Bismillahir Rahmanir Rahim   (1) 4:00pm     Ruwa ne yake ke sauƙa daga sararin samaniya a garin Gombe, hakan yasa baza ka ji sautin komai ba sai ƙaran ruwan dake dukan rufin gidajen mutane dalilin kowa ya shige cikin gidansa. A wannan daddaɗan yanayin kuma a wata unguwa da ake kira Tumfure wasu ma'aurata ke zaune a wani babban falo akan kujera ɗaya, manne suke da juna a lulluɓe da wani ƙaramin bargo suna magana jefi-jefi dalilin kallon TV da suke yi bai bari sun samu hankalin junansu ba, ana gama film ɗin da suke kallo suka ja ajiyar zuciya a tare kana suka dubi juna suna murmushi. Mijin ne ya gyarawa matarsa zaman bargon ganin ƙafarta ɗaya ta fita daga ciki, bayan yayi na'am da aikinshi sai ya dubeta da tsantsar soyayyarta a kwayar idanunshi. "Riya kin koya mini kallo, and the worst part of it shine wai Korean Series nake zama ina kalla ni Hafiz." Ya nuna kanshi da yatsa don emphasizing maganarshi.   Wacce ya kira da Riyan ta kama yatsar tashi tayi saurin kaiwa bakinta ta ciza wanda hakan yasa Hafiz ya janye cikin jin zafin cizon yana dubawa yana kuma ƙoƙarin tsumewa amma yanayinshi ya fallasashi, wato murmushin da yake yi har yanzu bai bar fuskarshi ba. "Sorry." Ta furta tana kama kunnenta ɗaya tana dariya ƙasa-ƙasa. "Kin ɗauki bashi kuma zan rama a lokacin da baki yi tsammani ba, I swear." Ya ƙarisa maganan yana ɗanɗana yatsarshi a harshenshi alamar rantsuwa. Murmusawa tayi wanda har sai da fararen hakwaranta suka bayyana gefen kumatunta ɗaya kuma ya lotsa. "You look childish idan kayi wannan abun. Amma Bee ba nace kayi haƙuri ba?" Ta zumburo baki cikin shagwaɓa wanda hakan yasa Hafiz ya girgiza kanshi. "Duk maganar da zaki faɗa ki faɗa amma ba zan haƙura ba sai na rama, shiyasa na rantse. Oya ki tashi mu yi sallah mu je gaishe da Muhammad, bana son har a sallameshi baki je ba." Ya miƙe tsaye tare da miƙa mata hannunshi ɗaya ta kama kana ta tashi suka fuskanci juna bayan ta yaye bargon daga jikinta gaba ɗata ta ajiye a gefe. Ido ta tsura mishi tana kallon surarshi dake burgeta tun mafarin haɗuwarsu. Hafiz baƙi ne mai tsantsar kyau a idanunta, ba kuma irin wanda ake faɗa a littafin Hausa da za'a ce ya zarce tunanin mai tunani ba, a'a, shi Hafiz ɗinta daidai ne wanda bata son a ƙara mishi komai haka kuma bata son a rageshi da komai. A gurinta Hafiz shine perfect example na namijin duniya da kowacce mace zata yi farin cikin samu. Dalilin tsayinshi yafi nata yasa dole sai da tayi ɗagelgel ta tsaya kan yatsun ƙafafunta kafin ta samu damar kissing ɗin bakinshi mai faɗi game da duhu.   Idanunshi ya lumshe yayi saurin zagayeta da hannayenshi wanda hakan yasa ta mannu da jikinshi har tana dafa ƙirjinshi a yayin da itama take rufe nata idanun. Sun kai minti ɗaya a haka suna exploring jikin juna kafin Hafiz ya sunkuceta duk da nauyinta yayi ɗaki da ita. A kan gado ya direta yana ƙoƙarin cire singlet ɗin jikinshi ta tashi zaune tare da mishi farii da ido tace, "Bee kace zamu je asibiti gaisuwa fa!" Hafiz da kashi casa'in na hankalinshi na ga abun da yake muradin yi ya hayo kan gadon yana cewa, "That could wait, but for now let's make love." Wani shu'umin murmushi tayi domin tun farko ƙudurinta kenan na hanasu fitan, babu wani dogon bayani ta biye mishi suka yada zango a sansanin ma'aurata. Awanni biyu da haka ruwan saman ya tsaya wanda hakan kuma yayi daidai da ƙarfe shida na yammacin asabar, Hafiz da matarshi ce suka fito daga cikin gidansu sun yi wanka sun shirya tana kulle ƙofa tana zumbura baki. Hankali kwance kuma cikin jindaɗin yanayin daminar Hafiz ya shiga cikin motarsa ta gani ta faɗa a gari da ke harabar gidan ya kunnata, maigadinsu na jin ƙarar motar ya fito daga ɗakinsa ya fara ƙoƙarin buɗe musu gate. Second biyar da haka itama buɗe gaban motar ta shiga tana kallon window fuskarta a kwaye. Briefly Hafiz ya dubeta a yayin da yake yin reverse zai fita daga gidan, murmushi yayi bai ce komai ba har suka fita daga gidan ya ɗagawa maigadin nasu hannu bayan ya aiko mishi da gaisuwa. Sai da suka fara tafiya ya ɗaura hannunshi ɗaya kan cinyarta yana mata tafiyan tsutsa yana kuma ƙara yin gaba wanda hakan ya fara canja mata yanayinta cikin ƙanƙanin lokaci.   Ture hannun nashi tayi tana ƙara zumburo bakinta ita ala dole tayi fushi amma shi bai bar murmusawa ba, a ƙarshe ma mayar da hannunshi yayi yana mai cigaba da tsokanarta. "Allah ka bari bana so." "Allah ka bari bana so." Ya kwaikwayi muryarta yana dariya kaɗan har Adam apple ɗinshi yana sama yana ƙasa. "This is not funny." Ta faɗa tana fuskantarshi a karo na farko tun shiganta cikin motar, harara ta dalla mishi wanda ya mayar mata da martanin alamar kiss har da hurawa a gareta. Kwafa tayi ta harɗe hannayenta saman ƙirjinta ta ƙara juyar da kanta ga window tana kallon gidajen da suke wucewa har suka hau titi tafiyarsu ta daidaita. "Seriously me yasa bakya son zuwa gaisheshi? Mutum ya kwanta bashi da lafiya har kwana uku kuma kina ƙawance da matarshi amma kice baza kije ki gaisheshi ba? Ranar da aka kwantar dashi nace ki kirashi kika ƙi, jiya nace muje in kaiki amma kika ce kanki na ciwo, yau kuma kika shammaceni na kwashi gara wai duk don kar mu je amma baki san na gane wayon naki ba and here we are, mun kashe arna kuma mun fito gaisuwan. Yanzu ki faɗa mini dalilinki na tsanarshi Juwairiyya, wallahi wani lokaci har kunya nake ji idan naga kina mishi wasu halayen, ke ko kunyar matarshi bakya yi?" Ya ƙarisa maganan fuskarshi babu yabo babu fallasa domin tun ba yau ba yake sane da rashin jituwan da ke tsakanin matarsa da babban abokinsa. First impression ɗin Muhammad a gurin Juwairiyya shi ya jawo duk wannan bashin gaban, faɗan da Hafiz ya yiwa Muhammad yasa yayi ƙoƙarin gyarawa amma ko da ya nuna sakin fuskarsa ga Juwairiyya wacce take cike da haushinshi sai ta basar ta nuna bata san yana yi ba. Hafiz ya so tankwara matarsa amma abun ya garara domin ta kafu ne a kan dalilanta na wasu halayyar Muhammad ɗin wanɗanda shi haka ya tashi da su babu mai canjashi kamar yanda itama tana da wasu halayen da mutane basa so kuma ba zata canja ba. "He is always grumpy kullum mutum a tsume kamar kashi, ga ɗan banzan wulakanci ana gaisheshi ba zai amsawa mutum da murya babba ba sai kace shi mace ce. Na rasa yaya aka yi ka iya abokantaka da wannan mutumin for all these years. You are nothing like him, kana da sakin fuska shi kuma kullum a tsume yake, kana da son mutane amma shi wulakanta mutane yake yi wanda har matarshi bai bari ba. Kana da son taimako shi kuma idan ya ga mutum na neman taimako baya ko tsayawa zai yi wucewarsa." Murmusawa kawai Hafiz yayi hankalinshi na kan titi ya ce, "First of all, thanks for the compliments. Wasu abubuwan da kika faɗa a kanshi haka ne wasu kuma ba haka bane, yana da wasa da dariya da kuma son mutane wanda ya ga sun dace da shiga circle ɗinshi. Batun taimako kuma sau nawa zan faɗa miki ki daina judging mutum akan laifi ɗaya? Don kawai bai miki taimako sau ɗaya ba a rayuwarki bashi zai sa kice kullum haka yake ko kuma haka yake da kowa ba. I know he is different kuma ba kamar ni yake ba, but that's how he is! And ba zai yiwu a canjashi ya zama yanda ake so ba don bakwa son halayenshi. And idan kika yi haƙuri sai kiga ya sake miki fuska ku zauna ana raha tare." "Allah ya sauwaƙe. Kuma dama kai kullum cikin karesa kake yi kamar biyanka yake. Ni nafi tausayawa matarshi da Allah ya haɗata da Rock irinsa." Faɗin Juwairiyya tana dunƙule hannunta guri guda don misalta yanda yake.   Wannan karon dariya Hafiz yayi yana kaɗa kanshi yace, "Wallahi duk ranar da ya ji kina kiranshi da sunan Rock ɓatawarku zata fi na yanzu." Itama Juwairiyya dariya tayi a karon farko tana hasashen yanda lukutar fuskar Muhammad zata turnuƙe idan ya ji. Ai kuwa nan take ta ayyana a ranta watarana sai ta faɗa ɗin yaji, domin idan hakan zai ɓata mishi rai ita daɗi zata ji. Tuni ta manta da wani ɓacin rai na tilastata da Hafiz yayi kan zuwa gaisuwan suka cigaba da hiransu gwanin ban sha'awa har suka tsaya a bakin hanya suka sayi fruits suka wuce asibitin FTH (Federal teaching hospital). Hafiz ne ya musu jagora hannunshi ɗauke da ledan da suka sayi fruits ɗin yayin da ɗayan hannunsa yake riƙe da na Juwairiyya wacce ke fatan Allah yasa an sallami Muhammad ba sai sun haɗu dashi ba. Male ward suka shiga daga nan kuma suka kutsa kai cikin side room B inda suka samu Salima matar Muhammad tana tattare kayansu tana sakawa a wani babban leda, shi kuma mara lafiyan yana kwance akan gado ya kuma ɗaura hannunshi daya a kanshi alamar yana tunani.   Shigowar Hafiz da Juwairiyya yasa Salima ta dakata daga tattaren kana ta faɗaɗa fara'arta tana musu barka da zuwa. "Ya jikin naka?" Faɗin Hafiz yana isa bakin gadon ya miƙawa abokin nashi hannu suka yi musabaha bayan ya tashi ya zauna. "Da sauƙi sun sallamemu, yanzu tafiya gida zamu yi." Muhammad ya bashi amsa yana duban Salima wacce ta tsaya magana da Juwairiyya ta daina aikin da take yi. "To Allah ya ƙara sauƙi. Kace da mun ƙara minti kaɗan baza mu zo mu sameku ba." "Kai ma rigima ce tasa ka dawo, ɗazu da safe kafin ka tafi office ka zo mun gaisa. Da mun tafi kam, don wannan mai nawar ta kasa gama kimtsa kayan ne amma da tuni mun isa gida." Yayi maganar da ƙarfi yanda Salima zata ji yana kuma aika mata wani mugun kallo. Ai kuwa tana juyowa ta haɗa idanu dashi ta bar gefen Juwairiyya ta koma bakin aikinta ba tare da ta ƙara cewa komai ba. A hankali Hafiz ya take ƙafar Juwairiyya wacce tun shigowarsu ta samu plastic chair ta zauna bata ko kalli in da Muhammad ɗin yake ba, ɗago kanta tayi suka haɗa ido yayi mata nuni da mara lafiyan da bakinshi. Ɓata fuska tayi sannan ta dubi sashen da mara lafiyan yake tace, "Ya jikin?" Bai amsa ba illa kawar da kanshi da yayi bayan itama ya aika mata mummunan kallon irin wanda ya yiwa matarsa ɗazu. Kwafa Juwairiyya tayi a ranta tana jin haushin wulakantata da yake yi tun ba yau ba, a ranta kuma zaginshi take yi tare da Hafiz ɗin da ya matsa mata tilas sai ta zo nan. "Ana gaisheka." Faɗin Hafiz ga Muhammad ganin bashi da niyyar amsa gaisuwar tata. "A ina?" Yayi tambayar kamar da gaske bai ji ba. Hafiz yayi ajiyar zuciya cikin gajiyawa da halinsu kana ya miƙawa Salima fruits ɗin yana cewa, "You know what? Ya wuce. Salima ga fruits and idan kin gama tattaren ku samemu a waje mu mayar da ku gida. Kai kuma ka tashi mu fita kasha iska kafin su fito." "Hafiz na kira Abbati zai taho da motata nasan yana hanya ko ma ya iso." Muhammad ya bashi amsa yana sauƙowa daga kan gadon sai ƙara take yi dalilin nauyin shi. Juwairiyya ce tayi siririyar tsaki tana ayyanawa a ranta cewa lukutancinshi kaɗai ma ta isa tasa cututtuka su dameshi tun da ba'a iya wata biyu sai ya kwanta rashin lafiya. Suna fita Salima ta dakata da abun da take yi tana murmushi tace, "Sorry fa ƙawata, yau laifina ya shafeki gashi ko gaisuwarki ba'a amsa ba." Tsaki Juwairiyya ta ja wannan karon ba tare da ta ɓoye sautinsa ba ta dubi Salima tace, "Kina haƙuri da wannan mutumin, amma gaskiya ko sau ɗaya ne ya kamata ki nuna mishi bakya tsoronshi kuma ke mutum ce. He should stop ordering you around da kakkausar murya cikin bainar jama'a saboda hakan bashi da daɗi kuma girmanki yake zubarwa."   Salima tana jin Juwairiyya ta fara faɗan data saba muddin tayi witnessing Muhammad yana treating ɗinta irin haka sai kawai taci gaba da aikinta wanda dama ta kusa gamawa. "Hmm, ba zaki gane bane. Mu tafi kar suyi ta jiran mu bamu fito ba mu ƙara yin wani laifin." Ta faɗi hakan tana ɗaukar ƙatuwar ledan tare da wani mini trolley wanda Juwairiyya ta tabbatar suturun Muhammad ne a ciki. "Ai komin rashin lafiyarsa bai kamata ya bar miki duk wannan kayan ki ɗauka ba, he had to atleast take the mini trolley tunda janshi zai yi yana da taya, ke kuma sai ki ɗauki ledan." Faɗin Juwairiyya tana tuna yanda Hafiz baya barin ta ɗauki komai idan sun je shopping ko kuma zasu fito daga gida. Cewa yake yi zai yi spoiling ɗinta saboda ita ɗin abar tattalawarshi ce. Salima ta kalli kayan hannunta cikin confusion don ita bata ga laifin hakan ba, ai shine mara lafiya bai kamata ma tun farko ta barshi ya ɗauki kaya ba, da haka suka fita daga ɗakin tana cewa, "Ni kuma dai bana ganin laifinshu, don sau da dama in ya mini faɗa to laifi nayi, kawai don Hafiz ya sakaltaki ne yana miki duk abun da kike so shiyasa kike ganin kamar ni a takure nake. But rayuwarku tana burgeni saboda yana nuna miki so da kulawa a duk inda kuke baya gajiyawa, ni kuma gogan nawa soyayyar ce bai iya ba kuma na kasa koya mishi." "Alhamdulillah Hafiz is good to me, but I really hope one day kema a nuna miki so kamar yanda yake nuna mini, wallahi daga ranar zaki gane zaman da kike yi da Muhammad akwai takura da kwara a ciki. Allah kuma ya ƙara miki haƙuri akan wanda kike yi shi kuma ya shiryeshi. Ni na manta ne ma nayi magana, don na lura daga ke har Hafiz bakwa son laifinsa ko kaɗan sannan kullum cikin karesa kuke kamar wanda ya muku asiri." Ta ƙarisa maganan cikin raha ganin Salima ta fara shiga damuwa akan maganar da take yi wanda har ga Allah ba wai kusheshi take yi don ta ji zafi ba, a'a ita ta ƙi jinin ta ga ana cin zarafin mutum ne kuma yana shiru ya kasa taɓuka komai. Halinta na rashin ɗaukan wulaƙancin mutane yasa wasu suke cewa tana da rashin kunya da kuma masifa.   Da haka ta canja musu hirar sannan ta karɓi ledan hannun Saliman suka fita daga building ɗin zuwa waje inda Hafiz yayi parking. Wayam babu su babu alamarsu sai wasu tsiraran motoci da kuma Keke Napeps da suke ficewa da mutane daga asibitin tunda lokacin visiting patients ɗin ya wuce. Juwairiyya ce ta ɗauko wayarta ta danna kiran Hafiz tana cewa, "To ina suka yi?" Hafiz yana ɗaukan wayar ya fara magana,"Riya dama yanzu nake da niyyar kiranki wani abu ne ya taso mana cikin gaggawa muka tafi amma ga Abbati yana zuwa zai mayar da ku gida. Ina fatan hakan ya miki?" Yayi maganan cikin sanyin murya kamar yaron da yayi laifi yana neman tuba. Wani sanyi ne ya ratsa zuciyar Juwairiyya tana tunanin ta yaya zata iya fushi mai tsawo da mutum kamar Hafiz? Mutumin da yake treating ɗinta kamar ita ce kaɗai mace a duniya kuma baya son fushinta? "Babu komai Bee, zamu ƙarisa gidan Saliman idan ka gama abun da kake yi sai ka biyo ka ɗaukeni mu koma gida." "Good girl. Sai na dawo." Kafin ya kashe wayar tayi saurin dakatar dashi da cewa,"Bee, ya naji muryarka wani iri, lafiya kam?" Tana saurara yayi ajiyar zuciya kana yayi murmushi mai sauti ya ce, "Har na daina mamakin yanda kike gane canji a tattare dani daga sauraran muryata kaɗai. I'm fine sai na dawo zamu yi magana." Bata musa mishi lallai sai ta ji me yake damunshi ba saboda ta lura kamar ma driving yake yi, sannan ta san ba zai ta6a ɓoye mata damuwarshi ba kuma kamar yanda yayi alƙawari, yana dawowa gida zai faɗa mata kuma da shi da ita zasu zauna su magance matsalarsu ba tare da kowa ya sani ba. Sallama suka yi ta juyo tana kallon Salima wacce ke waya har tana rage tsayinta idan tana magana, hakan yasa Juwairiyya ta gane cewa da Muhammad ne domin shi kaɗai take bawa wannan girman kamar zata nitse cikin ƙasa. Salima tana gama wayar ta mayar da ita cikin jakarta ta dubi Juwairiyya da ke waige-waigen ta ina zata hango mai ɗaukan nasu domin zaman asibitin har ya fara gundararta. "Zamu ƙara minti kaɗan domin Muhammad ya aikeshi kasuwa zai sayo karkashi zan mishi tuwo." Faɗin Salima tana gyara tsayuwarta. Wani takaici Juwairiyya ta ji domin ta lura Muhammad sam baya tausayin Salima, tunda ya kwanta rashin lafiya tare dashi take kwana kuma a hakan da safe zata koma gida ta mishi karyawa ta bayar a aiko mishi kafin nan ƙaninshi zai zauna dashi, da azahar zata dawo da abincin rana har dana dare wanda wai shi gogan baya cin abinci iri ɗaya sau biyu a rana. To idan ta zo tun azahar ɗin shine baza ta koma ba sai washe gari da safe, kuma ko ta koma gidan ba hutawa zata yi ba abinci zata dafa ta ƙara dawowa dashi.   To duk wannan ɗawainiyar da tayi mishi meyasa yau ba zai iya mata haƙuri ya barta ta huta ba? Anya mutumin nan yana da tausayi kuwa? Har ta buɗe baki zata yi magana sai kuma ta rufe domin yawan maganar ma bashi da daɗi, domin ita Saliman zata ga kamar faɗa take son haɗasu, sannan ita ta ganshi tace tana so kuma take son zama dashi a haka ba tare da ta yi ƙoƙarin canja musu Tafiyar tasu ba. Sannan Juwairiyyan ta sani idan ta yawaita magana da kusheshi wataƙila Saliman zata ji haushinta saboda har ga Allah ita ma baza ta so taji wani yana aibata Hafiz ɗinta ba. Wannan karon Salima ce ta canja musu hiran ta kawo musu hiran cikinta da ya shiga wata na uku amma tana nan garau babu rashin lafiya babu laulayi kamar ba ciki ne da ita ba. Ai kuwa ta taɓowa Juwairiyya gurin da yake mata ƙaiƙayi domin tana son duk wata hira da za'a sako maganar yara a ciki saboda tana son haihuwa, gashi yanzu shekarar aurensu ɗaya kenan da Hafiz amma ko ɓatan wata bata taɓa yi ba. Salima kuma sun shiga wata na shida kenan amma gata da ciki har na wata uku, ko dai ita juya ce bata haihuwa? Tana yawan yiwa kanta wannan tambayar wanda har ta kai bata ɓoyewa Hafiz damuwarta ba, shi kuma as usual kwantar mata da hankali yayi har yana tsokanarta da cewa dama bai gama moreta ba ta ƙara wasu watannin kafin ta ɗauki ciki. Ire-Iren wannan barkwancin Hafiz ɗin yasa ta rage nuna mishi damuwarta tana kuma addu'ar Allah yasa ta samu ciki ta riƙe ƴaƴanta a hannunta itama.   Minti goma da haka Abbati ƙanin Muhammad yayi parking a gefensu ya fito ya ƙarɓi abun hannunsu ya shigar cikin booth kana ya shiga motar suka wuce gidan Saliman kamar yanda suka tsara.   Wani gida madaidaici da ke unguwar Jekadafari  suka shiga wanda nan ne gidan Salima da Muhammad, Abbati ne ya fita ya buɗe musu gate kana ya dawo cikin motar ya shigar da su harabar gidan mai ɗaukan mota ɗaya. Suna tsayawa wata budurwa mai taya Salima aiki mai suna Nanayo ta fito daga cikin gidan ta musu sannu da zuwa tare da karɓan kayan abincin daga hannun Abbati ta shige dasu ciki bayan Salima ta umurceta da ta yanka karkashin ta kuma ɗaura mata ruwan tuwo. Sallama tare da godiya suka yiwa Abbati wanda ya ƙara fita da motar domin kaiwa mai ita. A falon Salima daya gaji da haɗuwa suka sauƙa wanda yake cikin tsafta ga ƙamshi sai tashi yake yi a ciki, tuni Juwairiyya ta cire gyalenta ta ajiye a gefe tana sauƙe ajiyar zuciya irin ta gajiya. "Wash Allah na." "Oh mutum sai sakalci. Tsakaninki da Allah aikin me kika yi yau da har kike cewa kin gaji?" Faɗin Salima tana ciro kayan cikin ledan tana ware wanda zata shigar kitchen da kuma wanda zata kai ɗakinsu a gefe.   Dariya Juwairiyya ta yi. "Baza ki gane ba. Amma in kina da miji kamar Hafiz kullum a gajiye zaki dinga jinki."   Shewa Salima tayi har da tafa cinya tana dariya. "Da alama ku bakwa gajiya da wannan harkan. Mu sai mu yi sati biyu ma wallahi wani abun bai shiga tsakaninmu ba musamman in ya kwanta rashin lafiyar nan. Wani lokaci ina so amma sai inyi shiru gudun kar in 6ata mishi rai idan na nema."   Fara'ar da ke fuskar Juwairiyya ce ta ɗauke domin ta tsani ta ga ana kwara ko cutar mutum alhali babu yanda ta iya. Ta lura duk hiran da zasu yi da Salima matuƙar maganan Muhammad ta shigo ciki sai ranta ya ɓaci saboda halinsa kaff da yake gwadawa matarsa babu na ɗauka. Tana kuma jin tausayin Saliman domin ta lura har da sonshi yake ɗawainiya da ita, wanda har ta kai bata iya ganin laifinsa. "Kin san kowa da halittarsa, wataƙila shi ba mai son yawan sex bane." Cewar Juwairiyyah wanda zata iya rantsewa wannan shine karo na farko data taɓa kare Muhammad bata kusheshi ba idan an gwada mata halinsa. To yaya zata yi? Yawan kusheshi a gaban matarsa zai iya jawo wani matsala tsakaninsu don haka tun suna asibiti ta yiwa kanta alƙawarin daina hakan tunda ita wacce take cikin rayuwar bai dameta ba, kuma a hakan suke zaman auren ba tare data nuna mishi bata son hakan ba. Murmushi Salima tayi tana cigaba da ware kayan. "Shima haka ya faɗa, yace inyi haƙuri da yanda na sameshi ba yin kanshi bane." "Ohh dama har wani haƙuri yake baki? Wallahi na ɗauka bai taɓa furta kalmar haƙuri ga kowa ba tun da yake. Ikon Allah, ashe idan kuka keɓance soyayya yake nuna miki mu kuma kin bar mu da jin tausayin ana takura miki." Juwairiyya ta ƙarisa maganan cikin mamaki tana murmusawa don har wani relief ta ji a zuciyarta. "Shiyasa kika ga ba komai ya mini nake ɓata rai ba, sometimes ya kan nuna mini kulawa sannan babu abun dana nema na rasa a gidan nan, shi dai ki barshi da saurin hawa idan aka yi abunda baya so." "Dama tsakanin mata da miji sai Allah, wanda kuma ya shiga tsakaninsu shi zai ji kunya." Juwairiyya ta furta ba tare data daina murmushin ba. Suna hiransu har Salima ta gama aikin nata ta sunkuci trolley ɗin tare da sauran tarkacen ta nufi ɗakin Muhammad sannan ta fito suka kwashi na kaiwa kitchen suka yada zango a can suna hira Juwairiyya na tayata girkin. Sune basu gama tuwon ba sai da aka kira sallan isha suka yi sallah sannan suka ci tuwon, bayan sun gama suka fara kallo Juwairiyya na recommending wa Salima wasu zafafan Korean series akan ta nema zata ji daɗin su.   Takwas da rabi suka ji ƙarar buɗe gate ɗin gidan mota ta shigo wanda suka ayyana a ransu mazajensu ne suka dawo, tun kafin a kashe motar wayar Salima tayi ƙara tayi saurin ɗauka tare da yin ƙasa da murya ta fara gaishe da wanda yayi kiran nata. "Ya jikin naka? Da fatan baka jin komai?" "Ki zo ki haɗa mini ruwan wanka." Ya faɗa ba tare da ya amsa gaisuwar tata ba, kafin ta amsa ma ya kashe wayar.   Juwairiyya ma wayarta ce tayi ƙara ta ɗauka cikin ɗoki da kuma murmushi a fuskarta tace, "Bee." "Awanni kaɗan da rabuwa da ke amma nayi kewarki. Gani a waje ki fito mu tafi gida." Lumshe idanunta tayi cike da annushuwan yanda yake nuna mata ƙauna a fili babu 6oye-6oye. "I missed you too. Bari in fito yanzu." Da haka ta kashe wayar ta dubi Salima dake jiranta ta gama wayar don ta mata magana. "Ba dai tafiya zaku yi ba?" Ta tambaya tana riƙe ƙugunta wanda yin hakan ya fallasa tumbi da kuma manyan hips ɗinta, da yake Salima irin matan nan ne chubby, farare kuma kyawawa masu jikin hutu don iyayenta suna da wadata, sai gashi kuma data tashi aure Allah Ya haɗata da ɗan lukuti irinta duk da cewa bata kaishi ƙiba da tumbi ba. "Wallahi tafiyan ne. Allah ya bashi lafiya sai kuma gani na gaba." Faɗin Juwairiyya tana yafa gyalenta kana ta ɗauki wayarta. "Ina son miki rakiya har waje amma Muhammad ya sakani aiki kar yayi ta jirana ban mishi ba. Kiyi haƙuri don Allah." Ta ƙarisa maganar tana marairaice fuska. "Wallahi kar ki damu babu komai I understand. Sai anjima kar shima ya gaji da jirana." Da haka suka yi sallama Juwairiyya ta fita daga gidan ta samu Hafiz a waje a cikin motarshi. Tana shiga ya jawota jikinshi ya fara kissing ɗinta tana dariya tana kaucewa. "Laaa me haka? Irin wannan ambush kamar kayi shekara baka ganni ba." Ta sa hannu ta riƙe kanshi da yake kwantarwa kan ƙirjinta. "Ina gwada miki irin kalar kewarki da nayi ne. Ya kike?" Ya zuba mata mayun idanunshi da suka canja kala dalilin abun da ya faru tsakanin su, duk da cewa cikin motar akwai duhu kaɗan bai hana Juwairiyya gano fitina a kwayar idanunshi ba. "Lafiya kalau." Kawai ta iya cewa dashi domin itama tuni ya canja mata yanayi saboda ta zama rainon Hafiz don ya mayar da ita kalarsa tuntuni. "Mu tafi?" Ya tambayeta cikin sarƙewar murya. "Yes Bee." Nan take ya tayar da motar suka fita daga unguwar suka fara tafiya akan babban titi zuwa unguwarsu. "Zan mana take away me zaki ci?" Ya faɗa yana ƙoƙarin karya kwana zai shiga wani restaurant da ke nan bakin hanya. "A koshe nake domin naci tuwo a can, da yake miyar karkashi suka yi shiyasa ban ɗauko maka ba saboda baka ci." Gyaɗa kai Hafiz yayi kana yayi parking ya fita zuwa cikin restaurant ɗin Juwairiyya ta bishi da ido cike da wani zazzafan sonshi dake fisgarta. Tafiyarshi ma kaɗai abun kallo ne domin bayan kyan sura da yake dashi, Hafiz ya san wankan da ya dace da shi.   Tana zaune a cikin motar tana kwatanta irin son da take mishi ya dawo ya miƙa mata ledojin hannunsa ta kar6a ta ajiyesu a seat ɗin baya. "Na saya miki ice cream ki sha yanzu kar ya narke." Ya tayar da motar ya fita daga harabar restaurant ɗin, ita kuma cikin murna ta ɗauko ice cream ɗin tare da mishi godiya ta fara sha suna hira har suka iso gida. Yana gama cin abincin ya jawota jikinshi suka fara hira har lokacin baccinsu yayi suka kwanta. Kanta dake kan damatsanshi ta ɗaga kaɗan tana duban fuskarshi tace, "Bee menene ya faru da kai ɗazu? Kace idan ka dawo zamu yi magana."   "Juwairiyya akwai maganar da nake so mu yi da ke amma bana son ki d'aukeshi da zafi ko kuma ki mini mummunan fassara don girman Allah. Kina ji na?" https://www.wattpad.com/story/286189663?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_reading&wp_page=library&wp_uname=amerrly&wp_originator=22UCP3G1XlTWnQof8RLLhEnGEraPiUaFHVmje7x6ztppyuMxuAbQeX%2B5E8vWHz3xuLa5QFovcwjtYpH2f1CVPBuVKyNHvB62dyAtnx8cYRlSnEVu27donXzr4lRYGR5P Mum Fateey 👌 TAFIYAR MU Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) Marubuciyar Matar Ƙabila Ruwan Zuma da Fatu A Birni (2) Hafiz Isma'il shine ɗa na huɗu a cikin mahaifiyarsa wacce ta kasance mace tilo wajen babanshi, sai ƙannenshi uku mata da duk sun yi aure suna ɗakin mazajensu, yayunshi uku kuma duk maza ne kowanne da iyalinsa. Hafiz mutum ne mai ilimin addini da kuma boko sannan yana da kyawawan halayen da yasa mutane su ke son hulɗa dashi. Yana gama NYSC ya samu aikin gwamnati inda ake biyanshi salary mai tsoka wanda cikin ikon Allah ya tara ya sayi fili yayunshi suka dafa mishi yayi gini mai kyau na gani na faɗa. Hafiz ya haɗu da Juwairiyya Ahmad ne wata rana da ya raka childhood friend ɗinshi Muhammad wani unguwa. Yana zaune shi kaɗai a cikin mota yana jin waƙa yana kuma danna wayarsa ya ɗago fuskarsa don ya gani ko Muhammad ya fito daga gidan da ya shiga amma bai ganshi ba, juya kanshi da zai yi gefen hagu ya hango wasu ƴan mata huɗu sun fito daga wani gida suna hira suna dariya, hankalinsa ne ya koma kan wata budurwa chocolate colored wacce ita ce ta ƙarshen fitowa daga gidan tana gyara hijabinta tana cewa ƙawayen nata su jirata ta musu rakiya zuwa bakin titi. Hakan ya tabbatar mishi cewa nan ne gidansu, kenan ziyara suka kawo mata.   Har suka zo suka wuceshi idanunshi na kan oval face ɗinta wanda yake cike da annuri ta kasa daina murmushi. Sai da suka ɓace mishi da gani ya rufe idanunshi yana hasko fuskarta mai ɗauke da manyan idanu irin nashi da kuma hanci daidai fuskarta, abun da ya fi ɗauke mishi hankali shi ne lips ɗinta da suke full ta shafa musu lip gloss sai sheƙi suke yi har yana jin ina ma ita ɗin tashi ce. Yana zaune a cikin motar ta dawo ita ɗaya ta shige cikin gidan tare da kulle ƙofar ba tare da ta gane cewa ana kallonta ba. Shiganta ke da wuya Muhammad ya fito ya shiga motar suka kama hanyar gida yana yiwa Hafiz hira wanda shi hankalinshi na kan yarinyar daya gani wanda zai iya rantsewa ya kamu da sonta ne at first sight. "Lafiyanka kam? Ina ta magana ka yi shiru ka shareni." Faɗin Muhammad cikin hasala. "Wata yarinya na gani ta burgeni matuƙa kuma wallahi in har na bincika na ji tana da hali mai kyau zan aureta." "Su kuma ƴan matan da kake waya kana chat dasu fa?" Ya harareshi ta gefen ido. Dariya Hafiz yayi ya sosa kai ya ce, "Duk cikin su babu matar aure sai budurwar soyayya. Zamu yi soyayya kam tsantsa amma ni nasan ba aurensu zan yi ba saboda bana son mace mara kamun kai da rashin aji. Amma ka ga yarinyar nan dana gani? Ina kallon fuskarta na gane ba shashasha bace she is a wife material. Yanzu dai kai zaka shige mini gaba tun da naga alamar ka san makwabtan gidansu yarinyar ka tambaya mini halinta." "Babu wanda zan je in tambaya wani abu, kuma gidan da kaga na shiga gidan wani distant relative ɗin Babanmu ne ya aikeni gurinsa nima ban ta6a zuwa ba sai yau." "Don Allah kar mu yi haka da kai mana." Hafiz yayi saurin faɗa cikin kwayewar fuska yana kallon Muhammad. "Mallam ka kalli gabanka kar ka juyemu a cikin kwalbati. Zan yi tunani a kai." Washe gari da yamma sakaliya Hafiz da abokin nashi suka isa ƙofar gidan su Juwairiyya suka aika yaro yayi kiranta bayan Muhammad ya faɗa mishi sunanta a binciken da yayi na dole. Tana fitowa ta samu Hafiz a tsaye suka gaisa ya gabatar da kanshi tare da faɗa mata dalilin zuwanshi babu ɓata lokaci domin shi aurenta yake son yi. Bayan ta ja mishi aji akan cewa bata tsayawa da samari sannan ya roƙeta da girman Allah kan ta bashi number wayarta kafin ya gabatar da kanshi gurin iyayenta. Kamar bata so ta bashi numbern, a nan yake faɗa mata tare da abokinshi yake wanda suna hangoshi a cikin mota a gaba dasu amma ko sau ɗaya bai waiwaya ba. Hafiz ne ya kwala mishi kira Muhammad ya juyo rai a 6ace kamar an mishi dole. "Ka zo ku gaisa mana." Hafiz ya faɗa yana roƙanshi ta cikin ido don kar ya kwafsa mishi. "No I'm good." Faɗin Muhammad flatly kana ya juyar da kanshi.   