan...Badai AKWAI dumus ba,Ai magana ta Kare," "Ajiyar zuciya Mansura tayi Cikin Jin Dadi tabi kawarta wacce tafita Zama guba Sahura kenan, Uwar daba lamba Daya!" "Yadda Sahura ta tsara hakan CE,ta kasance Nan akaci akasha aka chashe Duk da har Yan gulmace-gulmace anyi na rashin zuwan Angon," Nan dai aka Gama cin taro ya watse,"Daga Wurin event din Sahura Bata zame ko'ina ba sai gidan nakan tudu,"Kudi ta zuba Masa shi Kuma Babban Asiri ya bata Wanda Mansura zatayi amfani da shi,Idan Saddiq yazo gobe d'aurin aure,"( _Hmnnn..Daga kin gaskiya dai sai bata inji yar mutan Dikkawa_) "Bayan na farka na samu Jikina yayi min sauki a daddafe na karaso falon inda momy tare da gaidata itama ya jikin take min,Nan na zauna kusa da ita akasa,Duk da ba yadda batayi na hau kujerar ba,Amma na k'asa,"Shiyasa momy taji Dadi tare da yabawa da halayena "Abokin kuka!" akace shi ake fadawa mutuwa!"Tun fitar su momy Daga gidan Jawad ya Kira Saif sun Dade gidan suna neman yadda zasu shawo kan Matsalar!"Wanda akarshe gidan na momy suka nufa domin su bata Hakuri Alan Duk abinda ya faru!" "Ina zaune Ina kallo Amma Rabin hankalina na Kan tunani,momy mita ta dinga yimin Akan na daina tawan tunani,"Ana hakan naji kukan motar Jawad,"Zumbur na Mike nabar falon Wanda hakan da nayi yayiwa momy Dadi,saboda batason Jawad ya ganni!" "Gyara zamanta tayi tare da hade girar sama da ta k'asa!" "Da Sallama suka shigo falon sum-sum da su kamar barayin masallaci," "A can k'asan makoshi momy ta amsa, batare da ta kallesu ba!" "Saman kujera kowannen su ya zauna suna gaidata." "Harara ta watsa masu,Tace to marasa *TARBIYYA* Ni a saman kujera kuma samanta,to Ni Bari na sauko sai KU zAuna yadda Idan anzou za'a iya bambance Waye karami acikin mu!" "Da sauri suka dawo Kasan!tare da sunkuyar da Kai!" "Saif yace"Daman Momy mun...mun...munzo Domin mu roke ki....Dan Allah ayi Hakur...." "DakAta saifullahi fita idona na rufe!tun ban Saba maka ba!" "Idan Hakuri Kuka zo bani! to maza ga hanya KU fita...Domin Ni bani aka nemi kashewa ba!"KU nemeta!KU bata Hakuri..." "Momy Dan Allah kiyi hakuri Naga kamar ranki ya baci...!''Ay Jawad Bai karasa ba!"sai Jin saukar Mari yayi a fuskar SA!" "A hasale!momy Tace"Jawad yaushe ka koma marar Hankali wato ma Kama...ne ko!?"To saurareni kaji Raina ya baci ba Kama bane!"Kuma nayi Allah wadai da halinka..sai yanzu na yadda da Duk abinda ake Gaya min nakasa Ganewa" "Wato rashin imaninka har ya Kai,ka nemi aikata kisa!"kanaso ka kashe Nadiya! Duk bangon jaridar duniya yayi ado da fuskar ka akai!?"Kanason Ace Kai Kuma ka kashe matarkA!?A yayata ka a bakunan mutanen duniya,Kanason a fallasa Dukkan asirin ai mana kazafin abinda bamuyi ba!?"To ka kyauta Kuma na godewa Allah da burinka Bai cika ba!Ya tufa min asiri"Abinda nakeso da Kai ka rubuto takardar sakinta ka kawo min,Tunda baka sonta Toni da iyayenta muna sonta!"KU Tashi kubar min gidana kuje gaku ga duniya!" "Duk inda hankalin Jawad Yake yayi mugun Tashi...tun Kam Marin sa da Momy tayi, abinda Bai taba faruwa ba!"Har zuwa kalamanta da suka D'aga masa hankali!" "Kuka Yake Yana rokonta Amma banza tayi Masa akarshe barin falon tayi!"Cikin takaicin halayen Jawad "Saif ma Sai da yayi Hawaye! saboda tsabar tashin hankali!"Hakuri yake ba Jawad Amma ya k'asa yin shiru Domin Bai had a kowa da momynsa ba!"Haka suka fita daga gidan Basu ko San Nadiya tana Nan ba!" "Shawarar zuwa gidan Mallam Balarabe sukayi Domin su sameshi su bashi Hakuri Akan abinda ke faruwa,"Daga Nan su ga Nadiya su Bata Hakuri ko momy zata huce!" "A zuciyar Jawad Babu sauki! Domin haushin Nadiya yama qara ninkuwa,A ganinsa sanadinta ya samu matsala da farin cikinsa wato momy,nadamarsa daya bacin ran momynsa!"Amma ba Domin hakan ba,Shikam ko a aljihun wandonsa,Domin ya huce haushinta!Da takaicin bakinta da ya kirashi da kalmar da ta tsaya Masa arai. "Saif Addu'a yake Allah Yasa kada Jawad ya saki Nadiya, domin burinsa shi da Saudat agyara komai Amma Gashi Abu sai qara lalacewa yake!"Allah dai ya shiga lamarin, ya shirya shine Addu'ar saif da fatansa Wanda tuni jiki ya d'auki raw'a!"Saboda akwai SA ahannunsa acikin ta'asar,"bayaso asirin su ya tono. "Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba,"Domin harda wata k'aramar liyafa aka hada ta jin dad'in agidan Jalilar Saddiq,"Wanda akayo masu oder a Hilton Restaurant," "Madam Jalila Ita da Yan uwanta da Saddiq da Umaimah da mijinta kowa yaci gayu an canja tufafi anyi kwalliya,sai da aka bude tarou da Addu'oin da fatan Alheri,"Sannan aka Soma jawabai da nasihohi sannan aka Fara kwasar gara,"Jalila Kam an sha kyau Cikin wani hadadden material sabo dal Wanda Umaimah ta Bata shi kyauta,Domin ta dinka Bata SA ba!"gashi Anje saloon an wanke Kai,tayi parking dinsa,ga makeup an zuba na ji nagani na fad'a,sai kamshi ke Tashi gidan,"Domin batada maraba da Amarya,"Dan tuni ta d'auki aniyar kawo gyara a rayuwar ta Musamman tsafta,kwalliya,da iya girki Wanda umaima ce tayi Mata lacca mai zaman kanta Kuma jalila ta dauka Dan ko yanzu sai kamshi take zubawa. "Saddiq da Ali Sai murna suke har sun manta da wani dinner ga Babban Dinner anayi agidan uwargida Mai gayya Babban gorou sai magogin karfe,tsohuwar Zuma maganin cuta!"Jalila kainuwa dashen Allah Maman Mufeed da Mufeeda," "Fad'an irin farin Cikin da Jalila take ciki bazai misaltu ba, sai dai fatan Alheri,Su Anty Talatu, Rasheeda da su Tahir sun koma gida Cikin jin Dadi," "Haka Aliyu da Umaimah gida suka wuce," "Bayan fitar su ne Jalila ta Rungume Saddiq tana bashi Hakuri akan Dukkan abinda ya faru," "Share Mata Hawaye yayi tare da Kallonta ta koma Masa sabuwa har wani kyau tayi,"Yace na yafe maki Jalila Allah yasa MUDACE,"Daga Nan Tashi yayi,ya shige Dakinsa Domin ya samu ya kebe Nan ya Kira mahaifin SA Mallam Musa,Sun Jima suna tattaunawa Cike da fahimtar JUNA Wanda akarshe sukayi sallama," "Ko da ya dawo falon Bai Sami Gimbiyar ba! hanyar kofar da zata sadashi da gefenta ya nufa,yana shiga rufo kofar yayi Daman sun rufe komai nasu da bakin suka fita,Mai gadin gidan ma Yana bakin aikinsa mudi kenan Dan dashi aka dawo Kuma yaji Dadin dawowar Hajiya Domin ya fahimci ta sauya yanzun zai samu Abinci yadda ya dace,Fatan Alheri ya yi masu da asuba tagari. *'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍* _ZAFAFAN COMMENTS NAKESO FANS,KAMAR NA KASHE MAKU KUDINKU👌🏻_ [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 34* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *ANNABI (S.A.W) YACE" KUNYA TANA DAGA CIKIN IMANI(MA'ANA KUNYA ALAMA CE TA IMANI)* *HAKA KUMA A WANI WURIN YACE:* " *LALLE ITA ADDU'A IBADA CE* _ALLAH YA SANYA MA ACIKIN BAYINSA MASU BAUTARSA DA TSOROUNSA DA GASKE YASA MUYI KARSHE MAI KYAU,SANNAN MU RIBACI ILIMIN,DA RAYUWAR MU AMEEN._ _SANARWA....._ _"INA MASOYANA?INA MA'ABOTA KARATUN LITTAFAI NA?NESA TAZO KUSA,GA WATA DAMA TA SAMU,"DOMIN ZAKU IYA SAURAREN KARATUN LITTAFIN ALMAJIRANCHI KO AIKATAU!?"A DUK *RANAR TALATA* DA MISALIN KARFE *8:15 AM (NA SAFE)* A GIDAN REDIYON TARAYYA NA *EQUITY FM BIRNIN KEBBI* AKAN MITA *103.5* ZANGON FM,AYI SAURARE LAFIYA,NAGODE."_ ____________________________________ "Umaimah Bata Sha wata wahala ba,Wurin fahimtar da maigidanta Ali gadanga,"Duk abinda ya faru A tsakanin mansura da Jalila," "Ali yayi mamaki kwarai da gaske sai dai tun farko ya fahimci mansura 'Yar duniya CE,Amma Bai dauki zata iya shirya tuggu,da makirchi irin Wannan ba!"Har ta zamo sanAdin mutuwar Aure!" "Da Yake Daman yaune zasuje Dinner din Kuma ga Wannan zancen ga shi Umaima Tace"bazata ba!"Shima baza shi ba!"Domin tana gudun Kar ya hadou da shedaniya acikin kawayen Amarya ta manne Masa!" "Ali da farko yaso ya bijirewa zancen matarsa!"A karshe kuwa yadda yayi da hakan sai dai Zaije Yanzu ya samu Saddiq suyi maganar!" "Tun wayewar gari ya Tashi da wata irin kasala!"Ya k'asa Ayyanawa kansa komai,Da kyar yayi wanka yasha tea,"Abubuwa da dama ne aransa,Ya rasa meye mafita!"A gefe duk hankalinsa ya k'asa kwanciya tunanin matarsa da yaransa NE azuciyar sa,Kaddara kenan Gashi ta zamou Silar tarwatsewar iyalansa..."Tunani fita yayi yabar gidan ko zai samu nutsuwa key din Motar sa ya d'auka ya fice Daga Cikin katafaren sabon Gidansa," "Tun misalin karfe 12:30 na Rana masu aikin decorations ke faman gyara Wurin da za'ayi event din Dinner a plus center da ke Birnin Kebbi," "An k'awata Wurin sosai A can gidan su Amarya mansura,Ba karya yau kowa kure adaka zaiyi,"Qawayenta sun k'osa lokaci Yayi suje suyi sabon kamu,Shiyasa sukayi dinki tamkar ba 'ya'yan Hausawa ba!" yamma kawai ake jira afara zuwa," "Mansura tun jiya da dare take faman neman layin Saddiq sai dai akashe,Yanzu NE ta Kara kiransa wayar na ringing ba'a Daga ba!"Wani bakon lamari taji ya ziyarci zuciyarta!"Domin kuwa ko da Saddiq baya Nan ta kira ya samu missed call jiki na rawa zai kirata!"Bare ba Nan da Nan suna manne awaya!"Amma ace shi Bai kirata ba!"ita ta kirashi ya qasa daga wayar!" "Sahura ta katse Mata tunani..tana cewa Mansura ke Muke jira Wai meke faruwa Ana magana kinyi shiru!?" "Ajiyar zuciya ta sauke..Tace Sahura dole na damu Saddiq NE!" "Me ya faru da shi Saddiq din!?"Inji Sahura tana dubanta "Murmushi tayi ba komai kawai rabona da waya da shi tun jiya da Rana!"Yanzu ma na kirashi Bai d'auka ba!" "Mtwsssss...Dan Allah malama muje so Miji!"Ni Wallahi har kin bani tsoro!"kina nufin Yanzu Yana da time din waya da ke NE,!?"may be wayar ma Bata tare da shi!"Kinsani Sarai maza sunfimu shiga busy!"A irin Wannan time na aure..."Kinga muje ga Mai gyaran jikin can tazo tun d'azu nake nemanki!"A she kin kure daki kina tunanin Rabin ranki.."Hannunta Sahura ta Kama suka fita!"Tana kokarin kwantarwa Mansura da Hankali," "Zaune nake a lafiyayyen falona,Na kammala Duk ayyukan gidan,Da abinci da komai na gama Duka,Kallon wani film nakeyi Hankali na Wurin t.v." "Ban Ankara ba!"Sai ganin nayi an kashe t.v Duka!"Ban damu ba saboda nasan ba Wanda zaiyi aikin face Jawad." "Daman hakan Yake Shigowa gidan ba sallama,Key kawai zaisa ya bude kofar falon!"Wayata na laluba agefena Ina dannawa..Nan ma da zafin nama ya fizgeta yayi jifa da ita,Babu Bata lokaci ta tarwatse!A Kasan tails din falon,''Wani irin Abu naji araina Amma sai na jure!"Hanyar shiga bedrum Dina nabi,Har nafara Tafiya yace"Ke Yar rainin hankali ba'a koyar da ke yadda ake gaida mutane ba!"har sau nawa Zan fad'a Miki ki dinga gaida ni. "Banza nayi Masa!"Amma na tsaya zuciyata nayi min zafi!"Tamkar na bashi Amsa sai Kuma nayi shiru Kuka nake sonyi Amma zuciyata ta horeni Kar nabari Jawad yaga rashin jarumta ta!" "Kije ki kawo min lemon kankana Dana tsamiya sannan kimin Ginger drinks Yanzu,''Kafin nan sakwara da miyar agusi nake buqata ke nake jira!"Yar aiki kawai"Jawad yace"A gadarance" "Amsa Masa nayi da to,Nan take na fad'a Kichen na hada Wannan, nayi Wancan, Duk da agajiye nake Bai sani rashin sauri ba!"A cikin awa Daya na kammala komai,saboda gas dina Yana aiki sosai. "A daning place na jera Masa komai har Yanzu Yana falon Yana wayoyinsa da abokansa har da Yan Mata!" "Tashi yayi Daga falon yayi kan daning Yana wakarsa,Zama yay nikam kokarin Tafiya nayi,sai dai dakatar da Ni yayi,Abincin ya fara ci spoon daya ya Bata fuska!"tare da furzou min shi ajiki!" " gabana ya Fadi!"na dubeshi da tuhuma to me Yake nufi!?"Ba dai Babu Dadi ba!?"Duk yadda abincin Nan ya hadou yaji komai!"Dan bakin ciki zaice ba Dadi!" "Ashe Haka kike Baki iya girki ba!"Wannan abincin ko kusun masallaci ba zai iya cinsa ba!"Tsaki yayi tare da cewa"Shiyasa ban taba kuskuren SA Abincin ki a harshena ba!"Wato barnar kayan Abinci NE kikeyi!Baki iya komai ba!"to Ina kwarewar taki?"Nasan matakan iya girkin diya macce Yana Daga Cikin *TARBIYYAR* da akai Mata agidansu, Duk tinkahon ki nake Mai *TARBIYYA* ce Ashe Baki iya girki ba!"Amma anji kunya.."Jawad yace Yana kallona sama da kasa. "Nan ya d'auki glass cup yabi drinks din kowanne ya kurba,A gaskiya yaji dadin su dukan su, har Kasan ransa,acikin zuciyar sa," "Amma afili kallona yayi tare da watso min drinks kowanne ajiki!"Duk da sanyin da suke da shi!"A hasale yace'"Dan gidanku Haka ake lemon tsamiya!"Haka ake Wad'an nan drinks kinsan Baki iyaba bazaki Gaya min ba!" "Duk Jikina na duba Daga sama har k'asa!" ya Bata min tufafi da miyar sakwarar,da Duk lemukan da na hada Masa kowanne sai da ya watsa min ajiki!" "Wasu Hawaye suka dinga min zuba kamar famfo!"Cikin Kuka nace Wannan wane irin cin zarafi ne!"lalle jawad ka cika marar Tausayi!"Naso na kyaleka nabarka da Duk abinda zakayi min,Amma na k'asa jure wulaqancin ka!"Ko Yanzu burinka ya cika, Domin ka dauki fansa akaina!"Sai ka sallameni na koma ga iyayena!"Amma kasani Wannan abun da kayi min ya qara tabbatar min da cewa Muhammad Jawad Husamaddin cikakken Maras *TARBIYYA* ne........" "Ay ban karasa ba!"Sai saukar maruka da naushi nakeji ta ko'ina ajikina!"Belt dinsa ya zare ya dinga dukana kamar an bashi kwangilar kasheni..."Kuka nake Ina rokonsa yayi Hakuri tare da neman dauki awurin Allah!" "Amma Jawad ko jina bayayi!"saboda ranshi ya matuk'ar baci!" yace"kashe ki Zanyi Tunda bakinki da sauran magana idan yaso nayi prison sanadin rashin *TARBIYYA* Wannan NE kawai maganin bakinki...wani wawan naushi ya kaimin abaki..."Bansan lokacin da na saki wata irin gigitattar Kara ba!"Wanda tayi sandiyar shigowar mommy da Hajiya Maryam da gudunsu!"A falon sukai Turus suka tsaya cike da razana!" "Dishi-Dishi nake ganin su Wanda akarshe Numfashi na ya dauke cak!" "Jawad Kam atsorace ya jefar da Belt dinsa!"tare da gurfanawa Yana kokarin rokon momy wacce ke Kuka da Hawaye!"Tana binshi da kallon tsana da tuhuma!" "Innalillahi Wa'Inna ilaihir Raju'un!!"Shine kalmar da suke maimaitawa!"Yayinda suke kallon Nadiya wacce tuni ta, Suma ga hancinta da Bakinta duk jini ke zuba!" "Tashin hankali!!"Momy ta shiga sai tambayar kanta takeyi menene sila!?" "Hajiya Maryam ruwan Sanyi ta dauko tare da tallafo Nadiya zuwa jikinta tana zuba Mata ruwan afuska,tana fifita Mata gefen hijab dinta Amma har Yanzu ba Alamar Numfashi atare da Nadiya!!" "Dama Yan magana kance Idan kaga rakumi kaga buzu,"Saddiq na fita Bai zarce ko'ina ba,sai layin gidan Amininsa da ke unguwar,"Yana kokarin kunna Kan motarsa Shima ya fitowa da Tashi,"Nan suka tsaya,"Ali yace gidanka zanje Nima fa yanzun Nan," "Dariya Saddiq Yayi yace"to mu shige Daga ciki, Daman nayi tsumayen zuwan naka Naga bakazo Shiyasa Nace Bari na karaso." "Komawa sukayi Cikin gidan tare da parking motocin su." "Tuni Ali da Umaimah suka Gama shirya plan DINSU.. " "Umaimah na jinsu ta dannawa Jalila Kira Wacce tun d'azu sun kammala tsara komai zuwan ta ne kawai suke," "Ali da Saddiq fira suka fara nan NE Ali,yace shin KARFE nawa ne zamuje Dinner!?" "Saddiq yace to Ali ban Jin dadin jikina,mu Bari zuwa 4 mu tafi Tunda 6 ne za'a fara taron ko kuwa!?" "Ali yace"Ba damuwa Angon Mansura...Yana murmushi "Wani iri yaji aransa babu Dadi!"Wayarsa ya fitou Daga aljihunsa Wanda tun safe take a silent,misclls ya gani ma bambanta,Nan ya Kira Mutane!"A karshe mansura ya Kira ya shaida Mata zuwa yamma zasu zo,tayi Hakuri baya kusa ga wayar ko da take kira!"Nan ta dauki Munna tana Masa azo lafiya," "Saddiq yace naji hayaniyar su salima kenan suna gidan ko!'' "Ali yace"Eh...Kasan yau Alhamis ba Islamiyya, suna gida Ina ga lesson Suhaila ke masu itama free take.." "Yace"Amaryar CE ta kosa mu karaso ko!?" "Eh ita ce,Ay nagaya mata muna hanya.."Zuwa yamma zamu karaso,"Inji Saddiq, "Ina Umaima NE!? Saddiq ya tambaya "Tana dakinta bacci take,kanta KE Mata ciwo!" "Dariya Saddiq Yayi yace"Allah ya Bata lafiya ko Kukan Khairat NE,Kasan Mamana akwai fitina,ga hayaniyar su Salim," "Wallahi hakane, damar abin su na Tsoronta da zarar sun dameta! zata Saita masu hankali ko da ta hanyar kallo ne!"Inji Ali Yana murmushi "Ali ya qara da cewa "Shin Saddiq Wai bazaka mayarda Jalila ba!"Ya kamata ta dawo ta rike yaranta, ta kula da su,Kasan da wuya kasamu maccen da zata rikema yaranka tsakani da Allah har ta kula dasu,"Kayi Hakuri nasan Duk inda Jalila take ayanzu yaci ace tayi karatun ta nutsu!"Ka dawo da ita ku cigaba da rayuwar ku,ka manta komai ya wuce shine maslaha..." "Shiru yayi yau kaam Yana sauraren Ali,Abinda ya Dade rabonsa da yi,wato sauraren maganar da ta shafi Jalila!" "Nan Ali ya samu makami ya dinga zubawa Saddiq magana har da nuna Masa wasu halayen banza na mansura da Dan kusheta!"Har yayi nasarar rinjayar Saddiq wanda jikinsa yayi mugun Sanyi, kwanyarsa ta dauki zafi!"Dogon nazari ya yi da tunani barkatai komai na dawowa ga kwakwalwarsa, Yace, "TABBAS Ali nayi gudun gara na farma zago,sai dai Mai Riga tariga Tafaru Duk abinda kafada Akan mansura Yanzu nayi tunani na gane gaskiya ne,Amma hakan bazai hanani aurenta ba!"Sanin kanka ne Jalila Bata damu Dani ba bare yaranmu,batada kirki nifa ba Jalila CE banaso ba!"Ina sonta Domin so yasa na aureta. Halayenta ne ba na kwarai ba. Wallahi Banda niyyar ajiye macce fiye da daya agidana!"Amma gashi Akan mugun halinta Zanyi hakan,kai Kan ka kasan Bana da ra ayin aure, Amma shi kenan na hak'ura Zan mayarda ita saboda darajar 'ya'yanta da kuma alfarmaka......" "Bai karasa ba...sai ga Jalila da gudunta ta fadou falon tana Kuka!!" "Kallonta sukayi cike da mamaki!" "Ali yace lafiya Jalila!?" "Cikin