Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen2⃣) WHATSAPP NO: +2347039625239 *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* *AuntySis AuntySis AuntySis everywhere.* *Kowa AuntySis nima nace wacece AuntySis din nan.* *Lokacin da na san AuntySis I can say she is d simplest,* *best and sweetest person I eva come across in my entire life. She is so loving and caring,unique in her own ways.* _*Sadaukarwar taki ce gaba dayanta AuntySis💞. Allah yasa kifi haka.*_ *Jidderh luvs u much.*❤ *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *Da sunan Allah mai Rahma mai jink'ai Allah ya yi dad'in tsira ga shugabanmu Annabi Muhammad{S.A.W} da iyalansa da sahabbansa.* _Gargad'i:-Ban rubuta wannan labarin don cin zarafin wani ko wata ba wannan littafin k'irk'irarran labari ne idan ya yi dai-dai da halinki ko halinka ayi min Afuwa Akasi ne_ *Kano 2011* _12:22pm_ *1* Jerin motoci ne kirar land cruisers guda 3 bak'ak'e wulik da su sai shek'i suke yi suka fito daga Malam Aminu Kano Airport kamar yanda suka fito a Jeri haka suka hau kan titi a Jeri, sai faman sharara gudu suke daga karshe suka doshe Nassarawa GRA wani tanfatsetse gidan suka nufa kamar had'in baki a lokacin d'aya suka yi horn, Gateman ya wangale musu gate a tsakiyar compound suka yi parking a lokacin d'aya motoci 2 k'ofofinsu suka bud'e mutane 6 suka fito sanye da uniform na custom da gudu suka nufi d'ayan mota mutum 2 daga cikin mutane 6 suka bud'e k'ofofin na seat, d'in baya. "Controller General Alhaji Basheer Galadima ya zura k'afafunshi k'asa yafito daga cikin mota yana sanye da d'akakiyar farar shadda "everything's da ke jikinshi white colour ne. wasu kyakyawawa 'yan mata 5 suka fito daga cikin gida fusk'ok'insu d'auke da fara'a Direct wajen Daddyn nasu suka nufa cike da k'asaita da taqama ya zuro k'afafunshi suka sauka k'asa sannan gangar Jikinsa ta baiyana kyakyawan matashin saurayi Wanda shekarunshi na haihuwa, ba za su haura 28yrs ba wankan tarwad'a ne yana da tsawo sosai yana da manyan idanu da yalwa gashin gira yana da dogon hancin ga laulausan sajen kwance akan fuskarshi had'e da d'an gajeri gemu gashin kanshi a kananad'e kamar abunda yake sanyawa relexer goshinsa d'auke da abin sallah bak'i wulik da shi. ''Jikinshi na sanye da black Jean's da red long shirt yadaura black jacket akai jikin jacket d'in kamar gashin damisa, k'afarshi rufe cikin red boot Fuska na fitarda annurin murmushi Wanda yak'ara, baiyanar mishi da kyakyawar fuskarshi.'' "Da gudu 2 daga cikin 'yan mata suka nufe shi ya ware musu hannayenshi ya Ansar oyoyo abunda 'yan mata suke fad'a a lokacin da ya yi musu masauki a fad'add'e k'irjinshi _oh my little Siblings I really miss you_ Peck ya yi musu a kumatu sannan yasake su d'aya daga cikinsu take magana cikin shagwa6a ya Ansar ba ka d'agani ba zaro ido ya yi huh.... Nadee troublemaker can't you see you're big girl now"? "I'm not ya Ansar please pick me up'' Murmushi ya yi ya sunkuce ta had'e da d'agata sama, kamar teddy bear Yayinda Daddy da raguwar 'yan mata suke musu dariya, yana dira ta k'asa d'ayar ta ware hannanyeta nima ya Ansar waro idanu ya yi fiye da farko "you again Basmah 'yar lukuta kinsan fa ke nauyi ne da ke"? ''Juyawa ta yi wajen Daddynsu cikin shagwa6a tace Daddy kanajin ya Ansar koh"? Daddy yana dariya yace c'mom my Boy ita ma kadauke ta ka huta da rigimarta ,kamar zai yi kuka yadauketa yana nishi daga bisani ya ajiyeta yajuya wajen 'yan matan 3 ya rungume mai red colour lace _I miss you yaya Saleema mun same ku lafiya"_ ''Miss you too Boy lafiya qalau ya gajiyar zaman flight"? Ganinku ya watsak'ar mun da gajiya yak'arasa magana yana dariya, yak'ara rungume guda d'aya da ke sanye da Arabian gown yaya Abeeda naa ya kid's d'ina"? Lafiya qalau suke sunyi miss naka me too yafad'a yasaketa yanufi wajen wance da ke sanye da gown na shadda, ita ma rungumeta ya yi welcome Home Boy" "Thanks Yaya Baby ina Mommy naa"? Mommynka tana cikin tana jiran zuwanka, a shagwa6e yace shine ba fito tarbana ba"? ''Dariya Baby ta yi had'e da rik'o hannunshi suka nufi cikin gida yayinda Daddy da raguwar girls d'in suka Mara musu baya, Hajja Fatee na zaune Jikinta sanye da tsadad'en cotton swiss voile Idanunta manne da Medical eyeglasses, farace Sol kamar balarabiya fara'a take kamar gonar auduga ta tashi da sauri had'e da ware hannayenta "you're highly welcoming Home my boy da sassarfa yak'arasa wajenta yashige Jikinta ya yi hugging nata tightly _I miss you mom I really miss you mom_ sai fad'a yake yi yana nanatawa d'ago fuskarshi ta yi tana shafar fuskar nashi miss you too Boy sai kawai yasa mata kuka, had'e da k'ara qamqameta _Mom tsawon shekaru da nayi bana tare da ku nayi su ne cikin tsananin k'uncin wasu lukata idan na tuna da ku Allah kuka nakeyi kamar mace, sai naji na tsane karatun da naje yi please mom karku k'ara separated nawa daga gareku saboda ku ne farin cikina_ "In tears yak'arasa magana. "A karo na biyu da Hajja Fatee tad'ago shi ta share mishi hawaye Kadàina kuka boy this time kadawo gida kenan mu ma ba'ason ranmu ka tafi wata uwar duniya ka share share tsawon 4yrs batare da mu ba don kawai cigabanka ne da cikar burin Mahaifinka. "Daddy yak'araso wajensu yana dariya Boy ba ka girma har yanzu kananan da shagwa6arka, lallai kuwa akwai rikice babba tsakaninka da Basmah domin na tabbata ba za ta barmaka rank d'inta na Auta ba. ''Da sauri Basmah tak'araso cikin shagwa6a tace zancenka gaskiya ne Daddy indan ka ga na barmishi Mom aure nayi. "Gaba d'aya suka sa dariya Ansar ya ja hancinta ni kuma kingani nan komai wuya komai tsanani duk runtse duk wahala no thing separate me from them yak'arasa magana had'e da rik'o hannun Dad d'in nashi. "Dariya iyayyen nashi suka yi wance ke nuna sun ji dad'in zance nashi, har part d'inshi suka rakashi yayi taking bath saida suka ga shigarshi bathroom sannan suka dawo main parlour, yayinda Housemaids suke ta faman arranging dining table. "Ansar yafito daga wanka daure da towel a waist nashi, Direct dressing mirror ya wuce ya yi tsaye yana kallon kanshi ya shak'i iska cike da nishad'i ya furta Home, sweet Home ba abunda yakai gida dad'i yad'auki comb Shiga shace gashin kanshi mayunka kala-kala yadinga shafawa gashin nashi, tsawon lokacin ya6ata a gaban mirror sai kace mace Farar Jallabiya yasaka yafeshe Jikinshi da turaren Malik al-dud kaitsaye yanufi part d'in mom suna Zaune a parlour da alama suna zaman jiranshi ne, yana murmushi ya yi sallama, a tare suka amsa masa sallama yana dariya ya dubi Daddy yace Dad mutafi masallaci naga time d'in sallah azhar ya yi Girl's d'in suka sa Dariya Nadeeya tace Ya Ansar kananan yanda ka ke zaman abroad ba sauya ka ba har yanzu kananan da halinka na rashin wasa da lokacin sallah. Ya yi murmushi Wanda yak'arawa fuskarshi annuri yace Nadee zama abroad ba zai sa mutum ya watsarda kyawawan d'abi'unshi sai in dama yanada burin canza sheqa daga yanda aka sanshi zuwa dabi'un Nasara ko kuma Allah yayi nufi sauyawarka to anan kuma bakada mafita domin Ubangiji shi yake tsarawa 'yan Adam rayuwa amma ni Alhamdulillah! Yanda na tafi haka nadawo ba abunda yasauya a tare da ni. "Gaba d'ayan su hamdallah suka yi da jin furucinshi Daddy ya mik'e tsaye ya dube Mum da ke sharar hawayen farin ciki yasaki mata murmushi Ba kuka za ki yi ba Fatee ki godewa Allah da yanufe ki da wannan ni'ima domin samun 'ya'ya nagari irin Ansar a wannan zamani sai an tona "Alhamdulillah! Dukan godiya sun tabbata agareka Allah da ka nufe ni da samun d'a mai nazari da riqo da addini islama, ya Allah ka Albarka ce rayuwarshi kasa wa karatu da ya yi albarka. _Ameen Mum_ Girl's d'in suka fad'a a lokacin d'aya yayinda hawaye suka cikawa Ansar ido yakasa cewa komai farin ciki fal akan fuskarshi. "Dad yarik'o hannunshi suka fice mum ta dubi girls d'inta tace kutashi mu je mu yi sallah. _10 minutes later_ Gaba d'ayansu suna zaune akan dining table ba ka ji komai sai karar spoons sai faman kad'a kai Ansar yakeyi alama yana jin dad'in abincin da yake ci Bayan sun kamalla cin abincin suka yada zango a parlour. "Ansar ya yi doguwar hamma had'e da mik'a Dad ya dube shi cikin kulawa yace Boy ka je ka kwanta domin akwai gajiya mai d'ibin yawa a tare da kai. "Ansar yasaki murmushi to Dad yafad'a had'e da mik'ewa tsaye Mum zan je na kwanta in lokacin sallah La'asar ya yi a tashe ni. "Basmah ta riga Mum magana Ya Ansar ni da kaina zan je na tashe ka ya laqace mata hanci yana murmushi yajuya yanufi part d'inshi. "Yacire Jallabiya jikinshi ya ajiye a gefen bed ya kunna Ac ya haye k'aton Royal bed d'inshi bai jima da kwanciya ba bacci ya yi awon gaba da shi. *TUSHEN LABARI* "Alhaji Basheer Galadima su biyu kacal iyayyensu suka haifa a duniya shi da qaninshi Alhaji sa'eed Alhaji Basheer custom ne, Wanda a halin yanzu yana taka matsayin controller General mahaifinsu yarasu tun suna cikin ganiyar kurciya mahaifiyarsu Haj Hajjo tana nan a raye tana zaune a gidan Alhaji sa'eed a tangamemmen part d'inta. Alhaji Basheer Galadima matarshi d'aya hajja Fatee sunyi aure saurayi da budurwa asalinta bafulatana Yola ce kuma, tafito daga gidan sarauta Allah yabarkace su da 'ya'ya har guda 6 Abeeda ita ce babban ta yi aure har da 'ya'ya 3 saboda tana d'aukar long time kafin ta haihu, sai saleema ita ma kamar Abeeda ce ta yi aure 'ya'yanta 3 khadeeja wance taci sunan Hajjo shiyasa ake kiranta da Baby ita ma ta yi aure da 'ya'yanta 2 sai shalele d'an gaban goshi kwali d'aya Muhammad Ansar sai Nadeeya wance yanzu take level 1 a B.U.K sai Basmah auta tana final year a secondary school. "Hajja Fatee cikkakiyar 'yar kasuwa ce tana da manya-manya boutiques cikin garin Kano tana dauko kaya a kasashe duniya kamar, irinsu Indian, Dubai, Indonesia mace ce mai dogaro da kanta. "Alhaji Basheer Galadima burinshi ya gina company saboda da ya yi retired yanada babba kadara da za ta dinga kawo mishi k'udi, shiyasa yaware duk wani tanadi da yajima yanayi ya gina babban company Wanda yakeda burin mik'a alhakin kula da shi a hannun tilo d'ansa yayinda shi kuma in ya yi retired ya fantsama harkoki siyasa. "Alhaji sa'eed Galadima d'an kasuwa ne sana'arshi siyarda gwalagwalai matarshi ta aure guda 1 me suna Haj saudat ya'yanshi 5 Nafeesa ita ce babba ta yi aure da jimawa saboda tana kamalla secondary school akayi mata aure 'ya'yanta 4 sai Abdallah sa'an Ansar kuma amininshi a halin yanzu shine ke kula da ragama company Alhaji Basheer sai Fahad sai zuhura sai kuma auta Nazeeya zuhura sa'ar Nadeeya ce sannan kuma ita ce Ansar zai aura tun kafin ya tafi U.K akayi musu baiko jira kawai ake yadawo asha bikinsu. "Ansar yana matuk'ar son zuhura tamkar numfashinsa kamar yanda ita ma take sonshi kamar ranta zan iya cewa son da Zuhura take mishi yazarce Wanda yake mata. *Back to story* Karfe _4:03pm_ dai-dai Basmah tashigo d'akin Ansar ta tashe shi bayan ya yi wanka ya yi sallah yashirya cikin english wear's sai faman zabga k'amshin yake, yafito daga part d'inshi kaitsaye na iyayye shi yadosa a parlour ya iske 'yan uwanshi zaune shima yanemi sofa ya zauna ya dube su cike da jin dad'i yace......... Jeeddah Aliyu *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *This book is dedicated to only you my adorable, my super star Aunty Sis💞 thanks so much sweetheart, I don't know how to thanks you for the love,courage, kindness you have shown to me. Thanks so much I really appreciate it. Allah yahada fusk'ok'inmu a aljanna Firdausi. Ameen* *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *2* Mum fa"? Nadeeya ce ta amsa mishi ta hanyar cewa tana upstairs bedroom, ya juya ya dube Yaya Baby ya lamgwa6e kai yaya Baby yakamata kutashi ku rakani Gadon k'aya naga Tsohuwa mai ran karfe domin na tabbata ba don k'afafunta sun hanata watayawa ba da tuni ta tsofa a gidanan. "Gaba d'aya suka sa dariya yaya Baby tace ba wani tsohuwa da za ka je gani kadai za ka je ganin Zuhura. "Sosai k'eya ya yi yana dariya k'asa-k'asa Basmah ta mik'e ni dai bara na dauko mayafina ni ma ki dauko min nawa cewar Nadeeya kenan tana kallon Basmah. Sallama suka yi da Mum saboda Dad tuni yafita motoci 2 suka dauka saleema da Abeeda Nadeeya ce ke driving nasu yayinda Yaya Baby ke driving Ansar da Basmah. tafiya suke cikin nishad'i da haka suka iso gidan Alhaji sa'eed Galadima a lokacin d'aya suka yi parking Sannan suka nufi cikin gida part d'in Haj saudat suka nufa, gaba d'aya parlourn ya hargitsi da murna ganin Ansar bayan komai yalafa. ''Ansar yashiga rarraba idanu ko zai hango hasken zuciyarshi har idanunshi suka gaji da nemanta ya hak'ura shigowar Abdallah ne ya d'an haifar mishi da natsuwa, can dai yagaji da hak'uri ya dubi Nazeeya ya yi k'asa da murya yace Nazeeya ina Zuhura tashiga ne ko batasan na zo bane"? Dariya Nazeeya ta yi tace tana part d'in Granny tasha kwalliya tana zaman jiran zuwanka da alama batasan cewa tanan za ka fara zuwa ba. "Murmushi Ansar ya yi ya mik'e tsaye yanufi k'ofar fita Abdallah yace kai kuma ina zuwa ana fira za ka ta tashi"? Part d'in Granny yafad'a kaitsaye dariya suka sa kamar had'in baki suka Mara mishi baya, yana turo k'ofar glass ta parlourn Granny ya hango Zuhura kwance ta yi pillow da cinyoyin wata mata baquwar fuska saboda sai yau yafara ganinta kamanunta kadai da ya duba yagano cewa buzuwa ce. "Hayaniya su Abdallah ya ankarar da Zuhura ta kai dubanta bakin k'ofa idanunta suka sauka akan fuskar abin kaunarta zubur ta tashi daga jikin Ammah ta ruga da gudu tanufi wajen Ansar duk iya k'ok'arinshi ya yakaucewa rungumar da takawo mishi saida Zuhura ta yi nasara had'e jikinta da nashi yakiceta ya yi daga k'irjinshi yarik'o hannunta, yanufi wajen Granny da ke kishingid'e yasaki hannunta ya durk'usa ya daura kanshi bisa cinyoyinta mun same ku lafiya Granny"? Lafiya qalau Ansaru ya karatu da Masu jajaye kunnuwa"? "Ba Ansar kadai ba duk Wanda ke cikin parlourn saida yadara cikin shagwa6a Zuhura tace wai ke Granny sai yaushe bakinki za ki iya furta Ansar"? Harara Granny ta watsa Mata had'e da cewa bansaniba Ammah tana dariya ta mik'e tace Hajiya ni zan tafi naga kin yi ba'kon bature dariya suka k'ara kwashewa da ita Ammah na fita Ansar ya sauke idanunshi akan fuskar Granny wacece wannan matar domin ni bansanta ba, kuma batayi min kama da dangin mu ba"? Murmushi Granny ta yi tace Matar maigadin gidanan ce amma yanzu sun zame mana tamkar 'yan uwa na jini tun daga kanta har mijinta da muna jin dad'in zama da su, suna da matuk'ar kirki. "Ansar ya yi murmushi ya juya dube Zuhura da ke tsaye idanunta kyam akanshi ko kiftawa babu yace my wife mu je garden mu zanta saboda naga wad'annan mutane sun cika nan wurin yana magana ne had'e da nuna su Abdallah da yatsa. "Zuhura ta yi tsagal tace gaskiya da yafi nima ina buk'atar na ke6e da mijina. Yaya Abeeda ta rik'o hannun Saleema tace zo mu tafi Saleema wad'annan yaran ba kunya ne da su ba saleema ta mik'e yayinda Baby ta Mara mata baya suka fice daga parlourn. "Hannun Ansar Zuhura ta rik'o Honey tashi mu tafi mana, zare hannunshi ya yi daga nata Abdallah yace mu kan ba inda za mu je sai dai ku kubarmana parlour. Harararshi Ansar ya yi had'e da cewa sai ku sha zama ya mik'e tsaye yanufi k'ofar fita Zuhura na biye da shi. "A k'asan grass carpet suka zauna Zuhura ta zauna gabanshi tana facing nashi, ta lamkwashe k'afafunta, sai lokacin Ansar yak'are mata kallo Atamfar super exclusive ce sanye da jikinta d'inki riga da siket anyi mata style da co lace high neck raga-raga gaba d'aya ana iya hango boobs d'inta ta kusaye cut lace d'in da sauri Ansar ya d'auke fuskarshi da barin kallonta. "Ya Ansar U.K ta kar6e ka ga yanda ka K'ara kyau skin d'inka very fresh & smoothly tak'arasa magana had'e da riqo hannunshi tana shafar skin d'in hannunshi har wani lumsasshe ido take yi. "Tsigar jikin Ansar ya tashi yarrr...babu shiri ya firzge hannunshi ya kuma murtuk'e fuska Kidaina ta6a ni Zuhura addini bai yarje mana mu dinga ta6a junanmu anyhow ba beside shed'an zai iya qawata mana wani abu, daga baya mu dawo nuna danasani marar amfani. "Har ya dasa aya a zancenshi Zuhura tana mishi kallon mamaki kasa hadiye mamakin nata ta yi har sai da ta furta haba! Ya Ansar don na ta6aka shine me ko ka manta ne saura kiris a Shafa fatiha a tsakaninmu"? "D'an bazawari murmushi ya yi Wanda ke nuna Sam bai gamsu da wannan guntun bayani na ta ba, don saura kiris a Shafa fatiha a tsakaninmu Zuhura ba shi zai ba mu dama mu dinga tsallake iyaka ba. "Tabe baki ta yi a zuciyarta tana mamaki rashin wayewa na Ansar mutume da ya je abroad karatu ace bai waye ba har sai yaushe zai waye, tad'ago ta dube shi suka had'a ido ta kauda fuska. "Ansar ya yi murmushi kamar yasanta abunda zuciyarta take saka mata, cikin taushin halshe yakira sunanta Zuhura"! ''Na'am tafad'a kamar mai ciwo hak'ora ki yi hak'uri idan kalamai na sun b'ata miki rai kinsan ba abunda yake saurin ta6ani irin b'acin ranki. Dad'in kalamai shi suka lullu6e Zuhura sai wani rangwad'ar da kai take yi, ganin haka yashiga tsarata da dadd'an kalamai kiran sallah magarib ya mayarda su part d'in Granny. *WASHE GARI* Ansar ya rabawa su Nadeeya tsaraba da ya yo musu trolley guda yacikawa Zuhura da had'ad'u Arabian gowns da hijabai different colours had'e da shoes da handbags ga kyau ga tsada misalin 'karfe _2:30pm_ yanufi gidansu Zuhura yana Shiga layin gidansu idanunshi suka hasko masa wata matashiyar budurwa wance shekaru ta ba za su haura 17yrs ba tana sanye da Hijab har k'asa sky blue colour ta yane fuskarta da niqan, tana tafiya a hankali kamar mai tsoron taka k'asa yanayin tafiyarta cikin natsuwa yak'ara tafiya da imaninshi kasa d'auke idanunshi ya yi daga kanta hakan ne yabashi damar rage gudun mota yasoma tafiya slow-slow yana kallonta har tak'araso daf da motarshi ta ra6a ta gefenshi ta wuce kanta a sunkuye tana kallon k'asa tsintar kanshi ya yi da bin ta da kallo ta cikin mirror da ke jikin motarshi idanunshi na kanta har sai da ta6acewa ganinshi sannan ya yi nasara dawowa cikin natsuwarshi. "Cike da mamakin kanshi ya ja mota da k'arfi ya nusa cikin unguwar, horn yadanna a bakin gate d'in gidansu Zuhura maigadi ya bud'e masa gate, tsayawa ya yi ya gaisa da Abba buzu maigadi saboda tun jiya da Granny tabashi labarin kirkin mutume ya ji aranshi ya kwanta masa parking lot yanufa ya yi parking. "Yafito daga mota ya hango Fahad yafito daga cikin gida kai Fahad zo nan"! Ya kwadawa Fahad kira bayan Fahad ya zo ya bud'e boot d'in mota yanuna mishi nasu tsaraba ga tsarabanku nan kowane ku da sunanshi akai Fahad yashiga yi masa godiya ya kinkime kayan Indan kashiga ciki ka turo min Zuhura ina part d'in Granny. Fahad ya amsa da to..yawuce cikin gida yayin da Ansar ya ja trolley d'in da tsaraban Zuhura yake ciki yanufi part d'in Granny ''Ammah kadai ya tarar a parlour tana linkewa Granny kayanta da ta kwaso daga igiyar shanya, gaisawa suka yi Yanemi sofa ya zauna Ammah ina Granny"? Tana d'akin ko a kirata ne"? Noo.....ki barta kawai ae ba yanzu zan tafi ba Shikenan.... Ammah tafad'a had'e da kwashe kayan da ta linke tanufi cikin d'akin Granny Ansar yafito da phone d'inshi ya kira wani friend d'inshi Sageer da suka yi karatu tare a U.k ya shagala da firar da yake yi da Sageer. Ba ko sallama Zuhura tafad'o parlourn sai saukar numfashinta Ansar ya ji a kunnenshi yad'ago a rikice tana tsaye daf da shi tana zuba murmushi sallama ya yi da sageer yasauke idanunshi akan sutura da ke, sanye a Jikinta Black colour skintight da red colour d'in top a tsakiyar gaban top d'in anyi tsaga dai-dai saitin Nonuwa wannan yasa boobs d'inta a baiyane Fitinanai k'amshin na fita daga Jikinta kanta ba d'an kwali gashinta yasha gyara yana lullu6e da gashin attachment ya kwanto har gadon bayanta sai kace nata. "Ansar yasauke ajiyar zuciya had'e da janye idanunshi daga kanta a zuciyarshi yasoma aikawa kanshi tambayoyi anyya kuwa Zuhura tana da hankali"? wannan wace irin masifa ce kalli wad'annan watsatsu kaya da tasaka"? Yaushe Zuhura ta sauya kyawawa d'abi'aunta da nasanta da su"? Yasaukar hannanye ta ya ji a kafad'arshi tana matsa mishi jijiyoyin wuyanshi abun ka da lafiyayye namiji wanda baya tsallaka iyakokin ubangiji cikin d'an k'ank'anin lokacin ya tsince kanshi cikin wani yanayi gaba d'aya Jikinshi ya mutu. "Kamar Wanda aka tsakara yadawo hayyacinshi _A'uzubillahi minal shed'anin rajim_ yafad'a had'e da ture hannayenta daga wuyanshi ya mik'e tsaye Wawan tsaki ya ja cike da jin haushi yace wai meke damunki ne Zuhura"? Yatsine fuska ta yi had'e da dusuna duwawunta akan kujera na yi maka kama da Wance take cikin damuwa ne"? "Sororo ya yi baki bud'e yana kallonta daga bisani ya zauna nesa da ita ga tsarabanki nan na kawo miki ki bud'e ki gani ko na iya za6i"? Yak'arasa magana da murmushi akan fuskarsa. "Tana yatsina tasauko daga kan kujera ta janyo trolley d'in ta zuge zip tasoma fitowa da handbag's wow! Gaskiya Honey ka iya za6i gaba d'ayansu favorite colour's d'ina. Ansar yasaki murmushin jin dad'i harda su kada kai tana dauko shoes ta tabe baki, tad'ago tasauke idanunta akan fuskarshi cikin gadara tace Amma Ya Ansar wad'annan shoe's d'in ba nawa bane"? "Na ki ne mana yafad'a with full confidence k'ara yatsine fuska ta yi lalle ma Ya Ansar kana nufi har ka manta da size d'ina"? Sosa k'eya ya yi alamar jin kunya ni fa na dauka 37 ne size naki"? To in Kadauka ka sauke 39-40 shine size d'ina. Murmushi Ansar ya yi domin tun ba yau ba yasan halin Zuhura na rena arziki ba kasaifa yake mata kyauta ta ya6a ko tanuna farin cikinta ballantana har yasamu kalmar godiya daga bakinta, wannan yana d'aya daga cikin mummuna d'abi'aunta da yatsana ga kuma wasu sababbi da yadawo ya tararda ita d'auke da su. "Watsar da takalmin ta yi a gefe tashiga zaro raguwar kaya da ke ciki zaro ido ta yi miye wannan"? Tana magana ne had'e da d'ago hijab, da mugun mamaki Ansar yake kallonta bangane miye wannan ba ke bakida idanu ne"? Yak'arasa magana cikin b'acin rai Zuhura kuwa ko a jikinta sai ma jefar da hijab d'in da ta yi Ya Ansar ba zan 6oye maka ba ni bana saka irin wad'annan kayan duk wata sutura mai nauyi bana shiri da ita, saboda banason zafi shiyasa tsakanina da Hijabi sai in zan yi sallah bana saka Arabian gown ko last year da Daddy ya je Makka yasiyo muna Arabian gown ni nawa *Anaal* na ba wa domin anan gidan ita kadai ce take saka irin wad'annan kayan. "Tun lokacin da tafara magana Ansar yake mata kallon mamaki da takaicin wai yaushe notun kan Zuhura ya kwance"? Gani yanayin da yake ciki yasa ta tabe baki tace ni ina mamakin anyya kuwa wad'annan tarkace a U.K kasiyo su domin kwata-kwata ba su yi min kama da kayan da suka fito daga U.K ba"? "Ran Ansar yak'ara b'aci yashiga girgiza kai ya isheki Zuhura nace ya isa hakanan Yafad'a cikin tsawa da tafarfasa zuciya, wad'annan kayan su naga damar siya miki tunda ba za ki iya amfani da su sai ki ba wa Nazeeya ba wai kidinga gushesu a gabana ba. Taso mishi ta yi kamar za ta cinye shi d'anye Sam babu ladabi balle d'a'a tafara magana kai wane irin mutum ne Ya Ansar"? Daga nace banaso wad'annan tarkace shine za ka rufe ni da masifa"? to ni wallahi ba uban da ya Isa ya yi min dole A tsorace Ansar ya mik'e tsaye jikinshi har wani Mazari yake idanunshi sun canza kala zuwa jajaye....... Jeeddah Aliyu *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *4* Gaba d'aya hankalinshi ya raja'a da kallonta ya shagala sosai har bayaso yadaina kallon nata. Hakan yasa yarage gudun mota ya koma tafiya sannu-sannu. "Tafiyarta da shigar da ke jikinta suna masifar burgeshi, da yake glass d'in motarshi tinted ne shi yahana 'yan matan su gane yana kallonsu har suka 6acewa ganinshi idanunshi na kafe akan hanyar da suka bi yasauke k'arfafiyar ajiyar zuciya, ya ja mota a kasalance yanufi gidansu Zuhura. Horn ya yi Abbah buzu ya bud'e masa gate yana ganin Ansar ne yashiga fara'a kamar gonar auduga Ansar ya yi parking yafito yanufi wajenshi. ''Barka da zuwa Muhammadu lafiya kwana biyu muka daina ganinka ko ka yi tafiya ne"? Yauwa,,,,Abbah ina gari ba inda naje aiyuka ne suka yi min yawa da fatar yau za ka had'a mana ataye{green tea} na ranar naji dad'in shi sosai"? Dariya Abbah buzu yashiga kyakyatawa daga bisani ya katse dariyar tashi kai,,,,,,lallai Muhammadu in natashi tafiya Agadaz da kai zan tafi saboda na fahimcin kana matuk'ar so ataye. Dariya marar sauti Ansar ya yi yana Sosa k'eya yace ae Abbah na gayamaka in da rai lafiya wata rana kwatsan za ka ganin Agadaz, in kuma naje ba zan dawo ba har sai ka bani mata na aura yak'arasa magana cikin sigar wasa. "Abbah buzu yak'ara yi dariya kai Muhammadu me za ka yi da buzuwa kai da ka ke da 'yar gaye irin 'yata Zuhra shima yabashi amsa cikin raha. Ansar ya yi murmushi Abbah zan shiga ciki in ka had'a ataye kafin natafi zan sha. Toh,,,,,,,Muhammadu a fito lafiya. "Allah yasa Abbah Ansar yafad'a had'e da sa kai yashiga part d'in Granny da sallama yak'arasa shiga parlourn Granny da ke kishingid'e tana kallon sunnah tv tad'ago, had'e da amsa mishi yanemi waje ya zauna ya gaida Granny suka shiga fira daga bisani yafito da waya ya kira Zuhra ya Sanar da ita ya zo. ''Babu jimawa sai gata ta zo k'amshinta da yashaqa yasa ya yi saurin d'agowa ya dube ta, sanye take atamfar super exclusive d'ikin riga da skirt ya yi tight d'inta sosai kamar ta nisa rigar ya yake nonuwanta a fili d'an siriri veil tasa ta yane kanta duk haka bai hanawa Kalaba twisting d'in da ke kanta fitowa ba wance akayi mata combination da black & purple attachment, ta yi matuk'ar kyau Ansar yana kare mata kallo ya kauda fuska ya dubi Granny fuskarshi d'auke da b'acin rai kamanunshi gaba d'aya suka sauya fissibillahi! Granny Abunda Ku ke yi Sam bakwa kyautawa kalli shigar da Zuhra ta ke yi kuma haka take fita wani sa'in ba ko mayafi amma anrasa Wanda zai tsawata mata. "Cike da takaici Granny take kallonshi daga bisani ta girgiza kai tace ni a suwa da zan tsawata mata Ansaru"? A matsayinki na wance ta ke da iko da ita saboda kina matsayin kaka a wurinta, kin ga kenan kinada matsayin da za ki tsawatar mata. Huh,,,,,,,Ansaru kenan da ace na isa na fad'a aji da tuni ya yi tasiri akanta tadaina wannan shasshanci a wani gefen in ka yi la'akari ba laifinta bane, irin tarbiyyar da uwarta ta tabata kenan. ''shiyasa akoda yaushe nake la'anta baqin hali irin na saude. "Ansar yasauke numfashi ya maida ganinshi wajen Zuhra wance ta ja ta yi tsaye tana musu kallon mai cike da wulaqancin, suna had'a Ido ta ja dogon tsaki tajuya a fusace. ke! Zuhura zo nan,,,,,Ansar yataka mata birki cikin d'aga murya cak.....tai tsaye sai dai batada niyya dawowa ki zo nace zan yi magana da ke yasake bata umurni a harzuk'e tajuyo indan na dawo me zan maka"? Kasanni sarai bana iya jure wulaqancin musanman na d'a namiji. kisani muddin ki ka sake ki ka fita wallahi zan barki bari na har abada. A tsorace Zuhra tasauke idanunta akan fuskarshi, numfashinta na kai komo jiki a sa6ule tadawo cikin parlourn tai tsaye tana kallon Ansar idanunta tap da hawaye sai mutsu-mutsu take da baki. "Nemi waje ki zauna Ansar yafad'a fuskarshi a had'e zama ta yi hawaye da take k'ok'arin dannewa suka sulalu akan kunce ta. ''Granny ta dube ta ja tsaki batun yau ba Zuhra nake kuka da irin wannan watsatsiyar shiga da Ku ke yi gara ma Nazeeya da ke domin ita tana saka mayafi sa6anin ke da ki ke fita tsirara da sunan wayewa. ''Ansar ya kar6e zance ta hanyar cewa ina wayewa Granny ga talla tsiraici"? Bani na fad'a ba Ansaru haka suke cewa a duk lokacin da na zaunar da su ina musu nasiha. Wannan ba wayewa bane Zuhra asalima duk mai hankali da tunani Wanda yake da wadatace ilimin islama zai danganta hakan da Jahilci domin wayewa tana samo asaline da mutume da yake ka re hakokin Allah ta'allah. Kiji tsoron mahalincinki Zuhra ki dube kanki Sam ba ki yi kama da 'ya'ya musulme ba. su Kansu Wanda Ku ke kwaiwayo da su ba bu indan addininsu ya yarje musu su yi watsaysiyar Shiga. Gashin attachment ne akanki Najasa ne Zuhra kin dauka ki sakawa kanki shin a haka ki ke bautawa ubangijinki"? kalli faratanki zaqo-zaqo kin fente su da jan farce ki dubi girman Allah Zuhra ba don ni ba ki canza wad'annan mummuna d'abi'u da ki ka kwaso domin rankatakaf zuri'ar Galadima babu mai wannan d'abi'a sai ke da Nazeeya. "Zuhra takasa furta uffan sai sharar hawaye take yi zuciyarta na tuk'uk'i tun da take duniya ba'a ta6a ci mata fuska ba irin yau burin Granny yacika yau Ansar ya wulaqanta ta a gabanta. Granny ta kya6e baki tace Kadàina wahalarda yawun bakinka Ansaru domin wad'annan maganganu naka suna shiga kunnenta ne kamar ana busa zare a kunnen bebe tun da tana sonka kacigaba da yi mata Nasiha watakila Allah yasa adace tagano talla tsiraici ba abu mai kyau bane babban takaicin na shi ma sa'eedu ya zama shanyaye mijin tace duk lokacin da na yi mishi korafi akan shigar da yaran nan ke yi sai dai yadinga kad'a kai kamar k'adangare yana kyaci kamar zai d'auki mataki, ba kuma abunda zai iya saboda anriga an gama da shi Granny tak'arasa magana tana huci. ''Shikenan Granny zan yi iya nawa k'ok'arin na lurar da ita yajuya wajen Zuhra da ke shasshekar kuka yace yi hak'uri Zuhra nah zo mu je compound mu yi sulhu kinsan na tsani kukanki. "Kamar jira take ta tashi da sauri ya bi bayanta Granny ta bi shi da kallon tausayi, tasan lamarin so ne kawai ba wai don Ansar yadace da Zuhra ba domin ta ko ina halayyan su yasha banban da na juna. ''Nufin Zuhra tashige part d'insu da gudu Ansar ya cinmata yasha gabanta, yana kallonta k'asa-k'asa yanzu don mun gaya miki gaskiya Zuhra shine za ki fushi"? Ashe gyara kayanka zai zama sauke mu raba"? "Tad'ago cikin hawaye ranta na soya tafara magana ba zai zama ba Ya Ansar amma kasani ko za ka yi min fad'a ka jani privately ba wai a gaban Ganny ba domin da kunnenka ka ji yanda take aibanta mahaifiyata. "Ae dole ta aibanta mahaifiyarki saboda ita ce baqar uwa asarar dangin a zuciyar Ansar yafad'i haka a baiyane kuma sai ya yi k'asa da murya I'm very sorry babynaa kema kinsan Granny ta tsufa komai yafito daga bakinta fad'a kawai ta ke yi bata masa birki. ''Inasonki Zuhura sosai shiyasa nake kishinki banaso abunda zai 6ata miki rai har ki zubur min da hawayenki tun da kinaso saka iri-iri wad'annan kayan at last ki dinga daura after dress akai, domin nasan ko nace ki saka hijab ba sakawa za ki yi ba indan mu ka yi aure sai ki dinga yi min kwalliya. Ni da kaina zan dinga siyo miki english wear's har sai kince sun ishe ki muradina yakasance wannan kyakyawar halitta ni kadai nake kallon abata ba da 'kartti wajen ba. Yak'arasa magana yana murmushi "Dariya Zuhra ta yi shikenan zan dinga sakawa ko don na farantawa zuciyar da nakeso. "Kiran sallah magarib ya katse musu zance nasu Ansar ya dube ta cike da shau'kin so yace shiga gida ki yi sallah nima zan tafi masallacin maybe nadawo maybe kuma sai gobe. "Bara na kawo maka buta ka yi alwala noo,,,,,,ki barshi kawai zan yi a wajen Abbah Huh,,,,,,Ya Ansar nagano ka kadai kace za ka je shan green tea kai ko d'acinsa ba ka ji "Dariya ya yi mai sautin gaske ki je Ammah ta koya miki yanda ake had'awa inan mu ka yi aure kidinga dafa min. ita ma dariya ta yi sai kace ba ita bace yanzu nan tagama kuka har da su shassheka. Ansar ya juya yanufi bakin gate, cikin d'aga murya tace "Honey please in kayi sallah kadawo Allah ban gaji da ganinka ba. Batare da yajuya ba yace naji zan dawo amma fa sai nagama shan mutume nawa{green tea} Yana zuwa gate yatararda Abbah yana alwala ya ja kujerar roba ya zauna Abbah ya gama alwala ya mik'a masa buta tare suka jera zuwa masallacin sai da akayi sallah isha sannan suka juyo gida. ''Still a bakin gate suka k'ara yada zango Abbah yashiga room d'inshi na maigadi yafito da tarkace kayan ataye ya ajiye su kusa da k'afafuwan Ansar d'an k'aramin murhu waya yadauka ya dube Ansar yace muhammadu bari na debo mana garwashi, nasan yanzu Ammah ta isa sauke tuwo da sauri Ansar ya tashi tsaye ya kar6i murhun yi zamanka Abbah kawo na kar6o mana yanufi BQ Wanda a yanzu yazama muhallin Abbah da iyalansa shi ya kwana a bakin gate a d'akin maigadi matarshi ta kwana a BQ 'yarshi kuma ta kwana part d'in Granny. Yana k'arasawa ya iske Ammah tana kwashe tuwo ya yi sallama had'e da gaida ta Muhammadu Kaine atafe"? "Eh! Ammah ya gida"? Lafiya lau Muhammadu tak'arasa magana had'e da kar6a murhun ta zuba mishi garwashi kace ko yau ka zo shan mutume naka"? "Eh Ammah ae ni yanzu na zama buzu saura kawai Ku koya min buzanci da yanda ake nad'a rawani Allah Ammah wannan rawanin yana burgeni yak'arasa magana yana dariya. Ammah na tayashi kamar daga sama yafara jin zazzaqar murya mai matuk'ar dad'i tana rera karatun Qur'ani mai girma cikin suratul Al- araf tsit,,,,,,,ya yi kamar anyi ruwan sama andauke ya ba za fatun kunnayenshi biyu yana sauraron wannan muryar mai zak'i da gard'in gaske baisan lokacin da ya lumshe idanunshi ba. ''Lafiya Muhammadu ko kana buk'ata wani abu ne"? Muryar Ammah ce tadawo da shi natsuwarshi cikin jin kunya yashiga girgiza kai yajuya ya koma wajen Abbah. "Har ya kamalla shan green tea zuciyarshi na azalzalarshi akan ya tambaye Abbah wacece yaji tana karatun Qur'ani iya saninshi daga Abbah sai Ammah yasani baisan suna da 'ya ba yana kuma gudun kada Abbah ya fassara shi bai-bai dole ya mik'e ya kira Zuhra a waya tafito sai around _10:00pm_ ya baro gidan har zuwa lokacin zazzaqa muryarta tana shawagi a dodon kunnenshi....... Jeeddah Aliyu *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *5* Ansar yana zuwa gida ya kwa6e kayan jikinshi yashiga bathroom ya yi wanka yafito sanye da bathrobe, tsaye ya yi gaban mirror yana tunani Jikinshi a mace ya dauki robar lotion ya shafe skin d'inshi. Yasanya pajamas ya fashe jikinshi da turare mai sanyi k'amshin ya kwanta had'e da kashe light ya yi switch on d'in tv Kallo yake yi sai dai gaba d'aya hankalin nashi baya ga kallon ya yi nisa a tunanin 'yan mata 3 Zuhura, mai niqan, da Mai zazzaqar murya ya lumsashe idanu yana shafar sumar kanshi a hankali _me ke damuna miyasa nake tunanin wad'annan 'yan matan guda 2"?