Hafiz haushi da kuma kunya ce ta cikasa wanda bai ƙara minti biyu ba Juwairiyya ta mishi sallama ta shige gida akan cewa mamanta zata mata faɗa idan ta ga ta jima.   A mota Hafiz yayiwa abokin nashi tatas kan cewa ya wulaƙantashi shi dai Muhammad yana shiru bai ce komai ba, ƙarshe da yaga Hafiz ya fusata da gaske sai ya bashi haƙuri yace zai gaisheta idan suka sake haɗuwa. Abun da basu sani ba shine ita Juwairiyya tun a lokacin ta ji ta tsani Muhammad domin bata son duk wani abu da ya danganci wulaƙanta mutum. Daga ganin suturun jikinsu da kuma motar da suka zo dashi ta gane suna da wadata in dai ba arowa suka yi ba, amma hakan bashi zai sa abokinsa ya wulaƙantata ba don bata kai su kuɗi ba. Duk da cewa Hafiz ya burgeta amma halin abokinsa yasa ta ji baza ta iya kulashi ba, hakan yasa da dare da yayi ta kiranta ta ƙi ɗauka har ya gaji ya daina.   Washe gari da safe ta fito daga gidansu zata tafi islamiyya, da yake ta gama secondary school wata uku da suka wuce kuma mamanta ta hanata cigaba da karatu wai aure zata mata ta samu Hafiz rakuɓe a katangar gidansu da alama ita yake jira da fito. Yana ganinta ya sha gabanta fuskarshi abun tausayi da alama ko wanka bai yi ba ya fito. "Laifi ne na miki kika ƙi ɗaukan wayata?"   Tsabar mamaki kasa magana ta yi domin wannan abun da yayi a littafin Hausa ne kaɗai ta ji ana yi wato saurayi ya kasa runtsawa har sai ya shawo hankalin buduwarsa. "Ko dai ban miki bane tun farko sai ki faɗa mini ba wai ki bani numbernki sannan ki ƙi kulani ba."   Ganin ana wucewa ana kallonsu ga kuma uwa uba hakan da yayi na nuna damuwarsa a kanta yayi matuƙar burgeta, domin ita tana son a nuna mata kulawa da soyayya don haka ta buɗi baki ta ce, "Na yi bacci da wuri ne. Sorry."   Ajiyar zuciya ya sauƙe kana ya dafa ƙirjinshi saitin zuciyarshi ya ce, "Har na ji sanyi a zuciyata, we cool?" Murmushi ta yi don ta lura yana yawan saka turanci a maganarsa wanda ba forcing ɗinshi yake yi ba irin ta gane ya iya turanci, a'a ta tabbatar haka ya saba domin ko sau ɗaya bata ta6a kamashi da murɗewar harshe grammatical error ba. "Yeah, we are cool. Bye." Ta faɗa tana ratsewa ta gefeshi don kar ya sakata latti a sakata wanke banɗaki.   Bata yi taku biyar ba ta ji wayarta na ƙara ta zaro daga cikin jakarta domin tasan babu mai kiranta a wannan lokacin sai mahaifiyarta hala tayi mantuwa ne a gida zata kai mata asibiti inda take aiki, amma ganin numbern Hafiz wanda bata yi saving ba yasa ta juyo ta dubeshi yana tsaye a inda ta barshi da waya a kunnenshi alamar shi ɗin ne dai ya kirata.   Murmushi yayi ganin ta tsaya tana kallonshi kana ya mata nuni da wayar hannunta wanda hakan yasa ta farfaɗo ta amsa wayar gami da karawa a kunnenta, muryarshi ta fara ji yana cewa, "I know ko nace ki zo ki shiga mota in kaiki school ɗin baza ki yarda ba saboda it seems your parents raised you right, so Allah ya kiyaye hanya Ya kuma baki ilimi mai albarka. Take care." Yana gama faɗin hakan ya kashe wayarsa kana ya shige motarsa ya tafi ya barta a gurin zuciyarta na bugawa da ƙarfi ba don tsoronshi ba sai don a take a wannan lokacin ya sace zuciyarta ya tafi da ita. A ranar Hafiz ya zo da yamma bayan ta amince mishi amma bai zo tare da Muhammad ba, gefe guda kuma yasa an mishi binciken halayenta aka kuma sanar mishi cewa tana da hankali da nitsuwa kamar yanda yayi tsammani. Bai yi wasa ba ya turo iyayensa gurin dangin Babanta aka bashi izinin hira har aka musu baiko.   Tun rana ta farko da Hafiz yazo da Muhammad bai ƙara zuwa dashi ba har aka saka ranar aurensa da Juwairiyya wacce ta kaucewa duk samarinta tace shi zata aura. Sai ana ribibin auren nasu ne suka haɗu wanda shi Muhammad ɗin ne ya ɗaga mata gaisuwa amma tayi kamar bata ji shi ba.   Da yake tana yawan jin labarin shi gurin Hafiz yasa ta gane shi ɗin abokinshi ne na ƙut da ƙut, sannan ta fahimci yana da girman kai amma ita neman abu ta yi a gurinshi da zai wulaƙantata? Har aka yi bikin tsakaninta da Muhammad babu jituwa, sannan ko bayan auren bai je gidansu ba sai da suka yi wata biyu wanda ta lura Hafiz ne ya matsa mishi suka zo nan ma bai ci komai a gidan ba ya tafi. Juwairiyya Ahmad ita kuma ƴa ce ta farko a gurin mahaifiyarta sai sauran kannenta mata biyu da namiji ɗaya. Babansu ya rasu tun suna yara hakan yasa mahaifiyarsu ta zauna a cikin gidan mijin nata tare da ƴaƴanta ba tare da ta sake aure ba, kuma ta ɗauko mahaifiyarta tsohuwa da take ƙauye suna zama tare da yake ita ma mijin nata ya rasu. Cin su da shan su duk a kan mahaifiyarsu yake wacce take Nurse a wani Maternity wanda jajircewarta da kuma jimawanta tana aiki yasa aka bata matsayin Matron na asibitin gaba ɗaya. Hakan yasa ta samu ƙarin albashi ta kuma cigaba da kula da ƴayanta har ta aurar da Juwairiyya. Wata shida da aurensu suna zaman lafiya da nunawa juna so Muhammad ya tayar da maganar auren da zai yi. Ko da Hafiz ya nunawa Juwairiyya hoton matar da Muhammad ɗin zai aura sai ta buɗi baki ta ce, "Dama shi lukuti ai sai lukuta ce zata iya dashi. Wannan idan aka aura mishi yarinya ƙarama rana ɗaya zai karya musu ƴa da nauyinsa." "Riya baki da kunya fa, me ya kai tunaninki har can daga nuna hoto kawai?" Faɗin Hafiz yana harararta da gaske. "Sorry na taɓo rabin ranka." Ta mishi gwalo kana ta tashi ta shige kitchen don ɗaura musu abincin dare. Bayan auren Muhammad da matarshi Salima su Hafiz suka je gidan amaren a satin farko bayan Hafiz ya tilastawa Juwairiyya zuwa. Tar6an da Salima ta musu yasa Juwairiyya ta sassauto domin ta yi zaton itama Saliman zata yi girman kai ne irin mijinta, ai kuwa kafin su tafi hira suke yi sosai har suka yi musayar number a kan zasu dinga ziyartar juna akai-akai. Hafiz ya ji daɗin wannan ƙawancen nasu yayin da Muhammad kuma ya nunawa matarsa baya son hulɗarta da Juwairiyya yayi yawa, bisa la'akari da ya yi na cewa tana da raina mutane da kuma rashin da'a. Sai dai duk da cewa Salima na bin umurninshi amma wannan karon bai samu damar rabata da Juwairiyya ba, ƙarshe haƙuri yayi ya barsu sai dai Cold War da ke tsakaninshi da ita bai ragu ba sai ma gaba da yake yi. Tun bayan aurensu Muhammad ya fara kwanciya rashin lafiya domin Ulcer da Typhoid da suka mishi rufdugu, Hafiz na yawan bashi shawarar ya rage cin junk foods da suke sakashi ƙiba suke kuma ƙara mishi cuta amma baya ji, da yake haka ya taso a gidansu suna cin duk abun da suke so babu mai hana su. Wannan kenan. Present Juwairiyya ce ta gyara kanta data kwantar a kan damtsen Hafiz ta ce, "Ina jinka." Shiru yayi kamar ba zai ce komai ba sannan ya fara magana a hankali kamar mai raɗa. "Kin tuna ɗazu na faɗa miki abun gaggawa ya taso shiyasa muka tafi bamu jiraku ba?" Gyaɗa kai ta yi tana haɗiye wani yawu mai kauri don zuciyarta bugawa ta fara yi haka kurum ta kasa nitsuwa dalilin Hafiz bai ta6a cewa zasu yi magana sannan yayi using wannan tone ɗin ba. "Bayan mun fito ne na ga jikin Muhammad a sanyaye na tambayeshi me yake damunshi tun da na lura ba rashin lafiyar ce matsalar shi ba a lokacin. Riya ashe muna tafiya da mutumin nan ne amma shi har ya cire rai da tsawon kwana yana ganin lokacinshi ya kusa, hawayen da naga yana yi ne yasa nace mu shiga mota kar mutane su yi ta kallonshi babu daɗi ana magana. A nan ya nemi mu bar asibitin mu je wani guri zai yi magana da ni, bayan mun fita muka samu wani guri muka tsaya. A nan yake faɗa mini wata magana wacce har yanzu na rasa yaya zan ɗauketa."   Shiru ta yi tana jiransa ya ƙarisa maganan lokaci ɗaya kuma zuciyarta ta sassauto ganin akan Muhammad za'a yi maganar ba wai a kan Hafiz ba. "A nan ya sanar dani cire rai da yayi da rayuwa wanda bai bari muka rabu ba sai da yasa na yarda da wani alƙawarin da yace in ɗaukar mishi." "Alƙawrin menene?" Ta samu kanta da tambaya don a take zuciyarta ta dawo da saurin bugawar da take yi ɗazu.   Tunani kala-kala kuwa babu wanda bata yi ba kwakwalwarta na bata wild ideas na wannan alƙawarin da mijin nata ya ɗauka ciki kuwa har da cewa idan matarshi ta haihu Hafiz ya riƙe mishi ɗan kar a barwa Salima saboda mugunta. Ya saka na mishi alƙawarin duk ranar da ya mutu in auri matarsa Salima in kuma riƙe mishi duk abun da zata haifa kar yayi agolanci a wani gida."   Cikin azama juwairiyya ta tashi zaune har tana buge bakin Hafiz da kanta ba tare da ta sani ba, sosai ya ji zafi har ya ɗanɗani jini a bakinshi amma yayi shiru bai nuna mata ba saboda abun da yake gabansu yafi ƙarfin zogin ciwonsa. "Wannan wace irin banzar magana ce?!" Ta tambaya tana aikawa Hafiz wani mugun kallo wanda har lokacin yana kwance bai ko motsa ba yana ganin yanda fuskarta ta rikiɗa lokaci guda da tsantsan kishi, ɓacin rai da kuma wani abu kamar tsoro a kwayar idanunta. "I swear Juwairiyya ban san me yasa yayi wannan maganar ba, kuma kukan da yake tayi kamar ƙaramin yaro yasa na ɗauki wannan alƙawarin ba don na taɓa kawo hakan a cikin raina ba. Sannan gani nayi cuta ba mutuwa bace, don yana yawan rashin lafiya bashi zai sa ya gane mutuwa zai yi ba saboda wani yana kwance ma a gadonshi lafiyarshi kalau za'a zare ransa idan lokacinsa yayi. Wani yana tafiya yake faɗi ya mutu yayin da wani abinci ma yake ci zai yi lomarsa ta ƙarshe ya kwanta ya mutu. Na amsa mishi ne don ya daina kukan da yake yi kuma ya bani tsoro ne saboda ban ta6a ganin yana kuka cur-cur da idanuwanshi irin haka ba, ko lokacin da mahaifiyarsa ta rasu bai yi kukan da yayi yau ba. Juwairiyyah tsakanina dake babu 6oye-6oye, shiyasa nake faɗa miki duk abun da ya shafeni bana son na 6oye miki daga baya ki ji ranki ya 6aci kiyi zaton ban ɗaukeki da muhimmanci ba."   Shiru Juwairiyya ta yi amma tuni idanunta sun fara tara kwalla, wani irin tsana Muhammad yake mata da tun kafin ya mutu zai bada wasiyyar a ƙuntata mata ta hanyar mijinta ya auri matarsa wacce ta kasance ƙawa a gareta? Shanye hawayen idanun nata tayi ta hanyar kallon saman ɗakin ta buɗe bakinta a hankali tana jan numfashi ta nan tana kuma furzarwa. Sai da ta daidaita kanta sannan ta dubeshi har lokacin zuciyarta bai daina bugu ba wannan karon tambaya zata mishi wanda take tsoron amsar da zai bayar. "What if in ya mutun? Zaka cika alƙawarin ne ka auri Salima?" Ƙura mishi ido tayi tana ganin ruɗu a fuskarsa wanda ko bai faɗa ba ta gane amsarta. "Juwairiyya ki bar maganan nan haka, shima da yayi maganar bana tunanin yana cikin hankalinshi ne sannan who does that for God sake? Ki ɗauki abun tamkar ba'a yi ba, don ni wallahi har na fara dana sanin faɗa miki saboda ban yi tsammanin zaki ɗauki abun da zafi har haka ba. I thought zaki ɗauki hakan ne a matsayin shirme mu wuce gurin." "Zaka aureta ko ba zaka aureta ba?" Ta share duk zancensa ta ƙara mishi tambayar a karo na biyu.   Sai a lokacin Hafiz ya gane da gaske ta ɗauki maganar da zafi ya tashi zaune ya kai hannu zai jawota jikinshi ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga mishi hannu tace, "Just answer me." "Riya I told you...." "Hafiz don Allah ka amsa mini. Please." Ta yi saurin katseshi muryarta har ɓari take yi wanda har sunanshi da bata iya kira a gabanshi yau sai da ta kira.   Sunkuyar da kanshi yayi ƙasa kana ya ɗago a hankali yace, "He made me promised tare da rantsuwa da Allah akan zan nemi aurenta sai dai in ita ce ta ƙi amincewa sannan zan haƙura, and I know itama ba zata yarda ba saboda ƙawancen da yake tsakaninku." "Baka sani ba dai, babu macen da zaka je mata da zancen aure ta ƙi amincewa da kai Hafiz. Kana da qualities ɗin da mace baza ta iya bari ka wuceta ba." Sai a lokacin kafaɗun Juwairiyya suka sauƙa alamar defeat domin a yanda take faɗawa Salima labarin kyawawan halayen Hafiz zai yi wuya idan ya je mata da zancen ta gujeshi sai dai in ta ji kunyarta ne ta ƙi amincewa. Kwanciya ta yi nesa da Hafiz wanda yana ganin hakan yaji babu daɗi a ranshi domin bai ga abun tashin hankali a cikin wannan zancen ba, shi wanda ya kawo maganar ma yayi imanin tsoron mutuwa ce tasa yayi maganar amma ba don zai mutun ba duk da cewa cikinsu babu wanda yake da guarantee ɗin kai tsufa. "This is all stupid, da maganar da reaction ɗinki da kuma fushin da kike son ki mini Juwairiyya. But I will let you sleep on it zuwa gobe mu ga ko kema zaki yi tunani irin nawa. Sai da safe." Yana faɗin hakan shima ya kwanta zuciyarsa a cunkushe bayan ya kashe musu wutan ɗakin. https://www.wattpad.com/story/286189663?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details&wp_uname=suwaibamuhammad36&wp_originator=WLgoX5LRZroSfrBXS%2FvJrrmcD4YgBmuG2AZVLtFDowb3gKdO5KroKIOwg6bGrFV8QQ8fuBBc7AoDDvlLV9Nvw3NykipgrNBJaNLKpKqXzAcz2XEZcJ%2FQyfCE1gepfEdH Mum Fateey 👌 TAFIYAR MU Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) Wattpad https://my.w.tt/IKR4zCOYfbb (3) Washegari da safe Hafiz da Juwairiyya suka tashi dukkanninsu jiki a sanyaye. Ƙarfe goma na safen lahadin ta gama musu breakfast suna ci cikin silence kamar ba su ba, lokaci-lokaci tana satar kallonshi tana ganin yanda yake juya taliya da sauce ɗin a jikin fork wanda sai ya yi kusan minti ɗaya kafin ya kai bakinsa, bai gama cin abincin ba ya tashi ya kai plate ɗin kitchen ya fito yana cewa, "Zan je gidanmu, daga nan kuma akwai wani abokina da ya shigo gari zamu haɗu. Zan dawo bayan la'asar, akwai abun da kike buƙata ko kike so in dawo miki dashi?" "Babu komai. Allah Ya dawo da kai lafiya." Kawai ta faɗa tana kallonshi cikin ido tana jin zaman nasu a haka har ya gundureta. "Ameen. Take care, sai na dawo." Da haka ya sa kai ya fice.   Ajiye fork ɗin hannunta tayi tana sauraran duk motsinsa a farfajiyar gidan, bayan ya kunna mota yayi warming ɗinta na wasu mintuna sannan maigadi ya buɗe mishi gate ya fita daga gidan. Tana jin ƙarar rufe gate ɗin idanunta suka ciko da hawaye kana suka silalo kan ƙuncinta. Wai me yake damunta ne? Cewa aka yi Hafiz zai yi aure ko kuma ta ga Muhammad ɗin ya mutu? Sannan ta yaya ma Salima zata yarda ta auri Hafiz alhali suna ƙawance da ita? Menene laifin Hafiz? Shin ta mishi adalci ko kuma tayi aiki da hankalinta wajen auna wannan zancen? Me amfanin wannan cold shoulder da take bashi? Shi yayi laifin ne ko Muhammad? Bata kyauta masa ba, idan tayi haka bata mishi adalci ba, sannan hakan da tayi zai sa a gaba ya 6oye mata damuwarsa saboda tana amfani da emotions ɗinta ba kwakwalwarta ba. Babu mai laifi kuma mugu irin Muhammad da ya nemi a yi mata kishiya, sai yanzu ta ƙara tabbatarwa tsanan da yake mata ya wuce yanda take tsammani. While Hafiz did not deserve any of this!   Wannan duk tunani ne da Juwairiyya take yi a cikin zuciyarta tana jin tausayi tare da ƙaunar mijinta na ƙara shiga zuciyarta, ta wani gurin kuma tsanar Muhammad ne ya yawaita har tana jin da zata ganshi da ta kwaɗeshi da mari. Sannan ko mutuwa Muhammad ɗin yayi ba zata yarda Salima ta aure mata miji ba, kai Muhammad ɗin ma ba zai mutu ba, daga yau zata fara sakashi a addu'a Allah Ya bashi lafiya Ya ƙara mishi tsawon rai. Ita kuma wannan shine alƙawarinta.   Kafin la'asar Juwairiyya ta gama girki ta gyara gidanta ko'ina sai tashin ƙamshin yake yi tana jiran a kira sallah ta shiga wanka, ana fara kiraye-kirayen sallah kuwa ta shiga banɗaki ta sillo wanka sannan ta yi sallah ta zauna a gaban mirror ta fara ƙawata fuskarta. Jim kaɗan da haka ta gama tsara kwalliyar ta sanya Atamfa riga da siket ɗinkin Borno Style da yayi matuƙar karɓan jikinta mai kyawun shape. Falo ta koma ta nemi kujera ɗaya ta haye ta ƙame tana jiran maigidanta Hafiz.   Ƙarfe huɗu da rabi Hafiz ya dawo ya tarar da Juwairiyya ta kunna kallo a falo tana zaman jiranshi. Ajiyar zuciya ya sauƙe domin ganinta kaɗai kan tafiyar da wani kaso mai tsoka na damuwarshi da kuma gajiyarshi. Da murmushi a fuskarshi ya mata sallama ta amsa cikin fara'a kamar yanda kullum ta saba sannan ya shigo ya ajiye abun hannunshi a kan center table dake tsakiyar falon yana cewa, "Da ba don ina kishinki ba da na kai ki inda ake zaɓen sarauniyar kyau ta duniya, amma ni ɗaya nake son ganin wannan kyau da kwalliyan." Murmushi tayi mai ƙayatarwa har kumatunta na lotsawa don ba ƙaramin daɗi take ji idan Hafiz ya furta kalamai irin haka a gareta ba, ko ba komai bata yi asaran zama a gaban mirror tana shafe-shafen ba, domin kuwa wanda aka yi kwalliyar domin shi ya gani kuma ya yaba. "Bee kana ƙara zugani." Ta faɗi hakan don bata gaji da jin kalaman yabon daga gareshi ba. "Babu zugi Riya, shin kina kallon kanki a madubi kuwa? Da kina ganin me nake gani da baki kawo kokwanto a ranki ba, you are the most beautiful woman I have ever seen and you are mine, mine alone." Da haka ya miƙar da ita tsaye ya jawota jikinshi kana ya sumbaci goshinta affectionately. Irin wannan soyayyar da Hafiz yake nuna mata yasa Juwairiyya bata iya dogon fushi dashi sannan take toshe duk wata ƙofa da zai sa ranshi ya ɓaci balle har wani rashin fahimta ya jawo su nisanci juna. Gashi dai ita ce ta mishi laifi jiya da dare da safe kuma ya fita da ɓacin rai amma da ya dawo gareta sai ya nuna tamkar babu wani abu da ya faru tsakaninsu, haka rayuwarsu ta fara tun farko basa yarda fushi ko ɓacin rai ya yi tsawo har a ɗauki lokaci ana zaman doya da manja, basu iya ba kuma bata fata su fara irin hakan. Hafiz ɗinta mutum ne mai haƙuri da kuma sanin darajar ƴa mace, sannan zata iya rantsewa cewa Hafiz yana ɗaya daga cikin few mutanen da suka karanci halayyar mace suka kuma san yanda zasu bi da ita. Sauƙin halinshi yasa itama ta zama mai sauƙar da kai a gareshi da mishi biyayya ba tare da ta nuna gazawa ba. "I'm sorry da abun da ya faru jiya, I know it's not your fault amma zafin kishi yasa na kasa fahimtarka har ina ɗaga maka murya. I'm sorry Bee, I'm so sorry." Ta faɗi hakan bayan ta ɗago da kanta da yake manne a faffaɗan ƙirjinshi cikin sanyin murya da kuma nuna tsantsar nadamar laifin da ta yi. "Ya wuce Riya, na san son da kike mini ne yasa kika kasa ɓoye kishinki kuma kika kasa fahimtata, ko don wannan soyayyar da kike nuna mini ya isa yasa in miki uzuri. Kin yi hakan ne don kina sona and I should thank you for that." "Shikenan ka daina fushi kuma ka yi haƙuri?" "Dama ni ban yi fushi ba, haƙuri kuma na yi tun a jiya kafin in kwanta bacci. Mu bar maganan haka, feed me." "Right away Sir. Amma kafin nan ka rage kayan jikinka sai ka ci abincin da kyau." "Jiya kuwa na ji wani wa'azi a kan mu maza mu daina zama da singlets da boxers a gida saboda matanmu suna so mu dinga yi musu kwalliya a gida ba wai sai zamu fita ba, to gashi yanzu ke kuma kina cewa in je in rage kayan jikina ba kya son ganin kwalliyan nawa ne?" "To ai kayi da safe na gani kuma na yaba, yanzu kuma ka dawo cikin gidanka ka fi buƙatar ka samu sarari ka sha iska, but amma I would'nt mind watarana ka mini kwalliyar ka zauna a gida inyi ta kallonka." Ta ƙarishe maganan tana kashe mishi ido ɗaya. "Lallai bakya son a ci abincin nan da wuri." Hafiz ya faɗa yana jin kasala na shiga jikinshi. "Wani abinci ɗaya?" Ta tambayeshi innocently har tana kyafta idanunta cikin jan hankali. "Riya, you are driving me crazy. Mu je in baki saƙo a ɗaki the cooked food can wait." "Yes Sir."   Bayan kwana biyar da haka Juwairiyya ce kwance a kan gadon da ke cikin ɗakinta tana danne-danne a wayarta ta jiyo ƙarar doorbell ɗin falonta. Ta dakata kaɗan tana saurara ta sake jin an danna, hakan ya tabbatar mata baƙi ta yi kuma close one's domin in baƙi ne wanda maigadinsu bai sani ba baya buɗe musu har sai sun kirata a waya ta mishi magana. Babu tunanin komai ta miƙe tsaye kana ta zurma hijabi a kan riga da wandon da ke jikinta ta fita falon tana cewa, 'Ana zuwa' ganin wanda yake bakin ƙofar ya sake dannawa. Tana isa bakin ƙofar ta leƙa ta peekhole domin ta hango wanda ya ke bakin ƙofar.   Zuciyarta ce ta buga da ƙarfi da ta hango Salima tsaye tana danna wayarta daga bisani ta kara a kunnenta wanda hakan yasa Juwairiyya ta tabbatar ita take kira, gashi abun haushi ta yi magana wanda ta san Saliman ta jiyota da ba zata buɗe ƙofar ba, cikin seconds uku wayarta da ke ɗaki ta fara ringing ta ji kamar ta kwaɗata da ƙasa tsabar haushi. Tun ranar da Hafiz ya zo mata da wannan mummunan zancen ta ji bata son ta ci gaba da hulɗa da Salima don haushinta take ji duk da cewa bata mata laifin komai ba, kuma wataƙila ma ita bata da masaniya akan shirmen da mijinta yayi. Ta san tabbas Saliman ta zo jin ba'asi ne domin kuwa ta daina yi mata reply a WhatsApp, haka kuma ko ta yi tagging ɗinta a wani social media a irin post ɗin ƙaruwa ko kuma na ban dariya bata reply. Jiya kuma ta mata missed calls biyar bata ɗauka ba to gashi yau ta tako da ƙafarta don ta ji me yake faruwa. Kamar ta yi ihu haka ta buɗe ƙofar Salima ta shigo tana kallonta sama da ƙasa. Da kyar ta ƙaƙalo murmushin dole ta mannawa bakinta sannan ta matsa gefe kana ta maida ƙofar ta rufe tana cewa, "Sannu da zuwa. Mu isa." "To ai ko baki ce in isa ba zan isa." Faɗin Saliman tana ratseta ta wuce cikin falon ta sami guri ta zauna kan ta cire hijabinta ta ajiye a gefe. "Kunna mini A.c don wallahi zafi nake ji na haɗa gumi." Juwairiyya da take jin kamar ta shaƙeta ta isa gurin A.c ta kunna da remote sannan ta kunna musu tv da dawo ta zauna tana ganin yanda Saliman take fifita da hannunta don rigarta har ta fara jiƙewa da zufa, 'ƙattin banza kawai' Juwairiyya ta faɗa a zuciyarta tana nufin Salima da Muhammad. "Kafin in faɗi abun da yake raina zan miki tambaya ɗaya don Allah, shin na miki laifi ne?"   Yanda Salima ta yi maganar ya bawa Juwairiyya tausayi ainun nan da nan kuma ta ji kunya ya rufeta domin ta aikata abun da bata son mutane su dinga yiwa wani wato wulaƙanci. Laifi bana kowa bane sai Muhammad, amma zafin kishi yasa ta hukunta Hafiz sannan gashi Salima ma ta samu rabonta, me yasa ta kasa haƙuri har ta bari laifin wani ya shafi innocent souls irin waɗannan mutane biyun? "Me kike gani?" Ta mayar mata da tambayan ba don bata san amsar ba. "Kin sani ba sai na faɗa miki ba, kawai ki bani amsa." "Babu abun da kika mini wallahi." Juwairiyya ta faɗi iyakan gaskiyarta cikin nadama. "To meyasa kika daina mini reply a social media kuma ina ganinki online, sannan jiya na kiraki duk baki ɗauka ba kuma baki biyo baya ba. Ko dai rakiyar da ban miki bane last time da kika je gidana ya ɓata miki rai?" Sai da Juwairiyya ta yi dogon tunani sannan ta tuna cewa ranar da ta je gidan Salima bata mata rakiya zuwa bakin ƙofa ba saboda Muhammad ya kira ya sakata aiki. "Ya Salam! Gaskiya you think low of me. Yanzu fisabilillahi akan hakan ne zan share ki?" "Kin yarda kenan kin share nin? To me na miki bayan nan? Saboda lafiya muka rabu da ke, ko dai Muhammad ne ya ɓata miki rai?" Ajiyar zuciya Juwairiyya ta yi sannan ta dubi Salima ta buɗe bakinta zata fara magana sai kuma ta fasa. Me zata ce mata? Tana tsoron mijinta ya rasu ta aure mata nata mijin? Ba zata faɗa mata ba ma balle har ta je tayi tunani a kai ta ajiye a ranta cewa in Muhammad ya mutu zata auri Hafiz! In tayi haka ta zama sakarya. Abun da ya kamata ta yi shine ta ƙara ƙarfafa zumuncinta da Saliman ta yanda ko mijinta ya mutu zata ji kunyar aure mata miji sannan duk wanda ma ya bata wannan shawarar zata iya ɓatawa dashi. "You can say that amma ya wuce kuma ba laifinki bane. Ki yi haƙuri kaina bisa wuyata." Ta ƙarisa maganan tana murmushi har kumatunta na lotsawa ciki. "Don dai ke ce zan yi haƙuri amma wallahi da wata ce da tuni nima na fita a harkarta." Faɗin Salima tana hararar Juwairiyya cikin wasa. Da haka suka ɓarke da hira tamkar babu abun da ya taɓa giftawa tsakaninsu, a nan ne Salima take bata labarin cewa har Muhammad ta saka ya kira Hafiz don ta zaci ko bata da lafiya ne, a nan ya sanar da su lafiyarta kalau. Hakan ya sa Salima ta nemi izini a gurin Muhammad kan cewa tana son zuwa yace ba zata je ba. "Kin san Allah ban taɓa mishi musu ba sai jiya, rufe ido na yi nace mishi ina mishi biyayya amma this time around kar ya mini haka. Ina tunanin ya ji tausayina ne shiyasa yau da safe ya ce in shirya in zo." Juwairiyya kaɗa kai kawai ta yi tana murmusawa domin ta san ba ƙaramin so Salima take mata ba da har zata yi musu da Muhammad a kanta ba wanda idan ya ajiye kara bata iya tsallakewa. To ta yaya zata iya cin amanarta ta aure mata mijin da take so? Salima baza ta taɓa iyawa ba, tana da kawaici da kuma haƙuri. "Ni dai har gobe ina baki haƙuri ba zan gaji ba." "Trust me ya wuce. Amma nan gaba kika sake mini haka zaki ga the other side of me."   Da haka suka kwashe da dariya dukkansu aka shiga wata hirar ta daban. Sai yamma liss Salima ta koma gidanta don Muhammad ya kirata ya ce ta dawo gida ta ɗaura musu girki ya fasa barinta sai dare kamar yanda ya faɗa da safe. Tana fita Juwairiyya ta kaɗa baki ta ce, "Allah Ya haɗaki da wahala, ga rashin lafiya da kuzarin ɗa namiji, ga ci kamar gara sannan ga banzan hali kamar rainon fir'auna. Allah Ya kawo miki sauƙi." Abun da Juwairiyya bata sani ba shine sauƙin na zuwa wa Salima, sauƙin ma mai ɗorewa. Mum Fateey 👌 TAFIYAR MU Suwaiba Mubammad (Mum fateey) (4) Hafiz ne zaune cikin motarshi a yayin da yake tuƙi ya nufi gidanshi, lokaci-lokaci yana murmusawa in ya tuna surprise ɗin da zai nunawa Juwairiyya. Yana gama parking ya fito ya nufi ƙofar falon ya sanya key ya buɗe ya shiga da sallama a bakinshi.   