karajin Kuka!Ta jifar da i.v din auren akasa suka bishi da kallo!" "Saddiq hade Rai!"yayi yace"ke ciwon haukar naki ya taso har gidan Mutane!" "Da sauri Umaima ta bayyana falon tana haki,A Dan firgice!Tace subhanallahi!!! meke faruwa ne!?Jalila menene!"Tare da rungumo ta ajikinta sai faman kakkarwa take!"cike da kissa!"sukayi inkiya da ido.." "Muryar ta na rawa!"Tace"Umaima Ashe Saddiq mansura CE zai aura!?yanzu ya rasa maccen aure sai ita?"Hmnnnn...Duk fa rashin mutuncina sam ban Kama kafar na mansura ba!"Idan Saddiq zaiyi auren huce haushine to Bai tsira ba!"Saboda Mansura "Ita ce Yarinyar da ta cuceni! ki duba wayata Duk hotunan auren su NE!"Jalila ta karashe zancen tana Kuka!" "Ali da Saddiq Yan kallo suka koma sai dai jin ta ambaci sunan Mansura yaji bugun zuciyarsa ya karou!" "Umaima Tace To meye aciki Jalila!? bayan kinsan Saddiq mijin macce hudu NE!Dama kin San ta ne!?" "TABBAS nasan Mansura farin sani ma kuwa Umaima,mansura CE gubar da ta shayar da Ni cutar da ke neman illata rayuwata!"Mansura CE Silar mutuwar AURENA!?"Mansura CE ta gaya min Saddiq da Nadiya suna zaman banza!"Mansura CE Tace"muje ta kaini Wurin malami acire soyyayar Nadiyatu azuciyar Saddiq asaka tawa, amaimakon hakan sai akasawa Saddiq cutar son Mansura!"Ni Kuma Ya tsaneni!" mansura ta shahara gurin neman magani,batada kirki ba Mai tarbiyya bace.....Kuka ya ci karfinta ta dubesu dukansu Tace, "Meyasa zata cuceni!Meyasa zatayi amfani Dani wajen aure min mijina?Mutumen Dana keso!,wanda nake mugun kishi...Kama hannun Umaima tayi tana zubda Hawaye ta CE"Umaima Hakika mansura ta shayar da Ni mamaki nayi nadama,nagane meye illata!"Na yarda da ita ne dalilin Naga Kawar Nadiyatu ce,Kuma maybe tasan sirrinta!"Ashe ba haka bane. "Share hawayenta tayi tare da juyowa tana Fuskantar Saddiq Wanda Yayi mutuwar tsaye!"Har k'asa ta Kai tana dafa kafarsa...Cikin yanayin wahala da nadama Tace"Dan Allah Saddiq kayi hakuri ka yafe min nayi nadama!na tuba bazan sake ba!"sanin da kayi min ada, na canja fiye da tunaninka!"Na samu ilimin zaman rayuwar duniya!"nA samu ilimin da Zan zAuna da Kai,Har nayi wa yaran mu *TARBIYYA*," Duk abinda nayi sharrin Mansura NE,da Kuma mugun kishinka Wanda sonka da kaunar ka ne sanadi!"Wani sabon babin Kuka Jalila ta bude irin Wanda tasan cewa Saddiq ya tsani sauraren SA!" "Da sauri Umaima ta k'araso wurinta tare da tallafo ta!"Itama Hawayen takeyi!"Tace"ki daina Kuka Jalila tabbas mansura ba matar aure bace!ta cutar da ke!"Ta rabaki da yaranki da mijinki!"Ya kamata kiyi karatun ta nutsu Daga Wannan kuskuren!" "NA karantu na ilimantu Umaima har na haddace!"Yanzu da wane ido Zan dubi Nadiya!?saboda na cuceta nayi Mata kazafi!"Wanda Duk shirin mansura ne itace ta sanarda ni komai,Ashe tsarinta ne! "Ali yace to mun godewa Allah,Daya tona asirin Wannan bakar amaryar tun Wuri A gaskiya Jalila kinyi wauta da har zaki yadda da mutim,Domin abin tsoro ne!"Kai Kuma Saddiq kayi KOKARI ka mayarda matar ka,tun kafin akawo maka amaryarka!"Wannan shine shawarata!" "Ajiyar zuciya Saddiq ya sauke Idonsa Akan Jalila da ke faman zubda kwallah,wani tausayin ta da sabon sonta ya dawo Masa!"ga wata nadama Mai D'IMBIN yawa da ya hango akwayar idonta,don ta canja sosai"Yace"Shi kenan Zan mayarda ke Jalila yau ba Sai gobe ba!"Kuma ayau Zaki koma gidana,"Yanzu zanje inda magabatanki,Ga Ali nan shaidata ne, za'a daura auren mu,Umaima ki rakata kuje Sumayya furnitures,A sayi komai na sashenta,sai KU dauko masu jere ayi komai,ga ATM Dina ya mikawa Jalila jiki na rawa tana Murmushi ta amsa tana godiya,"Yace"Akula min da dukiyata kada ayi min barnar arziki kar kuga na bar maku wuqa da nama," "Ali alama yayiwa Umaima da hannu kenan sunyi nasara murmushi Yayi Yana tafa hannu yace"Umaima me ma naji kina cewa"Yar mutan Dikkawa" tana yawan rubutawa anovels," "Umaima na dariya Tace"Fadan masoya hutu ne....Inji Anty Nabeela Dikko"Jalila rufe fuskarta tayi tana dariyar Jin Dadi,"Tace Abban Mufeed meye pin dinka!?" "Murmushi Saddiq Yayi yace''umman Mufeeda ban canja pin ba,Yana Nan tun Wanda Kikasa min da kanki" "Umaima da Ali wani Dadi ya lullube su,Allah ya taimakesu Plan dinsu yayi normal,"Sun mayarda ma'aurata a inuwa Daya." "Jalila Tace ,Aliyu nagode maka Kai da uwargidan ka,abisa Taimakona da fahimta ta da kukayi Allah yabar zumunci," "Ameen,sukace dukansu,kallon JUNA suke suna murmushi," "Umaima hijab ta dauko da key din motarta, zasu fita.. Saddiq yace"Amma fa ina da sharadi Wannan abinda ya faru ba shine zai hanani AURENA ba!"Babu makawa aure nayi niyyar shi, Kuma Zanyi Jalila kayan fad'a. Kishiyarki na nan zuwa Anjuma da dare!" "Murmushi Jalila tayi,wanda yafi Kuka zafi!"tare da share kwallarta!"Tace ba komai habibi kana da damar kawo wasu uku agidanka Bayan Ni,kayan fadar kishiya Kuma na yafe maka duniya da lahira ko Yanzu kayi KOKARI Kuma nagode Allah ya bamu zaman lafiya," "Umaima Tace Amin ya rabbi," "Saddiq Kam mamakin Jalila Yake ta koma wata sabuwa, har imani sabo ya shigeta!"kamar ba Jalila ba!"sai kallonta Yake cike da murmushin kauna," "Duk da A rayuwarta ta tsani kishiya Amma ba yanda zatayi hakuri! Zatayi da hukuncin ubangiji....Hade wasu yawu tayi na karfin Hali!"Tace Abban mufeed Ina rokon ka,"Alfarma D'aya!" Dan Allah ka nemi wata maccen ka aura, Amma ba mansura ba!"Wallahi na tuba ga Allah, bazan Kara neman magani ba aikin shirkah!"Shakka banayi mansura ta k'ware gurin zuwa gidan malamai da Yan bori,Domin Ada can baya ita ta kaini!"Ina gudun ta sake maka wani Asiri,Da zata rabani da Kai ta koma tarwatsa rayuwar yaran mu!"ta karashe zancen Cikin damuwa da tashin hankali!" "Umaima Tace"gaskiya ne wannan tun tana waje ta iya neman magani bare ma ta shiga Daga cikin gidan,Kai Allah ya rabamu da masu hali irin na ta,"Allah ya tsare mu Muje Jalila!Abban Salim sai mun dawo," "Adawo lafiya, Ali yayi musu"kana suka fita," "Saddiq Kam ya shiga duniyar nazari, Domin Duk zantukan Jalila Gaskiya ne,saboda Ada can baya ya tsani Mansura! Shiyasa tayi Masa asiri ta rabashi da matarsa!"Ta Sanya matsananciyar tsanarta a zuciyarsa! Har Nadiya ya dinga Jin haushinta"Tunanin mafita Yake Amma ya k'asa samu." "Suna fita falon suka tafa ita da Umaimah suna murna suka karasa Mota!" "Umaima Tace"A gaskiya Jalila da ke Yar film ce da kinyi tagomashi dalilin iya acting dinki,Kinga yadda kinka burgeni kuwa!" "Dariya Tayi Tace"Ay na koyo karatu da dama na zaman duniya har kissa da kisisina,A Yanzu Kam Ba zanyi saken da wata macce zata fini a idon Saddiq ba!" sai dai idan ma wata kwararriya CE mu goga!" "Jalila Tace mu fara biyawa ta gidanmu na sanarda su Hajiya, sai mu dauki Anty Talatu muje Sayayyar da ita,"Kinga ita Rasheeda ta jiramu idan mun dawo muje da ita ayi sauran gyare gyaren da yadace." To shi kenan Inji umaima. "Haka ko akayi Dan sun Sami su Hajiya Atika a falon gidan umaima tayi masu bayanin KOMAI,Hajiya tayi murna kamar ta take Kan jariri Nan ta kira Abokin marigayi awaya ta shaida Masa abinda ke faruwa,yace sai su Saddiq din sun karaso za'a mayar da auren su Bayan an gama sallar la"asar,"Hajiya harda su sakawa Saddiq Albarka har waje tayi masu rakiyar tana Jin Dadi!"Anty Talatu da Rasheeda ma sunyi murna sosai," "Suna fita Hajiya ta Kira mah'mud da Tahir Domin su halarci d'aurin auren yayarsu a masallacin unguwar ta su,"Nan ta shiga hadawa Jalila kayan gyaran jiki da yaji da Dan sauran tarkace," "Saddiq ya Dade Yana neman mafita Amma ya k'asa samu a karshe barin gidan sukayi Domin suje su samu waliyin Jalila amayar da auran su,''Kudin sadaki ya rika naira dubu ashirin,"A zuciyar SA ya ma rasa me zaiyiwa mansura ya huce takaicin ta!"Ikon Allah kenan, Kuma Babu Wanda zaija da shi!"Domin Gashi Jalila zata dawo gareshi!," _YAU FA RANAR KUCE MASOYAN JALILA ALLAH YAYI_ *'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍* *SHARE,AND COMMENTS* [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 46-50* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ ❤❤ *SADAUKARWA GA KAKANNI NAH ABIN QAUNATAAH*❤❤ _HAJIYA FATYMA ADAMU DIKKO(FALGHA)_ _HAJIYA RAKKIYA ADAMU DIKKO(HAJIATAH)_ _HAJIYA ZAINAB MADAWAKI(TSOHUWA)_ _HAJIYA MARYAM MADAWAKI(MERI)_ _ALLAH YA SANYAWA RAYUWA ALBARKA, YA QARA NISAN KWANA KAKUS,ALLAH YASA AYI KARSHE MAI KYAU,ALLAH YA GAFARTAWA SAURAN MAGABATA,AMEEN.😍_ ______________________________________ "Bayan jama'a sun kammala, kowa yayi tsit!"Sai Sauraren liman da waliyyai ake,"Ana batun afara d'aurin auren ne,Malam Haliru kanen mahaifin Saddiq yayi ma liman wata magana asirrance,"Liman zaro ido!"yayi tare da rike Baki!"Nan ya fadawa waliyin mansura shima kanin mahaifinta ne,"Fuska ya hade tare da gyara zaman hullar sa!"Shima Juyawa yayi ya sanarda Sauran Yan uwansa da ke bayansa,Nan aka dinga zarar Ido Ana goge gumi!" "Saddiq da Ali wani tausayin su ya kama su,saboda agaskiya sunyi masu girshi!"Bai kamata su yanke hukunci ba!aranar aure!'' "Tattaunawa sukeyi har suka fahimci hankalin jama'ar Wurin ya fara dawowa kansu!''Sannan ne kanin baban mansura ya nemi a sasanta batun atufa Asiri, ayi auren ko Bayan auren ne idan ya so, shi Saddiq din ya saketa, tunda yace ya fasa aurenta saboda ita ce Silar KASHE Masa Aurensa da uwargidan sa,"Hakuri sosai dangin mansura ke baiwa su Saddiq,"Mahaifinta har da kwallah yayi!"Gwanin tausayi!" "Ali ya dubi Saddiq yace"ko zaka hakura a daura!?" "Saddiq ya bude Baki ya bashi amsa kenan sai ga Bimboy da Adams sunzo sun zAuna," "Kowa su Yake kallo da mamaki saboda Babu alamun hankali tare da su," "Adams ya ce,Tsoffi waye waliyin mansura anan!?"Cikin sigar rashin mutunci!" "Fidda Ido yayi waje!yace"Gani uban me Zan maku!?"Daga ina!?" "Dariya Bimboy yayi tare da tafawa da Adams," "Kudi Bimboy ya fitou da su aljihu yace"Dattijou Wannan naira dubu goma Sha biyar NE!" " Wannan dubu biyar nagani Ina so(BAIKO)na da Mansura," "Kaga sadaki sha biyar kudin shiga gida dubu biyar Ina son Yanzu Bai sai anjuma ba zaman ku da tsarinku da salonku duk su sauya ina nufin ku aura da Mana Aure Ni da mansbaby!" "A zabure kawun Mansura ya tasowa su Bimboy Yana fad'a da su har da zaginsu,yana cewa KU Wad'an me marasa hankali da *TARBIYYA* ne,"A Ranar aurenta Ana batun daura aure zaku wani ce Kun kawo kud'in aurenta saboda KU marasa hankali...." "DakAta Mallam karfa ka manta KU Mutane ke saurare saura sakan talatin lokaci Yayi cip!"Ba sa'insa ya kawo mu ba,kaga tawagar mu can..."Adams ya nuna abokansu da ke zazzaune agefe Duk da kananan Kaya,"Ya ce" Ya dubi Sadiq yace lallen Ango to karbi Wad'an nan takardun ka karanta!"Nasan Dole ka hakura da amaryarka ka barwa Mai rabo!" "Takardar Ali ya karba suka karanta shi da Saddiq," "Innalillahi Wa'Inna ilaihir Raju'un!!!"Shine abinda suke maimaitawa Alhamdulillah, Saddiq yace"Tare da mikawa Adams takardar....yace ko da abokinka bai zo ba,Kuma Banga Wannan takardar ba!Ayna fasa auren mansura!"Saboda ta cuceni!" "Murmushi Bimboy yayi yace mansura mayaudariya ce alqawarin aure NE atsakanin mu,Amma ta gujeni sai da naji labarin aurenta da Kai,Bayan duk abinda na Tara ta lashe,kudin gadona ta cinye idan sata nayi ita ke Moran kudin Kai har kidnapping din wani Alhaji saurayinta tasa mukayi Wallahi duk ita ta cinye kudaden da aka bamu,Amma yanzu tazo ta gujeni!" "Adams yace kai Hakuri bimboy ai bazata yaudareka taci bulus ba, ya dubesu yace Yawwa Kawu wannan takardar da kuke gani ta asibiti CE,wacce da ta mansura da Abdul Rahman CE, kuma an shaida masu da dadewa suna dauke da cutar HIV AIDS,"sannan Wallahi idan ba'a daura auren Nan yanzu ba!"zamu amshi microphones mu shaidawa kowa meke faruwa!"tun farko har karshe!" "Dariyar iskanci Adams yayi yace"Shin Bimboy Zaki iya tuna iya adadin Cikin mansura!?" "To zan iya tuna wad'anda nakeda masaniya akai kamar bakwai NE!"Inji Bimboy "Wata Dariyar Adams yayi inda maroki ya nufa ai da gudu kawun Mansura ya kwasa ya cafkoshi yace"tufa Mana Asiri Dan Nan......!!!!" "Asirinku atufe Yake Amma ayi a daura auren Nan,lokaci yayi,"nine waliyin Ango...Adams ya ce cike da Jin Dadi!"yadda Duk Yan uwan "Mahaifin mansura da yayyansa sai sunkuyar da Kai sukayi Saboda kunya!"Kawun ta ko fifita Yake Saboda zufa!yace"Ai ga irinta Nan.....ya dubi Yan uwansa Cikin Jin haushi da takaici!"Yace"Yaya me kuke Ganin yadace!"Kunji saddiq ya fasa auren!"Wad'annan kadagarun barikin Kuma zasu iya tona Mana Asiri wallahi...."Saboda basuda kunya,...." "Ay tun Kan ya qarasa Adams ya Tashi Rai bace!"Ya karbi abin sanarwa ga wani marobi...hurawa Yayi sannan yace To jama'ah!!" "Nan dayan marokin yace"To jama'ah kowa ya SAURARA..." "Adams cike da Daga murya yace"Ango yace ya fasa!" "Azabure Wasu Mutane suka tAshi..suna kallon Adams Nan hayaniyar ta kaure!" "Marokin...yace"To fa Ana wata ga wata Wai Ango ya fasa!" "Adams yace Amma baza a fasa d'aurin auren ba!" "Marokin yace"kowa ya zauna KU kwantarda hankalinku rabo ya rantse sai Mai shi Domin take away bazai wuce mu ba!"Aure dai sai an d'aura. " Adams yace sai abu na gaba da Baku Sani ba.... "kawun mansura NE ya rufewa Adams Baki ya jashi izuwa inda suke zaune Yana Hawaye!yace ka taimaka ka rufe Karla tona."Yace liman a d'aura dasu kawai ai duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwan Kan doka. "Suna Zama Liman yace ayi Salati,Nan aka fara gudanar da daurin Aure," "Mutane sai Rabon Ido suke da baza kunne Domin Cikin kowa ya cika fam da gulma,"Da mamaki da kuma Al'ajabi to ya Abin yake.....?." "A hankali numfashin Mallam BALARABE ya dawo,"sanda ya bude Idonsa Ganin an kewaye shi yasa ya fara tunawa da abinda ke faruwa, "Jawad da saif tallafo shi sukayi zuwa babbar kujerar da ke falon,Har Yanzu Hawaye yakeyi Yana kallon hoton...!" "Innerie da Sauran jama'ar falon sai sannu suke faman jera Masa," "Inda yake na zauna Ina kwallah!"Nace Baba lafiya meke faruwa!?" "Alh.malami sambo ruwa yaba Baba yasha kana yace"sannu Mallam ko Kasan Marigayi Husamaddin NE!?" "Wasu zafafan Hawaye suka zubowa Mallam BALARABE ya Nuna hoton da yatsa Cikin k'unar rai yace hakika nasan shi!"farin sani kunga Wannan hoton....yace tare da nuna masu dayan hoton da ke manne ajikin bangon...na farar kala NE,na Yara kanana uku,sai gudan na yaran su BIYU kamar Yaya da Kane,"Sai Kuma dayan na Babban mutim wato All.husamaddin Wanda yayi alokacin Yana Cikin ganiyar kudin SA gab da rasuwar SA," "Kowa hotunan ya duba..."sannan Mallam BALARABE yace"To Wannan hoton na Yara uku Ni da husama,da Aram ne," "Dukkan su shi suke kallo da mamaki... " "Muryar momy na rawa Tace Kar dai kace min Kaine Yaya Bello!?"Yayansa!" "Girgiza kansa Yayi yace nine Yayansa Bello....Hajiya nine...Yanzu Ashe Jawad jinana NE..."sannan kanena Husamaddin ya rasu!"kaicoh na dunia lallai nayi kewar gida da dangina!"wani sabon Kuka Mallam BALARABE ya bude!" "Momy da Jawad ma Kuka suke!" "Nikam Tuni na daskare Domin bakin CIKI Saboda banso makiyina ya Zama jinina ba Wai ma Yana daga Cikin ahlina da na Dade Ina son Gani!" "Alh.malami da Hajiya Maryam Alhamdulillah suketa faman nanatawa!" "Saif da Innarei sunji Dadi sosai sai hawayen murna suke!" "Momy Tace"Wallahi Marigayi ya mutu da son ganinka arayuwarsa. Nan dai momy ta labartawa Mallam BALARABE komai da tasani tun farko har karshe,"Tashi tayi ta dauko wata tsohowar ajiyar da marigayi mijinta yayi,ta kawowa Mallam BALARABE,"Tace"Wannan shine amanar da ya bani Kuma sirri CE,Daga Ni sai shi,yace min duk RANAR da Naga Yaya Bello na bashi..." "Jiki na rawa Mallam BALARABE ya bude akwatin,duk hotunan su ne Dana iyayensu,har da tufafin Mallam BALARABE da ya Bari agida SUDAN, Alokacin da ya Gudu zuwa Nigeria," "Kuka sosai Mallam BALARABE keyi!!"Har ya Gama ganin kayan akarshe takardun kudaden SA ne,Wanda aka raba aka ba marigayi Husamaddin nashi da na Yayansa Alokacin da mahaifiyarsu ta rasu,Wacce Yar kasuwa CE sosai Mai dinbim dukiyar zinarai, "Allah sarki Mallam BALARABE yayi Kuka shi da iyalansa sosai,saboda ya rasa uwa da kaninsa," "Momy Kam hankalinta ya kwanta yau ta sauke nauyin da ke kanta!"Tace"Yaya Bello sanadin nemanka marigayi ya dawo Nigeria har ya mutu anan,Kuma yaje da buri akanka!"ya shaida min watarana zamu hadou,Gashi dalilin Nadiya da jawad mun hadu!"saboda mun Sha nemanka,Rashin sani akace yafi duhu!"ashema muna gari Daya da KU..." "Goge hawayensa yayi yace"Allah ya jikan ummu da Husama," "Ameen kowa yace"Sai share kwallan Tausayi ake!" "Jawad ya rarrafo tare da rike kafafun Mallam Balarabe yace Baba Shi kenan na cutar da kanwata!"jinina!"Daman ance idan zaka Gina...Ramin mugunta Gina karami..." Gashi Ni na Gina ya farmin...na yaudare ku iyayena na cutar da kanwata Nadiya..."Ashe jinana ce jinin da muka Abbu na da mommyna su ka sha wahala Ni da wurin nema," "Dan Allah Nadiya kiyi Hakuri ki yafe min....Baba na tuba ku yafeni Jawad yace"Yana rusa Kuka!" "Mallam Balarabe yace"Ka DAINA Kuka!yarona komai ya wuce!"Kuma laifinta NE ba naka b....." "A'ah Baba Nadiya batada laifi mune masu laifi Ni da Abokina saif domin mun shirya mata gadar zare, Kuma mun yaudareku duk a Dalilin kalmar tarbiyya "Nan jawad ya labartawa iyayensa komai tun haduwarsa da Nadiya,har had'a bakin da sukayi da M Bala yasa aka koreta!Daga makaranta,Da kuma zuwan da sukayi Wurin Mallam yunus suka aibata tah!"Dan kawai Ya ce ya fasa aurenta!"Da irin can mutunci