_ Mtcsww....,,,,ya ja tsaki har k'arfe _3:00_ na sulasuli dare ya yi Ansar na kwance sai faman juyi yake yi yakasa bacci ya tashi zaune ya lankwashe k'afafunshi a tsakiyar gado yadafe k'ok'on kanshi idanunshi sun kad'a sun yi jajir alamar rashin samun baccin. ''Ya sauka daga gado yashiga bathroom yadauro alwala yafito yashiga jera nafila, har akayi kiran asuba sannan ya dakata da nafilla da yake yi yanufi masallacin ana sallame sallah bai tsaya sauraron wa'azin da liman ya ke gabatarwa ba yadawo gida. Tsananin baccin da yake ji idanunshi har wani yaji-yaji suke mishi ya haye gado yak'ara gudun Ac bai jima da kwanciya ba baccin ya kwashe shi. _Zuhra_ "Tsaye take a gaban dressing mirror tana caba make-up kamar wance za ta tafi za6e miss world wani d'akkake lace tasaka marrow colour da touch d'in white ga lace mai kyau da tsada amma anyi mishi style d'in Allah tsine skirt d'in yankar piece ne rigar kuma dai-dai saitin nonuwa akayi mata tsaga Wanda ya baiyanar da nononta tunawa da arta6o da tasha jiya da Ansar yasa taciro after dress white in colour ta daura akan kayan. tasaka white hill shoe's ta yi rolling da veil d'in rigar sai gashi ta yi kyau na ban mamaki. "Har tajuya tasake dawowa tak'ara Shafa powder da lipstick ta ware idanunta tasake tsuke bakinta kamar mai shirin yi kiss tajuya tak'ara juyawa a baiyane ta furta bravo,,,,, Alaiki I'm proud of myself gaskiya ni kyakyawa ce ina Alfahari da wannan kyakyawar halitta da Allah yabani tasaki murmushi ta d'auki black shade ta kwama ta zari brown handbag tanufi kan bedside drawer ta tattara handouts d'inta tafice a parlour ta iske Haj saudat Hajiya na fito Daddy yabada k'udin ki bani"? "Eh yabani gasu tasaka hannun kusa da ita taciro 5k ta mik'a mata ta kar6a ta zarce dining area ta yi taking breakfast tana gamawa tafita ta ja motarta tafice daga gidan. "A k'ofar gidansu leebeauty ta yi parking taciro wayarta ta kirata bayan kamar 3 minutes da kiran nata sai ga ta tafito cikin wani silk material yana shining style d'in fitted gown rigar ta matse ta sosai har ana iya gani layin pants da bra d'inta kanta yasha Kitso Ghana weaving Wanda akayi mata da brown in colour attachment hannunta rik'e da handbag d'ayan kuma tarik'o handouts ta balle k'ofa tashiga, ihu ta kurma tana zarar ido kamar wance ta ga abin tsoro. "Zuu Galadima what's wrong with you huh"? No thing's,,,,,,,, ko kin ga wani abu ne tare da ni"? ''Ofcourse yes,,,,,,look your dress tana magana ne had'e da nuna jikin Zuhra da yatsanta, ajiyar zuciya Zuhra ta yi tacire shade d'in fuskarta tashiga zayanewa leebeauty yanda ta yi da Ansar tacigaba da cewa leebeauty banida mafita da yawuce dole nayi yanda Ya Ansar yakeso Co's I love him so much banaso abunda zai haifar da problems a tsakaninmu,,,,,......ke! Dallah dakata wai me ke damun kanki ne huh"? Zuhra ina tausaya miki duk ranar da ki ka Shiga tarkon taskon d'a namijin ke yadace ki dinga juya Ansar Galadima ba wai shi yadinga juya ki ba. tun kafin Ku yi aure yafara kafa miki sharad'in yau yace kisaka after dress gobe hijab zai ce ki sa daga nan zai mayarda ke, local girl indan Ku ka yi aure yadawo waje yana friendship da wayayu 'yan mata ke kuma yariga yacuce ki yahanaki morar kuciyarki daga nan sai ya auro miki 'yar bariki ke ko yabarki da zunbulele hijabi ki yi tunani k'awata. ''Zuhra ta yi shiru tana nazari kalaman leebeauty wannan ce damar da leebeauty tasamu tacigaba da zuga zuhra wannan shigar da mu ke yi zamani ne ya zo da ita ba wai mu muka k'irk'ira ba kuma shine wayewa muna high school ace mu dinga saka local dress ae sai a raina mu. Zuu duk abunda zamani ya zo da shi ka tsunduma a dama da kai kada ayi ba da Kai ba daga baya kadawo kana kara'i kinga kenan anyi ba'ayi ba d'aukar makaho photo. wayewa ne yasa mu ke saka wad'annan kayan amma kowa yasan mu ba 'yan iska bane wata rana ko ance mu saka bara mu saka ba Co's mun riga mun cin lokacin mu, infact ko a school mutum nawa Ki ka ga suna local dress''? "A Wannan zamani ko matan aure basa 6oye kyakyawar halitta da Allah ba su kina kallo tsakanin mu 'yan mata da su masu aure har ba'a iya tantance waye mai aure waye marar aure. Kina shiga school da wannan rigar za'a fara zargin ko ciki shege ne da ke saboda baki saba sakawa ba. kuma kinfi kowa sani duk wance bata irin wannan shigar da tasaka ciki ne da ita ko kin manta da Raleeya Basheer a lokacin da ta yi ciki tadawo saka hijab da After dress tsananin gulmarta da akeyi yasa tabar school ba bu shiri ki yi wa kanki k'iyamun lailli kicire wannan katuwar rigar ki barta a mota. "Batare da dogon tunanin ko nazari ba zuhra tacire after dress d'in jikinta ta ja mota suka nufi school. "A lokacin d'aya suka balle k'ofar mota suka fito cikin yanga suke tafiya sai wani karkad'a hip's suke yi kamar 'yan makosa dance a haka suka nufi department d'insu. _ANSAR_ ''Ansar yana zaune a dining table sai fama juya fork yake a cikin plate. yakasa cin abincin shi kanshi in ka tambaye shi me ke damunshi ba zai baka amsa ba, domin baisan ainihin abunda yake dawainiya da zuciyarshi ba. har Hajja fatee tak'araso kusa da shi baisaniba sai jin ya yi tadafa kafad'arshi ya zubura a tsorace yasauke ganinshi aka fuskarta, cikin sark'ewar halshe yace....... Jeeddah Aliyu *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *6* Good morning Mum" bata amsa gaisuwa nashi ba sai ma Jan kujera ta yi ta zauna tana facing nashi, cigaba da karanta yanayi da yake ciki ta yi yayin da shi kuma ya sadda kai k'asa me ke damunka ne boy"? Ba komai Mum yafad'a a takaice ya za ka yi kace min ba komai bayan ga damuwa nan akan fuskarka, kuma ka kasa cin abincin sai wasa ka ke yi da fork oya,,,,tell me what's wrong"? "I'm not in mood Mum ni kaina ba zan iya ce miki ga takamame abunda yake damuna ba. ''Boy rashin samun wadatace hutu yana d'aya daga cikin abunda yake damunka, ace mutum bashida time d'in komai sai na aiki yakamata kai wa kanka fad'a kadinga hutawa sak halin controller kadauko naso ba Kai wahala. "Jin furucin Mum na k'arshe yasa Ansar ya yi murmushi had'e da cewa ni fa ba wani rashin hutu da ke damuna sometimes ina office nake sulalewa na bar Abdallah da ishaq da aiki natafi farmhouse na kwashi baccina. yak'arasa magana yana 'yar dariya Mum dariya ta yi tace to,,,,naji sarkin tsari yanzu abunda nakeso da kai ci abincin domin ba zan barka ba kafita batare ka ci abincin ba. "kamar zai yi kuka yace Mum na yi loosing appetite. in bakina yadawo normal zan ci a office. "6alla mishi harara Mum ta yi banaso gardama ka d'auki spoon ka ci abincin tun kafin mu 6ata da kai. " yad'aga fork yasoma cin chips with sauce ya ji k'oda da anta k'amshin spices na tashi kwara d'add'aya yake tsokaluwa a fork. gani haka yasa Hajja fatee ta kar6e fork daga hannunshi tashiga feeding nashi, kamar d'a yaye sai wani 6ata fuska yake yi kamar mai cin mad'aci. "Mum na k'oshi Ansar yafad'a kamar zai yi kuka, girgiza kai mum ta yi ta ajiye fork d'in hannunta. Ta had'a mishi tea mai kaurin gaske ya ji Ovaltine ta mik'a mishi cup, yana yatsina ya kar6i cup daga hannun Mum. "Sai da ya shanye tea d'in tass,,,,sannan Mum tabarshi yafita office. _Hour's later_ "Ansar yana zaune a office d'in shi da laptop a gabanshi yana operated nata. mtcsww,,,,ya ja guntun tsaki had'e da ture laptop yadafe goshi yunwa yake ji tun safe da Mum ta tilassa mishi yin breakfast bai k'ara cin komai ba. "A halin yanzu yana buk'atar abinci mai kyau yad'aga landline yashiga ''pressing digit ya kara a kunnenshi Ishaq ka zo office d'ina inason ganinka. Ba'a d'auki dogon lokacin ba sai ga ishaq ya zo, a kasalance Ansar yake kallonshi ishaq yunwa nakeji wane restaurants kasani da zan same abincin mai kyau da dad'i"? "Ishaq yashiga tunani daga bisani yace Bright restaurant suna da abincin mai kyau ga dad'i sune lamba d'aya sai dai akwai tsada. "Ansar ya tabe baki k'udi is not my problem ishaq mu je kawai ka kaini. _Bright restaurant_ Ansar da ishaq na zauna kowane da plate a gabanshi sai aika loma yake. Especially Ansar sai cika spoon yake sosai abincin yai mishi dad'i sai kada kai yake yi. "Table da ke opposite nasu wasu samari ne guda 2 ke zauna karaf idanun d'ayan yasauka akan wasu 'yan mata guda 2 da ke shigowa. "Jikinshi har rawa yake yi ya zungure d'an uwanshi zayyan dubi wasu hot chicks da ke shigowa gaskiya girl's d'inan sun yi ba k'arya lalle dole na gwada sa'ata anan. "Mtcsww,,,,zayyan ya ja tsaki kai fa Rasheed bakada hankali idonka idon mata ina gargad'inka da ka ji tsoron Allah duk abunda mutum ya yi sai anyi masa. "Matsala ta da kai kenan zayyan duhun kai da rashin wayewa ka dubi sutura da ke jikin wad'annan chicks d'in da kyau, sun yi maka kama da natsatsu ae da ganinsu 'yan hannu ne ka ga kuwa don na taya ba laifi bane. "Allah yashirye ka ni wannan iskanci ba da ni ba Allah ya haramta zina ba yanda za'a yi ina matsayin bawa mai neman gamawa da duniya lafiya, na aikata ta kai ma da ke yi Allah yaganar da kai. "Ameen sarkin wa'azi Rasheed yafad'a had'e da cigaba da kallon 'yan matan yana lasar lips kamar mayye. ''Duk abunda Rasheed da zayyan suke fad'a a kunnen Ansar sai kawai ya tsince kanshi da son kallon 'yan mata ko zai gansu da illar da zayyan ya hango tattare da su. "Rass-rass"!...gaban Ansar ya yanke ya fad'i. Cigaba da jujjuya kwayar idonshi ya yi akan Zuhura wance ta shagala da operating phone d'inta. "Ranshi ya yi mugun 6aci jiya-jiya nan ya gama kashewa Zuhura gargad'i da kaukausar murya bayaso tana saka watsatsu kaya. Shine ta yi biriss da maganata lalle zan nunawa Zuhura kuskure ta. ''Leebeauty ta zungure 'kafar Zuhura ta yi pointing finger a side d'in da Ansar yake zaune zuu kalli can kamar Ansar Galadima"?. "Jikin Zuhura har rawa yake yi ta mik'e tanufi wajenshi sai wani karkad'a hips take, kamar sabuwar karuwa "wow! What's presence surprise I don't expecting to see you here Ya Ansar. Mtcsww"! Ansar ya ja dogon tsaki cike da takaici yak'are mata kallo yak'ara Jan wani tsaki wanda yafi na farko, ya mik'e a fusace kamar zai kai mata mari. "Yajuya yanufi k'ofar fita ishaq ya tashi da sauri ya bi bayanshi, suka bar Zuhura tsaye sororo kamar bishiya kwakwa. "Zayyan ya dube Rasheed ya kyalkyale da dariya I told you since abokina duk mutume kirki ba zai mu'amalamta wad'annan 'yan mata ba. ''Dallah ya isa zayyan ni fa zan dinga biye maka ba nakasa more kurciya na ba, remember I'm just 25yrs I'm still young so its my time. "Zayyan ya tabe baki had'e da mak'e kafad'a. Rasheed ya mik'e yanufi wajen Zuhura yana shu'umin murmushi Hi! Beautiful naga wance tsamin ya 6ata miki rai karki samu damuwa ni zan kawar miki da 6acin ranki. Kallon sama da k'asa Zuhura ta yi mishi mtcsww"! Ta ja tsaki ta6angaje shi ta wuce ta fincike handbag d'inta da ke kan table tafita fuuu"! Kamar zan ta tashi sama. "Leebeauty ta tashi tana gunguni ta bi bayan Zuhura. "Ansar yana fita yanufi wajen mota zuciyarshi na tafarfasa a lokacin guda tsanar Zuhura ta lullu6e shi. ''Cikin sauri ishaq yakaraso ya bud'e mishi mota, yashiga ishaq ya ja mota suka d'auki hanya. "Ishaq"! Ansar ya kira sunan ishaq kamar zai yi kuka. Na'am maigida. "Ishaq zan tambaya ka dan Allah karka ji tsoron ganin idona ka bani, gansasshiyar amsa wance zata fitarwa zuciyata daga wasi-wasi. ''Ishaq ina tsananin son Zuhura tamkar numfashina, bani da wani buri da yawuce ta kasance mata ta uwar 'ya'yana. Ya d'an yi shiru had'e da shed'awa daga bisani yacigaba da cewa a matsayinka na wanda yake da kusanci mai k'arfi da ni, kana gani Zuhura ta dace da zama uwar 'ya'yana"? "Ajiyar zuciya ishaq ya yi yak'ara dafe steering ka gafarce ni maigida akan abunda, zan fad'a ba tun yau ba nake gani Sam Zuhura bata dace da kai ba. "Allah ya yi ka natsatse mutum ne kai mai tsananin kula da addini kana taka tsam-tsam da duk abunda zai shafi addininka sai na ke mamaki duk da kasancewar ka mai kamun kai me zai sa ka aure mace irin Zuhura. "Ba wai Zuhura tana aikata masha'a ba _a,a_ sai don ta kasance mace mai baiyanar da surar jikinta, ga mazaje da ke titi ita a ganinta wannan ba illah bace a na ta k'azamin tunani sai take ganin saka matsatsu tufafi shine wayewa. "Tun daga lokacin da na fahimcin haka a tare da ita sai nagano cewa kodai tana da karancin ilimin addini domin ba bu wata wayewa da addinin musuluncin bai zo mana da ita ba. "Ko kuma tana da ilimin kawai bata amfani da shi, to kuma anan akwai babbar illah domin tasani ta kuma take sani Allah yashiryar da mu yasa tagano illah da ke tattare da abunda ta ke aikatawa. "Ameen Ansar yafad'a cike da gansuwa da Amsar da Ishaq yabashi, 1 more question Ishaq Ina sauraron ka maigida" "A lokacin guda Ansar yasauke tagwaye ajiyar zuciya. Ishaq kana ganin wannan matsalar ta Zuhura wa ya yafi cancanta yafara tsawata mata"? "Mahaifiyarta domin ita ce tushen tarbiyyar ta, ita ce a yanzu tafi kowa kusance da ita sai dai 'yan magana suna cewa ice tun yana d'anye ake tankwara shi, idan ya bushe sai dai ya karye. "Indan har kwakwalwa ta ta auna dai-dai kana nufi abun da wuya ko Zuhura za ta daina saka watsatsun kaya"? Kwarai kuwa maigida domin ga dukan alama ta yi nisa ba lalle bane a d'an k'ank'anin lokacin tadaina sakawa ba. "Amma zan ba ka shawara a matsayinka na wanda ke sonta ka jajirce ka kawo mata illolin saka bankad'ad'un tufafi. "Saka irin wad'annan kayan yana d'aya daga cikin dalilai da zina ta yi yawa a doron k'asa. Maigida nasan kana matuk'a son Zuhura ka dage ka nuna mata illah da ke cikin kayan da take sakawa. "Yak'ara sauke ajiyar zuciya Ansar ya yi ya fesar da iska mai zafi daga bakinshi, ishaq na kasance ina cikin jinse maza masu zafin kishi indan har Zuhura bata daina aikata, wannan mummuna d'abi'a lalle zan barta bari na har abada, domin ba zan ga maciji da rana tsaka nayi sakacin da zai sare ni ba. "Ba zan aure mace da ba za ta bai wa 'ya'yana tarbiyya tagari ba, duk son nake wa Zuhura zan hak'ura da ita. _Zuhura_ "Tun a mota leebeauty tafara zugata kai,,,,,,,Jama'a a rayuwata banta6a gani wulaqancin tsirara irin wannan da Ansar Galadima ya yi miki, a baiyanar Jama'a zai kalle ki ko kallo mai cike da k'ask'ancin ya zanga miki dogon tsaki. "Wallahi Ansar ya gama da ke Zuu ke dai ki yi gaggawar d'aukar mataki ko kuma wankin hula yakai ki dare, yanzu dai dabara tarage ga mai shiga rijiya. Tak'arasa magana tana kya6e baki. "Zuhura ta share guntaye hawayen da suka zubo mata, babban abunda yake saka ni fargaba shin me Ya Ansar yake nufi da ni"? "Me ko yake nufi da ke da yawuce yana daf da 6arar da Gwamnatinki. "Zuu da kin ga kare yana shinshina takalmi wallahi ko na uban waye dauka zai yi. "Ni fa ban fahimce inda wannan zaurance naki yadosa ba"? Na ji kince takalmi, kare kuma Ya Ansar bai kasance d'aya daga cikin wad'annan ababen da ki ka lissafa ba. Dariya sosai leebeauty ta yi wance har ta k'ular da Zuhura rai a 6ace Zuhura tace look leebeauty kinsan duk duniya ba abunda yake saurin baiyanar da fushi na irin dariya, kidaina tun muna sheda juna. ''Leebeauty ta katse da dariyar da take yi I'm sorry tawan I don't mean to hurt you dariyan ne ya zo mun a bazata. "Zuu,,,,,ni a nawa fahimta sai nake ganin kamar Ansar Galadima yana daf da canza sheqa. Kamar ya yana daf da canza sheqa sai ka ce wani, d'an siyasa"? Ke ni fa ban fahimce inda ki ka dosa ba. "Ina nufi Ansar yana daf da canza ki yana daf da fatali da soyayyarki. "Wani mahaukacin birki Zuhura ta taka ta gangara gefen titi ta yi parking, duk ilahirin ga6o6in jikinta rawa yake sai kace 'yar tauri. "Kuttt....ta hadiye wasu miyau masu d'acin gaske sai kace tasha mad'acin yanayin tashin hankalinta tamkar na wance tasami sak'on mutuwar uwa-ubanta. "Da kyar tasamu ta yi controlling kanta ta tattara 'yan raguwar miyaunta masu d'aci ta yi amfani da su ta hanyar cewa..... Jeeddah Aliyu *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *7* Candijam ashe kuwa Ya Ansar yadauko ruwan dafa kansa, domin na tabbata fasa aure na tamkar yake da yada6awa kansa yunka. "Tabe baki leebeauty ta yi ke yanzu za ki iya auren wanda baya sonki"? Ke ubanwa ya gayamiki Ya Ansar baya sona"? "Ubana leebeauty tafad'a tana kallon fuskar Zuhura mtcsww"! Zuhura ta ja tsaki had'e da Jan mota da k'arfi ta haura kan titi. *5:44pm* Ansar yafito daga cikin gida yana tafiyar sauri yanufi parking lot ya ja motarshI kirar kia cerato dark blue in colour, da k'arfi yafizgi motar gateman ya bud'e masa gate yafice. "Kaitsaye unguwar su Zuhura ya dosa dai-dai wajen da yasaba ganinta anan ya yi parking, zullumin yake had'e da addu'a Allah yasa mai niqan ba ta wuce ba har aka yi kiran sallah magarib yana zaune yana jiran tsanmani daga bisani da ya tabbata tariga ta wuce, dole ya ja motarshi ya tsaya bakin masallacin ya yi sallah magarib ya jira isha. ''Bayan ya yi sallah isha ya yanke shawarar shiga gidan su Zuhura, yasha black tea wajen Abbah maigadi. "Horn ya yi Abbah ya bud'e masa gate Ansar ya yi parking yafito yanufi bakin gate ya tarar da Abbah har miyar da gate yarufe yana zaune, yasha rawani da baqin yanki irin nasu na buzaye. "Sallama Ansar ya yi mishi had'e da mik'a mishi hannu, suka yi musabaha daga bisani ya zauna Abbah akwai shi ko sai andafa"? Murmushi Abbah ya yi yace sai anfada muhammadu ban yi tsanmani za ka zo yau ba da tuni na dafa mana. "Shima Ansar murmushi ya yi ba damuwa Abbah ko yanzu za mu iya dafawa da zafinsa yana k'unar baki yafi dad'i sha. "Abbah ya yi dariya kai muhammdu lallai ka zama cikakke buzu saura kawai nafara yi maka nad'i. Dariya Ansar ya yi Abbah har nad'in ina so ni fa duk abunda zai fito daga gareku Abbah ina sonshi. Dad'i ya lullu6e Abbah yasan k'aunarsu da Ansar daga Allah ne domin yanda yake musu hidima, kamar su suka haife shi daga Abbah har Ammah suna matuk'ar k'aunar Ansar suna jinshi tamkar d'ansu Auwal da ya6ata shekaru masu dama da suka shud'e. "Kamar yanda Ansar yasaba d'aukar murhu yad'ebo garwashi ko yanzu hakan ce tafaru ya sunkuce murhu yanufi BQ wajen Ammah. "Da sallama yashiga Ammah da ke d'aki ta amsa masa muhammadu ne"? "Eh"! Ni ne Ammah ya gida"? Lafiya qalau muhammadu. Ammah tafad'a had'e da hankad'e curtain{La6ule} tafito k'ara gaisawa suka yi Ammah ta kar6i murhun ta zuba masa garwashi, yayinda Ansar ya baza kunnen ko zai ji qira'a da ya ji ranar. "Gashi Muhammadu Ammah ta katse masa tunani ya kar6i murhun a sanyaye har ya juya ya yi tak'o d'aya zuwa biyu sai ya ja ya tsaya, cike da jin kunya yajuyo yana kallon Ammah. Ya zame masa dole ya tambaye Ammah abunda yake azabtar da ruhinsa, ko zai same sauki ya kuma fita daga halin qila wa qala. "Muryar nan tashi asanyaye yace Ammah Dan Allah aron Cassette d'inan na qira'a da naji kina sauraro ranar za ki bani. Qira'a ya yi min dad'i inason na nemo irinshi. "Ga mamakinsa sai yaga Ammah tana dariya sai da ta yi mai isarta sannan, tace Muhammadu ba cassette bane Anaal ce. "Rass-rass.....gaban Ansar ya yanke ya fad'i zuciyarshi tashiga bugawa da sauri-sauri sai kawai ya yi murmushin yak'e yace ikon Allah ni na dauka a DVD plate ne. ''A'a bashi bane k'anwarka ce Anaal k'ara shiga rud'ani ya yi shi dai yana jin sunan nan a bakunan mutane gidanan, dai-dai da sau d'aya bai ta6a cin karon da mai wannan sunan _shin wacece Anaal"?_ lallai yakamata na nemo sanin akan wannan Anaal mai zazzaqar murya. A karo na biyu yak'ara juyawa jiki a mace yafita yana zuwa ya mik'awa Abbah murhun garwashin, ya ja kujera ya zauna yashiga tunanin wacece Anaal"? Ko ma wacece ita Allah yabarkace ta da dad'in murya gashi ta iya karatun Qur'ani kowane harafi tana bashi hakk'insa zuciyata tana mararin had'uwa da ke Anaal n.........muhammadu"! Abbah ya katse masa zancen zucin da yake yi. "Na'am,,,,,,Abbah. Muhammadu ka tayani murna k'anwarka Anaal saura surah d'aya ta hadace Al-qur'ani mai girma. Ba ka ji farin cikin da nakeji ba muhammadu nikan zuwa Najeriya ya yi min rana 'yata ta albarkatun da ilimin addini da na zamani. Allah yasakawa Alhaji sa'eed da gidan aljanna ya yi min alheri da har na ko ma ga ubangijina ba zan manta da shi ba. "Shi dai Ansar mutuwar zaune ya yi sai yanzu ya fahimcin Anaal 'yar Abbah da Ammah ce. To ya akayi duk zuwan da nake yi gidanan ko a bisa kuskure banta6a had'uwa da ita ba. Ansar ya had'iye yawu yace Ameen Abbah ai yi wa Kaine ita kuma Anaal Allah yasa mata albarka a karatunta yasa abunda za ka ci amfani sa ne. Ameen muhammadu ''Yayinda Abbah yacigaba da cewa waton Muhammadu ba yabon kai ba wallahi ina alfahari da 'yarta sai dai kashhh.....akwai abunda yake cin min tuwo a kwarya.....Abbah yad'an shed'a damuwa ta baiyana k'arara akan kyakyawar fuskarshi. Daga bisani yacigaba da cewa sanin kanka ne Muhammadu mu baqi ne kowane lokacin za mu iya komawa k'asarmu, Agadaz a can Agadaz muna zaune ne a wani k'auye dajin Allah Jama'a mazauna wannan k'auye ba abinda mu kasani sai kiwon awakai da rak'uma muna rayuwa tamkar wad'annan awakai da rak'uma kasan dalilin da yasa nace da kai haka"? "Ansar ya girgiza kai. Abbah yace saboda ba mu da wadatace ilimin addini islama balle aje ga ilimin boko shi ka ajiye shi a gefe domin ba mu basan menene shi ba. ''Zuwanmu Najeriya mu ka fahimcin menene addinin musuluncin har mu ke gudanar da ibadunmu adai-dai shiyasa nake da burin Anaal tana, gama sakandire na aurar da ita saboda ina fargaba komawa Agadaz da ita mahaifina zai iya aurar da ita ga jahilan k'auye. Abbah yak'arasa magana kamar zai fashe da kuka. "Sauke numfashi Ansar ya yi yace wannan ba abin damuwa bane Abbah insha Allah, kafin tak'arasa karatun nata Allah zai kawo mata mijin aure. Sai dai Abbah wani hanzari ba gudu ba a yanda naji kana yaba hazaqarta me zai hana kabarta ta je makarantar gaba da sakandire kafin Allah yakawo mijin sai ka aurar da ita. "Jikin Abbah yadauki rawa yana girgiza kai kul,,,,,muhammadu karka sake yi min maganar makarantar gaba da sakandire nan, banda tambad'ewa da lalacewa da rusawa 'ya'ya mutane tarbiyya ba abunda suke koyarwa. Ai ni na d'auki darasi daga kan yaran gidanan ada kafin su je makaranta nan duk fad'in unguwar nan ba 'ya'ya da suka fi su natsuwa da ingantattaciya tarbiyya sa6ani yanzu da ake buga misali da tarbarbarewa tarbiyya akansu. ''Ansar ya gyara zamanshi yak'ara fuskanta Abbah ya yi k'asa da murya ni a nawa gani Abbah duk mutume da ka ga ya je highschool ya sauya kyakyawan halinsa zuwa mummuna to dama can yana da burin yin hakan. A yanda naji kana yaba hazaqar Anaal bai dace ace karatunta iya secondary ya tsaya ba. ''Abbah kai kanka kana da yak'ini akan irin tarbiyyar 'yarka take da ita bai kamata kasa shakku akanta ba. Kabarta tacigaba da karatu irin basirar da take da irin wance al'ummar musulme za su amfana da ita ne. "Har Ansar yadasa aya Abbah yana kallonshi yana kad'a kai alamar yafara gansuwa da jawabin nashi. Abbah ya gyara zama Muhammadu ban k'i ta taka ba nima na gabarta maka da nawa uziri, ba wai ina shakka ko kwankwanto akan Anaal bane ina tausayawa irin rayuwar da za ta yi indan lokacinmu komawar mu Nijar ya yi batare da ta yi aure ba. "addu'a kawai za ka yi mata Abbah domin Allah yana saurin kar6a addu'ar iyayye akan 'ya'yansu. Shikenan Muhammadu Allah ya za6a mata abinda yafi zama alheri a rayuwarta. ''Ameen Abbah tana aji nawa ne"? Tana shekarar karshe Abbah yafad'a had'e da mik'ewa yasauke green tea ya zuba a cups sai tiriri yake ya zuba sugar kad'an ya mik'awa Ansar cup d'aya. Ahankali Ansar yake kur6a green tea saboda zafi da yake da yana sha Abbah na bashi labarin Anaal Ansar yana shanye green tea yadire cup cikin girmamawa ya dube Abbah bara na shiga ciki Abbah na gaida su Granny. Toh Muhammad a fito lafiya. Ansar ya amsa da cewa Allah yasa ya juya a natse yashiga part d'in Granny a parlour ya tarar da ita da littafin izziya ta kwama medical eyeglasses tana karatu. "Tsaye ya yi yana kallonta ya kwashewa da dariya a firgice Granny tad'ago sannu a hankali ta ajiye littafin hannunta ta zare eyeglasses d'in idonta ta dubi Ansar ta galla masa harara kai shak'iyi ni ka ke yi wa dariya"? "Dole nayi miki dariya Granny kinga yanda ki ka tak'ark'are kina karatu sai kace zamani da ki ke cikin ganiyar kurciyarki lallai tsohuwa nan kin mana wayo, nima ya zama dole na koma islamiyya. Yak'arasa magana had'e da zaunawa kusa da ita dariya Granny ta yi ba dole na tak'ark'are ba na fi wannan dak'iki'ya matar taka wance ko Hizzib 10 ba bu akanta sai d'an banzan fad'in ran tsiya. "Uhm,,,,,Uhm,,,,Granny karki yi wa matata sharri. Ba sharri nake mata ba gaskiya ce nake fad'a ga malama a gida a maimakon su dinga zama tana, daura musu karatu tunda sun karkare zuwa islamiyya shiririta ta hanasu. "Ansar ya girgiza kai takaicin ya baiyana k'arara akan fuskarsa Granny lamarin yaran ne sai addu'a especially Zuhura domin gara Nazeeya sau dubu da ita. "Granny ta yi ajiyar zuciya mai k'arfi bari kawai Ansaru hannunka ne baya ru6ewa ka yanke ka 'yar da tuni nace ka hak'ura da auren Zuhura babban takaicina da al'amarin Zuhura rashin kula da addini lokacin sallah ya yi ta yi zamanta tana latsar waya, har sai wata sallah ta riske wata sannan ta had'e su tagama ta kai tsakiyar dare tana latsar waya batare ta yi sallah isha ba, sai da safe ta yi ta wannan bala'in da me yai kama"? Mahaifiyarsu taana kallon wannan tabargaza da suke tafkawa bata iya kwa6arsu sai kace 'ya'yan ido, shi kuma sa'eedu baya iya aiyana komai tariga ta shanye shi. Hatta da girki yaran nan basu iya ba saidai Anaal tashiga kitchen su kuma, su hakince parlour suna latsar waya basu San cewa Kansu suke kwara ba Anaal ba domin duk namiji da aure Anaal wallahi ya yi dace da mace tagari mai nagartaciyya tarbiyya Anaal ga hankali da natsuwa ga ladabi da biyayya uwa-uba ilimin addini da na zamani a rayuwata banta6a gani yarinya mai natsuwa da kamalla irin Anaal ba. Kalle ni da tsofan nawa nake zaunawa Anaal ta daura min karatu sa6anin su da kurciyarsu sun k'asa yi a kullum cikin yi musu nasiha take akan su daure su koma islamiyya sai dai su yi mata dariya ko tsaki. Sai anan gaba za su gano amfani nasiha da Anaal take musu. "Gumi ya tsiyayowa Ansar saboda shi baisan bankad'a na Zuhura har ya yi k'amari haka ba. Haushi da tsanarta suka lullu6e shi ya ma tsani cigaba da zancenta domin zai iya hadasa masa bugawar zuciya hakan ne yasa yakawo karshen zancenta nata ta hanyar cewa........ Jeeddah Aliyu*SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *8* Granny wacece wannan Anaal d'in"? sunanta kawai nakeji banta6a ganinta ba. Murmushi Granny ta yi Anaal 'yar Abbah maigadi ce dalilin da yasa ba ka ganinta bata cika zama gida ba karfe 7:30am take tafiya makarantan boko tadawo k'arfe 3:00pm da tadawo ta yi wanka taci abinci karfe 4:00pm dai-dai ta wuce islamiyya sai misali k'arfe 6:30pm take dawowa gida da ta yi sallah magarib da isha taci abincin za ta kwanta bacci. "Ansar ya gyad'a kai tana k'ok'ari dama neman ilimi haka ya gada akwai wahala sosai, amma kuma akwai babbar riba. "Ai shiyasa a koda yaushe nake k'ara k'arfafa mata guiwa akwai lokacin da za ta ci ribarsa. Bara na kirata ku gaisa saboda yakamata kusan juna duk da ita tasanka Kaine dai bakasanta ba. "Anaal"! Anaa"l! Na'am Granny"! Ta amsa da k'arfi. Muryarta ta d'aki dodon kunnen Ansar ya lumshe idanu, ba ko shakka wannan mai zazzaqar murya ce ko ya kamanita suke"? Zo ga Ansaru ya zo ku gaisa. Kai Granny please kidaina kirana da Ansaru ki miye matsalarki ne in kin kirani da Muhammad"? Ba fa tilass aka yi miki ba akan sai kin kira ni da Ansar. "Kaima fad'a kawai ka ke yi Ansaru sunan dattijo zan kira da shi Ansaru nan da iyayyenka suka laqa maka sai dai ka yi hak'uri da shi zan kiraka. "Ki ka dai laqa min iyayye na da Ansar suka yi min laqabi ba Ansaru ba tsabar tsofa da rigima irin naki yasa ki ke k'ara d'ara guda a sunan. "Cikin muryarta mai dad'i da gard'i ta yi sallama wance takawo karshen muhawara da Ansar da Granny suke tafkawa. "Yarrr.....tsigar jikin Ansar ya tashi wani irin sanyi ya lullu6e shi wanda shi kanshi baisan ko na menene ba. "Granny ta amsa mata sallama gani Granny tafad'a had'e da zaunawa kusa da Granny, Ansaru yace bai ta6a ganinki ba shine na kira ki ku gaisa. "Anaal tad'ago dara-dara idanunta masu kama da madara fuskarta d'auke da k'ayatatcen murmushi tasauke su akan fuskar Ansar nan take Ansar yak'ara rikicewa, ya nemi natsuwarshi yarasa. ina wuni Ya Ansar"? La.....lafiya qalau Anaal ya karatu"? "Alhamdulillah"! Kina nan kina fama da wannan rud'ad'iya dalibar taki yak'arasa magana yana dariya had'e da nuna Granny. "Dariya Anaal ta yi Kadàina gani tsofan Granny Allah ba daganan ba brain d'inta har yanzu yana kawo light tana da saurin fahimtar karatu. Karka yi mamaki tafi ka saurin rik'e karatu. "Ansar ya yi dariya kai Amma Anaal kin kasheni wannan old woman ce za ta fini saurin rik'e karatu"? "Of course yes"! Saboda ita batada damuwa kowa akanta sa6ani kai da hayaniya office kadai ya isheka fama. "Ni fa bazan ta6a yarda Granny tafini ba. Wannan karon Granny ce tabashi amsa kai tafi can yaushe za ka had'a kanka da tsohon kai. Ansar ya gyara zama saboda yana jin dad'in firar tasu wance har ta yi nassara mantar da shi damuwa da Zuhura ta sanya shi. "Shikenan Granny ni kuma zan tabbatar miki da nafiki, insha Allah Gobe zan tattaro littafaina malama Anaal tasame k'ari dalibi mai hazaqa ba irin Granny ba. ''Zaro ido Anaal ta yi kamar ta ga abin tsoro cabdijam,,,,,,ba dai kai bane dalibin nawa ba koh"? Ni ne mana ko bakya farin ciki da zuwana nasha zamana"? Ni na isa nace bana farin ciki da zuwanka Allah yakawo ka lafiya". "Ameen yafad'a yana kallon kwaryar idonta kasa jure kallon nashi ta yi hakan yasa ta mik'e babu shiri sai da safe tafad'a had'e da komawa inda tafito Ansar ya bita da shu'umin kallo sai da ta6acewa ganinshi sannan yadawo da ganinshi kan Granny suka cigaba da fira sai dai sam baya fahimtar abunda take fad'a saboda zuciyarshi ta yi Nisan kiwo. Sai misalin 10:00pm yai sallama da Granny yawuce gida har yatafi bai had'u da Zuhura ba. Bai kuma nemi ta ba. _Washe Gari_ Around _11:30am_ Ansar yana zaune a office d'inshi abin duniya yataro ya yi masa yawa, sai faman tunani yake abinda baisaba da shi ba. Phone d'inshi ya yi ringing ya katse masa tunani nashi a kasalance yad'auki wayan _my love_ suna da ke yawo a screen mtcsww"! Ya ja guntun tsaki yana kallon Call d'in har ya katse wani kira yasake shigowa har ya tsinke yana kallon phone d'in kamar mai nazari about 5 missed calls Zuhura tana masa yak'i picking da karshe ma sai ya yi switch off d'in wayar nashi. Yadafe k'ok'on kanshi ya afka a tunani. "Abdallah ya turo k'ofa yashigo kunnenshi manne da waya yanemi kujera ya zauna yacigaba da wayarshi. Ta k'asan ido ya kalli Abdallah ya ta6e baki Abdallah ya k'are waya yak'ara facing Ansar wai ka me ke damunka ne"? 