SODANGI [4/8, 10:21 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 01 Bismillahirrah manirrahim I indecate this novel to my Hausa novel and all my fans,love you all 😘😘. MAZOJI. Rugace mai dauke da fulani yan asali masu hadin kai da kaunar juna,domin idan kaga yanda suke rayuwar su gaba daya abin sai ya burgeka. Alhaji abu shine (ardo)na wannan ruga yana da matarshi Hajjo,amma da mulasa ake kiranta saboda tsananin yawan gashin kanta. Allah ya albarkace su da yara guda biyu,Sada da kanwarshi saratu,amma duk fadin rugar babu mai kiran saratu da sunanta sai dai sodangi,saboda aranar haihuwarta akayi wata gaggarumar walima wadda ta hada kusan jama ar ruga biyar,shi yasa suke kiranta da sodangi. Sodangi yarinya ce duk da shekarunta basu wuci sha ukku ba,amma agirman jikinta sai kace tayi sha biyar,sannan gata da wayau matuka. Iyayen sodangi suna tsananin son yaransu,saboda basu samu haihuwa da wuri ba sai daga baya,shi yasa suka dauki son duniya suka dora masu sam basu son abinda zai taba masu su bama kamar sodangin. Alhaji abu yana da kani guda daya rak Audu da matarshi lailu,amma su suna da yara har guda biyar,saboda dayin aurensu basu samu matsalar haihuwa ba. Baffa Audu irin mutanen nan ne masu sanya ido akan abibda bai shafesu ba,don haka shiyasa ya sanyawasu sodangi ido akan kaunar da iyayensu suke nuna masu,sannan kuma yana jin haushin duk wani abin yayi na wannan zamanin,baka fara ganinshi wurin kowa sai wurinsu sodangi. Adalilin haka ne ya dauki karan tsana ya dora mata,duk abinda zatayi idan har agabanshi ne yoh bata iya ba,shiyasa ita kuma muddun yana wuri sam bata da sakewa,sai tayi ta rabe rabe. Duk wata al ada ta fulani,kamar kiwo da kai nono kasuwa babu wadda sodangi bata gwadawa,saboda ita acewarta abin ma burgeta yakeyi,don haka duk sadda sada yayanta ya kada shanu zai nufi jeji sai tayi rigimar binshi,shi yasa tun molasa na hanata har dai ta gaji ta kyaleta saboda idan ma bata barta ba zata iya wuni tana kuka,gashi ita kuma molasa batason bacin ran sodangin,shi yasa ba komai suke hanata ba. Maganar makaranta,sam sodangi bata damu da karatu ba,shi yasa zuwa makarantar ya zama sharuwan tsintsaye,don ba kullum take xuwa ba. A haka dai har aka samu ta gama primary, a wannan shekaran ne ya kamata ace tabi yan uwanta aji daya secondry amma taki wai ita bata so, su kuma suka kyaleta. Shekararta sha hudu yanzu,don haka girmanta sai ya kara bayyana,sannan kuma duk wasu halittun kyau sukayo mata kabbara. Sodangi kalar fatarta irin kalar nan ce da bazakace mata fara ba,kuma sannan bazaka taba sakata acikin jerin bakake ba,gaba daya kalar fatarta sai tayi kamar ta black Americans, Sodangi doguwa ce kyakkyawa ta gidan gaba,sannan gabbanta suna da kwari dumul dumul take,shi yasa kirarta duk ta bayyana,sodangi ta hadu matuka saboda yanda Allah ya tsarata da manyan idanuwa,ga dogon hanci kuma ya tashi sosai ya mike kamar tsayin biro,sai dan lifs dinta dan karami gwanin ban sha awa,kuma koda yaushe jajir dasu kamar ta shafa masu jan baki,sai akarkashin hancinta tana da wani dan digon baki dan karami,ance awurin kakarta ta wajen uwa ta gajeshi,don haka sai yayi kamar anyi mata kwalliya dashi kuma ya kara mata kyau,girar saman idonta kuwa Masha Allahu baki sidik da ita,kuma tsakaninta da tushiyar gashin kanta tazarar kadan ne,saboda itama sodangi tana da yawan gashin kai kamar na mahaifiyyarta. Duk da bata tsayar da hankalinta wajen karatu ba,amma tana da tsafta,saboda asali da abin ya samo,sam molasa bata barin ta ta fita kace kace,domin akullum duk da ta girma cikin gyaranta takeyi,shi yasa idan ta shiga cikin yan uwanta yara take tsere masu da komai. Ayau talata duk sun shiryo zasu kasuwar dake ci matazu,wasu da kwarewanin nononsu wasu kuma sako ne aka basu,don haka ilham tana cikin yan sako,a hamattar ta dan buhun da zata zubo kayan da zata sawo ne ta matse,suna tafe sai labari suke ragadam ragadam irin dai tafiyar yara wadanda hankali bai game jikinsu ba. Sun fito daga rugar,tsaitsaye sukayi abakin titi suna jiran motar da zata dauke su ta ida isa dasu a kasuwar. Tun fitowarsu suka hangi wata mota can daga gefensu ta tsaya,kuma dukkan alama motar akwai abinda ya sameta,saboda marfin gidan injin din motar abude yake an tokareshi. Sun dade atsaye, domin har wasu daga cikinsu sun fara kosawa da tsayuwar da sukeyi,sannan kuma ga uwar kwaryar nono akansu,dije ce ta juya ta kalli sodangi saboda itace uwar gayya uwar tafiya tace,"yanzu kinga da kin barmu mu tafi kasa da tuni mun mance da mun isa,jibi dadewar da mukayi do Allah." Sodangi ta dan ya mutsaya rai na alamar itama ta gajin tace,"don Allah dije ki kara hakuri,ta yiwu kuma yanzu muna tafiya mota ta samu,kuma ni harda wannan tafiyar ba sonta nake ba." Dan jim suka karayi,dije ta hassala tace,"nidai tafiya zanyi,don haka duk mai zuwa ya taho muje,idan kuma babu mai zuwa ni kam babu fashi.". Wasu daga cikinsu suka bi bayan dije sai sauri suke,sai aka bar sodangi da kawayenta guda biyu. Sun dade awurin har yanzu dai babu wata motar da ta taho empty,domin duk wadda zata zo kusan cike suke tahowa,haushi a wurin sodangi ba sai na fada maku ba,saboda yanda ta mayar da cin kasuwa tamkar wata ibada,shi yasa ayau takejin kamar ta kashe kanta don takaici. Wani mutum ne a mashin yazo ya gittasu tare da wani goye abayanshi,dai dai wurin motar nan suka tsaya,da sauri na goyen ya sauka tare da lekawa cikin motar yayi magana da oganshi da yake kwance tun dazu a motar. Mikewa yayi zaune,yayi wata yar mika saboda gajiya ya kalleshi rai bace yace,"tun dazu kaje kayi zamanka,kamar baka san tsawon tafiyar dake gaban mu ba." Rusunar da kansa yayi yace,"kayi hakuri yallabai,domin akokacin danaje ban samu mai gyaran da kace ba,dole na jira sai da aka kirashi". Bai sake cewa driver shi komai ba,wuri kawai ya samu ya tsaya yana jiran yaji abinda bakanikenshi zai ce,itatuwan dake bakin titin ya kallah,yanayin da suke kadawa ne abin ya burgeshi sai ya kara zuba masu ido har wani murmushi yake. Sodangi kuwa gaba daya abin duniya duk ya dameta,don haka wannan motar dake kusa dasu ta zubawa ido har bakaniken dake gyaranta ya gama,shiga motar yayi ya tadata,sannan ya bata wuta sosai. Ganin haka yasa sodangi ta kalli abokanta jikinta har rawa yake tace masu,"nifa waccer motar zanje in shiga,idan akwai mai zuwa ya biyo ni."tana gama fadar haka ta gyara zaman dan buhunta tayi wajen masu motar. Tani tabi bayanta, amma Rabi atu cewa tayi," ni kam bazan biku ba sodangi,kawai bamu san mutane ba,idan suka sace mu fa?" Duk daga cikinsu babu wadda ta tsaya saurarenta,tafiyarsu kawai sukai,kuma kai tsaye wurin motar suka nufa,don haka suna isa sodangi ta bude mota sai damben shiga take har ta samu ta zauna sannan ta kalli Tani tace,"to kema ki shigo mana zaki tsaya kina kallona." Jin haka yasa tani ta dauke idonta daga kallon da matashin nan yake mata,itama shigewa tayi kusa da sodangi,suka zauna sai kuma duka fara baza mazurai. Dan matashin nan da tunda suka tunkarosu idanuwanshi suka tsaya akan halittar sodangi,hade miyan bakinshi yayi sannan kuma ya gaza magana,don haka bude kusa da driver yayi ya zauna sannan ya kalli driven yace,"muje mana." Da sauri ya tayar da motar,amma zuciyarshi tana kan su sodangi,"ko wadanne irin mutane neh,kawai daga ganin mota sai ka shiga with out taking excuseπŸ€” Su sodangi kuwa sai baza ido ake ana kallon titi,shi kanshi safwan akwai mamakin acikin ranshi,amma saboda wasu abubuwa da suka dauke mashi hankali yasa zuciyarshi ta gaza tuna komai sai dai kallon sodangi da yakeyi ta madubin dake gabanshi. Gyaran murya yayi bayan ya gama zayyana komai akasan zuciyarshi yace,"yammata ya sunaku?" Tani tayi karaf tace,ni sunana Tani,sai yar uwata kuma sunanta sodangi." Sunan ya fada acikin bakinshi sodangi,kada kai yayi yace,"yanzu ina zaku neh?" Sodangi ta dago manyan idanuwanta tayi har dasu tace,"kasuwa zamu,tana nan bisa hanya da mun shiga matazu." Wannan juya idanuwan da tayi sai da yaji har ajikinshi,don haka murmushi yayi yace,"ok,toh amma ku awacce ruga kuke?" Tani har ta bude baki zatayi masu bayanin Rugar da suke,safwan ya tari numfashinta yace," da sodangi nake." Dole su tani akayi shiru,sai dai kawai taci gaba da mazurai,abinka ga shagwababbe,sodangi ta saki baki sai bayani take mashi cikin gwaba da jan murya,shi kuwa gogan har wani tsuma yake, saboda aduk shige shigenshi da leke lekenshi bai taba haduwa da yarinya kuma yar kauye mai irin halin sodangi ba,don haka nan da nan zuciyarshi ta kwadaita da sodangi. Wani tunani yayi toh ta yaya hakarshi zata cimma ruwa,domin irin su sodangi ne ake cewa Allah ya kai damo ga harawa,don ko bai ci ba ya watsar. ajiyar zuciya yayi dai dai lokacin sodangi tana cewa driver,"malam anan zaka ajiye mu fah." Da karfi ya taka burki,har sai da kowa ya dan tazgada saboda basu fada mashi da wuri ba har sai da ya kure,sannan kuma ga wata mota da ta shigo masu da karfi. Safwan kallon driver yayi tare da jan dogon tsaki yace,shi yasa sam wllh bana son yin tafiya atare dakai,don kawai daddy ya makala mani kai amma da tuni na yakatar dakai abisa hanya." Bai farga ba yana can wajen sababi yaji su sodangi suna cewa,toh malam mun gode kwarai,Allah ya biya ka.. Bude motar yayi da sauri ya fito ya zagayo inda suke,duk haduwarshi amma jikin shi rawa yake daya ganshi gaban sodangi,domin pace to pace da yayi da kirjinta,ji kawai yayi ina ma ina ma yajishi rungume da ita. Daurewa yayi yada wa kanshi natsuwar dole yace mata,"har gashi zamu rabu amma baki tambayi sunana na ba." Sodangi da hankalinta ya dauku,domin waige waige kawai take taga a ina zata hangi abokan tafiyarsu.don haka washe baki tayi tace,"yi hakkuri bawon Allah,"sai kuma yar kunya ta kamata saboda sai yanzu ta lakalci irin kallon da yake mata. Murmushi yayi yace,"sunana safwan Abdallah,kuma ina rayuwa agarin abuja."dariya tayi ta kalleshi tace,"safwan! ai kuwa sunan yana da dadi,kuma sunan na yan birni." Hannu ya zira acikin aljihunshi ya debo kudi,domin shi kanshi bai san ko nawa bane ya mika mata. Ita kuwa ganinsu sai hankalinta ya tashi saboda duk sakarcin halinta,kwata kwata iyayenta basu nuna mata son kashe kudi ba,don haka sai taja baya tana girgiza kai tace,"ka mayar da abinka,domin idan ardo ya ganni da su zai iya yanka ni." Shi kuwa safwan sai ya nace wai sai ta karba,ganin haka yasa ta juya da sauri ta nufi cikin kasuwar ta barshi anan. Duk abinda yake faruwa akan idon driver dinshi,don haka girgiza kai yayi ya dafe kanshi ya fada afili" ya Allah ka shiryar da oga nah,dubarshi don Allah duka shekarunshi badu wuce ishirin da biyu ba,amma yasan darajar mata." Dan tsaki yayi yaci gaba da kallonshi ya kara kada kai da mamakin yanda yaga jikin safwan yana rawa saboda mace. Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:21 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 02 Hello my fans,ina baku hakuri akan mistake da nayi wajen kiran sodangi na kira sunan ilham ta cikin ZUMUNCI, kun san yau da gobe sai Allah kuma dan adam ajizi ne,dole akwai mantuwa,please ku gafarce ni. Continue:- A sanyaye safwan ya dawo wajen driver dinshi yana ta saka abubuwa acikin zuciyarshi,don haka yana isa ya kalleshi fuska ba walwala yace," ina ganin fitowa zakayi ka shiga motar haya ka tafi Abujar ayau fon ka isar da sakon daddy,ni kuma zuwa gobe zan taho." Driver yayi kasa da kanshi cikin girmamawa yace,"yallabai ko ka mance da irin worning din da Alhaji yayi mani akanka.......?" Bai karasa ba safwan ya dakatar dashi da hannu,sannan kuma ya bashi umurni duk alokaci daya yace,"fito nace." Dole driver bai da yanda zaiyi ya fito daga motar,shi kuma safwan din ya shige ya zauna mazaunin driver. Driver dai bayyi kasa da gwiwa ba yadan leka ta window din motar ya sake cewa Yallabai ko ka mance akwai tafiya da zakayi acikin satin nan,kuma Alhaji yace Akwai wasu abubuwa da dama da zakayi kamin tafiyarka." Safwan ya dago ido cikin isa da kuma gadara yace,"what do you mean driver?"dan kauda kanshi yayi tare da tsaki sannan yaci gaba da cewa,"kai ma ka koma dan sa ido ko,watau kabi layinsu mummy da daddy da broth koh?" Toh kada ka bari ka bata mani rai wallahi, saboda kai ma ka sani idan har naja maka layi sam bazakaji dadi ba,kuma tafiya da kake fadi,inason idan kaje ka fara sanar da daddy cewa na dagata sai nan da wata daya zuwa biyu. Driver jin abinda safwan ya fada yasa duk jikinshi yayi sanyi,acikin ranshi yake fada yayin da ya kafawa safwan din ido,"watau yaron nan wannan karon ma ya kara rosawa Alhaji plain ke nan."amma kuma abayyane cewa yayi," ka gafarce ni yallabai, kuma insha Allahu zan isar da sakonka,sai dai kuma yallabai kwana nawa zakayi?" Takaici ne ya kara kama safwan ya kalli driver yace,kaje kawai,ni dai nasan muddun na gama abinda nakeyi ai dole aganni gida,don haka don Allah kada ka sake damuna," kudi ya mika mashi masu yawa yaci gaba da cewa,"amshi wadannan,idan kuma bazasu ishe ka ba sai kayi mani bayani. Hannu biyu ya mika ya amshi kudin don baida yanda zaiyi,shi kuwa safwan zamanshi yayi acikin motar har zuwa lokacin da su sodangi suka gama. Gaba dayansu suka rankayo,sodangi ce atsakiyarsu,duk da akwai farare tas acikinsu, amma gaba dayansu sodangi ce ke haskasu,saboda da ita kyanta tundaga nesa kake ganinshi ba wai sai ta iso kusa dakai ba. Don haka suna isowa kusa dashi ya kira sunanta,duk gaba dayansu suka cak tate da kallonshi,dariya tayi tace,"la ashe baka tafi ba?" Daga mata kai yayi shima yana murmushin yace"ke nake jira don in mayar dake gida."cikin mamaki ta dafa kirjinta tace,"ni,sannan ta kada kanta taci gaba da cewa," kayi tafiyarka kawai,kada mu bata maka lokaci." Mamaki ne yadan kamashi saboda ganin dazu bata tsaya neman izininshi ba ta shige mashi mota,domin yanzu gashi musamman sbd ita ya tsaya,amma zata ki shiga. Wani mugun kallo ya sakar mata tare dayin kasa da idanuwanshi,fuskar nan dauke da murmushi yace,"saboda ke na tsaya ke na tsaya sodangi,kuma don na damu dake neh,amma tunda bazaki shiga ba bati inzo in tafi." Jin yanda ya mayar da ita wata acikin kawayenta yasa taji dadi ya kamata ta dubesu tace,"ku muje ya kaimu gida."aikuwa fadarta keda wuya suka fara rubibin shiga,boat din motar ya bude masu duk suka zuba kayansu,sannan ya bude gidan baya,duk yawansu haka ya cusa su aciki ya rufe,sannan ya bude gidan gaban yace da sodangin ta shiga.dadi taji kwarai da gaske da irin karramawar da yake mata,don haka ta shige motar ta zauna,dan juyawa tayi ta kalli su dije da aka zakirasu kamar sardine, sannan kuma ga wani irin karni da tsami sunayi,ko ita dake mace sai da taji wani iri to ballantana da Namiji kuma dan boko dan kwalisa. A guje safwan ya rinka jan motar domin sautin da motar keyi duk ya dameshi,don haka saboda irin gudun da ya rinkayi dasu nan da nan sai gasu gaf da rugarsu. Parking yayi agefe,kafin ya bude ya fita sai da yayi locking din kofar dake kusa da sodangi,don haka alokacin da su dije suke fita ita kuma sai tayi ta kokarin ganin ta bude kofar tunda taga yanda akeyi,duk yana kallonta,dariya kawai yayi ya kauda idonshi har suka fita. Sodangi juyowa tayi tace " ko nima in biyo ta inda su dije suka biyo neh?" Bai amsa mata ba ya rufe kofar,sannan ya koma sit dinshi ya bude ya shiga yace,"bari dai in bude maki,amma kamin in bude maki inaso muyi magana ni da ke." Juyawa tayi ta hangi abokan tafiyarya,sai taga duk sunja tinga sun tsaya suna jiranta,dan hankalinta ne ya kwantq ta dago ta kalleshi,shima kallonta yake,kuma haka nan kawai sai taji wani irin abu ya ratsa mata acikin zuciya,don haka sauri tayi ta kauda idonta. Shi kanshi abinda yaji sai da yayi da gaske ya samu kanshi,dan shirun da sukayi ne yake tunanin kodai ya fara son yarinyar nan ne,saboda wannan yanayin dayaji bai tabajin shi ba don ya kalli mace,sai dai kawai yayi sha awarta. Kara daga idanuwanshi yayi ya sake kallonta sai kuma yaji gabanshi ya fara bugawa da sauri sauri,lumshe idanuwanshi yayi ya bude ya kira sunanta cikin wani salo da kashe murya yace,"sodangi ina son idan kin amince gobe inzo in kara kawo maki ziyara." Far tayi da idanuwanta ta kalleshi tace,gobe bazan wuni gida ba,saboda ina zuwa kiwo ni da yaya sada." Idonshi ya kai akan zara zaran yatsunta,kumbar yatsun sai ka rantse farin jan farce ne ta shafa,saboda yanda suke kyalli gwanin ban sha awa. Mika hannu yayi da niyyar kama nata hannun amma sai ya fasa,saboda kada tunda wuri ta zargi wani abu,don haka sai ya kalleta yace,toh zan zo goben,kuma daga wane wuri kukeyin kiwon?" Nuna mashi tayi da hannu tace," kaga waccar hanyar,to idan kazo tanan zaka bi,amma mota bata shiga,idan kaje sai kayi gabas,to anan zaka same mu da shanun mu." Murmushi yayi yace,ok toh shikenan sai kin ganni,sannan ya latsa ya bude mata kofar,bai bari ta bude da kanta ba sai ya rabo ta jikinta ya murda kofar. Gogar da jikinsu yayi sai da taji tsigar jikinta ta tashi,don haka nan da nan ta rufe idonta har sai da ya gama budewa ya janye jikinshi sannan ta bude idonta takalleshi akunya ce tace,"mun gode kwarai."sannan ta fita daga motar taci gaba da cewa," kai kuma Allah ya kiyaye hanya." Tana fadar haka ta juya ta nufi wurin da kawayenta suke jikanta, tana isa duk suka taso mata da tambayoyi,babu tambayar data amsa sai dai murmushi kawai da takeyi,saboda yanda ta farajin safwan acikin ranta yana burgeta sosai. Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:21 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 03 Shi kuwa daya tayar da motarshi katsina ya koma, wani hotel ya nufa ya kama daki saboda yasan idan ya koma gidan kawunshi fada zaiyi mashi,kuma idan gari ya waye zai iya sanya shi agaba ya mayar dashi gida. Kusan wunin yau sodangi yinshi tayi akasalance,saboda duk motsin da zatayi muryar safwance take ratsa mata kunnuwa,sannan abubuwan da suka faru atsakaninsu sai su rinka yi mata gizo acikin idanuwanta. Karshe dai sodangi sai kawai taji ta kagara safiyya tayi don kawai taga ta hadu da safwan. Don haka gari yana waye wa sodangi tayi kalacinta,sannan tayi wanka ta gyara jikinta harda shafa turaren innarta,sabon takalminta ta dauko ta zira duk molasa tana kallonta,can dai ta gaza daurewa tace,"ke sodangi wai ina zaki neh?" Sodangi tayi dariya dan dimple din dake gefen kumatunta ya lotsa tace,"kiwo mana molasa." Da yake sunan lakani neh shiyasa itama sodangin take kiranta dashi. Mamaki neh ya kamata tace"kiwo!! Keda zaki jeji shine kike kwalliya kamar zaki gidan biki?" Sodangi tadan shagwabe fuska kamar zatayi kuka tace,kai molasa,idan nayi kazanta kice mani kazama,amma kuma yau nayi kwalliya kince mani kuma kamar zani gidan biki,toh bari duk in gogeta shikenan koh?" Molasa tayi murmushi tace," ni bance ki goge ba,kawai dai naga kwalliyar tayi yawa neh shi yasa na tanka mah,ki barshi kawai ysr auta ta." Dariya sodangi tayi tace,"wai molasa ina ya ya neh ya shiga don tunda na tashi ban ganshi ba?" Molasa ta nufi daki tana cewa,"tunda safe ardo ya aikeshi katsina yakai manshanu da nono acan madattai,kuma ina ganin shida gida sai yayi yammaci." Wani dadi ne ya kama sodangi,saboda dama tunda ta tashi take tunanin yanda zasuyi da sada idan ya kyalla ido yaga safwan ayau,don haka hankalinta kwance ta dauki sandarta ta daga muryarta da karfi tace," toh ni dai inna na tafi,sai na dawo." Molasa tace,"toh auta sai kin dawo,kuma kada kiyi dare don Allah." "Toh",tace sannan tayi waje,akofar gida taci karo da mahaifinta tayi sauri ta durkusa tace "ardo na shirya zan tafi kiwo." Fuska dauke da murmushi ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye yace,sodangi Allah ya bada sa a,kuma yau tunda ke kadai ce kada kiyi nisa cikin jejin nan,ki tsaya nan kusa kusa." Dariya tayi tace"haka ma mosalasa tace mani," ardo yayi dariya yace,"yawwa toh maza ki tafi,saboda naga shanun ahanya kada su ja ki da nisa." Da dan tsallenta ta wuceshi tayi hanyar daji,shi kuwa sai da ta bulle duk yana kallonta fuskar nan sai murmushi yake, sannan ya maida hankalinshi ya nufi cikin gida. Sodangi da kyar ta samu ta cimmah shanunsu,sannan tayi dubarar tsayar dasu tunda wurin akwai danyar ciyawa sosai duk da damina batayi irin kankamar nan ba,ganin sun mayar da hankalinsu wurin ciyawar ita kuma ta samu wani katon dutsi a gindin wata katuwar itaciya ta zauna, time to time takan juya tana dan waige waigen ta wai ko taga safwan,amma shiru. Can wajen sha biyun rana tana nan zaune tana ta kallon shanunta,domin har ta fitar da ranta da zuwan safwan,kawai sai taji wani lallausan hannu ya rufe mata idanuwa. Da farko ta dan tsorata,don tana ta magana amma sai taji shiru ba a amsa mata ba,jikinta ne ya fara rawa saboda duk tunaninta sai ya koma ga ko wani mugu neh yazo inda take gashi babu kowa wajen sai ita kadai bare ta sa ran mai ceton ta. Roko ta farayi muryarta tana rawa,"don Allah wanene,kayi mani magana mana,kada ka cutar dani." Jin yanda jikinta keyi ne yayi maza ya juyo da ita tare da bude mata idanuwan yana yi mata dariya. Ganin shine yasa tayi yar ajiyar zuciya ta harareshi tace,wallahi ka tsoratar dani dayawa,domin ji nayi kamar ma mutuwa zanyi don tsoro." Dariya ta kara bashi don kuwa har yana tafa hannu.hawayene taji sun taram mata acikin idanuwa taji kamar ta fashe da kuka don takaicin dariyar da yake mata,wai dami zataji? Shin tsoron da ya bata ko kuma da dariyar muguntar da yake mata? Mikewa tayi afusace ta nufeshi shi kuma yana ganin haka sai ya juya ya ruga,haka sukayi ta zagaya wajen da gudu tana kawo mashi duka da sandarta yana kaucewa har sai da ya lura ta gaji sosai sannan ya tsaya. Da kyar ta iso inda yake,shi kuma ya gumtse dariyar da yakeyi saboda ya fahimci itace take hassala ta,don haka tana isowa itama tsayawar tayi tana share wasu hawaye da suka zobo mata cikin shagwaba irin ta sangartaccin ya'ya. Kara matsowa yayi gaf da ita yana murmushi yace,"yi hakuri baby tah," daga hannu tayi ta dokeshi cikin shagwaba,caraf yayi ya rike hannun yana dariya,ai kuwa dariyar daya ci gaba dayi yasa ta kara daga gudan hannun zata dokeshi,shima rikeshi yayi,sannan ya zuba mata sexes eye dinshi yana kallonta.cigaba tayi da dan sharben kukanta na shagwaba. Gaba daya ya jawo duka hannuwanta ta fada jikinshi,bai jira amincewarta ba shi kuma ya maida hannuwa ya rungumeta tsam ajikinshi. Love you my fans😘 08033481518 [4/8, 10:21 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 04 Narkewa tayi ajikinshi,shi kuma yaci gaba da rarrashinta yana shafar kanta,kuma acikin zuciyarshi wani dadi neh ya kama shi saboda ganin yanda take kwance akirjinshi ba tare data damu ba. Can acikin kwalwarta taji molasa ta kira sunanta da karfi tace," ke sodangi,asadda takeyi mata kashedi da maza,akul kika yarda wani namiji wanda baki san shi ba ya tabaki koda hannunki ne,saboda yanzun kin haihu ace kinyi abin kunya........... Ture shi tayi cicin karfinta tana kallonshi kamar wata zakayya zata zazzaga mashi masifa,amma kuma sai ta tafi ahankali tayi kasa da idanuwanta,komi yasa ta fasa oho. Juyawa tayi ta kama tafiya zata koma wajen shanunta, Safwan tsaye yayi yana mamakin abinda tayi mashi,ganin ta fara yi mashi nisa yasa yabi bayanta,amma bai tanka mata ba har ya samu ya isketa tunda tafiyar ta ta ahankali takeyinta. Kallonta kawai yayi yaga ta daure fuska sam babu wani fara a atare da ita,gindin iccen ta nufa ta koma kan dutsinta ta zauna,shima gefenta ya samu ya zauna yaci gaba da kallon shanun. Dan minti biyu suka dauka babu wanda yayi magana sannan ya dan juyo ya kalleta yana murmushi,tare da yar harararta yace,"I'm sorry sodangiπŸ‘ Duk da bata san abinda yace ba,amma kalmar tayi mata sanyi acikin ranta,itama harararshi tayi tace,"bana so ne shi yasa,kuma molasa tace idan har na yarda wata rana zan iya haihuwa." Jin abinda ta fada sai da yasa gabanshi ya fadi yaji kamar ya ruga saboda radhin gaskiya,amma da yake yq goge,sam bai bari ta gane ba sai yace," mi za ayi maki har ki haihu sodangi?" Dan sumbura baki tayi ta kalleshi tace,molasa cewa tayi idan yarinya na barin maza suna taba mata hannu cewa za ayi yar iska ce kuma a haka har sai ta haihu." Tsaf ya gane abinda take nufi sai yayi dariya ya zuba mata ido yace," nima yanzu tunda na tabaki na zama dan iska kenan koh?" Zaro idanuwa tayi tace,"ni dai bance ba,dama molasa ce tace." Daure fuskarshi yayi ya mike tsaye yace toh shikenan tunda dai kin zage ni bari inzo inyi tafiyata don kada ki haihu kice ni neh." Yana fadar haka ya juya ya fara tafiya yana takaicin yanda sukayi da sodangi.ita kuma zuba mashi ido tayi tana kallonshi,amma zuciyarta tana nadamar abinda ta fada mashi, sannan kuma tana tunanin shike nan ita dashi bazata kara ganinshi ba. Mikewa tayi tsaye taci gaba da kallonshi,can sai ji tayi ta kwala mashi kira ba tare data sani ba,kin jiyowa yayi,kuma yaci gaba da tafiya,amma kuma kiranshi da tayi yasa yaji wani irin dadi acikin ranshi. Tafiya ta farayi tana kiranshi,amma baida alamar tsayawa,ai kuwa sai ta fara gudu har ta samu ta iskeshi tasha gabanshi tana hawaye. Tsayawa yayi kawai yana kallonta,kuma sai yaji ta bashi tausayi,saboda har acikin zuciyarshi yana jin yarinyar,kuma daya isa aure babu abinda zai hana ya aureta amma idan tana da ilmi da wayewa,ahalin yanzu kuwa idan ya aureta gaskiya yaci baya kuma sannan abokanshi zasu iyayi mashi dariya. Dan daure fuskarshi yayi yace," ki bani hanya in wuce,tunda dai baki son gani na kusa dake." Yana fadar haka ya raba ta gefenta zai wuce,wuf tayi ta rike mashi hannu tace,"don Allah kayi hakuri, kada ka tafi da fushinah." Dariya yayi yace,mi yasa zaki tsaida ni,ko dai kina so na neh?"Kada kai tayi da sauri tace,wallah bana sonka sai dai ina so ka tsaya muyi labari." Murmushi yayi yace," toh kiyi hakuri tunda baki so na dole neh in tafi in barki sodangi." Kara rike hannunshi tayi gam tace,nace fa kayi hakuri,kuma ardo ya fada mani duk wanda akace yayi hakuri yaki,toh ya zama shaidan." Tabbas yasan abinda sodangi ta fada gaskiya neh,kuma mah miye tayi mashi wanda bazai iya hakura ba? Don haka murmushi yayi yace," toh shikenan na hakura sodangi,amma kuma ni da kikace baki sona toh ni ina sonki sodangi ina kaunarki." Duk da bata da wani cikakken hankalin manya sai na kurucciya,amma kalmar tayi mata dadi har acikin zuciyarta,don haka da sauri ta saki hannunshi taji wata irin kunya ta kamata har bata iya hada ido dashi. Murmushi kawai yayi ya kalleta yaga har yanzu kan nata asadde yake,sai ya dubi agogon hannunshi yaga har daya da rabi tayi. Dagowa yayi ya kalleta yace,"yanzu ina shanunki suke?" Cikin dubara ta daga kanta tana dan dube dube,can tace," gasu can wuri." Shima daga kai yayi ya kallesu yace," okay,dama gani nayi lokacin sallar azahar yayi don kada muje yin sallah su kama gabansu. Kada kanta tayi tace,"ai bazasu tafi ba har sai idan ni na korasu ko wani ya kore su." Murmushi yayi yace,toh zo muje wajen motata mu dauko kayan da zamuyi amfani dasu,sai mu komo inda zamu rinka hangensu,don kada su gudu yau ardo ya daki wata yarinya. Dariya tayi tana mamakin abinda yace,can dai ta gaza shiru tace,hai koda duka shanun nan zasu bace ardo bazai taba duka na ba,kuma duk inda sukaje idan lojacin dawowarsu yayi zasu koma gida." Murmushi yayi tare da yar harararta yace,"lallai ashe dai ke yar gatan ardo ce, saboda nasan dai yanda bafullani yake son shanunshi,amma ardo zai hakura dasu." Dariya ta rinkayi saboda yanda taga wai yana mamaki,ta sani don dai bai san yanda ardo da molasa da yaya sada suke son ta ba,amma da bayyi tunani ba. Shi kuma hakan da tace neh ya gane,lallai sodangi yar gata ce awajen iyayenta kamar yanda yake shalele,don shiyasa yake tsula tsiyarshi yanda yake so. Wurin motar suka isa ya dauko wata katuwar darduma da wani kwali cike da ruwan roba (swan water) sai wata leda duk kayan ci ne akayi take way din su da su chocolate da biscuit da chewing gum da sauransu,sai kuma wata malun malun (babbar riga) itama dauko ta yayi. Ledar kayan ciye ciyen kawai yaba sodangi ta dauka shi kuma duk ya dauki sauran har suka koma wajen babbar itaciyyar. Shimfida yayi masu ya dauki ruwa ya koma gefe daya ya fara alwallar,juyowa yayi ya kalleta yace,kema zo kiyi alwallar mana. Girgiza kanta tayi tace,"sai na koma gida nayi,tunda dama haka nakeyi duk sadda nazo kiwo." Kiranta yayi yai mata alama da kanshi na tazo. Nufarshi tayi ta tsaya gefenshi,mika mata ruwan yayi, ta kalli ruwan tace,kai safwan wannan kuwa ba almubazzaranci bane,ya za ai inyi alwalla da ruwa mai zaki?" Dariya yayi sosai har yana kyalkyatawa yace,"waya fada maki yana da zaki?" Mika mata yayi yaci gaba da cewa,"sha kiji." Amsa tayi ta sha,sai taji shi salaf.Dariya tayi ta kalleshi tace,"laa hai kuwa ashe baida zaki,cai nake zaki gareshi wallah. Gyarawa tayi tai alwallar kusa dashi, shima duk sai da yaci ta gyara,ahankali yayi ta koya mata har suka gama. Wannan babbar rigar ya mika mata yace ta lullubata,itama ta tsaya bata san yabda zatayi ba,matsowa yayi ya lulluba mata ita yana dariya har yana dungurar hancinta yanayi mata tsiyar bata iya komai ba. Tate sukayi sallarsu suka gama,sannan ya dauko snacks din daya sawo ya bude agabanta yace taci.dayake ta fara sakin jiki dashi,hannu tasa ta dan tsinci abinda take iya ci,saboda ba komai ne ta sani ba. Sai maraice lis sannan safwan yayi bankwanq da sodangi ya koma katsina,ita kuma ta juya ta nufi cikin rugarsu zuciyarta cike da tunanin safwan da irin dabi unshi kyawawa. Washe gari ma haka akayi,tana wajen kiwon ya sake samunta,wannan ranar tafi sakin jikinta dashi fiye da jiya,sai dai bai dade ba akayi kiranshi ta waya,duk tana jin shi yana wayar yana ba yar da hakuri har yace,gobe zai zo. Shiru tayi har ya gama wayar,ita babu abinda ya burgeta irin abinda taga yana magana dashi, saboda arugarsu mutum daya neh yake da ita,kuma danshi ne daya tafi lagos ya kawo mashi don ya rinka magana dasu. Bayan ya gama wayar ya kalleta tare da daga girarshi yace,"ya neh?"murmushi tayi tace,"abin maganar neh ya burge ni." Dariya yayi ya mika mata wayar ta amsa tana dubawa har zuwa lokacin daya mike tsaye yace mata zai tafi,kuma yana ganin gobe bazai zo ba sai dai jibi. Itama mikewar tayi tare da mika mashi wayar tana cewa,"gashi abin maganarka." Dan murmushi yayi ya kalleta yace," ki dauka na baki ita,kuma ba abin magana ake ce mata ba,phone zaki ce." Da kyar ta iya cewa phone din,shi kuwa yayi tayi mata dariya har suka isa jikin motarshi sannan ta karamika mashi. Kada kanshi yayi yace,"da gaske fa nake,ki dauka duka na baki,saboda ina dasu da yawa,kuma idan kina so zan kawowa ardo da molasa suma tasu." Girgiza kai tayi tace,"ko ka bani ita bazan ita amfani da ita ba,ka barta kawai,kuma kilama idan ardo ya ganta yau sai yayi fushi dashi dani." Dan murmushi yayi yasa hannu ya amsa yace,"ni kuma safwan bana son ran sodangi nah ya bace,amma ko ba dade ko ba juma kema zakiyi amfani da irinta ko ma wadda tafi ta." aikuwa wani dadi neh ya kamata tayi murmushi tace,"toh Allah yasa." Tun daga wannan ranar da safwan ya tafi bai kara dawowa wajen sodangi ba sai da ya kwashi wajen kwana goma babu shi babu labarinshi,ita kuwa sodangi gaba daya ta shiga damuwa saboda rashin ganinshi,kullum idan ka ganta cikin tunani take,gashi ta gaza fadawa kowa bare ta samu saukin abinda takeji. Molasa ita kanta ta fahimci akwai wani abu atate da yarta,saboda kwata kwata wannan surutun nata duk ya ragu sai dai ta zauna tayi jugum,kuma idan ta tambayeta sai tace mata babu komai. Ba tayi shawara da kowa ba ta fada daji ta ciccirowa sodangi magunguna saboda molasa irin mutanen nan da basu wasa da lafiyarsu,duk abinda tasan zai amfaneta ajiki ko yayanta nemo abin take kuma ta bashi muhimmanci har sai taga an wadatu dashi.don haka ko yanzu ma magunguna ta samo tare da addu o in tsari wurin malamai don gudun ko aljannu neh suke son shafar mata diya. Duk abinda aka bata bata musun shanshi,amsa kawai take kuma tayi yanda akace mata,amma kuma duk halin da ake ciki bata fashin zuwa kiwonta,don ko an hanata sai ta nace ta tafi wai duk tunaninta zata gamu da safwan. πŸ’πŸ’πŸ’ Shi kuwa safwan tunda ya rabu da sodangi kai tsaye abuja ya nufa,saboda daddyn shine da kanshi ya kira shi ta waya,shi yasa bai da yanda zaiyi dole ya amsa kiran. Lokacin da yayi parking a harabar gidan inda sashen motocinshi su,cikin gidan ya nufa,babu wanda ya samu afalon tunda yasan babu kowa sai umminshi da masu aikinta. Kai tsaye dakinta ya nufa ya sameta tana sallar magriba,don haka shima toilet dinta ya shiga yayi alwallah ya koma gefenta ya gabatar da tashi magribar sannan yayi addu o inshi ya shafa,zuwa lokacin ita kuma ummin take jiranshi. Dago idanuwanshi yayi ya kalleta cikin jin nauyi,saboda yasan zuwa wannan lkcn fushi takeyi dashi tunda wurin kwana ukku babu wanda yasan inda yake. Zuba mashi ido tayi tana kallonshi tace," safwan barka da dawowarka gida." Gaza amsawa yayi,don haka yanajinta taci gaba da cewa," daga ina kake." Sai alokacin yayi dariya saboda tambayar dayaji yace,ummi don Allah ki daina bata ranki akaina,nifa Namiji neh kuma ba yaro ba,amma kina tambayata daga ina nake." Dafa kafadarshi tayi tace,haba safwan,ai koda kaji na tambayeka to don na damu da kai neh,kuma bani da wanda yafi ku awurina kai da dan uwanka,toh dammi kai kuma baka son kwanciyar hankali nah?" Dan murmushi yayi ya langabe kai yace,"yanzu ummi ni mi nayi maki? Saboda duk iyakar sani nah banyi maki laifi ba." Harararshi tayi tace,ka sani safwan idan har kayiwa daddy dinka laifi toh tamkar ni kayi mashi, ka tafi ka barmu kullum daddy dinka baida wata magana sai taga,ya kira uncle dinka dake katsina yace rabonshi da kai tun ranar da kukaje kai da idi driver,kuma duk wayoyinka idan aka nema switch up,toh don mi hankali na bazai tashi ba?" Dago idanuwanshi yayi ya kalleta yace,"ummi shima daddy yaki ya gane abinda nake nufi neh." Dan shiru yayi tare da yamutsa fuska shima zai shagwaba sannan yaci gaba da cewa ,"maganar tafiyata a broad ni nace ba yanzu zan tafi ba." Daure fuskarta tayi tace,"saboda mi? Tun yaushe ake tambayarka,amma duk hujjojin da kake kawo wa babu na kamawa,saboda abinda na fahimta ka biyewa abokan banza suna neman su hana ka cigaban rayuwarka koh?sai dai kawai kuyi ta yawon banza na ba gaira ba dalili." Shiru yayi tunda yasan gaskiya take fada mashi,sai da ta gama sannan ya dago ya kalle ta yace,"kiyi hakuri ummi nah,kuma don Allah ki daina sanya abinda nayi acikin ranki,don bana son ciwo ya kamaki." Murmushi tayi saboda dama duk sadda zata zauna dashi tanayi mashi nasiha haka yake ce mata,don haka sai tace,"idan har da gaske kakeyi akan abinda ka fada why not ba zakayi abinda mahaifinka keso ba?" Ganin yanda take ta fada yasa yaji ta bashi tausayi yace,okay! Okay!! Ummi ya isa haka nan,kuma insha Allahu daga yau kin daina fada amma nima sai anyi mani abinda nake so." Kallonshi tayi anatse tace,minene kake so,har kake ta wahalar da kanka?" Murmushi yayi ya zuba mata ido don yaga yanda zata amshi maganar yace,"aure nake so kuyi mani." Zaro idanuwa tayi😳 tace, "what? aure lallai safwan kana da aiki agabanka,domin kasan daddy bazai taba yarda da wannan zancen ba." Murmushi yayi yace," mi yasa ummi? Watau kun fi gane inje inyi duk abinda naga dama da kuyi mani aure koh?" Jin jina kanshi yayi yaci gaba da cewa,"okay babu komai,duk zanyi abinda kukace but nan gaba don't blame at me." Mikewa yayi zai tashi ta yi maza ta tsayar dashi cikin tashin hankali tace,wait safwan,yanzu ina zaka?" Ranshi bace ya juyo ya kalleta yace,haba ummi ba nace ki dai na bata ranki ba,kuma ai nace babu inda zani har sai naga daddy." Yanayin da yayi neh kuma sai ya bata tausayi,don haka sai ta mike ta iskeshi inda yake tsaye tace,"ka kwantar da hankalinka,ni idan daddy din ya dawo zan kwatanta mashi akan maganar auren da kakeso kayi,amma wacece yarinyar da kakeso kuma yar wacece?" Wani dadi nehya kamashi yace,kai thank you very ummi,idan kikayi mani wannan taimakon ni bazan taba mantawa ba." Don haka zama yayi yai mata bayani komai akan sodangi,babu abinda ya boye mata don hatta da shekarun sodangi sai da ya fada mata. Irin girgicewar data nuba yasa [4/8, 10:21 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 05 Irin gigicewar da ya gani a fuskarta yasa ya dan sha jinin jikinshi ya zuba mata ido,"No No safwan,wai duka nawa kake da zaka dami kanka akan sai kayi aure?" Abinda kawai yaji ya fara fitowa kenan daga bakinta. Don haka runtse idanuwanshi yayi yaci gaba da sauraronta," ni wannan zabin naka sam bayyi mani ba saboda kai kanka kasan yarinyar daka kiyasta mani she's not your type, toh miye abin garaje aciki?" Dan numfasawa tayi sannan taci gaba da cewa," as your age wai duka nawa kake, ko baka ganin dan uwanka ma daya girmeka bayyi aure ba sai kai,toh ban amince ba,kuma idan zakaji shawarata ma kada ka sake ka tunkari dad dinku da wannan maganar,don wallahi zai ture duk wata kauna da yake maka ya ci mutunchinka,karshe ma kuma ya yanke maka hukuncin da bazaka taba tsammani ba." Tunda ya rufe idanuwanshi bai bude su ba har sai da yaji tayi shiru sannan ya cirasu da kyar ya kalleta,ita kanta jikinta yayi sanyi da irin kallon,amma ganin ya raba ya wuce bai ce komai ba yasa tadan maida numfashinta ta juya cikin dakinta tana mamakin yarinyar da safwan zai aura wai 14yrs. Hankali tashe safwan ya fada dakinshi,kwanciya yayi rigingine akan gadonshi yana kallon fan din da take juyawa ahankali,sai kuma can kasan zuciyarshi tunani ne fal acikinta,"shin wai sai yaushe neh parent dinshi zasu gane abinda yake nufi,saboda wannan shine Karo na biyu daya kawo masu zancen aure amma suka ki saurarenshi." Wuf yayi ya mije zaune gami da damkar zanin gadon dake jiki yaci gaba da tunaninshi," ni mutum ne mai tsananin bukatar mace akusa da ni,kuma suna sane amma suka share,tunda sunajin irin aika aikar da nakeyi acikin gari,amma damuwar da suke nunawa kadan ce akan idan nayi masu furucin aure," Numfasawa yayi tare da murmushin takaici ya fada afili,"sodangi tabbas ina sonki,kuma zuciyata batajin dadin yin tunanin bata rayuwarki kamar yanda na bata ta wasu 'yan matan,toh miye solution?" Mikewa kawai yayi ya nufi toilet dinshi,ruwa ya sakarwa kanshi don ya samu saukin tunanin daya ishe shi,ya jima sosai acikin ruwan,sannan daga bisa ni ya fito. Shiri yayi tsaf acikin kananan kaya,ke mai karatu da kin kalleshi sai ya burgeki,toh ballanta na yan matan da suka mutu kanshi. Wayarshi ce tayi ruri har ta katse bai ko kalleta ba saboda gyaran gashin kanshi daya dukufa yi,akaro na biyu ne tana farawa yayi dan tsaki ya suri wayar rai bace yace,"alo." Muryar dayaji ne yasa ya dan saki ranshi saboda kwana biyu yayi missing din mai muryar,ita kuma sai ta fara lankwashe harshe cikin yaudara da kinaya tace,sweet heart wai yaushe zakazo gareni neh,saboda har yanzu gaggan jikina ya kasa amincewa da kowa sai kai,ka taimaki rayuwata because I miss you so much😘." Murmushi yayi saboda jin abinda tace,shima kanshi yasan yayi missing dinta na kwana biyu,saboda tana daga cikin yan matan da suke dauke mashi hankali har ya fada wata duniya ta daban. "Kina inah?" Abinda yace mata kenan,wani dan ihu tayi tace," kada kace mani dai kana cikin gari?" Dariya yayi yace,"yes my dear,gani nan zuwa gareki." Jin abinda yace yasa ta ware ta hau yi mashi bayanin inda zai sameta,akarshe dai club sukayi mahada. Tunda safwan ya fita bai dawo gida ba sai karfe ukkun dare,shima don dad dinshi yasa mashi dokar indai yana gari toh ya tabbata ya kwana gida,amma da kila dai sai gari ya waye. Wurin sha biyun rana dad din ya kirashi awayarshi,da kyar ya samu ya iya daukar wayar saboda gajiyar dake jikinshi,"ina jiranka afalonah."abinda yace mashi kenan shi kuma ya zabura tare da fisgo rigarshi ya zira sannan ya nufi sashen dad din. A kishingide ya sameshi bisa wata resting chair dinshi yana kallon breaking news a CNN,hankalinshi ya tafi sosai awurin wani labari mai ban al ajabi,don haka sai da aka gama sannan yasa remote ya rage sautin maganar tv din sannan ya juyo ya kalli safwan da yake zaune gefenshi with his confidence yace,"my son safwan,ina ka boya cikin kwanaki ukku?" Sunkuyar da kanshi yayi yana murmushi yace,"daddy just forget kawai." Kuma don ummi dinshi taja mashi kunne,amma da kai tsaye yayi niyyar fada mashi zaiyi aure, tunda yana da dukiyar da zai iyayi wa kanshi abubuwa da dama ba tare da parents dinshi sun sanya hannu aciki ba. Murmushi Alhaji salmanu yayi yace," I love you my boy,saboda yanda kake aiwatar da al amurranka ba tare da tsoro ba,shi yasa nake son in doraka bisa wasu harkokina kamar yanda nayiwa dan uwanka yusuf,amma kurucciya ta hana ka tsaya ka fahimci komai." Dan shiru yayi sannan yaci gaba da cewa," don haka yanzu mi kake ciki akan plain dina na tura ka a broad? You are ready to go ko kuwa?" Safwan yayi jim bai ba dad dinshi amsa ba,saboda tunanin abubuwa da dama da yake ganin muddun ya tafi,duk zasu iya roshewa,tunda tafiyar zata iya daukarshi shekaru da dama ba tare da ya waiwayi Nigeria ba. Dagowa yayi ya kalli mahaifinshi da tun dazu shi yayiwa zuru yana kallonshi yace,"I'm sorry dad,saboda irin abinda zakaji daga baki na,domin ni kaina nasan ba haka kaso kaji ba,ina wasu abubuwa da dama da ban ida kammalawa ba,kuma idan na tafi zai zamo nayi failing akansu." Alhaji salmanu ya zuba mashi ido kawai,saboda babu abinda yake tunani sai wannan abu da danshi ya kafe akanshi ko minene shi? Domin tun kusan waccen shekarar yaso ya tafi ya ida digree dinshi acan amma yaki,kuma kila ba komai ba ne sai harkar mata da ya sanyawa kanshi,don haka girgiza kanshi kawai yayi yace,"inaso ka fada mani abinda ke hana ka tafiya." Safwan yayi dariya yace,dad kada ka damu about business ne,kuma I promise you next year zan tafi kamar yanda ka bukata. Babu yanda ya iya,saboda tun farko basu koya mashi bin ra ayinsu ba,sai dai duk abinda yakeso su ma shine abin son su komai rashin kyaun abin da muninshi. Don haka takarda ya dauko ta agreement yasa hannu sannan yaba safwan shima ya sashi yasa hannun yace,toh wannan shine kashen rigima ta dakai,saboda idan kuma har lokacin yazo kayi mani gardama toh a time din zan dauki kwakkwaran mataki akanka,don wallahi ko kai sai kayi nadamar bata mani lokaci da ka rinkayi. Safwan fuska a sake sai farin ciki yake, saboda yanda yaci galaba akan mahaifinshi ba tare daya sha wata wahala ba,kamar wancan karon ba. Kuyi hakuri my fans saboda banyi typing sosai ba saboda rashin caji. Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:21 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 06 I indicate this love story to my group Hausa Novels & my fans,love you all😘😘 Amsar takardar yayi hankalinshi akwance,domin babu abinda ya dameshi saboda shi kawai so yake yaga ya samu cikar burinshi ta mallakar abinda yake shawa a ajikin yar yarinya wadda bata san ko micece arayuwa ba,watau sodangi. Tsaf yasa hannu kamar yanda dad dinshi ya bukata,sannan ya mika mashi paper yana dan murmushin samun nasara,shima mahaifin nashi murmushin yake tare da zubawa paper ido yana cewa, amma kafin ka wuce kayi kokari kaga yusuf,saboda akwai wani sakonka daya biyo ta acct dinshi. Murmushi safwan din yayi,saboda jin wasu kayan tafiyar sun kara shigo masa watau (kudi)godiyya yayiwa dad dinshi tare dayi mashi bankwana,domin yace masa zaiyi wata tafiya da zata dauki tsawon wani lokaci, yana fita wurin dad dinshi ya nufi sashen ummin sa. πŸ’πŸ’πŸ’ Al amarin sodangi kuwa,kullum cikin tunani take da zaman jiran dawowar safwan,amma shiru kakeji shirwa taje kasuwa,don haka duk sai tabi ta zafge ta rame,ita ba kwanciya tayi ba,amma idan ka kalleta sai kayi tsammanin jinya tayi. Don haka gaba daya hankalin iyayenta duk yabi ya tashi, dama abinka ga yar lele wajen uwa da uba,kullum cikin tambayarta suke,amma amsar da take basu bata wuce ba komai,kuma tace ita lafiyarta kalau. Wani lokaci idan suka sanyata agaba suna rarrashi sai abin ya rinka ba sadah mmk,saboda yasan shi kanshi yana son yar uwarshi,amma irin wanda iyayensu keyi mata ba, domin shi yasan duk wazzhala da runtsi bai hanashi karatun arabi da bokonshi,kuma duk ranar da baida wani uzuri yaki zuwa makaranta sai ardo yayi kamar zai dakeshi,amma yana kallo idan har sodangi tace bazata ba toh babu mai takura mata,shi kanshi ya rasa miye dalilin haka? Yau kamar kullum,gari yana wayewa kowa ya tashi ya dasa hidimarshi,da yake weekend ne don haka sadah ya dauki nono da man shanu ya nufiv katsina,ita kuma sodangi ta fara azamar tafiya wajen kiwo. Ko yau din ma sai da ardo yaso ya hanata zuwa kiwon amma sodangi ta nace tace tana iya zuwa,ba don sun so ba suka kyaleta,amma ardo ya ja mata kunne akan kada ta dade kuma kada tayi nisa cikin jeji. Kada shanunta tayi tana tafe tana yan wake wakenta,amma acan kasan zuciyarta tunanin safwan takeyi tare da fidda ran sake ganinshi arayuwarta. Kamar kullum,bayan ta samu wurin da shanun ta zasuyi kiwo sai ta samu wani gajeren iccen mangwaro ta haye,ta samu reshe mai dan gwabi ta makale ajikinshi tana shan mangwaron. [4/8, 10:21 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 07 I indicate this love story to my group Hausa Novel &my fans,love you all 😘😘 Ta samu reshe mai dan gwabi ta makale ajikinshi tana ta shan mangwaronta,sai da tasha mai isarta sannan tayi lamo ajikin iccen tana kallon yanda shanunta suke kiwo,wani gyangyadi taji ta farayi mai dadin gaske saboda gajiya,ai kuwa tun tana gyangyadawa har ta fara sakin jikinta,nan da nan kuwa wani barci ci mai nauyi ya debe ta. Kamar yanda yacewa mahaifanshi zaiyi tafiya kuma zai dan jima kamin ya dawo,kuma duk daga cikinsu babu wanda yayi yunkurin tambayarshi inda zaije ko kuma idan yaje mi zaiyi (freedom) shi yasa yake tsula tsiyarshi. Don haka shima gari na wayewa ya biyo hanya,amma jirgi ya biyo don ya iso da wuri,kai tsaye guest house din babanshi ya nufa daya kankara acikin garin katsina,kuma gidan yana jimawa ba kowa cikinshi sai dai ma aikatan da aka zuba,kullum cikin gyaranshi suke,shiyasa idan ka shigeshi sai ka rantse akwai mai rayuwa acikinshi. Don haka ko da ya sauka wanka kawai ya sakeyi yasa kananan kayanshi,yayi kyau matuka,sannan ya dauki mota daga cikin motocin dake rufe a parking space. Tsaraba yayi sosai ya cika boat din motarshi ya nufi mazoji,kai tsaye inda sodangi tafi tsayawa tayi kiwonta ya nufa,agefe yayi parking sannan ya ida isa akafa yana takawa ahankali sbd kunyar shuka dake shigar mashi gaba. Ahankali ya zagaye wajen tsaf amma baiga sodanyi ba,sai dai shanunta dake ta shawagi awajen. Tsayawa yayi yana mmk tare da tunanin kodai yau ba ita tazo kiwon ba,kuma sai ya tuna ai yau asabar ta fada mashi yayanta sadah katsina yake tafiya tunda babu makaranta,don haka sai yaci gaba da searching dinta. A hankali yake leka can leka nan har ya iso wajen iccen mangwaron nan ya tsaya game da sarewa,domin har ya fara tunanin juyawa,sai yaji motsi asaman kanshi.da sauri ya daga kai yaga ko minene, sai kawai yaga sodangi makale abinta sai barshi take harda min shari. Mamaki abin ya bashi matuka yaga ko tunanin fadowa batayi,ai kuwa da gama tunaninshi sai yaga ta rikito gaba daya ta taho babu abinda ya riketa,kuma duk alokacin ta farka,ai kuwa da ta fara tsuwa da neman agaji ga harbe harbe tanayi.nan da nan safwan ya tarbeta ta fado jikinshin,shi kanshi yasan ayau yayi namijin kokari da har ya iya riketa ba tare da sun fadi ba. Ita kuwa dama tunda taga fadowa zatayi sai ta rufe idanuwanta bakin ne kawai ke neman ceto,don haka jinta da tayi a jikin mutum sai kawai ta kara makalmaleshi,gaba daya kuwa jikin ta rawa yakeyi. Dariya yayi yasa hannu ya rungumeta sosai ajikinshi har yana rufe idanuwanshi tare da sunsunar gashin kanta,kamshin dayaji tanayi neh mamaki ya kamashi saboda baiyi tsammanin abinda zaiji ba kenan,sumbatar kanta ya karayi tare da ajiyar zuciya wanda shi kanshi bai san dalilin yinta ba. A hankali sodangi hankalinta ya fara dawowa ajikinta ta fara tunanin a ina take,kamshin turaren jikinshi yayi mata dadi taji kamar tayi ta zama cikin wannan kamshin mai dadin sun suna,sai kuma kwalwarta tace mata toh waye kika makale? Da sauri ta fara janye jikinta shi kuma jin haka sai ya riketa gam saboda wata duniyar shagala dayaji ya lume cikinta ga wani dadi yana ta ratsa zuciyarshi.karfi ta fara sanya mashi,sunanta ya kira a setin kunnenta yace,"abokin ki neh safwan." Jin sunan da aka ambata yasa tayi saurin kallon fuskarshi,aikuwa ganinshi yasa ta washe fuska sai dariya tace,"lah yaushe kazo? Ka tafi ka barni kullum sai tunaninka nake,jibi yanda na rame." Ja bayan da ta fara kokarin yi don ta gwada mashi ramar da tayi yasa ya saketa ita kuma ta samu damar matsawa tana cewa jibi.bin ta yayi da idanuwanshi da suka canza yanayi yabi body dinta da kallo,aikuwa idanuwanshi sai kan kirjinta da sukayi dim dim,amma basu ida batsewa ba,wani miyau yaji ya hadiye saboda wani kwadayi daya taso mashi har tsakar kanshi.da sauri ya kauda idonshi saboda wani karatu da zuciyarshi ta farayi mashi. Ita kuwa haka da yayi sai taji bataji dadi ba,watau bai damu da ita ba kamar yanda ita takejin rashinshi da tayi kamar zata mutu.sumburar bakinta tayi ta nufi sandarta data jingine ta dauka zata wuce abinta.hannunta ya riko da sauri ya jawota kusa dashi yace,"kada kiyi fushi da abokinki,nima nayi missing dinki sosai, kuma rashinki da nayi shi yasa har kikaga na gaza magana saboda yanda najiki ajikina. Da zaki amince da kin dawo jikina kinci gaba da rayuwa ta har abada wadda bazata kare ba." Dariya maganar shi ta bata, aikuwa kyalkyatawa tayi har tana doka sandarta kasa,ga kuma wani dadi da taji wai yanaso tayi rayuwa ajikinshi,to kamar ya yake nufi? Don haka sai ta natsu ta bar dariyar ta kalleshi,wani kalli taga ya kara tsareta dashi,saboda safwan irin idanuwan nan gareshi wanda idan ya kalli mace bazata so ya dauke idanshi ba domin tafiya da imaninta da yakeyi lokaci daya. Toh abinda yaso ya faru da sodangi kenan,duk da kananan shekarunta.shiru tayi ta dauke idonta daga kallonshi,amma fuskarta murmushi take ta maida kallonta akan shanunsu tana wasa da sandar hannunta.takawa yayi ahamkali ya isa kusa da ita yace"mi yasa kike mani dariya don nace inaso mu rayu tare?" Satar kallinshi tayi ta gefe saboda tana gudun kada ta sake ganin wannan irin kallon da yayi mata dazu tace," mamaki nayi ta yanda zanyi rayuwa ajikinka," Bayyi mamakin abinda yaji ya fito daga bakinta ba,saboda dai yarinya ce,kuma gashi bata waye ba tunda bata da ilmin boko,don haka baiji komai ba yace mata,"yanzu dana rungumeki bakiji dadi ba?" Jin maganar da yayi sai taji kunya duk ta kamata,don haka da sauri tasa hannuwanta ta rufe fuskarta tana dariya tace,"banji wani abu ba, amma turarenka kamshinshi shi yayi mani dadi." Shima dariyar yayi yace,"okay thanks,kuma tunda shi kadai yayi maki dadi toh zan sawo maki wanda yafi shi dadi ma,amma ni abu biyu sukayi mani dadi,da yanda na rungumeki sai kuma kamshin turarenki." Jin zai kawo mata turare irin nasu na yan birni mai kamshin tsiya ta washe baki tace,"ai kuwa na gode,don dama nima na molasa ne nake shafawa." Murmushi yayi tare da zura hannuwanshi a aljihu duka biyun ya kira sunanta cikin wata siga ta yan boko yace," muje wajen mota ta kiga tsarabar da nayo maki."aikuwa cikin doki da murna tayi gaba yana biye da ita tana tayi mashi tambayoyi iri iri,wani ya bata amsa wani kuma yayi mata murmushi. Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:21 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na 08 I indicate this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all 😘😘 Tafiya yake cikin natsuwa,ita kuma sai yan tsalle tsallenta takeyi har suka isa wajen da yayi parking din motar,key yasa ya bude boat din ya daga marfin ita kuma tayi ta maza ta leka tana cewa,"ina tsarabar tawa?" Murmushi yayi ya nuna mata da hannu yace"duk abinda kika gani acikin boat din nan naki ne." Baya taja cikin mmk da tsoro gami da zaro ido 😳 tace," wa ni?duk ina zan kaisu πŸ€”kuma yau idan ardo ya samu lbr kila ya yankani."yanda tayi neh ta bashi dariya sosai amma sai ya gintse yace,"waya fada maki ana dukan yar gata? Sam ardo bazai taba dukanki ba tunda kince yana sonki." Kada kai tayi jikinta asanyaye tace,"na sani ardo yana sona sosai,don ma ina iya ce maka son da yakeyi mani har yafi wanda molasa takeyi mani,amma kuma shi mutum ne mara son wargi domin naira biyar ya hana in amsa awajen wani toh bare wannan tulin kayan haka." Zuba mata ido yayi yana kallonta,ita kuma sai sheka mashi bayani take har ta gama,ya fahimce ta sosai domin duk afuskarta yaga iyakar gaskiyar abinda take fada.murmushi yayi ya lumshe idanuwanshi ya bude yace,"kada ki damu sodangi,ki bari ni da kaina zan kaiwa hardo kayan ince ya ajiye maki,amma yanzu ina son ki duba kiga abinda kikeso sai ki dauka." Dan matsowa tayi ta sake leka kayan,sannan tasa hannu cikinsu tana daddaga,wani kwalin chocolate idonta yayi arba dashi takai mashi cafka tana dariya tace,"yawwa na samu wannan." Shima dariyar yake ya tufe boat din yana kallonta,tsaye sukayi ajikin motar suka ci gaba da hira ita kuma tana ta aikin cin chocolate din nan har taci kusan rabi.shi kuwa kallonta kawai yake da mmk,saboda yanda tasa zaki agabanta tana taci kamar mai jin yunwa,don haka sai ya tambayeta yace,"sodangi ko kinajin yunwa neh?" War tayi da idanuwanta ta kalleshi tace,"eh amma ba sosai ba." Hannu ya mika ya kama kwalin chocolate din yace," ki daina shan wannan amatsayin maganin yunwa,domin zai iya cutar dake ta hanyar kara maki kiba,kuma gashi ni bana sonta,don nafison mace yar dai dai watau ba ramamma ba kuma ba mai jiki ba kamar yanda kike yanzu. Duk sadda safwan ya yabeta ko ya yabi wani abinta sai takanji kunya ta kamata,don haka yanzu ma abinda taji kenan shiyasa tayi sauri ta saki kwalin ta rufe fuskarta da hannuwanta tana murmushi. Murmushin yakeyi shima ya bude sit din kusa da driver ya jawo hannunta ya turata ta zauna,amma bai rufe marfin ba,sannan ya nufi sit dinshi ya bude ya zauna. Lemu da biscuits ya mika mata yace," kici wannan kilaya rage maki yunwar da kikeji.amsa tayi ta far mashi saboda dama yunwar takeji kuma gashi yau batazo da komai ba shi yasa tun zowarta ta fara da mangwaro. Daga kanta da zatayi sai ta hango wani can nesa kamar ardonta,saboda duk kayan jikinshi da ya sanya ta sanshi dasu,ba wurinsu ya nufo ba,gittasu yayi,kuma time to time sai ya dago ya kalli inda take fuskarshi babu wata walwala acikinta. Tsoro taji ya kamata da sauri ta nemi fita daga motar jikinta yana rawa,safwan kuwa duk yana kallonta da canzawar da tayi cikin dan kankanen lokaci, don haka da sauri ya riketa cikin damuwa yake tambayarta," mi ya faru sodangi." Ture hannunshi tayi ta fita daga motar tana mazurai tate da daga hannunta tana nuna mashi ardon,amma bakinta rawa yake ta gaza furta komai.bin inda take nunawa da hannunta yayi ya hango ardo yana waiwayensu. Kallonta yayi da sauri yace,"ko ardo neh?" Daga mashi kai tayi dai dai wasu hawaye sun malalo daga idanuwanta,sai lokacin ne ta samu dakyar tace,"ni yau na shiga ukku!!! Kila ardo yau sai ya yanka ni tunda naga yanda yakeyiwa yaran da ake kawo mashi kararsu idan an gansu da wani." Yanayin da takeyin magana neh yaji duk ta bashi tausayi ya zagayo inda take yace,"kada ki tayar da hankalinki my friend, saboda babu abinda ardo zaiyi maki,ko kin mance kece shalelenshi?" Dago idanuwan ta tayi cike da hawaye tace,"wallahi ardo sam ba haka yake ba,nidai yau ban san yanda zan kare baπŸ™† zabura tayi taci gaba da cewa bari in tafi,don yana iya turo mani baffanah,kuma shi ba tausayi gareshi ba. Bin bayanta yayi yana kiran sunanta cikin damuwa,sabida ganin irin yanda ta rude yana cewa,sodangi ki jirani mu tafi tare sai inyi mashi bayanin komai. Tsayawa tayi ta juyo saboda tuni tayi mashi nisa tace da karfi"bayanin mi zakayi mashi?"safwan shima ya daga murya yace ,"zan fada mashi cewar,ina sonki." Duk da tana cikin rashin kwanciyar hankali sai da tayi dan murmushi wanda safwan ya gaza gane ma anarshi,saboda iyakar fuskarta ya tsaya,juyawa tayi taci gaba da tafiya cikin sauri mai kama da gudu. Tsaye yayi yana kallonta har sai da ta kai ga bai hangenta kwata kwata,sannan ya juya ya kalli shanunta da ta bari saboda rudewa.murmushi yayi ya saddar da kansa kasa yana wani tunani,toh komi ya tunah?????? Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:22 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 09 I indicate this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all 😘😘 Sodangi tayi ta ta sauri,ga zufa ta hada tayi sharkaf,amma kuma mi?tana isowa kofar gidansu sai ta gaza shiga ta samu wani wuri ta labe,amma duk hankalinta yana kan mai shiga da fita acikin gidansu har sanyin maraice ya fara sakkowa. Dafa kafadarta da akayi yasa ta juyo afirgice kuma idanuwanta suka karayo waje don tsoro,ganin sadah neh yasa ta mayar da ajiyar zuciya ahankankali harda lumshe idanuwanta,shi kuwa zuba mata ido yayi yana kallonta cikin mmk yace,"mi kikeyi anan wajen?" Hawaye neh kawai taji ya zubo mata cikin I ina ta fara fada mashi komai, babu abinda ta boye mashi,jin abinda tayi shi kanshi sai da ya tsorata yace,"lallai yau kin ba ardo kunya, sbd duk rugar nan babu wanda yake yabo kamarki,sannan kuma ko tsakanin ni dake kece kullum mai kirki bani ba,don haka sai kisan yanda zakiyi don ni kinga tafiyata. Da sauri ta cafko hannunshi ta rike ta fara kuka tana cewa,"don Allah kada ka tafi ka barni yayanah,ka taimaka ka kira mani molasa.shi kanshi ta bashi tausai tunda yana sonta don dai kawai yana son ya gwada mata kuskuren da tayi,domin ko kiwon nan da take tafiya inda za a biye mashi baza ta je ba,wannan shine ra ayinshi. Cisge hannunshi yayi data rike yayi kamar zaiyi tafiyarshi,ta kara wartoshi cikin kuka irin na shagwababbin ya'ya tana cewa"wayyawoo ni molasatah,don Allah ka kira mani ita." Kama hannunta yayi ya fara tafiya da ita,ada ta fara cijewa,amma ganin yafi karfinta yasa ta hakura dole ta rinka binshi kamar butun butumi sai dai hawaye shar kawai dake fita a idanuwanta.ganin har sun iso kofar gidan basu hadu da ardo ba yasa ta kwace hannunta tayi cikin gidan da gudu,kan ta tsaye dakin molasa ta nufa. A dai dai lokacin da sadah yake ajiye kayan dayazo dasu ne molasa ta fito daga bandaki,da yake alkunya take mashi bata faye damuwa da al amurransa ba don haka bata tanka mashi ba sai dai shine yayi mata sannu da gida, sannan yaci gaba da cewa ina ardo? Jim tayi kadan kamin ta bashi amsa,sannan cikin yanayin damuwa ta kalleshi tace," dazu dai ya shigo duk ba yanda yake ba,kuma na tambayeshi amma baice dani komai ba,kuma tunda ya kara fita bai sake dawowa".kamin sadah ya bata amsa ardo ya shigo don haka shiyasa sadah yayi shiru ya nufi ardon ya gaisheshi tare da mika mashi cinikin da yayi na nono da manshanu. Babu yabo ba fallasa ardo ya amshi kudin tare dayi mashi sannu,sannan ya kalli molasa yace,"ina sodangi?"molasa bata fahimci komai ba tadan waiga hagu da dama tace,"ai bata dawo ba." Hankalin ardo yadan tashi ya sake maimaitawa yace,"bata dawo ba?toh nima daga can nake kuma bata ba shanun mu." Juyawa yayi zai sake fita sadah yayi sauri ya zubar da gwiwoyin shi kasa ya kira sunan baban nashi da karfi yace,"ardo!!!don Allah ka yafewa sodangi laifintaπŸ‘ Ardo ya juyo da sauri yace,"a ina ka ganta,saboda ni bukatar ganinta kawai nake."sadah ya sunkuyar da kansa kasa yace,"tana cikin dakin molasa,saboda alokacin dana dawo tare muka shigo."ardo yayi ajiyar zuciya tare da dan guntun murmushi yace,"alhamdulillahi, ni dama tunani nah ko tayi wani wajen."kamo hannun sadah yayi ya mikar dashi tsaye yaci gaba da cewa,muje muyi shirin sallar magriba." Sadah cikin ladabi da biyayya ya mike tsaye,dayaji abinda ardo ya fada sai yaga ai da sauran lokacin magriba din,don haka sai ya dubi mahaifin nasu yace,"ardo ko kamin lokacin ya ida inje in nemo dabbobin don kada subi wata hanyar da ban."Ardo ya dafa kafadarshi yace,"ko kaje sadah bazaka gansu ba,saboda ni kaina naje jejin sau biyu,amma ban gansu ba,sai dai zuciyata tana bani sun taho sun bace hanya,na kuma san komai dare zasu dawo."don haka butoci suka dauka suka nufi kofar gida don su gabatar da alwallah,ita kuma molasa ta nufi daki da sauri wajen sodangi. Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:25 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 10 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all😘😘 Idanuwanta abude ta shiga dakin,sbd sodangi kawai takeso ta gani,amma sai taga wayam. Mamaki ne ya kamata saboda tuni ta riga tasan halin danta sadah sam ba yaro bane mai karya,don haka sai ta yanke shawarar ta bincike dakin lungu da sako,karkashin dan karamin gadonsu ta fara lekawa,wayam ta gani,don hatta da tulin kayan data san ta ajiye suma bata gansu ba,cikin sauri ta dago tana kara karewa dakin kallo sai idanuwanta suka dira akan kayan datake nema awata kusurwa an jibgesu. Cikin daurewar kai ta nufesu tana jawowa sai sukayi ido biyu da sodangi tana ta zare idanuwa (Masha Allahu) sai mazurai take,sannan fuskarta dauke take da tsoro da firgicin abinda zai faru da ita. Molasa abin yaso ya bata dariya,amma sai ta gimtse fuska,dama kuma sodangi tafi tsoron molasa akan mahaifinta,saboda yafi sakar mata fuska fiye da ita,don yanzu abinda yasa har takejin tsoron haduwa dashi saboda ganin hukuncin da yakeyiwa sauran yara idan har aka kawo mashi kararsu,gashi kuma tana tsananin tsoron duka. Molasa fuska adaure tace,"miye haka sodangi? Wane irin abu ne kikaje kikayo har yasaki tsuma haka?"sodangi haba na rawa ta fito daga cikin kayan data boye tanq cewa,"don Allah molasa kada ki tona ni,idan ardo ya yambayeki kice mashi baki ganni ba."molasa tayi murmushi tare da shinfida abinda zatayi sallah akanshi tace,"kinsan abinda ba zaiyiwu kenan ba,watau kina son inyiwa ardo karya kenan?"dan tsaki taja sannan taci gaba da cewa maza kije kiyo alwallah kamin ardon ya dawo inji abinda kikayi tunda kinki ki fada mani."tana gama fadar haka ta kabbara sallarta,ita kuma sodangi ta mike cikin sanda ta nufi waje,alwallah takeyi amma idanuwanta duka biyun sunyiwa kofar gida zuru saboda kada ardo yazo ya sameta. Sallar tayi amma duk ba a cikin natsuwa ba saboda muryar ardo dataji atsakar gida.molasa tana gama sallar tayi addu o inta ta nufi tsakar gidan wajensu ardo,gefe ta koma tare da tsugunnawa ta gaishe da ardon sannan shi kuma sadah ya gaisheta,wannan itace dabi arsu gaba daya gidan. Ardo yayi gyaran murya yace,"molasa ina sodangin,ko baki ganshi ba?"molasa cikin damuwa tace,"na ganshi ardo,amma kuma taki ta fada mani abinda tayi maka." Numfasawa ardo yayi sannan ahankali yayi mata bayanin iyakar abinda ya gani,sannan yaci gaba da cewa,"yanzu abinda nake tsoro shine,ko wani dan cikin rugarnan yaga sodangi da wannan mutumin?idan har kuwa an gansu dole ne inyi mata hukunci kamar kowa" Jin haka sadah ya dago idanuwanshi da sauri yana kallon ardo cikin firgici yace,"ardo sodangi bazata iya daukar wannan bulalar ba,kuma idan har kana tunanin ta aikata wannan laifin,to ni zan amsar mata hukuncin duk da ya hau kanta,amma yanzu inason ka bani izini inje in tambayeta iyakar abinda ta sani akan wannan mutumin." Ardo ya zubawa sadah ido yana kallonshi cikin tausayi yace,sadah sai dai kayi hakuri,domin nima komai zanyi bada son raina zanyi shi ba,don dai banda yanda zanyi ne shiyasa,amma yanzu kaje wurinta kaji abinda zata fada maka." Sadah yamike jiki asanyaye ya nufi dakin molasa,yana shiga sodangi ta taso jiki yana rawa,saboda duk tanajin abinda yake faruwa. Hannunshi ta rike ta mau tana zubar da hawaye tare da girgiza kanta alamar batayi komai.ji yayi tausayinta ya kamashi,don haka shima kama hannun nata yayi ya zaunar da ita akan gadon molasa,sannan shima ya zauna gefenta yana kallonta. Numfasawa yayi sannan ya kira sunanta,"sodangi."da sauri ta dago kanta ta kalleshi tare da amsawa.don haka sai yaci gaba da cewa,"a ina kika hadu da mutumin nan?" Sodangi bata boye mashi ba duk ta fada mashi har abinda ta fada mashi a dazu.shiru kawai yayi yana kallonta har ta gama sannan ya kada kanshi yace,"ya taba cewa yana sonki neh?" Sodangi tayi shiru tana tunani,can ta dago kanta tace,"eh ya taba cewa,don har yana cewa yana so muyi rayuwa tare." Sadah ya kara zuba mata ido,saboda yaro ne mai hankali da fahimta,don haka sai ya sake tambayarta,bayan kama hannunki da kikace yayi sai kuma mi?" Sodangi tayi kuri tana kallon shi ta rasa abinda zata fada,amma dayake tasan tsakaninta da dan uwanta akwai shakuwa kuma babu abinda yake boye mata na rayuwarshi,don haka sai tayi kasa da idanuwan ta cikin jin kunya tace," yana rungumeni ajikinshi don har yana cewa turarenah yanayi mashi kamshi mai dadi....." Bata karasa ba taji ya kama kunnenta da karfi ya murda cikin bacin rai yace,"kinji kunya sodangi, tunda har kin mance da Martabar gidanku kuma kinci amanar yarenki watau fullanci,domin duk inda bafullace yake yana da gadon kunya,amma ke na lura kin saki taki kare ya dauka." Wani uban tsaki yaja sannan ya kara fisgo kunnen da karfi,ita kuma zani tasa ta toshe bakinta da karfi tana kuka amma bata son iyayenta suji,saboda kara dan uwanta ya hukunta ta da iyayenta suji abinda tayi.sai da ya gama punishing dinta ta hanyqr murdar mata kunne sannan ya saketa tare da mikewa yayi waje. Kusa da ardo ya sake zama,amma baice komai ba har saida ardo ya zunguroshi yace,"ya mukaji kayi shiru sadah?kodai ta aikata abinda muke tunani?"sadah yayi wani dan guntun murmushi yace,"ardo bata aikata ba,amma shawarar da zan baka shine kayi gaggawar aurar da sodangi domin yaron dake zuwa wurinta ba irin ajinta bane,don haka idan har kun samu ganinshi ku tambayeshi idan aurenta zaiyi,idan yace a a toh ku nemi wani ku batashi." Shiru ardo da molasa sukayi suna kallon sadah kawai sbd dukkansu zuciyarsu ta basu wani abu,amma sadah ya boye masune.don haka babu wani tunani da ardo yayi ya dauki shawarar dansu,dai dai zaiyi mgn sai yaji kukan shanunsu suna wucewa garkensu,gaba daya suka mike tsaye cikin farin ciki,sallama kuma sukaji abakin kofa,don haka sadah da sauri ya nufi wajen yana amsawa. Bay san mai sallamar ba,amma duk da haka sai ya bashi hannu suka gaisa yace,"nan ne gidan ardo?"ardon ne ya karaso dai dai sadah yana cewa,"eh nan neh."ardo yana karasowa shima ya mika mashi hannu don su gaisa,amma sai bakon yaki yayi sauri ya zube kasa yana gaisheshi. Ardo yaji dadin yanda wannan matashin ya girmamashi don haka sai ya umurci sadah daya kawo masu tabarma.da sauri sadah ya juya cikin gida ya dauko tabarmar harda ruwan sha,shimfidata yayi ardo da bako suka zauna,shi kuma sadah ya koma gefensu ya tsugunnah Ardo suka kara gaisawa da bako,sannan ya nemi sanin kowa neneshi?dan matashin nan ya gyara zamanshi yace,"ni sunana safwan." Love you sis 😘😘 08033481518 [4/8, 10:25 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 11 I dedicated this love story to my Hausa Novels & my fans,love you all 😘😘 Jin sunanshi yasa sadah ya zabura ya mike tsaye rannan abace ya nuna shi da dan yatsa yace,"sake biyo ta kayi?to ta Allah ba taka ba,kuma idan har baka kama kanka ba duk abinda nayi maka kai kaja wllh." Ardo ne ya dakawa sadah tsawa yace,"kai ni bana son shashancin banza,daga ganin mutum kawai sai ka haushi da masifa."sadah ya bude baki zaiyi magana sai kawai safwan yayi maza yace," ardo ni ne safwan wanda ka gani tare da sodangi dazu,kuma nazo don in sanar da kai cewa ina sonta kuma zan aure ta."ardo yayi murmushi yace,"alhamdulillahi yaro ai ka kyauta,saboda tun dazu tunani nah ina zan ganka kuma q ina kake da kai da iyayenka,amma tunda ka gajerce mani wahala ka kawo kanka ai abu yayi dadi, don haka sai kayi mani bayanin ko kai wanene?" Safwan yayi kasa da kansa yayiwa ardo bayanin cewar shi dai mahaifinsa na abuja kuma babban dan kasuwa neh, amma asalinsu katsinawa ne,amma mahaifinsa bai faye zama ba,don haka zan turo maka kanin mahaifina sai ku ida jin komai daga gareshi. Daga ardo har sadah sunji dadin wannan bayanin na safwan,domin bayanin nashi ya nuna masu bada wasa yazo masu ba,don haka anan take ardo ya nunawa safwan jin dadin shi,kuma yace," ina jiran zowarku goben kai da wakilinki domin ko bakazo ba dama nayi niyyar bayar da ita ga wanda nakeso." Jin furucin ardo yasa safwan yayi wuf ya dago idanunshi yana kallon shi,watau ashe da tsoro ya hanashi karasowa da yayi asarar rasa sodangi arayuwarshi. Sai da yayi sallar isha I sannan yayi ban kwana dasu tare dayiwa ardo alkawarin dawowa gobe kuma da wuri. Abin yaro, sodangi jin ba wanda ya sakeyi mata mgn tun daga tambayoyin da sadah yayi mata yasa ta fito ta kama hidimarta kamar yanda ta saba. Don haka yauma kamar kullum data gama yan ayyukan da take taya mahaifiyyarta sai ta shirya tsaf ta fito zata kada shanunsu ta tafi kiwo,sadah ta gani acikin shanun yana kwance waddanda aka daure, fuskarshi asake ya dago ya kalleta yace,"sodangi sai ina neh?" Itama dariya take tace,"kiwo zani yaya sadah,kai yau bakaje makarantar ba?" Tsaf ya kwanto shanun ya kadosu waje yana cewa,"kin mance ne,ai yau lahadi ba a zuwa makaranta."dafe kanta tayi tace,"wai ni,wallah na manta sam yaya sadah,toh baka zuwa katsina kenan?" Sadah yayi dariya tare da amsar sandar hannuntq yana cewa,"yau bana zuwa ko ina sai kiwo,kinga na hutasheki kenan sai kije ki taya molasa aiki." Subbura dan bakinta tayi ta dan ya mutsa fuska tace,"ni bazan zauna ba,kiwo na zani."sadah yayi dariya yace,toh muje don yau kafana kafarki saboda na ganeki so kike kije kiga safwan." War tayi da idanuwan ta ta kalleshi,acikin zuciyarta tace,"oh ya akayi ya gane abinda yake acikin zuciyata,tabbas safwan kawai nakeso in gani,domin ayanda nakejinshi bani son ranar da za ace gata ban sanyashi a idanuwana." Don haka murmushi kawai tayi tabi bayan dan uwan nata. Kamar yanda safwan yayi alkawari haka ta kasance,saboda goman safe a mazoji tayi mashi shida kanin mahaifinshi. Bayan gaisuwa da kuma ruwa da fura da nono da madarar shanu sabuwar diba da aka jera agabansu safwan sai ardo ya gabatar da kudirinshi akan lamarinsu safwan da sodangi yace,"toh ni bayanin da nakeso inyi maku shine,nan da kwana bakwai nakeso in aurar da sodangi,shi yasa na nemeku inji ko kun shirya?" Jin maganar kanin mahaifin safwan yayi kamar daga sama,don haka sai ya gyara zamanshi duk da safwan ya riga ya gama tsarashi kamin su zo cewa,so yake ya shige mashi gaba wajen nemqn aurenta ba tare da sanin mahaifanshi ba,tunda ko sunji ba bazasu barshi ba,shi kuma kanin mahaifin nashi da yake ya dade yana kyamar irin dabi u na safwan shi yasa ya amince da shige mashi gaba tare da fatan Allah yasa auren ya zame mashi dalilin shiriya don haka sai yace,"amma ni aganinah ardo kamar sati daya an diba kadan ina ma laifin wata daya." Ardo yayi murmushi yace,"ai dama ban matsaba,domin sodangi tana da masoya sosai,don dai itace bata sauraronsu,don haka idan har baku shirya ba sai in ba wani,domin asati dayan nan babu fashi ba saba lokaci." Karaf safwan yayi ya kalli kanin mahaifinshi yace,abba kada ka damu don nima ashirye nake,amma akwai wani hanzari ba gudu ba,tunda sodangi yarinya ce bata ida mallakar hankalinta ba,idan akayi auren zan barta nan kusa daku har zuwa lokacin da zatayi wayau sosai ni kuma alokacin na kammala wasu shirye shiryena sai in dauketa mu wuce." Ardo ya zuba mashi idanuwa yana kallonshi,sannan yace,"duk ban fahimci nufin ka ba."safwan ya kara gyara zamanshi yayi kasa da muryarshi cikin ladabi yace,"zan ginawa sodangi gida acikin rugar nan mu zauna tare,amma da lokaci yayi sai in dauketa mu wuce tare gidana dake abuja." Ardo yayi murmushi yace,"na gane kwarai dan samari,ai hakan ma yayi babu matsala,shi kuwa kanin mahaifinshi shiru yayi yana sauraronsu har suka gama,sannan ya dago ya kalli safwan yaga sai wata fara a yake hankalinshi kwance,don haka shima sai ya kwantar da nashi hankalin yasa bakinshi aka ida shirya yanda auren zai kasance." Har su safwan suka gama tattaunawa amma baiga giccin sodangi ba,don haka sai yaji ya damu,kuma idanuwanshi ita kawai suke kwadayin son gani koda giccinta neh,amma shiru babu ita babu alamarta,haka itama acan sadah yana lura da duk wani motsin da takeyi,tun tanayi da walwala har yaga ta samu wuri ta takure kamar wadda tunani ya matsa mawa. Murmushi kawai yayi ya kauda kanshi daga kallonta,amma kuma akasan zuciyarshi yana mamakin irin saurin fadawa soyayya da sodangi tayi da wuri,saboda shi azaman yanzu makarabtar da yake zuwa yan mata da yawa sai a pro ching dinshi suke amma babu wadda ya kula,saboda ba abinda ke gabanshi kenan ba. Don haka maida hankalinshi yayi yaci gaba da kiwon shanun har zuwa lokacin dawowarsu gida yayi ya kalleta yace mata ta tashi su tafi. Sukuku tayi har suka iso gida bata da wata walwala sai dai zurfin tunani data afka.bayan sun hutane ardo ya kebe sadah gefe daya duk yayi mashi Bayanin yanda sukayi dasu safwan,da kuma sati daya daya sanya masu,sadah yaji dadi sosai don bama kamar daya samu labarin yar uwarshi bazatayi nesa dashi ba,don haka sai ya roki ardo da kada ya sanar da sodangi plain din aurar daita ga safwan,amma tasan kawai za ayi mata,kumaya hana sodangin fita sai ranar da za a kaita gidan mijintΓ . Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:25 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 12 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all😘😘 Sadah yayi farin ciki matuka dajin yar uwarshi bazatayi nisa dashi ba,don haka sai ya roki ardo da kada ya sanar da Sodangi cewar za a aurar da ita ga safwan,sannan kuma kamar yadda yake a al adarsu yanason a boye sodangi na tsawon sati daya tunda bikin ba wani lokaci zai dauka ba.haka kuwa akayi,domin tundaga ranar sodangi ta daina zuwa ko ina,ba tare data farga ba abubuwan suka faruwa da ita. Idan ta tashi tunda safe kamar kullum data fito don ta kada shanunsu zuwa kiwo sai dai taga basu nan,kuma ko ta bi hanya sam bata ganinsu dolenta ta koma gida.kuma idan ta koma gidan idan banda yan jike jike da ake ta banka mata babu abinda akeyi domin ita abin ma har ya fara isarta. Madarar shanu kuwa maida mata ita akayi tamkar abinci,amma da zuma ake hada mata ita,banda itatuwan magunguna,domin tayi wanka dasu,wasu kuma ayi mata hayaki,wasu kuma a babbar roba ake sanya matasu ta shiga ta zauna. Ita da kanta sodangi sai da ta gane acikin yan kwanakin nan ta canza sosai domin akoda yaushe cikin canza pant take saboda lema da take damunta. Shi kuwa safwan suna barin wajen ardo yaje yayi cinikin wata katuwar gona dake kusa dasu,kuma nan take ya basu kudinta,kuma babu wani bata lkc da yayi ya nemi ma aikata nan da nan suka fara gina mashi gidan tare da shawarwarin manya manyan artists da ingenious.don haka acikin kwana biyar har anyi an gama sbd yanda ma aikata suka rinka aikin gina shi ba dare ba rana. Yau saura kwana biyu kwanakin da ardo ya diba su cika,sodangi tana zaune gefe daya tayi tagumi,domin daga ganinta kasan tana cikin damuwa ta abubuwa da dama,gashi babu wanda ya bata fuska daga cikin dangin mahaifanta bare tayi tambayar abinda yake damunta. Lumshe ido tayi ta bude tare da furzar da iska ahankali ta kira sunan safwan acikin makoshinta,tunaninshi ta fada dama aikin kenan ba dare ba rana,"ko ina yake yanzu?kuma mi yasa ya tafi ya barni?"wasu hawaye neh taji sun taru acikin idanuwanta,don haka kokari tayi tayi don taga sunki fitowa saboda gudun maganar danginta da suke cewa ba a taba ganin mai hali irinta ba duk acikin danginsu,wai bata da kunya saboda kai tsaye take fiddo al amurranta kamar ba bafullatana ba. Shigowar sadah yasa ta dawo daga duniyar tunanin data tsunduma ta dago kai ta kalleshi sai zufa yake saboda daga kiwo ya dawo,shima kallonta yake tamkar yau ya taba ganinta,ganin yar ramar da tayi har ta fara bayyana yasa yaji wani tausayinta ya kamashi don haka da sauri ya kauda kanshi ya wuce tare dayin alwallar sallar magriba. Bayan yayi sallar isha insa ya dawo gida yayi wanka tare da canza kaya,idan ka ganshi bazaka taba tunanin shine yaje kiwo ba,saboda shima sadah yana daga cikin kyawawan matasan da yan mata ke ribibi a kauyensu da kuma zagayensu. Dakin molasa ya nufa yayi sallama,duk danginsu dake cike da dakin suka taso mashi bama kamar abokan wasansu,dariya kawai ya rinkayi masu saboda shi Allah bai sa ya iya irin wasan ba,idan da sodangi lami lafiya take da itace mai cashe masu. Kallo inda take yayi yaga duk ta dukunkune wuri daya, kamar batama san abinda akeyi ba,sunanta ya kira,"sodangi."ta dago ta kalleshi da zurmammin idanuwanta da suka rame yace,"zo muje ki dama mani fura kinji yar kanwata." Mikewa tayi duk jikinta babu kwari ga rashin cin abinci,saboda madarar shanu kadai take sha amatsayin abincinta,juyawa yayi ita kuma tabi bayanshi har zuwa yar bukkarshi.gefen yar tabarmar dake dakin ta raba ta zauna shi kuma akan katifarshi da yake kwana ya zauna sannan ya zuba mata ido yana kallonta cikin sigar tausayi. Sodangi ta dago ta kalleshi tace,"yaya sadah ina furar take in dama maka?"murmushi kawai yayi yace,"dama kin san kema babu wata fura da zaki dama mani,saboda bani iya shan damunki sai na molasa tah."sumbura baki ta danyi wai ita taji haushin maganar da yayi tace,"nima ai yau da gobe zan koyi irin na molasar,kuma molasata ce ba taka ba." Dariya yayi don dama yana sane yace haka,saboda duk ranar dayace mata haka wuni zatayi tana tsegumj shi kuma yayi tayi mata dariya yana kara tunzurita. Fahimta yayi ta dan saki jikinta sai ya natsu daga tsokanar da yakeyi mata yace,"sodangi kin san ke kadai ce na mallaka amatsayin yar uwata koh?"kada kanta tayi alamar amsawa,don haka shi kuma sai yaci gaba da cewa,"toh inason ki fada mani abinda yake damunki cikin yan kwanakin nan,saboda dai idan har maganar aurece ai ba kanki farau ba,tunda kina sane duk kusan yan matan kauyen nan kusan a haka ake aurar dasu." Sodangi tayi kwal kwal da idanuwan ta tamkar dama jiran dalili take,nan da nan kuwa sai hawaye shar suka gaggaro abisa kumatun ta,da bude bakinta sai kawai yaji ta ambaci"safwan". Daga nan kuma bata sake cewa komai ba. Mamaki ne ya kamashi matuka,wai wannan wanne irin so ne sodangi takeyiwa safwan,duk da ya fahimci shima safwan din yana son sodangi, amma kamar na yar uwarshi ya fi yawa,don haka sai ya kara matsawa kusa da ita ya dafa kafadarta yace,"Sodangi mi safwan din yayi maki?"sodangi ta dago manyan idanuwan ta ta kalleshi tace"ya tafi ya barni,gashi innah laure ta fada mani wai aure za ayi mani da kado." Murmushi yayi tare dasa hannu afuskarta ya share mata hawayen da suka fito yace,"kiyi shiru kanwata, saboda dama ita rayuwa duk haka take,domin ba kullum kake samun yanda kakeso ba,kuma miye a auren kadon?tunda dai ko safwan aka baki ai shima kadon ne,don haka ki kwantar da hankalinki wuri daya,sannan kuma ina baki shawarar duk abinda zaki so kisoshi don Allah kuma sese sese,haka nan ma duk abinda zaki ki shima ki kishi don Allah bada tsanani ba." Sodangi tayi shiru tana sauraron nasihar da dan uwanta yake mata,kuma da alama duk ta fahimce shi,don haka sai ta sake share hawayenta tace,"toh shikenan yayanah na gode da shawararka,amma inason ka taimakeni da wani abu guda daya?" Sadah ya kalleta sosai yace,"fadi ko minene kanwata zanyi maki idan har bai taka shara a." Kur tayi mashi da idanuwan ta tace don Allah inason in ga safwan yayanahπŸ‘.dafa kanta yayi yana murmushi yace "kiyi hakuri kanwata saboda shima safwan din kusan kullum abinda nake fama dashi kenan,wai yana son ya ganki,idan ba don ardo ba ni da tuni na kaiki gareshi,shi yasa nake ta baki hakuri. Love you sis 😘 08033481518 [4/8, 10:25 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 13 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all 😘😘 Sodangi tayi kasa da idanuwanta,sauran hawayen dake ciki suka ida zubowa ta rufe idanun. Yar karamar ajiyar zuciya tayi ta sake bude idanuwan ta kalli dan uwanta sadah tace,"ban san irin yanda nakejinsa ba araina,saboda idan ina tare dashi nakanji ni acikin farin ciki da walwala,kuma rashinshi yana sa inji gaba daya wani irin ciwo ya kamani wanda baida magani har sai na ganshi,don ko yanzu irin abinda nakeji kenan yaya sadah shi yasa kaji nace maka inason in ganshi." Sadah yayi shiru saboda gaba daya sodangi tasa jikin shi ya mutu da tunanin halin daya ganta aciki,don haka numfasawa yayi yace mata,"toh kiyi shiru ki daina zubar da hawayenki,insha Allahu zanyi bakin kokari inga kinganshi gobe da maraice,"bude idanuwanshi yayi sosai ya kalleta yaci gaba da cewa,"amma da sharadi guda sodangi." Goge hawayen dake fuskarta tayi tana murmushi tace,"minene shi yayanah? Ka fada mani ni kuma zan zamo mai bin umurninka."sadah ya kalleta yayi murmushi, saboda yanda yaga duk ta rude acikin dan kankanen lokaci yace,"zan kaiki ki ganshi amma kuma bazakiyi magana dashi ba." Dan jim tayi saboda ba haka taso ba,amma tunda bata da wani zabi daya wuce tabi umurnin yayanta dole tasa ta amince ta jinjina kanta tace,"toh na amince yayanah."murmushi yayi yace,"tunda kin amince sai sharadi na biyu,ki saki jikinki kici gaba da walwalah kamar kowa,kuma abinci ma daga yanzu ki daina barin har sai ance kici,ni kuma idan har naga wannan sauyin zan cika maki nawa alkawarin." Dariya sodangi tayi ta kalleshi fuska a sake tace,"nima zanyi duk abinda ka umurceni da inyi insha Allahu. Tundaga lokacin sodangi ta saki jikinta da sauran danginta taci gaba da hidimarta kamar yanda ta daukarwa yayanta alkawari.washe gari kuwa da safe komai ya kara canzawa daga walwalarta,domin har yan biki suka fara mamakin canzawar da tayi cikin dan kankanin lokaci. Ayau sadah bai dauki wani lokaci mai tsawo ba a wajen kiwo ya dawo gida,wanka yayi ya canza sannan suka fakaici idanun yan biki shi da sodangi suka bar gidan. Gidan da safwan yake ginawa ko acikin birni sai haka,saboda idan ka ga yanda aka tsarashi dole abin ya burgeka,domin babu abinda babu na more rayuwa da jin dadi. Wani wuri suka samu ya nunawa sodangi yace ta tsaya nan saboda zata iya haggen shi,sannan shi kuma ya nufi gidan kanshi tsaye,bai shiga ba amma sai yace ma wani cikin ma aikatan yayi mashi magana dashi. Jim kadan yana nan atsaye safwan ya iso fuska asake ya mika masa hannu suka gaisa. Daga inda sodangi take labe ta hango safwan,ai kuwa wani dadi ne ya kamata taji kamar ta ida isa wajen shi,amma sam bata da wannan damar,ganinshi tayi yayi kiba ya kara haske acikin 'yan kwanakin da bata ganshi ba. Da sauri ta kalli jikinta taga yanda ta rame duk ta ya mutse,sai taji duk ta tsani yanda ta koma, saboda idan da safwan zai ganta da wannan ramar wata kila bazai kara son ganin ta ba,kara makalewa tayi a inda take ta buye sosai ta zuba masu ido. Shi kanshi sadah ayanda yaga safwan ayau sai da gabanshi ya fadi,saboda kamalarshi da kimarsa da kwarjininsa duk sun bayyana,sannan ga wani tsananin kyau da yayi tamkar wani balarabe. Safwan ya kauda kai daga kallon da yakeyi mashi,shi kuma safwan yayi murmushi yace,"yaya sadah,"watau sunan dayaji sodangi na kiranshi dashi kenan,saboda agirme yasan ya girmeshi. Safwan yaci gaba da cewa,"ko ardo ya aiko ka awajena neh?"sadah ya furzar da iskar dake cikin bakinshi yace,ardo bai aiko ni ba,wannan zuwan kai na neh,saboda inason muyi wata mgn mai muhimmanci." Safwan ya gyara tsayuwarshi yace,"toh ko sai mun shiga daga ciki neh?"sadah ya girgiza kanshi yace,"ba sai mun shiga ba,saboda maganar bazata dauke mu wani dogon lokaci ba."gyara tsayuwarshi yayi shima yaci gaba da cewa,"ina wani nazari akanka,shin wanne irin so kakeyiwa sodangi"? Jin tambayar yayi tamkar saukar aradu abisa kansa,amma da yake wayayyene dan zamani sai yayi dariya yace,"yaya sadah wannan tambayar taka ta bani tsoro sosai,saboda sai naji acikin raina kamar baka yarda dani bane." Sadah yayi dan murmushi yace,"ba ban yarda dakai bane,amma ina ganin kamar kai da ita baku dace bane,saboda kai mai kudi ne na bammaki,ita kuma talaka ce wadda bata da komai sai rufin asirin Allah."safwan yayi kasa da murya yace,"duk wannan dalilin ba zai hana in auri sodangi ba,saboda ina sonta da yawa,son da bazan iya kiyasta maka adadinshi ba. Love you sis 😘 08033481518 [4/8, 10:25 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba Saleh daudawa 14 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all😘😘 Safwan yayi kasa da murya yace,"duk wannan ba zai hana in auri sodangi ba,saboda ina sonta da yawa,son da bazan iya kiyasta maka adadinshi ba."sannan ya dago idanuwanshi ya kalli sadah yaci gaba da cewa,"ina so ka yarda dani yaya sadah,ni da sodangi mutuwa zata raba mu." Sadah yayi murmushin jin dadi ya jinjina kanshi alamar yarda da abinda safwan yace ya dafa kafadarshi yace,"na yarda da kai safwan 100%but duk da haka zan kara tunasar da kai cewar,duk duniya bani da kamar sodangi,itace jini nice anta,don haka ka kula mani da ita kamar yanda ya kamata,please πŸ‘ kada ka bari tayi kuka ta dalilinka,domin sodangi tana sonka da yawa,yawan ma bazan iya kiyasta maka shi ba don she Love's you so much. Safwan yayi dariyar jin dadi,saboda tuni ya riga yasan da cewar sodangi tana sonshi,hannu yasa ya shafi sumarshi yana murmushi yace," kada kaji komai sadah saboda sodangi tawa ce har abadah." Sadah ya mika mashi hannu suka kara gaisawa saboda farin cikin abinda yaji daga safwan din,sannan yayi ban kwana dashi ya juya ya fara tafiya.safwan dake tsaye yana kallonshi ya sake kiranshi dadan karfi. Da sauri sadah ya juyo yana murmushi, sai safwan din ya matsa kusa dashi yana cewa,"mancewa nayi in tambayeka,wai miyasa ardo ya hana akawo lefen sodangi gida?"sadah yayi dan murmushi yace,"kasan mutanen mu,baka da bashin maganarsu amma su suna da taka,kuma ko yanzu wannan gidan da kake ginawa cewa sukeyi wai mun saida sodangi wajenka ne,toh bare kuma suga tulin kaya tunda mu nan ba haka mukeyi ba,kaga karshe bamu san kuma abinda zasu fada ba." Safwan yayi dariya yace,"da ardo ya barni naso inyiwa sodangi abinda ba a tabayi wa wata yarinya ba a kauyen nan,amma ko yanzu ma ba matsala saboda na tanadar komai acikin gidanta." Acikin farin ciki sadah ya rabu da safwan ya nufi inda sodangi take aboye ya sameta sai murmushi take.kallonta yayi shima yana murmushin yace,"hankalinki ya kwanta koh tunda kin ganshi?"sodangi ta daga mashi kai alamar eh tace," naji dadi yaya nah,amma naso ace ya ganni munyiwa juna magana." Sadah yace,"kada ki damu,wata rana zakuyi maganar."daga kanshi yayi ya kalli yamma yaga yanda rana keta haramar yin kasa ta koma ga mahaliccinta yaci gaba da cewa,"ki tashi mu koma gida kamin a farga bamu nan su fara cigiyar mu." Sodangi ta mike tsaye ta nufi hanyar da taga sun biyo amma zuciyarta cike da tunani kala kala,can ta gaza daurewa tace,"yaya sadah wai wannan wurin danaga safwan ya fito ina ne?"sadah yayi murmushi yace,"wata ma aikata ce ake ginawa."kada kanta kawai tayi sukaci gaba da tafiya. Washe gari wurin karfe sha daya na safe safwan ya iso tare da kanin babanshi da wasu manyan abokanenshi,sai kuma abokanen safwan din.anyi duk yanda amusulunci ya ta nada an daura auren Sarah (sodangi) & safwan.sai alokacin sodangi tasan kowa nene mijinta,ai kuwa murna fal cike da zuciyarta,amma sai ta boye bata bayyanar da farin cikin ta ba saboda ta fahimci rashin kunyar da ake cewa tanayi,domin kwata kwata bata iya boye son da takeyiwa safwan a duk inda ta shiga shi yasa ake ganin rashin ta idonta. Walima akayi sosai,saboda ardo ya yanka shanunsa har biyu,kuma duk abinda akeyiwa yar gata ardo sai da yayiwa sodangi,duk da safwan ya hana da yayi mata komai,amma sai da ardo yasa aka bashi wani bangare don zuba kayan sodangi daya sai mata. Ance biki wan shagali kowar raina shi ba nashi ba,haka akayi ta kai da komowa har zuwa bayan isha I,safwan da abokananshi sukazo da motocinsu suka kwashi amarya da jama arta suka kai sabon gidan da ya gina. Ganin cikin gidan yasa mutanen dan kauyen suka dasa surutun kyan da yayi da kuma yanda aka tsara shi.ita kuwa sodangi tunda aka kaita bata bude mayafinta ba bare taga abinda ake ta surutu akai. Da yake taro daya sukeyi,don haka yan kai amarya da suka gama yan leke lekensu da kayancinsu aka kara kwaso su duk aka mayar dasu gidan ardo,toh anan ne labari ya kara yaduwa na irin kyan da gidan sodangi yake dashi,anan fa masoyan ardo sukayi ta Allah sam barka dayi masu addu ar zaman lafiya. Gidan tsit yayi mata gashi duk an watse babu kowa acikinshi sai ita kadai saboda ko yar tsohuwar da ake bari ta kwana saboda washe gari da safe taje tayi masu tonon asiri safwan sai da yasa aka tafi da ita,don haka gidan babu abinda kakeji sai karar injin din daya ba dukkan gidan haske. Tsoro ne ya fara kamata,sannan ga wani irin sanyi da dakin yayi kamar an sanya ta acikin kankara,don haka sai ta kama jikin ta kankane sai rawar dari take,domin gaba daya jikinta ke jijjiga saboda sanyi. Safwan kuwa yana can cikin abokananshi suna tsara yanda zasu cashe adaren yau,saboda su da kansu suka hada mashi wata gaggarimar dinner da zasuyi a katsina motel,kuma zata iya daukarsu har zuwa karfe ukku na tsakar dare kamin agamata,don haka sai ya fara tunanin yanda zai zame masu ya gudu zuwa wurin matarshi ba tare da sun gane ba. Ba a fara kaddamar da shagalin ba sai wajen karfe sha dayan dare,babu abinda kakeji sai tashin kayan kida da aka zagaye da sifiku,shi yasa wurin babu mai jin abinda wani yake cewa,sai dai kuyi maganar kurame,su kuwa matasa dama abinda akeso kenan,don haka sai kai da komowa sukeyi,ga yan mata kala kala sun debo. Cikin isa da takama ta shigo filin kuma idanuwanta arufe suke,saboda kawai so take taga shin wacece wannan yarinyar da safwan ya aura kuma har bai fada mata ba sai dai taji afulanin tallah. Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:25 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 15 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all😘😘 Kai tsaye tsakiyar hall din ta nufa tare da yan take mata baya,suma kawayenta ne,kuma duk masu zaman kansu,saboda idan ba ka isa da naira ba,toh su ko kallonka bazasuyi ba,sannan kuma duk gaba dayansu babu wadda tayi shigar mutunci,kusan ina iya ce maku tsirara suke saboda kayan jikinsu dasu kwamma babu. Babban abokin safwan ne ya hangosu daga inda yake,aikuwa sai da gabanshi ya fadi,saboda ciki da waje yasan zinat ko wacece,domin halayenta ba aboye suke ba. Nufosu yayi yana murmushi tare dayi mata jinjina da hannu,dariya tayi har hakoranta suka bayyana,saboda yayi mata abinda take so,don haka itama kai tsaye ta nufeshi,duk da baiji abinda ta fada ba amma ya lura da abinda bakinta ya furta don haka sai yayi mata signal da hannu ya nuna mata wata hanya. Alama tayiwa friends dinta na su jirata,ita kuma tabi hanyar cikin yanga da rausaya kai sai kayi tsammanin karewa zatayi. Tundaga shigarta wajen ya hangota,kuma kai tsaye wajenshi ta nufa faskarta adaure,shi kuwa ganinta sai ya saki fuskarshi don haka tana isowa ya mike ya tarbeta tare da rungumarta ajikinshi yana dariya. Bata da yanda zatayi,don dole itama ta fada jikinshi,domin safwan yana daga cikin mutanen da baka isa ka wulakanta su ba,saboda kyanshi,sannan ga abokan rayuwa watau (kudi) Jikinshi ta fada kamar yanda ya bukata ta rungumeshi sosai tana kissing din shi,sai da taga ya shagala sosai tadan janye jikinta tana kallonshi cikin kissa da kisisi nah tace masa,"ina amaryar taka neh,don wannan zuwan da nayi saboda ita nayi shi tunda kai ka gaza fada mani." Dan yatsa yasa abakin shi yace,"shut up,kada kiyi maganar matata anan,saboda babu abinda zai canza atsakanin mu. Wata dariya tayi ta jin dadi ta kara fadawa jikinshi,don dama zulluminta kada ya wulakanta ta ganin yayi aure,don haka jin haka sai ta fara janshi suka nufi sashen da dakuna suke tana tayi mashi wasu abubuwa wanda zai sa hankalinshi ya gushe. Sai da ya bari ta gamarikicewa da salonshi na soyayya, sannan ya zame daga jikinta tare da dafe kanshi,agogon dakin ya kallah yaga karfe sha biyu saura minti biyar. Jim yayi yadan yi nazari kadan ya mike tsaye tare da daukar rigarshi yana kokarin maidata ajikinshi. Zumbur tayi ta mike zaune tana kallonshi tare da begging dinshi da idanuwanta,murmushi yayi ya zauna abakin gadon ya mika hannu ya shafi kyakkyawar fuskarta yace,"kada ki damu zinat,bazan dauki lokaci ba zan dawo gareki,please ki jirani zanje inyi settle wajen dinner din can don bana so suce nayi disappointing din su,domin ayau nan zamu kwana ni dake neh." Murmushi tayi saboda jin yanda yace,don haka sai ta sumbaci hannunta ta hura mashi tace,"sweet heart dina kada ka dade,saboda ayau akwai tanadi na musamman danayi maka." Fita yayi daga dakin yana dariya,sannan kai tsaye wajen motarshi ya nufa ya fiddo wayarshi ya kira tahir babban amininshi. Yayi kiranshi wajen sau ukku kamin ya dauka,sai akaro na hudu sannan ya dauka shima sam bayajinsa,don haka sai kawai ya tura mashi massege yace,"na wuce wurin amaryatah,don haka sai kasan yanda zakayi da mutanen daka gayyato,bye.' Yana gama tura sakon ya fada cikin motarshi ya tayar da ita cikin dan kankanin lokaci ya bar harabar motel din ya nufi hanyar barin garin. Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:25 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 16 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all😘😘 Gudu yake sosai saboda gaba daya hankalinshi ya koma wurin sodangi,domin hangen wannan katafaren katon gidan ace ita kadai ce acikinsa,kuma dama gashi yasan matsoraciyya ce ta karshe. Daya saura ya isa rugar fulani dake mazoji,gangarwa yayi ya shiga dan kauyen,gaba daya yaga duhu ya gauraye rukunin sai gidanshi kadai daya haske wurin gaba dayanshi,haka ne ya gane an dauke wutar lantarki,don haka gidan ya nufa kai tsaye yayi horn,sabon mai gadinshi ya fito aguje ya bude mashi gate din shi kuma ya shige,kai tsaye wurin parking ya nufa ya ajiye motarshi ya shige cikin gidan. Sashen da aka ajiye sodangi ya nufa,koda yaji tsit bayyi mamaki ba saboda tuni yasan gidan babu kowa sai ita kadai, kuma ba mamaki itama ya samu tayi barci. Tura kofar yayi,can bisa gado ya hangota atakure sai makerkyata take,kuma idanuwanta arufe. Da sauri ya ida karasawa har bisa gafon yana kiran sunanta,sam kasa amsawa tayi tunda dai ta bude ido ta kalleshi sannan ta mayar dasu ta rufe bata sake bude su ba,don haka sai ya rude aguje ya sungumeta ya nufi dakinshi da ita,a bisa gadonshi ya ajiye ta sannan ya nufi room heater dinshi ya kunna tare da sa highest number mai karfi wadda zata sa cikin dan kankanin lokaci dakin ya dauki dumi. Nan da nan kuwa dakin ya dauki zafi,domin shi kanshi zufa kawai yake,sai alokacin ya farga da yanda sodangi itama take jibin,don haka ahankali ya rabata da kayan duk dake jikinta daga vest sai under wear ya bar mata sannan ya fada toilet dinshi yayi wanka ya saka kayan barcinsa. Kashe room heater yayi ya haye saman gadon da sodangi take kwance tana barci,shima kwanciya yayi kusa da ita ya jawota ajikinshi yadan rungumeta. Rufe idanuwan sa yayi don yayi barci,amma sai mi?sodangi daya rungume yasa yaji tsigar jikinsa tana tashi. Ahankali ya bude idonsa ya kalli sodangin,duk da ya kashe wutar dakin sai yar karamar fitilar dake gefen gadon da suke kwance,yaga har yanzu barci dai take kamar wadda aka ba maganin barci, kirjinta yaga ya taso yayi dum dum,hannun sa ya kai ya taba,ai kuwa ya kara tadawa kansa hankali,don haka bai tsaya shawara da zuciyarshi ba ya fara sunsunarta yana kissing din ta. Duk da sodangi tana yar kauye kuma ba wayayya ba,amma sai da yaji fatar jikinta tasha bambam da wasu yan matan da yake mu a mullah dasu,shiyasa ma hankalinshi gaba daya ya dauku ya shiga sarrafata yadda yakeso. Farkawa sodangi tayi tajita ajikin mutum,kuma sannan ga wasu abubuwa ana tayi mata wadda bata taba gani ko jiba arayuwarta, don haka sai ta fara tureshi tana sonyin kuka tana rokonshi. Babu abinda yakeji bare har asa ran yana saurarenta,shidai kokarinshi ya cimma bukatarsa kawai. Hankalin sodangi ya riga ya gama tashi sosai tare da rudewa,kuma sannan sam kwalwarta ta gaza tunano mata a inda take bare ta gane wanene atare da ita,don haka dagewa tayi ta kafa masa bakinta ta dalla mashi cizo akirji. Yar kara yayi ya saketa babu shiri,ita kuma da sauri ta wuntsila kasan gadon ta mike tsaye tana haki tana kallon wanda ke kan gadon,amma har zuwa lokacin bata ga ko wanene ba. Jikinta ta kallah taga ashe ko kayan kirki babu,da sauri ta janyo bargon kan gadon ta daura tana salati.dariya taba safwan ya kira sunanta ahankali yace ta kunna glove din dakin. Juya idanuwa ta tsaya yi, saboda bata fahimci abinda yake nufi ba,kara cewa yayi ki kunna kwan lantarkin dakin tare da nuna mata sashen da zata nufa. Umurninshi tabi taje ta kunna,nan da nan haske ya gauraye dakin,ganin safwan da tayi dafe da kirji yasa ta gane shine ta ciza,ai kuwa sai kuma hankalinta ya tashi ta nufeshi ga uban bargo biya ta rufe jikinta dashi sai binta yake. Gefen gadon ta nufa ta zauna duk arude tana cewa,"yi hakuri safwan ban san kai bane,da ban cije ka ba,wallahi nasa wani neh keyi mani wannan abun kuma molasa tace mani duk iskanci ne,kuma duk wanda yace zaiyi mani kada in barshi har sai inda karfina ya kare." Kunya ce ta kama safwan sosai domin rasa abinda zaice mata yayi,domin yanda yaga ta rude sosai akanshi saboda har bargon ta saki ba tare data sani ba. Bai taba jin haushin kanshi ba irin ranar yau,saboda gajen hakurinshi yaja mashi jin kunyar sodangi,domin ya fahimci yanda ta dauke shi da muhimmanci sosai arayuwarta. Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:25 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 17 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all😘😘 Wayancewa yayi ya mike zaune yana kallonta,ita kuwa babu abinda bakinta yake ta fada sai hakuri take ta bashi. Kamo hannunta yayi ya rike yana murmushi yace,"is okay sodangi,saboda ba laifinki ba ne,is all my poult,don haka ki daina maganar haka nan." Kada kanta tayi alamar ta fahimci abinda yake fada mata,mikewa yayi ya nufi ward roof dinshi ya dauko wata rigar barci doguwar riga ya mikawa sodangi yace ta sanya. Kallon rigar tayi ta raina kwarinta ta dago ido ta kalleshi tace,"idan har akwai wata ka canzq mani wannan saboda ni kama tayi mani da matacin koko." Dariya yayi ya sake miko mata wata,sai kuma taga ai kara ta farkon da wadda ya sake mata. Amsa kawai tayi bakinta alaikum ta shige toilet din dakin ta sanyo su ,da kyar ta iya fitowa daga toilet din tana yan matse matse na jin kunya,shi kuwa tunda ya kalleta sau daya ya kauda kansa saboda gudun maimaita abinda ya aikata dazu. Agogon dakin ya kallah yaga biyu har ta wuce na dare,don haka sai ya kalleta yace,"sodangi zo mu kwanta,kinga dare yayi sosai,kada mu makara wajen tashi." Jim tayi dajin abinda ya fada,can sai ta mike ta nufi wata resting chair dake can gefe a cikin dakin ta haye abinta,sannan kuma ta lullube da bargo. Kallonta kawai yake,har sai da ta kwanta sannan ya mike ya nufi inda take,gaba daya ya daukota da ita da bargon sai kan gadonshi. Wuntsile wuntsile ta kama yi don ta kufce amma ta kasa,shi kuma dariya kawai yake yana cewa,"kada ki wahalar da kanki,domin bazan yarda da mu raba shimfida ni dake ba,kuma bazanyi maki abinda baki so ba." Jin haka yasa ta hakura,wutar dakin ya kashe ya dawo ya rungumata ajikinshi suka kwanta. Sodangi bata saki jikinta ba har sai da taji saukar numfashin safwan abayanta sannan ta rufe nata idanuwan. Ana fara kiran sallar asuba safwan ya farka,amma idanuwanshi cike suke da barci,haka nan ya daure ya mike zaune ya kalli sodangi da ita dukkan alama bataji kiran sallar ba. Kissing dinta yayi a lifts dinta wai ko ta motsa,amma shiru,don haka sai ya sake kissing din amma wannan karon tsayawa yayi yana tsotsar lifts din nata ba tare daya janye nashi bakinba. Wani yanayi taji acikin barcin mai dadi,kuma duk tunaninta mafarki ne takeyi,don haka sai itama taji taci gaba da kwaikwayon abinda ake mata. Ahankali ta fara jin abin abayya ne,saboda hankalinta duk ya gama game jikinta,firgigi tayi ta zabura ta mike zaune tare da tureshi ta bude idanuwanta sosai tana kallonshi. Mikewa yayi ya sauka daga kan gadon yace mata lokacin sallah yayi,ki taso muyi alwallah,kuma atare nakeso muyi. Yan waige waige tayi,don ta kara tabbataswa kanta,shin mafarkin ne ko kuma abayyane neh?toh amma wanda take tunanin shine yayi mata kamar bai san komai ba. Haka nan ta tashi sukuku tabi bayanshi,kamin ta isa ya shiga ya rufe kofar,yan mintoci kadan ya dauka ya bude mata yace itama ta shiga idan tana da lalurar da zatayi. Tare sukayi alwalla, sannan ya nuna mata wani akwati yace,"ta dauko kayan da zatayi sallah aciki."toh tace ta nufeshi,koda ta budeshi abin mamaki ya bata saboda babu komai acikinshi sai after dress da abayoyi kawai ne. Daya ta dauka ta nufi toilet ta cire na jikinta ta zirata,tunda ta fito yake kallonta har ta zira abayarta ta koma kusa dashi tace,"na kimtsa." Sai da sukayi raka a tanil fijir sannan suka gaba tar da sallar asuba,sun dade suna lazimi har sai da gari ya fara haske sannan suka tashi,sodangi tayi kasa da kanta ta gaisheshi. Murmushi yayi yasa hannu ya jawota ajikinshi ya zaunar da ita akan cinyarshi yace,"komai nace maki ki rinkayi mani,zakiyi?" Daga mashi kai tayi akunyace,saboda ganin yanda ya mayar da ita kamar wata karamar yarinya, don haka da sauri ta amsa mashi,"eh zanyi maka idan har kana so." Wani murmushin ya sakeyi,duk da dama da wuya kaga safwan yana fushi ko fuskarshi a murtuke,kadaran kadahan.nuna bakinshi yayi da hannu yace,idan zaki gaisheni ba sai kinyi magana ba,nan kawai zaki tsotsa shike nan har mun gaisa tunda ai tare muka kwana kinga nafi kowa sanin yadda muka tashi." Kunya ce ta kara lullubeta ta rasa yanda zatayi sai tayi saurin yin kasa da idanuwanta tana murmushi. Kama kanta yayi ya sumbaci bakinta yace,"toh kinga yanda akeyi kuma daga yau haka shine gaisuwarmu koda yaushe." Tashi tayi da sauri saboda kunya ta ruga ta fita daga dakin.dafe kanshi yayi yace,"wai! ni dai wannan kunya tana cutar dani wllh,amma zanyi bakin kokari na in ga na rabata da ita." Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:25 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 18 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,love you all😘😘 Mikewa yayi ya haye bisa gadonshi ya kwanta,saboda har zuwa alokacin akwai sauran barcin jiya acikin idanuwanshi,amma shirun dayaji har yanzu sodangi bata dawo ba yasa ya kasa rufe idonshi sai ma zuru da yayiwa kofar shigo. Sake sakkowa yayi yabi bayanta,kai tsaye dakinta ya nufa,ai kuwa acan ya sameta ta gyarashi fes duk da babu datti sai da ta shareshi,sannan ta haye bisa nata gadon saboda itama idanuwanta takeji wani iri. Tsaye yayi a bakin kofar dakin yana kallonta,ita kuma ganinshi sai tasa hannunta ta rufe idanuwanta tana murmushi. Kada kai yayi shima murmushin yake ya nufeta ya haye bisa gadon tare da rabawa jikinta ya kwanta,jawota yayi ya rungumeta ajikinshi sannan yasa bakinta agefen kunnenta yayi mata yar rada yace,"please ki dai na jin kunyata,saboda ni mijinki ne." Murmushi tayi ta kara sunnar da kanta ajikinshi,shima murmushin yayi msi dan sauti yaci gaba da cewa,"muyi barci sodangi." Ganin jiya da suka kwanta babu abinda yayi mata yasa yanzu ma ta kwantar da hankalinta ta lumshe idanuwanta,nan da nan barci yayi awon gaba dasu. Sai wajen karfe sha biyu na rana suka farka,shima yunwar cikinsu ce ta ishesu har tasa suka farka. Safwan ne ya riga tashi don haka kai tsaye kitchen ya nufa ya fara tunanin abinda zai girka masu. Laluba gabanta tayi taji babu kowa sai pilo,shi yasa tayi saurin bude idonta,fitowa tayi ta nufi dakinshi taga baya ciki,sai ta sake fitowa tazo tsakanin dakunan ta tsaya saboda baya san ko ina ba,daga dakinta sai nashi. Motsi ta rinkaji daga can wani bangare,don haka sai tabi motsin ta rinka tafiya ahankali tare da sanda tana dan lalle kawa har ta gano inda yake. aikin dataga yanayi ne tayi sauri ta ida isa gareshi ta dubeshi tace," mi yasa baka tasheni ba,domin wannan aikin ni ya kamata inyi shi." Dariya yayi ya nuna mata bakinshi yace,"baki gaisheni ba,don haka a yanzu babu wata amsa da zan iya baki har sai mun gaisa." Murmushi tayi tare dajin yar kunya ta mika hannu zata amshi abinda yake fere dankali dashi duk da bata san yanda ake amfani dashi ba,shi kuma sai ya juya mata baya yaki bata. Duk abinda ta nufa zata taba sai ya amshe ya ajiye gefe,idan ta kalleshi tana son sanin dalili sai ya nuna mata bakinshi. Rasa yanda zatayi tayi,gashi shi kuma ya zame Mata kurma kuma sam batajin dafin hakan,don haka sai ta fara tunanin yi mashi abinda yakeso. Yan kame kame ta farayi ga kuma kunya,can ta dake ta nufeshi,shi kuma yana ganin haka ya tsaya da abinda yakeyi ya zuba mata ido,koda ta iso gabanshi sai ta rasa ta yanda zata fara sai ta fara tunanin fasawa,shi kuwa yana ganin haka yayi wuf ya kamata ya jawota jikinshi yayi kissing dinta. Komawa tayi gefe daya duk ta takura kanta saboda kunya,shi kuma dariya kawai yake mata,sai da yayi mai isarshi sannan ya kalleta har zuwa lokacin fuskarshi fara a kawai yake. Wayancewa yayi ya kwala maya kira yace,"zo ki gani sodangi,dai dai ya saka dankalin turawan cikin wani dan injin tuliz nan da nan ya mayar dashi piece. Abin burgeta yayi ta raba jikinshi tana kallo,karshe ya mika mata taci gaba shi kuma ya tsaya ta bayanta yadan rungumota. A haka yayi ta nuna mata yanda akeyi har aka samu aka soya dankalin da kwai. Kararrawar gidan ta fara ruri,alamar suna da bako abakin kofa.safwan ne ya rabu da jikin sodangi yace mata,"bari inje in duba."yana fadar haka yayi waje. Bai dauki wani lokaci ba ya dawo dauke da kwanan sha na silver tare da cooler ahannunshi,dariya yake yana cewa lallai sodangi ke yar gata ce,wai molasa ce ta bayar akawo mana tun dazu muna ta faman barci. Barin abinda take ta tarbeshi ta amshi kayan cikin farin ciki,ganin kunun gyada sukayi da lafiyayyen kosai,kuma kunun bai huce ba,don haka safwan ya dauko katon flasks yace ta juyeshi aciki. Fasa sanya ruwan tea sukayi,sai safwan yasa suka kwaso kayan dazasuyi break fast din ya jata har dinning area ya kuma nuna mata duk yanda zata jerasu akan table din. Wasa wasa zaman da sodangi tayi da safwan ta koyi abubuwa da dama daga wajenshi,kuma kunyarshi da takeji duk ta ragu sosai saboda duk abinda yakeso shi takeyi mashi har yau kusan watansu ukku da aure. Shakuwa sosai ta shiga tsakaninsu har ta kai tsakaninsu babu mai iya kwanciya shi kadai,kuma sodangi idan bai rungumeta ba yayi kissing dinta sam bazataji dadin barcin ranar ba,amma duk da wannan shakuwa babu abinda ya shiga tsakaninsu sai tsabar soyayya da yake koya mata. Alhamdulillahi, yanzu sodangi babu abinda bata iya ba,kan fannin abinci da zuba soyayya da shagwaba,babu abinda za a gaya mata.shi kuwa safwan kullum cikin dauriya yake,saboda gani yake sodangi har yanzu karamar yarinyace,domin ahankali cikin dubara ya binciketa ko period bata fara ba shi yasa take bashi tausayi, aduk sadda ya nemi kusan tar ta. Yau wata hudu kenan,bayan sodangi duk ta gama ayyukanta ta dora sanwar abinci,sai ta fada toilet don tayi wanka. Blood ta gani apant dinta ai kuwa sai hankalinta ya tashi ta rasa yanda zatayi,fitowa tayi ta dawo falo ta hada kai da gwiwa tana ta zubar da hawaye. Safwan yau da wuri yaji yana sha awar dawowa gidansa,don haka bai jira su tahir ba yayi wuf ya baro su ya dauki hanya,saboda idan suka ganshi zai taho sunyi tayi mashi tsiya kenan wai rayuwarshi ta kare acikin kauye. Shi kanshi yayi mamaki dayaga sodangi bata zo tarbarshi ba,don haka yana yin parking ya nufi cikin gidan da sauri yana kwala mata kira,amma shiru yaji. Kara tako yayi ya nufi sashenta,bai same ta ba,haka ma bata asashenshi,don haka sai ya nufi falon dake kusa da kitchen. Anan ya sameta duk tayi wujiga wujiga kamat wadda aka ba kashi,da sauri ya ida isa gabanta ya zauna tare da tallabota yana tambayarta,"mi ya sameki? Mi akayi maki?"babu amsar daya samu daga gareta. Don haka gaba daya ya rungumeta ajikinshi yana rarrashinta da yake ya san halin shagwabarta don ta yiwu ba wani abin kirki bane yasa ta kuka. Lema yaji a tafin hannunshi ya dago da sauri ya duba sai yaga blood,kallonta yayi cikin tsokana ya nuna mata hannun yace,"wannan abin kikewa kuka?" Sharbe fuska tayi zata fasa mashi kuka ga tsoro fal afuskarta tace,"wllh ni banyi komai ba,ganin shi kawai nayi."safwan ya kalleta cikin rashin fahimta yace,"minene bakiyi ba?ai wannan abin ba sai anyi wani abu ba yake zuwa,lokaci ne kawai." Sodangi ta kara kwabe fuska ta harareshi tace,"ba wani nan,ai Dije ta fada mani cewa,duk wanda yaga jini ajikinshi dan iska neh." Zaro idanuwa yayi😳 cikin mamakin abinda ta fada yace,"watau kema iskancin kikayi kenan?"sai ya daure fuskarshi ya mike tsaye yana harararta yace,"yau sai kin fada mani yanda akayi har haka ta faru,kuma dawa kikayi iskancin." Fashewa tayi da kuka harda gaza,ga rantsuwa tana tayi wai don ya yarda da ita,surarta yayi yana murmushi ya kai ta toilet ya saka acikin kwamin wanka ya sakar mata ruwa. Ahankali yabita yayi ta zare kayan dake jikinta har ya rage daga brazier sai pant,duk bata damu ba saboda ruwan yasha har wuce kirjinta,sannan ga sabulan wanka kala kala na ruwa ya zuba tare da turaren ruwa shima duk na wankan neh. Sai da ya cudata fes yanayi yana canza ruwan kwamin har wurin sau ukku sannan ya umurceta data fito daga cikin ruwan ,aikuwa anan rigima take tana ganin yanda zata fito gashi atsaye yana kallonta,kuma sai alokacin ta kara shafa jikinta ta fahimci ya ida cire abinda ya rage mata ajiki. Kwalkwal tayi da idanuwa zata sake saka mashi kuka,sai kawai ya juya yana dariya. A daki ta sameshi ya gama shirya Mata komai,don dai dai da pant da pad shi ya nuna mata yanda zatayi amfani dasu,kuma sannan ya fada mata duk bayan awa biyu ta rinka canzawa koda babu komai ajikin ta. Tundaga lokacin kuma yasa mata ido wajen cimarta,duk abinda yasan zai amfane ta, shi yake kawo mata, bama kamar su fruits kankana da ayaba da abarba,su kara kaimi yayi wajen kara ajesu. Haka kawai sai ya sanyata agabanshi ya tura mata tayi ta sha har sai ta gaji don kanta,shi yasa yan watannin da tayi gidan safwan ta canza gaba daya ta koma kamar wata black american. Kwananta biyar ta samu tsarki,shima safwan ne ya koya mata,shi lamarin sodangi yana burgeshi,saboda duk abinda zai koya mata sai ta daukeshi acikin kanta,kuma bata da mantuwa. Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:25 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 19 I dedicates this love story to my Hausa novel & my fans,thanks & love you all😘😘 Kamar kullum yau ma da wuri ya dawo gida saboda zuciyarshi tana raya mashi abubuwa da dama akan sodangi,don haka yana dawowa ta rugo da gudu ta tarbeshi cikin shigar kananan kaya.wata body hook shirt ce ja ta sanya sai wando three quarter black,shima ya kama jikinta sosai. Fadawa tayi jikinshi shi kuma ya rungumeta sosai tare da sumbatarta,sannan ya dagata sama ta dage kafafuwanta tana kyalkyata dariya. Suna makale da juna suka shige har sashenshi,tayashi rage kayan jikinshi tayi,sannan ya langabe kai kamar karamin yaro yace,"baby wanka nakeso inyi,amma kuma yi mani nakeso ayi saboda agajiye nake." Yar kunya ce ta kamata ta sunnar da kanta tana murmushi tace,"baby ko kaci abinci tukunnah."makale kafada yayi yace,"ni banajin yunwa sodangi,please ke nake bukata in.........". Dariya ya bata sosai ta kyalkyalata har tana tafawa,sannan ta matsa kusa dashi tace,"ok gani,maza ka cinyeni ka koshi,amma faπŸ‘‰kada ka cinyeni duka😏. Baki ya rike yana kallonta da mamakin gatsen da tayi mashi,sannan kuma wai harda tsiwa,don haka sai ya jawota ajikinshi ya dauketa gaba daya ya nufi bath room dinshi. Sakata yayi duk da kayanta acikin kwamin ruwan,sannan shima ya zare dogon wandon dake jikinshi da vest din,ya zama dagashi sai short niker ya fada acikin ruwan. salon dataji yanayi mata ne yasa ta fara rudewa,saboda salon yasha bambam da wanda ya Saba yi mata. Tureshi tayi amma ya dawo ya manne mata saboda duk abinda ya taba ajikinta wani sauti ne ke kai mata har acikin kwalwarta,domin shi kanshi safwan din zai iyacewa arude yake shi yasa duk abinda ya kama ajikinta sai ya tsotseshi tas,sai da yaji tayi laushi sosai ajikinshi,sannan ya rungumeta ya fito da ita daga cikin ruwan,towel ya daura,haka itama sannan ya nufi gadonshi da ita. Ci gaba yayi da yi mata wasanni kala Kala wanda har kwalwarta ta gaza daukat karatun ta saduda gaba daya ta bashi wuka da nama. Dago idanuwa safwan yayi ya kalleni,ni kuwa tsumu tsumu nayi a yar kusurwar dakin sai mazurai nake na rashin gaskiya,wata uwar harara ya watso mani da idanuwanshi da suka kada suka canza launi,ni kuwa ganin haka yasa jikina yana rawa na kwashi takarduna da Biro nayi waje tare da tura masu kofar dakin. πŸ’πŸ’πŸ’ Falonsu na nufa ina share zufar data feso mani na nufi fringe din dake can gefe daya,na debo lemun exotic na coconut and pine Apple na samu luntsimemiyar kujera daga cikin kujerun falon na kame na cigaba da gashi kawai. Akallah na dauki kusan minti talatin ina kwadar lemu sai kawai na jiyo sautin kukan sodangi, kuma yinshi take babu kakkautawa,don haka sai na wurgar da kwalin lemun dake hannunah na nufi dakin da gudu,amma kuma sai na gaza shiga na koma ta jikin window dinsu na leka idona daya. Hango safwan nayi dukkushe akan gadon,kuma sam banajin abinda yake cewa,sai na hanzarta na zagaya da sauri na tura kofar dakin na kara labewa cikin jin tausayin abinda na gani. πŸ’πŸ’πŸ’ Safwan ya mika hannu zai dauketa ta sake fashewa da kuka tace,"don Allah kada ka tabani,ni duk jikina gaba daya ciwo yakeyi mani,kuma kai neh!wllh kai neh!!sai taci gaba da kuka. Safwan rasa yanda zaiyi yayi,saboda shi kanshi yasan ya kwareta da yawa,saboda babu yanda bayyi ba don ya tsaya sama sama amma ya kasa sai da ya shiga ciki sosai,shi yasa yake tsammanin yaji mata rauni saboda yanayin jinin daya gani yana fita ajikinta. Mikewa yayi bai tsaya kara neman shawararta ba ya sungumeta yayi toilet da ita,ruwan dumi ya hada mata masu dan zafi ya sakata ciki,tana kuka tana komai amma bai saurateta ba har saida yaji ruwan ya huce ya sake canza mata wani ruwan. Wanka yayi mata sosai harda na tsarki sannan ya barota toilet din yazo ya zai kwashe zanin gadon,abibda ya gani neh ya kara firgitashi saboda ya dade yana sanin yan mata amma bai taba ganin irin abinda ya gani ba yau,sannan kuma haka bai tabajin dadin dayaji ayau ba,wani mugun murmushi yayi ya kwashe zanin gadon ya shimfida sabo. Komawa toilet din yayi ya daukota ya kawota kan gadon ya kwantar da ita,duk wani motsi da zatayi sai yayi mata sannu,saboda ba karamin tausayinta yake ba,kuma bai tabajin haka ba sai akan sodangi. Shima wankan yayi ya kuma wanke bed shirt din sannan ya dauki motarshi ya nufi katsina,wajen wani babban likita yaje ya sakar mashi kudi makudai sannan ya fada mashi bukatarshi,ai kuwa babu wani bata lokaci ya biyo bayanshi har mazoji. Sanyawa yayi ya duba mashi sodangi in and out,domin baya son daga baya ace tana da matsala. Allurai yayi mata tare da bata magunguna masu karfi,sannan kuma ya bashi yan shawarwari yace muddun suka bisu babu abinfa zai faru kuma cikin sati daya zuwa biyu sata warware. Safwan yayi mashi godiyya sosai ya rakashi ya shiga motarshi,sannan ya dawo wurin sodangi yaci gaba da kulawa da ita. Ahankali sodangi ta rinka samun lafiya,amma duk sadda taga safwan yana shishshige mata sai taji tsoro yana kamata,domin ji take muddun aka kara taba wurin nan toh raunin da zataji sai yafi na baya. Adaddafe safwan ya kai kwana goma rabonshi da sodangi,domin har yar kulawar da take mashi duk ta rage saboda tsoro. Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:25 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 20 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks & love you all 😘😘 Cikin dubara irin ta yan boko safwan ya kara rabbatarta,amma wannan karan bataji zafi sosai ba,don haka sai ta saki jiki da safwan yaci gaba da koyar da ita wasa mai wuyar bari. Akwai wani lokaci suna kwance ita da safwan adakinta rungume da juna,sai taji kamar lema ahannun da take wasa da sumar gashin kanshi. Daga kanta tayi ta kalleshi,ai kuwa sai taga hawaye sosai,hankalinta neh ya tashi sosai ta zabura ta mike zaune tana tambayarshi,"baby mi akayi maka?"tare da sharbe fuska itama kamar zatayi kuka. Da sauri yasa hannunshi ya goge fuskarshi,kuma duk kan alamu shi kanshi bai san yanda akayi ba har suka fito,sai dai kuma bayyi mamaki ba saboda yasan ya lume cikin tunani kala kala na rayuwa. Kallonta yayi dauke da murmushi afuskarshi yace,"babu abinda akayi mani baby."kallon rashin yadda tayi mashi tace,"ba ayi maka komai ba kuma kake kuka?don Allah ka fada mani ko don in samu kwanciyar hankali."lakutar dogon hancinta yayi yace,"kina da kyau sodangi,kuma ina sonki da yawa acikin zuciyata,sannan kuma ina jin tausayinki acikin raina."shafa gefen fuskarta yayi yaci gaba da cewa,"duk wadannan abubuwan ne idan na tuna nakejin tausayin ki dani kaina." Komawa tayi ajikinshi ta kwanta tana murmushi, saboda abinda ya fada shi yayi mata dadi,don haka sai taji wani sonshi ya Kara shiga acikin zuciyarta sai ta juya ta fuskance shi suka rinka kallon juna,abinda yafi kauna tayi mashi watau kiss,maida mata martani yayi sosai,domin aranar kuma wani sabon darasin ya kara koya mata wadda taji arayuwarta bazata so abinda zai rabata da masoyinta ba. Kusan sukuku safwan ya ida wuninshi na yau,kuma duk abinda zaiyi sodangi tana ajikinshi har wurin karfe biyu na dare. Barci take,amma shi idanuwanshi sun bushe rayau ya gaza ko runtse su.don haka sadda agogon bango ta kada biyu dai dai sai ya mike daga kwanciyar da yayi ya koma dakinshi ya canza kayan dake jikinshi yasa irin jibgegiyar rigar nan ta sanyi,saboda lokacin na damuna neh,kuma garin yayi sanyi sosai ga walkiya ana tayi saboda hadarin dake da akwai. Dakin sodangi ya koma ya samu har yanzu barcinta takeyi,don haka sai ya ajiye wata farar takarda agabanta ya dauki mabudan motarshi ya fice. Fitarshi bude idanuwanta,saboda shafawar da tayi taji babu komai agabanta yasa ta fara wara ido. Tunani ne ta farayi na inda ya shiga,can kuma dai sai taji alamar motsi awaje.mikewa tayi da sauri ta nufi sashenshi,bata iskeshi ba,sai ta nufi wajen kanta tsaye. Safwan ta samu awurin motarshi yana kokarin shiga tayi maza ta rikeshi cikin razana tace,"baby ina zaka cikin wannan tsohon daren?" Bai amsa mata ba,kuma bai juyo ya kalle ta ba, sai ma kokarin ture hannunta da yakeyi.ai kuwa rikeshi tayi tamau tayi magana da karfinta tace,"da kai nake magana safwan,miya faru dakai neh?" Juyowa yayi kamar ahassale ya ture hannunta yace,"kada ki karayi mani tsawa,saboda zan iya hukuntaki idan kika sake."fasa shiga motar yayi ya juyo sosai ya tsaya aganta taci gaba da cewa,"sodangi zan tafi in ba barki,kuma tafiya wadda babu waiwaye acikinta,don bazan dawo ba har abada." Jin amsar tayi kamar saukar wata aradu abisa kwalwar kanta,don haka sai kawai taji ta gigice ta sake rikeshi tana cewa,"safwan mi nayi maka har zaka yanke mani irin wannan hukuncin?" Furzar da iskar dake cikin bakinshi yayi yace,"haka ra ayina yake,kuma ke ki godewa Allah dana biyo maki ta wannan hanyar,kuma don inajin tausayinki,amma ayau tsakani na dake the game is over,don haka kina iya tsayawa gari ya waye sai ki nufi gidanku,idan kuma anan gidan zaki zauna gashi nan na bar maki shi har abadan abada." Shafa idanuwanta tayi sannan tayi addu a,ya Allah kasa duk abubuwan nan da nakeji nake gani su zame mani a mafarki neh. Safwan ya bushe da dariya saboda addu ar da tayi duk awaje tayi ta,don haka yasa hannu ya damki kafadarta yace,"ba mafarki kike ba,ni safwan nace bana sonki sodangi,kuma na sake ki saki daya,don kada kiyi tunanin zan waiwayo gareki har abadan." Sandarewa tayi,don gaba daya taji na urorin dake jikinta sun tsaya cak sun daina aiki,domin ko yan hawayen da suke zuba sai da suka tsaya,saboda zuciyarta kadai ke bugawa. Shigewa yayi cikin motarshi ya bata wuta sosai,can kuma ko mi ya tuna πŸ€”? Sai ya fito daga motar yazo inda sodangin take ya damki hannunta ya turata acikin motar,sannan shima ya shiga ya bata wuta. Yana zuwa gaf wurin mai gadin ya tsaya,mai gadi ya fito jiki na rawa ya rusuna yace yallabai tafiyarce ta tashi neh?" Fuska ba yabo ba fallasa ya amsa mashi,"kamar dai yanda na fada maka,idan kaji zaka iya zama kaci gaba da tsaron gidan da babu kowa toh ga fili ga mai doki nan." Maigadi ya karayin kasa da kansa yace,aini yallabai ka riga ka gama mani komai a duniya,domin wanda ya dauko albashin shekara biyar ya baka kyauta,ba tare da tunanin komai ba,ai baka da kamarshi arayuwar duniyar nan.don haka ni ina nan ba inda zani zan zauna in tsare maka gidanka har zuwa ranar da zaka dawo." Safwan ya daka mashi wata irin tsawa da karfinshi yace,"waye ya fada maka cewar zan dawo kauyen nan?dama wani dalili ya kawo ni yanxu kuwa babu dalilin,gida kuma na sodangi ne don haka ita zaka tambaya izinin zama."yana gama fada mashi haka ya figi motar yaguje ya bar wajen. Maigadi dai bai damu da halin dayaga yallaban nashi ba,shidai sai rafga godiyya yake abinshi. Gaf da santar da zata kaika har kofar gidan su sodangi suka kai,don haka safwan tsayawa yayi ya sake fito da ita zai shige motarshi tayi wuf ta rikeshi tare da sakala hannuwanta aruwan cikinshi ta rungumeshi ta baya. Shi kanshi sai da yaji rikon da tayi mashi har acikin zuciyarshi,saboda ko alokacin runtse idanuwanshi yayi,daga bisa ni kuma komi ya tuna oho yasa hannunshi ya fincike nata hannuwan ya shige motarshi yaja ko waiwayenta bayyi ba. Love you sis 😘 08033481518 [4/8, 10:25 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 20 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks & love you all 😘😘 Bin motar tashi tayi da idanuwanta har ya bulle ta daina hangenshi sai dai kurar daya bado mata. Wata irin ajiyar zuciya taja tare da zube dukkan gwiwoyinta akasa,sannan kuma wasu hawayene masu zafi hadi da radadi suka gangaro mata.sam sodangi ta rasa gane shin asama take ko akasa ko. Anan tayi zaune har aka fara kiran sallar farko ba tare data san abinda yake faruwa da ita ba. Duk acikin wannan dare, molasa ta farka daga barcin data fara,sakamakon wani mummunan mafarki da tayi akan sodangi yasa ta tashi afirgice ta rasa abinda yake mata dadi. Tashi tayi ta nufi dakin ardo, ta tura kofar dakin ahankali tare dayin sallama. Cikin yanayin barci ardo ya amsa,da yake mutum ne mara nauyin barci,don haka sai ya tashi zaune har ta iso inda yake ta raba kusa dashi tace,"ardo na gaza komawa barci saboda wani mafarki danayi wadda ya tayar mani da hankali." Ardo ya tarbi numfashinta da sauri yace,"ina fata dai da kika farka kinyi addu a koh?saboda kusan mafarki duk daga shaidan ne,shi yasa manzon mu ya horemu dayin addu a kamin mu kwanta barci." Molasa ta numfasa sannan tace,"ardo duk nayi wallahi,amma zuciyata ta kare na rasa abinda yakeyi mani dadi." Hannu yasa ya rufe mata baki yace,"yi shiru molasa,nace kici gaba da addu a,saboda musulunci ya fada mana ba a son bayyanar da mumunan mafarki." Dole molasa ta dakata,saboda ji take idan bata fada ba abin zayyi ta damunta ita kadai. Kasa konawa dakinta tayi,don haka sai tayi kwanciyarta dakin ardo har sai da ta farajin kiran sallar asuba sannan ta fito ta taba kofar sadah,sai da ta tabbatar ya tashi sannan tayi alwallah ta wuce dakinta. Sadah da ardo kusan tare suka fita zuwa dan karamin masallacin da suka hada da kansu acikin yar rugar. Sodangi dake zaune cikin tubayar yashi sai kawai ta samu kanta da mikewa tsaye ta hau tafiya ta nufi hanyar gidansu ba umh ba umh umh har ta isa. Kanta tsaye ta shige cikin gidan, adai dai lokacin molasa ta fito daga inda suke dora sanwa zata koma daki,sai kawai taci karo da sodangi,yanda kasan sakago(robbot) haka take tafiya. Domin ita kanta molasa don gari ya fara haske da sai tace ko aljana ce,da sauri tabi bayanta har daki ta sameta zaune akan dan bonon molasa. Molasa ta samu kusa da ita hankali atashe ta zauna gami da dafa kafadarta ta kira sunanta,"sodangi kina lafiya kuwa?miya faru kika taho da duku duku haka,kuma ina mijin naki?" Babu amsar data samu daga wurin sodangi,illah binta da idanuwa kawai takeyi,hankalin molasa ya kara tashi ta kama sodangi ta girgiza sosai wai don ta dawo hayyacinta amma inaa........ Don haka sai kawai molasa ta samu kanta da fashewa da kuka tana cewa,"shikenan na shiga ukku na lalace sun salwantar mani da hankalin yarinya,oh ni molasa ina zan saka raina." Fasa kukanta shigowarsu sadah,kuma duk akan kunnensu take wadannan maganganun don haka cikin sauri suka nufi dakinta ardo yana ta faman kiran sunanta. Ganin sodangi firkai firkai jikinta ko abin rufa babu ga idanuwanta sun kyame sun bushe yasa su duka dukayi turus atsakar dakin. Sadah neh yayi ta maza ya isa gaban sodangi ya durkusa yana kiran sunanta,"sodangi!!! Miya sameki? Kuma ina safwan din?" Yanda tayiwa molasa haka tayi mashi shima,don haka afirgice ya juya ya kalli ardo yace,"ardo ko yan fashi duka shigar masu? Ardo daya sandare abakin kofa,amma dayake namij neh ba farat daya zaka gane haka ba,duk idanuwanshi suna akan sodangi yace,"bamu da tabbas sadah,amma taso muje gidan tunda sodangin ta gaza ce mana komai." Juyawa sukayi,tare da daukar sandunansu,ita kuma Sodangi sulalawa tayi ta kwanta akan gadon,amma molasa tana lura da wasu hawaye da suka gangaro mata ta gefen ido. Ardo da sadah babu wani bata lokaci da sukayi sai gasu gidan safwan,da yake maigadi yasansu da saurin shi ya fito suka gaisa da ardo,sannan ardo ya tambayeshi ko inah maigidan?" Maigadi yayiwa ardo bayanin tafiyar safwan,ya kara masu da bayanin cewar ya daiji yallabai din yana cewa ya tafi bazai dawo ba har abada." Dukkansu gabansu neh ya fadi dammm,saboda babu wanda yayi tunanin jin haka,sadah ne ya kalli ardo yaga jikinshi har rawa yake,watau duk yanda yaso ya taushe tashin hankalin dake ranshi sai da ya bayyana,zare sandar dake hannunshi yayi ya bugi kasa da ita yace,"wallahi kado baka isa ba,har ni zaiyiwa haka?nayi mashi dare shi zaiyi mani rana,idona idonshi wallah,sadah zo muje gida." Har sun hau hanyar komawa sadah da tunani ya isheshi yace ardo ina zuwa,bai jira amsar ardo ba ya koma gidan safwan,kai tsaye ya shige cikin gidan yana ta yan dube dubenshi har zuwa dakunan su,saboda babu inda aka rufe. Takardar daya gani asaman gadon sodangi ta dauki hankalinshi ya nufeta ya dauka tare da saurin budeta. Abinda ya gani rubuce acikinta neh ya kara razanah shi,saboda baro baro safwan ya rubuta ya saki yar uwarshi,tare dayi mata kyautar gidan da abinda yake acikinsa. Fashewa yayi da kuka,yayi yayi yay mai isarshi,saboda babu komai acikin zuciyarshi face tausayin yar uwarshi,domin yafi kowa sanin yanda sodangi take tsananin son safwan,a rana daya yazo ya karyawa yar uwarshi zuciya,fon haka shima nan take yasha alwashin muddun ya gamu da safwan sai ya ci mutunchinshi koda kuwa zaisa adaureshi ne. Share hawayen yayi ya zira takardar acikin aljihunshi ya fito,kai tsaye gidan su ya nufa ya samu har zuwa lokacin molasa tana ta matsawa sodangi akan sai tayi magana tayi masu bayanin abinda ya hadata da mijinta har ya gudu ya barta. Ba barci take ba,amma ta kama idanuwanta ta rufesu tamkar maiyin shi.sadah neh ya raba gefe daya ya zauna duk jikinshi babu kwari ya kalli molasa yace,"ku kyaleta hakanan,domin idan da zata iya magana da tuni tayi,kuma ni ban zargeta baba,saboda halin da safwan ya sakata aciki ba dan karami ba ne." Ardo dake gefe ya cika yayi faful saboda bacin rai ya kalli sadah yace,"ka gano wani abun hala?" Sadah ya zaro takardar dake aljihunshi ya mikawa ardo,da sauri ardo ya amsa tare da budeta ya fara karantawa abayyaneh. Assalamu alaikum. Ni safwan Alhaji sulaiman, na rubuta wannan takardar domin in baku hakuri akan abinda zakuji,watau na saki diyarku sodangi saki daya badan tayi mani laifin komai ba. Har gobe ina son sodangi sai dai ina da wani dalilina na dabam wanda bazan iya ci gaba da rayuwa da ita ba.sai dai kuma na bata gidana da abinda ke ciki kyauta,idan ta samu miji tayi aure . Inayi maku fatan alkhairi tare da cewa sai wata rana. Naku safwan. Wurgi ardo yayi da takardar yana ta zafga sababi,"gidanshi na banza,wallahi idona idonshi,domin wallah idan na hadu dashi sai yayi dana sanin abinda ya aikata mana." Sadah da rarrafe ya dauki takardar da ardo ya wurgas ya mayar da ita aljihunshi yaci gaba da sauraron ardo,kuma dama yasan halinshi idan ranshi ya bace. Yau kwanan sodangi biyu agidan,kuma har yanzu babu wani cigaban da aka samu,domin ko abinci sai dai molasa ta tayar da ita zaune ta rinka bata, dai dai da sallah itama sai an bata umurni sannan takeyinta. Arana ta ukku ne tana kwance tana barci sai kawai molasa taga ta zabura ta tashi tare da kwalawa safwan kira tayi hanyar kofar gida.inda Allah ya taimaki molasa cewa sadah yana nan zaune,domin tun faruwar wannan al amarin, sadah ya daina zuwa ko ina,idan bai zaune wajen sodangi duk yasan bazace mashi komai ba,toh yana zaune kofar gida. Ganin sodangin waje yasa ya mike da sauri ya nufeta,itama din tana ganinshi ta nufeshi ta rike tana tambayarshi "ina safwan? Kazo muje ka rakani gidah saboda yana can yana jira nah." Tausayinta ne ya kamashi yasa karfi ya riketa gam,ita kuma sai sambatu take kamar wadda ta zare.girgizata yayi da karfi ya kira sunanta yace,"sodangi! Ki saurareni mana." Tsayawa tayi cak tana kallonshi saboda tsorata da yayi wajen ihun kiranta,ganin ta saurara sadah yaci gaba da cewa, "dubi yanda kika fito,ko kina tsammanin idan safwan ya ganki ahaka zaiji dadi?" Kallon kanta tayi taga daga ita sai doguwar riga babu mayafi ajikinta,sai ta kada kanta tace,"a a yaya sadah."sunanshi data kira yasa yaji wani dadi ya kamashi,domin alamace ta hankalinta ya dawo jikinta. Hamdala yayi yace,"toh muje cikin gida,kinga molasarki can tana kallonki."daga ido tayi ta hango molasa tsaye abakin kofar gidan. Juyawa tayi suka koma cikin gidan gaba dayansu,sannan sadah yayi dubara ya zaunar da ita bisa yar kujerar tsakar gida ya koma dakinshi ya dauko wannan takardar ta safwan. Amma kamin ya bata ita sai da yayi mata nasiha mai shiga zuciya,sannan ya mika mata. Amsa tayi ta fara dubawa,ai bata kai karshe ba ta fashe da sabon kuka saboda komai ne ya dawo mata tsaf acikin kanta. Molasa ta matsa kusa da ita tana bata hakuri,amma sai da tayi mai isarta sannan ta lafa don kanta. Kuma tundaga lokacin ta dauki dangana ta sanyawa ranta,saboda molasa ma bata zauna ba wajen samo addu o I wajen malamansu,kullum cikin karantasu take tana tofa mata aruwa tana bata. aikuwa cikin sati biyu Sodangi ta warware sai dan abinda ba a rasa ba,domin ita kanta ganin yanda dan uwanta ya damu da ita da iyayenta yasa take kauda kanta daga tunane tunane. Amma kuma mee?ji take jikinta yana canzawa,kullum sai ta kwana da masassarar dare,ga cikinta ya fara gaza daukar ko wanne abinci,dataci sai tayi amai. Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:27 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 22 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thank you and love you all😘😘 Masoya na ina godiyya,saboda sakonninku suna samuna ta waya da online,kuma na gode da addu o inku,Allah ya barmu tare. Please ina mai baku hakuri,saboda na samu mistake wajen rubuta number, instead in sa 21 sai na kara repeating din 20. πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ Sannan kuma sodangi ta fara zabin abinda take so da wanda bata so,duk kan wadannan abubuwan da suke faruwa akan idon molasa,don haka sai jikinta yayi sanyi ta fara zargin diyar tata,kuma tana son fadawa ardo amma tanakin tsoron abinda zai biyo baya. Yau ma tunda safe tashin sodangi tayo waje ta nufi wurin da molasa take wanke wanke ta duka tana ta kakarin amai wanda yasa duk iyayenta suka yo waje tare da dan uwanta suna kallonta. Ardo ne rai abace yakeyi mata sannu,ita kuma molasa ta sanya mata ruwa tana dauraye mata bakinta,sannan sadah ya kamata ya rakata dakin molasa din. Molasa da ardo cikin damuwa suka koma dakin ardo suka zauna,numfasawa yayi yace,"kinsan Allah molasa,idan har yarinyar nan ciki gareta sai na zubar dashi da kaina,saboda banga dalilinshi ba,kuma babu wani amfani da cikin zaiyi mana. Molasa tayi tagumi cikin damuwa tace,"ardo kada muyi saurin yanke hukunci,mi zaisa bazamu kaita asibiti ba?" Jin jina kanshi yayi yace,"toh ya zamuyi,ai dole aje asibitin,sai dai kuma idan har akwai cikin bakinku kanin kafarku,don Allah kada ku fadawa kowa,domin ko yanzu garin nan ba tsira mukayi ba sai yan kananan maganganu suke akan auren nan,ni nasan wani abun ma don bai faduwa agabana da cin kashi za a rinkayi mana." Molasa ta kada kai tace,"haka neh ardo,amma idan muka kauda kan mu ai komai mai wucewa neh." Ardo yace,"nasan haka molasa,amma ni idan da zaki biye mani da mun matsa gaba,saboda shi mutum ko a ina yake, arzikinshi yana iske shi." Molasa tayi shiru tana nazarin maganar mijinta,ahankali ta dago kai ta kalleshi tace,"ardo kayi hakuri da abinda zance,saboda shawarar daka kawo ba kinta nayi ba,amma ko zamu bar rugar nan mu bari sai acan gaba ba tare da wani dalili ba,domin yanzu duk wanda yaji mun wuce cewa zaiyi munyi abinda yasha mana kai neh,kuma sannan ayanzu yan rugar nan suna amfanuwa dakai sosai ta fannin ci gaba da rugar ta samu kasan duk adalilinka neh,to shiyasa nake baka hakuri." Ardo ya jinjina kai yace,"kuma haka neh molasa,wallah kin fadi gaskiya,kuma na gode kwarai da tunasar dani da kikayi,don haka maza ki tashi kije ku kimtsa don ku samu shiga asibitin da wuri." Bayan sun shirya neh sadah ya rakasu har inda zasu samu motar zuwa karamar asibitin matazu. Anyiwa sodangi aune aune sosai tundaga fitsari har jini,a inda suka tabbatarwa molasa cewa sodangi tana da shigar karamin ciki na sati biyar, sannan kuma akwai maleria. Babu abinda ya dami sodangi,saboda ita farin ciki neh kawai takeyi,kuma tana ganin idan har safwan ya dawo ya sameta da cikinshi zai kara sonta matuka,don haka sai kawai ta samu kanta dayin murmushi, ita kuwa molasa abin duniya neh ya dameta tunda taji hukuncin da ardo zai yankewa cikin sodangi. Ganin farin cikin sodangi afili yasa taji tausayinta tace,"ke kuwa muye abin farin cikin,bayan uban dan ya tafi ya barki da wahala." Sodangi tayi dariya tace,"molasa wahala kikace fa,ina take?domin ya za ayi samun da ko diya su zama wahala awajen iyayensu?" Wannan maganar ta sodangi ba karamin gigita molasa tayi ba,don haka sai ta kama hannunta ta samar masu wani waje suka zauna sannan ta numfasa ta kira sunanta tace,"sodangi! Ba ina nufin ya'ya suna zama wahala ga iyayensu,duk inda kikaga haka toh iyayen neh basu ba yaran nasu tarbiyyar data kamata ba,amma ya'ya masu tarbiyya sune wadanda iyayensu suke alfahari dasu kuma sune ya'ya masu albarka." Sodangi tayi yar dariyarta tace,insha Allahu molasa, abinda zan haifa zai zamo mai albarka kuma duk zamuyi alfahari dashi wata rana." Molasa ta share zufar data feso mata ta zubawa sodangi idanuwa tana tunanin abubuwa daban daban,saboda yanda taga sodangi ta dauki so da kauna ta dorawa cikin da akace tana dashi.nazari tayi kawai kada ta boye mata komai akan shirin ardo,saboda gaba daya ardo ya tsani safwan da duk abinda ya jibence shi." Dafa kafadarta tayi tace,"sodangi zan fada maki wani abu,amma bana son ki tayar da hankalinki,don haka kiyi mani alkawarin zaki kwantar da hankalinki sannan in fada maki." Sodangi sam bata kawo wa zuciyarta komai ba tacewa molasa,"insha Allahu bazanyi abinda bakiso ba molasatah." Murmushi molasa tayi ta zauna ahankali ta fadawa sodangi komai,sannan ta dora da cewa,kinga ko a shekarunki sunyi kankanta ace kin fara haihuwa yanzu,kuma idan da ina da iko sodangi,dani zan amsar maki haihuwar nan don ki huta." Bata ankara ba sai gani tayi sodangi tana shirin tuntserewa tunda azaune take,da sauri tasa hannu ta rikota tana salati,sannan ta rungumeta ajikinta tana kiran sunanta. Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:27 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba Saleh daudawa 23 I dedicated this love story to my Hausa Novel group & my fans,thanks and love you all😘😘 Sodangi ta bude idanuwanta ahankali tana kallon molasa tare da langabe kai tace,"molasa ! Ardo yana sona kuwa? Mi yasa zai zamo mai son kanshi ba tare da tunanin ni wacce irin rayuwa zanyi ba........... Da sauri molasa tasa hannu ta rufe mata baki tace,"ya isa haka nan sodangi,don bana son kiyiwa mahaifinki wata fassara ta daban,kuma akul na karajin furucin wai yana sonki,domin fadi bannar baki neh,saboda son naki shi ya jawo mashi halin da yake ciki a yanzu." Share mata hawaye tayi taci gaba da cewa," ki daina zubar da hawayenki ya isa haka nan,insha Allahu ni zanyi maki tsaye inga cikinki ya zauna cikin koshin lafiya,amma sai idan kin bi shawarar da zan baki." Sodangi ta kalli molasa tace,"zan iya molasa!zan iya!! Molasa ta numfasa tace,kinsan goggonki laura dake bichi?"sodangi ta daga kanta tace,"nasanta molasa,kanwarki ce uwa daya uba daya." Molasa ta kada kanta tace,"idan kina iyawa can zan turaki wajenta,amma kuma kin san zama da laure sai hakuri,saboda koni da nake yar uwarta idan muka hadu bamu wuce kwana daya zata fara nuna mani miyagun halayenta,don haka idan har zaki iya jurewa sai ki koma wajenta da zama har Allah ya saukeki lfy." Molasa tayi murmushi tace,"zan iya zama da ita molasa."mamaki ya kama molasa sosai,domin batayi tsammanin zatace haka ba,sai kuma jikinta yayi sanyi,saboda ko ita hakuri take da laura toh ballantana yar cikintaπŸ€”. Kama sodangi tayi ta mikar da ita tsaye suka nufi inda zasu samu motar da zata mayar dasu gida. Akofar gida suka samu ardo zaune yana jiransu,don haka sai molasa gaba daya taji ta rude saboda mijinta yanayi mata kwarjini da yawa.suna shiga cikin gidan molasa ta nufi bandaki,ita kuma sodangi ta nufi dakin molasa. Molasa ta jima abandakin har sai da ardo ya soma magana,sannan ta fito da sauri tana share gumi. Ardo ya kalleta yayi mata sannu,domin shi duk tunaninshi da lalura ta dawo,wata yar inuwa suka samu suka raba sai ardo yace,"tun dazu na gaza zuwa ko ina molasa,zaman jiranku nakeyi." Molasa tayi murmushin karfin hali tace,"ardo godewa Allah zamuyi ai,saboda yarinyar na typoid da maleria ne sukayo mata caa." Murmushi ardo yayi gami da godewa Allah yace,"babu komai idan dai wannan neh sai mu nemar mata magani." Haka kuwa akayi,ardo ya shiga nemawa sodangi maganin gargajiya,ita kuma molasa idan ya bata taba sodangi sai ta samu wani wuri ta juyeshi,yana barin gidan sai ta tona rami ta ruba ruwan maganin ta rufe. Haka sukayi tayi har cikin sodangi ya tunkari wata biyar,toh alokacin neh hankalin sodangi da molasa ya fara tashi,domin masana ciki da sun ganta zasu iya cewa tana da ciki. Yau kamar koda yaushe da daddare idan har garin akwai zafi,sai molasa tayi masu shimfida atsakar gidan su zauna gaba daya su sha iska,don haka molasa ta gyara zamanta tace,"ardo ni kuwa ina neman alfarmarka idan har ka yarda." Ardo ya dago kai daga kishingiden da yayi ya kalleta yace,"ki fadi kominene,ni kuma idan har baifi karfina ba zanyi maki." Molasa tayi murmushi tace,"dama sodangi ce tace in fada maka tana son zuwa bichi." Ardo yace,mi ? Tare da tashi zaune yana kallon sodangin yaci gaba da cewa,"sodangi kina iya zama da laura kuwa?"sodangi tayi murmushi tace,"zan iya ardo,kuma idan na tafi zan dau lokaci kamin in dawo." Ardo yayi dariya tare dayiwa sodangi jinjinaπŸ‘πŸ»yace,lallai diyata zata zama jarumar jarumai,saboda idan har kika zauna da laura tsawon sati daya ban ga kin dawo ba,toh ba karamin namijin kokari kikayi ba,idan kuma kikayi wata daya ni kuma zan baki kyautar wannan dan marikin sa da aka haifa mani wancan watan." Gaba daya suka dau dariya,ita kuma sodangi ta jinjina kai tace,"yaya sadah harda kai koh akeyi mani dariya."sadah ya ida gumtse dariyar dake cikin bakinshi yace,"yi hakuri sodangi,ni kaina mmk nayi danaji kince zaki wurin goggo laura,alhalin nasan ko zowa tayi garin nan baku jituwa,toh bare kuma ke kin sameta har agidanta." Sodangi ta numfasa tace,"insha Allahu tunda ardo ya amince,ni kuma sai na baku mmk,saboda gaba daya zan koma wajenta da zama,domin ni tuni kauyen nan ya fita raina." Hakan data fada yasa duk sukayi shiru saboda sai a yanzu neh ardo ya fahimci dalilin tafiyar sodangi,don haka yace,"na amince maki sodangi,kuma insha Allahu goben nan sadah zai rakaki har bichi,mu kuma zamuyi maki fatan alkhairi arayuwarki." Sodangi tayi dariya tace,"na gode babana,muma muna fatan Allah ya bar mana ku,yaja tsawan rayuwarku." Tundaga daren suka fara shirye shiryen tafiyar sodangi da kuma bata shawarwari akan yanda zata tafiyar da al amurranta,da kuma kauda kai ga halayen laura. Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:27 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba Saleh daudawa 24 I dedicated this love story to my Hausa Novel group & my fans,thanks & love you all😘😘 Duk wata tsohuwar ajiya molasa ta kwalkwalota ta dankawa sodangi tace,"wadannan kudin ki adana su saboda tsaron lalura,kuma insha Allahu kamin ki haihu zanzo garin."wata takarda ce ta fiddo wadda ta rubuta ta da ajamin larabci taci gaba da cewa,"wannan wasikar kuma ta laura ce da mijinta,idan kinje kiba mijin shi zai karantawa laura din." Sodangi tayi wata irin ajiyar zuciya,tare dayin narai narai da idanuwanta,saboda idan ba don dole ba sam bata son rabuwa da iyayenta.kallon molasa tayi cikin jin tausayin kanta tace,"molasata ki yafe mani saboda rayuwa!!" Da sauri ta tsayar da ita,domin tun dazu take ta bakin kokarin ta don kada hawayen dake cikin idanuwanta su zubo tace,"Allah ya yafe mana gaba dayan mu, kuma insha Allahu zanzo in sameki cikin koshin lafiya."tana gama fadar haka ta juya ta nufi dakinta. Ardo ya raka su sadah har inda zasu hau mota sannan shima ya kawo kudi masu yawa ya dankawa sodangi. Sai kuma ya kawo wasu yaba sadah yace,"wadannan kuma kuyi na mota dasu da yar tsaraba don kada ku isa hannu biyu." Addu a yayi masu sosai,kuma sai da yaga sun shiga motar da zata tafi dasu sannan ya juya ya koma gida. πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ BICHI Babban gari ne na bammamaki,wadda sai ka shigeshi sosai zaka gane haka. Laura da mijinta suna zaune neh acikin wata rugar fulani gaf da shiga garin,domin ba wani nisa keda akwai ba,saboda kusan dukkan al amurransu da kafa suke shiga garin sunayin su.mijin laura kwata kwata baya da wani karfin kirki,shi yasa koda yaushe suke cikin cashewa da laura,domin ita irin matan nan ne masu son da bala I sai sunji dadi,ko kuma basu son tsara yafi su.shiyasa koda yaushe cikin sa ido take,na ya zatayi ta samu taro da ahu. Shi yasa zuwan sodangi daga farko,bata samu wata matsala wajen zama da laura ba,saboda yan kudin data fahimta akwai ajinta,shi yasa kullum cikin lelenta take,kuma tun daga lokacin cimar gidansu laura ta sake,domin kai tsaye take cewa sodangi ta kawo kudi kaza za ayi. Duk hakan bai taba damun sodangi ba tunda dai an barta ta zauna lafiya. Haka rayuwa tayi ta tafiya har cikinta ya tsufa,kuma alokacin duk wasu yan kudi dake jikin sodangi suka kare, sai rayuwa ta fara canzawa,laura ta rage kulawa da ita,sai ma yawan fada babu gaira babu sabab zataji ta kacame da mijinta,karshe sai dai ya fita ya bar mata gidan. Kwatsam suna zaune jugum sai sukaji sallamar molasa,ai kuwa farin ciki awurin sodangi da laura ba a cewa komai,bama ya sodangi. Mikewa tayi da sauri ta nufeta,don ko nauyin cikin bataji ba ta kama molasa ta rungume tana dariyar farin ciki. Tsara ba sosai tayi masu, laura ta zauna sai washe baki takeyi tana dubawa,ita kuma molasa ta mayar da hankali kan diyarta ga tausayi bayyane afuskarta tace,"sannu sodangi!sannu da kokari!!" Murmushi tayi tace,"yawwa molasa,ina ardo da yaya sadah?"molasa tace,duk suna lafiya, kuma duna gaisheki."sannan ta kara bude jikkarta ta dauko sakon da sadah ya bata ta kawowa sodangi, Cikin farin ciki sodangi ta amsa tare da godiyya.molasa ta sake kallon cikin sodangi tace,"kwana bakwai ardo ya yarje mani,inama haihuwarki ta riskeni acikin garin nan,wallahi dana fi kowa jin dadi sodangi." Murmushi kawai tayi ta zame jikinta ta kwanta abisa kafafuwan mahaifiyyarta tanajin wani sanyi acikin zuciyarta. Kwana daya molasa tayi tasa mijin laura ya kama naggenta da laure ke kiwo tace yaje ya sayar mata da ita,ai kuwa bai bata wani lokaci ba sai gashi da kudin. Acikin daren sodangi ta tashi molasa daga barci tace mata cikinta ne yakeyi mata ciwo,ai kuwa ta mike da sauri ta kamata tana kara tambayarta abinda takeji. Sodangi ta kama kugunta ta rike kam tana yarfe hannu,ai kuwa molasa ta fahimci nakuda takeyi,don haka ta debo ruwa ta karanta mata wasu addu o I ta bata tasha. Tundaga lokacin ciwo yayi tazowa babu kakkautawa har Allah ya sauketa lafiya. Molasa cikin godiyya ga Allah ta dago abinda sodangi ta haifa taga baby girl ce,kaudata gefe daya tayi taci gaba da kulawa da yarta hwr saida ta kimtsata tsaf sannan ta koma kan yar jaririyar ta gogeta fes. Gari na wayewa sai dai laura taga jaririya,aikuwa sai farin ciki da murna har ta rasa inda zata sanya kanta. Kudi molasa ta diba taba laura tare da fada mata abubuwan da zata sawo masu na amfani da kayan jarirai. Dai dai gwargwardo molasa ta tsayawa sodangi,domin duk abinda ya dace sai da tasa akayi mata na gata don kada tayi kukan rashin safwan,amma ina......saboda duk alokacin da sodangi zata kalli yar jaririyar nan tsaf kallonta take tamkar safwan.shiyasa kuma kaunar diyar take ta kara shiga ranta domin akullum zuciyarta tana bata safwan zai dawo gareta,amma yaushe???????πŸ€” Gobe ne adadin kwanakin da molasa ta debo zasu kare,shi yasa daren yau basu kwanta da wuri ba ita da sodangi sai kara tattaunawa suke akan rayuwa. Sodangi ce ta kalli molasa tace,"ni kuwa molasa mi zaisa bazamu sanar da ardo ba,tunda dai na sauka lfy kamar yanda mukayi ta fata."Molasa ta jinjina kanta tace," sodangi ki kyale ardo kawai,saboda ni din nan nafi kowa sanin halinshi." Dan numfasawa tayi sannan taci gaba da cewa,"ni idan da zaki bi shawarata,da sai kici gaba da zama gidan nan har zuwa sadda yarinyarki zatayi kwari,ni kuma kamin lokacin sai inga wacce dubara zamu shirya." Sodangi tayi shiru tare da sunkuyar da kanta kasa tana nazarin maganar mahaifiyyarta,can ta dago manyan idanuwanta da suka kara kyau ta kalli inda goggonta laura take kwance tana ta kwasar barci harda minshari tace,"molasa ni ba komai nake tunani ba sai yanda zaman mu zai kasance tsakanin nah da goggo,ni ba sana a ba bare ince zanci gaba da daukar nauyin kaina, sai dai kuma akwai wani nazari da nayi amma idan har zaku amince dashi." Molasa tace,"wanne abu ne?" Sodangi ta marairaice kai tace,molasa so nake inci gaba da karatuna in samu ko secondry neh in hada,sannan kuma akwai women center a nan bichi inason in shiga in rinka koyon sana a,wadda anan gaba zan iya dogara da ita." Molasa tayi sukwi tana sauraren sodangi tare dajin wani farin ciki aciki ranta,wai sodangi zata koma makaranta,sannan kuma har tana tunanin dogara da kanta nan gaba. Wasu hawayene suka sulalo daga idanuwanta ba tare data sani ba tasa hannu ta sharesu tace,"na goya maki baya sodangi,kuma dana koma zan sanar da mahaifinki,domin nasan idan suka ji shi da sadah, sai sunfi kowa farin ciki." Kudin da sukayi saura na saniyata ta damkawa sodangi su taci gaba da cewa,"wadannan ki boyesu har zuwa lokacin da zaki fara zuwa makaranta,sai kiyi uniform da sauran abinda ya dace kamin in turo maki wasu,kuma shima ardon zanyi kokari inga yana bada wani abu don ki kara." Sodangi tayiwa mahaifiyyarta godiyya mara adadi harda yan hawayenta.itama haka molasan hawayen take har sai da suka dan dauki lokaci babu wanda yayi magana sannan molasar tace,"ko kin tabajin sunan mahaifiyyar safwan?" Sodangi tayi shiru tana tunanin ranar da safwan yake fada mata yanda umminshi take sonshi da irin sangartashin da tayi,kuma idan da zai haifi diya mata koda sun kai gomane zai iya sanya masu sunan ummu salma,saboda ya nuna mata yanda yake kaunarta. Lumshe idanuwanta tayi ta bude tace,"molasa ban san sunan ta ba,kuma ni idan da zaki amince sunanki za a sanya mata."jin haka molasa tayi farin ciki tace,"toh na gode kuma Allah ya albarkace ku gaba daya." Ranar suna babing sodangi taci sunan molasa watau Hajara,amma kuma sai sodangi take kiranta da Afnan. πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ (After five years) Bayan shekara biyar Tsaye yayi abakin kofar jirgin yana kallon yanda aka kara kayata babban filin jirgin tarayya abuja,acikin shekara biyar da yayi da barin Nigeria sai yaga komai ya canza mashi. Shakar iskar wajen yayi tare da lumshe idanuwanshi for seconds, ahankali ya budesu yayi wani kayataccen murmushi ya fada in silent voice,"sodangi I'm back." Zira kafarshi yayi ahankali yake taka matattakalar yana sakkowa cikin wata irin tafiya ta maza isasshi wadanda naira ta zauna mawa. Wani brown Glass ya zaro daga aljihun gaban rigarshi ya mannawa idanuwanshi,tafiya kawai yake kanshi tsaye ba tare da yan waige waige ba Har zuwa wurin da yake sa ran ganin wadanda zasu daukeshi. Yusuf ya hango sabe da baby boy da bai wuci shekara ukku ba aduniya,yana ganinshi ya ganeshi,saboda tarin pics da suke Acikin wayarshi. Kara taku yayi har ya isa yusuf bai lura da tahowarshi ba sai da ya kure masu tukunnah. Gaba dayansu suka sakarwa juna murmushi saboda farin ciki.Rungume junan sukayi harda yar dariya,sannan safwan yasa hannu ya amshi khalifa da yake sunan mahaifinsu gareshi watau sulaiman. Fitarsu daga wurin safwan yaga Kusan motoci biyar ajere,kuma ga wasu garaden maza atsaitsaye Suna jiran isowarsu. Juyawa yayi ya kalli yusuf don yayi mashi karin bayani akan abinda ya gani.yusuf yayi dariya yace,"wannan aikin daddy neh,don haka sai ka bari idan mukaje gida sai kaji karin bayani daga bakinsa." Dan tsaki safwan yayi yace,"oh kada dai ace har yanzu ma suna nufin ban girma ba?toh idan har ban mance ba ya yusuf inaga yanzu I have 29 yrs,don haka na lura daddy rigima kawai yakeso muyi." Dariya Yusuf din yayi ya kama hannunshi suka shiga motar dake tsakiya, su kuma shiga sukayi cikin sauran motocin da suka rage. Bayyi mmkn ganin ba gida suka nufa ba,wani katafaren hall ne daya bari mahaifinshi yana ginawa,domin idan ka shiga cikinshi sai kayi zaton wata tafkekiyar cinema ce saboda yanda aka tsara cikinta sannan kuma tana da wadataccen fadi da tsawo. Jama ar daya gani aciki su sukafi bashi mamaki,kamar dai wadanda akayiwa gaggami,domin wurin fal yake da jama a sai hidimar su kawai sukeyi,wasu kuma sai ciye ciye sukeyi da tare da shaye shayen lemunan da servants suke ta aikin shigowa dasu. Kai tsaye inda daddy dinsu yake xaune tare da ummin su,can yusuf ya nufa dashi,su ma ganin shi duk sai suka mike suka nufosu cikin farin ciki, bama ya umminshi da rabon data ganshi shekara biyu kenan sai dai ta waya. Rungume juna sukayi yana dariya yayi mata rada acikin kunnenta yace,"yah ummina kin gano mani sodangita?" Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:27 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba Saleh Daudawa 25 Murmushi tayi irin mai sautin nan tace,"later on we will discourse my son."dagoshi tayi cikin fara a taci gaba da cewa,"ina farin cikin ganinka dana,sannan ina tayaka murnar cikar burinka dana mahaifinka." Yake kawai yayi mata saboda shi yanzu duk ba wadannan ke gabanshi ba. Matsowa daddyn shi yayi shima yayi hugging dinshi yana murmushi tare da tayashi murnar dawowa. Anyi bayanai sosai akan dalilin taron,sannan kuma akayi bayanin ci gaban da safwan ya samu tare da nasarorin da yayi akan business din daya kai shi dubai da china. Bayan duk wadannan bayanan sai aka bukaci safwan din daya fito ya karin bayani akan irin rayuwar da yayi da kuma ci gaban daya samu. Dukkan jama ar da suka taru sukayi tsit suna sauraronshi tare da sha awar dama nasu dan ne,saboda safwan ba karamin rawar gani yayi ba,kuma dagashi har dad dinshi sun samu ci gaba da daukaka sosai. Daga karshen bayaninshi yayiwa kowa godiyya tsre da fatan koma wa gidajensu cikin koshin lafiya. Gaba daya Hall din ya dauki tafi tare da dayi mashi jinjina shi kuma sai datiya yake,aduk lokacin da zai daga idanuwanshi ya kalli sashen ummi dinshi yana lura da wata tsaleliyar budurwa da tayi mashi kuri da idanuwana,kuma duk sadda zai hada ido da ita sai yaga ta sakar mashi wani kyakykyawan murmushi. A lokacin da yake kojarin saukowa daga stage din sai mahaifinshi yayi sauri ya hau ya tarbeshi tare da tsayar dashi ta hanyar yi mashi magana ta macro phone yace,"kamin ka safka ina son in gabatarwa jama a da wani abin alkhairi." Jin haka yasa safwan ya koma ya tsaya yana facing din jama a yana ta sakar masu wannan murmushin nashi. Daddyn shine yaci gaba da cewa,"tunda duk mun hadu anan inason inyiwa dana engagement in hadashi da diyar abokina inyi masu aure nan da wata biyu." Nan da nan fara ar dake fuskar safwan ta kama gabanta,kuma da sauri ya juya ya kalli daddy dinshi cikin mamakin mi zaisa yayi masa haka ba tare daya shawarce shi ba. Umminshi yaga ta hawo stage din tana murmushi ta nufo inda yake,tana zuwa ts dafa kafadarshi tare dayi mashi magana da idanuwa,saboda ta fahimci irin firgitar da yayi,kuma tasan halinshi domin kai tsaye idan har bai son yarinyar bazaiji kunyar kowa ba zai fadi abinda ke cikin ransa. Kiran sunan yarinyar yayi,watau Humaira Abdallah,takowa tayi cikin isa da rausaya dai kace yar fashion. Mahaifiyyarta ce biye abayanta har suka hau bisa stage din,shi kuma safwan yabisu da idanuwanshi da suka fara canzawa. A cikin zuciyarshi yake kiyasta ta,watau baby din babu laifi,domin tana da kyanta dai dai gwargwado,amma a inda gizo ke tashi sakar shine,duk kallon da yake mata baiji wani abu na yana sonta ko kaunar ta ba,saboda shi yanzu duk wannan sakarcin da yayi ada yanzu ya barshi kuma saboda rashin sodangi ne,domin tunda ya rabu da sodangi ya daina jin dadin duk wata diya mace arayuwarshi,don haka shi yasa ma ya hakura da matan tunda zuciyarshi kullum ba wadda take hararo mashi sai sodanginshi. Dan tsaki yaja tare da kauda fuskarshi gefe daya ya furzar da iskar dake cikin bakinshi,kara fahimtarshi umminshi tayi ta kara dora hannunta akan kafadarshi tana tausarshi. A haka ta samu aka gama taron suka sauka daga stage din,koda aka bukaci safwan yaba Humaira dan lokaci su gaisa sai yaki yace shi agajiye yake,amma idan ya huta zai je har gidansu ya ganta. Umminshi ce tayi irin dariyar tasu ta manya ta kalli mummyn Humaira tace," hakan ma yayi,kuma idan ya hutan zan tuna mashi yazo din". Mummyn Humaira tayi murmushi tare da jawo Humaira gefenta ta rungume tace,"babu komai Hajiya salma, ai kun gama mana komai sai godiyya." Sallama da junansu sukayi duk suka nufi motocinsu da zasu mayar dasu gida. Tunda safwan ya hangi motar da umminshi ta shiga sai shima kai tsaye ya nufi motar. Kawai sai gani yayi wadan nan dakaran kattin duk sun zagayeshi,daga ido yayi ya kallesu yagansu bakake wuluk ga kuma suit din jikinsu duk bakake. Daure fuskarshi yayi tare da maka masu harara yace,"miye haka?maza ku matsa daga gabana kamin inyi maganinku,kuma idan takamarku wai sanya ku akayi,toh ni din nan da kuke gani zan iya zama silar rabuwa da aikinku." Jin abinda yace yasa duk sukayi sauri suka sunkuyar da kansu kasa tare da cewa,"sorry sa!!!" Wucesu yayi yana harararsu ya bufi motar ummi din,ita kuma tunda ta hangeshi da sabbin body guards dinshi tasa driver ta ya tsaya don taga yanda zasu kare. Kanshi tsaye yasa hannu ya bude motar ya shiga kusa da umminsa ya zauna sannan ya rufe,shi kuma driver yaja motar sauran motocin da zadubi bayanta suka take masu baya harda body guards din safwan. Kallon umminshi yayi rai bace yace,"wai don Allah ummi duk miye haka?kawai daga dirowata kunsa wasu babbaku sai bi na suke,sannan kuma baku nemi shawarata ba kuka hadani da wata sakaran yarinya." Murmushi tayi tace,"safwan gaskiya sai dai kayi hakuri,saboda zancen aurenku da Humaira ba abu bane da za ace amfasa,domin kamar alkawari ne daddy dinka zai cika wanda ya daukarwa marigayi Alhaji Abdallah tun yana araye yau shekara biyu kenan." Zaro idanuwan shi yayi yana kallonta tare da maimaitawa,"Alkawari?? As how?kuma idan su can sunyi alkawari ai badani akayi shi ba." Dan numfasawa yayi sannan yaci gaba da cewa,"ummina kinsan everything about sodangi,toh don mi baki fadawa daddy ba?" Kallonshi kawai take cikin sigar tausayi tace,"ni bansan komai akan wannan sodangin ba,just you call me,kace in tura matazu,awata rugar fulani a mazoji,kuma duk abinda kace haka nasa aka je ayi maka bincike,kuma babu wanda aka samu daga family dinta,domin cewa akayi sun bi fulanin yawo,kuma ba asan inda suka sauka ba." Afirgice safwan yake kallonta,kuma nan da nan zuciyarshi ta kare sai hawaye shar suka zubo mashi,runtse idanuwanshi yayi yace,"No ummi ki daina fada mani,domin wallahi yanda nakejina idan har babu sodangi rayuwata ta zama useless." Tausayinsa ya kara kamata ta jawoshi ta dora kanshi abisa cinyarta tana rarrashinshi tace,"haba safwan,kaifa Namiji neh,ko ka mance neh?saboda tun kana yaro ban sanka da karaya ba,kuma baka da sarewa akan abinda ka sanya agaba." Da sauri ya kama hannunta da take shafar sumar kanshi yace,"ummina akan lamarin sodangi tuni na sare,domin kusan adaddafe na samu na kammala abinda ya kaini,saboda tsananin yanda tunanin ta ya matsa mani,kin kuwa dole neh in yi kuka tunda wata alamace ta watakila na rasa kenan." Hawayen neh yaci gaba da firta daga idanuwanshi,ita kuma umminshi sai ta kara rudewa tare da mamakin al amarin,saboda tasan wannan abin da danta yakeyi tasan jarabawace,domin tuni tasan irin yanda safwan yake karya zuciyoyin yan mata tun yana karaminshi. Yar ajiyar zuciya tayi tace,"toh shikenan,yanzu dai abinda nakeso da kai ka kwantar da hankalinka,kuma insha Allahu zan tayaka bincike duk da nasan kai ma ba zama zakayi ba,kuma idan har sodangi rabonka ce toh kwatsam wata rana Allah zai hadaku,sai dai kuma idan ka sameta da aure fah?" Karajin da yayine yasa shi kanshi driver sai da yaja burki da karfin gaske saboda tsoratar da yayi. Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:27 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh Daudawa 26 I dedicated this love story to my Hausa Novel Group & my fans,thanks and love you all😘😘 Kuma adalilin jan burkin da yayi ba tare da sa wata alama ba ga na bayanshi yasa suma duk sai da suka taka burkin tasu motar ba tare da sun shirya ba. Safwan ya zabura ya Mike zaune daga kwaciyar da yayi bisa cinyar umminsa yacigaba dayi mata wani irin kallo,saboda ayanda yakeji ayau wannan furucin daya fito daga bakinta da wani can yayi shi lallai yau dataga hukuncin da zaiyi mashi. Runtse idanuwanshi yayi tare da daga hannunshi daya yana cewa,"please ummina,don Allah idan har kina son in rayu agabanki kada ki sake maimaita wannan maganar agabana." Kada kanta tayi cikin nuna dana sanin maganar data fada mashi tace," is ok my son,sodangi takace kai kadai,kuma zan tayaka addu ar Allah yasa ka ganta cikin kankanen lokaci." Hakan data fada yasa ya danji sanyi sanyi,don haka ahankali ya sulala ya mayar da kansa bisa cinyarta ya kwanta tare da rufe idanuwanshi,idan ka ganshi alokacin sai kayi tsammanin karamin yaro neh,saboda har wani dan takurewa yayi acinyarta. Ahankali taci gaba da shafar sumarshi cikin kulawa da jin tausayinshi har suka iso gidah. πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ Tafe suke cikin sauri,sodangi tanayi tana duba agogon hannunta ta dubi kawarta surayya tace,"Allah yasa dai mu samu mota da wuri saboda gani nake kamar mun taushe hannu." Dan karamin galan din dake hannunta ta sake duba taci gaba da cewa,"ni wallahi duk ji nake wannan galan din da molasa ta hadoni dashi kamar in yarda saboda ji naje duk ya kara takurani." Surayya tayi dariya tace,"wannan kuma neh baki isa ba,tunda bake taba ba,afnan tace ki kai mawa,idan kuma bazaki dauka ba ni ki bani in rike mata." Murmushi sodangi tayi ta kalli surayya tace,"yi hakuri kawata,kai na abisa wuya." Suna isowa bakin titi Allah ya taimakesu sai ga wata mota ktsta matsakaiciyyar,kuma suna daga mata hannu ta tsaya saboda akwai space domin sun ajiye wasu abisa hanya. Basu bata lokaci ba surayya ce agaba ta fara shiga,kuma ta kofar gaba inda duk mazan motar suke azaune. Surayya na samu ta tsallaka sai sodangi tabi bayanta,aikuwa wurin kokarin tsallakawa dan galan din madarar shanun dake hannunta ya kufce mata ya fada abisa cinyar wani hadadden matashi wanda baimasan abinda akeyi ba saboda idanuwanshi arufe suke,kuma ga head phone makale akunnenshi. Faduwar dan galan din marfinshi ya bude,nan da nan madarar shanu ta fara zuba abisa cinyarshi. Cikin salati sodangi tayi maza ta kama galan din,kuma duk cikin lokacin tasa hannu tana kakkabe mashi inda ta bata mashi. Zabura yayi ya bude idanuwanshi tare da zare headphones din dake jikin kunnenshi yana kallonta,still bata fasa kakkabe mashi madarar ba saboda kusan arude take gashi mai mota ya fara tafiya bata zauna a sit dinta ba,kuma tana gudun kada ya jefar da ita saboda hanyar bata da kyau sosai. Sameer yasa hannunshi ya buge hannunta yace,"ke baiwar Allah ya isa haka nan,saboda naga kina neman ki wuce gona da iri." Sodangi bata fahimci abinda yake nufi ba,ta kara mayar da hannunta wurin tana cewa,"don Allah kayi hakuri saboda bada gangan na zuba maka." Rike hannunta yayi cikin bacin rai yace,"are you mad?kuma idan bakiyi sannun ba sai nayi kararki because for sexual harassment." Kwalo manyan idanuwanta tayi,😳saboda sai alokacin ta fahimci inda ya nufa da kalamansa,kallonshi tayi up and down tace,"what!!sannan ta kyalkyace da dariyar rainin wayau taci gaba da cewa,look at you malam,miye ke gareka da har kake tunanin kai kara?toh bazan hana ka ba,amma kafin ka tafi kai karar ka sani,kai din nan baka daga cikin samari da zan kallah bare har tunanin wani abu yazo mani,kuma idan kai baka kaini ba toh ni zan kai ka."tana kai aya wurinta ta nufa taje ta zauna,shi kuma ysyi mugun murmushi yace," ke yarinya πŸ‘‰nasan baki san ni kowanene ba shiyasa,amma kibi ahankali,domin idan bakinki yaci gaba da fadar abinda rankil keso ni kuma zan baki mamaki." Sodangi ta zaburo zata sake lafta mashi wata bakar maganar surayya tayi maza ta rufe mata baki tace,"yi hakuri malam don Allah,kuskure neh aka samu." Girgiza kansa yayi ransa kuma abace ya sake nuna ta da dan yatsa amma kuma bai ce komai ba ya koma sit din shi ya zauna yana ta bata rai. Sodangi da kyar ta samu ta kufce bakinta daga hannun surayya ta tsikara mashi bakin ta cikin rashin kunya tace,"bance ka fasa abinda kayi niyya ba,domin alokacin ne zanfi gane kaiko wanene koma dan wanene."wani dogon tsaki taja ta murguda bakin ta ta kauda kanta gefe daya tana yan harare harare,saboda gaba daya maza haushi suke bata,kuma kallo iri daya take masu na mayaudara amma banda ardonta. Tafiya motarsu kawai take,amma sameer idan ranshi yayi dubu ya gama baci akan abinda sodangi ta fada mashi,domin idan banda lalura ma da ya za ai ta ganshi a motar gwamnati. Maida headphones dinshi yayi akunne ,sannan ya zaro bakin tabaronshi ya sakawa idanuwanshi,saboda gani yake kamar duk yan cikin motar shi suke kallo a matsayin mace ta wulakantashi. Surayya ce ta zunguro sodangi cikin rada tace mata,"wallahi ki kiyaye wajen haye ma wadanda sukafiki karfi, da ya mareki fah?" Sodangi ta zaro idanuwan ta tace,wai lallai da kinga abinda zanyi,saboda wallahi da sai na rama ko kuma insa wani acikin motar nan ya rama mani." Surayya tayi dariya,saboda batun yau ba tasan kawarta da irin wannan karfin halin. Kano line suka isa motarsu tayi parking,nan danan fasinja sukayi ta fita,masu hawan keke napep suna hawa wasu kuma suna gangarawa da kafafuwansu kasa. Sodangi da surayya suna daga cikin masu hawan keke napep,don haka sai suka tsaya abakin titin suna jiran wadda zata daukesu. Wata hadaddiyar motace tazo ta gitta ta gabansu,tayi parking daga gefensu kadan. Sameer ne ya tako daga inda yake tsaye yazo ya gitta ta gaban su sodangi ko kallon inda suke ma baiyi ba,motarnan ya nufa ya bude gidan baya ya shige,shi kuma driver yaja sukayi gaba. Surayyace ta dafa sodangi tare da nuna mata, kingani koh,kawai muna zaman lafiya kije ki jawo mana fitina,saboda yau wannan guy din idan da ya iya rigima irin taki nasan da yau sai buzun mu." Sodangi ta kalleta ta tabe baki ta kauda kanta gefe daya tace,"ko jirgi yazo daukarshi ni bazai firgitani ba. Adai dai lokacin wata keke napep tazo gabansu ta tsaya,ai kuwa sodangi tayi maza ta shige abinta tace mashi sallari bakin ruwa,surayya itama sauri tayi ta fada cikin motar tana cewa,"kawata tafiya zakiyi ki barni don na fada maki gaskiya?" Sodangi tayi dan murmushi tace,"ni na isa in tafi in barki,don ko na tafi dole neh in dawo saboda kada ummah ta tuhumeni." πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ Surayya itace babbar kawar da sodangi tayi tun komawarta secondry har suka gama suna tare,kuma shakuwar da sukayi yasa har iyayensu suna zumunci da junansu. Surayya yar asalin garin kano ce a unguwar sallari,kuma iyayenta suma ba masu k,udi bane sai dai kuma suna tare da rufin asirin Allah. Ganin irin kwarewar da sodangi tayi wurin iya dinki ko wanne irineh yasa surayya takeyi Mata sha awar samun babban wuri inda kwarewarta zata bayyana,domin mafi yawan style din da takeyi wa jama a bawai sai taga samful ba,ita da kanta take zanawa sai dai ka zabe wanda kake so. Yayar surayya ,watau fatima itace lamarin sodangi yake burgeta ,don haka sai ta amshi result dinta na secondary da testimonial din women center da tayi takai mata wani babban company na designer's and fashion. Sodangi kuwa tayi sa a company suka nemeta interview shi yasa ta taho gidansu surayya ta kwana don tayi sammako tunda safe don kada ta makara. Love you sis 😘 08033481518 [4/8, 10:28 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 27 I dedicated this love story to my Hausa Novel group & my fans,thanks and love you all😘😘 Monday 7:00 am tayiwa sodangi abakin company,suna da yawa wadanda za ayiwa interview din,don haka itama layi tabi ta shiga cikinsu ta zauna. Tana nan ahankali suna shiga suna fitowa har layi yazo kanta,mikewa tayi tare dayin addu a acikin bakinta ta shiga office din. Office din wani dan madaidaicin daki ne dauke da dogon table ma dan tsawo,sai kusan mutane biyarne zagaye dashi,kowanne daga cikinsu da tulin takardu agabansu sai faman yan rubuce rubuce suke. Shigowar sodangi yasa duk suka dakata suka zuba mata idanuwa,ita kuma sai faman sunkuyar da kai takeyi cikin ladabi ta gaishesu da kalmar turanci. Dagowar da zatayi ta kallesu sai kawai tayi arba dashi, duk da fuskarshi rufe take da bakin tabarau sai da ta ganeshi,don haka sai tsoro ya kamata saboda kawai sai jikinta ya bata idan har kuwa ya ganeta da kyar zata samu yin nasara awurin interview din nan. Fara dan nokewa tayi tare da jan gyalenta tana kokarin rufe gefen fuskarta wai don kada ya ganeta. Dan murmushi yayi acan kasan zuciyarshi saboda ya fahimci abinda takeyi,baccin kuwa tunda ta shigo ya ganeta,saboda yace bazai taba mance abinda tayi mashi ba. Zare glass din dake idonshi yayi don ya samu hada ido da ita sosai,domin zaiso dalilin haka ma kada ta samu damar lashe jarabawarta. aikuwa hakan da yayi ya fara tasiri acikin zuciyarta,saboda ta tsorata sosai,don haka sai ta fara rawar haba maganarta ta fara rawa. Shugaban kamfanin gaba daya dake zaune tsakiyarsu ya fara fahimtar canzawar da sodangi ta farayi,don haka yayi gyaran murya yace mata,"ki natsu sosai,domin ki samu ki cimma gurinki,idan kuma kikasa wasa ke zaki rasa." Acikin zuciyar sameer yace,"ai nafison ta rasa tunda bata da kunya",don haka sai ya kara tamke fuska ya jeho mata tambaya da cewa,"duk sauran masu neman aiki suna zuwa da sample din da sukayi don aga irin kwarewarsu,amma ke sai na lura da hannu biyu kikazo." Sodangi tayi sauri ta bude file din dake hannunta ta fiddo wasu zaninnika da tayi jiya da daddare ta mika ma wanda ke kusa da ita.bayan ya gani ya mikawa na kusa dashi har dai takardun suka iso hannun mahaifin sameer saboda shine shugabansu,kallo daya da yayi masu ya yaba kyan zanen,kuma cikin mamaki ya kalleta yace,"kin tabbata ke kikayi wadannan zanen?" Sodangi ta dan rusuna kanta cikin girmamawa tace,"nice yallabai,kuma ma ina da wasu design din banda wadannan."sameer ya mika hannu da sauri ya amshi takardun a hannun mahaifinshi ya duba,saboda jin ta fara cika baki don kada tayi tsammanin wai kyau sukayi sai yace,"Abba ai atakardu ba yanda za ai mu iya gane kyan dinki,sai idan har mun gansu practically sannan zamu iya yarda da ita tayi su,saboda zata iya samun wani can daban ya zana mata,kaga kenan mu anyaudaremu kenan." Tabbas maganar da sameer yayi ta ratsa zuciyar mahaifinshi, don haka sai ya mayar da kallonshi kan sodangi yace,"yama sunanki?"sodangi data fara dakewa da kallon da sameer yake mata,sannan kuma kai tsaye ta fahimci abinda yake nufi sai tace,"sunana sarat Abubakar yallabai." Mahaifin safwan yace,"da kyau sarat,yanzu wacce shaidace ke gareki wadda zatasa mu yarda dake,saboda idan har da gaske ke kikayi zanen nan to lallai dolene muyi tafiyar nan tare dake,domin na hangi ci gaba aciki." Sameer najin abinda Abbanshi yace sai ya mike tsaye yace,"Abba ba yanda za ai muyi tafiya da ita har sai mun gwada kwarewarta tukunna." Alhaji yunus ya kalli danshi ya jinjina kai yace,"hakan is good,kuma ai kaine sectary sai ka tafi da ita ka gwadata sosai yanda ya kamata." Wani farin ciki neh ya kama sameer ya kalli sodangi yayi mata irin kallon nan na zaki gane kuranki,gaba yayi ita kuma tabi bayanshi duk jikinta asanyaye. Wani daki ya nufa da ita yasa key ya bude dakin,suna shiga sodangi ta kalli cikin dakin ta fahimci dakin daga ganinshi kasan an dade ba a bude shi ba saboda kurar data gani ko ina daddan kare. Juyowa yayi ya kalleta yace,"to Hajiya sarah,sai ashiga a kama aiki,kuma ki tabbatar kin yi mani sample kusan kala goma kuma daban daban koda kuwa zaki kwana anan wurin." Sadda ya fadi kala goma sai da taji gabanta ya fadi,amma data tuna goggo laura da afnan duk suna can suna jiranta,sai kawai taji wani gwarin gwiwa ya karu azuciyarta ta kalli sameer tayi murmushi tace,"koda kala ishirin kace inyi sam banda sarewa." Sameer ya kalleta cikin mamaki watau wannan yarinyar bakin ta bazai mutu ba koh? Kada kanshi kawai yayi,saboda shidai yasan ai ya hadata da babban aiki,don haka babu abibda yace mata yayi tafiyarshi ya barta anan. Sodangi ta shiga cikin dakin tayi tsaye tana kallonshi don taga ta inda zata fara,cire gyalenta tayi ta linke ta saka ajikkarta sannan tafarwa dakin. Nan da nan cikin dan lokaci kankani ta gyara dakin fes duk ta goge inda ya kamata ta share shi ta sake jera duk kan kekunan dake cikin dakin. Agogon hannunta ta duba taga har sha biyu saura,gabanta ne ya fadi taga toh yaushe zatayi ta gama aikin nan da aka bata,amma sai tayi wata shawara da zuciyarta ta zaro wayarta ta kira surayya. Bugun farko surayya ta dauka cikin zalki tace,"yaya sodangi? Har kin gama?Ina fata dai an samu nasara." Sodangi ta dan numfasa tace,"ina tukunna dai,sai ta kwashe duk abinda ya faru ta fadawa surayya,ai kuwa nan da nan surayya ta tsure saboda tafi sodangi tsoro, don haka sai tace,"don Allah sodangi ki tafi da komai ahankali saboda nasan halinki sarai,kuma komai zakiyi ki rinka tuna muhimmancin dalilin neman aikinki,please kada ki sakeki biyewa zuciyarki." Sodangi tayi kasa da murya kamar bata son wani yaji abinda zata fada tace,"nasani surayya,kuma insha Allahu zan bi komai ahankali kodan sanin tashin hankalin da nake ciki game da goggo laura,saboda ita kawai yanzu abinda take jira shine,dana samu aiki itama albashi zan rinkayi mata duk wata,kinga kuwa idan ban samu aikin ba akwai rigima kenan." Surayya ta jinjina kanta kamar tana a gaban sodangi tace,"duk nasan haka sodangi, don haka sai ki bi ahankali,kuma ma bari in hadaki da Anty fatima kiji idan har akwai matsala a company." Sodangi tace,"ok toh na gode surayya."yan mintuna kadan sodangi taji wayarta tana ringing,don haka sai ta dauka. Anty fatima bata saurara ba ta hau yiwa sodangi bayani saboda surayya ta fada mata komai tace,"kada ki damu sodangi,wannan company baida wata matsala,don haka ko kwana ya kamaki ki kwana saboda dama akwai masu aiki 24hours,don haka kedai kokarin da zakiyi shine kiyi dinkuna wadanda kikasan zasu gigitasu matuka,kuma kada ki damu da abinda sameer yake nuna maki,domin shima duk yanayi maki haka neh saboda abinda kikayi mashi,amma bayyanannun halayenshi masu kyau ne." Sodangi taji wani sanyi acikin ranta tace,"na gode kwarai Anty Fatima,kuma zanyi bakin kokarina." Anty fatima tayi murmushi tace,ok toh sodangi, munayi maki fatan alkhairi best of luck."daga nan ta kashe wayar. Numfasawa sodangi tayi ta kalli roll roll na material da shaddoji da wasu yadiddikan ma bata san sunansu ba saboda bata taba ganinsu ba. Sai da tayi sallar azahar sannan ta fara aikin,yi kawai take baji ba gani,kamin la asar sameer ya shiga wurin da sodangi take aiki,shi kanshi yanda yaga ta gyara dakin sai da ya burgeshi.ledar dake hannunshi ya ajiye gefe daya ya kalli sodangi yaga aikin yankanta kawai takeyi kuma yanda kasan batasan mutum ya shigo inda take ba. Sameer yq gyara tsayuwarshi ya zubawa sodangi ido,da yake akwai bakin glass a idonshi shi yasa bata fahimci abinda yakeyi ba. Shi kuwa gogan ahaka ya samu damar kallonta yanda yakeso,kuma awannan lokacin ne ya fahimci abubuwan dakesa sodangi takeyiwa maza wula,saboda yanda Allah yayi mata fasali da tsari ga kyan jiki,uwa uba kuma ga kyau dan asali. Tsaayuwar da yayi neh ba tare daya ce komai ba yasa ta fara tsaguwa ta dago kai ta kalleshi,ai kuwa taga ita kadai yake kallo don haka itama sai ta kalli kanta,ganinta tayi daga ita sai matsatstsin riga da siket na atamfa,kjma ga dinkin yayi fitting dinta sosai,kusan da gudu ta isa wurin hand bag dinta ta jawo katon gyalenta ta rufe jikinta dashi. Murmushi sameer ya taka har kusa da ita sannan ya tsaya tare kuma da tamke fuska yace,"ke baki iya magana bane idan har kinga mutane?kuma inason in fada maki ni bake nake kallo ba da zaki zabura ki rufe jikin ki, domin duk asurar jikinki babu abinda ya burgeni sai style din atamfar jikinki,don haka idan har kin tashi ki dinka da irin style din." Kada kai sodangi tayi alamar taji abinda yace,"sannan ta juya kan aikinta. Safwan yasa hannu ya amshi almakashin da take yankan dinkin dashi ya ajiye gefe daya sannan ya jawo ledar daya shigo da ita ya tura mata agabanta yace,"ki daina duk abinda kikeyi kici abinci,saboda mu wannan company masu adalci ne don bamu mayar da ma aikatanmu kamar injina." Don gudun kada ya bata mata lokaci,kuma dama gashi tun kusan dazu cikinta ya fara kiran ciroma saboda ko break fast batayi ba,don haka bude ledar tayi taga snacks ne da soyayyen naman kaji,sai gwangwanin lemu guda biyu. Maida hankali tayi sosai ta cinye snacks din nan tare da gwangwanin lemu daya,sai dan naman kajin taci kadan saboda idanuwan sameer ne suka hanata sakewa,amma da babu abinda zaisa bata cinyeshi duka ba. Murmushi kawai yayi ya juya ya sake fita,sodangi kuma ta mayar da hankalinta taci gaba da dinkunanta. Kayan da sodangi ta dinka kayane na gani na fada dana maza dana mata,don idan ka kalli kayan sai kayi tsammanin kayan mazan yan kanti ne saboda irin su suit suit din nan ta dinka kala kala,su kuma cikin na matan akwai wadanda idan ka gansu sai kayi tunanin daga sena gal aka jawo su. Dinkuna dai sunyi yanda ake so kuma ko abirnin hassada abin sai haka,kusan wajen karfe hudu na asuba ta kammalasu gaba daya. Mikewa tayi ta tana dafe da bayanta tare da kugunta sai mammatsasu take,sannan kuma idanuwanta cike suke da barci don har wani donko idanuwanta sukeyi,amma ganin alfijir ya fito,kuma muddun ta kwanta toh bazata samu sallar asuba bah,don haka sai taki kwanciya har saida tayi sallar asuba sannan ta raba jikin wata kujera da table agabanta ta zauna tare da dora kanta bisa. Duka batayi cikakkin minti biyu ba wani barci mai nauyi yayi awon gaba da ita. Gari na wayewa,ma aikatan da suka kwana suka fara haramar barin company, su kuma wadanda zasu amshi aiki sai shigowa sukeyi abin gwanin ban sha a wa. Sameer ne tafe cikin motarshi yanayi yana duba agogon hannunshi saboda bai son takwas tayi mashi sai acikin office dinshi,sodangi ya tuno sai kawai ya samu kanshi dayin murmushi yadan daki gefen sitiyarinshi yace,"nasan duk abinta bazata iyayin set din kaya har kala goma ba cikin wunin jiya,kai koda kwana tayi ma bazata iyaba,saboda yanda nasan mata da less ness." Murmushi ya sakeyi yaci gaba da cewa,"ta wannan hanyar ma kadai ya isa in kamata tayi feiling."tundaga nesa kamin ya iso bakin kamfanin ya fara horn,toh idan da sabo ma maigadi ya isa ya saba don haka ya tashi da sauri ya bude mashi,shi kuma yana isowa shigewa kawai yayi tare dayin parking wurin dayake ajiye motarshi. Office dinshi ya nufa,sai da ya shigar da wasu takardu sannan ya sake duba agogonshi yaga 45minute pass nine,numfasawa yayi tare dayin guntun murmushi yace,"duk delay dinta ya isa ace tazo yanzu,idan kuma tayi dubara tazo da wuri har tayi set daya. Aje duk abinda yakeyi yayi ya nufi dakin da yaba sodangi jiya,dan kasa kunnenshi yayi wai ko yaji motsin keken dinki,amma sai yaji shiru. Fusata yayi,watau ma bata zo ba,lallai yau zataga karshen rashin mutunchi kenan. Tura kofar yayi ya shiga with compedance,sai kuma yayi turus,saboda kayan dayagani duk anyi hanging dinsu,wasu kuma an zurawa irin dan butum butmin roba. Bude baki yayi cikin mamaki ya nufesu yana daddagasu,acikin zuciyarshi ya fada gaskiya kayan nan sunyi kyau,πŸ€”anya kuwa! zan iya cewa yaushe rabon da mu samu kwararre tela haka,sai daisu kware ahannun mu. Hango sodangi yayi can kwace abinta bisa dogon table din da take yankan dinki duk ta mimmike,sai dan gyalenta data rufe kafafuwanta dashi har zuwa wucewar kugu. Zuba mata idanuwa yayi,saboda yanda take Barcin daganinta hankalinta akwance yake tamkar tana kwance acikin dakinta. Kujera ya dauko ya zauna gaf da ita yaci gaba da kallonta saboda yanajin dadin yanayin da yakeji acikin jikinshi idan yana kallonta.fa I za ce ta fado mashi acikin zuciya,shin wai mi yasa bayajin abinda yakeji yanzu idan har suna tare da fa iza? Motsawa sodangi tayi,kuma duk alokaci daya ta bude idanuwanta,shi kuwa sameer rasa yanda zaiyi yayi,gashi ta riga ta ganshi a gabanta zaune bare ya tadhi,don haka sai ya wayence ya kauda idonshi daga kallonta,kuma ya mayar da glass din ya rufe idanuwanshi dashi. Mikewa tayi zaune tare da jan gyalenta ta ida rufe jikinta dashi tayi kasa da idanuwanta tace,"morning sir." "Morning"yace,ya mike tsaye yana dan kame kamen taba kayan data dinka yaci gaba da cewa,"nan kika kwana neh?"Ta sakko daga kan table din tace,"yes sir."jin jina kanshi yayi yace," mi yasa baki sanar da kamfani ba cewar anan zaki kwana?" Sodangi ta dago kai ta kalleshi taga har zuwa lokacin shafar kayan data dinka yake tace,"sorry sir." Wani murmushi keta yayi ,acikin zuciyarshi yace,"miye na saurin bada hakuri kuma,kya bari kiga yanda zamu kare." Juyowa yayi afusace yace,"you failed sarat !you failed !! Domin ni duk gaba dayan kayan nan babu wadda dinkinshi yayi kyau,kila da kin dinka irin na jikinki toh da dadan sauki sauki,amma kikakijin shawarata." Gaba daya sodangi tayi kasa da gwiwoyinta cikin tashin hankali ta kalleshi tace,"don Allah ka taimaka mani sameer,ka kara dubawa ka gani sosai,domin ni kaina dukkan wannan style din ban taba yinsu ko ganinsu wani waje ba." Love you sis😘 08033481518 [4/8, 10:28 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 28 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all😘😘 Sameer yayi wata irin dariya ya kalleta sosai yace,"that's why you failed, saboda ya za ayi ace baka taba ganin abu ba ka zauna ka kirkiroshi da kanka." Sodangi tayi kasa da idanuwanta,amma acikin zuciyarta sai kwakkwafar kanta kawai take don kada yace tayi mashi rashin kunya,amma idan banda abinshi sau nawa ake kirkirar abu kuma har yafi na asali kyau. Dago idanuwanta tayi da sukayi kalar tausai ta kara marairaice mashi wai don dai yaji tausayinta,ganin haka yasa ya kauda kansa saboda haka nan yakeyin abinda yakeyi mata amma badon yaso ba,shi kawai burinshi yaga ya bata mata rai don itama taji abinda yaji sadda ta farfada mashi bakaken maganganu iya son ranta. Tsallake ta yayi ya fita daga dakin domin bayason tasanya zuciyarshi ta karaya,don kada ta gane mashi. Share wasu hawaye tayi da suka gangaro mata ta mike tsaye ta nufi jikkarta ta dauka tare da ratayata akafadarta,sannan ta gyara rufa gyalenta sosai ta nufi hanyar fita,har ta kai bakin kofa ta juyo ta sake kallon kayan dake rataye taji kamar ta fashe da kuka saboda tuna wahalar data sha kamin tayi su,amma gashi wahalar ta tashi abanza. Runtse idanuwanta tayi kawai ta juya ta kama tafiya,hanyar fita companing ta nufa kanta a sadde saboda batason mutane suga tashin hankalin dake kwance a fuskarta. Sunanta taji an kira "sarat Abubakar mazoji" dago kanta tayi da sauri ta kalli sashen dataji an kirata,Alhaji yunus ne ta gani tare da wasu mutane suna biye dashi. Zubewa tayi kasa da sauri ta gaishesu,cikin fara arshi ya amsa mata yace,"yaya har kin gama gwajin da akeyi maki?"sodangi tayi kasa da idanuwanta sai hawaye shar suka zubo. Alhaji yunus yadan firgita da ganin sodangi tana kuka yace,"akwai matsala kenan?"dan jim yayi jikin shi asanyaye yaci gaba da cewa,"kiyi shiru hakanan,amma ki biyoni office dina inga idan akwai wani taimakon da zan iyayi maki." Wani sanyi sodangi taji acikin zuciyarta ta mike da sauri tabi bayansu. Sai da Alhaji yunus ya kammala da kowa a office dinshi sannan yaba sodangi dama ta shiga office din.tana shiga tayi maza ta tsugunna. Alhaji yunus yana fara arshi da komai yasa ta taso tazo kujerar dake kusa dashi ta zauna,tambayar farko daya fara yi mata shine,"ina fata kinyi breakfast?" Sodangi ta girgiza kanta ahankali tace,"a a banyi ba,saboda ai anan na kwana don in samu yin abubuwan da sameer ya umurceni,kuma yallabai duk nayi,amma dayazo sai cewa yayi duk babu wanda yayi mashi." Murmushi Alhaji yunus yayi irin nasu na manya yace,"kuma ke kin tabbata kayan sunyi kyau?" Kasa tayi da kanta tace,"ni dai anawa ganin tabbas sunyi sai dai ban sani ba ko wadanda nayi ba tsarin da kuke so bane,amma idan har haka neh ina rokon arziki daga gareka kasa in sanya kayan na mata dana dinka aga yanda sukayi mani,shi kuma sameer kasa yasa na mazan shima aga yanda zasuyi mashi." Alhaji yunus ya kada kanshi alamar ya gamsu da bayanin sodangi,kuma shi jikinshi yana bashi sodangi idan dai har ita ta zana wadannan takardun,toh lallai zatayi aiki mai kyau,don haka sai yaba sectary dinshi umurnin tasa akawo wa sodangi break don ta farayi don kada yunwa ta illata ta. Abinci mai rai da lafiya aka kawowa sodangi tare da lemuna da ruwan sanyi,dan ruwan tea kadai ta hada da plantain da kwai taci. Tana gamawa sameer yana shigo, kallo daya yayi Mata ya kauda kanshi ya nufi mahaifinshi yadan rusuna yace,"Abba gani."wuri ya nuna mashi yace,"ka zauna mana." Sameer ya samu wuri ya zauna,amma cikin dubara yake satar kallon sodangi,saboda ranshi ya bashi akwai wani abu. Sauran manyan ma aikatan wurin yaga suna ta shigowa daya bayan daya hsr suka hallara. Mikewa Alhaji yunus yayi yace,"duk ina son mu ziyarci dakin gwajin kaya(show room) Gaban sameer ne ya fadi saboda yasan idan har kayan da sodangi ta dinka za a gwada toh babu abinda zai hana bataci ba. Haka nan dai sameer yabi umurnin mahaifinshi suka nufi show room din,suna shiga kayan da sodangi ta dinka ya fara tozali dasu,kuma abinda ya kara tsoratashi shine yanda yaga gaba daya ma aikatan wurin sun nufi kayan arude suna ta washe baki da yaba masu. Gyaran murya yayi yace,"toh dama abinda yasa kenan nace muzo nan don kowa ya ganewa idanuwanshi kokarin da wannan yarinyar tayi,kuma dukkan alamomin da na gani atare daku yasa na fahimci kayan sunyi kyau,amma kuma duk da haka ina son in gane wani abu da ba kowa ne zai hango shi ba. Sameer ya kallah yaci gaba da cewa ina son ka dauki kayayyakin nan na maza ka shiga daga ciki kayi ta gwado mana su. Zaro idanuwa yayi 😳 ya kalli sodangi da fuskar nan tata sai fara a takeyi kamar wata gonar auduga,ganin sun hada ido sai ta tsokane shi ta daga mashi girarta daya tana dariya. Bay da yadda zaiyi, dolenshi ne yabi umurnin mahaifinshi, gaba yayi leburorin wajen suna biye dashi da kayan har ya shiga wurin da aka nuna mashi. Babu abinda yafi ba ma aikatan wurin mamaki sai yanda sameer yake sanya kayan nan sai ka rantse kamar dama can nashine,shi kanshi sameer din idan ya fito har wata fakkama yake, saboda yanda kayan suke fitting dinshi,sai alokacin ya kara tabbatar da kwarewar sodangi sosai. Bayan ya gama itama sodangi ta shiga ta Fara fitowa cikin nata kayan,kusan duk gaba daya dakin rudewa sukayi da sowa don wasu harda fito saboda jin dadi. Takaici ne kuma ya kama sameer saboda yanda yaga takadaran wajen har wani canza salo sukeyi wajen kallon sodangi,don haka tunda tayo shiga ta farko ta fito ta biyu sameer yabi bayanta yace mata ya isa haka nan. Kallonshi tayi cikin rashin sanin abinda yake nufi domin duk tunaninta kuma wata hanyarce zai sake don ganin bukatarta bata samu ba. Kaucewa tayi daga gabanshi ta dsuki wasu kayan ta shige toilet ta sanyo su ta fito.kallonta yayi tundaga sama har kasa yaga wannan shigar kayan sun dan kama jikinta bama kamar wadancan shigar guda biyu ba, sai kawai ya hango idan ta fita kila wani daga cikinsu sai ya nemi rungumeta tunda ba kunya ta ishe su ba,don haka da sauri ya fisgota kusa dashi suka rinka kallon juna cikin ido yace,"ke baki da hankali neh? Da kinsan irin bala in da zaki jawowa kanki idan kikayi wannan fitar da bazaki fara ba,saboda ba mace irinki takeyin show dress ba,domin dukkan jikinki babu inda bai motsawa,ita kuwa macen da takeyin show dress yar siririyace mara kwari wadda babu wani abu dayake motsawa ajikinta sai dai ita ta motsa jikinta da karfi,amma kuma idan kinji zaki iya daukar abinda zai biyo baya ga fili ga mai doki nan." Gaba daya jikin sodangi ne ya hau rawa duk sai taji ta rude saboda gaskiya ce sameer ya fada mata don haka da gudu ta koma toilet ta cire kayan ta mayar da nata,wannan karan gyalenta har abisa kai ta dorashi. Sameer ya kalleta yayi dan murmushi ya fada acikin ranshi "ashe matsoraciyya ce," abayyane kuma sai ce mata yayi "muje." Tare da dan daure fuskarshi watau babu wasa. Sukuku tabi shi har suka koma show room din,ganinta cikin kayanta sai suka fara guna gunin ya haka,saboda idan har idanuwansu basuyi karya ba kayan sun kai wajen kala biyar. Safwan ya kalli dukkan ma aikatan wajen sannan kuma ya kalli Abban shi yace,"Abba bamu bukatar ganin sauran kayan tunda dai abinda ake bukata an same shi." Alhaji yunus yayi murmushi, saboda halin sameer babu wanda bai sani ba na sanin ya kamata,kuma shima kanshi don sodangi ta bukaci ta gwada kayan,saboda ita dai bukatarta aga kwarewarta kuma bukatar ta ta samu aiki shi yasa. Jin jina kai yayi yace,"Tabbas sarat Abubakar ta cancanci yabo na musamman,kuma daga yau ta zama ta zama ma aikaciyyarmu saboda ban taba samun sabon ma aikaci mai kwarewa irin tata ba,don haka sameer ka kaita office dinka daga yau ta zama mataimakiyyarka." Turus sameer yayi yana kallon Abbanshi,su kuma ma aikata,shugaba yana gama bayani ya mike ya bar wajen su ma kowa ya kama gabanshi. Sodangi kuwa rabawa tayi daga gefe tana jiranshi tunda ance a office dinshi zatayi aiki. Sameer yayi murmushi, saboda gaba daya Abbanshi yayi surprises dinshi, domin bai taba tsammanin sarah zata zauna kusa dashi ba sai kawai ya kalleta yayi mata alama da idanuwanshi data biyoshi. Ganin tsarin office din da yanda aka shirya shi sai da ya burge sodangi,kuma sai ta fara jin kanta kamar a mafarki take. Afarkon office din kananan ma aikata ne,don haka suna ganinsu suka tashi tsaye suna gaishesu.bayan sun amsa sameer yayi masu bayanin matsayin sodangi awurinsu.matan dake cikinsu suka fara danyi msta guguni wai jibarta ko kwalliya bata iya ba,amma basu bari akaji su ba,su irin yan rainin wayannan. wucesu sukayi suka nufi wasu dakuna guda biyu da suke kallon junansu.dan juyowa yayi ya kalleta yace,"ga office dinki nan,amma ki dan jirani." Office dinshi ya bude ya shiga mai kallon wanda ya nunawa sodangi,yan mintoci kadan ya dauka ya fito da keys din office din ya mikawa sodangi,sannan yace mata,"ba ayau zaki fara aiki ba ki bari sai gobe saboda zai zama duk yau baki samu hutun kanki ba,don haka you can go now." Godiyya sodangi tayi mashi,sannan ta juya,kuma acikin ranta taji dadi sosai,saboda banda gajiyar da take tare da ita har wanka ma takeso tayi,domin ta farajin jikinta ya canza mata. Love you sis 😘 08033481518 [4/8, 10:28 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 29 I dedicated this love story to my Hausa Novels & my fans,thanks and love you all😘😘 (Masoyana ina sonku) ABUJA Safwan ne kwance sai birgina yake,ko ban fada maku ba zaku gane afuskarshi akwai wani abu da yake damunshi wanda har ya fara cin jikinshi,watau dan ramewa da yayi kadan. Hajiya ummu salma itama abin ya fara damunta,saboda koda yaushe ta tsareshi don ya fada mata damuwarshi sai dai kawai yace mata sodangi. Tagumi tayi ta shiga tunani,wai wacece wannan sodangin?Anya akwai ma sodangin nan kuwa?ni dai Allah yasa ba aljana ya gamu da ita ba can wajen yan leke lekenshi na mata. Mikewa tayi ta fito daga sashenta ta nufi sashen safwan data lura yau kusan kwana biyu kenan bai fita ko ina ba. Dan kwan kwansa kofar shiga sashenshi tayi,amma taji shiru,haka karo na biyu ma babu wani yunkuri da akayi na bude matan. Don haka sai tayi tunanin shiga kawai,tana taba kofar sai taga ta bude,ahankali ta sanya kanta cikin dan kayataccen falon da yasha kayan alatu,domin idan ka ganshi kai sai kayi tsammanin falon na mace neh. Wucewa tayi kai tsaye har zuwa kofar dakinshi, sunanshi ta kira ahankali.shi kuma jin muryar ummunshi kusa dashi yasa ya takarkara ya mike saboda jikinshi gaba daya yayi mashi nauyi ga rashin karfi. Budewa kofar yayi tare da danyin murmushi yace,"ummi! Kinji ni shiru hala banzo na duba ki ba?" Hajiya ummu salma ta kalleshi cikin sigar jin tausayinsa tace,"wai miye ya sameka safwan,don ni fa duk yan kwanakin nan duk na gaza gane kanka,don haka ayau babu inda zan matsa sai ka fada mani cikakkar damuwarka." Bi tayi ta gefenshi ta shiga cikin dakin,shi kuma yayi tsaye yana kallonta,saboda abinda bai taba gani ba neh,koma minene sai dai shi ya sameta cikin gida. Kallonshi tayi tana murmushi tace,"kana mamaki neh?hmm ka daina mamaki saboda yau magana nakeso muyi sosai ni da kai." Safwan shima murmushin yake ya rufe kofar sannan ya koma kusa da ita ya zauna yana cewa,"ummi matsalata dai kin santa, kuma insha Allahu nima komai ya kusa zuwa karshe saboda na tura wadannan body guards din da daddy ya bani suyo mani bincike akanta,sannan kuma abokina tahir ya sha alwashin nemo mani sodangi ta." Hajiya ummu salma ta zuba mashi ido kawai tana saurarenshi har ya gama,sannan tace,"toh kuma tunda har kasan haka minene na damuwar?" Numfasawa safwan yayi ya lumshe idanuwanshi ya budesu da kyar yace,"ina fargaba ummi,kuma idan har abinda nake tunani ya faru,toh ni ban san yanda zanyi ba,don dole ne rayuwata taci gaba da zama cikin garari." Mahaifiyyarshi ta mika hannu ta dafa kafadarshi tace,ka daina damuwa my son,saboda ganinka acikin wannan halin nima zai iya sakani acikin wani yanayi,kuma duk na gane damuwarka akan sodangi,amma kuma miye mahadinka da ita? Kuma a ina kuka hadu?" Wannan tambayar ba karamin dadinta yaji ba,saboda yana son tunanin rayuwar da sukayi da sodangi,to kuma bare ka tambayeshi labarinta. Gyarawa yayi yadan kwanta kusa da mahaifiyyarshi ita kuma ta dora hannunta abisa gadon bayanshi tana dan shafawa ahankali tana sauraren labarin da yake bata,bai boye mata komai ba,filla filla har aurenta da yayi,da kuma irin rayuwar da yayi bayan rabuwarsu daya tafi abroad. Hankalin Hajiya ummu salma yayi matukar tashi sosai dajin wai safwan har aure yayi ba tare da sun sani ba,kuma ya saki matar. Hawaye ta fara zubarwa saboda tashin hankali tace,"safwan dole neh Allah ya kama ka tunda ka dauki alhakin yarinyar mutane da sauran yan mata,kuma yanzu babu abinda ya rage maka sai addu a,saboda ba lallai bane ka samu sodangi free ba tare da aure ba sai dai wani iko na Allah,kuma sannan idan har sodangi tasan kanta da wuya ta kara amince maka akaro na biyu." Zabura yayi ya mike zaune yana kallonta cikin nadama yace,"don Allah ummi kada kiyi mani baki,domin sodangi tana sona fiye da yanda baki zato,kuma wallahi nima ina sonta,tunda saboda ita yanzu bani iya kallon wata diya mace da sunan so ko sha awa sai ita kadai." Hj ummu salma ta kalleshi sosai taga iyakar gakiyarshi yake fada mata,don haka sai tace,"toh shikenan, nima kullum addu a nake maka,kuma bazan fasa ba,amma abinda nakeso shine ka tashi ka fita kaci gaba da hidimarka don kada ciwon zuciya ya kama mani kai." Murmushi kawai yayi ya kauda kanshi,saboda ya fahimci umminshi bata fahimci pain din da yakeji ba,shi yasa kawai ya kyaleta tayi ta fadanta har ta gama ta tafi. Wayarshi ce tayi ringing,kuma tun dazu yake jiran shigowar kiran saboda aikin da ya bazawa yaranshi. Babban yaronshi ya gani a screen din wayar da yake video call ne. Rusunawa yayi yace,"yallabai barka da ranar yau."hannu kawai ya daga mashi ya koma ya kwanta. Babban yaron ya fara bayaninshi cewar,"yallabai mun gano inda iyayen sodangi suke acan wata rugar fulani dake daura." Dagowa yayi da sauri ya kalleshi arude yace,"umhm ina jinka,ci gaba kawai." Yawwa,amma duk iyakar binciken mu bata tare dasu ance ita tana bichi,awata rugar,don haka sai muka bar daura muka nufo bichi din,toh anan din muka samu labarin tayi wata makaranta ta secondry da kuma women center,amma yanzu bata acikin bichi ana tunanin ta kona kano neman aiki." Zaune ya tashi dirshanyana kallonshi harda kara tallabe wayar ,domin bai son abinda zai kawo mashi wata matsala awannan lokacin. Don haka yana gama mashi bayanin ya tari numfashinshi yace,"mi ake koyawa a women center din?" Babban yaro yayi mashi bayanin sana o in mata kala kala,shi kuma sai ya shiga nazari,can yace,"sodangita bazata koyon abinci ba saboda ta iya."πŸ€”tunani yaci gaba dayi ya tuna da saka,itama dan tsaki yayi yace,kai I dont think that." Babban yaro dake tsaye yana kallonshi yayi dariya yace,"ogah ni dai abinda naga yafi shine,kawai muyi bincike ta ko ina,idan ba a sameta ba nan asameta acan." Safwan yayi dariyar jin dadi yace,"ok haka za ayi babban yaro, don haka nima gani nan mu hadu a kano kawai." love you sis😘 08033481518 [4/9, 2:19 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 30 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 KANO Zuwan sodangi a company su sameer komai ya canza masu saboda ci gaban da suke samu,kuma duk adalilinta domin duk abinda ta sanya agabanta sai tayi bakin kokarin ta. Ganin haka yasa sameer ya sakankance akan lamarinta,domin ko da aiki aka fara lokacin tashi yayi idan har bata ida ba bata zuwa ko ina har sai ta gama,shi yasa baban sameer yake matukar sonta. Sameer kuwa ada mutum ne mara walwala da rashin fara a,domin idan da sabo har yarinyar da zai aura ta riga ta saba,kuma koda taji labarin an kai wa sameer assistant da irin yanda ma aikatan wurin suke kodata duk bata damu ba saboda tasan halin mutumin nata. Akwai wata rana bayan fa iza ta gama aikinta da yake itama duk cikin company take sai tayi tunanin kaiwa sameer ziyara office dinshi. Shi kuwa sameer yana zaune a office dinshi duk abubuwa sun fara damunshi saboda koda yaushe sai tunanin sodangi ya rinka bijiro mashi acikin zuciya,amma duk yanda ya samu ya tureshi sai kawai yaji ya dawo. Dan tsaki yayi ya mike ya fito daga office din ya zagaya ta bayan office din don ya shaki fresh air,yana cikin tafiya a hankali sai ya hango sodangi adan gabanshi kadan itama zaunen take ta fiddo photon afnan tana kallo tare dayi mata magana,"afnan I miss you 4 2dys,dan sumbatar photon tayi tayi mata murmushi sannan taci gaba da cewa insha Allah this week din bichi zanyi shi." Maganar dataji abayanta neh yasa ta juyo sai taga sameer da wani karamin ma aikacinsu. Mikewa tayi tsaye tana murmushi tana kallonshi har ya iso tace,"yallabai kai ma fitowar kayi kasha iskar?" Wannan murmushin da tayi mashi harda shi yake tsaya mashi acikin rai,don haka shima sai ya samu kanshi dayin murmushin yace,"zowa nayi in tayaki zaman shan iskar." Koma wa sukayi suka zauna atare,sannan duk sukayi shiru kamar masuyin tunanin wani abu,can dai ya wayance saboda rasa abinda zaice yayi yace,"dazu dana taho na hangeki kina duba pix,ko na masoyin neh? Shiyasa ma kika boyeshi don kada in gani?" Maganar tashi dariya ta bata,saboda dai ita yanzu bata da wani lokaci na soyayya,abin rufin asiri kawai takeso wanda zata kula da yarta da kuma laura mai kulawa da ita. Gudun kada yayi zaton itama halinta daya da sauran yan mata sai ta zaro pix din ta mika mashi,amsa yayi har yana saurin kai idanuwanshi sai yaga yar yarinya da shekarunta basu wuce hudu ba. Dagowa yayi ya kalleta yace,"naga fine girl,ta wacece?sodangi tayi shiru kamar baza tace komai ba sai can tace,"relative di tace kuma ta jini." Kallon pix din ya sakeyi yace,"babing tana da kyau, kuma daga ganinta tana da wayau sosai." Sodangi taji dadin yabon yar ta da yayi tace,"na gode da yabonta da kayi."daga nan kusan firar duk sai ta koma akan afnan tana fada mashi irin dabi in yarinyar da dubararta da kuma wayan ta. Shi kuwa abin sai dariya yake bashi yana sake tambayarta tana bashi labari. A haka fa iza tazo ta samesu sun shagala sai dariya sukeyi,dominshi har tsayawa yake yana zubawa sodangi idanuwanshi sannan ga smile kasa kasa yanayi mata. Fa iza tsayawa tayi daga nesa dasu ta gaza isowa saboda bakin ciki,sannan kuma,tsananin mmk ne ya cika mata ciki wai sameer ne ke fira harda Kyakyata dariya abinda bai taba yi mata ba. Kutawa tayi ta juya ta koma office dinta cike da takaici da bakin cikin abinda ta gani,kuma sai idan tayi magana yace ba haka ba,amma with a time wata rana zata kamashi a hannu. Wannan week end din sodangi ce har daura wajen iyayenta,bayan sun gaisa neh take ta ba sadah labarin irin ci gaban da take ta samu awurin aikinta,domin har tana ganin zata dauki su goggo laura ta mayar dasu cikin garin kano don ta samu saukin zaryar da takeyi. Duk labarin da sukeyi duk akunnen ardo,don haka sai kira sunanta yace,"sodangi ina labarin aure neh?domin na lura dake kullum baki da wani labari sai ta ya zaki samu kudin da zaki rike su laura ba mu ba." Dan numfasawa yayi yace,"toh gaskiya daga yau na gaji dajin haka,maza ki samo miji inyi maki aure,kuma tun yaushe nake fada maki su maza ba irinsu daya ba,domin idan Allah ya taimakeki sai ki samu wanda akullum zaiji tamkar ya hadiyeki don so,don haka daga yau ki fara shirin neman miji don inyi maki aure. Sodangi tayi kicin kicin da ranta,saboda ba ayau bane ardo ya farayi mata wannan maganar,don shi yasa idan tatafi take dadewa bata zo ta gansu ba,amma da yake su iyaye dolene a lallaba su don haka sai ta bashi hakuri tace,"kayi hakuri ardo,ni nasan dole zanyi aure idan lokacin shi yazo."ardo ya kada kanshi yace,"haka nakeso inji sodangi, saboda ga sadah nan shi kuma na rasa inda ya nufa sai tsabagen karatu kawai yakeyi." Ahankali sodangi ta lallabasu ta samu tayi bankwana dasu tace,"bari inzo in koma don kada dare yayi mani ahanya.Nasiha suka karayi mata sosai mai ratsa zuciya sannan tayi masu bankwana ta fito sadah yana biye da ita. Tafiya suke ahankali sadah ya kira sunanta yace,"sodangi,ko har yanzu kina tunanin safwan neh shi yasa kikaki yin aure?"shiru tayi don kamar bazata amsa mashi tambayarba,kuma shima sadah shiru yayi saboda koda bata bashi amsar ba sam bayyi niyyar sake tambayar taba. Numfasawa tayi ta kalleshi tace,ni kuwa yaya sadah wasu lokutta mutane suna bani mamaki,wai miyasa kowa zai bude bakinshi sai yace wai ko safwan kaza akaina,wai mi yasa?" Murmushi sadah yayi yace,mu din nan da kikaji magana kadan sai ace ko safwan kike jira,saboda mun san yanda kike tsananin sonshi."da sauri ta tari numfashinsa tace,"ada ba,amma ni yanzu sai ince maka nafi shekara biyu banyi tunaninshi ba,kuma wai mutumin daya tafi bai sake nema na ba toh don mi ni zan zauna zaman jiranshi?" Sadah yayi murmushi yace,"toh shikenan, sai dai idan,har baki son ayi ta fadin haka to ki fiddo miji kiyi aure."kuma ni akwai wani abu da yakedan damuna,sai inyi ta tunaninshi ni kadai,amma yau dai tundamun hadu sai muyi maganar." Sodangi tamayarda hankalinta wajenshi sosai shi kuma yaci gaba da cewa,"akwai wata jaririya gidansu goggo laura, so alokacin sai nake tunanin ko rainonta takeyi,amma kuma yanzu sai naga yarinyar har yanzu tana nan tare da ku,shin wacece?" Love you sis 😘 08033481518 [4/9, 2:19 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 31 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 Sodangi tadan firgita da tambayar da sadah yayi mata,kuma shi kanshi sai da ya ganeta,don haka sai ya tsayar da ita saboda ya fahimci saurin data kara,kuma zasu iya samun mota ta shige ta barshi ba tare data bashi amsa ba. Sodangi tayi tsaye tana yi mashi mazurai tace,"ni kaina ban san inda goggo laura ta sameta ba,amma dai tunanina diyar makwabta ce." Sadah ya zuba mata ido yanayi mata kallon rashin gaskiya yace,"ni ban yarda da ke ba,kuma jikina yana bani wannan yarinyar tana da alaka dake,saboda duk sadda ta kalleni sai in rinka ganin kamannunki kina karama,don haka kada ki boye mani komai ina kika samu diya kuma waye babanta?" Hawaye sodangi ta farayi ta hada hannuwanta wuri daya zata rokeshi,sai kawai ya ture hannunta cikin tashin hankali yace,"kada kice mani haihuwa kikayi sodangi!don Allah kada ki fada mani abinda zai tayar mani da hankali." Ganin irin yanda ya rude har yana neman tara masu jama ar da suke wucewa yasa ta kama tafiya kawai ta barshi anan,tana isa bakin titi ta samu mota.tana hangen sadah daga nesa ya biyota da gudunsa amma inaaa,saboda duk gudunshi gaza cimmasu yayi. Juyawa yayi cikin kunar rai ya juya zuwa gida,kai tsaye ya nufi dakin molasa ya sameta yana zubar da hawaye yana bata labarin yanda sukayi da sodangi. Molasa ta zaburo ta jawo hannun sadah ya ida shiga cikin dakin tare da rufe mashi baki tana cewa,"kada ka tona mana asiri sadah,ardo yana nan kada kasa yaji abinda kake fada." Sadah ne hankalinshi ya kara tashi saboda ganin wai molasa tasan wannan sirrin,amma tayi shiru tsayon shekaru hudu. Cikin tsoro da firgici yake kallonta,sannan ga wasu hawaye masu zafi sai malalo mashi suke ya kalli molasa yace bakin shi yana rawa,"molasa kema kin san sodangi ta haihu?" Kada kanta tayi tana hawaye tace,"na sa ni sadah,amma ba ta zinah ta sameshi ba,tana da ubanta." Sadah cikin mamaki yace,"waye uban nata! Waye shi?"molasa ta kara zaro 😳 idanuwa tace,"ba nace ka daina daga murya ba,ko so kake komai ya ida ya mutse mana,toh safwan daka san ya auri sodangi kusan shekara biyar da suka wuce,to shine mahaifin afnan." Sadah cikin mamaki ya share hawayen dake fuskarshi yace,"safwan?toh amma molasa mi yasa kuka boye?tunda kowa yasan mijinta ne." Molasa ta karayin kasa da murya ta fadawa sadah komai tundaga farko har karshe.sadah neh yaji wasu hawayen jin tausayin sodangi ya kamashi,tuhumar molasa ya farayi,"mi yasa ban san da wannan labarin ba molasa?dana taya yar uwata renon afnan,amma yanzu kunsa diyar sodangi bata sanni ba bata san matsayina agareta ba." Mikewa yayi ya nufi dakinshi,kayan jikinshi kadai ya canza ya fito da yar jikkarshi karama ya leka dakin ardo ya dan durkusa yace,"ardo zanje bichi yanzu." Ardo ya tashi daga kishingidar da yayi yace,"wacce irin bichi kuma?ince yanzu sodangi ta tafi,idan har wani sako ke gareka kaki bata ta tafi dashi." Sadah ya sunkuyar da kansa ya fara tunanin yanda zaicewa ardo sabodacya fahimci kamar bazai barshi ba,dago kai yayi yace,"ardo! Mantuwa sodangi tayi na ID card dinta na wajen aiki,toh shine zan bi ta in kai mata don kada ta samu matsala." Ardo yayi shiru na dan wani lokaci sannan ya kalli sadah yace,"kana ganin baza kayi dare ba?" Sadah yayi murmushi yace,bazanyi dare ba,kuma idan naje gobe zan dawo da wuri insha Allahu." Numfasawa ardo yayi ya kalleshi yace,"toh shikenan, Allah ya ya maido mana kai lafiya."sadah yace,"ameen."sannan ya mike yayi ban kwana dasu yabi hanyar bichi cike da doki na zaije yaga diyarsu afnan. πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ BICHI Sodangi sam bata cikin cikakken kwanciyar hankali har ta isa bichi,saboda duk tunaninta ya koma ga sadah daya fara tuntubar afnan ko wacece,domin ayanzu yanda takejin afnan azuciyarta sam bata son abinda zai raba ta da ita. Don haka tana shiga gidan kusan da dan gudunta ta shiga tana kwalawa afnan din kira.ita kuma tana jin muryar mamanta ta kufce daga hannun laura tayo kanta tana murna harda tsallenta ta dareta. Tsananin farin ciki yasa sodangi harda hawaye ta rungumeta sosai ajikinta tana cewa,"I love you my baby."ita kuma afnan din ta mayar mata da,"I love you too mummy." Idan da sabo goggo laure ta saba ganin haka atsakanin sodangi ds afnan. Rankayawa sukayi gaba suka shiga daki,yar tsarabar ciye ciye da ta sawowa afnan ta baza mata agabanta,ita kuma goggo laura ta amshi su fizza da bugger da aka sawo mata ta koma gefe sai zalama takeyi. Wayar Sodangi ce ta fara ringing ta jawo hand bag dinta ta fiddo wayar,sunan sameer ne ta ga ya bayyana a screen din wayar,don haka da dauri tayi picking tare dayin sallama. Dariya yayi yace,"gani nan kofar gidanku."cikin mamaki tace ,"da gaske? ko dai zolayata kakeyi?" Wata dariyar ya karayi yace,"da gaske nake mana,dama cewa nayi bazan fada maki ba don inyi surprise dinki." Mikewa tayi itama tana dariyar ta nufi hanyar fita daga cikin gidan tana cewa,"gani nan fitowa yanzun nan." Ganin sameer da gaske yake abin ya kara bata mamaki ta nufeshi fuskar nan ta ta dauke da murmushin da yake kara daukar mashi hankali tace,"my boss ur well come." Daukar mashi hankali tayi sosai,domin har ta isa gabanshi bai dauke idanuwanshi daga kallonta ba. Kunya ce ta dan kama sodangi har yasa ta rufe hannuwanta da tafin hannunta tace,"yallabai duk wannan kallon fa?" Kasa yayi da idanuwanshi yana murmushi yace,"gani nayi tsakanin jiya da yau kin canza mani." Dan duba kanta tayi tare da shafa fuskarta tace," mi ya sameni da har yasa na canza cikin kwana daya."acikin ranta kuma tuna yaya sadah tayi da rigimar da yakeso ya ballo mata,aikuwa tasan ko wannan tashin hankalin kadai ma ya isa yasa ta canza. Can kasa kuma ta jiyo muryar sameer yana cewa,"kyau kika kara mani da kwarjini." Kasa tayi da idanuwanta saboda jin kunyar abinda ya fada tace,"kai yallabai kai ma harda kai?" Dan fuska yayi ya harareta yace,"ba na hanaki kirana da wannan sunan ba." Kama kunnuwanta tayi tace,"kai na abisa wuya,ayi mani afuwa my boss."duk dariya sukayi gaba dayansu sannan sodangi tace wa sameer,"bismillah sameer ka shigo mana,amma kayi hakuri da yanda zaka ga gidan na mu na talakkawa." Murmushi yayi yace,"bama sai na shiga ba sarat, akwai wani abu mai muhimmaci dayasa nazo,saboda gani nake kamar bazaki fahimci yanda abin yake ba ta waya." Wasu takardu ya fiddo daga cikin motarshi ya mika mata,amsa tayi ta fara dubawa tana binsu daki daki,da sauri ta dago cikin fara arta tace,aikuwa sameer idan har muka jone da wannan babban company mun gama morewa,kuma company mu zai kara karfi,don haka mi zai hana mu amsa gayyatarsu." Sameer yayi murmushi yace,"shiyasa nazo gareki sodangi don muyi shawara,kuma idan har mun amince da amsa gayyatarsu to sai dai kizo mu koma kano yanzu,saboda sai munyi bincike sosai akan abinda zamu fada masu a gobe idan munje ganawar da zasuyi da mu." Sodangi ta jinjina kanta tace,"ok toh bari inje inyi bankwana dasu sai inzo mu tafi." Love you sis😘 08033481518 [4/9, 2:19 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Binta garba saleh daudawa 32 I dedicated this love story to my Hausa Novels & my fans,thanks and love you all 😘😘 Hello my fans, ina baku hakuri akan jina shiru da kukayi na kwana biyu,saboda nayi fama da ciwon kai mai tsanani,amma yanzu na samu lfy,duk da haka ina barar addu arku πŸ‘πŸ‘ ( ci gaban lbr) Da sauri ta juya ta shiga cikin gidan,ba wani lokaci ta dauka ba ta fito dauke da hand bag dinta,sai wani dan karamin akwati trolley tana jaye dashi. Ganin yaya sadah a wurin sameer yasa gabanta ya fadi har jikkar hannunta tana shirin faduwa saboda fargabar bata san abinda yasa ya biyo bayanta ba. Tsaye tayi kawai tana kallonsu har suka gama maganar da suke,sannan sadah ya nufota,murmushin dataga yanayi neh yasa zuciyarta tadanji sanyi sanyi,don haka itama sai dan saki fuskarta har ya iso gabanta. Abinda ya fara ce mata ne ya sakata cikin mamaki,"where is my beautiful doter afnan?????? Lakatar hancinta yayi yaci gaba da cewa,"fushi nake dake,tunda har akwai abinda zaki iya boye mani na tsawon shekaru." Nauyin yayan nata taji ya kamata ta sunkuyar da kanta tace,"ka yafe mani yayanah,kuma tun farko bansa zaka dauki lamarin haka ba shiyasa na boye maka,amma ka gafarce niπŸ‘ Murmushi yayi ya dafa kanta yace,"shikenan ya wuce,domin bana don kisawa ranki damuwa."dan juyawa yayi ya kalli sameer yaci gaba da cewa,"wancan guy din fah?"πŸ˜ƒ Sodangi tadanyi murmushi itama tana kallonshi tace,"abokin aiki na ne,"sadah yayi sauri ya tari nunfashinta yace,"nd then?" Sodangi tace,"No yayanah babu wani abu bayan nan."sadah ya kada kanshi yana murmushi yace,"zsiy fada maki komin daren dadewa,don haka ina kara tunasar dake da cewar duk inda kike ki kula da kanki kuma ki rinka tuna ke ba yar kowa ba ce arayuwarki." Jinjina kanta tayi tare dayi mashi godiyya akan shawarar daya bata,shi kuma yaji dadin hakan sosai,don haka sai yaci gaba da cewa,"maxa ki tafi kada yayi ta jiranku,kuma Allah yasa kuci sa ar cigaban da kuke nema." Ameen sodangi tace tana murmushin nan nata,sannan ta nufi motar sameer,shi kuma sadah ya shige cikin gidan su goggo laura. Abisa hanyarsu ta zuwa kano neh sodangi taga abubuwa kala kala awurin sameer,saboda sanyata hanya da yayanta yayi dhi yasa ta ganeshi,yanzu abu daya kawai take jira shine ranar da sameer zai furta mata Kalmar so,kuma ta ajiyewa ranta duk ranar dayace yana sonta ita kuma zata bashi goyon baya ko don saboda ardo daya farayi mata maganar aure. Yau moday tunda wuri sodangi ta fito cikin irin shigarnan ta manyan yara,watau tayi kwalliya irin wadda bata tabayi ba domin awurin aikinsu aka bata umurnin yin haka ita da sameer, saboda sune zasu wakilci company dinsu wajen gayyatar da akayi masu domin ci gaban kasuwancinsu. 