da muzguna Mata da yayi har zuwa karshe dukan da yayi Mata....." "A hasale momy ta taso ta dinga zabga Masa Mari!"Ta ko'ina tana Kuka ta CE,Ashe haka ka zalince ta batare da kowa ya Sani ba?" "Da kyar aka banbari hannunta arigar Jawad da ta cumuimuye!Tace Wallahi sai ka saki Nadiya,"Kaje ga Saif Nan ya isheka rayuwa..."Hakuri Hajiya Maryam da Alh.malami ke ba momy Amma sai surfa ruwan masifa take!" "Nikam jikin mamana na shige Ina rera Kuka!"Akan abinda su Jawad su Kai min Domin sun cuceni sun Zama Silar rushewar karatuna ga sunana da suka b'ata! A gurin malamina"Rarrashi na mama keyi tana share min kwallah!!!" "Kukan momy yaja hankalin kowa afalon kalar tausayi...."Muryarta na rawa Cikin kunar rai!"Tace"Daman marigayi ya guje min hakan!ya guje min irin Wannan Ranar da Jawad zai Sani Kuka!"Gashi abinda ake guje min Bana gani ya faru yanzu sanadin soyyayar da nake nunawa Jawad ya kaini ga Kuka!"TABBAS duk Wanda baiji Bari ba!"yaji hoho!" "Duk kulawa da soyyaya har gatan da nake nuna maka Jawad, Ashe akwai Ranar da zaka yaudareni? da karyan Labari,Ni ka yaudara!?"Ni kai yima karya!?" "Wato ka zabi aboki da shawarar SA akaina!?"Saboda baka gudun zuciyata!nice ke gudun zuciyar ka da bacin ranka!" "Na yarda na amince *TARBIYYA* ita kadai CE gatan da zaka yiwa yarou wataran ya taso Yasan gatane kayi Masa arayuwa........!"Kuka NE ya ci karfinta!"Hajiya Maryam Hakuri take bata!" "Alh.malami ya numfasa yace kiyi Hakuri Hajiya!"agaskiya Jawad Bai kyauta ba!"Kuma ya aikata komai saboda Yasan zaki tsaya Masa domin yadda kike Sonsa kike gudun fushinsa!" "Alhaji Nima nayi mamakin yadda Allah yabani iko na tsawata Masa a al'amarin Nan saboda Ni awurina komai Jawad yayi bana damuwa Kuma daidai Bana son in takura Masa ko in shiga rayuwar SA abinda duk yakeso ko yaga dama agurina shine daidai!"Wannan NE karou na farko da na nuna Masa bacin Raina,na tsawatarmasa a rayuwata da shi!"Har na daure na Masa hukunci!"Abinda Abbansa ya kosa yaga nafara aikatawa....tun yana da rai. "Hajiya Maryam Tace"Yanzu dai Kinga illar sangarta yaro, Gashi Nan D'an mu ya aikata laifuka da dama sabadin haka ya ci Amana,yayi k'arya sannan ya yaudari mutane!" Wannan ba hujja bace Domin daga farko har karshe shi ne basida gaskiya,Dan Yana takama da dukiya sai ya wulakanta talaka har Yake ganin titin nasu ne Bana Al'umma ba!"Shiyasa ta kirashi da maras *TARBIYYA* shine ya yi kokarin auren huce haushi da Daukar fansa Wannan ya Kara tabbatarwa da Nadiyan da gaske shi din bayada kirki.'' "Sai Kuma akayi Dace ya hadou da abokin da ba na kwarai ba wato Kai Saifullahi duk jirgi Daya ya dauko KU "Daman Annabi (SAW)ya ce _"Kwatankwachin Wanda ke zaune da mutanen kirki,da maras kirki,kamar yadda kake zaune da mai turaren Almiski da mai zugazugi ne,Ko dai kaji kamshi ko kuma kaji kaurin wuta.,"_ "To Haka Zama da Abokin kirki da marar kirki Yake,Domin Kodai mutim ya Zama Mai kyawawan dabi'u ko Kuma sabanin hakan,"Allah ya sauwaka, Mallam Balarabe Kai da Fatima kuyi Hakuri da abinda danku ya aikatawa Yar mu,"Hajiya Maryam ta karashe zancen da damuwa!" Dukkan su ba Wanda yace uffan Domin kowa da abinda ke Cin zuciyar sa falon tsit yayi na lokaci. ******************* "Bayan an kammala Salati waliyin Amarya mansura ya baiwa Adams waliyin Abdul-Rahman (Bimboy)Auren Mansura Akan sadaki naira dubu goma Sha biyar,Fatiha jama'a suka shafa!"Kowa na fadin ALBARKACHIN bakinsa,"Daga cikin gidan mansura ko kide-kiden da ake da raye-raye da hayaniya ya hana suji sautin sanarwar auren da Marok'a keyi awajen gidan," "Jiki Babu k'wari jama'ar Wurin ke kokarin tashi,yayin da Adams da Bimboy farinciki ne faal aransu Domin shirinsu ya tafi za Dadi," "Kamar Daga sama Saddiq ya karbi abin magana(microphone)"Ya ce jama'a Dan Allah kowa ya DakAta!"Nima AURENA za'a daura KU Sanya Albarka," "Nan kowa yayi cirko-cirko suna mamaki!"Lalle kallo ya koma sama,"Aliyu da mamaki yace"Aure fa Saddiq to da wa Kuma!?" "Hannun Ali ya Kama yace"Dan Allah ka taimakeni,Ina son na nunawa Jalila Ni mijin macce Hudu ne! Idan na koma ba tare da aure ba! Burinta zai cika na Lalle tafi karfin ayi Mata kishiya!duk da ayanzu nasan tayi laushi!"Amma Ina son na nunawa Mata masu ganin sunfi karfin ayi masu kishiya!"Karyar su. Domin Allah ne, ya bamu ikon Karin auren ba su ba!"Inji Saddiq Cikin yanayin damuw!" "Ali yace Yanzu me kake so NE Saddiq!?" "Ina son kazama waliyin Suhaila kabani aurenta Wallahi Ina sonta Kuma tun Ranar da nafara ganin ta agidanka naji ta shiga Raina!"Zan baka naira dubu asirin na baikoh sannan Zan bada sadaki naira dubu Hamsin yanzun Nan,ga Kawu Nan waliyina..." "Numfashi Aliyu ya sauke yace"TABBAS Ni Mai bada auren Suhaila ne,Amma to bamu sani ba ko zata soka banason asamu garaje!"Kuma umman kano bata sani ba!"zan ba da auren Suhaila," "Saddiq yace"Aliyu na dauki alqawarin da zarar mun je Suhaila Tace Bata Sona ko wata matsala ta kunno Kai ta gefenta ko danginta Wallahi Zan sauwake Mata!"Nidai Ina son burina ya cika na zamou Mai Mata Ayau!na koma gidana a matsayin Ango,"Itama Jalila labarin mijinta ya taba aure Bayan ita ya kasance acikin tarihinta" "Da kyar da magiya Aliyu ya amince...Nan jama'a suka koma shafa fatihar auren Saddiq da Suhaila Akan sadaki naira dubu Hamsin,"Godiya sosai Saddiq yayiwa liman da jama'ar Wurin har iyayen mansura tare da labarta masu komai da Mansura tayi Masa,"Sannan akarshe Hakuri ya Basu,"Nan suka nufi motarsu Domin zuwa Argungu," "Amota ma Ali Sai tunanin yadda zata kaya yakeyi... Saddiq Kam murmushin Jin Dadi Yake Saboda ya tabbata Suhaila zata so shi!"ko Domin yawan Kallonsa da take cike da kunya idan sun hadou!"A Mota kawunsa nasiha Yake Masa sosai tare da tsara duk yadda za'a bullowa lamarin... Domin Mallam musa Sam baisan da batun fasa auren mansura ba!"yace dai asanarwa iyayenta duk abinda ke faruwa Don gaba!" "Hankalin Aliyu ya k'asa kwanciya Shiyasa ya kira wayar umman kano kusan sau uku ba'a Daga ba Nan ya Kira layin Umaimah shima shiru,kamar hadin Baki na Suhaila baya zuwa,Dole ya hakura har su karasa!" "Jiki Babu k'wari Yan uwan mansura suka bar kofar gidan,"Sauran mutanen gari sai magangannu sukeyi Akan Wannan auren da akayi Angon kwarai yace ya fasa,sai wani Mai guntun Wanda aka daura da shi. Lalle mansura ta ga isharar rayuwa Wasu ma gwai suke cewa Dan batada mutunci,"Kan kace me zance yabi gari,Dan duk mazan da suka hallara taron sun bazu acikin unguwar su na yayatawa nan wasu idan sunji suyi Karin gishiri su sanarwa wasu,"Nan da Nan gidan buki ya cika timjin da Yan sai mungani da Yan sa Ido,da wadanda Basu barin labari da Yan Allah ya Kara!" A hankali aka dinga gulma Ana dariya wasu na alhini acikin gidan,sai dai ba'a Samu wanda zai fadawa Uwar buki ba wato Halima da yaranta," "Nan yarou ya shigo Wai Ango na Sallama da Mansura," "Yaya fariza da sauri ta Kara feshe amarya da turare har wani fari da Ido ake koyawa mansura,bayan ta sauya Kaya, sannan Sahura ta rakata har falon gidan Ana Tafiya kamar za'a karye!" "Sai kallonta Mutane keyi wasu da suka San da labarin har dariya sukeyi!" "Lullube da mayafi ta Isa falon Sahura na biye da ita,abaya,Sahura CE tafara cin karou da su zazzaune Akan kujeru kusan su shidda ba Mai fitar arziki,tsaki tayi cike da tsiwa tace''ku KUma Daga Ina!?"Dan Allah ku bamu Wuri zamuyi baki!"Idan abinci kuke jira zansa yarou ya kawo maku Yan yunwa kawai ku jira a kofar gida....!!!" "A fusace Adams ya zabga Mata Mari!"tare da nunata da yatsa yace''ke banza Kinga munyi Miki Kama da Yan yunwa!?Yanzu Zanyi maganin iskancin ki!" "Mansura gabanta ya fad'i!"A hankali ta yane gyalenta...yayinda Sahura ta rike kuncenta tana huci!" "Tana kokarin mayarwa Adams da martani sai dai jin sautin muryar mansura arazane ya tsayar da ita!" "Mansura Tace Bimboy tare da Kallonsa Ido Cikin Ido,Shikam wani sonta da kaunarta ya ninku azuciyar SA!" "Yace Amarya mansura kenan,Kinga Allah yayi nine mijinki!"duk da kin yaudareni kinci kudina,wanda akarshe kinka gujeni har da boye min aurenki,To Kinga hukuncin Allah rabou ya ratsa sai me shi!NAGODE Allah da yasa na sani kafin a daura. ba Dan hotunan ku na aure da nagani a media Suna yawo ba da ba zan San Anyi ba...Inji Bimboy Yana murmushi Yana Kallon sahibar SA," "Wayar hannun Sahura CE ta subuce Mata ta Fadi kasa,Nan take ta tarwatse!" "Mansura kunnuwanta ta danne da hannayenta!"Cike da tashin hankali tace"Bimboy ka ajiye zancen wasa agefe Yanzu ba Wannan lokaci ba NE!"nasan na yaudareka Amma Kayi Hakuri! Shi lokaci baya jira saika jira nakan Yana zuwa,domin ka makarou Ni matar wani CE!"Dan Allah ku fita kada suzou su sameku!"ran mijina ya b'aci!"ka bani kwana biyu Zan biyaka duk kudaden ka da naci. "Dariya yayi tare da jifanta da wani mayen kallo...ya CE"Mansu Baby kenan wallahi nine mijinki da aka d'aura maki Aure da shi yanzun Nan,"Saboda Shima Wanda Zaki aura kin yaudare shi,yace ya fasa aurenki domin kece Silar rabashi da iyalinsa!....."Ni Kuma Daman nazo da shirina Ashe ke rabona CE sai aka d'aura Dani shima tsohon saurayin naki an daura nashi da wata Suhaila,"zancen biyana kudina Bai taso ba Dan Bana Zaki iya ba,sannan Wanda like tunanin ki shiga gidansa ki tande ya Zama mijin wata,Ni Nan nine zaki zauna tare Dani ba kowa ba. "Wani jiri ya dinga kwasar mansura!Hawaye ke Mata zuba tace "Sahura me hakan ke nufi!?"Da GASKE! ne?"kice min mafarki nake!?"Na Tashi da mugun baccin da nakeyi...." "Cikin karajin Kuka Sahura tace "kyaikayi ne ya Koma Kan mashekiya!!Mansura," kenan asirinki ya tono awurin Saddiq!" Amma Sam ban yarda da ya fasa aurenki ba!"Wad'annan tsamaye karya sukeyi!!!" "Adams ya jimke hannu ya Kaiwa Sahura Duka da sauri ta sunkuya k'asa yasha iska!"Yace"Da naso na samu jibgegen bakin nan naki da Kinga aiki!"Tunda bakinki da Sauran magana!Yar bakin CIKI.."To aure an daura da Bimboy kuje KU tambayi duk uban da zaku tambaya shine Ango!"Sai Hakuri kananan Yan bariki..." "Hannu mansura ta aza aka ta fashe da mahaukacin Kuka!"Da gudu ta kwasa Cikin gidan,tana Kai kofar Dakin mamansu ta Fadi kasa somammiya!"Cike da tashin hankali akayo kanta,Ana fifita!"da yayyafa mata ruwan Sanyi!!!" har ta farfadou!"Sahura ma Kuka takeyi,"Kowa ita ake tambaya meke faruwa!?"Sai dai shiru tayi domin ita Kam ba za'aji mutuwar sarki abakinta ba!" "Mansura na farfadouwa Cikin Kuka ta Tashi zaune kamar zautacciya!! da tashin hankali take Maganganu barkatai......da sambatu sai da Yaya Farida ta rufe Mata Baki Ganin ga Mutane, najin yadda take tonawa kanta Asiri!" "Kanen mahaifin ta ne,ya zo ya fara labarta masu komai,ba tare da ya rufe ko ya sakaya ba!"Daman can haushin su Yake!"da muguwar mahaifiyarsu da ta rabasu da Dan uwanka su,"Nan gidan buki ya koma na Kuka Saboda yayyan mansura da mamansu sun fashe da Kuka ga kunya!" "Cikin mintoci gidan buki ya watse!"Baban su mansura ya shigo gidan ransa ajagule yaqara warware masu komai!"Har cutar da Mansura ke dauke da ita ta HIV.," "Tashin hankalin Mansura ya karou Cikin Kuka!take rokon Babanta tare da cewa karya ne!?"Ita Kam lafiyanta qlaw,"idan Anyi musu atafie asibiti ayi gwaji,wallahi Bimboy kazafi yayi Mata!" "Daga Hajiya Halima har yayyenta kanta sukayo Saboda haushi sai jibgarta sukeyi suna zaginta,har bakinta ya fashe!"Domin ta Bata masu suna!"Yanzu shi kenan mazan su da mutanen duniya sunji komai!" "Tun mansura na iya Kuka har ta kasa,sai gunji ta ke Tashi...."Sahura ce ta kamata tana rarrashi!"Saboda kowa ya watse agidan har Sauran kawayen su!"Daga Dangi Sai Yan Ganin kwakwaf," "Baban mansura da ya fita waje NE ya shigo gidan,A fusace Yana Kiran sunan mamansu da karfi!"Fitowa Hajiya Halima tayi Daga Dakin ta Tana sharar kwallah!" "Yace"Ina son yarki ta hada Komai nata tabi mijinta!Domin nagaji da ganinsu akofar gidana nace su tafi sunce amarya suke jira!" "Haba Alhaji Tayaya hannunka zai rube ka yaaaar!"A gaskiya nikam zan kaita asibiti ayi mata gwaji!"Domin tabbatar da gaskiya lamari!"sannan Wannan auren baiyi ba!Tunda Bata Sonsa harfa Suma tayi!"Ai dole ya saketa....ko Yana so ko...Bayaso...Dan Ina son 'yahtah." "Cikin ikon Allah yau Allah ya baiwa Alhaji Sa'a da damar mayarwa matarsa da Yake tsorou kamar wuta amsa......"Da tsawa yace"Wallahi kinyi kadan Halima ba Ruwana aciki!"Tama mutu Mana aike CE da asara!"Yanzu basai anjuma ta shirya ta fitar mini Daga gida!"Tasan batason SA zatayi mu'amala da shi!"Meyasa Bata Kama kanta da mutuncinta ba!?"To Bari kiji Halima bakin aurenki matuk'ar mansura Bata bi mijinta ba...." "Ba Hajiya Halima ba!"Har yaranta sun razana!da zantukan MAHAIFIN su!"ganin yadda ya sauya harda Samun yancin surfa ruwan masifa!"Sun shiga tashin hankali Domin komai ya jagule." Juyawa yayi abinsa ya koma waje tare da baiwa mansura mintoci ta fitou tabar Masa Gidansa..." "Hannu mansura ta aza aka tana karajin Kuka!kamar ranta zai fita! Yayyenta ma sun tausaya Mata!Haka Hajiya Halima Kuka takeyi!Domin kasuwa ta watse ba uwa ba riba!" "Sahura ta tausayawa kawarta kwarai da gaske nan ta TAIMAKA mata Wurin parking din Kayanta Amma azuciyar mansura ta kudurta guduwa!"Tabar Bimboy Domin idan Yasan wata baisan wata ba!"Dole ta dauki fansa akan mugun kazafin da yayi Mata Domin wani tabou NE arayuwarta!"Kowa yanzu Yana Mata kallon Mai kanjamau. "A kofar gidan su sai sautin kida da waqoqi ke Tashi,"Wanda su Adams suka kunna amotocin su," "Sai rawa suke suna kwasar shoki,"A Cikin shigar su ta banza!"kofar gidan ta cika tinjim Ana kallon su Ango Bimboy ke chashewa da abokan shi a tsakar unguwa," ********** "Kusan mintoci da sakanni falon ya d'auka shiru ba motsin komai sai sautin fanka da ke Tashi!" "A hankali mallam BALARABE ya numfasa tare da cewa"Dukkan abinda ya faru ya faru NE,A matsayin kaddara!"Da son zuciya!"Ba abinda zance face duk mu hakura da komai ya wuce!"Hajiya kiyi Hakuri ki yafe Masa!" "Momy Tace"Yaya Zan yafe Masa Amma Ina da sharadi!?" "Meye sharadinki Khaltumi,!?"Hajiya Maryam ta tambaya," "Ajiyar zuciya tayi tare da cewa sai Idan jawad zai saki Nadiya!?" "A firgice ya dubi momy bakinsa na rawa Yana zubda kwallah!......da razana ya Kama kafafun Mallam BALARABE Yana cewa Dan Allah Baba ka baiwa momy Hakuri na tuba......" *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 _Tukuichi neh gareku masoyan TARBIYYA kuyi Hakuri na jina shiru nayi typing ina kokarin maku post sai ya goge!Wannan ma nayi ne Domin farinciki ku,Ayi hakuri da kurakure!Banyi edit ba😭_ *SHARE & COMMENTS* [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFA NA 41-45* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ _Sadaukarwa Ga:Nordin Ambrat Muhammad_ _Hassan & Hussein 80k_ _Usman Ango Da Dan kanen mu Prince Kamal No luv_ _"Ina godiya abisa namijin kokarin ku,gurin kai littafan mu a inda ya dace,Allah ya saka maku da alheransa ya baku matan Aure nagari,masu sadaukar da zuciyoyinsu gareku da zuciya daya,Ameen_" *BAA DA KUD'I KAWAI AKE SADAK'A BA,ZIKIRI, ADDU'A,MURMUSHI, FARA'AH DA ZUMUNCHI DA DUK AIKIN ALHERI SUMA SADAK'A NE* *A WURI BIYU NE AKE GANE KIRKINKA YIN HAK'URI IDAN KA RASA!DA BAYARWA IDAN KA SAMU😊* _Dunia makaranta👌🏻_ ______________________________________ "Abdul-Rahman(Bimboy) da Abokinsa Adams zaune adakinsa suna karyawa da Yake tun jiya da ya shigo kebbin inda Adams ya sauka!" "Alokacin da yazo cike da bacin rai yaso yaje ya Sami Mansura har inda ake event din,"Sai dai Adams ya dakatar da shi da kiran Mansura awaya da zuwa dinner din,"Nan dai suka shirya wani tuggu da zasu gabatar zuwa Anjuma,"Ko Yanzu yadda lamarin zai tafi NE suke Shiryawa suna dariya da shewa,"Dole ne su shayar da Mansura mamaki,zatasan ba irin su Yan iskan bariki,"Ake yaudara akwashe lafiya,"Domin duk Wanda yaci tuwo da su miya yasha," "Saddiq ya Tashi Cikin farinciki da mamakin Jalila,saboda Tunda Asuba ta Tashi da karatun kur'ani sautin muryarta tamkar balarabiya,ga Addu'oin da take jerawa da larabci,"A gaskiya ya samu nutsuwa sosai yadda matarsa ta canja,Ruwan wanka ta hada masa,Bayan ya kammala shiri, a falonta ya sameta ta had'a masu lafiyayyen Breakfast," "Bayan sun gama da misalin 11 na safe sai ga Umaima da Ali da yaran da Suhaila Cikin shiga ta Alfarma sun zo gidan kowa yayi kyau sosai," "Wani bugu zuciya ya riski!"Jalila!" ganin Yan buki sun fara zuwa,Shi kenan kishiya za'a kawo mata Kuma Mansura!" "Da kyar ta kanne kishinta!ta tarbesu," "Saddiq Cikin shiga ta Alfarma,ya fito daga Dakinsa,Ashe ma shi da Aliyu dinkin su iri Daya ne,kalar shaddar CE kawai ba daya ba!"Idan ka gansu zaka dauka Duk Angayen NE,"Sallama sukayi da matan Nasu sannan suka Kama hanyar Kebbi,"Saboda 2:30pm za'a daura auren," "Nan Umaima ta dinga baiwa Jalila Baki,Da kyar ta sake!"Nan itama ta dauki wanka na mutunci tayi kyau sosai,Gashi mutuniyarta suhaila ta tsara Mata simple makeup,"Su Anty Talatu da Rasheeda da Kanwar Hajiya Atika suka zo nan aka dinga had'a abinci,"Anci an sha har makota sun shigo,"Yanzu kam yan jeren Amarya kawai uwargida da tawagarta ke jira." ************Tun jiya da yamma,jawad da saif,sukaso tafiya sai yanzun da safe suka samu zuwa,"Sunje gidansu Nadiya nemanta,"Amma sun fahimci Malam Balarabe da Innerie Basu san komai akai ba!"Shiyasa jawad ya lankwashe murya Yana Kuka!sanarda iyayen nata karya da gaskiya ya yi inda akarshe Yake nuna masu nadiya ce