'Yan kwanaki nan narasa gane kanka. ''Mtcsww"! Ansar ya tsaki bari kawai Abdallah Zuhura tana caza mini kai narasa yanda zan yi. "Aww saboda Zuhura ne ka ke haddasawa kanka damuwa"? "Ansar ya yi nodding head nashi. Kana da aiki kuwa domin nasha fad'a maka ka rabuda Zuhura kwatakwata ba ku dace ba ra'ayi da tsariku ba d'aya ba. Soyayya ta rufe maka ido ka kasa gano illar auren zumuncin. ''Ni naga Zuhura nace Inasonta Abdallah ba had'a mu akayi ba ra'ayi da tsari ba za su hanani aurenta ba inason Zuhura ita ma tana sona fiye da son da nake mata babban matsalar da nake fuskanta daga gareta bai wuce rashin d'aukar magana ta da mahimmancin ba ina tsoron sai mu yi aure na aza doka ta karya tun a waje bata gani daraja da k'ima ta ina da mu yi aure. Abdallah ya yatsine fuska tunda ba ita kadai bace 'ya mace ka hak'ura da Ita mana, ga matanan birjik kamar janfa a jos kowace kala ka ke so da gudu za ka samu. "Uhm..... Uhm....kaima kasan mata basa gabana ita nagani ita nakeso ba fa zan iya canza ra'ayina akanta ba. Zan cigaba da yi mata addu'a Allah yaganar da ita. "Kwa6e fuska Abdallah ya yi ya mik'e tsaye ni zan koma office ina mai shawartarka da ka ware lokacin, ka zauna ka yi tunani kada kwa6arka ta yi ruwa daga baya kadawo kana danasani. Yana k'arasa magana batare da yajira jin ta baki Ansar ba yafita yabar Ansar zaune talabe da kumatu kamar statues ya lumshe idanu yak'ara zurfafawa a tunani. _6:07pm_ Ansar ya yi parking motarshi inda yasaba jiran wucewar mai niqan, cikin Sa'a baifi 7 minutes da tsayawa ba sai ga ta saidai yau ita kadai ce. Yau Ansar ya k'udurta aransa sai ya yi mata magana, har wani gyaran voice yake tana kawowa daf da shi yayi k'undubala had'e da 'kunar ba'kin wake yafurta _sannu malama"_ Ga mamakinsa sai ga ta ja ta yi tsaye cikin _ba wani sannu malama ka tabbata ka zo d'aukar karatu da wuri domin Granny ba ta Lattin gashi kana cika bakin kafita_ tana k'arasa magana tajuya a rikice Ansar ya bud'e mota yafito _Anaal"!_ yakira sunanta a rud'e na'am Ya Ansar"! Yak'arasa kusa da ita yana dariya mai ban sha'awa sannu da zuwa malama Anaal ya makaranta ya karatu"? "Saida ta lumshe idanunta sannan ta bud'esu "Alhamdulillah"! Ansar ya gyara tsayuwarshi yasaka hannunshi na hagu cikin aljihun wandonshi fuskarshi na fitar da k'ayatatcen murmushi wanda yak'ara fitowa da kyaunshi da kwarjininshi. "Gaskiya Anaal ke miskilace a kullum sai kin wuce ni anan wajen dai-dai da sau d'aya ba ki ta6a nuna kinsanni ba. Dariya Anaal ta yi mai dad'i ta ratsa kunnnuwa Ansar ba Shari ya lumshe idanu daga bisani ya bud'e su yana mai cigaba da kallonta har yanzu dariya take yi. Ta d'an tsagaita da dariya "still da sanyaye murmushi akan fuskarta, Allah Ya Ansar kabani dariya. "Toh bani abata yafad'a yana kallon kwayar idonta domin ita kadai yake iya hangowa daga cikin niqan. "Sosai yanzu tasa dariya bata ce da shi komai ba tajuya tacigaba da tafiya yabita da kallo tashige lungu da yasa6a gani tana shiga take yagano shortcut ce na zuwa gida, yafi sauri bisa ga ta mik'e hanya street. ''Tana 6acewa ganinshi yasaki murmushi had'e da hargitsa laulausa gashin kanshi. Cikin nishad'i ya shure wata empty robar ruwan da ke k'asa. "Ya ja motarshi yanufi masallacin da yasaba sallah bayan ya gama sallah yanufi cikin gida zuciyarshi cike da burin sake tozali da Anaal. "Dama Anaal itace mai niqan itace mai zazzaqar murya gaskiya Anaal 'yar baiwace ji ko dariyarta mai dad'i, kamar ta dawama yi min ita. Da wannan yadana "Horn Abbah ya bud'e masa gate ya yi parking yafito yana murmushi yanufi wajen Abbah Yana zuwa miqa masa hannu suka yi musabaha Abbah yana fara'a yace Muhammadu ya gida ya aiki"? "Lafiya qalau Alhamdulillah! Abbah. Masha Allah"! Yau ka zo da sa'a domin har na dafa mutumin naka {green tea} Ansar ya washe hak'ora madallah Abbah mu k'arasa na d'an kora. Yana kur6a green tea suna ta6a fira saida ya shanye cup 3 sannan ya mik'e Abbah zan shiga daga ciki. Toh Muhammad a fito lafiya" Allah yasa Abbah yafad'a had'e da juyawa yanufi part d'in Granny. Da sallama ya tura k'ofar shiga parloun Granny da Anaal suka amsa masa, yanemi sofa da ke facing nasu ya zauna Anaal tacigaba da murzawa Granny maganin da ta ke Shafa mata na ciwon k'afa. Granny har yanzu k'afar bata sake bane"? Bata sake ba Ansaru gatanan ina fama musanman yau ta matsa min sosai. "Tausayinta yakama Ansar yace ki shirya Granny gobe zanzo mu je asibiti, ko za su canza miki magani. "Uhm... Ba inda zan je Ansaru nasan halin likitocin nan sarai ba wadatacen imani ne da su ba cikin mugun engine d'inan za su sakani su dinga gasa ni kamar sun same kaza. "Granny na dasa aya Ansar da Anaal suka bushe da dariya ba mai kama wani, Granny ta kama baki tana kallonsu kaga ja'irai yara ni ku ke yi wa dariya"? tun lokacin da naji Ansaru yace zai dinga zuwa d'aukar karatu nasan cewa ba wani karatu da zai yi ya zo ne bud'e Sabon rumbun dariya a parlourna. "Ansar da Anaal suka k'ara sa dariya Anaal har da dafe ciki hawaye na tsiyaya daga idanunta. "Ya Allah! Granny tafad'a had'e da mik'ewa da kyar bari na ba ku wuri maimakon karatu ku sha dariya ta nufi bedroom d'inta Anaal ta tashi da sauri ta kama hannunta sakamako gani yanda take taka k'afar da kyar har bedroom tarakata sannan tadawo, tarar da Ansar yana dariya ta yi tsaye had'e da crossing hands nata a k'irji tana kallonshi a zuciyarta tace kai wannan d'an taliki akwai dariya har na siyarwa. "Ya tsagaita da dariya nashi ya dube ta fuskarshi d'auke da yalwatatcan murmushi malama ke nake jira fa. "Tarausayar da Kai ta tak'o zuwa gabanshi ta zauna nesa da shi kad'an.... Jeeddah Aliyu *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *9* Kanta na sunkuye tana wasa da fingers nata ta furta ina littafai ka"? A maimakon yabata amsa sai kawai ya tsareta da idanu jikinta yabata yana kallonta a tsanake tad'ago eyes nata ta zube su a nashi, kallon-kallon suka shiga yi kasa jure kallonshi nashi ta yi sakamako d'an banzan kwarjini da yai mata ta sadda kai k'asa. "Nace ina littafai ka"? tak'ara watsa masa tambaya karo na biyu. ''Ya Shafa gashin kanshi har zuwa ga d'an siririn gemunshi yana kallonta, ta k'asan ido yana murmushi. ''Anaal ta kwa6e fuska tafara magana da zuciyarta wannan karatu ya zo ko kallon mutane"? Ni fa na tsani kallo ya wani kafe ni da idanu ba ko k'intawa. "Ya Ansar please ina littafanka dare yanayi fa"? Ya d'age giran ido yana kallonta banida su yafad'a kamar mai rad'a. ''What's doe's mean"? Babu ko ke bakisan kalma babu bane"? ''Amma kuma ka ce karatu ka zo dauka"? ''Yeah! Kuma bakada littafai"? ''Ya gyad'a kai Kana nufin ba ka shirwaya karatun ba zuwa kawai ka yi"? ''Nop "Tabe baki Anaal ta yi saboda Ansar yafara kaita bango, iya tsawon rayuwarka kata6a ganin wanda yaje gona ba fatanya kuma yace noma ya je yi"? "Murmushi ya yi ba sai ya ara a wajen makwacinsa ba, ko ke bakisan mutum zai iya aron abunda bashida shi ba"? Au.....kana nufi ni ce ma Zan ba ka aron littafi"? Eh man ko bara ki bani bane"? Batare da tabashi amsa ba ta tashi tashiga bedroom d'in Granny ta iske ta kwance tana jan casbaha, tad'auki Jakarta na islamiyya. ''Tafice ta zauna mazauninta na tun asali Qur'ani za mu fara ko wane littafi"? Ansar yasaki murmushi shi dama qira'arta yakeso yak'ara ji ba wani karatu da ya zo yi, mu fara da Qur'ani. ''Daga sama za mu fara ko daga k'asa sai mu yi sama"? ''Mu fara daga sama yafad'a cikin zumud'i. Taciro Qur'ani daga Jakarta ta mik'a masa za mu fara daga fatiha. Ya gyad'a kai cikin zazzaqar muryarta tafara karanto basmallah kanta na sunkuye tacigaba da karatu har ta kai karshe suratul fatiha. ''Tafad'a suratul Baqara a wannan karon Ansar kasa jurewa ya yi saida yad'ago ga mamakinsa sai ga ba Qur'ani a hannunta da kai take rero masa karatun. ''Yakoma jikin kujera ya lafe ya zuba mata na mujiya{idanu} tana karatu yana aikin kallonta duk da jikinta yabata ita yake kallo ba Qur'ani ba hakan bai sa tad'ago ta dube shi saida takai dai-dai ayan da yadace ta tsaya sadakallahul azim"! Tafad'a had'e da tad'ago kanta. "Mik'o min Qur'ani na. Kamar daga sama muryarta yadak'i dodon kunnenshi a kasalance ya mik'a mata ta miyar a jakka. "Taciro Ahalari me su'al wa jahab ta mik'a masa. Ya kar6a yana jujjuya shi ka bud'e shafi na farko ta umarceshi. ''Ya naga wannan kina nufi da shi zan yi karatu"? "Kwarai kuwa saboda yafi sauki ganewa. Toh ai ni nayi wannan. Humm.....za ka maimaita ne sai naga kamon ludayinka koda zan canza maka wani ka bud'a shafi na farko za mu fara karatu nafara jin baccin. "Saida yai murmushi sannan ya bud'e shafin na farko, kamar yanda ta karanta mishi Qur'ani batare da ta duba ba haka tafara karanto mishi wannan. Shafi d'aya ta karanta mishi ta dasa aya. Iya nan za mu tsaya gobe za ka yi mun bitarshi sauran littafai sai gobe zan zo maka da su. ''Na gode malama amma kuma sai naga kamar wannan da ki ka fad'a min ya yi kad'an ki k'ara mun mana yak'arasa magana yana wani langwa6e kai. ''Girgiza kai ta yi bazan k'ara ba kuma sunana Anaal ba malama sai ka kiyaye. "Huh....malama kenan ni fa d'alibinki ne fa ta ya zan dinga fad'ar sunanki kaitsaye ba ko dan sakayawa"? Ai sai ki dinga kallona a matsayin d'alibi marar d'a'a. ''Amma kuma ni nace Ka fad'in sunan nawa Dan Allah Ya Ansar karka ce za ka dinga kirana da malama Allah ba zan ji dad'i ba tak'arasa magana kamar za tai kuka, batasan hakan da ta yi ba ta yi masifar burge Ansar ya lumsashe idanunshi yadauki tsawon d'ak'ik'a 2-3 idanunshi a lumshe daga bisani ya bud'e su fasss"! akanta. "Kamar me koyon magana yafurta zan yi tunani akai malama tah. ''Cuno baki ta yi tana jujjuya kafad'arta alama shagwa6a ba sai gogan naku yasaki baki da hanci ya shagala iya shagaltuwa da kallonta. ''Da sauri ta mik'e tsaye ta sunkuce Jakarta sai da safe ka gaida su Nadeeya ko juyawa bata k'ara yi ba tashige d'akin tabarshi zaune. "Sai da yadauki tsawon lokacin a zaune kafin ya mik'e yafita yau ma bai nemi Zuhura ba yai tafiyarsa a gate ya tsaya ya yi wa Abbah sai da safe yafice. "Cike da nishad'i yake driving yana murmushi har ya iso gida murmushi bai gushe daga kan fuskarshi ba. "Yayi parking motarshi a parking lot gani securities birjik da kak'in custom ga kuma blacks cars d'in Daddy a Parke ya tabbatar mishi Daddy ya zo. "Ya kai duba ga wrist watch d'in hannunshi 10:15pm yanufi part d'inshi yasan irin wannan lokacin Daddy ya kwanta sai dai da safe koda zai same ganinsa. ''Yana rage kayan jikinshi ya fad'a bathroom yasakewa kanshi shower yana fitowa ya tsane jikinshi da towel ya Shafa lotion yasaka pyjamas d'inshi yak'ara gudun Ac ya haye gado ya karaton addu'a kwanciya bacci ba wai don yana jin baccin ba. Kasancewar baccin zai iya d'auke shi "at any time. "Ya lumshe idanu muryar Anaal ke yawo a kunnenshi in juya hagu yak'ara juyawa side d'in dama daga karshe yadauki pillow ya jefa a k'irjinshi ya matse shi gam he had a sleepless night duk lokacin da ya yi yunkuri rufe idanu Anaal yake gani yayinda kunnenshi ke jin sautin amon muryarta Yajuya side d'in damansa, Yak'ara zurmawa a tunani ba shi ne yai bacci ba sai around 2:30am. _"Washe Gari_ _11:00am_ Ansar yafito cikin shirinsa na tafiya office black trouser ne a jikinsa da red colour long sleeve ya tsuke wuyansa da black necktie k'afarsa sanye da cover shoe black in colour jikinsa na fitar da k'amshin turaren "mesmerized Cologne kafad'arshi na rataye da briefcase hannunshi d'aya yana sakad'e cikin aljihun wandonshi, fuskarshi d'auke da murmushin abin sallarsa sai walk'iya Yake. "Shigar ta yi masifar yi masa kyau Ansar irin mazanan ne masu murd'ad'e jiki he's very giants man kallo d'aya za ka yi masa kagano ba duk namiji zai iya karawa da shi ba. "Direct parlourn Mum Fatee yanufa tsit parlour yake ba kowa k'amshin turaren wuta ya gauraye parlourn. ''Ya ajiye briefcase da hannun kujera ya nufi staircase ya hango Mum Fatee da Housemaids a kitchen suna had'a breakfast. yafasa haura stairs yanufi kitchen d'in ta baya ya rungume Mum Fatee "Good morning Mum"! ''Morning Boy katashi lafiya"? Am Fine Mum" That's Good My Boy Daddy yadawo har yai bacci yana tambayarka. Jiya da nadawo daga gidan Granny naga Prado's d'inshi a parking lot lokacin naga dare ya yi shiyasa ban shigo ba bara naje mu gaisa yajuya yafice da d'an gudunsa ya haura staircase. "Controller General Basheer Galadima yana kishingid'e jikinsa sanye da farar Jallabiya da sallama Ansar yashiga parlourn, Daddy oyoyo Ansar yafad'a kamar k'aramin yaro. "Controller ya tashi zaune yana murmushi Ya kuma ware hannayenshi Ansar na zuwa yashige k'irjinshi hugging d'in Juna suka yi tightly Boy ya aiki da hak'uri da jama'a hope komai yana tafiya yanda yadace"? "Alhamdulillah Daddy ni kaina banta6a tsanmani abubuwan za su daidaita kamar haka ba. "That's Great I'm proud of you my Boy dama nasan za ka iya handle d'in company nan ka kuma tafiyar da shi yanda yadace, Allah yai maka albarka. "Ameen Daddy. Ansar yasaki Daddy ya zauna kusa da shi sai doka murmushi yake shi dai duk duniya in kacire Allah da manzonshi ba abunda yakeso sama da iyayyenshi, bashida burin da yawuce ya kyautata musu kasancewar shi kadai suka Haifa d'a namiji gaba d'aya hope d'insu yana kanshi. "Gyaran murya controller ya yi alamar zai yi magana mai mahimmancin, kwanaki baya sa'eed ya kirani akan zance aurenka da Zuhura so yake ayi kafin azumi nace yabani lokacin zan yi magana da kai naji naka ra'ayi. Ansar ya tsince kanshi da fad'uwar gaba ya rikice yashiga in da in da Dad...ddy...azumi fa"? Gaskiya ya yi sauri ni anawa tsari sai Zuhura ta gama karatu zuwa lokacin na kamalla gini na. "Murmushi controller ya yi shikenan Boy tunda haka ka za6a inda rai da lafiya kamar gobe ne. ''Mum Fatee ta yi sallama tashigo ta dube suna murmushi firar me akeyi shine ba'a jirani ba"? Controller ne yabata amsa cikin sigar wasa fuskarshi d'auke da murmushi ina ruwanki da ko firar me mu ke yi keda ki ke shigewa d'akin da 'ya'yanki kuna shawara abinku na ta6a tambayarki abunda ku ke tautaunawa akai"? "Au.....Daddy tanan ka 6ullo to ae shikenan sai kutashi mu je ku yi breakfast in tayi tsami ma ji. Ba abunda za ku ji domin wannany firar ta tsakanin d'a da uba ne ko Boy"? Controller yak'arasa magana had'e da kallon Ansar Dariya sosai Ansar ya yi yace haka ne Daddy. "Zaro ido mum fatee ta yi lallai Boy haka ma za ka fad'a in dai Daddy ne tafiya zai yi yabarni da kai gidanan mu had'e maka kai ni da Girl's d'ina. "Ansar yana dariya ya mik'e tsaye ya rik'on hannun Mum Fatee zo mu je Mum zan sanarda ke amma in ku ka had'e min kai ai na Shiga tara. Controller da Mum suka sa dariya cike da farin ciki suka nufi dining area, Ansar ya ja ma Controller kujera ya zauna sannan shima ya zauna mum Fatee ta yi musu serving. "Suna gama taking breakfast Ansar yai sallama da su yanufi office. _8:00pm_ Kamar yanda jiya Ansar yadira gidan Granny yau ma hakan ce tafaru, saida ya tsaya a main gate wajen Abbah yasha green tea sannan yanufi part d'in Granny a parlour ya iske Granny tana kallon sunnah tv. "Bayan sun gaisa suka shiga firar duniya Ansar yana yi yana kallon k'ofar d'akin Granny ko zai ga Anaal tafito. Kamar daga sama ya ji muryar Zuhura Granny Ya Ansar ne ya zo naga motarshi a parking lot"? "Ta bankad'o curtain tashigo tana gani Ansar tasaki murmushi idonka kenan my love yanzu abunda ka yi min fissibillah"! Kana gani yadace"?ko ba komai na ba ka hak'uri. Kallon hadarin kaji Ansar yai mata yadaure fuska tamau ya had'e rai. "please Ya Ansar I said am sorry ta zube gabanshi tashiga zuba masa magiya. Ko kallo bata isheshi ba sai ma kauda fuskarsa da ya yi. Bud'e curtain aka yi had'e da sallama cikin sauri Ansar yajuya ya kalli bakin k'ofa, sanye take da hijab sky blue in colour iya gwiwarta duk da fuskarta ba make-up ta yi masifar yi ma Ansar kyau. "Ina wuni Ya Ansar"? Anaal ta gaida shi Muryarshi har wani shacking take yi ya amsa da la...fi..ya....malama Anaal ya gida ya karatu"? Ta rausayar da kanta tace Lafiya qalau Alhamdulillah. Ta juya cikin tafiyarta a natse tashiga bedroom d'in Granny yayinda Ansar ya rakata da ido saida tabacewa ganinshi sannan yadawo da dubanshi ga Zuhura wance takafe shi da nata idanu... Jeeddah Aliyu *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *9* Kanta na sunkuye tana wasa da fingers nata ta furta ina littafai ka"? A maimakon yabata amsa sai kawai ya tsareta da idanu jikinta yabata yana kallonta a tsanake tad'ago eyes nata ta zube su a nashi, kallon-kallon suka shiga yi kasa jure kallonshi nashi ta yi sakamako d'an banzan kwarjini da yai mata ta sadda kai k'asa. "Nace ina littafai ka"? tak'ara watsa masa tambaya karo na biyu. ''Ya Shafa gashin kanshi har zuwa ga d'an siririn gemunshi yana kallonta, ta k'asan ido yana murmushi. ''Anaal ta kwa6e fuska tafara magana da zuciyarta wannan karatu ya zo ko kallon mutane"? Ni fa na tsani kallo ya wani kafe ni da idanu ba ko k'intawa. "Ya Ansar please ina littafanka dare yanayi fa"? Ya d'age giran ido yana kallonta banida su yafad'a kamar mai rad'a. ''What's doe's mean"? Babu ko ke bakisan kalma babu bane"? ''Amma kuma ka ce karatu ka zo dauka"? ''Yeah! Kuma bakada littafai"? ''Ya gyad'a kai Kana nufin ba ka shirwaya karatun ba zuwa kawai ka yi"? ''Nop "Tabe baki Anaal ta yi saboda Ansar yafara kaita bango, iya tsawon rayuwarka kata6a ganin wanda yaje gona ba fatanya kuma yace noma ya je yi"? "Murmushi ya yi ba sai ya ara a wajen makwacinsa ba, ko ke bakisan mutum zai iya aron abunda bashida shi ba"? Au.....kana nufi ni ce ma Zan ba ka aron littafi"? Eh man ko bara ki bani bane"? Batare da tabashi amsa ba ta tashi tashiga bedroom d'in Granny ta iske ta kwance tana jan casbaha, tad'auki Jakarta na islamiyya. ''Tafice ta zauna mazauninta na tun asali Qur'ani za mu fara ko wane littafi"? Ansar yasaki murmushi shi dama qira'arta yakeso yak'ara ji ba wani karatu da ya zo yi, mu fara da Qur'ani. ''Daga sama za mu fara ko daga k'asa sai mu yi sama"? ''Mu fara daga sama yafad'a cikin zumud'i. Taciro Qur'ani daga Jakarta ta mik'a masa za mu fara daga fatiha. Ya gyad'a kai cikin zazzaqar muryarta tafara karanto basmallah kanta na sunkuye tacigaba da karatu har ta kai karshe suratul fatiha. ''Tafad'a suratul Baqara a wannan karon Ansar kasa jurewa ya yi saida yad'ago ga mamakinsa sai ga ba Qur'ani a hannunta da kai take rero masa karatun. ''Yakoma jikin kujera ya lafe ya zuba mata na mujiya{idanu} tana karatu yana aikin kallonta duk da jikinta yabata ita yake kallo ba Qur'ani ba hakan bai sa tad'ago ta dube shi saida takai dai-dai ayan da yadace ta tsaya sadakallahul azim"! Tafad'a had'e da tad'ago kanta. "Mik'o min Qur'ani na. Kamar daga sama muryarta yadak'i dodon kunnenshi a kasalance ya mik'a mata ta miyar a jakka. "Taciro Ahalari me su'al wa jahab ta mik'a masa. Ya kar6a yana jujjuya shi ka bud'e shafi na farko ta umarceshi. ''Ya naga wannan kina nufi da shi zan yi karatu"? "Kwarai kuwa saboda yafi sauki ganewa. Toh ai ni nayi wannan. Humm.....za ka maimaita ne sai naga kamon ludayinka koda zan canza maka wani ka bud'a shafi na farko za mu fara karatu nafara jin baccin. "Saida yai murmushi sannan ya bud'e shafin na farko, kamar yanda ta karanta mishi Qur'ani batare da ta duba ba haka tafara karanto mishi wannan. Shafi d'aya ta karanta mishi ta dasa aya. Iya nan za mu tsaya gobe za ka yi mun bitarshi sauran littafai sai gobe zan zo maka da su. ''Na gode malama amma kuma sai naga kamar wannan da ki ka fad'a min ya yi kad'an ki k'ara mun mana yak'arasa magana yana wani langwa6e kai. ''Girgiza kai ta yi bazan k'ara ba kuma sunana Anaal ba malama sai ka kiyaye. "Huh....malama kenan ni fa d'alibinki ne fa ta ya zan dinga fad'ar sunanki kaitsaye ba ko dan sakayawa"? Ai sai ki dinga kallona a matsayin d'alibi marar d'a'a. ''Amma kuma ni nace Ka fad'in sunan nawa Dan Allah Ya Ansar karka ce za ka dinga kirana da malama Allah ba zan ji dad'i ba tak'arasa magana kamar za tai kuka, batasan hakan da ta yi ba ta yi masifar burge Ansar ya lumsashe idanunshi yadauki tsawon d'ak'ik'a 2-3 idanunshi a lumshe daga bisani ya bud'e su fasss"! akanta. "Kamar me koyon magana yafurta zan yi tunani akai malama tah. ''Cuno baki ta yi tana jujjuya kafad'arta alama shagwa6a ba sai gogan naku yasaki baki da hanci ya shagala iya shagaltuwa da kallonta. ''Da sauri ta mik'e tsaye ta sunkuce Jakarta sai da safe ka gaida su Nadeeya ko juyawa bata k'ara yi ba tashige d'akin tabarshi zaune. "Sai da yadauki tsawon lokacin a zaune kafin ya mik'e yafita yau ma bai nemi Zuhura ba yai tafiyarsa a gate ya tsaya ya yi wa Abbah sai da safe yafice. "Cike da nishad'i yake driving yana murmushi har ya iso gida murmushi bai gushe daga kan fuskarshi ba. "Yayi parking motarshi a parking lot gani securities birjik da kak'in custom ga kuma blacks cars d'in Daddy a Parke ya tabbatar mishi Daddy ya zo. "Ya kai duba ga wrist watch d'in hannunshi 10:15pm yanufi part d'inshi yasan irin wannan lokacin Daddy ya kwanta sai dai da safe koda zai same ganinsa. ''Yana rage kayan jikinshi ya fad'a bathroom yasakewa kanshi shower yana fitowa ya tsane jikinshi da towel ya Shafa lotion yasaka pyjamas d'inshi yak'ara gudun Ac ya haye gado ya karaton addu'a kwanciya bacci ba wai don yana jin baccin ba. Kasancewar baccin zai iya d'auke shi "at any time. "Ya lumshe idanu muryar Anaal ke yawo a kunnenshi in juya hagu yak'ara juyawa side d'in dama daga karshe yadauki pillow ya jefa a k'irjinshi ya matse shi gam he had a sleepless night duk lokacin da ya yi yunkuri rufe idanu Anaal yake gani yayinda kunnenshi ke jin sautin amon muryarta Yajuya side d'in damansa, Yak'ara zurmawa a tunani ba shi ne yai bacci ba sai around 2:30am. _"Washe Gari_ _11:00am_ Ansar yafito cikin shirinsa na tafiya office black trouser ne a jikinsa da red colour long sleeve ya tsuke wuyansa da black necktie k'afarsa sanye da cover shoe black in colour jikinsa na fitar da k'amshin turaren "mesmerized Cologne kafad'arshi na rataye da briefcase hannunshi d'aya yana sakad'e cikin aljihun wandonshi, fuskarshi d'auke da murmushin abin sallarsa sai walk'iya Yake. "Shigar ta yi masifar yi masa kyau Ansar irin mazanan ne masu murd'ad'e jiki he's very giants man kallo d'aya za ka yi masa kagano ba duk namiji zai iya karawa da shi ba. "Direct parlourn Mum Fatee yanufa tsit parlour yake ba kowa k'amshin turaren wuta ya gauraye parlourn. ''Ya ajiye briefcase da hannun kujera ya nufi staircase ya hango Mum Fatee da Housemaids a kitchen suna had'a breakfast. yafasa haura stairs yanufi kitchen d'in ta baya ya rungume Mum Fatee "Good morning Mum"! ''Morning Boy katashi lafiya"? Am Fine Mum" That's Good My Boy Daddy yadawo har yai bacci yana tambayarka. Jiya da nadawo daga gidan Granny naga Prado's d'inshi a parking lot lokacin naga dare ya yi shiyasa ban shigo ba bara naje mu gaisa yajuya yafice da d'an gudunsa ya haura staircase. "Controller General Basheer Galadima yana kishingid'e jikinsa sanye da farar Jallabiya da sallama Ansar yashiga parlourn, Daddy oyoyo Ansar yafad'a kamar k'aramin yaro. "Controller ya tashi zaune yana murmushi Ya kuma ware hannayenshi Ansar na zuwa yashige k'irjinshi hugging d'in Juna suka yi tightly Boy ya aiki da hak'uri da jama'a hope komai yana tafiya yanda yadace"? "Alhamdulillah Daddy ni kaina banta6a tsanmani abubuwan za su daidaita kamar haka ba. "That's Great I'm proud of you my Boy dama nasan za ka iya handle d'in company nan ka kuma tafiyar da shi yanda yadace, Allah yai maka albarka. "Ameen Daddy. Ansar yasaki Daddy ya zauna kusa da shi sai doka murmushi yake shi dai duk duniya in kacire Allah da manzonshi ba abunda yakeso sama da iyayyenshi, bashida burin da yawuce ya kyautata musu kasancewar shi kadai suka Haifa d'a namiji gaba d'aya hope d'insu yana kanshi. "Gyaran murya controller ya yi alamar zai yi magana mai mahimmancin, kwanaki baya sa'eed ya kirani akan zance aurenka da Zuhura so yake ayi kafin azumi nace yabani lokacin zan yi magana da kai naji naka ra'ayi. Ansar ya tsince kanshi da fad'uwar gaba ya rikice yashiga in da in da Dad...ddy...azumi fa"? Gaskiya ya yi sauri ni anawa tsari sai Zuhura ta gama karatu zuwa lokacin na kamalla gini na. "Murmushi controller ya yi shikenan Boy tunda haka ka za6a inda rai da lafiya kamar gobe ne. ''Mum Fatee ta yi sallama tashigo ta dube suna murmushi firar me akeyi shine ba'a jirani ba"? Controller ne yabata amsa cikin sigar wasa fuskarshi d'auke da murmushi ina ruwanki da ko firar me mu ke yi keda ki ke shigewa d'akin da 'ya'yanki kuna shawara abinku na ta6a tambayarki abunda ku ke tautaunawa akai"? "Au.....Daddy tanan ka 6ullo to ae shikenan sai kutashi mu je ku yi breakfast in tayi tsami ma ji. Ba abunda za ku ji domin wannany firar ta tsakanin d'a da uba ne ko Boy"? Controller yak'arasa magana had'e da kallon Ansar Dariya sosai Ansar ya yi yace haka ne Daddy. "Zaro ido mum fatee ta yi lallai Boy haka ma za ka fad'a in dai Daddy ne tafiya zai yi yabarni da kai gidanan mu had'e maka kai ni da Girl's d'ina. "Ansar yana dariya ya mik'e tsaye ya rik'on hannun Mum Fatee zo mu je Mum zan sanarda ke amma in ku ka had'e min kai ai na Shiga tara. Controller da Mum suka sa dariya cike da farin ciki suka nufi dining area, Ansar ya ja ma Controller kujera ya zauna sannan shima ya zauna mum Fatee ta yi musu serving. "Suna gama taking breakfast Ansar yai sallama da su yanufi office. _8:00pm_ Kamar yanda jiya Ansar yadira gidan Granny yau ma hakan ce tafaru, saida ya tsaya a main gate wajen Abbah yasha green tea sannan yanufi part d'in Granny a parlour ya iske Granny tana kallon sunnah tv. "Bayan sun gaisa suka shiga firar duniya Ansar yana yi yana kallon k'ofar d'akin Granny ko zai ga Anaal tafito. Kamar daga sama ya ji muryar Zuhura Granny Ya Ansar ne ya zo naga motarshi a parking lot"? "Ta bankad'o curtain tashigo tana gani Ansar tasaki murmushi idonka kenan my love yanzu abunda ka yi min fissibillah"! Kana gani yadace"?ko ba komai na ba ka hak'uri. Kallon hadarin kaji Ansar yai mata yadaure fuska tamau ya had'e rai. "please Ya Ansar I said am sorry ta zube gabanshi tashiga zuba masa magiya. Ko kallo bata isheshi ba sai ma kauda fuskarsa da ya yi. Bud'e curtain aka yi had'e da sallama cikin sauri Ansar yajuya ya kalli bakin k'ofa, sanye take da hijab sky blue in colour iya gwiwarta duk da fuskarta ba make-up ta yi masifar yi ma Ansar kyau. "Ina wuni Ya Ansar"? Anaal ta gaida shi Muryarshi har wani shacking take yi ya amsa da la...fi..ya....malama Anaal ya gida ya karatu"? Ta rausayar da kanta tace Lafiya qalau Alhamdulillah. Ta juya cikin tafiyarta a natse tashiga bedroom d'in Granny yayinda Ansar ya rakata da ido saida tabacewa ganinshi sannan yadawo da dubanshi ga Zuhura wance takafe shi da nata idanu... Jeeddah Aliyu *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *10* Zuhura ta yatsine fuska Ya Ansar ka yi shiru ba ka ce komai ba ko kana nufi har yanzu ba ka yafemin ba"? ''Ansar ya yi murmushi yana kallonta ta k'asan ido yayinda Zuhura tak'ara zurmawa a sonshi domin kallon ya yi mugun ratsa 6argo jikinta. Tak'ara langwa6e kai cikin shagwa6a tace ''Please my luv answer me. K'ara haska ta ya yi da k'ayatatcen murmushi sanin kanki ne Zuhura bana iya dogon fushi da ke matsala na d'aya da ke bakyajin magana. ''Ka K'ara hak'uri da ni my luv da mu yi aure zan dinga jin maganarka. Tabe baki ya yi yayinda Granny ta ja tsaki da sauri Zuhura tajuya ta dube Granny saida ta yatsine fuska kafin ta furta ke kuma ke da wa"? Banza Granny ta yi da ita tacigaba da kallonta Zuhura tak'ara yatsine fuska tadawo da ganinta wajen Ansar my luv I miss you so much especially your hot & romantic voice mu je daga waje na fayyace maka yanda nayi missed naka. Wannan tsohuwa ba za tabarmu mu sake ba tak'arasa magana had'e da nuna Granny da baki. ''Ansar yak'ara fad'add'a murmushinsa ki je kawai in na kamalla abunda na zo yi zan nemi ki. Zuhura ta mik'e tana dariya k'asa-k'asa shikenan my luv sai kafito tajuya tafita, Ansar ya bi ta da kallo daga bisani ya dube Granny me Anaal take yi a d'akin ne Granny ko yau ba za'a fad'a min karatun bane"? "Granny ta kya6e baki tasoma kwallawa Anaal kira sai ga ta tafito sanye da hajibi iya gwiwa Army colour ya yi matuk'ar k'awata fuskarta. "Gani Granny Ga me nemanki nan Granny tafad'a had'e da nuna Ansar da yatsa, kallo d'aya Anaal tayi masa ta kauda fuska saboda duk lokacin da tayi arba da kyakyawar fuskarsa sai ta tsince kanta da fad'uwar gaba ga wani masifar kwarjini da yake mata. "Yayinda Ansar ya kafeta da ido baya ko k'intawa ga wani shu'umin murmushi kwace a fuskarsa, yana wani shafar laulausan sajenshi. Batare da ta furta uffan ba tajuya ta koma d'akin tadauko jakkar littafanta kamar yanda ta zauna jiya nesa da shi ta langwashe k'afafunta, tana facing nashi ta bud'e jakka tafito da Al-qur'ani mai girma ta mik'a masa had'e da cewa ka sauko k'asa shine ladabin d'aukar karatu. ''Angama malamata ya furta can k'asan mak'oshi ya zauna k'asa ya langwashe k'afafu kamar yanda ya ga ta yi yasoma koro karatun da ta gayamishi jiya har izuwa inda ta tsaya, ta kar6i Qur'ani tak'ara mik'a masa ahallari yafara karatu da saninsa yake karanta fassara ba dai-dai ba dakatar da shi tayi ta hanyar cewa bawan Allah wa gayamaka wannan fassarar da ka ke yi"? "D'agowa ya yi yana kallonta da shegen murmushinsa mai tayar da hankali me kallonsa da sauri ta kauda fuskarta. "Kamar mai rad'a ya furta Ke! Da sauri tadawo da ganinta wajenshi cikin sark'ewar lafazi tace ni kuma"? "D'aga mata gira ya yi a maimakon yabata amsa tsigar jikinta yatashi yarr.... Ya Ansar ta kira sunanshi had'e da langwa6e kai kamar me shirin yin kuka. ''Anaaaal......shima yakira sunanta har da su qalqala wani bak'on yanayi Anaal tashiga wanda a tsawon rayuwarta bata ta6a riskar kanta a ciki ba. Sannu ahankali yarufe littafin hannunshi yajigina jikinsa a kujera ya lumshe sexy eye's d'inshi yana shafar gashin kansa. Jikin Anaal ya mutu mutuss...ta kasa koda kwakwaran motsi tad'ago ta sace kallonshi karaf suka had'a ido ya wanketa da murmushi batasan lokacin da ta mayar masa da Martani murmushin nashi ba. "Tsawon lokacin suka d'auka in ya dube ta ya yi murmushi ita ma ta kalleshi ta yi murmushi, muryar Granny ce ta ratsa dodon kunnensu ni zan shiga ciki na kwanta in kungama karatu Anaal ki kashe kayan kallo ki rufe k'ofa. "Toh Granny Anaal tafad'a cikin rawar murya. "Ansaru sai da safe ka gaida gida. Gida zai ji Granny sai da safe Allah yatashe mu lafiya. _Ameen Granny tafad'a had'e da shigewa d'akinta_ "Ya Ansar kacigaba da karatunka mana. Ba zan iya ba malama Anaal Saboda me ba ka iya karatun bane ko me"? "Na iya saidai ba zan iya karantawa ba. Toh bani littafina ta mik'a masa hannu kurawa hannunta ido ya yi fari tass da shi kamar kata6a jini yafito 'yan yatsunta zaro-zaro k'umbarta yasha adon Jan lalle sai zobe kwara d'aya tal na azurfa da ke sakade a yatsanta, Ansar ya yi nisa a kallon yatsan nata sai ji ya yi tafizge littafin hannunshi cikin zafin nama yajanye littafin. "Yashiga kallonta k'asa-k'asa cikin muryar shagwa6a tace Please Ya Ansar Kadàina kallona banaso. Ya yi murmushi had'e da zaro masifanfu idanunshi in a romantic voice yafurta wai meyasa Anaaaal"? "k'ara rikita ta ya yi saboda duk lokacin da yaja sunanta sai tsigar jikinta ya tashi ga wani sanyi da ke ratsa k'asusuwan jikinta. "Kawai ni banason kallo tafad'a har da murgud'a d'an k'aramin bakinta mai kama da gidan tsuntsu. "Ansar ya ja iska daga bakinshi yafesar idanunshi ya mayar akan pink lips d'inta cikin zuciyarshi yafara fassalta kyakyawar surarta. ''Anaal fara ce tass irin farin nan me surkin ja-ja-ja ita ba doguwa bace kuma ba za'a sakata a Layin gajeru ba tanada round face me d'auki da dogon hancin mai kama da pencil idanuta manya ne sosai shiyasa in tana magana take lumshe su kamar me jin bacci Anaal tana da jiki saidai ba sosai ba 'yar lukuta da ita, gashin girarta da na idanuta bak'i wulik da shi kamar tana saka na kanti duk lokacin da Anaal ta yi murmushi ko magana sai kumatunta ya lotsa{dimples}. "Ansar yasaki naunauyar ajiyar zuciya baisan lokacin da ya yi subul da baka ba ta hanyar furta _Anaal mai kyau_ A tsorace tad'ago na'am me kace"? _Anaal me kyau nace ko ke ba me kyau bace?