Shiru ya ji babu kowa a falon don haka ya tasamma cikin bedroom ɗinsu inda ya tabbatar zai samu Juwairiyya. Yana shiga ya samu nan ma bata ciki amma da alamar wanka take yi domin yana iya jiyo ƙaran ruwa a banɗaki. Buɗe ƙofar banɗakin yayi kana ya tura kanshi yana kallon yanda take wanka hankalinta kwance. "Yau kam dai ba zaka firgitani ba, na ji shigowar motarka." Faɗin juwairiyya tana mishi gwalo lokaci guda kuwa tana cigaba da wankanta. Shiru yayi bai yi magana ba sai ma tsayawa da yayi yana kallonta kamar yau ne karon farko da ya taɓa kallonta haka. Seconds kaɗan da haka Juwairiyya ta watso masa ruwa a bazata wanda ya jiƙa mishi fuska har da gaban rigarsa, ai kuwa ta kyalkyale da dariyar cin nasara domin ta jima tana son watarana ta kama shi off guard kamar yanda ya sha yi mata. Shima dariyar yake yi ya juya cikin ɗaki yana cire rigar yana cewa, "Eh lallai kin koya, ina ni kika watsawa ruwa kika jiƙa mini shadda mai tsada?" "Maganin pervets kenan. Kuma ba zan iya ƙirga sau nawa ka mini haka ba, yau kuma Allah Ya yi na rama." Juwairiyya ta amsa tana fitowa daga banɗakin ɗaure da towel a ƙirjinta fuskarta cike da annishuwa. "Magana ta ƙare ai, tunda kin koyi wannan zan canja salo." "Bring it on pervert. Sannu da dawowa, you are early today." Ta ƙarisa maganan tana isa gaban mirrow don tsantsane jikinta. "Ki gama shiryawa ki sameni a palour, ina jin yunwa sosai ba zan iya jira har sai kin gama shiryawan ba." "Okay, shikenan. Akwai salads a cikin fridge ka fitar please." "To Hajiya." Da haka ya sa kai ya fice daga shi sai singlet da boxers a jikinshi. Yana tsaka da cin abinci ya jiwo ihun Juwairiyya wacce ta fito tana tsalle-tsalle ta rungumeshi ta baya sai jijjigashi take yi duk a cikin murna. “Riya zaki sa in amayar da abun da na ci da wannan jijjigan naki.” Ya faɗi hakan yana mai kamo hannayenta ya ɓanɓaresu daga jikinshi. "Bee, wayyo Bee. A cikin aljihunka na gani. Wayyo nagode, nagode." Ta koma gefe tana karanta papers ɗin da ke hannunta bakinta har kunne. Zuba mata ido kawai yayi yana ganin tsantsar farin cikin da take ciki, she appreciate duk abun da ya mata komin ƙanƙantarshi kuma sai ta nuna farin cikinta ƙarara, hakan ya sa duk lokacin da ya samu dama yake faranta mata da gifts don kawai ya ga wannan murnar a fuskarta. Sai da ta gama karance duk wasu details na cikin papers ɗin sannan ta matso ta zauna kusa dashi fuska a washe tana cewa, "Suka ce nan da kwana uku zamu fara zuwa classes ɗin. Bee ka mini bazata ka kuma faranta mini. This is my dream coming true. Nagode, Allah Ya faranta maka kamar yanda nima kake faranta mini." Hafiz da tun ɗazu ya koma ga cin abincinshi yanzu kuma tauna ƙashi yake yi yace, "Ameen. Har yanzu dai na kasa fahimtan bayan kin iya girki amma kuma kina son ƙara koyan wani. A gurina abincinki ya fi mini na kowa daɗi." "Bee, shi girki da ka gani yana da sirrika kala-kala wanda yasa wasu experts suka koyi iliminshi sannan suke koyar da mutane. Ba lalle ne in mace ta iya girki ana ci da daɗin rai ya zama ita ta san sirrikan ba, sau nawa ne zaka ga macen ta ake yabon girkinta watarana a kasa cin abun da ta girka musamman in ta haɗa spices ɗin da ba'a son tarayyarsu? Ko kuma ta yi girki amma nama, kayan ciki, kifi ko kaza suna wari duk da kayan ƙamshin da aka saka musu? Ko kuma ka ga an ci abinci lafiya kalau amma daga baya ya zama food poisoning a dawo ana gudawa daga baya? To wannan ilimin sai an koyar da mutum kafin ya sani. Shiyasa nake son shiga catering class ɗin in koya sannan in koyi sauran dishes ɗin da ban iya ba." "Umm da gaskiyanki amma babu abun da na gane har yanzu.” Ya faɗa yana dariya. Da paper ɗin hannunta ta kwaɗe kanshi a hankali wanda kafin ta ankara ya kamo hannun ya riƙe kana ya fara mintsininta a hankali wanda is enough ta ɗan ji zafi kaɗan. “Bee da zafi fa!” Ta faɗa tana mutsu-mutsun kwatan kanta tana dariya. "Wai ki ji yanda nake ji ne.” Da haka ya saketa yana dariyar mugunta. A ranar da dare Juwairiyya ce kwance akan cinyar Hafiz tana chat a wayarta yayin da shi kuma yake danne-danne a laptop ɗinshi suna hira jefi-jefi. "Bee, yanzu na faɗawa Salima ka sakani a classes ɗin catering, itama tace tana so zata tambayi Muhammad ya sakata, Allah Ya sa dai kar ya hanata kaga sai mu dinga zuwa tare." “To ke wa yace ki faɗa mata har ta saka rai?” “Wallahi muna hiranmu ne nake faɗa mata zan fara zuwa koyan girki shine tace itama tana so akan bari ta tambayi mijinta.” “Ku dai kuka sani.” Juwairiyya ta yi dariya kana ta cigaba da danna wayarta can ta ja dogon tsaki ta ce, “Dama jikina ya bani zai hanata wallahi, wannan mutumin ba’a abun kirki da shi. Don Allah Bee ka mishi magana ya barta.” “Riya kenan! Yanzu sai in je in sameshi ince ya bar matarshi ta je koyan girki? Ni zata yiwa girkin ko ni na aureta? Duk friendship ɗin mu bama shiga harkan gidajen juna, kowa yana tafiyar da gidanshi ne yanda yake so. Bama yiwa juna shishshigi a al’amura irin haka.” Juwairiyya dai turo baki tayi gaba kana ta cigaba da chatting da Salima inda take bata haƙuri har da alƙawarin duk abun da ta koyo zata koya mata. Kwana uku da haka ta fara zuwa koyon girki a Ailisco Catering Class da ke nan cikin Gombe. Kwana biyu da farawarta ta bi gidan Salima daga can gurin koyon girkin, mai aikin Salima ce ta buɗe mata ƙofa ta gaisheta sannan ta faɗa mata matar gidan tana cikin ɗakinta. Kai tsaye Juwairiyya ta isa ɗakin ta yi knocking aka yarje mata ta shiga. A kan gado ta samu Salima ta kwanta amma fuskarta babu walwala kamar na kullum. “Hajiya me yake damunki, ko dai baby ne?” Juwairiyya ta tambayeta tana zare gyalen jikinta ta ajiye a gefe kana ta zauna tana fuskantarta. “Yau kuma na yi laifin da har a gaban cousins ɗinshi ya mini faɗa, ni wallahi faɗan bai dameni ba ma kamar a kan laifin.” “Hmm, yau kuma me ya faru?” “Girki na yiwa wasu ƴan'uwanshi da suka kawo mishi ziyara daga Dukku, na musu shinkafa da miya amma suka gagara cin naman miyan don hamami da yake yi. Wallahi ba zan wulaƙantashi da gangan ba, sannan ban san hakan zai faru ba da nayi wata dabarar." Salima ta ƙarisa maganan kamar zata yi kuka. "Wai cewa ya yi kin wulaƙantashi?" "Mai sauƙin ma na faɗa miki." "Kiyi haƙuri Salima sannan ki ci gaba da addu'a Allah Ya sanyaya zuciyarshi. Amma batun naman yau aka mana lecture a kanshi wallahi, don ita mai koyar mana ta yi eBook ga masu son gyara abincisu ba tare da sun shiga classes ɗin ba. Kwanan nan zata yi launching eBook ɗin wanda in ka biya da wuri ₦1000 ne, in aka yi launching ɗin kuma zai dawo ₦3000. Ga number ɗinta ki mata magana a whatsapp sai kiyi payment. 09123227777 AiLisco Venture." "Tunda ban samu shiga classes ɗin ba wanna ma will help wallahi, amma iyakacin abun da zata koyar kenan?" "Gaskiya ban san adadin abubuwan da zata koyar ba amma ina recommending wa amaren bana or teenager da basu da experience na girki. Basu iya gyara nama ba har yayi causing food poisoning, ta ce akwai su knife skills, cutting techniques, methods da kuma pro tips. In taƙaice miki da duk wani basic knowledge na kitchen wanda ya kamata mu sani." "Nagode ƙawata, Allah Ya bar mini ke." "Amin Amin, dama abun da muka girka yau na kawo miki don na san masu ciki da kwaɗayi." Nan da nan fuskar Salima ta washe ta jawo take aways ɗin tana buɗewa, ganinta cikin farin ciki ya sa Juwairiyya jindaɗi da kuma jin tausayinta. Salima deserve someone da ba zai yi taking ɗin haƙurinta for granted ba. Bata bar gidan ba sai yamma liss Hafiz ya zo ya ɗauketa suka koma gida. Bayan kwanaki da haka ta gama classes ɗin wanda ta koyi komai da aka koya musu sai dai AiLisco tace su cigaba da yin meals ɗin akai akai musamman snacks don hannunsu ya faɗa, don bature ya ce practice makes perfect. Yau ya kama ranar Friday Juwairiyya ce a kitchen tana haɗa breakfast Hafiz kuma yana can bedroom yana shirin tafiya office. Yana gamawa ya fito ya sameta tana juya pancakes ɗin da ke kan frying pan. "Ni dai tunda aka koyo girkin nan ban sake cin tuwo a gidan nan ba." "Are you complaining?" Ta faɗa tana mai bashi plate cike da pancake wanda aka zubawa pure zuma yayi puff dashi yayi kyau. "Wane ni? Kawai na yi missing ɗin tuwon ne, and I love every bits of abun da kike girka mini." "Bee ɗan siyasa, kana da wayo wallahi. To yau zan yi tuwon da rana, zaka dawo ka samu yana jiranka." Ta faɗa tana kashe gas cooker sannan suka koma dinning table da ke cikin falon suka zauna suna cin abincin suna hira. Yana gamawa ya miƙe ya tafi ta rakashi har bakin motarshi sannan ta dawo ta cigaba da cin nata tana danna waya. Ƙarfe biyu da wasu mintuna Hafiz ya dawo Juwairiyya ta tarɓeshi amma sai ta ga kamar baya jin daɗi. "Bee lafiya na ga jikinka a sanyaye?" "Kai na ne yake ciwo tun ɗazu a office. Na sha magani amma yanzu kam na san bacci nake buƙata. Gashi ɗazu Muhammad ba lafiya na rakashi asibiti, amma dai basu bashi gado ba." "To Allah Ya baka lafiya Bee. Ka je ka kwanta ko zuwa la'asar ne zan tasheka." Ta faɗi hakan tana mai karɓan abubuwan hannunsa kana ta yi gaba yana binta a baya. Bata ankara ba ta ji an make mazaunanta ta juyo tana hararanshi, shi kuma da yayi aika-aikan dariya yake yi. "Nace miki bani da lafiya shine kika yi gaba kina nuna mini abubuwa ko?" "Mutum mara lafiyan ne idonshi zai je can? Dama sakalcinka ne ya tashi kake son baccin rana." "Na ji." Kawai ya faɗa yana taɓa wani sashe na jikinta. "Bee." Ta furta a lokacin da suke shiga ɗaki. "Na bari, amma ina tashi zan baki saƙo." Ya ƙarisa maganan yana kashe mata ido ɗaya. Murmushi kawai ta bishi dashi kana ta taimaka mishi ya cire kayan jikinshi sannan ya kwanta ita kuma ta koma falo don bata jin bacci. Wayarta ta ɗauka ta kira Salima tana tambayarta jikin Muhammad don a yanzu bata son ko da wasa ta ji bashi da lafiya. “Jiki da sauƙi za'a ce, gashi can dai a ɗaki ya kwanta." Dariya Juwairiyya ta saka wanda daga ita har Salima sun yi mamakin hakan. "I'm sorry, amma wallahi ba dariyar rashin lafiyarshi nake yi ba, ɗazu Hafiz ya dawo shima wai kanshi yana ciwo ya kwanta yana bacci. Shine na yi picturing ɗin mu a matsayin Nannies abun ya bani dariya." Wannan karon itama Salima ta dara kana suka yi sallama. Da haka Juwairiyya ta cigaba da danna wayarta wanda karatun littafin Hausa take yi, lokaci-lokaci tana murmushi idan aka zo gurin soyayya wanda sai take ganin kamar ita ce da Hafiz ɗinta. Tana nan zaune har aka kira sallan la'asar aka shiga sallah sannan ta tashi don ta gabatar da nata kuma ta tashi Hafiz. "Bee ka tashi lokacin sallah ya yi." Ta faɗi hakan a yayin da take shiga banɗaki. Bayan ta gama alwala ta fito ta samu ko motsawa Hafiz bai yi ba, hakan yasa ta saɗaɗa a hankali zata watsa mishi ruwan hannunta sai ta sameshi idonshi a rufe yana murmushi. "Allah Ya taimakeka domin na tuno baka da lafiya. Ka tashi mu yi sallah." Shiru bai amsa mata ba, hakan yasa ta watsa mishi ruwan kaɗan a fuskarshi amma ko firgita bai yi ba haka kuma bai motsa ba. Nan take ta ji wani tsoro ya ɗarsu a zuciyarta ta sa hannu ta fara jijjigashi amma kamar bashi da rai. "Wayyo Allah na, Hafiz! Ka tashi bana son wannan wasan wallahi. Ka bari, ka bari, ka bari." Tana faɗan hakan tana jijjigashi amma babu alamar rai a tattare dashi. Ihu ta kwala mai ƙarfin gaske nan take kuma jikinta ya fara rawa ta kamo kafaɗunshi don ta miƙar dashi zaune amma ya fita nauyi sai ta gagara yin hakan. Wani ihun ta sake kwalawa kamar wacce ta zauce kana ta fara kiran sunan Allah. "Allah ka rufa mini asiri, Allah kar ka mini haka. Wayyo Allah na!!" Fita tayi da gudu zuwa gurin maigadi wanda tun ihunta na farko ya jiyota amma bai je ba, sai dai ya tsaya on alert, ihunta na biyu kuwa yasa ya zo bakin ƙofar falon ya fara kwankwasawa yana kiran sunan ubangidan nashi tunda yana gida. Tana buɗe ƙofar ta kamo hannunshi tana nuna mishi ɗaki tana cewa, "Baba... Hafiz... yana ciki baya motsi. Hafiz ya mutu." Kwace hannunsa yayi ya shiga ɗakin da gudu ita kuma tsabar ruɗewa ta ɗauki wayarta ta kira Salima wacce ringing ɗaya ta ɗauka amma kafin ta yi magana Juwairiyya ta rigata tace, "Ki tayar da Muhammad ya zo ya kai Hafiz asibiti baya motsi, don Allah ya zo da sauri kar ya mutu." Tana gama faɗin hakan ta shiga ɗakin inda ta samu Baba a durƙushe a gaban gadon inda kan Hafiz yake yana kallonshi with so much pain on his face. "Baba ya mutu ko?" Ta tambaya tana jin zuciyarta kamar ana toye mata shi, idanunta kuwa tuni suka fara zubar da hawaye babi-babi. "Ki kira yayunshi su zo su kaishi asibiti likita zai dubashi." Wayarta da ke hannunta ta duba ta kira babban yayanshi wanda dama a unguwar Tumfuren yake bashi da nisa da su. Yana ɗaukan wayar ta fara magana, "Yaya Aminu ka zo ka kai Hafiz asibiti bashi da lafiya kuma baya motsi." "Subhanallahi. Me ya sameshi?" "Bayan sallah Jumma'ah ya dawo yace mini kanshi na ciwo shine ya kwanta ya daina motsi, ni da Baba maigadi kuma baza mu iya ɗagashi ba." Ta ƙarishe maganan tana jan majina tana goge fuskarta da ɗan kwalinta. "Bani wayar in mishi magana." Faɗin maigadin yana miƙa hannunshi ta bashi babu musu. "Alhaji sai dai haƙuri, amma Hafizu ya rigamu gidan gaskiya." Ya faɗa a hankali amma Juwairiyya ta ji sarai. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un." Shine abun da Juwairiyya ta yi ta maimaitawa bayan ta durƙushe a gurin da take. Nan take kanta ya fara juyawa tana jin tamkar itama jan ranta ake yi dalilin mutane da ta fara kallo biyu-biyu zuwa uku, can kuma suka fara yawa har bata iya ƙirgasu. Can ta ji kamar ana saka mata hijabi zuwa can ta ji koke-koke kamar Umma ce mahaifiyar Hafiz. Daga nan kuma ta ji an ɗagata daga durƙushen an kaita ɗakinta bayan an lulluɓe fuskar Hafiz da mayafin da ta lulluɓeshi da zai kwanta bacci ɗazu. Hello dearest! Transform Your Cooking Skills, Banish Unpleasant Food Odors, and Prevent Food Poisoning Have you ever been put off by the unappetizing parts of chicken or the lingering odors from certain fish and chicken dishes? Perhaps you've encountered the off-putting residues from cow waste in some dishes. These issues can make mealtime less enjoyable and even contribute to food poisoning. Ga AiLisco ta zo da educative eBook ɗinta mai ɗauke da sirrin kitchen. Ku danna wannan link ɗin domin ku yi mata magana direct ta whatsapp https://wa.me/message/DR5SQZYEPBBEO1 ko kuma number wayarta (09123227777) Kar ku manta launch fee is ₦1000 only, in an wuce ranar zai dawo ₦3000. Ku yi sauri ku yi payment ɗinku tun yanzu. Mum Fateey 👌 TAFIYAR MU Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) 09023713064 Wannan littafi na kuɗi ne a ₦500 zaku tura ta wannan Bank account 5139579011 FCMB Suwaiba Babagana, ko kuma katin waya na Airtel a wannan number 09023713064, da number zaku yi amfani don nuna shaidar biya don a sakaku a paid group. Waɗanda basa son hayaniyar group zasu tura ₦650 don a dinga tura musu a private chat. Kar ku manta akwai sabon book da nake yi tare da wannan wanda shi kuma free ne mai suna CANJIN MUHALLI. Ku mini magana a number wayata don in sakaku a group da zaku dinga samunshi ko kuma ku duba Wattpad da ArewaBooks. Nagode. (5) Free page Kwanaki suka shuɗe suka dawo satittika, satittikan suma haka suka wuce suka dawo watanni. A hankali duk wasu alamu da zasu nuna ta taɓa rayuwa dashi suka fara ɓacewa. Bata sake ganin fuskarshi ba tun ranar da aka rufeshi da bargonta, sai dai a kullum yana cikin mafarkanta. Rayuwarta ta fara dawowa kamar da a lokacin da take budurwa a gidansu, zata ci zata sha amma tana cikin gida bata fita ko'ina. Komai ya dawo normal amma banda ita, domin kuwa bata jin kanta kamar yanda ta saba. Ya tafi ya barta da wani gurbi a zuciyarta da babu mai iya cikawa sai shi, Hafiz ɗinta. Tunaninshi yana bibiyarta a kowanne lokaci kamar baƙon da ba'a gayyaceshi ba. A ko'ina take sannan ko menene take aikatawa yana nan maƙale a zuciyarta da kuma kwakwalwarta wanda hakan yasa bata iya maida dukkan hankalinta akan abun da take yi. Da dare in ta kwanta idanunta zasu bushe daga ƙin yin bacci, zata shafe awanni tana tuno rayuwarsu wanda su suke gaskata mata cewa ta taɓa sanin shi. Da wannan tunanin zata tashi ta ɗauro alwala ta fara sallah tana nema mishi gafara a gurin ubangiji har kwakwalwarta ta nemi hutun dole ta sanyata baccin da bata yi niyya ba. ******** Salima ta haihu ta samu ɗa namiji wanda yau ake bikin suna amma Juwairiyya bata da niyyar zuwa. Tana kwance a ɗakinta ta jiyo sallamar yaro a tsakar gidansu, bata amsa ba don ba aikinta bane. Tunani take yi da Hafiz yana da rai da yanzu tana can gidan sunan tana shige da fice a matsayinta na matar abokin mijin mai jegon. Tana jin immediate ƙanwarta Sumayya ta amsa sallamar daga can bakin kitchen sannan ta bi yaron da tambayar dalilin shigowarshi. "Wai ana sallama da Juwairiyya a waje." "Je ka tambaya in ji waye." Jimawa kaɗan yaron ya dawo ya ce, "Wai in ji Hussaini ne wanda suka gama makaranta tare." Juwairiyya da take ɗaki ta ja wata doguwar tsaki tana jin kamar ta fita waje ta gaurawa Hussaini mari. Yaron ya rainata sosai yanda bata tsammani, zata iya tunawa shine mutum na farko da ya taɓa nuna yana sonta bayan ta gama takaba. Tsabar rashin kunyarshi har cikin gidansu ya shigo ya samu Mamanta wai ya zo yana sonta ta bashi izinin zuwa hira. Duk ransu ya ɓaci amma Mama bata nuna mishi a fuska ba ƙarshe tace ya je ya ƙara haƙuri sai mutuwar ta fita a ranta. "Wallahi in ya sake taka cikin gidan nan da sunan wai yana sona sai na sa yaran unguwa sun mishi wanka da kwata. Don uwarshi ni sa'arshi ce? Yaro ƙarami da shi wataƙila ma na fishi shine zai zo mini da maganar aure? To don ubanshi an ce mishi neman mijin auren nake? Kuma in zan yi auren in rasa waye zan aura sai kucakin yaro mara sana'a irinshi?" "Ina tunanin ya ɗauka a littafin Ruwan Zuma kuke, a ciki ne matar ƴar shekara arba'in (40) ta auri saurayi ɗan shekara ashirin da tara (29), suka yi ta soyewa wallahi har abin kunya yake bani." Faɗin Surayya ƙanwarta ta biyu wacce kwata-kwata shekarunta sha huɗu ne (14). Maman su da tayi kasaƙe tana kallonsu sai yanzu ta yi niyyar magana, da Surayya ta fara wacce sai da ta gama maganan sannan ta gane ta tafka uban kuskure. "Wato har yanzu baki daina karance-karancen littafin Hausan ba? Kenan duk nasiha da kuma faɗan da nake miki baki ɗauka ba? Laifina ne da na sayi waya na baki, ki tashi ki ɗauko mini wayar daga yau babu ke babu riƙeta har sai kin gama secondary school an kusa miki aure. Ina ce dama auren kike so shiyasa kike karatun soyayya? To ko yanzu wani ya zo yace yana sonki aurar da ke zan yi sai ki je can kiyi karatun da tushe." Kuka Surayya ta saka ta fara bawa Mamansu haƙuri amma ta kafe, ƙarshe ta zare mata ido ta ce in ta sake magana sai ta mata duka. Da haka ta tashi tana kuka ta tafi ɗakin baccinsu don ɗauko wayar tata. Nan ido ya dawo kan Juwairiyya wacce ta wani gefen ta ji daɗin karɓe wayar Surayya, domin watarana har ƙarfe biyun dare take kaiwa tana karatun novels wanda ta tabbatar ciki har da na batsa tunda ya zama tamkar ruwan dare a gurin marubutan online ɗin. Ta wani gefe kuma ta ji tausayinta domin in bata manta ba itama a baya Mama ta sha kwace nata tana ɓoyewa in tayi laifin da ya kai a hukuntata da haka, tana tunawa in aka kwace sai ta ji kamar ranta aka karɓe ta yi kuka har ta bonu kafin ta haƙura. "Ke kuma kika zauna kina ta ashariya a gabana ko? Mutum daga cewa yana sonki sai ki ce zaki tara yara su mishi wanka da kwata? Ke ƴar daba ce ko ƴar iskar unguwa?" Shiru Juwairiyya ta yi kanta a ƙasa tana wasa da ƴan yatsunta. "Ina tambayarki kina mini shiru." "A'a Mama." "To wallahi akul in ji ko baƙar magana kin mishi. Ki nemi yanda zaku rabu lafiya kar in kuskura in ji abun da zai ɓata mini rai, ba tarbiyyar da na baku ba kenan. Allah Ya gani nayi iya bakin ƙoƙarina kuma ina kan yi akan tarbiyarku har kika yi aure ana yabonki a cikin unguwar nan cewa kin fi sauran ƴan matan kamun kai. Baku tashi da uba ba amma ba'a zageku a dalilin rashin gurbinshi a rayuwarku ba. Kar ki ga kuma kin taɓa aure kiyi tunanin zaki ci gashin kanki a cikin gidan nan, as far as ni nake ciyar da ke, kike kuma zaune a gidana ni ce mai last say babu abun da ya canja." Sumayya mai bin Juwairiyya, tana da shekara sha takwas wacce a yanzu ta gama secondary school tana gefe tana jinsu, ita dama ba kasafai ake mata faɗa ba domin tana kiyayewa sannan kaff yaran Mama ita ce shiru-shiru. Autansu Walid kuma shine yake son gagaran Mamarsu, shekararshi yanzu goma sha ɗaya amma yawo ya saka a gaba sannan baya son karatu. Kuma duk dukan da zata mishi ba zai hana gobe ya ƙara abun da aka dakeshi a kai ba. Wannan kenan. "Adda Juwai wai Hussaini yana waje." Faɗin Sumayya daga can bakin ƙofar ɗakinsu. "A faɗa mishi na samu mijin aure har na ƙarɓi sadaki." Ta bata amsa a numfashi ɗaya. Dariya Sumayya tayi sannan ta wuce ta faɗawa yaron saƙon yayartata shi kuma ya fita don isar da nashi. Sai dai bai jima ba ya dawo. "Wai don Allah magana ɗaya zai faɗa mata ta yi haƙuri ta fito." Tun kafin Sumayya ta shigo Juwairiyya ta miƙe a hanzarce domin a yau tana son ta kawo ƙarshen rainin hankalin Hussaini, ta gane in ba ita ta sameshi suka yi magana ba zai yi wuya ya haƙura ya barta. A bakin ƙofa taci karo da ƙanwar tata, "Ohh ashe kin jiyo mu." "In ba saitashi nayi akan hanya ba yanzu zai buɗewa sauran ƙofar zuwa su dameni. Ba aure ne a gabana ba, kwata-kwata ma yaushe Hafiz ya rasu? Yanzu ne ma yake cikin wata na shida shine zai zo mini da maganar banza?" "Kiyi haƙuri, wasu mutanen basu da lissafi. Amma dai ki bishi a hankali kar yi abun da Mama zata miki faɗa." Bata amsa ba ta wuce waje tana rangaji domin ramewar da ta yi har yanzu bata maida jikinta ba. A ƙofar gida ta samu Hussaini jingine da gate ɗin gidan nasu yayi wata tsayuwa tamkar ciwon baya, shi ala Allah yayi hakan ne don ya burge Juwairiyya. "Gimbiya kuma tauraruwa cikin mata. Nagode kwarai da kika bani wannan damar na ga kyakkyawar fuskarki." "Shi ɗan aikan bai faɗa maka cewa na karɓi sadakin wani ba? Ko ƙarya kayi da ka aiko cewa magana ɗaya zaka faɗa mini mu rabu?" "Ashsha! Kin san Bahaushe ya ce matar mutum kabarinshi. Sau nawa ana taruwa don ɗaura aure amma ki ga an watse saboda Allah bai yi zasu zauna a rufin auratayya ba?" Wani malolon baƙin ciki ne ta ji ya zo ya tokare mata a maƙoshinta, so take ta kurma mishi ashar ta zagi uwarshi da ubanshi ta yanda ko labarinta ake yi zai bar gurin amma Mama ta mata katanga da aikata hakan. Don haka kamar zata yi kuka ta ce, "Hussaini ina ganin girmanka ina kuma tuna zaman da muka yi a school cikin aminci, don Allah ina roƙanka kar ka ɓata wannan zumuncin. Ba aure bane a gabana ba, in ma auren ne ba zan aureka ba dalilin na ƙarbi sadakin wani. Neman aure a cikin wani auren haramun ne kar ka saɓawa Allah don son zuciyarka. Na barka lafiya." Ta juya da niyyar shiga gida ya sha gabanta ya haɗe hannayensa guri guda. "Wallahi Juwairiyya tun muna makaranta nake sonki amma nasan kin fi ƙarfina shiyasa ban taɓa nuna miki ba, yanzu kuma da kike bazawara ni kuma nake saurayi na san akwai chance ɗin kasancewarmu tare kuma wallahi ba zan damu da maganar mutane cewa na auri bazawara ba. Ki ceceni ki karɓi soyayyata don wallahi na jima da sonki a birnin zuciyata." Yanzu kam ji take yi kamar ta rufeshi da duka har sai ya daina motsi, wani wawan kallo mai cike da tsana take bin shi dashi. A yanzu bata damu da duk hukuncin da Mama zata ɗauka a kanta ba, sai ta zage Hussaini zagin da ba'a taɓa mishi irinshi ba, zagin da ko a hanya ya ganta zai canja akalarshi. Ta buɗi baki da niyyar fara azalzalarshi motar Muhammad ta yi parking a ƙofar gidansu. Da ita da Hussaini tsayawa suka yi suna ganin lokacin da Muhammad ya buɗe marfin motarshi ya kwalawa wasu yara kira dake kan yashi suna wasa, da gudu suka iso gurinshi fuskar nan tashi kamar kullum a turnuƙe amma ba shine damuwarsu ba, ɗari biyu-biyu da zai basu in sun gama mishi aikin ne damuwarsu. Suka gaisheshi bai amsa ba, dama sun san za'a rina wai an saci zanin mai hauka. Nuni ya musu da booth ɗinshi ba tare da ya buɗe bakinshi ba, babu wani dogon bayani suka nufi bayan motar suka buɗe kana suka fara fito da kayan abincin da suke ciki suna shigarwa cikin gidansu Juwairiyya, ba kaya ne masu yawa ba illa ƙananun buhun shinfakar dafawa da ta tuwo, kayan haɗa shayi, sabulun wanka da wanki da kuma manja, mangyaɗa da maggi. Duk abun nan da ake yi Juwairiyya da Hussaini suna kallonsu amma shi ko kallo basu isheshi ba. Wani tunani Juwairiyya ta yi wanda yasa wani murmushi ya wanzu a fuskarta kana ta dubi Hussaini da ɗan damuwa a fuskarta ta ce, "Ga wanda na karɓi sadakin nashi, don Allah in ya fito ka nuna mishi gaisuwan rasuwa kawai ka zo ka mini, ka ganshi ƙaton nan wallahi in ranshi ya ɓaci dukanka zai yi." Muƙut Hussaini ya haɗiyi yawu kana ya dubi yanda Muhammad yake ƙoƙarin fita daga mota girman jikinshi na bashi wahala. Bayan ya fito ya miƙawa yaran ɗari biyu-biyu kamar kullum suka tafi murna fal a fuskarsu, abun ka da yaro, basu san cewa shimfiɗar fuska ta fi ta tabarma ba. Ganin ya nufosu fuska a tamke yasa Hussaini ya mata sallama ya tafi ba tare da ya tsaya sun gaisa ba, shi har cikin ranshi ya yarda Muhammad zai mishi duka, ina shi ina faɗa da wannan basamuden? "I see har kin fara tara zawarawa a ƙofar gidanku." Ya faɗa bayan ya iso gabanta. "Idan wannan ne ya kawoka kayi saurin tafiya don baka da amsa." "Salima ta haihu." "Ina sane." "Yau suna bikin suna." "Shima na sani." "Ta haifi yaro ɗa namiji." "Haka na ji." Da haka ta juya da niyyar komawa cikin gida amma ta tsinkayi muryarshi yana cewa, "Na saka mishi sunan abokina Muhammad Hafiz." Da haka shima ya juya ya koma motarshi don dama ya gaji da tsayuwar. Juwairiyya daskarewa ta yi a gurin tana jin kanta kamar ba'a duniyar take ba, wai da gaske Muhammad ya raɗawa ɗanshi sunan masoyinta Hafiz? Nan da nan sai ta ji kunya ya rufeta domin bata kyautata mishi duk da ƙoƙarin da yake yi a kanta. Sai dai tana juyawa ta ga yayi reverse ya tafi. Tun bayan rasuwar Hafiz ya koyi yi mata magana, ya mata ta'aziyya wanda daga shi har matarshi a gidan karɓan gaisuwar suke yini tun safe har dare har aka yi sadakan bakwai. Sannan ta samu labarin da Muhammad ɗin ya ga gawar abokin nashi kuka yake cur-cur da idanunshi har aka yi tunanin ƙin zuwa dashi maƙabarta don kar ya ga sa'ilin da ake saka abokin nashi a cikin ƙasa ya rasa hankalinshi. Sai dai babu wanda ya isa ya hanashi, ya je kuma tare da shi aka bunneshi bakinshi bai bar motsi ba har aka dawo yana mishi addu'a. Juwairiyya ta san Muhammad ba wani mai wadata bane amma ya ɗaurawa kanshi wahalanta, domin kuwa kowanne wata sai ya yi mata shopping na kayan masarufi daidai ƙarfinshi ya kawo mata ya kuma gaisheta. Daga nan ba zata sake ganinshi ba sai wani watan, abun mamaki shine ko sau ɗaya bata taɓa mishi godiya ba balle ta nuna a fuska cewa abun da yake mata yana taimakonta kwarai da gaske. Mahaifiyarta 'Mama' Nurse ce wanda kullum tana fita aiki da safe zuwa ƙarfe ɗayan rana, duk nauyin gidan na ci, sha, sutura, rashin lafiya da kuma abun da ya shafi makarantar ƙannenta a kanta yake babu mai taimaka mata. A hakan kuma ga kakarsu wato mahaifiyar Mama da kullum ake kashe kuɗi a kanta dalilin rashin lafiyan da tsufa ke kawoshi. Don haka wannan ɗawainiyan da Muhammad yake musu ba ƙaramin taimakon Mama yayi wajen samun sauƙin hidimar gidan ba. Kullum tana faɗawa Juwairiyya ta miƙa godiyarta amma bata da masaniyar ko sau ɗaya ita Juwairiyyan bata taɓa isarwa ba. Dalili kuwa shine, meyasa tun lokacin da Hafiz yake da rai baya mata magana ko amsa gaisuwarta sai da ya rasu zai nuna ya fi kowa tausayinta? Kuma bata nemi taimakonshi ba, jira take yi ta dawo hayyacinta ta fara sana'a don ta taya Mama kula da gidan. Aure kuma babu shi a babinta domin karatu take so ta fara a Gombe State University tun da daga unguwarsu Arawa sai makarantar ko da ƙafa zata dinga zuwa tana dawowa. Da wannan tunanin ta shige cikin gida ta samu Sumayya na tattara kayan tana kaiwa falon Mama wanda a da shine na Babansu. "Wannan bawan Allah bai manta da zaman amanan da yayi da abokinshi ba, Allah Ya biyashi da mafificin alkhairi." Faɗin Sumayya a lokacin da Juwairiyya ta tsuguna zata ware kayan shayin ta kai ɗakinsu domin Mama tace ta dinga ɗauka. Shiru ta yi amma a zuciyarta ta amsa, har ta miƙe da niyyar tafiya sai ta samu kanta da tsayawa ta dubi Sumayya da murmushi a fuskarta ta ce, "Hafiz ɗina dai ya yiwa takwara Sumayya, wallahi ko yanzu ban gama gaskatawa, ji nake yi kamar wasa yake mini." "Allahu Akbar!" Sumayya ta kama bakinta har tana jin hawaye na taruwa a idanunta. Itama Juwairiyya hawayen ne ya taru a nata idaniyar har suka kwaranyo kan ƙuncinta, saurin sharesu ta yi kana ta nufi ɗakin nasu don adana abubuwan hannunta. Minti goma da haka Sumayya ta gama girkin rana, hakan kuma yayi daidai da dawowar Mama daga aiki wacce ta kwaso gajiya ta nemi guri ta zauna a falonta aka kawo mata abinci. Tana cin abinci Juwairiyya ta shigo mata sannu da dawowa Mama ta amsa tana tambayarta ko ta ci nata. "Mama sai anjima zan ci bana jin yunwa yanzu." "Adda Juwai ki bata labarin abun alkhairin da ya faru." Faɗin Sumayya da take kwance akan kujera hannunta riƙe da wayarta tana chat da saurayinta da aka musu baiko. "Me za'a faɗa mini?" Mama ta kasa haƙura ta tambaya tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya. "Muhammad ne ya sakawa ɗanshi sunan marigayi Hafiz." "Allahu Akbar. Allah Sarki, mutumin nan ba ƙaramin so yake yiwa abokinshi ba. Allah Ya rayashi Ya sa ya ɗauko halin takwaranshi kyawawa, shi kuma Allah Ya gafarta mishi." "Ameen." Duk suka amsa cikin sanyin jiki. "Sai ki shirya ki je ki dubota da jaririn ki samu abun da zaki kai musu. Ƴan'uwan marigayin sun sani kuwa?" "Bana tunanin sun sani don da ƙannenshi sun kirani sun faɗa mini ko Ummarshi." "To ki kirasu ki sanar dasu, zai yi wuya su ji basu faɗa miki ba kam." Faɗin Mama domin ta san an yi zaman lafiya da mutunta juna tsakanin dangin Hafiz da ɗiyarta, wanda har yanzu suna zuwa dubata in an kwana biyu. Juwairiyya bata jima a gurin Mama ba ta koma ɗaki dama can ne gurin zamanta kamar matar Liman. Tana zaune tana tunanin me ya kamata ta yiwa Salima na fitan biƙi Sumayya ta shigo ta sameta. "Yanzu ke kina ganin me zan saya mata? Na san kaya kam iyayenta sun loda mata don masu kuɗi ne, haka sauran ƴan'uwa da abokan arziki. Ina son in yimata kyautan da zata yi amfani dashi kuma zata ji daɗinshi." Shiru Sumayya ta yi, can kuma fuskarta ta yalwatu da murmushi ta ce, "Babu kyautan da zaki mata yanzu ta ji daɗin shi irin Turaren wuta da kuma Humrah. Kuma shine zata yi amfani dashi ba zata kyautar ko ta sayar ba, kin san shi baya yiwa mace yawa sai dai ya mata kaɗan." "Amma kin kawo shawara wallahi. Yanzu ni da nake tunanin zuwa gobe ta yaya zan samu turaren wutan a ƙanƙanin lokaci haka?" "Ga Dukhan By Ain a Instagram 08088929221. A Abuja take kuma ana yabon turarenta sosai, don ina ganin yanda ake bada positive reviews a Highlights ɗinta. Kwanaki da aka yi auren ƙawata Salma a gurinta duk aka sayi su Turaren wutan, su Kulacca da Humrah. Bari in binciko miki page ɗin don ina following ɗinta, kuma na faɗawa Mama a gurinta za'a haɗa mini turarukana." Juwairiyya ta harari Sumayya cikin wasa tana cewa, "Yaran zamani baku da kunya wallahi. Yanzu baki ji kunyata ba?" "Ki ji Adda Juwai da wata magana, akan turaren wuta fa muka yi magana ba maganin mata ba." Sumayya ta amsa tana danna wayarta tana dariya. "Shi ɗin ma ai zaki iya, yaran yanzu menene baku sani ba." "Ni kam mu bar maganan nan kina sakani kunya, yauwa gata nan, ki duba daga ganin turarukan an san na ƴan gayu ne sannan na amare don kowanne ta bashi sunan da ya dace dashi." "Su kuma uwaren gidan fa?" "Suma zasu iya saya su saje cikin amaren." Murmushi kawai Juwairiyya ta yi kana ta karɓi wayar daga hannun Sumayya ta fara ganin pictures ɗin da sunansu da kuma yanda za'ayi amfani dasu. Nan Sumayya ta dawo ta bayanta ta fara mata bayani dalla-dalla. "Akwai 'Irresistible' wanda Sandal flakes ne ita mai sayarwan ta canja mishi suna. Ga kuma 'Coated Kajiji' wanda ta haɗa da secret ingredients ɗinta. Ga kuma 'Blissful' gab-gab, wanda ta ce it's best used on clothes, home & body because it's very strong & last long. Wa zata bari wannan ya wuceta? Not me!" "Ga kuma 'Soothing sandal' shi kuma Sandal Coconut ne, ta ce it has a very soothing scent, best use in ana neman sudden ƙamshi. Musamman in maigida ya kiraki a waya wai gashi yana zuwa da baƙi." "Wai dama haka kike da surutu Sumayya?" Faɗin Juwairiyya tana duban ƙanwar tata. "Adda Juwai ke kam ki saurara mana. Yauwa, sannan akwai 'Down to Earth' wato Halut kenan, sai 'Malaak' Halut-hawi mix ne, can be used for clothes, body and home. 