batada gaskiya,rashin mutunci take Masa tun aure!Hakuri Yake Kar aji kansu,har zagin mahaifinsa tayi Tace idan ya cika dan halal ya saketa!Shine ya hasala!ya daketa!" Amma da momy tazou gidan laifinsa ta gani!"Har maruka ta sharara Masa!"Gashi har yanzun Taki ta saurare shi ta bashi dama ko bayani yayi Mata,Nadiya kawai ta saurara yanzu hakan ita kadai tasan a inda Nadiyar take shi ne ya zo ya fad'a masu! ," Malam Balarabe baiji Dadi ba!"yadda aure ko wata Daya ba'ayi ba!"Amma har matsala!tafara kunno Kai!"hakuri yaba Jawad!" "Itama Innerie hakurin ta bashi,Duk da tasan ba halayen Nadiya bane!"Sai dai in a kwalejin da tayi tasamo Wannan rashin mutuncin har take kokarin sauya halayenta na kirki,"Harda Hawayen Innerie akan bacin Rai!"Amma ta kudurta saita ci mutuncinta idan ta hadu da ita Dan ba dabi'un kallabin fulani bane. "Saif hakuri yake Bata!" "Amma sai masifa take tana Allah wadai da abinda Nadiya ke neman d'aukou masu wato abin Fadi a unguwa!" "Malam Balarabe yace" an juma da yamma kuzou KU dauke mu sai muje gidan Hajiyar taka Domin ta ba ka matarka ku koma gidanku tun Kan wani kunne yaji!"Ni kaina zata hadou da fushina saboda ta sauya daga yanda muka santa"Wannan ba Halayen da muka santa da su bane!" "Innerie kwafa tayi tare da cizon yatsa!Tace barni da ita Mallam zata gane kurenta!" "Jawad Dadi ne,ya mamaye shi Yace"Baba Nima Ina da nawa laifi saboda dukanta da nayi adaiyi Hakuri!"mu zamu koma sai mun dawo Anjuma," "Malam Balarabe yace"To Allah ya kyauta!sai kunzou mungode Allah yayi maku Albarka!" "Amin sukace sannan suka fita daga gidan," "Innerie mamakin Nadiya take hakama Malam Balarabe Amma akasan ran Innerie tana ganin kamar Nadiya bazata aikata abinda jawad ya Fadi ba!sai dai rayuwa da hali Kan canja akowanne lokaci!"Amma idan ta ganta zatasan meye gaskiyar lamarin," "Jawad jinsa yake wasai ko ba komai yadda ran momynsa ya sosu,na iyayen Nadiya ya b'aci,fatan sa Allah yasa kafin su saurari Momy su k'ara mazgarta idan ya Kai su gidan,daga baya su saurari ba'asi,"Shi kenan burinsa ya cika akarshe shi ashirye Yake da ya saketa!" Saif kam Bai baiwa abokinsa goyon baya ba!Akan kudurin shi, saboda shi Kam haduwarsa da Saudat yarinyar kirki,Mai hankali tayi kokarin canja Masa saitin rayuwa," *************** "Mansura Amarya yau ta tashi acikin farinciki,"yan wa da Abokan arziki duk sun Hallara,"Sai Fadi banza Fadi wofi ake!"Tuni aka loda kayan furnitures dinta amota da zarar angama d'aurin Auren za'a wuce jere," "Ta kosa agama d'aurin auren tayi ido biyu,da Angonta saddiq Daga Nan Labari zai canja," "Yan uwa da Abokan Arziki kowa sai hidima suke masu kidan kwarya sai kidi suke dangina na rawa da liki,"Amarya an Sha kyau da kawayenta acikin Ankon yunin buki,sai chasu suke Ana karkada jiki," "Hajiya Halima mahaifiyar mansura Baki har kunne sai murna take Domin Bata da buri irin taga yaranta sun auri masu hannu da shuni," "Macece Mai mugun son kud'in tsiya,Wanda kaf yaranta Mata shidda halinta suka dauko,Domin ta Riga da ta Gina su Akan turbar son Rai irin na ta,"Salon nata kula da yaranta kenan ita kuma,"Duk da mahaifin su Alhaji Yana bakin kokarinsa Wurin Basu rayuwa Mai kyau Amma Tuni Halima ta Shure burinsa,"Ta aza yaranta a Kan mizanin da take ganin shine dai-dai," "Anty Fauzi ita CE babbar Yayar su mansura,sai Farida da fariza,Zeenat,Rahma,"Mansura CE auta acikinsu,wato karama,Dukkan su yayyenta sunyi aure suna da Yara Wanda ayanzu hakan suke fad'a aji agidajen mazajen su,Kuma ba laifi ko wacce a gidan maikou take aure,"Wanda Tuni suka mallake mazan sai abinda sukace akayi,"kamar yadda mahaifiyarsu tafi karfin mahaifin su,"Shiyasa suka tAshi asake Basu da mafadi," "Duk Cikin gidan mansura CE,tafi dauko halayen mahaifiyar su Hajiya Halima tsaf,"Duk rashin mutuncin su iri daya ne Shiyasa Halima ke ji da ita. Ko yanzu rawar sukeyi ne tayi tsaye tana kallo cike da Jin Dad'i. "Amarya da yayyenta sai rakashewa suke Ana wasa da ruwan kudi Hajiya Halima ce sosai ta fadou tsakiyarsu ta dinga tikar rawa tana juyi su Kuma sai liki suke Mata. Nan suka burge Mutane sai shewa ake," aka dinga shagali,"Mansura tana Cikin rawa da juyi sai Jin tayi an fizgo hannunta," "Sahura ce,da hanzari!"Tace ke shashasha!"Anyi kusa daura auren kina nan kina rakashewa!''Muje a dauko maganin," "Murmushi Mansura tayi,Tace Ina sonki my Sahura saboda kina son farin cikina"NAGODE da kulawarki har na manta!" "Haba yiwa Kai ne mansura,daman nasan hidimar Nan zata mantar da ke. muje ki shafa ki murza ki goga abin!"Amma fa Mallam na Kan tudu,yace sau uku toh!"Dan karki garaje!"Inji Sahura tana murmushi." "Hmnnnn Ba zanyi ba!"Sahura..."Inji mansura "Uwar daki suka nufa,can mansura ta dauko d'aurin ledar,Nan ta fitou da tandou da wani kwalli ta dauko,"Sahura kallonta takeyi,"Tace kawaliyya ki samamin abinci yunwa nakeji in ci anan sai mu Koma fili," "Babu musu tace to ta nufi hanyar waje Domin nemawa amarya abincin,Nan mansura ta dinga shafa kwallin tana murzawa,"A maimakon ta shafa sau uku,kusan sau bakwai ta shafa,Wai yadda zata Gama da Saddiq da rayuwar SA Baki Daya," "Ko da Sahura ta dawo ta samu mansura har ta kammala ta mayarda kwallin,"Tafawa sukayi da Sahura Tace"Kawata shi kenan kin Gama da Saddiq da zarar Kun hada Ido magana, ta Kare!"Mallam ya bani tabbacin hakan kin san Kuma Aikin SA Kam yankan wuka ne nidai nayi imani da hakan yayi min yafi a Kirga Kuma yaci....Bari dai Zaki gani. "Dariya Sukayi har da shewa!"Mansura Tace"Sahura Allah ya kai A'i ga rogou,Daga shi saddiq din har shegun yaransa Zan gasa su!"Ni Zan rike Dan kishiya Hmnnnn tatsuniya CE, Wannan!"Kedai Zaki Sha kallo," "Sahura ta kalli mansura Tace karki ragawa kowa tawan!" Kedai kiyi kokari ki Tara Kaya!" Kuma sauran ki manta damu Dan ubanki!," "Na yadda kudi da hutu kan canja mutim su sa shi aikata komai,Amma ko Zan manta da kowa Banda ke Sahura saboda kinyi min halacci arayuwa!"Mansura Tace"Da yanayin sanyin murya," "Ajiyar zuciya sahura tayi tare da cewa ki ci abincin mu fita Kar anemeki,"Sannan ki zAuna da shiri nan da mintoci Zakiji sanarwa akofar Gida an daura aurenki," "Rungume ta mansura tayi tana fari da Ido,Tace"Na koshi Sahura kibar abincin Nan, farin Cikin da ke tattare a kalbina,ya b'atar min da Duk wata yunwa kedai muje aita sha'ani..."Ai ko Tun Daga Dakin suke tikar rawa mansura na gaba Sahura na biye da ita,"Har suka Isa filin rawar inda yayyen Amarya ke danshewa," *********** "Akai-akai tana yawan duba agogon da ke daure a tsintsiyar hannunta,"Cike da fargaba!"Lokaci take dubi ko an daura auren Saddiq,"Jim tayi a Bedrum dinta na Dan lokaci Bayan ta kammala sallar Azzahar,"Wasu Hawaye ke Mata zuba ahankali ta Daga hannunta sama tana roqon ubangiji Domin ya kareta daga sharrin shaid'an ya yi Mata maganin kishin da ke neman zame mata wahala arayuwarta!" "A hankali ta dafata Tace"Jalila Kuka!fa!?"Fuskarta dauke da damuwa!" "Dan zabura tayi tare da goge hawayenta,ta shafa Addu'arta, Sannan ta dubi Umaima wacce ta zuba mata Ido cike da tuhuma,"Tace Haka Kawai nasamu kaina da kukan batare da son zuciyata ba!"Amma kin San me!?"sai Naji Sanyi araina!" Tace cike da sanyin murya," "Yake tayi tace Jalila kenan nan,"komawa tayi bakin kofar Bedrum din,tare da sakawa kofar Dakin key,"Sannan ta dawo, kusa gareta ta zAuna suna fuskantar juna!" "Tace Ina son kibani aron kunnenki da hankalinki ki saurareni Kuma ki fahimceni!"Shawara Zan Baki ta karshe Akan dukkan lamarin Nan,"Fatana ki d'auketa,saboda Ni na daukeki amatsayin Yar uwata!" "Abu na farko shi NE, ki yadda da kaddarar ubangiji,"Ki karbi rayuwa aduk yadda zata zo maki,Ki dogara ga Allah,"Sannan ki sani Duk fa abinda Kika Gani arayuwarki tsarin ubangiji NE," "Kisani tun farko bakin kishinki shi ne ya rufe maki Ido,har ya kaiki ga Danasani,To ko yanzu sai kin shirya kin neme makaman yaki da shi," "Dole NE kiyi Hakuri,ki rufe idonki,da Duk abinda Zaki Gani agidan Nan saboda Yanzu komai zai canja!"Ba kamar da can baya ba ne!" "Sannan da Mansura da wata can daban Duk matsayin su daya awurinki kodai ki daukesu kishiya ko Abokiyar Zama,"InA son kisan cewa Duk kwarkwasar mansura sai kin Bata fuska zata rainaki!"Ki dauki girmanki da mutuncinki shi ne kin waye!"Sannan ki kula da tsafta,girki,kwalliya,da iya magana mai Dadi,ke dama Duk sauran abinda kikasan ya Dace kiyiwa mijinki dole sai kin dage. "Jalila...Sai fa kinsou zaki baiwa mansura makami da kofar sanin Waye mijinki, Domin ke kin Dade da sanin sa halinsa da rayuwarsa da Duk abubuwan da yakeso da sabanin hakan,"Ita Kuma Yanzu tasa kafa karatun acikin karatun rayuwarsa," kin ga ke kin Dade da wuceta akaratun bazata tab'a kamo kafarki ba!"Sai abinda kikaso kika sanarda ita sadaqa. "Amma fa Idan kinji Zaki iya,"Dan Haka Ina son ki cire komai aranki ki fuskanci rayuwar gidanki da yaranki,"Mansura ki d'auketa Abokiyar Zama, ba abokiyar gaba ba,Idan ta cutar da ke can baya Yanzu asirinta ya tono Allah ya bayyanata,Kuma ko Yanzu kin huce haushinta Domin kina zaune agidan da take ikirarin nata NE,Kuma ta fitar da ke, sannan zata zo taga abinda batayi zatou ba,wato ganin ki acikin gidan,Kinga Idan Allah nayi maka fad'a baka fad'a,"Gaki ga mijinki da yaranki,"To meye aibu ko abin bacin Rai,"Kudi fa ya zuba maki a dakunanki gana Fadan Kishiyarki da yabaki to meye matsala?!"Kiyi tunani Mana komai ake saddiq ya maki shi Jalila," "Ajiyar zuciya Jalila tayi cike da nazari ta Kara share hawayenta," "Abu na karshe da zan gaya miki, Jalila...Shine ki zage damtse akan *TARBIYYA* yaranki,"Domin *TARBIYYA* na farawa NE,Daga garemu iyaye,Haka Idan *TARBIYYA* ta lalace iyaye na da Nasu kamisho,Khairan ko sharran," "Ka da kizamou uwa mai son Kai,"Mai nunawa yaranta so da qauna,Kuma mai nuna b'acin Rai!"Akan Duk abinda za'ayiwa yaranki," "Kiyi kokari kibi hanyoyin da ake bi Wuri ladabtar da yaro tun tashin sa har zuwa girman sa saboda icce tun Yana danye ake tankwara shi,"Matakan gyaran ta Kuma sune, *TARBIYYA* Sanya Ido, kula da abokan su,da kuma Addu'ah," "Kizamo Mai lura da ilimin su,Addinin su da Duk wani motsi nasu," "A karshe Ina maki fatan alheri,sannan ba mansura ba!"Ko macce uku zai auro yau karki ji komai,Aranki ki shirya Yadda Zaki Zauna da su,"Iyakaci ki Kare martabarki da mutuncin ki agidanki...." "Nagode Umaima... Jalila ta katseta...,Tace in shaa Allah ayanzu Babu sauran fargaba ko tsoroun kishiya azuciyata ko wacce iri CE tazo ashirye nake!,Daga Yanzu na saki kowa na Kama Allah,zan zamou kainuwa dashen Allah awurin mijina da gidana,Nagode Allah yabar zumunci," "Ameen kin wuce hakan awurina,"Inji Umaima tana Murmushi..." "Jalila Tace"Yanzu muje Falo naji Anty Talatu na kirana, Bari na Kara gyara makeup Dina,na baza turare!"..."Umaima Tace" Kinga zuwa Anjuma kadan, sai ki Kira saddiq idan an daure sai mu sauya sabon wanka,"Fitowa falon sukayi suna dariya kowa su Yake kallo," ko da suka karasou Ashe kawayen Jalila ne mariya da ikilima suka zo yunin buki, Jalila tayi mamaki ganinsu matuqa,ko da yake ance gayyar sod'i ba gayyatar su ake ba,"Saboda ita Kam Jalila Tuni ta watsar da su Saboda ba qawayen kirki bane,"Batasan ma ko wa ya gayyatou su ikilima ba!''Hidimar aka cigaba da yi,"Yan uwa da Abokan arziki,"sai taya uwar Gida sarautar Mata Jalila murna tare da fatan zaman su zauna Lafiya a gidan," ********** "Tun sanda ya dauko su Baba Balarabe da Innerie gabansa ke fad'uwa har suka karasou kofar gidan,"Tsoroun sa,Kada momy ta tona masa Asiri,"Haka agefen na hannun damansa saif tsoron yakeji shima,"Innerie da Mallam Balarabe sun k'osa su ga fitowar Nadiyatu," ''Bayan Mai gadin ya wangale masu get din ne,suka kunno hancin motarsu izuwa mazaunin da aka tanadar Domin ta,"Fitowa sukayi nan suka wuce hanyar Babban falon gidan,"Jawad key yasa ya bude suka shiga,Wurin Zama ya baiwa iyayen Nasu,"Inno Mai aiki ya kwalawa Kira,Da sauri ta fito ta Fadi tana gaisuwa," "Jawad yace ki kawo masu abin Sha,sannan ki gayawa momy tana da Baki afalon Abba," "To,Inno Tace tare da Tashi da sauri, ta fadawa Hajiya sannan ta kawowa bakin abin motsa Baki da Ruwa,"cike da tray," "Saif Jiki ba kwari ya Tashi yana tsiyayawa su Baba lemun yabasu..." "Innerie da Mallam Balarabe sai kallon Gidan sukeyi,A zuciyar su,suna mamakin irin Wannan arzikin nasu Jawad Amma basa nunawa,"Sam Basu dauki kansu komai ba gasu da mutunci da sanin girman mutane" "Duk zatoun momy Alh.malami sambo ne yazo,Domin tayi waya da shi Yace suna hanya shi da matarsa Hajiya Maryam duba jikin Nadiya,"Sai dai tana shigowa taga su Jawad,da iyayen NADIYA, ne zaune akatafaren falon Abba" "Fuska asake ta tarbesu tana murna," ko kallon su Jawad batayi ba!" "Gaisawa momy takeyi da su Innerie,tana kokarin Zama,sai ga su Hajiya Maryam sun karasou nan falon ya karade da gaishe-gaishe," "Daga Jawad har Saif k'asa suka dawo da Zama,suna wani kame-kamen Jin kunya saboda sun san Dole Abba malami yayi fad'a Daga ganin su duba Jikin Nadiya suka zo," "Ay ko kamar Daga sama sukaji Mallam Balarabe Yana Korou bayani tare da ba momy Hakuri akan ta daina ganin laifin Jawad saboda yafi Nadiya gaskiya," "Murmushi Mai ciwo momy Tayi tare da kallon su Jawad din da suka sunne Kai, Sannan tace Mallam BALARABE duk abinda wad'annan gamammun hauru suka sanar maku babu Gaskiya aciki,"Amma Bari na kira Nadiya tazo kuji Daga gareta,nikam ba yadda banyi da ita ba!"Amma Taki Gaya min Komai da ya faru Bayan Wanda mukaje idonmu ya Gane mana...." "Inno....momy ke Kira...da sauri ta zo ta zube agabanta!" "Tace,Hajiya Gani," "Yawwa Inno kije Dakin Nadiya ki gaya mata tazo, sannan ki kawowa su Hajiya Maryam Wasu cups su sha, Ruwa," "To Hajiya, Inji Inno ta Tashi tana Kokarin fita,"Zuwa sashen momy," "Alh.malami sambo da Hajiya Maryam Sai faman mita suke yiwa jawad Akan rashin kyautawarsa Saboda duk abinda matarsa tayi Masa Bai kamata ya daketa ba!"Fad'a sukayi Masa sosai," "Nan dai ya sunne Kai Yana Basu Hakuri, Mallam BALARABE Kuma sai faman gyaran lamarin Yake,Innerie taji sauki aranta, duk da Nadiya ce batada gaskiya Amma Sam dukan baiyi ba Sam bataji Dad'i ba!" "Momy in Banda Harara da take zabga masu ba abinda takeyi!" "Jawad mamaki Yake yanda momy ta canja Masa duk kulawa da soyyayar da take nuna Masa,Amma Yanzu har takai ga zabga Masa Mari da Harara oh!Duniya kenan," "Shigowata Cikin falon ya katse Masa tunani,kallona Yake nakara fari sai dai na rame sosai,Sanye nake da katon hijab,Da siririyar muryata nayi Sallama,"Ido ya zuba min Tunda Yake arayuwarsa baitaba yimin kallo irin na hau ba!" "Wani Abu yaji aransa shin Tausayi NE ko Kuma Dadi ya k'asa ganewa Saboda yayi missing duk wasu hidimomi nata,"A Yanzu hakan gidan Nasu ganinsa Yake kamar kwafai,Amma yafi dangana abin da kalmar Nan ta sabou turken Wawa," "Ganin iyayena azaune naji Sanyi araina sauri nake domin nakarasa na gaisa da su," "Mamana sai kallona take cike da tausayi da kewata, agefe tana Jin haushin rashin mutuncin da Jawad yace na aikata Masa," "Baba Kam k'asa Hakuri yayi da sunkuyar da kansa,Dagowa yayi Domin ya dubeni,sai dai caraf......Idonsa yayi arba da wani tangamemen hoton da ke manne ajikin bangon falon,Wanda Yake FUSKANTA Daga Gabas din Dakin," "Da sauri ya Mike tsaye ya Kama hanya,Nikam na dauka Baba inda nake ya nufo,Ay da guduna na isa gareshi na Rungume shi Ina Hawaye!" "Sai dai hankalinsa baya Jikinsa,janyeni yayi Daga gareshi Tafiya Yake Idonsa tsaf akan hoton har ya karasa," "Bugun zuciyar momy ya karou!ganin inda surukin nata ya nufa!" "Jawad ma ya shiga tashin hankali!" "Shiru falon ya d'auka Babu Motsin komai,Ba tare da kowa yayi tsammani ba sai ganin faduwar Mallam Balarabe akayi yana dafe da zuciyarsa da ke mugun buga Masa,'' "Da gudu Dukkan su sukayo Kan SA Amma Ina Babu Numfashi,"Nan falon ya hargitse da hayaniya da Addu'oi,"Alh.malami da hanzari ya nufi fridge ya dauko Ruwa,Saboda matan duk sun rud'e,"Ruwan ake yayyafa Masa,Duk kowa yayi jigum nikam sai Kuka nakeyi,"Ni Nadiya da wane zanji arayuwata!"Rashin masoyin kirki!?ko kuma uba!?"Allah yayi min mafita!!!"ya agaza min," "Wurin Kam ya cika timjin da jama'ah kowa ya hallara,"Ango da iyayensa Kawai ake jira Wanda har Yanzu basu karasou ba!"Gashi saura mintoci goma Sha biyar lokacin dauri auren ya cika," "Bimboy da Amininsa Adams sun Sha wankan kananun Kaya,sunyi kyau sosai acikin shigar gayu masu wankan sukari,"Kusan Mota uku ya ciko da Yan iskan Abokan shi,"Maroka da makida sai aikin su sukeyi,"taron daurin aure yayi taro gwanin sha'awa. "Bayan Yan sakanni sai ga Mota D'aya kacal ta kunno Kai, A harabar kofar gidan,"Nan Marok'a ta mawaka sukayi dandazou da microphones dinsu suna fadin JAMA'A GA MAI GAYYA UBAN TARO ANGO YA QARASOU!!!" "Aliyu da Saddiq ne suka fito sai kanin Mallam Musa mahaifin Saddiq su uku NE,"Nan suka Isa wurin da aka tanadar Domin su," "Bimboy kallon abokansa yayi tare da masu inkiya da su karasa inda su Saddiq din suke!"Suna dariya da shewa suka isa rumfar inda liman da waliyyai suke zaune," "Mansura da Sahura Tunda sukaji shelar ango Abbakar Saddiq ya qarasou,suka dinga tikar rawa suna murna,sukam kakarsu ta kusa yanke saqa,"Nan mansura aka canja sabon salon Tafiya da murya,aka sauya tufafi domin zuwan Saddiq dinta kawai take jirah," *'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍* *LUV U OL MY FANS SHARE POST AND COMMENTS DAN ALLAH❤* [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 46-50* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ ❤❤ *SADAUKARWA GA KAKANNI NAH ABIN QAUNATAAH*❤❤ _HAJIYA FATYMA ADAMU DIKKO(FALGHA)_ _HAJIYA RAKKIYA ADAMU DIKKO(HAJIATAH)_ _HAJIYA ZAINAB MADAWAKI(TSOHUWA)_ _HAJIYA MARYAM MADAWAKI(MERI)_ _ALLAH YA SANYAWA RAYUWA ALBARKA, YA QARA NISAN KWANA KAKUS,ALLAH YASA AYI KARSHE MAI KYAU,ALLAH YA GAFARTAWA SAURAN MAGABATA,AMEEN.