_ Humm....Ya Ansar kai koh tafad'a cikin sirriyar murya. ''Me nayi"? "A wannan jar fata nawa kamar Jan k'osai za ka kirani me kyau kawai malam kana zagina. "Dariya ya yi Anaal kenan ai ni ba abunda yafi tafiya da imanina a halitttarki irin farar fatarki. ''Eyeee.....tafad'a har da zaro ido nan take gogan naku yagano yasaki layi sai kawai yawaice ta hanyar cewa in tambaye ki mana Anaaal Gyad'a kai ta yi saboda a halin yanzu ta kagara ta tsince kanta alone ko za ta samu damar aikawa da Kanta tambayoyi. Shekarunki nawa"? Batasan lokacin da tasa dariya ba tashiga 'kya'kyatawa kamar wance taga comedy na emanuella. What's funny Baby"? Ansar ya watsa mata tambaya yana leqon fuskarta, tarufe bakinta da tafin hannunta tana cigaba da dariya abinta. "Shikenan tunda ba za ki gayamin ba zan tambayi Ammah nasan ita ba za ta yi min dariya ba kamar ke. ''Humm! Kasan da Ammah meyasa ka tambaye ni"? Saboda ke yafi dacewa na tambaya ko bakiji hausawa suna cewa waqa a bakin mai ita yafi dad'in sauraro ba"? ''Ta za'ayi nasani al'ahali ni ba bahaushiya bace. "Humm....! Anaal kenan komai naki yana burgeni har nakeji ina ma ace muna rayuwa a gida d'aya da kullum sai nasaka ki a gaba ina kallo. "Zaro ido Anaal ta yi tana dariya kai Ya Ansar wallahi kana da abin dariya meye abin burgewa a tare da ni da har za ka dinga kallona"? Ansar ya lumshe kyawawan idanunshi yana murmushi ba za ki gane bane Anaal amma a sannu zan ganar da ke. ''Ka ji da shi ni bani littafina na tafi baccin nakeji. "Ke da Granny kuna saurin kwanciya bacci jikinku baya tsami ne Kalli wall clock kigani yanzu _10:15pm_ ta yi"? Tabe baki Anaal ta yi kace bara ka iya karatu ba to zaman me zanyi anan"? ''Ki tayani fira. Fira, fira fa kace a maimakon karatu sai mu buge da fira"? Eh man"! Yafad'a yana kallon cikin idanunta. Humm...ni kan badani ba ka je part d'in Hajiya yaya Zuu na jiranka kusha fira abinku tak'arasa magana tana mai mik'ewa tsaye. ''Shima mik'ewa ya yi yana kallonta ad'age ai ba ke za ki nuna mun Zuhura ba nasan da ita nasan kuma tana jira na amma nace ki tayani fira "anyway tunda ba za ki iya ba za ki iya tafiya sai da safe yajuya yanufi k'ofar fita yabarta tsaye sororo tana mamakin miye abin fushi anan"? "Har ya yi tako biyu yadawo ya mik'a mata littafinta yak'ara juyawa yafita. _sai da safe Ya Ansar_ Anaal tafad'a cikin sanyi murya. Qala bai ce da ita ba ya bud'e k'ofa yafita tabe baki Anaal ta yi tajuya asanyaye tashiga d'akin. ''Ansar yana fita yanufi parking lot yaja motarshi Abbah ya bud'e masa gate yanufi gida yana isa gida Direct part d'in shi yawuce yacire kayan jikinshi yashiga bathroom ya yi wanka yana fitowa phone d'inshi na fara ringing kamar ba zai yi picking ba saida yagama Jan ajinsa sannan ya yi picking _Hello my luv_ Ya Ansar sarkin alqawali kace najira ka za ka zo shine ka yi tafiyar ka koh"? _"Oops! I'm very sorry my luv nima ba'a son raina na tafi batare da nemi ki ba amma kiyi hak'uri gobe inshaAllah zan zo har sai kinga ji da ganina_ Humm.....my luv har abada idanuna ba za su ta6a gajiya da ganinka ba karka manta Kaine farin cikin rayuwata jin dad'ina you're my everything Ya Ansar I love you so much. ''Yatsine fuska ya yi had'e da cewa I love too Baby ki kwanta kiyi bacci mai dad'i had'e da mafalkina. "Your wish is my command my luv kaima kayi mafalkina mai dad'i. ''Batare da yabata amsa ba ya katse kiran yasaka pajamas d'inshi ya haye bed, ya tsunduma a tunani _Anaal_ da kyar yasamu bacci yadauke shi. _7:10am_ Ansar yafito daga part d'inshi yana sanye da bak'ar jallabiya sai uban sauri yake kamar zai tashi sama, kaitsaye parking lot yanufa yashiga motarshi saida ya yi warming nata daga bisani yafizge ta da k'arfi maigadi ya bud'e masa gate. "Kaitsaye gadon K'aya yanufa layin gidansu Zuhura yashiga yanemi nesa da gidan ya yi parking lokacin-lokacin yana duba agogon da ke da jikin motarshi _7:15am_ Anaal tafito daga gida jikinta sanye da school uniform a hankali take tafiya ga k'atuwar schoolbag d'inta rataye a bayanta, bakin titi tanufa tasami adaidata da zai kaita school. ''Tun kafin tak'araso Ansar ya hangota yasaki ajiyar zuciya had'e da hamdallah. Yana kallonta har ta ra6a shi ta wuce yana ganin takai titi yaja mota ya bi bayanta, Horn yadinga dana mata juyowa d'aya ta yi ta kalli motar tadauke kanta batare da tagano wanda ke cikin motar ba saboda gilashi motar tinted ne. "Ansar yana gani tayi nassara tsayar da wani mai adaidata ya yi saurin saukar da gillasai _ke Anaal bakyaji ne tun d'azu ina miki horn"?_ "Muryar sa Anaal tagano saida gabanta yafad'i a d'an rikice tajuya ta dube shi Ya Ansar tafad'a abaiyane tadawo da ganinta ga mai adaidata malam dan Allah minti 1. "Okay hajiya amma ki yi sauri. Tajuya tanufi motar tadafa k'ofar da ke saiti da shi ta d'an tura kanta cikin motar _ina kwana Ya Ansar_ Lafiya kishigo nayi dropping naki. ''Shiru ta yi tana kallonshi tarasa kalma da za ta furta masa gani shiru nata ya yi yawa yasa yace kishigo mana kina 6atawa kanki lokacin. "Ba yanda ta iya dole tajuya sukuku kamar kazar da kwai yafashewa a ciki takoma wajen mai adaidata tabashi hak'uri. "Ta bud'e k'ofar seat d'in baya ta ajiye schoolbag d'inta ta zauna a seat d'in gaba ya ja mota suka halba kan titi. Shiru ya biyo baya Anaal tana nazari me Ansar yake yanufi da ita yayinda Ansar yake tunani shin me ke shirin faru d[truncated by WhatsApp]*SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *11* Anaaal yakira sunanta cikin tautasan lafazi Na'am tafad'a had'e da kallonshi nasan za ki yi mamakin faruwar wasu abubuwa tsakanina da ke, toh ba abin mamaki bane in ki ka yi la'akari da kyakyawar alaqa da ke tsakanina da Abbah. ''Ya d'an yi _shiru na kamar _5 seconds_ daga bisani ya nisa yacigaba da cewa banaso ki matsantawa kanki da tunani, ni na d'auke ki kamar K'anwata ta jini duk abunda ki ke da buk'ata kada ki boye min ki d'auke ni matsayin Friend wanda ba za ki iya boye masa duk wata damuwa da ki ke ciki, kamar yanda nima ba zan boye miki halin da nake ciki ba. "Anaal ta yishiru tana wasa da gefen hijabinta gaba d'aya kalaman Ya Ansar sun daure mata kai ta ya za'ayi tayi k'awance da namiji ko namiji Ansar Galadima gaskiya abun da wuya wai gurguwa da aure nesa. ''Anaal kin yi shiru ba ki bani amsa ba ko bakyaso na zama abokin shawararki"? Girgiza kai ta yi cikin sanyi murya tafara magana ba haka bane Ya Ansar na yarda da kai 100% saidai ba ka tunani wannan sabuwar alaqa tamu ba zai kawo matsala ba"? Domin ni ina gudu duk wani abu da zai kawo fitina daga gareni. "Murmushi ya yi bana tunani faruwa hakan in ma kina jin tsoro me zai hana mu dinga huld'a mu a 6oye"? Jikin Anaal yadauki rawa da kyar ta iya furta a 6oye kuma"? To wai me yasa za mu dinga 6oye alaqar mu al'hali mu ba wani mugun abu mu ke aikatawa ba''? Ansar yak'ara dafe steering cikin dabara da wayo yace saboda kina jin tsoro amma ni bayanshi banada wani dalilin kwakwara, amma kuma in kin amince kowa yasan cewa akwai k'awance a tsakaninmu ni a wurina ba matsala bane. ''Da Sauri Anaal tace No! Banaso kowa sani saboda gudun zargi Ansar ya yi murmushi jin dad'i yace shikenan daga yau mu zama friends koh"? ''Dariya marar sauti Anaal ta yi tace haka ne. Dai-dai Gate d'in Aminu Kano commercial ya aje ta yadube ta a tsanake k'arfe nawa za ku tashi"? Shiru tayi tak'i fad'a masa da kyar ya shawo kanta ta amince ta fad'a masa. ''Kina da waya"? Tambayar da yak'ara watsa mata kenan. Kamar tace A,a sai kuma ta tuna k'arya ba halinta bane. "Ta gyad'a kai phone d'inshi yadauko ya mik'a mata saka mun digit d'inki, hannunta har rawa yakeyi tasa mishi numberta ta mik'a mishi phone d'inshi har tayi yunkuri bud'e k'ofa yakira sunanta can k'asan mak'oshi _Anaaal..._ "Yanayin yanda yaja sunan nata ya haddasa mata kasala tajuya tana facing nashi _Na'am_ ta amsa had'e da kafe shi da idanu, shima tsareta ya yi da shu'umin kallo da sauri taje kauda fuskarta shima cikin sauri yadakatar da ita No...Anaal karki juya please akwai abunda nake kallo a fuskarki. "Narke fuska ta yi kamar za ta yi kuka Ya Ansar zan yi latti fa Shima kamar zai yi kuka ba za ki yi ba Anaal kallon 10 seconds zan yi miki. ''Ten seconds fa Ya Ansar"? Gaskiya ya yi yawa. ''Okay five seconds ya yi"? Eh! Tafad'a had'e da gyad'a kai Toh ki juyo mana kamar za ta fashe da kuka tajuya tana kallonshi kasa jure shu'umin kallon da yake mata tayi ta runtse idanuta gam yayinda Ansar yasami damar k'are mata kallo wani irin abu yakeji yana masa yawo tun daga d'an yatsar k'afarsa har zuwa tsakiyar kansa. "Ya lumshe idanu Jin shiru shi ya yi yawa yasa Anaal ta bud'e nata idanu gani nashi idanu a rufe-ruff, yasa tashiga kallonshi electric shock taji yana janta kamar zai karar da jini jikinta. Jikinta na mazari ta 6alle k'ofa tafita jin karar bud'e k'ofa yasa Ansar ya bud'e idanunshi. Ta bud'e seat d'in baya tad'auki schoolbag d'inta a kunyace tadafa k'ofar da ke saiti da shi _Na gode Ya Ansar_ A maimakon ya amsa mata sai kawai ya wanketa da murmushi yaciro k'udi ya mik'a mata _ga wannan ki yi breakfast_ ''Mak'e kafad'arta ta yi Uhm..... Uhm...kabarshi kawai Granny tabani two hundred kuma Abbah yabani na transport sun wadace ni. ''Ya galla mata harara k'udin Granny da Abbah daban wannan nawa ne ko kina nufi banida matsayin da zan miki kyauta ki kar6a''? Batare da tace komai ba tasa hannu biyu ta kar6a had'e da cewa na gode Allah yasaka da alkhairi amma gaskiya sunyi min yawa bara iya kashe su ni kadai ba. "Tabe baki ya yi cikin gatse yace ki kashe rabi ki jefar da rabi. "Anaal ta zaro ido har da su dafe k'irji k'udi ne zan jefar"? ''Eh! Man yafad'a cikin rashin damuwa. Humm....tasauke numfashi ni kan bara iya jefar da k'udi ba. Ansar ya yi murmushi yace toh ki je ki kashe su duka tunda ba za ki iya jefarwa ba. tajuya jiki a mace tanufi Cikin makaranta Ansar ya bita da kallo yana Shafa gejere gemunsa sai da ta6acewa ganisa sannan yaja mota yanufi gida. _10:33am_ Ansar yafito cikin shirin shi na tafiya "office jikinsa sanye da ash colour suit da blue colour long sleeve, kaitsaye part d'in Mum Fatee yanufa ya yi taking breakfast sannan yanufi office. _11:30am_ yashiga conference hall tsawon lokacin suka dauka a meeting d'in agajiye yafito daga hall yanufi office d'inshi Ishaq na biye da shi dauke da files. "Yana shiga office yacire coat yanemi sofa ya zauna ya dube ishaq yace ishaq yunwa nakeji ka je ka yi min order abincin me kyau. ''Okay Boss Ishaq yafad'a had'e da ficewa wannan ya ba Ansar damar afkawa tunanin Anaal baisan dalilin da yasa yarinyar take burgeshi ba yake jin kamar in yana tare da ita kada su rabo ''Komai na Anaal ya yi mishi musanman kyawawan d'abi'unta ina ma ace Zuhura ita ce Anaal ba shakka da na kasance me Sa'a a rayuwa. "Yanda ishaq yafita yabar Ansar cikin tunani haka yadawo ya tarar da shi yana cikin cin abincin idanunshi suka kai duba ga wall clock da ke manne a bango Office d'in nashi. ''Ba shiri ya yi dropping spoon ya mik'e tsaye ya kwashe phone's d'inshi had'e da car key yanufi k'ofar fita jikinsa ko ina rawa yafita a bakin k'ofa yaci karo da ishaq maigida Ansar ina zuwa haka''? "Fitan gaggawa ne yakamani ishaq ba zan jima ba zan dawo ka je office d'ina akwai Documents a locker ka dauka ka kai office d'in Abdallah, kace naje ya had'e su da wanda na bashi jiya yana magana ne had'e da tafiya Ishaq yana biye da shi har parking lot. Saida ya ja mota sannan Ishaq yakoma ciki domin aiwatar da abinda maigida Ansar yasaka shi. "Kaitsaye Aminu Kano commercial Ansar yadosa dai-dai wajen da ya ajiye ta anan ya yi parking yashiga rarraba idanu yana kallon students d'in ke wucewa, ko zai yi nasara ganinta saida yashare 10 minutes har students sun fara raguwa sosai har yafitar da ran ganinta sai gata tafito ita da 'yan d'alibai uwanta su biyu itace cikon ta 3 sun jero ita ce a tsakiya sai faman fira suke murmushi kwance akan fuskarta. "Ansar yasauke ajiyar zuciya yayinda numfashinsa yadinga hal6awa da sauri bai ankara ba har suka wuce shi a rikice yasauke glass d'in mota _ke Anaal_ ta tsaya cak kamar me amfani da remote control ko a mafalki za ta sheda wannan muryar, ta dubi k'awayenta Ramlah da zeenat cikin sanyi murya tace yaya na ya zo daukana sai anjimanku. ''Zeenat ta yi karaf ta shar6e zance dama kina da yaya shine ba ki ta6a gayamana ba"? Kafin Anaal tabata amsa Ramlah tarigata ta hanyar cewa zeenat kenan kamar bakisan halin Anaal na zurfin ciki ba ae ba za ta gayamana ba kada mu yi mata snatched d'in yayan nata. Oops......Anaal tadafe goshi abin ya zame mata biyu ga Ya Ansar yana dankara mata horn ga wad'annan fitinanu k'awaye nata biyu sun saka ta a gaba. "Tarausayar da kai kunga Ya yana min horn ku jira gobe in muka had'u ku tuhume ni yanzu dai ku barni na tafi kada ya yi min fad'a. Zeenat ta tabe baki kyaji da shi domin ni ban yarda wannan guy kuna da blood relationship da shi ba. ke da ki ka ce yayanki ya6ata tun kina jinjira shine don kin raina mana hankali za ki ce wannan yayanki ne. Ramlah ta kar6e zance ta hanyar cewa watakil boyfriend d'inki ne bakyason mu sani. Zaro ido Anaal tayi Ya Ansar ne boyfriend d'ina kanki d'aya kuwa Ramlah"? ''Rass nake Ramlah tafad'a tana wani rangwadar da kai cike da takaici Anaal ta galla mata harara daga bisani ta ja tsaki mtcsww"! Batare da tayi sallama da k'awaye nata ba tanufi motar Ansar ta bud'e seat d'in baya tasaka schoolbag d'inta kamar yanda tayi da safe. ''Ranta a 6ace ta balle k'ofa tashiga Ansar yana waya yajuyo ya dube ta yasake mata shu'umin murmushinsa mai tafiya da imani da zuciyar 'ya mace. Tsigar jikinta yatashi Yarr...ta kauda fuska Ansar ya ja mota suka tafi hannunshi guda yana dafe da steering d'ayan kuma dafe da waya yana kamalla waya yak'ara juyowa yana kallonta. daure fuska tayi dan Allah Ya Ansar ka kalli gabanka kada garin wannan kallon naka ka 6arar da mu. ''Dariya ya yi cike da nishad'i yace Anaal sarkin tsoro wai meke damunki ne naga kin wani daure fuska kina kunbure-kunbure''? Cuno baki tayi kamar za ta yi kuka tace ba su Ramlah bane suka ce wai....wai...kai...uhm... Uhm... Manta kawai. 6ata fuska ya yi miye haka za ki fara gayamun magana kuma ki ce na manta''? Ya Ansar maganar batada ma'ana balle tushe miye amfani jinta"? ''A gareki zai yu batada amfani amma ni a wurina tafi komai amfani gayamin me su Ramlah suka ce''? "Ni fa ba zan fad'a ba gara ka hak'ura kawai tak'arasa magana had'e da murgud'a baki. Shikenan Anaal tunda ba za ki fad'a ba amma kisani hak'ik'a kin jefa zuciyata cikin kwankwato, har nake tunani ko ba ki yarda da ni bane kina mini wani kallo na daban wanda Allah kadai yasan abinda ya ke nufi. "Cikin rauni murya Anaal tace kada ka fassara ni bai-bai ya Ansar, har ga Allah na yarda da kai na tabbata ba za ka iya cutar da ni ba. ''In har kinsan da haka meyasa ki kasa gayamin abunda k'awayenki suka fad'a Anaal ko kina tsoro abunda suka fad'a ya zama gaskiya"? Wani irin mashi yadak'i zuciyar Anaal ya haddasa mata matsanancin fad'uwar gaba a rikice ta yada ganinta akan kyakyawar fuskarsa, muryarta na rawa tace Ya Ansar kana nufi kaji abunda Ramlah tafad'a"? "K'ayatatcen murmushi ya yi Anaal kenan Sanin kanki ne ni ba kurma bane ta ya ki ke kwankwanto akan naji abunda Ramlah tafad'a"? Ba kwakwanto nake ba Ya Ansar ina mamaki ne ta yanda kunnenka ya ji alhali kana nesa da mu ''Kidaina mamaki domin wannan ba abin mamaki bane. Humm....Anaal tafad'a had'e da rafka tagumi Ansar ya kalle ta ganin yanda yanayinta ya nuna yasa yafara lullu6e ta, da dadd'ad'a kalamansa ta hanyar cewa Anaal karki sakawa kanki damuwa domin kowane dan-adam da kaddarar da Allah, ya yi nufi akansa kuma bai isa ya kauce mata ba kinganni nan nayi imani da kaddara me kyau da marar kyau domin shine cikar imanina, karkace za ki tsawaitawa zuciyarki domin ita zuciya ba kowane abu take juriyar dauka ba saidai ina gargad'inki kada ki kasance me tauyewa zuciyarki hakkin ta. "Gaba d'aya Anaal tashiga sark'ak'iya tarasa gane ina wad'annan kalaman na Ya Ansar suka dosa ba, rashin sani ma'anarsu yasa ta kauda fuskarta da barin kallonshi. ''Shima bai k'ara cewa da ita uffan ba sai ma k'ara volume d'in tape da ya tun kafin yak'arasa gida Anaal tace ka tsaya zan sauka anan. ''Batare da yace komai ba ya taka birki har ta rik'e k'ofa za ta bud'e ya kira sunanta{in a romantic voice} _Anaaal_ a kasalance ta amsa da _na'am_ kin wani bani baya Ki juyo ki kalle ni mana. Shiru tayi kamar ba za ta juyo ba daga bisani tajuyo suna had'a ido yasake mata shegen murmushi nan nashi. "Yace ubangiji shi yake tsarawa 'yan Adam rayuwa komai yasame ki ki kasance me tawakali da godiya ga Allah{S.W.T} wannan shawara ce nake ba ki a matsayina na amininki kuma yayanki. _"na gode_ tafad'a asanyaye ta bud'e k'ofa tafita tadauko schoolbag d'inta daga seat d'in baya, batare da tak'ara tanka masa ba tajuya tanufi gida. ''Yayinda Ansar ya bita da kallo rass"! rass"! Gabanshi ya yanke yafad'i ba ko tantanma Anaal ita ce yarinyar nan Mae niqan yanayin tafiyarsu d'aya yasauke ajiyar zuciya had'e da shafar sajenshi saida ya tabbata Anaal ta isa gida sannan yaja mota yanufi gidan.... Jeeddah Aliyu Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen2⃣) WHATSAPP NO: +2347039625239[4/24, 6:06 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* _this page is for you Maryam Muhammad Niger republic thanks for the love &care you shown to me I can't express how much I love you but I wants you to know that Jeeddah loves you More_ #Teams#SNS. *12* Horn ya yi Abbah ya bud'e masa gate Bayan ya yi parking yanufi bakin gate wurin Abbah. Yana k'arasawa Abbah ya bashi hannu suka yi musabaha Ansar yadauki buta Abbah ta ruwa yanufi bathroom d'in Abbah da ke gateman room Yakama ruwa, ya yi alwala tare da Abbah suka nufi masallacin. ''Bayan sun dawo daga masallacin Ansar ya yi sallama da Abbah ya ja motarsa yakoma office _5 dot_ yabaro office yanufi gida direct part d'inshi yafara yada zango ya yi wanka ya shirya cikin blue Jean's da yellow t-shirt Mae gajeran hannu ya feshe jikinsa da Elite gentleman Parfume ya had'a da favorite Parfume d'inshi mesmerized Cologne wani irin k'amshi na musanman yake fita daga jikinsa. Car key had'e da phones d'inshi yadauka yanufi part d'in Mum Fatee. "A parlour iske Basmah tasha kwalliya cikin Arabian gown ya ji adon Stone's sai fama kashe selfie take, tsaye ya yi yana kallonta ya girgiza kai yanemi kujera ya zauna har ya kai zaune Basmah batasan ya shigo ba sha'anin gabanta kawai take. "Tsawa Ansar yadaka mata ke"! Mahaukaciya. "A tsorace Basmah tajuya tana kallonshi OMG"! You scared me Ya Ansar tafad'a a shagwa6e. Harara ya galla mata Wai yaushe za ki yi hankali Basmah"? "Ni fa da hankalina Ya Ansar. Ina ki ga hankali Basmah ba hali ki yi wanka sai kin wahalarda camera wayanki, ke ba wani kyau ba sai dan banza d'aukar pic's dama ku munana kun fi kowa son pic's. "Basmah ta langwa6e kai tafara bubbuga kafa a rugs carpet "Allah Ya Ansar ina da kyau friends d'ina har cewa suke ina kama da kai. ''Zaro ido ya yi kamar ya ga abin tsoro wa ki ke kama da shi"? "Kai tafad'a had'e da nuna shi da yatsa. "You're completely mad Basmah kalle kanki lukuta da ke za ki wani had'a kanki da ni God forbid. "Basmah kamar za ta yi kuka tace ni wallahi slimming zan yi nadawo kamar wannan ta rik'e baki tana tunani wa ma za ta ce kamar daga sama tace _Anaal_ saboda ina son body structures nata. Ansar ya tsincin kanshi da fad'uwar gaba sakamako sunan Anaal da Basmah ta kira. ''Basmah tana dariya tak'araso kusa da shi Ya Ansar bari na kashe mana selfie guda da kai, na daura akan dp na kafin yabata amsa har ta kashe musu guda biyu tureta ya yi ke dallah banaso shirme ki je ki had'a min abincin yunwa nakeji. "Basmah ta mik'a masa phone d'inta fuskarta d'auke da dariya tace Ya Ansar duba ka gani yanda mu ka yi kyau kace wai ba ma kama hancin kawai za ka gwada min sai girman jiki da na fi ka Allah ba don wannan ba da kamanu mu sak d'aya. ''Fizge phone d'in ya yi naji sarkin sharhi ki je ki yi abunda nasaka ki. ''Tajuya tana mai cigaba da cewa yau Mum da kanta tahad'a maka favorite d'inka. "Da sauri Ansar yace com slow"? ''Eh Basmah tafad'a had'e da shigewa corridor da zai sadata da kitchen. Cikin d'aga murya Ansar yace shi kadai za ki zuba mun karki saka shinkafa. "Toh ita ma ta amsa cikin d'aga murya. "Da sauri Ansar yake scrolling pic's d'in mtcsww"! Ya ja tsaki had'e da ajiye wayan a hannun kujera, yadauki nashi ya yi dialling digit d'in Anaal wayarta a rufe mtcsww"! Yak'ara zuba tsaki. "Basmah tashigo d'auke da plate tajanyo k'aramin center table ta daura plate d'in akai tak'ara komawa kitchen ta dauko mishi drinks da ruwa. ''Yana cin had'in salad d'in yana lumshe ido saida ya cinye tass ya ture plate ruwa kawai ya sha yaciro chewing gum mai k'amshin strawberry daga pocket d'inshi ya 6are ya jefa baki. "Basmah ta mik'a mishi hannu nima zan cin Ya Ansar. Me za ki ci mayya"? Tana dariya ta furta chewing gum. Ciro d'aya ya yi ya jefa mata ta cafke. Yakoma jikin kujera yalafe idanunshi a lumshe ya furta Basmah me ki ka sani game da Anaal"? Da mugun mamaki baki bud'e Basmah take kallonshi takasa furta komai sai kallonshi take yi. Shi kuma sai tauna chewing gum d'inshi yake yi hankali kwance. "Ajiye zuciya Basmah ta yi ta mik'e daga mazauninta ta koma kusa da shi ta zauna bisa hannun kujerar da ya ke zaune. "Ya Ansar wannan tambayar naka ya sakani cikin rud'ani akwai wata alaqa ne tsakaninka da Anaal"? Banaso zuciyata tafara kintsa mini abinda ba shi bane ma'ana zargi. "Yad'ago ya dube ta a d'age ki fara amsa mini tambaya na firstly in yaso daga baya kya iya naki tambaya. "Langwa6e kai Basmah ta yi _Anaal yarinya ce Mae hankali da natsuwa tana da tsananin hak'uri, sai dai miskila ce tabugawa a jarida ba abinda yafi burgeni da Anaal irin iliminta ba irin bin Anaal da banyi ba akan mu qula k'awance amma tak'i sai dinga fuskewa kamar dae banyi mata ba duk da wannan har yanzu ina k'aunarta_ tak'arasa magana kamar za ta yi kuka. Tun lokacin da Basmah tafara magana Ansar yake zabga murmushi, hannun Basmah yarik'o don't worry 'yar lukuta zan had'a ki k'awance da Anaal kinsan duk gidanan tamu tafi zu wa d'aya duk abinda nakeso kema kinasonshi koh"? "Basmah ta yi dariya tak'ara dank'e hannunshi can kasan makoshi ta furta Ya Ansar do you love her''? Zaro ido ya yi who"? Anaal mana tafad'a tana kallon kwayar idonshi. Tabe baki ya yi had'e da girgiza kai capital No we are just a friends. "Sauke ajiyar zuciya Basmah ta yi thank God da har zuciyana yafara saqa mini, irin k'alubali da za ka fuskanta daga wajen Dad da Mum kasan ba abinda suka tsana irin Wanda bashi da shi. "Ansar ya mik'e tsaye karki damu k'anwata insha'Allah ba abinda zai Shiga tsakanina da Anaal ko kin manta da irin d'inbin son da nake wa Zuhura''? Ban manta ba Ya Ansar amma kuma zuciya tana canza sheqa daga nan ta koma nan. "Ban da tawa zuciya domin Zuhura takeso ita kadai na d'auki Anaal ne tamkar ke. Murmushi Basmah ta yi tace ni dae yanzu yaushe za ka had'a mu k'awance''? ''Tabe baki ya yi ke fa kin fiye gaggawa. Har Basmah tabude baki za ta yi magana ya katse ta sai na dawo Basmah karki 6ata min lokacin da wannan surutun naki yasa kai yafita Basmah tabishi da kallonshi. "Yana fita bai zarce a ko ina ba sai inda yasa6a jiran wucewar Mae niqan, so yake ya gasganta zarginsa shin Anaal ce ko ba ita ce ba. ''Cikin Sa'a bai fi _5 minutes_ da zama ba sai gata ta ta tsallako titi yau ita kadai ce, da sauri ya 6alle k'ofa yafito Anaal naganinshi tadauke kai kamar bata ganeshi ba ta ra6a shi za ta wuce cikin sark'ewar lafazi Ansar ya Kira sunanta Anaal''! "Ta tsaya cak da saurinsa ya k'arasa kusa da Ita Anaal shine za ki wuce ni ba ko gaisuwa ko kina tsanmani don kin rufe fuskarki da niqan ba zan gane ki ba''? "Dariya ta yi Mae sautin ka yi hak'uri Ya Ansar ban yi zaton za ka ganeni ba. Naga cewa nasha wuce ka amma ba ka ta6a nuna kasan ni ba. Shima dariya ya yi ba gashi yau na nuna nasanki ba. ''Tafiya tacigaba da yi zan wuce gida naji anfara kiran sallah magarib. "Okay....Ni ma da nayi sallah zan shigo ki ce da Granny ta aje min Mae dad'i. Ba wani Mae dad'i da za ta aje ma kadai sai kashigo. _8:30pm_ ''Ansar yana zaune a parlourn Granny suna fira Anaal ta yi sallama tashigo sanye da hijab har k'asa pink in colour. Tanemi kusa da Granny ta zauna ta k'asan idon ta kalli Ansar batasan cewa shima tun shigowarta yake aikin kallonta ba. "D'ago idanunta tayi gaba d'aya ta dube shi yau za mu yi karatu ne''? A maimakon ya6ata amsa sai ya kafeta da idanu d'auke fuskarta ta yi ta mayarda ganinta wajen Granny tace Granny na dauko maganinki na Shafa miki tun yanzu? "Girgiza kai Granny ta yi kije ku yi karatunku anjima ki Shafa min Anaal ta mik'e tashiga bedroom tadauka jakkar littafai. Tana cikin karatu sai ga Zuhura tafad'o parlourn kamar wance aka jefo. Da mugun mamaki take kallonsu Ya Ansar shine za ko gidanan ko kanemi ni"? Narasa me ke damunka a 'yan kwanaki nan ka ke share ni. Shhh......Ansar ya aza yatsanshi a lips alamar tayi shiru amma ita gimbiyar ko a jikinta sai ma k'ara kaimi ta yi wane irin shhh..."? Toh wallahi ba zan yi shiru ba har sai naji, dalilinka na shirya mini wannan wulaqancin. _"Sadakallahu-azeem_ Anaal ta dasa aya kada ta kwasawa kanta zunubi, saboda in ana karatun Qur'anic ba'a surutu. Ta mik'e tsanm tanufi bedroom Zuhura ta bi ta da kallon tuhuma. K'atuwar harara Ansar ya gallawa Zuhura wannan wane irin dabancin ne? Ya ana karanta Qur'ani za ki zo ki cika mutane da surutunki na banza da wofi? ''Idanu Zuhura ta zaro Ya Ansar ni ka ke kira da suna dabba? don kawai na nuna damuwata akanka? ''Eh! Na fad'a ke dabbace domin abunda ki ka aikata dabba ne kadai zai aikata shi. Shikenan Ya Ansar naji ni dabbace amma inason kasani komai wuya komai runtse kana nan tare da dabba, ba uban da isa yaraba ka da ita mutum zai gaji da tsohun munafuncinsa da zugaka yabari domin ni da kai mutu karaba ne takalmin kaza. "Rai 6ace Ansar ya mik'e har yaware hannu zai wanka mata mari, Granny ta taka masa birki kai Ansar kul karka daketa duk wad'annan zafafan maganganu da take fad'a ba da kowa take ba illah ni. Kabarta kawai abinda ta girma tayi wayo tarrarda da uwarta saude tana min kenan. Amma Granny haka zan cigaba da zuba mata ido tana gasa min magana iya son ranta haka za mu yi aure bata gani girma na? Hak'uri za ka yi Ansaru domin kace ka ji ka gani kana sonta, rashin mutumcin da bankad'a ba ka ma ga komai ba sai ranarda igiyar aure ta gita a tsakaninku. Mtcsww"! Zuhura ta ja dogon tsaki kamar za ta gutsere halshenta, tajuya fuuu.....tana wani jujjuya mazauna ita a dole ga shak'iyiya. Ansar yana huci yakoma ya zauna yayinda Granny tacigaba da rarrashinsa da kalamai masu kwantarda hankali sai around _10:30pm_ ya yi sallama da Granny yawuce gida har yatafi bai k'ara gani Anaal ba. _washe Gari_ Ba zato ba tsanmani Anaal taci kora da Ansar yana zaman jiranta zai kaita school. Jiki ba lakka ta bud'e k'ofar mota tashiga kallon d'aya ta yi mishi taga damuwa shinfid'e akan fuskarsa. Cikin sanyayiyar muryarta tace _ina kwana Ya Ansar_ Lafiya Anaal yau kin kusa ki yi latti. Wallahi kuwa yau bacci nayi sosai da kyar Granny ta tashe ni. Ansar ya kad'a kai kin more 'yan mata ni jiya ko runtsewa ban yi ba yanda naga rana haka naga dare..... Jeeddah Aliyu [4/25, 6:22 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* 13 Cikin yanayin na tausayi Anaal tajuyo tana kallonshi Ya Ansar bai kamata kadauki abunda yaya Zuhura tayi da zafi ba. Har ya yi sanadin hanaka bacci nata halaya ne haka dole sai kana hak'uri had'e da lurarda ita. ''Haba Anaal zuhura k'aramar yarinya ce da zan dinga tsara mata yanda za ta gudanarda rayuwarta? Ba k'aramar yarinya bace amma kafita hankali da tunani matuk'ar tana sonka toh dole ta bi abinda ka ke so. Anaal kenan lallai har yanzu ba ki San wacece Zuhura ba. In kina neman mace 'yar raini wayo marar tarbiyya, fitsarariya ki ka kawo ga Zuhura sai ki Shafa fatiha. Kina ji fa Granny ta kira da munafuka yak'arasa magana cike da takaici. ''Naji Ya Ansar anan Zuhura ta yi kuskure amma kamar yanda ka ji Granny tace, daga wajen mahaifiyarta ta koya domin ita ma ba ragawa Granny ta ke yi ba. ''Mtcsww! Ansar ya ja tsaki Allah ya kyauta dukansu ba laifinsu bane Baba sa'eed ne mai laifi shi da ya zuba musu ido suna wulaqanta mishi mahaifiya. Nima abinda nake fad'a kenan a zuciyata. A shekaru Granny bai kamata ace tana fuskantar irin wannan cin zarafi ba. Bari kawai Anaal Granny na zaman hak'uri dad'inta bata bari ta kwana balle ta tashi da yanzu, sun mayarda ita juji. ''Dariya Anaal ta yi ae Granny batada sauki muddin tsautsayi yasa kata6o ta za ka ji ba dad'i. Ni dai shawarar da zan ba ka kacigaba da hak'uri da Zuhura dama haka auren zumuncin ya gada. Ni shiyasa bai ta6a bani sha'awa ba, Saboda in zama bai yi dad'i ba nan take yake 6ata zumuncin. 