'Field of dreams' daga jin sunan kin san yafi daɗi a saka in ana ruwan sama, wai niƙeƙƙen kajiji ne mai sa nishaɗi. 'Habiby mix' kuma signature ɗinta kenan, 3 sticks ta haɗa for clothes, body and home. Gasu nan dai birjik sai wanda kika zaɓa." "Ni babu abun da yafi burgeni irin 'Earthly wonders' saboda sau nawa ina ɗaukan kaya amma sai in ji yana warin damshi? Shi kuma wardrobe ball ne da zaki jefa a cikin wardrobe yana saka ƙamshi sannan yana ɗauke warin damshin." (Mum Fateey ma tayi order) "Gurin Khumrah kuma akwai Khalty (normal Black Khumrah), Fatum (normal White Khumrah), Liquid Gold (oudbased white khumrah). Sai Maya (Oudbased black Khumrah), Royalty in a bottle (musk based Khumrah), sai uwarsu ubansu wato 'Ain's Signature' Bodymilk ne na jiki, ana iya sawa a ruwan wanka, da ke da bathroom ɗinki duk ku ɗau Ƙamshi. Yana hana warin zufa. Kuma both maza da mata can use it. It has the nicest scent." "Tana da Kulaccam, 'Malika' (Lotion Kulaccam) 'Ahlaam' (Vaseline kulaccam)." "Yanda kika zauna kina zayyane turarukan nan kamar haɗin gwiwa aka yi ke da ita. Yanzu dai zan saya mata kala huɗu ki tayani zaɓe." Da haka suka darje suka zaɓi turaren wuta kala huɗu, khumrah kala biyu da kuma Kulaccam kala biyu. Sai da suka zaba suka kira numbernta 08088929221, daga nan ta basu account number Juwairiyya ta tura kuɗi, kana ta musu alƙawarin gobe da hantsi kayansu zai iso su karɓa a tasha. "Ya kika ji muryarta?" Faɗin Sumayya tana murmshi. "Me muryan ya yi?" "Wallahi kalan ƴan gayu." Dariya Juwairiyya ta yi kana ta gyaɗa kanta ta ce, "Ba laifi tana da zaƙin murya." Kuma zaku iya kawo tallenku a muku cikin hikima da jan hankalin mai karatu a cikin farashi mai sauƙi daga 5k zuwa kasa. Mum Fateey 👌 TAFIYAR MU Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) 09023713064 (6) Washe gari asabar aikan Juwairiyya ya iso ta aika ƙaninta Walid tashan mota ya je ya karɓo mata. Da yamma ta shirya tare da Sumayya suna jiran ƙannen Hafiz biyu mata da zasu biyo su tafi tare. Ana idar da sallah la'asar suka shigo gidan da sallamarsu, gaishe da Mama kawai suka yi suka fita ƙofar gida inda motar ɗaya daga cikinsu mai suna Hafsat yake fake, dashi kuma zasu je gidan mai jegon. Suna tafiya suna hira tsakaninsu har suka iso gidan Salima, Hafsat ta buɗe booth suka fara ciro kaya ita da ƙanwarta Zainab suna ajiyewa a ƙasa. Daɗi ne ya ziyarci zuciyar Juwairiyya ganin irin hidiman da dangin Hafiz suka yiwa mai jego da jaririn, ta sani Hafiz ɗan'uwansu ne amma ita a gurinta sun mata kara ba kaɗan ba. A jiya da ta samu labarin ta kira ta faɗa musu, Umma mahaifiyar Hafiz har da kukanta, yau gashi sun aiko mata da kaya niƙi-niƙi tare da alƙawarin Umma da sauran family zasu zo ganin jariri daga baya. Almajirai suka samu a waje suka tayasu shigar da kayan, Salima da wacce take tayata zaman biƙi suka karɓesu hannu bibbiyu, aka kawo musu juice tare da soyayyen naman rago. Su Juwairiyya suka yi godiya sosai akan karamcin da aka musu na sanya sunan marigayi Hafiz da aka yi. Suma su Salima suka yi godiya bisa hidiman da aka musu. "Tun jiya nake ta zuba ido na ɗauka zaki zo, da naga baki zo ba shine na kira Muhammad nace ya miki albishir da kanshi. Da dai sunan Babana za'a saka amma nace ya mayar da sunan marigayi zaki ji daɗi ba kaɗan ba." Salima ta ƙarisa maganan hawaye na taruwa a idanunta. Juwairiyya share fuskarta ta yi dalilin hawayen da ya zubo mata, kana ta dubi jaririn da yake hannunta yaro fari kyakkyawa wai mai sunan Hafiz ɗinta. "Nagode da wannan karamcin Salima, Allah ne kaɗai ya san daɗin da naji a cikin zuciyata. Kin kyauta mana ba kaɗan ba, Allah Ya bar zumunci Ya kuma raya mana Muhammad Hafiz." Dukkan ƴan ɗakin suka amsa da 'Ameen'. Basu jima sosai ba suka tashi tafiya aka basu cincin ɗin suna. "Ni wallahi ku bari zamu hau napep ni da Sumayya, ke kuma Hafsat sai ki sauƙe Zainab a gidanta kar zagayen ya miki yawa." Faɗin Juwairiyya a lokacin da suka fito waje. "Ai yanda na ɗaukoki haka zan mayar dake har ƙofar gidan Mama, babu abun da zaki faɗa da zai hanani kai ku." "Ke dai kina son wahalar da kanki wallahi, mu je to kar maghriba ya sameku a hanya." Bayan sun sauƙesu suka shigo gida, a nan Juwairiyya take labartawa Mama irin karamcin da Salima ta mata, yanda ta sa aka fasa saka sunan Babanta aka saka na Hafiz." "Kai Masha Allah ta yi ƙoƙari sosai Allah Ya bar zumuncin da ke tsakaninku." "Da bata yi casting mijinta out irin haka ba, yanzu mu mun ɗauka shi yayi niyyar yiwa abokinshi takwara alhali ashe ita ce." "Koma yaya ne duk sun yi ƙoƙari amma ba zan taɓa mantawa da Salima ba, ta cika ƙawar amana." Mama kallonsu kawai take yi bata sake cewa komai ba, har suka gama hiransu suka watse. ***** Bayan shekara ɗaya. Juwairiyya ce zaune a gaban Mama tana mata faɗa kamar yanda ta saba kullum idan bazawari yayi sallama a waje tace ba zata fita ba. "Na san kina son mijinki kika rabu dashi amma kin ga rayuwar nan bata da tabbas, yanzu gashi nan rubibinki ake yi amma gaba kaɗan zaki ga yayinki ya wuce an rasa mijin auren. Ki yi amfani da opportunity ɗin da kike dashi a cikin maneman naki ki darje ki zaɓi wanda zuciyarki ta aminta dashi, kiyi aurenki ki rufawa kanki asiri. Juwairiyya baki da ɗa baki da jika aure ba zai baki wahala ba kuma ba zaki rasa kalan mijin da kike so ba, kar kiyi wasa da damanki har ya kuɓuce miki. Zawarawa masu ƴaƴa suke wahala wajen samun mazajen aure domin mazan yanzu basa son ɗawainiyar kowa, wani idan zai samu a riƙe mishi ƴaƴanshi ma zai yarda. Kuma na faɗa miki ba zaki koma makaranta ba muddin kina zaune a cikin gidan nan, wallahi ba zaki janyo mini bakin jama'a ba ana shigowa gidan nan ana ƙirga zawarawan ciki ba." Surayya har ta buɗi baki zata yi magana sai kuma ta rufe, da cewa zata yi a littafin Ruwan Zuma haka Ummii wato uwar Laila ta faɗa mata, sai dai da ta tuno irin ɓacin rai da zai biyo baya sai ta gimtse bakinta. Yaushe ma aka bata wayar? Kwata-kwata yau wata biyar ne shine zata ƙara yin wani wawancin? Ba dai ita ba! "Ina miki magana kin yi shiru." Mama ta faɗa a hasale. "Kiyi haƙuri Mama." "Ni ba haƙuri zaki bani ba, cewa na yi ki zaɓi miji kiyi aure." Shiru Juwairiyya ta yi kanta a ƙasa tana tunanin rayuwarta a gidan mahaifiyarta ya fara zama takura a dalilin maganar aure da ake mata kullum sai dai in ba'a yi sallama a waje ba. Karatun da take son farawa an hanata, sana'ar girke-girken ma Mama ta hanata a cewarta in Juwairiyya ta saba da riƙe ƙuɗi da zaman kanta zata ƙi auren. Yau shekara ɗaya kenan har da wata shida da rasuwar Hafiz, maza kala-kala sun kawo mata cafka, wasu da kyakkyawar niyya wasu kuma da neman banza babu ko kunya a tattare da su. Duk cikin maneman nata babu wanda ya mata, to ma yaushe ta yarda suka saba har soyayya ta samu shigowa? In Mama ta matsa mata fita waje bata wuce minti biyar da duk wanda ya ziyarcetan zata dawo gida, irin tarɓan da take musu kuma ya jawo da yawa basa dawowa sai ƙalilan masu naci, ciki kuwa har da Ilyas magidanci ɗan unguwarsu. Matarshi ɗaya da ƴaƴansu biyu, ba wani babba bane don ta tabbata zai yi sa'an Hafiz. Sosai yake mata naci har Mama ta san da zamanshi domin ya shigo sau biyu ya gaisheta. Sannan ga Hussani da yake damunta wanda har tana tunanin kanshi ba ɗaya ba, tun tana lallaminshi su rabu lafiya har ta dawo tana ɗaga mishi murya tare da faɗa mishi baƙaƙen maganganu, sai dai duk da wannan wulaƙancin da take mishi bai sa Hussaini ya nuna ko sau ɗaya ranshi ya ɓaci ba, naci kuwa sai abun da ya karu. (Da alama dai ya karanta Ruwan Zuma kuma yana son ya kwaikwaya). Sannan ga Muhammad, zuwanshi ya fi na kowa ɓata mata rai. Tana tunawa bayan haihuwar Salima da wata ɗaya ya zo kawo mata shopping ɗin monthly da ya saba ya nemi zai gaisa da Mamanta. Bata kawo komai a cikin ranta ba don haka ta mishi iso kana ta fita a falon ta barsu. Abun da ya bata mamaki shine tsawon lokacin da ya ɗauka yana magana da Mama, me suke cewa? Ta je bakin ƙofar da niyyar gulma suka ci karo a yayin da yake fitowa. "Sorry." Ta bashi haƙuri tana jin takaici a ranta domin bata samu ta ji komai ba. "Ki rakani mota akwai saƙon da zan baki." Ya ce da ita bayan ya sanya takalmanshi. "Ka bawa yara su kawo mana." Ta faɗa tana shiga falon. Sai dai irin muguwar kallon da Mama ta mata yasa ta dawo waje ba shiri ta bi bayanshi. "Lukuti kawai." Ta furta a hankali tana ganin yanda ƙeyarshi ta tara tsoka yana kuma tafiya ɗai-ɗai tsabar ƙiba. A bakin motarshi Juwairiyya ta tsaya wacce tun zamanin samartaka da ita yake yawo wanda a yanzu har ta fara gajiya dashi ta kuma tsufa. Zama yayi a cikin motar bayan ya ɗan wahala sannan ya dubeta fuskar nan babu annuri ya ce, "Tun ba yau ba naga kin fara tsayuwa da masu neman aurenki, hakan yasa nima yau na nemi izinin Mamanki don ina son fara neman yardarta kafin in zo gareki. Idan kin amince bana son dogon nema a ɗaura auren ki tare." Sai da ta ɗauki seconds goma maganarshi na yawo a brain ɗinta sannan ta kwashe da dariya. Sosai take yi har masu wucewa suna dubanta, hakan yasa ta tsuguna tare da ɓoye fuskarta a cinyarta taci gaba da yi jikinta na girgiza. Sai da tayi dariyar mai isarta sannan ta miƙe tsaye tana share hawayen idanunta lokaci ɗaya kuma tana danne wata dariyar da ke son kwace mata. Bai ce mata komai ba amma ya haɗe rai sosai har sai da fuskarshi ta ɗan yi ja. "Wai idan kin amince...Mwhahahaha....bana son dogon nema.... a ɗaura auren ki tare....Mwhahahaha" Ta ƙara kwashewa da dariya wannan karon har da riƙe ciki. "Me amsarki?" Kawai ya tambaya yana nazarinta. Sai da ta saita kanta sannan tace, "Maza baku da ta ido wallahi. Yanzu ni da nake ƙawar matarka kuma matar abokinka...." "Late, you should add late." Nan da nan annurin fuskarta ya ɗauke ta dubeshi sama sa ƙasa sannan ta ce, "Ba sai ka tuna mini cewa baya doron ƙasa ba, tsayawarka a nan tare da ni kaɗai ya isa ya tuna mini cewa mijina ya mutu. Kar ka ƙara zuwa ƙofar gidan nan da wannan zancen domin na farko, ni ba butulu ba ce, ina zumunci da matarka ba zan taɓa cin amanarta ba. Na biyu kuma har abada ba zan taɓa auren ɗaya daga cikin abokan Hafiz ba, domin hakan zai zama tamkar cin fuska ne a gareshi, ba zan wulaƙantashi ba. Sannan na uku, Muhammad, wallahi ko na rasa mijin aure ne ba zan aureka ba. Da mutum irina da mutum irinka ba zasu taɓa zama a ƙarƙashin rufi ɗaya ba, in kuma aka kuskura aka haɗasu to sai dai gobara. You hate me, nima kuma na mayar maka da daidai naka. Abu na ƙarshe da zan faɗa maka shine kar ka kuskura ka nunawa Salima cewa mun yi wannan maganan saboda bana son alaƙar mu ya samu matsala." "What if shi ya nemi hakan?" Muhammad ya tambayeta yana kafeta da ido. "Shi waye ya nemi me?" Ta mayar mishi da tambaya don yayi confusing ɗinta. "What if Late mijin naki ne yace in nemi aurenki idan ya bar doron ƙasa?" "Stop saying 'Late' i know he is late." Ta faɗa a harzuƙe. "Hmm." "And you are lying, kai ne ka sakashi ya maka alƙawarin idan ka mutu ya auri matarka Salima kuma ya faɗa mini tun a ranar saboda tsakanina dashi akwai kyakkyawar alaƙa bama ɓoyewa juna komai." "To bai faɗa miki duka ba, he asked me to marry you too." "Ƙarya ne." "Ba zan taɓa yiwa mai rai ƙarya ba balle mamaci, ƙarya bata cikin halayena." Ya faɗa a hankali kamar ba shi ake yiwa ihu a kansa ba. Shiru Juwairiyya ta yi domin ba haka ta so ba, ta so ne yayi losing mind ɗinshi ta cire filtern bakinta ta zageshi tatas, amma calm demeanor ɗinshi ya hanata hakan. He is too calm for her liking, kuma hakan na sakata jin baƙin ciki kamar ta kurma ihu. Ganin ta yi shiru tana cika tana batsewa yasa ya kunna motarshi kana ya ja ƙofar ya rufe ya dubeta ya ce, "Me kika ce? Zaki aureni?" "Ko sunana baka taɓa ambato a bakinka ba, ko sunana baka taɓa sauraron harshenka ya furta ba, balle a kai ga so har aure." "Ba wannan na tambayeki ba." "Ba zan taɓa aurenka ba ko mazan duniya sun ƙare." Ta bashi amsa a numfashi ɗaya tana hararanshi. "Shine final say ɗinki ko zaki yi tunani?" Wani malolon baƙin ciki ne ya zo ya tokare a maƙoshin Juwairiyya ta ji kamar ta fara kuka, wai bai ji abun da ta faɗa bane, meyasa ba zai yi fushi su yi uwaka ubanka ba? Bakinta har rawa yake yi tsabar ɓacin rai ta ce, "Har abada." "Dama mun yi dashi akan sai kin ƙi amincewa kafin in barki. Allah Ya gani na cika alƙawari, ke kuma kar ki ce ban taya ba. Allah Ya bada sa'an neman mijin aure." Da haka ya yiwa motarshi giya ya tafi. Daga ranar bai sake waiwayarta ba, sai dai kuma bai fasa aiko mata shopping kowanne month ba. Ko da ta dawo cikin gida Mama ta tambayeta me ya faru cewa ta yi ya nemi aurenta tayi declining domin ba zata munafurci Salima ba, Juwairiyya bata ga amfanin yiwa Mama ƙarya ba domin shi da bakinshi ya faɗa mata sun yi maganar da ita. "Allah Ya kyauta." Kawai Mama tace, daga nan kuma bata ƙara ɗago mata zancen Muhammad ɗin ba. A nan Juwairiyya ta dawo daga dogon tunanin da take yi ta dubi Mama da tayi kasaƙe tana kallonta tace, "Ki bani wata uku zan nemi ɗaya daga cikin zawarawan nawa in aura sai a haɗa aurena da na Sumayya." "Ke kika yankewa kanki lokaci ba ni ba, don haka idan lokacin nan ya cika baki fito da mutum ɗaya ba wallahi, wallahi Juwairiyya kin ji na rantse? Ni da kaina zan zaɓi ɗaya daga cikinsu a ɗaura muku aure! In kin ga dama ki bijire a nan ne kuma zaki gane duniya budurwar wawa ce." Mum Fateey 👌 TAFIYAR MU Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) 09023713064 (7) Yau Ilyas ya zo gurin Juwairiyya, abun mamaki yana aikawa kiranta bata ɓata lokaci ba ta fito, sannan ta ƙara bashi mamaki ta hanyar yi mishi sallama tare da ɗaga mishi gaisuwa. Tunani ta yi mai zurfi, duk maneman nata da suka rage Ilyas ne kaɗai ta ga zata iya rayuwa dashi in har ta faɗa son shi. Sauran kam ko tunaninsu bata so kwakwalwarta ta kawo mata. Shi kuma Ilyas tsabar murna kasa rufe bakinshi yayi, a jikin motarshi ta jingina yayin da shima ya fito ya tsaya a gefenta. Bayan ƴan gaishe-gaishe su ka ɗan yi shiru na wasu ƴan seconds kafin ya buɗi baki ya fara magana. "Alamu sun nuna addu'ata ta karɓu, na ɗauka akwai sauran aiki a gabana Hajiya Juwairiyya." "Hmm." Kawai tace don bata san me zata faɗa ba. Basu jima ba ta koma cikin gida domin tuni hirar ya gundureta ba don kuma Ilyas bai burgeta ba, a'a haka kawai ta ji bata son su tsawaita hiran. Tun daga ranar suka fara soyayya a hankali har ta kai Juwairiyya na iya hira da shi cikin walwala a nan kuma ta gane ta kamu da son Ilyas. Ita a rayuwarta idan namiji ya iya soyayya nan da nan zai sace zuciyarta, sannan ya dinga martaba mace ya ɗauketa a matsayin abu mai tsada abar tattalawa kamar yanda Hafiz yake cewa. Ta ɗauka ba zata taɓa samun namiji irinshi ba amma sai gashi Allah Ya kawo mata Ilyas duk da cewa bai kai Hafiz ɗinta ba. A hakan ma ta godewa Allah sannan tana ji a jikinta in dai ta aureshi zasu zauna lafiya domin tana da labarin matarshi tana da hankali bata da fitina ko kaɗan, to me ya fi ranta? Wata ɗaya har da sati biyu da fara soyayyarsu ta ji shiru bai mata maganar aure ba, hakan yasa da aka ƙara sati biyu ya zama saura mata wata ɗaya wa'adinta ya cika ta yanke shawarar mishi magana. Yau ma ya zo hira kamar kullum tana jingine a jikin motarshi wacce ya mata nacin su dinga shiga ciki suna hira amma ta ƙi. Saboda ko a lokacin da take budurwa bata shiga mota ta yi hira da saurayi, saboda bayan Mama ta haneta ita kanta ta san abun da zai iya faruwa a ciki ba mai kyau bane. "Ni fa sanyi nake ji a wajen nan, nayi da ke mu shiga mota mu yi hiranmu a ciki amma kin fi son sanyi yayi ta shiga jikinmu." Murmusawa kawai Juwairiyya ta yi kana ta fara tunanin ta yaya zata ɗauko mishi zancen tunda in a al'adance ne namiji ne yake fara kawo maganar aure ita kuma ta amsa. "Bikin Sumayya yanzu saura wata ɗaya." "Haka dai muke ta lissafi tare. Allah Ya nuna mana da rai." "Ameen Ameen." Ta amsa sannan ta yi shiru. "Ya dai naga kamar kina cikin damuwa?" Faɗin Ilyas yana matsowa kusa da ita. Idan za'a tambayi Juwairiyya aibun Ilyas abu guda zata furta shine bai ɗauki taɓa macen da ba nashi ba a matsayin zunubi. A farkon zuwanshi yana respecting space ɗinta, amma suna fara sabawa ya nemi ya riƙe hannunta tare da son su shiga cikin mota su yi hira, babu ɓata lokaci ta nuna mishi bata son hakan don bata manta da cewa laifi ne mai girma aikata hakan ba. "Wallahi Mama ce ta damu wai sai a haɗa aurena da na Sumayya. Na ce mata ni dai har yanzu baka mini maganan ba." Shiru Ilyas ya yi, can kuma yace, "Dama tuntuni ina son mu yi wata magana da ke amma na rasa ta yaya can ɗauko miki ita." Jin furucinshi yasa cikin Juwairiyya ya kaɗa, nan da nan kuma ta fara addu'an Allah Ya sa ba cewa zai yi ba zai aureta ba, domin in har ya mata haka ya kassarata. Duk manemanta dama ƙalilan ne suka rage, a hakan ma tana fara soyayya da Ilyas ta koresu don ita tace ba zata yaudaresu ba, ba zata haɗa manema da yawa a lokaci ɗaya ba. Ilyas kuma da niyyar aure ya zo mata domin har bincike ta sa anyi mata a kanshi aka ce bashi da aibu. To me zai faɗa mata? "Ina jinka." Kawai ta iya cewa dashi tana sauraronshi. Gyaran murya ya fara kana ya gyara tsayuwarshi ya fuskanceta tarr yace, "Juwairiyya ina sonki ina kuma da niyyar aurenki, sai dai a yanzu matata ta samu labarin ina nemanki muna ta fitina a gida. Yanzu abun da nake so dake shine ki yarda mu yi auren sirri tsakaninmu, zan baki sadakinki ba tare da kowa ya sani ba sai mu biyu, da zarar nayi settling ɗin matata sai mu bayyana auren ki zo ki tare." Shiru ta yi har na tsawon minti ɗaya kanta a ƙasa tana tunani, shi kuma Ilyas ido ya zuba mata yana ta gyara tsayuwarshi kamar mara gaskiya. Can Juwairiyya ta ɗago kanta da ɗan guntun murmushi a fuskarta tace, "Shikenan zan yi tunani a kai. Amma yaya batun....?" Ta nuna kanta sannan shima ta nuna shi. Ƙura mata ido yayi yana son fahimtar me take nufi, kashe mishi ido ɗaya ta yi wanda hakan yasa fuskarshi ta washe hakwaranshi suka bayyana cikin farin ciki. "Yauwa ƴar gari, wannan ba matsala bace. Nuhu abokina da name baki labarinshi yana da gida a nan cikin New GRA, unguwar ma ba'a gama cika ba kuma gida ne mai kyau. A can zamu dinga zuwa muna rage zafi har lokacin da zamu bayyana auren." "To idan nayi ciki kafin nan fa?" "Zamu yi amfani da protection ko kuma ki sha maganin hana ɗaukan ciki." Ya faɗa hankali kwance kamar dama ya jima da wannan nazarin. "Da alama ka jima kana tunanin nan, amma kuma meyasa tun zuwan ka baka faɗa mini hakan ba ai da yanzu an wuce gurin, nima da na samu sauƙi." Wata dariya Ilyas ya saka Juwairiyya kuma ta murmusa tana kallonshi. "Ke ɗin ce an bani labarin kina da zafi, gashi kuma in bakya son abu babu mai sakaki dole. Amma dai nace musu sai dai in ba'a bi dake yanda kike so ba. Kin ganni nan? Bana son na ga ana takurawa mace ko kaɗan, ku mata sai da lallami." "Hakane kam. Kuma idan mutum yana son yin zina da mace zai iya shafe har wata biyu yana bibiyarta don buƙatarshi ta biya. Su waɗanda suka faɗa maka ina da zafin sun manta basu faɗa maka cewa ina da ilimin addini ba, sannan ni ba shashasha ba ce." Nan take annurin fuskarsa ta ɗauke, domin sai a yanzu ya gane cewa shigo-shigo-ba zurfi ta mishi. Fuskarshi ya tamke don ya san daga yanzu duk wata kalma da zata fito daga bakinta ba lallai bane ta mishi daɗi ba. "Ilyas ka bani mamaki ka kuma saka na ƙara tsorita da mazan yanzu. Masu hali irin naka sun zo amma da buƙatarsu suke zuwa a tafin hannunsu babu ɓoye-ɓoye, kai kuma sai da ka yaudareni da kyawawan hali har na faɗa sonka. Wallahi ni ba mazinaciya bace Ilyas, sannan na ɗauka zuwa kayi ka rufa mini asiri ashe kai tona mini asiri ka zo yi. Ka yaudareni ka kuma cuceni, Allah Ya saka mini." Sai a lokacin muryarta ta fara rawa ta nufi cikin gidan su cikin sauri tana share hawayen da ya zubo daga fuskarta. Bata kai ga shiga ɗaki ba ta ji ya kunna motarshi ya tafi, ta yi tsammanin zai kirata ya ce gwadata yake yi, amma shirunshi har ta shigo ya nuna cewa da gaske yake. Kuma tunda bai samu abun da ya zo nema ba ya tafi. Baby wanda ya ga shigowar Juwairiyya balle ya ga halin da take ciki, tayi kuka sosai domin ta san in ba mutuwa ba bazata samu kanta a cikin wannan halin ba, da Hafiz ɗinta yana raye da babu wani ɗan iskan garin da zai zo ya nemeta da lalata, ashe an yi gaskiya da aka ce 'Mutuncin mace ɗakin mijinta' ashe aurenta ba ƙaramin rufa mata asiri yake yi ba. Yanzu ina zata saka kanta? Ga wa'adin Mama saura wata ɗaya ya cika! Da waye zata haɗata in bata nemo mijin auren ba? Da wannan tunanin Sumayya ta shigo ta sameta, amma ko da ta tambayeta me ya sameta bata iya faɗa mata ba, da haka ta lalatar da zancen. Sati ɗaya da haka Mama ta lura babu mai zuwa gurin Juwairiyya, hakan yasa ta kirata don a yanzu da biki ya saura sati uku tana son sanin halin da take ciki. "Mama shima Ilyas yaudarata ya zo yi ba aurena zai yi ba." "Ina jinki." Faɗin Mama tana tsareta da ido. A nan Juwairiyya ta faɗa mata yanda suka yi wanda ya bawa Mama mamaki kwarai da gaske domin itama ta sa an mata binciken halayenshi da ta lura hankalin ƴar tata ya fi karkata kanshi. Ashe a ɓoye yake iskancinshi shiyasa ba'a gane ba. "Kina da sauran sati uku, a cikin waɗanda kika koran sai ki kira wani ya dawo ku daidaita." "Mama don Allah ki yi haƙuri kar ki mini haka, ki ƙara mini wasu wata ukun wallahi zan zo miki da mijin aure. Duk waɗanda na koresu bani da masaniyar daga ina suke balle kuma in karɓi number wayarsu." "Ni dai na faɗa miki kuma na yi rantsuwa ba zaki sakani kaffara ba." Mama ta mayar mata da amsa kana tayi shigewarta ɗakinta. Cikin tashin hankali Juwairiyya ta fice daga falon Mama ta koma nata ɗakin, ta ɗauka idan ta bawa Mama labarin abun da ya faru zata barta tunda ba laifinta bane kuma ba ita ta ƙi auren ba. Ta yarda zata auri Ilyas shiyasa take soyayya dashi wanda ita kanta Maman ta sani tunda tana ganin fitanta in ya zo hira. To me yasa ba za'a mata uzuri ba? Me yasa Mama take son takurawa rayuwarta haka? Me yasa ba zata bari ta nemi mijin cikin kwanciyar hankali ba? Wa ya faɗawa Mama cewa har yanzu ana irin haka? Sai yanzu ta yarda mazan kirki na aure suna wahala. Tunanin duniyan nan ta yi don neman mafita amma babu solution, don bata da inda zata je ta kai Mama ƙara a bata haƙuri. Ƴan'uwan babanta da basu san cinsu da shansu ba ta sani sun fi kowa ma son tayi aure, domin da yanzu zata je musu da zancen haɗuwa zasu yi da Mama su uzzurata. Dangin Mama kuma babu mai sakata dole saboda duk wani da zata ganshi a matsayin uba ko uwa basa raye, shaƙiƙanta kuma ita ce babbarsu. Kakarsu kuwa wacce suke zaune gida ɗaya da ita da babu duk ɗaya, bata cewa kas balle as. Mace ce mai sanyin hali sosai wanda Juwairiyya take cewa sanyin halinta da haƙurinta ne suka sa tayi tsawon rai. To gurin wa zata je? Bata da kowa sai Allah, domin shi kaɗai ne zai sassauto da zuciyar Mama ko kuma ya sama mata mafita a cikin ƙanƙanin lokacin nan. A kwana a tashi yau ya rage saura sati ɗaya auren Sumayya da Juwairiyya wacce bata da mijin aure, abun duniya duk ya bi ya dameta domin har tunanin guduwa ta yi amma ina zata je? Bata da kowa sannan ta kasa faɗawa kowa damuwarta balle a bata shawara, Juwairiyya tana da ƙawaye amma ita a gurinta su yi zumunci ne kaɗai ba wai su yi sharing sirrukan juna ba. Wannan dalili ya sa babu wanda ya san halin da take ciki sai ƴan gidansu. Abun da Juwairiyya bata sani ba shine tuni Mama ta janye maganarta don har tayi azuminta uku na kaffara saboda ta sani mijin aure ba kamar zani bane da zaka je kasuwa ka siyo ka dawo dashi gida ba. Ta san ta uzzurawa Juwairiyya amma hakan da ta mata shine daidai. Kwata kwata a yanzu shekarun Juwairiyya ashirin da uku ne (23), yarinya ƙarama da ita bai kamata a barta tana zawarci har yayi tsawo ba. Tana da sauran ƙuruciyarta sannan zata samu mijin aure ba tare da an sha wahala ba, shiyasa tun lokacin da maza suka mata rufdugu ta so ta sauraresu har a samu wanda ya burgeta, ta matsa mata ta fita waje amma ta kasa hanata yi musu baƙin halin da suke tafiya basa ƙara waiwayarta. Wannan babban kuskure ne da Juwairiyya ta yi da zai sa gaba ta yi hankalin ba'a korar mai tayin soyayya, a duba a gani kafin a sallami mai tayin. Zata bar Juwairiyya a yanzu, amma ana gama bikin Sumayya zata tayar da zancen kuma ba zata zo mata cikin lallami ba. Ana saura sati ɗaya biki ɗaya wata ƙawar Juwairiyya mai suna Halima ta kawo mata ziyara. Tare suka yi secondary school kuma sun yi zumunci sosai har aka yi auren Juwairiyya basu rabu ba, hakan yasa da aka tashi auren Halima itama Juwairiyya ta halarci kowanne event har aka gama Hafiz ne mai kaita yana dawo da ita. Bayan auren mijin Halima ya samu aiki a ƙasar waje inda yayi karatunshi, hakan ya sa ya tattari matarshi suka koma can da zama. Sai dai bayan shekara mahaifiyarta ta rasu wanda hakan yasa suka dawo gida Nigeria, mijin nata sati ɗaya kawai yayi ya koma ita kuma ta zauna kula da Babanta don bayan an watse gida ya rage daga shi sai ita. Matarshi ɗaya ce sannan su biyu ne kaɗai ƴaƴanshi, daga ita sai yayanta namiji wanda yake karatu a ATBU. Wannan kenan. "I'm sorry to say, amma Juwairiyya kin ƙara ramewa. Ke da Daddy kuna fama wallahi, ban san raɗaɗin rashin masoyi ba amma na san rashin uwa, kuma a hakan naci gaba da rayuwa ban fasa ba. Kun fi kowa sanin ba zasu dawo ba, haka kuma yawan damuwarku ba zai amfanesu da komai ba, zasu so ku nitsu kuma ku cigaba da rayuwa sai ku aika musu da addu'a. Don Allah ki rage yawan damuwa, mutuwa kowa tana jiranshi babu mai zama a doron ƙasa." "Hmm, Halima ina cikin wani hali ne mai wuya." Faɗin Juwairiyya domin yanzu tana son ta buɗe cikinta ko zata samu a bata shawara. "To Allah Ya yaye miki amma na menene?" A man Juwairiyya ta zayyanewa Halima kaff halin da take ciki sannan ta ƙarishe da cewa, “Wallahi