😍_ ______________________________________ "Bayan jama'a sun kammala, kowa yayi tsit!"Sai Sauraren liman da waliyyai ake,"Ana batun afara d'aurin auren ne,Malam Haliru kanen mahaifin Saddiq yayi ma liman wata magana asirrance,"Liman zaro ido!"yayi tare da rike Baki!"Nan ya fadawa waliyin mansura shima kanin mahaifinta ne,"Fuska ya hade tare da gyara zaman hullar sa!"Shima Juyawa yayi ya sanarda Sauran Yan uwansa da ke bayansa,Nan aka dinga zarar Ido Ana goge gumi!" "Saddiq da Ali wani tausayin su ya kama su,saboda agaskiya sunyi masu girshi!"Bai kamata su yanke hukunci ba!aranar aure!'' "Tattaunawa sukeyi har suka fahimci hankalin jama'ar Wurin ya fara dawowa kansu!''Sannan ne kanin baban mansura ya nemi a sasanta batun atufa Asiri, ayi auren nan ko Bayan auren ne isan ya so, shi Saddiq din ya saketa, tunda yace ya fasa aurenta saboda ita ce Silar KASHE Masa Aurensa da matarsa,"Hakuri sosai dangin mansura ke baiwa su Saddiq,"Mahaifinta har kwallah yayi!"Gwanin tausayi!" "Ali ya dubi Saddiq yace"Saddiq ko zaka hakura a daura!?" "Saddiq ya bude Baki ya bashi amsa kenan sai ga Bimboy da Adams sunzo sun zAuna," "Kowa su Yake kallo da mamaki saboda Babu alamun kunya a tare da su," "Adams ya ce,Tsoffi waye waliyin mansura anan!?"Cikin sigar rashin mutunci!" "Fidda Ido yayi waje!yace"Gani uban me Zan maku!?"Daga ina!?" "Dariya Bimboy yayi tare da tafawa da Adams," "Kudi Bimboy ya fitou da su aljihu yace"Dattijou Wannan naira dubu goma Sha biyar NE!" "Dubu biyar nagani Ina so(BAIKO)na da Mansura," "Dubu goma Kuma sadaki NE Yanzu Bai sai anjuma a daura Mana Aure!" "A zabure kawun Mansura ya tasowa su Bimboy Yana fad'a da su har da zaginsu,yana cewa KU Wad'an me marasa hankali da *TARBIYYA* ne,"A Ranar aurenta Ana batun daura aure zaku wani ce Kun kawo kud'in aurenta saboda KU marasa hankali...." "DakAta Mallam karfa ka manta KU Mutane ke saurare saura sakan talatin lokaci Yayi!"Ba sa'insa ya kawo mu ba,kaga tawagar mu can..."Adams ya nuna abokansu da ke zazzaune agefe Duk da kananan Kaya,"Ya ce"Ango karbi Wad'an nan takardun ka karanta!"Nasan Dole ka hakura da amaryarka Mansura ka barwa Mai rabo!" "Takardar Ali ya karba suka karanta shi da Saddiq," "Innalillahi Wa'Inna ilaihir Raju'un!!!"Shine abinda suke maimaitawa Alhamdulillah, Saddiq yace"Tare da mikawa Adams takardar....yace ko da abokinka bai zo ba,Kuma Banga Wannan takardar ba!Ayna fasa auren mansura!"Saboda ta cuceni!" "Murmushi Bimboy yayi yace mansura mayaudariya ce alqawarin aure NE atsakanin mu,Amma ta gujeni sai da naji labarin aurenta!" "Adams yace Kawu Wannan takardar da kuke gani ta asibiti CE,wacce da ta mansura da Abdul Rahman CE,wacce aka shaida masu da dadewa suna dauke da cutar HIV AIDS,"Kuma Wallahi idan ba'a daura auren Nan yanzu ba!"zamu amshi microphones mu shaidawa kowa meke faruwa!"tun farko har karshe!" "Dariyar iskanci Adams yayi yace"Shin Bimboy Zaki iya tuna iya adadin Cikin mansura!?" "To zan iya tuna wad'anda nike da masaniya akai kamar bakwai NE!"Inji Bimboy "Wata Dariyar Adams yayi inda maroki ya nufa ai da gudu kawun Mansura ya kwasa ya cafkoshi yace"tufa Mana Asiri Dan Nan......!!!!" "Asirinku atufe Yake Amma ayi a daura auren Nan,lokaci yayi,"nine waliyin Ango...Adams ya ce cike da Jin Dadi!"yadda Duk Yan uwan "Mahaifin mansura da yayansa sunkuyar da Kai sukayi Saboda kunya!"Kawun ta ko fifita Yake Saboda zufa!yace"Ai ga irinta Nan karshen rashin *TARBIYYA* kenan....ya dubi Yan uwansa da Cikin Jin haushi da takaici!"Yace"Yaya me kuke Ganin yadace!"Kun saddiq ya fasa auren!"Wad'annan kadagarun barikin zasu tona Mana Asiri wallahi...."Saboda basuda kunya "Ay tun Kan ya qarasa Adams ya Tashi Rai bace!"Ya karbi abin sanarwa ga wani maroki...hurawa Yayi sannan yace To jama'ah!!" "Nan dayan marokin yace"To jama'ah kowa ya SAURARA..." "Adams cike da Daga murya yace"Ango yace ya fasa!" "Azabure Wasu Mutane suka tAshi..suna kallon Adams Nan hayaniyar ta kaure!" "Marokin...yace"To fa Ana wata ga wata Wai Ango ya fasa!" "Adams yace Amma baza a fasa d'aurin auren ba!" "Marokin yace"kowa ya zauna KU kwantarda hankalinku rabo ya rantse sai Mai shi Domin take away bazai wuce mu ba!" "Nan Adams yace sai Abu na gaban da.... "kawun mansura NE ya rufewa Adams Baki ya jashi izuwa inda ake zaune Yana Hawaye!" "Suna Zama Liman yace ayi Salati,Nan aka fara gudanar da daurin Aure," "Mutane sai Rabin Ido suke da baza kunne Domin Cikin kowa ya cika fam da gulma,"Da mamaki da Al'ajabi......." "A hankali numfashin Mallam BALARABE ya dawo,"sanda ya bude Idonsa Ganin an kewaye shi yasa ya fara tunawa da abinda ke faruwa, "Jawad da saif tallafo shi sukayi zuwa babbar kujerar da ke falon,Har Yanzu Hawaye yakeyi Yana kallon hoton...!" "Innerie da Sauran jama'ar falon sai sannu suke faman jera Masa," "Inda take na zauna Ina kwallah!"Nace Baba lafiya meke faruwa!?" "All.malami sambo ruwa yaba Baba yasha kana yace"sannu Mallam ko Kasan Marigayi Husamaddin NE!?" "Wasu zafafan Hawaye suka zubowa Mallam BALARABE yace Cikin kunar rai hakika nasan shi!"farin sani kunga Wannan hoton....yace tare da nuna masu dayan hoton da ke manna ajikin bangon...farar kala NE,na Yara kanana uku,sai gudan na yaran su BIYU kamar Yaya da Kane,"Sai Kuma dayan na Babban mutim wato All.husamaddin Wanda yayi alokacin Yana Cikin ganiyar kudin SA gab da rasuwar SA," "Kowa hotunan ya duba..."sannan Mallam BALARABE yace"To Wannan hoton na Yara uku Ni da husama,da Aram ne," "Dukkan su shi suke kallo da mamaki... " "Muryar momy na rawa Tace Kar dai kace min Kaine Bello!?"Yayansa!" "Girgiza kansa Yayi yace nine Yayansa Bello....Hajiya nine...Yanzu Ashe Jawad jinana NE..."sannan kanena Husamaddin ya rasu!"kaicoh na dunia nayi kewar gida da dangina!"wani sabon Kuka Mallam BALARABE ya bude!" "Momy da Jawad ma Kuka suke!" "Nika Tuni na daskare Domin bakin CIKI Saboda banso makiyina ya Zama jinina ahlina da na Dade Ina son Gani!" "Alh.malami da Hajiya Maryam Alhamdulillah suketa faman nanatawa!" "Saif da Innarei sunji Dadi sosaisai hawayenta murna suke!" "Momy Tace"Wallahi Marigayi yaje da son ganinsa arayuwarsa,Nan dai momy ta labartawa Mallam BALARABE komai da tasani tun farko har karshe,"Tashi tayi ta dauko wata tsohowar ajiyar da marigayi mijinta yayi,ta kawowa Mallam BALARABE,"Tace"Wannan shine amanar da ya bani Kuma sirri CE,Daga Ni sai shi,yace min duk RANAR da Naga Bello na bashi..." "Jiki na rawa Mallam BALARABE ya bude akwatin,duk hotunan sune suna Dana iyayensu,har da tufafin Mallam BALARABE da ya Bari agida SUDAN, Alokacin da ya Gudu zuwa Nigeria," "Kuka sosai Mallam BALARABE keyi!!"Har ya Gama ganin kayan akarshe takardun kudaden SA ne,Wanda aka raba akai ba marigayi Husamaddin nashi da na Yayansa Bello Alokacin da mahaifiyarsu ta rasu,Wacce Yar kasuwa CE sosai, "Allah sarki Mallam BALARABE yayi Kuka shi da iyalansa sosai,saboda ya rasa uwa da kaninsa," "Momy Kam hankalinta ya kwanta yau ta sauke nauyin da ke kanta!"Tace"Yaya Bello sanadin nemanka marigayi ya dawo Nigeria har ya mutu anan,Kuma yaje da buri akanka!"ya shaida min watarana zamu hadou,Gashi dalilin Nadiya da jawad mun sameka!"saboda mun Sha nemanka,Rashin sani akace yafi duhu!"ashema muna gari Daya da KU..." "Goge hawayensa yayi yace"Allah ya jikan Oummu da Husama," "Ameen kowa yace"Sai share kwallan Tausayi suke!" "Jawad ya rarrafo tare da rike kafafun Mallam Balarabe yace Shi kenan ma cutar da kanwata!"jinina!"Daman ance idan zaka Gina...Ramin mugunta Gina karami..."Baba Gashi Ni na Gina ya farmin...na yaudare ku cutar da Nadiya..."Ashe jinana CE Wanda muka Sha wahala Ni da iyayenah Wurin nema," "Dan Allah Nadiya kiyi Hakuri ki yafe min....Jawad yace"Yana rusa Kuka!" "Mallam Balarabe yace"Ka DAINA Kuka!yarona komai ya wuce!"Kuma laifinta NE ba naka b....." "A'ah Baba Nadiya batada laifi mune masu laifi Ni da Abokina saidf min shirya mata gadar zare NE,KU Kuma mun yaudare ku duk adalilin rashin TARBIYYA"Nan jawad ya labartawa iyayensa komai tun haduwarsa da Nadiya,har had'a bakin da sukayi da M Bala yasa aka koreta!Daga makaranta,Da kuma zuwan da sukayi Wurin Mallam yunus suka aibata tah!"Ya ce ya fasa aurenta!"Da irin can mutunci da muzguna Mata da yayi har zuwa karshe dukan da yayi Mata....." "A hasale momy ta taso ta dinga zabga Masa Mari!"Ta ko'ina tana Kuka ta share shi!" "Da kyar aka banbari hannunta arigar Jawad da ta cumuimuye!Tace Wallahi sai ka saki Nadiya,"Kaje ga Saif Nan ya isheka rayuwa..Hakuri Hajiya Maryam da All.malami ke ba momy Amma sai surfa ruwan masifa take!" "Nikam jikin mamana na shige Ina rera Kuka!"Akan Jawad da saif sun cuceni Kuma sun Zama Silar rushewar karatuna ga sunana da suka b'ata!"Rarrashi na mama keyi tana share kwallah!!!" "Kukan momy yaja hankalin kowa afalon kalar tausayi...."Muryarta na rawa Cikin kunar rai!"Tace"Daman marigayi ya guje min hakan!"Gashin sanadin soyyayar da nake nunawa Jawad ya kaini ga Kuka!"TABBAS duk Wanda baiji Bari ba!"yaji hoho!" "Duk kulawa da soyyayar da nake nuna maka Jawad Ashe zaka yaudareni da karyan Labari,Ni kake yaudara!?"Ni kawayiwa karya!?" "Wato ka zabi aboki da shawarar SA akaina!?"Saboda baka gudun zuciyata!nice ke gudun zuciyar ka da bacin ranka!" "Na yarda na amince *TARBIYYA* ita kadai CE gatan da zaka yiwa yarou wataran ya taso Yasan gatane kayi Masa arayuwa........!"Kuka NE ya ci karfinta!"Hajiya Maryam Hakuri take bata!" "Alh.malami ya numfasa yace kiyi Hakuri Hajiya!"agaskiya Jawad Bai kyauta ba!"Kuma ya aikata komai saboda Yasan zaki tsaya Masa domin yadda kike Sonsa kike gudun fushinsa!" "Alhaji Wallahi Nima nayi mamakin yadda Allah yabani iko na tsawata Masa al'amarin Nan saboda Ni awurina komai Jawad yayi bana damuwa!"Wannan NE karou na farko da na nuna Masa bacin Raina,na tsawatarmasa!"Har na daurena Masa hukunci!"Abinda Abbansa ya kosa yaga nafara aikatawa...."momy Tace tana shafe hawayenta!" "Hajiya Maryam Tace"Yanzu day Kinga illar rashin *TARBIYYA* saboda Gashi Nan Danmu ya aikata!"Saboda kawai yayi abinda ba dai-dai ba!"Anyi subul da baka!"An kirashi da maras *TARBIYYA* shine yayi aure Domin ya Kara tabbatar Nadiya shi din da gaske maras *TARBIYYA* ne," "Sai Kuma akayi Dace ya hadou da aboki maras *TARBIYYA*"Daman Annabi (SAW)ya ce _"Kwatankwachin Wanda ke zaune da mutanen kirki,da maras kirki,kamar yadda kake zaune da mai turaren Almiski da mai zugazugi ne,Ko dai kaji kamshi ko kuma kaji kaurin wuta.,"_ "To Haka Zama da Abokin kirki da marar kirki Yake,Domin Kodai mutim ya Zama Mai *TARBIYYA*,Da kyawawan dabi'u ko Kuma sabanin hakan,"Allah ya sauwaka, Mallam Balarabe Kai da Fatima kuyi Hakuri da abinda danku ya aikatawa Yar mu,"Hajiya Maryam ta karashe zancen da damuwa!" "Bayan an kammala Salati waliyin Amarya mansura ya baiwa Adams waliyin Abdul-Rahman (Bimboy)Auren Mansura Akan sadaki naira dubu goma,Fatiha jama'a suka shafa!"Kowa na fadin ALBARKACHIN bakinsa,"Daga cikin gidan mansura ko kide-kiden da ake da raye-raye da hayaniya ya hana suji sautin sanarwar auren auren da Marok'a keyi awajen gidan," "Jiki Babu k'wari jama'ar Wurin ke kokarin tashi,yayin da Adams da Bimboy farinciki ne faal aransu Domin shirinsu ya tafi za Dadi," "Kamar Daga sama Saddiq ya karbi abin magana(microphone)"Ya ce jama'a Dan Allah kowa ya DakAta!"Nima AURENA za'a daura KU Sanya Albarka," "Nan kowa yayi cirko-cirko suna mamaki!"Lalle kalko ya koma sama,"Aliyu da mamaki yace"Aure fa Saddiq to da wa Kuma!?" "Hannun Ali ya Kama yace"Dan Allah ka taimakeni,Ina son na nunawa Jalila iyakarta!Idan na koma batare da aure ba!burinta zai cika na Lalle tafi karfin ayi Mata kishiya!duk da ayanzu nasan tayi laushi!"Amma Ina son na nunawa Mata masu ganin sunfi karfin ayi masu kishiya!"Karyar su Domin Allah ne, ya bamu ikon Karin auren ba su ba!"Inji Saddiq Cikin yanayin damuw!" "Ali yace Yanzu me kake so NE Saddiq!?" "Ina son kazama waliyin Suhaila kabani aurenta Wallahi Ina sonta Kuma tun Ranar da nafara ganin ta agidanka naji ta shiga Raina!"Zan baka naira dubu asirin na baikoh sannan Zan bada sadaki naira dubu Hamsin yanzun Nan,ga Kawu Nan waliyina..." "Numfashi Aliyu ya sauke yace"TABBAS Ni Mai bada auren Suhaila ne,Amma to bamu sani ba ko zata soka banason asamu garaje!"Kuma umman kano bata sani ba!"zan ba da auren Suhaila," "Saddiq yace"Aliyu na dauki alqawarin da zarar munue Suhaila Tace Bata Sona ko wata matsala ta kunno Kai ta gefenta ko danginta Wallahi Zan sauwake Mata!"Nidai Ina son burina ya cika na zamou Mai Mata!na koma gidanku a matsayin Ango,"Itama Jalila labarin mijinta ya taba aure Bayan ita ya zamou acikin tarihinta" "Da kyar da magiya Aliyu ya amince...Nan jama'a suka koma shafa fatihar auren Saddiq da Suhaila Akan sadaki naira dubu Hamsin,"Godiya sosai Saddiq yayiwa liman da jama'ar Wurin har iyayen mansura tare da labarta masu komai da Mansura tayi Masa,"Sannan akarshe Hakuri ya Basu,"Nan suka nufi motarsu Domin zuwa Argungu," "Amota ma Ali Sai tunanin yadda zata kaya yakeyi... Saddiq Kam murmushin Jin Dadi Yake Saboda ya tabbata Suhaila zata so shi!"ko Domin yawan Kallonsa da take cike da kunya idan sun hadou!"A Mota kawunsa nasiha Yake Masa sosai tare da tsara duk yadda za'a bullowa lamarin... Domin Mallam musa Sam baisan da batun fasa auren mansura ba!"yace dai asanarwa iyayenta duk abinda ke faruwa Domin gudun gaba!" "Hankalin Aliyu ya k'asa kwanciya Shiyasa ya kira wayar umman kano kusan sau uku ba'a Daga ba Nan ya Kira layin Umaimah shima shiru,kamar hadin Baki na Suhaila baya zuwa,Dole ya hakura har su karasa!" "Jiki Babu k'wari Yan uwan mansura suka bar kofar gidan,"Sauran mutanen gari sai magangannu sukeyi Akan Wannan auren da akayi Angon kwarai yace ya fasa,sai wani kirki aka daurawa Lalle mansura ta ga isharar rayuwa,"Kan kace me zance yabi gari,Domin suka namijin da yaji maganar ya saka Mai da yaji ya sanarwa wasu,"Nan da Nan gidan buki ya cika timjin da Yan sai mungani ga Ido,da Yan Allah ya Kara!"A hankali aka dinga gulma Ana dariya wasu na alhini acikin gidan,sai dai ba'a Samu wanda zai fadawa Uwar buki ba wato Halima da yaranta," "Nan yarou ya shigo Wai Ango na Sallama da Mansura," "Yaya fariza da sauri ta Kara feshe amarya da turare har wani fari da Ido ake koyawa mansura ta sauya Kaya, sannan Sahura ta rakata har falon gidan Ana Tafiya kamar za'a karye!" "Sai kallonta Mutane keyi wasu da suka San da labarin har dariya sukeyi!" "Lullube da mayafi ta Isa falon Sahura na biye da ita,abaya,Sahura CE tafara cin karou da su zazzaune Akan kujeru kusan su shidda ba Mai fitar arziki,tsaki tayi cike da tsiwa tace''ku KU Daga Ina!?"Dan Allah ku bamu Wuri zamuyi bako!"Idan abinci kuke jira zansa yarou ya kawo maku Yan yunwa....!!!" "A fusace Adams ya zabga Mata Mari!"tare da nunata da yatsa yace''ke banza Kinga munyi Miki Kama da Yan yunwa!?Yanzu Zanyi maganin iskancin ki!" "Mansura gabanta ya fad'i!"A hankali ta yane gyalenta...yayinda Sahura ta rike kuncenta tana huci!" "Tana kokarin mayarwa Adams da martani sai dai jin sautin muryar mansura arazane ya tsayar da ita!" "Mansura Tace Bimboy tare da Kallonsa Ido Cikin Ido,Shikam wani sonta da kaunarta ya ninku azuciyar SA!" "Yace Amarya mansura kenan,Kinga Allah yayi nine mijinki!"duk da kin yaudareni kinci kudina,wanda akarshe kinka gujeni har da boye min aurenki,To Kinga hukuncin Allah rabou ya ratsa sai me shi!"Inji Bimboy Yana murmushi Yana Kallon sahibar SA," "Wayar hannun Sahura CE ta subuce Mata ta Fadi kasa,Nan take ta tarwatse!" "Mansura kunnuwanta ta danne da hannayenta!"Cike da tashin hankali tace"Bimboy ka ajiye zancen wasa agefe Yanzu ba Wannan lokaci ba NE!"nasan na yaudareka Amma Kayi Hakuri! Shi lokaci baya jira saika jira nakan Yana zuwa,domin ka makarou Ni matar wani CE!"Dan Allah ku fita kada suzou su sameku!"ran mijina ya b'aci!" "Dariya yayi tare da jifanta da wani mayen kallo...ya CE"Mansu Baby kenan wallahi nine mijinki da aka d'aura maki Aure da shi yanzun Nan,"Saboda Shima Wanda Zaki aura kin yaudare shi,yace ya fasa aurenki domin kece Silar rabashi da iyalinsa!....."Ni Kuma Daman nazo da shirina Ashe ke rabona CE sai aka d'aura Dani shima tsohon saurayin naki an daura nashi da wata Suhaila," "Wani jiri ya dinga kwasar mansura!Hawaye ke Mata zuba tace "Sahura me hakan ke nufi!?"Da GASKE!?"kice min mafarki nake!?"Na Tashi da mugun baccin...." "Cikin karajin Kuka Sahura tace "kyaikayi ne ya Koma Kan mashekiya!!Mansura," kenan asirinki ya tono awurin Saddiq!" Amma Sam ban yarda da ya fasa aurenki ba!"Wad'annan tsamaye karya sukeyi!!!" "Adams ya jimke hannu ya Kaiwa Sahura Duka ta Duke k'asa yasha iska!"Yace"Da nasamu bakinki Kika aiki!"Tunda bakinki da Sauran magana!Yar bakin CIKI.."To aure an daura da Bimboy kuje KU tambayi duk uban da zaku tambaya shine Ango!"Sai sorry kananan Yan