6ata fuska Ansar ya yi ba wani hak'uri da zan yi zan nemawa kaina mafita ae ba aurenta nakeyi ba ballatana nai hak'uri infact ba ita kadai bace 'ya mace da zan dinga shanye wulaqancinta. Zaro ido Anaal ta yi kai Ya Ansar banaso cika baki duk son da ka ke yi ma Zuhura za ka iya barita akan d'an k'ank'ani abu? Harara ya galla mata zan tabbatar miki ba cika baki nakeyi ba, muddin Zuhura bata sauya munana d'abi'unta ba ni kuma ba abinda zai hanani sauyawa. Yana k'arasa magana dai-dai yakawo gate d'in makaratansu ya yi parking. Tajuya fuskarta d'auke da k'ayatatcen murmushi _thanks_ tafad'a had'e da langwabe kai. ''Ya mayar mata da Martani murmushinta _you're welcome Dear_ Tadauki Schoolbag d'inta yaciro k'udi ya mik'a mata mak'e hannu ta yi, ya murtuk'e fuska ki kar6a mana. Ko na jiya ya Ansar da kabani suna cikin schoolbag ban kashe ko kwadala a ciki ba. Wannan kuma ke ya Shafa ki kar6a tun kafin raina ya 6aci. Girgiza kai tashiga yi kamar mai shirin yi kuka Ya Ansar Allah ba abinda zan y.....katse ta ya yi ta hanyar d'aga mata hannu ya balle k'ofa yafito ya ja schoolbag d'inta da k'arfi dole tasakarsa masa ya zuge zip yasaka k'udin a cikin ya mik'a mata tak'i kar6a ya ajiye a k'asa yashiga mota yaja yabarta tsaye tana mamakin wannan k'arfin halin nashi. Lokacin tashinsu school ya yi tana fitowa gate taci karo da shi bata yi mamaki ganin nashi ba. Saboda taji a jikinta zai zo. ''Tun daga lokacin Ansar ya mayarda kanshi driven Anaal shi yake dropping nata school ya kuma yi picking nata shaquwa mai ban mamaki tashiga tsakaninsu. "Ansar bai zai iya yini d'aya cur batare da yaga Anaal ba. kamar yanda ita ma in bataganshi ba batada kwanciyar hankali har sai ta kira shi a waya taji muryarshi sannan take samun natsuwa. dukansu a tunaninsu shaquwa da amintaka ce take hadasa musu hakan. _8:05pm_ Ansar yadano hancin motarshi a farfajiyar gidan Baba sa'eed yanufi parking lot ya yi parking. Yanayi na wanda ya kwaso gajiya yafito daga mota yana rataye da briefcase da tarin file's a hannunshi saida yanufi main gate ya gaida Abbah sannan yanufi part d'in Granny. Da sallama yashiga parlourn Anaal kadai ya tarar zaune tana Assignment Granny na bedroom tad'ago can k'asan mak'oshi ta amsa masa sallama, suna had'a Ido ta balla masa harara had'e da murgud'a baki ta maida dubanta ga Assignment d'in da takeyi. "Sanyaye Murmushi Ansar ya yi yanufi wajenta hannayenshi na zube cikin aljihu wandonshi. Ya yi tsaye a gabanta yana kallonta k'asa-k'asa yana shu'umin murmushi nan nashi. ''K'amshin turare shi ya baibaye k'ofufin hancinta kasala had'e da wani irin sanyi Mae ratsa k'asusuwan jiki yasauka mata. _Anaaal_ Yakira sunanta kamar Mae ciwon hak'ora. _Na'am_ Ta amsa had'e da d'agowa suka sake had'a idanu ta cuno baki tana gunguni. Wai laifin me nayi da Anaal take ta murgud'a min baki? Cike da zallan mamaki take kallonshi au baka masan laifin da kayi ba? "Saida ya zauna a kujera da ke facing nata yace of course yes! Kema kinsan da nasan laifin da nayi da tuni na fara ba da hak'uri. ''Humm! Jiya me hanaka zuwa gidanan? Ko kasan na kira all digit naka switch off? Murmushi ya subuce masa yashiga shafar laulausan sumar kanshi yana lumsashe idanu. ''Lallai Anaal kinfara damuwa da ni ada na dauka ni kadai ne nasan mahimmancin ki. Tabe baki tayi cikin rashin damuwa da furucin nashi tace karka damu wannan, yana d'aya daga cikin halayena duk dalibin da nake koyarwa in banganshi ba nakan nuna kulawa ta akai. ''Ta6e baki ya yi baisan lokacin da ya ja siririn tsaki ba. Daga haka ba wanda yak'ara tankawa d'an uwansa ita tacigaba da Assignment d'inta yayinda shi kuma yacigaba da aikin kallonta. Phone d'inshi ya yi ringing a wulaqance yake kallon wayan mtcsww"! Ya ja tsaki har kiran ya tsinke bai yi picking ba. Batare da mai kiran nashi yagaji ba yak'ara calling nashi back still ignoring call d'in ya yi. ''Anaal tad'ago ta dubeshi wulaqancin ba kyau Ya Ansar ka daure ka amsa kiran maybe, alkhairi ne yake binka kana gudunsa tak'arasa magana tana dariya. Ya tabe baki wannan kiran banajin akwai alkhairi a cikinsa tunda kin ce nayi picking, zan yi saboda ke. Kinsan ni d'alibi ne nagari bana tsallake umarnin malama tah. O'o....ka ji da shi. Tafad'a had'e da cigaba da rubutunta. Me zan ji da shi 'yan mata"? D'agowa tayi ta jefa Biro a baki tana kallonshi fuskarta d'auke da murmushi, lallai nayi k'oshin d'alibi ina matsayin malamarka ka kirani 'yan mata. To miye a ciki don na kira ki da 'yan mata ae ke ba 'yan maza bace? Ashe kuwa in haka ne magana na yana kan hanya. Please ka d'auki wayanka kada Mae kira yaji zafi ignoring nashi da kayi. Kafin ya yi magana kiran ya sake shigowa afusace ya yi picking _Zuhura_ yafad'a da kaukausar murya ya yi shiru yana sauraron abinda take fad'a mtcsww"! Ya zuba tsaki don kinga mota na a picking lot saime kina bi na bashi ne"? Oh" nayi tsanmani kina bina bashi ne da za ki dameni da kira. Mtcsww! Look Zuhura karki nemi ki takurawa rayuwata ki barni na huta mana. Ya yi shiru yana sauraronta hmmm! wannan kuka da ki ke yi ko a jikina domin nasan na munafuncin ne. Sai kin kwance min zariyan wando a kasuwa kidawo gida ki daura mun am tired I'm completely tired of your stupidity so let's me be.... Anaal da takasa kunne tana sauraron Ansar batasan lokacin da kyalkyace da dariya ba. Kasa cigaba da magana ya yi yana kallonta da mugun mamaki, dariya take yi har da su dafe ciki. Gani haka yasa yace da Zuhura shikenan naji. Na hak'ura mana yafad'a yana mushirikin murmushi. No....ki yi zamanki karatu Anaal za ta fad'a min karki damu in nagama zan nemi ki. I love you more. Ya yi hanging up ya maida ganinshi wajen Anaal wance ke kwasan dariya abinta ya talafe kumatu yana kallonta ganin yanda ya shagala da kallonta, yasa ta katse dariya da takeyi ta rufe bakinta da tafin hannu. ''Gyaran murya ya yi me ki ke yi wa dariya Anaal? Shiru tayi kamar bataji tambaya da ya yi mata ba. Yakira sunanta cikin laushin murya kamar Mae rad'a. _Anaal_ Ta amsa da _Na'am_ Nace me ki ke yi ma dariya? A maimakon ta bashi amsa sai tasa dariya cikin muryar dariya, tace maganarka ce tabani dariya iya jina banta6a jin ance a kwance zariyan wando saidai ace zani. Humm......toh ae ni bana daura zani wando nake sakawa kinga kenan ba zanyi zaurance da zani ba. mik'ewa tsaye ta yi ta dube shi kallon ido cikin ido tace duk da haka zani ake cewa. Murmushi yasake mata naji malama tah next time zance zanin Anaal cos na gayamiki bana daura zani. Turo baki tayi tajuya har tayi tako d'aya zuwa biyu ya dakatarda ita ta hanyar cewa wai ke ina za ki je naga sai wani rawan k'afa ki ke yi? Jakka zan dauko mu yi karatu tafad'a had'e da kallonshi. Ki dawo ki zauna yau ba zan yi karatu ba. Saboda me? Saboda yau alhamis a tsarin kowane makaranta islamiyya ana hutu, nima yau hutawa zan. ''Zaro ido ta yi yanzu a waya naji kana gayawa yaya Zuhura karatu za ka yi, shine za ka sauya ra'ayi da wuri haka? "A waya nace zan yi karatu a zahiri kuma nace ba zan yi ba, gara kidawo ki zauna ki cigaba da assignment d'inki zai fi miki sauki da wannan tsayuwar da ki ke yi. ''Tana gunguni tadawo ta zauna a mazauninta Yayinda Ansar yafito da laptop d'inshi yasoma shigar da bayanai da ke cikin file's. Annal tad'ago tana kallon yanda yake operating laptop d'in a yangance ta, ta6e baki had'e da yatsine fuska. Kamar ance Ansar yad'ago yaga tana kallonshi tana yatsina ya akayi ne 'yan mata naga kina mun kallon burgewa? yak'arasa magana yana kashe ido d'aya. Murmushi tayi wanda yak'ara k'awata ainihin kyaun fuskarta, kallon tausayawa nake maka ba na burgewa ba kalli yanda ka ke operating laptop kamar wanda bashida lakka kai komai sai ka sa yanga ko ni sa nake Mace nafika kama jiki idan, haka ka ke yi a office duk ranarda Dad yakamaka zai yi suspended naka ko ya yi firing naka gaba d'aya. "Tun lokacin tafara magana Ansar yake kallonta yana zuba murmushi. Shi dai komai Anaal take yi burgeshi yake yi musanman in tana magana jin yake kamar yana yawo a gajimare saboda tsananin dad'i da gard'i da muryarta take masa. ''Mik'ewa ya yi yanufi wajenta yadaura mata laptop a cinya ya tattaro tarin file's d'in ya aza a hannun kujerar da take kai. Jeeddah Aliyu*SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* 14 Da mugun mamaki Tad'ago tana kallonshi ya d'aga mata gira kince ina operating laptop a yangace, shine na kawo miki ke da bakya yanga ki yi min aikin nasan za ki iya. Muryarta na rawa tace ni....ni... Ke...ke...me? Ya katseta da hanzari ba abunda za ki fad'a sai kinyi shi ko na murd'e miki kunne. "Turo miki ta yi ni fa malamarka ce kuma ba kyau yi wa malami rashin d'a'a. Ina ruwana da zamanki malamata in ke malamata ce ni kuma yayanki ne. Ina da matsayin da zan saka ki aiki ki yi koda ranki bayaso. Ni fa ban iya ba zan maka jagwalgwale ki yi d'in ae ni nace inaso ba yanda ta iya dole ta ture takardan assignment nata a gefe, ta d'auki files tasoma karanta abinda ke ciki wani shegen murmushi ta yi tasoma shigar da bayanai duk abinda take yi Ansar yana tsaye gabanta, hannayenshi zube cikin aljihun yana kallonta cikin abinda bai wuce 1-2 hour's ba ta kammala aikin. Ta zungura masa laptop kar6i kayanka sarkin kallo na gama. Bai kar6a ba sai ma k'aimi yak'ara wajen kallonta ta ajiye laptop da files akan kujera za ta juya tashiga bedroom yasha gabanta ina za ki je? Baccin nakeji tafad'a tana kallonshi, yasauke gwaron numfashi ya langwa6e kai can k'asan mak'oshi ya furta Anaal banaso ki tafi. Murmushi ya subuce mata ta d'an zaro ido wai saboda me? Ni ma bansaniba kawai banaso ki tafi. Ya za ka yi da ni saboda bacci nakeji har wani yaji-yaji nakeji a idona? Ya zan yi Anaal dole na barki ki kwanta sai da safe. Toh sai da safe ka gaida su Basmah. Za su ji. Daga haka ta ra6a gefenshi ta wuce har ta tura k'ofar d'akin Granny, tajuya yana tsaye inda tabarshi idanunshi na kafe akanta. Tasake mishi sanyayen murmushi shi ma ya mayar mata da Martani tashige d'akin ya jima tsaye yana nazari daga bisani yadauki laptop da files d'inshi yafice. Tun kafin yak'arasa parking lot ya hangon Zuhura zaune akan farar kujerar roba, tana gyagyad'i da alama ta kashe lokacin tana zaman jiranshi tausayinta ya kamashi duk lokacin da suka sami sa6ani da Zuhura sai ta rasa kwaciyar hankali har sai sun daidaita. Files d'in hannunshi ya buga mata ta mik'e tsaye a firgice sai muzurai ta ke yi Ansar ya kyalkyale da dariya. A shagwa6e tafara bubbuga k'afa a k'asa Ya Ansar kai koh? Ya katse dariya da yakeyi Zuhura zaman me ki ke yi anan? Cikin rashin damuwa tace ina gadin motarka ne. Ya yi murmushi kamar bai fahimcin inda ta dosa ba. Ya Ansar Kadàina sona koh? Girgiza kai ya yi har abada ba zan daina sonki ba, halayenki ne kawai nafara gajiya da su da za ki canza kidawo Zuhurarki ta asali ni kuma da zan nuna miki nafi kowa sonki da k'aunarki. Lumshe idanu Zuhura ta yi Sabon sonshi na k'ara ratsa jinin jikinta. Nayi maka alqawali Ya Ansar duk abinda ba ka so zan daina burina banaso ka daina sona. Ya tabe baki in har bakyaso nadaina sonki ki gyara halinki. Zan gyara Ya Ansar Allah zan gyara. It's your own good domin duk son da nake miki zan iya barin k.....please Ya Ansar kar ka k'arasa In har kai za ka iya barina ni ba zan iya barinka ba. kariga ka zama jinin jikina farin cikina idan ka barni rayuwana za ta tagaryara zan shiga k'uncin mafi muni a rayuwa, ka tausaya min Ya Ansar karka barni tak'arasa magana had'e da zubewa gabanshi ta yi kneel tana kuka kamar ranta zai fita. Sosai tausayinta ya kama shi baisan lokacin da yad'ago ta ba, saida ta mik'e tsaye yashiga yarfe hannaye kamar wanda yata6a electric shock. Zuhura ta dube shi da kod'ad'in idanunta za ta yi magana yad'aga mata hannu Zuhura ki shiga gida gobe za mu yi magana kinga yanzu har _11:00pm_ ta yi. Kamar ba za tafi ba sai kuma tajuya jiki a sa6ule kamar kazar da kwai yafashewa a ciki. Yashiga mota yanufi gida agajiye yafad'a bathroom yasakewa kanshi shower, bayan Yafito daga wanka yasaka pajamas ya haye gado duk yanda yaso yai bacci yakasa sai faman juyi yake hannu ya mik'a akan bedside yadauki phone d'inshi yashiga dialling number Anaal cikin Sa'a wayan yana bud'e bata rufe ba. Anaal wance ta yi d'ai-d'ai akan gadon Granny tana sharar baccinta hankali kwance vibration d'in wayarta da ke k'asan pillow yashiga zayar a dodon kunnenta. A firgice ta falka ta tura hannun ta dauko wayan da kyar ta iya ware idanunta saboda masifafen baccin da takeji, ta kai duba akan screen d'in 'yar Nokian ta _Ya Ansar_ ta furta a baiyane cikin yanayi na kid'ima lafiya Ya Ansar zai kirani a tsakiyar dare? Tasauke ajiyar zuciya mae cike da tsoro ta lek'e kasan floor inda Granny take kwance akan k'atuwar mattress d'inta baccinta take haik'an har da su minshari, hannunta na rawa ta danna koren madanni takara a kunne in shock ta furta _Hello Ya Ansarrr_ Hello da ta furta had'e da yanda ta ja sunanshi ya haifar masa da kasala ya lumsashe idanu. _Ya Ansar kana jina kuwa?_ Takatse masa shauk'in da ya afka. _inajinki Anaal na katse miki bacci koh?_ Wannan ba damuwa bane damuwa na Allah yasa lafiya ka kirani a wannan lokacin? _lafiya Anaal amma ba lau ba_ Subhanalilah''! Me ke faruwa? _Na yi iya k'ok'arina Anaal domin nasami bacci nakasa sai wani k'uncin da zafi da nakeji zuciyata, tana mun shine na kira ki ko zami relief_ Mamaki ne yarufe Anaal takasa koda kwakwaran motsi ta zama speechless ko za ta iya magana a wannan yanayi me za tace da shi she's totally confused with shock. _Anaal ki yi magana mana_ Ajiyar zuciya ta yi me zance Ya Ansar? Kina nufi bakida abin cewa? Banida ya Ansar amma kai in kanada abin cewa ina sauraronka. _Anaal_ Na'am Kinsame? A'a sai kafad'a Kar nafad'a ki yi min dariya. Murmushi tayi had'e da cewa ba zan ba. Ya gyara kwanciya kamar Mae rad'a yafurta muryarki yana mun dad'i. Dariya tayi marar sauti tak'ara Jan blanket ta k'ududune yanda za ta ji ta very comfortable, Ya Ansar kenan. miye abin dad'i a wannan muryar nawa Mae kama da antashi engine markad'e. ''Ki godewa Allah Anaal domin ke mae Sa'a ce a rayuwa ubangiji ya albarkace ki da abubuwa da dama, wanda ba kowace 'ya mace ce take da su ba you're one of the talented, brilliant and intelligent girls komai naki yana burgeni fatana Abbah yabarki kicigaba da karatu banaso ya yi saurin aurarda ke. Ajiyar zuciya tayi Bana tunanin Abbah zai barni na je makaranta gaba da sakandire burinshi ina gama secondary nayi aure. Amma wallahi har ga Allah inason na cigaba da karatu ko domin na tallafawa iyayyena banaso, rayuwar Abbana tak'are a gadi. ''Indan kuwa haka ne zan ba ki shawarar da za ki cima burinki, kidaina kula samari ki nisanta kanki daga gare su idan Abbah yaga bakida takamame saurayi zai hak'ura yabarki ki cigaba da karatunki domin na tabbata irin son da Abbah yake miki ba zai miki auren dole ba. Murmushi Anaal tayi ae kuwa Ya Ansar ka zo da shawara Mae kyau da ingancin na gode fa. Kidaina gode min Anaal domin alqawalin ne na daukawa kaina duk wani buri da farin cikinki ni nan zan Samar miki da su. Ni dai burina kiyi fatali da samarinan na zamani, yawancinsu mayaudara ne. Shikenan Ya Ansar zan yi amfani da shawararka. Fira yashiga yi mata Mae dad'i sai murmushi take tana dariya marar sauti ta yanda Granny ba za ta jiyo ta ba around 2:56am baccin ya sace Ansar yana maqale da waya a kunne, sai saukar numfashinsa Anaal taji ta yi murmushi ''Allah sarki Ya Ansar kayi bacci a dai-dai lokacin ni kuma baccin yakauracewa idona. Kasa kashe wayan tayi tacigaba da sauraron saukar numfashinsa tsawon lokacin tadauka a haka, sai daga baya ta tuna tana karar mishi da credit ne a banza. Jiki a sa6ule ta katse kiran yayinda ta afka zance zuci. Gaskiya yaya Zuhura tayi Sa'a samun Ya Ansar a matsayin mijin aurenta ga kyau ga iya furta lafazi mai dad'i, ba abinda yafi burgeni da shi irin yanda yake d'aukar wanka uwa-uba ilimin Addini da na zamani da yake da shi. Tasauke ajiyar zuciya gaskiya Ya Ansar kahad'u 100% Allah yabani miji Mae irin d'abi'unka. Har akayi kiran sallah asuba a kunnenta jin anfara iqama yasa ta tashi, ta tada Granny tashiga bathroom tayi alwala saida tayi raka'atul fijir sannan ta sallacin sallah asuba. Tana gama sallah tashiga azkar d'in da take yi da safe tana ganin Granny tafita zuwa parlour ta zubura tadauko, wayarta saida tafara checking balance d'inta mtcsww"! Ta ja tsaki cike da jin haushi Naira biyu da kobo 56 suka rage mata, duk da haka sai tayi dialling numbernshi. A lokacin yadawo daga masjid kenan yana cire jallabiya yaji ringing wayarshi, share kiran ya yi saida yagama cire Jallabiya sannan yanufi bed ya kwanta yana d'aukar wayan kiran na tsinkewa. Har ya yi niyyar ya ajiyen wayan sai kuma wani tunani yafado masa ya duba miss call d'in sam bai yi tsanmani Anaal ce takira shi ba. Da sauri ya yi calling nata back. Anaal najin wayarta tad'auki vibrate dama tasaka wayan a meeting ne jikinta har rawa yakeyi tayi received. _Hello''! Ya Ansar_ Hi Lucky ya akayi ne? Dariya tasa yau kuma nice Lucky? Kwarai kuwa domin ke Mae Sa'a ce ko kinsan cewa ke ce mace ta farko da na ta6a raba dare ina waya da ita, dawowa na daga masallacin kenan gashi kuma ina waya da ke. Anaal ta kad'a kai kuma ni ce Mace ta farko da kafara hanawa bacci ba. Gaba d'aya suka sa dariya. Ae dole kayi dariya Ya Ansar kayi bacci abinka kabarni da sauraron minsharinka yanzu haka da headache na tashi tak'arasa magana cikin shagwa6a. Wani irin nishad'i ya kai masa ziyarar bazata ya lumshe idanu oh! Sorry my Lucky zan zo miki da extra ki d'an kora kinji? ''O'o ni banason magani. Shikenan sai nazo zan nemo abinda zai warkarda ciwon kan. Yanzu ki je shirya kada kiyi latti kice ni ne sanadi. Tana dariya ta katse kiran wani irin dad'i takeji yana ziyarta ta. Cike da nishad'i tashiga bathroom tayi wanka tana fitowa, ta goge jikinta tashafa lotion iya powder ta goga tasaka uniform, ta d'auki schoolbag d'inta tanufi parlour ta iske Granny tana sauraron Labarun BBC a 'yar k'aramar radio ta cikin girmamawa ta gaidata, Granny ta amsa had'e da cewa har kinfito? ''Eh Granny Toh Allah yabada Sa'a ki je cikin drawer purse d'ina na nan ciki kidauki N200. Na gode Granny akwai raguwar canji jiya ya isheni nayi k'udin adaidata har nayi breakfast. Shikenan adawo lafiya saboda ke ba Karin kumallo ki ke yi ba ballantana nace kisha koda 'yan ruwa shayi ne. Dariya Anaal tayi karki damu Granny nariga na saba in ba 10:00am tayi ba bana iya cin komai. Ke ki kasani da tsirfarki ta tsiya, sai kitafi kada kiyi latti a narke a banza ke ba wani abincin kirki ki ka cin ba. Tafice tana dariyar Granny kaitsaye BQ tanufa ta wajen Ammi ta jima wajen Ammi kafin tayi sallama da ita tanufi bakin gate wajen zaman Abbah bayan ta gaidashi yabata k'udin breakfast da na adaidata shi kan batace bazata kar6a ba domin tasan sai ya tuhumeta ina tasami k'udi shiyasa tarufawa kanta asiri ta kar6i k'udin. 7:06pm tafito daga gida tun daga nesa ta hango motar Ansar inda suka saba had'uwa, tun kafin tak'arasa tafara murmushi. Jeeddah Aliyu*SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* 15 Da yake gilasai motar tinted ne ita bata ganinshi amma shi yana ganinta. Kamar yanda take murmushi shima murmushi yake har yafi nata, tana Isa ta bud'e k'ofa tashiga had'e da sallama sautin wakar Indian ne ya amsa mata ta kai duba wajen Ansar sai faman kad'a kai yake yana bin wakar sai kace tare da shi akayi ta. Tayi dariya o'o su Indian boy ko sallama Ba'a amsawa? Yayi dariya yarage volume ya dube ta yi hak'uri my Lucky duk lokacin da nake sauraron wak'ar nan ni kadai nasan halin da nake shiga. Hmm,,,ta tabe baki kana jin abinda suke fad'a ne? Bai bata amsa ba sai kawai ya ja mota. Cike da nishad'i ya dube ta yace _inasonki tamkar bugun numfashina a duk lokacin da na rufe idanuna kyakyawar fuskarki nake gani. Banida buri da yawuce naji ki kwance akan k'irjina, nafara sonki tun daga ranar da idanuna suka fara tozali da ke ina sonki sosai fiye da son nake yi wa kaina_ Tun lokacin yafara magana har ya yadasa aya jikin Anaal rawa yake kamar mazari tsoro da rud'ani suka lullu6e ta. Ansar yacigaba da cewa _juyo ki dube ni ki yi min murmushi nan naki mai sanyaya zuciya, ba....._ ya Ansarrr da k'arfi cikin kururuwa Anaal ta kira sunanshi a tsorace ya hadiye sauran kalamansa yana mata kallon tsoro. A zafafe tafara magana kanka d'aya kuwa? Ka kuwa San abunda bakinka yake furtawa? toh wallahi indan ma mafalki ka ke yi ka falka wannan hauka da shirme har ina? Au dama shine dalilin da yasa kace mu zama friends ashe akwai wata, mummuna manufa a k'asan zuciyarka? Toh ni wannan cin amana ba da ni ba wannan ae abin kunya ne. Ansar ya dube Anaal baki bud'e daga bisani ya kece da mahaukaciyar dariya har yana had'awa da dukan steering, da kyar yai controlling dariyan cikin pity face yace nifa ina fassara miki abinda wak'ar take nufi ne Allah sarki poor girl ke kin dauka da ke nake? Ae ko giyar wake nasha Anaal babu kalma son a tsakaninmu. Ni fa banta6a yi miki wani kallo fa ce na k'anwata ta jini Anaal ina ba ki kulawa ne a matsayinki na wance batada 'yan uwa domin ba lallai bane wasu matsalolinki ki iya tunk'arar iyayyenki da su ba, shiyasa nake tunani ni ne zan maye miki gur6in yaya Auwal na rok'eki kada ki sake wannan mummuna tunani a tsakaninmu. ''Tsananin kunya ya lullu6eta, takasa koda motsa d'an yatsa gaba d'aya ta susuce gani haka yasa Ansar ya kira sunanta cikin laushin murya _Anaal_ Kasa amsawa tayi sai ma rufe fuskarta da hijabi da tayi abin ya bashi dariya sai kawai yadinga kwasan dariya shi kadai har ya iso gate d'in makarantarsu batasaniba saboda fuskarta na rufe. _Anaal mun iso ko yau ba za ki je school d'in bane mu koma gida?_ Da sauri ta bud'e fuska amma bata bari suka had'a ido ba ta bud'e k'ofa tafita yadinga kwalla mata kira tayi biris da shi sai da yaga shigarta cikin school sannan yaja mota yatafi yana dariyar shirmenta. "Direct Anaal tawuce class ta ajiye schoolbag d'inta tana fitowa taci karo da zeenat, 'yar buzuwa ashe kin shigo? Mtcsww''! Anaal ta ja tsaki rai 6ace tace banaso iskancin zeenat sau nawa ina kashe miki gargad'i kidaina kirana 'yar buzuwa? Oho"! Nasani miki da alama yau akwai wanda yata6a ki bara na ajiye schoolbag d'ina nadawo tashige class tabar Anaal tsaye. Har zeenat tadawo Anaal batasaniba tayi zurfi a tunanin, shirme da ta tafka. Dafa kafad'arta zeenat tayi meke damunki ne Anaal? Tayi ajiyar zuciya had'e da kallon zeenat mekika gani ne? Damuwa, damuwa nagani fal akan fuskarki. Hmm! Haka dai ki ka fad'a amma ni ba abunda ke damuna. Wai Anaal yaushe za ki rage zurfin ciki? Ni fa k'awarki ce, ki tuna daga ni har Ramlat ba ma 6oye miki duk wani abu da yashafe mu saboda mun yarda da ke sa6anin ke da har yanzu ba ki aminta da mu ba, gaskiya k'awance da ke Anaal akwai wahala ina amfani irin wannan zama ki sauya halinki ace ko abu zai kashe ki ba za ki iya bud'e baki ki fad'awa wani ba. Kisani Anaal barin kashi ciki baya maganin yunwa ki ta boye sirrinki mu kuma zamu cin gaba da gayamiki na mu domin mu yarda da ke d'ari bisa d'ari ke da ba ki yarda da mu ba chan ta matse miki. Tana k'arasa magana tajuya tanufi hanyar assembly tabar Anaal tsaye sororo taja jiki asanyaye ta bi bayanta. A wajen suka iske Ramlat domin yau tazo a makare Ana gama assembly Zeenat taja hannun Ramlat suka nufi class batare da sun kulata ba wannan ya tabbatarwa da Anaal zeenat ta warwarewa Ramlat zare da abawa. Tana shiga class tanufi seat d'insu cikin sanyinta tafara magana haba! K'awaye na bai kamata ku yi saurin d'aukar zafi akaina ba dama ba wani abu bane yau na tafka shirme da abin kunya shine ku ganni a haka, wallahi har yanzu kunya nakeji tamkar ina gabansa har inaji da wane ido zan sake tozali da shi tak'arasa magana tana yarfe hannaye. Zeenat da Ramlat suka kalli juna Ramlat ta mik'e ta zauna akan desk ta dafa Anaal wanene shi wane irin abin kunya ki ka tafka har da zai dame ki haka? Har ta bud'e baki za ta bata amsa uncle d'insu mai d'aukarsu darasin mathematics Yashigo dole Anaal ta hadiye sauran kalamanta. Uncle d'in yana cinye period d'inshi mai darasin physics yana jiranshi a bakin k'ofa yafita shi, kuma Yashigo a takaice Anaal batasami damar sanarda su damuwarta ba sai during breakfast. Direct shop d'in siyarda snacks da soft drink suka nufa. Ramlat da zeenat Suka nemi dogon bench suka zauna yayinda Anaal tashiga shop taciro 1k tasiyo recharge card na N200 tadawo ta zauna taciro 'yar Nokia ta daga pocket tasaka recharge card d'in Zeenat tace Anaal ki k'arasa mana labarin da ki ka fara ba mu nakagara naji waye wannan mutume da ki ke magana akanshi. Ajiyar zuciya Anaal tayi tashiga kwararo musu abinda yawakana da sanyin safiya tsakaninta da Ansar tana dasa aya suka sa mata dariya kamar zautacin. Anaal batasan lokacin da tashiga tayasu dariya ita kanta sai yanzu shirme nata yabata dariya sai da sukaci dariya iya son ransu sannan, Anaal ta lallube wayarta tashiga rubutawa Ansar text massage. _Sallam da fatar ka isa gida lafiya? Dan Allah Ya Ansar kayi hak'uri da abinda yafaru d'azu sharrin zuciya ne, domin ko makaho yashafa ka yashafa ni yasan kafi k'arfina me za kayi da 'yar masu gadi irina? A halin yanzu tunani nake tayaya zan had'a ido da kai, wallahi kunyarka nakeji fiye da tunaninka kahuta lafiya_ Tana gamawa tayi sending ta mik'awa Ramlat waya ku duba send items ku ga text d'in da na tura masa, na ban hak'uri ya yi kuwa? A baiyane Ramlat ta karanta zeenat tace anyya Anaal alaqarki da Ansar bata sauya daga yaya da k'anwa ba? Nima abin zan fad'a ki ka rigani Cewar Ramlat "Amma wallahi kun bani mamaki da har idanunku suka rufe ku ka manta da matsayina wanda haka yasa ku ke, dangatani da mutume da yafi karfina toh tunda kun manta bara na tuna muku ni Anaal ba kowa bace ba kuma, 'yar kowa ba face 'yar masu gadi banida dangin iya balle na baba a Nigeria cin rani mu ka zo ni da iyayyena kamar yanda nasha jin dubanan mutane suna kiranmu da 'yan ci rani. Tun farko ganinku da Ya Ansar ku ka fara wannan tunanin a tsakanimu, shin ban taka musu birki ba ta hanyar sanarda ku matsayi irin na Ya Ansar ba? *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *16* Zeenat, Ramlat kudaina had'ani da abinda yafi 'karfina Ya Ansar yafi k'arfina nesa ba kusa ba tuni ya girmewa ajina mutuncin da tausayina da yakeji sune sanadin alaqarmu kuma, har abada alaqarmu ba za ta sauya daga haka ba. Har Ramlat ta bud'e baki za tayi magana Anaal tad'aga mata hannu ya isa Ramlat mu rufe wannan zancen domin, duk abinda zan fad'a ba za Ku fahimce ni ba. Tana k'arasa magana ta mik'e kutashi mu tafi class. ''Ke ba za ki yi breakfast bane? Ta girgiza kai banajin yunwa in kum gama kusameni a class tajuya tai tafiyarta ta barsu da aikin kallonta. _Ansar_ Lokacin da Anaal ta tura masa text yana meeting phone nashi a rufe sai around _12:30pm_ yafito daga conference Hall, yana zaune a office d'inshi zamanshi kenan Abdallah yashigo yana waya da girlfriend d'inshi, har yagama wayan Ansar yana kallonshi. Mtcsww! Ansar yaja tsaki Wallahi ka ji tsoron Allah! Abdallah shin wace ri6a za ka ci in ka 6ata 'ya'ya wasu? Kai bakajin tsoron wata rana a 6ata naka domin zina bashi ce. 6ata fuska Abdallah ya yi kafara koh? Wai kai Ansar ba halin ka ji mutum yana waya sai kafara yi masa wa'azi? Wannan yarinya da ka ji ina waya da ita tana matuk'ar sona tamkar ranta. Ba tilassata nayi ba shaukin so ne ya d'ibeta tayi min alqawalin komai nakeso za ta mallaka min daga ciki harda kanta, shine don ina gaula irinka za'a bani kyauta abun irin wannan nace ba zan kar6a ba. Ni fa lafiyayyen namiji ne ina buk'atar jin dad'i a wannan zamani ba abinda ya kai mata musanman in kanada k'udi shiyasa na za6e su, don na dinga barje gumina akansu. Duk 'yar da k'addara ta fad'a kanta ta afka tarkona wallahi sai na moreta idan kuma na gama tsotse albarkatun jikinta nai mata wulaqancin da ko kare ba zai ci ba. "Girgiza kai Ansar ya yi haushin abokinshi ya kamashi ba tun yau ba yasan halin abokin nashi da neman matan tsiya amma bai ta6a tsanmani iskancin nashi ya yi tsamari haka ba. Abdallah lamarinka ba tsoron Allah a ciki kai ko tsoron cuta bakayi indan so ka ke ka more rayuwa kayi aure mana. Ubangiji ya yarje mana mu aure mata d'add'aya har guda 4 amma in za mu iya adalcin tsakaninsu, in ba za ka iya adalcin ba ka aure guda 1 ta isheka barje gumi domin zina bala'i ce kada sanadinka ya janyo mana masifa a zuri'a. Abdallah ya mik'e tsaye yana murmushi ya dube Ansar yace karka damu d'an uwa zanyi aure very soon duk wannan abin da nakeyi akwai wance zuciyata takeso, banida burin da yawuce na mallake ta a matsayin matata ta sunnah. Na yarda da ita za ta kai min budurcinta har gidana. Wad'annan tarkace da ka ga ina moresu a farmhouse d'in Dad ba ta aure a ciki kawai abokan jin dad'i ne. Inanan da matata kamila, malama mai nagartaciyyar tarbiyya tana jirana a gefe da zaran nagama more rayuwa za mu yi aure zan watsarda duk wani shashshancin na rungume halak d'ina. Mtcsww! Ansar yaja tsaki 'yar iska dai irinka dama mazinacin sai mazinaciya kuma inaji maka tsoro ranarda Dad zai kamaka da karuwa a farmhouse d'insa, wallahi za ka sha mamakin irin hukuncin da zai dauka akanka. A yatsine Abdallah ya dubeshi sai in Kaine munafukin da zai fad'a masa. Murmushi Ansar ya yi kaima kasan ni ba munafuki bane da na iya munafuncin da tuni kashinka ya bushe banza kawai bunsuru. Abdallah ya yi murmushi yana Sosa k'eya kanka akeji ni ka ga tafiya ya murda handle yafice tun fitar Abdallah Ansar baisan dalilin da yasa yakejin matsanancin fad'uwar gaba ba. Ya kifa kanshi a desk yashiga nazarin kalaman Abdallah lokacin yashare Mae tsawo yana fama da tunani, ganin zai wahalarda kanshi a banza yasa ya mik'e yashiga bathroom d'in da ke cikin office d'inshi ya wanke fuskarshi yafito yana goge fuskar tashi da k'aramin towel sai lokacin yatuna wayoyinshi da ke rufe yana budewa text message suka fara shigowa rututu na Zuhura yafara karantawa _Honey na kira duka layuka ka a rufe just to tell you how much I missed you in kayi switch on please ka kirani ina matuk'ar son naji sanyayiyar muryarka Mae sanyaya min zuciya. ILYSVM_ Ansar ya tabe baki yacigaba da karanta text d'in yana cin karo da na Anaal yafara doka, murmushi kamar Wanda akayi albishir da kujerar makka tun yana murmushi sai ga bawan Allah yana kwasan dariya shi kadai, ya duba wrist watch d'in hannunshi remains 15 minutes a tashi su Anaal daga school ya mik'e ahanzarce yadauki key yajefa sama ya chafe ya bud'e fridge yaciro gwagwanin coke Mae sanyi gaske yafice. Yaja mota cikin nishad'i yana driving da hannu d'aya, d'ayan kuma yana rik'e da coke lokacin zuwa lokacin yana kur6awa a haka ya iso gate na school d'insu yanemi wajen da yasaba tsayuwa ya yi parking. Ya zauna zaman jiran a tashe su. _2:15pm_ Anaal tana fitowa ta hango shi saida gabanta ya yanke yafad'i duk wannan uban sauri da take yi tunaninta ta sulale ba sai tajira shi ba koda zai zo ya tarar ta yi tafiyanta, sai gashi haqarta bai cima ruwa ba. 