Halima bani da maneman ma yanzu, in kika cire Hussaini babu kowa. To yanzu in ba Hussaini ba wa zata aura mini, wallahi in har aka aura mini Hussaini sai na gudu an rasani.” “Ya Salam! Juwairiyya kar ki sake faɗin haka, abun bai kai ga haka ba. Shi kuma Hussaini in banda rigima ina shi ina ke? Ya fi kowa daƙiƙanci a aji gashi har yau shi bai ƙaro ilimi ba kuma bai kama sana'ar komai ba." "Kuma ni Allah Ya sani ba zan auri sa’ana ba.” “To ga wani dalilin ma.” Shiru suka yi na ƴan wasu seconds sannan fuskar Halima ta washe da annuri tace, “What if na kawo miki miji na gani na faɗa har gida? Mijin da bashi da aibu sannan zai riƙeki amana tamkar ƴar cikinshi? Mijin da zaki zauna a gidanshi daga ke sai shi babu mai takura muku? Mijin da yake da rufin asirin da ba zaki nemi komai ki rasa a gidanshi ba? Kina so!?” “Halima ina zaki samo mini mijin aure mai duka waɗannan qualities ɗin a ƙanƙanin lokaci haka? Sannan in ma an samu shi zai yarda ya aureni ne daga haɗuwa da ni?" "Ina ji a jikina za'a yi auren nan shiyasa ƙaddara ta hankaɗoni gidan nan. Wallahi tun last month mijina yake ta damuna akan in koma Turkey amma hankalina ya ƙi kwanciya da in bar Daddy shi kaɗai a cikin gidan nan, ina nan ma kullum cikin damuwa yake ina ga kuma babu ni? To kwana biyu da suka wuce ya daina ɗaukan wayata Juwairiyya, na san ina cikin fushin Allah kuma ina ɗaukan alhakinshi amma Daddy fa? Ni kaɗai yake gani ya ji sanyi a ranshi saboda Abduljalil tuni ya koma school baya dawowa gida sai ƙarshen semester. Juwairiyya......." Bata kai ga ƙarisa maganarta ba Juwairiyya ta katseta da hanyar ɗaga mata hannu. "No, ba zan auri Daddy ba Halima! Wallahi ba zan auri Daddy ba.” “Juwairiyya….” “Kai ina! Mu bar maganan nan bana son jin komai.” “Don Allah ki saurareni in ya so zaki iya yanke duk hukuncin da kika ga dama. Ki saurareni please.” “Duk abun da zaki faɗa ba zai canja mini ra'ayi ba amma ki faɗa tunda kin kira sunan Allah. Haba Halima Daddy ne fa, Daddyn mu. A ƴa ya ɗaukeni fa.” “Ki dai saurareni.” “Ina jinki ai.” “Juwairiyya wannan aure da nake son haɗawa rufin asirinmu ne. Na farko ni zan samu in koma gurin mijina wanda yake fushi dani, na biyu Daddy zai samu mata wacce zata kula dashi sannan ta taimakeshi wajen ɗauke hankalinshi daga kan Mummy, he is lonely he really need a companion. Sannan na uku Juwairiyya ina zaki samu miji mai kyakkyawan hali kuma mai shirin aurenki a kwana bakwai? Kin san waye Mama zata haɗaki dashi? Bakya son kiyi zaɓinki kafin a haɗaki da wanda bakya so? Ki zauna ki yi tunani wallahi wannan shine kaɗai mafitan da in kin amince kin ceci mutane huɗu ne lokaci ɗaya sannan kema zaki samu kwanciyar hankali domin kin san waye Daddy halinshi na gari duk kin sani. Kiyi haƙuri Juwairiyya ki taimakeni, wallahi hankalina zai fi kwanciya idan na san a hannunki na bar Daddy." "Wayyo Allah na! Halima idan na auri Daddy me duniya zata ce da ni? Zasu kirani butulu na auri Baban ƙawata." "Da Mummy tana raye ne za’a faɗi haka, amma bata doron ƙasa. Sannan duk wani da zai kawo suka akan auren man ina nan ba zan bari ba wallahi. Ke dai amincewarki kawai nake nema.” Shiru Juwairiyya tayi tana aikin tunani, wannan shi ake kira ‘Ga samu ga rashi’. Idan ta ƙi wannan haɗin ita ce a cikin tashin hankali, in kuma ta yarda mutanen duniya ba zasu barta ba. To yaya zata yi? “Halima ki bani lokaci zan yi tunani amma wallahi ina tsoron bakin mutane, sannan shi Daddy zai amince ya auri ɗiyar cikinshi?" "Wannan duk ba matsala bace, zan kiraki anjima da dare in ji hukuncin da kika yanke Juwairiyya. Don Allah kar ki manta taimakonmu kike yi dukkaninmu sannan hakan shine kaɗai rufin asirinki." "To shikenan Halima." Mum Fateey 👌 ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 08138873799 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** TAFIYAR MU Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) 09023713064 (8) Juwairiyya ta kasa yanke hukunci, tun tafiyar Halima da yamma take kai kawo a ɗaki ta kasa samun nitsuwa, ana ƙoƙarin kiran maghrib yara suka yi sallama sun kawo shopping ɗin month. A tsakiyar gida suka jibge suka tafi Surayya da Walid suka fara ɗauka zuwa ɗakin Mama, daidai nan kuma Juwairiyya ta fito ta nufi gurin Mama da ke can cikin ɗakinta don ta bata shawara kan wannan gagarumin matakin rayuwar tata. Tana shiga ta samu Mama tana waya don haka ta samu guri ta zauna har sai da ta gama, "Kika ce duk waɗanda suka nemi aurenki kika koresu baki da number su, shi kuma Muhammad fa? Gashi yau ma an ce mini ya yo aika." "Mama don Allah mu daina ma ɗauko maganan Muhammad, fisabilillahi ina ni ina auren mijin Salima? Wallahi idan ita ce ba zata taɓa auren nawa mijin ba, sannan in dai na auri mutumin nan ko awa biyu ba zan yi ba zamu rabu. Ya tsaneni, nima kuma na tsaneshi." "Kar ki sake cewa kin tsani mutum, akul in sake jin kin furta haka ga ɗan'uwanki musulmi. Kuma don baki da mutunci duk ɗawainiyar da mutumin nan yake yi a kanki bakya gani shine zaki jefeshi da kalmar tsana? Uban me ya miki Juwairiyya? Kasheki ya yi ko bunneki ya yi da ranki? A zamanin nan mutum yana iya mutuwa ya bar ƴaƴa amma kaff cikin abokanshi ba za'a samu mai yiwa yaran nan hidima kamar yanda mutumin nan yake miki ba. Baki haihu da abokinshi ba amma a hakan ya nuna har yanzu ba'a rabu ba. Juwairiyya ki kiyayeni, tukunna ma wa kika fitar don ina son sanar da ƴan'uwan babanku da wuri ba sai an je gurin ɗaurin aure ba." "Na samu Mama. Daddyn Halima ne." Juwairiyya ta faɗa hawaye na taruwa a idanunta. ***** A can gidan su Halima rigima ce ta kacame tsakaninta da mahaifinta wanda ya ɗauki zancen a matsayin wasan yara da kuma rashin hankali. "Daddy don Allah ka amince ka aureta, wallahi tana cikin damuwa domin Maman rantsewa tayi akan in har bata fito da miji ba zata aura mata duk wanda ta ga dama. Gashi a cikin waɗanda ta ƙi har da ƴaƴan baffanunta da suke ƙauye, duk da cewa bamu da tabbacin a cikinsu Maman zata zaɓa mata miji." "Sau nawa zan faɗa miki bana son ƙara jin zancen nan Halima? In ba zamani da kawomu irin wannan lokacin ba yaushe ɗiya zata nemawa ubanta matar aure har ta dinga tura mishi ra'ayin da baya so?" "Daddy ka tsaya ka ji mana." "A zaune ma nake Halima, a zaune nake." Ya faɗa yana murmushi yana ganin wautarta a fili. "Daddy na san idan har na tafi baka yi aure ba wallahi zai yi wuya kayi ɗin, shiyasa na zaɓo maka matar da na san zaka ji daɗin zama da ita sannan zata kula da kai." "Gashi dama nace miki ina neman baby sitter ko?" "Daddy please mana." Shiru yayi yana ganin yanda ta dage ita da gasken-gaske so take yi ya auri ƙawarta. In banda shirme irin na Halima ta yaya zai auri ƴar cikinshi kuma ƙawar ƴarshi? "To na ji. Ita ta yarda ne zata auri tsohon ƙawarta?" "A'a tace mini zata yi tunani." Faɗin Halima tana jin tsoro a ranta kar Juwairiyya ta ƙi yin na'am da zancen. Daddy buɗe jaridarshi ya yi kana ya ɗaura ƙafarshi ɗaya kan ɗaya ya ce, "Idan ta amince sai ki mini magana in tura gidansu." Ya yiwa Halima je-ki-ƙarata. Cikin murna Halima ta miƙe tsaye tana cewa, "I promise you Daddy ba zaka yi dana sanin wannan haɗin ba." Da haka ta saka kai ta fita daga falon shi kuma ya bita da ido yana karkaɗa kai. "Yaran yanzu akwai shirme." Juwairiyya bata sha wahalan samun yardar Mama ba akan aurenta da Daddy, a farko ta nuna hakan ba zai yiwu ba, amma bayan Juwairiyya ta faɗi positive dalilanta na wannan aure sai Mama ta fara sauƙowa. "Yanzu Juwairiyya tsoho zaki aura kuma baban Halima?" "Mama ni tsufarshi bata dameni ba, kuma ke ce kika sa na kawo miki shi, kuma gaskiya Mama da in auri wani gwara na auri Daddy." "Na janye wancan maganan, zan ƙara miki wasu watannin Juwairiyya." Faɗin Mama ganin da gaske ƴar tata ta kafe akan zaɓinta. Shiru juwairiyya tayi tana tunani, ta sani Mama ba zata ƙara mata lokaci mai yawa ba, to don haka ba taga dalilin da zai sa tayi sake reshe kama ganye ba. Ta sani rayuwarta ta lalace tun ranar da Hafiz ya daina numfashi, jindaɗin da ta samu a baya ba zata taɓa samun irinshi ba a gaba in ba wani ikon Allah ba. Daddy bashi da aibu, yana da kyansa daidai gwargwado ga kuma iya gayu fiye da wasu matasan yanzun. Ɗan boko ne sosai sannan yana da sanin addini ga uwa uba sanyin hali. Sau da dama in ta je gidan su Halima ta ga yanda suke wasa da Daddy sai itama ta ji kewar nata uban, sakin fuskarshi ga ƴaƴanshi bai sa suka ɓaci ba, sai ma kyakkyawar alaƙa da ke tsakaninshi da su.   Tunda Allah ne Ya kawo mata shi zata aureshi don ta huta da matsalar Mamanta. Ta sani a yanzu ba'a yiwa yara auren dole ko kuma a matsa musu sai sun kawo mijin aure, zata iya yiwa Mama musu amma zuciyarta ba zata barta ta aikata hakan ba. Mama tana sonsu, son da a yanzu duk duniya babu wanda zai musu irinshi, Mama ta musu ƙoƙari tun bayan rasuwar mahaifinsu ita take kula dasu babu mai taimaka mata, a haka har ta aurar da ita ba tare da ta rasa wani necessitys na rayuwa ba. Don yanzu Mama ta matsa mata ta fitar da mijin aure sai ta zama maƙiyyarta? Sai ta bijire mata ta watsa mata ƙasa a ido yanda dangin babanta da ma wasu masu son ganin lalacewarsu su mata dariya? Idan ta bijire mata ta san wani irin bala'i zata tarar a gaba? No! Ta gwammace matsalarta ta tsaya a nan kar ta ƙara yawa. Rasuwar Hafiz kuwa ya sa ta gane duniya ba matabbata bace sannan komai mai wucewa ne. Itama bata da tabbacin ƙara wasu shekaru masu yawa. Wannan kenan. "Mama idan dai ba wani mugun hali yake dashi ba ki barni in aureshi, da yanzu da nan gaban duk ɗaya ne, duk ni ɗin ce." Shiru Mama tayi tana jin tausayin ƴar tata a ranta, ta san ta matsa mata amma hakan shine daidai in ba haka ba zama zata yi ba zata yi auren ba, yarinya ce mai jini a jika, in bata nemi namiji don zama a ƙarƙashinshi ba zata nemeshi don biyan wani buƙata. "Bashi da mummunan hali, Allah Ya sa hakan shi ya fi miki alkhairi. Amma ban taɓa jin ko sau ɗaya kin ce ya zo gurinki ba." Faɗin Mama cikin damuwa. "Sau ɗaya ya zo shine na nuna mishi bana ra'ayi, bai sake zuwa ba sai yau ya aiko Halima." Juwairiyya ta yi ƙarya. ***** "Daddy albishirinka?" Faɗin Halima cikin tsantsan farin ciki ga mahaifinta da ke shirin shiga bacci don lokacin har ƙarfe tara ta gota. "Gobe zaki tafi?" Ya tambayeta yana dakatawa. "Haha funny you. Ta amince Daddy, gobe ka shirya ka je ka samu baffanunta ku yi magana." "Halima wai dama da gaske kike yi?" Abun da ya faru a gaba ya jawo ɓacin rai tsakanin Halima da mahaifinta har ta kai tana kuka da idanunta, shi tun farkon zancen bai ɗaukeshi a matsayin maganar hankali ba, shiyasa da ta dameshi ya mata kora da hali. Saboda ya san ƙawar tata ba zata yarda ta auri tsoho mai shekara hamsin da biyu ba (52). Yana son ƴaƴanshi ya kuma sabar musu da su zauna su yi wasa da dariya dashi don haka da ta kawo wannan zancen sai ya ɗaukeshi a matsayin raha, ashe da gaske take yi. "Daddy kar ka mini haka, wallahi na kwaɗaita mata wannan auren har ta sanar da mahaifiyarta duk sun yarda kai kawai ake jira ka gabatar da kanka. Ka rufa mini asiri kar kasa in ji kunya." Faɗin Halima tana share hawayen fuskarta. "Ni da nake matsayin uba a gareki Halima ban miki auren dole ba saboda na san illanshi, amma yau ke kike neman tursasani in yi auren da ban shirya mishi ba? Babu batun aure a gabana Halima, rayuwar auren da nayi da mahaifiyarku ya isa sai kuma Allah ya haɗamu a Aljannah. Ki bata haƙuri, sannan ita ma mahaifiyar tata ki bata haƙuri." Kuka cur-cur Halima take yi da idanunta, Daddy na neman wargaza mata plan. Sannan ba zata iya tafiya ta barshi shi kaɗai ba sai dai ta kashe aurenta ta dawo su zauna. Zata iya haƙuri da auren nata don shi ya rayu, ta rasa Mummy ba zata so shima su rasashi ba. Shine kaɗai katangar su and she can do anything don ganin bai tafi ya barsu ba. "Shikenan Daddy, na san ban isa in maka dole ba amma wallahi ba zan barka kai kaɗai a cikin gidan nan ba. Zan kirashi ya sakeni sai in dawo mu zauna, wallahi na gwammace in kashe aurena da in rasaka ko in barka cikin halin maraici." "Kar ki kashe aurenki Halima, ki faɗa mata gobe zan je mu gana da iyayenta." Shine abun da Daddy ya faɗa kana ya tashi ya shige ɗakinshi zuciyarshi na mishi zafi. Yasan halin Halima, sosai zata iya kashe aurenta ta dawo su zauna, shi kanshi ya san zamanshi shi kaɗai bashi da amfani, saboda disadvantages ɗinshi ya fi yawa akan advantages ɗin. Amma me yasa ba zasu gane cewa Sadiya ita ce rayuwarshi ba? Sannan tafiyarta ya tafi da duk wani sha'awarshi na aure? Tsabar son da yake mata ya kasa yi mata kishiya, sannan tana haihuwar ƴa mace ya mayar da sunanta don ya nuna mata ta fi kowa a gurinshi. Ba haka ya so ba, amma tunda Halima ta kafe sai yayi auren, da ita da ƙawar tata duk zasu yi regretting daga baya, sannan ita Amaryar da kanta zata nemi saki ba sai ya miƙa mata ba. "Wai ana kiran Juwairiyya a waje." Faɗin wani yaro a can bakin ƙofar gidansu. Tsaki Juwairiyya ta ja kana tace a ranta an kusa daina mata wannan kiran domin haushi take ji ba kaɗan ba. Amma tunawa da ta yi cewa wataƙila Daddy ne sai ta yi saurin ɗauko hijabinta ta fita domin yau saura kwana huɗu a ɗaura musu aure wanda har gidansu ya fara tara baƙi na nesa amma ita ko ganin idon mijin bata yi ba. Sadakinta kawai aka aiko mata har dubu sittin, sannan Halima tare da wasu ƴan uwan mahaifin nata suka kawo mata ƙuɗi dubu ɗari uku da hamsin na wanda zata sayi sutura da kayan kwalliya. Tana fita ta ja tunga ta tsaya dalilin ganin motar Muhammad da ta yi, kamar ba zata je ba amma ta ga yanzu ne ya kamata ta mayar mishi da martanin kan addu'a mai  kama da gatse da yayi mata a ranar da zasu rabu. Tana isa bakin motarshi ya fitar da ƙafarshi ɗaya waje ya daidaita zamanshi kana ya ce, "Na ji labarin zaki yi aure, Allah Ya bada zaman lafiya. Sannan ina tunanin a nan zan dakata da turo miki aika da nake yi tunda zaki koma ƙarƙashin wani." "Dama ba ni na sakaka ba." "Nima ban ce ke kika sakani ba, kuma ba don ke name yi ba, ina yi ne don abokina." "Gori ka zo ka mini kenan?" Kallon ta yayi wanda in zai iya ƙirgawa yau na goma da tara kenan, murmusawa yayi wanda shi kanshi sai da yayi mamakin hakan. Kuɗi ya ciro a cikin aljuhunshi ya miƙa mata yana cewa, "Ga gudumawata dubu hamsin, ni ba mai kuɗi bane." "Bana buƙata, tukunna me ya kawoka ne?" Faɗin Juwairiyya cikin gajiyawa, domin ƴar tsiwar da take son ta mishi ma ta kasa. "Na zo miki bankwana ne, sannan in baki gudumawata. Ko kina tunanin akwai abun da zai kawoni?" Bata amsa ba kuma bata karɓi kuɗin da yake miƙa mata ba har hannunshi ya gaji ya mayar ya ajiye a gefenshi. "Ki matsa zan tafi." Yana faɗin hakan ya ja murfin motarshi ya rufe. Bai ƙara seconds uku ba ya bar ƙofar gidan. Ita kuma Juwairiyya jiki ba kuzari ta koma cikin gida, domin wanda take zato ba shi ne yazo ba, shi kuma Muhammad ta so faɗa mishi magana mai zafi amma bata samu damar yin hakan ba, dalilin yayi sanyi sosai ba kamar yanda ta sanshi ba. A da ko gaisuwarta ba ya amsawa amma yanzu har shi yake mata fatan alkhairi a aurenta? Ta wani gurin tana ganin laifinta domin riƙon nata yayi yawa. Kwanci tashi asarar mai rai. Biki ya zo domin har an yi walima ranar Jumma'a akan washe gari asabar za'a ɗaura auren. Ƙiri-ƙiri Juwairiyya ta ƙi yin kwalliya balle ta yi shiga na alfarma don waliman, a cewarta ba zata ci zamaninta sannan ta ci ta Sumayya ba. Don ita har yanzu bata gaskata cewa aurenta za'a yi ba dalilin har yau bata ga fuskar mijin ba, hakan ya sa a matsayinta na yayar amarya take shige da fice yanda ya kamata. Mama ta so hanata akan cewa ai itama amarya ce amma Juwairiyya ta kafe dole aka zuba mata ido aka barta. Washe gari aka ɗaura aurensu wanda Halima ce ta kira Juwairiyya cikin tsantsan farin ciki tana cewa cikin waƙa. "An ɗaura, an ɗaura. Kin zama matar Daddy Allah na gode ma." Jin haka ya sa zuciyar Juwairiyya ya buga da ƙarfi, kenan yau ta zama matar wani ba Hafiz ba? Bata iya cewa komai ba ta kashe wayar hawaye na zuba a idanunta. Ita kuma Halima tsabar murna bata ma gane ba domin tana cikin ƴan'uwansu da suka taru don yin ƙaramin wunin taya Daddy aure. Da rana aka zo ɗaukan amarya inda a nan ne Juwairiyya ta ga tijarar Mama. "Don baki da hankali sai ki fita ba tare da izinin mijinki ba?" Faɗin Mama kenan tana hararar Juwairiyya. Ihu ne kaɗai Juwairiyya bata kurma ba amma sai da hawaye ya ɗigo mata, juyawa ta yi ta shige banɗaki ta kira Halima don ta tambaya mata Daddy. "Wannan ba hurumina bane Aunty Juwai, zan turo miki numbernshi ki kirashi ki tambaya da kanki." "Halima kar mu yi haka da ke don Allah. Wallahi ba zan iya ba, ban san ta yaya zan fara mishi magana ba." Faɗin Juwairiyya tana jin kamar ta shiga cikin wayar ta shaƙe wuyan Halima. "A haka zaki koya matar Daddy, zan tura miki yanzun nan." Da haka Halima ta kashe wayarta, itama ta rama. Juwairiyya tsabar haushi sai da ta naushi gini da ƙafarta, zafin da ta ji yasa ta yi hankali ta sunkuya tana sosa gurin tana wash wash. Ƙarar shigowar saƙo ta ji a wayarta wanda tana dubawa ta ga numbern Daddy ne kamar yanda Halima ta mata alƙawari. Kamar ba zata kirashi ba amma ta ga in bata kira ba ita ce da asara, ta jima tana burin Allah Ya kawota ranar auren Sumayya ta yi ruwa ta yi tsaki, don haka ta yanke shawarar kiranshi. Ringing biyu ya ɗauka Juwairiyya ta ɗaga mishi gaisuwa cikin ladabi kamar yanda take gaisheshi idan ta je gidansu Halima a da. "Daddy dama ina son zuwa kai Amarya ɗakinta ne." "Babu komai zaki iya zuwa." "Ai idan na faɗawa Mama ka barni ba zata yarda ba, Daddy ko zaka mata magana?" Sai da yayi ɗan jimm wanda har ta fara tausayin kanta sannan ya ce, "Ki jirani zan zo na kaiki." Mum Fateey 👌 TAFIYAR MU Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) 09023713064 Marubuciyar Matar Kabila Fatu A Birni Ruwan Zuma Canjin Muhalli (9) Zuciya na lugude Juwairiyya ta koma ɗaki inda ta bar ƙawayenta da suka zo tayata murnar aure ciki kuwa har da Salima. Wasu a cikinsu gulma ce ta kawo su domin basu yarda da cewa wai Daddyn Halima ƙawar tasu ta aura ba, wasu kuma suna ganin hakan haɗine daga Allah kuma sun dace da juna, domin kuwa dukkaninsu sun rasa abokanen rayuwarsu zasu tausayawa juna, kuma zasu fi fahimtar juna. A gefen Salima ta zauna wacce take hira da sauran ƙawayen nata cikin sabo domin suna ɗan haɗuwa a gidan Juwairiyya lokacin da Hafiz yake da rai. Taɓa Salima ta yi wacce take bawa Hafiz Junior kunu a feeder ta rankwafo tana tambayarta menene. "Wai Daddy shi zai zo ya kaini gidan amaryar." Wata shewa Salima tayi wacce ta sa idon sauran ƴan ɗakin ya dawo kansu amma Juwairiyya ta yi saurin raba hankalinsu don kar su tambayi menene ya faru. Cikin dabara kuma tasa suka tafi don ta nuna musu itama zata bi tawagar Amarya Sumayya da za'a kai gidan iyayen mijinta da ke nan bayan gidan Sarki. Ɗaki ya rage daga Juwairiyya sai Salima da Hafsat (Ƙanwar Hafiz) waɗanda suma zasu je gidan amaryar. Suna zaune har ƴan tafiya da amarya suka tafi sannan Daddy ya mata text a waya. 'Ki fito ina waje.' Shine abun da ya rubuta ta ɗauki mayafinta zuciyarta na bugu wanda bata san dalilinshi ba. Kafin ta fita sai da ta faɗawa Mama wacce ta ƙaryatata sai da ta aika aka dubo mata eh lalle shine sannan ta bari suka fita. Ita ta fara isa bakin window ta russuna ta gaisheshi sannan su Salima ma suka rufa mata baya tare da miƙa gaisuwarsu cikin girmamawa domin ya musu kwarjini ba kaɗan ba, dukkansu kuwa sun san ya haifesu. Sanye yake cikin plain white yadi mai tsada da aka yiwa ɗinkin jumfa da gare sai kuma hularshi ita kuma dark blue, sosai yayi kyau kamar ba ɗan shekara hamsin da ɗori ba. Daddy cikin sakewar fuska ya amsa musu kana ya dubi Juwairiyya wacce tun fitowarta har lokacin bata kalli fuskarshi ba ya ce, "Mu tafi ko?" "Umm Daddy dama Hafsat tana da mota zamu tafi tare kar mu wahalar da kai." "Ba damuwa amma tunda na zo ku shigo in kaiku." Juwairiyya bata son musu dashi don dalilin da yasa kenan ɗazu bata ƙara kiranshi ta faɗa mishi cewa akwai mota a hannunsu ba, ita dama buƙatarta ya yiwa Mama magana ne amma kuma sai ya ce zai zo ya kaita. Juyawa tayi tana kyafta idanu ta kalli su Salima da suke mata dariya ƙasa-ƙasa ta ce, "Hafsat ki biyomu a motarki, ke kuma Salima ki shigo mu tafi." Ta faɗi hakan tana karɓan Hafiz Junior daga gurin Mamanshi. Da haka ta zagaya ta shiga gidan gaba tare da yaron sannan ta rufe marfin motar, tana jiran Salima ta shigo amma sai ta hangota ta mirror ta shiga ta Hafsat. Basu kyauta mata ba da suka barta daga ita sai shi, nan da nan kuma ta ƙara nitsuwa domin numfashin kirki wannan bata yi. Shi kuma Hafiz Junior wasanshi yake yi da agogon hannunta bai damu da cewa mamanshi bata kusa ba, ya saba da Juwairiyya domin tunda ya fara gane mutane Salima take turoshi gurin Juwairiyya tare da mai aikinta yayi awa ɗaya zuwa biyu sai a mayar dashi, sannan ita kanta Saliman tana zuwa gidansu Juwairiyya sa'i da lokaci. "Da alama ƙawarki ta fi son shiga can. Mu tafi ko?" Juwairiyya ta tsinkayi muryar Daddy wanda yake ƙoƙarin kunna mota. Gyaɗa kai tayi tamkar yana ganinta kana suka fara tafiya su Hafsat na bin su a baya. Hannun Hafiz Junior ta kama tana wasa dashi don ta rasa me zata yi ɗaya taƙamaimai, duk kuwa da sanyin A.C da yake cikin motar wanda ya haɗu da daddaɗan turaren Daddy bai hanata haɗa zufa kaɗan a goshinta ba. She is nervous, she really is. Sai da suka daidaita akan titi sannan ya tambayeta ina zasu yi, a hankali ta dinga mishi kwatance har suka iso wata magana bayan nan bata haɗasu ba. Yana yin parking ta mishi godiya tare da buɗe marfin motar zata fita ya dakatar da ita ta hanyar kama hannun Hafiz Junior. "Dama kina da ƙaramin yaro ne?" Ya tambayeta wanda sarai ya sani bata taɓa haihuwa ba. "Ɗan abokin marigayi ne, takwaranshi." "Allah Ya mishi rahama. Ga wannan ku yiwa amarya liƙi." Da haka ya damƙawa Hafiz Junior bundle ƴan naira ɗari yaron ya karɓe da sauri zai tura a bakinshi. "Daddy da ka barshi kawai." Faɗin Juwairiyya tana ƙoƙarin kwace kuɗin amma ya damƙe har yana shirin kokawa da ita. Bata yi aune ba ta ji sautin dariyar Daddy a hankali domin da alama abun ya ƙayatar dashi. "Yaro ma ya fiki sanin me ya dace, he meant to say ba'a maida hannun kyauta baya. Sai anjima." Yana gama faɗin hakan annurin fuskarshi ta ɗauke kamar wanda ya tuna da wani abu. Ganin haka yasa Juwairiyya saurin fita daga motar har tana cin tuntuɓe, tana matsawa daga jikin motar ya juya a hankali a bar gurin ba tare da ya ƙara kallonta ba. Sai a lokacin ta tuna cewa ba fa auren soyayya suka yi ba, aure ne na rufin asiri kuma wanda aka yi shi cikin gaggawa, aure ne da aka yi tsakanin ruhi biyu wanda suke cikin damuwar rashin masoyansu. Nan take ta ji ta ƙara tausayin kanta akan wanda take yi, ko yaya rayuwarsu zata kasance? Ko a wani matsayi Daddy zai ɗauketa alhali ya saba da ganinta a matsayin ƙawar ƴarshi. Bata gama wannan tunanin ba su Salima da suka yi parking a bayansu suka iso suna ɗaga nata signa suna dariya. "Me kika bashi haka har ya biya da tukuici?" Faɗin Hafsat tana leƙen fuskar Juwairiyya wacce ke ƙoƙarin shanye hawayen idanunta. "Kun fiye gulma wallahi. Masoyi (Hafiz Junior) ya gani wai ya mishi kyau shine ya bashi." Ta faɗi hakan tana miƙawa uwarshi kuɗin bayan ta yi nasarar kwacewa daga hannunshi ganin ya fara kaiwa baki. Kuka Hafiz J ya dalla yana miƙa hannu ga mamanshi da alama ya tuna da ita ne ko kuma don kuɗin ya koma hannunta ne sai Allah. Hakan yasa su Salima suka fasa faɗin abun da yake bakinsu suka dawo rarrashinsa daga baya suka ɗunguma cikin gidan ganin sauran mutanen da suke waje suma sun shige ciki. Da la'asar aka saka anko aka yi buɗan kai, zuwa isha kowa ya watse aka bar Amarya da Angonta da kuma halinsu. A daren ranar misalin ƙarfe sha ɗaya na dare Juwairiyya tana zaune a ɗakinta inda zata kwana da mutane biyar waɗanda suka zo biki ta jawo jakarta da nufin ɗauko igiyan charger sai ta ga kuɗi mai yawa har dami biyu. Nan da nan ta gane  Salima ce ta saka mata domin ɗayan babu makawa kuɗin da Daddy ya bata ne ta kasa gida biyu ta ɗauki rabi sannan ta ajiye mata rabi, ɗayan kuma dubu hamsin ɗin da Muhammad ya bata na gudumawa ne ta ƙi karɓa shine ya aiko matarshi dashi. Samun kanta ta yi da jin sanyi a ranta domin duk yanda ta kai da son riƙe Muhammad a ranta yanzu ta rage, sai yanzu take tambayar kanta dama me ya mata? Da wannan tunanin ta ɗauki wayarta bayan ta jonata a charge ta turawa Salima text ɗin godiya tare da cewa ta miƙa godiyarta ga Muhammad. Bayan kwana uku gida ya watse ya dawo na masu gidan su kaɗai, ko'ina an wanke an gyara tamkar ba'a yi biki ba sai kuma kewan Sumayya kowa ke yi musamman Iya (Kakarsu) da yake da ita Sumayya take kwana. Ba'a ƙara wasu kwana biyun ba Mama ta zauna da Juwairiyya akan maganar tarewarta a gidan Daddy. "Ina ta jiran ki mini maganan tarewanki amma sai naji shiru, yaushe ya ce zaki tare?" "Yace duk lokacin da na shirya domin gidanshi ba ya buƙatar wani gyara." "To kayanki na yanzu zaki tafi dasu ko kuma wasu zaki canja?" Mama ta tambayeta wanda ta san amsan ko ba'a faɗa mata ba. "Mama dama tun wancan lokacin na ce miki a sayar ba zan ƙara amfani da su ba, kayan kitchen kaɗai zan ɗauka da sauran ƙananun abubuwa amma banda gado da kujeru." "Shikenan, zan yiwa Bala Capenter magana sai ya sayesu a baki sabo, in ma za'a yi ƙari ne sai mu yi. Ana ribibin bikin nan masu hayan gidanki suka yi biya na shekarar gaba, sai ki rubuta ki ajiye, kuɗin kuma yana cikin account ɗina in kina so in turo miki." "A'a Mama ki ajiye, idan ina da buƙatar wani abu zan miki magana." Faɗin Juwairiyya tana jin tsoron Allah da kuma tsoron rayuwa na daɗa shiga jikinta. Wai yau ita ce mamallakiyar gidan ta da rayu ita da Hafiz a ciki? Bayan gama takabanta aka haɗu don rabiyan gado, a nan aka haɗa dukiyar da Hafiz ya mallaka wanda ya kunshi gidan da suke ciki, babban gona, mota da kuma wasu kuɗade da ke cikin banki. Iyayen Hafiz da suka tashi rabiyan sai basu yiwa Juwairiyya kyashi ba, a maimakon su sayar da komai sai a raba kuɗi kamar yanda wasu suke yi sai suka damƙa mata gidan a matsayin nata gadon sauran babban gona, mota da kudaɗe kuma suka raba tsakanin iyayenshi da ƴan'uwanshi. Bayan an gama rabiyan gado aka damƙawa Juwairiyya takardun gida da kuma makulli, a wancan lokacin tana tunawa itama miƙawa Mama ta yi domin kamar haushin kowa take ji, wai har za'a tsaya ana raba dukiyar Hafiz? Yaushe ma mutuwar ta fita a zuciyarsu? Abun da ta manta shine haka Allah Ya tsara domin gujewa fitina da kuma samun sauƙi ga shi mamacin. "To sai ku yi magana ku tsaida rana a kaiki a wuce gurin." "Mama wallahi sai in dinga ganin kamar bakya sona kin gaji da kallona, kamar zamana a gidan wani abu nake tare miki." Faɗin Juwairiyya a marairaice kamar zata yi kuka. "Sonki da nake yi yasa nake son ki shiga inda zaki zama mai mutunci abun mutuntawa. Shekaru aru-aru ina zawarci Juwairiyya, na ga mutane kala-kala a wannan journeyn nawa wanda da ba don ku ba da nima nayi auren na rufawa kaina asiri. Amma na ga bazan iya watsar daku ba, tunaninku kaɗai ba zai barni in yi zaman gidan mijin cikin kwanciyar hankali ba, I just couldn't. Ke kuma babu ɗa babu jika ga ƙanƙantar shekaru, aure ne kawai ya fi dacewa da ke. Zaki fahimceni komin daren daɗewa Juwairiyya." Sati daya da haka aka yiwa Juwairiyya jerenta a gidan Daddy gefen matar gidan ta da, falo ne madaidaici sai ɗakuna uku a ciki wanda ɗaya yake a rufe wanda nan ne ɗakin Mummy na da, ɗayan ɗakin shi aka barwa Juwairiyya yayin da ɗayan kuma yake na baƙi kuma na Halima a da. Gefen maigidan kuma shima falo ne babba mai ɗauke da ɗakin bacci ɗaya da kuma wasu ɗakuna biyu a waje wanda ɗaya na ɗanshi Abduljalil ne ɗayan kuma na baƙi maza. Yanayin tsarin gidan sosai ya burge ƴan'uwanta da suka mata jere, bayan sun koma suka faɗa mata har sabon fenti aka yiwa sashen nata. Washe gari kuma Juwairiyya ta shirya tarewa. Sosai Mama tasa aka mata gyara ciki da waje duk da cewa Juwairiyyan ta ƙi yarda a farko, amma da Mama ta zare mata ido sai ta dawo cikin hayyacinta aka mata gyaran fata, kitso da kuma kunshi mai kyau. Nan da nan ta fara walwali ta fito a Amarya sakk sai dai raman da tayi ne ya kasa ɓuya. Halima ce tare da wata ƙanwar Daddy wacce zata yi sa'ar Mama suka zo ɗaukanta bayan sallah isha, Juwairiyya kuka take yi kamar yau ne za'a kaita gidanta na fari. Sosai ta bawa Mama tausayi wacce ta kasa magana saboda ta san in dai ta buɗe bakinta itama zata taya ƴar tata kuka, tana ji tana gani aka fitar da ita daga gidan don zuwa bautawa ubangiji. Waɗanda suka mata rakiya basu jima ba suka tafi bayan sun mata addu'a tare da fatan alkhairi. Salima ce ta ƙarshen tafiya wacce Muhammad ya zo ya ɗauka jimm kaɗan da tafiyan sauran. Juwairiyya ta yi kuka har sai da ta ji kanta ya fara ciwo sannan ta tsagaita, duba agogo ta yi taga ƙarfe goma sha ɗaya na dare, to ina maigidan nata yake? Tashi tayi tana kallon tsarin ɗakin irin yanda tace tana so, babu hayaniya domin set ɗin gado ne mai haɗe da mirror da kuma wardrobe, sai ɗan decoration kaɗan a jikin bango don kar ginin ya zama wayam. Banɗakin da ke cikin ɗakin ta shiga nan ma ta sameshi tsaf irin yanda ta hasko a ranta, alwala ta ɗauro sannan ta zo ta tada sallahn shafa'i da witri. Tana idarwa ta ji ana kwankwasa ƙofar ɗakinta ta yi sauri miƙewa tsaye zuciyarta na bugawa ta dubi kanta a madubi, in banda ramar da ta yi babu abun da ya samu fuskarta don ta wanke duk kwalliyan da aka mata kafin a kawota. Ƙara kwankwasa ƙofar aka yi wanda hakan yasa ta isa ta buɗe tana mai matsawa gefe. Daddy ne ya shigo ɗauke da wasu ledoji a hannunshi bakinshi ɗauke da sallama amma fuskarshi babu walwala sannan ba'a tsume ba. Russunawa tayi ta gaisheshi bayan ta zauna a bakin gado shi kuma ya amsa yana mai shiga cikin ɗakin ya tsaya a gefen mirror sannan ya ajiye abun hannunshi akan ƙaramin carper ɗin da yake bakin gadon, "Ga abinci kici in kina jin yunwa, in kuma kin koshi ki adanashi." Ya faɗa yana kalle-kallen ɗakin wanda kwata-kwata ma hankalinshi baya ma kai. Gyaɗa kai tayi kana ta haɗa ta 'to'. Daga nan suka yi shiru na wasu seconds goma kana Daddy ya tako zuwa bakin ƙofa zai fita sai kuma ya tsaya ya fara magana ba tare da ya kalli inda take ba, "Farko zan fara baki haƙuri akan yanda zaki samu gidana, I'm not trying to belittle or humiliate you amma wannan auren bana sonshi Juwairiyya. Kema kuma na san kin yi auren ne don kaucewa wata matsala da ke shirin faruwa dake to kin ga babu batun ɓoye-ɓoye tsakaninmu. Kin samu abun da kike so, ƙawarki ma ta samu abun da take so sannan nima ta wani gurin na samu relief domin babu wanda zai ƙara mini maganan aure da illolin zama ni kaɗai a gida. Zan ƙara baki haƙuri Juwairiyya don ba zan taɓa zama mijin da kika rasa ba haka nima ba zaki iya maye gurbin matata da na rasa ba. Zan yi ƙoƙarin sauƙe duk wani nauyinki da ke kaina na ci, sha da sutura, in kuma kina buƙatar wani abu kar kiyi ƙasa a gwiwa ki sameni ki faɗa mini, I promise in dai bai fi ƙarfina ba zan saya miki ko in mallaka miki. You are free ki je duk inda kike so amma sai kin faɗa mini, sannan Halima ta faɗa mini kina son komawa Jami'a, zan nema miki addmission da zarar shekara ta zagayo kici gaba da karatunki. Sannan abu na ƙarshe ki kiyaye lafiyarki please, ko ciwon kai kike ji ki faɗa mini mu je asibiti. Kin ji? "Na ji Daddy." Faɗin Juwairiyya cikin sarƙewar murya kanta a ƙasa. "Allah Ya bamu haƙurin zama da juna, sai da safe." Da haka ya sa kai ya fice daga cikin ɗakin ya bar Juwairiyya cikin tausayin kanta da kuma sabon gurin da ta tsinci kanta a ciki. Itama ta sani babu soyayya a tsakaninsu amma yanda ya nuna mata da ita da babu duk ɗaya sai ta ji kuka ya kwace mata, minti kaɗan da haka ta share hawayen fuskarta don bata ga dalilin zubarsu ba, ko itama ma bata shiryawa zaman aure ba sai da Mama ta matsa mata sannan ta saduda, to tunda ta samu mai irin tunaninta ai faɗuwa ce ta zo daidai da zama. Zata rayu dashi duk da cewa babu ɗigon sonshi a zuciyarta amma zamansu shine rufin asirinta kuma rufin asirinshi, they are the perfect couple yet far away from perfect. You should read "TAFIYAR MU" on #wattpad #romance https://www.wattpad.com/1383895442?