7:00 am a office tayi mata,shi kuma sameer ya iso 7:30.ganin office din sodangi abude bayyi mamaki ba,saboda yasan halinta ba tun yau ba,murmushi yayi ya fasa shiga nashi office yayi mata knocking,cikin hanzari ta amsa mashi. Bude kofar yayi tare da tura kanshi ciki,cak ya tsaya yana kallonta,saboda irin yanda yaga ta tsaru tayi bala in kyau kamar wata sinderela. Shi kanshi bay san yanda akayi ba sai kawai yaga ya nufeta,tahowar da yakeyi neh yasa ta tsaya da abinda takeyi ta zuba mashi ido har ya iso gabanta ya tsaya tare da kiran sunanta,"Sarah kinyi matukar kyau,kin burgeni fiye da tunanina." Hannunsa ya mika zai shafi kumatunta cikin wani yanayi,ita kuma da sauri taja baya tana murmushi." Kunya ce ta kama sameer,amma sai ya share yace,"sorry sarah." Juyawa kawai yayi ya fita ya nufi nashi office din zuciyarshi cike da tunanin yanda yaga sodangi ayau, wuri ya samu ya zauna tare da dafe kanshi ya tsunduma cikin tunanin sauyin rayuwa da yakeji ya samu adalilin sodangi,domin duk halin daya shiga ko kuma yana tuna wasu abubuwa na rayuwarshi,amma sodangi na shigowa cikin tunanin zaiji komai ya wuce mashi, sai kawai murmushi da zakaga yanayi. Safwan:- Shi kadai ne awajen mahaifinshi da mahaifiyyarshi, kuma suna nuna madhi tsananin so da kulawa,kuma bai taba neman abu ya rasa daga garesu ba, Mahaifiyyashi zainab tana da wata da wata kawarta da ta mayar da ita tamkar yar uwarta,domin duk rayuwarta babu abinda take boyewa Hjy maryam saboda tayi tsananin yarda da ita. Shi kanshi sameer yasan tsakanin mummy dinshi da Hjy maryam,saboda wata rana har gidanta yake kwana ko yaje weekend. Sameer har ya kai ss2 a wata makarantar kudi data shahara agarin kano. Wata rana ya dawo school ya sami mummy dinshi tana jiranshi ya rakata gidan Hjy maryam saboda akwai wani business da suka fara sai Hjy maryam ta bukaci datazo suyi lissafi tare dayin wata shawara. Sameer yayi maza yaci abincin shi saboda doki gashi kuma mummy din tace shi zaiyi driving dinsu tunda ya iya ba sai sun tafi da driver ba. Tundaga hotoro yayi driving dinsu har dawakin dakata unguwar da Hjy maryam take. Ganinsu tare tadan bata rai tace,"kai kawata, miye na taho mana da wannan."tadan ja mai kunne tana wata irin dariya." Hjy Zainab bata kawowa ranta komai ba saboda tasan yanda take wasa dashi.don haka murmushi kawai tayi tace,wllh driver da zai kawoni na rasa shi yasa nace danki ya kawoni." Can cikin daki suka shiga suna ta tattaunawa,amma sameer bazai iya cewa ga abinda suke cewa ba saboda karar volume din tv data cika falon,kuma Hjy maryam da kanta ta kara madhi volume din kuma ta tafi da remote din. Mahaifiyyarshi yaga ta fito ranta abace ta kama hannushi suka fita daga cikin gidan ba tare data ce mashi yayi bankwana da kawar tata ba. Mota kawai suka shiga tace,"sameer na fasa biyawa kasuwan nan muje gida kawai. Sameer yadan marairaice mata yace,"amma mummy you promise me zaki bani kudi saboda akwai wasu abubuwa da nakeso da zankaiwa English club din mu." Hjy zainab tadan runtse idanuwanta da kyar ta bude baki tace mashi,"kayi hakuri my son idan muka koma gida sai driver ya kawoka kasuwar,saboda yanzu I'm not feeling better." Numfasawa yayi yace,"ok tom,kinga ma sai Abba ya kara mani kudin sai in sawo kayan decoration din enough." Faduwar da yaji tayi ne abisa sit din motar da karfi yasa yayi saurin juyowa ya kalleta tare da kiran sunanta. Ganin wata farin miyau mai kumfa yana fita daga bakinta yasa ya kara rudewa yayi maza yayi parking abakin hanya tare da wuntsilawa ta cikin motar ya kamata yana kiran sunanta," mummy miya sameki?baki da lafiya neh?" Shi dai kokarin da yayi tayi wai ta amsa mashi,wannan shine kuskure na biyu da yayi,saboda ahannunshi mummy dinshi ta galabaita har idanuwanta suka fata juyewa. Kuricciya da rashin cikekken hankali yasa sameer ya gaza tunanin kai Mahaifiyyarshi asibiti. A wahalce sameer ya bude kofar motar ya fito duk ya hada zufa yayi sharkaf ya fara bin mutanen dake wucewa abakin titi yana rokonsu suzo su duba mashi mummy dinshi, duk wanda ya leka yaga abinda takeyi sai yayi baya. Kuka sosai sameer yakeyi har yana gaza,kuma kwata kwata saboda rudewar da yayi yaji bai iya tuka motar da kanshi kuma ga kananan shekaru. Wani mutum ne yazo wuce wa yaga yanda sameer keta aikin gafzar kuka,dafa kafadarshi yayi yace,"kai yaro miya sameka kake kuka haka?" Nuna mashi motar yayi yana sharar hawaye,mutumin bayyi kasa a gwiwa ba ya leka sai kawai yaga Hjy zainab duk idanuwa sun kakkafe ga dafara ta ciko mata baki. Salati yayi yace,"ya akayi,kuma garin yaya?"sama sama yayi mashi bayani,amutumin nan bai tsaya wata Wata ba ya fada cikin motar ya umarci sameer daya shiga. Asibiti mafi kusa ya nufa ya shiga asukwane,nan da nan attendance suka rugo da zureren gadon su suka dauki Hjy zainab sukayi ciki Love you sis 😘 08033481518 [4/9, 2:19 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 33 Nan da nan attendance suka rugo da zungureren gadonsu suka dauki Hjy zainab da tuni ta sandare kamar bata da rai,ciki sukayi da ita. Likitoci ne sun kai hudu tsaye abisa kanta suke ta bakin kokarin ceto ranta. Alhaji yunus arude ya shigo asibitin don har hadawa yake da gudu gudu saboda rudanin da yake aciki. Cin karo yayi da sameer tsugunne abakin kofar dakin da aka shiga da Hjy zainab sai zubar da hawaye yake Ganin Abbanshi yasa ya mike ya nufeshi ya rungume,shima Alhaji yunus hawayen yake ya kama sameer tsam ya rungume ajikinshi yana rarrashinshi don karfin hali. Docters din dake kan Hjy Zainab Sunyi iya bakin kokarin su amma Allah bai nufa ba saboda dai duk wanda kwananshi suka kare babu tsimi babu dubara dole sai ya amsa kiran mahalicci,toh abinda ya faru da Hjy zainab kenan,sai dai kuma likitocin sunyi wa Alhaji yunus bayanin cewar matarshi guba taci mai karfi shiyasa har har hanjin cikinta suka tsintsinke. Hankalin Alhaji yunus yayi matukar tashi, saboda tunanin daya dameshi shin waye yayi poisoning din matarshi kuma akan wane dalili?????? Shiru yayi da maganar har sai da ta kwana goma da rasuwa,zuwa lokacin yawan dafifin jama ar dake gidan duk sun watse,agidan ya zama daga mahaifiyyar Hjy zainab watau kakar sameer sai sameer din. Alhaji yunus ya kira sameer da duk yabi ya zafge saboda rama ya fara tambayarshi bayan kunje gidan maryam ko kun biya wani waje? Sameer ya girgiza kanshi yace,"Abba babu inda mukaje,kuma abisa hanya ne abin ya faru." Nan da nan zuciyar Alhaji yunus ta fara zargin Hjy maryam da kashe mashi mata,kuma biri yayi kama da mutum saboda tunda Hjy zainab ta rasu baiga idon Hjy Maryam ba, kuma duk yanda suke. Mikewa yayi ya nufi telephone din dake ajiye acikin falonshi land line ya kira number Hjy maryam. Duk da ta gane number bai sa taji tsoron komai ba ta daga tare da make murya wai ita adole tayi zaki tace,"Hello." "Kizo gidana yanzu ina jiranki."abinda Alhaji yunus ya fada kenan ya datse kiran. Hjy maryam tadanyi shiru tana nazarin yanayin wayar da sukayi,bata ranta tayi tace,"baka isa ba Alhaji yunus,dole ne Kabi abinda boka ya baka umurni,amma bari inje gidan nasa inji,muddun babu wata biyan bukata dole ne nima in canza lago. Shiyawa tayi tsaf,ta kawo turarukan da bokanta ya bata tare da wani matsiyacin kwalli duk ta shafa sannan ta nufi gidan. Sallama kawai tayi Alhaji yunus yaji duk ya kidime yayo waje yana washe mata baki,itama tana ganin haka tayi yar siririyar ajiyar zuciya ta farin ciki. Kai tsaye falon shi ya nufa da ita,sai wata karairaya take ta kara jan hankalin shi. Suna zama ta fara bashi hakurin rashin ganinta da sukayi da akayi rasuwa. Nuna mata yayi bata da wata matsala kuma wanda ya mutu ai ya mutu..........😳 A dai dai sadda yayi furucin sameer yana shiga falon,kuma sai yaga Hjy maryam tana ta zafga fara a,sai kawai yaji ranshi ya bace ya kallesu gaba daya yana huci. Hjy maryam ce ta kara washe mashi baki tace,"zo nan da na mu gaisa,kuma inyi maka gaisuwar mummy dinka." Sameer ya zuba mata idanuwanshi yana huci yace,"kinji kunya!wallahi kinji kunya Hjy maryam,sai yau ne kikaga damar zowa gaisuwar?naso ace mummy na ta ganki data gane ke kowa ce ce awurinta......." Saukar marin da yaji neh yasashi yayi shiru yasa hannu biyu ya dafe fuskarshi yana zubar da hawaye,saboda wannan itace rana ta farko da mahaifinshi ya fara dukanshi,domin iya sanin shi dai dai da fada bai tabayi mashi ba balle dunguri. Alhaji yunus yana zare idanuwa yace,"ashe baka da hankali,uwar taka kake fadawa magana." Sameer ya kara roshewa da kuka yace,"wallahi Abba ka cuceni,don ni wannan ba uwata ba ce,kuma har abada bazan kara kiranta da mummy ba." Warto wata flower base yayi ya gurga mata kuma sai da ta sameta a kafa,don haka yana ganin ya sameta yayi waje da gudu yaba share hawayenshi. Tundaga wannan ranar idan har sameer ya gamu da Hjy maryam sai yayi mata rashin mutunci mara misali ko ya raunata ta,kuma buba wani kuri da Abbanshi baiyi mashi ba amma yaki dainawa. Kwatsam ranar da mummy dinshi ta cika wata biyu cif akace mashi an daurawa Abbanshi aure,wannan abu ba karamin bata ran sameer yayi ba,toh sai ma da yaga matar ji yayi kamar zai mutu. Ganin Hjy maryam a matsayin matar babanshi yasa zuciyarshi ta fara kokwanto akanta,sannan kuma ya fara zarginta akan mutuwar mahaifiyyarshi. Bude wuta yayi acikin gidan,don har ya nemi ya hanaya zaman auren saboda kullum cikin yi mata banna yake da tada mata hankali. Kwata kwata Hjy maryam ta rasa yanda zatayi da sameer,saboda bokanta ya fada mata cewa,shima sameer babu abinda zai kamashi na sihiri saboda addu o in tsari da mahaifiyyar tashi ta koya mashi,kuma gashi bai wasa da sallarshi,amma da ta samu yanda takeso da tuni anyi babu shi. Shawara tayi da muguwar zuciyarta taba Alhaji shawarar ya dauke sameer ya kaishi abroad ya ida karatunshi acan,haka kuwa akayi babu wani bata lokaci sameer ya bar nigeria aka kaishi Ghana. Dai dai da hutu Alhaji yunus ya hana sameer zuwa har sai da yayi masters dinshi,toh koda ya dawo bata canza zani ba,sai dai kwata kwata ya bsr gidan ya tare agidanshi da Abban ya gina mashi,kuma ganin ya girma yayi hankali yasa Abbanshi ya rage yi mashi abubuwan da yakeyi mashi ada na musgunawa,shi yasa shima sameer sai ya daina ci mata mutunci da lafta mata bakaken maganganu agaban Abba sai dai yaga daga ita sai shi,toh alokacin idan ya daba mata wata maganar sai tayi kamar tayi kuka. Har gobe irin zaman da yakeyi da ita kenan babu abinda ya canza. Kwankwasa kofarshi da akayi neh ya maido sameer daga duniyar tunanin daya lula,izinin shigowa ya bada tare da share wasu hawaye da suka zubo mashi. Sodangi tana shiga ta nufeshi tana cewa,"sameer akwai abinda yake faruwa neh?saboda appointment din da aka bamu ance kada mu wuce 8:00,amma yanzu har 8:30." Mikewa yayi da sauri cikin mamakin yanda lokaci yaja haka da tsawo ba tare da ya sani ba,"I'm very sorry sarat,ban san yanda akayi ba,muje kawai don kada mu kara bata lokaci." Sun isa wani babban company na kasuwancin kasa da kasa,dafifin jama ar da suka gani abin ya basu mamaki matuka,kuma hakan ne suka gane lallai sun makara. Wuri suka samu suka tsaya kamin jama ar wurin su dan rage yawa suga ko sun samu damar shiga,babu abinda kake gani sai security da suke ta zagayasu kamar wadanda sukayi laifi. Sodangi ta juya ta kalli sameer dataga hankalinshi akwance yake kamar babu abinda yake damunshi,kasa tayi da muryarta tace,"sameer kodai mu tafi,saboda yaushe aka gama duba wadannan har agammu?" Sameer ya kalleta yana murmushi ya bata amsa da cewa,"ke dai kice mani tsoro kikeji kawai,"Dariya tayi tace,"wllh kamar ka sani,ni idan da za biye mani da tuni mun dade da barin wurin nan." Sameer ya gyara tsayuwarshi yace,"munaciya tafiya,amma kuma sai kisan bayanin da zakiyiwa Abba,domin ni idan muka koma ko keyata ba zai gani ba." Wani security neh suka ga ya nufosu gadan gadan sai sodangi ta kara rudewa ta koma bayan sameer ta labe tana zare idanuwa ga tsabagen tsoro acikinsu. Cikin girmamawa security din ya gaishesu yace,"ku biyoni,saboda ance in shiga daku." Mamaki ne ya kamasu suka kalli juna cikin al ajabi sukace,"yallabai ai mu yanzu muka iso,tayiwu ba wajen mu aka turo ka ba. wani pix ya fiddo daga aljihunshi ya mika masu,photon sodangi ne tana dariya,kuma cikin shigar dake jikinta,watau dai photon ayau aka dsukeshi ba tare data sani ba. Matse idanuwanta tayi zatayi mashi kankanci da tuhumar miye na daukarta photo ko taci bashi neh bata biya ba?" Sameer da sauri ya riko hannunta yayi mata alama da idanuwanshi,tsit tayi tadan saurara,amma akasan zuciyar ta taso taji dalili. Sameer cikin danyin kasa da kai yace,"kayi hakuri yallabai mun bata maka lokaci." Bai tsaya cewa komai ba ya juya su kuma suka bi bayanshi har zuwa wani katon katafaren falo wanda yaji kayan alatu.agaskiya falon yayi kyau da tsari sosai. Wani dogon table aka kaisu kamar daining table aka nuna masu kujerun akace suzauna kamin oga ya iso. Kallon table din sukayi sukaga cike yake da kayan marmari da kayan sha masu sanyi na jika makoshi. Daga sodangi har sameer wani dadi ne ya kamasu duk suka kame akan kujeru suka jera da juna. Love you sis😘 08033481518 [4/9, 2:19 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 34 I dedicated this love Story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 Dama awaje kamin su shigo duk sun gaji ga rana data dan bugesu,don haka kowa jawo kalar lemun dayake so yayi ya farasha. Sodangi tayi mamakin yanda kusan lemun datakeso ne bisa table din nan,watau exotic coconut and pineapple, don haka fidda kunya tayi ta cika cup dinta ta fara sha. Safwan kuwa dake acikin wani dakin zaune ya zurawa wata yar computer ido yana kallon duk abinda du sodangi dukeyi,idan banda murmushi babu abinda yakeyi saboda jin dadin yau dai ya gano sodanginshi. Lemun datake sha ne ya dan zubo mata har ya dan sauka agefen bakinta,sameer ne yakeyi mata dariyar wai kada dai tayi masu kauyanci.itama dariyar takeyi wanda sameer da safwan shi dayake kallon su ta computer duk suka shagala suna kallonta. Ahankali safwan ya furta sai ka rantse tana jinshi yace,"ya isa haka nan sodangi,domin wannan dariyar ni kadai ya kamata kiyiwa ita." Hannu sameer ya mika Mata tare da tissue,kamin ta amsa tuni yakai hannunshi abakinta ya goge mata.ita kuma murmushi tayi mashi tare da cewa na gode. Wannan abu da safwan ya gani ba karamin dakar mashi zuciya yayi ba,don haka cikin zafin nama ya mike tsaye yana huci. Tahir ne ya shiga inda yake da sauri,yana ganinshi yace,"thank God,wallahi nasa har ka fita domin nasan ka baka da hakuri." Safwan ya kara bata rai yace,"idan dai akan sodangi ne,zanyi fiye da duk abinda kake tunani,wai Tahir who is that boy?saboda idan har bayyi sannu ba sai nasa an daure shi." Tahir yayi dariya yace,"kada ka fara abokina,saboda irin wannan takarar kowa gwada bajintar shi yakeyi har aga wanda zaiyi failing," Kara matsawa yayi kusa da safwan din ya dafa kafarshi yace,"ka cire idonka akan kowa,kullum ka rinka tunanin kai kadai ne awuri,don haka sai kaga kayi nasara." Murmushi yayi tare shafa sumar kanshi ya lumshe ido yace,"hakaneh abokina kuma na gode da tunasar dani da kayi."Tahir yayi dariya yace,"ok toh ka shirya ka fita don kada mu tsaya kallon ruwa kwado yayi mana kafa😜 Safwan yayi murmushi tare da kara gyara zaman rigarshi,duk da yasan ya hadu amma gani yake wankan nashi kamar baiyi ba,saboda sodangi ta dabance acikin zuciyarshi. Fita kawai yayi cikin irin tafiyar nan tashi mai birge matasa samari da yan mata ya nufi falon da su sodangi suke kanshi tsaye ya shiga. Dama kamin isowarshi security sun fada masu ga boss nan isowa,don haka sai su sodangi suka natsu harda wani kamewa. Shigar safwan falon wani kamshin turarenshi ya daki hancin sodangi,afirgice ta juyo domin taga maiyin wannan kamshin,saboda idan bata manta ba shekaru biyar da suka wuce ita kanta bata da turaren da safwan yake fesa mata sai shi. Gaba daya tayi mutuwar zaune,saboda kasa mikewa tsaye tayi kamar yanda taga sameer yayi,cikin girmamawa suka gaisa sannan safwan ya zauna kujerar da yake facing din ta sodangi, shima sameer din koma wa yayi ya zauna zuciyarshi cike da mamakin abinda sodangi tayi. Bakin glass ne manne da idon safwan shi yasa sodangi ta gaza ida tantancewar safwan ne ko kuwa mai kama dashi neπŸ€” Safwan yayi murmushin nan na shi ya zare glass din ya ajiye gefe daya,saboda ya fahimci irin kallon da takeyi mashi,ai kuwa gabanta ne ya fadi ras har ta nemi zarewa watau zumbur ta tashi tsaye ta kuma komawa ta zauna,saboda kwata kwata a rayuwarta bata taba kawowa tunaninta zata hadu da safwan ba acikin irin wannan lokacin. Hannu sameer yasa ya dafa kafadar sodangi,ita kuma ta juyo ta kalleshi,lumshe idanuwanshi yayi ya bude yana murmushi tare dayi mata alamar ta natsu mana don kada adalilinta su samu matsala. A lokacin da duk haka yake faruwa safwan kauda idonshi kawai yayi saboda wani abune mai radadi yaji ya ratsa mashi zuciya,don ji yayi kamar ya buge hannun sameer din dake bisa kafadar sodangin. Itama janye kagadarta tayi ta kuma nuna mashi ta gane abinda yake nufi. Sameer ya juyo ya kalli safwan cikin gimamawa yace,"yallabai gamu munzo ayi mana gwajin da akace,saboda muna so mu kasance tare daku wajen kasuwancin kasa da kasa. Murmushi safwan yayi ya zubawa sodangi idanuwashi yana cewa,"baka da matsala sameer,saboda when I heard she was leading the project, nayi matukar mamaki na rinka tunanin it was really her,sodangi's talent,isn't she? Wani murmushi yayi irin na ni na tuna wani abu ya kara tsare ta da idanuwanshi yaci gaba da cewa,"sodangi she's always been smart and ambitious." Sameer ne ya kalli sodangi da duk ta dururu ce,sai mitsilniyya take,kuma sannan kanta akasa kamar batason hada idonta da safwan,wanda shi kuma tuni ya tsareta da nashi idanuwan masu neman kashe mata jiki. Juyawa yayi ya kalli safwan din da har yanzu sodangin yake kallo yace acikin ranshi wannan guy fin ko mayen mata neh?kuma ko a ina yasan sodangin har yake fadin exactly halayenta. Ture tunanin yayi acikin zuciyarshi yayi murmushi yace,"tabbas baka fadi karya ba acikin halayenta daka lissafo,saboda Sarat mace ce mai hazaka ga duk abinda ta sanya agaban ta." Safwan ya matse kyawawan idanuwanshi yayi wani murmushi yace,"ko kasan she was both attractive and sweet tooooo.sannan kuma idan ta shiga zuciyar dan adam da wuya take fita daga cikin ta saboda quality din dake gare ta." Da sauri sodangi ta dago idanuwanta ta kalleshi,saboda gaba daya ta gama tsinkewa da al amarinshi,kuma daya san kallon da takeyi mashi da bakinshi ba zai zuge yayi ta lafto magana irin wanda zuciyarshi ta raya mashi ba. Shi kuwa sameer rudewar da yayi itace,wai kodai safwan yasan sodangi,domin wannan kodawa haka gaskiya da walaki acikin miya,don haka sai yayi kasa da murya yace,"wai yallabai ko dama kasan sarah neh?" Wata dariya yayi ya mayar da jikinshi jikin kujerar da yake zaune akanta yadan jingina da yace,"aw sodangi didn't tell you?"tasowa yayi ya zauna dai dai yaci gaba da cewa ai dani da ita.......... Sodangi tayi karaf ta tari numfashin sa tace, can wani lokaci daya shude mun taba zama friends,ai shikenan koh."ta bude mashi dara darar idanuwanta cikin daurewar fuska. Mamaki ne karara ya bayyana😳 afuskar sameer har safwan ya gano haka yace mashi,"is that strange to you?" Sameer yayi maza ya kada kanshi yace,"No not at all,sai dai kawai it's just very coincidental, saboda abinda ya kawo mu bashi naga munayi ba,yanzu dai minene matsayin company mu awajen ka?" Safwan yayi murmushi yace,"tun yaushe na amince,na amince da company ku ya zauna akarkashin company na just for soodaangissπŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜ƒ Gaba daya kunya ce ta kama sodangi ta rasa abinda ke mata dadi saboda ganin abinda safwan yayi mata agaban sameer,kawai hannu ta mika ta dauki cup din lemun dake gabanta saboda kame kamen da takeyi neh yasa cup din ya kufce mata,nan take ruwan lemun ya zube akan table din,gangarawa yayi har ya sami hannun safwan dake shimfide akan table din. Kuma sai ta rude tayi maza ta jawo tissue dake gefensu ta fara bashi hakuri,shima sameer jawo tashi tissue din yayi yana kokarin tayata don kada security dinshi su ce sunyi laifi,ya zama ga koshi ga kwanan yunwa. Da sauri safwan ya miko hannunshi ya rike duka hannayen sodangi yana cewa," is okay sodangi is okay."amma kuma ya gaza sakin hannun sai ma murza su dataji ya fara yana wani lumshe idanuwanshi saboda ido cikin idon da sukayi dashi. Sameer na ganin abinda yake faru sai kawai yaji ranshi ya baci yayi maza ya kauda kanshi tare da juya masu baya. A fusace sodangi ta fige hannunta tunda ta fara fahimtar abin nashi yana nema ya wuce gona da iri sai ta mike tsaye kuma sai taji jikinta rawa yake hakanan tasawa ranta juriya ta dake gami da kallon sameer da takejin kamar tana jin kunyarshi saboda abubuwan da suka faru agabanshi. Gyara zaman jikkarta tayi dake rataye akafadarta tacewa sameer amma ta gaza hada ido dashi,"I'm sorry,but I should get going, because I have apointment." Sameer da yake yasan halin sodangi dajin kunya sai kawai yaji wani tausayin ta ya ka mashi yace,"ki Bari mu tafi tare." Safwan ya dan harareshi yace,"ina zaku tare? Ka kiyaye,idan kuwa ka zake duk abinda nayi maka kai ka janyowa kanka." Kallon security dinshi yayi yace,"ku tsare mani shi,sannan ya mike yabi bayan sodangi. Love you sis😘 08033481518 [4/9, 2:19 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh Daudawa 35 Godiyya mara adadi zuwa ga masoyana,kuma inayi maku albishir da addu arku ta karbu,saboda na samu lafiya ingantacciya,na gode and love you all😘😘😘 Sodangi na fita ta rasa inda zata nufa,saboda lokacin da sukazo shigo dasu akayi kuma batayi tsammanin ita kadai zata dawo ba,ai da tayiwa hanya kuri don kada ta mance. Tunda ta dauki hanya ta fara tafiya safwan yake biye da ita,mamaki ne sosai yake kamashi wai ta ya sodangi ta zama yar gayu? Jibi dai dai da tafiyarta ma abin kallo ce,murmushi yayi irin na farin cikin nan ya fada afili,ada can yayi babban kuskure ayanzu kuwa bazai bari ya kara maimaita shi ba. Canza hanya yayi yana wani murmushi har ya bullo wani waje,wuri ya samu ya labe zuwa can sodangi ta iso,daka ganta ma kasan ta gaji sosai domin kafafuwanta har hada hanya sukeyi. Tana isowa safwan yayi caraf da ita ya jawota jikinshi,ita kuwa datayi mugun tsorata sai ta nemi yi mashi ihu tana yan zille zille. Rufe mata baki yayi ya dago fuskarta sosai don ta ganshi,aikuwa suna hada idanuwa taga shine sai ta fada yin ihun amma dai yan zille zille bata daina ba har sai da ta gaji don kanta sannan ta dan saurara tana kallonshi. Safwan ne yayi murmushi yace,"mi yasa kika tsaya? Zanso kici gaba,amma ina rokonki komai zaki yi mani kiyi amma kada ki bijire mani." Galla mashi harara tayi tace,"bijirewa kuma ka ajiyewa ranka kamar yanzu na fara,wai shin malam miye mahadina da kai,kuma waye kai?" Zuba mata ido yayi kawai yana kallonta wai ta manta shi,kada dai ace shi kadai neh yayi fama da ciwon zuciyar rashinta,murmushi yayi ya fada a fili ni nasan bazaki manta dani ba,amma kuma tunda kince baki gane ni ba ni bari in tunasar dake,kai tsaye bakinta ya nufa zaiyi kissing dinta. Wuf tayi ta kauce cikin tashin hankali,nan da nan kuma sai wasu hawaye suka gangaro mata wadda ta rasa ko na minene, shin bakin ciki take ko farin ciki? Safwan yaso ace yayi kidsing din sodangi 100%amma sai bai samu wannan damar ba saboda yana ganin ta wannan hanyar ne kafai zata iya tunawa dashi sosai,kuma shima ta nan ne zai gane iyakar yanda tayi missing dinshi. Dan dagowa yayi da idanuwanshi da suka fara canzawa yace,"sodangi ina fata dai kin tuna dani yanzu,saboda ni zan iya ce maki tunda muka rabu nake dana sanin guduwar da nayi na barki har zuwa ranat yau dana hafu dake." Kara sautin kukanta tayi,saboda idan da yasan yanda takeji idan yana tuna mata abinda ya wuce jivtake kamar numfashinta zai rabu da jikinta. Kufcewa tayi ta fito daga inda ya boye da ita ta fara sauri tana tafe tana zubar da hawaye.shima fitowa yayi yabi bayanta jiki asanyaye saboda ya fahimci abinda ke sanya sodangi kuka watau abinda yayi mata abaya. Kiran sunanta yayi har wajen sau ukku amma bata tsaya ba don haka sai ya kara sauri har ya samu ya sha gabanta ya tarbeta yana cewa,"don Allsh sodangi kiyi mani uzuri ki tsaya kiji reasons dina. Da yake wurin babu kowa tsit yake saboda da rashin jama ar wurin safwan ya samu damar sakewa da sodangi,kuma shiyasa yaso ta tsaya suyi ta ta kare a tsakaninsu, saboda shi yasan duk abinda zatayi mashi ba zai rabu da ita ba koda minene shi kuwa. Kaucewa tayi daga gabanshi taci gaba da tafiya abinta, wannan karon bai kirata ba,binta kawai yayi yana cimmata ya jawota ajikinshi ya sake rungumrta tsam yana mayar da numfashi yace,"sodangi so kike in mutu? Toh idan bakiyi sannu ba zan iya mutuwa,kuma saboda ke😭 Sodangi tayi shiru ajikin safwan tana mamakin maganganun dake fitowa daga bakinshi,can wata zuciyarta tace,"akul sodangi,wallahi yaudararki yakeyi,mugu neh azzalumi,kuma mayaudari,ya yaudareki daga farko kada ki sake ki barshi ya sake yaudararki." Wani sabon karfi ne yazo mata ta tureshi da karfin tsiya tana huttai,sannan ga idanuwanta sun kara fitowa saboda tashin hankalin da take gani karara agabanta. Love you sis😘 08033481518 [4/9, 2:19 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 36 I dedicated this love story to my Hausa Novel & fans,thanks and love you all 😘😘 Zafga mashi harara tayi ta nuna shi da dan yatsa πŸ‘‰ tace," kada ka sake taba ni,saboda idan har baka san kanka ba toh ni nasan kaina, kuma kada kayi tsammanin zan zama irin yammatan nan sakarkari dakake wulakanta wa,sannan daga baya ka koma masu."kutawa tayi ta duka ta dauki jikkarta ta juya taci gaba da tafiya ba tare data san inda zata nufa ba. Jiki asanyaye safwan yabi ta da idanuwa cikin mamakin janzawar da Sodangin shi tayi,kara binta yayi,amma awannan karon bai kira sunan ta ba,saboda Yadda yaga fuskarta yasan babu wasa,don haka yana isa ya juyota sosai suka fuskanci juna ya zuba mata kyawawan idanuwanshi yace,"kada kiyi tsammanin cewar zan rabu dake sodangi, saboda a yanda nakejinki tamkar yanzu na fara sonki arayuwata,please kiyi hakuri da abinda nayi maki mu koma normal." Wani matsiyacin murmushi tayi kawai ta nemi juyawa shi kuma ya sake riketa kam a hannunshi yace,wllh idan har baki tsaya kika saurareni ba toh duk abinda nayi maki ki dauka ke kika jawowa kanki." Wata irin dariya tayi tace,"wanne dare ne je mage bai gani ba,ai sai ranar mutuwar shi kawai,toh don haka kaje kayi duk abinda zakayi cheater kawai." Damkar ta yayi sosai ya tunkari bakinta cikin zafin nama,saboda kalaman data bi shi dasu su suka tinzirashi har saida yayi kissing dinta. Babu yanda sodangi batayi ba don ta kwace kanta amma ta kasa har sai daya saketa don kanshi. Da sauri ta matsa baya tana tofar da miyan bakinta cikin tashin hankali. Shi kuma kallonta kawai yake yana murmushi sannan yace,"I'm won you,if you attempt call me cheater sai nayi maki abinda yafi wannan,kuma sannan wannan miyau din da kike zubar wa,idan bakiyi sannu ba sai na mayar maki da wani yanzu." Jin haka yasa sodangi ta debi hanya da sauri har tana tuntube tana kuma waigenshi tana murguda mashi baki tare da fadin wasu maganganu da bai fahimci abinda take cewa. Dariya yayi ya shafi sumar kanshi ya zuba mata ido har ta nemi bacewa ganinshi.wayarshi ya fiddo a aljihunshi ya kira babban yaronshi yace,"ka tarbi sodangi gata nan zata fito ta bayan restaurant dina,kuma kayi bakin kokarinka ka dauketa,amma idan taki ka kyaleta kabi bayanta hat zuwa gidansu." Rusunawa yayi yace,"yes boss angama."sannan ya kashe wayar. Safwan ya samu wuri ya zauna yaci gaba da tunanin sodangi,watau bazai mance dadin dayaji ba lokacin daya rungumota ajikinshi,domin ji yayi komai na jikinta ya kara canzawa,can kuma daya tuna kissing dinta da yayi duk da batayi responding ba,sai da ya rasa yanda zai misalta dadin dayaji. Lumshe idanuwanshi yayi ya fada ahankali,"sodangi ke tawa ce ni kadai,saboda you are different then others." Wayar shi ce tayi ringing ya zura hannu ya daukota ya kanga akunne ba tare daya duba sunan mai kiran ba,muryar Tahir yaji yana kiran sunanshi. Gyara zamanshi yayi yace,"yeah my friend ya akayi neh?" Tahir yace,"ina ka shiga neh?kafa san jiranka muke don ya kamata kazo wajen sameer." Murmushi yayi saboda shi sam ya mance da yasa a tsare mashi sameer don haka sai yace kasa su sakeshi kawai,sannan kuma yaci gaba da cewa,"Tahir ka turo a daukeni." Tahir yayi dariya yace,"lover boy a ina zamu same ka?"kwatance yayi masu sannan yaci gaba da tunanin sodanginshi kamin su iso. Kusan lokaci daya Tahir da babban yaronshi suka iso,cikin farin ciki safwan ya nufi motar da Tahir din yazo da ita zai shiga,sai kuma ya dakata ya yafito babban yaro yace,"zo nan ka fada mani aiken da nayi maka." Tunda ya taho safwan yaso ya gane akwai wani abu,amma sai yasha jinin jikinshi ya natsu yace,"ya akayi neh?" Babban yaro ya rusunar da kanshi yace,yallabai babu yanda banyi da madam ba akan ta shiga mota amma taki saurarenna,toh shine na hakura nabi bayanta kamar yanda kace. Bayan mun iso sallari dai dai junction sai adaidaitar data shiga suka wuce ni kuma sai go slow ya rikeni har wannan adaidaitar ta fito, ni kuma dana samu na shiga sai ban........... ai bai bari ya ida fadin abinda zai ida cewa ba,saboda har ya gama karantar abinda zai ce sai ya kashe shi da wasu irin kyawawan Mari kusan ukku kuma lokaci daya. Kuyi hakuri gashi nan don kada ku jini shiru shiyasa nayi maku wadda ya sawwaka. Love you sis 😘 08033481518 [4/9, 2:28 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 37 I dedicated this love story to my Hausa Novel and my fans,thanks and love you all 😘😘 Nan take babban yaro ya zube kasa yana tuba a gabansu safwan,shi kuwa gaba daya farin cikin dayake ciki ya gushe,rannan bace ya kalleshi yace,"kana so ne kace mani zan kara rasa sodangi?" Wani huci yayi ya furzar da iskar dake bakinshi yaci gaba dacewa, "wallahi karya kakeyi,kuma idan har ka bari haka ta faru toh abakin aikinka kuma sai nasa an daure mani kai har igiya tayi rara." Nan da nan babban yaro ya tsure saboda yasan halin oganshi muddun ya fadi magana toh bai dagawa akanta. Anan suka barshi duk jiki asanyaye saboda tashin hankalin daya hango ya tunkaroshi. Sodangi kuwa kusan adaddafe ta isa gidansu surayya,babbar sa ar da tayi surayyar bata nan sai mahaifiyyarta,don haka shigewa tayi dakinsu ta kwanta ta darji kuka iyakar son ranta,saboda ganin safwan da tayi ayau yasa ya tado mata tsohon ciwon daya dade acikin zuciyarta. Sodangi tasan tana tsananin son safwan kamar ranta,amma abinda yayi mata ne take tunanin yanda zata iya yafe mashi ta ruwan sanyi kamar yanda yake tsammani,jikinta ne ya dauki dumi tamkar mai zazzabi saboda kukan data wuni tanayi,sannan ga tsananin tunani da ta matsawa kwalarta. Son ganin afnan ya bijoro mata acikin zuciya har take ganin kasancewarta akusa da ita zai iya sawa ta samu relief akan abinda takeji. Wayarta ta daga ta fara neman number sameer,amma gashi tana ringing ba a daga ba har wajen sau ukku,abinda bai tabayi mata ba tunda suka hadu,don haka sai taji ta damu,sake kiran da zatayi nrh taji ya rufe wayar gaba dayanta. Dan mamaki ne ya kamata tayi shiru hsr zuwa wani lokaci,kasa hakura tayi saboda ta riga ta sanya wa ranta tafiya gida,don haka sai ta yanke shawarar ta kira Abban sameer. Haka kuwa akayi tana kiranshi ringing daya tayi yayi karaf ya dauka yana dariya yace,"sarat Abubakar!" Sodangi ta sunkuyar da kanta cikin girmamawa ta gaisheshi. Amsawa yayi cikin fara arshi,domin dakaji yanayinshi kasan cikin farin aciki yake yace,"saratu nasa da kun gama kai tsaye waje na zaku nufo." Sai alokacin sodangi ta tuna da abinda ya kaisu company su safwan,don haka sai tayi sauri tace,"ranka ya dade ai abinda mukaje nema an dace,kuma duk sauran bayanai awajen sameer zakaji su." Numfasawa Alhaji yunus yayi yace mata,"ni da idanuwana har yanzu ban ga sameer ba sai dai ya bayar da sakonnin report din da yazo dasu wanda kukayi,toh nima anan naga sun amince da suyi kasuwanci damu." Alhaji yunus ya numfasa yaci gaba da cewa,"sarah ko wani abu ya faru daku neh awajen tafiyar,idan har akwai matsala ai ya kamata kuzo Kuyi mani bayani don mu shawo matsalar dani da ku." Sodangi tayi dan takaitaccen murmushi tace,"Abba ka kwantar da hankalinks,domin babu abinda zai faru da company ka sai dai alkhairi." Alhaji yunus yayi wani farin ciki najin dadin maganar da sodangi tayi,don haka sai yace,"ya zama dole in hadama wannan company nawa wata gaggarumar walima don atayamu murnar ci gaban da zamu samu." Sodangi tayi dan murmushi tace,"godiyya muke yallabai, amma kuma sai tadanyi shiru". "Umhum ina jinki sarah,ya akayi nrh?" Fadar Alhaji yunus. Sodangi tayi kasa da murya tace,"yallabai bana jin dadin jikina,shine nake neman alfarma inason inje gida inyi ko sati daya neh don in samu shan magani." Alhaji yunus yayi shiru kamar mai nazarin wani abu,sai can yace,"No problem sarah,dama nayi shiru neh don in tuna idan akwai wasu ayyuka,amma kada kiji komai Allah ya baki lfy,kuma yau monday sai ki dawo next monday,don haka ranar talata zamuyi celebrate insha Allahun" Wani farin ciki ne ya kama sodangi,don haka sai tayi mashi godiyya sannan suka ajiye wayar. Mikewa tayi ta shiga hada yan kayan da zatayi amfani dasu,sannan ta rubutawa surayya dan Note:surayya ina fata kin dawo cikin koshin lafiya,na tafi gida saboda naji duk jikina ban jin dadin shi,amma bazan wuce one week ba insha Allahu." Ajiye wasikar tayi inda surayya zata gani ta jawo Jikkar kayanta ta fito. Har daki ta samu mahaifiyyar su surayya ta fada mata tafiyar da zatayi.addu a tayi mata sosai sannan kuma tace ta gaida mata mutanen gidansu. Bayan ta fito daga cikin gidan ta fara tunanin ko ta fara zuwa Daura ta kwana biyu sai ta dawo bichi ta ida sauran kwanakin ta,don haka ta yanke shawarart kai tsaye ta hau motar Daura. Akofar gida ta sami sadah da afnan suna shan iska saboda maraice yayi sosai, cikin mamaki ta kalleshi tare da dan waigawa dama da haggu tace,"yaya sadah ya naga afnan anan?" Jin muryar sodangi yasa afnan ta juyo ta ganta,ai kuwa sai dariya ta tashi ta nufeta da gudu,cabata sama tayi tana dariya. Wurin sadah ta ida isa ta samu kusa da shi ta zauna tana cewa,"na tambaye ka amma baka bani amsa ba." Sadah yayi dariya yace,ai saboda ardo yana ciki shiyasa naki daga muryarta." Sodangi ta kara kallon afnan tace,"nima rudewa nayi shiyasa."sannan ta mayar da dubanta ga sadah taci gaba da cewa,"nasan dai kai neh ka dauko ta,yaya sadah baka tsoron ardo yasan tsakaninah da afnan?" Dan murmushi yayi yace,"wai ai zanso ace kina nan sadda na shigo da ita gidannan,saboda tambayoyin da ardo yayi ta watso mani sai da naji kamar in gudu,amma dana dake sai gashi don kanshi ya kyaleni." Sodangi tayi tagumi tare da wara manyan idanuwanta ta zubawa sadah ido tace,"toh ina kace mashi ka samota?" Sadah yadan kanga bakinshi kusa da sodangi ya rada mata, "cewa nayi diyar makwaftan su goggo laura ce,kuma wllh da kyar ya yarda,domin cewa yayi ashe acikin ruga akwai yan gayu haka πŸ˜ƒ Dariya sukayi gaba dayan su sai sadah yaci gaba da cewa,"tun ardo yana kauda kai ga afnan har ta kai idan bai ganta ba sai kiji yana tambaya,kuma kullum aka zauna sai kiji yaba cewa shi gani yake tanayi mashi kama da wata,amma har yanzu ya gaza gane da kowa cece." Kallonshi sodangi tayi,shi kuma yaci gaba da cewa,"don haka tunda yanzu kin zo sai kin kula sosai,kuma kada kiyi ta jawo afnan ajikin ki har ardo ya kai ga zargin wani abu,ko kuma kamar dayake tunani a ina ya santa kinga sai ya gano ta ajikinki." Sodangi ta firgita dajin zancen sadah😳 ta kuma kalli afnan tayi sauri ta ajiye ta kasa tace,"tabbas kuwa kasan ardo yana da saurin fahimtar al amurra,amma kuma yaya sadah ni yanzu muna kama da afnan?" Sadah ya jawo hannun afnan yana kallonta yayi murmushi yace,"duk kusan halittun dake jikin afnan na safwan ne,abu daya ta biyo ki wannan dan point din,sai dai nata sharara yayi akan naki." Sodangi ta yarda da duk bayanin sadah saboda ita ma tuni take kallon kamannin safwan a fuskar afnan. Mikewa tayi tace,"yaya sadah na gode kwarai da gaske da irin kulawar da kakeyi mani Allah ya bar mana zumuncin mu." Dariya yayi yace,"babu komai kanwata,ai ni duk farin cikinki shine nawa." Tana murmushin jin dadi ta shige cikin gidan su. Love you sis😘 08033481518 [4/9, 2:28 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 38 I dedicated this love story to my Hausa Novel & fans,thanks and love you all 😘😘 Madadin yanda sodangi ta tsara daga farko,watau ta kwana biyu daura ta koma bichi tayi sauran kwanakinta sai ta fasa tunda afnan tana gida,sai dai bata da wata sakewa da ita ibdai ardo yana nan sai idan bai gida,haka ta cija kwanakinta ta fara shirin komawa kano wajen aikinta. A yanda molasa tasan halayen sodangi sai taga canji wannan karan,saboda tana fahimtar yanda sodangi take matsawa kanta da yawan tunini,domin wani lokaci da molasa ta fito daga kitchen tayiwa sodangi magana taji shiru bata amsa ba,sai ta waiga ta kalleta,tunanin dai taga tanayi,aikuwa ta matsa mata sai ta fada mata dalilin tunanin,wayancewa tayi tace mata babu komai wai kanta yake mata ciwo. Hakanan molasa ta kyaleta amma badon ta yarda ba. Tsarabar nono da madarar shanu suka hada mata harda man shanun sukace ta kaiwa mahaifiyyar surayya,kuma tace suna gaishesu A wajen tafiyarta ne afnan taso tona masu asiri ta fara kuka wai sai tabi sodangi,da kyar da dubara suka samu ta hakura,ita kuma sodangi tayi hanzarin barin gidan. Sai da ta biya ta bichi don taga gwaggonta laura,aikuwa tana isa laura ta far mata da fada,"wannan wacce irin rayuwace neh sodangi?" Sodangi cikin rashin fahimtar dalilin fadan goggonta sai tayi dariya tace,"kai goggo tundaga daura nake ta doki da murnar son ganinki,amma gashi ina dira kin tarbeni da fada ban san hawa ba ban san sauka ba. Goggo laura ta harareta tace,"ya akayi kikayi tafiya oganki bai sani ba?saboda nan yayi ta zarya kusan kullum sai yazo,kuma ada na fara tunanin turashi daura sai kuma wani tunanin yace mani idan bakije can ba fah.toh shiyasa na kyaleshi sai dai ince har yanzu bakizo ba." Tana rufe baki taji sautin tsayawar mota sai tayi dariya tace,"shikenan ma gaya nan ya sake dawowa,kuma dama dai dai wannan lokacin ne lokacin zuwanshi,don haka sai ki fita ki gani." Sodangi tayi dariya tace,"ho goggonah, ko dai sameer ya baki cin hanci ne ban sani ba?" Itama dariyar take saboda ta gane sodangi yanzu tasan halinta tsaf shi yasa ma har take zolayarta. A jiye dan trolley din kayanta tayi ta juya zuwa kofar gidan. Ganin sameer tsaye ajikin motarshi bai sa tayi mamaki tunda dama shi zuciyarta ta aiyano mata,don haka sai taci gaba da takawa ahankali ta nufeshi,tunda ta fito yake kallonta,domin ayanda yakeji acikin zuciyar shi kamar ya tarbeta ya rungumeta ajikinshi saboda ba karamin missing dinta yayi ba. Face taja mashi,ba yabo ba fallasa har ta isa gabanshi, gaishe shi tayi ya amsa fuskarshi asake,ita kuma yana amsawa taji gaba da kallon gefenshi,kuma bata kara ceawa komai ba. Zuba mata idanuwanshi yayi yana kallonta,har sai da ya gama karantar tsaf ya gane fushi takeyi dashi,don haka sai yayi murmushi yace,"Sarah fushi kikeyi dani koh?toh I'm sorry I'm very really sorry,saboda wallahi alokacin da kika kirani ko na dauki wayar ban san irin abinda zan fada maki ba,saboda gaba daya raina bace yake akan abinda ya faru,amma tunda har kikaga nazo gareki yanzu ke kanki kinsan na huce,please nima kiyi hakuri." Dan numfasawa yayi sannan yaci gaba da cewa,"sarah ban san kina da wani matsayi acikin zuciyata ba sai da kikayi wannan tafiyar ta bazata,wanda ni kadai ce nasan halin dana shiga saboda rashin ganinki kusa dani." Sodangi wata irin kunya ce ta kamata tun sadda sameer ya fara bata hakuri,saboda sai yanzu ta tuna ranar da suka rabu tsateshi safwan yasa akayi,kuma bata san abinda akayi mashi ba.don haka tanajin yayi shiru ta dago kanta ahankali ta kalleshi tace,"ka daina bani hakuri,saboda komai ya faru ta sila ta ce,don haka nima ina mai baka hakuri sameer." Ba karamin dadi yaji ba,nan da nan fuskarshi ta kara washewa yace,"Na gode sarah ! Thank you very much !! Itama murmushin takeyi ta kalleshi tare dayi mashi wani kallo wanda shi ya dauka duk na soyayya ne tace,"idan zaka kira ni ka rinka ce mani sodangi saboda duk dangin mu babu mai kirana da saratu,kilama wasu sun mance da asalin sunana." Rage fara a yayi,tare da kada kanshi yace,ni kuma bana son sunan na sodangi,saboda idan da ina da hali da babu wanda zai kara kiranki dashi." Dan tsaki ya ja ya kauda kanshi gefe yaci gaba da cewa,"wallahi idan da nasan zuwan mu wannan wurin zan gamu da wannan guy din da tun farko bamuje ba,abin ban haushi da takaici sai idan kinji yanda yake pronouncing din sodangi sai ka rantse kamar tun farko shi ya rada maki sunan ba iyayenki ba." Dariya sosai sodangi ta kamayi,wai sameer ne ke fada,ko kuwa dai wannan shine kishin da ake cewa. Tsayawa yayi yana kallonta yace,"watau dariya ma na baki koh? Hmm ya kuta ya canzakan zancen yaci gaba da cewa kije ki dauko kayanki kizo muje saboda nasan duk abinda kike dole ne gobe kije wajen aiki,kuma sannan ga shirye shiryen walima da Abba zai kaddamas." Tana dariyar ta shige cikin gidan,ban kwana tayiwa laura tare da bata abinda tayi niyya,sannan ta fito daga cikin gidan. Hada idon da sukayi da sameer sai taji wata dariyar,saboda idan ta tuna wai kamar shi yara maki sunan sai abin ya bata dariya. Bari yayi sai da suka shiga mota suka fara tafiya ya kalleta yace,"idan har baki daina dariyar nan ba duk abinda nayi mski kada kiyi kuka dani,so you should blem your self." Wannan furucin da yayi sai yayi mata dai dai dana safwan,wanda karshe ya matseta da karfin tsiya yayi kissing dinta,don haka nan da nan ta natsu harda kara gyara zamanta. Shi kuma ganin haka yasa ya juyo ya kalleta yayi murmushi ya juya yaci gaba da driving din da yakeyi. Al amarin safwan kuwa,duk da babban yaro bai san inda sodangi ta sauka ba, amma kullum sai safwan din yasa ya kawo shi sallari sannan babban yaron ya fita yayi ta yawo har sai magriba ta kawo jiki sannan su bar wajen. Kamar kullum, yau ma tafe suke amma dokokin da safwan yake gindayawa babban yaro sune suka fitgita shi,domin duk AC din da cikin motar amma babban yaro sam bai jinta,don wata irin zufa da yakeyi sai ka rantse ruwa aka kwara mashi. Safwan ya numfasa cikin takaici yaci gaba da cewa,"yau na fada maka idan har baka gano gidan da ta shiga ba abakin aikinka,kuma kada kayi tsammanin zakaje wani waje adauke ka sabon aiki,Noo duk wata hanya da zaka bi sai na wahalar dakai,don haka dubara ta ragewa mai shiga rijiya." Wasu hawaye tare da zufa suka hadewa babban yaro duk ya rasa abinda yakeyi mashi dadi,kuma sannan sarai yasan halin uban gidanshi bai magana biyu. Dai dai junction din sallari suka iso zasu gaggara su shiga inda rukunin centocin gidajen suke safwan ya daga ido sukayi ido biyu da babban yaro ta madubin gaban motar yace,"idan ka sauka kuma kaje baka samo gidan ba,toh kada ka sake ka dawo mani,then daga can kayi can." Gaba daya cikin babban yaro ya murda kuuuuuu kakeji kamar wanda zaiyi tsugunno,ga habar bakin shi sai rawa take,kuma yana son ya kara bashi hakuri amma safwan ya riga yayi worning dinshi,dole ya fita daga motar yana tafe yana waiwaye,domin ranshi ya bashi kallon bankwana yakeyiwa oganshi tunda idan dai har anan sodangi take toh daya gano ta tuni. Love you sis 😘 08033481518 [4/9, 8:08 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 39 I dedicated this love story to my Hausa Novels & my fans,thank and love you all 😘😘 Zaune yayi acikin motar har kusan gaf da magriba,amma babu alamar dawowar babban yaro,wani takaici ne yaji har acikin zuciyarshi ya rasa abinda yakeyi mashi dadi,ya dago kanshi yana kallon jama ar da suke ta kai da komowa yace acikin ranshi,kada dai ace yanzu ma ya rasa sodangi???? Wani karaji yayi ya fito daga motar yana cewa,it's impossible."bude sit din driver yayi ya zauna yana kokarin rufe motar sai kawai wata mota ta gitta ta gefenshi,sodangi ce kame agaban mota ita da sameer suna ta fesa murmushi,domin daka gansu zaka gane fira sukeyi atsakaninsu. Wani kululun bakin ciki neh yazo mashi iya wuya,da sauri ya tayar da motarshi yabi bayansu. Wata kwana ce suka shiga,ada yayi niyyar shigarta sai ya fasa saboda ya fahimci bata da zurfi sosai. Parking yayi can gefe daya ya taka da kafarsa ya shiga lungun. Wani wuri ya samu ya dan labe ta yanda zai rinka hangen duk abinda yake faruwa. A dai dai kofar gidansu surayya sameer yayi parking,sun dan jima acikin motar kamin su fito,wanda har safwan ya kosa ya rinkajin kamar ya fito yaje ya samesu,amma dole ya hakura ba don ranshi yaso ba. Sodangi ta bude motar ta ziro kafarta ta fito,duk da wajen ya fara duhu,amma safwan yana kallonsu tsaf. Shima sameer din fitowa yayi duk fuskokinsu dauke dariya,tabbas magana suke amma safwan yaso yaji shin wacce magana ce yake fada mata har take sanyata dariya. Wasu manyan envelops ne a hannun sameer ya mikawa sodangi yana murmushi yace,"ki rike wadannan envelopes din,saboda suna da matukar muhimmanci awajena,kuma zan kira around nine don ki bani amsar tambayoyin da kika gani." Murmushi sodangi tayi tace,"babu wata amsa da zan baka da bakina,domin yanda ka bani arubuce haka nima zan maido maka ansarka arubuce." Dariya kawai sameer yayi yace,"ni kuwa zan baki mamaki,gobe zan fada maki duk abinda yake acikin zuciyata,don haka sai kizo da shirinki. Sodangi tana dariya ta mika hannunta ta amshi envelopes din tace,"Allah ya kaimu goben." Tsayawa tayi gefe daya har sai da ya fita da motarshi,sannan ta kalli envelopes din dake hannunta tayi murmushi, sannan ta duka ta dauki trolley dinta ta shige cikin gidansu surayya. Ashe alokacin da sodangi ta duka jan trolley dinta daga cikin envelopes din guda daya ta sullube mata,kuma daga inda safwan yake ya hangi fadowarta,shiyasa ya fasa yi mata magana har ta shige. Envelope din ya dauka yana juyata kamar ya dauki kashi,dan tsaki yayi ya raba jikin dan dakalin kofar gidansu surayya ya zauna. Budeta yayi ya zaro wani hadadden card mai dauke da kalmomin soyayya masu tsima zuciya, yana sake juya shi sai ga wata yar karamar takarda ta fado daga cikinshi. Ranshi bace ya duka ya daukota,sannan ya fiddo wayarshi ya kunna don hasken wurin ya karu. Har ya bude takardar zai karanta sai ya fasa,saboda words din kadai daya gani ajikin cards din sun sa tunaninshi yana neman jirkicewa,toh kuma bare abinda ya rubuta da hannunshi. Matse takardar yayi da karfi ya runtse idanuwanshi yana maida numfashinshi da karfi.gaba daya ya canza,idanuwanshi suka kada sukayi jajir. Ahankali ya samu ya fara komawa dai dai,saboda duk alokacin ya tuna ko sallar magriba baiyi ba,don haka mikewa yayi ya fita daga center ya nufi wani masallaci mafi kusa yayi sallar magriba da isha'i sannan ya dawo. A dai dai kan lungun da zai shiga ya nufi gidansu surayya yaga wani atsugunne gefen hanya,zuba mashi ido yayi don ya kara tantancewa. aikuwa abinda yake tunani shi ya gani,watau babban yaronshi,shima babban yaron yana ganin oganshi ya taso kanshi a sunkuye yana cewa,"wallahi yallabai yau babu gidan da ban shiga ba,amma idan nace masu sodangi sai suce duk rukunin nan babu mai irin wannan sunan." Safwan ya kalleshi yaga duk yanda ya yamutse,saboda wahala,don dai dai da kott din dake jikin shi ya cireta ya rike ahannushi,har necktie dinshi ya zazzageshi,kai duk dai abin gwanin ban tausayi. Safwan baice mashi komai ba,sai key daya mika mashi yace,"kaje wurin motar ka jirani kamin in fito. Jikinshi yana rawa ya amshi key din,kuma can a cikin zuciyar shi wani farin ciki ne ya cikashi ya nufi motar yana jin dadi. Wani yaro ya tura cikin gidansu surayya yace,"kaje kace ana sallama da saratu." Cikin sauri yaron ya shiga yayi sallama,sannan ya isar da sakon safwan. Sodangi tadan bata ranta ta kalli surayya dake kishin gide gefenta suna shan iska saboda zafin da akeyi tace,"nifa kananan samarin unguwar nan banson abinda sukeyi mani,domin nasan sun kyalla idon su dazun sunga dawowata." Dariya surayya tayi mata tace,"toh ai ba a san inda ake dacewa ba,kika sani ko acikinsu mijin yake." "Allah ya sawwake".cewar Sodangi cikin hassala ta mike tsaye taci gaba da cewa, je kace gata nan zuwa."sannan ta juya kan surayya ta kalleta cikin takaici tace,"wallahi duk kin ja masu domin babu wanda zan Kara gani da gashin arziki acikin su." Dan gyalenta ta jawo ta dora akan English wears din dake jikanta, sannan ta zari plat shoe din dake gefe cikin takalmansu tayi waje rannan abace. Kamshin turaren dataji tundaga zauren gidan yasa jikin ta yayi sanyi,ta tsaya cak,saboda kirjinta ne taji ya fara dukan ukku ukku.zuciyarta ce tfara ra tambayarta anya kuwa shine?