'kamar wance za ta fashe da kuka ta nufi wajenshi kunyarshi takeji matuk'a jin take kamar za ta nitse k'asa cikin tatata tak'arasa hannunta na rawa ta bud'e k'ofa bata bari suka had'a ido ba cikin laulausar muryarta tace _ina wuni Ya Ansar?_ Batare da ya amsa ba ya kur6a coke d'inshi kallonta yake yi ba ko kiftawa, yayinda ita kuma ta sadda kai k'asa tana wasa da yatsunta. Tsawon lokacin suka dauka ahaka shi bai tanka ta ba ita kuma bata k'ara cewa komai ba. Anaal so take ya tayarda mota tun kafin su zeenat su fito tasan halinsu da fassara yanzu nan za su fassara ta da cewa saboda Ansar ta sulalo bata jira su ba. Kamar za ta kurma ihu ta kalle shi, ta sauke idanunta a fuskarshi eye's ball d'inshi suka had'e da nata yasauke gwangwani coke ya cije lips yana kallonta turo baki tayi _Ya Ansar Dan Allah kayi hak'uri ka ja motar nan banaso su zeenat su gani_ ''Ya tabe baki daga bisani ya yi murmushi ya yiwa mota key suka halba kan titi, ya kur6i Coke ya dube ta ta k'asan ido ya mik'a mata raguwar Coke d'in _Anaal, Anaal, Anaal sarkin kunya kar6i Coke ki jik'a mak'oshi ki ko zai rage miki wannan kunyar_ Uhm! Tai ajiyar zuciya kallo d'aya tayiwa gwangwanin ta kauda fuska, tasake takurewa cikin hijabi. Ke kan yarinyar nan bakida mantuwa abunda yafaru tun safe ace har zuwa yanzu ba ki manta da shi ba. Lokacin da naga text naki dariya naci sosai "Ta galla masa harara harda su murgud'a baki, tai masifar burgeshi musanman yadda d'an k'aramin bakinta yajuya. Yasake mik'a mata Coke _na k'oshi_ tafad'a a gajarce, kina nufi ba za ki sha raguwa na ba? kina kyankyamin aza bakinki a inda na aza nawa? ''Ta kalle shi da mamaki tana nodding head nata, Uhm.... Uhm..ni ba haka nake nufi ba. Mekike nufi da kin k'oshi? Cikina a cike yake abinda nake nufi kenan. Uhm... Anaal kenan abinda ki ka fad'a azahiri bashi bane a bad'ilinki jikina yabani cewa kyankyami na ki Ke, da Auwal ne yasha abu yarage miki da bara ki ce ba za ki sha ba. Wai ni Lucky har sai yaushe zan maye miki gur6in Yaya Auwal ne? Duk wani hanya da zabi na zame miki d'an uwa na bi amma ke sai kora da hali ki ke mun, ayanda nakeji ko abincin da yafito daga bakinki zan iya ci saboda inajinki ajinina tamkar Basmah. Ba shiri ta katse hamma da takeyi tashiga kallonshi tai yi murmushin ta mik'a hannu yabata Coke saida ya yada idanunshi akan fuskarta kafin yabata. Tayi Bismillah ta kur6a sau d'aya sai kawai tashiga jujjuya gwangwani saida ta d'auki ''long time kafin tak'ara kur6awa a karo na uku tana kur6awa sai tayi kamar takware, ta mayarda na bakinta cikin gwangwani tafara tarin karya, duk abunda take yi Ansar yana kule da ita yashiga yi mata sannu. _sannu Lucky ko na tsaya ne na nemo miki ruwa?_ Girgiza kai tayi ya kar6e coke d'in daga hannunta yi hak'uri my Lucky na matsa miki kinsha abunda ranki bayaso gashi garin haka har kin kware. "Tayi murmushi batare da tace komai ba daga haka ba Wanda yak'ara magana. Ga mamakinta sai taga Ansar yana shan Coke d'in ba abinda yasha mishi kai, a rikice takira sunanshi ya Ansarrr! Wannan coke da ka ke sha yalalace na mayarda na bakina ciki. "Ya zaro ido na baki fa? Eh! Tafad'a tana kallonshi. Shine ba ki fad'a mun ba? "A tunanina ka ga lokacin da na mayarda shi. Wannan tunaninki ne ni ba abunda nagani yasake kur6a abinshi, da sauri tace ''please Ya Ansar Kadàina sha Àllah nasaka na baki a ciki. "Ya tabe baki aikin gama yariga ya gama duk abunda yakai ciki, ya zama nama k'azantar da bakagani ba tsafta ni ba ruwana Coke nasha ba yawun bakinki ba. "Anaal ta rausayar da kai tana kallonshi sauk'in kanshi ya burgeta matuk'a suna isa inda yasaba ajeta ya yi parking, alokacin yak'arasa shanye Coke d'inshi yasauke glass yajefarta gwangwani. Yadawo da ganinshi kanta, ita ma shi take kallo yasake mata shu'umin murmushi ya akayi ne an Lucky nah? Naga sai wani kallona ki ke yi ko nayi miki kyau ne? ''Tayi murmushi had'e da cewa ina yaba kirkinka ne a zuciyata. Na jima banci karo da mutum Mae kirki irinka ba. Ga ka da sauk'in kai komai naka Mae sauk'i ne ba ka d'auki rayuwa da zafi ba, na gode da irin kulawarka akaina ina Mae maka albishir tuni ka maye gur6i yaya Auwal a zuciyata yaya Auwal yariga ya6ata ko su Abbah sun fitarda da rai sake ganinshi shekaru 16 da 6atanshi tun ina 'yar shekara 1 ya6ata har yau ba Wanda yaji labarinshi, tana k'arasa magana idanunta suka ciko da hawaye. "Girgiza kanshi yashiga yi karki yi kuka Lucky shaquwarmu daga Allah ne, nai miki alqawalin daga yau zan tayaki da addu'a indan yaya Auwal yana raye Allah da yabainarshi. _''Ameen_ tafad'a tana kallonshi lokaci d'aya suka sakewa junansu murmushi ta bud'e k'ofa tafita yabita da kallo har ta6acewa ganinshi sannan yaja mota. _zuhra_ *4:00pm* Zuhra na kwance a parlour akan kujera tana chat wayarta tayi ringing, tayi picking had'e da karawa akunne _Hello Leebeauty!_ kinsan banida wadatace k'udi amma zan kira Ya Ansar yakaimu ta d'an yi shiru tana saurare abinda leebeauty take fad'a tayi dariya haba! Leebeauty kema kinsan k'udi ba matsala bane, a wurin Ya Ansar kedai ki shiriya da wuri za mu biyo gidanku mu d'auke ki. _okay ya yi kyau sai nazo_ ta kashe kiran tashiga dialling number Ansar ringing d'aya zuwa biyu Ansar yadauka _Hello!_ yafad'a akasalance Hi! My luv yakake ya office? _Lafiya Alhmdllh_ Ya akayi ne? Dama my luv shopping nakeso ka kaini kayan kwalliya na sun k'ara banida k'udi a hannuna kuma Alhaji ya yi tafiya. Ansar ya girgiza kai yana mamakin zuhra ita dai bata buri da yawuce yadinga kashe mata kudi, gashi bata jin maganarshi kuma ba gode mishi takeyi ba. shikenan naji zan zo na kai ki da k'arfe nawa za ki je shopping d'in? Ka zo around 5:30pm ya yi. Okay ba matsala sai nazo Ya yi hang up. _5:30pm_ A gidansu zuhra ya yi masa ya tsaya bakin gate ya gaisa da Abbah, sannan ya zarce parking lot ya yi parking yaciro wayanshi ya kirata yafad'a mata yazo saida ta6ata 8-10 minutes kafin tafito sanye cikin wata arniyar fitted gown na material golden colour shara-shara da shi yalafe a fatar jikinta wuyan rigar shown me your back ne anjara duwatsu a Ingiya kamar sark'ar wuya {necklace} a wurin shown me d'in. D'inki ya yi kyau saidai babbar matsalarshi yanda ya baiyanar da ilahirin surorin jikinta k'afarta sanye da hills blue in colour,hannunta d'auke da wata 'yar k'aramar purse ita ma blue ta yane kanta da d'an siriri mayafi har ana iya hango dogon kiston attachment d'in kanta, ba laifi tayi kyau matuk'a a fuska saidai sutura jikinta ce za ta dusashe kyaun da tayi. Domin duk Wanda yasan ciwo kansa sai ya yi tir da ita, yayinda samari 'yan bana bakwai za ta tafi da ruhi da gangar jikinsu musanman yanda Allah ya yi mata kira ta jiki zuhra akwai diri hips d'inta kadai abin kallo ne ga gaba ga baya. ''Tana rausaya kamar ganye bishiya yana kad'awa alokacin iskan damina, tun kafin tak'araso Ansar yafara cika yanayi batsewa ranshi ya yi mugun 6aci wai matar da zai aura ce wance za ta zame masa uwar 'ya'yanshi anan gaba ita ce cikin wannan bak'ar shiga. Jeeddah Aliyu*SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *17* Hankalinta kwance ta bud'e mota tashiga k'amshin turare ta yadak'i hancinsa ya lumshe idanu Wanda suka kad'a sukayi jajir saboda 6acin rai. _sorry my luv na barka kanata jira_ Harara ya zuba mata cikin hargowa yafara magana wai ke zuhra wace irin yarinya ce me taurin kai da naci? Sau ina gayamiki banaso irin banzaye tufafin nan da ki ke sakawa? Na fahimcin kinfiso sai na nuna miki 6acin raina k'arara akan wannan mummunar d'ab'ia taki....Dallah dakata Ya Ansar akan wane dalilin za ka dinga yi mun ihu aka? Aure na ka ke yi da za ka kafamin doka na bi, duk tsiya da azarbabinka ka jira har a zarga min igiyoyin aurenka alokacin ka ke da iko akaina ba yanzu da nake gidanmu ba don haka ka saurara mun. ''Ke ashe bakida tarbiyya har ni za ki kalla ki gayawa magana? An gayamaka magana kai da karufe ido kafad'amin son ranka fa? Ko angayamaka tsoro nakeji? Idan ma haka kadauka kayi gaggawa ka sauke domin ni ba uban da nake tsoro. Zuhra! Yadaka mata tsawa had'e da nunata da yatsa kallon wulaqancin take aika masa tana yatsina da tabe baki. ''Ki natsu ki saita tunaninki dosashiyar kwakwalwarki ta hasko miki, da Wanda ki ke magana kada garin rashin tarbiyyarki ki furta abinda zai zame miki danasani marar amfani. "Idan akan irin wannan cin zarafi da ka ke min ne Ya Ansar ba zan jin d'ar ko shakka furta maka, kowace irin kalma ce tafito daga bakina balle har nayi danasani. Ka bi ka takurawa rayuwata ka hanani shakat ni ba iskanci nakeyi ba balle kace ina wannan shagar ne don nasami customers ko akwai uban da yata6a gayamaka yaga k'ato akaina? Wani irin k'ololo ya tokarewa Ansar a mak'oshi yasaki baki da hancin yana, kallon zuhra bai ta6a tsanmani rashin mutuncin zuhra har ya kai haka ba. Zafin zuciya yadebe shi ya wanka mata bahagon mari sai da taga wuta jahanama{lol ta bakin yara} ya bud'e k'ofa azafafe yadank'o hannunta yaciro ta daga mota ya yar6e ta waje da6ass.....tayi fad'uwa 'yan bori. ''Tir! da wannan rashin tarbiyya naki tir! Da wannan halin naki wallahi ayau zuciyata cike take da nadama furta miki so tabbas na yarda da 'yan magana da suke cewa so makaho ne{love is blind} cikin hukuncin ubangiji yaji tausayina ya haska mini ganina. Idanu na sun waye daga makata da na shiga, ba ki dace da rayuwata ba wallahi zuhra ba ki dace da zama uwar 'ya'yana ba. Zuhra ta mik'e da kyar idanunta sun canza launi hawaye na zuba kamar anbud'e famfo bak'ar zuciyar nan ta ta, ta motsa idanuta suka rufe ruf yanda ka ke tunani ban dace da kai ba, Ya Ansar nima abin haka yake yanda ka ke nadama akaina nima haka nake nadama saninka arayuwa na tsaneka, Ya Ansar wallahi na tsaneka bana sonka I hate you kafita daga rayuwata, mari da kayimin Allah yasa isa banyafe ba mugu bak'in azzulumi Wanda uwarshi ta haifa ba jini Mae zuciyar fir'una d'an tasha asarare...... kukan kura Ansar ya yi yadank'e wuyanta yadinga zuba mata mari baki da hancinta na jini. _subhanalillah!_ Muhammadu me nake shirin gani? Muryar Abbah ce ta d'aki kunne Ansar yasaki zuhra ba shiri kunya ta lullu6e shi da sauri har yana tuntu6e yashige motarshi, yafizge ta da k'arfi yanufi gate wani abin takaici gate d'in arufe yake yafito a harzuk'e ya bud'e yak'ara fizgar mota da k'arfi. Abbah yaduk'a gaban zuhra tashi, tashi zuhra me yahad'aki da shi? Domin wannan ba halin Muhammadu bane yi hak'uri ki tashi. Haushin Abbah yaturnuk'e zuhra ba don da tana ganin girmanshi ba da ba abinda zai hanata fad'a mishi maganar da har ya mutu ba zai manta da ita ba. duk da haka bata barshi kara zube ba saida ta zabga Mae tsaki ta mik'e tana kuka mai sautin gaske tanufi cikin gida. Tana Shiga main parlour ta zube tashiga kururuwa _wayyo ni Allah na shiga uku na lalace wayyo bakina hancina_ Da gudu Hajiya saudat da Nazeeya suka fito daga rooms d'insu tsananin tashi hankali ya baiyana a tare da su har suna had'a baki ta hanyar watsawa zuhra tambaya meke faruwa ne zuhra? Accident ku ka yi ne? Hajiya saudat ce tak'ara watsa mata wannan tambaya. ''Zuhra takasa amsa tambaya ko d'aya sai birgima da gunjin kuka ta ke yi. Da kyar da sud'in goshi Hajiya saudat ta ciyo kanta tadaina kuka. Tana shassheka tashiga kwararowa Hajiya abinda yafaru tana dasa aya Hajiya saudat da Nazeeya suka lailayo ashar kamar masu fad'in karatu suka aikawa Ansar. Dama ya lafiyar kura Hajiya saudat masifafiyar mace ce 'yar tijara tun tana yarinya yara suka laqa mata suna Sauda 'yar bala'i in tana fad'a har da bakinta ke kunfa kamar tasha omo. ''Akan 'ya'yanta da uban kowa za ta iya karawa ko ubansu bata yarda yakai hannun akansu ba ballantana wani banza Ansar lallai Ansar ya tsokano tsuliyar dodo. Jakkar uban nan duka tun kafin aure lallai Ansar yanuna min shi d'an tunkiya ne, don tsabar kazar uba zai ware dantse yadake ki a cikin gidanku ni tun da nake duniya banta6a jin wannan abin uban ba duk kwarewa iskanci irin na d'a namiji sai akai mishi mace a gidanshi yake dukanta. Sai ga wannan d'an k'ashi bishi abin kazar uba yakafa tarihi ga 'yata ke Nazeeya bani wayata na kira uwarshi naji ita ce tabashi k'arfin guiwa dukan 'yata tun kafin aure. Jikin Nazeeya na rawa tadauko mata waya tana Mae cigaba da masifa da kumfar baki tasa kiran Mum Fatee, tana jin mum Fatee tad'aga kiran nata bata ko tsaya amsa sallama da gaisuwa da take mata ba, tashiga 'yayyafa ruwan rashin mutunci wato Hajja fatee da saninki Ansar ya zo har gida ya yiwa zuhra dukan akawo wuk'a? ''Haba Hajiya saudat wannan wane irin magana ne? In rai ya6aci hankali akesawa yanemo shi ta ya Boy zai daki zuhra da Sanina? Kuma ita zuhra da tace da ke Boy yadake ta shin kin tambaya ta dalilin dukan nata? ''Kan ubanan lallai Hajja fatee kin cika cikakkiyar 'yar reni wayo d'anki ya sauke k'arfin da Allah yabarkace da shi akan 'yata don tsabar wulaqancin kice na tambayeta dalilin. Toh ba za'a tambayeta d'in ba wannan ae son kai ne in har ke ba za ki tsawata masa ba zan tabbatar miki ni uwace da ba za ta lamunce aci zarafi 'ya'yata ba, wallahi sai na d'auki mummuna mataki akansa sai ya gane ba irin 'ya'yana ake duka a zauna lafiya. ''Mum fatee ta ja tsaki mtcsww! Ke ni saurara min banda k'addarar so me Boy zai yi da tsatsonki 'ya'ya Sam ba tarbiyya sun lalace sun bandare, ae ke sa'a ki kayi da har Boy yafurta kalma so akan fitsarariyar 'yarki. Au! Haka ma za ki ce Hajja fatee? A maimakon kibani hak'uri sai ki buge da fad'amin maganganu banza? Eh! An fad'amiki d'in ko kindauka ke kadai ce ki ka iya yankar k'auna da tijara? Shikenan Hajja fatee ki zuba ido ki ga irin hukuncin da zan dauka domin 'yata ba jaka bace balle wani k'aton banza majiyi k'arfi yadinga dukanta. Kafin mum fatee tabata amsa har ta datse kiran tana huci kamar kubunbuwa. Jeeddah Aliyu*SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *18* Ansar yana tuk'i{driving} yana had'a gumi duk da Ac mota da ke bud'e bai hanawa zufa tsatsafowa daga, sasssa jikinsa ba. Gudu yake shararawa kamar zai tashi sama bai ta6a shiga 6acin rai kwatankwacin wannan ba, tsanar zuhra ta baibaye shi a k'asan zuciyarsa da raguwar sonta. "Yana isowa gida a fusace yashiga danna horn kamar zai tashi unguwa, da gudu maigadi yabud'e masa gate yanufi parking lot ya yi parking batare da ya kashe wutar mota ba yakifa kansa a steering yasoma tunanin, ranar da yafurtawa zuhra Kalmar son Kalmar da a yanzu tazame masa tamkar dafin maciji ya yi nadama marar iyaka jin yake ina ma zai iya komawa baya da ba abinda zai hanashi goge wannan kalma saidai kash! Abinda yake gudu yariga yafaru. Kiran sallar magarib yadawo da shi natsuwarshi jiki ba kwari ya kashe mota yafito yanufi masallacin, bayan sallar isha yadawo gida kaitsaye part d'inshi yanufa ya zube parlour ya yi matashi{pillow} da hannayeshi yak'urawa pop ido yana nazari ta ya zai bar zuhra batare da hakan yata6a Zumuncin iyayyesu ba. Domin ahalin yanzu bayajin zai iya aurenta gaba d'aya tafice mishi arai. Basmah tayi sallama bai iya amsa mata ba saima zuba mata rinanun idanunshi da ya yi, jiki na rawa Basmah tak'arasa wajenshi ta zube guiwowita gabanshi ta rik'e hannunshi meke faruwa da kai ne Ya Ansar banta6a ganinka cikin wannan yanayin ba? Shiru ya yi yakasa bata amsa domin wani Sabon tafarfasan zuciya yakeji. Kayi min magana Ya Ansar a ciki na baro Mum tana fad'a ita ce ma ta aikoni na kira ka sai gashi na tararda kai cikin wannan yanayin, ka sanarda ni abinda yake faruwa ''please. Ansar yasauke gwaron numfashi mai d'auke da wata zazzafar iska Basmah nayi danasani marar adadi na furtawa zuhra kalmar so. Ashe yarinya nan batada mutuncin? Rashin tarbiyya ya yi mata katutu wai har ni zata zaga a cikin gidansu. Zaro ido Basmah tayi ranta a6ace tafara magana, zagi fa kace Ya Ansar? Kwarai kuwa zagi Basmah infact ba kalan zagin da batayi min ba. Har ce min tayi an haifeni ba jini. Ran Basmah yak'ara sosuwa ba shakka zuhra batada mutuncin ita yanzu ko mai zaginka tagani ba sai inda k'arfinta yak'are ba, shine don tsabar rashin tarbiyya za ta ware k'aton bakinta ta zage ka. Wallahi sai na nuna mata kafi k'arfi a zage ka sai na nuna mata k'aryan rashin kunya takeyi sai nacicin mata mutuncin wallahi. Sai lokacin Ansar yaji ranshi ya yi sanyi yasaki murmushi yacigaba da kallon Basmah da takarkare tana ta faman zabga fad'a. Matse hannunta da ke cikin hannunshi ya yi ya ja dogon hancinta c'mon 'yar lukuta ni basanki da fad'a ba ki kyaleta kawai ni nasan matakin da zan dauka akanta. Girgiza kai tayi ka dubi girman ''Allah Ya Ansar ka fitarda yaya zuhra daga zuciyarka ka manta da ita tun fil'azal batadace da kai ba. ka d'aukar min alqawalin za ka barta bari na har abada wallahi banaso ka aureta tak'arasa magana hawaye na zuba daga idanunta. ''Rud'ewa Ansar ya yi yad'ago fuskarta yana kallon cikin idanunta, haba! Basmah meyasa za ki zubarda hawayenki akan wata banza? Ni nace inason zuhra ba wani ya tilassani ba nayi miki alqawalin Basmah komai wuya komai runtsi ba zan auri ta ba koda kuwa sonta ne sanadin bari numfashina. Dad'i ya baibaye Basmah ta k'ank'ame Ansar tana zuba mishi godiya ita dama ta tsani Zuhra Sam basu shan inuwa d'aya saboda d'an banzan girman kanta da d'agawa ta dauki kanta wata tsiya alhali ita d'in ba kowa bace. Ansar yacireta daga jikinshi ya mik'e had'e da rik'o hannunta, a tare suka Jera zuwa cikin gida a parlour suka iske mum fatee suna had'a ido da sauri Ansar ya sukunyarda kai zo nan Boy! Kanshi na k'asa yak'arasa wajenta zai zauna k'asa ta katse shi zauna anan tanuna kusa da ita Cikin laushin murya Mum tafara magana Boy meyasa ka biyewa son zuciyarka kayiwa 'yar mutane duka? Shin ko kasan Hajiya saudat takirani sai abunda bakinta ya manta? Boy banaso harka da tashin hankali maganin bari kar afara tun farko bason wannan al'amarin nakeyi ba. kanace sai ita dama shine burin Mahaifinka shi a dole mai son zumuncin ba wani kwakwaran bincike halayen yarinya ya goyi bayanka, alokacin duk ilolin da nake zaiyana masa akan zuhra sai ya yi biris! Da ni daga karshe sai ya yi min kashedi muddin inason zaman lafiya na iya bakina akan aurenka da zuhra, wannan yasa najawa bakina linzami domin fad'a da yafi k'arfinka tilass! Ka mayarda shi wasa. Gashinan tun kafin tafiya tayi nisa kafara dukan 'yar mutane. Sai lokacin Ansar yad'ago zai yi magana Mum ta katseshi ta hanyar d'aga masa hannu, banason jin komai daga bakinka wane irin nuni ne ban maka ba? kana tsirowa da zance zuhra ka keso, daga ni sai kai sai ubangijin da ya halicemu nasaka d'akin nasawa k'ofa key don kada kowa yajimu nace, da kai zuhra batadace da kai ba. Kaje kanemi saleema 'yar gidan former controller 'yar abokin Mahaifinka kuma 'yar aminiyata Hajiya Maryam duk duniya banida aminiya kamar Maryam amma ka watsa mun k'asa a ido kace bakasonta tacika fari kamar zabiya zuhra ita ce dai-dai kai. ''Don haka wallahi ba ruwana duk tsuntsu da yakira ruwa shi ruwa kan doka, yanda kaje har gida ka dake 'yar mutane haka za ka wanke k'afa kaje ka bata hak'uri ita da mahaifiyarta, domin ina ji maka tsoro wannan maganar taje kunnen tijarare ubanka, wallahi ba zai maka da dad'i ba. ''Ansar yarik'o hannunta ya yi k'asa da murya Mum ki yi hak'uri ki bani dama na fad'a miki dalilai na nason barin zuhra ba wai don banasonta ba Har yanzu da raguwar sonta a zuciyata. Mum ta dubeshi ta tabe baki toh! Tunda da raguwar sonta a zuciyarka ba sai kacigaba da hak'uri da ita ba. Mum ba zan iya ba wallahi tsanar da nake mata tafi son da nake mata yawa a zuciyata. Mum zuhra ba matar aure bace kuskure ne nariga nayi tun farko da nakasa karanta halayyenta. Ba wani kuskure da kayi Boy tun asali son zuciyarka ka bi lokacin da nake zaiyane maka munanan d'abi'unta me kace da ni? Ansar ya yi shiru yakasa amsawa. Nace me kace da ni? Saida yasauke ajiyar zuciya yadawo kalar tausayi sannan yace cewa nayi _*SO* ba ruwanshi da hali ko d'abi'u muradi zuciya tasamu amincewa zuciyar da takeso_ A nawa shirme Mum tunda inaso zuhra ita ma tanasona fiye da son da nake mata d'abi'u da halayyamu za ta iya dawowa d'aya ashe ba haka bane. ''Boy ni ba abinda zan maka karka manta a tsarin Mahaifinka da d'an uwanshi suka yi, kafin azumi ko kuma bayan sallah za su aurarda Ku bakin al'kalami yariga ya bushe. "Ansar yadafe kai jin yake kamar ya kurma ihu, Basmah ta kalli Mum tace Mum bakin al'kalami bai bushe ba domin Ya Ansar shi yakeyi auren a yanzu kuma yace bayayi a wannan zamani ko 'ya mace andaina yiwa auren dole balle d'a namiji, Mum ansha taro za'a daura aure ango yace yafasa dole a hak'ura jama'ar da aka tara a basu hak'uri shikenan kowa yakama gabansa ballantana wannan ba'a tsayarda takamame lokacin ba. Jeeddah Aliyu*SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *19* Mum ki fahimcin inda Ya Ansar yadosa a halin yanzu bayason zuhra sonta yafita daga, zuciyarsa ke ce mutum ta farko da yadace ki goyi bayansa yanemawa 'ya'yansa uwa tagari amma wallahi mum zuhra Sam bata cancancin zama matar Ya Ansar ba kaddara ce tasa ya furta mata Kalmar so. Ke! Dallah rufemin baki in har ke kinmanta da waye ubanku ni ban manta ba, in har ke bakya guje masa masifar da bala'in mahaifinku ni ina guje masa, Boy karka bari shed'an ya yi tasiri akanka har Mahaifinka yaji wannan maganar wallahi zai yi masifar sa6a maka watakila har tashafe ni karufawa kanka asiri karufa mini ni uwar da na haifeka. ''Da kyar Ansar yafurta shikenan Mum komai yawuce zan je na basu hak'uri, cike da farin ciki Hajja fatee tashiga sa masa albarka. Ansar yafad'i haka ne don kawai ya kwantarwa Hajja fatee da hankali ba wai hakan ne har cikin ranshi ba. Ya mik'e jikinsa a mace yanufi part d'inshi yayinda Basmah tanufi kitchen ta had'a mishi abincin Hajja fatee tabisu da kallo tana mamakin irin tsananin shak'uwar da ke tsakanin Ansar da Basmah. _Anaal_ *9:33pm* Tana zaune a parlourn Granny abin duniya yataru ya yi mata yawa, rashin ganin Ansar ba k'aramin halin damuwa yajefata ba, gashi har _9:33pm_ tayi tasan kuwa a irin wannan lokacin mayuwacin abu ne Ansar ya zo tadauki wayarta tayi checking balance taga ko na plashing batada sai kawai ta haddace digit d'inshi tayi masa please call me'' Alokacin yana kwance a parlour yajingina rabin jikinsa a kujera yaji shigowar text a wayarshi da ke ajiye akan ''center table kallo d'aya ya yi mata yadauke fuska, yawan kawo haske da takeyi tadauke yabashi haushi Basmah tayi sallama tashigo d'auke da tire mai d'auke da foodflask ta ajiye a gefen center table a kasalance yafurta Basmah miko min wayata. Wance daga ciki tafad'a tana kallonshi da yatsa ya yi pointing d'in wance yakeso ta tadauko masa. Tadauko ta mik'a masa yana yadanna text d'in yaga Anaal ce tayi mishi please call. Hannunshi har makyaryata yakeyi wajen kiranta, Anaal har tafitarda ran zai kira unexpected taji phone d'inta yadauki k'ara cikin zumud'i ta amsa kiran _Hello_ tafad'a cikin sanyi murya mai cike da damuwa. "Saida ya lumsashe idanunshi daga bisani ya bud'e su yakike my Lucky? Lafiya lau tun d'azu nake baza idanu zuwanka gashi har 10:00pm ya kawo jiki banganka ba hope lafiya ce ta rik'eka? Huh! Abubuwa ne sukayi min yawa amma gobe insha-Allah zan shigo ya Granny? Granny tana d'akin watakila tayi bacci naga tasha magani, kuma bacci yakesata sosai. Ke kadai ce kenan? Eh! Ya gyara kwanciya can! K'asan mak'oshi yafurta nayi missed naki sosai sai kace ba d'azu da rana mu ka rabu ba. ''Anaal ta rausayarda kai ta kalli bakin k'ofar d'akin Granny taga ba kowa, tace nima haka Ya Ansar yau rana d'aya da ba ka zo da dare ba duk sai naji ba dad'i ko abincin nakasa ci. Ansar ya yi k'ayatatcen murmushi had'e da cewa nima bancin abincin ba ban fahimci inajin yunwa ba, saida ki ka ce ba ki cin abincin ba kitashi kije ki zubo abincin ki zo mu ci tare. Mamaki ne ya lullu6e Basmah ta yi zugun tana kallon Ansar sai aikawa kanta tambaya takeyi da wacece ya Ansar yake waya, da har tayi saurin gusarda b'acin ranshi da wuri haka? "Zaro ido Anaal tayi Uhm! Ya Ansar karka tsorata ni kadai ka ke nesa da ni ta wace hanya za mu ci abinci tare? Ke dai kawai ki je ki d'ebo kuma karki kashe waya. Uhm! Anaal tashiga kitchen ahankali tafurta nashigo kitchen Toh! Ki yi mana saving Na bud'e foodflask. Menene a ciki? Tuwon semo ne da miyan kubewa. Wow! Delicious ashe za mu ci dad'i? Uhm! Haka dai kafad'a. ta zuba tuwon semovita Leda d'aya da miya ta bud'e roban man shannu Granny ta tsiyaya tadauko plate d'in da hannu d'aya d'ayan kuma na dafe da waya tadawo parlourn, kasan me? A'a sai kinfad'a Har da man shannun Granny na zuba. _iyeee lallai yarinya nan za ki ci dad'i_ Zan ci ko za mu ci kana nufi kafasa cin ne? Dariya ya yi no! Banfasa ba sai lokacin ya dube Basmah wance mamaki yahanata motsi, Basmah yi min saving mana. Ajiyar zuciya Basmah tayi tad'auki plate tasa mishi ledan tuwon shinkafa fari fat! da shi tak'ara d'aukar plate mai zurfi ta zuba mishi miyan agusi taji stockfish. ''Ta6angare Anaal kuma bayan ta ajiye plate tanufi fridge tadauko ruwa had'e da cup tadawo ta zauna gaban plate tana sauraron Ansar da ke zayyano mata kalan nashi abinci. Narke fuska tayi Wanda hakan yasa ta manta da wa take waya, tasa shagwa6a Allah Ya Ansar naka yafi nawa dad'i ni ba zan ci nawa ba naka zan ci. Tashi zaune ya yi yana dariya da ke nuna tsantsan nishad'i da yake ciki, shikenan ki jirani zan zo yanzu nan na kawo miki nawa na kar6i naki. Uhm! Uhm! Yi zamanka nima zan ci nawa ko ba komai nawa da man shannu, naka ba bu tak'arasa magana tana dariya mai ban sha'awa. Huh! Kinsa yawuna ya tsinke amma ba komai nima zan yi manage da nawa, sai kifara ci kinsan kinfini k'atuwar loma. ''Tasa dariya na dai ji d'in. shiyasa nafika kwari sai da safe. Da sauri yace ina za ki tafi? Zan ci abinci mana. Karki kashe waya ki ci ahaka inaso naji karar shigar loma bakinki. Dariya sosai Anaal tayi daga bisani tayi Bismala tafara cin tuwonta. Jin tayi bismillah! Yasa Ansar ya wanke hannunshi yafara cin nashi, tariga shi k'oshi amma sai tayi mishi wayo sai da ta tabbatar da yacinye nashi tass! Sannan ta ture nata plate tana dariya tace _yeee nai maka wayo ko rabi bancinye ba_ Shima dariya ya yi ya tara hannunshi a robar wanke hannu Basmah ta zuba mishi ruwa ya wanke hannunshi. Tayagi tissue ta goge mishi hannu _thanks my 'yar lukuta_ yafad'a kamar Mae rada duk da haka saida Anaal ta ji _wacece 'yar lukuta?_ ta watsa masa tambaya. Saida ya yi murmushi kafin yabata amsa Basmah ce bara na bata Ku gaisa, ya mik'awa Basmah waya had'e da cewa Anaal ce za Ku gaisa. Wani zaro ido Basmah tayi za ka yi tsanmani kwayar idonta zai yi tsalle yafad'o k'asa cikin kid'ima tafurta A....Anaal? Ita ce mana kiyi magana kudaina k'ona min credit a banza yak'arasa magana yana harararta. Cikin rawar murya ta gaisa da Anaal daga bisani ta mik'a masa waya yacigaba da magana da Anaal cikin nishad'i da Annashuwa sai kusan around 10:44pm, ya yi sallama da ita yajuya yana kallon Basmah wance ita ma shi take kallo ba ko kiftawa. Ya yi murmushi yadai 'yar lukuta naga kina kallona kamar bak'auye yashigo birnin? Huh..ba dole na kalle ka ba ka zo min da abin mamaki Mae rikitarda kwakwalwa. Yaushe alaqa Mae k'arfi irin wannan tashiga tsakanika da Anaal? Saida ya yi ajiyar zuciya ya ajiye wayar da ke hannunshi ya rik'o hannayen Basmah yana kallon cikin idonta, wannan yakasance sirri tsakanina da ke ba za ki fad'awa wani ba. Har sai lokacin da yadace ya yi da zan bankad'o sirri kowa yaji. ''Basmah tayi murmushi karka damu Ya Ansar tsakanina da kai sai Allah, wannan alqawalin ne na d'aukarwa kaina insha-Allah wannan maganar ba za ka ji ta a bakin kowa ba. Basmah! Na'am'' _Tun daga ranar farko da nayi tozali da Anaal zuciyata ta kamu da sonta so mai tsananin gaske har, nakanji a jikina sanadin sonta zan iya aikata koma menene domin na mallaketa ni kadai. Kada kiyi zaton kyakyawar fuskarta ce tajani wallahi ba ko d'aya domin ranar da na fara ganinta fuskarta na lullu6e da niqabi abu d'aya zan iya ce miki kyakyawar tarbiyyarta, kamun kanta, uwa-uba iliminta sune suka k'ara jefa zuciyata a tarkon sonta._ Basmah inason Anaal Sosai fiye da tunaninki rasata tamkar rasa wani sasshe ne a jikina, Babban farin cikina na kasance tare da ita har k'arshen numfashina. Anaal ita ce ta dace da tsarina ita ce mace da nake mafalki na, mallaka ba zuhra ba. Kurciya da rashin sani su suka debeni har na furtawa zuhra kalmar so a yanzu nayi nadama had'e danasani marar adadi. Zufa ya karyowa Basmah bata damu da ta goge ba saboda hannayenta na danke da na Ansar, ta rankwadar da kai tana kallonshi saida tagama karantarshi tass! Sannan tafara magana. Jeeddah Aliyu *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *20* Banyi mamakin jin wannan maganar tana fitowa daga bakinka ba. Domin nasa ran faruwar haka tun daga, ranar da kayimin tambaya akan Anaal zuciyata tabani akwai wata a k'asa, saboda ba halinka bane tambaya akan mace da bakada alaqa da ita. "Ba shakka Ya Ansar na yabawa za6inka d'ari bisa d'ari saidai tana k'asa tana dabo kafi kowa sanin baqar ak'ida iyayyenmu na k'yama da tsanar talaka, anyya kuwa za su amince da Anaal musanman yanda suka d'auki dogon buri suka aza akanka? "Nasani Basmah ban kuma manta ba shi so ba ruwanshi da k'udi da talaka, zuciyata Anaal takeso duk runtsi ba Wanda ya isa yarabani da ita. Dad da Mum suna son farin cikina don haka ba za su k'i Anaal ba domin ita ce farin cikina. "Toh amma wani hamzari ba gudu ba ita Anaal d'in tasan kanasonta? Girgiza kai ya yi. Meyasa baka fad'a mata ba? Tsoro, tsoro ne Basmah yahanani fallasa mata sirrin zuciyata. "Dariya Basmah tasa kai Ya Ansar a yanda ka ke d'inan akwai mace da za ta ba ka tsoro? Ba tsoron Anaal nakeji ba tsoron yadda za ta kar6i tayin soyayyata. Toh yanzu menene mafita"? Mafita guda d'aya ne nakeda shi ahalin yanzu nafara aiki da shi, da alama haqata za ta cima ruwa. Ban fahimcin ka ba? Za ki fahimta idan na fahimtarda ke na nemi kusancin da Anaal ba don komai ba sai don nayi mata kissan munmunk'e kissan da, da kyar in za ta mik'e. Zaro ido Basmah tayi cikin kad'uwa tace kissa fa kace Ya Ansar dama ba son gaskiya ka ke mata kai kuwa me za kai ka da kissan mutum? Dariya sosai Ansar yashiga kyalkyatawa daga bisani yace ke banza ce Basmah sai kace ba bahaushiya ba. Banda shirme irin naki ta ya zan kashe abinda nakeso? Basmah ta rausayarda kai ni kan ban fahimcin inda ka dosa ba d'ourani akan haske. Bari na tambaye ki idan magge za ta kama bera ya takeyi? ''Shiru tayi tana tunanin daga bisani tace kwantarda kai takeyi ta dinga sand'a tayi wuf! Ta cafke wuyanshi. K'ara kyalkyalewa da dariya Ansar ya yi yasakin hannun Basmah guda yadungure mata kai yanda ki ka ga magge tayiwa bera haka zan yiwa Anaal, na cafke zuciyarta na dasa mata zazzafar soyayyata ta yanda duk lokacin da na furta inasonta jikinta na mazari za ta amince da ni. Hum....you're very smart Ya Ansar. ''Yes! I'm yafada cikin jin dad'in yabon nashi da Basmah tayi Lallai ba ko kwankwato Anaal za ta fad'a tarkonka baiwar Allah har nafara tausaya mata, saboda ba za ta iya fito-na-fito da zuhra ba. Mtcsww! Ya ja tsaki in ana maganar sarauniyya mata kidaina sak'o zancen zuhra domin tenure ta yak'ara. Dariya Basmah taci kamar cikinta zai fashe Allah sarki duniya ashe akwai ranarda za ta zo da za Kadàina son zuhra? Gashi ta zo kuma kingani da idonki ke ni fa sai daga baya nagano son Anaal ne sanadi dusashe soyayyar zuhra a zuciyata. Basmah ta mik'e tsaye had'e da cewa sai da safe saboda na fahimce in ana firar Anaal Sam baka gane dare ya yi, Ansar ya mik'e yana dariya mu je na rakaki suka jera had'e da ficewa daga parlourn suna tafiya Ansar yana cigaba da bata labarin Anaal, saida yakaita har main parlourn sannan yadawo part d'inshi sai ke ji kamar Anaal d'in ce yagayawa yana sonta, ashe gaskiyar bahaushe da yake cewa barin kashi ciki baya maganin yunwa gashi dae ba Anaal ya fad'awa ba amma yaji sauki a zuciyarsa. _Washe Gari_ _7:15am_ Kamar yadda yazamewa Ansar jiki kai Anaal school ko yau hakan ce tafaru, bayan yakaita yadawo yak'ara kwanciya sai misalin k'arfe _10:30am_ yafito cikin shirin tafiya office yana sanye da material Mae taushin gaske transparent brown in colour k'afarshi sanye da brown sandal yana, rataye da briefcase fuskarshi lullu6e da fara'a yashiga parlourn Hajja fatee yana shiga mum na fitowa daga bedroom d'inta ya gaidata cikin girmamawa ya ajiye briefcase d'inshi bisa kujera yanufi dining area, Hajja fatee da kanta tayi mishi saving tana Mae k'ara jaddada masa yaje gidansu zuhra yabata hak'uri sai binta da toh ya yi, yana gama breakfast yadauki briefcase d'inshi dai-dai lokacin Basmah tafito _Good morning bros_ _morning my 'yar lukuta yau bakida lectures ne?