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create_writer&wp_uname=suwaibamuhammad36&wp_originator=htUPDrz2G495Ia5Bld7VFwthiy1sT1wSebwHtQS7HISK4qDx1GxoviT1wc%2BKX%2BSPJgQAPULmkO3t2ba363Vlw2gx%2FskopTrLIAQf1Tu6FO6pDjACQv3dsR46vyTupZVi Mum Fateey 👌 TAFIYAR MU Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) 09023713064 Wannan littafin na kuɗi ne a naira ₦500. Masu buƙata zasu biya ta wannan account ɗin 5139579011 FCMB Suwaiba babagana. Ga waɗanda basa son hayaniyar group zasu biya ₦650 a dinga tura musu kullum ta Private. Free page (10) Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah. Yau wata ɗaya har da sati uku da auren Juwairiyya da Daddy, sosai ta dawo da jikinta ta murje tayi kyau. Hutu ta samu a gidan Daddy wanda take samun irinshi a gidan Hafiz, bata aikin komai sai girki domin kuwa tana da mai wanke-wanke da shara da take zuwa kullum tana tayata aiki domin har falon Daddy ita take sharewa ta goge, ita kuma sai ta gyara mishi ɗakinshi idan ya fita Office. Juwairiyya bata da damuwan komai sai ta maigidanta da yake treating ɗinta kamar ƴar cikinshi, kullum da safe kafin ya fita aiki zai shigo har sashenta ya dubata ta bashi breakfast ɗinshi a cikin basket ya tafi dashi bayan ya tambayeta ko tana da buƙatar wani abu. Idan tana son fita zai barta baya hanata amma da sharaɗin ta dawo kafin maghrib. Yana dawowa daga aiki da yamma kuwa zai yi wanka ya ci abinci wanda shine na rana kuma na darenshi sannan ya zo ya ƙara dubata ya ji yaya ta wuni sannan ko tana da matsala. A yanzu da ta fara sabawa dashi ta sake sosai har tana iya kallonshi cikin ido idan tana mishi magana wani lokaci akan abun da yake son a dafa mishi da yake yana da ciwon Diabetes ko kuma wata magana ta daban. Rayuwarsu ta zama kamar na Boss da employee wanda gaskiya ita Juwairiyya ta fara gajiya. Zamanta da Hafiz ya koya mata juriya a fagen auratayya wanda har daga baya itama ta kama hannu ta zama daidai shi, matsalar da take fuskanta a yanzu shine Daddy ko hannunta bai taɓa riƙewa ba balle ya kirata shimfiɗarshi. Gashi ita ba itace bace domin kuwa tana buƙatar ɗa namiji a rayuwarta musamman yanzu da ta samu hutu, cima mai kyau ga kuma kwanciyar hankali. Sai yanzu ta fara gane dalilin da yasa Mama ta matsa mata tayi aure don ita kanta ta fara gajiya da wannan zaman. Yau ma video call take da Halima mutanen Turkey wacce tun bayan aurensu da kwana biyu ta koma gurin mijinta. "Ya zaman naku dai? Da fatan babu wata matsala?" Faɗin Halima tana kwaɓa batter ɗin cake a kitchen ɗinta yayin da laptop ɗin ke gabanta tana kallon Juwairiyya ta ciki wacce take shan Mango a wani ƙaramin bowl. "Kullum maganarki kenan, ke bakya gajiya ne ko ke uwamu ce?" Juwairiyya ta bata amsa tana cakan guda ɗaya da fork kana ta kai bakinta tayi rolling ɗin idanunta ga Halima. "You know you two are my responsibilities, dole ne in dinga bibiyarku don na ga alama kuna da taurin head." "Halima baki da kunya, Daddyn ne mai taurin kai?" Ta yi dariya. "Ni kin ji na kira sunan Daddy?" Itama ta yi dariya ta fara juye batter ɗin cikin baking pan. "Ohh da ni kike kenan?" "Ni na isa Aunty Juwai matar Daddy? Amma seriously ya kuke?" "Wallahi muna zaman lafiya bamu da matsala, bai taɓa ɓata mini rai ba sai dai ban sani ba ko ni na taɓa ɓata mishi." Ta faɗi iyakar gaskiyanta. "I'm sorry to ask and I know it's not my place amma ya batun 'the do'?" "Ya Salam Halima! Zan yi kamar ban ji me kika ce ba." Juwairiyya ta faɗa cike da kunya tana hararan Halima. "Mu bar maganar wasa Aunty Juwai, da ni da ke duk ba yara bane, kuma mun san yaya aka yi auren nan sannan ciwon ƴa mace na ƴa mace ce. Wallahi burina yanzu bai fi in ga kuna walwala tare ba kamar kowanne normal mata da miji, I'll love to see that day." Shiru Juwairiyya tayi tana tunani domin itama tana son ta samu wani su yi maganan ko za'a bata shawara, har yau kuma har gobe babu wanda ya san yaya aka yi aurenta da Daddy bayan Halima. To wa zata je gurinshi ta buɗe mishi cikinta in ba Haliman ba? Hakan ya sa ta kaɗa baki tace, "Halima babu wannan batun domin ko yatsata bai taɓa kamawa ba." Runtse ido Halima tayi sannan ta buɗe ta isa gaban oven ta saka cake ɗin sannan ta dawo ta zauna kan dogon stool ɗin da ke kusa da kitchen island ɗin. Sai a lokacin dukkan hankalinta ya dawo kan Juwairiyya wacce ta ajiye bowl ɗin Mangon a gefe kamar ya fita a kanta. "Aunty Juwai wallahi ban yi tsammanin Daddy zai ɗauki wannan lokacin ba tare da ya saisaita tsakaninku ba. Wallahi shi mutum ne mai fara'a da kuma sauƙin kai, tun bayan rasuwan Mummy na lura ya canja sosai but I thought daga baya zai dawo yanda yake ashe I was wrong. Lokaci yayi da zai cire komai a ranshi domin mutuwa tana kan kowa." Juwairiyya bata ce komai ba illa kaɗa kanta da tayi tana aikin tunani, itama tana son Hafiz ya tafi ya barta sannan har yanzu bata mantashi ba balle ta daina sonshi, amma a hakan take son ci gaba da rayuwa kamar kowa tunda mutuwa bata hana walwala. "Ko kuma ina zaton bai yi tsammanin zaki so ku zauna a matsayin ma'aurata bane domin sai da na mishi barazanar kashe aurena sannan ya yarda." "Me kika ce?" Juwairiyya ta faɗa da ƙarfi tana zaro idanunta waje cikin mamaki. "I'm sorry ban faɗa miki ainihin abun da ya faru ba amma hakan ba hujja bace da zai sa ya ƙi ƙarfafa auratayyanku ba. Ke mace ce Aunty Juwai, kiyi amfani da iliminki da wayonki da kuma young jikinki ki jawo hankalinshi kanki ki nuna mishi kina son a gyara wannan auren. Please try." "Mu bar maganan nan kawai Halima. Ya batun cooking classes ɗinki?" Da haka Juwairiyya ta shashantar da zancen ba don ba zata gwada abun da Halima ta faɗa ba sai don tana jin nauyinta domin Daddy da yake uba a gareta. Bayan sun gama hiran Juwariyya ta zauna ta fara tsara yanda zata canja musu Tafiyar tasu, bata ce tana mishi so irin na soyayya ba amma kyautatawan da yake mata yasa ta ji tana ƙaunarshi domin kuwa ai zuciya ma tana son mai kyautata mata. To ko a haka aka tafi ta sani zata ji daɗin zama dashi sannan itama zata yi ƙoƙari wajen kyautata mishi da kuma bashi girmanshi. Sai da aka yi sallan azahar sannan ta tashi ta ɗaura musu abincin rana wanda zai zarce ya zama na dare kamar yanda suka saba kullum. Kafin la'asar ta gama komai ta sallami mai aikinta kana ta faɗa wanka, cikin lokaci ƙanƙani ta gama shiryawa cikin farar riga mai V neck da baƙin wando wanda yake da adon lace a can ƙafan wandon. Sosai tayi kyau kamar wata ƴar tsana hakan yasa ta dinga juyawa a gaban madubi tana kallon kanta, in ba wanda ya sani ba babu wanda zai ce ta taɓa aure domin jikinta yana nan da ƙuruciyarsa. Ajiyar zuciya ta sauƙe bayan ta nitsu tana ganin suturan da ta saka, yau ne karon farko da zata taɓa saka English wears a gidan Daddy domin kuwa kullum a cikin atampa take watarana har da gyale ko Hijab. Tana jin ƙarar shigowar motarshi zuciyarta ta buga da ƙarfi amma ta danne kana ta shiga kitchen don kai mishi abinci sashenshi. A da tun kafin ya dawo zata kai ta ajiye shi kuma idan ya ci zai zo ya duba lafiyarta to shikenan sai wata safiyar ko kuma in ya kawo mata abun kwalama da dare. Sai da ta bari ya shiga ɗakinshi ya gama abun da zai yi yana fitowa ita kuma ta shigo hannunta ɗauke da tray mai ɗauke da warmers ɗin abincin. "Daddy sannu da dawowa." Ta faɗa cikin ladabi har tana russunawa kamar yanda ta saba. Daddy da bai yi expecting ganinta haka ba sai ya tsaya yana kallonta da alama tafiyar zata yi kyau. Bai amsa ba hakan yasa ta yi gyaran murya ta matso kusa dashi tana kallonshi innocently tace, "Daddy baka da lafiya ne?" Firgigit ya dawo daga duniyar tunanin da ya shiga sannan ya juyar da kanshi kan dinning table inda ta jera mishi abincin ya ce, "No, lafiyata kalau. Kina lafiya?" "Lafiya kalau, sai zaman kaɗaici. Gidan shiru babu kowa watarana har tsoro nake ji." "Uhm, zaki saba a hankali Juwairiyya. And ki daina jin tsoro babu abun da zai sameki." "To Daddy." Ta faɗa tana murmushi sai can kuma murmushin nata ya faɗaɗa tayi wani guntun tsalle ta riƙo hannunshi tana cewa, "Daddy albishir!" Ƙaramin ruɗewa yayi ko kasa numfashi yayi ne bata gane ba amma bai amsa wannan albishir ɗin da wuri ba sai da ta ƙara maimaitawa. Hannunshi kuwa da ta maƙale a ƙirjinta tana bouncing shi Daddy yake kallo sai kuma ya dawo ya kalli fuskarta. "Goro." Yayi gyaran murya yana ƙoƙarin zame hannun nashi amma ta ƙi sakinshi. "Na duba internet na samu dishes irin naku masu diabetes da yawa shine yau na maka kunun acca da cookies sugar free." "Sounds amazing, to nagode bari in ci abinci da cookies ɗin sai anjima da dare in sha kunun. Kin ga yau babu shan fruits." "To Daddy, bari in ɗauko maka Cookies ɗin." Da haka ta fita daga falon cikin walwala har ta ɓace masa da gani. "Ya Allah." Faɗin Daddy yana takawa zuwa dinning table. Yana fara zuba abinci a plate Juwairiyya ta dawo hannunta ɗauke da wani kyakkyawan ƙaramin tray da cookies ɗin a ciki, a gefen Daddy ta ajiye sannan ta matso kusa dashi har jikinsu na gogan na juna ta ce, "Bari in saka maka." Da haka ta karɓe serving spoon ɗin ta ƙarisa saka mishi ya fara cin abincin jiki a sanyaye. Abun da ta lura dashi shine kamar ya rage walwala, ko dai da gaske baya son mu'amala da ita. Ji tayi gwiwanta yayi sanyi ta fara waswasi a ranta ko dai bata burgeshi bane? Ko dai tayi zumuɗin yayi yawa ne? No! Bata fara don ta bari ba! Dama ba lokaci ɗaya zata karkato da hankalinshi gareta ba, dole sai ta ɗauki lokaci kuma sai ta jajirce. A ƙarshe tana fatan Allah Ya sa wanka ya biya kuɗin sabulu. "Abincin yayi daɗi?" Ta tambayeshi bayan ta dawo da walwalar fuskarta sannan ta zauna a gefenshi. "As always Juwairiyya. Na faɗa miki girkinki yana mini daɗi, nagode." Murmushi ta yi wannan karon har cikin ranta wanda yasa kumatunta suka lotsa ciki kana ta miƙe tsaye tana duban agogon hannunta ta ce, "Bari in barka ka huta, sai anjima Daddy." Ta haka ta fita daga cikin falon bayan ta ɗauki Cookie ɗaya tana humming waƙa a hankali. Tana shiga ɗakinta ta rufe ƙofar kana ta jinginu da gini tana gwalalo idanunta waje, lallai ta cancanci a jinjina mata. Daddy da take jin kunyarshi yau shi take ƙoƙarin seducing? But amma bature yace desperate times call for desperate measures, Daddy mijinta ne halalinta ba wani random mutum a waje ba don haka zata iya yin komai don ganin ta inganta wannan zama nasu da bata san yaushe ne ƙarshenshi ba. A ƙa'idan Daddy idan ya dawo daga office zai zauna a gida har sai an kira maghrib, daga nan kuma in ya fita ba zai dawo ba sai an yi isha. Don haka Juwairiyya tana ganin an yi isha ta yi wanka tare da canja kaya wannan karon zuwa wata doguwar riga ɗinkin bubu da aka yiwa aiki da stones. Sosai take walwali sannan ta yiwa kanta simple kwalliya wanda ba zai sa ace she is trying so hard ba. Da haka ta kallaba ɗauri mai ƙayatarwa kana ta nufi sashen Daddy bayan ta ɗauka mishi kununshi. Da sallama ta shiga ta samu yana zaune a ƙasan carpet yana karatun Jarida da gilashi a idanunshi, sanye yake cikin jallabiya fara tass wacce ta mishi kyau ba kaɗan ba a fuskar juwairiyya. Ta lura in dai ya dawo gida kayan sakawanshi kenan don yana dasu design kala daban-daban kusan ashirin a wardrobe ɗinshi wanda take gani in ta je mishi gyara. "Daddy sannu da dawowa. Ga kununka." Ta faɗa tana ajiye flask ɗin a kan dinning table. "Sannunki da ɗawainiya, ki sako mini a kofi." Da haka ya koma karatun jaridarshi Juwairiyya kuma ta zuba mishi kunun tare da saka mishi irin sugarn su sannan ta gauraya ta tako zata kawo mishi. Da gangan tayi ɗan tuntuɓe kaɗan wanda tayi kamar zata faɗi amma ta tare kanta, Daddy cikin azama ya miƙe yana tambayarta lafiya kana ya yiwo kanta ya kamo hannunta tare da karɓan kofin yana mata sannu. "Subhanallahi, Juwairiyya garin yaya haka? Ina baki ji ciwo ba kuma kunun bai zuba a jikinki ba?" Ya faɗi hakan yana duba dukkan jikinta har lokacin bai saketa ba. Marairaice fuska ta yi kamar zata yi kuka cikin shagwaɓa tace, "Ina tahowa zan kawo maka kunun shine na ji nayi tuntuɓe, amma bai zuba a jikina ba." "To Masha Allah, amma ki dinga kula next time Allah Ya tsare na gaba. Ki zo ki zauna na ga kamar kina karkarwa." Juwairiyya tana son cewa shine yake karkarwan amma ta kunshe bakinta tayi shiru tana dariya a ranta. Halima ta faɗa mata weakness ɗinshi shine Cuta. Da zarar ya ji ahalinshi basu da lafiya to fa duk wata kulawa ta duniya zai nuna musu, yana tausayawa mai cuta sannan baya raina cuta ko da ciwon kai ne dalilin abun da ya faru da tsohuwar matarshi shiyasa a daren da aka kawo Juwairiyya yace ko ciwon kai ta ji ta faɗa mishi su tafi asibiti. A kan kujera ya zaunar da ita kana ya ajiye kofin akan center table sannan ya dawo gefenta ya zauna yana kallon yanda take numfashi ɗai-ɗai alamar dai ta tsorita. "Daddy ka ji har yanzu zuciyata bata daina bugawa ba wallahi." Da haka ta ɗauki hannunshi ta manna a ƙirjinta saitin zuciyarta. Daddy dai bai ji bugun zuciyar ba amma ya ji wani abun na daban, cikin dabara ya sauƙe hannun nashi ya ce, "Na ji, sosai take bugawa. Sannu, ko zaki sha ruwa?" "A'a, sai dai chocolate." Hararanta yayi cikin wasa ita kuma ta mishi gwalo wanda hakan yasa yayi dariya yana karkaɗa kai. "Ku yaran nan na rasa gane meyasa kuke da son zaƙi. Ban taɓa jin mutumin da aka yiwa offering ruwa don ya kwantar mishi da hankali ba yace shi sai chocolate sai ke Juwairiyya sweet tooth." "Daddy ni ba sweet tooth ba ce." Ta faɗa a shagwaɓance. Bai ce komai ba amma kuma murmushin bai bar fuskarshi ba ya jawo kofin kunun ya kurɓa sannan ya ƙara na biyu. "Marigayiya tana mini kunun nan kusan kullum, watarana kuma tayi mini na Tamba. Yayi daɗi sosai nagode." A gurin wata hakan zai zama kamar ya ɓata musu yanayinsu ne amma a gurin Juwairiyya ta ga hakan ne a matsayin wani babban cigaba domin bai taɓa mata maganar tsohuwar matarshi ba, kenan a hankali ya fara sabawa da ita har yau ya kawo musu hiranta. "Nima akwai ranar da na zo gidan nan Halima ta kawo mini na sha amma dai da sugarn mu, Mummy bata gane an taɓa mata kununta ba sai daga baya." Ta ƙarisa maganan tana dariya domin da gaske hakan ya faru, a lokacin suna secondary school aka tashi daga makaranta suka biyo gidansu Halima akan zata ƙarbi wani style ɗin ɗinki amma suka samu ba'a gama abincin rana ba sai kunun Daddy da ya rage, Halima ta sato musu suka sha. Daddy murmusawa yayi kana ya kaɗa kanshi ya ce, "Ta faɗa mini hakan ya faru, Halima akwai rigima. Tun tana ƙaramarta tafi Abdul jalil kiriniya, there was a time da ta mari wasu yara a waje....." Da haka hiran ya canja salo ya dawo kan Halima, Juwairiyya tayi dariya domin labaran rigiman Halima da Daddy yake bata, ta wani guri kuwa daɗi take ji sosai domin zata iya rantsewa wannan shine karon farko da ya zauna suna hira. Kullum maganarsu bata tsayi amma yau ta ga improvements, kenan nisanta kanta daga gareshi da take yi a da shi yasa shima ya ja baya ko dai menene? Sai da goma ta wuce sannan suka farga dare yayi, Daddy kuwa ya sha kunu har kofi biyu sannan yace a ajiye mishi sauran zai sha da safe. Sallama ta mishi ta tattari kwanukan da zata kai kitchen ta nufi ƙofar fita amma ta ji Daddy ya kira sunanta. "Juwairiyya." Juyowa tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa. "Cookies ɗin sun yi daɗi na cinye su duka. Thank you." "Aikina nake yi Daddy, in kana buƙatar wani abun ma ka faɗa mini. Good night." Murmushi kawai yayi kana ya juya ya fara kashe tv itama ta juya ta tafi sashenta tana jin farin ciki a ranta. Sati biyu da haka zamansu ya ƙara daɗi domin zasu zauna su yi hira, wani lokaci kuma zasu zauna a falonshi yana karatun jarida ko yana aiki ita kuma tana kallon Korean series ɗinta da ya zame mata jiki. Duk abun da yace ta dafa mishi tana yi hakan yasa yanzu ta san menene favorites ɗinshi da kuma waɗanda baya so. Sai dai abun da ta kasa canjawa shine Daddy baya son taɓa jikinta, sannan ko ita ce ta taɓashi zai yi dabarar da zasu rabu ba tare da yayi hurting feeling ɗinta ba. Ita kuma a yanzu da suke zama su yi hira sai buƙatarta ya fi na da, domin ganinshi kaɗai kan sa ta jita a wani yanayi. Tana buƙatar mijinta amma bata san meyasa har yanzu bai gane ba balle ya bata abunda take so ba. Yau ta ƙuduri aniyar kawo ƙarshen wannan zama shiyasa tun tashinta da safe tsokanar nata ya fi na kullum, a yanda ta lura ta birkita Daddy ba kaɗan ba don haka da yamma ma da ya dawo ta ƙara akan na safe, wannan karon bai bari maghrib tayi ba ya fita. Bayan isha Juwairiyya ta ci kwalliya kana ta sanya wando three quarter tare da wani cotton riga sky blue mai siririn hannun wanda bata saka komai a ciki ba, hakan yasa albarkatunta suka fito da ainihin siffarsu har in ta sunkuya za'a iya hangosu sarai. Tana jin Daddy ya shigo ta nufi falon nashi da flask a hannunta wanda yake cike da kunun Tamba. “Welcome Daddy.” Ta faɗa tana mai adanawa kafin ta tsiyaya mishi a kofi ta nufoshi ƙirjinta na rawa. "Thank you." Faɗin Daddy yana kallon duk wani motsinta. Sai da ya kusa shanye kunun sannan ta tashi ta je ta tsaya a bayanshi ta fara massaging kafaɗunshi tana cewa, "Daddy idan na gama maka nima zaka biyani." Murmushi yayi kawai ya kaɗa kanshi kana yace, "To rigimatu, zan miki." Seconds kaɗan da haka ya ajiye kofin kunun yana jin daɗin yanda take matsa mishi kafaɗun nashi yana lumshe ido. Ana cikin hakan ne ta fara haɗawa da kunnenshi da kuma kanshi cikin salo mai rikitarwa ta wani gefen kuma tana manna mishi ƙirjinta wanda ta lura suna ƙara gigitashi ba kaɗan ba. Bata yi aune ba ta ji ya kamo hannunta ya zagayo da ita gabanshi kana ya zuba mata ido ya ce, "What do you want?" Shiru ta yi kanta a ƙasa tana jin wata muguwar kunya na lulluɓeta, hakan yasa ta rufe fuskarta da ɗayan hannunta wanda bai riƙe ba ta fara ƙoƙarin zillewa. "Juwairiyya look at me." Ya umurceta wanda babu musu ta buɗe fuskar tata tana kallon cikin nashi idon amma bata iya jurewa ba ta sauƙe nata ƙasa tana murmushi. Bai ƙara cewa komai ba ya tashi tsaye har lokacin hannunta na cikin nashi ya kashe kallon da take yi kana ya jata zuwa ɗakinshi. Minti goma da haka Daddy ya koma gefe yana kallon yanda Juwairiyya ta gama rikicewa tana buƙatarshi amma ba zai iya biya mata ba. "Kiyi haƙuri Juwairiyya, ki tashi ki saka kayanki zamu yi magana." Waɗanda suka yi payment zasu samu cigaba a weekend, masu jiran free pages kuma mu haɗu ranar monday In shaa Allah. Mum Fateey 👌 TAFIYAR MU Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) 09023713064 (11) Babu musu Juwairiyya ta tashi ta mayar da kayanta sannan ta jawo bargo ta lulluɓe jikinta, duk wannan abun da tayi Daddy na can bakin gado yana dafe da kanshi ya juya mata baya. "Juwairiyya." Ya kira sunanta yana mai juyowa gareta. "Na'am." Ta amsa can ƙasan maƙoshinta domin har a wannan lokacin baza ma ta iya faɗin a wani hali take ciki ba, tsananin buƙata ne, kunya ce, takaici ne ko zullumi? "Da farko zan fara da baki haƙuri, I'm so sorry Juwairiyya domin na cuceki na ɓoye miki wani babban al'amari game da ni. Sai dai kuma na yi hakan ne for my selfish reason saboda gudun kar Halima ta nemi saki a gurin mijinta don kawai ta zauna dani. Juwairiyya wannan matsala da kika ganni da ita ba haka nake ba, shekara biyu da suka wuce wannan cuta ta Diabetes ta bayyana a jikina. Bayan an ɗaurani akan magani na fara samun lafiya sai ya kasance bana iya gamsar da iyalina. A lokacin mun yi tunanin ko don rashin lafiyan da nayi ne ya jawo hakan amma da aka shafe watanni har biyar babu sauƙi sai muka tafi asibiti don duba me yake damuna. Marigayiya ita tayi ta yawon zuwa asibiti dani amma sai abu yayi kamar yayi sauƙi sai kuma ya dawo da ƙarfinshi wanda a yau da ni da jaririn da aka haifa duk ɗaya muke. Kina jina?" Gyaɗa kai Juwairiyya tayi kanta a ƙasa tana sauraron labarin Daddy zuciyarta na bugawa, kenan ba wai itace bata mishi kyau ba kuma ba wai ba ya sha'awarta bane! Dama ya jima da cutar a jikinshi a hakan kuma ya yarda ya aureta? "Allah Ya yi ni mutum ne mara son magani amma da na samu cuta biyun nan sai na mance ma dalilin da yasa bana son maganin. Marigayiya babu irin maganin da bata kawo mini ciki har da na gargajiya wanda ta tabbatar ba zai taɓa lafiyata ba, amma duk shan da zan musu duk kuma ka'idarsu da zan bi abun yaci tura na rasa ƙarfina na ɗa namiji. A haka muka cigaba da zama tana tare dani tana riƙe da sirrina har ta koma ga mahaliccinta dalilin ciwon kan da tayi na awanni kaɗan. Daga nan kuma na ƙara tsinkewa da rayuwa na ji ba zan sake aure ba har abada amma Halima ta tursasa mini na aureki. Wallahi bana dana sanin aurenki Juwairiyya, zaman da nayi da ke yasa kika shiga zuciyata yanda bakya tsammani amma duk lokacin da na kalleki kika burgeni ko kika bani sha'awa bana jin kaina. Hakan yasa ban nemi mu keɓance ba har sai da na ga da gaske kina buƙatata, Wallahi Juwairiyya ban yi tsammanin zan baki kunya ba, na yi tunanin tunda kina da ƙuruciya wataƙila zan iya performing amma sai abu ya zama haka. Ki yi haƙuri domin na san ko a musulunci wannan auren namu ba zai ɗore ba, sannan na cuceki kiyi haƙuri ki yafe mini." Ya ƙarisa maganan cikin sanyin murya mai cike da nadama da kuma tausayi. Kuka Juwairiyya take yi a hankali kanta a ƙasa hawayen na ɗiga kan bargon da ta lulluɓa dashi. Kuka take yi na tausayin Daddy da kuma ita karan kanta domin wannan shi ake kira ga samu ga kwanan yunwa. Ta shigo gidan Daddy ne da niyyar in zaman bai mata daɗi ba zata fita, amma da ta ga kyawawan halayenshi da kuma yanda yake kula da ita sai ta ayyana a ranta cewa babu mai rabata da gidan sai kuma wani ikon Allah. Me yasa ita rayuwarta ba zai tafi daidai ba? Me yasa a kullum jarabawa yake faɗowa kanta? Me yasa wannan karon wahalarta ba zai ƙare ba? Why her? Tana jin lokacin da ya miƙe tsaye ya shiga banɗaki har ya fito ya mayar da kayanshi ya dawo gurinta ya zauna bata daina kuka ba. "Juwairiyya kiyi magana, ban san me yake ranki ba. Wataƙila kin tsaneni ko?" Girgiza kanta tayi tana share hawayenta, sannan ta ɗago ta ce, "A'a Daddy." Ajiyar zuciya ya sauƙe kana shima yayi shiru yana tunani, can ya ƙara dubanta fuskarshi kamar wanda zai yi kuka ya ce, "Shikenan, ba zan cigaba da cutanki ba Juwairiyya zan sawwaƙe miki sai ki samu....." Bai kai ga ƙarisa maganan ba Juwairiyya ta sukwano cikin sauri ta rufe mishi bakinshi tana girgiza kanta tana cewa, "Ka rufa mini asiri kar ka sakeni. Zamu cigaba da neman magani har Allah ya baka lafiya Daddy. Wallahi zan yi haƙuri har lokacin da Allah zai baka lafiya. Ina son zama da kai kuma ba zan yi gaggawan rabuwa da kai akan ciwon da yake da magani ba. Wallahi zan yi haƙuri, zan tayaka zan kuma yi supporting ɗinka wajen neman maganin." "Kayya. Da zan samu lafiya da tun wancan lokacin na samu Juwairiyya. Nima ba zan so rabuwa da ke ba don na saba da ke ina jinki har cikin raina, wallahi rabuwa da ke zai ƙara fame mini wani ciwo a cikin zuciyata. Amma ba zan ƙara cutar da ke ba, wanda na miki a baya ma ya isa kuma ina neman gafararki." "Daddy don girman Allah kar ka ƙara kiran rabuwarmu. Ka tsaya ka saurareni." Duk da irin raɗaɗin zafin da yake ji a zuciyarshi bai hanashi yin murmushi ba dalilin kalmarta na ƙarshe. "A zaune ma nake Juwairiyya, a zaune nake." "To Daddy. Ka ga bamu jima da yin auren ba, yanzu in aka ji mun rabu ni duniya zata zaga a ce wani mugun halin nake maka ka kasa zama dani. Kuma ba zamu yi gaggawa ba tunda a da ba haka kake ba, rashin lafiya ce kuma kowacce cuta Allah Ya ce tana da maganinta. Don Allah kar ka yanke hukunci ba tare da ka duba yaya rayuwata zata ƙare ba, ka rufa mini asiri. Kuma nima ina son zama da kai bana son rabuwa da kai. I will stay with you in sickness and in health. Mu ɗauki hakan a matsayin jarabawarmu kuma mu roƙi Allah Ya sa mu iya cinta." Juwairiyya bata samu Daddy ya yarda da uzurinta ba sai da suka yi doguwar debate, tun tana kan gado har ta dawo ƙasa ta durƙusa a tsakanin ƙafafunshi sannan ya nisa ya ce, "Abun da nake so ki fahimta shine ke yarinya ce Juwairiyya, ba lalle bane ki gane cewa wannan auren akwai cuta a ciki ba. Amma ba zan ƙi taki ba, zamu nemi magani Allah kuma Ya bani lafiya. Sai dai in ba'a samu waraka ba kiyi haƙuri da duk hukuncin