iskan...." "Hannu mansura ta aza aka ta fashe da mahaukacin Kuka!"Da gudu ta kwasa Cikin gidan,tana Kai kofar Dakin mamansu ta Fadi kasa somammiya!"Cike da tashin hankali akayo kanta,Ana fifita!"da yayyafa mata ruwan Sanyi!!!" har ta farfadou!"Sahura ma Kuka takeyi,"Kowa ita ke tambaya meke faruwa!?"Sai dai shiru tayi domin ita Kam ba za'aji mutuwar sarki abakinta ba!" "Mansura na farfadouwa Cikin Kuka ta Tashi zaune kamar zautacciya!!da bakinciki da tashin hankali take Magana,sai da Yaya Farida ta rufe Mata Baki Ganin ga Mutane, najin yadda take sambatu da tonawa kanta Asiri!" "Kanen mahaifin ta ne,ya zo ya fara labarta masu komai,ba tare da ya rufe ko ya sakaya ba!"Daman can haushin yaran marasa *TARBIYYA* Yake!"da muguwar mahaifiyarsu da ta rabasu da Dan uwanka su,"Nan gidan buki ya koma na Kuka Saboda yayyane mansura da mamansu Suma Kuka sukeyi!" "Cikin mintoci buki ya watse!"Baban su mansura ya shigo gidan ransa ajagula yaqara warware masu komai!"Har cutar da Mansura ke dauke da ita ta HIV.," "Tashin hankali Mansura ya karou Cikin Kuka!take rokon Babanta tare da cewa karya ne!?"Ita Kam lafiyanta qlaw,"idan Anyi musu atafie asibiti ayi gwaji,wallahi Bimboy kazafi yayi Mata!" "Daga Hajiya Halima har yayyenta kanta sukayo Saboda haushi sai jibgarta sukeyi suna zaginta,har bakinta ya fashe!"Domin ta Bata masu suna!"Yanzu shi kenan mazan su da mutanen duniya sunji komai!" "Tun mansura na iya Kuka har ta kasa,sai gunjin ta ke Tashi...."Sahura ce ta kamata tana rarrashi!"Saboda kowa ya watse agidan har Sauran kawayen su!"Daga Dangi Sai Yan Ganin kwakwaf," "Baban mansura NE ya shigo gidan,A fusace Yana Kiran sunan mamansu da karfi!"Fitowa Hajiya Halima tayi Daga Dakin ta Tana sharar kwallah!" "Yace"Ina son yarki ta hada Komai nata tabi marar *TARBIYYA* mijinta!Domin nagaji da ganinsu akofar gidana sunce amarya suke jira!" "Haba Alhaji Tayaya hannunka zai rube ka yaaaar!"A gaskiya nikam zan kaita asibiti ayi mata gwaji!"Domin tabbatar da gaskiya!"Wannan auren baiyi ba!Tunda Bata Sonsa harfa Suma tayi!"Dole ya saketa....ko Yana so ko...Bayaso..." "Cikin ikon Allah yau Allah ya baiwa Alhaji Sa'a da damar mayarwa matarsa da Yake tsorou kamar wuta amsa......"Da tsawa yace"Wallahi kinyi kadan Halima ba Ruwana aciki!"Tama mutu Mana aike CE da asara!"Yanzu basai anjuma ta shirya ta fitar min Daga gida!"Tasan batason SA zatayi mu'amala da shi!"Meyasa Bata Kama kanta da mutuncinta ba!?"To Bari kiji Halima bakin aurenki matuk'ar mansura Bata bi mijinta ba...." "Ba Hajiya Halima ba!"Har yaranta sun razana!da zantukan MAHAIFIN su!"Yadda ya ke surfa ruwan masifa!"Sun shiga tashin hankali,"Juyawa yayi abinsa ya koma wane tare da baiwa mansura mintoci ta fitou tabar Masa Gidansa..." "Hannu mansura ta aza aka tana karajin Kuka!kamar ranta zai fita! Yayyenta ma sun tausaya Mata!Haka Hajiya Halima Kuka takeyi!Domin kasuwa ta watse ba uwa ba riba!" "Sahura ta tausayawa kawarta kwarai da gaske nan ta TAIMAKA mata Wurin parking din Kayanta Amma azuciyar mansura ta kudurta guduwa!"Tabar Bimboy Domin idan Yasan wata baisan wata ba!"Dole ta dauki fansa akan mugun kazafin da yayi Mata a Domin wani tabou NE arayuwarta!" "A kofar gidan ko sai sautin kida da waqoqi ke Tashi,"Wanda su Adams suka kunna amotocin su," "Sai rawa suke suna kwasar shoki,"A Cikin shigar su ta banza!"kofar gidan ta cika tinjim Ana kallon su Adams da ango Binboy da ke chashewa a tsakar unguwa," "Kusan mintoci da sakanni falon ya d'auka shiru ba motsin komai sai sautin fanka da ke Tashi!" "A hankali mallam BALARABE ya numfasa tare da cewa"Dukkan abinda ya faru ya faru NE,A matsayin kaddara!"Da son zuciya!"Ba abinda zance face duk mu hakura da komai ya wuce!"Hajiya kiyi Hakuri ki yafe Masa!" "Momy Tace"Yaya Zan yafe Masa Amma Ina da sharadi!?" "Meye sharadinki Khaltumi,!?"Hajiya Maryam ta tambaya," "Ajiyar zuciya tayi tare da cewa sai Idan jawad zai saki Nadiya!?" "A firgice ya dubi momy bakinsa na rawa Yana zubda kwallah!......Arazane ya Kama kafafun Mallam BALARABE Yana cewa Dan Allah Baba ka baiwa momy Hakuri na tuba......" *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 _Tukuichi neh gareku masoyan TARBIYYA kuyi Hakuri na jina shiru nayi typing ina kokarin maku post sai ya goge!Wannan ma nayi ne Domin farinciki ku,Ayi hakuri da kurakure!Banyi edit ba😭_ *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *SHAFI NA 51-60 ___________________________________ "Cikin yardar ubangiji su Sadiq suka sauka Argungu Lafiya inda suka sami Yan uwa sun tarou agidan suna Taya gwaggo yunin Bukin,Suna ganin Ango sai tsokanarsa suke cike da Raha har da hotuna akayi cike da Jin dadi" "Bayan sun huta abinci suka ci Daga bisani Baba Haliru yayiwa Mallam Musa bayanin Komai yadda abin ya faru har da asirin mansura da Bimboy ya tona!"Da irin cutar da take dauke da ita," "Da farko Mallam Musa yaso ya ga laifin su, Amma Daga bisani da ya fahimci komai, Hamdala yayi tare da godewa ubangiji da Bai kaddari kaddara ta gittah!"Akayi auren ba!" "Godiya sosai yayiwa Aliyu sannan ya karbi Lambar wayar umman kano Acewarsa zai kirata ya Bata Hakuri Akan auren bazata!"Da akayiwa Suhaila," "A lokacin da Labarin auren ya zo kunnen gwaggo Murna tayi sosai tare da sanya Albarka,"Nasiha suka hada Baki dukkansu su kaima Sadiq Mai ratsa zuciya!"Akan adalci da rikon Amana,da Sauran Jan kunne," "Daga Nan kayan Mufeed da Mufeeda gwaggo ta had'a,da 'yan tarkacen kayan yaji da daddawa tace akai ma Jalila,"Yaran sai Murna sukeyi sun ga Abbansu," Gashi Kuma zasu ga mommyn su,"Da farin ciki suka Kama hanya,sai dai Aliyu Yana Jin nauyin yadda zai sanarwa Suhaila ya aurar da ita!"Agefe Kuma bai san yadda Umaimah da Umman kano zasu dubi abin ba!"Amma shi Kam baya da haufi ko kwankwantou akan dacewar Sadiq Domin namiji NE da Kowacce maccen kirki Mai Hankali ke burin mallaka," ************ "A gidan Jalila ko tun su na jiran shigowar Yan jere har suka debe Rai saboda yamma likis,tayi basu ba labarinsu," "Sha'anin su suka cigaba da gudanarwa da hidimomin su,"Umaimah tace Jalila ta sake sabon wanka, kwalliya Mai kyau Suhaila tayiwa Jalila ta tarbon Ango," "Duk da haka kawai taji yanayin jikinta ya sauya yayi sanyi lakwas ga faduwar gaba na damunta"Amma daurewa tayi ta Koma yiwa jalila kwalliya. Dan ta k'asa sukuni A daddafe! Dai"ta kammalawa Jalila light make-up,ta wuce dayan Bedrum din ta kwanta tare da fad'a masu kanta ke ciwo,A Lokacin da su ka tambayeta. Da sigar damuwa! Jalila ke faman jerawa suhaila sannu saboda tana son ta, Kuma ba komai ke burgeta da ita ba sai halayenta na kirki da nutsuwa. Magani da Ruwa Rasheeda ta kawo ma Suhaila Tasha ahankali wani bacci Mai nauyi ya dauketa!" "Umaima da Anty Talatu share gidan sukayi tsaf tare da gyara ko'ina turaren garwashi Dan maiduguri da na Tsintsiya akasa Nan gidan ya dauki kamshi,"Haka Uwar gida ran gida an Sha wankan less Dan Dubai sai zuba kamshi take kamar anyi barin humra ajikinta," "Yanzu Kam komai yayi tsaf, zaune suke Ana jiran zuwan Ango ko Ahlin Amarya,"Domin Uwar gida ta KASHE dauri Yana kallon kudu masu yamma,agefe Yana dubin Gabas maso Arewa,duk hanyar da aka bullou agidanta tana maraba," **********"Duk da Nasan Jawad ya aikata laifi Amma hukuncin sakin Nadiya ba shi NE maslaha ba!Wanda kike son d'auka khaltumi!"Inji Alh.malami Yana dubanta. "Hajiya Maryam Tace"Wannan gaskiya NE!Alhaji,"Dole Hakuri zamuyi Hajiya Kar arabasu!"tunda Abin ma tuwo na Mai na ne.Allah ne ya gadasu jini D'aya ko Dan sanadin su aka San juna ya kamata ki ajiye zancen sakin nan. "Momy Tace Haba ya kamata ku fahimce Ni Mana!Jawad ya zalunci yarinyar Nan, Daman na gaya Masa sai ya saketa! saboda Ba sonta Yake ba! auren manufa da huce haushi yayi!sannan burinsa ya cika ayayinda ita ya tarwatsa natan!to me yayi saura!?"sai ya sallameta Mana, Makaranta Zan sata tayi karatu Mai tsawo,!"Daman na fahimci itama Nadiyatu biyayya ce tasa ta karbe shi amatsayin Miji....!ba sonsa take ba hasalima hamayya ce a tsakanin su"Auren Biyayya tayi ba Auren so ba,ya kamata ai Mata adalci a Bata dama ta karshe Kar mu cutar da ita akan Wannan Dalili na jini D'aya.," "Wani Sanyi naji araina Alokacin da kunnuwana sukayi arba da zantukan mommy,"Share hawayena nayi tare da ajiyar zuciya," _Na yadda Idan Allah nayi maka fad'a baka fad'a_ "Alh.malami sambo yace agaskiya ba za'ayi hakan ba!kuskure dai Anyi shi Amma yanzu jini ya had'a Dole a hakura!"tayi karatun agidansa,"Wannan shi ne abinda ya Dace Hajiya khaltum. "Tayaya za'a hakura Alhaji!?"Dole NE atambayi ita Nadiyatu idan har tana sonsa da buqatar zaman aure da shi!"ko kuwa!?"Momy ta tambaya akufule saboda ta kawo iya wuya Domin tana son taga iya gudun ruwan Jawad Amma an hanata!" "Na fahimceki khaltumi Domin ciwon 'ya macce na 'ya macce NE!?"Hajiya Maryam Tace tare da dubina Tace"To Nadiya gareki...kinji abinda momynki Tace"Shin kina buqatar Zama da Jawad ko kuwa araba auren KU.....!?" "Dan Allah Nadiya kiyi Hakuri Wallahi Ina sonki!ke jinina CE!Kanwata karkice arabamu!"Bazan Kara wulaqanta ki ba!"Na yadda na amince Ni maras *TARBIYYA* kamar yadda Kika fad'a a baya. Wanda sanadin sa na cutar da ke. Amma kisani haduwata da ke ya canja min halayena da dama!"Har aka dinga kirana Mutumen kirki idan Kika barni zan Kara lalacewa ke alheri ce. "Nadiya ke haske ne arayuwata!"Dan Allah ki Soni, matukar kina son Marigayi Husamaddin ya samu labarin ganin jininsa, da mukayi akushewar sa to ki min rangwame. Akwai aure atsakanin mu Amma Momy naso ta rabamu karki Bari Dan Allah....."Na yadda na amince ki kirani da Koma meye har sai kin gaji Zan amsa..." kamar mahaukaci haka Jawad ke rokona Yana Hawaye!" "Saif wani Dadi yaji aransa tare da tausayin sa Amma fargabar SA Daya Kar Nadiyatu Tace "Bata son Jawad din!" "Hajiya Maryam Tace"ke muke saurare NADIYA....." "Hawayena na goge tare da kallon Babana da Mamana Nace Ni Banda abinda zance face abinda iyayena suka zartar dama can nabi umurnin su na yarda da aurensa!"Yanzu ma ashirye nake da daukar duk wani hukunci da suka yanke akaina!"Bazan gaji da masu biyayya ba!" "Hawayena na kara gogewa!Nace Mama......Baba na shirya amsar umurnin KU a Karo na biyu !nikam bani da zab'i sai naku....."Duk yadda kun ka zartar ashirye nake zanbi," "Innerie Tace"Haba Nadiyatu ai ke ce Zaki zAuna shi bamu ba!"Ki Fadi abinda kikeso saboda ayanzu kina da damar zabin abinda ranki ke so Domin gujewa Danasani! ta karashe zancen a Dan hasale!saboda ranta ya sosu da irin cin kashin da su Jawad sukayi min," "Duk Wanda ke falon ya fahimci inda zancenta ya dosa musamman momy da Jawad Amma Sam ba Wanda yaga laifinta!Domin D'a Cikin Rai Yake!Kuna duk Wanda aka cutarda nashi ba zaiji Dadi ba!" "Mallam BALARABE gyaran murya yayi, sannan yace NADIYA hakika mungode, da yarda da kuma amincewa da kikayi damu, da kuma zabin mu A baya!"Sannan muna Baki Hakuri da jajanta maki Akan Duk abinda ya faru!"Ina son ki manta da komai ya wuce duk abinda kinka samu ko Kika rasa!"hukuncin ubangiji NE!"Nasanki da kawaici da alkunya,Ina son ki Kara hakuri akarou na biyu!"Kibi umurni na,ki Koma gidan D'an uwanki Jawad," "A firgice na dubi Babana idona taf da kwalla!" "Mamana b'ata fuska tayi tare da Kara kumbura ta cika fam Dan haushi!"wato Mallam ya goyi Bayan dansa ita akashe Mata yarinya Lalle bazata sabou ba...." "Jawad wani Sanyi ya ziyarci kokon ransa ya washe baki...wani kallon so ya jefini da shi,"Bansan sanda na watsa Masa muguwar Harara ba!"tare da hade fuskata babu Alamar annuri atattare dani.!"kirjinsa ya buga...saboda shi Yanzu wani tsoron ta Yake da gudun bacin ranta!"Dole a lallaba Kar liqi ya kwance!" "Masha Allah,shi ne abinda Alh.malami, Hajiya Maryam da saifullahi ke ta nanatawa Cikin Jin dadi," "Momy Kam son tayi sai an gara Jawad yayi laushi sannan,Amma ko yanzu tana da dabarar da zatayi Wanda bazata koma da Wuri ba!"Sai ya gane shayi Ruwa NE,Domin kaunar da takewa Nadiya Daga Allah NE," "Mallam Balarabe yace nasan dalilin da yasa Nace ki Koma Nadiyatou,saboda Ni aganina abin kunya NE na raba aurenki da Dan Husama,ke da shi jini Daya NE!"Dukkan KU 'ya'yana ne,"Babu bambancin atsakanin KU....."Sannan Wannan hadin Allah ne ba namu ba!"Dan Haka ba abinda mukeso sai mu ga Kun zAuna lafiya,"Fatana Allah ya baku zaman lafiya da ZURIYA dayyaba...."Kamar yadda muka taso da Husama acikin soyyayar juna hakan nakeso zuriya ta da Tashi su kasance!"Hawayen Idonsa ya goge tare da kallon su yace kuyi hukuri da hukuncina nasan wasun KU basuji Dadi ba!"Amma nasan saboda Baku San Waye Bello da Husama bane,"BazAn manta rayuwata ta baya ba! *WAIWAYE* *ASALIN MU*"Ni da Husamaddin Yan kasar *SUDAN* ne, A garin Kharfum, muna zaune a unguwar Al-kubrih...sunan mahaifin mu Abu sufyan As-sultaan,Sai umman mu da ake kira Rajjah, "Mu shidda ne iyayen mu suka Haifa Aduniya; Ni Muhammad Bello nine na farko, sai Kanwata Awadiyah, sannan Husamaddin, da Sausal, da kuma wisam sai autar mu Abrar,"Daga Ni sai Husamaddin ne,maza awurin iyayen mu,Dukkan k'annai na baqaqe ne,sai dai Baki Mai haske irin na Yan asalin Sudan,sana'ar safarar Kaya shine sana'ar gidan mu,"muna dauko abinda babu Wannan kasar mu Kai Wannan kasar,"Umman mu ma sayarda zinarai da azulfa shine kasuwancin da tayi fice da shi agarin," "Tun muna Yara iyayen mu suka Gina rayuwar da ilimin Muhammadiya,"suna kula damu da Kuma *TARBIYYAR* mu sosai," "A lokacin bamu wani damu da ilimin boko ba, Shiyasa kannaina Mata na tasawa akayi masu aure ya saura Daga Ni sai Husamaddin," "Tun da Husama ya Zama saurayi ya nuna Yana son karatun boko, Wanda da kyar Assultaan ya amince ya turashi Bahri karatu...."Ni dama ban damu da son karatun boko ba!"Nan na Cigaba da Zama Ina taya Assultaan kasuwancin sa,"Da maman mu Rajjah,Ina Cigaba da neman ilimin Addini. "Ana Cikin hakan naji Ina sha'awar siyasa a lokacin Ina matashi, Kuma Mai ilimi da dukiya. Kasancewar duk Wanda yasan kasar SUDAN to Yasan yadda Muke ba siyasa muhimmanci fiye da komai arayuwar kasar mu. Bamu damu da sarauta ba, kamar yadda Muke Jin mulkin gwamnati ajinin mu,"Ganin matasa na Sona Kuma Ina da ilimin addini kwarai da gaske Daman can harshen mu na larabci da shi Muke tafiyar da komai," "Shiyasa matasan suka Goya min baya dalilin taimakon da nake masu,suka ingiza Ni na fitou takara,A lokacin da Assultaan yaji hankalin SA ya Tashi Domin sanin kowa ne Akan siyasa Ina iya rasa rayuwata!"makiya zasuga bayana,Shiyasa yace ba Zanyi ba!"Ni Kuma Alokacin nasa siyasar araina ga alqawarin da na daukarwa matasa Akan Zan tsaya musu!" "Tunda Naga iyayena da dangina Duka basa son inyi siyasar,Domin Dukkan su sunfi mayarda hankali Akan nazou nayi aure Duka tsarana sunyi Banda Ni," "Wannan NE Dalilin komawata garin Ubayyid da Zama Nan na fitou siyasa Cikin ikon Allah na ci,Bayan gwagwarmayar da Nasha da mahassada,"Shekarata Daya Cikin ta biyu da mulki Amma ban samu na shirya da Iyayena ba!"saboda suna fushi da Ni,"Da taimakon Husamaddin suka yafe min na koma rayuwa da su lafiya. Ina taimakon su Domin Arziki na ya karou,"Ina Shirin auren Yar Kanwar Assultaan Mai suna Ritaj,"Sai ga iftila'i ciwo ya sameni Wanda ake zargin Yan siyasa NE suka jefeni,"Iyayena da dangina sun shiga damuwa musamman kanena Daya tal namiji wato Husamaddin Wanda nake matukar so arayuwata......Hawaye Mallam BALARABE ya share tare da cigaba da labarinsa...." "Yace tun lokacin da na kamu da cutar da ba'asan maganinta ba sai dai Addu'a,"Farin Cikin gidan mu ya ragu!"Ana hakan mahaifin mu ya rasu..."Duk gadon da yabar Mana Wurin neman magani na ya Kare kanin ma afinmu Mai Suna tajjudin ya zame Mana uba..."Watarana Ina kwance naji kamar an tsakurene da allura...wani karfi naji ajikina da sauri nabar gidan,Daga can filin jirgi na nufa da Duk sauran kudaden da nake da su,Kwana uku Ranar na Hudu na Sami biza nabar SUDAN zuwa Nigeria saboda na tsani k'asata da komai dake cikinta,"Tun lokacin na dawo Nan da Zama,Wanda Zamana a Nigeria Zama NE na wuya da azaba,saboda bansan kowa ba!"babu Mai taimako na! da kyar na shigo Nan Kebbi na dinga sana'oi da dama har Naga sayarda gwanjou yafi amsata,"Wanda silarsa na hadou da Yayan Fatyma(Innerie)shine ya taimakeni!Har aka warware asirin kurciya da akai min!"Daga nan sai samu lafiya,"Wanda akarshe ya had'ani da Innerie,wanda har Yanzu Muke rayuwa anan Argungu"Bayan mun dauki tsawon shekaru Babu haihuwa Daga baya ne Allah ya bamu Nadiyatu," "Ban taba Jin son kasata ba!Daga Ranar da na barouta sai yau,Saboda na Riga na fidda Ran da komawa can,Domin banida kudin da zanje Ni da iyalina,"Amma ayau da Naga hoton Dan uwana abin kaunata jininah kanena Husamaddin naji komai ya dawo min sabo!"Allah sarki!Ashe shima sanadin nemana ya dawo Nigeria da Zama har da iyali ya samu!!!!! Har Rai!yayi halinsa....Kaicoh rayuwa....Bansan ya kannaina Mata da dangina suke ba!"Allah ya jikan ka Husama Kai da iyayenmu Allah ya yafe maku,.....Kuka yakeyi Alh.malami NE Mai dauriyar bashi Hakuri saboda Duk falon kowa Kukan Yake saboda Tausayi!!!" _Illar rashin bin umurnin iyaye kenan Wanda kesa Dana sani_ *CIGABAN LABARI....