_ Ina da amma sai 2:00pm Okay ya yi kyau in kindawo da wuri ki had'a min fruit salad. Toh tafad'a had'e da bin bayanshi har parking lot tarakashi cikin sigar tsokana tace ka gaida Lucky. Saida ya murmushi sannan yace za taji yaja mota yanufi gate maigadi ya bud'e masa yafita. _2:30pm_ Ansar yafito daga office yana tare da Abdallah wai kai ina za ka je ka ke wannan saurin? Abdallah ya watsawa Ansar tambaya. Bayan na gayamaka akwai magana Mae matuk'ar mahimmancin da nakeso nayi da kai. Ina ruwanka da inda zan je kai da ka ke fita gantalinka na ta6a tambayarka? Huh...Abdallah yata6e baki abin naka ne da matuk'ar daure kai, kullum a irin wannan lokacin ka ke fita ae dole na tuhumeka. Bakada ikon tambayana domin ba zamanka nakeyi ba Shikenan Allah ya kiyaye hanya in kadawo kanemi domin maganar ta k'aruwa ce. Ameen sai kajira in nadawo kayi maganar taka yak'arasa magana had'e da shiga mota kaitsaye makarantar su Anaal yanufa bai wuce _5 minutes_ da tsayuwa ba tafito tare da su zeenat tayi sallama da su tanufo motarshi ta bud'e k'ofa tashiga fuskarta d'auke da murmushi ta gaidata shi. Ya amsa yana kallonta Lucky ya karatu? Alhamdulillah! Ya ja mota suka d'auki hanya ya dubeta cikin kulawa yace jiya fa nasami matsala da mutuniyarki da alama k'arshen rabuwarmu ne yazo. Cikin kid'ima da firgicin ta zaro ido kana nufi yaya Zuhura? ''Kwarai kuwa ita nake nufi. _innalillahi wa'inna illaihim raji'um_ kai kuwa Ya Ansar me ya yi zafi haka wane laifi ta aikata maka da ka za6i kabarta adai-dai lokacin da Ku ke yunk'uri zama inuwa d'aya? Ya yi ajiyar zuciya yashiga bata labarin abinda yafaru bai 6oye mata komai ba. Mamaki ne ya baibayeta daga bisani ta dubeshi cikin natsuwa da kwantarda murya, tabbas yaya Zuhura ta tafka babban kuskure duk da haka bai kamata kace kafasa aurenta ba ko don albarkacin tsawon lokacin da ta share, tana jiranka ga kuma dangantaka ta jini da ke tsakaninku. Ka dai k'ara hak'uri kacigaba da lurarda ita har Allah yasa tagane. K'atuwar harara ya wulga mata cikin b'acin rai yafara magana banta6a tsanmani Lucky bakya k'aunata ba sai yau yarinyar da tak'are min zagi uwa da uba ita ce za ki ce na cigaba da zama da ita, wallahi ko ita ce autar mata na barta. "Na shiga uku Ya Ansar me kawo maganar rashin k'auna anan? Daga kai har yaya Zuhura kuna masifar son junanku a tunanina bai kamata abu d'an k'ank'ani ya zama silar rabuwarku. Mtcsww..ya ja guntun tsaki kurciya ke damunki Lucky ke k'aramar yarinya ce, banda shirmen kurciya irin naki ta ya za ki danganta zagi a matsayin d'an k'ank'anin abu? Ya Ansar kenan ni a ganina in har son da ka ke yi wa yaya zuhra na gaskiya ne za ka iya shanye duk wani cin zarafi da takeyi maka domin tun asali kasan halinta kasan wacece ita duk da haka ka za6e ta, sai yanzu da tafiya tayi nisa za ka bijiro da irin wannan babbar magana. Kinga Lucky in har ba za ki iya gayamin maganganu masu dad'i da sanyaya zuciya kibarni naji da b'ac[truncated by WhatsApp]*SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *21* _ina alfahari da ke Ummi A'isha Allah yabarmu tare tawan_ Note:- _masu yi min magana a pc na turo musu SONKI NE SANADI daga farko Dan Allah kuyi min uziri ba zan iya ba ku nema a blog d'ina da fatan za Ku kar6i uziri na karku danganta hakan da wulaqancin_ Ikon Allah Anaal tafad'a baki bud'e ka ga bawan Allah ni fa banina kai zomo kasuwa ba rataya akabani. Da can kasan za ka iya ji da b'aci ranka wayace kafad'amin? Tak'arasa magana tana murgud'a baki. Ta k'asan ido ya dubeta ya yi murmushi Saboda nasan za ki kwatarmin da hankali ta hanyar dad'ad'a kalamanki. Huh.. Ta ta6e baki Indan fad'anka ne da yaya zuhra ba mai shiga saidai a ba Ku hak'uri, kamar gobe ne za Ku shirya bakaji ance fushin masoyi hutu? Tsaki ya ja mtcsww! Lallai a wannan karon zan shayarda ke zallan mamaki. "Dariya tayi cikin dariya tace sau nawa kanamin irin wannan cika baki? Bansaniba yafad'a a fusace. Anaal tak'ara kyalkyalewa da dariya tana lek'on fuskarshi Ya Ansar na yaya zuhra Allah nuna min ranar aurenku. Ba ameen ba bakinki ya sari d'anye kashi. Tak'ara tintsirewa da dariya, banza ya yi da ita ya mayarda hankalinshi ga driving traffic lights ya tsayarda su can! Ya hango Mae siyarda rakke yasauke glass ya kirashi yanka mun ta N500 Mae rakke jikinshi na rawa yashiga yankawa. Anaal ta zaro ido rakke N500 bawan Allah duk kai kadai wannan zarin har ina? Harara ya galla mata ina ruwanki k'udinki ko nawa? Na ka iya nawa kallo tafad'a tana murmushi. Ya kar6e rakkenshi ya d'ora ledan a cinyarta dai-dai lokacin aka basu hannu ya ja mota batare da ya kalleta ba yace Lucky taimaka ki tsaga mun Me zan tsaga ma? Rakke! Yaf'ada kaitsaye. Au! Dama ba ka iya tsagawa ba ka siya? Ban iya ba in za ki tsaga mun bissimillah! In kuma bara iya ba karki cika ni da surutu. "Ta ta6e baki ta bud'e leda taciro rakke gudu d'aya tashiga tsagawa, tana cikin tsagawa ta dube shi ina fatan kana da labari ba'ashan rakke ana driving? Dariya Ansar ya yi ke dallah banason iyayi in kin tsaga gutsuro min. Ta gutsira taciro ta daga bakinta ta mik'a masa ni dai ba ruwana mutum zai sha raguwar yawuna, tafad'a tana dariya. Ae ba yau nafara sha ba balle ki tayarmin da hankali. Murmushi kawai tayi bata k'ara cewa da shi komai ba. Yana isa inda yasaba drooping d'inta ya yi parking ya kashe mota, ya dubeta anatse ki k'arasa ladanki mana Wane lada? Ki k'arasa tsaga mun rakke Wanda nasha bai isheni ba. "Ta girgiza kai batare da tace komai ba tacigaba da tsagawa tana mik'a masa gard'in rakke yaja su Sam sun manta a inda suke ga ra6ar Ac na ratsa su, tsawon lokacin suka dauka a wurin batare da sun saniba kiran sallar la'asar ne ya ankarar da su zaro manyan idanunta tayi tana kallon Ansar Wanda yashagala da shan rakkenshi. Na shiga 3 Ya Ansar kiran la'asar ne akeyi? Kasa magana yayi sakamakon dad'in rakke sai girgiza kai ya yi, guntun rakke da ke hannunta tajefa mishi had'e da cewa ashe agogon motarka dai-dai yake shine da na tambaye ka kace min ba dai-dai yake ba. Dariya yasa kinga mallama miye abin tayarda hankali? Bansaniba tafad'a tana kiciniyar bud'e k'ofa. K'asa bud'ewa tayi ta juya tana kallonshi ta marairaice Dan Allah Ya Ansar bud'e min Allah sai Abbah ya tuhume ni ina na tsaya. Ya lumshe idanu daga bisani yaware su akan fuskarta narasa dalilin da yasa duk lokacin da nake tare da ke banason mu rabu. Ta kad'a kwayar idonta ni nasan dalilin sai ka bud'e min k'ofa zan fad'a maka. Yana dariya ya bud'e mata tana fita tayi mishi gwalo nima bansaniba sai ka tambayin kanka, tajuya tai tafiyarta sai da yaga ta6acewa ganinsa sannan yaja mota cike da shauk'in sonta. _8:03pm_ Ansar yadanno hancin motarshi afarfajiyar gidansu zuhra ba don ranshi naso ba ya zo gidan sai don matsanta mishi da Hajja fatee tayi. Yayi parking yanufi wajen Abbah, bayan sun gaisa Abbah ya tambaye shi ba'asin abinda yahad'ashi da zuhra Ansar bai 6oye mishi komai ba tirya-tirya yabashi labari. Nasiha sosai Abbah ya yi mishi akan yak'ara hak'uri dama aurin gida ya gadi haka. Ansar ya bishi da toh ba wai don ya aminta da kalmar hak'urinan da Abbah yace ya yi ba saida yasha ataye{green tea} sannan yanufi cikin gida kaitsaye part d'in Hajiya saudat yanufa, da sallama yashiga parlourn gidan mutane gidan suna zaune tsabar wulaqancin ba Wanda ya amsa mishi ya durk'usa ya gaida Hajiya saudat adak'ile ta amsa duk da wannan tsohon wulaqancin da akayi mishi bai sa ya yi k'asa da guiwa ba. "Yanemi kujerar da ke facing zuhra ya zauna cikin tattutasan lafazi yafara magana Hajiya dama zuwa nayi na ba Ku hak'uri akan abinda yafaru jiya sharrin shed'an ne da kuma laifin zuhra da tarufe ido tak'are min zag.....kai mallam dakata! Hajiya saudat ta daka masa tsawa cikin hargowa ta taso kamar za ta dake shi, idanunta suka k'ank'ance tsabar masifa da bala'i ta d'age lebb'e sama tafara zazzaga masa rashin mutuncin ba shakka Ansar ka cika cikakke maras kunya ka dake 'yar tawa don tsabar iskancin da kazar uba ka debo k'afafunka ka zo gidanan bakinka d'auke da Kalmar ban hak'uri. "Toh da hak'uri ta mutu sadaka nawa tabaka? Kai! Bari ka ji tanuna shi da yatsa ka gaugauta bud'e fatun kunnuwa ka guda 2 da Allah{s, w, t} ya albarkace da su ka saurarani da kyau domin gargad'in na farko na kuma k'arshe zan kashe maka. "Zuhra ba baiwar ubanka bace da za ka ware kwanji ka daketa Ansar ya zaro ido cike da firgicin yana kallon Hajiya saudat. Zuhura ta kad'a kai tana yatsinar fuska tace fad'a mishi dai Hajiya shi ana shi rashin basira yadauka ni baiwar gidansu ce. "Idan ma yadauka yasauke domin ba ki gadi bauta ba Hajiya saudat ta kar6e zance wannan ya zama maka auta ya zama maka d'an fari duk ranarda shed'ancinka ya tashi kasake dukan zuhra wallahi, ta'allahi! Sai na kafa tarihi akanka nan da ka ke ganina ba k'aramar 'yar tasha bace. ''Ansar ya ta6e baki yace ae naga alama. Ba ka ma ga alama ba sai tsautsayi yasake d'ebarka ka dake zuhra alokacin za ka zahiri, kai! bari nayi maka ta mahaukata ko aureta ka keyi ka daketa sai nai maka wanka tsalki, ballantana ba uban da ya zarga mata igiyoyin aurenka, ina fatan ka fahimcin karatun nawa? "Gyara zama Ansar ya yi yana kallon Hajiya saudat anatse na fahimta Hajiya kiyi min gargad'in mai cike da kaukausar murya, watakila ke daga bakinki kadai yafito ni kuma zan fad'a miki abinda yake k'asan zuciyata ya d'an numfasa. "Hajiya zan iya shanye komai amma ba zan lamunce ana cin zarafin iyayyena ba ta hanyar zunduma musu zagi, ni dai naga zuhra nace inaso ba Wanda yahad'ani da ita tun kafin rayuka su b'aci kafin ta kai har kiyi min wankan tsalki ni zan yi wa kaina domin na sauk'ak'a miki debo ruwa, Hajiya na hak'ura da zuhra Allah ya had'a kowa da rabonsa na alkhairi. "Jikin zuhra yadauki rawa idanunta suka fito turu-turu numfashinta yafara kai kawo, murya na rawa tace haba! Ya Ansar yanzu adalilin wannan d'an k'ank'anin abu za ka barni? "Kallo mai cike da k'ask'ancin yake mata ke a wurinki yake D'an k'ank'ani amma ni awurina yazarce duk yanda ki ke zato, wallahi a yadda nakeji zuciyata tana k'una da tafarfasa ko aurenki nakeyi zan iya dank'ara miki saki d'add'aya har saki 3 sai gashi kin taki sa'a mahaifiyarki da bakinta tace ba uban da ya zarga miki igiyoyin aurena da yau kinga tsiya ta zahiri. Jeeddah Aliyu[6/28, 8:49 PM] YAYA HAYAT: *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* _wannan shafin naki ne qanwata ta kaina Khadijat Abdullahi shehu{Hajja ce} na gode da irin k'aunar da ki ke nuna min_ *22* Hajiya saudat tasaki baki galala tana kallon Ansar bata ta6a tsanmani wannan kalma za ta iya fitowa daga bakinshi ba, sakamakon yanda tasan yana matuk'ar son Zuhura. Kukan Zuhura ne ya katse mata zance zuci, ta dubeta ta daka mata tsawa ke! Daiña rok'onshi ko giyar wake yashi bai isa yace yafasa aurenki ba. Bayan yasan kin share tsawon lokacin kina zaman jiranshi. "Zuhura ta dube Hajiya tana kuka haik'an Hajiya kinji abunda yafad'a wallahi da gaske yakeyi, na shiga 3 na lalace Hajiya ba zan iya rayuwa ba Ya Ansar Dan Allah ki bashi hak'uri tak'arasa magana had'e da rik'o hannun Hajiya saudat. "Buge mata hannu Hajiya tayi wai ke wace irin banza yarinya ce? Namiji ki ke wa kuka ashe duk iskancin da yake miki ke ki ka siya da k'udinki, don yafasa aurenki sai me? Shine autan maza da za ki zubarda hawayenki a wofi? Mtcsww! Ansar ya ja tsaki ya mik'e da gudu Zuhura tanufi wajenshi ta zube gabanshi tana kuka kamar ranta zai fita, ta cukume k'afarsa ka dubi girman Allah Ya Ansar ka yi hak'uri kayafemin in kafasa aurena zan iya haukacewa kai kadai zuciyata takeso sharrin shed'an ne na gane kuskurena ba zan k'ara sa6awa umurninka ba. Kallon sama da k'asa ya yi mata yafincike k'afarshi da k'arfi, ba hauka ba idan kin iya ki had'e zuciya ki mutu ba abinda yashafe ni. Yajuya cikin zafin nama yanufi k'ofar fita Zuhura ta zabura da gudu ta bi bayanshi tana kwalla masa kira. Nazeeya ta dube Hajiya wance tun zamanta parlourn sai yanzu ta tofa albarkacin bakinta anya Hajiya Ya Ansar banza yabar yaya Zuhura kuwa? kalli yanda ta daka da gudu ta bishi, sai kace zararriya. Takaicin yak'ara turnuk'e Hajiya tace ba abinda ya yi mata tsabar dakarci da komawa baya ne yake dawainiyya da ita. Ta6e baki Nazeeya tayi idan kuwa haka ne yaya Zuhura na cikin wahala ni yaushe zan d'auki soyayar k'ato nasa araina har yasame damar wulaqantani haka. Yana isa parking lot Zuhura na karasawa ta ware hannayenta ta tare masa k'ofar mota, ka ji tausayina Ya Ansar karka juya baya wallahi inasonka fiye da tunaninka. Tsanarta ce tak'ara baibaye shi na tsaneki Zuhura tsana mai tsananin gaske na gwanmace na mutu da na aure jahila, dak'ik'iya irinki yatureta yashiga mota ya ja ta da k'arfi dai-dai Anaal tafito daga BQ wurin Ammah, Zuhura ta bi motar da gudu tana kuka had'e da kururuwa afirgice Anaal ta watsarda kayan da ke hannunta ta daka tsalla ta koma gefe atunaninta Ansar zai bankad'e ne sakamako yadda ya ja mota yanufo ta gadan-gadan, tun kafin yak'arasa Abbah ya bud'e masa gate. Zuhura tana gani yafice tak'ara fasa ihu mai k'aran gaske, tafad'i k'asa cikin kid'ima Anaal tanufi wajenta tad'ago ta lafiya yaya Zuhura mekike yiwa kuka? Kuka yaci k'arfinta ta dank'e hannun Anaal saboda tsabar kuka muryarta bata fita sosai _Anaal Ya Ansar yace yafasa aurena, ni kuma ba zan iya rayuwa ba shi_ "Ajiyar zuciya Anaal tayi cikin laushin murya tafara magana fad'a kawai yakeyi don yad'aga miki hankali shima ba zai iya rayuwa ba ke. Kiyi hak'uri kitashi mu Shiga gida yadda yatafi haka zai dawo da kanshi. Da kyar Anaal ta ciyo kanta tashiga gida. _BAYAN KWANA UKU{3 DAY'S LATER_ A parlourn Granny bakajin komai sai sautin kukan Zuhura hawaye sha6e-sha6e majina na fita daga k'ofofin hancinta cikin kwanaki 3 tafita hayyacinta walwala da farin ciki sun k'aura gareta saboda ta tabbata za'a sha artabo kafin Ansar ya amince da zance aurensu. Ansar yashigo bakinshi d'auke da sallama daga Hajja fatee sai Granny ne suka amsa masa, tun kafin ya zauna Daddy yafara 6al6ale shi da masifa wannan wane irin shashshacin ne za ka barmu zaune muna jiranka sai kace wasu sa'annika? Kayi hak'uri Dad koda ka kirani ina bacci sai da nayi wanka da sallah sannan na fito. Mtcsww! Daddy ya ja guntun tsaki ya dube Ansar da masifafin idanunshi Wanda su kadai sun isa su murd'a antar cikin k'aramin jarumi sa6ani Ansar da ko darr! Bai ji ba saboda shi ma irin idanun yake d'auke da su. Kai! D'ago ka kalleni da kyau Daddy yafad'a cikin kaukausar murya mai cike da b'acin rai, Ansar yad'ago yana kallon Daddy ido cikin ido ba ko tsoro balle fad'uwar gaba atare da shi. "Yayin da Daddy sake dank'e fuska Boy wace maganar banza ce ka zo da ita agidanan? Sadda kai k'asa Ansar ya yi cikin tausasa halshe yace Allah ya huci zuciyar Daddyna ba maganar banza bace. Magana ce mai Mae ma'ana nazo da ita ataimaka a dubi uzirina da idon basira. Daddy ya kad'a kai ya yi k'yaci ya kafe Ansar da idanu kenan duk abinda aka zaiyana min akanka gaskiya ne? Eh! Toh ba zan iya cewa eh ko a'a ba domin bansan me akace da kai ba iya abu d'aya nasan yakeda mahimmancin ko iyayyemu kusani ba wai cin fuska ko tozarci ba a'a sai don gudun lalacewar zumuncinmu. Dad, Alhaji yakira sunayensu ku gafarce ni adalilin wannan maganar da zan fad'a tun farko ni nace inason Zuhura ayanzu kuma ba zan iya aurenta ba koda daga ni sai ita mukayi saura aduniya. "Yana dasa aya zuhra tasake barkewa da kuka, Alhaji yadaka mata tsawa ke! Dallah ki yiwa mutane shiru, shi yake iko da kanshi ne da zai yanke irin wannan d'anye hukuncin? Daddy yad'agawa Alhaji hannu ya isa sa'eed ba don Alhaji yaso ba yahadiye sauran kalamanshi. Zuciyar Daddy na tafarfasa yafara magana Boy idan har ni ne na haife ka nakeda cikakke iko akanka daga yau sai yau karna k'ara jin magana kwatankwacin wannan tafito daga bakinka, aure kuma da kai da Zuhura ba bashi muddin ka ga ba ka aureta ba bana numfashi kaje kafara shirye-shiryenka nan da sati 3 za'a d'aura aurenku Zuhura tayi azumi ad'akinta. Ansar jarumin namiji ko kad'an bai razana da jin wad'annan kalaman na Daddy ba, saima wani mushirikin murmushi da ya yi nan take kwakwalwarshi ta lalla6o masa mafita ya gyara zama cikin ladabi da kwarewa da sace zuciyar iyayye yafara magana godiya nake Daddyna duk hukuncin da ka yanke akaina dai-dai ne bana fatar zuwan ranar da zan yi jayaya da umarninka, amma nima yakamata ayimin uziri abar zance aurenan zuwa bayan sallah da sati 2 kafin lokacin na kamalla gini na. Controller Basheer Galadima ya yi murmushi da ke baiyanar da jin dad'inshi indan wannan ne karka damu ina da gidaje sai ka za6i d'aya daga ciki. ''Girgiza kai yayi no! Daddy ni nafison nawa ko Zuhura tafi sonshi kayi hak'uri abar aurenan zuwa bayan sallah kamar gobe ne in ga rai da lafiya. "Kafin Dad yabashi Amsa Granny tayi karaf tace shikenan Ansaru Allah yanuna mana bayan sallah. _Ameen Granny_ Ansar yafad'a yana murmushi mugunta ya mik'e yace Daddy ni zan fita akwai documents d'in da nakeso amsa wajen Alhaji Faruq gidan Rina. Adawo lafiya Allah yasa Ansar yafad'a had'e da ficewa daga parlourn. Jikin Zuhura na rawa ta bi bayanshi, Ya Ansar! Ya Ansar! Ya tsaya cak batare da yajuya ba ta gabanshi ta tsaya tana kallonshi tana murmushi Yayin da shi kuma yake mata kallo Mae cike da tsana fuskarshi ahad'e yace ya akayi ne? Dama Ya Ansar hak'uri ne zan ba ka. Ki adana kayanki watakila nan gaba zai miki amfani domin ba wannan bane right time da ya dace ki Kalmar hak'uri tafito daga bakinki ba. Yana k'arasa magana yanufi motarshi yafizgeta da k'arfin tsiya. Mtcsww! Zuhra ta ja tsaki can! Ta matse maka Mae bak'ar zuciya da fad'in ran tsiya ubanka yariga ya kashe Boss kai baka isa ka tada shi ba. Za ka gaji da cin ranka ne kadawowa zuhra wallahi ni da kai mutu karaba ne takalmin kaza. _1 WEEK LATER{BAYAN SATI D'AYA}_ Ansar yana zaune a office d'inshi Abdallah yashigo da file a hannunshi, ya zauna had'e da mik'awa Ansar file ka duba documents d'in gidan ne ka daure Ansar ka siye gidanan wallahi za ka ji dad'inshi koda anan gaba ne. "Ajiyar zuciya Ansar ya yi akasalance yace wai kai miye matsalarka na matsanta mun na siye gida bayan kasan banada buk'ata da shi? Ba za ka gane bane Ansar ajiye kadara komai k'ank'anta ta yana dad'i da amfani ni kaina narasa dalilin da yasa nakeson ka siye gidanan. Shikenan naji zanyi magana da Dad in ya amince sai a siya. 6ata fuska Abdallah ya yi haba! Ansar komai kace sai Dad yasani wannan bayi bane, 10 millions ne bakada a account d'inka da za ka ce sai Dad yasani? Shiru Ansar yayi yana nazari da sauri Abdallah ya katsi shi karka tsaya tunani ka zari k'udi kawai mallam ka siye wannan gidan zai maka amfani anan gaba. Shikenan naji na amince zan siya anjima da yamma sai muje naga gidan in yaso on Monday sai abiyasu k'udinsu kace dai na KB ne? Eh! Nashi ne. ''okay ba matsala. _Zuhura_ Tun zuhra nasaka ran Ansar zai zo yabata hak'uri kamar yanda yasaba mata, sai taji shiru wai mallam yaci shirwa gaba d'aya yak'auracewa zuwa gidansu ita kuma d'an banzan girman kanta yahana tanemi shi. A6angagare d'aya kuma Ansar yana had'uwa da taurarwarshi Anaal yakaita school yadauko ta da dare yakira ta a waya su raba tsakiyar dare suna waya cikin d'an k'ank'anin lokacin ya yi nasarar saye zuciyarta soyayyarshi mai zafin gaske ta kanainaye mata zuciya tun daga lokacin Anaal tashiga wani yanayi domin Ansar ko da kuskure baita6a Sa6ul da bakan furta mata Kalmar so ba shiyasa take tausayin kanta gashi suna daf da fara final exams batada lokacin karatu sai na tunanin Ansar. Jeeddah Aliyu [6/28, 8:49 PM] YAYA HAYAT: *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *23* Yammaci ne mai d'auke da sanyaye iska su Kansu bishiyoyi suna jin dad'i yadda suke kad'awa. Anaal ce tsaye a k'ofar gida tare da malamin islamiyyarsu mallam Naseer sai doka murmushi take. Ansar yadanno hancin motarshi tun kafin yak'araso ya hangota rass!rass! Gabanshi yafad'i ba Shari yataka birki zuciyarshi tashiga tafarfasa masifafen kishi ya lullu6e shi gumi sai tsiyayo mishi yake, yaja numfashi da k'arfi yak'urawa Anaal ido dai-dai ta rufe fuskarta da gefen hijabinta da alama malam Naseer yagaya mata maganar da tasata jin kunya. Ansar yasake harzuk'a yana kallo har suka gama fira malam Naseer ya hau mashin d'inshi yawuce shi fuuu! Binshi da kallo Ansar ya yi ya ja tsaki mtcsww! Yafito daga mota Anaal na k'ok'arin shiga gida ya kwalla mata kira Lucky! "A rud'e tajuyo saboda yanda muryarshi ta ratsa dodon kunnenta, jiki asanyaye tanufi wajenshi lah! Ya Ansar Kaine? Harara ya zuba mata ahasale yafurta bansaniba wane k'ato ne naganki tare da shi? Ta zaro ido tay kamar taga abin tsoro Ya Ansar ba k'ato bane malaminmu ne na islamiyya malam Naseer shi yake d'aukarmu daras...ke dallah! shiru kin saki baki sai zuba ki ke yi don yana malaminku sai me? Ae bashida hurumin da zai zo gidanku ko kece ki ka gaiyyace shi? Girgiza kai tayi. Toh! Me yazo yi wajenki? Hmm!Uhm! Cewa ya yi wai yana Uhm!.... Yana me ya katseta cikin tsawa Tak'ara rud'ewa haba! Ya Ansar miye kuma na daka min tsawa? Tsareta da idanu ya yi yana cika yana batsewa jin yake kamar ya kwada mata mari. "Wai lafiya Ya Ansar kai tsarini da masifafun idanunka? Ya motsa sumar kanshi ya yi had'e da lasa lips d'inshi na k'asa takaicinta yak'ara kamashi. Nunata da yatsa ya yi look! Anaal karki rena min hankali za ki fad'amin abinda wannan k'ato ya zo yi a wajenki ko kuwa? Innalillahi wa'inna illahim raji'um! Haba Ya Ansar Dan Allah Kadàina kiran malam Naseer da k'ato ba fa wani abin tashin hankali bane cewa kawai ya yi yana sona. "Dif wutar kan Ansar ta d'auke yashiga muzurai yana kallon Anaal, tsawon _20 seconds_ yadauka ahaka daga bisani yace ke kuma wace amsa ki ka bashi? Kanta asunkuye tace cewa nayi yabani lokacin zanyi shawara da zuciyata. "Bakya buk'atar shawara da zuciyarki ba sai kin wahalarda shi ba ki fad'a masa bakya sonshi. Ba ki shirya yin aure ba karatu za ki yi. Girgiza kai tayi cikin sanyinta tace ba zan iya ci masa fuska nace bana sonshi ba malam Naseer yana da matukar k'ima da daraja a idanuna, bai kamata kaitsaye na fad'a masa irin wannan maganar ba. "Ranshi a b'ace yake kallonta kwaryar idonshi ya kad'a ya yi jajur, da kyau Lucky Yau kin nunamin banida matsayin a wurinki kinfifita wani akaina shi kina gudun b'acin ranshi ni kuma bakya gudu nawa kije kicigaba da soyayya da malam Naseer ni na amince da shukar da nayi ba Wanda ya isa ya gir6e ta. Batare da yajira abinda za ta fad'a ba yajuya cikin tafiyar sauri yashiga motarshi ya fizgeta da k'arfi. Anaal tayi tsaye sororo tana mamakin wannan k'arfin halin na Ansar jikinta amace tashiga gida kaitsaye BQ tanufa tashige d'akin Ammah ta tararda Ammah na cikin gida tafad'a kan mattress tayi ruf da ciki, tarasa me kedamunta duk duniya ba abinda ta tsana take adawa da shi irin fushin Ansar ahankali hawaye ke zuba daga idanunta suna sauka agefen wuyanta, cikin tausayawa kanta tafara magana da zuciyarta kaicho na ni Anaal na kamu da son abinda ba zan ta6a samu ba meyasa nayi sake zuciyata ta kaini mahalaka? Zuciyata tana sonka Ya Ansar so Mae tsananin gaske, saidai kashe! har abada ba zan sameka ba shiyasa na yanke shawara zan mallakawa waninka zuciyata duk nasan ba wani d'a namiji da zai goge shafin sonka azuciyata. Kuka mai sautin gaske ya kubce mata taja pillow ta daura akanta yadda ba za'a jiyo kukan nata ba, saida taci kukanta Mae isarta tashare hawayenta, adaddafe tayi sallah magarib da isha ta lalla6o wayarta ta kira Ansar wayar na ringing yak'i dauka bata hak'ura ba tacigaba da kira almost 5 missed call tayi mishi yak'i picking tayi mishi text tana rok'onshi da yadauki kiranta ya yi banza kamar bai ga text d'in ba. "Anaal tak'ara rikicewa hawaye na abaliya afuskarta tana sake kira taji ya kashe wayarshi, ranar bata runtse ba ta matsu garin Allah ya waye su had'u tabashi hak'uri ko za ta sami kwaciyar hankali. . *6:48am* Anaal tafito cikin shirin tafiya makaranta tawuce BQ ta gaida Ammah sannan tanufi bakin gate, wajen Abbah yabata k'udin breakfast. Cikin natsuwa da kamun kai take tafiya har ta isa inda tasaba had'uwa da Ansar har ltagaji da tsayuwa ba Ansar ba labarinsa tanemi wani k'aton dutse ta zauna tafito da wayarta daga schoolbag d'inta ta kira shi still wayarshi arufe idanuta suka ciko da hawaye kiris take jira ta fashe da kuka ta maida wayar inda tadauko ta karo na farko arayuwarta da ta6a makara _8:30am_ dai-dai ta mik'e taja sanyayu k'afafunta tanufi bakin titi ta hau adaidaita. Har aka tashi breakfast ba abinda ta fahimta daga cikin darussa da aka koya musu bayan classes suka nufa ita da su Ramlat. Zeenat tanufi shop d'in siyarda snacks da drinks tasiyo musu Ramlat da zeenat suna cin snacks suna korawa da drink sa6ani Anaal da ta rafka tagumi, zeenat ta dubeta cikin kulawa tace 'yar Agadez meke damunki ne? Tasauke ajiyar zuciya Mae k'arfin gaske tayi rau-rau da ido, sani tayi za ta same kyakyawar shawara daga k'awayen nata yasa ta fede musu biri daga kai har wutsiya ba abinda ta 6oye musu cikin rauni murya da neman mafita tacigaba da cewa, ni kaina basan lokacin da nakamo da matsananciyar soyayyar Ya Ansar ba. Narasa inda zan jefa kaina da wannan abin kunya, Ina tausayawa kaina domin koda ba soyayyar yaya Zuhura azuciyarshi ba abinda zai yi da ni tak'arasa magana had'e da kifa kanta a cinyoyinta tashiga rera kuka Mae tsuma zuciyar Mae saurare. Zeenat ce tayi karfin halin dafa kafad'arta tace hak'ik'a 'yar Agadez kinfad'a tarkon so Mae wuyar fita, inaso Kisani ba wai don akwai baiko tsakanin Ansar da Zuhura zai hanaki sonshi kada wannan ya sanyaya miki guiwa duk Wanda yasan alamomin so tabbas yasan ke da Ansar kunyi zurfi a son junanku a rikice Anaal tad'ago jajaye idanunta ta watsa su akan fuskar zeenat numfashinta na hawa da sauka. Zeenat ta gyad'a mata kai ki yarda da duk wani furucin da zai fito bakina, Ya Ansar yana sonki Anaal kawai dai bai furta miki bane amma ga dukan alamu shima yana sonki don haka ki kwatar da hankalinki akwana atashi wata rana zai fad'a miki sirrin da ke zuciyarshi. Ramlat ta kar6e zance ta hanyar cewa kinga saura 2 weeks mu fara exams rashin kwanciyar hankalinki zai iya shafar exams d'in da za ki rubuta, idan Allah ya k'addara sai Ansar ya aure Zuhura ba za ki rasa gur6i ba zai iya aurenki saboda shi mijin mace hudu ne. kidaina haramtawa kanki Ansar domin Allah bai haramta aure a tsakaninku ba, koda ace akwai dangantaka ita jini tsakaninki da Zuhura ballantana babu ki rufe idanunki ki toshe kunnayenki karki daka ta munafukai kicigaba da son Ya Ansar har Allah yanuna mana ranar da shima zai furta yana sonki. Da wannan gurguwa shawara Anaal ta zauna akai daram! Ta shiryawa tunk'arar kowane k'alubali ta sha arwashi mutuwa kadai ta isa ta ja Katanga tsakaninta da Ansar duk abinda zai faru saidai ya faru Mae rabata da Ansar sai Allah. _hour's later_ Anaal tsaye a inda Ansar yasaba zuwa d'aukarta, tun tana tsaye har ta koma zaune ba Ansar ba labari har d'alibai 'Yan uwanta suka watse tass! Kowane ya tsufa agidansu amma ita tana zaune ta rafka tagumi lokacin-lokacin tana share hawaye da bayan hannunta. Ta kira wayarshi yafi akirga tana rufe. Daga k'arshe dole ta hau adaidata tanufi gida. Da dare ta zuba ido ko zai zo shiru bai zo ba .ranar ko kad'an bata runtsa ba bacci yak'auracewa idanunta damuwa ta lullu6e ta ciwo so ya yi mata katutu a zuciya. Jeeddah Aliyu [6/28, 8:49 PM] YAYA HAYAT: *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *24* _Few day's later_ Ansar yagaji da shan k'amshinsa yadawo da kanshi, ana tashi school Anaal tana fitowa ta hango motarshi, wani irin sanyi dad'i ya ratsa k'asusuwan jikinta ba shiri ta k'ank'ame hannun Ramlat jikinta na bari tace _wayyo friends Ya Ansar d'ina ya zo ina zan sa kaina wayyo dad'i zai kashe ni_ dariya sosai Zeenat da Ramlat sukayi Ramlat ta fizge hannunta tace kinshiga 3 'yar Agadez ba ko jan aji kinfara zumud'i. Wane aji zan ja? Ae yanzu ba sauran Jan aji tun da nayi sake zuciyata kamu da sonshi babban takaicina kada ya yi sauri hal6o jirgina. Hmm..toh gaskiya yakamata ki kiyaye ki koyi ta yanda za ki dinga boye sirrin zuciyarki wannan zumud'i da ki ke yi kamar mayye ya yi bak'o nan take zai gano ki. Zeenat tak'arasa magana tana Mae kallon fuskar Anaal. Ansar yafara gajiya da zama yaga Anaal batada niyar sallama da k'awayeta sai ma Sabon shafi ta bud'e na fira yadana horn, zeenat turata ga dukan alama yafara gajiya kitafi kawai gobe za mu k'arasa magana. Anaal tajuya tanufi wajenshi fuskarta ahad'e sai da ta isa daf da shi ta ra6a tawuce kamar batasan da zamanshi ba, mamaki ne ya lullu6e shi musanman da ya hangonta tana tsayarda Mae adaidaitasahu baisan lokacin da yafito daga mota ba yanufi wurinta da sauri. Muryarshi asark'e yafurta Lucky ba ki ganni bane da za ki tsayarda Mae adaidaita? A yatsine ta dube shi ta kauda fuska tacigaba da sha'anin gabanta, yanda tasha toka yai masifar burgeshi yakafe ta da idanu kinga Lucky ni fa yayanki ne bai kamata ki yi min wulaqancin akan titi ba kishiga mota mu tafi in yaso a mota ki sanarda ni laifi da nayi. "Tayi shiru na 5-7 second's daga bisani tajuya tashiga mota ya yi murmushi ya zagaya yashiga ya ja motar suka tafi tun shigar shi mota Anaal ta kauda fuska tana, kallon titi. "Anaaal ya kira sunanta cikin tattausan lafazi had'e da jan sunan batare da yajira ta amsa ba yacigaba da cewa wai fushi ki ke yi da ni? Shiru ba amsa sai ma sake mayarda hankalinta kan titi da tayi. Ni yadace nayi fushi da ke Lucky ni da na baki umurni amatsayina na yayanki ki kasa bi, sosai raina yab'aci yanda ki ka nuna ban isa da ke ba. Sai daga baya nayi dogon nazari nagano ko kina son malam Naseer shiyasa