da zan ɗauka." Cikin murna Juwairiyya ta miƙe tsaye ta rungumeshi tana mishi godiya domin ita a gurinta ba ƙaramin cetonta yayi ba. Da ace ta koma rayuwarta ta zawarci gwanda ta zauna tare da Daddy har Allah Ya bashi lafiya. Wannan kenan. Wata huɗu da haka Juwairiyya ce zaune da Daddy a gaban Doctor yana sauraran bayanansu wanda idan Daddy ya faɗi nashi sai Juwairiyya ta ƙarisa, yanda suke magana sosai ya bawa Doctor sha'awa da kuma dariya amma saboda profession ɗinshi ya hanashi nuna waɗannan emotions ɗin sai ya cigaba da gimtse fuskarsa yana jeho musu tambayoyi suna amsawa. Magani ya rubuta musu kamar yanda sauran Doctors ɗin da suka ziyarta a baya suka basu kana ya ƙara musu da shawarwari yanda zasu shawo kan matsalar, yanda Juwairiyya ta maida hankali tana sauraron Doctor tana gyaɗa kai sosai ta bawa Daddy tausayi har yana jin zuciyarshi na mishi nauyi, kar cutar tayi yawa fa. Suna fitowa daga asibitin suka nufi gida bayan sun sayi magungunan, a falonshi suka yada zango Daddy ya shige ɗaki don zai yi amfani da banɗaki ita kuma Juwairiyya ta fara rage kayan jikinta sannan ta jawo ledan magungunan tana dubawa don sanin dosage ɗin su. A haka Daddy ya dawo ya sameta zaune a ƙasa daga ita sai leggings da half vest. "In ba dole ba bazan sha duka waɗannan magungunan ba. Ganinsu kaɗai idan nayi sai in ji zuciyata ta tashi." "Ohh Daddy ka fiye tsoron magani wallahi, to ko za'a maka alluransu?" Ta faɗa cikin zolaya tana murmushi. "No, bani maganin in sha." Ya amsa yana zama a saman kujera ta fara miƙo mishi yana zubawa a bakinshi yana korawa da ruwa. Sai da ya shanye sannan ta tattarasu ta zuba a leda kana ta miƙe tsaye don zuwa adanasu Daddy ya riƙo hannunta ya jawota ta tsaya tsakanin ƙafafunshi kana ya ɗaga kanshi yanda zai ga fuskarta ya ce, "Juwairiyya anya akwai haske a lamarin nan? Anya kuwa zan warke? Aurenmu yanzu wata shida wanda ko sau ɗaya ban taɓa biya miki buƙatarki ba Juwairiyya. Abun yana damuna sosai." Ajiye maganin tayi a kan kujera a gefenshi kana ta tallafo kanshi da hannayenta duka biyu ta kalli fuskarshi wacce take tattare da damuwa ta sumbaci goshinshi kana ta ce, "Neman magani muke yi wanda dama ba lokaci ɗaya zamu samu waraka ba, dama mutum kan iya shan magunguna kala goma sai a na sha ɗaya yayi dace. To mu ma bamu fara don mu bari ba, da yardar Allah zaka samu lafiya ka daina ma kawo waswasi a ranka. Ka ji Babyna?" Murmushi yayi mai ƙayatarwa yana jin sanyi a ranshi domin Juwairiyya ta san yanda zata kwantar mishi da hankali muddin ya furta mata cewa ya karaya ko kuma ya nuna mata alamun hakan. "Juwairiyya bana son cutar da ke, kullum buƙatarki ƙara ƙaruwa take yi...." Bai kai ga ƙarisa maganan ba ta tari numfashinshi ta ce, "Mu bar zancen nan, yanzu ba magani aka ɗauraka a kai ba?" "Hakane." "To ka gani. Don't lose hope. Ka ji?" "Na ji rigimatu." Ya faɗa yana dariya. Itama darawan ta yi kana ta ɗauki ledan da ta ajiyen ta je ta adana kana ta nufi sashenta don ɗaura musu abincin rana dama fitan hantsi suka yi. A daren ranar Juwairiyya ce kwance a jikin Daddy a ɗakinshi suna hira kaɗan-kaɗan yana danna wayarshi, can ya dakata da danne-dannen ya ajiye wayar a gefe yana jin yanda Juwairiyya take mutsu-mutsu a jikinshi kamar wacce ma hankalinta baya jikinta. Ji yayi hawaye ya taru a idanunshi amma yayi saurin maidasu domin gudun kar ta gani, a jikinshi kuma bai ji wata alama da zata nuna zai iya taimakonta ba wanda hakan shine abun da ya fi tsoro a yanzu. Hannunshi ya kai wani sashe na jikinta wanda ya sa ta ƙara birkicewa ya ce, "There, there, let me help you a little." Bayan wata ɗaya Daddy ne tsaye a falonshi tare da Juwairiyya wacce take mishi shagwaɓa dalilin tafiyar da zai yi na sati biyu. "Daddy to ka tafi dani mana." Ta faɗa tana bubbuga ƙafanta a ƙasa. "Ke da kika fara zuwa school shine zaki yi tafiyan har sati biyu? A'a kiyi zamanki a gida, next time idan zan yi tafiya kuma kina hutu sai mu tafi tare." "Ni dai wallahi ba'a kyauta mini ba, sai da na shiga school sannan zaka yi tafiya mai daɗewa haka?" "Juwairiyya Rigimatu, to ki barni in tafi kar in yi missing ɗin flight ɗina." Da haka ya mata sallama ya fita harabar gidan inda Abdul Jalil zai tuƙashi zuwa Airpot. Har ya zauna a cikin mota ya rufe sai kuma ya buɗe ya fito ya koma cikin gidan ya samu Juwairiyya tana tattare kan dinning inda ya gama cin abinci. Tana jin shigowarshi ta juyo tana tambayarshi ko ya manta wani abu ne amma bai amsa mata ba ya rungumeta tsamtsam a jikinshi. Murmushi tayi ta fara tsokanarshi ko zai fasa tafiyan ne ya dawo su zauna? "Duk abun da ya faru ki sani ina sonki Juwairiyya, and please take care of yourself for me. Kin ji?" "Na ji Daddy kuma Babyn Juwairiyya." Da haka ya saketa yayi kissing goshinta kana ya fita cikin sauri ta bishi da addu'a fuskarta ɗauke da murmushi. A bakin window ta tsaya tana leƙenshi har ya shiga mota suka fita daga gidan sannan ta juya ta cigaba ta aikinta. Tana gama gyaran falo ta koma ɗakinshi nan ma ta fara gyarawa tana tattare kayanshi da ya cire tare da sauran tarkace. Sai da ta gama ta hango wani damin kuɗi mai yawa akan bedside tare da wani paper a ƙasanshi. Murmushi ta yi domin ta san Daddy ya manta ne dasu domin ya tura mata kuɗi cikin Account ɗinta wanda in tana buƙatar wani abu ta saya duk da cewa suna da komai a gidan. Kuɗin ta matsar gefe sannan ta ɗauki takardar kamar ba zata buɗe ba amma ta buɗe, contents ɗin da yake ciki yasa ta kwala ihu ta zube a gurin tana kama kanta da dukkan hannayenta, nan da nan kuma kuka mai ƙarfi ya kwace mata har numfashinta na ɗaukewa. "Mugun mutum! Coward! Ka cuceni ka tona mini asiri. Me yasa ba zaka ƙara haƙuri ba?" Da haka ta tashi ta ɗauki wayarta hannunta na karkarwa har bata ganin me take dannawa, hakan yasa ta goge fuskarta da hannunta sannan ta samu numbern Daddy ta danna kira amma aka ce mata is switch off. Da haka ta nemo na Abdul Jalil ta kirashi ya ɗauka babu ɓata lokaci, "Aunty Juwai...." Bai kai ga ƙarisawa ba ta katseshi. "Ina Daddy?" "Tun ɗazu na sauƙeshi ni kuma ina dawowa gida. Wani abu ne ya faru?" Wannan tambaya da ya mata shi yasa ta ƙara fashewa da kuka har tana sarƙewa, shi kuma Abdul jalil hankalinshi ne ya tashi ya fara tambayarta me yake faruwa. Da kyar ta saisaita kanta ta ce, "Daddy ya sakeni, ya raba auren da ke tsakanina dashi Ya Abdul jalil." "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Me yasa?" Bata bashi amsa ba ta jefar da wayar ta ƙara zama a ƙasan ɗakin tana kuka tana tausayin rayuwar da zata fuskanta nan gaba. "Hafiz mutuwarka tonon asiri ne a gareni, rayuwata tana ta gararamba saboda rashinka. Allah ka kawo mini ɗauki, Allah ka ji tausayina ka taƙaita mini wannan wahalan rayuwar." Mum Fateey 👌 TAFIYAR MU Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) 09023713064 (12) Kafin Abdul Jalil ya dawo gida Juwairiyya ta kwashi iya abun da zata iya ɗauka na buƙatunta ta bar gidan. Tana shiga ta samu Mama tana gurin aiki sai Nan (Kakarsu) da kuma mai aiki ne kawai a gidan. Babu ɓata lokaci ta buɗe ɗakin da tayi zawarcinta a ciki ta kwanta akan katifa taci gaba da kuka har Nan ta shigo ta sameta a haka. "Ke ƴar nan ina miki magana kika ƙi kulani sannan kika shigo nan kina kuka? Me ya faru kika bar gidan mijin naki?" "Don Allah Nan ki barni da abun da yake damuna ki daina mini wasu tambayoyi." Ta faɗi hakan tana mai juyar da kanta ɗayan gefen inda ba zata ga Nan ba. "Ki ji mini ja'irar yarinya da rashin kunya, don na tambayeki shine ya zama laifi. To mutuwa aka yi kike kukan?" Ta ƙara wata tambayar don bata haƙura ba. "Ni nace miki wani ya mutu? Babu wanda ya mutu." "To menene ya faru?" Daga haka Juwairiyya bata ƙara kulata ba, hakan yasa Nan ta juya ta tafi tana cewa, "Kici kanki ke ɗaya." Tunda Juwairiyya ta shiga ɗakin bata fito ba har Mama ta dawo daga aiki, Nan tana ganin ta dawo ta bata labarin cewa ga can Juwairiyya a ɗaki ta zo tana kuka. Gaban Mama ne ya faɗi rass wanda sai da ta ga duhu ya wuce lumm ta gabanta sannan ta dafe ƙirjinta ta nufi ɗakin da Juwairiyyan take tana haɗa hanya. "Menene ya faru kika zo kina kuka Juwairiyya? Ki tashi ki faɗa mini abun da ya faru." Faɗin Mama tana shiga cikin ɗakin ta tsaya kan Juwairiyya. A hankali ta miƙe fuskar nan tata ta kumbura idanunta sun yi jajur kamar garwashi sannan sun ƙanƙance duk da girmansu. Hijabin da yake jikinta kuwa ya jiƙe da zufa, hawaye har da guntun majina. Buɗe baki tayi da niyyar magana sai kuma wani kukan ya kwace mata har tana sheshsheƙa. "Juwairiyya ki faɗa mini abun da yake faruwa domin hankalina ya tashi wallahi. Ki daina kukan nan ki faɗa mini." Faɗin Mama wacce a yanzu tsoron ya yawaita a zuciyarta. "Daddy ya sakeni Mama, ya mini saki ɗaya." "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un." Haka tayi ta maimaitawa bayan ta samu guri ta zauna."Me kika mishi Juwairiyya ya sakeki? Rashin kunya kike mishi ko kuma wani abun?" "Wallahi Mama babu abun da nake mishi mara daɗi, lafiya kalau muke zaune yau yayi tafiya muka rabu lafiya amma ina shiga ɗakinshi na samu takardar akan bedside. Ko a fuska bai nuna mini ya sakeni ba har muka yi sallama Mama." Faɗin Juwairiyya tana ƙara jin haushin Daddy a ranta. Dama ga abun da take gudu domin duk yanda za'a yi babu mai yarda da cewa ba laifi ta mishi ya saketa ba. Kwata-kwata auren nasu yanzu ya cika wata bakwai da ɗori! Me yasa ba zai ƙara haƙuri har su shekara ba kafin ya ɗauki matakin ba? "Haka kawai ba zai sakeki ba Juwairiyya dole akwai wani dalili. Ki faɗa mini tun wuri sai mu san yanda zamu gyara al'amarin." Ga kuma abun da take tsoro! Wato duk yanda zata kai ga faɗa musu cewa ba laifi tayi mishi ya saketa ba ba zasu yarda ba. Idan kuma ta fito fili ta faɗi gaskiyan al'amarin ta tona mishi asiri ne sannan wasu ba zasu yarda ba zasu ce ƙarya take mishi tana son wulaƙantashi ne a cikin mutane. Ta sani kuma zata iya rantsuwa Mama ma ba zata yarda da ita ba, to me amfanin bayyanawan? A zaman da tayi dashi ya kyautata mata don haka ba zata so ta kwaye mishi zani a kasuwa ba, ta wani gurin kuma Daddy uba yake a gurin Halima ƙawarta. Idan ta fito ta faɗi matsalarshi da wani ido zata ƙara kallon Halima? Zata rufa mishi asiri ko don waɗannan dalilai biyun amma ba zata taɓa daina jin haushin yanda ya saketa ba. Me yasa ba zai iya bata takardarta a hannunta ba sai dai ya ajiye ta je ta ɗauka? Ashe tun kafin ya tafi sunanta sakakka ce a gurinshi bata sani ba! Wannan sakin da yayi mata da kuma salon da yayi amfani dashi wajen sakin zai kasance a cikin zuciyarta har ƙarshen rayuwarta, ba zata taba mantawa dashi ba har abada. "Wallahi, wallahi babu laifin da nayi mishi." Shiru Mama tayi tana zaune a gurin har na tsawon minti biyu tana kallon Juwairiyya sannan ta ce, "Idan zaman hakan kika zaɓa gaki ga ita Juwairiyya, amma sai dai zan faɗa miki ba lallai bane ta miki daɗi ba. Sannan ba a kanki aka fara yiwa mutuwa ba, hakan da kika yi kin nunawa Allah kenan baki da tawakkali baki san ƙaddara ba. Ga ki ga gidan Juwairiyya, in kuma kina da wayo sai ki san yanda zaki yi mijinki ya mayar da ke gidanshi." Tana faɗin hakan ta tashi ta koma ɗakinta, abincin ranar yau kuma bai samu ya shiga cikinta ba. Fitan Mama daga ɗakin yasa Juwairiyya ta ƙara fashewa da kuka domin gashi nan hatta uwar da ta haifeta bata yarda da ita ba, haka kuma duk duniya ita za'a bawa laifi babu wanda zai yi tunanin laifinshi ne. Wannan shine ƙalubalen da Juwairiyya ta fara fuskanta bayan aurenta da Daddy ya ƙare. **** "Gata can zata tafi makaranta, ka ganta sulum-sulum kamar in ka saka mata yatsa a baki ba zata iya ciza ba amma nan jarababbiya ce." Faɗin Garbati mai shago da yake can ƙasan layinsu Juwairiyya. "Cewa aka yi Jarababbiya ce?" Wani baƙon mutumi ya tambaya yana mai kallon lokacin da ta tari mai napep akan titi ta shiga suka tafi. "Haka dai ake faɗa, wai tsohon tafi ƙarfinshi saboda jarabarta shine da ya ga ba zai iya ba ya sallameta." Garbati ya amsa mishi yana bawa wani saurayi sigari. Saurayin yayi caraf ya karɓi zancen yace, "Ba haka aka faɗa ba fa, cewa aka yi yana zarginta da ɗan cikinshi ne amma bashi da shaida shine ya saketa." "To in dai hakane ai abubuwan da aka faɗa da yawa, ni wannan na ɗauka don shi zai fi zama gaskiya. Gaskiya ana mata kyakkyawar shaida zai yi wuya a ce fasiƙanci take yi da ɗanshi, sai dai baka san halin mutum na ɓoye ba amma gaskiya zai yi wuya." "Wai menene sauran abun da ake faɗin?" Mutumin ya sake tambaya amma Garbati yayi shiru kamar bai ji ba don ya lura kamar takanas mutumin ya zo domin binciken halin Juwairiyya. "Ai ka san baban ƙawarta ta aura, to an ce wai ƙawar tata ce bata son auren shine tayi yanda ta rabasu. Wasu sun ce ta rainashi ne, wasu kuma suka ce sata take mishi tana kawowa gidansu...." Saurayi mai sigarin ya fara zayyanowa Garbati yayi saurin katseshi da cewa, "Wannan kam duk wani mai hankali ma ba zai ɗauka ba, da tana da waɗannan halayen da mutanen unguwan nan ne zasu fara sani. Lukman don Allah kayi tafiyarka kar da sassafen Allah ka ɗauki alhakin ƴar mutane." Ya bugi tsuntsu biyu da dutse ɗaya. Wannan magana ta sa Lukman ya tafi yana busa sigarinshi shi kuma mutumin yayi jimm kamar ba zai tafi ba, can kuma ya miƙe ya karkaɗe rigarshi ya shiga mota ya tafi. "Mutane sai shegen gulma da bin diddigi." Faɗin Garbati bayan ya ga tafiyar mutumin ya manta cewa da shi aka fara kafa chaptern Juwairiyyan. Juwairiyya ce zaune a class tana jiran lokaci yayi Lecturer ɗin ya fita don ta samu ta koma gida da wuri. Yana fita ta bi bayanshi ta fita daga makarantar ta tari napep sai gida, a can ta tarar da aikin da yake jiranta na girkin rana da kuma gyaran ɗakin Mama kafin ta dawo daga aiki, domin kuwa Mama ta kori mai aikinsu tace bata ga amfanin zamanta a gidan bata aikin komai ba, duk kuwa da cewa Juwairiyyan tana zuwa makaranta watarana ma a can take wuni amma a haka zata dawo ta samu wasu aikin suna jiranta. Wani abun da ta lura dashi shine ko Surayya ƙanwarta da yanzu take SSS 3 bata kaita tiƙan aiki a gidan ba, kamar Mama tana mata kora da hali ne. Amma wannan bai dameta ba kamar maganar aure da Mama ta fara matsa mata a kai. Tun bayan mutuwar aurenta Daddy bai nemeta ba haka itama bata sake nemanshi ba sai Halima ce da take yawan kiranta wanda Juwairiyya ta yi blocking ɗinta don bata ga me zata faɗa mata ba. A yanda ta lura Daddy bai faɗawa Halima dalilin rabuwarsu ba sai cewa yayi wai a tambayeta, to kenan ita ce mara rufin asiri mara kunya da zata buɗi baki tace ga matsalar da suka fuskanta har ya kai ga datsewar zaman nasu? Duk irin tambayar duniyar da Mama tayi mata akan dalilin sakinta da aka yi kuwa ta ƙi faɗa mata domin tayi alƙawarin rufawa Daddy asiri har ƙarshen rayuwarta, na biyu kuma ta sani ko ta faɗa Mama ba zata yarda ba zata ce karya take mishi don bata son komawa. To wa ya fita son komawa gidan Daddy? Ita ta ji ta gani zata iya zama dashi duk da lalurar da yake fama da ita amma bai nemi shawararta ba ya saketa, duk hakan bai isheshi ba sai da ya ƙara da kin kiranta har sai da ta gama iddah sannan ya nemeta a waya yana tambayar wai ya take. Kalma ɗaya ta 'Coward' ta furta mishi daga nan shima tayi blocking ɗinshi. Ana haka kuma sai gashi wai ya zo ƙofar gidansu, babu yanda ta iya haka ta fita don a gaban Mama aka yi kiran nata. "Juwairiyya kina lafiya?" Ya tambayeta yana mai mata kallon tausayi domin har ta canja ta ƙara ramewa. "Kalau. Me ya kawoka ƙofar gidanmu?" Ta tambayeshi kai tsaye domin ta so ta tsigeshi tass amma kwarjininshi da girmanshi sun haɗu sun danne wannan tsiwar tata. "Na zo ne na dubaki, sai na lura kuma bakya murna da ganina." Wannan magana da yayi shi jawo hawayen da Juwairiyya take ta dannewa suka zubo kan fuskarta ta dubeshi duk jikinta a sanyaye ta ce, "Daddy sakina dai kayi, sakina kayi ka ajiye mini takardar sai da naje na ɗauka na gani sannan na gane ni sakekkiya ce. Bamu yi haka da kai ba sannan ba haka muka yi alƙawari ba, ka mini gaggawa ka datse mini farin cikina ka dawo dani rayuwar da nake gudu. Wallahi baka kyauta mini ba, zuwanka kuma ya ƙara fame mini wani ciwo a zuciyata don Allah kar ka sake zuwa inda nake, zaman da muka yi a baya ma ya isa. Don Allah ka tafi." Da haka ta juya ta shige cikin gidansu ta barshi tsaye a gurin shima yana jin kamar yayi kukan. Bata jima da shiga ba yara suka yi sallama suka fara shigowa da kayan masarufi mai yawan gaske, hakan yasa Mama da ta tareta a tsakar gida tana tambayarta dalilin zuwan nashi ta dakata har aka gama shigo da kayan sannan yaro na ƙarshe ya shigo da envelope mai kauri ya miƙa mata wai in ji Alhajin waje. Tana buɗewa ta ga kuɗine a ciki wanda a baya ya ɗaura mata a kan takardan sakinta wanda zai yi kimanin dubu ɗari biyu, sai kuma wata wasiƙa wacce kamar yanzu ya rubutata. Saboda rashin sanin me ya rubuta a ciki yasa Juwairiyya ta miƙawa Mama kuɗin ita kuma ta shiga da wasiƙar  ɗaki ta fara karantawa kamar haka.... 'Zan fara da ƙara baki haƙuri Juwairiyya duk da nasan yayi kaɗan ya goge laifin da na miki, amma kiyi haƙuri ki kuma yafe mini domin rabuwarmu shine mafi alkhairi kuma ba zan iya cigaba da zama dake ina cutar da ke ba, wallahi ba zan iya ba. Sannan ina sonki ina ƙaunarki zaman da nayi da ke kin shiga zuciyata ba zan taɓa mantawa da ke ba har ƙarshen rayuwata. Kafin ki aureni I'm a broken man, bayan haka kuma ya ƙaru da cewa ba zan iya biya miki buƙatunki ba, you deserve someone better someone who can take care of you. A ƙarshe ina miki fatan alkhairi, Allah Ya miki albarka Ya kuma baki miji nagari wanda zai riƙeki amana don you are a rare gem Juwairiyya, da ina da lafiya wallahi babu abun da zai sa in rabu da ke. Allah Ya miki albarka. Daddy.'   Tun daga ranar bata sake jin ɗuriyar Daddy ba haka kuma Halima ma ta daina nemanta don da alama tayi fushi ne, sai dai bata sani ba cewa ba laifinta bane kuma ba zata iya faɗa mata gaskiyan abun da ya faru ba. Mama kuma ta mata faɗa ta mata nasiha amma kullum maganarta shine 'ba laifina bane ya sakeni'. Labaran da ake faɗa a kanta kuwa duk yana dawowan kunnensu wanda Mama tafi kowa shiga ɓacin rai don ta san ɗiyarta ba zata taɓa neman ɗan mijinta ba ko kuma tayi sata ba. Ire-iren waɗannan ƙalubalen yasa Mama ta fara mata kora da hali wai duk don ta gaji tayi aure. Wannan kenan. A yanzu itama Juwairiyya tana son yin auren domin ta huta da faɗan Mama sannan ta huta da tsegumin mutane, hakan yasa wannan karon duk wanda yayi sallama da ita zata fita ba tare da an mata dole ba. Ita kanta mamaki take yi wato idan duniya ta bugeka zaka yi hankali babu wanda ya sani. Sai dai matsalar da aka samu shine duk cikin masu zuwa gurin nata a yanzu ƴan iskan sun fi yawa musamman da suka samu labarin cewa wai ita jarababbiya ce, waɗanda suka zo da niyyar aure kuma tayi rantsuwa da Allah su ba ajin aurenta bane. Duk da cewa tana son auren tayi alƙawarin ba zata auri wanda zata dawo tana dana sanin aurenshi daga baya ba. Ana cikin haka Hussaini ya dawo da jarabarshi tare da wani magidanci mai suna Salisu wanda gurin aikinsu ɗaya da Mama sannan Maman ne da kanta ta bashi izinin neman Juwairiyyan. Ranar farko da ya fara zuwa ta nuna bai mata ba don haka kawai ta ji tana jin haushinshi, a zuwanshi na biyu kuwa da ta kalli cikin idanunshi da ya sakawa kwalli sai ta ji wani sashe na hankalinta ya kau, abun bai tsaya a nan ba domin kuwa bayan tafiyanshi duk waɗanda suka zo sai ta koresu kuma abun mamaki Mama ta daina cewa komai, hakan yasa babu mai zuwa gurinta a yanzu sai Hussaini mai baƙar jaraba da kuma Salisu mai kwalli a ido. Juwairiyya tana shigowa gida ta kai jakanta ɗaki kana ta fito tsakar gida ta ɗaura musu abincin rana wanda shinkafa ce da wake da mai da yaji. Tun da ta dawo Nan bata fito ba hakan yasa bayan ta sauƙe abincin ta gama rabiya ta kai mata nata har ɗakinta ta ajiye ta sameta tana bacci, bata tasheta ba ta fice don zuwa gyaran ɗakin Mama, tana gamawa Maman ta dawo daga aiki wanda kai tsaye ta wuce ɗakin Nan don dubata da yake ta kwana da zazzaɓi. A nan ta tarar da gawar mahaifiyar tata wacce ta mutu cikin baccinta, tana hawaye ta gyara mata kwanciyarta sannan ta lulluɓeta ta fita zuwa ɗakinta ta samu Juwairiyya na adana tsintsiya don ta gama mata sharan. "Mama me ya faru kike kuka?" Juwairiyya ta tambaya cikin kiɗima don ta jima bata ga mahaifiyarta tana kuka ba. "Allah Ya yiwa Nan rasuwa, wahalarta ta ƙare. Ki kira kannena a waya ki faɗa musu." Tana faɗin hakan ta fice ta koma ɗakin Nan ta bar Juwairiyya itama hawayen na zuba a idanunta. Ya za'a yi Mama ta barta da wannan aikin? Me yasa ita ba zata kirasu ta faɗa musu ba sai ita? Me zata ce musu? Tana tsaye a gurin Mama ta dawo ta ɗauki wayar ta fara kiransu tana faɗa musu don kamar itama ta ga ita ya dace ta kirasu ba Juwairiyya ba. Wannan abincin da ba'a ci shi cikin daɗin rai ba kenan, ana sallar la'asar kuwa aka kai Nan makwancinta na gaskiya. Mum Fateey 👌 TAFIYAR MU Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) 09023713064 (13) Bayan rasuwar Nan da sati biyu Mama ta koma bakin aikinta, hakan yasa in zasu fita sai dai su rufe gidan tunda babu kowa a ciki domin Surayya yini take a school sai yamma take dawowa, Walid kuma da Mama ta lura zai fi ƙarfinta sai ta mayar dashi boarding school na wani babban malamin addini da yake can Kano, cikin ikon Allah kuwa ya fara nitsuwa domin bayan karatu da ake koya musu a can har da tarbiyya. Idan kuma Juwairiyya bata da lectures sai ya kasance ita ɗaya za'a bari a gida, wannan tsarin yasa Mama ta tashi haiƙan da cewa Juwairiyya ta zaɓi miji tayi aure bata son zamanta ita kaɗai a gidan. Yau Salisu ya kawowa Juwairiyya ziyara wanda da ya aiko yaro cewa yana waje sai da zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske kamar kullum, domin ta lura kamar shakkarshi take ji bata kuma iya mishi musu. Sau da dama sai ta fita da niyyar korarshi sai ta kasa, haka zai gama surutunshi ya tafi tana biye mishi domin kuwa bata son ta ɓata mishi rai. Fuskarta babu walwala ta fita ta sameshi a cikin motarshi yana zaune, gaisheshi ta yi daga waje ya ƙi amsawa kana ya dubeta a lalace yace, "Ki shigo motar mu yi hira." Girgiza kanta tayi alamar a'a amma kuwa zuciyarta lugude take yi don bata san yanda Salisu zai ɗauki hakan ba. Gimtse fuskarshi yayi sosai ya dubeta a karo na biyu ya gyara zamanshi ya ce, "Ki shigo bana son musu Juwairiyya. In kuma kina son raina ya ɓaci ne to bismillah." Kamar zata yi kuka haka ta shiga cikin motar wanda zata iya rantsuwa bata taɓa shiga motar duk wani mai nemanta ba sai a kanshi. Zuciyarta ta haneta ya fi sau a ƙirga amma kuwa gangan jikinta ya kasa kin aikata abun da aka umurceta a kai ɗin. Suna hiran kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta ta ji ya kamo hannunta ya fara murzawa, wannan abun da ya mata shi yasa ta zabura ta kwace hannun nata tana mai jin tsanarshi a cikin zuciyarta. Zagi da baƙaƙen maganganu kuwa babu irin wanda bai zo cikin zuciyarta ba amma ta kasa furtawa a harshenta, ji tayi hawaye sun taru a idanunta tana jin ta tsani kanta da shi Salisun amma babu yanda ta iya. "Yaya dai?" Ya tambayeta kamar bai san me yayi ba. "Don Allah kar ka sake taɓani wallahi bana so." Ta faɗa a sanyaye kamar mai neman gafara. "To don na riƙe hannunki shine ya zama laifi? Ba aurenki zan yi ba?" Ya tambayeta kamar mai yin faɗa. Girgiza kanta tayi sannan ta ɗago fuskarta wacce tayi kalar tausayi ainun ta ce, "Na sani amma ni bana jin daɗi ana taɓani ne. Kayi haƙuri." "To naji ba zan sake ba, amma dai ki barni in riƙe hannun naki one last time. In kin barni na riƙe ba zan ƙara tambayarki ba." Ya faɗa yana mai ware tafin hannunshi akan ta ɗaura nata a kai. Miƙar da hannunta tayi don yin abun da ya buƙaceta da yi amma suka ji an kwala mata kira da wata kakkausar murya wacce ta sa hanjin cikinta suka kaɗa. "Juwairiyya!" Da sauri ta juyo a razane tana ganin mutumin da yayi kiran nata. Muhammad ne tsaye a bakin window ta gefen Salisu da alama ya ji kuma ya ga duk abun da ya faru. Fuskar nan tashi ta turnuƙe har sai da tayi jaa tsabar ɓacin rai yana tsaye yana kallonsu. "Ki fito daga motar ɗan iskan nan." Ya umurceta yana nuna Salisu da yatsa. Har ta juya da niyyar fita sai kuma ta juyo tana kallon Salisu kamar mai neman izininshi shi kuma Muhammad yake kallo yana mishi wata murmushin mugunta. "In fita?" Ta tambayi Salisu domin kuwa itama tana son fitan bata son ƙara ko second ɗaya ne a ciki. Bai amsa ba sai da ya ɗauki seconds talatin suna kallon-kallon tsakaninshi da Muhammad sannan ya gyaɗa mata kai ta fita da sauri ta samu guri ta tsaya tana kallonsu. Sai a lokacin Muhammad ya dubeta kamar wanda zai daketa ya ce, "Yanzu ke baki ji kunya ba? Yanzu wannan mutumin ne zai sa ki saɓawa ubangijinki? Ina hankalinki da iliminki yake?" "Mallam kai waye zaka zo har ƙofar gidansu kana zaginta? Ta sanka ne ko ƙarfin hali ne irin naku na ƴan sa ido?" "Ba da kai nake yi ba, ka kuma riƙe sauran guntun mutuncinka." Da haka ya ƙara maida dubanshi kan Juwairiyya wacce ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta amma idanunta na zubar da hawaye. "Wannan ba halinki bane kar kuma ki bari wani ya zo ya ɓata miki tarbiyyar da aka jima ana baki. This is not you at all! Me yake damunki?" "Don Allah ka tafi." Ta samu kanta da faɗi ba tare da ta kalleshi ba. "Mallam ka ji tace ka tafi." Faɗin Salisu yana kaɗa kanshi kamar yana jindaɗin draman da suke yi. Takawa Muhammad yayi da niyyar zuwa gurinta amma tayi saurin dakatar dashi ta hanyar ɗaga mishi hannu tana cewa, "Just ka tafi, ba ya buƙatar ganinka a nan." "Something is wrong with you, this ain't you! Yaushe kika damu da abun da wani yake so?" Wannan magana yasa ta harareshi sannan tace, "Wato a haka ka ɗaukeni? Muguwa wacce kanta ta sani bata damu da wasu ba?" Zai yi magana Salisu ya rigashi don ya lura spotlight ɗin ya bar kanshi ya koma kansu, hakan bai mishi daɗi ba don haka yace, "Juwairiyya ki shiga gida sai gobe idan na dawo." Yana gama magana ƙafafunta suka fara takawa ta nufi cikin gida. Muhammad da hakan ya bashi mamaki yayi mata magana na ƙarshe don ya ga reaction ɗinta ya ce, "Muhammad Hafiz bashi da lafiya suna kwance a asibiti, mamanshi tace tana son ganinki." Tsayawa tayi cakk sannan ta juyo fuskarta ɗauke da matuƙar damuwa ta ce, "Subhanallahi me ya sameshi?" "Juwairiyya ki koma cikin gida bana son tsayuwarki da wannan mutumin. Ki kirasu a waya ki gaishesu ya isa." Faɗin Salisu a hasale domin zuwan Muhammad yana ƙoƙarin ɓata mishi shirinshi. Bata ƙara magana ba ta shige cikin gida da sauri, hakan yasa Muhammad ya juyo ya kalli Salisu wanda shima shi yake kallo irin 'me zaka yi akai?' Bai ce komai ba ya shige motarshi ya tafi, ganin haka yasa shima Salisu ya kaɗa tashi motar ya bar unguwar yana ayyanawa a ranshi cewa Juwairiyya ta fara mishi musu ya kamata ya ƙara ɗaukan mataki a kanta. Da daren ranar aka aiko wani yaro gurin Juwairiyya da wani leda babba tare da wani guntun note a paper wanda ta karanta kamar haka... 