πŸ€” Idan har shine toh miya kawo shi,kuma ya akayi ya gane gidan nan tunda rannan ina sane da yaronshi yana bin mu,shi yasa tayi dubarar da suka bace mashi. Mits ! dan tsaki tayi ta dunguri kanta tace,"kilama ni ke tunani banza,tayiwu ma ba shi bane." Ci gaba da tafiya tayi ta fito daga cikin gidan.gaba daya numfashin ta ne taji ya tafi daukewa saboda ko acikin barci taga safwan acikin duhu dole ne ta ganeshi ballanta na idanuwanta abude. Love you sis😘 08033481518 [4/9, 10:51 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 40 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 Tsaye tayi cak ta gaza motsawa daga inda take tsaye,sannan kuma idanuwanta sun gaza daukewa daga kallonshi,saboda tsan tsar mamaki ne abayya ne afuskarta. Fahimta yayi bazata iso inda yake ba,shiyasa shi ya mike tsaye ya isketa inda take tsaye ya lalubo hannunta ya jawota har zuwa bida dakalin,sannan yace,"ki zauna mana."yanda kasan an sanya mata remote control haka ta koma. Sulalewa tayi ta zauna kamar yanda ya umurce ta.dan shiru sukayi nadan wani lokaci saboda shi safwan gaba daya ya rasa ta inda zai fara,shin ta sameer zai fara ko ta samarin cikin unguwa,saboda fitowar da tayi ba tare data tambayi ko wa nene ba yasa ya gane ba sameer kadai bane. Numfasawa yayi ya kalleta yaga ko kallon inda yake ba tayi sai wasa da yan yatsun hannunta take,amma dazu ya gama ganinta da wani wai shi sameer ta saki baki tana ta bude hakoranta agabanshi,shi kuwa ayi mashi yar dariyar ko don yaji sanyi acikin zuciyarshi amma ya gaza samu. Sunanta ya kira ahankali cikin sigar da zata tausaya mashi yace,"mi yasa kika daina so na?sai wasu wadanda rayuwarki bata dace da ta su ba?" Sai alokacin ta dago ta kalle shi,amma wannan karon babu tsiwa atare da ita tace,"saboda sune sukace sunji sun gani zasu iya dani duk ayanda nake." Tsam yayi da ranshi dayaji abinda tace,sannan ya kalleta yace,"nima zan iya fiye da tunanin ki sodangi nah." Fadin sodangi nah da yayi sai da taji har acikin ranta,sannan kalmar ta tafi ta ba sauran jijiyoyin jinin jikinta. Dagowa tayi ta kalleshi,shi kuma yaci gaba da cewa,"har yanzu sodangi na lura dake kallon da kikeyi mani na dawo ne zan sake yaudararki,baccin ni kuma yanzu ina tafiyar da rayuwata akan abinda nakeso,saboda a shekarun baya kurucciya ce ta ja ni har na aikata maki abinda nayi,amma ayanzu babu abinda nake so da gani sai ke,shi yasa na ajiye duk wasu ayyuka nah saboda ke sodangi please kiji tausayina ki yafe mani abinda nayi maki." Zuciyar ta ce ta fara karewa hat taji kamar zatayi kuka saboda tausayin safwan wai shine yake begging dinta,wuf tayi ta mike tsaye zata tafi yayi caraf ya riko hannunta yace,"sodangi yaushe tausayinki ya rabu da jikinki?domin sodangin dana sani zuciyarta cike take da tausayi da tsananin son mijinta safwan." Kokarin kwace hannunta tayi niyyarshi shima yayi maza ya mike tsayen ya fuskance ta sosai tare da shan gabanta don kada ta samu damar shigewa cikin gidan ta barshi. Sun jima ahaka kowanne daya daga cikinsu suna jin saukar numfashin dan uwansu safwan ya numfasa yace,"sodangi wanene sameer a zuciyarki?"saboda ya fahimci duk ta lalamar daya bi mata tana son ta zame mashi. Shiru tayi bata amsa mashi ba,har ya sake maimaita mata tambayar. Cikin yar rashin kunya ta harareshi tace,"miye kakeso kaji? Murmushi kawai yayi yadan kauda kanshi gefe na yan seconds sannan ya maido ganinshi kanta yace,"ina son in sani neh,saboda wannan card din dana tsinta anan kofar gidan." Mamaki tayi sosai saboda dama taga babu daya daga cikinsu,amma sai tayi tunanin ko sameer ya manta shi acikin motar. Hannu ta daga da sauri zata amshi card din sai yasa hannunshi daya ya rike nata hannun yace,"har sai kin bani amsar tambayar da nayi maki sannan." Bude idanuwanta tayi sosai ba tare dataji komai ba tace,"son shi nake, kuma aurenshi zanyi,sai kuma mi?" Murmushin karfin hali yayi yace,"okay naji,toh ni kuma ya zakiyi da nawa son dake cikin zuciyar ki?saboda koda kika ce mani baki sona sam ban yarda ba." Sodangi tayi dariya irin ta ka gaji ka bari tace,"please ka daina yaudarar kanka,saboda na dade da daina sonka." Safwan ya kara matsawa kusa da ita yace,"idan har kin daina so na da gaske ki tsaya in gwada in gani,kuma nayi maki alkawarin ni kuma zan rabu dake har abada." Da daya matso har taja baya,amma dataji abinda yace sai ta tsaya cak tace,na amince ka gwadani din." Safwan yayi murmushi ya Kara matsawa kusa da ita ya tsaya yace,"kici gaba da kallona har tsawon minti ishirin." Sodangi ta gyara tsayuwarta ta dake da bala I tana son ta gwadawa safwan cewar ta fa daina son shi,shi kuma cikin dubara ya kara matse mata ba tare data sani ba,suna cikin kalon juna safwan ya dafa kafadarta,kamar dama jira take kawai sai ta tafi da idanuwanta luuuuuu ta samu dai ta budesu ta tsayar da idanuwanta. A haka bata ankara ba fuskokindu suka kusa hadewa har sunajin hucin numfashin junansu,kai tsaye safwan ya nufi bakin sodangi,madadin ta hanashi kamar yanda sukeyi sai kawai ta lumshe idanuwanta ta ta bar madhi euka da nama saboda kwata kwata kasa janye jikin ta tayi,domin sai ta rinkajin kamar magnet aka sanya atsakaninsu take janta zuwa gareshi. Kissing dinta yayi wanda ya sha bambam da wanda yayi mata akwanaki tana yan tirje tirjr,wannan karon tesponding tayi ba tare data sani ba,shi kuma da yake ya samu dama,jawota yayi ya mannata ajiki shi ya shiga sarrafa ta yanda yakeso. Numfashinta taji ya fara season kamar zai dauke sai ta ida fadawa jikinshi shi kuma ya rungumeta sosai saboda yanda yaji kamar faduwa zatayi,acikin kunnenta ya shiga rada mata,"thank you sodangi,dama tuni nasan kina sona,don dai kawai kina fushi dani neh,kuma zan iya komai arayuwata don in baki hakuri." Hankalinta ne ya dawo jikinta taji ta ajikinshi,tunani ta farayi wai ya kayi haka,kada dai da gaske har yanzu tana son safwan din? Wani haushin kanta taji ga kuma kunya,toh ta ya ya zata amshi kanta awajenshi?kai lallai yau tayi abin kunyar da bata tabayi ba a rayuwarta. Dakewa tayi ta dago da kanta tare da zame jikinta,saboda kunya kuma sai ta gaza hada ido dashi ta juya tana kokarin shigewa cikin gida." Wuf yayi ya kamo hannunta yace,"ki tsaya please,ina son ki furta mani da bakinki sodangi." Sodangi ta harareshi tace,"kada ka sanyawa ranka wai sodangi tana sonka,sam saboda abinda kayi yaudara ce,don haka bari kaji da kunnenka,"ni sodangi bani sonka." Love you sis😘 08033481518 [4/11, 12:33 AM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 41 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 Murmushi safwan yayi yakai hannunta abakinshi ya kissing dinshi yace,"komai zaki ce ni bazan damu ba,amma ina son ki sani ki daina kula samari idan har kina son zaman lafiyar,saboda zuciyata bazata jure ganinki tare da wani ba." Yana fadar haka ya saki hannunta ahankali yaci gaba da cewa,"sai mun sake haduwa,kuma ki sanyawa ranki akowanne lokaci zaki iya gani nah." Sodangi ta murguda baki 😏 tace,"kada kayi tunanin zan bi wata dokar ka,saboda kai ba komai bane awajena,kuma ada ban saurari samari ba,sai yanzu ne zan fara,don haka idan ka tashi kayi mani duk abinda kaga dama." Tana fadar haka tayi wuf ta shige cikin gidan,saboda tasan halin safwan yanzun nan anyi ba ita. Shi kuwa murmushi kawai yayi tunda yasan duk abinda take fada abaki ne kawai. Juyawa yayi ya nufi motarshi cikin farin ciki da annushuwa,saboda ayanda yake jin kan nashi ayau tamkar wani sabon ango😜 yana shiga motarshi ya zauna ya lalubi wayarshi ya kira umminshi. Da yake video call ne,nan da nan sai gata ta bayyana,gaisheta yayi cikin fara arshi wadda tana iya cewa rabon da taga yana yin irinta har ta mance. Murmushi tayi tace,"yaya my son,ina fata kana cikin koshin lafiya?" Safwan shima murmushin yake yace,"ummi na gano sodangi tah." "Haba koh inji,shi yasa naga bakinka yaki rufuwa safwan." Dariya yayi har yana kyakyatawa yace,"ina nan zan kawo maki ita,kuma da kin ganta zakisan danki bai yi zabin tumun dare ba." Jinjina kanta tayi tana murmushi tace,"okay ina jiranka,amma kuma ya za kai da Humaira yarinyar da Daddy dinka ya baka?" Dan tsaki yayi ya bata ranshi yace,"ni ai bance ina sonta ba,kuma ummi ki tambayeta kiji koh na tabayi mata wata maganar so?kawai ki fadawa daddy cewar ya nemar mata wani mijin,idan kuma broth Yusuf yana so sai ya kara ta amatsayin ta biyu." Dafe kanta tayi cikin damuwa tace,wallahi safwan kana sanya mani ciwon kai da yawa,ta ya za a ce kai baka amshi mata ba sai yusuf,toh ina jan kunnenka akan kada ka sake yaji ka." Safwan yayi murmushi yace,"I'm sorry ummi,kuma duk ranar da kikaga sodangi ciwon kanki zai warke." Dariya ya bata sosai,sai da ta numfasa tace,"toh bari in fada maka ko yau Humaira sai da tazo gidan nan,baccin dama kusan kullum kafafuwanta suna gidan nan,don haka sai kazo ka warware wannan matsalar da kanka." "Okay zan zo,amma sai naga anan komai ya ida dai daita sannan.kici gaba da hakuri ummi ko kuma idan kin gaji ki korata gidansu kawai."yana fadar haka yayi maza ya kashe wayar saboda yasan abinda ya fada ba mai yiwuwa bane. Babban yaro dake gaba yana driving shima farin ciki ya kama shi saboda yaji oganshi yace ya saga farin cikin rayuwarshi. Ayau haka safwan ya kwana cikin farin ciki da kwanciyar hankali.hakama sodangi, saboda ita duk wata rayuwa da sukayi lojacin tana yarinyarta,itace tayi ta dawo mata tamkar tana kallon majigi,babu yanda surayya batayi ba akan ta fada mata kowanene amma taki ce mata safwan ne saboda surayya ta dade tana yi mata addu ar dawowar safwan ko don saboda afnan.ita kuma sodangi bata so neh saboda abinda yayi mata,kuma Ardo yace idon shi Idon na safwan,idan kuwa yace haka yana nufin bai yafe mashi ba. A haka tayi ta tunane tunanen ta har barci mai karfi ya kwashe ta. Washe gari tunda wuri sodangi ta nufi wurin aikinta saboda ayau suna da manyan bakin da suka gayyato domin taya su murna. 7:30 am tana cikin office dinta,domin akwai wasu kayayyaki da suka dinka,kuma sukayi shawarar bayyanar dasu acikin taron domin suyi tallarsu ga ya'yan masu kudi da attajiran garin,saboda kayan ba na masu karamar harka bane. Tana cikin aikin sameer ya shiga office din nata ya samu kujera ya zauna,dole ne ta bar duk abinda takeyi itama ta zauna ta zuba mashi ido. Yar harararta yayi yace,jiya bayan na tafi ina kika shiga,saboda nayi ta kiran wayarki amma bakiyi responding ba." Shiru sodangi tayi ta shiga tunani,tabbas jiya bayan rabuwarta da safwan taga missed call din shi har guda goma sha daya,amma kuma batasan dalilin dayasa bata kira shi ba,sai ma rufe wayar da tayi. Dago idanuwanta tayi ta kalleshi ta marairaice tace,"I'm sorry sameer,saboda jiya gajiya ce tasa na kwanta da wuri,kuma sadda na farka naga cajin wayata ya kare." Sameer ya numfasa yace,"toh shikenan is okay, komai ya wuce."hannunta ya jawo ya rike yana wani lumshe mata ido yace,"toh miye labari?" Sodangi ta zame hannunta tana murmushi ta mike daga inda take zaune ta nufi wata wardrobe dake dauke da manyan yadiddika da take amfani dasu wajen yin dinkuna tana cewa,"sameer ai labari yana wajenku saboda mu mata yan zaman gida ne." Sameer yayi yar dariya yace,"Toh tunda baki da labarin da zaki bani,ina reply dina?" Sodangi dai ta san bata samu wata takarda ba,amma zuciyarta tana bata wannan card din da safwan ya tsinta kuma ya tafi dashi,tabbas takardar tana Wurin shi." Rasa abinda zatace mashi tayi ta nufi yar kwarangar da take hawa idan zata dauko kaya asama ta haye,gashi takalman kafarta high Hill's ne,don haka ashe data hau bata dora kafarta daidai ba sai kawai ta nemi rikitowa,ai kuwa tayi saurin kama wani rool na material tana ganin zai iya riketa. Gaba daya tayo kasa tana kwarara ihu da neman a gaji wurin wanda zai taimaketa. Sameer ne ya zabura daga inda yake ya kai mata dauki cikin zafin nama ya tarbota,,aikuwa yanda ya samu ya rikota sai su rool rool din material din suka biyosu,kuma gashi wani irin nauyi tsiya gareshi,don haka bayan ya samu ya tarbeta sai ya kanga bayanshi wadannan rool din duk suka sauka ajikin. Acan kuma abakin kofar office din, fa iza ce ta biyo bayan sameer,saboda taje nashi office din bata ganshi ba,sai tayi tunanin yana office din sodangi don haka tana bude kofar akan idonta accident din ya faru,kuma da kayan suka gama zuba abisa gadon bayan sameer sai yaki sakinta ya zuba mata idanuwanshi. Tsoro neh ya kama fa iza,saboda ganin irin mugun kallon so da sameer yake aikawa sodangi. Da sauri fa iza ta juya cikin mamaki da kutawa,acikin zuciyar ta tace,"lallai wannan yarinyar,sai nayi maganin ta wallahi. Love you sis😘 08033481518 [4/11, 9:29 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 42 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 Sodangi da duk jikinta rawa yake ta kalli sameer tayi mashi sannu,amma shiru yayi mata bai bata amsa ba,sai dai wannan kallon daya tsare ta dashi. Zame jikinta tayi daga jikinshi ta dan matsa tana daddauke roll roll din tana tayar dasu tsaye. Numfasawa yayi shima ya fara taya ta,sai da suka mayar dasu tsaf sannan ya kalleta yana murmushi yace,"na dade ina Worning dinki akan ki daina hawa saman nan da kanki,amma baki daina ba,toh yanzun idan da bani cikin office din nan ya zakiyi?" Murmushi sodangi tayi tace,"shiyasa nake ta kara godewa Allah,don nasan babu abinda zai hana ni jin rauni." "Ashe kuwa da nayi punishing dinki,tunda har kikayi sakacin jiwa wannan kyakykyawar fatar taki ciwo."jin abinda yace neh yasa ta kalleshi,hada idon da sukayi neh yasa yayi mata murmushi,itama murmushin tayi mashi,sannan ta kauda kanta gefe daya.saboda sodangi tana bakin kokarinta tasa sameer acikin ranta,amma ko kallonta yayi batajin abinda takeji idan tana tare da safwan,shi yasa abin ya fara damunta,saboda iyakar kokarinta shine ta yakice safwan daga rayuwarta amma sai kara shige mata yake kamar wani magnadiso. Amsakuwar wayar dake cikin office din ita ta farkar da ita daga tunanin data tsunduma,sameer ne ya dauki phone din tare dayin sallama. Muryar mahaifinshi yaji cikin fada yana cewa,"ina kuka shiga neh wai tun dazu?"inda inda sameer ya fara Alhaji yunus ya datse shi yaci gaba da cewa,"maza ku tahovina jiranku,saboda ga bakin da muka gayyato sun fara isowa."yana gama fadar haka ya kashe wayar ba tare daya jira jin abinda sameer zai ce ba. Numfasawa sameer yayi ya juyo ya kalli sodangi da tun dazu shi take kallo,kuma ta fahimci da wanda yake waya,don haka sai ta tambayeshi,"abba neh koh?" Daga mata kai yayi yace,"idan ina tare dake sarat,wallahi mancewa nake da komai nawa na rayuwa." Kasa tayi da idanuwanta tayi murmushi tace,"yanzu dai mi Abba yace,don kada kasa muyi wani laifin." Sameer ya mike tsaye yana shafar sumarshi yace,"our guests har sun fara zuwa inji Abba." Salati sodangi tayi ta mike da sauri ta fara ridar kayan data harhada tana cewa,ba haka mukayi da Abba ba,ya kamata muyi sauri don kada ranshi ya kara bace." Da sauri suka fita suka nufi inda suka tana da don ajiye bakinsu,aikuwa mamaki ne ya kamasu saboda yanda suka ga wurin kusan cike da jama a sai kai da komowa sevants din su sukeyi. Daga kan da zatayi sai ta hango safwan acan kan high table inda aka ajiye manyan baki, shi kanshi tunda ta shigo hall din yake kallonta,shi yasa taji ajikinta. Ganin safwan sai da gabanta ya fadi,saboda bata taba tunanin zai halarci wannan taron ba na karamin kamfani kamar nasu,duk a zatonta ko daga shiyyarshi wasu zasuzo sai dai yayi aiken yaranshi. Dakewa tayi taci gaba da hidimar ta kamar yanda kamfanin ya tsara mata,saboda ita da sameer sune masu gabatar da duk wani abu na kamfanin. Shi kuma sameer yana nan kafa da kafa da sodangi,komin su atare sukeyinshi gwanin ban sha awa,amma gasu safwan da fa iza su basuga abib birgiwa ba sai ma haushi da suke basu. Fa iza ce ta nufi table din da Hajiya maryam take zaune da kawayent,amma daka gansu kasan duk zubin yan duniya ne,saboda babu wata mai shigar mutunci da zaka fidda. Hajiya maryam tana murmushi ta tari fa iza,saboda bata son magana ta hadata da ita gaban wani don bata son aji sirrinsu,"ya akayi neh fa iza,naga fuskarki baki cikin walwala kamar yanda na saba ganinki?" Fadar Hjy maryam. Fa iza ta kara yamutsa fuska tace,"kwanaki na kawo maki karar sameer da waccar abokiyar aikin tashi kikace mani babu wani abu atsakaninsu,toh yau na kamasu dumu dumu acikin soyayya 😭😭😭 Hankalin Hjy maryam ya tashi tace,"what ??😳 hakan bazata yiwu ba har sai idan kece kikace mani kin fasa,toh ni kuma sai in sake neman wata in hadasu,harda dama ganin da nayi ke kina sonshi sosai shiyasa zanyi amfani dake don cikar gurina." Gaban fa iza ne ya fadi,saboda duk sadda Hjy maryam tayi irin wannan maganar tayar mata da hankali take,saboda ita dai tasan tana son sameer da zuciya daya shine baya damuwa da ita shiyasa har tayi tunanin bi ta hannun Hjy maryam don ta samu karbuwa awajen iyayenshi,kuma haka akayi kuwa saboda Hjy maryam sai da ta shiga ta fita har Alhaji yunus yayi amanna da maganar fa iza. Fa iza ta kalli Hjy maryam da raunanniyar zuciya tace,"wallahi har yanzu inason shi har acikin raina,shi kuma ko ada bai son sodangi toh yanzu ya fara sonta." Hjy maryam tayi murmushi tace,"toh idan har kin yarda dani inason kije ki kwantar da hankalinki,saboda aure babu fashi sai anyi shi." Wani farin ciki neh ya kama fa iza har sai da tayi dariya tace,"na gode mummy." Hjy maryam itama murmushin take taci gaba da cewa,"yanzu dubara ta rage taki sai kije kiyi yanda kika raba su kamin lokacin bikinku yazo,kuma kema sai kinje kin rinka shige mashi ko yana ko baiso. Godiyya fa iza tayiwa Hjy maryam ta komawa sit din zamanta. Ayyuka sun dan natsawa sodangi ta dan samu wuri ta raba don kafafuwanta su huta da zaryar da sukayi tayi ayau. Kasa daurewa tayi ta daga idonta ta kalli inda safwan yake,ilai kuwa shima din kallonta yake,kuma cikin tausayi,saboda duk akan idonshi yaga irin hidimar da takeyi,"sorry,"yace mata in silent, amma bakinshi da take kallo ne yasa ta gane abinda ya fada. Haka nan kawai sai taji dadin tausaya mata da yayi, hannunta ta sa akafarta tana murzawa ahankali saboda tafiya da high hill dole kafa tayi ciwo. sake daga kai tayi ta kalleshi cikin dubara tana mashi wani irin murmushi,wanda ita kanta bata san tana yinshi ba. Motsa bakinshi ya karayi yace," ko inzo inyi maki massege?"fahimtar abinda yace yasa ta zaro idanuwanta tare da gyara zamanta ta girgiza mashi kai. Sallamar da akayi mata ne yasa hankalinta ya dawo jikinshi ta dago da sauri tare da amsawa,wata kyakkyawar yarinya ta gani akanta tsaye. Sodangi tayi murmushi ta bata damar zama kusa da ita,gaisawa sukayi sannan yarinyar tace,"sunana Humaira sulaiman." Love you sis😘 08033481518 [4/18, 9:42 AM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 43 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 Sodangi ta kalleta sosai taga dai bata santa ba,amma saboda tasan ko kan kayan da tayi tallarsu dazu dole ne su samu customers, don haka fuska asake ta amsheta tace,"ni kuma sunana sarat Abubakar sodangi in braket." Kada kanta Humaira tayi ta sake daga kanta ta kalli wurin da safwan yake taga dai har yanzu sodangi yake kallo,wani sabon kishi ne ya sake turnuko mata ta kalli sodangi tace,"acikin kayan da kika yi mana tallarsu akwai wata gown ta material, gaskiya ta burgeni kuma Ina son kiyi mani ita zanyi amfani da ita wajen kamu,sai shi kuma angon kiyi mashi nashi zubin irin nasu na maza wanda kika san zasu kayatar." Sodangi tayi murmushi tare da numfasawa tace,"duk babu matsala,yaushe ne bikin naku?" Humaira ta kalli sodangi ido cikin ido tace,"end of this mouth ne." Sodangi ta bude idanuwanta tana murmushi tace,"ah abin yazo kusa,kinga idan da angon yana kusa da sai in gwadaku tunda ayanda na lissafa bai wuci two weeks ba. Humaira tana dariyar mugunta ta kalli sodangi tace,"kin san duk inda zani muna atare,saboda barci ne kadai yake raba mu". Sodangi ta jinjina kanta tana murmushi tace,"that's good Humaira,ai haka akeso,don haka kiyi mashi magana don inga size dinshi." Daga idanuwanta tayi ta kalli inda safwan yake ta nuna mata shi da danyatsa tace,"kinganshi can." Gaban sodangi ne ya fadi,saboda bata taba zaton shi zata nuna mata ba,don haka sai kawai taji ta rikice ta mike tsaye tana kallonshi. Shi kanshi daga inda yake duk ya fahimci abinda yake faruwa don haka sai ya tashi ya bar wajen. Sodangi jiki asanyaye ta koma ta zauna tana mayar da numfashi. Humaira tayi dariya,sannan ta harari sodangi tace,"kada dai ace kema ya burgeki kamar yanda naji sauran mata suna cewa?" Sodangi ta numfasa ta dago ta kalli Humaira tace,"sam bai burgeni ba,tausayi kawai kika bani,saboda safwan mayaudari neh,ko ya taba fada maki yana da wata matar bayan ke?" Humaira ta zaro yan kananan idanuwanta gaba daya tace,"what?mata fa kika ce,No impossible abinda bazai taba yiwuwa ba kenan." Cikin fushi ta mike tsaye tana huci saboda wani malolon kishi neh ya taso mata ta kalli sodangi tace,"wacece matar,don yau bazan iya yin barci ba har sai nayi tozali da ko wacece." Sodangi da takeji kamar ta maketa don haushi,saboda yanda ta kagara ta matsa daga gabanta don ko son ganinta bata sonyi tace,"kije ki tambayeshi,saboda awurinshi neh kawai ya kamata kiji wannan amsar." Cikin fushi Humaira ta juya har tana shirin faduwa don sauri ta nufi inda take tunanin zata ga safwan. Tana tafiya sodangi ta dafe kanta dataji ya somayi mata ciwo,saboda dama ga gajiya sannan kuma ga tension din da Humaira tasa mata. Mikewa tayi ta nufi dakin da suke hutawa,tana tafe tana rangaji kuma kusan idanuwanta arufe suke saboda babu wanda take gani sai duhu. Cikin taimakon ubangiji ta samu ta isa dakin ta tura kofar,kai tsaye doguwar kujerar dake dakin ta nufa ta samu ta kwanta. Tsananin tunani neh ya dameta saboda zuciyarta gida biyu ta rabu,dayar tanayi mata kashedi da ki fita harkar safwan saboda ba sa anki ba ne yafi karfinki,kuma koda kin koma mashi zai iyayi maki fiye da abinda yayi maki abaya. Numfasawa tayi ta mayar da idanuwanta ta rufe,sai dayar zuciyar ta bijiro mata,"kina nufin zaki iya rayuwa idan baki tare da safwan?safwan shine ginshikin rayuwarki,madogararki abin so da kaunarki,dan da baki son ganin wata diya mace ta rabeshi,kuma gashi mahaifin yar ki da baki da kamanta acikin fadin duniyar nan." Kara matse idanuwanta tayi,saboda babu tunanin dayafi wahalar da ita irin wannan. Har ya shigo dakin bata sani ba,saboda dogon tunanin data fada aciki,domin ko kamshin turarenshi yau bataji ba har ya tsugunna agabanta. Zuba mata idanuwanshi yayi yana kallonta,ayanda take yamutsa fuskarta ga hannunta daya dafe da kanta ya gane lallai akwai abinda yake damunta. Hankalinshi ne yaji yadan tashi,tare da tunanin kodai Humaira ce ta fada mata wani abun da zai tashi hankalinta,idan kuwa har haka neh ayau sai yayi maganinta. Duka hannuwanshi biyu ya dora abisa kan sodangi,side to side ya rinka murza mata jijiyoyin kan ahankali cikin dubara har sai da taji tunaninta ya fara dawowa normal sannan ta fara fahimtar abinda yake faruwa. Bude idanuwanta tayi a hankali tana kokarin ganin wanene kusa da ita,shi kuma ganin yanda idanuwan da yakeso da gani yaga yanda suka canza kala yasa ya firgita,don haka ganinshi da tayi sai ta fara kokarin tashi shi kuma da sauri ya riketa yana tambayarta,"mike faruwa dake sodangi?jibi idanuwanki yanda suka canza,miya same ki?" Ganin yanda safwan ya rude yasa ta zuba mashi ido kawai tana kallonshi,sai da ya gama duddubata yaga babu inda take da rauni sannan shima ya tsayar da idanuwanshi akanta,sam baida yanda zaiyi,amma kwatata baya son ganin yanayin da idanuwan sodangi suka koma,amma haka nan dai ya daure yaci gaba da kallonta. Kallon da sodangi takeyi mashi kallo ne wanda yake kunshe da tsanin so da kauna da kuma neman atausaya mata,don haka shima haka ya zuba mata nashi idanuwan da yakeji kamar ya jawota ya rungume ya lashe abinshi tas saboda irin abubuwan dayaji suna ratsa mashi ta cikin bargo da jinin jikinshi. Numfasawa sodangi tayi tadanyi kasa da idanuwanta daga kallon da takeyi mashi tace,"ka tashi daga gaba na,because I don't want to see you in front of me." Madadin yayi abinda tace sai yayi caraf ya riko hannunta ya rije kam acikin nashi hannun yaci gaba da kallonta tare dayin kasa da murya yace,"ni kuwa kece kadai hasken idanuwana,kuma babu abibda nakeso da gani irinki,don haka babu inda zani har sai kin fada mani damuwarki." Yanayin data faraji ne yana ratsa mata jiki ta dalilin murza hannunta da safwan yakeyi acikin nashi yasa ta fara kokarin janye hannunta,amma shi kuma yaki sakinta. A hassale ta mike tsaye,shima da sauri ya mike tsayen saboda ya fahimci so take ta rikitashi,saboda sam baya son abinda zai tashi hankalin sodangi koma minene shi abin. Jawota yayi a jikinshi yana kallon idanuwanta yace ,"bazan sake kiba har sai kin fada mani abinda ya sameki,idan kuma ba haka ba,wannan janbakin dake bakinki sai na lashe maki shi tas,tare kuma da worning dinki duk ranar da kika kara shafashi idan har ba a cikin gidana ba toh ko agaban wanene sai na gogeshi da nawa bakin." Abinda taji ya fada ne sai yasa jikinta ya fara rawa tace,"wacece Humaira?kuma miyasa kasan kana da Humaira kakeson yin yawo da hankalinah?" Wani irin kayataccen murmushi yayi ya kalleta ido cikin ido yace,"are you jealous sodangi?" Sodangi ta dago ido ta kalleshi da sauri tace,"Allah ya sawwake,akan mi zanyi jealous akanka?just kawai ina son in fada maka cewar kaje ka auri Humaira kamar yanda ta fada mani ni kuma ka rabu dani,please ka bar zuciyata ta huta πŸ‘πŸ‘ Babu abinda yace mata sai kara jawota da yayi ajikinshi,hannu yasa ya lakaci wata kwalla data biyo gefen idanuwanta ba tare data sani ba ya dago ya nuna mata yace,"sodangi please ina son ki taimakeni ki ajiye duk wani abu daya wuce agefe,saboda sam bana son ta dalilina kici gaba da zubar da hawaye.ada can kinyi kuka saboda ni kuma still yanzuma gashi kina kuka saboda ni,don Allah komai ya wuce atsakanin mu ki amince dani injiyar dake da dadi na har abadan abada." Yana gama fadar haka yakai bakinshi ga idanuwanta ya sumbace su daya bayan daya sannan ya rungumeta ajikinshi yana mayar da numfashi. Tun shigar safwan adakin hutu inda sodangi take sameer yani bayanshi,kuma duk irin maganganun da sukayi da abinda ya faru duk akan idanuwanshi,don haka safwan yana rungume sodangi sameer yayi sauri yaja baya saboda ayanda yakeji idanuwanshi ba zasu jure ganin safwan da sodangi ahaka ba. Love you sis😘 08033481518 [4/18, 9:46 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 44 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 Karar Wayar sodangi ce ta tsayar da safwan ga yunkurin rungumeta,saboda gaba daya ta tureshi ta nufi hand bag dinta dake kan table din farko da shigarka dakin,bude hand bag din tayi ta jawo wayar,ganin sunan yaya sadah akan screen din ne kawai sai taji gabanta ya fadi,don haka wayar tana shirin tsinkewa ta samu ta dauka saboda dadewa da tayi tana ringing din. Babu sallama bare gaisuwa sadah yana samu sodangi ta dauka yace mata kina ina? Sodangi adan tsorace tace,"ina wajen aiki,lfiya dai koh?" Sadah ya numfasa yace,"da sauki sodangi,saboda ayau ardo ya gane sirrin dake rufe na afnan." Sodangi tayi salati da karfinta wanda har yaja hankalin safwan ya juyo yana kallonta cikin adan firgice. Sodangi tace,"ya akayi har kuka bari haka ta faru,kuma yanzu ina afnan din?" Sadah ya numfasa yace,"muna cikin daki nida molasa muna maganar afnan,ashe ardo ya dawo mu bamu sani ba,kuma acewar shi wai har sallama yayi mana bamu amsa ba,toh daya taho sai yaji duk zancen da mukeyi,kai ardo jiya yayi iyakar wulakancin sa son rai,ni kuma ganin haka sai kawai na daukota na maidota bichi wajen goggo laura na koma ajiyan. Dan numfawa yayi sannan yaci gaba da cewa,yau tunda safe naga ardo yana shiri sai kawai jikina bai bani ba har ya bar gidan. Daga baya nima da tunani ya dameni sai kawai na taho bichin,ai ina shiga na iske goggo laura tana ta kuka wai ardo ya dauke afnan yace gidan marayu zai kaita." Yana kawowa nan sodangi ta fashe da kuka tare da kashe wayar ta jefa jikka,gyalenta ta dauka ta zira takalminta ta dauki jikkar tayi hanyar fita. Safwan da bai gane abinda ya faru ba ya biyo bayanta da sauri ya riko hannunta yana cewa,"mi yaya sadah din yace maki? Mi ya sami ardo din?" Juyowa tayi tana kallonshi,kuma sai takejin kamar ta fada mashi ko ya taimaka mata,amma kuma sai ta fasa saboda tana ganin muddun yasan da afnan rabata da ita zaiyi,ita kuma tana ganin ba mai rabata afnan sai Allah,saboda duk kiciniyyar da takeyi duk saboda afnan takeyin shi,domin bata son yar tata tayi maraici ko ta nemi wani abu ta rasa. Fisge hannunta tayi tayi waje ba tare data kara saurarenshi ba,fita tayi bakin titi sai fama take da yan adaidaita don ta samu akaita tasha,amma abin kamar hadin baki babu mai tsayawa. Motar safwan ce ta gani agabanta ta tsaya,amma bashi bane aciki sai babban yaronshi,fitowa yayi yazo kusa da ita yadan rusuna ya gaisheta,sannan yaci gaba da cewa,"oga ne yace inzo in kaiki inda zakije." Ada kin shiga tayi,amma da ta fahimci lokaci sai kara tafiya yake kawai sai ta fada cikin motar shi kuma yaja suka nufi bichi. A kofar gida suka sami sadah atsaye duk ya hada zufa sai sintiri yace kamar mai exercises, ganin sodangi yasa ya nufeta harda dan gudunshi yace,"duk cikin bichi babu gidan marayun da banje ba,amma banga afnan ba." Roshewa da kuka sodangi ta sakeyi ta nemi zube mashi yayi maza ya kamata sukayi cikin gidan goggo laura. Sun jima azaune suna jimamin lamarin,kuma duk daga cikinsu babu mai iyayin maganar kirki sai dai sharben kuka da sodangi da goggo laura sukeyi. Wayarshi sadah ya fiddo ya kira molasa,da tuni sodangi ta saya masu ita da ardo,tana dauka yace mata,"ardo ya dawo?" Molasa tace,"bai dawo ba,amma tun dazu nake nemanshi wayar tashi arufe take." Kashewa yayi kawai don dama babu abinda yayi niyyar fada mata,saboda tana da hawan jini,yasan muddun taji cewar ardo ya dauke afnan hankalinta sai yayi mugun tashi. Mikewa yayi ya kalli sodangi yace,"tashi mu shiga garin kano mu bincika gidajen marayu ko acan ya kaita. Babu musu ta mike,ita kuma laura tabi su da adduar Allah yasa a dace su ganta. Gaba daya sukace ameen,sannan sukayi waje,ganin har yanzu motar da yaron safwan ya kawota tana nan yasa sodangi tayi hamdala acikin ranta. Babu inda basu shiga ba agarin kano,sukayi yawo har suka gaji amma basuji duriyar afnan ba har wajen goman dare. Gidansu surayya sodangi tace ya kaisu,haka kuwa akayi,yana ajiyesu sadah yayi mashi godiyya duk da bai san kowane shi ba. Mutanen gidan su surayya mutanen kirki ne matuka,saboda ganin yau harda sadah agidansu sai dawainiyya ta karu, ita kuwa surayya abin ba acewa komai saboda kamar tafi kowa farin ciki duk agidan,domin tanajin sadah har acikin ranta haka nan bata san dalili ba,amma bata taba fadawa sodangi ba sai dai itama sodangin tana fahimtar haka duk ranar da sukaje da surrayya daura,amma jin batan afnan sai da duk wanda ke cikin gidan ya girgiza saboda rudewa. Ayau dai haka sodangi tayi kwanan bakin ciki,saboda ayanda tace,wannan shine abu na biyu da bazata mance arayuwarta ba. Washe gari,tunda wuri sodangi ta nufi wurin aiki don ta dauki excuses, sannan ta dawo su fada gari suci gaba da neman afnan ita da sadah. Shigarta office ba dadewa sameer ya shigo ya nufeta fuskarshi ba yabo ba fallasa,wuri ya samu ya zauna tare dazuba mata idanuwa yana kallonta cikin tuhuma yace,"jiya ina kika tafi with out taking permission?" Sai alokacin ta tuna kuskuren da tayi,don haka sai tayi kasa da idanuwanta tace,"I'm sorry my boss πŸ‘ Wallahi arude na fita daga company nan,saboda wata my relative dita ce ta bace shine muka tafi nemanta." Dan shiru yayi yana nazarin maganarta sannan ya sake tambayarta da cewa,"ranar da mukaje interview company su safwan,akwai wata magana da yayi yace,"baki fada mani abinda ke tsakaninku ba,kikace mani you just a friend,amma ni abinda na gani jiya a resting room zuciyata ta gaza natsuwa,kuma sai nake kokonton abinda kikace,please ina son ki fitar dani daga duhu." Sodangi tayi shiru tana sauraronshi,sannan kuma ta rasa shin wacce irin amsa zata bashi,ahankali ta dago ta kalleshi tace,"I will explain you everything, but ba yanzu ba saboda sam bani da kwanciyar hankali,shiyasa ma nazo in dauki permission awajenka." Sameer ya zuba mata ido kawai yana kallonta,saboda abinda yaso shine sodangi ta fitar dashi daga tunanin daya dameshi,amma kuma tunda har tace mashi haka,watau kenan dai din akwai wata akasa. Numfasawa yayi yace,"shikenan zaki iya tafiya,amma kuma ki sani duk sadda muka sake haduwa zakiyi mani bayanin tambayar da nayi maki." Sodangi ta mike tare da jinjina kanta,alamar ta yarda sannan tayi mashi ban kwana ta fita. A can gefen company ta hango ire iren motocin safwan,kauda kanta tayi taci gaba da tafiyar,horn taji abayanta sannan ya matso kusa da ita yayi parking, cikin girmamawa ya fito daga motar yazo kusa da ita ya rusuna sannan ya gaisheta. Wani card ya fiddo ya mika mata yace,"dama boss yace,idan kin amince yana son ganinki." Kallonshi kawai tayi ta sake kallon card din taga yana dauke da full address na hotel din daya sauka,don haka ta kalleshi tace,"ka koma kace mashi ina da abinda zanyi,kuma bazai samu damar gani na ba." Babban yaro ya firgita dajin amsar da sodangi ta bashi don haka da sauri ya kara kasa da kanshi yace,"sorry madam,don Allah ki taimaka muje saboda kwata kwata bazan iya fada mashi amsar da kika bani ba." Dariya kawai tayi taci gaba da tafiyarta,ai kuwa cikin sa a ta samu adaidaita ta shige ta barshi nan wurin. Wunin yau ma haka su sodangi sukayi ta yawo babu wata nasara har ta gaji,wurin la asar suka fara tunanin komawa gida,kuma ayanzu sodangi ta fara tunanin son ganin safwan,saboda sai take ganin kila zai iya taimaka mata. Kallon yaya sadah tayi tace,"zan koma wajen aikina,amma bazan dade ba zan dawo,don haka kayi gaba sai in sameka agidan su surayya.. Tun anan suka rabu,sodangi ta fiddo dan card din da safwan ya aiko mata dashi taba mai adaidaita,shi kuma ya shiga dubawa yana bin address din har suka isa wani tafkeken hotel wanda duk agarin kano baida na dayanshi. Reception ta nufa ta fiddo card din ta mika masu,kai tsaye akasa wani ma aikacinsu har ya kaita bakin kofar dakin ya nuna mata sannan ya juya. Love you sis😘 08033481518 [4/20, 8:01 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 45 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 Shi kuwa safwan tunda ya samu sakon sodangi nakin zuwanta hankalinshi ya tashi,saboda shi duk azatonshi sodangi ta yafe mashi laifin dayayi mata,amma dawowar yaronshi sai duk gaba daya yaji jikinshi ya dauki zafi tamkar mai zazzabi,haka yayi kwance jikinshi ya mutu saboda tsananin tunanin daya tsunduma acikinshi. Ringing din da kofar dakinshi tayi yasa ya dawo daga dogon tunanin daya lula,zubawa kofar ido yayi tare da mamakin kowane ne yazo mashi adai dai wannan lokacin?saboda baiyi appointment da kowa ba. Ringing ta karayi ya tashi dakyar yana jan jikinshi har zuwa bakin kofar saboda gaba daya jikinshi yayi nauyi,ahankali ya bude kofar idanuwanshi atsaye don ganin kowaneneh,kuma cikin sigar bacin rai. Sodangi daya gani yasa ya saki fuskarshi tare da washe baki yadan matsa gefe kadan yace,"you're well come my dear." Sodangi ta yamutsa fuskarta ta kalleshi ranta abace,saboda duk gani take har mtslr afnan da take aciki duk shine sila,don hakasai cewa tayi,"ba sai na shigo ba,domin wasu tambayoyi ne kadai suka kawo ni inyi makasu." Numfasawa tayi ta zuba mashi duk idanuwanta taci gaba da cewa,"How you tossed me aside,when you let me go,did you feel that you'd regret it for life?" Dama jikinshi asanyaye yake,amma wannan tambayar da sodangi tayi mashi sai yaji kamar ya zubar da gwiwoyinsa akasa,don ji yayi gaba daya basu iya daukarshi.ga bakinshi yana motsi amma kalmar dazai furta ta gaza fitowa,can dakyar ya iya furta sunanta,"please sodangi ! Sodangi don't........... Ganin ya gaza iya furta komai tayi murmushin takaicin tace,"Never mind,I should get going."kawai sai ta juya rannan abace,dama kuma fuskarta gaba daya duk akumbure take saboda kukan datasha wajen neman afnan. Da sauri yayi ta maza ya cafkota ya rungumota ta bayanshi yana mayar da numfashi,ahankali muryarshi take fita,I regret it ! I regret it sodangi !! Please kada ki guje ni kamar yanda nayi maki abaya,na dade dayin nadama kamar yanda nake fada maki aduk haduwar da mukeyi." Kokarin kwacewa ta farayi ya kamata ya rike gam ajikinshi ta yanda bazata subuce mashi ba yana cewa,No! No sodangi,if there's a life after this one,I'll regret it in that one too,kuma Even if you want to hste me,please hate me at my side." Shiru sodangi tayi tana sauraronshi,idan banda hawaye babu abinda takeyi saboda tunanin afnan da kuma halin da take aciki,saboda ayau sun molasa,kuma ta tabbatar masu da cewa ardo ya dawo shi kadai ba tare da sanin inda ya kai afnan ba. Cikin dubara safwan ya juyota suka fuskanci juna,marairaicewa yayi yanda kasan zai fashe da kuka,saboda gaba daya idanuwanshi suka kada sukayi ja saboda tashin hankali yace,"please sodangi ki bani dama,saboda awannan lokacin nayi maki alkawarin rikeki da amana,kuma zan kula dake fiye da yanda ake rainon kwai,please stay with me sodangi." Lumshe idanuwanta tayi,sauran hawayen dake ciki suka tsiyayo,sannan ta budesu da kyar ta kalleshi tace,"why did you do that to me?saboda ina son in sani neh ko don agaba,nasha wuyar rayuwa duk saboda kai,nayi kuka mara adadi,sannan kuma adalilinka wanda baiji bai gani ba shima ya fada wahalar rayuwa." Tureshi tayi daga jikinta ta rinka dukanshi akirji,saboda tana ganin yin haka kamar zaisa ta samu safsafcin bakin cikin rashin afnan acikin zuciyarta,sai da tayi mai isarta sannan ta sulake ta zube kasa agabanshi taci gaba da zubar da hawaye,saboda muryarta har ta fara dusashewa don yawan kukan da take. Safwan kuwa, tunda sodangi ta fara dukanshi sai ya kame,yanda kasan gunki haka ya tsaya,saboda yayi amanna a rayuwarshi,idan dai har sodangi zata huce ga laifin da yayi mata,toh tama sa mashi dorina mai baki ishirin,amma bayan tace ta yafe mashi. Sheshshekar kukan da takeyi ne ya rinka ratsa zuciyarshi yana tsumashi,da sauri yasa hannu ya dagota,sannan yasa dan yatsanshi ya share mata hawayen dake fitowa yana girgiza kanshi,please sodangi kukan ya isa haka,kiyi shiru my sweet heart 😘 Love you sis😘 08033481518 [4/20, 10:26 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 46 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 Kiyi shiru my sweet heart, bazan kara ba."yana gama fadar haka ya ida jawota ajikinshi ya rungumeta yana shafar bayanta. Shiru tayi ajikinshi,shi kuma yaci gaba da rarrashinta har sai da yaji jikinta yayi sanyi sannan ya dagota ya kalli idanuwanta da duk suka kumbure,tausayinta neh yaji ya kamashi yaja hannunta zuwa gefen kujera ya zaunar da ita,sannan ya nufi dinning area inda ya tanadar mata lunch,don lokacin daya samu amsar baza tazo ba shi kanshi bai kara bi ta kansu ba sai yanzu. Jerasu ya dingi yi agabanta,don jikinshi har rawa yake. Sai awannan lokacin sodangi taji tausayinshi ya kamata,saboda tuna matsayinshi da kamalarshi,amma gashi agabanta har yana karkarwa kamar karamin yaro. Binshi take kawai da idanuwanta,shi kuma sai kaiwa da komowa yake,don karshe har rasa abinda zai aje yayi. Mikewa tayi ta nufeshi ta rike hannunshi tace,"na gode da kulawarka,amma kabarshi hakanan, saboda duk abubuwan da ka ajiye babu abinda zan iyaci sai ruwa." Tsayawa yayi kawai yana kallonta,csan ya numfasa yace,"sodangi ko baki huce ba neh?" Kara matsa yatsun hannunshi tayi tana murmushi tace,"na yafe maka safwan,sai dai........... Wani farin ciki neh ya lullubeshi don har bai san lokacin daya rungumeta ba,kuma fuskar nan tashi awashe sai dariya yakeyi,dagata sama yayi ya rabata da kasa sannan ahankali ya sulalota ajikinshi har ya sauketa,amma idanuwansu atsaye akan junansu,sun jima suna kallon junansu safwan ya kalli bakinta ya hadiye miyau,nan take ta fahimci abinda yake niyyaryi,don haka sai tace,akwai wata matsala guda daya,watau ardo." Safwan yayi murmushi yace,"kada ki tayar da hankalinki,saboda nafison daga yau ki dore cikin farin cikin rayuwa,kuma zancen ardo duk irin hukuncin da zai yanke mani ni bazan ga laifinsa ba,saboda na can canci punishment mai tsananiiii......... Wuf tayi ta rufe mashi baki da hannunta tana girgiza kanta tace,"ni kuma ai bazanso inga kana wahala ba,mudai kawai muyi adduar komai zai zo yazo mana da sauki." Hannun data dora mashi a baki sai yayi cak saboda taushin hannun sai yaji kamar ya rinka sidar yatsun da tsananin kaunar da yake mata. Yanayinshi neh da ya fara canzawa sodangi tadan firgita da sauri ta janye jikinta daga nashi,wurin kujera ta nufa ta zauna da sauri ta zuba lemu acup ta fara sha,amma idanuwanta akasa don bata son kallon yanayin da safwan ya koma. Jiki asanyaye yazo kusa da ita ya zauba,don haka shima sai ta zuba lemun ta mika mashi,murmushi kawai yayi ya amsa yana kallon cup din,amma bai sha lemun ba. Sodangi ce ta numfasa tace,"yaushe ne ka fidda don kaje kaba ardo hakuri?" Safwan yayi kasa da murya yace,"ko yanzuma zan iya zuwa."sodangi tayi murmushitac,"banda yanzu safwan." Shima murmushin yayi yace,"gobe insha Allahu zanyi tafiya zuwa Holland, saboda wani business ne zai kai ni,duk sauran tafiya yaranah nake tura masu ko kuma yaya yusuf yaje,toh wannan karon ne sukace basu amince ba ni suke son gani,kuma tafiyar bazata wuce sati biyu ba insha Allahu,then dana dawo ni kuma zan dira agaban ardo don ya bani matata,saboda akagare nake akanki sodangi." Zumbur tayi ta mike tsaye saboda jin maganqr da yayi sai taji tsoro ya fara kamata saboda tsaf babu abinda ta mance game da halinshi arayuwar aurensu,don haka sai tace mashi,"tafiya zanyi,sam nama mance yaya sadah nacan yana jirana, kuma yau komin dare daura yakeso ya kwana." Safwan yayi murmushi ya kalli agogon hannunshi yaga kwata pass six, don haka sai ya mike tsaye shima yana lalubar key din motarshi yace,"yau kuwa sai yaya safah ya hukuntaki,saboda kinzo kin hadu da masoyinki ki manta dashi."yana maganar yana dariya irin ta tsokana. Tafe suke ahankali,saboda safwan ji yake kamar kada ya rabu da sodangi,sannan kuma ga go slow,saboda maraice da yayi. Sai da magriba tadan gota kadan gari har yayi duhu sannan suka iso sallari,sunzo har zasu wuce don su nufi kwanarsu surayya sai sodangi ta hangi yayanta sadah sai dube dube yake kamar mai neman wani. Da sauri sodangi ta nunawa safwan shi,don haka sai yayi parking abakin hanya duk suka fito daga cikin motar. Yaga ana tunkaroshi,kuma ya gane dodangi amma bai gane wanda suke tare ba har sai da suka iso,sai yaji gabanshi ya fadi saboda safwan ya gani. Dakewa yayi da sukayi mashi sallama ya amsa,safwan ne ya mika mashi hannu suka gaisa sai fara a yake mashi, sodangi kuwa ganin haka sai taji dadi sosai,saboda daga cikin wadanda hankalinta yake tashi harda yayanta sadah,amma hakan da yayi sai taji kamar ta rungume dan uwanta don farin ciki. A kasa suka ida takawa har kofar gidansu surayya,sannan sadah ya kalli sodangi yace,"zan tafi gida,komai kenan sai kinji ni awaya." Godiyya tayi mashi sosai sannan ya bata umurnin ta shiga cikin gida saboda dare yayi,kuma ya kamata ta huta hakanan. Dago idanuwanta tayi ta kalli safwan,taga shima ita din yake kallo,sai sadah ya danyi gaba yace,"kuyi ban kwana ni zan wuce,amma kamin in tafi inason in ganka safwan."yana gama fadar haka yayi gaba abinshi. Safwan da tun dazu idanuwanshi na kan sodangi yace,"toh baby sai na dawo kenan koh?" Sodangi tayi mashi addu a sosai shi kuma yaji dadi ya rinka amsawa har yana lumshe ido.data gama sai ya dan kashe mata ido yace,"saura hugging din ban kwana."yana fadar haka ya mika mata hannu wai tazo ya rungumeta. dariya kawai tayi ta shige cikin gidansu surayya ta barshi nan da hannu a sage. Murmushi yayi ya kada kanshi ya tafi,sai alokacin ya tuna da yaya sadah yana jiranshi,don haka sai ya kara sauri,ai kuwa ajikin motarshi ya sameshi yana jiranshi. Safwan yana zuwa cikin girmamawa ya mikawa sadah hannu wai su kara gaisawa ta yaushe rabo sai kawai sadah ya daukeshi da mari kyawawa guda biyu. Love you sis😘 08033481518 [4/21, 6:22 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 47 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 Safwan dafe dukka kumatunshi yayi saboda wani azababben radadi dayaji sun ratsa shi a lokaci daya,ahankali ya dago ya kalli sadah cikin nadamar abinda yayi masu yace,"ko da yanka ni kayi,ni bazanga laifinka ba,saboda nasan pain din da sodangi taji kai ma ya shafe ka,don haka kaci gaba da mari na har bakin iyakar dakaji ka huci daga fushin da kakeyi dani." Yaya sadah ya kalli safwan cikin takaici tare da girgiza kai yace,"ina son ka sani,wallahi banyi farin cikin ganin ka ba ayau,kuma duk kan alamomin dana gani,ka kara yaudarar mani yar' uwa koh?" Numfasawa yayi sannan yaci gaba da cewa," watau ka fahimci yanda take sonka da yawa koh?toh ka sani a wannan lokacin bazan bari ka sake maimaita abinda kayi mata ba,don haka nake son ka gaggauta barinta,idan kuma ba haka ba wallahi duk abinda nayi maka kayi kuka da kanka,don nasan bai wuci ace za a kamani akulle a prison ba don na taba ka,idan dai har bukata ta ta biya to komin ta fanjama fanjam." Yana gama fadawa safwan abin yake acikin cikinshi sai kawai ya kama gabanshi yaci gaba da tafiya cikin kunan rai,saboda yau hatta da sodangi ji yake kamar ya koma ya bata kashin tsiya,domin ya lura sam bata da zuciya. Shi kuma safwan ya jima tsaye ajikin motarshi yana nazarin maganganun da sadah ya fada mashi,watau tsugunne bata kare mashi ba,domin yana ganin kamar matsala ta kare tunda sodangi ta hakura kuma har ta yafe mashi, ashe abin ba haka ba ne.numfasawa yayi tare da bude bude motarshi ya zauna jiki asanyaye ya fada acikin ranshi,komin rintse da wuya,sodangi bazan bari a raba ni dake,idan kuma har sukaki amincewa dani toh lallai kuwa zasu ga matakin da zan dauka,don sai sun gwammace kida da karatu." Wani murmushi yayi sannan yaja motarshi cikin kwanciyar hankali ya sulala ya bar wajen. Washe gari sodangi ta tashi cikin yar wal wala,duk da bata san halin da afnan take aciki ba,amma zuciyarta sawai take. Cikin dan kankanin lokaci ta gama shirin tsaf ta fito,surayya dake ta duminiyya ita har yanzu bata gama shiryawa ba ta daga kai ta kalleta tace,"sodangi wai saurin miye haka kikeyi,har bazaki tsaya kiyi breakfast ba." Sodangi tayi murmushi tace,"kinga jiya ban zauna aiki ba,don haka nasan aiki na can jibge akan desk dina,shi yasa nakeso inje da wuri don in samu in kammala shi in time." Surayya tayi dariya tare da yar harararta tace,"kaji agogo sarkin aiki,amma kuma anyi aiki ciki ba komai?" Sodangi ta kalli surayya akagare tace,"kada ki damu kawata,idan naje office nayi breakfast din." Tana gama fadar haka tayo waje ta nufi dakin mahaifiyyarsu surayya. Durkusawa tayi har kasa ta gaisheta,sannan ta mike tace mata,"ummah zan wuce wurin aiki." Itama taso ta tsayar da sodangi,amma data fada mata uzurinta sai ta kyaleta sannan kuma tabi ta da addu a,wannan hali na mahaifiyyar surayya yana burge sodangi,gashi bata raba daya biyu atsakaninta da yayanta,don wani lokacin ma sai tayiwa sodangi abu ba tayi wa surayya ba,shi yasa itama sodangin take tsaye wajen taimaka mata ga duk abinda take bukata tunda su surayya marayu ne,saboda mahaifinsu ya rasu can shekarun baya. Tunda dan adaidaita ya ajiyeta wurin company su take zafga sauri,don haka babu bata lokaci ta isa office dinta,sai da ta gama gaisawa da na kasa da ita sannan ta kalli office din sameer,alamomin da ta gani neh ta fahimci bai kai ga isowa ba,don haka sai ta shige nata office. aiki tayi sosai ba kama hannun yaro,ai kuwa nan da nan ta kammala tsohon aikin dake kanta,don shi kanshi aikin yau din taci karfin shi. Around 12:00 sameer ya karaso ma aikatar,saboda akwai wasu abubuwa da suka kare yayi odarsu,toh ayau ne aka basu tabbacin isowar kayan shi yasa yayi sakko ya nufi filin jirgin don komai ya sauka akan idonshi,don haka agajiye ya dawo,kanshi tsaye office din sodangi ya nufa yayi knowking. A can kasa yaji amsawarta,don haka sai ya bude kofar ahankali tamkar mai shirin kama wani abu ya shiga. Hango ta yayi cikin tulin kaya duk tayi wujiga wujiga sai aiki take kamar yar ina da aiki. Kyalkyacewa da dariya yayi har yana nunata da dan yatsa yana cewa,"wallahi sodangi kin iya over working,dubi duk yanda kika koma kamar mai jin yunwa." Zuba madhi ido tayi tana kallonshi da mamaki,watau ashe sameer ya iya dariyar mugunta,don Allah jibi yanda har wani tsalle yake don dariya. Kin tanka mashi tayi har sai da yayi mai isarshi,sannan ta dafe kanta tace,"wallahi sai yanzu na tuna da ban sanyawa cikina komai ba,"wai sai alokacin kuma ya daure fuska zai farayi mata fada,"so kike ciwo ya kamaki neh?kuma sau nawa kikeso na fada maki." Cikin fushi yayi waje ya tura daya daga cikin ma aikatanshi yaje ya hado masu abinci shi da sodangi. Cikin dan lokaci kankani sai gashi da manyan ledoji guda biyu yazo ya ajiyesu akan table cikin girmamawa. Sallamarshi sameer yayi sannan ya umurci sodangi data taso tazo suci abincin saboda shima yunwar yakeji,don taka maimai shima yau bazaice ga abinda yaci ba. Babu musu ta taso tazo ta zauna,shi kuma ya zazzage ledojin duka ya dingi tura mata agabanta tana ci,sai da ya tabbatar data koshi tayi dam sannan ya fara cin nashi,amma idanuwanshi suna kanta. Dagowa tayi ta kalleshi suka hada ido sai yayi mata murmushi tare da daga girarshi yace,"yah ina labari,don bai kamata ki mance da alkawarin da kikayi mani ba." Sodangi tayi kasa da idanuwanta,kuma sai taji gabanta ya fadi,saboda duk da son safwan yayi zarra acikin zuciyarta,amma kuma bata son abinda zai tashi hankalin sameer domin yayi mata halacci a dan zaman da tayi dashi. Shirun da tayi ne yasa sameer ya tsaya cak da cin abincin ya kura mata ido yace," ke nake sauraro." Sodangi tayi murmushin karfin hali ta kalli abincin gabanshi tace,"ka gama cin abincin mana,kaga sai muyi maganar da zamuyi." Sameer yasa hannu ya ture abincin dake gabanshi yace,"idan dai wannan abincin neh zai hana afada mani abinda na kwana ina tunaninshi toh na koshi." Sodangi ta bata ranta ta juya mashi baya tace,"ni kuma idan har bazaka ci abincin ba,toh babu abinda zakaji daga gareni." Fushin da sodangi tayi yasa sameer ya matso da abincin ya rinka cin shi ba don dadi ba,hakanan yayi ta cusa shi saboda gaba daya dama tun jiya jikin shi yayi sanyi akan lallai akwai wani abu atsakanin safwan da sodangi kamar yanda ya fara zargi. Love you sis😘 08033481518 [4/21, 8:53 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 48 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 Dariya yaso ya bata,amma ta gumtseta tare da kauda kanta gefe daya tasha mur,saida taga ya gama ta taimaka mashi ta zuba mqshi ruwa ya wanke hannunshi fes sannan ta tura mashi cup din lemu agabanshi ta gyara zamanta ta fara cewa,"nasan ko ba dade ko ba juma dole wannan ranar zatazo,amma inason ka kwantar da hankalinka kuma ka sanya wa ranka cewar ita matan mutum kabarinsa. Dam sameer yaji acikin zuciyarshi,kuma nan da nan wani zafi ya taso mashi sai ka rantse dakin babu Ac ko fanka,firfita ya fara da wasu takardu da suke agabanshi. Ita kanta sodangi bata so ganin abinda yakeyi ba,don haka sai tayi shiru har sai da ya dawo cikin hayyacinshi yace,"ya kikayi shiru? Kici gaba kawai." Sodangi ta numfasa ta kwashe duk rayuwarta da tayi da auren safwan ta fadawa sameer sannan kuma ta fada mashi wannan hoton daya taba gani na afnan diyar ta ce. Gaba daya wutar lantarkin dake jikin sameer ta dauke mashi saboda har numfashinshi yaji yana shirin daukewa,da kyar ya samu ya dai daita. Kifa kanshi yayi akan table din dake gabanshi yayi shiru ya fada cikin tunani kala kala. Kyaleshi sodangi tayi,saboda sam batayi wani yunkurin yi mashi wata magana ba,domin tasan dole ne duk wanda ta fada mawa cewa ta taba aure har ta haifi diya,sai shock ya kamashi. A hankali ya dago kai ya kalleta,murmushin da yayi mata ne ya daure mata kai,saboda tasa uwaka ubanka zasuyi ita dashi,don haka sai ta bude gaba dayan kunnuwantaπŸ‘‚πŸ‘‚don taji abinda zai ce. Numfasawa yayi yace,"yanzu abinda na fahimce ki shine,so kike ki koma gidan safwan tunda he's your ex husband?kuma gashi har ya baki baby koh?" Gaza amsa mashi tambayarshi tayi kawai sai tayi kasa da kanta saboda wani irin kallo da yake bin ta dashi,sun dan dauki dan lokaci wurin tsit babu wanda ya sake yin wata magana,sannan ta dago kanta still dai ita yake kallo kuma bata san abubuwan da yake kiyastawa acikin zuciyarshi ba,don haka sai ta kauda kanta gefe daya tace,"why not bazaka auri fa iza ba,saboda dai ita fa iza duk da ta girmeni amma kaga ai budurwa ce ba kamar ni ba da har............. Mikewar da yayi da karfi yasa tayi shiru ta bishi da ido,don tsammanin ta tafiya zaiyi,amma sai akasin haka sai wani duka da taji ya kaiwa table din dake gabansu yace,"No sodangi,kada ki sake hada kanki da wannan yarinyar,saboda kwata kwata ba irin tarbiyyarku daya ba." Juyowa yayi yana kallonta cikin kunar rai yaci gaba da cewa,"fa iza da kike gani yarinya ce mai tsanin son abin duniya da zalunci,saboda idan ba haka bane miye zata hada kai da wadda naki jini arayuwata,kuma baccin tasan banda makiyar data wuce Hajiya maryam,ta kashe mani mahaifiyya,sannan kuma ta mallake mahaifina saboda ayanzu bashi da mai bashi shawara sai ita." Ahankali yaja kujerarshi ya sake zaunawa yana kallonta yaci gaba da cewa,"sarat na kwadaitu da tarbiyyarki kuma na amince da dabi unki,please kada ki kini,don wallahi ina tsananin sonki da kaunarki,idan har zaki amince dani ayau ni kuma a gobe zan aure ki. Love you sis😘 08033481518 [4/24, 4:23 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 49 I dedicated this love story to my Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 Gaba daya sodangi ta fiddo idanuwanta ta zuba mashi tana kallonshi,tare da mamaki fal acikin zuciyarta,domin ita dai bazata ce bata son sameer ba,amma agaskiya tafijin safwan acikin ranta,tana son shi,tana son takonshi da yanda yake tafiyar da ita idan har tana agabanshi. Numfasawa tayi tare dayin kasa da manyan idanuwanta ta lumshesu ta kara afkawa cikin tunanin ta,can bata ankara ba sai taji ansa hannu an tallabe mata gefen fuskarta yana shafa ahankali. Ware idanuwanta tayi da sauri ta dago ido ta kalleshi,shi kuwa murmushi yayi mata yace,"mi kike tunani?your husband koh?" Girgiza kanta tayi,sannan da sauri ta mike tsaye kamar zatayi kuka tace,I'm sorry sameer,kuma please I need your for give ness, saboda bana son anan agaba kace banyi maka dai dai ba,don Allah ka yafe mani..... Wasu hawayeneh suka da ke makale a idanuwanta suka fara sulalowa,ai kuwa sai ta suri jikkarta da sauri ta nufi hanyar fita daga office din. Dai dai fitowarta taga alamar wani ya kauce daga bakin kofar,amma da yake hankalinta ba akwace yake ba, sai bata damuba ta wuce da sauri ta na share hawayen dake sauka akan fuskarta. Ashe tun lokacin da sameer ya shigo companing fa iza take bin bayanshi har zuwa lokacin daya shiga office din sodangi,don haka duka abinda suka tattauna duk akan kunnenta,shiyasa gaba daya jikinta yayi sanyi saboda abinda sameer ya fada akanta,kuma sannan sai yanzu ne tasan asalin kiyayyar dake tsakanin sameer din da matar Abbanshi. Fitowa tayi daga inda ta labe ta wuce office dinta zuciyarta cike da damuwa tana tunanin abinda zatayi ta wanke kanta awajen sameer. Sodangi na fita daga wajen aikinta taci karo da yayanta sadah cikin sauri yake tafiyar shi yasa har ya kusa banke ta bai lura ba. Hannu biyu yasa ya rike kafadunta yana dariya yace,"kanwata na gano inda afnan take,zo muje kada mu bata lokaci mu daukota." Wani sanyi ne ya ratsa zuciyarta itama sai dariyar take tace,"tana ina yaya sadah? Kuma ya akayi kasan inda take?" Ci gaba da tafiya sukayi ya fara bata labari yace,"tunda na koma gida idanuwana suna kan ardo,don haka duk wata waya da zaiyi ko kuma bako da zaizo sai nayi mashi labe don inji abinda ya kawo shi. Don haka yau tunda muka tashi da safe sai na fahimci ana yawan kiranshi ta waya,shi kuma ya gaza zaune ya gaza tsaye sai shiga da fita yakeyi kuma cikin damuwa. To ahaka nayi ta bin bayanshi har naji,wai afnan sai kuka take,kuma takicin duk abinda aka bata,kuma hadeja ya kaita can wajen wani abokinshi na kurucciyya. Sodangi ta rike hannunshi tana kuka da kuma dariya,kuka don tausayin yarta sai kuma tana dariya don farin cikin yau zata ga farin cikin idaniyarta. Sadah babu inda bai sani ba a Hadeja,saboda can wasu lokutta da suka wuce ardo yana zuwa dashi,don haka kai tsaye suka nufi gidan abokin ardo sukayi sallama. Ana amsawa suka sanya kai cikin gidan,sodangi na gaba sadah yana biye da ita. Yar tsuwwar dariyar da afnan ta fasa ita ta jawo hankalin duk wanda ke cikin gidan,saboda tunda aka kΓ‘wo ta babu wanda ya ga farin cikinta sai yau. Da gudu ta nufesu tana kiran mammy ! Mammy !! Da isarta sodangi tayi sama da ita,sannan ta rungumata ajikinta tana dariya. Bayan ta sauke ta ne ta nufi sadah shima ta makalkaleshi ya dauketa,aikuwa nan da nan ta fara basu lbr,dama afnan baki abin magana. Mutanen gidan suka tarbesu cikin farin ciki,dakin mahaifiyyar abokin ardo aka kaisu suka zauna,aka kawo masu ruwa mai sanyi na tulu suka sha,sannan suka gaisa. Sadah ya gyara zamanshi ya kalli yar dattijuwar nan yace,"dama munzo ne don mu dauki afnan." Dattijuwar nan tayi murmushi tace,"kai amma ardonku ya kyauta wallahi,saboda yarinyar nan tunda tazo bataci wani abin kirki ba,shi hankalin mu ya tashi kwarai da gaske,saboda kada adalilinmu yunwa ta kamata." Duk dariya sukayi