* "Duban mu Baba yayi,"Sannan yace"Yanzu idan na amince aka raba auren Nan, kuna ganin nayi ma Husama da sauran kannaina Adalci kenan!?...."Gashi Ni ko da nabar kasata SUDAN Mahaifiya ta na Raye!"Yanzu Kuma itama ta mutu!"Tunda ga gadona Nan da Husama ya ajiye min...."Da Sauran tsabar kudin mu,Amma Duk da hakan baisa ya KASHE su,ko ya banzatar da su ba!"saboda kaunata da Amanar da Yake da,"Nadiya kiyi Hakuri babu rabuwa har abada ke da D'ana Jawad," "Kai Kuma Jawad Karka sake kuskure irin Wannan shi lamarin aure daraja NE da shi, Kuma ba abin wasa bane! bare adauki fansa da shi!"Ga matar ka nan idan ta shirya sai KU koma gidanku,"Bana son Jin kowanne korafi ta kowanne fanni Dan Allah komai ya Wuce..."Inji Mallam Balarabe wanda muryar SA tayi Sanyi..." "Murya araunane.... Innerie Tace"Nadiya Kibi mijinki ki Masa ladabi da biyayya kamar yadda Kika SA ba!"Nasan ki da halayen kirki to ki Cigaba biyayyar aure Allah Yana tare da ke..." "Hawayen Jawad suka gangarou a fuskar SA yace"Nagode Allah ya bamu ikon muku biyayya iyayena, Daga Yanzu Zan koyi halayen da dabiu na gari awurin matata Nadiya..." "Saifullahi ma kwallah yayi tare da neman gafarar Nadiya da momy da su Mallam Balarabe Akan duk abinda suka aikata," "Momy cewa tayi ta yafe masu Allah yayi masu Albarka sai dai Tace"Har Yanzu Nadiya bataji sauki ba,anan gidan zata Cigaba da Zama har ta warke sosai,"sannan Jawad yayi biko a wajenta Nadiya sannan zata koma," "A hakan kowa ya hakura, Ana dariyar mommy, Alh.malami da Hajiya Maryam sunyi farin Cikin yadda lamarin yazou da sauqi, Sallama sukayi masu suka wuce, Mallam Balarabe da Innerie kokarin Tafiya suke Suma,Amma fafur mommy da Jawad suka Hanasu Tafiya tare da rokonsu da magiya Akan su dawo da Zama Cikin gidan,"A sashen Jawad da ya Tashi saboda komai akwai aciki part NE Mai zaman kansa agidan,"A cewar momy gidan yayi Mata girma ita kadai tun da shi ya yi aure," "Ba Domin Mallam Balarabe ya so ba Haka ya amince Innerie Kam Dadi taji matuka,sai dai tana kewar kawayenta na tudun wada," "Dukkan su suka dunguma acikin motoci suka nufi unguwar domin Sallama da mutane da Sauran makota,"Nan suka kwasou Yan kayan da suke so na buqata,wasu Kuma akai kyauta wasu Kam zubarwa akayi,"Mallam Musa yaji Dadi matuka Alokacin yaji Amininsa ya ga jininsa da Kuma irin daular da Zaiyi rayuwa aciki,Ashe Daman shi ba karamin mutum bane,Mai arziki NE kuma Dan masu arziki,rayuwace ta mayarda shi goro ko abin saye!Talauci yayi Masa d'aurin Magi dunia kenan!"Nan shima dai Mallam Musa ya labartawa Mallam Balarabe duk abinda ke faruwa har dukanda Jalila ta lakadawa Nadiya aka Kaita asibiti da irin tuggun da Mansura ta had'a agidan Sadiq..."A karshe Hakuri ya baiwa Innerie da Nadiya wacce kamar Ruwa ya cita,"Domin bataso atada zancen ba!" _(Sai Hakuri Nadiya domin shi zancen dunia Baya boyuwa!"Ko acikin k'asa Kayi ka turbude Wataran zai taso,Muyi KOKARI mu shuka hairan,ko don mu girbi abin kirki gaba")_ "Malam Balarabe yayi mamaki, saboda su dai Basu San komai ba!"Domin ban fasa Kwan ba.."Nan dai aka dinga yabona da irin Hakuri na, Albarka suka samin tare da mana fatan alheri Ni da Jawad,"Daga muka tattara harda kawata saudat Cikin Yan rakiyarmu sai gidan Marigayi Husamaddin kanin mahaifina Mallam Bello Wanda akafi sani da BALARABE," "An gyara sashen da su mama zasu zAuna Sarai, Daman can komai sabo NE aciki Dan Ba'a Dade da canjawa Jawad kayan furnitures ba akai auren mu,"Naji Dadi Sosai yadda iyayena zasu zAuna acikin Daula mussamman Mamana da Bata taba rayuwa irin Wannan ba,"Domin su a ruggar su a Cikin bukkoki NE suke rayuwa Kuma adaji suka Saba Zama,'' "Jawad da saif sun ji Dadi sosai, Hankalin su ya kwanta Domin Nadiyatu Bata subuce masu,"inda Mallam yunus ke Zama sukaje suka sameshi, tare da yimasa bayanin sune suka kawo Masa sukar Nadiya A baya,"gaskiya suka fad'a Masa Akan kazafi NE,sukai Mata Dan kawai ya daina sonta,Dan Allah yayi Hakuri," "Wa'azi Mallam yunus yayi ma su Jawad,Akan suji tsorou Allah su daina irin Wannan halin Domin sun sun tsunduma shi a bak'in yanayi!"Akarshe fatan shiriya yayi masu, yace ba komai shi Yanzu ma da Aurensa ya yafe masu,"Wucewa sukayi tare da mashi Godiya," shi Kuma Cikin gidan SA ya shige inda Uwar gida ran gida Badi'atu (Maman Islama)" "Tana Tafiya tana Jan trolley dinta!In Banda Hawaye Babu abinda ke Mata zuba!"Mahaifiyarsu k'asa Mata rakiya tayi,Su Yaya Farida NE biye da ita suna share kwallah!tare da Bata baki!"Akan zasu nemi Mafita tayi Hakuri!"Sahura Sauran Kayan ta kinkimou zuwa waje!" "Har Yanzu chasu sukeyi akofar gidan,mutanen unguwa sai Kallon su suke, mansura hijab tasa har k'asa da nikaf a fuskarta suna fitowa waje aka sa kuwwa da shewa....tare da Kara sautin Waqa Nan Suka KASHE rawa Wai ga amaryar su mansura baby ta fitou,"Motocin dama abude suke Adams ya dinga jera kayan akwatu nan,"Sannan yace Ina Yan Kai Amarya!?"Sahura Tace Ni kadai CE Zan Mata rakiya...murya adisashe!" "Ko ajikinsa ya nuna...tare da buga kafarsa ya shura!yace wato ga alama amaryar Bata da dangi,ko Kuma tsabar bakin ciki NE oho!!in Banda bakin ciki da rainin wayo ko Yar tsana ce ai Ana hadata da abin kwarai su Mata rakiya!" "Ya dubi abokansu yace"Kai KU shige Muje Ina ma direban Nan na motar Kaya!?"Ya Banga Dan iska ba!?Ina ya tafi NE!? "Nezy boy yace Mai gida munyi ma direban bayani harda hankali munyi ma shi,"Kuma mun hada shi da Dan iska su tafi tare..."ya Kai shi har gidan oga Bimboy idan sun shiga sokoto!?" "Yaya Farida afusace Tace Wai KU Wad'an me irin marasa *TARBIYYA* NE to da izinin wa Kuka tura motar kayan Amarya!"To Wallahi idan dukiyar mu tayi ciwon Kai zaku sani!wa ya sani koma KU barayi ne....! "Ke malama rufe min akwatin bakinki,Koh Yanzu lahira tayi bakuwa! in KASHE in Kashi banza!"mu Zaki Kira da barayi to uban KU shine barawon!saboda shi Yace direban ya tafi tare da mu akai hegun tsoffin furnitures dinku!"Duka nawa ma NE suke matsiyaciya!?" da har Zaki Mana rashin mutunci akan gwanjoun Kaya!"To kije ki tambaya gidan rashin mutunci kika zo!" Domin Ni Adams nina yankewa iskanci cibiya...."Tsaki yayi Yana kokarin tafiyarsa...." "Farida Tace"Anyi asara hegu!"Idan Kun zalunci Yar uwarmu ku da Allah....." "A hasale!Adams ya waigo tare da KASHE Yaya Farida da wawan Mari!"Yace Ina raga Miki NE Saboda Mansura!"sannan ya wuce Nan kowa ya shiga Mota suka tafi abin su suna sauraren kide-kiden su,"Mansura Kuka take Mai tsuma zuciya!" "Su yaya fariza sun Sha mamaki musamman Farida da aka watsawa Mari!"Haka suka shiga gida Jiki ba kwari, suka Sami mahaifiyarsu da ke alhini,"Kokarin tattara komai Nasu sukayi, Domin Kowacce ta koma gidanta, domin zaman Jin haushi da bakin ciki, NE ZASUYI idan sun tsaya!"Ga Babansu ya canja sai Dan ya samu bakin masifa" "Bimboy wani so da kaunar mansura ya Kara shiga zuciyarsa aduk lokacin da ya dubeta sai kaunarta ta karu ta narke acikin jininsa. Ya dauki Alqawari ko da zai rasa rayuwarsa ba zai iya rabuwa da Mansura ba!"Adams yayi laushi saboda shifa tsiwar Sahura na burgeshi amota ma Sai janta da Fira yake amma tayi Masa banza saboda haushin marinta da yayi d'azu!" "Farin Cikin su mufeeda ya karou Alokacin da mudi Mai gadi ya wangale masu get,Murna suke har tumami amotar, da sauri suka fitou sanda motar ta tsaya!" "Daga kofar falon Salim da Salima suka fito da gudun su, suna tarboun Mufeeda da Mufeed da iyayensu,"Cikin falon suka shiga cike Jin Dadi,"Yaran sunji dadin ganin sabon gidan nasu Mai kyau da tsari," "Suna shiga sukayi arba da Mommyn su ai da gudu suka fad'a jikinta suna murna....ita Kam Jalila harda hawayenta saboda murnar ganin gudan jikinta!" _Ayanzu kam Tayi nadamar barin gidan mijinta da yaranta_ "Umaima da Anty Talatu sai da idonsu suka canja launi,Akan tausayinsu...."Sallamar mu Saddiq CE ta katse hayaniyar da ake," "Maraba Umaima tayi musu ita da Jalila,suna Zolayar su da An gaida Ango da baran Ango"Gaban Ali ya buga baima San ta Ina zasu fara ba!" "Sai yanzu Sadiq yaji wata fargaba ta darsu azuciyar SA,ya raba idonsa afalon sai dai ba Suhaila ba alamarta!" "Anty Talatu da Rasheeda fatan alheri suka yiwa Sadiq din suna kokarin Tafiya....."Sai dai Aliyu cewa yayi Anty Talatu ki tsaya!A warware komai agabanki Domin wasu matsaloli sun kunno Kai ba'a daura auren da Mansura ba!" "Wani Sanyi Jalila taji Azuciyarta Alhamdulillah ta fad'i tana Murmushi Wanda batasan ya fitou fili ba.." "Meke faruwa aka fasa auren!? Umaima ta jefi Ali da Tambaya..." "An daura auren Saddiq sai dai ba da Mansura ba Akan wasu dalilai!"kuyi Hakuri da abinda zAkuji da Suhaila aka d'aura auren....Inji Ali," "Wani kallo Umaima ta watsa masu tare da Tashi tsaye!"Tace Abban salim shin Wace Suhaila!?" "Suhaila dai tamu kanwarki nine na baiwa baba Haliru kawun Sadiq aurenta Kinga kudin baiko da sadaki da Abokina kuma yayanta Sadiq ya biya!" "Jalila ma tsaye ta Tashi da mamaki suka dubi juna ita da Umaimah tare da kallon Damen kudin da Ali ya ajiye agaban Umaima," "Anty Talatu da Rasheeda Dadi sukaji saboda Suhaila tafi mansura nesa ba kusa ba!" "Suhaila Daga bedrum din da take kwance ta dinga jiyo muryoyinsu ahankali ta fito ganin kowa ita Yake kallo yasa ta Dan razana....Da sauri Umaima ta kamouta Tace Suhaila shin gaske NE ko wasa Wai Aliyu ya aurar da ke ga Saddiq batare da sanin mu ba!" "A firgice Tace aure kuma!?"Ni Suhaila akai ma aure!?"Anty da gaske!?"Yaya Saddiq NE mijina...!?" "Eh da gaske NE Suhaila Inji Ali da sanyin murya.. " "Suuuuuuuu.....Suhaila tayi sai ajikin yayarta ta some!"Hankalin kowa ya Tashi afalon kokarin zuba Mata Ruwa ake," Umaima kaam har da kukanta saboda tashin hankali!...." *'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍 _Acigaba da Gashi fans, suya sai Ranar sallah, comments dinku na sakani nishadi, Kuma Yana Kara min fetur Wurin sambadou maku post, NAGODE da Addu'oin KU Alhmdllh...na samu sauki,Kusani Anatare Ni da KU masoyanah, na ciki da wajen Nigeria,"iya wuya muna tare, sai nazou kawo ziyarata Domin ku mutan Niger,Ghana,Gabon, Cameron,da Sudan Amma kune Zaku biya min biza😍😝NAGODE DA K'AUNAR KU_ [2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲 *NA* *NABEELA DIKKO* *PEN WRITERS ASSOCIATION* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 _ALHAMDULILLAH....._ ______________________________________ "Gidan da Bimboy da ya saya ba laifi domin,"Da dadewa tun Yana cikin ganiyar KASHE kudin gadon SA,ya sayi wannan gidan, daki biyu ne da Falo sai Kichen da bayi," "Ko da suka karaso gidan, su Dan iska sun share gidan tatas,Har sun zuba kayan furnitures sun jera kamar Mata,"Bayan sun gama suka sallami direban ya wuce," "Sahura ta dan ji dadin Ganin gidan Saboda Yana da damar SA,"Kallon yadda aka aza gadajen da kujeru tayi sunyi kyau sosai,sai dai babu fenti da tails,An dai shafe ciki da wajen gidan da sumunti,"Mansura Kuka take kamar ranta zai fita,sanda ta gama kallon ko'ina na gidan, dan burinta ya wuce rayuwa a irin wannan gida,Dan ita tasawa sabon gidan Sadiq rai Dan kuwa sunje zagaya gidan yafi a kirga.mafarkinta ta rayu agidan daula karyarta ta karu Amma Wai karshenta Nan gidan....Inaaa bazata sab'ou ba Kuka ta dinga rerawa tana toshe bakinta da mayafi...Sahura Hakuri take Bata Amma Taki tayi shiru.," "Duk mutan unguwar Gwuiwa sunji dadin auren na Bimboy,domin zasu samu sassauci Dan ko Yana cikin manyan shaidanun unguwar Masu Tara Yan Mata da samari. "Abin ci da drinks Dan iska ya kawowa sahura,"Yace Ranki ya Dade ga abinci inji oga Adams kuci ku koshi ke da amarya sai ke ki fitou mun Tashi komawa za'a saukeki Kebbi," "Sahura yunwa takeji Haka ma mansura na buqatar abincin,Shiyasa ta karbi abinci,"Tana zabgawa Dan iska Harara,Tace dama hanyar Mota da ta jirgi daban...KU wuce abinku nasan hanyar garin mu,"Dariya Dan iska yayi har shewa yace kanki akeji Yar Shan miyar Amarya, sannan ya wuce abinsa,"Nan Sahura ta bude abincin Fried rice da nama ne acikin kowanne takeway,Sahura Zama tayi ta ci shinkafar, kana ta aza lemon fanta,"Mansura Kam cin dole NE take ma abincin Domin maganin yunwa,"Bayan sun gama Sauran kayan gidan Sahura ta gyara,sannan Tace to Ni mansura Zan tafi!Kiyi Hakuri har muji me Mallam na Kan tudu zaice," "Share hawayenta tayi,Tace Sahura karki manta....da zancen karye asirin Nan, Saboda na fahimci duk yadda Mallam ya fada Mana saddiq Zaiyi,Kinga shi NE Bimboy ke nuna min,Idan har asirin yayi akansa akwai matsala!"Saboda Ina son nayi Masa rashin mutuncin da zaiyi zucia ya sakeni!" Kinga idan maganin nan yaci ba yadda zai fusata har ya sallameni. "Karki damu mansura za'a warware asirin sai ayi Masa Wanda zai sakeki Ido rufe!"karki damu...Kuma in shaa Allah Sadiq zai gane kuransa!"Kedai KAWAI Inji dumus....." "Jikkarta ta dauko da kyar ta had'a dubu Sha UKU,Tace Kinga Wannan Sahura ki kaiwa Mallam dubu goma,Wannan ukun Kiyi na Mota!"Kinsani Banda sauran Kudi yanzu,Duk Bikin da na samu awurin kawayena da dangi, sune na hada na baki Kika amso min wancan kwallin..."Yanzu dubu biyun nan da kike Gani su kadai NE ragowa, Zan ajiye su hannuna har Naga yadda Tafiya zata kasance!" _(Asarar duniya da ta lahira naga masu neman magani bazasu taba tara komai ba,Allah ya shirya amin,)_ "To ba Komai mansura Zanyi masa bayani idan yaso Daga baya in kin samu ragowa kudinsa,Kuma aikin yayi kyau,sai ki biyashi Sauran, kinsan na Kan tudu da kudi, baya kananan aiki Daga ashirin zuwa sama ne..."Sahura Tace cikin Alamar rashin Jin dadin kudin..." "Ba damuwa Sahura inji mansura,tana kallon kawarta, sannan tace"kije gidan mu ki duba min mamana...."Nagode Inji mansura Alokacin da take kokarin ma Sahura rakiya...." "A kofar gidan Dan iska NE...zaune sun tare hanya Saboda tsarou..."Yace madam akoma gida hakan ke Kuma umma ta gaida Aysha," "Tsaki Mansura tayi ta wuce!Azuciyarta Tace Hmnnnn....wato gadinta ma akasa wad'annan Yan daba suyi,"Sahura Koh sum sum ta wuce abinta tayi tafiyar ta, Domin ta fahimci Su Dan iska Basu da mutunci..." "Bimboy da Abokinsa Adams ne zaune awani Babban zaure...."Bayan wani lokaci Mutumen ya Gama rubutu da Zane ature mai kasa sannan ya dubesu yace"Samari kunzou da nasara an daureta...babu ita Babu fita har abada matuk'ar ba Kai ka Bata umurni ba!"Kai Wataran da hannunka zaka tura keyarta waje ta rigeka dawowa Cikin gidan,Na kafe maka ita agidanka sai yadda kaga dama da ita,"sannan na rabata da kowa nata matuk'ar ba masu sonka ba ne," "Dariya Bimboy yayi yace Nagode Dan mallam... hakika kayi min maganinta...Adams yace Shiyasa muke yinka Dan mallam...." "Kudi suka bashi sannan suka wuce suna murna Domin da yardar Allah sun gama da Matsalar mansura," "Bayan an zuba ma suhaila ruwan Sanyi ta farfadou ahankali take kallonsu,"Nan aka samu kowa ya zauna,Yaran ko Dakin su aka tura su suje suyi wasa, Anty Talatu ta kira Hajiya Atika," "Falon ya cika da Yan uwan jalila duk sun karaso,Hajiya Atika,Tahir da Mahmud,"suhaila sai kallon su take ta rasa me ke damunta arayuwarta tsoro!fargaba!ko Kuma farin cikin samun Sadiq da take tunani akowacce Rana,"Domin halayen SA da kirkinsa na burgeta,"Amma Bata taba Jin Sonsa arayuwarta ba!"Burgeta KAWAI Yake," "Umaima da Jalila suna zaune awuri Daya Kowacce da tunanin da takeyi aranta,"Haka Sadiq da Ali tunanin Mafita suke fatan su Allah yasa Kar asamu akasi!" "Hajiya Atika ta numfasa tace''Aliyu KU sanar Mana meke faruwa!?"Tayaya ka daurawa suhaila aure batare da saninta ba!!?"Sannan ita mansura Meyasa aka fasa aurenta!?"Duk Ajere Hajiya ta antayo masu Wad'an nan tambayoyin...." "Gyaran murya Ali yayi yace"Hajiya kamar yadda kuka sani mansura ta cutar da Sadiq shiyasa yace ya fasa aurenta,Kuma akayi sa'a ma Ashe mansura na dauke da cutar HIV sannan ta yaudari wani saurayinta shine ya tona Mata Asiri,Kuna yace zai sanarwa kowa matuka ba'a daura auren da shi ba,"Shi kuma Sadiq ganin an daura auren mansura da wani,Shiyasa ya nemeni alfarmar Akan nabashi auren suhaila Yana sonta,Kuma ya yaba da nutsuwarta, hankalin ta,"Yasan cewa In shaa Allah zasu fahimci juna da Jalila Kuma zataso yaransa,"Ban yarda ba Sai da yace"idan har Suhaila ko Yan uwanta Basu amince ba zai saketa!"tun Kan wani kunne yaji,"Nan dai Ali yayi kokarin masu bayani tare da kwantar masu da hankali har ya fahimci sun gamsu sosai da bayaninsa..." "Da kan shi ya Kira wayar umman kano,Cikin Sa'a ta d'auka,Ali fannin tsara zance ba baya ba!"zaune yayi ya labartawa surukar SA komai tun farko har karshe,"Inda ya Bata Hakuri Akan rashin tuntubar ta amma ya shaida mata ya kira Alokacin sai dai Kash!ba a dauki wayar ba!" "Umman Kano Tace ba komai Ali,zanyiwa dangin Babanta bayani, Yanzu Nan Mallam Musa ya kirani yayi min bayani tare da rokona alfarmar na fahimci lamarin. saboda Haka na amince da auren Allah ya Basu zaman Lafiya,sai dai ta zAuna agidanku har Yan uwanta suzou ayi taron bukin akawo furnitures dinta,"Sannan ta tare kaga ayi walima hakan," "Godiya sosai Saddiq yayi ma umman kano,Hajiya Atika ma wayar ta amsa suka gaisa tare da Mata bayani Nan dai suka tattauna sannan aka KASHE wayar," "Ali ya dubi Suhaila Tace"to kinji yadda mukayi da Umman kano saboda Haka Kiyi Hakuri Suhaila ki amshi Wannan auren Amma har Yanzu kina da dama,Kodai ki yarda ko Kuma ki bijire!"Kiyi tunani akai Wannan ita CE kaddarar KU," "Suhaila sunkuyar da kanta tayi tana wasa da zoben hannunta..."Ta rasa yadda zatayi da kunyar Sadiq da Anty Jalila," "Umaima ajiyar zuciya tayi...tare da share hawayenta Tace"Hakika Wannan lamarin shine