'Ina ta duba hanyarki amma baki zo ba, jikin Hafiz har yayi sauƙi an sallamemu. Amma kafin nan sai da muka haɗa maganin da na gida kamar mayu ne suke son tsoritashi. Ga wannan ganyen magarya ne da wasu haɗi da aka yi don kare jikin mutum daga miyagun mutane, its 100% halal and sunnah kuma na karya sihiri ne. Ki tafasa ganyen kiyi wanka dashi sai kuma ki dinga karanta waɗannan addu'o'in a ruwa kina sha.' Juwairiyya tana gama karantawa ta ɗauko wayarta don ta kira Salima amma ta samu wayarta is switch off, hakan yasa tashi ta je ta tafasa maganin tayi wankan dashi sannan ta karanto Du'a'ul Kanzul Arsh tare da wasu addu'o'i na karya sihiri ta sha ruwan, bata jima da gamawa ba bacci mai nauyi ya ɗauketa. Da ta tashi da asuba da ciwon kai ta tashi wanda ta alaƙantashi da kwanciyar da tayi wuyanta ya lankwashe. Tana idar da sallah ta ƙara ɗaukan addu'o'in kamar yanda Salima ta umurceta ta karantasu ta sha a ruwa wani kuma tayi ta shafa a jikinta. Gari na gama wayewa ta gama aikinta ta tafi makaranta akan idan ta dawo tayi abincin rana zata je ta dubo Hafiz Junior, ta ma manta da cewa wani mai suna Salisu ya ce kar ta je. Bayan ta dawo gida ta ɗaura girki tana yi tana duba wayarta wacce Salisu yake kira akai akai. Tsaki ta ja da taga kiranshi na ashirin da uku tun safiyar yau, ita sai yanzu ma take mamakin yaya aka yi ta iya cigaba da fita tana hira dashi alhali tun farkon zuwanshi bai burgeta ba! Tana gama abinci Mama ta dawo daga aiki take tambayarta me ya samu wayarta Salisu yana ta kiranta bata ɗauka? "Wallahi haushinshi nake ji Mama, kawai ki bashi haƙuri ba zan aureshi ba. Zan jira har Allah Ya kawo mini wani." Ta faɗa tana ajiyewa Mama abinci a gabanta. "Me kika ce? Sai da auren naku ya matso sannan zaki ce ba zaki aureshi ba?" Faɗin Mama tana dafa ƙirjinta kamar wani babban laifi Juwairiyya ta yi. "Mama ni yaushe nace zan aureshi? Sai dai in da ke yayi maganar amma ni ban taɓa cewa zan aureshi ba wallahi. Shi ya faɗa miki haka?" "Kar ki yarda ki fara wallahi domin dukkaninmu ranmu zai ɓaci. Ni zaki watsawa ƙasa a ido Juwairiyya? Ni ce nan na tambayeki ko kina sonshi kika amsa mini ehh zaki aureshi shine yanzu zaki ce kin manta?" Shiru Juwairiyya tayi tana tunani sannan ta tuna lallai an yi hakan. To amma ina hankalinta yake da zata auri mutum irinshi kamar ɗan daudu? "Sai yanzu na tuna wallahi, amma ni gaskiya na fasa. Ba zan iya auren irinshi ba." Shiru Mama tayi tana kallonta kamar mai kallon wata baƙuwar halitta, rainin wayon Juwairiyyan har ya kai haka ko dai barinta da tayi tana karatun ne yasa ta fara haɗuwa da ƙawaye masu hure mata kunne? Me yake damun Juwairiyya? Abun da Mama bata sani ba shine Juwairiyya na fama da sihirin da Salisu ya mata a zuwanshi na biyu. Malaminshi ya bashi kwalli da zai zizara a idanunshi wanda da zarar ta kalli cikin idon nashi shikenan zata faɗa sonshi sannan zata dinga bin maganarshi kamar raƙumi da akala. Haɗuwan Muhammad da Salisu yasa Muhammad ya gane ba haka banza ya barta ba domin kuwa babu abun da bai sani ba game da rayuwar Juwairiyya. Labarin da ake bashi mara kyau akan Salisu yasa ya yanke hukuncin zuwa ya gani da idanunshi. A nan ya gane lalle Salisu yayi halin nashi don dama an ce yana biye-biyen malamai wasu kuma sun ce yana bin ƴan'uwanshi maza, shi Muhammad wannan ba damuwarshi bane, damuwarshi ita ce rayuwar Juwairiyya yanda zai kareta daga sharrinshi domin ya ɗauki alƙawari mai wuya, alƙawarin da yake wahalar dashi har ya jefashi a wani halin da bai shirya masa ba. "To wallahi baki isa ba. Ba zaki mayar dani mutumiyar banza ba mai baki biyu. Wato karatun da na barki kici gaba da yi yasa kike son ki gagareni ko? To wallahi ba'a gidan nan ba. Sai ki zaɓa karatunki ko aure! In ba zaki yi auren ba ki zauna a gida kin daina fita zuwa makarantan kenan, don haka daga yau na soke zuwa makarantar." A bazata Juwairiyya ta ji furucin Mama wanda ya saka ta zaro idanunta tana kallonta cike da mamaki da kuma tsoro. "Mama don Allah kar ki ce haka, nan da sati ɗaya fa zamu fara exams na second semester sannan kice ba zan ƙara fita ba? Ya zan yi da exams ɗin?" "Sai ki bari wata shekara mai zagayowa ki yita idan kin yi aure kenan, in kuma wata shekarar ma ta zagayo baki yi auren ba sai ki bari sai wata. Batun makaranta kam na sokeshi dama mutane sun fara saka miki ido a kanshi." Kuka Juwairiyya ta fara wiwi da idanunta don ta lura da gaske Mama ta hanata cigaba da karatun akan wani banza Salisu. To wai ita ina hankalinta yake da ta amince zata auri sakarai irinshi har kuma take fita su yi hira? Tana cikin wannan kukan ne tana bawa Mama haƙuri aka aiko wani yaro wai Salisu yana kiranta a waje, tsabar haushi bata san lokacin da ta fita ta ɗauki takalmi a bakin ƙofa ta jefi yaron dashi ba, Allah Ya taimakeshi ya gani yayi saurin duƙawa takalmin ya wuce ta saman kanshi kana ya fita da gudu bayan ya ɗura mata ashar. Mama da ta ga komai sai abun ya ƙara ɗaure mata kai game da Juwairiyya, lallai da alama ta fara kufce mata, yaushe ta bari rashin hankalin nata ya kai haka? "Sannu isheshshiya, nace sannu! Yanzu in takalmin ya bugeshi ya ji ciwo me zaki cewa uwarshi? To wallahi Juwairiyya ki fita a idona in rufe. Karatun na sokeshi sannan idan ba zaki yi auren ba ki fita ki faɗa mishi da bakinki ya daina damuna a office a kan zancenki, wallahi na gaji da fitinarki Juwairiyya. Kullum idan na doso gidan nan na tuna cewa kina ciki kina zawarci sai na ji gabana ya faɗi, na samu kin amince zaki aureshi shine yanzu zaki toɓare? Haba, yarinya ke kaɗai kin hanani kwanciyar hankali? Ke ce wannan gobe ke ce wannan? Kullum maganar da za'a kawo mini a kanki daban nan ma na yarda da tarbiyyar da na baki ne amma ko faɗin bana son in ji ana yi. Da kina gidan mijinki babu wanda zai dinga bin diddiginki shiyasa na gwammace kiyi auren ki huta nima in huta. Haba!" Tana gama faɗin haka ta shige ɗakinta ta bar Juwairiyya na kuka wanda tsananin mamakin kalaman Mama take yi. Wato ashe ta gaji da kallonta a gidan? Wato gulmarta ake kai mata duk dama bata aikata komai na alfasha ba, in banda riƙe hannunta da Salisu yayi jiya nan ma bata san dalilin da yasa ta yarda har ya shammaceta haka ba. Ai kuwa baƙin cikinta ya ninku ya zo mata har wuyanta ya toshe mata maƙoshi, duk sai ta sauƙesu yau a kan Salisu tunda dama a kanshi ake mata wannan faɗan har aka hanata cigaba da karatunta alhali yanzu shine kaɗai yake ɗebe mata kewa da kuma ɗauke mata hankali kan damuwarta. Kamar iska ta figi hijabinta dake bakin ƙofar kitchen ta fita waje ta samu Salisu a cikin motarshi ya harɗe hannunshi ɗaya, ɗayan kuma yana riƙe da waya ya kara a kunnenshi da alama ita yake kira domin yana ganinta ya ajiye wayar yana mai tamke fuskarshi. Tana isa gaban motar ta ja tunga ta tsaya tana huci kamar zata ci babu, tsabar masifar da yake nuƙurƙusarta har ta rasa ta ina ma zata fara azalzalarshi. "Menene ya faru tun da safe ina kiranki kin ƙi ɗauka? Kin san bana son irin haka, in ma wata damuwa ce nace ki kirani ki faɗa mini ba wai ki barni ina ta wahala ba." "Sannu ubana! Na ce sannu ubana Salisu. Kai ka ganka? Wallahi ka kiyayeni don in ba haka ba sai na maka rashin mutuncin da kullum ka tuna da ni sai ka koka. Mugun mutum mai shiga tsakanin uwa da ɗanta kawai. Auren da nace zan yi kuma na fasa, dama ni ban san ina hankalina yake da har na yarda zans aureka ba. Macuci azzalumi ɗan iska mai riƙe matar da ba tashi ba, ashe dama kai ma  ɗan iskan ne ban sani ba? Ashe kaima zuwa kayi ka cuceni ka watsar ko? To wallahi ka ganni nan? Na fi ƙarfinka! Na fi ƙarfi  mutum irinka, kuma in kana da zuciya a ƙirjinka kar ka sake tako ƙofar gidan nan da sunan ka zo gurina." "Yauwa, ga Juwairiyyan da na sani." Faɗin Muhammad yana takowa a hankali yana murmushi mai ƙayatarwa. Ta juya shima zata masifeshi ya ɗaga hannunshi sama alamar surrender ya ce, "Na zo tambayar meyasa baki zo kin duba Muhammad Hafiz bane." Ai kuwa nan da nan ta sassauto ta matso gurin Muhammad tana cewa, "Ya jikin nashi? Jiya nayi ta kiran mamanshi wayarta a kashe, dama akan idan na gama aiki zan je na dubasu ne. Kai kuma me kake jira? Ta juyo ga Salisu ta zare mishi ido wanda sai da ya ji ɗarr a ranshi. Mamaki kuwa yana cikinta tsulum domin har yanzu ya kasa gaskatawa wai Juwairiyya ce take mishi masifa ba! Juwairiyyan da bata mishi musu tana bin umurninshi kamar shi ya haifeta yau shi take yiwa masifa tana zaginshi? Ba dai aikin da Mallam ya mishi ya karye ba? Dama ba wani mai ƙarfi aka yi ba saboda baya son mutane su ankara don a yanzu ma an fara ganoshi. Dubanta yayi a karo na biyu ya ga tana watso mishi harara da alama ba zata daina ba har sai ya bar ƙofar gidan, hakan yasa ya rufe marfin motarshi ya tafi ba tare da ya ce musu komai ba, amma kuwa fuskarshi ta fallasa zuciyarshi wato bai haƙura ba kuma sai ya rama cin mutuncin da Juwairiyya ta mishi. Dandandandandandan! "Juwairiyya ina so mu yi magana da ke amma kafin nan ina so ki nitsu ki bani hankalinki." Confused take kallonshi don bata san me zai faɗa mata ba. "Lafiya kam?" Ta tambayeshi tana mishi iso zuwa inuwar katangar gidansu. "Ba lafiya ba. Aikan da jiya aka ce miki Salima ce ta aiko miki ba ita ba ce, ni ne! Sannan na saka ta kashe wayarta ne don kar ki kira ta faɗa miki ba ita ba ce ki ƙi amfani da maganin." "Innalillahi wa inna ilaaihir raji'un! Maganin mallaka ka bani?" Kallonta yayi kamar wata wawuya yace, "Kin taɓa ganin an yi maganin mallakar mutum Du'a'ul Kanzul Arsh? Addu'an da yake karya sihirin ne zai zama na sihiri?" "To na uban me ka bani?" "Da alama kin samu kanki, da kuma a nan kika tsaya kina kuka wancan wawan ya tasaki a gaba yana miki ihu kina bin umurninshi blindly." Faɗin Muhammad yana hararta don ya lura she is ungrateful duk da cewa bata san ceton da ya mata ba. "Wallahi nima sai yanzu abubuwan suke ta dawo mini, na rasa gane meyasa nake bin duk maganarshi kamar wacce ya yiwa asiri." Ta faɗa tana murza goshinta a hankali tana tunani kanta a ƙasa. Jin shiru Muhammad bai yi magana ba yasa ta ɗago kanta tana kallonshi. Gyaɗa mata kai yayi wanda nan da nan kwakwalwarta ta fara haɗa mata nan da can! "No!" Ta faɗa a hankali hawaye na taruwa a idanunta. "Yes." "No!" Hawayen suka zubo ta rufe bakinta da hannunta jikinta ya fara ɓari tana kuka. "Look at me! Ki daina kukan nan kar ki jawo mana hankalin mutane kanmu." Faɗin Muhammad yana mata katanga da jikinshi kar masu wucewa su ga halin da take ciki. Sai da ta ɗan nitsu sannan ta dubeshi tace, "Ya aka yi ka gane? Sannan kai ka kawo mini maganin da ya karya sihirin?" "Baki da kunya, kina da raini sannan ba'a sakaki kiyi, da haka na gane." In a wani lokaci ne ya faɗa mata haka zata ce zaginta yake yi amma wannan karon godewa Allah ta yi da ya har yasa ya gane cewa wai ba'a hayyacinta take ba. Godiya ta shiga yi mishi babu ƙaƙƙautawa domin wa zai so akalar rayuwarshi ta zame daga hannunshi ta sauƙa kan hannun wani? Shikenan mutum ya zama kamar mutum mutumi bashi da tunanin kanshi sai abun da wani yace yayi! Akwai baƙar ƙaddarar da ta wuce wannan? Ai sai ta ji ashe a da hankalinta ma a kwance yake, yanzu kuma da ta san me ya faru da ita sai tsoro ya shiga ranta. "To yanzu ya zan yi? Kar fa ya ƙara mini wani. Wayyo Allah na." Nan kuma ta sake birkicewa sai da kyar Muhammad ya saitata nan ma sai da ya ɓata rai ya mata tsawa. "Idan ba zaki nitsu ba sai in yi tafiyata, ina da ayyuka da yawa na bari na zo ina babysitting ɗinki." "Why are you helping me? Na ɗauka ka tsaneni." Kamar ba zai amsa ba sai can kuma ya tsura mata ido ya ce, "Saboda abokina Hafiz! Na mishi alƙawari kuma ba zan taɓa karyawa ba duk da cewa you are insufferable. And I don't hate you, halayenki ne bana so." Harara ta watsa mishi kana tace, "To yanzu ya zan yi kar mutumin nan ya samu galaba a kaina again? Gashi yau ɗin nan Mama ta datse mini farin cikina wai ba zan sake zuwa school ba sai dai in bari ko kuma in yi aure in ci gaba da yi." Ta nemi shawaran Muhammad wanda a da in aka ce mata zata zo ta kalleshi a matsayin mai bata shawara zata zagi duk wanda ya faɗi hakan. Kaɗa kafaɗa yayi sannan ya gyara tsayuwarshi domin ya fara gajiya ya ce, "Ki yawaita addu'a ko kuma kiyi auren, auren kuma shine rufin asirinki domin idan ya ji kin yi zai haƙura sannan zaki samu kici gaba da karatunki, nima kuma na huta da bibiyar rayuwarki don na fara gajiya." "Na yarda zan aureka Muhammad. Ka aiko sadakinka gobe a ɗaura mana aure." Ta faɗa da murmushi a fuskarta domin sai yanzu ta gane ɓullowar Muhammad a rayuwarta kullum ba haka banza bane, they were meant to be together ne. Salima zata fahimceta tana da tabbacin hakan. (Ohh, you don't!). "No!" Muhammad ya faɗa da sauri yana ɓata fuskarshi. "Yes." Ta ƙara faɗaɗa murmushinta. Juyawa yayi ya nufi motarshi yana karkaɗa kanshi ta bishi tana cewa, "Ka turo gobe a ɗaura auren." "Ke ki barni fa." "But you promised him cewa zaka aureni idan na yarda. You promised Muhammad!" Wannan magana yasa ya carke ya tsaya kana ya juyo ya dubeta bata daina murmushi ba ya ce, "You will be the death of me. Ki faɗa musu gobe zan taho da magabatana a ɗaura auren da safe." "To maigida." Rayuwar auren masoya biyun na tafiya daidai yanda suka tsara tun farkon fari, kwanciyar hankali da son juna ya kafu a cikin gidansu wanda hakan yasa suka zama abun burgewa ga jama'a da dama har wasu suna fatan ina ma su ne! Suna tsaka da wannan jindaɗin ne rayuwarsu ta canja salo wanda hakan yayi sanadiyyar bankaɗuwar wani tsohon alƙawari mai wuyar cikawa. To yaya rayuwar tasu zata ƙaya? Ku biyo Mum Fateey domin yanzu zamu shiga gundarin labarin. Mum Fateey 👌 TAFIYAR MU Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) 09023713064 (14) “Cewa aka yi da ta ji labarin auren suma ta yi." "Nima na ji wannan, to amma kuma wasu sun ce ita ce tace ya auri ƙawar tata." "Ɗazu kuma na ji wai asiri ta yiwa ƙawar da mijin suke bibiyanta a gindi sun kasa rabuwa da ita, to in ba asiri ba don tana matar aboki kuma abokin ya mutu shekara uku da suka wuce babu ɗa tsakaninsu sai kuma su ci gaba da zumunci da ita? Ni dai wannan cin amanan da tayi yasa na daina kallonta a mutumiyar kirki, dama an ce ba'a shaidan ɗan kuturu sai ya mutu da yatsa." "Ku naku duk mai sauƙi ne, ni abun da na ji sai da yasa na ja baya. Wai ashe bibiyar mijin ƙawar take yi har ya mata ciki shine ƙawar ta fahimta tace zata tona musu asiri suka yi gaggawan yin aure don su rufe." "Ni dai koma menene gaskiyar ban ji daɗin auren mijin ƙawar tata da tayi ba. Haba ai da kunya da kuma nauyi, suna zumunci sosai har mijinta da ya mutu sai da ƙawar ta sa maigidanta ya mishi takwara. Yanzu duk wannan bai isa ya haneta aurenshi ba?" "Kuna ta wani cece kuce, kuma duk maganar akan ita macen ce! Shi mijin ba zaku ga laifinshi bane da yake bibiyar ƙawar matarshi? An ce maza sun fi mata hankali to me yasa ba za'a ɗauki laifin kacokam a ɗaurawa namijin ba tun da ya fi hankali? Sai a mata uzuri tunda dama bata da hankali, ba haka mazan suke cewa ba?" "Ku dai mu bar maganan nan haka, Allah Ya basu zaman lafiya kawai." ***** Juwairiyya ce zaune a gaban Mama tana mata nasiha sannan ta ɗauki dubu hamsin ta miƙa mata tana cewa, "Ga sadakinki nan, Allah Ya baku zaman lafiya Ya kuma sa gidanki ne na har abada Juwairiyya. Allah Ya kaɗe hau Ya kuma haɗa kanku kuyi zaman lafiya." "Amin." Juwairiyya ta amsa kamar ma hankalinta baya gurin. Da haka Mama ta sallameta ta koma ɗakinta ta samu guri ta zauna tana tunani. Wai shikenan da gaske ta zama matar Muhammad? Mutumin da ta tsana a da har take zaginshi tana kusheshi yau shine mijinta? Bayan wannan yaya zata yi da Salima wacce aka ce suma tayi da ta ji labarin mijin nata yayi aure kuma wai ita Juwairiyya ya aura? Anya bata tafka babban kuskure ba wajen auren Muhammad? Anya kuwa shima ba asirin ya mata ta nemi ya aureta ba? Kai da hankalinta! Don tana tunawa ta gwammace ta zauna da Muhammad akan ta rasa karatunta ko kuma worse Salisu ya mata wani asirin ya ɓatar mata da hankali har ya aureta. Sai dai da akwai wani option da zata samu a wannan lokacin ba Muhammad ba to da shi zata zaɓa. Lallai ta ƙaryata zancenta da take cewa ko mazan duniya sun ƙare ba zata aureshi ba. Gashi yanzu akan gujewa wani namijin ta zaɓi zama dashi don tsoro. Fatanta Salima ta fahimceta domin ba son mijinta take yi ta aureshi ba, tayi hakan ne don shine only hope ɗinta don gujewa mummunar ƙaddara. Sannan da zarar ta samu ta gama makarantarta ta kama aiki zata nemi ya saketa a lokacin kuma ta san tayi girman da Mama zata barta taci gashin kanta. Da wannan tunanin ta ɗauki waya ta kira Salima amma ta ji wayarta a kashe, ko dai har yanzu bata farfaɗo bane? Tun jiya ta so kiranta fa faɗa mata amma sai ta ji ta gagara, don haka ta barwa Muhammad wannan aikin. Shi kuwa tunda suka gama magana jiya bata sake jin ɗuriyarshi ba sai sadakinshi da aka damƙa mata bayan an ɗaura aurensu da misalin ƙarfe tara na safe. Kwata-kwata mutanen da suka halarci wannan ɗaurin auren mutum goma ne, biyar daga gareshi haka biyar daga fanninta. Wani ƙanin babanta da bai san cinta ko shan ta ba ya buɗi baki yake faɗawa mamanta wai shi fa ya gaji da zuwa ɗaurin aurenta! Wannan magana ya yiwa Juwairiyya zafi da take sauraronsu daga can ɗakinta yayin da su kuma suke tsakar gida. Ta so ta fita ta faɗa mishi baƙar magana amma da ta tuna cewa Mama ba zata goya mata baya ba, kai karshe ma hakan zai jawo musu matsala yasa ta kame kanta amma ta mishi addu'a shima ya ji yanda ta ji. Ai ba yin kanta bane aure-auren, mijinta na farko mutuwa yayi wanda in ba don mutuwa ba babu abun da zai rabasu, na biyu kuma lalura yake dashi ya saketa ba da son ranta ba. Sai kuma wannan na ukun zata yi shi ne na wasu shekaru uku zuwa huɗu tsanani kafin ta samu ƴancin kanta ta kasheshi. Wannan kenan. Duk ƙoƙarin da Juwairiyya ta kai ga neman Salima bata sameta ba, hakan yasa ta ji shakka ya shiga zuciyarta ba dai tayi fushi da ita bane? Ta ɗauka Saliman zata nemeta saboda tafi kowa sanin yanda ta tsani mijinta, zata tambayeta ba'asin yaya aka yi har hakan ya faru? A nan ita kuma zata mata bayani sannan ta ƙara da bata haƙuri don zata shigo gidanta ne ba da niyyar zama ba sai don ta yada zango kaɗan ta wuce. Har maghrib tana nemanta amma bata sameta ba, gashi Mama har ta kafa mata doka kamar kwanakin can wai ba zata fita ba sai da izinin Muhammad mijinta. Abun dariya ya so ya bata, wato shi Muhammad ɗan lukutin zata tambaya idan zata fita? Ganin babu sarki sai Allah yasa Juwairiyya ta danna kiran Muhammad wanda bata ma san ya aka yi ta samu numbernshi ba. "Don Allah ka zo ina son ganinka." Shine abun da ta faɗa da ya ɗauki wayan. "Ba zaki iya jira har ki tare ba kenan?" Ya bata amsa daga cikin wayar. Sai da tayi jimm sannan ta gane inda maganarshi ta dosa. Kunya da kuma takaici ne ya zo ya rufeta wai yau ita Muhammad yake faɗawa maganar banza? Ko da yake laifinta ne da ta faɗi wannan sentence ɗin don koma waye ne ya ji zai ɗauka wani abun take nufi. "Dalla ni ba abun da nake nufi ba kenan. Allah Ya sauwaƙe God forbid bad thing. Magana nake son mu yi." Ta faɗa a hasale tana ɗaga murya. "Idan kin koyi magana da miji ki kirani sai mu yi maganar a natse." Da haka ya kashe wayarshi ya bar Juwairiyya da ɗan banzan mamaki a fuskarta. Wai da gaske kashe wayar yayi? Lallai bai san wacece ita ba. Shiru tana zaune tana tunanin zai kirata amma har aka shafe minti ashirin bai kirata ba, kuka ne kaɗai bata yi amma haushi kam ya kusa kasheta. Ashe dama bai daina wannan halin nashi ba? Ganin babu Sarki sai Allah yasa ta kirashi ta fara magana a hankali. "Don Allah magana nake son yi da kai in zaka iya zuwa." "Na ji." Kawai ya faɗa ya ƙara kashe wayarshi. Wannan karon hanjin cikin Juwairiyya ne ya kaɗa domin da alama ta manta waye Muhammad, ta manta ɗan banzan halinshi da take kushewa kullum a gaban kowa. Ashe bai daina ba? Yanzu ta yaya zata iya zaman auren dashi na shekara huɗun yana gwada mata wannan halin? Lallai watarana zasu yi kokawa, amma da ta tuno siffarshi sai ta girgiza kanta, ba zata fara ba! To yanzu kam yana zuwa ne ko dai? Bayan wani minti ashirin ɗin ya kira wayarta, tana ɗauka ya faɗa mata yana waje. Sai da ta faɗawa Mama kafin ta fita ta sameshi a cikin mota yana zaune, ganin ta fito yasa shima ya fito suka tsaya gefe da gefen juna. "Ina ta neman Salima amma har yau wayarta a kashe. Lafiyanta kam?" "Shine maganar?" Ya tambayeta da ɗan mamaki a fuskarshi. "Akwai wasu amma wannan ne farko." "Wayarta ce ta fashe." "Don Allah yaya ta ɗauki zancen auren nan? Ta yi fushi ko?" Ta tambayeshi cikin zullumi. "Ba zan iya faɗa miki ba amma dama ta san hakan zai iya faruwa." "Ban gane ba." Ta faɗa cikin ruɗu. "Sai wanne?" "Ba zaka fahimtar da ni ba kenan?" "Eh." "Sai kuma batun tarewa ta ina so sai bayan na gama exams kafin nan mutanen da suke cikin gidana sun fita." "Me kike nufi kenan?" Ya tambayeta yana ɗaga girarshi ɗaya wanda bata gani ba dalilin duhun dare. "A can zan zauna." Ta bashi amsa zuciyarta na bugawa. Dama ta san sai sun kai ruwa rana kafin ya yarda. "Kina nufin ba zaki zauna a gidana ba kenan ni zan dinga binki gidanki?" "Ni ban ce ka dinga bina ba, ba lalle sai ka zo inda nake ba." "Juwairiyya me kika ɗauki aure ne? Wasan yara ko shiririta?" "Yau karo na uku kenan kana kiran sunana a rayuwarka." Ta faɗa duk kuwa da irin taraddadin da take ciki. "Kar ki canja mana magana. A gidana zaki zauna har lokacin da Allah zai buɗa mini in canja muhalli, but for now a can zamu zauna." "Don Allah Muhammad ka rufa mini asiri kar ka kafe akan wannan maganar, aurenka da nayi ma na san Salima zata ji zafinshi shiyasa nake son yin nesa da ita ta yanda ba zata dinga kallona ba balle ranta ya dinga ɓaci. Ka ga kuma gidan ka na zaman mace ɗaya ce ba zai ishemu mu biyu ba. Don Allah ka yi haƙuri." "Yanzu bari in tambayeki. Wancan mutumin da kika aura kin faɗa mishi cewa a gidanki zaki zauna?" Girgiza kanta ta yi don bata san ina maganarshi ta dosa ba. "Sai nine da kika rainawa arziki zaki nemi tarewa a gidanki? No. Sai kuma wani magana?" Wani mololon baƙin ciki ne ya zo ya tokarewa Juwairiyya wuya, ji take yi kamar ta ɗauki sanda ta yita zabga mishi tsabar haushin shi da take ji. Zai ɓata mata tsari, ba haka ta tsara ba. Ta so ta tare a can gidanta da marigayi Hafiz ta yanda zata yi nesa da Salima haka kuma Muhammad ba zai dinga damunta ba saboda zata san yanda zata dinga ɓata mishi rai yana nisantarta, a haka tayi ta cin karenta babu babbaka ita ɗaya har ta gama makaranta ta samu aiki ta kashe auren. Duk wannan tsarin da tayi Muhammad na neman wargaza mata shi. "To na ji ba zaka bini gidana ba amma ai zaka iya kama mini haya a wani guri kafin Allah Ya buɗa maka ɗin." "Bani da kuɗin karɓan hayan wani gida alhali ga nawa." "Muhammad ka yi haƙuri don Allah, wallahi ko tsugunawa kace in yi zan yi don kar ka haɗamu gida ɗaya." Ta faɗa da bakinta amma zuciyarta na jin takaicin furucin. "Ke ma ki yi haƙuri amma ba zan raba muku gida ba, tun farko haka ne tsarina kuma ba zan canja ba." Tsabar baƙin ciki komawa ta yi cikin gida ba tare da ta mishi sallama ba. Tana shiga ɗaki kuwa ta ji wayarta na ringing wanda tana dubawa ta ga sunan Salima ce a jiki wanda ta sanya mata 'Maman Masoyi'. Tsoro ne ko fargaba ya hanata ɗauka sai Allah! A haka ya tsinke can kuma aka sake kira ta ɗauka hannunta na rawa bakinta kuma ya fara rasa yawu. "Hello." Ta furta muryarta na rawa kaɗan. "Amaryar mu! Baban Hafiz yace kina ta nemana a waya baki sameni ba, wallahi jiya ne yace in kashe wayar ban san dalili ba, daga nan kuma na ajiyeta a kan kujera Masoyinki ya jawo ya dokata a ƙasa sai da taci screen. Yanzu aka dawo mini ita daga gurin gyara shine nace bari in kiraki. Kar in cikaki da surutu, Congratulations! Allah Ya bamu zaman lafiya da fahimtar juna." Faɗin Salima ta cikin wayar da alama bata da damuwar komai a ranta. "Ranki bai ɓaci ba da na aure miki miji?" Juwairiyya ta tambayeta tana jin hawaye na taruwa a idanunta. "Ko bai aureki ba zai auri wata, to na gwammace a kawo mini ke domin na sanki kema kin sanni kuma zamu fi fahimtar juna mu lallaɓa rayuwar mu. Kin san yanda mijin namu yake, yanzu idan nace ma zan ɗaga hankalina sai na  gwammace kiɗa da karatu." Hawaye ne ya zubowa Juwairiyya domin da alama ta manta halayen Muhammad, da gaske ta manta. To in ba haka ba sau nawa Salima tana faɗa mata abubuwan da yake mata tana jin haushi a ranta har take jin da tana da iko dashi da sai ta hukuntashi! Yau gashi itama tun kafin aurensu ya kwana ya shirga mata baƙin ciki, kuma babu yanda ta iya dole ta bishi saboda babu yanda zata yi. Duk masifanta ta sani cewa ba zai yi amfani akan Muhammad ba. "Da gaske baki yi fushi ba?" Ta ƙara tambayarta don sanin zuciyar Salima. "Na faɗa miki ban ji komai ba, fatana Allah Ya bamu zaman lafiya. Maganganun da yawa amma sai gobe zan kiraki zan je in yiwa Muhammad aiki kar ya dawo ya samu ban yi ba." Da haka suka yi sallama Juwairiyya na jinjina haƙuri irin na Salima, ta wani gurin kuma tana tausaya musu dukkansu domin Muhammad ya cika mugun mutum kuma mara tausayi. Sati ɗaya da haka Juwairiyya ta fara exams wanda Muhammad ya nema mata mai napep da zai dinga kaita yana dawo da ita domin ya ce baya son tana zuwa bakin titi taran abun hawa, sannan shi kuma ba zai iya kaita ba domin yana da ayyuka. A haka taci gaba da rubuta exams ɗinta cikin nitsuwa domin bata da damuwar komai yanzu in ba ta Muhammad ba, yana zuwa dubata kullum sannan ya tambayeta ko tana da wata buƙatar da zai iya biya mata? Idan tana dashi sai ta faɗa ya saya mata, wani lokaci kuma sai ta ƙureshi ta tambayeshi abun da ta san ya fi ƙarfinshi, to a nan ne zasu yi dramansu su rabu. Sai kuma Mama ta daina tsangwamarta, Salima kuma da take tunanin za'a samu matsala da ita sai ta bata mamaki domin kuwa sai ta ga kamar ma sun ƙara shaƙuwa akan yanda suke a da, domin duk gyaran gidanta da ake yi na toshe-toshe tana faɗawa Juwairiyya watarana har ta mata video. Dama gidan Muhammad ba wani babba bane, da ka buɗe gate ka shigo zaka samu farfajiyar gidan mai ɗan faɗi amma mota ɗaya zata iya ɗauka, ƙofofi biyu zaka gani a jikin ginin gidan wanda na gefen dama ƙofa falon Muhammad ne da kuma ɗakinsa da banɗaki a ciki, a cikin falon kuma akwai wata kofa wacce ita ta raba tsakaninshi da falon Salima, wanda ita nata gefen ɗaki take dashi da kuma kitchen ɗinta wanda yake da ƙofa ta bayan ɗakunan nasu. To wannan ƙofar tsakanin falon Salima da Muhammad ɗin aka toshe, sannan aka yanki wani guri kaɗan a cikin tsakar gidan nasu aka yiwa Juwairiyya ƙaramin kitchen kamar ɗakin maigadi. Duk lokacin da Salima ta nuna mata progress ɗin aikin sai tayi tsaki tana jin haushi a ranta sannan sai ta fara kushewa, tana faɗa mata cewa ita ba haka ta so tun farko ba, sannan ga plan ɗinta na zama a gidanta amma Muhammad ya hanata. Wannan kenan. Tun kafin ta gama exams Mama ta fara bata kayan gyara amma da ta je ɗaki sai ta watsasu bayan wardrobe, ana saura kwana huɗu tarewanta Mama ta kawo mata ci da kaza wanda Juwairiyya tsabar kwaɗayi ta kasa haƙura sai da ta cinye tass ta shanye romon, a cewarta ta karanta Suratul Fatiha a ciki ba zai mata maganin komai ba. Sannan wa ya faɗa musu wani abu zai shiga tsakaninta da Muhammad? Mutumin da zai iya karyata a dawo ana jinyarta! A ranar da aka mata jere a ranar aka kawo Juwairiyya ɗakinta da daddare wanda tsabar haushi da kuma takaicin ɓata mata plan da Muhammad yayi sai ta samu kanta da zubar da hawaye bayan kowa ya watse. A haka Muhammad ya shigo ya sameta tana zaune a ƙasa tana zubar kwalla. "Me ya sameki? Baki da lafiya ne?" Ya tambayeta yana ajiye ledan kaza a gabanta. "Babu ruwanka da ni." Ta faɗa cikin tsiwa. "Hakan na nufin lafiyarki kalau kenan." Da haka ya fara cire kayan jikinshi wanda yasa Juwairiyya ta ji kunya ta juyar da kanta taci gaba da matsar kwalla. Tana ji yayi wanka ya fito sanye da jallabiya sannan yace ta shiga tayi alwala su yi sallah amma tace ba zata yi ba. Shi yayi sallanshi ya idar ya jawo ledar kaza ya buɗe ƙamshinta ta doki hancin Juwairiyya amma tsabar taurin kai tace ba zata ci ba. Bai ƙara kulata ba ya ci kazarshi ya bar mata saura sannan ya shiga banɗaki ya wanke hannunshi da bakinshi ya fito ya hau kan gado yace, "Idan kin gama kukan ki zo ina buƙatar matata." Dandandandandandan!!! Wai yaya rayuwarsu zata kasance a rufi daya? Wai shin salima har cikin zuciyarta take murna da auren Muhammad da Juwairiyya? Wai kuwa burin Juwairiyya zai cika na datse igiyar aurenta da Muhammad idan ta samu sarari da Yancin kai? Wai yaya za’a yi wannan zaman ne tsakanin Salima mai sanyin hali, Muhammad Mugu da Juwairiyya Yar rigima? Jama’a wai ina Daddy yake? Shin ya rabu da Juwairiyya har abada ne ko Akwai sauran rabo? Ina Salisu mai kwallin sihiri? Ya rabu da Juwairiyya ne ko zai dawo da karfinshi? Duk masu son cigaban wannan TAFIYAR sai su turo ₦500 ta 5139579011 fcmb Suwaiba Babagana sai su turo shaidar biya a 09023713064. Wandanda basa son hayaniyar group su turo ₦650 a dinga tura musu ta private kullum. Akwai wani sabon book da nake yi which is free a wattpad da su whatsapp mai suna Canjin Muhalli. 26-09-2023 ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 08138873799 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** Mum Fateey 👌