suka kalli afnan dake makale ajikin sadah,bayan yar tattaunawa kadan sadah yace,"so muke mu juya a yanzu don kada dare yayi mana ahanya." Dattijuwar nan ta kalli yanayin garin tace,"ai dan samari daren Ma ya riga yayi,amma da atunani nah zaku jira wannan yaron ya dawo sai ku gaisa tunda an kwana biyu baku hadu ba. Sadah yayi murmushi yace,"idan aka kwana biyu zan dawo,amma yanzu idan har muka tsaya jiranshi wannan kanwar tawa zata iya samun mtsl awajen aikinta." Toh da haka suka samu suka baro garin Hadeja,saboda gani suke idan har suka tsaya jiran aminin babasu toh zai iya basu matsala ya amshe afnan din ya hanasu tahowa da ita,ko kuma yace sai yayi magana da ardo. A kano suka kwana,don haka gari yana wayewa suka nufi daura gaba dayansu,kuma sukayi sa ar samun ardo agida. Molasa tana kitchen suka iso,don haka bakinta abude ta fito tana murnar ganinsu,don ma ba kamar data gansu da afnan. Ardo ne shima ya fito daga nashi dakin fuskarshi adaure ya dakatar dasu yace,"kada wanda ya wuce mani cikin gida da wannan yarinyar." Gaba dayansu suka ja tirjiya suka tsaya suna kallonshi,don ita sodangi mah har idanuwanta sun ciko da kwallah cikin yanayin kuka tace,"ardo mi nayi maka da har zaka ki jininah?" Ardo bai amsa mata ba har sai da ya samu wuri Ya zauna yace,"ina jin dai ai nan gida na neh ko? Toh kuma nace bazan amince da zaman wannan yarinyar agidana ba,ya'yanah guda biyu,kuma su kafai nake so in gani agabana." Sodangi da tuni kuka ya ci karfinta ta fada cikin karaji,"haba ardo,kada ka zama mai son zuciya mana,kana tunanin idan har ka kori afnan ni zan iya zama agidan nan neh? Har abada wallahi ,saboda yanda kakeson diyanka daka haifa nima haka nakeson afnan,kuma insha Allahu daga yau zan bar maka gidanka.......... Caraf sadah yayi da bakinta ya rufe yana girgiza mata kai yace,"kada ki sake fadar haka,idan kin tafi kina da inda yafi nan ne?" Kura mata ida yayi don ta bashi amsa,don haka wani gajeren murmushi tayi ta matso hawayen dake cikin idanuwan tace,"idan har afnan bata da wuri ni zaman mi zanyi acikin gidan?komi afnan tayi mani bazan taba rabuwa da ita ba." Sadah ya harzuka da kalaman sodangi,domin ya fahimci baza tayiwa ardo uziri ba,saboda ai dole ranshi ya bace da abinda ya faru sai ya dakatar da ita,"kada in sakejin kin fadawa ardo irin wannan maganar,kuma daga yau afnan ki mayar da ita wajen mahaifinta tunda kin gano shi ,don shi Allah ya dorawa nauyin rikonta ba ke ba ko iyayenki ba." Daga inda molasa take arude ta zaburo tacewa sadah,"tasan inda dafwan yake?amma kuma bata taba fada ba?kuma kai ya akayi ka sani?" Sadah yayi wani murmushin takaici yace,"nima ba itace ta fada mani ba,ganinsu nayi da idanuwana,kuma bakin cikin hakan yasa har yanzu ban tada mata maganar ba saboda hankali na yana kan inga mun gano afnan. Love you Sis😘 08033481518 [4/24, 8:14 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 49 I dedicated this love story to my Hausa Novel group & my fans,thanks and love you all 😘😘 A ranar dana gansu,raina ya bace matuka,don har rasa irin hukuncin da zan yake mashi nayi, amma duk da abinda ya faru ardo ina mai baka hakuri daka bar mana afnan har zuwa ranar da safwan zai amshi abinshi." Sodangi ta juyo ta kalleshi tace,"tunda na haifi afnan nake dawainiyya da abina,kuma har zuwa yanzu haka,don haka babu wanda zan ba diyata,don ni kadai na isheta gaba da baya,kuma maganar barin gida,insha Allahu yanxunnan zamu tafi mu barshi. Tana fadar haka ta mike daga tsugunnen da take,nan da nan itama molasa ta Mike ta nufi dodangi ta rike tace,"haba Sodangi,ya za ayi ki tafi ki barmu,ko kin mance da mune iyayenki?" Sodangi ta girgiza kanta tace,"ban mance ba molasa,kuma bazan taba fatar mancewa daku ba,amma kuma kada ki manta da ni na haifi afnan,kuma bata da kamata aduniya don haka dole neh in yi kokarin fita hakkinta da Allah ya dora mani." Wccewa tayi ta nufi dakin molasa don ta ida hado sauran kayansu dake gidan,tana hawaye tana tattara kayan kuma zuciyarta cike take da bakin cikin abinda ardonta yayi masu ita da yarta,watau ta yanda ya korar mata diya ba tare daya damu da ita halin da zata shiga ba. Jawo akwatin tayi ta fito ta sake durkusawa agabansu tana share hawayenta tace,"ardo da molasa ina rokonku daku yafe mani duk wani laifi da nayi maku." Da tun lokacin da molasa ta fahimci sodangi tafiya zatayi ta barsu ta fara kuka tare da zargin hukuncin da arfo ya yanke bai yi ba,da sai ya bi abin ahankali ba tare da an bata ran kowa ba. Share hawayenta tayi ta kalli atdo tace,"don Allah ardo ka yafe mata,kuma kayi hakuri ka barta ta zauna da yarinyarta." Shi kanshi ardo gaba daya jikinshi yayi sanyi dajin yar shi zata tafi ta barshi amma sai ya dake kawai yace,"bazan karya dokar dana kafa da kaina ba,kuma aini ban kori sodangi ba,diyar safwan na kora tunda ba mu keda hakki akanta ba,kuma abu daya kawai nakeso kiyi mani shine,tunda har safwan ya fara bibiyarki acan din to kiyi kokari ki kawo mani shi agabana don ya fada mani abinda yake nufi da hakan." Sodangi ta mike tsaye tare da kamo hannun afnan dake zaune akan cinyar sadah tace,"insha Allahu zan fada mashi sakonka." Shima sadah mikewar yayi ya amshi katon akwatin sodangin suka nufi hanyar fita. Da gudu molasa ta nufi dakinta tana kuka sosai saboda gaba daya ta gaza daurewa da radadin da zuciyarta take mata,shi kuwa ardo kusan ince mutuwar zaune yayi anan inda yake,saboda bai taba tsammanin sodangi zaya iya tafiya ta barsu ba,kuma sai wasu maganganun da tayi suka rinka dawo mashi acikin zuciya. Numfasawa yayi ya fada afili,"tabbas nasan sodangi babu yanda za ai ki bar afnan ki zabe mu,saboda jinin tane,kuma afnan bata san kowa ba sai mahaifiyyarta,don haka zanyi bakin kojarina inga safwan ya amshi yarshi don itama sodangin ta huta. Akan hanyarsu ne sadah yayi ta kwatantawa sodangi cewar,dole ne fah wata rana ta hakura da afnan,tunda mahaifinta yana raye adoron kasa,kuma shike da hakkin riketa ba ita ba,sai dai idan kin san zaki koma gidan safwan din ne,toh wannan sai ince zaki iya ci gaba da rayuwa da ita,amma kuma kin san ardo ba zai yarda da wannan iya shegen ba." Dago idanuwa sodangi tayi da sauri ta kalleshi har shi kanshi ya fahimci hakan shima ya kalleta cikin mamaki yace,"ya kika kalleni?ko har kun shirya zaki koma gidansa neh?" Sodangi tayi kada da idanuwanta tare da girgiza kanta tace,"banyi mashi alkawarin zan koma gidansa ba,na dai ce yazo yaga ardo suyi magana." Dan maida numfashinta tayi tace da murya can kasa,"amma yaya sadah idan ban auri safwan din ba,waye zan aura?" Daure fuskarshi yayi yace,"SAMEER,sameer zaki aura tunda naga yana sonki sosai,kuma naga dukkan alama ba yanayinsu daya da safwan ba." Kwabe baki tayi alamar maganar batayi mata dadi ba tayi kamar zatayi kuka,amma kuma batace komai ba,shi kuma duk yana kallonta don haka sai yaci gaba da cewa,"dana koma gida duk zanyiwa ardo bayani akan sameer din saboda na fahimci babu wanda kika fada mawa yana sonki." Sodangi ta kara bata fuska tace,"nidai ban sanya ka ba,kadai bari kawai kaga yanda zasu kare tsakani Ardon da safwan din,toh baya nan idan ta kama sai suji labarin sameer din." Dariya kawai yayi ya girgiza kanshi,amma akasan zuciyarshi ya kara tabbarwa kanshi lallai har yanzu sodangi tana son safwan kilama fiye da tana karama. Kai tsaye ta samu motar da zata kaita kano,sadah ne yayi sauri yace,"amma zaki tsaya ta bichi koh don ki ajiye afnan." Sodangi ta girgiza kanta tace,"da ita zan wuce,saboda har yanzu ban amince da ardo ba,yana iya kara dauketa." Sadah ya amince da bayaninta sannan yayi bankwana da ita,saboda afnan dataji ta ajikin sodangi sai tayi barci. Ba karamin farin ciki surayya tayi ba ganin sodangi ta taho da afnan,amma kuma sodangin bata fada masu cewar ardo koro afnan yayi ba,sai dai kawai tace afnan rigima ta rinkayi shi yasa ta taho da ita. Washe gari week end ne ya kama watau Sunday, shi yasa sodangi basu tashi da wuri ba sai da suka hantse ita da surayya,amma ita afnan tunda ta tashi ta fara damunsu da surutu sai suka korata wajen mahaifiyyar surayya,su kuma suka samu damar hutawa sosai. Duk yau babu inda sukaje sai zaman hutawa,amma duk da hak sun bi gidan lungu da sako sun gyarashi fes saboda rashib zaman da sukeyi,kuma gashi mahaifiyyar surayya tayi taushi ba komai bane take iyawa. Sai da maraice neh bayan sallar la asar surayya ta kalli sodangi tace,"ko ki shirya muje gidan Anty fatima." Sodangi tace gaskiya ban dade da zuwa gidanta ba,kije kawai idan an kwana biyu zan kara komawa." Surayya ta harareta tace,"shi yasa take cewa wai kin fini kirki,toh bazan yarda ba." Sodangi ta kyalkyace da dariya tace,"ai bata yiwuwa don zanje gidan Anty fatima ace dole sai na fada maki,kin san wata rana ma daga wajen aiki nake nake wucewa." Sumayya ta mike tana cewa,shikenan nima daga yau zan rama,bazaki karajin ranar da zan tafi ba." Haka sukayi ta tsokanar juna har ta shirya ta tafi,bayan kuma ta tafi sai ta rinkajin gidan duk yayi mata wani iri saboda rashin abokin surutu,don haka sai itama ta shirya tsaf tare da shirya afnan da niyyar ta fita su dan tattaka don su motsa jinin jikinsu. Tafe take ahankali tana rike da hannun afnan suna takawa ahankali akan babban center unguwarsu,sai taji abayanta wata mota tanayi mata horn,ada bata damu ba ci gaba da tafiyar ta tayi sai taji kuma mai motar yaci gaba da horn din,juyowa tayi ahassale ta kalli mai motar. Wanda ta gani neh sai mamaki ya kamata tayi dariya ta tsaya,shi kuma parking yayi ya fito yana kallonsu yana murmushi har ya isa inda take tsaye shi da afnan. Yana isa idanuwanshi suka fada akan afnan yace,"wow nice girl,ina kika samo wannan kyakykyawar yarinyar mai kama da ke?" Sodangi tayi tsam da rai ta kalli safwan sannan ta maida ganinta ga afnan tace,"she's my relative." SaFwan ya sake zubawa afnan ido yace,"kai lallai wannan kamar taku har ta bace sodangi,kawai sai naji inason babing ko zaki bani ita?" Sodangi ta gaza bashi amsa kawai sai yan kame kame data farayi mashi tace,"wai ya akayi na ganka yanzu,baccin kace tafiyarka ta sati biyu ce." Safwan ya zuba dukkan hannayenshi acikin aljihun wandonshi ya zubawa sodangi idanuwanshi yace,"bakiyi farin cikin gani na ba kenan tunda sai nan da two weeks." Sodangi tayi murmushi tace," ni dai bance ba safwan." Kama hannun afnan yayi ya nufi cikin motarshi da ita,gidan baya ya sakata,sannan ya budewa sodangi gefenshi ya nuna mata da idanuwanshi tazo ta zauna. Love you sis😘 08033481518 [4/25, 2:13 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 50 I dedicated this love story to my Group Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 Sam sodangi ji tayi bazata iyayi mashi musu ba,sai dai kuma zuciyarta tana yi mata tunanin inda zai kai su,dakewa tayi ta nufoshi tana murmushi tazo ta shiga,shima da sauri ya zagaya wajen zamanshi ya zauna tare da rufe kofar. Dan zaman shiru sukayi kadan na takaitaccen lokaci sannan ya dago ya kalleta yace,"na lura bakiyi missing dina ba ko kadan,bayan na tafi." Sodangi tayi dan murmushi saboda ta fahimci safwan sarai,shi mutum ne mai son akula dashi,kuma bai ki ba yanda yazo din nan yayi mata bazata ita kuma don murna sai tayi tsalle ta rungumeshi ta nuna mashi farin cikin ganinshi. Cikin fuska asake ta dago ta kalleshi taga ashe shima ita din yake kallo,don haka sai ta lumshe idanuwanta ahankali ta bude tace,"nayi missing dinka mana,kuma don ba don sai ta nuna madhi afnan da ifanuwanta taci gaba da cewa da yau abinda zanyi maka da sai kayi mamaki." Tana gama fadar haka tayi maza ta rufe idanuwanta da tafin hannunta tana dariya. Wani irin abu yaji ya ratsa mashi zuciya tare da zubawa yan yatsun hannunta ido yanajin kamar ya jawota ajikinshi,amma juyawar da zaiyi sai yaga afnan su ta zubawa idanu tana kallo,ganin ya kalleta sai cewa tayi,"daddy mi kacewa mammy take kuka?ko ka doke ta ne?" Wannan kalmar data kirashi da ita ba karamin dadi tayi mashi acikin zuciyarshi ba,ita kuma sodangi dagowa tayi da sauri ta kalleta tace kinga ni ba kuka nakeyi ba,kuma wanene ya fada maki ki rinka kiran mutane da sunan daddy?" Afnan tayi yar dariyarta ta yara tace,"uncle sadah ne ya fada mani." Safwan ne ya juya sosai ya riko hannunta yana murmushi yace,"na gode afnan da kika kirani daddy,kuma inason daga yau kici gaba da kirana haka kada ki daina koda da rana daya neh kin ji my baby." Dariya tayi tace,"toh Daddy,kuma ai kaima daddy din mammy na neh koh?" Sodangi ta zaro idanuwa,shi kuma safwan ya bushe da dariya yana kallon afnan yace,"ni boss din mammy dinki neh I'm her husband insha Allah." Kalmomin sunyiwa afnan gauri,sai dai kawai ta kada kanta tana kallon mamanta. Sodangi tana kallon afnan sai ta fahimci wata tambayar takeso ta yanko saboda tasan halinta sarai,don haka sai ta canza mata halshe da fullanci ta kwabeta,suu safwan yaga ta koma cikin sit din kujerar ta kwanta kamar ba ita ba. Jinjina kai safwan yayi ya juyo yana hararar sodangi yace,"watau ni kado koh?nima zan koyi fullancin sai inga yanda za ayi arinka linke ni abaibai. Dariya kawai sodangi tayi ta kauda kanta,shi kuma ya juya wajen afnan yace,"Hello my babyβœ‹πŸ?. Afnan tayi murmushi itama ta daga mashi hannu,amma batace kala ba. Safwan yayi dan tunani watau har yanzu dai tana karkashin dokar da aka bata don haka sai ya sake ce mata,"my baby kina shan ice cream?" Kauda kan da sodangi tayi babu abinda takeyi mashi sai dariya,amma tana jin ya ambaci ice cream sai da ta rumtse idanuwanta saboda tasan anzo karshen roshewar dokar data bata,ai kuwa yanda afnan ta zaburo har sai da ta ba safwan tsoro,don makalkale sit din da yake zaune tayi tana ta dariya da yan tsalle tsallenta. Safwan cikin farin ciki ya tayar da motarsji suka nufi wani wuri kusan park din na yara neh sai iyayensu dake rako su ko drivovin gida. Ice cream kala kala safwan ya saiwa afnan ya mika mata guda biyu ahannunta sannan sauran aka zubosu asit din baya. Wajen masu biscuits da chocolate ya nufa suma ya kwaso mata masu din bin yawa yazo ya jibga acikin motar,ita dai sodangi sai kallon ikon Allah take kawai har ya gama. Wurin wasu kayan wasa ya kaita ya biya ma aikatan wajen yace,"suyi ta turata da lilata har sai ta gaji,shi kuma ya koma cikin motar wajen sodangi data nutsa cikin dogon tunani,domin har ya shiga ya zauna bata sani ba sai da ya jawo hannunta daya ya rike sannan ta dago idanuwanta ta kalleshi tare dayin murmushi. Safwan ya zuba mata dukkan idanuwanshi yace,"ina kika samu waccan babing?" Sodangi jin tambayar tayi kamar daga sama tace,"ban gane abinda kakeson kaji ba? Tunda nasan na fada maka she's my relative, kuma daga nan mi kake so kaji?" Safwan yayi wani irin murmushi wadda ta gaza gane manufarshi yace mata,"why she call you mammy,amma kuma take kiran yaya sadah da uncle?" Duk da gabanta ya fadi sai da tayi dariya tace,"wannan dabi ar afnan ce,tunda kai ma ai yau ta fara ganinka amma kuma ta kira ka da daddy,kaga don tace mani mammy ba abin mamaki bane." Safwan yayi shiru kawai yana sauraronta,sabod shidai akwai wani abu da yakeji acikin zuciyarshi game da afnan,amma kuma ga abinda sodangi tace mashi,kada kai yaui yace,"okay shikenan, yanzu ya maganar ardo?kina ganin idan naje gobe wajen shi babu wata matsala?" Sodangi tayi murmushi tunda taji ya saki maganar afnan sai tace,"na riga nace masu sai nan da sati biyu zaka dawo,amma yanzu zan sake fada masu cewar ka dawo sai kuyi appointment." Safwan ya kada kanshi alamar ya fahimci abinda take nufi. Sai gaf da magriba suka bar park din ya dauki hanya sosai ya fara tafiya.sun dan jima suna tafiya sannan ya juyo ya kalli sodangi yace,"ina da gida anan garin ko in kaiki ki ganshi?" Sodangi duk ta fahimci abinda yakeso ya fada mata watau bai son yaga ya mayarsu dasu gida yanzu,don haka sai tayi dan murmushi tace,"da tun dazu ka fada mani da munje,amma kaga yanzu dare yafarayi sai dai ko wani lokaci idan mun fito da wuri." Duk da ba haka yaso ba,amma bayyi begging dinta ba sai ya hakura domin yasan tunda tace haka ba amincewa zatayi ba. Ayau har cikin lungun su surayya ya shiga da motarshi yayi parking gefe daya. Juyawa yayi wajen afnan yaga har tayi barci,yar dariya yayi yace,"dama tana yin barci da wuri neh? Sodangi tace,"eh mafiyawan lokutta da anyi isha I take kwanciya,yau ina ganin harda gajiyar da tayi neh yasa ta barci da wurin." Sodangi ta zagaya da niyyar daukarta safwan ya hana yace,"ki barta ni zan kaita da kaina." Sodangi tayi murmushi tasa hannu ta kwashe kayan malakin da safwan ya sawowa afnan ta kalleshi tace,"bari in fara shiga in sanar da masu gidan shigowarka."tana gama fadar haka ta wce cikin gidan. Dan lokaci kadan ta dauka ta fito shi kuma ya dauki afnan akafarshi yabi bayanta,dakinsu surayya suka nufa kai tsaye ya kwantar da ita saman gadonsu sannan duka gaisa da surayya.,ai kuwa surayya kallo daya tayi mashi ta ganeshi,saboda sodangi ta taba nuna matashi a photo ta kuma fada mata shine daddy din afnan,don koda ta ganshi sai wani farin ciki ya kamata ta mike ta fara hidima dashi,ruwa da lemu tduk ta kawo agabanshi ta ajiye mashi. Wurin mahaifiyyarsu surayya suka kaishi ya gaisheta sannan suka dawo dakin su surayya suka zauna gaba dayansu suka dasa fira. A nan gidan duk yayi sallolinshi gaba daya,sannan ya kalli sodangi ya kalli agogon dake like a jikin hannunshi yace,"lokaci yana ta wucewa,ya kamata inzo in tafi." Sodangi ta dan shagwabe fuskarta tace,"nasa anan zaka kwana?" Safwan ya dago ya kalleta cikin damuwa yace,"watau har tsokanata kike koh?" Tsam surayya ta mike ta fita daga dakin tana dariya,shi kuma dama kamar yana jira yayi wuf ya jawota bisa cinyarshi ya rungumeta ajikinshi yana cewa ,"ayau sai nayi maganin tsokanata da kukeyi, sumbatar ta ya farayi a fuskarta yana sunsunata ta ko ina,ita kuma tana dariya tana kokarin tureshi don ta samu ta tashi daga jikinshi. Kam ya riketa har sai da ta gaji ta tsaya don kanta tana kallonshi,hannu yasa ya zame kallabin dake kanta. aikuwa tufkakken gashinta ne ya zubo gabadaya har ya rufe mata fuska. Wani murmushi yayi tare da numfasawa yace,"ashe gashinki yana nan." Yasa hannu ya fara wasa dashi yaci gaba da cewa,"yaushe zaki koma gida na sodangi?wallahi hakuri kawai nake da rashinki,please ki taimaka ko gobe neh πŸ‘ Dagowa tayi da sauri ta kalleshi gami da zaro idanuwanta sannan tayi kasa da idanuwan ta yi magana can kasan makoshinta tace,Allah yasa ardo ya yarda ya baka ni." Shiru yayi ya zuba mata ido cikin damuwa yace,"kina ganin bazai yarda ya bani ke ba?" Shirun da tayi ne ya tabbatar mashi da amsarshi,don haka da sauri ya kara sa hannu ya tallabo fuskarta suka rinka kallon juna yace,"kina sona sodangi ?don Allah kada ki yarda akara raba mu,don wallahi wannan karon bazan amincewa rabuwarmu ba,please ki amsa mani sodangi." Sodangi ta dago ta kalleshI tace,"ina sonka safwan,kuma babu mai raba mu sai Allah,please ka kwantar da hankalinka,kuma babu abinda zai faru tsakanin mu sai alkhairee." Tunda ta fara magana ya zubawa bakinta ido,don haka tana yin shiru ya nufi bakin yayi kissing dinta,da niyyar ya kauda kanshi sai yaji ya kasa,kuma yanda kasan ya hada kanshi da magnadiso. Sun jima ahaka,domin ita kanta sodangi ji tayi bata iya janye jikinta daga safwan saboda sonshi Ya fara Cin zuciyarta. Saurarawa sukayi suka numfasa sannan da kyar ya iya cewa saboda yanda jikinshi ya mutu gaba daya,"bazan amincewa rabuwa dake ba,kuma idan aka nemi ahanani ke,toh zan iya sace ki gaba daya in rabaki da kasar sai muje can muyi rayuwar auren mu." Love you sis 08033481518 [4/26, 10:50 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 51 I dedicated this love story to my Hausa Novel group & my fans,thanks and love you all 😘😘 Sodangi tayi murmushi ta kalleshi,ta fahimci lallai hankalinshi ya tashi sosai,don haka sai ta kama hannunshi suka mike tsaye tare,ta sake jawo gudan hannunshi ta rike cikin nata suka rinka fuskantar juna,ahankali cikin irin muryarta mai sanyi tace,"safwan ka kwantar da hankalinka,kuma ina son kabi komai a sannu,saboda ni kadai sodangi ta safwance,domin babu wani a zuciyata sai kai.........." Bai bari ta karasa ba ya jawota ya sake rungumeta ajikinshi har ya rasa inda zai sanya ta don jin dadin maganar da ta fada mashi. Sun jima ahaka,saboda ayanda taji kwata kwata bai da niyyar sakin ta,don haka sai tayi mashi magana can kasa kasa tamkar mai yin rada tace,"safwan dare keyi,baka gudun........ Hannu yasa ya rufe mata baki yace,"kiyi shiru my dear,kada ki datse mani mafarkin dana farayi,yana da dadi,ga wani sanyin dadi yana ratsa mani zuciya." Dariya tayi a hankali ta zame jikinta daga nashi,saboda ta lura idan ta biye mashi sai su kwana a tsaye. Kallabinta ta dauka ta daura akanta ta yafa gyalenta ta kama hannunshi suka fita daga dakin,ban kwana yayiwa mutanen gidan sannan ta rakashi har cikin motarshi,saboda anan ma kokarin tsayar da ita ya rinkayi,domin ayanda yakeji sam baya gajiya da ganinta,kuma baya son abinda zai raba su. Wasu manyan jikkuna ya hadota dasu yace,"tsarabar da yayo mata ce." Godiyya tayi mashi, sannan kuma da kyar ta samu ya tafi,saboda sai da ya kai wajen karfe goma da rabi na dare. Washe gari monday,sodangi ta shirya tsaf kamar kullum ta nufi wurin aikinta,aiki sosai ta kamayi, saboda tasan idan har sameer ya shigo bazai barta tayi aiki sosai ba. Around 2:00pm taji knocking abakin kofarta,ranta ya bata sameer ne don haka sai ta dauko babban gyalenta ta rufe jikinta dashi,saboda tasha alwashin duk wasu abubuwan data san zasu rinka hadata dashi zatayi bakin kokarinta ta kauda su har sai ya fahimci abinda take nufi. Madadin ta amsa,sai ta mike da kanta taje ta bude mashi kofar gami da kaucewa gefe daya tana murmushi. Safwan neh agajiye yake kallonta yace,"nayi fushi sarah,saboda kinji ni shiru amma bazakiyi jajena ba kota waya koh?" Sodangi tana nan cikin murmushin nan nata tace,"sorry my boss,nima aikin ne ya rikeni sosai,saboda kasan tunda muka samu junewa da company su safwan hutu ya kare mana." Sunan safwan data fada sai da yasa shi yamutsa fuska kamar wanda aka ambaci wani mugun abu agabanshi,ture maganar yayi ya kalleta yace,"sarat yunwa nakeji." Sodangi tace,"okay ko ka shigo sai asanya akawo maka abincin anan." "No sarah,sam na gaji da abincin company nan,kizo muje waje muci kinga daga can ma sai in maida ke gida." Sodangi tayi jim tana nazarin Idan har ta bishi bazata samu matsala awajen aikinta ba,numfasawa tayi ta kalleshi tace,"sameer akwai sauran aikin da ban ida ba,ko kawai ka tafi." Sameer ya dan daure fuskarshi yace,"okay to nima na fasa cin abincin,amma kuma ki sani cewar babu inda zani,anan office din naki zan zauna kuma babu wani aiki da zan barki kiyi." Sodangi najin haka tayi murmushi acikin ranta tace watau shima sameer rigima gareshi kamar safwan,kuma tasan tunda yace haka toh komai ma yana iya faruwa atsakaninsu,don haka sai ta tsayar dashi ganin yana kokarin shigewa office din nata tace,"bari in dauko jikkata mu tafi." Sameer ya tsaya yana wani murmushi afuskarshi,jikkarta ta dauko ta nufeshi suka juya tare suka bar office din. A bisa hanyarsu ne sameer yayi ta bakin kokarinshi wajen ganin yaja ra ayinta akan soyayyarshi amma sodangi tayi ta fashewa,saboda daya dauko zancen tsananin son da yake mata sai tayi maza ta canza mashi topic har abin ya fara damunshi. Burki yaja da karfin tsiya ya tsayar da motar cikin bacin rai yana kallonta yace,"sarat na fahimci baki sona,kawai ina bata lokacina neh akanki." Sodangi ta kalleshi ta girgiza kanta tace,"sameer ai ban ha ince ka ba kuma ban boye maka komai ba,Kai ne idanuwanka suka rufe kake nuna mani ka mance komai." Sameer ranshi ya kara bace ya kalleta yace," sarah kina ganin wai sonki zai iya saurin rabuwa da zuciya ta ne?ko kadan ki sani har yanzu ina jinki kwance ale ale a zuciyata,don haka sai kiyi hakuri saboda ban fidda rai daga samunki ba." Sodangi ta dago kai ta kalleshi sai taji gaba daya duk ya bata haushi,sai kawai ta bude motar ta fito,shima fitowar yayi har yana wani huci tare da kiran sunanta. Ko a mafarki yaji mai irin wannan sunan sai ya motsa,don haka bada bayan da yayi yaji ana kiran sarat ! Sai kawai ya juya da sauri,ai kuwa idanuwanshi suka dira akansu sodangi da sameer. Mamaki ne ya kamashi sosai ya zuba masu ido kawai yana kallonsu,acan kuma kadan zuciyarshi ce take zuga shi,"dama wannan shine aikin da sodangi take zuwa?aiki ko yawo?ji yayi zuciyarshi ta hassala kawai sai ya nufesu kai tsaye. Har ya isa inda suke basu farga dashi ba sai dai kawai sukaji ance,"what brings you two here?" Dukkansu juyowa sukayi suna kallonshi,sodangi ta firgita sosai da ganin safwan a wurin nan unexpected,juyawa tayi ta sake kallon erea wurin,taga ashe cike yake da manyan kantina da wurin shan coffee irin na matasa wadanda suka amsa sunansu. Sameer ne taji daga inda yake yana watsawa safwan shima tambayar kwatankwacin wadda yayi masu,"what are you doing here too?" Da sauri ta waiga ta kalli safwan taga yayi kucin kucin da rai,kuma babu abinda yake shirin yi sai wulakanci,kai karshe ma yana iya kiran waya yace azo akama sameer ko kuma ya dauki matakin da hannunsa. Yanda taga sameer ta tabbatar shima adhirye yake ya rama duk abinda akayi mashi,don haka sai ta matsa kusa dashi tace,"sorry sir,kayi hakuri,kuma na gode kwarai da gaske,but you should go." Sameer da yake kallon kallo da safwan sai yayi maza ya juyo ya kalleta cikin tuhuma da mamaki watau shine ma abin kora. Da sauri sodangi tayi kasa da idanuwanta,saboda yanda sameer ne yake kallonta taji bata iya jurewa. Kutawa yayi cikin jin haushi ya juya ya koma wurin motarshi ya shiga,ya jima yana kallonsu ta glass din motar sannan ya figi motar a guje ya bar wajen cikin kunar rai. Love you sis 😘 08033481518 [4/27, 6:57 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 52 I dedicated this love story to my Hausa Novel group & my fans,thanks and love you all😘😘 Safwan daya bi motar sameer da kallo yayi dan tsaki sannan ya juyo ya kalli sodangi ya harareta fuskarshi a daure yace,"dama sameer yake maido gida idan kuka tashi aiki?" Sodangi tayi murmushi tadan kauda kanta saboda yanda taga safwan har wani huci yake tace,"bazan ce maka a ah ba,saboda idan kayi la akari da wuri daya muke aiki,kaga dole wata rana ka ganmu tare." Safwan yace,"Hmm,zaki bar aikin a companing su sai inga ta takamar wurin aikin ku daya."kutawa ya karayi saboda ayau ganin sameer da yayi da sodangi ji yake kamar ya shakeshi sannan yaji ya huce. Sodangi ce ta datse mashi tunanin da yake tace,"mi kazoyi anan wurin,kuma ina abokan tafiyar ta ka?" Safwan yayi dariya yace,"shan coffee nazoyi nida girl friend dita." Kici kici tayi da ranta ta dauki hanya taci gaba da tafiyar ta ba tare data sake kallon inda yake ba,amma a kasan ranta ji take kamar ana tafasa mata zuciya don jin haushin amsar da safwan ya bata. Safwan yayi wata dariyar jin dadi shima yabi bayanta yanayi mata magana,banza tayi dashi kamar ba da ita yake ba. Ganin mutanen dake wajen sun fara kallonsu yayi maza ya kamata ya shiga wani tafkeken wajen shan coffee dake kusa dasu. Kai tsaye ya samu wani table da babu kowa akanshi ya jawo kujerar ya zaunar da ita,sannan shima ya zauna ya zuba mata ido don yaga yanayin da take ciki. Kauda kanta tayi gefe daya taki kallonshi,murmushi yayi yace,"sorry dodangi! I'm very very sorry please !! Kuma wallahi wasa nake maki,nasan dai munyi appointment da kawarki surayya,kuma koda tazo ban samu abinda nake son ji ba,amma na riga nayi wata shawara da zuciyata,don haka kada ki damu." Sodangi tayi mamakin abinda yake fada,toh komai zai cewa surayya?gashi kuma yace kada ta damu,don haka sai ta share kawai,kuma sai ta saki ranta tunda taji gaskiyar lamarin. Safwan yayi murmushi ya jawo hannunta ya rike yana kallonta yace,"please sodangi ina rokon arziki awajenki." Ji tayi abin yayi mata girma sai taji kunya ta kamata sai tace,"minene wannan abun da har sai ka roke ni shi?" Safwan ya zama serious akan abinda zai fada mata yace,"so nake gobe ku raka ni unguwa keda afnan." Sodangi tayi kasa da idanuwanta tana nazari,sannan ta dago ta kalleshi tace,"ka mance gobe working days neh?" Safwan yace kada kanshi yace,"ina sane sodangi,idan dai har kin amince ni da kaina zanje in daukar maki permission." Yanda yayi neh ya bata dariya,don haka sai ta amince da bukatarshi. Farin ciki ya kamashi ya tattara hannuwanta duka ya yi kissing dinsu yace,"na gode kwarai sodangi,Allah ya bar mani ke har mutuwata." A kasan ranta ta amsa addu arshi,sannan ta mike tsaye tace,"inason in koma gida,don kada suji ni shiru." Cup din coffee din dake gabanta ya kallah yaga duka dan kadan tasha,don haka ya nuna mata da ido ta koma ta zauna ta kuma shanye coffee din ta. Haka nan cikin jin kunya ta koma ta zauna kamar yanda ya umurce ta. Washe gari around 10:00am safwan ya nufi wurin aikin sodangi,kai tsaye wurin Alhaji yunus ya nufa Mahaifin sameer,bayan sun gaisa Alhaji yunus sai rawar jiki yake saboda ziyarar da safwan ya kawo masu ta unexpected,shi kuwa kamewa yayi ya dora kafarshi daya bisa daya yana kadata. Bayan ya fahimci Alhaji yunus ya samu natsuwa sai yace,"nazo ne don in daukarwa sarat Abubakar permission, saboda zatayi wata tafiya ta kwana biyu,kuma bayan nan inason kuyi transfer dinta ku mayar da ita kamfanin kasa da kasa." Alhaji yunus jin maganar yayi kamar daga sama,saboda bai taba tunanin sodangi zata rabu da companing su ba a dan wannan lokacin,don haka sai ya dan rusuna yace,"yallabai kayi mana uzuri don Allah,ka bar mana sodangi saboda munajin dadin zama da ita kuma akwai ci gaba da muka samu adalilinta." Safwan yadan hade ranshi yace,"just do what I say,please I dont want any complain." Alhaji yunus yayi maza yace,"toh shikenan, yanda kace haka za ayi,kuma yaushe neh kakeso transfer din tata ta fito?" Sameer ya mike tsaye yana wata ginshira yace,"any way,"yadan shafi kanshi sannan yaci gaba da cewa,"tun daga yau ku fara shirya ta,har zuwa ranar da zata dawo daga wannan tafiyar." Yana gama fadar haka ya mika mashi hannu yayi mashi ban kwana,sannan ya nufi hanyar fita. Yana fita babban yaro da sukazo tare yabi bayanshi,akan street din suka hadu da sameer shima yana shirin zuwa office din mahaifinshi. Safwan tsayawa yayi cak inda yake har sameer ya iso inda yake,cikin rainin wayau safwan ya mika mashi hannu don su gaisa,sannan yace,"sannu da babban ma aikaci mai adalci,tunda yake daukar ma aikatanshi ya kaisu har gida don gatantasu." Zuba mashi ido kawai sameer yayi saboda bayyi tsammanin jin haka ba Daga bakin safwan. Shi kuwa safwan ci gaba da cewa yayi,"ina gayyatarka nan da yan kwanaki zan mayar da matata sodangi gidana,don haka muna jiranka cikin yan tayamu murna." Shima yana gama yaba mashi maganar da yakeso ya kauce yayi tafiyarshi. Duk abinda ya faru agaban Alhaji yunus ya akayi shi,saboda ya fito da niyyar yayiwa safwan rakiya sai ya jiyo irin zantuttukan da safwan [4/28, 12:18 AM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 53 I dedicated this love story to my Hausa Novel group & my fans,thanks and love you all 😘😘 Yake fadawa danshi,don haka sameer yana shigowa wajenshi sai ya fahimci yanda yake ta fushi kamar afusace yake. Alhaji yunus yayi murmushi yace,"ka zauna mana,sai wani harare harare kakeyi." Sameer ya samu kujera ya zauna ranshi abace yana fuskantar mahaifinshi yace,"mi ya kawo safwan awannan lokacin?" Alhaji yunus ya kada kanshi yana dariya yace,"kaji wata tambaya awajen sameer,ko ka mance mu dashi mun zama hadin gwiwa neh?to ka saurare ni sosai kaji abinda zan fada maka da kunnuwan basira,duk da ban fahimci maganar da kukeyi ba,kuma ban san abinda ya hadaku ba,toh ka bashi abinda yake so,kodon tsira da martabar wannan kamfanin." Sameer ya bude baki zaiyi magana,Alhaji yunus ya tsayar da shi da hannu yace,"ban son musu bare gardama,kaje kawai ka zartar da abinda nace." Sukuku sameer ya mike jikinshi asanyaye yake tafiyar tamkar wanda kwai ya fashe mawa acikin ciki ya nufi office dinshi. Yana budewa office din ysyi tozali da fa iza akan kujera tana zaman jiranshi,don haka tana ganin shi ta zabura ta Mike tsaye tana kallonshi. Kauda idonshi yayi daga kallonta yaja kujera ya zauna tare da kifa kanshi akan table yana mayar da ajiyar zuciya. Fa iza tayi kasa da murya tace,"kayi hakuri sameer saboda nasan matsalarka tunda naga oga safwan yau ya shigo cikin kamfanin nan. Dago kai yayi da sauri ya kalleta irin kallon nan na mi kika sani akai? Fa iza ta kada mashi kai tace,"na san komai sameer,kuma na daina jin haushinka dakai da sodangi tunda duk naji ayanda kake kallona,shi yasa na shiga na fita don in fidda kaina daga tunanin da kakeyi mani." Wayarta ta zaro ta danna mashi recording din da tayi na firar da sukayi da Hajiya Maryam,a inda ta saki baki ta fada mata tsohon sirrinta data kashe Hajiya zainab mahaifiyyarshi,tare da fada mata kudirinta na nan gaba,watau idan ta samu sameer ya auri fa iza,sai ta kashe Alhaji yunus don ta samu damar mallake sauran dukiyar daya bari shi kuma sameer su rinka juyashi yanda suke so,shima daga baya idan sukaga zai kawao masu matsala shima sai a kaudashi ya bi bayan iyayenshi. Duk wani bakin ciki dake kwance azuciyar sameer sai da ya wanke,saboda yana ganin karshen Hjy maryam yazo,saboda lokacin daya fada cewar ita ta kashe mashi uwa cewa akayi miye shaidar shi. Mikewa yayi da sauri,bayan ya amshi wayar ya tura duka recording din acikin wayarshi ya nufi kofar fita. Fa iza ta kira sunashi,ya waigo cikin zafin nama tace mashi,"kabi komai ahankali sameer." Murmushin daya aiko mata da shine taji kamar ta narke don jin dadi,sannan kalmar data biyo bayan murmushin,"kada kiji komai fa iza,saboda ayau kin fanshi kanki da kanki.sai dai na dawo." Komawa tayi kan kujerarta ta zauna cikin farin ciki,tare dayin addu a,ya Allah ka dubi al amarina,saboda ina tsananin son sameer har karshen raina,Allah kasa ya zamo miji agareni." Tana gama addu ar ta zauna zaman jiran dawowarshi. Shi kuwa yana fita office din Abbanshi ya koma ya kunna madhi wannan recording din yaji,gaba daya yaji wata zufa ta karyo mashi, hankalinshi yayi matukar tashi don rasa abinda zaicewa sameer yayi sai dai hawaye saboda gaba daya hankalinshi ya dawo jikinshi,matarshi ya tuna da irin tsananin son da yake mata amma tunda ta mutu bai sake tunawa da ita ba sai yau. Mikewa yayi da sauri ya dauki wayarshi ya kira abokinshi DPO Ya fada mashi tsaf abinda ake ciki,sannan kuma ya tabbatar mashi da akwai sheda mai karfi wadda zasuyi amfani da ita wajen kamata." Koda Alhaji yunus ya gama wayar,da kyar sameer ya kamashi suka nufi motarsu,lokaci kusan daya suka isa da yan sanda,don haka kai tsaye suka shiga suka kama Hjy maryam tare da wasu yan koranta da aka samu acikin gidan. Hjy maryam kuwa gaba daya ta saduda,saboda dama bokanta ya fada mata duk ranar da Alhaji yunusa yasan sirrin data boye to a ranar duk wani mugun kullinta zai kare,kuma daga ranar babu abinda zatayi ya kara tasiri arayuwarta. πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ Safwan kuwa tunda ya bar kamfanin su sameer dashi da babban yaro sai suka nufi unguwarsu surayya. Kamar yanda sukayi alkawari da sodangi cewar zasuyi tafiya,ita haka ta tashi da wuri ta shirya afnan sannan ita ta shirya kanta sukayi tsaf gwanin ban sha awa,don haka su safwan suna isowa fitowa sukayi tare dayin ban kwana da ummah mahaifiyyar surayya,don ita surayyar ma bata kwana gida ba sai dai ta kira wayar sodangi tace ta fafawa ummah cewar ta wuce gidan Anty fati,koda dodangi taso ta tambayeta game da haduwar da sukayi da safwan sai tace kawai ta bari sai ta dawo zatayi mata bayani. Fitowa tayi tana jaye da afnan,shi kuma yana ganinsu ya fito daga motar ya tarbesu,saba afnan yayi ajikinshi yana tsokanarta ita kuma tanayi mashi dariya. Bude sit din gaba yayi kusa da babban yaro ya zaunar da afnan tare da sanya mata belt na jikin sit din motar,ita kuwa babu abinda take cewa sai,"daddy ka taho mani da ice cream dina."shi kuwa idan ta kirashi da daddy dinnan ba karamin dadi yakeji ba,don haka dama ledar tana anan gaban sit din,don haka yana budewa ya hadata da katuwar roba da dan spoon din da zata sha,shi kuma ya koma baya kusa da sodangi ya zauna,sai alokacin ya kalli sodangi ya numfasa yace,"sorry my dear,tunda kuka fito afnan ta dauki hankalina,gashi ni dake ko gaisawa bamuyi ba." Rusunawa tayi cikin dan girmamawa ta gaisheshi,kin amsawa yayi sai hannunshi daya zira ya damko nata cikin dubara ba tare da babban yaro ya fahimci komai ba,saboda shi idan banda aikin driving babu abibda yakeyi sai dan lokaci lokaci idan afnan tayi mashi tambaya yana bata amsa. Safwan tunda ya rike hannun sodangi bai saketa ba har saida suka kawo gidan da za su. Sodangi ta daga idanuwanta ta kalli gidan,taga zubinshi tun awaje ma ya tsaru iyakar tsaruwa. Safwan ne ya zuba mata ido kawai yana kallonta don yaga iyakar yabawarta akan gidan,aikuwa gaba daya hankalin sodangi ya dauku akan gidan,bama da suka shiga taga komai acikin tsari aka gina gidan,saboda kwata kwata ma gaza misalta yanda ginin gidan yake. Safwan yana gaba shi da afnan ita kuma sodangi tana biye dasu har ya kaisu wani tankamemen falo hadadde irin wanda ya amsa sunanshi. Wuri ya nuna masu suka zauna,shima gefen sodangin ya zauna,dago kai tayi ta kalleshi tace,"kazo nan ka zauna bazakaji kunya idan masu gidan sukazo suka samemu ahaka ba?" Safwan yayi dariya yace,"this house is ours,ya kika ganshi?idan har bayyi ba yanzu insa azo acanza shi." Sodangi ta kara juya idanuwanta acikin falon tayi murmushi, kuma sai ayanzu ne ta fahimci lallai gidan babu kowa sai masu aiki. Safwan ne ya tabo kafadarta da tashi kafadar ya daga mata girar idonshi daya yace,"ya dai naji kinyi shiru,kodai bayyi ba nrh?" Sodangi tayi murmushi gami da mikewa tsaye tace,"gida yayi kyau matuka,yanzu tunda na gani sai ka tashi ka mayar damu gida." Bai kai ga bata amsa ba wayarshi tayi ringing yayi maza ya fiddota dama kamar kiran wayar yake jira,don haka ya dauka,daga can bangaren akayi mashi magana,amma shi baice komai ba har wayar ta tsinke. Kallon sodangi yayi murmushi kamar wanda baida gaskiya yace,"kiyi hakuri sodangi,akwai wani abu kadan da zanyi sai inzo mu tafi,amma kamin time din afnan zoki rakani wani waje yanzun muje mu dawo kada mammy ta gaji da jiran mu. Love you all sis😘 08033481518 [4/28, 7:13 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 54 I dedicated this love story to my Hausa Novel Group & my fans,thanks and love you all 😘😘 Afnan tayi tsalle ta rike hannun safwan cikin nuna farin cikinta suka tafi har tanayiwa sodangi bye bye. Safwan ya kama hannunta suka nufi wani bangaren amma duk dai acikin gidan ne,har suka kai wani daki da yake killace gefe daya. Knocking yayi sannan ya tura kofar suka shiga,wani babban mutum ne zaune akan kujera mara jiki sosai,yana ganin safwan da afnan ya zare farin glass din dake like da idanauwanshi ya rinka kallon afnan cikin mamaki yace,"Kasan wani abu kuwa?" Safwan yace,"a ah,sannan ya kama afnan ya zaunar da ita akan cinyarshi suka rinka fuskantar mutumin. "Kamar ka da yarinyar nan,abin har ya bace,gaskiya sai yanzu na kara yarda da abinda kake cewa." Inji wannan mutumin. Safwan yayi murmushi yace,"ni sam bani ma ganin kamar da muke kwatankwacin yanda nakejinta acikin zuciyata,don shi yasa ma na gaza hakurin ranar da sodangi zata fada mani da kanta,please docter yi maza kayi aikinka,saboda mammy dinta ta fara maganar tafiyarsu." Wannan mutumin da safwan ya kira docter kabir yayi maza ya fiddo dan akwatin dayazo dashi duk ya fito da kayan da zaiyi yan aune aunenshi. Jinin afnan ya diba cikin dubara ta yanda bazata ji zafi ba bare har ta kai gayin kuka. Kallon safwan yayi yace,"Haji safwan kana iya mayar da ita,ni kuma zanyi kokari kafin ka dawo in samu in kammala gwajin." Hakan kuwa safwan yayi,amma koda suka koma wajen sodangi sai ya rinka jin kwata kwata bai da kwanciyar hankali,saboda zullumin bai san amsar da docter kabir zai bashi ba,idan har result ya nuna afnan ba diyarsa bace,toh ko ya zaiji? Zumbur yayi ya mike tsaye sai kuma wata zufa ta karyo mashi duk sai yaji ya rude. Duk abinda yakeyi akan idanuwan sodangi,don haka sai ta taso ta koma kusa dashi ta zauna tana kallonshi tace,please safwan mi yake faruwaneh? Domin na lura tun dazu kake zufa kamar mai ciwon ciki,kuma nima nace ka mayar damu gida haka nan kayi kamar baka fahimta ta,why !! Ka fada mani mana." Safwan ya koma ya zauna daga mikewar da yayi ya dafa kafarta cikin murmushin karfin hali yace,"kada ki damu my sweet heart,domin komai yazo karshe,saboda matakin dana dauka shine zai zamo kwaciyar hankalina,tunda ke dama tuni hankalinki akwance yake." Irin kallon nan tayi mashi na ban fahimci abinda kake nufi ba,sannan kuma taki dauke idanuwanta akanshi,kwata kwata ji yayi idan har taci gaba dayi mashi wannan kallon bazai iyayi mata musu ba,kuma tuni zai iya amayar mata da sirrin zuciyarshi. Kiran da docter kabir yayi mashi ya tsayar dashi daga abinda zai fadawa sodangi don haka ko wayar bai dauka ba ya nufi hanyar barin falon yana cewa sodangi,"just a minute sodangi,I will be back." Kafin ace miye haka ta nemeshi bat ta rasa afalon. Safwan harda gudu ya hada,kuma ko sallama bayyiwa docter kabir ba sai dai ya ganshi kamar daga sama aka tulloshi,amma fara ar da ya gani docter kabir yana yi ne ta kara bashi kwarin gwiwa ya samu ya ida karasawa agaban shi yana cewa,"please kada ka fada mani abinda zai tarwatsa mani zuciya,don Allah ko ba diya ta bace kace mani kawai itace don in samu jin sanyi a zuciyata." Docter kabir yayi wata irin dariya ya zare glass din fake idonshi ya dafa kafadar safwan yace,"Haji safwan ka kwantar da hankalinka saboda afnan diyarka ce halak malak,kuma babu wanda ya isa ya amsa sunan mahaifinta sai kai kadai sawan." Wani salati da yayi cicin karfinshi ya suri docter kabir yayi sama dashi yana dariya,shi kuwa docter da abin yazo mashi bazata,saboda bi taba tunanin safwan yana da karfin da zai iya dagashi ba,shima dariyar yake yana cewa,"bi ahankali Haji safwan kada ka kayar dani kasa." Ajiyeshi yayi fuskar nan tashi kamar gonar auduga yace,"daga yau motar da nake hawa na baka ita kyauta ta zama taka halak malak,kuma zan sa atura maka 2milions,sune goron albishir dinka." Shi kanshi docter kabir ji yayi ya rude dajin kyautar da safwan yayi mashi ta bazata,duk da dai dama yasan kadan da halin safwan kenan,don haka sai ya shiga zafga godiyya kamar zai durkusa mashi. Safwan ya dakatar dashi yace,wllh docter ji nake kyautar da nayi maka kamar batayi ba,amma tunda dai kai har kaga tayi shikenan." Amsar duk takardun da suka zama sune cikakkun shaidarshi ta afnan yarsa ce yayi,sannan ya sallami docter kabir suka rabu cikin farin ciki. Ashe lokacin da safwan yake wannan salatin da karaji sai da sodangi ta jiyo voice din shi amma kuma sam bata fahimci abinda yake cewa ba sai dai amon muryar kawai da takeji,mikewa tayi tsaye ta fara sintiri acikin falon domin gaba daya hankalinta ya tashi matuka saboda rashin sanin abinda yake faruwa da safwan dinta,don haka bude kofar da yayi ya shigo yasa ta nufe shi gaba daya cikin nuna kulawarta take tambayarshi,"mi ya sameka safwan naji kana karaji kai kadai,mi ya faru neh?" Suna haduwa bai saurari abinda take cewa ba ya rungumeta tare da kadaddabeta gam ajikinshi yana cewa,"thank you so much sodangi,kin biya ni kuma kin gama mani komai arayuwata." Sam bata fahimci abinda yake cewa ba,kuma dama tun dazu yake tayin wasu abubuwa da yake ta sanya ta tunani,don haka ciro kanta tayi da tsiya daga jikinshi ta tureshi tace,"don mi zakayi tayiani wasu abubuwan da ban ganewa?domin tun dazu nake ta bib kanka akan ka fada mani abinda ya sameka amma har yanzu kaki ce mani komai." Haka ta karasa maganar cikin nuna mashi ranta ya baci. Dariya kawai yayi cikin jin tausayin kanshi ya nufi afnan da take ta baza duk abinda ta samu wai ita nan wasa takeyi ya daukota cak ya nufi wurin sodangi suka rinka fuskantar juna yace mata,"don mi zakiyi fushi dani,baccin ni banyi fushi dake ba sodangi?" [4/28, 10:54 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ 55 Kasa yayi da idanuwanshi cikin takaici ya numfasa yaci gaba da cewa,"why you do this to me,mi na rage ki dashi,saboda tsananin son da nake maki har kashe raina zan iyayi,amma abinda na fahimta kamar ni ke haukan banza sam bani bane aganki,domin idan har ba haka bane,toh minene na boye mani afnan baki bayyanar da ita gareni ba har sai da ni na bincika da kaina." Sodangi shiru tayi tunda safwan ya fara watso mata tambayoyi saboda tasan dai itace bata da gaskiya,duk da itama tana ganin tana da ta ta hujjar data sa ta boye afnan ga mahaifinta,don haka bude baki tayi zatayi magana sai kawai ya dakatar da ita,"babu abinda zaki ce mani daga yanzu in sake yarda dake tunda dai baki sona,kije kawai na hakura da soyayyar da nake maki tunda ke baki amince dani ba." Yana fadar haka ya juya mata baya amma kuma ya gaza matsawa daga inda yake atsaye. Kuka neh yaci karfin sodangi saboda hankalinta ba karamin tashi yayi ba da jin irin kalaman da suke fitowa daga bakin safwan,don haka sai ta dauki mayafinta ta juya da gudu ta nufi wani daki da yake jrer da wasu dakunan dake cikin falon,sa arta tana turawa kofar taga ya bude don haka shigewa tayi ta samu wani gado aciki tayi rufda ciki akanshi taci gaba da zubar da hawayen da suke ta ambaliyya a idanuwanta. Shigarta dakin yasa safwan ya juyo da sauri yabi sawayenta da kallo cikin takaicin abinda tayi mashi. Kwata kwata ba ayi minta talatin ba da fadan safwan da sodangi su Hajiya ummu salma suka iso tare da mahaifin safwan da yusuf da iyalinshi. Ganinsu yasa safwan ya ajiye afnan dake hannunshi tun dazu,don ko gajiya baiyi. Ita kuma afnan yanda kasan ta sansu da gudu ta nufesu tanayi masu oyoyo. Hajiya ummu salma ce ta tarbeta cikin mamakin ganin yar baby agidan safwan,can kuma sai taji gabanta ya fadi kodai wata ta haifa mashi ita daga cikin yan matanshi na banza suka maido mashi ita,saboda yanda taga kamar ta da danta ma har ta bace,tuna kiran da yayi masu tayi da kuma bukatar son ganinsu cikin sauri saboda yana cikin wani hali da bai iya misalta masu shi ba. Har Hajiya ummu salma ta zauna tunanin daya addabi zuciyarta kenan,ita kuwa afnan tana kufcewa daga hannun ummin safwan sai ta nufi Alhaji muhammad shima ta kama hannunshi tana dan surutunta. Zuba mata idanuwa yayi yana kallonta shima cikin mamaki ya kalli safwan yace,"kai zo nan ina ka sami diya? Saboda wannan yarinyar duk yanda akayi baby dinka ce." Safwan ya zube agabansu yana murmushi yace,"ku bari daddy ku huta sannan zan fada maku dalilin taso daku da nayi ba tare da kun shirya ba." Alhaji Muhammad ya kalleshi yace,"wane hutu kakeso muyi agidanka gidan gwauro,ai duk kyan gida idan har babu matar aute acikin shi ya zama hoto,don haka maza ka fadi mana dalilin kiran mu da kayi ba tare da bata lokaci ba." Safwan ya dago ya kalli umminshi saboda yasan babu wanda zai iya dakatar dashi idan ba ita ba,itama kauda kanta tayi alamar ba zatayi supporting dinshi ba ayau. Safwan ya dafe kanshi ya juya ya kalli yayanshi yusuf da matarshi,suma yi sukayi tamkar basu san yana kallonsu ba,su junior ya kalla shida afnan da suke ta wasansu tamkar dama can sun san junansu. Murmushi yayi ya kalli mahaifinshi yace,"insha Allahu daga yau komai zai wuce,kuma idan ayau kake son inyi aure ni kuma na amince maka." Wani farin ciki ne ya bayyana a fuskar Alhaji Muhammad yace,"alhamdulillahi, safwan babu abinda nakeso ayanzu sai don ganin kayi aure ka zama kamilin mutum." Safwan yayi dariya yace,"daddy tun yaushe na zama kamilin mutum,ai na dade da zama irin yaya yusuf,kuma duk dalilin mammy din afnan."ya nuna afnan dake ta faman goya dan teddy din junior. Maida idanuwanshi yayi akan ummi din shi yace,"ummi ban boye maki komai ba akan sodangi,kuma ko alokacin dana gano inda sodangi take sai da na fada maki,amma abinda na fahimta daga baya shine,sam ummi bata dauki maganar sodangi da wata muhimmanci ba shiyasa daga baya ma na daina fada maki komai akanta. A duk binciken da nayi watau shine, alokacin dana bar sodangi ashe na barta da karamin ciki wanda ita kanta bata san dashi ba sai daga baya,gashi ni kuma babu wani address dana bar wa sodangi wanda zata iya nemana ko don irin wannan lalurar. A hankali safwan ya shiga fede masu biri har wutsiyarshi,kai harda fushin da iyayen sodangi sukeyi dashi sai da ya fada masu. Gaba daya falon sukayi tsit suna kallonshi,saboda abinda sukaji ba karamin daure madu kai yayi ba wai safwan da diya within five years,bama kamar daddy dinshi da ada daukar labarin yake tamkar tatsunniya idan mahaifiyyar safwan ta fada mashi, amma yanzu dayaga zahiri harda diya yada mamaki yayi kamar ya kashe shi sai kawai sukaji ya bushe da dariya harda dan tafi yana kallon Hajiya ummu salma. Sudai falon babu wanda ya motsa tunda basu gane manufar daddy dinsu ba,sai da dukaga ya mike tsaye ya nufi safwan ya rungumeshi yana ci gaba da dariyar da yakeyi tajin dadi. Dago safwan yayi yace,"lallai dana ya girma,ada safwan kallon da nake maka a matsayin ka na karami kafi kowa karamin tunani,amma yanzu abinda ka aikata koni gani nake bazan iya aikata shi ba,saboda kayi kuskure daga farko, kuma yanzu ka dawo daga baya kana kokarin gyaran mistake dinka,na goyi bayanka kuma zan tsaya maka har sai naga sodangi ta dawo hannunka da yarka." Jin abinda daddy dinshi ya fada yasa ya kara rungumeshi don dadi ya rinkayi mashi godiyya mara adadi. Yusuf ne ya taso shima ya rungume dan kaninshi yana taya shi farin cikin abinda ya faru. Ita kuwa Hajiya ummu salma saboda farin ciki kasa cewa komai tayi iyaka ta shafi kan safwan ta sumbace agoshi tace,Allah ya albarkace ka ya albarkaci zuri arka." Ameen safwan yace ya sumbaci hannun umminshi. Hada junior da afnan ummi salma tayi ta tafi dasu masaukinsu,sannan Alhaji Muhammad ya tabbatar masu safwan cewar gobe idan Allah ya kaimu zamu nufi katsina daga can sai mu leka daura wajen surukkan safwan din. Yusuf da matarshi cewa sukayi su ba inda zasu anan gidan safwan zasu zauna kafin zuwa gobe din. Safwan ya marairaice kai yace,"haba my senior sister kija mijinki kawai ku tafi makwancinku,ni kuma ku barni in huta." Yusuf ya mike tsaye yana dariya yace,"ku idan ku ka hadu sai anji kanku." Kai tsaye ya nufi dakin dake kusa dana sodangi,shi safwan azatonshi dakin ma zai shiga,toh sai da yaga inda ya shiga ne ya mayar da numfashinshi. Tsaf khadija matar yusuf ta zuba mashi ido,kuma duk taga irin tashin hankalin da safwan ya shiga,don haka sai ta zargi lallai akwai wani abu da safwan yake boye ma wa,don haka wuri ta samu ta baje ta nuna mashi bata da wata alama ta zata tashi,shima zaman dirshan yayi a bisa carpet fin tsakar falon,amma kuma ba haka yaso ba. Can dai yaga bata da wata alama ta zata tashi don haka sai yace,haba Anty nah ki tashi kije ga mijinki can yana jiranki,kuma har fa lokacin sallar azahar yayi." Khadija tayi murmushi ta mike tsaye tace,"ni dadina da kai sai ka rinka kokarin korar mutum don yazo gidanka,Hmm,toh bari kawai muzo mu bar maka gidanka duk sai ahuta." Wani dadi ne ya ka mashi yace,"da kin kyauta wllh." Khadija tayi wuf ta mike tsaye ta nufi dakin da mijinta ya shiga,tana zuwa dai dai kofar kawai sai ta bude dakin da sodangi take aciki ta shige. Love you sis😘 08033481518 [5/2, 12:37 AM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 56 I dedicated this love story to my group Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 Ina jinjina a gareku dukkan masoyana,saboda sakonnin ku da kuma yabawar ku duk suna isowa a gareni,na gode kwarai kuma ina roko ga ubangijina ya barmu tare har karshen rayuwata. Gaba daya wuta ta daukewa safwan saboda bai san da yanda Anty khadija zata ci gaba da kallonshi ba idan har taga sodangi. Dafe kanshi yayi ya nufi bakin kofar dakin ya labe tare da dan saurarawa,amma tsit yaji babu wani sauti dayaji yana fitowa,ashe lokacin da Anty khadija ta shiga dakin bataga kowa ba,don haka sai taci gaba da sanda tana kokarin dan lallekawa don taga ko boyewa akayi. Sai da ta juyo tana shirin fita sannan taga gyalen mace aje akan gadon,daukarshi tayi ta kaiwa hancinta tana sunsunawa,kamshin dataji neh ya kara tabbatar mata da gyalen mace ne saboda turaren da akayi amfani dashi na mata ne. Ranta ne ya bace,watau safwan har yanzu yaudarar iyayenshi yakeyi kenan,kuma yasan baida gaskiya shi yasa yake ta kokarin korarsu. Wuri ta samu akan gadon ta zauna tana kada kafarta tana cewa,"yau ko wacce shegiya ce sai tayi maganinta,kuma shima safwan din bazata barshi ba sai ta hada shi da umminshi. Sodangi dake cikin toilet tana alwallah sam bataji shigowar wani acikin dakin ba,don haka hankalinta kwance ta fito,amma sai idan ka natsu ka kalli fuskarta ne zaka gane tana cikin damuwa,fitowa tayi da dan kwalinta ahannu tana yarfe sauran ruwan dake jikinta na alwalla. Ganin