ki ka bad'a min k'asa a ido. Da k'arfi tajuyo tana kallonshi tayi rau- rau da idanu hawaye suka fara kara-kaini a kumatunta,dama Anaal raguwar zuciya ne da ita d'an k'ank'anin abu ya isheta kuka batada juriya ko kad'an. Jikinshi yabashi tana kallonshi yana juyawa yaga hawaye kwance a kumatunta. Ya gangara gefen titi ya yi parking had'e da kashe mota. Hankalinshi atashe yafara magana haba! Lucky miye kuma abin kuka? Ko kinsan babban tashin hankalina naganki cikin b'acin rai? Ba zan iya juri ganin hawaye akan fuskarki ba Ki taimake ni kiyi gaggawa ki goge su, tun kafin ki jefa zuciyata cikin mayauwacin hali. Bayan hannunta tasa ta goge hawaye saidai takasa tsayarda su, Ansar yak'ara rud'ewa jikinshi na rawa yafito da handkerchief fari kal da shi ya mik'a mata. ta kar6a ta goge fuskarta harda su fayyace majina, da sauri Ansar ya d'auke fuskarsa yana yayatsine fuska. Ta maido masa da handkerchief d'in ba yanda ya iya dole ya amsa, ya gyara muryà yafara tsarata lucky banaso na takura ki indan aure ki ke so ki fad'amin na fitarda rai akan karatunki da nake da burin ki yi. Ko inason aure wa kake tunani zan aura bayan na riga na mallaka maka zuciyata, kai nakeso Ya Ansar sonka yariga ya mamaye ni. "Lucky please ki yi magana kin tsare ni da idanu ba ki ce min komai ba ya katse mata zancen zuci. Tayi ajiyar zuciya Mae k'arfi ina mamakin yanda ka kasa fahimta ta Ya Ansar ba son malam Naseer azuciyata asalima, soyayya bata gabana burina nayi karatu Mae zurfi gaske yadda zan taimakawa dangina na tallafawa iyayyena su fita daga rayuwar gadi. Farin cikin marar misaltuwa ya lullu6e shi cike da jin dad'i yasake yiwa mota key, ya dubeta cikin shauk'in so yace kalamanki sun gusar min da fargaba da tsoro da nake ciki ba malam Naseer kadai ba Lucky karki sake ki kula kowane d'a namiji da sunan soyayya yin hakan zai iya haifarda gagarumar matsala a karatunki. Naji Ya Ansar insha-Allah zan kasance Mae biyayya ga dukan abinda ka umurce ni. Ya lek'a fuskarta yana dariya da kyau my Lucky hakan nakeso ji daga bakinki. Da sauri ta kauda fuska Haba! Lucky kwana nawa rabona da naga wannan kyakyawar fuska taki ma'a6ociya murmushi, shine za ki haramta min ganinta? Ta juya tana kallonshi ta ta6e baki ba wani nan da ka damu da fuskar da ba ka yi fushi da ita ba. O'o! Abinda yawuce kidaiña tadashi daga ni har ke masu laifi ne, d'an juyo ki haskani da murmushinki yak'arasa magana cikin tsokana. Mak'e kafad'a tayi had'e da furta nak'i. Bakisan cewa in ki ka had'e da fuska bakya kyau ba? Gara kiyi murmushi 'Yan k'anana hak'oranki masu kama da na bera su fito. Anaal batasan lokacin da ta kyalkyale da dariya ba sosai furucinshi na k'arshe yabata dariya, shima yashiga tayata har isa inda yasaba ajiyeta suna kwasan dariya abinsu. Tana fitowa daga mota leebeauty na danno hancin motarta dai-dai lokacin Ansar yafito yana cigaba da tsokanarta tana dariya, jakkar ubanan leebeauty ta furta akid'ime had'e da firfito da idanu tak'are musu kallo tass! Daga bisani ta kyalkyale da dariya har tana had'awa da dukan steering. Ta girgiza kai taja mota kaitsaye gidansu Zuhura ta tanufa bakinta d'auke da mugun labari. Da kyar Ansar yabar Anaal tawuce gida shi kuma yaja mota yakoma office, hankalinta kwance ta tura k'ofar gida tashiga ta gaida Abbah sannan tanufi cikin gidan tun kafin tak'arasa k'ofar da za ta saddata da part d'in Granny ta hango zuhura da leebueaty tsaye kowace fuska kamar ta nagge. Rass! ta tsince kanta da fad'uwar gaba, ke Anaal zo nan...Zuhura ce ta kwalla mata kira kamar kazar da kawai yafashewa a ciki tanufi wajensu, tana zuwa Zuhura ta firzge hannunta tanufi garden leeabeauty ta mara mata baya batasaki hannunta ba saida ta saddata da garden, tayi wulgi da hannunta da k'arfin gaske tashiga zagayenta had'e da k'are mata k'ank'antace kallo daga bisani tafara magana cikin izza da taqama Anaal meke tsakaninki da mijina? Leebeauty ta zo min da wani banzan labari wai taganki amotar Ya Ansar kuna nishad'i tamkar masoya, shine nakeso na gasganta hakan ta hanyar tambayarki menene had'inki da shi? Duk da nasan ba abinda Ya Ansar zai yi da ke ko tsirara yaganki ko darr! Ba zai ji ba domin bakya cikin jinsi matan da yakeso. Jikin Anaal yadauki rawa dama gata da shegen tsoro, kamar farar kura tun kafin tafara magana hawaye yafara wanke mata fuska, tayi yunk'uri bud'e baki takasa kuka yaci k'arfinta ta durk'ushe k'asa tacigaba da kuka. Zuhura ta dube leebeauty tana yatsina tace yanzu kin yarda da abinda nake gayamiki? D'an banzan tsoron Anaal kadai ya isa yahanata son abinda nakeso, ita kanta tasan bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane, duk yawan 'yan mata da ke garinan birjik me Ya Ansar zai yi da ita kalli skin d'inta adalilin saleema tana fara yakek'ashe k'asa yace ba zai aureta ba Anaal tafi saleema fari nesa ba kusa ba, Ya Ansar ya tsani farar mace ba abinda zai yi da Anaal sai in so yake yalasa zumar ta kuma Ya Ansar ba mazinaci bane, ba ta inda hasashenki zai zama gaskiya leeabuearty. Mushirikin murmushi leeabeauty tayi tace ina mamakin yanda ki ka yarda da Ansar Galadima, ko kinmanta da halin d'a namiji ne...? Namiji hankaka ne gabanshi fari bayanshi bak'i amma tun da kin yarda da shi miye nawa aciki.....? Ba shakka leebeauty na yarda da Ya Ansar 100% ba wata 'ya mace da zai so fiye da ni, na mallaki duk wani abu da Ya Ansar yakeso awajen 'ya mace ta ya Wanda yakeda ni me zai yi da Anaal, karki manta Anaal 'yar Matsiyata ce 'yar masu gadi duk duniya ba abinda iyayyen Ansar suka tsana irin fak'iri Anaal kuma fak'iriya ce, ta ko ina nayi mata zarar Ya Ansar kuma yai mata nisa. Zuu kenan lallai idanunki sun rufe Sam bakya hango abunda nake hangowa, na yarda kina da Body structure da Ansar Galadima yakeso amma abin tambaya anan shin kina da kyakyawar tarbiyyar da Ansar Galadima yakeso matarshi ta kasance da ita ko kina da ilmin islama da yake burin matarshi ta mallaka....? Shiru Zuhura tayi takasa bata amsa Toh tun da kin kasa bani amsa ni bara na bawa kaina bakida ko d'aya daga cikin abubuwa da na lissafa, Anaal kuma tana da su Kidàina taqama da kyakyawar sura wani namiji ba ruwanshi da wannan. Komai za ki fad'a ba zan yarda ba Co's ba yanda za'ayi Ya Ansar yaso Anaal never! wallahi, ta6e baki leebeauty tayi cike da takaicin tajuya tanufi k'ofar fita daga garden, Zuhura tabita da harara daga bisani tadawo da ganinta ga Anaal ke kuma bana ko shakka hanya Ya Ansar yarage miki ko ba haka bane tafad'a cikin tsawa..? "Ha...ka...ne Anaal ta amsa cikin rawar murya. ''Daga yau wannan yakasance na farko na k'arshe da za ki sake shiga motar Ya Ansar muddin kinason kanki da arziki, ki nisance shi ba ke ba shi ko karatu da ki ke fad'a masa na kashe karki sake naganki ko naji labarin anganki da shi kinji ko bakiji ba....? Na....ji Kin samawa kanki lafiya da Matsiyatan iyayyenki, tajuya tafice tabar Anaal na kuka nashiga 3 ni Anaal nadaukowa kaina ruwan dafa kaina zuciyata ba ki yi min adalcin ba kin kamu da son mutume da yafi k'arfina, ashe Ya Ansar bayason mace mai irin Body structures d'ina yatsani farar mace mafi alheri atare da ni na rufawa kaina da iyayyena asiri na datse duk wata hanya da zata had'ani da shi. Ta share hawayenta ta mik'e tanufi part d'in Granny sauk'inta d'aya Granny batanan tafita unguwa tawuce bedroom tafad'a bisa gado tayi kwance rub da ciki ta bud'e Sabon shafi na kuka, fuskarta tayi jajur idaunta sukayi luhu-luhu abunka da farar fata. Da tagaji da kukanta ta mik'e tashiga bathroom tayi wanka da alwala ta gama sallah tad'aga hannayenta sama idanunta na fitarda hawaye tashiga rok'on Allah ya yaye mata son Ya Ansar ta Shafa addu'a ta mik'e ta linke pray mat tasaka gown na atamfar deviva wax bata damu tashafa mai ba takoma ta kwanta ta d'auki wayarta tacire battery tayi mata mugun 6oyo, ranar kasa zuwa islamiyya tayi da Granny tadawo ta tambayeta meke damunta sai cewa tayi batada lafiya Granny ta tausaya mata sosai harda su bata panadol extra batasan bashi bane ainihin maganin ciwon Anaal ba. _Dare_ 9:00pm Ansar yafito daga bedroom zuwa parlour yana sanye cikin kayan bacci, yaciro wayarshi daga charging yanemi kujera ya hakince digit d'in Anaal yakira ga mamakinsa sai yaji wayar rufe. Jeeddah Aliyu [6/28, 8:49 PM] YAYA HAYAT: *SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *25* _HBD my beautiful shaning angel *ZARAH B~b* wish you long life & prosperity Allah yakawo miji nagari_ Cike da takaicin ya ajiye wayar haushin kanshi yaji yanda yakasa chanzawa Anaal waya tun lokacin da yaga 'yar kwamarta{lol Nokia} yakeso yasiya mata waya 'yar zamani hidimomin da sukayi masa yawa yasa ya manta, domin da ganin wayarta ba lallai bane tayi rik'on charging ya k'udurta aranshi ya zama dole ya chanza mata waya. _Washe Gari_ Anaal bata tsaya jiran Ansar ba gargad'in Zuhura yashige ta, tahau adaidaita tafi school su Ramlat naganin yanayinta suka San ba lafiya wai kare yasha taba titseta sukayi har saida tafad'a musu musabbabin damuwarta amaimakon su Ramlat su goyi bayanta tabar Ansar saima sake k'arfafa mata guiwa sukayi hannunta zeenat tarik'o karki yi sauri karaya 'yar Agadez dama dole ki fuskance irin wannan k'alubali don haka sai kin jajirce kirage wannan masifafen tsoron naki, ki zama jaruma ta haka za ki mallaki Ansar Galadima karki manta matsoracin bai ta6a zama gwani. Ramlat ta kar6e zance ta hanyar cewa wannan somi ta6i ne ki ka fara gani dole sai kinsaka juriya da hak'uri sannan za ki cima gaci, kinason Ansar so ba na wasa ba Inkika hak'ura da shi yin hakan zai iya zama barazana ga lafiyarki. Jin su kawai Anaal takeyi ba wai don za ta yi amfani da shawarar su ba. Ana tashi daga school tana fitowa gate ta hango motarshi mtcsww! Taja tsaki ranta a6ace ta chanza hanya daga cikin mirror ya hangonta mamakine ya kamashi me Lucky take nufi...? Laifin me nayi mata da safe tayi tafiyarta bata jirani ba yanzu kuma nazo daukarta ko kallo ban isheta ba. Bai gama tunanin ba yaga ta tsallaka titi da sauri ya 6alle k'ofa motar ya bi bayanta yana isa wajenta tana tsayarda Mae adaidaitasahu, bai kamata ki hukunta ni da laifin da banida masaniya akai iya Sanina ba laifin da nayi miki infact koda nayi miki laifi yakamata kiyi min uziri domin ni d'an Adam ne dole wata rana ki sameni da aikata ba daidaiba. Batare da ta dubeshi ba tace ba laifi da kayimin kawai inason na d'auke maka wahalar kaini da daukoni school da ka ke yi yakamata ka huta kaji da naka hidimomi. Tana k'arasa magana bata jira jin ta bakinshi ba ta shige adaidaita tsananin mamakinta yahanashi yunk'urin tsayarda ita sai kawai yabi bayan adaidaita da kallo yana cizo le6e jikinshi asanyaye yasake tsallaka titi yakoma wajen motarshi. Duk abinda yake faruwa akan idon su Ramlat cike da haushin Anaal, zeenat ta ja tsaki mtcsww! Banta6a sanin 'yar Agadez batada wayo ba sai yau in banda rashin wayo miye na Ansar Galadima aciki da zata dau fushi da shi? Ta6e baki Ramlat tayi tana girgiza kai kinsan me...? Zuwa mu yi musami Ansar mu warware masa zare da abawa domin guy nan yabani tausayi kalli yanda, ya yi tsaye turuss! Gwanin ban tausayi kai *so* masifa ne. Batare da dogon nazari ba suka nufi wajenshi kafin su isa har yashiga motarshi da sauri suka k'arasa zeenat tayi knocking glass da ke side d'in da yake zaune ahankali yasauke glass d'in ganin k'awayen Anaal ne yasa yasaki murmushin yak'e zeenat, Ramlat ba Ku tafi gida bane ko drivenku baizo ba? Ramlat tace baizo ba amma yana hanya Ya Ansar dama zuwa mukayi musanarda kai abinda yafaru domin, Anaal ba sanarda da kai zatayi ba nan take Ramlat ta kwashe labarin da Anaal ta basu tafad'a masa jikinshi ya yi bala'in sanyi yarasa abin fad'a dole ya yi musu sallama yakoma office. Zuhura da leebeauty suna la6e a lungu suna jira su ga ta inda Ansar da Anaal za su 6ullo akan idonsu mai adaidaita yawuce da Anaal, Zuhura ta dube leebeauty tace nafada miki k'awata ba abinda Ya Ansar zai yi da 'yar masu gadi, ita kanta Anaal gargad'in da nayi mata yashigeta mu tafi kawai office d'inshi na bashi hak'uri. What's? Hak'uri fa ki kace zuu...? Abisa wane dalilin za ki bashi hak'uri..? Shi yadace fa yabaki hak'uri ba ke ba, ki natsu ki gane inda yake miki ciwo zuu kina biyewa son zuciyarki d'a namiji yana wulaqantaki. Kallon sama da k'asa Zuhura tayi mata daga bisani ta taso mata kamar za ta cinyeta kinga leebeauty ba shawararki nake nema ba, ballantana kifad'amin son ranki da Ya Ansar yabani hak'uri da kada yabani wannan ba matsalarki bane ni naji nagani naji zan iya sauke girman kaina na nemi sulhu da shi toh ke miye naki aciki? Babu amma Kisani inajiye miki wulaqancin da zai biyo baya. Huh!..leebeauty kenan ba fa yau muka fara samun misunderstood ni da shi kuma mu daidaita kanmu kada wannan yadameki ina da tabbacin shima amatse yake da son ganina soyayarmu ajinin jikinmu take mutuwa ce kadai ta isa taraba mu ba dai mutum ba wallahi. Tana gama magana tai gaba abinta tabar leebeauty cikin tausayinta mtcsww! Taja tsaki had'e da fara zance zuci Iska yana wahalarda mai kayan kara Zuu idanunki sun rufe kink'i gane abinda ni na gano miki amma ba komai ajuri zuwa da tulu rafi wata rana zai fashe. "Ansar na zaune a office abin duniya yadame shi tunani yake ta wace hanya zai bi domin ya gyara, tsakaninshi da Anaal yakai k'ololuwa a sonta ba zai iya jure wannan Sabuwar hanya da tadauko ta nisanta kanta daga gareshi ba. Sallamar Ishaq ce ta katse masa tunani ya amsa chan! K'asan mak'oshi maigida kayi bak'i sunasu ganinka batare da ya tambaye su waye ba, yace su shigo domin bai ta6a kawowa aranshi Zuhura ce ba. Ba knocking balle sallama ta turo k'ofar office d'in tashigo bodyguard d'inta tana biye da ita a baya{leebeauty}. Tayi tsaye rik'e da kugu tana aika masa kallo Mae cike da kwayar so yayinda shi kuma yake mata na mamaki da tsana ko uban me yakawota office d'inshi adaidai lokacin da yake, cike da haushinta ta 6atawa abar sonshi rai har tana yunk'uri wargaza masa budget ya lumshe idanunshi Wanda ke cike da zallan k'iyayyarta. ''Cikin yanga da rangwad'a taja kujera tana facing nashi ta zauna, ta mak'e murya kamar mutuniyar arziki nasan za ka yi mamaki ganina a office d'inka toh ba abin mamaki bane, in kayi la'akari da irin son da nake maka ya Ansar na kasance mai 6ata maka kai hak'uri kayafemin kadauki hakan a matsayin k'addara ko kuskure insha-Allah hakan ba zai sake faruwa ba. Kasan inasonka Ya Ansar son da baki ba zai misaltashi ba, ba za gane ina tsananin sonka ba har mu yi aure ka k'ara hak'uri da ni da kamar yanda kasaba da sannu zan gyara halayena da d'abi'una nadawo yanda ka ke so. "Har tadasa aya Ansar yana kallonta adage yana Shafar d'a siriri gemunshi, kingama...? Ta gyad'a kai. inaso k'ibud'e kunnenki da kyau ki saurarani nasoki zuhura ban kuma ta6a tsanmani zan daina sonki ba, munana halayenki su suka jagorancin goge sonki a zuciyata ba zan 6oye miki ba domin banga amfani yin hakan ba Zuhura ayanzu banasonki na tsaneki bana fatan duk wani dangantaka da zai hadani da ke ko zan mutu wallahi ba zan aurenki ba domin kinficemin arai. Ni da ke Sam bamudace ba ki je kiyi rayuwarki nima nayi tawa, so tsuntsu ne ayanzu tsuntsun sonki yatashi na kuma tabbata ba zai ta6a dawowa kanki ba don haka ki shafamin lafiya kifita daga rayuwata. Tashin hankali Wanda ba'asa masa rana Zuhura jin maganganu Ansar take kamar, saukar aradu wani k'aton k'ololo yatokare mata mak'oshi duhu ya mayewa ganinta numfashinta yana k'ok'arin barin gangar jikinta, ashe akwai irin wannan ranar da za ta zo Ya Ansar zai bud'e baki yace bayasonta ya tsaneta. Ki tashi maza ki ja k'awar cin mushenki kubarmin office tun kafin nai miki wulaqancin Wanda atarihin rayuwarki ba'a ta6a yi miki irin shi ba. fad'uwa tayi daga kan kujera ta zube guwaiyu biyu-biyu k'asa tarusa kuka tashiga rok'oshi karka yimin haka Ya Ansar wallahi insonka in narasaka zan iya mutuwa Dan Allah kayi hak'uri kayafemin. Kin riga kin makaro Zuhura tuni na yage sonki daga zuciyata ayanzu cike take da k'iyayyarki, da tsanarki Mae zafin gaske duk abinda zai faru saidai yafaru ba zan aureki ba na fahimce kinada sha'awar zama office d'ina sai ki yi ta zama har abusa k'aho. Ya kwashe wayoyinshi da makulin mota da sauri Zuhura ta tashi ta rik'eshi gam-gam tana kuka haik'an! Da kyar ya yi nasarar yakiceta daga jikinshi azuciyarshi yace shegiya sai k'arfi tsiya kamar namiji, yafice da sauri har yana had'awa da gudu. Leebeauty ta tafa hannaye huh! Dad'i na gobe saurin zuwa Wanda baiji bari ba zai ji hoho! Sai ki tashi mutafi ke kan tak'are miki, ayanzu ke da kazar da aka tsumata aruwa bakuda banbancin. "Haba! Leebeauty ki tausayimin mana ahalin da nake ciki bai kamata kidinga fad'amin bak'ak'en maganganu ba. Uhm... Sai kiyi ni ki tashi mutafi domin inada abinyi ba gadin office na zo yi ba. "Dole ta mik'e tana mashalo kamar wance tasha syrup suna fitowa suka ci karo da Abdallah cikin kuka tafad'a masa wulaqancin da Ansar ya yi mata, harara Abdallah yadanna mata ya zage ta tass! Yak'ara da cewa Ansar yamin dai-dai gara da yabarki sai ki je can! Ki k'arasa da fitsara da rashin kunyarki, kuma duk ranarda nak'ara ganin k'afarki a company nan sai na karya miki ita heartless kawai. Rana zafi inuwa k'una Zuhura tarasa tudun dafawa da matsanancin kuka takoma gida Hajiya saudat naji abinda yafaru ta harzuk'a matuk'a tasha alwashi sai tadawowa da Zuhura farin cikinta. _4 day's later_ Duk wata hanya da Ansar zai bi yaga Anaal ya bi abin yaci turu gudunshi takeyi kamar naman daji tsawon kwanaki nan ya yi su ne cikin tashi hankali. Yamma lis! Anaal tadawo daga islamiyya ak'ofar gida taci karo da Ya Abdallah zaune a boot d'in motarshi yana waya yana ganinta ya katse wayar. "Sannu da zuwa Baby Anaal{dama haka yake kiranta} Tana murmushi ta amsa da yauwa. Ya Abdallah ina wuni...? Lafiya lau Baby ya karatu? Alhamdulillah! Yaushe za Ku fara exams...? On monday insha-Allah Dan Allah atayamu da addu'a. In wannan ne bakida matsala Baby Anaal. Na gode Ya Abdallah! Har tajuya yadakatarda ita d'an tsaya Baby Anaal akwai wata magana nakeso da nayi da ke. Taja tayi tsaye agabanshi Baby Anaal dama najima ina jiran zuwan wannan ranar da zan baiyana miki sirrin da ke zuciyata. Alhamdulillah! Yau Allah yacika min burina gani gaki zan bud'e miki sirrin z[truncated by WhatsApp]*SONKI NE SANADI* _A Romantic love story 2017_ Na Hauwa shehu Aliyu *®NWA* www.jeeddahaleeyu.blogspot.com *°°°In dedication to Aunty Sis°°°* *Goron Sallah*:- _*Walk humbly talk politely dress neatly Treat kindly pray attentively donate generously, may Allah bless & protect all of you my fan's*_ _Happy Eid mubrak_ *26* Jikin Anaal yadauki rawa gabanta yafadi rass! Yayin da Abdallah bai lura da halin da take ciki ba, yacigaba da cewa Baby Anaal najima da sonki azuciyata so kuma ba na wasa ba aurenki nakeso yi kafin na sanarda ke abinda ke raina sai da na fad'awa Abbah yace na nemi yarda ki in kin amince shi bashida matsala. Baby Anaal nafara sonki tun kafin ki mallake hankalin kanki Dan Allah ki amince da ni zan jiyarda ke dad'i da ba kowace mace take samu irinshi ba. "Ajiyar zuciya Anaal tasauke yafi akirga wannan shi ake kira Ana wata ga wata, k'asa magana tayi sai kawai ta sadda kanta k'asa kamar mai nazari k'asa da murya Abdallah ya yi yadawo kalar tausayi karki damu kanki da tunani zan ba ki wadatace lokacin ki yi nazari da kyau duk da nasan banida makosa kowace mace nace inaso da gudu za ta kar6e ni ki je kawai ki yi tunani. "Da kyar ta ja k'afafunta tashiga gida tun daga ranar Abdallah ya nace mata kamar chewing gum ya siya mata waya mai tsadar gaske, sai kashe mata k'udi yakeyi kamar hauka daga Abbah har Ammi sun ji dad'i al'amari musanman Abbah da yake gani Abdallah shi yafi dacewa da 'yarsa ko ba komai yasan asali da tushenta. Ta6angare uwar gayya Anaal Sam ba bu son Abdallah aranta tana, kulashi ne don ba yanda za ta yi tsakaninta da shi daga Uhm.... Sai a'a yayinda Abdallah yadauki hakan a matsayin kunyar da take da ita. _5:44pm_ Tun daga nesa Anaal ta hango Ansar da Abdallah zaune a k'ofar gida akan boot d'in mota dama duk yammacin matuk'ar tana zuwa islamiyya za ta dawo ta tararda Abdallah yana jiranta, matsanacin fad'uwar gaba da tsoro suka lullu6eta domin rabonta da tasa Ansar a ido kusan 1 week gaba d'aya ta dabarce had'e da susucewa, tun kafin tak'araso Abdallah yafara washe hak'ora _oyoyo my sweetest love tun d'azu nake baza ido naga ta inda za ki 6ullo_ "Hmm!...tayi murmushin yak'e kawo jakkar na rage miki nauyi k'ok'arin yake ya kar6e jakkar littafanta da ke rataye a kafad'arta, da sauri tadafe jakkar tana girgiza kai barshi Ya Abdallah na gode! "Da k'arfi tsiya ya fincike jakkar duk abinda yake faru tsakaninsu Ansar yana kallonsu ta k'asan ido jin yake kamar ya shak'e wuyansu yaita dukansu har sai sun nemi agaji. Mtcsww! Ya ja guntun tsaki ya mayarda hankalinshi wurin wayar hannunshi bayaso ko kad'an su gano halin da yake ciki yak'ara murtuk'e fuska ya had'e rai. "Ina wuni Ya....An...sar tafad'a cikin sark'ewar lafazi. Banza ya yi da ita kamar bai ji ba Abdallah ya zungure shi kai kurma ana gaidaka. A yatsine yad'ago kamar yaga kashi ya d'an waiga wa ke gaidani''? Anaal ce gatanan tsaye gabanka. Ya kya6e baki kamar Mae ciwon hak'ora ya amsa da sannu. "Sam bataji dad'in yanda ya amsa mata gaisuwa ba shi kanshi Abdallah saida yaji ba dad'i ya mik'a mata jakkarta ki shiga gida my Baby bayan salla isha zan shigo mu sha fira. Batare da tace komai ba ta kar6i jakkarta tashiga gida. "Haba Ansar wannan wane irin lokacin ne..? Yarinya ta gaidaka kana amsa a wulaqancin baya tuni na sanarda kai matsayin da takeda shi awurina, wallahi ka gyara wannan sabuwar d'abi'ar taka wulaqanta d'an Adam ba halinka bane. Mtcsww!... Yasake Jan tsaki kana ya gyara zamanshi yakara gwa6e fuska Wanda yak'ara k'ularda Abdallah, kafi kowa sanin halina Abdallah banaso raini su kuma wad'annan k'ananan yara kana furta kana sonsu aji da girmanka zai fad'i a idonsu don haka kasani kana siyawa kanka rashin girma ne. "Kai kadamu da girma soyayya ba ruwanta da wannan inason Baby Anaal tamkar numfashina insha Allah sai na aureta sai dai girman nawa ya zube gaba d'aya a idonta. Kallo uku saura kwata Ansar yakewa Abdallah daga bisani yadiro yace ba sai in tana sonka za ka aureta ba..? Ran Abdallah yak'ara b'aci ubanwa yace da kai bata sona...? Hmm....Abdallah kenan dad'ina da kai shasshasha ne, ae alamar k'arfi tana ga Mae k'iba kai yanzu awannan shekarur naka ace ba ka iya bambance tsakanin so da rashinsa..? Shiru Abdallah ya yi yana kallon Ansar daga bisani yaja tsaki mtcsww.... Ta soni ko kada tasoni ni inasonta ko ana hamaza hamata sai na aureta. Ansar yata6e baki daga haka har suka rabo ba Wanda yasake tankawa d'an uwanshi kowane da abinda ke cikin ransa. _washe Gari_ Anaal tafito cikin shirin zuwa school ta hango motar Ansar gabata yafad'i rass...sauri take kamar za ta tashi sama so take takai bakin titi ta yanda za ta tare adaidaita, gani abinda take shirin aikatawa yasa yafito daga mota yafara kwalla mata kira Lucky....!Lucky...! Ki tsaya ki saurareni gani ba za ta tsaya ba yasa yabita da d'an gudunsa yana cinmata ya rik'e hijabinta da k'arfi dole ta tsaya cak...wuce mutafi yafad'a cikin kaukausar murya. Hawaye da take 6oyewa suka zubo mata sharr....dole tajuya tafara tafiya kamar barauniya yana rik'e da gefen hijabinta sauk'inta d'aya safiya ce ba mutane sosai da ba abinda zai hana tadawo abin kallo. Ahaka suka k'arasa mota yabude mata tashiga yazagaya yashiga ya ja motar suka dauki hanya. Menene tsakaninki da Abdallah..? Batayi mamakin jin wannan tambayar daga bakinsa ba, atsanake tad'ago kaitsaye tace sona yakeyi da aure. _sonki yakeyi da aure_ ya maimaita abinda tafad'a yana kad'a kai Yakamata ki taka masa birki da wuri kada ki wahalarda shi. "Ban fahimcinka...? Tafad'a tana kallon gefen fuskarsa. Ki sanarda shi bakyasonshi domin ki hutarda shi yawan hidima da yake miki. ''Huh......wa yagaya maka bana sonshi...? Ba sai angayamin ba nakan karanta zuciya duk wani mutum da yazo kusa da ni Dan haka ina umaurtaki da ki yi gaggawa fitarda shi duhu kada kwa6arki ta yi ruwa. Domin Abdallah yana da naci da sa'a tamkar ni yakan jajirce iya 'karfinsa har sai ya mallake abinda yakeso, shiyasa nake gargad'inki ki rabuda shi banaso alaqarki da shi karatu za ki yi ba aure ba. Ajiyar zuciya tayi ta tsince kanta da zance zuci Abdallah da Ya Ansar akwai inda halayensu yazo d'aya ashe wata rana zan iya kamuwa da sonshi kamar yanda na kamu da son Ya Ansar...? "Kidaina wahalarda kwakwalwarki da tunani ke da Abdallah ba Ku dace ba, ki yiwa kanki kiyamunlaili ki rabuda shi. _Ba zan iya ba_ Tafad'a kaitsaye had'e da d'auke fuskarta tana kallon titi. Shikenan ni zan sanarda shi domin ba zan zuba ido ina kallo ki cigaba da yaudarar d'an uwana domin nasan babu sonshi azuciyarki. Cike da d'ibin mamaki tadawo da ganinta akan fuskarshi kai kuwa wagayamaka banasonshi..? Cikin natsuwa yajuyo ya dubeta yasaki k'ayatatcen murmushi zuciyarki ce tafad'a min. "Firfito da idanu tayi tana kallonshi cike da tsoro ya akayi yasan sirrin da ke zuciyarta Tun daga lokacin bakinta ya mutum mutus ga wani mutuwar jiki da ya lullu6e ta, yana isa school d'insu ya yi parking inda yasaba yi tabud'e k'ofa akasalance tafita. Ya dakatarda ita ta hanyar furta sai nadawo d'aukar ki kuma ki tabbata kin jirani, kada barazanar Zuhura ta tsorata ki domin ayanzu bata cikin tsarina ina fatar kin fahimcin inda na dosa..? ''Bata tanka masa tajuya tashiga gate d'in makaranta. Tana shigewa yaja mota yatafi, ana tashi yazo daukarta cikin yanayi na tsoro tashiga motar tashi tsoronta d'aya kada tsautsayi yagita Zuhura taganta ta tabbata kashinta yabushe. _*Few Day's Later*_ Fuskar Ansar had'e kamar baita6a dariya ba Yashiga parlourn Daddy da ke farmhouse, ya yi tsaye turus yana k'arewa Abdallah kallo Mai cike da haushi Abdallah da ke waya da Anaal yad'ago ya kalleshi kauda fuska yacigaba da wayarsa mtcsww!..Ansar yaja tsaki yak'arasa shiga parlourn yanemi kujera da ke kallon Abdallah ya zauna, muryarshi adak'ile yafara magana ka katse wannan banzar waya marar amfani da ka ke yi mu yi magana ta fahimta. Girgiza kai Abdallah ya yi had'e da furta Baby zan kira ki anjima domin naji inda maganarmu ta kwana kinji...? Yayi shiru yana saurarenta yasaki murmushi _I love you_ bai jira jin ta bakinta ba ya kashe wayarshi domin yasan ba amsa mishi za ta yi ba. ''Wace irin maganar fahimta ce za mu yi...? Ina fatar contract ka samu mana yak'arasa magana yana dariya. Ansar ya yi ajiyar zuciya ya mik'e yadawo kan hannun kujerar da Abdallah yake kai d'an uwa bansan yanda za ka d'auki maganar tawa ba watakila kasaka fahimta aciki ko kuma sa6ani hakan.... Ya d'an nisa daga bisani yacigaba da cewa Abdallah so nake ka rabuda Anaal ka fita daga harkata ni kuma nai maka alqawali duk abinda ka keso, daga gareni zan maka. Abdallah yasaki baki yana k'arewa masa kallo mai d'auke da mugun mamaki, yahadiye yawu ko zan iya sani dalilinka na bijiro min da wannan maganar mai Kama da dafin kunama...? Za ka iya amma kafara amsa min firstly za ka iya rabuwa da ita ko kuwa..? Zan iya in har ka zo min dalilinka mai k'arfi. Ba dole bane sai kaji dalilina ba Uhm"! Tun da bara ka iya fad'ar dalilinka ba nima ba zan iya rabuwa da ita ba sonta yanzu nafara. Murmushi takaicin Ansar ya yi yad'age gira sama yana ma Abdallah kallon wulaqancin, anyway zan biyanka ladan rabuwa da ita da za ka yi daga Naira million 1 har zuwa million 10 zan iya mallaka maka na kuma sanka farin sani akan k'udi za ka iya yin komai domin, son da ka ke mata bai taka kara ya karya ba. "Zancenka gaskiya ne zan iya komai akan k'udi amma ba zan iya siyarda soyayyar Anaal ba alfarma d'aya zan iya yi maka amatsayinka na d'an uwana shin miye dalilinka nayin hakan...? Anaal tayi maka wani laifi ne ko kuma iyayyenta...? "Ba ko d'aya kawai inason ka nisanta kanka daga gareta. ''Ba zan iya ba Ansar muddin ba ka fad'amin dalilinka ba. Shiru yabiyo baya kowane su yana fama da d'acin zuciya. "Shikenan Abdallah komai yabiyo baya kada ka zargeni ka zargin kanka domin taurin kanka da son jin abinda bai shafaka ba yajanyo maka. Yana k'arasa magana yai tafiyarsa yabar Abdallah cikin zullumi da mamakin me yake nufi da wannan Sabon fi'ili da yazo da masa da shi...? Kasa hak'uri yayi har saida yalala6o Anaal a waya tambaya duniya nan yai mata tafad'a masa menene tsakaninta da Ansar ta tsaya kai da fata ita ba komai atsakaninsu sai mutuncin daga karshe sai cewa tayi wani abu yafaru ne da zai mata wannan tambayar, yace ba komai ya kashe waya ya zunduma kogin tunani _1 week later_ Ansar na zaune a office d'inshi dafe da kai shi fa yanzu dabara tafara k'are masa, da farko dai yana jin kunya yafito fili yacewa Abdallah shi yakeson Anaal shiyasa ya umurce shi yarabuda ita. A6angaren d'ayan zuciyarshi yace da shi idan baka fad'a masa ba ta ya zai barta kana kallon yanda yake k'ara cusa kansa gareta ba ka tsoron tafara sonshi jikinsa yadauki rawa ga sanyi Ac amma zufa yakeyi. Ya yi cilli da Biro da ke hannunshi ya mik'e zubur yanufi k'ofar fita saura kiris suci karo shi da Ishaq da sauri Ishaq yaja baya maigida ba dai fita za ka yi ba...? A maimakon yabawa Ishaq Amsa sai cewa yayi Abdallah yana office d'inshi...? _Eh yananan maigida yanzu ma daga office d'inshi nake yace na kawo maka wad'annan documents kayi sign_ Ansar yaja tsaki mtcsww had'e da furta banida lokacin yature Ishaq yawuce cikin zafi nama yashiga elevator da zai sada shi da office d'in Abdallah da gudu Ishaq yafad'a elevator d'in yana mai cigaba da tambayar Ansar lafiya maigida naganka a hargitse kamar akwai d'ibin damuwa atare da kai..? Saida ya yamotsa sumar kanshi sannan yace bari kawai Ishaq wannan d'an iskan yanason ya tarwatsa min rayuwa inason Anaal fiye da son yake mata akan wane zai nace mata bayan yasan shi da ita Sam basu dace ba. Ishaq yasauke ajiyar zuciya domin shi tuni yagano take-taken maigidan nashi son Anaal yakeyi, maigida ban fahimcin wa ka ke nufi ba..? Wa nake nufi bayan wannan tsohon d'an iska Abdallah ni nasan ba son tsakani da Allah yake mata ba, akwai wata mummuna manufa a k'asan zuciyarsa. Kafin Ishaq ya yi magana elevator ya tsaya suka fito Ansar yana gaba cikin tafiyar masu k'arfi Ishaq yana biye da shi da d'an gudunsa. "Da k'arfi yabanki k'ofar office d'in Abdallah yashiga Abdallah da ke zaune yana waya da girlfriend d'inshi zeely yad'ago atsorace yana kallon Ansar ba shiri yakatse wayar. Lafiya Ansar za ka banko min k'ofa...? Wallahi ni har ka tsorata ni. Abdallah zuwa nayi na rok'e ka abinda banta6a yi ba arayuwata domin ni mai sa'a ne duk abinda nakeso sai na mallakesa ko ta halin yaya amma wani abin mamaki awannan karon wanki hula yakaini dare. Abdallah nasan son da ka keyiwa Anaal bai taka kara karya ba na rok'eka Kadàina 6atawa kanka lokacin kafita harkata Kadàina bani umurni kaitsaye kamar wani d'anka mace allura ce cikin ruwa me rabo kan dauka, domin tuni na fahimcin sonta ka ke yi tsabar girman kanka da miskilancin tsiya yahanaka fad'amin amma kasani *Kayiwa kanka* Jeeddah AliyuCopied By YAYA HAYAT (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ Cool novel, makeup and kitchen2⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen3⃣) WHATSAPP NO: +2347039625239