rubutaccen Al'amari,kana taka Allah na nashi,"Kuma matar mutum kabarinsa....."Jalila Kiyi Hakuri da hukuncin ubangiji nasan kishiya ba Dadi,Shiyasa banso ace Suhaila CE taki kishiyar ba!"Saboda Ina gudun zaman KISHI ya tarwatsa alaqata da ke agaskiya banji dadi ba......" "Da sauri Jalila ta rufe bakin Umaima...Tace Haba!kawata karki sabou Mana Ni Wallahi naji dadin Wannan kaddarar da Bata kaddarou min mansura amatsayin kishiya ba!"Umaima zamana da Suhaila ba zaisa abokantaka da ke ta lalace ba!sai Idan kece kikaso hakan!"Na yarda na amince da Suhaila Kuma na d'auketa kanwata kamar Rasheeda,"In shaa Allah Babu zaman KISHI!"A tsakanin mu Suhaila kanwa CE kuma Abokiyar zamana,"Ki daina tunanin komai na tabbata wani hanin Daga Allah baiwa CE,"Domin ga yarinyar kirki,Mai tazo gidan Nan amatsayin Abokiyar rayuwar mu, Allah mun gode maka,"Jalila ta karashe zancen tana Daga hannayenta sama tare da Hawaye da murmushi.." "Murmushi Saddiq yayi tare da godewa Allah,Ya ce Allah yayi Miki Albarka uwargidan Sadiq," "Duk Wanda ke Wurin dariya yayi,saboda jalilah ta burge kowa Suhaila Tashi tayi da gudu zuwa inda take suka Rungume juna suna Hawaye!"Ali Kam yaji dadin ganin hakan, kenan Suhaila ta amince da auren Abokinsa,"Nan aka Tsayarda Ranar walima da tarewar Suhaila sannan akayi Addu'oin da fatan alheri,"Ali da ahlinsa har Amarya suka wuce haka Yan gidan su Jalila suka koma," "Saifullahi Yanzu an Zama Mutumen kirki an tsayar da Ranar auren SA da Saudat,Anyi komai na hidimar aure,har lefe an Kai,kusan saitin akwati biyu,Ranar farinciki awurin Hajiya lantana da yaranta,Ba'a magana,Haka Talatu tayi bakin ciki kamar me ita da yaranta,"Akarshe Hakuri sukayi Domin dai Hajiya lantana da su Saudat sunyi gaba sai Labari,ita Kuma dole tabisu ta ci Arziki,Hakan tayi watsi da Komai Domin aci Arziki da ita," "Bayan tsawon wata D'aya Al'amurra da dama sun faru ciki harda tarewar suhaila agidan mijinta saddiq da ke unguwar sama road,"Bayan Yan uwanta da danginta da ke Kano,sun shigo anyi gagarumar walima,An kashewa Amarya Kudi afannin kayan daki ba laifi,dama can suna da arzikin su," Suhaila tana zaune da uwargidan ta Jalila da yaransu lafiya,"A hakan ta Cigaba da karatunta, Umaima taji dadin hakan Domin tasamu Abokiyar rayuwa agarin sokoto,A gefe alakarta da Jalila tana Nan daram,"Mufeeda da Mufeed sun warware Basu da damuwa,karatu suke sosai,"Haka Sadiq hankalinsa ya kwanta,"Yana zaune da iyalansa lafiya ga girki na gagari Yana kwasa dare da rana," Wata na D'aya cif Ina zaune agidan momy tana kulawa da Ni sosai,shiri take min naji na Gani na fad'a,"Kayan gyaran Jiki take bani,Ina amfani da su na gidan momy Murja Hashimu( _Babbar macce maganin kananan Mata_),"sai kayan _Anty meena na'amore_ itama ba baya ba!"Shiyasa sai santsi da sheki nake,"Jikina ya qara kyau nayi kiba da haske kamar Balarabiya,"A Yanzu Kam bani da damuwa ta kowane fanni Ina SAMUN kulawa da soyyaya,"Ga iyayenah akusa da ni Shiyasa nake zuba sangartata son Raina," "Mamana da Babana duk suna zaune agidan sai dai sashen su daban,"Na momy daban,"momy ta nemo masu Mai aikin,sai dai mama ita ke abinci da kanta, shara da mopping NE KAWAI ladi keyi," "Jawad duk ya rikece ya firgice ya lalace saboda damuwa,ta ko'ina ya kasa shawo Kan momy sai garashi take Yana nuna Mata Yana son matarsa ta Koma Amma ko ajikinta,"Gefena ma babu sauki,Domin bana kula shi,"Wulakancin yau daban na gobe daban,Yasha Kuka agabana Yana rokona na yafe Masa Amma ko ajikina bana kula shi,"Ya rasa ya Zaiyi damu duk ya rame ya fita hayyacinsa,"A hakan yake Cigaba da Hakuri damu yana dakon Ranar da Zan Koma gareshi. "Saifullahi da mamansa da yayyensa duk sun zou gidan sun baiwa kowa Hakuri dangane da abinda ya faru ,"Momy Tace"bakomai Ya wuce Allah ya tsare gaba," "Haka gefen Amarya Saudat Anyi Shirin Aure Gwanin sha'awa,Duk da Hajiya lantana taso Hana auren Akan Labarin abinda su ka aikata da Taji awurin Innerie,"Amma akarshe komai ya daidaita Dan tagano cewa Saifullahi ya shiryu kuma ya canja kaf halayensa da dabi'un sa sun sauya. Talatu da yaranta sun saduda saboda sun gane Ramin karya kurarre NE Kuma Hassada ga Mai rabou Taki,Shiyasa suka bi Lantana da yaranta Yanzu suna zaune lafiya agidan babu hayaniya abinda da masu kwadayi ana shafa Masu harkar Arziki Suna lashewa.," "An d'aura auren Rasheeda da mijinta, haka Tahir da amaryar sa Nan akai Sa'a Kuma tsohon mijin Anty Talatu yadawo Domin tsawon watanni uku da mutuwar amaryasa wajen haihuwa,da ita da jinjirin duk suka rasu,shiyasa yadawo aka gyara auren su da taimakon malam shugaban Islamiyyar su hasalima shine ya gyara auren,Farin Cikin Hajiya Atika da su Jalila baya boyuwa Domin sunji Dadi matuka," "Gefen Anty Tala ba'a magana Domin Burinta ya cika,zata koma ta rike yaranta tayi musu *TARBIYYA* Mai kyau,"A Yanzu Kam taga ishara Kuma ta wa'azantu fatanta mutuwa CE kadai zata sake rabata da iyalinta sanyin idaniyar ta," "Rasheeda an Kai karshe Domin Gashi aure zai kaita gidan macce biyu Kuma Babban gida,karshen iyayi da munafunci...Tun Kan ta shiga gidan taji labarinsa,Babu sani Babu sabou gidan Yan tujara ne,ga Alhajin da manyan Yara,wasu ma zasuyi sa'anta Allah dai ya kyau," "Umaima da suhaila tare da sauran yaransu duk sun Hallara gidan nasu Jalila anata hidiman bukinsu Anty tala lafiya kalau batare da wata damuwa ba, har aka kammala amare da angwaye kowanne ya tare sai dai fatan SAMUN zAman lafiya da zuriya dayyaba," "Mansura anyi laushi duk ta kanjame!ta lalace ta rame,kamar ba ita ba!gashi Kuma yanayin fuskarta da jikinta sun canja tayi Baki da Kore!saboda man bilicin ya Kare!"A hakan take Hakuri agidan Bimboy ga rashin abinci Domin ba aikin yine da shi ba!zaune gari banza NE!baida sana'a iyakachinsa bangar siyasa da fad'a Nan fad'a can,"Wahala tayi ma mansura yawa ga Sahura ta DAINA zuwa tunda sukayi fad'a Akan kudin aikinta da ta cinye saboda Mallam na Kan tudu yace aiki bazai warware ba!har sai Lokaci yayi!"Haka dai rayuwarta ba Dadi da walwala wahaloli sun yawaita watarana ta Kan Sha Kuka!da tuba Akan abinda ta aikata ma Nadiyatu, Jalila da Saddiq da sauran Alhazawan da ta cutq aganinta amanar su CE ke bibiyarta! "Duk kayan lefenta da Sadiq ya yi mata da na dakinta wasu ta sayar saboda ta ci abinci," gashi a Cikin irin masifar da take ciki Bata iya fita ko'ina ji take tamkar an daureta,"Tun aurenta har Yanzu Bata taba fita ko kofar gidan ba!"sai dai makota da yam matan unguwa su shigo Mata,"Ko da kasheta Bimboy Zaiyi Bata iya guduwa,"Ana hakan maman ta Hajiya Halima da su Yaya Farida suka kawo Mata ziyara,sun sameta ayanayin wahala!"Nan Suma suka labarta Mata suna Cikin damuwa Domin komai ya canja magani ya saki mazansu ita Yaya Farida ma mijinta yayi aure ya saketa!"Itama fariza da sauran duk ankaro masu kishiyoyin,"Ita ma maman su za ai Mata Dan babansu wata bazawara zai aure,komai ya lalace,"Mansura Tasha Kuka Saboda Bata da labarin kowa hatta wayar batada ita. Nan dai suka rarrasheta tare da had'a mata Yan Kudi taja jari,"Bayan sun koma ta dinga sana'arta ta Kayan magi da Ruwa da zobou Amma ahankali jarin ya karye saboda da su NE take ci ta Sha da sauran lalurorin bugu da kari tana dauke da juna biyu Nan tasa kudin gaba da taimakon Bimboy suka Kai karshen su," *BAYAN SHEKAROU GOMA* "Abubuwa da dama sun faru tare da cigaban rayuwa,"Iyalan Gidan Alhaji Abbakar Saddiq Musa (Commissioner of Education) zaune a dining place suna lunch,"cike da Jin Dadi da farin ciki," "Ga Baki Daya Ahlin gidan sun canja kamar Basu ba,Yaran barkallah an girma, Mufeeda da Mufeed Yanzu suna sakandare da ke Nan garin sokoto watou IMAN,"sai kanwar su Salma (Ilham)Mai sunan marigayiya mamansa Saddiq,"da Atika(Mimah,)itama takwaran Hajiya Atika,da Kuma karamin kanin su Abbakar Saddiq (Abbati)shima takwaran Alh.saddiq NE,"Dukan su yaran Hajiya Jalila ne masu kyau da haiba barkallah," "Haka gefen Hajiya Suhaila tana da yara,"D'anta na fari Musa (Hanif)sai Kuma takwaye Nabeel da Nabeela,sai tsohon Cikin da take dauke da shi Wanda haihuwa ko yau ko gobe," Jalila ta canja tayi kyau da haske ta koma Uwar Mata Domin tayi Jiki,ba laifi kamar ba ita ba!ga Yara tasamu barkallah,Wanda tuni ta daura su Akan turba Mai kyau,Wanda Daga su har yaran suna Cigaba da neman ilimin addini," "Suhaila Kam Bata wani canja ba,tana Nan cylinder dinta sai dai ta Kara kyau itama Kuma kalar fatarta chocolate tana Nan sai sheki take da yaran ta sai San barkah," "zaman Suhaila da Jalila zama ne,na Amana da Jin Dadi ba laifi suna da fahimta sosai,Kuma kowa Yana Hakuri da Dan uwansa,"Sai dai can ba'a rasa idan an samu sabani tuntuben harshe!"Domin Zama yau da gobe ba za'a rasa ba!"sai dai kowannen su Yana danne abinda ke damunsa Shiyasa suke lafiya ba mai Jin kansu," "Har kasuwancin su tare sukeyi na oder kayan manya da yara zanna laces s,bags, shoes, veils da sauran su, Duk daukowa sukeyi daga kasashen wajen kamar India, Dubai da malesia, da sauransu. Business sukeyi sosai, har sun shahara, Saddiq ne ya basu kyautar makudan Kudi,"Domin ya hanasu aiki duk da kowaccen su ayanzu tana da takardun digirinta afile, sai dai shi ayanzu ya nuna masu baya son aiki ba san me gaba zata haifar ba!"Amma Yanzu Kam su hakura Domin Yana son abawa yaran kulawa Mai kyau tare da *TARBIYYA* yadda ya kamata,"Shine dalilin damka masu kudade su ja jari, sannan ya dauki Alqawarin biya masu Dukkan buqatun su ko da kuwa na naira daya ne," "Shiyasa Sam Basu damu ba!"suka mayarda hankalin su Wurin Sana'a wanda Hajiya umaima ma tana daga cikin alqaryar ta su ba laifi naira ta zAuna masu atafin hannu sun zama hamshaqan mata,masu arziki sai Hamdala," "Kwanciyar hankali da arziki da wadata ya wadaci rayuwar Alhaji sadiq Wanda ayanzu commissioner of Education ne na jihar sokoto,"Arzikinsa ya yawaita ga Mata Nagari Allah bashi da zuriya dayyaba Mai albarkaa,Domin yaransa sun taso ahade ga ilimin addini dana zamani ba laifi sun Zama mahaddata kur'ani,"Domin sun samu *TARBIYYA* Mai kyau awurin iyayen su,"Komai Yake nema Aduniya ya samu burinsa ya cika. Domin ya Sami iyali Nagari masu nagarta ga zuriya na yawaita agidan SA sai GODIYA,"Tuni ya ginawa iyayensa da shi kansa katafaren gida a Argungu Kuma Yana taimakawa danginsa sosai"Duk wani Abu ya taso sallah ko buki ya Kan kwaso iyalansa suzo ayi hidima da su sannan su koma, Suhaila da Nadiya an Zama kawaye Jalila ma ta roki Nadiya gafara Haka dai komai ke Tafiya babu matsala," "Daman ance komai nisan jifa k'asa zai dawo haka duk nisan dare gari zai Waye!"Bayan duk mun gama tasko da wulaqancin da mukewa Jawad na koma gidan da dadewa tun lokacin bukin auren saifullahi da saudat,"Ko Bayan na koma na wahaladda shi sosai Kafin na ba da kai,"Haka muke rayuwa kamar komai Bai faru ba!"A Yanzu na fahimci soyyayar da Jawad kemin ya nunka Nawan ba Adadi ya samu aiki a Abuja,"A can muke rayuwa da yaran mu," Tsawon shekaru goma da suka wuce a baya,nayi karatu Burina ya cika Ni da mijina Dan kuwa shi burinsa na Zama barrister Ni kuma Burina nayi karatu. "BARRISTER NADIYA BALARABE kenan hamshakiya Kuma matashiya Wanda ayanzu gwamnatin tarayya ke damawa da ita," "Duk wani burina ya cika Domin da taimakon mijina nayi karatu Mai zurfi har na zamou Barr.Nadiya ga shi na samu haihuwa uku Duk twins ne",Akhram da Ikhram wato (Muhammad Bello da Fatima Batula) sai Hanif da Hanifa(Khaltumi da Husamaddin) Wanda Duk sunan iyayen mu, sai Auta Juwairiyya. Alhaji Jawad ne yayiwa iyayen mu takwarori da tagwayen mu biyu,"Yaran Masha Allah fafare tatas masu kyau, wad'anda iyayen mu keso da kauna da sosai,"Musamman momy da na lura duk soyayyar da takewa Jawad ta daurata akan yaran," "Sadaut ma tana lafiya ita da Saifullahi Wanda ayanzu suna jigawa acan ya samu aiki CBN zaman lafiya suke ga arziki ya daure,yaranta biyu maza mah'mud da Almustafa,"Itama tana aikin asibiti acan jigawa din ko da yaushe tana turowa mahaifiyarta da kannanta Sak'o harma da su baba laraba da baban su tana TAIMAKA masu sosai," "Umaima da Aliyunta suna zaune qalau shima ya samu Karin girma,suna zaune lafiya da yaran su,"Salim,salima,Salma da Salman sai autansu Saiman," "Mansura da Bimboy Yanzu Kam da sauki Domin ya samu an dauke shi aiki a local government,Ana Masa albashi sai dai baya wadatar su....Da sauki dai akan da can baya,itama ta samu tana karantarwa a sakandaren Mata,tana albashi, suna zaune lafiya Bayan watanni ya Kan d'auketa da yaran ya Kai Kebbi su Kwana biyu su dawo"Haka suke zaune Asiri tufe Ana Hakuri da juna,"Yaran su ZAINAB da Maryam (Ummi) sun tasa ba laifi,'Duk abinda ta samu Yana ciki ga lalurorin Yara sai ahankali,"Da kyar mansura ta samu haduwa da Jalila ta roketa gafara, Nan ma take Jin labarin suna Nadiya suna Abuja, Yanzu ma basa Nigeria sun fita kasar waje(U.S)hutun karshen shekara,","Duk da taso taga Nadiya ta roketa gafara Wanda akarshe Lambar wayarta ta amsa awurin Jalila domin ta kirata,ta roketa,"Nan Jalila da Suhaila su kai ma mansura goma na arziki,Domin ta Basu Tausayi sosai,ko suturar jikinta Dana yaran abin kallo ne,"Tufafin su Dana yaran suka had'a mata,"Tana godia har hawayen ta tabar gidan cike da kunya da danasani da Kuma nadama," "Tuni Rasheeda ta KASHE aurenta Domin zaman gidan Yan bala'i ya gagareta Bayan wuya da azaba ga dukan da take Sha awurin su,"Tahir Kam Yana zaune lafiya da matarsa safina ya samu MD a company da Yake aiki,yaran su uku Yaseer,Yaseera da Yasmeen,"Shine rike da Gidansa da kuma mahaifiyarsu Yana taimakawa Yan uwansa sosai," "Bayan su Barrister Nadiya da Ambassador Jawad sun dawo gida Nigeria,"Suka dunguma su da iyayen su zuwa kasar SUDAN inda suka gana da Yan uwa da Abokan Arziki,Nan Jawad da Nadiya suka ga gwaggonin su Wad'anda suke Kama da su, watan su daya suna zaga Dangi gari wa gari,"tamkar kada su dawo sai dai ba yadda zasuyi hutun yaransu ya Kare,"Haka suka dawo tare da alqawarin duk Bayan Lokaci zasu dinga kawo masu ziyara," Amma su Innerie da momy da Baba suna can SUDAN din acewarsu sai Bayan sati biyu ko uku zasu dawo,"Domin dai mutan Sudan su rikesu kamar kada su dawo," "Bayan sun dawo gida Nigeria da sati uku su momy suka dawo cike da kewar Dangi,"Ba'a Dade ba!"Sai ga ciwon ajali ya Kama Innerie,Wanda aka wayi gari babu ita adunia!"tashin hankali marar Adadi iyalanta suka shiga Wanda akarshe Hakuri ne magani!" "Nasha Kuka!har nagodewa Allah shi kenan na rasa Mamana ,Ba yadda Zanyi sai Addu'a Fatana da Innata mu hadou Aljannah fiddausi,"Ganin zaman gidan babu Dadi awurin Baba da momy wani baranbaran,Shiyasa su Mallam Musa da sauran dangin mu na Sudan suka hada Auren momy da Baba," Day farko Momy ta so ta bijire a ganinta tayaya zata auri yayan mijinta,Amma Yan uwanta da Hajiya Maryam sun Nuna Mata bakomai bane,gashi ta jima batayi sure ba gwara ta tufawa kanta Asiri. Shi Baba Daman yasan ya halatta Shiyasa Bai damu ba a hakan suka amince akai aure Suna zaune Lafiya da girmamata juna. na samu Sanyi araina Domin momy ta rikeni kamar Yar cikinta,tana kula da ni sosai,"Haka rayuwarmu ta kasance cike da farin ciki da Jin Dadi agefe Ina maraicin Mamana,"Yaran mu sun girma ba laifi suna karatu a makarantu masu kyau,"sun taso acikin kulawar mu na k'ara haihuwar namiji akayiwa baba malami takwara (Abbati)"Ina fita aiki a higher court Abuja yayin da ayanzu mijina ya samu Ambassador na Nigeria,"Shiyasa baima cika Zama Nigeria ba!"Yana Camaro idan Anyi hutu muna bin shi tare da zaga kasashen duniya. "Anty Talatu ma ba laifi ta sake haihuwar da namiji Ibrahim, Daga shi Bata Kara ba, Saboda dama can tana da uku Mata ga yaran da aka bar Mata marayu biyu maza,"Shiyasa ta hadesu da Duka ta rike cike da Amana da kauna,"Anty Talatu ta zamou uwa Tagari awurin yaranta Domin ta Basu *TARBIYYA* kamar Kowacce uwa Tagari Mai Nagarta"ke kokarin baiwa yaranta Domin su taso da ladabi, Biyayya da nutsuwa," " _Ikon Allah akace sai kallo Domin tun duniya kake Gane illarka,wani ko Allah Yana raga masa sai alahira,"Duk abinda mutim yayi Khairan ko sharran shi zaya girba,"Allah yasa MUDACE mu aikata ayyukan ALHERI,"_ " _Anan na kawo karshen Wannan littafi na *TARBIYYA* abinda na rubuta dai-dai Allah ya bani Lada,Abinda nayi kuskure Allah ya yafe min Ni da KU Baki Daya,"_ " _Masoyana KU sani Ina sonku kuma Ina Jin dadin comments naku,Anatare Ni da KU iya wuya,"_ _A karshe Wannan LITTAFIN na *TARBIYYA* na rubuta Shine Domin fadakarwar da ilimantarwa sai nishadantarwa,"A dauki darasi Mai kyau azubar da abinda baya da kyau,"_ " _Iyaye Mata da maza Musa Ido Akan *TARBIYYAR YARAN MU*,mu Kula da ibadarsu,mu'amalarsu da abokansu mu sa Ido Akan duk wani Motsin su,"Mu daina nunawa Yara tsantsar so da kauna,Idan Anyi musu hukunci mu daina nuna bacin ranmu,"TABBAS iyaye Mata musani mune kashin Bayan rayuwar yaranmu Domin idan sun gyaru mune Kuma zamuyi alfahari da su,"Tayaya!?_ " _Ta hanyar basu " *TARBIYYA* Mai kyau,"_ " _Allah ya taimake mu ya daura mu Akan tafarkin gaskiya,ya shirya Mana zuriyar mu,yasa Mana hannu akan *TARBIYYA* yaran mu *AMEEN*_ _GODIYA MARAS ADADI 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI_ _MASOYAN TARBIYYA GAISUWAR KU TA DABAN CE_👍🏼👍🏼👍🏼 _TAMMAT BII HAMDULLAH......_ *YAR MUTAN ARGUNGU CE*😍 *2020* _"SANIN GAIBU!...." COMING SOON IN SHAA ALLAH_ 👍🏼👍🏼👍🏼PEN WRITERS ASSOCIATION