khadija da tayi azaune ne sai gabanta ya fadi itama tayi tsaye turus saboda rashin sanin khadija kowace ce awurin safwan din. Khadija tana ganin sodangi tayi maza ta mike tsaye tana kallonta abaki bude,saboda yanda taga sodangin,kyau,cikar kamala da kwarjin su suka hana khadija yi wa sodangi wulakancin datayi niyyar yi,sai kawai tayi mata murmushi ta nuna ta da dan yatsa tace,"koh sodangi ce?" Sodangi cikin mamaki da jin kunya ta amsa mata da "eh nice." Khadija tayi dariya tace,"kai amma naji dadi da na ganki,saboda yanda safwan yake ta kiranki a family dole ne mu kagara don muga wacece wannan mai babbar sa ar data samu damar saye zuciyar safwan,saboda safwan ba kowacce 'ya mace bace take burgeshi,amma kuma sai naga ke din sodangin ba ta wasa bace,kema u are different to others,woooo gaskiya kunyi marching sodangi." Sunkuyar da kanta tayi cikin jin kunyar abinda Anty khadija take cewa,sannan gashi duka yau suka fara ganin juna,amma ta barke da surutu irin sai kace sun saba da juna. Ganin sodangin tayi shiru ta kuma tsunduma cikin dogon tunani sai tace,"sorry my dear na dameki koh,ai sai dai kinyi hakuri da halina saboda ni irin mutanen nan ce da duk abinda na gani idan har ya burgeni zan fada idan kuma bayyi ba kai tsaye zance bayyi mani ba,don haka kada ki damu da halina kawai kije kiyi sallar nima ita zanyi sai mu danyi labari kadan sannan in koma wajen mijina yana can na barshi shi kadai. Sodangi najin ta bata go a head kawai sai ta dauki gyalenta tana murmushi ta rufa ta fara kokarin kabbara sallah,ita kuma khadija ta nufi toilet din tanayi tana waigen sodangi tare da yaba tsarin halittar dataga sodangin da ita. Bayan sun gama sallah khadija ta nemi sodangi data tashi su koma falo,saboda kawai so take taga yanda safwan yake yi agaban wannan tsaleliyar yarinyar,domin ta sanshi da rawar kai. Sodangi tayi shiru gami da sunkuyar da kai,domin maganganun da safwan ya fada mata har yanzu suna nan kwance acikin ranta. Da kyar ta samu ta dago idanuwanta ta kalli khadija tace,"don Allah wani taimako nake nema agareki πŸ‘. Khadija tayi sauri ta kamo hannuwanta da take rokonta dasu ta rike tace,"haba haba please,miye wannan abun da har sai kin rokeni." Sodangi ta kara karya wuyanta don ta bata tausai tace,"gida nakeso in tafi,amma na rasa ta yanda zan tunkari safwan,kuma baby dita tana nan wajenshi,so nake in tafi tate da ita." Zuba mata idanuwa khadija tayi kawai tana kallonta har tayi shiru,sannan ta numfasa tace,"ko baki fada mani ba,amma idanuwanki sun tabbatar mani da akwai matsala atsakaninku,please sodangi kada ki boye mani komai,saboda ni yayarku ce dake da safwan din. Daga nan khadija ta zauna ta warware wa sodangi alakarta dasu safwan,banda ma auren yusuf da takeyi ita cousin dinsu ce,sannan kuma ta bata labarin cewar ai su afnan sun dade rabon su da gidan nan,ummi ta tafi dasu sai gobe da safe zadu dawo. Jin an ambaci mahaifan safwan har sunzo gidan nan bata sani ba,sai ta godewa Allah da basu ganta ba saboda kunyar da zataji idan ta gansu. Mikewa tayi da sauri tace,don Allah Anty khadija ki taimaka mani na bar gidannan don kada su sake dawowa su sameni acikin gidan nan." Murmushi tayi ta mike tsaye tace,"ok ki taso muje wajen safwan din,sai insa ya mayar dake gidan. Lulluba gyalenta tayi tabi bayan khadija,shi kuma yana jin tahowarsu sai yayi baya ya koma akan kujera ya zauna tamkar bashi ba,kuma illahirin abinda suka tattauna a tsakaninsu duk akan kunnenshi,don haka suna shigowa falon sai kawai yayi tamkar bai gansu ba ya kauda kanshi. Sam sodangi har acikin ranta bataji dadin kauda kanshi da yayi ba,don haka sai taji kamar ta fashe da kuka saboda agaskiya zuciyarta bazata juri wadannan abubuwan Da safwan yakeyi mata ba,don haka sai ta juya da sauri ta nufi hanyar fita daga cikin gidan tana share wata kwalla data fito mata. A lokacin dayaji motsi sai yayi satar kallonsu yaga sodangi ta juya zata bar gidan,da sauri ya mike ya bi bayanta,sai da yayi da gaske sannan ya iya shan gabanta ya riketa. Ya jima yana kallonta sannan yace,"mi akayi maki kikeson tafiya?" Sodangi tasa hannu ta share hawayen da suka gangaro mata tace,"ba kai bane....... Sai kuma tayi shiru taci gaba da share fuskarta tana sharben kuka cikin shagwaba. Dariya kawai yayi yace,"haba sodangi, miye laifina aciki,ko kin mance kece mai laifin,mi yasa kikayi mani haka,mi yasa kika raba ni da gudan jini nah? Sodangi ta rasa abinda yake mata dadi,don haka sai ta fada jikin safwan tana ci gaba da kukanta. Shi kuwa abinda yaji neh acikin jikinshi yasa ya rumtse idanuwanshi da karfi,kuma bai san lokacin daya ida jawota ajikinshi ba ya kara rungumeta ba. Love you sis 08033481518 [5/2, 10:15 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ 57 Ita kuma dama so take a rarrasheta,don haka sai tayi kwance cikin jikinshi,shi kuma yaci gaba da rarrashinta yana shafa mata gadon bayanta. Sai da ya tabbatar ta samu sassauci acikin zuciyarta sannan ya dagota ya na kallon fuskarta,dan shafar gefen fuskarta yayi ya lumshe idanuwanshi ya budesu ahankali,amma duk idanuwanshi suna zube akan fuskarta yace maya,"kiyi hakuri sodangi,na rasa yanda zanyi da abinda nakeji acikin zuciyata shiyasa har na biye mata nayi fushi dake." Da sauri ta riko hannunshi ta rike tace,"wallahi ina tsoro ne safwan,shi yasa naki fada maka komai akan afnan,da farko sadda nayi niyyar fada maka sai na fahimci yanda kake tsananin son yara,ni kuma sai tsoro ya kamani naga duk ranar daka fahimci yarka ce,toh zaka iya raba ni da ita,ni kuma shiyasa nayi shiru tunda ban san irin hukuncin da ardo zai yanke mana ba." Wani dan gajeren murmushi yayi ya tarbi numfashinta da crwar,"ke yanzu har kina tunanin akwai abinda zai sake raba mu? Never bana son zuciyarki ta sake tunani irin wannan saboda ke donni ubangijin mu ya halitto ki,haka nima naki neh ke kadai." Sodangi tayi murmushi jin dadi,shi kuma yasa hannu ya goge mata sauran lemar dake fuskar ta ta yaci gaba da cewa,"kuka daga yau nace ki daina yinshi,wanda kikayi abaya duk ya isa." Hannunta ya kama ya maida ita cikin gidan cike da kulawa. Anty khadija dake tsaye tana kallonsu,sai duk abin ya burgeta har acikin ranta don haka sai tayi baya itama ta koma cikin gidan don ta basu damar sakewa a tsakaninsu. Safwan ne bai mayar da sodangi gida ba sai bayan la asar,itama don ta matsa shi yasa,amma ada niyyarshi anan yaso ta kwana don gobe idan suka tashi tafiya daura kai tsaye wucewa zasuyi,ita kuma kwata kwata bata son bin su daura din,domin bata son agaban idonta taga irin hukuncin da ardo zai yankewa safwan din,shi yasa da zasu rabu ta kara rokonshi akan idan sun tashi kawai su tafi kada ya biyo mata don bazataje daura ba. Safwan ada ba haka yaso ba,amma ahankali sai ya fahimce ta,don haka sai ya nemi da tayi masu addu a,sannan kuma ya kara tabbatar mata da cewa idan fa har ardo ya nemi rabasu toh shi bazai amince ba zai zo ya tafi da ita neh kawai. Murmushi tayi ta daga mashi kai alamar ta amince da bukatarta,amma acan kadan zuciyarta kukan zuci kawai takeyi saboda tasan muddun ardo bai amince da safwan ba,to ita kuma bata da wata hujja da zata bi shi,sai dai kawai tasan tunda ga wannan lokacin rayuwar ta zata fada cikin garari. Wasu hawaye ne taji suna kokarin fito mata sai ta samu da kyar ta mayar dasu har ta samu suka rabu da juna. πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ Washe gari babu wani bata lokaci da sukayi,gabaki dayansu suka nufi katsina,domin sai da suka tsaya ta wurin yan uwa da abokan arziki sannan suka hadu harda kanin mahaifinsu safwan wanda ya nema mashi auren sodangi akaron farko. Wurin bai basu wata wahala ba,domin dandanan suka ganeshi tunda aruga neh. Yanda motocin su suka biyo layi suka shiga cikin rugar yasa suka dauki hankalin sauran mutanen kauyen,domin wasu daga cikinsu sai suka rinka tsammanin ko gwamna ne da tawagarshi suka kawowa kauyensu ziyara. Parking sukayi gaba daya agefen gidan suka fito,kai tsaye duka nufi gidan ardo da aka nuna masu. Yusuf ne yayi sallama,daga can ciki sukaji an amsa masu. Yaya sadah neh ya fito,ganin safwan acikin masu sallamar yasa ya fahimci ko su wanene,don haka fuska asake ya tarbesu yayi masu shimfida,sannan yace masu bari ya sanar da ardo. Koda ardo ya samu labarin zuwan iyayen safwan sai yayi hamdala ya sanar da ubangiji,saboda ya dade yana jiran wannan ranar don yasan zatazo ko dan afnan dole safwan ya kawo kanshi. Mikewa yayi ya zaro sandarshi ya nufi zauren gidanshi inda bakin suke,yana isa duk suka mike cikin walwalar fuska suka mika mashi hannu don su gaisa. Kallonsu yayi kawai ya dogara sandarshi akasa yana mazurai yace,"kai wallah kado sam baida kunya,kai yanzu wannan yaron minene ya kawoka agidanah?ko kasan adalilinka,na rasa diyar cikina ta tafi ta barni saboda 'yar ka?to dama wallah nace idona idonka,don ni ba ayi mani rainin wayau a zauna lafiya." Kawai yana fadin haka sai ya daga sandarsa ya rafkawa safwan agadon bayanshi sau biyu yana mazurai. Love you sis😘 08033481518 [5/3, 10:01 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba Saleh daudawa 58 I dedicated this love story to my Group Hausa Novel & my fans,thanks and love you all😘😘 Gaba daya yan uwan safwan suka mike tsaye, amma banda daddy dinsu,domin shi ko motsawa baiyi ba daga inda yake azaunen,sannan kuma ganin su yusuf sun harzuka da kannenshi sai yayi wuf ya tsayar dasu,"kada in sake inji wani yace mashi wani abu,saboda alokacin da safwan ya bata mashi mu muna ina?" Dan numfasawa yayi sannan yaci gaba da cewa,"don haka ku rabu dashi ya hukunta shi iyakar yanda ya bata mashi rai." Gaba daya sukayi turus harda shi ardon,saboda shi kawai da zuciya biyu yazo,watau zaiyi wa safwan hukuncin abinda yayi mashi,koda iyayen safwan din zasu sa adaureshi,shi yasa da yaji furucin da Mahaifin safwan din yayi duk sai yaji jikinshi yayi sanyi. Wuri ya samu ya zauna kamar yanda su yusuf sukayi da daddy dinsu yayi masu magana. Sai da Alhaji Muhammad ya fahimci zuciyar ardo ta lafa sannan yayi gyaran murya ya kalli safwan da yayi kasa da kanshi tunda ardo ya fara suburbudashi bai daga ba yayi murmushi yace,"ardo ina magana neh da yawun bakin safwan,don Allah kayi hakuri akan abinda yayi maka,ka yafe mashi, kuma wannan zuwan da kaga munyi munzo ne don neman alfarmar ka kara bamu yarka sodangi akaro na biyu,tare dayi maka alkawarin insha Allahu,abinda ya faru abaya bazamu sake bari a maimaita shi ba πŸ‘ Ardo ya hade rai ya kalli safwan yana kada kai yace,"gaskiya Alhaji sai dai kuyi hakuri,saboda kwata kwata auren kado ya fice mani arai,kuma duk saboda danka neh." Safwan dayaji abinda ardo ya fada sai hankalinshi ya kara tashi,saboda koda yaji saukar sandar ardo abayansa baiji abinda yaji ba yanzu,rarrafowa yayi da gwiwoyin sa har gaban ardo yana zubar da hawaye yace,"wallahi ardo na gane kurena,ina son sodangi fiye da tunanika,kuma nayi maka alkawari zan kula da ita har karshen rayuwata." Kunsan fillo da dakiya,ga taurin zuciya,shiyasa ardo ko ajikinshi,domin magiya sosai safwan yayi tayi mashi har yana rike mashi kafafuwa,amma ardo yayi biris sai ma cewa yayi,"shi tuni yayiwa sodangi miji,kuma dama wannan ranar yake jira safwan ya amshi diyarshi sai shi kuma ya aurar da sodangi ga dan uwanta bafullatani." Cikin sauri safwan ya dago idanuwanshi da suka kada sukayi jajir saboda tashin hankalin dayakeji kiri kiri,kawai jikinshi ne ya kama rawa ya zabura ya mike tsaye yana kallonsu daya bayan daya,sannan ya juya ya fita da zauren cikin sauri. Mikewa yusuf yayi ya bi bayanshi cikin tausayawa dsn uwanshi,saboda ya gane babu abinda yake tafiyar da dan uwanshi sai jarabta ta ubangiji. Bayan fitarsu kannen mahaifinshi dashi kanshi Alhaji Muhammad din sukaci gaba da ba ardo hakuri,amma shiru yayi bai tanka masu ba suma har suka gaji suka mike sunayi mashi ban kwana. Shima mikewar yayi yabi bayansu,amma kafin su tafi ardo yadan kebe da Alhaji Muhammad gefe daya don ya kara bashi hakuri,sunyi magana sosai a tsakaninsu wanda babu wanda zai iya cewar ga abinda suka tattauna.jiki asanyaye mahaifin safwan ya kara ban kwana da ardo sannan suka tafi. πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ Gudu kawai yakeyi da motar,irin gudun da ka ganshi kasan bana hankali bane. Yusuf dake gefenshi ya farayi mashi magana,"safwan kana cikin hankalinka kuwa?wannan wane irin gudu ne?" Kwata kwata safwan driving kawai yake saboda kunnuwanshi sai amsakuwwar maganar ardo yakeji dayace,"sodangi surar da ita zaiyi ga dan uwanta bafullace" Dukan sityarin motar yayi tare da wani irin karaji,ga kuka kuma yanayi,hawayenshi sai shatata sukeyi tamkar karamin yaro. Hankalin yusuf ne ya kara tashi,saboda ya fahimci idan har yaci gaba da zubawa safwan ido lallai zai iya halakar dasu,tunda ya lura ba a cikin hayyacinsa yake ba,don haka cikin dubara da bam baki ya samu dakyar safwan ya tsaya,aikuwa yana tsayawa yusuf ya bude motar da sauri ya fito yaje ya budewa safwan, Safwan ya ziro kafarshi cikin rangaji ya fito sai ka rantse abuge yake,yana fitowa yausuf ya tsinkeshi da mari cikin zafin nama,sannan ya fara zazzaga mashi masifa,"kai baka da hankali ne? Ko kana so ka fada mani cewar saboda mace kakeson ka hallaka mu?" Safwan yayi wuri wuri saboda saukar marin da yaji unexpected ya kalli yusuf tare da dafe kumatunshi. Shi kuwa yusuf sai yaci gaba da zuba mashi bala I,don ta ibda yake shiga bata nan yake fita ba har ya samu zuciyar safwan tayi sanyi,kuka mai karfi ya saki cikin karaji yake kiran sunanta yana kallon yayan nashi yana cewa,"babu wanda ya isa ya rabani da rayuwata,domin idan babu sodangi ku dauka nima babu ni adoron kasar nan." Da sauri yusuf ya kamashi yana kiran sunashi kuma yana rarrashinsa,lafawar da yaga yayi neh yayi sauri ya tura shi acikin motar saboda a inda suke daji ne don motoci basu faye wucewa ba. Yusuf yaci gaba da driving din motar don haka komawa baya yayi,cikin saa yaci karo da motocin su daddy,don haka bin bayansu yayi har suka sauka. Bayan sunyi sallar la asar daddy din su safwan ya nemi yan uwanshi maza da matarshi da yusuf da iyalin shi dasu hadu a babban falonshi anan katsina din. Duk yanda sukayi da ardo ya zayyano masu,sannan ya kara da cewa tunda dai yaki amince mana daya bamu yarshi toh ni na yanke shawarar zan aurar da safwan ga Humaira diyar amininah,saboda yin haka ba karamin taimakawa safwan din zaiyi ba,domin kila idan har akwai mata agabanshi zai samu saukin rashin sodangi da yayi." Safwan dake zaune gefen umminshi sai kawai yayi maza ya riko hannunta yanaci gaba da zibar da hawaye,saboda gaba daya karfinshi ya kare ji yake tamkar bazai iya tafiya da kafafuwanshi,zamewa yayi ya dora kanshi abisa cinyarta tare da mayar da idanuwanshi ya rufe. Love you sis 😘 08033481518 [5/4, 11:01 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 59 I dedicated this love story to my group Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 Gaba daya jikinshi ne ya kama rawa kamar mai jin sanyi. Dago idanuwanshi yayi da suka yamutse saboda tashin hankalin da yake aciki yace,"ummi nah ki lullube ni,ban lfy,kuma ina ganin mutuwa zanyi." Wannan furucin da safwan yayi ba karamin tayarwa mutanen dake zaune a falon yayi ba,bama ya umminshi,itama nan da nan jikinta ya fsra rawa tana cewa,"bazaka mutu ba safwan,insha Allahu zaka rayu,amma sai ka sanya hakuri da dangana acikin zuciyarka." Rumtse idanuwanshi yayi da karfi,watau umminshi ma na nufin yayi hakuri da sodangi kenan,lallai akwai aiki agabana,taya zan rayu ba tare da farin cikina ba? Zumbur ya zabura ya mike ya nufi hanyar fita daga falon cikin rangaji tare da sarkewar kafafuwa yanda kasan mashayin daya sha yayi tatul. Hajiya ummu salma mikewa tayi itama tabi dan nata da idanuwa cikin jin tausayinshi tamkar zatayi kuka,aikuwa yana zuwa dai dai kofar da zai fita wani jiri ya debeshi sai gashi akasa yaraf ya zube,sai alokacin mazan dake falon suka zaburo gaba dayansu suka nufeshi,don su Hajiya ummu salma da khadija kuka kawai sukeyi. Yusuf ne ya ciccibeshi yayi ciki dashi ya dorashi akan gado,shi kuwa safwan sai kokarin tashi yake amma jiri yana mayar dashi akan gadon haka yayi tayi yusuf yana hanashi har ya gaji don kanshi ya hakura ya kwanta tate da mayar da idanuwanshi ya rufe. Mahaifin safwan da kanshi ya fara laluben number docter kabir,cikin sa a wayar ta shiga ya dauka cikin kankan da kai ya gaida mahaifin safwan din,sannan Alhaji Muhammad yace,"docter kana gari kuwa?" Docter kabir yayi murmushi yace,"ina gari ranka ya dade,amma ina cikin katsina. Cikin jin dadin inda docter kabir din yake Alhaji Muhammad yace,"nima ina cikin katsinar,don Allah inason kazo gidana dake lay out ba lafiya." Yana fadar haka ya kashe wayar ya koma kan safwan da suke tunanin ko suma yayi. Cikin wasu yan mintoci da basu da yawa docter kabir ya iso,ganinshi yasa duk suka matsa ya fara duba safwan cikin kwarewar aikinshi ya juyo ya fadawa Alhaji Muhammad cewar safwan ba suma yayi ba amma rayuwarshi dai tana cikin hadar don haka sai anyi da gaske wajen kulawa da abinda yake bata mashi rai har ya kai shi ga shiga irin wannan yanayin,domin kara ace suma yayi sai a yayyafa mashi ruwan sanyi da halin daya shiga yanzu. Gaba daya dakin idanuwansu suka raina fata,sai kallon kallo sukeyiwa junansu,tare da mamakin abinda ya hadassa mashi wannan yansyin cikin dan lokaci kankani. Drief ya daura mashi don asamu jikinshi ya samu karfi,sannan kuma ya basu shawarar su dan bashi wuri don ya samu hutu,domin bazaiyi mashi allurar barci ba,saboda kada abin yayi mashi yawa. Shawarar docter kabir suka dauka,don haka gaba daya suka bar sashen suka koma wani bangaren,ita kuwa Hajiya ummu salma tana nan zaune kusa da danta saboda gaba daya hankalinta ya koma gareshi,domin dama tunda taji yace,rayuwarshi bata da amfani tasan lallai akwai abinda yakeji tunda har yayi wannan furucin. Shafa fuskarshi tayi cikin nunajin tausayin shi ta furta da cewa don Allah safwan kayi hakuri kada ka wahalar da rayuwarka,ni umminka ina sonka kuma daddy dinka ma yana sonka,kuma haka ma yusuf yana tsananin kaunar,idan har ka bari muka rasa ka safwan,ka sani bazamu taba yafe maka ba." Wannan furucin na umminsa ya darsu acikin zuciyarshi,saboda kwancen kawai yake amma duk abinda akeyi ko ake cewa yanaji acikin kunnenshi,karfin jiki ne kawai baya dashi sai kuma wata irin kuna da zuciyarshi takeyi. Wasu hawaye neh masu zafi irin na gefen ido suka ziraro mashi,juya kanshi yayi dayan gefen saboda ya fahimci ummun tashi zira mashi idanuwa tayi. Numfasawa tayi tasa hannunta ta share mashi hawayen tana ci gaba da cewa,"safwan ka tashi kada ka lahanta kanka,kuma nayi maka alkawarin zan tsaya maka tsayin daka inga ka mallaki abinda kakeso,saboda nima inason abinda kakeso kuma dai dai da rana daya ban tabajin kin son sodangi ba a rayuwata, saboda halin da kake aciki ba laifinta bane safwan,ka dauka jarabawa ce daga Allah." A hankali safwan ya bude idanuwanshi yana kallonta dishi dishi,hannun ta da ta dafashi ya mika hannu ya kama,amma bai iya ce mata komai ba sai kallonta kawai yake,amma acikin zuciyarshi so yake taci gaba dayi mashi zancen sodangi data fara,gashi ji yake bazai iya magana ba daya fada mata abinda yakeso yaji. Ita kuma ganin har ya bude idanuwanshi sai wani farin ciki ya kamata ta mike da sauri ta nufi wurin kanshi tana tambayarshi ko yana bukatar wani abu,kada mata kai yayi tare dasa hannunshi daya ya dafe kanshi alamun yanayi mashi ciwo. Da sauri Hajiya ummu salma ta daga wayarta ta kira mahaifinsu safwan tanayi mashi albishir din tashin safwan. Ba ayi cikakkun minti biyu ba Alhaji Muhammad ya iso dukkanin idanuwanshi zube suke akan safwan ,don haka shima ganin safwan din ido bude sai farin ciki ya kashi,shi yusuf kuwa kasa daurewa yayi har sai da ya dan rungumo dan uwanshi yana dariya. Murnar kawai sukeyi amma duk gaba dayansu basu fahimci safwan bai magana ba,har suka gama murnarsu,sannan Alhaji Muhammad ya dubi karin ruwan dake jikin safwan yaga ko rabi bayyi ba yace,"zuwa dan anjima kadan idan ya kara samun sauki yusuf kuyi magana acire mashi karin ruwan,idan yayi sallolin dake kanshi sai ku bashi koda ruwan tea neh sannan sai asake mayar mashi da drief din." Yusuf ya dan rusuna yace toh daddy,sannan ya ci gaba da gyarawa safwan kwanciyarshi.shi kuma daddy ya kalli umminsu yace mata," muje koh Hjy tunda dai ya dan autan naki ya farfado,ai kema sai muje ji huta koh." Hjy ummu salma tayi dariya gami da mikewa tsaye tana kallon safwan tace,"ai sai hamdala,tunda safwan ya tashi,donni wallahi nasa mutuwa zaiyi." Gaba daya dakin suka dauki dariya suna kallon safwan din,shi kuwa sai raba idanuwa yakeyi tare da tunanin yanda zai samu damar fita daga cikin gidan ba tare da wani ya ganshiba. Love you😘 08033481518 [5/5, 10:04 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 60 I dedicated this love story to my group Hausa Novel & my fans,thanks and love you all 😘😘 Mahaifiyyar safwan da daddy suka fara fita daga dakin,sannan dan wani lokaci kadan yusuf suma suka tafi da zummar anjima kadan zai sake dawowa wajen safwan din don ya taimaka mashi yayi sallolin dake kanshi. Fitarsu kenan safwan ya fara tunanin inda wayarshi take,aikuwa ahankali ya laluba aljihun wandonshi ya zarota ya fara neman wayar sodangi,sai alokacin ya iske missing calls dinta ratata,saboda wayar silent take shi yasa bai ji ba. Dan nazari yayi idan har ya kira sodangi mi zaice mata,tunda halshenshi yayi nauyi sam ji yake bai iya furta wani furuci da bakinshi,don haka sai kawai ya tura mata massege yana cewa,"kada ki damu masoyiyata,gani nan zuwa gareki,babu tsimi babu wata dubara nine mijinki na har abada,sai naxo komai dare." Murmushin karfin hali yayi ya kuma nemi number tahir,shima ya tura mashi,"duk inda kake maza kazo ka daukeni,please I need your help my Friend. ina gidan daddy dake katsina, kuma ka sani komai dare a kano zamu kwana." Alokacin da Tahir ya samu sakon safwan sai da hankalinshi ya tashi,saboda duk abinda ake ciki ya sani,don haka shiyasa zuciyarshi ta bashi lallai safwan ya samu matsala awajen iyayen sodangi. Agogon hannunshi ya duba yaga a round four,kuma gashi a garin Abuja πŸ€” koya zaiyi? Aje duk wani abu dake gabanshi yayi ya dauki past port dinshi ya nufi filin jirgin dake abuja. Da duhun magriba Tahir ya isa gidan kowa yana ta harabar tafiya masallaci, sam bai bari kowa ya ganshi ba daga cikin gidan don haka ana kabbara sallah ya shige,kai tsaye sashen da safwan yayi mashi kwatance ya nufa. Safwan na ganin tahir ya fara kokarin tashi zaune saboda jikinshi ya kara samun sauki,wayarshi ya dauko da sauri ya yi dan note ya mikawa Tahir. Mamaki ya kama tahir ya dai amshi wayar kawai ya duba yaga abinda ya rubuta cewar,"ka dauke ni maza ka rabani da gidan nan,fomin so kawai suke inga na mutu." Tahir yana karantawa ya zabura cikin sauri ya nufeshi ya kamashi ahankali cikin dubara ya kaishi har wurin motar da zasuyi tafiyar ya sakashi gidan baya,shi kuma ahankali ya sulale ya kwanta. Tunda tahir ya fara jan motar nan yake sheka gudu sosai,saboda ko dai yace zasuyi wata mgn da safwan babu hali,shi yasa ya mayar da hankalinshi yayi ta tuki har suka shiga kano. Ji yayi safwan ta bayanshi ya dafashi,don haka sai ya rage gudun da yakeyi sannan yayi parking abakin hanyar ya fito,kamo safwan yayi ya mayar dashi kusa dashi, sannan shima ya zagaya ya zauna yana kallon safwan,ji yayi ya bashi tausayi saboda yanda yaga ya rame sosai tamkar bashi ba, Numfasawa yayi yace,"safwan wai duk mai yayi zafi har haka ta faru?jibi yanda ka canza gaba dayanka." Yunkurowa safwan yayi da niyyar ya maida mashi amsarshi amma sai yaji ya tsaya cak,shi kanshi yana mamakin abinda yake faruwa dashi. Numfasawa yayi sannan yaci gaba da tunaninshi,"kodai yayi losing voice din shi ne?" Wasu hawayeneh kawai yaji suna kokarin fito mashi,wayarshi ya kara zarowa ya rubuta mashi,"ka kaini gidansu sodangi." Tahir ya kada kai yace,"safwan ba zuwa gidansu sodangi ya kamata ba,asibiti kawai ya kamata in kaika don su fara duba matsalarka." Safwan yaki amincewa da shawarar Tahir,ya nace akan sai ya fara gano sodangi,wayarshi ce ta fara ringing,don haka da sauri ya kalli wayar saboda yana zaton daddy dinshi ne ko umminshi. Sunan sodangi ya gani don haka ba tare da bata lokaci ba ya dauka,acan kasa cikin wayar yaji tana kuka tana cewa,"safwan gani nan daura ardo ya tsareni,kuma yace bazan sake zuwa ko ina ba saboda sati mai zuwa zai aurar dani ga bafullace dan uwana,kuma ni bamma sanshi ba,please ka taimakeni safwan,domin bani son kowa sai kai.......... Wani karaji yayi da karfin tsiya cikin tashin hankali ya kira sunan ta sodangiiiiii,aikuwa muryarshi yaji ta fito fes kamar bashi ba,jin haka yasa ya zabura ya damko Tahir yana dariya,amma kuma cikin zuciyarshi wata irin kuna yakeji yace,"sodangi kiyi shiru ki daina kuka,ai kin san ina son ki koh?" Daga kanta tayi tace eh, yanda kasan yana ganinta,shi kuma yaci gaba da cewa,"toh kiyi dubara ki taho gareni sodangi,wallahi ina son ki,kuma bazan taba wulakanta ki ba because Ur my life & my everything. Sodangi ta kara fashewa da kuka tace,"bazan iya ba safwan,bazan iya ba,saboda ina tsoron hakkin iyayen mu ya kamamu." Firgicewa yayi yace cikin kunar rai mi kike nufi kenan?badai mu hakura ba koh,domin ni ki sani bazan iya ba wallahi." Wani jiri ne ya kamashi ya tafi kamar zai fadi, tahir yayi maza ya taroshi da sauri,sannan ya amshi wayar daga hannunshi ya kashe,taimaka mashi yayi ya zaunar dashi cikin motar sannan ya rufe,shima shiga motar yayi ya tasheta kai tsaye ya nufi gidan safwan. Love you sis😘 08033481518 [5/6, 8:04 AM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 61 I dedicated this love story to my group Hausa Novel & my fan,thanks and love you all 😘😘 Lamarin sabo ya komawa safwan,amma awannan karon voice dinshi bata shige ba,sai dai kara yamutsewa da yayi duk ya fita hayyacinshi ya firgice,gaba daya zuciyarshi ta raunana saboda dai ya fahimci da gaske ardo yake son rabashi da sodangi. Wasu hawaye neh suka malalo mashi daga kwanciyar da yayi tun lokacin da tahir ya zaunarshi akan 3siter,sai ya zame don ya raba kanshi bisa wani abu mai taushi saboda yanda kan yake sara mashi, ji yake tamkar zai rabe gida biyu don azabar ciwon da yakeyi. Babu irin abinda Tahir bai fada mashi ba amma yaki saurarenshi,domin ji yayi ma tamkar zugashi yakeyi. Tahir daya gaji da magana ba tare da ya samu amsa ba sai ya mike ya nufi dakin safwan yaje ya canzo kayan jikinshi ya sanyo marasa nauyi, sannan ya koma falon wajen safwan yadan dafa bayanshi yace,"ka tashi kaje ka watsa ruwa ko kaji karfin jikinka." Ture hannun tahir din yayi yace,"Ka rabu dani kawai,idan har nayi wankan amfanin mi zaiyi mani?" Tahir cikin tausayin abokin nashi yace,"zakaji karfi ajikinka,bama kamar idan ka daure kadanci abinci." Safwan yayi wani takaitaccen murmushi mai sauti ya kauda kanshi daga kallon Tahir yace,"so kake in rayu neh?idan na rayu wa zanyiwa amfani?" Numfasawa yayi tare da goge wasu hawayen da suka malalo mashi yaci gaba da cewa,"wadda zan amfana an rabani da ita,don haka nima haka zan kasance har zuwa lokacin da rayuwata zata kare,ina ma ji ajikina rayuwata tazo karshe don bazan dauki wani dogon lokaci ba zan tafi." A tsorace Tahir yayi sauri ya zauna kusa da safwan yana cewa,"A uzu billahi,akul safwan na haneka da irin wannan maganar, don wallahi babu kyau kada kayiwa Allah shishshigi,saboda dukkan rayuwa da mutuwa daga wajen Allah ne,kuma idan har ka tafi da rayuwarka a haka har ka mutu,toh tabbas kai ka kashe kanka da kanka,kuma nasan kasan makomar wanda ya kashe kansa awajen Allah." Hannunshi ya kamo ya rike yaci gaba da cewa,"don mi zaka zama haka?ko ka mance jarumtar da kayi a baya da irin gwagwatawar da mukayi da makiya,please be a man safwan,be a man." Bai san lokacin da Tahir yaji idanuwanshi suna zubar da hawaye ba,don haka sai ya kama kuka saboda tsananin tausayin abokinshi,bama kamar idan ya kalleshi yaga yanda gaba daya ya canza ya zama wani kazamin karfi da yaji. Safwan ya dago yafan kalli Tahir yaga yana zubar da hawaye saboda shi sai yayi wani murmushi wanda ko kyau bayyi mashi ba yace,"ka daina kuka abokina,kuma ka yafe mani saboda nayi giving hope,don gaba daya ban san yanda zan juya tunani na ba don ya zama dai dai." Tahir ya share hawayenshi yace,"idan ka yarda dani zan taimake ka,amma kuma banda gardama,domin inason duk abinda nace maka kayi obeying don't complain." Safwan da idanuwanshi ke rufe ya numfasa yace,"kayi duk yanda ya kamata kayi dani tahir." Zumbur tahir ya mike tsaye cikin tashin hankali yana cewa,"bazan iya kallonka ahaka ba safwan, zanyi bakin kokarina don naga ka rayu ka koma kamar da." Drowers din da safwan yake ajiye muhimman abubuwanshi tahir ya nufa ya farayi mashi bincike,past port dinshi ya nemo wanda yake fita waje dashi ya hafa da nashi. Tahir baiyi shawara da kowa ba,domin gsri yana wayewa ya nemar masu biza zuwa Egypt ba tare da wani ya sani ba ya tattara safwan ya tafi dashi. Duk wayoyinsu suka kashe saboda tahir bai son iyayensu su san inda suke har sai safwan ya warware ya samu sauki. Agida Nigerai kuwa duk gaba daya dangin su safwan sai da hankalinsu ya tashi,saboda rashin sanin inda safwan ya nufa gashi ba isassar lafiya gareshi. Duk wata kafa da ake tunanin za a sameshi anje an duba amma babu shi babu labarinshi,hatta da friends dinshi suma sunce basu san inda yake ba. Mahaifiyyar safwan ita tunani ta ya bata akan abinciki Tahir,shima sai aka rasa inda yake,kuma iyayenshi ma sunce bai fafa masu inda yake ba saboda ko sun nemi wayarshi bata shiga. Samun wannan labarin neh yasa daddyn safwan yayi dariya ya kalli yan uwa da abokan arziki da suke ta kaiwa da komowa akan batan safwan yace,"maganar auren da xaiyiwa safwan babu fashi kawai aci gaba da gashi." Haka kuwa akayi,duk abinda akeyi iyayen safwan sai da suka tsaya tsayin daka sukaga anyi komai. Ranar daurin aure suka rankaya suka je aka dauroshi akan sadaki dubu dari biyu. Lamarin sodangi kuwa abin ba a cewa komai saboda gaba daya ta saduda akan ta kara rasa safwan akaro na biyu,kuka ya zama shine tamkar abincinta,saboda ba dare ba rana kullum cikin zubar da hawaye take har ta fara nemansu ta rasa. Abubuwa neh guda biyu suka taru sukayiwa sodangi tsaye acikin rai,na daya rasa masoyinta na gaskiya da tayi,sai kuma na biyu Wanda mahaifinta yake ta ikrarin shi zai aura mata bata sanshi ba,kai ba takarar haka ba ma ko labarinshi bataji anayi ba. Gaba daya karfinta ya kare saboda kuka,sannan kuma duk tabi ta fita hayyacinta,a haka tanaji tana gani aka dawo akace ai har an daura auren,sameer da yaya sadah sune suka kawo mata wannan albishir din na bakin ciki,kuma har yake fada mata shima an sanya bikinshi da fa iza,aikuwa sameer sai da yayi dana sanin fada mata haka,saboda Wani irin ihu tayi mai sauti amma babu wasu hawaye da suka biyo baya,saboda idanuwanta sun kame sun bushe,mikewa tayi kamar zata ruga,sannan ga sambatu kamar wadda ta zare don sai maganganu take babu wanda yake gane abinda take cewa. Ganin halin da sodangi take aciki yasa aka fasa kaita gidan mijinta aranar,har sai da aka amso mata taimakon addu o i da rubutu akayi ta bata na dangana. Da yake addu a bata faduwa banza,ahankali aka samu kan sodangi tayi shiru ta daina cewa komai sai dai bin jama a kawai take da idanuwa. Ganin ta samu sauki ardo ya bada izinin afara shiri kawai don akai sodangi gidan mijinta. Love you sis😘 08033481518 [5/7, 2:54 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 62 Jinjina agareku,dukkan masoyana na gida dana waje da kuma members na Group dina,watau Hausa Novel. Ina godiyya da irin hadin kan da kuka bani har zuwa yau ranar dana kammala wannan littafin nawa,inda nayi kuskure ina neman yafiya zuwa ga ubangiji na,wadda kuma take ganin banyi mata dai dai ba,itama ina mai bata hakuri ta kuma yafe mani,saboda idan mune ayau,toh bai zama lallai mu kasance mune agobe ba. Second to the last page. Motoci ne dankam acikin rugar tasu sodangi na yan daukar amarya,domin su kansu yan kauyen fitowa sukayi gaba daya suka ja layi suna kallon wadannan motocin saboda abin burgesu yayi. Yan uwa da abokan arziki suka fito sai shiga motocin sukeyi,ita kuwa amarya sodangi wata tsahowace yayar ardo da goggo laura su suka kamota suka kaita har motar da zata dauketa. Kuka dai sodangi Tasha shi,domin har suka dauki hanya bata daina ba kukan nan kawai take. Tafiya kawai sodangi taji ana tayi kamar ta masu neman uwa,hsr ta ksi da ta fara gajiya,dan yane mayafinta tayi kadan ta kalli hanyar da suke bi,kwata kwata bata san kowacce hanya ba ce,saboda batayi kama da hanyar data taba sani ba. Mamaki ne ya kamata, shin wai ina za a kaita ne?itace tambayar da takeyiwa kanta acikin zuciya,gashi bata da damar tambayar wani ace tayi rashin kunya,dolen ta ta hakura ta mayar da kanta kasa,can wajen karfe hudu da rabi suka shiga garin abuja. Jin su goggo laura suna ta yaba tsarin garin yasa ta kara dago kanta ahankali cikin dubara ta kalli window din dake kusa da ita,lallai garin ya tsaru iyakar tsaruwa,kuma itama garin ya burgeta amma ba har acikin zuciysrta ba,saboda kwata kwata bata da wani farin ciki acikin zuciyarta bare har wani dadi ya samu hanyar ratsawa. Wata unguwa suka isowa,kamin su shiga inda tsarib gidajen suke taga an rubuta maitama street,gaskiya unguwar ta hadu,saboda gidajen gaba daya atsare suke,kuma kowanne yana da irin tsarinshi daban. Wani tafkeken gida aka nufa dasu,nan da nan gate din ya bude motocin suka dinga shiga daya bayan daya saboda tunda suka fara tafiya kusan atare suka rinkayinta har suka iso. Goggo Laura suka kara dukunkune ni da mayafin dake jikina,ya zama tafiya kawai nake ina jefa kafafuwana saboda sam bana ganin komai bare kuma inda zan taka. Muna shiga falon gidan naji wasu matan suna tayi mana maraba da sannu da isowar mu tare dayi mana jagora har zuwa wani daki daga can cikin gidan. Ni dai sai dai inji voice amma bani da ikon ganin fuskokin mutanen dake gidan,saboda gaba daya zuciyata ta kagara taga inda aka kawoni tare da mutanen da zanci gaba da rayuwa dasu. A hankali na daina jin bakin muryoyin dake cikin gidan sai yamu yamu da muka zo,ai fa dangi sun samu abinda suke so,watau abinci ne kala kala da snacks da lemuna,sai wanda kakeso zaka kaci ka sha. Nidai ina nan takure awaje Allah sai kallon ikon Allah nakeyi. Washe gari tunda duku duku aka kara shigo masu da wasu kayan abinci,don haka sunayin sallah suka kara far masu sai da sukayi kat,sannan suka fara shirye shiryen tafiya gida,ni kuma ganin haka neh idanuwana suka fara raina fata duk na shiga damuwa. Sha tara ta arziki aka hadowa yan kawo amarya daga fannin ango,su kuma sai washe baki suke suna ta raraka godiyya tare dashiwa aurensu sodangi albarka. Ganin sun fara fita sunayi mata bankwana yasa taji jikinta ya fara rawa,nan fa nan hawayen dake kwance acikin idanuwanta suka fara zubowa. Hannu biyu tasa ta riko hannun laura dake shirin fita bayan tayi mata bankwana cikin rawar murya tace,"don Allah goggonah kada ku tafi ku barni acikin wannan gidan na yan yankan kanu." Ganin yanda ta rude da yawa neh yasa laura itama taji ta shiga damuwa,don haka sai ta koma ta zauna kusa da ita ta fara rarrashinta tace,"sodangi kiyi hakuri ki daina kuka,kuma inaso ki sani mai wannan gidan ba dan yankan kanu bane,saboda duk inaji ana fada cewar mutumin kirkine ga tausayin talakkawanshi,don haka ki kwantar da hankalinki ki zauna kiyi biyayyar aure kamar yanda Allah ya tsara mana...... Daga can wajene taji motocin da zasu mayar dasu gida wasu sun fara tafiya don haka goggo laura sai ta rude gudun kada atafi abarta ta janye hannunta daga cikin na sodangi ta mike da sauri ta nufi hanyar fita tana cewa,"toh ni dai sodangi kinga tafiya sai ince sai wata rana sai kunzo." Tashi sodangi tayi da sauri tabi bayanta tana kuka,haba inaa,ai kamin ta nemi hanyar da laura tabi ta fita sai dai taji tsit gidan alamun motocin har sun gama fita. Turus tayi acikin wani katon falo wanda ita kanta ganinshi da tayi kara tsorata tayi saboda irin kayan alatun da aka dankara mashi. Wata yar kara ta saki cikin daga murya tace,"wayyo ni sodangi yau naga ta kaina😳 kodai su ardo sayar dani sukayi?" Kara fashewa da kuka tayi😭ta dora hannunta abisa kai ta juya da gudunta harda na tsiya ta koma wannan dakin da aka kaita tun farko,harda rufe kofa. Zamane mara dadi sodangi tayi a wannan gidan,saboda kadaici,domin yau kwananta bakwai acikin gidan amma bataga angonta ba sai dai akullum wata Hajiya tana kawo mata ziyara tare da abubuwan ci da sha dana amfani,sannan kuma har yanzu Hajiyar bata fada mata ko ita wacece ba,sai dai kamalar da take ganin Hajiyar tana da ita yasa take girmamata sosai. Lamarin safwan kuwa,suna isa Egypt kai tsaye Tahir asibiti ya nufa dashi,don haka treatment na kwana biyar sukayiwa safwan ya wartsake,sai dai damuwar kadai data mallake mashi zuciya. Wani tafkeken hotel Tahir ya neman masu suka zauna kuma adaki daya.a kullum safwan yana nan kwance adaki,amma Tahir sai ya fesa wanka yayi gayunshi ya shige cikin gari abinshi. Haka suka zauna har sai da suka kwana goma sannan safwan ya fara nazarin bude wayarshi don ya kira sodangi. Harya bude wayar kuma sai ya fada cikin tunanin ranar da sukayi wayarsu ta karshe da sodangi tace mashi ardo zaiyi mata aure acikin satin da wani banza wanda bai san darajarta ba. Hawayeneh kawai yaji suna malalo mashi agefen idanuwanshi,bude wayar yayi cikin tsanan shawkin son sodangi da kuma son ganinta ya shiga gallary inda yayi saving din pics dinta ya shiga shafasu cikin lumshe idanuwanshi yana kissing din pics din. Ji yayi tamkar da gaske abin yake faruwa,lumshe idanuwanshi yayi ya rungume wayarshi ajikinshi yana sunsunarta,don karya hancinshi ya fara jiyo mashi kamshin sodangi akusa dashi,jawo pilon dake gefenshi yayi ya rungume sosai,rasa yanda zaiyi da kaunar sodangi yayi acikin zuciyarshi da gangan jikinshi kawai sai ya kama kuka riris yanda kasan karamin yaro agaban iyayenshi haka safwan ya koma. Yana cikin hakane Tahir ya turo kofar dakin,agefenshi wata zukekiyar yarinyace take rungume dashi,kuma dukkan alama abuge Tahir din yake,saboda sai layi yake ga wasu sambatu da yake tayi. Dago kanshi dake cikin pilo yayi yabisu da ido har ta kwantar dashi agefen gadon. Cite mashi riga tayi da dogon wandan dake jikinshi ta barshi dagashi sai vest da short niker,sannan itama ta rage kayan jikinta duk da dama ba kayan kirki bane ajikinta. Safwan daya zubawa yarinyarnan ido sai yaji hankalinshi zai ida tashi dama kuma dama can acikin hali yake,don haka da sauri ya mayar da kanshi acikin pilonshi yana mayar da numfashi sama sama. Babu yanda yarinyar nan batayi ba don Tahir ya tadhi yayi mata abinda takeso amma yaki saboda barci ya fara cin karfinshi. Tsayawa tayi tana harararshi cikin takaici tayi tsaki harda dukan bayanshi. Komawa tayi gefen gadon ta zauna ta dafe kanta cikin bakin cikin dake damunta,watau tahir idan da yasan baza ya iyayi mata komai ba,toh mi yasa ya rabo da ita daga club? Tsaki ta karayi ta juyar da idanuwanta sai akan safwan dake kwance rufda ciki agefensu,Cikin shigar singled da three quarter na jeens. Wani murmushi tayi ta hauro kan gadon cikin sanda,sai dai kawai safwan yajita abisa shi tana ta shashshafa shi tana tsotsar fatar jikinshi kamar zata cinyeshi. Cikin rudani ya birkitota ya mayar da ita akasan shi yana kallonta ido cikin ido... Love you sis 😘 [5/8, 9:45 PM] binta garba: πŸ’πŸ’πŸ’SODANGIπŸ’πŸ’πŸ’ Na Binta garba saleh daudawa 63 Wannan page din nawa na karshe na musamman ne,kuma zan sadaukar dashi ne akan babbar kawata kuma aminiyyata "FIDDAUSI SODANGI"Ranki ya dade,ina jinjina agareki,love you for ever & ever. LAST PAGE Cikin rudani ya birkito ta ya mayar da ita kasanshi yana kallonta ido cikin ido,ita kuwa ganin haka sai tayi tsammanin har taja ra a yinshi,sai tayi sauri takai bakinta anashi,shi kuma wuf yayi ya kauda kanshi yana murmushi ya kalleta yace,"ki godewa Allah,domin haka da kikayi mani idan da kin sameni kamar yanda nake ada,wallahi da sai kinyi dana sani arayuwarki,saboda aikin da zanyi maki ba a tabayi makishi ba arayuwarki." Dariya tayi cikin jan ra ayinshi taja wani irin numfashi mai dan sauti ta shafi dan sajenshi dataga yayi luf luf gwanin ban sha awa tace,"ina jiranka,kuma babu wani tsoronka da zanji,saboda irinka nakeso dama." Kallonta yayi sosai ya fahimci itama tadan kora,don dai bata sha da yawa ba. Zame jikinshi yayi niyya amma sai ta rikeshi gam,tare da jawoshi jikinta tana makalkaleshi cikin wata kissa irin ta yan duniya. Ranshi ne ya fara baci saboda ya fahimci muddun yayi mata lakwa lakwa sai ta rabbace shi ta mayar dashi ruwa,karfi yasa mata ya kakkashe ta da mari kusan ukku sannan ya mike daga kan gadon. Gaba daya taji kamar an dauke da wutar lantarki,saboda dif taji,watau bata ji kuma idanuwanta suka tafi suka rufe sai duhu kawai take gani. A hankali jinta ya fara dawowa sannan ganinta,ai kuwa arude ta mike tsaye cikin gigita ta fara hada kayanta ta fita da gudu tana waiwayenshi. Murmushi yayi ya kalli wayarshi dake gefen gadon,kuma adai dai lokacin kira ya shigo pix din sodangi ya bayyana. Murmushi yayi ya shafi fuskar sodangi yana cewa,"ke kadaice macen data can canta data mallakeni,kuma kema tawace ni kadai I love you my life."yana fadar haka sai ya amsa kiran wayar ba tare da sanin mai kiranshi ba saboda numberce babu suna. "Safwan" sunanshi dayaji ankira tare da kuma jin sautin muryar can tsakiyar dodon kunnenshi yasa ya zabura ya mike tsaye ya sake kallon cream din wayar still dai number ce,arude yace,"yes daddy." Alhaji Muhammad ya tamke fuskarshi tamkar safwan yana agabanshi yace,"baka da hankali koh? Kum Mi kakeso kace mani?ka tafi ka barmu ba tare da tunanin halin da masoyanka suke ciki ba ko? What up your ummi?" Wadannan tambayoyi da daddy dinshi yake ta jero mashi su yasa hankalinshi ya tashi, kuma sai alokacin ya tuna da ummi da irin soyayyar da take mashi, anya kuwa ya kyauta mata kenan." Ji yayi Daddy dinshi yaci gaba da cewa,"so let me tell you one thing safwan,idan har kana son rahamar ubangijinka to maza ka dawo zuwa ga mahaifiyyarka,kuma yau yau dinnan,idan kuwa har ka saba ka kuka da kanka,saboda kasan dole watan wata rana zamu hadu dakai." Safwan yayi dif saboda yanda daddy yake ta daureshi da jijiyoyin jikinshi,don gaba daya rasa yanda zaiyi yayi,don sai da daddy din yace,"kai safwan ! Kana jina kuwa?" Da sauri ya amsa yace,"yes dad ina ji,kuma zanzo din." Mahaifin safwan ya kashe wayar cikin yin fuska babu wat dariya. Hajiya ummu salma dake gefe a kagare da son jin yanda sukayi dashi ta kara matsawa kusa da maigidanta tace," ya kukayi dashi ?" Wani murmushi ya saki yana kallonta yace,"yau safwan zai dawo insha Allahu, saboda babu musu babu gardama,domin idan da yayi daya daga cikinsu to tabbas alamace ta baxaizo ba,don haka sai kisan dubarar da zakiyi domib na nuna mashi kina cikin hali." Daboda jin dadin danta safwan zai dawo gida yasa takejin sam bata iya rufe bakinta,don haka nan da na ta kira khadija matar yusuf tac fada mata dawowar safwan ayau,don haka tana son ta shiryo mata su afnan da junior tasa driver ya kawo mata su." A gain kuma ta sake kiran wayar amaryar safwan watau HUMAIRA ta fada mata dawowar safwan ayau,don haka tana son tayi shirin tarbar angonta😜 Kamar yanda ya faru agidan humaira,hakace ta faru agidan sodangi. Hajiyar dake kai mata ziyara kullum,ayau ma tazo,bayan yan tambayoyi kadan don sanin halin da sodangin take ciki sai tace mata,"yau ne ranar da angonki zai zo gareki,don haka ina son ki kimtsa kanki tare da sanya ma aikata su kara kalailaice maki ko ina na gidan,saboda mijinki abocin tsafta ne da son ado da kamshi." Gaban sodangi ne ya shiga halbawa da karfi don ji take tamkar zai rabe gida biyu,amma kuma sai daurewa take don batason wannan hajiyar mai daraja da karamci a idonta ta fahimci akai firgita atare da ita. A yau Hajiyar bata dauki wani dogon lokaci ba ta mike tace,"toh sodangi zan tafi,kuma idan mijinki ya dawo bance kiyi banza dashi ba,nasan baki sanshi ba,amma ki daur ki jure,ibsha Allahu cikin kwana biyu zaku saba ke da shi." Sodangi cikin jin kunya ta rusuna tace,"insha Allahu Hajiya,zan kasance mai bin umurninki,domin baki da wani bambanci atsakaninki da mahaifana,kuma na gode da duk shawarwarin da kike bani." A haka suka rabu Hajiyar nan taji dadi kwarai da gaske,kuma ta yaba da tarbiyyar sodangi dari bisa dari,don haka ta shiga sawa sodangi albarka,kuma bata fasa ba har sai da ta shiga motar data kawo ta suka tafi sannan sodangi ta juyo jiki asanyaye ta koma cikin gidan. Zubewa tayi afalo tana kallon tire din jus da ruwan data kawo wa Hajiya tare da tunanin maganganun data fada mata akan mijinta. Kawai bata farga ba sai ji tayi ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya,don haka mikewa tayi da gudu ta nufi dakin datake kwana tunda tazo gidan,kuka taci mai isarta har daga karshe wani irin barci ya kwasheta maraddadi. Safwan kuwa tunda sukayi waya da Mahaifin shi sai ya gaza zaune ya gaza tsaye sai sintiri yake atsakar dakin kamar wanda yayiwa sarki karya. Gaza jiran Tahir yayi ya farfado kawai ya yanke hukuncin tafiya shi kadai saboda zuciyar shi ta kagara yaga halin da mahaifiyyarshi take aciki. Duk abinda yake bukata nashi ya dauka ya kuma rubutawa Tahir dan Note ya ajiye mashi inda yasan zaiganta sannan ya fice daga dakin cikin sauri tare dayin addu ar Allah yasa kada ya samu wata matsala afilin jirgi don xuwa Nigeria. Around five ya isa gidan iyayenshi,duk da gajiyar dake jikinshi,amma azama kawai yake don yaje yaga lafiyar umminshi. Afalo ya gamu dasu afnan suna ta wasansu,ai kuwa yana ganinta sai wani farin ciki ya kamshi da jin tausayinta,ai kuwa da sauri ya nufeta ya kamata ya rungume ta ajikinshi yana cewa,"I miss you my doter! I miss you!! Afnan na ganinshi ta gane shi itama makalkaleshi tayi sosai tana kwaratsin daddy oyoyo oyoyo oyoyo,shima junior rugo wa yayi da gudu yaje ya makalkalshi yana murna ganinshi. Wannan kwaratsin dasu afnan sukeyi na ganin daddyn su ne ya fargar da umminshi tazabura da sauri ya haye bisa gadonta ta lullube da katon bargonta ta mashashshare tare da juye idanuwanta yanda kasan ta wahala sosai haka ta koma. Safwan yayi sallama a dakin umminshi yaji shiru sai jikinshi ya karayin sanyi da sauri ya saki hannunsu afnan ya nufi uwar dakinta ya sakeyin sallamar. Amsawa tayi can kasa kasa kuma da kyar,shi kuma yana shiga kai tsaye bisa gadon ya haye har inda take akwance ya jawo kanta ya for abisa cinysrshi yana hawaye yana cewa,"ummi nah miya sameki,kiyi hakuri ki tashi ga danki ya dawo." Hajiya ummu salma ta rinka numfashi sama sama ta kalleshi tana kokarin yin murmushi na karfin hali tace,"haba dana ! Ya zaka tafi ka barni cikin tunaninka? Sannan kuma ban san awane irin hali kake aciki ba." Safwan ya kara tallafar kanta yace,"kiyi hakuri umminah,gani na dawo cikin koshin lafiya,kuma babu abinda ya same ni." Hannu tasa ta shafi fuskarshi tace,"naji dadi safwan Allah yayi maka albarka,sannan kuma ina rokon wani arziki awajenka safwan πŸ‘ Safwan cikin sauri ya rike hannuwan datake rokonshi dasu yace,"haba ummi nah ki daina don Allah ki daina rokona,ni danki neh,don haka umurni kawai zaki bani,ni kuma insha Allahu zanyi maki biyayya. Wani farin ciki neh ya shiga acikin zuciyar ta,amma sai ta dake ta dafe kanta tace,"inason kayi hanzari ka tafi gidanka,saboda amaryarka da aka kawo maka tana nan har yanzu tana zaman jiranka,ka taimakeni kaje ka zauna da ita har karshen rayuwarka. Wata faduwar gaba ce ta diro mashi yaji kamar ya baje akan gadon saboda yanda yaji ta daki zuciyarshi. Hadiye miyau yayi da kyar ya kalleta da idanuwanshi masu rauni yace,"insha Allahu ummi zanyi abinda kikace mani." Ita da kanta tayi mamakin jin abinda danta yace,sannan acikin zuciyarta ta kara godewa Allah da danta yacanza hali ya zama mai biyayya,tashi tayi da kanta ta zauna tana murmushi tace,"Allah yayi maka albarka safwan,ya kuma albarkaci dukkan zuri arka,maza ka tafi safwan, kuma nima daga yau bazaka sake gani nah akwance ba,tunda kayi abinda ya dace da rayuwarka,kuma ka faranta ran iyayenka." Dafa kafafuwanta yayi yana murmushin karfin hali ba tare dayace mata komai ba ya kama hanyar fita dakin duk jikinshi asanyaye. Ita kuwa sodangi tunda ta kwanta wannan barcin mai nauyi ya dauketa,itace bata farka ba sai wajen la sar ta farka ta mike da sauri ta duba lokaci,gabanta ne ya fadi data tuna da maganar da sukayi da wannan hajiyar,kuma gashi don karfin hali har wani alkawari tayi mata. Fita tayi jikinta asanyaye ta nufi wajen yan aikinta ta duba abubuwan da sukayi,yaba masu tayi sannan ta sanya daya daga cikin ma aikatan ta jera abincin da sukayi a dining table,sannan ta koma dakinta don itama ta shirya jikinta kamar yanda tayi alkawari. Sai yau sodangi ta bude akwatunan data gani adakin amatsayin na lefenta tadan dudduba kayan taga duk kusan dinkakkune,kuma anyi design masu kyau da burgewa. Wata riga ta dauko ta shadda Yellow anyi mata aikida red zare kuma zubin bubu style,kallabin rigar shima red ne,don haka sai ta samu takalma red axcikin lefen 'yan flats shoe. Kwalliya tayi yar simple mara hayaniyya afuska sannan ta zira kayan ta koma kan gashin kanta shima ta fesheshi da turaren gashi,sannan tasa ribom ta daureshi waje daya sauran ya sauka akan kafadarta sannan tabi da daurin kallabi irin na wannan zamanin. Karar mota taji tare da bude gate din da maigadi yayi,jikinta ne ya dauki rawa ta nufi window dakinta da sauri ta leka wai ko zata ga kowanene,giccin motar kawai ta gani ya shige,amma bazata iya cewa taga na cikin motar ba,dan tsaki tayi ta koma bakin gadonta ta zauna ranta ya dan sosu tare da tunanin yanda zata yi da mutumin da bata sani. Zamewa tayi tayi kwanciyarta akan gadon ta afka tunanin rayuwar data wuce da kuma wadda ke shirin haye mata anan gaba. Wasu hawaye neh suka taru acikin idanuwanta,ahankali ta mayar dasu ta rufe tana mayar da numfashinta sama sama. Wayar dakinta ce ta haw ringing har sai da ta dan tsorata saboda tunda tazo bata taba jin tayi ringing ba,mi kewa tayi jikinta duk kerma yakeyi ta nufi wayar,tana gaf da katsewa tayi sauri ta dauka. Muryar msi aikinta taji mai kula da kitchen tace,"anty sannu da hutawa." Sodangi ta mayar da numfashi tace,"yawwa Ramatu." Ramatu tayi kasa da murya cikin girmamawa tace,"dama boss ne yakeson ganinki a babban falonshi."tana gama fadar haka tayi kasa da wayar ta ajiye,ita kuma sodangi kasa ajiye wayar tayi saboda fargabar data shigeta. Cikin kasala tayi kasa da wayar ta kalli hanyar fita daga dakinta taji duk tsoro ya kamata,amma tunda tasan bata da yanda zatayi dole ta zira flat Shoes ta bi hanyar zuwa falon cikin sanyin jiki. Kamshin daya ziyarci hancinta ne yasa tadan firgita tare da karayin sauri, zuciyarta cike da son ganin kowa nene wannan ma abocin kamshin mai yanayi dana masoyinta abin kaunarta. Juyawa yayi ya bata baya yana kallon window dake cikin falon,zubawa flowers din da yake hagge yayi amma akasan xuciyarshi kuwa sakata kawai Yake yana kwancewa ta yanda zai iya zama da wannan amaryar tashi. Sodangi zuba mashi idanuwa tayi,saboda gani take kamar idanuwanta ne keson yi mata gizo,saboda safwan kawai take gani cikin shigar three quarter da yar amless. Tsaye tayi cak taci gaba da son tantanceshi,kodai angon kama yake da safwan ne,shi dai aikin kurbar lemunshi kawai yakeyi cikin takaici da bakin ciki. Gama tantance shi tayi ta kuwa nufeshi da gudu fuskarnan tata cike da farin ciki,ga wasu hawaye da suka fara tunkudowa. Sam bayyi aune ba sai kawai yaji ta bayanshi an rungumeshi da karfi ga kuma sheshshekar kuka anayi Ada mutuwar tsaye yayi yanda kasan ya mutu haka ya kame,amma sautin voice din dayaji yana fita yasashi sakin cup din dake hannunshi da sauri ya kama hanunta ya juyo duk idanuwanshi awaje,aikuwa tunaninshi ya zama dai dai,saboda ganin sodangi agabanshi kuma agidanshi yasa duk ya rude ya dago fuskarta data dukun kune ajikinshi tana kuka,hada idanuwa sukayi yayi dariya tare da sakin wani ihun jin dadi ya jawota ya rungume yana cewa,"wayyo Allah sodangita,waye ya kawo mani ke don yaga karshen farin cikina?" Sodangi tana kuka mai hade da dariya tace,"nice matarka safwan,da aka daura mana aure kusan sati biyu da suka wuce." aikuwa yanajin haka ya dukacya sungumeta ya rungumata ajikinshi ya nufi dakinshi da ita yana cewa,"bazan iya ba sodangi,sam bazan iya jurewa ba har sai naji dumin jikinki matata rayuwata." Sam kasa bin bayansu nayi saboda yanda safwan yasa matakan tsaro abakin kofar dakin nashi,shi yasa kawai naga ya kamata nima in hakura hakanan,amma inason readers dasuyi nazari da kansu akan abinda zai faru awannan yammaci tsakanin safwan da sodangi. My next Novel is KARSHEN MASOYA,till we meet again my fans 😘😘😘😘😍 ALHAMDULILLAHI WABIHAMDIHI ALAKULLIHALIN